Ummu Haydar!

Written by Amrah Mashi APublished on 2018-12-12 14:31:50Category Non-fictionLabari ne a kan wani na'kasasshen yaro da ya tashi tun yana dan shekaru bakwai cutar shan'inna ta kama shi ya zama nakasasshe. Ya samu tsana daga wurin mahaifinsa da sauran mutane. Mahaifiyarsa kadai ke kaunarsa kuma take karfafa masa guiwa a kodayaushe. A karshe ya tabbatar da cewa don kana nakasasshe ba shi ne zai sa rayuwarka ta munana ba. Ya samu daukaka fiye da tunanin kowa. tags: #Musaki #Nakasa #Haidar #NadiyaDuba was labarai »

[2/28, 8:39 AM] Khadija: *º~º~UMMU HAYDAR~º~º*


*Na Amrah ®NWA*


1⃣-3⃣

Tafiya nake cikin hanzari kamar mai shirin tashi

sama. Banci burki a ko ina ba sai bakin wani

tafkeken gida zagaye dashi shukoki ne masu

matuk'ar kyau wanda suka k'ara k'awata gidan.

Sallamah nayi mai gadi ya wage min gate ba tare da

nasan sashen da zan dosa ba, nayi tafiya mai nisa

kafin in isa wani kyakkwan gini wanda da alama

nan ne masu gidan suke.

Nayi sallamah cikin sakin fuska matar gidan ta

amsa min,

Nuni tayi min da wurin zama na zauna, bayan mun

gaisa ne tace min "sai dai kuma ban waye ki ba",

Murmushi nayi nace "ehh dama nasan bazaki gane

ni ba, sai dai nasan bazaki rasa sanin sunana ba,

Suna na Amrah amma wasu sunfi sani na da

Princess Amrah, aiki na kuma shine d'aukan rahoto

domin kaiwa mutane su fad'akartu, su ilimantu su

kuma nishad'antu",

Ina kaiwa nan nayi shiru ina kallon ta, ruwan roba

da lemo mai sanyi ta kawo min, kamar kar insha

sai kuma na daure nasha.

Tace "aikuwa kamar kin san dama ni (fan) d'in ki

ce, ina don novels d'in ki sosai da sosai.

Cike da jin dad'I nace "Allah sarki! Sai gashi kuma

yau nazo har gidan ki da nufin d'aukar rahoto in

bazaki damu ba",

"Babu komai wallah" ta fad'a cikin farin ciki. Mun

dad'e shiru kafin tace "sai dai kuma babu abunda

zaki tsinta a labarin mu face TAUSAYIMMU NIDA

'DANA *HAYDAR*, bazan fad'a miki komai yanzu ba

har sai kin fara ganewa da idon ki",

Dan danan ido na suka kawo ruwa, dan dama

wadda tace min inzo gidan ta fad'a min haka,

Saurin goge hawaye na nayi naci gaba da kallon

*MUSAKIN* d'an ta HAYDAR.

[9:23pm, 19/07/2016] Amrah : *º~º~UMMU

HAYDARº~º~*

*Na Amrah ®NWA*

'Karar mota *UMMU HAYDAR* taji wanda ta

tabbatar da cewa mai gidan ta ABBAN HAYDAR ne

ya dawo.

Tuni farin cikin da yake fuskar *UMMU HAYDAR*

ya kau, fuskar Haydar ta kalla da tuni shima idon

shi ya kawo hawaye zafafa.

Nikam aiki na kallo ne,

A hankali ta taka inda Haydar yake ta goge mashi

hawaye kafin tace "kayi hak'uri Haydar, sanin

kanka ne bana son kukan nan naka, a duk lokacin

da kake yin shi zuciya ta tana k'una sosai",

D'an murmushi tayi tace "ka daina kaji? Komai yayi

farko zayyi k'arshe, bana so ka d'auka tamkar

Abbanka baya son ka ne",

Shiru yayi yana ajiyar zuciya,

Ummu Haydar tace " _oya smile my babe_".

Murmushi yayi wanda bai kai zuci ba, yana yi yana

lek'en k'ofa dan ganin shigowar Abban shi.

Shigowa yayi mai gadi rik'e da jakar shi fuskar shi

babu annuri,

Bai koyi sallamah ba ya shigo d'akin, mai gadin ya

ajiye jakar a kujerar dake kusa dashi.

"Oyoyo Abbana" Haydar ya fad'a cikin maganar shi

da ba'a ko gane ta sai miyau dake dalala daga bakin

shi,

Dak'arfi Abban yayi tsaki ba tare daya kalli Haydar

ba,

"Nadiya ina jin yunwa" ya fad'a cike da tsabar tsana

da tsangwama a fuskar shi.

Sai a lokacin Ummu Haydar tace "sannu da zuwa

Abban Hay..."

Bata k'arasa ba sanadiyyar katse ta da yayi ta

hanyar cewa

"Wai bana hanaki danganta ni da wannan musakin

yaron naki bane? Nace bana so na hak'ura dashi na

bar miki, saboda haka kar na kuma ji kin had'a

suna na da nashi"

Kukan da take k'ok'arin 6oyo ne ya kufce mata, ba

tare da tace komai ba ta nufi kitchen domin kawo

mashi abinci.

[9:35pm, 19/07/2016] Amrah : *º~º~UMMU

HAYDARº~º~*

*Na Amrah ®NWA*

Dafa dukar shinkafa da wake ne ta dafa, _cooler_ ta

d'auko ta d'ora akan _dining table_,

Ta bud'e _fridge_ ta d'auko _jug_ d'in data cika da

_coconut drink_ da yasha madara, yayyanka ayaba

tayi k'anana a ciki tana yi tana goge hawaye.

Bayan ta gama ne ta bud'e _dining cabinate_ ta

d'auko cokali da pilet da ludayin zuba abinci.

Komawa tayi cikin _parlor_ ta shaida mashi ta

kammala had'awa,

Bai ko kalle ta ba ya wuce _dining_ yaci gaba da cin

abincin sa.

Jakar shi ta d'auke takai d'akin shi. _Suits_ d'in shi

ma ta had'a duk takai d'aki. Bayan ta dawo tace

"Ab.."ta rik'e baki sanadiyyar tunawa da tayi da

maganar shi, kuma tasan shi sarai duk abinda yace

zayyi tou fa zai iya yin sa,

"Na had'a maka ruwan wanka idan ka gama" ta

fad'a cikin girmamawa.

Baice mata komai ba ya tashi ya shige d'akin bayan

ya gama cin abinci.

Ganin yabar _arean_ d'akin yasa ta matsa kusa da

Haydar tace "bazan gaji da baka hak'uri ba Haydar,

kayi hak'uri duk kan tsanani yana tare da sauk'I,

haka. ALLAH yace da manzon sa a lokacin da

kafiran makka suka matsa masa "

Kuka sosai Haydar keyi, cikin maganar shi da

Umman shi kawai ke iya ganewa yace "Umma me

yasa Abbana baya sona? Me yasa ya tsane ni

kamar bashi ne ya haife ni ba? Ko dan yana gani na

musaki ne yasa ya tsane ni?",

Saurin dakatar dashi tayi ta hanyar cewa "haba

Haydar! Me yasa kake fad'in haka? Ka tab'a ganin

inda uba zaice baya son d'ansa? Abbanka yana son

ka kuma kar na sake jin wannanmaganar daga

bakin ka".

Tuni kuka yaci k'arfi na, sai yanzu na tabbatar da

maganar Sisi nah Rabee'art Sk, ashe da gaske

hakan tana faruwa, ni duk a tunani na sai a _films_

ko labaran hausa ne ake yin haka, tabbas banda

TAUSAYI babu abunda yake cikin labarin *UMMU

HAYDAR*, kuci gaba da kasancewa dani domin jin

cigaban labarin.

©Princess Amrah

[2/28, 8:39 AM] Khadija: *º~º~UMMU HAYDAR~º~º*


*Na Amrah ®NWA*


4⃣ - 5⃣

Fitowa yayi cikin farar jallabiya mai hula ta hau jikin

shi, babu annuri a fuskar shi bai kuma kalli inda

Ummu haydar take ba, cike da takaici yace "Hajiya

tace min zatazo, saura kuma idan tazo ki mata

rashin kunya saboda wannan MUSAKIN" yana

kaiwa nan ya fita abinsa.

Ajiyar zuciya tayi bayan fitar sa tare da kallon inda

Haydar yake ta saki wani lallausan murmushin daya

k'ara fito da kyawun ta.

Shima murmushin ya mayar mata da alama duk

sunji dad'in fitan Abban Haydar ne.

Fitowa nayi daga inda na lab'e nace "lallai Ummu

Haydar na gani, na kuma shaida da abinda sis d'ina

ta fad'a min,

Yanzu ina so ki bani labarin rayuwar ku, tun farko

har k'arshe idan babu damuwa",

Murmushi ta saki kafin tace "babu damuwa mana,

sai dai kuma kinji yace Hajiyar sa zatazo, ina so

idan tazo ki k'ara fahimtar wani abu kafin na fara

baki labarin",

Murmushin nima na mayar mata nace "babu komai

Ummu Haydar, muje in taya ki aikin",

Haka muka mik'e na taya ta tayi wanke wanke,

girki ta d'aura ma surukar ta lafiyayyar _Coconut

rice da miyar dankalin turawa_, cikn lokaci kad'an

muka kammala, mun fara jerawa a _dining_ne muka

ji sallamar ta, a bayan ta wata budurwa ce ta bazata

wuce shekara 17 ba,

Cikin sakin fuska Ummu Haydar ta amsa sallamar

tare da duk'awa har k'asa ta gaishe ta,

Sai dai kuma abun mamaki sam! Matar tak'I ko

kallon inda Ummu Haydar take, d'ayar budurwar

kuwa sai faman yatsina take tana kallon inda

Haydar yake dan itakam k'yamar sa take.

Ba tare data nuna damuwar ta ba tace "Hajiya anzo

lafiya? Ya hanya?",

"Da banzo lafiya ba zaki ganni ne? Iye tambayarki

nake",

Sunne kanta tayi tare da mik'ewa tsaye ta nufi

_kitchen_ babu kuzari a tare da ita.

©Princess Amrah

[7:09pm, 22/07/2016] Amrah : *º~º~UMMU

HAYDAR~º~º*

*Na Amrah ®NWA*

Tray ta d'auko ta jero lemu _exotic_akai, ta d'auko

k'ank'ara ta zuba akan _tray_ d'in tare da _cups_

guda biyu makimanta.

A gaban Hajiya ta ajiye ta farfasa k'ank'arar ta zuba

a _cups_ d'in sannan ta zuba lemun a ciki, cikin

lokaci kad'an kuwa yayi sanyi.

"Hajiya ku fara da wannan kafin a kawo abinci"

Ummu Haydar ta fad'a cikin girmamawa.

"Wai kekam mun fad'a miki muna da yunwa ne

kome? Sai wani rawan jiki kike kamar wacce muka

fad'awa mun kwaso yunwa, mtsw" Hajiya taja tsaki,

Jiki ba k'wari tabar wurin, sam! Wannan furucin na

Hajiya baisa ta fasa abunda tayi niyya ba, kulolin

abincin ta d'auko tare da pilet da abun zubawa,

A gaban su ta ajiye ta juya zata tafi,

Wannan budurwar ta bud'e abincin cikin raini ta

k'wala mata kira

"Nadiya!",

Juyowa tayi tana jiran kalar rainin da Ummi zata

mata,

"Wannan wane irin k'azamin abinci ne? Wai mutun

da gidan yayan sa amma sai abunda ake so za'a

masa, wama yasan ko kalar wannan sakaran

abincin ne kike ci yasa kika haifo MUSAKIN yaro?",

Maganar Ummi ta soki Ummu Haydar sosai, sai dai

tayi shiru dan jin furucin Hajiya, amma koda Hajiyar

ta bud'e baki sai cewa tayi "daina kallo na

MUSAKIN banza! Kar kasa in amaye d'an abincin

dana ci" tanayi tana kallon Haydar da idon sa ya

cika taf da k'walla.

"Hmmm!" Kawai Ummu Haydar ta fad'a tabar wurin

cike da takaicin abubuwan da kishiyar uwar mijin ta

ke mata, tasan inda uwar mijinta na raye da baza'a

mata haka ba, tou ma miye abun mamaki tunda

shima mijin nawa yayi min? D'akin ta ta koma ta

samu ta fiddo hawayen da take ta 6oyo.

©Princess Amrah

[2/28, 8:39 AM] Khadija: *º~º~UMMU

HAYDAR~º~º*


*Na Amrah ®NWA*


6⃣ - 8⃣

Can tajiyo kukan Haydar sama sama, fita tayi da

gudu dan ganin abunda ya saka d'an ta kuka,

Ganin shi tayi kawai yana ziraro fitsari daga inda

yake, cikin mamaki ta k'arasa kan kujerar da yake

kwance tace "yanzu Haydar fitsari kayi daga

kwance? Me yasa baka kira ni na d'auko maka fo

ba?",

"Umma ina ta kiran ki baki ji ba, shine waccan

Antyn ta jefe ni da makulli tace wai idan banyi shiru

ba zata duke ni wai zata iya yin amai idan ina

magana, nayi k'ok'arin rik'e fitsarin amma na kasa"

kuka ya fashe dashi miyau na fita daga bakin shi,

Kallon Ummi tayi sannan ta mayar da kallon ta ga

Haydar tace "kayi hak'uri Haydar, bazata kuma ba,

tana maka wasa ne",

Cikin zafin rai Ummi tace "au! Ashe gulmata ya

kawo miki dan yasan bana gane yaren sa, tou ai

aikin banza tunda koke bazaki iya dani ba",

Ko a jikin Ummu Haydar ta juya ga yaron ta tace

"kayi hak'uri Allah yana tare dakai, kuma yasan

halin da kake ciki, ba wai dan ya manta dakai ko

baya sonka bane ya barka a haka, shima wanda

yake da lafiyar idan Allah yaga dama zai iya rabashi

da ita".

Cikin haushi Ummi da Hajiya suka mik'e, Hajiya na

fad'in "tou da ubanwa kike? Nan gani nan bari inma

kina nufin mu samu ciwo ne Allah ya fiki",

"Hajiya ni bada ke nake ba ba kuma ba da Ummi

nake ba, magana ce ta gaskiya",

Mari Ummi ta wankama Ummu Haydar amma ta

kasa tab'ukata komai, Hajiya ma marin takai mata,

nan sukaci gaba da dukanta sosai.

©Princess Amrah

[8:30am, 23/07/2016] Amrah : *º~º~UMMU

HAYDAR~º~º*

*Na Amrah ®NWA*

Kafin kace me har sunyi ma Ummu Haydar lilis,

Ummi ke fad'in "duk wanda yaja damu to ko zai

wahala",

Nan suka tafi suka barta bata iya tab'ukama kanta

komai.

Sun d'auki dogon lokaci da tafiya ne ta samu da

k'yar ta tashi ta nufi _Kitchen_ ta d'ora ruwan zafi

ta gaggasa jikin ta, ta fito ta samu Haydar ya

rarraho a hankali yana k'ok'arin binta kitchen,

"Haydar! Me yasa ka sauko? Ina zakaje?" Ta fad'a

a hankali saboda wani irin ciwo take ji jikinta na

mata,

"Umma zan biki ne, nasan duk abunda ake miki

saboda nine Ummah, nasan kafin ki haife ni lafiya

lau kuke zaune da kowa kamar yanda nake ji daga

bakin Abbah a duk lokacin da yaso yayi miki gori,

kiyi hak'uri Ummah kawai mu daure mu nisance su

ko zamu samu sassauci",

Ajiyar zuciya tayi tana wani zazzafan hawaye,

tabbas tasan duk abunda Haydar ya fad'a gaskiya

ne, tou amma idan sun nisance su ina zasuje? Babu

wanda zai iya zama dasu, itama abunda yake hana

ta tafiya kenan koda Abban Haydar ya kore ta.

"Haydar ka daina wannan maganar bana sonta

daga bakin ka, idan muka nisance su Abban ka fa?",

"Ummah tou ai shima baya sona, kinga idan muka

tafi sai yaji dad'in rayuwar sa sosai",

"A'a Haydar, Abbanka yana sonka, ka daina fad'an

haka, kullun ina magaka fad'a me yasa baka ji? Kar

na k'ara ji kaji ko?",

Kai kawai ya d'aga mata ba wai dan ya gamsu da

maganar ta ba.

©Princess Amrah

[8:41am, 23/07/2016] Amrah : *º~º~UMMU

HAYDAR~º~º*

*Na Amrah ®NWA*

Fitowa nayi jiki babu k'wari dan dukan da su Hajiya

sukayi ma Ummu Haydar ba k'aramin tadan hankali

yayi ba, a hankali na iso inda take rarrashin Haydar

na zauna.

Murmushi tayi min irin na k'unar rai d'in nan tace

"Amrah ina fatan kin gani kuma kin fahimci abunda

nake fad'a miki ko?",

"Ehh na gani Ummu Haydar, saura kuma daga bakin

ki" na fad'a ina kallon ta.

Gyara zama tayi tace "yau kam zakiji labari na

insha Allahu",

Bance komai ba sai kallo dana ke binta dashi,

"Sunana Nadiya Umar, ni haifaffiyar jihar Kano ne,

sai dai kuma na tashi cikin rashin gata tun ina

k'arama nake hannun matar abokin baba na

kasantuwar baba na ya rasu kuma tun yana ciwon

ajaliyya ya bada ni ga aminin shi Alhaji Saminu,

Babana mutun ne mai dukiya amma tunda ya rasu

alhaji Saminu ya d'auke ni ban k'ara jin labarin

dukiyar shi ba,

Ansha daru da Mamana kafin ta yarda ta bada ni

dan tasan halin Momy Zee sarai na raini da

wulak'anta mutane, haka ta hak'ura dan tasan a

gaban kowa Baba ya bayar dani.

Na koma gidan Alhaji Saminu ina da shekara biyar a

duniya, tun daga lokacin mamana bata k'ara

waiwaya ta ba, haka nima duk lokacin da zance

akaini wurin mamana sai Momy ta daka mun tsawa

ita da Dady dole na nayi shiru dan ina tsoron su

sosai.

Makarantar gwamnati suka sama min har ana

mamakn yanda babana yabar dukiya mai tarin yawa

amma kuma nake makarantar gwamnati. Haka

rayuwa taci gaba da tafiya har na kammala

_primary school_ na shiga _secondary_ _though_

dai itama d'in ta gwamnati ce amma itakam da

sauk'I tunda tana da kyau. Rayuwa taci gaba da

tafiya haka kowa ya raina ni saboda yanda nake

tafiya makaranta da datti dan momy bata bari na

inyi wanki, amma 'yar ta Deejah mai wankin tama

gare ta, kuma ita _prvate school_ take mai kyau da

tsada.

©Princess Amrah

[2/28, 8:39 AM] Khadija: *º~º~UMMU HAYDAR~º~º*


*Na Amrah ®NWA*


9⃣ - 1⃣0⃣

Wata rana na tashi tun da asubah kamar yanda na

saba ni nake aikin gidan kafin inyi shirin makaranta,

kasantuwar ranar na tashi da zazzab'i mai zafi

yasa na kasa aikata komai, zama nayi sai wani

zazzafan hawaye dake bin kumatu na, a haka har

gari ya fara wayewa.

Deejah ce ta fito sanye da rigar bacci tana ta faman

hamma da alama sai lokacin ta tashi daga bacci,

"Ke kije ki kunna min _heater_ a _toilet_ ki had'a

min ruwan wanka yanzu dan nayi _late_,

Ba musu na tashi a hankali na taka har na isa d'akin

ta, yanda ta umurce ni nayi sai da na gama sannan

na fito na shiga kitchen,

Shara na fara yi kafin na fara k'ok'arin d'aura

kalacin safe, a hankali na ringa yin komai yasa ban

gama da wuri ba har takwas ta wuce Deejah na

jirana ban gama ba, aikuwa nasha masifa sosai

daga wurin Dady da Momy dan basu had'a kowa da

Deejah ba,

Bayan na gama na had'a mata a launch box driver

ya tafi da ita.

Ni kuwa sai lokacin na fara shirin makaranta na

saka _dirty uniform_ d'ina na tafi, da k'afa nayi

tafiyar har na isa makarantar wuraren k'arfe taran

safe.

Da fad'uwar gaba na shiga dan nasan tabbas za'a

tare ni a duke ni _though_ dai na saba da dukan

makara.

Da hawaye na na shiga na samu har an gama tare,

murna nayi na nufi gefen da ajin mu yake, sai dai

kuma nayi rashin sa'a har malamin farko ya fito na

biyu ya shiga, na biyun kuma shine Uncel Hamza

wanda kowa yake jin tsoron sa. Haka na shiga ajin

jiki ba k'wari.

_"Good morning sir!"_ Na fad'a tare da nufan _seat_

d'in mu.

©Princess Amrah

[10:43am, 24/07/2016] Amrah : *º~º~UMMU

HAYDAR~º~º*

*Na Amrah ®NWA*

_"hey come here!"_ Uncle Hamza ya fad'a da k'arfi,

A tsorace na juyo ina rawa jiki ga zazzab'i na

matuk'ar azabtar dani, ga wani Irin ciwon mara da

nake ji.

Gaban shi na isa nayi _kneel down_ hawaye na fita

daga ido na,

Ci gaba yayi da darasin shi har lokacin sa ya k'are,

_"follow me"_ ya fad'a ba tare daya kalle ni ba,

"Nikam na shiga uku yau naga ta kaina ni Nadiya"

maganar dana fad'a kenan a raina,

_staffroom_ ya tafi dani yasa ni rage tsawo na, mun

dad'e a haka kafin wani malami daga gefe yace

"wai kekam bakya gajiya da laifi ne? Ke gaki da

k'ok'ari amma kullun ina kula dake fa banga ranar

da baza'a duke ki ba, in ba'a duke ki kan makara ba

tou za'a duke ki kan rashin tsafta, yanzu dubi

_uniform_ d'in ki kamar ba 'yar _SS 1_ ba",

Kuka mai k'arfi nake ina tuno rayuwa ta a baya,

yanda Baba na da Mamana suka gwada min gata,

ko ina Mamana take yanzu?,

Tsawar da Uncle Hamza ya daka min ce ta dawo

dani, "uban me ya tsayar dake gida sai yanzu

kikazo makaranta?",

Cikin rawar murya nace "wallahi uncle" sai kuma

nayi shiru,

"Wallahi me? In kika min k'arya sai na 6a66alla ki,

ki kuma yi min shiru da kukan nan",

Shiru nayi ina ajiyar zuciya sannan nace "uncle na

tashi da zazzab'i ne da ciwon ciki, shine ban gama

aiki na da wuri ba, kuma da k'afa nake tahowa daga

gida",

"Aikin me kikayi? Ke 'yar aiki ce dama?" Tambayar

da Uncle Chem ya jefo min kenan,

"Ni ba 'yar aiki bace amma kuma ni nake duka aikin

gidan mu, Deejah ce ke hutawa ni kuma kullun aiki",

Sosai Uncle chem ya tausaya min,

(Uncle chem shine _chemistry teacher'n_ su,

d'alibai suka saka masa wannan sunan a dalilin iya

_chemistry_ da yayi, shi kad'ai ne yake kula da

yanayin Nadiya da yanda take zuwa makaranta, ya

dad'e yana neman ranar da zayyi nata wannan

tambayoyin)

©Princess Amrah

[2/28, 8:39 AM] Khadija: *º~º~UMMU

HAYDAR~º~º*


*Na Amrah ®NWA*


1⃣1⃣

"Ita Deejar yayarki ce ko k'anwar ki?" Uncle Hamza

ya fad'a fuskar shi babu annuri.

"Sa'ar haihuwa ta ce, ta girme ni da kwana hud'u

haka mahaifina yake fad'a min kafin ya rasu"

"Babanki ya rasu kenan? Tou a hannun wa kike?"

Uncle Chem ya k'ara jefo min wata tambayar,

Sai dana goge hawayen fuskata sannan na basu

labarin kaf rayuwa ta tun farko har k'arshe, da kalar

wahakar da nake sha a gidan Alhaji Saminu, sunyi

mamaki sosai da na fad'a masu Alhaji Umar Turaki

shine mahaifina dan sun san irin dukiyar da yake da

ita da kuma wadda ya mutu ya bari,

Cikin nadama Uncle Hamza yace "Allah sarki

Nadiya! Ki gafarce ni dukan makara da nake miki

*_A RASHIN SANI NE_* (A novel by Ummul-

Fadeelah) hakan ta faru, inda ace tun farko na sani

da banyi miki haka ba,

Hawaye na goge kafin na tashi nabar _staffroom_

d'in. Na samu _Aunty Food and Nutrition_ ta shigo,

cikin fara'a na zauna dan Ina son _subject_ d'in

sosai kuma ina gane shi, itama kuma tasan haka

yasa idan bata ganni ba take nema na kuma take

sona.

Bayan darasin ta ya k'are ne na shaida mata banda

lafiya mukaje har clinic d'in makaranta akayi min

_blood test_, nan aka shaida min ina da typhoid ne

har 2+, magunguna aka had'a min sosai tare da

bani takardar _permission_ har sai lokacin dana

samu sauk'i, nikam hakan bayyi min dad'i ba dan

nasan zaman gidan banda wahala ba abinda zanyi,

k'asa na koma gida ina yi ina zama hutawa har na

isa gidan,

Tun daga nesa na hango mai gadi ya ri'ke bakin shi

yana jiran shiga ta,

Gaishe shi nayi har na wuce ya kira ni "Nadiya!" Na

juyo da busasshen hawaye a fuska na,

"Me yasa kika dawo lokacin tashi bayyi ba?"

Tambayar daya jefe ni dashi kenan,

Cikin mamaki na dube shi, a raina nace "tou ina

ruwan shi da dawo wa na gida?" A zahiri kuma nace

"banda lafiya ne aka bani hutu har sai na samu

lafiya",

Ajiyar zuciya yayi yace "me kikayi wa Deejah ne

kafin ta tafi makaranta?",

"Ban mata komai ba baba, wani abun ya faru ne?",

"Ba komai Nadiya, shiga gida kawai Allah ya

kyauta",

Shiga nayi cikin gidan ina sauraron abunda zai biyo

baya dan nasan Baba mai gadi bazayyi min

maganar nan a banza ba.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *º~º~UMMU HAYDAR~º~º*


*Na Amrah ®NWA*


1⃣2⃣ - 1⃣3⃣

_Toilet_ na shiga na watsa ruwa sannan na shiga

_Kitchen_, naci karo da sauran doya da k'wan dana

soya aikuwa na d'auka naci sosai sannan nasha

maganin da aka bani a _School clinic_, d'akina na

koma na kwanta ina sauke ajiyar zuciya dan har a

lokacin banji alamun da kowa a gidan ba, hakan ya

bani damar rintse idona cikin lokaci kad'an bacci

yayi gaba dani. Can cikin bacci na jiyo muryar

Momy tun daga nesa tana fad'in "kunga munafukar

yarinya wato tasan abunda ta aikata gashi can tana

bacci, aikuwa yau dole kici ubanki tunda ke

muguwa ce", firgigit na tashi zaune ina tunanin

abunda nayi, a iya sani na nikam tunda gari ya waye

ban san nayi wa wani komai ba, amma da yake

kullun neman laifin d'ora min ake sai banyi mamaki

ba. Shigowa tayi d'akin tana fad'in "uban me kika

saka mana a abinci yau? Gashi kinja mana bala'i

Deejah nacan asibiti tana amai da gudawa, tou

wallahi kema dole ki d'and'ani wahala yau", na

bud'e baki zanyi magana amma momy ta daka min

tsawa ta fice abinta, ban san lokacin da kuka ya

sub'uce min ba, na tuno da abunda ya faru jiya

lokacin da wata k'awar Deejah tazo, nidai naji suna

wata magana banji farkon ba amma daga k'arshe

naji 'kawar tace zai iya sakata amai da gudawa, tun

a lokacin nake tunanin tou menene? Sai na basar

kawai saboda ba abunda ya shafe ni bane. Dady ne

ya shigo shima yana fad'in "dole kije gaban 'yan

sanda kiyi _depending_ kanki, dama nasan kina

bak'in ciki da Deejah saboda tafiki kyau, tafiki gata

ta fiki komai" kallon kaina nayi dan nasan wallahi

nafi Deejah kyau nesa ba kusa ba, haka zalika na

fita diri da gashi, koda nake bak'a ce ni amma bak'i

na mai kyau ne, ina da dogon hanci da k'aramin

baki, ina da dara-daran idanuwa wanda aduk

lokacin da nake kallon Momy takance in daina

kallon ta da mayun idanu na, sannan ina da dogon

gashi har k'ugu na, gani da shape irin wanda

matasa ke kira da _Coca-Cola shape_, ji nayi Dady

na fad'in ku shigo gata nan, so nake kulallasa ta sai

ta fad'a maku abunda ta bama 'yata har take amai

da gudawa. Cikin kuka nake fad'in "dan Allah Dady

kayi hak'uri wallahi bani bace, ban bata komai ba

Allah kuwa, kuma abunda Deejah taci nima shi naci

amma gashi bana yi", "rufe min baki kar na kuma

jin maganar ki, dama zaki yarda kiyi ne? Ita dai da

kike son kashewa zaki mawa" a daidai lokacin 'yan

sanda suka shigo har d'aki na.

©Princess Amrah

[9:09am, 26/07/2016] Amrah : *º~º~UMMU

HAYDAR~º~º*

*Na Amrah ®NWA*

Macen cikin su ce rik'e da ankwa ta saka min, a

cikin raina ina fad'in "kamar dai wacce tayi sata ko

kisan kai?" A zahiri kuwa banda kuka da ban

hak'uri babu abunda nake, sai k'ara tuno da gatan

dana samu daga iyaye na nake, ga wani azabtaccen

ciwon mara da nake ga zazzab'i na nuk'urk'usa ta,

haka suka fita dani inayi ina waigen ko Dady zaiji

tausayi na yasa a sake ni amma ina, ko kallon inda

nake ma baya yi. A bakin _gate_ muka had'u da

Baba maigadi na kalle shi ina fad'in "dan Allah Baba

ka taimake ni, ka fad'a masu wallahi bani bace, bani

nasa Deejah zawayi da amai ba", ina kallon shi ya

goge hawaye kawai ya kad'a kai ya shige d'akin sa,

fitar mu waje naga k'atuwar motar su suka saka ni

a ciki muka tafi. A bayan kanta suka jefar dani a

wulak'ance, na dad'e a ciki har lokacin sallar

azahar yayi, wani dake bakin k'ofar na rok'a akan

zanyi sallah amma fuskar shi babu annuri yace "ki

bari har sai lokacin da aka bada belin ki sannan ki

had'a duka kiyi, nima ba'a bani umurnin barin ki

sallah ba", wani kukan na k'ara fashewa dashi ina

fad'in "wallahi ban saba yin sallah ba'a lokacin taba,

dan Allah ka rufa min asiri ka barni nayi", tsaki

kawai yayi sannan yace "idan baki min shiru ba zan

shigo har ciki in fasa miki baki", jin haka yasa nayi

shiru kaina a k'asa, wannan macen naga tazo ya

bud'e mata ta shigo, tun daga nesa take fad'in

_"Case_ d'in ki babba ne, kinyi _attempting_ kisan

kai ne, yanzu ina so ki bani cikakken bayani akan

abunda ya faru, bana son kimin k'arya, wallahi da

zarar kika min k'arya zan gane kuma kotu kawai

zamu tura ki". Hawayen fuskata na goge na kalle ta

sannan na sunkuyar dakai na k'asa nace "wallahi

yallab'ai ban mata komai ba, abincin da Deejah taci

shi kowa na gidan yaci, Dady da Momy shi sukaci,

hatta Baba mai gadi shi yaci kuma wallahi a kira a

tambaye shi, jiya da yamma wata k'awar Deejah

tazo naji suna fira, tabbas banji farkon maganar ba

kasantuwar ina _kitchen_ a lokacin, sai bayan na

fito ne naji k'awar tana cewa "amma fa zai iya saka

ki amai da gudawa", shiga nayi d'akin a daidai

lokacin Deejah ta daka min tsawa tace "me ya

shigo dake d'akina? Kin san k'azamai basu shigo

min a d'aki", k'awarta mai suna Saudah tace "haba

Deejah! Ashe dai har yanzu baki daina wannan

mugun halin nake ba, yanzu miye a ciki dan ta shigo

d'akin ki? Ba 'yar uwarki bace?", Deejah ta yamutse

fuska tace "Allah ya tsare ni wannan ta zama 'yar

uwata", cikin in-ina nace "dama na gama abinci ne

nazo in fad'a miki ko zakici", "bazanci ba" kawai ta

fad'a a wulak'ance. Saudah tamin murmushi tace

"jeki kawo min ni zanci", nima murmushin na

mayar mata tare da kai mata abincin.

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *º~º~UMMU

HAYDAR~º~º*


*Na Amrah ®NWA*


1⃣4⃣ - 1⃣5⃣

Washe gari yau kenan na tashi da zazzab'i da ciwon

mara, cikin wahalar na tashi na had'a kalaci na

gyara ko ina na gidan sannan a dudduk'e kusan

k'arfe tara na tafi makaranta, ganin banda lafiya

yasa aka bani _permission_ shine na dawo gida,

kuma ko kafin insha magani sai dana k'ara cin

abincin safen amma bai min komai ba". D'aga kaina

da zanyi naga wannan 'yar sandar tana hawaye,

ganin ina kallon ta yasa tayi saurin gogewa tace

"Allah sarki! Insha Allahu zaki fita daga nan, zamuje

asibitin ita Deejah ta kwatanta mana gidan su

Saudah, kinga da shaidar ta kawai sai a kashe

maganar ba sai an shiga kotu ba", ajiyar zuciya na

sauke sannan na mata godiya na fad'a mata ina son

yin sallah, "bari zan dawo yanzu dan nima sai an

bani izini sannan", gyara zaman da zanyi naga

kayana sunyi kaca-kaca da jini, a tsorace na kalli

'yar sandar naga ni take kallo, kuka na fasa da

k'arfi dan bansan ko miye ba, ganin na rikice yasa

ta dawo ta zauna tace min "dama baki fara period

bane?" Kai na d'aga mata dan ban san ko miye

hakan ba, ko a makaranta bani da k'awa barin in

san wannan daga bakin ta, bayani tayi min dalla-

dallah, tun daga yanda zan tsaftace jikina, yanda

zan gyara ibada ta idan inayi da sauran su, fita tayi

ta d'an jima sai gata ta dawo da leda a hannun ta, ta

zauna tace "kiyi hak'uri na jima ko?" Murmushi na

mata da busasshen hawaye a fuska na, bud'e ledar

tayi naga doguwar riga ce bak'a da wando skiny,

sai bak'ak'en pants guda uku, ga kuma ledar pad a

ciki, "nasan baza'a barki kiyi wanka ba" ta fad'a

sannan ta gwada min duk yanda zanyi, na cire

under wear da taimakon ta na saka kayan, wanda

suka b'aci da jinin kuma ta saka a ledar, tace min

"ni zan tafi, sai ki ringa canjin pad d'in akai akai,

gobe da safe koda banzo ba kiyi k'ok'ari kice ma

wancan zakiyi fitsari kije ki samu ko tsarki kiyi ki

canja pad d'in da wando, barinma nasan insha

Allahu zan dawo", godiya na mata sosai sannan ta

tashi ta tafi. Shiru naji har kwana bakwai babu

Madam, hakan yasa hankali na ya matuk'ar tashi, a

raina nace "shikenan itama sun saye ta da kud'i, ya

Allah ka kawo min agaji, kai kad'ai kasan abunda

kake nufi da rayuwa ta, Allah ka fitar dani ya Allah"

kuka sosai yaci k'arfi na, a ranar kuma jini ya

d'auke min, sai dai kuma bazasu barni inyi wanka

ba barin inyi wankan tsarki, haka na hak'ura na

fawwalawa Allah komai, nasan dai inda ace ruwan

hawaye yana k'arewa tou da tuni nawa ya k'are.

Uncle Chem ne tafe ya nufi ajin mu, ganin har a

lokacin ban je makaranta ba suka yanke shawarar

zuwa gidan mu shida Uncle Hamza, sai daikuma

basu san gidan mu ba gashi bani da k'awa barin su

tambaye ta gidan mu, hakan yasa sukaje har

_Office d'in principal_ neman _Address_ d'ina,

saboda a gurin shi akwai _addresses_ na kowane

_student_, nan suka duba na Nadiya Umar kuma

suka samu.

©Princess Amrah

[9:44am, 26/07/2016] Amrah : *º~º~UMMU

HAYDAR~º~º*

*Na Amrah ®NWA*

A bakin _gate_ suka paka mashinan su, sallamah

sukayi Baba maigadi ya nufi k'ofar da sauri,

bud'ewa yayi ganin bak'in fuska yasa shi cewa

"ince dai ko lafiya?", "lafiya lau" Uncle Chem ya

bashi amsa, Uncle Hamza yace "dan Allah nan ne

gidan su Nadiya Umar?", "ehh nan ne" Baba ya

fad'a, Uncle chem yace "dama munzo muji ne ko

lafiya ta daina zuwa makaranta, yau sati d'aya

kenan da taje take fad'a mana batada lafiya", d'an

guntun hawaye Baba ya share sannan yace "ah

lafiya lau babu komai ai", ganin yana shirin b'oye

masu yasa Uncle Hamza yace "kar ka b'oye mana

komai baba, saboda duk halin k'untatawar da

Nadiya take ciki mun sani, ka fad'a mana kawai",

ajiyar zuciya Baba ya sauke sannan ya basu labarin

komai, ba k'aramin tausaya min sukayi ba, aikuwa

ya fad'a masu _Police station_ d'in da nake, can

suka jiyo muryar Deejah tana fad'in "koda kuke

ganin kun san komai kuma a haka zaku fita

rayuwar Nadiya saboda bazaku iya komai ba, Dady

na ya bama 'yan sandan kud'i sosai akan suci gaba

da ajiyar Nadiya har sai lokacin dana bada izinin a

sake ta" tana kaiwa nan tayi murmushin mugunta ta

koma gida. Uncle Hamza ya k'uta sosai yace "ni

kuma insha Allahu Nadiya bazata k'ara kwana ba

acan, ko nawa zan kashe sai nayi yanda ta dawo

gida yau d'in nan". Mashinan su suka hau suka nufi

_station_ d'in da Baba yace ankai ni, koda sukaje

kuwa Madam d'in nan ce a wurin, nan suka shaida

mata suna so su karb'i beli na, itama hawaye tayi

tace "har ga Allah naso na taimaki Nadiya, amma

Oga ya hana ni har yayi k'ok'arin hukunta ni akan

na nace sai na taimake ta, yace karma na sake

shiga harkar ta inba haka ba zan iya rasa aiki na,

hakan yasa na fita sha'anin ta, amma tunda gaku

Alhamdulillah", wurin _Inspector_ sukaje jin Uncle

chem d'an gidan Comarade Alk'ali Abu ne yasa

_Inspector_ ya saurare su, aikuwa ya bashi kud'i

sosai wanda suka ninka na su Dady, nan ya fara

tand'ar lab'b'a yana murmushi.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


2⃣1⃣ - 2⃣3⃣

Haka rayuwa taci gaba da tafiya har yanxu da nake

_SS3,_ wato shekara ta ta k'arshe kenan a

makaranta, nikam a halin yanzu banga sauran wani

aikin wahala da bazan iya yinsa ba, ina tsoron

abunda zai shiga tsakani na da Deejah sosai,

saboda da inyi wa Deejah abu k'wara inyi wa Dady

yafi min sauk'i, saboda abu kad'an zanyi mata

amma ta canja maganar tayi min sharrin da baxan

iya warwarewa ba.

Yau ta kama _Friday,_ ranar da muka kammala

makaranta, a ranar ne kuma Uncle Hamza ya

bayyana min SIRRIN DAKE RANSA, nayi mamakin

jin kalmar so ta fito daga bakin sa, sai dai kuma

idan na tuno da d'awainiyar daya ringa yi a baya sai

inji kuma na daina mamaki, dama tun a lokacin sai

da Ruky tilon k'awata ta fad'a min taga alamar

Uncle Hamza yana sona, har fushi nayi da ita

saboda wannan maganar. Maganar da Uncle Hamza

ya k'ara yi min ce ta dawo dani daga tunanin dana

lula, "ya dai kinyi shiru? Ki bakya sona ne? Wallahi

idan bakya sona bazan tirsasa kiba Nadiya, kina da

damar bayyana min kome kika yanke, zan baki

kwana uku duk hukunci da kika yanke kar kiji haufin

sanar dani, amma ki sani Nadiya na dad'e ina

DAKON SOn ki, ina k'aunarki kuma ina tausayin ki,

amma kuma hakan bazai hana ni gamsuwa da duk

hukuncin ki ba, na barki lafiya" tafiya yayi ba tare

da ya waiwayo ba, haka kawai naji hawaye nabi na,

na rasa ko hawayen miye, ji nayi an dafa ni koda na

d'aga kaina naga Ruky ce tana murmushi tace "ai

dama na fad'a miki hakan kika k'i yarda, ai gashi

yau daya furta da kanshi kinji, nidai shawarar dazan

baki Nadiya ki amince da soyayyar sa, wallahi

uncle Hamza mutumin kirki ne gashi da tausayi da

jink'an na gaba dashi, kin san _neighbors_

(makwafta) d'in mune, nasan duk halin da 'yan

gidan su suke ciki, in banda ra'ayi kuwa babu

abunda zai saka shi koyar wa _(teaching)_ saboda

baban shi mai kud'i ne sosai da duk fad'in jihar

Kano babu wanda baisan da zaman sa ba, ba wai

ina fad'a miki haka dan kiso shi saboda abun duniya

bane, kawai na fad'a miki ne dan kisan koshi waye,

'yan mata da dama suna kai masa tallar kansu

amma yak'i amincewa, mahaifiyar sa kuwa 'ya'yan

'yan uwanta babu adadi data masa tallar su sam

yak'i yarda, ashe ashe dai 'yar kyakkyawar k'awata

yake jira ta gama makaranta" ta k'arasa maganar

tana dariya tana kallona. Dukan wasa na d'aka

mata ina fad'in "tou naji haka nan ki k'yale ni".

Da haka muka gama bankwana da _friends_ d'in

mu. Ni kuma na kama hanyar zuwa gida da k'afa.

Na isa gida a gajiye na samu na cire _uniforms_ d'in

na ina ajiyar zuciya, maganganun Uncle Hamza

dana Ruky ne keta min yawo a kwanya ta. Haka

kawai nayi murmushi tare da fad'in _"I love youh too

my Uncle"._ Wanka na shiga na watsa sannan na

saka tsummokaran kaya na. Fita nayi rai na k'al na

nufi sashen su Momy, har k'asa na duk'a na gaishe

ta amma ko kallon inda nake Momy batayi ba.

Deejah ce ke kallon tv na isa har inda take na duk'a

ina fad'in "sannu da hutawa autar Momy", tsaki ta

min kafin tace "wai ke uban waye sa'anki? Kinzo

kinyi magana mun miki shiru amma hakan bazaisa

ki k'yale muba? Daallah tafi kibani wuri! Kije kuma

ki gyara min d'aki na yanzu", "Deejah kiyi hak'uri

inci abinci wallahi yunwa nake j..." katse ni tayi da

cewa "ina ruwa na da yunwar da kike ji? Kin san

bana magana biyu, kiyi abunda na saka ki ko kuma

ranki ya b'aci yanxu", ba shiri na tashi duk da

yunwar sai dana gyara mata d'akin ta da yayi kaca-

kaca kamar d'akin yara sannan naci abinci.

©Princess Amrah

[5:27pm, 1/08/2016] Princess :

*```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah®NWA*

*Bayan kwana uku.*

Baba maigadi ne ya k'wank'wasa min k'ofa yana

sallamah had'e da kiran sunana, hijabi na saka

sannan na tashi na fita fuskata d'auke da

murmushi, "Nadiya kinyi bak'o yana waje yana

jiranki", cikin mamaki nace "bak'o? Bak'o daga

ina?", "ehh haka yace in kiraki, amma nagane

fuskar sa, mutumin nan ne da suka tab'a zuwa

neman ki har na fad'a masu kina wurin 'yan sanda".

Sai a lokacin na tuna da yau ne ranar da Uncle

Hamza zai dawo, cikin farin ciki nace "tou ina zuwa

Baba". Tafiya yayi ya nufi bakin _gate_ ya shaidawa

Uncle Hamza cewa gani nan xuwa.

Ni kuwa d'aki na na shiga nayi kwalliya na canja

wasu kayan da suma dai tsumma ne, amma sunfi

wanda na cire kyau, tsohon hijabi na daya gama

lalacewa na d'auko na saka sannan na fito. A k'ofar

gida na ganshi zaune bisa wata bak'ar mota k'irar

elentra, riga da wandon wani milk d'in yadi ne jikin

shi da dark brown hula yana latsar waya, sosai

yamin kyau, cikin ladabi nayi sallamah ya d'ago

kanshi cike da farin ciki ya amsa sallamar, na

gaishe shi kenan Dady ya dawo da motar sa zai

shiga gida. Sosai hankalina ya tashi dan nasan yau

kashi na ya bushe, da mamaki sai naga Dady ya fito

daga motar yana gaishe da Uncle Hamza, bayan

sun gaisa ne yace "ka shigo daga ciki mana, ai da

girman ka bai kamata ka tsaya waje ba", cikin

d'aure fuska Uncle Hamza yace "dama kuwa ina

son ganin ka, amma sai nayi magana da Nadiya inji

daga bakin ta, mu shiga daga cikin", anan Dady

yabar motar shi cikin rawar jiki yayi gaba muna biye

dashi a baya, tun daga nesa naga yayi ma Momy

Signal dasu kad'ai suka san abunda suke nufi,

"oyoyo 'yata, ina kikaje ne haka?" Momy ta fad'a

tana kallo na, baya na na kalla dan a tunani na koda

Deejah take, tabbatarwar da nayi dani take yasa

nayi k'arfin halin cewa "naje waje ne Momy", Dady

yace "mu basu wurin zama zasuyi magana ne"

hankalin Momy tashe tayi yak'en dole ta nufi d'akin

ta, Dady ma ita yabi.

Ajiyar xuciya na sauke tare da zama kujerar nesa

da wadda uncle Hamza ya zauna, Deejah ce ta

shigo cikin shigar banza, wando ne _tree quarter_

da wata riga marar hannu kanta babu d'akwali,

hannun ta rik'e da _tray_ ta ajiye a gaban uncle

Hamza, ruwa ne da lemo sai _cups_ a ciki, kaina

d'aure na kalle ta Ina mamaki, "sannu da zuwa

dear!" Ta fad'a tana wata kwarkwasa, "yauwa"

kawai uncle Hamza ya fad'a ba tare daya k'ara

kallom taba, "ya kake ya aiki? Ina fatan ka zo

lafiya?" "Wannan kuma bai shafe kiba, dan Allah ki

tafi ba wurin ki nazo ba" tafiya tayi tana bani wani

mummunan kallo, ni kaina nasan yau sai na yabawa

aya zak'i. D'akin momy ta shiga ashe duk abunda

ya faru akan idon momy da dady ne, shiga sak'e-

sak'e sukayi, su k'ulla wannan su kwance.

"Ina fatan kin gama yanke shawara akaina", cikin

kunya nace "ehh na gama" "tou menene amsa ta?",

kaina k'asa nace "na amince ina sonka", a daidai

lokacin momy ta buga uban tsaki ta koma d'aki

daga lab'en da tayi mana, cigaba mukayi da hirar

mu sosai, anan yake shaida min ya aje koyawarwa

yanzu ya kama _companyn_ baban sa, ashe dama

duk saboda ni ne yasa yak'i daina _teaching_ d'in,

agogon hannun sa ya duba yace "kinga lokaci na

tafiya, shiga kiyo min magana da dady dan bana so

a d'auki lokaci ba'ayi auren nan ba", kunya sosai

naji na nufi d'akin momy, ba kad'an ba na tsorata da

yanayin dana gansu, kowanen su hankali tashe,

"dady yace wai yana son ganin ka" kawai na fad'a

tare da hanzarin barin d'akin.

©Princess Amrah

[5:30pm, 1/08/2016] Princess :

*```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah ®NWA*

D'akin Deejah dake gabana na shiga, ina jin duk

maganganun da yayi da dady, ya shaida masa cewa

zai turo magabatan sa sati mai zuwa akan maganar

auren mu, dan dama shi kawai ake jira a gida. Dady

yayi na'am da maganar shi, cikin sakin fuska

sukayi bankwana ya tafi. Jin alamar ya tafi me yasa

nayi saurin fitowa daga d'akin, nan naji momy na

fad'in "wallahi bazai yiwu ba, waccan k'azamiyar

yarinyar ce zata auri Hamza? Daga baya ta waye ta

nemi dukiyar ta? Kuma duk k'azantar ta shi bai gani

bama, ga auta ta Deejah 'yar gayu wayayyiya

amma bata masa ba, alhaji dole fa ka tashi dan

musan abunyi", dady ya sauke ajiyar zuciya yace

"nikam ban san yanda zanyi ba wallahi, baban sa fa

shine oga na a aiki, kinga kuwa baxan tab'a iya

hana shi auren Nadiya ba", Deejah cikin kuka tace

"dady tun yaushe nake fad'a maka ina son Hamzy?

Ni yanzu bazan tab'a iya auren wani namiji idan

bashi ba, dole ne asan abunyi indai ana son farin

ciki na", momy tayi murmushi tace _"I have an

advice wadda indai anyi amfani da ita ko?

Hmmm...bashi ba auren Nadiya"._ cikin mamaki

duka suka kalle ta, ganin ina kallon su yasa momy

ta daka min tsawa tare da korana daga d'akin, fita

nayi daga nan ban sake sanin abunda suke

tattaunawa akai ba.

Bayan kwana biyu da faruwar haka ne Uncle Hamza

yazo wuri na idon sa jajur kamar yayi kuka, anan ne

yake shaida min cewa Iyayen shi sun hana shi aure

na, ya rok'e su akan su fad'a masa dalili amma

sunk'i, sunce lallai idan 'yan gidan mu yake son

aure tou sai dai ya auri Deejah, shi kuma yace

bazai auri Deejah ba, amma dai sun yarda akan kar

ya auri Deejah da sharad'in nima bazai aure ni ba,

wani kuka naji ya kwararo min, hankali tashe nace

"dama nasan bazasu bar iyayen ka su barka ka

aure ni ba, nasani dama, ya Allah ka sama min

mafita akan wannan gurguwar rayuwa tawa", shi

kanshi kukan ne ya kufce masa, tafiya yayi ba tare

da munyi bankwana ba. Na dad'e a tsaye ban shiga

gida ba, haushi da bak'in ciki cike da raina, ina

murna na kusa samun gata amma yau gashi an

ruguza d'an farin cikin da nake samu, wayyo ni

Nadiya!, Allah ka fitar dani daga wannan kurkukun

rayuwa da nake ciki. Gida na koma na samu momy

da Deejah tsaye a bakin d'aki na suna ta kwasar

dariya harda rik'e ciki suke, bance dasu komai ba

na shiga d'aki na zuciya ta kamar zata fashe.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


2⃣4⃣ - 2⃣5⃣

Haka rayuwa ta zame min kullun cikin bak'in ciki,

uncle Hamzan da nake rage k'unci idan Ina tare

dashi gashi an raba mu. Ni Nadiya na shiga uku, ya

Allah ka min sakayyar muguntar da ake min, Allah

kuma ya bayyana min inda Ummana take. Da

wannan tunanin bacci 6arawo yayi awon gaba dani.

Washe gari da asubah na tashi da wani

matsanancin ciwon kai da k'afa, kaina sosai yake

min nauyi, tunda nake ban ta6a yin ciwon kai irin

shiba, har ido na nake ji yana min nauyi tsabar

ciwon kai, k'afata kuwa da k'yar nake iya d'aga ta.

Haka na tafi sashen su momy da jan k'afa har na

isa a daddafe. Kaina na rik'e na tofa addu'ar ciwon

kai kamar yanda aka koya mana a islamiyya. Haka

na kama aiki na da k'yar da k'yar dan nasan dole

na inyi aikin ko bana so. Na samu na gyara

_corridor_ na share _kitchen_ sannan na tada mai

aiki ta fara had'a kalacin safe. _Parlor_ na shiga na

share shi ina k'ok'arin fara _mopping_ ne na fara jin

jiri yana neman kwasa ta, ban ankara ba naji ni na

fad'i k'asa da k'arfi. Tun daga nan kuma ban kuma

sanin abunda ya faru ba sai dana kwana biyu a

haka, farkawa nayi na ganni akan gadon asibiti

hannu na lik'e da _drip_ ana min k'arin ruwa.

A rikce na tashi zaune ina rarraba ido, gashi dai

tabbas asibiti nake amma kuma babu kowa a tare

dani, sai a lokacin na tuno da bani da lafiya fa ashe,

"tou waye ya kawo ni asibiti?" A iya tunani na nasan

momy da dady baza su iya kaini asibiti domin

neman lafiya na ba. Ga fitsari ina ji na rasa yanda

zanyi in cire k'arin ruwan.

Sallamah naji na d'aga kaina don ganin mai

sallamar, mutumi na gani sanye da _lab coat_

hannun shi rik'e da wasu takardu, cikin sanyin jiki

na amsa sallamar shi ina kallon shi. "Sannu Nadiya!

Kin farka? Ya jikin naki?" A tare ya watso min

wannan tambayoyin. "Jiki alhamdulillah! Naji sau'ki,

amma ina son yin fitsari _please!",_ "ina zuwa" ya

fad'a tare da fita daga d'akin.

Wata _nurse_ ce ta shigo da saurin ta ta iso inda

nake, cire min tayi na tashi nayo fitsarin sannan na

koma makwanci na, har a lokacin ban daina tunanin

wanda ya kawo ni asibitin ba. Bayan ta mayar min

da _drip_ d'in ta fita da sauri kuma sai ga likitan ya

dawo, "yanzu mai kike ji?" Ya fad'a idon shi a kaina,

"kaina yana min ciwo har yanzu, amma k'afan da

sauk'i", gyaran murya yayi sannan yace "amma ke

kuwa Nadiya wane irin tunani kike yi daya haifar

maki da wannan hawan jinin da yarintar ki?" Hankali

na ya tashi sosai nace "dr. Hawan jini?" Kai ya

d'aga min alamar "ehh" yaci gaba da fad'in "ya

kamata in ma kina yawan tunani tou ki daina,

saboda matuk'ar hawan jini yana kada ke k'asa tou

wata rana bazaki tashi ba, irin shi ne yake zama

_paralysis,_ sannan kuma idan ya tsananta ko aure

kikayi kika haihu tou abunda kika haifa d'in zai iya

gadon ki, saboda ana gadon hawan jini, _better_ tun

kafin ya shahara a jikin ki ki janye ko wane irin

tunani a ranki, ki zama cikin farin ciki koda

yaushe", kallon shi nake Idona cike da hawaye "in

zama cikin farin ciki koda yaushe? Taya hakan zata

faru bayan bani da hanyar samun farin ciki?" Tafa

hannu yayi da k'arfi saboda maganar da yake min

amma na nisa a tunani. "Ki yawaita kallon abunda

zai saka ki a farin ciki, ki rage kad'aici, ma'ana ki

ringa zama cikin mutane, koda ace babu mutane a

tare da ke sai ki ringa latsa wayar ki, kiyi _charting,

games,_ da sauran su" (abunda ya kamata masu

cutar hawan jini su ringa yi kenan, yawan kad'aici

yana k'ara masu damuwa a ransu, Allah ya k'ara

mana lafiya ameen).

©Princess Amrah

[6:45pm, 5/08/2016] Princess :

*```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah ®NWA*

"Insha Allahu zan kiyaye dr. Amma waye ya kawo

ni asibitin nan?", murmushi yayi sannan yace "mai

aiki ce ta kawo ki, tamin bayani yanda ta same ki

kwance baki da lafiya, shine wai dama an biyata

kud'in aikin ta a gidan, dasu ne ta kawo ki asibin

nan ta kud'i, tausayin ta naji da wannan bayanin

yasa na kar'bi rabin kud'in na yafe rabi, itace kullun

take zama dake, sai dai bata kwana saboda aiki

yana mata yawa, a bakin ta naji bayanin duk

wahalar da kike sha a gidan, tamin bayanin irin

taimakon da kike mata na aikin da kike taya ta duk

da kema kina da naki aiki, shi yasa itama ta taimaka

miki a lokacin da kike buk'atar taimaka". Hawaye na

share nace "Allah sarki Uwani! Allah ya saka miki

da alkhairi". "Ameen" naji an fad'a daga bakin k'ofa,

na duba naga itace gaba sai baba maigadi a bayan

ta, na sauke ajiyar zuciya fuskata d'auke da

murmushi har suka k'araso. Hannun ta d'auke da

wani tsohon kwano wanda Ina ganin shi na gane na

baba maigadi ne wanda yake cin abinci a ciki.

"Sannu Nadiya, ya jiki?" Uwani ta fad'a, na kalle ta

nace "jiki yayi sauk'i Uwani, nagode da taimako na

da kikayi, Allah ya saka miki da alkhairi", baba

maigadi yace "ameen Nadiya, ai yanda kike

kyautata mana muma dole mu kyautata miki, a

kwanakin nan biyu da bakya nan ji nake kamar babu

kowa a gidan, jiya likita ya mana bayanin ciwon ki

kuma dole ki rage yawan tunani, tabbas nasan kina

cikin damuwa, damuwar da Allah ne kad'ai zai iya

fiddaki, amma kiyi k'ok'ari kina ragewa kinga har

ciwo ya kama ki", hawaye ya bi min kumatu nace

"tou baba Insha Allahu zan rage".

"Tashi kici abinci gashi an kawo miki" tashi nayi na

bud'e kwanon, abinci ne shinkafa da miya amma da

gani had'e-had'e ne, ina tunanin sauran wanda

Uwani taci da sauran maigadi ne suka had'e suka

kawo min. Haka na fara cin abincin kamar mayya

babu ko k'ak'k'autawa har na cinye, ruwa na

d'auka daga cikin ledar nasha sannan nasha

maganin da dr. Ya bani.

Kwana uku aka sallame ni saboda yanda dr. Yaga

na murmure sosai kamar bani ba, saboda nikam

zaman asibitin yafi min dad'i akan zaman gida. Yayi

min gargad'i sosai sannan ya bani d'ari biyar yace

in hau mashin. Godiya nayi sosai sannan na tari

adaidaita na tafi gida.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


2⃣6⃣ - 2⃣7⃣

Da zuwa na d'aki na na wuce na shiga wanka, ban

ma san wani ya ganni ba kawai sai jin masifar

momy da Deejah nayi, Deejah ce ke fad'in "gidan

uban wa kuma ta shiga? Nafa ga shugowar ta da ido

na momy", gyaran murya nayi yadda zasuji ni,

momy tace "ashe kina jin mu shine kika mana

shiru" nan ma dai wani gyaran muryar nayi, "wai ba

dake ake magana bane kike mana wani gyaran

murya kamar mai shirin yin amai?" Deejah ta fad'a

a hasale. Shirun na kuma yi ina sauri domin in fito.

Ban ankara ba naga sun banko k'ofar _toilet_ d'in

sun shigo, saurin kare jiki na nayi a kunyace dan

nak'i jinin wani yagan min jiki, kuka nake sosai

ganin suna janye min hannu suna duka na sosai, da

tsiya suka jawo ni suka fitar daga ban d'akin, hakan

bai ishe suba sai da suka fitar dani daga d'akin

duka, hakan yasa na k'ara fashewa da ihu sosai ina

tittirjewa alamar bazanje ba, basu tsaya ko ina dani

ba sai tsakiyar gida. Deejah sai huci take alamar

gajiya, runtse idona nayi sosai ganin baba maigadi

da driver sun fito suna kallo na. Sosai Deejah ke

dariya tana fad'in "dan uwarki sai inga k'arshen

ciwon k'arya, wato dan ki huta da aiki yasa kika

tsiri ciwon k'arya ko? Tou yau Jimbo zan fiddo in

barshi dake ya yagi rabon shi" tana kaiwa nan ta

nufi d'akin Jimbo tana kiran shi yanda ta saba

mashi idan zata bashi nama ko kifi. Tun ina kuka da

k'arfi har na daina, sai huttai da nake tayi ina ajiyar

zuciya, ganin da gaske take zata saki kare tabarni

dashi yasa baba maigadi saurin shiga gabanta yana

fad'in "haba Khadeejah! Kamar dai baki da hankali?

Taya zaki sakar mata kare bayan kuma kin san har

kashe ta yana Iyayi? Yanzu duk wulak'ancin da

kuka mata bai ishe kuba sai kun mata haka?", cike

da tsiwa Deejah tace "kaga malan ba ruwan ka dani

ka k'yale ni, bana son shishshigi" kauce mashi tayi

tana son isa inda nake, driver ne ya k'ara shigewa

gabanta yace "wallahi ko zan rasa aiki na sai dai in

rasa, amma ina ji ina gani bazan bari ki sakar mata

kare ba" ganin ya d'auke hankalin ta yasa baba

maigadi yazo ya jani ya shiga dani d'akin sa ya rufe

ni ta waje, ina ji tana masu masifa amma ganin duk

sunfi k'arfin ta yasa ta mayar da Jimbo d'akin shi

suka koma ciki suna dariyar k'eta. D'aki na Baba

ya shiga ya d'auko min kaya na da hijabi, ta

window'n shi ya jefo min su yace Idan na gama sai

in mishi magana ya bud'e ni, hakan kuwa nayi. A

ranar dai ji nayi dama ban dawo daga asibiti ba, har

dare yayi ban daina kuka ba, duk jijiyoyin kaina sun

tashi. Ganin tunani bazai fishshe niba yasa na

kawar da komai a raina, da wannan bacci yayi gaba

dani.

©Princess Amrah

[6:55pm, 5/08/2016] Princess :

*```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah ®NWA*

A kwana a tashi babu wuya wurin Allah, yau na

wayi gari cikin murna dan tun dare baba maigadi ya

shaida min yaji a _radio_ cewa jarabawar mu ta fito

duk wanda yasan yayi yaje makarantar su ana

neman sa, sai dana gama aiki na duka sannan

nama momy bankwana, ko kallo ban ishe taba na

tafi da k'afa kamar yanda na saba. Mun gaggaisa da

_classmates_ sosai sannan na isa gurin _exam

officer_ inda ake nunawa, sai da nabi layi kafin azo

kaina, da shiga ta na fad'i sunana aka duba min,

_principal_ dake zaune gefe ya fara gani sannan

yace _"congratulations Nadiya Umar Turaki,

jarabawar ki tayi kyau sosai, kuma kina d'aya daga

cikin mutun goma da wani bawan Allah ya d'auki

nauyin karatun ku a duk inda kuke so, sai dai yace

kar a fad'a maku koshi waye, gobe Tuesday zaki

kawo takardun ki duka sannan ki fad'i inda kike

so",_ farin ciki fal a fuskata nace "alhamdulillah!

Allah ya saka masa da alkhairi ya biya masa

buk'atun sa na alkhairi, _thank youh sir!"_ Fita nayi

hak'ora na bud'e ina jinjina maganar, "kodai mafarki

nake ne" ni kad'ai nake magana ta, "tou waye

wannan da bazai bayyana mana kansa mu masa

godiya ba?" "Gaskiya bazan fad'awa su dady da

momy ba har sai komai ya kankama, idan ba haka

ba kuma zasu iya lalata komai" da wannan tunanin

na isa gida cike da murna, baba maigadi kanshi yayi

mamakin bayyanannen farin cikin dake fuskata.

Washe gari na had'a komai nawa na tafi, na

shaidawa _principal_ cewa _medicine_ nake son

karanta kuma ba sai naje wata k'asa ba, BUK Kano

ma tunda suna yi kawai zan tsaya anan Inyi,

_principal_ yace "Nadiya duk k'asashen nan da ake

karatu cikin sauk'i amma ke nja kike so?" Kai na

d'aga mashi yace "tou babu komai ai, dama Inda

kike so can zaki, insha Allahu nan da wata biyu

zuwa uku komai zai kankama zaki fara zuwa

makaranta, sai kiyi k'ok'ari kamar yanda kika saba

mayar da hankalin ki, banda wasa saboda jami'a

ba'a wasa a cikin ta, sai ki ringa zuwa akai-akai

dan kiji abunda ake ciki" na d'aga kaina na tafi,

anan nabar takardu na na nufi gida.

© Princess Amrah

_pls ayi hak'uri da rashin jina kwana biyu, wallahi

mun koma skul ne banda isasshe tym, sai dai ku

ringa jina akai-akai. youh all my fans_

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


2⃣8⃣ - 2⃣9⃣

*☆☆BAYAN SHEKARA BAKWAI☆☆*

Abubuwa da dama sun faru a cikin wannan

shekarun, ciki kuwa har da zama na cikakkiyar

likitar mata, a lokacim dasu Momy suka samu

labarin ina karaatun likita sunyi k'ok'arin hana ni,

sai dai ganin za'a min santatta yasa naje har

_former secondary school_ d'ina na fad'awa

_principal,_ har gida yaje yayi wa Dady fad'a

saboda dama abokin shine, babu yanda suka iya

dole suka barni naci gaba da zuwa. A tsawon

lokacin ne kuma samari suka fara kunno kai amma

ni basa gabana, karatu na kawai na rik'a.

Alhamdulillah! Yau ne muke _sand-up_ na gama

_medicine_ d'in mu, mun sha kyaututtuka sosai

daga gwamnati, a ranar da muka gama kuwa aka

fara rububin d'aukar mu aiki musamman ma ni dana

fita da _result_ mai kyau a duk cikin mu. A gajiye na

koma gida na kwanta d'aki na ina sauke ajiyar

zuciya, ji nake tamkar a mafarki, wai yau nice na

zama cikakkiyar likita abar alfahari ga al'ummah,

likitan da kowace mace take burin ta zama, dariya

nayi bayyananna sannan na cire kayan jiki na na

saka marasa nauyi. Muryar momy na jiyo tana

fad'in "wato dan uwarki ashe kin dawo shine kika

k'i zuwa ki gyara min d'aki ko?" Murmushi nayi

nace "ayi min hak'uri momy, yanzu zanje inyi"

haushi ya kashe momy, ita a tunanin ta tayi hakan

ne dan inji haushi saboda taganni lokacin dana

shigo gida, tasan dole ina a gajiye, amma sai taga

sab'anin haka. Nikam bata san raina fal yake ba,

banga sauran abunda zai b'ata min rai ba, indai da

sabo ya isa ace na saba da kowace kalar wahalar

gidan. Fita tayi fuuuuuu cike da haushi, dariya nayi

da k'arfi sannan nabi bayan ta.

A bakin k'ofa naji tana fad'awa dady wai tana min

fad'a dan na d'auke ta mahaukaciya ina mata

dariya. Sallamah nayi na shiga cikn ladabi na gaishe

da dady, baice dani komai ba har na shiga na fara

gyaran _kitchen._ Yanzu bani da sauran damuwa

daya wuce in gano inda Ummana take, sai dai kuma

ban san inda zan samu ko labarin taba, wurin dady

da momy ne nake tinanin zan samu labarin garin su

amma banga fuska ba. Hakan yasa na fawwalawa

Allah komai, nidai fatana aduk inda take tana raye.

Da wannan tunanin na gama share-share na koma

d'aki na.

Can na jiyo muryar Deejah ta shigo da motar ta, tun

kafin ta shiga sashen su take fad'in "dady wallahi

malamin nan macuci ne, kaga yanzu ma ya sake

bani wata _carry over,_ shi kad'ai ya hana ni

karb'ar _result_ d'ina, shekara uku kenan ina

gyaran _course_ d'in amma abu ya gagara", dady

ne ya fito jin muryar Deejah tana mishi magana,

"kema dai Deejah ai maganin rashin kunya kenan,

tun _last year_ naje akan maganar ya shaida min

kalar rashin kunyar da kika masa, na samu na rok'e

shi ya hak'ura kuma sai kika k'ara masa wani,

kinga indai haka zakici gaba dayi sai kiyi har karatin

duka ya lalace".

Kuka ta fasa da k'arfi tana fad'in "dady dama nasan

baka sona momy ce ke sona" a shagwab'e ta fad'i

haka tare da bubbuga k'afa a k'asa ta shiga ciki.

Nikam aiki na dariya, a fili nace "maganin mai

rashin kunya da bak'in ciki kenan".

Wanka na shiga nayi tare da d'auro alwalar sallar

la'asar.

©Princess Amrah

[5:19pm, 6/08/2016] Princess :

*```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah ®NWA*

A cikin 'yan kud'ad'en da muke samu a makaranta

dama na samu na siyi waya, na d'unkawa kaina

suturu da dama, duk wani abun da zan na

makaranta dama b'oyayyen mutumin nan yana yi

min, sai dai kuma har yanzu ban san ko waye ba,

tun ina neman sanin shi har na hak'ura.

Wayata naji tana _ringing_ da sauri na d'auka,

muryar namiji naji yace "Dr. Nadiya Umar Turaki,

nine dai wanda na buk'aci d'aukar ki aiki a asibiti

na", ajiyar zuciya na sauke tare da cewa "ok zuwa

ranar _monday_ zan zo asibitin da _credentials_

d'ina insha Allah". Bankwana mukayi na masa

godiya tare da tsinke wayar.

Data na bud'e na shiga facebook, nan kuma naga

sanarwar FMC KANO suna neman ma'aikata. Dariya

nayi nace "sai inda na zab'a", kira ya kuma shigowa

a wayar na d'aga, nan ma dai wani likiya ne da

yake da _private hospital_ ya nunar min da yana so

ya d'auke ni aiki a asibitin sa, shima na fad'a masa

ranar _monday_ zanje wurin shi.

Rayuwa tayi min dad'i saboda yanzu bana bari

Deejah tana zalunta na, duk abinda tayi min sai na

rama sai dai daga baya su tarar min ita da momy su

dake ni yanda suke so, haka zanyi kuka na in share

saboda nasan wata rana sai labari.

Tafe nake safiyar _monday_ rik'e da _credentials_

d'ina _originals,_ sai dai me? Bani da ko sisin da

zanyi _photo copying_ d'in su barin in rarraba su,

hankali na ya tashi ga _trekking_ inayi har k'afa na

tayi ciwo, wata mota ce ta gitta ta gaba na har ta

tafi kuma ta dawo, ban d'aga kaina bama barin inga

ko waye a ciki, _horn_ yamin amma nak'i tanka

masa, ganin haka yasa ya sauke _glass_ d'in

motar, wata sassanyar murya naji yace "Assalamu

Alaikum", nan ma dai shiru na masa naci gaba da

tafiya shima yana bina da motar a hankali, "haba

baiwar Allah! A yanda kike da dattako da kamala bai

kamata a miki sallamah kiyi shiru ba",

Ganin gaskiya ya fad'a min yasa nace "wa

alaikumussalam", "idan babu damuwa zan sauke ki

inda zakije saboda ina son yin wata muhimmiyar

magana dake kuma bai kamata na miki ita a hanya

ba",

"Kayi hak'uri zan tsaida a daidaita in tafi" (Nadiya

da k'arya bayan bakki da ko sisi),

"Dan Allah ki daure ki shigo", jin ya had'a ni da Allah

yasa na karanto addu'ah a raina sannan na zagaya,

a lokacin yayi parking har ya bud'e min k'ofar. Wani

daddad'ar sanyi naji had'e da k'amshi. Rufe k'ofar

nayi nayi shiru ina fuskantar gaba na.

"Nadiya ko?"

Cike da mamaki na kalle shi, bance ce dashi komai

ba sai shine ya datse min tunani na ta hanyar cewa

"kina mamaki nasan sunan ki ko?", kai na d'aga ina

kallon shi, murmushi yayi yace "kusan shekara uku

kenan ina neman ki, tun wata rana da nazo nan

Kano wurin bikin wani aboki na, kasantuwar ni ba

ma'abocin son hayaniya ba ne yasa na koma d'akin

shi a lokacin su kuma suna ta k'ok'arin tafiya _get

together,_ shi d'in ma dai baya so dan bada son sa

ba zayyi auren, iyayen sane suka tilasta shi sai yayi

dan shi yana da wadda yake so, _tv_ na kunna a

daidai ana fira dake a _AIT_ akan cutar _TOILET

INFECTION_ data yawaita ga mata yanzu, bayanin

ki ya burge ni sosai daga k'arshe kika fad'i sunanki.

Tun daga lokacin na kamu da soyayyar ki, so

dayawa nakan shigo kano domin ki kawai in shiga

BUK amma bana ganin ki, kwatsam kuma yau sai

gaki Allah ya had'a mu, ina fatan zakiji tausayi na ki

soni",

Kaina sunkuyar k'asa ina tunani, tabbas ya burge ni

_the way_ yake maganar sa cike da natsuwa, a ido

in aka ganshi _he is a gentle man,_ "sai tafiya muke

baki fad'a min inda zamuje ba" ya fad'a idon shi

kyam a kaina.

"Ka kalli gaban ka malan kar ka kayar damu, _FMC_

zanje", "hmm! Bazan kadake ba Nadiya, taya zan

kayar da abunda na d'auki dogon lokaci ina nema?

Yanzu yanda za'ayi kawai ki fad'a min _address_

d'inki zan neme ki a gida, kinga yanxu har kin kusa

sauka", kai na d'aga a raina ina tunanin ta yanda

zaizo gidan mu, a daidai _gate_ nace ya sauke ni

dan bana so a ganni a mota nida namijin daba

muharrami na ba, da k'yar ya samu da bashi

_number_ na sannan ya tafi idon shi cike da

soyayya ta.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


3⃣0⃣

Ban sha wahala ba na gano inda nake nema, na

shiga da sallamah na gaishe su, manyan mutane ne

a ciki, babu wani layi dan mutun biyu ne kawai a

gabana. Bayan an gama _screening_ d'in akace

muje za'a neme mu karb'ar _offer,_ cike da murna

na kama hanyar gida dan a gajiye nake.

Da shiga ta d'aki sai ga kira ya shigo min, na d'aga

wayar cikin sallamah ta, muryar wannan na d'azu

naji ya amsa sallamar sannan yace "ina fatan kin

koma gida lafiya", "lafiya" na bashi amsa a tak'aice.

_"Am glad to hear that,_ nasan baki gane waye ba",

"ehh" na sake mayar masa da amsa kuma na gane

shine. _"Ok, am Usman Aliyu,_ wanda na karb'i

_numbern_ ki d'azu", "au, sannu yaka koma gida?"

"Lafiya lau Nadiya, ina fatan kin samu nasarah",

"ehh na samu", "barin barki ki huta dan naga kamar

a gajiye kike, _stay cool dear"_ ya tsinke wayar bai

jira abunda zan fad'a ba. Haka kawai na samu

kaina da jin dad'in waya dashi "me zuciya ta ke

nufi? Kar dai tace min ta fara son wanda bata san

asalin sa ba" tambayar da nayi wa kaina kenan.

*☆☆BAYAN WATA BIYU☆☆*

Soyayya mai k'arfi ce ta shiga tsakani na da

Usman, domin kuwa har iyayen shi ya turo sunyi

magana da dady, abunda yasa momy bata hana ba

saboda yazo masu ne da shigar talaka, kuma ni na

bashi wannan shawarar, na samu aiki na har na

karb'i albashi d'aya, sauran asibitin da sukayi

_requesting_ d'ina kuma na basu hak'uri saboda

aikin yawa zai min. Da albashi na na fara saiwa

kaina kayan _kitchen_ masu kyau da tsada ina ajiye

a d'akin baba maigadi dan bana so su momy su

gane. Deejah kuwa shekara bakwai da watanni

kenan tana _degree_ amma ta kasa k'arasawa.

Magana mai k'arfi ta kankama, maman Usman da

kanta take kira na muna gaisawa tana kuma bani

hak'uri akan zaman rayuwa saboda Usman ya bata

labarin halin da nake ciki.

Ba'a wani d'auki lokaci ba aka saka ranar auren

mu, Usman da kanshi ya neman min _transfer'n aiki

daga FMC KANO TO FMC KATSINA,_ kuma yace

baya so a kaini da kayan d'aki saboda yana da

komai a gidan shi.

Ranar da aka kawo min lefe ne asiri ya tonu,

saboda akwati saiti biyu yayi min masu tsada sosai,

kayan lefen kuwa duk _super_ da manyan _laces_

ne, takalma da jaka duk masu tsada, momy taji

bak'in ciki sosai ita da Deejah amma saboda basu

da yanda zasuyi dole suka hak'ura. Ranar aure

kuwa babu wanda aka gayyata, da k'yar dady ya

zama mad'aurin aure na, lokacin da za'a tafi dani

kuwa Momy, dady da Deejah suka tarar min suna

fad'in "kuma tunda abin na k'arya da munafusrci ne

basu so su sake gani na a gidan su, babu su babu ni

har abada" nasha kuka sosai har motar d'aukana

tazo, abun takaici babu ko d'an rakiyar amarya

haka muka isa Katsina ta dikko d'akin kaaraa.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


3⃣1⃣

A bakin wata tangamemiyar _estate_ muka tsaya,

mai gadi ne ya bud'e tare da fad'in "barkan ku da

zuwa", "yauwa barka, wane _road_ ne na su Usman

Aliyu? Wanda za'a kai amarya yau?", cikin

girmamawa _gateman_ d'in yace "wallahi ban sani

ba, _inshort_ ban ma san Usman d'in ba, amma

barin tambayar maku Sani gashi can xaune",

matsawa yayi inda Sanin yake ya tambaye sa, bai

dad'e ba kuwa sai gashi ya dawo yace _"Mashi

road ne, house number 14",_ godiya _driver'n_ ya

masa tare da jan motar.

A daidai k'ofar gidan yayi _parking,_ babban gida ne

an mashi haraba da wani kyakkyawan gini daya

banbanta shi da sauran gidajen. _Horn_ yayi mai

gadi ya bud'e masa _gate,_ ya shiga da motar ya

_parka_ ta adaidai inda aka tanadar domin

_parking_ _(parkin space)._

Muryar mata naji da k'arfi suna gud'a suna fad'in

"tou ga amarya ta iso", wata mata ce naga ta fito

sai faman yatsina take ta iso har bakin motar, dan

har a lokacin ban fito ba.

fiddo ni tayi tare da d'aga min mayafi na tace "ba

laifi" a yatsine.

Mata da yawa suka fito suna fad'in "sannu da zuwa

amaryar Usy" wata mata mai matsakaicin jiki tace

da _driver'n_ daya kawo mu "ina sauran motocin

'yan kawo amaryar? Ko basu iso bane?",

Take naji gabana ya fad'i, wani hawayen naji a

fuska ta nayi saurin sharewa, a raina ina tunanin

"ya zanyi in fad'a masu ni kad'ai aka kawo babu

kowa?" Muryar Usman naji yace "ni nace bana

buk'atar kowa ya rako ta, saboda amarya ta kawai

nake son gani",

Duka matan wurin suka k'yalk'yale da dariya, wata

daga cikin su tace "wai nikam Usman yaushe ka

b'aci da rashin kunya ne?" Dariyar ya mayar mata

yace "ai gaskiya tace, idan suka zo zasu takura

mana ne".

Ajiyar zuciya na sauke tare da jin wata irin kunya

kamar zan nitse katsa. Da haka suka shiga dani

cikin gidan. Na dad'e a tsaye bakin k'ofa ina

karanto addu'o'i kamar yanda addini ya koyar mana,

sai daga baya na shiga da k'afar dama kaina a rufe.

A _parlor_ wasu 'yan mata ne guda biyu da alamar

tsarakin juna ne, cikin sakin fuska d'ayar ta taso

tana fad'in "sannu da isowa Aunty'n mu, yau dai

zanga Nadiyar nan da Ya Usy ke mana wulak'anci

saboda ita" jaana tayo har wani _bedroom_ yana

fuskantar wani, a mai kallon gabas d'in ta kaini ta

cire min mayafi na, _"wow! So cutey,_ ashe da

gaskiyar yaya da yake fad'in baturiya ce ya aura"

bata rufe baki ba sai ga d'ayar budurwar babu fara'a

a fuskarta ta kalle ni ta tab'e bakin ta tace "ehh da

sauk'i kam" sai a lokacin na k'are mata kallo naga

tayi min kama da wannan matar wadda ta jawo ni

tana b'ata fuska.

Mai sakin fuskar ce tace _"please_ ki saki jikin ki

sosai Aunty" murmushi na sakar mata ina kallon

tsabar kamar ta da Usman, daka ganin ta 'yar

d'akin su ce wadda yake fad'a min sunan ta Zainab

suke kiranta da Futha.

Sune basu tafi ba har dare, duk sauran matan suka

watse aka barmu mu uku, itakam d'ayar budurwar

da naji an kira da Ummi in banda _charting_ d'in ta

babu abunda takeyi. Futha kam bakin k'ok'arin ta

take shirya ni, wata _drawer_ naga ta bud'e ta fiddo

da wani sabulu mai kyau, take k'amshin shi ya

had'e d'akin, mik'o min shi tayi na karb'a tace

"Momma ce tace in baki hannu da hannu, tace ki

ringa wanka dashi idan ma ya k'are zata aiko miki

da wani", "tou nagode, dan Allah kimin godiya wurin

ta", "yanzu kije kiyi wanka kinga har duhu ya fara,

daga nan sai kiyi alwala dan kar kiyi kwalliya ta

b'aci" kamar yanda tace d'in nayi, wanka nayi na

d'auro alwala nayi sallar magrib. Bayan na gama ne

ta jawo wani babban _kit_ akan _mirror_ ta zaunar

dani, wani mai ne ta shafa min mai _soft_ k'amshi

sannan ta sake shafa min wani _creamy

foundation_ a fuska, _brush_ ta d'auko daga _kit_

d'in ta fara kwantar min da ita har sai data kwanta,

"dama yaya yace min _number one_ ce daidai

fuskar ki, gashi kuwa ta miki kyau" nidai aikina

murmushi ne, wata _foundation_ d'in ta sake shafa

min akan waccan take na fito kamar wata jar

balarabiya abunka da dama ni jar fata ce, nan taci

gaba da lakuce lakucen ta wani abun ma ban san

sunan shiba dan dama can niba ma'abociyar

kwalliya bace. _Black liner_ ta fiddo daga _kit_ d'in

tace "yadda kike farar nan ai dole sai dai black d'in,

idan _brown_ ne bazai fito ba sosai" (hakan ya

kamata Idan zakiyi kwalliya, idan ke fara ce tou kiyi

_eye brow black,_ idan kuma bak'a ce ke sai kiyi

_brown)._ _Pink lips stick_ ta shafa min bayan ta

saka _mouth concealer._ Take na fito d'as dani

kamar wata _celebrity._

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


3⃣2⃣

Gashi na dana nad'e da d'an k'aramin _ribbon_ ta

warware, a _drawers_ d'in _mirror'n_ ta sake fiddo

da _bands_ manya masu kyan gaske, wata 'yar

kwalba mai kyau ta fiddo ta a jiki an rubuta _"hair

freshner"_ ta feshe _bands_ d'in dashi, mayuka

masu k'amshi ta shafa min sannan ta fesa

_freshner'n_ a gashi na ta nad'e da _bands_ d'in.

"Kalli kanki ki gani" ta fad'a fuskar ta d'auke da

murmushi. Kallon kaina nayi nace _"wow! Futha

makeover kenan, kamar bani ba"_ dariya tayi sosai

sannan ta nufi _wardrobe,_ wani _yellow lace_ ne

marar nauyi amma da zarar ka mishi kallo d'aya

zaka tabbatar ba k'aramin _lace_ bane, alkyabba ta

sake fiddowa irin wadda ake yayi marar nauyi

_transparent_ yadda za'a iya ganin kayan ciki idan

mutun ya saka, "ummi mu bata wuri ta canja kaya"

Futha ta fad'a tare dayin gaba. Ummi ta kalle ni tayi

tsaki sannan tabi bayan Futha. Tun a lokacin ne

nace "wannan ummin kuwa bata da hali" kayana na

saka ina jinjina kyawun kayan da yanda suka amshi

jiki na kamar dama angwada ni. Bayan na saka na

d'aura d'ankwali na yayi kyau sosai sannan na

d'aura alkyabbar. A lokacin har lokacin sallar isha

yayi, hijab na saka na gabatar da ita sannan nayi

addu'ah na cire hijabin. Koda na gama naga Futha

zaune tana kallo na kafin tace "wallahi Aunty kinyi

kyau sosai", "hmm! Futha ai kece kika fiddo da

kyan ko?" Dariya tayi tace "a'a Aunty dama can

kina da kyan ki".

Nan mukaci gaba da fira har tara tayi, bayan na

feshe jiki na da turaruka iri iri na fara jin sallamah

daga nesa ta muryoyin maza, gaba na ne ya fad'i

dan nasan su Usman ne suka shigo. Muryar sa naji

yana fad'in "ke Ummi me kuke da baku tafi gida ba

har yanzu?" Abokin sa Abdul ne yace "tou zaka fara

rashin kunyar taka ko? Dawa kake so abar amaryar

idan basu zauna ba?" Nikam murmushi nayi jin

Futha na fad'in "shifa Ya Usy kamar kanshi farau

yin aure", "a'ah Futha ina jin kunyar ki fa, angon

nawa kike fad'a ma haka?" Na fad'a ina mata

dariya, "yo Aunty ai shima d'in ne bashi da kunya

tun da ya fara maganar aure" ban bata amsa ba jin

sallamar su a _bedroom_ d'in da muke ciki. Futha

ta amsa sallamar bayan ta rufe min fuska ta da

hular alkyabbar.

"Amarsu ta ango" Abdul ya fad'a yana murmushi,

Raheem ne yace "amarya bakya laifi koda kin kashe

Futha auta ne", "yaa Raheem zaka fara ko?" Futha

ta fad'a a shagwab'e, dukan su suka kwashe da

dariya harda Usman. "Auta ai dama kin san duk

muka had'u sai na tsokane ki tun da kece kika ja

hakan" Raheem ya fad'a yana kallon ta. "Ya Raheem

tou kai yaushe zakayi auren? Ko sai ka tsufa ka

zama tuzuru ka rasa matar aure?" "Ke dai da

k'wak'war cin kazar amarya bazaki ci ta ba gida

zamu tafi daku yanxu" Raheem ya sake fad'a dan

yana so ya k'ular da Futha ne.

Addu'ah akayi duka d'akin sannan suka mana fatan

alkhairi, Futha tace min _"good night Aunty, may be

gobe idan za'a kaimu School zamu biyo tanan mu

gaishe ki",_ murmushi na mata tare da rik'e hannun

ta nace "ai nayi zaton anan zaki kwana Sister na"

dariya suka d'auka su duka tare da fita na kalli

bayan su har suka fita.

Sun jima kafin naji alamar Usman ya dawo, ya rufe

k'ofar _parlor'n_ sannan ya shigo. _"Huhhh! Am

tired wallahi"_ ya fad'a tare da cire babbar rigar sa

yabar ta cikin. _"Besty tashi muyi sallah"_ ya sake

fad'in "ko sai na tashe ki?" Saurin tashi nayi lokacin

har ya isa bakin _toilet_ d'in. Bayan yayi alwala ya

fito sannan nima na shiga na d'auro tawa.

Shi yaja sallar kamar yanda sunnah ta gabatar

mana, yayi min tambayoyi akan tsarki da komai

bakin gwargwado na bashi amsa. Wata babbar leda

ya jawo yace "nasan bakici komai ba, ga wannan"

"na k'oshi" na bashi amsa. "Wallahi sai kinci shi kin

ji na rantse, _better_ ma ki fara ci ko ni kike so nayi

_feeding naki?"_ Jin hakan yasa na fara ci kad'an

kad'an har na gama.

Gado ya hau ni kuwa nayi kwanciya na akan

_carpet,_ ina jin shi yana dariya yace "ki dawo nan

mana, koni zan biyo ki k'asan?" Shiru na mishi, jin

shi nayi ya sauko ya kinkime ni ya dire a gado yana

fad'in "a daren nan nake so a samar min Aliyu

HAYDAR d'ina" yana dariya.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


3⃣3⃣ - 3⃣4⃣

Sarrafa ni ya fara yi ta wasu hanyoyi da bazan iya

fassara suba, tun ina iya tab'uka wani abu har nayi

shiru ina sauraren ikon Allah, a wannan daren ne

Usman ya samu farin cikin shi a tare dani, yasa min

albarka sosai tare da kyaututtuka da ban iya rik'e

wasu ba. A daren nan dai sai da ya biya buk'atar shi

sau hud'u bai gaji ba, nikam banda kukan

shagwab'a babu abunda nake. Da asubah da kanshi

yayi min wanka ya gasa ni, a daddafe nayi sallah

Usman kuma ya tafi masallaci, a inda nayi sallar

nan baccin wahala ya kwashe ni, nice ban farka ba

sai k'arfe goma na safe. Usman ne idon shi kyam

akaina, bayan na gaishe shi ya amsa cikin sakin

fuska yace "su Futha sunxo tun d'azu da _break

fast_ lokacin da zasu tafi makaranta, ni na hana su

tashe ki dan naga kin gaji da yawa", kukan

shagwab'a na fashe dashi "ai kaine kasaka min

gajiyar", "tou yi hak'uri *UMMU HAYDAR* bazan

kuma ba ai, kinga inda rabo ma Haydar d'in mu

_may be_ yana nan ajiye" ya shafa mara ta tare da

kashe min ido d'aya.

"Ya kaje ka karya kafin inyi wanka" na fad'a tare da

nufan _toilet,_ "ai nine zan miki wankan bana so ki

wahala" "a'a yaya nidai na gode maka, yanzu zan

fito baran dad'e ba" ban jira amsar shiba na shige

_toilet_ na datse ina ajiyar zuciya. Ban wani jima ba

na fito d'aure da d'an k'ramin _pink towel,_ da wani

_hand towel_ kuma wanda na yafa a kafad'a na,

kaina kuwa na rufe shi da _shower cap_ dan bana

son ruwa ya shige shi. Na same shi har a lokacin

yana zaune akan sofa yana latsar wayar shi. "Yaya

baka nufi _break fast d'in ba?"_ Na fad'a ina kallon

_mirror._ _"No_ ke nake jira, bazan iya karyawa ni

kad'ai ba dole sai dake, _and pls_ bana so kina kira

na da yaya, nafi son ki kira ni da Abban Haydar

kamar yanda nake kiran ki da Ummu Haydar, babu

abunda Alhajin mu yafi so kamar yaga anyi masa

takwara, ni kuma na d'auki alwashin _first born_

d'ina insha Allahu *HAYDAR* ne", "hmm! Tou Allah

ya kawo mana mai albarka" na fad'a a lokacin da

nake bud'e _wardrobe._ _Holand vlisco_ ce na fiddo

_red_ da manyan flowers fari da bak'i, an mata

d'inkin _half gown_ da zani _wrapper,_ d'inkin

_stone works_ ne mai kyau sosai. Idon Usman a

kaina har na saka _inners_ sannan na fara d'aura

zanin na saka rigar, d'ankwali na d'aura yayi kyau

kamar gwaggwaro, na saka sark'ar _fashion red_

da d'ankunnen ta, _simple make up_ nayi amma ba

k'armin kyau nayi ba. _Treajar perfume spray_ na

fara feshe jiki na dashi sannan na fesa _nutt_ a

kayana, na juyo na kalle shi har a lokacin bai daina

kallo na ba. "Na gama Abban Haydar sai muje muyi

_break fast_ ko?", "ai ni najini ma na k'oshi, wannan

kwalliya haka kamar mai shirin zuwa gasar

sarauniyar kyau?" "Yaya ka cika tsokana wallahi,

nidai muje mu karya nasan _you are hungry",_ tashi

yayi yana gaba Ina biye dashi dan ban san inda

_dining_ yake ba.

©Princess Amrah

[2:15pm, 8/08/2016] Princess :

*```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah ®NWA*

Babban _basket_ ne cikin shi da _coolers_

makimanta, ta farkon na bud'e naga dankali da kwai

ne da _plantain,_ d'ayar kuma miyar kwai ce mai

hanta da k'oda, taji _curry_ k'amshi sai tashi yake,

sai kuma _flask_ d'in ruwan zafi da kayan _tea_ a

leda. Nayi _serving_ d'in mu yana bani ina bashi har

muka k'oshi, na kauda kayan na wanke su sannan

na fara share sharen ko ina, Usman ya zagaya dani

duka gidan na k'ara ganin irin tsaruwar shi, har da

gefen shuke-shuke an k'awata sh da _flowers_

masu kyan gaske, ga kujeru guda biyu irin wanda

akeyi na _cement_ d'innan, abun dai ba'a cewa

komai.

Wuraren k'arfe uku na rana na fara jin hargowar

Futha, naji dad'in zuwan su sosai _though_ dai

Usman yana tare dani bana tare da kad'aici,

rungume ni tayi tana fad'in "sannu Aunty, ya

kad'aici?"ta fad'a bayan ta sauka daga jiki na.

"Lafiya lau Futha, d'azu Abban Haydar ya fad'a min

kinzo ina bacci, ya _school_ d'in?" "Alhamdulillah

Aunty, Momma tace tana gaishe ki", "ina amsawa

insha Allahu anjima da dare zamuje da Abban

Haydar in gaishe ta", sai a lokacin na kula da Ummi

dake yatsina fuska tana kallo na, batayi min

magana ba sai nice nace "sannu Ummi ya karatu?"

"Lafiya" kawai ta fad'a bayan ta ajiye _basket_ d'in

abincin data d'auko.

Sun dad'e sosai har wurin la'asar sannan suka min

bankwana, nace "Futha _pls_ ku tsaya har dare sai

mu mayar daku", Futha tace "eyyah Aunty akwai

islamiyya ne yanzu, amma insha Allahu ranar

_Friday_ zanzo na muku yini", _Kitchen_ na shiga

na had'o wancan kayan na basu, har bakin _gate_

na raka su sannan na dawo ciki.

Da dare kuwa na sake wani wankan na saka bak'ar

abaya mai kyau na yafa d'an kwalin ta. Tafiya

mukayi marar nisa sai gamu bakin wani

tangamemen gida mai kyau da tsari.

Mun shiga gidan na gaishe da Mommah mace mai

kamala da mutunci, ban dad'e ba kuma sai ga

maman Ummi ta fito fuskar ta cike da tsana ta

zauna daga gefe, "Hajja ga Nadiya fa sunzo gaishe

mu" Momma ta fad'a ranta sake. K'asa na koma na

zauna nace "Sannu da fitowa Hajja! Ina yini?"

"Lafiya" ta fad'a ba yabo ba fallasa. Nikam a raina

nace _"like mother like daughter kenan"_ Momma

tace "koma kan kujera ki zauna mana Nadiya! Ni

bana son d'ari-d'arin nan fa da kike, nafi so ki

d'auke ni tamkar mahaifiyar ki ba uwar miji ba" baki

na washe sannan na koma kan kujerar na zauna.

Mun dad'e tana jana da fira ita da Futha kafin daga

baya Abban HAYDAR yace in tashi mu tafi, kamar in

ta zama a wurin Momma naji, amma babu yanda na

iya dole na tashi, wata 'yar kwalba k'arama Momma

ta kawo min tace "ga wannan 'yata, miski ne _pure

one_ babu had'i a cikin sa", karb'a nayi na mata

godiya sannan nabi bayan Abban Haydar da shi

harma ya isa bakin mota, Futha ta d'ago min hannu

bayan nashiga motar muka kama hanyar gida.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


3⃣5⃣

Haka rayuwa taci gaba da tafiya tsakani na da

Abban Haydar soyayya mai k'arfi ke k'ara shigar

mu, yana son na haifa mashi yaro namiji kawai dan

ya saka masa sunan baban shi. Sai dai akoda

yaushe nakan yi masa nasiha akan ya barwa Allah

zab'i saboda shine yafi mu sanin daidai, amma sam

nasihar bata shigar shi.

Yau ta kama _Monday_ tun da safe na fara shirin

zuwa wurin aiki dan na fara zuwa tun sati biyu da

suka wuce, amma tunda na tashi nake jina jikin duk

babu dad'i ga kasala data mamaye ni, a hakan na

gama shiri a lokacin Abban Haydar ma ya gama

shirin tafiya aiki, bayan mun karya ne yaganni duk a

kasale yace "Ummu Hayar me yake damun kine

yau? Naga kamar bakya lafiya", "na tashi da

zazzab'i da ciwon kai ne, ina so inje asibiti ne in yi

awon jini" na mayar mashi da amsa.

A raina ina tunanin ciki ne dani dan na fahimci

hakan, amma dai nafi so na fara gwaji idan ya

tabbata sannan na mashi albishir. Bayan mun gama

duka na tsaftace wurin sannan muka fita. A _FMC_

ya fara sauke ni sannan shima ya wuce aikin sa. Da

kaina nayo fitsari na auna sai gashi kuwa zahirin

ciki ne a jikina na sati biyu, sai dana tottofa wa cikin

addu'ah nayi hamdala ga Allah, ranar dai ban zauna

_Office_ ba dan kasalar k'aruwa kawai takeyi na

kasa aikata komai.

Da dare nake ma Abban Haydar albishir da cikin da

yake jiki na, yayi farin ciki sosai kafin yace "Allah

dai yasa namiji ne ba mace b..." Shiru yayi

sanadiyyar rufe masa baki da nayi, nace "haba

Abban Haydar! Bana son kana wannan furucin, da

namiji da mace ai duk d'aya ne a wurin Allah, mudai

fatan mu Allah ya bamu mai albarka", shiru kawai

yayi bawai dan ya gamsu da abunda na fad'a ba. Da

haka har lokacin kwanciya yayi bai kuma yi min

magana ba, ganin hakan yasa na bashi hak'uri da

kalamai masu dad'i tare da saka masa farin ciki har

ya hak'ura da fushin da yake.

Washe gari ya kira Momma yake shaida mata, tayi

farin ciki sosai ta kira ni, cikin kunya nake amsa ta

har mukay bankwana tace zata turo Futha ta dawo

wuri na saboda ta ringa taimaka min da aikace

aikacen gida.

Hakan kuwa akayi, Futha ta dawo gida na da zama,

tana nuna min soyayya sosai tamkar k'anwa ta ta

jini, bata bari na aikin komai, dama kuma sunyi

hutun gama WAEC kafin su fara NECO, idan na tafi

aiki ma itace take komai.

Sannu sannu har ciki na yakai watan haihuwa, na

d'auki hutu daga wurin aiki na koma zaman gida

kawai nake, sai dai duk bayan kwana biyu ina fita

da k'afa ina d'an _exercise._

Kwance nake ina cin d'anyar dabino (tana saka

sauk'in nak'uda sosai), naji ciki na ya fara

murd'awa tare da mara ta kamar zan mutu, "Futha!"

Na fad'a a hankali cikin zafin ciwo. "Na'am Aunty!"

Cikin sauri ta shigo d'akin.

"Kira min Abban Haydar da sauri mu tafi asibiti"

wayar ta ta d'auka ta kira shi, in banda sannu babu

abunda take ce min cikin tausayi, har da hawaye

takeyi dan yanda taga ina murd'e murd'e dole aji

tausayi na, dan danan sai ga shi ya iso, sungumata

yayi yace "Futha ki d'auko duk abunda ya dace ki

hau _keke napep_ ki same mu a _Alheri Clinic",_ bai

jira amsar taba ya fice dani yakai mota muka kama

hanyar asibiti.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


3⃣6⃣

Da zuwan mu aka karb'e ni ban kuma sanin inda

kaina yake ba, likita yace Abban Haydar yayi

_signing_ dan dole sai an min aiki bazan tab'a iya

haihuwa da kaina ba, haka yayi _signing_ d'in cikin

tausayi aka shiga _theater room_ dani, sunyi bakin

k'ok'arin su suka fitar min da jaririya mace.

A lokacin su Momma duk sun hallara suna jiran

fitowa dani, sunyi farin ciki lokacin da sukaji an

fiddo da jinjira kuma lafiyayya banda Abban Haydar

daya had'e fuska shi a dole baiso na haifi mace ba,

Momma tace ya shigo yaiwa yarinyar hud'uba

amma sam yace bazai shiga ba wai ya bar min ni

inyi tunda mace iri na na haifa, duk sunyi mamaki

da abunda ya fad'a, amma ni banyi mamaki ba dan

nasan dama hakan sai ta faru indai na haifi mace.

Kwanana uku aka sallame ni, sai dai har a lokacin

bai san ya fuskar yarinyar take ba, nikam ina son

abata tunda nina haife ta na kuma san wahalar da

nasha a lokacin dana haife ta, ranar suna yarinyar

taci sunan Momma (Saudah) a ranar kuma yarinyar

ta amsa kiran mahaliccin ta. Nayi kuka sosai babu

wanda bai tausaya min ba, Abban Haydar kuwa

farin cikin shi ya nuna zahiri.

Sai dana warke tas sannan na koma aiki Futha ma

ta koma gida, tsakanin mata da miji sai Allah, ya

lallab'a ni na hak'ura tare da yafe masa duk abunda

ya faru.

Rayuwa taci gaba da tafiya ina aiki na ina kuma

farantawa Abban Haydar rai, sai dai ko kad'an bai

canja k'udurin saba, tun ina magana har na gaji na

fawwalawa Allah komai dan Abban Haydar yayi nisa

baya jn kira.

Haka na kuma samun wani cikin Futha ta dawo gida

na, tun cikin nada wata biyar na d'auki hutu daga

wurin aiki, dan ina so in kula da _baby_ na sosai.

Lokacin haihuwa yayi aka sake yi min wani _cs_

d'in, nan ma dai macen ce aka fiddo min, abunda ya

faru a baya yanzu ma dai shine, dan na yanzu ma

har yafi wancan, har magana ya daina yi min, ranar

dana cika uku da haihuwa kafin a sallame mu

yarinyar ta amsa kiran Ubangiji, tace mana ga

duniyar nan mu zauna itakam tayi gaba sai mun iso.

A nan fa na fara tunanin anya kuwa lafiya ta lau?

Haka muka bar asibitin jiki babu k'wari, Hajja kam

cewa take "haka zaku k'are kuna kukan mutuwar

jarirai, ni ina ganin indai haihuwa kuke so kawai

Usman ya k'ara aure hakan zaifi maku". Babu

wanda yace mata komai ta k'arace surutan ta ta tafi

Ummi tabi bayan ta.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: : *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


3⃣7⃣

Abu wasa ba wasa ba sai da nayi haihuwa hud`u

duka mata amma babu wacce ta zauna, hankali na

kullun cikin tashi yake musamman yanda Hajja ke

yawan kira na da mayya mai cinye jarirai, a duk

lokacin da zatayi wannan maganar momma na

kwab'ar ta akan ta daina amma bata bari. Futha

kam ta samu miji har an saka ranar auren su, a gida

na ta dawo ina kula da ita ina koya mata wasu

abubuwan duk da bana cikin farin ciki domin Usy

yana yawan yimin gori wai na kasa haifa masa d`a

namiji.

Kwance nake akan _three seater_ ina latsar waya

Ummi a gefe na tana _controlling d'in remote,_

sallamar Hajja da Momma mukaji, cikin k'arfin hali

na tashi saboda laulayin cikin da nake, har k'asa na

gaishe su Futha ma ta gaishe su, momma ce kawai

ta amsa Hajja kam ko kallo ban ishe ta ba, _dining_

na tafi na d'auko masu ruwa a _water dispenser_

na sako a _plate_ na kawo masu, Momma ta fasa ta

fara sha, bud'ar bakin Hajja tace "nikam bazan sha

ruwan da dangin mayu suka kawo ba, duk labarin ki

fa Nadiya cike yake a tafin hannu na, duk mayyar

data iya lashe yaran data haifa ai sai muyi ta kan

mu da ita", kuka na fashe dashi nace "wallahi

Hajja..." Ban k'arasa ba naji muryar Usman yace

"wallahi me? Ta miki k'arya ne? Kin kasa haifa min

yaro namiji ki sama min farin ciki na, kin kasa cika

min buri na".

Momma tayi saurin dakatar dashi tace "haba

Usman! Me yasa kai ka girma amma baka san ka

girma bane? Matar taka kake fad'awa haka? Ai sai

ka kaita inda ake siyo yaro namiji ta siyo idan akwai,

shashashan banza da wofi!".

Juyowa tayi gare ni taga har a lokacin kuka nake

sosai, kusa dani ta dawo ta rungume ni tsam tana

bubbuga baya na kamar k'aramar yarinya, mun

dad'e a haka kafin tace "kiyi hak'uri ki daina kuka,

kuma wannan cikin da yake jikin ki insha Allahu mai

zama ne, ina ji a jiki na zaki haifi d'a namiji a

wannan karen, ki daina kukan nan kici gaba da

fawwalawa Allah lamurran ki, shine kawai yake da

mafitar da zai fitar dake",

Cikin mamaki na d'ago na kalli Momma, a raina

nake tunanin ya akayi tasan akwai k'aramin ciki a

jiki na? Lallai ma Momma.

Murmushi tayi min ganin nayi shiru sannan taci

gaba da fad'in "zamuyi tafiya zuwa India nida

Baban ku gobe insha Allahu, zamu gano kanwar

mahaifiyar sa ne da akayi wa aikin mahaifa amma

bazamu dad'e ba zamu dawo, nazo ne na miki

bankwana kuma in k'ara jaddada miki akan ki k'ara

wayar da Futha akan yanda zatayi rayuwar aure,

dan har yanzu Futha yarinya ce na kula bata san

komai ba".

Na amsa mata da "insha Allahu momma zan wayar

da ita komai, idan ban koya mata ba waye zai koya

mata? Kar ki damu sai ma ta fini sanin komai".

Murmushi momma tayi tace "bana haufin ki 'ya ta,

Allah ya baki ikon cikawa".

Da farin ciki dai muka rabu muna masu fatan sauka

lafiya, Usman dai tunda momma ta masa fad`a yayi

fushi ya tafiyar sa bai ko tsaya sunyi bankwana ba,

ina matuk'ar mamakin halin Usy, ace wai har da

mahaifiyar sa ma fushi yake da ita idan ta masa

fad'a, wannan sam ba halin kirki bane kuma mai

iriwan wannan halin Allah zai hukunta shi ranar

gobe kiyama.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


3⃣8⃣

Washe gari tun da safe momma ta kira ni, ta shaida

min suna _airport_ yanzu jirgin su zai tashi, na mata

fatan alkhairi ta k'ara min naseehohi sosai akan in

kara hak`uri da halin Usman saboda

*MAHAK`URCHI* mawadaci ne, mukayi bankwana

na kashe wayar. Haka kawai na samu kaina da

fad`uwar gaba, Futha ma ta fahimci hakan ne yasa

ta tambaye ni dalilin canjawar da nayi, na fad`a

mata kawai babu komai.

Abban Haydar ne ya shigo fuskar shi babu annuri,

caraf na mik`e nace "Abban Haydar wai me kake

nufi dani ne? Babu ruwan ka dani ka fita harka ta,

shin ni na hana ma kaina haihuwar namiji ne ko

kuwa? Haba Usman , bai kamata da ilimin ka kana

haka ba, kuma ina son shaida maka yanzu haka ina

d`auke da juna biyu, sai mu dage da addu'ah wata

k`ila anan zamu dace", tsaki kawai yaja yai tafiyar

sa, Futha dake zaune gefe tace "gaskiya Aunty

Nadiya kina hak`uri wallahi, nikam inda ni miji na

yake wa haka da tuni mun rabu, nifa bazan iya

d`aukan wulak`ancin d`a namiji ba", murmushi na

mata nace "ban so jin wannan furucin daga bakin

kiba Futha, komai namiji zai miki ya kamata kiyi

hakuri kar ki dauki wani mataki akan sa saboda

aljannar ki tana k`ark`ashin sa, kuma duk abunda

zai miki Allah yana ganin sa kuma zai miki sakayya,

duk wanda yayi hak`uri a rayuwa tou daga k`arshe

shine mai cin riba, zaman aure hak`uri ake da juna

dan dama ba lallai mutun ya samu yanda yake so

ba".

Jikin Futha yayi sanyi tace "haka ne Aunty, Allah ya

k`ara bamu ikon hak`uri da juriyar ko wane salon

wulak`ancin maza".

"Ameen" na fad`a tare da nufan _kitchen_ domin

d`ora girkin rana.

Dambun alkama da miyar zogale nayi da taimakon

Futha, na had`a _mango juice_ da k`ank`ara na juye

a _jug,_ na fiddawa Abban Haydar nashi daban

sannan na zuba mana nida Futha mukaci muna

santi, sosai muka kwashi abincin har ya k`are.

K`oshin da nayi yasa na hau bisa _carpet_ na jawo

_throw pillow_ na kwanta, Futha ta kunna _tv_ ta

fara k`ok`arin kai _NTA,_ cikin haushi nace "wai

kekam bakya gajiya da kallon labarai ne? _Please_

ki barmu mu huta haka".

"Aunty idan kika saba da kallon _news_ bazaki iya

dainawa b....",

Shiru tayi a dalilin wani mummunan abu da aka

nuno, jirgin sama ne ya jirkice sai wuta keci a cikin

shi, cikin kid`ima nace "INNA LILLAHI WA INNAA

ILAIHI RAAJI'UN, anya kuwa wannan za`a fidda mai

rai a cikin sa?",

Futha ido cike da hawaye tace "gaskiya bana

tunanin akwai mai rai Aunty, kiga fa wuta keci kuma

an kasa kashe ta",

Mu duka kuka muke sosai kamar mun san mai zai

biyo baya. Kwatsam aka nuno mai labaran yana

fadin "INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN, an

samu labari akan mummunan hatsarin jirgin daya

auku akan hanyar _Nigeria zuwa India,_ shidai

wannan jirgi ya taso ne daga jihar kano zai tafi

_India,_ anyi bakin k`ok`arin fitar da mai rai a ciki

amma abun yaci tura, kamar yanda kuka ga jirgin

yana ci da wuta tou a haka aka same shi kuma har

yanzu bai daina wutar ba, ya ku al`ummar musulmai

wannan bayin Allah suna buk`atar addu`an ku a

halin yanzu, idan akwai wanda yake da masaniya

akan mutanen cikin jirgin sai ya garzayo nan domin

d`aukar gawar d`an uwan sa, da zarar wutar ta

gama ci zaa fiddo su idan zasu fiddu, k|arshen

rahoton kenan, Abdullahi Alhassan Jigawa..."

Zumbur na kashe _tv,_ ji jake tamkar a mafarki ne,

juyawar da zanyi naga Futha ta zube tamkar bata

numfashi.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


3⃣9⃣

Na rasa yanda zanyi na nufi Futha ina bubbuga ta

amma shuru bata tashi ba, waya ta na d`auka na

danna kiran Abban Haydar tai ta _ringing_ bai

d`auka ba, sai dana masa kira goma har tayi

_ringout_ shiru, zama nayi na buga tagumi kusa da

Futha, wani zazzafan hawaye na fita daga ido na.

Mun d`auki tsawon lokaci a haka har kusan awa

biyu Futha bata farka ba, naci gaba da kiran Abban

Haydar _still_ dai bai _picking_ ba, shawara kawai

na yanke dan nufan Tudun wada gidan su Usman in

fad`awa Hajja, takalmi na saka na jawo hijabi na

zira zan fita, sallamar Abban Haydar naji, take naji

hankali na ya d`an kwanta, cikin kuka nake sanar

dashi abunda ya faru, da k`arfi ya fasa kuka tamkar

k`aramin yaro yana fad`in "ALLAHUMMA AJIRNI FI

MUSIBATI, WAKHLIFNI KHAIRUN MINHA". Bai sake

bi takai na ba naga ya fita waje yana kuka da

_key'n_ mota a hannum shi, "zan bika Abban

Haydar" na fad`a ido jajur alamar nasha kuka, bai

bani amsa ba sai jinjina kanshi da yayi, hakan yasa

na fahimci yana nufin zaije dani, a daidai nan kuma

Futha ta tashi, tare muka tafi da ita. A hanya ya kira

wani abokin shi da yake aiki a _NTA branch d`in

Kano,_ ya mishi bayani sosai yace gawawwakin

duka suna _Aminu Kano international Airport._ Nan

muka k`ara tabbatar da gaskiya ne.

Tafiya muke sosai da gudun gaske, babu mai cema

kowa komai sai dai da an kalle mu za`a ga tashin

hankali k`arara a fuskokin mu, da haka muka isa

babban _airport_ d`in Aminu Kano dake cikin birnin

kano.

A lokacin kuma muka k`ara shiga wani tashin

hankalin, ganin yanda mutane ke fitowa da gawar

`yan uwansu suna koke koke, istighfari kawai nake

ina nemawa su Momma gafarar Allah. Da haka

muka shiga inda gawarwakin suke, mutane ne sunfi

karfin dubu biyu, wasu za`a iya gane fuskar su

wasu kuma sun k`one sosai baza`a gane su ba.

Abban Haydar yayi ma masu wurin magana, aka

bamu damar mu duba gawar ko Allah zai sa mu

gane su, a hankali muke duddubawa har muka

gama zagayawa duka babu Baba babu Momma, sai

da muka duba sau uku amma bamu gansu ba, har

mun hak`ura jiki babu k`wari zamu tafi can naci

karo da warwaron Mommah wanda ta sai mana ni

da ita da Futha, da saurin na isa wurin gawar, sai

dai kuma fuskar ta k`one sosai da jikin, hannun ta

mak`ale da na wani namiji da shima ya gama

k`onewa, hakan yasa muka tabbatar da Baba ne.

A tsorace nace "Mommah! Me yasa kika tafi kuka

barmu? Kun sani muna da buk`atar ku a halin

yanzu, yau saura sati biyu bikin Futha, pls kar ku

mutu!!!"

Fad`uwa nayi tun daga nan ban kuma sanin abunda

yake faruwa ba.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


4⃣0⃣

A hankali na bud`e ido na da k`yar saboda

kumburin da yayi, kalle kalle na farayi dan ina

tunanin a inda nake, caraf na dora su akan *Dr.

Rafiq* dake gyara min _drip,_ ganin na farka yasa

Futha ta taso da sauri tana min sannu, na amsa

mata tare da fad`in "Futha pls ki fad`a min mafarki

nake Momma da Baba basu rasu ba",

Kuka yaci k`arfin Futha ta kasa furta komai, cikin

tausayi dr

Rafiq yace "pls ku daina kukan nan bashi da wani

amfani, hasali ma sai ciwo da zaku k`arawa kanku,

haba Dr. Nadiya, bai kamata a matsayin ki na likita

kina samun wannan abun ba, yau fa kwanan ki biyar

kenan a haka, kinga yanzu jinjirin da yake cikin ki

zai iya samun lahani a dalilin haka",

Sai a lokacin na tuna ma da ina da ciki, maganar sa

bata sa nayi shiru ba sai ma wani kukan da na sake

fashewa dashi jin da gaske ne sun rasu.

Kwana na uku da farkawa aka sallame ni, Ahmad

wanda zai auri Futha yazo ya duba ni, nan yake

sanar damu cewa iyayen shi sunce a k`ara wata

d`aya ko biyu kafin auren su, _may be_ kafin nan

mun k`ara warwarewa da rashin su mommah.

Munyi na`am da maganar shi, bai tafi ba sai da yaga

mun sake sosai muna hira har yamma.

Da dare muna kwance kowa da abunda yake

sak`awa, sallamar Abban Haydar mukaji biye dashi

Hajja ce da Ummi ko wacen su fuska ba annuri, na

gaishe su na masu gaisuwar rashin da mukayi,

daga nan kuma yake shaida min wai su Hajja sun

dawo nan gidan anan zatayi takaba saboda bazata

ji dad`in gidan su ba dan bata saba da rashin su

momma ba, tabbas a raina naji babu dad`i dan

nasan halin ummi batta da dad`in zama, amma

babu yanda na iya dole in hakura in bisu har sanda

zasu koma gida.

Daren ranar dai haka na kwana da juyayin rashin su

momma da kuma tunanin irin zaman da zamuyi da

hajja da ummi, nasan bazamu ji dad`in su ba, a

raina nake tunanin wai ma yaushe Usman ya fara

shiri da hajja? A iya sani na dai baya son hajja

saboda munafurcin ta, haka kuma baya shiri da

ummi saboda bata da kunya bata k`yale kowa ba

har shi usman d`in.

Ganin har ukun dare na kasa bacci yasa na d`auro

alwala na fara salloli ina fad`awa Allah damuwa ta,

sai a lokacin na tuno da furucin Dr Rafiq cewa abun

ciki na zai iya samun matsala, na kuma gasgata

hakan saboda akwai wata da mukayi wa aikin

haihuwa da irin haka ta kasance, saurin kawar da

tunanin nayi naci gaba da addu`o`i har asubah tayi

na tashi Futha tayi sallah.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


4⃣3⃣

*NOTE*

*kuyi hak'uri na rashin jin posting d'ina for a long

time, hakan ya faru ne bisa wani dalili tsayayye, ina

fatan zaku kar'ba uzuri na, Amrah mai son

kyautatawa fans d'in ta ne a koda yaushe, yanzu

kam zakuci gaba da jin posting lokaci lokaci, but not

kullun kullun fa (lol)*

*****************

Haka muka k'araci zaman asibitin Abban Haydar

bai K'ara zuwa ba har aka sallame mu, Futha da

mijin ta Ahmad ne kawai ke ziyara na kullun. Yau ma

kamar kullun Futha tazo ta rik'o min kular abincin

da kullun take kawo min, tana zaune aka kawo min

takardar sallamah saboda na warke sosai a halin

yanzu.

Nan muka fara haramar kwashe kayakin mu,

Ahmad ta kira yazo ya d'auke mu a motar sa.

Bayan mun shiga gida muka samu Usman kwance

a three seater yana kallon news, kamar in share shi

kuma sai na tuno da addinin musulunci ya bamu

umurnin idan ka samu mutun a wuri tou fa kai ne

zaka masa sallamah, hakan yasa na masa

sallamah tare da gaishe shi amma ko kallon inda

nake bayyi ba, Ya dai amsa sallamar amma bai kula

ni ba wai a cewar sa baya so Ya kalle ni wata k'ila

ko musakin yaro na yana hannu na.

Haka muka k'araci wannan yinin har Futha ta tafi,

wannan irin zama wai har ina? Ace kana zaune da

mutun amma bai San darajar kaba? Ina amfanin

zama da Usman? Nikam inda zai sawwak'e min da

yafi min sauk'i Akan wannan wahaltaccen zaman,

tou amma Idan na rabu dashi Ina zanje? Wa nake

dashi a halin yanzu? Dady da momy dai sunce kar

in kuma waiwayar su, kuma ma yanzu yanda nake

jina da dai in koma Kano tou gwara in kama gida in

zama na ni kad`ai zaifi min sauk`i.

Kwance nake tunani kala kala a raina, muryar sa

naji yana cewa "gobe za'a kawo ragon sunah,

amma ki sani, matukar kika tara mutanen suna to

kece da hawalar nauyin su, dan ni nan ban ga abun

tara mutane ayi taron suna ba" yana kaiwa nan ya

fice ya bar ni, Haydar rik`e a hannu na ban san

lokacin da na fashe da kuka ba, wasu irin zafafan

hawaye na fita daga ido na, a iya rayuwa ta ban

tab'a ji ko ganin tab'arb'ararrar rayuwa irin wannan

ba, ko a fina finan hausa ko littattafai ban tab'a ji ba,

mutun ya haifi d`a amma yafi kowa tsanar sa.

Washe gari da safe kuwa sai ga rago madaidaici an

shigo dashi ta bayan gida, ina zaune ina bama

Haydar nono naji sallamah a dak`ile, daji ko ba`a

fad`a min ba nasan Hajiya ce, amsa sallamar nayi

tare da gaishe ta cikin girmamawa, bata amsa

gaisuwar ba sai neman wurin zama da tayi, "sannu

Hajiya, a kawo abinci?" Nan ma dai shiru tamin

babu amsa, "ga Haydar d'in, sai dai kuma yanzu na

cire masa diper kar ya miki fitsa..." ban gama fad`a

ba naji ta d`auke ni da marin daya mugun rikitar

dani, "miye dalilin marin Hajiya? Me na miki?" Na

fad`a hannu na dafe da kumci na, "wannan shine na

farko kuma ya zama na k`arshe da zanzo ki nemi

had`a ni da wannan *musakin,* tou wallahi ahir d`in

ki, matuk`ar yau na kwanta na kasa bacci sai na

wulak`anta ki, inji uban da ya tsaya miki" cikin

k`arfin hali nace "haba Hajiya! Ki sani bafa ni na

d`ora ma Haydar kalar halittar shi ba, haka shima

Haydar d`in ba shine ya d`aura ma kan sa ba, Allah

a hakan yaso ganin shi shi yasa ya bar shi hakan,

kuma da kike ganin shi a haka baki san kalar ranar

da zai miki nan gaba ba, indai kin san wulak`anci

zaina kawo ki gida na tou kar ki kuma zuwa tun da

ba kece kika haifi Usman d`in ba, na tabbata inda

umman Usman bata rasu ba bazata tab`a tsanar

jinin Usman ba, kema kuma dan ba jinin sa bace

yasa kike kiran sa da *musaki,* shiru shiru fa ba

tsoro bane Hajiya, kuma kar ki k`ara mari na dan

wallahi idan kika k`ara zakiyi mamakin abunda zan

miki" mamaki k`arara a fuskar Hajiya tace "ai da

kike fad`an dan ba jini na bane me yasa shi Usman

d`in daya haife shi yafi kowa tsanar sa? Wato ke

kin samu wuri har kin fara min wulak`anci ko? To

sai na nuna miki halin Katsinawa" shiru nayi dan

bani da abun cewa, nasan tabbas gaskiya Hajiya ta

fad`a babu Wanda yakai Usman tsanar Haydar.

Usman ne ya shigo fuskar shi babu annuri, koda

ganin shi kuwa Hajiya ta fasa kuka tana fad`in

"yanzu Nadiya ni kike cema ba jinin Usman bace?

dan kin ga ba ni na haife sa ba? Har ki iya d`aga

hannun ki ki mare ni kawai dan nak`i d`aukar

Haydar?" Tana kaiwa nan tayi shiru tana jiran

hukuncin da Usman zai d`auka, nikam mamaki yayi

min yawa, murmushi kawai nake ina tunanin

makirci irin na Hajiya, ashe dai gaskiyar marubuta

ne da suke yawan nuna mana hakan, ni duk a

tunani na dad`in rubutu ne kawai yake saka su

fad`in hakan. Kyakkyawan mari Usman ya wanka

min wanda ya dawo dani daga tunanin dana lula.

©princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


4⃣4⃣

"Nadiya dama baki da hankali baki da tarbiyya?

Yanzu hajiyar ce kika fad`awa munanan kalamai har

kika iya d`aga hannun ki kika mareta? Baki san

matsayin Ummah na gareta ba? Wallahi na rantse

miki matuk`ar hakan ta sake faruwa sai kun bar

gidan nan keda *musakin* d`anki, kuma ai gaskiyar

Hajiya ne dan tace bazata d`auki Haydar ba, koni an

fad`a miki zan iya d`aukar sa ne? Ki kiyaye ni

Nadiya" kuka sosai yaci k`arfi na, ban san ya zanyi

in fad`a masa sharri Hajiya tamin ba, nasan Usman

yayi nisa baya jin kira. Kafin in ankara na duba

Usman har ya shiga d`akin shi, dariya sosai hajiya

ta kece da ita, "Nadiya kenan! Ba`a ja dani wallahi,

kad`an kika gani daga halaye na, idan baki bi sannu

ba sai nasa an fitar dake daga gidan n.." bata gama

fad`i ba Usman ya fito, tayi sauri ta juya maganar

tace "ai banice na miki fad`an ba da zaki nemi ki

huce a kaina in danni ne ma yanzu zan tafi, kinga

tafiya ta" ta kama hanyar barin gidan. Lallai

makircin hajiya makirci ne, Haydar kawai na d`auka

na ruga d`aki na cike da takaici na haye gado na

had`a kai da guiwa sai cizgar kuka nake. Ina cikin

kukan ne Futha tazo, ta tambaye ni dalilin kuka na,

ban b`oye mata komai ba na labarta mata,

murmushi tayi tace "kad`an daga aikin Hajiya

kenan, haka take mana lokacin da Dady da Ummah

suna raye, sharri kala kala take k`ulla mana kuma

dake karfar baka gare ta sai su yarda, akwai lokacin

da tama yaya Usy wani sharri da girman shi Dady

ya mare shi, saisa nace gaskiya hajiya ta asirce

yaya Usy ne, kin san kalar tsanar daya mata a baya

kuwa? Amma wai yanzu shine har da dukan ki

saboda ita, kiyi hak`uri Aunty Nadiya, komai yayi

farko zayyi k`arshe, insha Allahu akwai ranar dana

sani, ranar da duk zasu nema a wurin ki keda

Haydar, kici gaba da rainon d`anki, ki cire duk wata

damuwa a ranki, Allah yana tare dake"

Sosai naji dad`in kalaman Futha, koba komai ta

k`ara kwantar min da hankali, murmushi na mata

tace "ya maganar suna? Gobe ne ko?" "Bazanyi

taron suna ba Futha, duk wanda yazo zaiji tsoron

Haydar ne, ni kuma saboda haydar zan iya fad`awa

mutun maganar da zata b`ata masa rai, kawai abar

taron sunan",

Futha tace "hakane Aunty, Allah yasa hakan yafi

zama alkhairi" "ameen" na fad`a cike da jin dad`in

soyayyar da Futha ke gwada min.

Sai dare Futha ta tafi, nikam har a lokacin ban k`ara

fitowa koda parlor ba, tunanin wulak`ancin da

Usman zai min idan na fito nake dan tunda hajiya

tamun sharri ban kuma fita ba, abinci ma futha ce ta

girka, dama kuma Usman ya daina cin girki na wai

saboda yana ky`amar Haydar.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


4⃣6⃣

Cikin kwana uku Futha ta samo min `yar raino, naji

dad`i sosai saboda nasan yanzu kam zan samu

sauk`i in ringa zama wurin aiki, ga yanzu ana

samun patients sosai a asibiti, musamman ma

yanda nake gaenicologist, duk fad`in FMC katsina ni

kaid`ai ce gaeny, kuma mafi yawan mata sun fi son

mace ta duba su.

Ranar da `yar rainon ta fara zuwa tare muka tafi

aiki, sai dai yanda naga zahirin tsoro a tattare da

fuskar ta, banyi mamaki ba dan ba itace ta farkon

da take tsoron halittar Haydar ba, da k`yar ta iya

d`aukar sa lokacin da muka isa asibitin, ina kallon ta

yanda take d`auke fuskar ta idan ta kalle shi, baby

bag d`in shi na bata wadda take d`auke da tissue,

feeder, handky, da sauran su, nace mata ta kula

dashi sosai, albashin ta duk wata naira dubu biyar

ne, na kuma shaida mata idan yayi kuka ta kai min

shi ina office d`ina, na gwada mata office d`in.

*

Kwanan Nafee (Nany d`in Haydar) uku a gida na

neme ta na rasa, hankali na ya tashi sosai na rasa

yanda zanyi, "kar dai `yar mutane ta b`ata, in kuwa

hakane da na shiga uku" ina cikin wannan tunanin

ne naji wayata na ruri, koda na duba Futha ce take

kira, cikin sauri na d`aga, banyi ko sallamah ba

nace "Futha `yar mutane ta b`ata"

"Kwantar da hankalin ki Aunty, maganar dana kira

na miki kenan, yarinya dai ta gudo wai bazata iya

zama ba, ba wai dan bakya kyautata mata ba sai

dan tsoron Haydar da take, nayi bakin k`ok`ari na

ganin na fahimtar da ita amma tak`i yarda wai

bazata dawo ba, amma insha Allahu zuwa gobe

zanzo miki da wata, budurwa ce nasan zakiji dad`in

ta",

Shiru nayi ina sauraren ta, raina ya b`aci sosai,

gumn fuskana na goge nace "to ba damuwa Futha,

idan kunzo gobe zan baki kud`in aikin kwana biyar

data min, naso yarinyar sosai saboda tana da

tarbiyya, amma babu komai sai na ganku goben",

Sallamah mukayi da ita, ban ankara ha naji hawaye

na bimin kumatu, Allah dai yasa wadda za`a kawo

min yanzu ta zauna.

Washe gari ta kama asabar babu aiki, zaune nake

da safe ina kalaci Haydar kuma kwance a katifar

shi yana ta wasan shi hankali kwance, sallamar

Futha naji ita da wata budurwa a bayan ta, bayan

mun gaisa Futha tace "kamar yanda nayi alk`awari

gashi na cika, na kawo miki nany sunan ta Sadiya,

ina fatan ta miki",

Cikin jindad`i nace "tamin mana, sai dai wani

hanzari ba gudu ba, Sadiya ina fatan an fad`a miki

aikin ki"

"Ehh an fad`a min" ta fad`a cikin girmamawa,

"Tou masha Allahu, Sadiya kinga yaro na ba

lafiyayye bane, yana da buk`atar kyakkyawar

kulawa saisa ma nace ma Futha ta nemo min mai

hankali, ina fatan zaki rik`e min amana ki kula da

Haydar tamkar k`anin ki na jini"

"Insha Allahu Aunty na miki alk`awarin kula da

Haydar, zaki same ni mai rik`e amana, zan kula

dashi kamar yanda zaki kula dashi, zan taya ki

bashi tarbiyya ingantacciya".

Sosai kalaman Sadiya suka min dad`i, ina fatan

hakan yanda ta fad`a ya kasance.

*¶¶ BAYAN WASU SHEKARU ¶¶*

A wannan shekaru masu kimanin uku zuwa hud`u

abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa har da k`ara

aure da Abban Haydar yayi, ya ajiye matar shi a

new lay out ne ni kuma ina Goriba road inda nake

tun asali, baki d`aya ya daina kula dani, ko abinci

baya kawo min sai dai ni nake saye a albashi na,

yana iya yin wata d`aya baizo inda muke ba, Hajiya

da Ummi kuwa idan kin gansu gidan mu tou

wulak`anci ya kawo su, Futha ma ta haifi `yan biyu

duka mata, Sadiya kuwa ta rik`e alk`awari, don

yanda take kula da Haydar koni bana mishi haka, ya

shak`u da ita sosai, a lokacin kuma halittar shi take

k`ara munana koni wani lokacin idan na kalle shi

har da hawaye nake yi, itaka Sadiya ko a jikin ta,

dan wani lokacin ma itace take min nasiha idan taga

ina kuka.

Kwance nake bayan na dawo aiki saboda tunda na

yaye Haydar na daina zuwa aiki dashi, a gida nake

barin su shida Sadiya, Sadiya tace "Aunty dan Allah

in babu damuwa gobe ko jibi ina son ziyartar gida

na kwana biyu banje ba",

Murmushi na mata nace "babu damuwa Sadiya,

amma zaki bar Haydar da kewa, waccan tafiyar da

kikayi haka yaita kuka baya bari na bacci",

"Ai bazan dad`e ba Aunty, bazan wuce kwana d`aya

ba, kud`i kawai zan kaima Innah ta dan nasan tana

da buk`atar su",

"Tou Sadiya babu damuwa Allah ya kaimu, zan baki

sak`o sai ki tafi masu dashi".

Washe gari da safe Sadiya ta gama shiri, na had`a

mata kayana wanda basuji jiki ba da man shafawa

da sabulu masu yawa nace ta kaima innar ta,

murnar ta k`arara na gani, nace mata ta gaishe da

`yan gidan dan ta fad`a mun tun tana yarinya Baban

ya ya rasu k`annen ta biyu kacakal.

Kamar yanda ta fad`a d`in kuwa haka tayi, kwanan

ta d`aya ta dawo, sai dai kuma na fahimci damuwa

a tattare da ita, na zaunar da ita na tambaye ta

"Sadiya me ya faru ne? Na fahimci akwai damuwa a

tattare dake? Ko innah ce ba lafiya?"

"Innah lafiya k`alau take"

"To meya faru Sadiya?"

"Kawu na ne yace ya tsaida min miji, nan da wata

d`aya za`a d`aura min aure",

"Wani irin fad`uwar gaba naji, nayi k`arfin hali nace

"to ai wannan ba abun tashn hankali bane, abun

alkhairi ne Sadiya, dama ai ba zakita zama babu

aure ba dole zakiyi, ki cire duk wata damuwa kinji

ko?",

Kai kawai ta kad`a min, a raina na tunanin idan

Sadiya ta tafi ina zan samu wata nany wadda zata

rik`e min amana ta kula min da Haydar?, akwai

matsala kam.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


4⃣7⃣

Ranar dai haka na kwana cike da tunanin yanda

zanyi idan Sadiya ta tafi, ita kanta Sadiya abun bai

mata dad'i ba dan bata son wanda za'a had'a ta

dashi d'in ba, ganin ina ta juyi har k'arfe ukun dare

na kasa bacci yasa ni d'auro alwala na gabatar da

sallar nafila raka'a biyu tare da jero addu'o'i, ciki

kuwa sai dana yi wadda na saba yi a koda yaushe

akan Allah ya bayyana min inda Mahaifiyata take.

Washe gari da sassafe na shirya zuwa aiki, Haydar

daga kwance kan cinyar Sadiya yai min dariya tare

da d'ago min hannu bakin shi yana fitar da yuwu

dalala, peck na masa a goshi sannan na d'auki key

na na tafi.

K'arfe biyu da rabi na fara haramar komawa gida, na

gama had'a komai ne wata nurse ta shigo da sauri

jikin ta sai rawa yake tace "Dr. Nadiya an kawo

wata patient haihuwar fari tun jiya da dare muke

kanta amma har yanzu ta kasa haihuwa, munyi

tunanin zamu iya ne yasa bamu fad'a miki ba,

amma abun yanzu kamar yaci tura dole sai kin

agaza mana",

"subhanallahi! Amma kuwa kunyi ganganci, me

yasa zaku bar baiwar Allah tun jiya tana abu d'aya

wai har yanzu getting to three amma babu wani

mataki da kuka d'auka? Sai yanzu zakizo kina fad'a

min rubbish, muje da sauri",

Nurse d'in tayi gaba ina biye da ita har mukaje

labour room d'in, da sauri na isa bakin gadon

baiwar Allah'r duk ta fita a hayyacin ta sai sabbati

take, nan na fara dudduba ta ga kan jinjirin yana ta

k'ok'arin fitowa amma wani abu ya hana shi, baki

d'aya kaina a d'aure yake, tou miye dalilin hakan?

Ga jini nata zuba duk ta b'aci amma still babu

haihuwa, cike da tashin hankali nace ma nurses d'in

"ai duk laifin ku ne non-sense, ace wai nurses

masu kula da lafiya amma basu san aikin su ba,

maza maza a nemi danginta a samu jini a k'ara

mata kafin in dawo",

Jinin da take zubarwa d'in na samu container na

d'ibi kad'an sannan na tafi.

Office d'in Dr. Rafiq naje nayi nocking, "enter" yace

min, ban ko jira ya gama maganar ba na banka

k'ofar na shige.

"Dr. Nadiya lafiya na ganki haka?",

Kwatakwata na kasa samun natsuwar da zan masa

bayani, dan patient d'in nan ta matuk'ar bani

tausayi, da k'yar na iya bud'e baki na na masa

bayani, shima yaji tausayin ta yace "tou yanzu miye

abunyi? Ko aiki za'a mata ne?",

Da rawar murya nace "dole aiki za'a mata, amma

ina son bincikar dalilin da yasa hakan ta faru ne, ga

jinin nan na d'iba zan auna shi insha Allahu sai na

gano matsalar dake sakawa yawancin mata yanzu

suke kasa haihuwa da kansu sai an masu aiki,

yanzu dai mu fara haramar fiddo mata jinjirin daga

baya duk zanyi wancan, na saka su su mata k'arin

jini kafin mu gama had'a kayan aikin",

Dr. Rafiq yace "hakan yayi, gaskiya nima koda nake

likita amma ina mamaki wannan al'amarin, me yasa

matan da duk basu san a yanka su a fitar da jarirai

ba? Dole akwai dalili".

Cikin minti arba'in da biyar muka shiga aiki da

wannan mai cikin, mun samu an fitar da jinjirin lafiya

sai dai kuma mahaifiyar yaron Allah ya mata

cikawa, har da kuka nayi dan abun ya matuk'ar bani

tausayi, cike da tausayi muka fito duk na had'a

zufa, nan muka fara neman danginta dan a basu

gawar ta da yaron da aka fitar mata amma cikin

mamaki babu dangin ta, nurses d'in na tambaya "a

ina kuka samu danginta d'azu har suka baku jinin

da aka k'ara mata?",

D'aya daga cikin su tace "bamu samu dangin ta ba

dama itace ta kawo kanta jiya, ganin kamar mune

silar komai yasa na siyi jinin da kud'i na kawai aka

k'ara mata",

Kai na dafe na sake jin wani hawayen dana kasa

controlling nasu, "tou yanzu ya zamuyi da gawar da

jaririn?" Na tambaye su,

Dr. Rafiq dake daidai shigowa yace "wannan ba

maganar da za'ayi shiru bace, ya kamata mu sanar

ma hukuma yanzu",

Wayar shi ya kira d'an sanda, nan da nan kuwa

suka zo,

Anyi cigiya anyi cigiya amma an rasa danginta, har

gidan tv an gwada hoton gawar koda wanda ya

santa amma babu, ganin kar gawar ta fara wari

yasa kawai aka kaita masallaci dubban mutane

suka sallace ta aka kaita gidan ta na gaskiya, jinjirin

kuwa gaban mutane na d'auki al-k'awarin d'aukar

shi zan rik'e shi tsakani na da Allah tamkar ni na

haife shi saboda *D'A NA KOWA NE,*

Kowa ya jinjina min da wannan taimakon dana

d'auki aniyar yi.

A ranar dai nice ban koma gida ba sai bayan

magrib,

Sallamah nayi na shiga gidan da jinjiri d'auke a

hannu na, cikin mamaki Sadiya tace "Aunty ina kika

samu jariri?", nan na mata bayanin komai itama ta

tausayawa yaron da mahaifiyar shi.

Nan da nan na tsaftace yaron na saka mashi cikin

kayan Haydar tun na jarintakar sa, take ya fito d'as

dashi tamkar a gaban mahaifiyar shi yake.

Waya ta na d'auka na kira Abban Haydar, sau biyar

ina kiran shi amma bai d'auka ba har na gaji na aje,

text d'in shi ya shigo min kamar haka:-

_kar ki dame ni da kira kuma nasan ba wani abun

kirki zaki fad'a min ba, na manta ban fad'a miki ba

Salmah ta haifi 'ya mace gobe suna._

Wani irin takaici ya mamaye min zuciya, wai ace

Salmah amaryar Usman ta haihu amma v

Bai fad'a min ba sai yau kuma ma wai gobe suna,

ni gudu na d'aya ma kar suyi zaton na sani kishi ne

ya hana ni zuwa, tsaki nayi a bayyane sannan na

lula duniyar tunani. "To ni yanxu idan akace wannan

yaron ba d'an halak bane bafa? Ban fa san asalin

mamar shi ba, kuma ni gashi na d'auka" wata

zuciyar tace min "to saime idan ma shegen ne? Ai

bashi ne da laifin ba, ki rik'e yaron ki saka mashi

duk sunan da kikaga ya dace, ki raine shi tamkar

kece kika haife shi",

Shawarar zuciya ta na d'auka, murmushi nayi nace

"zan saka maka sunan Abba na Umar, zan raine ka

zan baka kyakkyawar tarbiyya".

©princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: : *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


4⃣8⃣

Goya shi nayi na saka hijabi na d'auki key'n mota ta

nace ma Sadiya "zan tafi matar Abban Haydar ne ta

haihu har gobe suna ban sani ba, daga nan zan biya

in ma Umar siyayya da madara nasan SMA zata

karb'e shi insha Allah",

"Tou Aunty a dawo lafiya, amma yanxu ai dare yayi

da kin bari sai gobe" Sadiya ta fad'a tare da tada

Haydar zaune tace mashi "me Ummah zata siyo

maka?",

Magana yayi da ban san abunda yace ba, murmushi

kawai naga Sadiya tayi tace "Aunty yace wai irin

chocolate d'in ranan yake so",

Cikin mamaki na kalli Sadiya, lallai tayi k'ok'ari dan

ni a tsare ni ban san abunda ya fad'a ba amma ita

har ta gane, ba-bye na masu sannan ba fita Umar

nata k'ok'arin yin kuka.

A daidai *SHA'ABAN SUPERMARKET* na paka mota

ta na fita da sauri jin Umar na so ya ida fashewa da

kukan,

SMA na d'auka guda biyu na biya kud'in sannan

naja motar na koma gida dan bazan iya zuwa wani

wuri dashi yana wannan kukan ba,

Da komawa na na d'ora ruwan zafi na dama mashi

madarar a hankali na soma bashi, da sauri ya ringa

sha alamar yana jin yunwa, kaina na gyad'a cike da

tausayin shi, yanxu shikenan shi bazai sha ruwan

nono kamar yanda ko wane jinjiri yasha ba? Allah

sarki! Rayuwa kenan.

Sai da na gama bashi ya k'oshi sosai sannan na

goya shi yayi bacci,

A ranar dai ban samu zuwa na gano jaririyar

Salmah ba, washe gari da sassafe na shirya zuwa

aiki saboda ina son in dawo da wuri dan inje wurin

suna, banda ma ina da abunda zanyi a office d'in

ma da hak'ura zanyi da zuwa sai gobe.

Ina zuwa office na sauke Umar daga baya na a

lokacin har ya tashi daga bacci, jaka ta na bud'e na

fiddo flask d'in da na dama mashi madarar shi

wadatatta yanda bazai nema babu ba har in koma

gida, nan na hau bashi har na samu yayi bacci.

Nan na d'auko container'n da jinin nan yake na tafi

laboratory da ita, a iya bincike na nidai banga komai

a jinin ba, hakan yasa na tafi office d'in Dr. Rafiq

bayana goye da Umar.

Na masa bayanin banga komai a jinin ba, na kuma

k'ara da "Dr. Ina tunanin zan tafi India zanyi course

akan wannan matsalar, ya kamata ace by now an

gano dalilin yawan yanka mata da ake wurin

haihuwa sanadiyyar rashin haihuwa da kansu da

basu iyawa, zan rubuta application ta hanyar ka ko

za'a min approving nasa da sauri",

Dr. Rafiq yace "kinyi tunani mai kyau Dr. Nadiya,

wannan baiwar Allah da alama ta shiga ranki da

yawa kamar 'yar uwarki",

"Dr. Ai koba jini na bace yanzu ta zama tawa tunda

gashi d'anta ya xama d'ana, dan Allah kasa min

hannu komai ya fito da wuri, ina tunanin course d'in

bazai wuce wata biyu zuwa uku ba dukan shi dan

ina ji a jiki na ba wani abu mai wahala bane",

Dr. Rafiq yace "ba damuwa ki rubuto kawai na miki

al-k'warin zan tsaya miki komai ya fito da wuri",

Godiya na masa sannan na shaida masa gida zan

tafi saboda akwai inda zanje.

Gidan sunan na zarce direct, tun daga nesa na

hango Usman zaune kan babbar tabarma da

abokanshi ya d'auki jinjirar sai hotuna ake d'aukar

su, cikin mamaki na kalle shi naga yanda yake ta

washe baki kamar yau aka soma masa haihuwa, da

sauri na fito daga motar ko gyara parking banyi ba,

a gaban shi na isa cikin rashin tsoro nace "Sannu

Usman! Wai yaushe ka fara son haihuwar 'ya mace

ne ni banda labari? Hmm! Namiji kenan! Namiji

k'anin ajali", ina kaiwa nan na koma mota ta na tada

na koma gida, da k'yar nake tuk'in dan wani irin

kuka da nake mai cike da tashin hankali, kenan

dama Usman nice baya so? Jini na ne baya so?" Na

k'ara fashewa da wani kukan.

da k'arfi na jera horn har guda uku, shi kanshi mai

gadi yayi mamakin yanda nake horn d'in, cikin

hanzari sai gashi yaxo ya wage min gate na shiga

da motar.

Da sauri Sadiya ta sauke Haydar daga jikin ta ta

kwantar dashi kan kujera tana fad'in "Aunty lafiya?

Me ya faru na ganki haka? Ko gidan sunan ne aka

b'ata miki rai?",

Ban bata amsa ko d'aya ba sai Umar dana mik'a

mata naci gaba da rero kuka na mai cike da ban

tausayi.

©princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


5⃣0⃣

Misalin k'arfe uku na dare jirgin mu ya dira a babbar

airport d'in dake cikin Mumbai, tsananin gajiya ce a

tattare dani dan tafiyar India akwai nisa ba kad'an

ba.

Koda na fito daga jirgi na goya Umar sannan na hau

jan trolly na, tafiya nayi kad'an wadda ta sada ni da

babban reception d'in airport d'in, nan naga jerin

mutane da uniforms d'in su kowa akan kujera jere

da juna, wanda yake gaba na naga ya mik'awa na

farkon jakar sa aka bincike ta sosai sannan ya

koma ga na biyun, nan ma wani binciken aka sake

masa, ganin hakan yasa nima na mik'a tawa jakar

aka bincike ta, haka naita bi ana bincike jakar har

naje ga mutumin k'arshe wanda ya had'a ni da wata

mace ta lalube jiki na wai a nufin su idan akwai wani

makami ko wani abun cutarwa a tare dani,

Sai da aka gama duka sannan na hau tattara

kayana cike da takaicin yanda duk suka b'ata min

su kamar ba gogaggin kaya ba. Bayan na gama

had'awa naja trolly'n na fita ina tunanin inda zan

samu masauki kafin gari ya waye in nemi inda

gwamnati ta kama min.

Sai da nayi tafiya mai nisa har na gaji sannan na

samu wuri na zauna ga wani irin bacci da nake ji,

can naji an tab'a ni a hankali da sauri na waiga dan

ganin wanda ya tab'a ni,

Wata kyakkyawar mata na gani wadda daka ganta

kasan dattijuwar kirki ce, duka shekarun ta bazasu

wuce 42-43 ba, sai dai da ganin ta ba baindiya bace

siffar ta tayi kama da zallar hausa fulani,

"can youh hear English?" Ta fad'a tana min

murmushi,

"Yes I can" na mayar mata da amsa ina kallon ta.

Murmushi ta sake min a karo na biyu wanda ya

bayyanar da fararen hak'oran ta.

"From which Country you came from?"

"Am from Nigeria"

Mamaki na gani a fuskarta had'e da jindad'i.

"Daga ina kike haka? Na ganki da jaka kuma ga

goyo amma kinyi zaune anan" ta tamabaye ni.

Cike da mamaki na kalle ta dan kwata kwata banyi

tunanin fitowar hausa daga bakin matar ba, saboda

yanda ta saje dasu tamkar itama 'yar k'asar ce,

"daga Nigeria nake, yanzu jirgin mu ya sauka shine

nake neman masauki kafin gari ya waye in tafi inda

gwamnati ta kama mana",

Rungume ni tayi tana farin ciki sosai "naji dad'i da

kika kasance 'yar Nigeria, nima 'yar Nigeria ce

amma anan nake aure har na haifi yara uku anan,

kin min yanayi da yaro na Khalil sosai wlh, a wane

gari kike?",

"Daga Katsina nake, nazo yin wani course ne na

wata biyu",

Matar tace "to idan babu damuwa zaki bini muje?

Nima nazo d'aukan yaro na daya dawo daga

America gashi can a mota yana jira na",

Tashi nayi tsaye naja trolly na nabi bayan ta, amma

still hankali na bai wani kwanta da ita ba.

Booth ta bud'e d'an nata ya saka akwati na a ciki

sannan ta kama hannu na ta saka ni a bayan motar,

d'an ta kuma ya shiga gaban motar ta ja ta muka

tafi. A raina nace "to k'ila wannan yaron shine Khalil

d'in, dan gashi nan yayi yanayi da ni amma kad'an,

hancin shi da idon shi ne kawai yayi kamar amma",

da wannan tunanin na gan mu gaban wani katafaren

gida mai matuk'ar kyau.

Da murmushi matar ta kalle ni tace "ki fito gashi har

munzo, ki saki jikin ki damu kinji?",

Kai na kad'a mata tare da fita daga motar a lokacin

kuma Umar ya fara min kukan yunwa. Rirrigar shi

nake amma yak'i yayi shiru, matar tace "may be

yana jin yunwa ne, ki bashi nono yasha mana, ki

koma ki zauna a motar yanda zakiji dad'in bashi",

kai na kad'a mata nace "babu komai mu shiga daga

ciki zan bashi".

Shiga mukayi tana gaba ina biye da ita, har muka

sake kaiwa ga wata k'ofa da alama itace main k'ofa

ta gidan, sallamah tayi sai ga budurwa kyakkyawa

ta fito tana fad'in "sannu da dawowa momy" cikin

yaren indiyanci.

Da saurin yaron ma ya shigo ta rungume shi tace

"Welcome back my brother" shima rungumar tata

yayi tare da fad'in "nayi kewar ki sosai kanwa ta"

shima a cikin yaren indiyancin.

Sai a lokacin ta kula dani, wani irin kallon raini tabi

ni dashi fuskar ta babu annuri, cikin yare tama

maman ta magana sai dai ban san abunda tace

mata ba, amma da alama maganata tayi mata, kallo

na naga maman tata tayi tamin murmushi sannan

tace mata "nayo miki 'yar uwa ne, itama 'yar

Nigeria ce..." nan ta labarta mata komai kamar

yanda na fad'a mata.

"Haba Maamah! Gaskiya nidai bazan yarda ba ki

barta ta tafi can inda zataje kin cika kwashe kwashe

da yawa", ta fad'a cikin hausar ta da bata gwanance

da ita ba.

Take raina ya b'aci, bana son raini ko kad'an, ni

bana raina mutane kuma nima bana son a raina ni,

ganin haka yasa matar ta jawo ni ta shigar dani

wani d'aki tace "this is your room, akwai komai a

ciki, idan akwai wani abu da kike buk'ata ki sanar

dani kafin gobe muyi magana".

"Babu abunda nake buk'ata, Thanks alot for the

help",

"you are welcome my dear, you can call me

Maamah kamar yanda yara na suke kira na dashi,

ki kula da yaron ki yana kuka, good night" tana

kaiwa nan ta fice daga d'akin.

Sosai hankali na ya kwanta da matar yanzu, sai dai

kuma wannan yarinyar tata da alama 'yar rainin

wayo ce, bazan tab'a iya zama da ita ba.

Toilet na shiga na kunna heater na dama ma Umar

madarar shi, na fara bashi yana sha sosai dan

yunwa yake ji tun cikin jirgi rabon shi da wani abu.

Washe gari da safe na tashi nama Umar wanka na

shirya shi sannan na bashi madara, yana gama sha

yayi bacci sannan na goya shi na hau gyaran

d'akin. Sai da na gama gyaran shi tsaf sannan

Maamah ta shigo, har k'asa na duk'a na gaishe ta

ta amsa min da sakin fuska, "ya gajiyar tafiya?"

"Alhamdulillah Maamah, dama ina so ne idan na

shirya zan fita in fara abun da ya kawo ni",

"To babu damuwa 'yata, ki bari amma sai kin karya

sannan, sai dai kuma baki fad'a min sunan ki dana

yaron ba"

"Sunana Nadiya, yaro na kuma Umar",

Take naga sauyi daga fuskar Maamah, wasu irin

hawaye suka fara kwaranya daga idon ta, sosai

hankali na ya tashi nan na fara tambayar ta dalilin

kukan ta, da k'yar ta iya saita kanta tace min "babu

komai Nadiya, nice name" "thanks" na fad'a ba wai

dan na gamsu da maganar ta ba. Sai a lokacin takai

duba ga gyara d'akin da nayi tace "ai da baki ba

kanki wahalar gyara bama akwai masu aiki zasu

gyara",

"a'a Maamah, ai ni na kwana a ciki dole ni zan

gyara"

Murmushi tamin sannan tace "idan kin shirya ki

same ni a parlor" ta fita har a lokacin walwalarta

bata dawo daidai ba.

"Ko miye dalilin kukan oho?" Kaya na hau cirewa na

d'aura towel na shiga wanka na.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah ®NWA*


4⃣9⃣

Sadiya keta bani hak'uri har nayi shiru, nan na

labarta mata duk abunda ya faru, in banda hak'uri

babu abunda take bani.

Washe gari ya kama Friday, na shirya Umar cikin

overall light blue na sab'e shi a kafad'a na shiga

mota, direct asibiti na wace, kai tsaye office d'ina

naje, na rubuta application sannan na tafi office d'in

Dr. Rafiq na kai masa, ya yaba da yanda kalamn

ciki sukayi ma'ana, yace zai neme ni duk yanda

ake ciki.

*

A gida na samu Usman zaune yana jira na, da ganin

shi gabana ya fad'i dan nasan wulak'anci yaxo yayi,

ban ko kula shiba na shige d'aki na, kirana yayi da

k'arfi na dawo, cikin rashin tausayi yace "nasan dai

ke ba mai bin maza bace barin ince kin haifi shege

ne, kuma nasan na daina ciyar dake barin ince Allah

ya isa idan kika ciyar da yaron nan da abinci na,

saboda haka wannan bai shafe ni ba kuma bashi ya

kawo ni ba, nazo ne dan na miki gargad'i akan karki

kuma yimin irin tozarcin da kika min jiya a gaban

abokai na wallahi in baccin darajar Momma kafin ta

rasu tace kar na kuskura na rabu dake duk rintsi da

tuni nayi waje dake, amma ki kula ni ba'a min haka"

yana kaiwa nan ya fice daga gidan.

Baifi minti talatn da tafiya ba kuma sai ga Hajiya da

Ummi sun zo,

Na gaishe da Hajiya tamun banza aikuwa nima na

fita batun su dan duk na dawo daga rakiyar su,

Ummi ce tace "munafurcin banza da wofi! Duk

bak'in cikin ki sai dai ki mutu, Aunty Salmah ta

haihu kuma ta haifi lafiyayyar yarinya ba

*MUSAKA* ba, kuma insha Allahu ta dasa haihuwa

kenan har sai ta cika mana zuri'ah da yara

lafiyay...." dakatar da ita nayi ta hanyar cewa "ke

Ummi ki iye bakin ki, ni nafi k'arfin inyi dake sai dai

da mahaifiyar ki, kuma ku fita min daga gidan tun

kafin in tara maku mutane",

Sum sum suka fice ba tare da Hajiya tace komai ba,

"da haka zan ringa magance ku munafukai kawai",

na fad'a tare da d'aukar Umar naci gaba da bashi

madarar da nake kan bashi.

*BAYAN SATI BIYU*

A lokacinne approval letter na ta fito nan da kwana

uku zan tafi, wanda kuma yayi daidai da saura

kwanaki goma a d'aura auren Sadiya.

Futha na kira na shaida mata komai tace min zatazo

dama bata tab'a xuwa taga Umar d'ina ba,

Washe gari kuwa sai gata, tace min ita zata tafi da

Haydar gidan ta tunda nace ni zan ma Umar visa

tare zan tafi dashi, Sadiya kuma na shaida mata na

sai mata komai na kayan d'aki dana kitchen masu

kyau komai na waje, dama adashe na ne dana

d'auka miliyan d'aya da rabi shne na mata siyayyar

sauran kuma dasu ne zan ma Umar visa saboda ni

gwamnati tamin komai.

Sadiya har da kukan farin ciki tayi ranar, Futha ta

tafi da nufin Sadiya zatazo mata da Haydar idan na

tafi.

Wayata na d'auka nama Usman text kamar haka:-

_a matsatin ka na miji dole na ko bana so idan zan

tafi wani wuri na sanar dakai, zan tafi India course

zanyi na wata biyu insha Allah, ina neman yarda da

amincewar ka._

Babu jimawa kuwa sai ga reply:-

_idan kin iya ma kifi ruwa gudu ni ba ruwa na, you

are free to go anywhere ba sai kin tambaye ni ba

tun da bana sauke hak'k'in ki ko d'aya daya rataya

a wuya na._

Dama nasan bazai taba hanani ba, sai dai kuma

dole na in fad'a masa saboda haka addinin mu ya

koyar damu.

Ranar dazan tafi kam munsha kuka nida Sadiya, ina

tunanin yanda Haydar zai iya rayuwa babu Sadiya,

sun shak'u da junan su kusan shekarar su biyar

tare, amma gashi lokaci d'aya aure zai masu

*YANKAR K'AUNA.* Haka muka rabu dasu cike da

kewar juna, na mata nasiha sosai akan zaman aure

sannan na tafi.

Motar haya na hau inda takai mu har Kano, daga

tasha na hau taxi ta kaini airport, babu b'ata lokaci

kuwa jirgin mu ya lula sai K'asar India.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah ®NWA*


5⃣1⃣

Bayan na fito wanka na bud'e akwati na na ciro

kayana, atamfa ce riga da zani wrapper green da

zanen red, green hijab na fiddo sannan na hau saka

kayan. Sai da na gama duka sannan na saka hijabin

na d'auki Umar na fice parlor, acan na samu

Maamah zaune tana jira na,

Da murmushi ta karb'i Umar a hannu na sannan

tace min "muje muyi breakfast ke nake jira dama",

Dining area ta nufa ina biye da ita har ta zauna nima

na zauna,

Serving d'ina tayi naci na k'oshi taf sannan na karb'i

Umar itama ta karya.

Bayan mun gama duka sai ga Khalil d'an ta ya shigo

shida wannan budurwar, wani mugun kallo ta watsa

min nima kuwa na bita dashi karaf sai a idon

maamah,

D'an murmushin yak'e tayi sannan tace "Nadiya

wannan itace Nadra sai k'anin ta Khalil, suna da

yaya d'aya wadda tayi aure a Nigeria tana Abuja,

shekarar ta d'aya kenan da yin aure kuma muna sa

ran ta kusa haihuwa ma yanzu, baban su ya rasu

kusan wata takwas kenan da suka wuce, naso

komawa Nigeria amma saboda wani babban dalili

k'wak'k'wara yasa nace kawai gwara muci gaba da

zama anan tunda dai mun zama tamkar 'yan k'asa

kuma har ina aiki anan, ga Nadra ma ta fara karatu,

Khalil kuma America yake secondary School yanzu

ya gama duka shine ya dawo gida. Ina fatan ki

zauna damu lafiya har lokacin da zaki tashi

komawa Nigeria".

Murmushi na mata nace "insha Allahu Maamah,

Allah ya bamu ikon yin hak'uri da juna, yanzu ina

son tafiya kan waccan maganar data kawo ni".

"To babu komai Nadiya, nama driver magana zai

kaiki duk inda kike so kuma zai jira ki gama".

Godiya na mata tare da goya Umar na kama hanyar

fita bayan na d'auko ID CARD da duk abubuwan da

zan iya buk'ata.

Internet na shiga tanan na gano komai da inda

zanje, koda na fad'a ma driver'n yace min ya gane

wurin, babu b'ata lokaci kuwa mukaje, a ranar na

gama komai nawa, da nufin washe gari zan fara

zuwa babbar makarantar *INTERNATIONAL

MEDICAL SCHOOL* dake cikin Mumbai.

Da misalin k'arfe d'aya na rana na gama muka nufi

gida. A gajiye na koma gidan na samu Maamah bata

dawo daga aiki ba dan dama ta shaida min sai

k'arfe biyu take tashi. Umar na fara dama ma

madara dan tashi ta isa ta zama contaminated,

bayan na gama bashi ne masu aiki mutun biyu suka

shigo d'akina, nan suka hau yi min indiyanci amma

ban san abun da suke fad'a ba, ganin haka yasa

d'ayar tace "what do you want to eat? ma"

Murmushi nayi na mayar mata da ansa "anything

good"

Fita sukayi a tare basu jima ba sai gasu kowace

d'auke da tray a hannu, a gabana suka ajiye sannan

suka fita, bin bayan su nayi da kallo dan yanda

d'ayar ta tufk'e gashin ta abun ya bani tsoro, tsawo

da yawa duka ya had'a, koda nake gani na da gashi

ashe bani da komai akan indiyawa,

Saukowa nayi na bud'e tray d'in nan naci karo da

wani irin abinci wanda banyi marmarin k'ara kallon

sa ba, a yatsine nayi sauri na rufe food flask d'in

sannan na bud'e na d'ayan food flask k'aramin, cat

fish pepper soup ne lafiyayye sai k'amshin pepper

take tashi, da sauri kuwa na fara turawa dan dama

yunwa nake ji ban wani tsaya nayi karin kirki ba da

safe.

D'ayan tray d'in na duba inda naci karo da drinks

kala kala, hamdala nayi wa Allah sannan na fara

shan strawberry drink, sosai nasha shi sai da naji

ni nayi nat sannan na rufe jug d'in. Na kwashe

kayan a daidai parlor naci karo da d'aya daga cikin

'yan matan da suka kawo min abinci, da sauri ta

karb'i kayan cikn girmamawa ta nufi kitchen dasu.

Koda na koma Umar har yayi bacci, gyara masa

kwanciya nayi sannan na d'auki wayata na kira

Futha, bugu d'aya ta d'auka tace "hello Aunty",

"Hello futha" nima na fad'a cike da farin cikin jin

muryar ta.

"haba Aunty ai kin manta damu",

"Wace ni na manta dake futha? Ki fad'a min ta inda

yaya zata manta da k'anwar ta",

"To na yarda aunty, ya kuka sauka?",

"Lapia k'alau wallahi, ina yarana?",

"gasu zaune suna wasa, Haydar nata jajen ki jiya,

amma tunda ya fara sabawa da Hassan da usaina

kuma sai ya daina maganar ki, bai da wata

damuwar rashin ki a halin yanzu, ki kwantar da

hankalin ki, Haydar tamkar a hannun ki yake",

Da sauri na katse ta nace "Futha duk ban tambaye

ki wannan ba, nasan Zaki kula da Haydar sosai,

abunda na manta ban fad'a miki ba shine; dan Allah

Futha idan zakiyi baak'i kiyi k'ok'ari ki kai Haydar

d'aki ki b'oye shi, saboda bakin mutane",

"Tou insha Allahu Aunty, Allah dai ya bada ikon yin

abunda akaje yi",

"Ameen" na fad'a tare da tsinke wayar.

A daidai nan naji sallamar Maamah a d'aki na, na

gaishe ta ta amsa min da sakin fuska tace "kiyi

hak'uri da halin Nadrah, nasan Nadrah bata da hali

'yar wulakanci ce ta raina talaka, dan Allah kikai

zuciyar ki nesa",

Murmushi na mata nace "babu komai Maamah"

"Kinci abinci dai ko?",

"Ehh wannan 'yan matan sun kawo min"

"To masha Allahu, d'aya sunan ta Mariyatu, d'ayar

kuma Kareenah, zaki iya neman su duk lokacin da

kike da buk'atar wani abu" tana fad'in haka ta fita.

Binta nayi da kallo dan yanda matar take da

mutunci, sosai ta kwanta min a rai dan yanda nake

jinta a raina tamkar jini nah.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: : *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah ®NWA*


5⃣2⃣

Abu wasa ba wasa ba yau na cika wata biyu a India,

yaune kuma na gama duk abunda ya kawo ni

k'asar, cike da murna na koma gida dan na samu

nasarar abunda ya kawo ni.

Bayan na koma gida naci karo da Nadrah itama ta

dawo daga school, kallon raini ta bini dashi nima

kuwa na rama, tsaki tayi a bayyane wanda yayi

daidai da fitowar maamah parlor'n,

"Wai ke Nadrah baki da hankali ne ko me? Me yasa

kika raina Nadiya kamar ba yayar ki ba?", maamah

ta fad'a cike da haushin tsakin da Nadrah tayi min

duk da ba wai yaune ta saba min ba,

"Allah ya kyauta min wannan ta zama yayata, ni

yayata tana Nigeria d'auke da cikin baby'n mu, can

dai taje ta nemi k'annen ta",

Kyakkyawan mari Maamah ta d'auke Nadrah dashi,

sosai take jin haushi idan taga an b'ata min rai,

"Yanzu maamah abun har ya kai ga ki d'aga

hannunki ki mare ni saboda wannan matar? Hmm!

Wallahi sai kin raina kanki dan sai kin gwammaci ki

koma hotel ki zauna akan zaman gidan nan"

Nadrah ta fad'a da hausar ta da bata gwanance ba.

Murmushi kawai na mata tare da nufar d'aki na,

sosai taji haushi yanda taga ban kula taba, ina jin

maamah na fad'in "amma dai kinji kunya wallahi,

gashi wadda kikayi saboda itan bata da lokacin ki".

Nikam da shiga ta na kwantar da Umar sannan na

nufi toilet, wanka nayi sannan na fito na saka

k'ananan kaya sannan na d'ora 'yar after dress

akai na fita parlor, naci karo da Mariyatu daidai ta

fito daga d'akin Nadrah,

"Am hungry Mariyatu", na fad'a tare da yin hammar

gajiya.

"Sorry ma, Aunty Nadrah said.." sai kuma tayi shiru

tayi raurau da ido kamar mai shirin yin kuka.

"Said what?" Na fad'a ina kallon ta,

Tana k'ok'arin bani amsa ne najiyo muryar Nadrah

tana fad'in "daga yanzu idan kina jin yunwa sai dai

ki shiga kitchen da kanki ki dafa saboda babu

baiwar ki a gidan nan, Mariyatu da Kareenah

bazasu k'ara yin girki dake ba, na daidai cikin mu

mu 'yan gidan zasuna ringa yi, idan kin matsu kya

dafa da kanki".

Dariya nayi bayyananna tare da fad'in "kiyi hak'uri

Nadrah, nima insha Allahu by next tomorrow I will

be back to my own land, so ki kwantar da hankalin

ki, zan barki kici gaba da jin dad'in ki daga inda kika

tsaya dan naga alamar kamar na hana miki kad'an

daga walwalarki", ina kaiwa nan na shige kitchen

d'in da kaina,

Fridge na bud'e naci karo da fruits da kazar

k'ank'ara, fruits d'in na fara d'iba kad'an na

b'ab'b'are su na had'a fruit salad na saka a deep

freezer saboda yayi sanyi kafin in gama girki. Sake

bud'e fridge d'in nayi naga kazar a guda

d'ad'd'ayan ta, d'aukar d'aya nayi sannan na d'ora

tukunya a wuta, bayan na wanke naman na zuba a

tukunyar na yanka albasa da kayan k'amshi, maggi

da gishiri kad'an sannan na kunna wutar, bugu

kad'an wutar tama naman na sauke dama ban zuba

ruwa a ciki ba saboda nasan k'ank'arar zata narke

ta zama ruwa, tsane ta nayi sosai sannan na saka a

oven na kunna, sai data gasu sosai sannan na fiddo

na barbad'e ta da borkono na d'ora a plate na rufe,

farar shinkafa na dafa da sauran ruwan stoke d'in

da ya rage sai maggi kad'an a ciki, juyewa nayi a

k'aramn food flask na d'ora duka a tray har da fruit

salad d'in dan a lokacin yayi sanyi sosai.

Fita nayi a dining na ajiye na koma d'aki na dan

ganin ko Umar ya tashi, a daidai bakn dining naci

karo da maamah,

"Ina ta jin k'amshi ne nace barin xo inga me ake?

Ashe kece a kitchen d'in? Ina su Kareenah ne me

yasa baki kira su sun miki girkn ba idan bakya son

wanda aka dafa?",

Duk a tare ta jefo wannan maganar,

Murmushin ya'ke na mata nace "haka kawai nayi

ra'ayin shiga kitchen yau maamah, nayi girki dake

kizo muci",

Maamah taji dad'i sosai tace "aikuwa zanci girkin

'yata",

"Ok ki zauna maamah, zanje inga ko Umar ya

tashi",

"Daga can nake yanzu na same shi yana bacci bai

tashi ba, da alama yaji dad'in baccin".

Komawa nayi na zauna jin ta fad'i haka, nan muka

hau cin abincin, sosai mukaci shi, maamah tace

rabon ta da taci abincin da taji dad'in shi tun tana

Nigeria, girkin Nigeria daban yake dana kowace

k'asa.

Da dare bayan na kwanta na fara tunanin maganar

wani babban Gaeny Doctor da yace "babbar

matsalar da take haifar wa matan yanzu dole sai an

yanka su shine rashin juriya, wata matsalar daga

likitocin ne wasu kuma daga masu haihuwar ne, wai

da zarar *EDD* d'in mace ya cika bata haihu ba sai

ta fara tunanin anya lafiya take kuwa? *EXPECTED

DAY OF DELIVERY* fa akace, shi kanshi likitan ba

wai yana da tabbacin a ranar bane zaki haihu,

kawai dai yayi hasashe ne, daga ranar taxo kawai

sai su mik'a kansu ayi masu aiki, wai bazasu iya

haihuwa da kansu ba, su kuma likitocin da yake

wasu hankali bai ishe su ba sai su hau yankar

mace.

Wasu matan kuma ciwon tsakani da Allah ne,

*TOILET INFECTION* na d'aya daga cikin giggan

abubuwan dake sawa mace ta kasa haihuwa da

kanta, da zarar lokacin haihuwa yayi sai jini ya fara

fita baji ba gani amma babu haihuwar, sai kan baby

yazo tahowa sai cutar dake gaban mace ta tokare

shi yak'i fita ga kuma jini ta gama fitarwa har ya

kusa k'arewa, shine daga k'arshe dole sai an mata

aiki, tou ta wace hanya za'abi don ganin an

magance cutar *TOILET INFECTION?* (niko Amrah

nace ku tambayi Members na *MU FARKA MATA

GROUP CHARTS,* munyi wannan darasin inda

muka zazzak'ulo matsalolin cutar, abubuwan dake

haifar da ita, abubuwan da take haifarwa da kuma

hanyoyin magance ta)."

"Exacly wannan shine matsalar maman Umar,

saboda yanda ta ringa zubar da jini amma kan jariri

yak'i fita" na fad'a a fili har da guntun hawaye na,

dan yanda na tuno da mutuwar maman Umar sai

abun ya dawo min sabo, yarinya kyakkyawa

haihuwar fari kamar ita tayi kanta saboda kyau.

Da wannan tunanin naji kukan Umar ya tashi,

shayar dashi nayi da sauran madarar d'azu, nan na

hau yi masa wasa yana wangale baki kamar ba

yaron wata biyu da kwanaki ba.

Washe gari na fara harhad'a kayakina, bayan na

gama duka nace ma maamah "ina so driver zai

kaini kasuwa zanyima dangina tsaraba"

"To zan rakaki mu tafi tare saboda in kaiki inda za'a

baki komai da sauk'i",

"Aikuwa da naji dad'i maamah"

"A shirye nake mu tafi kawai".

Kasuwa mukaje inda nayo siyayya sosai, saboda

dama so biyu naji alert na salary na ban fitar ba sai

yanxu da zanyi siyayya, Haydar da Umar sun sha

kaya sosai, Hassan da Usaina yaran Futha ma na

masu siyayya sai kuma ita Futha d'in.

Sai yamma lik'is sannan muka koma gida a gajiye

na harhad'a kayan a wata babbar jaka da aka sako

min kayan a ciki,

Bayan ma gama had'a kayan a lokacin har dare

yayi, maamah ce ta shigo d'aki na kamar zatayi

kuka tace "yanzu shikenan Nadiya tafiya zakiyi? A

yanda na saba dake ji nake kamar kici gaba da

zama dani har abada, dama nayi rashin tawa

Nadiyar shekaru masu tsawo.." kuka sosai ta

b'arke dashi, jin ta fad'i haka yasa nace "pls

maamah ki daina sakawa kanki damuwar nan da

yawa, da alama kinyi mai irin sunana ne ta rasu, ina

so ki d'auke ni tamakar madadin 'yar ki Nadiya data

rasu, zan tafi gida gobe amma ba wai ina nufin na

rabu dake ba har abada, akwai waya zan ringa

neman ki akai akai ina jin lafiyar ku, kuma dan Allah

duk lokacin da 'yar ki ta Nigeria ta haihu ki fad'a

min insha Allahu zanje duk da nisan Katsina to

Abuja",

Shiru tayi da kukan ta rungume ni sosai tace

"nagode dajin kalaman ki Nadiya ta, Allah ya bamu

ikon rik'e zumunci, had'uwa ta dake ina ji a jikina

alkhairi ne babba, ga wannan" ta mik'o min wata

babbar leda da ta shigo da ita, "naki ne wannan

keda Umar, shi kuma Haydar tunda bada shi akazo

ba nashi kad'an ne".

Bud'ewa nayi naga kaya ne da yawan gaske,

Hawaye naji yana zirara daga ido na na k'ara matse

ta tsam a jiki na nace "nagode sosai maamah, Allah

ya saka da alkhairi".

Da haka ta fita ta koma d'akin ta, ina jin muryar

Nadrah tana ta habaice habaicen ta cikin yaren

indiyanci, amma da yake ban san abunda take fad'a

ba sai ban damu ba kawai naci gaba da abunda

nake na duba takardu na.

Washe gari da asubah maamah da khalil suka kaini

har airport, khalil yace "am going to miss you

sister",

Murmushn k'arfin hali na masa nima nace "me too

brother" da wannan maganar aka fara shiga layi,

kayana na fara d'aurawa a layin sannan nima

nahau, babu b'ata lokaci aka fara shiga jirgi. Su

maamah basu tafi ba har sai da jirgin mu ya tashi.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah*


5⃣3⃣

*note:- kuyi hak'uri na rashin jina kwana biyu, muna

ta faman tests ne a school ga kuma exam d'in mu

yana matsowa, am in need of your prayers pls.*

Na sadaukar da wannan page d'in ga fans d'ina

*Asmau Abdu Haro and Kareemah Hassan,* tanx

alot for your caring, Allah yabar k'aunah.

************

Da misalin k'arfe takwas na dare jirgin mu ya sauka

Kano, tunani nake ta yanda zan tafi Katsina a

wannan daren duk da yake tafiyar ba wata mai

yawa bace amma ina tsoron tafiyar dare sosai, nan

na fara tunanin inda zan kwana, na d'aukarwa kaina

alk'awarin bazan tab'a komawa gidan su Dady da

Momy Zee ba har abada, hakan yasa kawai na

yanke hukuncin zuwa hotel kawai in kwana acan

saboda akwai kud'i a hannu na wadatattu. Hakan

kuwa nayi, Hotel d'in kusa da airport d'in na kama

k'aramin d'aki, a gajiye na shiga na gabatar da

sallolin da suke kaina sannan na cirema Umar

diper, ina cire mashi yana wangale min baki alamar

yaji dad'in cire masa da nayi dan tunda muka shiga

jirgi ban canja masa wata ba.

Washe gari da sassafe bayan na karya na dama ma

Umar madarar shi sannan na kama fidda kaya na,

sai dana fitar duka sannan na tari napep ya kaini

babbar tasha, da zuwana kuwa babu b'ata lokaci na

samu mota muka kama hanyar katsina.

Daga tashar ma napep na hau ta kaini har gaban

gida na, bayan na sallame shi na kira mai gadi ya

kwashe min kayan yana shiga dasu ciki sannan

nima na shiga.

Waya ta na d'auka na kira Futha, na shaida mata

cewa na iso yanzu haka, tayi murna sosai sannan

tace "Baban twince baya nan sai dai zuwa anjima

kad'an zamuxo, idan bai dawo ba har yamma kuma

sai kawai mu hau napep muzo, na k'osa inga yanda

Haydar zayyi idan ya ganki" murmushi na mata

nace "fUtha bakya gajiya da tsokana, kice dai kin

k'osa kiga yanda Umar d'ina ya zama saurayi"

"A'a aunty, Umar ai tunda na kula kinfi ji dashi na

bar miki shi, d'an lele na dai kawai kike son gani"

Da wasa da dariya muka gama wayar sannan na

tura ma Abban Haydar text kamar haka:-

_assalamu alaikum, ina mai shaida maka cewa na

dawo jiya amma na kwana a kano saboda nayi

dare, amma yanzu haka ina gida tun d'azu na iso

daga kanon._

Ajiye wayar nayi tare da shiga kitchen domin d'ora

girkin rana duk da gajiyar da nake da ita,

Shiga ta kenan sai ga Futha, hannun ta d'auke da

Haydar da halittar shi ta k'ara canjawa sosai ya

k'ara muni kamar ba mutun ba, biye da ita kuma

twince d'inta ne kyawawa mace da namiji suna ta

faman surutu. Da sauri na goge hawayen daya fara

gangaro min sannan na fita parlor'n ina fad'in "gani

anan" fuskata d'auke da murmushin k'arfin hali.

Bayan ta gaishe ni na karb'i Haydar da har yanzu

kamar jinjiri yake, dariya ya kama yi min sosai nima

dariyar na mayar masa, da alama dai yaji dad'in

gani na, Umar d'ina ta d'auka dana saka shi a baby

seat yana wasa,

"Aunty yaron nan fa yayi kama dake wallahi" Futha

ta fad'a tana k'are masa kallo, nima kallon na bishi

dashi kafin ince "nima dai nakan ga hakan wani

lokaci, amma na kasa gaskatawa saboda banga ta

hanyar da zayyi kama dani ba"

"Wallahi da gaske nake Aunty, har yanayi da Haydar

ma yana yi dan dai kawai Haydar baida isasshiyar

lafiya ne"

"A naki ganin kenan, nidai barin shiga kitchen rana

nayi" na fad'a tare da mik'ewa tsaye dan nufan

kitchen d'in, da sauri Futha tace "a'a Aunty ki zauna

zan girka, ki huta abunki" tana kaiwa nan ta tafi

kitchen taci gaba daga inda na tsaya.

Bayan ta gama girkin munci ne nake mata magana

"Futha yanzu ya za'ayi maganar new nany? Kinga

ga aiki na gashi kuma nauyin ya k'aru, ga Haydar

ga Umar ban san ya zanyi dasu ba, dole sai da 'yar

raino".

"Ehh gaskiya ne, zan bincika miki insha Allahu daga

nan zuwa gobe ko me kenan zan sanar dake".

Da haka mukayi bankwana da ita ta tafi, Haydar har

da kuka yayi wai dan Hassan da Usaina sun tafi

sun barshi, yana ta maganar shi da har yanzu bana

gane ta.

_Washe gari_

Da sassafe na fara shirin tafiya asibi dan inyi

reporting na dawo, ina cikin shirin ne naji wayata na

ringing, koda na duba naga Maamah ce, da fara'a na

d'auki wayar na mata sallamah tare da gaishe ta

"Ni bazan amsa miki ba Nadiya, wai ace kin sauka

tun shekaran jiya amma kin kasa kira na ki fad'a

min ko? Ai na b'ata dake tunda abun haka ne"

Kunya naji sosai nace "nayi laifi Maamah a gafarce

ni"

"Haba Nadiya, wato kin koma wurin mijin ki da

Haydar shine kika ma manta damu ko? Babu

komai"

"Dan Allah kiyi hak'uri maamah, wallahi bazan tab'a

mantawa daku ba kuna raina"

"Tou yayi babu komai ya wuce, ya kika koma gida"

"Lafiya lau ina Khalily?"

"Gashi yanzu ya karb'o admission d'in shi, wai yana

gaishe ki"

"Ina amsawa a gaishe da Nadrah" da haka na

kashe wayar tare da saka hijabi na bayan na goya

Umar.

A daidai fuskar Haydar na matso nace "Haydar zan

tafi in barka anan kayi hak'uri bazan dad'e ba kaji?",

Kai kawai ya gyad'a min ya b'ata fuskar shi kamar

zayyi kuka,

A hankali na ringa bubbuga mashi baya nace "bazan

dad'e ba insha Allahu, kaga aiki zanje kuma ban

san ya zanyi dakai ba, ga Umar gaka, shi Umar

dole in tafi dashi saboda babu mai kula dashi inba ni

ba",

Kai ya kad"a min bayan yayi maganar da ban san

me ya fad'a ba,

"Yauwa tou kamin murmushi yaro na",

Murmushin ya k'irk'iro yamin, sosai ya bani tausayi

kamar in masa kuka naji,

"Idan kaji fitsari ko kashi kawai kayi abunka anan

idan nazo zan gyara",

Nan ma dai d'aga min kai yayi, fita nayi ina d'aga

masa hannu shima yana d'aga min.

©Princess Amrah

[9:47am, 1/10/2016] Amrah Pinky durling :

*```º~º~UMMU HAYDAR~º~º``

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah*


5⃣4⃣

Ranar dai signing kawai naje nayo na dawo, saboda

baki d'aya hankali na naga Haydar dana baro gida,

Sai dana biya wata shop na siyo masa chocolates

da sweets masu tsada sannan na saima Umar ma

madarar sa saboda tashi ta kusa k'arewa, koda na

koma gida haydar yayi bacci, sosai ya bani tsausayi

saboda yanda yake kwance cikin kashi da fitsari

kasantuwar pampers tashi ta k'are,

A hankali na sauke Umar daga baya na na kwantar

dashi kan carpet, Haydar na fara d'auka na kaishi

toilet na wanke masa jikin shi sosai, a lokacin ne ya

tashi daga bacci, murmushi yamin tare da wata

magana, nan ma dai ban gane abunda yace ba,

nima murmushin na miyar masa dashi tare da

d'aukar sa na kai parlor.

Cikin lokaci kad'an na gama gyagygyara wurin yayi

kyau, dawo wa nayi na zauna da gajiya a jiki na na

kira Futha,

"Hello Futha"

"Na'am Aunty ya gida?"

"Lapia k'alao, ya maganar mu?",

"Dama ina da shirin kiran ki yanzu, an samu 'yar

aikin, k'anwar Sadiya ce ma, insha Allahu itama

zakiji dad'in ta, anjima zan kwatanta mata gidan sai

tazo",

"Yauwa nagode kuwa, kinga dama ina son zuwa

gidan Sadiya idan tazo sai ta kaini kenan",

"Ehh hakane"

"Tou shikenan sai tazo d'in, ki gaishe min da yara

na",

"Zasuji insha Allahu"

Na kashe wayar d'if cike da jin dad'i.

Da yamma bayan la'asar sai ga Safarah k'anwar

Sadiya taxo, tana zuwa na gane ta saboda kamar su

d'aya sak da Sadiya,

Bayan ta gaishe ni ne na fara mata bayanin komai a

hankali, sai dai lokacin da taga Haydar naga

yanayin ta ya canja lokaci d'aya, sosai abun ya bani

tsoro amma sai na dake, saboda a tunani na dan

ganin farko ne bata san shi ba,

Murmushin k'arfin hali nayi nace "zaki iya gane

gidan Sadiya daga nan?",

"Ehh zan gane" ta fad'a tana ma Haydar satar kallo.

"Tou muje ki kaini, kinga sanda akayi bikin bana

k'asar".

Shirya Umar nayi yayi kyau, Haydar kuma dama a

shiryen sa yake, ita nace ma ta d'auke shi amma

tsoro ya hana ta d'aukar shi, Umar na bata ni kuma

na d'auke shi baki d'aya hankali na bai kwanta da

yarinyar ba.

Sadiya taji dad'i sosai da ta gan mu, na bata

tsarabar ta ta k'ananan kayan dana siyo mata, taji

dad'i da taga k'anwar ta ce mai rainon Haydar

yanzu, bamu wani jima ba muka tafi, nan ma dai

Safarah bata d'auki Haydar ba nice na d'auke sa.

Washe gari na koma aiki na sosai, inda na bar mata

Haydar da Umar dan ta kula dasu, sai dai da

mamaki na na dawo gida na samu Umar sai kuka

yake alamar yana jin yunwa, Haydar kuma har ya

gangaro k'asa daga kan kujera yana k'ok'arin zuwa

inda Umar yake ya rarrashe sa,

Cikin kid'ima nace "Safarah! Ina kika shiga kika bar

min yara haka?",

Sam bata ma jini ba barin insa ran zata tanka min,

"Safarah!!" Na k'ara fad'i da k'arfi,

Can naji muryar ta ta amsa, nan da nan sai gata, a

daburce ta gaishe ni, ban ko amsa ta ba nace "ina

kika shiga ne wai kika bar min yara haka? Kinga

Umar yanda yake bud'e baki alamar yunwa yake ji,

Haydar kuma ji yanda ya sauko k'asa, idan fa yaje

ma wurin b'arna? Wai ma me kike ne da kika kasa

kula min da yara?",

Kasa fad'in komai tayi sai hak'uri da take bani, sai

can daga baya tace "bazan sake ba Aunty" tsaki

kawai nayi na jawo flask d'in madarar Umar, empty

naji ta alamar bama a had'a masa ba, "kenan duk

yau baki basa komai ba Safarah?",

Shiru tamin bata ce komai ba,

Kai kawai na gyad'a na tafi kitchen, cikin lokaci

kad'an na dama masa madarar, da sauri sauri ya

ringa sha, Haydar ma naga alamar baici komai ba,

indomie na dafa masa na bashi yaci ya k'oshi.

************

*BAYAN SHEKARA HUD'U*

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah*


5⃣5⃣

Na sadaukar da wannan page d'in ga *Ilham

Muhammad* na gode da yanda kike nuna kulawar ki

a gare ni, Allah yabar k'auna.

***********

A tsawon wannan lokacin Umar ya girma har ya

shiga School, Haydar kuwa har yanxu baya girma

sai dai kad'an ya fita daga siffar jarirai saboda da

xarar anga fuskar sa za'a gane. Waya ta kuma an

sace ta ranar sunan Futha (ta k'ara haihuwa) hakan

yasa nayi loosing number'n Maamah tun daga nan

bamu sake yin waya ba, naso inji labarin ko 'Yar ta

dake Abuja ta haihu amma babu hanyar da zan sani.

Aiki na kuwa nayi resigning (tsaida aiki) na zama na

gida naci gaba da kula da yara na, babu yanda

abokan aiki na basuyi ba akan na koma aiki amma

nak'i, duk mai aikin dana samu bata zama, wasu

kuma cutar da yarana suke, ganin hak'k'in su zai

iya kama ni kawai yasa na yanke wannan shawarar

amma da xarar suka fara mallakar hankalin su zan

koma saboda yanda likitoci sukayi k'aranci da xarar

na koma da wuri za'a karb'e ni musamman ma

yanda na zama consultant kafin a samu iri na mace

sai an tona.

Abban Haydar kuma yanxu ba laifi yana xuwa wuri

na amma sam baya son ganin fuskar Haydar,

amma yana yawan jan Umar wasa kamar shine ma

d'an nasa.

Yau ma kamar kullum ya dawo daga aiki yayo gida

na direct, sai dai da anga fuskar sa za'a gane lallai

ba lafiya ba, da hanxari na karb'i jakar hannun sa na

kai d'akin sa,

Har na dawo parlor bai cire hannun sa daga tagumin

da yayi ba,

Magana nake masa amma yayi zurfi a tunanin sa,

Da k'arfi na tafa hannu na yayi saurin zabura, a

gefen sa na xauna cike da mamikin yanda Haydar

ke kallon sa amma ya kasa ce masa komai a

wannan lokacin.

"Usman lafiya Nagan ka haka?",

Shiru yamin baice komai ba hakan yasa na sake

cewa "though dai nasan bani da matsayin da zaka

fad'a min damuwar ka amma dole na tambaye ka,

babu walwala a tare da kai sai faman tunani, nasan

dole akwai damuwa a tattare da kai".

Hawaye naga suna sauka daga idon sa wanda

tunda mukayi aure ban tab'a gani ba, ko sanda su

Mommah suka rasu bayyi kuka ba,

Kafad'ar sa na hau bubbugawa kamar k'aramin yaro

ina tambayar sa, da k'yar ya iya bud'e bakin sa

yace "taci amana ta Nadiya! Ta yaudare ni, wallahi

bazan tab'a yafe mata ba" yaci gaba da hawayen

shi sosai kamar k'aramin yaro,

"Wacece ita? Me ta maka?" Na fad'a a daburce dan

sosai hankali na ya tashi,

"Humayrah ta cuce ni, ashe zaman cin amana

kawai take dani, na kama ta da namiji a daki na a

gadon mu na sunnah.." Yaci gaba da kuka sosai,

Cike da mamaki nace "subhanallahi! Yanzu tana

ina?"

"Na sake ta saki uku Nadiya, bazan iya zama da

mai bin maza ba, ashe har yarinyar data haifa ba

jini na bace, ita ta fad'a da bakin ta bayan na sake

ta, abun haushi ma wai ko kad'an bata nuna

damuwar ta ba sai ma jin dad'inta data bayyana

k'arara".

Nayi mamaki sosai a wannan al-amarin, ashe da

gaske irin hakan tana faruwa?

"Kayi hak'uri Usman ka kwantar da hankalin ka,

kayi addu'ah Allah yasa hakan shine mafi alkhairi,

bana son ganin ka a cikin damuwar nan, muje kayi

wanka sai kaci abinci"

Tashi yayi muka shiga band'aki, ni na masa

wankan sannan muka fito, k'ananan kaya ya saka

muka fito dining ya hau cin abincin kamar mai

ciwon yunwa.

Yana cikin cin abinci sai ga Driver ya shigo hannun

shi rik'e dana Umar, tun daga nesa Umar ke fad'in

"Ummah nayi karatu sosai yau, har ma Aunty'n mu

ta bani kyautar chocolate",

Murmushi na masa nace "ahh lallai ta kyauta kuwa,

kaga sai kaci gaba da miyar da hankalin ka yanda

zata na ringa baka kyaututtuka anytime".

Da sauri ya fixge hannun shi daga hannun driver,

inda Haydar yake ya nufa, murmushi ya masa tare

da fad'in "na rago maka chocolate d'in brother,

gashi" ya zaro ta daga school bag d'in sa,

Murmushi shima Haydar d'in ya masa ya mik'o

hannun sa marar lafiya yana k'ok'arin karb'a amma

ya kasa, a baki Umar yaci gaba da bashi chocolate

d'in har ta k'are sannan ya tashi da sauri yace

"Ummah ai dai yau babu islamiya ko?"

"Babu islamiya yau Umar, amma nayi magana da

malamin dake koya ma Haydar karatu kaima zai

ringa koya maka, kaga idan kaje islamiya wani abun

ka riga da ka sanshi sai kana koya ma malamin

ma",

Murmushi yamin yace "Ummah naso tamin wayo,

na gano ki ai"

Cikin mamaki na kalle shi, lallai Umar akwai shi da

wayo, wayo kamar wani d'an shekara goma, ga

wata irin shak'uwa mai k'arfi da take tsakanin shi

da Haydar.

Sai a lokacin ya kula da Abban Haydar daya buga

uban tagumi,

Da sauri ya koma wurin sa a dining d'in yace "laah

Abbah mesa kake kuka? Ashe babba yana kuka" ya

fashe da dariya shi abun ma dariya ya bashi, duk a

tunanin sa manya wai basa kuka.

Saurin goge hawayen yayi yace "ba kuka nake ba

Umar, nayi hamma ne taxo min da hawaye"

"Kai dai Abbah kuka kake shine zaka min wayo, tell

me ba dai Ummah ce ta duke ka ba ko?",

Ido zare Usman yace "ai nafi Ummanka k'arfi,

baxata iya dukana ba, oya kaxo kaci abinci nasan

kana jin yunwa",

Abincin yazo yana ci yana surutu har ya gama.

Kuyi hak'uri da wannan insha Allahu gobe da safe

zaku jini, na gode da nuna kulawar ku a gare ni,

masu bina ta pchart suna min fatan alkhairi duk na

gode maku, har ma wanda basu min fatan alkhairi

na gode, yanzu zamu ci gaba da gundarin labarin

saboda da duk labari ne take bayawar.

Shin su Maamah zasu sake waiwayar Nadiya? Yar

Maamah dake aure a Nigeria ta haihu kuwa? Waye

wannan wanda idan masu karatu bazasu manta ba

yana ma Nadiya kyuatuttuka? Waye abokin Usman

wanda har yaje auren sa a Kano lokacin daya fara

ganin Nadiya a ana hira da ita tun kafin ta gama

karatun ta? Nasan wasu duk sun manta da wannan,

duk zakuji wannan amsosshin indai kukaci gaba da

kasancewa da 'yar mutan mashi insha Allahu. Muje

zuwa dai.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah*


5⃣6⃣

Haka dai rayuwa taci gaba da tafiya, tsakani na da

Abban Haydar kuwa ba yabo ba fallasa, sai dai

kuma a duk lokacin danayi kuskuren kiran sa da

*Abban Haydar* tou ko wace magana ta fito bakin

sa yana iya fad'a min ita, shi dai kawai baya son

Haydar kamar ba jinin sa ba, har ma yafi son Umar

da bai had'a komai dashi ba.

Yanzu kam ba laifi yana kula dani, ganin bana aiki

yasa yana iya k'ok'arin shi ganin ya biya min duk

wasu buk'atu na, abinci kuwa tun kafin wata ya

k'are yake siyen wasu.

Haydar kuma na samo masa malamin da yake koya

masa addini kuma alhamdulillah yana gane komai

duk da har yanxu bai iya magana ba sosai, idan ma

yana yin maganar yawu na fita daga bakin sa, daga

ni sai Umar ke gane maganar sa sai kuma Malan

Jabir (na *WANI HASKE* ) Shima yana gane

maganar saboda duk lokacin da zai koya masa

karatu idan ya dawo baya k'ara masa har sai ya

karanto masa wanda ya masa baya,

Sosai yake mamakin k'walwa irin ta Haydar, duk da

yake *MUSAKI* amma hakan bai hana sa gane

karatu ba, dama haka Allah yake ikon shi, idan ya

hana ka ta nan sai ya baka ta can kamar yanda

Haydar yake da k'arancin lafiya amma ga kalar

baiwar da Allah ya bashi, da an masa karatu yake

ganewa koni da nake babba wani abun bana

fahimtar sa kamar yanda Haydar yake saurin

fahimta.

Tsakanin shi da Umar kuwa tausayi ne da jink'ai

sosai, duk da Umar yaro ne amma bai hana shi

tausayawa Haydar ba ganin bashi da isasshiyar

lafiya, a duk lokacin da yayi sallah duk da ba iya ta

yayi ba yana saka d'an uwan shi a addu'ah kamar

yanda na koya masa, shima kuma Haydar d'in

malam Jabir ya koya masa yanda zayyi sallah daga

kwance, yanzu sallah bata k'wace masa kafin yayi

kuma sai ya kira ni na masa alwala ko kuma Umar

ya masa.

Hajiya da Ummi kuwa har yanzu bana samun

sassauci daga wurin su, wani lokacin ko Abban

Haydar ya sauko sune suke k'ara d'ora shi akan

munanan hanya shi kuma yabi ya d'auka maganar

su.

Zaune nake ina koya ma Haydar turanci duk da

yanxu kam ya iya kuma yana picking wasu words

d'in masu sauk'i, Umar ne zaune yana game da

waya ta kwata kwata ma banyi tunanin yana

sauraren mu ba, jin muryar shi nayi yana fad'in

"Brother kace ma Ummah ta daina koya maka ni

zan koya maka tunda kaga ni na iya, a School d'in

mu ba'a mana hausa idan ma mutum yayi hausa

dukan sa akeyi sosai kuma a fad'awa parents

nashi".

Shiru nayi ina kallon shi kafin ince "tou ai sai kaxo

ka koya masa, dama kitchen nake son shiga nasan

Abban ku ya fara jin yunwa yana d'aki har yanzu"

daidai na mik'e zan tashi kenan naji sallamar Hajiya

da Ummi biye da ita,

Sai da gaba na ya fad'i dan nasan babu alkhairi a

tare da zuwan su.

Gaishe da Hajiya nayi amma ko kallo ban ishe ta ba,

d'akin Usman ta zarce ita da Ummin ba tare da

nace masu komai ba na shige kitchen abu na,

K'asa k'asa na jiyo muryar Hajiya na fad'in "na

fad'a maka dama matan yanzu na kirkin su kad'an

ne, gashi ita Humayrah taci amanar ka ashe ma ba

'yar ka bace, saisa nake yawan maka addu'ah Allah

dai yasa shima wancan *MUSAKIN* naka ne tunda

ga wancan yaron da tace wai taimakon shi tayi tana

rik'on shi amma siffar su d'aya, ai raina mu ma tayi

da har take nunar da ba jinin ta bane, kawai dai ta

haifi shege ne take gudun tonuwar asirin ta, amma

ina mai tabbatar maka da cewa Haydar ba d'anka

bane shege ne".

Sosai gabana yake dukan uku uku, tunda nake ban

tab'a gani ko jin sharri irin wannan ba, me na ma

Hajiya data min wannan tsanar haka? Nidai koda

nayi rayuwa a gidan su momy Zee basu min tsanar

da har zasu min irin wannan k'azafin ba, kuka sosai

nake ina rok'on Allah ya kawo min mafita.

Kamar ance inyi shiru kuma naji muryar sa yana

fad'in "na dad'e ina wannan tunanin Hajiya, babban

abunda yake mani mamaki ma shine; a duk xuri'ar

mu babu *MUSAKI,* taya ni kuma zan haife shi? Na

yarda da duk maganar ki, sai dai kuma babu yanda

za'ayi in rabu da Nadiya duk yanda naso saboda a

gaban ki Mommah kafin ta rasu tace matuk'ar na

rabu da Nadiya bata yafe min ba, kawai dai zan fita

harkar ta ne har sai lokacin da dan kanta ta gaji da

zama dani ta nemi saki, kinga anan tsinuwar

Mommah bazata bini ba saboda itace ta nema".

Ummi tace "good idea yaya Usy, kama shegiya

haka" (ta manta da itama mace ce zatayi auren

kuma duk abunda kama wani kaima sai an maka).

Kuka naci gaba dayi sosai, girkin ma na kasa yi sai

ma wurin xama dana nema a cikin kitchen d'in ina

nazarin kalaman da kunnuwa na suka jiye min, ji

nake a raina inama ace mafarkin wannan rana

nake, amma ina, abu ne wanda ya faru xahirin shi,

"Allah kai kasan halin da nake ciki kuma kai kad'ai

kake da mafitar da zaka fitar dani, Allah kasan

k'azafin da wannan bayin Allah suka min, kai kace

mu rok'e ka a duk lokacin da muke da buk'atar

taimakonka, Allah kamin sakayya ya Allah" naci

gaba da kuka sosai har da sheshsheka.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: : *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah*


5⃣7⃣

Jina shiru ban fita ba yasa Umar ya biyo ni, ina jin

motsin shi nayi saurin share hawaye na amma

hakan bai hana wasu fitowa ba, dafa ni naji yayi a

hankali ba tare da yace komai ba,

D'aga kaina nayi naga idon shi taf da hawaye har

suna k'ok'arin gangarowa,

"Umar mesa kake kuka? An maka wani abu ne?"

Shiru yamin a lokacin har hawayen sun fara fitowa.

"Umar my son dakai nake fa, wats wrong with

you?"

"Ummah ba kece kike kuka ba?"

Murmushi na k'ak'alo nace "tou nayi shiru kaga har

na maka smiling ma, kaima kayi dariya"

Dariyar shima yayi wadda ta fiddo kamar shi dani

sosai, ni kaina ina mamakin yanda nake kama da

Umar duk da yake ban had'a komai dashi ba, amma

da yake nasan ikon Allah ya wuce komai yasa na

daina mamaki.

Fried indomie na mana nan da nan na kammala, a

food flask na zuba ma Usman nashi na had'a da

plate na kai masa dining, na xuba mana namu a tray

na tafi parlor dashi.

D'akin shi na shiga a lokacin su Hajiya sun tafi, na

shaida masa cewa na gama girki nashi yana dining ,

baiko tanka min ba har na fito na baro shi.

Zama mukayi Umar naci ni kuma inayi ina bama

Haydar a baki har muka k'oshi, bayan na kauda

kayan ne na koma d'aki nabar Umar yana ci gaba

da game d'in shi a waya na, ni kuma koda na koma

d'akin kuka na naci gaba dayi har na k'oshi.

Can naji sallamar Malam Jabir,

Bayan na wanke fuska ta na had'o littattafan su

Haydar na kawo parlor, gaishe shi nayi ya amsa

min cikin sakin fuska, nan na tambaye shi "malam

ya su Al-ameen da maman shi and Goodness?"

"Suna lafiya" ya bani ansa,

"Haydar ayi karatu da kyau kaji ko? Umar ka ajiye

wayar nan sai an gama karatu" ina fad'an haka na

koma d'aki na, a lokacin kuma naji fitowar Abban

Haydar domin cin abinci.

**********

Yanzu kam Haydar ya gama fahimtar tsanar da

Abban shi ya masa, wani lokacin idan muna tare sai

yana tambaya na "wai Ummah mesa Abbanah baya

sona? Mesa baya k'auna ta? Kodan yaga kalar

halittar da Allah ya min ne? Bayan kuma malam

Jabir yace min in daina damuwa da yanda Allah ya

yini haka yake son gani na, yace min insha Allahu

zan ji dad'i a rayuwa ta, koda ban warke ba tou

akwai ajiyar da Allah ya min, amma Abbanah baya

duba haka, yafi son Umar fiye dani" ya fashe da

kuka bayan ya gama maganar.

Nasiha na hau yi masa sosai kuma da alama yana

d'auka, ban daina ba har sai da yayi bacci da

busasshen hawaye a fuskar sa.

Washe gari ta kama safiyar Monday, da sassafe na

shirya Umar ya tafi School Abban Haydar kuma ya

tafi aiki,

Ina kwance ina ma Haydar karatu tunda a halin

yanzu ya san abubuwa da dama akan karatun boko,

har yama fi wani yaron da yake zuwa school,

Sallamar ki naji shine naje na bud'e miki kofan".

Shiru Ummu Haydar tayi sannan taci gaba da

"wannan shine tarihin rayuwa ta, har yanzu ban san

farin ciki ba, ban san gata ba, na rasa iyaye na tun

ina yarinya, na taso a hannun abokin baba na sun

gana min azaba bayan sun danne min gado duk da

yawan dukiyar da na samu ta gado, mamana bata

kuma waiwaya ta ba duk da nasan bata san inda

nake ba saboda Dady da Momy Zee canja gida

sukayi lokacin, nasan ta neme ni ta rasa, naxo nayi

aure nan ma dai babu farin cikin, mutane uku kawai

suka soni a baya, Dady, Mommah sai Futha, yanzu

kuwa mutun d'aya ce futha sai kuma yara na, Umar

kuwa babu ko labarin iyayen shi, hakan yasa na

d'auki aniyar rik'on shi har k'arshen rayuwa ta,

haihuwa kuma kamar yanda na fad'a d'in haka nayi,

na tsaida ta da Abban Haydar duk da shima yanzu

babu ruwan shi da shimfid'a ta, girki na kawai yake

ci sai kuma yana mana duk wani abun da zamu

buk'ata nida Umar amma banda Haydar, hakan

yasa na fahimci lallai ya yarda da maganar Hajiya

cewa Haydar ba jinin sa bane, so da yawa yakan

fad'a min ya tsani yaji na kira Haydar da wannan

sunan saboda sunan baban shi ne, ni kuwa tun abun

yana damuna har ya daina, tarbiyyantar da yara na

kawai na tasa a gaba, yanzu haka Umar yana

School bai dawo ba amma nasan yana gaf da

dawowa saboda driver ya tafi d'aukar shi, Abban shi

kuma a gabam ki ya dawo, a gaban ki kinga abunda

Hajiya da Ummi suka min.". Shiru tayi daga nan

tana goge hawayen fuskar ta.

Cike da tausayi nace "Allah sarki *UMMU HAYDAR!

* lallai na tausayawa rayuwar ku, amma ki kwantar

da hankalin ki, insha Allahu akwai ajiyar da Allah ya

maku koda ba a duniya bane, zanci gaba da bibiyar

rayuwar ku domin ina da sha'awar kaiwa Fans d'ina

k'arshen labarin ki saboda akwai waazantarwa a

cikin sa",

D'an murmushi tamin tace "babu komai Amrah,

nagode".

Haka naci aniyar ci gaba da d'auko maku rahoton

wannan gida, ina fatan zakuci gaba da kasnacewa

dani har lokacin da labarin xai kai k'arshe.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah*


5⃣8⃣ & 5⃣9⃣

Zaune take sai ga Umar da gudu ya shigo d'akin,

hannun shi rik'e da launch box da skul bag a bayan

shi,

Da sauri ya rungumi umman shi itama ta sumbace

shi a goshi,

Abinci ta kawo masa amma yace shi baxaici ba sai

Haydar ya tashi daga bacci suci tare, dole ta

hak'ura ta k'yale shi dan tasan ko ta hana shi ba ji

zayyi ba.

*BAYAN SHEKARA D'AYA*

_MUMBAI INDIA_

Zaune take ta had'a kai da guiwa in banda kuka

babu abunda take yi, 'yar ta Nadrah ma kukan ne

yaci k'arfin ta babu mai rarrashin wani a cikin su,

Suna cikin haka ne Khalil ya shigo hanun shi rik'e

da makullin mota,

Bayyi mamakin yanda ya gansu ba saboda yanxu

aikin su kenan, har wurin aiki ta daina zuwa saboda

tsananin damuwar da suke ciki.

Kafad'ar Maamah ya dafa yace "haba Maamah! Ya

kamata by now kun hak'ura kun daina kukan nan

saboda bashi ne zai maku magani ba, addu'ah itace

ya kamata kuyi ba kuka ba, wata cutar ma zata iya

kama ku adalilin haka",

D'ago rinannun idanuwan ta tayi ta kalli Khalil take

wasu sukaci gaba da mata ambaliya,

"Yanxu khalil shikenan babu labarin Humairah?

Shikenan mun rasa ta? A gaban ka kullun sai na kira

number'n Salman mijin ta amma baya d'auka, wani

lokacin kuma idan ya d'auka sai ya min shiru, daga

k'arshe ma kashe layin akayi baki d'aya ba'a samu,

ban san ya labarin 'ya ta ba" ta k'ara fashewa da

wani kukan.

Khalil yace "duk nasan wannan Maamah, amma ni a

tunani na kawai mu tafi Nigeria, tun farko ma inda

haka akayi wata k'ila da an samu mafita, zanyo

mana visa duk kan mu sai mu tafi ko zuwa jibi ne

saboda gobe zan gama exams",

Maamah tace "kana ganin Salman zai yarda ya

zauna a gidan da muka san su ne? Nidai fata na

Allah yasa ba siyar min da 'yata yayi ba"

Saurin d'agowa Nadrah tayi tace "aikuwa da ya

siyar wa kan sa bala'i, dan wallahi sai naji uban da

ya tsaya masa, hukumar India zamu fad'a mawa

kuma nasan sai sun kamo shi a duk inda ya shiga".

Da wannan maganar suka tsayar da kukan da suke

su duka, Khalil kuwa take ya samo masu Visa zasu

tafi jibi da sassafe.

Bayan kwana uku jirgin su ya taso daga babbar

Airport d'in Mumbai inda zai sauka a babban birnin

tarayyar Nigeria wato Abuja.

K'arfe tara da rabi na dare jirgin su ya sauka,

Khalil yace su kama hotel su kwana kafin gobe

amma maamah tace ita lallai sai dai su tafi yanxu,

da k'yar ya samu yayi convincing nata ta hak'ura

sai safe,

Hotel d'in cikin airport d'in suka kama, maamah da

Nadrah d'aki d'aya sai khalil nashi daban,

Wannan shine zuwan su na farko Nigeria shida

Nadrah,

Kwana maamah tayi tana salloli tare da fatan

bayyanar 'yar ta.

Da sassafe aka kawo masu breakfast d'in su, basu

wani ci da yawa ba saboda basu saba cin abinci irin

shi ba sai na India, maamah kuwa damuwa ce ta

hana mata cin abincin da yawa.

Idan bazata manta ba a sanin ta sunan unguwar su

Humairah Loko goma, house number 19, duk da

itama bata tab'a zuwa ba kawai dai Humairan ne ta

fad'a mata haka,

Tafiya kad'an sukayi sai gasu Loko goma, a daidai

gaban House number 19 me taxi d'in ya tsaya tare

da fad'in "anxo",

"Nawa ne kud'in ka?" Khalil ya tambaue shi a cikin

rashin k'warewa da yaren hausa,

"Dubu d'aya da d'ari biyar ne"

Zaro kud'in yayi ya bashi sannan ya fitar masu da

kayakin su ya tafi.

Haka kawai maamah ta samu kanta da fad'uwar

gaba,

A daidai gate d'in suka tsaya, Khalil yayi knocking

sai ga mai gadi ya fito yana tambayar "waye?",

"Mune" khalil ya miyar masa da amsa.

Fitowa yayi ba tare daya bar su sun shiga gidan ba,

"Kun zo wurin waye?" Ya sake tambayar su,

Da sauri maamah tace "munxo wurin Humairah ne

matar Alhaji Salman"

Shiru yayi yana nazari kafin yace "ok! Alhaji Salman

sune wanda suka tashi daga gidan nan tabbas haka

naji a bakin mai gadin wancan gidan, tou amma

gaskiya ban san inda suka koma ba yanzu, wannan

gidan sabuwar amarya ce bata dad'e da zuwa ba

dan koni yau sati na uku da fara aiki a gidan, sai dai

ko zaku tambayi wancan mai gadin ko Allah zai sa

ku dace" ya masu nuni da wani gida na kusa da

wannan d'in.

Take hawaye suka fara gangara daga idanuwan

maamah, a ranta tana tunanin "kodai Salman ya

siyar min da 'yata ne?"

Suna cikin haka sai ga wasu mata guda biyu sun

fito daga cikin gidan, ta farkon yarinya mace ce

daka ganin ta itace amaryar, sai ta biyun kuma ta

d'an girme ta,

Yarinyar ce tace "tou maman Munauwarah nagode

sosai sai na shigo, wane ne kike min nufin gidan

ki?"

Inda mai gadin nan ya gwada ma su maamah nan ta

gwada mata tace "can ne gida na, sai kin zo ko?"

"Ehh sai nazo, a gaishe da yaran" ta fad'a tare da

komawa ciki har a lokacin basu kula dasu maamah

ba.

Da fitowar wadda aka kira da maman munauwara

taci karo dasu maamah a k'ofar gida, da sauri taja

burki tana tunanin inda ta san su,

Sake d'ago kanta tayi ta kalli Khalil a karo na biyu,

tsantsar kamar shi da Humairah ta gani a bayyane,

Har k'asa ta duk'a ta gaishe da maamah cikin

girmamawa.

©Princess Amrah

[9:11am, 12/10/2016] Amrah Pinky durling

: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah*

Tsayar da tunani maamah tayi tare da amsa

gaisuwar,

"Bayin Allah lafiya dai na ganku tsaye anan?"

Maman Munauwarah ta fad'a tana kallon su,

Maamah tace "lafiya ba lafiya ba, dan Allah

tambayar ki zanyi in bazaki damu ba",

Da sauri tace "ina jin ki babu damuwa"

Ajiyar zuciya maamah ta sauke tace "'yata ce take

aure a nan garin, mu kuma a india muke zaune,

mun san tana da juna biyu wanda ya isa ace yanzu

ta haifi uku ko biyu ma bayan shi amma shiru babu

labarin ta, lambarta kuwa bata shiga ko an nema,

shi kuma mijin nata idan na kira shi baya d'auka

daga baya ma sai aka kashe layin, sai nayi amfani

da address d'in data bamu tace gidan ta shine

muka xo nan, amma mai gadin ya shaida mana

masu gidan sun tashi wata amarya ce anan, sunan

mijin 'yar tawa Alhaji Salman, ita kuma Humairah".

Da sauri maman Munauwarah ta dafo kanta cikin

kid'ima tace "kune dangin Humairah!?",

"Ehh mune" Nadrah tayi saurin miyar mata da

amsa,

"Ehh gaskiya sun jima da tashi daga nan, amma mu

shiga gida na gashi can sai ku huta akwai labarin da

zan baku",

Maamah tace "to Allah dai yasa lafiya, Allah kuma

yasa alkhairi ne"

Maman munauwarah tayi gaba suna biye da ita a

baya, khalil janye da trolley bag d'in su.

Bayan mai gadi ya bud'e masu k'ofar suka shiga

har cikin gidan, izini ta masu da su zauna kafin ta

shiga kitchen,

Lemu ta kawo masu tare da kofuna akan tray,

"Ga lemu kusha Mama" ta fad'a fuskarta da d'an

murmushi.

Kad'an suka sha dan Maamah a matse take da jin

abunda ya smau 'yar ta, dan itakam a iya tunanin ta

ba lafiya,

Maman Munauwarah ce ta kaste mata tunanin da

take ta hanyar fara basu labari kamar haka:-

_"Humairah mak'wafciya ta ce wadda muka shak'u

sosai da ita har ina jinta kamar 'yar uwa ta har ma

tafi min wata 'yar uwar tawa, ta d'auke ni da

muhimmanci sosai saboda bata b'oye min ko wace

irin damuwar ta nima kuma haka, hatta sanda ta

samu ciki ni ta fara shaida mawa sannan na bata

shawarar ta hanyar da zata sanar da mijin ta, koda

naga fuskar wannan namijin naga tsantsar kamar

shi da ita sai dai kawai shi namiji ne ita kuma mace,

tana yawan bani labarin mahaifiyar ta suna India da

k'annen ta amma tace min mahaifin ta ya rasu bada

jimawa ba. Bayan cikin ta ya cika watan haihuwa ne

wata rana taxo min a rikice tamkar bata cikin

hayyacin ta, a kid'ime nace mata "Humairah lafiya?

Me ya same ki? Ko labour ne?" Kai kawai take

kad'a min, hankali na ya k'ara tashi sosai nace "tou

me same ki?" Bakin ta na rawa tana k'ok'arin fad'a

min amma ta kasa, da k'yar ta iya furta "yace sai

ya kashe ni" da mamaki nace "waye zai kashe ki?

Me kika masa da zai kashe ki?" Kuka sosai takeyi

tace "naji shi yana waya ne akan safarar miyagun

k'wayoyi, shine nace masa "Salman dama aikin ka

kenan ban sani ba? Amma nayi nadamar auren ka,

kuma wallahi idan baka daina ba sai nayi k'arar ka

ka sake ni tunda sana'ar ka haramtacciya ce" mari

ya wanke ni dashi bai ko duba tsohon cikin dake jiki

na ba, da k'yar na iya jan jiki na koma d'aki na,

daga bayan gida ta saitin toilet d'ina naji shi yana

fad'in "in har ban sa an kashe ta ba zata tona mana

asiri, dama boka na yasha fad'a min cewa in har

ban bi a hankali ba tou matata itace matonan asiri

na, gashi kuwa hakan yana neman faruwa, yanzu

zanje wurin Zax zance masu suxo yau da dare a

matsayin arm robbers su kashe min ita kawai"

dariya yayi sosai sannan naji ya tayar da motar sa

ya fita, shine da sauri na ziro hijabi na nayo nan ki

banii shawara miye mafita tun kafin ya dawo" tana

maganar jikin ta yana rawa sosai. Nima nawa jikin

rawa yake, saboda ban tab'a tunanin Salman zai

iya aikata haka ba, da k'yar na iya cewa "ki shiga

d'aki na kiyi wanka kafin in san miye abun yi" da

saurin ta kuwa ta shiga d'akin nawa, tana shiga naji

sallamar mai gadi, biye dashi Alhaji Salman ne a

rikice, hankali na ya gama tashi sosai nace "sannu

Alhaji, lafiya na ganka haka?", da k'yar ya iya saita

kanshi yace "Hu...Hum...Humairh tazo nan kuwa?"

Ta yanda yayi maganar ma kawai ya isa ya tabbatar

min da bashi da gaskiya, "bata zo nan ba kuwa, ko

ta tafi asibiti ne?" "Mai gadi yace min ba a mota ta

fita ba da k'afa ta fita, barin je in saka abi min cikin

unguwar nan ko za'a ganta" tafiya yayi yana yi

yana waige, ganin bana b'oye masa komai yasa ya

yarda da abun da na fad'a masa"_

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: : *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah*


6⃣0⃣

_"ganin ya bar harabar gidan yasa da sauri na dawo

d'aki, na same ta bakin window jikin ta sai rawa

yake da alama taji abun da ya fad'a, "yanzu ya

zanyi? Wallahi kashe ni zayyi" ta fad'a tana kuka,

nima kukan nake sosai ina tausaya mata,

"Humairah guduwa zakiyi daga garin nan baki d'aya

yanzu, dan nasan matuk'ar ba'a ganki ba dole sai

ya dawo nan, kuma wallahi idan ya ganki bazai

barki da rai ba, hatta ni d'in ma bazai k'yale ni ba

saboda zayyi tunanin kin fad'a min abun da yake

aikatawa, ke har miji na ma bana tunanin zai k'yale

wallahi" baki na rawa tace "idan fa na fita suka

ganni? Ban ma san ina zanje ba saboda ban san

kowa a dangin maamah ba barin inje can wurin su"

shiru nayi ina nazari kafin ince "yanxu daidai tashin

'yan Islamiyan can na matan aure ne, ina da dogon

hijabi kalar nasu sai ki saka niqab d'ina tunda dama

niqab suke sakawa suma, sai ki jira a bakin gate

har sai kinga wasu masu wucewa a cikin su kawai

sai ki bisu, nasan insha Allahu bazasu gane ki ba"

kai kawai ta d'aga min alamar ta gamsu da magana

ta, tace "zan tafi Kano ko Katsina, yana yawan fad'a

min baya huld'a da can wajejen musamman ma

Katsina, ina tunanin kawai zanje can", da sauri nace

mata "kije Katsinan kawai ma, bazai tab'a tunanin

kinje can ba saboda yasan ta miki nisa kuma baki

san ko ina ba a Nigeria" wardrobe na bud'e na fiddo

mata wata doguwar riga ta ta atamfa wadda nasan

xata shige ta, hijab da niqab d'in na d'auko mata,

take ta saka kuwa suka mata daidai a jikin ta kamar

dama dan ita akayi su, ina kuka tana kuka muka

rabu nace mata "ina miki fatan alkhairi Humairah,

Allah ya raba lafiya, idan kin sauka Katsinan sai ki

kira ni dan Allah" "tou" kawai tace min ta d'auki

wayar ta data kashe ta fita. Tun tafiyar ta hankali na

bai kwanta ba ina tsoron kar asirin ta ya tonu, da

yamma lik'is ta kira ni take shaida min ta sauka

Katsina, naji dad'i sosai ta kuma fad'a min "zan

kashe waya ta dan idan tana kunne Salman zai iya

tracing layi na har ya gano inda nake" nayi na'am

da maganar ta sannan ta tsinke wayar, tun daga

nan ban k'ara jin labarin Humairah ba, yau kimanin

shekara hud'u da watanni kenan, nasan inda

Humairah tana raye data neme ni, amma ban sani

ba ko tana tsoron kar ta dawo Salman ya kashe ta

ne, shi kuwa Salman d'in gudun kar asirin sa ya

tonu tun a lokacin yabar unguwar nan ban k'ara

sanin inda ya koma ba, mai gida na ma bai sani

ba"._

Taci gaba da kuka sosai bayan ta gama basu

labarin, suma kukan suke har da Khalil yana

tausayin 'yar uwar shi.

"Tou shikenan baiwar Allah mun gode sosai, Allah

ya baki ladar kema, zamu tafi Katsinan ko Allah zai

sa a dace" Maamah ta fad'a cikin muryar kuka.

Bankwana sukayi suna kuka suka rabu, kai tsaye

tashar mota suka nema, motar saura mutun biyar ta

cika amma khalil yace kawai su tashi zai bayar da

kud'in mutun biyun da basu cika ba.

A motar Maamah ke tunanin yanzu inda zata samu

number'n Nadiya da sai ta neme ta wata k'ila ta

hanyar ta zasu samu sauk'in neman Humairah,

sake neman wayar Nadiyan sukayi amma basu

samu ba saboda wayar ta fad'i tun tuni.

Bayan isha'i suka iso Katsina cike da fargaba, nima

Amrah fargabar nake ta inda zasu samu Humairah

dan nasan neman mutun a wannan yanayin akwai

wahala, barin ma su da basu san ko ina ba, basu

san ta inda zasu fara duba ta ba.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah*


6⃣1⃣ & 6⃣2⃣

*I dedicated this page to my dear ZARAH~B~B,

you means a lot to me, really love and cherish you

*

******

Da tambaya aka kai su Sahara Suits view motel,

kasantuwar dare yayi sosai yasa suka nemi wurin

bacci, babu jimawa kuwa bacci ya sace su banda

Maamah data kwana nafilah tana neman mafita a

wurin Allah saboda labarin da Maman Munauwarah

ta bata ba k'aramin saka ta a tashin hankali yayi ba,

ita babbar damuwar ta ma kar ace Salman ya gane

Humairah na Katisna ne ya biyo ta ya kashe ta, sai

wurin k'arfe hud'u sannan wahaltaccen bacci ya

sace ta.

Washe gari da misalin k'arfe tara na safe suka

gama shiri, anan suka bar kayan su saboda Khalil

yayi masu booking na one week.

Fita sukayi amma su kansu basu san ta inda zasu

fara ba, sai wani hoton ta da tayi kyau sosai tun

kafin tayi aure, Nadrah ce tayi ajiyar xuciya tare da

cewa "amma Maamah me zai hana mu nemi Police

station tunda ga hoton ta? Ina ganin ta haka ma

zasu iya bincika mana ita",

Maamah tace "to amma kuma Nadrah ki tuna

almost four years kenan da zuwan Humairah

Katsina, bamu ma da tabbacin ko nan d'in taxo fa".

Hawayen dake k'ok'arin fitowa daga idon khalil yayi

sauri ya goge sannan yace "Maamah gaskiyan

Nadrah ne, can d'in ya kamata muje first, idan ma

da wasu shawarwari sai su bamu idan munje".

Maamah tayi na'am da hakan sannan suka tsaida

mai napep suka ce ya kaisu babbar police station

d'in garin. Babu b'ata lokaci kuwa sai gasu a police

head quarter dan dama bata da wani nisa daga

motel d'in da suka sauka.

Shiga ciki sukayi kai tsaye suka samu ana solving

wani case na wata budurwa data kawo k'arar wani

saurayi , suna nan zaune suna mamakin yanda

budurwar ta bayar da kud'i take aka goyi bayan ta

duk da itace bata da gaskiya. Bayan an gama duka

ogan wurin ya juyo gasu Maamah yace "me ke tafe

daku?",

Khalil yayi saurin gyaran murya yace "Oga munzo

ne akan wani magana.." sai kuma yayi shiru saboda

rashin k'warewar sa da yaren hausa, fahimtar

hakan da maamah tayi yasa tayi saurin cewa

"yallab'ai 'ya ta ta zo garin nan kimanin shekara

hud'u da watanni da suka wuce..." ta labarta masa

komai tun daga farko har k'arshe.

Shiru mutumin yayi yana nazari kafin yace "wannan

ba k'aramin case bane saboda yama fi k'arfi na

gaskiya, amma barin kira maku oga na sai ki

maimaita abun da kika fad'a min".

Kiran ogan nasa yayi maaamah ta k'ara fad'i kamar

yanda ta fad'a ma wancan. Ya jima shiru yana 'yan

rubuce rubuce kafin ya d'ago kansa yace "Lallai

wannan babbar magana ce, to amma abun duba

anan shine; shin ta haihu da tazo nan d'in ko kuwa?

Saboda kunce cikin ta ya kai minzalin haihuwa, zata

iya yiwuwa a hanya ta haihu, zata iya yiwuwa kuma

Kanon ta tafi tunda ta ambaci haka, amma babu

komai abunda ya kamata kawai a sanar a gidan

jarida, sannan kuma tunda ga hoton ta sai akai

gidan television insha Allahu indai nan d'in taxo to

baxa'a rasa wanda ya ganta ko yasan inda take ba".

Sosai maamah taji ta d'an samu natsuwa da

bayanin shi, "yallab'ai tare zamu tafi ko?" Ta fad'a

tana kallon shi.

"Ehh barin xo yanzu saimu tafi, amma fa mota ta

babu mai" yayi wani shu'umin murmushi. "Ashe dai

yanda nasan k'asata haka take har yanxu, wasu

mutanen basu abu dan Allah sai dan abun duniya"

ta fad'a a ranta har d'an sandan ya fito bata ma san

ya fito ba.

"Hajiya muje na fito, sai wani tunani kike ance miki

ki kwantar da hankalin ki indai nan d'in tazo insha

Allahu za'a samu labarin ta, ki daina wannan

damuwar".

Tafiya sukayi a hanya Khalil ya bashi dubu biyar

yace ya zuba mai, suna kallon shi ya bayar da dubu

d'aya da sukaje gidan man.

Vision FM sukaje, take suka bayar da sanarwar

sannan suka wuce gidan television nan ma suka

bayar har da hoton ta da number'n wayar Khalil,

maamah da Nadrah sai kuma ta d'an sandan da

suka tafi dashi.

Sai da ya fara kaisu masaukin su sannan ya koma

ga nashi wurin aikin shima.

A gajiye suka koma saboda tun barowar su India

har yanzu basu samu wani hutu ba, musamman ma

Nadrah da bata saba da wahala ba ko kad'an.

Kamar ko yaushe maamah ta fara tunanin data saba

na Nadiya, dan bata so ta tafi basu gana ba tunda

tasan 'yar katsina ce dama kuma ta fad'a mata a

FMC take aiki, ya zama dole ta neme ta kafin su tafi

ko dan taga yanda Umar ya koma, taga kuma

Haydar d'in ta da take fad'a mata bashi da

isasshiyar lafiya.

©Princess Amrah

[1:52pm, 19/10/2016] Amrah Pinky durling

: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah*

Ranar da suka cike kwana biyu a Katsina ne wayar

Nadrah ta hau ruri, da mamaki ta ga number'n

Nigeria ne dan ita a sanin ta bata da number'n wani

d'an Nigeria sai ta Humairah, kuma layin Humairah

yanzu baya functioning.

D'agawa tayi da tsiwa tace "who is online?",

Daga d'ayan b'angaren wata mace tace "sunana

Asma'u.." bata ko gama maganar ba Nadrah tayi

saurin katse ta da cewa "to me kike so na miki? Ke

ina ma kika samu number na da har kika k'ira ni?"

Maamah na jin haka tayi saurin fizge wayar daga

hannun ta ta kanga ta a kunne tace "kiyi hak'uri

baiwar Allah, me ya faru ne kika kira ta?",

"Amma baccin zuciyar musulunci wallahi da kashe

wayata zanyi, wannan ma ai wulak'anci ne, daga

taimako sai ta hau wulak'anta ni? Kowa fa yana da

darajar shi a doron k'asa, kuma nima d'in data

wulak'anta bata san ko ni waye ba",

"Ai saisa na baki hak'uri baiwar Allah, ni mamanta

ce, yarinta ce wallahi kiyi hak'uri me ya faru?",

"Naga hoton wata mata ne ana cigiyar ta kuma an

saka lambobin waya a jiki shine na d'auki wannan,

tun wasu shekaru da suka wuce mun had'u da

matar a asibiti taje haihuwa ni kuma naje scanning,

to daga k'arshe dai naji nurses suna maganar sai

an mata aiki, tun daga nan ni kuma na tafi na bar ta

acan, shine nace me zai hana kuje asibitin k'ila

baxasu rasa masaniya da inda take ba",

Saurin mik'ewa tsaye maamah tayi tana fad'in

"wace asibiti ce baiwar Allah!?"

Suma su Nadrah'n mik'ewa tsayen sukayi,

"FMC ne",

"Tou nagode baiwar Allah, Allah ya saka miki da

alkhairi",

"Ameen Allah yasa ku same ta" ta tsinke wayar.

"Kin gani ko Nadrah? Wannan mugun halin naki yau

da yaja mana, gashi yanzu ta min bayani ta tab'a

had'uwa da Humaira, alamar Humairah garin nan

taxo kenan, ku tashi mu tafi asibitin mu bincika ko

zamu dace".

Basu tsaya jiran komai ba suka tafi, kasantuwar

akwai tazarah daga Sahara suits yasa suka jima

basu isa ba, gashi kuma napep bata shiga cikin

asibitin sai dai suyi trekking. Da tambaya suka isa

reception, ta gefen masu haihuwa aka kwatanta

masu suka tafi.

Bayan sun ma matar wurin bayanin komai da

shekarun ta hau bincikar wasu files, d'aya bayan

d'aya take zaro su tanayi tana duba date da suna.

Ta fiddo da yawa amma bata gano na Humairah ba

gashi har tana neman ta kai na shekara kusan

goma da suka wuce, a gajiye ta d'ago tace "to cikin

wannan dai babu su gaskiya, amma barin duba cikin

wanda aka ma CS wata k'ila ita shi aka mata"

maamah tace "tabbas matar data kira ta fada min ta

hadu da ita tace wai a lokacin taji ana magabar

zaayi mata CS, ina tunanin file din ta yana cikin na

CS din, nasha duk a ahde suke ne saisa ban fada

miki ba har kika sha wannan wahalan", "babu komai

ai hajiya", nan ta koma d'ayan b'angaren nan ma ta

fara dubawa. Bata wani sha wahala ba ta gano shi,

Humairah Sharoukh ne bayyane daro daro a jiki, da

sauri maamah tace "nata ne wannan, wallahi shine"

baki d'ayan ta ta gama rikicewa, tama rik'e file d'in

tak'i sakarwa matar ta duba.

Matar tace "ki saki to a bincika hajiya" saki

maamah tayi jiki sai rawa yake tana jiran

sakamakon da zasu gani a file d'in, saboda a file

d'in ake rubuta address d'in mai haihuwa da komai

nata.

A hankali matar ta fara karanto masu komai a nitse,

har ta kai inda aka rubuta rasuwar ta da kuma inda

wata likita ta d'auki alk'awarin rainon abunda

Humairah ta haifa.

Kuka sosai su duka ukun suka b'arke dashi babu

mai rarrashin wani a cikin su, matar data gano

masu file d'in ce ta fara cewa "amma yaron data

haifa d'in yana wuri mai gata saboda likitar data

d'auke shi tana kula dashi sosai fiye da wanda ta

haifa, yanxu haka yaron yayi wayo sosai kuma har

yanxu bai san ba Nadiya ce ta haife shi ba, Nadiya

sananna ce saboda ma'aikaciyar wannan asibitin

ce, sai dai kuma da kanta ta nemi barin aiki saboda

bata da wanda zai kula mata da yara, saboda kirkin

matar yasa nake yawan kai mata xiyara, munyi

zaman mutunci da aminci da ita, ta kula dani sosai"

Maamah ce ta tsayar da kukan da take tace

"Nadiya! Nadiya dai wacce na sani? Itama ai a

wannan asibitin take aiki, kuma ta fannin mata tayi

karatun ta"

Matar tayi saurin cewa "tabbas itace, saboda a duk

asibitin nan ita kad'ai ce Nadiya, matar kirki wadda

tasan darajar mutane kenan, indai a asibitin nan

kika san waccan tana aiki to itace saboda tun barin

Dr. Nadiya nan bamu sake sanin wata mai irin

sunan ta dake aiki a duk fad'in asibitin nan ba"

"Kenan Umar ko Haydar akwai jika na a cikin su?

Ko kuwa bayan taje India ta dawo ne ta karb'e shi?"

A zuci tayi maganar amma bata san ta bayyana ba.

"Umar shine yaron Humairah, saboda tun a asibitin

kafin ta tafi dashi tayi mashi suna, tace wai sunan

babanta ne" matar ta fad'a tana kallon maamah.

Cike da mamaki maamah tace "sunan Baban ta

Umar kenan?",

"Nadiya Umar Turaki shine cikakken sunan t..."

zumbur maamah ta mik'e tsaye, cike da al'ajabi ta

kasa furta komai sai rawar lab'b'a take, "Nadiya

Umar Turaki?!" Ta fad'a a rikice bata ma san ta

fad'a ba.

"Nadiya 'ya ta? Wadda na rabu da ita tun tana 'yar

shekara hud'u? Wadda har yanxu nake da tsananin

burin ganin ta? Wadda aka rabani da ita ta k'arfi da

yaji? Itace ta zauna a gidana India? Ashe da rabon

zan sake ganawa dake a matsayin 'yata Nadiya?

Ashe saisa nake jinki sosai a jini na? Saisa na kasa

hakuri a lokacin dana fara ganin ki a airport dole sai

da na miki magana kika zauna a gida na? Me ya

dawo dake Katsina kika baro kano?"

Ni kuma Amrah nace masu karatu kuyi hak'uri da

wannan, wallahi karatu ya taso ni gaba a cikin

watan nan zamu fara exams insha Allahu, ku k'ara

hak'uri novel d'in ma ya kusa k'arewa duka da

izinin Allah, addu'ar ku kawai nake nema to pass

my papers in flying colours, insha Allahu zanna

ringa maku typing time to time yanda kafin mu

gama exams d'in duka na gama dashi, sai mu fara

daga sabo insha Allah.

©Princess Amrah😘

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah*


6⃣3⃣ - 6⃣4⃣

Kuka Nadrah keyi sosai na rashin 'yar uwar ta, a

lokaci d'aya tayi shiru jin maganganun da maamah

keyi,

"Maamah! Wace Nadiyar kike magana ne? Bamu fa

gane inda zancen ki ya dosa ba"

Shiru maamah tayi in banda kuka babu abunda

take, Khalil yayi k'arfin halin cewa "pls maamah

talk, kin barmu a duhu fa".

Da kyar ta iya bud'e baki tace "Nadiya itace wadda

tun kuna yara kuna yawan gani na ina kuka amma

nak'i fad'a maku dalilin kuka na, Papa d'in ku kafin

ya rasu ne kad'ai yasan dalili, naso ace yana raye

yaga Nadiya ta da idon shi" ta k'ara fashewa da

kuka.

Jin maganganun su ba masu k'arewa bane yasa

matar nan tace "hajiya barin rubuta miki address na

Nadiyah"

Paper ta samu ta rubuta address d'in tare da mik'a

mata.

Godiya suka mata sannan suka fita duk babu

walwala a tare dasu.

Basu wani jima a hanya ba suka samu napep, khalil

ya ringa karanto masa yace ya gane gidan ma wai

ya tab'a kai wata mata a gidan,

Sunyi tafiya mai nisa kafin su isa kasantuwar akwai

taxara tsakanin Goriba road da FMC.

Da shigar su bakin gate sukaci karo da mai gadi

yana wanki, hannu ya mik'a ma khalil suka gaisa

sannan ya gaishe da maamah, sosai yaga kamannin

Khalil dana *UMMU HAYDAR,*

"Dan Allah ko nan ne gidan Nadiya? Ummu Haydar

nake nufi" Maamah ta fad'a tana jiran amsar sa.

"Ehh nan ne, Nadiya maman Haydar da Umar

kenan, kunyi sa'a kuwa yanxu ta dawo gidan ma,

ina jin mijinta ma yana gida, ku shiga tana daga

ciki",

Sosai Maamah taji dad'i, su dai Nadrah da Khalil

sun kasa fahimtar komai sai kukan rashin 'yar uwar

su da suke.

shiga sukayi mai gadi na masu jagora har suka isa

parlor d'in ta.

"Hajiya kinyi bak'i"

Mai gadin ya fad'a yana jiran martanin ta.

Bata bashi amsar ba sai jin muryar ta sukayi tana

kuka tana fad'in

"Nagode da wulak'ancin ka *ABBAN HAYDAR!*

Dama haka rayuwa take, wai yau da bakin ka kake

furta ka sake ni har saki uku, lallai namiji ba d'an

goyo bane, yanxu duk kalar wahakar daka bani a

baya bata isa ba sai da saki zaka saka min? Ka

sake ni Abban Haydar!?" Ta k'ara fashewa da kuka

sosai.

"Ehh na sake ki saki uku Nadiya, ke d'in waye da

baza'a sake ki ba? Ko dan kinji Mommah kafin ta

rasu ta haramta min sakin ki? Tou na sake ki d'in

kuma ki fitar min daga gida bana son ganin ki,

Hajiya da Ummi na nan zuwa su fitar dake inhar

kika k'ara awanni biyu a gida na, zaki iya kwasar

kayakin gidan ki tafi dasu bana buk'ata dan na siyo

ma su Hajiya wasu zasu dawo nan da zama in yaso

itama Futha sai kice mata kar ta sake zomun gida

dan dama tace saboda ke take xuwa" yana

maganar a wulak'ance kamar bai tab'a ganin ta ba.

Umar ne da sauri ya fara sharewa Umman su

hawaye yana fad'in "sorie Ummah, tunda ya

koremu ki tashi mu tafi sai mu koma gidan su aboki

na Anwar"

Haydar kuwa kuka yake sosai abun tausayi yana

fad'in "Ummanah kiyi hak'uri ki yafe min, duk ni

naja miki komai, inda baki haife ni ba da duk hakan

bata kasance ba, ki daina kuka Ummah ki tashi mu

bar masa gidan sa insha Allahu baxamu tab'a

tagayyara ba" su duka ukun kuka suke basu ma

san da shigowar su Maamah ba.

"kai gafara min can *MUSAKIN BANZA,* kai idan

mutanen kirki na magana ka daina saka naka bakin,

kuma ka daina alak'anta kanka dani dan ni bani

bane babanka, kaje can ka nemi ubanka a tasha

dan kai shege n.." bai gama maganar ba

kasantuwar kyakkyawan marin da Maamah ta

wanka masa.

"Kai wane irin wawan miji ne? Baka da hankali

abunda na fahimta kenan, ka sake ta kuma miye na

binta da munanan kalamai? Inaso ka sani Nadiya

zata bar maka gidan ka yanxu bama sai an dad'e

ba, amma ka sani wallahi sai kayi dana sani, yaron

ka da kake kira da shege dan kagan shi *MUSAKI*

wallahi sai ya maka rana a rayuwar ka, ka daina

ganin ka kai mai kud'i ne to babu tabbacin zaka

dauwama a haka, wallahi bana tunanin kana da ko

linki d'aya na dukiyar Nadiya, ta fika gata, kud'i

martaba da komai na rayuwa" tana kaiwa nan ta ja

Nadiya ta fitar waje, ta d'auki Haydar daga kan

kujera ta d'ora a kafad'ar ta sannan taja Umar da

d'ayan hannun ta shima ta fitar waje.

Nadiya dai kuka take amma tana mamakin zuwan

su Maamah, tana kuma mamakin kalaman dake fita

daga bakin ta.

"Zan koma in d'auko key'n mota nah" Nadiya ta

fad'a idonta ya kumbure sosai tsabar kukan da

tasha.

"Nadrah shiga ki d'auko mata, a ina kika ajiye shi?",

"Yana kan tv stand"

parlor'n ta koma ta tayar da Usman tsaye yana

rawa da k'afa shi a dole mai zuciya.

Sai da ta d'auki makullin sannan ta juya ga Usman

tace "wallahi yanda ka wulak'anta Nadiya kaima sai

ka wulakanta a rayuwar ka, wanda ka fifita akanta

d'in kuma sune zasu wulak'anta ka, banza

matsiyaci" ta fita abunta cike da tsiwa.

Mai gadi ma kamar yayi kuka saboda a gaban shi

akayi komai, har k'asa Nadiya ta duk'a tace

"Baabah ya kore ni zan bar masa gidan sa, a iya

zaman da mukayi da kai inhar akwai abunda na

maka wanda ban kyauta ba ina neman yafiyar ka,

saboda na tafi kenan baxan k'ara dawowa gidan

Abban Haydar ba"

Kukan da yake b'oyo ne ya fito yace "ki tashi tsaye

Nadiya, zamana dake in ba alkhairi ba babu abunda

kika min, inma akwai wani abunda kika min a b'oye

to na gafarta miki, kuma insha Allahu zaku samu

d'aukaka keda yaranki"

"Nagode Baabah, na tafi SAI WATA RANA" ta shige

mota abunta.

Khalil yaja motar Umar da Nadrah gaba sai Maamah

da Nadiya rungume da Haydar a baya, kuka kawai

take Maamah na rarrashin ta amma tak'i shiru sai

tuno baya take, a iya tarihin rayuwar ta tun tana

yarinya rabonta da samun wani farin ciki.

A Hotel d'in da suka sauka suka tafi da Nadiyah da

har yanxu bata daina kuka ba.

Da shigar su d'akin Maamah ta kwantar da Haydar

da yayi bacci yana ta ajiyar zuciya, Umar kuwa idon

shi biyu amma yayi shiru ya kasa fad'in komai

tsabar xuciya da gare shi.

Da k'yar Maamah ta samu ta rarrashi Nadiya tayi

shiru, abinci Khalil yayi masu ordering dan suci

amma kowansu ya kasa ci, Nadiya kuwa ta tasa

abincin a gaba wasu siraran hawaye na fita daga

k'wayar idon ta.

©Princess Amrah

[2:38pm, 22/10/2016] Amrah Pinky durling

: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah*

Jin shiru d'akin yasa maamah ta fara da "Nadiya

nasan kinyi mamakin ganin mu a wannan lokacin,

abun da ya faru shine...." ta bata labarin komai har

xuwan su Abuja da dawowar su Katsina da yanda

sukayi a asibiti. Sannan taci gaba da _"Tunda naji

sunan ki Nadiya Umar Turaki na rikice saboda kece

'yata Nadiya, kece wadda aka rabani dake ta k'arfi

da yaji"_

Da sauri Nadiya ta m'ike tsaye tace "Maamah! Kece

mamana? Ya akayi kika san haka? Mesa kika tafi

kika barni?" wani sabon hawayen ya fara fita daga

idon ta,

_"Nadiya nice mamanki da gaske, tun bayan

rasuwar baban ki Alhaji Saminu yace ai babanki ya

bashi ke halak malak shi xai rik'e ki, ni kuwa nasan

halin Alhaji Saminu sarai da son kud'i shida matar

sa, nasan badan komai yace haka ba sai dan

dukiyar da babanki ya rasu ya bari, a duk fad'in

garin kano babu wanda bai san Alhaji Umar Turaki

ba, sananne ne saboda shi d'in tsohon d'an siyasa

ne sannan kuma d'an kasuwa ne.

Mun sha kuka nida ke lokacin da za'a raba mu,

babu yanda na iya dole na hak'ura suka tafi dake

amma takardun komai naki suna hannu na, dama

tun haihuwar ki baban ki ya miyar da komai nasa da

sunan ki kamar yasan bazayyi tsawon kwana ba,

Haka naci gaba da rayuwa babu ke amma kullun

cikin kuka nake har ciwo ya fara kamani,

Wata rana ina kwance banda lafiya sai sheshsheka

nake zuciya ta na bugawa da sauri da sauri sai ga

wasu maza bak'ak'e sun shigo, da ganin su irin

mugayen nan ne sosai, da mamaki naga suna

shigowa d'aya bayan d'aya su goma sai Alhaji

Saminu a bayan su,

Naji matuk'ar tsoro a hankali na tashi xaune ina

k'ok'arin yin magana na kasa,

Dariya sukayi su duka da k'arfi kafin sukayi shiru,

Alhaji Saminu yace "Hajiya kenan, kina tunanin zan

rik'e 'yar ki saboda Allah ne? kinyi kuskure indai

hakan kikayi tunani, dukiyar 'yar ki itace kawai buri

na, kuma yanxu ita naxo karb'a kuma a kashe ki

idan kika bayar" ya k'ara fashewa da dariyar

mugunta.

Take zuciya ta ta tsananta bugawa, idona ya kawo

k'walla ina rok'on Allah ya kawo min d'auki,

"Ki d'auko min takardu!" Ya fad'a a tsawace har sai

da na gigice.

Saurin shiga d'aki nayi na kwaso kaf takardun ki,

amma a raina cike da jin dad'i saboda duk photo

copied ones ne, originals d'in suna dak'in waje na

ajiye su inda babu wanda zai tab'a zargin akwai

wani abun amfani a d'akin,

Mik'a masa su nayi duka sannan ya masu signal da

fuska nan suka hau duka na sosai yana fad'in "kar

ku k'yale ta har sai tabi mijinta"

Tun ina sanin abunda ke faruwa har na daina jin

komai,

Na d'auki tsawon kwanaki a haka kafin wata irin

muguwar yunwa ta tashe ni,

A hankali na fara rewinding d'in abubuwan da suka

faru dani,

Cike da hanxari nayi k'arfin halin tashi amma jiki na

yayi tsami sosai na kasa tashi,

Tsoro naji sosai dan nasan zasu iya dawowa a

kowane lokaci kuma yace dasu su tabbatar da sun

kashe ni,

A hankali na fara rarrafawa har na fita daga d'akin,

d'akin waje na tayar a rufe na sake komawa d'akina

cikin wata drawer na d'auko makullin,

bud'e d'akin nayi na shiga na kwaso duka takardun

ki duk da sunfi k'arfi na amma a haka nake jansu a

cikin wani babban file,

Kasantuwar unguwar mu abun hawa yana wahala

yasa ina ganin mashin kawai na tsayar nace ya

kaini Hotoro duk da nasan bani da ko sisin da zan

biya shi,

A hankali na hau mashin d'in saboda ciwon da jiki

na yake min,

Koda muka isa gaban gidan na bashi hak'uri akan

zan shiga ciki in karb'o masa kud'in sa,

Abunda na tayar ne ya matuk'ar tayar mun da

hankali, babana da mamana ne kwance jini sai

malala yake daga jikin su duk basa numfashi, kuka

na fasa da k'arfi ina neman d'auki,

Mak'wafcin mu malam Saleh ne ya shigo a rikice

yace "au! Dama basu kashe ki ba? Na baki shawara

tun wuri ki gudu kibar garin nan dan wallahi idan

suka san baki mutu ba sai sun kashe ki, ina lab'e

ina jin su suna maganar wai sun gama dake shine

suka dawo ma iyayen ki dan sun san su kad'ai

gare ki, kuma idan suka gane kashe ki akayi zasu

sa ayi bincike kuma asirin su zai iya tonuwa, ki tafi

kawai zan kula da gawar su, za'ayi masu duk

abunda ya dace kafin akai su gidan su na gaskiya",

Jin haka yasa na duk'a jikin gawar su nayi masu

addu'ah sosai sannan da sauri na fita,

Mai mashin d'in na bama hak'uri yace mun babu

komai sannan ya tayar muka kama hanya ba wai

dan nasan inda zanje ba, kuma har yanxu file d'in

yana hannu na.

wata shawara ce ta fad'o min a rai nace dashi "ka

kaini new GRA" ina kwatanta masa har muka isa

gidan Barrister Kamal wanda komai na mahaifin ki

shi yake sakawa a gaba,

Da sauri na shiga gidan ba tare da na masa bayanin

komai ba kawai nace "Barrister ka ajiye wannan,

kar ka bama kowa har sai lokacin dana dawo da

kaina nace ka bani, ko kuma ka samu wani sak'o

mai inganci daga gare ni, ka taimaka min da ko d'ari

biyar ne dan Allah"

Ganin ina rikice ne yasa ya zaro kud'i masu yawa

ya bani yana tambaya ta abunda ya faru amma ban

ko saurare sa ba na fita abu na na sallami mai

mashin d'in dan nasan za'a iya gani na a akan

mashin.

Yana tafiya sai ga mai napep,tsayar dashi nayi na

shige ciki ba tare dana fad'a masa inda zanje ba.

Haka yaita yawo dani cikin gari har ya gaji yace in

fitar masa daga napep, d'ari biyar na bashi ya tafi

kuka mai k'arfi ya k'wace min,

Da sauri da sauri xuciya ta ta ringa harbawa,

Tun daga nan ban k'ara sanin komai ba sai farkawa

nayi na ganni kwance kan gadon asibiti,

Wani kyakkyawan ba'indiye gefe na yana kallo na,

cike da damuwa nace "malam kai waye? Waya

kawo ni nan?",

Murmushi yamin dan bai san abunda nake fad'a ba,

Ganin haka yasa na tambaye sa da turanci,

"Ni bak'o ne nazo yin wani course ne anan shine na

tsince ki a wani daji ke kad'ai kamar kin mutu,

shine na d'auko ki na kawo nan asibitin, kwanan ki

biyar kenan a haka" ya fad'a cikin yaren turanci,

"Dan Allah na rok'e ka kar ka cutar dani",

"Bazan tab'a cutar dake ba yarinya, ki yarda dani ni

musulmi ne mai gaskiya da amana",

Jin shi musulmi ne yasa na d'an samu sassauci,

"Ki fad'a min gidan ku zan miyar dake" ya fad'a da

turanci,

Kuka ya kufce min sosai na k'ara tuno yanda na

samu gawar iyaye na,

Ganin ina kuka yasa hankalin shi ya tashi,

"Ki daina kuka kimin bayanin komai yarinya, wallahi

baxan cutar dake ba",

Na bashi labarin komai tun farko har k'arshe, ya

matuk'ar tausaya min yace

"Zan tafi dake garin mu India indai zakije, wallahi

kinji na rantse zan rik'e ki da amana, mamana mai

mutunci ce tasan darajar mutane,nasan zata d'auke

ki tamkar 'yar ta",

Take kuwa na amince masa babu ko tantama ya

tafi dani Mumbai babban birnin India, naji dad'in

zama da maman sa sosai har soyayya ta fara shiga

tsakanin mu,

Cikin lokaci kad'an aka d'aura mana aure dashi

shine na haifi Humaira, bayan shekara biyu na k'ara

haihuwar Nadrah, shekarar Nadrah uku na sake

haihuwar Khalil, bayan auren Humairah ne Allah ya

karb'i rayuwar Papan su, nasan insha Allahu in dai

Barrister Kamal yana raye zan karb'o miki takardun

ki kuma zamu shigar da Alhaji Saminu k'ara,

takardun ki shune evidence saboda sune originals,

dukiyar ki zata dawo gare ki da izinin Allah".

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah NWA*


6⃣5⃣ - 6⃣6⃣

*Assalamu alaikum my fans*

*Alhamdulillah! Komai yayi farko zayyi k'arshe,

kamar jiya ne nace maku zan fara exam bazaku

sake ganin posting d'ina ba, to nagode Allah na

kammala exam d'in kuma daga yanzu insha Allahu

zaku ci gaba da jina akai akai har lokacin da labarin

zai kai k'arshe, nagode da soyayyar ku a koda

yaushe*

*****

Washe gari da sassafe suka gama harhad'a kayakin

su kaf suna haramar tafiya Abuja domin booking na

flight d'in India.

fitar su suka tsayar da taxi domin isa tasha, sai dai

kuma tun shigar su Nadiya ke kallon wata mota

k'irar elantra, ba komai take kallo a motar ba face

fuskar mutumin dake tuk'a motar, a iya tunanin ta

dai tasan fuskar koma ina ne, to amma a ina ta san

shi? Tunanin da take kenan.

Caraf idon shi ya kai ga na Nadiya da ta k'ura mashi

ido har a lokacin bata daina kallon shi ba,

Hankali tashe yake kallon ta shima d'in dan ya

tabbatar da abunda zuciyar sa ke fad'a masa,

Babu shiri ya taka burki tare dayiwa taxi d'in horn

alamar ta tsaya,

Take kuwa mai taxi ya tsaya fuskar shi d'auke da

alamar tambaya dan bai san ko me mutumin ya

taka ba da har ya tsayar dashi, kuma dai gashi da

alamar babban mutum ne.

Ganin driver'n taxi d'in ya tsaya yasa mutumin ya

fito daga mota har yanzu idon shi na kan Nadiya,

Hannu ya mik'a masa suka gaisa kafin ya bud'e

bayan motar inda Nadiya take zaune,

Cike da mamaki Nadiya ke kallon shi dan ita har

yanzu bata gama tabbatar da tunanin ta ba,

"Ina yini mama" ya gaishe da Maamah dake kallon

shi cike da mamaki dan yanda taga yana kallon

Nadiya,

"Lafiya lau bawan Allah! Lafiya dai ka tsayar damu?"

Maamah ta tambaye shi cike da son jin amsa.

Shiru yayi ya kalli Nadiya da idon ta ya kawo k'walla

a wannan lokacin,

Cikin rawar murya Nadiya tace

"Maamah wannan shine uncle Hamza, wanda da

zan aura su momy zee suka kife min ciki suka

hana auren, har gidan su sukaje suka hana iyayen

shi ya aure ni" ta k'ara fashewa da kuka.

Shima Uncle Hamza'n kuka yake yana tuna irin

soyayyar da sukayi,

"Nadiya a rayuwa ta ban tab'a tunanin akwai ranar

da zamu sake had'uwa ba,

Sai gashi yau Allah ya had'a mu, kiyi hak'uri bai

kamata ina magana dake a matsayin ki na matar

aure ba".

Shiru sukayi su duka kafin Nadrah ta fito daga mota

ta zagayo ta inda Uncle Hamza yake tace "da kenan

kasan wannan, yaya Nadiya bata da aure yanzu",

Cikin mamaki Uncle Hamza ya maimaita "bata da

aure? Kenan Usman Aliyu sakin ta yayi?",

"Kama san shi kenan, ehh sakin ta yayi, kuma ba

abun mamaki bane saboda mugun abun daya guma

mata a baya, rabuwar tasu itace tafi masu alkhairi"

Nadrah ta miyar masa da amsa.

"K'warai nasan duk abubuwan da Usman yayi ma

Nadiya a baya, ina sane da komai amma ban tab'a

tunanin zai sake ta ba, saboda yanda nake masa

nasiha a duk lokacin da ya tado labarin irin abunda

yake mata a cikin abokai, abunda yasa bana nunar

da b'acin rai na shine; dan kar ya fahimci cewa

naso Nadiya a baya saboda ban tab'a fad'a masa

ba,

Ko a lokacin da Usman ya nunar min da yana son

Nadiya ban nunar masa da komai ba face fatan

alkhairi dana masa, a lokacin ni kuma iyaye na sun

had'a ni aure da wata 'yar uwata",

Shiru maamah tayi tana sauraren Hamza har a

lokacin daya ci gaba da

"Tun lokacin dana auri 'yar uwata Maryam ban

kuma samun kwanciyar hankali ba, a daren farkon

mu Maryam ta fara gwada min zak'ewar ta gare ni,

hakan yasa na fita batun ta saboda dama nasan

yarinyar bata jin magana ga kuma yanda take min

kamar ba amarya ba,

Haka dai mukaci gaba da rayuwa ba tare dana

kusance ta ba, itama kuma tun tana kawo min

kanta har ta gaji ta daina,

Ashe duk zaman da muke yi akwai wanda Maryam

ke kawo wa gida na idan na tafi aiki, ban tab'a sani

ba sai wata rana da nayi mantuwa na koma gida

zan d'auka, anan ne na kama Maryam da kwarton

ta, abun takaici turmi da tab'arya na kama su,

Hankali na ya tashi sosai na zaro belt d'ina na basu

kashi su duka biyun, da k'yar kwarton ya k'waci

kan sa ya gudu,

Ita kuma take nayi mata saki d'aya ta tafi gidan su.

Bayan komai ya nitsa ne iyayen mu suka bani

hak'uri na miyar da maryam d'akin ta, suka kuma yi

mata nasiha sosai sannan muka koma gida.

wata irin muguwar tsana na k'ara yima Maryam

dan ko kallon ta nayi sai na k'ara tuna yanda na iske

ta da namiji kwance bisa gado na,

Watan mu biyu Maryam taci gaba da fita yawon

banzan ta har tayi wata fita da Abban mu da kanshi

ya ganta a gaban motar wani namiji, binta yaitayi a

baya har suka isa bakin Ruky Hotel Abbah bai daina

bin su ba,

Ganin su yayi sun fita sukayi booking room 12 yana

dai bin su a b'oye itama kuma Maryam d'in bata

gane ba,

Ganin haka yasa Abbah ya koma motar shi cike da

mamakin halin Maryam,

A ranar Abbah yasa ni na saki Maryam duk da

yanda yake son ta.

Tun bayan rabuwa ta da Maryam har yanzu ban

sake yin aure ba dan bana sha'awar rayuwa da

kowace mace bayan ke Nadiya,

Kece macen dana fara so kuma nake kan so har

yanzu, ban tab'a tunanin akwai ranar da zan sake

ganin ki ba saboda na riga da na yanke duk wata

hanya da zata had'a ni dake barin har na k'ara

sha'awar ki,

Idan bazaki manta ba akwai wani lokacin da akace

gwamnati ta d'auki nauyin mutum goma zasuyi

karatu a duk inda suke so, ba wata gwamnati bace

ba face ni, nine na k'irk'iri hakan kawai dan in cika

miki burin ki na zama babbar likita,

Akwai k'anana k'ananan abubuwa wanda nake

sakawa ana miki duk a b'oye bada sanin ki ba,

Na saka wani yana bibiyar ki ga duk abunda kike so

yana fad'a min inyi miki shi a b'oye,

Nadiya *KECE ZAB'I NA!* kece kad'ai macen da

nake so tun da nake a rayuwa ta, ina fatan

soyayyar da kikayi min abaya zata dawo sabuwa a

halin yanzu,

Ki sani Nadiya kasancewar ki bazawara ba zai tab'a

sawa in guje ki ba face ma wata soyayyar ki dana

k'ara ji a raina,

Na miki alk'awarin zan rik'e ki da amana, zan rik'e

miki yaran ki tamkar nine Abban su".

Shiru sukayi su duka suna sauraren Hamza, ga

wani irin mugun tausayin shi da suke ji su duka

ukun,

Khalil ya share hawayen shi yace "kar ka damu

Hamza, insha Allahu yaya Nadiya zata aure ka, ka

daina kuka kaji?"

Nadrah uwar tsiwa ma kukan take dan sosai uncle

hamza ya bata tausayi, Maamah kuwa ci gaba tayi

da kwantar masa da hankali har ya daina kukan.

Bayan sunyi shiru duka ne ya sallami mai taxi d'in

sannan ya hau fitar masu da kayakin su daga cikin

motar yana sakawa a tashi,

Bayan ya gama duka ya tada motar,

A ciki ne maamah ke labarta mashi duk irin

abubuwan da su Alhaji Saminu sukayi, bayyi

mamaki ba saboda yasan halin Alhaji Saminu da

son kud'i,

Ya basu shawara akan kar su koma India har sai

sun tafi Kano sun shigar da k'arar Alhaji Saminu an

k'watar wa Nadiya hak'k'in ta,

Sun amince da shawarar shi,

Bayan Hamza ya tafi ma'aikatar da Abban shi ya

aike shi a katsina ya gama komai sannan suka

kama hanyar Kano.

Isar su Kano Hamza ya kai su gidan shi da komai

akwai a cikin sa,

Sunji dad'in yanda ya karrama su sosai,

Haydar da Umar kuwa sai wasan su suke Umar na

tura shi a keken shi na guragu,

Fita Hamza yayi sai gashi da kayan abinci masu

yawan gaske da kuma dafaffe wanda ya siyo masu

a restaurant,

Sai da suka k'oshi sannan suka fara jejjera kayakin

a cikin kitchen,

Maamah cike da k'aunar Hamza, sosai take jin son

shi a ranta, a wani b'angaren na zuciyar ta tana

tunanin yanda zatayi a gano barrister Kamal domin

amsar takardun dukiyar Nadiya a hannun shi.

©Princess Amrah

®NWA

[3:21pm, 15/12/2016] Amrah Pinky durling

: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

*Na Amrah NWA*

A b'angaren *ABBAN HAYDAR* kuwa tun tafiyar

Nadiya yaji tamkar ya sauke k'aya ne daga bayan

shi,

Hajiya da Ummi suka dawo gidan shi da zama,

Futha kuwa lokacin data fara zuwa neman *UMMU

HAYDAR* wulak'anta ta Ummi da hajia sukayi

tamkar basu tab'a ganin ta ba,

Haka ta tafi cike da takaicin abunda suka mata, wai

ace ita da gidan d'an uwanta amma abunda suka

mata kenan, gashi tana ta neman lambar Nadiya a

waya ta rasa saboda tun tafiyar su Nadiya ta kashe

wayar ta dan bata son a dame ta da kira tana

neman natsuwa ne.

Washe gari,

Da sassafe kafin Hamza ya tafi aiki saida ya biyo ta

gidan, anan ne Maamah ta bashi address d'in Barr.

Kamal wanda bata da tabbacin har yanzu yana

gidan kasantuwar yanda Kano ta koma a wannan

lokacin,

Tafiya yayi bayan Nadiya ta raka shi har bakin mota

ya mata bankwana da cewa idan ya tashi daga aiki

zai fara biyawa ta gidan barr. Kamal sannan ya

dawo.

Haydar kuwa wani irin dad'i yake ji na rashin Abban

shi a kusa dashi, saboda duk wata hantarar shi da

yake yi yanzu ya huta da ita, Maamah na faranta

masa rai sosai, gashi kuma Khalil da Nadrah suma

suna bakin k'ok'arin su dan ganin sun farantawa

Haydar rai, suna so duk wani farin ciki daya rasa a

baya yanzu ya same shi.

Bayan Hamza ya tashi daga wurin aiki yabi address

d'in da Maamah ta bashi ya gano gidan barr. Kamal,

sai dai da rashin sa'a ya tashi daga gidan tunda

dad'ewa,

Wani gida mai kallon shi Hamza ya buga sai ga mai

gidan ya fito,

Bayan sun gaisa ne Hamza yace "nazo ne gidan

Barr. Kamal, so wai ashe ya tashi da dad'ewa ban

sani ba",

"Ehh wallahi ya tashi kusan shekara biyar zuwa

shida kenan da suka wuce, amma dai ka dad'e

rabonka dashi ko?",

"Wallahi kuwa malam, nima wata baiwar Allah ce ta

aiko ni wurin shi itace ta bani address d'in, ko zan

samu lambar wayar sa?",

Shiru mutumin yayi kafin yace "kasan su barristers

basu cika so ana bada lambar wayar su in bada

izinin su ba, amma barin kira maka shi sai kuyi

magana idan ya amince zan baka",

"Ok to babu komai bawan Allah, ka kira shi d'in".

gida ya shiga ya fito sai gashi da wayar shi a hannu,

kiran Barr. Kamal yayi bugu d'aya kuwa ya d'auka,

bayan sun gaisa ne yace "dama wani bawan Allah

ne yazo neman ka, yace wai wata mata ce ta aiko

shi wurin ka amma su basu san ka tashi ba, ya

nemi in bashi lambar ka nace sai na nemi izinin ka",

Daga d'ayan b'angaren Barr. Kamal yace "ka bashi

muyi magana".

Amsar wayar Hamza yayi suka gaisa sannan yace

"Wata mata ce ta turo ni wurin ka, matar marigayi

Alhaji Umar Turaki, tace idan na fad'a maka haka

kawai zaka gane",

Cike da mamaki Barr. Kamal ya maimaita "Alhaji

Umar Turaki? Malam da gaske kake koko dai kai

d'an damfara ne?",

"Da gaske nake Barrister" Hamza ya fad'a cike da

yak'ini,

"Miye hujjarka bawan Allah?" Barr. Kamal ya fad'a

suprinsingly,

"Ni kuwa keda hujjah barrister, nidai buri na ka bani

address d'in ka zan kawo maka ita har gida har ma

da d'iyar ta Nadiya",

"Dama suna raye? Mamar Nadiya tana da rai bata

mutu ba?",

"Tana da rai Barr. Yanzu haka nasan inda take, ka

fad'a min inda kake zamuzo gobe",

"Malam bazan fad'a maka inda nake ba har sai ka

bani ita a waya munyi magana sannan zan yarda da

kai",

"Indan wannan ne babu matsala, ka amince a bani

lambar ka yanda idan naje gida zan kira ka sai kuyi

maganar",

"To to to to shikenan, shikenan bashi wayar" barr.

Ya fad'a,

Bayan an bawa mutumin wayar shi ne barr. Kamal

ya bashi izinin ya ba Hamza lambar shi sannan yayi

godiya ya tafi,

Cike da farin ciki ya koma gida, oyoyo Haydar da

Umar suka masa kamar dama can sun saba dashi,

Bayan ya zauna Nadiya ta kawo masa abinci yaci

sannan Maamah ta fito, nan ya labarta masu duk

yanda sukayi da Barr. Kamal,

Murmushi Maamah tayi sannan tace "dama nasan

kafin barr. Ya amince da kai zaka wahala, dan

yasan yanda na jaddada masa kar yaba ma kowa

takardun ki idan bani ba, kira shi muyi magana".

take Hamza ya kira barr. Kamar,

D'auka yayi suka gaisa sannan yace "nine wanda

mukayi magana d'azu kace dole sai kayi magana da

maman Nadiya, gata kuyi maganar" ya mi'kawa

maamah,

Sallamah tayi take Barr. Kamal ya tuna da wannan

muryar, bazai tab'a manta lokacin data zo masa

cikin tashin hankali ta bashi ajiyar dukiyar 'yar ta

ba,

Jin yayi shiru yasa Maamah tace "hello, barr. Bakaji

na?",

"Ina jin ki Maamah, ke d'in dai ce da gaske?",

"Nice da gaske kamal, ka fad'a min inda zamu

same ka gobe, gani tare da Nadiya, shirye muke

dan k'watarwa kan mu fansa da izinin Allah indai

zaka bamu had'in kai",

"Me zai hana Maamah? Zan baku had'in kai d'ari

bisa d'ari, komai naku zai dawo maku kuma kotu

zata gurfanar da Alhaji Saminu a gaban kuliya,

zamuyi nasarah da yardar Allah",

"Nagode sosai Kamal, sai ka turo min d'in",

Sallamah sukayi sannan maamah ta mik'awa

Hamza wayar, take text ya shigo mai d'auke da

address d'in Kamal.

Washe gari Hamza, Maamah, Nadiya da Khalil suka

rankaya gidan Barr. Kamal, Nadrah, Haydar da

Umar aka barsu gida,

Sosai Barr. Kamal yayi farin cikin ganin Maamah,

yayi mamkin Yanda yaga Nadiya ta girma kamar ba

ita ba,

Matar shi ta tarbe su hanu bibbiyu da sakin fuska,

D'akin shi ya shiga sai gashi d'auke da wata

k'atuwar jaka,

A gaban maamah ya ajiye jakar ya fito da abubuwan

dake ciki,

Da mamaki bai fitar da komai dake cikin takardun

ba, da alama ma babu abunda aka tab'a tunda ta

bashi ajiyar su,

Maamah tayi mamaki sosai kafin tace "lallai barr.

Na gaishe ka, kayi k'ok'ari sosai wallahi, yanzu ya

za'ayi kenan?",

Barr. Yace "maamah wannan ai k'aramin case ne, a

cikin rana d'aya ma za'a iya kawo k'arshen shi,

ranar Monday (jibi kenan) zan shigar da maganar

kotu sai a kaima Alhaji Smainu sammaci, ranar

laraba sai a fara shari'ah, ku kwantar da hankalin

ku, yanzu dai ina so kuci gaba da b'oyon kanku,

bana son Alhaji Smainu yasan kuna nan dan komai

zai iya yi maku nasan halin shi sarai, koda yake ai

kin ma fini sanin halin shi".

Murmushi Maamah tayi tace "hakane Barr. Nafi

kowa sanin halin mutumin nan, zamu kiyaye insha

Allahu"

Da wannan maganar suka tashi suka nufi mota, har

motar Barr. Ya raka su sannan ya koma gida su

kuma suka nufi gida.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: : *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*.


*Na Amrah NWA*


6⃣7⃣

Komawa gida sukayi Hamza ya sauke su ya kama

hanyar gidan su,

Yau kam cike suke da farin ciki saboda gani suke

k'arshen Alhaji Saminu ya kusa zuwa,

Nadiya ta labarta ma Nadrah duk yanda sukayi tace

"insha Allahu karshen hege ya kusa zuwa, daga shi

har makirar matar shi zee d'in",

Caraf Nadiya tace "ai baki sani bama Nadrah, nifa

nafi jin haushin Deejah 'yar su, saboda ko wahalar

da suka bani a gidan su duk Deejan ce ke had'a min

makirci, wallahi sister nasha wahala a gidan nan",

"Ki daina tado wannan sister, bana so ki sake shiga

wata damuwar, ki saka a ranki cewa insha Allahu

komai yazo k'arshe, shima kuma wannan

munafukin Salman d'in tsohon mijin yaya Humairah

k'arshen shi ba zayyi kyau ba",

"Hmm! Kin tuna min shi sis, Allah zai tona masa

asiri insha Allahu saj kowa yasan cewa shi d'an

safarar miyagun k'wayoyi ne",

Da wannan firar har aka kira sallar magrib kowa ya

tashi ya nufi yinta.

Bayan kwana biyu

~~~~~~~~~~~~~~~~~~~

Yau ta kasance Monday, ranar da Barr. Kamal yace

zai shigar da maganar kotu,

Tun da wuri ya shiga kotun kuwa ya gama komai

sannan aka rubuta sammaci aka bama messenger.

Zaune suke TV kunne Dady na kallo Momy Zee tana

masa massage,

Cikin shagwab'a Deejah ta fito da cup da spoon a

hannun ta tana shan corn flakes,

kan resting chair d'in da Dady yake ta zauna daga

gefe ta turo baki irin na k'ananan yara tace "Dady fa

corn flakes ya k'are, sai da na dama madara ashe

saura kad'an shikenan na juye kuma bazai ishe ni

ba" ta k'arisa maganar tana bubbuga k'afa a k'asa.

"Mtsw! Ke amma kin raina mana hankali, ke kin

girma amma baki san kin girma ba? Sai ki ri ga yin

abu kamar k'aramar yarinya ke baki san kin tsufa

bane wai? baki ma jin kunyar wannan dire diren da

kike? shekarar ki fa talatin har da d'oriya amma

kike wannan sakarcin, daalla gafara ki bani wuri"

Dady ya fad'a cike da tsawa,

Rai b'ace Deejah tace "wai kai Dady yanzu duk ka

tsane ni ban sani ba, ai ba kaina farau zaman gida

ba aure ba, akwai ma wanda suka fini amma basu

da auren, nidai gaskiya a shafa min lafiya da

zancen auren nan, ba sai mijin yazo ba sannan

akeyin auren?",

"Taya miji zaizo miki kina da bak'in hali, ke wallahi

kibi a hankali, babu namijin da zai auri macen da

bata da aiki sai zuwa club, party da duk wurin

lalata" Momy Zee ta jefo mata wannan maganar.

"Nidai ku shafa min lafiya inba haka ba wallahi in

bar maku gidan sai inga wanda zakuci gaba da

yima fad'ace fad'acen ku" Deejah ta fad'a cike da

rashin kunya.

kyakkyawan mari Dady ya wanke Deejah dashi

"Ki tafi d'in sai me? Wawuya mai bak'in hali, daga

ma mun huta idan kika tafi d'in? Kullum banda

d'auko mana magana me kike yi? Ciki nawa kika

d'auka ana zubar miki? Ai ni farin ciki ma zanyi idan

kika tafi" Dady ya fad'a cikin halin ko in kula.

Sosai maganar ta bak'antawa Deejah rai, hakan

yasa ta shiga d'akin ta ta hau kwasar kayanta tana

had'awa cikin wani trolly bag, a b'oye ta shiga

d'akin momy ta bud'e side drawer ta sace duk

dollars d'in dake ciki bata bar komai ba,

D'akin ta ta koma ta tura kud'in can k'asan kayan ta

sannan ta rufe ta fito,

Dady da momy babu wanda ya kalle ta, hakan yasa

taci gaba da k'as k'as da chewing gum d'in ta ta

fice,

Sosai sukayi mamikin ta,

Basu gama mamaki ba mai gadi ya shigo da takarda

a hannu yace "yallab'ai gashi wani mutumi ne ya

kawo yace a baka",

Karb'a Dady yayi yace "mutumi? Bai fad'a maka

koshi waye ba?",

"Ehh bai fad'a ba yallab'ai, nima na tambaye shi

kowa zance yace kawai in baka idan ka karanta

zaka gane"

"Ok jeka kawai" Dady ya fad'a tare da komawa ya

zauna ya bud'e takardar.

_"Assalamu alaikum, wannan sammaci ne daga

kotu, ana neman ka ranar 16/12/2016 a High court

domin amsa wasu tambayoyi"_

Wata irin zufa ce ta ketowa Dady a fuska,

"Sammaci? Waye ya kai ka k'ara Alhaji?" Momy

zee ta fad'a cike da mamaki.

"Tambayar da nake wa kaina kenan Zainabu, waye

ya kaini k'ara? Amma, Allah ya kaimu jibin zanji

koma miye, nafi k'arfin su, ina da kud'in da zan

saye kowa dasu, saboda haka ba abun damuwa

bane Zainabu",

"Hakane Alhaji, ni yanzu damuwa ta shine; ina

wannan yarinyar ta tafi?",

"Ki barta taje duk gidan uban da take so, ita ba 'yar

iska bace? Ni nafi ta tashanci, ko rabi rabi na batayi

a iskanci ba, k'arshen ta dai tace zata kama gida ta

fara karuwanci ko? Ko anan gidan ma ai karuwancin

take yi, tafi ruwa ma gudu".

Ni dai Amrah iyakaci na kallo, lallai akwai rayuwa a

gidan nan, kenan bayan rabuwa ta dasu karuwanci

Deejah ta fara? Dama hausawa sunce alhaki

kuikuyo ne, Allah bazai tab'a k'yale su akan azabtar

da *UMMU HAYDAR* da sukayi ba.

©Princess Amrah

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*

.

*Na Amrah NWA*

6⃣8⃣

Yau ta kama 16/12/2016 kuma yau ne za'a fara

zama kotu,

Kotu ta cika mak'il inda kowa ya halarta face Alhaji

Saminu da ake jiran zuwan shi,

Ba'a fi minti talatin ba kuwa sai gashi shi da momy

zee,

Wurin zama suka nema har yanzu basu kula dasu

Nadiya ba,

Bayan mai gabatar da k'ara ya gabatar ne kotu ta

buk'aci Maamah da ta fito tayi bayanin abunda ta

sani,

Hankalin Alhaji Saminu ya mugun tashi ganin

Maamah da yayi tsaye gaban alk'ali, take ya fara

tariyo mafarkan daya ringa yi a kwanakin nan, ashe

abunda mafarkan shi ke nufi kenan,

Shikenan yasan asirin shi ya gama tonuwa,

A ranshi yace "ai kuma basu da wata shaida" take

yayi murmushin mugunta sannan ya miyar da

hankalin shi ga bayanan da Maamah keyi,

Bayan ta gama ne aka buk'aci Alhaji Saminu daya

fito,

Hawayen k'arya ya k'irk'iro ya fara da "ni Alhaji

Saminu babban aminin Alhaji Umar Turaki ne, akwai

babbar alak'a a tsakanin mu, hakan yasa yana daf

da rasuwa ya bani amanar 'yar sa Nadiya,

Tun a lokacin na kula da matar shi bata so da hakan

ba, har Allah yayi masa rasuwa, dan dole ta bani

Nadiya amma daga k'arshe ta gudu da duk dukiyar

Alhaji Umar bamu sake sanin inda take ba, haka

naci gaba da rainon 'yar su Nadiya cikin amana har

na aurar da ita duk da dukiya ta amma wannan bai

dame ni ba nidai fatana shine inga na farantawa

Nadiya rai, wai yanzu dan dukiyar data sata ta k'are

shine take bak'in ciki da tawa tazo ta kawo k'ara ta,

ya mai girma mai shari'a kar ka saurari wannan

matar, munafuka ce duk zancen k'arya ne ta kawo".

Murmushi Barr. Kamal yayi kafin ya mik'e tsaye

yace "ya mai girma mai shari'ah! Ina so kotu ta bani

dama domin gabatar da shaida ta, wadda itace ta

farko kuma ta k'arshe a wannan shari'ar",

"Kotu ta baka dama" alk'ali ya fad'a yana 'yan

rubuce rubuce.

Wannan k'atuwar jakar ya bud'e ya fiffito da duk

original copies na takardun Alhaji Umar Turaki,

Mik'a su akayi ga Alk'ali ya dudduba sannan aka

mik'o su ga Alhaji Saminu,

Koda ya duba takardun har da fitsari yayi, ya

tabbatar da babu makawa asirin shi ya tonu tunda

ga shaidu nan, su kad'ai ma sun isa su nuna cewa

Maamah nada gaskiya, ga uwa uba barr. Kamal da

kowa ke tsoron karawa dashi, a ranshi yace "lallai

yau tawa ta k'are, kar ma na wahalar da kotu barin

tonawa kaina asiri ko zan samu sassauci"

Hakan yasa ya karaya ya fara kwararo bayani har

da mutanen daya kashe duk saboda wannan

dukiyar, ya kuma k'ara da "daga k'arshe na kashe

kaf yara na wanda mukayi aiki tare dasu dan bana

so na basu ko sisi a cikin kud'i na, ban tab'a

tunanin cewa ba original copies bane ta bani, sai

gashi yau k'arshe na yazo, tawa ta k'are, babu

dukiyar kuma za'a yanke min hukunci, lallai nayi

dana sanin abunda na aikata, dana sani wadda bata

da wani amfani a yanzu, tir da hali irin nawa, tir da

son kud'i irin nawa, yau gashi babu abunda ya

haifar min face mummunan k'arshe, na sangarta

'yata ta ciki na gashi tafi k'arfi na, na cuci *'YAR

AMANA* na zalunce ta" ya k'ara fashewa da kuka

rurus cike da nadama, nadama mara amfani.

Babu wahala aka yanke masa humuncin kisa ta

hanyar harbi da bindiga, an sassauta hukuncin ne

saboda sauk'ak'awa kotu da yayi yayi bayani da

bakin shi,

Momy Zee kuwa jin hukuncin da aka yankewa mijin

ta kuma an k'wace kaf d'in dukiyar sa gashi kuma

tilon 'yar ta ta gudu yasa ta fad'i k'asa bata

numfashi, koda aka duba ta har zuciyar ta ta buga

ta mutu.

Wani irin kuka Alhaji Saminu ya fashe dashi, take

aka wuce inda za'a yanke masa hukunci ko sallah

ba'a barshi yama matar shi ba. Gama shari'ar ne

aka kawo wasu mutane su goma sha biyu duk an

nad'e masu hannun su da hand cuff, kallon shi

Maamah tayi sosai ta gane lallai Salman ne mijin

Humaira, nan aka gabatar da k'arar su akan

mummunan halayen su, kuma an tab'a kama su a

Abuja suka gudu shine suka dawo da harkar su a

Kano, dawowar su kenan asirin su ya tonu.

Su maamah basu tafi ba har sai da sukaji laifin su

Salman, wai an kama su da safarar miyagun

k'wayoyi ne, an yanke masu hukunci shekara talatin

a gidan yari. Cike da farin ciki su Maamah suka tafi,

yau kam burin su ya cika, an kama mugayen

mutane biyu da suke da haushin su, amma sunji

tausayin Momy Zee data rasu.

Wannan shine k'arshen Alhaji Saminu, Momy Zee

da kuma Salman tsohon mijin Humairah (iyayen

Umar). Allah yasa mu cika da imani ya raba mu da

son zuciya, masu hali irin wannan kuma Allah ya

shirye su.

©princess Amrah

®NWA

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah NWA*

*Second to the last page*

********************************


6⃣9⃣

*BAYAN SHEKARA ASHIRIN (20)*

Yau ta kama safiyar talata wanda yayi daidai da

goma ga watan March,

Tafiya nake sosai ko waige banayi har saida naci

tuntub'e da wasu mutane maza biyu mata biyu,

Cikin razana babbar macen cikin su tace "baiwar

Allah baki da hankali ne ko me? Ke bakya gani da

zaki bangaje mu ki wuce? Me kike kallo ne da har

baki iya kula da abunda yake gaban ki?"

Cikin rawar murya nace "kiyi hak'uri baiwar Allah!

Ina sauri ne zanje wani gida na dad'e rabona dasu,

ina da buk'atar sanin halin da suke ciki, na d'auki

tsawon lokaci ban kai masu ziyara ba",

Shiru matar tayi kafin tace "to babu komai baiwar

Allah, ki tafi kawai Allah ya tsare gaba".

Godiya na mata sannan na kama hanya har da gudu

gudu nake had'awa.

Misalin k'arfe sha biyu na rana na isa gidan da nake

son zuwa d'in,

Sallamah nayi mai gadi ya bud'e min tare da

lek'owa yace "lafiya baiwar Allah?",

"Lafiya lau Baba, nazo wurin masu gidan ne" na

fad'a ina kallon shi.

"Masu gidan basu nan kuwa, basu dad'e da fita ba

su duka",

"Eyyah! Gashi kuma ina da buk'atar ganin su Baba,

ina sukaje ne?"

"Ehh to! Naji dai suna fad'in yau babban yaron gidan

zai dawo daga Madina, ina tunanin shi suka tafi

d'aukowa daga filin jirgi".

Mamaki falala a fuskata nace "babban yaron gidan?

Haydar kenan?",

"Ehh Haydar fa, ya gama karatu ne zai dawo yau,

ina tunanin ma har ya iso".

Fuska kyam da mamaki nace "to Baba barin bisu

mu had'u acan d'in, Allah sarki Haydar ashe an

kammala karatu",

"To shikenan hajia, sai kun dawo"

Daga nan na tafi babbar airport d'in Aminu Kano

dake cikin birnin Kano.

Da zuwa na naci karo da wasu family guda cike da

farin ciki,

Daka gansu zaka gane lallai suna cikin annashuwa

saboda firar su kawai suke yi suna dariya.

Sallamah nayi inda suke suka amsa sannan suka

bani izinin zama,

wata babbar mace ce daga gefe wadda daka ganta

kaga dattijuwar mace, zata kai kimanin shekara

hamsin da biyu zuwa da uku,

Kallo d'aya na mata na gane lallai Nadiya ce

*UMMU HAYDAR,*saboda sak kamannin ta suna

nan basu canza ba,

"Hajiya kin gane ni kuwa?" Na fad'a ina kallon ta,

Shiru tayi ta d'anyi tunani kad'an sannan tace "ehh

to! Na dai san nasan fuskar a ko ina ne, amma

bazan iya tuna a ina na santa ba".

Murmushi na mata nace "dama nasan ba lallai bane

ki gane ni Hajiya, sunana Amrah, wadda ta bibiyi

labarin ki a baya",

Farin ciki fal a fuskar ta tace "Allah sarki Amrah!

Kwana da yawa ashe kina nan",

"Ina nan Nadiya, na d'an ziyarci wani k'auye ne

inda nake kwasowa fans rahoton *DODON JATAU,*

saisa kika jini shiru, naje gidan ki mai gadi yace min

kuna nan shine na biyo ku".

"Wayyo Amrah sannu da k'ok'ari, na kula cewa a

rayuwar ki kina da burin nishad'antar da fans d'in

ki, bama nishad'antarwa kad'ai ba, har da fad'akar

dasu kina dashi, kamar a labari na ne, kin fad'akar

sosai a cikin shi, ina fatan dai fans d'in naki zasu

amfana da abunda suka karanta a cikin shi, saboda

haka nake bama fans d'inki shawara da su daure su

nemi *DODON JATAU* su karanta shi dan nasan

yana d'auke da tarin ma'anoni, nima zan nema dan

bazan bari a bani labari ba".

"Nagode sosai *UMMU HAYDAR,* Haydar d'in bai

iso bane?",

"Ehh bai...." bata gama maganar ba kasantuwar

k'arar jirgin da sukaji da k'arfi yana saukowa a filin

jirgin.

Murna sosai family'n suka ringa yi, a hankali suka

miyar da kallon su ga mutanen da suka fara sauka

daga jirgin,

Wani kyakkyawan matashi mai cike da k'warjini da

haiba ne tafe cikin keken guragu ana tura shi har ya

sauka,

Wata daga cikin family'n cikin farin ciki tace "laaa

Ummu kinga Ya Haydar can wallahi",

Duk kansu farin ciki suka d'auka tare da gudu har

suka shiga inda Haydar yake,

Nima basu barni a baya ba sai da na bisu dan

tabbatar ma ido na cewa wannan Haydar ne ya

koma kamar balarabe, lallai na dad'e ban ga Haydar

ba.

Tabbas kuwa Haydar d'in ne, domin kuwa

kamannin shi suna nan sai dai kyau daya k'ara, ya

k'ara zama ja sosai ga sumar kanshi kamar ta

larabawa,

Bayan an gaggaisa ne aka gama masu screening

k'anin shi Umar ya karb'ar masa jakar sa da sauran

tarkacen kayan shi yakai a mota,

Mota biyu akayi nima suka rab'ani a ciki sannan

muka luka gida.

Yau kam wannan babban family'n cike yake da farin

ciki,

Abinci kala kala suka girka kafin su tafi airport,

bayan Haydar yayi wanka ya huta ne aka fara 'yan

cinye cinya da lashe lashe, nima dai basu barni ba,

saboda rangem da naman kaza ne aka ajiye a

gabana na hau loda su, sai da naji ni nayi dam

sannan na sha ruwa na tashi nayi sallah.

Bayan sallar la'asar ne nace "Hajiya Nadiya baki

bani labarin bayan rabuwa ba, ina su Maamah,

Nadrah da Khalil?",

Shiru Nadiya tayi kafin tace "ahh lallai Amrah kin

dad'e baki ziyarce mu ba,

Maamah ai ta rasu kusan shekara goma sha biyu

kenan da suka wuce, Nadrah tayi aure tana

America ita da mijin ta da yaran su uku,

Khalil ma yayi aure amma shi yana India dan shi

yake kula da company d'in Papa, yana da yara biyu

twins duka maza,

Ni kuma nida miji na Hamza mun hayayyafa, yanzu

haka yaran mu bakwai dashi,

Duk yaran nan da kika gani yaran mu ne,

Umar dai kin sanshi dama, sai d'an mu na farko da

Hamza shine Abdul-wahab, mai bi masa Rabi'atu,

daga Rabi'atu sai Zarah, sai Ruk'ayya, Raheem kebi

mata sai Salmah auta ta kuma takwarar ki ce

Amrah,itace wannan" ta nuna min wata kyakkyawar

yarinya 'yar shekara tara zuwa goma,

Kallo d'aya naji yarinyar ta shiga rai na.

"Allah yaji k'an Maamah da rahama, matar kirki ta

rasu kenan? Insha Allahu 'yar aljannah ce,

Lallai kam Hajiya Nadiya kun tara zuri'ah, to naji

ance Haydar ya dawo daga Madina ne, me yayi

acan?",

Murmushi tayi tace "shekarar shi sha takwas (18)

kenan a Madina, rabon shi da Nigeria tun sanda

yazo da Maamah ta rasu, baya dawowa sai idan

wani babban abu ne,

Tun bayan rabuwar mu dake Baban Amrah ya nema

masa admission a Madina, acan yayi tun daga

primary shcool har secondary, bayan ya gama ne

saboda hazak'ar shi aka bashi admission direct to

University of Madina, yanzu haka maganar da nake

miki yayi ph. D akan *ULUMUL-QUR'AN* ne, ina

alfahari da yanda ake yawan fira dashi a gidan

television d'in su,

Muma muna kallon shi a Islam ko Iqra' cikin dstv,

yana bada fatawa sosai, Haydar dai ya zama d'aya

daga cikin abun alfahari a Nigeria, saboda samun

mai irin karatun shi a halin yanzu abu ne mai

wahala".

Kukan farin ciki na fashe dashi nace "kin gani ko

*UMMU HAYDAR?* idan bazaki manta ba aduk

lokacin da kike kuka a baya nakan fad'a miki cewa;

ki daina kuka insha Allahu Haydar sai ya zama

abun alfahari wata rana, gashi kuwa yanzu ya

zama",

"Ban manta ba Amrah, tabbas maganar ki gaskiya

ne, duk da kalar halittar sa bai sa mutanen madina

sun k'yamace shi ba, sai ma tarairayar shi da

sukayi,

Bayan tafiyar shi can sunyi bakin k'ok'arin su dan

ganin sun nema masa magani, amma da yake idan

aka haifi mutum da ciwo yana da wahalar warkewa

duka, sai bai warke dukan ba amma dai yaji sauk'i

sosai saboda maganar shi ta gyaru, gurguntakar ce

dai bata gyaru ba",

"Haka rayuwa take *UMMU HAYDAR,* Allah yasa

mutane zasu gane wannan lamarin, saboda wannan

babbar ishara ce ga mutane, ina fatan zasu d'auki

darasi a cikin labarin ki Nadi..." ban gama maganar

ba sanadiyyar wani bawan Allah da aka nuno a AIT

ana sanarwa a kanshi.

©Princess Amrah

®NWA

[2/28, 8:40 AM] Khadija: *```º~º~UMMU HAYDAR~º~º```*


*Na Amrah NWA*

*LAST PAGE*

****************************

7⃣0⃣

Kallo d'aya nayi ma wanda aka nuno d'in na gane

shi,

Cike da kid'ima Nadiya tace "Haydar!"

A yanayin kiran data masa ya tabbatar ma Haydar

cewa ba lafiya ba

Da sauri ya turo keken shi ya shigo parlor inda

muke zaune,

"Lafiya dai Ummu?",

"Haydar ka kalli wanda ake bayani a kansa a tv d'in

nan" Nadiya ta fad'a cikin hanzari dan bata so a

d'auke hoton.

Kallo na k'ara yi na tabbatar da lallai wannan fuskar

*ABBAN HAYDAR* ce,

"Ummu me kenan? Waye wannan? Me ake fad'a

akan shi?" Haydar ya fad'a dan shi sam bai gane ko

waye ba.

"Haydar Abban ka ne Usman, baban ka ne wanda

ya haife ka, wai wasu ne suka tsince shi baya cikin

hayyacin shi, kusan ma ya haukace a yanda suka

nunar, wai tsirara suka tsince shi anan Hotoro",

Ido Haydar ya bud'e yace "Abbana? Abbana fa

kikace Ummu? To me same shi ya haukace? Ummu

ba dai kina nufin muje wurin shi ba ko? Bazan tab'a

manta lokacin da ya kore mu daga gidan shi ba,

yace kar mu sake kusantar shi, idan ke kin manta

ni ban manta ba",

"Haydar bana son jin wannan maganar daga bakin

ka, ka shirya mu tafi sun bada address inda za'a

karb'e shi, ka tashi mu tafi",

"Gaskiya Ummu am sorry to say, bazan tafi ba,

saboda muma ya guje mu a lokacin da muke da

tsananin buk'atar taimako, shima kuma yanzu da

yake da buk'atar taimkon ai sai su Hajiya da Ummi

su taimake shi, babu inda zanje, kema kuma indai

zaki bi ta tawa babu inda zakije Ummu".

"Haydar!" Nadiya ta fad'a cike da fad'a "bana so ina

magana ana magana, hannun ka fa bazai tab'a

rub'ewa ba yanke shi ka yar, ka shiga taitayin ka

Haydar, kai fa babban mutum ne yanzu ka wuce

ace ina maka fad'a saboda kasan daidai, baban ka

baban kane duk abunda ya maka dole dai naka ne,

saboda haka ka tashi mu tafi yanzu Umar ya

kaimu".

Ba dan yaso ba ya tura keken shi ya fita waje, hijabi

kawai Nadiya ta zira ta shiga d'akin Umar ta fad'a

masa, shima kanshi yayi mamaki, amma da yake

baida lokacin tambaya key kawai ya d'auka ya

same mu a waje.

A bakin gidan tv'n AIT mukaje, bayani Nadiya tayi

masu akan abunda ya kawo mu,

Babu b'ata lokaci kuwa aka kaimu inda Usman

yake,

Kuka Nadiya ta fashe dashi a lokacin da taga Abban

Haydar, yanayin shi da kamannin shi baki d'aya sun

canza kamar ba shi ba,

Shi kanshi Haydar d'in kuka yake saboda tausayi,

kayan jikin Usman kansu abun k'yama ne, gashi

duk ya manyanta fuskar shi da kanshi cike da

furfura.

Bayan sunyi cike ciken forms ne aka basu izinin

tafiya da Usman, sai a lokacin Nadiya ta kira

Hamza ta sanar dashi halin da ake ciki,

"Ku tafi dashi asibiti kawai gani nan zuwa yanzu"

Hamza ya fad'a cike da tausayi.

AKTH ne yafi kusa dasu, saboda haka can kawai

aka nufa dashi har yanzu dai ba um ba um um sai

rarraba ido yake yana kallon su one by one,

Da zuwan su emergency aka karb'e shi, raunukan

dake jikin shi aka fara treating sannan aka fara 'yan

gwaje gwaje,

Nan likitoci suka tabbatar da yana da mental

problem,

Direct psychiatry aka tura su, suna can ne Hamza

ya iso ya same su,

Ba kad'an hankalin shi ya tashi ba, saboda halin da

Usman yake ciki dole ko mutum baya da imani ya

tausaya mashi.

Haka dai akaci gaba da kula da Usman a asibitin

mahaukata har sai da yayi sati biyu a haka,

Nadiya, Umar, Haydar da Amrah ne sukazo asibitin

domin duba Usman,

Suna zaune a bakin gadon shi ya farka,

A hankali ya fara motsa idon shi har suka bud'e,

bakin shi ya fara furta "kar ku kashe ni, dan Allah

kar ku kashe ni" da haka har ya dawo hayyacin sa,

Su dai su Nadiya aikin su kallo ne, Haydar kuwa

kuka kawai yake kamar ba namiji ba,

Kallo d'aya yayi ma Nadiya ya zabura ya mik'e

zaune,

Idon shi ya kama mitsittsikawa wai a tunanin shi ko

mafarki yake, tabbas ba zai tab'a manta fuskar

Nadiya ba, matar shi wadda ta k'aunace shi

tsakanin ta da Allah amma shi ya zalunce ta,

"Nasan dai gizon da kika saba yi min ne yau ma

kikayi, Nadiya na rok'e ki idan ma fatalwar ki ce to

kiyi hak'uri ki daina zomin, nasan na cuce ki kuma

ina fatan Allah ya kawo min ranar da zan had'u

dake in rok'e ki gafara, idan kuma kin mutu ina

fatan kin yafe min kafin mutuwar ki, ina fatan kar in

mutu da alhakin ki, nasan duk halin dana shiga a

baya duk zaluntar ki da nayi ne alhaki yake bibiya

ta".

Mamaki kowa keyi dake d'akin har da Hamza da

shigowar shi kenan d'akin,

"Ba mafarki kake ba Usman, ni d'in ce dai Nadiya

tsohuwar matar ka kuma uwa ga d'an ka Haydar".

Wani irin kuka ya fasa da k'arfi tare da sauka daga

kan gadon,

"Nadiya da gaske kece? Da gaske ba gizo ido na

yake min ba?",

"Tabbas nice Nadiya, wannan shine Haydar,

wannan Umar, sai kuma miji na Hamza da autar mu

Amrah" ta gwada masa su da yatsar ta.

"Allah sarki Nadiya, tabbas gaskiyar hausawa da

sukace duk abunda ka shuka shi zaka girba, na

shuka sharri kuma na girbe sharri koma ince ina

kan girbar shi ban gama ba, kafin komai dai Nadiya

ina mai neman gafarar ku, dan Allah Nadiya ki yafe

min, duk da nasan zayyi wuya abunda na miki tashi

d'aya ki iya yafe shi ina mai rok'on afuwar ki" ya

k'ara fashewa da kuka.

"Usman kenan, ni bana rik'on kowa a raina, kuma

ina so ka sanda cewa na dad'e da yafe maka, a

baya dai rai na ya b'aci amma tunda na auri Hamza

ya huce min duk wani takaici na, sai na manta da

wata rayuwa data faru tsakani na da kai, ka

kwantar da hankalin ka in danni ne na yafe maka,

Haydar dai shine ya shak'a da kai, ko ranar da

muka fara ganin sanarwar da k'yar na shawo kansa

ya biyo ni, ka rok'i gafarar shi ko zai yafe maka".

Juyawa yayi ga Haydar ya duk'a har k'asa yace

"Haydar na rok'e ka dan Allah ka yafe min, nasan

cewa ni mai laifi ne, laifin ma kuma babban laifi,

dan Allah ka yafe min, ina cikin wani hali wanda in

har baka yafe min ba ban san ya zanyi ba".

Kasa fad'in komai Haydar yayi in banda kukan da

yake ta sharb'a har yanzu,

"Haydar d'a na kaji? Dan Allah ka yafe min",

"Abba kenan, wato sai yanzu kasan cewa ni d'anka

ne, yanzu da kake cikin wani mawuyancin hali ko?

Babu komai rayuwa ce" Haydar ya fad'a tare da

juyawa zai bar d'akin.

"Haydar!" Nadiya ta fad'a cikin sigar fad'a,

"Wai kai baka san ko Allah muna masa laifi kuma

ya yafe mana ba? Kai wane irin mutum ne wanda

baya yafiya? Kowa fa yana laifi a rayuwar nan, haba

Haydar! Ban zaci haka kake ba, ban zaci zakayi

haka ba, duk rayuwar da kayo a k'asa mai tsarki

baka karanta cewa ana son bawa da yafiya ba?

Baka san falalar yafiya ba kenan? Amma kuwa ka

bani kunya Haydar, tir da hali irin naka na rashin

yafiya" ta tofar da yawu k'asa ta goge da k'afar ta.

Baki d'aya jikin shi ya mutu sai wasu hawayen dake

sintiri a kumatun shi, kallon k'asa yayi ya share

hawayen ya maida kallon shi ga Usman yace "na

yafe maka Abbah, na yafe maka duk abubuwan da

suka faru, ina fatan nadamar ka ta gaskiya ce, Allah

ya yafe mana baki d'aya".

Nannauyan ajiyar zuciya Usman ya sauke tare da

fad'in "nagode maka Haydar, hak'ik'a samun mace

mai hali irin naki *UMMU HAYDAR* ba abu ne mai

sauk'i ba, Allah ya k'aro zaman lafiya a tsakanin ki

ke da mijin ki",

"Ameen" ta fad'a sannan tace "to wai ina Hajiya da

ummi ne?".

Hawaye ya kuma sharewa yace "labari ne mai

tsawo Nadiya, ku bani ruwa insha kafin in fad'a

maku".

Ruwa aka bashi yasha sannan ya fara da

"Tun bayan rabuwar mu daku su Hajiya suka dawo

gida na kamar yanda nace maku dama,

Tunda suka dawo na fara wata sabuwar rayuwa

wadda ni kaina tamkar bana cikin hayyaci na nake

yinta,

Duk abunda hajiya zata nema a wuri na jiki na rawa

nake bata shi,

Idan zata rok'e ni kuma ma masu yawa take nema

ni kuwa jiki na na rawa nake bata,

Idan Futha tazo wuri na su mata korar kare ina

zaune bana ce masu komai har ta gaji ta daina

zuwa,

Da haka suka fara raba ni da komai nawa har aiki

suka hana ni zuwa kullum ina gida ina masu bauta,

Hatta da wankin su nine nake masu, girkin abinci

nine komai nine,

Haka rayuwa taci gaba da tafiya har aka shekara

da shekaru a haka,

Kwatsam wata rana ina zaune Hajiya da Ummin

basu nan sai ga wasu mutane sunzo,

Na tambaye su ya akayi sukazo sukace ai an siyar

masu da gida ne har notice d'in da aka d'iba ya

cika,

Sosai hankali na ya tashi babu yanda na iya dole na

harhad'a kayana wanda nake so na tafi ina kuka.

Tun daga nan rayuwa ta ta koma cikin wani hali,

duk gidan da naje sai a kore ni saboda ban kyautata

masu ba a baya, gashi ban san inda su Hajiya suke

ba, baki d'aya takardu na na dukiya sun sa na masu

signing sun tafi dasu.

Kwatsam wata rana ina tafiya bakin titi naga anyi

dafifi daga gefe ga wata mota can da alama

accident ne akayi,

Kamar ance in matsa wurin naga mata ne biyu sai

namiji d'aya wanda da alama shine yake tuk'a

motar,

Hankali na bai gama tashi ba sai da naga fuskar

Hajiya duk tayi damage da k'yar ma na iya gane ta,

D'ayar matar ma dai babbar macece ita ba'a ma

gane fuskar ta,

Hajiya bata mutu ba saboda tana motsi ita, amma

sauran duk sun mutu,

Taimakon gaggawa aka ba Hajiya nan da nan ta

farfad'o, koda ta had'a ido dani ta fashe da kuka

tana neman yafiya ta,

Nan ta fara bani labarin wai Ummi sunyi fad'a da

wata k'awar ta akan saurayi k'awar ta watsa mata

acid a fuska fuskar ta ta lalace duk ta rub'e, yanzu

haka tana can rai hannun Allah ga wari tana yi, duk

dukiyar ka mun gama wulak'antar da ita ta lalace,

Yanzu mu kuma wurin biki zamuje nida k'awata,

shine mukayi had'ari kuma wanda ya bugi motar

tamu ya gudu".

Daga nan ta fara sabbatu tana tonawa kanta

mugayen abubuwan data aikata har ta mutu.

Wata rana ina tafiya a hanya wani mutumi yayi min

horn, tsayawa nayi har ya bud'e mota ya fito,

"Bawan Allah naga alamar kana buk'atar taimako,

shine nace ga kud'i kaje ka biyawa kanka buk'ata",

Jiki na rawa na amsa nayi godiya, sai dai ina rik'e

su na b'ace, ban b'ullo ko ina ba sai wani mugun

daji an zagaye wurin da ganye,

A gaba na aka ringa yayyanka mutane ana shanye

jinin su,

Amma ni sun kasa yi min komai kullum sai suce sai

gobe,

Yanda ake yima mutane a gaba na yasa a hankali

k'wak'walwa ta ta fara juyewa har na daina sanin

komai,

Ban k'ara sanin rayuwata ba sai yanzu dana

farfad'o na ganni gaban ku".

Kowa na wurin kuka yake har da Hamza ma, Amrah

da bata san komai bama kukan take ganin iyayen ta

suna kuka.

Nadiya ma ta labarta mashi komai daya faru bayan

rabuwar su, yaji ma Haydar dad'i sosai da yaji

cewa yanzu haka an bashi aiki a Madina, nan da

wata d'aya zai koma can yaci gaba da aikin shi.

[5:37pm, 17/12/2016] Amrah Pinky durling

: *BAYAN KWANA BIYAR*

Komai ya lafa har Usman ya warke sarai an sallame

shi,

Zaune suke a gida suna ta fira cike da nishad'i

Usman yace "to Haydar maganar aure fa? Sai

yaushe zakayi? Kaga shekarun ka sun fara tafiya

har ka wuce talatin, dan Allah ka fiddo mata haka

nan, koko dai 'yar balarabiya zata zama surukar

tawa ne?"

Sunkuyar da kanshi yayi k'asa ya sosa k'eya yace

"ehh Abbah akwai wadda mukayi maganar aure da

ita, tace zata jira ni har in koma",

"To masha Allah, hakan yayi ai, Allah yasa albarka,

nima gobe nake son komawa Katsina, kaga babu

yanda za'ayi in zauna nan gidan, abun akwai kunya

a cikin shi",

"Haka ne Abbah, Allah ya kaimu goben" Haydar ya

fad'a tare da rarrafawa ya hau keken shi ya koma

d'aki.

Washe gari Usman ya k'ara neman gafarar su sosai

sannan ya tafi tasha, bayan sun shiga mota ne aka

karb'i lambar wayar next of kin na kowa, shima ya

bada ta Haydar da yake ya rubuta masa a paper

yanda idan ya koma gida zai ari waya ya fad'a

masu cewa ya sauka lafiya.

Barowar su Kano kenan suka tafka wani mugun

accident wanda babu wanda ya fita da rai har

driver'n.

Allahu akbar! Alhaji Saminu ya mutu, matar shi

momy zee ta bishi, 'yar su Deejah ta shiga

karuwanci yanzu haka ta kamu da cutar k'anjamau,

Salman mijin Humairah ya mutu, Hajiya ta mutu,

'yar ta Ummi ta gama rub'ewa k'arshe ta mutu!

Yanzu ma ga Usman ya bisu, rayuwa kenan, Allah

kasa mu cika da imani, ina rok'on Allah yasa

wannan labarin zai zama ishara ga sauran mutane

baki d'aya, da masu irin halin su da wanda suke da

shirin yin kwatankwacin halin su, Allah ya yasa

muyi kyakkyawan k'arshe.

Daga nan nima Amrah sai na gudu, na ma Haydar

da 'yar balarabiyar shi fatan alkhairi saboda ina da

fushin zuwa kotu domin sauraro *WATA SHARI'AH.*

*ALHAMDULILLAH!*

Glory and thanks be to Allah, the most gracious, the

most merciful, for the successful completion.

I would like to thank *NAGARTA WRITERS

ASSOCIATION* (Adda Bena, Lubee maitafseer

Aunty YBK, M. Jabo, Bebeelo, Chuchungaye and

Ummul-Fadeelah) for the inestimable support and

the companionship and the other special reasons

that cannot be mentioned here, I cannot thank you

enough.

Special appreciation goes to my sisters (Rabi'atu sk

msh and Zarah bb) kun zamo wata jijiya a jiki na,

wadda idan babu ita bazan iya motsi ba. Much love

to you guys

To my Friends;

Kausar love,

Ayusha Iliasu,

Autar Hajia,

Baby Zahra,

Haneefa Usman,

Miemiebee,

Mrs. Umar,

Munayshat,

Nuceeluv,

Stylish,

Khairat up,

Sdy Jegal,

Maryama Garba,

DEEJAH abdul,

Pherty,

Ummi Aysha,

Sirdear,

Nafee Anka,

Sahaf,

Aneelurv,

Fido sodangi,

Futha,

Ayshat one,

Asea b Aleu,

Hauwa Damary,

Ashnur,

Feenat Ja'afar

Miss Hafsy.

Ba wai dan na manta da wasu ba, wallahi duk kuna

raina, lissafo ku ne ba abu mai sauk'i ba, amma duk

ina k'aunar ku.

Ilham Muhammad, Asma'u Abdu Haro and Hadiza

Usman Tunau kunfi kowa son wannan littafin, ina

godiya da k'aunar ku.

Littafin UMMU HAYDAR sadaukarwa ce ga d'ana

Haydar Rumah, ina k'aunar ka Allah ya raya min

kai.

Tukuici ne ga duk masu 'ya'ya Haydar, Allah ya

raya mana su bisa tafarkin addini.

Excellent writers,

Writers Planet,

Duniyar mu,

Amrah and Rabi'at sk fans,

Zarah bb Fans,

Nafee anka novella,

Pherty novels,

Mrs Umar novels group,

Mu farka mata group chart

da sauran wanda ban fad'a ba duka nagode da

bibiyar labari na da kukayi.

Ku kasance tare dani a novel d'ina na gaba mai

suna *WATA SHARI'AH* wanda zaizo maku cikin

sabuwar shekara insha Allahu.

Zakuci gaba da ganin posting na novel d'in *DODON

JATAU* insha Allahu wanda RAZ ke kawo maku

akoda yaushe.

Amrah A msh kema duk wani masoyinta na nesa

dana kusa fatan alkhairi, Allah ya had'a fuskokin mu

a aljannah.


Tags: #Musaki #Nakasa #Haidar #Nadiya
5641
0
2
2
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!