Yazeed Ko Yaseer!

Written by Ayshart FaruqPublished on 2018-12-13 15:38:52Category FictionIta kad'ai ce macen da Mahaifinta ya mallaka. Yana k'aunarta, yana tsananin burin ganin ya ilmantar da ita ta tsaya da k'afafuwanta. Sai dai kash! Lokaci d'aya wani mutum ya chanja mata duniyarta, ya shiga cikin burin mahaifinta yayi mata tabo maigirman gaske. tags: #Betrayal #married #jealousy, hatred.Duba was labarai »

Yazeed ko Yaseer

              

             Nah

     

         Ayshart Farouq


              NWA


            1_5


     Zaune take kan sallayarta ta idar da sallar la'asar tana istigfari, mace ce 'yar kimanin shekara arba'in da biyu zuwa da uku, amma Sam batayi Kama da shekarunta ba saboda irin kyaun jikin da Allah ya Mata da kuma kasancewar ta 'yar Hutu, idan ance ka fadi shekarunta zaka iya rantsewa 'yar talatin ce,

Kyakkyawa ce mai cikar mutunci da kamala,


   Wata kyakkyawar yarinya naga tafito cikin shirinta da alama fita zatayi don sanye take da hijab Mai hannu iya gwiwa, hannuwanta riqe da yar post dinta kalar takalminta ko ba'a fada ba kasan cewa diyar hajiya zainab ce saboda tsantsar kamar da sukayi duk da cewa yarinyar bazata wuce shekara goma shatakwas ba.


  Gurfanawa tayi gaban mahaifiyar tata tana murmushi tare da cewa,

" momy naga kina ta kallo na " ta fada cikin shagwaba,


" ba dole in kalleki ba naga kinci uban ado haka kuma kinsan yau ba islamiya"


b'ata fuska tayi , " haba momy nafa gaya miki ina so inje gurin kawata maryam in karbo wani littafi da nake so in koya gurin malaminmu"


Cikin fada fada momyn tata take magana,

" kin San dai mahaifinki baya son irin wannan yawon ko ? Ko so kike yadawo bai ganki ba ya hauni da fada? Gskiya abunda kike mun Afnan Sam ba na son shi kin fi kowa sanin halin mahaifin ki amma ke Sam ba kya gudun abunda kanje ya dawo,"


Cikin ladabi da girmamawa Afnan take magana " Dan Allah momy kiyi hakuri insha allahu Abba bazai dawo yasame bana nan ba amma idan har bakya son fitar na hakura sai wani lokaci sai inje in karbo"

Ta karashe maganar tare da mikewa idanuwanta cike da kwalla ta juya zata koma,


Cikin sanyin ta ta kirata da " Afnan kije amma kada ki dade kinji autar momy plz kada kiyi kuka ki b'ata kwalliyar ki",


Cikin murna da jin dadi Afnan tayi godiya sannan ta juya ta fita tana murna.


   Ahankali ta ke tafiya saida tayi nisa da gida kadan sannan ta bude post dinta ta fidda wayarta kusan 12 miss call ta gani kasancewar wayar silent take,

Murmushi tayi lokaci daya ganin wani kiran ya shigo da number da akayi saving da maryam2,


Cikin muryarta Mai dadin sauraro take karba wayar, " dan Allah kayi hakuri gani nan na kusa karasowa kasan fitar saida dubaru, OK toh sai na karaso ta fada tare da kashe wayar ,


Tafiyarta takeyi cike da nutsuwa har takai bakin wata mota kirar prado jib baka wulik sai sheki take,


Murmushi suka sakarwa junan su lokacin da idanuwan su suka sarke guru daya ,


  Ahankali ya bude motar ya fito wanda lokacin da naganshi saida nakusa fita hayyaci na saboda tsananin haduwar shi wadda duk yanda ka Kai gurin kushe mutum bazaka taba kushe shi ba don bazaka taba iya cewa ga munin shi ba,


Cikin fari'ar shi yake cewa, " amma fah gskiya ya kamata ace nayi fishi da ke my princess sai dai kuma kash bazan iya ba,

     

Murmushi Afnan tayi irin Wanda ke karamata kyau da annuri ,


" ki daina min irin wannan murmushin yana kara zuzutar da ni, wani murmushin ta sakeyi Wanda yafi na farko kayatarwa,


" kaifah YAZID akwaika da abun dariya wlh" ta fada tana duban shi 


" Allah ko princess?" Ya fada shima yana Mata wani irin shu'umammen kallo tare da cewa,

" kin San wani Abu?" 

Tace ," sai ka fada"


Kanshi ya dan sosa " Allah KO wace irin shiga kikayi kyau kike yi"


Wannan Karon tuntsirewa Afnan tayi da dariya " Allah yazeed ka cika abun dariya nufah duk daukana abun kwarai zaka fada"


Shima cikin dariya yace, " au wannan ba abun kwarai ne ba kena?"


Murmushi tayi tare da cewa,

" toh yanzu ya ake ciki ne? Kasan karya na zubawa mom tace kada nadade banaso nabata Mata rai gobe ta hanani,


" haka ne kam" ya fada tare da sosa keya " gashi kuwa ma naso ki rakani wani guri"


Zaro idanuwa tayi tare da daure fuska "amma dai wasa kakeyi ko?"


  

Ayashart one


Yazeed ko yaseer 

         Nah

    Ayshart Farouq 

          

         NWA

   


       5_10


Dariya Yazeed din yayi tare da lakuce Mata hanci " sarkin tsoro to wasa nakeyi",


Afnan tayi ajiyar zuciya tare da cewa "toh bana son irin wannan wasar ka daina plz"


" Allah ya huce ran gimbiya nadaina"


Yanda yayi maganar saida yabata dariya kasancewar shi mutum ne Mai barkwanci,


Shima dariyar yayi tare da cewa,

" wallahi Afnan Ina son aure "


Gaskiya ya bata tausayi yanda yayi maganar sai dai tafishi zama abun tausayi kasancewar cewa ita mace ce tanada rauni sosai hardai wannan zamani da muke ciki a yanzu,


Muryarshi ce ta katse Mata tunanin ta, " Afnan nasan bakya jin yanda nakji ko?" Ya fada tare da zuba Mata idanuwa,


Cikin muryar tausayi tace, " ko inaji ya muka iya? dole mu hakura da abunda iyayen mu suke so shekara biyu ai kaman gobe ne,"


" ai bama tani ba ni, ke nake dubi tunda kema ra'ayin mahaifin ki kenan kiyi karatu Mai zurfi kinga kuwa ba shekara biyu ba akwai sauran lokaci da yawa tunda na tabbatar da cewa ko mahaifin ki zai miki aure sai kin Kai UG 4 ko five gashi yanxun kike UG 1"


Gabanta ne ya Fadi tuna maganar mahaifinta, lokaci daya damuwarta ta karu harma da guntuwar kwallarta

Cikin sanyin jiki ta dubeshi,

" toh ya kenan? Nasan bazaka iya jirana ba ko?"


Murmushi ya kakalo " haba ya zakice haka? Zan jiraki mana ko shekara goma ne kuwa na miki alkawari"


Wani sanyi taji a ranta tare da Kara jin sonshi yana shigarta ta KO ina,

Cikin ranta kuwa haushin akida takeji irin ta mahaifinta,


Hannunta ya Dan Kama tare da murza yatsunta, " me kike tunani ne?"

  

Da sauri ta kwace hannunta tare da hararan shi, " miye haka? bana son irin haka fah"


Kunnuwan shi ya Kama tare da marairaice fuska " am sorry plz"


Wayarta ce tayi ringing da sauri ta duba ganin mahaifiyarta ne yasanya taji gabanta ya fadi,

Cikin tsoro ta dube Yazeed dake kallonta,

Tace, " nashiga uku momy ce"


" dauka kice Mata kina hanya" ya fada cikin rada,


Cikin ladabi ta dauki wayar, "momy Ina hanyar dawowa," tafada tere da katse wayar ,


A gurguje sukayi sallama da Yazeed duk da cewa ba haka yaso ba ita kanta ma ba haka taso ba sai dai don ba yanda suka iya ne, haka suka rabu cikin kaunar junan su tare da kewa Mai tsanani, 

Kasancewar satinsu uku basu hadu ba ta dalilin Hutun da Afnan din keyi na makaranta.


Ayshart one

[12/29/2016, 8:36 AM] Ayshart one:  Yazeed ko Yaseer

       Nah

   Ayshart Farouq 

   

        NWA

       

       10-15


Aisha Afnan 'ya ce gun Alh Umar Adam, Wanda ainihin shi mutumin kano ne, yanada diya uku Ibrahim, Sagir da Aisha Afnan, matar shi daya wato Hjy Zainab,

 akwai tazarar haihuwa sosai tsakanin yaran su kuma tun bayan haihuwar Afnan basu sake samun haihuwa ba shiyasa suka dauke son duniya suka daura Mata, 

tun Afnan tana karama burin mahaifinta tazamo lawyer, shiyasa kwata kwata bata kula samari har ta gama secondary school batada wani saurayi ko wani Wanda take so ba kuma don babu masoyanba sai dai don wannan ne ra'ayin ta da na mahaifinta,

Ibrahim kuma ya qare karatun shi na medicine a jami'ar england yayin da sagir yake karatun business admin a malesia yayin da Afnan take UG one a jami'ar bayaro da ke jahar kano tana karatun law.

Tunda take karatun ta Kawai tasama gaba bata damu da harakar kowa ba sai ta karatunta,

Tun lokacin da wani guy ya kyalla ido yaganta yake bibiyar ta amma Ina yayi duk yanda zaiyi don yaga ya mallaketa amma ya kasa saboda ita ba irin matannan ne ba da zaka samu lokaci daya kasanar dasu bukatar ka ba,


Wata Rana ta fita shopping tare da driver sai motar su tasamu matsala ta tsaya musu kan hanya ganin lokaci zai kuremata kafin a gyara yasanya ta yanke shawarar shiga a dai daita, 


bayan tashiga shop rite din ne tafara diban kayan da take so, takai hannunta gurin wani turare kenan sai aka dauka da sauri ta juya don ganin KO waye, sai dai kallo daya ta mishi ta sauke idanuwanta kasa saboda kwarjinin shi da tsabar haduwar shi, murmushi yayi tare da cewa,


" wannan turaren nawa ne nariga ki ganin shi ki zabi wani, ko in zabar miki ne? don Sam wannan ma bai dace dake ba,"


Karo na farko a rayuwata da taji wani namiji ya burgeta, gyada mishi Kai kawai tayi tana kallon shi, wani Kala ya dauko Mata ya mika mata , karba tayi tare da yi mishi godiya ta wuce abunta taci gaba da dibar abunda take so,


 saida takare kaf sannan taje gurin biyan kuddin, card dinta ta cire ta mika, ba zato taji ance Ai anbiya Mata mamaki ne ya kamata ganin kusan kayan 25k 

"toh waye ya biyamin?" ta tambaya nuna Mata shi akayi yana tsaye sai murmushi yake mata,


 daure fuska tayi ta isa kusa dashi,  

" malam miye na biyamin kuddi alhalin kuwa ban saka ba?"

Murmushi yayi tare da cewa, 

"Afnan kenan"


Zare idanuwa tayi tana kallon shi jin ya ambaci sunan ta mika hannu yayi tare da karbar kayan hannunta " banan ya dace muyi mqgana ba kinga mutane sunata wucewa a gurin,


Yanda yayi maganar sai taji ya sake burgeta saboda yasan mutuncin kanshi da darajar diya macce, sake mishi kayan tayi tare da bin bayanshi har bakin motar shi,


 sanya kayan yayi a motar tare da cewa, "oya shiga muje "

Girgiza mishi Kai tayi 

"a'a bazan shiga motar ka ba tare nake da driver,"

Murmushi yayi 

"ai har yanxun bai gyra motar ba" 

ya fada yana kallonta,


" Anya kuwa wannan mutum ba aljani ne ba" ta fada a ranta,


Ganin ba sarki sai allah ne yasanya ta shiga motar tashi tare da jero mishi tambayoyi " Kai waye? Kuma a Ina kasanni?" 


Murmushi yayi am yazid kuma nasanki da dadewa ya bata amesa batatare da ya kalleta ba,


" so why did u do all this to me ?" Ta sake tambayar shi,

 

Kai tsaye yabata amsa da saboda Ina kaunar ki, wlh Afnan soyayyar ki ta Dade a cikin raina ban San ta yanda Zan gaya miki ba saboda naga baki damu da kowa ba,

Ni sunana Yazid Ahmad Abdulrahman mutane suna kirana da Ahmad Y Abdulrahman Ina masters ne a bayaro university anana na sanki faculty dinmu daya dake I hope wannan ya gamsar da ke,?"


Ita dai Afnan kasa cewa komai ta yi saboda mamakin shi da yakamata ganin har saida yakawota bakin motarsu da ake gyara,


" idan baxaki damuba Ina son ki bani number ki ko don murika zumunci,"


Ba musu sukayi musayar number, toh tun daga ranar suka fara waya kuma suna haduwa a school tun dai Afnan tana dari dari fashi har ta daina ta saki jikinta dashi soyayya mai tsanani tashiga tsakanin su,

Nan ta fayyace mai ra'ayin mahaifinta akanta inda Shima akayi sa'a iyayen shi sunada wannan ra'ayin duk da bai Kai irin na mahaifinta ba, haka yasa Yazid ya daukarma alkawarin aure duk wuya duk rintsi..

[12/29/2016, 8:36 AM] Ayshart one: Yazeed ko Yaseer


       Nah


Ayshart Farouq


      NWA


    15-20


 Da sauri ta Afnan ta is a gida gabanta sai faduwa yake ganin motar mahaifinta, Mai aikinsu taxi Karo da ita a falo cikin faduwar gaba tace, " momy fah?"


Salah Mai aiki tace," tana sama gurin Alhaji,"


Dakinta ta wuce jikinta duk ya mutu tayi zaune tare da rafka uban tagumi Allah Allah take tana addu'a Allah yasa baima momynta fada ba, tana cikin hakane taji wayar mimynta ta sake shigowa, da Sauri ta dauka " momy na dawo tun dazu Ina daki"


Can bangaren aka amsa da cewa, " Afnan kizo dadyn Ku na neman ki,"


Batare da bata lokaci ba ta nufi part din mahaifinta cikin faduwar gaba don har ga Allah ta tsane kiran mahaifin nata duk da tasan baima fiye yimata tsanani ba akan sauran yayunta.


Da sallama ta shiga dakin tare da gaida iyayenta, cikin fari'a Abba ya ce, " zo nan uwata" murmushi Afnan ta Saki ganin ba wata matsala,


Can ta matsa kusa da abbanta yayin da wayarta tayi Kara, da sauri mahaifinta ya kalleta tare da mika hannu ya karbi wayan don ganin ko waye yake kiranta,


Cikin tashin hanakali Afnan ta mika mishi wayar ganin sunan dake rubuce wato maryam2 ,


Ganin sunan ne yasanya yamika Mata wayar tare da cewa, " dauki wayar tukun, 


Hannunta har rawa yake gurin karbar wayar, kafin tayi wani abu har Call din ya tsinke, ajiyar zuciya tayi har saida abban Nata ya kalleta, 


Kafin suce komai wayar ta sake daukan ruri, a hanakali ta Kara wayar a kunne " assalamu alaikum" can bangaren aka amsa da "my princess da fatar kin isa gida lfy", marar gaskiya Ko a ruwa sai yayi jibi duk a.c dake dakin bai Hana Afnan yin zufa ba don ganin take tamkar mahaifinta najin abunda Yazid ke fadi ,


A sanyaye tace, " eh wlh maryam nazo ban sameki ba , ok to sai mun hadu islamiyar gobe,"


 tayi saurin datse wayar tare da mikawa Abbanta wayar,


Cikin murmushi ya karba, sai da ya duba contacts dinta kaf duk tana zaune tana kallon shi, wata kwalla Ce ta zubo Mata wadda batasan lokacin da ta zubo ba.


Momy dai zaune kawai take tana Lura da halin da diyar tata take ciki, nan take duk tausayin ta ya kamata yayin da cikin ranta take tir da hali irin na mijinta da ya kasa gane halin da rayuwa take ciki a wannan zamani,

 

Kasa hakura tayi saida tayi magana 

" amma dai fisailillahi alhaji abunda kakewa Afnan Sam bai dace ba kaine ka haifeta amma ace ka kasa yadda da ita wannan wace irin rayuwa ce,


Dagowa yayi ya kalleta fuskarshi tamke,

" bana son irin abunda kike mun zainab ni Ina hango abunda baki hango ba, kun matsa abata waya na bata waya don haka dole ne a gareni matsayina na mahaifinta in Lura da abunda take da wayar don bana so Allah ya kamani da wani laifi akan tarbiyar Afnan gobe kiyama, don haka idan kinji kina iya taimaka min mu tarbiyantar da ita walillahil hamdu idan kuma kinji baki iyawa kuwa kada ki sake min magana akan abunda nake ganin shine dai dai."


Cikin bacin rai momy tace, "ai wannan abun da kake ba shine tarbiya ba, tarbiya duk bai wuce ka aurar da ita ba "


Daga Mata hannu yayi " kinfi kowa sanin cewa ni mutum ne wanda yake so yaga Dan Adam ya dogara da kanshi don haka maganar aure ba matsala bace, idan lokaci yayi ni da kaina Zan zabo Mata mijin da ya dace da rayuwarta,"


Afnan najin wannan maganar Bata San lokacin da ta fashe da kuka ba Wanda saida yabaiwa iyayen nata mamaki dukan su ,


Da sauri Abba ya dubeta " miye haka Afnan? Mi kekewa kuka ne?


Cikin bacin rai momy tace, " ai dole tayi kuka tunda taji kana nema ka tauye Mata hakki, wallahi alhaji kaji tsoron Allah kasani yanda mukeda hakki akan yaranmu haka suma suke da hakki a kan mu," 


Jikin Abba yayi matukar sanyi baice komai ba ya mikawa Afnan wayarta tare da cewa ,

" tashi kije daki Afnan yi hakuri share hawayen ki, jeki Zan sake nemanki ,"


Jikin Afnan sanyi kalau ta tashi taje daki da tunani da yawa a zuciyarta ,

Number maryam2 ta lalubo wato Yazeed dinta, fira suka shigayi sosai tamkar za su cinye junan so saboda so da kauna, basu sukayi sallama ba saida aka fara kiran sallahr magriba..


Ayshart one

[12/29/2016, 8:36 AM] Ayshart one: Yazeed ko Yaseer 

      

      Nah 


 Ayshart Farouq 

      

      NWA


      20-25

Bayan sati biyu da faruwar haka Afnan suka koma makaranta wannan karon komawa hutun ya Mata dadi don kusan kullun tana tare da Yazeed dinta karatun ma yanzu tafara ja baya dashi don wani lokaci ko attending lectures batayi tana can gurin yazeed suna soyewa haka kuma idan tadawo gida matukar tana daki to kuwa suna manne a waya,


Afnan! Afnan!" Taji muryar yayanta sagir yana kwala mata kira,


Harararsa tayi , " miye ne" tana kwance kan gado rungume da wayarta tana waya da Yazeed, hankalinta kwance saboda ba kowa zai fahimce waya takeyi ba amma duniya taki jinin tana waya dashi a katseta ,


Ganin hararar da take ta zuba mishi ne yasanya sagir din karasowa cikin dakin,


" ni kike harara?, Allah Zan buge idanuwan nan" 


Turo baki tayi " to miye ne na kwalamin Kira haka kaman kaban ajiya ne"


Tsaki yaja " to Abba ne ya aikoni in kiraki, idan kuma bazakije ba sai inje in fada masa kina waya bakida lokacin amsa kiransa",


Zaro idanuwa tayi "Allah gaya sagir ba waya nakeyi ba waka ce nake sha kada kamin sharri wlh bazan sake hararanka ba kayi hakuri Dan Allah kace, Ina zuwa"


"Kyat" yayi kyafci tare da banka Mata harara, " yace, " kinyi sa'a wlh da kinga sharri,"


Nan ya fice ita kuma ta mike da sauri,

Ta bangaren Yazeed kuwa sai tsokanarta yakeyi da yake headphone ne a kunnen ta,


" kicewa Abba kina biyayya Wa miji ne kina faranta masa rai kina masa fira Mai dadi yana jin muryarki Mai dadi tana ratsa jikinsa kina samun lada,"


Dariya Afnan din tayi tare da cewa, 

"Yazeed kenan!, kwarai kuwa Zan gaya mishi idan yazo min fada har Kai sai a tattara a hada"


Shima dariya yayi "ba komai ai kin San dama dadi da wuya munyi alkawarin rabashi nida ke,"


Murmushi tayi tamkar yana ganinta, " Zan dauki wuyar ka dauki dadin"


"_a'a ni Zan dauki wuya ke ki dauki dadin"


" ni dai a'a" ta fada cikin muryar shagwaba,


A kasalance yace, "kin ganki ko? kin Fara kashe min jiki da shagwabar nan taki ko? Yanzun tunanin ki sai ya fitine ni ya hanani sakat,"


Dariya tayi " ai haka nake so tunanina kadai yafitine zuciyarka "


"Afnan" ta sake jin muryar mahaifiyarta, da sauri ta katse wayar ta fita da gudu, tace,

" gani nan zuwa momy ina toilet ne "


" toh maza kiyi sauri Abban Ku na son magana dake tun dazu"


Ta karba da " toh momy"


Nan da nan ta nufe falon nasa zuciyarta cike da tunanin KO wane Kira ne yake Mata ?,


Ganin Ibrahim da sagir ne da tayi da kuma mahaifan nata yasanya gabanta yashiga faduwa dole ne tasan akwai maganar da Abbanta zai mata.


Ayshart one

[12/29/2016, 8:36 AM] Ayshart one: Yazeed ko Yaseer 

       Nah

 Ayshart Farouq


Nagarta Writes Association

    ©NWA©

.


       25

Guri ta samu ta zauna tare da cewa, " Abba Ina wuni, gani ance kana nemana"


" lafiya kalau Afnan" ya karba yana kallon ta cikin fari'a da kulawa irin ta da da mahaifi,

Ci gaba yayi da magana yana kallon Ibrahim da Sagir, "dama ba komai yasanya nataraku anan na ga face Ku zamo shaida a gare ni akan Afnan a matsayinku na yayunta"


Gaban Afnan yayi matukar faduwa toh me Abbanta ke nufi ne? Tsura mishi ido tayi cikin tsanani tashin hankali don jin me zai fada,


Wannan Karon baki daya annaurin fuskar shi ya chanja lokacin da yake magana, "Alhamdulillahi nasan nabaku tarbiya gwargwadon ikona musamman ma ke Afnan, saboda babu wani Dare da zan runtsa face nayi tunani matsayin hakkin ki da yarataya a kaina, wani lokaci banma sanin lokacin da hawaye suke zubo min idan na tuna cewa ke diya mace ce tarbiyantar dake yanada matukar wahala saboda idan kika lalace toh duka al'umma sun lalace haka kuma idan kika gyarau duka al'umma sun gyaru, hakika ban fahimce abunda nake miki na shiga hakkin ki ba sai jiya da mahaifiyar ki take Kara tuna min, ban kara gane maganar ta tayi tasiri a kaina ba saida naji kina waya jiya misalin karfe biyu na dare" 


Wannan karon Afnan fashewa tayi da kuka tana kallon mahaifinta, cikin ranta kuwa sai cewa ta keyi, " nashiga uku ni Afnan yanxu duk Abba yaji maganar da muke jiya,

Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" ta fadab tuna firar da sukayi jiya duka akan aure ne tana bawa Yazeed hakuri akan cewa suma iyayen su biyayya suyi abunda suke so ita kanta tana bukatar auren,.....


Katse Mata tunani yayi da cewa, 

"hakika sai jiya na tabbatar da cewa aure shine mutuncin duk wata diya macce da take rayuwa a doron kasar nan, tabbas Afnan na tauye miki inci, na shiga rayuwarki da yawa na hanaki walwala da sukuni akan kawai ingina rayuwarki don zamowa Mai dogaro da Kai Ashe ban sani ba kara ruguza miki rayuwa nayi, ta hanyar tsananin da nake miki gashi kin koyi yin karya karatun ma da nakeso kiyi shi kanshi yanzun bayi kikeyi ba soyaya kikiye right ?" Yafada yana kallonta,


Girgiza mishi Kai tashigayi "a'a Abba Dan Allah kayi hakuri kamini rai wlh Allah bazan karaba Abba wayar tawama ka karbe duk wani Abu dazakayi min kamin amma Dan Allah abbana kada kayi fushi dani, ka hukunta ni ta ko wace hanya amma Abba kada ka hukuntani ta hanyar yin fushi Dani" kuka ta fashe dashi Mai tsanani,


Mikewa mahaifin nata yayi tare da komawa kusa da ita yajawota jikin shi,

" yi shiru Afnan bakimin laifin Komai ba facema birgeni da kikayi da kika nuna biyayya ma iyayenki yafi komai muhimmanci a gurin ki dukda cewa wani guri ki kaucewa iyayen naki amma duk da haka ni nafi kowa laifi akan abunda kika aikata na saving number namiji da sunan mace," 


Juyawa yayi tare da kallon momy da dasu Ibrahim " Ku zama shaidata ni Usman nabaiwa Afnan damar 

ta gayawa wanda takeso ya turomin magabatan shi"


Wata irin dagowa tayi tana kallon mahaifinta,

Duk da cewa maganar tamata dadi amma ita harga Allah ba haka taso ba,


Gyada mata Kai yayi am serious Afnan kice mishi ya turo min magabatan shi, Ina so infita hakkin ki ne, inaso inaga magabatan shi shi zai sanya in yadda da gaske yakeyi koda kuwa ba da wuri za'ayi auren ba idan da wuri za'ayi ma walillahil hamdu a shirye muke",


Kunya ta Kama Afnan "a'a Abba ni nafasa karatuna zanyi"


" kaji ja'irar yarinya karatun ma da kika jama baya taya zakiyi karatu ai idan muka barki zamu tabka babban kuskure a rayuwar mu gashi tun yanzu anfara haka ina gaba" inji momy


Abba yace, " a'a zainab ko gaba bama ganin komai da yardar Allah,

Afnan ai aure baya hana boko hakama boko baya hana aure kaman yanda mahaifiyar ki ta gayamin,

Idan har minjin ki ya baki damar kici gaba da karatu walillahil hamdu idan ma hanaki ci gaba yayi duk daya ne Allah dai yamana jagora a rayjwarmu kawai,"


Dukan su suka karba da "Amin"


      26

Afnan kam har kaguwa tayi Abba ya sallameta taje ta fadawa Yazid dinta wannan good news din,


Kaman Abba yashiga ranta " toh uwata aje a gayawa surikin nawa Ko"


Kunya ta kamata "uhm ni fah Abba na fasa"


Ibrahim dake zaune ya galla Mata harara " ai haka zakice ki rika mawa momy karya kina satar hanya kuna haduwa"


" ya subhanallah wai me suke nufi ne? Ba dai duk abunda take suna hankalce da ita ba?"

Kukan shagwaba tasanya " Abba ka ganshi ko?"


" kyaleshi uwata shima na bashi nan da sati biyu yafadi yarinyar da yake so aje amishi magana"


" zaro idanuwa yayi yana sosa keya, "uuhm dama wlh Abba Ina so muyi magana da Kai kan wata yarinya amma ban San ta inda Zan Fara ba,"


Dariya akayi duka momy tace, " yanzu ai kanwarku ta buda muku ta inda zaku Fara don ko sagir nasan can akayi"


Sagir yace, " tab momy rufa min asiri ni ai har yanzu yaro ne ga dai su big bros nan masu shema'u da Hafsa"


Harara Ibrahim ya watsa mishi " Ina wasa da kai ne?"


Dady yayi murmushi yace, " kasameni anjima muyi maganar" ya fada tare da mikewa, 

Momy ma mikewa tayi tabi bayan shi,


Afnan dai kasa mikewa tayi don gudun tsokanar Sagir don tasan tana mikewa zai hauta da tsokna,


Ibrahim ya harareta "toh ai sai ki tshi ko kinxo kin muna zaune kina kinibibi"


Zunburo baki tayi tare da mikewa dama abunda take so kenan,


Dariya suka hauta da ita don tune sun ganota, bata kulasu ba ta wuce abunta tana murna,


Tana shiga daki kan gado ta fada tare da kiran Yazid,

Bugu daya ya dauka tamkar dama jiraye yake da ita,

" albishirinka habibina" yanda tayi maganar saida ya lumshe ido saboda dadin muryarta,


" goro" yafada a kasalance, " amma Allah yasa bani ke akayi"


Dariya tayi,

" Kai wani lokaci haka kake tamkar aljani,"


Mikewa yayi daga kwancen da yake don jin me zata fada,

" Ina jin ki plz na kagara inji"


Dariya tayi tare da kwashe duk yanda sukayi da abbanta ta gaya mishi,


Yanda yaji maganar yana tunanin a duniya ba Wanda yakaishi jin dadi " Afnan da gaske kikeyi kuwa ko tsokana na kikeyi" ya fada cikin tsantsar farin ciki,


" Allah da gaske nakeyi Yazid Abba yace ka turo magabatan ka"


"Alhamdulillahi Afnan nayi farin cikin jin wannan maganar taki sosai insha allahu nan da 1 wk zasuzo amma kafin hakanan yau zanzo zance gidanku nasan dai ba matsala ko?" Ya fada tamkar yayi tsale yaganshi gurinta,


" Zan sanarda Abba duk yanda yace sai in sanar dakai duk da bana tunanin zai hana,"


" toh ba damuwa sai naji ki".


Haka dai sukata waya suna jin su tamkar sunfi kowa farin ciki a fadin duniyar nan,

 Bama kaman Yazid da yake ganin yakusa cimma burin shi kan Afnan don yana ganin wannan hanyar ce kadai zaibi don ganin yasamu abunda yake so a gurinta.


Dan Allah masu karatun wanna novel kuyi hakuri da yanda kuka samu typing din nasan dole a samu kura kurai da yawa a ciki kasancewar wayata tanada matsala don mota ta takata wannan ma da kyar nayi shi saboda sizing din da wayar keyi.

Nagode


©Ayshart one©

[12/29/2016, 8:36 AM] Ayshart one: Yazeed ko Yaseer

       Nah

 Ayshart Farouq 


Nagarta Writers Association 

   ©NAW©


     27


Haka Afnan taje ta sanar da mahaifinta yanda sukayi da Yazid din,

Yaji dadi sosai har yabashi damar yazo amma yau ka dai don shi baya son yawan firan nan ba tare da anyi tsayayar magana ba,


Haka taje ta sanar da Yazid, yayi murna sosai da jin maganar ta ai kuwa 8:00 ya isa gidan su. 

Lokacin Afnan taci kwalliya tamkar wadda zataje gasar kyau, falon baki ta kaishi yayin da ta hada mishi kayan motsa baki iri iri,


Lokacin da ta shigo falon suma ne kawai baiyi ba gurin kallonta, don baki daya ta tafi da tunanin shi da hankalin shi har baima San lokacin da mike yaje gabanta ba.


Ganin haka ne yasanya tayi tsaye cak tana kallon shi don ganin abunda yake shirin aikatawa,


Ai kuwa kafin kace mi tuni ya rungumota yana shin shinar kamshinta duk ilahirin jikinshi rawa yake idanuwan shi sunyi jajur tamkar mayunwacin maye,


Cikin tsananin tashin hanakali ta tureshi daga jikinta,

Cikin tsawa take magana, " meye haka ne Yazid? Me yasa kai sam baka tsoron aikata abunda Allah yayi hani dashi? nifa ba matarka ba ce meyasa kake son tabamin jiki?,"


Dafe kanshi yayi da hannayen shi duka biyu, " oh my God! Me nake shirin yi ne?, Afnan am totally out of my control wlh jina nake yau tamkar ankawo min ke a matsayin matata plz Dan Allah kiyi hakuri wlh shaidan ne ya rudeni plz Afnan,"

Yanda yayi maganar tamkar yayi kuka,


Abunka da so nan take tausayin shi ya kamata,

Hararan shi tayi, " toh naji amma kaji kasake min irin haka Dan Allah"


" insha allahu bazan sake ba" ya fada yana sosa keya, " but plz kimin alfarma in rika hannunki in kaiki ki zauna" ya fada cikin sigar zolaye harda kanne ido,


Dariya tayi tare da wucewa "idan zaka zo ka zauna ka zo idan bazaka zo ba ga hanya nan Allah raka taki gona,"


Shima cikin dariyar yazo ya zauna kusa da ita yana kallon ta "wai kin ganki? Allah tamkar amarya"


" uhhm! Allah ko?"


Gyada Mata Kai yayi "sosai kuwa my Afnan"


Agogon hannunta ta duba "kaga fah lokaci na wucewa gashi bakama ci komai ba" ta fada tare da Fara zuba mishi abincin,


Haka yaci abincin dukda bayaji yunwa, yasan idan yace bazaici ba rigima kawai zasuyi,


Fira suka shigayi sosai tamkar ranar suk Saba haduwa,


Bashi yabar gidan ba sai kusan 10:30 shima ba don yaso ba sai dai don ba yanda zaiyi ne.


Yau sati biyu da faruwar haka amma ba Yazid ba samatar sa, hankalin Afnan yayi matukar tashi gashi ko ta Kira wayar shi bata zuwa,


Kwance take kan gado idanuwanta na kallon sama hawayene keta sintiri a fuskarta, tunani da yawa a zuciyarta " toh me yasame Yazid ne?, ko kuwa dama bayada ra'ayin aurena ne?, Kai wannan bazaima yuyuba Yazid yana sona nasan bazaimin haka ba"


Wata zuciya tace, " kika sani ko matsala ya samu daga iyayen shi ne" wata zuciyar kuwa cewa tayi, kila kuwa wani Abu ya sameshi Kai kilama mutuwa yayyi baki sani ba.


Ai kuwa tamkar wani ne ya gayamata, ta shiga rera kuka tamkar ranta zai fita,

Wayarta ce tayi ringing da sauri ta mika hannu ta dauko tana addu'ar Allah yasa Yazid dinta ne,


Sai dai kash! Ba Yazid idanuwanta suka gani ba sunana mahaifinta ta gani, ai kuwa lokaci daya hankalinta ya sake matukar tashi don tasan wannan kiran bama na lafiya ne ba, 


Cikin muryarta da ta dusashe ta dauki wayar,


Sallama kawai mahaifin Nata ya karba tare da cewa, " uwata kizo Ina neman ki yanzunnan" bai tsaya yaji Mai zatace ba kawai ya kashe wayar,


     28

Wayar Afnan ta tsurawa ido " toh me ke shirin faruwa ne? Dole ne ma nasan maganar Yazid abba zaimin toh me zance masa?" 


Ganin batada mahita ne yasanya ta mike taje ta wanke fuskarta sannan ta nufe gurin kiran da Abban nata ke Mata.


Da sallama ta shiga dakin mahaifin nata, bayan ta gaidashi ya karba cikin fari'ar shi, yamata izini da ta zauna, bayan ta zauna ya dubeta " me yake damun ki ne naga idanuwanki sunyi ja,"


Murmushi ta kakalo "ba komai Abba daga bacci na tashi,"


" eyya ai kuwa da nasan bacci kike da ban takura miki ba"


" a'a wlh Abba ai ba komai dama lokacin tashina yayi ai"


Yace, " OK dama na kiraki ne kan maganar yaron da kika ce kina so,"


Ras! Gabanta ya fadi 


Yaci gaba da magana, " naji dadi sosai kan abunda yaron yayi don haka da yayi shi zai nuna yaron kirki ne kuma da gaske yakeyi don kusan kwana biyu kullun sai ya kirani ya gaidani, yanzu haka ma bamu dade da kare waya dashi ba shida mahaifin shi,

Ya bani hakuri kan cewa basu samun zuwa wannan satin sai bayan sati biyu saboda ankwantar da Yazid din bashida lafiya kuma wai zaiyi tafiya a wannan satin sai dai yadawo," 


Gaban Afnan ya fadi hankalinta yayi matukar tashi, duk da kwarai taji dadin maganar da mahaifin nata yayi amma jin rashin lafiyar Yazid sai taji duk ta kara rikicewa,


Abba yaci gaba da magana "yanzu dai nace masu suyi hakuri nan da sati biyu masu zuwa sai ayi maganar saboda nima tafiya zanyi a yau kuma ina tunanin zanyi sati biyu ban dawo ba shi yasa na kiraki ingaya maki don infitar miki da hakkinki dukda nasan wannan maganar ba dole ne sai kinjita ba amma abun ne yayi matukar birgeni na ganin mutanen sun San hakkin Dan Adam sosai.


Afnan tayi murmushin jin dadi, " adawo lafiya Abba Allah ya tsare yakai lafiya"


"Ameen" ya fada tare da cewa, "amma fah uwata baki kyauta ba da baki gayamin surukin nawa ba lafiya ba"


Rufe idanuwanta tayi "ai Abba yaji sauki"


" toh Allah bida lafiya" yafada tare da mikewa,

" ki kiramin momyn ki lokacin tafiyata na matsowa,


"Toh abba" ta fada tare da mikewa.

 

KaromKaroma taci da momyn zata shiga falon shi yasa bata gaya Mata ba ta wuce kawai dakinta ta fada kan gado tana hamdala.


Number Yazid ta sake dialing amma still number bata zuwa, tsaki tayi tare da wulgar da wayar,

Hakika tasan tana muradin jin muryar shi tare da marmarin ganin kyakkyawar fuskar shi.


Safiyar yau ma haka ta tashi da mafalkan Yazid iri iri, ji take yau bata iya rayuwa idan bata ganshi ba ko taji muryar shi ba, haka ta shirya taje makaranta jikinta duk ba dadi 


Bayan sun kare lectures ne sun fito tana zaune kan wata kujera tana Danna wayarta taji anmata sallama,


Amsawa tayi ba tare da ta dago fufuskarta ba jin ya Kira sunana ta da Afnan ne yasanya tayi saurin dago fuskarta,

 


       29

Karaf suka hada ido da Yusuf abokin Yazid,


Murmushi tayi tere da cewa,

" a'ah manya gari kwana biyu ka buya kaida abokin ka ya jikinshi?"


Murmushi yayi shima, " Alhamdulillahi he's getting better amma fah fushi ya keyi da ke,"


Zaro idanuwa tayi "fushi fah kace?, "


" eh mana, ace yanzu duk rashin lafiyar da Yazid yayi kikasa zuwa dubasa gashi kullu cikin kiran sunan ki yake duka gidansu ba Wanda bai sanki ba har su Kansu sunyi mamakin rashin zuwanki asibiti duba shi,"


Jin an ambace asibiti yasanya tayi saurin dagowa ta dube Amnu, asibiti fah kace? shi Yazid din ne ya kwanta asibiti?


" uhum sosai kuwa yanzu haka ma yana can"


Idanuwanta cike da kwalla, "Allah ni ban san ma bashida lafiya ba sai jiya don kona Kira wayar shi bata zuwa"


Aminu ya dubeta cikin tausayawa " gaskiya Yazid bai kyauta ba amma yanzu ya kamata kije ki dubasa tunda kinji "


" wane asibiti aka kwantar dashi?"


Ya gayamata sunan asibitin yayi,


Duban shi tayi cikin damuwa " kash gashi nasarawa hospital ba a shiga yanzu sai 4"


" gskiya kam ba a shiga amma idan yanzu zakije muje in ajiyeki don Ina cikin masu jinyar shi za'a barni nashiga dake"


Ganin wannan ce kadai damar da zata iya zuwa dubashi ya sanya ta amince,


Cikin farin ciki aminu ya dauketa a motar shi suka nuface asibiti,


Suna isa likaita ya tabbatar musu da an sallameshi yanzunnan,


Haka suka fito jikin Afnan duk yayi sanyi gskiya tana son ganin Yazid,


Ameenu ya dubeta " yakamata gsky kije gidansu ki dubashi"


"A'a gaskiya bazan je gidansu bah idan naje mi zance?"


Murmushi yayi " ai ba kya isko mum dinshi sai daiko kannen sa"


Afnan bata so zuwaba amma aminu yata yimata dadin baki har ta amince da maganar shi ta bishi gidansu Yazid,


Kallo daya zaka Mata ka gane cewa bata cikin nutsuwarta, har suka isa gidan ita dai bite kawai take da shi gidan


Gidan ba Kara min kyau yayi Mata ba, cikin ranta tace, " gske dai Yazid yake Dan gata"


Batare da fata lokaci ba aminu ya kaita dakin Yazid din, nuni yamata da ta zauna, zama kawai tayi amma duk ilahirin jikinta rawa yake,


Yazid ne yafito daga wata kofa tamkar wand bai taba ciyoba don har kiba yadan Kara,


Wanni kallo sukayiwa junan su shida Aminu, take aminu yabi ta kofar da yazid din yafito yafita yana Dan murmhshi,


Ganin haka ne yasanya hankalin Afnan yakara tashi,


Cikin fari'a Yazid ya karaso yana cewa,

" wow Ashe dai kinyi missing Dina da yawa my princess"


Wani kallo tayi mishi cikin tuhuma, " me kake nufi Yazid ba dai lafiyarka kalau ba"


Murmushi yayi tare da zama kusa da ita tamkar ya shiga jikinta,

",dama gwadaki kawai nayi don Inga irin son da kikemin"


Mikewa tayi, " miye haka Yazid? Kada kasake min irin wannan wasar bana so?"


" oh common baby" ya fada tare da fizgota ta fado jikin shi "am sorry plz baby na wlh nayi missing dinki,

Yanda yake maganar yayi matukar bata tsoro don haka ta ganshi tamkar ba Yazid dinta ba idanuwan shi sunyi jajur,


" don girman Allah ka sakeni in wuce gida jirana akeyi"


"Nasani mana amma ai bazakije haka ba bakisha ko ruwa ba"


" uuhm a'a ni nagode"


" murmushi yayi tare da sakinta ya mike yayi gurin fridge, tana ganin hakanan tayi wuf zata fita sai dai kash an rufe kofar ta baya,


Tana ganin haka ta fashe da kuka,

" na shiga uku ni Afnan don girman Allah Yazid ka budemin kofarnan infita,


Bai kulata ba sai murmushin ketar da yakeyi, molt ta dauko ya nufota,

"Sai kinsha ruwa zan bude miki kifita " ya fada yana mika Mata molt din,


Da sauri ta amsa ta Dan kurba,

" toh gashi nasha muje"


" naki wayon" ya fada tare da amsar molt din ya shiga dura Mata ita saida yga ta shanye kaf sannan yajata da karfi suka fada kan kujera,


Kallo daya zaka mishi ka gane baya cikin hayyacin shi,


" plz Afnan dan Allah ki taimaka min wlh ina cikin tsananin bukatar ki"


Kuka tashigayi na tashin hankali tana rokon Yazid da yayi hakuri kada ya keta Mata mutuncin ta amma Ina baxai iya ba shedan yariga yayi mishi huduba.


Tun tanada karfi tana kokowa dashi tana tureshi har ta galabaita kasancewar karfi ba guda ba.


Tanaji tana gani Yazid ya rabata da mutuncin ta Wanda koni kaina marubuciyar saida nayi kuka ganin halin da Afnan take ciki.


©Ayshart one©

[1/2, 10:42 PM] Ayshart one: Yazeed ko Yaseer

      Nah

  Ayshart Farouq 


Nagarta Writers Association

  ©NWA©


      30

Kuka sosai Afnan keyi, yayin da Yazid yayi kwance reran yana maida nunfashi, ganin kukan nata bamai karewa ba ne yasanya yajawota jikinshi yana lallashinta, 


" plz Afnan Dan Allah kiyi hakuri ki yafemin wlh bada son raina nayi miki haka ba, i just don't know what to do, Ina cikin tsananin bukata ne shiyasa naga ke kadai ya dace ki taimaka min keda Zan aura believe me Afnan wlh ban taba aikata zina ba ya karashe maganar cikin kuka,


Tureshi tayi jikinta,

" bakada abunda zakace min in yarda da Kai Yazid, kuma kasani Alla yana ganin ka bazai taba barinka ba Allah ya isa tsakanina da Kai, ta fada tare da mikewa sai dai wani azbtacen ciyo taji Wanda yasanya ta sake komawa zaune tana fitarda hawaye.


Da sauri Yazid ya yunkuro don ya kamata sai dai cikin zafin nama ta bige mishi hannu,


" kada ka sake tabani macuci azzalumi, ka bude min kofa infita wlh ko inma abunda baka tsammani" 

  

" Dan Allah Afnan kiyi hakuri ki gyara jikin ki sannan ki je plz Dan Allah ba Dan halina ba"


" Kai har kasan Allah ne? Ai ni bana tunanin kasan Allah don da kasan shi da bakayimun abunda kayimin ba, ka bude mun kofa infita nagaya maka," ta fada cikin tsawa,


Haka ya mike jikinshi duk a mace yaje ya bude Mata kofar,

Da kyar ta mike tana dingirshi hawaye nafita idanuwanta ta bar gidan tana jin dama ba a haifeta ba da ganin rana irin ta yau,


Keke napep ta samu tashiga ta isa gida, amma kallo daya zaka Mata ka gane cewa ba lafiya ba,


Cikin faduwar gaba tana bin gini ta isa falon gidan, mahaifiyarta taci karo da ita zaune tana kallon sunnah tv,


" subhanallah Afnan lafiya kuwa? Me yake damunki ne?" 


Kasa bata amsa Afnan din tayi sai kawai ta fashe da kuka,


Hankalin momy yayi matukar tashi ta mike tsaye ta isa gurinta tana girgizata 


"Ki fada min Afnan me yake damunki?, lahaula walakuwati illah billa, Afnan miye a zanenki haka?"


Jin wannan tambaryane ya sake jefa Afnan cikin rudani,

K'ank'ame momy tayi 

" wayyo momy mutuwa zanyi marata ciyo takemin sosai "


Momy tayi ajiyar zuciya sannan ta ja diyar tata cikin tausayawa " kai wannan ciyon mara ya gwada miki bone Allah dai ya miki maganin shi, muje ciki ki wanke jikin ki kisha magani kinji"


Haka tajata takaita har daki tare da fitar Mata da magungunanta sannan ta fita tanata jimamen ciyon Mara irin na diyar tata,


Afnan kuwa ba abunda takeyi a toilet idan ba kuka ba, rayuwarta ta Mata zafi ji take tamkar Allah ya dauki ranta ta mutu ta huta da wannan rayuwar duniyar,, ganin kuka bazai Mata magani ba yasanya ta daure ta gasa jikinta a ruwan zafi sannan tayi wanka ta fito,.

Pain relief ta samu ta Dan sha sannan ta kwanta cikin kankanen lokaci bacci ya dauketa Wanda ya kasance baccin bakin ciki mafi muni a rayuwarta.


Sai bayan la'asar ta falka, jikinta ba laifi taji sauki sosai sai abunda ba'a rasa ba, arwalla ta Doro tayi sallah sannan ta sake kwantawa Sam bata damu da yunwar cikinta ba don tasan ko kadan bazata iya cin abinci ba,

Miss call din Yazid kan sunfi a kirga a wayarta tare da texts dinshi na ban hakuri amma ganin suma kara tunzarata yayi wata irin tsanar shi takeji a cikin zuciiyarta, kashe wayar tayi baki daya sannan ta kwanta, sai gab da magrib ta tashi, momy ce ma ta matsa Mata tadan ci abinci,


       

       31


Saida Afnan ta share kwana da kwanakki tana ignoring call din Yazid duk da tasan ba karamin takura zuciyarta tayi ba, saida taga ta gasa shi da kyau sannan tafara daukan call dinshi, shima idan ta dauka duk maganar da tazo bakinta gaya mishi takeyi sai daga baya ya samu ya lallasheta da magangannu masu dadi har yasamu ya shawo kanta ta hakura suka koma kaman yanda suke a da, amma wani lokaci idan ta tuna abunda ya Mata takanji ta tsane shi da duk ma wani namiji a fadin duniyar nan ita dai fatan ta Allah ya tabbatar da auren su ko zata samu kwanciyar hankali.


Bayan sati uku da faruwar haka Afnan ta shiga tashin hankali na rashin ganin call din Yazid har na tsawon sati daya tun tana sharewa har abun yafara damunta kasancewar tun lokacin da ya Mata fyade tabar kiran shi sai dai shi ya kirata, ganin haka ne ya sanya ta yanke shawarar kiran shi taji ko lafiya sai dai yanzu kusan kwana biyu tana kiran wayar a kashe, hankalinta ba karamin tashi yayi ba gashi Abban ta yace, iyayen yazid basu kirashi ba don haka ta gaya ma Yazid din jibi ya turo magabatan shi tunda ya dawo tun last week su kadai yake jira don yanada abunyi. 


Kwance ta ke ta kudndunne cikin bargo kasancewar yau da zazzabi ta tashi da ciyon Kai ga wata irin kasala da takeji,


 Momy ce ta turo dakin ta shigo da sallama,


" Afnan lafiyarki kuwa mahaifin ki na kiranki bakya dagawa,?"


"Rass rass! Gabanta ya fadi lafiya kalau momy kaina ne yake ciyo shiyasa nasanya wayar silent banji ba"


" eyya Allah ya sauwaka, tashi kije mahaifinki na neman ki sai kisha maganin" ta fada tare da wucewa


Haka Afnan ta mike jikinta duk ba dadi kanta tamkar ya cire saboda tsananin ciyo,


Falo ta same shi zaune kamar ko yaushe sallama tayi, tagaida shi tare da neman guri ta zauna,


Kallonta yayi cikin kulawa sannan yakira sunan ta da "Afnan"


"Na'am Abba" ta karba muryarta na rawa


Yaci gaba da cewa, "ina so ki san cewa duk abunda ya faru ga bawa daga Allah ne kuma Allah yana son bayinshi masu hakuri da tawakkali, Afnan yanzu Yaron da kike so ya kirani ya shaida min cewa ya fasa auren ki"


Wata irin Kara Afnan ta buga tare da faduwa kasa sumamma......


Har yanxu dai Ina Mai baku hakuri kan errors din da zaku gani manage ne kawai nake Ina typing din luv you all my fans


©Ayshart one©

[1/8, 9:53 PM] Ayshart one: Yazeed ko Yaseer 

      Nah

 Ayshart Farouq


Nagarta Writes Association

  ©NWA©


      32

  Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Abba ya shiga fadi tare da kwalawa momy Kira, itama momy da sauri tashigo dakin, ganin Afnan kwance ya sanya ta rude ta shiga tambayar Abba " me yafaru da ita ne alhaji?"


 Cikin dakakkiyar murya ya kwashe abunda yafaru ya gayamata, kuka momy tashiga rusawa tana fadin, "toh me tayiwa wannan yaron ne da zai saka Mata da haka? Gashi yanzu yaje ya kaimu ya baro",


Ganin kukan momy ba Mai karewa ba ne saima kara daga mishi da hankali da takeyi ne ya sanya ya rarume ruwa ya shiga zuba mata yana kiran sunanta.


 A hankali ta bude idanuwanta tar kan mahaifinta kanta ne takeji wani irin gingirim da shi, yunkurawa tayi zata tashi momy tayi saurin tayar da ita tana mata sannu, kallon mahaifiyar tata tayi idanuwanta cike da hawaye,

" momy kinji wai Yazid yafasa aure na"

Momy ta shafe Mata kwallar da ta zubo fuskarta " kiyi hakuri Afnan komai mukaddari ne, ko yanzu ma ai ba'a cire rai da tsammani tunda baki mishi komai ba"

 Gyada kanta tayi " momy Yazid ya cuce ni ya cuce rayuwata ya........... Bata ida fada ba taji zuciyarta ta hautsine wani irin amai ya taso mata, da gudu tayi toilet tamkar zata amaye yan hanjinta gashi dama cikin ba komai a cikin sa,


 Momy da ke bayanta sai sannu take mata cikin ranta tana matukar tausayin diyar tata da ta fada tarkon soyayya, 


Tana kare aman momy ta rikota jikinta duk ya gashe yayi zafi sosai ba wanni karfi a tattare da ita,

Momy tace, " alhaji inaga fah ya kamata aje da ita asibiti a dubata don naga jikinta yayi zafi sosai kar wani Abu yazo ya sameta daga baya,"

Abba yace, " nima abunda nake tunani kenan, yanzu dai abunda za'ayi kije kibata abinci taci nama Ibrahim waya tun dazu zaizo ya dubata.


 Haka momy taja Afnan ta kaita daki ta tsareta saida taga taci abinci amma abincin ko minti biyu masu kyau bai samu ba ta amayar da shi, hankalin momy ya tashi sosai, nasifa ta shiga yiwa yar tata don ita ganinta duk damuwar da tasawa kanta ne yasanya ta shiga wannan halin, saida taga hankalinta ya Dan kwanta sannan ta tashi tabar dakin,


Tana fita Afnan ta dora daga inda ta tsaya kuka ta shiga yi tamkar ranta zai fita, wata irin tsanar Yazid da soyayyar shi suka bijiro Mata lokaci daya, cikin ranta kuwa sai fadin takeyi, " Yazid ka cuceni ka rabani da mutunci na dama ashe ba sona kakeyi ba?, dama jikina kake so kuma ka samu Allah ya isa tsakanina da kai" haka taci gaba da kuka da surutai Kala kala ita kadai tamkar mahaukaciya, haka Ibrahim yazo ya sameta, shi kanshi ba karamin tausayi ta bashi ba allura ya Mata tare da wasu magungunna.


  Abba da momy kuwa haka suka sata gaba sunata kwantar Mata da hankali da magangannu masu dadi har takanji ta Dan fara samun relief din damuwarta.  


(Iyaye kenan Allah Kara mana son iyayen mu baki daya. Ameen)


Bayan kwana biyu da faruwar haka, ba wani chanji da aka samu kan rashin lafiyar Afnan saima abunda yayi gaba, zazzabi da amaye amaye kam ba'a ma magana abun ba karamin tayarda hankalin iyayenta yayi ba, shi yasa yau Abba ya yanke shawarar kiran likitansu don ya dubata yaga abunda ke damunta, tashin hankalin su daya kar ace ciyon zuciya ya kamata kan damuwar da ta sanya kanta a ciki.

       

      

       33

 Kasancewar yau asabar dukan su suna falo Afnan da ba wani karfi a jikinta tana kwance ta dora kanta kan cinyar mahaifiyarta kallo daya zaka Mata ka gane tana cikin matsala saboda yanda ta Kara haske ta rame tayi fau da ita, yanzu haka ma aman tayi ga ciyon kan da yazame Mata tamkar kadangaren bakin tulu idanuwanta ma bata iya bude su sosai saboda azabar da takeji,


Doctor ne ya shigo da sallamar shi, bayan sun yi 'yan gaishe gaishe Abba ya bashi damar duba Afnan ba tare da bata lokaci ba yafara aikin shi.


Bayan ya kare yi Mata tambayoyi ne ya karbe fitsarinta,

Ya dube Abba " just give me five to ten minute I will be right back" doctor ya fada tare da mikewa.


Batare ko da bata lokaci ba ya dawo duk suna nan zaune suna firar su,


Result din ya mikawa Abba, gwajin farko ya tabbatar da Afnan tana dauke da ciki na tsawon wata daya da kwana biyu.

Abunda idanuwan shi suka gani kenan mikewa tsaye yayi yana nuna likiti,

" amma dai likita wannan ba gaskiya ba ne ko?"

Doctor yace, "gaskiya alhaji abunda ka gani shine gaskiya 'yarka tana dauke da ciki"


" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Afnan kin cuce ne" Abba ya fada yana dafe zuciya saboda wani irin zafi da take mishi, ita kanta momy bata San lokacin da ta mike tsaye ba tana kalima, itama Afnan din mikewa tayi tana wani irin kuka Mai ban tausayi , yayin da Ibrahim da ke kokarin shigowa dakin yayi tsaye chak tamkar Wanda ruwa suka cinye,


 Cikin tsananin tashin hanmali Abba yayo kan Afnan din yana "fadin kin cuce ni Afnan kin wargaza min tsari kin tuddamin mutunci na kin............" Bai ida fadi ba ya fadi kasa warwas saboda bugawar da zuciyar shi tayi lokaci daya,


Momy dake tsaye sai lokacin hawaye suka zubo mata, da gudu tayi kan Abba tana girgiza shi su Kansu su Ibrahim din kanshi sukayo suna salati,

Afnan ma cikin tashin hankali ta matsa kusa dashi tana fadin, " wlh ba laifina ba ne fyade ya min wlh fyad........."


Marin da Ibrahim ya watsa Mata ne ya sanya ta katse maganar, 

" kika kashe mana uba wlh kema sai na kashe ki" ya fada cikin tashin hankali,


Doctor ya dube su "yanzu dai duk ba wannan ba mu dauki 

Alhaji mu kaishi asibiti tunda nan ba kayan aiki"

Haka ko akayi aka kama shi akayi dashi asibiti cikin ikon Allah aka samu kanshi sai dai yana tashi ba abunda ya ce face " na yafeki Afnan har abada" wannan furucin ba karamin tayarwa momy da hankali yayi ba,


Afnan kuwa daga waje ta tsaya kasancewar an hanamata shiga dakin, sai rusar kuka takeyi tana cewa ba laifinta ba ne fyade ya Mata,


Sai da aka samu aka mawa Abba allurar bacci sannan Ibrahim ya dube momy yace,

" momy miye mafita yanzu akan Afnan don nasan Abba bazai taba barinta ta zauna mishi gida ba"


Momy ta dubeshi cikin damuwa tace,

" inaga tunda tace fyade ya mata kaman abun zaizo da sauki, yanzu kamata yayi aje a same yaron a gaya mishi idan ma ta Kama a shiga kotu shiga za'ayi don a fitar Mata da hakkinta"

Shawarar tama Ibrahim dadi shima,

waje ya sameta zaune rakube tana kuka

"Ke" ya Kira sunanta fuskar shi tamke, "waye yamiki ciki? Kuma kikamin karya wlh yanka ki zanyi"

Saida ta fyace majina sannan tace,

"Yazid ne kuma wlh fyade ya min" 

" kin san gidan su Yazid din?"

Gyada mishi Kai tayi,

" eh nasani"

"Ok tashi muje ki kaini ingan shi"


Batare da gaddama ba ta mike, momy tace,

Itama zata bisu sai Sagir ya tsaya gurin Abba don tafi son ayi komai a idonta, ba yanda Ibrahim baiyi ba don ta tsaya tace ita alan balan sai taje, ba yanda ya iya dole suka tasa Afnan gaba har gidan su Yazid din.

     

    

         34

 A yanda Afnan keji ko daga bacci aka tadata zata iya zuwa gidan su don gidan bazai taba bace Mata ba har abada,


Hon sukayi maigadi ya bude musu suka shiga Ibrahim yayi parking duk suka fito,

Dai dai kofar da zata sada su da gidan suka bi wani mutum sukaci karo dashi, Wanda yanayin shigar shi ma zai tabbatar ma da shine mamallakin gidan,


Dakatar dasu yayi da cewa, Ina zaku masu gidan fah duk basa nan, hala bakuyi waya da hajiyar ba ne?" 


Hannu Ibrahim ya bashi suka gaisa, yayin da momy ta gaidashi, ita kuwa Afnan kallo kawai tabishi da shi,

  Ibrahim ya dube shi yace, " Dan Allah ko Ina zamuga Yazid?"


" Yazid kuma? Ku kuwa me koke nema da Yazid?" Alhajin ya fada cikin mamaki,


Momy ta dube shi tace, "ko Kai ne mahaifin shi?"


Gyada musu Kai yayi " tabbas kuwa nine mahaifin shi wani Abu ne ya faru?"


Ibrahim yace, "kwarai kuwa wani Abu ya faru don kanwata tana dauke da cikin shi na tsawon wata daya"


" what?" Ya fada da karfi, cikin tashin hanakali " u most b mistaken, Yazid dina bazai taba ai kata wannan aikin ba, tun wurima kuje Ku nemo wanda yama yarku ciki amma ba Yazid ba"


Afnan ta fashe da koka " wallhi Allah shi yamin fyade Allah shine"


Jin maganar fyade da Afnan tayi ba karamin tashin hankali alhaji ya Kara shiga ciki ba, 

Cikin mamaki ya sake kallon su " fyade fa ki kace?"

 

Afnana ta gyada Kai tana fyarce majina,


Saida yadan yi Jim na lokaci kadan sannan yace, " wannan magana bata yiyuwa anan Ku shigo daga ciki" ya juya suka bi bayan shi,


Falon shi suka shiga suka zazzauna ya sake dubin Afnan " kin dai tabbatar da abunda kika fadi gskiya ne ko"


Sake gyada Kai tayi "eh"


Wayar shi ya dauko ya Kira Dan nashi, " kazo yanzu ina falo ina nemanka"


Cikin minti biyu yaron ya sauko daga sama cikin tafiyar shi ta kasaita hannuwanshi duka biyu suna cikin aljihun shi, sallama yayi ba tare da ya kalle mutanen da ke zaune ba, gurin mahaifin shi ya nufa " Abba gani kana nemana"


Cikin nutsuwa mahaifin nashi ya dube shi tare da nuna mishi Afnan "me yarinyar can ta maka ka Mata fyade?"


Yanda ya dube Afnan d'ai zai tabbatar maka da cewa Kalmar mahaifin nashi ba k'aramin ruda shi tayi ba,


Ita kanta Afnan din tana hada ido dashi taji wata irin mumunar faduwar gaba don ita bata taba gani shi ba ma,


Haka Ibrahim ma da yakasa b'oye mamakin shi ganin abokin aikin shi da yayi,


Cikin tashin hankali yace,

"Dad fyade fa kace? Ni fah ban ma taba ganin wannan yarinyar ba" ya fada yana kallon mahaifin nashi,


Ran Ibrahim da ya gama baci bai San lokacin da ya cakume wuyan shi ba yana cewa,

"Karya kake yi macuci, Yazid ka cuceni ka cuce zaman tare"


Shi kanshi Yazid din rayuwar shi ta gama baci, cikin tsananin fushi ya ture hannuwan Ibrahim daga wuyan shi, "dakata Ibrahim kada kayi da nasani daga baya wallahi tallahi ban taba ganin wannan yarinyar ba" ya fada yana nuna Afnan,


Afnan kuwa kuka ne yaci karfinta ita kanta tasan bata taba ganin shi ba toh amma me ke shirin faruwa da ita,

Cikin kuka tace, " ya Ibrahim ba shine yamin fyade ba"


Baki daya kallonta sukeyi Ibrahim kuwa kanta yayi yafara jibgarta tamkar Wanda Allah ya aiko " don uban ki yau sai kin gayamin Wanda ya miki cikin nan"


Momy kam kuka kawai takeyi tana kiran " ku Kama min shi kada ya illata ta" 


Baki dayansu kasa tare shi sukayi,

Afnan naganin zai kasheta ya sanya tace,

" wlh shi ne yamin yace idan nace shi yamin kashe ni zaiyi "

Jin abunda ta fada ne ya sanya Ibrahim ya saketa ya koma kan kujera yana dafe Kai saboda tsananin tashin hankalin da yake ciki,


Yazid kanshi cikin tashin hankali yace, " ni mukayi haka da ke?"


Gyada Kai tayi alamar eh.


Kafin kace, me tuni mahaifin shi ya kwashe shi da wani irin wawan Mari, " irin wannan tarbiya na baka? Wallahi Yazid ka cuce ni"


Afnan kuwa tsanani tausayin yaron ne ya kamata saboda tasan taci amanar shi ba kadan ba, sai dai dole ne yasanya tayi haka don ta ceci kanta,


Muryar da bazata taba mantawa a rayuwarta ba taji "wai dad hayaniyar me akeyi ne?"


Mikewa Afnan tayi tana nuna Mai maganar "wallahi wannan Yazid din ne yamin fyade"


Baki dayan su kallon shi sukayi, 


Cikin mamaki mahaifin nasu yace, " ikon Allah YASEER din ne kuma yanzu ya miki fyade? Toh me kike nufi? Su fah ba yan biyu ba ne kuma basa Kama da juna, Kai wannan yarinyar Sam bakida gaskiya kawai ki fadi tsakani da Allah Wa ya miki fyade a cikin su yazeed ko Yaseer?,?


Ni dai marubuciyar nace daya daga cikin su ne ya Mata fyade, toh waye daga ciki YAZEED KO YASEER?


Masu karatu Ku biyoni next post don jin waye yazeed da Yaseer kuma Wa yamata fyade a cikin su


©Ayshart one©

[2/17, 1:08 PM] Ayshart one: Yazeed ko Yaseer 

      Nah 

Ayshart Farouq 

      NWA


   

        35


Kuka Afnan ta shiga yi tana nuna Yaseer din da ya shigo Wanda shima kanshi mutuwar tsaye yayi yana kallonta sai dai sanin abunda ya aikata ne yasanya yayi tamkar bai taba ganin halittarta a duniya ba, ganin haka ya sanya Afnan tayo kanshi tare da ciyo kwalar shi, "wlh Allah shi yamin fede wlh shine Yazid kaci amanta ka cuce ni"

Buge hannuwanta yasir din yayi, " ke kinada hankali kuwa waye ke? Meye hadina dake da zakimin sharri?" Alh ya dube Yasir din yace, " ya isa haka yasir zo ka zauna abunda ta gama cewa Yazid kenan "

Jin haka ne ya sanya Afnan tayi wata uwar Kara tare da fashewa da wani matsananci kuka, cikin ranta tambayar kanta take, me ke shirin faruwa Dani ne? meyasa Yazeed zai min haka? taya Yazeed ya koma Yaseer ? Gigitaccen Marin da aka dauketa da shi ne ya dawo da ita cikin hayyacinta, sake daga hannu yayi ya sake dauketa da wani Marin Wanda saida taga wuta cikin tsananin fushi yake magana,

"Kin cuce mu Afnan, kin cuce kanki, kin kuma cuce kauna da tarbiyar da mahaifinmu ya baki".

 momy kam tunda ta zauna banda hawaye ba abunda takeyi, duniyar baki daya ta Mata zafi, mikewa tayi tana dubin su Yazeed din da suka zuba ma ikon Allah ido suna kallo, " Dan Allah bayin Allah kuyi hakuri da Abunda ya faru" ta fada dakyar tana maida nunfashi, jin yanda take maganar ne ya sanya Ibrahim yayi saurin dubota amma kafin kace me daga kafarta keda wuya ta sulale ta fadi kasa, Ibrahim yayi kanta da sauri yana jijjigata, 

Afnan da ke tasaye baki daya kasa komai tayi dakin kanshi duhu yake Mata wata irin juwa take gani ga wani irin matsanancin ciyon marar da ya taso Mata wata irin Kara ta kwala ta zube kasa yayin da jini yaketa bin kafafuwanta,


Ibrahim kam ya rude iya rudewa yarasa kanwa zaiyi ga mahaifiyar shi ga kanwar shi, duk da tsanar Afnan din da yake kasan cewar ita taja komai, yasan tana bukatar taimako Ruwan da Yaseer yayi saurin kawowa ne yazubama momy amma Ina ko motsi batayi ganin haka yasan ya,

Ibrahim din cewa "pls Yazeed Ku taimaka min mu kaisu asibiti Dan Allah."

Yazeed kam har zuwa lokacin haushin Afnan yakeji saboda tamishi abunda ba'a taba yi mishi ba. Yaseer kuwa wani irin tausayinta ne ya kamashi sai dai ba yanda zaiyi don yasan ba yanda za ayi yace shi yamata ciki a zauna lfy.


Cikin motar Ibrahim aka sanya momy yayin da aka sa Afnan cikin mota Yaseer suka nuface asibiti,


Direct emergency aka nufa dasu don ceto rayuwarsu bama kaman Afnan da taketa bleeding.


Cikin ikon Allah momy ta farfado sai dai jininta ya hau sosai don harma yafi na dady hawa.

[3/19, 12:54 PM] Ayshart one: Yazeed ko Yaseer 

       Nah

  Ayshart Farouq 

       NWA


      36

Afnan kuwa har kusan magrib bata San inda kanta yake ba, cikin jikinta ma ya zube saboda wahala da damuwar da ta shiga saida ma aka Kara Mata jini.


Har zuwa wannan lokacin kuma Yazeed da Yaseer suna nan a asibitin, shi Yazeed yana zaune ne kawai don amincin da ke tsakanin shi da Ibrahim, Yaseer kuwa Abubuwa da yawa suka sa shi zama a asibitin.

 Ibrahim ne yafito dakin da momy take, hannu yabasu sukayi musabuha tare da ce musu, " nagode kwarai fah da dawainiya Allah ya saka muku da alkhairi" suka karba da ameen,

Yaseer yace, " mushiga daga ciki munganta don wucewa zamuyi lokacin sallah na gabatowa,

Harararshi Yazeed yayi don shi bai so haka ba son yayyi su wuce tunda ga Ibrahim nan yazo, ba yanda zaiyi dole yabi bayansu suka shiga dakin da Afnan din take ciki,


Kwance take har zuwa lokacin, kallo daya zaka Mata kagane tana cikin mawuyacin hali saboda yanda take jan nunfashi da yanda take maida shi.


"Har yanzu bata falkla ba?" Cewar Ibrahim yana duban nurse din da ke daura Mata drip a hannu,

"Gaskiya yanada wuya ta falka yanzu saboda Injections din da aka Mata masu karfi ne, inaga sai zuwa dare ko tana falkawa"


Cikin damuwa Ibrahim ya bude baki zaiyi magna, wayar hannnushi tayi kara, cikin ladabi yake karba wayar, Wanda ya nuna alamar da mahaifin shi yake magana, kallo daya zaka mishi ka tabbatar da baya cikin nutsuwar shi saboda yanda yaketa bawa mahaifin shi hakuri, jikinshi mace ya ajiye wayar.


Yazeed da Yaseer kuwa zuba mishi idanuwa sukayi ganin yanda yaketa gumi,

"What happen friend?" Yazee ya fada yana kallon shi,


Shafe zufan da ke karyo mishi yayi, "their is problem friend I need you helps"


"Ok inajin ka how can we help u?"


Cikin damuwa Ibrahim ya ce, " dady yace yanzu yanzun nan inzo yana nemana kuma bayq so kafata ta sake takowa wajjen Afnan ya yafeta bata cikin 'ya'yan shi idan kuma na sake nayi bai yafe min ba",


" subhanallah" Yazeed ya furta, yayin da Yaseer ya fadi jagwab zaune kan gado yana dafe Kai,


" yanzu to ya zamuyi mu" Yazeed ya tambaya yana maijin haushin iyaye irin na Ibrahim da basu San kaddara ba.

Ibrahim ya ce, " Ina so Dan Allah Ku taimaka min ku Dan kulamin da ita, har zuwa lokacin da za'a sallameta nasan mahaifinmu ya fada ne kawai saboda fushin zuciya m sure kafin lokacin ya sauko daga fushin da yake da ita, pls friend don't say no",

[3/19, 1:40 PM] Ayshart one: Yazeed ko Yaseer 

      Nah

 Ayshart Farouq 

      NWA


       

       37

  Yaseer yayi saurin cewa "kada ka damu zamu taimaketa insha allahu", yafada yana kallon fuskar Yazeed da ta chanja kala,


Ibrahim ya ce, " thank you very much guys am really appreciate, zamuyi waya idan Ana bukatar wani abu" ya fada yana basu hannu, yafita da sauri,


Cikin bacin rai Yazeed ya juyo ya dube Yaseer "me yasa kayi haka? Ko Kai kanada maccen da zata zauna ma da ita ne?"


Shima Yaseer fuskar shi tamke yayi magana" ko babu ni Zan zauna da ita,"


Tsaki Yazeed din yaja "wayasani ma ko Kaine kayi aika aikan"


Murmushi Yaseer yayi, " nagode Allah dai da kowa yasan waye tace ya Mata na tabbatar da ko yanxu ta buda baki zatace Yazeed ne ya Mata fede so nasan ko miyema Kai ne zaka hada mata cox at the first place Kai............."

"Just shout up crazy boy" Yazeed ya katse Yaseer cikin tsawa, idanuwan nan nashi sunyi jajur kallo daya zaka mishi kasan yana cikin bacin rai,


Tsaki Yaseer din yayi tare da fita kasancewar anfara kiraye kirayen magrib,


Bayan sallahr isha'i duka su biyu suna dakin ba Wanda yace da wani ci kanka kowa dannar wayar shi kawai yakeyi.


Nurse ce ta shigo dakin da sallamarta tana ce musu " yakamata fah mace tazo tayi jinyarta don akwai Abubuwan da ake bukatar mace ta mata,"


Yaseer ya ce, "dole sai mace zatayi?,"

"No ba dole ba tunda ita kadai take a daki amma idan da mace zaifi, anyway ko mijinta ma zai iya, tunda dole mutum daya zai rika kwana da ita, Kai Doctor Yazeee kasan dokar ai,"

Gyada Mata kai kawai yayi, 

tayi yana abubuwan da zatayi ta wuce.


" duk tsun tsun da yaja ruwa shi ruwa kan doka, ka daiji abunda nurse ta fada yanxu" inji Yazeed,


Tsaki Yaseer yayi " mai uwa a gindin murhu ba ya kukan ban koshi ba," wayar shi ya dauko ya Kira mahaifiyar shi cikin shagwaba da sakuwa yake magna,

" pls mom wlh yarinyar tana cikin mawuyacin hali, hava mom ko fadeela ce ki turo Dan Allah, oh my god yaushe fadeela ta tafi? Banji me ake cewa bangaren can ba amma ga alama bai samu nasarar convincing mahaifiyar tashiba ko da ganin yanda ya ajiye wayar,


Hada idanuwa sukayi da Yazeed " yadai zata zo ne?" Yazeed ya fada yana yamutsar fuska saboda baki daya asibitin ta gundure shi.


" bazata bar mijinta shi kadai ba" Yaseer ya bashi amsa.

Yazeed ko yaseer 

        Na

  Ayshart farouq

       NWA

        


Www.ayshartfarouq.blogspot.com


         38


  Tsaki yazeed yayi tare da dauko wayar shi, number mahaifiyar shi ya kira, ringing daya ta dauka, cikin ladabi da biyayya yake magana hadi da magiya, " Dan Allah Ammi kiyi hakuri ki zo ki kwana da yarinyar nan wlh bamu San ya zamuyi da ita ba tunda mu ba muharamanta ba ne, ok Ammi mungode kwarai, zan miki text din room no sai kin zo".


   Kashe wayar yayi batare da yace ma yaseer komai ba, shima kuma bai damu da yasani ba tunda yaji abunda ya ke fada.

    

  Kusan karfe Tara da rabi mahaifiyar yazeed ta shigo dakin dauke da food flakes, cikin ladabi yazeed da yaseer suka gaidata, 

Yaseer ne ya karbi kayan hannunta ya Dora kan bedside drawer, yayin da ita kuma ta zauna kan gadon da Afnan ta ke tana kallon fuskarta, tare da cewa, " ikon Allah yarinya kyakkyawa an bata mata rayuwa,"


Tabe baki yazeed yayi tare da cewa, " ko dai ta batawa kanta ba"


" ai duk Dan Adam baya wuce kaddararsa" yaseer ya fada yana kallon fuskar Afnan da ta ke ta sharar bacci,


"Hakane kam, Allah dai ya kawo mana kaddara mai kyau" cewar Ammi 


Dan shiru ya ratsa na 'yan wasu dakiku kafin Ammi ta soma magana,

" ni dai abunda nake gargadinku dashi dukanku da kuji tsoron Allah idan a kwai Wanda ya ma wannan boyar Allah fede da ya fadi, don tabbas nasan cikinku dole ne wani ya aikata,"


Baki dayansu kallon junan su suka yi kowa da abunda yake sakawa a ranshi,


Ammi taci gaba da magana, "dukan Ku nan maza ne, kuna da kanne kuna da iyaye, wallahi tallahi duk abunda kayiwa diyar wani, kanwar wani, matar wani, kaima sai anma taka.shiyasa nake gargadin Ku da kuji tsoron Allah Ku tausayawa wannan boyar Allah Ku fadi gskiya ko Allah nasa ta sasanta da iyayenta, I will ask you for d last time, " wa ya ma wannan yarinya ciki a cikin ku?,


Kallo daya zakawa yazeed da yaseer ka tabbatar da sun rude, hankalin su yayi matukar tashi, magangannun Ammi sun ratsa su sosai.

 

"Ku nake saurare" ammi ta katse musu tunani,


Yazeed yafara magana cikin dakakkiyar murya, 

" wlh ammi ban taba ganin yarinyar nan ba sai yau don haka banida masaniya kan abunda take zargina da shi"


"Kai fah yaseer? Amma ta tambaya,


Natsuwar shi ya tattaro duka batare da ya daina kallon innocent face din Afnan ba yace, "ammi bani nayi ba Nima ban taba ganinta ba sai yau".

  

   Ammi ta danyi murmushi tare da furzar da wani iska mai zafi, ita ka dai tasan abunda takeji game da yarinyar ba don komai ba sai don kasancewar ta DIYA MACE,


" Allah yabi miki hakkin ki da duk Wanda ya aikata miki wannan abun" ta fada tare da Dan shafe kwallar da ta tarar mata,


Haka dai suka zauna har karfe 10 sannan suka ma ammi sallama suka wuce zuciyar su duk ba dadi kowa da abunda ke damunsa,


Waye yazeed da yaseer,


          39

  Yazeed da ne tal gun alhaji Ahmad abdulrahman, mahaifin shi alhaji Ahmad ya rabu da mahaifiyar shi hjy ameena tun yana Dan shekara biyar kasancewar dama ba son junansu suke ba,

Bayan sun rabu ne tasake aure ta haifi diya biyu hafsat da usman bata Dade da haihuwar usman ba Allah yayima mijinta cikawa kasancewar shi mai hali yasanya ta gaji dukiya mai yawa, ta fada harakar business, bayan rasuwar mijinta da 'yan shekaru Allah yayiwa usman rasuwa, yanzu daga ita sai diyarta hafsat suke zaune sai kuma yazeed da ke kai mata ziyara lokaci lokaci,

Mahaifin shi kuma tunda suka rabu da mahaifiyar shi ya sake auren hajiya zuwaira tsohuwar budurwar shi wadda tayi aure wani guri ta fito da diya biyu yaseer da nabeela, ganin mijinta mai shahararren kudi yasanya ta kwaso yaranta ta maidosu hannunta sai abunda sukaga dama suke aikatawa, ganin har ta shekara biyar ba ta samu haihuwa ba ya sanya ta doki karan tsana ta dorawa yazeed ganin shi kadai alh Ahmad ya mallaka, ko mutuwa yayi shi kadai zai gade shi, tun tana lurar da yaseer abun da take nufi kan yazeed yana kin fahimta har ya yarda ya sanya hannun shi gurin ganin anyi ruining future din yazeed. Kusan duk campanonin alh Ahmad shi ke kula dasu.


Tunda yazeed da yaseer suka girma suka mallaki hanklin Kansu, yaseer ya kasance mutum mai Neman matan tsiya, kuma duk maccen da zai nema ba zaije mata da ainihin sunan shi ba sai dai yace yazeed sunan shi, sai tafiya tayi tafiya ya tabbatar da yar hannu ce sannan zai gaya mata gaskiyar sunan shi, saboda duk friends dinshi da Abdulrahman y Ahmad suke kiran shi, ma'ana, yaseer Ahmad Abdulrahman, da wannan ya samu yake yaudarar 'yan mata, sai dai duk Neman matan shi bai taba yima wata fade ba da yawa ma su suke kawo kansu gare shi, Afnan ce macce ta farko da ya nema ta karfi ganin sha'awarta na nema ta illata shi, 


Yazeed kuwa ganin abunda hajiya zuwaira keyi ya sanya yayi kudurin ganin bai dogara ga mahaifin shi ba, yaje ya karanci fannin lafiya, yanzu haka yana aiki a babbar asibitin Aminu kano, Abu daya ke ci mishi tuwo a kwarya yanda mahifin shi yayi kane Kane gurin ganin ya hadashi aure da nabeela kaunar yaseer, yasan ba shirin kowa ne ba face hajiya zuwaira.


Wannan kenan.


Bayan wucewar yazeed da yaseer ne Ammi ta tsurawa Afnan ido tana nazarin wani Abu da nima ban San ko miye ba.


A hankali Afnan ta bude idanuwanta tana kallon Ammi, ganin haka ya sanya Ammi karasawa kusa da ita tana mata sannu.


Tunawa tayi da abunda ya faru, nan ta ke ta mike zaune tana kiran sunan momyn ta, kuka ta ke yi sosai tana cewa, " shi kenan ta mutu ko? Na kasheta ko?

Wayyo ni Allah nashiga uku na kashe mahaifiyata,"


Rungumeta Ammi tayi ta na bubbuga bayanta "yi shiru 'ya ta mahaifiyar ki na Raye bata mutu ba, yi shiru daina kuka kinji"


Cikin kuka Afnan ke tambayarta, "dan Allah ke wace ce?"


Murmushi Ammi tayi tare da fada mata ko waye ita,


Cikin sauri Afnan ta zame jikinta daga gareta ta kwanta wasu zafaffin hawaye nafita daga idanuwanta, cikin ranta tunani ta keyi, ya aka yi haka tsawon shekara daya tana tare da mutum amma ta rasa gane takamammen sunan shi, kai lallai namiji a barshi kawai, ita bata ma San ya zata kira kanta ba marar HANKALI KO DABBA?.


Lol, masu karatu Ku gaya mata sunanta


©Ayshart one©

[7/20, 10:38 AM] Ayshart One: Yazeed ko Yaseer

       Na

Ayshart Farouq

      

      NWA


         39


  Dafa kafadarta Ammi ta yi, "kiyi shiru Afnan ki daina kukan hakanan kada ki sake sanyawa kanki wani ciwo

  Dago idanuwanta ta yi da suka rine sukayi jajur ta dube Ammi tare da dafe zuciyarta,

 " ciwo duk yafi wannan da nikeji a zuciyata, ai bana tunanin akwai ciwon da yafi wanda nakeji a yanzu"

   "Uhum! Nasan yanda kikeji Afnan amma ki sani duk abunda yayi tsanani maganin shi hakuri duk abunda hakuri bai yi ba rashin shi bazaiyi ba,"


Wani kallo Afnan ta mata na baki San yanda nakeji ba,

 " shekara daya ban San true identity dinshi ba, ya yaudare ni ya rabani da mutunci na, ya rabani da iyayena da yayu na ta yaya bazanyi kuka? Ki gaya min mama ta yaya?"


Ammi ta tausaya mata matukar tausayawa,

"Zan tai maka miki in dawo miki da duk abunda ya rabaki dasu matukar kika gaya min gaskiyar lamarin ki"


"Har da mutunci na" Afnan ta tambaya da sauri,


" harda mutuncinki"

Ammi ta bata amsa,


Murmushi Afnan ta yi tare da shafe hawayenta, ta soma ba Ammi labarin duk abunda ya faru, tun farkon haduwarsu da yaseer har zuwa yanzu,


Kuka sosai Ammi tayi, ita da Afnan ba mai lallasar wani, Sai da sukayi mai isarsu suka gama sannan Ammi ta soma magana,

" amma gaskiya yaseer ya yaudare ki afnan, ni tunda ma nake duniya ban taba jin yaudara irin wannan ba"


Haka suka raba dare suna fira Ammi na kara bata hakuri tare da shawarori masu amfani.


Shi kuwa yaseer tunda suka koma gida yakasa zaune yakasa tsaye baccin ma baki daya kasa yin shi yayi yarasa takamammen abunda ke damun shi, hakika da ba don gudun fushin Daddy ba da ba yanda za'ayi ya karyata abunda Afnan ta ce tunda ya San shi ya aikata Sai dai yanzu is to late ba zai yarda yayi losing trust din daddy ba, tabbas Sai yanzu ya yarda da ba sha'awar Afnan kawai yakeyi ba harda kaunarta yanayi kuma kauna mai tsanani, toh yanzu ya zai yi? wata zuciya ta ce, kawai ka sameta kuyi magana zata rufa ma asiri ta aure ka tunda tana son ka, haka dai yayita sake sake har garin Allah ya waye.


Bangaren yazeed kuwa tunda ya tashi guraren karfe takwas ya shirya zuwa aiki saboda shi ke duty,

Yana fitowa yaci karo da Daddy da Yaseer, cikin ladabi ya gaida daddy, kallo daya yama yaseer da ke zaune tamkar ya fasa kuka, "yauwa dama yanzu nake shirin kiranka Sai gashi Allah ya kawo ka" cewar daddy da ke gyara babbar rigar shi,

" lafiya dai ko? Yazeed ya tambaya,"

" lafiya lau, yarinyar jiya nake so Ku kaini gurinta ina so inkara tambayarta tsakani da Allah kan lamarinta, saboda abun yana daure mun kai, a ce duk gidajen da ke unguwar nan ta rasa inda zataje tace an mata fyade Sai a nan, abun na matukar bani mamaki, zuciyata ta kasa karyata ta sai dai kuma ta yaya za ayi ace cikin Ku wani ya aikata wannan danyen aiki impossible muje dai kawai, kuma ina so Ku kira yayanta ayi komai gaban shi don ya zama shaida.


Baki daya hankalinsu tashi yayi kowa da a binda yake tunani, bama yazeed da yake ganin kamar shi zata sake lakawa tunda at the first place shi tafara cewa.


Yaseer kuwa har wani gumi ke taso mishi ganin yake ma daga asibiti daddy zai Kore shi gidan shi.


Yazeed ya kira Ibrahim ya gaya mishi abunda daddy ya ce, Ibrahim yaji dadi sosai kan halaccin da sukai mai, yace ba komai su hadu assibitin duk da shi yaso a kashe case din tun da yadan Afnan din karya takeyi sharri ne kawai ta musu.


Da isar su assibitin, direct dakin da Afnan take suka nufa, da sallama suka shiga, kallo daya Afnan ta musu ta dauke kai saboda wata irin faduwar gaba da taji, kwarjinin su ya bala'in tafiya da ita don sai ma ta rasa gane tsakanin yazeed da yaseer wanne yafi kyau,


Gabanta ya shiga dukan uku uku ganin daddy din su, wani Abu ta ke jin yana ta so mata yana tokare mata zuciya, "anya zan iya abunda ammi ta ce kuwa?"


Sallamar Ibrahim ce ta dawo da ita daga dogon tunanin da takeyi,

Hankalinta ba karamin tashi yayi ba ganin yanda fuskar shi take tamkar ba yayanta da tasani ba mai kaunarta, rusunawa yayi ya gaida daddy da Ammmi sannan ya bawa yazeed da yaseer hannu suka gaisa, ko kallon gefen Afnan baiyi ba saboda yanda yakeji,


" ya jikin ki? Da fatar kin samu sauki" cewar daddy 

"Naji sauki Alhamdulillah," ta fada tana kallon yaseer da ya sunkuyar da kanshi,


"Allhamdulillah haka muke fata, dama ba komai ya kawo ni ba face ina so ki dubi girman Allah ki gaya min gsky Wanda ya miki fyade cikin yazeed da yaseer ni kuma na dauki alkawarin zan bi miki hakkin ki"


Kallon Ammi tayi, da tun shigowarsu kanta ke duke, anyi sa'a itama ta kalleta suka hada ido, a hankali ta girgiza mata kanta alamar karta ce komai.


Wasu sirarran hawaye suka fito mata, toh me ammi ke nufi da tace kada ta fadi? Ga dama ta samu damar da take nema, tabbas bazata bari ta kubce mata ba, wata zuciya ta ce, kiyi abunda Ammi tace, kiyi saboda duk abunda babba ya hango yaro ko ya hau tsani bazai hango shi ba."


"Ina jinki, kar kiji tsoron komai gaya min gsky kinji?"

[7/20, 11:13 AM] Ayshart One: Yazeed ko Yaseer 

        Nah

  Ayshart farouq 


Nagarta writers association 


        40


Murmushin yake tayi Wanda yafi kuka ciyo,


"Yazeed ne........!" Maganarta ta tsaya cak ganin wani irin mugun kallo da Abba ke ma yazeed yana nuna shi da yatsa,


Shi kanshi yaseer mutuwar tsaye yayi me Afnan ke nufi na dorawa yazeed alhali bashi ya aikata ba?


Cikin sauri Afnan tayi saurin zuwa gaban daddy ta rike kafafun shi,


"Tabbas yazeed ya ce min sunan shi sai dai ba wannan yazeed din ne ba,"


Wani mugun kallo daddy ya watsa mata, 


" believe me wallahi tallahi ba wannan yazeed din ne ba, hasali ma Wanda yamin ba yazeed ne sunan shi ba"


Wannan karon kallon mamaki daddy ke mata, 

 

Ibrahim kuwa, cikinta yayi da niyar marinta yaseer ya tare shi tana bashi hakuri,


Ci gaba ta yi da maganarta tana shafe kwalla,

"kawai dai ya yaudare ni ne ta hanyar boye min true identity nashi har ya rabani da mutunci na"


Kuka ta fashe dashi mai tsanani,

"Dan Allah kayi hakuri ka gafarta min na bata zuri'ar ka da nayi ta hanyar yi musu sharri, kawai nayi ne don inkare kaina gurin iyayena saboda bana cikin hayyaci na abun ya faru nan gidan ya nuna min ya ce nan ne gidan su, Dan girman Allah Ku yafe mun, cikin yaranka ba Wanda ma na taba gani sai jiya"


Wani sanyi daddy yaji at list dai ta fadi gaskiya, 

Hannu ya sanya ya taddo ta tsaye kasancewar shi mutum mai matukar tausayi,


" ya isa haka nan daina kuka, nayafe miki amma kada ki sake aikata irin haka ba kyau kinji?,


Gyada mishi kai tayi tana share hawayenta,


Gurin yazeed taje ta gurfana, "Dan Allah kayafe mun abunda nayi maka"


Ko kallonta baiyi ba saboda yanda yakeji tamkar yaje ya shaketa ta mutu.


"Bakaji ana baka hakuri ba ne?" cewar Ammi da ke kallon shi,


Tabe baki yayi "naji mana, na yafe mata" 


Mikewa tayi takarasa gurin yaseer da ya zuba mata shanyayyin idanuwan shi, wani kallo yake mata, na, ina son ki, kin rufa min asiri,kin birge ni.

 

Ita kuwa wani kallo ta watsa mishi, na, sai na dau fansa, sai ka gane kuren ka, kaina ka kare yaudarar DIYA MACE. Sannan ta gurfana gbn shi,


"Kayi hakuri da sharrin da namaka"


Ji yayi tamkar ya rungumeta, what a good drama! Kai gaskiya yarinyar ta birgeshi yasan ba don komai ta rufa mishi asiri ba sai don tana son shi,


"Thank you beb" ya fada cikin muryar da ita kadai taji sannan daga baya, ya ce, "Allah ya yafe mana baki daya" 


Harara ta watsa mishi sannan ta mike tana kallon Ibrahim da ke mata kallon karma ki matso nan.


Ganin haka yasanya ta samu guri ta rabe tana matsar kwalla.


" toh yanzu ina shi yaron da ya miki fyaden yake?"

Cewar daddy,


" ban San inda ya ke ba, don jiya na amshe wayar Ammi na kirashi, ya tabbatar min bazan sake ganin shi ba don ba Dan garin nan ne ba. Tana kaiwa nan ta fashe da kuka.


"Allah bimiki hakkin ki" daddy ya fada cikin nuna tausayawa,

Suka karba dukan su da Ameen.


Sallama yayi musu sannan ya wuce.


Bayan sun fita ne Afnan ta kalle Ammi, 


"Ammi me yasa kika hana ni fadin gaskiya? Anya ban cuce kaina ba?"


Murmuahi Ammi tayi,

" bazaki gane abunda yasa na ce miki kada ki fada ba, toh bari kiji in gaya miki abunda baki sani ba, ko kin ce yaseer ya miki fyade hajiya zuwaira bazata taba bari alhaji ya yarda ba saboda wannan aika aikar da ya miki sai da yatsara ta ya miki ita, anmiki fyade wata biyu kmar yanda cikin ki ya nuna, a gurin alhaji kuwa yaseer yayi tafiya ta wata hudu jiya satin shi daya da dawowa, ni kaina da ba don naganshi ba da bazan yarda ba. Don haka ko kin ce shi ya miki ba yanda za'ayi a yarda saboda baya gari lokacin da abun yafaru.


Wannan karon ma Afnan kasa kuka tayi, ta zuba ma Ammi ido tana sauraren irin yaudara ta yaseer da zai shigo jirgi tun daga Lagos har kano don kawai ya cimma bukatar shi gurinta, lallai namiji a barshi kawai.

[7/22, 9:16 PM] Ayshart One: Yazeed ko Yaseer

       Na

 Ayshart Farouq


Nagarta Writers Association


        41


Kwanan Afnan biyu Assibiti aka sallameta, ko yaushe yaseer sai yaje dubata sau uku safe da rana da maraice sai dai yakasa samun damar yi mata magana saboda ko yaushe suna tare da Ammi,

 shi kuwa Yazeed tun ranar bai koma ba sai dai yakira Ammi a waya.


Gidan Ammi suka wuce gida ne babba don idan ba sani kayi ba bazaka ce gidan mace ne ba.


Dakin Hafsat Ammi ta kaita kasancewar Hafsat din bata nan tana gidan kakaninta na gurin Babanta.


Kwance ta ke duk abun duniya ya mata yawa, ko jiya ta kira number momyn ta a wayar Ammi ba a dauka ba, ko wane hali take ciki? Zumbur tayi ta mike, gurin Ammi ta nufata,


" Ammi bani aron wayar ki Dan Allah" 


Murmushi kawai Ammi tayi tare da mika mata wayar.


Number mommy ta saka ta sake kira, ringing daya a na biyu a ka daga,

 

Jin muryar mahaifiyarta ba karamin dadi taji ba, kasa magana tayi sai ajiyar zuciya,

Sai da mommy tayi magana kusan sau biyu sannan tayi magana.


"Mommy na " kawai ta ce, sai ta fashe da kuka,


Hankalin mommy ba karamin tashi yayi ba najin yanda Afnan ke kuka, duk da har zuwa lokacin tana cikin tsananin bakin cikin abunda Afnan din ta aikata,


Tsaki taja tare da cewa, "zan kashe wayata idan kuka kika kirani ki mun"


"No mommy plz kada ki kashe min waya Dan Allah, na tuba NAYI NADAMA kan abunda na aikata Dan Allah mommy Ku gafarta min"


Kasa hakura mommy tayi kawai itama sai tasa kuka,


"Karasa mana ita ki ke so kiyi ne?" 

ta jiyo muryar sagir na fada cikin tsawa,

 

D'if!, taji an kashe wayar,


 Kuka ta fashe da shi tana fad'in,

"Nashiga uku ni Afnan"


"Baki shiga uku ba Afnan" inji Ammi da taji duk abunda ya faru, "ki kwantar da hankalin ki Afnan, nariga na daukar miki alkawarin sada ki da iyayenki ko ta halin yaya, don haka ki bani daga yau zuwa wani sati insha Allahu everting will be alright,"


"Allah ya sa" ta fad'a tare da k'ank'ame Ammi tana kuka.


 Mommy zaune duk abun duniya ya mata yawa, tayi kuka har ta godewa ubangiji, kewar diyarta take yi sosai duk da taji Ibrahim ya gaya mata inda ta ke Amma hankalinta Sam bai kwanta ba, 


Sallama Abba yayi, amma batama San yana yi ba sai da yayi kusan sau biyu sannan taji, firgit ta Amsa mishi tana maida kwalar da ta zubo mata,

"Kuka ki ke har yanzu ko?" ya fada yana mai tsura mata idanuwa.


Wannan karon kam bazata iya boye damuwarta ba tafi so ayi duk wacce za'ayi,


"Saboda me bazanyi kuka ba?, sabida Allah yanzu abunda kayi kana ganin ka kyauta?,shin ko kana ganin korar da kayi ma Afnan Allah bazai tambaye ka ba? Yanzu idan tashiga duniya kana ganin zaka iya goge abun kunyar da kake tunanin ta jama? Me yesa bazakayi mata adalci ba ne?, kuskure ne kai ma kayi shi a matsayinka na uba, tun farko kai ka tauye mata hakkinta ka fifita boko kan aure, Dan Allah alhaji ina rokonka da kayi gaggawar maida diyarka hannunka tun kafin ABUNDA AKE GUDU ya faru.


Duk dauriya irin ta d'a namiji sai da Abba yayi kwalla jin kalaman mommy, tabbas yasan gaskiya ta gaya mishi sai dai aikin gama ya riga ya gama, ba safiyar Allah da bazai tuna bakin cikin da Afnan ta cusa mishi a zuciya ba, yayi da nasanin tsaurin da yayi mata babu iyaka, duk lokacin da ya tuna lokacin da aka ce tana dauke da juna biyu sai yaji tamkar a ce mafalki yake yi, farin cikin shi daya cikin da ke jikinta ya zube, wannan kad'ai yake tunawa ya d'an ji sanyi cikin ranshi, mutunci kuma ta riga ta sayar a titi.


Rungume mommy yayi, "ya isa hakanan dai na kukan, nasan ni kaina ina da laifi kan abunda ya same Afnan sai dai fushin zuciya yasa na mata hakanan, kar ki damu munyi magana da mmarikiyarta maman yazeed din takirani yafi a kirga tana min nasifa kan rayuwar Afnan kuma tabbas abunda ta fada gaskiya ne, insha Allahu zamuje zuwa jibi, Afnan zata dawo gida muddun ta cika SHARADINA daya tak".


Da sauri mommy ta dago ta kalle shi, " wane sharadi kuma?"


Murmushi yayi iya lebe, "calm down I won't repeat that mistake again, zakije ko miye idan munje.


Dadi sosai Mommy taji, at list dai ta samu peace of mind kuma ta San duk wani sharadi da zai gindaya mata mai amfaninta don tasan ba zai kuskura a sake maimaita 'yar gidan jiya ba.


Ayshart one

[7/23, 10:08 PM] Ayshart One: Yazeed ko Yaseer 

      Na

 Ayshart Farouq


Nagarta Writes Association 


       42

Yau assabar misalin karfe 3 na yamma Afnan na zaune falo abin duniya duk ya mata yawa kallo takeyi amma Sam bata fahimtar abunda ake yi,


Sallama yayi ya shigo falon, tunda ya ganta ita kadai yaji wani irin sanyi ya mamaye mishi zuciya, dama yau yazo ne ayita ta k'are,


Sai da ya tsaya ya kare mata kallo tsaf, sannan ya karasa gurinta, durkusawa yayi gabanta, tare da hura mata idanuwa, firgit ta dawo hayyacinta, "miye haka?" Ta fada cikin tsawa,


Ko a jikinshi murmushi kawai yayi, "maida wukar Afnan I mean no harm Nazo ne kawai in kara Neman gafarar ki kan abunda na miki, kuma ina godiya kan rufa min asirin da kikayi a assibiti, ina so in shaida miki cewa a shirye nake da auren ki idan har kin Amince, sa........!"


Uwar tsawar da ta daka mishi ne ya sanya maganar tashi ta katse, "lallai yaseer sai yau na tabbatar da kai Dan akuya ne marar kunya, kai banda ma jakkanci har kanada bakin da zaka zo min da wannan magana?, toh bari kaji in gaya maka, natsaneka yaseer, nayi bakin ciki da Nadamar saninka a rayuwata, Wallahi da ganinka kara ganin bakin maciji, da in aure ka kara in aure kare"


Cikin tsananin bacin rai yaseer ya katseta idanuwan shi sunyi jajur, zai iya jure komai amma bazai iya jure Jin Wadan nan kalamai na Afnan ba, "k'arya kike wallahi Afnan, nasan har yanzu kina so na, saboda da bakya so na da baki rufa min asiri a assibiti ba, nasan kina so na kuma wallahi dole ki aure ni saboda ni kadai zan iya rufa miki asiri"


Wani mugun murmushi tayi Wanda na kasa ko na mine ne,

"Da wannan ka dogara? Toh bari kaji ingayama abunda ba ka sani ba, rufama asirin da nayi ba komai ba ne face tonuwar asirinka, wallahi wallahi yaseer yadda ka tozartani ka keta min mutunci na ta karfin tsiya toh ka sani sai nama abunda yafi haka sai na dasa maka ciyon da har ka mutu bazaka manta dashi ba" 


Nuna kanta tayi da yatsa "ni Afnan sai na FANSHE BUDURCI na da ka yage ko da kuwa zai zamo min silar bakin cikina"


Yaseer kam mutuwar zaune yayi jin wannan kalamai na Afnan sai dai yasan ta fada ne kawai bazata iya aiwatar da komai ba, wani mayunwacin murmushi yayi tare da lashe lebinshi na kasa,

Babban yatsan shi ya daga mata alamar jinjinawa,


Sallamar Yazeed ce ta sa ya fasa fadar abunda zai fada,


Gudun kar ya fahimce wani Abu yasa Afnan ta karkaro murmushi, "ina wuni ya Yazeed"


"Lfy" kawai ya ce ba tare da ya kallesu ba yace, Ammi fah? 


"Tana sama" ta bashi amsa tana satar kallon yaseer da zaka iya rantsewa bai San da zamanta gun ba.


"Munafuki, zaka gane kurenka" ta fada cikin ranta.


Cikin minti daya sai ga Yazeed da Ammi suna saukowa, Ammi na cewa,

"Ayi haka kaiko? Me yasa baka shigo da su ba, ai yanzu sun zama 'yan gida"


Kira ta kwalawa Afnan da ta kusa shigewa daki,


"Dakaata Afnan, zo nan ga bak'i nan munyi bari Ku gaisa tukun"


Haka kawai Afnan ta tsinci gabanta na faduwa, da sauri ta juwo tana murmushin yak'e,


Gaisawa ammi tayi da Yaseer, "dama tare kake da su Yazeed din?"


"A'a ba tare muke ba nima yanzu ne shigowata aka ce kina sama"


"Allah sarki, ai da sai ka wuce saman"


Kafin ya kago abunda zai fadi akayi sallama aka shigo,


Abba ne da mommy da kuma Ibrahim sai yazeed da ke musu jagora,


Maraba maraba Ammi keta fadi tana nuna musu gurin zama, Afnan kan mutuwar tsaye tayi don jikinta baki daya daukar rawa yayi, shin mafalki ta keyi ko da gaske abbanta take gani da mommy ta?


Dan Allah kuyi hakuri da wannan banida charge ne,


Love you all my fans.


Ayshart one

[7/26, 10:02 PM] Ayshart One: Yazeed ko Yaseer

       Na

 Ayshart Farouq


Nagarta Writers Association


       43

Ganin yanda hankalin Afnan ya tashi ne ya sanya Ammi taja hannunta ta zaunar da ita tana cewa,

"Ki kwantar da hankalinki Afnan ba abunda zai faru sai alkhairi kinji" 

 

Kai kawai ta iya gyad'awa saboda bakin ya riga ya mutu,

Duk yanda take d'okin ganin iyayen nata kasa daga kai tayj ta kalle su, mommy ce ma keta kallonta tun shigowarsu ganin yanda duk ta rame. Abba kuwa kallo daya ya mata bai sake marmarin k'ara kallonta ba don kar zuciyarshi ta karaya kan abunda yake shirin aikatawa.


Bayan an gaggaisa ne Ammi ta soma magana,

"Alhamdulillahi, naji dadi sosai yau ga Afnan ga Abbanta da momynta muna fatar komai zaixo cikin sauki kamar yanda Allah ya kawo saukin rashin shigar Afnan wata muguwar rayuwa kan kuskure daya tak" Ammi ta fada tana kallon Daddy,


Murmushi Daddy yayi sannan ya soma magana,

"Ban San da wane baki zan muku godiya ba kan halaccin da kuka min na rike min Afnan hannunku , tabbas da ba don Ku ba da ban San ko wace rayuwa 'yata zata tsinci kanta ciki ba saboda kuskuren da na aikata, hakika yazeed da Yaseer kun cencenci yabo, nagode kwarai Allah yabar zumunci "


Suka karba dukan su da Ameen,

 

Cigaba Abba yayi da magana "mutunci ne kam Afnan ta riga ta zubar dashi don haka bana fatan wani Abu makamanci haka yasake faruwa har akai ga dauko abun kunyan da Allah ya tsare ba a dauko ba".


Juyawa yayi ya kalle Afnan da tunda aka fara magana take shafar kwalla, cikin kakkausar murya, yace,

" Afnan dawo nan" ya nuna mata k'asa gurin k'afafunshi,


Jikin Afnan ya kara daukar mazari don ganin takeyi tamkar dukanta Abba zaiyi, Hada idanuwa sukayi da Ammi, ta d'aga mata kai alamar taje.


Mik'ewa tayi tamkar ta fad'i saboda tsoro.

Gurfanawa tayi gabanshi kanta k'asa ta kasa kallon shi,


Abba ya sake maida kallon shi gurinsu Yaseer "ina so dukan Ku nan ku zama shaida a gareni matsayinku na mataimakan Afnan"

 

Wannan karon kam idanuwan shi sunyi jajur saboda bacin rai,

"Afnan, Afnan, Afnan "

Ya kirata har sau uku "nabaki daga yau zuwa wani sati ki fitar da mijin aure, kuma wallahi wallahi bakya bina bashin rantsuwa idan baki kawo ba zan hadaki da Wanda raina ke so koda kuwa maigadi ne"


Tashin hankali, zo kiga yanda Afnan ke wani gunjin kuka mai ban tausayi.


Kuka take sosai tana rokon Abba, "Dan Allah abba kayi hakuri kayafe min, natuba Abba Dan Allah kamin duk hukunci da zakamin amma banda wannan"


Tsawa ya daka mata "wallahi bazan taba yafe mikiba matukar baki bi umurnina ba," 


Dafe kai Afnan tayi ta nuface mommy tana fadin "nashiga uku mommy Dan Allah kice wani Abu mommy kinji abunda Abbana yake fada kuwa?"


Mommy kam kuka ta fashe dashi tausayin Afnan ya kamata sai dai ba abunda zata iyayi kan hukuncin da Abba ya zartar,

"Kiyi hak'uri Afnan kibi umurnin mahaifinki, ba don bai sonki yayi miki haka ba sai dan ganin ya sauke nauyin hakkinki da Allah ya daura mishi matsayin ki na diya mace"

 

Tsit dakin yayi bakajin komai sai kukan Afnan, tausayinta duk ya kamasu bama kamar Ammi da ke zubar da kwalla,


Yaseer kam wani irin dadi yakeji ko ba komai yanzu dole Afnan ta saurare shi tunda batada wani saurayi sai shi. Da ba don gudun wani Abu ba da ya fadi yana sonta don ayita ta kare sai dai zai lallabata yanda take so tunda yasan batada wani zabi dole ta aure shi,


Maganar Ammi ce ta dawo dashi daga tunanin da yakeyi,


"A gaskiya Baban Afnan wannan hukunci da ka yankewa 'yata ya muna tsauri, amma insha allahu zaka sameta mai cika umurninka"


Wani kallo Afnan tama Ammi don bata San inda zancenta ya nufa ba,


cigaba da magana ammi tayi,

"Ina rok'on alfarma daya, Dan Allah kabarmin Afnan nan gurina har zuwa lokacin da zaka buk'aci jin Wanda ta fidda matsayin mijin aure"


Murmushin jin dadi Abba yayi don dama haka nan yaso yi don bai San yanda abun zaizo musu ba, "ba komai hajiya ai Afnan 'yar ki ce don yanzu kun riga kun zama 'yan uwan mu"

[8/3, 11:10 PM] Ayshart One: Yazeed ko Yaseer 

       Na

Ayshart Farouq 


Nagarta Writers Association


       44


Murmushin jin dadi Ammi tayi, " mungode kwarai alhaji Allah yabar zumunci"


Yakarba da "Amin"


Bayan sun Dan taba fira kadan sukayi musu sallama suka wuce,


Yaseer ma wucewar shi yayi don yasan bazai same kan Afnan din yanzu ba,


Bayan sun wuce d'aki Afnan ta shiga ta fad'a kan gado tana rusar kuka baki daya notukkan kanta sun kwance, tambayar kanta takeyi "shin me Abba ke nufi? Me yasa ya mata haka?, shin bai San batada Wanda take so ba idan ba Yaseer ba?" Wata zuciya tace "yana nufin ki tsaida Yaseer din"

"No bazan taba auren Yaseer ba koda kuwa son shi zai illata ni I hate him for what he did to me I can't forget it,"

Can wata zuciya tace "ki bari kawai Abba ya zabar miki Wanda zaki aura dama can wannan ne ra'ayin shi"


Dafe kanta tayi "oh Allah ka kawo min mafita ta alkhairi"


Haka tayita sak'e sa'ke har aka kira magariba. Bayan ank'are sallah ne Ammi tashigo dakin, zama tayi kan gado ta dafa kafad'ar Afnan, "Afnan nasan kina cikin rudani sosai jin hukuncin mahaifinki, ina so ki kwantar da hankalinki ki barmin wuka da Nama insha allahu zan cika miki alkawarin da na daukar miki,"


Murmushin yak'e Afnan tayi, "ko yanzun ma haka nagode tunda kin sadani da iyayena Allah ya saka miki da alkhairi"


"Yima kai ne Afnan kada ki damu yanzun dai ki kwanta kawai ki samu kiyi bacci kar kanki ya kama ciyo"


Haka Ammi tayita lallashinta da magangannu masu dadi har tayi bacci.


Bayan kwana biyu Afnan nata dubin taji me Ammi zata ce amma taji shiru, kallo daya zaka mata ka gane tana cikin rudani duk ta jeme tayi bak'i, Ammi na lura da ita tausayinta takeyi sosai jinta take tamkar Hafsat fatanta kawai Allah ya cika mata burinta ta taimaka mata,


Misalin 12 na rana Afnan ta kama hanyar dakin Ammi don jin makomarta ganin saura kwana uku cikin sati dayan da Abba ya bata gashi Ammi batace komi ba ga Yaseer nata mata magiya tak'i ta saurare shi, 


Maganar da taji ne dakin Ammi yasanya tayi tsaye turus tana saurare,

Muryar Yazeed tajiyo yana cewa,

"Haba Ammi ya zaki ce in aure Afnan alhalin kin San taje ta zubar da mutuncinta a waje harda ciki fa tayi"


"Eh nasan da haka nace ka aureta, kai baka San kaddara ne ba, fyade fa aka mata"


" ni fah Ammi gaskiya ban yarda da fyade aka mata ba don yarinyar nan Sam batada gaskiya"


Cikin bacin rai Ammi tayi magana, "yaushe kazamo haka ne mai taurin kai toh wallahi tsaya kaji, idan dai har ni na haifeka kuma na isa da kai toh kaje ka same Afnan yanzu kace kana so ka aureta kuma wallahi idan ka nuna mata tursasaka nayi sai dai kaje ka nemi wata uwar amma bani ba"


"Subhanallahi me yayi zafi haka Ammi? Ai abun bai kai can ba duk yanda kike so haka za'ayi amma dai kin San akwai maganar nabeela kaina ko? Saboda Daddy ya rik'e wuta kan lallai lallai sai na aureta"


Murmushi Ammi tayi, "shi yasa nace sai ka aure Afnan saboda bana son aurenka da wannan yarinyar saboda nasan duk makircin uwarta ne zuwaira,"


"Toh yanzu kina ganin idan naje mishi da maganar Afnan din zai Amince?"


"Yo ai idan kace kai ke so bazaice a'a ba tunda yasan dama ba son nabeelan kake ba"


Baki daya kan shi ya dau chargy shin me iyayen nashi zasu mayar dashi ne? Shin shi baza'a bari ya zabi abunda yake so ba ne? Nabeela Afnan ba wadda yake so cikin su amma zaima iyayen shi biyayya ne kawai ya aure su"


Muryar Ammi ce ta dawo dashi daga tunanin da yakeyi,

" ka tashi kaje ka sameta kuyi maganar ko hankalinta zai kwanta"


Jin haka yasa Afnan ta juya da gudu tana hawaye, kan gado ta fad'a ta rushe da kukan bak'in ciki


Da sallama yashiga dakin, ganin yanayin da take cikine yasanya shi yin tsaye yana kallonta, ganin bazata daina kukan ne ba yasanya ya karasa kusa da inda take, zama yayi tare da cewa,

"Wan nan kukan fah na meye ki keyi? Najin dad'i ko?"


Bata San lokacin da ta kalleshi da rinannun idanuwanta ba,


Wani banzan murmushi yayi, "koma miye nasan bazai wuce saurayin da kika bawa kanki ba ya tsere ya barki am i right?"


"Pls just gate out from here idan magana kazo ka gayamin" 


"Ba magana nazo in gaya miki ba taimakonki nazo inyi"


"Kabarshi kawai bana buk'ata, taimakon Allah kawai nake nema"


"Ki ka sani ko nine Allah yasa zan taimake ki, ko ba kya son in samu lada ne?"


Kallonshi kawai tayi Wai Ashe ya iya magana haka lallai wannan za'ayi d'an rainin hankali. 

Katseta yayi da cewa, "nasan dai yanzu bakida wani tsayayye shiyasa naga ya dace in taimaka miki in aure ki ko dan kar a sake aikata 'yar gidan jiya"


 

Wasu sirarran hawaye ne suka ziro mata, lallai yazeed dinnan ji yanda ya soka mata magana hankalinshi kwance,


"Yazeed kenan, bari kaji in gayama abunda baka sani ba, mai hali ai baya barin halinshi, don haka ko aurena kayi bazan fasa aikata abunda nake aikatawa ba, shi yasa tun farko na shaida maka bana buk'atar taimakon ka Dan ni bazan iya auren Wanda bana so ba"


"Ke kisan fah irin maganar da zaki rik'a gayamin, bawai Dan ina sonki Nazo nan ba sai don in taimaka miki in fitar dake daga k'angin da kike ciki, any where jibi idan abbanki yazo Sai ki gaya mishi ni kike so amma fah ki sani ni fah bana sonki kuma bazan taba sonki ba ko aurenki da zanyi na wani k'aramin lokaci ne, da zaran kin dai daita da mahaifinki zan sakeki kije can ki k'arasa rayuwar da kika daukarwa kanki"

      


         45

Wani irin K'ululun bak'in ciki ne ya tokare zuciyar Afnan har wani d'aci bakinta ke mata, 


Cikin kuka tace, "wallahi ni ba karuwa ba ce, kuma kaje kacewa Ammi da ta turoka ni bana sonka"


Murmushi yayi, "tank god da kika San turoni akayi, Sai dai ni mai biyayya ne ga iyayena da zaki taimaka min kije kice bakya sona da kin taimaka min" yana kaiwa nan yayi waje yabarta tana rusar kuka.cikin ranshi addu'a yake Allah yasa taje ta gaya ma Ammi bata son shi.


Shi kuwa yana fita gida ya zarce gurin mahaifin shi cikin sa'a kuwa ya same shi, bayan sun gaisa ne yake sanar dashi maganar Afnan din,


Kallon shi daddy yayi cikin tuhuma, kana nufin ba Wanda zai taimaka mata ya aureta Sai kai alhali kuma kasan akwai maganar nabeela kanka",


Dum! Gabanshi ya fadi dama yasan Sai dad yayi wannan maganar,


Sosa k'eya yayi "ba haka bane Daddy, yarinyar tana buk'atar taimako ne saboda takunkumin da mahaifinta ya samata kuma ni yarinyar ta kwanta min gaskiya ina sonta"


 Murmushi daddy yayi "naji dadin jin haka bakinka, tunda kana son ta ba damuwa amma kasani maganar nabeela tana nan"


"Daddy ni fah bana son Nabeela gaskiya"


"Toh ita tana sonka kuma Sai ka aureta, don haka ka shirya ko duka biyu hali yayi Sai a wanke ma akaima"


Murmushi yayi tare da yin godiya sannan yayi mishi sallama ya wuce,


Tunda yazeed yabar gurinta take rusar kuka har wani jiri ke d'ibarta haka Ammi tazo ta risketa,


"Lafiya kike kuwa Afanan?"


"Lafiya kalau nake Ammi kaina ne kawai ke ciwo"


"Eyya injin kinsha magani?"


Gyada kai tayi, "eh nasha"


"Toh Allah ya sauwak'a"


Afnan ta karb'a da Ameen,


Ammi tace,

"Dazu Yazeed yake shaida min Wai yana so ya aure ki, shine nace toh yazo ya ji ta bakinki idan kina son shi, ina fatar dai kun dai daita kanku? "


Wani murmushi Afnan tayi mai ciyo, "Ammi kina ganin abun baiyi yawa ba, gaskiya ni bazan iya auren yaya Yazeed ba ko yanzu haka ai kunyi kok'ari kawai dai Abba zan barwa zab'i duk Wanda ya zab'armin zan aureshi amma gaskiya bazan iya rushe future din ya Yazeed ba"


Fuskar Ammi tuni ta koma ta damuwa, "haba Afnan ya zakice haka, shi fah ya ganki yace yana so, kin San hala ko wane mutum mahaifinki zai hadaki dashi ne?, ki sani fah yazeed zai kare miki mutuncinki tunda yasan abunda yafaru dake amma Wanda duk Abbanki zai hadaki dashi ba kare miki mutuncinki zaiyi ba tunda ba gaya mishi abunda yafaru dake za'ayi ba,"


"Dan Allah Ammi kiyi hkuri amma gaskiya bazan iya Auren ya Yazeed ba"


Ran Ammi ba k'aramin b'aci yayi ba hankalinta ya bala'in tashi bata so Afnan ta mata nisa tana kaunar yarinyar sosai ita kadai take ganin ta dace da Yazeed dinta, toh yanzu ya zatayi? Gashi Bata so ta takurata kar taga kamar wani abu, "anya kuwa Afnan ko dai wani Abu Yazeed din ya gaya miki na b'acin rai?"


"A'a wallahi Ammi ba abunda ya gayamin kawai dai bana so na cutar da Wanda ya taimakeni shiyasa nabashi hakuri nagaya mishi bazan aure shi ba"


"Ki dai tsaya kiyi tunani da kyau Afnan ki zabi abunda ya dace," 


Tana kaiwa nan ta mata sallama ta wuce ranta duk ba dad'i,


Tana fita taci karo da yaseer gaidata Yayi sannan ya tambayeta Afnan, nuna mishi d'aki kawai tayi ta haye sama,


Dakin Afnan din ya shiga saida yayi sallama kusan sau uku sannan taji saboda hankalinta Sam baya kanta, ganin mai sallamar ne ya sanya ta k'ara daure fuska,


"Malam me ya kawoka d'akina, ko fyaden kazo ka sake yimin?"


Murmushi yayi tare da takowa kusa da ita ya zauna,

Matsawa tayi tana hararashi,


Wani shu'umammen murmushi yake mata 

" ina kika tab'a ganin miji yawa matarshi fyad'e?"


"Ka gyara maganarka ni ba matarka ba ce"


"Toh naji ba matata kike ba mai shirin zama matata" ya fada yana kashe mata ido,


"God forbid ni bazan aure mayaudari irinka ba"


Gurfanawa yayi k'asa kan guwayyun shi,


" plz Afnan let begone be bygone, wallahi Allah ba halina ne ba rud'in shaida'n ne kawai, Dan Allah ki bani wani chance in nuna miki son da baki tab'a mafalkin shi ba wallahi tallahi Afnan ina miki K'aunar da ban tab'a yiwa kowa ba, Afnan ina son ki bazan iya rayuwa ba Sai dake Dan Allah kada ki bari Abba ya hadaki da wani wallahi idan Abba ya hadaki da wani mutuwa zanyi, pls Afnan kiyi hakuri ki yafemun mu inganta rayuwarmu, ke kanki kin San ni kadai zan iya rufa miki asiri nida na aikata miki ba dai dai ba, Dan Allah Afnan kar ki barni".


Yana kaiwa nan ya rik'e k'afafuwanta ya fashe da kuka,


Tausayin shi taji ya kamata ta ko ina, hak'ik'a taga sonta cikin idanuwan yaseer, Sai dai meyasa ya mata haka, meyasa ya mata fyade? Lallai wannan itace damar da zatayi amfani da ita don ta dauki fansar abunda ya mata.


Ganin tayi shiru ne yasan ya shi jin dad'i tabbas hakonshi yacimma ruwa zai mallake Afnan matsayin mata,

Cikin rawar murya yayi magana


"Pls Afnan kice kin yafe mun mana"


"No Yaseer bazan iya ba"


Dafe kanshi yayi, "naji Bazaki yafe mun ba amma pls kada kice bazaki aureni ba"


Murmushi tayi, "ko na aureka kada kayi tunanin jin dad'i don wallahi baxaka tab'a jin dadi ba don haka kaje zuwa jibi kadawo Dan har yanzu bangama shawara da zuciyata ba "


Wani irin dadi yaji yasan tadaice ne kawai Amma bazata iya yimishi komai ba, tadai aure shi zaiyi maganin koma miye,


Cikin murna yake magana, "nasan bazaki watsan kasa a ido ba, nagode kwarai, zanzo jibin don jin abunda kinka yanke"


Haka yabar gidan cikin murna da d'okin jibin.


Yana fita Afnan ta dafe kai "inalillahi wa'inna ilaihirrajiun allahumma ajirni fi musibati wa khalifni khairan minha" addu'ar da taketayi kenan, zucitarta sai sake sake take mata, tasan tabbas abunda yaseer yace gaskiya ne shi kadai zai iya rufa mata asiri shaida ya keta mata haddi tabbas zata iya auren shi ko don ta FANSHE BUDURCINTA,


Wata zuciya tace, idan kika aure shi kinma Ammi adalci kuwa, duk halaccin da ta miki ki watsa mata ka'sa a ido?


"Ina bazan iya auren Yazeed ba, tabbas idan na aure Yazeed WULAKANTANI zaiyi"


Wata zuciya tace, toh wa zaki zab'a ciki 

YAZEED KO YASEER?


Zubewa tayi kan gado ta fashe da kuka saboda rashin samun takamamiyar Amsar tamabayar da zuciyarta ta mata.


Masu karatu Ku bata Amsa wa zata zaba YAZEED KO YASEER?


Ayshart one

Yazeed Ko Yaseer

       Nah

Ayshart Farouq


       NWA


         46

     Ganin tarasa samowa kanta mafitane ya sanya taje ta doro alwala tafara sallah tana kai kukanta ga Allah.

Ba ita ta tashi kan dardumar ba sai da aka kira asuba, bayan tayi sallah ne ta samu bacci ya kwasheta mai cike da mafalkai iri iri.


Misalin shabiyun rana tayi wanka ta nufe d'akin Ammi domin ta gaidata,


Da sallama tashiga d'akin, kallo d'aya tama yazeed da ke zaune gefen Ammi fuskarshi ba yabo ba fallasa ta kauda kanta gefe sakamakon wata uwar harara da ya banka mata,


Gurin Ammi ta nufa ta rusuna cikin ladabi ta gaidata, cikin far'a Ammi ta kamo hannunta "yau kam Afnan kinsha bacci naga har ten baki fito ba har nayi zaton ko ba lafiyaba sai da na lek'a na tarar kinata sharar bacci"


Murmushi Afnan tayi "wallahi nima ban San lokaci yaja haka sosai ba"


"Dafatar dai kinyi break fast?" Ammi ta tambaya,


"Eh nayi Ammi"


Ammi ta maida kallonta gun yazeed da yaketa shan k'amshi, "me zakaci ne Afnan ta girkama?"


Tab'e baki yayi "babu nafasa idan nafita waje zanci" ya fad'a tare da mik'ewa,


Kallonshi Ammi tayi galala, "ina zakaje ne?"


"Wucewa zanyi"


"Koma ka zauna ka jirani inshiga mak'ota in fito akwai maganar da nake so muyi"


Ba musu ya koma ya zauna yana dannar waya,


Jin Ammi zata fita ne ya sanya Afnan mik'ewa tace "ammi zan biki Dan Allah in Dan mik'e k'afa"


Murmushi Ammi tayi, "a'a Afnan ga kayana can da aka karb'o min wanki ki had'a min a wardrobe, ba dadewa zanyi ba yanzu zandawo, idan kuma kika k'are hadawa ban dawo ba sai yazeed ya kaiki nan gidan hajiya safiya ina can"


Amsata kawai Afnan tayi amma Sam wannan abun bai mata dad'i ba,


D'agowa yazeed yayi ya kalle Ammi, itama shi take kallo.


"Sai na dawo" ta fad'a tana wucewa,


"Adawo lafiya" ya fad'a tare da maida kanshi K'asa yana ci gaba da danna wayarshi, "wato dai ammi so take in saba da yarinyar nan ko ta k'arfin tsiya ne" ya fad'a a zuciyar shi tare da sakin wani malalacin murmushi.


Ita kam Afnan batama samu damar magana ba kawai gurin kayan taje tafara had'awa.

  

   Bayan Ammi ta fita ne Yazeed ya dubi Afnan da taketa sauri taga ta hada kayan tabar d'akin don jinta takeyi tamkar bisa k'aya,


" ke" yakira sunanta

Kyaleshi tayi,

"Ke ba kyajin ina magana ne?"


Sai lokacin ta juyo,

"Ni ba ke ne sunana ba"


"Oh haka ne fah toh ya sunanki? Kin San fah ni ko sunanki ban sani ba"


"Wannan kuma ya rage naka dama bana buk'atar ka San sunana" ta fad'a ciki ciki,


Mik'ewa yayi tare da matsawa kusa da ita, nan take jikinta ya d'auke rawa sai zarar ido takeyi tamkar (zee kaura) kunneta ya kama ya matse, "sake maimaita abunda kika ce"


"Wash Allah zafi! Dan Allah ka sake min kunnena"


K'ara matse kunnen yayi "ni tsaranki ne da zaki shigo kik'i gaidani?"


Idanuwanta sunyi hajur harda kwallar wahala saboda azaba, "Dan Allah kayi hak'uri bazan sake ba"


Ganin yanda taketa hawaye ne ya sanya ya saki kunnen tare da kafeta da manyan idanuwan shi,


" Inafatar kin gayama Ammi abunda kika ce zaki gaya mata saboda ni ban shiryama auren karuwa ba"


Cikin rawar baki Afnan tayi magana "duk abunda zakamin kayi min amma ka daina kirana karuwa don ni ba karuwa ba ce, kuma ni nariga nagayawa Ammi bazan aureka saboda da auren irinka da bai San kaddara ba k'ara in aure duk Wanda mahaifina zai zab'a min koda kuwa maigadin gidanmu ne, kuma nagode kwarai da halaccin da kukamin Allah yasaka muku da alkhairi daga gobe bazaka sake ganina gidanku ba ballantana ka wulak'anta ni," tana kaiwa nan ta rab'a ta gefen shi ta wuce tana sharar kwalla


Shi kam yazeed tsaye yayi tamkar an shuka dusa kalaman Afnan ba k'aramin tasiri sunkayi mai cikin zuciya ba, wani Abu yaji yana ratsa jinin shi da gangar jikin shi, zuciyar shi har wani tururi take "me yasa Afnan zata gayawa Ammi bazata aure shi ba?" Wata zuciya tace, "bakai kace ta gayama Ammin ba?


"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" ya fad'a tare da dafe kanshi, shi kadai yasan yanda yakeji. 


Anya kuwa YAZEED ba ka fad'a TARKO ba? Muje zuwa 


Ayshart one

Yazeed ko Yaseer 

       Nah

Ayshart Farouq


Nagarta writers Associations


         47


Yau Assabar kallo d'aya zakama Afnan ka gane bata cikin nutsuwarta duk tabi ta dabirce jiran zuwan su Mommy kawai takeyi, 


Ammi na lura da ita ta kawo ido kawai ta zuba mata, tabarta da dabararta, don ita harga Allah bata son ta takurawa Afnan, ita dai fatanta kawai Allah ya zab'ar mata miji nagari.


Su Abba basu iso ba sai bayan la'asar, koda suka zo tune yazeed da yaseer sun garzayo don dama Abba yakira su saboda su ne shedun shi.


Zaune suke babban parlour din Ammi dukan su "yau dai nazo karb'ar alk'awarina gurin 'yar ki" cewar Abba yana kallon Ammi,


Murmushi Ammi tayi, "yata kuwa 'yar halarce bazata baka kunya ba" Ammi ta fad'a tana kallon Afnan da gabanta ke dukan uku uku,


Kallonta Abba yayi "Wa kika tsaida? Kuma a ina yake waye shi?"


Ba Afnan ba duk da da Yazeed da Yaseer saida suka same Kansu da Fad'uwar gaba dukda cewa kuwa kowa yasan makomarshi.


Rudewa Afnan tayi bakinta sai kakkarwa yake tama kasa furta komai,


"Da ke nake magana" Abba ya daka mata tsawa yana zare mata idanuwa."


Maida dubanta tayi gun Yaseer da Yazeed da suke zaune guri daya duk sun zuba mata idanuwa, sake maida kanta tayi k'asa tare da furata,


Ya Yazeed na tsaida matsayin mijin da zan aura.

  


TASHIN HANKALI GOBARAR GEMU, 


Wani irin zufa ne ya ketowa Yaseer tun daga kanshi har zuwa yatsan shi na k'afa idanuwan shi sun k'an k'ance har wasu ruwa ruwa kake gani na tashin hankali.


Shi kanshi Abba bai gasganta ba sai da ya sake tambayarta,


"Shin wane yazeed kike nufi?" dadi ya tambaya cikin mamaki,


Nuni tayi da Yazeed d'in da yashiga shock saboda baiyi tunanin jin abunda yaji ba,


Ammi kam bakinta k'in rufuwa yayi saboda farin ciki,


Cikin yanayin jin dad'i Abba ya dubi Yazeed "kana da masaniya game da abunda Afnan ta fad'a"


Murmushi yayi tare da Sosa k'eya "eh Abba ai tun kafin ka mata magana muka dai daita kanmu"


Ba Afnan ba dudda da Ammi saida ta kallai saboda jin k'aryar da ya fesa,


"Masha allahu amma naji dad'in wannan abun sosai wallahi, Dan haka gobe katuro min da magabatanka a daura muku aure"


Shin aure? Afnan ta tambaya cikin tsananin mamaki,


"Tabbas abunda kika jima kunnenki haka ne, don da baki fito da miji ba da yau yau zan d'aura miki ga duk Wanda zuciyata ta aminta da shi"


Yaseer ta kalla da sauri ta janye idanuwanta don bazata iya kallon yanayin da yake ciki ba, tausayin shi taji na Neman kamata bata San lokacin da ta fashe da kuka ba,


Shi kam yazeed bazaka iya cewa ga yanayin da yake ciki ba, farin ciki ko akasin shi, kallon Abba yayi. "Amma dai Abba da an d'an k'aramin lokaci dai dai nashirya ko nan da wata d'aya ne"


Murmushi Abba yayi "kar ka damu auren kawai za'a daura idan yaso daga baya sai ta tare"


Mommy dai bata CE komai ba, amma da ganin yanayinta kasan tana cikin farin ciki marar misaltuwa, haka Ibrahim da sagir murna kawai suke ganin zabin 'yar uwar tasu.


Abba ya kalle Afnan "tashi kije ki kwaso kayanki mu wuce gida" ya fad'a yana mikewa,


 "A'a fah alhaji baza ayi haka ba, bakai zakaje da ita ba mu zamu maida ma ita zuwa anjima" Ammi ta fad'a 


Momy tace,

"Allah sarki hajiya ai hidimar tayi yawa ko yanzu ai kun mana HALACCI,"

 

Murmushi Abba yayi "toh shi kenan ga Afnan din nan ko yaushe kike ra'ayi sai ki kaimuna ita"


"Naji dadi sosai alhaji insha allahu zuwa anjima zan kaita dama Hafsa nake jira ta dawo sai in kaita kar ta tafi tabarni cikin kadaici"


"Allah yadawo da ita lafiya" suka fad'a ,

Baki dayansu mikewa sukayi bancin yaseer da ya kasa gane duniyar da yake ciki don jikinshi har rawa yake saboda tsananin tashin hankali.


Ba Wanda ya kula da halin da Yaseer din yake ciki sai Afnan da take satar kallon shi tun dazu.


Bayan sun fita ne yaseer yayi saurin jawo Afnan da ke baya, kofar guarding ya turata da karfi, wata irin shak'a ya mata idanuwan nan nashi sunyi jajur tamkar garwashin wuta, 


Wata irin kakkarwa tarika yi tamkar ta shud'e,


" u are hutting me yaseer" ta fad'a tana k'ok'arin k'watar kanta,


Ganin ya kusa illatata ne ya sanya ya wulgar da ita sai da kanta ya bugu da bango,


Nunata yayi da yatsa,

"Wallahi baki isa ki wulak'anta ni, Afnan me namiki haka da zaki min wannan hukunci? Kin ko San yanda nake son ki? toh wallahi ki gaggauta zuwa ki warware wannan abun da kika k'ulla"


Duk azabar da take ciki bai hanata yin magana ba,


"Wannan k'ulli bazai tab'a warwarewa ba mudddun bakaje ka gayawa iyayenmu cewa, kai kamin FYADE ba sannan kuma kamin k'aryar suna, kanada daga yanzu zuwa gobe da safe, idan ba haka ba kanaji kana gani zan zama malakin waninka,"


Tana kaiwa nan ta mik'e zata wuce,


Wata irin tazga ya mata 

"K'arya kikeyi wallahi kuma baki isa ki aure wanina ba, ni kike so kuma ni zaki aura, ke miyasa bakida imani ne, meyasa bakida yafiya ne Afnan?"


Wani irin murmushin rainin wayo tayi, "rashin imani fah kace? Ai Inaganin duk wani marasa imani yana bayanka yaseer, kuma da kake cewa yafiya, ni ban San Kalmar ba, kuma ka sani ina matuk'ar sonka ina k'aunar ka, amma wallahi sai dai sonka ya kasheni muddun bakaje ka fad'ama iyayen mu kai kamin Fyade ba, wannan hanyar kad'ai ce hanyar FANSAR BUDURCINA.

 Tana kainan ta rab'a gefin shi ta wuce tana sharar k'walla.


Yaseer kam baki d'aya k'afafuwan shi kasa d'aukar shi sukayi, zubewa nan yayi yana wani irin nishi, shi kad'ai yasan abunda yakeji, ganin yake duniya bai tab'a shiga tashin hankali irin wannan ba, yasan bama yanda za'ayi Yajema Iyayensu da wannan magana, kuma ya tabbatar da idan bai aure Afnan ba zai iya rasa ranshi. Da k'yar ya samu ya lallab'a ya tashi yana bin bango, Allah ne kad'ai ya kaishi gida lafiya.


Yana shiga d'akin mamar shi ya zube k'asa yana rusar kuka tamkar wata macce,


Ganin halin da yake ciki ne ya sanya hajiya zuwaira tayo kanshi da sauri,

" me yasameka haka Yaseer?"


"Mamie mutuwa zanyi,"


"Me kake fad'a haka ne wai?, anba da Afnan d'in ne ga wani"


"She left me Mamie, she choose some one over me, she choose some one that I hate the must"


"Wace irin magana kake haka?"


"Mamie she choose Yazeed over me"


Wata irin uwar ashar Mamie ta saki, Yazeed fah ka ce? Chab uban nan ai wallahi ba zai yiyu ba, Nabeelah fah? Ina, it can't be bazan tab'a bari Yazeed ya aure wata ba idan ba Nabeela ba, taya zai rushe min plan d'ina ba zai yiyu ba, shin wai yama akayi haka ne? Dama yana son yarinyar ne?


"Nima ban sani ba" yaseer ya fad'a tare da kwashe labarin yanda sukayi da Afnan din kaf ya gaya mata.


Hankalin hajiya zuwaira idan yayi dubu ya tashi, "kam uban nan lallai wannan yarinyar tazo da abunda bazai tab'a yiyuwa ba, ta yaya zakaje ka gayawa Alhaji kai kayi mata fyad'e kuma da sunan gudan jinin shi?, kai gaskiya wanna ba zai yiyu ba"


"Mamie bazan iya bari ta aure wanina ba must especially Yazeed zanyi duk abunda take so don in aureta"


Da tsawa Mamie ta katse shi, "ka kuwa San abunda kake fad'a?"


"Na San abunda nake fad'a, ai ko miye ke kika ja min da tun farko kin bari na fad'i gaskiya ai da duk haka bata faru dani ba"


 

"Kayi hakuri son duk haka ba zata faru ba idan dai har sunana Zuwaira toh sai ka aure Wannan yarinya, bari kawai alhaji ya dawo"


Jin haka ya sanya hankalin yaseer ya d'an kwanta saboda yasan waye mamien shi ya San yanda take son Yazeed ya aure Nabeela don suci dukiya, ya tabbatar da zata iya aikata komai don ta hana auren Yazeed da Afnan, yasan duk abunda ta gayawa daddy ya zaunu dole ne ya mallaki Afnan muddun mamien shi ta nunawa daddy haka take buk'ata.


Ayshart one

[11/6, 11:20 AM] Ayshart One: Yazeed ko Yaseer 

       Na

Ayshart Farouq


Nagarta writes association


      49-50


Misalin karfe goma sha biyu na rana, Mamie na zaune gurin bokanta, duk ta kwashe abunda ke tafe da ita ta gaya mishi na son a hana auren yazeed da Afnan,


Bancin boka ya k'are 'yan surkullen shi, ya dube Mamie yayi dariya. "Kika ce gobe ne daurin auren ko?"


"Eh gobe ne"


Wani turare ya dauko ya bata, "wannan turaren da kike gani muddun kika sanya shi, alhaji ya shak'i kamshinsa toh da zaran kince afasa daura auren da yazeed a daura da yaseer ba za'a daura da yazeed din ba sai da yaseer"


Murmushin jin dadi mamie tayi, "toh su iyayen yarinyar ya za'ayi su amince?"


Wata dariya yayi, "ki bari in mutu kan ki binneni mana, ai turaren har alhajin zaki sanyama, shima da zaran mutane suka shak'e turaren shikenan duk abunda kikace mai shi zai fad'a kuma ta zaunu ba Wanda zaiyi gardama,"


Mamie taji dad'i sosai "toh ya maganar auren shi yazeed din da Nabeela?, kasan ka ce kar mu sanya gaugawa ciki,"


"Kar ki damu, matukar bai aure kowa ba toh bashida mata sai Nabeela".


Da murna Mamie tabar gurin bokanta. 


  Misalin karfe tara na dare, Mamie zaune parlour ta cika tayi fam, saboda ganin daddy bai dawo ba, kuma tayita kiran wayarshi bai dauka ba.


Yaseer sai faman kiranta yake, don shi ya k'agu ayita ta k'are.


 

Sai guraren karfe goma daddy ya shigo, tunda ya doso falon yakejin gabanshi na fad'uwa, saboda bai San abunda zai tardaba.


Da sallama ya shiga falon, kallo d'aya yama Mamie bai sake marmarin sakewa ba.


Murmushi yak'e yayi "uwargida ran gida, ayi hak'uri fah naga kinata kirana wlh ina cikin taro ne, banga miss calls din ba sai yanzu da na shigo gida"


Wani kallon uku saura kwata ta mishi, "ai haka zaka ce, yanzu saboda Allah tun yaushe nake jiranka har kwalliyar da nama ta goge" ta fad'a cikin salon kissa.


"Ayya ayi hakuri, ai ke kin San ta daban ce ko bakida kwalliya" ya fad'a yana sakar mata murmushi.


 

Dawowa tayi kan hannun kujerar da yake zaune, ta zauna tana shafa fuskar shi.


"Yanzu Dan Allah alhaji abunda aka min a gidan nan an kyauta?"


Sai kawai ta fashe da kukan kissa, taci gaba da magana,


"Don anga bani na haife yazeed ba za'a ce a daura mishi aure gobe ba tare da an neme shawarata ba"


"Wlh Zuwairah ba haka abun yake ba nima kaina ban San da maganar ba sai yau da yazeed din ke gayamin Mahaifin yarinyar na nemana"


" ban San ko yaushe zaka daina nuna banbanci tsakanin yazeed da yaseer ba, don kawai ba kai ka haifi yaseer ba sai ka rik'a tauyema hakkin shi"


Duniya idan akwai abunda daddy ya tsana toh bai wuce wannan Kalmar ba. Don shi bai tab'a nuna cewa yazeed ne d'anshi ba ba Yaseer ba hasalima yafi yima Yaseer abunda yake so kan Yazeed, don gudun irin haka. Amma ko yaushe hajiya zuwairah sai ta jefeshi da wannan mugun kalami,


"Me kike nufi zuwairah?" Ya fad'a cikin b'acin rai


"Yarinyar da Yazeed ya cema yana so ya aura bayin kanshi ba ne, mahaifiyar shi ta tilasta mai ya aureta don kawai ta kuntatawa Yaseer tunda taga yana son yarinyar"


Kan daddy ya daure, "ban gane inda zancenki ya dosa" ba, ya tambaya cikin mamaki,


"ka gane sarai abunda nake nufi alhaji, don ba komai yasa Ameenah tayi haka ba sai don ta raba auren yazeed da Nabeela ne ta kuma kuntatawa yaseer ya sanya ta had'a auren Yazeed da Afnan"


"Haba zuwairah me yasa kike son ki kawomin rudani cikin wannan lamari, idan dai don Nabeela kike haka, ki sani Yazeed dole ne zai aurenta ko yana so ko bata so tunda dai ita tana sonshi"


"Gaskiya alhaji ba zaiyiyu ba, Nabeela bazata taba zama da kishiya ba kasan sarai tun tana yarinya take son Yazeed, taya lokaci d'aya ta dawo ta tarar yazeed yayi aure, wani irin hali kake so ta shiga? Sannan Yaseer kanshi yanzu haka baida lafiya saboda wannan lamarin yana son yarinyar sosai itama kuma tana sonshi,"


"Amma ni yaseer bai gayamin yana son Afnan ba, da ya gayamin da tun farko ban dauke zancen Yazeed din ba, tunda tun farko shi yanada wadda zai aura, sai dai yanzu bakin alk'alami ya Riga ya bushe Dan an Riga an DAURA AUREN YAZEED DA AFNAN,


Wani uban ashar Mamie ta kwararo, tare da d'ora hannu a kai tayi zaman 'yan bori,


Ganin abun nata bana lafiya ne ba yasanya ya shige d'aki yana shafar gumie.


Wani irin kukan bak'in ciki takeyi, saboda baki d'aya plan din da take shiryawa shekara da shekaru yau ya rushe, wata irin tsanar Afnan taji ta rufeta ganin take duk itace sanadin komai, don da tayi hakurin abunda yaseer ya mata da yanzu an wuce gurin, yanzu batama San abunda zata gayawa Yaseer ba.


Tafi k'arfin awa da'ya zaune tana sak'awa da kwancewa, ganin bata samo wata mafitaba yasanya ta mik'e tayi d'akinta.

[11/6, 11:20 AM] Ayshart One: Yazeed ko Yaseer

       Nah

Ayshart Farouq


Nagarta writers association 


       51-52


Mamie na shiga daki taci karo da yaseer Wanda ya kasa zaune ya kasa tsaye jira kawai yake yaji ance Afnan zata zama mallakin shi. Kallo daya ta mishi taji hankalinta ya kara tashi saboda batama San ta inda zata fara ba.


Ganin yanda Mamie tasha jinin jikinta ne ya sanya shima ya sake rud'ewa,


"Mamie ya kukayi dashi?, Ni za'a baiwa auren Afnan gobe ko?" Ya tambaya cikin tashin hankali,


Zama Mamie tayi tana mai tausayin d'an nata ganin yanda duk ya d'aga hankalin shi,


"Aikin gama ya riga ya gama Yaseer"


"Tsaya Mamie, me kike so ki gayamin kina nufin kin kasa convincing dad ne?"


Gyada mishi kai tayi "ko kad'an son an Riga dai an daura auren Afnan da Yazeed yau din nan"


Wata irin k'ara ya buga tare da zubewa k'asa yana wani irin kuka mai cin rai,


Hankalin Mamie yayi masifar tashi, tunda take duniya bata tab'a ganin yaseer ya shiga hali irin na yau ba,


Zubewa tayi itama kusa dashi tana fad'in

"Nashiga uku yau ni zuwairah, Yaseer me kake son maida kan Kane kan mace? Wayyo ni Allah Dan Allah yaseer kayi hakuri kar ka kashe kanka wallahi na daukarma allawarin sai na kashe wannan auren"


Wani kallo ya mata da idanuwan shi da suka rine,


"Bazaki iya yimin komai ba Mamie, amma ki sani ni yaseer sai na dauki mataki a hannuna Afnan tawa ce ni kadai, wallahi ba shegen da ya isa ya rabani da ita most especially yazeed I hate him to d baddest level, I hate him, he snatch everything from me, I can't spare him this time, he will pay for all he did to me, I will kill him i don't want see him all over again"

Yana kaiwa nan ya mik'e ya fita tamkar guguwa, 


Mamie kam biyar bayan shi tayi tana kiran shi saboda tasan zai iya aikata aikin Dana sani.


          Bangaren Yazeed kuwa tunda aka gaya mishi an daura auren shi da Afnan ya same kanshi da tsantsar farin ciki, yayan mahaifin shi alhaji Aminu ke bashi labarin yanda abun ya kasance, "lokacin da kasanar da mahaifinka cewa mahaifin Afnan na Neman shi sai ya shaida min mukaje tare, bayan munje ne ya Sanar damu buk'atar shi ta son a daura aurenka gobe, sai nace gskiya dauren auren nan gobe baxai yiyuba saboda munada uzuri dani da mahaifinka na tafiya zuwa kasar Dubai sai dai idan mun dawo zuwa next week, yanda naga ya nuna tamkar baiji dadi ba sai nace, idan har yaga ba damuwa sai a daura yau tunda nine waliyinka kuma akwai kuddi tare dani na sadaki, yaji dadi sosai nan take yakira wasu aminashi da yan uwan shi, in takaita ma dai ana sallame sallahr isha'i aka daurama aure nan masallaci, maganar tarewa kuma sai yanda kuka tsara kaida mahaifinka don yace yana ganin kamar nan tare dashi zaku zauna part din ummanka kafin a karkare gininka, sai Ku koma can har Nabeela idan an daura aurenku"

Jin jina kai kawai yazeed yayi jin wannan al'amari yana tashi daga nan gurin Ammie kawai ya wuce,

Itama tayi mamaki sosai da taji wannan labarin, saboda bayan la'asar takai Afnan gida itada hafsat, tasha kuka lokacin da suka barota Allah sarki Afnan yanzu kin zamo diyata ta jini tunda kika aure yazeed dina. Sun Dade sosai suna fira da Ammie da Hafsat, ganin har sha biyun dare yayi yasa dole ya kwana nan gidan.


Washe gari, da kyar Mamie tabari karfe Tara tayi, don jiya da ita har yaseer ba Wanda ya runtsa don ma kawai Allah yasa ta samu ta shawo kan Yaseer din da Allah dai yasan ta'asar da zai aikatawa,

  


Zaune take gurin bokanta,

"Ranka ya Dade kaji jiya an daura auren ko?"


Wata irin dariya yayi, "nagani ai,"


" boka yanzu saboda Allah ka gani kuma kak'i yin wani Abu akai?" Mammie tayi magana cikin b'acin rai.


Dariya ya sake kyal kyacewa da ita, " wannan al'amari yafi karfinmu"


K'ara gyara zama tayi,


"Ban gane wannan abun yafi karfinku ba,"


Daura fuska yayi sannan yaci gaba da magana,


"Wannan al'amari da kike gani akwai wani boyayyen Abu tattare dashi Wanda ni kaina na kasa gane ko miye, saboda wadannan yaran iyayensu na tsaye a Kansu musamman ma shi yazeed mahaifiyar shi bata wasa da yi mishi addu'a"


Wani zufa ya karyewa Mamie idan bata mantaba wannan shine boka na uku da yace mata haka game da Yazeed.


" toh yanzu miye mafita, saboda ni ina son auren nan ya mutu kafin yarinyar ta tare, kai ni boka koda bazata aure Yaseer din ba a dai kashe auren, don idan yarinyar nan ta haihu da Yazeed karyata ta kare"


Wata dariya boka yayi,

"Ba makawa sai ta tare tunda aka Riga aka daura auren, sai dai zan baki wani magani ki zuba mata a kofar daki, da zaran ta tsallaka maganin zata rik'a tsoron shi a gurin kwanciya. Shi kuma za'a sanya mishi matsananciyar sha'awa, kinga kuwa dole ya nemi mafita,


" toh idan ya nemeta ta k'arfi fah," ta tambaya cikin damuwa,


"Kada ki damu bazai tab'a nemanta ta k'arfi ba saida amincewarta"


Wannan abun Sam baima Mamie dadi ba don dai tasan ba'a musanyama boka ne kawai ya sanya ta Amshe maganin,


B'angaren Afnan kuwa, tunda Abba yazo ya shaida mata an daura aure take kuka har zuwa yanzu da Mommy ke mata magana,


"Yanzu saboda Allah Afnan rayuwar da zaki daukarwa kanki kenan,? Keda ya kamata ace kinyi farin ciki amma Sam naga wannan abun bai miki dad'i ba shin ko baki son Yazeed d'in ne?


Gabanta ne ya fad'i idan tace tana son yazeed tabbas tayi karya, toh wa kike so wata zuciya ta tambaya? 


Mommy ta katse mata tunani "dake fah nake magana"


Hawayenta ta shafe, "mommy bana so ne nasake rabuwa daku"


Murmushi mommy tayi, "ai irin wannan rabuwar ita ake so, ki kwantar da hankalin ki aure shine mutuncin diya macce nima nan da kika ganni haka nayi, da sannu zaki saba"


Haka dai mommy tayita bata baki har saida taga hankalinta yafara kwantawa.


Fitowarta wanka Kenan kamshi kawai ke tashi saboda tunda aka daura aure mommy take sata wanka da wasu turarruka bayan tsimin da ake dura mata, 


Wayarta ce tayi kara, ganin bata San number ba ne yasa bata dauka ba sai da aka kira gurin sau uku sannan ta d'aga.

[11/7, 10:26 PM] Ayshart One: Yazeed ko Yaseer

       Nah

Ayshart Farouq


Nagarta writers association 


       51-52


Mamie na shiga daki taci karo da yaseer Wanda ya kasa zaune ya kasa tsaye jira kawai yake yaji ance Afnan zata zama mallakin shi. Kallo daya ta mishi taji hankalinta ya kara tashi saboda batama San ta inda zata fara ba.


Ganin yanda Mamie tasha jinin jikinta ne ya sanya shima ya sake rud'ewa,


"Mamie ya kukayi dashi?, Ni za'a baiwa auren Afnan gobe ko?" Ya tambaya cikin tashin hankali,


Zama Mamie tayi tana mai tausayin d'an nata ganin yanda duk ya d'aga hankalin shi,


"Aikin gama ya riga ya gama Yaseer"


"Tsaya Mamie, me kike so ki gayamin kina nufin kin kasa convincing dad ne?"


Gyada mishi kai tayi "ko kad'an son an Riga dai an daura auren Afnan da Yazeed yau din nan"


Wata irin k'ara ya buga tare da zubewa k'asa yana wani irin kuka mai cin rai,


Hankalin Mamie yayi masifar tashi, tunda take duniya bata tab'a ganin yaseer ya shiga hali irin na yau ba,


Zubewa tayi itama kusa dashi tana fad'in

"Nashiga uku yau ni zuwairah, Yaseer me kake son maida kan Kane kan mace? Wayyo ni Allah Dan Allah yaseer kayi hakuri kar ka kashe kanka wallahi na daukarma allawarin sai na kashe wannan auren"


Wani kallo ya mata da idanuwan shi da suka rine,


"Bazaki iya yimin komai ba Mamie, amma ki sani ni yaseer sai na dauki mataki a hannuna Afnan tawa ce ni kadai, wallahi ba shegen da ya isa ya rabani da ita most especially yazeed I hate him to d baddest level, I hate him, he snatch everything from me, I can't spare him this time, he will pay for all he did to me, I will kill him i don't want see him all over again"

Yana kaiwa nan ya mik'e ya fita tamkar guguwa, 


Mamie kam biyar bayan shi tayi tana kiran shi saboda tasan zai iya aikata aikin Dana sani.


          Bangaren Yazeed kuwa tunda aka gaya mishi an daura auren shi da Afnan ya same kanshi da tsantsar farin ciki, yayan mahaifin shi alhaji Aminu ke bashi labarin yanda abun ya kasance, "lokacin da kasanar da mahaifinka cewa mahaifin Afnan na Neman shi sai ya shaida min mukaje tare, bayan munje ne ya Sanar damu buk'atar shi ta son a daura aurenka gobe, sai nace gskiya dauren auren nan gobe baxai yiyuba saboda munada uzuri dani da mahaifinka na tafiya zuwa kasar Dubai sai dai idan mun dawo zuwa next week, yanda naga ya nuna tamkar baiji dadi ba sai nace, idan har yaga ba damuwa sai a daura yau tunda nine waliyinka kuma akwai kuddi tare dani na sadaki, yaji dadi sosai nan take yakira wasu aminashi da yan uwan shi, in takaita ma dai ana sallame sallahr isha'i aka daurama aure nan masallaci, maganar tarewa kuma sai yanda kuka tsara kaida mahaifinka don yace yana ganin kamar nan tare dashi zaku zauna part din ummanka kafin a karkare gininka, sai Ku koma can har Nabeela idan an daura aurenku"

Jin jina kai kawai yazeed yayi jin wannan al'amari yana tashi daga nan gurin Ammie kawai ya wuce,

Itama tayi mamaki sosai da taji wannan labarin, saboda bayan la'asar takai Afnan gida itada hafsat, tasha kuka lokacin da suka barota Allah sarki Afnan yanzu kin zamo diyata ta jini tunda kika aure yazeed dina. Sun Dade sosai suna fira da Ammie da Hafsat, ganin har sha biyun dare yayi yasa dole ya kwana nan gidan.


Washe gari, da kyar Mamie tabari karfe Tara tayi, don jiya da ita har yaseer ba Wanda ya runtsa don ma kawai Allah yasa ta samu ta shawo kan Yaseer din da Allah dai yasan ta'asar da zai aikatawa,

  


Zaune take gurin bokanta,

"Ranka ya Dade kaji jiya an daura auren ko?"


Wata irin dariya yayi, "nagani ai,"


" boka yanzu saboda Allah ka gani kuma kak'i yin wani Abu akai?" Mammie tayi magana cikin b'acin rai.


Dariya ya sake kyal kyacewa da ita, " wannan al'amari yafi karfinmu"


K'ara gyara zama tayi,


"Ban gane wannan abun yafi karfinku ba,"


Daura fuska yayi sannan yaci gaba da magana,


"Wannan al'amari da kike gani akwai wani boyayyen Abu tattare dashi Wanda ni kaina na kasa gane ko miye, saboda wadannan yaran iyayensu na tsaye a Kansu musamman ma shi yazeed mahaifiyar shi bata wasa da yi mishi addu'a"


Wani zufa ya karyewa Mamie idan bata mantaba wannan shine boka na uku da yace mata haka game da Yazeed.


" toh yanzu miye mafita, saboda ni ina son auren nan ya mutu kafin yarinyar ta tare, kai ni boka koda bazata aure Yaseer din ba a dai kashe auren, don idan yarinyar nan ta haihu da Yazeed karyata ta kare"


Wata dariya boka yayi,

"Ba makawa sai ta tare tunda aka Riga aka daura auren, sai dai zan baki wani magani ki zuba mata a kofar daki, da zaran ta tsallaka maganin zata rik'a tsoron shi a gurin kwanciya. Shi kuma za'a sanya mishi matsananciyar sha'awa, kinga kuwa dole ya nemi mafita,


" toh idan ya nemeta ta k'arfi fah," ta tambaya cikin damuwa,


"Kada ki damu bazai tab'a nemanta ta k'arfi ba saida amincewarta"


Wannan abun Sam baima Mamie dadi ba don dai tasan ba'a musanyama boka ne kawai ya sanya ta Amshe maganin,


B'angaren Afnan kuwa, tunda Abba yazo ya shaida mata an daura aure take kuka har zuwa yanzu da Mommy ke mata magana,


"Yanzu saboda Allah Afnan rayuwar da zaki daukarwa kanki kenan,? Keda ya kamata ace kinyi farin ciki amma Sam naga wannan abun bai miki dad'i ba shin ko baki son Yazeed d'in ne?


Gabanta ne ya fad'i idan tace tana son yazeed tabbas tayi karya, toh wa kike so wata zuciya ta tambaya? 


Mommy ta katse mata tunani "dake fah nake magana"


Hawayenta ta shafe, "mommy bana so ne nasake rabuwa daku"


Murmushi mommy tayi, "ai irin wannan rabuwar ita ake so, ki kwantar da hankalin ki aure shine mutuncin diya macce nima nan da kika ganni haka nayi, da sannu zaki saba"


Haka dai mommy tayita bata baki har saida taga hankalinta yafara kwantawa.


Fitowarta wanka Kenan kamshi kawai ke tashi saboda tunda aka daura aure mommy take sata wanka da wasu turarruka bayan tsimin da ake dura mata, 


Wayarta ce tayi kara, ganin bata San number ba ne yasa bata dauka ba sai da aka kira gurin sau uku sannan ta d'aga.

[11/7, 10:26 PM] Ayshart One: Yazeed ko Yaseer

        Na

 Ayshart Farouq


Nagarta writers association 


       53-54

 Tana d'auka tayi shiru jin Wanda ya kira bai yi magana ba har kusan minti biyar ya sanya taja tsaki tare da katse kiran,


Har cikin zuciyarshi yaji tsakin, saboda tsaki na cikin abunda ya tsana a duniya.


Lumshe idanuwanshi kawai yayi tare da sake kiranta,


Wannan karon cikin masifa ta dauka "Hello wai waye da bai magana"


"Hey slow ur voice," ya fad'a a dak'ale


Yanda yayi maganar saida tsigar jikinta ta tashi saboda yanda muryarshi ta doki kunnenta, dama can muryar shi na bala'in yi mata dad'i, batada numbershi amma ta gane mai kiran,


"Wake magana" ta fad'a dukda tanada tabbacin ko waye,


Murmushi yayyi har saida taji sautin cikin waya,


"Ki rantse baki gane ko waye ba"


"Ni ban gane ko waye ba" ta fad'a tana turo baki,


Har cikin jikinshi yaji maganar saboda cikin shagwaba ta fad'a.


"Toh naji, kifito plourn bak'i zaki gane ko waye, kuma Kar ki b'ata min lokaci" ya fad'a tare da kashe wayar.


Tab'e baki tayi, cikin ranta tana jinjina abun Yazeed.


Tana kare makeup d'inta tabi lafiyar gado ta kwanta don dama bacci takeji.


Tsakaninta da Allah tafara bacci, can taji an kai mata duka a cinya, firgit ta mik'e tana sosawa,

"Haba Ya Sagir wannan wane irin muganci ne mutum na bacci a tada shi"


"Wallahi idan baki tashiba zan k'ara miki, wannan wane irin iskanci ne kibar mutum yana jiranki kusan awa biyu"


Harga Allah bata dauki abun da muhimmanci ba don Sam bata d'auka zai jirata ba saboda tasan halinshi baya son jira,


Cikin gunguni ta tashi tare da sake mitsitsika powder ta wuce tana magana K'asa K'asa,


Munafuka ana so ana kai kasuwa, andaiji kunya,


"Eh anji d'in" ta fad'a tan murgud'a baki.


Da sallama ta shiga palourn, kamshin shi duk ya cika guri, yana zaune yana danna wayar shi, bata tab'a ganin shi cikin manya kaya ba sai yau, manyan kaya namishi kyau sosai,


Guri ta samu ta zauna, sannan ta gaidashi,


Amsawa yayi yana k'aremata kallo,


"Kayi hak'uri ban San kai ne ba" ta fad'a kanta k'asa don bazata iya ci Haba da kallonshi,


Murmushi kawai yayi batare da yace komai ba,


"Bari inje inkawo maka ruwa"


"Barshi kawai mommy ta kawo min"


Sai lolacin ta lura da kayan dake gabanshi harda food flaks, sai dai ba alamar an tab'a komai a ciki.


Kusan minti goma ba Wanda ya sake cewa komai, ganin haka yasa Afnan ta mik'e ta isa gaban shi domin serving dinshi.


Karaf ya rik'e hannunta yana mata wani irin shu'umin kallo.


"Me zakiyi ne?" Ya tambaya yana murza 'yan yatsunta,


Naga baka tab'a komai ba shiyasa zan zubama,


"Barshi kawi nagode"


"Mommy bazataji dad'i ba idan bakaci ba" ta fad'a tana k'ok'arin kwace hannunta,


"Ba gurin mommy nazoba gurinki nazo kika shanya ni"


"Kayi hak'uri bazan sake ba" ta fad'a tamkar tayi kuka saboda yanda yake murza yatsun gashi takasa kwace Hannun,


Sakinta yayi Dan kanshi tare da kafeta da idanuwanshi, 


Baki d'aya ta kasa sukuni ganin kallon da yazeed ke jifanta da shi, dakyar ta mik'e da zumar ta koma gurin da take ta zauna,


Bata Ankara ba taji ya sake rik'e hannunta "ina zaki?"


"Komawa zanyi in zauana"


"Saboda me zaki koma can ki zauna bancin ga guri nan kusa ga mijinki, ko don ba ina saurayin da aka baiwa jiki yayi abunda yaga dama ba"


Cikin b'acin rai ta fizge hannunta, 


"Ban San dalilin da yasa ko yaushe kake jifata da irin wannan kalamai ba" ta fad'a tare da goge hawayen da suka zubo mata,


Mazauninta ta koma ta zauna tana sharar kwalla, 


Tausayinta yaji ya kamashi, bai San dalilin da yasa yake kasa controlling kishinshi ba idan yaga Afnan, zuciyarshi har yanzu takasa gasganta cewa fyade aka mata.


Ahankali yaje kusa gareta ya zauna tare da kama hannanyenta duka biyu ya rik'e.


"Kukan me kike?"


Kiji tambayar rainin wayo ta fad'a cikin ranta,


Murmushi yayi, 


"Ki daina kuka, badan kiyi kuka nazoba, zuwa nayi mu fahimci juna, kinga kafin ki tare kin koya min yanda zan soki, cox ni har yanzu banjiki a raina ba"


Cikin sauri ta d'ago idanuwa ta kalleshi 


Wai hala baisan tasan komai ba?, amma bari ta kyaleshi taga iya gudunshi, ta fad'a cikin ranta,


Hannun shi taji kan fuskarta yana goge mata hawaye,


"Kinga goge wannan Kar mommy tagani ta dauka wani Abu na miki" yana k'are goge mata hawan ya mik'e.


"Ni zan wuce, kin cinye min lokaci"


"Allah ya tsare a gaida su Ammie" ta fad'a kanta a K'asa,


D'an sunkuyowa yayi cikin rad'a.

"Ko d'an kiss d'in goodbye bazan samu ba?"


Jinta tayi wata iri "lallai yazeed d'innan bashida kunya" ta fad'a cikin ranta,


Bata Ankara ba taji ya kai mata peck a goshi, "goodbye tunda baza'a min ba"

Ya fad'a tamkar bashi yayi ba.


Koda ta Ankara har yakai bakin k'ofa, kawi sai tda

samu kanta da murmushi,


Yazeed nafita motar Yaseer na kunnu kai, ganin haka yasanya Yaseer d'in yin Rivas ya bi bayan Yazeed don dama Neman shi yake ruwa jallo, yasan yau mai rabasu sai Allah.

[11/7, 10:26 PM] Ayshart One: Yazeed ko Yaseer

       Na

 Ayshart Farouq


Nagarta writers association


       55-56

 Yazeed bai nufe ko ina ba sai gida, yana parking motar shi yaseer na shigowa tamkar ya tashi sama, fitowa kawi yayi batare da ya rufe motar ba, idanuwanshi sunyi jajir tamakar Wanda yasha wani Abu,

Batare da b'ata lokaci ba kawai ya kaima Yazeed da ke k'ok'arin fita daga motarnshi naushi,


Cikin zafin nama yazeed ya fito tare da nad'e hannun rigar shi ya rama naushin da yaseer d'in ya kai mishi, nan take fad'a ya kacame tsakaninsu, dak'yar maigadi da abokinshi suka shiga tdakani.


Wani kallon tsana Yaseer yakema Yazeed tare da cewa,

"Kayi gangancin shiga gonata Yazeed, don wlh bazaka tab'a jin dad'in rayuwarka ba, sai ka gwammacewa mutuwarka da abunda zanma"


Cikin rashin gane inda maganar yaseer ta dosa yasanya Yazeed yin murmushi,


"Ga alama kafara shaye shaye yaseer, coz ni banma San inda maganarka ta dosa ba, kafito fili ka gayamin matsalarka idan kanada, don wlh duk ranarda kasake gigin tab'ani sai ka kwamacema kid'i da karatu"


Yana kaiwa nan ya juya, ya nufe d'akinshi,


Da sauri yaseer ya sake shiga gaban shi,

"Tun muna yara kake samun duk abunda nake so, wannan karon kam tun muna mu biyu ka sakarmin mata don Afnan tawace ni kad'ai, ni Afnan ke so, don wlh Afnan bazata tab'a sonka ba, ta aureka ne kawai don ta huce takaici, amma zuciyarta ba kowa ciki sai ni"


Yana kaiwa nan yayi fu ya wuce yabar Yazeed nan sake da baki,


"Shin me yaseer ke nufi da cewa nashiga gonatai?, me yake nufi da cewa Afnan ta aureni don huce takaici?, wane takaici Afnan d'in ke son hucewa, shin dama akwai wani Abu tsakanin Yaseer da Afnan ne?,"

Wad'annan tambayoyin ne Yazeed kema kanshi, ganin bashida amsar wannan tambayr ne ya sanya ya koma motar shi sai gidan Ammie,


Su Ammie na falo zaune itada Hafsa suna fira, Yazeed ya shigo tamkar Wanda aka harbo,

Kallo d'aya Ammi ta mishi ta gane ba lafiya, 


"Lafiya kake kuwa?" Ammie ta tambaya,


"Ammie me kike sani tsakanin Yaseer da Afnan"


Nan take hankalin Ammie ya tashi, shikenan abunda take gudu ya afku, Yazeed ya gane gaskiya,

Cikin dakiya tace,

"Bangane abunda kake nufi ba"


"Ammie Shin kinada masaniyar Yaseer da Afnan suna soyayya kika sani na aureta"


Ajiyar zuciya Ammie tayi,


"Eh Afnan ta gayamin cewa Yaseer yace yana sonta ban cin kaima ka gayamata kana sonta"


Ajiyar zuciya yayi at list dai ba abunda yake zargine ba,


"Toh Ammie me yasa kika sanya ta aure ni bancin kin San Yaseer take so"


Murmushi Ammie tayi yazeed kenan he never change, har yanzu shi bai considering kanshi sai yaseer, wannan karon kam bazata yarda ba dole Yaseer ya Dan da'ana abunda Yazeed ke d'an d'anawa idan aka hanashi abunda yake so aka bama Yaseer,


Basar da tunani tayi tare da cewa, "wannan yin kanta ne, saboda shawara na bata ta zab'i Wanda zuciyarta ta aminta dashi,"


"Yana nufin kenan dani zuciyarta ta aminta?"

Ya tambaya cikin zumud'i


"Lallai dakai zuciyarta ta aminta tunda kai ta zab'a"


Lokaci guda Yazeed ya saki murmushi tare da cewa,


"Alhamdulillah"


Kallonshi Ammie tayi "dama kana sonta kake wani kakkaucewa?"


Sai lokacin yagane abunda yayi, Sosa k'eya yayi tare da cewa,

"Zan dai koyi sonta tunda kin Riga kin lik'a min" ya fad'a yana mik'ewa.


Dariya su Ammie sukayi, har Hafsat na tsokanarshi,

"Nifah Ammie da naga shigowar shi har na d'auka gobara ce Ashe kishin d'iyar Ammie ne , kai gaakiya wannan salon soyayyar yana birneni"


Hararanta yayi yana d'aure fuska

"Yaushe raini yashiga tsakanin mu? Allah zan b'ab'allaki "


"Dan ta fad'i gaskiya" Ammi ta fad'a tana dariya.


Ganin zasu maidashi wani laughing stuff yasanya yabar musu gidan.


B'angaren Yaseer kuma haka yaje ya samu Afnan itama ya gayamata magangannu masu k'ona zuciya, yana ik'irarin sai tayi nadamar auren Yazeed da tayi.


Afnan kam tasha kuka har ta gode Allah ganin irin halin da yaseer d'in yazo mata dashi, har cikin ranta ta tausaya mishi sai dai yanda yayi mata wasa da hankali dole itama ta nuna mishi kuskuren shi.


Mamie kuwa hankalinta yayi k'ololuwar tashi ganin yananyin da yaseer yake ciki, kullun cikin kuka yake, duk yabi ya lalace saboda bala'i, ganin yana so yaje ya tona asirin cewa shi yayiwa Afnan fyade da sunan Yazeed ya sanya taje gurin boka aka daure bakin shi, saboda boka yace, duk lokacin da daddy yaji cewa shi yayiwa Afnan fyade da sunan d'anshi asiri bazai sake tasiri kanshi ba, kuma korarshi zaiyi gidanshi da company d'in shi. Ita kuma tasan duk lokacin da haka ta faru k'aryarta ta k'are.

[11/7, 10:32 PM] Ayshart One: Yazeed ko Yaseer

       Na

Ayshart Farouq


Nagarta writers association


      57-58

  

    Tun lokacin da Yazeed yabar gurin Afnan bai sake komawa ba kuma bai nemeta a waya ba.


 Misalin karfe 5 na yamma Afnan na zaune itada mommy suna fira. text taji ya shigo wayarta, kamar karta duba sai kuma ta kasa sharewa dukda tana tunanin ko mtn ne saboda yanzu ko charting ta dainayi kuma batada number kowa saita 'yan gidansu, da su Ammie.


Koda ta duba sai taga Yazeed ne, murmushi tayi da ta bud'e text d'in.


"Hi!

Ki shirya nan da minti ashirin zaki rakani wani guri.


Daga mijinki"


Wani murmushi Afnan tayi mai hade da Jan tsaki.


Mommy ta kallata,

"Lafiyarki kuwa?"


"Lafiya lau mommy"


Tab'e baki mommy tayi tana cewa wannan d'abi'a taki ta tsaki ki dainta don ba d'abi'ar kwarai ba ce, "


Daga haka sukaci gaba da firarsu,

Ibrahim ne ya shigo yana cewa,


"Mommy ga fah surukinki nan Yazeed yazo yace bazai shigo ba"


Gaban Afnan yayi ras ya fad'i tana mai zubawa k'ofa idanu.


"Haba dai shikuma Yazeed don me bazai shigo ba?, ai yanzu ya wuce haka ni ba surukar shi ba ce mahaifiyar shi ce, kaje ka shigo dashi mana".


Bata ida rufe bakinta ba yayi sallma ya shigo fuskarshi dauke da murmushi, suit ne jikin shi dark blue, da bak'ak'en takalmi kanshi sai shek'i yake da gani Daga assibiti yake, masha allahu yayyi kyau sosai.


Har k'as ya duk'a ya gaida mommy.


Sai lolacin Afnan tadawo Daga duniyar mamakin da ta tafi.


"Lalala, shine zaka shigo bazaka jira amaka iso ba?" Ibrahim ya fad'a yana kallon Yazeed,


Mommy tace, "oh dama kai ne ka dakatar dashi a waje kazo kana cewa yace baxai shigo ba?"


Yazeed yayi murmushi "wai har ya kulla min sharrin"


Duk suka sanya dariya,


Afnan kam sunkuyarda kanta tayi k'asa tana wasa da yatsunta, mommy sai jefa mata harara take ganin tak'i gaisheda Yazeed,


Sunfi minti goma suna fira sannan Yazeed yace, "mommy dama Ammie ce tace, inzo in dauki Afnan in kaita gidan wata aminyarta da take saro kaya daga dubai don ta zab'i Wanda take so, yau aka bude kayan kar a zab'e, shine nake so ki mana izini muje ta zab'a"


Murmushi mommy tayi, "haba yazeed kaida matarka har sai nama izini?, Allah dai ya tsare, bari inshiga ciki, ke kuma Afnan ki tashi kije kishirya kada ki b'ata mishi lokaci" tana kaiwa nan tayi mishi sallma ta haye sama.


Ita kam Afnan dakyar ta samu ta mik'e tashiga daki saboda yanda k'afafuwanta suka mata nauyi, ita harga Allah bata dauka da gaske zaizo ba.


Bata wani b'ata mishi lokaci ba, ta shirya cikin bakar jallabiya, ta yane kanta da mayafinta. ba kara min kyau tayi ba, sai tafito tamkar wata balarabiya.


Har lokacin suna fira da Ibrahim, kallo d'aya ya mata saida yayi tasbihi ga ubangiji don kam yayi dace, ya fad'a cikin ranshi,


"Allah sa dai kar kaje ka zubarmin da k'anwa bisa hanya gurin kallonta" Ibrahim ya fad'a yana kyalkyalewa da dariya,


Murmushi yazeed yayi tare da Sosa k'eya "kasan ni kyawon mace baya rud'ani wane dare ne jemage bai gani ba"


Tabe baki yayi "ohon maka kyawon kanwata dai ya rud'aka, idan kuwa ba hakanan ne ba ka rantse bai rud'aka ba"


Mik'ewa Yazeed yayi "Allah dai ya baka lafiya, kaga tafiyata Nikam"


Ba tare da yace mata uffanba ya wuce, Ibrahim sai tsokanarshi yakeyi.


Itama sai ta samu kanta da biyar bayanshi, har suka shiga mota ba Wanda yacewa wani ci kanka. shi driving sinshi kawai yake ita kuwa sai dannar wuya, dukda ita kanta batasan takamammen abunda takeyi da wayar ba.


Wakar shine word ya kunna ta no promises,


Kalaman wakar suna shigarsu da kyau, sai wani lullumshe ido yakeyi yana biyar wak'ar, ita kuwa Afnan lakwas tayi tana sauraren baitocin wak'ar.


Bata Ankara ba sai ganinsu tayi cikin gidan Ammie yana k'ok'arin yin parking, kallonshi tayi ta daure fuska, "ya akayi na ganmu nan kuma?"


Batare da ya kalletaba yace, " yau zaki fara duty matsayinki na matar aure,"


Dukda bata fahimce maganar tashi ba sai da taje hankalinta ya tashi, "bangane me kake nufiba"


"Ki shigo ciki zaki gane abunda nake nufi"


"Ni ba inda zan shiga saboda ba nan kace zaka kawoni ba"


"A ina nace zan kaiki?"


"Ni dai pls ka mayar dani gida ban San da wane ido zan kalle Ammie ba da kunya gaakiya"


"Waye ya gaya miki Ammie ta nanan ne?"


"Inallillahi wa'inna ilaihirrajiun me yazeed ke shirin yi mata ne?" Ta fad'a a ranta hankalinta yayi kololuwar tashi,


"Me mukaziyi toh tunda Ammie ba ta nan" ta fad'a cikin tashin hankali,


Murmushi yazeed yayi don ya hango tsoro a kwayar idanuwanta


"Meye abun tada hankali keda kika iske saurayinki gidanshi ina ga mijinki?, ke dai ki shigo kawai ba abunda kike tunani zai faruba, aiki kawai zan sa ki, idan kinyi sauri kin kammala Ammie bazata iskomu nan ba, idan kuma bakiyi sauri ba komai zai iya faruwa don bata nesa da dawowa"


Yana kaiwa nan ya fito ya zagaya ya bud'e mata, bata kalleshi ba sai sharce kwàllar da takeyi,


"Ki fito mana kina kara batawa kanki time".


Dan dole ta fito motar tana tafe tana hawaye. 


Shi kuwa sai murmuahin mugunta yakeyi.


Suna isa ya zube kan kujera yana nishi sai kace Wanda yayi dambe.


Ita kuwa boyar Allah Afnan komawa tayi daga gefe tayi tsaye duk jikinta yayi sanyi.


Kallonta "ki zauna mana kinyi tsaye kamar wata bakuwa" yakare maganarshi yana lumshe ido,


A hankali ta samu guri nesa dashi ta zauna,


"Wane irin aiki zanma? Marece nayi"


Kamar bazai tamka ba can yayi mata nuni da hannunshi alamar tazo,


Gabanta ne yashiga dukan uku uku, dakewa tayi tare da zuwa kusa dashi, "gani" ta fad'a tana turo baki,


"Ni kike turowa baki?"

 

Shiru tayi ta kyaleshi tana gunguni,


Janyota yayi da k'arfi ta fad'a kirjinshi.


Wani yar sukaji dukkansu,


Mutsu mutsun kwacewa take amma takasa, 


Ganin haka yasanya ya sake matseta ya saka kanshi a wuyanta yana zagaya.


Afnan kam kasa tab'uka komai tayi kawai sai ta fashe mai da kuka.


Ganin haka yasanya ya dago da idanuwanshi da suka zama jajaye ya kalleta,


Zaune ya mike amma still yaki bari ta sauka daga jikinshi,


Hab'arta ya dago,ya kalle idanuwanta da ke zubarda hawaye,


"Wannan hawayen na miye?"


Ya fad'a a kasalance,


Itama cikin wata murya race "Dan Allah ka maidani gida"


"Zan maidaki gida idan kikayimin Abu uku"


"Abu uku kaman me?"


Kanne mata idanu yayi, 

"Ranar kin min tsaki kuma tsaki na cikin abunda na tsana sosai don haka zaki wanke laifinki yanzu idan kikamin massage"


Zaro idanuwa tayi "wallahi Allah banma tsaki ba, kuma ma kace ka hakura Dan Allah wlh ban iya ba"


Abun yaso yabashi dariya ya d'aure "Ashe kuwa zamu tabbata a nan" ya fad'a tare da juya mata baya,


Ganin da gaske yake ya sanya taje gurin kafafunwan shi tana daddannawa,


"Aush! Wannan ai sai ki karyani" yayi maganar yana yamustar fuska


"Ya kakeso nayi? ai na gaya maka ban iya ba"


"Idan baki iyaba sai kice a koya miki"

Kafin ta yi magana tune ya sauko k'asa yana marmatsa mata cinyoyinta,


Ya ilahi!, fad'ar yanayin da suka shiga ciki dukansu b'ata lokaci ne, 


Dakyar ta iya janye kafafuwanta ta sunne kanta k'asa, amma har lokacin hannayen yazeed takeji a jikinta,


Gyaran murya yayi, "bissimillah zo ki fara tunda kinga yanda akeyi"


Haka dai ta mamatsa mai, tanayi yana lumsar ido saboda yajishi a wata duniya ta daban wadda ba kowa a cikinta sai shi da ita.


Saida tayi kusan 15mnts sannan ya dakatar da ita, yana kwance ya kasa mikewa shikadai yasan abunda yakeji a jikinshi,


Cikin sarkakkiyar murya yace, Abu na biyu kin b'ata min lokaci ranar da naje gidanku kuma lokaci na cikin babban abunda nake baiwa muhimmanci don haka yanzu ki tashi kije kitchen ki samu Abu mai sauki ki girka min, kitchen din Ammie dai ba bakonki ba ne"


Agogonta ta duba taga baifi 20 mnt a kira magrib ba,


"Mommy fah zatamin fad'a maraice yayi"


"Tare da mijinki kika fita ba fad'an da mommy zata miki" 

yana kainan ya mik'e baima kalletaba yayi sama, direct bathroom ya wuce ya sakarma kanshi shower ko ya samu sassaucin radadin shaawar Afnan da ke damunshi, yasan Afnan matarshi ce amma bazai iya nemanta a ko ina ba sai a gidanshi, haka dai yata zubawa kanshi ruwa saida ya dau lokaci sannan ya fito tare da alwala, wasu kananan kaya yasa marasa nauyi ya nufe masallaci.


[11/7, 10:28 PM] Ayshart One: Yazeed ko Yaseer 

           Na

     Ayshart Farouq

Nagarta writers association

        

        59-60


 Afnan kam rasa abunda zata girka mishi tayi, can dai ta dafa mishi macaroni wadda taji kifi da naman rago, Allah Allah take yi kar yace ba zaici ba, don ta sanshi da bodaddin ra'ayi.


 Yazeed kuwa bayan yayi sallah ya dawo, ya taradda Afnan na sallah nan cikin Palo, tsura mata idanuwa yayi ganin yanda take sallarta cikin nutsuwa, 


Bayan ta kammala ta juyo karaf suka had'a idanu, "wato kallo ya k'are mata" ta fad'a cikin ranta.


Dauke idanuwanta tayi saida ta kammala azkar d'inta sannan ta mik'e,


Kallonta yayi "ki kawo min abincina",


Turo baki tayi, ", ni dai Dan Allah ka maidani gida"


"Wasa kikeyi ai ba inda zani inajin yunwa, oya je ki kawomin kina b'atamin lokaci"


Haka taje ta kawo mishi ta ajiye mishi duk ranta ba dad'i.


Yana kula da ita sai dai ko a jikinshi.

Kyaleta yayi ba tare da ya ce mata komai ba, yayi serving kanshi, yana ci yana lumsar ido saboda ba k'aramin dad'i abincin ya mishi ba, cikin ranshi cewa yake Ashe zan mori girki.


Suna cikin haka su Ammie suka dawo, zo kiga Afnan duk ta tsure, ta rasa inda zata saka kanta saboda tsananin kunya,


Shi kam gogan ko a jikinshi asalima hakan ba k'aramin dad'i ya mishi ba,


Cikin jin kunya Afnan ta gaida Ammie,


"Shikenan kawai Afnan sai kika gujemu ko?" cewar Ammie tana mai zaunawa kusa da Afnan d'in,


Yazeed yayi karab, ya ce, "ai fah Ammie yanzu haka ita ta matsamin sai nazo da ita ta ganki"


Jin k'aryar da ya sharara yasanya Afnan ta d'ago ta kalleshi,


Kashe mata idanuwa yayi batare da Ammie tagani ba,


"Allah sarki 'yata, shine kika bari ya wahalar dake yasaki girki?"


"Nifah Ammie bani na sakata girki ba, ganin tayi ina jin yunwa shine ta taimaka ta girka min don bata son ganin mijinta da yunwa".


Harara Ammie ta doka mishi,

"Marasa kunya, yaushe ka maidani kakarka ne?"


Murmushi yayi yana ci gaba da cin abincinshi.


Afnan kam duk'ar da kanta tayi k'asa, da me zataji? Da karyar da yake fesamata ko da kunyar Ammie da takeji?,


Bata San lokacin da tafara sheshekar kuka ba,


"Ya salam! me yafaru ne Afnan?"

Ammie ta fad'a cikin rud'ewa,


Cikin kukan shagwab'a Afnan ke magana,


"Ammie wlh fah ba gaskiya yake gaya miki ba, ba haka a kayi ba sam"


Murmushi ammie tayi "nasani d'iyata kyaleni dashi kawai"


Yazeed kam zuba mata idanuwa yayi ganin yanda take kukan shagwab'a tamkar wadda akama wani abun,

Ji yayi duk ta burgeshi,


Sosa k'eya yayi 

"Kar kimin sharri don kinga Ammie ta dawo, ke dai kawai kice kunya kikaji tazo ta taradda ke"


Hafsat da tun da suka shigo take dariya k'asak'asa ta ce, "kai wannan Amaryar ta yayanmu badai shagwab'a ba mudai ayi a tare musha shagali tun kan su kai Kansu don naga dukansu matse suke"


Ba Afnan ba duk da, da Yazeed saida yaji kunya,


 ita kuwa hafsat ko a jikinta don dama can ita chab'a ce batada case.


Harara Afnan ta doka mata "Ammie kin ganta ko?"


"Hafsat zanfa ci mutuncinki, ba yayarki ba ce da kike mata shak'iyanci?" ammie ta fad'a tana dubin Hafsat,


"Allah huce zuciyarki" ta fad'a tana ci gaba da dariyanta k'asa k'asa.


Kayan da suka shigo dasu ammie ta zazzaga tana nunawa Afnan, Ashe dama su sukaje karb'a yazeed yafito da ita,


Kayan ba k'aramin birgeta sukayi ba,


Sai bayan isha'i suka wuce, shima saida Afnan tasa rigima.


Suna cikin mota ba Wanda yacema wani ci kanka,


Afnan haushin barint da yayi har Ammie ta iskota, da kuma k'aryar da ya shatata mata ya sanyata cika da batsewa, nema kawai take ya tab'ata yaga bori.


Shi kuwa tamkar yasan tsiyar da take kitsawa ya Sanya ya shareta,


Saida yakawo bakin wani restaurant yayi parking ya shiga ya siyo mata kibab da ice cream.


 Suna isowa gida ya tsaida motar.


Afnan ba tace mishi komai ba ta yunk'ura zata fita motar, yayi sauri yasaka lock, 


"Malam ka bud'e min infita" ta fad'a cikin zafin rai


Bai kulata ba saima sit d'inshi da ya d'an kwantar yana mai haskata da d'an hasken gaban wayarshi.


"Wai meye hak...?"


Bata ida rufe bakintaba taji ya janyota jikinshi ya rungumeta.


Mutsu mutsu ta ringayi don ta kwace kanta sai dai ko gizau yazeed baiyi ba, saima kara matseta da yayi yana shak'ar kamshinta mai dad'i.


 ganin haka ya sanya itama tayi lakwas a kirjinshi tana maida nunfashi,


A hankali yake shafan kanta,


"Nasan kin matsu mu tare ko?"


"Ji wata tambayar rainanin wayo" ta fad'a cikin ranta.


 Murmushi tayi, yau fah zata tona asirin wannan mutumin don tagaji da abunda yake mata.


"Saboda me zan matsu?" ta fad'a tana d'ago kanta,


Kallonta yayi "saboda kina sona"


"Waye ya gaya maka ina sonka?" Ta tambaya cikin isgili,


Murmushi yayi "saboda kin zab'eni kin bar Yaseer alhalin kuma kin San shi yana sonki ni kuma taimaka miki Ammie tasa nayi"


Saida ta d'ago fuskarshi ta k'are mishi kallo sannan ta shek'e da dariya,


Kallonta yayi don bai tab'a ganin dariyarta ba sai yanzu, sai yaga duk ta k'ara burgeshi.


Idonta a nashi tayi magana,

"Yazeed kenan, ni ban San kome ka dauke kanka ba, toh bari kaji in gaya maka abunda baka sani ba, ni Afnan nasan Yazeed yana sona from d first time he set his eyes on me, taimakon da kake ik'irarin kamin ka sani ba kai ka taimaka min ba, ni na taimakama na dube karamci da halaccin da Ammie tamin na zab'eka, cox nasan zaka iya rasa rayuwarka idan har baka mallake ni ba"


Kallonta kawai yake yana nazarinta,

"Wannan wace irin magance kikeyi?, ni ban gane inda kika dosa ba, cox ni nafi k'arfin taimakon ki",


Gira ta d'aga mishi, "Allah ko?"

 hannunta ta saka cikin jakarta ta dauko wani k'aramin littafi Wanda da ganinshi kasan deary ne.


Yazeed naganishi yaji hankalinshi ya tashi, shikenan yarinya ta Riga ta gama dashi, ta riga ta san duk wani sirrinshi da yake binnewa.


Mik'a mishi tayi tana kallon idanuwanshi da suka fara k'ank'ancewa,


Kasa cewa komai yayi kuma ya kasa karb'an littafin sai binta kawai yake da idanuwa. chan ya nisa, ya ce cikin taushin murya "me ya kaiki kan kayana Afnan?"


Bazata iya jure kallon da yake mata ba ta sada kanta k'asa,


"Bud'e mun kofa in wuce"


"Bazakije ko ina ba sai kin gayamin abunda ya kaiki gun sirrina"


Kasa cewa komai tayi sai gabanta da ke dukan uku uku,


Ganin bazatayi maganaba ya sanya ya jawota yafara kissing dinta ta ko ina,

K'ara yayi mai dalili tunda ta riga ta gano komai,


Saida yaga abun na nema yafi karfinshi ya sanya ya saketa yana maida nunfashi.


Dukansu jikinsu ya mutu ba mai iya cewa komai, ganin haka yasa ya janyo ledar da ya shigo da ita ya mik'a mata tare da yin unlock din motar,


"Ki tanade hujjojin da zaki ban na daukarmin deary da kikayi zuwa anjima idan nakiraki, idan kuma kika k'i daukar wayata ni kad'ai nasan irin hukuncin da zan yanke miki,".


 ganin yanda ya kafeta da ido yasa ta karb'e ledar tare da mishi saida safe ta fita motar.


Yafi 20 minute kafin ya iya Jan motarshi ya wuce.

[11/7, 10:28 PM] Ayshart One: Yazeed ko Yaseer

       Na

Ayshart Farouq


Nagarta writers association 


     61-62


  Misalin k'arfe goma shad'aya na dare, Afnan na kwance deary din Yazeed ne hannunta da yak'i karb'a. jujjuyashi take tana mai tuna lokacin da ta tsince shi,


Wata rana Yazeed ya dawo daga asibiti, direct gidan Ammien shi ya isa, koda yaje bai isketa gida ba, parlour ya zauna ya fitarda system dinshi yana daddannawa, lokacin ita kuma Afnan ta fito da niyar kallo ko ta ragewa kanta kada'aici, tana fitowa taci karo da Yazeed d'in a parlour, ganin bazata iya zama ba kawai ta gaidashi tare da zagayawa tayi guarding, ta dad'e nan zaune kafin ta mik'e ta koma cikin gida, ji tayi ta taka wani abu, tana dubawa taci karo da littafi d'an k'arami mai shegen kyau, daukan littafin tayi tana jujjuyawa, sannan ta bud'e saida na wuce kusan page biyar sannan taga rubutu, da ta d'aukama littafin bashida komai, saida taga abunda ke cikin fifth page sannan ta fahimce ko miye.


Har ga Allah batada niyan karanta abunda ke ciki tunda ta fahimce deary ne, sirrin yazeed ne a ciki.


Kaishi tayi ta ajiye da niyar idan yazo ta bashi abunshi, ko ta bawa Ammie ta ajiye mishi, sai Allah ya mantar da ita.


Ana gobe Daddynta zaizo don jin Wanda ta zab'a matsayin miji, har zuwa dare bata da wata mafita face auren Wanda duk mahaifinta ya zab'ar mata.


Bayan ta kammala nafila ta k'are karatun qur'ani, can idanuwanta suka hango mata deary wajen ajiye Qur'anin.


Haka kawai taji zuciyarta na ingizata da ta karanta, taga ko wace yarinya ce yazeed yake so da har yake jifanta da miyagun kalamai saboda Ammie tace ya aureta. Tasan dolema ne ya sanya wadda yake so a dearynshi.


Dauka tayi ta fara karantawa sai dai har tayi rabi ba macce a ciki, har zata ajiye idanuwanta suka hango mata wasu pages masu kyau na k'arshe kawai sai ta bud'a.

Abunda taga an rubuta shi yayi matuk'ar d'aukan hankalinta.


27 April 2017


Daga KALLO DAYA,

Na kamu da matsananciyar soyayyarta.


Ba kowa bace face AFNAN yarinyar da ta min k'aryar na mata ciki saboda wata manufa tata.


Duk lokacin da nayi arba da ita zuciyata tana min kunci inajin kirjina tamkar zai fita saboda tsananin kishinta,


Me yasa ta baiwa wani namiji jikinta ba ni ba? A duk lokacin da na tuna wannan nakanji tamkar in mutu inbar duniyarnan baki d'aya.


Nayita k'ok'arin in yak'uceta a zuciyata Dan ganin na nuna mata tsananin tsanarta a fili, sai dai zuciyata takanji zafi fiye da tata, zuciyata takan k'untata fiye da tata.


Inajin tsananin soyayyarta da kaunarta mai tsanani, tun randa na had'u da ita ba wani dare da zan kwanta face nayi tunaninta.


Inaji a raina idan ban mallaketa ba zan iya rasa rayuwata. Sai dai hak'ik'a bazan iya tunkararta da k'ok'on barata ba har sai na tabbatar da gaskiyar lamarinta.


Haka Afnan tayita karatu har takai k'arshe duk magangannun akanta ne, tayi kuka ranar har ta godewa Allah.


Tabbas tasan akwai wata fa'ida da ta sanya Yazeed ya yadda deary d'inshi, hak'ik'a ta tabbatar da cewa Allah ne ya sanya zuciyarta jajircewa sai ta karanta abunda ke ciki, ba don komai ba sai don ya tak'aita mata wahalarta, tabbas tasan Yazeed zab'in Allah ne a gareta ko don jin da tayi zuciyarta ta nutsu dashi.


Wannan ne dalilin da yasa Afnan ta zab'i Yazeed.


Wayarta ce da ta d'auki k'ara ta sanyata dawowa daga duniyar tunanin da ta tafi.


Tun bata dubaba tasan mai Kiranta, samu kanta tayi cikin fad'iwar gaba.


Kasa d'auka tayi saida aka kira sau uku, shima saida ya kusan tsinkewa,


Dauka tayi ta kara a kunnenta ba tare da tayi magana ba, shima baiyi magana ba saida sukayi kusan minti uku suna sauraren nunfashin junansu, cikin kasala Yazeed ya ce,


"Kar dai kice min bacci kikeyi" ta tsinkayo muryanshi yana fad'a


"Uhum" kawai ta iya cewa,


"Bud'e baki fah zakiyi kimin magana, kina jina"


"Uhm ina jinka" ta fad'a cikin wata Siririyar murya,


"So bani labari" yanda yayi maganar saida tayi murmushi,


"Wane labari zan baka?"


"Labari mai dad'i Wanda zaisa inyi bacci cikin nishad'i"


"Da baka bacci cikin nishad'i ne?"


"Inayi idan nayi mafalkinki, amma nasan na yau zaifi na ko yaushe dad'i kawai ki fara ina jinki"


"Baka ganin yanzu dare yayi?,"


"Bana gani, saboda yau muna tare dake har safe, wannan punishment dinki ne na sani wanka biyu"


"Wanka kuma?" Ta fad'a cikin son gane inda ya dosa.


"Uhum wanka kuwa, d'azu kin sakani a gidan ammie da kika min tausa, bayan na kawoki ma kin sake sakani"


Dif! ta kashe wayar saboda ta gane abunda yake nufi,


"Ya ilahi wannan mutume bashida kunya da alama"

Ta fad'a cikin ranta,


Tana niyar kashe wayar baki d'aya don kar ya sake kira, taji k'arar shigowar sak'o.


Budewa tayi,

"Wannan ya zama na k'arshe da zaki kashe min waya ina magana, zan sake kiranki, kada ki kuskura kik'i daga wayata coz idan kikayi gobe zanzo gidanku da kaina in sakaki wankan, idan kuma kina ganin ba gaskiya ba ne kik'i d'agawa".


Dafe kanta tayi, kunya tamkar ta nutse cikin k'asa,


Sake kira yayi, batada zab'i face ta d'aga don tasan tsab zai iya aikata abunda yace.


Tana d'agawa ya sanya mata dariya,


" kar dai kin fara shakkata tun kan aje ko ina?"


Batada amsa amma tabbas tafara jin shakkunshi,


"Kinyi shiru"


"Toh me zance?" Ta fad'a tamkar tayi kuka


Murmushi yayi har saida taji sautinshi a wayar.


"Toh yanzu dai ki fad'a min yanda akayi deary na ya kawo hannunki, kafin in yanke miki punishment d'in karanta min sirri da kikayi"


"Nifah tsinta nayi, kuma Allah ban karanta komai ba" ta fad'a cikin shagwab'a kamar zatayi kuka,


Shagwabarta na matuk'ar burgeshi,


Kwai kwayon muryarta yayi, "ba ruwana sai kin karb'i hukunci"


Dariya tayi jin yanda yayi maganar, "kayi hak'uri Allah bada gangan ba, kuma ma pages d'in k'arshe ne kawai na karanta"


"Uhum kuma su sukafi komai muhimmanci cikin deary d'in, don haka punishment d'inki sai randa kinka tare"


Zaro idanuwa tayi,

"Haba, nafa ce Allah,"


"Naji toh amma fah ba fashi sai kin karb'e hukunci, Allah dai yakai damo ga harawa ko baici ba yayi birgima"


Bata San lokacin da ta k'yalk'yale da dariya ba,


"Ashe dai kaji Hausa"


"Sosai kuwa, yanzu dai ki gayamin ya akayi kayana yakai hannunki coz nata nemanshi, har na fitarda rai"


"Nagayamaka tsinta nayi kan hanya"


Nan ta kwashe labarin yanda akayi ta tsinta ta gaya mishi.


Jin jina kai kawai yayi saboda yasan tabbas Wannan yin Allah ne, 


"Kin San wani abu?" Ya fd'a cikin sanyin murya,


Girgiza kanta tayi tamkar yana ganinta,


"Ban tab'a shiga tashin hankali ba irin ranarda aka ce ki fad'i Wanda kike so, ranar da kin fad'i wani ba niba da ina ganin mutuwa zanyi, I can't hide it any more. Afnan ban tab'a son wata 'ya mace ba sai ke, ban tab'a sanin ciyon so ba sai kan ki, Ban San yanda zan kwatanta miki irin yanda nakeji ba idan nayi arba dake, shiyasa duk ganin da zan miki sai na rubuta yanda naji na ajiye a deary nan, Wannan da kikaga kin tsinta faduwa yayi lokacin da naje dauko sabo don rubuta ganin da na miki a ranar"


Haka yazeed yayita fayyacewa Afnan sirrin zuciyarshi tun tana uhum har ta fashe da kuka saboda ita mutum ce mai son a sota, mutum ce mai son a nuna mata kulawa, a kaunaceta, da wannan damar Yaseer yayi Amfani har ya yaudareta.


Saida yaji tana kuka sannan ya tak'aita.

"Afnan kukan me kike, bakya sona ko?" Ya fad'a cikin wani yanayi,


"Ba haka ba ne ya yazeed, kukan farin ciki nakeyi, ban tab'a aza zan samu mai sona haka ba, ban tab'a aza mace irina zata samu irin Wannan soyayyar ba, na dauka bazan tab'a samun irin Wannan soyayya ba har abada, nagode kwarai ya Yazeed, nagode da HALACCIN ka a gareni, nagode da soyayyar da kake min a yanda ka ganni, hak'ik'a banida abunda zan saka maka Allah ne kad'ai zai saka maka.

Haka sukayi sallama jikin kowa a mace.


Afnan dafe kanta tayi wani abu takeji game da Yazeed sai dai bazata iya cewa ga ko miye ba, tasan a zuciyarta Yaseer ne mutum na farko da ta so, sai dai abunda takeji game da Yazeed bata tab'a jinshi a kan Yaseer ba, tana tunanin ba soyayya bace, sai dai a ranta ta k'udurce zata sanyawa zuciyarta soyayyar Yazeed kota halin yaya.


 shi kuwa Yazeed kasa komai yayi sai juya waya ji yake da yana samu yayi kuka da yayi coz yau ya fidda abunda ya dad'e yana ci mishi zuciya, bai k'ara son Afnan ba sai lokacin da Yaseer yake mishi bore kan cewa shi yake sonta. Tabbas Allah ne yakawo Afnan cikin rayuwarshi don ya kaunace ta, Allah ne ya kawo Afnan cikin rayuwarshi don ya nunawa Yaseer da Mamie cewa ba ko yaushe mutum ke samun abunda yake so ba.


 Afnan ce abu ta farko da sukayi tarayyar sonta da Yaseer ya mallaketa ba tare da Yaseer ya mallaketa ba, basu tab'a tarayya son wani abu ba shida Yaseer face Yaseer ya mallakeshi, duk abunda yake so Yaseer shi ke mallakarshi ciki kuwa har uban da ya haifeshi.


Haka dai Dukansu suka kwanta kowa da abunda ke cikin zuciyar shi.


Bangaren Yaseer kuwa, soyayya ta maidashi wani iri, sai yanzu yake regrating abunda yayiwa Afnan, bai San yana sonta ba sai yanzu da Yazeed ya aureta, tabbas da wani ya aureta da zai iya hank'ura amma bazai tab'a lumuntar ganinta da Yazeed ba, yanda yakejin tsanar Yazeed tamkar ya kasheshi.

Ko yaushe yana so ya gaya mishi cewa shi Afnan ta baiwa jikinta, amma bakinshi sam sai yayi mishi nauyi yakasa fad'a sai dai ya rik'a jifanshi da miyagun kalamai. Inda hankalinshi ya kwanta jin maganin da Mamien shi ta karb'o gurin bokanta. Da wannan ya dauke d'amarar shiga ciki ya tarwatsa auren Yazeed da Afnan.


Yazeed ko Yaseer 

       Na

Ayshart Farouq


Nagarta writers association,


       63-64


Sannu sannu soyayya da shak'uwa mai tsanani suka shiga tsakanin Yazeed da Afnan, duk da basa yawan had'uwa amma ko yaushe suna mak'ale a waya.


Ciki haka aka sanya ranar tarewar su sati biyu kasancewar daddynshi ya dawo har an kammala gyaran part d'in da Afnan zata zauna, Yazeed yaso a bari ya tare a gidanshi tunda ya riga ya kammala sashen Afnan, amma daddy yace Sam sai lokacin da zai aure Nabeela sai su tare baki d'aya.

 Har ga Allah yasan Yana yawan tauyewa Yazeed incinshi har dai kan lamarin Yaseer da Nabeela, abun na matuk'ar damunshi sai dai ba yanda zaiyi bazai iya ja da maganar Mamie ba duk yanda take so haka yakeyi duk da wani lokaci abun na ci mishi tuwo a k'warya.


Bangaren Mamie ko wata Yayarta tak'ara bata k'arfin guiwar Amfani da maganin da aka bata, a kan haka ta sanya Nabeela dawowa daga egyp dama tana gurin wata yayarta, bata san abunda ake shukawa ba. Ranar da Mamie ta fad'a mata maganar auren Yazeed da Afnan sai da ta suma, daga baya tayita yi mata kuka kan bazata yarda ta zauna da kishiya ba, don yanda take son Yazeed tamkar ta fad'awa Allah. Mamie ta mata alkawarin bazata tab'a zama da Afnan matsayin kiahiya ba har abada. Kan haka tasanya daddy yasa aurensu nan da shekara d'aya tasan kafin nan ta raba auren Yazeed da Afnan.


Afnan na zaune falo domin karb'a kiran Abbanta.


Zaune suke dukansu Abba, mommy, Ibrahim da sagir. kasancewar ranar ta zamo ta weekend.


Abba ya kalle Afnan ya soma magana,

"Hak'ik'a da na kasance mutum mai tsananin son kanshi, Wanda hakan ne yajawo min na tafka babban kuskuren da ya tashi jefani cikn wata makunyaciya Rayuwa" Ya d'an ja iska sannan yaci gaba, " ba komai yasa nake irin wannan magana ba, face duba da irin rayuwar da na tashi jefa Afnan a cikin ta, da ba don Allah ya kawo muna wad'annan mutane masu tsananin Adalci da Halacci ba da bamusan yanda rayuwa zata kasance ba nan gaba, da ba musan wane irin hannu Afnan zata fad'a ba, amma da Allah yake karimun Rahimun ne sai ya sanya lamarin yazo cikin sauk'i. 

Wannan magana ina yinta ne ba don komai ba sai don jan kunne da gargad'i gareki da ki bi mijinki sau da k'afa, saboda Yazeed ya gama yi miki komai a rayuwa. Ki sani idan naji ko nagani kin mishi wani Abu Wanda bai dace ba sai nayi tsananin sab'a miki fiye da yanda bakya zato.

Na zab'i in miki wannan maganar ne yau don nasan daga gobe gidan zai fara kachamewa da hayaniyar 'yan uwan da zasuzo daga nesa. Ban yarda ki kawomin k'arar mijinki ba, ban yarda da kiyi fishi kiyi yaji kizo gida ba koda kuwa ke kikeda gaskiya. idan d'aya daga cikin wannan ta faru, ni kaina ban San irin hukuncin da zan yanke miki ba.


Afnan kam tuni hawaye sun gama wanke mata fuska, 

Haka Abbanta yayita mata fad'a da Nasifa masu matuk'ar shiga jiki.


 Tana kuka tana magana, "Abba naji duk abunda kace kuma insha Allah zaka sameni mai yima biyayya, insha Allahu Abba bazan sake bijirewa magnarka ba, Abba na bijirema sau d'aya banji da dad'i ba, Abba Allah ya nuna min kuskurena tun a nan duniya, Naga sakayyar kin bin maganar iyaye, Abba naga sakayya." Ta fashe da kuka mai tsanani tunawa da irin yaudarar da Yaseer ya mata.


Janta Abba yayi jikinshi yana lallashinta tare da kalamia masu kwantar da hankali, haka suma su Ibrahim lallashinta suke har ta saki jiki akaci gaba da tsara shagalin biki.


Bayan sun kammala ta koma d'akinta. Wayarta da ta bari kan gado ta d'auka. miscall biyar ta tarar na Yazeed, murmushi tayi tare da zaunawa bakin gadon tana kiran wayar tashi.


Ringing d'aya a ka dauka,


"Habibty ina kika shiga ne kinka tada min da hankali?"


"Calm down yazafna, ba Wanda zai sacema ka amarya"


Murmushi yayi har saida taji sautin shi a waya,


"Uhm, ni bazan gane ba, ganinan ma nakusa karasowa gidan,"


Zaro idanuwa tayi, "kai ya Yazeed, kasan fah alk'awarin da kayi,"


"Bazan iya cikawa ba Afnan, baki ji yanda hankalina ya tashi ba da na miki two miss call baki d'auka ba, gashi naji ance an sace wata amarya ana saura sati biyu biki, naji kawai k'ara inzo inga lafiyar amaryata"


Rufe fuska tayi kamar yana ganinta,


"Yanzu ai kaji ba'a saceta ba, lafiyanta k'alau sai ka koma inda ka fito,"


"Wasa kike, kinga ni nama k'araso ki fito kawai ki sameni falon bak'i naganki, ba dad'ewa zanyi ba" yana kai nan ya katse wayar.


Biyar wayar tayi da kallo tana jinjina lamari irin na Yazeed, idan bata manta ba yau kusan satinshi uku bata sanyashi a ido ba, wai yayi alk'awarin bazai sake ganinta ba sai randa za'a kai mishi ita.

Da ta tambaye dalili sai ce mata yayi gudun yake yayi b'arna gidan mutane. Tasha kunya da ta gane abunda yake nufi.

Murmushi tayi tare da d'aukan hijab d'inta har k'asa ta saka sannan ta fita.


Da sallama ta isa gurinshi, yana zaune kan d'aya daga cikin kujerun da aka k'awata falon dasu, fuskar nan tashi cike da Annuri, ga kamshinshi da ya game falon duka.


Shi kuwa gogan zuba mata idanuwa kawai yayi don ba k'aramin kyau ta k'ara ba, fatarta ta k'ara haske da shek'i sanadiyar gyaran da ake mata, ga wani uban kamshin da take fitarwa mai matuk'ar dad'i da sanyaya zuciya.


K'afafauwanta har sassarfa suke, saboda yanda Yazeed ke kallonta, ganinan haka nan ya sanya, ta samu wuri nesa dashi ta zauna tana murmushi tare da gaidashi.


"Bazan karb'a gaisuwarki ba, shine kika koma cen kika zauna don kar in d'an more wannan k'amshin"


Turo baki tayi "toh ai Kaine"


"Da nayi me?" Ya tambaya yana kwai kwayon maganarta,


Sunkuyarda kai tayi k'asa tana murmushi.


"Gaskiya ni bazan yarda ba, ki dawo nan kawai idan kina so a zauna lfy" ya fad'a yana nuna mata cinyarshi.


Rufe fuska tayi da tafin hannuwanta tana mak'e kafad'a alamar bazata je ba.


"Toh bari kiga ni inzo in rage miki wannan kunyar"


Batayi aune ba taji ya dauketa baki d'aya yana lilo da ita,


Dariya takeyi, "saukeni Dan Allah zan zauna, ta fad'a kamar zata shid'e saboda dariya.


Ajiyeta yayi tare da janyota jikinshi, ya dorata kan cinyarshi,yana maida nunfashi.


''Wai kinjiki, ashe dai nauyi ke gareki,"


B'ata fuska tayi, "Allah banida nauyi,"


"Ba wani nan" ya fad'a yana k'ok'arin d'aga mata hijabi,


"Wannan hijab haka sai kace, wadda zataje wurin wa'azi"


"Uuhm ai gurin waazi zani" ta fad'a tana mai son hanashi d'aga hijabin,


"Aw hakane fah, na manta nine alaramman, yanzu kuwa zaki fara d'aukan wa'azi,"


Bakinshi yasa cikin nata, ya shiga tsutsa tamkar Wanda ya samu sweet, nan take jikin Afnan ya mutu, tuni ya sauke hijabin jikinta ya shiga yamutsata son ranshi.


Ganin wa'azin nashi na Neman yafi k'arfinta tunaninta ya sanya, ta janye jikinta dakyar tana maida nunfashi, 


Kallonta yayi da idanuwanshi da suke fara chanja kala, da sauri ta kauda kanta don bazata iya kallon kwayar idanunshi ba.


Jawota yayi ya rungumeta, tamkar zai maidata ciki,


"Control ur self Yazeed"


Ta fad'a tana k'ok'arin zame jikinta,


"Stay still pls" ya fad'a cikin taushin murya,


Sun dad'e hakanan sannan ya saketa tare da kama hannunta yana murza yatsunta,


"Kinada fah babban aiki dani, shi yasa na da'uke k'afa coz nasan idan ina ganinki bazan iya controlling kaina ba, ni kuma gashi bana so in aikata komai a gidan surukai na"


Ya fad'a yana kashe mata ido,


Tamkar ta notse k'asa don kunya,


"Kinga bari in tashi inje, kar a tafka abun kunya a gidan sirikai"

Ya fad'a yana mik'wa.


Tare suka fita sark'e da hannuwa, saboda yak'i sakinta, saida sukaje har bakin motarshi, cen ma saida ya d'an rage zafi sannan ya wuce.


Yazeed ko Yaseer

       Na

 Ayshart Farouq


Nagarta writers Association


       65-66

  Biki ya kan kama, anyi shagulgulla masu k'ayatarwa. 


kasancewar yau juma'a ranar ake mothers night wanda Ammie ta shirya. 


Amarya ta had'u iyakar had'uwa, wani danqareren less ta sanya milk mai ratsen light blue, aka d'aura mata head d'inta light blue. Idan ka kalleta dole ne sai ka sake kallawa saboda irin had'uwar da tayi.


Shima ango irin shigarta yayi.ya sanya shadda light blue dinkin babbar riga.

 Sunyi kyau sosai har sungaji.


Suna zaune bayan mota, yayin da wani aminin ango ke gaba yana tuk'i.


Hannunta Yazeed ya kama da yasha kunshi, ya sumbata.


"Amaryata kinyi kyau sosai har sai naji kamar kar muje mothers night d'innan"


Murmushi tayi,


"Akan me zamu fasa zuwa bancin donmu aka shirya"


"Ina kishin wasu maza su gane min wannan kwalliyar taki, nafi so ingani ni kad'ai, kin San fah inada kishi sosai musanma ma kanki,"


Hancinshi ta ja, "am ol yours, so karka kawo komai a ranka dai rana tsawo,"


Yaji dad'in kalamanta sosai, shima ja mata hanci yayi yana mak'e kafad'a 

"Uhmuhm ni dai ba zan yarda ba"


Dariya tayi saida fararen hakoranta suka bayyan

Kafin tayi magana taji mota ta tsaya alamar sun iso.


Ba karamin haduwa gurin yayi ba. Wasu kananan yara ne da suka sha gyara suka zo suka take musu baya.


Su na shiga wuri ya d'auki sowa.


Bayan an d'an tsagaita aka fara k'addamar da programs. 


Nan aka buk'ace ango da amaratya su fito suyi rawa.

 Ai kuwa sunsha b'arin nera gurin yan uwa da abokan arziki, ranar idan kaga ammie bazakace ta haifi kamar yazeed ba.


Zuwan su Mamie ne tada hankalin Afanan don kallo d'aya tama matar tagane ko waye saboda tsantsar kamarsu da Yaseer.


Mamie ta neme amarya da ango su sake fitowa nan ta bare bakin jaka tanata ruwan kudd'i mawak'a sai k'ara wasata suke yi, ga uwar ango. can Yaseer da Nabeela suma suka fito mutane suka dau kuwa ga kannen ango, Yaseer kam Afnan yashiga yiwa lik'i tamkar ba gobe, abunda yayi matuk'ar k'ona zuciyar Yazeed, yayin da itama Nabeela tashiga lik'awa Yazeed d'in. Amma hankalinshi Sam baya kanta idanuwanshi sun rufe da tsananin kishin Yaseer d'in, ita kanta Afnan ba k'aramin tashin hankali tashiga ba, don ganinshi a yau ba k'aramin haifar mata da wasu abubuwa yayi ba, bama kaman yanda taga yana nema ya shige mata cikin jika, wani kallo yake mata mai tattare da wasu manufofi da shi kad'ai yasansu. Wani mayaudarin murmushi ne d'auke a bakinshi lokacin da ya d'an rankwab'a gurin kunnenta ya na mata magana.


"Kar ki d'auka na hak'ura da ke ganin na wofantar da lamurranki tsawon wani lokaci,

 ki sani ina nan tare da ke ina ganin duk wani moving naki. 

Kuma ki rik'e wannan a ranki wallahil azim ba d'an da ya isa ya mallakeki face ni, saboda ni kike so kuma nine zab'inki, don haka the game is just the beginning. Nabarki lafiya sai mun had'u a gida gobe" ya fad'a tare da sakar mata wani shu'umammen murmushin da shi kad'ai yasan ko na miye. Amma k'asan zuciyarshi zafi yakeji da rad'ad'in wannan ranar, bama kamar da yaji ana cewa ma'auratan sun bal'in dacewa da juna.


Afnan kam hankalinta yayi kololuwar tashi, bama kaman da ta daga idanuwanta ta kalle Yazeed da yake kallonsu.


Kallo d'aya zaka mishi ka ganne yana tattare da masanancin b'acin rai, idanuwan nan nashi har sun kankance saboda tsananin kishin da ke addabar zuciyarshi.


 Damar abun gurin ya cika da yan lik'i so ba kowa ya lura da abunda mutanen uku suke ciki ba.


 Hanyar fita daga gurin take nema saboda yanda taji tsayuwar na Neman ta gagareta. 

Wucewar da zatayi cikin rashin sa'a takalmenta ya malgwad'e tatafi tagal tagal zata fad'i Yaseer da ke ta kwasan shoki a zahiri amma a bad'ini zuciyarshi na gurin Afnan d'in, yayi wani yunkuri don ya tareta cikin zafin nama Yazeed ya bangajeshi tare da yin saurin tallafota ta fad'a saman kafad'arshi.


Haka ya rrungumota ya fito da ita, maimakon ya kaita gurin zamansu, kawai sai ya fita da ita hall d'in baki d'aya.


Bai ce mata komai ba sai zuciyarshi da keta halbawa, ita kanta tanajin yanda zuciyarshi ke bugawa saboda yanda take lafe kan kafad'arshi.


Gurin ajiye motoci ya nufa ya bud'e motarshi ya turata ciki, shima ya zagaya ya shiga ya tada.


 ganin yanda yake sharara gudu gashi ko kallonta yak'i yayi ya sanyata fashewa da kuka mai tsuma zuciya.


A hankali ya sauka kan titi yayi parking.


Hannuwanashi yasa duka biyu ya dafe kanshi, saboda yanda yake jin kukanta har cikin b'argonshi.


A hankali ya d'ago ya sauke kwayar idanuwanshi kanta, "me yasa kika bari aka daura muna aure bancin kinada Wanda kike so?"


Tamabayar tazo mata ba zata shiyasa tayi saurin d'ago kanta ta kalleshi.


"Ki gaya min gaskiyar abunda ke tsakaninki da Yaseer, shin Dama kinyi soyayya dashi lokacin da kina gidan Ammie ko ya?"


Girgiza mishi kai take, har lokacin hawayenta sai k'ara tsananta sukeyi saboda yanda takejin zuciyarta, tatabbatar da ko ana dab'a mata wuk'a a halin yanzu da takejin soyayyar Yazeed bazata iya cewa wani Abu ya tab'a shiga tsakaninta da Yaseer ba, ada kam ta zab'i Yazeed ne don ta huce haushin abunda Yaseer ya mata amma a yanzu tanajin soyayyar Yazeed fiye da yanda take jin soyayyar Yaseer a baya.


 A hankali ta furta,

"Ba komai tsakanina da Yaseer hasalima inajin tsanarshi fiye da yanda kakeji a halin yanzu"


Wata wawuyar aziyar zuciya ya sauke, "me yasa kika tsaneshi"


Saida ta d'an yi jim kad'an tunawa da kalaman Ammie da tayi kada ki bari Yazeed yasan Yaseer ya miki fyad'e saboda idan kika fad'a mishi da kanki ba k'aramar illa hakan zata yi mishi ba, hasalima bazai tab'a yarda da ke ba, saboda yaseer din zai karyata hakan. ki bari yaji a bakin Yaseer din lokacin da duk gaskiya zata yi halinta.

 Tunawa da wannan yasa tace,

"Saboda naga shine mutum na farko da yake son ya rushe mana farin cikinmu"


Hular kanshi ya iyar da cirewa tare da d'an kwantar da sit d'in motar.


"Me yake fad'a miki ne a kunne hala?"

Ya fad'a cikin nuna jin zafin abun.


"Taya zata fad'a mishi abunda ya ce" ta fad'a a zuciyarya,


Amma a fili sai tace, "yana tayani murnar aure ne"


"Uhum" ya fad'a tare da lumshe ido don Sam bai yarda ba amma zai barta yasan ba laifinta ba ne.


"Sai yaushe Yaseer zai barni ne? Sai yaushe Yaseer zai barni na rayu da abunda na ke so?" Ya fad'a tare da furzar da iska.


"Nasan halin Yaseer nasan ko waye shi tabbas baxai Kyaleni na huta ba, nasan zai iya komai Dan ya rabani da ke"


Mik'ewa yayi idanuwanshi sun kad'a sunyi jajur,


"Wannan karon bazai ci galaba kaina ba I will fight for my love"


Hannuwan Afnan ya kama"promise me u will never leave me no mater how the situation is"


"I promise u Yazeed bazan tab'a rabuwa da kaiba har abada"


Rungumeta yayi yana cewa, "nagode Afnan namiki alk'awarin kare mutuncinki har abada"


Sun dad'e a haka kafin yaja motar su wuce. Saida yakaita gida sannan ya wuce gidan Ammie saboda yanda yake jin zuciyarshi idan yaga Yaseer zai iya illatashi.


Asabar akayi waleema, da maraice aka kai amarya d'akin mijinta. Part dinta yasha gyara sosai d'akunanta ma an zuba mata kaya naji da fad'a, abun sai Wanda ya gani.


Bayan 'yan kai Amarya sun watse akabarta ita kad'ai.


 yanayin da takeji ba zata iya misiltashi ba saboda yanda takejin fad'uwar gaba mai tsanani, ga wani irin tsoro da ya risketa lokaci d'aya.


Aysahrt one

Yazeed ko Yaseer 

       Na

Ayshart Farouq


Nagarta writers association 


THIRD TO THE LAST PAGE


        67-68


  Tana nan zaune cikin wannan yanayin taji an turo k'ofa anshigo had'e da yin sallama.


Yanda taji sautin muryarshi ne ya sake jefa zuciyarta cikin rud'ani,

Dafe kirjinta tayi dake mata barazanar fitowa, jikinta har wani cira yakeyi, wani irin tsoro take jin ya dabaibayeta.


A hankali Yazeed ya karaso d'akin fuskarshi cike da annuri.


Gefen gadon ya zauna kusa da ita yana mai zuba mata idanuwa.


Hannunshi ya saka ya tallabo fuskarta, ga mamakinshi sai yaga idanuwanta rufe gam, ga hawayen da ke fitowa tamkar saukar ruwan sama.


"Ya rabb" ya furta tare da sanya manyan yatsunshi guda biyu yana shafe mata hawayen.


"Ya isa haka Afnan, yau ba ranar kuka ba ce, yau ranar farin ciki ce, bai dace kina barnata hawayenki ba"


Maganar tashi maimakon ta kwantar mata da hankali sai ta sake d'aga mata hankali don wannan karon jikinta har kyarma yakeyi.


Idanuwa yazeed ya zuba mata ganin yanda jikinta keyi, ajiyar zuciya yayi cikin sanyin murya yace, 


"Wannan rawar jikin kuma fah na miye?, Afnan ke fa ba yarinya ce ba, ya kamata ki nutsu ki kwantar da hankalinki sanin kanki ne ni bazan tab'a cutar dake ba, nasan abunda kike jiwa tsoro, kadama ki kawo wannan a rayuwarki ni a wurina na dade da binne wannan shafin, nasan kaddara ce abunda ya faru dake, don haka ki kwantar da hankalinki, ni ke nake so ba jikinki ba, Dan haka idanma tunanin kike yanda zan sameki ki ajiye wannan a gefe nasan yanda kike na aureki. Yanzu ki tashi kije ki watsa riwa ki doro alwala muyi sallah Dan mu nuna godiyarmu ga Allah, nima zanje d'aki nayi wankan nayi alwala."


Yana kai nan ya mike ya fita, yana fita Afnan ta maida wata wawuyar ajiyar zuciya, magangannun da yayi suka shiga dawo mata, tausayinshi taji ya kamata, wato shi duk daukarshi tsoro take ji ya sameta ba budurwa ba, baisan ita Sam ba wannan ne a gabanta ba, duk da cewa wannan d'in ma ta dad'e tana tunanishi a ranta kuma har tashigo gidanshi tanajin ba dad'i a rayuwarta na kasancewarta wadda batada budurci, sai dai, lokaci d'aya wani bak'on al'amari wanda bata tab'a kawoshi a zuciyarta ba a cikin rana irin ta yau, sai gashi lokaci d'aya ya zarce wannan abunda takeji.

Don a halin da take ciki ji takeyi idan Yazeed ya kusanceta zata iya rasa rayuwarta tsabar tsoron abun da takeji.


Da sauri taje tayi wanka, tana kammalawa ta dawo ta sakawa kofar key, tabar makulin a jikin kofar don kar yayi amfani da na hannunshi ya shigo.


Yazeed na kammala abunda yakeyi ya fito ya nufe dakin Afnan, yana turawa yaji kofa a rufe, bai kawo komai a ranashi ba ya buga kofar. sai dai ya buga yafi a kirga amma ba alamar zaa bud'e.

 Nan take hankalinshi yafara tashi, yashiga kiran sunanta, kasancewar yafara jin shashekar kukanta, tun yana magiya yana had'ata da Allah har ya fara fad'a ganin batada niyar bud'ewa ya sanya yaje ya dauko key dinshi. Yana sawa yaji da wani a jikin kofar.


"Ya ilahi" ya furta tare da dafe kanshi saboda yanda yake jiyo shasshekan kukanta.


Ganin Yazeed din yaki barin jikin kofar ya Sanya Afnan ta tura mishi text,

"Kayi hakuri yaya yazeed, nasan zakayita sak'e sak'e a ranka, amma kasani cewa har a gurin Allah ban so wannan rana ta kasance haka a garemu ba, nasan na cutar da kai sai dai kasani ina jin tsanar kaina fiye da yanda kake tsammani, kayi hakuri ya Yazeed kaje ka kwanta Dan Allah, wallahi bazan iya bude wannan kofar ba."


Yazeed na gama karantawa har wani jiri yaji yana dibarshi sai da ya samu daya daga cikin kujerun falon ya zauna, don ji yake komai zai iya faruwa dashi a halin da yake ciki, saboda wata irin matsananciyar sha'awa da yaji ta taso mishi. shi Sam text din da Afnan din ta mishi bai San inda ya dosa ba, ya karanta yafi a kirga amma Sam ya kasa gane abunda take nufi.


Yafi hour biyu zaune cikin wani mawuyacin hali don ji yake idan bai kusance macce ba komai zai iya faruwa saboda yanda mararshi ke ciyo, bai tab'a aikata zina ba, hasalima ya tsane duk wani mai aikatata, amma yau kam ji yake komai zai iya faruwa.


Dakinshi ya koma tare da daukan key din motarshi, har ya kai bakin kofar fita wata zuciya ya gargad'e shi da yaji tsoron Allah kar ya aikata abunda yake son aikatawa komai yayi zafi maganinshi Allah, nan take yaji ba zai iya aikatawa ba, komawa yayi dakinashi ya sake doro alwala yazo ya kabbarta sallah, bayan ya kammala ya dauko qur'ani yana karantawa, nan take yaji duk wani abunda yakeji ya kau.

 Haka ya kasance har kusan assuba sannan bacci ya daukeshi.


Afnan kam kasa bacci tayi kuka kawai take har garin Allah ya waye, sai da tayi asuba sannan ta samu ta kwanta.


Misalin karfe goma ta tashi tayi wanka ta shirya cikin wasu Riga da zane na atamfa, ta dauko gyalen da ke shiga da atamfar ta yafa, simple make up tayi, sai dai kallo daya zaka mata ka gane tana cikin damuwa, ga idanuwanta har yanzu basu sacce ba daga kumburin da sukayi sakamakon kukan da tasha jiya.


A hankali ta bud'e kofar tamkar munafuka, zaune ta hangoshi ya hard'e cikin wasu riga da wando na wani milk din yadi bai tsantsi, kayan sun bala'in amsarshi sai kamshi yake zubawa, tafi minti uku tsaye ta kasa k'arasawa.


Dago kanshi yayi ya sauke idanuwanshi kan kyakkyawar fuskarta, murmushi ya sakar mata tamkar ba wani abu tsakaninsu.


Nan take Afnan taji jikinta yayi sanyi,


Ganin yanda tayi tsaye ta kasa matsawa ya sanya ya mik'e ya isa gurinta hannuwanta ya kamo yana murza 'yan yatsunta, 

"Gud morning my princess"


Zame hannunta tayi ta d'an rusuna "ina kwana Ya Yazeed,"


Murmushi ya sakar mata "an tashi lafiya"


Gyada mishi kai kawai tayi ta sunne kanta k'asa,

 

Sake kama hannunta yayi ya tasar da ita, ya jata ya kaita har kan dining da kanshi ya had'a mata breakfast d'in da Mami ta aiko musu. kad'an tasha ruwan tea din da farfesun kayan ciki. 

tana ci tana satar kallonshi, cikin ranta tana mamakin halayya irin ta Yazeed, a ce duk abunda ta mishi baiyi fushi da ita ba,


Ganin yanda tayi nisa cikin tunani ya sanya ya ajiye spoon din hannunshi yana kallonta, "hey tunanin me kike haka kin kasa cin abinci sai satar kallona kike, ki daina kallona kici abinci am all yours" 

Ya fad'a yana kashe mata idanuwa,


Wata irin kunya taji ta kamata tamkar ta nutse cikin k'asa, idanuwanta tuni sun cika da kwalla, cikin karfin hali tayi murmushi "ni na koshi"


"Kina so in miki dure kenan?"


Girgiza kanta tayi alamar a'a,


"Toh kici abincinki idan bakya so".


Haka tayita d'ura abincin ba don tanada appetite ba.


Bayan sun kammala ta kwashe kayan takai kitchen, sai da ta tabbatar da ta tsabtace su sannan ta dawo,


Mikewa Yazeed yayi tare da cewa " tashi muje mu gaida mami sai mu dawo ki min fira"


Murmushi tayi, ita dai duk jinta take wata iri, kunyar Yazeed takeji har bata so ta had'a ido dashi, tsoron da takeji jiyama ga mamakinta yanzu duk ya tafi sai dai faduwar gaba, idan yazeed ya tab'ata, yanzu ma hakane ta faru sakamakon kama hannuta da yayi suka fita, tayi tayi ta zame hannun ta kasa dole ta hak'ura ta barshi.


Suna cikin tafiya sun kusa kai part din Mamie sukaci karo da Yaseer, kallo d'aya ya musu ya kauce idanuwanshi sakamakon zuciyarshi da take wani irin tiriri, kasa tafiya yayi yayi tsaye kamar Wanda aka shuka,


Yazeed na ganin hakanan ya k'ara kamo Afnan ya mannata da jikinshi ya sanya hannunahi daya ya riko k'ugunta, wani irin murmushi mai k'ayatarwa ya sakarma Yaseer tare da cewa "morning bros, har za'a fita aikin ne"


Tsaki Yaseer Yayi, yaji Sam ba zai iya kyale Yazeed bai soka mishi magana ba, ya danyi murmushi ya ce,

 

"Ango ansha mai" ya d'an rufe bakinshi "koda namanta ba wani mai da ango yasha sai wahala kasancewar garar ba complete take ba"


Maganar tashi ta soke Afnan ba kad'an ba, sai dai jin yanda Yazeed ya kara matseta jikinshi alamar kar ta damu yasa ta d'an ji sauki.


"Idan dai haka irin wannan incomplete gara take toh nikam sai godiyar Allah Dan tamin Dari bisa Dari, coz kasancewar ta haka naga anbar complete din ana wawusu kan incomplete din, any ways tanks god tunda na zama champion"


Yana kai nan ya sake sakar mishi murmushi yaja matarshi suka wuce abinsu.


Yazeed ko Yaseer 

       Na

Ayshart Farouq


Nagarta writers association 

 


SECOND TO THE LAST PAGE


       69


Sashen Mamie suka nufa, da sallama suka shiga falon, Nabeela ce kadai zaune tana kallo, sanye take da wata arniyar rigar bacci kusan duk surar jikinta ana gani, kuma haka ta fito falo ta zaun tana kallo ko a jikinta.

kallo daya Yazeed ya mata ya kauce idanuwanshi, wannan d'abi'a ta Nabeela tana cikin abunda Yazeed ya tsana don Sam batada kamun kai ko kad'an. Afnan kam kallonta takeyi tana mamakin ace karfe kusan goma shadai mutum na sanye da kayan bacci, kuma kayan ma ba kayan albarka ba.


Nabeela kuwa tunda ta karb'a musu sallama ta fara yatsinar fuska tamkar wadda taga kashi.


"Mamie fah?" Yazeed ya tambayeta yana d'an dubanta,


"Tana ciki" ta fad'a tare da mikewa. da alama kiranta zatayi, tana tafiya tana wani jujjuya jiki, abunma sai yaso yaba Afnan dariya don dam nabeela batada k'irar kwarai, irin jikin mahaifiyarta ke gareta Abu kamar an ajiye baho.


Dan murmushi tayi lokacin da suka had'a idanuwa da Yazeed Wanda ya tafi duniyar tunanin yanda zai Aure wannan yarinya a haka.

Shima murmushi ya sakar mata tare da kara matse mata Hannu.


Suna cikin haka Mamie ta shigo da fari'arta irin ta 'yan duniya,


Har kasa Afnan ta duk'a ta gaidata,

 

Tana murmushi tace "amarya ya bakunci?"


Murmushi Afnan tayi kanta na k'asa ta Amsa da "Alhamdulillah"


Mamie taci gaba da magana tana ma Afnan wani sh'umin kallo, " pls Dan Allah amarya a kula mun da d'ana kin San sabon shiga ne bai saba ba, A lallab'a kar a zure, har a kai ga shanye mai ruwan kai"


Afnan tune ta gano inda maganar Mamie ta dosa, wani irin Abu ta rik'a ji yana taso mata har ya toshe mata zuciya, nunfashinta taji ya fara yin sama alamar ranta yayi kololuwar b'aci.


Batare da Mamie ta lura da yanayin Afnan din ba taci gaba da magana, "kinga ke kin riga kin San abunda an nan don haka Dan Allah a kula a Dan rik'a daga mishi k'afa don ya samu damar sauke wani nauyi dake bisa kanshi".


Yazeed na lura da Yanayin Afnan d'in yayi saurin mik'ewa ya isa gabanta hannunshi ya mik'a mata batare da b'ata lokaci ba itama ta mik'a mishi nata ya tayar da ita tare da yima Mamie sallama.


Mamie na ganin haka tashiga surfa mishi zagi ta uwa ta uba, wai ya mata rashin kunya, bai kulata ba yaja matarshi da zuwa lokacin har ta fara kuka. 


Ganin yanda take kuka ne ya sanya ya jata zuwa jikinshi, tsam ya rungumeta yana shafa bayanta alamar lallashi.


Duk abunda ke Faruwa Yaseer na nan yana kallonsu bakin ciki tamakar ya kasheshi, tun da ya had'u dasu dazu rik'e da hannun juna yake jin wani kishi na taso mishi don ganin yake tamkar komai ya faru a Daren jiya, nema kawai yake ya ganshi gurin Mamie don jin mafita sai gashi yanzu yagansu rungume da juna abunda ya kara tayar mishi da hankali fiye da tunanin mai tunani.


Saida Yazeed yaga ta nutsu sannan ya kara sukayi gurin dadyn shi, daddy yayita sanya musu albarka da fatar samun zuri'a dayyaba sunfi minti talatin gurin daddy sannan suka wuce parta dinsu.


Yaseer kuwa yana ganin su Yazeed sun doshe bangaren Daddy yayi saurin zuwa gurin Mamie tamkar Wanda aka koro, cikin tashin hankali ya isa falon Mamie yana zuwa ya taradda Nabeela na kuka Mamie na lallashinta, ya tabbatar da ba komai ya sakata kukan ba sai ganin Yazeed da Afnan.


Zama yayi tare da dafe kanshi duk abun duniya ya mishi yawa ga kukan Nabeela da yakeji har cikin zuciyarshi, wata irin tsanar Yazeed yakeji tamkar ya kasheshi, tabbas Yazeed ya mishi tambon da har abada bazai warke ba ya sashi cikin bala'i shida kanwarshi da mahaifiyarshi. Ya tabbatar da Nabeela na mahaukacin son Yazeed duk da cewa Mamie ba hakanan taso ba taso kawai ta aureshi ne don ta haihu dashi daga baya su salwantar da rayuwarshi.


Mamie ce ta katse mishi tunani tana cewa "son me yafaru dakai kar dai kaima wannan Karamin Dan rainin wayon ne ya tayarma da hankali?"


Wani kallo ya watsawa mahaifiyar tashi yana huci, "Mamie kinga su kuwa?"


Tsaki taja "toh meye a ciki ban cin Dan lokaci kalilan ke garesu"


"Anya kuwa Mamie wannan Yaron bai kusanceta ba kuwa" ya fad'a cikin tsananin damuwa.


Wani murmushi Mamie ta saki "ai idan har uwarshi zata barinshi saduwa da ita toh Afnan zata bari ya sadu da ita, don haka wannan magana ma ka barta kawai Yazeed ba zaitaba iya saduwa da Afnan ba, don ina tabbatama jiya duk abunda ya faru na sani. Nan Mamie ta kwashe labarin laben da tayi har zuwa lokacin da taga Yazeed ya dauko key zai fita kuma ya fasa.


Wani sanyi Yaseer yaji. Ko ba komai hankalinshi ya kwanta da wannan don ya tabbatar da cewa duk Yazeed ya sadu da Afnan bazai iya tab'a rabuwa da ita ba har abada, shi yasa yake tausayawa Nabeela saboda yasan muddun Yazeed ya lashe zumar Afnan toh yasan itada bola duk daya, saboda zata zama bora a gidan shi. saboda Afanan na dai daga cikin matan da samunsu sai an tona. Allah ya mata wata baiwa ta daban wadda ba kowa zai gane ba sai Wanda ya mallaketa. tun lokacin da ya sadu da Afnan bai sake jin abunda yaji gareta ga ko wace macce ba, ya tabbatar da idan ya mallaketa ba karamin morewa zaiyi ba.


Wani murmushin samun nasara yayi, tare da kallon Nabeela da duk idanuwanta suka kumbura kan kukan da tayi.


"Ku tabbatar da Wayar Afnan tashigo hannunku nan bada dadewa ba, ta ciki zan shiga in ruguza wannan auren" Yaseer ya fad'a yana mai furazarda wani iska mai d'aci,


Kallonshi Mamie tayi me "wayarta zata maka?"


Kallon Nabeela ya sake yi "ki tabbatar da kin kawo min wayar Afanan"


Nan ya kwashe duk wani Abu da zaiyi da wayar ya gaya musu.


Nan take sukaji duk matsalarsu ta yaye ba kamar Mamie da har yar rawa ta taka tana sanyawa danta albarka don ganin take komai yazo karshe.


Bangaren su Yazeed kuwa, tun lokacin da suka bar gurin daddy ya fara jin mood dinshi ya canza ba kamar Yanzu da suke zaune gab da juna, Dan janyota yayi cikin dabara ya fara shafar jikinta yana fad'a mata kalamai masu nutsar da zuciya cikin kogon soyayya,


A hankali taji yafara wuce gona da iri, nan take irin makamcin abunda taji daren jiya ya sake taso mata, jikinta ya fara rawa, cikin tashin hankali ta kwace jikinta ta fad'a daki da gudu tana kuka.


Da mugun mamaki Yazeed ya bita da kallo, baiyi yunkurin bin bayanta ba, zaune kawai yayi yana anbaton sunan Allah,


Saida yafara jin nutsuwa ta safkar mishi sannan ya tashi ya dauke makullinshi yayi gidan Ammie,


Ya dade sosai gidan Ammie sannan ya dawo gida, zuwa lokacin har ya dawo normal.


Ganin har karfe hud'u ba alamar Afnan ta fito taci Abinci ya sanya shi yaje ya buga mata kofa, tana jinshi sai takara takurewa kan gado, saida yayita had'ata da Allah tare da alkawarin ko hannunta bazai tab'a ba yasanya ta fito.


Tana fitowa ko kallonta baiyi ba ya isa dining ya zuba mata abinci, kasa cin abincin tayi sai sharb'ar kuka takeyi, harga Allah tasan bata kyautama mijinta ba, sai dai Ba yanda ta iya da lalurar da ta sameta.


Ganin taki cin abincin ne yasa ya shiga lallashinta dakyar ta samu taci kad'an.


Yazeed naganin yanayinshi yafara chanjawa, yasa yabar

 mata falon yayi dakinshi.


Ganin haka yasa itama ta koma d'aki jiki ba kwari,


A haka har sukayi sati d'aya kuma kullun zasuje gaida Mamie a tare da safe, amma da sun dawo kowa zai kama gabanshi.


 Afnan na kokarin ganin ta sauke duk wani hakki na Yazeed da ya shafe dafa abinci da kuma tsabtar muhallinshi, ita kanta yanzu abun yafara damunta ba kamar ma da taga Yazeed yafara yimata halin ko in kula, don yanzu duk wata hanya da zata sadata dashi ya dwadeta tunda sassafe idan ya fita gidan baya dawowa sai dare, tayi kuka har ta gaji ba Wanda zata iya kaiwa matsalarta saboda cikin kashi Dari bisa tamanin tasan laifinta yafi yawa itada ta kasa bashi had'in kai don sauke hakkinshi da ya rataya kanta, har ciyo ta jimishi kwanakkin baya da ya neme amsar hakkinshi, ganin haka ya sanya yafita hanyarta baki d'aya, hawayen da suka zubo mata ta shafe, yau kam ji take Sam bazata iya jurar wannan zaman da suke a haka ba. 


Yazeed bai shigo gida ba sai wuraren sha dayan dare, yana shigowa direct dakinshi ya shiga saida yayi wanka ya sanya kayan bacci sannan ya nufe dining, yana kammala cin abinci har zai koma dakinshi yakai dubanshi dakin Afnan, nan take wata zuciya ta tunasar dashi hakkinta dake kanshi, idan bai manta ba yau kusan sati biyu bai sata a idonshi ba, wani Abu yarika jin yana taso mai mai kama da shakku da tsoro.


A hankali ya murda handle din kofar duk da baiyi tunani yaji kofar bude ba amma ga mamakinshi sai yaji kofar ta bud'e.

Cikin sand'a ya shiga d'akin ko ina tsab sai kamshi ke tashi.


Can ya hangeta makure tana ajiyar zuciya da alama kuka taci har ta gaji, hijab ne sanye da jikinta duk ya makureta, nan take yaji tausayinta ya kamashi karasawa yayi inda take yana mai zuba mata idanuwa fuskarta tayi fayau ga alamar hawaye nan sun bushe mata, hannunshi ya sanya da niyar cire mata hijab, zumbur tayi ta bud'e idanuwanta, kurawa juna idanu sukayi na Dan lokaci kad'an kafin Afnan ta fad'a jikinshi tana mai fashewa da kuka, matset yayi a kirjinshi tamkar wani zai kwace mishi ita.

"Ba zan iya ba ya Yazeed ba zan iya jurar rashinka atare dani ba" ta fad'a cikin shashekar kuka,


"Ki daina kuka haka Afnan, ki yafe min bazan sake nisantarki ba,"


Wata ajiyar zuciya ta sauke, tana mai jinjina halacci irin na Yazeed.


A hankali yayi kokarin zame jikinshi daga gareta yana mai sakar mata murmushi. Saboda abunda yaji yana son taso mishi, gashi yayi alkawarin bazai sake nemamta ba har sai randa ta kawo kanta da kanta.


Mikewa yayi yana mai zare mata hijabinta kwantar da ita yayi tare da Jan Zane ya rufeta, Ac ya kunna tare da kashe mata fankar dakin ya manna mata peck a goshi, sannan ya kashe mata wutar dakin yayi mata saida safe.


Dakinshi ya nufa da tunani barkatai a zuciyarshi yarasa dalilin da yasa sai yaga Afnan duk wata sha'awa ta jikinshi ke tasowa.


Kwantawa yayi tare da dafe kanshi tunawa da zancen da daddynshi ya mishi na sanya ranar aurenshi da Nabeela nan da wata biyu idan Yazeed din ya dawo daga wani aiki da zaije yi a kasar Turkey. Sam auren Nabeela bai cikin tsarinshi sai dai yanzu zai iya aurenta ne kawai ko Dan gudun fadawa wata hanya marar kayau Tunda ta kasa samun hadin kai daga matarshi. da wannan tunanin bacci ya sace shi.


Tun daga lokacin zaman nasu ya Dan chanza Yazeed na kokarin yaga ya sauke hakkinta da ke bisa gareshi ko yaushe, ba laifi sukan Dan tab'a fira sai dai da mood dinshi ya chanza zai tashi yabar gurin da Afnan din take. Ita kuwa Afnan ba karamin tashin hankali tashiga ba jin ansa ranar auren yazeed dinta da Nabeela gashi yanzu kusan kullun Nabeela tana gurinta wai fira ta kawo mata don su saba kafin ta shigo, tun tana daukar abun da wasa har abun yafara damunta don yanzu kusan har Yazeed din ya fara sake mata ko Afnan din bata falo zama yake su sha firarsu da Nabeela kuma duk firan tasu ta soyayya ce.


Afnan duk ta rame tayi baki abubuwan duniya sun mata yawa, yau tana zaune Nabeela ta shigo wani kallon wulakanci ta mata, "ina yaya yazeed?" Ta fad'a tana yatsinar fuska,


Wata uwar harara Afnan ta galla mata, "me kike nema gareshi"


Murmushi Nabeela tayi tare da Dan rage sauti "abunda kika kasa bashi zan bashi, kin San gari da yawa"


Wani irin kololon bakin ciki ya tokare zuciyar Afnan wato bararata yaje yayi gurin Nabeela. bata san lokacin da wasu siraran hawaye suka fito mata da sauri ta mike ta yi daki ko wayarta bata dauka ba.


Nabeela na ganin haka tayi saurin daukar wayar tana murna cikin saa taga wayar ba code da sauri ta kira number Yaseer tana shaida mai ga wayar Afnan ta samu gaya mata irin text din da zata tura mai tayi, nan take ta tura mai, yace mata ta zauna har zuwa lokacin da Yazeed zai shigo tamai flashing da wayarta.


Bata dau lokaci ba Yazeed ya shigo zama yayi nan kusa da Nabeela tana mishi sannu.


Ba don komai yake zama da ita cikin gidan shi Ba sai Dan Ya fuskance irin kishinshi da Afnan keyi har ta sauya hali.


Cikin dabara Nabeela tama Yaseer flashing ba a dauki lokaci ba wayar Afnan din ta dauke ruri 

Saida tayi ta katse ta sake dauka ankira kusan sau ukku Nabeela ta kalle yazeed tace, "kaga fah tun dazu ake Kiran wayar Afnan ka Dan taimaka ka kaimata mana"


Bata ida rufe bakinta ba aka sake kira, cikin sauri Yazeed ya dauke wayara yana mamakin wannan kiran haka, don bai ma cika ganin tana waya da ita ba, yafi ganin tana waya da karamar.


Duba mai kiran yayi yaga ansa my Y, "waye haka ya fad'a cikin ranshi,


Kafin ya shiga cikin d'akin yaji karar shigowar text kasa hakura yayi ya bude text din.


Innalillahi waiina ilaihirraji'un, kawai yake ambata, jikinshi baki daya rawa yake kafafunshi suka kasa daukarshi sulalewa yayi nan kasa Ya zauna tare da dafe kanshi.


Yazeed ko Yaseer

       Na

 Ayshart Farouq


Nagarta writers association


        70

Conversation dinsu yabi da kallo yana karantawa, hawaye kawai ke zubar mishi a idanuwa, ganin irin sakonnin da suke turawa juna, Wanda ciki ne take gayawa saurayin cewa "dama kasan ba son Yazeed nakeyi ba rashinka ne, da kuma tsoron irinin mutumin da Abbana zai had'ani dashi ne yasa na amince zan aure Yazeed shima Dan kawai yaci albarkacin sunanka ne da kuma nacin mahaifiyarshi. amma nayi maka alkawarin ba zatan tab'a bari wani Abu yashiga tsakanina dashi ba, sannan nayi maka alkawarin zan kashe aurena dashi nan bada dadewa ba domin in mallaka maka kaina kai kad'ai saboda Kaine zab'ina. Idan na tuna ranar da muka kasance tare da juna nakan yi farin ciki, dan haka ka shirya ko yaushe zan iya kiranka dan ka d'ebe min kishin da ke damuna.

Yours Afnan.


Inda shi kuma yake kara jaddada mata cewa kar ta kuskura ta bari Yazeed ya kusanceta saboda duk lokacin da hakan ta faru zai iya rasa rayuwarshi, Sahidaa ita d'in ta daban ce shi yasa ya kasa hakura da ita har kaddarar samun ciki ta shiga, shi kuma lokacin baya kasar shi yasa suka shirya plan kan Afnan tace Fyade aka mata, Amma ba wani fyade sun more rayuwarsu ne kawai don suna son junansu.


Massege din karshe da ya turo ce mata yayi "ki tabbatar da cikin satin nan duk yanda zaayi mu had'u saboda ina son jin dumin jikinki kin sannan nayi missing pink lips dinki masu taushi da zak'i, sannan nazo mana da wata hanya mafi saukin da zaki kashe aurenki ba tare da Ammie ko wani ya zargeki ba. daga mai kaunarki .

Yazid Mahmud 


Bud'e kofar toilet din da akayi ne Ya sanya Yazeed ya mik'e cikin wani irin yanayi mai wuyar Fassarawa.


Wani mugun kallo yashiga jifar Afnan da shi tare da tunkararta yana dafe da zuciyarshi sai wani huci yake tamkar kwamarcin maciji,


hankalin Afnan yayi matuk'ar tashi, nan take ta neme wani bacin ran da Nabeela ta haddasa mata ta rasa, " yaa Yazeed.........."


Bata karasa ba taji saukar wani gigitaccen marin da bata ma San lokacin da ta kai ka'asa ba, wata wahaltatta kara ta sanya saboda azaba,


Nan take Yazeed yashiga Dukanta ta ko ina yana kuka, tana kuka 


"Kin cuceni Afnan, kin cuce ni, kin cuci kauna da soyayyar da na nuna miki, na tsaneki na tsaneki" wani Abu yaji ya tokare mishi zuciya baki daya jikinshi yaji ya saki, nan take ya sulale ya Fad'i k'asa sumamme.


Cikin tsananin tashin hankali Afnan ta yunk'ura ta tashi duk da tsananin zafin da taji jikinta na mata,


Wata irin razanannar Kara ta saki tare da Fad'in sunanshi, tana girgizashi. 

Jin haka yasa Nabeela ta shigo da gudu tana salati, ganin ko Shed'a Yazeed bayayi yasa ta fita waje da gudu tana kiran Yaseer da mamie, 


Ba a dau lokaci ba suka shigo cikin tashin hankali, Mamie harda kukan munafurci aka daukeshi aka nufe Asibiti dashi.


Sai bayan anshiga dashi emergency ne, sannan Afnan ta nemi karamar wayarta da bata San ma ya akayi ta daukota ba, Ammie ta kira, cikin kuka ta shaida mata halin da Yazeed yake ciki, cikin kankanen lokaci Su Ammie suka iso, 

 Afnan na ganinta ta fad'a jikinta tana wani irin kuka mai cin rai, cikin kalamia masu dad'i Ammie ta shiga lallashin Afnan tana kwantar mata da hankali.


Saida likitoci suka shafe hour d'aya kan Yazeed sannan suka samu ya dawo hayyacinshi. allurar bacci aka mishi don ya samu nutsuwa.


Suna fitowa su Ammie sukayi saurin mikewa suna tambayarsu halin da Yazeed yake ciki,


Doctor ya dube su yace, "Ku kwantar da hankalinku he's out of danger now, sai dai mun mishi allurar bacci yan bukatar Hutu sosai, saboda shock din da ya shiga saura kiris ya haifar mishi da hawan jini, Amma yanzu alhamdulillahi komai yazo da sauki idan ya farka zuwa anjima ma za'a iya sallamarshi"


Ammie da Afnan sukayi hamdala tare da yima likitan godiya.


Yaseer kam yaso a ce zuciyar Yazeed ta buga don ya d'and'ana irin azabar da ya d'and'ana lokacin da ya rabashi da Afnan.

wani murmushin samun nasara yayi don yasan yana gaf da cika burinshi.


Ammie ce ta katse mishi tunani da cewa, "Yaseer da kun wuce gida tunda Abun yazo da sauki idan yaso nida Afnan sai mu jira har lokacin da zai tashi," ta fad'i haka ne saboda tana so ta keb'e da Afnan don jin abunda ya faru da Yazeed.


Sosa keya Yaseer yayi, saboda bazai iya wucewa ba har sai yaji hukuncin da Yazeed zai yankewa Afnan.

"ba komai Ammie zamu jira muma har lokacin da zai tashi"


Mamie tayi saurin cewa, "da dai mun wuce zuwa anjima sai mu dawo kasan halin yan Asibitin nan basa son ana zama haka da yawa yanzu sai su yiwa mutane rashin mutunci,"


Nabeela tayi saurin cewa, "nikam Mamie ba inda zanje sai Yaa yazeed ya tashi"


Murmushi Mamie tayi, dama haka take so, tafi son duk hukuncin da Yazeed zai yanke ya zamana wani daga cikinsu yana kusa, ita kanta da ba don kar Ammie tayi suspecting wani Abu ba, da tsayawa za tayi sai taga abunda ya kwancewa buzu nad'i.


Dubin Nabeela tayi cikin kissa "dama ai ba tare da ke zamu je ba, waya iya daukeki gurin yayanki?, Ki zauna kawai har lokacin da zai tashi ko hankalinki zai kwanta"

Ta fad'a tana kallon Ammie da Afnan.


Tab'e baki Ammie tayi saboda tasan shu'umanci da makirci irin na Mamie.


Afnan kam Sam hankalinta baya Kansu saboda tayi zurfi cikin tunanin abunda ya faru, shin me tayiwa Yazeed da har ya birkice mata haka?, kar dai ace ya gane Yaseer ne ya mata ciki, idan kuwa hakane lallai tashiga uku saboda ita ya kamata ta gaya mishi gaskiya tun farko gashi yanzu ya gane da kanshi har yana ikirarin cewa ta cuceshi, babban abunda yafi daga mata hankali irin Cewar da yayi mata ya tsaneta, dafe kanta tayi wasu sirarran hawaye suka fito masu zafin gaske, 

daga idanuwanta tayi ta kalle gefen da Su Yaseer suke tsaye, karaf suka had'a idanuwa, murmushi ya sakar mata tare da kashe mata ido,


Wata Harara ta watsa mishi mai nuna tsantsar Tsana da bak'in ciki, a halin da take ciki ji take duk anka bata wuka ba abunda zai hanata ta chakawa Yaseer ita. 


Dauke kanta tayi taci gaba da sakawa da warwarewa tana sharb'ar kwalla.


Yaseer ya so yaci gaba da kallon Afnan saboda ba karamin farin ciki yake ji ba idan yana kallonta, har dai idan ya tuna ta kusa zama mallakinshi sai yaji duk duniya ba Wanda ya kaishi farin ciki.

 ba yanda baiyi ba su sake had'a idanuwa amma Sam Afnan ta k'i yarda, ba yanda ya iya dole sukayi musu sallama suka wuce shida Mamie aka bar Ammie, Afnan da Nabeela.


Bayan sun wuce ne Ammie ta maida dubanta gurin Afnan tana tambayarta abunda ya faru,


Cikin kuka Afnan ta kwashe komai da ya faru ta gayawa Ammie.


Ba karamin tashin hankali Ammie ta shiga ba jin harda duka, saboda Sam baya cikin halayyar Yazeed, sau da yawa Hafsat take mishi laifi tun tana yarinya amma bai tab'a daga hannu ya doketa ba. "Akwai wata a kasa" Ammie ta fad'a tana mai Jan Afnan suka koma gefe don gudun kar Nabeela taji maganarsu.


Saida suka same wuri suka keb'e sannan Ammie tace, "kin tabbata baki mishi komai ba Afnan"


Daga kanta Afnan tayi "wlh Ammie sanina ban mishi komai ba, sai dai gani nake kamar ya samu labarin zamana da Yaseer ne"


"Wannan ba zaisa Yazeed ya miki haka ba, akwai dai wani Abu" ammie ta karashe maganarta tana Nazari.


Dukansu shiru sunkayi na d'an wani lokaci, Afnan na tunanin ko ta gayawa Ammie matsalar da take ciki ta tsoron Yazeed ya kusanceta tun lokacin da aka kaita, wata zuciya tace, idan kika fad'a mata kin tona asirin aure, kuma bama Ammie ce ya kamata ki gayawa wannan ba, Ki tuna fah Ammie tamkar yar cikinta ta dauke ki, bai kamata ki boye duk wani sirrinki gareta ba, nan take Afnan taji wani karfin guiwa ya shigeta ba b'ata lokaci ta kwashe matsalar da take ciki tun lokacin da aka kaita ta gayawa Ammie.


Nan take zufa ya karyewa Ammie ta ce, "haba Afnan me yasa baki gayamin wannan matsalarba ai wannan matsala ba matsalar da zaa boyeba ce, tun lokacin da abun ya faru ya kamata ki fad'a gaskiya banji dad'in boye irin wannan babbar matsala da kikayi gare ni ba, ko baki daukeni matsayin mahaifiya ba?"


Girgiza kai Afnan tayi tare da bawa Ammie hakuri,


Hannunta Ammie ta rik'e "ki kwantar da hankalinki insha allahu komai zaizo da sauk'i, mujira Yazeed din kawai ya falka muji abunda ya faru"


Sun dad'e gurin sannan suka koma mazauninsu.


 Nabeela na ganinsu ta jefawa Afnan harara, cikin ranta tana fad'in duk abunda ya faru a gabana ya faru barin kinbibi kikeyi, da yaa Yazeed ya tashi zakiyi waje ya zama nawa ni kad'ai,

Wani murmushi tayi tana mai hango kanta a gidan Yazeed maysayin matarshi.


Misalin karfe takwas na dare Yazeed ya falka, da sauri su Ammie sukayo kanshi suna mishi sannu,

A hankali yake kallonsu d'aya baya d'aya, can 

 idanuwanshi suka kai kan Afnan, da sauri ya runtsesu yana jin wani Abu yana mishi yawo a jiki, cikin miryarshi da bata fitowa sosai yace, "Ammie ki ce ta fita bana son ganinta kusa dani"


Cikin mamaki Ammie ta kalleshi "wa kenan?"


Hannunshi yayi pointing gefen da Afnan take tsaye, still idanuwanahi na rufe,


"Yazeed kana da hankali kuwa, matarka ce fah taya zaka ce ta fita?"


"No Ammie ta fita kawai bana son na sake ganinta har Abada"


Afnan najin furucin Yazeed da gudu ta fita dakin tana kuka mai kona zuciya.


Kallon Yazeed da Ya tsurawa silin ido Ammie tayi, "ka kuwa San abunda kayi?, anya kuwa Yazeed kana cikin hankalin kanka kuwa"


Ba ta damu da shirun da yayi ba, ta juya ta kalle Nabeela da ke murmushin jin dad'i 

"d'an fita ki bamu wuri ina son inyi magana dashi" Ammie ta fad'i ba alamar wasa a fuskarta,


Cikin sand'a Nabeela ta juya ta fita tamkar munafuka, cikin ranta wata tsanar Ammie take ji, zaki gane kurinki nakusa rabaki dashi har abada tayi kwafa ta wuce tana mai jin haushin rashin jin maganar da Ammie zata gaya mishi.


Tana fita Ammie taja tsaki tare da maida dubanta gurin Yazeed, "me yafaru tsakaninka da matarka?"


Dama yasan wannan tambayar ce zata mishi, sai dai yanajin bazai iya tab'a amsa mata wannan tambayar ba, saboda yasan muddun taji abunda Afnan ta aikata zata tsaneta fiye da yanda ya tsaneta, Wanda hakan na nufin duk duniya zata iya Sanin abunda ta aikata, wata zuciya na mishi tuni da cewa ko ka manta kama Afnan alkawarin zaka kare mutuncinta har abada? Bazan iya tona mata asiri ba kamar yanda ba zan iya zama da ita ba.

 ya fad'a cikin ranshi.


Ganin yayi shiru yasa Ammie ta sake tambayarshi cikin fad'a "Ashe bada kai nake magana ba Yazeed me 'yar mutane ta maka ka daketa?"


Wasu hawaye suka zubo mishi ya sanya tafin hannunshi ya shafe, "na rok'eki da girman Allah Ammie kada ki matsa da jin abunda Afnan ta aikata a gareni ,saboda jinshi Sam ba alkhairi ne ba a tattare da ke, Ammie ke kika had'a wannan aure dan haka ina so ki bani dama in rabashi saboda bazan iya zama da wannan yarinya ba, idan naci gaba da zama da ita tabbas nasan ita zatayi ajalina, zafi da kuncin da zuciyata ta shiga bana fatar ta sake shiga makamancin irinshi har abada, Wanda kuma zama da ita yana nufin zanci gaba da zama a cikin kunci na har abada, bazan iya ba Ammie, bazan iya ba, ya fad'a tare da fashewa da kuka mai tsuma zuciya.


Jikin Ammie yayi matukar yin sanyi batada wata sauran dabara, kukan da Yazeed yake ba karamin tab'a mata zuciya yayi ba.


Cikin karfin hali Ammie tayi magana " naji duk abunda ka fad'a amma Sam ba zan amince ka rabu da Afnan ba har sai kabani kwakkwaran dalilin yin haka, kasani bazan tilasta maka zama da ita a inuwa d'aya ba sai dai kuma ban amince ka saketa ba har sai lokacin da ka gayamin abunda ta maka kuma nayi bincike na gane gaskiyar lamarin, saboda makiyanka da ke zagaye da kai suna iya haddasa komai don rushewar farincikinka, zanje da Afnan gidana har lokacin da ka yanke shawarar sanar dani abunda yafaru.


Shigowar doctor ne ya tsaida maganarsu.

bayan ya kare yan dube dubenshi ne ya yiwa Yazeed bayanin halin da ya sameshi tare da tambayarshi ya sallameshi yanzu ko sai da safe idan ya kara hutawa,


"I can take care of my self, sallameni kawai" ya fad'a yana kallon doctor 


Ba tare da b'ata lokaci ba akayi discharging dinshi. 


Koda suka fito Nabeela na zaune bisa daya daga cikin kujerun karfen da ke kusa da d'akin da aka kwantar da marasa lafiya tana danna waya, yayin da Afnan take can makure wurin step din da zai fitar da kai harabar Assibitin hawaye kawai ke mata sintiri a fuska kallo d'aya Yazeed ya mata bai sake marmarin sake kallonta ba.


Gurinta Ammie ta isa ta kama hannunta suka fita, shi kuma Yazeed ya jera tare da Nabeeela tana famar yi mishi sannu,


Ammie ke Jan motar, yazeed na gaba ya Dan kwantar da sit din motar saboda bayada karfin da zai zauna, he's week, idanuwanshi lumshe tamkar mai bacci, Afnan da nabeela suna baya, har suka isa ba Wanda yace ko kala.


Suna isa direct part dinsu suka wuce, Ammie ta baiwa Afnan damar ta debo kayanta su wuce, jikin Afnan yayi sanyi sosai tunani take yazeed ya saketa, nan ta barsu parlour ita kuma ta wuce bedroom d'inta Dan dibar kayanta,


Cikin kankanen lokaci ta had'a kayanta wayarta ta tsaya dubawa ganin bata ganta ba yasa tayi tunanin ko ta yaddata a assibiti tunda ko karamar bata San ya akayi taje da ita ba.

Bata b'ata lokaci ba ta fito janye da trolley da handbag dinta.


Har lokacin Idanuwanshi rufe suke saboda bayason yana kallonta, saboda idan yana kallonta zuciyarshi rauni takeyi,

 

"Allah ya sada mu da Alkhairi yaa yazeed, Allah ya baka lafiya ya kuma yi maka tsaye a dukkan lamurranka" ta fad'a cikin raunanniyar muryata mai nuni da tsantsar kukan da tasha,


Bai tankata ba kuma bai bud'e idanuwanshi ya kalleta ba, sai dai maganarta ba karamin sukar mishi zuciya tayi ba,


Ammie ma sallama ta mishi taja Afnan suka wuce,


Nabeela kuwa da komai ya faru gaban idonta ji take kamar ta zuba ruwa a fako tasha, suna fita ta dawo kusa da Yazeed ta zauna, " Ya yazeed wai me Afnan ta maka ne haka harda su sak........"


Uwar tsawar da ya daka mata ne yasa tayi saurin yin shiru ba tare da ta shirya ba "get out" ya fad'a cikin hargowa


Da sauri ta fita har tana tuntub'e, 


Tana zuwa sashen mamie ta fad'a jikin Yaseer tana murna, tare da kwashe duk abunda ya faru ta gayama Mamie da Yaseer, murna suka rik'a yi Yaseer harda dan takawa yayi don bashida kunya.


Afnan nata zuba ido taga Ammie ta kaita gidansu sai dai, ga mamakinta sai taga ta nufe gidanta da ita.


"Ammie ai da kin kaini gida kawai, tunda wannan ba abunda za'a boyewa su mommy ne Ba, dole ne sai sun sani," ta fad'a kanta a k'asa.


Murmushi Ammie tayi saboda tagane abunda Afnan ke nufi "bana son su mommyn ki su San wannan abun Afnan tunda mijinki ba sakinki yayi ba, zaki zauna ne nan har zuwa lokacin da abubuwa zasu daidaita.


Ajiyar zuciya Afnan tayi ko ba komai ta samu sauki tunda Yazeed bai saketa ba. Bata sake cewa komai ba har suka isa gidan Ammie.


Ammie tasa a kai mata kayanta d'akin Yazeed na dori saboda akwai bak'i a gidan bata son su fahimce wani Abu.


    Bayan sati biyu da faruwar wannan, Yaseer ya shirya yaje gidansu Afnan soboda a tunaninshi Yazeed ya saketa tana gidansu.


 Bayan yaje ne sun gaisa da Mommy take tambayrshi ko su Afnan suna lafiya? 

Yana jin haka yasha jinin jikinshi, nan take ya gane Afnan bata gurin gidansu, alama ma ta tunana 'yan gidan basuda masaniya da abunda ya faru. Bari day lokaci ba ya mata sallama cikin mutuwar jiki ya fita, cikin ranshi yana tunanin cewa Afnan tana gidan Ammie, yasan kuwa ko giyar wake yasha ba zaije gidan Ammie ba saboda tsaf zata iya zargin wani Abu daga gareshi. Haka ya koma gida ranshi bace saboda ya gane Yazeed zai sake Afnan ba.


B'angaren Yazeed kuwa, shirye shiryen zuwa seminar yake, wadda kungiyar WHO suka shirya a kasar Germany ta tsawon mako uku.   Kuma da ya dawo za'a fara shirye shiryen bikinshi da Nabeela.


Ana gobe zai wuce yazo daukar wasu takardunshi a gidan Ammie, saboda marabinshi da ita tun lokacin da sukabar gidanshi itada Afnan sai dai yakirata a waya ya gaidata.


Ta kofar baya yabi saboda baya son abunda zai had'ashi da Afnan shiyasa ma ya dauke k'afa daga gidan. 


A hankali ya bud'e kofar da zata sadashi da palon shi ya shiga..................


Ku min afuwa dan Allah ba haka naso ba amma insha allahu zuwa gobe zan karasa muku.


Ana tare. love u oll fisabilillah


Yazeed ko Yaseer

       Na

Ayshart Farouq


Nagarta writers association 


       71


Last page


Bai damu da ganinshi tsaf tsaf ba don yasan ko yaushe Ammie na kokarin sa a gyarashi ko ba kowa a ciki,

Direct bedroom dinshi ya nufa. 

Afnan na zaune tayi nisa cikin tunanin da take, motsin da taji ne yasa ta fara magana duk a daukarta Hafsa ce saboda ita tafita ta kawo musu abinci, kasancwar ko yaushe suna tare bacci kadai ke rabasu. Saboda ita hafsa d'akinta take kwanciya, a cewarta bata iya kwana dakin Yazeed saboda Ac dinshi bashida sanyi sosai.

"Hafsat ina son Yazeed kasancewarshi inuwa a gareni a dukkan lokacin da nake muradi, ya kasance babban jarumi a birnin zuciyata mai tsumayi, yakan sani farin ciki da nishad'i a ko wane sa'i, sautin muryarsa na kawar da dukkanin damuwata, tamkar yanda murmushinsa ke sanyaya zuciyata.

  Kyawawan halayensa na kan gaba wurin janyo dukkanin soyayyata, ba tare da tunanin komai ba na mika masa ragamar rayuwata. A ko wace safiya na bud'e idanuwa da kyawawan sakunansa, sukan zauna a cikin tunanin har yammaci, a gareni ya kasance wata tsoka a cikin jikina, wannan tsokar ba kowace tsoka ce ba face zuciyata" 

 ta fad'a tana nuni da zuciyarta.

 bata damu da rashin jin maganar Hafsat ba taci gaba da cewa 

" tabbas mukan samu sab'ani a tsakaninmu saboda harshe da hakora ma wani lokaci sukan sab'a sai dai hakan baya tab'a kawo nakasu cikin soyayyarmu, muna fahimtar juna a dukkan matsalolinmu muna kuma bawa juna uzuri a laifukkanmu. Amma me yasa Yazeed ya k........."

 

Maganar da taji ce ta latse mata magana ta juyo cikin tsananin tashin hankali,


"Bravo," ya fad'a yana mata wani kallo mai kama da warning, " lallai kin cika babbar marasa kunya da har zaki iya dubin kanwata ki gayamata wannan kalamai naki na yaudara Wanda aka shiryasu domin wanin Dan uwanata, ban tab'a tsanar sunana ba saida kika shigo rayuwata, babbar nadamar da na tab'a yi a rayuwata da kika zamo a bar yarda a gareni. duk lokacin da na tuna wannan lokacin nakan ji bakin ciki ya mamaye zuciyata, hakika Yau nakara tsanarki fiye da yanda na tsaneki a baya.


Yana kaiwa nan ya nufe wardrobe ya bud'e tare da d'auakar wata briefcase dinshi ya juya ya bar d'akin.


Afnan kam kasa kwakkwaran motsi tayi har ya bar d'akin yana fita ta fashe da kuka mai ban tausayi.


Yazeed kuwa ikon Allah ne kawai ya kaishi gida, yana isa d'aki ya fad'a ya d'auko wayar Afnan da ke hannunahi, chargy ya jona wayar saboda tun ranar da abun ya faru wayar ta dauke, ba komai yasa ya sanya wayar chargy ba sai Dan ya kaima Ammie taga abunda Afnan ta aikata a gareshi ko tana bashi damar ya saketa ya huta da wahalar da zuciyarshi take ciki, me yasa zuciyarshi take tausayinta ne? Me yasa ya kasa sanarda wani abunda ta mishi? Sam baya son abunda zuciyarshi take mishi. yafi so ta tsaneta tsana mafi muni, sai dai kash bazai iya ba, yana yiwa Afnan wani irin mahaukacin so wanda shi ke sanya duk lokacin da yayi yunkurin nunawa Ammie wayar sai ya fasa. 

kwanakkinan da yayi ba tare da Afnan ba Allah kadai yasan irin azabar da ya d'an d'ana. Yanzu kam ya d'au alwashin nunawa Ammie sakwannin ko ya samu sassaucin zogin da zuciyarshi take mishi. haka yayita sak'e sak'e har bacci ya kwasheshi. Bashi ya tashi ba sai karfe shiddan safe, ba karamin mamaki yayi ba da yasamu wannan baccin haka, cikin gaggawa ya tashi yayi wanka yayi arwala yayi sallah, bai b'ata lokaci ba ya shirya saboda jirginsu karfe takwas ne, wayar da yasa chargy ya cire maimakon ya sanya ta ajaka sai ya ajiyeta ya saka charger.


Gidan Ammie ya nufa Dan yayimata sallama, ya kuma nuna mata wayar yaji hukuncin da zata yanke idan ta bashi damar ya sake Afnan ya saketa kafin ya wuce. 


Bayan sun gaisa da Ammie ya bud'e jakar don ya nuna mata sakkonnin wayar, yaga charger ce ya saka, tsaki yayi tare da yima Ammie ban kwana yana jaddada mata da ya dawo zai rabu da Afnan, fatar dawowa lafiya ta mishi tare da rakashi har gurin mota ta koma cikin gida.


Afnan kam tun lokacin da Yazeed yabar gurinta ta shiga wani mawuyacin hali, duk tayi bak'i ta rame ko yaushe cikin damuwa ta ke, ko yaushe Ammie tana bata ruwan zam zam da aka tofe da adduo'i na karya sihiri.


Su Mamie kuwa shirye shiryen biki kawai suke da neman hanyar da Yazeed zai rabu da Afnan wata kanwaarta ta kira Aina'u kasancewarta shahararriya gurin shiga bokaye, aina'u ta tabbatar ma mamie zata iya ganinta ko wane lokaci don suje Ilorin gurin bokanta. (ta Allah ba taku ba)


Yau ta kasance ranar Friday misalin karfe bakwai na dare jirginsu Yazeed ya iso Nigeria. tunda suka sauka ya dauki drop sai gidan Ammie, kasancewar wannan na d'aya daga cikin dabi'arshi, duk lokacin da yayi tafiya ya dawo sai yafara zuwa gurin ammie kafin yaje ko ina, shiyasa yake barin motarshi a gidan idan zaiyi tafiya.


Koda ya shiga d'akinta ta sallame sallar isha'i tana lazimie, zama yayi bakin gadonta ya d'an kishingid'a, tana karewa ta maida dubanta gurnishi, "a'a mutanen Germany saukar yaushe dawowa babu notice"


Murmushi yayi tare da gaidata "wlh Ammie kasarce sai a slow nayi kewar gida shiyasa muna karewa na biyo jirgi na dawo"


"Masha allahu Allah sa anyi a sa'a" ta fad'a tana ci gaba da laziminta,


"Amin ammin Ammie " yazeed ya fad'a yana sake kishingidawa, saida yayi minti talatin sannan ya mik'e


"Ammie zan wuce gida in d'an sarara sai dai zuwa gobe"

 Ya fad'a yana mik'ewa.


"Yazeed" Ammie ta kirashi, 


"Na'am Ammie"


"Ina so gobe idan zaka dawo ka dawo min da takardar sakin Afnan na janye buk'ata ta ta son sanin abunda ya had'a ka da ita, nagaji da ganin yarinyar mutane cikin kunci da rashin sanin makomarta ka kawo mata takardarta ta koma gidansu Allah ya had'a kowa da rabonshi. ba baki nama ba, amma wlh muddun ka rabu da Afnan sai kayi nadama." Tana kaiwa nan ta mik'e tare da lunke dardumarta ta shiga toilet.


Yazeed kam tsaye yayi kamar an shuka dusa zufa yaji ya karye mishi ta ko ina, nan take yaji gajiyar da ya kwaso ta sake koma mishi sabuwa , dakyar ya iya d'aga k'afa ya wuce yana tunanin magangannu Ammie, ya rasa gane abunda yakeji game da magangannunta.


Yana cikin saukowa bisa step yaji yayi karo da mutum, idanuwanshi da suka chanja kala ya watsa ma Afnan dake k'ok'arin shiga gurin ammie Dan samo maganin ciyon kai.


Tagal tagal tayi zata fad'i saboda tsoratar da tayi, cikin zafin nama Yazeed ya rik'ota har tana fad'awa kirjinshi saboda rashin karfin da batada,


Abunda yaji ya tsarga mishi ne tun daga kanshi har yatsarshi yasa yayi saurin tureta daga jikinshi, yana watsa mata mugun kallonshi da ta tsana.


Allah ya taimaketa tayi saurin dafe gina da tayi k'asa rab'ata yayi da niyar ya wuce.


Cikin sauri Afnan ta riko hannunshi tare da kiranshi, cikin kuka "yaa Yazeed,"


Janye hannunshi yayi saboda komai zai iya faruwa, yaci gaba da tafiya,

"Dan girman Allah ka saurareni Yaa Yazeed"


Cak ya tsaya tare da juya mata baya, zuciyarshi bugawa take da sauri da sauri,


Durkusawa tayi tare da rik'e k'afafuwanshi "yaa Yazeed Dan girman Allah kayi hakuri ka yafe min duk laifin da na maka, zuciyata bazata iya ci gaba da jurar wannan hukunci naka a gareta ba, yaa yazeed ka daure ko yaya ne ka fitar dani daga cikin duhun da nake ciki ka sanar dani abunda na maka, wlh zan iya jurar ko wane irin hukunci daga gareka koda kuwa hukuncin rabuwa dani ne, Amma bazan iya jurar hukkuncin wannan kallon tsanar da tuhuma da kakeyi a gareni."


Wani murmushi Yazeed ya saki Wanda yafi kuka ciyo, "kukanki da mayaudaran kalamanki sun daina tasiri a gareni, ki sani baki fara kuka ba sai randa, na bayyana mugun halinki, da kuma bakin aikinki ga idanuwan duniya, saboda kinci Amanar Allah, kinci amanar iyayenki, kinci Amanar mijinki da Duk wani Wanda ya yarda dake, ina maitabbatar miki da cewa kin kusa zama abun kwatance a cikin mutane. Hakika hankalina bazai tab'a kwanciya ba sai ranar da naganki da keda wannan mutumin da kika baiwa damar sab'awa mahaliccinki yare dashi ba kun wulakanta a idon duniya ni kuma ranar zanyi murna inyi farin ciki.


Yana kaiwa nan ya juya yaci gaba da tafiyarshi zuciyarshi na matukar yi mishi kuna.


Afnan kuwa kasa 'kwakkwaran motsi tayi sai hawayen da ke zubar mata masu tsananin zafi.

 Dakyar ta iya juyawa ta koma d'aki saboda yanda take jin kanta na bala'in sarawa kafin kace me har zazzab'i mai tsananin ya kamata, sai kakkarwar sanyi takeyi.


Shi kuwa Yazeed sai da ya bari yayi controlling kanshi sannan ya iya jan motarshi ya wuce.


Bayan yayi parking ya fito ne ya hango Daddy dinshi yashigo, tsayawa yayi har daddy yayi parking sannan ya isa gurinshi dan su gaisa.


Bayan sun gaisa Daddy yake tambayarshi "saukar yaushe?"


"Ban dad'e da isowa ba daddy, na d'an tsaya gurisu Ammie ne"


"Masha allahu ya gurinsu Aminar da fatar duk suna lafiya"


"Lafiya lau suke"


Kallonshi daddy yayi "lafiyarka kuwa naga duk ka wani fad'awa, kayi wani zuru zuru da kai, hope ba Auren Nabeela ne ke damunka ba"


Murmushin yak'e yazeed yayi "a'a dad gajiya dai ce"


"Toh kaje ka gaida Mamien Ku kafin kashiga gida dan nasan kila bazaka sake fitowa ba idan ka shige sai gobe saboda naga ka gaji da yawa, gashi ita kuma gobe tace biki zasu a abuja itada aina'u inaga tunda sassafe zasu fita"


Yazeed baiyi gardama ba dukda ba haka yaso ba yabi bayan mahaifinshi suna tafiya suna tab'a 'yar fira.


Suna taka step d'in da zai sadasu da falon Mamie suka tsince fad'uwar gaba dukansu.


Ba Wanda yayi magana har suka isa bakin k'ofar d'akin har Daddy ya kama handle d'in kofar da niyar bod'ewa, maganar da yaji ne tasa yayi saurin sakin k'ofar tare da kallon Yazeed cikin tsananin tashin hankali.


Yaseer ne ke magana, "wallahi anty Ainah ban San son Afnan din nike ba ba sha'awarta ba, saida na Yaudareta da sunan Yazeed,"

 

 Nan ya kwashe duk yanda yayi ya yaudare Afnan har da fyaden da ya mata da sakonnin da ya tura mata a waya shida Nabeela don su kashe aurenta duk ya fad'awa anty Ainah.


Yana karewa Anty Ainah ta kwashe da dariya, "lallai Yaseer baka saki nono ba, wannan irin aiki haka ai ko Anty zuzu bata iyashi, koda yake Anty zuzu babba ce dan har jinin al'adarta ta zubawa Alhaji a sob'o dan ta mallakeshi ita kad'ai, kaga kuwa sai yanda tace," ta fad'a tana kashewa itada Mamie.


"Aina'u bakida kunya yanzu gaban Yarana kike fad'in haka" ta k'arashe tana harararta.


Dariya tayi, "kai anty zuzu ai duk jirgi d'aya ya kwasomu kin manta ko su waye zuri'armu hala"


Dariya sukayi dukkansu, anty Ainah taci gaba da magna "ai duk laifin anty zuzu ne saboda kudd'i take Jin wuyar fitarwa da tuni an wuce gurin, yanzu abunda za'ayi gobe idan munje gurin boka sanya zamuyi a kashe uwar Yazeed d'in muga iyakar k'aryarta in yaso sai mu sanya a karkata zuciyar Yazeed d'in gurin Nabeela sai ya sake Afnan, itama sai a karkata zuciyarta gurin Yaseer d'in, a rufe bakin mutane ko ya kuka gani?"


Dukansu suka Amsa da "wannan shawarar taki tayi"


Mamie tace barima kigani in fesa turaren nan dan inji dad'in tatso kud'ad'e masu kauri gurin Alhaji, nasan yanzu ba zai dad'e ba zai dawo" 


Dangwala mata Anty Ainah tayi tana mata kirari.


Yazeed da Daddy da sukaji komai.

baki d'ayan su kasa motsi sukayi.


 jijiyoyin kan Yazeed har sun firfito idanuwanshi sunyi jajir tamkar garwashi.

Daddy kuwa kasa ima kanshi yayyi saida Y ya d'an jingina da gina saboda babu wata gab'a ta jikinshi da keda kuzari.


Cikin azama Yazeed ya tafi ya bud'e kofar d'akin daddy yayi saurin rikoshi. 


jikinshi tsuma yakeyi ta ko ina, fatanshi kawai ya Ganshi cikin d'akin Mamie yana hukunta duk wani azalumin da ya sanya katangar k'arfe tsakaninshi da Afnan.


Kallon Daddy yayi da rinannun idanuwanshi, daddy bashida bakin da zai iya yi mishi magana saboda duk wasu harrufa da ya sani sun goge a kwakwalwarshi, hannunshi kawai daddy ya iya kamawa dukda irin kyarmar da jikinshi keyi bai hana shi biyar bayan Daddy ba har falonshi.


Zaune sukayi bisa kujera dukansu sunfi minti ashirin ba Wanda yayi wani kwakkwaran motsi, can daddy yayi karfin halin fitarda wayarshi a aljihu ya kira police.


Kafin su zo ne daddy ya nemi karin jin bayanin abunda ya faru tsakanin Yazeed da Afnan,


Dakyar Yazeed ya iya labarta mishi kad'an daga cikin abunda ya faru.


Suna cikin haka police suka iso, daddy duk ya kwashe abunda yaji su Mamie na fad'a ya gayawa inspector Umar,


Basuyi wata wataba aka yimusu jagora har part din Mamie. Bud'e kofar da akayi ne yasa duk suka waigo, ganin yan sanda yasa suka mik'e suna tambayar abunda ya faru, daddy yace "idan kukaje police station za'a muku bayani" wani kallon tsana Yazeed ya kema Yaseer yayinda Daddy ya bada umurnin aje dasu duka har Nabeela.

 ba b'ata lokaci aka buga musu ankwai aka tasa k'eyarsu gaba zuwa police station.


 Mamie sai kururuwa take tana tambayar abunda sukayi, ko kallonta daddy baiyiba yayi sallama da inspector ya shige cikin gida yana jimamen butulci da son kai irin na d'an Adam.


 Sai wuraren shabiyu sannan Yazeed ya samu kanshi. magangannun Afnan ne suka shiga dawo mishi akai, yasan tabbas ya cuceta sai dai washi nan da zaija da hukuncin ubangiji? Allah ya Riga ya hukunta da hakan sai ta faru kuma babu mahani.


Tunawa yayi da zazzafan kalaman da ya fad'a mata d'azu, nan take yayi zumut ya mik'e saboda ya tabbatar da babu yanda zaayi konanan kalamanshi subar Afnan ta runtsa, shi kanshi ji yake bazai iya kwantawa ba tare da yayi tozali da fuskarta ba.


"Ya illahi, wat I did to my wife was not be forgiven" ya fad'a yan d'aukar wayarta domin ya nuna mata abunda yasa ya mata haka.


Cikin k'ank'anen lokaci ya isa gidan Ammie, keys d'inshi yayi Amfani da su ya bud'e kofar main Palo, bai tsaya wata wata ba ya wuce d'akinshi.


Can ya hangota nad'e cikin bargo, da ganin yanda take kwance kasan akwai abunda ke damunta.

 cikin sauri ya isa inda take ya gurfana saitin fuskarta tare da yaye bargon da take ciki yana kiran sunanta.


A hankali take d'aga idanuwanta da suke mata nauyi da zafi, tar ta bud'esu kan fuskar Yazeed da ke gurfane.


Kasa janye idanuwanta tayi saboda bata son ta falka daga mafalkin da take, tafi so ta dawwama har abada tana kallon fuskarshi a haka saboda bata hango kallon tsanar da yake mata a idanuwanshi ba, saima tsantsar kaunarta da ta gani a kwayar idanuwansa, wannan idanuwa sune nata, sune na Yazeed d'inta ba wad'an can da tagani d'azu ba.


"wannan shine Yazeed d'ina" ta fad'a tana runtse idanuwanta


"Yes nine Yazeed d'inki Afnan nine" ya fad'a yana had'e hannayinshi duka biyu alamar rok'o

"How can I begin to say I'am sorry, I know that u can't forgive me easily but keep this in ur mind, that, I have always loved u, and I will always love u. I was thinking of you all d time, seeing your face in my mind. I am really hurt for hurting u Afnan. Pls accept my apology am on my knees....." Ya fad'a idanuwanshi cike da kwalla.


Sai yanzu Afnan ta tabbatar da ba mafalki takeyi ba. 

Bata San lokacin da ta fad'a jikinshi ba tana kukan farin ciki "don't leave me again yaa Yazeed I can't do with out u, I promise I will never hurt your feelings again, pls yaa Yazeed don't......."


Yanda yaji zafin jikinta da kuma d'umin hawayenta da ke zuba a jikinshi yasa yayi saurin d'agata tare da sanya yatsarshi a bakinta yana girgiza mata kanshi " u are sick Afnan, jikinki yayi zafi sosai" lumshe idanuwanta tayi tare da jingina kanta a gado. da sauri ya mik'e tare da tallabota ya d'orata kan gado. Toilet ya nufa sai gashi d'auke da towel k'arami da ruwa a ciki, zama yayi kusa da ita, ya rik'o hannunta " pls let me help you Afnan, dan Allah kar kice a'a jikinki yayi zafi sosai kuma ba magani, this is the only thing that can help now pls" sunkuyar da kanta tayi k'asa bata iya cewa komai tana jin lokacin da ya d'orata kan cinyarshi yana zuge zip d'in rigarta, runtse idanuwanta tayi gam saboda tsananin kunyar da takeji, shi kuma ido ya tsurawa albarkatun kirjinta yana yiwa Allah tasbihi da ya mallaka mishi wannan halittar, towel din ya rik'a tsomawa cikin ruwa yana shafe mata jiknta dashi.


 cikin kankanen lokaci ya kammala ya kwashe kayan da yayi Afmani dasu ya maidasu muhallinsu.


Afnan kam sake tattakewa tayi cikin bargo tana kakkarwar sanyi, ganin haka yasa Yazeed ya mik'e tare da cire rigarshi, saida ya rage daga shi sai boxer sannan ya kashe wutar d'akin tare da shiga cikin bargon da Afnan ke ciki ya janyota jikinshi.


Matseta yayi sosai a jikinshi yanda zai bata damar ta samu d'umin jikinshi yanda ya kamata, cikin k'an k'anen lokaci bacci ya kwasheta,


Yazeed kam bai runtsa ba har asuba saida yaji Kiran sallah sannan ya iya mik'ewa, toilet ya shiga ya watsa ruwa tare da doro alwala baije masallaci ba nan yayi sallah yana cikin yin lazima Afnan ta falka, jikinta yayi sauk'i sosai dan ba zafin sai dai ciyon kai.


Kallonta yayyi tare da sakar mata murmushi itama murmushin ta maida mishi tare da mikewa tashiga toilet.


Koda ta fito har Yazeed ya fara bacci kan sallaya kasancewar bai samu yin bacci jiya ba.


Tausayinshi taji ya kamata, tasan jiya baiyi bacci ba, d'an motsi kad'an idan tayi sai yayi mata sannu.

gefenshi ta tsaya tare da kabbarta sallah.


Bayan ta kammala azkar d'inta ta maida dubanta gurin Yazeed tana nazarin fuskarshi, idonshi ya bud'e tar cikin idanuwanta, mikewa tayi da sauri tana mishi ina kwana, kunya duk ta rufeta ya kamata tana kallonshi murmushi yayi tare da janyota ta fad'o jikinshi, " me kike kallo a fuskana?" 


sunne kanta tayi a kirjinshi "bafa kallonka nakeyi ba" 


"Uhum toh ko kallona kike sai me ba mijinki kika kalla ba" ya fad'a yana kara kankameta a kirjinshi, tare da cewa "ya jikin hope yayi sauk'i?"


Gyad'a mishi kai kawai tayi saboda yanda yake wasa da hannunshi ba karamin kashe mata jiki yayi ba.


"Yaa Yazeed!" Ta kirashi cikin wata murya.


Jin yanda ta kira sunanshi ne yasa ya kasa Amsawa, lumshe idanuwanshi kawai yayi tare da d'an bubbuga bayanta alamar yana jinta.


Zamewa tayi daga jikinshi tare da gurfanawa kanta na kallon k'asa "Yaa Yazeed me yasa ka juya min baya?" Ta fad'a muryarta na rawa.


Baiyi zaton jin wannan tambayar ba duk da yasan dole sai ta tambayeshi amma baiyi tsammanin zata yi mishi ita a wannan lokaci ba,


Mikewa yayi zaune yana fuskantar ta da idanuwanshi da suka fara chanja launi, "me yasa kika b'oyemin gaskiyar abunda ke tsakaninki da Yaseer


Ta faru ta k'are ta fad'a cikin ranta, dama tasan wannan ne dalilin da yasa Yazeed ya juya mata baya, "ya illahi" ta fad'a idanuwanta cike da hawaye.


Ganin yanda ta ta d'aga hankalinta ne yasa ya kamo hannuwanta duka biyu ya rik'e yana murza yasunta.

"B'oye min da kikayi yasa Yaseer yayi Amfani da wannan dama yaso ya rusa zamantakewarmu,"


Yana kai na ya mik'e don dauko waya ya nuna mata.


Afnan jikinta rawa ya shiga yi hankalinta yayi matuk'ar tashi. Wayar da Yazeed ke mika mata ta karb'a hannunta na makyarkyata.


Tun kafin ta kammala karantawa ta fara zubar da hawaye masu matuk'ar d'aci. ganin haka yasa Yazeed ya dawo ta bayanta ya rungumeta yana bubbuga bayanta.


"Me yasa Yaseer yamin haka?, Me yasa ya neme ya zubar min da sauran mutuncina da ya rage a idon duniya? Shin duk abunda ya min na keta min haddi da yayi bai ganiba sai da ya neme ya rabani da Wanda ya rufamin asiri, ya rufe mugun aikin da na aikata a idon duniya, hakika da na don kai da Ammie ba da yanzu ban San yanda rayuwata zata kasance ba, bazan tab'a yafewa Yaseer ba har abada" ta karashe maganarta tana fashewa da wani matsananci kunka.


Kukanta da Yazeed keji har cikin ranshi ya k'ara haddasa mishi k'iyayyar Yaseer mai zafi, sai yanzu da yakejin kukanta abunda Yaseer ya aikata a gareta ke k'ara k'ona mishi rai, sai yanzu yakejin haushin kanshi na rashin illatashi da baiyi ba ya barshi gurin police.


Wasu sirarran hawaye suka zubo daga idanuwanshi.


D'imin hawayenshi da taji a bayanta ne ya k'ara d'aga mata hankali. Tsagaita kukanta tayi

 tare da juyowa tana fuskantarshi.


Bud'e idanuwanshi yayi yana kallota kafin ya kwantar da ita kan cinyarshi yana shafe mata hawayen fuskarta. 


A hankali ya kwashe duk makircin da sukaji su Yaseer sun Fad'a ya gayamata, Afnan kasa cewa komai tayi sai ajiyar zuciya da take cikin ranta kuwa tana jin jina girman makirci irin na wad'an nan mutane.


Sun d'au lokaci tana kwance tayi matashi da cinyarshi shi kuma ya rankwabo ya d'ora kanshi a kirjinta.


Bod'e kofa da sallamar da Ammie tayi ne ya dawo dasu daga duniyar da suka tafi, cikin sauri Afnan ta mik'e tana jin tamkar ta nutse cikin k'asa don kunya, shi kuwa yazeed ko a jikinshi mirmushi ne dauke da fuskarshi yana kallon Ammie da tayi galala tana kallonsu.


Cikin jin kunya Afnan ta gaidata, Amsawa tayi tare da matsowa tana kallon Yazeed, bakinta dauke da tambaya " kai me kakeyi anan? Yama wai akayi wai ka shigo gidan dan ga dukkan alamu ma nan ka kwana"


"Ammie d'akina ne fah, kuma matata tana ciki ita ta bud'e min k'ofa" ya bata Amsa yana Sosa k'eya tare da kallon Afnan da har fuskarta ta fara jaa saboda kunya.


Tab'e baki tayi, "kar kaci Amanar Afnan, kasan dai yanda akayi ka shigo, kuma da kake cewa d'akinka, hala wa ya baka? D'akinka yana can gidanku ba nan ba, nan aro na baka kuma na karb'e kayana don haka a tattara a koma inda aka fito"


Bai sake cewa komai ba sai yar dariyar da yake k'asa k'asa saboda ya gane inda Ammie ta dosa,


Rik'o hannunta yayi "Ammie hankuri fah nazo na baku keda 'yarki"


" ka rik'e kayanka bama buk'ata, ai kasan na gayama ba'a saurin yanke hukunci kan abunda ba'ayi bincike ba, amma Sam kai ka k'i ji saida ka sanya d'iyar mutane cikin tashin hankali"


"Nasan banyi dai dai ba Ammie amma ki tsaya kiji dalilin da yasa nayi haka pls" ya fad'a cikin magiya.


Hararanshi tayi tare da zaunawa "ina saurarenka".


Bai rage komai ba ya fayyace mata duk abunda ya faru tare da nuna mata wayar Afnan d'in.


Jikin Ammie yayi sanyi sosai, nasifa ta musu mai ratsa jiki sannan ta umurcesu da su fito su karya.

Fita tayi tanata jimamen abunda ya faru, MUTUM MUGUN ICCE ta fad'a a ranta tana mai Allah wadan da hali irin nasu Yaseer.


Saida suka sake wanka sannan suka shirya suka fito gurin breakfast.


Suna cikin breakfast d'in ne Daddy ya kira Yazeed don zuwa police station, saida ya kammala sanna ya musu sallama ya tafi.


Koda suka isa idonsu Mamie ya raina fata, takardar saki biyu daddy ya bata, ai kuwa kuka Mamie ta ke harda su majinnu tana rok'on daddy ya maidata d'akinta bazata sake zaluntarshi ba, ko saurarenta Daddy baiyi ba yasa Abasu takarda su saka hannu komai ya same d'ayansu daga yanzu har zuwa gaba sune.

 


Saida suka saka hannu sannan aka sakesu daddy yace kar yaga k'afar ko wannensu gidanshi zai sanya a kwashe musu kayansu a kaimusu.


Dan dole su Mamie suka tattara suka koma gida d'auke da tsantsar nadama da danasani sun rasa tsuntsu sun rasa tarko.


 Yaseer kuwa takarda ya rubuta tare da rokon Yazeed alfarmar ya kaiwa Afnan dakyar yazeed ya karb'e takardar saboda tausayin Yaseer d'in da ya kamashi hak'ik'a yaga tsantsar nadama a idanuwanshi don kasa had'a ido yayi da shi sai sharar kwallar da yakeyi.

 daga nan mota yashiga yabar garin saboda ya tabbatar da Afnan ta mishi nisa har abada kuka ya rik'a yi yana nadamar abunda ya shuka, ya tabbatar da jarabashi ne Allah yayi da sonta don ya fitar mata da alhakinta saboda ya cuceta ba kad'an ba.


Misalin k'arfe takwas nadare Yazeed na zaune gaban Ammie yana mata magiya kan tabarsu su koma gidansu tunda komai ya wuce, ganin yana so ya saka mata kuka yasa tace, "ba wai nak'i barinka ka dauke matarka Ku koma ba, inajin tsoron kar wani Abu ya same d'iyar mutane kasan halin zuwaira Sam batada imani zata iya biyar bayan fage don ta dauke fansa" 


"Ba wani Abu da zata iya Ammie saboda anriga anyi yarjejeniya dasu a court, kuma wlh Ammie idan kika gansu zaki tabbatar da ba k'aramar nadama sukayi ba course they are helpless, don ni har tausayi suka bani wlh"


"Allah yasa har cikin zuciyarsu sunyi nadamar, ai dama haka muke fata, Allah dai ya ganar dasu idan Suna da rabon ganewa, cewar Ammie tana murmuahin jin dad'i taci gaba da cewa,

" dama ba rik'e maka mata zanyi ba, kaje ka dauke matarka Ku tafi gida Allah kauda fitina tsakaninku."


"Ameen" ya fad'a tare da

 rungume ammie yana murna.


d'akinshi ya nufa, Afnan na zaune taci kwalliya, tayi kyau har ta gaji, saboda marabinta da kwalliya har ta mance, da isarshi daukarta yayi yana juyi da ita kamar wata yar tsana, ita kuma sai dariya take kyalkyatawa.


Direta yayi yana dariya "Ammie ta amince ki koma d'akinki",


Bata fuska tayi " gaskiya ni Ba yau zan koma ba" ta fad'a fuskarta a d'aure,


"Pls Afnan kar kimin haka, kar ki hukuntani ta wannan hanya dan Allah" ya fad'a tamkar yayi kuka.


Kauda kanta tayi gefe ba tare da tace mishi komai ba.


Mikewa yayi yashiga had'a mata kayanta, saida ya had'a komai ya kai mota sannan ya dawo, mayafinta ya mik'a mata tare da fad'in "pls ba don ni ba"


Karb'a tayi tana hararanshi. Murmushi ya sakarmata tare da bata peck a goshi "good girl"


Sallama sukayiwa Ammie har bakin mota suka rakosu Hafsa na tsokanar Afnan wai tunda taga mijnta ta yaddata, dariya suka sanya dukansu sannan suka shiga mota suka wuce Suna d'aga musu hannu.


Basu isa gida ba sai kusan karfe goma saboda sun d'an tsaya sayen abunda zasuci idan suka je gida.


Afnan nashiga gidan taji jikinta yayi sanyi ta dauka bazata sake dawoshi ba har abada, kamar Yazeed ya San abunda take tunani ya kamo hannunta ya na mata murmushi, "insha allahu bazaki sake barin gidannan da sunan wata matsala ba har abada"


Wani sanyi taji cikin ranta.


Har d'aki ya kaita sannan ya kai mata kayanta, shi kuma d'akinshi yaje don ya d'an watsa ruwa.


Har ya kammala abunda yake Afnan na nan zaune inda ya barta tariga tayi nisa cikin tunani. (Ko me take tunani? Oho)


Kusa gareta ya karasa ya zauna yana karanta damuwar da take tattare da fuskarta, mayafinta ya cire tare da zare d'ankwalin kanta "wannan kayan basu miki nauyi ba? Kinbi kin takura kanki kamar wata bak'uwa, ni kitashi ki bani abinci inci yunwa nakeji" ya fad'a tare da d'ora kanshi kan cinyarta yana lek'en fuskarta.


Abun dariya yaba Afnan, Wanda yace ta bashi abinci kuma shine yayi Kane Kane kan jikinta,


Hancinshi ta ja "toh ka hayemin k'afa taya zan baka abinci?"


Murmushi yayi tare d'agata ya maida kanashi kan gado yana lumshe ido shi kadai yasan yanayin da kamshin turarenta ke sakashi.


Plate da cup ta dauko ta zuba musu naman da suka siyo tare da fresh milk, bata wani ci da yawa ba kasancewar taci abinci gidan Ammie.


Saida suka kammala ta kwashe kayan da sukayi Amafani dasu ta maidasu sannan ta dawo ta dauki kayan baccinta tashiga toilet,


Saida tayi wanka tayi brush sannan ta fito sanye da rigar bacci mai d'an tsawo,


Koda ta fito bata iske Yazeed d'akin ba, turarrukkanta da Ammie ta had'ata mata ta feshe jikinta dasu.


"Toh ko yazeed ba nan zai kwana ba?" Ta fad'a cikin ranta turo k'ofar da akayi yasa ta yi saurin dubawa.


Murmushi ya sakar mata tare da ware hannayenshi alamar tazo,


Nok'e kafad'a tayi tana sunne kai kasa bata Ankara ba taji ya tallabeta ta dorata kan gado yana dariya,


Takardar hannushi ya mik'amata, "gashi inji Yaseer"


Kamar bazata karb'a ba sai kuma ta karb'a ta warware tana karantawa Kamar haka "hak'ik'a ni na kasance butulu mai rama sharri da alkhairi, nasan ban cancanci yafiyarki ba Afnan saboda na cutar dake mafi muninin cutarwa, amma dan Allah ina rokon ki da ki dubi girman Allahn da ya sauya miki da mutum mafi alkhairi a rayuwarki da ki yafe min abunda na aikata a gareki, hakika idan har baki yafe min ba rayuwata tana cikin had'ari, Afnan ki sani ban tab'a son wata 'ya macce a duniya ba Kamar yanda nake sonki kuma ba komai yasa haka ba sai irin yaudararki da nayi tun farko. dan Allah afnan ki yafe min kuma ki tayani rokon Allah da ya sassautamin wannan musibar ta kaunarki. Na miki alkawarin zan tafi nesa dake inda bazaki sake ganina ba har Abada, ina miki fatar alkhairi a rayuwarki.


Yaseer."


Wata irin zufa ce ta karyewa Afnan, magangannun Yaseer sunshiga jikinta sosai, hawaye suka shiga zubowa daga idanuwanta "RAYUWA KENAN" ta fad'a tana shafe hawayen idanuwanta.


Amsar takardar hannunta Yazeed yayi tare da ajiyeta ya janyota ya rungumeta sosai a jikinshi yana lallashinta " dan allah ki yafewa Yaseer Afnan"


"Na yafe mish yaa yazeed Amma bazan tab'a mance abunda ya rabani dashi mafi daraja a rayuwata ba" 


"I will make you forget it I promise" ya fad'a tare da kashe wutar d'akin, bakinshi da nata ya had'e guri d'aya yashiga tsotsarsu tamkar babu gobe, saida ya tabbatar da ya kashe mata jiki, sannan ya rabata da Duk wasu kaya na jikinta ya shiga sarrafata son ranshi. 

Asuba ta gari Yazafnah.


Tunda Yazeed ya tashi yake kallon Afnan dake sharar bacci wani sonta da kaunarta ke k'ara mamaye duk wata gab'a ta jikinshi a hankali ya duk'a tare da sumbatarta sannan ya tashi yashiga toilet yayi wanka tare da doro alwala.


Ruwan hannunshi yashiga yayyarfa mata, bud'e idanuwanta tayi suka had'a ido da Yazeed dake jifarta da wani mayen murmushi, kara dukunkunewa tayi saboda wata irin kunyarshi take ji, "ki tashifa kar lokacin sallah ya wuceki ko sai na tallabeki na kaik?", tanajin haka tayi saurin mikewa dakyar ta shiga toilet tana murmushi.


Koda ta fito har ya kabbarta da alama rakaatanil fajri yayi, da sauri ta sanya kayanta sannan tabi bayanshi ya kabbarta asuba sukayi tare.


Suida suka kare azkar d'insu sannan ya juyo ya kalleta " ina sonki" ya fad'a yana sanya idanuwanshi cikin nata don yaga kalar son da take mishi.


"Ina sonka nimabYaa Yazeed son da ban tab'a yiwa kowa kwatankwacin irinshi ba"


"Harda Yaseer? Ya fad'a yana kafeta da manyan idanuwanshi.


Hab'arshi ta d'aga da hannayenta tana kara sanya idanunta cikin nashi sosai, dan ya fahimce yanda take jinshi a ranta

" ka daina kwatanta son da nakema da Wanda nayiwa Yaseer a baya, kai sonka nake tsantsar so, Yaseer kuwa mayaudaran kalamanshi da kyawunshi suka rud'ani har nayi tunanin sonshi nakeyi Amma zallar son da babu Algussu kai nake yiwa shi"


Kalamanta ba kramin farinciki suka sanyashi ba har baima San lokacin da ya fara kissing dinta ta ko ina ba, cikin kankanen lokaci wasa ta chanja.


Ganin haka yasa na tarkato kayana nabar musu gida don su samu damar kwasar soyayyarsu dakyau da kyau.


Bayan wata biyu aka daura auren daddy da Ammie, farin ciki gurin Yazeed baya fad'uwa.


Lokacin Afnan na fama da yaron cikinta d'an wata d'aya soyayya Yazeed ke nuna mata itada abunda ke cikinta tamkar ba gobe.

Bayan wata Tara ta sumbolu yaronta kyakkyawa sak Kamar ubanshi ranar Suna yaro yaci sunan Abban Afnan, ana mishi lakani da fu'ad.


Haka suka gudanar da rayuwarsu cikin soyayya da kaunar juna.

Tammat bi hamdulillahi.

 Nan na kawo karshen littafina Yazeed ko yaseer Allah ya yafe min kura kuran da nayi a ciki.


Fatan alkhairi ga makarantata Allah yabar kauna nagode sosai da sosai. Sai kun jini a sabon littafina nagaba 


Taku har kullun 

Ayshart one.


Tags: #Betrayal #married #jealousy, hatred.
8159
0
1
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!