Soyayya ce!

Written by Maryamerh AbdulPublished on 2019-03-27 20:44:58Category RomanceLabarin Elmansoor da Aisha. Dadadden gaban da yake tsakanin iyayensu ya yi qoqarin rabasu, shin iyayen nasu zasu samu yanda suke so na raba ‘ya’yan nasu da soyayyar juna ta mamaye dukkan zuciyarsu? Ku biyoni dan jin cikakken labarin tags: Elmansoor #soyayya #gaba #miskili #surutacciyaDuba was labarai »

Elmansoor jingine yake jikin mota yana waya, bazaka tab'a gane yanayin da yake ciki ba. Farinciki yake ko akasin haka, babu alamu a fuskarsa, ya dai yi shiru yana sauraran abinda ake sanar dashi a wayar.


Saurayi ne mai kimanin shekaru 27, ba bak'i bane sannan baza a kirashi fari ba, jinginuwan da yayi bai hana nuni da shi d'in mai tsawo bane, fuskarsa kuma dogon hancinsa zaka fara gani sannan ka kai ga idanuwansa wanda ya k'ara masa kyau, a tak'aice dai idanunsa are sexy, lips din nan nasa pink kuma ba k'ato ba dai-dai misali, k'asumbarsa da ya sha gyara sai yalk'i yake ya k'ara bawa halittar fuskarsa fitowa da kyau.


Ya kai mintuna 5 tsaye da wayan a kunnensa sai dai yace um ko um um bai iya furta komai ba. Toh meh dama ake tsammani daga wurinsa bayan hakan? Yaro ga kyau, ga kudi, ga tak'ama da k'asaita, kallonsa farat d'aya zaka gano hakan. 


Sanye yake da blue shirt mai zane fari sai wandon jeans da takalmansa masu nuni da gidan naira. Fahad ne ya fito daga gidan da yake facing Elmansoor, ba tare da yayi masa magana ba ya bud'e gidan gaba ya zauna. 


Ba tare da ya kashe wayar ba ya shiga mazaunin driver ya fara driving a hankali, har a sannan bai furta ko da kalma d'aya ba yana sauraren d'aya b'angaren. 

"Ni bana ma jinki fah" 

Ya tab'e baki had'e da danna wayar ya kashe.


Can ciki ya ja tsaki yana mai k'ara gudun motar nasa, babu wanda yayi magana cikin motar har ya isa bank yayi parking.

"Fahad zamu shiga ne ko kana jirana anan?"

Kallon fuskar Fahad yake yayi maganar, hannunsa sak'ale a mab'allin k'ofar motar.


"dama da kace in rakaka ajiyeni zakayi a mota? ko dan an b'ata maka rai zaka huce kaina?" 

Bai jira amsar Elmansoor ba ya fice had'e da rufe k'ofar.


Kimanin awa d'aya sukayi a banki suka fito babu wanda yake yiwa d'an uwansa magana. 


******


Wani tanqamemen gida ya tsaya bayan ya yi horn a bakin gate. Sakanni kad'an mai gadi ya bude bayan ya tabbatar da yasan mai motar. 


Bayan ya yi parking kai tsaye ya shige cikin gidan, ko jiran abokin nasa baiyi ba bare ya kulle motar. A main parlour ya had'u da momynsa na kallo, ya d'an russuna alamar girmamawa

"sannu da hutawa mommy" 

Ya furta yana mai k'awata fuskarsa da murmushin da bai kai ga zuciya ba. Bai tsaya wani hira da ita ba ya wuce d'akinsa.


K'ofar d'akinsa Fahad ya kwankwasa yasa kai ba tare da ya bashi izini ba, sanin cewa ba amsawa zaiyi ba muddin yana wannan halin. 


Wuri ya samu a gefensa ya zauna yana fuskantarsa

"wai Elmansoor meh ya faru ne?"

Jin shirun da yayi ya bashi damar cigaba da magana

"Ka kirani d'azu lafiya k'alau, daga fitowana daga gida sai in ganka a murd'e, lafiyanka kuwa?"


Kwanciya yayi yana mai juya masa baya ba tare da ya amsa masa tambayoyinsa ba. Tsaki Fahad yayi yana mai d'aura hannunsa a kafad'arsa had'e da juyo dashi dan su fuskanci juna. 


"Common tell me, meh problem na Jamila this time?"

Kaman an mitsine shi ya zauna yana cewa "problem nata daya, irin na kowace mace, bansan ko nine bana dacen 'yan mata ba"


Yayi tsaki tare da dafe kansa da dukkan hannayensa. Fahad murmushi yayi mai sauti yana girgiza kai.

"Elmansoor ka koyi yanda ake canjawa tun wuri dan wallahi mata basu son irin halin nan naka, muddin kanason ka samu mace toh dole sai ka canja".


"Fahad kafi kowa sanin waye Elmansoor Yuri, and am not willing to change, infact i promise myself to be that way har sai nayi aure, akan meh zan nunawa mace so tana waje? Bani da wannan lokacin. In na aureki baki ga na nuna miki so ba kiyi complain kina da gaskiya amma kina girlfriend dina sai kiyi ta min surutu, wai sai na kiraki kullum kuma kullum sai nace miki i love you, to hell with that idea, mata basu ganewa ko kad'an".


Fahad da yake yasan abokin nasa baiyi mamakin furucinsa ba bare yayi k'ok'arin fahimtar dashi abunda ya kasa ganewa.

"Allah ya bada sa'a toh".

Fuskantarsa yayi yana mai nazarin kalaman da yake son furtawa abokin nasa. 


Can ya nisa yace

"Kai ka fad'a mata ra'ayinka mana, in tana sonka ai zata gane, kuma ma ai gaskiyanta ne bata yi k'arya ba, ni banga laifinta dan tayi maka maganar rashin damuwan da baka yi da ita ba, ko ni nan bansan yanda kake sonta ba, ai ba a haka Elmansoor"


Ganin alamar Elmansoor zai tanka yasa shi d'aga hannunsa dan dakatar dashi, "Kawai dai ka fad'a mata yanzu dan a samu zaman lafiya, ni ban ga laifinta ba, in akwai mai laifi anan toh kai ne, kuma ya zama dole ka gyara komai in kana sonta da gaske".


Kallon da Elmansoor ya watsawa Fahad kad'ai ya nuna k'in amincewar shawararsa.

"Wannan ai ba shawara bane so kake kawai ta raina ni, kai kasan meh kake cewa ma kuwa? Sai in zauna zaman yi mata jawabi? Akan meh?"


Bai tambaya dan neman amsa ba, kwanciyarsa ya koma yana mai lumshe idanunsa, Fahad kuma wayarsa ya janyo yana mai gyara zamansa a gefen gadon.


~~~~~~~~

1sh chapter is here💃🏼

Kunsan Editing yafi sabon rubutu wahala? Ohh🤥 har naji kaman kada inyi aswear. 

But ya na iya tunda na fara?

Sai dai please shower your love with comments on every line, vote and share with your love ones. 


Thank you 😘😘😘

MaryamerhAbdul 💯


"Dan Allah ki tashi mu fita strolling" 

Aisha ke maganar da Mufeeda bayan ta fito daga d'aki ta samu Mufeeda kwance akan kujerar falo tana karatun littafin hausa. Wuri ta samu a gefenta ta zauna ta cigaba da cewa

"Na gaji da zama wuri d'aya Allah" tana mai turo baki ta fad'i hakan.


Ko kallonta Mufeeda bata yi ba tana mik'a hannunta cikin bowl din da ke cike da magarya tana kaiwa bakinta, idanunta akan littafin da take karantawa ko kiftawa batayi, littafin ya tafi da ita da alama. 


Aisha kallonta take yi tana mai tunanin abunda ya dace tayi mata a wannan lokaci dan ita ma taji kwatankacin b'acin ranta na k'in amsata. Mik'ewa tayi ta warce littafin sannan ta sa gudu ta shige dakinsu. 


"Amma Aisha kin raina ni, zan ko b'ata miki rai yau d'in nan".

Ta mik'e rai a b'ace ta bi bayanta tana mai cigaba da mitar abinda Aisha tayi mata.


*****


Mintuna 20 suka fito kowacce sanye da abaya bak'i da takalmi lophos, babu abinda suka rik'e a hannunsu sai wayoyinsu da ke rufe da fancy covers masu adon stones sai shek'i suke.


D'akin Mama suka wuce dan sanar da ita fitan da zasuyi.

"Toh a dawo lafiya kuma kada kuyi nisa, kunga 4:30 ya gota" ta nuna agogon bangon da ke mak'ale a saman gadonta ta fad'i hakan.


Fitowa sukayi suna taku a hankali suna hira tsakaninsu kamar ba su sukayi fad'a ba.


Aisha da Mufeeda yara ne kaman tagwaye dan kamannin da sukeyi, saidai d'aya tafi kauri da haske, chocolate colour suke kuma kyawawa ne na k'in k'arawa. Mal. Musa shine asalin sunan kakan Aisha wanda aka fi sani da Nemi, matarshi d'aya da 'ya'ya uku. 


Hajara itace farkon 'yarsa sai Abdullahi mahaifin Aisha kenan sannan Amina wacce ake k'ira Auta. Asalinsu 'yan garin Damaturu ne, a can aka haifesu suka taso cikin 'yan uwa. Akwai tazara mai yawa tsakanin yaran guda uku, dan Hajara na da shekara 9 sannan akayi mata k'ani Abdullahi, shi kuma na da shekara 11 saka yi masa k'anwa bayan an fidda tsammanin sake haihuwa.


Hajara na gama secondary school aka yi mata aure da Yunusa, auren soyayya sukayi dan sun had'u lokacin da yazo NYSC makarantarsu, d'an Kano ne, a lokacin tana aji 5 na gaba da firamare wato Ss2, bayan ya koma gida soyayyar bai tsaya anan ba yayi tattaki har zuwa wurin iyayenta dan neman izini, daga k'arshe iyayensa suka shiga maganar aka d'aura musu aure bayan kammala makarantarta. Abdullahi na junior class lokacin. 


Mahaifinsu na da wadata, dan yana sauk'e duk wani hak'k'i da ke rataye a wuyarsa, na dangane da tufafi, abinci, magani, muhalli mai kyau da dai sauran abubuwa na rayuwa, suna da fahimtan juna tsakaninsu, gida ne da ke cike da soyayya, tausayi da kuma jin k'ai. 


Lokacin da Abdullahi ya gama secondary school ya fito da sakamako mai kyau, hakan yasa aka nema masa university a can Kano B.U.K kenan, da taimakon mijin yayarsa ya samu admission inda ya samu gurbin karanta business administration.


Sosai Hajara tayi murnar dawowarsa Kano wurinta, a lokacin tana da yara biyu, namiji mai suna Nu'aim sai k'anwarsa Zainab.


Cikin shekaru hud'u da 'yan kai Abdullahi ya kammala karatunsa lafiya, ya dawo gida cike da murna da fatan samun sakamako mai kyau. 


Mahaifinsa yayi murna sosai da dawowarsa, dan Abdullahi ne tilon d'ansa kuma yana matuk'ar k'aunarsa dan biyayyarsa garesa. Kud'i mai d'imbin yawa ya damk'awa Abdullahi dan yaja jari ya rik'e kansa, shi a nashi bai son d'ansa yayi aikin gomnati. Ra'ayinsu yazo d'aya da Abdullahi, tuni ya kama sana'a yana mai anfani da dabarun ilimin da ya karanto a makaranta. 


Abdullahi yayi namijin k'ok'ari wurin tafiyar da kud'in yanda ya kamata, a lokaci k'alilan kudin yayi albarka ya fara sayan filaye yana sayarwa.


Bayan shekaru biyu da kammala makarantar Abdullahi Amina k'anwarsa ta gama nata makarantar, kamar yanda akayi wa Hajara aure haka ita ma aka umarceta ta fidda miji, batayi k'asa a gwiwa ba ta fito da gwaninta, anan Mahaifinsu ya umarci Abdullahi fitar da mata dan a had'a auren gaba d'aya ganin yana aikinsa zai iya rik'e kansa da matarsa.


Alankatafir Abdullahi yace baisan da zancen ba, shi bazaiyi aure ba, aka kad'a aka raya yace inaa shi bazaiyi aure ba, ya fad'i dalili kwak'k'wara yak'i bare a bashi lokaci, ganin bayi da dalili yasa iyayensa suka jajirce akan bakansu, sun nuna b'acin ransu sosai sannan ya amince da maganar auren, sai dai ya nemi alfarmar su kawo matar da zai aura dan bayi da wacce sukayi maganar aure, zai iya cewa ko budurwa bayi dashi.


Maman Abdullahi tayi murna sosai jin zancensa, dan dama akwai 'yar k'anin mijinta wacce ta kasance 'ya ga aminyarta da take masa hari tuntuni mai suna Asma'u. 


Lokacin da aka tuntub'eshi da maganarta dan jin ra'ayinsa game da ita ya tabbatar musu bayi da matsala da zab'insu, bare Asma'u da ta kasance kamar k'anwarsa, ya amince d'ari bisa d'ari baiyi gardama ba.


Ba'a b'ata lokaci mai tsawo ba aka shiga hidimar biki, ranar juma'a aka d'aura aurensu bayan an sauk'o daga sallar juma'a. Sai dare aka kai kowacce d'akinta kamar yanda al'ada take. Amina k'anwar Abdullahi k'awa ce a wurin Asma'u ko ma ince aminai ne kaman yanda iyayensu mata suke. 


Ba'ayi shekara ba asma'u ta gama kanainaye zuciyar Abdullahi kamar da yaddarsa akayi auren, da yake asma'u yarinya ce mai shiga ran mutum nan da nan Abdullahi ya dulmiya cikin kogin son matarsa. 


Shekara d'ai-d'ai har uku ko b'ari babu wacce tayi acikinsu, ya kai ga dangin mijin Amina sun fara k'orafin ya auro juya, kwatsam rana tsaka Amina ta tashi ba lafiya, mijinta ya sungumeta ya kaita asibiti, anan ne aka tabbatar masa tana da ciki 2months, sunyi murna sosai Amina harda hawaye lokacin da ta k'ira aminiyarta ta sanar da ita abun farincikin da ya sameta, ta tayata murna sosai ita ma lokacin ciki ne manne k'asar mararta bata sani ba. 


Wata tara cif da kwanaki Amina ta fara nak'uda da misalin k'arfe 3 na dare, ciwon nata yayi tsanani samnan mijinta ya samu motar da zai kai ta asibiti. Kafin su isa ta jikita jini ya b'alle mata, iya tsurewa mijinta ya tsure ganin halin da matarsa take ciki. 


Suna isa aka shige da ita d'akin haihuwa, likitoci sunyi iya k'ok'arinsu ta haihu da kanta abun yaci tura, sai da akayi mata aiki sannan aka samu damar fidda 'yarta samb'aleliya, sai dai ita Amina lokacinta yayi ta koma gidanta na gaskiya.


~~~~~~~


Drop your comment, 

Like and share with your love ones 

Thank you.
Mufeeda and Aisha
Fahad and Elmansoor Asma'u na jin mutuwar aminiyarta na'kuda ya taso mata, bayan gajeruwar nak'uda ta haifo nata yarinyar kyakkyawa gwanin sha'awa. 


Mutuwar Amina da sati d'aya aka sa wa yaran suna, duk da ba taron suna akayi ba saboda rasuwar. Yarinyar marigayiya Amina an mayar da sunanta wato Amina amma suna kiranta da Mufeeda, yarinyar Asma'u kuma Aisha aka sa mata, sunan mahaifiyar Abdullahi, ba a b'oye mata suna ba dan mai sunan tace batason a k'ira takwararta da sunan turawa, a cewarta canja suna ba komai ke sawa ba sai b'atar da sunan yara.


Asma'u ce ta shayar dasu dukka, tana matuk'ar nuna kulawarta garesu musamman ga Mufeeda, haka kawai watarana zata ajiyesu tana kallo tana hawaye wai Mufeeda na tuna mata marigayiya. 


Bayan shekaru biyu bayan an yayesu mahaifin Mufeeda ya nemi a dawo masa da ita, basu yi jayayya ba suka tattara suka kaita gidan mahaifinta, kamar tana sane da za'a rabata da da uwar goyonta ana shiga da ita gidan ta fara tsala ihu, bata tsagaita kukan ba har Abdullahi da matarsa suka bar gidan hawaye taf idanun Asma'u. 


Dak'yar ranar tasha madarar da amaryar babanta ta had'a mata, har dare tak'i bacci sai zabga kuka take, wasa wasa kwana uku Mufeeda tak'i daina kuka, tun ana cewa bata saba bane har aka gaji aka d'auke ta aka mayar da ita gidan goyonta, sanadiyyyar zamanta wurin iyayen Aisha kenan. 


Suna shekaru 9 mahaifin Abdullahi ya rasu, a lokacin Abdullahi da iyalansa sun koma Abuja da zama. Abdullahi yaji rasuwar mahaifinsa, kuka yayi ta yi kamar k'aramin yaro, da aka gama sadaka ya nemi ya tafi da mahaifiyarsa tace bazata bar gidan mijinta ba, ita ma anan mutuwa zai d'auketa kaman yanda ya d'auki mijinta.


Ba dan yaso ba ya barta a can Damaturu. Yanzu da suke shekaru 17 suna ss2, Aisha na da k'anne uku, biyu maza autarsu mace, ko wane hutu a Damaturu suke yinsa, ko a gidansu Mufeeda ko gun kaka tsohuwa.


 Hutun 1st term ss2 suka samu, tuni suka shiga shirin tafiya. 

"Irin dariya haka? Meh kuka samo mana yau? Ko duk murnar tafiyar ne?" 

Shigowar Mama kenan d'akinsu taji suna hira had'e da yin dariya, Aisha na tsaye gaban wardrobe tana ciro musu kayansu da zasu tafi dashi Mufeeda kuma na sawa a akwati. 


Bakin Mufeeda ta toshe da iya k'arfinta tana kallon mamanta,

"Wallahi Mama ni zan baki labarin nan" Mufeeda sai k'ok'arin k'wacewa takeyi, sai ta samu ta cire hannun tana fara magana sai Aisha ta sake toshewa. 


Mama dariya suka bata tana tsaye tana kallon dramarsu, 

"Toh ku rik'e hirarku nikam bana son ji dukka, anjima in Abbanku ya shigo yana nemanku a palonsa, kada ku manta dama"


Turo baki Aisha tayi tana kallon Mufeeda da ke toshe dariyarta ganin an gwale Aisha ba'a ji labarin kakar tasu da take son bayarwa ba. Kayan nasu suka cigaba da gyarawa tun tana matsewa har ta sake suka cigaba da hirarsu.


Bayan sallahr isha'i suka samesa a palonsa yana kallo, yana son zama da yaransa guda biyun nan, gwanayen hira ne musamman Aisha da aka ce tafi Mufeeda surutu, ya sake sosai da yaransa sun saba duk da k'arancin samun lokacinsa. 


"Yauwa har kun mantar dani abinda yasa na nemeku, baza fa mu biku ba gobe" shagwab'e fuska sukayi jin abinda yace

"Meh yasa?" Suka tambaya a tare suna kallonsa.


Murmushi yayi idanunsa manne jikin talabijin d'in da yake kallo.

"Akwai meeting d'in da zamuyi this week, so dole in gama komai anan sannan in tafi ko? Mamanku kuma zata jirani, dan bazan zauna anan ba mai min tuwo ina ci ba, zaku tafi da sauran yaran in yaso daga baya sai mu biyoku. Kunsan inda key yake in a side namu zaku zauna in kuma wurinta zaku zauna kuma toh, mu dai sai munzo".

Addu'ar samun sa'a sukayi masa sannan suka tafi makwanci dan tafiyar da zasuyi washe-gari.


***


   Sanye yake da black suit yana danne-danne cikin laptop d'insa, wayarsa da ke ajiye a kujerar da ke gefensa wanda ya zagaye parlon yayi k'ara, janyowa yayi ya kara a kunnensa bayan ya duba sunan. 

"Ka iso?"

"ok gani nan zuwa".


 Wayar yasa a aljihu yasa laptop d'in a jakarsa ya fice zuwa wurin parking. Wurin motarsa ya wuce kai tsaye ba tare da ya ko kalli inda motar Fahad yake ba, horn d'in da yaji yasa shi d'ago kansa daga bud'e motar da yakeyi.

"Muje a motana kawai mana"

"Are you sure? Kasan dai ni bazan bika yawo ba"

Idanunsa Fahad ya juya sannan ya d'aga hannunsa yayi masa nuni da ya iso, makullinsa ya cire ya isa motar.


Hira sukeyi jifa jifa sai kuma wak'ar da ke tashi a hankali har suka isa office, k'arfe 4 Fahad ya samu Elmansoor a office d'insa dan ya ga alamar bayi da niyyan sanar dashi dalilin nemansa a safiyar yau, 

"Ka rigani zuwa, ka kyauta wallahi, yanzu nake shirin samunka, mantawa nayi akan zamuyi magana, sai da na duba time sannan na tuna".


Ajiye takardun hannunsa yayi inda ya dace sannan ya koma mazauninsa, 

"Fad'i gaskiya dai yallab'ai"

Kujerar da ke kallon Elmansoor ya zauna yana kallonsa. 

"Fad'i buk'atarka in biya maka" 

Hannunsa biyu ya had'e ya d'aura akan teburin da ke gabansa.


Elmansoor bai kula da maganarsa ba ya janyo envelope da ke ajiye a gefensa ya mik'a masa,

"Take a look" 

Ya furta a k'asan mak'oshinsa yana murmushi. Zazzage envelope d'in Fahad yayi bai ga komai ba, bud'ewa yayi yasa idonsa sannan ya zaro hoto k'waya d'aya, fuskarsa kad'ai ya nuna tambayar da ya furta.

"Meh wannan?"

Bai samu amsa ba ya cigaba da kallon matashiyar yarinyar da ke manne jikin hoton. 


"A ina ka samu? Wacece?" 

Elmansoor bai ansa ba, Fahad ya cigaba da kallon hoton daga bisani ya d'aga kai ya kalli Elmansoor.

"Don't tell me you are in love? So soon? Wai dama da kace kun rabu da Jamila da gaske kake?"


Elmansoor tab'e baki yayi yana mai kawar da kansa gefe dan maganar Jamila da Fahad ya kawo.

"Shareta nikam, bazan iya matsalarta ba, zan iya cewa nata matsalar yafi na 'yan baya ma, kaga yanzu wannan yarinyar nakeso, ban santa ba bansan komai a kanta ba kawai naji ina sonta, she looks innocent, halinmu zai zo d'aya".


Baki bud'e Fahad yake kallon Elmansoor, mamakin furucinsa yake yi. Ganin kallon da Fahad ke masa yasa ya kalli kansa.

"Meh wai?"

"Ai dole in kalleka Elmansoor, ban tab'a ganin ka zak'alk'ale akan mace kana rattaba bayani ba".


Idanunsa ya juya yana mai hura iska da bakinsa.

"Kai dai bazaka yi abu me kyau ba, baka iya banbance lokacin wasa da lokacin abu mai anfani".

"Ohh wannan meh anfani..."


Dakatar dashi yayi da hannunsa da ya had'e biyu alamar rok'o.

"Please let's be serious, a wayar Humaira na ga hoton, i know nothing about her, ina nufin ko sunanta ban sani ba, naga kuna shiri da Humaira, please aboki ka bincika min".


"Umm! Ba matsala amma this will be the last time da zan nema maka abu akan mace, na gaji da nemo maka 'yan mata wata uku ko biyu ku rabu, in har na samo maka wannan toh ka tabbatar mata kenan, ka tashi mu wuce".

"Haka fa kace akan Jamila ma, kuma gashi..."


"Rik'e abunka ka nema da kanka" mik'a masa hoton yayi ya had'e rai.

"Haba Aboki, daga wasa kuma sai ka d'auka wani abu?" 

Hannunsa ya rik'e yana mai k'ara damk'a masa hoton idanunsa na yi masa magiyar da bakinsa ya gagara yi.


"Mu tafi nikam yunwa nakeji, ka sa a kwanyarka, wannan shine na k'arshe"

Kai Elmansoor ya gyad'a yana mai nuna yardarsa.


~~~~~~~

Ayi min afuwa jiya baku ji ni ba, shekaran jiya aka min rasuwa, k'anin mahaifina ya rasu ku sa shi a addu'arku, Allah ya kai haske kabarinsa.


Nagode sosai.

Comment, comment on every line, ku fad'i min ra'ayoyinku. Vote please, views d'in da nake samu za'a iya rabashi uku sannan a samu votes d'in da nake samu, please ghost readers, comment and vote, please, please and please.


MaryamerhAbdul


Elmansoor babban d'a ne agun Alh. Bala yuri, yana da k'anne biyu, Humaira da take ss2, sai Mubarak k'aninta. Abotan Elmansoor da Fahad ya faro ne tun primary school, sunyi aji d'aya kuma seat nasu d'aya, har suka gama secondary suna tare, dalilin abotansu iyayensu suka san juna ana mutunci sosai. 


Sun tafi makaranta a Cairo inda suka karanci architecture har masters acan sukayi, da suka dawo sukayi forming organisation, abu da masu kud'i nan da nan ya bunk'asa kowa na cin gashin kansa. 


Tun bayan kammala makarantarsu da bunk'asar masana'antarsu aka fara yi musu maganar aure suke basarwa, shi Elmansoor bayi da tak'amaiman budurwa, yanda yake treating mata yasa babu wacce ke iya jimawa dashi, duk kyau da kud'in da Allah ya bashi, duk wacce ta iya shanye wulak'ancinsa ta zauna dashi shi da kansa yake gudu dan kud'insa kawai suke hari. 


Fahad kuwa jinkirin Elmansoor yasa ya cire yin aure da wuri wai dan tare za su ajiye iyali da amininsa. (lallai Fahad kana da jira)


*****


  Tun ranar da sukayi magana da Elmansoor yake ta tunanin yanda zai samu layin yarinyar wurin Humaira, toh bai ma san sunanta ba taya zai samu d'aukan numbanta? Abun da kamar wuya.


Yau dai ya fito daga gida da k'udirin samo lambar, ya d'au alwashin samun layin ko ta yaya. Cikin nishad'i ya shigo harabar gidan da motarsa ya ajiye, kai tsaye kamar kullum ya shigo cikin gidan. Humaira ya hango zaune kan kujera ita d'aya tana rik'e da wayarta, tsintar kansa yayi da yin hamdala a ransa. 


Sallama ya zabga mata sannan ya k'araso ciki ya samu kujera ya zauna a d'an nesa da ita, tunani ne fal ransa, yau ga dama ta samu, murmushin da ta sake masa ya sa shi mayar mata da martani.


"Ina wuni Ya Fahad?"

Had'iye miyau yayi sannan ya iya amsa ta cike da fara'a.

"meh kikeyi ne haka tunda na shigo sai danne-danne kikeyi a waya".


Ba tare da komai yazo ranta ba ta amsashi

"yaushe ma ka shigo Ya Fahad? Hotunan da mukayi ranan hutu nake kallo, nayi kewar makaranta".

Hotunan ta cigaba da kallo hankali kwance, murmushin murna ne ya bayyana a fuskarsa, yau dai da k'afar dama ya fito, alamu sun nuna zai samu dukkan amsoshinsa.


"Mu gani mana tare tunda nazo, bansan k'awarki ko d'aya ba dama, sai mu fara daga farko ana fad'a min sunayensu, zai ma fi dad'i ko?" Da murnarta ta isa gefensa ta mik'a masa wayar yana scrolling ita kuma na masa bayani. 


A kan hoton Humaira da 'yan mata biyu ya tsaya, suna bala'in kama, ido ya tsura musu yana mai tantance abubuwa a ransa.


"Wa d'annan twins ne?"

Kallon hoton tayi tana mai murmusawa

"No, Aisha da Mufeeda kenan, wannan ita ce Aisha" ta nuna wacce tasa jan jambaki a bakinta.

"Wannan kuma Mufeeda ake ce mata asalin sunanta Amina, cousins suke amma suna zama gida d'aya".


Hoton ya ku'rawa ido yana kallon 'yan matan nan guda biyu, a shekaru bazasu wuce ita Humairar ba, kama ne dasu sosai hakan yasa ya nuna wacce yake kyautata zaton ita Elmansoor ya bawa aikin farauta akanta yace

"Aisha ko?".


Kad'a kai tayi tana mai yi masa dariyar da shi kad'ai ya gano ma'anarsa, "tsaya, dan na tambaya ba wai wani abu ke raina ba madam, kawai ina son banbance su ne naga suna kama, kinga gobe in naga 'yar kub'uta da 'yar siririya masu kama d'aya zan iya gane wacece Aisha da kuma Mufeeda".


Dariya ta shiga yi masa tana mai jin bayanansa.

"Um-um dai Ya Fahad fad'i gaskiya, tun da muka fara kallon hotunan bakayi tambaya irin wanda kayi akan nasu ba, anya babu wacce ta..." kallon da yayi mata ya sa ta shanye maganarta, bai tanka ta ba ya cigaba da kallon hotunan.


Wayarsa ya ciro daga aljihu yayi danne-dannensa ya ajiye ba tare da ya daina kallon hotunan ba yana scrolling da hannunsa na dama. 


*****


Kwance yake bisa gadonsa yana aiki cikin laptop wayarsa yayi k'ara alamar message ya shigo, kamar bazai duba ba sanin yanda kanfanin mtn suka damesa kwana biyu da aiko masa sak'onni maras anfani. Kansa ya d'aga ya lek'a sunan kafin wayar ya d'auke haskensa, ganin sak'on daga Fahad ne ya sa shi janyo wayar had'e da bud'ewa.


"Zo ka janye Humaira daga nan".

Fuskarsa ya kwab'e yana nazarin maganar abokin nasa, a fili ya furta "lafiyansa kuwa?". Bai nemo amsarsa ba ya d'auko rigarsa ya sa ya fito daga d'akinsa ya isa main parlor. 


Ganin Fahad da Humaira zaune da wayarta hannunsa ya amsa masa tambayarsa, had'iye yawu yayi daga inda yake ya ambaci sunanta a dake.

"Humaira" 

Juyowa tayi ta kallesa sannan ta amsa masa "Abinci nakeso, ki kawo min d'akina".

Yana gama bata umarnin ya juya zai koma d'akinsa ya tsinkayo muryarta.


"Abincin fa na dining, ko baka da lafiya ne" kallonta yayi yana karantar fuskarta, mamakin umarnin nasa take dan bai saba cin abinci a d'aki ba. Sassauta dakewar nasa yayi yace

"Banson zama anan, ki sa min a plate ki kawo min d'aki, wani aiki nake yi yakamata in gama shi tun jiya ban samu dama ba." Bata tashi ba har ya k'arashe maganar nasa, "Ki tashi mana Humairah yunwa nakeji". Ya furta da alamar fusata a muryar nasa, yana gama fad'an haka ta mik'e shi kuwa ya juya ya koma d'akinsa.


Yana ji ta gama zuba abincin ta yi hanyar d'akinsa, da hanzari ya koma kan gadonsa ya janyo laptop d'in gabansa.

"Ya fahad in bar maka wayar inje in dawo ko kuwa?". 

Bai jiyo amsar Fahad ba dan yana nesa dasu, takun k'afarta da ke tunkarosa yasa shi mayar da hankalinsa kan komfutar nasa da bai san meh yake kallo ciki ba. 


*****


"Ba matsala je ki dawo" ya amsata, tana shiga d'akin Elmansoor yayi minimizing ya shiga contacts na wayar, searching na Aisha yayi lambobi hud'u suka bayyana.

"Aisha Lk, Aishaluv, Aysha, Aisha skul" ya furta sunayen a fili, "toh wannene na Aisharsu Mufeedah?"


Wayarsa ya zaro ya d'auki lambobin dukka, jin takunta yayi kawai kusa dashi ba tare da ya ankara ba, da hanzari ya fita ya koma hotunar kafin ta iso garesa, tunawa da yayi baiyi clearing inda ya shiga ba ya sashi mik'ewa tsaye kafin ta iso ya goge page na contacts d'in sannan ya koma kan hotunan.


"Tafiya zakayi?"

"Umm?" Yace yana d'ago idanunsa da yake wik'i-wik'i, alal hak'ik'a bai ji meh tace ba.

Kallonsa tayi bata iya maimaita tambayar ba.


Wayarta ya mik'a mata dan kawar mata da tunanin da yaga tana yi, ya tabbata tana shinshino wani abu cikin mu'amalarsa da ita yau.


"Barin shiga wurin Elmansoor, k'awayen nan naki ba k'arewa zasuyi ba" ya furta yana k'awata fuskarsa da murmushi.

Bai jira amsarta ba ya bar wurin yana mai rok'on Allah kada yasa ta gano abunda yayi girma ya fad'i.


*****


Fuskar Fahad kad'ai yasa zuciyarsa tsinkewa, ya had'e rai kamar wanda aka jefe shi da kashin akuya. Bai iya ce masa k'ala ba Fahad ya samu mazauni ya kishingid'a had'e da lumshe ido. 


Mamaki yasa ya tsaya kallonsa, sabon salo k'iran sallah da wisir, ai ko magana ne ya masa yasan plan yayi failing. 


Bai gama mamakinsa ba yaga ya tashi ya isa gaban mirrornsa ya bud'e drawern ya d'auki agogonsa da ya manta daren jiya. 

"ni zan wuce gida, sai mun had'u a office, in akwai wani abun call me, bacci nakeson in d'an yi kafin maghrib".


"Wait, dole sai ka k'ureni akan mace kenan?Toh bani layinta d'in kafin ka tafi ai na tambaya yanzu".

"Wani layi kuma? Wa yace maka na samu lambar?".


Fuskarsa ya tsaya kallo dan ya karanci yanayin Fahad, bai nuna alamun wasa ba, bil hakk'i bai samu lambar ba. Cikin sanyin murya yace

"Dan Allah da gaske? Toh sunanta fa?" 

"Sunanta kuma? In nasan sunanta ai zan samu layin kenan. Kuma ma tsaya, tunda ban samu layinta ba meh zakayi da sunanta? It's not important you know".


Dariya ya shiga yi dan Fahad ya bala'in raina masa hankali yau, ganin dariyan da Elmansoor ke yi yasa Fahad yin hanyar waje.

Hannunsa Elmansoor ya rik'o yana mai rik'e dariyar nasa. 


"Are you serious? Duk aikin da nayi na k'iranta ta barka tare da wayanta a banza kenan?"


"Kaga barni, ban samu ba nace maka ai sai ka hak'ura". Ganin alamun gaskiya a fuskarsa ya sa shi barin hannun nasa, iska ya furzar daga bakinsa zuciyarsa na hautsina. Har Fahad ya bar d'akin bai iya furta komai ba.

"Ta ina zan samo yarinyar nan a garin Abuja?" Lalubo amsar tambayar da yake yi kenan cikin kwanyarsa.


~~~~~~~~


Dan dan dan, meh Fahad yake nufi?

Meh yasa ya hana sa lambar Aisha bayan ya samu har yayi saving a wayarsa? 

Inason jin raayoyinku. 


ashnurpyaar thank you so much, kinsan ina yinki ba? Ina matuk'ar jin dad'in yanda kike min b'arin comments a kowani gab'a. Nagode sosai. 


'Yan uwa na rok'eku kuna comments sannan ku danna wannan tauraron, bazai d'auke ku wani lokaci mai tsayo ba. 


Zanyi matuk'ar jin dadi in kukayi sharing labaraina ga 'yan uwanku makaranta littafin hausa. Nagode masu comments da kada k'uri'u, ina sonku sosai. Nagode da du'ainku gareni.


Vote 

Comment 

And share


MaryamerhAbdul💯


"Mr. Elmansoor Yuri, wai haka yarinyar ta dameka ban sani ba? Na d'auka tun satin da ya gabata muka rufe babinta, ashe tana nan cikin ranka har yanzu, ni ta ina kake sa ran zan fara nemanta cikin garin Abuja? Who told you ma a Abuja take zama? Dan kawai ka ganta a makarantarsu zai iya yiwuwa makarantar kawai take zuwa in anyi hutu ta koma gida, meh yasa kake wahalar dani akan mace, mata nawa a garin nan ka samo wata mana".


Fahad ke wannan zance ba tare da ya nuna damuwa a tare dashi ba, zaune yake a kujerar teburinsa wanda yake damk'e da files da komfutarsa da yake aiki ciki, hankalinsa bai wurin Elmansoor da yake zaune a kujerar mazaunin bak'i da ke fuskantar Fahad.


"Ya Rabbi" Elmansoor ya furta a k'asan mak'oshi yana mai shafa fuskarsa da hannunsa had'e da jan numfashi ya sauk'e. 


Dubansa Fahad yake yana karantar damuwar da ke fuskarsa, can ya nisa ya matsar da komfutar gefe ya ajiye hannunsa dukka biyu saman teburin bayan ya had'esu wuri guda.


"Lets talk dude, naga alamar ka fara zaucewa"

Idanu Elmansoor ya zuba masa ba tare da ya amsa ba, bai tab'a samun matsala akan mace ba sai wannan da bai ma san sunanta ba, anya lafiyansa? Daga ganin hoton yarinya shikenan sai ta canja masa tunani da komai?


"Ban tab'a ganinka haka ba Elmansoor, yakamata in bawa Aisha kyauta mai tsoka dan naga alamar ta sauya maka kwanya tun kafin kayi magana da ita".

Murmushi yake sakar masa yayi wannan furucin, tabbas yau zai iya shan naushi wurin abokin nasa in ya gano shirinsa, sosai yayi mamakinsa da ya sake dawo da maganar Aisha, duk miskilancinsa ya ajiye gefe yana neman hanya d'aya da zai samu Aisha.


A yau da yayi tattaki zuwa ofishin Fahad yaje ne dan ya yanke shawarar tambayar k'anwarsa abu game da ita, anan ne Fahad yace girma zai zube shi ba dashi wannan aika-aikar ba. 


Tun ranar da ya samo layin nan guda hud'u yake k'ok'arin karantar abokin nasa, bai son hali irin nasa, yafi kyautata zaton bai samu mace da ya sha wahala akanta ba shiyasa yake sakainar kashi dasu.


"Aisha? Wacece Aisha kuma?"

Fuskarsa bayyane da alamar tambaya, idanunsa na kan Fahad ko kiftawa baya yi yana mai jiran amsarsa.


Kai tsaye ya amsa masa tambayarsa yana mai kawar da kai dan dariyar da yake kunshewa kada ya fito.

"Yarinyar taka mana da ka dameni akanta".


Mik'ewa yayi tsaye ya zagayo inda yake 

"Wai dama ka samu layin yarinyar nan shine kake wahalar dani haka? Aisha? Sunanta kenan?".


Fahad bai iya amsawa ba ya fashe da dariya yana nuna Elmansoor, sosai yake dariyar yana buga teburinsa. Lumshe ido yayi ya koma mazauninsa yana jin kaman ya hau Fahad da duka, dan yana son yarinya shikenan sai ya zama masa abun dariya? Har zai masa wasa da sunan k'arya dan kawai yaga ya zai yi? Meh zai yi wa Fahad ya gane abunda yake ji can cikin k'albinsa?


Kamar daga sama yaji muryar Fahad na cewa

"Sunanta Aisha, tana da cousin sister Mufeeda, kamanninsu d'aya sai ka gansu, numban ne aka samu matsala, Aisha hud'u na samu cikin wayanta..."


"Tsaya Fahad, wai da gaske kake ko kuma kawai kana wasa da hankalina ne ka samo labari irin haka? Me yasa kake min haka ne?".


"Ahh, da gaske nake mana" wayarsa ya mik'a masa yana cigaba da cewa "ga numbers d'in guda hud'u, dukka suna whatsapp, biyu sun d'aura hotonsu akai, d'aya hoton namiji naga ta saka d'ayar kuwa bana iya ganin DPnta, nafi kyautata zaton ita ce, dan Aisha Skul naga Humairah tayi saving".


Wayar ya karb'a yana duba numbers d'in, "Fahad, ka jira in d'auki layin nan mu had'u, dama all this while dariyana kakeyi ka samu layin? Amma baka kyauta min ba".


Idanunsa na kan wayar yana copying layin yake maganar, Fahad dariya reaction nasa ya basa yana cewa "Elmansoor na Aisha komai dozen".


~~~~~~~


Aisha da Mufeeda zaune a gaban kaka tsohuwa, Hajiya sai hira take yiwa jikokinta tana raha suna darawa. 


Wayar Aisha ya fara ruri yana neman agaji a daidai lokacin da ta basu labari mai ban dariya, bata samu daman d'auka ba dan dariyar maganar Kakarsu da takeyi.


Mintuna uku bayan nan wayar ya sake shigowa, kallon numban ta tsaya yi tana tunanin waye ta bawa layinta nan kusa da take tsumayin k'iransa? 

"Dan Allah kashe min wak'ar yahudawan nan in bazaki 'dauka ba, sai ayi ta k'iran mutum bazai d'auka ba, iyayin yaran zamani".


"Um-um Hajiya, wa ya sani ko kema haka kikayi lokacinki?" Cewar Mufeeda.

"Ji ja'irar yarinya, mu lokacinmu ina muka ga kayan turawa bare muyi yanda kuke yi? Ai lokacinmu dad'i, baka da tashin hankali irin wannan na salula, Allah ya raba mu dashi lafiya". Tayi addu'ar tana mai nuna tsantsar kyamarta ga abun.


Dariya hakan ya basu dukka nan ma wayar ya yanke bata d'auka ba. Ganin ba a sake k'ira ba ta danna k'ira bayan dariyarsu da hirar nasu ya lafa.


"Assalamu alaikum" ta furta da siririyar muryarta bayan an d'auki wayar. Amsa sallamar yayi yace "barin k'iraki". Bai jira amsarta ba ya katse, bakinta a hangame taji ya latse wayar, niyyarta tace masa ba matsala zasu iya magana, meh yake nufi? Waye mutumin nan?


Bata samo amsoshinta ba ya k'irata suka gaisa ya gabatar da kansa.


"I'm Elmansoor Yuri, shin da Aisha nake magana?"

Idanunta take juyawa tana son gano muryar, anya ta tab'a jin muryar nan bare tasan mamallakinta? Ta jinkirta sannan ta iya amsa masa.


"Eh Aisha ce. Sorry amma ban ganeka ba, wani Elmansoor?"


~~~~~~


Fahad da ke zaune gefensa ya k'ura masa ido yana kallonsa, shirun da yayi yasa ya d'aga masa gira yayi masa nuni da hannu alamar meh ke faruwa?


Elmansoor shiru yayi yana neman yanda zai gabatar da k'udurinsa, bai san ya yayi da 'yan matansa na da ba, wannan yana neman yi masa wahala.


"Hello? Please wanene?" 

Furucinta ya dawo dashi hayyacinsa, katse wayar yayi ya kalli Fahad.

"Toh in ba ita ba ce fa?"


Baki bud'e Fahad ke kallonsa, sai da suka sake duba kowacce a whatsapp sannan ya k'ira wannan layin wanda suke kyautata zaton ita d'in ce. 


Rasa abun fad'a yayi ya tashi ya bar d'akin yana cewa "na tafi gida nikam, tun jiya ana abu d'aya an kasa gaba, bansan ranan canjawanka ba". 


Elmansoor bai iya hana sa ba dan shima yana jin haushin kansa, yarinya 'yar shekaru 17 ko 18 ke wahalar dashi haka. Shiru yayi yana tunanin mafita, daga k'arshe ya yanke shawarar kiranta ya sanar da ita komai had'e da tura mata hoton da ya gani, in ba ita bace sai ya bata hak'uri ya k'ira sauran layin. Ya gaji da kwane-kwane.


Hakan kuwa akayi, bayan yayi mata bayanin ko shi waye bai b'oye mata ba ya sanar da ita hotonta ya gani ya samo layinta, ya tura mata hoton nata ta whatsapp. Bayan ta duba tambaya d'aya tayi masa wanda bai iya amsawa ba, taya zai ce mata ya samu hotonta a wayar k'anwarsa? Salon raini ya shiga tsakani? Ko meh?


~~~~~~


"Ke Aisha baza ki nutsu ba koh? Shiryuwa dubu dubu nake rok'a miki"

Cewar Mufeedah da ta shigo d'aki ta samu Aisha na tik'an rawa da earpiece a kunnuwanta, bata ma ji ta ba dan k'arar wak'ar k'arshe ta kai sa.


Sai da ta gaji dan kanta ta kashe wak'ar ta fad'a kan gado ta kwanta, sai nishi take kaman wacce tayi gudu mai nisan gaske.


"Sannunki da wahala, kin gama?"

Bata iya amsata ba ta mik'e dan kunna na'urar sanyaya d'aki, zufa ke ketowa daga jikinta sosai tana fidda nishi. Ba rawan hankali tayi ba, irin rawar nan da gani na hauka da jin dad'i.


"Ke yaushe nutsuwa zai zo miki? da Umar na kallon iskancin da kikeyi a million zaice ya fasa".


Tsaki Aisha taja tana mai juya k'wayar idanunta. "A gidanmu fa nayi, da wani wuri naje nayi shine da matsala amma a gidanmu kuma a d'akinmu for that matter ba cikin gida ba bare wani ya iya shigowa, kada ki 'bata min rai da wani wai Umar".


Wayarta ta janyo bayan ta kwanta ba tare da wani ya sake magana ba cikinsu.


Mintuna biyar tsakani ta tab'o Mufeeda da ke kishingid'e rik'e da wayarta.

"Zo kiga". 

Mufeeda matsowa tayi kusa tana sa idanunta kan wayar Aisha, cikin hotunanta ta shiga ta tsaya dai-dai hoton Elmansoor da ya turo mata.


"Waye wannan kuma? New catch mukayi bani da labari" ta k'arashe maganar tana washe baki had'e da karb'an wayar daga hannunta.


Aisha tace "kin tuna rannan na fad'a miki wani ya kirani nake tambayansa shi d'an sarauta ne?"

Mufeeda da ke k'arewa hoton kallo ta kad'a kai ba tare da ta kalli Aisha ba, "kar ki ce min shine? No wonder, ai dole yayi yanga yaga yana da kyau".


"Bar wannan ma, ni ban tab'a ganin inda ake tsara mace haka ba, babu d'an hirar nan na maza dan jawo attention na mace, kawai "sonki nakeyi na samo layinki"" ta kwaikwayi muryarsa tana mai juya kwayar idanunta.


Mufeeda ta fashe da dariya ta k'ara k'ulad da ita, wayar ta kwace tana cewa "bana son iskanci".


Mufeeda cikin dariyar tace "yi ha'kuri kin bani dariya ne, bani labari, ya kukayi?".

Guntun tsaki Aisha ta ja ta ajiye wayarta gefe

"Ya mukayi kuwa? Daga ranan fa bai k'ara k'irana ba yau kusan sati, hana rantsuwa shekaran jiya ya kira wai dan ya gaisheni, bai ce komai ba fa bayan gaisuwa kawai ya kashe wayan, bansan ko ni ne nake sonshi ko shine yake sona ba".


"Serious, lallai shi wani iri ne, amma ai kuna chating?" 

"Ba sosai ba wannan ma, kuma bansan ya akayi ba sai ina jin sonshi, ban tab'a ganinsa ba amma yace in na koma Abuja zai zo, kawai kin gane ne, yana burgeni, ban sani ba ko dan nayi fad'a da Umar shiyasa nakejin hakan. Amma ni nasan bazan iya halinsa ba, miskili ne and not romantic at all".


"Don't judge him now Aisha, ki fahimcesa tukunna, ki karanci waye shi sannan ki fara fadan haka. Kada ki manta da addua, kiyi addu'a kiyi istikhara, Allah ya zaba mafi alhairi".


A cikin kwanakin nan Aisha ta karanci Elmansoor tsaf, tafi kyautata zaton yana daga cikin mutanen nan shiru-shiru, da wuya yayi mata doguwar magana ko da tambayarsa tayi, maganar soyayya kam tuni yayi fatali dashi, a ganinsa tunda ya fad'i kudurinsa kuma tana magana dashi ta aminta kenan.


Shirun ta da rashin damuwarta akan hakan ya k'ara sakewa da ita, a ganinsa hali yazo d'aya bai san karantarsa ake ba.


A hirar da tayi da Mufeeda ta sanar da ita abunda ta gano game dashi, kuma ta bata shawarar da ya dace, tunda tana jin sonshi meh zai hana ta gwada yin nata bajintar ko zai dawo yanda takeso? 


~~~~~~~~


Sun gama hutu a Damaturu suna shirin komawa gida, mama da Abba sunzo sunyi sati d'aya tare zasu koma, kowa ya fito da jakarsa da kayan da zasu tafi dashi, kaka tsohuwa ta had'a musu tsaraba irin nasu na tsoffi irin su magarya, kurna, kuka, daddawa, busasshen kub'ewa da sauran kayan marmari da na miya.


Mufeedat ta 'dauki leda tana 'diba magarya kaka tsohuwa ta shigo d'akin.

"Ki fito da sauran kayan shine kika zo kika zauna ko?"


Kallon Mufeedah ta tsaya yi ganin d'iban mata magarya take.

"Lallai yarinyar nan, tsaraban nawa kike kwashewa? Ki juye min abuna kafin in sab'a miki".


Ganin bata da niyyar magana yasa ta cigaba da cewa "meh zakiyi dashi ne wai?".

Shagwab'e fuska Mufeeda tayi tana kallon kakar tata.

"Yau fa zan tafi amma kike min haka? Ci zanyi a mota, har kin manta yanda 'yar jikallenki take son magarya, tsufa dai yazo".


Washe-baki tayi tana mai gyara tsayuwarta a bakin k'ofar, "in ke zaki ci da sauk'i, na d'auka wani zaki baiwa, abinda na sayawa d'ana ki kaiwa wasu, ai da sai kin biyani".


D'auko wani ledan Mufeeda tayi tana bud'ewa

"Ai kin ma tuna min in d'ibarwa saurayina, shima son abin nan yakeyi sosai...".


Bata ida maganar ba Hajiya ta warce ledan, "wallahi baki isa ba, ba dai a wanda na sayawa 'dana ba, ki saya masa in kinason birgeshi ne, in kuma sai nawa yakeso yazo ya gaisheni da kayan dad'i nan zan fara yi masa tsaraba shima". 


Sosai ta fashe da dariya ganin da gaskiya Hajiya ke maganar, shigowar Abba yasa ta tsagaita dan k'aramin aikin Hajiya ne ta fallasa ta wurinsa bayan ita tsokanarta take son yi, fita tayi daga d'akin ta basu wuri bayan ta d'auki sauran kayan.


~~~~~~


Abba da driver ne a gaba, sai mama da sauran yaran a tsakiya, Mufeeda da Aisha kuma a baya, irin motar nan ne mai gida uku, dan tafiya irin wannan musamman aka sayo.


Suna cikin tafiya Elmansoor ya fad'o mata a rai, rabonta dashi tun shekaran jiya bai nemeta ba ita ma haka, wayarta ta d'auko dan tura masa sak'o, bazata yi zuciya tun wuri ba, zata bashi lokaci ta ga yanayin yanda zasu kaya.


 ~~~~~~~


Cikin bacci yaji wayarsa alamar message ya shigo, jiki a mace ya lalubo wayar ba tare da ya bud'e idanunsa ba. 


A hankali ya bud'e idon dan duba wanda yayi masa sak'o da safiyar lahadi bayan ansan ranar hutu ne ga kowani ma'aikaci. Aisha ya gani rubuce saman screen nasa kamar yanda yayi saving layinta.


Bud'ewa yayi ya karanta:-

"on my way, jiya bamuyi magana ba ban samu daman sanar dakai zan dawo yau ba, nayi kewar hira da kai... i love you''. 


Murmushi ne ya mamaye fuskarsa dan yaji dad'in kalamanta, bazai ce yayi kewarta ba amma yana jin wani sashe na zuciyarsa na kwad'aitar dashi son magana da ita, basu fahimci juna ba, bai san komai game da ita ba, ya bar wannan har bayan dawowanta gari yaje har gida su gana, hakan kamar yafi dacewa ko?


Ajiye wayar yayi ba tare da yayi mata reply ba ya lumshe idanunsa zuciyarsa fes yana mai jin farinciki a ransa, kalamanta ya dad'ad'a masa rai, bata tab'a yi masa hakan ba, tayi kewarsa tace, har ma da tana sonsa, tunda yake da ita bata tab'a rubuta masa hakan ba. 


Kamar bazai mayar mata da amsa ba ya tashi ya shiga kewaye yayi brush ya wanke fuskarsa ya dawo ya zauna dan ya amsa ta, meh zai ce mata? I love you too? Ko kawai yayi mata addu'ar isowa lafiya? Numfashi ya ja ya sauk'e sannan ya fara rubutu.


"Nagode A'ish habibty, Allah ya kiyaye hanya..."


Da hanzari ya danna wurin goge rubutu yana magana a fili "What? Ni nake rubuta wannan abun? Habibty?" Dariya ne ya kufce masa yana kallon inda ya rubuta A'ish habibty, shi yake tsarawa mace kalamai haka? meh zata 'dauke shi in ya tura mata wannan sak'on? Da girma ya zube kuwa. 


Dukka rubutun ya goge ya rubuta sabo sannan ya tura mata, sai da ya tabbatar ya isa gare ta sannan ya mik'e ya shiga wanka dan lokacin k'arfe 11 ya goce.


~~~~~~~~


Aisha kam she is stuck in the car, tun tana jiran amsarsa har ta fidda rai ta tsuke baki tana kallon Mufeedah da ke game a wayanta, bata da damuwan komai, tunda ta rabu da saurayinta Shaheed bata sake kula wani ba, ta soshi kamar ranta, daga k'arshe iyayensa suka bashi cousin d'insa, hakan yayi sanadiyyar rabuwarsu.


Hira ta fara yi mata dan kad'aici da takaicin Elmansoor na neman b'ata mata ranarta, ta cire tsammanin ganin sak'onsa taji k'arar wayarta. Da farincikinta ta bud'e ganin Elmansoor ne ya dawo mata da martani.


Idanunta ta kifta dan sak'onsa da ya shigo ko layi d'aya bai kai ba, rubuce yake kamar haka "Safe, nima haka...

        Elmansoor!" 


Baki bud'e take kallon wayar tana mamaita karanta sak'on, tsaki ne ya kufce mata bata san lokacin da tayi ba, Mama tuni ta juyo tana kallonta.


"Meh hakan? Bance banson tsakin nan naki ba? Yaushe zaki ji magana wai?". Cikin fad'a tayi mata maganar.


Aisha bakinta ta rufe da hannunta bata iya cewa komai ba, dan dama kullum fad'ansu da Mama kenan tsaki, Mufeeda kuma dariya ke cinta ta k'asa tana toshe baki, taso gano dalilin tsakin nata dan taji lokacin da sak'o ya shigo wayar, sai da Mama ta juya sannan ta nuna mata message d'in.


 "Ki ga mutumin nan, duba message d'ina ki duba nasa. Nima haka? Son ne shima haka ko missing d'in da nace nayi?"


K'asa-k'asa take maganar dan kada Mama taji, bata jira amsar Mufeedah ba ta shiga whatsapp ta nuna mata hirarsu, kusan rabin hirar tambayoyin Aisha ne da take masa, amsarsa bai wuce eh, a'a ba, sai kuma similey na dariya ko blush. Taya zata iya rayuwa da mutum irinsa? Ta fara kokwanton son da yace yana mata.


********


Ba laifina bane da kuke jina shiru, votes naku da comments naku are not encouraging at all, I told you people editing nakeyi, daga na fara sai inji jikina ya mutu in na tuna qarancin votes din nan. Kuna danna wannan tauraron ku fadi min raayinku dan mu gama da wuri dan Allah, sabon littafina na nan, nafison in gama da wannan sannan in d'aura sa. In dai a hakan zamu cigaba zamu kai shekara mai zuwa sannan in fara sabon littafi, nasan bazaku so hakan ba🤥 pages 33 ne kacal dama.


Comment a kowani layi

Danna tauraron nan 

Kuyi sharing labarin zuwa ga masoya da abokan arziki.


Nagode 

MaryamerhAbdul


Sun iso garin Abuja da yamma, a gajiye lis suke dukkansu. KFC suka tsaya dan samun abunda zasu ci, soyayyar dankalin turawa da kaza suka saya akayi packaging suka wuce gida.


Bata neme shi ba haka shima bai nemeta ba, tayi tunanin zai k'irata yaji ya ta iso amma har bacci ya saceta bayan taci abinci tayi wanka, bai mata message ba bare ya k'ira yaji ya hanya.


~~~~~~~


A kwana a tashi ba wuya watanni biyu sun shud'e Aisha na garin Abuja Elmansoor bai nemi zuwa wurinta ba, tun tana tsumayin jin ranar da ya yanke na zuwa wurinta har ta cire a ranta, ta ajiye maganar zuwansa a gefe ta duk'ufa da karatunta.


Har wa yau babu abunda ya sauya tsakaninsu, yana k'iranta a waya kowani bayan kwana uku ko hud'u, bata fiye k'iransa ba sai dai chating, sosai take sakewa dashi tayi masa hira ko zai sake da ita, amma hakan bai canja komai ba, bai canja yanayin yi mata reply ba, kamar an sa shi dole magana da ita, amsar dai a kullum shine eh ko a'a, in kuma abunda bai jib'anci amsa ba sai dai yace ko? Ko kuma ya tura mata dariya.


Tun tana iya d'auka bata fushi abun ya fara zarce tunaninta, wani mutum ne zaiyi irin haka? Bai nemi ganinta ba bare ala'karsu ta k'ara gaba, shin haka ake soyayya? Haka ake jan ra'ayin mace? A hakan yake tunanin ala'k'ar tasu zai kai ga aure? Ko ba aure ya kawo shi ba? Tana yawan tambayan kanta wannan amma har ila yau bata samu amsoshinsu ba.


Tana mamakin irin zuciyarta na fad'awa soyayyar mutum irin haka, ko dan ya kasance halayyarsa daban. Dalili d'aya da take bawa kanta kenan a duk lokacin da ta tambayi kanta meh yasa take jin yana burgeta, halinsa daban yake in ba hakan ba babu wani abun so ko burgewa a wurinsa, ko akwai ma bata da tabbas dan bata san dasu ba.


A duk lokacin da tayi doguwar tunani akan yanayin zamansu tana yanke shawarar rabuwa dashi da sharesa, amma hakan baya yiwuwa, na kwanaki biyu kacal take iya hakan, a halin nan nasa na ko in kula ya samu gurbi a k'albinta. Ko da tayi fushi dashi baya sani bare yayi biko, a wurinsa ba wani abu bane dan ta kyalesa na kwanaki biyu, hutu take buk'ata a ganinsa kaman yanda shima yake buk'ata daga wurin 'yan matansa na da. 


~~~~~~~~~


"Kalan! Kalan!! Kalan!!!"

k'arar k'ararrawar da aka buga a tsakiyar makarantarsu Aisha kenan, hakan ya jawo karad'e makarantar da hayaniyar yara dan ribatar lokacin hutu da aka basu na mintuna 30.


Wasu yaran na wasa, wasu na cin abincin da suka zo dashi daga gida, wasu na zuwa shagon makarantar dan sayan abun marmari, wanda akasarin masu wannan hidimar yara ne daga 'yan aji hud'u na gaba da firamare zuwa k'asa. Su Aisha manyan aji suke, yawancinsu na aji suna hira tsakaninsu, basu cika fita break ba.


    Aisha na tare da sauran k'awayenta suna hira, bata cika zama da Mufeeda ba dan k'awayenta manyan 'yan matan nan ne masu kama kansu, ita kuwa Aisha ta fi son inda za'a bata labari tayi dariya ba tare da nuna ita d'in babba bace, idan bata ji dad'in rayuwarta na sakandare ba yaushe zata ji? Bayan ta gama girma yazo mata? Lokacin abu ayi shi a cewarta.


Mufeedah na tare da Humaira(k'anwar Elmansoor), hira sukeyi hankali kwance irin na manyan matan ss2.

Humaira ce ta ciro wayarta daga jakarta tana kunnawa,

"Cikinku wa yake da gallery vault a wayanta ta tura min, nayi ta downloading in zansa password sai yayi min hauka, kuma bansan wani app wanda zan na boye abubuwana ciki ba". 


Duk matan wurin suka amsa da basu dashi, ciki harda Mufeeda da ta k'ara da cewa "ki tambayi Aisha tana da shi, nikam meh zanyi da vault a wayana? Sai ku masu b'oye hotunan samari". Tana mai juya kwayar idanunta ta k'arashe maganar.


Dariya dukka sukayi ta mike ta isa wurin Aisha.


Wayarta ta mik'a mata ta bar wurin dan ta tura mata bayan Aisha ta tabbatar mata tana dashi, bata sha wahalar turawa ba dan dukkansu na anfani da Xender, turawa tayi ta mata installing. Bayan ta gama ta duba wurin zamansu duk basu nan sun fita, ko ina suka je?


Bayan ajin ta koma ta samu lungu ta zauna ta shiga pictures, an hana su zuwa da waya makaranta, in an gani za'a kwace, hakan yasa ta bar mazaunin gaba ta koma baya, zamanta ita d'aya yasa ta shiga mazaunin hotunan Humaira. Bata yi nisa ba suka dawo duk suka iso wurinta suka zauna tare da ita.


Humaira a gefen Aisha ta zauna suka cigaba da kallon hotunanta da Mubarak k'aninta. Suna kallo tana basu labarin wautarsa da shirmensa suna darawa.


Kamar daga sama ta ga hoton Elmansoor zaune a kujera da laptop nasa yana danne-danne, da alamu bai san an d'auki hoton ba, dan ya duk'ufa aikinsa. Maganar Humaira ne ya dawo da ita hayyacinta.


"Bai ma san na d'auke shi ba, yayana ne, ke baki sanshi ba ko? Elmansoor, ko da yake bakya zama cikinmu bazaki gane sa ba".


Wayar ta karb'a tana nunawa sauran k'awayenta. "Wannan shine yayan nawa da nake fad'a muku".


Zancensu bai shiga kanta ba sai duniyar tunani da ta fad'a, Humaira Bala Yuri sunanta, ya akayi bata tab'a lura da sunan nasu ba? Ya akayi bata tab'a ganin kamanninsu ba? Ya akayi hakan? Rashin kula? Meh yasa bai sanar da ita tana tare da k'anwarsa ba? Meh dalilinsa na b'oye mata? Bata gama yiwa kanta tambayoyin ba aka buga k'ararrawar komawa aji, kowacce ta koma mazauninta dan cigaba da d'aukan darasi.


~~~~~~~


Tun cikin mota ta gagara hak'urin isowa gida, gefen Mufeedah ta zauna duk da ya dace ta zauna bakin k'ofar saboda k'annensu. Amma maganar bazai iya jira ba dole ta yi sa tun a mota kafin zuciyarta ya tarwatse.


"Ashe Elmansoor yayan Humaira ne? Ya akayi baki gane sa ba Mufeedah?"

A k'asa take maganar dan kada kowa ya ji maganar da suke yi.


"Ni sai da ta fad'a sannan na gano kamanninsu, kinsan tana bamu labarinsa amma bamu tab'a ganinsa ba. Baki zama cikinmu da kema kinsan labarinsa". 

Cikin nuna son jin labarin ta tambayi Mufeedah ta bata labarinsa da k'anwar ke fad'a musu, nan ta shiga rattabo zance har suka iso gida.


Bayan ta gama bata labarin irin miskilancinsa da shan k'amshi ta k'ara da cewa "amma yana da hankali fa, miskilancin dai nake guje miki, ke ga surutu shi kuma silent, lallai anyi had'i". Dariya takeyi ta k'arashe maganar tana cire hijabin makarantar.


"Sai ya ha'da da paracetamol irin surutunkin nan, abun da bai saba ji ba duk zaiji". Aisha da ke tsaye wurin ajiye takalmansu tayi murmushi tana mai kallon gadon d'akinsu wanda a zahiri kallon kawai takeyi amma hankalinta na wani wuri tana tunani.


"Indai haka halinsa yake sai na canja shi tsab, I want to see him(ina son ganinsa)". Cikin murmushi take furta kalaman hankali kwance.


~~~~~~~~~


Elmansoor sanye yake da gezna ruwar sararin samaniya, agogonsa ruwan silver yake murzawa a hannunsa, fuskarsa cike yake da annuri bakinsa ya kasa rufuwa, ya dad'e yana jiran wannan ranar, ya dad'e yana tsumayin ranar da zata nemi ganinsa, tun dawowarta daga hutu yake jiran ta nemi hakan amma ta k'i.


Ita ya dace ta gayyacesa zuwa gidansu ai, ko kuwa? Bazai nemi ganinta ba bare ta d'auka wani abun, shi dai ya san akwai wani abu tare da ita wanda yake burgeshi yaja raayinsa zuwa gareta, amma hakan ba shi zai sa ya sauk'ar da kai ya bi ta ba, Elmansoor yake, bazai yu ta canja masa ra'ayinsa ba, yanda yake a da haka zai kasance muddin ba aure sukayi ba.


Makullim motarsa ya d'auka ya fice ba tare da ya bari mommynsa ta gansa ba, yanzu zata kafesa da tambayoyin da bazai iya amsata ba, bai san meh yasa take yawaita tambayarsa ko wurin budurwa zai je a duk ranar weekend in yayi shigen manyan kaya ba, duk da yawancin lokutan wurin Fahad yake zuwa su wuce wurin abokai amma yau daban yake a wurinsa, bazai so ta gansa ba dan bazai iya sanar da ita inda ya nufa ba, ta bari sai komai ya kankama sai taji labari ko? Ai hakan kamar yafi dacewa.


Gidansu Fahad ya isa ya shiga cikin gidan, d'akinsa ya isa ba tare da ya biya main part ba, yau dai bai son had'uwa da manyan nasa, ji yake kamar suna ganinsa zasu gano inda ya nufa, kuma bazai so hakan ba, a k'alla ba yanzu ba.


A shirye ya samesa ya sha hula yana zaman jiransa, mik'ewa yayi daga shigowarsa ya d'auki turare ya fesa ya mik'a masa yana mai cewa "ka k'ara turaren ya fita zan-zan, dan yau gun amaryarka zamuje ba budurwa ba, daga fuskarka na gano kana jin dad'i yau. Ko meh Aishar nan take baka oho". Ya d'age kafad'a bayan Elmansoor ya karb'i turaren.


Bai tanka sa ba ya fesa turaren murmushi fal fuskarsa. 

"Alamu dai sun nuna Aisha na son canjaka". Hular kansa yake gyarawa yayi maganar. Elmansoor ba tare da ya kallesa ba ya fad'ad'a murmushinsa.

"Bazata iya ba ai, hak'uri zata yi har muyi auren a haka". 


Fahad ya tab'e baki ya fice Elmansoor na biye dashi a baya har wurin motarsa.

~~~~~~~


Yanda ta bashi address 'din haka yabi, Asokoro gidansu yake, bai sha wahalar gano hanyar ba kasancewar komai a rubuce yake, ko wani layi da sunansa sannan kowani gida da lambarsa.


Da misalin k'arfe 4.00 ya k'irata ya sanar da ita isowarsa. Mayafinta kawai ta d'auka wanda zai shiga da material 'din da tasa blue, ta feshe jikinta da turare ta kalli Mufeeda da ke kwance tana kallonta.


"Tashi mana mu shigo dashi".

"Oh oh nikam, zan dai kai masa ruwa in ya shigo" gyara kwanciyarta tayi tabbacin bazata rakata ba, dole ta fito ita d'aya. 


Tun fitowarta yake kallonta ta madubinsa, da gamgan yak'i parking a bakin k'ofarsu, yana kallon yanda take kalle-kalle tana neman inda yake, motoci uku a layin bata gane wanne ne shi ba. Wayarta ta latsa yana kallonta har wayarsa ya fara ringing.


Da gangan yak'i fitowa dan ya k'are mata kallo, doguwa ce, haka zalika kyaunta yafi fitowa a zahiri fiye da hotunanta. Fahad ne ya dawo dashi daga duniyar hasashensa game da yarinyar da ke gabansa.


"Malam wayanka na ringing".

"Ita ce, ga ta can ta fito". Annurin fuskarsa bai kau ba yayi furucin.

"Shine ka kyaleta bazaka fita ba, baka da dama wallahi Elmansoor".


K'ofar motar ya bud'e ya sauk'o da k'afarsa d'aya dan ya bata daman ganinsa. Wurinsu ta isa kai tsaye tana mai sake masa murmushi kamar yanda yake mata.


"Sannunku da zuwa". Ta furta cikin sanyin muryarta kanta a k'asa, gogan bai amsa ba Fahad ne ya ari bakin nasa ya amsa, sai da suka gaisa sannan tayi musu iso zuwa ciki. 


Parlorn bak'i ta kai su, Mufeeda ce ta kawo musu ruwa, shiru parlorn yayi babu mai magana. Can Fahad ya nisa ya gabatar da kansa, a tak'aice dai Fahad ne yayi hiran, gwanin surutu ne dama, tuni ya kwace masa gurbi ya shiga barkwanci. Mintuna arba'in zuwa awa d'aya babu wani hirar da ya shiga tsakanin Elmansoor da Aisha, hirar gaba d'aya da Fahad akayi, kamar yanda yake yi mata a chatting haka yake amsa ta, kamar mai cin magani ko wanda aka d'aukosa dole sai yazo wurinta.


Lokacin da ta nemi ganinsa taji alamar farinciki a tare dashi, ta d'auka ganinta zai sauya shi, tayi masa kwalliya tasa kayan da tafi so cikin kayakinta, ta dai san ya kalleta irin kallon da saurayi ke wa budurwarsa wato na k'auna, amma akwai saurayin da zai ga budurwarsa bai yi hira da ita ba? Shin Elmansoor yana da cikakken lafiya? Anya yana sonta?


Haka suka gama hirar ya tattara komacalansa ya k'ara gaba ya barta cike da zullumi da tunanin mutum irin Elmansoor. Rai a dagule ta shigo cikin gida ta samu Mufeedah, tun kafin ta sanar da ita tasan an samu matsala.

"Aisha in bazaki iya ba tun wuri ki sallami bawan Allahn nan ki huta".


"Nima hakan nake gani Mufeedah, amma bakya ganin ya sace zuciyata? A murd'en fa nake jin yana burgeni". Tayi maganar kamar wacce zata yi kuka. Hannunta Mufeedah ta rik'e ta zaunar da ita.

"Ya zakiyi toh yanzu Aisha? Wani shawara kika yanke?".


D'ago kanta tayi ta kalli Mufeedah, kamar bazata amsa ta ba ta furta cikin sanyin muryarta da yake rawa.

"Ina sonshi Mufeedah".


"Ummm ya kike Humaira?".

Cikin i'ina ta iya maganar bayan Muryar Humaira ya karad'e wayar a k'irar da tayi mata karo na uku kenan. Tayi wautar k'iranta ta sani, dan basu saba waya tsakaninsu ba, bare yau k'iranta da yazo da sabon salo, taya zata k'irata dan tambayar yayanta? Me zata d'auketa? Duk tambayar nan bai zo kanta ba sai da taji amon muryarta ya karad'e kunnuwanta.


"Lafiya k'alau Aisha, yau an tuna dani ne warhaka? Yaushe rabon da muyi waya? Rabona dake tun ranar hutu".

Murmushi tayi wanda bai kai ga zuciya ba, a halin da take ciki yanzu bazata iya k'wak'waran murmushi ba ma bare dariya, zuciyarta a cunkushe yake tana neman dalilin da zai sa ta fashe da kuka ko malulun da ya daskare a zuciyarta zai narke ta samu sa'ida.


"Yi hak'uri, kin fad'o min a rai ne kawai na k'iraki, dan in ban k'ira yanzu ba zan sake mantawa laifin ya k'aru". 

Murmushi Humaira tayi a nata b'angaren ta furta "kin kyauta" tana mai nuna jin dad'in k'iranta da tayi.


"Ya kowa a gida? Su mama da Mubarak?" Bata iya furta sunan Elmansoor ba dan nauyin hakan, basu saba irin wannan gaisuwar ba, taya zata fara yi mata shi a yau kwatsam? Abun bai bada ma'ana ba. Muryarta ne ya dawo da ita "kowa lafiya k'alau alhamdulillahi, ya naki mutanen gidan? Ya Mufeedah? Ita ma kinga bamuyi waya ba tun da kuka tafi Damaturu, wai ku bazaku iya hutu a Abuja ba sai kunje garin naku?".


Idanunta ta juya dan bata samu gamsashiyar amsa ba gashi tana neman jan ta da wani hirar da bata ra'ayi a wannan lokaci, dan dole ta amsata dan kada ta d'ago wani abun, basuyi hira mai yawa ba suka yi sallama ta katse wayar. Fuskar wayar ta kalla dan duba lokaci, a fili ta furta "11:05".


Layin Elmansoor ta dannawa k'ira tana mai fatan samun wayar a kunne, duk da tasan zai yi wuya hakan. "The number you're trying to call is switched off, please try again later" muryar na'urar da ke bada bayani a duk lokacin da ta k'ira wayarsa kenan a satin nan ya doki kunnuwanta. Hawaye masu zafi ne suka zubo mata.


Kwanaki uku take k'iran wayarsa a kashe, tun ranar da ta gama jarrabawa ta bar garin Abuja basu sake magana ba, bai nemeta ba ita ma hakan, bazata iya fad'an dalilin rashin samunsa ba, dan sunyi magana lafiya sukayi sallama yayi mata fatan isa Damaturu lafiya.


Tun ranar da ya je wurinta a gida bai sake komawa ba, bata nemi zuwansa ba ita ma har suka fara jarrabawa suka gama, bai nemi ganinta ba har ranar da ta k'ira ta sanar dashi tafiyarsu hutu. Shin mutumin nan na da isashen lafiya? Tana shakkun hakan.


"Lafiyansa k'alau" wani sashen zuciyarta ya sanar da ita, "sonki ne kawai baya yi" tunawa da hakan yasa ta fashe da matsanancin kuka, 


Kukan Aisha ne ya tada Mufeeda da ta dad'e da yin bacci. Da mamaki take kallonta dan kukan da take yi mai tsuma zuciya, hannunta ta rik'e tana kallonta cike da tausayawa da kuma fargaban abunda ya sameta.

"Lafiya Aisha? meh ya sameki kike kuka haka?".


Rungume Mufeeda tayi tana mai cigaba da kukanta, dan kanta tayi shiru ba wai dan hak'urin da Mufeedah ke bata ba, saida ta tsagaita kukan ta iya cewa "Elmansoor ba sona yake ba, kinga ya kashe wayarshi tun da nazo bamuyi magana ba, sati kenan fa".


Jan majina tayi ta goge hawayenta da bayan hannu ta cigaba.

"Ya cuceni da yasa na fara sonshi, har cikin raina ina jin sonshi Mufeeda bansan me yasa ba, meh yasa yazo wurina yasan baya sona? Meh yasa ya barni na fara sonshi? Wa ya aiko shi yazo ya tarwatsa min farin-cikina?".


Kuka ta cigaba da yi ba tare da ta saurari rarrashin Mufeedah ba. "Ki masa uzuri Aisha, baki san meh ya samesa ba da ya kashe wayoyinsa, haka kawai bazai shigo rayuwarki dan cimma wani manufa nasa ba, kiyi hak'uri ki kwanta kiyi bacci, dare yayi zuwa gobe zamu san abun yi". Gyara kwanciyarta tayi bata tanka ta ba, tasan bazata gane komai ba dan bata san meh yake faruwa ba, mutumin nan baya sonta ne bai damu da ita ba.


Tana jin Mufeedah na shafa mata addu'a tayi bacci, ita kuwa tunani ne fal ranta, bata san lokacin da bacci b'arawo ya saceta ba.


~~~~~~~


    Washe gari tun safe Aisha taje gun kaka tsohuwa dan ta rage zafi, hira da ita a ganinta zai sa ta manta dashi ta cire damuwar da ke ranta, hakan dai bai yu ba, dole ta bar parlorn ta koma d'akin kakar tasu ta kwanta tana mai addu'an samun sauk'in rad'ad'in zuciyarta.


"La'ilaha illa lahu, yau Aisha meh ke damunki kin shigo uwar d'aka kina ta zabga kuka, baki da lafiya ne?". Muryar kaka tsohuwa ya dawo da ita hayyacinta, bata san hawaye ya malale fuskarta ba sai da ta ji furucinta.


Kallonta tayi ta turo baki had'e da langab'e kai da lumshe.

"Banida lafiya ne". Cikin bargo ta nitse ta rufe idanunta, jin hannun kakarta tayi a jikinta tana tab'a ta.

"ina ke miki ciwo? Yanzu dan baki da lafiya sai ki zauna kuka? baki fad'a ba zaki kashe kanki a d'aki a banza".


Hannun kaka tsohuwa ta rik'e tana cewa "ni ciwon so ke damuna, ko shima yana da magani?" hawaye ne ya gangaro kan kuncinta. Baki bud'e kaka tsohuwa ke kallonta, daga bisani ta ja tsaki ta janye hannunta daga gun Aisha.


"Ku yaran zamani baku da kunya, yaro yace baya sonki dole ne? Kinzo nan zaki kashe kanki bai san kina yi ba. Oh ni Aishatu". Ta dafe goshinta.


"Ba haka ba ne fah hajiya, sati d'aya yau wayanshi baya shiga kuma lafiya muka gama waya da zanzo nan, shine duk na damu". 

"Ayyo, d'auko wayana ki k'irashi in naki ba kud'i kiji ko lafiya, ai ba lafiya in kika ji haka".


"Ai wayan baya shiga ne?" Hawayen fuskarta ta goge dan bata son kukan nata.


"Kuma babu wanda kika sani nasa bare kiji abunda yake faruwa?"


Shigowar Mufeedah yasa ta yin shiru, hakan yayi dai-dai da rurin wayarta. Kallon wayar tayi dan ganin wanda ke k'iranta, tashi tayi da hanzari ta nuna wa Mufeedah fuskar wayar ta fice, tana ji Mufeedah na cewa.

"D'an halak, Hajiya shi yake k'ira".


~~~~~~~~~~~


"Hello"

Shiru tayi tana karantar muryarsa, babu abunda ya canja daga muryarsa bare yace bayi da lafiya ne. Jin tayi shiru shima yayi shiru, sakanni masu yawa tsakani sannan ya iya cewa

"Ya kike?".


"Lafiya, sai yau zaka nemeni? Kuma ka kashe wayanka dan bakason in nemeka, 1week Elmansoor ka iya shareni haka kuma kace kana sona? Kasan halin da na shiga akan..." bakinta ta rufe da hannunta wani sashe na zuciyarta na kwab'anta. "Kin kofsa Aisha, ke da yakamata ki nuna bai dameki ba", zuciyarta ke kwab'arta da hakan, shiru tayi bata k'ara magana ba.


Ajiyar zuciya ya sauk'e.

"I'm sick ne fa". Shiru tayi tana neman maganar da zata furta, amma sick? Bayi da lafiya shine ya shareta? 

"Shine baza ka iya nema na ba ko wani naka ya nemeni ya fad'a min? Meh kake nufi Elmansoor?"


"God! kema zaki fara koh Aisha? I'm sick fa nace amma baki damu da lafiyar nawa ba kin fara complain". 

Shiru tayi kamar yanda yayi, tsintar kanta tayi da fad'in "I'm sorry!".


D'if ya kashe wayar bai sake furta komai ba, mamaki tuni ya bayyana a fuskarta, ya kashe wayan? Meh yake nufi? Meh laifinta? Ko ta fad'i abunda ya b'ata masa rai ne? 


Kawar da dukkan tunanin tayi ta danna masa k'ira, sai dai meh, samun wayarsa tayi yana waya, bak'in ciki da malulun wuyarta da yaso narkewa ne ya sake kumbura, wayar nata ta wurga kan gado tana mai takaicin halinsa, waya fa yakeyi? Da gangan ya katse wayarta dan ya d'auki na wacce ta fita muhimmanci. Anya akwai abunda zaiyi kyau tsakaninsu? Hawaye masu zafi tuni suka wanke fuskarta.


***********

This chapter is yours addaummi nagode sosai da comments naki, Allah ya bar k'auna. msspurplesglam thank you too


Anya Elmansoor na son Aisha? Kun yadda yana sonta?


Aisha ya kike bada mata ne kam, ki d'an ja aji mana, ki gwara mana kanshi ko zai daidaita.


Wai shin ma meh kuke ganin zai iya saita kwanyar nan nasa mai taurin tsiya?


Anya akwai ranar da zai shigo hannu? Nidai ina ganin da wuya🙄, ku fa?


Waiting for your comments 

Vote

Share and don't forget MaryamerhAbdul na k'aunarku dukka.


"Wayarta ma na kashe na d'auki naka, meh ya faru?" Yayi maganar yana sosa karan hancinsa.


"Yi hak'uri na k'ira ba lokacin da ya dace ba, in ka gama da ita muyi magana kawai". Fahad ne yayi maganar ta d'aya b'angaren yana k'ok'arin kashewa muryar Elmansoor ya dakatar dashi.


"Tsaya mana tunda na d'auka, kasan meh? Maganan Aisha ne, ni fa halinta ya fara damuna, anya tana sona kuwa?".


Shiru Fahad yayi dan kalaman bakinsa sun samu wani rami sun rufe kansu ciki. A asibiti yayi ta tambayarsa shin Aisha ta nemesa dan taji ya yake? Bai b'oye masa ba yace a'a, shi kansa Fahad yayi mamakin rashin nemansa da tayi duk da yasan bata da lambarsa, ba'a tab'a samun budurwar da Elmansoor yayi ba har sati basu yi waya ba bata k'ira Fahad ba sai akanta, da alamu hakan ya b'ata ran Elmansoor, hakan ya fara sa shi kokwanton soyayyar da take masa.


"Elmansoor haka kakeyi fa ita ma tayi maka? Kai kace kana son mace mai ra'ayi irin naka, ka samu kuma sai ka fara complain?"


K'aramin tsuka Elmansoor ya ja yana lumshe ido, zuciyarsa na masa zafi, bai san ya zai sa masa maganar ta yanda zai fahimta ba.


"Ka gane Fahad, yarinyar nan bata k'irana fa kamar sauran, in kaga ta k'irani toh wallahi da dalili, kuma yanzu nayi sati bamuyi magana ba bazata nemi layinka ta k'iraka ba? Kuma tana da layin Humaira, abun nata lafiya? Anya tana sona? Yanzu da na k'irata ma instead a tarbeni da magana mai dadi complain wai take min? Wai ban k'irata ba for a week? Toh in ban k'irata ba meh yakamata ta yi?"


Fahad daga d'aya b'angaren murmushi yake sakarwa ba tare da Elmansoor ya gane ba, irin matan da ya dace Elmansoor ya samu kenan tun farko baiyi dace ba, da sannu zai gane kurensa, da sannu zai fuskanci abunda kullum Fahad ke sanar dashi, Aisha ce kad'ai daidai shi, tafi dacewa dashi, ga dukkan alamu ta samu matsaguni cikin zuciyarsa.


"Kasan meh Elmansoor, abun nan guda d'aya ne, in kana son ka gane tana sonka ko bata sonka ka nuna mata so, in bata nuna maka kamar yanda ka nuna mata ba nan ne zaka yanke hukunci, amma yanzu watak'ila halinka yasa take d'aga maka k'afa, wata k'ila ta d'auka hakan kakeso shiyasa take maka..."


"Fahad" ya dakatar dashi muryarsa na nuni da gajiyar jin shawararsa, yasan bazai tab'a yi ba meh na fad'a masa?


"Su sauran 'yan matan haka sukayi? In tana sona ai irin nasu zatayi"


"Halinku yazo d'aya, ku canja juna"


"Sai anjima" yace a k'ufule tare da katse wayar.


Mintuna masu yawa tsakani sannan ya k'irata bayan ya gama bawa kansa baki.

"A kashe kuma? Haba Aisha, wannan yarinyar zata zautani, so take inyi ta binta kenan?"

Dafe goshinsa yayi yana mai sauk'e nunfashi.


~~~~~~~~


Kuka takeyi mai shiga rai, ji take kamar zuciyarta na iya tarwatsewa a kowani lokaci, kanta sarawa yakeyi amma ta gagara tsagaita kukan, so take a kowani hali ta yakice wannan murd'ad'en saurayin wai shi Elmansoor, bazata iya rayuwar nan ba, bazata iya d'aukan haka daga wurinsa ba, wato ita ya mayar sidechick? Lallai ya raina mata wayo.


Sim nata ta cire daga wayar dukka ta ajiye cikin jakar hannunta, alk'awari tayi bazata kunna ba bare ya samu daman k'iranta.


Sosai tayi k'ok'arin kawar da damuwarta, bugun duniya Mufeedah tayi amma tak'i sanar da ita yanda sukayi, kuma tak'i nuna damuwarta a fuska sai dai wayarta da ta kashe.


Sati da faruwar hakan Fahad ya k'ira Mufeedah.


Bata san ta ina ya samo layinta ba, gani kawai tayi sabuwar lamba na k'iranta, yana fad'an sunansa ta ganesa, a lokacin tana tare da Aisha.

"Ohh Fahad na Elmansoor, na ganeka"

Can bayan wasu sakanni tace 

"Toh barin bar wurin, muna tare kuwa dama"

Aisha na kallonta ta bar d'akin, zuciyarta na son sanin meh yasa ya k'irata amma fuskarta na nuni da haushin k'iran da yayi mata.

"Ko ma meh zasuyi dai ni bazan k'ara magana dashi ba".


Mintuna goma da 'yan kai ta fito daga d'akin tana kallon Aisha, sai da ta iso wurinta ta mik'a mata wayar ba tare da tayi magana ba. Ita ma Aishan kallonta ta tsaya yi idanunta na jefa mata tambayar da tak'i bari harshenta ya furta.


"Ki karb'a mana"

"Waye? Kinsan dai bazan karb'i waya bansan da wanda zanyi magana ba".

"Saurayinki ne" ta fad'a kai tsaye, tab'e baki Aisha tayi ta kawar da kai.

"Ni bani da saurayi". Dariya ne ya kufce ma Mufeedah ganin yanda Aisha ke nok'ewa, sa wayar tayi a kunnenta tace 

"Bata son magana dakai"

"Toh" ta furta bayan taji d'aya b'angaren.


Mik'a mata wayar ta sake yi tana cewa "Aisha Fahad ke son magana dake". Jim tayi kamar bazata karb'a ba ta sa hannu ta karb'a ta kai kunnenta, bakin nata a cune ta turb'une fuska kamar yana kallonta.


Can ciki ta furta "ina wuni".

"Malama Aisha, fushin bai k'are bane har yanzu? A tausaya mana haka".

"Ni ba fushi nakeyi ba".

"Indai ba fushi kikeyi ba gashi yana son magana dake".

"A'a ka bari zan k'irasa".

"Fushin bai k'are ba kenan, ayi hak'uri a saurareshi, in yaso daga baya a yanke shawarar cigaba da fushin ko a hak'ura".


Shiru tayi bata yi magana ba, hakan yasa ya mik'a masa wayar ya tashi ya bar wurin.


Shiru dukka b'angaren sukayi, kowannensu da abunda yake sak'awa a ransa.

"Ehm! Aisha?" Yayi maganar kamar mai tambayarta, idanunta ta juya tana mai cewa a ranta mai hali bazai tab'a barin halinsa ba.


Kallon da Mufeedah ke mata yasa ta mik'e sak'ale da wayar a kunnenta ta koma d'aki.

"Ina jinka"

"Yau ko gaisuwan bazan samu ba?"

"Ina wuni" ta furta a k'ufule wani malulu na taruwa a mak'ogoronta.


Numfashi ya sauk'e yana taro maganganun da Fahad yace ya sanar da ita, jin muryarta yasa duk kalaman da bayanin nasa suka b'ace.

"Let me explain myself, ranan da na k'ira ki dawowana daga asibiti kenan, kuma ina k'iranki kika fara min complain bayan ni yakamata inyi dan kink'i ki nemeni sati bamuyi magana ba bayan bamu saba yin haka ba, shiyasa na kashe wayar fa".


Tuni idanunta ya cika da hawaye, ita ta manta da wannan matsalar, dan k'aramar matsala ce a wurinta muddin aka d'auko maganar budurwarsa da yake waya da ita, shi bai ma san dalilin fushin nata ba kenan.


"Kinyi shiru".

Sheshshek'ar kukanta yasa shi duba fuskar wayar, goshinsa ya tattare yana son gano abunda yake ji.


"Aisha?".

"Meh ya sameki?"

"Ka daina k'irana, ni na gane komai yanzu, bazan iya zama da mutumin da ya ajiyeni a sidechick nasa ba, kaje kayi ta zama da wacce kakeso".


"Aisha maganar meh kikeyi haka?"

"Ai kasan meh nake fad'a, taya zaka zo wurina kace kana sona ka k'ira wata daban kana hira da ita bayan ni nake waya dakai lokacin, toh ka barni kaje kayi ta magana da ita, ni na yafe na hak'ura".


"Aiishahh!" Ya furta sunan cikin wani sigar da bata tab'a ji ba, daga k'afafunta har tsakiyar kanta sai da taji sautin muryar. Lumshe idanunta tayi dan bazata iya jure wannan salon nasa ba.


Cikin sanyin murya yake maganar "in kina maganan ranan da na k'iraki ne Fahad ne ya k'irani bayan na katse wayar, Aisha bazan zauna ina miki k'arya ba haka kawai dan ina ra'ayi, da girmana da shekaruna sai in ajiye 'yan mata ina musu k'arya? Ki fahimceni ki fahimci ya nake ba wai kiyi hasashe ba".


Shiru tayi bata amsa shi ba, jira take ya bata hak'uri amma taji akasin haka, shiru yayi kamar yanda ta yi, ganin bazai k'ara mata magana ba yasa tace "Naji".


"Zaki kunna wayan? Kuma kin daina kukan?"

Bakin ta turo kamar yana kallonta

"Ni ba kuka nakeyi ba dama, in na kunna wayan muyi magana".


Bai k'ara wani maganan ba ta katse wayar.


*******


Ayi min afuwa, am very sorry 

Charger ne ban samu mai kyau ba kuma ga makaranta, amma na samo yanzu.

Mu cigaba daga inda muka tsaya, zaku cigaba da jina akai-kai daga yau InshaAllah.


Thank you 

MaryamerhAbdul


"Ina jinka".

Ta furta tana mai gyara zamanta akan gadon d'akin, hankalinta da dukkan nutsuwarta ta mik'a masa kamar yanda ya buk'ata.


"Kinsan dalilin da yasa na k'iraki, so nake muyi maganar da zata sa mu saita tunanin Elmansoor, abokina ne, na sanshi fiye da sanin da kikayi masa, gani nayi abunda aka sha yi yana neman maimaita kansa duk da a wannan karon ya banbanta daga wurin nasa".


Shiru yayi bai cigaba da yi mata bayanin da ya d'auko ba, ya zai fara mata bayani a dagule kuma ya tsaya a tsakiyar hanya? Duba fuskar wayar tayi ko wayar ce ta tsinke bata lura ba.


"Ban gane ba, kayi min yanda zan gane Fahad"

Ta furta bayan ta mayar da wayar kunnenta.


Numfashi ya sauk'e kana ya cigaba da maganar, zuciyarsa na wasu-wasin hukuncin da ya yanke ba tare da sanin abokin nasa ba, anya ya kyauta masa? Wani sashen na zuciyarsa na nuna masa dacewar hakan.


"Abubuwan da ke faruwa tsakaninki da Elmansoor nakeson gyarawa, gani nayi dukkanku babu mai shirin gyarawa, naga rashin dacewar hakan shine na kawo d'auki amma ta wurinki, dan ina da tabbas da abokin nawa, kece dai ban sani ba".


Idanunta ta juya kamar yanda take juya maganarsa a k'asan zuciyarta.

"Bazan ce ban gane maganarka ba Fahad, amma ina son gane abubuwa dangane da abokin naka, gaskiya ina mamakinsa, bazan b'oye maka ba ina shakkun son da yake cewa yana min, asalinsa haka yake ko kuwa ni kad'ai yake yiwa haka?".


"Meh yake miki wanda ban sani ba? Ki sanar dani".

"Bai k'irana, bai min hiran da zamu fahimci juna, komai nashi daban kawai, ya zaka so mutum kana fatan aurensa ka kasa bashi daman ya fahimceka kai ma ka fahimcesa? Meh anfanin furtawa juna kalmar so in fahimtar juna bazata biyo baya ba? Da wurin babana yazo kawai aka aura min shi bansan da maganarsa ba akan haka, dan ban ga anfanin soyayyar ba".


Murmushi Fahad ya sake yana mai jinjina irin tunaninta a shekarun da take dashi.


"Malama Aisha kenan, duk cikin 'yan matansa ke kad'..."

"'Yan matansa kuma?". Ta katseshi muryarta na rawa tana mai ware idanunta, zuciyarta kuma na sanar da ita kinyi kuskure, dama namiji kamar sa dole ya ajiyesu da yawa. Hawaye ta ji yana barazanar zubo mata tayi saurin sharewa da bayan hannunta.


Dariya ne ya kubce masa, muryarta kad'ai ya tabbatar masa kishin ne ya motsa, shi ko bai fad'a da wani manufa ba sai don yayi mata bayanin da bata sani ba game da Elmansoor.


"Haka kike da kishi?" Ya furta bayan ya tsagaita dariyar.

"Mamaki dai nayi ba kishi ba, taya mutum irin sa zai iya tara 'yan mata".


"Ok, ba wai ina nufin yanzu haka yana dasu ba, ina nufin duk 'yan matan da yayi babu wacce ta tab'a tunani irin naki, kuma ina kyautata zaton kece kad'ai zaki iya zama dashi a hakan, clear your mind".

"Ban gane ba, asali haka yake?".


"Eh toh zan iya ce miki haka yake in rashin magana ne, amma rashin kulawa ne gaskiya ba halinsa bane, babu d'an Adam a duniya da Allah bai sawa feelings ba sai dai na wani yafi na wani, ra'ayinsa dai da wasu dalilansa suka sa ya zama haka, kowacce mace yake wa haka kuma dukkansu dalilin rabuwansu kenan rashin damuwa dasu".


"Zan iya sanin dalilan nasa? I want him to change".

"Kafin nan, ina son ki yadda da abu d'aya, Elmansoor na sonki, ni nasan meh na gani yasa na fad'i haka. Jiya kafin in k'iraki ta wayan Mufeedah ni kad'ai nasan abunda ya faru wanda ko da wasa bai tab'a yi akan wata mace ba sai akanki, dalilina ma kenan na k'iranki yau, banson kiyi tunani irin na sauran na tafiya".


Murmushi tayi tana mai tona sirrin zuciyarta na farin ciki.

"Kuma yana sona yake min hakan? Abun da kamar wuya".

"So nake ki kwantar da hankalinki, ki yadda da duk kalmar da zai fito daga bakina, bazan miki k'arya ba, ni da nake neman abu wurinki ai bazan b'ata kaina ba". Ya k'arashe maganar cikin dariya.


"Taya zan kwantar da hankalina ina doubting d'insa? Haka zamu yi ta zama kenan?".


Shiru yayi daga bisani yace "bari zan k'iraki gobe, yanzun bansan ta ina zan fara sanar dake dalilan nasa ba".


~~~~~~~~~


Elmansoor na kwance idanunshi a rufe da alamu ba bacci yakeyi ba, Momy na gefensa tana basa labarin da tana da tabbacin ba sauraronta yakeyi ba.


Wani lokaci tana mamakin hali irin nasa, tana rasa gane yanayin da yake ciki, duk da bai saba yi mata hakan ba a yau ta kasa tantance yana cikin damuwa ne ko miskilancin ne ya motsa?


Tv ta kunna ta fara kallo tana mai kawar da tunaninta. Mintuna biyu da hakan wayarsa tayi k'ara alamar sak'o, dubanta ya dawo kansa kamar bazai duba ba taga ya d'auka ya bud'e sak'on, murmushi ne ya mamaye fuskarsa, ji tayi zuciyarta ya sake, farinciki ya mamayeta ganin murmushin d'an nata.


Ajiye wayar yayi bai daina murmushin ba, samun kanta tayi da murmusawa tare da fatan hasashenta ya kasance gaskiya.

"Elmansoor".

Kallonta yayi sannan ya amsa k'iran nata.


"Dama ba bacci kake ba?"

"Kaina ke d'an ciwo ba bacci nake ba".

 "Sannu, amma Elmansoor kai yanzu haka zaka yi ta zama ba tare da ka kawo mana mata ba a gidan nan, budurwar kirki ma baka dashi? Yanzun wace ce ta maka message?".


Kallon momy yayi yana mamakin tambayar nata.

"Taya kikasan wata ne ta min message yanzu Mommy?".


Murmushi tayi ta kawar da kai bata tanka shi ba. Can ciki ya furta sunan

"Aisha ce".


Dad'i sosai taji a ranta, murmushi ta sakar masa tana mai kallonsa.

"Ita ce surkuwar tawa?"

Murmushi kawai yayi bai iya amsa ta ba.

"Elmansoor kana d'an magana mana ko ka'dan-kad'an ne, matar taka ma haka zaka na mata?".

"Mommy mana, zanyi ai, in ina mood na magana ai ke shaida ce inayi". Cikin shagwab'a yayi maganar.


"Eh na sani, amma dai ka mata reply tunda ita ta tunaka, ka nuna appreciation naka mana".


"Soyayya zaki koya min yau kuma?" Cikin dariya yayi maganar yana kallonta. Ita ma dariyar tayi.

"kai d'in ne ai na rasa gane iyawa ne bakayi ba ko meh, inaga sai na fara maka lectures zan ga suruka na shigo min".


Murmushi yayi sannan ya tura mata reply kamar yanda mamansa ta nema.


~~~~~~~~~~~~


"Thanks... Me too, love you more".

A fili Aisha ta karanta sak'on bayan ta bar tsifan da take taya Mufeedah. A lokacin da taji sak'on nasa ya shigo bata d'auka daga wurinsa bane.

"Awwnn" ta mik'e tana mai juyawa alamar murna.

"Mtsw, layi d'ayan kike wa ihu?".


Aisha bata daina rawar ba tace "toh ai na samu, ban d'auka zaiyi ba ma, kuma ai yace me too".

"Shawaran waye amma? Baki iya godiya ba? Meh ma kika tura masa?".


Gyaran murya tayi tana mai gyara d'aurin kanta da d'ayan hannunta.''Credit d'in dai nawa ne tunda ni na had'a message. Barin karanta miki kiji, kema zakiyi flying bare shi.

Thinking of my man right now, hope all is well with you? I cant deny the fact that i love you so much... wishing you fastest recovery my one!".


Mufeedah tsaki tayi tana mai kallon wautar Aisha.

"Dallah yi min tsifa nikam kada raina ya b'aci, thanks nashi ne ya burgeki ko love you more".


Aisha tuni ta had'e rai ta kwanta ta shareta, wai ta fasa tayata tsifan.


Mufeedah ce ta bata shawarar tura masa sak'o bayan ta sanar da ita maganar da sukayi da Fahad, ta bata shawarar koya masa abunda take so yayi mata, kuma hakan bazai yu ba sai tana yi masa ita da kanta, a sannu zai fara mayar da martani ba tare da ya sani ba.


~~~~~~~~~~


   "Wash!! Jikina duk ciwo yake min, da zan samu massage".

Cewar Elmansoor lokacin da yake kwanciya akan gadonsa bayan ya idar da sallah.


Kallonsa Fahad yayi yana mai lura da yanayinsa.

"Ka auri Aisha Sharp-sharp kaga yanda ake massage".

"Ai zanso hakan, amma tana makaranta, ss3 take yanzu ko? shekara d'aya nan gaba".

Yayi kwafa ya kauda kai. 


"Elmansoor". Ya furta sunan a hankali yana mai karantar fuskarsa, bai d'ago ya kallesa ba ya amsa da "umm".

"Kai yanzu baza ka iya rabuwa da Aisha kamar yanda ka rabu da sauran 'yan matanka ba?"


Juyowa yayi da kyau yana fuskantar Fahad da alamun mamaki a fuskarsa. Fahad bai jira amsa ba ya cigaba da maganarsa.


"Ai gani nayi kak'i canjawa ne, ita ma rabuwa zata yi da kai kamar yanda sauran matan suka gudu, ko baka tunanin haka?".


Numfashi ya sauk'e yana mai kawar da dubansa daga garesa.

"Whatever, nidai bazan canja ba, I have my reasons, ni bansan ya kakeso inyi bane ma, ta ina zan fara abunda na shekara aru-aru banyi ba? Na manta yanda ake yi ma".


"Kana sonta a hakan?"

Elmansoor baki ya bud'e yana kallonsa, wani irin tambayoyi ake masa kamar ya shiga ajin jarrabawa, tambayoyin masu zafi kuwa.


"Bazan iya amsa tambayar nan ba kai tsaye, amma ka tab'a ganin na tsaya ina magana da kai ko da wani ma akan mace? Mommy fa tasan da maganarta, in bana sonta meh yasa zanyi duk wannan?"


"Kana sonta kenan?"

A kufule ya amsa da "eh, ina sonta, natacce". Murmushi Fahad yayi yana mai kallon abokin nasa.

"Fine, ni kuma zan san yanda zanyi Aisha ta zauna dakai har kuyi aure ba tare da tayi tunani irin na sauran matan ba".


Murmushi ne ya kufce masa jin furucin Fahad, a kwanakin nan sosai ya shiga damuwa akan Aisha, b'oyewa kawai yakeyi yana nuna bai damesa ba, amma can cikin ransa yana tsoro da fargaban barinsa da take barazanar yi.


"Da gaske Fahad?" Tashi yayi ya rungumesa cike da murna, yana furta masa kalmar Godiya.


"Thank you friend, shiyasa nake k'ara sonka". Fahad a ransa yaji dad'in ganinsa haka, hakan ya k'ara masa k'arfin gwiwa, yayi alwashin karkato da hankalin Aisha zuwa garesa shi kad'ai. A k'asar zuciyarsa yace "abunda baka son a sani zan sanar da ita, shine kad'ai hanyar b'ullewa, Kayi hak'uri abokina".


~~~~~~~


Bansan ta ina zan fara ba, a dai cigaba da min uzuri, nasan kuna sona zaku fahimceni. Nagode da kulawarku gareni, na gaisheku kyauta.


MaryamerhAbdul na sonku matuk'a😘😘


Kada ku manta, ku danna wannan tauraron tare da yin comment a kowani layi, kowace kalma ma bazank'i ba😂, ku fad'i min ra'ayoyinku. 

Thank you all


Kamar yanda Fahad yace zai kirata a yau hakan kuwa akayi, ya k'irata da dare bayan ta gama hirarta da Kakarsu sun koma d'aki dan bata damar runtsawa.

"Allah yasa inji meh kyau"

Ta furta bayan ta amsa wayar.


"Uhmmm! Aisha kenan, ina fata in na fad'a miki bazakiyi wani abu mara kyau akai ba? Kuma kafin in sanar dake inason kiyi min alkawarin bazaki barshi ba, sai ma kiyi k'ok'arin d'auko gingimemen hak'uri muyi aiki tare dan daidaita komai, in har bakiyi hak'uri ba bazamu samu abinda mukeso ba. Ina mai tabbatar miki bazakiyi da na sani ba".


Abun yazo mata banbarakwai, wannan abun anya zata iya? Zuciyarta ya fara zargin wani abu, meh take shirin sa kanta ciki? Wani dalili ne da zai sa mutum ya zama kamar Elmansoor mai murd'add'en d'abi'u?


"Gaskiya bazan iya maka alkawari ba, kasan zama da irin Elmansoor akwai wuya, amma ka sanar dani koma meh ne, in ka sanar dani sai musan nayi koh? Anan ne zan iya yanke shawarar zama ko tafiya, ko ba haka ba?".


"Haka ne kam, toh da farko dai kinga Elmansoor abokina ne, kuma yayi soyayya da dama amma duk suna rabuwa dashi dan suna ganin fooling nasu yakeyi, shi mutum ne mara yin magana, miskili ne sosai, sai dai hakan ba shi ne dalilin rashin sakewarsa da mace ba, dalili yasa yayi anfani da miskilancin nasa dan cikan burinsa".


"Ban gane ba, kayi min bayani yanda zan gane please". 


"Kada kiyi sauri, zaki ji komai yau insha Allah".

Ajiyar zuciya ya sauk'e sannan ya cigaba da cewa.

"Elmansoor yayi believing duk namiji mai nanata yana son mace ko kuma yayi ta fa'da mata romantic words mayaudari ne, ba sai kace wa mace kana sonta zai nuna kana so ba your actions will say everything about the love you have for her...".

Katse shi tayi da cewa "ai shi actions d'in ma bai nunawa".


"Zan kai ki malama Aisha, zakiji komai a sannu tunda kika nemi ki sani, kwantar da hankalinki ki saurareni."

"Gani yake mata yawanci kwakwalwarsu yafi tafiya akan mazan da suke yawaita maimaita musu kalmar so bayan k'arya ne, a k'arshe sai kiga yarinya with a broken heart, wanda yake sonta da gaske d'in baza ta saurareshi ba, kuma yana ganin irin matan ba son tsakani da Allah suke son mutum ba they fall for his words kawai, in zaka soshi ba tare da yaudara ba fine, ka soshi yanda yake babu k'arya kuma ba yaudara".


"Maganar rashin nunawa ma'ana rashin kulawa ya samo asali ne daga abunda ya same shi a baya game da wata, hakan yasa ya d'auki wasu dalilai nasa wanda baza su wuce biyu zuwa uku ba, na farko dai mace d'aya ya dace ya nuna wa so a cewarsa, ita ce matar sa kenan. In ya nuna wa budurwa soyayya bai aureta ba yana ga kaman ya cutar da kansa kuma ya cutar da matar da zai aura..."


"Tafsha!" Cewar Aisha tana kad'a kai, tunaninta ya bazama neman mafita daga murd'ad'd'un halayen Elmansoor.


"Ban gama ba fa, ai saura dalili na gaba koh?"

"Ina jinka" ta furta tana mai dawo da dukkan hankalinta garesa.

"Cewa yayi bai son ya fara nunawa mace tsantsar kulawa dan sha'ani na rayuwa, ma'ana kada ya fara yi mata wani abu in anyi aure ya daina tayi tunanin ko sonta ne ya daina ko kuma dai wani tunani na daban irin naku na mata, gwanda in anyi auren kiga komai daban, rayuwan ku na aure should be much more better than rayuwar da kukayi na saurayi da budurwa, dalilinsa na k'arshe kuma raini da wulak'anci, dan hakan ya tab'a faruwa dashi".


"An tab'a betraying nasa kake nufi?"

Murmushi Fahad yayi cikin nutsuwa

"Kinsan ku mata in ku ka gano ana sonku toh nan za a fara wulak'anci kamar makarantarsa kuke je kuka koyo, abunda tayi masa kenan, ta gano yana sonta sai ta fara yawo da hankalinsa, shiyasa yace toh bazai bari mace ta gane ba bare tayi masa wani abun da zai tada mishi hankali, bazai sa mace a rai ba bare har ta sashi hawan jini".


"Indai maganar gaskiya kakeso toh fa bazan iya ba, a wani dalili zai had'a past relationship nasa da na yanzu? Bazan iya ba gaskiya, zai yi wuya in iya d'auka, tun wuri mu hak'ura yaje ayi masa auren had'i yafi".


"Barinsa zakiyi kenan?"

"Exactly".

"Baki min adalci ba in kikayi haka kin sani, kika barni na fad'a miki komai sannan kice haka, zai zama nayi aikin banza kenan? Na san waye shi, nasan abunda zamuyi mu fahimtar dashi abunda bai gane ba, in kika tafi kika barsa meh kikayi kenan? Try your best before leaving, trust me yana sonki, bazakiyi da na sanin zama dashi ba, he is good in any way".


Shiru tayi tana nazarin maganarsa, wani zuciyar na zungurinta akan ta yadda wani kuwa na nusar da ita akan bazata iya ba. Shirunta yasa ya cigaba da maganarsa

"Kada kiyi mana haka, am ready in taimaka ki janyosa ki juyasa yanda kikeso, zan baki every information da kikeson sani, Elmansoor na sonki fiye da duk wata budurwar da yayi, kiyi tunani akai. Idan baki yadda da soyayyarshi gareki ba ki bashi daman zuwa gidanku, a san da maganarsa, in akayi hakan zaki yadda yana sonki dalilai kawai suka hana shi nunawa".


"Zanyi shawara, zan nemeka insha Allah zakaji duk shawarar da na yanke, amma abun da kamar wuya gaskiya bazan b'oye ba. Ba wai ban yadda baya sona bane, tunda ka fad'a min na yadda, kawai ina tsoron sa kaina abunda bani da tabbas akai".


"Na gane nufinki, kiyi tunani meh kyau, kina sonshi kema na sani, you can do that for him, fight for your love".

"Nagode, insha Allah zan sanar dakai in na gama shawarar".

"Allah yasa inji alhairi, everything will be fine InshaAllah. sai da safe".


~~~~~~


  Washegari Aisha ta zayyanewa Mufeedah yanda sukayi da fahad, bata b'oye mata komai daga abunda ya sanar da ita da amsoshinta garesa ba.

"Ya zanyi Mufeedah".

Ajiyar zuciya Mufeedah ta sauk'e bayan ta gama sauraronta, tambaya d'aya take son yi mata a wannan lokaci duk da tana da tarin maganganun da take b'oye mata, shin tana mata adalci? Shin abunda take son sa Aisha zata iya sa kanta? 


Maganarsa ta k'arshe ya dawo mata

"Trust me, I love you kuma ina son k'aruwarki da dukkan mutanen da ke kusa dake, bazan cuceta ba". 

Yawu ta had'iye sannan ta iya jefa mata tambayar

"Kina sonshi?".


Shiru Aisha tayi tana mai tantance abunda yake ranta game dashi, kamar zatayi kuka ta bata amsar da bata san zai gamsar da ita ko akasin hakan ba.

"Ni yanzu haka bansani ba, ko ina sonshi ko bana sonshi oho, ina tsoro, ina tsoron shiga abunda bazan iya fita ba, sai dai bana tunanin zan iya barinsa, kenan ina sonsa?".


Ta k'arashe tambayar tana mai kallon Mufeedah, so take ta ji ra'ayinta, tana son ta samu matsaya d'aya cikin lamuranta da Elmansoor, tasan zata wahala in rabuwa zasuyi duk da bai saba mata abubuwa masu yawa ba, sai dai tana sonshi, so ta gaskiya ba tare da wasu dalilai kwakkwara ba.


"Ki yadda da Fahad, don ban ga anfanin rabuwarku ba, barinshi ba zai kawo maslaha ba, kuma kina sonshi, in har yana sonki shima kamar yanda Fahad ke fad'a toh gwanda ki hak'ura ki rungumi rayuwa duk yanda tazo miki. Kiyi iya k'ok'arinki ki gano abubuwan da baiso sai ki kiyaye, bare ma kina tare da fahad ai komai zai yu yanda muke so, ki cigaba da addu'a".


"Kin tabbata in cigaba da zama dashi a hakan? Bani da tabbacin zai canja ko bazai canja ba?"

Hannunta Mufeedah ta rik'e tana kallonta cikin ido

"Ki yadda dani, nasan meh nake cewa. Allah ya zab'a mafi alhairi".


 ~~~~~~~~~


Da misalin k'arfe takwas na dare Elmansoor, Fahad da mommy na zaune a parlor suna hira cike da annashuwa, Elmansoor ne yau ya zage yana bata labarin shirmen Fahad a makaranta, shima Fahad ba'a barshi baya ba, gwani ne wurin surutu, Elmansoor in ya fad'i nasa d'aya zai irgo na Elmansoor goma, cike suke da nishad'i dukka suna dariyar labaran.


Ba tare da kowa ya lura ba Fahad ya turawa Aisha sak'o. 


"Happy mood, text him'' 


Bata d'auki mintuna biyar masu kyau ba ta tura masa romantic text wanda a k'arshe ta tabbatar masa cewa tana matuk'ar k'aunar ganin murmushinsa.


Sak'onta tabbas ya shigesa dan lumshe ido yayi bakinsa yak'i daina murmusawa, ji yayi ina ma yana da yanda zaiyi ya mallaki wannan yarinyar, ina ma ita ya fara had'uwa da tun farkon rayuwarsa, da komai yana tafiyar masa yanda yake so.


Duk a idon Fahad akayi komai, dan yana kallonsa tun lokacin da sak'on ya shigo masa har ya karance wanda fuskarsa bai iya b'oye asirin zuciyarsa ba.


*******


Shin shawarar da Aisha ta d'auka zaiyi anfani? 


Anya bata yi kuskure ba?


Meh Mufeedah ke b'oyewa? Nidai naga alamar tana b'oye mana abu, shin menene? 


Wacece wannan yarinyar da ta b'ata mana Elmansoor? Shin ya akayi hakan ya faru? 


Kenan dama Elmansoor ya iya soyayya ko dai kawai zance ne irin na Fahad dan karkato hankalin Aisha?


Muje dai, amsar na gaba InshaAllah 

A cigaba da min uzuri.


Yau an cika wata d'aya da sati biyu cif ana yiwa Elmansoor gata, tun tana Damaturu ake aiki d'aya har ta koma Abuja dan komawa makaranta, amma duk a banza dan babu abunda ya canja cikin d'abi'unsa na farko, tana yi masa sak'o a duk lokacin da Fahad ya umarceta amma ko uhm bazai turo mata ba bare um-um, duk ya fita kanta wannan mutumin.


A farko ta d'auka zata iya shanye dukkan bak'in cikinsa, amma a yanzu ta saduda, ta bar sa kanta wahala da tashin hankali, tunda shi ya iya b'oye soyayyar da yake yiwa mace meh zai hana ita tayi irin nasa? Wani lokaci in tunani ya mata yawa abu ya dagule mata sai ta shige d'aki tayi kuka mai isarta ta bawa kanta hak'uri, tana mai rok'on Allah da ya sassauta mata abunda takeji a k'albinta. 


A yau Aisha ta gama yanke shawarar fad'awa Fahad k'udurinta, ta gaji da wannan shirin nasu da babu ci gaba, tasa a ranta idan Elmansoor ne k'arshen namiji a duniya toh ta rabu dashi kenan har abada sai dai ta zauna ba tare da miji ba iya rayuwarta, bata tsaya shawara da Mufeedah ba ta kira Fahad dan ma kada ta sa ta fasa k'udurinta.


Kamar yanda tayi addu'a hakan ta samu, dan Fahad bai iya hanata abunda tayi niyya ba, hak'uri kawai ya iya bata tare da fatan alhairi. Shi kansa yana ganin k'ok'arinta da ta iya zama dashi har zuwa wannan lokaci.


Kuka ta zauna yi mai cin rai bayan ta gama magana dashi, ji take ina ma tun farkon had'uwarsu ta barshi ba tare da ta sa rai akansa ba, meh yasa zuciyarta bata yi mata adalci ba wurin zab'an wanda ya dace da ita? Meh yasa take jin bata da k'arfin iko akan zuciyarta? Dan alamu sun nuna yana son rinjayarta.


Tabbas wannan karon zatayi yak'i da zuciyarta, dole ya bi abunda kwakwalwarta da gangar jikinta suke so ba wai abunda shi tallin tal yake muradi ba.


Lumshe idanunta tayi a k'ok'arinta na tare hawayen da ke zuba, sai dai kash, hakan bai samu ba, hawaye ke silalowa saman k'uncinta kamar ana ambaliya samar fuskarta. 


A haka Mufeedah ta shigo d'akin ta sameta, da hanzari ta iso wurinta tashin hankali bayyane saman fuskarta.

"Aisha lafiyanki? Meh ke damunki?"

Hannayen Aisha ta rik'e tana mai tambayarta damuwarta.


Aisha bata iya amsata ba sai ma kukan da ta samu damar fashewa dashi mai k'arfi tana ajiye kanta a cinyar Mufeedah. Mufeedah sosai ta firgita da lamarinta, bata iya hanata ba sai shafa bayanta da take yi a hankali.


Bata samu damar sa Aisha tsagaita kukan ba dan da gaskiyarta takeyi, tana son cire duk wani bak'in cikin da take ji, so take daga yau ta rufe babin Elmansoor a rayuwarta. 


A hakan wayar Mufeedah ya fara k'ara, bata iya d'auka ba sai da Aisha ta mik'e ta shige ban d'aki ta bata damar d'aukan wayar. Ajiyar zuciya ta sauk'e sannan ta iya d'auka cikin sanyin muryarta ta gaishesa.


"Meh kuka sake yiwa k'anwata?"

Shiru tayi na 'yan sakanni tana mai sauraron d'aya b'angaren.

"Look, ya isa haka, bazan sake sa ta yin abunda zai wahalar da ita kaman yanda nayi yanzu ba, laifina ne tun farko da na k'arfafa mata gwiwa bayan ba hakan ya dace inyi ba".


"Ni fa bazan iya ba, kayi hak'uri kawai". Katse wayar tayi duk da tana jin yanda yake yi mata magiya, bazata iya sauraronsa ba a yanzu, ganin Aisha cikin wannan hali ya karya mata zuciya, tana ganin da laifinta cikin abunda take ji a zuciyarta, a yanzu duk shawarar da Aisha ta yanke zata goya mata baya, bazata so ta k'ara ganinta a irin wannan yanayin ba.


Rurin wayarta yasa ta danna mab'allin kashe wayar dukka dan ta huta, babu abunda zai fad'a mata da zai karkato da hankalinta, ya nemi ta yarda dashi kuma ta yi amma bai musu anfanin komai ba, meh zai sake fad'a mata? Jaddada mata soyayyarshi ta k'arya a gareta kamar yanda abokinsa yayi? Bazata iya saurara ba, ta gaji da jin k'aryar maza da kalmar so, maza basu da tausayi.


~~~~~~~~~


"Ki d'auki wayar mana Aisha, na fad'a miki k'in d'aga wayarsa bazai canja komai ba, kwana uku ana abu d'aya ba canji? Ke dai kawai ki zama shi, in ya k'iraki kun gaisa ki masa shiru yanda yake miki, hirar da kika saba yi masa ki daina, in ya miki magana ta WhatsApp yes or no shine amsarki, yanda dai yake haka zaki koma masa".


"Ni fa so nake yasan na rabu dashi ne ba wai ina son ya canja ba". Cewar Aisha cike da b'acin rai.


"I know Aisha, abunda nakeso ki gane shine, Elmansoor da baya sonki bazai na damun kansa da k'iranki har na tsawon kwanakin nan bakya d'auka kuma ya cigaba da kira ba, daga lokacin da ya fara tambayan kansa ko ya tambayeki lafiya kika canja he misses the real Aisha, hakan na nufin kin saba masa da kanki, kin saba masa da salonki, kenan aikinki bai yi a banza ba. Ki gwada yin hakan, daga hakan in bai dawo miki ba kinga sai kowa ya kama gabansa. Aisha nasan ya kikeji, nasan yanda rad'ad'in so yake, nasan irin wahalar da zuciyarki ke ciki, ki bani dama a wannan karon ba wai dan wani ya sani ba, ra'ayin kaina ne, inason mu gwada wannan tare, in bai yu ba sai ki canja layi ki bud'e sabon shafi a littafin rayuwarki".


Aisha bata iya furta komai ba sai kallonta da take yi, a dai-dai nan wayar ta ya shiga ruri.

"Aisha I'm warning you, kada ki kuskura ki sake d'aukar waya da sunan yiwa Elmansoor waya ko text. Oya d'auki wayar".


Wayar ta d'auka tare da dannawa handsfree dan Mufeedah taji komai. Sallama tayi sannan ta k'ara da gaisuwar da ya dace da wannan lokaci.


"Ina wuni?"

"Lafiya k'alau, ya kike?"

"Lafiya alhamdulillah".

Shiru tayi tana sauraronsa kamar yanda shima ya yi. Sakanni sun gota babu wanda ya furta kalma d'aya tsakaninsu.


"na kiraki in gaisheki ne dama".

"Nagode" kawai ta furta Mufeedah ta katse kiran tana mai dariyar abunda sukayi masa, Aisha ma dariya abun ya bata tana tunanin yanda zai ji, lallai yau ta tsokano tsuliyar dodo.


~~~~~~~~~~


Wayarsa a hannunsa ya kasa ajiyeta tunda ta katse masa waya, mamakinta yake yi, ko dai akwai abunda ke damunta? Bata tab'a yi masa hakan ba, meh ya faru?.


Ajiye wayar yayi yana mai sa wa a ransa an b'ata mata rai ne ko kuma yau bata mood na magana dashi, kafad'a ya d'age ya cigaba da harkokinsa.


Washe-gari kamar yanda ya sa a ransa zata nemeshi ko da sak'on waya ne kamar yanda ta saba shiru bai ga komai ba, shima bai k'irata ba har dare.


Wasa-wasa kwana hud'u bata nemeshi ba, tun yana bawa kansa uzuri har ya fara tunanin rabuwa dashi tayi, dolensa ya d'auki waya ya k'irata, sai dai kamar rannan, bata ce masa komai ba bayan gaisuwa kuma ta katse wayar bayan shi ya dace ya katse tunda shi ya k'irata. 


Ranan da aka cika kwanaki bakwai Elmansoor ya kasa hak'uri, dole ya nemi Fahad dan samun taimakon gaggawa. A gida ya samesa cikin d'akinsa, da ganin fuskarsa kasan damuwa ce fal ya cika sa.


Wuri ya samu ya zauna, bayan sunyi musafaha da Fahad. 

"lafiya dai malam duk ka birkice?"

"Kayi magana da Aisha?".

Zuciyar Fahad tuni suka tarwatse jin tambayarsa, bai iya amsa shi ba ya wulla masa nasa tambayar.

"Meh ya faru? Lafiya dai ko?"

"Lafiya zance, amma na rasa gane kanta, ta canja min, ina kyautata zaton tafiya zatayi ta barni kamar yanda Najwa ta yi min a baya, rabuwa dani zata yi Fahad bayan ina sonta, wallahi ina sonta".


Baki bud'e Fahad ke kallon Elmansoor, taya zai had'a Aisha da Najwa? Ya tabbata Elmansoor bai san meh yake fad'a ba.


"Aboki, kada kayi kuskuren had'a Najwa da Aisha, akwai banbanci mai tarin yawa, Aisha tayi k'ok'arinta na zama dakai bayan baka nuna mata hak'ik'anin abunda ke zuciyarka ba, kana had'a rayuwar da Najwa tayi da kai da rayuwar da kake shirin tsarawa da Aisha, ka zauna da ita kamar yanda ka zauna da Najwa ka ga in zata barka. Elmansoor sau nawa zan tunasar da kai ba kowace mace ke da zuciya irin na Najwa ba? Sau nawa zan nuna maka kowa da irin halinsa? Idan har Aisha ta barka ba laifin kowa bane sai naka, kayi k'ok'arin gyarawa ba b'atawa da tunani irin wannan ba, kayi mata kyakyawar zato, ka so ta da zuciya d'aya, kayi mata komai da zuciyarka d'aya, idan ta yaudareka ta cuceka Allah yasan zuciyarka, amma yanzu bata san hak'ikanin soyayyarka gareta ba, ko ni nan zan tafi bare mace irin Aisha".


Shiru Yayi ya kasa yiwa Fahad magana, sosai maganganunsa suka shigesa, tunaninsa d'aya yanzu, ya zai gyara b'arakar da yayi? Ya zai dawo da Aisharsa garesa? Ya zai nuna mata irin son da yake mata? Anya zai iya? Najwa ta b'ata duk wani jin dad'i nasa, a ya barta ma tana shirin had'asa da abar k'aunarsa? Anya Najwa tayi masa adalci a rayuwarsa?


Dafa kafad'arsa Fahad yayi yana mai kallonsa.

"Elmansoor kada ka bari Aisha ta su'buce maka, yarinyar na da hankali da nutsuwa, in har ka rabu da ita bana tsammanin zaka iya samun mace kamar ta, ka zubar da abubuwan da ka d'aura wa kanka ka nemi yardarta da amincewarta, ka tura magabatanka gida a gama komai, na tabbata hakan zai kawo canji tsakaninku".


"Fahad kasan rayuwar da nayi a baya akan Najwa, kasan irin halin da ta sani, anya zan iya maimaita hakan? Yarinyar nan duk ta birkita ni a yanzu, da nayi mata yanda nayi wa Najwa kuma ta barni meh zai sameni kenan?"


"Kana sonta, ko da baka nuna mata ba Elmansoor ka yadda dani in Aisha ta barka zaka shiga hali makamanciyar wanda Najwa ta sa ka, ko ma fiye dan Aisha is unique, kuma ita ta dace dakai".


Fahad bai barsa ba sai da ya dasa masa abubuwa masu yawa game da Aisha, sai da ya nuna masa illar halinsa da kuma anfanin canjawarsa. Sosai maganganun suka shigesa, zaiyi iya k'ok'arinsa dan gano yanda zai warware duk abunda yake damun kwanyar Aisharsa.


*************


Drop your comments 

Vote 

And share with your loved ones 

I love you all


MaryamerhAbdul


"Muje gidansu yanzu, ina son ganinta, inason magana da ita Fahad".


Bai jira amsarshi ba ya mik'e yana kallonsa.

"Ina zanje wai? Fad'an masoya zanje in gani ko meh".

"Kasan tana kunyarka, nasan in ta ganmu tare zata hak'ura".


"Ba inda zanje fa yallab'ai, dan gaskiya in naje nasan ni zaka bari da bada hak'uri, kaje kawai Allah ya bada sa'a".

Kallonshi ya tsaya yi ya rasa kalmar da zaiyi anfani dashi dan jan ra'ayinsa, numfashi ya sauk'e sannan ya zauna kusa da Fahad.


"Ba dan ni ba fahad ka tashi muje, abun nan na damuna kai baka iya gani ne? Meh yasa ka canja min akan Aisha? Kana taya ta wahalar dani, dan kaga ina sonta? A ganina kai kad'ai ne mai fahimtana kuma kasan dalilina, meh yasa kake son juya min baya a dai-dai wannan gab'a?"


Hannayensa Fahad ya d'aga sama,

"Ka d'aureni, muje na yadda, amma ni bazan yi magana ba, in naga kayi min yanda nakeso zan taya ka amma in kayi shiru nima kai zan zama dan in anyi auren ba ni zan zauna da ita ba". 

A hakan suka fice a tare dan ziyartar Aisha.


~~~~~~~


"Haba Aisha, ina zuwa wurinki yanzu kice bakya gida? Yaushe kika fara yawo da yamma?"


Muryarta ne ya sark'e cikin rashin abun fad'a sai i'ina takeyi. Bai saurari k'aryar da take nemowa dan hana shi zuwa ba ya cigaba da maganarsa.


"Nasan fushi kikeyi, kuma kina da gaskiya, amma hakan ba shi zai sa ki hanani ganinki ba, nan da mintuna biyar zaki ganni, in na zo kada ki fito wurina".


Katse wayar ya yi bai tsaya jin maganarta ba, ta fara bashi haushi, yasan tana gida meh na yi masa k'aryar bata nan? Dan bata son ganinsa? Ta daina sonsa? Zuciyarsa ne ya buga da wani tambayar ya fad'o masa, ko dai tana tare da wani?


"Fahad ko dai Aisha na tare da wani shiyasa bata son inje?".

"Ohhh Elmansoor". 

Kallonsa yayi sannan ya mayar da hankalinsa kan tuk'in da yakeyi.

"Ka yawaita kyakykyawan zato, kada ka manta fushi takeyi, kaman baka san mata ba da su kansu wani lokaci basu gane kansu?".


Bai iya amsawa ba ya cigaba da tunaninsa, ganin haka Fahad bai sake cewa komai ba ya barsa dan yayi tunaninsa ko zai dawo da wani b'angare na hankalinsa da ya b'ace tun rabuwarsa da Najwa.


   Mai gadin gidan kamar yanda aka sanar dashi bak'in Aisha zasu zo a shigar dasu parlor haka ya yi. A cikin gidan sukayi parking wurin ma'adanin motoci sannan suka zarce b'angaren da suka hango mahaifin Aisha da ke zaune akan kujerar roba wurin shak'atawa.


Har k'asa suka tsugunna suka gaishe shi cike da girmamawa, da murmushi a fuskarsa ya amsa yana mai kallonsu d'aya bayan d'aya, tunda matarshi ta sanar dashi akwai wanda yazo wurin Aisha yake fatan ganinsa tun kafin komai ya kankama tsakaninsu, sai yau da Allah ya kawo sa yana gida.


"Wurin Aisha kuka zo? Wanene daga cikinku?"

Murmushi bai bar fuskarsa ba yayi tambayar, ganinsu cikin manyan kaya cike da kamala ya burgeshi, da alamu batayi zab'en tumun dare ba.


Fahad ne ya gabatar da kowannensu, ya nuna Elmansoor yana cewa 

"Shine Elmansoor Yuri, abokinsa ne ni".

Murmushin manya yayi yana kallonsu, ba sai anyi masa k'arin bayani akan wannan jimlar ba, idan ya gano Fahad shi d'an rakiya ne, Elmansoor ne mai ziyarar.


"Ai kuwa nasan familyn Yuri sosai, kamar ma ka so min kama da wani wanda na sani?"

Kallonsa dukkansu suka tsaya yi dan neman k'arin bayani daga wurinsa, tunani ya shiga yi wanda dukkansu babu wanda ya san meh ke yawo cikin kwanyarsa. Daga bisani yace "ku shiga ciki ba komai, Allah ya tabbatar da mafi alhairi".


Ciki suka shige bayan sun amsa addu'ar da Ameen.


Mufeeda da Aisha ne suka shigo palorn bayan mintuna k'alilan da isowarsu. Idanun Elmansoor taf kan Aisha ya kasa ko da kifta idanunsa, can gefe ta zauna Mufeedah kuma ta ajiye trayn hannunta ta juya zata koma.


"Mufeedah".

Muryar Fahad ya dakatar da ita, idanunta ta sauk'e a kansa tana mai wasa da yatsun hannunta.

"Ga wuri nan, zo muyi hira mu barsu suyi nasu".

Wurin Aisha ta kai dubanta, idonsu ya sark'e cikin juna, tuni ta kawar da idonta dan bata d'auka tare da Fahad suka zo ba, kuma bata d'auka zai iya yi mata hakan ba bayan yasan babu wanda ya san abunda ke shirin afkuwa tsakaninsu. Sum sum ta isa inda ya nuna mata ta zauna kamar wacce kwai ya fashewa a ciki.


Elmansoor da yasan abokinsa ya d'auke kai ba tare da yayi tunanin wani abu game da hakan ba, a ganinsa yayi ne dan kawai kada ya bawa Aisharsa hak'uri, a ransa kuwa yace, yau dai baya buk'atar taimakon wani, kwanyarsa da k'albinsa sun wadatar dashi dai-daita mata nata kwanyar.


Sai dai abun da kamar wuya, dan ya kasa katab'us sai kallonta yakeyi yana tunanin ta inda zai fara, gani yayi yau wulak'anci take son yi masa, meh na zama a kujerar nesa dashi bayan ga kujerar da ke kusa? Yaya takeso suyi maganar? So take ya jefa mata magana ta cafe ita ma tayi masa hakan? Ko dai so take Fahad da Mufeedah suji maganar da sukeyi?


Ganin ba sarki sai Allah yasa shi mik'ewa had'e da isa wurinta, Aisha tuni ta had'e hannayenta wuri guda tana murzawa had'e da jin d'umin hannunta da ta tabbata zufa ke d'id'ika daga cikinsu. Yawu ta had'iye "muk'ut!" Jinsa da tayi a kujerar gefenta tare da amon muryarsa da ya doki kunnunwanta.


"Baki son magana dani yau da alama".

Kallonta ya tsaya yi yana mai mamakin rashin sakewarta dashi, sakanni ya d'auka yana mai karantarta.

"Pretty" ya furta kalmar can k'asan mak'oshi, kwanyarta da kunnuwanta suka d'auki maganar suka kai mata kasa tantance ma'anarsa tayi, kalmomin da suka biyo bayan kalmar ya k'ara dagula mata kwanya.


"Ya zama dole in tona sirrin da ke raina, ya zama dole in nuna miki soyayyata ta gaskiya gareki, please ki saurareni, ai ni inason magana dake tunda na kawo kaina. Pretty nazo in amsa laifina, ki fad'a min laifina am ready to apologise, rok'ona bai wuce ki daina wahalar da zuciyata ba, ki daina tsoratani da barina, bazan iya d'auka ba".


Shiru sukayi babu wanda ya sake magana, dak'yar Aisha ta iya had'o kalmomin bakinta ta furta can k'asan mak'oshi, bata yi tsammanin zai ji ta ba amma dole ta furta dan ta cika umarnin Mufeedah.

"Ba komai fa, ni baka min komai ba, ni bansan meh ka gani da kake tunanin laifi kayi min ba".


Iska Elmansoor ya furzar yana mai kawar da kai, bai d'auka a gaban idonsa zata iya yi masa hakan ba, ko nauyinsa bata ji ba take neman wulla zuciyarsa wata duniyar da baya fatan sake komawa cikinsa?


"Pretty nasan laifina, abunda ya kawo ni kenan in gyara laifukana gareki, kiyi min uzuri, ki gafarceni, pretty am sorry, kina wahalar dani da yawa".


Shiru ne ya ratsa tsakani, maganganunsa take juyawa tare da mamakin sabon salon da bata tab'a gani daga garesa ba, rashin kalmomin kwanyarta yasa ta yin shirun dole, sosai take k'ok'arin bin umarnin Mufeedah, yakamata tayi masa hakan, yakamata ya gane kurensa, yakamata ya nemi soyayyarta.


"Kin daina sona ne Aisha?"

Tambayar sosai ya doketa, ya zaiyi mata irin wannan tambayar? Idanunta ta d'ago ta sauk'e akansa. Dole ta mayar da idanunta saman carpet na parlon sannan ta iya sarrafa harshenta.


"Bana son in saba da kalmominka, banson in saba da kai bayan banga alamar soyayyata tattare dakai ba, gwanda inyi nesa dakai tun kafin rabuwa dakai ya zame min abu mai wahala".


"Rabuwa? Haba pretty, ya zaki fara kawo maganar rabuwa tsakaninmu? Kuma wa yace miki bana sonki? Yanzu ma fa sai da na fad'a miki, duk baki yadda ba?"


"Kai fa kace action speaks louder than voice".

"Meh kikeso in miki ki yadda dani? In turo iyayena ayi maganar aurenmu? Hakan nasan zai tabbatar miki da ba da wasa nazo ba, ko gobe ne am ready Pretty, just say yes. Please".


Baki bud'e take kallonsa, tuni ta mance da Mufeedah da gargad'inta na garasa, murmushi ta sakar masa bayan ta tabbatar da maganar da yake fad'a iya gaskiyarsa kenan.


"Mu tafi Elmansoor".

Cewar Fahad bayan ya mik'e daga mazauninsa. 

A nan ne suka tuna da zamansu cikin parlon, tuni suka mance da akwai wasu mutane biyu bayan su. Kan Mufeedah a k'asa tana wasa da yatsunta, shi kuma Fahad da alamu ransa ya b'aci, fuskarsa ba kaman yanda suka shigo ba cike da annuri.


"Ai ban gama bada hak'urin ba".

Cewar Elmansoor yana kallon Aisha.

K'aramin tsuka Fahad ya yi ya fice zuwa wurin motarsu, Mufeedah ko ji tayi kamar ta fire ta bar wurin dan kallon da suka zuba mata. Murmushin dole ta sakar musu ta mik'e ta koma ciki.


"Ehmmm, ka tafi, mu gama magana ta waya, kaje kaji meh ya samesa".

Baiyi musu ba ya bi bayan Fahad, tambayoyi ne fal ransa game da canjawarsa lokaci k'alilan, iya saninsa da Fahad ba abu k'ank'ani ke b'ata ransa har haka ba.


*********


Uhm uhm!!! Abun sai da gyaran murya


Meh ke faruwa tsakanin Fahad da Mufeedah wai? Na fa kasa ganewa.


Elmansoor fa? Shin a ganinku zai d'aure a haka? 


Shin Aisha tayi saurin sauk'owa ko dai a ganinku ya ci ta k'ara gwara kansa? 

Most of you will say yes I know, ku dai tuna da cewa Elmansoor yana da dalilinsa, shin ko kunsan meh Najwa tayi masa?


Kuna son sani?


Let's keep going then💃🏼💃🏼

MaryamerhAbdul na jiran comments naku.

Ina mai tabbatar muku samunsu zai bani k'arfin gwiwar baku page biyu a yau dan warware mana dukkan tambayoyinmu.

Wait, mace dukka? Um um, banyi alk'awari ba, kad'an dai daga tambayoyin zaku iya samun amsarsu.


Muje zuwa


MaryamerhAbdul


"Meh yasa baka fad'a min ba tun farko Fahad? Yanzu meh abun yi? Samunta kakeson inyi? Mun dinga shiga tsakanin juna dan gyara b'arakar da mu da kanmu zamu iya gyarawa kenan? Ita kuma ya zatayi haka? Meh yasa zata yi tunanin halinmu iri d'aya bayan kai daban ni daban".


Elmansoor ke wannan zancen bayan Fahad ya gama yi masa bayanin komai.

"Kasan da haka? Kasan kowa da irin halinsa kake k'ok'arin hana kanka abunda kakeso dan wata aba can ta b'ata maka? Yanzu gashi nan ka ja min, Mufeedah tace bazata tab'a saurarona ba, duk bayanaina na k'arya ne tunda kai abokina ne, abokin b'arawo shima b'arawo ne".


"Fahad, Fahad, kai kasan dai ba a son raina nake hakan ba? Ko wani namiji aka yi wa abunda Najwa tayi min tabbas sai ranshi ya b'aci kuma yayi tunanin mata basu da tausayi bare b'urb'ushin imani".

D'auke kai yayi idanunsa ya canja launi tunawa da Najwa da yaudararta garesa. Yawu mai d'aci ya had'iye yana mai damk'e hannayensa da runtse ido.


"Mu bar wannan maganar Fahad, mu nemi hanyar gyara ba tuna baya ba, kana son Mufeedah naji, tak'i yadda dakai kuma kace laifina ne, shima naji, kuma ina k'ok'arin gyarawa, shawara d'aya zan baka, kada kayi zuciya da abunda tayi maka, ka sake k'ok'artawa, na tabbata zata fahimceka, laifina bazai shafeka ba".


~~~~~~~~~~


"Aisha bazan iya fad'a miki komai ba, dan bana tunanin zan iya sauraronsa, ki bar maganar kawai ki bani labarin Elmansoor, ya kukayi?"


"Nice wawuya mai kwashe komai ta sanar dake dan neman shawara ko? Ni kike k'ok'arin b'oyewa abu Mufeedah? Lallai, kin kyauta".

Juyawa tayi ta fice daga d'akin ta k'yaleta, ta gaji da binta dan ta fad'a mata abunda ke tsakaninta da Fahad, tun jiya ta kasa samun tak'amaiman magana daga gareta bare Elmansoor da ko zancen bai kawo mata ba.


Bata dawo d'akin ba sai dare lokacin bacci, bata yadda sun zauna su biyu ba tun ficewarta daga d'akin dan bata buk'atar lallashin Mufeedah, tayi fushi da ita ta nuna mata matsayinta.


Kwance take tana lume cikin bargo idanunta lumshe ta shigo d'akin. Wanka ta shiga dan samun dad'in bacci, bayan ta fito ta sanya kayan baccinta ta samu gefenta ta kwanta ba tare da ta kulata ba.


Mufeedah da ke jin duk motsinta ta zauna tana mai kwaye bargon jikinta da na Aisha.

"Tashi muyi magana, ni bana son sabon salon iskancin nan".

"Bana son magana dake, kowa ya rik'e abun ransa". A dake ta fad'i maganar tana mai janyo bargon dan rufe jikinta.


"Aisha wai Fahad sona yake, ni kuma tsoronsa nake dan bana son abunda Elmansoor yake miki, gani nake shima haka zai yi min, shine fa yayi zuciya ya tafi dan nace bazai yu ba yayi hak'uri, kuma na tabbata ba wai rejecting d'insa da nayi bane ya b'ata masa rai, d'aura masa laifin da ba nasa ba da nayi shi yafi b'ata ransa".


Juyowa Aisha tayi tana kallonta duk da k'arancin hasken d'akin. 

"Tun yaushe yace yana sonki? Ki bani labari daga farko har k'arshe sannan in hak'ura".

D'auke kai tayi had'e da hard'e hannayenta a k'irjinta tana mai sauraronta.


"Kin tuna farkon maganarki da Elmansoor ta wayana? Ranan da Fahad ya k'irani? Toh tun lokacin, bansan ina ya samo layina ba, daga ranar ya fara damuna da k'ira da sak'o, ban tab'a amsa shi ba dan ina son ganin yanda zaku kaya da Elmansoor, ban dai ce masa bana sonshi ba amma ban amshi tayin nasa ba, har lokacin da kikace kin rabu da Elmansoor, Fahad ne ya sa nace ki yadda ki gwada abunda yace miki duk da ba a son raina ba dan ni kinsan bazan baki shawarar bin namiji haka ba, nayi masa hakan ne dan kawai ya rok'i alfarmar hakan, kuma ya nemi in yadda dashi, kuma bayan nayi hakan babu abunda ya canja, sai na fara jin haushinsa dan ya taimaka wurin b'ata ranki, da bai sa ki yin hakan ba da mun samu solution tsakaninmu. Sai na daina d'auka wayarsa, na daina magana dashi, maganar gaskiya ba ma rakiya yayi ba jiya, zuwa yayi dan ya bani hak'uri kuma ya nemi soyayyata, shine na gaya masa magana ya tattara takalmansa ya k'ara gaba, har yau bai ma k'irani ba. Kinsan ni banson irin wannan, yanzu zan ajiye babinka in k'ara gaba, banbancina dake kenan".


Aisha kallonta ta tsaya yi tun fara maganar ta har i zuwa k'arshe.

"Haba Mufeedah, yanzu laifin Elmansoor sai ya shafi Fahad? Toh mun dawo daidai sai ki laluboshi ki bashi hak'uri, sai in ko baki sonsa bakya ra'ayin zama dashi, wannan kuma daban".


"Ai kin ganki, ni zan nemesa? Shi yake neman soyayyata sai in bi in basa hak'uri dan kawai ina jan ajina? In kinga bai dawo ba dama ba serious bane, kinga ya hutar dani".


"Kina k'ok'ari Mufeedah, bana tunanin zan iya yin hakan ga wanda nakeso".

"Shiyasa nace miki akwai banbanci tsakaninmu, haba Aisha, ki koyi jan aji dan Allah, namiji na son hakan, ke yanzu baki ga anfaninsa ba? Kin share sa kin nuna zaki iya rayuwa babu shi ya dawo miki? Ko ba jiya dashi naji kina waya ba har da kashe murya da dogon waya? Kin tab'a waya dashi haka?"


"Na yadda da zancenki, amma sai dai kada yayi yawa, lokacin soyayya a yi shi, in ya kama kuma ki d'aure, ai zan iya hakan kin sani? Elmansoor ne daban".

Idanunta ta juya bayan ta k'arashe maganar.

Mufeedah kad'a kai tayi ta gyara bargon ta kwanta tana mai yi mata sai da safe.


~~~~~~~~~


Watanni biyu da faruwar hakan


Kwanaki sun ja, abubuwa masu yawa sun sauya, Elmansoor yana iya k'ok'arinsa dan gyara tsakaninsa da Aisha, ba dan komai ba sai don samun abinda zuciyarsa da gangar jikinsa ke buk'ata sai kuma dan taimakawa abokinsa samun abunda yakeso, baya son ya zama dalilin rugujewar farin cikin Fahad, aboki ne garesa amma tabbas abunda yayi masa a rayuwa baya tunanin ko d'an uwansa na jini zai iya yi masa, ya kasance tare dashi lokacin jin dad'i, haka ya kasance dashi lokacin da ya fad'a bak'in rayuwa, ba ta fannin soyayya kad'ai ba, Fahad ya kasance tare dashi a dukkan lokuta na rayuwarsa, mai dad'i ko akasin hakan. 


Yayi wa kansa alk'awarin yin duk yanda zai yi dan samar wa abokinsa farinciki, da alamu canjawarsa bai yi a banza ba, dan hakan ya kawo sauyi tsakanin Mufeedah da Fahad, soyayya ya k'ullu tsakaninsu sosai, wanda zai iya cewa yafi wanda yake tsakaninsa da Aisha. Ba wai baya son Aisha bane, fahimtan juna da sakewa tsakaninsu yafi na wanda yake tsakaninsu, ba laifinsa bane, akasari yana samun sauyin yanayi a duk lokacin da wani b'angare na zuciyarsa ya bijiro masa da Najwa, yana iya k'ok'arinsa dan yakice komai a ransa, farin cikinsa d'aya, Aisha ta fahimcesa a yanda yake, duk da har i yau bai iya sanar da ita komai game da Najwa ba, bata nemi sani ba shi ma bai so sanar da ita ba. 


Hakan yayi masa dai-dai, sai fatan samunta da kasancewa da ita matsayin tasa, Aisha ta tafi dashi, ta tafi da ruhinsa da dukkan soyayyarsa. Yana matuk'ar sonta, baya fatan wani k'addara ya gifta tsakaninsu wanda zai raba su, ko da a mafarki yaga hakan yakan b'ata lokaci mai yawa dan addu'ar samun alhairi a rayuwarsa, yana addu'ar samun sassauci a soyayyar da yake yi mata indai babu alhairi ciki.


~~~~~~


"Yace yana son ya turo, ya zan fad'awa Mama?"

Baki Mufeedah ta toshe dariya na son kufce mata. Tuni Aisha ta had'e rai tana kallonta, ya zata mata dariya bayan ta kawo mata magana mai muhimmanci irin wannan?


"Kada kiyi fushi, dariyan kaina nake da ko ke na kasa fad'awa yanda mukayi da Fahad bare Mama, Allah had'a baki sukayi dukkansu".

Dariyar kansu suka tsaya yi, daga bi sani Mufeedah ta tsagaita.


"Har fad'a mukayi jiya akan maganar zuwansa, ya kasa gane cewa bansan ya zan fad'a a gida ba".


"Ni kuma Elmansoor da nace taya zan fad'awa mama har da gwada min fa. Wai in kinje ki zauna a gefenta ko a k'asa ma, ki gaisheta ko da kun gaisa da safe, sai kice mata Elmansoor na son zuwa ayi maganar aurenmu".


Fashewa sukayi da dariya dukkansu, yanayin yanda yake maganar Aisha ke kwaikwaya. Sai da sukayi mai isar su sannan suka tsaya tunanin abun yi. A k'arshe suka yanke shawarar zuwa wurin mama dukkansu, Aisha ta fad'i sak'on Mufeedah ita ma ta fad'i na Aisha.


***********


Chapters biyu yau💃🏼💃🏼


Nayi qoqari ko?


Naji dad'in comments naku da votes shiyasa. 

Ina godiya😘


Ya kuka ji wannan shafin?


Dad'i?


Kada dai kuji dad'in da yawa, banyi muku alkawarin samun farinciki har k'arshe ba, bomb d'in na nan zuwa. Wata k'ila a shafi na gaba.


Ku cigaba da bina a hankali, a sannu zaku samu dukkan labarin a tafin hannunku.


Ina godiya 

Vote 

Comment

And 

Share


MaryamerhAbdul


"Maganar da nace zamuyi akan yaran nan ne dama".

cewar mama da take zaune gefen mijinta, fuskarta cike da annuri tun daren jiya da tayi magana da yaranta.

"ina jinki, meh ya faru?"

Zamanta ta gyara tana mai sake masa murmushi.


"Kasan sun kusa fara jarrabawar gama makaranta, toh kaman yanda na sanar dakai akwai wad'an da ke zuwa wurinsu, toh sunyi magana suna neman a basu daman zuwa gareka dan a san dasu, in yaso bayan jarrabawar sai ayi bikin kowa ya huta".


Bai iya b'oye farin cikinsa na jin zancenta ba, murmushi mai k'ayatarwa ya wadata fuskarsa dashi.


"Gaskiya naji dad'in hakan, yaron nan Yuri da yazo nan ko?"

"Eh, wannan ai shi ke neman Aisha, toh akwai abokin nasa, Fahad, shi ke neman auren ita Mufeedah".


"Toh! Ai ko na ganesa, sai dai hanzari ba gudu ba, kamata ya yi Fahad yaje wurin mahaifinta neman aurenta ko?"


"Eh, amma a nawa shawarar ka binciki halayensa sannan ka tura shi, in bai yi ba kaga ba sai an wahalar da kai ba a b'atar da zancen, ko ba haka ba?"


"Kin kawo shawara meh kyau, sai wannan yaron na Aisha, nayi iya bincikena bayi da matsala gaskiya, matsalar dai guda d'aya ne wanda har yanzu na kasa ganowa".


Hannunsa ta rik'e cikin nata idanunta na kansa tana kallon yanayin fuskarsa.

"Abban Aisha, kayi hak'uri ka cire abunda ke ranka, babu abunda zai faru sai alhairi".


"Akwai Yuri fa cikin sunan mahaifinsa", numfashi ya sauk'e yana mai jin rad'ad'i a k'albinsa, bata iya furta komai ba ganin yanayinsa ya sauya.


"Bana tunanin zan iya bashi Aisha muddin na tabbatar da hasashena".

Cikin i'ina ta furta sunansa, rashin samun kalmar da ya dace ta furta masa yasa ta kad'a kanta.


~~~~~~~~~~~


Bayan makonni biyu


  K'arfe 3:30 dai-dai horn na motoci biyu suka doki mai gadin gidansu Aisha, da hanzari ya lek'a dan tabbatar da hasashensa, bud'e tangamemen gate d'in yayi yana mai wage musu baki had'e da d'aga musu hannu cikin russunawa alamar girmamawa.


Kai tsaye suka shigo suka yi parking wurin ajiyar motoci. D'aya daga cikin abokan Abban Aisha ne ya fito tarbansu cike da farincikin ganinsu. Cikin girmama juna sukayi musafaha sannan ya musu jagora zuwa parlon da aka tanadar domin su.


"Ai kuwa suna masallaci, nima yanzu isowana na tarar suna sallah nake zaman jiransu, sannunku da zuwa".


Dukkaninsu farincikinsu bai b'oye ba, bakin nasu ya gaza rufuwa. 


Kayan shaye-shaye da tand'e-tand'e da aka tanadar musu Mama tasa masu aikinta kai wa wurinsu kafin Abba su iso. Mintuna biyar basu cika ba Abba da sauran abokansa da 'yan uwa da ya gayyata dan tarban bak'insa suka dira parlorn, da murnarsu suka shiga palorn ganin motarsu wurin parking ya tabbatar musu cewa bak'in nasu sun iso yayin da suke sallahr la'asar.


Cike da farin ciki suka shiga musafaha da juna ana gaisawa. Wasu daga cikinsu sun san juna, hakan ya kawo hayaniya tsakaninsu na yaushe gamo da kuma tambayar iyalin juna.


Abba ne k'arshen shigowa parlon nasa, murmushi bai bar fuskarsa ba yana mik'a musu hannu d'aya bayan d'aya. Wurin abokinsa da suka dad'e basu had'u ba ya tsaya yana mai mamakin rayuwa.


Alhaji Samaila rungumeshi yayi yana mai farin cikin ganinsa.

"Ashe 'yar wajenka d'an namu yake nema? Ikon Allah". 

"Duniya, ashe zamu sake had'uwa Alhaji Samaila? Ina ka b'oye haka?".

Hannunsa cikin nasa yake tambayarsa yana mai jinjina rayuwa, bai tab'a tsammanin zai sake ganin Samaila ba, tun rayuwar makaranta rabonsu da juna.


"Ikon Allah kenan, yanzu dai gama gaisawa da sauran mutanen ai zamana dakai na musamman ne". Yana dariya ya fad'i hakan, shima Abba dariya yayi.


Hannu ya mik'a ma Daddyn Elmansoor ba tare da ya d'aura idanunsa akansa ba dan hankalinsa na tare da abokin nasa da yake yi masa wani zance na raha. 


Muryar d'aya daga cikin magabatan Elmansoor ne yasa shi waigowa dan ganin wanda yake gaisawa dashi.

"Mahaifin surukin naka kenan".


Idanunsa ya sauk'e akan Bala Yuri, yawun bakinsa ya kafe kamar yanda fara'arsa da murmushinsa a lokaci guda ya b'ace, jinin jikinsa da dukkan wani kuzari nasa ya nema ya rasa, jinsa yayi cikin wani duniya daban, baya iya tantance maganganun mutanen parlon.


Idanunsa yayi k'ok'arin rufewa bayan ya samu damar janye hannunsa daga musafahar da sukayi da wanda ake ik'irarin shine mahaifin Elmansoor, manemin auren 'yarsa da yake matuk'ar so wato Aisha.


Cikin mutuwar jiki ya nemi kujera ya zauna, bai iya sake murmushi ba har suka gama tattaunawa suka tashi tafiya, ya nemi a bashi lokaci zai nemesu daga baya.


Har wurin motarsu ya raka su bayan sunyi musayar lamba da abokin nasa, bai samu damar shigowa gida ba sai da dukkan wad'an da ya gayyata suka bar gidan. 


~~~~~~~~~~


D'akinsa ya wuce daga shigowarsa ba tare da ya tanka kowa daga cikin 'ya'yan nasa ba. Mama da tasan mijinta ta biyosa d'akin dan jin abunda ya samesa. Ta sameshi zaune gefen gado ya zabga tagumi ya lula duniyan tunani, a gefensa ta zauna sannan ta dafe kafad'arsa.

"lafiya dai Abban Aisha".


Nannauyar numfashi ya sauk'e yana mai shafe fuskarsa da dukkan hannayensa.

"Elmansoor d'an Alh. Bala Yuri ne?"

Kallon mamaki take masa, ganin bayi da niyyar yi mata k'arin bayani yasa ta muskutawa.

"wani Bala Yuri kuma?".


"Bala Yuri dai guda d'aya da kika sani, am sure kin gane ko wa nake magana".

Kawar da damuwar fuskarta tayi ta kallesa da kyau. 

"Meh a ciki dan shi d'an Bala Yuri ne? D'ansa kace ba shi da kansa yazo neman auren 'yar ka ba".


Kallonta yayi cikin ido, idanunsa sosai ya tsoratar da ita, ya canja launi yana fitar da wani nau'i na b'acin ran da bata tab'a gani tare dashi ba.

"Ki sanar da Aisha ta kawo ko ma waye ne in aura mata amma banda Elmansoor Yuri".

Mik'ewa yayi da niyyar barin d'akin ta rik'e hannunsa.

"Ban gane ba? meh kake nufi? Ba dai wulak'anta bak'in namu kayi ba?".


Kafad'unta ya rik'e idanunsa na kallonta, yawu mai d'aci ya had'iye, bakinsa na rawa ya furta mata kalaman da harshensa zai iya furtawa a wannan lokacin.


"Bazan iya bawa Elmansoor Aishata ba, ki sanar da Aisha ta fita hanyar Elmansoor, babu ita babu shi har abada". 


Hawaye tuni ya taru idanun Mama ta sunkuyar da kanta k'asa. Motsin tafiyarsa taji wanda ta tabbata idan ta barsa ya fita ta rasa wannan damar kenan har abada.


"Abban Aisha" ta k'ira sunansa bayan ta mik'e tsaye, wurinsa ta isa ta rik'e hannunsa, bata iya hana hawayen idanunta sauk'a bisa kuncinta ba.

"Ya kake neman lalata farin cikin 'yar ka da kanka? Ya kake neman d'aukan hukunci da hannunka akan abinda kasan bazai tab'a gyaruwa ba? Past is past, kayi hak'uri ka manta komai, ka ba wa 'yarka farincikin da take buk'ata". 


Hannunsa ya cire daga nata ya fice daga d'akin ba tare da ya furta ko da kalma d'aya ba. Zaman dirshan tayi tana kuka mai tsuma zuciya, tasan yanda Aisha ke mutuwar son Elmansoor, taya zata fara sanar da ita sak'on mahaifinta? Taya zata mata wannan maganar mai d'aci da zai iya tarwatse mata zuciya?


~~~~~~~~


Ku taya Aisha kuka tun kafin taji wannan mummunan sak'o


Meh yasa Abba yake k'ok'arin hana auren Elmansoor da Aisha?


Shin Aisha zata iya jure rashinsa?


Ya rayuwar Elmansoor zai kasance in yaji wannan mummunar sak'o?


Kada ku manta, comment and vote 


Gobe bazan samu damar baku ko da shafi d'aya ba saboda zanje makaranta tun safe. Insha Allah zuwa jibi zan k'ok'arta.


Ban sanar muku ba, shin kun karanta matar k'abila? Bazan so wannan littafi ya wuceku ba 

Ku garzaya Suwaiba36 don karanta wannan littafin, trust me bazakuyi da na sani ba. Ya had'u matuqa. addaummi kada ayi babu ke, ki hanzarta 🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️🏃🏻‍♀️


Nagode 


MaryamerhAbdul


"Ku bani aron hankalinku da nutsuwarku na d'an lokaci, inason ku fahimci kowace kalma da zan furta, bana fatan sake maimaita kalmomina saboda nasan irin d'acinsu a harshena da kuma zuk'atanku".


Mama ke wannan bayanin bayan shigowarta d'akinsu dan sanar dasu sak'on Abba, kallonsu tayi d'aya bayan d'aya sannan ta cigaba da cewa.


"Ina son ku sani kuma ku sa a ranku ba komai mutum ke nema yake samu ba a rayuwa, akasarin lokaci sai mutum ya so abu kuma ya zama ba alkhairi bane garesa amma in ya barwa Allah sai abun ya wuce, shi kuma yaje ya samu alkhairinsa a gaba, k'addara baya wuce mutum, ba wayonka bane ko dabararka, sanin hakan yasa nake umurtanku da duk abinda ya sameku kusa a ranku its a test, sai kuyi hak'uri, hak'uri da yadda da hakan daga wurin mahaliccinka shine imanin, ina mai tabbatar muku in kukayi haka har lahira kun samu rabo, in kuma ku ka d'auki akasin haka ku ka d'auki son zuciya kuka aikata sab'on Allah ta dalilin jarrabawar rayuwa ina mai tabbatar muku bazaku ji dad'i ba, dan bazaku samu yanda kukeso d'in ba kuma a lahira kasonka mai girma na azaba musamman in ka had'a da shirka wurin biyan buk'ata, duk abinda ya sameku a rayuwa kuyi addu'a, Allah baya bacci kuma baya manta bawansa, in kunga bai ansa muku addu'a ba kada ku hasala, Allah yafi ku sanin abinda ku baku sani ba, kuma shi yasan abinda ya dace daku ba wanda kuka tsarawa kanku ba".


Numfasawa tayi tana mai kallon yaran nata da ke kallonta jiki a mace suna mai sauraron kowani kalmar da ke fita bakinta, in da sabo sun saba da nasihar mama sai dai na yau suna jinsa da wani amo na daban, sigar nasihar ya banbanta da wanda ta saba yi musu.


Murmushin k'arfin hali tayi ta d'aura hannunta akan Mufeedah, idanunta na yalk'i dan hawayen da ke taruwa a kwarmin idanunta.

Sunanta ta k'ira a hankali tana mai son b'oye sirrin zuciyarta.


"Kina sane da cewa Fahad yaje wurin Abban Damaturu ya nemi aurenki an bashi?".

Kai Mufeedah ta iya kad'awa alamar eh dan bazata iya amsa ta ba, muryar mama a yanzu ya tabbatar mata akwai matsala babba ma kuwa.


"Bikinku insha Allah da zarar kin kammala jarrabawarki na makaranta kaman yanda Abbanku suka tsara". 

Murmushin da bai wuce labb'anta ba Mufeedah tayi ta sauk'ar da kanta k'asa dan gujewa idanun Mama.


"Aisha!".

Ta furta sunan da raunanniyar muryarta, bata iya amsawa ba, hawaye fal ya cika idanunta tana kallon mahaifiyarta da tuni ta kashe mata dukkan na'urar da ke aiki jikinta.


"Kina sane da cewa iyayen Elmansoor sun zo gidan nan yau?" Kai ta gyad'a cikin hanzari cike da son jin k'arashen maganar, ta tabbata ba lafiya ba.


Shiru Mama tayi tana mai had'e kalmominta tana warwarewa.

"Mahaifinki bai yadda da aurenku ba Aisha, yace a sanar dake ki fito da wani mijin amma banda Elmansoor".


A firgice Mufeedah ta d'ago idanunta tana kallon Mama dan tabbatar da zancen da suka doki kunnuwanta. Shiru ne ya ratsa d'akin na 'yan sakanni, Aisha da ta kasa tantance meh kunnenta yaji ta kasa tab'uka komai, hawaye mai zafi ne ya biyo kuncinta, idanunta na bisa fuskar mahaifiyarta da ta zame mata kamar hoto.


Mama bata iya cewa uffan ba ta fice daga d'akin hawaye na neman hanyar fita daga idanunta. Mufeedah tuni ta fashe da kuka mai tsanani tana mai jin zafi a k'albinta, ji take bata da wani farinciki a rayuwarta, in Aisha ta rasa nata farincikin bata tunanin ita zata iya samun nata.


Aisha kallon k'ofar d'akin da mama ta fita take tana mai jin kukan Mufeedah a tsakiyar kwanyarta kamar ta fasa ihu, so take ta tashi daga wannan mummunar mafarkin da ta tabbata zata yi sati bata manta shi ba. 


Maganar mama take maimaitawa a kanta dan ta fahimci inda maganar ya dosa, bata gama tsaida hankalinta ba Mufeedah ta rik'ota zuwa jikinta ta k'ank'ame tana furta "innalillahi wa inna ilaihi raji'un".


Kamar tab'ab'biya ta tsaya kallon Mufeedah da ke nanata kalmomin. Kukan da ta ga Mufeedah na yi yasa ta tunani ko dai Mufeedah aka raba da Fahad ba ita ba, gani tayi kukan nata yayi yawa. Lumshe idanunta tayi tana mai jin rad'ad'i a zuciyarta da dukkan sassan jikinta.

A hankali ta furta "innalillahi wa inna ilaihi raji'un".


*********


Washe gari:-


Kaman yanda tayi tsammanin ganinsu cikin damuwa haka ta iskesu kowa da tunanin da yakeyi, fuskokinsu ya canja launi ya kumbura dan kukan da suka sha a daren jiya.


"Baku fito breakfast ba, kunsan dai bana son hakan ko?".

Mufeedah ce ta iya d'ago rinannun idonta wasu hawayen na taruwa a idanunta tana kallon mama da ta shigo d'akin nasu a karo na biyu a safiyar yau.


Wurinsu mama ta isa ta zauna a tsakiyarsu tana mai jin tausayinsu dukka, janyosu tayi jikinta tana k'ok'arin kokuwa da hawayen da ke neman fitowa. 


Kuka Aisha ta fashe dashi mai shiga rai, ita kanta bata d'auka wasu hawaye zasu iya fitowa ba a yau dan tayi kuka a daren jiya kamar zata shid'e. 


Mama bata iya cewa komai ba sai hawayenta da ke sintiri saman kuncinta hannayenta na shafa bayansu alamar rarrashi. 


"Meh yasa Abba zaiyi haka Mama, Elmansoor na da wani hali ne wanda mu basu sani ba? Mama yakamata ku sanar da ita dalilin yin hakan wata k'ila zuciyarta ya iya karb'an wannan hukuncin". Cikin muryar kuka Mufeedah tayi maganar.


"Hak'uri zata yi, bai nemi ta san dalilinsa ba da ya sanar da ita tun kafin ku tambaya".

"Mama, bazan iya auren Fahad ba, indai kuka guji Elmansoor toh yakamata in guji Fahad, dan abokai ne na kusa, duk halinsu d'aya ne, bazan aureshi ba na hak'ura".


"Kul Mufeedah, wa yace miki hakan? Munyi binciki akansa, sai da muka tabbatar da halinsa sannan muka turashi gun abbanki, a ganinki zamu zab'a miki wanda zai cutar dake ko bai dace dake ba".


Bata iya sake magana ba, tunani ne fal ranta, ta yanke nata shawarar, bazata auri Fahad ba kaman yanda aka hana Aisha Elmansoor, abunda suka gujewa Elmansoor dominsa ta tabbata Fahad na dashi, fitowa ne kawai bai yi ba.


Aisha da take sauraronsu ji tayi wani abu ya tokare mata a ma'kogoro, kamar tayi ta kwala ihu takeji ko zata samu sa'ida amma ba daman yin haka, tunaninta duk ya toshe, kwanyarta a dagule ga matsanancin ciwon kai da yake son zautar da ita.


Rabuwa zata yi da Elmansoor kenan bayan gwagwarmayar da tasha akansa? Ko dai shine yace bai sonta? Amma taya zai ce baya sonta bayan ya turo iyayensa? Bazai tab'a cewa bai sonta ba ma in tayi la'akari da maganan da sukayi kwanaki biyu da suka wuce da yaga missed calls nata a wayarsa.


"Pretty" ya furta a karo na biyu bayan ya k'irata.

"Uhum!"

"I'm sorry, naga missed calls naki bansan zaki kirani ba na bar wayar a mota".


"Wai haka in munyi auren aikinka zai hanani magana dakai? Tun safe nake kiranka, after 3 sannan kake kirana".


"I'm sorry nace, duk da kinsan haka bazai faru ba in munyi aure, ni auren nake jira ma kin sani".

"Kamar ya, ban gane ba".

"I just cant wait to have you as mine, Aisha i love you so much, bana son ki rabu dani, i cant live without you, ai bazaki barni ba koh? Nima bazan tab'a barinki ba no matter what happens".


Hawaye mai zafi ne ya zubo mata ta lumshe ido tana mai tuna wannan hirar nasu mai dad'in gaske, zata iya sa wannan ranan cikin ranaku masu dad'i a rayuwarta, dan bata tab'a jin magana irin haka daga wurin Elmansoor ba.


K'arar wayarta ya dawo da ita hayyacinta, idanu suka zuba mata dan ta d'auki wayar, bata yi niyyar dubawa ba dan tasan bazai wuce Elmansoor ba, yak'i daina k'iranta tun daren jiya, bazata iya magana dashi ba, bazata iya sanar dashi komai ba, bazata so jin muryarsa cikin bak'in ciki ba, bazata iya d'aukan hakan ba, tana matuk'ar sonshi, meh yasa Abba bai duba wannan soyayyar ba ya yanke wannan d'anyen hukuncin akansu?


Duk tunaninta da abubuwan da ta k'issima akansa ya tashi a banza? Duk wahalarta na son canja shi a banza wata ce zata samu moriyar hakan da tayi? Taya zata iya d'aukan hakan a rayuwarta? Taya zata iya ciresa a zuciyarta ta bi umarnin mahaifinta? Taya zata iya mantawa da Elmansoor habibynta?


Kuka mai sauti ke fitowa ta kasa d'aukan wayar, idanunta ta lumshe tana mai jin duniyarta yazo k'arshe, bazata iya sake rayuwa ba tare da Elmansoor ba, ta gina sauran rayuwarta dashi, bazata iya ba.


~~~~~~~


Wa ya yi kuka😫 nidai na tab'a amma kad'an.


Banson rabuwa da masoyi.


Ya labarin Elmansoor wai? Ya yake ciki?


Fahad? Meh laifinsa da Mufeedah zata kopsa mana?


MENENE DALILIN ABBA NA HANA MASOYA SAMUN JUNANSU? Nasan shine babban tambayan, sai dai amsar na gaba, bazan iya amsaku ba sai Abba yayi niyyar sanar daku.


Muje a hankali komai zai warware


Nagode sosai 


Nayi dare i knw, banson inyi disappointing naku na tsaya typing 😒

I tried ehhn???


Danna wannan tauraron insan ban hana kaina bacci a banza ba.

Comment please 


MaryamerhAbdul


Zagaye d'akin yake yi hannunsa hard'e ta bayansa, idanunsa ya fad'a damuwa bayyane a fuskarsa. Zama yayi a karo na uku a safiyar yau da ya kasa tab'uka komai sai tunani da yakeyi. Nunfashi ya furzar ta bakinsa ya hard'e hannunsa wuri guda tare da ajiye kansa akai yana mai lumshe ido.


"Salamu alaikum".

Muryar Fahad ya doki kunnuwansa, can ciki ya amsa ba tare da ya d'ago ya kallesa ba. 


A gefensa ya samu wuri ya zauna da nasa damuwar bayyane a fuskarsa. 

"Wai har yanzu bata d'aga wayanka ba? Kwana uku Elmansoor ana abu d'aya? Ba Mufeedah ba bare Aishan".


"Naka fa da sauk'i an baka aurenta Fahad, amma ni raba mu Abbanta yake son yi, bansan ya zanyi ba, ta barni cikin damuwa bata fad'a min komai ba ina ta hasashe. Ya zata k'i magana dani? Meh nayi mata? Gaskiya na k'ure malejin hak'urinah Fahad, gidansu zanje, in yaso a hanani ganinta, amma na tabbatar maka sai naji abunda yake faruwa, in ma rabamu ake son yi ta sanar dani insan abunyi tun wuri kafin in rasa na yi".


"Alhamdulillah ka ceceni, muje kawai, nima na damu da rashin d'aga wayana da Mufeedah ke yi, shawarar da na yanke kenan ka hutar dani. Amma ka d'an gyara jikinka Elmansoor duk ka fige lokaci d'aya". 


Bai amsa shi ba ya mik'e ya shiga wanka wanda tun safiyar yau yaji baya ra'ayin yi, wankan bai ma zo kansa ba bare yayi niyya. A hanzarce ya gama ya fito dan zuwa wurin Aishar da take barazanar zautar dashi.


~~~~~~~~~~~


Sallama mai gadi ke dokawa cikin parlorn amma babu wanda ya amsa. Mintuna biyu da isowarsa parlorn bayan ya cire ran amsawar sallamarsa yaji hajiyarsa na amsawa daga d'akinta tana doso inda yake. Gaisuwa ya mik'a mata bayan ta fito.


"Bak'insu Aisha ne suka iso shine na shigo sanar musu".

"Okay, bari zan sanar dasu, ka shigar dasu parlon ne ko kuwa?"

"Eh sun shiga ciki Hajiya, ai bana barinsu a waje indai nasan bak'inku ne".


Cikin murmushi ta amsa masa sannan ta koma d'akin yaranta dan sanar dasu.


~~~~~~~~~~


"Bak'inku sun iso, nasan kunsan da zuwansu, ku kimtsa ku isa wurinsu, behave well. Kada ku ce zaku fita musu a haka kamar anyi muku mutuwa. Kun ma yi wanka kuwa tun safe?"


"Munyi". Mufeedah ta amsa a tak'aice tana turo baki, bata son fita wurin Fahad, meh zata ce masa? Bazai yu ta aureshi ba bayan bata san hak'ik'anin halayensa ba, ta tabbata halin Elmansoor babu kyau shiyasa Abba yake neman raba su.Powder ta d'auko ta shafa a fuskarta, rabonta da shafa shi tun ranar da taji mummunan sak'on Abba. Wurin Aisha ta isa ta mik'a mata dan ita ma ta shafa ko fuskar nata zai yi kyaun gani.


Babu alamun zata karb'a ta shafa dan ko kallonta bata yi ba. Dangwalawa tayi ta goga mata da kanta, ta d'auki lip balm ta shafa mata ita ma ta shafa a nata lab'b'an. Drawer ta bud'e wurin ma'adanar turarensu ta d'auko ta feshe jikinta sannan ta feshe Aisha, ta d'auko mayafin da zai shiga da kayansu ta feshe da turaren ta mayar dashi ma'adanarsa.


"Mu tafi, ga mayafinki".

Bata iya d'aga ido ta kalleta ba, hawaye ne ya rufe mata ganinta, taya zata iya fita wurinsa ta sanar dashi wannan sak'o? 


Ajiye mata mayafin tayi a cinyarta tayi hanyar waje, a tunaninta Aisha zata biyota in taga hakan, sai dai tayi mamakin waigowa ta ga Aisha zaune a mazauninta ko motsi bata yi ba bare ta yafa mayafin.


Wurinta ta koma tana mai jin zafi a zuciyarta, yanzu ba lokacin da zata tsaya tana rarrashinta bane, kamata yayi su gama da bak'insu sannan su dawo gyara nasu rayuwar. 


Kafad'arta ta dafa tana kallon yanda hawaye ke zarya a fuskar Aisha, zuciyarta tuni ya sosu ganinta cikin wannan hali.


"Ba kuka zakiyi ba Aisha, this is the right time da zaki sanar dashi komai, in kika zauna a haka babu abunda zai tafi yanda kikeso ko yanda Abba yakeso. Ki nemo nutsuwarki ki isa garesa, hakan yafi dacewa a yanzu".


Hannunta tayi anfani ta goge mata hawayen fuskarta.

"Please ki daure". Bata iya amsata ba ta mik'e tana mai goge hawayen fuskarta. 


Mufeedah ke gaba Aisha na biye da ita a baya, babu wanda yayi magana cikinsu har suka isa parlon inda suke kyautata zaton bak'in nasu na ciki.


Can ciki ta furta sallamar, bakin Aisha ko motsi bai iya yi ba zuciyarta na bada sautin da zata iya cewa bata tab'a ji ba karaf rayuwarta. Dukkansu suka amsa sallamar, hakan ya basu damar shigowa d'aya na bin bayan d'aya kansu a k'asa kamar marasa gaskiya.


Kujerar bakin k'ofa Aisha ta samu ta nok'e ba tare da ta d'ago fuskarta ta kalli inda suke zaune ba, ji take bazata iya k'arasawa inda suke ba, k'afafunta bazasu iya d'aukanta ba. Mufeedah wurin Fahad ta isa ta zauna gefensa, ji take ita ma zuciyarta na bugu, bata tunanin zata iya canja ra'ayinta akan k'udurinta.


Dogon nunfashi Fahad ya sauk'e ya shafe fuskarsa da hannunsa.

"Ina wuninku" ya furta musu a k'ufule dan da alamu sun manta yanda ake gaisuwa.


"Sorry".

Mufeedah tayi k'arfin halin furtawa.

"Ina wuninku" ta cigaba ba tare da ta jira amsar d'aya daga cikinsu ba.


Babu wanda ya amsa gaisuwar kowa da abunda yake nuk'urk'usan zuciyarsa. 


"Malama Aisha, lafiya dai? Ko laifi mukayi ne ake purnishing namu haka?"

Fahad ne ya jefa tambayar b'angaren Aisha da tun shigowarta bata furta uffan ba, bata iya d'ago kanta ba bare su samu damar ganin yanayinta.


"Ba laifin komai". Cewar Mufeedah tana kallonsa.

"Zan iya d'auka a tsakaninki da Fahad babu komai, amma tabbas tsakanina da Aisha akwai matsala, babbar matsala ma kuwa".


Elmansoor bai jira amsar kowa daga cikinsu ba duk da yasan da wuya su tanka shi ya mik'e ya isa wurinta yana mai zama a kujerar da ke gefenta, idanunsa na kanta ya kasa d'aukewa, so yake ya kalli kwayar idanunta ko zai iya gano yanayin da take ciki, wata k'ila yasan inda matsalar yake ta kwayar idanunta.


"Pretty".

Ya furta a hankali ta yanda babu wanda zai iya sauraronsu.

"Please ki daina purnishing d'ina haka in laifi nayi, yayi min yawa bazan iya d'auka ba, please".


Shiru tayi bata iya masa magana ba, kukan da ke son cin k'arfinta take k'ok'arin yak'i dashi dan ya koma mazauninsa, bata son tada tarzomarta a wannan fadar, bazai iya jure ganinta hakan ba, kuma tabbas rabuwa ya zama dole a tsakaninsu.


Kallonta ya tsaya yi yaga alamar kuka take k'ok'arin hana kanta.

"Pretty, look at me, Elmansoor ne, your love, your baby".


Furucinsa yasa ta tuno da ranar da ta fara k'iransa da "my baby". Bata san lokacin da kukan da take ta dannewa ya fito ba, bakinta ta rufe da hannayenta had'e da ajiye kanta bisa cinyoyinta. Kuka mai shiga rai take yi mai sauti.


A tsorace Fahad ya dawo da hankalinsa garesu.

"Elmansoor meh kayi mata? Lafiya kuwa?"


"Ya salam!" Elmansoor ya furta yana mai lumshe ido, ji yake wani abu mai tsini na sokinsa a wani fanni na zuciyarsa da yafi ko ina jin rad'ad'i. Idanunsa tuni ya kad'a tashin hankali da ru'dani k'arara ya bayyana a fuskarsa, jijiyoyin jikinsa sun bayyana ya rasa abunda ya dace yayi a wannan lokaci. 


Sautin kukanta ba k'aramin tada masa hankali yayi ba. "Ais... amm! Ya rabb" ya fara kame-kame yana neman kalmomin da ya dace yayi anfani dasu dan ta tsagaita kukan nata.


Tashi yayi tsaye cikin rashin sanin abun yi, ji yake kamar zaiyi hauka, kukan nata sai k'aruwa yakeyi yana dagula masa lissafi. A gabanta ya tsugunna yana kallonta, hawaye na barazanar zubowa a fuskarsa. 


"Na rok'eki, ki taimakeni ki ceci rayuwata ki sanar dani laifina Aisha, kina dagula min lissafi, kiyi hak'uri ki daina kukan nan ki sanar dani laifina, believe me I can't take all this, zuciyana zai iya bugawa cikin sa'o'i kad'an in kika cigaba da min hakan".


B'angaren Fahad ya jiyo sheshshek'a, yana da tabbacin Mufeedah ce ta shiga sahunta, sunan Allah kawai ya iya furtawa yayi zaman dirshan zufa na mai tsatsafo masa a goshinsa.


"Mufeedah kuyi magana mu san abinda yake faruwa, kun samu a ru'dani, ke kuka ita kuka, ya kukeson muyi muku".

Fahad ne yayi k'arfin hali had'a kalmominsa.


Cikin sauri Mufeedah ta iya furta kalaman da a ganinta zai yi saurin kai sak'onta garesu.

"Abba ya hana Elmansoor auren Aisha, kaga nima bazan iya aurenka ba Fahad".


Sheshshek'ar kukansu kawai ke tashi a d'akin, jinin jikin Elmansoor zai iya cewa ya d'auke a wannan lokacin dan baya tunanin yana nunfashi, ji yayi rayuwarsa ta koma cikin duhun da tun tasowarsa bai tab'a shiga irinta ba. 


A razane Fahad ya tsaya kallon Mufeedah da ke k'ok'arin share hawayen da ke kwaranya daga idanunta. Tuni nashi idanun ya sauya, ya rasa samun tambayar da ya dace ya yi.


"Meh kike cewa Mufeedah? why? Meh yasa Abba zai yi haka? Mufeedah meh yasa zakiyi min haka?".

Kad'a kai Mufeedah tayi alamar bata da amsar da zata iya basa a wannan lokaci.


Shiru yayi bai iya k'ara furta komai ba sai kallonta da yakeyi, meh matsalarta guda d'aya da take k'ok'arin b'ata masa duk wani shiri nasa, meh matsalarta da a kullum burinta ta bak'anta masa? Shin bai cancanci samun soyayyarta bane da a rayuwarta bazata iya nuna masa shi d'in ya kai ba? Lallai yau ya tabbata Mufeedah bata sonshi, a da in ya samu kansa da wannan tunanin yana k'aryata kansa dan baya son zuciyarsa ta bijiro masa da abunda zai b'ata masa jin dad'insa da farin cikinsa, sai gashi yau a idanunsa ya samu tabbacin hakan.


Shiru yayi ya kawar da kansa daga ganinta yana tunanin abunda ya dace ya yi ba tare da yayi nadama ba a nan gaba.


"so you're planning to leave me? Aisha? Dalilin kenan na k'in d'aukan wayana?".


Ganin bata da niyyar masa magana ya sa shi mik'ewa dan barin gidan, bazai iya d'aukan abunda yake faruwa ba a yau.


Cak ya tsaya jin hannunta mai taushi ya rik'e nasa, yawu mai d'aci ya had'iye yayi k'ok'arin mayar da hawayensa da ke barazanar zubowa.


Hannunsa da ta rik'e ta d'aura a fuskarta tana mai jin zuciyarta na k'una. Daga yau ba za ta sake ganin Elmansoor ba, bazata sake jin muryarsa ba, duk soyayyarta garesa ya tashi a banza tunda bazata tab'a samunsa ba.


Kukanta ya k'ara tsanani, hawayenta tuni ya gama wanke bayan hannunsa. Kasa cewa komai yayi dan kwakwalwarsa ta cushe, ji yayi ina ma Aisha halalinsa ne, tana buk'atarsa a wannan lokacin da bayi da hurumin kasancewa da ita, ya zai mata? Zuciyarsa bazata iya d'aukan yanayi irin wannan ba.


"Elmansoor don't try to leave me, ina cikin mawuyacin hali wanda bazan iya kwatanta maka ba, in ka juya min baya irin haka da wanne zanji?" Cikin muryarta da ya disashe ta iya furta hakan.


Hawayensa yaji akan kumatunsa, rad'ad'in da yake ji a zuciyarsa bazai iya misaltuwa ba. Juyowa yayi bayan yayi dabarar goge hawayensa.


"I promised to be with you for ever, ko kin manta? Zan dawo miki pretty, Elmansoor is yours, yours alone, banson kukan nan kina karya min zuciya in kinayi, let's be strong, ba'a tab'a samun abu meh kyau sai ansha wahala. Zan tafi in baki sararin yin duk yanda kikeso dan bazan iya ganinki haka ba Aisha, bazan iya jurewa ba".


B'angaren zuciyarsa ya d'aura hannunsa akai ya furta can ciki, muryarsa cike da rauni.

"A nan nake jin duk kukan nan da kikeyi, bana son in mutu ban samu Aisha ba, bana son in tafi ban samu damar kasancewa da farin cikina cikin inuwa guda ba, you mean everything to me, ina sonki fiye da yanda kike zato".


Cikin idanunta yake kallo ya furta wad'annan kalaman, ko da zai zama shine had'uwarsu na k'arshe a rayuwa dole ya tona mata asirin zuciyarsa, yana sonta fiye da duk wata d'iya mace a duniya, bazai iya rabuwa da ita ba, rayuwarsa dole sai da ita ciki.


***********


Soyayya dad'i tafi zuma dad'i. 😂

Wannan dai guba sunansa.


Oh ni Maryamu abu, lafiya dai? Anya zan iya k'arasa wannan fannin, kuka na son hanani rawan gaban hantsi. 


Kunji kalaman nasa? OMG I'm in love


Please comment on every line and

Vote 


Thank you so much 

Ina qaunarku yanda Elmansoor ke son Prettynsa.


Sunan da ya rad'a mata ma yafi sa ni jin dadi.


Mu cigaba da tafiya. 


Thank you


Aisha ta kasa furta komai dan mamakin furucinsa na yau, kukan nata tuni ya tsaya sai hawayen da ke sintiri a fuskarta, kallon juna suka tsaya yi kowa da abunda yake k'issimawa a ransa.


Numfashi ya sauk'e sannan ya daidaita tsayuwarsa, so yake kalaman da zai sanar da ita su shiga kwanyarta, dole ya nuna mata gaskiyarsa, kuma bazata gane gaskiyar nasa ba sai ta fuskarsa da ya tabbata a yau bazai iya b'oye sirrin ruhinsa ba.


"Pretty, kin dad'e kina cewa bana sonki, kin dad'e kina cewa bana kula da ke, ki bani dama wannan karon, na miki al'kawari bazan barki ba sai na isa inda bazan iya yin komai ba nan gaba, ina so in sameki Aisha, in na rasa ki nayi babban rashi. Ki sanar dani duk abunda Abbanki yace, halina ne ba kyau? Ko wani abu nayi wanda bai son surukinsa yayi a rayuwarsa? Ki sanar dani wallahi zan daina ko da kuwa hakan zai hanani abunda nafi so a rayuwa, nasan kaina duk wani abunda aka sanar masa na daga halina zan iya d'aukansa sharri ne, bana neman mata, bana shaye-shaye, ba d'an daba bane ni, na fa yi islamiya Aisha da girmana bare ace bani da ilimin addini ko bana sallah. Ki sanar dani laifina a garesa zan gyara amma dan Allah kada ki bari a rabamu, bazaki tab'a da na sanin aurena ba, zan miki duk abunda kikeso, zan baki soyayyata da duk wani abunda kowace mace ke buk'ata a gidan aurenta".


Idanunta ta sauk'e k'asa bayan ta gama sauraronsa, hannunta tayi anfani dashi wurin share hawayen fuskarta.

"Duk babu abunda ya sanar dani cikin maganar da ka jero min, umarni ya bani in rabu dakai ba tare da ya sanar dani dalilinsa ba".


"Kuma baki nemi ki sani ba? Kin yadda a raba mu kenan bazaki iya komai akai ba? Kin yadda ki rasa mutumin da kike ik'irarin kina so? Haba Aisha. Dan Allah kada ki min haka".


"Zan tambaya, in yaso sai in sanar dakai ko ta waya ne"

"Yauwa, kenan zaki na d'aukan wayana? Promise me ko meh zai faru bazaki daina d'aga wayana ba".

"InshaAllah"

"Promise?"

Shiru tayi kamar bazata amsa ba, ta d'ago ta kallesa sannan ta furta "promise".


~~~~~~~~~~~~


Aisha ke durk'ushe gefen Mama tana mai zubar da k'wallan da a yanzu ya zame mata abinci, tayi da safe, rana har ma da dare.


Waya Mama ta d'auko tayi danne-dannenta sannan ta sa a kunne.


Ba'a kai ga d'auka ba ta sauk'e wayar tasa a handsfree.


"Salamu alaikum" 

Muryar Abba ya karad'e kunnuwansu.


"Ina hanyar dawowa gida yanzu, lafiya ko?"

"Lafiya k'alau, bazan iya jiran dawowanka ba shiyasa na k'iraka, ni uwa ce, bazan iya ganin 'ya'yana cikin wannan halin ba".


"Meh kuma ya faru?"

"Gata nan, Aisha ce ta sani gaba, kukan nan ya isheni, dalilin hana ta Elmansoor take son ji, ka taimakeni ka raba ni da wannan matsalar, na gaji da jinsa".

Muryarta na rawa ta k'arasa maganar.


"Wai ba mun gama maganar nan ba? Bana son hakan fa, meh kukeson mayar dani? Ban isa ba ko meh?".


"Allah ya huci zuciyarka, amma zan so kayi magana da ita in ka dawo, dan ni bani da sauran kalaman da zan iya anfani dasu dan gyara wani abu".


Wayar ya kashe bai ce uffan ba. Hakan ba k'aramin d'aga hankalin Aisha yayi ba, kuka ta shiga yi kamar ranta zai fita.


~~~~~~~~~~


"Maganar nutsuwa zamuyi kuma inaso ya zama na k'arshe".

Abba ke rage muryar talabijin d'in da yake kallo bayan shigowar matarsa da yaransa biyu, Aisha da Mufeedah.


"Nasan kunsan abinda yasa na k'iraku, saboda haka zan shiga kai tsaye ba tare da b'ata lokaci ba. Kada kuyi tunanin na k'iraku saboda in sanar daku dalilina na hana auren Elmansoor da Aisha, dan babu wani dalili guda d'aya da zai sa in sanar daku. Wai shin bani da hurumin hana 'yata abunda naga bai dace da ita ba sai na fad'i dalili?"


Kallon Aisha yakeyi yayi tambayar. Kanta a k'asa tana wasa da carpet na d'akin.


"Shin bani da daman hana ki abu dole sai na fad'i dalili sannan zakiyi? Bani da wannan girman a wurinki?".

Idanunta ta d'ago tana kallonsa, bai kamata yayi mata irin wannan furucin ba, taya zata amsa shi bayan yasan amsar? Bata d'auka nacinta zai sa mahaifinta yayi wannan tunanin ba.


Kukan da takeyi ya hanata amsa shi. Mufeedah ce ta rik'e hannunta cikin nata dan ta tsagaita kukan.


"Aisha, umarni nake baki a yanzu, na raba ki da Elmansoor, bana son zamanki dashi, ki rabu dashi dan bazaki tab'a aurensa ba, dalilin haka yasa na kawo miki wanda yafi dacewa dake, wanda yafi kwanta min a rai sannan ina da tabbacin zai kula dake ko da bayan bani nan, mutumin da ko ba komai hankalina zai kwanta dashi bazanyi tunani mara kyau game da tarbiyyar 'yata ko jikokina ba".


"Abban Aisha..."


Hannu ya d'aga ya dakatar da mama da take son katsesa daga zancensa, idanunsa na kan Aisha da ta kasa tab'uka komai. 

"Nu'aim, na zab'a miki Nu'aim matsayin mijinki, kuma za'a had'a auren tare da na Mufeedah. Ku tashi ku bani wuri".


"Abba Nu'aim? Yaya Nu'aim kake nufi?"

Muryarta na rawa Mufeedah tayi tambayar idanunta yayi ja hawaye na bin kuncinta.


Numfashi Abba ya furzar ya kawar da kansa.

"Nu'aim dai da kuka sani, shi na zab'a mata matsayin miji, dan bazan tab'a iya aura mata Elmansoor ba".

"Abba..."

Hannu ya d'aga mata, bata iya furta komai ba, yanayin fuskarsa ya nuna mata b'acin ransa.


"Ku fice, na gama maganana, bana son sake jin maganar wannan yaron a gidan nan, yau ya zama magana ta k'arshe da zamuyi akansa, mun rufe babinsa kema kin rufe Aisha".


Fuskarsa bai bawa Mufeedah damar furta kalmanta ba, hannun Aisha ta rik'e suka fita daga d'akin kuka yaci k'arfinsu.


K'arar muryar talabijin nasa ya k'ara bayan fitarsu. 

"Abban Aisha baka gama dani ba, ban gane nufinka ba. Dalili d'aya da nake son sa wa kaina akan zancen nan na nemesa na rasa, ya kake neman d'auko abunda ya wuce ka ajiyesa gaba kana anfani dashi akan 'yarka? Meh yasa kake son nuna min matsayina da baka tab'a nuna min ba iya shekarun da na zauna dakai? Meh yasa kake k'ona raina ta wannan hanyar?"


"Asma'u kina d'aukan maganar ta wani siga daban".

"Ni bance kana d'aukan maganar ta wani siga daban ba kai zaka ce min haka? Kai kasan irin halin da ka jefa gidanka cikin lokaci k'ank'ani? Meh yasa kake haka Abban Aisha".


Kuka ta fashe masa dashi, bazata iya jurewa ba, zuciyarta na tafasa, abubuwan da mijinta yakeyi a wannan karon yana bak'anta ranta.


"Ummu Aishah! Ki daina kashe min jiki akan wannan Elmansoor d'in. Baki san ya nakeji ba a raina, baki san yanda na rayu da wannan bak'in cikin ba tsawon rayuwata...".


"Tsawon rayuwarka? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Abban Aisha meh yasa baka tab'a sanar dani bana sauk'e maka hak'k'okinka da ke kaina ba? Meh yasa sai yau ne ranar da zaka sanar dani haka da kalmomi irin wannan?"


"God!!!"

Abba ya furta yana mai kad'a kansa jin yanda ta juya kalamansa.

"Zaki gane nufina wata k'ila nan gaba, ni dai bazan aurar da Aisha wa Elmansoor ba, that's final".

Tashi yayi ya fice ya barta wurin zaune tana mai zubar da hawaye. Bata tab'a d'auka gidanta zai iya tarwatsewa haka ba.


Tun da tayi aure ta d'aukarwa kanta alk'awarin bada duk wani gudunmawar da ya dace dan tsayar da gidanta, ta bar makarantarta da aikinta saboda kula da gidanta da mijinta. Iya saninta bata rage mijinta da komai ba, ashe hakan bazai k'areta da komai ba sai ma tab'arb'arewar gidanta akan idanunta? Ashe bata cika mace da zata iya kawar da bak'in cikin da ya wuce a rayuwarsa ba? Kenan duk kyautatawar da take masa bai sa ya manta da abunda ya samesa tun shekaru ashirin da ya gabata ba?


Kwanciya tayi a inda take tana mai cire abunda take ji a zuciyarta ta hanyar fashewa da kuka hawaye na malala a fuskarta. Sautin muryarta kawai ake ji a d'akin na tashi.


~~~~~~~~~~


Elmansoor na zaune a palor tare da momynsa suna kallo wayarsa yayi k'ara. Murmushi ne ya mamaye fuskarsa ganin sak'o daga Pretty.


Lokaci guda far'arsa ya d'auke, duniyarsa yayi duhu, ya furta kalmar "innalillahi wa inna ilaihi rajiun".


Hankalin Mommy tuni ya dawo kansa, a kid'ime ta taso ta matso wurinsa ganin yanayin da ya shiga.

"Wa ya rasu Elmansoor? Meh ya sameka?"


Bai iya furta komai ba sai rufe fuskarsa da yayi da tafin hannunsa. Wayarsa mommy ta d'auka ta d'aura idonta kan sak'on da d'an nata ya samu wanda ta tabbata shi ya tada masa hankali.


"Elmansoor I'm sorry, mu karb'i k'addararmu muyi gaba. Abba ya bani Nu'aim matsayin mijina, Allah ya baka wacce ta fini. Nagode, umarnin mahaifina nake cikawa".


Saman wayar ta duba dan ganin wanda ya turo sak'on. "Pretty" da ta gani ya tabbatar mata Aisha ce.


Hannunta ta d'aura akansa tana shafawa a hankali, rashin sanin kalmar da ya dace tayi anfani dashi dan sauk'o masa da nutsuwarsa yasa ta yin shiru had'e da lulawa duniyar tunani.


"Nayi tunanin hakan zai faru, amma ban d'auka Abdallah zai iya aurar da ita ga wani dan rabata da d'ana ba, ban san Abdallah da rik'o ba, ban sanshi da irin wannan zuciyar ba. Meh abun yi?".


********


Nu'aim ya faso fa, Abba ya kawo mana shi tsakanin Elmans & A'ish, shin aurensu zai yu?


Mommyn Elmansoor kamar ta san abu akan dalilin Abba, abun bai baku mamaki ba? 


addaummi an raba Elmansoor da Aisha, dama baki son zamansu☹️ Nu'aim yazo, wata k'ila ya dace da ra'ayinki😂


Comment please 

Labarin ne yazo da haka. A hankali komai zai warware mu isa inda muke buk'ata.


Nagode


MaryamerhAbdul


Agogon hannunsa ya duba k'irar Ebel.
"Mama zan makara fa kuma yau nake son dawowa".


Daga cikin kitchen ta amsa masa

"Zaka tafi baka ci komai bane Nu'aim? Dan kai fa na tashi tun safe kuma kace ko kunun nawa bazaka sha ba?"


"Mama mana, na girma fa. In na ji yunwa a hanya zan tsaya incu abinci. Kunun ma dan naki ne na tuna da dad'insa shiyasa na tsaya jira, kuma shima ashe baki gama ba".


Tashi yayi tsaye lokacin da ta fito daga kitchen d'in rik'e da mug a hannunta. Bakinta yak'i rufuwa hak'oranta farare sol suna shek'i.


Karb'a yayi a hannunta ya kurb'a ya lumshe ido. Murmushinta bai kauce ba tana kallon yanayinsa.


"Ba sai ka yaba ba Nu'aim, kullum cikin yaba kunun nan kake, dole in koyawa Aisha irinsa dan tana maka kullum".


Murmushi yayi ya k'ara kai kurb'a.

"Mama dole in yaba, yafi na kullum dad'i, madarar ya fito rad'au yau ba'a min rowanshi ba".


Dariya tayi shima ya taya ta.

"Zauna mana ka shanye, a tsayen zaka sha?"

Zama yayi bai amsata ba ya cigaba da shan kununsa.


Idanunta ne ya sauk'a akan k'afarsa da ke sanye da takalminsa bak'i k'irar dr. Scholl's
"Haba Nu'aim, sai ka b'ata min carpet d'in sannan zaka tafi? Jiya fa aka kawo daga wurin wanki".

"Mama mana, yau fa kince inyi komai ba komai, bare ma k'asan ba komai, sawa biyu kacal na masa kuma duk ban taka wurin k'asa ba".


Tashi yayi rik'e da kofin a hannunsa.

"K'arfe bakwai ya yi, zan tafi yanzu"

Karb'an kofin tayi tana mai yi masa murmushi

"Zan kai kitchen kada ka damu. Sa hulanka in ga yanda zaka fito".


Hular da ke ajiye akan kujera ya d'auka yasa a kansa, sosai ya shiga da launin shud'in kayansa. Hawaye ta ji ya taru a idanunta tana kallon zuk'ek'en d'anta.


Kyakkyawa ne son kowa k'in wanda ya rasa. Kalar fatarsa irin na Aisha kasancewarsu dangin juna. 


Matsowa yayi daf ita ya rungumeta

"Mama mana, meh na kukan kuma?"

"Na farin ciki ne Nu'aim, Allah yayi muku albarka da kuka karb'i tayinmu, Allah ya kai mu bikin. In kaje ka bi ta a hankali, kasan yarinya ce, lallabata zakayi kaji?".


"Zanyi yanda kika ce Mama, ki kula min da kanki, zan k'iraki da zarar na isa, and please kada ki bar yaran nan su fita yau dan bana nan". A marairaice yayi maganar dan ta amince da rok'onsa.


Gefen fuskarsa ta shafa tana murmushi.

"Allah ya kiyaye hanya, babu inda zasu je sai islamiya, ko ka manta akwai islamiya ranar lahadi?"


"Haka fa, na tafi toh, komai dare a yau zan dawo dan aikin gobe mama, kice wa Uncle Abdallah kada ya hanani dawowa yau, bazan iya zaman Abuja ba".


"Ka tafi d'in dai, Allah ya kiyaye hanya".

Har wurin motarsa ta rakasa ya shiga tana mai d'aga masa hannu har ya bar harabar gidan.


~~~~~~~~~~~~~


"Gani kusa da gida, wurinka nake son zuwa ka k'irani".

"Ina jiranka, sai ka iso".


Minti sha-biyar da katse wayar Fahad ya shigo d'akin had'e da sallama, Elmansoor idonsa ya bud'e ya kalli Fahad ya amsa can ciki.


"Nasan hakan zan sameka shiyasa nazo kafin in wuce kai sak'on Amma".

Zama yayi a gefensa yana mai furzar iska ta bakinsa. 

"Ya zaku kashe kanku akan matsala irin wannan?".

"Kashe kai? Fahad aure za ayi wa Aisha, ya kakeson inji? Tana sona ina sonta ya za'a rabamu? Meh dalilinsa?".


"Elmansoor a ganina wannan tsakaninsa da 'yarsa ne, tsakaninsa da iyayenka yace zai nemesu, ka bari ya nemesu sannan muji komai ba wai ka tada hankalinka ba, kayi addu'a insha Allah komai zai dawo yanda kakeso".


Kad'a kai yayi yana mai juya maganar nasa a kwanyarsa.

"Tare fa za'a yi muku aure, kana ganin wasa yake akan maganar had'a ta da Nu'aim ko meh?".


"Wait, aurena da Mufeedah? Wai haka yace? Wa yace muku zan auri Mufeedah?".

Kallonsa Elmansoor yayi jin furucinsa.


"Ban gane ba, an baka aurenta, dan tace bazata aureka ba ai ba ita ke da kanta ba".

"Auren dole za'a mata kenan? Hmm, lallai Elmansoor, ni na fasa auren Mufeedah ko meh zai faru, bata sona, kunyar Aisha take ji ta karb'i tayin soyayyana".


"Fahad..."

"A'a kada ka fara, ni da nake tare da Mufeedah nasan meh yasa nace maka haka. Tunda nake da Mufeedah bata tab'a nuna min muhimmancina a wurinta ba, abu kad'an zata nuna min zata iya rayuwa babu ni, ni ke damuwa da ita ko meh zai sameni bata damu ba muddin ta samu abunda yake ranta. Kai tsaye zata nuna min ban kai ba, taya zan aureta a hakan? Taya zan auri mace bata sona? Ya mace zata nunawa namiji ya zauna ko ya tafi duk daya ne a wurinta? A hakan hankalina zai kwanta da ita? A hakan zan yadda da ita in bata ragamar komai nawa? Haba Elmansoor, tunda tayi wannan furucin har yau ban k'irata ba, meh ya kamata ta yi? Ta k'irani ko? Toh bata yi ba, ita meh zuciya? Inyi fushi ko in sauk'o bai dameta ba? Ta b'ata min rai bata iya bani hak'uri ba, ita wai mace dole in bita? Ace bana mata yanda take so, amma ina mata komai dan kawai a zauna lafiya, bata ganin hakan, abu kad'an sai ta kawo kalmar rabuwa tsakaninmu? A hakan zamuyi aure in ka b'ata ran Aisha sai tace mu rabu? Rayuwarku daban namu daban, i can understand in tace min in bata lokaci ko a d'aga sa ranar har komai ya daidaita, amma mu rabu? This is not the first time da take min hakan, am tired, ta nemi mu rabu kuma na karb'i hakan d'ari bisa d'ari".


"Baza'a yi haka ba Fahad, ya zaka had'a mana abu biyu a kanmu lokaci guda? Wanne zamuyi tackling? Naka ko nawa?"


"Naka mana"

Ya furta kai tsaye yana kallonsa

"Ka daina wahalar da kanka, Mufeedah da ni babu wani alak'an da ya rage tsakaninmu".


Shiru Elmansoor yayi yana mai jin kansa na juyawa.


"K'ira min Mufeedah da wayanka".

"Bazan k'ira ba".

"Malam, ba maganarka zan mata ba, da Aisha nakeson magana dan wayanta baya shiga".


Dariyar takaici yayi

"Kada ka mayar dani yaro mana Elmansoor, bazan baka ba".


"Inason inji ya Aisha take, idan nasan ya take zan samu k'warin gwiwar gyara komai, tsakaninka da Mufeedah sannan tsakanina da mahaifinta. Yanzu duk tunanina ya toshe ba abunda zan iya yi, ta kashe wayanta haka kawai? Ta ina zamu samu mafita?".


"Zan k'irata, amma sai ka min alk'awari bazaka mata maganana ba, in tana da hankali ita da kanta zata yi tunanin abunda ya dace, amma indai bata yi ba, am sorry to say dama ba matata ba ce".


"Fahad...."

"In bazaka yi alk'awari ba bazan k'irata ba, simple".

"Okay, na yadda bazan mata maganarka ba, amma kasan yau ne kawai nayi alk'awari? Dan bazan iya gani a dalilina kana rasa abubuwa masu muhimmanci a rayuwarka ba".


Bai amsa shi ba ya ciro wayarsa daga aljihu ya k'irata.


Baice uffan ba lokacin da ta d'auka ya mik'awa Elmansoor.

"Hello"

"Matar abokina" Cewar Elmansoor bayan ya d'aura wayar a kunnensa.


Murmushi tayi sannan ta amsa shi. Aisha ya tambaya ya rok'i ta bata wayar ba tare da ta sanar da ita Elmansoor ke kan layi ba."Pretty haka mukayi dake? Kin fa yi alk'awarin zama dani, kinyi alk'awari bazaki daina kulani ba, yanzu kashe wayanki ma kika yi gaba d'aya dan kin daina sona koh? Meh yasa kikeson purnishing d'ina? Ke in baki zauna dani ba taya zan fuskanci wannan matsalar da ta tunkaro mu har in samu nasarar aurenki?"


Maganar da ya jero mata kenan lokacin da ya ji muryarta cikin wayar. Bata iya amsa shi ba sai hawaye da ke sintiri a fuskarta.


Jan majina tayi sannan ta gyara muryarta dan ta samu damar amsa shi.

"Babu abunda zamu iya yi ne Elmansoor, mu hak'ura da juna kamar yanda na fad'a maka, umarni ne daga gun Abbanah, bai fad'a min dalili ba amma ya tabbatar min rabuwa da kai shine farincikinsa, Ni bazan iya k'in bin umarninsa ba, yayi min komai a rayuwa, na tabbata yana da dalili mai k'arfi kuma na karb'i zab'insa, maganar da nakeyi dakai yanzu ma ina jiran isowarsa a yau. Ka karb'i naka k'addarar kamar yanda na karb'i nawa".


"Aisha kinsan meh kike cewa? Kinsan bak'in cikin da nake ciki yafi wanda Najwa ta sabbaba min shi a baya? Aisha ki..."


"Elmansoor ka gane mana, ba laifina bane, rayuwar da Najwa tayi dakai daban da wanda ni nayi dakai, bansan meh Najwa tayi maka ba amma ni nasan ban cutar dakai ba, umarnin mahaifina kawai nake bi. Sai anjima".


Bata saurari ansarshi ba ta kashe wayar.


~~~~~~~~


"Mufeedah bana so, kada ki sake bani waya dan inyi magana da Elmansoor, kinsan meh yake faruwa dani, meh yasa kikeson k'ara min bak'in ciki akan wanda nake ciki?"


Kuka takeyi da iya k'arfinta. Akan gado ta kwanta had'e da lumshe idonta hawaye masu zafi na sauk'owa, babu abinda take tunawa sai rayuwar da zata cigaba ba tare da Elmansoor ba, meh yasa Abba zai mata haka? Meh yasa rayuwa ta juya mata baya?


"Inaga mutuwa kawai zanyi dan yanda nakejin zuciyata kaman ya fito waje cike da tashin hankali". Bata d'auka kalamanta sun fito daga gurbin da take tunanin a nan tayi wannan tunani ba ma'ana zuciyarta.


Mufeedah da take zaune gefenta a razane take kallonta.

"Kina da hankali kuwa? Kinsan meh kike cewa? Haba Aisha, ke fa musulma ce wacce tasan k'addara, ki karb'esa da hannu biyu zaki samu ribar hakan". 


Idanunta ta bud'e da yayi jawur tana kallon Mufeedah. Ta kasa ce mata komai, ji take kaman an d'aura mata dutse akan k'irjinta, wannan bala'i da meh yayi kama?


"Mufeedah zo ki kai wa Yayanku ruwa, ya iso yana parlor".


Muryar Mama suka ji daga bakin k'ofa, da hanzari Aisha ta goge hawayen fuskarta ta mik'e ta shiga bayi dan gyara fuskarta gudun kada mahaifiyarta ta gane ta sha kuka, bazata so hakan ba, bazata so zama silar b'ata zumuncin da ke tsakaninsu ba, zata karb'i Nu'aim kamar yanda ta karb'i Elmansoor, tabbas zai yi wuya ta so shi amma hakan ba shi zai hanata zama dashi tare da sauk'e duk nauyin miji da yake kan matarsa ba.


~~~~~~~~~


"Kunyana kuma kika fara Aisha? Tun shigowarki nan kike wani nok'ewa, nine baki sani ba ko dai kawai kunyana ya taso miki tunda kika ji sauyawar alak'armu daga 'yan uwa zuwa ma'aurata?"


Cikin murmushi yayi mata maganar, tun bayan kawo masa ruwa da akayi ta shigo inda yake a takure, bayan gaishesa da tayi bata iya samun damar yi masa dogon surutu ba, shi ke ta sak'a da warwararsa.


"Um-um, ba fa haka bane Ya Nu'aim".

"Ohhh!!! Har yanzu Ya Nu'aim? Mun gama maganar wannan sunan tun jiya, ki k'irani da sunana in bazaki iya canja min suna ba, masoya ai da sunan soyayya suke k'iran junansu. So kike in koma wurin Mama ina bata labarin har yanzu kin kasa sakewa da ni?".


Ji tayi wani malulu ya mak'ale mata a wuya, wannan wani irin mutum ne? Dole ta lalumo murmushi ta d'aura a fuskarta. Kallonsa tayi ta kawar da kai ganin idanunsa akanta.


Jinta take a takure, tunda ta shigo ta lura idanunsa bai bar kanta ba, yana iya k'ok'arinsa dan jawo hankalinta garesa, sai dai ita baya gabanta, hankalinta da kwanyarta baya tare dashi. Damuwa da tunani duk ya cikata.


"Aisha fad'a min matsalarki".

Ta ji muryarsa daf ita, wanda a saninta yana zaune ne a kujerar da ke fuskantarta.


Idanunta ta d'aga ta kallesa, a gefenta yake zaune a yanzu yana kallonta had'e da karantar yanayin fuskarta. Bata furta komai ba ya k'ara da cewa.


"Zanyi matuk'ar farin ciki idan kika zauna dani ba tare da kin b'oye min matsalarki ba, ina son mu gina rayuwarmu akan gaskiya, soyayya, tausayi da jin kai, ina son ki fahinceni kamar yanda nima nakeson fahimtarki. Bazan iya cewa kai tsaye ina sonki ba, amma tunda Mama ta kawo min zancenki kwanaki biyu da suka wuce na nemi ganinki, kuma hakan bai k'ara min komai ba sai ma bani daman ganin Aisha a matsayin wacce zata zame min uwar yarana ba wai k'anwa a gareni ba".


"Aisha" ya k'ira sunanta yana mai d'ago fuskarta da hannunsa.


"Meh yasa nake ganin baki amshe ni ba? Meh yasa nake ganin baki karb'i tayin iyayenmu ba? Ban miki bane? Bani da qualities d'in da kike nema a wurin mijin da kikeso? Ko dan na dameki da surutu tun isowana bayan ba hakan kika sanni ba? Am sorry, but ina son ki sanni a yanda nake ba wai a yanda nake mayar da kaina wurin k'annena ba, you are different Aisha tunda kika samu matsayin zama wacce zan aura, ki bamu lokaci mu fahimci juna ba wai kina ignoring d'ina haka ba, am here for you in akwai matsalar da ni ban sani ba, trust me, i can help".


*************


Ya kuka ga Nu'aim namu?

Anya ba shi yafi dacewa da Aisha ba?


Mu dai je zuwa mu gani 


Comment

Vote 

And share


MaryamerhAbdul


"Zanyi farinciki idan ka daina bincike akan b'oyayyar bayanin cikin zuciyata, tunda nak'i sanar dakai a ganina a barsa kawai, idan zaka iya zama dani kuma ka aureni a hakan bismillah, nidai nasan ban koreka ba, ban k'ika ba kuma ban furta mummunan kalma gareka da zai b'ata ranka har ya kai ga b'ata ran mahaifina ba, kayi min uzuri, wata k'ila in sauya a nan gaba wata k'ila kuwa har abada bazan sauya ba. Shawarata a gareka shine, ka koyi zama da wacce kake ikirarin uwa ga 'ya'yanka".


"Idan na gane nufinki kenan, baki karb'eni ba sai don biyayya?"


Shiru tayi ta kawar da kai, duk wani kalma da yake furtawa yana soka ranta, shin ya zata fassara masa yanda take ji a yanzu? Ya zata nuna masa yanda zuciyarta ke bak'antuwa in ta tuna wani ne zai maye gurbin Elmansoor? A yau da safe ta d'auka zata iya zama da Nu'aim tunda shi ne zab'in mahaifinta, amma ya akayi a yanzu ta kasa d'aukan hakan? Ba wai Nu'aim bai mata bane, ba wai bai dace da soyayyarta ba, son nan dai guda d'aya shine take yiwa Elmansoor ba Nu'aim ba, maganganun bakinsa bai sata komai ba sai jin haushinsa da bak'in ciki.


Gyarar murya yayi ya gyara zamansa hannunsa hard'e da juna.

"Aisha kinsan cewa kamar yanda aka baki ni haka kwatsam nima aka nemi inzo wurinki? Kinsan da cewa na d'aukeki k'anwa a gareni tun tasowarmu? Ki yarda dani, baki san sirrin da ke raina ba, ki sanar dani damuwarki, zan miki abunda kikeso, kada kiyi tunanin zaki b'ata raina, believe me i will understand kuma zan sanar dake duk abunda yake raina dan mu samu sauk'i mu samu maslaha a tsakaninmu".


Zuciyarta ya murd'e, hawayenta suka samu damar sauk'owa saman kuncinta. Shin ta yadda da kalamansa ta sanar dashi bata sonshi? Ta sanar dashi auren dole ake son yi mata? Toh meh zai iya yi in ta sanar dashi? In yana sonta fa ya zai ji in ta sanar dashi matsalarta?


Muryarsa ne ya dawo da ita.

"Baki yadda dani ba?"

Kallonta yakeyi ya furta kalaman, zuciyarsa a yanzu ya karaya da yanayinta, ya kasa tantance abunda yake damun Aisha.


"Aisha look, ki bar maganar iyayenmu a gefe, ki bani matsayin da nake dashi tun da wato yayanki da zai yi miki duk abunda kikeso dan samar miki da farinciki. Nasan ni da ke babu soyayya tsakaninmu, sai dai yanayinki ya bani damar gano akwai matsalar da kikeson b'oye min, shin kinfi son ki sa kanki wahala akan ki sanar dani? Kika sani ko zan iya gyara komai?"


Kukan da ta fashe dashi had'e da barin parlon ya sa shi dakatawa had'e da kallonta har ta fice.


D'aki ta shiga da gudu ta kulle k'ofar dan kada wani ya shigo ya takurata. 


Wurin wayarta ta isa ta d'auko ta kunna, wanda rabon da ta kunnasa tun jiya bayan maganar da sukayi da Nu'aim da ya nemi ta kunna wayarta.


Layin Elmansoor ta lalumo ta danna masa k'ira. Shi kawai take son magana da a wannan lokacin, shi kad'ai take so shi kad'ai zata iya fad'awa damuwarta ta cire bak'in cikinta.


Wayar ta d'aura a kunne tana jin k'ararsa, zuciyarta bugu yake kukanta na tsananta. Har ya katse bai d'auka ba, bata yi k'asa a gwiwa ba ta sake k'ira, nan ma shiru bai d'auka ba. Tuni ta k'ara fashewa da kuka tana mai jin zuciyarta kamar zai tarwatse. 

"Shikenan tayi wa kanta ta kori masoyinta bayan bazata iya auren Nu'aim ba". Cewar zuciyarta


~~~~~~~~~


K'ofar d'akin Daddy ya kwankwasa a karo na biyu.

"Salamu alaikum"

Ya furta yanda wanda yake cikin d'akin zai jiyo sa.


 K'ofar daddy ya bud'e masa ya basa hanyar shigowa

"Shigo ciki ina ta amsawa baka ji na, lafiya dai ko?".


Zama daddy yayi a kujerarsa da ke d'akin yana mai kallon d'an nasa da ya samu wurin zama ya hard'e k'afadunsa a k'asa.


"Ehhmm, ina wuni?"

Murmushi mai sauti mahaifin nasa yayi 

"Sau nawa zamu gaisa yau Elmansoor? Menene ya faru? Go straight to the point, nine fa". Ya furta cikin farinciki.


"Ehmm, Dama daddy akan maganar nan ne, naji shiru ne baka ce baban nata ya nemeku ko bai nemeku ba, shine nace why not ku kuje ku tambayo ko lafiya?".


Cikin i'ina yayi maganar yana mai jin nauyin harshensa.


"Elmansoor!"

"Na'am Daddy"

"Bana tunanin yakamata mu tunkaresa, tunda yace zai neme mu mu jirasa d'in, in bai nememu ba bai kamata mu takurasu ba ko? Kowa yana da irin nasa hanyar na isar da sak'onsa".


Cikin rashin fahimtar maganarsa yake kallon Daddy. 


"Ka k'ara masa lokaci, in kaga bai neme mu ba ka tuntub'i 'yar nasa, na tabbata tana da amsar baka ba sai mun koma ba".

Mik'ewa yayi daga mazauninsa ya koma wurin ajiyar littafansa yana dubawa.


Da alamu ya gama magana tunda yayi hakan. Elmansoor na zaune a mazauninsa na 'yan mintuna sannan ya mik'e yaja k'afarsa ya bar d'akin. Bai d'auka haka mahaifinsa zai masa ba, iya saninsa da Daddy yana yin iya iyawarsa dan samar masa da farincikinsa, meh yasa wannan karon ya sauya? Meh yasa bai nuna damuwarsa kamar yanda ya nuna akan Najwa ba?


D'akinsa ya koma bayan fitarsa daga wurin mahaifinsa. Fahad ya samu kwance bisa gado yana danna wayarsa. 


"Ka dawo?"

Ya furta bayan ya zauna a gefensa.

"Eh, na shigo baka nan, yau ai ina nan, bazan rasa kayan sawa gobe wurinka ba".


"Da ka tafi fa, bana buk'atar surutunka, kada ku zautar dani dukkanku".

Kokuwa yake da k'ullutun da ya mak'ale a mak'ogoronsa yayi maganar. Kawar da kai yayi gefe ta yanda Fahad bazai gano yanayinsa ba.


"Elmansoor, na fahimceka, na fahimci damuwarka, abunda kake gudu shi yake k'ok'arin faruwa dakai. Meh yasa bazaka yi yak'i dashi ba? Ka daina sa wa a ranka bare ya dameka, duk abunda zai faru da bawa a rubuce yake, kasan da hakan".


Juyowa yayi ya fuskancesa idanunsa jawur.

"Bazaka gane ba Fahad, bazaka gane yanda nake ji ba, idan nace maka ina jin bak'in cikin da yafi na Najwa bazaka yadda ba. Dan wannan yafi komai zafi a duniya".


Kafad'arsa ya dafa sannan ya sauk'e numfashi.

"Ka d'auka a yanda ka d'auki na Najwa, ka d'auka Aisha barinka tayi kamar yanda Najwa tayi...".


Kallon da Elmansoor ya watsa masa yasa shi dakatawa.

"Kasan meh kake cewa kuwa? Ya zaka had'a Aisha da mace cruel irin Najwa? Ya zaka had'a Aisha mai gaskiya da mak'aryaciya irin Najwa? Kai kasan kuwa meh Najwa tayi min?".


"Ni ko nasan meh tayi maka, dan na rigaka sanin duk wani abunda Najwa ke yi, nayi k'okarin sanar dakai amma ka rufe ido ka bar ta tayi duk yanda taso da zuciyarka. Ni nayi jinyarka lokacin da Najwa ta barka bayan ta gama yi maka k'aryan da a ganinta zai wanketa a wurinka".


Kad'a kai yayi yana murmushin takaici.


"A hakan kake had'a Aishata da Najwa? A hakan Fahad? Najwa fa ina tare da ita shekaru uku, uku Fahad ba wai kwanaki ba Shekaru. Duk wani soyayyar duniya babu wanda ban nuna mata ba, kai shaida ne na nuna mata duk wani siyayyar da mace ke buk'ata wurin miji, kud'i, kulawa, k'auna, tausayi, kai komai ma. Da kaina na kawo ta wurin Mommy suka gaisa matsayin matar da zan aura, bayan kawo ta da nayi da kanta in ta kwana biyu zata zo gaisheta dan kawai ta sayeni ta sayi mahaifiyata, ina ma ace ni kad'ai ta yaudara, amma har da mahaifiyata? Ta nuna mana tana sona kamar yanda nakeyi".


"A lokacin da na nemi isa gidansu tace a'a, sai ta gama diplomanta. Nayi hak'uri kamar yanda ta nema ashe yarinyar nan duk zamana da ita tana da wanda zata aura? Ashe duk maganar da ake sanar dani akan akwai maganar wani akanta gaskiya ne bayan duk ranar da na tambayeta tana k'aryatawa? Fahad bayan naji zata yi aure yarinyar nan bata tashi sanar dani ba sai bayan wata d'aya duk ina kallonta ina sauraran ranar da zata sanar dani. Kuma ka tuna meh tace min? Wai auren dole za'a mata".


Murmushin takaici yayi hawaye na zuba a idanunsa.

"Saboda ta mayar dani yaro mara hankali? A hakan kake tunanin zan had'a Aisha da ita bayan halayyarsu da komai ya banbanta? Akanta na rabu da 'yan mata daban-daban dan rashin yarda da tsoron fad'awa tarkon mace..."


Lumshe idonsa yayi hawaye na sauk'o masa ya share da hannunsa yana mai jin rad'ad'i a ransa.


"Shine zaka ce in d'auka Aisha ma barina tayi? Taya ma zanyi hakan? Kamar diramar hausa? Tana sona ina sonta, ta dawo min da walwalana da farincikin da Najwa tayi sanadiyyar tafiyar dashi, in na barta ko na yadda aka raba mu ya zanyi? Ya zan fara sabon rayuwa Fahad? Najwa ita ce mace ta farko da na fara so a dukkan rayuwana kuma ta yaudareni ta barni ta sabbaba min HAWAYEN ZUCIYA, Aisha kuwa ita tayi k'ok'arin dawo min da dukkan farincikina duk da nasan na b'ata ranta kuma nayi mata abubuwa masu yawa marasa kyau".


"Elmansoor, hak'uri zakayi".


"Bazan iya hak'uri ba Fahad, tunda babu wanda yake son taimakona akan Aisha ni zan samu hanyar dawo da ita. A wannan karon ban samu dafawar kowa daga cikinku ba, bansan meh iyayena da iyayen Aisha ke b'oye min ba kuma tabbas sai na samo dan in samu hanyar samun Aisha kafin ta kub'uce min, ita tafi dacewa dani, ina sonta tana sona, bazan barta ta wahala da ciwon so kamar yanda na wahala ba, nasan rad'ad'in rasa masoyi duk da ina da tabbacin yaudara ne, amma tabbas da ciwo ka rasa wanda kakeso".


**********

Manage please 

Zanyi k'ok'arin yi muku gobe. 1600words ya samu kawai.


Najwa!!!! yau kunji labarin Najwa, kunji abunda tayi wa Elmansoor. 


Shin har yanzu baku tausayawa Elmansoor? Shin bai dace ya samu Aisharsa ba?


Comment please 

Nagode da addu'o'inku

I really appreciate 


MaryamerhAbdul


"Aisha lafiyanki?"

K'ofar ta cigaba da k'wank'wasawa cike da damuwa. Jin bata da niyyar bud'e k'ofar yasa ta wuce wurin Mama ta sanar da ita Aisha ta kulle kanta a d'aki tana ta kuka kuma ga Nu'aim zai wuce yana son suyi sallama.


Dukkansu biyu suka iso k'ofar suna k'wankwasawa had'e da yi mata magana mai taushi. A hakan Nu'aim ya shigo jin bugunsu da hayaniyarsu.


"Lafiya dai Mama? Kullewa k'ofar ya yi?"

Shiru sukayi dukkansu basu iya amsa shi ba. Daf k'ofar ya isa yasa kunnensa yaji sheshshek'arta.


Kallonsu yayi d'aya bayan d'aya sannan ya dawo da dubansa ga k'ofar da ke a gark'ame.

"Aisha", ya furta sunanta a hankali sannan ya bata umarnin bud'e k'ofar.

Ko alamun bud'ewa batayi ba sai ma sheshshek'an kukanta da ya k'aru.


"Aisha"

Ya sake k'iran sunan cikin dakakkiyar muryarsa.


K'in amsawa tayi ta cigaba da kukanta.

"Aisha ni sa'anki ne ina miki magana bazaki amsa ba, ki bud'e k'ofar nan yanzu ko wallahi in shigo in sab'a miki, ki fad'i abunda yake damunki kink'i kin kama kin kulle k'ofa kin tada wa kowa hankali, ki bud'e k'ofar nan".


Cike da b'acin rai yake maganar kamar zai doke k'ofar ya bud'e. Bai samu damar k'ara furta wani kalmar ba ta bud'e idanunta a k'asa ta kasa kallonsa.


Kallonta yayi cikin rashin abun yi, fuskarta yayi jawur idanunta luhu-luhu sai ajiyar zuciya take sauk'ewa. Numfashi nauyayya ya sauk'e ya juya ya bar wurin bai iya furta komai ba.


~~~~~~~~~~~~


A bakin gate Elmansoor yayi parking motarsa ya isa ga mai gadin gidan yayi sallama.


"Baba ina wuni? Abban Aisha na gida?".

"Ahh, Yallab'ai yau bazaka shigo da motar ba?".

"A'a babu komai. Yana gida ne? Wurinsa nazo".


"Bismillah shigo. Sai dai akwai bak'o a falon duk da d'an gida ne, zaka shiga daga ciki ko zaka iya zama a can kafin in sanar dashi isowanka?"

Fararen kujerar robar da ke ajiye k'ark'ashin rumfa yake nuna masa ya k'arashe maganar.


"Zan zauna nan babu matsala, Nagode".

Ya furta yana mai yi masa fara'a.


A hanyar shiga ciki mai gadin yaci karo da Nu'aim.

"K'aramin Alhaji ka fito?"

Ya wangale baki yana kallonsa har yabi gefensa ya wuce ba tare da ya tanka shi ba. 


Mamaki matuk'a yanayin Nu'aim ya basa, amma ya share ya isa ciki dan isar da sak'on Elmansoor wurin Mai gidansa.


Elmansoor na zaune idonsa manne da hanyar da mai gadi ya nufa ya hangi wani d'an saurayi na fitowa fuskarsa da yanayinsa kaman ba lafiya ba.


A gefensa ya tsaya yana mai juya masa baya, kallonsa Elmansoor yake yi daga sama har k'asa, tabbas a shekaru zai fi wannan saurayi, shin bai gansa bane bare yayi masa sallama ko gaisuwa?


D'auke tunaninsa yayi yana mai kai hankalinsa ga Nu'aim da yake magana cikin wayarsa.

"Ni bansan ya zanyi ba, yarinyar ban ma san meh damuwarta ba, bazan iya ba yanzu ma dawowa zanyi". Shiru yayi yana sauraron d'aya b'angaren na wani lokaci.


Daga k'arshe ya furta "toh, zan k'ok'arta, sai anjima".


Waigowa yayi dan ya isa wurin motarsa ya ga Elmansoor. Kallonsa yayi yana meh tunanin inda yasan wannan fuskar.


Wurinsa ya isa yana b'oye damuwarsa a bayan murmushinsa mai d'auke hankali.

"Salamu alaikum".

Ya mik'a masa hannu dan suyi musafaha.


Mik'ewa Elmansoor yayi daga mazaunin nasa sannan ya mik'a masa nasa hannun yana mai amsa sallamar.


"Kaman na wayeka, amma na kasa gane a ina".

"Elmansoor" ya furta sunan yana mai janye hannunsa daga na Nu'aim.

"Sunana Elmansoor, maybe ka tuna in kaji sunan nawa".


Idonsa ya juya yana kai tunaninsa nesa.

"Ban dai tuna ba, sunana Nu'aim".


Yawu Elmansoor ya had'iya idanunsa na canja launi. Juyawa yayi zai wuce Elmansoor ya dakatar dashi da tambayar da bai san ya iya furtawa ba.

"Kai ne kazo wurin Pretty??"

"Pretty?" Nu'aim ya tambaya yana mai had'e fatan goshinsa.


"Ohh, sorry ina nufin..."

"Kai ne dama?". Muryar Abba ya katsesa daga yi masa bayanin da yayi niyya.


"Nu'aim har ka fito? Tafiya kenan?"

Kai ya sunkuyar yana sosa bayan kansa.

"Eh, gobe akwai aiki wanda ya zama dole in hallara dan samun kammaluwarsa a kan kari, zuwa gaba zan nemi hutu insha Allah".


Dariyar manya yayi sukayi sallama ya shiga motarsa ya wuce.


Russunawa Elmansoor yayi ya mik'a masa gaisuwarsa cikin nutsuwa. Sai da ya samu zama a kan kujerar da Elmansoor ya tashi sannan ya amsa gaisuwar.


Tsugunawa Elmansoor yayi yana mai muhawara da zuciyarsa game da abunda ya kawosa. Muryar Abba ne ya katsesa.


"Kaga wanda ya fice yanzun? Shi na bawa 'yata Aisha, gwanda da kuka had'u ma dan inyi maka bayanin gwari-gwari. Nasan meh ya kawo ka, na tabbata ta sanar dakai shiyasa kayi tattaki dan jin ba'asi ko hak'ik'anin bayani, ko kuma iyayen naka ne suka sanar dakai komai suka hutar dani suka hutar da kansu?"


Kallonsa yakeyi yake maganar, fuskarsa babu alamar wasa. Shirun da Elmansoor yayi yasa shi cigaba da cewa.

"K'arin bayanin kazo nema a wurina kenan? Shin ka sanar da mahaifinka sannan kazo nan?".

"A'a" Elmansoor yace kansa a k'asa.


"A ganina banida gamsasshen bayanin da zan iya yi maka, mafi kyawu kaje ka samu mahaifinka ya sanar dakai komai, shi yafi dacewa ya sanar dakai ba ni ba".


Kallonsa Elmansoor yayi da mamaki, bakinsa rawa yake ya rasa kalaman da zai furta masa. Cikin i'ina ya furta "Ban gane maganar ba Abba. Ka sanar dashi dalilin kake nufi? Ya akayi bai sanar dani ba yau bayan munyi maganar?".


"Kaje dai ka tambayesa, ina kyautata zaton bazai 'boye maka ba. Maganar Aisha ka barta ka ajiyesa gefe, Allah ya kawo maka wacce ta fita alhairi".


Yana isa wannan gab'a ya mik'e ba tare da ya jira wani maganar ba ya shige ciki ya barsa a wurin tsugunne.


***********


Elmansoor tun da ya dawo yake tunanin yanda zai tunkari mahaifinsa da maganar. Da wannan batu ya runtsa bayan ya yanke shawarar tunkarar mahaifinsa washegari.


Bai samu sunyi magana da safe ba kowannensu ya wuce office wurin aiki. Sai bayan sallar isha'i ya isa falonsa. Zaune yake kaman yanda ya saba yana kallon BBC, da sallama ya shigo ya samu wuri ya zauna sannan ya gaishesa.


"Ya dai Elmansoor? Akwai matsala ne? Ka zauna ka tsareni kaman mara gaskiya kuma ka kasa cewa komai".


"Dama akan maganar rannan ne, munyi magana da ita yarinyar kuma naje na samu mahaifin nata".


"Toh, ai hakan na da kyau".


"Sai dai, ehmm.. yace, Daddy yace in zo wurinka zaka fad'a min dalilin da yasa ya hana min Aisha".


Murmushi yayi ya mayar da dubansa zuwa ga talabijin sannan ya juyo ya kallesa cikin neman daidaitacciyar furucin da yakamata ya furta.


"Tun farko da yace zai nememu Elmansoor na d'auka ka cireta a ranka ka gogeta daga babin rayuwarka. Yarinyar nan ka bar maganarta kawai Elmansoor, ka nemo wata zan aura maka ko 'yar wanene".


Da mamaki Elmansoor ya tsaya kallon daddy, "Amma Daddy da bana son yarinyar nan bazan kawo maganarta wurinka ba. Ita ce mace ta biyu da na kawo maka maganarta, ya kake tunanin zan iya kawar da ita daga tunanina da duniyana?".


"Ba wai nak'i maganarka ba Elmansoor, mahaifinta yak'i baka aurenta, ya kakeso muyi?"


Elmansoor yaji sauk'i a ransa, ko ba komai zai ji dalilin da duk suke b'oye masa.


"Daddy dalilin nakeso inji, na tabbata ka sani kaman yanda yace, sanin inda matsalar yake shi zai kawo mana yanda zamuyi mu shawo kansa".


Shiru yayi yana kallon yanayinsa, idanunsa tuni sun canja launi hawaye na taruwa, har ransa yake jin bacin ran Elmansoor, duk cikin yaransa yafi sonsa, amma ya zaiyi? Laifin da yayi a baya shi yake bin d'an nasa. Ya zai iya fad'a masa shine dalilin hana shi wacce yake so? Bazai tab'a iya sanar masa ba, hak'uri ya zama dole yayi akan Aisha, babu yanda za'ayi Alh. Nemi ya basu auren 'yarsa.


Kafad'ansa ya dafa yana mai kawar da tunaninsa.

"Solution na matsalan nan 'daya ne, shine rabuwa da Aisha, ka nemo wata shi zai fi mana alkhairi gaba d'aya".


Hawayen da yake tarewa masu zafi suka gangaro saman kuncinsa, ya lumshe ido sannan ya rik'e hannun mahaifinsa da ke kafad'ansa ya sauk'e idonsa akan hannayen sannan ya d'aura dai-dai zuciyarsa


"Daf kuke da rasa ni in na rasa abunda nakeso a karo na biyu. Daddy kana jin heartbeat 'dina ya canja koh? Wallahi in na rasa Aisha zai daina motsi kwata-kwata. In na rabu da ita na rabu da farincikina kenan wata k'ila har da numfashina".


A hanzarce Abba ya janye hannunsa yana kallon Elmansoor kaman tab'abb'e. Sosai ya tsorata da kalamansa, bugun zuciyar Elmansoor ya sa nashi zuciyar matsanancin bugu da tsoro. 


"Kana da cikakkiyar hankali kuwa Elmansoor? Akan mace kake ik'irarin rasa ranka? Yaushe ka mayar da kanka haka ban sani ba?".


"So nake ka gane ina sonta".

Mik'ewa daddy yayi yana mai juya masa baya. Yana huci zuciyarsa na bugu da sauri.


"Mun gama maganar Aisha a gidan nan daga yau, ka wuce kaje ka kwanta".


"Amma Daddy..."

Katseshi yayi cikin tsawa

"Cewa nayi mun gama magana, ko ka daina jin Hausa Elmansoor?".


Bai samu damar sake magiya ba ya tashi ya fice ganin ran mahaifin nasa ya b'aci matuk'a.


******


Bansan ta ya zan fara baku baki ba, kuyi hakuri kuyi hakuri, kunsan yanayin rayuwa. A min uzuri, in kuka lura da kyau zaku ga shafin nan ya banbanta da sauran shafukan nawa, hakan ya samu ne sakamakon rashin nutsuwar zuciya akan rubutun, da na fara sai inji ya fita kaina dole in ajiye, dakyar na samu na rubuta wannan shafin, zan k'ok'arta in idasa in shiga hutun rubutu, gaskiya kwanakin nan ina wahala.


Ina buk'atar du'a'inku, Allah ya tabbatar mana abunda muke so na alhairi, Allah ya amshi du'a'inmu. 


Nagode sosai 

Allah ya bar kauna

Zan kokarta inyi muku gobe, in baku gani ba kada kuce na saba sab'a alkawari😣 a cigaba da min afuwa.


Comment 

Vote 

Share


K'urar da ke kan littafan cikin drawern ya fara kad'ewa dan samun ganin sunan envelope d'in da yake nema. 


"Mi...." Attishawa yayi mai k'arfi bai ida karanta sunan ba. Bakinsa bud'e yana jiran sauran attishawan da yake jin alamarsa, jin ya koma bai fito ba ya sa shi bud'e envelope d'in yana k'arasa sunan "Mine!!!".


Wurin wutan d'akin ya isa ya kunna a karo na biyu ko zai kawo. Cike da takaici ya kai wa makunnin mari yana jan tsaki.


Komawa yayi wurin k'aramar kujerar da ke d'akin ya ciro wayarsa da ke aljihu ya haska. Tsugunawa yayi ya hure k'uran da yake kai sannan ya zauna yana mai zazzage papers d'in da suke ciki had'e da hotuna guda biyu.


Hotunan ya d'auka ya k'urawa d'aya daga ciki ido, yafi fito da kamannin da yake son gani, yafi fito da komai nata. Idanunsa ne ya sauk'a k'asar hoton ya ga an rubuta "Fatima".


D'aya daga cikin takaddun ya d'auka, "yours Fatima" aka rubuta a bayan, da hanzari ya bud'e dan tabbatar da zarginsa. 


Bayan gaisuwar da tayi masa wanda bai tsaya karantawa dukka ba ya isa inda yake son ji.

"Nayi ta nemanka a makaranta ban sameka ba, ina buk'atarka..." kalmar da yake gaban yasa ido sosai dan ya karanta kasancewar mai turo sak'on ta goge. Da kyar ya had'e harufan ya furta a fili "Habiby". Idanunsa ya juya sannan ya cigaba da karantawa.


"Abdallah, ina son ganinka, ko da bazan iya samun abunda nakeso ba ka bani daman ganinka a karo na k'arshe. Nagode"


Nunfashi ya furzar zuciyarsa na mai raya masa abubuwa da yawa. A hankali ya cigaba da bin sak'onnin nata, ganin bazai iya gamawa dukka ba ya tattara ya mayar ma'adaninsu rik'e da d'aya daga cikin hotunan.


Wurin mahaifiyarsa ya isa bayan ya cuss hoton cikin aljihunsa. Bayan yayi mata sallama ta amsa ya zauna a gefenta ba tare da yayi mata wata maganar ba.


"Nu'aim, yau kwana biyu da dawowanka kak'i min magana guda d'aya da zan gane yanda kuke ciki. Kun daidaita d'in ko kuwa? Abunda kazo sanar dani kenan ko?"


Kallonsa ta tsaya yi tana karantar fuskarsa, tun dawowarsa daga Abuja bai basu damar tattauna abunda ya kai sa ba. Duk lokacin da ta bijiro da maganar yana da abun yi ya lallab'a ya gudu.


"Mama, bansan meh zan fad'a miki bane akan Aisha..."


"Lafiya dai ko? Meh ya faru?"


"Akwai abunda yake damun yarinyan nan, kuma ni nafi kyautata zaton akwai wanda take so sannan kuka kawo mata maganana".


Fuska ta had'e tana kallonsa sama da k'asa.

"Bana son iyayi Nu'aim, ka shiga taitaiyinka kana jina? Dan kana neman dalilin barinta bai zama zaka d'aura mata laifin ba, gwanda ka fad'a min kai tsaye bata min ba, a'a bamu daidaita ba".


Fuska ya marairaice yana kallonta.

"Mama mana, akwai abunda yasa nayi tunanin hakan, tunda naje wurinta bata yi murmushi ba fa, kuma...."


"Hakan shi zai sa ya zama akwai wanda take so?"


"Kiyi hak'uri ki jini har k'arshe, in yaso ke da kanki sai kiyi judging. Da farko da ta fito kamar tayi kuka, na d'auka bacci ne ko bata da lafiya, da muka fara magana tak'i amsani, kuma ni ba haka nasan Aisha ba, kinsan tana da surutu kaman ni anan, daga k'arshe ma Mama da na kawo mata maganan tsakaninmu kuka ta fashe dashi ta gudu ciki, wai in zan iya aurenta a hakan bismillah, kaman dole aka sa ta babu yanda ta iya".


Shiru Mama tayi kamar bazata amsa ba, daga bisani ta furta kalamanta

"Bata saba dakai bane"

"Mama har da wannan saurayin da na gani ya k'irata da Pretty? Kuma ya san da zuwana wurinta? Shima bai isa ya sani tunanin akwai wani abu ba?"


"Wani kuma? Ban gane wani ya k'irata da pretty ba, ka sani ko d'an makarantansu ne? Babu komai ma Nu'aim, da akwai wani abu Abdullahi zai sanar dani, meh yasa zai 'boye min sannan ya nemi had'aku? Anya Nu'aim bakayi kuskure ba?"


"Babu wani kuskure Mama, wannan saurayin ya girmi d'an Ss3, ya girme mani ma. Ki ga wannan hoton". 

Ya ciro ya mik'a mata yana cigaba da cewa

"Wannan ba ita ce wacce Uncle Abdallah ya nema a da tun suna BUK ba?"


Kallon hoton tayi ta dawo da dubanta garesa, ta sake d'aura idanunta akan hoton.

"Meh had'in maganar mu da wannan hoton?"


"Wannan saurayin da na gani yana min maganan Pretty kamanninsu d'aya da wannan matar, kinsan lokacin da na shiga wurin ajiyarmu na d'auko hoton ina tambayanki wacece kika k'i sanar dani kika ce in mayar na Uncle Abdallah ne? Ai ban mayar ba sai can daga baya, ina ganinsa naga ya min kama da wanda na sani, a lokacin bai zo kaina ba sai da na dawo gida ina tunanin abunda ya faru, dan tabbatar da zargina shine na koma yau na d'auko hoton, kuma sai da na tabbatar da cewa eh budurwarsa ce sannan nazo wurinki, dan nasan bazaki fad'a min ba".


"Nu'aim, binciken kayan mutane ka fara yi dan cimma wani manufa naka? Yaushe ka koma haka?"


"Mama dan Allah ki gane abun nan, ba ina nufin wani abu bane, Aisha na cikin damuwa, kuma tabbas damuwarta na had'e da wannan matar da kuma saurayin nan, akan mu b'ata komai ba gwanda mu had'u mu gyara kowa ya zauna cikin farinciki ba? Kinfi son inyi aure matata na tunanin wani? Kinfison inyi aure inyi mata abu ta ji ina ma wane ne yayi mata? Instead muyi zaman lada sai muyi zaman zunubi? Bana fatan hakan wa Aisha, indai akwai wanda take so a hak'ura a bata shi, yafi mana sauk'i mama".


Numfashi ta sauk'e tana mai kawar dakai, tunaninta d'aya kada abunda take zargi ya zama gaskiya.

"Mama baki ce komai ba"

"Tashi kaje Nu'aim, zanyi magana da shi baban naka, zan nemeka".


Ficewa yayi jiki ba kwari ya koma d'akinsa.


********


Wayanta ta kunna da niyyar k'iran Elmansoor. Tun ranar da ta k'irashi bai d'aga ba ta kashe wayar sai yau tayi niyyan kunnawa. 


Tun kafin ta kai ga k'iransa ta canja shawara ta kashe wayar.

"Meh yasa bazan iya cireka a raina ba bayan umarni aka bani? Meh yasa na kasa bin abunda Abba ya gindaya min? Allah ka bani ikon bin umarnin Abbanah".

A fili tayi maganar tana mai zubar da hawaye. Kanta ta sa tsakanin cinyoyinta tana kuka mai tab'a zuciya wanda bata san ranan da zata daina ba.


Mama da ke tsaye bakin k'ofa tuni hawaye ya sauk'o mata ta runtse ido. Komawa tayi bata iya shiga d'akin nasu ba. 


D'akin mijinta ta wuce kai tsaye a ranta tana k'issima abunda zai faru a yau, bazata yi shiru tana ganin 'yarta bak'in ciki na nuk'urk'usanta ba, wannan wani irin rayuwa Abba ke son sa 'yarsu ciki? Shin bayi da zuciya ne da baya jin yanda ita take ji a ranta?


A tsaye ta samesa ya gama waya kenan. Takowa tayi ta tsaya a bayansa tana kallonsa.


"Meh Aisha tayi wa Nu'aim da har ya fara tunanin akwai abunda yake damunta? Shin ban isa in sa ta abu ta yi ba kenan ko meh?" 


Waigowa yayi yana kallonta dan jin amsar da zata basa. 

"Abban Aisha, naga alamar kana son kaini mak'ura akan maganar nan, abu yak'i ci yak'i cinyewa? in kai baka son farincikin 'yar ka ni uwa ce, ina son 'yata ta kasance cikin farinciki har k'arshen rayuwarta, ganinta cikin irin halin da ka sata yana cin raina, i can't take it anymore". 


Kuka mai k'arfi ne ya kufce mata tana mai jin zuciyarta na zogi.

"kina son mayar da hannun agogo baya Asma'u. Kin manta mun gama maganar Aisha da Elmansoor a gidan nan? Kuna ta ruruta maganar da bai kai ya kawo ba".


Rinannun idanunta ta d'aga tana kallonsa cikin ido.

"Na rayu cikin gidanka na tsawon lokaci cike da farinciki da annashuwa, Na 'dauka kaima haka ka rayu dani, na 'dauka duk tabon da akayi maka a baya na wanke shi da biyayya da soyayyar da na nuna maka, ashe kai har yanzu akwai wacce ke ranka? Zaman biyayya kakeyi dani har yanzu ba so ba?".


Kukanta ya ci k'arfinta ta kasa amayar da dukkan kalaman da yake cikinta. Ashe Abba baya sonta? Duk rayuwar da sukayi ashe yana kyautata mata ne dan ya samu abunda zai kawar dashi daga tunanin abunda ba nasa ba? 


Kuka takeyi kaman ranta zai fita, jin k'amshin turarensa kusa da ita yasa ta gane yana tsaye daf ita. 


Hannunta ya rik'e ya tsaya kallonta cikin rashin kalmar da ya dace yayi anfani da ita. Kan gado yayi mata jagora ya zauna gefenta hannunshi cikin nata.


"Ina son magana da ke na fahimta Amman Aisha".


Numfashi ya sauk'e sannan ya cigaba da magana dan babu alamar zata amsa shi.


"Ni nasan meh nakeji a raina in na tuna abinda akayi min, kuma...".


Dakatar dashi tayi sanin maganar da zai furta mata, in hadda ne tuni ta haddace akanta.


"Ba sai ka tuna min son da kake mata ba, kada ka manta ni matarka ce, kace kawai cin fuskata zakayi".


 "Asma'u, an k'untata min kin sani, hakan ya min ciwo, meh laifina dan nayi ramako? I'm sure in nayi akan Elmansoor, Yuri zaiji exact yanda naji a can baya, please understand, ni ba son wata nakeyi ba, ke shaida ce na manta da rayuwarsu tunda kika shigo tawa rayuwar, having you is a blessing, wallahi kin fiye min Fatima, farincikin da kika bani nasan bazata iya bani ba, I'm proud of you. Trust me".


Hawayenta ta share da bayan hannunta.

"Meh yasa kake tunanin bak'in cikinsu su kad'ai baka tuna Aisha? Kaman yanda kaji zafin so haka ita ma takeji a yanzu". 


Tashi yayi had'e da jan k'aramin tsaki.

"Ina miki maganar fansar soyayyata kina min maganan Aisha? Yanda nayi hak'uri haka ita ma yakamata ta yi".


Tashi tayi tazo gabansa ta tsaya hawayenta sun lafa a wannan lokaci, b'acin rai ya mamaye fuskarta. 


"Abban Aisha, kaso ko kada kaso kana son matar da ta haramta a gareka, wakeup, kuma wallahi kana gab da rasa ni in ka cigaba da nuna min matsayina a gidan nan, ka cigaba da nuna min ni ba komai bace wata can a waje ta fini matsayi a wurinka".


"Asma'u".

Rik'eta yayi niyyan yi ta dakatar dashi ta hanyar matsawa baya tana mayar da hawayen da ke barazanar sauk'o mata.


"Kinyi misunderstanding d'ina ummin Aisha, kishi ke yawo da ke".


"Kai ba kishin ke yawo dakai ba? Shekara ashirin da biyu sai yau zaka nuna min matsayina? Ba duk akan mace kake son ka b'ata rayuwar 'yarka ba? Ba ma ita kad'ai ba har da nawa, kasan muddin 'yata ta rasa farincikinta nima na rasa nawa".


Sosai kuka yaci k'arfinta a wannan gab'a. Kafad'anta Abba ya rik'e dan kada ta zube a k'asa, yasan Asma'unsa tana da hak'uri da dauriya, bai kamata akan wannan maganar ta kasa anfani da halayenta da ya santa dasu ba.


~~~~~~~~~~~~~~~~~~


Thank you so much da kuka min uzuri

Na dawo yanzu kam, kuma da yardar Allah bazan koma ba sai na idasa dan inji dad'in ajiye alk'alamina inyi ta bacci hankali kwance😂


I'm sorry 

Bazan gaji da baku haquri ba

Ku cigaba da min uzuri

Maryamerh na godiya da kulawarku

Ina sonku matuk'a


Toh ya kuka ga wannan chaptern? 


Nu'aim ya nemo mana wata kuma wai Fatima


Wacece Fatima?


Meh had'in Yuri da Fatima?


Shin Nu'aim ya damu da halin da Aisha ke ciki ko dai yana da wacce yake so shiyasa yake hakan?


Muje zuwa dai

Comment please 

Nagode


Zaune yake ya dafe kansa da hannayensa hawaye na zuba daga idanunsa, mafita kawai yake nemarwa kansa. 


Rinannun idanunsa ya d'aga yana kallon Fahad, bai iya furta komai ba ya sauk'ar da kai yana mai share hawayen da ke bisa kuncinsa. 


"Yanzu baka jin shawara Elmansoor, kak'i zuwa office kana zaune dan k'arawa kai damuwa? Shin mantawa kake da Allah ne ya k'addara maka abinda ya sameka? Meh yasa ba zaka iya d'aukan wannan matsayin k'addara ba? 'Yan mata nawa ka rabu dasu sai wannan ne bazaka iya wucewa ba bayan kai kasan auren nan ba mai yiwuwa bane, babu mai supporting naka. Yanzu kana zaune anan meh ribarka bayan ciwon zuciyar da kake d'aura wa kanka?"


"I'm ready to face any challenge indai akan auren Aisha ne, ban 'dauka abun zai zo min haka bane, anya daddy na sona yanzu? Ni nasan daddy ba haka yake ba, yana son duk abinda nakeso, amma yau ga shi ina neman abinda nasan zai iya bani amma yak'i". 


Shigowar Mommy da tray a hannunta ya hana Fahad furta kalaman bakinsa. Karb'a yayi ya ajiye gefen Elmansoor.


"Tun jiya rabon ka da ka ci komai, kai baka jin yunwa ne?".

Juyowa tayi wurin Fahad tana fuskantarsa ganin d'an nata bayi da niyyar amsawa.


"Abokinka na neman kashe kansa akan abunda bai taka kara ya karya ba, rabon da inga yaci abinci spoon biyar wallahi na manta, sai tea da nake d'ura masa wani lokacin kaman yaro k'arami. Kana masa magana akan abinda ya 'daurawa kansa kuwa? Abun nasa yayi yawa Fahad".


"Hak'uri zakuyi ai Mommy, lokaci ne wannan ma zai daina, ina iya bakin k'ok'arina akan hakan".


Tashi Elmansoor yayi dan shiga toilet, baya son jin maganarsu akan hak'ura da Aisha da kullum ake nanata masa, bazai iya yin hakan ba, yana son su gane cewar yana sonta fiye da duk wata d'iya mace da ya tab'a zama da ita, ciki kuwa har da Najwa.


Jinsa yayi kwance jikin Fahad sakamakon jirin da ya d'ibesa. Gadon ya dafe sannan ya daidaita zamansa yana mai dafe kansa had'e da lumshe ido. 


"Sannu"

Ya tsinkayi muryar Mommy tana shafa kansa damuwa bayyane fuskarta.


Bai iya amsata ba dan jin kansa yayi na juyawa. Sai da ya daidaita kansa sannan ya mik'e ya shiga ban d'aki dan watsa ruwa.


Wanka yayi ba tare da ya shafa mai ba ya sanya jallabiyarsa bak'a. Kallo d'aya zaka masa ka gane ramar da ya yi. K'asumbarsa ko gyara babu, kwalliyar da yakeyi duk babu a yau.


Komawa mazauninsa yayi ba tare da yayi niyyar cin abincin da Mommy ta kawo masa ba.


"Mommy kafin ta fita tace kaci abinci".

"Uhmm, bana jin cin komai ne. Daddy na gida?"


"Yanzu fa ka gama mana layi anan, kuma kace baka jin cin komai?"

"Daddy na nan ko baya nan?"

Ya maimaita tambayar yana mai kawar da tambayar da Fahad yayi masa.


"Eh, kaman naji Mommy na cewa ya dawo daga meeting amma zai sake ficewa".


Hanyar fita yayi bayan ya taso daga mazauninsa, idanunsa da ke rufewa yake k'ok'arin daidaitasu dan ya ga hanyarsa.


"Lafiya dai Elmansoor, menene?".

Bayansa yabi yana yi masa wannan tambayar. 

Shirun da Elmansoor yayi yasa shi jefa masa tambayar da yasan bazai tab'a samun amsa ba.


"Baka da hankali ko? Kwanyarka ya samu rauni ko? Wai meh yasa baka tunanin halin da kake sa kanka da wanda kake sa wad'an da ke damuwa dakai? Baka tausayin iyayenka?"


"Tausayinsu yasa nakeson zuwa garesu, in mutum lokacinsa yayi yana ji a jikinsa, ko ba haka ba? Ina ji a k'albina lokacin nawa ne yazo, ka barni in isa garesu in nemi yafiyarsu tun kafin lokaci ya k'uremin".


Kallonsa Fahad ya tsaya yi yana mai mamakin furucinsa, kad'a kai yayi ya koma ciki yana mai jin zuciyarsa na harbawa, kwanyarsa kuwa na juya maganganun Elmansoor, ya tabbata zafin da yake ji a ransa ya sa shi furta hakan.


~~~~~~~~~~


Daddy na zaune a kujera momy na zaune gefensa, hira suke tsakaninsu duk da babu alamar annashuwa a fuskarsu, da alamu abu mai muhimmanci suke tattaunawa. 


Sallamar da yayi ne ya jawo hankalinsu zuwa bakin k'ofar da yake tsaye. Idanu suka zuba masa bayan sun amsa sallamarsa, cikin mutuwar jiki ya iso ya zauna kusa dasu.


Daddy sai da ya had'iye miyau mai d'aci sannan ya iya dawo da nutsuwarsa. Duk kwanakin da ya shud'e baya barin lokaci ko da minti biyar ne dan sauraran k'orafin d'an nasa. Rashin samun cikakken bayanin da zai yi masa ya sa shi kaucewa duk wani hanya da zai basu damar keb'ewa, a yau dai da alamu bayi da hujjar tafiya, kayan da ya sauya kad'ai ya isa nuna masa fitan da yayi niyya ya fasa.


"Lafiyanka? Meh yake damunka haka duk ka fad'a ka canja kamanni?".


Murmushi Elmansoor yayi wanda aka fi sani da na k'arfin hali dan bai wuce labb'ansa ba.


"Lafiya k'alau, nazo dan neman...?"

Mik'ewa Mommy ta yi dan basu wuri Elmansoor ya dakatar da ita.

"Wurinku nazo dukka, please ki zauna".


Idanunsa cike suke da hawayen da bai san anfanin fitowarsu ba a wannan lokaci. Ba tare da ta amsa shi ba ta zauna tana mai share hawayen da yabi gefen idanunta.


"Daddy... Na sani ba sai ka furta ba baka son magana dani saboda wasu dalilai naka wanda nasan bazai wuce fushi da kakeyi dani ba. Nayi laifi dana kasa d'auka maganarku game da Aisha, nazo ne dan in baka hak'uri akan hakan, kayi hak'uri ka gafarta min, InshaAllah na barta har abada, daga yau bazan sake samun damar k'in bin duk umarninku ba, wata k'ilama bazan k'ara jin sautin muryarku ba bare har in bijire. Mommy ku yafe min, ku yafe min da na sabbaba muku tashin hankali a iya kwanakin nan, kuyi hak'uri ku gafarceni".


Hawaye masu zafi ke zubo masa, rik'e yake da hannun mahaifiyarsa yake maganar. Hannunta ya damk'e yana mai jin d'aci a ransa sakamakon hawayenta da ke zubowa a dalilinsa, jin zuciyarsa yayi kamar an d'aura masa dutsi dan bak'in ciki.


Kallonsa daddy yake yi cike da tausayi, matsowa yayi kusa da d'an nasa ya d'aura hannunsa akansa yana mai shafawa a hankali alamar rarrashi.


Can ciki ya furta kalaman da yake ta nanatawa a ransa.


"Allah yayi maka albarka, Allah yayi maka Albarka ya baka wacce ta fita, wacce zata baka farincikin duniya da lahira, wacce zata tausaya

maka taji k'anka. Baka yi min laifi ba Elmansoor, Nagode da ka fahimci nauyin kalaman da na b'oye maka, Nagode da ka gane ba tare da ka d'aura min wahalar da na dad'e da mantawa ba, zan ma iya cewa ban tab'a d'auka zan ci karo da wannan ba. Allah ya yi maka albarka".


Janyosa Mommy tayi kusa da ita hannunta damk'e da nasa, hawayen idanunta basu daina sauk'a ba ta nemo kalamanta.


"Mu zamu baka hak'uri, ka yafe mana Elmansoor baza mu iya samo maka farincikinka ba...".


Hannunsa ya daura akan labb'anta yana kad'a kansa.

"Haba Mommy, ni ai bazaku tab'a min laifi ba bare har ku bani hak'uri, ki daina irin furucin nan na rok'eki".


Babu wanda ya sake furta komai na tsawon mintuna biyar, daga bisani ya mik'e yayi musu godiya sannan yayi hanyar fita daga d'akin.


A bakin k'ofa duhu ya mamaye idanunsa, kansa na juyawa dashi, yayi k'ok'arin dafe bangon da ke gefensa amma bai samu damar yin hakan ba ya tsinci kansa a wata duniyar.


Muryar Mommy ya iya tsinta a can nesa tana tunkarosa a inda yake kwance tana furta kalmar "innalillahi wa inna ilaihi rajiun". 


Daga nan bai sake jin komai ba.


~~~~~~~~~~~~


"Abdallah, ka fito b'aro-b'aro ka sanar dani dukkan abunda yake faruwa tun kafin hak'urina ya k'are akan wannan zancen".


"Duk bayanina baki yadda ba kenan Yaya? Na sanar dake babu abunda nake b'oye miki, babu ko d'aya daga cikin hasashen da kikeyi game da Aisha ko Fatima, rayuwar baya ya wuce na manta dashi, waye yake kitsa miki wannan maganar?"


Shiru ya ratsa tsakanin wayar da suka dad'e suna yi.


Daga bisani ta numfasa wanda a nashi b'angaren yake jin dukkan motsinta, zuciyarsa na barazanar b'arkewa da abunda take shirin sanar dashi.


"Baka bani wani dama ba da ya wuce sanar da Hajiya, tun da ni na zama bare a wurinka, kana neman cutar dani ka cutar da kanka, muddin abunda nake hasashe kake shirin yi Abdallah toh kana gaf da tafka babban kuskuren da dukkanmu zamu cutu, wanda bazan tab'a d'aukan hakan daga wurinka ba dan son zuciya da rik'o irin naka".


"Yaya ki yadda dani, maganar nan bai kai har aje wurin Hajiya ba".


"Ka sanar dani gaskiya in baka son in sanar da ita".


"Eh toh, hakan ne, bana son bawa Aisha yaron Bala Yuri, hankalina bai bani yadda da hakan ba, shiyasa na nemi Nu'aim ya aureta dan kawai in raba su".


"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Abdallah, shin kai ne Abdallah da na sani k'anina? Abdallah akan abu irin wannan kake son b'ata rayuwar yara biyu? Uku ma dai da wanda take so. Abdallah zuciyar taka macewa tayi da wannan k'addarar ta sameka? Ashe dama baka d'auki hakan a jarrabawar rayuwa ba? Na haneka da irin wannan rik'on, na haneka da d'aurawa 'yarka bak'in cikin da ka tab'a tsintar kanka a ciki, na haneka da yiwa 'yata auren dole".


"Haba Yaya, 'yata ce fa..."

"Nu'aim kuma d'ana ne, maganar aurensu na datse daga yanzu".

"Ko da Nu'aim ya fad'a soyayyarta? Ko da ya fara sonta a iya kwanakin nan da muka nuna masa son kasancewarsu tare? Kiyi tunani, shin kema kin yadda d'anki ya fad'a bak'in ciki dan kawai kada d'an wani wanda ba naki ba ya samu farin ciki?"


"Abdallah" 

Cikin tsawa tayi maganar, a wayar kad'ai sai da ya iya gano irin b'acin ran da ya sabbaba mata.


"Ka dawo hayyacinka, ka farfad'o daga wannan haukan da kake yi, Abdallah shin kana azkar ma? Anya ba wani ne ya jefeka ba yake saka tunani irin na mutane marasa hankali marasa tausayi?"


Hannunsa na dama ya dawo da wayar sannan ya amsata.

"Babu ko d'aya, abunda yake raina nake sanar dake, bana son had'a 'yata da zuri'ar Yuri muddin hakan zai jaza masa bak'in cikin da ya sabbaba min shekaru da dama".


*************


Comment on every line if possible 


Shin meh ya samu Elmansoor?


Shin Abba bai kamata ya janye k'udurinsa ba ganin kowa na bashi rashin gaskiya?


Shin Nu'aim na son Aisha?


Fahad da Mufeedah fa, meh ke faruwa tsakaninsu? Ko dai tun da yace ya hak'ura bai sake waiwayarta ba?


Saura k'iris mu idasa littafin kacokan, duk amsar na nan zuwa cikin shafuka goma masu zuwa.


Share

Comment 

Vote

Vote

Vote 

Yes 

Vote please 

Thank you 


MaryamerhAbdul


"Kwata-kwata ma yaushe min da aure man, banson k'in bin umarninsu ne, duk da ba dole suka sa ni ba, naga suna son kasancewarmu tare".


Robar Inab da ke ajiye yasa hannu yana d'auka idanunsa na kallon hanyar tafiyarsu.


"Toh yanzu ya ake ciki? Zaka aureta in hasashenka bai zama gaskiya ba?".


"Ya na iya Salman, babu wata da nake so, da akwai wacce nakeso ne zan samu matsala, amma ba kowa duk rud'u ne, kaga kenan bani da wani zab'i da ya wuce in aureta duk rigimarta, bare ma na tabbata akwai abunda take b'oye min".


"Ka sake magana da Mama?"

"Bansan meh take b'oye min ba, tayi maganar dashi amma bata ce komai ba, jiya ne ma ta kawo maganar. Ni fa duk na rud'e, abun yana damuna kada ka d'auka wasa, duk na birkice".


Dariya Salman yayi yana mai tauna Inab d'in da ya sanya a bakinsa. 


"Look, iya bincikenmu ya nuna masa kana da gaskiya, so chill, yarinyar akwai wanda take so, in Mama ta d'auke maganar bata d'auki hakan da muhimmanci ba ka sanar da ita bazaka iya auren wacce bata sonka ba".


"Salman kana magana kamar zan iya yin hakan".


"Ohh, so kake ka aureta bata sonka? Tana sonka ma ya aka k'are bare bata sonka? Nidai bazan baka wannan shawarar ba, tun wuri ka samu hanyar lauyewa tun kafin mu isa inda bazamu iya yin komai ba, ko da bai tabbata tana son wani ba ka jawo hankalinta gareka sannan ayi aure in ba haka ba akwai matsala fa abokina ina fad'a maka".


Gudun motar ya rage dan isowa anguwarsu da yayi. Kai Nu'aim ya kad'a yana mai jin horn d'in da Salman yake bugawa har cikin kwanyarsa. A hankali ya shige cikin gidan bayan an bud'e masa Gate.


~~~~~~~~~~~~~~


Safa da marwa Daddy yakeyi tun isowarsu asibitin ya hard'e hannayensa ta baya bakinsa bai bar addu'ar samun lafiyar d'ansa ba.


Mintuna talatin kenan da shigar da Elmansoor A & E, hankulansu tashe babu wanda ke iya rarrashin wani. Humaira da Mubarak na zaune gefen Mommy kowannensu na zubar da hawaye.


Fitowar Dr. yasa su mik'ewa had'e da isa wurinsa.


"Dr. Lafiya? Ya yake Dr.?

Mommy ke masa wannan tambayar fuskarta hawaye ya malale.


"Alhamdulillah mun samu damar daidaita numfashinsa, a yanzu dai yana buk'atar hutu".


"Alhamdulillah, zamu iya ganinsa ai ko? Ya farfad'o kenan?"

"Sister Fa'iza zata iya yi muku jagora zuwa wurinsa, sai dai bacci yakeyi, kamar yanda nace yana buk'atar hutu".

Nurse d'in da ke gefensa mai suna Fa'iza tayi musu jagora shi kuwa ya mai da hankalinsa zuwa ga Daddy.


"Mu isa Office?"

Ba tare da sun tanka ba Daddy da Fahad suka bi bayansa.


"Elmansoor na cikin mawuyacin hali, ban d'auka matsalar da muka gama da ita ta sake tasowa har fin na da ba, ya kuka bar b'acin rai ko ince damuwa yayi masa lahani har haka?"


"Dr. Kayi mana bayani yanda zamu gane, ciwon zuciyar ne har yanzu?".


"Toh a yanzu dai kai tsaye bazan ce shi bane sai mun gama gwaje-gwajenmu, sai dai alamu sun nuna shi d'in ne in kukayi la'akari da yanda kuka zo dashi yau da kuma na kwanakin baya, sai kuma yunwa da ya sanya masa mummunar ulcer. Ku k'ara bamu lokaci dai zuwa sa'ilin da sakamakon gwaje-gwajen zai fito".


"Dr. Kai fa ka bamu assurance na samun lafiyarsa, ya akayi lokaci d'aya ciwo zai dawo sabuwa?" Cewar Fahad


"Har ma ya wuce na da, kamar yanda na sanar daku a k'arshe bayan ya gama komai da muka d'aurashi akai, ku kiyaye tado masa da abunda zai mayar dashi ga samun rauni a zuciyarsa, ku sa shi gaba ya sanar daku damuwarsa, ku zama abokai a garesa dan tare duk wani abunda zai assasa masa mummunar damuwa".


"Dr. Muna iya bakin k'ok'arinmu, sai dai a wannan karon ban d'auka abun zai kai haka ba". Cewar Daddy idanunsa na kallon Dr. cike da damuwa.


"Eh toh, kasan zuciyarsa bata da k'arfi sosai, abu kad'an zai tado masa ciwon, shiyasa nake ta nanata muku ku kula da yanayinsa".


"Mun gode Dr."

"Allah ya bashi lafiya, zuwa anjima in ya farfad'o zamu gama d'aukan duk bayanan da muke buk'ata, zuwa gobe mu amshi sakamakon, Allah ya bashi lafiya".


Musafaha sukayi suna mai yi masa Godiya.


~~~~~~~~~~~~~~


Kayanta take gyarawa cikin wardrobe karatun qur'an na fitowa daga wayarta da ke ajiye akan gado. 


Shigowar Aisha yasa ta rufe k'ofar wardrobe d'in bayan ta gama sanya kayan ciki, wayar ta janyo ta kashe karatun idanunta manne a fuskar Aisha tana karantar yanayinta.


"Aisha, Fahad fa bai nemeni ba"


Shiru Aisha tayi kamar bazata amsata ba idanunta lumshe.


"Laifin waye?"

Ta furta can ciki had'e da bud'e idanunta a hankali.


"Duk abunda Fahad yayi bazan ga laifinsa ba Mufeedah, sau nawa nake miki magana akan wulak'ancin da kike masa, kina tare da mutum amma hankalinsa bazai tab'a zama akan kina jin yanda yake ji akanki ba? Ko da ake cewa mace ta ja ajinta wurin saurayi ba irin naki ba, yayi yawa, ki bashi muhimmancinsa, jan ajinki da soyayyarki garesa daban".


"Yanzu laifin meh nayi? Shi bai kamata ya gane cewa b'acin rai bane yasa na yanke wannan shawarar ba".


"Da kika sauk'o daga b'acin ran meh yakamata kiyi? Kin nemesa kin basa hak'uri?"


"Shi yakamata yayi haka, bazan bi sa ba"

Tana mai kawar da kai ta k'arashe maganar.


"Mufeedah, Fahad na sonki kin sani? Kin kai sa mak'ura, ba sau d'aya ba, ba sau biyu ba kinyi masa abubuwan da wallahi wani namijin bazai k'ara kallonki ba. A yaushe namiji zai zauna dake baki tab'a k'iransa dan ra'ayin kanki ba? Raini? Dake nan muke zagin halin Elmansoor, dan ke mace sai mu baki gaskiya? Bayan naki ya dangwale na Elmansoor ya shanye? Kai tsaye zaki nuna masa in yana rayuwarki ko baya nan duk d'aya? I can understand in ya b'ata miki rai ki sharesa ya baki hak'uri, amma banga dalilin da zai sa bai miki komai ba zaki tsokalosa ki k'i basa hak'uri dan kansa ya hak'ura ya dawo, ki d'auki waya kawai ki k'irasa ki bashi hak'uri, shine shawarata, in kuma kina ganin hakan ma raini zai jawo miki bismillah kiyi ta zama a haka".


"Ki kira min shi mana, ni bansan meh zance masa ba".


"Kiyi ta zama baki san abunda zaki fad'awa wanda kuka dad'e tare ba". 


Juyawa tayi tana mai bata baya. Tun ba yau ba take nanata mata abunda ya dace tayi, tak'i bin shawararta yanzu da abu ya kwab'e zata dawo mata? A hakan ma ta bata shawara tak'i bi? Meh take son tayi mata? Dan an hanata wanda take so sai kuma ita Mufeedah ta hana kanta farin cikinta dan kawai jin dad'i ya mata yawa? Rashin hankali dai, waye zai guje wa farin cikinsa yana sane dan wani dalili maras asali?


Muryar Mufeedah ta tsinkayo 

"I will call him, yanzu, na gaji da shareni da yakeyi".


~~~~~~~~~~~~~~


Mommy ke zaune gefensa tana mai cigaba da zubda hawaye hannunta rik'e da hannunsa. 


A hankali yake fidda numfashi ledar ruwa d'aure a d'ayar hannun.


"Sai da na fad'a maka mu sanar dashi komai wata k'ila ya cire abunda yake ransa, gashi yanzu mu da kanmu muke son hallaka d'an da Allah ya bamu".


"Ki bari ya farfad'o, yanzu ba lokacin maganar nan bane".


Rinannun idanunta ta d'ago tana kallonsa

"Ba lokacin maganar ba kake cewa? Sai mun rasa shi kake son mu tattauna? Wallahi zan fad'a mishi komai, bazan zuba ido ina kallonka kana yin duk abunda kayi niyya ba. Bazan iya rasashi bayan zan iya samo masa abunda yake buk'ata ba".


"Mommy kuyi hak'uri, yana buk'atar hutu likita yace". Cewar Fahad


Tashi tayi ta fice daga d'akin.


A dai-dai wannan lokaci wayar Mufeedah ya shigo masa.

Kallon fuskar wayar ya tsaya yi daga k'arshe ya danna answer ya d'aura a kunnensa yayi hanyar waje ba tare da ya furta komai ba.


"Salamu alaikum"

Cikin rawar murya ta iya fad'an hakan bayan ta d'auki lokaci.


Can ciki ya amsa zuciyarsa na gudun fanfalak'i. Bai san da me tazo dashi ba a yau.


"Mufeedah ce, kamar baka gane ni ba".


"Na ganeki, lafiya?"


Shiru tayi jin tambayar da yayi mata, wato ta fad'i buk'atarta bayi da lokacin b'atawa? Kawar da tunanin tayi tana mai d'aurawa kanta laifin sauyawarsa.


"Dama, uhhmmm.... kayi hak'uri".


Shiru ne ya ratsa tsakani, bai iya cewa uffan ba dan bai d'auka abunda yasa ta k'irasa kenan ba.


"Kayi hak'uri Fahad, nasan nayi laifi shiyasa na k'ira dan in baka hak'uri".

Ta cigaba bayan ta tabbata bazai amsata ba.


"Inyi hak'uri in barki? Ko inyi hak'uri kin gane abunda nake son ki gane?"


"Ina sonka fa, bansan yanda zan nuna maka bane, Fahad ka gane halin da muka shiga a lokacin..."


"Na tabbata halin da Aisha ta shiga bai kai na wanda Elmansoor yake ciki ba a yanzu, na nemi mu rabu dan bai samu damar auren k'anwarki ba? Kenan ke baki da ra'ayin kanki sai na wasu? In akwai wanda ya dace yayi maganar rabuwa tsakaninmu Mufeedah ni ne, ina da dalilai masu yawa da yakamata in tafi amma ban tafi ba saboda ke d'in nakeso da dukkan imperfections naki. Na kula ne baki sona baki damu dani ba, shiyasa na baki sararin da kike buk'ata, da halin da Elmansoor ya shiga Aisha ce ciki nasan ko kallona bazaki sake yi ba bare ki so jin muryana".


"Fahad kayi hak'uri, na sani kuma na gane kuskurena, ka bani dama in gyara".


"Baki sani ba har yanzu Mufeedah, ki zauna kiyi tunani ki gano abunda kikeso na karan kanki ba wai a saki kiyi ba, na tabbata ba yin kanki bane k'irana da kikayi, nafi son kiyi shawarar da kanki, ki gane kina buk'atana a rayuwarki ko a'a, ki gane kina sona ko kawai wasa da feelings d'ina kikeyi dan na nace miki babu yanda kika iya dani".


"Fahad..."

"Um-um Mufeedah, na baki lokaci, kiyi tunani, ki gane abunda kike so na karan kanki ba wai ra'ayin wasu ba".


"Ra'ayina ne..."

"Sai anjima".

Ya furta cike da b'acin rai sannan ya katse.


Abubuwa masu yawa cunkushe akansa, ya rasa samun mafita guda d'aya a dukkan matsalolin da ke tunkud'owa garesa.


Yana son Mufeedah, so na gaskiya mai tarin yawa, amma hakan ba shi zai sa ya aureta ba bayan bata jin sonshi yanda yake ji game da ita.


~~~~~~~~~~


Nayi wuta #dancing

Ga wani shafin


Comment 

Vote 

And share


ILYA fisabilillah


MaryamerhAbdul


"Aisha"

Ta tsinkayo muryarsa cike da rauni. Kallonsa ta tsaya yi tana mai rik'e hannunsa, yanayin bakinsa ya tabbatar mata sunan dai yake maimaitawa, hawaye tuni ya samu damar sauk'o mata, tausayin d'an nata na mamaye zuciyarta.


A hankali ya bud'e idanunsa yana mai k'ok'arin daidaita hasken da yayi masa yawa. Sakanni masu yawa sannan ya iya daidaita idanunsa ya bud'esu tangaram yana zagaye d'akin da kallo.


Humaira da tuni ta matso kusa da Mommy ta dafe kafad'arta had'e da kad'a kai tana bata k'arfin gwiwa dan ta danne kukan da ke k'ok'arin kufce mata. 


Bata iya yin hakan ba, mik'ewa tayi cikin hanzari ta fice daga d'akin kukanta na tsananta. 


Sunansa Humairah ta furta bayan ta zauna a mazaunin mommy hannunsa cikin nata.

"Aisha taka ce, babu wanda zai kwace maka ita, babu wanda zai hanaka ita".


Cike da kasala ya d'aura kwayar idanunsa akanta. Murmushi ya sakar mata sannan ya mayar da dubansa bakin k'ofa inda Mommy ke tsaye tana lek'osa.


Hannunsa ya d'aga yayi mata nuni da ta iso garesa, murmushi bai bar lebb'ansa ba. Dak'yar ta iya goge hawayenta sannan ta shigo ta zauna a gefen gadon da yake kwance.


"Na daina Mommy, meh yasa kike kuka bayan nace muku na rabu da ita? ki daina kuka please".


Bata samu damar amsashi ba sakamakon shigowar Daddy da Dr., hankalinsu suka mayar garesa suna mai bashi wuri dan ya samu damar duba shi yanda yakamata.


~~~~~~~~~~~~


"Kwarai nayi kuskure, sai dai hakan ba shi zai sa ka kasa bani dama ta k'arshe da nake buk'ata ba. A lokaci irin wannan kamata yayi muyi hirar yanda rayuwa zata kasance a gaba, tsara rayuwar aurenmu da kuma nuna d'inbin soyayyar da muke yiwa juna, we are meant to be together, ka kasance tare dani. Ina k'aunarka...


               MufeedahrFahad"


Sak'on da ya sanya shi murmusawa kenan a safiyar yau, ya tabbata yau bazai samu damar gusar da ita daga kwanyarsa ba, sak'onta ya fara cin karo dashi tun farkawarsa, sak'on da ya k'unshi abubuwan da tun saninsa da Mufeeda bata tab'a bud'an baki ta tabbatar masa ba.


Driving yakeyi zuwa asibiti amma bakinsa a wangale yana ayyana abubuwa masu yawa a ransa. Wuri ya samu ya tsayar da motar ya zaro wayarsa dan amsa mata sak'onta, bazai bari wannan damar ta wucesa ba, ya ja wa Mufeedah aji? Shi a su wa? Salon ta birkice masa ya kasa gane kanta? Hakan ba shawara bane.


Mintuna biyar ya d'auka yana mayar mata da martani, daga k'arshe ya tura bayan zuciyarsa ta tabbatar masa sak'onsa yayi dai-dai babu nakasu a ciki. Sai a sannan ya sauk'e ajiyar zuciya ya cigaba da tafiyarsa zuwa inda aka kwantar da abokinsa Elmansoor.


~~~~~~~~~~~~~


A guje ta fito daga ban d'akin jin k'arar sak'on wayarta. Juyowa Aisha tayi tana kallonta, brush cikin bakinta, kumfan ya wanke labb'anta sauran kuma cike a bakinta. Anya lafiyar Mufeedah kuwa?


Bud'e sak'on tayi bata ma lura da yanayin Aishar ba, tana karantawa tana komawa cikin toilet ko hanyarta bata gani, d'ayar hannun na rik'e da waya d'ayar kuma tana kiciniyar goge hak'oranta da brush har ta shige ciki.


Zubar da abun bakin tayi ba tare da ta wanke ba ta lek'o ta k'ofar.

"Aisha, Elmansoor is sick".


Idanunta ta iya d'agowa ta d'aura akan Mufeedah, wacce a yanzu wangale k'ofar tayi ta koma ciki tana wanke bakinta tana mai kallon Aisha ta madubin da ke gabanta.


"Da gaske? Wa ya fad'a miki? Meh ke damunsa?"


Ta furta bayan ta mik'e daga kwanciyar tana mai bawa Mufeedah dukkan hankalinta.


Bakin k'ofar ta sake dawowa ta cilla mata wayarta.

"Karanta kiji". 


Bata k'ara komai ba ta kulle k'ofar tayi haramar wanka ta bar Aisha da kiciniyar danna password d'in da a yanzu take da tabbacin kid'imewa ya hanata sa shi daidai.


"Nagode da kika gane hakan, kiyi min afuwa, a jiya da kika k'irani abubuwa sun sha kaina dan Elmansoor na kwance cikin mawuyacin hali. A yanzu dai Alhamdulillah, na samu Mufeedahta kuma abokina na samun cikakken kulawa. Ki kula min da kanki, ina hanyar zuwa asibiti, idan na koma gida zan tab'oki, nayi kewarki sosai.

            Fahad na Mufeedah"


Tana gama karanta sak'on ta zaro wayarta daga ma'adanarsa ta kunna. Layin Fahad ta shiga k'ira kai tsaye ba tare da ta duba sak'onnin da suka shigo wayarta ba. Sau biyu ta k'ira bai d'aga ba, hakan yasa ta lalubo layin Humairah. 


Bata kai ga k'ira ba wayar Nu'aim ya shigo wayarta.


Can ciki ta ja k'aramin tsuka sannan ta amsa ta sa a kunnenta had'e da yi masa sallama.


"Meh yasa kike kashe wayarki wai? Baki ga sak'ona ba? Kenan bazaki iya k'irana ba kamar yanda na buk'ata har zaki sake kashe wayar?"


"Ya Nu'aim yanzu na kunna wayar".

"Kuma yanzu zaki kashe, da banga delivery report a yanzu ba bazan ma san kin kunna wayar ba".


"Kayi hak'uri"


"Babu komai, magana nakeson muyi dama, zan zo Abuja Friday, sai sunday zan dawo, Mama kamar ma tace zaku zo nan hutu, kenan zamu dawo tare, kinga kenan zamu samu lokaci mai yawa na fahimtar juna. Aisha ki tabbatar kin samu k'arfin gwiwar bani dukkan amsoshin tambayoyina, dan wannan karon shine karo na k'arshe da zan baki daman yin zab'i, in har ya wuce toh tabbas zab'ina zaki bi, ko da kuwa shawarar da na yanke shine aurena da ke".


Shiru tayi bata iya amsa shi ba, zuciyarta tuni ya shiga dukan uku-uku, yawu mai tauri ta had'iye.


"Sai nazo".

Ya furta cikin dakakkiyar muryarsa wanda ya tabbatar mata cewa wannan karon bazai so rainin wayo ba. 


"Yaya zanyi?"

Ta furta a fili bayan taji k'arar katse wayar. Hawaye masu zafi taji sun sauk'o mata, bata bari wannan tashin hankalin ya gusar mata da Elmansoor ba, kai tsaye ta dannawa Humairah k'ira tana mai addu'ar Allah yasa ta amsa.


~~~~~~~~~~~~~~~~


Sun shigo asibitin da misalin k'arfe sha-d'aya na rana. Sanye suke da atamfa da manyan mayafi. Aisha ce ta k'ira Humaira ta sanar da ita isowarsu. Inda d'akinsa yake ta kwatanta musu had'e da sanar dasu room no.


Mintuna biyar suka iso, Humairah na tsaye bakin k'ofar tana jiransu. Ganinsu yasa ta sake musu murmushi had'e da rungumesu.

"Sannunku da zuwa". 


Ta furta cike da tsantsar farinciki.

Ita tayi musu jagora har cikin d'akin da yake. 


Mommy na zaune gefensa idanunsa lumshe, Daddy kuwa na kujerar da ke ajiye kusa da k'ofar d'akin wayarsa a hannunsa. 


Sallamar da sukayi ya jawo hankalinsu dukka banda Elmansoor da yak'i bud'e idanunsa.


"Sannunku da zuwa".

Mommy ta furta tana mai sake musu murmushi, har cikin ranta take jin farincikin ganinsu. 


Humairah ta sanar da ita zuwansu tun k'irar da Aisha ta mata na farko. Shigowa sukayi dukkansu suna sunne kai, Aisha yatsunta take wasa dasu bata iya furta komai ba tun dosowarsu d'akin. 


Har k'asa suka tsugunna suka gaishe da Daddy, cike da fara'a ya amsa sannan ya fice daga d'akin ya basu wuri.


Gaishe da Mommy sukayi cike da girmamawa.


"Wannan ce Aishar ko?" 

Bayan ta amsa gaisuwar tayi tambayar, tana mai nuna Aisha da ke rakub'e a baya ta sunne kai. 


"Ita ce mommy". 

Cewar Humairah suna mai murmusawa dukka.


Sai a wannan karon ya bud'e idanunsa dan ganin bak'in nasa.


Bai yi tsammanin ganinta a wannan lokaci ba, bai d'auka zai sake ganinta a rayuwarsa ba, ya d'auka ya rasata kenan har abada, ya d'auka ta barshi ta fad'a soyayyar zab'in mahaifinta.


Meh ya kawo ta? Shin tana sonshi? Wa ya sanar da ita rashin lafiyarsa? Tazo jaddada masa soyayyarta garesa? Ko dai tazo sanar dashi ya cireta a ransa ta zama mallakin wani? Ko dai an bashi ita babu maganar wani Nu'aim? 


Tambayoyin da yake jerowa kansa kenan idanunsa na kanta ya kasa ko da kiftawa. 


Muryar Mama da take yiwa Aisha iso wurin kujerar da ke gefensa shi ya dawo dashi hayyacinsa. 


"Bismillah, ku iso ku zauna".


Ficewa tayi daga d'akin ganin Aisha ta kasa sakewa kuma ta kasa zama a kujerar da take nuna mata.


Ala dole Humaira ta sa Aisha zama a kujerar da Mommy ta tashi. Mufeedah da Humaira kuwa suka zauna a kujerar bakin k'ofar.


Kanta a k'asa sai wasa da yatsunta da ta tsaya yi ta kasa furta komai, shi kuwa ya tsura mata ido ko kiftawa ba ya yi.


Caraf idanunsu suka had'e da ta d'ago dan kallon fuskarsa, ramar da yayi yafi komai d'aga mata hankali, yayi bak'i, duk ya canja kamanni, lallai yana cikin mawuyacin hali kamar yanda Fahad yace.


Hawaye ta ji ya cika idanunta.

Sauk'owarsu yayi dai-dai da gaisuwar da Mufeedah ke mik'a masa, hakan ya bata damar goge hawayenta dan ya kawar da dubansa daga gareta.


"Ina wuni".

Ta furta can k'asa bayan ya gama amsa gaisuwar Mufeedah.


"Pretty! na d'auka bazan k'ara ganin fuskarki ba".


Bakin k'ofar ta kai dubanta, ta ko yi sa'a hankalinsu baya wurinsu, bazasu ji maganar da sukeyi ba.


"Elmansoor, ka daina magana irin haka, kaga damuwar da kakeyi duk shi ya kawo ka nan".


"Kin damu ne? Kin damu da halin da nake ciki shine kika iya shareni?"


"Ya kakeso inyi? It's the best solution, though painful, but hakan ya dace inyi, nasan ka gane komai, kada ka kawar da kanka ga gaskiyar da kake gani".


"Na sani Aisha, I'm sorry, ki daina sa damuwa a ranki, kin rame kema sosai, meh yasa kika daina kula min da kanki bayan kinsan na baki amanar kula da kanki?".


Sauk'ar hawayenta ya sa zuciyarsa macewa, lumshe idanunsa yayi yana mai jin zafi sosai a ransa.


"I'm sorry Elmansoor".

Cikin sheshshek'ar kuka tayi maganar.


"Pretty, na warke, sosai na samu sauk'i, abunda kikeyi yanzu zai iya b'ata duk wani taimakon da nake samu daga wurin likita, you have to be strong, for us, Ina sonki, kuma in ke tawa ce babu abunda zai hanani samunki, ki daina sa damuwa a ranki".


Hawayenta ta goge tana mai gad'a masa kanta alamar yarda da kalamansa. 


"Kai ma ka daina toh".

"Meh zan daina? Kada kice in daina sonki, hakan na nufin mutuwana".


Bakinta ta turo tana kallonsa.

"Kuma yanzu a ganinka zan iya cewa ka daina sona? Har kake furta kalmar mutuwa akanka dan kawai nace ka daina?"


Yatsarta tayi anfani dashi ta dangwalo hawayen da ke gefen idanunsa. Nuna masa tayi ba tare da ta sake furta wata kalmar ba.


"Na daina, ke kika sani ai, in kina kuka wani tsoka daga jikina kamar ya tarwatse, bana son ganin hawayenki, yana sani inji na kasa yi miki abunda kike buk'ata, ban cika namiji ba nake ji na, ina susucewa in rasa meh yake min dad'i".


"Na daina nace kuma shine kana son ka sake sani wani kukan". Cike da shagwab'a tayi maganar tana turo bakinta.


"Bazan sake magana ba, tunda duk kalamaina kuka suke sa ki".


Shiru tayi, ta sauk'ar da kwayar idanunta k'asa.


"Aisha mu wuce ba, Baba kada ya dawo bai same mu a gida ba".


Kallonsa tayi sannan ta mik'e. Hannu ya d'aga mata yana mai yi mata murmushi.


"Ki kunna wayarki, i have alot to tell you. Please".

Cikin sanyin murya yayi maganar. Kad'a kai tayi sannan suka fice zuciyarta na samun nutsuwa.


~~~~~~~~~~ 


A bakin k'ofa suka ci karo da Fahad, murmushi ya sakar wa mutuniyar tasa yana mai tona sirrin da ke ransa.


"Har zaku koma? Sannunku da zuwa Aisha".


Ya k'arashe maganar yana mai kai dubansa gareta.


Murmushi tayi sannan ta mik'a masa gaisuwarta, ta rik'o hannun Humaira suka yi gaba suna mai barin Muneerah a gefensa.


A hanya suka had'u da Mommy sukayi mata sallama sannan suka wuceta tana k'ok'arin komawa d'akin d'an nata.


Har inda driver ke tsaye Fahad ya rakosu shi da Humaira, sai da suka ga tafiyarsu sannan suka koma ciki kowannensu da abunda ke ransa.


"Elmansoor kayi hak'uri, zan sanar dakai duk abunda ya faru, bazan iya b'oye maka ba, damuwan da kake ciki ya isa, in akwai hope zaka gane haka in babu, ka daure ka kai zuciyarka nesa, ba duk abunda bawa ke so yake samu ba".


Kalaman Mommy suka tsinkaya da suka shigo d'akin. 


"A'a Fatima, ba ke yakamata ki sanar dashi ba, ni ya dace in sanar dashi duk abunda na aikata, ni ya dace in furta kalaman nan masu d'aci garesa, bai kamata ki sa kanki cikin wannan ba".


Hawayen fuskarta ta goge idanunta manne fuskar d'anta wanda tun tafiyar Aisha ya lumshe idanunsa yana korar hawayen da ya tabbata zasu iya zubowa.


Babu wanda ya iya magana har Daddy ya gyara zamansa yana mai sauk'e ajiyar zuciya.


Cikakken Labari:-


Kamar yanda kuka sani, sunana Bala Muhammad Yuri, mahaifina cikakken d'an kasuwa ne, Allah ya bashi dukiya mai d'inbin yawa. Haifaffen garin Kano, matarshi d'aya wato mahaifiyata Hajiya Maryamerh. Mu biyu kacal Allah ya rayar cikin 'ya'yansu. Daga ni sai k'anwata, "FATIMA"


Soyayya da jin dad'i babu wanda bamu gani ba ta gun mahaifiyata da mahaifina, ban tab'a neman abu na rasa ba, haka k'anwata wacce ta kasance sanyin idaniyarmu. 


Irin rayuwar da na tashi yasa na yardarwa kaina duk abunda nake buk'ata toh ya samu ne, bana shakkar kowa bana tsoro.


Nayi makaranta a Cyprus, bayan na kammala na dawo gida Najeriya cike da d'umbin nasarori. Duk da rashin tsorona da rashin jina bai hanani karatu ba, na samu sakamako mai kyau. 


Dawowana kenan mahaifina ya bani company nawa na kaina halak malak, bayan haka ni ya barwa ragamar kula da duk wata hanya nasa na kud'i. A lokacin Fatima na Baze university a nan Abuja. Rayuwa tana tafiya yanda yakamata har bayan wasu shekaru, a k'alla shekaru hud'u, lokacin da k'anwata ta sanar dani akwai wani da take so kuma yana buk'atar isowa garemu dan a san dashi.


Daga wannan lokaci komai ya canja, komai ya d'auki wata hanyar da ni a sanina bamu tab'a samun kanmu a ciki ba.


~~~~~~~~~~~~~


Ya Rabbi 

Bani da bakin magana 'yan uwa. Kuyi min afuwa 


Bansan ta ya zan fara baku uzurina ba, abubuwan da yawa, daga ciki har da samun matsalar wayana, ya kama dole in canja, sai dai nafi kwad'ayin in kammala wannan kafin in sauya, hakan ke bani wahalar rubutu. 


Ayi min afuwa

addaummi naga sak'onki, rashin samun gamsashshiyar bayani ya hanani amsaki, naji kunya🙈 ayi min afuwa.


Toh ga dai chapter da ban tab'a yin mai tsawonsa ba. Almost 2500words😄 Lubbatu_Maitafsir zata ce ban k'ok'arta ba😂 amma ayi hak'uri, shafuka kad'an suka rage mana.


Toh ga wata Fatimar, k'anwa ga Yuri, shin dama ba matarsa Abdullahi ya nema ba??


Ko dai akwai wata b'oyayyar al'amari da bamu kai ga sani ba?


Fahad da Mufeedah an shirya, shin k'arshen fad'an nasu kenan?


Nu'aim fa, wani magana yake son yi da Aisha? 


Shin Abba zai sassauto ya yarje wa masoyan nan samun burin zuk'atansu?


Muna daf da samun dukkan amsoshinmu, comment 

Like

And share.

Nagode matuk'a.


1love

Maryamerhabdul


"Ban amince da wannan auren ba Abba, ya zata kawo mana mutum irin wannan matsayin surukin gidan nan? Bai dace damu ba, sanin kanta ne ko aiki cikin gidan nan bai dace dashi ba bare ya zama suruki garemu".


"Akan meh? Shin kayi binciken nan yanda yakamata Bala? Yana da takardar digiri kake had'ashi da ma'aikatan gidan nan da ko sakandare da wuya suyi?"


Kad'a kai nayi cike da b'acin rai, ni ina ma na tsaya sauraron wani k'arin bayani game dashi? Iyaka abunda nakeson ji game dashi naji, shi ba d'an kowa bane, mahaifinsa ya dad'e da mutuwa, kasancewarsa d'a na fari rayuwa tayi musu tsauri, k'annensa uku da mahaifiyarsu na k'ark'ashinsa, ina da tabbacin wannan kwalin digirin da wuya ya samo ta, dan aiki mai kyau bayi dashi ina sane da hakan.


"Bala, sanin kanka ne kuna da gurbi mai girma a wurina, yaron nan iya bincikena banga wani aibu tattare dashi ba, yana da hankali, yana buga-buga bai zauna zaman banza kamar yawancin samarin yanzu da suka dogara da aikin gomnati ba, bai samu aiki ba yana da business d'insa yana samun wadatacciyar dukiya mai tsafta. In sana'arsa yayi maka kad'an ka manta irin d'umbin naka dukiyar? Shin in baka taimaka masa matsayin surukinka ka basa aiki cikin kanfanoninmu ba wa zaka taimakawa? Ban taso dakai da wannan zuciyar ba, kayi tunani tun kafin ka tarwatsa farin cikin k'anwarka".


Iska na furzar ina kawar da kaina. Aikin gama ya riga ya gama, na sanar da Fatima shawarar da na yanke, sai dai komai ya faru amma bazan yarje mata ta auri wahala ba, bazan yarje mata tana da takardar masters ta k'are da wanda yake da digiri ba, bazan yarje mata ta zame miji shi ya zama mata a cikin gidan aurensu ba, ina da tabbacin hakan yake da niyyar yi muddin ya aureta, komai na gidan bar mata zaiyi, ni wani irin hali ne na talaka wanda ban sani ba? Ai talaka daga farkonsu har k'arshensu babu wani hali nasu da ban sani ba, sabo ne ko tsoho.


Ban sake yi masa magana ba na fice daga parlonsa, kai tsaye na koma wurin Fatima da har yanzu take yiwa Umma kuka, a nan na jaddada mata babu ita babu wannan saurayi nata, in kuma ta d'auka wasa nake aikin nata da take matuk'ar so zan hanata zuwa.


Bai dameni ba, saboda ban tab'a samun kaina cikin soyayyar wata d'iya mace ba, ban tab'a soyayya wanda za'a k'irasa "eh wannan shine soyayya ba". Na dai san rayuwar kowani d'a namiji akwai 'yan matan nan da wani lokaci zakayi maganar soyayya dasu, wanda a zahirin gaskiya babu wani d'igon soyayyarta a cikin zuciyarka.


Ana cikin wannan wata rana na samu k'ira da bak'uwar lamba, kamar bazan d'auka ba wani zuciyar ya ingiza ni na amsa na kara a kunnena. 


"Baka da kirki Bala Yuri".

Muryar kenan da naji wanda ko bai sanar dani shi waye ba, na ganesa.


Dariya nayi ina mai nuna tsantsar farin cikin jin muryarsa.

"Na karb'a abokina, kai ne kuwa? kana nan?".

"Ka min shiru! ka tafi makaranta na maka uzuri, amma ka dawo kayi shekaru muna Nigeria ka kasa nemana? Haka zamuyi da kai Bala?".


"Kayi hak'uri, nayi laifi, dole inzo baka hak'uri har gida".


"Bazan yarje maka kazo gidana ba, bana tarban tuzuru a gidana gaskiya".

Cike da tsokana yayi maganar, hakan yasa muka shiga barkwanci irin yanda muka saba.


Hamza kenan, tare mukayi sakandare, na tafi Cyprus shi kuwa ya kammala karatunsa a nan Kano. Rabona dashi a k'alla shekaru shida zuwa bakwai.


Anan yake sanar dani ya fara aiki a BUK, muka sa ranar da zan kai masa ziyara ganin amaryarsa da kuma d'ansa guda d'aya.


~~~~~~~~~~~


Ban samu na kai ranar da muka yanke ba tafiya mai muhimmanci ya sameni, hakan yasa na k'irasa na sanar dashi a yau zan bar gari, ala dole yasa ni zuwa cikin makarantar BUK dan mu had'u ko na mintuna ne kafin in tafi, a cewarsa in na tafi shikenan ba ranar had'uwa, duk da na tabbatar masa tafiyar na kwanaki biyar ne zuwa shida.


Da misalin k'arfe uku na shigo harabar makarantar. Kai tsaye na isa inda ya kwatanta min na ajiye motana.


A waya na sanar dashi isowata na katse wayar ina kallon d'aliban makarantar na giftawa. Babu mai iya ganina sakamakon tint d'in da ke manne da gilasan motar da nake ciki.


A d'an nesa dani na hangosa, hakan yasa na bud'e motar na fito ina mai d'aga masa hannu. 


Isowarsa gareni yayi dai-dai da giftawarta, sanye take da atamfarta kalar ruwan madara da hijabi. Fuskarta fayau yake ba kwalliya amma kyawunta ya d'auke min tunanina, ban san dalili ba, haka kawai naji zuciyata ya tafi akanta.


"Hey yallab'ai, ya dai ko musafahar ma an daina karb'a ne?"


Muryar Hamza ne ya dawo dani daga duniyar da na lula, ban biyewa shak'iyancinsa ba na cafe hannunsa ina mai juyasa dan ya ga yarinyar kafin ta b'ace wa ganina.


"Kasan yarinyar nan? Yau nayi sa'an shigowa makarantar nan, dan Allah kada kace baka santa ba".


"Ai kuwa kazo gidan sauk'i, anguwanmu d'aya, Fatima sunanta, sai dai gaskiya in ba auranta zakayi ba bazan tab'a had'aka da ita ba, yarinya ce me hankali, nutsuwa da addini".


"Dan Allah bani layinta, ban tab'a ganin mace karo na farko naji ta burgeni ba sai wannan, ina ka sani ko ita ce matar tawa? Zuwana BUK ya min rana".


Motar muka shiga dukka muka cigaba da tattaunawa, a nan yake sanar dani bayi da layinta amma zai nemo min, bai b'oye min akan cewar Fatima na da saurayi wanda ake sa ran shi za'a bawa ba, dan sun fahimci juna. Ban d'auki hakan da muhimmanci ba dan banga laifi a ciki in kowa ya gwada sa'ansa ba.


Kafin in tafi sai da na bada assignment na binciken komai game da Fatima. 


Kwanaki biyar kacal na dawo, an samo min komai da na buk'ata akanta kafin dawowana, unguwarsu, number wayanta, infact har halayenta da na wanda take zaune wurinsa wato k'anin mahaifinta. 


An tabbatar min iyayenta sun rasu, tana zama ne tare da uncle nata. Hatta saurayinta sai da aka nemo inda yake, anguwarsu d'aya a wancan lokacin, shine silar shiganta BUK dan ta jirasa ya kammala nasa makarantan sannan ayi musu aure kamar yanda suka tsara.


Ban damu da jin labarin soyayyarta da wani ba, a ganina in na tunkareta da soyayyata zata yadda ta aureni, nafi saurayinta kud'i, ilimi kai komai ma na fi sa, sai dai kash kud'i da duk wani abu da nake tunk'aho dashi bai dameta ba, burinta ta cika ma saurayinta alk'awarin da ta d'auka masa. 


Ta watsa min k'asa a ido, ta tabbatar min babu wanda zata so sai Abdullahi Nemi. 


Abdullahi Nemi mahaifin Aisha shine wannan saurayin nata. Nayi iya k'ok'arina dan yarinyar ta yadda ta aureni amma fir ta k'i, bansan ya akayi na kasa cireta daga zuciyata ba, ta ko wani hanya nayi k'udurin samunta, ban damu da talaucinta ba, ban damu da komai ba, burina in samu Fatima mai hankalin da ban tab'a ganin wata d'iya mace ma da shi ba.


A dalilin fad'awata soyayyarta na yarjewa Antynku Fatima ta auri mijinta har na bashi aiki a d'aya daga cikin kanfanoninmu, kuma har wa yau banyi da na sanin amincewa da aurensu ba.


Fatima mace ce mai rik'e amana, ganin bazata sake wannan saurayi nata ba nayi tattaki zuwa wurin Uncle nata, da shirina naje wurinsa, dan halayensa na son kud'i a tafin hannuna yake, sai da na cika sa da arziki na sanar dashi buk'atata. Bai bani wahala ba ya yarje min in turo magabatana dan ayi mana aure.


Da naje na samu iyayena da maganar sunyi murna sosai, ba tare da wani b'ata lokaci ba suka nema min aurenta, banyi gigin sanar dasu ba da yardar yarinya ake wannan shagalin ba, dan da mahaifina ya sani bazai tab'a yarda a tauyewa Fatima hakk'inta ba.


An bada sadaki sannan aka sa ranan aure wata biyu kacal ba tare da sanin yarinya ba. Sai da aka gama komai sannan uncle nata ya sanar da ita. 


Tashin hankalin da ta shiga ita da Abdullahi ba abun so bane, daga shi har ita sunyi kuka kaman yanda Elmansoor yakeyi a yanzu, Abdullahi ya k'irani a waya dan in janye aurenta amma nak'i, yaje har office na koresa, ba sau d'aya ba, ba sau biyu ba ina koransa bayan na jefesa da bak'ak'en maganganu ina sanar dashi bai dace da Fatimana ba.


Abdullahi bai saduda ba, ya sauk'ar da kai ya rok'eni kamar ransa ne a hannuna in na murk'ushe ya rasa rayuwarsa, a hakan na k'ek'ashe na masa rashin mutunci nasa aka fice dashi daga harabar office d'ina a karo na hud'u.


Makonni biyu ya saura a yi biki na tsinkayi muryarsa a harabar gidana, ban tsaya na saurareshi ba nayi masa rashin mutuncin da ni kaina ban d'auka zan iya yiwa mutum ba, nasa masu gadi su dakesa kuma su jefarshi waje kada su sake barinsa ya shigo min gida.


Wannan shine ganina na k'arshe da Abdullahi, sai bayan aurena da mahaifiyarku take sanar dani halaccin da yayi min. 


A lokacin da yazo gidana nasa akayi masa duka Fatima ce ta nemi da su gudu suje ayi musu aure tunda nak'i janyewa, bai zo da niyyar rok'ona dan in janye batun aurena ba, yazo ne dan ya sanar dani abubuwa masu muhimmanci game da Fatimar da na kwace masa, yazo ne ya sanar dani ya janye k'udurinsa, in rik'eta da amana dan ta cancanci hakan.


In tak'aice muku komai, Abdullahi shi ya bawa Mahaifiyarku k'arfin gwiwar zama dani, ya tausashi zuciyarta ta amince dani matsayin mijinta take min biyayya daidai gwargwado.


Wannan shine abunda ya faru shekaru ashirin da shida da suka gabata.


~~~~~~~~~~~~~~~~


"Akwai wani da nake tare dashi, amma Abba bai so".


Idanunta cike da kwalla ta fad'i wad'annan kalmomi masu nauyi. 


"Kayi hak'uri ya Nu'aim, banga anfanin sanar dakai bane shiyasa, banyi dan in b'ata maka rai har haka ba".


Idanunsa ya d'aura akanta, zuciyarsa ta murd'a ganin yanayin da ta shiga, bai d'auka nuna b'acin ransa akan k'in sanar dashi gaskiya zai mayar da ita haka ba, shin tsoronsa taji? Ko kuwa sonshi ta fara da har damuwarsa ya iya sata cikin wannan halin?


Mik'ewa yayi daga mazauninsa yana mai kawar da tunaninsa. Yawu mai tauri ya had'iye 


"Ki daina kukan nan, matsalata bai wuce k'in sanar dani gaskiyarki ba, nagode da kika sanar dani hakan, duk da a tak'aice kika min na gane abubuwa masu yawa. Zanyi magana da Abba, zakiji shawarar da na yanke daga garesa".


Tashi yayi ya fice daga parlon, bata kai ga mik'ewa daga mazauninta ba taji muryarsa.


"Tare zamu tafi Kanon? Ko inyi wucewata?"


"A'a, zamu fara lesson na NECO bazamu samu zuwa yanzu ba sai bayan mun kammala jarrabawarmu".

"Ok" kawai ya furta. 


~~~~~~~~~~~~~~


   Yau kasancewar Lahadi Abba na gida tare da iyalinsa. A kowani mako yana ware lokaci na musamman dan samun lokacin iyalinsa.


Shigowarsa d'aki ba da dad'ewa ba Mama ta biyo bayansa ta sanar dashi yayi bak'o kamar yanda mai gadin ya sanar da ita. 


Ta window ya lek'a bak'on nasa, ya bata daman a isar da bak'on parlor. Shima parlon ya wuce murmushi manne a fuskarsa.


Da sallama daddy ya shigo yana mai lullub'e fuskarsa da murmushi dan b'oye fargaban da yake zuciyarsa. 


Sallamar Abba ya amsa ya tashi daga mazauninsa murmushi bai bar fuskarsa ba.


"You are highly welcome, ashe kai d'in ne". 


Hannunsa ya mik'a masa fuskarsa bai b'oye tsantsar farin cikinsa ba. 


Duk da Daddy ya sha jinin jikinsa matuk'a ganin irin tarban da Abba yayi masa bai hanasa fad'ad'a nasa murmushin ba had'e da had'e hannayensu wuri guda. 


"Ni d'in ne kuwa, na sameka lafiya?"

"Lafiya k'alau! Bismillah".

Kujera ya nuna masa ya zauna sannan shima ya koma mazauninsa.


Cikin girmama juna suka shiga gaisuwa fuskokinsu a sake. Da sallama Mufeeda ta shigo d'auke da tray, a gabansa ta ajiye sannan ta duk'a ta gaishesa cikin kunya. Bayan ya amsa ta mik'e ta fice ta basu wuri. 


Shiru ne ya d'an gifta na wasu mintuna bayan ficewarta.


"Nasan kayi mamakin ganina koh?"

Ya furta bayan ya sauk'e numfashi.


"Ko kad'an" ya fad'a fuskarsa a sake

"ai nayi expecting zuwanka ba tun yau ba, sai kuma ka jinkirta". 

Idanunsa na kan Daddy yayi maganar.


Rashin amsawar Daddy ya sa shi gyara zama ya cigaba da magana.


"Ya jikin Elmansoor? Naji bayi da lafiya har ya kwanta asibiti?".


Yawu Daddy ya had'iye yana jin sanyin d'akin na kafewa. can ciki ya iya fad'in 

"Da sauk'i, har an sallamosa gida".


Kallon Abba ya dakata yi ganin yana girgiza kansa.


"Ntsa! Ntsa!! Ntsa!!! Har an sallamosa? Ko da yake soyayyar Elmansoor ga Aisha bai kai Soyayyar Abdallah ga Fatima ba".


Cikin dakewa ya k'arasa maganar.


"Sati biyu, sati biyu Alh. Bala na kwanta asibiti dalilin rashin Fatima da kuma rashin imaninka, shekaru uku da d'oriya nayi jinyar rashinta a rayuwata, Allah yaga zuciyata ya aiko Asma'u rayuwata, tayi anfani da kwanyarta da iliminta na d'iya mace ta cire min wannan rad'ad'in da ka shuka min. naso ka d'and'ana kaji yanda zafin rashin masoyi yake Bala, amma ban rok'a maka hakan ba, na duba aljannar Fatima da take nema wurinka na kawar da son zuciya dan ta samu lahira ko da bata samu duniyar ba, which I'm sure ta samu duniyar ma a yanzu".


"Na fahimci dukkan abunda kake nusar dani akai Abdullahi, nazo ne dan in nemi afuwarka, nayi laifi na sani, hakan yasa nazo dan ka duba hukuncin da ka yanke wa yaran nan. kayi hak'uri ka hukuntani ba wai ka hukunta 'ya'yan da tun kafin halittansu komai ya wakana ba".


Murmushi mai sauti Abba yayi yana kad'a kai, zuciyarsa na k'ara bak'i dan tuna abubuwan da ya faru a baya.


"Kazo nan saboda d'anka? Soyayya ce ke damun d'an naka ko? I went through this Mr. Bala, d'anka zai iya warkewa daga wannan cutar, na son matar wani kaman yanda nima na warke. in bazaka damu ba, lokacin iyalina ne yanzu, zaka iya tafiya, kuma Nagode da ziyara".


Tashi yayi daga mazauninsa ya fice ba tare da ya saurari kalma d'aya da Daddy yake son furtawa ba. 


Shi kuwa kansa ya sauk'ar k'asa yana mai da na sanin aika-aikar da yayi, laifinsa d'aya da yayi anfani da k'arfin ikonsa a wancan lokacin ya samu abunda yakeso, dad'insa d'aya Fatima ta kai ayi hakan akanta, bazai tab'a da na sanin aurenta ba.


Bayan wata d'aya


  Alh. Bala Yuri zaune bisa kujeran palonsa yayi zurfi cikin tunani. shigowar Mommy bai sa ya dawo daga duniyar da ya lula ba har sai da ta iso daf dashi had'e da yi masa magana.

"Lafiya?"

Zama tayi a gefensa tana mai karantar yanayinsa.


"Na koma wurin Abdullahi, yau sawuna uku a gidansa, babu wani improvement fa, yanzu haka mahaifin Fahad ne ya k'irani, cewar ansa auren Mufeeda da Aisha wata biyu, da sun gama NECO kenan".


"Innalillahi wa Inna ilaihi rajiun"

Idanunta tuni suka kawo ruwa

"Ya zanyi da Elmansoor? Ya zamu fara sanar dashi auren yarinyar da ya k'wallafa rai akai? Yaushe na samu hankalinsa ya fara dawowa garesa? Ka tuna jiya nake sanar dakai Elmansoor ya ci abinci sau uku a rana yazo wurina munyi hira? Duk zan sake rasa wannan kenan".


Hawayenta tasa hannu ta goge

"Ya Abdullahi zai min haka? Ban sanshi da irin wannan halin ba".


Kallonta Daddy yayi bai iya furta komai ba. cikin muryar kuka ta cigaba da cewa "muje wurinsa, ni zan rok'esa, zan rok'i ya taimakawa jinina Elmansoor, ina son farincikinsa, ina son ya samu Aisha, ita ta dace dashi, ka taimaka ka bani izinin zuwa wurinsa".


"Fatima wannan ma bata taso ba, tsorona kada Elmansoor yaji labarin auren nan. Ni nasan yanda zanyi in shawo kan lamarin, amma ya zama dole mu guji sanar da Elmansoor".


"Duk abinda ya dace ayi ya kamata mu yi shi kafin yaji, in mu mun 'boye masa ai ba dole duniya ta b'oye masa ba. Yanzun ma wa ya sani ko yaji?".

Ta k'arashe maganar wasu sabbin hawaye na sauk'o mata.


"Haba Fatima, ya zaki k'ara min zafi akan wanda nake ciki, ki daina kukan nan, ki sanar dani yanda kikeso muyi".


"Muje wurin Abdullahin, in kai baka masa yanda yakeso ba ni zanyi, amma ya bar yarannan suyi aure".


"Ba fa zan yadda da zuwanki wurinsa ba, ya zakije wurinsa bayan kin san abinda ya faru? So kike ya koma sonki Elmansoor ya rasa ni in rasa? Bazai yu ba".


Kuka ta fashe dashi wanda har ranta take jin maganar na sukanta, wani irin tunani ke kansa? Tun da Abdallah bai raba su ba sai yanzu da shekaru ya ja? 


Kukan da ta shiga yi yasa shi cewa "ki tashi ki shirya mu tafi, amma ban yadda ko kallonsa kiyi ba, kuma ban yadda ki sa mayafi ba, hijabi zaki sa, ina wannan da na kawo miki satin da ya gabata kikace yafi sauran hijabanki tsawo da kauri? Shi zaki sako muje, in kinje kin kasa ai kya barni in huta".


Bata amsa shi ba ta mik'e ta wuce shirinta. kaman yanda ya sanar da ita hakan ta yi, fuskarta kawai ta wanke ta d'auko hijabin ta maka ta dawo d'akin dan sanar dashi ta gama shirinta.


~~~~~~~~~~~~


   Fahad kanshi juyawa yake jin maganar da mahaifinsa yake masa. Bai tab'a d'auka zai samu kansa cikin wannan yanayin ba in yaji sa ranansa da Mufeedarsa, ya d'auka farinciki zaiyi dan mafarkinsa ya kusa kasancewa gaskiya.


D'ago kansa yayi ya kalli mahaifin nasa.

"Baba yanzu ba yanda za'ayi a d'aga bikin nan?".

"A d'aga kuma? Baka shirya bane? Ko baka ji meh nace maka ba? Mahaifin yarinya ya nememu dan musa rana, kuma mun zauna tare mun zab'i ranan da ya kwanta wa dukkan fanni ba tare da takura ba". 


"Amma Baba ni da Elmansoor ke neman..." 

"Kaga Fahad, kaje ka fara shirinka in ma baka fara ba kenan, dan babu yanda za ayi mu d'aga. Mahaifin yarinya yana so a had'a auren yaransa biyu Aishatu da Mufeeda, da wata d'aya ya nema ayi biki muka nemi k'arin wata guda ya zama biyu, da bakinmu muka ce mun amince bazamu koma muce a d'aga ba, mijin d'ayar yana son ayi auren da wuri ba tare da an b'ata lokaci ba, kuma mu ma mun amince a had'a. ka tashi ka tafi, hakk'inka ne in sanar dakai kuma na sauk'e, Allah ya kaimu lokacin lafiya".


Sum-sum ya mik'e jiki a sanyaye ya bar d'akin, tunanin Elmansoor da Aisha fal ransa.


Wurin motarsa ya isa yana mai lalubo layin Mufeeda a wayarsa, sai da ya zauna a mazaunin driver sannan ta d'auki wayar.

"Mufeen Fahad, meh nakeji yanzu?"


"Yanda kaji nima haka naji, Aisha ma aure zatayi". 

Kuka ta fashe masa dashi 

Bai iya magana ba jin irin kukan da takeyi. 


Idanunsa ya lumshe yana mai ambaton sunan Allah.


Cikin sanyin murya ya k'ira sunanta.

"Mufeeda, kukan da kikeyi shi zai gyara komai? No, right? Ki daina kukan nan kiyi musu addu'a, inshaAllah everything will be fine".


Cikin sheshshek'a ta iya amsa shi da toh.

"Kun fad'awa Elmansoor?"

"Um-um"

"Ina Aisha?"

"Gata nan, tun d'azu ina fad'a mata ta daina kuka amma tak'i dainawa, bansan ya zan mata ba".


Cikin kuka tayi maganar, da alama halin da Aisha ke ciki yana matuk'ar d'aga mata hankali.


"Now listen, ke yakamata ki bata k'arfin gwiwa, in kika tayata kukan wa zai bata hak'uri? Ko so kike ni inzo kina yi ina baki hak'uri sai na gama dake sannan mu koma kan Aisha?"


"Um-um, na daina. Bansan ya zan sa tayi shiru ba, dan duk wani abunda zan fad'a mata ba ganewa zatayi ba".


"Talk to her yanda ya dace, ki tuna mata dukkan abunda aka sanar dake a islamiya akan yadda da k'addara, kinji ko? Ki tunosu dukka Mufeeda".


"umm" tace sukayi sallama ya katse wayar ya tada motar ya fice.


Gidan su Elmansoor ya mik'a yana danna masa k'ira. Ringing biyu ya d'auka,


"Kamar kasan kai nake da niyyan k'ira yanzu. Ina key na wannan drawer d'in ne? Nazo office d'aukan files d'in nan na tarar a kulle kuma babu key inda muke ajiyewa, ina ka ajiye?"


Bugun da zuciyarsa yakeyi ya lafa sakamakon jin yanayin abokin nasa, tsoronsa da fargabansa bai wuce Elmansoor ya samu labarin da shi ya ji a yanzu ba.


"Gani nan zuwa office d'in".


Katse wayar yayi ya karya kan motar zuwa ofishinsu.


Isowarsa yayi dai-dai da shigowar sak'o wayar Elmansoor. Musafaha sukayi ya koma mazauninsa yana mai danna wayarsa dan karantar text message d'in da ya isosa daga mutum mai muhimmanci a garesa.


Lokaci d'aya yanayin fuskarsa ya sauya, idanunsa ya canja launi. A hankali ya lumshe idanunsa cikin mutuwar jiki ya ajiye wayar a teburin da ke gabansa.


"Ga key d'in"

Cewar Fahad a karo na biyu yana kallon abokin nasa.


Sakanni masu yawa sannan ya iya bud'e idanunsa, bai iya d'agowa ya kalli Fahad ba bare ya karb'i makullin, sai ma damk'e hannunsa da yayi wuri guda yana jin zuciyarsa na barazanar tarwatsewa.


~~~~~~~~~~~~~~


Da misalin k'arfe biyu da rabi motarsu ya isa gidan Abba. Mai gadi bai basu damar shigowa ba dan Abba baya nan.


A waje sukayi parking suna jiran ya sanar da matar gidan kaman yanda suka nema.


Mintuna uku ya dawo ya bud'e musu gate ya basu daman shigowa.


Mai gadin ne ya jagoranci Mommy cikin gidan, Daddy kuma ya shige parlor kaman yanda matar gidan ta sanar da mai gadi yace masa.*


**********


Bani da bakin magana... Ayi min uzuri, ni nasan meh laifi ce. Ga 3599 words, ban tab'a dogon shafi irin wannan ba. A gurguje nakeson mu ida labarin. 


Shafi d'aya tal ya rage mana da yardar Allah.

Thank you so much for reading

Jazakumullah

Iloveyou all fisabilillah.


"Nan ne k'ofar Hajiya".


Yayi mata nuni da hannu yana mai d'an rusunawa.


Fad'ad'a murmushinta tayi, ta mik'a masa naira dubu d'ayar da ke hannunta.


"Nagode" 


Ta mayar masa, tana mai matsawa gefe dan bashi hanyar wucewa. Sai da yayi godiya ya wuce sannan ta samu damar shigewa ciki zuciyarta na bugawa.


A bakin k'ofar ta tsaya, ta danna k'ararrawar da ke mak'ale gefen k'ofar.


Ba a d'auki lokaci mai tsawo ba taji muryar Mufeeda na tambayar wanene mai buga musu k'ararrawa.


"Nice!"

Ta furta cikin sark'ewar murya da tunanin shin zata gane muryarta ko kuwa?


K'ofar ta bud'e jin muryar mace. ganin Maman Elmansoor yasa ta sunne kai leb'b'anta na rabewa da juna, murmushi ya karad'e fuskarta.


"Sannu da zuwa, bansan ke ba ce shiyasa ban bud'e da wuri ba".


Murmushi Mommy ta mayar mata tana mai shigowa ciki.


"Ba komai, Maminku na ciki?"


Ta tambaya bayan ta shigo Mufeeda ta rufe k'ofar.


"Eh, bismillah bari in kai ki wurinta".


Gaba ta shiga Mommy na binta a baya har zuwa k'aramin falo. Ta ajiyeta a nan tana mai sanar da ita zata sanar da mama isowarta.


Mama bata fito ba sai da aka kawo ma Mommy ruwan sha da kayan marmari. Da murmushi a fuskarta ta fito, hannunta rik'e da awarwaronta da ta cire lokacin shiga ban d'aki.


Kamar sun san juna suka shiga gaisuwa, kowacce fuskarta a sake.


"Tare da Baban nasu muke, an shigar dashi can falon. Mai gadi ya sanar damu mai gidan baya nan, muka ce bari mu jirasa kawai tunda munzo".


Ta furta bayan shiru ya d'an ratsa tsakani. Idanunta na kallon kafet da ke tsakiyar falon tayi maganar.


Murmushi ne saman leb'b'anta, sai dai fuskarta da yanayinta ya nuna b'oye sirrin zuciyarta takeyi da wannan murmushi.


Mama cike da fara'a ta amsata, fuskarta a sake, muryarta na fitar da wani amo wanda ita kad'ai ta san sirrin.


"Yanzu na k'irasa na sanar dashi zuwanku, yana ma gaf da gida ya sanar dani..."


Bata idashe maganar ba k'arar motarsa ya doki kunnuwansu.


"Gashi nan ma ya iso".


Ta mik'e tana isa ga k'ofar da zai sadata dashi.


Mintuna biyu ya iso gareta murmushi bisa leb'b'ansa. 


"Uwar gida ran gida!"

Ya furta yana mai mik'a mata jakar hannunsa.


Cike da farin-cikin ganinsa ta karb'a tana mayar masa martanin murmushinsa.


"Yau kuma da zolayan ka dawo? Kana dai da bak'i kada su jiyoka bayan farin gashi ya kusa mamaye gashin kanka".


Kusa da ita ya matso yana mai jin dad'in yanda ta biyewa wasarsa a yau.


"Kuma a hakan kike k'ara sona ba"


Bai jira cewarta ba ya shige ciki yana mai dariya k'asa-k'asa.


"Ga fa d'ayar bak'uwar taka kafin ka isa ciki".


Nisan da yayi mata yasa ta d'aga murya yayin fad'an hakan. Amonta ya canja, farin-ciki ko akasin hakan kai tsaye bazaka iya canka ba.


Kallonta yayi daga bisani ya kai dubansa kan kujerar da Mama ke kallo tana mai b'oye fargabanta cikin murmushi.


Annurin fuskarsa tuni ya d'auke ganin matar da bazai tab'a mantawa da kamanninta ba, matar da a duk lokacin da ya tunata yake jin zuciyarsa na karaya.


Matar da yayi burin samu a duniyarsa, matar da aka k'wace masa k'arfi da yaji aka hanasa samun muradin ransa.


Dad'insa d'aya, ya samu sanyin idaniya a garesa, ya samu sauyin rayuwa daga wurin matarsa, ta goge masa tabon da ya dad'e yana fama dashi...


"Ina wuni?"

Yaji amon muryarta cikin sigar tambaya.


Kawar da kansa yayi gefe yana mai dawo da tunaninsa wuri guda.


"Lafiya k'alau"

Ya furta cikin dakewa.


"Kwana da yawa Fatima? Ya yaranki da kuma mijinki?".


Hannayenta take wasa dasu, zuciyarta na matuk'ar bugawa.


Cikin sark'ewar murya ta lalubo kalamanta

"Komai lafiya alhamdulillah, tare dashi muke, yana ma falo..."


Bata kai aya ba ya juya yana cewa

"Ok, gani nan fitowa. Maman Aisha kawo min jakar nan".


~~~~~~~~~~~~


   "Ansa ranar aurena, kayi hak'uri... It's over(ya k'are). Goodbye Mr. Elmansoor".


Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un yake nanatawa a ransa.


Kallon Elmansoor yayi jikinsa babu lakka. wayar ya ajiye akan table d'in cikin rashin sanin abun yi.


Bai kai ga furta wata kalma ba wani sak'on ya shigo. Elmansoor bai d'ago kai ba bare yayi niyyar dubawa, ji yake babu wata sauran rayuwa da ta rage masa.


Jinsa yake a wani duniya da babu mahaluk'in da ya tab'a zuwa sai ma'aboci so da ya rasa muradinsa, idanunsa yaji suna dishi-dishi, hakan yasa shi lumshe idon hawayen da ke rufe masa gani suka zubo.


"Assalamu alaikum, kazo gida yanzu ina buk'atar ganinka. Abban Aisha".


A fili ya karanta masa sak'on, sai dai hakan bai sa Elmansoor motsawa ba, bai sa shi jin cunkushewar zuciyarsa ya watse ba, sai ma k'ara cunkushewa da yayi.


Dafasa Fahad yayi yana mai neman magana d'aya da zai iya yi masa wanda zai kawo nutsuwa ga ruhin amininsa.


"insha Allah alkhairi ne Elmansoor. Ka tashi muje wurinsa, ka yawaita yin addu'a, ka sani duk wani jarabawar da Allah ya mik'o setinka yana tattare da alhairinsa, baya hana bawansa abu sai ya basa wani mafi alhairi a duniyarsa da kuma addininsa."


Numfashi ya sauk'e yana matse hannunsa a jikinsa dan basa k'arfin gwiwa.


"la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin, a kullum ina baka shawarar yin wannan addu'an, ba dan komai ba sai don falalar da yake tare da ita. Addu'an da annabi Yunus yayi kenan lokacin da yake cikin kifi, Annabi Muhammad S.A.W yace "duk wanda ya lazimci karanta wannan addu'ar Allah zai amsa masa buk'atunsa" in farin ciki kake nema, mata ta gari, aiki mai kyau ko 'ya'ya, ka lazimci yin wannan tare da jero buk'atunka".


Hawayen da ke fuskarsa ya goge, ya d'ago rinannun idanunsa yana kallon abokinsa, aboki na kwarai wanda yana da tabbacin yayi dace a irin wannan zamanin da muke ciki.


"Ka yawaita kalmar shahada, ka yawaita istigfari, istigfari na kankare zunubi, kuma k'arancin zunubi na sa amsar addu'a. Elmansoor! Bayan addu'ar da zaka yi inason ka yadda Allah ne kad'ai zai biya maka buk'atarka, sannan ka yadda da k'addara, duk yanda Allah ya sauk'o maka dashi, ka karb'a hannu biyu kayi hamdala dan ni'imominsa da yawa garemu, kuma baya d'aurawa bawa abunda bazai iya d'auka ba".


Hannunsa ya d'aura akan na Fahad da ke kafad'arsa, yana mai jin dad'in kalamansa.


Bai iya furta komai ba sai murmushin da yake yi masa, hakan bai ishesa ba, ya mik'e ya rungumesa hawaye na cigaba da sauk'a a kumatunsa.


"Nagode, Allah ya biyaka da mafificin alhairi, ka yarda dani ina matuk'ar sonka kuma ina alfahari dakai".


Bayansa Fahad ya shafa shima cikin jin dad'i, daga bisani ya furta masa kalamansa na k'arshe.


"Mu tafi gidan nasu, nasan kana da dauriya, Allah ya baka ikon cinye wannan jarabawar, muna tare dakai duk rintsi Elmansoor".


Dan kansa ya sake sa daga cikin rik'onsa, ya zaro tsummar da ya gani cikin aljihun Fahad yana mai goge fuskarsa.


~~~~~~~~~~~


   "Assalamu alaikum!" 


Muryar Nu'aim ne ya karad'e falon, sakamakon shirun da kowannensu yayi suna jiran bak'in da Abba ya sanar dasu suna zuwa.


Duk sun hallara cikin falon, ciki juwa harda yaransa Mufeeda da Aisha. 


A tare suka amsa sallamar ya shigo cikin girmamawa ya tsuguna ya gaishesu.


Ba sai an sanar dashi sabbin fuskokin da ya gani ba, ya ganesu daga kallo d'aya, musamman mahaifiya ga abokin takararsa.


"Saura d'aya da nake saurare, ku k'ara hak'uri dan komai ya tafi dai-dai a idon kowa".


Cewar Abba da yake magana cikin kwanciyar hankali.


Mintuna biyar sallamar Fahad ya doso su, amsawa sukayi sannan suka samu damar shigowa.


Mamaki kwarai ya bayyana a fuskarsu, ganin iyali biyu na zaune wuri guda, abunda ba'a tab'a yi ba.


Zama sukayi cikin sanyin jiki suka kwashi gaisuwa. Sai da kowa ya nutsu aka gabatar musu da abun sha sannan Abba ya gyara zama yana mai ajiye wayarsa da ya duba.


"Toh gasu nan kowa ya hallara, ayi maganar gaban kowa, mai laifi a basa laifinsa mara laifi ma a basa sai kowa ya watse a wuce wannan babin".


Cikin dakewa yayi maganar, yana kallonsu d'aya bayan d'aya.


Hakan ya k'ara hautsina kayan cikin Elmansoor da Mommynsa da take ji kamar ta gudu ban-d'aki, idanunta yayi rau-rau tana kallon d'anta.


Nauyayyar numfashi Daddy ya sauk'e, cikin sanyin murya da alamun sauk'ar da kai ya fara magana.


"Abunda ya kawo mu dai bai wuce bada hak'uri akan abunda ya gabata ba, na san nayi kuskure kuma na duk'ar da kai na nemi afuwa a wurinka. Na yi iya k'ok'arina dan in nuna maka tsantsar nadamata amma ka kasa fahimtana, a yau dai gani na kawo matata dan ta taya ni bada hak'uri, wata k'ila ka karb'i nata sanin muhimmancin farin-cikinta a gareka. Ko da baka bawa d'ana Elmansoor d'iyarka ba ina fata ka karb'i rok'ona ka yafe min".


Maganar mijinta ya bata k'arfin gwiwa, jin shirunsa ya sa ta jero nata bayanin duk da muryarta na rawa hawaye na barazanar sauk'o mata.


"Munzo ne da k'ok'on bararmu Abban Aisha, ayi hak'uri a manta baya a fuskanci gaba, bayan son da yaran nan suke wa junansu akwai fahimta da girmama juna tsakaninsu, kuma na tabbata baza kuyi da-na-sanin bawa Elmansoor Aisha ba, kayi hak'uri ba dan mu ba".


Yawu ta had'iye had'e da goge siririn hawayen da ya sauk'o mata sannan ta mayar da hannunta cikin hijabinta.


"Bazan b'oye ba, mak'asudin zuwana nan nikam dan bada hak'uri ne a had'a auren Elmansoor da Aisha. D'ana ba cikakken lafiya ne dashi ba, bazai iya d'aukan wannan horon ba. Dan Allah na rok'eka ko wani irin horo kayi mana mu iyayensa tunda mu muka yi laifi, bai kamata ya hau kansa ba, my child is innocent(d'ana bai san komai ba)".


Hawaye tuni ya wanke fuskarta, muryarta na rawa ta ida maganar. Mama da ke gefenta ta rik'e hannunta tare da matsewa alamun rarrashi, tuni ita ma hawaye ya cika idanunta tana k'ok'arin hanasu sauk'owa.


"Toh Alhamdulillah, naji duk bayananku sai dai gaskiya ban so ayi zama irin wannan a yau ba, duk da banso yayi tsauri haka ba. Ganin Alh. Yuri ya matsa yasa na taraku dan kowa yasan shawarar k'arshe da na yanke. Sai dai bana son kowa yayi min mummunar fahimta game da hukuncina".


Shiru yayi na 'yan sakanni sannan cmya cigaba da magana.


"Ina so duniya ta sani, ta kuma d'auki darasi cikin rayuwarmu, duk wani abunda kayi zai dawo maka ta inda baka zato, idan baka ganshi a duniya ba toh tabbas zaka ganshi a ranar da bazaka iya neman yafiya ba, wanda ya samu sakamakonsa tun a duniya rahama ya samu babba, dan zai baka daman neman yafiya daga wanda ka zalunta kuma ya baka damar yin istigfari. 


Har cikin raina Alh. Yuri na yafe maka har abada, tun kafin had'uwar Aisha da Elmansoor na manta duk abunda ya faru, Allah ya azurta ni da mata ta gari, na yadda da cewa Allah in ya karb'i wani abu daga wurinka yana baka wani wanda yafi alhairi a gareka.


Shigowar Elmansoor rayuwarmu yasa nayi tunanin nuna maka illar abunda ka aikata akaina, ko ba kai ba na tabbata wanda yaji labarin nan kuma yasan halin da kowannenku ya shiga zai kiyaye anfani da dukiyarsa ko kuma ikonsa dan samun abunda yake so.


Nasa auren Mufeeda har ma da ita Aishar nan da watanni biyu".


Zuciyar Elmansoor ji yayi kamar ya tarwatse, ya tabbata an rabasa da sahibarsa, Pretty d'insa.


"Alhaji Yuri! Elmansoor!!" 


Ya furta sunayensu, dubansa sukayi ba tare da sun furta komai ba.


"Zaku iya hada-hadar hidimar biki a watanni biyu banyi katsalandan ba?".


Ganin basu fahimci bayanin nasa ba yasa ya fad'ad'a da cewa.


"Bana fatan a k'ara bikin nan, kuyi shirin biki cikin watanni biyu, Aisha zata bar gidan nan ta koma naku gidan".


D'ago kansa yayi baki bud'e yana kallonsa dan gaskata abunda kunnensa yaji.


Ganin murmushi shimfid'e saman leb'b'an Abba ya sashi jin kaman ya fire sama dan dad'i, kallon fuskar Nu'aim yayi dan yaga yanayinsa, murmushi shima yake sakar masa, ya tabbata kunnuwansa sunji dai-dai.


"Alhamdulillah!" 

Yaji muryar mahaifiyarsa cikin farin ciki.


Ganin Abba bai amsa ba tuni ya ari bakinsa wurin karb'an wannan tayi kafin ya wucesa.


"Abba wallahi babu komai a shirye muke..."


mintsini Fahad ya sake masa a cinya, bai san lokacin da ya d'an yi k'ara ba yana kallon abokin nasa.


Sai a sannan ya tuna abunda yayi, ta k'asa yake kallon mutanen falon, dariyar da Mufeeda ke tarewa ya kufce mata, duk suka fashe da dariya banda shi da yake ta faman sunne kai.


Tattaunawa aka shiga yi cikin farin ciki, a nan Abba yake sanar dasu Nu'aim yayi k'ok'ari matuk'a wurin shawo kansa, shine silar canjawar ra'ayinsa.


Godiya sosai Elmansoor yayi masa, yana mai cewa yazo ya basa k'anwarsa muddin ya samu soyayyarta.


Cikin murna aka watse, sai hidimar bikin da kowannensu yasa a gaba.


Nu'aim kuwa tuni ya shige cikin abokan nan biyu, ta nan ya samu damar magana da Humairah.


~~~~~~~~~~


SATI D'AYA ZUWA BIKI


"She will be mine very soon(zata zama tawa kwanan nan), meh na b'uya? Sati nawa kin hanani ganinki?".


Murmushi tayi cikin wayar bata iya cewa komai ba.


"Kinsan ina ji kaman in goya ki in zagaye garin Abuja da ke tun da Abba ya bani daman aurenki? Sosai nake jin nayi dace, dole in bawa Nu'aim Humairah, Nagode masa sosai".


Dariya sosai take masa, wasu lokutan tana mamakin Elmansoor, kamar ba shi d'in tayi rayuwa dashi kwanakin baya ba, murd'ad'd'e.


"Wai tun d'azu baza ki min magana ba? Maganin magana kika sha?"


"Meh zance bayan Godiya ga Allah da nake yawaita yi. Har yanzu ban gama farin-cikina ba".


"Ban fa yadda ba. Wai murna ne yake hanaki min magana? Na kula bayan dariya babu abunda kike min kullum in na k'iraki, kamar ba Prettyn Sweet Elmansoor ba".


"Mamakinka ke hanani magana Elmansoor, wai haka ka koma? Kaga yanda kake min kaman ba sweet Elmansoor d'ina ba? completely ka canja, ban tab'a d'auka zan sameka haka ba".


Murmushi yayi had'e da canjawa wayar mazauni zuwa d'aya kunnen.


"Ina sonki, meh zai hana ki sameni haka? Ki fara shirin barin gida, ki fara shirin shiga duniyar Elmansoor wanda yake cike da farinciki, pretty baza ki yi da na sanin aurena ba. Tun bamuyi auren kinga duniyar da na tanada miki ba kike mamaki? Baki tab'a sanin Elmansoor na son soyayya ba? Amma fa bayan aure".


Ya k'arashe cike da zolaya.


Haka rayuwarsu ta sauya, komai na tafiya cikin tsarin addini da kuma al'ada.


Tuni suka sake yiwa gidan da suka zana da hannunsu fenti. Tuntuni aka kammala gidan, rashin matan auren ya hana su tare.


Gida ne meh sassa biyu, d'aya na Fahad d'ayar kuwa na Elmansoor. Burinsu ne tun da su zauna gida d'aya, hakan ya tabbata, dan sun had'a k'arfi da k'arfe suka tsayar da wannan gida.


Ranar alhamis aka fara biki, hidima biyu kawai Abba ya yadda ayi, wannan ma dan yaran sun takura, sai kuma walima wanda za'ayi ranar juma'a.


Kamu aka yi ranar alhamis, amare sun sha kyau sai k'yalli suke.


21st july 2014 yayi daidai da ranar asabar kuma ranar da aka d'aura auren Elmansoor da Aisha, Fahad da Mufeeda.


Da misalin k'arfe 2 na rana, a tsakiyar farfajiyar gidan Alh. Abdullahi Nemi aka d'aura auren.


Biki yayi biki, dan an samu mutane masu tarin yawa, duk girman gidan sai da aka samu mutane a waje dan rashin wurin zama, waliyyai sun karb'a kuma an bada aure, an bada sadaki, anyi siga, duk wani sharudd'an aure an cikata, Alhamdulillahi, yau an d'aura auren masoyan juna, anyi rabon goro da minti kamar yanda akeyi a al'adar hausa/fulani.


Da dare misalin k'arfe takwas aka tafi gagarumin dinner wanda angwayen suka had'a a Evelyn event and garden da ke gwarimpa 3rd avenue.


Amare biyu sun sha kyau, kowacce kalar kayamta daban. Mufeeda ta sa purple, Aisha kuwa ta sa blue.


Tun daga nesa Elmansoor ya hangosu suna fitowa daga cikin gida. Duk da sauran k'awayen na taresu hakan bai hanasa kallonta ba, duk inda tayi idanunsa na kanta, haka yake wurin Fahad da Mufeedarsa.


Fahad ji yayi kamar ya sureta ya gudu, alal hak'ik'a bata tab'a masa kyau irin yau ba.


Kallon k'urilla yake mata, ganin sunk'i isowa inda suke yasa shi tab'o Elmansoor


"Kaga yanda sukayi kyau?"

"Na d'auka idona ne, ashe kai ma haka ka gani?".


Ba tare da ya dubesa ba ya kad'a kai yana mai k'issima abu a ransa.


"Ashe da gan-gan suka k'i mu gansu, sati uku fa bamu gansu ba".


'Kwank'wasa gilashin motar akayi, hakan ya dawo dasu daga duban amarensu da suke yi.


"Anan amaren zamu cusa muku ku zama ku hud'u d'aya akan d'aya? Ko d'aya zai fito ya shiga motar Jamil tare da amaryarsa? Ko ma dai a wuce daku su shiga motar Jamil kawai".


"Kai kuma ya zaka mana haka Nu'aim"

Cewar Fahad yana mai bud'e k'ofar motar.


"Gani nayi kun lafe kamar ku ne amaren".


"Nu'aim Fahad ai motarka zai shiga da Mufeedah, meh ya kawo Jamil kuma?"


"No(a'a"

Ya d'aga hannayensa sama had'e da kad'a kai.


"Kun manta na sanar daku nima matata zan d'auka? Haka kawai ina nan zan bari wani k'ato ya d'auki princess? Hell no".


Baki suka bud'e suna kallonsa, duk sun girme masa bai hana su sabo ba, hankalinsa da nutsuwarsa ya kawo fahimtar juna tsakaninsu.


"Yaushe ka fara min rashin kunya?"

Fahad ya furta mamaki bai bar fuskarsa ba.

" Zan fasa baka ita? Elmansoor wannan yaron ya manta da surukansa yake zance"


Dariya Elmansoor ya shiga yi, bai iya ce musu komai ba suka gama shashancinsu suka wuce Aisha ta shigo tasa motar.


Idanu ya zuba mata tun shigowarta, bai kula da Mus'ab da yake tuk'asu ba. Fuskarta ta rufe da net cike da jin kunya, kallon da yake mata yana shiga har cikin zuciyarta.


A hankali ya lalubo hannunta, kalmominsa sun gushe, ya rasa tak'amaimai meh ya dace ya furta a wannan lokaci. 


Matsewa hannunta yayi cikin nasa, yana mai sauk'e ajiyar zuciya. A hankali ya lumshe idanunsa yana mai shak'ar k'amshin turarenta.


Wayarsa ya lalubo ya rubuta wasu kalmomi ya tura yana mai d'auke kai. 


K'ara wayarta yayi, sai dai motsin kirki ta kasa yi bare ta duba wanda ya k'irata. Hannunsa da yake cikin nata bai iya ajiyesa wuri guda ba, sai wasu abubuwa yake mata da ta kasa gane ina ya dosa.


Can ciki ya furta

"Duba wayarki"

Hannunta take k'ok'arin cirewa yak'i saki.


Idanunta ta d'ago suka yi ido hud'u, runtse idon tayi had'e da kawar da kai.


Daa kanshi ya lalubo wayar cikin purse nata ya mik'a mata. A dai-dai lokacin suka isa inda ya dace ayi shagalin.


"Kinyi kyau, kin sace ragowar zuciyata da kikace kin bar min. Ina sonki matuk'a"


Idanunsa na kanta, tasan kallonta yake. Hannunsa na cikin nata, tasan ba saketa zaiyi ba.


Jinta take a takure, tana jin zuciyarta na tsinkewa, ga kunyarsa da yake shigarta.


Yawu ta had'iye mai tauri tana addu'ar samun mai cetonta.


Ahankali ta ji bugun window, bata san lokacin da ta furta ana kwankwasawa ba.


Ware ido yayi yana kallonta, jin an sake bugawa ya sauk'e gilashin.


"Zaku iya fitowa"

Ya furta ya basu wuri.


"Pretty baki son zamanmu haka? Ba fa abunda nake miki".


Motar ta bud'e dan ta gujewa kalamansa, amma fir yak'i sakin hannunta yana mai mamakin sabon salo irin nata.


Ganin k'ok'arinta na kwace hannun yasa ya saketa shima ya bud'e nasa b'angaren ya fito.


~~~~~~~~~


washe-gari da yamma aka tattara su zuwa gidansu da yake Jabi. Kowacce b'angarenta aka shigar da ita.


Sunyi addu'ar shiga gida sannan sukayi anfani da k'afar dama don shiga.


'yan kawo amarya basu bar gidan ba sai bayan maghrib, sai fatan Alkhairi ake musu ana yaba tsarin gidan, kowa da albarkacin bakinsa, wasu na musu farin-cikin zamansu gida daya, wasu kuwa na mamakin irin abotan da ke tsakanin mazajen amaren guda biyu.


~~~~~~~~


K'arfe tara suka shigo gidan, kowanne ya wuce b'angarensa murmushi ya kasa barin fuskarsu.


Elmansoor ya sameta kwance ta duk'unk'une cikin bargo sai sheshshek'ar kuka takeyi.


A bakin k'ofar ya tsaya yana kallonta, daga bisani ya sauk'e ajiyar zuciya ya iso inda take.


Abun hannunsa ya ajiye ya bud'e bargon.

Bata bari ya kalli fuskarta ta cigaba da kukanta. 


Lumshe idanunsa yayi yana mai jin kukan da takeyi a k'albinsa. 


D'agota yayi yana mai cire mata gyalen da take kare fuskarta dashi. Janyota yayi zuwa jikinsa, yana mai rungumeta dukkanta.


Sai da ta tsagaita kukan ya iya samun kalamansa.

"Ni ki daina min kukan nan in ba so kike mu taru muyi ta kuka a daren nan ba"


D'agota yayi yana mai dubanta. Ya d'aura hannunsa gefen kanta yana mai jin yanda wurin ke rawa.


"Kanki na ciwo koh? Kiga yanda nan ke rawa pretty, meh yasa kike kuka?"


Baki ta turo tana mai goge hawayen fuskarta.


"Banason in farka daga mafarkin da nakeyi, in na farka naga ban aureka ba mutuwa zanyi".


Dariya ne ya kufce masa yana mamakin yaranta irin na Prettynsa.


Hannunsa da yake kan nata ta ture ta juya masa baya.


"Haba my pretty! Tsaya kiga"


Yasa hannunsa ya mintsineta, k'aramin k'ara ta saki tana sosa wurin.


"Kinji ba mafarki kike ba? Aure aka mana, Aishar Elmansoor".


Ya d'aga mata gira murmushi a fuskarsu dukka.


Sun gabatar da sallah sukayi addu'a kamar yanda annabi ya koyar, suka ci suka sha.

Hakan ya wakana a b'angaren Fahad da amaryarsa Mufeeda.


~~~~~~~~~~~


   Komai na rayuwa ya canja musu, rayuwa mai dad'i suke yi suna shimfid'a tabarmar soyayya mai dad'in gaske mai wuyar fassarawa, su kad'ai suka san irin yadda tasu soyayyar take. 


Bayan wata biyu Aisha da mufeeda suka fara zuwa Baze university, tare suke zuwa suke dawowa, sai dai fatan Allah ya basu sa'a da nasarar samun sakamako mai kyau a karatunsu.


Shekaru uku sannan Mufeeda ta samu haihuwa, bata sha wahala sosai ba ta haifi santaleliyar budurwarta. 


A lokacin ita Aisha na da nata cikin wata bak'wai.


Nu'aim da Humaira a shekarar da ya wuce akayi aurensu, suna zama cikin so da k'auna da mutunta juna.


Rayuwar Elmansoor ya sauya, yana cikin kwanciyar hankali da nuna tsantsar soyayyarsa gareta.


A kullum in ta kallesa yana zuba mata salonsa sai tayi mamaki, taji ina ma dukkan maza zasu zama irin Elmansoor a gidan aurensu, da duniya ta gwada dawowa saiti.


Abubuwa da yawa zasu ragu sakamakon hakan. 


K'arshe.


****************


Banso ya k'are iya nan ba, dalilai yasa na tak'aita iya nan. Ayi min afuwa zuwa sabon littafina, bazan yi irin wannan ba.


I told you tun farko edit yafi sabon typing wahala, abunda yake kashe min jiki kenan


Alhamdulillah na kammala a yau, duk da ba yanda naso ba. 


A cigaba da yi min uzuri


Sabon littafina na Tafe


AKWAI ILLAH


Nagode da kulawa

Nagode matuk'a

Ina k'aunarku

From my heart.


Tags: Elmansoor #soyayya #gaba #miskili #surutacciya
10158
0
0
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

2019-10-11 11:40:25