Sune Sila!

Written by Maman Ja’afarPublished on 2018-12-12 18:09:49Category FictionYana magana ne akan mahimmiyar rawarda iyaye kan taka wajan rusa tarbiyar yaransu mata, ta yanda suke daukat buri su dora akansu ko kumama suce su zasu dauki dawainiyarsu dukda sunsan yaran nan yan mata ne kuma ba wata sana'a sukeyi ba, karshe abin ya haifar masu da da marar ido tags: Maman Ja’afar #iyaye #’ya’yaDuba was labarai »

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [21/04, 8:49 p.m.

*💘SUNE SILA💘*


        2Daga alkalamin 

MamanJa'afar✍Jiki na kyarma ta bar Umar a nan zaune inda suke ta ruga cikin gida wajen kiran babban yayan nata domin tasan kwanan zancen


Bata k'araso inda yayan nata yake tsaye ba a cikin gidan, saima k'ara ra6ewa da tayi a jikin bango tana mai rarraba idanuwa tsakanin uwar da kuma yayan nata


"Ubanwa ya baki izinin tsayawa da wancen d'an iskan iye?" Ya fad'a cikin alamu na fusata


"Ammifa na nan sadda na fit........


"Da ina nan d'in tambayata kikayi sadda zaki fitan? Nidai kawai naga kin zari gyalenki kinyi gaba, ni wallahi Kabiru babban tsoronama kar yarinyar nan taje ta jawo mana wani abin kunyar domin kasan y'an Aca6an nan y'an iska ne na k'arshe bafa wani mutunci suka cika ba"


"Ai Ammi dukma abin bazai kai nan ba insha Allahu" Ya fad'a tare da duban fuskar Lauratun


"Ke ba kince dai soyake ya aureki ba?"


Jijjiga kai tayi alamun amsawa


"To ki fad'a masa gidanku ance ya turo magabatansa"


"Shikenan kuwa, wasalam wa kitabihi, nasan dai ba iya turowan zaiyi ba, kaga daga haka sai ayi masu katanga hankalin kowa ya kwanta, ni babbar matsalatama yawan takura matan da yakeyi a wajen aikin nata, danko kwanakima ta dalilinsa ne Hajiyar tasu ta koreta daga aiki, ni idan akayi hakama hankali na zaifi kwanciya wallahi, mu samu ya barta tayi aikinta cikin kwanciyar hankali kafin Allah ya kawo mata mijinda zata huta muma iyayenta mu huta"


Ita dai Lauratu sumui-sumui ta shige cikin d'akin nasu duk kuwa da uban zafin da ake gabzawa, domin koda tayi shinfid'ama a tsakar gidan ba komai bane zai biyo baya face y'an k'ananun magan-ganu daga bakin mahaifiyar tata, dan wani abinma idan mahaifiyar tata tayi mata har k'ok'onto takeyi a cikin zuciyarta tana cewa anya kuwa Ammi ita ta haifeni da cikinta? Domin indai y'ay'aye agidajen iyayensu suke samu farin ciki ita kam bata samunsa a nasu gidan, saboda idan har kukaga Lauratu a cikin farin ciki da annashuwa to kuwa tabbas tana tare da abin k'aunarta ne Umar, babu dad'i a gida kuma babu dad'i a gurin aiki.


Da wannan tunane-tunanen ne bacci 6arawo ya kwasheta acikin wannan matsanancin zafin da ake rabkawa.


*****

Washe gari a daidai lokacin da matasa irinta suketa shirye-shiryen tafiya makaranta, a kuma daidai wannan lokacin ne itama take k'okarin shiryawa domin tafiya gurin aikinda iyayenta suka za6a mata a matsayin makarantar boko da kuma ta islamiyya


Dayake band'akin yau nasu akwai layi da yawa shiyasama bata samu damar yin wanka ba, saidai tsaka tsami da tayi ta nufi gurin aikin nata, duk da dai a ranta ba hakan taso ba.


"Sannu Hajiya, sai yanzu akaga damar fitowa?" Cewar uwar aikin nata kenan yayinda take dubanta cikin gatse da kuma izgili


"Kiyi hak'uri Hajiya na tsaya had'a mana kokon karin kumallo ne shiyasa kikaga nad'an makara, amma takwas d'inma bata ida yi ba ai"


Da gama fad'ar haka ta cire mayafinta ta shige cikin ma'aikatan domin gudanar da abinda suka saba


Dayake dama doka ne a shagon ba'a zama da mayafi ko hijabi, a cewar Hajiyar wai zai dinga dabaibayeka har ya hanaka yin aiki yanda ya kamata, amma acan k'asan zuciyarta ba haka take nufi ba, tana fad'ar hakan ne kawai dan idan babu mayafi y'an matan zasufi birge kwastomomin nata.


Ruwan wanke-wanken ta had'a tare da tattaro dukkan wani abu da yakamata ace an wankeshi yanzu


Yau kam ba'a zaune take wanke-wanken nata ba, a duk'e take yinsa, wanda hakan nema ya bawa wasu sassa na jikinta damar bayyana kasancewar d'inkin nata yanada d'an bud'ad'den wuya sosai.


Umar na hango tsaye a daidai gurin wani mai tireda yana niyar sayen omo, wanda yake sana'ar tasa a dab da indasu Lauratu suke sayar da abinci


Wani lokacin Umar ko baiyi niyar sayen abu gurin mai tiredar ba yakanzo ya sayi ko cingam ne ko kuma biskit badan komai ba sai dan kawai ya hango abar k'aunarsa.


To yauma irin hakan ce ta faru, muradin ganin Lauratun ne kawai ya fad'o masa shinema ya d'auko nera gomarsa yazo siyen omo badan komai ba sai dan yad'an kalleta ko yaya ne shi dai yaga ta sakar masa wannan murmushin nata mai sanyaya mashi zuciya.


Tunda ya kalleta so d'aya bai k'ara marmarin maimaitawa ba, saboda wani 6angare daya bayyana a jikinta kasancewar a duk'e take.


Mashin d'insa ya tada bai zame a ko ina ba sai a Green House inda ake sayar da d'inkakkun hijabai anan cikin garin Katsina kenan


"Dan Allah Malam hijabi nakeso d'an matsakaici haka kunadashi?" Ya fad'a bayan ya shiga cikin shagon sayar da hijaban


Lissafo mashi kud'aden hijaban akayi kana ya d'auki na daidai kud'insa wato d'ari takwas


Dayake a zuciye yake cikin mintinanda basufi biyar ba ya dawo K'ofar Marusa d'in a inda su Lauratun suke sayar da abincin kenan


Inda take wanke-wanken babu cikowar mutane sosai, kuma dama gurin an ke6ance shi ne badan komai ba sai dan saboda wanke-wanken shiyasa Umar baiji shayin komai ba wajen mik'a mata bak'ar ledar dake hannunshi ba


Cikin tsoro fuska cike da tuhuma alamomin tambayoyi fal a tattare da ita ta dubesa, domin bata saba ganin fuskarshi a irin wannan yanayin ba


"Akwai guntuwar takarda aciki ki duba zaki gani"(Ina baku labarin abinda ya faru shekaru sama da goma ne kunga kenan a lokacin ai rike waya sai wane da wane ko) Yana gama fad'ar haka ya haye mashin d'insa ya figesa cikin 6acin rai wanda ba kasafai ya saba yin irin hakan ba sai dai idan an 6ata masa rai sosai.


D'ayan shagon nasu ta shiga inda suke ajiye itace da dai sauran tarkacensu ta bud'e bak'ar ledar


Hijabi ta gani ruwan toka da y'ar guntuwar takarda a ciki


_Ga hijabi nan ki saka. daga yau bana buk'atar k'ara ganinki babu hijabi a jikinki, kome zakiyi karki kuskura na k'ara ganinki a haka, ina fatan zaki kiyaye?_


Abinda taga ya rubuta ajikin y'ar guntuwar takardar kenan, dayake dama yana koya mata karatun hausa shiyasa batasha wahala gurin karantawa ba


Hijabin ta saka kamar yanda ya buk'ata taci gaba da ayyukan nata, domin muddin ta kuskurewa hakan tasan abinda zai biyo ba


Wanna yana d'aya daga cikin dalilanda yasa Lauratu take matuk'ar k'aunar Umar, domin duk wani abu da zai lalata mata rayuwa Umar yana k'okarin kaffa-kaffa dashi tunda yasan iyayenta babu ruwansu da kulawa ta wannan 6angaren, sudai babban fatansu su ganta tana tafiya gurin aiki kuma tana dawo da kud'i kawai.


Koda fitowarta sauran ma'aikatan gurin me zasuyi inba dariya ba


"Wai dariyar me nake jiyowa haka ne?" Hajiyar ta fad'a yayinda take nufo gurinda suke dariyar


"Lauratu yau kuma wani sabon salon iskancin ne ya motsa maki?" ta fad'a yayinda take k'arewa Lauratun kallo


"Hajiya bafa komai bane ba hijabi ne kawai na saka" Ta fad'a murya na rawa domin tsoron abinda ka iya zuwa yadawo


"Yau dai nagaji da halayenki Lauratu, ke shikenan ba'a isa a aikeki sayen sigari ba, ke ko d'an sakin fuskar nanma ayi wasa da dariya bakya yiwa jama'a ta, ga saurin fushi sai kace d'iyar kuturwa, da anyi magana kuma ki hau yiwa mutane kuka kega mai idanuwan Aliyara(Wani ganye ne mai zubar ruwa akoda yaushe)Saboda haka kinga hanya?" Ta fad'a yayinda take nunawa Lauratun hanyar fita


"Kama gabanki, yau dai ko kinfi kowa iya aiki na hak'ura da aikinki kije d'an iskanda yake zugaki kina k'in aikin ya dinga sallamarki kullum"


Kusan shekaru uku kenan ana fama da abu d'aya, masifar yau daban kuma ta gobe da ban


Amma wannan karon Lauratu tayi alkawarin kamar yanda ta baro cikin mahaifiyarta insha Allahu tayi alkawarin tabar gurin aikin nan kenan, a cewarta idan har iyayen sukaga babu aikin yazama dolensu su kaita makaranta tunda bazasu tasata agaba suna kallo ba.


Da wannan tunanin Lauratu ta kama hanyar gida.


"Sayen Sigarin ne aka aikeki naga kina tafiya kinata faman kuka ko kuwa wani abin ne na daban ya sake faruwa?"


Cewar Umar kenan yayinda ya faka mashin d'insa a gefen hanyar da take tafiya


Hawaye na bin fuskarta ta dubesa"Kaima kasan matsala indai aguna ne kullum ai wata sabuwa ce ke 6ullowa"


"Yanzu me kuma ya faru" Ya fad'a a tak'aice


"Kan dai wannan hijabin ne daka kawo mani, tofa shine taita faman fad'a harda cewa ta koren...


Bata k'arasa zancen nata ba saboda kukanda ke nema ya kubce mata


"Miye kuma abin kuka Lauratu? kukan nan nakifa ba k'aramin tada mani hankali yakeyi ba, ina keda bakinki kike fad'a mani kin gaji da wannan wahalar? to dan Allah ya kawo k'arshenta kuma madadin kiyi godiya agaresa sai ki tsaya kina faman zubda hawayenki?"


Cikin kukan ta dubesa"Umar kenan, ya kake magana sai kace bakasan wace ce Ammi na ba? Wallahi yau nasan 6acin randa zan gani a gida nan Allah ne kad'ai yasan iyakarsa"


Shuru yayi alamun nazari domin har yanzu bai manta maganar da Ammi ta ta6a fad'a masa ba lokacinda ya kawo mata shawarar cewa tunda Lauratu ta fara girma kamata yayi ace ta daina zuwa gurin aikin nan haka, da bud'ar bakin uwar babu amsar da ta bashi face d'ari biyar biyar ne ake biyanta agurin aikin nata kullum, idan kanada halin biya sai ka dinga biya ita kuma ta zauna tayi karatun kamar yanda ka buk'ata, idan kuma bakada hali kaga kenan dole Lauratu ta fita ta nemo mana abinda zamu rufawa kanmu asiri.


"To yanzu Lauratu ya kike ganin za'ayi ashawo kan wannan matsalar kenan?"


"Bara dai na k'arasa gidan kome ake ciki zan bawa yara wasik'a sai su kawo maka"


Har ya tada mashin d'in nasa zaiyi gaba ta tuna da sak'on da aka bata jiya ta fad'a mashi


"Am na manta ban fad'a maka abinda yaya Kabir yace na gaya maka ba jiya"


"To Allah yasa dai alkhairi ne? Ina saurarenki" Ya fad'a batare da ya kashe mashin d'in nasa ba, domin bai cika son yana tsayuwa da ita abakin hanya ba saboda kare mutuncinta


"Wai sufa har yanzu basu amince cewa da gaske so kake ka aureni ba, shiyasama sukace na fad'a maka wai ka turo iyayenka domin su gane manufarka akaina"


Shuru yayi na d'an wani lokaci, tunani kala-kala acikin zuciyarshi


Dan so kam babu wanda ya kaishi son ya mallaki Lauratu a matsayin mata agaresa, to amma ba anan gizo yake sak'arsa ba, da wane kud'in zai tura gidansu neman aurenta? da wane kud'in kuma zai auretan? shin idan anyi aurenma a wane gidan zai ajiyeta bare kuma akai ga maganar abubuwanda yakeyi mata tanadi wad'anda zasu inganta rayuwarta? Gashi har yanzu bashida Mashin d'in kansa domin na haya ne a hannunsa kuma kullum Balans yake kaiwa.


Duk tsare-tsarenda yake tayi kwata-kwata ko a mafarki bai ta6a kawo maganar aurensu nan kusa kusa ba, domin shi a nashi tunanin shekara biyu masu zuwa ko uku yake hari kamin sannan ya riga ya gama tanadar duk wani abinda yadace ya tanada, anya ba wata mak'ark'ashiya ake shirin shirya masa ba?


"Umar kodai da wata matsalar ne naga kayi shuru tun d'azu?" Ta fad'a jiki a sanyaye


Ajiyar zuciya yayi


"Babu komai Lauratu insha Allahu babu abinda zai gagara kinji?"


Da wannan sukayi sallama kowa ya tafi yana mai d'auke da tunani kala-kala na neman mafita acikin zuciyarsa.....


Har yanzu dai sharar fage mukeyi domin bamu kai ga shigowa cikin labarin gadan-gadan ba
*Maman Ja'afar ce*

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [21/04, 9:09 a.m.]

*💘SUNE SILA💘*


       1Daga alkalamin 

Maman Ja'afar✍*GODIYA*


Ina farawa da godiya ga Allah (S.W.A)mai kowa mai komai daya nufeni da fara wannan littafi na SUNE SILA lafiya kuma ina rokonsa cikin yardarsa da Kuma amincewarsa yasa na kammalasa lafiya kamar yanda na fara batare da ansamu wata tangarda ba.


Yauma bara nayi amfani da wannan damar na k'ara bawa masoyana amsoshin tambayoyinds suketa tambayata kullum


_Sannu sannu_ da nayi ba buk bane ta'aziyya ce kawai na zauna na tsarata zuwa ga sirikina Kakansu Ja'afar da ya rasu


_Azumi a Karkara_ shima ba buk bane y'ar tunatarwa ce kawai na zauna na tsara zuwaga mutanenmu na karkara domin gabatowar watan Ramadan


_Yar Ghana_ shima ban fasa yinsa ba yana hanya insha Allahu bayan kammaluwar wannan.


Ina Masu neman nasakasu a group da masu sakani ina fita? Ina mai baku hak'uri wallahi bana yin group kuma banida group amma badan bana so ba sai dan wani dalili na daban, hakan nema yasa nake saka lambata a k'arshen littafin nawa saboda mai buk'atar ci gabansa


Ina masu cewa bana saka soyayya a cikin books dina ko kuma bana canza salon rubutuna?To Albishirinku yaudai ga SUNE SILA nan d'auke da sabon salo wanda babu tafiya ko kad'an acikinsa nazo maku dashi, a Katsina na farasa kuma anan nake fatan kammalasa insha Allahu.


Nagode sosai da irin k'aunar da kuke nuna mani ko nace kuke cikin nuna mani masoyana, domin k'aunarku agareni wani lokaci dan tsabar jin dad'i idan na zauna har hawaye ke zubo mani. Insha Allahu bazan baku kunya ba. *SADAUKARWA*Wannan littafin Sadaukarwa ne ga duk masoyanda suka so juna kuma suka zauna da juna bisa ga gaskiya da amana. Ina rokon Allah ya barmu tare da masoyanmu na gaskiya.Da yake yau jumma'a dank'am shagon sayar da abincin nasu yake da jama'a ta ko ina babu masaka tsinke, yayinda ma'aikatan suketa faman kai komo wajen hidima da kwastomomin nasu


Wasu na girki, wasu na kai abincin a mutane, wasu kuma y'an share-share sukeyi da dai sauransu.


Can na hango y'ar matashiyar budurwar, siririya fara y'ar kimanin shekaru kusan goma sha shidda a duniya(Lauratu kenan) ta tasa tulin kwanika da kofunan sayar da abincin agaba sai faman wankewa takeyi tana sharce zufa, ga dukkan alamu dai ina tsammanin a gajiye take.


Amma duk da wannan gajiyar da Lauratu tayi hakan bai hana Hajiya Laraba wacce ta kasance uwar d'aki agaresu azal-zalarta akan tayi sauri ba


"Lauratu wai mi kikeyi ne haka tun d'azun kamar wata wacce batada lakka cikin ajikinta? Wanke-wanken kwanikan da basufi a k'irga ba amma tun d'azun kin tasasu a gaba sai faman lailaya kikeyi sai kace kin samu k'wai kina tsoron fashewar sa?"


Cewar bak'ar matar kenan kakkaura wacce shekarunta ina zaton bazasu wuce arba'in da biyar ba a duniya


Ta bararraje akan dogon benci ta tasa kwanon kud'inta a gaba sai faman surfa masifa takeyiwa ma'aikatan nata daga nan inda take zaune


"Hajiya kiyi hak'uri wallahi ina sauri, gashima har na kusan gamawa" Ta fad'a yayinda take ci gaba da yin wanke-wankenta cikin sauri-sauri domi gudun 6acin ran Hajiyar tasu.


Kamin ta k'arasa wanke-wanken nata ne ta hango giftawar Umar na k'okarin wucewa ta gefen shagon nasu


Da sauri da sauri yake tafiyar tasa amma koda yazo dab da shagon su Lauratun sai ya fara tafiya a hankali a hankali badan komai ba sai dan kawai ya k'arewa abar k'aunar tasa kallo, domin a cewarsa koda zaiga Lauratu sau goma a rana baik'i ace ya k'ara ganinta cikon na sha d'ayan ba idan da zai samu hakan.


Murmushi ya sakar mata irin murmushin nan na masoyanda suka dad'e da macewa akan son junansu


Batare da tayi la'akari da abinda ke gabanta ba taci gaba da mayar masa da martanin murmushin da yakeyi mata har bata san lokacin da Tangaran d'aya daga cikin wad'anda take wankewa ya sulale daga hannunta ya tarwatse a k'asa ba, ji kake tasssss k'arar fashewar tangaran d'in


" Me zanji me zan gani haka Lauratu?" Hajiyar ta fad'a masifa tattare a fuskarta


Jiki na kyarma Lauratun take bawa masifaffiyar uwar d'akin nasu hak'uri


"Dan Allah Hajiya kiyi hak'uri wallahi bada gangan na fasa shi ba..


"Wane irin bada gangan ba bayan ina kallon lokacin da wancen d'an iskan yazo wucewa kuka yiwa juna wani k'uri sai kace wasu tsofin mayu, wallahi Lauratu wannan iskancin naki ya kusan kaini k'arshefa, kuma idan har kika sake iskancin naki yazo mani iya wuya kema kinsan babu wani mataki da zan d'auka wanda ya wuce sallamarki, kuma wallahi wannan k'aron idan na sallameki babu wani d'an iskan da zai k'ara bani hak'uri na hak'ura, dan ni aikinma naki na fara gajiya dashi kawai dai hak'uri nakeyi dan nasan ina sallamarki bani ba zaman lafiya, ban hak'uri ne ta ko ina har sai nagaji na maidoki sai kace kunada gadona, y'an anaci kawai" ta fada tare da jan wani dogon tsaki


Tana fad'an nata tana taunar cinyar kazar dake hannunta cikin nishad'i, yayinda zuciyar Lauratu takeci gaba da k'una tamkar an watsa mata fetur an tilla ashana a cikinta


Hakanan jiki a sanyaye Lauratu ta kammala wanke-wanken nata zuciyarta naci gaba da k'una, domin a duniya babu abinda ta tsana fiye da wulak'anci, amma ta wani 6angaren idan tayi tunani sai taga ba kowa bane yaja mata wannan wulak'ancin da k'ask'ancin da take fuskanta ba face iyayenta, saboda badan sun mayar da ita wata haja ta neman kud'i kuma madogara agaresu ba da a daidai wannan lokacin kamata yayi ace ta dawo daga makarantar boko ne tana k'okarin tafiya ta islamiyya, amma duk hakan bai samu ba, daka ta6asu basuda hujjar da zasu kafa maka sai suce maka duk talauci ne ya kawo haka, ita kuma Lauratu tana ganin talauci ba wata k'wakk'warar hujja bace da zata hana iyaye kula da y'ay'ayensu wajen k'okarin sauke duk wasu nauye-nauye da Allah ya d'ora masu(Koma dai minene maji ma gani wai an binne tsohuwa da ranta)


Sai wajejen k'arfe shidda daidai na yamma abincinsu Lauratun ya k'are


Bayan sun kakkauda komai ne sun wawwanke duk wani abu da ya dace ace sun wanke kamin safe Hajiyar ta sassallami kowa kud'in aikin nasa, manyan gurin dubu d'aya d'aya, k'ananun cikinsu kuma irinsu Lauratu d'ari biyar biyar dama ake basu.


"Lauratu yaufa d'ari hud'u zaki samu saboda tangaran d'ina da kika fasa, ungo" Ta fad'a yayinda take mik'owa Lauratu kud'in


Kar6a tayi tare da yin godiya, ta zari mayafinta dake kan k'yauren shagon ta nufi hanyar gida bayan tayiwa sauran abokan aikin nata sallama.


**********


D'an matsakaicin gida ne mai d'auke da d'akuna guda shidda na haya uku na kallon uku kuma band'aki d'aya


D'aki uku ya kasance mallakinsu Lauratu ne, d'aya nasu itada mahaifiyarta sai d'an k'aramin k'aninta da suke kwana tare wato Saminu, d'ayan kuma na babansu ne Malam Harisu, yayinda d'ayan d'akin kuma ya kasance mallakin yayunta ne guda biyu wato Kabiru da Kuma Zubairu


Sauran d'akunan kuma mallakin Malam Tanko ne dashi da matansa guda biyu da kuma y'ay'ayensu.


Sallama tayi a tsakar gidan cikin natsuwa kamar dai yanda ta saba kullum


"A'a Lauratu har andawo daga shagon ne yau da wuri wuri haka?" Uwar ta fad'a yayinda take a duke' tana k'okarin hura wutar abincin dare, wutar tak'i kamawa sai faman hurawa takeyi tana sharar hawayen wahala


"Eh wallahi Ammi har mun tashi, ai kinsan yau jumma'a akwai cikowa da yawa a shagon namu shiyasa ai kikaga duk ran jumma'a ma nake dawowa da wuri" Ta fad'a tare da mik'awa uwar kud'in hannun nata


"Ya kuma naga d'ari hud'u Lauratu?" Uwar ta fad'a tare da warware kud'in y'an d'ari-dari


"Wallahi Ammi haka ta bani dan kawai na fasa mata tangaran bada gangan ba, kuma na bata hak'uri ma amma tak'i hak'ura, bakiga irin ruwan masifar da taita yayyafa mani ba acikin jama'a, nikam da zakubi ta tawa wallahi da hak'ura akayi da wannan aikin nima na dinga zuwa makaran...


Katseta uwar tayi"Aidama nasan k'arshen tika-tika tik, ashe dama da saninki kikayi mata 6arnar ko? wato nufinki kizo ki tsara mani k'arya da gaskiya nace maki zauna, daina zuwa aikin ko? To indai kuwa wannan kalmar kikeso kiji ta fito daga bakina wallahi har abada bazakijita ba, idan kika zauna a gidan uwarki zamuci? dawa kikeso naji daga cikinku? da wancen uban naki daya kasa d'aukar nauyin gidansa ko kuwa da wad'ancan sakarkarun yayun naki da zuciyarsu ta riga ta gama macewa babu abinda suka iya sai bani-bani? To wallahi ki kiyayeni Laure kuma ki kiyayi dukkan wani abu da zaisa Hajiya Atika ta koreki da gurin aikin nan, kin jini ko baki jini ba?" Ta fad'a tare da rik'e kunnenta alamar gargad'i ga Lauratun


Ita dai Lauratu bata bi ta kan uwar ba saima shigewa d'aki da tayi ta fara rage kayan jikinta domin shirye-shiryen yin wanka, saboda nan bada jimawa ba takesa ran zuwan Habibinta Umar.


******


Dayake lokacin zafi ne shiyasa duk mutanen gidan suka kasance a tsakar gida kwakkwance suna shan iska, kowa shinfid'arsa a gefe guda shida iyalansa


"Salamu Alekum wai ance ana sallama da Lauratu" Cewar Almajirin kenan yayinda yaketa faman rarraba idanuwa a tsakankanin jerin mutanenda ke kwakkwance a tsakar gidan kai kace gidan biki ne


Zunbur Uwar tayi ta mik'e daga kwancenda take tamkar cewa akayi da ita ake sallamar a k'ofar gida "Waye ne ke sallama da ita?"


Bada jimawa ba yaron ya sake dawowa"Wai yace acemata Umar ne"


Tsaki uwar tayi gami da gyara kwanciyarta"Ni nama zaci wani mutumin arziki ne yazo ashe wancen matsiyacin yaron ne d'an Aca6a"Ta fad'a yayinda take ci gaba fifita da mahucin kabar dake a hannunta


Da dai Lauratu ta fahimci uwar bata da niyar bata izinin tafiya gurin Umar d'in, gyalenta ta zara daga saman igiyar shanyar dake tsakar gidan nasu ta nufi k'ofar gida kai tsaye inda Habibinta ke zaune a bisa dakali yana jiran fitowarta.


"Kayi hak'uri Farouq ka dad'e kana jirana ko?"


Murmushi yayi kana ya dubeta tare da had'a hannayensa a k'irji "Assalamu alaikum" Ya furta yana mai duban fuskarta


Rufe fuskarta tayi alamun jin kunya, kana da bisani ta koma baya ta d'anyi taku kad'an kana ta sake dawowa inda yake zanue "Assalamu alaikum" Ta furta yayinda take k'umshe dariyar da take 6o66oyewa


Shima dariyar yayi"Ashe baki manta da hukuncin da nake yiwa wanda ya manta da sallama ba?"


Umar Farouq kyakkyawan saurayi ne dai dai misali, bak'i ne dogo d'an siriri mai d'auke da wushirya a bakinsa


Shima dai iyayensa talakkawa ne kamar yanda nasu Lauratu suke talakkawa domin suma a gidan haya suke, sai dai ansamu banbanci tsakaninsu domin shi iyayensa dukda irin talaucin da suke fama dashi hakan bai hanasu saka y'ay'ansu makarantar boko data islamiyya ba, suna kuma k'okarin kula da yaransu daidai iya iyawarsu.


Soyayyar Umar da Lauratu ta samo asali ne kusan shekaru bakwai da suka gabata, inda yake yawan had'uwa da ita idan ta fito tallar gyad'a(Dayake unguwarsu d'aya dama) tun yana ganin abin kamar tausayi ne a hankali a hankali tana girma har abin yazo ya birkid'a zuwa soyayya, a lokacinma idan ta gansa har guduwa takeyi kamin daga baya ta fara sabawa dashi, har dai zuwa wannan lokacinda yake fuskantar tsana da kuma tsangwama daga gurin Familynta.


Bayan sun gaisa ne ya d'aure fuska tare da dubanta cikin alamu na tuhuma "Ina littafin naki yake?"


Kwa6e fuska tayi cikin yanayi na shagwa6a"Dan Allah yaudai Sahibin ayi mani hak'uri da karatun nan domin wallahi har yanzu ban har dace wanda ka bani na shekaran jiya ba"


Dayake dama a tsarin firar tasu ba kullum ne suke zama suyita fira suna kalaman soyayya ba, a'a duk Alhamis da jumma'a ne sukeyin firar yayinda sauran ranakun kuma karatu ne yake koyar da ita na addini, irinsu qur'an hadis fiqhu da dai sauransu domin gyaran ibadunta, na boko kuma yayi mata alk'awarin sai bayan sunyi aure zai sakata, saboda Umar babu abinda bai sani ba dangane da tarihin rayuwarta, shiyasama yayiwa kansa alk'awarin indai yana raye zaiyi iya bakin k'okarinsa wajen ganin ya taimaki Lauratu da duk iya abinda zai iya


_(Inama ace haka sauran matasanmu na yanzu sukeyin firarsu, madadin ace su zauna suita shararawa jinansu k'arya da gaskiya a k'arshe harma su rasa abin cewa akai ga zantukan batsa da ta6a jiki da sauransu, wani lokacinma har akai ga tsintar kai a inda ba'ayi tsammani ba, wa iyazu billahi. ammafa inji ni Maman Ja'afar)_


Suna cikin wannan musun ne Kabir yazo shigewa cikin gida


Cikin ladabi Umar ya mik'a masa hannu da nufin su gaisa dukda Kabirun ba wani girmewa Umar d'in yayi ba, saboda dukkansu a tsammanina bazasu wuce irin ashirin da biyar d'in nan ba ko zuwa da shidda , amma ko kallon arziki Umar d'in bai ishi Kabiru ba ya wuce abinsa kai tsaye cikin gida


Marairaicewa tayi cikin nuna alamu na rashin jin dad'in irin dizgin da Kabirun yayi masa ta dubeshi "Dan Allah.."


Dakatar da ita yayi ta hanyar d'aga mata hannu"Karkice mani komai Lauratu indai akan wannan ne, domin zan iya jure duk wani abu da zan fuskanta indai a dalilinki ne, ko zagi ko duka koma miye ne ashirye nake dana d'aukesa duk tsanani kuwa"


Murmushi tayi domin kalamansa ba k'aramin dad'i sukayi mata ba a cikin rai


"Kayi alk'awari?" Ta fad'a tana mai duban fuskarsa cikin d'an k'aramin haskenda ke zuwar musu a bisa dakalin k'ofar gidan da suke zaune


"Aiko ban...


Bai k'arasa maganar tasa ba suka jiyo muryar Kabirun na k'walawa Lauratu kira daga bakin zaure inda yake tsaye.......Oni jama'a wai yau Maman Ja'afar ce d'auke da littafin soyayya anya kuwa zata iya? Waifa a k'aryarta har shafi sama da ashirin takeso tayi mana. Hmm kuzo dai mu bita tiryan-tiryan domin ganewa idanuwanmu abinda ke shirin faruwa, ni babban matsalata ma kar taje tayiwa mutane kwa6a domin bata ta6a yin irin wannan rubutun ba tunda ta fara yin rubuce-rubucenta.  *NICE TAKU*

*MAMAN JA'AFAR*

  +966592551785

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [23/05, 9:17 p.m.]

*💘SUNE SILA💘*


        4


Daga alkalamin 

MamanJa'afar✍Yau kam d'akinsu Lauratu basu tashi da gasarar yin koko ba, gashi Saminunma mai siyo kokon tunda ya tashi daga bacci yasa k'afa ya bar gidan har yanzu ko k'eyarsa basu gani ba


"Lauratu zo kar6i talatin d'in nan kije ki siyo wani abu kici, ko taliya ce tunda naga kina sha'awarta, karki tsaya jiran Saminu kije kuma ki makara a gurin aikin"


Cikin mamaki ta dubu mahaifiyar tata "Ammi wane aiki kuma bayan Hajiyar ta riga ta koreni?"


"Af nafa mantafa ban fad'a maki ba jiya nasamo maki wani aikin a Sabuwar tasha, kuma ga dukkan alamu matar zatayi mutunci"


Marairacewa tayi "Amma kuma Ammi shine tun jiyan baki sanar dani ba?"


"Yi hak'uri y'ar albarka nasanki da biyayya ne a dukkan abinda na umarceki, shiyasama banyi shayi wajen yanke hukunci akanki ba dukda kuwa ban nemi amincewarki ba, yi sauri ki siyo abinda zaki karya dashi d'in, ungoma hamsin d'in rike duka na bar maki" Ta fad'a fuska cike da fara'a, dama haka takeyi mata wannan sakin fuskar a duk lokacin da ta buk'aci wani abu agareta.


"Wai hayaniyar me nake jiyowa ne haka? ko yauma fad'an ne kukeyi kalar wanda kuka saba kullum?" Cewar Malam Harisu kenan yayinda yake zura takalma a k'afarsa ga dukkan alamu fita zaiyi


Cikin dariya matar tasa Tani ta dubesa tare da labarta mashi dukkan abinda ya faru jiya har zuwa sabon aikin da ta samarwa Lauratun


Malam Harisu Mutum ne da yazama kamar akwai kamar babu a gidansa, domin bashida wani kata6us a gidan nasa, matar tasa itace keyin jagoranci na dukkan wani abu daya shafi gidan, har jagorancin auren yayun Lauratun mata su biyuma duk itace tayi, bansan dalilinsa na yin hakan ba, shin talauci ne ya saka shi yin hakan ko kuwa asirin mallakar da aka dad'e ana yi masa ne ya jawo hakan? mai yiyuwa kuma haka zuciyar tasa take fankan fayau bamu sani ba.


Koda ta gama bashi labarin murmushi yayi kana yace"To Allah yasa ta zauna acan d'in idan taje, kinsan Lauratu ba daidai akeyi mata ba"


"Insha Allahu ma zata zauna Malam"


Kwano Lauratun ta zara tare da saka sabon hijabinta ta nufi hanyar gidan da ake sayar da abincin, sai dai kamin ta isa gidan saida ta biya ta gidansu Umar ( Dama na fad'a maku babu nisa a tsakaninsu)


Cikin sa'a kuwa ta samesa a k'ofar gidan nasu sai faman goge mashin d'insa yakeyi wanda hakan ya zame masa jiki akoda yaushe


"Yanzun nanfa nake k'okarin aiken K'awar taki gidanku" (Wato K'anwarsa Hadiza kenan) Abinda ya fad'a kenan bayan ya amsa sallamar abar k'aunar tasa


"Yau bataje makaranta bane?" Ta fad'a a tak'aice yayinda take y'an waige-waigenta sai kace wata 6arauniya, inaga tsoro takeji kada babban yaya yazo wucewa ya ganta anan gurin ne


"Kin manta yau asabar babu makaranta ne?" Shima ya mayar mata amsa a tak'aice


"Toda me zaka bata ta kawo mani?" Ta fad'a yayinda take murmushi tana jujjuya kwanonda ke hannunta


"Wasik'a ce dama na rubuta dan na sanar dake yanda mukayi da baba jiya sadda nayi masa maganarki"


Kamin ta basa amsa ne mahaifin nasa yazo wucewa ta gefenda suke tsaye


Durk'usawa tayi har k'asa cikin ladabi da biyayya ta gaisar dashi, shima fuska cike da fara'a ya amsa gaisuwar tata hardama k'arin shi albarka da yayi mata.


Nan take dai suka bawa junansu labarin dukkan abinda ya faru dasu a jiya da yamman


Labarin da Umar ya bata ba k'aramin girgiza ta yayi ba, domin hakan na nufin wata matsala zata iya k'ara kunnowa kenan a tsakaninsu bayan wacce ake ciki yanzu


"Karki damu Lauratu nidai babban fatana da rok'ona gami da addu'ata, ya kasance kin rik'eni daram acikin zuciyarki kamar yanda nima na rik'e ki a cikin zuciyata, idan har hakan ta faru to nasan duk wata matsala da zata iya biyo baya mai sauk'i ce" Ya fad'a tare da duban fuskar abar k'aunar tasa"Indai dan wannnan ne Umar karka samu damuwa, insha Allahu nida kai mutu ka raba, zan jure dukkan wani tsanani da matsi da k'uncin da zan fuskanta agida indai a dalilinka ne, kai kad'ai ne a cikin zuciyata daga kai babu wani, kuma akanka na rufe k'ofa insha Allahu koda kuwa bayan mutuwarka ne""Naji dad'in wannan furuci naki Lauratu ina rok'on Allah ya bamu damar cika wannan alk'awari da muka d'aukarwa junanmu kuma ya bamu hak'urin jurewa duk wata jarabawa da zamu fuskanta nan gaba"


"Ameen ya rabbi Angona" Ta fad'a tare da juyar da fuskarta gefe guda alamun jin kunya


Dariya yayi kana ya dubeta "Hmm har na tuna lokacin da kike sayar da gyad'a idan nace Lauratu amaryata, sai ki wani zun6uro baki kice mani, ni wallahi ba amaryarka bace shege d'an iska kawai, daga nan sai ki fara kuka ko?" Ya k'arashe maganar tasa yana dariya harda k'yak'yatawa


Da gudu ta bar gun tana dariya sai kace wata k'aramar yarinya 


"Idan kin gama cin taliyar kizo na kaiki gurin aikin ina nan ina jiranki" Ya fad'a da k'arfi domin ta riga ta fara yin nisa.


*********


Basu sha wahala sosai wajen gano shagon Hajiya Mariyar ba domin sananne ne a cikin Sabuwar tashar


Bayan sun gaggaisa ne Umar ya dubi Hajiyar "Dan Allah Hajiya ga amanar K'anwata nan a hannunki, ki kula da ita sosai dan Allah, idan tayi ba daidai ba a tsawatar mata domin har yanzu yarinya ce ita"


"Karka damu yaro insha Allahu zan kula da Lauratu tamkar y'ar da na haifa a cikina"


Da wannan sukayi bankwana Umar ya tafi gurin aikinshi itama ta fara nata aikin.


 ***********


_Bayan sati biyu_


K'ofar gida na hango Umar zaune akan mashin d'insa, ga dukkan alamu dai wani yake jira


Can bada jimawa ba na hango Mahaifinsa shima yana k'okarin shiga cikin gidan


"Baba" ya kira mahaifin nasa, juyowa mahaifin nasa yayi yazo dab da inda yake ya tsaya


"Hala maganar sirri ce ta motsa? Naga ka tsaya a k'ofar gida baka shiga ciki ba"


Marairaicewa Umar d'in yayi kana ya fara bayaninsa "Baba dama kan dai maganar ran nan ce ta Lauratu na kuma canza wata shawarar"


"To ina sauraronka mai sunan Baba wace shawara ka kuma canzawa?"


Cikin k'warin guiwa d'an ya dubi mahaifin nasa 


"Wai nace Baba mi zai hana ko gaisawa ne kaje kuyi da iyayen Lauratun dan su k'ara tabbatarwa da ba yaudarar y'arsu nakeso nayi ba? Inyaso daga nanma sai kuyi shawarar lokacin da ya kamata ace anfara maganar auren, irin nanda shekara biyu d'in nan haka ko d'aya da rabi ma, amma dai yanda ka gani Baba" Ya fad'a murya a marairaice tamkar mai shirin yin kuka


Shuru mahaifin nasa yayi alamun tunanin, can kuma ya lumfasa "Kaima kam tanan 6angaren ka kawo shawara mai kyau"


Dafa kafad'ar d'an nasa yayi kana yace "Karka damu mai sunan Baba insha Allahu cikin satin nan zanyi k'okari na nemi abokaina koda guda biyu ne sai muje mu gaisa dasu mahaifan nata, ammafa bazan 6oye masu komai game da sharudd'an da na gindaya maka ba, ka yarda? kasan ita magana ta aure ba'a cika son y'an 6oye-6oye"


Dariya Umar d'in yayi harda d'an wani tsalle da direwa"Na amince Babanda yafi Baban kowa" Sunanda yake kiransa dashi kenan aduk lokacin da yayi masa wani gagarumin abu na farin ciki


********


Zaune take akan turmi ta tasa tulin wankinta agaba sai faman duzarza takeyi, da y'ar k'aramar cocilarta wadda ta had'a da d'an kwalin da ke kanta ta daure domin ta ringa haska bokitin wankin saboda duhun dare daya fara shigowa


Lauratu kenan kullum batada lokacin yin wani uzuri nata na daban idan ba da daddare ba, kasancewar daga safe har zuwa yamma duk tana gurin aiki.


"Idan dai har Umar ya rayu to kowama ya mutu" Ya fad'a cikin alamu na zaulaya domin kirarinda yakeyi mata kenan idan yanason wani abu a gurinta


"Wannan maganar haka take yayana na kaina" Ta fad'a d'auke da murmushi a fuskarta, domin duk cikin danginta babu wanda yake k'aunar abinda take k'auna fiye da yayanta Zubairu, shiyasa itama ba k'aramin k'aunarsa takeyi ba


"Allah dai ya kaimu ranar bikin nan naku musha shagali, ranar dukda bana son babbar riga saina wataya a cikinta" Ya fad'a yayinda yake lode mata nasa tulin wankin a gefenta


"Haba, nifa nayi mamakin irin wannan fara'a taka ta yau haka, ashe dai da walaki wai goro cikin miya"


"Karki damu y'ar kanwata, had'a ki wanke mani kinji? ni kuma nayi maki alk'awarin insha Allahu a dukkan sallolina na gobe, sai nasako buk'atunki na alkhairi dake da habibinki Umar a ciki"


Bata san lokacin da wata dariyar farin ciki ta kubce mata ba "Idanko hakane bayan wankinma har da guga zan had'a maka kana kuma na feshe makasu da turare" Ta fad'a yayinda take k'okarin ajiye nata wankin gefe guda tana k'okarin jawo nasa


********


_Bayan sati d'aya_


"Kai yaro jeka cikin gidan nan dan Allah kace ana sallama da Malam Harisu kaji?" Cewar d'aya daga cikin mutanenda Malam Garba yazo dasu kenan


Bada jimawa ba yaron ya fito ya sanar masu da cewar yana zuwa.


 A cikin d'akin sa yayi masu masauki, kana kuma ya bawa Saminu umarni da ya kawo masu ruwa.


Bayan sun gama gaggaisawa ne suka gabatar masa da buk'atarsu na nemawa d'ansu Umar auren Lauratu amma nanda wani lokaci kad'an, anan ne mahaifin Umar d'in ya kwashe dukkan sharudd'an da ya gindayawa Umar d'in ya sanar masa.


Shuru Malam Harisu yayi alamun nazari, can dai ya lumfasa yace "To wannan maganar taku babba ce, amma dai bara naje na kira mahaifiyar yarinyar inyaso sai ayi komai a gabanta"


Kallon kallo iyayen Umar d'in suka farayi a tsakaninsu, a tunaninsu maganar maza me kuma ya kawo mace aciki?Hmm inaga basu san cewa talauci yasakashi sakarwa matar tasa dukkan ragamar gidan nasa ba.
 *Nice taku*

*Maman Ja'afar*

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [ 25/04, 2:23 a.m.]

*💘SUNE SILA💘*


        5


Daga alkalamin

MamanJa'afar✍Sallama tayi masu kana ta kutsa kai a cikin d'akin


Bayan sun gaggaisa ne suka k'ara jaddada mata buk'atarsu ta neman auren Lauratu, amma ba yanzu ba sai nanda wani lokaci


Gyara zama tayi kana ta fuskancesu cikin natsuwa


"Gaskiya naji dad'i sosai da baku 6oye mana komai game da yaronku ba, to amma sai dai wani hanzari ba gudu ba, mai d'iya mace yakamata ace anjira bawai shi namijin ajira shi ba, ko ba haka ba jama'a?" Ta fad'a yayinda take duban fuskokinsu d'aya bayan d'aya


Jijjiga kai sukayi alamar maganarta haka take


"Saboda haka maganar gaskiya mu yanzu mukeso mu aurar da d'iyarmu, idan Umar ya shirya ya fito ayi masu aure, idan kuma bai shirya ba to gaskiya kar ya k'ara zuwa gurin y'armu domin zaita yi mata yawo da hankali ne yana 6ata mata lokaci, a k'arshe azo shi bai aura ba kuma ya hana mai son aura aure, kunga kenan zai 6ata ruwa ne badan yasha ba, saboda haka maganar gaskiya kuyi hak'uri ku fad'a mashi ya dakata da zuwa gurin Lauratu haka nan har sai lokacin da ya shirya yin auren, idan kuma kamin lokacin Allah ya bata wani ta aura, shikenan shima sai muyi masa addu'a Allah ya basa wata madadinta" Ta daddage sai bayani takeyi dalla-dalla sai kace itace uban y'ar.


Jiki a sanyaye sukayi masu sallama suka kamo hanyar zuwa gida, amma basu daina jimami gami da tattauna irin tarbiyyar gidan nasu Lauratu ba."Waini Ammi me Umar d'in nan yayi maki ne haka kika tsanesa har haka da yawa?"Cewar Zubairu kenan wanda tun d'azun ya kasance raka6e a k'ofar d'akin yana sauraren dukkan abinda ke wakana


"Me kuwa yayi mani? Kawai dai dan yana d'an iska ne bana sonshi, kuma kaima kasan duk duniya anyi ittifaqin cewa duk wani aikin alfasha y'an aca6a suna kan gaba wajen aikatashi, tun daga kan sata, zina, caca, da dai duk wani abu daka sani na fasiqanci duk d'an aca6a yanayi, waye bai san hakaba?"


Zaro idanuwa Zubairu yayi tare da duban fuskarta "Amma Ammi kin tabbatar da hakan? karfa ranar gobe k'iyama a kiraki sheda ki rasa abin cewa"


"Fito fili kawai ka k'aryatani d'an banza kawai" Ta fad'a a fusace


"Kobaya ga iskancin nasama ai bazanso na k'arashe rayuwata a gidan haya d'iyatama ace tayi k'arashe rayuwarta anan ba, babban gurina tayi aure inda zata huta muma kuma mu huta"


"Aiko Ammi indai haka akeyi y'ar talaka ace bazata auri kowa ba sai mai kudi tabbas muma kam bazamu sami matar aure ba, tunda...


"Tunda uwarka ba, tashi kabani guri marar kunyar banza marar kunyar wofi"


Sumui-sumui Zubairu ya bar d'akin tare da yin Allah wadai da wannan irin hali na mahaifiyar tasu.


*********


Tun barowar mahaifin nasa gida da niyar tafiya nema masa auren Lauratu ya kasa zaune kuma ya kasa tsaye, jiran mahaifin nasa kawai yakeyi ya dawo domin jin irin amsarda iyayen nata suka bayar.


"A'a Mai sunan Baba yau baka fita aikin dare bane?" Uban ya fad'a lokacin da ya k'araso bakin k'ofar gidan inda Umar d'in yake zaune akan mashin d'insa fuskar mahaifin babu yabo ba fallasa


"Wallahi Baba yau ban fita ba, ina nan ina jiran naji yanda kukayi ne dasu" Ya fad'a tare da duban fuskar mahaifin nasa ganin d'azu ya fita cikin fara'a yanzu kuma gashi ya dawo sai a hankali


"Muje ciki nayi maka bayani" Uban ya fad'a a tak'aice


Cikin gidan suka rankaya, kai tsaye d'akin mahaifin nasa suka wuce, bayan sun zazzauna ne mahaifin nasa ya dubesa


"Kamar yanda dai nayi maka alk'awari nida abokaina munje nema maka auren Lauratu, to amma sai dai gaskiya anyi rashin sa'a domin iyayenta acikin wannan lokacin sukeso su aurar da d'iyarsu kai kuma gashi yanzu baka shiryama aure ba, bari dai in gajarce maka magana, a k'arshe dai iyayenta cewa sukayi kadaina zuwa gurin y'arsu domin karka hana maison zuwa neman aurenta zuwa idan yana ganinka da ita....


Katse mahaifin nasa yayi cikin alamu na rud'ewa "Wai Baba hakan na nufin anrabani da Lauratu kenan kwata-kwata ko kuwa dai yaya abin yake?"


Jingina Mahifin nasa yayi a jikin bangon d'akin kana ya dubesa "Hak'urifa ya kamaka Umar, dole ka hak'ura ka bar masu y'arsu tunda baka shiryama aure yanzu ba, koni ne nan Mahifinta iya hukuncin da zan iya yankewa kenan akanka"


"Gaskiya Baba bazan iya rabuwa da ita ba, haba dan Allah wallahi kwata-kwata a wannan hukuncin babu batun adalci aciki, dame akeso mutum yaji ne wai? wannan irin bala'i haka sai kace a mafarki" Yana magana tamkar mai shirin yin kuka, domin lokaci guda duk ya fita hayyacinsa"To ai sai kaje kaci gaba da zuwa gurin nata, tunda soyayya ta rufe maka ido har kana neman mantawa da mutuncinka da kuma namu iyayenka, tashi ka bani guri, d'an Laila Majnun d'in uwa"


Sumui-sumui Umar d'in ya bar d'akin mahaifin nasa ya nufi k'ofar gida jiki a sanyaye, tunani fal a cikin zuciyarshi, uwarma nata k'wala masa kira akan yazo ya kar6i abincinsa na dare amma ko waiwayowama baiyi ba.


********


"Ke yar tasha! kawo mani shinka da miya na d'ari da hamsin" Cewar wani d'an Bunburutu kenan wanda yake zaune acikin shagon cin abincin yana jiran nasa shima, ta dad'e y'an tashar suna kiranta da sunaye kala-kala, tun tana damuwa akan hakan tana fad'awa Ammi, har dai ta kai ga ta saba domin babu wani mataki da aka d'auka ko kuma ake shirin d'auka akan hakan, a k'arshema Ammin cewa tayi bata san surutan banza marasa ma'ana.

 

Cikin sauri Lauratun ta harhad'a masa abincin ta kawo masa domin tasan halinsa sarai ba mutuncin kirki ya cika ba


Aje abincin nata keda wuya d'an Bunburutun ya mik'o hannu sururuf da niyar ta6a wani sassa na 6angaren jikinta


Da ranta ya 6aci kuwa batasan kokacin da ta suri abincin dake a hannun nata ba ta antaya masa a jiki


Gaba d'ayan kayan jikin nasa kuwa saida suka 6aci, yaji kuwa har a cikin idanuwansa bayan k'onewa da yayi a k'afa


"Banza kawai d'an akuya masu lalata yaran mutane, toni ba irin y'an matan nan bane da kuka saba maidawa tumakai kuna dabbanci tare dasu ba, koda ka ganni anan nasan mutuncin kaina bawai ban sani ba ne a yanda wasunku suke tsammani" Ta fad'a hannu dafe a k'ugu tamkar mai shirin yin danbe


Bai yi wata-wata ba kuwa ya wanka mata wasu lafiyayyun mari har guda biyu akan kuncinta


Rarumo marfin tukunya tayi da niyar kwad'a masa aka, kana uwar aikin nata ta lura da abinda ke shirin faruwa, domin ita tana harabar gurin ne inda ake yin girke-girke shiyasa bata lura da abinda ke faruwa a cikin shagon ba


"Yaya dai? Lauratu ya haka meke faruwa ne?" Ta fad'a yayinda take nufo cikin shagon


Tana kuka take mayarwa da uwar aikin nata abinda ke faruwa


"Keko Lauratu daga wasa me kuma yayi zafi hardasu zage-zage inbaya ga rashin wayo irin naki wanda kika saba?"


"Ai Hajiya da kin bari na koya mata hankali wallahi, banza kawai y'ar tasha, karuwa, ko kin zaci bamu san komai bane game dake? kawai dai ana fakewa da sayar da abincin ne amma ba abincin kawai ake sayarwa ba ana sayar da wani abincin ne na daban, ko dan kin d'aukeni gaula na taya kike tunanin kamar ni baho ne bansan komai ba?" Yana magana yana wani huci tamkar ya samu wani k'ato d'an'uwanshi suna karawa 


Dama wannan bashi ne karo na farko da masu sayen abincin sukeyi mata irin wannan cin kashin ba, kawai takan daure ne tana barin abin acikin zuciyarta domin kota fad'a a gida ba wani mataki za'a iya d'auka akan hakan ba, amma duk a ciki wannan daya faru na yau shiyafi k'ona mata rai.


Cikin kukan take mayar masa da amsa domin duk acikin kalaman duniya na cin fuska da kuma cin mutunci tafi tsanar wanda za'a kirata da karuwa


"Wallahi niba karuwa bace, karuwa na gida ka baro a zaune, kuma insha Allahu bazaka gama rayuwarka ba sai kaga karuwa a cikin danginka" Masifa kawai Lauratun ke faman zubawa danko sauraren Hajiyar da ke bata hak'urima batayi ba


"Wai dama haka kike da shegen taurin kan tsiya Lauratu? Ya inata magana ko sauraratama kin k'i yi? Gaskiya wannan halin naki bazan iya dashi ba, a k'ara gaba, dan idan kina haka ai wata ranma nemar masu sayen abincin zanyi na rasa"


Lauratun batace mata komai ba saima figar hijabinta da tayi ta k'ara gaba.


*****


Tafiya takeyi amma hawaye bai daina safa da marwa akan fuskarta ba, tunani takeyi a cikin zuciyarta wai yaushe iyayenta zasu farga ne su fara tunanin kare mutuncinta? A hakan ana yi mata d'aukar karuwa suke tunanin wani mai kud'i zai iya fitowa da niyar neman aurenta? A tunaninta ai bama mai kud'i ba ko talakkanda yasan mutuncin kansa kuma yake k'okarin nemawa y'ay'ansa uwa ta gari bazaiyi tunanin za6arta a matsayib uwar y'ay'ansa ba, zuwanta gurin aikin nan ta had'u da mutane kala-kala amma dukkansu babu wanda ya ta6a yi mata tayin aure sai dai tayin lalata, koma a ganinta ba komai ya kawo hakan ba sai dan ganin yanda take gararanba acikin tasha ne tamkar wata marar

galihu


Umar shi kad'ai ne wanda yaji ya gani ya kuma k'aunaceta a wannan halinda take ciki batare da tunanin komai ba, to Umar d'inma gashi ana neman yi mata katangar k'arfe dashi, wai shin haka rayuwarta zataita tafiya ne a cikin bak'in ciki da kuma k'uncin rayuwa? Da wannan tunanin tayiwa kanta alk'awarin insha Allahu duk duniyar nan babu wanda ya isa ya hanata auren Umar, saidai wata gagaruwar qaddara daga cikin qaddarorin da Ubangiji ya tsara mata, domin Umar shine gatanta anan gidan duniya kuma shitake fatan yazamo sila ta ingantuwar rayuwarta.


********


Bata samu mahaifiyar tata a gida ba kuma ga yunwa ta kwaso, gashi a gajiye take bare tayi k'okarin d'ora wani abin taci, shiyasa tace bara ta nufi gidansu K'awarta Rukayya kota samu d'an wani abun ta6awa acan.


"Uwani dan Allah idan Ammi ta dawo ki fad'a mata naje nan gidansu Rukayya" ta fad'a yayinda take k'okarin fita daga cikin gidan, dayake Hafsatu Mamansu Umar bata nan shiyasa ta bawa kishiyarta sak'on dukda ba wani shirin kirki sukeyi ba


"Adawo Lafiya" Ta fad'a a fili a cikin zuciyarta kuwa tana mai k'ok'onton inda Lauratun zata tafi, domin itama tana daga cikin y'an jam'iyar da ke ganin duk wata mace wadda ke harkar sayar da abinci a waje batada maraba da karuwa.*******


"Salamu alaikum" Cewar Lauratun kenan bayan ta shiga gidan nasu Rukayya wacce ta kasance aminiya a gareta, da gidansu da kuma gidansu Rukayyar babu wani nisan kirki a tsakani dama.


A barandar tsakar gidan ta samu Rukayyan ita da mahaifiyar tata su shinfid'a k'atuwar tabarmar roba, sun tasa wani littafin larabci a gaba, ga dukkan alamu karatu ne uwar take koyawa y'ar tata, ajiyar zuciya tayi kana a zuciyarta tace" Inama ace nice haka zaune nida Ammina take koya mani karatu cikin farin ciki da k'aunar juna?"


Tabbas rayuwar gidansu Rukayya ba k'aramin burge Lauratu takeyi ba, domin zama ne iyayen sukeyi na fahimtar juna tsakaninsu da y'ay'ayensu da kuma k'aunar juna, wani lokaci ma idan suna wani abin kai kace K'awa da k'awa ne ba y'a da mahaifiya ba, kai tsaye suke tunkarar junansu da shawara babu wani shamaki ko d'ari-d'ari


Ita kam tunda take a rayuwarta zata iya cewa hakanan babu dalili wasa da dariya bai ta6a shiga tsakaninta da Amminta ba, ko a kusa da itama bataso ta zauna bare akai ga maganar wasa da dariya ko shawara da dai sauransu, duk inda zakaga Lauratu acikin gidansu to a raka6e zaka ganta tamkar wata marainiya.


"A'a yau su Lauratu ne a gidan namu?" Cewar Mahaifiyar Rukayyar kenan cikin sakin fuska


Bayan sun gaisa ne Innar ta dubi Lauratu "To ai sai ki gyara zama kema ayi karatun dake ko?"


"Ehto hakane Inna, amma dai kamin hakan yunwa nakeji tukun" Ta fad'a yayinda ta nufi kicin kai tsaye domin batada shamaki na ko ina a cikin gidan


"Acici, ke kullum cikin jin yunwa kike sai kace wata mai fama da Olsa" Cewar Rukayyar kenan cikin zaulaya


Saman tabarmar ta dawo ta zauna tana sauraron karatun nasu bayan ta zubo abinci


"Yauwa kuna jina ko?" Cewar Innar kenan yayinda take duba littafin dake a hannunta


"Muna jinki Innarmu" Lauratu ta fad'a a tak'aice yayinda take kai lomar Danbun a bakinta tana korawa da ruwan Sabuwar Randa mai sanyi


Innar taci gaba dayi masu bayani kamar haka


1 Mace takan fara haila ne daga shekara tara, amma idan taga jini kamin cikar wad'annan shekarun to jinin ciwo ne bana haila ba, amma da yawan mata suna haura hakan kamin su fara"


2 K'arancin kwanakinda jini zai iya tsayawa mace sune kwana d'aya, amma idan ya gaza hakan to shi ake kira jinin ciwo


3 Kwana goma sha biyar mace take gama hailarta gaba d'aya, idanma bai kai hakan ba ba laifi bane, (wasu suna kwana uku su gama, ko sati ko kwana goma, ko har dai zuwa sha biyar din) amma idan ya wuce kwana sha biyar to ya zama jinin ciwo


4 Kamin mace ta sake yin wata hailar tsakanin wata hailar akan samu tsawon kwanaki goma sha uku ne a tsakani, idan kuma jini yazo mata kamin cikar kwana sha ukun shima jinin ciwo ne zamu kirasa


5 Mata suna gane daukewar jininsu ne ta ganin farin ruwa agabansu ko kuma bushewar farjin nasu


6 Idan jinin haila ya daukewa mace ko bai kai kwanakinda takeyi ba dolenta tayi wanka taci gaba da ibadunta.


Ajiye littafin Innar tayi kana ta dubesu"To anan zamu dakata kuma sai zuwa gobe idan Allah ya kaimu sai mu ida hukunce-hukuncen jinin hailar harma mu shiga cikin hukuncin jinin haihuwa idan Allah yaso"


"Inna ai bamuyi jinin ciwo ba ko?"Cewar Rukayyar kenan yayinda take duba littafin hannunta


Murmushi Lauratu tayi "Dukda ba'a dad'e ana yin karatun dani ba har naso nafiki fahimtarsa, Inna ai hukuncin jinin hailar tare dana ciwo kike tafiyar mana dasu ko?"


Murmushi Innar tayi"Yauwa y'ar gari ashe kin gane kan karatun kenan?"


Saida Lauratun ta faki idon Innar kana tayiwa Rukayya gwalo.Mik'ewa Innar tayi ta barsu anan zaune ko da zasu tattauna wani abu na daban wanda ya shafesu.


"Nasan dai mak'asudin zuwanki nan gidan bai wuce aike wajen Umar ba ko? kuma ba zuwa zanyi ba wallahi tunda har kikayi mani gwalo dan ban gane karatu ba"


"Haba Aminiyata yi hak'uri na daina kinji?" Ta fad'a tare da marairaicewa kamar zatayi kuka"Ammafa yau kun dawo da wuri, bayan kuma naga ba yanzu kuke dawowa ba, ko yau abincin naku ya k'are da wuri ne?"


"Inafa ya kare" Nan take ta kwashe duk yanda sukayi a gurin aikin nata ta labarta mata


"Allah dai ya karo k'arshen wannan lamari naki Lauratu" ta fad'a a tak'aice cike da tausayi


"Yauwa dan Allah taimaka mani zakiyi na d'an aikeki wajen mutumin nawa dan Allah, anjima gurin k'arfe biyar na yamma nasan yana gida a lokacin, dan Allah ki fad'a masa mu had'u a nan gidan bayan Magariba ina son ganinshi kinji Aminiyar?"


"Gaskiya tsoro nakeji, kemafa kinsan Ammi ba son zuwanki gidan nan takeyi ba, kuma babban dalilin shine dan karki had'u da Umar"Marairaicewa tayi "Dan Allah ki taimaka mani Kawata idan baki taimakeni ba wa zai taimakeni? Ai zafin sai yayi mani yawa kuma"


Da k'yar dai ta samu ta shawo kanta ta amince......*Maman Ja'afar*

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [23/04, 5:40 a.m.]

*💘SUNE SILA💘*


        3


Daga alkalamin 

MamanJa'afar✍
"Lafiya na ganki kinata faman wani raka6e-rakabe sai kace wata tsohuwar munafuka?" Cewar Ammin kenan yayinda take lillinke kayanda ta shanya a saman igiyar tsakar gida


"Tunda naga kina kuka nasan wata tsiyar kikaje kika k'ullo, fad'a mun me kuma ya faru? Ni wallahi narasa gane kanki Lauratu, kullum ke bakyason ganina cikin farin ciki, daga wannan matsalar sai wannan anya kinaso ki gama damu lafiya kuwa?"


Kukanta ne ya k'ara tsananta domin ta tsani jin irin wad'annan kalaman da suke fitowa daga bakin mahaifiyar tata


"Ina tambayarki kinyi mani shuru, nace me kuma ya faru?" Ta fad'a da tsawa


"Dama..Dama Hajiya ce ta koreni" Ta fad'a murya na rawa


"Dama ba dole ta koreki ba wancen tsinannen yaron ya sakaki agaba, ji nayima ai ance duk rana kusan sau goma yake zagayawa gurin aikin naki, ai sai kizo ki zauna a gidan muna ririri da rarara tsakanina dake" Tana gama fad'ar haka ta shige d'aki abinta tabar Lauratun nan tsaye a bakin k'ofar d'aki."Kiyi hak'uri Lauratu wata rana sai labari kinji? babu wani yanayi mai zama din din din, inma tsanani ko sauk'i, farin ciki ko kuma bak'in ciki, share hawayenki kinji? bara na kawo maki abinda na dafa kici, nasan Gero da wake yana d'aya daga ciki abincin da kikafi so shiyasa da nayi nace bara na ajiyewa Sirikata"


Murmushi Lauratun tayi tare da duban Hafsatu d'aya daga cikin matan gidan nasu kenan wacce ta kasance tana lura da duk wani bakin k'unci da kuma halin k'unci da Lauratun take ciki


"Nagode Hafsatu da irin kulawarki agareni, Allah ya raya mana su Umar"


"A'a abin kuma harda son kai? bazakice Allah ya raya su Husna ba sai kice su Umar?" Ta fad'a tana dariya duk dan ta kwantar mata da hankali


"Nikam Hafsatu indai Umar ya rayu a duniya ai kowama kar ya...


"Wato mu mutu tunda bama k'aunar Umar ko? Ai gaki ga Umar d'in naga ta yanda za'ayi ki aureshi muddin ina raye"


Cewar Mahaifiyar tata kenan wacce tazo wucewa ta bakin k'ofar dakin Hafsatun saye da hijabi, ga dukkan alamu fita zatayi.


Babu wanda yace mata uffan daga cikinsu saima binta da kallo da sukayi.


**********


Kamar dai kullum yauma gurin cike yake da jama'a, amma dukda haka saida Ammi ta ratsa ta cikin mutanen har ta samu isa inda Hajiyar take zaune akan dogon bencinta tana kar6ar kudi.


Hajiyar na hangota ta had'e rai ta murtuke fuska domin tasan kwanan zancen bai wuce ban hak'uri akan korar Lauratu da tayi ba.


Washe baki Ammin ta fara yi kana daga bisani ta samarwa kanta matsugunni a gefen da Hajiyar take zaune


Gaisawa sukayi fuskar Hajiyar babu yabo kuma babu fallasa kana daga bisani Ammin ta dubi Hajiyar wacce taketa faman lissafa kud'i abinta


"Am Hajiya nace kaddai agaji damu, wannan karonma dan Allah a k'ara hak'uri wallahi harda yarinta ke damunta, yo inba yarinta ba ka dinga wulak'anta hanyar da take rufa maka asiri...


Katseta Hajiyar tayi"Kinga Tani wannan karon dai ina ganin sai dai kuyi hak'uri domin bakin alk'alami ya riga ya gama bushewa, aiki kam da Lauratu bazan sakeyi ba, Allah ya bata wani a gaba" Tana gama fad'ar haka ta mik'e abinta ta shigewarta shago tabar Ammi nan zaune inda take baki sakatooo.


**********


DA YAMMA


Umar ne na hango durk'ushe agaban iyayensa cikin ladabi ya tasasu agaba sai faman sosa k'eya yake tayi.


"Mai sunan Baba lafiyarka kuwa? kace kana son magana damu, munyi shuru kuma muna saurarenka ka tsaya sosar k'eya kodai bakada gaskiya ne?"


Cewar Mahaifinsa kenan Dattijon arziki Malam Garba


Murmushi Umar d'in yayi kana yaci gaba da sosa k'eyar tasa "Am dama Baba akan maganar Lauratu ne(Dayake mahaifan nasa sun dad'e da sanin irin soyayya da kuma shak'uwar dake tsakaninsu tun suna yara)"


"Um ina jinka, sai akayi yaya na Lauratu?" Uban ya fad'a cikin alamu na zaulaya


"Baba dama iyayenta ne..sukace wai na..na turo magabatana akan.. akan maganar auren namu" Yana magana baki na rawa sai kace wanda aka kama yayiwa sarki k'arya


Dariya mahaifin nasa yayi kana daga bisani ya dubi matar tasa wacce ta kasance uwa ga Umar d'in kenan Baba Lami, itako tayi wani kicin-kicin da fuska sai kace an aiko mata da sak'on mutuwa


"Nikam ka dubeni? Ai wannan maganarku ce, ni ta 6angarena kam bazan amince ina ji ina gani d'ana namiji tilo da na mallaka yaje ya kwaso iri daga wannan gidan marar tarbiyya ba"


"Ai kamin ma akai ga wannan kai Mai sunan Baba bari in tambayeka?"


Cikin marairaicewa da kuma jin zafin kalaman mahaifiyarsa ga abar k'aunarsa yace "Ina jinka Baba"


"Wai shin da kake maganar aure dame dame ka shiryawa auren ne? Kanada gidan da zaka ajiyeta? Ko kuwa kana nufin mashin d'in hayar ne zai isheka ka ciyar da ita da yaran da zaku haifa nan gaba? Da wane kud'in zaka biya haya kuma ka biya balans kana ka cida iyalanka? Umar kayi tunani mana, ko kana nufin ni zan d'auke maka dukkan wannan nauyin? Kaima kasan bazan siyar da Akuya ta dawo kuma tana cimani Danga ba


Shuru Umar d'in yayi na d'an wani lokaci alamun nazari, domin tabbas magan-ganun Mahifin nasa haka suke babu kuskure a ciki, kuma dama shima ya hango hakan tun kamin ya tunkaresu


"Nifa Malam koda wad'annan sharudd'an da ka gindayo masa sun cika bafa amincewa zanyi da auren wannan gantalalliyar yarinyar wacce ta k'are rayuwarata a gindin karuwai ba, ga y'aya' nan na mutunci ako ina yaje ya nema mana"


"Ke dalla rufewa mutane baki, dan tana gindin karuwai kuma sai akace maki itama karuwarce? Haba ku mata meyasa bakuda tunani ne wani lokacin? yandafa Umar yake d'a a wajenmu itama haka takeda iyaye, kuma yanda muke sonshi haka itama iyayenta suke k'aunarta, talauci da kike gani Lami babu abinda baya sawa, wasumafa har fitar dasu daga cikin musulunci yakeyi, saboda haka ahir d'inki kar na kuma jin wannan maganar daga yau, mudai tunda Allah ya bamu wadatar zuci to mu gode masa kawai, su kuma wad'anda bai bawa ba muyi masu fatan shiriya"


Juyowa gurin Umar d'in yayi wanda zuwa wannan lokacin zufa ta riga ta gama jik'e shi sharkab


"Kai kuma abinda nakeso da kai, kaje ka cika dukkan wad'annan sharudd'an da na gindayo maka, idan ka tabbatar sun cika ni kuma nayi maka alk'awari insha Allahu da kaina zanje nema maka auren Lauratun, tashi ka bani guri.********


Daga gun Hajiya Ammi bata zame ko ina ba sai a Sabuwar tasha gurin wata mata mai sayar da abinci


Saida ta jira matar ta gama sallamar mutanenta kana suka sami damar gaisawa


"Saidai kiyi hak'uri baiwar Allah ban wayeki ba?"


Murmushi Ammin tayi "Gaskiya kam baki sanni ba, domin yau na fara zuwa nan"


"Allah yasa dai lafiya?" Matar ta fad'a a tak'aice


"Lafiya kalau Wallahi dama yarinya ce y'ar budurwa haka nake da ita, to shine nazo tambaya ko kinada buk'atar mai kama maki y'an aikace-aikace?"


Shuru matar tayi na d'an wani lokaci kana kuma daga bisani ta dubu Ammin


"Yarinya babba ce ko k'arama?"


"Ehto, ina tsammanin dai da kad'an waccen mai wasa da d'an saurayin can zata fita" Ta fad'a tare da nuna d'aya daga cikin ma'aikatan matar da d'an yatsa


"Ah indai hakane ai zata iya, ki turo ta babu matsala" Ta fad'a fuska d'auke da murmushi, domin mafi yawancin masu sayar da abinci suna buk'atar y'an mata masu jini a jika a gurin sana'arsu, koba komai sa jawo masu kwastomomi


"To nagode nagode Hajiya Allah ya saka da Alkhairi"


Har ta mik'e zata tafi tace "Am Hajiya nace albashin duk wata ne kuke biya ko kuwa kullum ne?"


"Kullum ne muke biya saidai bana ce maki ga abinda zan dinga bata ba sai tazo d'in dai munga kamun ludayin aikin nata tukun"


"Ai Hajiya yarinyar tawa akwai hazak'a, indai aiki ne Lauratu badaga nan ba"


Nan dai sukayi sallama Ammin ta kamo hanyar gida.


****

A wannnan ranar dai haka Umar da Lauratu sukayi kwanan bak'in ciki, domin kowa abinda yake sak'awa zuciyarshi daban


Sai dai dukkansu sun yake shawarar gobe insha Allahu zasuyi k'okarin had'uwa domin samawa kansu mafitar wannan babban al'amari dayake k'okarin tunakarosu.Hmmmm za'a fara Chakwakiya kenan? Muje zuwa masu karatu wai mahaukaci ya hau kura.*Maman Ja'afar ce*

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [26/04, 9:57 p.m.

*💘SUNE SILA💘*


       7


Daga alkalamin 

MamanJa'afar✍Da dai Ammin ta lura Lauratun batada niyar bin umarninta wannan karon kuka ta saka wiwi, tana kukan tana kiran


"Oni! Jama'a yau naga ta kaina, yaya akeso inyi da rayuwata ne? sunan kawai na haihu ne amma har yanzu nidai haihuwar banga wata ranarda tayi mani ba, haihuwa babu huce takaici ina amfaninta saboda Allah da Annabi? Su wad'annan yan'uwan naki maza babu tausayi, kema macen da nake ganin zaki rufa mani asiri abinda zakiyi mani kenan?""A'a lafiya, meke faruwa ne haka?" Yaya Kabiru ya fad'a yayinda yake k'okarin kutso kai a cikin d'akin inda mutanen gidan sukayi dafifi a k'ofar dakin suna kallon diramar da akeyi, wasunsu hak'uri suke bayarwa yayinda wasunsu ke Allah wadai da irin wannan hali na Tani da tak'i sakarwa yarinya mara tayi fitsari sai kace itace babban d'a a gidan.


Cikin kukan Ammin ke mayarwa da Kabiru labarin abinda ke faruwa


Ba komai bane ya tadawa Kabiru hankali duk acikin abubuwanda suka farun face ganin hawaye shar6e-shar6e a fuskar mahaifiyar tasu, ai kuwa baiyi wata-wata ba ya zare Belt d'in jikinsa ya fara labtawa LauratunTun Lauratu na kukan neman d'auki da agaji har dai jikinta yayi lak'wasa ta gaji ta daina


Ganin hakan nema yasa Ammi ta samu ta kwaceta da k'ayar a hannun Kabirun


"Wannan irin duka Kabiru kasheta kakeso kayi ne?" Ta fad'a yayinda ta k'wace Lauratun daga hannun Kabirun


"Ke d'in banza ke d'in wofi, har kinma isa kice zaki saka mahaifiyarmu kuka? Wallahi da dai Ammi tayi kuka a dalilinki gara ke ki kwana kina yin kukan jini" Yana magana yana huci tamkar wanda yayi danbe da wani k'ato ya gaji.


********


Washe gari tun safe Lauratu ta nufi d'akin yayun nata saboda buk'atarta ta son ganin Yayanta Zubairu.


Kamar kuwa yanda ta tsammata shi kad'ai ta samu kwance a d'akin, ga dukkan alamu ma ko sallar asuba bai samu yayi ba.


Da k'yar ta samu ta tasheshi a wannan asararren baccin da yayi nisa a cikinsa.


"Waike lafiya kikazo kina damun mutane? Yanda kika ganni d'in nan ziro na nake idannma neman kud'in taliya kikazoyi" Yana magana da murya irinta wanda aka datsewa baccin nan al halin bai gaji dashi ba


"Idan mutum yace zaiyi maka kyautar riga, ai tashin farko ta jikinsa ya kamata ace ka fara dubawa tukun, kai d'inma nasan yunwar kakeji bakada kud'in siyen abincin bare kuma nazo maka da tawa buk'atar, yaukam aini ba maganar cin taliya tunda nadaina biyawa Ammi buk'atunta"


Canza akalar zancen tayi"Yanzu dai zuwa nayi ka kaini islamiyyar can ta K'ofar dur6i dan Allah idan kanada lokaci"


"Amma gaskiya kinyi tunani mai kyau wallahi da kikace zaki shiga makarantar islamiyya, sai dai wani hanzari ba gudu ba, ina kike ganin zaki samu kud'in siyen fom dana littatafai da kuma su kayan makarantar kansu?" Ya fad'a yayinda yayi mata k'uri da idanuwa yana jiran amsarda zata bashi


Shuru tayi alamun nazari domin maganar Yayan nata Zubairu gaskiya ce yake fad'a"Dole ana buk'atar kud'i kamin na zama d'aya daga cikin dalilanda suke zuwa makarantar islamiyya, to amma ina zan samu kud'in kenan?"


Cikin k'warin guiwa ta dubesa"Kasan miye Yaya Zubairu? Bara nayi k'uru kawai naje na tambayi Ammi mai yiyuwa na samu koba yawa"


Murmushin k'eta yayi"To Allah yasa a dace" Ya fad'a tare da gyara kwanciyarsa domin yasan ba lallai ne adace d'in ba


"Wai Yaya kamayi sallar asuba kuwa?" Ta fad'a yayinda takai bakin k'ofar d'akin zata fita


"Kabarinmu d'aya ne da zakiyita bincikata ibaduna, ina ruwanki?"


"Maida wuk'ak'en, Allah ya baka hak'uri, bani na kashe zomon ba rataya aka bani" Ta fad'a yayinda ta ida ficewa daga cikin d'akin.


********


Tun lokacin da Lauratu tace bazata sake zuwa gurin aiki ba suke zaman doya da manja ita da Ammin nata


Yanzunma kawai dai tayi k'uru ne tazo neman kud'in amma bata tunanin zata samu abinda tazo nema d'in.


"Wai nace Ammi ko zan samu dubu biyu a gurinki na d'an sayi kayan makaranta da kuma littatafan zuwa islamiyya?" Tana magana amma gabanta na dukan tara-tara tamkar irin wacce taje yin maula d'in nan


"Ita makarantar allon kuma har wasu kaya ake d'inka mata da kuma ware kud'i domin biyan kud'inta?" Ta fad'a yayinda take ci gaba da yin tulin wankinda ke gabanta, ga dukkan alamu wankau ne aka kawo mata daga mak'wabta


"Ammi bafa makarantar allo nake nufi ba ta islamiyya nake nufi?"


"Au wai makarantar y'an izala kike nufi zaki fara zuwa kuma? A lallai Lauratu abin naki ya fara yin k'amari, yo in baya ga iskanci me akeyi a makarantar y'an izalar? Muna nan labari yake samun mu ana cewa Malaman nasu inbaya ga lalata babu abinda sukeyi da y'ay'an jama'a, inka gansu kamar wasu na Allah da Annabi amma acikin zuciyarsu Allah kad'ai yasan abinda suke aikatawa, ko rannanma naji an.....Matsanancin kukan da Lauratun ta rushe dashi ne yasa ta datse maganar tata batare data k'arasa inda takeso ba


"Haba Ammi! Haba Ammi! waini miyasa kikeyi mani haka ne? Duk wani abinda nakeso ke a gurinki iskanci ne da kuma lalata? ban ta6a cewa ina son abu ba kika saka mashi albarka, kullum ke cikin Allah wadai kikeyi da dukkan lamurranda suka shafeni, anya Ammi kinaso rayuwata tayi albarka kuwa?" Tana magana tana kuka abin tausayi, ga dukkan alamu halayen Ammin nata sun fara kaita k'arshe


Dariya Ammin tayi"A'a daga fad'ar gaskiya sai cibi ya zama k'ari, k'ari kuma ya zama k'ababa? To yanzu dai banida kud'in da zan iya baki tunda kina gani dai da idanuwanki banma gama wankinba bare har akawo mani kud'in na d'auka na baki, ina shikenan ko?"


Jiki a sanyaye Lauratu ta baro bakin kwatar inda Ammin nata takeyin wanki ta dawo tsakar gida ta samu kujera y'ar tsugunno ta zauna ta had'a hannayenta duka biyun a kuncinta ta buga tagumi, ga dukkan alamu tunani ne ke addabar zuciyarta


Tunanin inda zata samu kudin shiga makarantar shiyafi tsaya mata a rai, shin babanta zata jira ya dawo daga gurin gadinda yakeyi ne ta tambayesa, ko kuwa gurin Umar zata nufa? Tunaninta yafi rinjaye ne akan tafiya gurin Umar domin babanta tasan kota tambayesa amsar da ya saba bata kullum itace zai bata, wato "Muda bamyi karatun ba gani kikayi mun mutu? karatu a wajen d'iya mace idan ya wuce na salla ai sai taje gidan mijinta tanayi masa kallon kwal da kobo" Kullum amsarda mahaifin yake bata kenan idan tayi mashi zancen karatu.


*******


Saida ta bari yamma tayi lokacin da yake dawowa gida domin yin wanka kamin ya sake fita ta nufi k'ofar gidan nasu


Bata sameshi a k'ofar gida ba kamar yanda tayi tsammani, wannan dalilin nema yasa ta samu yaro ta aika a cikin gidan nasu akan cewa idan an tambayesa yace baisan ko waye ba


Cikin mintinan da basufi uku ba sai gashi ya fito, jikinta yayi sanyi matuk'a yanda taga Umar d'in duk ya wani fad'a ya rame sosai


Murmushi ya sakar mata tare dayi mata sallama


Bayan ta amsa ne ya dubeta"Naso naji dad'in ganinki a daidai wannan lokacin, sai dai kuma abin takaici banji dad'in ganin naki ba"


Cikin mamaki ta dubesa "Kamar yaya bakaji dad'in ganina ba? bansan inda maganarka ta dosa bafa"


"Ba sai na tsaya yi maki wani dogon sharhi akan dokar da aka gindaya mana ba Lauratu, yanzu ke a tsammaninki me kike tunanin zai iya faruwa idan iyayena suka san kece kika aiko kirana? Me kuma kike tsammani idan wani daga y'an gidanku ya ganki anan tsaye tare dani? Ya kamata muyi hak'uri mubi komai a hankali kamin zuwa lokacin da Allah zai yanke mana wannan wahalar"


Shuru tayi batare data bashi amsar komai ba, amma a cikin zuciyarta gasgata magan-ganunsa takeyi


"Lauratu ina sonki kuma ina k'aunarki, saboda haka ni a gurina dana ganki da karna ganki babu wani abu da zai iya canzawa daga cikin sonda nakeyi maki, ko soyayya a idanuwan mutane take ne?" Ya k'arashe maganar tasa yayinda yake duban fuskarta alamun amsa yake jira


Jijjiga masa kai tayi alamun amsawa kana ta d'ora dayi masa bayanin takamaimen abinta ya kawota gurin nasa


Murmushi yayi tare da saka hannu a cikin aljihu "Allah ya taimakeki ban riga nakai kud'in zubin Adashi ba, da nima fankan fayau zaki same ni" Ya fad'a yayinda yake mik'a mata dubu ukun da ya zaro daga cikin aljihun nasa


Kar6a tayi da hannayenta guda biyu cikin ladabi tare dayi masa godiya "Wai dama kana adashe ne ban sani ba Umar?"


"Ba dolena nayi adashe indai inason mallakar kyakkyawar yarinya irinki ba? Adashe mukeyi kuma d'auka dubu d'ari uku ne, dasu nakeso na sayi fili da kuma sabon mashin, kinga idan nayi haka bana fara cika sharudd'an da aka gindaya mani ba a gidajenmu?" Ya fad'a tare da duban fuskarta yana murmushi


Itama murmushin tayi tare da jinjinawa irin wannan so da k'auna da Umar yake nuna mata


"To kuma gashi na rabaka da kud'in zubin naka na yau gaba d'aya"


"Karki damu yanzun nan zan sake fita ai, kuma gobe idan na fita ba maganar dawowa gida sai na had'osu duka da zubin yau da kuma na goben insha...


"Ga Yaya Kabiru can na hango kuma ga dukkan alamu tanan zaibiyo, na shiga uku yaya zanyi Umar? ta fad'a cikin alamu na rud'ewa


"Kinga yi sauri shiga wannan gidan na bayana kamin ya ankara damu"


"Na dai shiga gidanku ko? Kamanta nan d'in da kake nuna mani gidan maza ne?" Ta fad'a duk a diririce


"Kidai shiga nace maki, gidanmu ai chakwakiyar da zaki tarar tafi wannan girma domin na tabbata bazaku kwasheta da dad'i ba keda mamana"


Da sauri ta shiga gidan da yake nuna matan ta la6e a bayan k'yauren gidan


Baifi minti biyu da shigarta ba Yaya Kabirun yazo wucewa, tana lura da lokacin da Umar ya mik'a masa hannu ya buga masa wata uwar harara ya wuce abinsa


Bai dad'e da wucewa ba ta fito da gudu ta nufi hanyar gida.


********


"Kina ina dan ubanki fito?" Cewar Yaya Kabiru kenan yayinda ya shigo cikin gidan gadan-gadan cikin matsanancin fushi


"Dayake kin d'aukeni gaula marar hankali kin zaci banga sadda kika fito daga wannan gidan mazan ba ko?" Yana magana yana nufota hannunsa d'auke da wata zungureriyar bulala


Dafe k'irji Ammi tayi tare da maiamaita abinda ya fad'a"Gidan mazafa kace Kabiru?"


"Wallahi kuwa Ammi can na ganta d'azun itada wannan d'an aca6an"


A ranar dai Allah kad'ai ne ya k'waci Lauratu daga hannun Yaya Kabiru amma dukda haka tasha mazga.


_(Abinda masu karatu baku fahimta ba shine, dukfa abinda Ammi takeyiwa Lauratu anata tunanin wai gata ne da kuma fatan tayi aure a inda zata huta suma su huta takeyi mata, shi kuwa Kabiru yana yin abinda yakeyi ne domin kare mutuncin k'anwarsa ammafa a ganinsu koko nace a jahilcinsu)_


********


_Bayan kwana biyu_


Zubairu ne na hango zaune a ofishin babban malamin makarantar islamiyyar yana k'okarin siyawa k'anwar tasa fom


"To Malam Zubairu anan zaka saka mana hannu shi kuma fom d'in ko ananma zaka iya cike mata" Cewar babban Malamin kenan


Wuri-wuri Zubairun yayi da idanuwa, domin maganar gaskiya ko saka hannunma bai iya ba bare kuma akai ga zancen cike fom


Cikin k'arfin hali ya dubi malamin "Allah gafarta Malam aiko ku sai ku saka hannunma duk d'aya ne ai, shi kuma fom d'in inyaso idan naje gida sai na bata ta cike kayanta"


Murmushi Malamin yayi tare da Jijjiga kai alamun tausayin yaron karara akan fuskarsa, saboda ya fahimci Zubairun iyawa ne kawai baiyi ba shiyasa yaketa wasu y'an kame-kame


Murmushi yayi ya k'arayi kana ya mik'awa Zubairun hannu"To shikenan Malam Zubairu zan saka hannun shi kuma fom d'in idan kun cike randa zata fara zuwa sai kuzo mana dashi, ammafa karka manta tayo kayan makarantar kuma ta siyo littatafan da na rubuta maka a wannan takardar dake a hannunka"


Amsawa yayi da"To Malam" kana ya fice daga cikin ofis d'in ya nufi hanyar gida yana mai jin kunyar abinda ya faru dashi yanzu-yanzun nan a cikin makarantar, a zuciyarshi kuwa cewa yakeyi "Duk su suka jamana wallahi......Allah sarki rayuwar talaka nada ban tausayi musamman ma idan akace ya had'a da jahilci.Maman Ja'afar

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [26/04, 3:27 a.m.]

*💘SUNE SILA💘*        6Daga alkalamin

Maman Ja'afar✍
"Nasan dai wannan magulmacin Zubairun bazai rasa sanar dake abinda ya faru jiya da daddare ba ko?" Cewar Ammi kenan yayinda take duban fuskar Lauratu wacce ta dage sai faman lailayar fuskar tata takeyi da hoda, ga dukkan alamu tana yin hakan ne domin had'uwa da abin k'aunarta wato Umar


"A'a Ammi bai fad'a mani komai ba, wani abinne kuma ya faru?" Ta fad'a tana mai duban fuskar Ammin nata yayinda ta dakata da shafa jan bakinda takeyi


"Dama kan Maganar wannan yaron ne Umar, iyayensa sunzo jiya a lokacin kina barci"


Murmushi Lauratun tayi a zuciyarta tana mai cewa"Ga dukkan alamu Allah ya kusan yanke mani wannan wahalar da nake ciki


Numfasawa Uwar tayi kana ta ci gaba dayi mata bayani, inda ta labarta mata dukkan yanda sukayi jiya da iyayen Umar d'in


Batasan lokacin da wasu zafafan hawaye suka dingi safa da marwa akan kuncinta ba


"Yanzu Ammi kina nufin anrabani da Umar d'in nawa kenan?" Ta fad'a murya na rawa domin kuka ne ke shirin kubce mata


"K'warai kuwa an rabaku dashi, amma idan kina jin maganarmu kenan mu iyayenki, idan kuma bakiji gaki ga shi nan, shima na tabbata indai yana jin maganar iyayensa bazaki k'ara ganin k'afarsa a k'ofar gidan nan ba"


Jiki a sanyaye ta ta dubu Ammin nata"To Allah ya za6a mana mafi alkhairi" Ta fad'i hakan ne kawai dan a zauna lafiya, amma a cikin zuciyarta babu abinda ya canza dangane da k'aunar da takewa Habibinta Umar


Murmushin farin ciki Ammin tayi na ganin hak'arta ta kusan cimma ruwa "Yauwa kokefa? Allah yayi maki albarka"


Mik'ewa Lauratun tayi tare da saka hijabinta gami da d'auko wani littafin hausa dake ajiye a k'asan katifarsu "Ammi bara na lek'a nan k'ofar gida wajen Abba mai tireda na mayar masa da wannan littafin nasa na kar6o wani


K'ara tamke fuska Ammin tayi tamkar ba itace d'azu takeyin dariya ba "Nifa wallahi wannan karance-karancen naki Lauratu ba sonshi nakeyi ba, dan dai kin dage ne kawai sai kinyi, amma harga Allah inda son samu na ne ki barsa zanfi jin dad'i"


Danne 6acin ranta tayi kana ta dubi mahaifiyar tata "Ammi shi kuma littafin laifin me yayi maki?"


"Ba laifin da yayi mani illa 6ata tarbiyyar yara dasu marubutan sukeyi, domin duk ire-iren wad'annan littatafan na hannunki babu abinda suke koyarwa face iskanci da kuma rashin tarbiyya...


Cikin mamaki Lauratun ta dubi mahaifiyar tata"Ammi iskanci kuma a wannan littafin?" 


"K'warai kuwa Iskanci mana, inbaya ga kwanciyar aure me suke koyawa a aciki? saifa koyar da jarababbiyar soyayya irin wannan wacce kikeyiwa d'an iskan yaron can, nasan wani abinma duk aciki kike koyonsa, shiyasa zuciyata ba k'aramin tsana takeyiwa irin littatafan nan ba wallahi"


"Wallahi tallahi Ammi ba haka bane, da yawanfa littatafan nan darussa suke koyarwa ga al'umma bama d'an kad'an ba, wani littafinma idan ka karantashi tamkar wa'azi ne ake yiwa mutane kai tsaye, domin wani lokacinma har ibada yake koyarwa da zamantakewa da dai sauransu, masu koya iskanci acikin marubutan qalilan ne wallahi, kuma manyan marubutanmu irinsu Aunty Sadiya Jegal dasu Aisha Maman Ansar suna bakin k'okarinsu wajen ganin an kawo gyara akan marubuta masu yin irin wannan ta'asar a cikin al'umma....


_(Anan kam yakamata nayi sara batare da nayi duba izuwa bakin gatarina ba.Da yawa ana samun marubutanmu masu yin rubutun batsa, ko kuma ba batsar kawai akeyi ba amma acikin labarin batsa yafi yawa, sai kaga har wani salon kwanciya ake koyawa a cikin buk, koko wance an sameta da budurci wance ba'a sameta dashi ba da dai sauransu, ni a ganina kamata yayi mu dinga yin rubutun da ko a gaban waye za'a iya bada labarin books d'inmu batare da an tsallake feji ko d'aya ba, kama tun daga kan iyaye, kakanni, k'anne da kuma yayu da sauran y'an'uwa baki d'aya, wallahi wani buk d'inma koda kud'i aka hadaka bazaka iya karantashi a gaban yan gidanku ba, duk wad'annan rubuce-rubucen batsar ke sakawa iyayenmu suke tsanar littatafan hausan wallahi)_


"Kinga! jeki adawo lafiya, dan duk bayaninda zakiyi mani akan littatafan hausa basa 6ata tarbiyya ba ganewa zanyi ba koda kuwa tsabar rantsuwa qur'ani zaki had'iya a gabana"Da fitowarta daga gidan nasu ko shagon Abba mai tiredarma bata kalla ba, kai tsaye gidansu Rukayya ta wuce domin tasan yanzu haka Umar na can yana jiranta tunda an dad'e da yin sallar isha'in.


Kamar kuwa yanda ta tsammata, zaune ta ganshi acikin zauren gidansu Rukayyar ya rufe fuskarsa da hularsa hana salla yayi jigum, ga dukkan alamu dai tunani ne yake addabar zuciyarshi.


Sau biyu tana masa sallama a saman kansa amma ko gezau, ga dukkan alamu baima san abinda takeyi ba, sai ana ukun ne da tayi da k'arfi yayi firgigit tamkar wanda aka tasa daga bacci, idanuwan nan sunyi masa ja jawur sai kace wanda yaci kuka ya gaji.


"Lafiyanka kuwa Farouq naganka duk a wani birkice haka tamkar wanda yaci kuka ya gaji?""Lauratu kenan! Inda ace kukanma zaizo mani aida nayi farin cikin hakan, domin koba komai zan samu sa'ida daga k'unci da Kuma bak'in cikin da ke addabar zuciyata a daidai wannan lokacin, amma hakan bai samu ba, zuciyar nan tawa tsabar damuwa tamkar ta fashe ta fito nake jinta" Ya k'arashe maganar tasa tare da nuna mata k'irjin nasa da hannu


Jikinta yayi sanyi matuk'a da jin wad'annan kalamai nasa, murya a sanyaye ta dubesa "To yanzu Umar ya kake ganin zamu 6ullowa wannan d'aurarren al'amarin namu?"


"Wallahi Lauratu tun jiya naketa tunanin mafita, har zuwa yanzu da tunanina ya kusan k'arewa nakasa samo bakin zaren wallahi"


Shuru sukayi nad'an wani lokaci kowa na sak'e-sak'en abinda yake sak'awa acikin zuciyarshi


"Ni yanzu babbar matsalatama da aka kafa maka dokar hana zuwa gurina, to ina zamu dinga had'uwama kenan? maganar karatu dama nasan ta riga ta tashi shiyasama nake k'okarin shiga waccen islamiyyar ta K'ofar Dur6i"


"Idan kuwa kika shiga islamiyya zanfi kowa farin ciki Lauratu, to amma aikin naki fa ya zakiyi dashi?"


Nan take ta kwashe labarin komai ta sanar masa


K'ara dafe kai yayi, yayinda zuciyarsa take ci gaba da yi masa k'una "Kumafa a haka sai Ammi ta sake cewa sai kin koma gurin aikin ko?"


"Gaskiya Umar wannan karon kotace na koma bazan sake komawa ba, tunda su basu san mutuncina ba bare su kareshi, yanzu lokaci yayi da yakamata ace nima na kare mutuncin kaina da kaina"


Cikin 6acin rai ya dubeta "Ba nace kar nasake jin kin fad'i wani kalami makamancin na 6aci ga iyayenki ba? Babu yanda za'ayi iyaye su haifi d'a a cikinsu su dinga wulak'anta rayuwarsa, kiyi masu uzuri mana, suma ba laifinsu ba ne talauci ne da k'uncin rayuwa kawai yasa sukeyi maki hakan"


"Amma meyasa sauran talakawan basa...


Tsawa ya daka mata "Kinga bar wannan maganar muyi maganar abinda zai fisshemu kawai"


"Allah ya kamaka munafuki, ashe dama kai ke zugata takeyi mana duk abinda takeyi mana ko?" Cewar Ammi kenan yayinda ta iso cikin zauren nasu Rukayya indasu Lauratun ke tsaye


Duk'awa yayi cikin ladabi yana gaisar da ita "Ammi ina wuni?"


Ko kallon banzama bai isheta ba bare kuma na arziki, saima juyawa da tayi wajen Lauratu


"Ke kuma kin kyauta, dama wannan ne Abban mai tiredar ko? Daga yau kuwa bazaki sake zuwa wajen Abba mai tireda ba bare har ki samu damar had'uwa da wannan d'an iskan yana hure maki kunne"


Juyowa tayi gurin Umar wanda yaketa faman sharce zufa tun isowarta


"Kai kuma Babanka bai gaya maka sak'ona bane? To wallahi ka kiyayenu dan inba haka ba kotu ce kawai zata iya rabamu da kai"


Cikin mamaki ya dubeta "Koti kuma Ammi?"


"K'warai kuwa kotu, kana mamaki ne? idan kuma kana tantama kaci gaba da ra6ewa da ita kaga abinda zai biyo baya, dan garin wannan raka6e-raka6en bansan abinda zai iya biyowa baya ba"


Lauratu batasan kokacin da wani matsanancin kuka yazo mata ba, wannan irin zubar da mutunci haka har ina? Shiko Umar Sumui-sumui ya ra6a ta gefenta ya wuce ya hau mashin d'insa ya tafi, yayinda zuciyar take ci gaba da yi masa k'una.


"Ke kuma zaki wuce mu tafi gida ko kuwa sai na kira Kabiru ya tattaka mani ke?"


Lauratu na kuka tabi mahaifiyar tata suka nufi gida, yayinda duk inda sukazo gilmawa sai an d'ago kai an dubesu.


"Abokina kalla can Inna Tani ce ta taso Lauratu a gaba sai faman kuka takeyi, anya lafiya kuwa?" Tattaunawar wasu samari kenan guda biyu wa'yanda suke zazzaune a bakin k'ofar wani shago dab da gidansu Lauratun


"Ina kuwa zan sani? Ka tambayi kaza hanyar rafi? Tanbayi Agwagwa man kasha labari? Ya wuci da wani k'ato ta kamata suna abinda suka saba acikin lungu? inba hakaba to me zaisa ta tasota agaba suna tafiya tana kuka acikin daren nan? Idan ka lurama ai suna tafiyar amma uwar sai faman zuba mata masifa taketayi"


"Allah dai ya shirya mana zuri'armu" Cewar d'ayan saurayin kenan.


*********


Washe gari sukuku Lauratu ta tashi domin tunda tayi sallama bata tashi akan sallayar ba


"Lauratu lafiya kuwa naga yau bakya shirin tafiya gurin aiki?" Cewar Ammi kenan yayinda take tsaye akan Lauratun


"Ta koreni" Ta fad'a a tak'aice


"An ta6a yin kora babu dalili? Sai dai idan halin naki ki kuma yi mata itama kamar yanda kika saba"


Nan Lauratu ta kwashe dukkan abinda ya faru jiya ta labartawa uwar


"Zancen banza kenan zancen wofi, har wannan abin ya isa yasa kice bazaki tafi gurin aiki ba? Idan kikaje kika bata hak'uri ba shikenan ba?" Ta fad'a cikin alamu na fusata


"Ai kuwa Ammi wannan karon gaskiya sai dai kiyi hak'uri domin kuwa nariga nayiwa kaina alk'awarin aiki ko dubu d'ari'-d'ari ake biyanq kullum nayi bankwana dashi har abada insha Allahu, ina nan tare daku inma dusa zamuci a gidan muci, amma maganar aiki kam anbarta har abada insha Allahu" Tana magana hawaye na bin fuskarta domin ta san abinda zaije ya dawo sanadin wannan maganar Allah kad'ai yasan iyakarsa


Sallallami uwar ta farayi tare da tafa hannaye "Lauratu anya kanki daya kuwa? Kodai bakisan dawanda kike yin magana bane? To tun muna shaida juna tsakanina dake ki tashi ki tafi gurin aikin nan, in kuma ba haka ba muyita ba dad'i tsakanina dake wallahi" Ta fad'a yayinda take nunawa Lauratun hanyar fita


Cikin kuka Lauratun ke mayarwa uwar amsa "To Ammi nace ta koreni, ta koreni ina akeso na nufa kuma saboda Allah?"


Hafsatu ce tazo tana bawa Ammin hak'uri, amma dukda haka Ammin ta inda take shiga ba tanan take fita ba, ita ta kafe akan sai Lauratu ta tafi gurin aiki, yayinda itama Lauratun ta kafe akan bazata tafi ko ina ba......Wasa farin girki, muje zuwa number 7 domin jin chakwakiyar dake gaba.Maman Ja'afar

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [29/04, 1:29 a.m.]

*💘SUNE SILA💘*        9Daga alkalamin

Maman Ja'afar✍
Da daddaren ranar da abin ya faru da misalin k'arfe goma sha biyu na dare na hangosa kwance a k'ofar wani shago sai sharar baccinsa yakeyi hankali kwance, shagonda ya kasance wajen kwanciyarsu dashi da sauran matasa ire-irensa


Kasancewar cikin yanayi na zafi ne ake, shiyasa kwanciyar cikin shagon bazata yiyu agaresu ba sai dai a wajen shagon.


Yayi nisa sosai acikn baccin nasa harda munshari, ga dukkan alamu baccin na yau yayi masa dad'i sosai, tunda harma wani mafarki yakeyi wai yayi kud'i, ya sayi k'aton gida da k'atuwar mota, ya auri Lauratu ya wadatata da dukkan wasu abubuwa na more rayuwa.


Saukar bulalanda yaji ajikinsa ne suka fara dawo dashi cikin hayyacinsa, a zuciyarsa yana mai cewa "Anya wannan duk cikin mafarkin ne kuwa? Kamin ya ida wartsakewa har wasu bulalan sun sake kawo masa ziyara a gadon bayan nasa


Ihu ya saka tare da neman d'auki a gurin jama'ar dake gurin, domin shi a tsammaninsa wannan dukan bana mutane bane sai dai ko aljannu ne


Cocila matasan suka fara hahhaskawa domin tabbatarwa idanuwansu abinda ke faruwa


Kabiru suka gani a tsaye rik'e da wata shar6e6iyar bulala sai huci yakeyi, yayinda abokansa guda biyu suke tare dashi, suma kowannensu da tasa bulalar a hannunsa


"Yaya Kabir! Lafiya? Me nayi maka da har kayo gayya kukazo kuna yi mani irin wannan dukan? Umar d'in ya fad'a yayinda yake shafa bayansa da yayi masa burd'u-burd'u


"Ai indai zakaci gaba da bibiyar k'anwata, wannan somin ta6i nema ka fara gani tukun" Yana gama fad'ar haka suka juya shida abokan nasa sukayi tafiyarsu


Hayaniya ce ta kaure a cikin wannan daren tsakanin Umar da kuma magoya bayan nasa


"Dan Allah ku saurara, ku saurara nace" Ya fad'a da k'arfinsa tare da duban fuskokin abokan nasa


"Ina dukan nan dai ni akayiwa ko?" Ya tambaya tare da dubansu d'aya bayan d'aya


Jijjiga kai sukayi alamar amsawa, amma har yanzu ransu a 6ace yake da irin wannan wulak'anci da Kuma cin mutuncin da akazo akayiwa abokin nasu har gurin kwananshi


"To nidai da aka yiwa dukan nace na hak'ura kuma na yafe masu, ina fatan kuma zaku manta da maganar anan inda abin ya faru? kuma dan Allah ina rok'onku da ku taimaka ku 6oye mani wannan sirrin nawa" Ya fad'a tare da dubansu a marairaice alamun neman alfarma


"Kai kam Umar wallahi anyi lusarin namiji, waime Kabirun ya fika ne da har kakejin wani tsoronsa? wannan irin duka aiko d'an da ya haifa sai haka"Cewar d'aya daga cikin abokan Umar d'in kenan


 "Nikam wallahi inda ni akayiwa haka babu abinda zai hana nayiwa d'an banza shegen duka, inyaso na bar masa k'anwar tasa suje su jik'ata su ringa sha kullum" Cewar wani daga cikinsu kenan a alamun fushi sosai a tattare dashi


"Wannan soyayya da kake yiwa Lauratu Umar ai ta wuce soyayya, wannan ai saidai mu kirata da masifa ko kuma ciwo, nidai ina rok'on Allah ya yaye maka wannan wahalar"D'aya daga cikinsu ya fad'a tare da gyara shinfid'arsa da duk aka cukuikuye masa ita


"Soyayyar da nakeyiwa Lauratu ta wuce duk inda kuke tsammani abokanaina, dan baku san so bane shiyasa kuke fad'ar haka, so da kuke ganinsa Makaho ne kuma kurma ne Kana kuma mahaukaci ne, saboda idan ya tashi shiga cikin zuciyar mutum baya tunanin ko hangen abinda kaje ya dawo"


Mumushin k'arfin hali yayi kana ya sake dubansu "Idan k'arfi ne tabbas Kabiru bai fini k'arfi ba, haka idan abokanai ne y'an tasha Kabiru bai fini su ba, amma me? Ku sani koda Kabiru da wuk'a zaizo yana daddatsar naman jikina, wallahi tallahi bazan iya cemasa uffan ba, idan zan iya jure hakan zan jure, idan kuma bazan iya jurewa ba sai na cikawa wandona iska" Ya fad'a yayinda yake murmushi sai kace bashi ne yasha d'an banzan duka yanzu baCikin mamaki d'aya daga cikin abokan nasa ya dubesa "Kai ko miyasa kace haka Romiyo?" Dayake idan suka tashi zaulayarsa babu irin sunanda basa kiranshi dashi"Saboda matsayin Lauratu a gurina ya wuce duk inda kuke tsammani, kai nifa ba mutanen gidansu Lauratu ba, ko karen gidansu Lauratu ya cancanci girmamawa da kuma karramawa a gurina saboda abar k'aunata" Har yanzu dai Murmushin bai kau a fuskar Umar ba


Cikin fushi kowannensu ya rarumi shinfid'arsa ya kama gabansa sukaje suka kwakkwanta suka barsa anan inda yake tsaye.


*****


_Washe gari_


"Ammi Saminufa ya manta bai siyo sigar da za'a zubawa kokon ba gashi kuma ina sauri nasha na wuce makaranta dan kada na makara" Ta fad'a yayinda take duban fuskar mahaifiyar tata


Idan dutsi ya tanka to itama ta tanka mata, saima k'okarin saka sabbin kayanta da takeyi ga dukkan alamu wata unguwa ce zata tafi mai mahimmanci


D'akin Mahifinsu ta nufa domin tanada tabbacin yanzu dai baikai ga fita ko ina ba.


Tana d'aga labulen d'akin ta hango Mahaifin nata sai faman lissafa kud'i yakeyi, ga dukkan alamu wata ne ya k'are ya d'auki albashinsa na dubu bakwai


"Waiku wad'anne irin yara ne marasa tarbiyya da zaku dinga shigowa mutane d'aki batare da yin sallama ba?" Yana magana yana sak'a kud'in nasa a k'ark'ashin tabarma gudun kada Lauratun ta gani, bai san cewa ta riga ta gama ganin komai ba tun d'azun


Samun guri tayi ta tsugunna"Baba dama zuwa nayi kabani kudi nasiyo siga" Ta fad'a yayinda take kallon inda Baban nata ya 6oye kud'in nasa


Hayayyak'o mata yayi"Kuje gurin Amminku ta baku kud'in mana, ni ina naga wasu kud'i daku baku iya komai ba saidai abaku abaku? kina gani dai wata ba k'arewa yayi ba bare kiyi tunanin ko anyi mana albashi"


"Waida Baba bayan kud'in sigar har d'ari biyuma nakeso kabani na siyo Zadul-muslimati saboda tun satin da ya wuce muka gama Arba'una" Ta fad'a d'auke da murmushi a fuskarta, a tunaninta shima murmushin zaiyi kasancewar gidansa anfara samun wanda ya sauke Arba'una hadis


K'ara d'aure fuska yayi kana ya dubeta"Ke kikasan wani Arba'una da Zadul.. Zadul mema kika ce? Koma dai miye ni banida kud'i, kije Amminki ta baki ai bazata rasa kud'i a jikinta ba, yanzu dai ga goma na sikarin" Ya fad'a tare da mik'a mata nera gomar


Jiki a sanyaye ta dawo K'ofar d'akin nasu ta zauna ta buga wani uban tagumi.


******


Saminu ne na hango tun daga kofar gidansu Umar yaketa faman falfala gudu yana numfarfashi, ga dukkan alamu wani sabon labari ne yake d'auke dashi


A bakin k'ofar d'akin nasu ya sameta tare da dafa k'afafuwanta "Yaya Lauratu ga Y'an sanda can a k'ofar gidansu Umar d'inki, wani ya rik'e masa hannu wani kuma ya rik'e masa wando, kuma wai cewa naji anayi wai Ammi ce ta..


Bata tsaya ta ida jin k'arshen labarin ba ta suri silifas d'inta sai K'ofar gidansu Umar, a lokacin ma har sun riga sun tafi dashi


Batayi wata-wata ba ta tari mai mashin"Hajiya ina zamuje ne?" ya fad'a murya na tangad'i tamkar wanda yasha abin shaye-shaye yayi d'ib


"Folisteshan din K'ofar Soro zaka kaini" ta fad'a a tak'aice


Suna isa ta runtuma a guje sai gurin Y'an sandan, Mai mashin d'in yanata k'wala mata kira akan tazo ta bashi kud'inshi amma ko waiwayowa batayi ba, da dai yaga alamar ba biyansa zatayi ba sai yaja mashin d'insa yayi gaba kasancewar kada K'ilu taja masa Bau, tunda a bugensa yake kuma yasan idan suka cabkeshi sai sun gama k'wak'walesa tatas kana zasu sakeshi"Dan Allah Malam ankawo wani saurayi mai suna Umar anan?" Tana magana tana y'an waige-waigenta ga dukkan alamu Umar d'in take nema"Gaskiya duk cikin Sel d'in nan namu babu wani saurayi mai sunan Umar"


Kallonta d'an sandan yayi tare da k'ara kashe mata ido karo naba adadi "Y'an mata ko zan iya sanin sunanki dan Allah?"


Saida tayi nisa kana ta waiwayo"Sunanmu d'aya da Tsohuwarka"


Sauran y'an sandan kuwa me zasuyi inba dariya ba


Wani mashin d'in ta kara tara "Folisteshan d'in Sabon gari zaka kaini" Ta fad'a yayinda take hawa mashin d'in sai kace wata mai kud'i a jikinta...

 Maman Ja'afar

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [29/04, 11:50 p.m.]

*💘SUNE SILA💘*       10Daga alkalamin 

Maman Ja'afar✍
Koda isarta batare da wani 6aba lokaci ba ta bar mai mashin d'in anan farfajiyar inda ake ajiye abin hawa ta rufta a cikin Folisteshan


Batayi mamakin ganin Ammi a gurin ba domin dama Saminu ya riga ya fad'a mata komai


A can bayan Kanta ta hango abin k'aunarta Umar yayinda wani d'an sanda yake caccaje abinda ke jikinshi domin zubashi a cikin Sel


Hararta Ammi tayi kana ta dubi muk'ek'en d'an sandan mai gashin baki buzu-buzu a bakinsa sai kace wani matashin bunsuru "Y'alla6ai gata nan ma tazo ai"


Cikin matsanancin 6acin rai ta dubi mahaifiyar tata "Yanzu Ammi me kikayi kenan? Yanzu zubar da mutuncin nawa kuma har ya kai haka? Dukda abin nan da kikeyiwa Umar har yanzu girmanki koda k'wayar zarra ne bai gushe a idanuwansa ba, Ammi bakya tunanin ranar da zaiyi fatali da wannan girman naki?" Tana kuka take gayawa uwar tata wad'annan magan-ganun domin izuwa yanzu zuciyarta ta riga ta gama k'ek'ashewa, a shirya take jinta da ta d'auki dukkan wani bala'i da masifan da zai tunkarosu, domin Umar shine gatan ta, kuma har abada bata tunanin canzawa akan wannan ra'ayin nata


Tun Umar yanayi mata nunu da ido akan tayi shuru, har dai ya gaji ya koma yanayi mata alama da hannu, da dai yaga batada niyar yin shurun d'aga muryarsa yayi da k'arfi "Lauratu wai wannan wane irin hauka ne haka? Banace maki kiyi shuru ba?"


Rarraba idanuwa y'an sandan suka farayi a tsakaninsu, yayinda wasu suke mamakin ganin irin wannan soyayya, wasuko laifinta suke gani a tunaninsu wai tana yiwa mahaifiyarta rashin kunya, yayinda wasu kuma suke ganin kamar ba Ammi ita ta haifi Lauratun ba, domin a tunaninsu muddin da ita ta haifeta duk abinda Lauratun zatayi mata bazataso ta d'aga murya wani yaji ba bare har tayi tunanin kawo wannan maganar Folisteshan, a tunaninsu wannan zubewar mutunci yakai inda ya kai


"Ke! Babban dan sandan ya daka mata tsawa"Ke baki san girman manya bane da kike yiwa marik'iyarki magana haka garan-gatsagai sai kace bata ta6a yi maki wani abin alkhairi ba? Ai ko mu hukuma mun cancanci girmamawa a gurin ki bare kuma ita"


Murmushin takaici Lauratu tayi kana ta dubesu "Mahaifiyata ce amma tunda na fara mallakar hankalin kaina ban ta6a samun wata kulawa a gurinta daya cancanci ace uwa tana bawa y'ay'anata ba, ko kad'an bata san damuwata ba, kullum ita kanta ta sani, da in zama ta kirki da in watse duk ita wannan ba damuwarta bace madamar zan dinga zuwa gurin aiki ina kawo masu kud'i suna yin hidimomin gida, kenan haka zanta zama Kyandiri yayinda nake k'ona kaina ina haska wasu? maganar...


"Lauratu dan Allah kiyi shuru zafa ki k'ara dagula dukkan lamurran" Ya fad'a yayinda hawayen tausayin Lauratu ke bin fuskarsa


Cikin kukan ta dubesa "Umar ka barni na fad'a kona samu sassauci daga damuwar da ta dad'e tana d'awainiya da zuciyata tsawon shekara da shekaru"


Murmushin k'arfin hali ta sakeyi "Umar shine gatana shine farin cikina, shi yasan damuwata da kuma rashin damuwata, shi nake fatan samun ingantacciyar rayuwa ta falilinsa, to shi d'inma gashi anason rabani dashi ta k'arfi da yaji, danme bazanyi magana akan hakan ba?" Ta k'arashe maganar tata tana mai d'aga sauti cikin kuka


"Wallahi Y'alla6ai k'arya takeyi, nice mai kula da duk wasu hidimomi da kasani na cikin gidan nan, hatta kud'in haya sai ayi shekara biyu mahaifinsu bai bada ba, kullum fad'i tashina ya k'are ne a tunanin yanda zanyi rayuwarsu ta inganta, ashe sakayyyar da zakiyi mani kenan Lauratu?" Ta k'arashe maganar tata yayinda itama hawaye ke bin fuskarta


Juyawa tayi inda Umar d'in yake a tsaye"Y'alla6ai wallahi da Lauratu ba haka take ba, yarinya ce mai ladabi da biyayya, amma wannan d'an banzan yaron da kuke gani duk shi yabi ya birkita mata lissafi, nidai rokona agareku dan Allah ku taimaka mani kuyi masu tsakani, ya zamto babu shi babu ita har abada"


Cikin kid'imewa Lauratu ke fad'in "Wallahi baku isa ku d'aure shi ba, azzaluman banza azzaluman wofi kawai....


"Gaskiya Hajiya sai dai kiyi hak'uri, amma ya zama dole mu zaunar da d'iyarki anan domin koya mata hankali, koba komai ta koyi y'anda ake girmama manya, kigafa yanda taketa faman yi mana 6a6atu sai kace taje gidan biki, dole tasan cewa nan gurin hukuma ce tazo" Ya fad'a yayinda yake dukan teburinda ke gabansa


"Sajan! Ya kira sunan wani na kusa dashi"Shigo mana da ita bayan kanta, shi kuma kuna gama Sacin d'insa ku iza k'eyarsa zuwa Sel kawai"


Cikin kuka Umar ya dubi Ammi "Ammi dan Allah ki saka baki su bar Lauratu ta koma gida, wallahi kwata-kwata kwana anan bai cancanci d'iyar mutunci ba"


"Dama dole ka kirata marar mutunci mana tunda ka riga ka gama rabata da mutuncin nata"


Duban y'an sandan ta kumayi "Y'alla6ai karku damu ku had'a da ita d'in inyaso itama idan taji jiki ta samawa kanta mafita idan ta fito" Tana gama fad'ar haka ta fice daga cikin Folisteshan d'in yayinda zuciyarta takeyi mata k'una na irin magan-ganun da Lauratun taita fad'a mata a bainar jama'a


"Y'alla6ai dan Allah ku bani belin Lauratu, akwai kud'i a cikin aljihun wandona inagama zasu kai dubu biyar ku d'auka dukama na bar maku indai zaku fitar da ita" Umar d'in ya fad'a yana mai dafe kai domin ji yake kan nasa kamar zai tsage gida biyu


"Kai dan ubanka ka ta6a jin inda mai laifi yayi belin mai laifi ne?" K'aramin d'an sandan ya fad'a yayinda yaketa faman busa sigari abinsa


"Umar karka damu, ni idan suka kashenima zanfi jin dad'in hakan, domin koba komai zan huta da irin wannan bak'in cikin da kuma k'unci da naketa fama dashi tun tasowata har ya zuwa yanzu" Ta fad'a yayinda ta had'a kanta da guiwa a bisa teburin da take zaune akai na bayan Kanta.


Tun kamin a shigar da Umar Sel d'an titti6in d'an sandan yazo dab da inda Lauratu take a zaune shima ya zauna dab da ita


"Abinfa da mamaki, wai kina yarinyarki k'arama amma wai har kin san dad'in namiji, koda yake hakan ba yawa bane tunda nima gashi nan na samu damar tallata hajata zuwa gareki, ya zaki amince dani kuwa? Ko ba kyau akwai kud'i fa yarin..


Tun bai k'arasa yin Kamfen d'in nasa ba Umar ya dakatar dashi "Wai dama har acikinku masu kula da rayukkanmu, dukiyoyinmu, da mutuncinmu ana samun Bunsuraye kenan?"


Juyowa d'an sandan yayi tare da duban fuskar Umar


Jijjiga kai Umar d'in yayi kana yaci gaba da cewa


"K'warai dubeni sosai, inada mutunci akan kowa da kuma komai amma bani da mutunci ko kad'an ga wanda ya nemi ta6a mani Lauratu, iyayenta kawai nake d'agawa k'afa a kanta, danko ita kanta wani ta'addancin da nakeyi saboda ita basani tayi ba, walllahi tallahi tsab zan iya yi maka yankan rago akan Lauratu, inyaso ku kuma sauran sai kuji dad'in yanke mani duk hukuncinda kukaga dama" Ya fad'a yayinda yake duban sauran y'an sandan


Kusan su duka suka kama dukansa babu ji babu gani, tun yana k'okarin karewa da hannunsa har dai hakan ta gagara jikinsa yayi lak'was


 Itako Lauratu inbaya ga ihu da kururuwa babu abinda takeyi.


******


"Ammi wai ina Lauratu taje ne tun safe fa ban ganta ba, ga kayan islamiyyarta kuma a shanye saman igiya bare nace ko makaranta ta tafi ne?" Cewar Zubairu kenan yayinda yake duban Mahaifiyar tasu


Rararraba idanuwa Saminu ya farayi "Nidai babu ruwana, saurama kuce ni na gaya mata" Yana magana yana wani cin magani waishi nan mai gaskiya


"Nima ban san inda take ba, tashi ka bani guri" Ta fad'a yayinda taketa faman safa da marwa acikin d'akin


Jiki a sanyaye Zubairu ya fito daga cikin d'akin ya dawo K'ofar gida gurin Abba mai tireda ya zauna yana jiran fitowar Saminu domin jin cikakken bayani akan abinda ke faruwa da kanwar tasa


******


Koda shigowarsu ofishin y'an sandan basu fara yin araba da kowa ba sai Lauratu dake a bayan kanta


Malam Garba yayi mamakin ganin wannan abu matuk'a, matarsa ya duba "Kiga Lauratu anan, ita kuma kome ya kawota anan d'in?"


"Malam kenan! Ina ruwanmu da abinda ya kawota? mudai kawai belin d'in d'anmu mukazoyo, kuma shi zamuyi mu tafi"


"Sannunku dai" Dattijon ya fad'a yayinda yake duban yan sandan cikin girmamawa


"Dan Allah Umar mukazo beli idan babu damuwa" Ya fad'a tare da zura hannu a cikin aljihu


Murmushi sukayi su duka saboda ga dukkan alamu bazasu rasa na goro ba anan


Bayan fitowar Umar d'in ne mahaifinsa ya dubi yan sandan "Ita kuma waccen yarinyar lafiya naganta a tsare anan?"


"Lafiya kalau Baba kawai dai batada kunya ne shiyasa, kuma bata iya girmama na gaba da itaba, idan kaji yanda ta daddage tana gayawa uwarta bak'ar magana, kai kace batasan daga inda ta fito ba, shiyasa mu..


Katseshi yayi "Dan Allah ko zaku taimaka itama ku bamu belin d'inta?"


Carab mahaifiyar Umar d'in tayi "Malam babu wata maganar belin d'inta, itama nata iyayen suzo su fitar da ita tunda ba daga sama ta fad'o ba, inma baya ga abinka malam duk irin rashin mutuncin da iyayenta suka karta mana har wani tausayinta kakeji? Wallahi indan tani ne ta mutu ma anan"


Dattijon bai bi ta kanta ba saima k'ara fuskantar Yan sandan da yayi alamun amsarsu yake jira


"Baba kayi hak'uri gaskiya itama sai iyayenta sunzo da kansu sunyi belinta tukun"


Badan yaso ba ya hak'ura ya fuskanci d'an nasa Umar "Ina fatan wannan zai zama izina agareka, idan zaka bar musu y'arsu ne to, idan kuma zakaci gaba da tarayya da ita ne, nidai wannan shine na k'arshe daga gurina, duk abinda kaje ka jawo kanka, yanzunma badan mahaifiyarka ta matsa ba wallahi banida niyar zuwa nan, tunda ai tun farko na riga na fad'a maka dama"


Umar kafewa yayi fafur akan bazai bar gurin nan ba sai tare da Lauratu, da k'yar da masifa iyayen nasa suka tasa k'eyarshi agaba har zuwa gida.


*******


Ammi ce ta kawowa Lauratu abincinda tafiso wato taliya, fafur Lauratu tak'i kar6ar abincin nan, akayi-akayi da ita amma tak'i kar6a, bansan me uwar ta gani ba ta nemida abata belin d'inta


Itama nan dai saida tayi ta wajen dubu biyu kana suka bata Lauratun


Fitowarsu daga Ofishin yan sandan keda wuya suka nemi abin hawanda zai kawosu gida


Amma me zai faru? Mashin d'insu Lauratu ne agaba nasu Ammi kuma yana a baya, sai dai hanyar da yakamata ace sun bi ba ita su Lauratun sukebi ba


"Dan Allah yaro k'ara gudu bansan inda yarancan sukeson nufa ba" Ammin ta fad'a tare da dukan bayan mai mashin d'in


A kuma daidai wannan lokacin ne naji Lauratu na fad'awa d'an mashin d'in nata "Malam dan Allah tashar da zan samu motar Funtuwa nakeso ka kaini, yi sauri banason wad'ancan masu binmu su cimmana kaji?"


Ai kuwa batare da 6ata lokaci ba d'an mashin d'in ya k'ara tsuga wuta tare da shiga lunguna-lunguna ta yanda zai 6acewa su Ammi cikin gaugawa...


 

Yaufa ake yinta, jama'a wai ina Lauratu ta take shirin nufa ne? Ku biyoni dai domin ganewa idanuwanku abinda ke shirin faruwa.
Sai dai fa ga dukkan alamu littafin nan dai bai samu kar6uwa a gurinku ba kamar sauran litattafan nawa, koda yake bara dai naji daga gareku tukun kana mu wuce number 11
 Maman Ja'afar

+966592551785

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [28/04, 2:12 a.m.]

*💘SUNE SILA💘*        8Daga alkalamin

MamanJa'afar✍Allah mai iko! Wai yau Lauratu ce na hango a cikin aji zaune akan teburi tasha sabbin kayanta na makaranta ta tasa littatafanta agaba tana daukar darasi tare da sauran d'alibaiMalamin nasu tsaye na hangosa yasha Sunnah ya k'oshi, ga gemu ga aswaki, gashi yasaka wandonshi daidai misali kamar dai yanda Sunnah ta tanadar


Tsaye yake jikin a

Allo sai faman yi masu bayani yakeyi akan darasin da ya gama koyar dasu yanzu, saida ya tabbatar da kowa ya fahimci abinda yake nufi kana ya bisu d'aya bayan daya yana tambayarsu domin tabbatarwa


Wacce ke zaune a kusa da Lauratu ya fara tambaya domin yaji ko itama ta gane karatun nasa?


"Malam dan Allah kayi hak'uri wallahi har yanzu dai ban gane wasu hukuncin a ciki ba" Cewar y'ar matashiyar budurwar kenan wacce take zaune a gefen Lauratu


Lauratu tayi mamaki k'warai ganin cewa wannan maimaicin da malamin yaitayi ko k'walwar mutum ta kaza ce yaci ace ya gane, shima Malamin baiji dad'in rashin ganewar tata ba, inagama shiyasa ya k'ara d'aure fuskar tasa.


Wacce ke bayansu ya tambaya itama domin tabbatarwa kamar ta farkon


Mik'ewa tayi tsaye kamar yanda dokar makarantar ta tanadar duk wacce aka tamabaya zata mik'e tsaye ne kana ta bada amsar da aka tambayeta


"Malam kayi mana bayani ne akan hukunce-hukuncen wad'anda ya halatta su ajiye azumi inada kace1 Ya haramta wanda bashida wani uzuri a watan Ramadan ya ajiye azumi hakanan kawai madamar shi musulmi ne kuma baligi mai hankali ba mahaukaci ba2 Kuma ya wajaba ga mai haila ta ajiye azumi, ko mai jinin haihuwa, da kuma wanda yake buk'atar ku6uta daga halaka3 Sunna ce ga matafiyin da ta kai tafiyar yin qasaru ya ajiye azumi idan azumin yayi masa wahala, ko marar lafiya da yake gudun cutuwa4 Kuma ya halatta wanda zaiyi tafiya da rana ya ajiye azumi, ko mai ciki ko mai shayarwa saboda tsoron kansu ko kuma yaron nasu


Dukkan wad'annan ramuwa ne kawai akansu babu ciyarwa, amma mai ciki ko mai shayarwa zata yi k'ari da ciyar da miskini a kowace rana, idan ta ajiye azumin nata kenan don yaron kawai badan ita kanta ba


5 Wanda ya kasa yin azumi saboda tsufa ko kuma wani ciwonda ba'a tunanin za'a iya warkewa, to a kullum sai ya rik'a ciyar da miskini d'aya, kuma babu ramuwa akanshi shima


6 Wanda kuma ya jinkirta ramuwa saboda wani uzuri har wani Ramadan d'in ya riskeshi, shima ramuwa ce kawai zaiyi babu ciyarwa, idan kuma ba tare da wani dalili bane zaiyi ramuwar kana kuma ya dinga ciyarwa a kowane yini".


Matashiyar na gama yin bayanin nata duk ajin aka d'auki kabbara, "Allahu Akbar"shima malamin da tunda ya shigo ajin yaketa faman yin muzurai saida ya murmusa domin jin dadin irin amsarda Khadija Ibrahim ta bayar.


Batare da 6ata lokaci ba Lauratu ta tashi daga mazauninda take zaine ta koma mazaunin baya inda Khadija Ibrahim take zaune kenan itama ta zauna, domin ta lura zama da Khadija ba k'aramin fa'idantuwa zatayi ba akan zama da waccen Dasusuwar da tun d'azu aketa faman maimaita abu amma tak'i gane komai a ciki._(Shiyasa ni Maman Ja'afar ko a makaranta bana son zama da wanda nafi ilimi, A to idan na zauna tare dashi me zan karu dashi kenan? Ai sai dai ya dameni da neman satar amsa kawai, shi bai sani ba nima kuma ban sani ba, huhun ma'ahun kenan, amma wanda ya fini ilimi koba komai idan nayi tilawa agabansa ya gyara mani inda yaji nayi kuskure a ciki ko anan na k'aru dashi ai)_


Bayan antashi makarantar tare suka jero ita da Khadija domin nufar hanyar gida, basuyi nisan kirki ba Khadija ta dubi Lauratun"To nifa Lauratu anan zan barki domin ga gidanmu can ni na iso" Ta fad'a yayinda take nunawa Lauratun gida mafi kusa dasu inda wasu matasa suke a zazzaune k'ark'ashin bishiya suna firarsu irinta samari, ga dukkan alamu irinsu Kabiru ne marasa aikinyi.


Sallama sukayiwa juna tare da alk'awarin gobe idan Allah ya kaimu Lauratun zata biyowa Khadija su wuce makaranta tare.


******


A fusace ya shigo cikin gidan tare da nufar inda k'anwar tasa Khadija take tana k'okarin rataye jakarta ta islamiyya a jikin k'usar dake buge a jikin bangon d'akin nasu


"Khadija! Wace ce can na ganki tare da ita yanzu? kamarfa mai sayar da abinci nan ce a bakin sabuwar tasha wajen karuwan nan ko?"


"Sabuwar tasha? Sayar da abinci kuma? Wallahi Yaya ban fahimci abinda kake nufi ba har yanzu" Ta fad'a ga dukkan alamu batasan inda tambayoyin nasa suka nufa ba


"Ina nufin waccen yarinyar dana ganku tare da ita yanzu" Ya fad'a a tak'aice


"Au Lauratu Harisu wai kake nufi Yaya? Wallahi nima ban santa ba yau kawai na fara ganinta a makarantar islamiyyarmu"


"To dai koma miye daga yau bana son na k'ara ganinki da ita, irin yaran nan nefa masu gararanba a tasha da sunan sayar da abinci, ba tarbiyya ba mutunci inbaya ga wasa da maza babu abinda suka iya, taya kuwa hankalina bazai tashi ba na ganki tare da ita? To nidai na fad'a maki daga yau sai yau, wannan ya zama na farko kuma na k'arshe, Kina jina ko baki jina?"


Jijjiga kai tayi alamun gamsuwa da maganarsa "Insha Allahu Yaya hakan bazata sake faruwa ba" Ta fad'a gami da jimamin abinda aka fad'a akan Lauratun, domin ita ko alama bataga ko makamancin hakan a tattare da ita ba.


Tun daga wannan lokacin Khadija ta canzawa Lauratu fuska, tun Lauratun na bibiyarta tana shareta hardai itama Lauratun ta gaji ta daina kulata kuma ta ware kanta ita kad'ai a cikin ajin babu ruwanta da kowa.


********


_Bayan wata hudu_


Acikin wad'annan watannin abubuwa da dama sun faru, domin haka wata hud'un nan ya shud'e ba tare da masoyan suna ganin junansu ba, sai musayar wasik'a kawai da sukeyi a tsakaninsu idan hakan ta samu kenan


Amma dukda da haka soyayyarsu na nan daram tana gudana acikin zukatansu ba tare da samun wani gi6i ko kad'an ba.


A zamanta da Ammi kuwa babu abinda ya canza, domin Lauratu tamkar wata mai zaman kanta ta koma acikin gidan babu sakawa bare kuma hanawa, kullum tana k'umshe a cikin d'aki, wani lokaci tayi karatun ta na islamiyya wani lokaci kuma tayi karatun hausa, yayinda wani lokacin kuma hoton Umar kawai zata tasa agaba tana kallo tana zubar da hawaye.


Yayantama Zubairu yayi yayi da ita akan taje ta bawa Ammin hak'uri kuma ta koma gurin aikin domin a zauna lafiya, amma fafur ta k'ek'ashe k'asa tace indai har sai na koma tasha ina zubar da mutuncina sannan zata hak'ura na gwammace muyita zama a haka dani da ita har k'arshen duniya.


********


Yau a garin hadari aka tashi dashi, hadarin ya had'u yayi bak'ikk'irin kuwa, sai cida aketa famanyi tun d'azun.


Lauratu ce na hango ita da sauran d'aliban a bakin makarantar tasu a tsaitsaye, ga dukkan alamu jimamin hadarin sukeyi saboda mafiya yawansu daga nesa suka fito, daga y'an K'erau, sai y'an Mad'attai, da irinsu Dutsin Amare haka d'in nan, y'an kusada makarantar qalilan ne.


Umar ta hango daidai masallacin dake kusa dasu ya ajiye wani mutum, mutumin yana k'okarin mik'a masa kud'insa.


Da gudu ta nufi inda yake tana mai k'okarin tsayar dashi kamin yayi gaba


"A'a har yanzu baki tafi gida bane na ganki anan kusan Magariba?" Ya fad'a yayinda yake dubanta cike da mamaki


"Wallahi ban tafi ba tsoro nakeji kar sai na d'au hanyar gida a fara ruwa gani kuma da tsoron walk'iya kamar me, kuma kasan irin lungunan dake cikin eriyar tamu, idan ruwa yayi ruwama har hanyoyi rufewa sukeyi"


Dariya yayi tare da sake dubanta karo naba adadi "Meye kuma na yin wani dogon sharhi hak Lauratu? Ai dani da abinda na mallaka duk bakida shamaki dasu, hawo kawai muje na ajiyeki a gidan, sai dai dani dake kamata yayi muyita runtuma addu'a tun daga yanzu har zuwa lokacin da zamu isa gidan kada Allah yasa wani nawa ko naki ya ganmu a tare"


"Insha Allahuma babu mai ganinmu a cikinsu" Ta fad'a a tak'aice tare da hawa mashin d'in.


Saida sukazo kusan k'ofar gidan nasu Lauratun kana aka fara wata cida mai k'arfin tsiya tare da walk'iya duk a lokaci guda, tsabar tsoron da Lauratu taji batasan lokacin da ta cukuikuye rigar Umar ba


A kuma daidai wannan lokacin ne Ammi ta lek'o k'ofar gida domin neman Saminu, kasancewar idan ruwan sama ya dakeshi zazza6i yakeyi na inna'naha


Kwatsam kuwa idanuwanta sukaci mata karo da Lauratu k'ank'ame a bayan Umar yayinda shi kuma yake kici-kicin k'wacewa har mashin d'in nasa yana sakin hanya, ga dukkan alamu ma mashin d'in ya kusan kayar dasu


"Allah ya isa tsakanina dakai Ummmaru, yanzu dama abinda nake tunani akanku gaskiya ne kenan? Duk lalatar da kukaje kukayi bata isheku ba har sai kun biyo titi rungume da juna? Wai karuwa kakeso ka mayar min da d'iyar tawa koko me kake nufi?Ni dama nasan badan Allah aka tarki zuwa wannan makarantar ba dan dai kawai kuringa samun damar had'uwa da juna ne kawai kuna holewarku, to yau Allah ya toni asirinku munafukai, kuma kai Ummaru hukuma ce kad'ai zatayi mana tsakani dakai yau d'in nan" Tana gama fad'ar way'annan magan-ganun ta shigewarta gida cikin matsanancin fushi da Kuma 6acin rai


Lauratu kuwa tsabar kid'ima da kalamanda ke fitowa daga bakin mahaifiyar tata kasa cewa komaima tayi, saima wasu zafafan hawayen bak'in ciki da kuma k'unci daketa faman safa da marwa akan fuskarta.


Dukda Umar yana jure ire-iren wad'annan hayaniyar, hayaniyar yau kam shima saida ya zubar mata da hawaye


A zuciyarsa tunani yakeyi yana mai cewa "Anya Ammi ita ta haifi Lauratu da cikinta kuwa? Idan ita ta haifeta wane irin laifi tayi mata haka da har takeyi mata wannan irin mummunar fata?


Da wannan tunanin yasamu ya lallla6a ya kai kansa zuwa gida, domin tsabar 6acin rai har wani jiri-jiri yakeji yana d'ibarsa...........
Chakwakiyar na cikin Sune Sila number 9 muje zuwa masu karatu domin jin irin badak'alar da ke gaba.Maman Ja'afar

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [01/05, 9:32 p.m.]

*💘SUNE SILA💘*       12Daga alkalamin

MamanJa'afar✍"Kina ina Ta Assubi? Fito kiga kuma wani bala'inda d'anki ya sake jawo mana, d'an kuka mai jawa uwarsa jifa"


Cikin hanzari tare da fad'uwar gaba ta fito daga cikin d'akin nata yayinda take gyara d'aurin d'ankwalinta dayake shirin warwarewa


"Malam wani abin kuma Ummarun ya sake jawo mana?" Ta fad'a yayinda take duban fuskar mai gidan nata wanda rabon da taga irin wannan 6acin ran akan fuskarsa har ta manta


"Wato bayan rigin-gimun da akai tayi na Folisteshan, yanzu kuma zuwa yayi ya 6oye masu yarinya, yau kwana hud'u kenan ba'a san inda take ba, to a tak'aice dai in k'are maki magana yanzu haka iyayen yarinya sunkai magana zuwa Koto, kingama Sammacin" Ya fad'a yayinda yake mik'a mata takardar dake hannunsa


Kuka dattijuwar ta saki wiwi tare da mugayen kalamai akan Lauratu, wacce ta kasance sila na wargaza masu dukkan wani farin ciki nasu.


*****


_Da yamma_


Tafe yake yana tunanin inda zai k'ara zuwa domin neman Lauratu, kasancewar duk inda yake tsammanin ganinta babu inda baije nemanta ba amma har yanzu shuru kakeji tamkar an aiki loma gewayar mak'oshi, da wannan tunanin ya samu isowa gida domin yin wanka da cin abinci kana kuma ya sake fita, da sana'a da kuma neman Lauratu.


"Mama na duba kicin banga abincina ba, kodai yau akason anmanta dani ne?" Ya fad'a cikin alamu na zaulaya


Shuru tayi masa ba tare da tace masa komai ba, saima zura masa idanuwa da tayi


Ganin mahaifiyarsa a cikin wannan halin ta buga uban tagumi hawaye sai faman bin fuskarta yakeyi, ba k'aramin tada masa hankali yayi ba


Cikin kid'ima ya iso inda take zaunen"Mama lafiya kuwa? me ya faru? kodai wani ne ya mutu? Ina Hadiza ne ko itace ta mutu?" Yana magana yana waige-waige tamkar mai neman wani abu daya 6ata


Numfasawa tayi cikin alamu na 6acin rai "Babu wanda ya mutu Umar, kai dai ne keson kashemu tun kwananmu basu k'are ba"


"Mama wani abin kuma akace nayi ne?" Har yanzu dai rud'ewar bata kau akan fuskarsa ba


"Babu abinda kayi Umar sai 6oye masu yarinya da kayi, saboda haka Ummaru tun wuri ka fito masu da y'arsu inda ka 6oyeta inba so kake mu tsine maka albarka dagani har mahaifinka ba"


Cikin kuka yakeyi mata bayani "Wallahi tallahi Mama bani na 6oye Lauratu ba, ni kainama bansan inda take ba wallahi saboda ko yanzu da kika ganni daga gurin nemanta nake ban dace ba"


"Wannan kuma duk kai ta shafa idan Litinin tayi kuka shiga Koto komi kenan kayiwa Alk'ali bayani"


"Koto kuma Mama? Waye ya kaini koton akan wannan y'ar maganar? Lauratun nanfa ba saceta akayi ba, kuma ba 6ata tayi ba, ita ta san inda take tunda ba k'aramar yarinya bace, amma saboda Allah wannan y'ar maganar da batafi ayi sasancinta agida ba sai anje wani koto?"


"Kaidai ka sani" uwar ta fad'a tare da mik'awa tsaye ta bar masa gurin gaba d'aya.


******


Lauratu ce na hango zaune a tsakar falon nasu Jamila itada yara sai faman yi masu tarihi takeyi, suko yaran sai murna da tsalle sukeyi


"Aunty amma zaki zauna damu anan kullum kina mana irin wannan tarihin ko?" Cewar Ahmad kenan yayinda ya rik'o hannun Lauratun


Murmushi mamansa tayi wacce take a gefe tana kallon duk abinda ke gudana"Ai kuwa Lauratu bazata zauna damu ba Ahmad, dan gobe-goben nanma zata tafi garinsu"


Cikin hanzari Lauratun ta dubeta alamun tambaya


"K'warai kuwa gobe zaki koma gida, kinsan kuwa irin tashin hankalinda kika baro acan d'in? Yanzu haka nasan suna can suna zargin Umar akan abinda bai sani ba, kinga kuwa indai har da gaske sonda kikeyi masa na gaskiya ne yazama wajibi agareki da kije ki fitar dashi daga cikin wannan chakwakiyar da kika sakashi, kinsan halin Ammi dai basai na fad'a maki ba, wallahi duk abinda baki tsammani zai faru sai kiga ya faru akan hakan"


Nan take tunanin Umar da kuma tunanin irin halinda yake ciki zuwa yanzu ya fad'o mata a rai"Allah sarki Farouq yanzu ko a wane hali yake ciki?" Ta fad'a a cikin ranta


"Yaya ai yanzuma dare baiyi ba, kodai natafi yau kawaima?" Ta fad'a yayinda take mik'ewa tsaye, ga dukkan alamu zuwa yanzu hankalinta ya karkata zuwa gida


Rik'e baki yayar tata tayi cikin alamu na zaulaya take ce mata "Waini tunda can mantawa kikayi da halinda Umar d'in naki yake ciki ne sai yanzu na tuna maki ko kuwa dai yaya abin yake?"


"Haba yaya, mantawa da Umar aiba k'aramin aiki bane ba agareni kawai dai tunanina baikai akan zai samu matsala bane akan tafiyata sai yanzu da kika tuna mani"


"To yanzu dai zauna, tafiya ba yau ba sai gobe idan Allah ya kaimu saboda yanzu yamma tayi kuma tafiyar dare ba dad'i ne da ita ba" Ta fad'a yayinda take zaunar da Lauratun daga tsayenda tayi.


*******


_Washe gari_


Jiki a sanyaye ta shigo cikin gidan domin ta tabbatar ba wata tarbar kirki zata samu daga gurin mutanen gidan nasu ba.


Babansu kawai ta samu a gidan sai Saminu da kuma Yayanta Zubairu duk acikin d'akin baban nasu kowa ya buga tagumi


Cikin murna da farin cikin ganinta Zubairu da Saminu suka tarbeta, yayinda babanta ko kallon tsiyama bata isheshi ba, dan koda ta gaishe shima ko amsawa baiyi ba, saima jifanta da yayi da bak'aken magan-ganu"Yaga dama ya maidoki gida kenan?" Yana gama fad'ar haka yayi ficewarsa daga gidanma gaba d'aya


Bata bi ta kansa ba saima matsawa da tayi inda Zubairu yake ta zauna"Yaya Allah yasa dai wannan maganar bata bayyana kowa yaji ba?"


"Bayyana kuma na nawa Lauratu? Ai yanzu haka magana har inda bakya tsammani taje, domin Ammi takai maganar Koto, yanzu hakama inaga can ta nufa kinsan gobe ne za'a fara sauararon shari'ar taku"


Canza akalar zancen nasu yayi "Wai Lauratu ina kikaje ne haka kika manta damu har na tsawon kwanaki hud'u ba labarinki, nidai nasan abinda su Ammi suke tsammani akan Umar ba gaskiya bane, dan dai ba yanda za'ayi na k'aryatasu ne kawai shiyasa nayi shuru na bisu a hakan?"


"Wallahi yaya ina Funtuwa gidan Yaya Jamila dukda dai nasan kai kad'ai ne wanda zai iya yarda da hakan" Cikin kuka take mayar masa da amsa, domin aik-aikar uwar tata ta wuce duk inda take tsammani.


*******


Durk'ushe take agaban mahaifiyar tata sai faman rok'onta takeyi akan tayi hak'uri ta janye wannan k'arar data shigar tunda ga wacce akeyi dominta gata ta dawo gida


Da bud'ar bakinta sai cewa tayi"Ai Lauratu dama kin daina 6atawa kanki lokaci domin aikin gama ya riga ya gama, maganar k'ara banga ubanda ya isa yasakani na janyeta ba, saboda Umar ya cuceni iya cuta, inba Kotun ba banga wanda zai iya yi mana tsakani dashi ba, kwana hud'u fa kina 6oye a gunsa, Allah kad'ai yasan abinda ya faru acikin wad'annan kwanakin" Tana gama fad'ar haka ta rushe da kuka, ita kuka d'iyarma kuka, saidai kowannensu da dalilin kukan nasa.


******


_Da daddaren ranar_


Kwakkwance suke a tsakar gida kamar dai kullum saboda yanayin zafin da ake ciki, yayinda Lauratu ta k'umshe kanta a cikin d'aki ita kad'ai, domin ta tabbata koda ta fito habaici ne da k'ananun magan-ganu zataita cin karo dasu a wajen mutanen gidan.


"Salamu alaikum, wai ance ana sallama da Lauratu" Cewar wani Almajirin kenan yayinda yake tsaye a tsakar gidan


Farat Ammi tayi ta mik'e daga kwancen da take"Muje ka nuna mani mai kiran nata" Ta fad'a tare da bin yaron a baya domin ganewa idanuwanta, dan ko mayafima babu akanta


Ba kamar yanda ta tsammata ba, domin kuwa mota ta gani fake a k'ofar tsohon gidan nasu"Mai waccen motar ne ke kiran nata?" Ta fad'a tare da duban fuskar yaron


Daga mata kai yayi alamar amsawa


Sumui-sumui ta koma cikin gidan domin ba haka taso ba, taso ace Umar ne da yaga ruwan rashin mutunci, sai akayi sa'a bashi d'in bane


"Idan kinga dama kya iya zuwa ana nemanki a waje, idan kuma kinga dama kya iya yin zamanki domin dama ba jin maganar iyayenki kikeyi ba sai maganar ubanki Ummmaru" Ta fad'a tare da sakin labulen d'akin data d'aga


Badan taso ba ta nufi k'ofar gidan inda akace ana kiran nata, domin inma bataje ba tasan wani k'arin laifin ne zatayi, itako so take ta lalla6a uwar domin janye k'arar data shigar akan Umar.


"Akace wai kana kirana lafiya daiko?" Ta fad'a fuska a d'aure yayinda ta k'arasa bakin k'ofar motar inda mamallakin motar yake zaune yana dubanta


Murmushi yayi kana ya kuma dubanta "Yanzu duk islamiyyar nan da kiketa zaryar zuwa har yanzu baki iya sallama a mutane ba?"


Harara ta kuma galla masa karo naba adadi"Ban iya ba d'in, inda na iya aida kaji nayi maka, fad'i abinda zaka fad'a kai tsaye ina sauri ne domin inada aikinyi a ciki" Ta fad'a tare da kallon hanyar gida


Murmushin dai ya kumayi "Ni banida abin fad'a tunda inada budurwa, bansani ba ko wannan matsoracin na bayan mota yanada abin cewa agareki ba" Ya fad'a tare da nuna mata kujerar baya inda Farouq d'inta yake kwance


"La! Umar ashe dama kaine a ciki kuka tsaya kuna zaulayata" Ta fad'a fuska cike da fara'a gami da annashuwa


"Ato ai na zaci zakiso mai mota ne ki bar mai tsohon mashin irina?" Ya fad'a cikin alamu na zaulaya


"Haba, Haba, mai jirgima ai yayi kad'an bare kuma wani mai mota can" itama ta mayar masa


Canza akalar zancen nasu yayi domin sauri sukeyi"Yakamata dai nayi sauri nayi abinda ya kawoni kamin a kai ga samun matsala, kinsan marar gaskiya wai hausawa sukace ko cikin ruwa gumi yakeyi"


"Ina jinka" Ta fad'a yayinda take y'an waige-waigenta domin gudun yin kaci6us da yaya babba


"Kamar dai yanda kika sani Lauratu, abubuwa da dama sun faffaru a cikin wa'yannan kwanakin, da wad'anda kika sani dama wad'anda baki sani ba...


"Ciki kuwa har wasu y'an bulalai da wani bawan Allah yasha a lokacinda yana bacci" Cewar abokin nasa kenan yayinda yake dariya tare da duban fuskar Umar d'in


"Kamar yaya bulalai?" Ta tambaya tare dadubansu su duka cikin alamu na mamaki


"Kinga manta dashi dan Allah wai labarin wani mafarki da nayi ne yakeso ya baki"


Dariya itama tayi kana taci gaba da duban masoyin nata cikin shauki


"Lauratu babana yazo yasami iyayenki akan janye maganar k'ara da sukayi, akan yanaso su sasanta su fahimci juna basai ankai maganar a bainar jama'a ba, amma fafur sunk'i yarda da hakan, sun kafe akan cewa lallai saidai na fito ayi mana aure yanzu ko kuma Alk'ali yayi mana tsakani dake, a cewarsu idan kuma kin kafe a lallai bazaki rabu dani ba, tofa saidaifa Alk'ali ya baki za6i kodai su ko kuma ni, saboda haka nazo na fad'a maki duk runtsi Lauratu karki kwayewa iyayenki baya a bainar jama'a, domin ni zaki iya canzani a kowane lokaci, su kuwa har abada bakida sunan da ya wuce Lauratu d'iyar Harisu kuma d'iya ga Ammi, ina fatan zakiyi mani Kyakkyawar fahimta?"


"Abinda ban fahimta ba Umar, wai kana nufin Alk'ali zai iya rabani dakai kenan haihata-haihata?" Tafad'a yayinda hawaye ke bin fuskarta


"Lauratu dan Allah kidaina wannan kukan naki, idan ina ganinki cikin damuwa nima hankalina bazai ta6a kwanciya ba, yakamata mu k'arfafawa junanmu guiwa, bakigama ni dariya nakeyi ba? ko kina nufin ni abin baya damuna ne? Allah ne kawai zai iya kawo mani d'auki acikin wannan matsalar ba dabararmu ba"


"Umar wannan karon kaina ya d'aure sosaifa, saboda bansan me zai faruwa damu ba idan akaje koton, kuma kaga..


"Karki damu da wannan Lauratu, Umar naki ne har abada, babu Alk'alinda ya isa ya rabamu sai Alk'alin Alk'alai rabissamawati, da sannu komai zai zama tarihi insha Allahu Lauratu"


Suna cikin tattaunawa ne Yaya Kabir yazo wucewa"Umar ga Yaya Kabir nanfa zai wuce ta nan" 


Cikin sauri ya sake kwanatawa a kujerar baya kamar dai yanda yayi sadda sukazo


Ko kallon inda sukema baiyi ba yayi shigewarsa cikin gida abinsa


"Yakamata ki shiga gida hakanan tun kamin asirinmu yakai ga tonuwa, sai kuma goben idan mun had'u a kotu"


Murmushin k'arfin hali tayi"To Allah ya kaimu goben lafiya" Ta fad'a a tak'aice


Har ta juya zata shiga gida ya dakatar da ita domin sakata nishad'i ko yaya ne"Am wai nace yaushe zaki biyasa kud'insa ne?"


Cikin mamaki ta juyo tare da dubansu yayinda suke k'yak'yata dariya su duka "Waye zan biya kud'insa kuma?"


"Kin manta wanda ya kaiki tashar mota inda kika hau motar zuwa Funtuwa?" Har yanzu dai basu daina yi mata dariyar ba


Itama dariyar tayi tare da rugawa a cikin gida, domin ba shakka ta tabbatar mashin d'in da ta hau na abokinsu ne, "lallai nayi abin kunya ta fad'a acikin ranta.Shi kam hankalinsa ya kwanta domin dama buk'atarsa bata wuce ta ganin abar k'aunarsa tayi dariya ba...
*KOTU*
Koda yake muje zuwa dai number 13 domin jin chakwakiyar da za'ayi a can d'in.
Maman Ja'afar

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [01/05, 12:03 a.m.]

*💘SUNE SILA💘*       11Daga alkalamin

MamanJa'afar✍
"Ina ganinfa da tsohuwar tasha da sabuwar tasha duk ba zaki sami motar zuwa Funtuwa a can ba, ina ganin sai dai mu nufi tashar K'ofar y'an d'aka kawai" Cewar mai shin d'in kenan yayinda yake sassauta gudun nasa kasancewar yanzu su Ammin sun daina bin nasu tunda sun riga sun 6ace masu


"Nidai koma ina ne nidai kaini kawai indai ka tabbatar agun zan samu motar zuwa inda nakeso" Ta fad'a masa a tak'aice


Cikin mintinan da basufi biyar ba suka samu isowa K'ofar y'andakan


Tun kamin su iso taketa faman tunanin yanda zatayi da mai mashin d'in kasancewar babu ko sisi ajikinta, gashi kuma yayi tafiya mai nisa da ita bayan y'an zagaye-zagayen 6adda sawu da yayi tayi da ita


A daidai lokacin da suka faka a bakin tashar ne a kuma daidai wannan lokacin wata dabara ta fad'o mata a rai


"Yauwa Malam d'an jirani anan dan Allah na mik'awa yayana sak'o gashi can sai ka mayar dani" Ta fad'a yayinda take nuna masa wani mai sayar da takalmi


"Ba damuwa ai duk cikin aiki ne, wai d'an sanda ya kama kare" Ya fad'a da zaulaya yayinda ya kashe mashin d'in nasa ya gyara zama domin jirantaGurin wannan mai sayar da takalman ta nufa tare da fara tayawa, shi kuma mai mashin d'in a tsammaninsa mai takalman shine yayan nata, shiyasama tun yana lura da ita har dai yakai ga ya shareta, saima d'auko dasta da yayi yaci gaba da goggoge mashin d'in nasa


Saida taga ya daina kallon nata kana ta samu damar kutsawa a cikin tashar inda motoci suke


"Ina na Funtuwa? Ina na Funtuwa?" Cewar wani kare kenan daga cikin karnukan motar


Batare da 6ata lokaci ba Lauratu ta kutsa kai cikin motar Funtuwar, cikin mintinanda basufi talatin ba motar ta gama cika


Da d'aya d'aya karen motar yake kar6ar kud'in motar fasinjojin nasu har zuwa lokacin da ya iso kan Lauratu ya mik'o mata hannu alamun ta mik'o masa


"Ban gane abinda kake nufi ba" Ta fad'a tare da yin fuska sai kace wata mai gaskiya


"Kud'in motarki nake nufi d'ari bakwai baiwar Allah"


"Sau nawa ake biyan kud'in motar taku ne? Bayan wanda na baka sadda zan shigo wasu kud'in kuma kakeso na k'ara maka na daban?"


Nandai rigima ta kaure tsakanin karen mota da kuma Lauratu


Mutanen cikin motar wasu na bayar da hak'uri wasu kuma banbami sukeyi akan za'a 6ata masu lokaci


Da dai direban motar yaga babu sarki sai Allah, dole ya bawa karen motar hak'uri shi kuma ya d'auki asara yaja motar suka lula badan ransa yaso.


********


Anan gida Katsina kuwa hankullan kowa sunyi k'ololuwa wajen tashi, musamman ma Ammi da hawaye suka kasa gabcewa akan fuskarta, ta kasa tsaye kuma ta kasa zaune, sai faman safa da marwa takeyi tana k'ara nanata tsinuwa da la'anta akan Umar, domin ita a tsammaninta wai Umar ne ya shirya wannan gadar zaren ta 6atan Lauratu


Duk inda ake tsammanin ganin Lauratu anje amma ba'a sameta, hatta islamiyyarsu saida Zubairu yaje nemanta, amma shuru kakeji tamkar an shuka dusa


Tun Mahifin Lauratu bai yarda akan cewa Umar ne ya sace Lauratu ba hardai shima yazo ya fara yarda da hakan, domin izuwa yanzu basuda wani abin zargi daya wuce shi Umar d'in.


********


_Da daddare_


Bayan an idar da sallar isha a masallacin unguwar tasu ne Malam Garba ya mik'e domin nufar hanyar gida


"Am dan Allah Malam idan badamuwa inason ganinka a waje" Cewar Kabiru kenan yayinda yaketa wani ciccin magani sai kace bada sa'an ubanshi yake magana ba


"Allah yasa dai lafiya?"Ya fad'a a tak'aice domin yasan ba wata girmawa bace ba a tsakaninsu da Kabirun tun lokacin da soyayyar Umar da Lauratu ta fara bayyana


Wajen masallacin suka fito kana Malam Garba ya dubi Kabirun "Ina jinka Allah yasa dai ba wani abin ne ya faru ba?"


"Ai bama wani abu ya faru ba, abubuwa da dama sun faffaru, a ciki kuwa harda sace mana k'anwa da d'anka Umar yayi, saboda haka nake jan kunnenku tun wuri tun muna shaida juna, wallahi ka fad'awa d'anka ya fiddo Lauratu duk inda ya kaita ya 6oye, in kuma ba haka ba, za'ayi maimaici wallahi" Yana gama fad'ar haka ya juya yayi tafiyarsa tare da barin Malam Garba anan tsaye yana binsa da kallon mamaki, a zuciyarsa kuwa cewa yakeyi "Ba laifinka bane ba Kabiru "duk haihuwa ce taja mani wannan, badan na haifi Umar da babu abinda zai had'ani da kai harda zakazo kana gaigaya mani magan-ganu haka sai kace wani sa'anka.

*****

Tun safe ake neman Lauratu amma har gashi yanzu kusan k'arfe sha biyu na dare na shirin yi amma har yanzu ba'a jiyo labarin ko alamun inda take ba


Hankulla kam sun tashi matuk'a, musamman ma hankalin Umar da kusan yafi na kowama tashi, domin bansan yama zan kwatanta maku iya tashin hankalinda Umar ya shiga ba.


********


Matsakaicin gida ne mai kyawun gaske, saidai ba'a iya sakashi a jerin gidajen masu kud'i ba, kamar kuma yanda baza'a iya sakashi a jerin gidajen talakawa ba


Farkon gidan get ne zaka fara tararwa kana farfajiya, idan kuma ka d'anyi gaba kad'an shine zaka samu damar shiga gurin ahalin gidan


Matsakaicin falo ne mai d'auke da d'akunan kwana guda biyu, sai dai kowannensu da ban d'akinsa a ciki sai kicin da akayi a gefe guda na falon.


Zaune take ita kad'ai tayiwa Tv k'uru tamkar mai yin kallon a gaske, sai dai a zahirin gaskiya ba kallon film d'in Indian bane a gabanta, tunanin da ta sabayi ne kawai ke faman d'awainiya da zuciyarta.


"Assalamu alaikum" Lauratu ta fad'a yayinda take kutso kai a cikin falon yayar tata


Kamar a mafarki taji muryar K'anwar tata Lauratu


Cikin murna da farin ciki da annashuwa Jamila ta tarbi k'anwartata


Bayan sun natsune Lauratu ta dubi yayar tata "Yaya wai ina yaran nawa ne yau na ganki ke kad'ai a cikin gida shuru?"


"Lafiyansu kalau Wallahi kinsan yau asabar ba karatu shine babansu ya d'aukesu ya kaisu gun Hajiyarsa, inaga k'ilan su dawo anjima ko kuma ya barosu can su kwana shi kuma ya dawo shi kad'ai"


Canza akalar zancen nasu tayi "Wai Lauratu lafiyanki kuwa na ganki wujiga-wujiga haka tamkar ank'watoki daga cikin bakin kura? Nidai kin sakani a shakku wallahi domin tunda nayi aure ban ta6a ganinki kinzo gidan nan ke kad'ai ba saidai ko tare da Zubairu koda Ammi"


Numfasawa tayi"Hmm yanzu dai kamin wannan zancen abani abinci tukun, yunwa nakeji, wallahi rabona da abinci har na manta, ruwa kawai naketa d'add'aka har cikina ya kusa k'ulle...


Cikin firgici yayar ta dubi K'anwarta "Meke faruwa dake haka Lauratu?"


Bata tsaya mayar mata da amsa ba, saima afkawa kicin da tayi domin nemawa kanta abinda zataci


Saida ta gama cin abincin natane tsab kana ta dubi yayar tata d'auke da murmushin k'arfin hali a fuskarta "Ke kam yaya Jamila kinji dad'inki wallahi, zamanki kawai kikeyi bakida wata damuwa, muko kinbarmu can sai faman neman na abinci mukeyi"


Murmushin takaici yayar tata tayi kana ta dubeta "Nidai ba wannan ba fad'a mun damuwarki dan Allah domin dukda na dad'e ban ganki na tabbatar da jikinki ba haka yake ba kin rame sosai wallahi"


Nan take Lauratu ta kwashe dukkan labarin abinda ke faruwa tsakaninta da Ammi ta fad'a mata, hatta kwananda tayi a Folisteshan da kuma guduwar da tayi zuwa nan d'in duk saida ta kwashe ta sanar mata


Tun kamin ta k'arasa bata labarin hawaye keta faman safa da marwa akan fuskar yayar tata, itama Lauratun tana bata labarin amma kuka na neman yaci k'arfintaSaida suka natsu da kukan nasu kana Jamilar ta dubi Lauratu


"Nikam a cikin iyaye na rasa gane kalar Ammi ko wace iri ce wallahi, ke shikenan kullum gurinki na akan y'ay'a mata? kullum tunanki ta sanadiyarsu zakiyi azziki? wannan wace irin rayuwa ce haka? Inda ace sun kula damu matan da mazan gaba d'aya, su bamu ilimin addini dana zamani, su kula da tarbiyyarmu yanda yakamata, na tabbata acikinmu mu biyar d'in nan baza'a rasa wanda zai tallafa masu ba zuwa yanzu, to amma...


Katseta Lauratun tayi"Amma Yaya ai naga ke bakida wata matsalar komai kamar Yaya Halima da Miji ya tsangwameta dan bata ta6a haihuwa ba"


K'ara yin murmushin tak'aici tayi karo na ba adadi "Lauratu kedai ki ganni kawai, mutane sai suyita ganin kamar ina cikin hutu ko jin dad'i da makamancin haka ne, amma ni kad'ai nasan abinda ke d'awainiya da zuciyata tsawon zamana a gidan nan wallahi"


"Abin mamaki" Lauratu ta fad'a a tak'aice tare da sake dubanta


"Wallahi tallahi Lauratu kinji dai rantsuwar d'an musulmi ko? tunda na auri babansu Ahmad ban ta6a samun farin ciki na daidai da rana d'aya ba a rayuwata, kullum zuciyata cikin k'unci da bak'in ciki take"


Duban Lauratun ta kumayi "Lauratu kedai ki ganni ina dariya kawai iya fuska, amma rabona da nayi dariya tun daga fuska har zuci na dad'e da manta lokacin wallahi"


Da mamaki Lauratun ta kuma dubanta, Jijjiga kai tayi"K'warai kuwa Lauratu, tunda nake da babansu Ahmad ko daidai da k'wayar zarra ban ta6a jin ina k'aunarsa a cikin zuciyata ba, kawai dai nayi biyayya ne ga Ammi na danne zuciyata na aureshi amma badan inaso ba, har yau har gobe Aminu nakeso kuma Aminu ne acikin raina, Lauratu har na koma ga mahaliccina bana tunanin zan daina k'aunar Aminu, kawai fa dan bashi da kud'i Ammi ta hanani aurenshi, wai a lallai sai inda zan huta suma su huta, to gashi nan su basu hutan ba ni d'inma kuma zuciyata bata huta ba, hutun gangar jiki ai iska ne domin....


"Amma Yaya kiyi hak'uri karkice nayi maki rashin kunya dan Allah, wai shin tayaya kikayi hak'uri kika zauna da wanda bakyaso har na tsawon shekaru nan kusan goma, dad'in dad'awa kuma harda albarkar yara a tsakaninku?"


"Lauratu kenan! Idan ban zauna ba, ya kikeso nayi? Na dawo gidanku na zauna Ammi tana kasa rayuwata a faranti tana siyarwa kamar goro? Na tabbata wallahi idan da za'a ce na dawo gidanmu da sunan yaji, wallahi wata ran na tabbata abincin cima sai ya gagareni, shiyasa a kullum na tuna da hakan nake lallasar zuciyata tare da tuna halinda yarana zasu shiga idan bana nan, da kuma wanda ni zan shiga agun mahaifiyata sai nayi hak'uri nayi zamana a gidana, nidai rok'ona a gurin Allah yasa iya wahalar kenan ta nan gidan duniya zan sha, ya bani ladar hak'uri da Kuma juriyar da nayi a gobe k'iyama" Tana magana tana kuka abin gwanin tausayi


Itama Lauratun kukan takeyi domin k'warai tausayin yayar tata ya ratsa zuciyarta matuk'a


"Kuma Yaya a...haka kuke kwanciyar..aure dashi?"


"Yana iya Lauratu? kana auren mutum ba dole ka kwanta dashi ba koda azuciyarka ba haka kaso ba? Ina kwanciya dashi mana lafiya lau saidai ban ta6a jin dad'in hakan ba ko kad'an acikin zuciyata, Lauratu kedai kiga ina dariya kawai a fuska amma Allah kad'ai yasan adadin damuwata a 6oye"


Ajiyar zuciya Lauratun tayi "Wallahi da ace ana canza uwa da tuni na....


"Kul kar na kuma jin irin wannan maganar Lauratu"


*******


_Bayan kwana hud'u_


Zaune yake a bakin k'ofar gida da butarsa a kusa dashi yana alwalla domin tafiya sallar magaribaSallama yaji anyi masa tare da mik'a masa hannu kai tsaye "Ina fatan kaine Malam Garba ko?" Mutumin ya fad'a a tak'aice


"Kwarai kuwa nine Malam Garba ina fatan lafiya dai ko?" Ya fad'a d'auke da mamaki akan fuskarsa domin bai ta6a ganin mutumin ba ko a hanya"Ehto lafiya sai dai ba lau ba, domin Sammaci ne aka bani daga Kotu akace na kawo maka" Ya fad'a tare da mik'awa Malam Garba takardar dake a hannunsa


"Anya sak'ona ne kuwa bawan Allah? kodai kayi 6atan kai ne ba nan aka turo ka ba?" Ya fad'a tare da mik'awa tsaye har yanzu dai mamakin bai kau a fuskarsa ba


"K'warai naka ne Malam Garba, domin na tabbata bazaka rasa sanin Umar wanda ake zargin ya 6oye Lauratu ba ko?"

Maman Ja'afar

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [03/05, 12:35 a.m.]

*💘SUNE SILA💘*       13Daga alkalamin

MamanJa'afar✍
Yau mun wayi gari ranar Litinin ranarda tazowa dukkan 6angarorin guda biyu wata kalar rana, domin tun daga kan gidansu Lauratu har izuwa gidansu Umar babu wanda ya wayi gari a cikin farin ciki, kowannensu da akwai abinda yake sak'awa a cikin zuciyarsa.


"Waike har yanzu baki gama shiryawar bane kika tsaya sai faman Dibi-dibi kikeyiwa mutane? Cewar Ammi kenan yayinda take a tsaye a bakin k'ofar d'aki tana jiran fitowar Lauratun


Itako Lauratu inbaya ga fad'uwa babu abinda gabanta yakeyi, domin tunda take a rayuwarta ko kallo ko sheda bata ta6a zuwayi a kotu ba, amma wai sai gashi yau saboda tsabar son zuciya da kuma kwad'ayin abin duniya irin na mahaifiyarta, wai a wad'annan k'ananun shekarun nata wai itace zata tsaya a gaban Alk'ali da sunan ana yin shari'a da ita, kai wannan zubewar mutunci ya kai inda ya kai.


"Kinga Ammi muje kawai idan ta gama shiriritar ta biyomu daga baya, ni dama kunyar jerawa nakeyi da ita, wai ace dan tsabar rashin mutunci bazaki iya rabuwa da saurayi ta cikin ruwan sanyi ba har sai ankai magana zuwa koto, wato ke kinfi sonshi akan iyayenki ko? Kin gwammace ki mutuntashi su kuma iyayenki ki wulak'antasu a bainar jama'a ko? Indai duniya ce ai gaki gata nan ta ishi kowa riga da wando" Cewar Yaya Kabiru kenan yayinda shima yake a tsaye a k'ofar d'akin suna jiranta


"Yaya kuje kawai, inyaso zan jirata ta gama sai mu taho tare kawai" Cewar Yaya Zubairu kenan murya a sanyaye, yana magana tamkar mai shirin yin kuka


Kamar kuwa yanda suka fad'a tafiyar tasu sukayi, da Ammi da Yaya Kabir sai kuma Saminu da kuma babansu.


Cikin d'akin Yaya Zubairu ya shigo tare da zama a bakin gado inda take a zaune


"Lauratu kinsan me nakeso dake?" Ya fad'a yayinda yake duban fuskarta


Girgiza masa kai tayi alamun amsawa, domin idan ta bud'a baki da niyar yin magana babu abinda zai hana kukanda take k'umshewa ya su6uce mata


"Lauratu duk runtsi karki juyawa Umar baya kinji? Umar shine mai sonki da gaskiya kuma shine wanda zai k'aunaceki ya mutuntaki a duk halinda kika samu kanki a ciki, wallahi Lauratu idan har ba Umar d'in ba bana tunanin akwai wani namijin da zai iya aurenki kuma ya mutuntaki a wannan halinda iyayenki suke ciki na zubar maki da mutunci, Lauratu su Ammi sun riga sun shafa maki bak'in fentin da har abada bazai ta6a kankaruwa a tattare dake ba, amma ina mai tabbatar maki idan har kowa na duniyar nan zaiga wannan fentin naki wallahi na tabbata Umar bazai ganshi ba" Yana magana hawaye na bin fuskarsa abin tausayi


Hafsatu ce ta shigo d'akin tare da zama a gefen gadon itama inda Lauratu take zaune


"Lauratu maganar Zubairu gaskiya ce, duk runtsi karki yarda a rabaki da farin cikin ki kinji? Domin ko kin rabu da Umar bana tunanin Ammi zata baki farin cikinda yakamata ace ta baki a matsayinta na uwa agareki, haka kuma duk wanda zaki aura idan ba Umar ba, bana tunanin zaki samu natsuwa dashi yanda kikeso bare kuma ayi tunanin samun wani farin ciki a cikin zamantakewar auren"


Dago kai Lauratu tayi tare da duban fuskarta alamun tambaya


"K'warai kuwa Lauratu domin duk wanda zaki aura gangar jikinki kawai zai aura amma ruhinki na tabbata yana tare da Umar, saboda haka ku tsaya tsayin daka wajen ganin kun k'watowa kanku farin cikinku da kanku, karki manta da addu'a yayin shiga koto kinji?" Ta fad'a tare da dafa kafad'un Lauratun d'auke da murmushin k'arfafa guiwa akan fuskarta


Jijjiga kai Lauratun tayi alamun amsawa kana ta jawo hijabinta ta saka suka rankaya itada Zubairu sai kotu.


********


Zugar mashina ya gani a kofar gidan nasu sun kusan ashirin a jejjere tamkar ana d'aurin auren d'aya daga cikinsu


Cike da mamaki yake duban fuskokinsu d'aya bayan d'aya


"Wai ku da kukayo wannan irin zugar haka ina kuke nufin zakuje ne?" Ya fad'a d'auke da murmushi a kan fuskarsa dukda Allah ne kad'ai yasan iya damuwar da yake tattare da ita a cikin zuciyarsa


D'aya daga cikinsu ne ya fara magana cikin d'aga murya


"Munji ance ne ankaika k'ara koto, to shine mukazo dan muyi maka rakiya koda buk'atar tsageru irinmu zata taso a gurin koya kukace?" Ya fad'a tare da duban fuskokinsu


Dariya yayi kana ya k'araso inda suke a tsaitsaye duk ya mimmik'a masu hannu suka gaggaisa


"Abinma duk bazai kai haka bama insha Allahu, karku manta iyayenfa Lauratu ne zamuyi shari'ar nan dasu, kunga ko aiko a lahira wani nacin albarkacin waniko?" Ya fad'a tare da dubansu yana murmushi (Kunsan da yana aca6a da kuma yan Tasi akwaisu da had'in kai da kuma nuna kara akan abinda ya shafi waninsu)


Da k'yar dai ya samu ya lalla6asu suka kama hanya sukayi tafiyarsu.


********


Kotun ta cika tayi mak'il da jama'a, wasunsu k'ara suka kawo, wasunsu kuma kallo sukazoyi, domin kuwa har y'an unguwarsu Lauratu mafiya yawansu saida sukazo kallon wannan 6arin mutunci da za'ayi a kotun.


Lauratu da iyayenta suna gefe guda a zaune, yayinda shima Umar yake gefe guda a zaune tare da iyayensa da saun y'an'uwa.


******


Tsawa Alk'alin ya daka ma mutanen da keta faman surutu tare da buga gudumarsa akan teburin da ke gabansa alamun jama'a su saurara kenan


Domin a lokacin cikin sauraren wata k'arar yake kamin ya juyo kan tasu Lauratu


Bayan an saurara ne ya dubi matar dake tsaye agabansa tare da mijin nata dake gefe guda


"Baiwar Allah kikace kinaso a raba aurenku da mijinki ko ba haka ba?"


"Eh Allah gafarta Malam haka nace" Ta fad'a a tak'aice


"Ko zaki iya fad'awa kotu dalilinki na son rabuwa dashi?" Ya fad'a yayinda yake duban fuskarta


"Babu wani dalili Allah gafarta Malam" Ta k'ara fad'a a tak'aicen dai


"Duk wasu hakk'oki naki da suka rataya a wuyansa yana k'okarin sauke makisu duka ko kuwa dai akwai inda ya gaza?"


"Eh Allah gafarta Malam babu abinda ya gaza gurin kula dani, kawai dai sonshi ne banayi yanzu"


"Dama can auren dole akayi maku ke dashi ne ko kuwa ya abin yake?" Ya fad'a yayinda yake dubanta ta cikin gilashin idonsa


"A'a, Allah gafarta Malam auen soyayya ne mukayi dashi, ina sonshi yana sona" Ta fad'a kanta sunne a k'asa


Ammi ce ta ta6o Lauratu daga inda take zaune a kusa da ita "Kinga irinta ba"


Juyawa Alk'alin yayi inda mijin yake a tsaye "Bawan Allah ka tabbatar abinda matarka ta fad'a gaskiya ne babu wata k'ulalliya a ciki?"


"Haka maganar take Ya mai shari'a, lokaci d'aya kawai naga ta canza mani ta dawo kamar ba ita ba" Ya fad'a a tak'aice Cikin ladabi


Shuru Alk'alin yayi na d'an wani lokaci "To Baiwar Allah Kotu zata raba aurenki da mijinki kamar yanda kika buk'ata tunda bamu san irin cutuwar da kikeyi a zamantakewarku dashi ba, amma a bisa sharad'i guda d'aya"


D'ago kai sukayi su duka tare da duban Alk'alin


"Tunda ke kika nemi sakin zaki biya mijinki kud'i kwatankwacin yanda zai iya auren wata matar kana sai ki dawo nan mu sawwak'e maki idan shi bai sawwak'e makin ba, sannan kuma kotu ta d'age saurar wannan k'arar taku zuwa ashirin da biyar ga wannan watan da muke ciki, Maga takarda karanto mana k'ara ta gaba" Ya fad'a tare da mayar da gilashin shi


Mik'ewa maga takardan yayi kana ya fara bayaninsa kamar haka


"Allah ya gafarta Malam k'ara ta gaba da zamu saurara itace tsakanin Malama Tani da kuma Umar, wanda take k'ararsa akan yak'i auren d'iyarta k'arshema sai ya koma yana yin lalata da ita y'ar tata, bayan kuma ya hanata kula kowa acikin manema aurenta, da wannan ne take rok'on wannan Kotu mai alfarma akan tayiwa Umar da Lauratu tsakani tunda ba aurenta zaiyi ba" Yana gama fad'ar haka ya koma ya zauna a mazauninsa


Da jin wannan kalami na maga takarda Lauratu batasan lokacin da wani matsanancin kuka ya su6uce mata ba


Shima Umar ba k'aramin firgita yayi da jin wannan kalamin na Ammi ba, shi kam baiyi kuka ba, amma idanuwansa sun kad'a sunyi jajir alamar 6acin rai k'arara akan fuskar tasa


"Kotu tana buk'atar ganin Umar da kuma Lauratu agabanta" Alk'alin ya fad'a a tak'aice


Ckin kukan dai daya riga ya gama zame mata jiki ta mik'e ta nufi inda aka tanada ga wad'anda ake tuhuma


Shima jiki a sanyaye ya nufi d'ayan gurin ya tsaya inda yake fuskantarta


"Lauratu kinji abinda mahaifiyarki ta fad'a, gaskiya ne abinda ta fad'a ko kuwa ba gaskiya bane" Ya fad'a yayinda yake duban fuskarta"A'a Allah gafarta Malam ba haka maganar take ba, domin ko wani abu makamancin hakan data fad'a bai ta6a shiga tsakanina da Umar ba, kawai dai yace abashi lokaci ne ya ida shiryawa kana muyi aure shine take ganin kamar haka abin yake" Tana magana hawaye na bin fuskarta


"Umar haka maganar take ko kanada wani k'arin bayani akai?" Ya fad'a yayinda yake duban fuskar Umar d'in


"Allah gafarta Malam hakane kamar yanda Lauratun ta fad'a" Ya fad'a kansa a duk'e a k'asa saboda kunyar jama'ar gurin da yakeji wad'anda sukayo masu k'uri da idanuwa sai kace zasu cinyesu"Da gaske kana sonta kuma itama tana sonka?" Ya fad'a yayinda yake dubansu d'aya bayan d'aya 


"Hakane Allah gafarta Malam muna son junanmu" Ya fad'a a tak'aiceItama Jijjiga kai tayi alamun amsawa"Kotu tana son ganin iyayen wad'annan yaran maza a gabanta" Cewar Alk'ali kenan yayinda yake duban mutanenda ke zazzaune gabansa


Batare da 6ata lokaci ba Malam Harisu da kuma Malam Garba suka harrala a gaban Alk'ali


"Kai Malam Harisu idan akace Umar ashirye yake zaka iya bashi auren y'arka Lauratu ko kuwa bakada niyar yin hakan?"


"K'warai kuwa ya mai shari'a a shirye nake dana bashi aurenta mana, domi duk wani mai d'iya mace datakai kamar wannan ai bashida wani gurinda ya wuce ace ya aurar da ita"


Juyawa yayi gurin Malam Garba "Me yasa bazaka amincewa d'anka akan auren wannan yarinya Lauratu ba?"


"Ai Allah gafarta Malam ni ba hanawa nayi ya aureta ba, kawai dai cemasa nayi ya bari ya samu k'wakk'warar sana'a ne tukun yayi auren dan kada yaje ya wahalar masu da d'iya, amma tunda abin ya zama da haka, ko yanzu a shirye nake dana amince Umar ya auri Lauratu a lokacin da iyayenta suka buk'ata, amma ina neman alfarmar kotu akan ta barmu muje gida mu sasanta kanmu damu da iyayen ita yarinyar""To ku kunji abinda mahaifin yaro ya fad'a, mu kuma a kullum sasanci mukafiso akan a ringa rigin-gimu, amma ku ya kuka gani tunda kuma iyayen yarinya kunada hakk'i akan hakan?"


"Ehto ai kowa dama ya fison sasancin, nima dai na amince da hakan, amma a iya tambayar mahaifiyar ita yarinyar aji ta bakinta tunda itace mai k'arar" Yana magana yana wani waige-waige sai kace Ammin ce mijin shi kuma matar


"Maganar maza akeyi Malam Harisu ba maganar mata ba, ka amince ko baka amince ba faqat?"


"Ehto na amince Allah gafarta Malam, na amince" ya fad'a murya a sanyaye tamkar mai jin tsoron wani abu


"Kotu tana umartarku dakuje gida ku sasanta kanku, idan kuma hakan ta gagara kwa iya dawowa bayan sati uku"


Da wannan shari'ar tasu ta tashi kowa ya kama gabansa.


A 6angaren Ammi ba k'aramar kunya tasha ba a gurin, domin ita a tsammaninta kotu zatayiwa Umar da Lauratu tsakani ne kawai, sai kuma taga akasin hakan, shiyasa ta d'au alwashin indai tana raye bazata ta6a bari Lauratu tayi irin wannan wulak'antaccen auren ba, ta d'auri aniyar saita tsaya tsayin daka wajen ganin wannan tantirin talakan bai auri y'arta ba, dama can ta tsanesa, sai kuma ga abinda ya faru a yau wanda shima ya k'ara lillinka tsanarda takeyi masa a cikin zuciyarta.


A 6angaren mahaifin Umar kuwa shima yayi alwashin indai yana raye sai ya tsayawa d'ansa tsayin daka wajen ganin ya mallakin burin zuciyarsa tunda abin yazo da haka kodanma ya k'unsawa Ammi haushi sai yaga abinda ya turewa buzu nad'i.


Lauratu kuwa da Umar bazamu iya fasalta maku halinda suka shiga ba, shin farin ciki zamu kira hakan ko kuwa bak'in ciki? Muje zuwa dai number 14 domin chakwakiyar bata k'are ba.....
Maman Ja'afar

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [05/05, 12:06 a.m.]

*💘SUNE SILA💘*       14Daga alkalamin

MamanJa'afar✍
Yauma dai kamar yanda ta saba kullum, cikin sand'a tare da y'an raka6e-rakabenta ta shigo cikin gidan nasu


Batayi k'okarin nufa cikin d'aki ba domin tasan kota shiga ba wata tarbar kirki zata samu daga gurin wad'anda ke cikin d'akin ba


"Lauratu! Lauratu! Yaya Kabiru ne keta faman k'wala mata kira daga can cikin k'uryar d'akin


Gabanta yana fad'uwa ta kutsa kai a cikin d'akin, daidai kutungar k'ofar d'akin ta zauna kasancewar tasan abinda zai biyo baya tunda ta riga ta fad'i gaskiya a kotu wanda su aganinsu tamkar k'aryata mahaifiyarta tayi, murya a sanyaye tace"Gani yaya"


Tun kamin ta rufe bakin nata ta fara jin saukar bulalai tako ina ajikinta


"Yanzu ke dan ubanki dan bakida kunya marar mutunci Ammin zaki k'aryata a bainar jama'a? Kina nufin kin fifita wancen d'an iskan akanmu iyayenki ko? To wallahi wannan iskancin badai a nan gidan ba, dole ki tashi ki bishi inda kika saba binsa, mun sallama masa ke har abada" Yana dukan nata yake fad'ar way'annan magan-ganun, itako Ammi babu abinda take cewa face "K'ara ma shegiya, ai duk ita taja mana wannan masifar da muke ciki, wallahi ji nake kamar na shak'eta ta mutu kowama ya huta gaba d'aya"


Da k'yar dai Lauratu ta samu ta k'wace kanta daga hannun Kabiru da taimakon Hafsatu da Uwani tayi hanyar k'ofar gida a guje


Har k'ofar gidan Kabirun ya biyota yana duka sai kace wata wadda aka kama da kwarto, har saida jama'a suka tsawatar masa kana ya daina dukan nata ya kuma cikin gida yanata faman banbamin fad'an.


*****


Tun azahar take raka6e a k'ofar gidan nan tanata faman razgar kuka har zuwa wannan lokacin da aketa faman kiraye-kirayen sallar mangariba


 Duk wanda yazo wucewa ya ganta a wannan gurin da akwai abinda yake sak'awa a cikin zuciyarshi, wasuma tunaninsu mai yiyuwa cikin shege tayo tunda da dama da yawa mutanen suna ganinta a gurin masu sayar da abinci, wanda wasunsu sukeyiwa kallon karuwai.


Zubairu ma yayi yayi da ita akan ta tashi ta shiga cikin gidan saboda jama'ar daketa kallonta amma fafur tak'i, sai cewama da tayi "Wallahi babu inda zan matsa daga nan, kowa yazo yaga wacce iyayenda suka haifeta suka tsana tamkar basu suka haifeta da cikinsu ba saboda tsabar son zuciyarsu kawai"


A ranar dai haka tayi kwananta rabi a cikin gida rabi kuma a k'ofar gida.


******


A 6angaren mahaifin Umar kuwa babu irin k'okarin da baiyi ba wajen ganin sun sasanta da iyayen Lauratu kan su amince ayi auren a kwanan d'in kamar yanda suka buk'ata, amma abin yaci tura, sun dage akan a lallai sai an sake komawa kotun, wanda mahaifin Umar din yake ganin yin hakan kamar k'ara zubar da wani mutuncin ne


Shiko bawan Allah Umar har Jibiya saida yaje gurin dangin mahaifin Lauratun akan suzo su agaza masu a samu ayi sasanci, amma abin duk yaci tura, domin a k'arshe cemasama sukayi "Aimu mun dad'e da sallamawa Tani Harisu, dan tunda ya aureta komai ya canza daga garesa, yanzu haka rabon da mu gansa ga baki ga hanci dai amma anfi shekara sama da biyar, saboda haka suje can su k'arata mu babu ruwanmu" Jiki ba k'wari Umar d'in ya nufo hanyar gida.


******


Tun daga wannan lokacin Lauratu ta koma y'an ra6e-rabe a gidajen K'awaye, domin kota zauna a nasu gidan ba wani jin dad'in zaman takeyi ba, daga kyara sai tsangwama da habaice-habaice, wani lokacima duka takesaha agurin yayanta Kabiru na ba gaira babu dalili, dan kawai ta musanta maganar Ammi a kotu.


Wani gidan idan taje a sakar mata fuska, yayinda wani gidan kuma za'a d'aure mata fuskar, domin su a tsammaninsu lalatacciya ce shiyasa suke tsoron suma karta lalata masu nasu yaran.


Acikin hakane har ta samu isowa gidansu wata tsohuwar K'awarta wato Halima, wacce rabonta da ita ina tsammanin tun suna tallar gyad'a a tare, da suka fara hankali ne Lauratun ta fara janye mata kasancewar ganin irin y'an take-taken Halimar na yawan son wasa da maza da takeyi.


"Salamu alaikum" Lauratun ta fad'a yayinda take tsaye a tsakar gidan nasu Halima


Saida tayi sallama gurin sau uku kana aka samu damar amsa mata daga can d'akin k'arshe nasu Haliman kenan, domin suma a gidan hayan suke mai d'auke da d'akuna kusan takwas, a tsammanina ma a gidan nasu Halima har maza y'an haya baza'a iya rasawa ba a ciki.


"Wai waye ne ya cika mana kunnuwa da ihu ne haka? Shigo kawai in zaki shigo, inkuma zaki koma ne koma, duk ruwanki keta shafa" Ta fad'a tare da k'ara sautin kid'an da ta kunna acikin babbar rediyon d'akin nasu


Jiki a sanyaye Lauratu ta shigo cikin d'akin tare da yin wata sallamar kuma


Ihu Halimatu ta saka tare da yin tsalle ta rungume Lauratun cikin alamu masu nuni da farin cikin ganin K'awar tata data dad'e bata gani ba


"Lauratu Mai gyad'a yau kuma kece a gidan namu?" Ta fad'a tare da zaunar da K'awar tata a gefenta inda sauran k'awayen nata suke a tsaitsaye sunata tik'ar rawa tare da d'aga wasu kwalaben maganin mura, suna sha cikin nishad'i abinsu.


Halima dai itama yarinya ce da shekarunta bazasu gaza na Lauratun ba, idanma zatafi Lauratun to da kad'an ne, Halima bak'a ce sosan gaske, sai dai da k'arfi da yaji ta mayar da kanta fara ta hanyar siyowa a kanti, doguwa ce mai y'ar k'iba kad'an


Maganar halayenta kuwa ko kad'an baza'a iya kamantasu dana Lauratu ba, domin Halima bayanma shaye-shaye da takeyi har neman maza tana d'an ta6awa, matanma idan ta samu wani lokaci ba bari takeyi ba, shiyasanya akoda yaushe d'akin nasu baya rabo da y'an mata kala-kala


Mahaifin Halima ya rasu ne tun tana y'ar k'arama, a wani qaulinma cewa naji mutane sunayi batada wani uba duk zancen bogi ne


Mahaifiyar ta kuwa irin halinsu d'aya da Ammi, inaga wannan dalilin nema yasa suke k'awance da Ammin, domin itama Halima haka ta taso babu karatun boko bare kuma na arabi, tun tasowarta talla kawai ta bud'e ido da ita, kamin ta fara wayo masu juye suka fara yi mata juyen kayan tallar tata, kuma abin mamaki tunda take kawowa uwar kud'i har yau uwar bata ta6a tambayarta a ina take samu ba, ada uwar aikatau take zuwa yi gidajen masu kud'i, amma tunda Halima ta fara kawo kud'i masu yawa ta daina aikin komai, domin Halima itace komai na gidan, hatta ashana idan babu Halima ce za'a tambaya.


Gaggaisawa sukayi da k'awayen Haliman kana daga bisani Haliman ta kashe rediyon tare da duban Lauratun "Anya lafiyanki kuwa Lauratu naganki duk wani a sukuku kinbi duk kin rame, kodai duk cikin ustazancin ne haka?" Ta fad'a tare da duban sauran k'awayen nata


"Au yau kuma Haly Baby a kwashen naki harda su ustazai a ciki?" D'aya daga cikin k'awayen ta fad'a yayinda suke k'yak'yata dariya su duka wai dan sunga Lauratu da dogon hijabi har k'asa


"Dan Allah Lauratu meke damun ki ne haka?" Ta tambaya yayinda ta tattara hankalinta gaba d'aya akan Lauratun


Nan dai Lauratu ta kwashe komai ta sanar mata har zuwa kotun da sukayi itada Amminta


Cikin alamu na tausayawa ta sake dubanta "Wayyo K'awata, wallahi na tausaya maki sosai, rabuwa da masoyi ba k'aramin ciwo ne dashi ba"


"Wallahi kina 6atawa kanki lokaci yarinya, ai a zamanin da muke ciki yanzu, mutum bashida wasu masoyanda suka wuce kud'i, amma ke har zaki wani tsaya kina 6atawa kanki lokaci akan wani banza can wai d'an aca6a" Dariya suka k'arayi su duka harda k'yak'yatawa a karo na ba adadi


Mik'ewa Lauratun tayi tare da gyara hijabinta ganin izgilancin ya fara yin yawa"To ni zan wuce Halima sai wani lokacin kuma idan Allah ya sake had'amu"


"Haba haba! Ya da tafiya tun yanzu? Dan Allah dawo zauna K'awata, rabu da wad'ancan y'an iskan, haka suke dama da bawa mutum haushi, barama na kira Musty ya siyo mana abinci a Katsina City" (Wani gidan abinci ne a Katsina)


Dayake su Halima bariki ya zaunar masu harda su waya take rik'ewa, nan take ta kira d'aya daga cikin samarin nata Musty ta fad'a masa abinda takeda buk'ata, batare da 6ata lokaci ba kuwa sai gashi ya kawo mata, hardama k'arin abinda bata tambaya ba.


Rabon da Lauratu taci irin kalar wannan abincin harta manta ranar, shiyasa ta saki ciki ta kwashi abinta son rai


Bayan sun natsu ne Halima ta dubeta tare da mik'a mata d'aya daga cikin kwalabenda ke baje a gurin"Dan kur6i wannan, cikin mintina kad'an zakiji kin manta da damuwar da kike tattare da ita gaba d'aya wallahi, mu dukan nan da kika ganmu duk shi muke sha shiyasa kika ganmu ako yaushe cikin farin ciki muke abinmu"


Hararar hannun nata tayi"Shi kuma wannan d'in miye?"


"Sunanshi manta da damuwa" Ta fad'a yayinda take duban fuskar k'awayen nata, suko babu abinda sukeyi inba dariya ba, waisu sunga sabon shiga


Lauratu batayi tunanin komai ba sai damuwar da take ciki, kuma ayanzu dai bata da matsalar da ta wuce wannan d'in, shiyasa batayi wata-wata ba ta kar6i wannan Totalin d'in dake hannun Halima ta kwankwad'e.


*******


Gidan dank'am yake da mata da yara kai kace assibiti ne a wajen, assibitinma 6angaren mata da yara


Da d'ai d'ai matan suke shiga cikin d'akin, suna fitowa tamkar dai masu zuwa kar6ar magani a assibiti, koda yake zamu iya kiran abin da haka, domin nan d'inma maganin ne suke kar6a, ammafa a gurin Malamin tsubbu, ma iya kiransama da boka ko d'an sihiri, har kafirima ma iya kiran sunansa dashi.


Ammi ta dad'e a gurin kana layi ya iso kanta, kiranta y'ar koren bokan tayi tamkar dai yanda ake kiran mutum a assibiti idan layi ya iso kansa.


Koda zamanta a d'akin bokan batare da 6ata lokaci ba bokan ya farayi mata bayani kamar haka"Kinada d'iya Lauratu mai shegen taurin kan tsiya koba haka ba?"


Jiki na kyar ta amsa masa da d'aga kai, saboda muranar ganin ta kawo kukanta inda za'a share mata hawaye


"Idan dai har akayi sa'a wannan yaron Ummaru ya rabu da ita, ba k'aramin farin ciki zakuyi ku duka ba, domin tabbas Lauratu itace sila ta yankewar talaucinku gaba d'aya dake da sauran y'an'uwanku duka, sai dai kuma ga wannan yaro yazo yayi mana tsaye, ya kike ganin zamuyi dashi? A kasheshi kikeso ko kuwa a lahanta maki shi?" Ya tambaya tare daci gaba da y'an rubuce-rubucenda yakeyi akan Allonsa na k'arfe


Murmushin jin dad'i Ammi tayi "Allah gafarta Malam duk abinma bazai kai haka ba, nidai buk'atata kawai a saka mata tsanarsa acikin ranta kawai, koda shi yana sonta indai itan ta tsanesa aita k'are, koya ka gani Malam?"


"Hakane kuwa kema kinyi tunani, saidaifa akwai aiki ja agabanmu, domin wannan d'an banzan yaron ba haka ya bar y'arki ba, wani mugun asiri ne yayi mata wanda ake had'awa da zuciyar Kare da kuma ta Kaza, kinsanko Kare da Kaza ba wata zuciya ne dasu ba, dan indai da tsaba a guri duk yanda zakiyi wajen korar kaza ba tafiya zatayi ba, to haka shima karen yake idan yaga d'anyen nama"


Sallallami ta farayi tare da k'ara nanata la'antar ta akan Umar d'in


"Ni dama wallahi saida na zargi hakan, ace duk irin wannan biyayya ta Lauratu lokaci d'aya ta canza mana? Ashe ba hakanan ba da walaki wai goro a miya, nake ganin laifinta a banza, to yanzu Malam miye mafita kenan?"


"Kayan sawarta zaki kawo mana kala d'aya akwai abinda zamuyi dasu, sai kuma shi wannan turaren da zaki saka mata acikin kayan sawar nata, wannan kuma rubutun shansa zata ringayi kullum da safe kamin taci wani abu" Ya fad'a tare da mik'a mata tarkacen tsubbun


"Ai Malam duk inda kake tsammanin Lauratu ta wuce nan wallahi, dan itafa ko rubutu basha takeyi ba, wani lokacima idan na matsa mata sai tasaka mani kuka, wai a cewarta k'azanta ne batasan kodame dame aka had'a akayi rubutun ba"


"Shima wannan ba matsala bane Tani, kya iya tarfa mata acikin abincinta, mu dai buk'atarmu ya shiga cikin cikinta kawai"


Da wannan Ammi ta dawo gida, kuma ta maida himma wajen yin ayyukanda bokan nata ya bata....Turk'ashi wata sabuwa kuma wai inji y'an caca, anya duk mai raba masoya zai gama da duniya lafiya kuwa? Nidai nace A'a, kufa masu karatu?


Maman Ja'afar

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [05/05, 10:53 p.m.]

*💘SUNE SILA💘*       15Daga alkalamin

MamanJa'afar✍Tun k'arfinsa yake tik'ar gudu akan mashin d'in nasa saboda so yake yayi k'okari ya cimma abokin nasa Umar, mai yiyuwa wani labarin ne ya samo da d'umi-d'uminsa


Saida Umar d'in ya fara shigowa cikin gari kana ya sassuta gudun nasa, domin daga can wani k'auye ya fito Kwanar Dutsi anan cikin garin Katsinar


"Kai banza mahaukaci tun d'azun naketa binka nake d'aga maka hannu amma kak'i tsayawa ka wani shareni sai kace zaka bani wani abu" Cewar Yakubun kenan wanda ya kasance aboki ga Umar koko nace abokin sana'a, (Domin akwai banbanci tsakanin aboki da kuma abokin sana'a)


"Ni ina nasanma kana wani bina, tuk'in kawai nakeyi amma wallahi kwata-kwata hankalina ba'a kan tuk'in yakeba, Allah dai ya kawo mana warwara kawai" Ya fad'a tare da fakawa da mashin d'in nasa a gefe guda domin su samu damar tattaunawa tsakaninsa da abokin sana'ar tasa"Kai kullum bakada wani aiki saina damuwa damuwa dai, ka rabu da itaman ka shafawa kanka lafiya, yarinya sai kace y'ar gwal duk kabi ka wani nanik'e mata, ana korarka kana lik'ewa sai kace wanda babu zuciya a jikinsa?"


"Aini a gurina farashinta yafi na gwal d'in idanma tantama kakeyi kasani, yanzu dai fad'a mani dalilinka na tsayar dani dan sauri nakeyi akwai y'ay'an wani uban gidana da zan d'auko daga makaranta ina tsammanin ma yanzu an kusan tadasu"


Shuru yayi na d'an wani lokaci, alamun maganar da zata fito daga bakinsa tanada d'an nauyi


"Nace maka saurifa nakeyi dan ankusan tadosu kodai bakada abin cewa ne nayi gaba" Ya fad'a a tak'aice Cikin alamu na k'osawa


Sosa k'eya yayi"Dama dai kan maganar y'ar gwal d'in taka ce, shekaran jiya nakai wani mutum can bakin Y'ar kutungu, ina saukesa na hangota ta fito daga cikin gidansu Halima, ita batama...


"Kardai kace mani Haly Tasi?" (Dayake haka jama'a suke kiranta kasancewar ta ballagar da kanta kowama kawo kai yakeyi)Ya tambaya tare da zaro idanuwa alamun mamaki k'arara akan fuskarsa


"K'warai kuwa ita nake nufi, dan a jere ma na gansu sun fito daga cikin gidan, ga dukkan alamu Haliman rakiya tayowa Lauratun"


Shuru Umar d'in yayi na d'an wani lokaci, ga dukkan alamu mamaki ne yakeyi ko kuma zuzzurfan tunani


Mik'awa Yakubun hannu yayi "Nagode sosai da irin kulawarka agareni, ammafa ka k'aryata zuciyarka, domin abinda kake tunani akan a bar k'aunata ba gaskiya bane, mai yiyuwama wani uzurin ne na daban ya kaita gidansu Haliman, amma koma miye zanyi bincike"


Yana gama fad'ar haka ya tada mashin d'insa yayi gaba tunani fal a cikin zuciyarshi, bai zame ako ina ba sai a gidansu Rukayya, baisha wata wahala wajen samun yaron aike ba


Ciki zauren su Rukayyar ya shiga domin jiranta gudun kar ya tsaya a waje wani daga daga gidansu Lauratun yazo wucewa ya gansa


Cikin kayanta na makarantar boko ta fito daga gidan tare da yi masa sallama lokaci d'aya kuma da mamakin ganinsa a gidan nasu k'arara tattare a kan fuskarta, domin tun lokacin da Ammi tayi masa wani korar kare anan kuma ta shiga tayiwa Innarta rashin mutunci Umar bai k'ara zuwa gidan ba sai yau d'in nan da take tunanin yau d'inma da walaki wai goro a cikin miya.


Bayan sun gaisa ne ta dubesa"Kayi sa'ar samuna gida kuwa domin daka ganni nan dawowata kenan daga makaranta ko kayanama ban cire ba"


Cikin zaulaya ya dubeta "To ai dama kinsan ni d'in mai sa'a ne tun ba yau ba"


Dariya tayi "Na yadda kam kanada sa'a tunda gashi nan har anbaka auren Lauratu"


Sosa k'eya yayi"Ta nan d'in kam sai a hankali, yanzu dai dan Allah taimakon nan dai da kika saba nakeso kiyi mani, dan Allah a taimaka a fito mani da mutuniyar tawa, wallahi son ganinta nakeyi sosai" Ya fad'a tare da marairaicewa alamun neman alfarma


"Karka damu na Laure, basai ka wani marairaice mani ba, aikin kud'i ne zanyi maka ai kaima kasani, kasan Gwamnatinmu ta wannan karon ta hana aikin banza" Ta k'arashe maganar tata cikin alamu na zaulaya


"Yana iya? Na amince kai makarantar kwana nawa kuma wannan karon zanyi?" Ya fad'a jiki a sanyaye


"Karka damu sati guda ne kawai ai ba yawa" ta fad'a a tak'aice tare da rugawa a guje gidansu Lauratun.


********


"Lauratu ki daure mana kisha rubutun nan ko kad'an ne, k'aik'ayi nefa koma kan mashek'iya, har maganin sammu da kambun baka duk yanayi, ke har farin jinima yake k'arawa wani lokacin"


Tun d'azun Ammi keta faman lallashinta akan ta daure tasha rubutun dake hannun nata wanda taketa faman mik'a mata, amma fafur tak'i ta k'ar6a sai jayayya sukeyi


"Nifa Ammi lafiyata k'alau babu wani ciwon sammu dake damuna, farin jini kuma dama inada kayana kawai dai kula mazan ne bana son yi tunda na riga na sayar" Yau su Lauratu ansamu bakin magana dayake Ammin ta d'an sakar mata fuska kwana biyu


"Amma dai Lauratu ko kanada kyau ai ya kamata ace ka k'ara da wanka, domin inaji a jikina kece silar magance mana wannan talaucin da yaketa faman bibiyarmu tun iyaye da kakanni, kuma kome kikayi mana a baya yanzu na fahimci ba yin kanki bane, saka maki hannu akayi...


"Salamu alaikum" Rukayya ta fad'a tare da d'aga labulen d'akin nasu cikin daburburcewa


Sama-sama suka gaisa da Ammin domin dama ba wani k'aunarta takeyi sosai ba, kana daga bisani Rukayyan ta dubi Lauratun"Lauratu wai kizo inji uwar aikinki ta Sabuwar tasha, tun d'azun taketa faman neman gidan nan bata samu ba, to data shigo gidanmu ne tana tambaya shine nace mata ta zauna nazo na kirata matake" Tana magana tana wani Wuri-wuri da idanuwa tamkar wata marar gaskiya


Cikin fara'a Ammi ta dubi Lauratu "Yi maza to ki shanye rubutun sai kije ki sameta, k'ilanma sasanci tazo nema, daga nan sai ku taho tare mu gaisa da ita"


Badan taso ba ta kar6i rubutun tasha, kawai tasha ne dan Ammin ta barta fita, tasan babu wata uwar aiki Umar ne kawai keson ganinta, dan indai Umar ya aiko Rukayyan babu irin k'aryarda bata shigarwa domin tasaka Ammin a kwana ta samu ta fito da Lauratun, tun Lauratun bata ganota hardai ta kai itama tana ganewa.


"Ammafa k'awata kin iya shirga k'arya, wai uwar aiki, k'aryar takifa ta yau taso ta bani dariya, kawai dai na doje ne dan kada Ammi ta harbo jirginmu" Ta fad'a d'auke da murmushi akan fuskarta akan hanyarsu kenan ta zuwa gidansu Rukayyan"Ke kam ba dolena na dage naita shararo k'arya baji ba gani ba, sati d'aya fa yace mani zaiyi yana kaini makaranta kyauta, kingako ai dole nima nayi mashi aikinshi da kyau koba haka ba?"


Duka ta kai mata a baya cikin alamu na zaulaya "Macuciya kawai da bata taimakon masoya don Allah sai dan akaita makaranta"


Cikin raha da nishad'i suke tafiya abinsu har suka iso gidan nasu Rukayya inda Umar d'in yake a tsaye


Cikin gida Rukayya ta wuce yayinda ita kuma Lauratun ta dubi Umar d'in da yayi wani kicin-kicin da fuska sai kace wani mai shirin yin fad'a "Lafiya kuwa Umar yau na ganka gaka nan dai ba fara'a ba komai, ko wani ne ya ta6o mani kai?"


Numfasawa yayi tare da dubanta, har yanzu dai fuskar tasa a d'aure take "Ance mani anganki gidansu wata y'ar iskar yarinya Halima ko? me ya kaiki gidansu?"


"Zumunci" Ta fad'a a tak'aice tana wani ciccijewa


"Kinsan kuwa ko wace ce Haly tasi da kike k'okarin k'ulla alak'a da ita? Dama da kika ganni kwatsam zuwa nayi naja maki kunne akanta, daga yau sai yau bana son k'ara ganinki da ita indai kina son farin cikina, ki daure kici gaba da kare mutuncinki Lauratu kamar yanda kika saba wata rana sai labari komai zai wuce, amma idan kina zama tare da irinsu Halima komai zai iya wargajewa, abubuwa duk su dawo baya, karki manta ko a gobe k'iyama mutum ana tadasa ne akan addinin abokinsa inji Annabi ( S.A.W) shiyasama yace d'ayanku ya duba yaga waye abokinsa, shin na kirki ne koko na banza ne? Toko anan duniya idan kanaso kagane halin mutu abokinsa ya kamata ace ka fara tamabaya, saboda haka duk yanda za'ayi Lauratu kiyi k'okarin abota da mutanen k'warai bana banza ba, domin yanzu mutum ake kiwo ba dabba ba, ki barmu muji da yak'inda ke gaban Lauratu bawai ki tattago mana wani ba, ai sai abubuwan suyi mani yawa" Yana magana tamkar mai shirin yin kuka


Katsesa tayi tare da zun6uro baki, cikin k'unk'uni alamun ta gaji da surutun hakanan take fad'in


"Nifa gaskiya na fara gajiya da wad'annan y'an fad'ace-fad'acen naka, komi kai shikenan kaita yiwa mutane fad'a, abin laifi da bana laifi ba kai duk fad'a sai kace ubana ba saurayina ba, ni kama barni naji da abinda ke damuna amma duk kawani zo ka isheni da ihu dame akeso naji?"


Mamaki k'arara a kan fuskarsa yake dubanta, anya kuwa wannan Lauratunsa ce? Lauratun da har zanzari takeyi ya bata umarni tabi wai yau itace yana fad'a tana fad'a, anya ba gajiya ta farayi da tashin hankalinda suke ciki ba?


"Lauratu Umar nefa kike mayarwa da magana, kodai baki ganeni bane?" Har yanzu dai mamakin bai kau a kan fuskarsa ba


"Nafa dad'e sosai anan bara na tafi gida kada Ammi tayi mani fad'a" Ta fad'a tare da kama hanyar tafiya tayi tafiyarta ta barshi anan tsaye.


"Anya yarinyar nan ba fara shaye-shaye tayi ba kuwa? Abin da mamaki lokaci guda haka duk tabi tawani canza, anya kuwa...?


Shi kad'ai yaketa faman surutansa har dai ya gaji da zama acikin zauren shima ya nufi hanyar gidansu, domin ko k'warin jikinsama baji yake ba bare yayi tunanin nufar wajen aiki.


**********


_Bayan kwana biyar_Kamin zuwan wad'annan kwanakin ansamu canji sosai daga gurin Lauratu, kuma dai duk acikin kwana biyar d'in ne aka samu damar janye maganar zuwa kotu gaba d'aya saboda wacce akeyi domintan itama tabi ayarin y'an adawar, ga dukkan alamu dai bokan Ammi ya iya aikinsa sosai.


******


Ko sallama babu ta kutso kai a cikin gidan, tsakar gidan ta tsaye tare da y'an waige-waigenta ga dukkan alamu d'akinsu Lauratun take nema


Uwani ta kalla dake zaune a bakin k'ofar d'akinta "Dan Allah Malama d'akinsu Lauratu nake nema?" Ta tambaya babu wani alamun lada ko kad'an akan harshen nata


Da baki Uwani ta nuna mata d'akin, a zuciyarta kuwa cewa takeyi "Shikenan kuma su Lauratu an d'au hanya, abin kuma harda masu suffar karuwai?


D'aga labulen d'akin tayi tareda yin sallama, cikin fara'a Lauratu ta tarbi Haliman "Yau kuma ina aka nufa da kaya nik'i-nik'i haka a hannu? Kinsan ko shekaran jiya da jiya duk naje gidanku akace bakya nan?"


Ta fad'a yayinda take duban ledojin dake a hannun Haliman wad'anda taketa faman d'agawa da k'yar


Yamutsa fuska tayi "Wallahi kuwa, kinsan ba cika zaman gida nayi, yanzu dai kar6i wannan kwancen kayana ne na kawo maki dan naga naki har sun fara yagewa suna nema su 6ata maki kyawu, idan kuma bakyaso kya iya zubarwa agaba sai na kawo maki sabbi"


Zazzage kayan tayi akan gado ta fara dubawa "Halima ai wad'annanma kusan sabbin nema, wallahi inaso, kice nima na kusan zama y'ar gayu irinki?" Cikin fara'a take magana tana d'add'aga kayan


"Bak'i mukayi ne a agidan namu nake jiyo hayaniya?" Cewar Ammi kenan domin dawowarta kenan gidan, dama ita haka tsarin rayuwarta yake, zata fita duk sadda taso kuma taga dama, batare da tambayar izinin kowa ba, ko mijin saidai tace masa saina dawo, bare kuma yaranda ta haifa datake ganin kamar duk talaucin da take ciki yaran ne suka ja mata shi(Wai dama talauci nasa mutum ya fita hayyacinsa har haka)


"Mama ina wuni" Haliman ta fad'a yayinda ta durk'usa har k'asa cikin ladabi da biyayya na munafunci


Cikin fara'a take amsawa "Lafiya k'alau, lafiya k'alau yarinya, kamar Halima d'iyar Memuna ko?" Ta fad'a yayinda take duban fuskar Haliman tana mai nazari


Murmushi Haliman tayi cikin alamu na kunya (Sululu kenan macijin k'aik'ayi Su Halima sari ka nok'e) "Eh nice Mama" Ta fad'a a tak'aice


"Ammi wallahi tanada kirki, kingama kayanda ta kawo mani" Lauratu ta fad'a yayinda take nunnuna mata kayan dake baje akan gadon


Godiya Ammi taita zubawa Haliman ba kakkautawa tamkar zatayi mata Sujjada


Kudi Halima ta zaro a cikin jakarta kimanin dubu biyar tare da mik'awa Ammin "Ammi ga wanna kwa sayi ko goro ne, na biyama ta wajen masu goron waida na siyo maki sai kuma ban samesu ba"


"To aike y'ar nan sai dad'in yayi mani yawa, ga way'annan kaya kuma ga k'arin kud'i? Allah dai yayi maki albarka d'iyar nan, Allah yasa ki gama da duniya lafiya, Allah kuma ya baki miji na gari wanda zaki huta iyayenkima ta dalilinki suma su huta, Allah kuma ya cida y'an baya" Ta fad'a yayinda take nad'e kud'in a ha6ar zaninta


Murmushi Haliman tayi batare da tace mata komai ba, itako Lauratu abin sai mamaki yake bata, wai dama Ammi ta iya saka albarka har haka amma bata ta6a saka mata ba?


Rabon da taga Ammi acikin wannan irin yanayin ai har ta manta, kenan kuwa idan hakane ya zama wajibi agareta ta dawowa mahaifiyarta da farin cikinda ta dad'e da rasawa ta dalilinta, to amma ta yaya?
Inama ace Lauratu zataji shawarata? Danace mata karta kuskura tabi wannan hanyarda take tunanin bi, domin hanyar bamai 6ullewa bace ba kwata-kwata, sai dai kash kona fad'a matama maganata bazatayi wani tasiri a gareta ba domin a yanda na fahimta ita kanta Lauratun izuwa wannan lokacin ba cikin hayyacinta take ba....

*Maman Ja'afar ce*

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [06/05, 9:08 p.m.]

*💘SUNE SILA💘*       16Daga alkalamin

MamanJa'afar✍Dandazon mutane ne na hango sai faman hayaniya sukeyi kuma kowa so yake ya ganewa idanuwansa abinda ke faruwa a gurin, ga dukkan alamu dai wani babban al'amari ne ke shirin faruwa ko kuma ya riga ya farun


Kuma a daidai wannan lokacin ne naga an tado su Lauratu daga makarantar islamiyyarsu


Dayawan y'an islamiyyar tasu ba hanyar gida suka nufa ba, gurin wannan dandazon suke tunkara domin ganewa idanuwansu abinda ke faruwa a gurin, itama dai Lauratu ba'a barta a baya ba wajen bin ayarin masu kallon


Yayanta Zubairu ta hango jama'a sai faman dukansa sukeyi suna kiran "6arawo! 6arawo"


Shiko in baya ga ihu da neman d'auki da agaji babu abinda yakeyi"Dan Allah kubarsa hakanan, ku barsa nace, tunda dai ya maido mani kayana ba shikenan ba?" Cewar dogo bak'in matashin saurayin kenan wanda ke jingine ajikin dank'areriyar motarsa irin ta manyan masu kud'i ko kuma y'ay'ayensu, ga dukkan alamu dai ina ganin shine wanda akayiwa satar


Lauratu batasan lokacinda ta yada jakar karatun nata ba tayi kukan kura ta fad'a acikin taron tare da rungume yayan nata ba


"Dan Allah kuyi hak'uri jama'a ku daina dukansa hakanan, wallahi sata ba halin Yaya Zubairu bane, tsautsayi ne kawai, dan Allah kuyi hak'uri ku daina dukansa" Tana kuka take fad'ar way'annan kalaman abin tausayi


Da k'yar da ji6in goshi da wannan mai motar wanda akayiwa sata da kuma Lauratun suka shawo kan way'annan matasan suka daina dukansa, kamin zuwa wannan lokacin kuwa yayan nata Zubairu ya jigata sosai


"Kinga Baby daina kukan hakanan ya isa, ai sun bar dukan nasa ko? Yanzu dai kamasa mu kaishi wancen Kyamis din mafi kusa a duba mana shi domin yanzu ko munje assibiti bin layi ne zai 6ata mana lokaci"


Matashin ya fad'a tare da nuna mata kyamis d'in da hannunsa lokaci guda kuma yana cicci6ar Zubairun


Baiji ciwo sosai ba sai d'an guggurjewa dai da yayi aka saka masa Aidin a guraren


"Yaya zaka iya takawa kuwa zuwa bakin titi mu samu abin hawa ko naje na kira yaya Kabiru" Ta fad'a tare da y'an waige-waigenta


"Karki damu Baby ku shigo motata ba damuwa ai sai na ajiyeku a gidan" Cikin jin kunya su duka suka shiga cikin motar tasa


Akan hanyarsu ta zuwa gidan ne matashin saurayin ya dubi Zubairu dake baya ta cikin gilashin motar


"Abokina koko nace yayana miye sunanka ne?"


Cikin jin kunyar dai yake mayar masa da amsa, domin yanzu ba k'aramin jin kunyar mutumin yakeyi ba"Zubairu" Ya fad'a a tak'aice


"Amma Yayana Zubairu nayi mamaki k'warai ganinka a cikin irin wannan halin alhalin bakayi mani kama da masu yin sata ba koko nace 6arayi, kana zuwa makaranta kuwa?" Ya k'arashe maganar tasa da tambaya tare da dubansa


Girgiza masa kai yayi alamun amsawa da a'a a tak'aice


"Ok ashe wannan ne sila? Domin na tabbata da kana zuwa makaranta bazaka samu lokacin d'aukar kayan wani ba sai dai kuwa idan son zuciyarka yayi yawa"


Lauratu data buga uban tagumi hawaye na bin fuskarta a cikin zuciyarta cewa takeyi "SUNE DAI SILA koma me ya faru akanmu ko muka zama"


"Gaskiya sata ba halin mutanen kirki bane yayana, yanzu kaga da sun hallaka ka a banza a wofi, ni wallahi layikan wayoyinma nafi ji shiyasa kaji na nemi agajin jama'a, amma dan ta waya ai mai sauk'i ne tunda ana sayarwa sai na sayi sabuwa, kud'i kuwa da ka d'auka yanzuma zan mayar maka dasu" Ya fad'a tare da zura hannunsa a cikin aljihu ya zaro dubu bakwai d'in da Zubairun ya satar masa acikin mota ya mik'a masa


"A'a, ka barsa kawai wannan karamcinma da kayi mani nagode" Ya fad'a tare da sunkuyar da kai hawaye na bin fuskarsa


Da k'yar dai ya samu Zubairun ya kar6i kud'in kamin su iso gida.


Har cikin gida ya rakasu, domin gidan hayar ba irin mai doka bane bak'on kowama zai iya shigowa gaba gad'i


Ganin Zubairu a cikin bandeji ba k'aramin tadawa Ammi hankali yayi ba, tuni mutanen gidan sukayo ca akansu suna tambayar ba'asin abinda ya faru


Kalllon kallo suka farayi a tsakanin Lauratu da kuma Zubairun kowa ya rasa abin cewa


"Dan Allah kuyi hak'uri, wallahi tsautsayi ne, nazo wucewa da mota shi kuma yazo tsallaka titi, to rabon ayi shine na d'an bankesa, yanzunma shigowa nayi na k'ara baku hak'uri" Cewar matashin kenan yayinda yake daddanna wayar dake hannunsa


Ba k'aramin dad'i su Lauratu sukaji da wannan k'aryar da bawan Allahn yayi ba


Dubu biyar ya zaro a aljihunsa tare da mik'awa Ammi "Mama ga wannan koda jikin nasa ya motsa a iya kaishi assibiti"


Nan take su Ammi baki ya washe sai faman zuba masa godiya takeyi "Kuma in baya ga yaran zamani da tun kuna yara kuke sakawa kanku damuwa, me kake tunani da har zaisa ka fad'awa mota batare daka sani ba?" Ta fad'a yayinda take duban Zubairun


"Mama ni zan wuce Allah ya basa lafiya, Baby d'an rakani mana akwai maganar da zamuyi" Ya fad'a tare da duban fuskar Lauratu


Harara Ammin ta galla mata alamun ta bisan kenan tun kan ranta ya 6aci


Sumui-sumui Lauratun ta bisa har k'ofar gida inda ya ajiye motarsa


Sai yanzu Ammi ta k'ara tabbatar da maganar bokan nata, inda yace mata Lauratu ce zata zamo sila na warwarewar dukkan matsalolinsu, to kuwa gashi tun ba'aje ko ina ba ga magana ta fara tabbata tun daga zuwan Halima gidansu har zuwan da wanna bawan Allahn yayi yanzu.


"Baby shigo daga ciki mana muyi magana, ko bakya jin zafi ne?" Ya fad'a tare da duban fuskarta


"Ina jin zafi mana, amma ai jin zafin ya riga ya gama zame mani jiki tunda a cikinsa na taso har nakai ga zama haka, kuma me kake tsammani daga gurin mutane idan suka ganni a cikin motarka?"


Murmushi yayi tare da sake dubanta karo naba adadi "Gaskiya Baby kina burgeni matuk'a, domin wannanma ya k'ara tabbatar mani da cewa kinsan mutuncin kanki kuma ke d'in mai mutunci ce, ba irin y'an matan zamanin nan ba da idan akace masu su shigo mota jiki har kyarma yakeyi suga sun shiga ba"


Canza akalar zancen nasu tayi "Nagode sosaifa da rufa mana asiri da kayi nida d'an"uwana, Allah ya saka da Alkhairi kuma kaima Allah ya k'ara rufa maka asiri"


"Karki damu Baby ai yiwa kai ne, gobema zan dawo na sake duba jikin nasa insha Allahu"


"Allah ya kaimu goben lafiya" Ta fad'a a tak'aice tare da nufar hanyar gida.


*******


"Lauratu Allah dai yasa abinda nake tsammani gaskiya ne? Idan muka samu wannan yaron ya aureki ai mun haye kowa namuma ya haye kamar dai yanda Mal....


"Haba Ammi daga ganin sarkin fawa kuma sai miya tayi zak'i? Toba abinda kike tunanin bane domin ba cewa yayi yana sona ba, amma dai yace gobe zai dawo ya k'ara duba jikin yaya"


Dan tsananin murna Ammi harda su taka rawa da rangad'a gud'a tayi"Magana ta kusan tabbata kenan y'ar nan? Allah dai ya tarfawa garinmu nono, kuma ki kama bakinki kiyi gum karki fad'awa kowa, kinsan mutane basaso suga wani yaci gaba, yanzu zakiji anfara y'an magan-ganu ana bin malamai saboda a lalata komai, saboda tsananin hassada da bak'in ciki, shiyasama naji Malamanku na izala suna cewa a 6oye neman aure kuma a bayyana d'aurin auren saboda y'an hana ruwa gudu" (Hmm yau su Ammi anjik'e da kud'i harda su kawo hadisi dai dai da son zuciyarta)


*******


Kwance Umar yake yana bacci, amma a zahirin gaskiya idanuwansa kawai ne a rufe amma ba baccin yakeyi ba


Tunanin kawai yakeyi a cikin zuciyarsa akan dalilin canzawar da Lauratu tayi masa lokaci guda, alhalin yasan baiyi mata komai ba, tun dai daga ranar nan da yayi mata magana akan Halima shikenan ta d'auki karan tsana ta d'ora masa, har yanzu ya rasa gane kanta kwata-kwata


Yayi bakin K'okarinsa wajen ganin ya gano laifin da yayiwa abar k'aunar tasa amma har yanzu da kansa yake k'okarin tarwatsewa saboda tsananin tunani ya kasa gano dalilin


Ko wasik'ar da ya aika matama tafi a k'irga amma ko d'aya babu wacce ya samu amsa daga gareta


Kullum shine akan hanyar zuwa gidansu Rukayya dan kawai ta fito masa da Lauratu amma itama wannan karon abin yaso yafi k'arfinta, domin duk amsoshin da take maido masa ba masu dad'in sauraro bane


Tunani yakeyi wai meke shirin faruwa dashi ne kamar a mafarki? Yaya zaiyi da kunyar iyayensa da kuma ta sauran jama'a? Wai hakan na nufin sai ya bar Lauratu kenan ko yanaso ko bayaso?


Da wannan tunanin bacci 6arawo ya sace shi amma badan ya shiryama hakan ba.


*********


Rayuwar gidansu Lauratu kuwa ta fara dawowa sabuwa kamar yanda Ammi ta dad'e tana mafarki, domin ko yau d'in nan Sakwara da miyar Kara-kara da naman rago suke watanda da ita a gidan nasu*(Miyan kara-kara)*


_Zaki samu namanki mai kyau ko kifi ki wanke, ki zuba a cikin tukunya ki yayyanka tumatiri da albasa yankan yayi manya-manya, ki wanke ki zuba akan wannan naman, idan kinaso kya iya k'arawa da tattasai ko guda d'aya ne, kana ki saka tattarugunki daidai yanda kike da buk'ata a ciki amma basai kin yanka ba, ki zuba kayan k'amshi daidai buk'atarki, ki d'ora akan wuta suyita dahuwa har sai duka kayan nan sun dahu sunyi luguf, kana ki tsame cefanen dake ciki ki markad'a ko ki daka amma sama-sama kar ya niku sosai, sai ki mayar acikin wannan naman naki na kan wuta, ki zuba kayan d'and'ano, idan ruwan yayi maki kad'an ki k'ara kardai yayi kauri sosai, ta d'an kara dahuwar mintina kad'an akan wutar sai ki sauke kayanki (Ba a saka maifa aciki)_


_Zaki iya cinta da Sakwara ko teba ko shinkafa, har tuwoma kya iya ci da ita kamar dai yanda nafiyi kenan, nima a gurin y'an ghana na koya domin ba miyar hausawa bace_


"Yaya dan Allah bawa Saminu kud'i ya siyo mana lemun kwalba a gurin Abba mai tireda, idan kuma kayi mani musu na tona wallahi" Ta fad'a tare da dubansa cikin alamu na zaulaya


Zaro idanuwa yayi alamun tsoro "Ai abin bama zai kaimu ga haka ba K'anwata" Dubu d'aya ya zaro ya mik'awa Saminun "Ungo Saminu siyo mana lemu guda shidda har mak'wabta suma yau sai sun saka albarka"


"Yau dai gidan nan wariya kuke nuna mani, kodai zakka kuka samu ne banida labari?" Cewar Yaya Kabiru kenan yayinda yake duban fuskokinsu yana murmushi


"Salamu alaikum, wai ance Lauratu tazo inji Usman"


"Ya kamminsa suke shi Usman d'in?" Ta tambaya yayinda take taunar wani k'ashi mai dad'in gaske a cikin bakinta


"Um wani bak'i ne, dogo mai babbar mota" Ya fad'a tare da in ina


"Maza jeka kace masa tana zuwa" Ammi ta fad'a d'auke da farin ciki akan fuskartaSaman dakalin k'ofar gidansu ta hangoshi zaune yana daddanna waya, yasha manya kaya harda hula abinsa cikin suffa ta kamala, yayi mata kyau matuk'a


Taji dad'i k'warai ganin duk yanda yake da yawan jin zafin nan amma ya hak'ura da sanyi motarsa ya zauna a kan wannan dakalin duk dan saboda ita


Sallama tayi masa cikin girmamawa kamar dai yanda takeyiwa Umar


Cikin ladabin dai har wayau ta sake gayar dashi "Ya zafi" ta fad'a a tak'aice


Murmushi yayi kana ya dubeta "Lafiya k'alau, tunda kikace zafi ya riga ya zame maki jiki ai nima ko inaso ko banaso dolena ya zame mani jiki"


Murmushin dai ta sakeyi domin batasan ya'akayi ba, kawai jin dad'in kalamansa takeyi


"Yauwa ga tsaraba na kawo maki, ammafa sai kin rufe idonki zan baki domin naga irin farin cikinda zakiyi"


Dariya tayi kana ta dubesa "Ikon Allah, tsarabar kuma har sai na rufe idanuwana? To na rufe a bani" ta fad'a tare da rufe idanuwan nata


Minti biyu a tsakani ya dubeta"To bude yanzu ga tsarabar nan agabanki"


Abinda ta gani ba k'aramin farin ciki ya sakata ba, domin har tama kasa 6oye farin cikin da take ciki


Kayan kwalliya ne irin na zamani ta gani da turarika da kasassukan karatun Alqur'ani mai girma, dashi kanshi qur'anin a cikin gidansa mai kyau da d'aukar idanuwa


"Nifa Usman duk kabi ka rud'ani da wanann irin kyaututtuka naka, waini wace irin godiyama kakeso nayi maka tukun?" Ta fad'a duk a wani firgice saboda tsammanin farin ciki


"Niba sai kin gode mani ba, babban abinda nafi buk'ata daga gareki bai wuce ki mallaka mani zuciyar ki ba, idan har nasamu hakan to burina na duniya ya kusan cika"


Allah sarki tun d'azun na hango Umar raka6e a gefensu yanata faman kallonsu cikin mamaki da tsoro, yayinda zuciyarsa take ci gaba dayi masa k'una tamka Taransfoma ce cikinta


Da dai ya kasa dannewa zuciyarsa tunkarar inda suke yayi, tare da yi masu sallama, mik'awa Usman d'in hannu yayi suka gaisa kana ya dubi Lauratu wacce ko kallon arzikima bai isheta ba


"Lauratu ind'an ganki mana minti biyu?" Ya fad'a tare da duban fuskarta wacce tayi kicin-kicin kamar an aiko mata da sak'on mutuwa


Kallonsa tayi a wulak'ance kana ta juya ta dubi Usman da yaci gaba da y'an danne-dannensa a waya


"Ranka ya dad'e naje nagansa ko kuwa dai na basa hak'uri yayi gaba kar ya 6ata mana fira?" Ta fad'a yayinda take duban fuskar Usman d'in


"Ok badamuwa Baby kya iya tafiya ammafa karki dad'e kiyi sauri saboda inada abinyi a gida" Ya fad'a kansa a k'asa


Dan tsananin bak'in ciki Umar bai san lokacin da hawaye suka fara safa da marwa akan fuskarsa ba


"Wai dama haka kud'i suke da canza mutum lokaci guda? Ashe Lauratu zata iya sayar da sonda na dad'e inayi mata tun kamin tasan wacece ita? Anya kuwa ba mafarki nakeyi ba?"


Abinda Umar yaketa faman maimaitawa kenan acikin zuciyarsa har zuwa lokacinda ta samu isowa a inda yake zaune akan mashin d'insa yana jiranta.....
*Maman Ja'afar ce*

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [07/05, 7:36 a.m.]

💘SUNE SILA💘*


 

       17Daga alkalamin

MamanJa'afar✍K'erere tayi agabansa cikin alamu na rashin kunya, yau ko y'ar sallamar ma daya koya mata har yasa doka akanta bai samu ba


"Lokacinka na tafiyafa Malam, domin idan baka manta ba minti biyu kacal ka d'auko daga gun mai gidana kuma yanzu inagama anyi sakan talatin a ciki" Ta fad'a tare da dubansa ga dukkan alamuma hankalinta ba'a wajensa yake ba


Yana hawayen dai ya dubeta karo na ba adadi "Wai Lauratu meke faruwa ne haka wanda ban sani ba? Idanma wani laifi nayi maki ai bai kamata ace kin hukuntani ta wannan hanyar ba, Lauratu ina azabtuwa fa sosai da wannan hukuncin da kikeyi mani, wallahi da Allah zai baki ikon shiga cikin zuciyata da zanso ki shiga kodan kiga irin wutar dake ruruwa a cikin zuciyata Lauratu, dan Allah karki gujeni Lauratu ki tausayawa rayuwata, dab nake da in zama maraya dukda kuwa iyayena suna raye" Ya fad'a murya na rawa, ga dukkan alamu kukan nasa yake k'okarin 6oyewa


Kukansa yaso ya bata tausayi amma kuma sai bai bata tausayin ba, kuma ta rasa gane dalilin hakan


Agogonda ke manne a hannunta wacce Halima ta bata ta duba tare da dubansa a shek'ek'e"Lokacinkafa ya cika, sai anjima" Tana gama fad'ar haka tayi gaba wajen Alhaji Usman d'inta matashi mai tashen kud'i kenan


Da k'arfin tsiya ya figi mashin d'in nasa, har yaso ya kaiwa wata mota karo Allah ya taimaka mai motar ya kauce masa.


******

"Dan Allah kayi hak'uri na 6ata lokaci" ta fad'a yayinda ta k'araso inda Usman d'in yake zaune


Murmushi yayi tare da dubanta


"Ba damuwa, sai dai fa gaskiya ba girmanki bane kula irin wa'yancan y'an aca6an, yo me na samama yaci bare kuma jeho mani? Ni zan wuce gida sai kuma gani na biyu" Ya fad'a tare da Mik'ewa tsaye alamun tafiya


"Kodai ranka ya 6ace ne?" Ta fad'a jiki a sanyaye


"Da raina ya 6aci da zaki dawo ki sameni ne? Dama kinsan na fad'a maki yau sauri nakeyi saboda zan kai Dady mitin gidan Gwamna"


Wani sanyi taji yana ratsa mata zuciya kasancewar wannan babban kamu ne tayi, domin ko shakka babu mahaifinsa wani k'usa ne daga cikin k'usoshin Gwamnati


Da wannan sukayi sallama kowa ya kama gabansa.


********


_Bayan wata goma_


Kamin zuwan wad'annan watannin abubuwa da dama sun faffaru a tsakanin familyn guda biyu, a ciki kuwa harda kwanciya assibiti da Umar yayi duk adalilin juya masa baya da Lauratunsa tayi


A 6angaren Ammi da Malam Harisu kuwa abubuwa sai k'ara ta6ar6arewa sukeyi suna rinca6ewa, domin kullum Zubairu Saminu Kabiru babu abinda sukeyi masu face d'aukar magana, ta yau daban ta gobe daban


Shi dai Kabiru d'an bangar siyasa ya zama, yayinda shi kuma Zubairu bai canza daga kan sana'ar da yakeyi ta sata ba, Saminu kuwa ya kangare yanzu ko aike ba son zuwa yakeyi ba, shekarunsa basufi sha uku ba amma har ya fara bin matasa y'an shaye-shaye


 A kullum Malam Harisu da bak'in cikin hakan yake kwana kuma yake tashi, saidai bashida wani kata6us a gidan nasa barema har yayi tunanin d'aukar mataki.


Itako Ammi duk wad'annan abubuwanda ke faru ita gani takeyi ba yin kansu bane asiri ne kawai akayi mata domin yaranta su tarwatse, su lalace ta yanda bazataci moriyarsu ba, shiyasa kullum bazaka sameta a gida ba tana hanyar bin gidajen Malamai da bokaye y'an tsubbu da y'an bori, duk inda taji sabon Malami sai taje, duk Malaman de ke cikin k'auyukan nan na Katsina kusan babu inda Ammi bataje ba.


A 6angaren Lauratu kuwa soyayya suke zuk'a itada Usman d'inta ba kama hannun yaro, inda Usman yake wadatata da dukkan wasu abubuwanda takeso, yanzu hakama su Ammi shirye-shiryen aure akeyi domin Usman har ya turo magabatansa gidansu Lauratun akan atsayar da maganar aure amma ba za'ayi bikin ba a cewarsa wai sai ya dawo daga wani karatu na shekara d'aya da zaiyi a K'asar waje. Wannan kenan a tak'aice.


**********


Zazzaune suke shida abokanansa a cikin farfajiyar gidansu akan motarsa suna tattaunawa irin wacce suka sabayi kullum


"Waini abokina ya labarin mutuniyarka ustaziya ne? Kaddai har ka bige aiki batare daka gayyatomu ba?" Cewar d'aya daga cikin abokan nasa su ukun kenan


Murmushi yayi kana ya kur6i lemun kwalbar dake a hannunsa "Ai ingaya maku ustaziya ta dai taurin kan tsiya ne da ita, idan na d'ana mata tarko ta can sai ta zame ta can, idan na tare can sai ta ware ta can, amma insha Allahu komai ya kusan zuwa k'arshe tunda na gano lagonta"


"Kaddai fyad'e zakayi mata?" Cewar d'ayan abokin nasu kenan wanda sai yanzu ya tsoma masu baki a cikin firar tasu


Girgiza masa kai yayi alamun amsawa da a'a"Haba fyad'e dai sai kace wani sabon shiga? Muna nan daku da kanta zata kawo kanta, kasan babu abinda tafiso irin firar addini ko ta makarantar islamiyyarsu, ko kayi mata tarihin annabawa, ko kuma kaita yi mata fira akan ta kama kanta saboda ita mai mutunci ce, tofa sakaryar sai kaga tanata washe baki wai ita nan aganinta sonta akeyi da gaske, to da wannan damar nakeso nayi amfani wajen ganin na bigeta na k'ara gaba, dan akwai wasu ustazan irinta akan layi"


Dariya sukasa su duka harda k'yak'yatawa "Wallahi abokina kasan kan tsiya, nima kaga da nayi ilimin addinin nan kamar kai aida naji dad'in yaudarar ustazai, amma ina? Duk yanda naso hakan dole na hak'ura, data fara kawo mani ayoyi da hadisai sai na cikawa wandona iska domin bazan iya mayarwa ba, wata shegiyafa ingaya maku wai tuk'eni tayi sai na kawo mata sunayen Kulafa'u... mema ake cewa k'arshe?"


"Kulafa'urrashidina" Usman ya k'arasa masa


"Yauwa sufa, tace na kawo mata sunayensu, wai daga nace mata su goma ne aiko me zatayi mani inba dariya ba, tun daga wannan ranar bata sake ganina ba har zuwa yanzu"


Dariya suka k'arayi su duka harda tafaw


"Ai Malam ka samu ko hadisin nan na Ummu Zar'in ka hardace, wallahi ina mai tabbatar maka kodashi zaka yaudari ustazai da yawa, yau ka bata misali d'aya, gobe ka k'ara mata wani, kamin dai ta kaika k'arshe ka d'ebi abinda zaka d'iba ka ware"


"Kai kam kaji dad'inka Usman, gaka da ilimin addini gana zamani, ga kud'i ga babanka wani k'usa a cikin k'usoshin Gwamnati, kaga sai ka tsula tsiyarka yanda kaga dama, duk a yanda ka samu yarinya kasan salonda zaka 6ullo mata dashi"dariyar dai suka sakeyi su duka


Da wannan firar tasu ta tashi, sukayi y'an shaye-shayensu kana kuma daga bisani suka shiga cikin gari domin ganawa da y'an matansu wad'anda suka saba watsewa dasu.


********


Yauma dai kamar kullum suna zaune a k'ofar gida suna fira cikin nishad'i itada Habibinta Usman ya dubeta


"Waini Baby idan mukayi aure wane suna kikeso mu sakawa yaronmu na farko?"


Murmushin jin dad'i tayi domin tana jin dad'in yanda Usman bashi da wani burin da ya wuce ace ya mallaketa a duniya, shiyasa kullum maganarsa idan mukayi aure kaza da kaza


"Nikam in son samu ne Usman mu fara da Abubakar sana sai Umar da kuma takwaranka Usman sai Kuma Aliyu, sauran masu zuwa kuma sai mu binciko daga cikin sunayen Annabawa ko kuma Sahabbai sai mu saka masu"


Murmushin yaudara yayi irin wanda ke kashe mata jiki kullum"Wannan dalilin Lauratu na d'aya daga cikin dalilanda yasa nake k'ara k'aunarki akoda yaushe, domin ke komai a addinance kike binsa, ba ruwanki da wannan y'an k'ak'ale-k'ak'alen irn na y'an matan zamani, to naji sunayen maza su kuma matanfa?"


Shuru tayi na d'an wani lokaci alamun tunani, kana daga bisani ta lumfasa "Ehto Idan son samu ne su kuma matan mu saka masu sunayen matayen Annabi da kuma y'ay'ayensa ko ya kagani?"


Addu'a yayi tare da shafawa akan fuskarsa har zuwa jikinsa"Nagodewa Allah da ya bani mace d'aya tamkar da dubu, wacce mazaje da dama suke neman irinta ruwa a jallo amma basu samu ba, Babyna ni kad'ai, bani bada aronta bare kuma d'ani, Allah ya rayamu tare Babyna sana kuma ya kashemu a tare, domin bazan juri rashinki atare dani ba Baby...


Kamin ya k'arasa maganar tasa hawaye sun fara wanke masa fuska


Cikin tashin hankali ta dubesa "Haba Usman yayinda muke cikin nishad'i, meye kuma na zubar da hawaye?"


"Babyna dole in zubar da hawaye, domin bansan irin rayuwar da zanyi ba a ranar da kika juya mani baya" Ya fad'a tare da kallonta ta gefen idonsa


Murmushin jin dad'i tayi, domin a wannan lokacin ji takeyi tamkar ta rungumesa dan tsananin so da kauna


"Karka damu akan wannan Usman, insha Allahu ni takace har abada, mutuwa ce kad'ai zata iya rabamu"


Ajiyar zuciya yayi cikin farin ciki "Alhamdulillahi"ya fad'a a bayyane kana ya canza akalar firar tasu "Okasha abokinafa bashida lafiya tun shekaran jiya, wallahi ingaya maki zama da k'yar tashi da k'yar, gayen har tausayi yake bani, da zaki samu lokaci ai da kin rakani munje mun dubosa" Ya fad'a tare da fad'uwar gaba, domin bai sani ba wannan karon ko zaiyi nasarsla ko kuwa akasin hakan


Cikin alamu na tausayawa tace "Allah sarki, ashe shiyasa nadaina ganin kunzo tare kwana biyu, zan tambayi Ammi insha Allahu idan ta amince zaka jini (Dayake tun basu dad'e da had'uwa ba Usman d'in ya bata waya)


"Ai Ammina batada matsala insha Allahuma zata amince"


Da wannan sukayi sallama kowa ya kama gabansa.


*******


"Ammi kin gane wannan abokin Usman d'in kuwa Okasha?" Ta fad'a yayinda take gugar kayanta ita kuma uwar tana sharar d'aki


"Ina zan manta yaron arziki, koba wanda Usman ya aiko ya kawo mana kayan azumi da kuma atamfofi ba dab da za'a fara azumi?"


"Yauwa shifa nake nufi, ashe kin ganesa? Wallahi shine bashi da lafiya kuma yana jin jiki sosai, to shine Usman d'in yace na tambayeki ko zaki amince ya kaini na dubosa gobe?"


Cikin tausayawa ta ajiye tsintsiyar dake a hannunta "Allah sarki, koni da inada lokaci aida zanje na dubosa, yaushe yace zai kai kin, eh to, yadai ce duk yanda mukayi dake na sanar masa ko gobe ko jibi"


"Yaron arziki, shiyasa nake sonshi wallahi domin baya yin abu kai tsaye kome zaiyi sai ya nemi izinina"


Da wannan suka ajiye shawarar gobe Usman d'in zaije ya kaita ta gano abokin nasa.....
Y'an mata ku lura sosai da ire-irensu Usman acikin samarinku, a fuska dai idan ka gansu kamar na Allah da Annabi, saboda zakaga sunsha manyan kaya suna zubo maka ayoyi da hadisai kai kace duka kenan, amma a zahirin gaskiya Shed'anma da kansa sara masu yakeyi.Muje zuwa number 18 mu gani shin Lauratu zata iya fad'awa wannan tarkon da Usman ya d'ana mata kuwa, ko kuwa zata zame masa ne kamar kullum?
*Maman Ja'afar*

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [08/05, 11:03 p.m.]

*💘SUNE SILA💘*        19Daga alkalamin

MamanJa'afar✍
Cikin nishad'i mahaifan suka rako y'ay'ayen nasu bakin get inda mai kaisu makarantar yake zaune akan babur d'insa yana jiransu.


Cikin girmamawa Umar d'in ya gaida mahaifan yaran kamar yanda ya sabayi kullum idan yazo daukarsu


Bayan yaran sun hawo mashin d'in ne na baya ya hau baya na gaba ya hau gaba mahaifin yaran ya dubi Umar


"Dan Allah Umar idan ka dawo daga d'aukosu daga makarantar ka sameni nan gida akwai maganar da nakeso zamu tattauna dakai"


Cikin ladabi da girmamawa Umar d'in ya amsa masa da "To ranka ya dad'e sai mun dawo d'in"********


Bayan sun k'ara gaisawa ne mahaifin yaran Alhaji Manniru ya dubi Umar


"Na dad'e ina lura da kai Umar, musamman ta 6angaren gaskiyarka da kuma rik'on amana, hakan nema yasa nayi sha'awar jawoka a cikin harkokina na kasuwanci inda nake sayar da Atamfofi a Santara Maket, ba komai yasa nace maka haka ba, sai dan samun mutane masu amana irinka a wannan zamanin yanada wahala, saboda kowa ka jawo a harkarka maimakon ya zauna dakai sabida Allah kasamu shima ya samu, a'a tsabar bak'in ciki k'okari yakeyi shi ya gina kansa, kai kuma mai dukiya ko oho, wai maima sauk'i sauk'in kenan, wanima k'okarin da zaiyi shine ya watsa gurin kai ka rasa shima ya rasa ku dawo ku duka kuyi tagumi, wai shi idan akayi hakan buk'atarsa ta gama biya"


Godiya Umar yaita ratatowa babu kakkautawa, dan tsananin murna harma rasa kalar godiyar da zaiyi masa yayi.


********


_Bayan wata uku_


Tun daga lokacinda Usman ya fara sanin Lauratu a matsayin d'iya mace ya mayar da ita tamkar wata matarsa ta sunnah, zuwa yanzuma ya daina zuwa gidansu da sunan zance sai dai ita ta samesa a inda yake, gidajen abokansa ko kuma hotel daga cikin hotel-hotel d'inda yake shanawarsa.


A 6angaren zuciyar Lauratu kuwa badan komai yasa take biye masa ba, sai dan kawai ta samu ta lalla6asa ya aureta, domin a tata wautar wai tsuntsu biyu takeso ta jefa da dutsi d'aya, na farko dan ta cikawa iyayenta burinsu na son ganin ta auri mai kud'i badan komai ba sai dan su wuta d'in kamar yanda suka k'wallafa rai, na biyu kuma tanaso ta auresa ne dan aganinta duk wanda zai aureta idan bashi ba ba wani ganinta da mutunci sosai zaiyi ba.


******


Yau kusan wata uku kenan bataga al'adarta ba, hankalinta duk yabi ya tashi, ta shiga damuwa iya damuwa, sai dai babu wanda take ganin zata tunkara da neman shawara akan wannan babban al'amarin da yake tunkarota


Halima ce ta fad'o mata rai, batayi wata-wata ba kuwa nan take ta bugawa Haliman waya


"K'awata kina ina ne dan Allah? Akwai matsalafa"

Ta fad'a yayinda Haliman ta d'aga wayar


"Wallahi bana kusa K'awata, dan yanzu hakama maganar da mukeyi ina Fadama Hotel nida Sanatana


"Ok badamuwa bani lambar d'akin da kike gani nan zuwa yanzun nan" Ta fad'a a tak'aice


Lambar d'akin ta bata kana sukayi sallama ta kashe wayar.


*******


Kamin Lauratun ta iso har ta sallami Sanatan nata ya kama gabansa


"Meke faruwa ne na ganki duk a wani rud'e?" Ta fad'a shek'ek'e tare da dubanta


"Wallahi al'adata ce ban gani ba kusan wata uku kenan, ni babban tsoronama kar ace ciki ke gareni, kinga idan ciki ya bayyana aiba maganar aure kenan ko?" Ta fad'a d'auke da damuwa a kan fuskarta


Dariya Haliman tayi harda k'yak'yatawa "Ashe kema y'ar hannu ce ban sani ba kiketa wani 6o6uoye mani?"


"Yanzu dai ba maganar hannu ko k'afa ta kawoni ba, maganar neman mafita nakeyi"


Tattaro natsuwarta tayi guri guda

"Wannan ba matsala bane nasan gurare da dama inda ake zubar da ciki, zan rakaki sai su aunaki, idan shine a zubar idan kuma bashi bane kinga sai ki k'ara kiyayewa saboda gaba"


Ajiyar zuciya tayi, domin batayi tunanin za'a samu mafita nan kusa kusa ba haka"Kuma k'awata kud'in zubarwar zasu kai har nawa?" 


"Umm ba yawa, dan inaga kwanakima da na raka wata K'awata dubu goma ne aka zubar mata da kamar naki din nan dan wata uku"


Ta gumi Lauratun tayi da hannaye biyun duka, domin tunanin inda zata samo dubu goman takeyi kasancewar yanzu Usman d'in ya fara caccanza mata


"Miyema abin damuwa kuma keda bake zaki biya kud'in ba? Wai wama yayi maki cikin ne? Bani labari mana K'awata" Ta tambaya d'auke da murmushi akan fuskarta


Ajiyar zuciya ta sakeyi "Wani Usman ne inaga baki sanshi ba, amma shine wanda zan aura" Ta fad'a a tak'aice


Dariya Haliman tayi sosai harda k'yak'yatawa "Lallai Lauratu har yanzu ke sakarai ce koko nace yarinya ce ke har yanzu, tayaya wanda zai aureki zai yadda yayi maki ciki? Wai tsaya wane Usman d'inma kike nufi ne? Allah yasa dai ba wanda nake zato bane?"


Nan take gaban Lauratu ya fara dukan tara-tara "Badai Usman d'ina kika sani ba ko? Idan kika san Usman d'ina ai zance dad'a ya tarwatse"


"Indai bak'i ne mai matsakaicin jiki mai yawan saka manyan kaya da hula, mai hawa motoci kala-kala, shine Usman d'inki, to ba shakka shine Usman d'in K'awata, yanzu hakama ina mai tabbatar maki suna Hotel d'in Zamburush suna hutawa"


Nan take kan Lauratu ya fara sarawa, domin har wata jiwa-jiwar banza da wofi ta fara gani


Lura da halinda kawar tata ta shiga ne yasa ta fara lallashinta cikin hikima"Haba K'awata, miye na damun kanki har haka akan wani banza d'a namiji? indai bariki ne damafa ya gaji haka, garama ki saki jikinki kici duniyarki da tsinke, ki manta da wani Usman can kizo na had'aki da manya-manyan mutane wad'anda ma suka fishi komai, shifa dama ba shine mai kud'in ba idanma baki sani ba ki sani, ubansa ne mai kud'in sai abinda ya sammasa, su kuma wad'anda zan had'aki dasu sune masu kud'in da kansu"


"Halima ba zaki gane bane, nifa bawai kud'in nake yiwa ba, a'a aure nakeso nayi wallahi, na gaji da wannan rayuwar haka nan, kullum ganin rayuwata nakeyi tamkar a farki, har fata nakeyi Allah ya kawo mani ranarda zan farka daga wannan naunnauyan baccin da nakeyi, amma ina? Kullum komai sai k'ara ta6ar6are mani yakeyi na rasa dalili Halima" Cikin kuka ta k'arashe maganar tata


Dariya Haliman ta kumayi "Yanzu Lauratu in baya ga rashin tunani irin naki, kin ta6a ganin inda gaye mai ji da komai kamar Usman ya auri talaka y'ar talakawa marar galihu babu ilimin addini dana zamani irinki? Ire-irensumafa ba kasafai suke auren bare ba sunfiyin auren zumunci, ma'ana kud'i+kudi"


Kukan Lauratu kara tsananta yayi


"Wallahi Halima tun farko banyi wannan tunanin ba kaina a kulle yake, aida duk hakan bata kai ga faruwa akaina ba"


"Dama ina zakiyi tunanin haka? Ai kowama baya tunanin hakan saidai kawai ya wayi gari ya ganshi a hakan, nima duk ba daga haka muka faffara ba, wai Kuturu yaga mai k'yabsi"


Zaro idanuwa Lauratun tayi "Wai kina nufin kema d'an mai kud'in ne ya fara watsaki kika tarwatse haka da wuri?"


"Ai bama d'anba uban ne da kansa, ke dai ayi sha'ani kawai wai d'an birni ya cuci na k'auye"


Murmushin takaici Lauratun tayi "Koko na k'auyen ya cuci na birnin ba? Tunda na tabbata inda ace a k'auyen muke dagani harke mun fara tara yara, mai yiyuwama ke kinada uku ni inada biyu"


Dariya sukayi su duka, da wannan firar tasu ta tashi, amma kamin ta tashin saida Halima tayiwa Lauratu saurayi daga  cikin samarinta K'usoshin Gwamnati duk dan ta kwantar mata da hankali.


**********


A fuska assibiti ce har assibiti lafiya lau idan ka ganta, amma daga ciki babu abinda akeyi face zubar da cikunna.


Cikin jerin matan da ke gurin su Lauratu sukazo suka zauna domin bin layi


D'aya bayan d'aya matan suke shiga cikin 6oyayyen d'akinda ake zubar da cikin, inda ba'ayin minti talatin zuwa arba'in sun fito angama komai kenan.


Kowa ya gama shiga saura su biyu kacal wato Lauratu kenan da kuma wata mata, ita kam Halima tana daga waje tana jiran agama da Lauratun ta fito su tafi


"Dan Allah baiwar Allah kiyi hak'uri zan tambayeki, naga zubinki kamar bana y'an duniya ba, kinfi min kama da matar aure amma kuma na ganki anan? Tun d'azun inata mamaki a cikin raina har dai gashi na kasa 6oye mamakin nawa na fito dashi fili"


Cewar Lauratun kenan yayinda take duban fuskar matar da tasha kayan alfarma da hijabinta da komai


Murmushi matar tayi kana ta dubi Lauratun "Ba kama bane K'anwata ni matar aure ce kuma ciki nazo zubarwa kamar yanda kika gani"


Zaro idanuwa Lauratun tayi alamun mamaki k'arara akan fuskarta "keko baiwar Allah me ya kaiki yin wannan d'anyen aikin da mutuncinki da komai?"


"Wallahi nima badan naso ba K'anwata, dole ce tasakani yin hakan, wannan ba shine na farko bama dana ta6a zubarwa, ina tsammanin kusan na hud'u nema wannan"


K'ura mata idanuwa tayi alamun tambaya k'arara akan fuskarta


"K'warai kuwa yarinya, wallahi wani aure ne akayi mani gashi nan dai, tun ina yarinya nakeda wanda nakeso, amma ina girma lokaci guda aka had'ani da wani na daban, nayi masu biyayya na zauna fashi amma kam nayi alk'awari a cikin raina insha Allahu bazan ta6a haihuwa a gidanshi ba, nida haihuwa sai dai a gidan Kamal insha Allahu, idan kuma hakan bai samu ba, to kuwa ina ganin haka zanta dauwama babu y'ay'a har k'arshen rayuwata""Keko me yayi zafi haka? Ai ya kamata ki yadda da kaddara tunda Allah yayoki cikin musulmai, kuma duk musulmi anaso ya yadda da k'addara mai kyau da kuma....


Lauratun bata k'arasa zancen da ta d'auko mata ba aka buk'aci da mutum d'aya daga cikinsu ya shigo daga ciki


Lauratu ce ta mik'e ta nufi 6oyayyen d'akin tare da fad'uwar gaba tattare da ita, domin tunda take a rayuwarta ko mafarkin hakanma bata ta6a tunanin zatayi ba bare kuma wai ido biyu.


K'aramin d'aki ne mai d'auke da gadaje guda biyu, d'ayan gadon Inyamurin ya umarceta data hau bayan ta cire zaninta da kuma k'aramin wandonta


Hawa tayi ta kwanta rigingine tare da mak'ala k'afafuwanta a jikin k'arafunan dake jikin gadon guda biyu, har yanzu dai gabanta dukan tara-taran yakeyi, dan tamkar tace masa ta fasa takeji, saidai kuma idan tace ta fasa me hakan zai iya jawowa kenan?


Wasu k'arafuna ya d'auko guda biyu daga cikin lodin k'arafan dake lode a gurin tamkar na gyaran mota


Tura matasu yayi acikin gaban nata duka a tsaitsaye kuma


wani uban ihu tasaka saboda tsananin azabar da taji tamkar ranta ne za'a zare mata a daidai wannan lokacin takeji


Tsawa ya daka mata alamun tayi shuru, cikin gwarancin hausarsa yake ce mata "Kasan kana jin soro kaje kabada kanka a wani banza saboda kwadayi naku na mata?"


Wani k'aton sirinji ta kuma ganin ya sake d'aukowa tare da danna mata shi agabanta, anan kam ji tayi tamkar ta suma dan tsananin azaba


Cikin mintina kad'an ya gama zuk'o abinda ke cikin mahaifar tata da wannan sirinjin tare da taimakon wad'annan k'arafunan ya zare sirinjin ya zubar da jininda ya zuk'o, kana ya cire mata k'arafunan ya bata umarni data mik'e


Data mik'en da k'yar ta samu ta rarrafo inda Halima take zaune tana jiranta ta jingina a jikinta


Da dai taga zaman bayayi Kwanciya tayi bisa dogon bencin dake gurin domin bazata iya zama ko tsayuwa ba saboda kwata-kwata jikin nata wani kala take jinsa


"Kuyi hakori na sallami wancen mata sai na baku magani ku duka da ita ko?" Ya fad'a da gwarancin hausansa tare da nufar 6oyayyen d'akin ita kuma matar tabi bayansa.


*********


Gurin awa d'aya suna zaman jiran likitan, amma shuru kakeji ba Inyamurin likita ba kuma wannan matar kamar an shuka dusa su dukaSaida akayi kusan awa d'aya da rabi kana Inyamurin ya fito tare da duban indasu Lauratu suke ya mik'a masu wayar dake a hannunsa, ga dukkan alamu wayar matarda yayiwa aiki ce yanzu


"Gashi ku kira wani nata ku fad'a masa ta mutu, munyi-munyi amma Blood nata yaki tsayawa saboda ciki nata yayi girma yayi wajen 7 Month, mun yayyankashi a ciki nata amma du da haka saura bai fito ba"Inbaya ga Inna lillahi wa inna ilaihirraji'una babu abinda Lauratu take maimaitawa


Itako Halima ko ajikinta, saima dubansa datayi


"Muma bamu santa ba nan muka had'u da ita, saboda haka bamu maganinmu kawai mu wuce tun kamin y'an sanda suzo suyi awon gaba da kai kamaryanda aka sabayi kullum"


Cikin sauri ya harhad'o masu magungunan suka shiga tasi sukayi gaba abinsu, shima cikawa wandonsa iska yayi, dan bai dad'e da dawowa daga gidan yari ba, yana tsoron kuma ace ansake mayar dashi.....
Kuyi hak'uri masu cewa na tsanantawa Lauratu da yawa, da sannu insha Allahu zan warware maku dukkan zarirrikan dana sak'a maku na labarin, kudai kuci gaba da bina domin jin yanda zata kayaOni Maman Ja'afar wai nida nace shafi 20 nakeso nayi gashi har 20 d'inma ta gabato amma labarin har yanzu yak'i k'arewa😭😭😭

Maman Ja'afar

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [08/05, 3:26 a.m.]

*💘SUNE SILA💘*        18Daga alkalamin

MamanJa'afar✍Kwance yake akan mashin d'insa yayi rigingine idanuwansa a rufe tamkar mai yin bacci yayinda yake rairo wakar Mahmud Nagudu, acikin wani baitinsa inda yake cewa_Ba kaina ba farau ko k'arau ba_


_Laifukana agareki ina tuba_


_Zanen so a zuciya bai goge ba_


_Banyi zaton naso ince zan k'ara ba_


_So da nauyi bance ban dauka ba_


_Nai shirin aure dake yau munyi bankwana._Yayinda ta gama sauraron wad'annan baitocin nasa wani bak'in ciki ne taji ya turnik'eta har ya neman tarwatsa mata zuciya, domin tasan babu wacce yake tunani a daidai wannan lokacin face Lauratu, ma'ana wacce tayi mata katangar k'arfe a tsakaninta dashi tunba yau ba.


Zaliha kenan, Kyakkyawar yarinya son kowa k'in wanda ya rasa, shekarunta bazasu wuce sha takwas ba a duniya, kuma iyayenta nada d'an rufin asiri bakin gwarwado, hakan nema yasa ta samu ilimin addini dana zamani


Tun ba yau ba take mutuwar son Umar, saidai tayi bakin iya yinta, amma abin yaci tura, domin kullum nuna mata yakeyi tamkarma bai san inda ta dosa ba."Sannu da hutawa" ta fad'a a tsorace, domin tsabar wulak'ancin da yakeyi mata har takai tsoronsama takeji


Firgigit ya tashi zaune rai a 6ace tare da harararta duk a lokaci guda


"Ke matsalata dake kenan wallahi dabbanci, dama haka akace maki ana soyayyar ne mutun na bacci a wani zo a bashi tsoro? To na tashi, gani fad'a mani abinda zaki fad'a mani na koma dan ban gaji da baccin da nakeyi ba" Ya fad'a tare da k'ara d'aure fuska


Cikin in ina take mayar masa "Um..Um..dama cewa nayi zuwa wannan lokacin nasan kana gida, shine nace bara nazo mu gaisa tunda ba zuwa gidanmu kakeyi ba" Ta fad'a murya na rawa alamun tsoro


"Dama a garinku mace ce ke zuwa fira a wurin Namiji ba namijin ne ke zuwa fira a gurinta ba ko? Tomu anan namiji ne ke samun budurwa har gida saboda kima da kuma darajarta ba ita ke samunshi a nasu gidan ba"


Mik'ewa yayi tare da nufar cikin gidansu yana surutai "Haba! Matan wannan zamanin sai kace ba matan hausawa ba, namiji da yakamata ace ya biki saboda k'ima da darajarki, amma kin wani zo zororo ke ke binsa, to taya zaiga mutuncinki idan ya aureki musamman ma idan takura masa kikayi har ya aurekin kamar dai yanda kikeson tilastamani?"


Ita dai baiwar Allah koda ya fara surutansa bata tsaya ta ida jin abinda yake fad'a ba Sumui-sumui ta cikawa wandonta iska tayi gaba.


*********


Babu abinda kakeji acikin motar face muryar Babban Malaminmu Shaik Yakubu Musa Hassan Katsina Sautussunnah, a cikin wa'azinsa mai taken Sunnah Sak.


"Waini mutane idan basu bi sunnah ba me sukeso su bi ne saboda Allah? Kijifa abinda yake fad'a wai har wasu y'an addini ke akwai masu sunan Tayi tsab"


Dariya tayi kana cikin dariyar ta dubesa "Kome kuma suke tsanewa yayi tsab?"


"Alwalla mana, wai su idan sukayi alwalla sai ta tsane tayi tsab, kana sukeyin salla, shiyasa sunan ya bisu"


Dariya sukayi su duka harda k'yak'yatawa, kuma a daidai wannan lokacin ne suka samu isowa Dutsin Safe inda anan ne Okasha yake zaune a matsayin mai jinyar k'arya.


******


Babban gida ne mai d'auke da d'akuna barkatai kusan ashirin kuma magewaya guda d'aya, ga dukkan alamu dai ina tsammanin babu matan aure acikin gidan nan.


Cikin mamaki ta dubesa "Wai anan Okashan yake zaune ko kuwa dai ya abin yake? Amma kuma baiyi kama da wanda zai zauna a wannan k'azamin gidan ba, gaskiya kaina ya d'aurefa Usman"


Murmushi yayi tare da K'wank'wasa k'ofar d'aki na biyun farkon shigowa gidan, kana ya fara mayar mata da amsa "Kinsan ance wai ganin dama ne cin Biredi da Aidin shi kuma d'anwake acishi da gatari"


"Amma dai wannan ganin damar tayi yawa da har zatasa mutum ya takura kansa har haka"


Bai samu damar mayar mata da amsa ba Okashan ya bud'e masu k'ofar d'akin cikin alamu na rashin lafiya, rashin lafiyarma irin wanda ke jin jikin d'in nan


Murmushin k'arfin hali yayi


"Kace yau munada manyan bak'i a gidan namu? Ranki ya dad'e kece yau a gidan namu? To bisimillanku ku shigo" Ya fad'a tare da matsawa gefe guda domin su samu damar shigowa.


Har yanzu dai mamaki fal a tattare da ita take dubansa, musamman ma lokacinda ta gama k'arewa d'akin na Okasha kallo, daga y'ar katifa sai kayan kallo, gefe guda kuma kayan sawarsa ne a rarrataye, har yanzu dai zuciyarta bata tabbatar mata ba, shin d'akin Okashan ne ko kuwa dai akasin hakan?


"Bara naje na kawo maku ko ruwa ne ko? kunsan Annabi (S.A.W) Yace duk wanda yayi imani da Allah da kuma ranar lahira to ya karrama bak'onsa"


"Amma dukda haka dai dan Allah daka barsa, kaida bakada lafiya inakai ina wani zuwa kawo ruwa?" Ta fad'a yayinda take dubansa yana layi kamar wani marar lafiyar gaske


"Kinga barsa kawai ya kawo mana ruwan, dan wallahi mak'oshina a bushe yake, gashi d'akin nasams ko y'ar firizar nanma ta gayu babu a ciki" Ya k'arashe maganar tasa cikin zaulaya


Bai k'ara bi ta kansu ba yayi ficewarsa waje domin kawo masu ruwan, a cewarsa kenan


Shuru sukayi daga ita har shi na d'an wani lokaci, kowa da abinda yake sak'awa a cikin zuciyarshi, har kusan minti talatin da tafiyarsa amma har yanzu shuru kakeji tamkar an aiki bawa garinsu


Ta bud'a baki zatayi magana kenan wayar Usman d'in tayi k'ara


Duba wayar yayi tare da katse kiran cikin fushi


"Subhanallahi kiga yarinya tun d'azun sai faman kirana takeyi, nace mata ni mijin aure ne ni mijin aure ne, amma dan rashin kamun kai irin nata wai harda cemani wai itama matar aurence"


Nan take Lauratu taji babu dad'i a cikin zuciyarta, amma sai tayi masa shuru ba tare datace masa komai ba


Can kuma bada jimawa ba wayar ta k'ara yin ringin


Yanzu kam d'agawa yayi "Malama tunda baki yarda da maganar da na fad'a maki ta cewa inada aure ba bara na baki matar tawa domin ki k'ara tabbatarwa" Ya fad'a tare da mik'awa Lauratun wayar


A fusace ta mik'o hannu da niyar kar6ar wayar, a nufinta ta zazzagi koma wacece, sai dai kuma bai bata wayar ba ya mayar da ita a d'ayan hannun nasa, d'ayan hannun ta kaiwa cabka, nanma ya sake kaucewa ya canzawa wayar hannu


Kukan shagwa6a ta saka masa "Dan Allah ka bani ita ko zagi d'aya ne nad'anyi mata kona huce haushin data dasa mani a cikin zuciyata"


Bai bata wayar ba saima saka wayar da yayi a cikin aljihun wandonsa


Itako batayi wata-wata ba ta zura hannunta acikin aljihun nasa da niyar kaiwa wayar cabka


Nan take kokawar wasa ta kaure a tsakanin masoyan guda biyu, yayinda kowa acikinsu yakeson wayar ta zama a hannunsa, kamin kace me ba zato ba tsammani sai ga Lauratu rungume a k'irjin Usman


Kici-kicin k'wacewa ta farayi, amma ina, abu ga tsohon d'an duniya sai 6ullo mata da wani sabon salon na daban yakeyi, a k'arshema rufe mata baki yayi da nasa bakin


Kamin kace me, zance ya fara shan banban...Wa iyazu billahi


_Ya Allah ka kare mana y'ay'enmu da k'annenmu da sauran y'ay'ayen musulmi fad'awa tarkon lalatattu la'anannun Allah irinsu Usman_


Bayan hankali ya kwanta ne ta dubi jikinta taga yanda ya zama, batasan lokacin da ta saka wani sabon kukan ba


Jawota yayi ajikinsa gami da rarrashi "Ya isa mana kukan haka Baby, haba ya kike yin wani abu ne sai kace ba Usman d'inki ba, idan har kina kuka akan hakan ai sai zuciyatama ta shiga shakkun cewa k'ilan dama baki aminta dani yanda na tsammata ba, kodama dai ba zaman yarda da amana mukeyiwa junanmu ba?" Ya fad'a tare da duban fuskarta cikin suffa ta mai yin lallashi


Girgiza masa kai tayi alamun amsawa da a'a "To amma idan bakai na aura bafa? Me kake tsammanin zai iya faruwa" Cikin kukan take tambayarsa


"Karma ki sake yin irin wannan maganar Baby, bakida mijinda ya wuceni insha Allahu, nidai buk'atata bata wuce ki kwantar da hankalinki tamkar komai bai faru ba ta yanda Ammi ba zata iya fahimtar komai ba, ki mun alk'awarin zaki kwantar da hankalinki kinji Babyna?"


Nanma Jijjiga masa kai tayi alamun amsawa.Da wannan ya samu ya lalla6ata taje tayi wanka ta gyara jikinta yazo ya sauketa agida tare da yi mata babbar kyauta.


********


Abin mamaki ko kad'an ko alama Ammi bata lura da wani canji da y'ar tata ta samu tun bayan dawowarta daga dubiya ba, Uwani cema mai karan banin lura da hakan


"Lauratu wai lafiya kuwa k'afafuwanki suke naga sai faman wani rarrabasu kikeyi?" Ta fad'a yayinda taga Lauratun tana lallla6awa tana yin shanya a igiyar tsakar gidan nasu


Harararta Lauratun tayi "Miye kuma a k'afafuwan nawa wanda har ya zama nasa ido?"Murmushin na ganoki Uwanin tayi kana ta dubeta "Babu komai y'ar lelen Ammi kawai dai naga bakya tsalle ne agurin shanyar kamar yanda kika sabayi kullum"


Tsaki tayi kana taci gaba da yin shanyarta.


********


Yau sati biyu kenan da faruwar wannan lamarin a tsakaninsu, amma ko aikowa kiranta Usman yayi bata zuwa, wayarsama ta daina d'agawa, har abokansa ya turo ban hak'uri amma tak'i sauarararsu.


K'warai Ammi ta Lura da wannan canzawar da Lauratu tayiwa Usman na k'in kulasa, saidai bata zurfafa tunaninta akan gano silar samun canjin ba, ita tunaninta kawai akan mahassada sun kutso kai a cikin lamarin ne ya k'are


Yau dai ta gaji da ganin y'an kunbure-kunburen da Lauratun takeyi kwana biyu a cikin gidan ta zaunar da ita a cikin d'aki


"Waini Lauratu mike faruwa tsakaninki da mutumin naki ne? Kodai wani magulmacin ne yayi k'ulalliya yake neman ya rabaku? Dan Allah Lauratu kar kiyi mana salalar tsiya azziki yana K'wank'wasa mana k'ofa ke kuma kina k'okarin hanashi shigowa" Ta fad'a cikin suffa ta mai yin lallashi


"Wallahi Ammi babu komai kawai dai sonshi ne banayi yan...


"Kul karki k'arasa abinda kikayi niyar fad'a, idan bakya sonshi ubanki kikeso? So kike ki mayar damu mutanen banza mutanen wofi? rumui-rumui anzo anyi magana kina neman 6ata mana sha'ani, kodai d'an banzan yaron nan ne Umar ya sake kunno wata wutar ta daban?"


Da fad'a da lallashi da komai Ammi ta samu ta shawo kan Lauratu akan zata kira Usman d'in su sasanta.


*******


Da buga wayar bata dad'e tana ringin ba ya d'auka "Baby an huce kenan? Nasan dai zuwa yanzu kin warware, yaushe zanzo mu k'ara fita ne?"


Wani k'unci taji yana k'okarin tokare mata zuciya "Niba wannan maganar tasa na kiraka ba, kan maganar aurenmu ne dama nakeso mu tattauna"


"To ai Baby bankai ga tafiya karatun ba bare kuma har nadawo ayi maganar auren...


"Dama Ammi ce tace na fad'a maka wai ka turo ayi auren inyaso ina gidanka sai katafi karatun""Na tafi na bar matata a wata k'asa ni kuma ina wata k'asar ta daban? Gaskiya bazai yiyu ba Baby saboda inada tsananin kishi a kan abinda nakeso musamman ma ke"


Nan dai yayita tsattsarata da kalamai harta mancema da damuwarda take ciki sukaci gaba da firarsu cikin nishad'i tare dayi mata alk'awarin zai shigo unguwar tasu zuwa dare.......


Wai ya labarin bawan Allah Umar ne? Ko wane hali yake ciki zuwa yanzu?


*Maman Ja'afar*

[5/10, 11:11 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [09/05, 10:11 a.m.]

*💘SUNE SILA💘*       20Daga alkalamin

MamanJa'afar✍
"Nifa Lauratu gaskiya wannan kukan naki ya fara isata, haba tunda muka shigo motar nanfa kiketa faman yin abu d'aya, itama ai harda laifinta tunda ta riga tasan cikinta ya girma kuma da ubansa meye na wani zubarwa? Kodai jikin naki ne yakeyi maki ciwo kika fakewa da motuwar waccen matar?"


Murmushin k'arfin hali tayi "Waike Halima meyasa bakida imani ne har haka? D'an mutum ya mutu a gurinki sai kace mutuwar d'an tsako? Ni wallahi mutuwar batama tsaya mun a rai ba irin yanda labarin wani da takeso ya tsaya mani arai, na rasa gane dalilin da yasa labarin matar yake tayi mani kai komo a cikin zuciyata" 


"Yanzu dai ina muka nufa? Kinsan dai bazai yiyu mu tunkari gidanku a wannan halinda kike ciki kina langa6e-langa6e ba ko?"


Gabanta ne ya fad'i lokaci guda "Ehto hakane kam, to amma ke a ganinki ina ya kamata muje yanzu?""Gidanmu mana, ai can ya kamata ace kin kwana zuwa gobe kin d'an ji k'arfin jikin ki sai ki wuce gida koya kika gani?"


Shuru tayi na d'an wani lokaci alamun nazari "Gaskiya Halima akwai matsala, saboda tunda nake a rayuwata banta6a kwana a wani waje ba inba gidanmu ba, kuma kinga dama mutane da yawa zargina sukeyi akan ina bin maza kasancewar yanda rayuwata ta taso tun farko a gurin masu abinci, to kuma me kike tsammani idan akaga na fara kwana a waje? Musamman ma wannan Uwanin ta gidan namu y'ar sa idon tsiya"


K'asa-kasa sukeyin maganar tasu ta yanda ba lallai ne mai tasin ya fahimci abin suke cewa ba"Malama idan zakisha giya gwara kisha ta dubu, tunda har aka fara zarginki da iskanci, to wallahi sammakal, ko kiyi ko kar kiyi, su agurinsu a matsayin mai yi kike, gwarama kiyi d'in kisan kinyi, kinga sai su samu damar yin zaginsu da hujja"


Da wannan firar suka samu damar k'arasowa gidansu Haliman.


********


A tsakar gida suka samu mahaifiyan Haliman ta tak'ark'are sai faman wanke kayan Haliman takeyi (Wannan lalacewa har ina haka)


Sallama sukayi a tsakar gidan tare da shigowa kai tsaye, Lauratu ce ta tsaya tana gaishe da Maman Haliman amma ita uwar gayyar d'akima ta wuce kai tsaye abinta, saima uwar data bita da sannu da zuwa.


D'aki Maman Halimar ta biyosu tare da dubansu d'aya bayan d'aya 


"Wai daga ina kuke ne tun yamma haka sai yanzu cikin wannan daren kuke dawowa?"


"Lauratu ce bata lafiya shine na rakata assibiti" d'iyar ta fad'a a tak'aice tana wani ciccin magani


"Kwanta ki huta Laure ni bara na fita na nemo maki abinci, daga nan sai na wuce gurin Ammi nasan abinda zance mata idan naje, Mamar tawa dai nasan abinda tayi bazai wuce tuwo ba" Ta fad'a tare da duban mahaifiyar tata cikin zaulaya


Dariya uwar tayi kana daga bisani ta maida hankalinta akan Lauratun wacce ke kwance malala


"Waike me yasameki ne da bakya iya zama sai kwanciya Lauratu?"


Zuge jakar hannunta Halima tayi, tare da k'irgo kud'i sabbin y'an dubu-dubu har guda goma ta dannawa uwar a baki


"Kai Halima, madadin ki bani kudin a hannuna shine sai kuma ki wani cusa manisu a baki sabida Allah?" Uwar ta fad'a yayinda take murmushin jin dad'i


"To ai mama bakin ne naki ya cika tambaye tambaye nakeso yayi shuru shiyasa"


Dariya sukayi su duka kana Haliman tayi waje batare dako cewar uwar saina dawo ba


A zuciyar Lauratun kuwa tunani takeyi shin tsakanin mama da Ammi kowa yafi wani lalacewa? Da kanta ta bawa kanta amsa "Kai gara Ammina wallahi"


(Ni kam nace duk dai sammakal k'waryar sama ce ke dukan ta k'asa)


********


Bayan sun gama gaisawa da Ammin ne ta dubeta cikin alamu na tuhuma"Ina kika baro K'awar taki kuma na ganki ke kad'ai?"


Murmushi tayi cikin ladabinta na munafunci "Ai dama Ammi kan maganarta ne nazo"


Firgita Ammin tayi "Allah yasa dai lafiya?"


"Lafiya kalau Wallahi, dama wai ce mata nayi dan Allah inaso ta rakani 6atagarawa gurin bikin d'iyar kanwar mamana gobe jibi sai mu dawo, shine tace mani wai tunda take baki ta6a barinta tayi tafiyar kwana ba, wai tsoro takeji ta tunkareki da wannan maganar, shine nace to ni bara nazo na nemi alfarma gurin Ammina" 


"To ita ina Lauratun take wai yanzu?" Ta tambaya a tak'aice


Wuri-wuri da idanuwa tayi alamun rashin gaskiya, kana kuma daga bisani tayi dariyar k'arfin hali


"Tana can gidanmu ai na barota wai kunyar tambayarki takeji shiyasa tace bara ta zauna a gidanmu inyaso duk yanda mukayi dake wai na sanar mata"


Shuru tayi na d'an wani lokaci alamun tunani "Dan kwana kam ba son tafiyar kwana nakeyi ba gaskiya, saboda yanda zamanin nan namu ya lalace musamman ma kai mai d'iya mace, amma ba komai dan Allah Halima karku wuce jibin kinji?"


Murmushi Haliman tayi "Insha Allahuma bazamu wuce ba Ammi, yauwa idan baba ya dawo sai ki fad'a masa inda mukaje"


"Kudai Allah ya tsare hanya kawai, Babanta ko wata d'aya zatayi bata gida ai basani zaiyi ba tunda idan ya fita tun safe bashi yake dawowa ba sai lokacin bacci"


Da wannan sukayi sallama Haliman ta dawo gida.


********


Yauma dai fad'an sukeyi itada aminiyar tata kamar yanda suka sabayi kullum tun bayan warwarewar Lauratun


"Waini Lauratu me kike nufi da Alhaji Lawal ne? Kullum bawan Allahn nan sai faman binki yakeyi yana kashe maki kud'i amma har yanzu kin k'i bashi had'in kai, yanzu harmafa ya fara ganin laifina, tun ina kare kaina har takai nama rasa k'aryar da zanyi masa" Ta daddage sai faman fad'a takeyiwa Lauratun sai kace ta samu wata d'iyarta


"Kinga Halima nifa tunda wannan matar ta mutu a gabana nayi alk'awarin daina wannan harkar, dama can ba halina bane ba, kawai tsautsayi ne ya abka mani da kuma la'anannen Allah Usman, amma yanzu nagane gaskiya babu abinda zansa agabana da ya wuce karatuna, sai kuma istigfari da fatan samun miji nagari"


"Yanzu ke wannan hanyar kike ganin ta fiye maki?" Ta fad'a a tak'aice d'auke da mamaki akan fuskarta


"K'warai kema da zaki bi hanyar saita fiye maki alkhairi" Ta mayar mata da amsa rai a 6ace.


Duk yanda Halima tayi akan ta shawo kan K'awar tata suci gaba da harka abin ya gagara, k'arshe dole sai dai hak'ura tayi tayi tafiyarta.


Dama Lauratu badan taso takeyin harkar ba, kawai tanayi ne dan ba yanda zatayi, ita kanta idan ka tambayeta miyasa take yin wannan harkar batada amsarda zata iya baka.


*********


Kacokam ta mayar da hankalinta akan karatunda ta saka gaba na islamiyya, kuma dama ba laifi tana gane karatun sosai, domin ko wani taro za'ayi na makaranta ko Musabaqa da makamancinsu tana a cikin sahun gaba, yanzu kam hankalinta ya fara kwanciya, sai dai kuma wata sabuwar matsalar dake neman kunno kai, wato damunta da iyayenta sukeyi akan a dole sai ta fitar da wani mijin tunda ta kori Usman.


Yauma babanta ne da kansa ya tasata a gaba a cikin d'akinsa yana yi mata fad'a


"Yaunzu Lauratu rayuwa ta yiyu haka babu aure? Dafa kamar abin arziki kika kawo wannan yaro d'an arziki Usman, kuma kwatsam kikazo kika koreshi, to yanzu wa kika fitar a matsayin wanda zaki auran kuma?"


Shuru tayi har saida Ammi ta maimaita mata tambayar kana ta bud'a baki "Baba wallahi banida kowa, kudai kuci gaba da tayani da addu'a Allah ya bani nagari kawai"


"Maganar banza maganar wofi, duk manyan masu kud'in da suke zarya gidan nan kina nufin duk bana gari acikinsu ko kuwa me kike nufi? (Ammi batasan cewa duk yan abi yarima bane asha kid'a)


Shuru tayi batare datace masu komai ba, nandai suka k'araci fad'ansu ta tashi takoma d'aki, tunani fal a cikin zuciyarta.


Kusan kullum takanji k'unci da damuwa a cikin zuciyarta amma har yanzu ta rasa gane dalilin yin hakan


Takanji kamar tayi rashin wani abu mai mahimmanci a tattare da ita, amma har yanzu ta rasa gane kome ta rasa d'in, haka nan take gama tunaninta ta watsar da komai


*********


Tsana da tsangwamafa a gurin Ammi ya fara dawowa sabo fil, sai dai wannan karon matsin lambar tata ya k'are ne akan afitar da miji, inda suke ganin kawai Lauratun tak'i fitar da mijin ne dan son ranta amma badan babu ba.


A hankali a hankali kulawar da take samu a gurin mahaifiyar tata ta fara raguwa, tun tana jurewa akan rashin wasu abubuwan na bukatun rayuwa har dai takai ga ta kasa jurewa, domin wani lokacinma har kud'in Audugar da zata siya idan tana al'ada gagararta sukeyi, maganar y'an k'ananun matsaloli dama batasu akeyi ba.A irin wannan halin ne tadai gaji da rashin wasu abubuwan harta samu damar kiran Alhaji Lawal (Shikenan ta koma ruwa)


Ba zato ba tsammani saiga Lauratu ta tsinci kanta ta koma ruwa tsundum, amma dukda hakan ruwanda ta koma bai hanata ci gaba da zuwa makarantarta ba.


Yanzu kam zamanta da Ammi ya dawo kamar da koko nacema ya wuce nada d'in, saboda yanzu lokutta da dama itace mai d'aukar nauyin gidan nasu gaba d'aya, wani sa'inma har rancen kud'i take bawa Ammin nata ko kuma ajiya, amma abin mamaki har yanzu Ammi bata ta6a tunanin ina Lauratu take samo wad'annan mak'udan kud'aden ba, ita kawai gani takeyi duk masu sonta da aure ne suke kawo mata, shiyasa kullum take damun Lauratun da kice masu su turo, su turo, ayi agama hankalin kowa ya kwanta.**********Zaune suke acikin aji kamar yanda suka saba kullum, malamin ya dage sai ratattabo masu bayani yakeyi akan hanyoyin da akebi domin warware sihiri inda yake cewa.


"Asamu ganyen Magarya guda 7 a nike shi sai a zuba acikin ruwa mai kyau mai tsabta sai a karanta..


Ayoyi na 117 zuwa na 122 a cikin Suratul-Aaraf


Da kuma Ayoyi na 79 zuwa na 81 acikin Suratul-Yunus


Sai kuma Ayoyi na 65 zuwa na 70 daidai a cikin Suratul-Taha


Sai Ayatul-kursiyyu, Suratul-Kafirun, sai Suratul-Iklas, da kuma Falaqi da Nasi, k'afa uku uku


Sai kuma a Had'a da addu'o'in neman waraka da neman sauk'i agurin Allah (S.W.A) kamar yanda Sunnah ta tanadar


Za'a karanta wad'annan ayoyin na sama acikin ruwan Ganyen Magarya guda 7 da aka nik'e sai a dinga bawa wanda akayiwa sihirin yana sha kuma yana wanka, insha Allahu duk wani sihiri da akayi masa zai karya


Kuma ayawaita karatun Alqur'ani mai girma musamman ma Suratul-Baqra saboda tsarinda takeyi kamar dai yanda ya tabbata a cikin hadisi ingantacce, sai kuma a yawaita azkar na shiga band'aki dana fitowa, dana kwanciya bacci da kuma na tashi, da yawan tuba daga zunubbai.


"Ina fatan kun gane?" Malamin ya fad'a tare da dubansu d'aya bayan d'aya


Jijjiga kai sukayi alamun amsawa da Eh.


Bayan Malamin ya fita ne Ummi ta dubi Lauratu wacce ta dage sai faman rubuta bayanin malamin takeyi a takarda


"Ke kuma miye na wani rubutawa a takarda sai kace wacce akayiwa sihirin?"


Murmushi Lauratun tayi "Inma ba'ayi mani sihirin ba ai idan na hardace agaba zan iya taimakawa wani da akayiwa ko? barema ni da kaina jin kaina nakeyi tamkar wacce akayiwa sihirin"


Cikin mamaki ta dubeta "Ke d'in kuma a wa da har mutum zai tsaya yana 6ata lokacinsa akanyi maki sihiri? Ni naga manyan mutane sunfi fuskarta ire-iren wad'annan matsalolin bake da kikazo duniya yanzu ba"


Dariya tayi "Nima dai wani lokacin idan tunanin hakan ya fad'o mani har k'aryata kaina nakeyi, saidai fa Ummi abinda baki sani ba shine, wasu lokuttan da dama nakan jini tamkar bani din bace idan inayin wasu abubuwan, ke wani lokacimafa gani nakeyi duk wasu abubuwanda ke faru dani tamkar a mafarki ne nakeyinsu, a tsammanina shaid'an ne yakeso yayi mani yawo da hankali, amma dai zan gwada wannan maganin insha Allahu, inma Shed'an d'in ne nasan zai kama gabansa tun ayar Allah ce akace a karanta"


Ita dai Ummi ba wani gane kan firar Lauratun takeyi ba, kawai dai tana biye mata ne har lokacin tashinsu yayi aka tadasu kowa ya kama gabansa.


*********


_Bayan wata d'aya_Tun daga wannan lokacinda aka koya masu hanyoyin warware sihiri Lauratu ta duk'ufa wajen aiwatar da wannan maganin baji ba gani, itama kanta idan ka tambayeta dalili batasan meyasa takeyi ba, kawai dai tanayi ne saboda zuciyarta ta natsu da yin hakan.


Yauma dai kamar kullum ta gama yin na dare tayi alwalla tare da yin addu'o'inta na kwanciya bacci kamar yanda hakan ya zame mata al'ada tun karatun da malamin yayi masu a baya.


Can cikin baccin nata ne ta farka a firgice tare da yin wasu sabbatu naba gaira babu dalili


Cikin rud'ewa Ammi ta rik'eta tana tambayarta "Lafiyanki kuwa Lauratu? Kodai mummunan mafarki ne kikayi?"


Waige-waige Lauratun ta farayi tamkar wata mahaukaciya sabon kamu "Ammi wallahi mafarki nayi wai Umar zai fad'a rijiya, inata kiransa bayaji, kamin na iso inda yake wai har ya fad'a, anya Ammi ba wani abune zai sami Umar d'ina ba? Kuma Ammi kwana biyumafa bana ganinsa, kodai ya aiko Rukayya tazo ta tarar ina bacci ne?"


Nan take hankalin uwar ya tashi domin tabbas tasan yau komai nasu ya gama wargajewa, gashi bokan natama yau satinsa biyu da rasuwa, kanta ya kulle tunanin mafita kawai takeyi


Mik'ewa Lauratun tayi tare da saka hijabinta wanda Umar ya bata, rabon da naga ta saka hijabima ai inaga har na manta sai dai kuwa idan islamiyya ce zata tafi


Rik'eta gam uwar tayi

"Haba Lauratu ina zakije cikin wannan tsohon daren? Duba agogofa ki gani kusan k'arfe biyu na dare yanzu"


"To ai Ammi bansan halinda Umar d'in yake ciki bane shiyasa nakeso naje na gani"


Uwar ta tsorata k'warai da ganin canzawar da y'ar tata tayi lokaci guda, amma bata nunama y'ar tata hakan ba saima lallashin y'ar dataci gaba dayi akan ta bari zuwa goben da safe sai taje ta gano Umar d'in nata.


********


_Washe gari_


Tun safe taso zuwa ganin Umar d'in nata, amma hakan bai yiyu ba saboda wani matsanancin ciwon kai data tashi dashi, ina tsammanin tunani ne yayi k'wakk'walwar tata yawa


Sai zuwa dare ne bayan sallar isha ta d'an samu sauk'in ciwon kan nata


"Hafsatu ina mutumina ne ko har yayi bacci?" Ta fad'a yayinda tazo wucewa ta K'ofar d'akin Hafsatun


Cikin mamaki Hafsatun ta dubeta "Wane mutumin naki kuma kike tambaya Lauratu?" Dayake tun lokacinda Lauratu ta juyawa Umar baya suka daina wani shirin kirki da Hafsatun


"Umar mana, ko inada wani mutumi ne daya wuceshi? Yanzu hakama gidansu zanifa"


"Allah mai iko, to dai Umar nawa yana d'aki yana bacci, kodama ba baccin yakeyi ba nasan ba zuwa wajenki zaiyi ba, domin duk sadda ya tunkareki dukane da zagi da hantara ke rabaku dashi, tun yana lik'e maki har ya gaji ya fara gudunki"


Nan take kan Lauratun yaci gaba da sarawar da yakeyi, domin sai yanzu take tuna irin abubuwanda sukayita faruwa da ita marasa kyau a baya


Bata mayarwa Hafsatun da amsa ba, domin koda tayi niyar mayarwama batada abin cewa akan hakan, saboda abinda ya faru dai ya riga ya faru.


*******


Kai tsaye gidansu Umar d'in ta shiga, domin yau ko d'an aikenma bata tsaya nema ba


A firgice tayi sallama a tsakar gidan tare da y'an waige-waigenta, ga dukkan alamu dai ina tsammanin Umar d'in nata take nema


Hadiza na tsakar gida ta kunna fitila tana bitar karatun ta, yayinda sauran matan duk suka k'umshe kansu a cikin d'aki saboda yanayin sanyi da ake ciki, duban Lauratun tayi shek'ek'e "Baiwar Allah lafiya daga ina?"


Cikin in ina take mayar mata da amsa "Lafiya k'alau, Hadiza baki..ganeni..bane?" Ta fad'a d'auke da murmushi k'arfin hali akan fuskarta


"Mama! Mama! Fito kiga Lauratu yau a gidanmu" Ta fad'a yayinda take k'walawa mahaifiyar tasu kira 


Cikin sauri Uwar ta fito d'auke da Muciya a hannunta, domin ganin Lauratu a gidansu tamkar ganin annoba ne


"Ke lafiya kika shigo mana gida cikin daren nan haka?" Uwar ta fad'a d'auke da masifa fal a kan fuskarta


"Um..Um..Dama nazo gurin Umar ne..


Da hanzari Uwar ta nufeta da wannan muciyar, badan ta gudu ba na tabbata da Mamar saita 6alla mata k'afa


"Mutuniyar banza mutuniyar wofi, nasamu Allah ya taimakeni ya dawo cikin hayyacinsa shine kika sake lalla6owa dan ki mayar dashi ruwa? Ni badanma yak'i yarda ba aida tuni yayi aurensa ya huta, wai nazo gurin Umar ne, Umar d'in ubanki"


Lauratu na raka6e a zaure take jin abinda uwar ke fad'a


"Mama yaufa Yaya Umar zance ya tafi gurin Zaliha, saidama yace na rakashi nace bazani ba saboda yarinyar jiji da kan tsiya ne da ita"


Murmushi uwar tayi "Har naji dad'i wallahi Allah yasa dai su daidaita kansu mu huta da waccen jarababbiyar"


Babu abinda Lauratu take maimaitawa acikin zuciyarta face sunan Zaliha.


*******


Da barinta gidansu Umar d'in bata zame ako ina ba sai a gidansu Zalihar da take tsammani 


Zaune ta hangosa akan mashin d'insa Tsuntsun soyayya irin wanda matasa ke yayi a daidai wannan lokacin, yasha manyan kayansa masu kyau harda wata hula ya d'ora akai, idan ka gansa kai bakace Umar d'inda ka sani abaya bane, saboda wannan Umar d'in ya kere wancen had'uwa da kuma alamun hutu nesa ba kusa ba


Ita kuma Zalihar jingine take ajikin bangon gidan nasu, sai wani jifan Umar d'in takeyi da murmushi


Saida Lauratu ta samu gefe guda ta natsu taci kukanta ta gaji kana ta tunakari inda su Umar d'in suke


Sallama tayi masu jiki a sanyaye, nan take gaban Zaliha ya yanke ya fad'i, domin tana murna Umar ya fara saurararta har yana zuwa gidansu yanzu kuma ga wannan annobar ta sake kunno kai


"Umar inason ganinka idan bazaka damu ba?" Ta fad'a a tak'aice (Hhhhh tarihi ya sake maimaita kansa)


Shek'ek'e ya kuma dubanta karo naba adadi "Ai gani kina kallona ko, k'are mani kallon sai ki tafi"


"A'a waida ina nufin magana nakeso nayi da kai?" Ta fad'a murya na rawa


"Allah mai iko! Da Wuri-wuri haka har kin gama y'an yawace-yawacen naki a hotel, da fira a cikin motar samari da bin alhazawan birni? Gaskiya abin yayi wuri sosai, kodai har sun gama yayinki ne sun watsar dake?"


Batasan lokacin da kukanda take k'okarin 6oyewa ya bayyana kansa ba


Duk'awa tayi har k'asa "Dan Allah dan Annabi Umar kayi hak'uri kayi mun rai, nasan duk abinda kake tuhumata akai na aikata, amma wallahi tallahi bansan ta yaya na aikata hakan ba, Umar nasan cewa fushi ne mai tsanani kayi dani amma har abada na tabbata duk yanda nake duk kuma yanda nazama Umar d'ina zai k'aunaceni, kayi mun uzuri Umar wallahi na gyara halina na tuba bazan sake ba...


Kukane yaci k'arfinta ta dakata da maganar da takeyi hakanan


Tabbas yaso jin k'amshin gaskiya a cikin magan-ganunta, saboda abubuwanda taitayi sun wuce hankali, tunaninsa a guri d'aya ya tsaya, wato wani hauka ne na wucin gadi ya sameta


Cire bak'in gilashin idonsa yayi tare da share k'wallar da ta tarar masa a idon


Zaliha na ganin haka batayi wata-wata ba ta shige cikin gidansu yayinda itama hawaye ke bin fuskarta, saboda samu data gani gashi kuma tun ba aje ko ina ba tana k'okarin ganin rashi (Ta bani tausayi fa)********Ba k'aramin aiki Lauratu tasha ba kamin ta shawo kan Umar d'inta, amma abisa taimakon Aminiyarta wato Rukayya suka samu ya yada makaman yak'in nasa.


Allah sarki Umar duk tsawon lokacin nanfa da aka d'auka dama son Lauratu bai ta6a gushewa daga cikin zuciyarsa ba, kuma kullum a cikin addu'ar nema mata shiriya yake, kana kuma daga bisani idan yagama yi mata addu'ar shiriyar sai kuma ya rok'i Allah daya karkato masa da hankalinta zuwa gareshi.


Hmmmmm na rasa gane ko wane kalar so Umar yakeyiwa Lauratunsa har yanzu.


********


A 6angaren iyayen Lauratun kuwa wannan karon basuyi wani musu ba akan auren Umar d'in, inaga hakan ya samo asali ne na rashin ganin tsayayyen manemin da yazo gunta har yanzu, koko dai ganin sunan y'ar tasu ya fara 6aci ne yasa suka amince da wuri-wuri haka? Oho.


Lamarin sauran y'an'uwan Lauratu kuwa maza, sai abinda yayi gaba domin yanzu haka Kabiru baya yin cikakken wata d'aya agida ya koma gidan yari, saboda yawan aika-aikar da y'an jam'iyarsu suke sakasu suna aikatawa (Sare-sare da yanke-yanke)


Zubairu kuwa sai ya tuba da yin sata, sai kuma ya sake dawowa ruwa, ko me yakesa hakan? Ina tsammanin k'ilan rashin karatu ne da kuma sana'ar yi da ba'a koyar dashi ba tun farko ba.


*******


Da k'yar da ji6in goshi iyayen Umar suka amince masa akan Auren Lauratu, musamman ma mahaifiyarsa da saida dangi suka babbata baki kana ta amince, ammada ta tu6ure akan cewa d'anta bazai auri karuwa ba.


*******


Allah yayi, wai aure da marar kwabo


Yaya Zubairu na hango acikin taron jama'a sai faman baza babbar rigarsa yakeyi, baki kuwa har kunne saboda murnar auren k'anwarsa da aka d'aura yau, kuma itada Habibinta Umar.


*******


_Bayan shekara 7_


Cikin fushi ya dawo ya sameta, sai faman kukkunbura takeyi tana batsewa


Murmushi yayi tare da rungumeta a k'irjinsa "Haba Mai gyad'a, me kuma nayi da ake nema a hukuntani ta wannan hanyar?" Ya fad'a cikin alamu na zaulaya


K'ara d'aure fuskar tayi "Dazu ne nadawo daga makaranta (Dayake yanzu Da'awa take zuwa ta asabar da kuma Lahadi saura shekara d'ayama ta kammala) Abubakar yake shaida mani wai kai dashi kunje gidansu Ammi har kuka kai masu kayan abinci masu yawa, bayan nasha fad'a maka indai dan ni zaka taimakesu wallahi har abada na yafe maka, domin basu cancanci yin hakan daga gareni ko kuma daga gareka, Umar ka tuna bayafa sadda nake neman taimakonsu ido rufe sun taimaka mani? Duk suwa suka jawo lalacewar tarbiyyata? Kuma...Katseta yayi tare da d'aure fuska alamun babu wasa


"Lauratu kullum sai na fad'a maki banason irin wannan tsanar da kike nunawa iyayenki, wallahi hakan ba k'aramin k'ona mani rai yakeyi ba, iyayefa iyayene koda kuwa iyayen d'an akuya ne, ki manta da abinda sukayi maki a baya, kiyi amfani da ilimin da Allah ya baki kisan yanda zaki zauna dasu, ko kin manta kissar Annabi Ibrahim ne?"


"Nasani Farouq amma idan na tuna ta sanadiyarsu ba kaine ka kar6i budurcina ba abin yana yi mun ciwo matuk'a a cikin raina, wallahi wani lokacinma har ji nakeyi tamkar na kashe kaina na huta, harda wannanma yake k'ara mani tsanarsu acikin raina wallahi"


D'ora hannunsa yayi akan bakinsa shiiiit alamun tayi shuru


"Tun ba yau ba Lauratu nake fad'a maki banason irin wad'annan magan-ganun da kikeyi na budurci ko makamancin haka, nidai Allah na gani Lauratu nakeso ba budurcinta ba, kuma Lauratuna na aura danme zan dami kaina akan wani budurci can na daban? Karki manta kodama kin kawo mani budurcin naki ai ba dawwama zakiyi dashi ba, dole dai zai gushe, amma Lauratuna har abada bazata ta6a gushewa daga cikin zuciyata ba, saboda haka daga yau sai yau nasaka dokar hana ambatar sunan budurci a cikin wannan gidan har abada indai na isa kuma ana jin maganata"


Rungumesa ta k'arayi tare da sakin kukan murna da godiya ga Allah (S.W.A) daya azurtata da miji d'aya tamkar da dubu


"Nifa ina mai tabbatar maki ko aure na tashi k'arawa bazawara zan aura badan komai ba sai dan karkiji wani k'aik'ayi acikin ranki nacewa kodan ban sameki da burci ba na auro budurwa, barema bana tunanin k'ara wani insha Allahu, dagaani saike acikin gidan, sai kuma y'an yaranmu" Ya fad'a tare da k'ara rungume abarsa


Da wannan yasamu yayita lallashinta har dai yaga ta fara dariya alamun ta manta da komai


"Waini ina Masu manyan suna ne naji gidan shiru?" Ya fad'a tare da y'an waige-waigensa


"Abubakar da takwaranka dai sun dad'e dayin bacci, Rukayya kuma gata can saman kujera a bayanka tana yin nata baccin, Shehu ne dai yayi ta rigima wai bazaiyi bacci ba har sai ya ganka, yanzuma baifi mintina da yin baccin ba na kaishi dakinsu na kwantar"


D'aure fuska yayi cikin wasa"Wai dan Allah yaushe zaki daina kiran yarona da suna Shehu?"


"To ai sunan Usman d'in ne ba dad'inji wallahi, amma duk ranar da ka daina kirana da mai gyad'a ni kuma zan dinga kiransa da asalin sunansa" ta fad'a cikin shagwa6a.Tammat bi hamdullah.
*GODIYA*Godiya da yabo da jinjina sun tabbata ga Allah (S.W.A) mai kowa mai komai daya nufeni da fara rubutun wannan littafi lafiya har gashi kuma cikin yardarsa da amincewarsa na kammalasa lafiya kamar yanda na fara batare da ansamu wata tangarda ba .
Bara nayi amfani da wannan damar nayi kira ga mutane kamar haka


1 Da farko kirana akan iyayenmu ne zanyi shi talakawa


Ku sani cewa yayayenku amana ce Allah ya baku ta 6angaren cinsu shansu tarbiyarsu, da sauran duk wasu hakkoki da suka rataya akanku nasu, talauci ba hujja bane da zaisa ku banzatar da y'ay'ayenku yanda kukaga dama, domin shi Allah babu ruwanshi da hujjarku ta talauci amanar da ya baku kawai zai tambaya ranar gobe k'iyama ta yanda kuka tafiyar da ita


Karku ce dan Allah ya baku yaya mata tamkar wani makami ne ya baku wanda zaku yak'i talaucinku dashi, a'a, Allah nefa ya d'ora maku wannan talaucin da kuke ciki ba yaran ba, kuma duk wata dabararku bazata iya fitar daku ba face shi wanda yaga damar ganinku a hakan ya cireku, yanzu dai ga rayuwar gidansu Lauratu yanda ta kasance wa gari ya waya? Da sunyi hak'uri da wannan talaucin da Allah ya d'ora masu sun d'aukeshi a matsayin jarabawa na tabbata da Allah bazai barsu hakanan ba sai ya samar masu mafita kuma ya azurtasu ta inda basuyi tsammani ba2 Yayayen masu kud'i dasu masu kud'in kansu


Dan Allah indai kunsan ba auren y'ar talakawa zakuyi ba ku daure kudaina zuwa gurinta da niyar yaudara, domin mafiya yawan yayan talakawa sunfi son auren yayan masu kud'i ko masu kud'in da kansu, ku kuma sai kuyi amfani da wannan damar ku dinga yaudararsu kuna lalata masu rayuwa, k'arshe kaga yara sai zama karuwai sukeyi, a karshe kuma kune na farko da zaku fara tsine masu albarka kuna kiransu da karuwai bayan kune silar shigarsu wannan halin da suka samu kansu aciki


3 Yayan talakawa mu rage buri, domin yawan burinmu shiyake kaimu ga halaka


Indai har kika samu miji nagari mai addini da sana'a daidai gwarwado to ki daure ki auresa domin ba'a san arzikinda ke gaba ba, amma yayan masu kud'i kosu masu kudin kansu da kuke likewa wallahi tallahi da yawansu ba auren ne yakawosu ba, kawai sunzo subi yarima ne asha kid'a4 Ina kira ga jama'a baki d'aya a duk lokacin da kaga wani yana cikin hali marar kyau kayi k'okari kayi masa addu'a da fatan shiriya ba tsinuwa ba, domin shi wannan mutumin bakasan ta yanda akayi ya tsinci kansa a irin wannan rayuwar ba, inma da son ransa ko kuka akasin hakan kamar dai na Lauratu.5 Masoya mu ringa yin soyayya ta gaskiya badan kyalekyalen duniya ba, kuma mu dinga rike junanmu da amana, kar muyi so dan kyalekyale domin shi kyalekyale mai k'arewa ne ya barka da masoyinka, karku manta so baya ta6a tsufa saidai masu yinsa su tsufa (Abinda Umar yake rubutawa kenan a bayan mashin dinsa lokacin da suke cikin ganiyar soyayya)6 Shawara ga Matasa ko magidanta idan har kuka auri mace kuka sameta babu budurci a tattare da ita kuyi mata uzuri, ku hakura ku manta da komai ku zauna da ita a hakan batare da canzawar komai ba, domin bakusan ta yanda akayi ta rasashi wannnan budurcin nata ba, ita kakeso ita kuma ka aura, to kayi hak'uri ka zauna da ita a hakan kamar dai yanda Umar yayi.7 Mata a kiyaye kuma a kama kai, domin duk namijinda yasan ciwon kansa mata ta gari yake nema domin ta zamo uwa ga y'ay'ansa.
*GODIYA*


    1


Har yau har gobe godiyata da fatan alkhairi bazasu taba gushewa agareki ba


Malamata *Sadiya Jegal* da taimakonki da shawarwarinki na fara rubutu har gashi cikin ikon Allah na kammala litattafai har guda 4 lafiya, kuma Alhamdulillahi duk sun samu kar6uwa a wajen al'umma, badan keba da bansan taya zan fara yin rubutu ba


Nagode sosai Malamata Allah ya saka da Alkhairi kana ya bar so da kaunar da ke tsakaninmu kuma ya albarkaci zuri'a 
*GODIYA*


    2


Ga dukkan masu bin litattafaina tare da godiya da kuma bani kwarin guiwa akoda yaushe, musamman ma


Auntynmu Jiddah

Rabi'atu Umar

Maman Mu'azzam

Maman Suhaima

Ummi Adamu

Khadija Katuru

Firdausi & Maryam Al'Mustapha Mijin yawa

Aisha M Waziri

Mrs Al'ameen

Zainab Meema

Zaituna (Ummu Ammar wa Ashraf)

Haji Umma

Leyatou Ali

Maman Maryam

Fatima Ibrahim

Ummu Sadiq

Hadiza Aliyu

Suhairat Bawadi


Da sauran wadanda ban ambata ba, kuyi mani hakuri idan danbu yayi yawa baya jin mai yakeyi ba wallahi, amma dukkanku kuna raina, da sauran groups groups d'in da suke kaunar books dina musamman group din Auntynmu Jiddah *MUSHA KARATU*


Nagode sosai da irin so da kaunar da kuke nuna mani sai kuma Allah ya sake had'amu a wani littafin na daban, mai d'auke da labarin wata matsalar kuma ta daban, Mai yiyuwa Mu tsaya a birni gun talakawa, ko kuma mu lek'a k'auye inda suke fama da talaucin da kuma jahilci, mai yiyuwa kumama mu bar k'asar Nigeriar gaba d'aya mu lek'a wata k'asar domin jin yanda mutanenmu hausawa suke yin rayuwa acan.


Amma me kukace masu karatu? Ina kukeso mu nufa wannan karon? Zabinku nima shine zabina.
Ammafa yakamata kuzo ku tayani bawa Lauratu hak'uri, domin duk sadda na tura mata shafi d'aya daga cikin shafuffukan da nake rubutawa sai tayi kuka harta gode Allah, kasancewar tuna mata da nakeyi da binda ya faru shekara da shekaru da suka gabata


Domin labarin nan da nake baku ya faru a gaske ne ba k'irk'irarsa nayi ba, saidai kawai canji gari da kuma sunaye.

 Maman Ja'afar

+966582285035

[5/10, 11:12 PM] ‪+966 58 228 5035‬: [10/05, 9:53 p.m.] MAMAN JA'AFAR: SU NE SILA 
BY MAMAN JA'AFARIdan kaji wane ba banza ba, kinyi mun gani kuma mun yaba.


Ni kalmar Malama da kike faɗa ta fara yimn nauyi yanzu, saboda yanzu kina batun wuce malamar, saboda baiwar da ke tattare cikin kwanyarki tafi ta malamar, musamman irin labaranda kike ta zakulo muna masu faida, maana, da tarin faɗakarwa a cikinsu.


Lallai tabbas baiwa daga Allah ce, kowa da yanda ya bashi tashi.


Tabbas sune sila ya faɗakar ya ilmantar ya kuma nishaɗantar musamman da naji cewa labarin gaske ya faru sai ma wasu abubuwan da kike sakayawa.


Munada babbar matsalar da iyaye ke saka yaransu a cikinta ta kwaɗayin abin duniya da har xasu manta cewa yayayensu amana ce a garesu, su dai muradinsu kawai kuɗi su fito kota halin yaya, Allah ya shirya mna yaranmu ya bmu krfin imanin ɗorasu akn turba ta kwarai, ya kauda idonmu daga kwaɗayin abin duniya.


Gaskiya Zulaihat kinyi namijin kokari da kika kawo muna wannan labarin, Allah yakara basira ɗaukaka da kuma xakin hannu, ya raya mana su Jaafar akn turbar musulunci.


Umar ban masan abnda xance aknka ba sai dai ince tabbas kayi jihadi kuma ka tabbata masoyi nagari kuma na gskiya, Allah ya kara dankon so a tsakaninku ya shirya maku yaranku, a isar da sakƙn gaisuwata zuwa ga Lauratu da kuma taya ta murna da dace da namiji ɗan baiwa mai girmama so da kanshi na gsky da amana.👌🏻👌🏻🤙🏻🤙🏻


Daliba zata rikiɗe i zuwa malama, lolx.


Fatan alkhairi da godiya da irin yanda baki manta dani ba, samun mace mai halacci a cikin mata tamkarki sai an tona. Ban ɗauki abinda na yi maki akan komai ba saboda nayi wa wasu kamin ke, kuma nayi bayanki, but ke ta daban ce don gashi sai zuzuta malama kike ƴi tamkar wacce ta karantarda ke yun tashinki kawo yanzu, Allah yabar zumunci a tskaninmu ya haɗa fuskokin mu wani lokaci.


Nima ban manta da tawa malamar ba Sanah Matazu (Ummu Beenah) Allah ya nunamn aurenki.Mai kaunarki Zulaihat har kullum da fatan Alkhairi *Sady Jegal*👌🏻👌🏻


[10/05, 9:54 p.m.] MAMAN JA'AFAR: *sune * *sila*           shi dae talaucin ba hauka bane haka kuma idan ya hadu da jahilci to sae dae abin da Allah yyi.                 Lauratu taga Aya kala da kala a sanadin son zucia irin na mahaifiyarta da mugayen kalaman da ta dnga jifanta dashi had'i da zargi su sukayi tasiri akan lauratu koda kuwa ba taje ga boka ba tabbas bakin uwa ynada matuqar illa ga 'ya'yanta. *k'alu* *bale*garemu don ance *idan* *kunne* *yaji* to lallai gangar jiki ya tsira. Allah ya shiryar damu da zuria baki d'aya. Allah ya qara basira ummu ja'afar.     Zaituna Ummu Ammar.


[10/05, 9:54 p.m.] MAMAN JA'AFAR: 💘 *SUNE* *SILA*💘


*NA*  maman ja'afar 


YABAN GWANI YA ZAMA DOLE 


NA JINJINA MIKI KUMA NA SARA MIKI DA IRIN TAKI BASIRAR DA MUKE KARUWA DA KE 


Komai yayi farko dole yayi karshe A yau kin kawo mana lbrn mai girma da rikitarwa mai dauke da darussa da dama, kuma wlh ko ba true life story wannan novel ynx haka ake rayuwar wasu suke ciki


Kallube ne ga iyayenmu Allah ya baku amanar yara kuma zai tambayeku yadda kuka tafiyar da rayuwar su 

Amma rayuwa irin tasu Ammi gsky rayuwa mara kyau mara tsafta kuma wlh iyaye kukula ku hankali kar san abin duniya ya rufe muku ido ku manta da Amanar da ya baku ta yaranku, kuma hakkin ku ne ku bawa yaranku ilimi da kula da dawainiyar su da kuma damuwar su amma ba wai ku dauki nawinku da nasu ku daura musu dole a samu gurbataciyyar rayuwa 


Abota, ya kamata iyaye su san dawa yaransu suke abota kuma ku karfafa musu gwauwa da abokan arziki ba latattun kawaye ba 


Soyayya gaman jini na yarda da soyayyar umar da laurat soyayyace ta gsky ba algus a cikinta,sbd duk yadda laurat ta lalace a titi umar bai kyamace ta ba wannan itace soyayyar gsky 


Dukkan abin da zan fada kin rigani sai dai nayi karanbani na gara haske 


Novel ya fadakar ya nishadantar ya ilmantar sai fatan Allah ya baki ladan fadakarwa ya yafe miki kurakuranki Ameen 


Allah ya raya miki zuriya 👏🏻👏🏻


Mun gode sosai da sosai 


A madadina da yan MU SHA KARATU. Mike miki fatan alkhairi 


Anti maiji musa


[10/05, 9:54 p.m.] MAMAN JA'AFAR: Alhamdulillah inatayaki murnan kanmala wannan littafi lpy yanishadantar yakuma fadakar uwa uba kuma ya ilmantar allah yasakada alkaori

Tags: Maman Ja’afar #iyaye #’ya’ya
3231
0
3
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

sameerah2018-12-15 13:00:47good