Sanadin Kiyayya!

Written by Rabiatu Mashi SkPublished on 2018-12-12 17:22:38Category Mystery/ThrillerTun kafin ta ganshi, tsanarsa da duk wani abu daya shafeshi ta ɗarsu a zuciyarta, iyayenta sun matsa sai anyi aurensu, tasha barazanar sai ta kasheshi, sai ga wani abu ya faru daren auren nasu, farkawa tayi taga gawarshi kwance jinajina a gabanta, shin waya kasheshi?? tags: #kiyayya #Kabeer #AleesaDuba was labarai »

/8, 13:12] Rabiatu sk msh✍🏻: ♠SANADIN K'IYAYYA♠

      (︶︿︶)

         1-2


©️Rabiatu sk msh

      NWA


Dedicated to Mrs Umar and Maman Adnan


Tsaye suke bakin titi sai faman chatn take, Ummie ta mik'a hannu zata anshe wayar tayi saurin janye wa, ta buga tsoki,

   "Haba Aleesa sai kace bak'uwar chatn? A hanyar ma bazaki saurara ba?"

  "kindai jira na gama reply ko? Kinsan dai bada wani k'ato nakeyi ba"

  Bata tsaya maida mata amsa ba, ta faɗaɗa fara'arta, "wow! ɗago idonki kiga wata haɗaɗɗiyar mota"

  "Miye sunanta?" Aleesa ta tambayeta ba tare data ɗago ba,

  "benz ce fa" Aleesa ta kwashe da dariya, "benz ɗin zan ɗago gani, kinsan dai nama tsani motar?"

  "Na sani, kece fa kike cewa ba'a cika samun mota yellow colour ba" inji ummie

   "ke nifa ba son ganinta nake ba, kinsan yanda nakejin haushin colour ɗin,"


  Shiru tayi ta k'yaleta, ta rii

ga da tasan halin Aleesa idanta kafe kan Abu, sai data ajiye wayar don kanta, har lokacin basu samu abun hawa ba,

   "kinga motar nan bansan inda ta shige ba?" Aleesa banza ta mata don taa fara bata haushi,

  "Mota kamar babu gidanku Ummie?"

  "ta burgeni ne sosae, kalan ba'a cika samunta ba"

  "yauwah kin ganta nanma ta taho, don Allah ki kalla"

  "ke wlhy bazan kalla ba" Aleesa ta faɗa don Ummie ta fara k'ureta,


  "Munfa kusan Makara Ummie, anya zamu samu lecture nan?"

  "nima tunanin da nake kenan, anya bazamu hau mashina ba?"

  "A'ah ni bazan hau ba"

 K'aran buɗe mota sukaji, Ummie ta dinga taɓo Aleesa anma tak'i waigawa,

  "kefa banza ce, mai motarnan ne ya tsaya"

  "don Allah ki daina, karma yace mun damu dashi..."  maganarta ta rik'e saboda ganin mai motar ya buɗe hardasu fitowa, ya nufo inda suke yana washe baki kamar gonar auduga,

  Daga nesa hasken hak'oran kawai nake hangowa, bak'ine sosae, da sajenshi da yafi gashin gemun tsayi, sai kanshi yasha rantali ko hula babu, sannan kuma idonshi ɗaya nada er matsala, ba wani babba bane sosae, irin 30yrs haka, yana sanye cikin bugaggiyar shadda yellow, ta mishi kyau sosae a jiki, a fuska ne kawai baida k'oshin kyau,


  Aleesa da ganinshi ta fara dariya harda duk'ewa, bata damu da a bakin titi suke bama, Ummie kamar ta nutse don kunya, ta fara taɓota anma kamar batasan tanayi da ita ba, har ya k'araso inda suke,

  A hankali cikin sanyin murya yace "Sannunku en matah"

  "Yauwah, ina wuni" inji Ummie,

  "lafiya lau," ya amsa yana kallon Aleesa da har lokacin dariyarta kawai take,

   "da alama yau abun hawa yayi wuya, kuma bai kamata en matah kamarku sunashan ranarnan ba, idan kun yarda zan kaiku har inda kukeso"

  "Ba komi ai bamu daɗe da fitowa ba, zamu samu insha Allah" 

   

  Aleesa ta kalleshi shek'ek'e, ta k'ara tuntsurewa da dariya,

   "Anma dai ba donmu shiga ka tambayemu ba ko?"

  "Idan na rasa k'warin gwiwa ai bazanma tsaya ba"

   "A'atoh, don koda mun rasa abun hawa bazamu shiga motarka ba, kai don Allah ko kunya bakaji ba ka tsaya wurinmu?" Ummie ta ɓata rai tana kallonta

  "Haba Aleesa ba haka akema mutane ba, don Allah ki daina?"

  "Dole ne sai nayi abunda kowa keyi? Wannan ma ai cin mutunci ne ace kamarshi ya rage mana hanya, jibarshi fa abun tsoroma dashi"

  "Haba Aleesa, wai miye haka?"

  "kaga malam zaka kama hanya koko?"

  "hak'uri zaki hajia, naga alaman kamar kina cikin ɓacin rai"

  Harararshi tayi son ranta, sannan ta tsaida mai napep ɗin da taga ya taho, ko saurarar Ummie batayi ba ta wuce ta shiga,

  "kayi hak'uri fa, ba halinta bane...."

  "ba komi na fahimceta, daman ya za'ai kyakkyawa kamarta tayi faɗa haka, anma gida zakuje ne?"

   "A'ah makaranta dai, daga gidan muke"

  "owk, ban sani ba ko zaki taimakamun da kwatancen gidansu? don daga ganinta nema zuciyatah ta tilastamun tsayawa "


  "Malama zakije ne, ko saikin gama kallon bak'in Akuyar nan?" yaji ciwo sosae anma ya kanne, da hannu Ummie ta nuna mishi gidansu Aleesa,

  "Yauwah nagode, don Allah ki k'ara bama k'awarki hak'uri," ta ɗaga mishi kai sannan taje ta shiga napep ɗin,


  A makaranta mai napep na saukesu, ta fito da sauri ta baro Ummie na sallamarshi, sai sauri take taje hall ɗin da suke lecture don lokaci ya kusan cika, bata ankara ba taji ta kusa karo da abu, tayi baya da sauri sannan ta ɗago kanta, take sauran fara'ar dake fuskarta ta ɓace,

   "Kai wani irin dabba ne, da bakajin kunyar shiga hanyar mutum?"

  "Dabba kuma Aleesa? Yanzu cin mutuncin har yakai haka?"

  "Yamafi haka idan har bazaka daina shiga rayuwatah ba"

  "bazan taɓa dainawa ba kuwa, don Soyayyar da nake miki a shirye nake dana karɓi duk wani cin mutunci naki, don nasan dole wata rana zaki soni"

   "Allah ya sauwak'emin, don kana da kyau da kuɗi, banga dalilin da zaisa in soka ba, en matan dake kulaka ma na tausaya musu"

  "ki fara tausaya ma kanki kema" ya faɗa yana wani shu'umin murmushi,

  Ta wuceshi zata tafi, yasha gabanta, "ya zaki tafi bamu gama magana ba?"

  "banson iskanci Hadid ka matsamun a hanya"

  "idan nak'i fa?" kafin ya rufe baki yanata wani murmushi ta ɗaukeshi da zazzafan mari, abinda bai taɓa tunani ba daga gareta,

  Ɗagowa yayi dafe da kuncinshi, idanunshi sunyi jajir da ɓacin rai, ya waiga ko ina, ba laifi mutane sun taru, kuma duk hankalinsu na wurinsu suna daria ciki-ciki,

  Ummie taja hannunta "Menene kika yi Aleesa? Kina manta halin hadid ko"

   "Ke Malama naga duk kin wani ruɗe, ke kin manta nawa halin ne?"

  "ba mantawa nayi ba, anma gaskiya baki kyauta ba"

  "ban taɓa dana sanin abunda nayi dana sani ba Ummie, wata k'ila wannan zai sanya ya fita hanyata"

  "Allah yasa tohh"

 A haka suka k'arasa hall ɗin, suna fira, sunyi sa'a saida suka shiga lecturer n ya shigo,


©️Rabiatu sk msh

[2/8, 13:14] Rabiatu sk msh✍🏻: ♠SANADIN K'IYAYYA♠

      (︶︿︶)

          3-4


©️Rabiatu sk msh

      NWA


Dedicated to Mrs Umar and Maman Adnan


Sun gama lecture sun fito, A hanyarsu ta komawa ne, Ummie ta kasa hak'uri saida tayi mata magana,

  "Waini Aleesa wace kalan K'iyayyace wannan kike nunama maza? Kinsan dai abunda kike baki kyautawa ko?"

 "Ni menayi na rashin kyautawa? Bakimun adalci ba idan kikace ina nunama maza k'iyayya Ummie, Soyayyah daice bani da lokacinta, hadid kuma da kikaga inama haka ke kanki kinsan halayenshi basu dace dani ba, ko kaɗan baida tarbiyya, son mata ga shaye-shaye, sai kuma guy ɗinki na ɗazu, wlhy tun kafin in ganshi bazan ɓoye miki ba k'iyayyarshi ta shiga zuciyatah, kawai na tsaneshi"

  "tofah! Wannan wacce irin tsanace?"

  "kawai dai, kinga mu daina maganarshi ma plz,"

 “Ya Allah kasa ko a hanyama kar in k'ara ganinshi”

 Ummie tace "Ameen" duk jikinta yayi sanyi,


  Firan exam ɗin da zasu fara ta shiga 200lv suka ci gaba dayi, har sukazo k'ofar gidansu Aleesa, aka fara ajjeta sannan ya wuce da Ummie da yake gidansu na gaba,

  Earpiece ta saka a kunnenta, tana saurarar wak'ar Rihanna (Complicated), tana son wak'ar sosae sai rausayar dakai take cikin nishaɗi, zata shiga fallo suka haɗu da Momie ta tsaya ta cire earpiece ɗinnan sannan ta mata sannu da gida,

  "ina kika tsaya tun ɗazu kin bar mutum yana jiranki?" ta tattaro duk mamakinta tana kallon momie,

  "ni kuma?"

 "Akwai wata ne bayan ni dake? Baki ganshi ba da kika shigo?"

  "ni banga kowa ba momie"

  "tohh kije yana can waje yana jiranki"

  "tohh" kawai tace tana niyyar shigewa ɗakinta, hakanan taji batason fitar, duk da daman ba fira take ba,

  "ina kuma zaki?"

  "zan ajje jakarne"

 "ajiye tanan, banson jira, bawan Allahnnan ya daɗe yana jiranki", duk taa ɓata rai, ta jefar da jikkar da fito, 

  Yana hango fitowarta ya fara washe baki, tuni wani k'unci ya ziyarci zuciyarta, guy ɗinnan ne na ɗazu, wannan wane irin rashin zuciyah ne? Wani abu ya tokare mata zuciyah, babu abunda bata ayyanah ba a ranta kafinta isa inda yake,

  "Barka da fitowah gimbiyar Matah, ay kin wuce inata magana bakiji ba, da alama kina cikin nishaɗi shiyasa ma ban takuraki ba" tayi matuk'ar daurewa kafin ta buɗe baki ta mishi magana,

  "Don Allah nikam wanne rashin zuciyar ne ya kawoka gidanmu?" murmushi mai kyau yake, duk ba bakyaun ne dashi ba,

  "Har kin lura da rashin zuciyar tawa kenan? Ay tuni na mallaka miki ita shiyasa ma nake bibiyarki, don kin sacemun abunda yafi komai muhimmanci a sassan jikina"

  "Tohh sannu bunsuru" Aleesa, ta faɗa da alama ko maganar batason yi,

  K'ok'arin shanye rashin jin daɗin maganarta yayi,  "Kabeer ne sunan"

   


  "ban tambayeka ba, kuma ban buk'atar sani, na tsaneka dakai da sunan naka harda shegiyar zuciyar, ka fita hanyata, idan baso kake na maka rashin mutuncin da baka taɓa tunani ba"

  "Haba Hajia Aleesa! Ay halinki ma sam bai kama dana masu wulak'anci ba"

  "zan ko ara in yafa! Ka fice mana daga gida, don k'aramin ganin (dodon jatau) da kallon fuskarka, don Allah kalleka, ko kyaun gani babu anma a haka kakeso na, mtsww"

  'tsayawa wurinnan ma tare dashine babban horon da za'amun a rayuwa, nima na tsaya da har nake maida mishi magana', ta juya kawai zata bar wurin da sauri ya tsaida ta, "Zan tafi, anma don Allah ki tsaya ki amsa" batace mishi komi ba taci gaba da tafiya, ba shiri yasha gabanta,

  "haushi ya kawota iyakar wuya" ta kalli hannunshi, bandir ne guda biyu na dubu-dubu,

  "Don Allah ki amsa, nasan kinfi k'arfinsu, anma don Allah ki amsa"

 Bata ce mishi komi ba ta raɓashi zata wuce, ya k'ara shan gabanta, ga wani irin haushinshi da takeji idan tana ganinshi a gabanta, haka ya dinga nace mata saita amsa, mik'a hannu tayi kawai kamar abin k'yama ta amsa, ta kalleshi sai daɗi yakeji, sannan ta saita goshinshi a dun'kulen ta jefa mishi, har saida yayi baya ya kusan faɗuwa, ba k'aramin buguwa yayi ba dafe da goshinshi yake kallonta idanunshi sunyi jajir,

  Ta nunashi da yatsa,

 "karka taɓa tunanin abun hannunka zai burgeni, baka ganni da yunwa ba, ni kaina sai inyi kyautar fiye da wannan, yanda na tsaneka, haka na tsani duk wani abun daya shafeka, kuskurenka na k'arshe shine sake, sako k'afafunka cikin gidannan," ta juya taci gaba da tafiya,

  Ya fara magana, abun mamaki fuskarshi sam babu damuwa, murmushi ma yakeyi,

  "Alhamdulillah, bazan iya fasalta farin cikin da nake ciki ba, addu'ar dana daɗe inayi ne Allah ya amsa Aleesa, Mata da yawa sun nunamun soyyaya, ban taɓa cin karo da wacce takemun k'iyayya ba, Mata da yawa dukiyatah sukeso Aleesa, sai yaune naci karo da wacce kuɗina ma basu burgeta, banso ki soni don wani abu dake tare dani Aleesa, ki soni don Allah kawai, naji daɗi da dukiyatah bata burgeki,"

  Tsabar takaici ma kasa ce mishi komi tayi, kallon wanda ciwon hauka ya kama kawai take mishi, ɗaga kanta tayi can saman bene, daddy ne tsaye yana hangen duk abun dake faruwa, tuni hanjin cikinta suka kaɗa, ba shiri ta shige gidan da gudunta,


©️Rabiatu sk msh

[2/8, 14:36] Rabiatu sk msh✍🏻: ♠SANADIN K'IYAYYA♠

      (︶︿︶)

          5-6


©️Rabiatu sk msh

      NWA


Dedicated to Mrs Umar and Maman Adnan


  Tana shiga falon ta hango Daddy na saukowa daga upstairs, da sauri jikinta yana kyarma ta wuce ɗakin Momie, ta lafe bayan labule tana lek'enshi,

  Waje ya fita, gabanta yaci gaba da faɗuwa, Momie na tsaye tana kallonta a haka batace mata komi ba, ya daɗe a wajen kafin ya shigo, ɗakin Momien ya nufa, ta wani irin wuntsilawa ta shige bayanta, 

  "Miye haka Aleesa, so kike ki nakasa ni?"

  "Momie don Allah ki bama Dad hak'uri ba laifina bane"

  "Ai daman tunda naga yanayinki nasan da abunda kikayi, kwata kwata baki da gaskiya"

  "ina fa take da gaskiya? Sakarar yarinya kawai" Daddy dake shigowa ya faɗa cikin ɓacin rai,

  "Ashe yarinyar nan bata da wayau? Yanzu a gidana zaki wulak'anta ɗan Adam Aleesa? Babban Mutum ba sa'anki ba, wannan inda a k'auyene ya isa haifarki, y'ar k'arama dake cikin ka**nki kin iya rashin Kunya"

  "wai me tayi ne Alhaji?"

 "ta faɗa miki da bakinta mana" tana can duk taa haɗa zufa can murya a mak'ale tace "Yi hak'uri Daddy" 

  "ni kikama laifi da zaki bama hak'uri? Idan da gaske kike ki tashi kije ki bashi hak'uri idan da gaske kike" wani ɓacin ran ne ya k'ara baibaye zuciyarta, k'iyayyar Kabeer na k'ara ninkuwa cikin zuciyarta, bazata iya ja da maganar daddy ba, don tsoranshi take sosae ko kaɗan bai musu wasa, haka ya sakata gaba har inda kabeer yake,

  Da yake Daddy bai ganinta, wani irin harara take aikama kabeer kamar idonta zai faɗo,

  "Yi hak'uri" ta faɗa, ko saurararshi batayi ba ta juya tayi cikin gida, shima shiru yayi duk baiji daɗin yanda aka ɓata mata rai ba, yama Daddy sallama sannan ya tafi,

  Tana jiyo Daddy yana bama Momie labarin yanda akayi, ya k'ara da cewa,

 "Kuma yaron ɗan gidan mutumci ne, tare mukayi makaranta da yayanshi, gidan akwaisu da hak'uri da kawaici, gidan Manyan mutane ne, anma ita zata wulak'antashi"

  "ba komi Alhaji, yaran zamani ne sai ana musu addu'a" shiru ya mata kawai,


  Wani haushin kanta ma ta dingaji da hak'urin data bashi, ta saka hannu ta murɗe bakin don tsananin ɓacin rai, ita kaɗai keta faman murguɗa baki a ɗaki,

  "Hege Uban naci kawai" ta faɗa a bayyane,

  Yinin ranar ko fitowa batayi ba waje, ita kaɗai keta k'uncinta cikin ɗaki,


 Washe gari lecturen safe gareta, tana shiryawa Ummie ta mata waya ta fito su haɗu, cikin lokaci kaɗan ta gama saka kaya, ko break fast bata nema ba, ta lek'a dai ta gaishe da Momie, ta mata Addu'ar dawowa lafiya,

  Tun daga k'ofar gida ta k'arajin wani k'unci ya tunkushe mata zuciyah, fuskarta ko kaɗan babu walwala ta fito daga gidan, suka kaɗu da Ummie, tare suka jera har bakin titi da yake babu nisa da gidansu Aleesa,

  Yananan inda ya tsaya jiya, ba k'aramin ɓacin rai taji da ganinshi ba, ta kauda kai kawai ko kallan inda yake batayi ba, ta matsa can nesa, 

  Ya fito da fara'arshi suka gaisa da Ummie, itama sai murmushi take mishi kamar wadda suka saba,

  "ina fata dai yau za'a bani damar kaiku makarantarnan" ta murmusa tana kallon inda Aleesa take,

  "banga alama ba, don yau mutuniyar taka da alama ko maganar batason yi"

 "nima naaga hakan, kinsan saraki, anma ki lallasheta plz"


 Tana jin haka, ko kallansu batayi ta tsaida wani mai napep, da sauri ta tafi ta shige tana shirin tafiya tabar Ummie ta matsa da sauri tana tsaidata, sannan ta shiga tana daria,

  "ke yanzu saiki tafi ki barni?"

 "Randa kika k'ara tsayawa wurinshi zaki tabbatar da amsar tambayarki" 

 Dariya kawai Ummie keyi

   "lallai naga alama, nikam bani nakar zomon ba ay"

  "ta kusa shafarki kema kau"

Ganin da gaske Aleesar take ya sanya Ummie bata k'ara cewa komi ba, sai dariya kawai take,


  Lecture 3hours sukai, yau sai addu'ah take cikin sa'a kuwa har suka fita daga ckul ɗin bata ga Hadid ba, ta sauke ajiyar zuciya, sai dai kuma tana ɗaga kai idonta ya sauka kan sarkin nacin nata kabeer,

  Yananan tsaye jikin motarshi da Key a hannu, idanunshi na kan hanyar da suke fitowa sai washe baki yake,

  Ummie saida dariya ta kusan k'wace mata, 

  "Anya kuwa Ummie mutuminnan yana da hankali? Hegen naci kamar tsohon kwarto" inji Aleesa da abun nashi ma ya fara bata mamaki

 Ummie tace "Karkiga laifinshi Aleesa, duk so ne, wlhy yana sonki sosai, baki taɓajin wak'ar Nura M Inuwa da yake cewa 'Komai mai yin so yayi karku kirashi zautacce' ba"

  "ke oho, ba So ba koma minene matsalarshi yanzu zan sauke mishi, zan nuna mishi gaskiyar wacece Aleesa,"


©️Rabiatu sk msh

[2/11, 16:18] Rabiatu sk msh✍🏻: ♠SANADIN K'IYAYYA♠

      (︶︿︶)

          7-8


©️Rabiatu sk msh

      NWA


Dedicated to Mrs Umar and Maman Adnan

  

  Aleesa na niyyar tafiya wurinshi, Ummie ta jawo hannunta ta rik'e,

  "Haba Abokiyah, don Allah karki mishi wulak'anci, mutuminnan iyakar hak'uri da kawaici ya nuna miki, na tabbatar miki da wani mugu ne, Asiri kawai zai miki ya rama abunda kika mishi"

  "Asirinshi na banza, wlhy ko ban cikin hayyacina na aura wannan kasheshi zanyi sai dai nima a kasheni" cewar Aleesa, Ummie ta rik'e baki,

  "A'uzubillahi, meya kawo maganar nan? Duk bai kai nanba" Aleesa ta harareta,

  "Ayna ɗauka zaki tare mishi ne," ita dai Ummie lallaɓata take har suka samu abun hawa, suka shige kawai babu wanda ya kulashi cikinsu,


Bayan Shekara Uku

Da haɗuwar Aleesa da kabeer, shekara ukunnan kullum yana hanyar gidansu, bai taɓa tsallake rana ɗaya baije makarantarsu ba indai yasan tana da lecture da niyyar ɗaukota, kuma so ɗaya ko kallonshi bata taɓayi ba, kullum K'iyayyarshi ce ke k'aruwa a cikin zuciyarta,

  Ɓangarensu Daddy kuma sun ansheshi hannu bibbiyu, kowa a family ɗinsu da k'annanta suna yabawa da Kabeer, harta da kuɗin neman aurensa an amsa shekara biyu da suka wuce,


*****

Aleesa ce zaune k'asa, ta ɗaura kanta saman cinyar momie kuka kawai take rusawa, tun bayan da taji ana niyyar saka ranar aurenta da Kabeer,

  "Ki taimakeni Momie, wlhy k'iyayyarshi ce zatayi ajalinah idan aka auramunshi, banison shi Momie, na kasa lallashin zuciyatah ta rage koda kaɗanne daga cikin k'iyayyar da take mishi,

  Momie ta shafa kanta cikin lallashi "Hak'uri dai zaki Aleesa, kinsan halin mahaifinku baya canja magana, kuma ni banga abun k'i ba a wurin Kabeer"

  "Nidai Momie bazan iya aurenshi ba wallahi...."

  "Idan baki aureshi ba wa zaki aura?" inji Daddy da yake laɓe yana sauraransu, ta k'ara fashewa da kuka,

  "Bawai na gaji da zamanki a gidannan bane Aleesa, anma duk mutuncin ɗiya mace yana ɗakin mijinta, kullum fa kwanaki shuɗewa suke, Shin idan bashi ba wa zaki aura?"

  Tana shesshek'ar kuka tace "ni kowama ka auramun Daddy, Anma wlhy nidai banison kabeer", ya nisa kaɗan, sosae kukan da takeyi yake bashi sosae, kuma k'iyayyar da Aleesa take ma Kabeer a bayyane take da bazai iya cewa bai ganinta ba,

  "Bazan aura miki kowa ba, anma zan iya baki dama ki kawo wanda kike so, duk da ba wannan ne karo na farkoba, anma ki sani wannan ce dama ta k'arshe dazan baki, idan har kika kasa kawo mini wanda kikeso, nan da sati Uku ki fara kallon kanki a matsayin matar kabeer"

  Tana share hawaye cikin farin ciki tace "Na gode Daddy" ta mik'e da gudu ta nufi ɗakinta tana murna,


 Anma sai dai Murnar tata ta koma ciki data fara tunanin to wa zata kawo a matsayin mijin da zata aura? Babu saurayin data taɓa kulawa da matsayin soyayya, Hadid ne ya faɗo mata a rai, tun wani wulak'anci data mishi ko a hanya bata k'ara ganinshi ba, cikin damuwa ta fara tunano abun daya faru ranar,

  Birthday ɗinta ne, tunda safe take samun sak'onni daga en uwanta da Abokan Arzuk'a, wani irin farin cikine take ciki a ranar, da misalin K'arfe 9pm, wata k'awarta Hanan ta mata waya, 

  "Birthday girl ya kike?"

  "lafiya lau hanan, ya mama"

  "Qalau take, wai me aka shirya mana ne?"

  "kedai ba komi wallahi, kinsan ban shirya ma abun bane"

  "Tohh Albishirinki" cikin zumuɗi tace "Goro fari k'ar hanan faɗamun mana"

  "bazan faɗa miki ba, kedai kizo address ɗinnan dazan turo miki ki gani"

  "Haba tawan kiɗan gutsuramun ko kaɗan" tana dariya tace "Naak'iya, kedai sai kinzo"

   "Tohm bara in tashi in shirya" sannan ta yima Ummie waya, dak'yar ta lallaɓata akan zata rakata, sannan ta fara shirin tafiya tana tunanin wanne irin Albishir ne hanan zata mata?


©️Rabiatu sk msh

[2/11, 16:18] Rabiatu sk msh✍🏻: ♠SANADIN K'IYAYYA♠

      (︶︿︶)

         9-10


©️Rabiatu sk msh

      NWA


Dedicated to Mrs Umar and Maman Adnan


Www.babymsh.blogspot.com


  K'arfe 10 dai dai suka isa wurin partyn, sunci kwalliya sosai kamar masu zuwa gasar sarauniyar kyau, suna takunsu ɗai-ɗai har suka shiga daga ciki, wurin cike yake da course mate ɗinsu, da sauran en makarantarsu dai, kowa ya gama k'ure adakarshi,

  Aleesa ta fara k'are musu kallo tana hangen inda zata gano Hanan, saiga Hadid ya fito yana murmushi, ya fara rairo mata "Happy Birthday to you" gaba ɗaya wurin suka amsa, suna tayata murnar zagayowar haihuwarta,

  Tun ganinshi yanayinta ya canja, Hadid ya mik'a hannu ya amsa loud speaker zai fara magana,

  "Ina farin cikin gabatar muku da tauraruwar mata, kuma tauraruwa a cikin zuciyar Hadid watau Aleesa, ina miki barka da zuwa wannan wuri, tare da tayaki murnar zagayowar ranar haihuwarki," duk wurin ya kaure ta tafi, 


  Cikin ɗaga Murya Aleesa tace "waye ya haɗamun birthday partynnan?" 

  Hanan dake can gefe tace "Hadid mana, kina da masoyin daya fishi?"

  Murmushin mugunta kawai tayi bayanta girgiza kai, ta fara taku zuwa inda yake, Ummie ta rik'o hannunta, kallonta kawai tayi ta saketa, shikam sai murmushi yake ganin tana k'arasowa gareshi,

  Hannu kawai ta saka ta ture birthday cake ɗin da ba k'ananun kuɗi aka kashe wurin tsara su ba, da sauran drinks ɗin komai ya zube k'asa, sannan ta nunashi da ɗan tsaya,

  "A rasa wanda zai haɗamun birthday party sai kai? Mayaudari, mai bin en mata, mara aji ma da kowacce bi kake," sannan tayi shiru don tsabar k'uluwa ma taa rasa me zatace,

  "Duk yanda zaka gwada bazan taɓa sonka ba Hadid, baka cikin jerin mazan da zanso, nacin yaa isa haka, ka gwada sa'arka wani wurin" tunda ta fara magana ya fara huci, ɓacin rai kamar zuciyarshi ta fasa k'irji ta fito, cikin hargagi ya fara magana,

  "Da wuri haka Aleesa? Ki rubuta ki ajje ni Hadid saina rama duk wulak'ancin da kikamun, bazan taɓa k'yaleki ki shani a banza ba, sai kinga SANADIN KIYAYYAR, da kika nuna mun"

  "kanka dai akeji, namamajo kawai" wata irin tsawar ya k'ara daka mata cikin ɓacin rai, ta k'ara harararshi son ranta sannan taja hannun Ummiee suka bar wurin,


***

Sauke ajiyar zuciyah tayi bayan ta gama tunano rabuwarsu da Hadid, gashi yanzu ya gama makaranta batasan inda zata k'ara ganinshi ba,

  Dubara ce tazo mata, numbers ɗin Abokanta ta ringa kira tana tambayar ko akwai mai numbershi, anma cikin rashin sa'a babu wanda yake da, wannan fa shine ga k'oshi ga kwanan yunwa, 


Kullum cikin neman Hadid take harya rage sauran sati ɗaya bikinta da Kabeer kamar yanda Daddy ya saka ranar, kullum damuwarta k'aruwa take, gaba ɗaya taa rame sosae kowa ya ganta zai san tana cikin tashin hankali,

  Yau a gajiye ta dawo daga makaranta, tun daga can Kabeer ke biye da ita, ko kallanshi batayi ba har ya gama parking motarshi, ta shige cikin gidan kawai, 

 Cikin jan jiki ta gama duk abinda take, tana sane da yana waje yana jiranta, ko falo ma tak'i fita don kar Momie ta tilastata fita wurinshi, saima ta nema wuri ta kwanta ta fara sharar barci hankalinta kwance,


  Can cikin barci take jiyo muryar Haisam Autah yana mata magana kamar mai shirin fasa mata kunne "Aunty Momie na kira, Aunty, Aunty kije inji Momie" ta mirgina cikin barcin muryarta cike da gajia yace "Mezan ma Momien?"

  "wai uncle Kabeer ne yake jiranki, tun ɗazu" cikin masifa ta tashi Zaune

  "kuma shine zakazo ka tadani a barci na? Ficemin daga ɗaki, kuma ka faɗa mishi yabar gidannan, inba haka ba saina ɓallamaka kunnuwan nan" da sauri ya juya ya nufi ɗakin momie, yana rik'e da kunnuwanshi, sai gashi sun dawo tare da momien,

  "Kikace a gayamun bazaki zo ba?"

  "nifa A'ah momie, cewa nayi yanzu na dawo daga makaranta duk na gaji ya tafi sai anjima"

  "tunda kin maidashi yaronki ba? Ki tashi ki fita tun kafin Daddynku ya dawo ya haɗamu harni harke, tun yaushe kika dawo daga makarantar, kinsan kuwa ko awanshi nawa yana jiranki? Ki tashi ki fita nace" tayi k'asa da kanta,

  "zan tashi momie"

 "ki tashi nace inanan ina jiranki" ba don taso ba, ta tashi ta zari mayafi tayi gaba tana tunanin kalar masifar da zata sauke mishi,


 ©️Rabiatu sk msh

[2/12, 16:30] Rabiatu sk msh✍🏻: ♠SANADIN K'IYAYYA♠

      (︶︿︶)

         11-12


©️Rabiatu sk msh

      NWA


Dedicated to Mrs Umar and Maman Adnan


www.babymsh.blogspot.com


  Tana shiga falon bak'in, daga ganin yanayinta Kabeer yasha jinin jikinshi, yasan yauma cikin ɓacin rai take, ta nema wuri ta zauna ba tare da tace mishi komi ba, kamar ma batasan akwai wata halitta a wurin ba,

  "Ranki shi daɗe an dawo lafiya? Ya gajiar makarantar? ya hanya?"

  Wata banzar kallo ta watsa mishi "nayi maka kama da wacce zata amsa maka duk wannan tambayoyinne? Kokai makaho ne da bazaka iya gani ba?"

  "Allah ya huci Zuciyarki, ai tun ɗazu daga makarantarku nan na taho, baki kula ba har wayarki na kira ban samu ba"

  Taja tsoki tana k'ara mishi wani kallon sama da k'asa "Ai indai aikinka ne naci da duk number da nayi saika nema, ni kuma bazan gaji da canja layi ba,"

  "wai menene ma ya kawoka gidanmu?"

  "Haba Aleesa yanzu bazanzo ganinki ba sai wani abu ya faru? Ga biki nata matsowa ya kamata mu shirya yanda kikeso ya kasance ko" 

  "kai wannan ya dama"

 Sai kuma ta canja yanayinta ta ɗan rage zafin da tazo dashi kamar wacce ta tuno wani abu,

   

  "Yauwah daman inason muyi magana" duk ya tattara hankalinshi da nutsuwarshi gareta, farin ciki ya kasa ɓoyuwa a fuskarshi ganin yau Aleesa ce keson magana dashi kuma ba tare da tana masifa ba, 

  "ki faɗa kawai Aleesa duk wani lokacina naki ne"

  "Naji anma bazaka faɗama kowa ba?"

  "Haba Aleesa nida na daɗe inason ki faɗi wani abunda kikeso in miki, sai wannan er k'aramar Alfarmarce zata gagareni in miki? Ki faɗa koma minene na miki alk'awarin zan miki"

  "ba wani babban Abu bane, so nake ka janye maganar aurennan, kaasan dai ba sonka nake ba"

  "na daɗe da sanin hakan, anma bayan wannan babu wani dalilin? Don k'ara kicemun in baki rayuwatah zan iya mallaka miki, anma bazan iya hak'ura da aurenki ba"

  "koda na faɗa maka cikine dani?" ta faɗa tana kallon yanayinshi, aykam gaba ɗaya hankalinshi ya tashi,

  "Ciki kuma Aleesa?"

 "sai kaa buɗe murya kaa gama faɗa kowa yaji sannan zangane kasan me nace," ta faɗa tana harararshi,

  "kaa san dai babu kyau aure da ciki, kuma kisan kai ma babu kyau, don haka tunma kafin kowa yaji k'ara ka janye maganar aurennan"

  

 Ya daɗe yana tunani, duk rikice yake kamar wanda yaji sak'on mutuwa, dak'yar ya iya buɗe baki ya fara magana,

  "Tohh anma Aleesa kinsan inajin Kunyar Daddynku, kidai nema wata buk'atar banda wannan, anma zuciyatah bazata iya jure tayi nesa dake ba"


 Tuni ya gama bata haushi, harta fara murnar samun nasara sai kuma gashi zai k'ara ɓata mata rai,

  "Shikenan tunda bazaka janye ba, zan samu su Daddyn in faɗa musu da bakina cikinne dani, sannan kuma ince kaine kamun"

  Duk ya fiddo idanunshi a waje yana mamakinta,

  "Ni kuma Aleesa?"

 Ta ɗaga mishi kai cikin jin daɗin samun nasara 'k'warai ma kuwa"

  "son gaskiya nake miki Aleesa, kuma a dai dai wannan lokacinne ya kamata in tabbatar miki da son da nake miki, duk wani abunda ya shafeki kamar nine ya shafa, wlhy har a zuciyatah nake faɗa miki, zan karɓi abunda yake cikinki, zan zame mishi gata, ban damu da sanin koma wanene ubanshi ba, nine zan zama mahaifinshi tunda inason mahaifiyarshi,"

  "wai kai wane irin dak'ik'ine da bakasan me yake maka ciwo ba?"

 Yayi murmushi "indai akan sonkine ki kirani da koma menene"

  "koba taurin kai da naci ba? Wlhy Ajaline yake kiranka don zan iyayin komai Sanadin Kiyayyar da nake maka" cikin ɓacin rai tayi maganar anma saida ya tsorata, don yasan komai zata iyayi akan k'iyayyar da take mishi,

  Har takai k'ofa ta kusa fita, ya ɗaga muryarshi,

  "Na yarda da tarbiyarki, nasan bazaki taɓa kusantar zina ba," 

 Kamar yanda ya zata ko saima k'ara saurin da tayi tabar ɗakin, tana k'arajin wani haushin,


 ©️Rabiatu sk msh

[2/13, 19:24] Rabiatu sk msh✍🏻: ♠SANADIN K'IYAYYA♠

      (︶︿︶)

         13-14


©️Rabiatu sk msh

      NWA


Dedicated to Mrs Umar and Maman Adnan


www.babymsh.blogspot.com


 Kwana biyu anata shirye-shiryen biki, duk yanda Aleesa taso a janye maganar aure anma babu mai saurararta, duk irin tijarar da take sauke mishi, harce mishi tayi H.I.V ne da ita, anma ya nace shidai sonta yake,

  Ana gobe ɗaurin aure dubara ta gama k'are mata, ga k'iyayyarshi dake k'ara yawaita a zuciyarta, ji take kamar ta haɗiye zuciyah ta bar mishi duniyar duk don tsanar data mishi, wayarta ta ɗauka ta tura mishi text kamar haka,

  Zagi sosai ta dinga mishi harma da wanda batasan anayi ba, sannan ta k'ara da cewa "Wallahi idan har bazaka janye maganar aurennan ba nice zan zama ajalinka, k'ara in kasheka nima a kasheni, da inyi zaman aure dakai, banza mai naci kawai" 

  Wayar na hannun wani Abokinshi text ɗin ya shigo, ya bala'in tsorata da kalamanta, a rikice ya nuna ma kabeer message ɗin, murmushi kawai yayi cikin nuna rashin damuwa,

  "wannan ba sabbin kalmomine dana taɓaji daga bakin Aleesa ba, ballantana su tsorata ni, barazana ce kawai, da kuma yarinta dake damunta"

  "Yarinta kuma kabeer? Yarinyar da har degree taa gama kacemun wani yarinta, kada fa So ya rufe maka ido ka kai kanka a halaka, wlhy bazan taɓa yarda tunda ta furta komai zata iya aikatawa, yanzunnan zan samu su baba k'ara a janye maganar aurennan, tunda dai iyakar k'iyayya taa nuna maka, " da sauri ya fara k'ok'arin tsayar dashi, anma bai saurareshi ba ya fita da wayar a hannu,


****

Tana kwance bayan taa gama tura mishi text ɗin, kanta ne ke mata ciwo bayan kukanda takesha kullum, ga kuma zullumin da take ciki na auren kabeer, gobene kuma lokacinda Abba ya bata zai cika, sai dai a ɗaura masu aure kawai,

  Sak'one ya shigo wayarta, har sauri take ta buɗe tana tunanin kona Kabeer ne, amma bashi bane, text ɗin Hanan ne,

  "ki fito ina harabar gidanku wurin Ajje motoci, kiga wani abin mamaki" tsoki taja, ita Hanan abun mamakinta duk ban haushi ne dasu, tanata tunaninta dai ta fito harabar gidan da sauri ta k'agara taga yau kuma me tazo mata dashi,

   Tsaye ta ganta jikin mota, tun kafin su gaisa tace,

  "Menene zan fito in gani da bazaki iya shiga ki nunamunba"

  "daɗina dake zumuɗi Aleesa, shiga ki gani mana" tana nuna mata cikin motar, ta buɗe kawai ta shiga, da sauri da fito ko zama batayi ba,

  Hanan ta kwashe da dariya "lafiyanki kamar wacce taga abun tsoro?"

  "Hanan dagaske Hadid ne cikin motarnan ko kuma Gezau yakemun?"

  "shine dai Aleesa, ki tabbatar da kanki mana"

  Da sauri ta koma cikin motar, farin cikinta ya kasa ɓoyuwa, sai murnar ganinshi take, shi kuma duk yaa haɗe rai ya kauda fuskarshi gefe ɗaya,

  

  "Hadid daman kananan? Nasha wahala wurin nemanka Hadid, anma yanzu ma wuri bai k'ure mana ba, don Allah taimakonka nake nema"

  "kinga malama, ni wallahi banmasan gidanku zamuzo ba da babu abinda zai kawoni, tuni na fiddaki cikin rayuwatah"

  "Haba Hadid nasan kana sona, don Allah koda wasa ne ka taimakeni in gabatar dakai a wurin Daddyna, wallahi auren dole za'amun, kaaga dai gidanmu cike da mutane duk bikina ne sukazo, don Allah ka taimakeni, ka manta da duk wani abu daya faru tsakaninmu" shiru kawai yayi yana saurarenta yanda taketa rok'onshi, wani irin haushinta yakeji, sai kuma ya tuna da abunda ta mishi, bai manta da marinshi da tayi ba, ga kuma wulak'ancin data mishi a ranar birthday ɗinta, yanzu yaa samu damar dazai rama duk abunda ta mishi,

  "Ya isa haka Aleesa, wannan rok'on da kikaimun ya goge duk wani laifi da kikamin a baya, saboda har yanzu akwai sauran soyayyarki a zuciyatah"

  "da gaske kaa amince Hadid?" ta faɗa cikin farin ciki, ya ɗaga mata kai yana murmushin mugunta,

  "na gode sosae da wannan farin cikin daka bani, insha Allah yau ɗinnan zan kaima Daddy maganarka"

  Ya ɗaga kai cikin gamsuwa, bai wani daɗe ba sukai sallama zai tafi, tana fitowa daga motan ta hango Daddy naa tsaye yana hangenta duk ya gama haɗe rai,


©️Rabiatu sk msh

[2/15, 10:41] Rabiatu sk msh✍🏻: ♠SANADIN K'IYAYYA♠

      (︶︿︶)

          15-16


©️Rabiatu sk msh

      NWA


Dedicated to Mrs Umar and Maman Adnan


www.babymsh.blogspot.com


  Da sauri ta raɓa ta gefenshi zata wuce, ya daka mata uwar tsawa ba shiri taja burki, yaja hannunta k'iii har ɗakinshi don kar yayi magana mutane suji,

  "Wane ɗan iska ne kikazomun dashi cikin gidannan?"

  "Hadid ne Abba, shine wanda zan aura ɗin" ta faɗa bakinta na kyarma,

  "wannan tantirin ɗan iskan Aleesa?" ya faɗa cikin mamaki, don har ganin Hadid ya taɓayi da wata a mota suna shafe-shafe, harya gwada yi mishi nasiha, bai saurareshi ba duk da ganinshi babban mutum anma saida Hadid ya karta mishi rashin mutunci,


  "ba'a gidana ba Aleesa, daman shi yake zugaki kina mana yanda kikaga dama ko? Ke yanzu har kinyi tsaurin idon da zaki tura ma Kabeer sak'on barazana ko?" dagajin yanda yake maganar abun na matuk'ar mishi ciwo a zuciyah,

  "Suɓutar bakine Daddy, anma wlhy nidai bazan iya aurenshi ba....."

  "ke kika sani, nidai bazaki taɓa sakani inyi k'aramar magana ba, sannan kuma sak'on da kika tura mishi bazai taɓa sakawa a fasa aurennan ba, nida kaina na kai maganar nan police station, don abun naki ya fara fin k'arfina" kukanta ne ya k'ara tsawaita, ya k'ara daka mata tsawa,

  "ficemun a ɗaki" da gudu ta ɗita ɗakinta tana kuka ta faɗa saman gado, ta iske Ummie tazo, ita taɗan kwantar mata da hankali sai dare ta tafi, 

  

  Daman abunda take jira kenan, zuciyarta a k'ek'ashe ta nemo number Hadid ta fara kiranshi, bata daɗe tana ringing ba ya ɗaga, kuka kawai ta fashe mishi dashi, duk ya rikice,

  "lafiyanki kuwa Aleesa? Meke faruwa dake?"

 Cikin muryar kuka tace "ka taimakeni Hadid kazo mu gudu, Daddy bazai taɓa yarda da aurenmu ba, don Allah ka gudu dani ko bazaka aureni ba ka kaini can wani wurin"

  "Haba Aleesa ki kwantar da hankalinki mana,....."

  "taya hankalina zai kwanta? Gobene fa ɗaurin Aurennan, wallahi k'iyayyarshi zata iya jamun in aikata komai, don Allah ka ceci rayuwatah" jin rok'on da take ta mishi, gashi a hakanma zaifi samun damar dazai rama abun data mishi, harya gama tunani a ranshi fyaɗe kawai zai mata ya yasar da ita tsakar gari,

  "shikenan ganinan tafe"

 Cikin farin ciki ta kashe wayar, daman ta riga da taa gama haɗa kayanta, tun kafin yazo ta ɗauka jikkar ta fito a sulale, cikin sa'a mai gadi bainan harta fita babu wanda ya ganta


  Kusan Awa ɗaya tana jiranshi a bayan gidansu, harta fara k'osawa saiga motarshi ta taho, da sauri ta tafi zata shiga tun kafin ya gama parking duk a tsorace take, 

  Fitowa yayi ya zagayo inda take zai buɗe mata, sai kawai ji yayi abu yaa bugi kanshi, wasu manyan k'arti guda huɗu kowanne da mugun makami, tuni Aleesa ta fara matse fitsarin dake k'ok'arin zubo mata, akan idonta k'artinnan suka dinga jibgarshi,

  Ba k'aramun buguwa yayi ba, akan idonshi Daddyn Aleesa yazo yaja hannunta, ashe daman ya lura da fitarta, shiyasa ma ya saka ayi gadin wanda zaizo ya tafi da ita bayan ya bada umarnin duk wanda aka gansu a tare a mishi mugun bugu,

  Hadid kallon Daddyn Aleesa ya shigayi duk da azabar da yakesha, bai manta da fuskarshi ba, wata wutar ɗaukar fansarce ta k'ara ruruwa a cikin zuciyarshi, daman cike yake da haushin Daddynta,

  Laifukan da Aleesa da mahaifinta suka mishi ba masu yafuwa bane, Bayan marin data mishi a cikin jama'a, da kuma wulak'ancin data mishi, ga tozarcin da mahaifinta ya mashi, da kuma wannan dukan daya saka aka mishi sanadin Aleesa, dolene ma ya ɗauka fansa,

  Wani irin kallo ya bisu dashi har suka shige gidan yana jan Aleesa tana faɗuwa, shi kuma ya faɗi sumamme,


  Suna shiga gidan ba tare da kowa ya sani ba, Daddy ya jefata ɗakinta ya rufe, har saidata bugu a k'asa, ta zube nan tana rusar kuka har barci ya kwasheta,

  Washe gari ɗaurin aure, anata neman amarya babu ita, ga ɗakinta a rufe, don tsananin ɓacin rai Daddy da safe ya mayar da ɗaurin auren, babu ma wasu mutane masu yawa aka ɗaura, kuma ba'ayi wani shagalin biki ba, ita dai daman ko k'awayenta babu wacce ta sani sai ummie,

 Ba'a fiddo Amarya ba sai da dare ana shirin kaita....


©️Rabiatu sk msh

[2/15, 14:27] Rabiatu sk msh✍🏻: ♠SANADIN K'IYAYYA♠

      (︶︿︶)

         17-18


©️Rabiatu sk msh

      NWA


Dedicated to Mrs Umar and Maman Adnan


  Abba da kanshi ya saka Aleesa a motah ba tare da neman Rakiyar kowah ba, tana kuka tana komai, har cikin ɗakinta ya kaita, don tsananin jin haushinta ko nasiha bai tsaya mata ba,

  Anan ta duk'e tana kuka, donma karta taka ginin gidan kabeer, saita haye can saman hadaɗɗen gadon da aka kai mata, tana ci gaba da kukanta don tsananin k'iyayyar da take mishi, ta manta ma acikin gidan take, 

  Wani abu ta tuna, da sauri ta mik'e ta nufi kitchen, tana dudduba kayanda aka kawo mata, saida tasha wahala duk taa birkita kayan, sannan ta samo wata er k'aramar wuk'a mai kaifi sosae, ta dawo ɗakin zuciyah nata mata huɗuba kala-kala, wani iri takeji a zuciyarta komai ma haushi yake bata, ta rink'a dukan kanta da hannunta tana kuka, ji take daman ta mutu kawai ta huta da tsanar data mishi,

  

  Ta mik'e ta fara jifa da kwalaban humra da aka jera mata dana turaren wuta, suka dinga fashewa suna zubewa, ta jefa wani tsakiyar madubi shima duk ya tarwatse, har ya dawo mata kusa da ido wurin ya fashe, jini ya fara zuba, duk da haka bata saurara ba ta fara waigen ɗakin tana neman abunda zata fasa,

  Tunda ya shigo gidan ya fara jiyo k'arar fashe-fashen da takeyi, daman shi kaɗai yazo don duk Abokanshi haushinta sukeji saboda k'iyayyar da take nuna mishi shi kuma yana nace mata, en uwanshi ma babu mai sonta, saboda ik'irarin da tayi na kasheshi, duk basu so auren ba,

  Cikin tashin hankali ya k'arasa cikin falon duk ta mishi kaca-kaca, ga jinin dake zuba a goshinta, a rikice ya fara ɗosana k'afarshi don karya taka kwalaban da suka fashe, ya nufi inda take,

  "karka kuskura kazomun inda nake,"

  "Haba Aleesa ya zakice kar nazo inda kike? Don Allah karki illata kanki"

  "Don Allah Aleesa kiyi hak'uri kinji, nasan na aikata miki laifi, anma kiyi hak'uri karki jima kanki ciwuka koma me kikeso zanyi" wani murmushin takaici take mishi,

  "Ai kaa riga da kaa makaro Kabeer, tunda ka aureni kaa gama illatamun rayuwah, idanda abun daya rage kamun kawai karka k'ara nuna mummunar fuskarka a gareni, na tsaneka! na tsaneka!!, na tsaneka kabeer, idan har kanasona meyasa ka k'wacemun farin cikina? Don Allah ka rabu dani?"

  "Haba Aleesa, taya zan iya rayuwa ba tare da ganin fuskarki ba? Wallahi ina sonki Aleesa, ki bani dama koda sau ɗayane in gwada miki irin sonda nake miki"

  "Wai wannan wanne irin naci ne? Anya babu taɓin hankali a tare dakai? Mutum sai shegiyar k'wak'wa"

  "kiyi hak'uri...."

 "Ka wuce ka fita nace!!" ta faɗa da wata irin tsawa muryarta na rawa, 

  "Ka tashi ka fita tun kafin ɓacin rai ya sakani yin abunda mu duka zamuyi nadama daga baya, ka tashi ka fita kawai"


  "Ya za'ai in fita in barki cikin wannan halin? Kimin Alk'awarin bazaki aikata ma kanki komai ba"

  "Bazaka fita ɗin ba kenan? Ina zuwa" ta ɗaga filo ta ɗauko wuk'ar data samo kitchen ta nunashi da ita,

  "hak'urina ya fara k'arewa, ka fita kawai nace,"

 Ya zaro ido yana kallonta, "me zakiyi Aleesa?

  "SANADIN K'IYAYYAR da nake maka babu abunda bazan iya aikatawa ba!"

  Ya fara ja baya yana kallonta,

  "Don Allah kiyi hak'uri, ki fahimceni Aleesa, nasan bazaki iya kasheni ba,....."

  "k'warai ma kuwa, anma zan iya kashe kaina"

 Ya k'walalo idonshi yana kallonta ta harareshi,

  "komai zan iyayi don in bak'anta maka, idanna kashe kaina wa za'a tuhuma? Idan duk duniya zata taru babu wanda zai yarda akan bakai ka kasheni ba, tunda kowa yasan abunda ke tsakaninmu, harma a rink'a cewa donka huce haushin abinda nake maka ne, kai maganganu dai gasunan"

   Tunda ta fara magana kallonta kawai yake ya kasa ko motsi,

  "Ya zakaji idan na mutu gaba ɗaya? Kuma ace kaine ake tuhuma da laifin kasheni? Kodan in dasa maka wannan bak'in cikin zan iya kashe kaina, don haka kai nake jira, ka tashi ka fitarmin a ɗaki, kuma duk ranar dana k'ara sakaka idona saina aikata abunda na faɗa,"

  

©️Rabiatu sk msh

[2/15, 15:40] Rabiatu sk msh✍🏻: ♠SANADIN K'IYAYYA♠

      (︶︿︶)

         19-20


©️Rabiatu sk msh

      NWA


K'ARSHEN PART ONE


 Kallonta yake sai faman girgiza kai yake yana hawaye, duk hak'urinshi da kauda kai a abu yau saida ta sakashi kuka, bai taɓa tunanin k'iyayyar da take mishi yakai haka ba,

  Ganin kallon da yake mata ya saka ta ɗaura wuk'ar a hannunta ta lumata sosae anma bata yanka ba,

  "Kamar baka yarda da abinda na faɗa maka ba," da sauri ya nufo inda take cikin tashin hankali, kafin ya k'araso taa jaa wuk'ar ta yanketa sosae jini ya fara zuba, sannan tayi saurin ɗaurata a mak'ogwaranta,

  "karka kuskura ka k'arasomunnan, kana k'ara saka k'afarka wallahi saina aikata abunda na faɗa"

 Yaja baya ya tsaya, kuka kawai yake kamar k'aramin yaro, gaba ɗaya ya tsani kanshi, ga jini yana zuba a hannu da goshinta anma babu damar dazai taimaka mata, 

 Ta k'ara ɗaura wuk'ar a wuyanta,

  Yayi saurin mik'a hannunshi kamar zai rik'eta duk da nesa suke, muryarshi na rawa, 

  "Shikenan Aleesa, shikenan zan fita, don Allah karki yanka" ya faɗa yana jaa da baya, sai kuka yake,

 A haka yabar ɗakin, sannan ta sauke hannunta, ga zafin da hannunda ta yanka yake mata, ga jinin dake zuba har a goshi, wani irin jiri takeji, anan ta sulale ta kwanta, 

 

****

Saukar ruwan data fara ji a fuskarta ne, ya sakata buɗe ido a hankali, gaba ɗaya kanta yaa mata nauyi dishishi take gani, a hankali ta k'ok'arta ta tashi zaune, sannan ta ɗaga idonta taga waye a kanta?

 A razane ta k'arasa buɗe idonta tana kallonshi,

  "Ɗan sanda kuma? Waya kawoshi?" ta fara k'are ma ɗakin kallo cike yake da en sanda, ga Daddynta tare dasu da mahaifin Kabeer,

  Ta mik'e tsaye tana tunanin meya kawosu? Bakinta ma ya kasa furta komi, Ganin yanda Daddy ya haɗa kai da bango yana kuka sosae abinda bata taɓa gani ba, ga wani irin kallon tsana da Mahaifin kabeer yake mata,

  Ta mik'e tsaye dak'yar, sannan ta hango mutum kwance cikin jini, ga wuk'ar data gama mishi barazana da ita jiya nan an yayyankeshi da ita sannan aka luma mishi a ciki, jikinta na kyarma take kallon gawar Kabeer harta kusa faɗuwa,

  A hankali ta nufi inda gawar take shi ɗinne dai, ta ɗago fuskarta maganarta ma dak'yar take fita,

  "Daddy waya kasheshi?" a zuciye yakai mata wani wawan mari da har saida ta rasa jinta na wani lokaci,

  "Akwai sa'anki anan ciki da zaki maida mu wawaye? Kin cuceni, kin cuci kanki Fatima (ya faɗi sunanta na gaskia), bazan taɓa yafe miki ba akan hakan" da sauri ta rik'e baki,

  "Na shiga Uku Daddy don Allah karka tsinemun, wallahi bani na kasheshi ba"

  "kina tunanin akwai sakaran da zakima wannan maganar ya yarda dake? Ai kin faɗa da bakinki Aleesa, idan kinje can station kin musu bayani, kuma daga yau karki k'ara tunanin kina da wani uba a duniya"


Hannu biyu ta ɗaura saman kai tana kuka "Naa shiga uku ni Aleesa me yake shirin faruwa dani?" maganganunsu da Kabeer ne na daren jiya suka ringa faɗo mata, Sharrin da take niyyar k'ulla mishi sai gashi ya dawo a kanta, tasan idan duk duniya zata taru babu wanda zai yarda da ba ita ta kasheshi ba, shiyasa idan zaka gina ramin mugunta ka yishi gajere, ita dai ga abunda SANADIN K'IYAYYA ya jawo mata, da kuma illar auren dole,


 Waya kashe kabeer? Shin Hadid ne ko kuma shida kanshi ya kashe kanshi don ya maida ma Aleesa abunda tayi niyyar mishi? Ko kuma wani ne can daban? Aleesa ta kasheshin da gaske? Wanne hali zata shiga gaba? Ina labarin ɗaukar fansar hadid? Tambayoyi da yawa.... Ku biyo ni a Part 2 don jin amsoshinsu, wanda ni kaina a yanzu ban sani ba saina koma ɗauko rahoto😳


 Alhamdulillahi,

  Godiya ga Allah (S.W.T) daya bani ikon kammala wannan tak'aitaccen littafin, kuskuren dake ciki Allah ya yafe mana, 


  SADAUKARWA

 wannan tak'aitaccen labarin sadaukarwa ne hazik'an marubutannan, MRS UMAR, da kuma MAMAN ADNAN (ummieluff), Allah ya k'ara basira, Ameen


RAZ

A friends like you can never replace, deep in my heart you will always stay, Allah ya barmu tare cikin haɗin kai da k'aunar juna, Ameen😍


Ina godia ga duk masoyana, da kuma makaranta littafinnan, Allah yabar k'auna, ga wanda ke neman part one ɗinnan daga farko zasu iya dubawa a blog ɗina


 www.babymsh.blogspot.com


Gaisuwa da jinjina ga dukkan marubuta Online, Allah ya k'ara basira, Ameen


©️Rabiatu sk msh

Tags: #kiyayya #Kabeer #Aleesa
3424
0
5
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

2019-10-01 14:54:46

2019-07-21 10:48:37