Sanadin Haduwarmu!

Written by Pharty B BPublished on 2018-12-12 17:47:25Category FictionLabarin matashiyar budurwa mai cike da tsantsar tausayi da rashin gata Soyayya da rashin taimako... tags: #PhartyBbDuba was labarai »

BISMILLAHIR RAHMANEEN RAHEEM


NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


SANADIN HAD'UWAR MU

©Pharty BB


(1)


   ANGUWAR LIMAN

 Anguwar liman wani k'auyene dake jahar katsina a kar'kashin k'aramar hukumar Batagarawa.

'Kauyene da Rashin Ilimin Boko da Islamiyya yayi 'karanci, K'auyene da jama'a cikinta suke fama da rashin wadatattcen ruwa balle wutar lantarki, babu hanyar mota sai burji saboda halin ko in kula da gwamnati ta nuna akan garin.

Akasarin mafi yawancin mutanen garin Fulani ne sannan kuma manoma ne, sukan noma hatsi su kai cikin birni su sayar, a haka dai suke rayuwar su.


Yammacin Wata Litinin

Yarinyace y'ar kimamin shekaru goma sha biyu a duniya, sauri take sosai kanta d'auke da tulu sai hard'e kafafuwanta take sakamokon saurin da take yi, Allah-Allah take ta isa bakin rafin ta d'ibo ruwan da mahaifinta ya sata dan a samu a dafawa mahaifiyarta magani dashi, da isarta ta samu layi a bakin rafin kasancewar shine babban rafin garin kuma ruwansa yafi kyau, rokonsu ta fara yi tare da durkusawa ko zasu tausaya mata, duk da sun girmeta a d'ari d'ari take rokonsu karsu mata duka dan tasan halinsu da sun girmi yaro dukansa suke a kauyen.

D'aya da suke tsayene cikin 'yan matan k'auyen ta kalli k'awartan dake zaune kusa da ita ta juyar da kai.

"Ramme kiyi magana mana, kinsan waccan mayyar ba barinmu za tayi ba in bata d'iba ba."

Wacce aka k'ira da Rammen ne ta juyo ta watsawa Ummu dake tsugunne wani kallo, cikin tsawa tace.

"Matsamin daga nan kar naci ubanki shegiya bak'a mummuna."

Cikin sauri ta matsa gefe tana sharan kwalla, sai da suka gama iskancin su da iyayinsu kafin suka d'au tulunsu su kayi gaba, sai lokacin Ummu ta samu ta d'iba ruwan sauri-sauri ta baro wajen, a haka har ta iso gidansu dake kewaye da zana da kaba da d'akin biyu na jar k'asa sai dan kewaye na kiwon kajin Babanta guda biyu sai kewayen band'aki.

Da sallama ta shiga ba kowa tsakar gidan, d'akin mahaifiyarta ta shiga nan ta tarar mahaifinta zaune kusa da mahaifiyarta yana mata firfita saboda zafi ga zafin ciwo, kusa dasu ta k'arasa tace.

"Baffa ga ruwan na debo layi na samu, Inna sannu kinji."

Ta fad'a tana goge hawayen fuskarta, kallonta mahaifinta yayi yana mik'a mata maficin hannunsa.

"Zoki mata firfita bari insa Abu ta d'aura ruwan."

Karban maficin tayi ta fara mata firfita shiko ya fita ya nufi d'ayan d'akin, sallama yayi shuru ba amsa, labulen d'akin ya daga yaga wayam bata nan, komawa yayi ya nufi inda suke ajiye dan kara da budu da suke hura wuta, d'auka yayi yasa a murhunsu da manyan duwatsune guda uku, dakyar ya hura wutan ya d'ora ruwan maganin da aka bashi, bayan ya tafasa ya juye a daro yakai wani d'an karamin bangida an kewayeshi da zana da langa langa, bayan yakai yaje d'akin ya taimakwa Inna ta fito ya kaita bangidan, wanka tayi da ruwan maganin ta fito ta koma d'akin ta kwanta, lokacin ana kiran sallar la'asar, alwala Baffah yayi ya musu sallama zai tafi masallaci.

Bayan tafiyarsa da taimakon Allah dana Ummu Inna ta samu ta fito da guntun ruwan da Baffah yayi alwala tayi dakyar ta koma d'akin, nan itama Ummun tayi yar shafe gudun kar ruwan ya kare kuma ba dama su tab'a na Abulle, zaune ta tarar da mahaifiyartan tana sallah duk da ba yau ta saba ganinta tana sallah haka ba amma duk lokacin data ganta sai taji tausayinta duk da kasancewarta k'aramar yarinya sosai amma tanajin tausayin mahaifiyarta.

Sallah tayi ta fito tsakar gidan ta share ta wanke kwanukan da Abulle da yaranta suka b'ata ta saka itace a murhun kamar yanda Abulle ta koya mata kafin ta koma d'aki, kusa da Inna ta zauna tana mata firfita can tace.

"Inna banyi wanka ba tin jiya da safe."

Kallonta Inna tayi kafin dakyar ta bud'e baki tace.

"Ki bari gobe in kunje debo ruwa da safe sai kiyi sawu uku a maimakon biyun da ki keyi sai kiyi wanka da d'ayan."

"To Innata."

"Budd'ona Tashi ki shirya makarantar Allo."

"Innah inna tafi wazai kula dake."

"Karki damu Baffanku zai dawo yanzu kuma bana bukatan komai yanzu."

Tashi tayi ta d'auki wani ko'dadden hijab nata duk yasha faci ya mutu murus, bayan tasa ta d'auki Allonta tama mahaifiyarta sallama ta fita, a kofar gidan ta had'u da Abulle da yaranta uku, Dije ta girmeta da shekaru biyu sai Laure sa'arta da Ja'afaru dan shekaru uku.

Durkusawa tayi da sauri tana cewa.

"Sannu da zuwa Dadah, kin dawo lafiya."

Ko kallo bata isheta ba tayi wucewarta da yaranta cikin gidan, Laurece ta tsaya tace.

"Ummu jirani in d'auko allona."

"To." Tace mata tana tashi daga tsugunnon da take, baifi minti uku ba ta dawo d'auke da allonta suka fita a gidan.


Abulle ko tana shiga taga abinda Ummu tayi kwafa tayi ta hura wutan ta d'aura ruwan tuwon garin masara, tuwon masara da miyar kuka ta musu ruwa-ruwa dagashi sai kalwansa da gishiri sai magi biyu, bayan ta kwashe ta zuba malmala biyu a wani kwanon kafi dish duk yayi lamba da tsatsa ta tura Ja'afaru ya kaiwa Inna itada Ummu, sauran ta kwashe itada yaranta da Baffa.


Baffah bai dawo ba sai biyar saura da sallama ya shiga gidan Abulle ce da Ja'afaru sai Dije suna zaune tsakar gidan sai hira suke suna ihu kamar zasu tsaga gidan, bak'uwar da yake tafe da itane suka tsaya kallonta, bakuwarce tayi karfin halin gaishe da Abulle, a yatsine ta amsa dan taga kamarta da Munira(Inna).

"Ki shiga tana cewa." 

Cewar Baffah yana dosan kofar dakin, da sallama suka shiga yanda take kwance haka suka sameta, bak'uwar na ganin halin da y'ar uwarta take ciki ta fara hawaye.

"Yanzu halin da kike ciki Munira da gatanki da iyayenki, meke damunta Ahmadu?"

Da kyar Baffa yace.

"Kamar jejine(Cancer) ya kama kafar d'aya."

"Na shiga uku ni Salamatu jeji Ahmadu kuma ka sata gaba kana kallo wato in ta mutu kai baka da asara ko to walli tafiya zanyi da ita, tana da gatanta ka ganta ka aurota ka kawota wannan bakin garin da ruwan shama gagaran mutum yake yi, ka raba da kowa nawa."

"Dan Allah Adda Salamatu kiyi hakuri wallahi ba haka bane ina iya bakin kok'arina ganin na sama mata magani ko dazu na karbo mata na wanka daga gurin abokina."

Ina sam Addah Salamatu ta dage gobe gobe zata tafi da Munira garinsu dan nema mata lafiya, wannan kauyen da ko makaranta boko babu balle asamu wani mai magani tasan in dai ta barta to sai dai suzo su d'auki gawarta, shiko Baffah hakuri yake bata kamar ya ari baki, suna cikin haka Ummu ta dawo, tayi murnan ganin Addanta bayan ta gaisheta ta zauna danjin abinda suke yi nan suka yi shuru dan karta fuskanci wani abu.

Da magriba Baffa ya tafi masallaci suma suka yi sallah yan zuma da taimakon Adda Salamatu Inna tayi alwala tayi sallah a zaune ta koma ta kwanta, dan daga kwanciya sai sallah sai wanka abinda ke d'agata kenan, bayansu Ummu sun idar da sallah ta jawo kwanon data gani a rufe ta bud'e nan tayi karo da tuwon masara miyar kuka, d'auka tayi takai gaban Adda Salamatu suci, abincin ta kalla ta kare masa kallo bakin ciki kamar ta zubar, yanzu wannan shine abincin da suke ci kuma a hakan marar lafiya yaci, tafiya kam takama dole tayi da kanwarta dan sama mata lafiya.

"Addah muci tuwo."

Cewar Ummu tana tsoma hannu, dadi takeji yau za suci dadi kamar Abulle tasan da zuwan Addanta ta musu tuwo da miya dayawa.

"Ah a Budd'o kici ni na koshi."

"Haba Addah to me za kici?"

"Na koshi nace kici."

Shuru tayi taci gaba da cin tuwonta harta koshi ta rufe sauran ta fita ta wanke hannunta ta dawo d'akin nan ta tarar da Addah tasa Innarta a gaba tana hawaye itama na hawaye, taji magana inda Inna take cewa Addah ya zanyi da Budd'o? Shine kawai abinda taji bayan ta shiga taji sunyi shuru, bata kawo komai a kanta ba taje ta kwanta a kasa bayan ta shimfida zanin Innarta haka bacci ya d'auketa.


Baffa kam bai dawo ba sai bayan Isha'i da biredi da shayi yasha madara yan kulli, wanda dakyar ya samu ya ranci kudi ya siya, da sallama ya shiga gidan ba kowa a filin gidan, d'akin Inna ya shiga ya gaishesu ya tambayesu ya jikin ya ajiye musu shayin ya musu saida safe ya nufi d'akin Abulle, daga ita sai Ja'afaru, Laure da Dija sunje gidan makotansu kawarta Lami Abulle dan nan suke kwana in Baffah na d'akinta. 

Abincinsa Abulle ta kawo masa dakyar ya iya ci yana tunanin maganganun Addah Salamatu, bayan yagama yayi shafa'i da wutir ya kwanta Abulle kam ta dade dayin bacci sai munshari take zubawa.

Can d'akin Inna kwana Addah Salamatu tayi a kanta dan yau jikinta ya 'kara tsanani, ta gama yanke shawarar tana komawa garinsu zata fad'awa Mai martba halin da 'yarsa take ciki ko zaiyi wani abu akai, da wannan shawara ta kwanta bayan ta samu bacci ya d'auki Inna itama ta kwanta.


Washegari ya kama ranar alhamis da asubar fari bayan sun idar da sallah, Ummu ta d'auki tulunta ta tafi rafi d'ibo ruwa, baifi mutane uku ta samu gabanta ba , bayan sun d'iba ta ibi nata ta taho gida, haka har tayi sawu hudu ta k'ara kan wanda mahaifiyarta tace tayi, bayan ta gama ta share gidan tayi wanke wanke tashiga wanka, cuccud'awa tayi dan ba sabulu balle soso haka tayi wankan.

Bayan ta gama ta fito tasa wani kod'addiyar doguwar riganta, ganin kayan da tasa saida idon Addah Salamatu ya ciko da hawaye, wai 'yar uwarta y'arta take sanye da wannan kayan, share hawayenta tayi ta jawo kwanun da Laure ta kawo musu inji Abulle abincin karyawa, dumamen tuwon jiyane, da sauri Addah Salamatu ta juyar da kanta ta turawa Ummu gabanta.

"Kici Budd'o in zaki iya."

Jan kwanon tuwon tayi ta faraci.

"Addah kici akwai dadi jiyama baki ciba kika kwanta."

Girgiza kanta tayi tama kasa magana, Ummu kam cin tuwonta take kamar ba gobe, bayan ta gama ta fitar da kwanon.


Da Azahar Addah Salamatu ta musu sallama tace zata koma, Innah sai hawaye take tana girgiza mata kanta akan karta yarda ta fad'awa danginsu halin da take ciki amma bata kulataba, haka ta musu sallama ta koma kauyensu Batagarawa.


Cikin kwana uku da tafiyar Addah Salamatu jikin Inna yayi tsanani ko magana bata iyayi tsakaninta da mutum sai ido, Baffah na duk bakin kok'arinsa ganin ya sama mata magani d'an tumakinsa duk ya siyar gashi dama su biyu iyayensu suka haifa, Yayansa da baisan k'asar da yake ba bai san ta inda zai fara nemansa ba tin suna k'anana da suka rabu, tin lokacin har iyayensu suka rasu duk bai zoba balle yasan inda yake, Ummu ko duk da yarinta tana tausayawa mahaifiyarta, haka duk safiya ya zama yanzu ita take cika manyan tulunan gidan tayi shara da wanke wanke taje can bayan gari ta iyo itace wani lokacin Laure ke taimaka mata dan Dije tsakaninta da ita duka.


Yau ya kama ranar a Asabar da safe tin duku duku taje rafi ta d'ibo ruwa sawunta shida kafin randunan gidan suka cika, tayi shara da wanke wanke ta d'auki wani d'an dumamen da Abulle ta d'iba mata a wani roba, lomanta biyar ya k'are ta wanke hannunta taje d'akinsu, gurin Inna tayi ta durkusa.

"Inna zanje makarantar Allo."

Kai ta d'aga mata kafin a hankali ta kamo hannunta, da kyar ta furta.

"Allah na tare dake Allah ne gatanki, duk inda kike ki tsare mutumcinki na y'a mace, Allah albarkaci rayuwarki Budd'ona."

Daga haka ta saki hannunta, Ummu ko dad'i taji jin Innarta ta mata addu'a, hijab natan ta saka tad'au allonta ta fita.

Karfe sha daya na rana aka dinga doka sallama a cikin gidan, Abulle dake d'aki ta fito da katuwar muryanta tace.

"Wannan iskancin har ina, tsakar rana ana dokawa mutane sallama."

Ganin masu shigowan ya sata yin tsaki ta koma d'akinta, Addah Salamatu da wasu mata biyu da namiji daya sai Baffah, d'akin Inna suka shiga yanda take haka yanzu ma take kwance, kuka sauran matan suke yi suka yi gurinta suna tab'ata tsammaninsu ma ta mutu sai da sukaga ta bu'de idonta ya sasu yin shuru dayar tace.

"Munira haka kika koma? Ashe gaskiyarki Salamatu, tashi zamanki gidannan ya kare."

Tashar da ita tayi dayar mai suna Habiba ta fara dube dube a dakin dan d'aukawa Inna kaya ganin ba komai sai kwongoron akwati ta bud'e ba wani kayan da zata mora.

"Addah kinga ba komai akwatin."

"Kamamin ita mu fita, bar kayan zata samu na sawa a gida."

Da taimakon Habiba suka daga Inna, ganin da gaske suke zasu tafi masa da mata yasa Baffah cewa.

"Addah yanzu tafiya za kuyi da ita."

Wani kallo ta watsa masa bata kula sa ba, bai daddara ba ya kara cewa.

"Addah in kun tafi da ita wazai kula da Ummu."

Juyowa Addah Indo tayi ta kallesa.

"Ka manta Sharad'in Magari da yace in har Munira ta aureka bashi ba ita, amma yanzu sanadin labarin da yaji halin da take ciki yasa a daukota sanadin soyayyar d'a da mahaifinta yasa ya janye sharad'in sannan yace bashi ba abinda ta haifa dan haka ka rik'e abinka, muna jiran sakinta inko yanzu za kayi bismillah."

Girgiza kansa yayi ya runtse idonsa.

"Bazan iya sakin Munira ba, Fatana Allah bata lafiya muci gaba da rayuwarmu, Ummu kuma Allah rayata."

Basu jira jin karshen zancen shi ba suka fita da Innah, a motar akori kuran da suka samu ya shigo dasu kauyen suka sata suka shiga yajasu suka fita a kauyen basu tsaya ko ina ba sai garin Batagarawa cikin fada.

Dangin Munira sun girgiza da ganin halinda take ciki kafarta ya kumbura suntum, nan Mai martaba ya kira Dansa Magaji dake Kaduna ya fada masa halin da y'ar uwarsa Munira take ciki, take yace gobe gobe zai turo azo a dauketa itada Addah Habiba tayi jinyarta kuma aurenta da Muhammadu kamar an raba.


Bangaren Baffah kam ranar yaji bakin ciki da haushin d'auke masa mata da akayi, tabbasa yasan Munira tafi karfinsa kaddara da tsautsayi da kuma rabon Ummu shiya kaddara aurensu, bazai tab'a mantawa ba a SANADIN HA'DUWAR SU yawonsa na bin motaci tsakanin kauyuka ranar yaje Kauyen Batagarawa babban birnin kauyen Unguwar Liman Allah ya kaddara haduwarsu, bata nuna masa ita y'ar sarkin garin bane ta boye masa sai da suka zurfafa a soyyyah kafin ya fara samun matsala daga danginta dan kiri-kiri suka nuna basa son sa, itako ganin ta samu d'an uwanta bafulatani kyakkyawa irinta dan itama bafulatanace sai dai bata kaisa fari ba ga son da take masa yasa ta nace tace sai shi, duk iya bakin ko'karin Sarkin garin ya hana aurensu hakan bai yi ba har yasa yace in har ta auresa ta tabbata tabar cikin y'ay'ansa, tayi kuka jin furucin mahaifinta amma so ya rufe mata ido haka ta dage akayi auren aka kaita can Kauyen Unguwar Liman bakin kauye kamar yadda su Adda Salamatu suka sa masa suna dan kauyen Ba wuta, ba ruwa, ba ishasshen abinci, ba masugunni mai kyau, ba makarantar boko balle islama sai zangaya, shekara biyar da aure bata tab'a ko barin wata ba har lokacin mahaifiyar Baffa rai yayi halinsa dama ita kadai ta rage masa, shekaransu takwas ta matsa masa yayi aure ko zai samu rabo kuma har lokacin bata tab'a takawa 'kauyensu ba, badan yaso ba ya auri Abulle yar makociyarsu, watanta uku ta fara laulayi nan fa habaici ya fara bullowa a gurin Abulle wai juya, itako Munira bata kulata, cikinta wata tara ta haifo katuwar yarta mai kama da ita, da sati ya zagayo aka rad'awa yarinya sunan mamar Abulle Hadiza suna kiranta Dije, shekaran dije biyu kwatsam Abulle ta k'ara samu ciki nan murna sabon haibaici ta farama Munira dama tsakaninta da Dije kallo bata ta b'ata dan tana tab'ata Abulle ta dinga zagi a gidan da haibaici.

A ranar da taji Abulle nada ciki tayi kuka sosai dan har ta fara zargin kanta ko itace take da laluran rashin haihuwa, a haka Baffa ya sameta tambayar duniyarnan ya mata tace masa ba komai, cikin Abulle nada wata biyar itama Munira ta tashi zazzabi sai da cikin yayi wata uku ta gane cikine da ita, ita da Baffa sunyi murna sosai sukaci gaba da rainon cikinsu har ya girma, Abulle na haihuwa aka rada ma y'arta suna Lauratu ita kuma Munira sai bayan wata uku ta haiho itama y'arta kyakkyawa mai kama da mahaifinta, ranar suna aka rada mata suna AISHATU da suna kiranta Ummu itakam Munira cewa tayi bazata 'kirata Ummu ba sai dai Budd'o.

Da haka Ummu ta fara tasowa cikin kula da soyyayn iyayenta shekaransu uku Abulle ta haifi Ja'afaru, Ja'afaru nada shekara Hudu Munira ta fara ciwon kafa bata iya ko takwa mai kyau, bamai taimaka mata a gidan sai mijinta sai y'arta yar shekara goma sha d'aya, tin daga nan ciwo yaki ci yaki cinyewa ya zamana ko tafiya bata iya yi, shekara 'daya tana kwance ciwo yaki ci haki cinyewa, ganin haka yasa Baffah shiryawa yaje garinsu Munira ya fad'a musu halin da take ciki, ba wanda ya kulasa sukace Allah ya bata lafiya, daganan ya dawo ya fara saida 'dan tumakansa da yake kiwo yana mata maganin gargajiya, Ummu ko lokacin Abulle ta samu dama nan ta dinga koya mata ayyukan gida da zuwa rafi d'ibo ruwa harta koya wani lokaci Laure ta rakata, kuma a hakan duk yamma sai taje makarantar Allo banda Alhamis da jumma'a, rana d'aya kwatsam bai san ya akayi dangin Munira suka sauko ba suka turo Addah Salamatu dubata ba.


SADAUKARWA GA UMMU A'ISHAT(UMMI SAFWAAN)


PhartyBb.Wordpress.com

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


  SANADIN HA'DUWAR MU

  ©Pharty BB


(2)


  Ajiyar zuciya ya sauke bayan doguwar tunanin daya fad'a tare da share hawayen fuskarsa daya sauko, fita yai a dakin yayi kofar gida dai-dai lokacin Samha da Laure sun iso gidan da gudu ko wacce da Allonta a hannunta, har kasa suka durkusa suka gaishe da mahaifinsu kafin suyi cikin gida, d'akin iyayensu suka shiga, nan Ummu tayi turus ta tsaya ganin Innarta bata kwance inda ta saba ganinta, hijab nata ta cire ta yar ta fita waje gurin mahaifinta, da gudu tayi gurinsa tana tambayarsa.

"Baffah ina Innata?"

Hannunta ya rik'o ya zaunarta kusa da shi can yace.

"Ummuna kinsan wacce tazo ranar."

Da sauri ta daga masa kanta.

"Yaushe?"

"Kwanaki biyu da suka wuce."

"Addah Salamatu, Addan Innata."

"Ya akayi ki kasan Addar tane?"

"Innah na fad'amin tana da yayu da kanne kuma naga suna kama da Innah ta."

"To kiyi hakuri yau tazo ta d'auki Innarki sun tafi garinsu dan ayi mata magani ta samu lafiya, watarana zamuje kinji."

"To Baffa har zuwa yaushe?"

"Wani lokaci, jeki gida zanje wajen maigari."

Tashi tayi ta shiga cikin gida, hanyar dakinsu tayi da karfi taji ance Ke!!

Cikin sauri ta juyo, Abulle ce tsaye gefenta Dije, da sauri tazo ta durkusa jikinta na rawa tace.

"Gani Dada."

Wani kallo ta watsa mata.

"Tashi maza ki hura wutancan ki d'aura tukunya kizo kiyi tankad'e."

Da sauri ta tashi ta harhad'a itacen batama iya ba ta kyerta ashana har d'an yatsarta ya kone, dakyar ta hura wutan ta cika tukunyar da ruwa ta daura ta rufe, gurin da taga an ajiye tankad'en garin masar taje ta d'auka ta zauna tana tankad'ewa duk yazama biski dan inda wannan sau uku ana tankad'esa asamu kad'an na girkawa, yauma kam dakyar ta samu ta cire na tuwon yau ta ajiye a gurin ta tashi tabar gurin ta shige d'akinsu, bincike ta fara a d'akins har ta gano inda Innarta ta ajiye wani sarkanta na murjani, d'auka tayi ta boye cikin ghana most go dinta inda nanne tsummokaren kayanta suke ciki.

Kwanciya tayi ta fara kuka a hankali dan yunwar da take ji, tin d'umamen safe data ci bata k'arasa komai a bakin ta ba gashi har karfe biyar tayi, sai da tasha kukanta ta koshi kafin ta tashi ta fita lokacin Abulle ta gama abinci harta kashe garwashin tana son zuwa rokonta tana tsoro haka ta hakura ta d'auki tulunta ta nufi rafi.

A hankali take tafiya dan yunwar da take ji haka ta d'ibo ruwanta ta dawo kafin ta gama magriba tayi, alwala tayi tai sallah ta zauna bakin kofa taji ko Abulle zata kirata ta karbi abincinta shuru, ganin shurun yayi yawa ga yunwa na cinta yasa ta leka wajen ba kowa a filin gidan, kofar dakin Abulle taje kamar mai jin tsoro tace.

"Dadah."

"Na'am uban me kike nema da daren nan."

"Dadah yunwa nake ji banga tuwona ba."

Dariya Abulle tayi.

"To dan kaniyarki dama darajar uwarki da ubanki yasa nake baki yanzu ko kinga uwarkin tabar gidan, ubankin baya nan saiki nemi abinda za kici dan ni Zainabu Abu baki kai na miki tuwo kina zaune sannan ki bude ciki kici ba, gafara ki ban guri."

Kuka Ummu tasa haka ta tashi taje gurin girkin nasu ba komai sai tukunyan da suka yi tuwon shima an jikashi da ruwa, d'aki ta koma ta fara kuka can taji motsi lekawa tayi da sauri taga Baffan tane, fita tayi taje gurinsa ta rik'o hannunsa cikin muryar kuka tace.

"Baffa yunwa nake ji Dadah bata ban tuwo ba."

Hannunta yaja ya d'auki tabarman kaba ya shimfida ya zaunarta ya shiga d'akin Abulle sun baje itada yayanta sai hira suke.

"Kawo min abincina waje yau."

Ya fad'a yana fita a d'akin, kwanon tuwonsa ta d'auka ta fita waje dashi yana zaune kusa da Ummu, ajiyewa tayi ta koma d'akinta, bayan tafiyarta ya jawo kwanon ya bud'e ya tura gaban Ummu yace.

"Kici Badd'o."

Bata jira ya k'arasa ta matso ta rike kwanon kamar za'a kwace mata ta fara durawa a cikinta, sai da taci tayi kat tace.

"Baffah kai fa."

Murmushi yayi yace.

"Ni naci abinci a waje kawo sauran in cinye."

Tura masa tayi ta tashi ta wanke hannunta ta dawo ta zauna kusa dashi yana cin guntun abincin data rage, kwanciya tayi tin tana amsa masa har bacci ya d'auketa a gurin, bai koshi ba ya k'ara da ruwa ya d'agata ya kaita d'aki ya fito ya wuce d'akin Abulle tana zaune, kallonsu yayi.

"Dije yau baza kuje gidan Lami din ba?"

Bai k'arasa ba caraf Abulle ta cafke.

"Ai d'ayan d'akin zasu koma tinda ita Muniran ba ranar dawowarta."

Shuru yayi can yace.

"To shikenan."

A daren suka jida kayansu suka koma d'akin Munira kan gadon Dije ta haye taba Laure katifarta wanda duk ta tsomare, ta sauko da Ummu k'asa tayi kwanciyarta, shikam Baffah bai so haka ba haka suka kwana.


    BATAGARAWA

 Washegarin da suka iso aka taru gaba d'aya Dangin a fada har Babbar yayar Munira ta iso da take Katsina, nan suka tattauna tsakaninsu suka yanke shawarar babban yayansu dake Kaduna zai tafi da ita da Addah Habiba da batada aure dan kula da Munira duk da matarsa tana nan, da haka su Addah Salamatu ta harhad'a musu abinda za suyi amfani dashi a ranar suka 'dauki hanya.


 Munira itace y'a ta biyar gurin iyayayenta, Babanta shine sarkin kauyen Batagarawa dake karkashin k'aramar hukumar jihar katsina, yaransa shida, biyu maza, mata hudu, Babba shine Kawu Saminu sai Kawu Idrisa, Kawu Saminu yanada mata da yara biyu Mukhtar da Aminu, yana zaune cikin Kaduna, sai Kawu Idrisa yanada mata da yara hudu shikuma a Funtua yake, sai Adda Halima tana aure a Kaduna sai Adda Salamatu tana aure a Daura sai Munira sai Habiba, Adda Halima duk cikinsu mijinta yafi kudi da wadata dan duk cikinsu ta fita daban bata son shiga cikinsu haka kuma tinda yaranta suka fara girma ta fara d'auke kafarta, sai ita Munira SANADIN HAD'UWARTA da Baffah ya aureta ya kaita kauyensu wanda aurensu ba k'aramar gwaggwar maya aka shaba kafin danginta su amince.  Wannan kenan!!!PhartyBb.Wordpress.com

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


   SANADIN HA'DUWAR MU!!!

    ©Pharty BB

  

(3)


  Washegari asuban fari Abulle ta tashi Ummu da ruwan sanyi, a gigice ta farka tana karkarwa.

"Dan ubanki fito kijemin d'iban ruwa, kinsan jiya ba ruwa muka kwana kin baje kina ta bacci kasa kawai."

Mitsistsike idonta tayi tabi bayan Abulle tana d'aukan tulunta lokacin gari ya fara haske, haka ta fita tana had'a hanya har taje ta dawo, sawu biyar tayi lokacin rana ya fito sosai, bayan ta gama ta share gidan ta wanke kwanukan gidan sai lokacin ta samu tayi sallar asuba ta fito, yauma da kyar da sud'in goshi Abulle ta bata d'umamen tuwon jiya.

Bayan ta gama Abulle ta bata masara da kud'in ni'ka naira talatin, taje can bakin gari inda nanne injin nika yake, d'auka tayi ta 'dora a saman kanta ta tafi, layi ta samu kasancewar kaf k'auyen shi kad'aine Injin nik'a, har gurin la'asar bata samu an mata ba sai wajen karfe hudu, haka ta d'auko ta nufi gida kafin ta iso biyar saura.

Da sallama ta shiga gidan ba kowa, jin muryanta yasa Abulle fitowa da sauri ta fincikota.

"Ke dan uwarki, tin karfe taran safe na aikeki sai yanzu ki kaga daman dawowa, uban me kika tsaya yi a hanya."

Cikin kuka Ummu tace.

"Wallahi Dadah layi na tarar..."

Mari Dadah takai mata.

"Shegiya rufemin baki ai naji labari maza kike bi suna lalubarki, za kici ubanki yau a gidannan shegiya y'ay'ana basu sani magana ba ke kwaya d'aya b azaki sani ba, zaki jawomin abun kunya ko."

"Wallahi Dadah sharri akemin, kuma wallahi layi na tarar ki tambayi Sauden gidan Babah Hansai."

Dukanta ta hau yi baji ba gani sai da ta mata lis kafin ta saketa, da jan jiki ta shige d'aki ta kwanta tana ta kuka, ranar haka Abulle ta hanata abincin dare sai da Baffa yazo ya kasa cin nasa dan rashin lafiya bayajin dadin jikinsa, ya bata nasa taci, lokacin da take ci idon Baffah har hawaye yayi dan tsabar tausayi dan yadda take dura abincin kamar ba gobe, dakyar ta iya barin kwanon abincin ta wanke hannunta tasha ruwa ta shige d'akinsu ta kwanta inda jiya Dije ta kwantarta nan ta kwanta yauma.

Shiko Baffa dakyar ranar yayi bacci ga tausayin Ummu ga rashin lafiyar da yake damunsa, iya tausaya mata rayuwar da zata shiga nan gaba ga ba uwa a kusa, da wannan tunanin bacci ya d'aukesa.


******

  Rayuwa kenan haka rayuwar Ummu yayi ta tafiya cikin rashin dad'i da tsantsan hantara da mugunta da zalincin Abulle da y'arta Dije, in taji dad'in gidannan mahaifinta yana nan, har tsawon shekaru biyu lokacin tanada shekaru goma sha hudu a duniya, mak'erin yan matanci da budurci ya fara bayyana a jikinta da kyanta, sai dai hakan baya nunawa saboda rashin samun gyara da kulawa, dan sai tayi kwana biyu Abulle bazata barta tayi wanka ba, kullum tana cikin bauta mata, dalilin wahala yasa ba'a ganin kyan da Allah ya bata sai tsantsan muni, makarantar zangayar da take zuwa kam dakyar Abulle ta barta ta 'karasa tayi sau'ka.

Baffa kam jiki yau dad'i gobe lafiya haka yake dan fafutukarsa ya samu na abincin da zai ciyar da iyalansa, komai nasa ya kare kaf, ga tunanin Munira ko wani hali take ciki shiya haddasa masa hawan jini da rashin lafiyar da yake damunsa.

Yau kam tin safe ya kasa fita yana kwance dan tsananin jiri da yake gani da rashin karfin jiki.

Abulle kam ta saida awakinta da take kiwo tana saida Kosai da safe da rana ta d'aurawa Ummu tallar Shinkafa da wake da Yamma kuma mandawa(soyayyiyar gyad'a).


 Yau da safe bayan ta gama d'ibo ruwa daga rafi ta share gidan ta d'aura musu ruwan koko dan ita ke girkin da ayyukan gidan gaba d'aya, koko ta dama musu ta juye a kwanon silba takai 'dakin Abulle ta gaishe da Baffanta dake kwance ba lafiya ta fito ta wanke kwanuka ta afita waje, wajen Abulle dake ta suyar kosenta ta tara maza da mata sai shewa ake, can gefe Dije ce tsakiyar maza zaune tana ta dirkan kosen da wani saurayi ya siya mata shi kuma hannunshin cikin hijab nata sai mai hankali da lura zai kula da hakan.

Kusada Abulle ta matsa ta tsugunna tana cewa.

"Dadah na gama ayyukan ba wani aiki."

Wani uban tsawa ta daka mata.

"Dallah can matsa kar kisa na kasa yin ciniki da wannan daudar taki, k'azama kawai."

Tashi tayi ta matsa can gefe ta zauna ita kanta ma kyamar kanta take dan kwana uku ba wanka ga kayanta duk sunyi datti dan Abulle ta hanata ruwan wanka balle na wanki duk da kayanta duka duka kala hudune amma duk sunyi datti.

Zaman da akayi a gefen tane ya sata juyawa, saurayin da yasa hannunsa cikin hijab din Dije ne, bata rai tayi tana kokarin tashi ya sha gabanta kadan jikinsu ya had'u tayi saurin komawa ta zauna.

Wani dan iskan murmushi yayi na gefen baki.

"Haba yar bak'a kyakkyawa, kinci sa'a nazo gurinki ma, na kula duk k'auyennan baki da saurayi shine na kawo kai ko zan samu na latsawa."

Harara ta buga matsa tabi ta gefe ta wuce, cikin gida ta shige ta zauna, can ta tashi ta leka mahaifinta yana kwance yadda ta barshi, kusa dashi ta karasa ta d'auki mafici tana masa firfita, gumi ta gani kwance saman fuskarsa tasa hannu ta share masa, ji tayi jikinsa sanyi kalau, ganin alamar bacci yake yasa ta ajiye maficin ta fito ta shiga d'akinsu ledar kayanta ta binciko ta d'auki murjanin Innarta tana kallo, a hankali ta fara murmushi can sai ga hawaye ya fara sauk'a rike abin tayi gam a kirjinta sai kuka, sai da tasha kukanta sosai tinda take bata ta'ba jin kewar Innar ta ba sai yau, ko ina take? Shine kawai tambayar da take so Baffanta ya amsa mata yaki sai yace saita k'ara girma zai fad'a mata sunan garinsu Innarta.

Warware murjanin tayi dama sark'ane da igiyan ta had'ashi ya zama awarwaro biyu tasa a hannunta, hawayenta ta share ta fito ta leka kofar gidan Abulle ta gama soyar kosan tana harhad'a kayan aiki da sauri ta k'arasa ta tayata suka shigo da kayan ta wankesu ta ajiye, bayan ta gama Abulle ta kirata ta bata birbidin kosai da koko, karb'a tayi ta koma gefe ta hau ci.

Itako Abulle daki ta shiga ganin har yanzu Baffa na nan yanda yake kwance itama ta kwanta dan hutawa, bata dade da kwanciya ba bacci ya d'auketa, ba ita ta farka ba sai karfe sha biyu, yanda ta barshi ta kwanta bacci haka ta tashi ta tarar dashi, bata bi ta kansa ba ta fita lokacin Ummu ta gama dafa shinkafa da waken da take siyarwa a bakin tasha ta zuzzuba tana ko'karin d'auka.

"Tsaya ke."

Tsayawa tayi tana kallonta.

"Ke a haka zaki fita jiki duk wari, d'auki butan can ki zuba ruwa kije ki wanke jikinki ko na samu masu siya, kalan kije haka mutane suji kyamarki suki saya na tashi da asara."

Sauk'ar da roban tuwon tayi ta d'aukaki butan ta zuba ruwa ta shiga ban gida ta d'anyi kwaskwarima ta fito ta gyara jikinta kafin ta d'auki roban shinkafar ta fita.

Abulle kam d'aki ta koma taci gaba da baccinta, Ummu kam direct bakin kasuwar garin tayi duk da dattin jikinta haka matasa su kayi cincirodi a kanta suna siya dan sun san me suke hanga daga gurinta nan gaba, bata dad'e ba ta siyar abinta dama na dari uku da talatinne, daga nan gida tayi abinta.


Da sallama ta shiga ba kowa gurin wanke wanke tayi ta wanke kwanukar tayi sallar azahar, tana yin sallah ta kwanta bacci, bacci ya fara fisgarta kenan ihun da taji shiya farkar da ita ta fito da gudu da Abulle su kayi kicibus tana ta ihu, take zuciyarta ya buga.

"Dadah mai ya faru?"

"Badd'o mun shiga uku mun lalace babanku ya mutu."

Dum taji kamar an soka mata kibiya a kirji.

"Dadah ya rasu kuma, d'azuma fa na shiga mun gaisa."

"Dan uwarki ki tsaya iya yi jeki ki k'iramin mai gari kiyi sauri."

Ta kasa ko da motsi balle ta d'aga kafarta.

"Shegiya bada ke nake ba jeki 'kiramin mai gari."

Da kyar taja kafarta ta fita a gidan, tana had'a hanya haka ta nufi gidan maigari, tana zuwa ta zube musu tama kasa magana, da sauri suka nufi wajenta.

"Ke lafiya ko jinkin Malam Muhammadu dinne?"

"Baffa ne...Baffana."

"Baffanki mai ya samesa?"

Kasa basu amsa tayi numfashinta ya d'auke, salati suka saka aka 'kira mata a gida suka shiga da ita cikin gida, su kuma mazan suka nufi gidansu Ummu dan ganin meya faru.

Da ihun Abulle s ukaci karo tin a soron gidan lokacin makota sun taru a gidan dan ciki gidan tayi da ihu da kuka, da sallama mai gari suka shiga cikin gidan.

Tabbas Baffah lokaci yayi fatan Allah yaji kansa, da taimakon su mai gari aka fito da shi aka masa wanka da sallah aka kaishi gidansa na gaskiya, Allahu akbar.

Rayuwa kenan ranar duk tsiyar Abulle sai da tayi kuka dan tsakaninta da Baffa ba fa'da ba hantara mutum mai hakuri da juriya samun namiji irinsa sai an tona, tasha kuka yarantama sunyi sosai sukama mahaifinsu Addu'an samun Rahma.


Sadaukarwa ga Ummu A'ishat(Ummi Safwaan)
PhartyBb.WordPress.com

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


 SANADIN HADUWAR MU!!!

   ©Pharty BB


(4)


  Ummu ko sai daf da magriba ta farfad'o, ganinta sabon d'aki dakyar ta iya tuna mai ya kawota, kuka tasa musu nan matar mai gari tayi ta bata hakuri har ta samu tayi shuru sai ajiyar zuciya take, ita kam tasan gatanta ya 'kare.

Kwanan Baffah biyu da rasuwa har lokacin Ummu na gidan mai gari, da yamman ranar Abulle ta turo Laure ta k'irata, badan ta so ba ta musu sallama suka tafi gida, gidan ba mutane sosai sai 'kalilan y'an unguwa da k'anwar Abulle da abokiyar Abulle mai suna Lami.

Da sallama suka shiga gidan har 'kasa ta durkusa ta gaishesu ta wuce d'akinsu, bayan tafiyarta Lami ta kalli Abulle tace.

"Ke aminiyar ya za kiyi da wannan yarinyar wai?"

"Yako zan yi da ita banda muci gaba da zama da ita ko ba komai tana min tallah da ayyukan gida."

"Cabdi kina nufin ki zauna kici gaba da ciyar da katuwa, ita ba zata tashi ta tayaki nema ba."

"Lami kenan duka duka sha hudu take kuma wannan kauyen me zata taimakin dashi."

Shuru lami tayi can tace.

"Ta fara al'ada?"

"Ah a bata fara ba, lafiya kike min wannan danyar tambayan?"

Cewar Abulle tana ma Lami wani kallo.

"Ina da babban shawara gareki duk lokacin data fara ki sanar dani, insha Allah da wannan yarinyar har Makkah za kije Abu, kai nima sai kin kaini."

"Allah aminiyar."

"Dagaske ke kam Allah kaimu lokacin."

Babin hira suka bude a gidan makokin dako sadakar uku ba'ayi ba.


 Bayan kwana hudu da rasuwan Baffa aka had' akayi sadakan bakwai, washe gari Abulle ta fara sana'arta na kosai da rana tasa Ummu ta dafa shinkafa da wake ta fita dashi talla, haka da yamma ta kulla gyada ta bata ta fita dashi, da dare ma ta k'ara d'aura mata ta kai dandali.


 Haka rayuwar ya kasancewa Ummu banda bautawa Abulle da yaranta bata da aikin yi, Saurayin Dije ko ya sata gaba bata isa ta fita ba yana gadinta sai ya bita ko ina, ita ko da zaran ta gansa take sauri kuma bata bin gun daba mutane, dan taji labarinsa gurin Laure ba imani ba tsoron Allah yake danne yaran kauyen k'anana yake musu fyade, bata tab'a barinsa su hadu ba, ko a dandali in ya zauna kusa da ita tashi take ko taki basa fuska haka zai zo ya zauna, tana taka tsantsan da rayuwarta, dan rashin gata da maraicinta, tasan komai ya mata ba mai tsaya mata.


 Bayan Shekara d'aya, abubuwa da dama sun faru, lokacin Ummu alamun budurci ya zauna mata sosai duk da wahala da talaucin da bautan da take ciki bai hana dirinta fitowa ba, Dije ko lokacin sau biyu itada Abulle suke zubar da ciki in Dije tayosa a waje, ta zama tantiriyar y'ar iska mazan kauyen har tsakar gida wani lokacin har d'akin da suke zasu shigo suyi abinda suke so da ita su fita, Abulle sai dai ta shige d'aki in sun tafi ta fito.

Ummu ko abinda yafi mata dadi bata wuni gidan in ta fita tin karfe sha d'aya tallar Shinkafarta sai karfe biyu ta dawo tayi sallah ta 'dauki gyadarta in ta dawo da yamma ta musu ayyukan gidan da dare ta 'dau sauran gyadarta taje dandali.


******

  Yau Jumma'a tin dare ciwon mara yasa Ummu a gaba tayi kuka har kanta ya fara ciwo, bata samu bacci ba har asuba wani wahalallen bacci ya d'auketa, cikin bacci taji an kwara mata ruwa mai tsananin sanyi, a firgice ta farka tana ja baya kayan jikinta yayi jakab.

Abulle ce tsaye a kanta.

"Shegiya kin san karfe nawa kika tsaya kina bacci, wazai karb'omin nikan kosan da dibo ruwan."

Cikin muryar kuka ga muryan baya fita dan kukan da tasha da da dare muryan duk ya toshe.

"Dadah kiyi hakuri jiya kwana nayi banyi bacci ba, banda lafiya."

"Asibitine a kanki, zaki tashi ko saina jibgeki."

Cikin sauri ta fara ko'karin tashi bashiri ta sake k'ara ta koma.

"Dadah na kasa tashi."

"Mike in ganki."

Da kyar ta iya tashi dan kafarta kasa d'aukarta yayi, ji tayi abi na bin kafarta da sauri takai dubanta ga inda Abulle take gani, jinine ya bata mata kaya, ido ta zaro tana kallo.

"Na shiga uku." shine abinda ta fa'da a ranta.

Abulle kam murmushin mugunta tayi tace.

"Ina zuwa."

Fita tayi ta tafi gidan kawarta Lami nan ta labarta mata abinda suka dade suna jira, gyalenta ta figo a saman igiya suka nufi gidan Abulle har d'akin su, tana durkushe tana kuka.

Dagota Lami tayi tana cewa.

"Ke banza bar kuka ko wace mace haka take yi muje ki gyara miki jikinki."

Da taimakon Lami ta gyara jikinta ta nuna mata yadda za tayi tana canza kunzugunta suka fito, lakacin Abulle ta gyara inda Ummu ta b'ata dan yau ba maganar kosai.

Zaunarta Lami tayi ta jika mata kanwa tasha dan samun sau'kin ciwon ciki ta kwanta suka fito suka nufi d'akin Abulle.


"Ke Lami yau Allah ya kawomu Badd'o ta fara Al'ada sai ki fad'amin abin kike shirin aikatawa."

"Aminyata kenan kin cika sauri."

"To ba dole ba ina nan ina zaman jiran shekara 'daya."

"To bud'e kunnenki kiji da kyau, birni zamu turata karuwanci kinsan kawata wacce muka taso tare Magajiya, dalilin yin kudinta kenan daga nan kauyen aka 'dauketa aka kaita birni karuwanci tayi kudi iyayenta sunyi kudi, yanzu ita take d'aukan yara daga kauye ta kaisu gidanta dan haka kema zan mata magana mu tura mata Badd'o."

Tin da ta fara magana ta sake baki take kallonta har ta dasa aya.

"Ke Abu magana fa nake miki kar dai duk bayaninnan dana miki baki jiba."

"Naji mana, amma Lami yarinyarnan zata iya mana abinda muke so."

"Zata iya mana waye zai kalleta yace shekaranta goma sha biyar."

"To Lami ku had'a da Dije mana kinga nan ma sana'arta kenan kuma a banza suke kwasarta amma in birninne ai za'a biyata."

"To shikenan ki lura da ita nan da ta gama sai su shirya kayansu, zan ma Magajiya magana dama wancan watan tazo tace zata dawo nan da sati 'daya."

"To to shikenan, wai ni Abu zanyi kudi."

"Har Makkah za kije."

Bayan sun gama kulle kullensu Lami ta fito ta nufi gidanta tana ma Abulle dariya, dan itama tasha alwashin saita samu kudi fiye dana Abu ta hanyar Ummu, da haka ta shige gidanta.


 Kwana uku tayi ta gama, cikin kwanakin a takure tayi sa gani take duk kauyen ansan abinda take yi, ta k'ara zama shuru shuru, kuma tana ko'karin ta saftace jikinta.

Yau tin safe bayan ta gama tallarta tayi na gyand'a ta da yamma tana zaune a 'dakinsu ta kula abin tin daren jiya ya d'auke tana son ta fad'awa Abulle tana kunya da tsoron me zata 'dauketa, sallaman Abullen ne ya sata tashi.

Tana daga tsaye tana kallonta sai yanzu ta hango abinda Lami take hange daga Ummu duk 'yan matan kauyensu dakyar asamu me kyan dirinta gata da karacin shekaru amma sai uban diri kamar 'yar sha takwas.

"Ke tambayarki zanyi, Al'adar takin bata dauke bane har yau."

Kanta k'asa cikin kunya tace.

"Tin daren jiya ya d'auke."

"Shegiya shine baki fad'amin ba, to tashi had'a kayanki kaf birni zan turaki ke da Dije muma mu samu muyi arzikin kanmu."

"Birni kuma Dadah."

"Eh ko ban isa ba."

"Dadah ni banason zuwa y'/an iska sunyi yawa ki barni na zauna nan abina."

"Kinci gidanku sai kinje in yaso su cinyeki tashi maza karna bubbugeki."

Tashi tayi tana kuka ta had'a kayanta Abulle ta bata daya cikin na Laure mai d'an kyau wanda za tasa gobe.

Daren ranar kasa bacci Ummu tayi tana ta tunanin kome za suje yi birni? Aikatau, shine amsar data tsayar a ranta, ta tsani aikatau dan tana jin labarin gurin y'an matan kauyensu duk yarinyar da aka kai aikatau ko yaron mai gidan ya lalatasu ko maigidan da kansa, ko wasu daban, addu'a tayi tasa a ranta duk inda take Allah zai kareta dan shi kad'aine gatanta.


Washe gari....


Sadaukarwa ga Ummu A'ishat(Ummi Safwaan)PhartyBB.WordPress.com

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


 SANADIN HADUWRMU

   ©Pharty BB


(5)


  Asuban fari Abulle ta tashi su Ummu su kayi wanka su kasa kayansu suka zauna zaman jira.

Karfe shidan safe Lauri ta doka sallama tace su fito, Abulle ce ta lek'a d'akin ta k'irasu su Dije ansha jambaki da hoda za aje birni ita ko Ummu kuka ta fara bata son zuwa, fita su kayi nan suka tarar da akori kura, bayansa suka shiga Magajiya a zaune zagayawa Abulle tayi har k'asa ta durkusa ta gaishe da Magajiya tana cewa.

"Hajiya gasu nan su biyune."

Cikin yamutse fuska Magajiya tace.

"To shikenan duk karshen wata zaki na ganin kudinki."

"To to hajiya Allah tsare."

"Mungode, ga wannan ki rik'e kafin zuwa nan da wata."

Cewar Magajiya tana mik'awa Abulle rafar 'dari-d'ari na dubu biyu, cikin sauri ta k'arba kafin ta matsa mai motar yaja suka bar gurin, duk inda suka wuce sai Dije ta d'agawa wanda ta sani hannu, ita kan Ummu kanta tasa cikin cinyoyinta tana kuka a hankali.

Tafiya suke baji ba gani har suka iso Batagarawa, a nan suka tsaya suka samu abinci, Ummu kam ruwa kawai tasha suka canza mota zuwa motar haya kafin su kaci gaba da tafiya, sai wajen la'asar suka isa Dije sai kalle kalle take tazo birni tana washe hakora, Ummu kam kanta a katsa tsabar kukan data sha idonta yayi ja kanta har ciwo yake, kallon cikin gari take gidaje manya manya ga mutane har tsoro suka fara bata ta kankame jikinta ga wani kwalta a sama ihu za tasa tayi saurin toshe bakinta, haka su kaci gaba da tafiya har suka iso tasha, aka sassauk'a dakyar ta fito dan har fitsarine ya ka mata, Napep Magajiya ta tsayar suka shiga.

Gaban wani gida suka tsaya mai kofa karami, bayan sun sassau'ka Magajiya ta biyasa tace musu.

"Ku kwaso kayanku mu shiga."

Daukan kullinsu su kayi suka shiga nan fa suka fara cin karo da mata y'an bariki kala-kala, gidan da ka gansa gidan karuwaine ga dakuna a jere kusan goma, yan mata ko wannan ya shiga wannan ya fito wasu da k'ananan kaya wasu da d'aurin kirji, wani d'aki ta kaisu can karshe 'yan matane cike a d'akin kusan su biyar duk manyane sai daya yar shekara goma sha tara.

Bayan sun shiga sun zauna Magajiya take fad'awa y'an matan.

"Kai ka sabin d'auka a koya musu wanka da tsafta da kwalliya, wannan tsohuwar hannuce wannan kuma sabuwar 'dauka ce dan haka amin taka tsantsan da ita dan mai tsadace."

Shewa y'an matan suka sake d'aya daga cikinsu tace.

"Angama ranki ya dad'e Allah ja zamaninki."

Dariya tayi tana fita, bayan fitarta Ummu ta tusa kanta tsakanin cinyoyinta ta sa kuka sai yanzu ta gane inda aka kawota gidan karuwai, wato suna nufin karuwanci za tayi...

Dafa kafad'arta da akayi yasa ta d:ago kanta yar shekara goma sha taran nanne , murmushi ta mata tace.

"Sannu baiwar Allah hakuri za kiyi yawanci da haka suka fara, wasu da son ransu wasu kuwa forcing nasu akayi kamar yadda kema naga alama forcing naki aka yi."

Shuru Samha tayi sai binta da ido take.

"Ya sunanki? Ta tambayeta.

Nan ma taki bata amsa, murmushi tayi.

"Ni sunana Zulfah a d'akinnan nake, muje kiyi wanka sai in karb'o miki abinci."

Tashi Zulfa tayi ta d'aga Ummu ta d'auki kullin kayanta ta d'aura saman akwatinta taja hannunta suka fita sai bin Ummu da kallo y'an matan suke, har band'aki ta kaita ta tara mata ruwa a fomfo ta kai mata, ta bata sosonta da sabulu tace tayi tazo 'dakin da aka kaisu.

Bayan ta shiga tayi wankarta irin wanda bata taba yiba ta wanke kanta kafin ta fito, d'akin ta koma har yanzu sunanan yanda ta barsu su Dije sai shishige musu take, kusada Zulfa taje ta d'auki kayanta ta saka ta bata mai ta shafa da turare, ta turo mata kwanon abinci tace.

"Kici abinci na karb'o miki."

Murmushi tayi taja abincin biskine da miyar kubewa bushasshe, ci tayi sosai ta koshi tasha ruwa kafin ta zauna Zulfa tace.

"Har yanzu baki fad'amin sunan ki ba."

"Sunana Aishatu mahaifiyata na kirana Bodd'o mahaifina na k'irana Ummu."

"Suna mai dadi."

Murmushi Ummu tayi tace.

"Nagode."

"Ummu zan fada miki wani abu, dokar gidannan na farko duk safiya sai munje gaishe da Magajiya, na biyu sai mun bata kudin da idan aka kwana damu, zata raba kashi uku tad'au biyu ta baka d'aya, sannan na karshe duk dare za muyi wanka muyi kwalliya akwai inda muke zuwa mu tsaya samari da Alhazawa suna zuwa su 'dauki na d'auka akwai kuma masu zuwa har gida su 'dauki na dauka."

Kuka Ummu tasa.

"Wallahi Zulfa bazan iya rayuwar barikanci ba ni bansan komai ba, duka duka shekarata sha hudu fa mezan iya ki tausayamin ki nema min mafita."

"Kiyi hakuri baki da yanda za kiyi tinda har aka kawoki nan dole kiyi abinda suke so."

Kuka sosai Ummu tayi dan ganin irin rayuwar da zatayi, dakyar Zulfa ta rarrasheta tayi shuru.

Daren ranar a tsorace ta kwana dan tana kallo y'an matan su kayi wanka suka sa k'ananan kaya suka fita su Dije sune gaba, ba yanda ba suyi da ita ba tace baza taje ba bata da lafiya, haka suka tafi suka barta ranar Zulfa bata jeba ta zauna kula da ita, baccine ya d'auketa bata san lokacin da suka dawo ba.

Da safe suka taru 'yan 'dakin su kaje gaishe da Magajiya bayan sun gama kowacce ta ciro kudin data samu ta mik'a mata, bayan ta kirga ta sallamesu suka koma 'dakinsu sai bacci, ita kam Ummu wanka tayi ta fito ta tsefe kanta ta taje ta kama taci abincin da Zulfa ta kawo musu suka zauna suna d'an taba hira.


 Haka rayuwar gidan yayi ta tafiya har yau su Ummu suna neman sati daya dede da rana daya bata ta'ba binsu ba, kullum da karyan da take yi, bata da aikin yi sai dai taci ta kwanta tayi wanka.

Yau kam da kuka da roko Magajiya ta sata tayi wanka ta shirya dole sai taje dan cewa tayi bazata zauna tana ciyar da ita ba bata samu daga gareta ba, wani riga da wando ta bata cikin kayan da take siyarwa ta sata ta saka kuka take yi dan kayan ya fito da shape nata ga bata sababa, amma dole suka sata ta shirya suka 'dauketa

 Wani layine y'an mata da maza sai sha'aninsu suke motoci sai fakawa suke suna daukan mata.

Can gefe ta rakube ta tsaya hawaye nabin kumatunta tasa hannunta tana kare jikinta.


*********


 Kidane yake tashi maza da matane cike agurin wasu na rawa wasu suna cin abinci wasu suna tsaye da cup a hannunsu, can gefen matasane uku daya yana tsaye shida wata budurwa dayan ko yana dandanna wayarsa sai daya daya saka mujallah ya rufe fuskarsa.

Mai danna wayarsan ne ya tashi yana murmushi.

"Kai Gaye gafa can Babyn an kawota."

Wanda ke tsaye da budurwane ya kai kallonsa gurin bodyguard nasu da sukasa su nemo musu yar shekara goma sha shida (16 years) ya gani sunata kokuwu da ita tana tirgewa har suka kawota gabansu.

"Ranka dade ga wannan tayi?"

"Yes tayi ga Ladanku."

Rafar dubu yaciro ya mika musu suka fita kallonsa yakai kanta gata sweet 16 yasan yau zai kwashi dadi in akayi sa'a ya zama shine ma zai fara yagata.

"Kai gayen yau munyi sa'a fa."

Cewar na tsayen.

"Nayi sa'a ko munyi sa'a nine first saboda ni na kawo shawaran nan."

"Haba guy kar muyi haka kaga ni na nunama hanyar abinnan amma kana nema ka fini zakewa."

"Sai kuma kayi tayi."

Yana fad'ar haka yasa hannu zai d'agota ta fasa ihu tana ja baya.

"Y'an mata kar ki mana haka mana ki tsaya bazamu wahalar da ke ba."

Girgiza kanta tayi tana kokarin gudu yasa kafa ya hard'eta ta fadi, ihu tasa ta riko kafar da tsammaninta kafansa ne dan yanda ya hardeta taji zafi, jin an ta'basa ya bude idonsa da sauri duk abinda suke yi yana jinsu idunsa rufe, kallonsa yakai kanta tana ja baya suna binta, maida kansa yayi ya kwanta ya rufe idonsa, shi duk zuwa club nasa baya iya neman mace ko shan giya barshi da shan taba shima sai ya kama ko ransa a 'bace, yanzu ma su suka k'irasa,

Yanajin tana kuka tana rok'ansu haka suka d'agata iya karfinsu, ko mai ya tuna kamar an tsikaresa ya tashi ya nufi wajensu, fizgota yayi ta fasa masa ihu yasa hannunsa ya buge mata baki tare da kai mata lafiyyen mari.

Ido su Bashi suka bisa dashi kafin su fara kallon-kallo tsakaninsu.

Ko kallon inda suke baiyi ba yaja hannunta ya nufi d'aki daya cikin d'akunan Hotel din, suna shiga ya wurgata ya rufe kofar har dasa key, baya taja tana kuka ganin ya nufota gadan-gadan, yana isowa ta durkushe a gurin, d'agota yayi ya zuba mata mari tare da wurgata gefe ta fad'i saman hannunta, 'kara ta saki kafin ta fadi numfashinta ya d'auke ta daina gani.

Wayarsa dake ringing a aljihunsa ya d'auko ganin mai kiran yasa yayi rejecting tare da kashe wayar gaba daya, gajiya suka yi da 'kiransa akan ya bud'e kofar suma su danata ganin sun kira ya kashe musu waya yasa suka bar Club din cikin jin haushi.

Rasa mai zaiyi yayi ya zauna gefe ya dafe kansa, da sauri kuma ya tashi ya nufi inda take kafa yasa ya turata bata motsa ba k'ara tureta yayi bata motsa still, ya sashi duk'awa yasa hannun cike da fargaba ya 'dagata gani yayi bata numfashi, a razane ya d'agata cak ya bud'e kofar ya fita da ita wajen motarsa ya nufa ya sata sit din baya ya zagaya ya shiga yaga sai asibiti.

Da isarsa likitoti suka k'arbeta, nan suka gano ta samu gurdewa a hannu sakamakon faduwar da tayi akai, gyara mata akayi ta farka tana ihu sam taki tsayawa, Doctern ne ya fita wajen Sadeeq yace.

"Me tsakaninka da Patience dinnan?"

Shuru yayi ya rasa amsa komai ya tuna yace.

"Sister nace."

"Yawwa yazo da sauk'i, ko zaka iya taimakamin ka riketa ko ka mata magana ta tsaya a gyara mata hannunta dan ya samu targade."

"What Docter targade kuma?"

"Yes muyi sauri please karya mata tsami."

"Ok muje to."

D'akin da take ciki suka shiga kallo d'aya ya mata ya juyar da kansa har suka iso bakin gadon da take zaune, rikicewa Ummu tayi ganinsa dan mugun tsoronsane ya kamata.

"Kamata please ka rik'emin kafad'arta."

Takaicine ya kama Sadeeq shifa tsakaninsa da mace ido ko k'annensa sai ya kama yake ta'basu balle wannan da bai san asalintaba.

"Brother ka rik'eta mana, in yayi tsami zai mata zafi."

Bismillah yayi ya d'ago hannunsa dakyar ya d'aura saman kafard'ar hannun daya samu targaden, komai yaji ba shiri ya 'dauke itama baya taja hawaye ya taru a idonta, ganin Docter ya damesa kawai yayi yace.

"Docter in ta'ki tsayawa ka barta, hannuntane zai rube."

"No baza ayi haka ba, riketa kawai."

Girgiza kansa yayi ya bata rai kamar bai taba dariya ba ya juya yana kallonta.

"Zaki tsaya a duba miki hannunki ko sai na baki mari, banza kawai 'yar tasha." 

Cikin jin zafin kalmarsa na karshe yasa ta runtse ido hawaye na zuwa batace komai ba.

A hankali Doctern ya fara ja mata hannun, har tsakiyar kanta take jin zafin, a haka aka gama ya tofe mata gurin da addu'a ya rubuta mata magunguna yace zuwa safe za'a sallamesu, godiya Sadeeq ya masa kafin Doctern ya fita.

Bayan ya siyo maganin ya dawo ya tarar har bacci ya d'auketa, tsaki yayi ya ajiye ya fita, inda yayi parking motarsa yayi ya shige motarsa ya koma gidansu ba kowa a babban falon, direct d'akinsa ya wuce bayan ya gama abubuwan da zai yi ya kwanta.


Sadaukarwa ga Ummu A'ishat(Ummi Safwaan)PhartyBb.Wordpress.com


NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


 SANADIN HADUWARMU

  ©Pharty BB


( 6 )


 Da asuba da yayi sallah bai koma ba, bayan ya idar da sallah yayi azkhar nasa har gari yayi haske, wanka yayi ya shirya ya sau'ko babbar falon gidan ba kowa dama yasan ba wanda zai tarar dan sai karfe goma ko shad'aya suke fitowa, kitchen ya wuce mai aikinsu tana ta hada-hadar had'a breakfast, tana ganinsa ta durkusa ta gaishesa.

"Ina kwana?"

"Lafiya lau, ina bukatar abinci zan fita dashi."

"To angama bari in had'a."

Bai jira amsarta ba ya fita, cikin sauri ta had'a mishi a warmers masu kyau ta saka basket tak'ai masa parking space, fita yayi direct sai asibiti a hanya ya tsaya a wani plaza kafin ya wuce asibitin.

Bayan yayi parking motarsa ya fito ya nufi female word 'dakin da take ya shiga da sallama tana kwance idonta biyu jin sallama yasa ta kalli kofar ido biyu suka yi dashi ko'karin tashi ta fara yi tana ja baya dan ita tsoro yake bata sosai.

D'auke kansa yayi ya 'Karaso bakin gadon ya ajiye basket da ledan hannunsa bai kalli inda take ba yace.

"Kinyi sallah ko da yake irinku baku damu da bautar Allah ba."

Taji zafin maganarsa amma tayi shuru can ciki tace.

"Banida Hijjab din da zan rufu nayi sallan."

Ledan da ya shigo dashi ya mik'a mata kin karb'a tayi saida ya buga mata tsawa.

"Karb'i dallah banason munafurcin karya."

Hannu na rawa ta karb'a ta diro a saman gadon ta nufi ban'daki, Allah ya taimaketa bangidan da ruwa a bucket a cike, wanka tayi ta dumama hannunta da ruwan zafi ta d'auro alwala ta bu'de ledan, dogon rigane da hijab bak'i, sakawa tayi ta fito kanta a kasa, kwatanta Alkibla tayi tai sallah bayan ta idar ta zauna shuru, shima bangarensa shuru yana zaune a saman kujera duk abinda take yi a idonsa yana kallo ta gefe.

Sun kwashe minti biyar a haka ganin shurun yayi yawa yasa yace mata.

"Ke zoki zuba abinci kici kisha magani in mai daki gidanku."

Hawaye ta fara jin zai mai data gida, gidan data tsana kamar mutuwarta tasan in shi jiya ya ceceta gobe waye zai ceceta.

"Ba kiji mai nace ba." Ya katse mata tunani.

Kuka tasa masa.

"Dan Allah ka mai dani garinmu bana son gidannan."

"Ni a wa, na dauk'owa kaina jaraba KARUWA fa kike."

Sunan daya kirata dashi ya bugita har cikn ranta.

"Wallahi ni ba irinsu bane dole suka min karka mai dani gidannan."

Shuru yayi yace.

"Yanzu yi breakfast."

"Uhmm me kace." Dan tsakaninta da Allah bata san abinda yace ba kauyensu dako makarantar islamiyya babu balle boko.

Ido yasa mata, mai take nufi yanzu ai ko wanda baije makaranta ba in dai a birni yake yasan menene breakfast.

"Ki karya nace."

Sosa kanta tayi ta tashi taja basket din, food flask din tabi da kallo bata san ta inda zata budewa ba sai jujjuyawa take, ganin haka yasa ya sauko yace.

"Bani."

Mik'a masa tayi ya kar'ba ya bu'de ya zuba mata chips ne da ferfeson hanta, tura mata gabanta yayi ya tashi ya koma gurinsa shi haushima ta fara basa yanda take nuna kauyenci zata raina masa hankali.

Da kyar ta iyasa hannu ta fara ci jin da da'di yasa ta faraci ba kakkautawa, sai da taci tayi kat ta tashi ta wanke plate din ta fito lokacin ya tashi daga zaunen da yake.

"Muje ko in maidaki inda na dau'ko ki."

Cak ta tsaya taki motsawa.

"Muje mana."

Girgiza kanta tayi.

"Ka taimakamin ka mai dani garinmu dan Allah."

"Bazan taimakan ba."

"To ka kaini gidan marayu dama Baffana ya rasu Innata kuma ta barni tin ina k'arama."

"Bazan kai kin ba, ke kinga zanfa barki in ki kamin wasa oya muje na kaiki ni zaki rainawa wayo."

"Dan Allah fa nace karka kaini gidannan, zasu b'atamin rayuwa."

"Dama rayuwarki batacciyace, muje."

Zata sake magana ya fizgota ya fara ja tana turjewa, sata cikin mota yayi kafin ya zagaya ya shiga yaja ya fita a asibitin tu'ki kawai yake shi kansa bai san ina yake nufa ba, can wani unguwa inda ba mutane yayi parking, jin ya tsaya ya sata dogo kanta idanuwanta har sun rine tsabar kuka.

"Fita min a mota."

Da sauri ta fara kok'arin fita ya fizgota.

"Dan Allah karka kai ni gidannan."

Buge bakinta yayi cikin bacin rai.

"Yimin shuru dallah, karna kai ki karna kai ki ba nan bane gidanku ko ba anan akaje aka daukoki ba ko zaki cemin duk zamanki gidan Karuwan baki taba iskanci ba."

"Wallahi sati daya da kawoni kuma ban taba yi ba, kuma bada son raina aka kawo ni ba."

Wani kallo ya watsa mata.

"Waya kawoki?"

"Dadah, kishiyar Innata."

"Ina Innarkin?"

"Tana garinsu."

"Ina ne garinsu?

"Ban sani ba."

"Karfa ki rainamin hankali."

"Wallahi na rantse tana garinsu tin ina k'arama ta tafi na dawo daga islamiyya na tarar batanan na tambayi baffana ina take yace ta tafi garinsu."

"Ina Baffanki bai fad'a miki garin su ba."

"Eh, yarasu kuma bai fada min ba."

Jikinsane ya fara sanyi a hankali yace Allah yaji kansa, can ciki tana share hawaye tace.

"Ameen."

Shuru yayi ya 'dora kansa a saman kujera, Taimako shine kalmar da zuciyarsa ya raya masa, kallonta yayi.

"Kinga kar'bi."

Tissue ya mika mata ta karb'a tana share hawayenta.

Numfashi ya sauke yace.

"Kina ji, dole zan mai daki gidannan amma kar kiji tsoro zan bawa wacce take rike daku kudin kwana biyu karta barki ki fita ko wani yazo 'daukarki kwana, insha Allah nan da kwana biyun zanzo in kai ki garinku na miki Alkawari"

Kallonsa tayi ya 'daga mata kai tare da 'dauke kansa.

"Alkawari kayane 'daukarsa da sauki saukesa da wuya, Allah baka ikon cikawa in kuma wayo ko dabara kamin Allah yakawo wani da zai fitarni a cikin wannan halin."

Har zuciyarsa yaji maganarta, motarsa ya tada ta fa'da masa sunan unguwar ya nufa tana nuna masa layin har kofar gida, tabbas dole ko wace ya mace mai daraja da mutunci zata kyamace gidan, shikan sa kyankyamine ya kamasa, kallonta yayi.

"Yimin magana da Hajiyar."

D'aga kanta tayi tana fita, cikin gidan ta nufa da sallama ta shiga kowa na harkan gabansa, babban falon gidan tayi wajen Magajiya, d'urkusawa tayi har 'kasa ta gaisheta, amma tsayawa tayi tana binta da kallon tuhuma ganin suturan dake jikinta.

"Hajiya ana miki magana a waje."

"Wayene?" Ta tambayeta cikin ya mutsa fuska.

"Wani ne za kuyi magana."

"Da mota ko da kafa?"

"Da motane Hajiya."

"Je kice ina zuwa."

Fita tayi taje ta sanar mishi tana zuwa fitowa yayi a motar ya tsaya karkashin wani bishiya dake kusa da gidan irata kan wani dutse ta zauna, fitowar Magayiya shiya katse masa tunaninsa da yake yi, 'karasowa tayi gurin tana binsa da kallo ganin saurayi kyakkyawa d'an kwalisa.

"Sannu d'an samari."

"Yawwa sannu Hajiya."

"Mu shiga daga ciki."

"Ah a Hajiya nan ma yayi maganar ba wani mai tsayi bane."

"Ok ina jinka."

"Dama Hajiya kan yarinyar nan ne, na gani ina so."

Cikin sauri Magajiya ta tare sa.

"Wani irin so kuma, dama kune masu nuna musu so su bijere mana ko, to kaga hanya tin ina ganin darajarkar bar nan gurin kafin in tara maka jama'a."

"Ah a Hajiya baki fahimta bane, so bafa so na aure ba, kudi za ina baki ina d'aukarta muna wuni in ta kama zamu kwana, so bana son yin sharing nata da wani kuma zanyi tafiya nan da kwana biyu shine zan baki kudin kwana biyun karta fita kar kowa yazo ya 'dauketa kafin na dawo."

"Waya fad'a maka ana haka?"

"Alfarma nake nema." 

Ya fad'a yana zaro bandir din y'an dubu dubu har gudu biyar dubu hamsin ya mika mata, ganin nairori ya sata muzurai, hannu tasa zata karb'a ya janye.

"Kimin alkawari ba zaki bari wani yayi mu'amala da ita ba."

"Nayi dama ni ita ban takura mata ba ko Badd'o."

Ita kam tinda suka fara maganar ta sunkuyar da kanta sai yanzu jin ta k'ira sunanta ta 'dago kanta.

"Eh ba kyayi."

Ta fad'a ciki ciki.

"Good for you." 

Yace yana mik'a mata, ta karb'a tana cewa.

"Sai ka dawo bari in shiga ciki Bodd'o sai kinzo."

Fit ta shige cikin gida, murmushin takaici yayi ya juyar da kansa kanta.

"Ki shiga ciki sai nazo ko, ga wannan ko zaki bukaci wani abu."

Girgiza kanta tayi.

"Taimakon da kake niyar yimin kadai ma ya isheni nagode."

"Karbi nace ba kyauta na baki ba ajiya amma in kinada bukata ki kashe duk ranar da kika samu ki biyani."

Karb'a tayi shi kuma ya nufi wajen motarsa bayan ya shiga ya kallota hannu ta 'daga masa shima ya 'daga mata tare da yin murmushi sai yanzu ta kula kyakkyawane karshe irin wanda suke gani a takarda(mujalla) gashi fari tas.

Suna d'agawa juna hannun har ya bace da ganinta, dakyar taja kafarta ta shiga ciki d'aki direct ta wuce nan ta tarar dasu y'an matan Zulfa bata nan, kwanciya tayi bayan ta boye kudin daya bata ta fad'a tunanin rayuwarta, tin bayan rasuwan Baffanta ta rasa komai nata da duk wani farin ciki da jin dad'in rayuwarta, To wacce tayi SANADIN zuwanta duniyama tayi nesa da ita balle wasu.

Juyi tayi ta gyara kwanciyarta tana k'ara tunanin ko wayo ya mata ko zai taimaka mata, Oho?


Sadaukarwa ga Ummu A'isha(Ummi Safwaan) 


  


PhartyBb.WordPress.com

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


  SANADIN HADUWARMU

  ©Pharty BB


( 7 )


  Yana shiga gidan bayan yayi parking motarsa ya fito ya shiga babban falon gidan, Mami ya tarar da y'an matanta su uku suna kallo Hauwaty, Rahma da Biebie, kallo d'aya ya musu ya nufi dinning area, abinci ya fara kok'arin zubawa, jin motsin mutum ya sasu juyawa dan ko sallamarsa ba suji ba hankalinsu yana kan abinda suke kallo.

Ido Mami tama Biebie ta tashi ta nufi gurinsa lokacin ya gama zuba dankaline yana ko'karin ha'da bakin shayi(Black tea), tana isowa ta karb'i flask din shayin murya k'asa k'asa tace.

"Kawo in had'ama kar ka wahalar da kanka."

Bai ko kalleta ba harta gama ta ajiye masa taja kujera ta zauna, tana zama ya tashi.

"Ina za kaje kuma Yaya Sadeeq? naga breakfast ka keyi."

"Ba ruwanki." Abinda yace yana barin wajen, shifa yarinyarnan ta takura masa sam bata burgesa ta cika yanga.

Stairs ya wuce ya nufi 'dakinsa ya kulle.


 "Yau yan bak'in halin suna kusa."

Fadi'n Hauwaty tana gyara farcen na kafa.

"Kece dai mai bak'in hali ba d'ana ba."

"Haba Mami ke ba dama a fad'i gaskiya akan Yaya Sadeeq, sai kinci ah a, ki gafa abinda yama Biebie yarinyarnan duk kok'arinta na ganin ya kulata yaki sai ma gwaleta da yake yi."

"To uwata yimin nasiha, Biebie ita ta gani tace tana so ba wanda ya sata dole."

"Au hakane ma kina jin Mami, Rahma."

Wacce aka k'ira da Rahma ne tayi dariya tace.

"Tsakaninku ba ruwana."

"Biebie!"

Hauwaty ta kwala mata k'ira wacce tin bayan da ya tashi ta dauke plate din ta kai kitchen ta zauna kuka dan irin abinda Ya Sadeeq ke mata, ita kuwa gani take ba laifinta bane laifin zuciyartane data nace sai shi, jin Hauwaty na k'iranta ta goge d'an guntun hawayenta ta fito zuwa falon, kana ganinta kamar ba abinda ya sameta amma ita tasan meke damunta.

"Gani Sister."

Ta fad'a tana zama.

"Yawwa kina jin Mami tana karewa wannan mugun dan nace yau 'yan bak'in halin suna kusa."

Murmushin yake tayi.

"Kika san ko baya jin dad'ine."

"Eyyeh watoma kema bi masa baya za kiyi, to kuyi tayi in dai Yah Sadeeq ne ba'a masa gwaninta."

"Baki dai fahimce saba amma yanada saukin kai."

"Ke kika sani soyayya ta rufe miki ido."

Dariya Biebie tayi sukaci gaba da hiransu, Rahma ko hankalinta duk yana kan kallo bata kulasu dan ita da kallo kamar me, Mami kam sulalewa tayi ta nufi d'akin d'antan.

Bubbuga kofar tayi jinta a kulle.

Cikin magagin bacci yace.

"Waye?"

"Nice Maminka."

Tashi yayi ya bud'e kofar ta shiga ta zauna saman stool shi kuma ya zauna bak'in gado.

"Lafiyarka kuwa Abba."

"Lafiya lau, me kika gani?"

"Ka shigo ba sallama sannan baka yi wani breakfast ba."

"A gajiye nake kuma bana jin yunwa."

"Daga ina kake tin safe ka fita yanzu ka dawo kuma ka kulle kanka ka hau bacci kuma nasan jiya baka dawo gidananan da wuri ba, Abba karda ka jawo min abin magana a gari."

"Mami ba komai fa ki tayani da addu'a kawai."

"Abba in baka fada'min matsalarka ba wa zaka fadawa, fad'amin menene?"

Murmushi yayi ganin yadda Mami take lallashinsa kamar wani yaro k'arami.

"Wato ma dariya na baka ko, to karka fad'a ka zauna haka, gaskiyan k'annanka da suke cewa kanada bak'in hali."

"Haka suka ce?"

"Ban sani ba."

Ta fad:a tana fita a d'akin, kwafa yayi a ransa yace.

"Zanyi maganinku ni zaku cewa d'an bak:in hali zan nuna muku bak'in hali."

Kwanciya ya sake yi yanata sak'e sak'e a ransa.


****

 Kwana 'daya, biyu shuru tin tana zuba idanu harta hakura tabarwa Allah dad'inta har yau Magajiya bata kulata ba balle ta takura mata ba, amma tasan kwanaki suna cika zata fara rayuwar data tsana, duk gidan ba wanda yake kulata banda Zuhrah ta d'auketa kamar k'anwarta ita kanta bata so Ummu ta fara irin rayuwar da ita kanta ma Zuhran bata so, Dije kam liyafa yaci gaba kwanama a gidan ta rage yi, tsakaninta da Ummu ko, ko gaisuwa.

Yau kwana hudu kenan da yamma tana ba'kin fomfo tana musu wanki ita da Zuhra, Zuhra na shanya su kaga maza na shigowa gidan kusan su biyar dirka-dirka ga Magajiya a gefensu, cigaba su kayi da wankinsu amma haka kawai Ummu taji zuciyarta na bugawa tama kasa yin wankin.

Sunan y'an matan gidan ta fara yi wadda suke gida, jin ta ambato Zuhra yasa cikin Ummu murd'awa ta durkushe, bata gama durkushewa ba taji tace, "Ummu."

Tsananin firgici da tashin hankali ta shiga tama kasa tashi.

Cikin tsawa Magajiya tace.

"Ba dake nake ba kina jina, k'araso nan."

Jikinta har rawa yake ta tashi tazo kusa da Zuhra ta durkushe dan kafofinta sun kasa d'aukarta.

Muryar Magajiya taji tana cewa.

"Gasu su bakwai suka rage a gidan ku zab'a na zab'a."

Daya daga daga cikin mazanne yace.

"Kai ni wannan ta karshen nake so."

"Nima haka."

Cewar d'aya na gefe.

"Kwana ko wuni?" Magajiya ta tambayesu.

"Ni zan wuni da ita, kai ka kwana."

"Dubu talatin ko wani wuni kwana kuma dubu hamsin."

"Karki damu Hajiya kudi ba matsalar mu bace."

Zaro bunch su kayi suka mik'a mata dubu dari cib, tsabar murna Magajiya ta rasa ya za tayi arzikinta yazo har gida lallai zuwan Ummu yazo mata silan yin arzikinta.

"Ke Ummu tashi ki bisu, maza jeki canza kaya zasu jiraki a falona, ku kuma sauran ku gama zaba."

Yanda take durkushe ta tusa kanta cikin cinyoyinta kuka take a hankali jin yadda ake cinikinta kamar wata marar gata dama ina gatan Mahaifiyarka ta tafi ta barta, ta manta da tana raye ko ta mutu ko taci ko tasha ko tanada lafiya ko taka dashi, wanda ya rage mata shima ya tafi ya barta wanda ya fita sonsa ya karb'i abinsa.

Tsawan da taji daga kanta shiya sata d'ago kanta idonta duk yayi jajir dan kuka.

"Tashi nace ki kimtsa ana jiranki kin tsaya yin kukan munafurci."

"Dan Allah kiyi hakuri Hajiya wallahi bazan iya abinda kuke so ba haramunne fa."

"Ubanki ni zaki fad'awa haramun tashi karna make ki."

Tashi tayi tana kuka ta nufi hanyar fita waje, fixgota tayi ta bata mari.

"Shegiya baga can hanyar d'akinkun ba, ina za kije?"

Fizge jikinta tayi tai hanyar fita da sauri suka rufo bayanta, gudu tasa maza biyun da suka bada kudi suka bi bayanta ganin za suyi asara, a guje ta fito a gidan suna binta, kyisss yaja birki da sauri ganin ya kusa bugeta, Ummu ko tsabar tsoro fa'di tayi ta sume da sauri ya fito ganin mazan na kok'arin d'aukarta, fizgota yayi ya nufi motarsa da ita ya sata gidan baya ya koma driver sit yana kok'arin tayar da motan suka rike murfin motar .

"Ina zaka kaita?"

Wani kallo ya watsa musu ya ja motarsa da karfi yabar unguwar, tu'ki yake har ya fita a cikin garin ya samu karkashin wani bishiya yayi parking, ruwan gora ya d'auko mai sanyi ya watsa mata a firgice ta farka tana surutai.

"Dan Allah karku tafi dani bana so, bana so..."

"Keee!!"

Ya daka mata tsawa, kallonsa tayi da kyau ta kalli inda take ta kamkame jikinta ta fashe da kuka.

"Dan Allah ka kaini gidanmu zasu tafi dani."

"Ina zasu kai ki?"

"Nima ban sani ba, ka kaini gidanmu."

"Kinga karb'i kisha."

Ruwan ya mika mata ta girgiza.

"Karbi nace." ya sake mata tsawa, da sauri ta karb'a ta kafa kai ta hau tasha sai da tasha ta koshi tana sauke ajiyar zuciya.

"Ina ne garinkun?"

"Wani kauyene dake karkashin Batagarawa, me suna Uguwar Liman."

"Cabdi." yace aransa shi baima tab'a jin wani gari ko kauye me suna haka ba.

"Zaki iya ganewa daga Batagarawa."

"Eh zan gane."

Ta da motarsa yayi yace.

"Allah kaimu lafiya."

"Ameen" Tace k'asa 'kasa tana kallonsa, ya 'dauki hanyar Rimi Local Government.


 Awanni Hudu cib suka 'dauka suna tafiya kafin suka shigo garin Batagarawa gefen titi ya tsaya yayi parking, kafin ya juya baya inda take, bacci take hankalinta kwance ta dukunkunu cikin hijab nata, dan tinda suka soma tafiyan taji sanyin AC na ratsata bacci ya d'auketa.

K'aramin tsaki yaja ya kalleta yarinyace k'arama sosai ba zata wuce shekaru sha hudu ba amma dirinta, halittarta na y'an shekaru sha bakwai,, ba zaka kallo kankantan shekarunta ba sai ka k'are ma fuskarta kallo, bak'ace amma bak'inta mai kyaune kuma bakin ba har can ba, tana da hanci da dan tsukekken bakinta, ga gashin ido dana gira Allah ya bata, gaban goshinta da gefen fuskarta ko gashine kwance.

Kawar da kansa yayi daga kallon abinda bai kallesa ba, hanki yasa ya bugeta dashi yana cewa.

"Ke! Ke! tashi mun iso."

A tsorace ta farka tana binsa da kallo dan dad'in bacci tama manta a ina take.

"Ina ne hanyar garinkun?"

"Eh amm...."

"Kinji mai nace ai, ina ne za mubi."

"Ni wallahi ban sani ba sai dai ka nemi wani yama jagora dan ka fitarni a garincan yasa nama karya."

Tsabar mamaki yama rasa mai zai ce mata sai kallonta da yake yi kamar hoto tama raina masa hankali.

"Fitamin a mota."

Ya daka mata tsawa, taki motsawa balle yasa ran zata fita.

"Fita nace karna makeki ni zaki rainawa hankali, oya get out of my car."

Koka'rin bud'e motar tayi ta fita ta fara tafiya yana kallonta har tayi nisa, kome ya tuna ya kunna motar ya bi bayanta, hon ya mata ta juya, da hannu ya mata alamar ta shigo, make kafad'a tayi taci gaba da tafiyarta, parking din motar yayi ya fito ya fizgo hannunta tana tirjewa ya bud'e motar ya jefata ya zagaya ya shiga yaja, bai tsaya ko ina ba sai a tashar mota, fita yayi yaje gurin yan kwandasta su kayi wata magana ya koma motar yaja.

Tindasuka d'auki hanya bai kalli ko inda suke ba jifa-jifa yakan kurb'i ruwan maltina dake gefensa yana sha, sai da suka iso mashigar k'auyensu ta kalla ta k'ara kallo ta juya tana kallonsa fuskarta da murmushi ganin yanda ya bata rai yasa ta maida murmushinta ta juyar da kanta gefe.

Yasha mamaki mutuka ganin 'kauyensu, k'auyene daya amsa sunansa rugama ba k'auye ba danko yaga alama akwai abubuwa da dama da k'auyen ke bukata, dama akwai mutane a irin gurinnan kuma suke rayuwa a cikinta, shine tambayar da yake ma zuciyarsa.

Sai da suka shiga cikin garin bai kalli inda take ba yace.

"Ina ne gidan mai gari?"

"Nan za mubi."

Ta nuna masa wani layi, hanyar yabi tana nuna masa har kofar gidan mai gari, bayan yayi parking ya kallota.

"Muje ko."

F ita tayi yai shima ta fito suka nufi wajensu, da kallo mazaunan kofar gidan suka bisu ganin Ummu da wani bako wanda basu tab'a kallonshi a garinnan ba, sallama ya musu bayan isarsu, suka nuna masa wajen zama ya zaune, tana ko'karin zama mai gari yace.

"Ummu shiga cikin gida."

Tashi tayi ta shiga bayan tafiyarta Mai gari ya kallo Sadeeq yace.

"Bawan Allah lafiya? Me ya had'aka da Ummu?"

Zama Sadeeq ya gyara nan ya fad'a masa had'uwar da su kayi yau da Ummu ta fito a gidan karuwai tana neman taimako ya taimaka mata ya kawo nan, ya boye musu farkon silan SANADIN HAD'UWARSU.

Shuru su kayi can Mai gari yace.

"Abulle zata aikata komai dan ganin ta b'ata rayuwar Ummu, ba wanda nake zargi da kai Ummu Birni sai Abulle, shisa naga kwana biyu bana ganin tana wucewa tazo gaishemu, Allah zai saka mata."

"Yanzu me abin yi Maigari kasan dai duk yanda akayi aka bar Ummu a garin nan sai Abulle ta sani karshema in bata samu masara akanta ba ta nemi kasheta ko ta halin yayane."

Fad'in wani mutum dake zaune a gurin abokin Baffan Ummu mai suna Malam Haruna.

"Shine nima abunda nake tunanin yi nesa da Abulle dan gudun shiga wani tarkonta."

"Bawan Allah ko zaka taimaka mata?" CewarMaigari yana kallon Sadeeq.

"Ni ko Baba da mai zan taimaka mata ni daba garin nake ba."

"Ko da, da aurenta ne?"

Ras gabansa ya fad'i wani duhu ya lullub'esa ya rufe idonsa ya bud'e da kyar ya iya bud'esu yayi murmushin karfin hali.

"Haba dai Baba ina aka tab'a yin haka aure ba dangina ba nata ba waliyai."

"In ka amince zan zame maka waliyi."

Fad'in Maigari yana kallonsa.

"Ni kuma zan zama waliyin Ummu."

"Kuyi hakuri dan Allah amma sam abinnan bamai yiwa bane."

Cewar Sadeeq yana kok'arin tashi.

Caa mutanen gurin su kayi a kansa manyan maza dattijawa suka sauk'e girmansu suna rok'ansa ya aureta ciki harda Mai gari.

"Ya Allah."

Yace a cikin ransa yama rasa tunanin da zai yi Zuciyarsa gefe daya yana tausayawa rayuwar Ummu gefe daya kuma yana tunanin in ya amince da auren wacce bai san komai game da rayuwarta ba da danginta ba karya jawowa kansa matsala gashi bai san ya Mami da sauran y'an uwansa ba za su d'auki auren.

"Ba zamu takura maka ba taimako za kayi in baka amince ba shikenan taimakonta da kayi Allah ya biyaka."

Fad'in Maigari yana kok'arin tashi idonsa cike taf da hawaye dan yana mutukar tausayawa rayuwar Ummu.

"Na amince Allah yasa shi yafi Alheri."

Ya fad'a a hankali.

Kabbara gurin suka d'auka, ya zaro kudi dubu talatin ya mik'a take Maigari ya wakilcesa, Malam Haruna ya wakilci Ummu, mutanen guri suka shaida, aka d'aura auren Aisha Muhammad Bello da Abubakar Sadeeq Sulaimann kan sadaki mafi sauk'i dan neman albarkan aure.

Bayan angama Maigari ya aika cikin gida aka kira Ummu bayan ta iso ta durk'usa kusa dashi kud'in hannunsa ya mik'a mata.

"Karbi wannan dukiyar kine Allah ya miki albarka, na sanki da hakuri ki k'ara akan wanda kike dashi sannan ki jure duk wani abinda za kigani a inda za kije nasan dan zamanki kauyennan babban hadarine ga rayuwarki, nasan bazai cutar dake ba insha Allah, Allah baku hakurin zama da juna."

"Ameen Ameeen."

Jama'ar gurin suka d'auka kafin Sadeeq ya tashi ya musu sallama jikinsa duk yayi sanyi kamar wani marar lafiya haka ya koma.

"Muje ko."

Har gurin motarsa Maigari da mukarrabansa suka kaita suka shigar da ita sai fa lokacin hankalinta ya tashi ta fara kuka.

"Baban Saude ina zai kai ni ni bazan bi saba."

Da kyar da lallashi suka sata motar suna d'aga masa hannu har yayi nisa, itako kanta ta kifa tasa kuka tsammaninta duk gidan Magajiya zai maidata.

Sai da suka bar k'auyen ya kallota.

"Ke kimin shuru kar kisa a biyoni a tsamman saceki nayi."

Kin kulasa tayi taci gaba da kukanta har suka isa Rimi dan Babban store ya samu ya siya mata cake da Malt ya fito a kan cinyarta ya ajiye mata.

"Zaki iya ci kafin mu 'karasa."

Ko kallonsa ba tayi ba ta juyar da kanta idonta sun kumbura dan kuka, tada motarsa yagi ya d'auki hanyar Katsina, awa biyu suka d'auka suna tafiya ganin yunwa na neman sata kuka ya sata ta bud'e cake din taci kad'an jin ba dad'i, ta shanye Malt din ta jinjina kanta bata san lokacin da bacci ya d'auketa ba.

Shikam tuki yake yana tunanin.

"Ta yaya Mami zata d'auki wannan k'addararren auren."

Murmushi yayi dan ganin ya samu mafita, haka har suka isa cikin Katsina.

PhartyBb.WordPress.Com

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


 SANADIN HA'DUWARMU

  ©PhartyBB


( 8 )


  A kofar gidansu yayi hon maigadi yazo ya bud'e masa ya shiga, tinda suka shiga ta saki baki take kallo ita tsorone ma ya kamata ganin gida kan gida kamar na aljanu, bayan yayi parking ya bud'e ya fito shuru bata fito ba tak'i.

Kallonta yayi yadda ya ganta duk a tsorace take ta kankame jikinta kam-kam kamar kace ke ta ruga da gudu.

Murfin motar ya bud'e cikin jin haushi yace.

"Dallah bakyauyiya fitomin a mota."

A tsorace ta fito tana kalle-kalle.

"Biyoni."

Yace da ita, ya fara tafiya tana binsa a baya har babban falon gidan, bayan ya shiga ya tsaya ta shigo ya rufe kofar.

"Muje."

Ya fad'a yanayin gaba, cikin manya manyan kujerun falon ya zauna ya nuna mata k'asa yace.

"Zauna ina zuwa."

Tashi yayi ya nufi falon sama dan nan ba kowa, a falon saman ya samesu Hauwaty, Biebie da Rahma, Mami bata nan.

"Sannu da zuwa Ya Sadeeq."

Suka had'a baki wajen fad'a, bai ko kallesu ba yace.

"Ina Mami?"

"Tana dakinta." Cewar Biebie tana kallonsa.

Wucewa yayi ya nufi d'akin Mami tana zaune tana waya kusa da ita ya samu ya zauna ta gama wayan ta juya tana kallonsa tace.

"Ya akayi Abbana."

"Mami alfarma nake so."

"Alfarman me kuma Abbana."

"Mami y'ar aiki na samo miki sabuwa, naje gidan abokina aka kawowa matarsa ita kuma tana dashi shine na kawo miki."

"Y'ar aiki kuma Abba, duk 'yan aikin gidannan."

"Mami ki duba mata wani aikin tana yi."

"Ni bani da wani aikin da zata min ka sallameta kawai."

"Haba Mami dan Allah fa nace, to ni zan d'auketa tana gyaramin dakina."

"Ban amince ba."

"Please Mami kin ganta fa abin a tausaya matane."

"Kar dai har ka shigomin da ita gida."

Ta fad'a tana tashi, shima tashin yayi yabi bayanta, tana zaune inda yace ta zauna, jin alamun saukowane ya sata d'ago kanta ido biyu su kayi da Mami tana kama dashi, k'arasowa tayi ta tsaya kanta tana 'kare mata kallo.

"Mun wuni kalau Hajiya."

Ummu ta fad'a murya na rawa, tsaki taja ta kallo Sadeeq dake tsaye gefenta ya marairaice mata.

"Kin tab'a yin aikataune?"

Girgiza kai Ummu tayi alamar ah a.

"Kai Abba a hakan za tayi aiki bata tab'a yi ba."

"Mami zata koyane nan gaba a hankali."

"Tinda kace dole sai tayi za tayi amma zata zaunane anan ba jeka ka dawo ba."

"To Mami dama haka nafi so nima."

"Aikinta shine goge-goge da taya Iyami yanke-yanken kayan miya da sauran k'ananan ayyukan kitchen, sai kuma gyara d'akin su Biebie da wanke musu toilet mai gyara musu tayi tafiya garinsu shikenan aikinta."

"To Mami kudin albashinta nina d'auki nauyin biya."

Bata kulasa ba ta koma sama badan ya nace ba, ba zata barta ba ita bata son tarukucen masu aiki a gida.

Bayan ta wuce ya kallo Ummu.

"Kinga wannan itace mahaifiyata ki guji bacin ranta idan kika kiyaye zamu zauna dake lafiya sannan ina da kannai uku biyu mata d'aya namiji, matan su za kina gyarawa d'akinsu duk safiya ki wanke musu band'aki da d'akinsu sannan waccan gurin, gurin girkine za kina shiga ciki akwai mai girki za kina tayata ayyuka, kinji."

"Naji zanyi duk abinda kace Insha Allah."

Ta fad'a kanta a kasa.

"Yawwa muje in nuna miki d'akinki."

Gaba ya wuce ta bishi a baya har zuwa wani d'aki dake kasa kusa da kofar fita ta baya inda zai kai mutum garden din gidan.

Bayan sun shiga yace mata.

"Ina zuwa."

Fita yayi ya koma d'akinsa kafin ya sauko ya wuce store ya dawo dakin d'auke da tsintsiya da faka da sabon zanin gado (bedsheet) ya ajiye mata.

"Gashi ki share ki shimfida wannan sabon, sannan ki wanke band'akin daga gobe zaki fara aikinki in Allah ya kaimu, in kina da bukatar wani abu ki fad'amin."

Kanta a kasa tace.

"Kayan sawana ban d'auko ba."

"Nasan da wannan ba wani abu."

"Babu nagode Allah ya saka."

Bai kulata ba amma a ransa yace ameen, daganan ya fita ya koma d'akinsa, wanka yayi ya saka kayan shan iska, yabi lafiyar gado.

Bai farka ba sai karfe biyar na yamma fita falon k'asa yayi daga Mami sai Rahma a zaune suna kallo kujera ya samu ya zauna.

"Ke kawomin ruwa."

Tashi tayi tana gunguni shi wai ba zai kira sunan mutum ba sai dai ke.

Bayan ta kawo masa yace.

"Muje d'akinku zan duba abu."

Tashi tayi tai gaba yabi bayanta suka shiga kofar d'akin ya kulle a tsorace take kallonsa tasan ba k'aramin aikinsa bane yace zai zaneta.

"Dena kallona da idonki irinna mayu, bud'emin Wardrobe naki keda Biebie."

Bud'ewa tayi ta nuna mishi ya zaro atamfa kala bibbiyu da dogun riga d'add'aya ya 'daga ya kara d'agawa ya tabbatar zasu mata kafin ya d'auka yace.

"Kuma ki cewa Mami ko Biebie ni nasa hannu na d'auka, bake kika bani ba sai bakinki ya kurbi jini."

Ita dai tana gefe ta rakube tana kallon ikon Allah kayan da suke so ya d'auke ko mai zaiyi dashi, bayan ya fita ta fito ta koma gurin Mami.

"Ke Rahma bak ida hamkali kayanku zaki d'auka kibawa 'yar aiki."

Cewar Mami cikin fad'a.

"Ma...Mami, Mami ni na basa ya bata."

Ta fada cikin in ina ganin Ya Sadeeq ya shiga wani 'daki.

"Dan kuma zaki basa sai ki bashi mai kyau."

"Mami sun min kad'anne shiyasa."

"Ke kika sani tinda y'ar aiki zaki mai da mutum, waya san ma ko y'ar tsintuwace"

"Uhmmm." Rahma tace tana maida kanta ga TV.


 Ya Sadeeq ko yana d'aukan kayan direct d'akinta ya wuce tana rakub'e tayi tagumi yadda su kazo haka ya ganta da mugun mamaki yace.

"Ba kiyi wanka ba balle Sallah."

Cikin tsoro tace.

"Ruwa ta sama yana zubowa."

Bai kulata ba yace.

"Biyoni."

Binsa tayi ya shiga bathroom din ga shower a kunne ruwa na zuba, kashewa yayi ya nuna mata pompom da buket yace.

"Nan za kina kunnawa ki tara ruwanki a ciki sai kiyi wankanki, ba ruwanki da can sai nan kuma za kina wanke bakinki ga brush da Maclean nan."

Ya nuna mata inda ya ajiye mata harda soson wanka da sabulu.

"Abinda ka fada a karshen ne ban gane ba me zanyi dashi?"

Salati yayi a ransa a fili ko yace.

"A garinku ba'a wanke baki?"

"Anayi mana."

"Dame ake wankewa?"

"Da karan maina ko gawayi da gishiri."

Dariyane ya kamashi ya danne lallai fatara, rashin ilimi da rashi na damun k'auyen nan.

"Motso kiga."

Matsawa tayi ya matse maclean a brush ya rik'o kanta da bismillah yace.

"Bud'e bakin."

A tsorace tace.

"Kayi me?"

B'ata rai yayi.

"Bud'e nace."

Za tayi magana ya tura brush din bakinta ya hau gurzawa, sai da ya wanke tass har sau uku kafin ya saketa yace.

"Kullum kina wankewa sau uku safe, rana, dare kinji kuma wankama haka kina yi sau uku kinji."

"To." Tace fuska duk hawaye.

Ruwa ya tara mata a buket.

"Kiyi wanka ga kaya na ajiye miki a waje in kin fito kisa za'a aiko miki abinci.

"To nagode Allah biyaka da alherinsa."

Murmushi yayi yace. "Ameean."


 Bayan fitarsa tayi wanka da ruwan da ya tara mata wanka wanda bata tab'a yin irin saba tinda tazo duniya, tabbas hakane dan ita kanta ajikinta taji sauyi ta wanke gashinta, ji tayi iska na shigarta gabobin jikinta, kanta da bakinta yafi komai mata dadi yanda iska ke shigansu har bacci-bacci take ji.

Fitowa tayi ta saka d'aya daga cikin kayan daya ajiye mata sauran ta ajiye a wani katon dorowan jikin bango data gani ta koma ta zauna, taji sallama hijabinta tasa ta amsa.

Rahma ce hannunta rik'e da plate da goran ruwa, mik'a mata tayi.

"Gashi aci abinda ba'a saba ci ba in za'a iya."

Bata ce komai ba ta kar'ba ita kuma Rahma fuu ta wuce ganinta wannan zubda ajine kawowa y'ar aiki abinci.

Bayan ta kulle kofar ta zauna ta baje, ta bud'e abincin shinkafa da miyane da nama gefe kuma Coslowne yaji kwai da bama, da bismillah ta faraci harta koshi tayi kat tasha ruwa ta ajiye a gefe batayi karambanin fita ba dan ita girman gidanma tsoro yake bata.


Sadaukarwa ga Ummu Aishat.PhartyBb.Wordpress.com

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION.


  SANADIN HADUWARMU

   ©Pharty BB


( 9 )


  Da dare su Hauwaty suka dawo daga gidan Uncle nasu Baban Biebie, duk da Momyn Biebie tayi-tayi ta zauna mata tak'i ta biyo Hauwaty suka dawo, nan Rahma ta kwashe komai da Ya Sadeeq ya d'auka ta fad'a musu.

Wani uban tsalle Hauwaty tayi daga kwanciyar da take, dama duk cikinsu ta fisu rashin kunya, sai Biebie kuma girman kai da wulakanci, Rahma ko zigine da ita.

"Kan uba fatan bai tab'amin kaya ba?"

Cewar Hauwaty tana bud'e gefen kayanta.

"Bai tab'a ba, dan sun mata yawa ina ga shi yasa yak'i yace a bud'e."

"Tab Allah yaso kowa wace shegiyace da wallahi duk ranar data sa sai na cire mata na mata tsirara a gidannan sai dai ya kasheni."

"Ni ko shida ya d'auki hannu ya d'auka ya bata, shi zai 'dau hannu ya bani kudi na siya."

Fad'in Afnan tana kwanciya ko a jikinta dan tasan meta shirya masa.


Daren ranar ma dole yasa Rahma takai mata abinci, yace mata kuma in taci ta fito da plate din duka.

Kamar zata zubar haka ta d'auka abincin sai da ya daka mata tsawa.

"Kika zubar dashi zan taka ki a anan gurin, rik'e mai kyau."

Kuka ta kusa sawa ta d'auka ta kai mata ta kudura a ranta sai ta muzguna mata kamar yanda tasa yayanta yake takura mata.   Da misalin karfe tara da rabi da minti biyar na dare (9:35pm), Mamine da Sadeeq sai Hauwaty suna zaune saman dining.

"Abba ko kasan Biebie suna da bikin kawarta wani sati."

Mami ta fad'a tana kallonsa yana cin abincinsa.

"Ban sani ba."

"To yanzu ka sani gobe ka d'auketa kuje ta siya duk abinda take bukata."

"Zan bata dai kudi ta siya abinda take so, amma ba inda zan kaita danni ba driver nata bane."

"Ko baka zama yanzu ba gaba kad'an zaka zama."

"Me kika ce?"

Ya fad'a yana kallon Hauwaty da tayi magana k'asa-k'asa.

"Ni bance komai ba." Ta fad'a a tsorace dan tsammaninta bai ji abinda tace ba.

Gurinta yayi ganin ya nufota ta tashi zata gudu ya fincikota ya watsa mata mari.

"Yaushe na fara wasa dake ni sa'an kine."

"Kayi hakuri ni wallahi bance komai."

Mari zai sake kai mata Mami ta rik'o hannunsa.

"Ya zaka dinga dukarmin 'ya a gabana, karya tayi ne?"

Sakinta yayi ya haura sama ya rufe kofarsa da karfi, Mami ce ta lallashi Hauwaty kafin suka wuce d'akunansu.


 Washegari karfe takwas ya sauk'o yayi breakfast nasa ya wuce office nasa inda yake aiki.

Da karfe biyu da mintuna na rana ya baro wajen aikinsa ya dawo gida, kamar yanda ya saba yana dawowa d'akinsa yake wucewa yayi wanka ya canza kaya ya sauko cin abinci haka yauma, yana zaune kan dining, su Biebie suka fito cikin shirin fita sun sha bak'aken dogon riga, bayan sun ma Mami sallama zasu fita ya 'kira sunansu ta hanyar daka musu tsawa.

"Hauwa, Rahma da ke Biebie kuzo nan."

Dawowa su kayi suka zauna saman kujerun dining din, sai da ya gama cin abincinsa ya kallosu tare da buga tsaki.

"Ina zaku?"

Caraf Biebie tayi magana.

"Shopping kasan bikin k'awarmu Zee ya kusa."

"Allah ko."

"Eh ko zaka kaimu Yayanmu."

Wani kallo ya watsa mata kafin ya tashi, can ya dawo suna zaune yanda ya barsu, kud'in hannunsan dubu goma ya watsawa Biebie.

"Ga kudin da kika ro'keni kin san ni ban gaji roko ba."

Yana fad'ar haka ya fita a falon, bakin ciki da Biebie ta shiga baya misaltuwa duk da yanda take jinsa a ranta bata son wulakacin da Ya Sadeeq ke mata, a sanyaye ta kwashe kudin kafin suka fita Hauwaty tayi drivern nasu suka fita.


 Ummu ko a ranar ta fara aiwatar da ayyukanta cikin gidan, tsakaninta dasu sai dai gaisuwa shima sai sunga dama, 'yan matan ko ba magana su sata wannan in tayi ba dai-dai ba sun dinga mata fad'a.


 Sati biyu da zuwanta ta fara kwarewa a aikin da take yi, duk tsawon kwanakin bata 'karasa Sadeeq a ido ba, safe zata farka in tayi sallah tayi wanka da brush kamar yanda Ya Sadeeq yace tana yi, inta idar da Sallah ta fito ta shiga kitchen ta taya Iyamee mai aikinsu dan aikace-aikace in sun gama ta wanke kwanukan da suka 'bata ta goge kitchen din sai ta wuce 'dakin yan matan ta gyara ta share ta goge ta wanke band'akin, tasha wuya kafin ta kware da aikin.

Bangaren ci da sha ba laifi da zaran sun gama girki Iyamee zata dib'a mata taje 'dakinta taci.


*****

 Yau (Weekend) hutun karshen mako, tin daren jiya ciwon baya ya sata gaba motsi ka'dan tayi ya dinga ciwo, bayan ta idar da Sallar asuba dakyar ta kwanta akan abin sallar dan bayan ciwo yake sosai.

Karfe tara da mintuna taji ana buga kofar kamar za'a balla, dakyar ta iya tashi abinda ta gani a jikinta shiya mutukar tsoratata dai-dai lokacin an turo kofar da karfi, Rahma ne da Biebie, cikin matsifa Biebie tace.

"Kina ji ana kiranki ki kama mutane shuru dan iskanci ubanwa zai gyara mana d'akin."

Tana kare mata kallo, kallon mai cike da wulakanci.

"Ke Sister kalli fa 'kazanta anan."

Fad'in Rahma na nuna leman da yake bin 'kafar Ummu.

"Mtsw 'Kazanta ma d'aya ko biyu, zomu fita kar ta sani amai."

Da sauri suka fita, Ummu ko kuka tasa ganin abin wancan watan ya dawo mata jan jikinta tayi ta shiga band'aki ta gyara jikinta ta wanke kayan da bata ta fito ta sake kwanciya tana kuka.

Jin bud'e kofa yasa ta kalli kofar da sauri tsammaninta duk sune suka dawo, tsaye yake yana kallonta, kanta ta d'auke ya 'karaso 'dakin ya zauna gefen katifan a hankali yace.

"Meke damunki?"

Bata kallesa ba tace.

"Ciwon baya."

Kallonta yayi da kyau.

"Dama in za kiyi period haka yake miki?"

Shuru tayi dan bata gane me yake nufi ba.

"Sorry ina nufin in za kiyi Al'ada haka yake miki."

Tusa kanta tayi cikin filo cike da tsananin kunya ta kasa magana.

"Tambayarki nake."

"Sau biyu nayi inda wannan."

Ta fad'a cike da kunya, kallonta yayi da kyau cike da mamaki.

"Shekarunki nawa?"

"Sha hudu." Ta bashi amsa takaice.

Shuru yayi can ya tashi ya fita, bai dad'e da fita ba, Iyamee ta shigo da breakfast nata da kaya a leda, sai da tasa taci ta bata magani ta koya mata yanda zata gyara jikinta ta tambayeta ko ta iya wankan tsarki, shuru tayi ta girgiza kanta dan ita batama san me wankan tsarki ba, shuru Iyamee tayi cike da mamaki dan musulmi bai iya wankan tsarki ba.


  Kwana hudu tayi ta gama, maganin da tasha yasa ciwon bayan ya daina mata, taci gaba ayyukanta cikin kwanakin Iyamee ta koya mata wankan tsarki in ta gama, haka kuwa akayi bayan ta gama tayi kamar yadda ta koya mata.

Tin ranar daya shigo ya mata ya jiki bai k'ara shigowa ba basu k'ara haduwa ba.


Wata ranar Asabar yan matan suna gida Biebie da Rahma Hauwaty sunyi tafiya da Mami, kasancewar suna hutun karshen zango (Second Semester).

 Da yamma tana kitchen tana wanke kwanukan da Biebie ta b'ata ita da kawayenta taga an shigo kitchen din Biebie ce ta shigo ta d'auki cup zata had'a cornflask, kamar tsautsayi taji abu ya fad'o saman kafarta, Ummu ce ta d'auko food flask zata ajiye tsantsin omon hannunta yasa ya sabule, kafin ta d'ago daga sunkuyen da tayi ta d'auki flask din daga saman kafar Biebie, taji an kwasheta da mari dafe kuncinta tayi dan marin ya shigeta.

Cikin kuka tace.

"Kiyi hakuri ban sani ba wallahi."

"Rufemin baki wawiya kawai."

Shuru tayi taja gefe ta tsaya tana share hawayenta.

"Fitarmin a kitchen k'azama kawai."

Fad'in Biebie tana nuna mata hanyar kofa.

Cikin sauri tana shirin fita gib tayi karo da Rahma, wani marin ta saukar mata a fuska itama wanda yafi na Biebie zafi.

"Baki da hankaline ko tsabar raini ke damunki zaki bigeni bakya kallo.."

Bata k'arasa taji sukar marin daya gigitata, d'ago kai tayi yana tsaye yana kallonta ransa a mutukar 'bace.

Fizgota yayi ya tura kitchen ya shiga ya kulle, belt na jikinsa ya cire ya had'ata ita da Biebie ya zane ciki da waje dan duk abinda sukewa Ummu gidan yana kula kawai yana kawar da kaine dan kar a fahimci wani abu.

Tsaf ya zanesu dama Mami bata nan duk bugun duniyarnan da Ummu take yi ya bud'e kofar yaki sai da ya gama ya fita tana durkushe tana kuka hannunta yaja ya nufi d'akinsa da ita tana turjewa.
PhartyBb.wordpress.com

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


SANADIN HAD'UWARMU

 ©Pharty BB


( 10 )


  Yana shiga cikin d'akin jifa yayi da ita ta fad'i kasa, dafe kansa yayi tare da zama saman gado, Ummu ko kuka take sosai, tashi yayi ya nufi gurinta tana jin ya nufo gurinta ta fara ja baya sai da taji ta jinginu da kujera ta takure jikinta ta runtse idonta, fizgota yayi kafin ta bude ido ya bata mari tare da jan hannunta sai da yakai bakin kofa ya tsaya cikin bacin rai yace.

"Kika kuskura kika ga Biebie da Rahma a guri baki matsa musu ba ko kika bar gurin, har ki kayi ko'karin yi musu laifi suka dake ki, ke zan daka a maimakonsu ko insa su, su dake ki, ficemin a 'daki."

Kafin ya gama rufe bakinsa ta fisge hannunta daya rike ta fice da sauri, dakinta ta wuce bayan ta shiga har dasa key ta haye kan dan k'aramin katifarta ta takure guri d'aya, gani take za suzo su rama dukarsu akanta.

Biebie da Rahma kam bayan sunsha kukansu suka fita a kitchen din su kayi d'akinsu.

"Yanzu Biebie haka zamu bari Yaya ya daki banza akan wancan 'yar aikin kucaka."

Fad'in Rahma ya yinda take rage kayan jikinta dan wanka.

Wani murmushin mugunta Biebie ta sake kan tace.

"Ni Ya Sadeeq zai daka akan wata kucakar ai y'ar aiki, dashi da ita duk zanyi maganinsu."

"Me kike shirin yi?"

Rahma ta tambaya tana zama kusa da Biebie bayan ta rage kayan jikinta ta d'aura tawul.

"Kar ki damu y'ar uwa, in lokaci yayi zaki gani."

"Allah kaimu lokacin, amma shawarata gareki kar kiyi abinda za kiyi dana sani."

"Ko kad'an ciki ba dana sani."

"Allah yasa."

Cewar Rahma tana tashi ta wuce band'aki(bathroom).


  Ranar Ummu bata ko lek'a falo ba dan tsananin tsoro, duk da yunwar dake cinta haka ta daure, data fita su daketa ko su wulakantata ta gwanbace tayi ta zama, har dare bayan isha'i tana d'akinta.

Duk gidan ba wanda ya damu da cinta balle shanta wanda ya kawota ma ya watsar da lamuranta balle wasu da suke nuna mata tsantsan kiyayya da tsana.

Ganin har karfe tara Ummu bata fito ba yasa Iyamee ta nufi d'akinta, kwankwasawa tayi.

A tsorace ta tashi daga kwancen da take.

"Waye?" Ta tambaya cikin tsoro.

"Ummu nice."

Jin muryan Iyamee ya sata bu'dewa ta shigo da sauri ta 'kara mai da kofan ta rufe.

"Ina wuni."

Ummu ta gaisheta tana sunkuyar da kai.

"Lafiya lau Ummu, Ummu mai yasa zaki rufe kanki tin safe baki fito ba baci ba sha."

"Amma babu komai."

"Kin tabbatar."

"Eh." Tace tana d'aga kanta.

"Kinci abinci?"

"Ah a." Ta girgiza mata kai.

"To ina zuwa."

Bud'e kofar Iyamee tayi ta fita can gata ta dawo da abinci a plate ta mik'awa Ummu, karb'a tayi ta zauna ta cinye tas ta kora da ruwan data kawo mata ta bata plate, kafin ta mata sai da safe ta fita, rufe kofarta ta sake yi ta kwanta dama ta riga da tayi sallar isha'i.


  Washegari har karfe goma bata fito ba, sha d'aya dai-dai taji ana kwankwaso kofar d'akin, tsammaninta Iyamee ce ta bud'e da saurinta, ido biyu su kayi dashi taja baya a tsorace ta d'an duka tana cewa.

"Ina kwana."

"Lafiya, biyoni." Yace da ita yanayin gaba.

"Ummm." Ta fad'a kamar za tayi kuka.

"Biyoni nace."

Dama da hijab nata jikinta dan bata rabuwa dashi ta fito, kalle kalle take ko za taga su Biebie sai dai har suka fita a falon bata ji ko motsinsu ba, wajen motarsa taga sunyi ya bud'e ya shiga.

Kyam ta tsaya taki shiga, glass din motar ya rage.

"Zaki shigo ko sai na fito na mammakeki."

A tsorace ta bud'e ta shiga a takure ta zauna, ya fizgi motar da karfi ya fita a gidan, gudu ya fara bai fi tafiyan minti talatin ba yayi ya tsaya a wani kofar guri babba, parking yayi ya fito, kafin yace mata fito ta fita da sauri dan ita sanyin motar ma ya mata yawa.

Tafiya ya fara tabi bayansa bayan shigar sune ta fara cin karo da yara sanye da kaya duk iri daya ba babba ba yaro, tana binsa suna tafiya har office din principal(Shugaban makaranta) da sallama ya shiga aka amsa masa kafin ya samu guri ya zauna, ta zauna a k'asa kusa da shi bayan ta gaishe da principle, shima sun gaisa da principal yace masa.

"Sir gata nan ita nake fad'ama jiya."

"Shekarunta nawa?"

"Sha hudu."

Form ya ciro ya mik'a ma Sadeeq ya karba ya cika ya mik'a masa, bayan principal din ya gama kallo yace wa da Sadeeq.

"Wani class za'a bata."

"Sir Jss 1 fannin arabic mai ha'de da boko kad'an dan ba tayi boko ba shi na zab'a mata ."

"Na karfe biyu zuwa biyar kenan."

"Ko shima yayi in dai zaku dauketa."

Fadin Sadeeq cikin sauri.

Wani dan paper ya ciro yayi signing ya mik'awa Sadeeq.

"Nan da sati mai zuwa zata fara fita dan za'a dawo a ranar, yanzu ana hutu."

"To nagode Sir."

Sai da Sadeeq ya siya mata komai kafin suka fito yaja motarsa suka koma gida, bayan yayi parking ta fita yaja motar ya fita a gidan.


 Bayan kwana biyu, ba abinda su Biebie suka mata tsakaninta dasu gaisuwa tana gaishesu take barin wajen.

Kwana uku da faruwar haka Mami ta dawo da yamma ran alhamis, gaba d'aya yarantan sun zagayeta suna hira.

Da sallama ta isa wajensu rik'e da tire da cup da goran ruwa da juice a sama, durkusawa tayi gefen Mami tana ajiye tirin saman center table.

"Mami ina wuni? Sannu da zuwa."

Kallo Mami ta k'are mata kan taja tsaki ciki-ciki.

"Lafiya."

Tace tana mai da hankalinta kan yaranta.

"Ke mayyace wai tace miki Lafiya kam ai sai ki bamu guri musha iska."

Cewar Hauwaty cikin tsawa, cikin sauri tabar gurin ita din ma tasan mai zai biyo baya zamanta gurinsu.


*****

 Bayan kwana biyu da dawowan Mami ita da yaran suka shirya su kayi tafiya garinsu, kwanansu biyu da tafiya ta fara fita makaranta, shiya kaita yace in an tashi ta dawo da kafa tinda ba nisa, ranar tasha wuya harda kukanta ganin yanda ake karatu ga rubutu ba laifi kuma bata san ko A ba da kyar ta iya gano wazu bak'ak'e a Arabic, bagaren rubutu kam kamar wasan yara da kyar ta iya rik'e pencil din tayi rubutu sama da kasa, haka aka tashi ta dawo gida da kafa kasancewar ba nisa da gida.

Kwana uku tana zuwa a ranar ta tafi wajen karfe hudu su Mami suka dawo, bisa matsawan da yaranta suka mata bazasu iya zama a kauyen ba, karfe biyar an ta shesu ta kamo hanya kasancewar kusa da gida take da kafa take zuwa ta dawo, tsakaninta da Sadeeq tin ranar daya kai ta makarantar islamiyyah har yau.

Da sallama ta shiga falon ba wanda ya kulata sai Rahma data juyo ta kalleta ta bugi cinyar Biebie tana mata signal da ido, kallonta ta kai kan Ummu kafin ta kwashe da dariya.

Durkusawa tayi tace.

"Ina wuninku, kun dawo lafiya."

Dariya suka sa mata Rahma harda fad'uwa k'asa tana cewa.

"Ba sabin ba na shiga class, ga wani uban rik'e jaka kamar za'a kwace."

Dariya suka sa gaba dayansu harda Mami, Ummu ko kanta sunkuye kasa.

Bude kofa da shigowar mai bud'ewan shiya sasu dakatawa da dariyan, ko kallon inda suke bai yi ba ya wuce stairs har yayi taku biyu zuwa uku ya juyo.

"Ke! me kike anan?"

Kallonsa tayi fuskar nan a had'e rabonta dashi harta manta, sunkuyar da kanta tayi k'asa-k'asa tace.

"Babu."

"To bar nan."

Yana fad'ar haka ya wuce, ita kam Ummu ta samu dama cikin sauri tabar gurin ta fad'a dakinta, kwana biyu da basa nan tana jin dadin gidan..


Sadaukarwa ga Ummu A'ishat(Ummi Safwaan).PhartyBb.WordPress.com

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


 SANADIN HA'DUWARMU

  ©Pharty BB


( 11 )

  

   'KAUYEN UNGUWAR LIMAN

 Wata 'daya, biyu, uku shuru Abulle na zuba ido taga kud'i sun fara shigo mata amma shuru kake ji kamar an aika bawa garinsu, ganin haka ya sata takanas taje gidan Lami wata ranar jumma'a da yamma.

Da sallama ta shiga gidan Lami na zaune tana tsefewa 'yarta k'arama kai, jin mai sallamar Abulle ya sata yin tsaki ciki-ciki kafin ta amsa, Abulle ta shigo.

Kujera da ta gani kusa da inda Lami take zaune taja ta zauna.

"Lafiya Abulle da yamma sakaliya haka."

"Ina ko lafiya Lami, yara yau ana neman wata hudu basu ba labarinsu ba labarin kud'i."

Wani bahagon dariya Lami ta saki.

"Allah ko Abu iyayen son kudi, ni ma yanda kika ganni jiran zuwan Magajiya nake nanda karshen watan nan."

"Amma Lami cemin ki kayi karshen ko wani wata tana zuwa."

Fad'in Abulle cikin bacin rai.

"Hakane kam tana zuwa, bansan me ya hanata zuwa wata uku da suka wuce ba."

Shuru Abulle tayi ta rasa ta cewa karfa Lami da Magajiya yaudaranta za suyi.

"Lami rantamin kudi mana."

"Bani dashi."

"Haba Lami jaka biyu fa zaki rancha min kafin nan da karshen wata muga ikon Allah."

Tashi Lami tayi bayan ta gama tsefewa 'yarta kai ta turata d'aki.

"Abulle banda kud'in da zan ranta miki sanin kan kine bashinki ba dad'i."

Tashi itama Abulle tayi ganin yanda Lami ta rik'e kugu.

"Ba zaki ban bane ko baki dashi."

"Abulle, Bani dashi kuma ko ina dashi bazan baki ba."

"Ya isa haka Lami, ba komai ni na yarda dake ki kemin abinda ki kaga dama."

Tana fad'ar haka ta nufi kofar fita a gidan.

Tsaki Lami tayi tana shigewa d'akinta.

Tin daga ranar tsakanim Abulle da Lami ya fara zama ba dadi, ita Abulle haushin Lami take ji ga fargaban ina Magajiya takai yaran musamman d'yarta Dije, dan Ummu bata dameta ba, wacce ta haifeta ma ta iya tafiya ta barta balle ita danta salwanta bata da matsala.


  *****

  Tin lokacin da zaran su Biebie sun ganta da Uniform ko Takarda a hannunta zasu hau mata dariya bata da sakewa a gidan tayi nazarin littafanta sai a d'akinta, tin abin baya damunta har ya fara damunta wani lokaci tasha kukanta a ranta take fad'in, ko dan sunga ta fito daga kauye bayan hakama da girmanta ta shiga makaranta, yanzu ya zama abin har yabi jikinta ko sunayi saidai tayi shuru tasa musu ido.


Kwanaki sunja sun zama satikai, sati takwas da fara zuwa makaranta lokacin tana neman wata uku a gidan, abubuwa da dama sun faru ciki harda rana 'daya bata da lafiya Hauwaty ta sata wankin undies bata samu ta mata ba ranar duka ta mata na fitar hankali, dan daga baya sai da tasha zazzabin kwana biyu kafin ta warware.

 Yau tana cikin wata uku da fara zuwa makaranta Allahamdulillahi ba laifi tana fahimtar wasu abubuwa na arabic sosai ta fara gane bak'i, abu dai da boko ne dai har yanzu lami yana mutukar bata wahala, suna tayin C.A zasu fara Exam, sosai ta dage da karatun abinda take fahimta.


  Yau asabar misalin karfe bakwai da arba'in da biyar (07:45am). Aiki suke ita da Iyamee suna hada-hadar had'a abincin karyawa (Breakfast), da sauri Mami ta shigo kitchen din, har kasa ita da Iyamee suka durkusa suka gaisheta, bayan ta amsa ta umarci Iyamee da tayi Breakfast kala uku zuwa hudu dan Maigidan yana hanya, kafin ta fita.

Aiki kam ranar Ummu tasha ita da Iyamee dan kafin karfe goma suka gama had'awa suka jera a Dining, Ummu sai mamaki take dama Mahaifinsu na nan tsammaninta duk ya rasu, dan bata tab'a ji sun ambaci sunansa ba ko suna waya dashi ba.

Bayan sun gama aikinsu Mami ta sasu suka wuce d'akinsu tare da gargadin karsu yarda su fito duk lokacin da su kaga Maigidan na falo.

Bayan ta shiga d'aki tayi wanka ta dauk'i littafinta tana muraja'a, wajen karfe sha biyu taji hayaniya ya cika falon nan ta tabbatar da mai gidan ya dawo, sun dad'e suna yi kafin suka haura sama, ta daina jin hayaniyar su.


 Ran litinin suka fara jarabawa(Exam) sati biyu su kayi suna yi aka basu hutun sati uku, ranar da aka basu sakamakon jarabawa(Report sheet), tayi murna sannan tayi kuka dan cikin dalibai talatin da biyar tazo na ashirin da hudu, haka ta dawo gida idonnan yayi ja dan kuka, amma in ta tuna yanzu tasa makaranta a gaba sai tayi murmushi ko wannan ma ta godewa Allah daya bata ni'iman nan, dan bata taba tsammanin shiga makaranta ba.


 Ranar wata laraba da yamma, tsaye take kitchen tana wanke-wanke taji Biebie na kwad'a mata kira da sunan da suka rad'a mata Villager, da sauri ta d'auraye hannunta ta fito tana zaune saman kujera, gefe ta durk'usa tana cewa.

"Gani."

Gyale kusan kala biyar ta watsa mata.

 "Ki tabbatar sun fita, akwai sauran Omo nawa da sabulu a gurin Isa mai wanki ki karb'a ki wanke dashi."

 "To."

Ta fad'a tana tashi ta nufi baya can inda ake musu wanki, tana ganin ta tashi itama Biebie ta tashi ta haura sama da sauri sai d'akin Mami.

 Bayan ta isa wajen wankin tasa kayan cikin bucket ta nufi wajen d'akin Isa, baya nan ganin alamar d'akin a bud'e yasa ta fara kwankwasawa tare da sallama.

"Shigo." Taji ance daga ciki.

"Anti Biebiece ta aikoni, kaban guntun Omo din daka mata wanki."

"Shigo ki d'auka gashi nan saman window."

"Ah a ka mik'o min."

"Bana jin dad'i bazan iya tashi ba, ki shigo kawai."

Ita kam har ga Allah tsoron shiga take d'akin namiji ko ba komai ai ba kyau, shuru tayi tana tunani in bata karb'a tayi ba tasan duka ne zai biyo baya a wajen Biebie, da sallama ta d'aga labulen kofar ta shiga.


*****

A razane ta saki labulen windown takai kallon kan a y'ay'anta da suke gefenta.

"Biebie dama da gaske kike."

Murmushin mugunta ta sake.

"Gashinan Mami kin gani da idonki, yarinyar nan Karuwan cikin gidace."

"Na shiga uku, Sadeeq ya kawomin jaraba, yau yau zata bar gidannan."

Tana gama fad'ar haka ta fita a d'akin ta sauk'a k'asa su Biebie da Rahma na bin bayanta suna dariya, dan dama alkawari Biebie tayi sai ta rama dukan da Ya Sadeeq ya mata kwanaki akanta, kuma ga alama tarkonta ya d'anu. Sadaukarwa ga Ummu Aishat(Ummi Safwaan).phartyBb.wordpress.com

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


 SANADIN HA'DUWARMU

  ©Pharty BB


( 12 )


 Wani wawan fisga taji an ma hijab din jikinta ta baya, a tsorace ta juyo kan ta bud'e baki tayi magana taji saukar tagwayen mari masu rai da lafiya, kafin tayi kwakkwaran motsi taji an rufeta da duka, dukanta 'yan matan suke tako ina tana durkushe tasa hannunta tana karewa tare da basu hakuri duk da bata san laifinta ba.

Mami ko fa'da take tana k'ara yi.

"Ku dake y'ar banza, Karuwa ce, a cikin gidana zaki nunamin karuwanci, dama nasan tsintacciyar mage bata mage, yau sai kin fita a gidan nan."

Sai da su Biebie su kaga Ummu taji jiki kafin suka kyaleta, Mami taja hannunta tayi bakin get da ita sam sai tabar mata gida.

"Musa bud'emin kofar nan."

Wanda aka 'kira da Musa yana shirin bud'e get aka danna hon, lekawa yayi ganin mai yin hon din ya sashi wangale get din gaba daya ya shigo da motarsa, bai 'karasa wajen fakin ba yai fakin ya fito da sauri ya nufi wajen su Mami cikin tsananin mamaki.

"Mami lafiya?"

Wani kallo Mami ta watsa masa.

"Ina lafiya ka kawomin karuwa har gida."

Dum yaji maganar ta shigesa.

"Mami karuwa kuma?"

"Kamata mu kayi tana shiga d'akin Isa mai wanki, inba karuwa wace 'ya macece zata shiga 'dakin namiji baligi."

 Cewar Biebie cikin sauri.

Kallonsa ya maida kan Ummu da take durkushe tana kuka, takawa yayi ya isa gurinta, zata matsa yasa kafa ya take kafarta, tsananin zafin da taji na shigarta ya sata sakin wani kuka tama kasa magana.

"Sadeeq fitarmin ita a gida."

Fad'in Mami tana kallonsa.

Yanda yasa mata ido yana kallo sai kuka take, shi yasashi sa hannu ya d'agota ya nufi cikin gida da ita, shan gabansa Mami tayi cikin tsananin mamaki.

"Ina zaka kamun ita?"

Kallon Mami yayi a nutse.

"Mami AMANATA CE, sai na tabbatar da gaskiya kafin in yanke hukunci."

"Sadeeq kanka d'aya kuwa."

Murmushi karfin hali yayi.

"Mamina lafiyana lau, tambaya kawai zan mata."

Yana fad'ar haka yayi cikin gida bai tsaya a babban falon gidan ba ya wuce d'akinsa da ita, rufe kofar yayi har dasa key kafin ya zaunarta gefen gado yaja stool ya zauna saitinta yasa mata ido yana kallon yanda take kuka, tsaki yaja cikin fad'a-fad'a yace.

"Rufemin baki karna bugesa."

Tsit tayi sai hawaye dake zuba tana sa bayan hannunta tana sharewa.

Kallo ya kare mata tsaf shikam yasan ya d'aukowa kansa jaraba, tin shigowarta rayuwarsa yake samun matsala.

"Abinda su Mami suka fad'a gaskiyane kin shiga d'akin Isa?"

Shuru tayi kafin a hankali ta d'aga masa kanta, ido ya zaro cikin tsoro da kaduwa ya tamabayeta.

"Dagaske, me ya kai ki?"

"Anti Biebie ce ta aikeni."

"What?"

A tsorace taja baya jin tsawar da yayi kamar zai daketa.

"Me ta aikeki yi wajensa."

Shuru tayi kafin ta kwashe komai ta fad'a masa tin daga tana wanke-wanke Biebie ta kirata ta ta sata aiki da karb'an sauran Omo nata da tayi a gurin Isa.

Shuru yayi tabbas wannan abin sharrin Biebie ne kuma zai yi maganinta in banda neman ta kullawa yarinya sharri me na karban guntun Omo da sabulu wajen mai wanki duk Sabulu da Omon gidannan, ransa in yayi dubu ya baci.

Kallonta yayi kafin ya tashi yace.

"Biyoni."

Fita yayi a d'akin tana binsa har falon Mami, zaune ya gansu suna kallo hankalinsu kwance, yana zuwa wajen Biebie bai yi wata wata ba ya kwashe Biebie da mari wanda ya sata sakin ihu har Mami ta fito daga bedroom nata, zai sake kai mata wani yaji ance.

"Kul Sadeeq." Daga bakin kofar falo.

Juyawa yayi ya kalli mai maganan, Mahaifinsune, 'karasowa yayi cikin falon yana zama a d'aya daga kujerun falon, Biebie ko tashi tayi zata bar falon cikin kuka ita dasu Rahma taji muryan Abbansu na cewa.

"Dawo nan Biebie, kai ma Sadeeq zauna, Halima(Mami) kema zauna magana za muyi."

Gaba d'aya guri suka samu suka zauna, kallon Sadeeq Abba yayi yana cewa.

"Mai ta maka kake mata irin dukannan? baka san bakyau dukan mace ba."

Kansa a katsa ya kwashe komai ya fad'awa Abba kamar yanda Ummu ta fad'a masa da yanayin da yazo ya samesu.

"Wacece kuma Ummu a gidannan?" Cewar Abba yana dube-dube.

"Wata tsintacciyar ya kawo mana."

Fad'in Mami cikin sauri.

"Ina take?" Abba ya tambaya.

D'ago kai Sadeeq yayi ya kalli kofar falon bata nan bata cikin falon.

"Abba bari in kirata." Cewar Sadeeq na kok'arin tashi.

"Jeka 'kirata."

Tashi yayi ya fita ya sauk'a falon k'asa ya nufi d'akinta, tana zaune tana kuka jin an shigo 'dakinta ya sata d'ago idonta da suka yi ja dan kuka.

"Biyoni, kuma ki tsaya ki k'i shiga ki juya sai na 'bata miki rai."

Fita yayi ta tashi tabi bayansa har falon da sallama ya shiga ya zauna itama ta shigo cikin sallama ta rakub'e ta zauna.

Kallonta Abba yayi.

"Kece Ummu?"

Kanta ta d'aga cikin sauri.

"Me had'inki da Biebie, ma'ana mai ya had'aku da ita har ya kai Sadeeq ya mareta a kanki."

Shuru tayi kafin ta kwashe komai ta fad'a, gaba daya falon shuru aka yi cikin sauri Biebie tace.

"Abba wallahi sharri tamin."

"Rufemin baki." Ya fad'a a tsawace, dan yasan Biebie da raina mutum musamman na 'kasa da ita.

Shuru tayi tana ta hararan Ummu da kanta ke k'asa.

Nan Abba yayi musu fad'a sosai kafin ya sallamesu ya dakatar da Sadeeq, fad'a ya masa sosai akan saurin yanke hukunci, nan kuma ya nemi sanin wacece Ummu?

Sadeeq bai boyewa Abbansa komai ba ya fad'a masa sai dai ya boye masa da aure tsakaninsu, Abba ya tausayawa rayuwar Ummu, sun dan dade suna hira da Sadeeq kafin ya sallamesa ya wuce d'akinsa.


 Can d'akin Mami kam kuka Biebie tasa sam sai tabar gidan akan y'ar aiki za'a mareta dan anga ita ba y'ar gidan bace, ai itama tana da nata iyayen da 'kannai, gidansu zata tafi, dakyar Mami ta iya lallashinta tare da mata alkawari ta 'kara hakuri nan da shekaru biyu ta gama makarantarta ayi bikinsu ko baya so sai anyi, ballema lokacin tana sa ran tayi duk wani ko'karinta na 'ya mace taga ta jawo hankalinsa, sannan ta fita harkan y'ar aikin nan, da wannan ta samu ta hakura.Sadaukarwa ga ummu Aisha(Ummi Safwaan).PhartyBb.wordpress.com

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


 SANADIN HA'DUWARMU

  ©Pharty BB


13


 Kwanaki sun juye sun zama satikai, sati ya juye sun zama watanni, watanni sun shud'e sun zama shekaru biyu.

Tin lokacin baya tsakanin Ummu da ahlin gidan Alhaji. Sulaiman Mai Shadda sai dai tsananin bauta da aiki, bata aiki sai aikin y'an matan Mami ba duka ba zagi amma tana bautuwa, tsakaninta da Sadeeq kam sai gaisuwa in ta had'u dashi zata gaishesa ko ba zai amsa ba, bangaren karatu ko tana Jss 3, Masha Allah tana fahimta amma tafi fahimta bangaren Arabic akan boko.


****

 UMARU MUSA 'YAR ADUWA UNIVERSITY KATSINA STATE.

'Yan matane manya da yara, matan aure da budurwaye, tsaye suke filin makarantar y'an bangarori daban-daban (Department) kowanne ka duba fuskarsa murmushin jin dadine kwance suna murnar a yau sun kammala degree nasu ciki harda y'an matan Mami, Biebie da Hauwaty, inda Hauwaty ta karanci Biochemistry, Biebie ta karanta Accounting.

Sun dad'e tsaye filin makarantar suna shagalinsu kafin aka fara watsewa d'aya bayan d'aya.

Bayan sunyi parking motar suka fito da sauri sai Babban falon gidan y'an uwansu har sun fara zuwa dan taya su murnar kammala makaranta ciki harda y'an Funtua da Daura saura y'an Kaduna da zasu zo gobe.

Da gudu Biebie tayi wajen Mami bayan ta rumgumeta ta taya ta murna kafin ta saketa ta fad'a kan Momynta.

"Mommyna."

"Na'am Daughter na, yau dai angama karatu ko."

'Daga kanta tayi tana cewa.

"Mommy saura Masters ."

"Masters ko aure, Masters sai dai a gidanki."

Tashi tayi tabar wajen ciki da kunya ganin iyayenta maza suna wajen, su ko dariya suka saka, suka ci gaba da hiran duniya.


 Washe gari karfe goma y'an Kaduna suka iso Yayan Mami mai suna Alhaji. Saminu da Matarsa Zainab da K'anwarsa dake gabansa bayan rabuwanta da mijinta shekaru shida, sun samu kyakkyawar karb'a kamar yadda aka saba karbarsu, Mami murna ta rasa inda za tasa y'an uwanta da matansu da y'ayansu.

Bangaren Ummu ko baiwar Allah ranar ko makaranta ba taje ba sai dirkar aiki suke ita da Iyamee daga d'aura wannan sai saukewa, girki sunyi yafi kala shida kowa da irin nasa.


 Karfe uku aka fara tafiya wajen babban hall din da suka kama dan bikin kammala makarantarsu, iyaye mata da y'an mata da samari na Ahlin(Family) suka halarci wajen sai y'an makarantarsu k'awayensu, karfe Hudu na yamma aka fara gudanar da bidirin bikin da suka shiryawa yaransu, ansha shagali an wataya anci ansha, y'an mata sun dirka rawa kamar ba gobe, karfe takwas na dare aka watse inda Mami ta bada kyautar motar da Abba ya bawa Hauwaty da Biebie.

Bayan sun dawo gida nan aka baje a babban falon gidan tin daga kan Babban yayansu har k'aramar cikinsu Adda Habiba suna hira abinsu kowa hankalinsa na ga hirin da suke na son had'a auren zumunci, banda kwaya d'aya cikinsu data sa musu ido tana kallonsu.

Nan manya mazan suka yanke shawaran had'a Biebie da Yaya Sadeeq, Samii Yah Mukhtar, sai Hauwaty da Ya Aminu inda za'a d'aura auren nan da wata uku, a garinsu fadar Mahaifinsu sannan ayi biki daga baya akai kowacce gidanta, iyaye mata sunyi na'am da batun dama Hauwaty suna soyayya dashi haka Samii ma da Yah Mukhtar, matsala dai Yah Sadeeq ne kuma shima suna fata ya amince.

"Munira ba kice komai ba."

Fad'in Mommyn Biebie tana dafa cinyar kanwartan.

Murmushin yake tayi dan ita kad'ai tasan me take ji a ranta.

"Ba komai Addah kawai ku manya kuna magana bai kamata musa baki ba."

"Haba ke kuwa ki daina fad'in haka, ki daina ware kanki cikinmu duk d'aya muke hatta Habiba da take 'karamar cikinmu baki ga tana bada nata shawaranba kuma muna karb'a, dan haka ki daina."

"To Addana na daina."

"Yawwa kanwata ko kefa, me zaki bawa yaranki na gudun mowa."

Murmushi tayi.

"Kinsan ni fannin dana fi karfi dan haka biki saura wata zan tattarasu mu tafi in fara aikina kafin ku iso."

"Shikenan kin hutar damu ba sai mun kawo wata ta kalle mana yara ba, Allah kaimu lokacin."

"Ameen." Cewar Munira tana tashi bayan ta musu sallama ta wuce Upstairs, nan ta tarar da y'an matan suna bud'e kyautattukansu da suka samu, samari da y'an mata kawayen arziki da yan uwa duk sun basu gudun mowa banda mutum daya wanda suka fi kusa dashi wato ya Sadeeq danshi ko halartan bikin da suka yi bai yi ba.

Wucesu tayi ta shiga d'akin bata dad'e da shiga ba Biebie ta biyota, da sallama ta shiga bayan ta amsa ta zauna kusa da ita kanta a k'asa.

"Biebie." Adda Munira ta k'ira sunanta.

"Na'am." Ta fad'a cikin muryan kuuka.

"Lafiya, Biebie? Me ya faru?"

Kuka tasa mata harda shessheka, rumgumota jikinta tayi ta hau lallashinta duk da bata san musabbabin kukantan ba, sai da tasha kukanta ta koshi kafin ta fara magana a hankali.

"Anti Munira tsawon shekaru biyar ina sonsa, tin da na taso na mallaki hankalin kaina zuciyata ta kamu da sonsa, Anti duk tsawon lokacinnan bai tab'a d'aga ido ya dubeni da sunan tausayi bama balle soyayya, Anti ya zanyi? Mezan yi ya soni?"

Tana gama fad'an haka tasa wani kukan.

"Hakuri za kiyi Biebie akan wanda ki keyi balle kuma kin kusa zama mallakinsa, ko ba Sadeeq ba?"

Da sauri ta d'ago kanta fuska duk hawaye.

"Anti me kike nufi?"

"Iyayenku sun tsaida ranar aurenku ke da Sadeeq, Hauwaty da Amin, Samii da Mukhtar, nan da wata uku."

Har zuciyarta taji dadi amma kuma tana tsoron yanda Sadeeq zai kar'bi aurenta, a kunyace ta sunkuyar da kanta.

Murmushi Adda Munira tayi.

"Ba kunya tsakanina dake kuma Biebie Love."

Dariya tayi jin sunan data k'irata dashi ta fita da sauri ta fad'a d'akinsu.

Bayan fitarta baya tayi ta jingina da gado a hankali wasu siraran hawaye suka zubo mata tasa hannu ta shere, inda sabo ta saba duk ranar Allah sai ta zubar dasu.


 Washegari har karfe d'aya na rana kafin y'an Funtua, Daura da Kaduna suka d'au hanya, sai y'an matan Samii da Kausar suka zauna dan 'karasa hutunsu a gidan.

Karfe d'aya da rabi ta fito cikin shirinta na Islamiyya dasu ta fara cin 'karo a falo suna zaune, har k'asa ta durkusa ta gaishesu Samii kad'aine ta amsa sai Kausar data juyo ta bita da kallo kafin ta juyo.

"Wannan Babyn fa." Cewar Kausar.

"Y'ar aikice ta samu guri." Rahma ta fad'a tana jan 'karamin tsaki.

"Y'ar aiki dai." Fad'in Kausar na zaro k'ananun idonta.

"Eh Ya Sadeeq ya kawota mana."

Murmushi Kausar tayi a ranta tana k'ara hasko diri na Ummu.

Hiransu su kaci gaba dayi har karfe biyar, Mami ko na wajen mijinta, Ya Sadeeq ko bai dawo ba tin fitarsa na safe.

Karfe biyar da rabi suka taso yanda take dawowa kullum haka yauma ta dawo da shigarta gidan yanda ta tafi ta barsu haka ta dawo ta samesu sai dai Biebie da Rahma basa wajen, jin muryanta yasa Kausar d'agowa da sauri ta bita da kallo harta iso inda suke yanzu ma durk'usawa tayi ta gaishesu da saurinta Kausar ta amsa kafin Samii ta amsa, banda Hauwaty da hankalinta ke kan waya.

Ta tashi zata wuce d'akin ta dan rage kayan jikinta, taji Hauwaty tace.

"Na baki two minutes kiyi kizo ki had'amin cornflakes yunwa nake ji."

"To." tace tana wucewa da sauri ta canza kayanta ta d'aura hijab nata kamar yanda ta saba ta fito ta wuce kitchen shigarta ta d'auki cup ta zuba cornflakes din taga Rahma ta shigo ta tsaya.

"Had'amin black tea."

"To dan Allah bari in ha'dawa Anti Hauwa Cornflakes tana jirana."

"Dallah had'amin ko in make ki stupid."

Da sauri ta ajiye cup din ta fara hada-hadar had'a mata Allah ya taimaketa akwai ruwan zafi, bayan ta gama ta mik'a mata ta fita kafin ta gama had'awa Hauwaty nata ta kai mata.

Kar'ba tayi tana kai bakinta ta dawo dashi ba zato ta watsa mata na cup din jikinta cikin masifa.

"Shegiya kasheni za kiyi, gishiri fa kika samin."

Baya taja a tsorace ita bata lura ba kwata kwata da gishirine tsabar sauri, hannu ta d'aga zata mareta Kausar ta rike hannun.

"Haba Sister budurwa kamar wannan zaki daka, ai ta wuce duka kuma DAN ADAM ajizine yana kuskure, may be garin sauri yasa bata luraba, sorry kinji Sis."

Daga haka ta saki hannunta.

"Da kin barni Kausar na koyawa yarinyar nan hankali dan taga Ya Sadeeq na goyan mata baya zata kawowa mutane iskancin tsiya."

"Sorry Sister a madadinta."

Cewar Kausar na nufan wajen Ummu dake durkushe d'agota tayi ta nufi d'akin ta da ita kan katifarta ta zaunarta.

"Haba Baby bai kamata kina haka ba, kina lura da kyau dan gudun b'ata musu rai, yanzu shiga ki gyara jikinki muje ki bata hakuri."

"To." Ummu tace tana tashi, Kausar na binta da kallo ganin zata shiga Bathroom da hijab ya sata dakatar da ita.

"Baby haka zaki shiga da kaya, d'auki tawul ki rage kayan jikinki mana."

Ita dai Ummu abin natan ko tsoro ya fara bata, wajen kwaba nata tayi ta ciro zani ta nufi Bathroom dashi, gyara jikinta tayi ta fito daga ita sai zani ta rufa dankwalin kayan data cire a jikinta, a tsorace ta fito dan bata saba fita haka ba wani ya ganta, tinda ta fito tasa mata ido zuciyarta na raya mata abubuwa.

Kaya ta ciro ta koma Bathroom tasa kanta fito, murmushi ta sakar mata.

"Muje kiba Hauwaty hakuri."

Ba zato taji Kausar ta damk'o hannunta tasa cikin nata ta damk'e tsam, wani iri taji ta fara kok'arin kwace hannunta ta k'ara rik'ewa gam, bayan isansu ta durkusa har kasa ta ba Hauwaty hakuri, da kyar ta hakura kafin ta tashi ta wuce kitchen dan taya Iyamee girkin dare.

Da dare bayan isha'i wajen karfe tara, zaune take tana duba littafinta na makaranta, taji ana kiranta, ajiyewa tayi ta fita taje wajen gaba daya y'an matan suna zaune.

"Zo nan Baby ni na 'kiraki."

Fad'in Kausar na mik'a mata hannu, kusa da ita taje ta durkusa, kafad'unta ta dafa tayi 'kasa da kanta dai-dai fuskar Ummu.

"Baby had'omin Black tea."

"To." Ummu tace tana tashi dan abin Kausar ya fara damunta, bayan ta had'a mata ta kawo mata gurin karb'ama saida ta rik'o hannunta kafin ta saketa ta wuce d'akinta.

Daren ranar Kausar da kyar ta iya bacci sai juyi take tare da wani kudiri nata daban akan Ummu.Sadaukarwa ga Ummu Aisha (Ummi Safwaan)


PhartyBb.Wordpress.com

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


 SANADIN HA'DUWARMU

  ©Pharty BB


14


 Kwana biyu Kusar na shisshigewa Ummu da kyautata mata dan wani cikar burinta, Ummu ko tin abin na bata tsoro har tazo ta sake dan zuwa za tayi ta sata gaba a d'akinta tana mata hira tin bata sakewa da ita har tazo ta saba da ita.

Kasancewar gidan kowa harkan gabansa keyi ba mai shiga harkan wani sai ta kama in sun zauna waje d'aya ma to hiransu sama-sama ba wanda ya lura da irin zamantakewan Ummu da Kausar, dan shi ya bawa Kausar daman shigewa Ummu.

Yau ya kama (Weekend) hutun karshen mako, tin asuba da tayi sallah ta kwanta bacci ba ita ta farka ba sai takwas ganin lokacin ya sata fad'awa bangida (Bathroom), brush tayi ta fito ta nufi kitchen da shigarta ta samu Iyamee ta gama breakfast, har k'asa ta durkusa ta gaisheta.

"Ina kwana."

"Lafiya lau Ummu, yau bacci ya hanaki farkawa da wuri."

Murmushi Ummu tayi ta nufi wajen wanke-wanke (Sink).

"Wallahi Ba'aba daga cewa bari in kwanta kafin gari yayi haske wani nannauniyan bacci ya d'aukeni."

Murmushi Iyamee tayi tana nufan kofar kitchen din.

"Ga wanke-wanke kiyi shi kad'aine aikinki, in kin gama ga abincinki a flask."

"To Ba'bana." Ta fad'a tana murmushi dan ganinta take kamar Yayarta, bayan fitar Iyamee ta nutsu ta hau wanke wankenta, ta kusa minti biyar ba taji shigowar mutum ba sai ji tayi an mata wani kyakkyawar rumguma.

A tsorace ta juya su kayi ido biyu da Kausar daga ita sai kayan bacci, cikin wani irin murmushi tace mata.

"Morning Baby."

Juyar da kanta tayi ganin abin natan zai fara wuce gona da iri tace.

"Ina kwana."

"Lafiya lau Babyna, me kika dafa mana."

"Ba'aba Iyamee ce tayi bansan mai ta girka ba."

"Ok bari in gani."

Cewar Kausar na barin wajen, fita tayi tai dinning table ta bubbud'e food flask din kafin ta koma kitchen din.

"Baby in kin gama kiyi wanka zaki rakani shopping."

"To." tace mata kafin tabar mata kitchen din ta k'arasa aikinta ta d'auki abincinta, bayan shigarta d'akinta tayi breakfast nata, ta shiga wanka ta fito ta shirya ta zauna jiranta.

Bata dad'e da zama ba ta bud'e ta shigo d'akin cikin shirin dogon Riga na atamfa ta yafa siririyin mayafi da handbag, Kausar na ganin Ummu ta tashi, kallo ta k'are mata ita kanta tasan tayi babban kamu.

"Baby kin shirya."

Kai ta 'daga mata ba tace komai ba.

"Muje ko."

Cewar Kausar nayin gaba ta biyota a baya suna tafiya har wajen parking, Kausar ta bud'e motar ta shiga Ummu na kok'arin shiga taji an fizgota ta baya.

Ido hudu su kayi da Ya Sadeeq rabon data gansa harta manta.

"Ina zaki? Ke dawa zaki fita?"

"Ni da Anti Kausar zan rakata siyayya."

Zai yi magana yaga Kausar na fitowo, sakinta yayi daga rik'on daya mata.

"Angonmu."

Fad'in Kausar na zagayowa inda suke, wani kallo ya watsa mata.

"Yaushe raini ya shiga tsakaninmu."

Dariya tayi tana cewa.

"Ai ya kusa tinda ka kusa zama Angonmu."

"Me kike nufi?"

"Abinda na fad'a shi nake nufi, baka da labarin an tsayar da ranar aurenka da Biebie, Hauwaty da Ya Amin, Samii da Ya Mukhtar..."

Bata gama ba ya buga mata tsawa.

"Shut up stupid, wa zai auri wannan yarinyar mai shegen ji da kai, ni Allah kiyaye."

Yana gama fad'ar haka ya nufi cikin gida ya barsu nan tsaye ransa a mutukar bace, kafad'a Kausar ta d'aga alaman bai dameta ba ta juyo ta kalli Ummu.

"Baby shiga muje." Ta fad'a tana zagayawa.

Motar taja suka fita a gidan ta nufi babban wani plaza, siyayya tayi sosai tama Ummu ma kafin su dawo gida, tana shirin parking motarta wayarta tayi k'ara ganin mai kiran ya sata sakin murmushi ta d'auka.

"Hello Dear."

Ta fad'a tana murmushi.

Daga daya bangaren muryar mace ta amsa da.

"Sweetna ya kike."

"Lafiya lau Dear, ya garin?"

"Lau sai dai nayi missing naki."

"Sorry Dear na d'anyi tafiyane shi yasa bakya ganina Online saboda kinsan abin sirrine."

"Hakane, Amma ke Kausar haka zaiyi kuwa har yanzu kinki shigowa daga ciki sosai yanda zaki ji dadi."

Ajiyar zuciya Kausar ta sauk'e har ranta tana son shiga cikinsu sosai amma tana tsoron ranar da a gida za'a gane, ga ganin Ummu ya k'arasa ta kara sha'awan abin a ranta.

"Kausar ba kice komai ba."

Kawarta da suke wayan ta katse mata tunani.

"Dear na kusa shiga saboda yanzu haka nayi babban kamu."

"Dan Allah fa, wace ce?"

Dariya Kausar tasa jin 'kawartan ta rud'e.

"Wata Babyce."

"Ina take?"

"Muna tare da ita."

"Fatan ta amince miki."

"Insha Allah."

Sun dad'e suna hira kafin suka katse wayan ta nufi cikin gida dan Ummu ta dad'e da shiga.


Bangaren Sadeeq.....


Sadaukarwa ga Ummu Aisha (Ummi Safwaan).PhartyBb.WordPress.com

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


 SANADIN HA'DUWARMU

  ©Pharty BB


15


 Bangaren Yah Sadeeq tsananin bak'in ciki ya shiga da jin wacce za'a aura masa, dama ya kula da take-takenta da dalilin zamanta gidan, ranar kulle kansa yayi a 'daki har dare bai fitoba, duk da irin bugu da Mami tayi harta gaji ta hakura.

Bai fito ba sai washegari ba wanda ya kula gidan ya shirya ya tafi office ko takan breakfast bai yi ba, har sai da yaje Office ganin yana neman illata kansa yasa ya aika Eatery(Wajen saida abinci) aka siyo masa, kad'an yaci ya fitar sauran.

Ranar haka ya wuni ba wanda yaga walwalar fuskarsa dama ba sake fuska yake ba balle an kunsa masa bak'in ciki, har yamma lis kafin ya dawo gida.

Kwana uku ya d'aukewa kowa wuta a gidan k'annensa ko sun had'u in sun gaishesa baya amsawa, in dutsi zaiyi magana to haka in sun gaishesa zai wucesu, Mami ko ya daina zuwa gaisheta tin ranar data tabbbatar masa bashida matar aure bayan Biebie.

Bangaren Mami ganin halin da d'an natan ya shiga yasa ta sakko ta samesa har falonsa suka yi magana, tsakanin uwa da d'a a ranar suka shirya amma fa da kyar ta shawo kansa ya amince da auren.


  ***

 Biki saura wata d'aya Adda Munira tazo ranar Litinin da Yamma ta kwana, washe gari litinin ta kwshe amare suka wuce Kaduna dan gyarasu banda Rahma da Kausar da suka k'i binsu, Kausar da nata dalilin, Rahma na makaranta tana Jarabawa saura biyu ta gama ta samu hutu.

Tafiyar su Biebie Kaduna shiya bawa Kausar dama na shigewa Ummu sosai inda ta fara bullo mata da wasu abubuwa kamar cire k'aya a gabanta, kwanciya duk yanda taso da uwa uba abinda ke damun Ummu shine yawan tab'ata da take yi abu kad'an ta shafa fuskarta ko bayanta, abin na damun Ummu amma ba wanda zata fa'dawa balle ya bata shawara yadda zata kuace mata, ganin irin abubuwan da Kausar ke mata yasa ta fara zama can ta baya inda wajen shuke shukene da lilo sai kujeru wajen kamar wajen shan iska.


 Sati d'aya da tafiyan su Biebie, ranar asabar suka samu isowar bak'on turai wato Sultan K'ani ga Ya Sadeeq wanda yake karatu a Australia, shekaransa uku da barin 'kasar sai yau da yazo bikin k'anwarsa Hauwaty da y'an uwanta.

Ranar gidan ya kaure da hayaniya da murna musammam Mami, Ya Sadeeq ma yayi farin cikin dawowar k'aninsa sosai, a take Mami tasa Iyamee da Ummu dafa masa abincin da yafi so Semo miyar Allayahu da man shanu suka had'a masa, nan Iyamee taba Ummu takai masa da kyar ta iya daidaita nutsuwarta dan Ya Sadeeq na falon, ita kuma haka kawai tak'i jinin su had'u a guri d'aya, d'aukan tiren dake d'auke da kulan abincin da filet da cokali sannan goran ruwa da juice, tayi ta nufi falon.

A tsakiyar falon suke baje gaba 'dayansu, sallama tayi ciki-ciki suka amsa banda bak'on da bai ji ba hankalinsa nakan hiran da kanwarsa ke masa, a saman center table din dake tsakiyar falon ta ajiye ta durk'usa har kasa murya k'asa-k'asa tace.

"Ina yini? Sannu da zuwa."

A nutse ya kallo inda yaji ana masa sannu da zuwa, murmushi yayi.

"Yawwa sannu y'an mata, Ya kike?"

"Lafiya."

Ta fad'a tana tashi ganin wani irin bahagon kallo da Ya Sadeeq ya watsa mata, kitchen ta fad'a ta jingina da fridge ita ta rasa mai ta tsarewa Ya Sadeeq, zata rantse rabon dasu had'u harta manta, amma da zaran sun had'u sai ya bata wani rikitacciyar kallo dake tsorata ta.

Ta dad'e tsaye cikin kitchen din taji sallama, juyawa tayi zuciyar ya tsinke tare da wani irin kunci ya ziyar cesa ganin mai yin sallama, b'ata fuska tayi kanta amsa.

Matsowa tayi tana rik'o fuskarta.

"Babyna ya dai naga fuskarki a had'e, wani abu ya 'bata ranki?"

Kwace fuskarta Ummu tayi tare da matsawa ganin tana shirin kai hannunta zuwa kan lebenta.

"Babu kaina ke ciwo."

Bata daddara ba ta matso dab da ita yayinda ta d'aura hannunta saman goshinta.

"Sorry Dear, kinsha magani."

"Nasha."

Shine amsar data bata tana shirin barin wajen taji ta cafko hannunta, ba zato taji ta rumgumeta, tsoron da tsananin tashin hankaline ya ziyarci zuciyar Ummu ta fara koka'rin kwace kanta.

"Shish Babyna ki bari muji dumin juna please...."

Ummu bata bari Kausar ta 'karasa abinda zata fad'a ba ta fizge jikinta ko ina rawa yake, hawaye ko ya cika idonta.

"Me kike nufi dani?"

Fad'in Ummu naja baya-baya tana neman hanyar fita.

Murmushin y'an duniya Kausar ta sake ta k'ara matsowa kusa da Ummu.

"Kina son sanin me nake nuf,i ki jirani da daddare karki kulle d'akinki dan ko kin kulle ina da (spare key)"

Tana fad'ar haka ta shafi gefen fuskarta ta fita a kitchen din, kuka Ummu ta fashe dashi ta durkusa nan k'asar tiles din kitchen din, sai da tayi mai isarta kafin ta tashi ta wanke fuskarta ta fita.

D'akinta ta shiga ta kwanta tana ta juyi, tsananin tsoro da tashin ya shigeta, iya tunaninta yanda ta fahimta Kausar mai neman mace y'ar uwar tane kamar yanda taji ana fad'a musu a makaranta akwaisu yanzu anan gida Africa sun fara yad'uwa, hawayen kan fuskarta ta goge tino irin tsananin azaban da Allah ya tanadarwa masu irin halin.

Wuni tayi a d'aki har yamma, kukan da tasha shiya haifar mata zazzafan zazzabi ko fita taya Iyamee aiki ta kasa yi.

Can ko Iyamee ganin Ummu bata fito ya bata ba lafiya ba, hakan yasa tana gama aikinta ta nufi d'akinta, da sallama ta shiga a zabure Ummu ta farka daga kwancen da take tsammaninta Kausar ce, ganin Iyamee yasata komawa ta kwanta, k'arasowa ciki tayi ta zauna bakin katifarta tana k'arewa fuskarta kallo ganin idonta ya kumbura.

"Lafiyarki kuwa Ummu?"

Murmushin yak'e tayi.

"Lafiyata lau Ba'aba kaina ke d'an ciwo kuma nasha magani."

"Waya ba ki?"

"Amm..umm..tsinta nayi ranar ina shara saina boye shine yau na d'auka nasha."

Daga yanayin maganarta ma ta gane k'arya take.

"Ina kwalin."

"Na'am me kikace?"

"Kinji mai nace ina kwalin."

Shuru tayi dan bata tsaba k'arya ba ta rasa mai zata ce mata.

Tashi Iyamee tayi ta fita can ta dawo d'auke da abinci da paracetamol guda biyu, a gaba ta sata taci abin kafin tasha maganin ta kwanta, Iyamee ta fito taja mata kofar, wani baccine ya d'auketa mai da'di..


Da dare misalin karfe sha d'aya da mintuna....!!!


Kuyi hakuri dani kwana biyu kunji shuru.
Sadaukarwa ga Ummu A'isha (Ummi Safwaan.)


PhartyBb.WordPress.com


NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


 SANADIN HADUWARMU

  ©pharty BB


16


 Karfe sha d'aya na dare da mintuna biyar, Ahlin gidan duk sun kwanta banda mutum d'aya data bud'e kofar d'akinsu ta fito, da hasken fuskar wayarta tayi amfanin take haska hanya, haka har ta sau'ko falon k'asa ta wuce d'akinta, a hankali ta murd'a kofar jin abud'e yasa ta saki ajiyar zuciya kafin ta shige, da shigarta ta rufe kofar d'akin, wutan d'akin a kashe ta kunna can ta hangota cikin bargo tana bacci, lallabawa tayi ta zauna tare da yaye bargon, fuskarta ta tsurawa ido wani abu na fizgarta.

A hankali takai hannu ta fara shafa fuskar, cikin bacci kamar a mafarki taji ana shafa mata fuska a ahankali bud'e idonta suka yi ido biyu da Kausar, take ta tuno mai ta shirya mata, wani irin zabura tayi taja baya cikin tsananin tsoro jikin ko ina rawa yake, tama kasa magana sai hannu tasa tana toshe bakinta kar tayi ihu.

Matsawa Kausar ta kara yi cikin wani irin desire take magana.

"Please ki tsaya muyi abu cikin sirri ba wanda zai san mai ya faru."

Dakewa Ummu tayi cikin karfin hali tace.

"A'uzubillahi, haramci mafi muni fa kike kok'arin aika tawa."

Girgiza kai Kausar tayi dan gaba daya yanayinta ya canza haka ta nufo Ummu gadan-gadan, ganin tayo kanta yasa ta daka wani uban tsalle tare da sakin wani gigitacciyar ihun da dai-dai ya shigo falon yaji ihun har cikin kansa, kallonsa ya kai inda yaji ihun yaga hasken kwan lantarkin d'akin a kunne, hakan yasa ya nufi wajen cikin sand'a.

Cikin d'akin ko Kausar tayi nasarar kamo Ummu ta danneta tana ko'karin fizge mata 'yar rigan jikinta, Ummu ko banda kuka da addu'an da duk yazo bakinta tana tureta ba abinda take yi, dan Kausar ta fita karfi nesa ba kusa ba kuma ta gwada mata shi.

Banko kofar d'akin yayi ya shigo, ganin abinda ke shirin faruwa yayi wani kukan kura ya fizgo Kausar dukanta ya shiga yi tana kok'arin fizgewa, burinta ta jita cikin jikin mace, ganin dukan ba abinda yake mata yasa ya had'a kanta da gini, ihu ta sakar tare da sulalewa a gurin ta sume.

Sakinta yayi ya nufi gurin Ummu data takure guri 'daya banda kukan tashin hankali ba abinda take yi, ganin ya nufota tsammaninta dukanta zai yi yasa ta tashi tana neman hanyar fita, fizgota yayi tana kok'arin kwacewa ya bata mari, tsit ta tsaya ya jata suka fita d'akin yasa key ya kulle, yana janta tana binshi tana share hawayen fuskarta har cikin d'akinsa, suna shiga yayi wulli da ita ya rufe kofar da mukulli.

Durkushewa tayi nan tsakiyar d'akin, shiko bangida(bathroom) ya wuce, tin tana jiran tsammanin fitowarsa har bata san lokacin data sulale ta kwanta bacci gurin ba.

Ruwan sanyin daya watsa mata a fuska shiya farkan da ita, saman dogon kujera ta ganta kwance rabinta lullube da bargo.

"Hala har yanzu akwai sauran jahilcin a kanki baki san lokacin sallah yayi ba."

Kallonsa tayi kafin da sauri ta sunkuyar da kanta ganin irin kallon da yake mata, tashi tayi ta nufi hanyar fita.

"Ina zaki?"

Ya tambayeta yana bud'e Laptop nasa.

"D'aki..na." ta basa amsa muryarta na rawa.

"Ok you can go (shikenan zaki iya zuwa.)"

Tuno abinda jiya ya faru da dare shiya hanata bud'e kofar d'akinsa ta tsaya, Sadeeq na lura da ita ya ki tankawa, kusan minti ashirin ya d'ago yaga tana mammatse cinya ga hawaye tana sharewa.

"Ki kamin fitsari anan sai jikinki ya gaya miki, zaki wuci kizo kiyi sallah ko saina baki mari."

Hannunta take yarfewa ji take kamar ta saki fitsari a wajen, cikin tsoron mai zai ce tace.

"Tana d'akin."

Shuru bai kula ta ba yasa ta bud'e kofar zata fita ya daka mata tsawa.

"Ke! Dawo."

Dawowa tayi cikin sauri, ya nuna mata bathroom nasa.

"Shiga nan."

Cikin sauri ta shige, kafin ya tashi ya fita kasa ya sauka ya bud'e d'akinta ya shiga, ganinsa yasa Kausar tashi da sauri dan tin karfe hudu na asuba ta farfad'o, kuka take tana ja baya.

"Dan Allah Ya Sadeeq ka rufamin asiri, wallahi sharrin shaid'anne da sharrin k'awa, dan Allah."

'K'awa." ya maimaita kalmar a ransa.

"Wace k'awarki?"

Ya watso mata tambaya.

"Watace a Facebook muka had'u."

Kallonta yayi duka-duka in zai iya tantance shekarun Kausar ba zata wuce shekaru ashirin da biyar ba amma ta jefa kanta cikin mummunar a kida SANADIN waya da banzan kawayen da baka san kansu da asalinsu ba.

"Ya Sadeeq dan Allah kar kace zata fad'awa Mommy wallahi zata kasheni kota tsinemin ka rufamin asiri, kamin duk hukuncin daya dace."

Wani kallo ya watsa mata daya hargitsa mata ciki.

"In na boyewa mahaifiyarki kina ganin zan boyewa Allah, kina sane da in mahaifiyarki ta gane abinda kike aikatawa, kalar hukunci da zata miki kika biyewa son zuciya da k'awar banza da baki san asalinta ba ta jefa rayuwarki cikin had'ari, rufin asirinki d'aya a gurina kiyi gaggawar tuba ki nemi yafiyar Allah, sannan yau ba gobe ba ki had'a kayanki kibar gidannan karki lalatamin AMANATA, a karshe ina mai umartanki da ki cire mijin aure a had'a aurenki da y'an uwanki, in ko ba haka ba za kiji maganar nan bakin wanda ba kiyi tsammani ba."

Yana gama fad'ar haka ya nufi wajen kayan Ummu ya d'auki dogon riga da hijab sanna ya d'auki wayan Kausar da ya gani a k'asa a jefe ya fita a d'akin.

Yana shiga d'akinsa ya ganta zaune k'asa kusa da kujeran data kwanta, ajiye kayan da ya d'auko mata yayi ta d'auka ta shiga bathroom tasa ta fito, har k'asa ta durkusa ta gaisheshi.

"Ina kwana."

"Lafiya."

Yace yaci gaba da binciken wayar Kausar, ya girgiza da kallon hotounan Ummu kusan ashirin a ciki duk bata san ta d'auketa ba, gaba d'aya yabi ya goge Application na wayan, karshema kashe wayar yayi gaba d'aya ya jefa drawer nasa kan ya tashi ya shiga bathroom nasa, ganin ya tashi yasa ta lallaba ta gyara d'akin sama-sama duk da ba wani kurane da shi ba, tana cikin had'a takardun da ta gani saman center table taji ana kwankwasa kofar falon.

A hankali ta lallaba ta bud'e su kayi ido hudu da Sultaan ya had'e cikin k'ananan kaya, kamarsu d'aya da Sadeeq sai dai yafi Sadeeq haske da kuma alamar yana da fara'a.

"Ina kwana."

Ta fad'a tana basa hanya, murmushi yayi yana cewa.

"Lafiya, ina Yayan?"

"Yana ciki."

Tace tana barin wajen.

"Bari in jirasa."

Ya fad'a yana zama saman d'aya daga cikin kujerun falon, taci gaba da aikinta, lokaci-lokaci yakan d'ago ya kalleta yana mamakin ko ita din wacece haka?.

Sadeeq ko bayan ya fito ya shirya cikin k'ananan kaya ya fesa turare sai kamshi yake ya fito falon, ganin k'aninsa yasa haka kawai yaji zuciyarsa bugawa dalilin kallon da yaga yana bin Ummu dashi.

Zaman Sadeeq gefen Sultaan shiya ankarar dashi.

"Babban Yaya sannu da fitowa."

Cewar Sultaan na shafa kansa.

"Yawwa sannu, ya gajiyan hanya?"

"Allahamdulillahi."

Shuru dukkansu suka yi, Sadeeq ji yayi zuciyarsa ta kasa nutsuwa da irin kallon da Sultaan ke bin Ummu dashi.

"Ke! Barnan, wawiya kawai."

Ajiye mofan dake hannunta tayi tabar d'akin cikin sanyin jiki, bayan fitarta Sultaan ya kalli Yayansan.

"Yaya wacece?"

"Yar aiki ce, wani abu tama."

"No kawai haka naji taban tausayi, me iyayenta suka nema suka rasa da zasu bar y'arsu yin aikatau ba karatu wanda a zamanin yanzu kowa burinsa d'ansa yayi karatu ya tsaya da kafafunsa."

Tashi Sadeeq yayi daga zaunen da yake.

"Fatana ka tsaya iya kacin tausayi karka shiga hurumin daba naka ba."

Yana fad'ar haka ya bar masa falon, bayansa Sultaan yabi suka nufi d'akin mahaifiyarsu tare, sai da suka mata sallama ta amsa ta basu izinin shiga kan su shiga, tana zaune gefenta Kausar ne ga jakan kaya gefenta, ganin Sadeeq yasa Kausar kasa kwakkawaran motsi.

Gaishe da Mami su kayi nan ta take sanar musu da Kausar ta nace sai ta tafi, ko kallon inda take Sadeeq bai yi ba ya tashi yabar musu d'akin.

Dole yasa Mami ta bar Kausar ta tafi dan ta matsa mata, ta bata kudi dayawa Sultaan ma ya k'ara mata, drivern su Mami ya kaita garinsu.Sadaukarwa ga Ummu Aishat(Ummi Safwaan.)


PhartyBb.Wordpress.com

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

  

  SANADIN HADUWARMU

  ©Pharty BB


17


 Tin ranar da Ummu ta tabbatar Kausar tabar gidan hankalinta ya kwanta, a cikin satin suka fara jarabawar karshen aji uku na sakandire(Jss 3), sati biyu suka yi aka basu hutun wata d'aya inda in sun dawo zasu shiga ajina hudu(SSS 1).


   WATA SABUWA.

 Tin dawowar Sultaan haka kawai Sadeeq ya tsani yaga Ummu na aiki a guri Sultaan na zaune gurin ransa na baci, nan fa hantarar da yake ma Ummu ya k'aru, tin Sultaan baya ganewa har yazo ya fahimta, ranar da ya masa magana kuwa baram-baram su kayi da Sadeeq yace ya fita harkanta ba ruwansa da ita, shiko Sultaan ya dage sai yasan Wace ce ita.

Cikin haka aka fara shirye shiryen tafiya biki kasancewar saura biyu daya d'aurin aure.

Wata ranar laraba da yamma Sadeeq ya dawo gidan da leda hannunsa, d'akinsa ya shiga saida ya gama abubuwan da zaiyi ya fito ya nufi kitchen, Iyamee kad'ai ya tarar kitchen, din bayan sun gaisa yake tambayarta Ummu, nan ta sanar masa tana wajen Dam tana wanke tsumman goge-goge, fita yayi ya nufi wajen, sunkuye ya sameta tana d'auraya tsumman.

Jin takun mutum na nufota ya sata d'ago ido, ido hudu su kayi da Sadeeq zuciyarta ya hau bugawa, ta rasa dalili duk lokacin da zasu had'a ido sai taji fad'uwar gaba, ci gaba tayi da aikinta har ya iso daf da ita.

"Biyo ni."

Yace da ita, d'auraye hannunta tayi, tabi bayansa har wajen motarsa ya shiga, ta bud'e d'ayan gefen ta shiga yaja suka fita a gidan.

Wani wajen Toiler ya kai ta, a haka telan ya ganta ba tare da ya gwada ta ba ya biyasa kud'insa cash kafin suka kamo hanyar gida, tinda suka soma tafiyan bai ko kalli inda take ba sai da yayi parking filin gidan ya k'ira sunanta rana ta farko da taji ya kirata da d'ayan sunanta, wanda shi kansa ya rasa mai yasa ya kirata da sunan.

"Ayeeshat."

Har cikin ranta taji sunan, a hankali tace.

"Na'am."

"Gargad'inki zanyi tsakaninki da Sultaan ya wuce gaisuwa ban yarda wani abu ya biyo baya ba, in kunne yaji jiki ya tsira."

"To." Tace tana fita a motar kafin yaja ya fita a gidan.


Kwana uku da kai d'inkin ya karb'o har d'aki ya kai mata yace ta shirya kayanta za suyi tafiya daga haka ya fita a d'akin, bayan fitarsa ta bud'e kayan leshi kala d'aya ne da atamfa kala biyu duk dinki sun fita mai kyau kuma duka riga da skirt, da d'ankunne da sark'a sai hijjabai shi kansa bai san mai yasa yasa mata hijab ba maimakon gyale.

Tayi murna sannan tayi farinciki sai fargabar kuma ina za suje, haka ta shirya kayanta cikin dan jaka da duk abinda take bukata.

Washegari gaba d'aya gidan suka kama hanyar Batagarawa,Abba, Mami, Sultaan, Rahma duk motarsu daya dan Sadeeq cewa yayi zai biyosu daga baya, suna fita ya tura Iyamee 'kiran Ummu ta fito cikin shiri tasa atamfa 'daya cikin atamfar daya dinka mata, tayi kyau abinta, bayan shigarta mota yaja suka bar gidan.

Tafiya suke har cikin Batagarawa a gaban wani gida d'an karami flat yayi parking ya fito yace mata.

"Fito."

Fitowa tayi da ta d'auki jakarta tana binsa ya bu'de ya shiga har cikin gidan mai d'auke da d'akuna biyu sai wani 'karami alamar bangidane(Bathroom), d'aya d'akin ya bud'e ya shiga ta bisa ciki, ba laifi d'an babbane yana d'auke da katifa d'aya babba da kafet sai filo, ajiye jakar kayansa yayi, itama ta ajiye nata.

Fita yayi yayo alwala yazo ya tada sallah, itama alwala ta fita tayi ta dawo ta tada sallah, bayan sun idar jugum suna zaune ba magana, wayar sane ya katse musu shurun da suke ya d'auka, jin yace yana zuwa ya sata kallonsa, idonsa a kanta tin fara wayar yasa k'ura mata ido yana kallonta.

D'auke idonta tayi ta mayar k'asa, bayan ya gama ya k'ira sunanta.

"Ayeeshat."

Yar taji a jikinta jin sunan da ya k'irata dashi, kanta sunkuye tace.

"Na'am."

"Nasan baki san dalilin zuwanmu garinnan ba ko, to nan garinmu ne asalina Kakana mahaifin Mami shine sarkin garin, then jibi Jumma'a d'aurin aurena da Biebie dalilin zuwarmu kenan, bana son barinki a gida dan ban san mai zai faru ba ke din AMANATA CE."

Wani irin yanayi mai wuyar fasssarawa ta tsinci kanta jin wacce zai aura wai Biebie.

"Kinji mai nace?"

Ya tambayeta yana lura da yanayinta.

"Naji, Allah sanya alheri ya bada zaman lafiya."

  Bai tanka ba ya mik'e.

"Zanje in dawo ana nemana, karki fita ko ina, zan taho miki da duk abinda kike bukata."

Kanta ta d'aga masa bata iya magana ba yasa kai ya fice, haka kawai kuka ta fashe dashi tana jin bak'in cikin rashin sanin dangin mahaifiyarta, gashi karfi da yaji an maidata 'yar yawo bata da gata balle jik'o, kukanta tasha anan bacci ya d'auketa.


 Can Fada ko wasan Al'adar Fulani suka had'a kowa yasha kayan fulani maza da mata 'yan mata, hatta yara 'kanana, yan mata sunyi d'igo-d'igo a fuskarsu gashin kansu kuwa sun kitsa gefe da gefe yana reto, mazan ko hula da sanda suka rik'e, wasa sosai aka yi aka sha fura da nono kindirmo, Amare da angwaye sun fito sun taka rawar fulani banda mutum d'aya da ko kayan jikinsa bai canza ba, abu d'aya daya ji yad'an faranta ransa.

Bayan komawar Kausar gida tasa Mommynta gaba akan a had'a bikinta dana su Biebie, Momynta tayi fad'a tayi fad'an ta gaji, har maganar takai gaban mahaifinta yace ta fad'i dalili nata ta rasa, ganin bata da mafita yasa tace in har basu had'a ba ita da aure har abada, jin abinda tace yasa mahaifinta yin tunani tinda har ita ta fito ta fada tana so a shekarunta to dole su mata gudun fad'awarta halaka, dan su suka hanata auren sai ta gama karatunta ta samu aiki, hakan yasa mahaifinta zuwa Fada ya fad'a Sarki, sunyi na'am da zancen, ta turo wani Lecture da yake sonta aka yi magana aka sanya ranar bikin d'aya dana su Hauwaty.


 Ganin magriba ta gabota yasa ya koma cikin gida bayan ya gaisa da iyayensa maza ya musu sallama zai tafi k'aramin gidansa dake Gangare, basu so haka ba da kyar Abbansa ya barsa ya tafi dan fad'a yayi tayi.

Ta kasuwa ya biya ya siya mata abin da take bukata dai-dai na kwanakin da za suyi, yaga mai soya doya da kwai ya siya musu tare da Maltina mai sanyi kafin ya dawo.

Bayan yayi parking ya jida duk abinda yake bukata ya shigar ya kulle motar ya shiga cikin gidan, d'akin ya nufa ya ganta kwance tana bacci, shigo da kwalin indomie da katan na ruwa da ya siyo yayi ya ajiye sauran su risho da kayan miyan a waje saman barenda, yai alwala ya shiga d'akin.

Kafadunta ya bubbuga.

"Ke! Ayeeshat."

"Uhmm." Tace tana 'kara gyara kwanciya.

 "Tashi magriba tayi."

A zabure ta tashi tana kalle-kalle, sai kuma da sauri ta mik'e ta fita alwala tayi ta shiga d'akin, sallar tayi ta zauna tana lazimi shi ko Sadeeq hankalinsa naga sakwannin taya murna da abokansa suka turo masa yana bud'ewa, 'Ko wa ya fada musu?' shine tambayar da yama zuciyarsa.

Bayan ya gama ya ajiye ya kallota.

"Jawo min ledan can."

Ledan daya nuna mata ta d'auka ta kai masa ya karb'a.

"Zauna." Yace da ita yana bud'e ledan, zama tayi ya bud'e ya tura gabanta tare da d'aukan Maltina d'aya ya bud'e yace mata.

 "Bismillah ci."

A hankali tasa hannu ta fara ci kad'an taci dan duk a takure take tace.

"Na koshi.

Maltina d'ayan ya d'auka ya bud'e ya mik'a mata, karb'a tayi shima rabi tasha zata ajiye sauran yace.

"Shanye."

"Na koshi..."

"So kike na zubar sauran ko me? Shanye tas."

Dole yasa ta kafa a bakinta ta shanye, tana ajiye gwangwanin wani juyi da cikinta yayi tare da tashin zuciya shiya sata tashi a gigice ta fita ta fara kwara amai, bayanta ya bi ganin tana amai yasa yad'an ja baya, bayan ta gama ya mik'a mata ruwa ta kuskure bakinta, ta lallaba ta gyara wajen, bangida(Bathroom) tayi tai wanka ta fito ta shiga d'akin, kayan da zata sa ta dauk'a ta fita ta koma ban gidan(Bathroom) tasa ta fita ta koma d'akin sallar isha'i tayi, tana shirin kwanciya a k'asa ga yaga jikinta kamar zazzabi yanda take takurewa yasa shi tashi saman katifar yace mata.

"Kwanta a nan."

Girgiza kanta tayi alamar ah a, ta kwanta k'asa, barinta yayi ta kwanta yaci gaba da abinda yake yi har wajen karfe goma, bayan ya gama komai nasa yayi wanka ya shirya cikin kayan baccinsa, inda take yayi ya d'agota a hankali ya cire mata hijab na jikinta ya d'agata cak har saman katifar ya kwantarta ya lullube da bedsheet, ido ya sa mata yana kallo a hankali SANADIN HA'DUWARSU ya fara dawo masa har zuwa yau, tabbas bai kyautawa rayuwarta ba kamar yanda ya d'auki alkawarin kyautata masa ba, yana tausayinta musamman in ya tuna da k'arancin shekarunta tana ganin matsaloli daban-daban, ba abinda yafi d'aga hankalinsa kamar na Kausar.

Kawar da tunanin yayi ta hanya fara addu'a yayi ya shafa ya shafa mata tare da sumbatar goshinta wanda shikansa bai san dalilin yin haka ba, har tsakar kansa yaji wani sako na shigarsa wanda bai taba jin irinsa.

Juyi yayi ya kwanta tare da jan bedsheet ya rufu.


 Washe gari!!!


Sadaukarwa ga Ummu A'ishat (Ummu Safwaan)


PhartyBb.WordPress.com

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


SANADIN HA'DUWARMU

©Pharty BB


18


Da asuba ya rigata farkawa, yayi mamakin ganinta daf da jikinsa kamar zata shige, tashi yayi ya fita ya d'auro alwala ya tasheta kan ya wuce masallaci dake layin unguwar, a tsorace ta farka ganinta saman katifa ya sata dirowa daga saman da sauri ta lalubi hijab tana ta saka ta fita, alwala ta d'auro tazo ta tada sallah bayan ta idar tayi lazimi nata da addu'o'int ta kwanta nan saman abin sallar, tsorone ya kamata duk da tasan Sadeeq ba zai cutarta ba amma tana tsoro kasantuwarsu guri d'aya saboda an fad'a musu a makaranta in mace da namiji sun kasance waje d'aya to cikotan na ukun shaitanne.

Haka ya dawo ya sameta, zama yayi yana lazimi har gari yai haske sosai kafin ya d'an rinsa, karfe bakwai da mintuna ta farka, lallab'awa tayi ta fita, rishion da ta gani ta bud'e taga an had'a an zuba kalanzir da komai, kunnawa tayi ta d'auka kayan miya da duk abinda take bukata ta musu jolof na Macaroni da kifin gwangwani dan ba laifi zama da Iyamee ta koyi girki da dama, bayan ta gama ta bud'e foodflask din da taga gani a kwali alama duk a jiyan ya soyosu dan komai kamar sabone, bayan ta zuba takai d'akin ta wanke plate da spoon ta kai tana shirin shiga dai-dai ya farka daga dan kwanciyar da yake, bayan ta ajiye ya fita wanka yayi ya shigo ta bar masa d'akin ya shirya cikin wani farin yadi me shegen kyau, wani haske ya k'ara da kwarjini.

Bayan ya gama shirin ya k'irata, ita kanta sai da taga ya k'ara mata kwarjini da kyau da kamala, umartanta yayi ta zuba masa abinda ta girki, yaci kad'an kafin ya mata sallama tare da gargad'in karta fita ko ina.

Bayan fitarsa ta samu ta gyara d'akin tayi wanka tayi breakfast ta wanke kwanakun da su 'baci da d'an abubuwan data 'bata, kafin ta kwanta tana ta tune tune nata kalar Rayuwar kenan.


Can Fadar Mai martaba, dumbin mutanen da suka taro tare da shaidu su suka shaida d'aurin auren Sadeeq da Biebie, Mukhtar da Sami, Amin da Hauwaty, Na'im da Kausar, anyi taro lafiya an d'aura aure lafiya anci ansha taro ya watse lafiya.

Bangaren iyaye mata sun ma yaransun rawar gani dan ganin wannan shine karo na farko da suka had'a yaransu aure kuma ba tare da samun matsala ba kamar yadda sauran auren zumunci yake kawo matsala, basu san nan gaba ba wanda basa fatan hakan.

Sadeeq bai samu kansa ba daga rik'esa da abokanansa da suka yi masa murna ba har wajen karfe hudu, yana samu yana yin sallah ya shiga motarsa yaja yabar Fadar.

Bayan yayi parking ya shiga gidan shuru kamar ba kowa cikin d'akin ya tusa kansa, tayi d'ai-d'ai tana bacci hankalinta kwance, dan hijab din da tasan ma wuyan ya fita, matsawa yayi ya zare hijab din yabi gashin kanta da ya kwanto, garin zare hijab din d'ankwalinta ya zame, yayi mamakin ganin yawan gashinta irin na fulani ga cika ya tsayi, komai ya tuna ya kawar da kansa daga abinda zuciyarsa da gangan jikinsa ke muaradin kallo, a rayuwarsa yana son mace mai gashi, kwantarta yayi ya mik'e.

"Ayeeshat." 

Ya k'ira sunanta da d'an karfi bayan ya zauna gefen katifar, a dan tsorace ta bud'e idonta, da hanzari ta jawo hijab nata tasa.

"Kinyi Sallah?"

Fad'in Sadeeq na zare safar kafarsa, girgiza kanta tayi sannan ta tashi ta fita alwala ta d'auro ta tada sallah bayan ta idar tayi addu'o'inta ya nemi ta kawo masa abinci data dafa, dan ya kasa cin abincin gidan auren, ita ko tsammaninta duk zai ci acan yasa ta girka abinda take so taliya da mai da yaji, wanda dakyar ta samu yajin cikin ledan doyar da daren jiya ya siyo.

Zubo masa tayi ta kawo, yamutse fuska yayi cikin had'a rai yace.

"Me wannan?"

"Abincin."

Ta fad'a tana jan baya ganin yanda yake magana fad'a fad'a.

"Yanzu wannan kika ci?"

"Eh da dadi fa."

"Dallah d'aukemin kar nayi ball dashi aka ce miki kowa irin kine baya wayewa, Mtsw."

Fita yayi a d'akin yabar gidan gaba d'aya ma, itako Ummu abincin ta d'auke ta fitar ta dawo ta zaune abinta, ganin har bayan magriba bai dawo ba nan tsoro ya fara kamata ta takure guri d'aya a haka ya dawo ya sameta bayan taci kukanta ta koshi har ciwon kai yasa mata.

Bai ko kalli inda take ba ya ajiye mata ledar hannunsa a gabanta, kayan jikinsa ya rage ya fita wanka yayi dama already yayi sallar isha'i, bayan yayi shirin kwanciya ya kallo inda take ganin yanda take k'ankame jikinta yasa yace.

"Ke lafiyarki?"

Shuru ta masa tak'i amsawa dan muryanta baya fita dan kuka, tashi yai ya nufi gurinta hawaye ya gani na bin kumatunta daga kwancen da take.

"Wani abu aka miki, ko dad'in kukan kike ji."

Girgiza kanta tayi a hankali tace.

"Kaina ke ciwo."

"Dan kanki na ciwo shine zaki hau ma mutane kuka."

"Sosaine fa."

Hannu ya d'aura saman goshinta yaji zafi rau, sai kuma yaji jikinsa yayi sanyi, d'agota yayi tana kakkaucewa ya d'aura saman katifa, ledan da ya shigo dashi ya bud'e kazane.

"Ci kad'an sai in siyo miki magani."

Girgiza kanta tayi alamar ah a.

"Kad'an fa."

"Ko naci amai zanyi."

Tinowa da jiya tilasta mata da yayi ta amayar da abinda taci yasa ya hakura ya barta badan ya so ba, kwantarta yayi lullubeta da bargo.

"Kwanta bari in nemo miki magani."

Bata ce komai ba ta lumshe idonta shikuma ya fita, chemist dake bakin hanya ya siyo mata magani ya dawo tararwa yayi tayi bacci, ajiyewa yayi ya kwanta gefenta, bini-bina duk motsin da tayi yana dubata.

Tsakar dare zazzafan zazzabi ya zuba mata ruf, ya bata maganinma yaki sauk'a, rasa ya zai yi da ita yayi da kyar ya samu ya tina wani abu, ruwa ya d'ibo da k'aramin dankwalinta ya duba cikin kayanta, dashi ya goge mata jikinta, fuskarta, cikinta, da cinyarta zuwa kafanta.

Yin haka bai dade ba yaji jikin zafin ya ragu, rufeta yayi ya kwanta gefenta motsi kad'an ya kai hannu kan goshinta, da kyar bacci ya d'aukesa ranar.


Washegari da safe karfe tara ya samu bayan ya farka yayi wanka, Allahamdulillahi ta danji sauki, Fadar Mai martaba yayi bai dade ya musu sallama duk da sauran y'an uwansa amgwayen sun so ya shiga ciki ya gaishe dasu Mami yace yana sauri, zaune ya sameta saman sallaya a bakin barenda, tashi tayi tana shirin basa wajen yace.

"Ki shirya mu koma gida."

"Yanzu." Ta tamabayesa.

"Eh." Yace da ita yana d'an harhad'a kayansa, itama shirya nata kayan tayi, bayan sun kimtsa komai suka d'auki abinda suke bukata, ya kulle gidan suka d'auki hanyar Katsina, sai da suka d'au hanya ya k'ira Mami ya fad'a mata k'iran gaggawa ya samesa daga office dan fad'anta.


Da isarsu direct asibiti ya fara biyawa, asibitin abokinsa bayan ya ganta ya rubuta mata magani suka kama hanyar gida, bayan yayi parking ya mik'a mata ledan maganin tare da jaddada mata ta tabbar tana sha, godiya ta masa ta d'auki jakar kayanta da ledan maganin ta nufi cikin gida, shima ya wuce nasa d'akin.


Yan bika kam sai da suka k'ara kwana uku kafin suka tattaro aka mik'a ko wacce gidan mijinta, kafin suka watsa, ba laifi Sadeeq ya gyara gidansa haka aka kai masa amaryarsa, da daren ranar da aka kaita ya tarkata ya d'auki komai nasa daga gidan Mami ya koma gidansa.


RAYUWAR BIEBIE GIDAN SADEEQ..


Sadaukarwa ga Ummu A'shat(Ummi Safwaan).PhartyBb.WordPress.com

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


 SANADIN HADUWARMU

  ©PhartyBB


Wattpad @PhartyBB


19


 Rayuwar Biebie gidan Sadeeq, rayuwace kowa yana harkan gabansa, shi kwata-kwata bata gabansa bai jin zai iya zama guri d'aya da ita balle har yaji zai iya neman abu gurinta, ganinsa bata kai wannan matsayin ba.

Bangaren Biebie kam tin ba'a je ko ina ba ta fara dana sani dan zaman kad'aici ya fara isanta, a haka suka cinye wata d'aya, had'uwarsu ya zamana in tana falo ya shigo zata gaishesa ya amsa ya wuce d'akinsa ba zata k'ara kallonsa ba har sai yaji 'kiran sallah in zai je masallaci, abincinta ma baya ci a Restaurant yake siya, tin abin baya damunta har yazo ya fara damunta amma tayi d'amarar karkato da hankalin mijinta kanta.


 Kusan kwana uku Sadeeq na fama da abokansa akan sai sun zo ganin Amarya daga nan suci abincin amarya, duk kok'arinsa na ganin ya kauce musu sunk'i, dole yasa yace musu su bari gobe, da haka ya samu suka bar maganar, a hanyar dawowa gida yana ta tunanin meye mafita amma ya rasa, dole yasa bayan ya koma gida ya tarar tana falon, falon tsaf-tsaf ya kula bata da 'kazanta, kallo take ganinsa yasa ta mik'e tare da gaishesa.

"Ina wuni?"

"Lafiya."

Yace da ita yana wucewa d'akinsa, da kallo ta bisa tana mamakin hali irin na Sadeeq.

Sadeeq ko bayan ya shiga wanka yayi ya canza kaya tare da 'dauro alwalan sallar la'asar jin ana k'iran sallah, ya fito Masallaci ya wuce, bayan yayi sallah daga can gidan Mami ya wuce, da isarsa bayan yayi parking ya fito ya wuce cikin falontan, Sultaan ne kad'ai a falon, bayan ya amsa masa sallama ya zauna suna gaisawa nan yake tamabayarsa ina Mami, Sultaan ya fad'a masa tana sallah.

Nan suka maida hankali kan Labarun da ake yi, Sallamartane ya katse musu tunani, saman center table ta ajiye farantin dake hannunta mai dauk'e da kwalin juice da snack.

"Ya Sultaan ga ruwan."

"Yawwa A'ishat nagode, zuba min."

Cewar Sultaan na tashi daga gishingid'en da yake, batama lura da Sadeeq dake gurin ba, bayan ta zuba masa juice din ta mik'a masa, ya karba'.

"Yaya za kasha ta zuba ma?."

Jin ya ambaci Yaya ya sata kallon wajen, ido biyu su kayi da Sadeeq ya watsa mata wani kallon.

"Ina wuni."

Ta fad'a murya yana rawa, bai amsa ba ya tashi yabar gurin ya nufi d'akin Mami, ji yayi zuciyarsa na masa zafi, Me Sultaan yake nufi da shisshigewar da yakewa Ummu, a karshen Stairs suka had'u da Mami ba daman ya k'arasa dole yasa suka juyo tare suka dawo falon, Sultaan ne kad'ai Ummu ta dad'e da barin wajen, zama suka yi shikam Sadeeq ya kasa zaman ji yayi zaman gurin ya gundaresa, tashi yayi ya nufi d'akin Sultaan kwanciya yayi, ya fad'a duniyar tunani.

Sallar magribane ya d'agasa, alwala yayi ya fita suka had'u da Sultaan suka tafi masallaci dan Abbansu baya nan yayi tafiya, bayan sun idar da sallar suka dawo, basu tarar Mami a falon ba asalima ba kowa, Sultaan wucewa yayi d'akinsa shi kuma Sadeeq ya wuce d'akin Ummu.

Tana zaune ta idar da sallah, ganin wanda ya shigo sai da zuciyarta ya buga, ta sunkuyar da kanta k'asa, takowa yayi har inda take ya tsugunna kan kafafunsa ya zuba mata ido, zuciyar Ummu sai lugude take ji take kamar tasa kuka ganin yadda ya sata gaba haka.

"Rashina kusa shiya baki damar sakarwa Sultaan fuska har yana neman shiga gonar daba nasa ba, Eh?"

Girgiza kanta tayi alamar ah a.

"Ok, Ki had'a kayanki tare zamu tafi gidana."

Ji tayi kamar ta kurma ihu, rayuwa inuwa d'aya da Biebie, shi me yasa yake takura rayuwarta, yana gani ta fara samun nutsuwa da kwanciyar hankali a rayuwarta yana neman dawo da ita rayuwarta ta baya.

"Kayi hakuri ka barni anan ko dan saboda karatuna."

Taji bakinta ya furta haka, kallo ya bita dashi kafin ya tashi.

"Na baki mintuna biyar."

Fad'in haka yabar d'akin tare da jan kofar da karfi, kuka tasa a haka ta tashi ta dinga had'a kayanta harta gama ta fito dashi, lokacin shida Sultaan da Mami ne a falon, ganinta yasa Sultaan tashi.

"A'ishat lafiya? Ina zuwa da kaya haka?"

"Tare zamu tafi."

Fad'in Sadeeq na tashi daga zaunen da yake.

"Zuwa ina?"

"Gidana."

"Saboda me, mai aka mata."

Cewar Sultaan na neman 'karin bayani.

"Saboda AMANA TACE."

"Please Ya Sadeeq ka barta nan mana ko don saboda karatunta."

"Za tana zuwa ta can, okey."

"Ya Sadeeq....."

"Is okey Sultaan."

Fad'in Sadeeq na d'aga hannunsa ransa a b'ace ya nufi hanyar fita a falon.

"Sadeeq."

Mami ta k'irasa wanda har yayi taku biyu, baya ya dawo ya zauna.

"Na'am Mami."

"Me yasa ba zaka bar Ummu a gidannan ba."

"Kawai Mami."

"Oh kawai ne, to ba inda zata."

Kallonta ta mai da kan Ummu.

"Ke koma ba inda zaki."

Ummu da saurinta ta koma d'akinta, ganin tana hawaye yasa Sultaan tashi zai bi bayanta Sadeeq ya fizgosa ransa a mutukar bace.

"Ka daina gigin shiga hurumin daba naka ba."

Fisge jikinsa Sultaan yayi yana bin yayan nasa da wani kallo, zuciyarsa na raya masa wani abu, zargi ya fara ratsa zuciyarsa.

"Me kake nufi."

"Abinda kaji shi nake nufi, ka daina shiga harkan Ummu, ni na kawota gidannan AMANA TACE, ba ruwanka da ita."

"Ok banga wani babban hujjarka da zai hanani shiga harkanta ba, dan haka kasa ido ka gani kawai."

Mami sanin halin d'an nata Sadeeq da shegen zuciya yanzu in Sultaan ya k'ara wani magana zai iya cewa zai kai masa mari ya sata tashi taja hannunsa.

"Mami ki barni."

Bata kulasa ba ta jashi zuwa d'akinta, zaunar dashi tayi ta d'an masa nasiha sannan ta nuna masa ba abinda zai samu Ummu kafin ya danji wani sanyi amma har lokacin zafin Sultaan yake ji, da haka ta samu ya mata sallama ya wuce gidansa.

Yana tafiya ta sauko taci sa'a Sultaan baya nan, d'akin Ummu ta wuce ta sameta zauna, ganin Mami yasa Ummu mik'ewa tsaye, tsoron matar take.

Baki ta bud'e za tayi magana ta bata mari har biyu, dafe kumatunta tayi cikin kuka tace.

"Mami me nayi?"

"Uwarki ki kayi, shegiya dangin jarababbu, kina neman ki rabamun kan y'ay'a, uban me tsakaninki da Sadeeq da Sultaan?"

Kuka take ta kasa magana daga durkushen da take.

"Nace miki ubanme tsakaninki da Sadeeq da Sultaan."

Fadin Mami na neman igiyar wuta, ganin haka yasa Ummu sakin wani kukar, a tsorace tace.

"Wallahi Mami ba komai."

"Ba komai."

"Wallahi ba komai Mami."

"Kin tabbatar."

Kai ta d'aga mata.

"Last warning tsakaninki dasu gaisuwa daga Sadeeq har Sultaan din, kinji."

"Naji Mami."

Bata jira amsar taba tabar mata d'akin, kuka tasha ranar son ranta kafin bacci ya kwasheta.


Sadeeq bayan isarsa gida, tarar da falon yayi ba kowa ga kayan kallon a kunne anci abinci an bar plate da spoon din a wajen, abin sai ya k'ara bata ransa, ya nufi d'akin Biebie, bum ya bud'e kofar wanda ya sata firgita har abun busar da gashin dake hannunta ya fad'i, fitowarta daga wanka kenan daga ita sai rigar wanka iya guiwa, bai damu ba ya k'araso d'akin.

"Ubanwa kika barwa TV a kunne ga plate a ajiye anci abinci an bari."

Itama bata damu da ganinta da yayi haka ba tace.

"Ina fitowa zan d'auke."

"Zoki wuce ki d'auke kafin in bata miki rai."

"To." tace tana ajiye hand-drayer din hannunta tazo ta gifta ta gabansa ta wuce, tsaki yaja yabar d'akin ya wuce d'akinsa.

Wanka yayi yasa kayan bacci ya kwanta nan ya hau saka da warwara tsakanin Ummu da Sultaan, har ya gangaro zuwa abinda ya gani yanzu tashi zaune yayi jin zuciyarsa na hasko masa abinda ya tsana, 'sam ba zai yibu, wannan zubar da aji nane a gurinta.' Cewar wani sashi na zuciyarsa.

'Matar kace fa.' yaji wani sashi na zuciyarsa ya fad'a.

Kawar da tunanin yayi ta hanyar tashi ya d'auro alwala ya tada sallah.


 Washe gari har takwas kafin ya fito cikin shirin office, a dinning ya sameta tana breakfast, gurinta ya nufa.

"Ina kwana." Tace dashi.

"Lafiya, by 1pm zan zo da abokaina ki dafa abincin rana dasu."

Shuru tayi ta rasa me zatace.

"Ko ba kiji mai nace ba."

"Naji, amma..."

"Amma what?"

"Shikenan."

Barin falon yayi, a hankali ta tashi ita ba girkin kirki ta iya ba, dabarane ya fad'o mata ta shiga d'akin ta fara bincike nan taci karo da takardun girkin da suke saya itada su Hauwaty suke tarawa, d'aya ta zab'o ta fito dashi ta shiga kitchen dinta ta ajiye.

Sha biyu nayi ta koma kitchen din nan ta zage ta zabi abinci mai dad'in girkawa kala biyu tana bin yanda ake girkawa tana yi harta gama ta saka a flask ta wahala ba kad'an ba dan bata zaba ba bata tab'a yi ba, bayan ta jera a dinning tayi wanka ta zura dogon riga maroon kala ta danyin simple makeup nata tana cikin d'aura gyalen kayan taji sallama a falo.

Yafa gyalen kayan tayi ta fito tare da amsawa murmushi kwance saman kyakkyawar fuskarta, su ukune abokansan, iso ta musu cikin falon bayan sun zauna ta suka gaisa ta tashi ta kawo musu ruwa da juice, sallah suka wuce masallaci za suyi ta koma d'akinta.

Bayan sun idar suka dawo nan Sadeeq ya shiga mata magana ta kawo musu abinci tare da gargadinta ta sako mayafi babba, murmushi tayi sannan taji dad'in nuna kulawarsa gareta tasan kishine ya jawo hakan, fita tayi ta gabatar musu abincin zata bar gurin k'asa-k'asa Sadeeq yace.

"Zuba min."

Plate ta jawo ta zuba ta tura masa gabansa, ta zuba masa juice din ma ta ajiye tabar gurin.

"Mu fa Sadeeq."

Cewar d'aya cikin abokansa.

"In wani zaku bawa karku zuba."

Fad'in Sadeeq na d'aukan spoon ya faracin abincin da bismillah, nan suma suka zuba suka faraci, ba laifi abincin yayi musu dadi, suka ci suka koshi suka d'an taba hira kafin suka sashi ya 'kirata suka mata sallama tare da bada tukuicin kud'ad'e.

Sadeeq yaji dadin ganin yanda abokansa suka yaba girkin gidansa ko ba komai ta ciresa a kunya, bayan ya dawo daga rakasu ya sameta tana tattare wajen, tsayawa yayi har ta iso kusa dashi ba zato ya rik'o hannunta ya juyo da ita suna facing na juna.

"Thank you."

Yace da ita tayi kasa da kanta tana murmushi duk da ta tsorata da rik'on da ya mata, dan tinda suke bai tab'a rik'e ko da hannunta ba, sakinta yayi ya wuce d'akinsa ta juya ta bisa da kallo wani sonsa na fizgarta, cikin wani irin yanayi ta k'arasa gyara gidan tasa turaren wuta gidan ya d'au kamshi.


 Haka rayuwar ma'auratan ya kasance cikin satin, zai ci abincinta inta girka, gaisuwarta yana amsa mata cikin sakin fuska ba kamar da ba, hakan shiya bata damar k'ara kula da duk wani abu da tasan zai burgesa ya faranta masa ransa, sannan duk dare sai ya duba lafiyarta kafin ya kwanta, kuma duk wayewan gari in ya taso daga office sai yaje gidan Mami ba zai bar gidan ba sai yasan yanda ya duba lafiyar Ummu da shiga da fitanta ba tare da wani ya lura ba.


Ummu da Sultaan ko.......


Sadaukarwa ga Ummu Aisha(Ummu Safwaan)


PhartyBb.WordPress.comcom


NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


  SANADIN HA'DUWARMU

   ©Pharty BB


  Wattpad PhartyBB

20

  

 Shak'uwace ta shiga tsakanin Sultaan da Ummu dan irin sakin fuskar da yake nuna mata da mutumta ta da nuna mata itama mutumce kamar kowa, shi ya haddasa take mutum tasa, duk da tana kokarin boye masa asalinta tana fad'a masa ita y'ar aikice kamar yanda ya gani, shi kawai ya yardane badan ya amince ba.


Gidan Sadeeq kam sun shimfad'a rayuwarsu cikin kwanciyar hankali, Sadeeq na kula da Biebie dai-dai gwargodo, cikin wannan halin ta samu aiki a wani banki, da farko Sadeeq yaso hanata amma yanda tayi fushi ta sasa gaba da kuka tana rok'o shiya sashi amincewa badan ya so ba, haka ta fara aikinta cikin kwanciyar hankali inda ta samu kawa mai suna Lubbatu.

Rayuwar gwanin sha'awa yana sauk'e hakkinta dake rataye a wuyansa, yana bata kulawa itama tana basa kulawarta a matsayinta na matarsa.


   K'auyen Anguwar Liman

 Liyafa taci gaba tin bayan da Deejah ta zowa Abulle cike da tsaraba da kayan more rayuwa, hatta Laure na samun rabonta, sun zama Hajiyoyin 'Kauye sai wanda suka ga dama suke mu'amala dashi.

Deeje rayuwa tayi dadi, shuka tsiyarta take son ranta, sun manta da wata wai mai suna Ummu.

Liman da mai gari kuwa kullum cikin zullumi suke ganin har ana neman shekara hudu ba Ummu ba labarinta, suna tsoron ranar da zasu mutu a tambayesu ina suka kai marainiya, wani hannu take? wani kalan rayuwa take? duk basu da amsan wannan tambayoyin, addu'a sosai suke yi duk inda take ya kasance tana cikin kwanciyar hankali, shine kawai burinsu.


Yau ta kasance hutun karshen mako (Weekend), misalin karfe sha biyu na rana, a hankali motar ta shigo cikin k'auyen, mutane nata kallon motar ganin duk garin ba mai irinsa, kuma ba wanda ya ta'ba zuwa k'auyen da irinsa, matuk'yar motar a hankali ta dinga tuka motar cikin kwarewa har ta iso wani gida dake zagaye da bulo da bulo, tabbas nanne gidan amma tayi mamakin ganin komai ya canza daga tsarin data bari.

Fitowa tayi ta shiga cikin gidan tare da sallama, tabbas gidanne amma ya sauya gaba daya daga yanda ta barsa, sallama ta k'arayi.

"Assalamu Alaikum."

"Walaikis salamu, waye haka da tsakar ranar Allah ke doka sallama."

Daga cikin dakin aka amsa, amma ba alamar za'a fito.

"Bak'uwa ce."

"To ana fitowa."

Kusan minti biyar aka d'auka, har ta gaji da tsayuwar kafin aka bankad'a labulen d'akin aka fito, Abulle ce tasha wani uban kwalliya, ganin wacce ke tsaye ya sata shan jinin jikinta, ta burma ta shimfid'a tace mata.

"Bismillah zauna."

Murmushi matar tayi dan ba zata taba mance fuskar Abulke ba.

"Ina wuninki?" Cewar Munirat na zama saman tabarman.

"Lafiya lau, sai dai ban gane fuskar ba."

"Abulle, Munirat ce mahaifiyar Ummu Budd'o."

Wani razana da Abulle tayi hanjin cikinta ya murd'a, cikin rawar murya tace.

"Mu..ni..raat kece.?"

"Eh Abulle nice."

'Wayyo na shiga uku' Abulle tace ranta dan bata tab'a kawo rana ita yau zata zoba, ranar da Munirat za tazo neman Ummu ba.

"Abulle."

"Eh ehh na'am, me kika ce?"

Gaba d'aya ta rud'e.

"Abulle lafiya kuwa?"

"Eh lafiya, ina zuwa."

Tashi tayi ta suri buta ta ke waya bangida, minti biyar ta fito gaba daya ta gama jikewa da gumi, zama tayi nesa da Munirat.

"Abulle ina Baffan Ummu?"

Shuru Abulle tayi sai da Munirat ta sake maimai ta mata tambayar kafin cikin inda-inda ta fara magana.

"Tin bayan lafiyarki da shekaru biyu Allah yama Malam rasuwa."

"Innahlillahi wa'innah ilaihi raji'un Allah yaji k'an Malam yasa Aljannah makomarsa."

Kawai abinda Munirat tace taji idonta ya cika da hawaye.

"Ameen Ya Allah."

"Ina Ummuna?" Ta tambayeta

Ras gaban Abulle ya fad'i

 "Eh."

 "Nace ina Ummu?"

Rasa mai za tace tayi, dakyar ta furta.

"Ummu na turasu Aikatau birni ita da Dijeh."

"What, Aikatau Ummu ita za tayi aikatau ina raye."

"Kina rayen kika watsar da rayuwarta kika tsallaketa kika tafi kika barta gani baiwa na kula miki da ita, na turata birni ta nemi na kanta."

Dafe kanta Munirat tayi danjin yanda ya sara, idonta yayi ja dan bacin rai, komai ya samu Ummu itace sila, ta watsar da rayuwar y'arta kwaya d'aya da Allah ya bata, da kyar ta iya daidaita kanta ganin itama Abulle na neman hawa sama.

"Abulle ko kinsan gidan da take aikatau din."

"Ni ban sani ba."

"To gari fa."

"Nan cikin garin Katsina ne."

Duk yanda Munirat taso Abulle ta fad'a mata wani abu dangane da Ummu 'ki tayi, ita dai kawai ta dage da aikatau ta turata birni kuma bata san gidan ba, har yamma wajen la'asar tana gidan da kyar ta iya barin gidan ta kamo hanyar Katsina a lokacin, Allah kad'ai ya kaita gidan Mami lokacin karfe taran dare.

Bayan shigarta tayi parking, cikin gidan ta nufa, gaba daya ahalin gidan suna falo, zama tayi d'aya daga cikin kujerun falon bayan ta gaishe da Abba da Mami ta wuce d'akin Mami.

Da shigarta bangida ta wuce tayi wanka ta d'auro alwala ta fito, sallah tayi bayan ta idar ta dad'e tana addu'a akan Allah bayyanar mata da y'arta duk inda take ya kare mata ita da mutuncinta.

Bayan ta gama ta kwanta ahankali wasu siraran hawaye suka dinga zubo mata tana sharesu, tana cikin wannan halin Mami ta shigo, kusa da 'yar uwartan taje ta zauna.

"Munirat."

"Na'am Anti."

Tace tana tashi.

"Allah yasa an dace."

Girgiza kanta tayi hawaye na sauk'a a idonta.

Shuru Mami tayi cikin jin tausayin k'anwartan tace.

"Muyi ta addu'a duk inda take Allah ya kare mana ita ya sada fuskokinmu da alherinsa."

"Ameen Anti."

"Ki fito kici abinci."

"Anti bazan iya ba."

Tashi Mami tayi ta fita, ta samu ba kowa a falon sai Ummu dake tattare inda suka ci abinci, Sultaan a gefenta yana murmushi ita kuma kanta a 'kasa.

Wani kallo ta watsa musu.

"Sultaan ya baka tafi d'akin ka ba."

"Coffe nake jira A'ishat ta had'omin."

"To me take jira, wuce ki had'a masa."

"To." Tace tana wucewa Kitchen ta had'o masa ta kawo masa, duk kok'arinsa na son sa kwayar idonsa cikin nata tak'i yarda.

Murmushi yayi k'asa-k'asa yace.

"Thank you Beauty."

Bata bari kunnuwanta sun jiyo mata sauran maganarsa ba ta bar gurin da sauri, shiko tashi yayi ya ma Mami sallama ya wuce d'akinsa cikin murmushi da farin ciki, ji yake kamar ya sameta.

Bayan ta gama tattara wajen ta share itama ta wuce d'akinta.


Washegari har karfe takwas tana d'akinta tak'i fitowa, bata son fita ta had'u da Sultaan yana jifanta da murmushinsa mai sata kunya, karfe tara Mami ta turo Iyamee ta sata shirya kayanta zata gidan Hauwaty ta zauna mata na kwana biyu bata jin dadi.

Bada son ran ta ba ta shirya driver ya kaita.

Karfe goma Munirat ta sauk'o cikin shirin tafiya, da kyar Mami ta barta cewarta ta zauna kwana biyu, nuna mata tayi tana da abubuwan yi amma zata dawo nan da wata biyu, da haka su kayi sallama, ta d'auki hanyar Kaduna.


Sadaukarwa ga Ummu Aishat (Ummi Safwaan).


PhartyBb.WordPress.com

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION.

  

  SANADIN HADUWARM

   ©Pharty BB


  Wattpad @PhartyBB

21


 Tin zuwan Ummu gidan Hauwaty bata da zama, kullum cikin aiki take ba dare ba rana, aikin gidan kwacakom Hauwaty ta d'aura mata, shara, wanke-wanke, girki, duk ita take yi.


***

Misalin Karfe goma na safe ya fito cikin shirinsa na manyan kaya, falon k'asa ya sauko, da sauri Rahma ta taro sa.

"Yaya Sultaan ina zuwa haka da safen nan?"

Murmushinsa mai kyau yayi yana gyara link na hannunsa.

"Zance zanje."

"Yaya wajen budurwarka, zan raka ka."

"Sai watarana, yau yak'i zanje na siyar zuciyarta, ki tayani addu'a."

"Insha Allahu Yaya Allah sa ta amince cikin gaggawa, dan nasan Yayana ba abin yadawa bane."

"Allah yasa, in Mami ta fito ki sanar mata na fita."

"To Yaya sai ka dawo."

 Cewar Rahma tana komawa kan kujeran data tashi.

Sultaan motarsa mai kyau ya d'auka ya fita a gidan ya d'auki hanyar gidan Hauwaty, tafiya ka'dan ya isa gidan a kofar gidan yayi parking ya shiga, door bell ya danna, Ummu tazo ta bude.

Ido hudu suka had'a ta sunkuyar da kanta, murmushi yayi yace.

"Beauty."

Bata amsa ba ta basa hanya tace.

"Bismillah."

Shiga yayi cikin falon ta rufe kofar, zama yayi cikin kujerun falon.

"Bari na 'kira Anti Hauwan."

"Ni gurinki nazo."

Taji maganarsa ya daki kunnenta.

"Ni kuma?"

"Eh." yace yana 'daga kansa.

 Shuru tayi ta kasa cewa komai tana tsaye kanta k'asa tana wasa da yatsun hannunta.

"Zauna mana A'ishat, ba fa wani abu bane just na zo mu gaisane kwana biyu ba kya nan nayi kewarki."

Ta kasa ko motsi a yanda taken, ganin haka ya sashi tashi ya isa wajenta, kallonsa tayi karo na biyu tin bayan shigowarsa.

"Kina jin kunyana ko?"

Girgiza kanta tayi.

"To menene?"

"Tsoro nake ji."

"Tsoron me, a hakan za muyi aure kina jin tsoro?"

Wani kallo ta watsa masa mai cike da mamaki, al'ajabi, tsoro, kunya.

Murmushi yayi zai sake magana yaji alaman sauk'owa a stairs ya koma kan kujera ya zauna.

Ummu barin gurin tayi da sauri ta fad'a kitchen dan shine daf da falon.

"Ya Sultaan dama kaine?"

Fad'in Hauwaty na k'arasowa cikin falon, tayi fari sol ta 'kara kyau sai rama da ta d'anyi, kana ganinta kaga alamar mai laulayi.

Murmushi yayi.

"Nine Maman biyu, ya kike ya gida."

"Lafiya lau, ina Mamina?"

"Lafiyanta lau, ya karfin jiki?"

Cike da kunya tace.

"Allahamdulillahi, ko ruwa bata kawo maka ba yarinyarna, Ummu!"

"Na'am." ta amsa tsum ta fito daga cikin kitchen ta durk'usa gefe kanta a k'asa dan kunyar Sultaan take ji sosai.

"Ke wai yaushe za kiyi hankali, kawo masa ruwa mana."

Tashi tayi ta wuce kitchen ta had'o masa juice dasu snack ta kawo masa ta ajiye gabansa.

"Thanks B." yace k'asa-k'asa.

Hira kad'an suka tab'a da Hauwaty yace mata zai tafi tayi masa rakiya har bakin motarsa kamar yace ta k'ira masa Ummu amma yana shakkan wani abu ya biyo baya.

Jan motarsa yayi yabar gidan, gidan Ya Sadeeq ya wuce, nan ma bai dad'e ba ya musu sallama ya wuce gida.


 Kwana biyu da zuwansa da yamma Sadeeq yazo shi da Biebie, iyayen sunyi farin cikin da ganin yanda suke rayuwarsu da yanda Sadeeq ke kula da Biebie, ita kuma sai wani Kunya-kunya take yi.

Tin zuwansu bai ga shiga da fitan Ummu ba, da farko ya so ya bar abin ganin har dare yasa ya kasa daurewa ya kalli Mami.

"Mami ina yarinyarnan?"

"Wacce ke nan kake nufi."

"Ummu A'isha."

"Au tana gidan Hauwaty bata jin dadi."

"What Mami? Waya kaita?"

"Ni na turata, Wani abune?"

Shuru yayi ya kasa cewa komai.

Har bayan isha'i suna gidan kafin su musu sallama su tafi, maimakon ya d'auki hanyar gidansa, hanyar gidan Hauwaty yayi bayan isarsa yayi parking a kofar gidan ya fito, Biebie zata fito ya hanata, badan ta so ba ta zauna jiransa ya shiga ciki.

Da shigarsa, filin gidan da hasken farin wata da hasken kwan lantarki, gefen hagunsa ya kai kallo, motace da mutum jingine a jiki gefensa kuma budurwace da hijab nata har kasa kanta a sunkuye kamar saurayi da budurwa.

Zuciyarsane ya buga a hankali ya dinga takawa har ya iso gurinsu, Sultaanne ya ankara da zuwansa ya juya ganin Yayansa ya sashi fad'ad'a murmushinsa.

"Ya Sadeeq."

Jin wanda aka ambata take tasha jinin jikinta ta juya a razane suka had'a ido, gaba d'aya lokaci d'aya zuciyoyinsu suka buga.

"Ya Sadeeq." Sultaan ya k'ara k'iransa.

Wani kallo ya watsa Sultaan din kafin ya juya har yayi taku biyu ya juyo ya fizgo hannun Ummu ya fara janta.

Gabansa Sultaan yasha cikin dakewa yace.

"Ina zaka kaita?"

Bai kulasa ba yabi ta gefensa zai wuce, Sultaan ya riqo d'ayan hannun Ummu, juyawa yayi ya kallesa kallon mai tattare da bacin rai, ya fizge hannunta yaci gaba da janta har suka fita a gidan, bayan motarsa ya bud'e ya jefata ya rufe kafin ya bud'e gidan gaba ya shiga ya figi motar.

Bai tsaya ko ina ba sai cikin gidansa, fita yayi a motar yabarta ita da Biebie, itama fitowa tayi ta juya tana kallon Ummun cikin jin haushinta.

"Munafuka kawai duk inda mutum yana nan kina binsa ba zaki bar mutum yaji dadin rayuwarsa ba, zaki fito ko saina ci mutumcinki."

Tsum Ummu ta fito cikin kuka take a hankaali, Biebie ta rufe motar ta nufi cikin falo, binta tayi a baya har cikin falon.

D'akinta Biebie ta wuce, ita kam Ummu durkushe tayi nan falon tasha kukanta son ranta.

Shigar Biebie d'aki ta dad'e kafin ta fito cikin shirin bacci ta wuce d'akin Sadeeq, zaune ta samesa yana duba wasu file.

Gefensa ta zauna tana karb'an file d'in hannunsa.

"Kar ka sawa kanka Headaches, ya kamata ka huta."

"Bani." yace da ita yana mik'a hannu, 'ki tayi ta tattare ta ajiye inda yake ajiyewa, ta wuce bathroom nasa ta had'a masa ruwan wanka ta fito, ta koma gurinsa.

"Kaje kayi wanka na had'ama ruwa please."

Murmushin dole ya sakar mata yana wucewa bathroom, wanka yayi ya fito ta ciro masa kayan bacci yana cikin shiri ya kallota.

"Please Biebie jeki nunawa yarinyarnan extra room din can."

"To." tace tana tashi ta fita.

Zaune ta sameta ta durkushe.

"Ke biyoni."

Ta fad'a tana yin gaba, wani d'aki ta nuna mata ba abinda babu a d'akin.

"Zaki zauna anan kafin gobe ki tafi, ki kula da komai."

Tana fad'ar haka tabar wajen, shiga Ummu tayi, wanka kawai ta iyayi ta kwanta.

Komawar Biebie d'aki ya gama shirinsa ya kwanta, gefensa ta kwanta taja musu bargo.Sadaukarwa ga Ummu Aishat(Ummi Safwaan).

Gaisuwa gareki Biebie (Ummi Afnan).PhartyBb.WordPress.com

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION.


  SANADIN HADUWARMU

   ©Pharty BB


  Wattpad @PhartyBB

22

   

 Misalin karfe tara na safiyar Litinin, garin an tashi da tsananin sanyi kasancewar lokacin tsakiyar hunturene, ma'aikata da dama suna faman tafiya wajen aiki, yan kasuwa suna kok'arin tafiya wajen sana'arsu.

Zaune yake gefen Mahaifinsa kansa a k'asa, yafi minti goma yana son fad'a masa takamammem abinda ya kawosa wajensa amma yana tsoro ya zai kar'bi abin, ya zai fuskance sa ya gane nufinsa, taimako yake son yi ga rayuwarta, yasan abinda zai yi shi kad'aine zai dawo da farin cikinta, duk da, da wuya ta samu sauran farin cikin rayuwarta amma yana fatan samar mata shi nan gaba kad'an.

Kallonsa Mahaifinsan yake tin bayan da suka gaisa yasan bakin d'ansan da magana, murmushinsa na manya yayi yana dafa kan d'ansan.

"Ya akayi Sultaan, na kula tin zamanka akwai magana tattare da kai."

K'ara k'asa da kansa yayi cikin fad'uwar gaba da kyar ya iya bud'e baki yace.

"Abba dama..dama dai..."

"Dama dai menene, feel free and tell me."

"Abba dama na samu matar da zan aure, amma ban san ya zaka d'auki maganar tawa ba."

Murmushi Abbansan yayi a 'karo na biyu.

"Akan maganarnan shine kake jin kunyan fad'amin, in dai har yarinyar nada asali mai kyau da tarbiya ai shikenan Allah zaba mana abinda yafi alheri."

"Ameen ya Allah." 

Cewar Sultaan k'asa-k'asa.

"Y'ar ina ce?"

Dum zuciyar Sultaan ya buga, dama yana tsammanin tambayarnan a ko wani lokaci.

"Abba bansan y'ar ina bace asalima boyemin asalinta take, ba wata bace Ummu A'ishat."

"Ummu y'ar aikin gidannan kake nufi."

"Eh ita Abba, Abba so nake in taimaki rayuwarta in sadata da farin ciki kamar yanda kowani 'Dan Adam ke buk'ata, tana buk'atar taimako, wanda ya kawota bai damu da ita ba."

Shuru Abbansan yayi shikam yasan bai isa ya hanasa ba, sannan bai isa yace ya aureta ba, in Allah yayi matarsa ne dole sai ya aureta in ko akasin haka to sai dai ya hakura.

"Kaje Office naka yanzu zuwa anjima da dare zan nemeka."

"To Abba nagode."

Fad'in Sultaan na tashi, da fitarsa sallama yama Maminsa ya wuce.

A office din ma ranar kasa duba marasa lafiya yayi har aka tashi addu'a yake tayi akan Yayan nasan, dan ya kula da take takensa akan Ummu amma duk tunaninsa ya kasa gano menene.

Da yamma karfe hudu ya baro Office isansa gida a wajen parking ya ga motar Sadeeq, bayan yai parking ya fito ya wuce babban falon gidan, Rahma ce da Mami sai Sadeeq a falon bayan sun gaisa ya wuce d'akinsa, wanka yayi ya canza kaya kan ya fito falon Rahma ta zubo masa abinci.

Abinci yaci kad'an ta d'auke saura, nan su kaci gaba da hiransu na 'yan uwa har Abbansu ya dawo, bayan sun gaisheshi ya wuce 'dakinsa, Mami tabi bayansa.

Kiran Sallar magribane ya fito dashi suka had'u dashi da y'ay'ansan suka wuce masallaci, bayan sun idar suka dawo a falon Abbansu suka yada zango, da sallama Abbansu ya bud'e gurin kafin ya fad'awa Sadeeq buk'atar Sultaan, inda suke so ya fad'a musu garin Ummu dan zuwa binciken Asalinta tinda shine silarta na zuwa gidan.

Shuru Sadeeq yayi da jin maganar Abbansa kansa a k'asa.

"Abba naji komai amma ina mai bada hakuri akan buk'atar Sultaan ba zai yu ba."

"Ko zaka fad'a mana dalili?"

Kallonsa Sadeeq ya kai kan Sultaan kafin ya watso masa tambaya.

"Shin ya halarta Mace ta auri maza biyu?"

Girgiza kansa Sultaan yayi cikin dakewa yace.

"Ah a."

"Good, sannan shin ya halarta Namiji ya auri matar aure."

Nan kam girgiza kai Sultaan ya sake yi dan ya kasa furta ko kalma d'aya.

"In kasan har haka bazai tab'a faruwa to ba zai faru ba, dan Ummu da kake ikirarin zaka aureta, matar aurece akwai igiyar aure uku a kanta."

Gaba d'aya shuru falon yayi Abbane yayi karfin halin magana.

"Sadeeq auren waye akanta?"

"Abba kayi hauri bisa boyema da nayi, nayi hakanne badan komai ba sai dan gudun ban san ya Mami zata d'auki auren ba, nima kaina bada son raina aka d'aura auren ba sai dan tana bukartar tsananin taimako a lokacin...."

Nan ya kwashe labarin farkon SANADIN HA'DUWARSU ya fad'a musu bai boye musu komai ba hatta da zamanta gidan magajiya.

Daga Abba har Sultaan sun tausayawa rayuwar Ummu da irin rashin gata da take fama dashi, Sultaan ji yake zuciyarsa tayi zafi da jin irin rayuwar da tayi da wanda yanzu take ciki na rashin halin ko in kula da Yayansan yake mata, hakan kuma yake ikiraran 'kiranta matarsa.

Tashi yayi ransa a bace yana cewa.

"Abba nagode dama duk tunani bai taba nunamin da ita din matar aure bace, duk da wani hali da wasu abubuwa da Ya Sadeeq ke nunawa akanta ban taba zaton haka bane, amma ya sani k'ani na auran matar Yayansa idan har ba abinda ya shiga tsakinsu."

Tashi Sadeeq yayi a fusace yana watsawa Sultaan wani kallo.

"Me kake nufi?"

 Shima Sultaan cikin b'acin rai yace.

"Abinda kaji shi nake nufi, kasa yarinya gaba ka rabata da 'yan uwanta da kowa nata akan kana tak'ama da cewa ka taimaki rayuwarta, to ka sani ni Aliyu Sultaan sai Ummu ta zamo matata in dai ina numfashi."

Yana gama fad'ar haka yabar falon, Sadeeq zai bi bayansa Abba ya dakatar dashi.

"Zonan Sadeeq."

Baya ya dawo ya zauna yana huci.

"Kar kuban kunya mana duk zamanku da shak'uwarku mace na shirin shiga tsakaninku, nasan Sultaan b'acin rai ya sashi haka amma nanda wani lokaci zai sauk'o, abu na karshe jibi ka shirya kai da Ummu za muje garinsu dan yin bincike a kanta."

Ajiyar zuciya Sadeeq ya sauke.

"Allah kaimu Abba."

"Ameeen, zaka iya tafiya."

Fita yayi a falon ko sallama bai ma Mami ba yaja motarsa yabar gidan, a ransa ya kudiri a aniyar d'an tazarar da ya rage Sultaan ya samu Ummu sai ya kawar dashi a daren yau, tinda dashi yake ikirarin sai ya aureta, wanda faruwar hakan yasan zai sa aure ya haramta tsakaninsu sai ko bayan ransa.

Yana isa gida bayan yayi parking motarsa ya fito ya nufi falon, a nan ya tarar da Biebie na kallo gabanta Laptop nata ne, rufewa tayi ta isa wajen ta rumgumesa.

"Wellcome home My Dear."

Kanta ya shafa yana k'irk'iran murmushin dole.

"Ya gida."

"Lafiya lau, muje kayi wanka in kawo maka abinci."

Kai ya d'aga bata bai jin zai iya magana, da shigarsu d'akin wanka yayi ya shirya da taikamon Biebie, kafin su fito ta kawo masa abinci, lomarsa ta farko ya gane d'and'anon abincin bana Biebie bane, kad'an yaci ya ture sauran ta d'auke ta dawo ta shige jikinsa.

A haka suka d'anyi kallo suka wuce d'akunan baccinsu, wanka tayi ta shirya cikin kayan bacci ta wuce d'akinsa, kwanciya su kayi shikam kasawa yayi sai da ya tabbatar tayi bacci kafin ya lullubeta da bargo ya fita yaja mata kofar.

D'akin Ummu ya shiga wutan d'akin a kashe sai hasken farin wata daya hasko d'akin kad'an, can kan gado ya hangota tana bacci, lallab'awa yayi gurin gadon ya zauna ta inda fuskarta yake.

Ido ya zuba mata, tabbas yasan yaci amanar daya d'auka ya kasa taimaka mata, ya rabata da kowa nata dan ya taimaka mata amma ya kasa, bawai bashi da halin taimakon bane kawai shi kansa ya rasa mai yasa ya kasa aiwatar da hakan.

Hannu yasa saman fuskarta ya gyara kitsonta na kalaba daya rufe mata gefen fuska, kyakkyawar fuskarta ya sawa ido, boy'ayyen kyau gareta wanda ba lalle in ka kalleta sau d'aya ka gane hakan ba, sai ka saka mata ido sosai.

"Ayeeshat."

Ya k'ira sunanta yana d'an shafa fuskar, motsi tayi tana gyara kwanciyarta, cikin bacci taji ana shafa fuskarta ta farka a zubure tana kok'arin sauk'a a gadon ya rik'ota, ihu za tasa ya toshe bakinta da hannunsa.

"Ke nine."

Ya fad'a yana rik'eta da kyau, duk da ta ganesa kok'arin kwace jikinta take, yaki sakinta ya k'ara rik'eta da kyau, kuka tasa masa dan tinda suke da ita bai tab'a mata haka ba.

Cikin kuka tace.

"Dan Allah ka barni Ya Sadeeq."

Ko kulata bai yiba ya kwantarta ya kwanto jikinta yana rik'e da ita yaja musu blanket.

Daren ranar duk kok'arin Ummu da kuka da roko da magiya ba wanda ba tama Sadeeq ba amma ko a jikinsa haka yabi da ita ya maida Ummu cikakkiyar mace, da kyar kafin ya saketa lokacin banda ajiyar zuciya ba abinda take yi dan ta jik'ata ba kad'an ba.

Wahallalen baccine ya d'auketa shiko ya tashi ya bar d'akin, d'akinsa ya shiga sai da ya tsarkake jikinsa kafin ya iya kwanciya shima baccin ya d'aukesa.


 Washegari da safe karfe tara Biebie ta fito, ganin falon yanda ta barshi jiya shiya b'ata mata rai ta wuce kitchen nan ma ba a gyare ba balle har taga ta d'aura breakfast.

Cikin masifa ta fito ta nufi d'akin da Ummu take, banka kofar d'akin tayi ta shiga, kan gadon da take kwance ta isa wajen ta daka mata duka a baya.

"Shegiya tashi, uban wa zai miki aikin gidan kinzo kin wani baje kina bacci."

Cikin hawaye Ummu ta mik'e gaba daya ji take ta tsani rayuwarta, ta tsani Sadeeq da kowa nasa, ya cuceta yaci amanarta.

"Tashi ki fita ki gyaramin gida kafin naci mutuncinki."

Da kyar da azaba Ummu ta mike ji tayi kafafunta sun kasa d'aukarta ta koma ta zauna.

Nan fa Biebie tasha jinin jikinta ganin abinda idon ya kai kallo, me zata gani? Me yake shirin faruwa? Me yarinyarnan take nufi?


Sadaukarwa ga Ummu A'ishat(Ummu Safwaan)


PhartyBb.WordPress.com

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

  

  SANADIN HADUWARMU

   ©Pharty BB


  Wattpad @PhartyBB

23

  

  Wani wawar cakuma Biebie ta kaiwa Ummu, jijjgata take iya karfin tsabar masifa idonta ya 'kank'ance.

 "Dan ubanki me zan gani? uban wa ya miki haka? Tsabar iskanci ki rasa ina za kiyi iskancinki sai cikin gida, eh."

 Kwakkwaran motsi Ummu ta kasa yi tsabar yanda take jinta, hawayenma sun kafe sunk'i zubowa balle taji sanyi a ranta.

Wulli da ita Biebie tayi ta fita, masifa take.

"Yau sai kinbar gidannan, gidan Mami ma baza ki zauna ba shegiya karuwa kawai."

Bata tsaya ko ina ba sai d'akin Sadeeq, kwance yake yana baccinsa hankali kwance, kyam taje ta tsaya masa akai, y'an rashin kunyar sun motsa.

"Ya Sadeeq! Ya Sadeeq!!."

Take fad'i da karfi tana jijjiga jikinta ta rike kwankoso.

Bud'e idonsa yayi yana jan k'aramin tsaki.

"Ya akayi? Lafiyarki kuwa?."

"Ina lafiya wannan karuwan da ka kawo ka ajiyemin a gida ita nake so ta fita a gidan yanxu tinda bana ubanta bane..."

Kanta 'karasa Sadeeq ya mik'e ya bata mari lafiyayye, rik'e kuncinta tayi ta bisa da kallo.

"Akan wannan y'ar iskar zaka maren."

"An mareki ko zaki rama, and last warning karki k'ara kiranta da karuwa ko y'ar iska dan yanda kike da igiyana uku na aure a kanki haka take dashi tsawan shekara hudu."

Mutuwar tsaye Biebie tayi kafin tai zaman y'an bori a tsakar d'akin, tsaki yayi ya fice a d'akin, d'akin da Ummu take ya shiga ya k'arasa bakin gadon da take kwance a zube.

D'agota yayi yana kallon fuskarta, hannu ya kai kan wuyanta yaji 'dumi gau, kwantarta yayi ya wuce bathroom, ruwan zafi ya had'a ya fito da taimakonsa ta gyara jikinta ta fito ta shirya cikin dogon riga, ya kwantar da ita saman dogon kujeran d'akin, fita yayi ya wuce d'akinsa.

Wanka yayi ya fito wayarsa nata ringing, sai da ya gama shiryawansa cikin 'kananan kaya yasha turare, wayarsan ya d'auka yaga 8 missed call, 4 missed call daga Mami 2 daga Abba, 2 daga office, office ya fara 'kira ya sanar musu ba zai samu fitowa ba kan ya k'ira Abbansa, cikin b'acin rai yace masa yazo yanzu shida Ummu yana nemansa.

Bai jira jira mai Sadeeq zai ce ba ya katse wayar, fita Sadeeq yayi a 'dakin bayan ya d'au mukullin motarsa, d'akin Ummu ya shiga yanda ya barta kwance haka ya isketa, hijab ya d'auka mata kafin ya ta data, da kyar ta tashi dan zazzabine jikinta.

Da kyar ta iya mik'ewa ya rik'e hannunta suka fita a d'akin, wajen parking su kayi ya bud'e motarsa suka shiga kan yaja suka bar gidan.

Da isarsu gidan ya danna hon mai gadi ya bud'e masa ya shiga bayan yayi parking ya fito, Ummu kam kin fitowa tayi har sai da ya zagayo.

"Fito mana."

Gurgiza kanta tayi hawaye na sauk'a a kuncinta, wanda sai yanxu suka samu damar zuba.

"Oya fito kona fito dake."

A hankali ta d'aga kafarta ta fito ya rufe motarsa kan su nufi cikin falon gidan yana gaba tana binsa.

Da sallama ya shiga, ba wanda ya kulasa duk da kaf ahlin gidan suna zaune a falon daga Abba har Mami Wanda banda sa'kon harara ba abinda take sika masa, abinda ya d'aure masa kai, Kallonsa ya kai gefen damarsa Biebie ce zaune da Rahma, sai abinma ya kusan basa dariya, yasan dalilin zuwantane ya haddasa komai, sai yaji kunyar Abbansa ya kamasa, yasan Biebie ta fad'a komai, murmushin karfin hali ya d'aura saman lebensa yana k'arasawa wajen Abbansa.

"Abba ina kwana."

"Lafiya."

Yace dashi yana tashi da sauri, cikin sauri Sadeeq ya kai kallonsa inda Abba yayi, me zai gani, Biebie ce ta danne Ummu sai jibga tak, wani tsalle Sadeeq yayi ya finciko Biebie tareda watsa mata maruka biya yana shirin na uku Mami ta rik'e hannunsa.

"Zaka nunamin y'ar tsintuwa tafi jininka duk da abin kunyar da ka aikata."

"Abin kunya Mami?"

 "Eh Sadeeq ko aka ce ma bani da labarin abinda kuka aikata da wannan y'ar iskar."

Fad'in Mami cikin tsawa.

"Halima!"

Abba ya k'ira sunanta wanda shi yayi sanadiyar sata shuru.

"Ki zauna, duk ku zauna."

Zama gaba d'aya falon aka yi kamar yanda Abba ya umarcesu.

Da sallama ya bud'e taron kafin yama Mami bayanin jiya da Sultaan yazo masa da maganar na son auren Ummu, ya nemi Sadeeq ya masa magana in da shi Sadeeq din ya tabbatar masa da akwai auren Ummu a kansa tin zuwanta gidan har yanzu.

Ai Abba bai k'arasa maganarsa ba Mami ta buga wani uban tsalle.

"Aure aure dana sani shi Sadeeq ke auran wannan tsintacciyar magen, billahil azim bai isa ba in dai ina raye sai ya rabu da ita."

"Haba Halima da girmanki gaban yara kina irin wad'annan abubuwan, kibi komai a hankali mana."

Fad'in Abba cikin nuna 'bacin rai.

"In bi a hankali a cuci d'ana?" 

"Ba maganar cuta, yau ba gobe ba za mu garin su Ummu dan binciken asalinta."

"Da wa?"

"Ni da Sadeeq."

"Ai wallahi kafata kafarku muje ya sakar musu y'arsu a gabana a gabansu."

Takaici ya hana Abba cewa komai ya tashi ya kalli Sadeeq.

"Tashi muje Sadeeq."

Tashi yayi daga zaunen da yake ya mike tsaya, Abba yayi gaba ya bisa a baya bayan ya d'aga Ummu suka bi bayansa, parking space su kayi, motar Sadeeq suka shiga, Abba da Sadeeq a gaba, Ummu a bayan wacce kwanciya tayi dan zazzabine ya zuba mata ga uban yunwar da take ji.

A haka Sadeeq yaja motar suka fita a gidan, sunyi nisa da tafiya Sadeeq ya tsaya a wani restaurant ya tsiya Ummu abinci, kan su d'au hanya, kad'an taci abincin wanda yake dankaline da kwai, bayan ta gama tasha ruwa ta kwanta bayan motar, nan bacci ya d'auketa,

Bayan fitarsu a cikin garin Katsina, hanyar k'auyen Anguwar Liman Sadeeq ya d'auka.


 HASKE YA BAYYANA...Sadaukarwa ga Ummu A'shat(Ummi Safwaan)PhartyBb.WordPress.com

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


 SANADIN HA'DUWARMU

  ©PhartyBB


   Wattpad@PhartyBB

24


 Karfe sha daya na rana da mintuna suka iso 'kauyen, a hanakali yake bin hanyar da yasan zai sa dasa da cikin k'auyen kamar yanda ya tab'a zuwa shekaru hudu da suka wuce, an samu ci gaba da sauyi da d'an dama cikin k'auyen.

Bangaren Abba ji yayi zuciyarsa ta shiga wani irin yanayi marar misaltuna, jini da jijiyoyinsa na aika masa wani sak'o zuwa ga kwakwalwansa, hasko masa wani hoto yake wanda shud'ewarsa kusan shekaru arba'in da wani abu, ya kasa k'aryata abinda idonsa ke gane masa, 'Tabbas nanne' abinda zuciyarsa yace masa.

Jan motar Sadeeq yayi har kofar gidan Mai Gari, gefe yayi parking, mutane da dama na kallon motar ganin bak'uwar mota.

Juyawa Sadeeq yayi ya kalli Abbansa da gaba d'aya yanayinsa ya canza gaba d'aya.

"Abba."

Kallonsa Abbansan yayi yana murmushin yake.

"Na'am Sadeeq."

"Mun iso fa ga can fad'ar Mai Gari zamu 'karasa sai a nuna mana gidansu."

"To muje."

Fita Abba yayi Sadeeq ma ya fito ya bud'e gefe inda Ummu ke kwance, ta data yayi ta farka ras suka had'a ido, ta sunkuyar da nata idon k'asa.

"Sauk'o."

Yace da ita, ta fito tana bin garin da kallo, tabbas garinsu ne, kallonsa tayi da sauri taga ita yake kallon dan ganin reaction nata, sunkuyar da kanta ta k'ara yi k'asa, ganin haka ya sashi yin gab,a yayi inda Abba ke tsaye yana jiransa.

Sadeeq ne ya musu jahoran zuwa wajen jama'ar gurin, sallama suke musu gaba d'aya suka amsa suna binsu da kallon, mutan gurin sun gane Sadeeq da Ummu banda Abba da mutum d'aya yaso gane mai irin fuskar da rabonsa dashi shekara arba'in.

"Kamar Abubukar da Ummu nake gani."

Fad'in Mai gari yana murmushi.

"Mune Mai gari sai yau Allah yayi dawowar mu."

Fad'ad'a murmushinsa Mai gari yayi yana bada umarnin a shimfid'a musu darduma.

"Bismillanku ku zauna."

Zama su Abba su kayi nan aka umarci Ummu data shiga gida wajen matan Mai gari, da shigarta nan aka gaggaisa, Sadeeq ya gabatar da mahaifinsa wato Alhaji Sulamain Ahmad.

"Sulaiman Ahmad wanda na sani tsawon shekaru arba'in da wani abu nake kallon gizon fuskarsa akan fuskar Mahaifinka duk da jikin girma da yake tattare dashi."

Fad'in Malam Haruna daga gefe.

Abbane ya kai kallonsa ga inda yaji muryar mai maganar, yaso gane fuskar amma ya mance ina yasan fuskar, dan fuskar ya tsufa sosai yanayin rayuwar k'auyen.

"Tabbas bawan sunana Sulaiman Abba kuma ina ganin k'auyen kamar wani guri dana tab'a fara rayuwata shekarun baya, sai dai na mance fuskarka da fuskar mutane da dama."

Cewar Abba na juye-juye ko zai ga wani abu da zai bayyana masa duhun da ya shiga tin zuwansa k'auyen.

"Alhaji Sulaiman zaka iya tuna Muhammad da Innah."

"Muhammad! Innah!."

Shine abinda Abba yace zuciyarsa na bugawa.

"Ka tuna su?"

Cewar Malam Haruna daya gama fahimtar komai, 'Tabbas shine' cewar zuciyansa.

Dum Abba yayi ya rik'e kansa da yayi nauyi, a hankali ya fara tuno rayuwarsa na baya.

Su biyu mahaifiyarsu ta haifa shida kaninsa Muhammad, tin suna k'anana Mahaifinsu ya rasu, sunyi karatun islamiyya dai-dai gwargodo, in da bayan kammalawansu, shi ya nemi sana'a wajen wani mai shago a cikin kasuwa, yana zama masa in ya tashi yana biyansa, haka har ya tara d'an kud'ad'ensa ya bud'e d'an k'aramin shagonsa, nan Allah ya albarkaci abin, da d'an sana'arsan yake kula da Mahaifiyarsa da k'aninsa, cikin wannan halin har ya fara fita cikin garin Katsina shida Uban d'akinsa suna saro kaya, anan cikin garin Allah ya had'a jininsa da wani mai Babban Plaza inda suke saran k'aya, nan ya d'auki Sulaiman tamkar d'ansa kyautata masa yake sosai, nan cikin k'auyen ya zama shida k'aninsa sun zama abin kwatance, cikin wannan halin samarin k'auyen suka fara jin haushinsa, kwatsam rana d'aya aka nemi Sulaiman aka rasa, wanda hakan baya rasa nasa ba da asirin da wani saurayi cikin samarin kauyen ya masa.

D'ago idonsa Abba yayi ja da kyar ya furta.

"Haruna ina suke? Ku fad'amin ina suke?"

Shuru gurin ya d'auka, wasu na mamakin wannan na gabansu Alhajin shine abokinsu, wasu na al'ajabi.

Sadeeq kam kansa ya d:aure gaba daya ya rasa meke shirin faruwa, shi abinda su kazo daban abinda yake shirin faruwa daban. 

"Haruna ka fad'amin mana, ku fad'amin, ina suke?"

Ajiyar zuciya Malam Haruna ya sauke kan a hankali cikin nutsuwa da dabara ya fad'a masa cewa, bayan tafiyarsa Mahaifiyarsu ta rasu, inda shi kuma Muhammad yayi aure har mata biyu d'ayar sun rabu wanda basu san dalilin rabuwarsu ba, ta bar yarinya 'daya, dayar kuma na nan ita da y'aranta uku, shi kuma Muhammad Allah ya masa cikawa shekaru shida da suka wuce.

Duk juriyan Abba ji yayi zuciyarsa ta karaya, hawayene suka zubo masa yayi saurin d'aukesu, tabbas shi kansa lokacin bai san me yake damunsa lokacin da abin ya faru ba, rana daya yaji zaman k'auyen ya ishesa, ya tsani k'auyen.

Kallonsa ya maida kan Mai Gari.

"Ko za'a iya nuna min iyalan Muhammad."

Murmushi Mai gari yayi yana cewa.

"Ai Ummu itace d'ayar y'arsa da matarsa ta bari, d'ayar kuma gidanta na can layi na biyu."

"Wace Ummu?"


  CAKWAKIYA...._Wannan page din naku ne Aunty Sis, Aunty Mejiddah, Mum Fateey, Hajjah ce._Sadaukarwa ga Ummu A'ishat (Ummi Safwaan).

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


   SANADIN HA'DUWARMU

     ©Pharty BB


  Wattpad @PhartyBB

25 


  "Ummu matar Sadeeq."

Fad'in Maigari murmushi kwance saman fuskarsa.

  "Allahu Akbar, Allahu Akbar."

Haka Abba ya jera yana fad'a kusan sau goma kafin ya iya bud'e baki yace.

  "Allah kenan mai yin yanda yaso, SANADIN HADUWAR Ummu da Sadeeq ya bayyana wani 'boyayyan sirrin dake rufe, Allah na gode maka daka sadani da ni'imarka na dawo dani mahaifata."

 Nan gurin aka yi ta mai da zance, Sadeeq kam ya zama d'an kallo dan gani yake abinda ke faruwa tamkar a shirin film, sun dan jima a wajen a gidan mai gari aka kawo musu abinci da fura da nono kindirmo mai kyau.

Sunci sunsha Abba yayi hira ya gana da mutanen gari da dama wanda ya sani ada, kafin yasa Malam Haruna yi masa jagoran gidan Abulle bayan an k'ira Ummu.

A motar Sadeeq ne da Ummu a baya, ta takure, gaba kuma Malam Haruna da Abba.

 Da kwatancen da Malam Haruna yake musu suka isa har kofar gidan, fiffita su kayi gaba d'ayansu, ganin duk suna fita yasa Ummu ma fitowa, ganinta gaban gidansu ya sata yin baya a tsorace.

"Y'ata."

Abba yace yana isowa kusa da ita.

Kanta a k'asa tace.

"Na'am Abba."

"Kin gane nan gidan?"

Ya fad'a yana nuna gidansu Ummu, kai ta daga masa alamar eh.

"Shiga ciki ki mana sallam da matar gidan kice tayi bak'i ta basu izinin shigowa."

"To Abba."

Tace tana fara takawa da bismillah a bakinta dan ba zata tab'a mance Abulle da halinta ba, matar da ta kusa jefa rayuwarta a halaka.

Sallam tayi a zauren gidan, shuru sai kukan yaro da ke fitowa, sau uku tana yi ba amsa ya sata kusa kai cikin gidan, ba kowa a filin gidan sai yaro dake zaune d'an shekara goma yana kuka, kallon gidan ta tsaya yi ba abinda ya canza daga yanda yake sai dan gyara da aka masa.

Hawayen daya zubo mata ta share tino da tayi da Mahaifiyarta data watsar da ita tayi tafiyarta, sai kuma Marigayi Mahaifinta, sallam tayi jin motsi a d'ayar dakin da yake mallakin Innarta a da.

Daga ciki aka amsa.

"Wai waye haka yake kwad'a sallama da yamma sakaliya haka."

Fad'in Abulle na d'aga labulen kofar, tabbas ko za'a shekara dubu baza ta manta fuskar ba.

"Ummu!"

"Na'am Dadah."

"Kece kika koma haka? Ina kika shiga?"

"Dadah..."

Sallamar Laurene ya katse Ummu daga abinda zata fad'a, juyawa Ummu tayi.

"Ummu!"

Laure ta fad'a da karfi tana yin kan Ummu, itama Ummu gurinta tayi, suka rumgume juna sai kuka, tabbas sunyi kewar juna ba kad'an ba.

"Ummuna ina kika shiga? Nayi addu'an Allah bayyanar min ke har na gaji."

"Ina nan Laure cikin koshin lafiya."

"Allahdulillah."

Cewar Laure na kama hannun Ummu ta shimfid'a mata taburma ta zauna.

Juyawa Laure tayi ta kalli Innartan dake tsaye kamar gunki.

"Innah wasu baki a kofar gida da babbar mota."

"Ni na taho da su, mutanen da nake hannunsu tsawon shekarun dana d'auka a gurinsu nake."

Tashi Laure tayi.

"Bari in shigo dasu."

Ta fad'a tana dosar kofar gida, nan ta gaishe dasu wanda har sun fara gajiya da jira, jagora ta musu zuwa cikin gidan ta shimfid'a musu taburma suka zauna, ta shiga d'aki kiran Innarta data shige d'aki tin jin sallamarsu.

Da kyar Laure ta shawo kan Abulle suka fito, kujera ta zauna tana gaishesu.

Amsawa su kayi shuru ya biyo baya kusan mintuna biyar kafin Abba yace.

"Kamar Abulle."

Kai ta d'ago tana kallon mai maganar, taso ganesa amma ta mance.

"Eh nice."

Ta fad'a tana juyar da kanta sai wani ciccin magani take.

"Zaki iya tunawa da Yayan Muhammad, Sulaiman."

Birkito da kallon tayi kansa tana tashi tsaye.

"Sulaimanu kai ne?"

"Nine Abu Allah yayi zan dawo."

Komawa Abulle tayi ta zauna tana sauk'e ajiyar zuciya.

"Bayan tsawon lokaci da aka d'auka bana nan, na dawo tare da y'ar kanina wacce ta fad'a hannunmu wato Ummu, inda a rashin sani muke zaune da ita tsawon shekaru hudu."

Banda bugu ba abinda zuciyar Abulle ke yi, tabbas tasan Sulaiman yYyane ga Muhammad kafin barinsa garin, yana nufin Ummu y'ar 'kaninsa ne.

"Ga d'ana miji ga Ummu."

Fad'in Abba na nunawa Abulle Sadeeq.

Kallonsa Abulle tayi, ta kallesa ta k'ara kallo, tasan Ummu ta musu nisa, nesa ba kusa ba.

"Allah sanya alheri."

"Ameen." suka ce.

Ummu ko ido ta d'go da sauri jin abinda Abba yace, Miji, Miji, Ya Sadeeq Mijinta, 'Yaushe aka yi auren? Shine abinda ta fad'a a zuciyarta.

"Ina sauran Yaran in gansu."

"Ga d'ayar Laure ga can d'aya Ja'afar babbar bata nan."

"Allah ya musu albarka zaki ban d'aya na tafi dashi."

"Wa! Ni Allah kiyaye."

Fad'in Abulle na tashi tsaye.

"Haba Abulle kar kice haka mana, ina son had'a kan yaranne in sada su da y'an uwansu, akwai y'ay'ana saura uku gida ina son had'asu su gaisa."

"Kaga Sulaiman ina jin kunyarka tin kan na daina ku fitarmin a gida, ba abinda ya had'a yarana da yaranka, Ummu ce taku kuje nabar muku ita."

Tana fad'ar haka ta shige d'aki.

Laure ta kalli Abba kwata-kwata ta tsani halin mahaifiyarta, kanta ta sunkuyar k'asa.

"Abba kayi hakuri dan Allah, ni zan biku muje, gani ga Ummuna."

Murmushin manya Abba yayi yana tashi.

"Shikenan, Allah miki albarka."

"Ameen."

Tace tana tashi, gaba d'aya tashi suka yi daga zaunen da suke basu bi takan Abulle suka fita bayan Abba yaje ya damk'a Ja'afar kufi dubu talatin.

Da fitarsu anan ma Abba sallama yayi da Malam Haruna bayan ya masa kyautan kudi.

Mota suka shiga , Sadeeq ne ke ja haka suka d'au hanyar Katsina.


Karfe taran dare suka isa gida, bayan yayi parking suka fito, nan Laure ta saki baki tana kallon gidan duniya.Babban falon gidan suka nufa da sallama, bayan shigarsu gaba d'aya ahlin gidan suna zaune, jin sallamarsu yasa su juyowa.

Tashi Mami tayi bayan ta taro mai gidantan ta kallo Ummu ta watsa mata harara.

D'akin Abba suka wuce Sadeeq ma ya wuce nasa, gaishe da Sultaan, Ummu tayi ya amsa, taja Laure suka wuce d'akinta na da.

Wanka su kayi suka gabatar da sallolinsu, kafin suka zauna hiran bayan rabuwa, nan Ummu taba Laure rayuwar da tayi baya da wanda take ciki yanzu, Laure ta tausaywa rayuwar Ummu sosai harda guntun hawayenta.

Banko kofar d'akin aka yi aka shigo, Rahmace.

"A fito a ci abinda ba'a saba ba."

Tana fad'ar haka ta fita a dakin, kallon Ummu, Laure tayi tana girgiza kai.

"Haka kike rayuwa dasu?"

Kai Ummu ta d'aga.

"Tab nikam bazan d'auki wannan rainin ba, zan saita yarinya tsaf."

"Kai Laure na ban sanki da haka ba, please karki kulata."

"Matsoraciya har yanzu kinanan da tsoronki, tashi muje muga abinda bamu saba ci ba y'ar rainin hankali."

Tashi Ummu tayi ta saka Hijab nata suka fita.

Gaba d'aya Ahlin suna saman dinning, 'karasawa su kayi Laure taja kujera ta zauna, Ummu ta tsaya kanta k'asa.

"Zauna mana Ummu."


Abba ya fad'a mata, Kujera taja ta zauna.

Bayan kowa ya nutsu Abba ya bud'e taron gurin da addu'a sannan ya sanar dasu komai tin daga farko har karshe.

Kowa gurin ji yayi jikinsa yayi sanyi dan jin Ummu wai yar 'kanin Abbansu ne, banda Mami da jin abin take kamar tatsuniya.

Bayan Abba ya gama jawabinsa ya tambaya ba mai magana su kace babu.

"To masha Allah, Allah had'a kanku, kai kuma Sadeeq kasa a gyara d'ayan side din dake cikin main falon, upper Week Ummu zata tare."

"To Abba."

Abinci su kaci kafin suka watse ko wanne ya wuce dakinsa.


******


 Washegari karfe tara na safiyar laraba, da sallama ya shiga d'akin mahaifiyar tasa cikin shigar coat baki da fari, saman kan kujeran dake cikin dakin ya zauna yana fuskantar Mami dake zaune tana duba wasu kaya.

"Mamina ina kwana."

"Lafiya." Tace tana cigaba da abinda take.

Ganin haka ya sashi tashi yana nufan inda take, zama yayi.

"Mami tin jiya naga kina fushi dani, Lafiya? Laifin mai na miki?"

Kallonsa tayi, kallon tara saura kwata.

"Ka yarda da abinda Abbanku yace kenan."

"Na yarda Mami, jinin muce, 'yar uwar muce."

"Kuma za kayi abinda ya fad'a?"

"Eh Mami."

Kallonsa Mami tayi da kyau.

"To ban amince maka ka d'auki wannan yarinyar ka kai ta gidanka ba, in kayi haka ban yafe ma ba."

A razane ya juya ya kalleta.

"Mami...."

"Shiiish bana son musu Sadeeq, na riga na gama magana."

Shuru Sadeeq yayi ya rasa ta cewa kafin a hankali ya mik'e.

"Shikenan Mami Allah yasa haka shi yafi alheri.

Bata ce masa kala ba har ya fita a d'akin.
Sadaukarwa ga Ummu A'ishat (Ummi Safwaan).

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


  SANADIN HA'DUWARMU

   ©Pharty BB


  Wattpad @PhartyBB

26


  Sati biyu da kwanaki da maganar da Abba yama Sadeeq amma ya kula Sadeeq bai fara komai ba na daga gyaran gidan ba, hakan yasa ya tambayesa dalili.

Boye gaskiyar abinda ke faruwa Sadeeq yayi, ya nuna da abarta ta gama makarantarta nan da wani shekara, Abba dai a jikinsa yaji akwai abinda ke faruwa amma ya bari nan da lokacin yayi, in ya zo masa da wata magana, zai nema mata takardan saki.

Haka Rayuwar taci gaba da tafiya, Ummu taci gaba da zuwa Makarantarta inda take Ss2 zata 3, tsakaninta da mutanen gidan gaisuwa sun daina hantarar da da suke nuna mata banda mutum d'aya Mami, sai Sultaan da yake sakar mata fuska sosai suka rik'e zumuncinsu da 'yan uwantakansu, tsakaninta da Sadeeq ba abinda ya canja daga gaisuwa in sun had'u ba komai, ita mugun tsoransa take ji, shi kuma gani yake zata rainasa in ya sakar mata.

Laure ma na rayuwarta a gidan dai ba laifi, gidan duk wanda ya mata ba dadi mayar masa take, Rahma har shakkan fad'a mata magana take, dan ramawa take wanda in ta fad'a mata ji za tayi dama bata fara fad'a mata ba.


   BAYAN WATA 'DAYA

 Su Ummu sun gama jarabawar aji biyar zasu tafi aji shida, hutu aka basu na wata biyu.

Bikin Rahma da akasa rana saura sati biyu, murna suke sosai musammam Mami jin wannan karon bikin a gida za ayi ba sai sunje Batagarawa ba.

Tin ana bikin saura sati mutane y'an uwa dake Batagarawa suka fara zuwa, ana kwana hudu Uncke nasu Saminu Yaya ga Mami, ya iso shida matarsa da yaransu da Adda Munira daga Kaduna, wacce a gurinsa take zaune.

Mutan Funtua da Daura duk sun iso, Mami sai murna ta rasa inda za tasa yayyunta da k'annenta.

Su Ummu kam sune kan aikin abincin gida su da Iyamee, girki za suyi sau kusan shida a rana, Gajiya kam suna kwasarta.

Yau aikin da su kayi shi ya haddasawa Ummu zazzabi, da kyar ta iya wanka tasha paracetamol ta kwanta ko abinci ta kasa ci, lokacin karfe bakwai na dare.

Sallama a kayi daga bakin kofar d'akin, Laure ce ta amsa tana tashi, lekawa tayi taga y'ar budurwa tana tsaye, da murmushi Laure tace.

"Sannunki."

"Yawwa Sannu, ina Ummu?"

"Tana Bacci bata jin dadi."

"Ya Sadeeq ke kiranta a Parking Space ko zaki iya tashinta."

"Kice masa bata da lafiya."

"To Allah sauwake."

Yarinyar ta fad'a tana barin wajen, komawa Laure tayi d'akin taci gaba da abinda take yi, zamanta bai dad'e ba aka kara sallama, tashi tayi tana tsaki ta bud'e kofar, budurwance.

Mik'a mata ledan hannunta tayi guda d'aya.

"Gashi inji Ya Sadeeq a bawa Ummu, wannan kuma naki."

"To kice masa mun gode."

Ta fad'a tana karb'an ledodin, ta koma d'aki.

Da shigarta ta warware kayane dinkakku had'addadu ko wanne da d'ankunnensa da sarka da gyale, na Ummu kala uku nata kala biyu, tsannan na kowa da kalarsa.

Mai dawa tayi ta rufe ta ajiye inda ya dace.


****


 Washe gari Laraba a ranar za suyi Kamu, an ma gurin kofar shiga da hoton cartoon Kitty pink kala, kana dosar kofar zaka hango inda amarya zata zauna.

An kwata filin gidan da kujeru da tables da rumfa a saman table, komai na gurin Pink, kasancewar a gida za suyi suka 'kira mai Decoration ya musu.

 Inda Amarya zata zauna har yafi kyau dan da kwalliyar Pink aka kawata gurin a gaban gurin an rbutu kalmar ANGELA1 da manyan bak'i, ga cake a saman Table din gabanta a ajiye shima pink mai hawa biyu, ga hoton cartoon kitty.


Karfe bakwai suka soma gabatar da hidima, kawayen amarya sun sha farin gown, inda ya kara kwata gurin, can na hango Hauwaty da Biebie suma cikin gown fari, na Biebie sak irin wanda Laure ta ware cikin kayan da Sadeeq ya aikowa Ummu.

Kid'a ne a gurin ke tashi na fitar hankali rawa kam ranar sun shata ba kad'an ba, har karfe sha biyun dare abu d'aya suka d'auka suna yi.

Bangaren Ummu kam zazzabine ya sata gaba ko gurin bata samu zuwa ba, sai Laure da ta tsaya ganewa idonta daga baya

****

 Washe gari Alhamis suka yi dinner inda shi kuma hall din aka kara k'awatasa da adon pink da fari mai hoton twinkle-twinkle.
Kamar jiya inda Amarya zata zauna da adon pink aka kawata gurin haka yau, dan har yaso yafi na jiya kyau, aka jera kujeru da dogon table, ga baloons blue.Karfe takwas suka fara dinner inda amarya taci kwalliyarta cikin farin gown kawaye kuma light blue, sai kwalliyar suka kara k'awata gurin.


Karfe takwas suka fara dinner inda amarya taci kwalliyarta cikin farin gown kawaye kuma pink, sai kwalliyar suka kara k'awata gurin.

Manya da yara da Aunties duk sunzo, anci ansha an darje, ansha rawa, karfe goma suka gama suka dawo gida.

Duk wannan bidirin da suke ba ko d'aya da Sadeeq ya halarta, rabonsa da gidanma tin ranar da ya bada sakon Ummu akai mata.


 Washegari Jumma'ah karfe goma aka d'aura auren Rahma da Angonta Mahmud, da dare aka kai Amarya gidanta, washegari mutane suka fara tafiya.

Kan kwana uku kowa ya watse ya rage gidan sai 'kannen Mami mata.

  

****

  Zaune suke a babban falon Mami gaba d'ayansu matan dasu da yaransu, lokacin karfe biyun rana, abinci suke ci banda kwaya d'aya da take duba wani littafi.

"Munni ke baza ki ci abincin ba?"

"Eh Mami ba yanzu ba, dama zan samu kunu."

"Kunu, gashi yarannan basu dama ba, bari in sa su dama miki."

"Su wa kenan?"

"Wasu mana wai dangin Abban Sadeeq, dole wai yaran 'kaninsa ne."

"Ok daga ina kenan suka zo?"

"D'ayar muna tare da ita tsawon shekaru hudu ba wanda ya sani sai zuwansu garinsu yarinyar ya gano wai y'ar k'aninsa ne, Jameela lek'a dakin can kice Ummu tazo."

"To Mami."

Yarinyar da aka k'ira da Jammela tace tana tashi ta nufi hanyar d'aki.


   


       TO FA!!!!


Sadaukarwa ga Ummu A'ishat (Ummi Safwaan)

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


SANADIN HA'DUWARMU

 ©Pharty BB


  Wattpad @PhartyBB

27


 Tashi Munirat tayi daga, zunen da take, kallonta ta mai da kan Mami.

"Bari in shiga ciki, in ta gama ta kai mun sama."

"To shikenan."

Da kallo Mami ta bita kallon tausayi, kwana biyu tana kula kwata-kwata bata jin dadi.


 A hankali ta doso cikin falon dan amsa kiran Mami, da isarta sallama tayi k'asa k'asa cikin sanyin muryarta, kalilanne su kaji sallamar suka amsa.

Kusa da Mami ta k'arasa ta tsugunna.

"Mami gani."

"Kunu zaki had'a na gyad'a."

"To Mami."

Ta fad'a tana tashi, kitchen ta nufa nan ta tarar da Iyamiee na wanke-wanke, bayan ta gaisheta, Iyamiee ta bita da kallo ganin duk kamar jikinta yayi sanyi.

"Lafiyarki Ummu?"

Murmushin karfin hali tayi.

"Lafiya lau."

"Anya? Kin tabbatar."

"Umm." tace tana d'aga kanta

Kokarin had:a kunun ta fara tana yi tana hutawa dan karfin hali take yi bata jin dad'in jikinta kwata-kwata.

 Da kyar ta samu ta gama, ta zuba cikin Jug mai kyau wanda ba zai huce ba, ta dauk'a ta fita, falon ta koma, yanda ta barsu haka tazo ta samesu, gefen Mami ta ajiye had'e da cup.

"Mami gashi nan na gama."

"Ce miki a kayi ni nake so, kaiwa Munirat tana d'akina."

"To Mami."

 Tace tana dauk'a ta nufi saman beni dan kai mata, tana cikin tafiyar taji zuciyarta yana buguwa da sauri wani sanyi na ratsata, a haka ta daure ta ka rasa bakin kofar d'akin.

Kwankwasawa tayi aka bata damar shiga, da sallama ta bud'e ta fara zura kafarta kafin ta shigo gaba d'ayanta, a hankali ta d'ago idanuwanta ta fara kalle-kallen dan neman inda zata ajiye, nan tayi arba da wacce Mami ta kira da Munirat.

Zaune take ta juya bayanta tana duba wani littafi dake hannunta.

Kan wani center table d'an k'arami idon Ummu ya kai ta taka a hankali ta ajiye.

"Ga kunun."

Kuwww muryanta ya doki dodon kunnen Munirat, jini da jijiyoyin jikinta suka d'an dena aiki na dakiku, muryar na mata yawo a kwanyar kwakwalwarta.

Juyawa Ummu tayi ta fita jin tak'i mata magana, Ummu ji tayi ta k'ara kin jinin Mami cewarta duk suna da girman kai da wulakanta talaka.

A razane Munirat ta juyo gani tayi ba bata nan ga kunun ta ajiye, da hanzari ta tashi ta fita a d'akin.

Ummu ta sa kafarta d'aya zata gama sauk'a a stairs ta tsaya cak sakamakon kiranta da taji tayi daga sama.

"A'ishat."

Muryar ta ratsa zuciyarta, kamar tasan mamallakiyar muryar, juyo da kanta tayi dan jin abinda zata ce, ido hudu suka had'a.

Wasu abubuwane masu muyan fassarawa suka dinga ji game da junansu, tabbas in ba ita bace mai kama da itane, bata kai haka girma ta barta ba, bata kai haka haske ba, bata kai haka wayewa ba, uwa uba mai ya kawota gidannan, 'Aikatau'.

Abinda zuciyarta ya fada mata, sauk'owa tayi tana binta da kallo har ta 'karaso.

D'ago ido Ummu tayi tana binta da kallo.

Murmushi Munirat tayi tana d'aura hannunta saman fuskar Ummu.

"Allah kasa burina da mafarkina da nake tsawon shekaru shi nake gani a zahiri, Allah ka sadani da 'yata farin cikin rayuwata, burina ako da yaushe."

Kan Ummu tayi wani yunkuri Munirat ta rumgumeta tsam tare da fashewa da kukan da ya jawo hankulan mutanen falon.

Da sauri zuka taso suna k'arasawa wajensu.

"Ke lafiyarki Munirat, ko duk son yarki ke neman zautaki kina rik'e yarinyar mutane."

Sakin Ummu, Munirat tayi gani tayi ta kasa tsayuwa da kafafunta ga idonta rufe, ihu tasa musu.

"Ku taimakamin karta mutu ta barni wallahi y'atace, itace, Badd'ona ce, Ku taimakamin."

Gaba d'aya mutanen gurin ji su kayi abin wani irin, barin Mami data tabbatar kanwarta ta fara zautuwa, in ba haka ba ya za tayi tace Ummu y'artace yarinyar da ba a san asalin uwarta ba.

Cikinsu Adda Salamatune tayi karfin halin d'aga Ummu suka ajiye kan kujera.

"Jameela duba Sultaan in yana waje yazo ya dubata."

Yarinyar da aka k'ira da Jameelah ce ta tashi ta fita da gudunta ta fita 'karasa wajen da su Sultaan ke zaune.

"Ya Sultaan kazo inji Mama zaka duba wata yarinya ta suma kuma Adda Munirat nata kuka."

Cikin sauri Sultaan ya tashi ya nufi cikin gida, Sadeeq ma dake zaune shida Ameen suka bi bayansu dan ganin meke faruwa.

Da isar Sultaan cikin falon yaga Ummu a kwance saman dogon kujera, yana kok'arin d'agata Sadeeq ya shigo, ya mutukar tsorata da ganinta a kwance.

Da sauri ya 'karaso wajen.

"Let me help you."

"Ok."

Cak Sadeeq ya d'auketa bai tsaya ko ina ba sai d'akinta, duk wannnan budirin da ake Laure na bacci, jin hayaniya a d'akin ya sata bud'e idonta ganin mutane tseye saman kanta ya sata tashi a tsorace.

Kwantarta Sadeeq yayi, Sultaan ya rok'esu da su jira a waje, gaba d'aya suka fita banda Sadeeq, cikin sauri Sultaan ya fara bata taimakon gaggawa, da kyar numfashinta ya dawo dai-dai ya mata alluran bacci.

"Ta samu bacci, zata iya farkawa ko wani lokaci."

Sultaan ya fad'awa Sadeeq dake tsaye ya hard'e hannunsa a kirjinsa.

"Okey Thanks."

"It's my pleasure."

Fita su kayi a 'dakin, da sauri Munirat ta k'araso wajen su, hawaye duk ya bata fuskarta.

"Ya take, ta farfad'o, ku fad'amin ya jikin 'yata."

Kallon-kallo suka tsaya yi tsakanin Sultaan da Sadeeq jin abinda Munirat take fad'a.

Rik'o hannun Sultaan Munirat tayi dan sanin shine Dr.

"Sultaan ya jikinta."

"Anti Munirat ki kwantar da hankalinki, numfashinta ya dawo dai-dai na mata alluran bacci, zata iya farkawa ko yaushe, sannan akwai abu d'aya da take dashi wanda sai anje asibiti dan tabbatar da abin."

"Zan iya shiga?" Ta tambayesa.

"Eh amma banda hayaniya."

Bata jira ya k'arasa ba ta shege 'dakin, k'arasawa su Sultaan su ka yi wajen iyayensun.

"Wai meke faruwa?"

Shuru su kayi da kyar Adda Salamatu tayi karfin halin fayyace musu cewa, sam Munirat ta dage wai Ummu Y'artace data bari tin shekaru shida da suka wuce.

Jin zance su kayi wani a juye, ya hakan zata faru, Abbansu ya gama fad'a musu y'ar k'aninsane, yanzu kuma ana kawo wani magana, suna nufin y'ar kanwar Maminsu.

Sadeeq ne ya kai kallonsa kan Mami, ido ya raina fata, fuskarta ya karye sosai, ya san Mami ta tsani Ummu tsani mai tsanani wanda Manzon Allah yayi hani a kansa, gashi ta tsani yarinyar 'yar uwarta wacce tamkar ita ta haifeta.

Kawar da kansa yayi yana barin wajen.


 Ba Ummu ta farka ba sai karfe biyar na yamma, da salati ta bud'e bakinta, tsaf idonta akan Munirat.

Runtse idon tayi, hannu Munirat ta d'aura saman gashin kanta.

"Nasan kin tsaneni y'ata, na tafi na barki a lokacin da kike tsananin buk'atana, yin hakan gareni nima ba ason rai na bane, ki yafemin, ki bud'e idonki ki kalleni, na san duk duniya ba abinda kike da buri kamar ki sake kallona, ga lokaci yayi Allah ya had'amu, Sadeeq ya fad'amin komai, da duk irin wahalar rayuwar da ki ka sha, SANADIN HA'DUWARKU alherine, ya sadamu, please ki bud'e idonki."

A hankali Ummu ta bud'e idanuwanta hawaye na zuba, kok'arin tashi ta fara, Munirat ta taimaka mata ta tashi.

"Kin min Alkawarin ba zaki 'kara yin nesa da rayuwata ba, zaki ban farin cikin dana rasa da jin dadi a baya."

"Zan baki 'yata, zan baki."

"Nayi kewarki Innana, kin tafi kin barni lokacin da nake tsananin bukatarki, Baffa ya zamemin shine jik'on rayuwata, shima ya tafi ya barni, na zama marainiya, marar gata, marar asali."

Rumgumeta Munirat tayi.

"Insha Allah ba zaki kara kukan maraici ba, insha Allah."

Kuka suka sa gaba d'ayansu sai da su kayi mai isarsu sannan Munirat tayi karfin halin sake Ummu.

"Kiyi Sallah, muje kici abinci, in nuna miki y'an uwana."

Tashi Ummu tayi ta nufi bathroom, Alwala ta d'aura ta fito tayi sallolinta kan su fita, gaba d'aya familyn suna falo, jin fitowarsu ya sa su mai da kallonsu garesu.

Har suka k'araso falon munirat ta zauna, Ummu ta zauna 'kasa.

"Badd'ona ga y'an uwana mata duk uwa d'aya uba d'aya muke, duk da kamar baza ki mance Addah Salamatu ba, gata nan, sai mabiyarta Adda Halima, sai Addah Habiba, sai ni."

D'ago kanta tayi tana binsu da kallo, me take nufi? 'Yan uwan Mami sune 'Yan uwanta?

"Inna wad'annan ai 'yan uwan Mami ne?"

"Eh, nima 'yan uwa nane, Mami Yayatace."

Zaro idonta tayi tana tashi.

"Inna..."

Hannunta ta kamo ta zaunarta.

"Kiyi hakuri a madadina na rok'awa Mami gafararki a bisa hantara da duk abinda ta miki duk cikin rashin sani ne, wad mun yare(Kiyi hakuri)."

Girgiza kanta tayi, dan ita kad'ai tasan kalar wahalar da tasha a hannunta.

Tashi Mami tayi daga zaunen da take ta k'araso wajensu, ba shiri Ummu ta zauna dan ita har yanzu tsoranta take ji, d'agota tayi, jikinta har rawa ya fara.

"Ki sawa ranki hakuri ki yafemin da irin abubuwan dana miki, dama ance in zaka tsani mutum ka tsanesa dan wani hali nashi wanda yake sab'awa Allah, ba irin nawa tsanar ba, wanda ba abinda ya haifar sai dana sani, in zaka taimaki mutum ka taimakesa ko ba kowa naka bane dan baka san wa zaka taimaka ba, wala d'an uwanka na jini ko wani, nayi watsi da damata da komai na, ina neman yafiyarki bisa abinda na miki."

"Mami ki daina rok'ona, na yafe miki nasan duk a rashin sanine."

Hawayen kan fuskarta Mami ta share mata.

"Na gode 'Yata."

Btace komai ba dan jin sunan data kirata dashi.

Ranar Iyalin gaba daya sunyi farin ciki da jin Sirrin B'oye ya bayyana, har Batagarawa aka kira aka fad'a, yan matan da suke gidansu ko Allah-Allah suke gari ya waye suje kallon 'yar uwarsu, yar Antinsu Munirat.

Bangaren Sadeeq har dare abinda Sultaan ya fad'a na damunsa akan akwai abinda Ummu take dashi dan duba da gaskene suje asibiti.

Ko meke damunta?.


***

 Da safe karfe tara gidan ya fara cika da 'Yan uwa, su Biebie sai karfe goma ta zo ita da Sadeeq sai wani yauki take, su Hauwaty tazo da 'dan cikinta daya fito.

Gaba d'aya familyn na babbar falon gidan, sai hayaniya ake, karfe sha d'aya Kausar ta iso itama da d'an cikinta, a tsorace ta zo gidan Mami dan gudun had'uwarta da Ummu kar har yanzu kallon baya take mata.

'Yan matan sai baza ido suke su ga bak'uwar fuska, amma basu gani ba sai ma ganin abinda yasa su mamaki, Ummu ce zaune kusa da Mami, ba alamar tsana da a tattare da fuskarta.

"Anti Munirat wai ina k'anwarmun."

Fa'din Hauwaty na zama gefenta.

"Gata gefen Maminta."

"Wa?"

"Gata Ummu, yar Antinki, Mata ga Yayanki Sadeeq."

Fad'in Addah Salamatu da take zaune gefensu.

Da karfi Hauwaty ta fara magana.

"Wannan tsintacciyar ita ce y'arkin kuma mata ga Ya Sadeeq, yaushe hakan ya faru."

Ai jin ance mata ga Sadeeq yasa Biebie tashi tsaye dan jin abin da gaske.

"Wani Sadeeq kike magana akai Hauwaty."

"Akwai Sadeeq ya wuce Mijinki, shike auren wannan abar."

Tas Mami ta kwashe Hauwaty da mari.

"Karki kara k'iranta da wani aba, in ba zaki k'irata da sunanta ba karki sake, kuma ko kun k'i ko kun so y'ar uwar kuce tamkar ciki d'aya kuka fito gaba d'ayanku."

Shuru falon ya d'auka har Mami ta gama magana duk cikinsu ta fisu zafi.

Maganar da Biebie za tayi ma'kalewa yayi a bakinta jin Mami na fad'a, tab akwai bala'i da masifa in har da gaske abinda suka fad'a gaskiyane, Wai Matar Ya Sadeeq.

Barin gurin tayi ta haye Sama, nan Hauwaty ta bita suka karaci jin bakin cikinsu.

Har dare kafin suka fara watsewa, anan Kausar ta samu daman rok'ar Ummu gafara, Ummu ta nuna mata ba komai ta yafe mata tasan wannan din K'addarartane, kuma ta taya ta murnar yin aure dan tasan shi kad'aine rufin asirinta.

 Har karfe goma kafin Sadeeq yazo d'aukar Biebie, bayan komawarsu gida ta sashi gaba da fad'a akan sai ya rabu da Ummu ita ba zata iya zama da kishiya ba, kishiyarma Ummu.

Kallonta kawai yayi tare da jan tsaki ya wuce d'akinsa.


  Kwana uku bala'i Biebie ke ji dashi har ya zama abin ya kai da Sadeeq marinta, tin lokacin ta daina basa duk wata kulawa, ta dai na basa abinci, ta daina had'a shimfid'a dashi.

Duk wanna abinda take yi bai ko kulata ba burinsa ya had'u da Ummu amma har yau bai samu dama ba kasancewar Munirat na nan Ummu ta koma gurin gaba d'aya.


 Can gidan Mami duk an watse Munirat kad'ai ta rage wacce ta zauna dan Ummunta, kulawa take bata sosai wanda ko wace uwa na burin bawa y'arta.

A cikin haka Ummu ta koma makaranta in da ta shiga SSS3, karatu suke sosai ta dage da karatu dan tana da sha'awar shiga Jami'a.


  BAYAN SATI BIYU.

A yau Munirat zata tafi, tin karfe takwas na safe ta gama shirinta, har ranta bata son barin Ummu amma ya za tayi saboda makarantarta bayan hakama ta kula Mami na iya bakin kok'arinta ganin ta goge tsohon tabon dake ranta na tsanar Ummu, inda ta Mamaye da son kyautata mata da bata kulawa.

Ummu ma ji take kamar ta bita, amma ba yanda ta iya tazo karshen shekara a makarantarta bata son yankewa, kuma a gidan Mami yanzu tana samun duk wata kulawa, sun d'auketa tamkar su in aka cire mutane biyu, Biebie da Hauwaty.

Karfe goma Munirat ta kama hanyar Kaduna, tafiyarta da awa d'aya Sadeeq ya k'araso gidan, lokacin tana 'dakin Mami tana gyara mata wasu kayaki, Mami na zaune tana duba wani littafi jifa-jifa Mami na kawo mata hira, daga Eh sai Ummm take iya bata amsa dan bata saba ba.

 Da sallama ya shigo cikin 'dakin, suka amsa masa, guri ya samu ya zauna gefen Mami.

"Ina kwana Mamina."

"Lafiya lau, ya Biebie?"

"Lafiyarta." yace yana mai da kallonsa kan Ummu.

"Ke baki iya gai da mutane bane."

"Ina Kwana."

Tace murya k'asa-k'asa.

"Bangansa ba, get out."

Tsum ta tashi ta fita.

"Kai ya zaka korarmin yarinya tana tayani hira."

Fa'din Mami na bata rai.

"Mami ya kamata yarinyar ta tare gidanta hakanan ta zauna gidan aurenta kamar ko wace mace."

Wani kallo Mami ke binsa dashi, dama yasan da kyar ta yarda, shi kad'ai yasan cikin matsalar da yake ciki.

"Mami na san ban kyauta ba, amma ina neman afuwarku, ya isa haka ta tare gidanta, in yaso ta gama sauran karatuntan a can."

"Hmmm Sadeeq kenan, kabar maganarnan ba yanzu ba please, in kuma kana ganin yuwar haka bazan hanaka ba in har da amincewar yarinya, ka je ka nemi yardarta, fakat na gama magana."

"Amma Mami..."

"Amma me? Kai kanka sanin kanka Sadeeq mun takura rayuwar yarinyarnan a da, dan haka yanzu bazan k'ara ba na tuba, kaje can in ta amince zata zauna da kai to, in kuma ah a to ka sauwak'e mata."

Ai bai jira Mami ta gama magana ba ya tashi.

"Shikenan Mami, zanyi yanda kice."

"Da yafi ma."

"Bari in wuce Mami, sai anjima ki gaishe da Abba."

"To Allah tsare."

Fita yayi a d'akin ya sauk'a kasa, har zai wuce zuciyarsa ta kwad'aita masa ganinta, 'dakin ya dosa, a hankali ya tura kofar d'akin ya shiga.

D'ago kai tayi daga inda take zaune tana gugan kayan makarantarta ta amsa sallamar.

Kallo ya bi d'akin dashi har ya sauk'e a kanta, k'arasowa yayi kusa da ita ya tsugunna kan kafafunsa.

Bata d'ago ba amma zuciyarta bugawa yake da karfi, muryansane ya daki dodon kunnenta, jin abinda ya fad'a ta d'ago kanta.

"Zaki iya zaman gidana matsayin matata?"

Mai da kanta tayi 'kasa, bata jin zata iya basa amsar tambayarsa.

Ganin ta masa shuru ba amsa, dama ya tsammaci haka daga gareta, shuru shurunta ya cika yawa shine abinda ke cutarta a ko ina, hannu yasa ya d'ago habarta, idonsa yayi kok'arin sakawa cikin nata, ta juyar dasu gefe.

"Bazan ta kura miki ba, kiyi shawara nanda gobe war haka, zan zo jin amsana."

Yana gama fad'in haka ya tashi har ya kai bakin kofa tayi gaggawar tattaro nutsuwarta.

"Ni karatuna zanyi ban shirya zaman aure yanzu ba."

Juyowa yayi, yayi mamakin jin abinda tace, amma bata da laifi tana da damar zabarwa kanta abu.

"Karatu baya hana zaman aure, cikin uzurin da zaki kawo banda na karatu, dan nima ina da burin ki samu ilimin sosai."

Yana gama fad'ar haka ya bud'e kofar ya fita.

Shuru tayi ta rasa abinda za tayi, da kyar cikin rashin kwarin jiki ta gama guganta da tin shigowarsa ta kashe iron din.

Bayan ta gama zama tayi ta fad'a duniyar tunani, wa zata fad'awa wannan abin.

"Ammina.' shine sunan da zuciyarta ya raya mata, tabbas itace ka'dai ya kamata ta fad'awa duk wata matsalarta kasancewarta mahaifiyarta.

Daren ranar ta k'irata da k'aramar wayar da ta bata kafin ta tafi, bayan sun gaisa ta tambayeta ta isa lafiya, ji tayi ta k'asa fad'a mata komai kawai ta mata sallama ta fashe da kuka.

A haka bacci ya d'auketa, washegari jikinta ba kwari ta farka kasancewar tsakiyar dare kukan da ta sha ya sata zazzabi, da kyar ta lallaba ta gaishe da Mami kan ta koma d'akinsu, abincin da Laure ta kawo mata ma kasaci tayi, da kyar ta lallabata tasha bakin tea, shima tana sha ta amar dashi sai kuka.

Da lallashi Laure ta samu Ummu tayi shuru, nan wani baccin ya d'auketa, ita kuma Lauren ta fita sanarwa Mami halin da take ciki.

Ita da Sadeeq har rige rigen sauk'a suke, da isarsu bayan sun isa suka tsaya kallonta ganin yanda ta rame lokaci d'aya.

"Mami ko za muje asibiti."

"A tana baccin."

 Juyawa Mami tayi ta kalli Laure.

"In ta farka, kimin magana."

"To Mami."

Fita Mami tayi ta bar Sadeeq nan tsaye, ganin bashida niyar barin d'akin yasa Laure fita ta bar masa d'akin.

Bak'in gadon da Ummu ke kwance ya zauna, ido ya zubawa fuskarta, kan a hankali ya gangaro ya bita da kallo, gaba d'aya ta canza, ta rame daga jiya zuwa yau, amma tayi haske a yan kwanakinnan.

Ya d'an dad'e yana nazarinta kafin ya tashi ya fita.


Ummu kam baccinta tayi har wajen sha biyu kafin ta farka, wanka tayi ta fita falo, ba kowa sai Laure da Rahma wanda suke kallo jifa-jifa suna hira, da sallama ta zauna saman kujera d'aya.

"Kin farka."

Laure ta tambayeta.

"Eh, yunwama nake ji."

"Ga can abinci a dining."

 Tashi Ummu tayi ta zubo kad'an ta dawo ta zauna kan ta fara ci.

"Yawwa Mami tace a fad'a mata in kin farka, bari in sanar mata."

"Bari zan sameta in na gama cin abinci."

"To shikenan."

Ci gaba tayi da cin abincin, kad'an taci ta tashi ta wuce sama dan amsa kiran Mami, da sallama ta shiga d'akin, Mami ta amsa mata, guri ta samu ta zauna.

"Mami gani."

"Ya jikinki."

"Naji sauk'i Mami."

"Allah k'ara afuwa."

"Ameen."

"Ummu."

Mami ta k'irata, dago kai tayi tana mai da dukkan hankalinta ga Mami.

"Na'am Mami."

"Ko Sadeeq ya fad'a miki wata magana."

Sunkuyar da kanta tayi k'asa tai shuru.

"Ummu kar kiji tsoro ko shakkana ki fad'i abinda ke ranki, kina jin zaki iya zama gidansa matsayin matarsa ko baki shirya hakan ba?"

Nan fa shuru tayi, ita bataki hakan ba ko dan SANADIN HA'DUWARSU dashi ya Had'ata da Mahaifiyarta, za taso ta saka masa da sakayya mafi kyau, matsalarta Biebie, bata jin zata iya zaman kishi da ita, duk da Haske ya bayyana hakan bai hana sa soyayyarta a zuciyar Biebie ba sai tsantsar tsana da ya k'aru.

"Ummu amsarki nake jira."

Maganar Mami ta daki kunnuwanta.

Kai ta d'aga a hankali.

"Mami na amince, Allah sa haka shine mafi alheri."

"Ameeen Ummu Allah muku albarka."

D'an nasiha Mami ta mata kafin ta fita ta wuce d'akinsu, kan gado ta kwanta, kuka ta fara yi sai da tayi mai isarta kafin ta hakura tayi shuru.


Cikin Sati biyu Mami ta k'ira dangi ta fad'a musu cewar sati uku masu zuwa Ummu zata tare gidan Sadeeq, ba wanda yafi Sadeeq murna dan shi kad'ai yasan dalilinsa na yin haka.

Sati biyu saura Munirat ta tattaro nata yanata ta taho Katsina dan gyara 'yarta, da isowarta ta fara aiki cire kunya tayi ta fara gyarata, ita Ummu tin tana kunya tazo ta fara sakewa, cikin satin biyun tayi wani uban kyau da haske, fatarta sai shek'i yake, turare kuwa tamkar barinsa aka yi a jikinta.

A ranar da zata tare da yamman akayi gaggarumin walima na mata zallah, da dare aka d'auketa sai gidan mijinta inda tasha nasiha daga bakin danginta da Mahaifiyarta, kuka kam ranar ba kanta, har aka kaita aka watse bata bar yi ba.

Karfe goma ango ya shigo gidansa shi d'aya ba wani taron abokai da ya gayyato, Babbar falon ya shiga shuru, hanyar da zai sadasa da falon Ummu yabi, bai tsaya nan ba har cikin bedroom nata ya shiga.

Tana kwance ta dukunkune jikinta, k'arasawa yayi bak'in gadon ya lek'a fuskarta, bacci take, ajiye abin hannunsa yayi ya fita ya nufi d'akinsa, sai da ya gama shirin baccinsa yabi lafiyar gado ya kwanta cike da farin cikin burinsa na son abinda yake so ya tabbar ya kusa cika.


_Gaisuwa gareki Biyoncy kinfi kowa son SH, Allah bar kauna_
Sadaukarwa ga Ummu Ayshat(Ummi Safwaan).

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


   SANADIN HA'DUWARMU

    ©Pharty BB


   Wattpad @PhartyBB

28


 Washe gari da safe har wajen karfe takwas kafin Sadeeq ya farka daga bacci da ya d'aukesa bayan dawowarsa daga Masallacin sallar asuba.

Wanka ya fara yi ya shirya cikin k'ananan kaya dan ba zai je office ba, bayan ya gama shiryawarshi, fita yayi a d'akinsa ya nufi na Biebie, kwance take bacci take bata san inda kanta yake ba, bakin gadon ya k'arasa ya tashe ta.

"Biebie, Biebie."

"Ummmm." Tace tana mik'a, ba salati.

"Tashi mana."

Da kyar ta iya tashi ta zauna dabas.

"Ba zaki d'aura breakfast bane 9 ya kusa fa."

Shekeke tayu tana kallonsa, yama raina mata hankali.

"Bazan yi ba, me amfanin waccan da aka kawo aka ajiyeta, ta fito ta girka mana."

Murmushi ba'kin ciki ya sake bashi da niya.

"Kin san dai Amarya sai tayi kwana bakwai kafin ta fara girki."

Dariya tayi tana tafa hannu.

"Kama rainamin hankali wallahi, itace Amaryan, kamar yanda naji ita aka fara d'aurwa aure da kai, nasan tsawon lokacin da ka d'auka kana mu'amala da ita, sai yanzu za kace wata Amarya, ni ba dan gudun bacin ran Momy ba ma Sakina za kayi kaje can ka k'arata da guntun wasu."

"Biebie!" Ya daka mata tsawa.

"Irin wannar rainin bai kai ya shiga tsakaninmu ba, dan yanzu ki kimin tsiya zan ajiye batun da aurenki a kaina na koya miki hankali, banza wawiya kawai."

Bai jira mai zata sake fa'da ba ya fita a d'akin dan yana jin zai iya kai mata mari ta masa iskanci.

Babbar falon gida ya zauna saman kujere ya ciro wayarsa dan yi musu odern abinci ya ji an danna door bell, tashi yayi ya bud'e yaga drivern Mami.

"Ina kwana? Mami tace a kawo."

"Lafiya, Bismillah 'karasa dasu kan dinning."

Warmers masu kyuane gudu uku ya jera saman table, kafin yama Sadeeq sallam ya fita, yana fita Sadeeq ya bud'e abincine masu rai da lafiya, rufewa yayi ya nufi 'dakin Biebie.

Ta fito a wanka tana saka kaya, bai ko kalli inda take ba.

"In kinga dama ki fito kici."

Yana fad'ar haka ya fita, d'akin Ummu ya nufa, da sallama ya tura ya shiga, tana zaune gefen gado, game take da wayar hannunta, sanye take cikin dogan rigar atamfa da hijab nata d'an ma daidaici, fuskarta fiyau ba makeup sai kwalli da hoda da tasa.

Jin sallama tare da bud'e kofar shi ya sata d'ago idonta, ganin Sadeeq ya sa ta mai da kallonta k'asa.

"Ina kwana." Tace dashi.

"Lafiya, ki fito kici abinci."

Yace da ita yana fita, tashi tayi tabi bayansa.


Jin alamar zuwan mutum ya sata kwantawa gefen kafad'arsa har wani shige masa take, mamakine ya cika Sadeeq yarinyar da d'azu ta gama masa rashin kunya.

"Dearna ni yunwa nake ji, har yanzu bata fito ba ko baza taci bane."

Bai kulata ba sai ma kok'arin raba jikinsu da yake tana kara lafewa, dai-dai lokacin Ummu ta k'araso wajen ganin yanda suke ya sata yin k'asa da kanta sosai ita taji kunya yanda suke manne da juna.

Kujera d'aya taja ta zauna kanta a 'kasa.

"Biebie yi serving namu."

Cika sauri ta tashi ta ja plate, cikin kissa tace.

"Dearna mai zan zuba maka."

"Ko me kika ga ya dace."

Chips ta zuba masa ta ajiye gabansa tana jawo wani plate din.

"Ke fa k'anwata."

Sai lokacin Ummu ta d'aga kanta.

"Ki bari zan zuba."

"Fad'a mana."

"Barta Biebie ta zuba da kanta."

Ajiye spoon din Biebie tayi tana zama, cibi ta d'auka ta fara cin abincin da Sadeeq ke ciki.

Kad'an Ummu ta zuba fara ci, bata ci wani sosai ba dan a takure take ganin yanda Biebie ke shigewa Sadeeq, ta tashi ta bar gurin, da harara Biebie ta bita a zuciyarta tace.

'Kissa da kisisina kad'ai ya isheki, zan nuna miki ni y'ar bariki ce yarinya."

Bayan sun gama ci ta kwashe kwanukan ta kai kitchen ta fito.

Ummu kam bayan komawarta d:aki mita tayi tayi da gunguni ganin abinda Biebie ke yi a gabanta ko kunya.

Da rana ma daga gidan Mami aka aiko abinci, abinda yanzu Biebie tayi a gabanta har yafi na d'azu dan sai da tayi taja hankalin Sadeeq ya fara kok'arin kissing na ta, ba shiri Ummu ta bar musu wajen, da shigarta d'aki kuka tasa wanda bata san dalili ba.


 Cikin satin maimakon ko wani ango na tattalin Amaryarsa amma Sadeeq ya biyewa Biebie sai abinda taga dama dan tana wadatasa da abinda yake so wanda nemansa gurin Ummu cewarsa raina zai shiga tsakaninsu.

Sati biyu ta nemi komawa makaranta, driver ya nema mata wanda zai kaita ya dawo da ita, farko yaso in Biebie za taje Office ta ajiyeta sai yaga rashin dacewar hakan.

Sadeeq ya raba musu girki kwana bibbiyu ranar girkin Biebie zai kwana d'akinta amma ranar girkin Ummu d'akinsa yake kwana, hakan da Biebie ta fuskanta shi ya k'ara bata damar yin yanda take so.


Yau ya kasance Weekend girkin Ummu ne, tin karfe bakwai ta shiga kitchen ta d'aura breakfast, bayan ta gama ta jera tsaf a saman dining kafin ta wuce d'akinta.

Wanka tayi ta saka kayanta cikin riga da skirt na atampa, kayan ya bi dirinta ya zauna das, hoda da kwalli kawai ta shafa sai jambaki tayi circling da brown ta d'aura pink a sama kalar kayanta, tayi kyau sosai, hijab nata ta duba cikin kayanta mai kalar kayan jikinta ta saka ta feshe jikinta da turare ta fito babbar falon gidan.

A nan ta samu Sadeeq zaune cikin shirin k'ananan kaya alama yanzu ya fito, risina tayi ta gaishesa, bayan sun gaisa yace ta k'ira Biebie, hanyar da zai sa data da d'akin Biebie ta yi, d'akinta ta shiga da sallama ta amsa a yatsine.

Kawar da kanta Ummu tayi.

"Ki zo inji Ya Sadeeq."

"Mtsww fitarmin a d'aki banza kawai, kije kici bazan zo ba."

Ummu bata kulata ba ta fita sum-sum ta koma babban falon.

"Tana zuwa." Tace da Sadeeq tana zama can nesa da inda yake.

"Ok to." Yace yana binta da kallon, ta masa kyau dan kwalliyar ta burgesa ba taron tarukucen Makeup a fuskar, a lips nata idonsa ya tsaya yanda yasha pink ya bala'in tafiya da tunaninsa.

Jin tahowar mutum shi ya sashi d'auke idonsa a kanta, isowar Biebie direct gurin Sadeeq ta wuce ta zauna gefensa.

"Morning Dear."

"Morning, How was the night."

"So boring, missing you."

 Murmushi yayi bai ce komai ba dan yasan ya biyewa Biebie yanzu zata sashi abinda bai yi niya ba, tashi yayi tsaye.

"Let take a breakast."

Kan dining suka zauna Ummu tayi serving nasu suka fara ci, wani salon jan hankali ta farama Sadeeq wanda tin baya kulata ya juyo gaba d'ayansa ya fara biye mata.

Ummu ji tayi ba zata jure haka ba an kai gabar da ya kamata ta fara kwatan y'ancinta, tsaki ta buga da karfi tana tashi, wanda shi yayi sanadiyar dawowa hankalinsu.

"In ba kunya a kwai kara."

Cewar Ummu na barin wajen, da kallo suka bita gaba d'ayansu, tashi Sadeeq yayi zai bi bayanta.

"Ina zaka Dear."

"Ina zuwa."

Bayan Ummu yabi har side nata, bedroom nata ya shiga, kwance ya sameta tayi cilli da hijab din jikinta ta ba kofar d'akin baya , jin shigowar mutum ya sata ta share hawayen da ya taru a gefen idonta, zama yayi gefenta ya 'kira sunanta.

"Ayeeshat."

Bata kula sa ba kuma bata juyoba.

"Ayeeshat."

Ya fad'a yana sa hannu ya juyo da ita, ganin hawaye kwance cikin kwayar idanta sai yaji ba dadi, yasan ba dadi.

Kwayar idonsa yayi kok'arin sawa cikin nata ta sunkuyar da kanta 'kasa, habarta ya d'ago yana rik'o fuskarta.

"Kina kishina ne?

Sai lokacin ta d'ago idanuwanta ta kallesa, fuskarta ta kwace.

"Banga abin kishi akan abinda baka so baya sonka, sanin kan kane Ya Sadeeq na amince da zaman gidankane saboda SANADIN HA'DUWARMU shi yayi sanadiyar had'uwata da Mahaifiyata, darajar da yasa nake zaune da kai."

Murmushi yayi duk da yaji zafin maganarta na rashin nuna kwata-kwata bata kaunarsa.

"Na sani Ayeeshat, amma ki yarda cewa kina kishina."

Yana fad'ar haka ya tashi ya fita a d'akin, kwanciya tayi tana tunanin maganarsa.


 Bangaren Biebie kam ganin haka ya b'atawa Ummu rai shi sa ta dage da duk abinda tasan abinda za tayi ta hana Sadeeq shige mata.

Abin na damun Ummu sosai ta rasa wa zata fad'awa, har haushin kanta take ji, yanda take jin kishin abinda Biebie ke yi.


  'Shikenan ya yarda ina kishinsa."

Abinda ta fad'a tana zaman gefen gadonta, dan fitarta falo ta tararsu cikin yanayin da ba zata iya jurewa ba, wayarta dake kusa da itane yayi ringing, d'auka tayi taga new number special, receiving tayi tana sawa a kunnenta tare da sallama.

Bayan ya amsa ya k'ara da fad'in.

"Kin yarda kina kishina."

Sai lokacin ta gane mai maganar.

"Abinda kake so shi kake kishi."

"Hakane, amma sai da kishi kafin son ya biyo baya."

"Uhmmm a wajenka ba."

"Har a wajenki, yarinya ki yarda kawai kin fad'a tarkon so."

"Kaga in abinda ka k'ira ka fad'a kenan sai anjima, ina da abin yi."

"Shiekan Uwargidana tinda kin 'ki yarda sai anjima muga zaki iya jure wani salon, byee I Love You."

Kan tace wani abu ya katse kiran, wayar ta bi da kallon kafin ta ajiye tana tashi, ringing ya fara yi kamar ba zata d'auka ba ta d'auka wani number ta gani ta d'auka tare da sallama.

"Haba Ummu ana ta kiranki sai kace za a saceki ta wayar, a ajiye mana abu mai dadi ni da Laurat muna hanya, Rahma ce."

"Ayya Sorry Anty Rahma sai kun zo."

"Kece Anty ba ni ba, bar fad'a kar Ya Sadeeq yaji ya zaneni."

Dariya su kayi dukansu kan ta katse kiran, tashi tayi ta fita, kitchen ta shiga ta had'a musu abubuwa masu dadi ta ajiye tana shirin fita suka shigo, k'arasawa tayi da gudunta ta taro Laure.

"Ke baki da hankali za kina gudunnan."

Sadeeq dake shigowa Falon ya fad'i haka dan yaga lokacin da tai gudun, shikam yana zargin wani abu tattare da ita.

Baki ta turo, tana kama hannun Laure.

"Bismillanku Anty Rahma, mu k'arasa ciki."

Zama su kayi cikin falon nan ta kawo musu abinda ta had'a musu, su kuma lokacin suka gaisa da Ya Sadeeq, sallar azahar ne ya 'daga su a wajen suka 'karasa side din Ummu.

Suna shiga text ya shigo wayar Ummu, numbern d'azu ta gani, bu'dewa tayi.

'Ki daina gudu kuma ki daina d'aukar abu mai nauyi umarni na baki.'

Tsaki tayi ta goge, duk Rahma na lura da ita, sallar suka gabatar kan suka zauna suna ta hira, nan Rahma ta tambaye meke damunta taga duk kamar da damuwa tattare da ita.

Shuru tayi ta kasa bata amsa.

"Kar ki damu Ummu, mu ynnzu 'yan uwan junane, fad'amin mene matsalarki."

Nan ma shuru tayi, wanii bangare na zuciyarta na umartarta da ta fad'a wani na hanata, ganin bata da mafita yasa a hankali ta fad'a mata komai.

Shuru Rahma tayi, ba tasan yaushe Biebie za tayi hankali ba.

"Kiyi hakuri kinji nata salon kishin kenan, amma kema da laifinki, ya zaki bari mace y'ar uwarki na nuna miki tsiya, zagewa za kiyi ki nuna mata kema kinsan komai ba kullum kina cikin zumudeden hijab ba, gaki ustaziya ko kamar makwogoron Liman, gaki Allah ya baki diri, tana nan ita kamar igiyan shanya ba shape, ita har zata nuna miki diri, tashi nuna min inda k'ananan kayanki suke."

Tashi Ummu tayi ta nuna mata, nan ta fara bincike gasu nan masu kyau masha Allah.

"Yau girkin waye?

Rahma ta tambayeta tana daga wani wando.

"Ni ." Ummu ta bata amsa

"Good, kinga wannan rigan da wandon nan wallahi ki tabbatar kinsa kin fita dashi Ya Sadeeq ya gani itama ta gani, ki nuna masu kema wayayyiyace Dallah."

"Anty Rahma wannan yar ficiciyar rigar, ko ita bata sa irinsa."

"K'aniyarki da ficiciya, ita duk tsiyarta bata sawa, to ke kisa ki musu yawo dashi, ki juya ki jujjuya su gani kina dasu Allah ya baki, sannan ba kunya kike ji ba kawai kara kike musu."

"Amma Anti..."

"Yimin shuru." ta mata tsawa.

Shuru tayi nan Rahma ta inda take shiga ba tanan take fita ba, har tazo ta fara mata nasiha, 'yan matan yanzu ba a sak'e, ta dage ta rik'e mijinta ta karkato da hankalinsa kanta ba boka ba malam.

Har yamma lis kafin suka taimaka mata ta d'aura abincin dare, karshe suka korata tayi wanka ta saka kayan da Rahma ta bata, da kyar ta iya kallon kanta dan yanda kayan suka kamata, ya fito da dirinta, gashinta mai yawa ta taje ta kama da ribbon kalar adon rigar, simple makeup tayi abinta tayi kyau sosai.

Jin shuru yasa suka biyo sawunta, ganinta zaune yasa su yin turus tsayawa kallonta.

"Wow Y'ar uwa kinyi kyau."

Fad'in laure na murmushi, Rahma ma murmushi tayi.

"Za mu tafi Ummu, zan zo bayan kwana biyu naji kuma kinci gaba da musu yawo a gida da hijab kamar limamiyar gidan, abincinki a kitchen ki jera saman dining."

"To Anty nagode."

Da kyar suka jata ta fito haka bayan ta shiga kitchen suka fita, a da dare ta dinga d'auko foodflask tana jerawa a dinning, so take ta gama ta wuce d'aki kafin wani ya shigo.

Ba taji shigowar mutum ba, ta d'auko plates zata juya taji tayi karo da mutum, ido hudu suka had'a, mamaki al'ajabine suka kama Sadeeq, Ummu kam tsorone ya kamata har jikinta ya fara rawa.

"Ke kam anyi matsoraciya, karki fasa mana plates."

Karb'an plates din yayi ya ajiye, zata wuce ta gefenshi ya rik'ota, ba zato taji ta baya ya rumgumota, wayyo ji tayi zuciyarta kamar zata faso kirjinta.

Kansa ya kwantar kan kafad'arta.

"Ashe Matar nawa ta iya kwalliya, amma shine kullum kina cikin hijab, Kishina da Sona ya fara aiki tin yanzu."

Kok'arin kwace jikinta take, ya k'ara kamk'ameta.

"Kinyi kyau, dole na biya kwalliyarnan."

Kafin tayi wani yunk'uri ya juyo da ita, hannu yasa ya tallafi kumatunta ya had'e fuskarsu, goshinsu ya had'a kan a hankali ya had'e bakinsu.

Ya shafe mintuna yana abu d'aya kan ya sake bakin yana rik'e da ita, Ummu kam tin lokacin daya fara mata kasa motsi tayi, sai hawaye da take.

Yana rike da ita suka fita a kitchen din dai dai Biebie ta shigo falon, ta mutukar tsorata da ganin yanda suke, babban abinda ya dameta illa ganin shigar ummu.

Wani kukan kura tayi ta shiga tsakaninsu.

"Dama nasan Karuwa, Karuwace...."

Marin daya sauk'a saman kuncinta shi ya hanata k'arasa sauran maganar bakinta.

"Ka maren."

"An marenki ko zaki rama."

"Akan wannan ka maren to ka shirya wallahi sai ka biya."

Tsaki ya buga yana jan hannun Ummu su kayi Side nata, bedroom nata ya wuce bayan shigarsu ya zaunarta gefen gado.

"Sorry Wife, kiyi hakuri, ban san yaushe Biebie za tayi hankali ba."

Rumgumeta yayi yana shafa bayanta ganin yanda take neman yin kuka.

"Ya Sadeeq kowa yana min kallon karuwa ko?"

D'agota yayi daga kirjinsa yana girgiza mata kai.

"Ba wanda yake miki kallon haka."

"Mai yasa to ba za subar 'kirana haka ba.". "Kinga kar ki sawa ranki damuwa, bayan Biebie ba kowa, itama wataran zata gane gaskiya balle zanyi mawa tufkar hanci."

Ba tace komai ba, shuru ya biyo baya.

"Abinci fa Ya Sadeeq."

"Za kici."

"Eh, kai fa." Tace tana 'daga kanta.

"Na kula kin koyi mugun ci kwannan, ni yau bazan ci abinci ba."

Baki ta turo ba tace komai ba, fita yayi ya kawo mata abincin da ta dafa, Cous-Cous yasha kayan lambu da miyar karas .

Karb'a za tayi ya hanata ya zauna ya fara bata, da kyar ta yarda, ji tayi kasantuwarsu haka ya mata dadi.

"Wife in tambayeki."

"Ina ji."

"Yaushe rabonki da yin Period naki."

Dun maganar ta tsinkar da zuciyarta, wannan watan bata gani ba gashi har ya kusa mutuwa.

"Ke nake sauraro."

"Amm...ummm...Watan nan."

Murmushi yayi bai ce komai ba, bayan ta gama cin abincinta ya fitar da plate din, bai dawo ba har bayan sallar Isha'i, tin Ummu na jiran zuwansa har ta hakura tayi wanka tayi sallolinta, ta canza kayanta zuwa na bacci ta kwanta.

Karfe goma ya shigo gidan ransa a 'bace daga 'kiran da Abbansa ya masa na k'aransa da Biebie ta kai ya mata dukan tsiya yana fifita Ummu akanta, nan Abba ya masa fad'a sosai akan ya daina hakan karya yarda ya banbantasu yayi abinda har zai tab'a zumuncinsu.

Yasha alwashin sai ya koya Biebie hankali sai tayi nadamar abinda tayi, kuma bazai je bikonta ba, kafarta da tasa ta fita shi zai dawo da ita.

D'akinsa ya shiga yayi wanka ya shirya cikin shirin baccinsa, har ya kwanta akan gadonsa yaji ba zai iya ba ya fita ya nufi d'akin Ummu, kwanciya yayi gefenta tare da jawota jikinsa ya rumgume a haka bacci ya d'aukesa.


Washe gari.....
Sadaukarwa ga Ummu A'ishat.

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

  

  SANADIN HA'DUWARMU

   ©Pharty BB


  Wattpad @PhartyBB

29

  Washegari da safe bayan Ummu ta kammala had'a breakfast, ta share side nata ta goge, turaren wutan Saudiya tasa sai kamshi yake, cikin bedroom nata ta shiga ta tarar har yanzu Sadeeq bacci yake, kasa yin yanda za tayi ta tashesa tayi, wajen Wardrobe nata tayi ta d'auki riga top baki da jacket nasa a sama mai laushi, da adon duwatsu mai kamar stone a jiki, bathroom ta wuce.

Wanka tayi ta shirya a ciki ta fito, kwalliya tayi simple makeup ta taje gashinta mai yawa ta kama, tayi kyau sosai.  Kan gadonta nufa dan tashin Sadeeq, zama tayi gefensa, baccinsa yake hankali kwance, ido ta kura masa sai yau ta kare masa kallo.

Kyakkyawane, fari, mai yalwar gashin gashin kai da jiki, yana da kyan jiki da fuska.

'Dauke fuskarta tayi ganin ya motsa tana kok'arin tashi.

Tin zamanta ya farka yana jira yaga ta inda zata fara tashinsa, ganin shuru yasa ya motsa, gashi tana shirin tashi.

Hannunta ya cafko ya jawota jikinsa ta kwanto, tana kok'arin tashi ya k'ara rik'eta da kyau, kan a hankali ya bud'e idonsa ya d'aura saman nata, ba shiri ta sauk'ar da nata idon k'asa.

Hannu yasa ya shafo fuskarta.

"Ya aka yi Wife?"

Cikin inda-inda duk ta daburce tace.

"Ah babu, dama...dama."

Kara matseta yayi yana mata murmushi.

"Dama me?"

"Umm...dama nace ka tashi kayi wanka lokaci na tafiya."

Murmushin nan dai bai d'auke a saman fuskar ba kuma har lokacin yana rik'e da ita ya mik'e zaune.

"Ok muje kimin."

Idonta ta zaro cikin tsoro tama kasa magana.

Mik'ewa yayi yana rik'e da ita har bakin kofar bathroom din su kayi ya saketa yana lakutan kumatunta.

"Matsoraciya, dauk'omim kayan sawa a d'akina"

Yana fad'ar haka ya fad'a bathroom, ajiyar zuciya ta sauke tana nufan waje, d'akinsa ta shiga ta ciro masa kayan sawa ta koma nata d'akin, har lokacin bai fito ba, kan gadonta ta gyara bayan ta gama ta fita, a falon ta zauna zaman jiransa.

Bata dad'e da fita ba ya fito, shiryawa yayi bayan ya gama shirin saf ya fita falon, direct kan dining ya wuce ta taso tabi bayansa, bata zauna ba ta tsaya.

"Wife yunwa nake ji, zubamin abinci."

Sai lokacin tayi magana.

"Dama nace bari in kira Anty Biebie."

"Barta zo kiyi serving nawa."

"Amma Ya..."

"Kiyi abinda na saki."

Ya fad'a yana bata rai.

Itama bata ran tayi ta tako tayi serving nasa tana shirin barin wajen ya rik'o hannunta, kan kujera ya zaunarta yana rik'e da hannunta.

"Dan nace karki k'ira Biebie shine ki kayi fushi, ummm."

Kin yin magana tayi, hakan yasa ya dago habarta, kiss ya kaiwa goshinta daganan ya gangaro bakinta

Sai lokacin tayi kok'arin magana ya rufe bakin da nasa, ya dad'e yanayi dan kansa ya saketa.

"Sorry to."

Kanta ta d'aga da sauri, murmushi yayi yaja plate din ya d'auki spoon ya debi abinci ya kai bakinta.

"Bismillah ha."

Bakin ta bud'e ya zuba mata, tana taunawa a hankali, dai-dai da cin abincinta burgesa yake.

A tare su kaci bayan sun gama ta dauk'e warmers da plates da spoons ta kai kitchen sai da ta wanke ta ajiye a ma'ajiyarsu kanta fito, shiko yayi shirin office, sallama ya mata ya wuce.

Ayyukanta ta gama har girkin rana wajen sha biyu kafin ta yi wanka ta shirya makaranta, karfe biyu driver ya kaita.


   SABON RAYUWA

  Haka rayuwarsu ya kasance cikin farin ciki da kaunar jununsu, tin Ummu na shuru ganin Biebie bata nan harta kasa hakuri ta tambayi Sadeeq in ya fad'a mata tayi tafiyane, daga nan bata k'ara masa magana.

Cikin wannan halin suka fara registration na final exam, har makarantar Sadeeq yaje ya mata, sun gama da sati uku suka fara exam, tin daga nan bata da zama, karatu take sosai abinta, su ka yi exam suka gama lafiya.

Wata biyu da gamawarta Hauwaty ta haihu, a ranar suka je ya kaita ta mata barka, duk da bata samu fuska wajen maijegon ba, kafin suna zuwanta uku kuma duk bata had'uwa da Biebie anan ta tabbar kenan tayi tafiya, amma tana mamakin wannan wani itin tafiyane tsawon wata uku har yanzu shuru, ganin wanda ya ajiyeta bai damu ba yasa taja bakinta tayi shuru.

Washegari sunan Hauwaty ba irin rok'ar da Ummu bata ma Sadeeq ya barta ta kwana ba yak'i, tayi kukan har ta gaji ta hakura, fushi ta masa tak'i masa magana, da kyar ya shawo kanta ta hakura ganin irin yanayin da take ciki ba'ason yawan bacin ran irinsu.

Ranar suna karfe bakwai tana can, acan ta had'u dasu Rahma, Samii, Kausar duk cikinsu ya fito sosai, su Laure ma duk suna can an waye an goge kamar ba ita ba.

K'iri k'iri Rahma ta hanata yin aikin komai daga ta tambayeta dalili, sai tace mata, taje ta tambayi Ya Sadeeq shi ya hanata barinta tayi aiki saboda shi yasan da abinsa.

Sai dai tayi murmushi dan ita bata gane kan maganarba.

Allahamdulillah anyi taron suna lafiya an watse lafiya yarinya taci sunan Mami Halima suna kiranta Mommah.

Karfe tara Sadeeq yazo d'aukarta, waya ya mata ya 'kirata, sallama ta musu ta fito, a gingine a jikin motarsa ta samesa yana gaisawa da mijin Hauwaty, bayan ta 'karaso sunyi sallama dashi ya wuce ciki.

Hannu yasa ya jawota jikinsa ya rumgume.

"I miss You."

Murmushi tayi tana kok'arin raba jikinsu.

"Ka bari mana, har yanzu ba'a gama watsewa ba fa."

"Ina ruwana ina matata na rik'e."

"Pleasena." Tace dashi cikin shagwaba.

Bai kulata ba ya d'agata cak ya zagaya ya bud'e motar ya sakata ya za gaya ya shiga yaja suka bar harabar gidan.

Bayan isarsu gida shi ya k'ara d'aukarta suka shiga cikin gidan, bayan sunyi wanka yana zaune tayi matashi da cinyarsa a saman dogon kujera mai zaman mutum uku, kallon TV suke.

"Yawwa Ya Sadeeq wallahi ka jawa Rahma kunne ta samin ido?"

Sai lokacin maganar Rahma ya fad'o mata a raina.

"Me ta miki." ya fad'a yana dariya dan shi yasan za'a rina da ya bada ajiyarta hannun Rahma.

"Tinda mu kaje gidan suna Anti Rahma ta hanani ko kwakkwaran motsi, da na tashi tayi magana ko zama zanyi sai tayi magana."

"Umm me take cewa?"

"Wai inbi a hankali kar na maka asara, asaran me zan maka bayan ba ajiyarka a gurina ba komai."

D'agota yayi suna fuskantar juna, lokaci yayi da ya kamata ta san matsayin da take, dama yana boye matane dan samun ta kammala makaranta kuma ta gama me na 6oye 6oye.

"Ayeeshat."

Ya fad'a yana kallonta.

"Na'am." ta amsa jin ya kirata da asalin sunanta tare da mai da hankalinta gaba d'aya kansa.

"Ya alamomin masu ciki suke?"

Dariya tambayarsan ya kusa bata, da murmushi a fuskarta tace masa.

"Suna amai suna zazzabi."

"Shikenan."

"Eh iya abinda na sani."

Murmushi yayi ya rik'o hannunta jin amsar da ta bashi.

"To ke naki cikin ba amai ba zazzabi, ko zan ce ma kinyi bai fi sau biyu ba in zaki tuna lokacin bikin Rahma."

A tsorace take duban sa.

"Ciki kuma Ya Sadeeq? A ina? A jikina? Ni wallahi banda komai."

Rik'ota yayi ganin duk ta rud'e ya d'aura hannunta saman cikinta.

"Bi a hankali mana, duk zamanki baki san kina da ciki ba, watanki nawa ba kiyi period ba, in zan iya lissafawa wata uku kenan, na'ki kai ki asibitine dan gudun tashin hankalinki nafi so sai kin gama makaranta kuma kin gama, sai shirin karb'an Babyna."

Shuru tayi tabbas tayi wauta da rashin kula, bata taba kawo wai cikine da ita ba, gani take tamkar tatsuniya yake mata.

Fuskarta ya d'ago yana kallo.

"Gobe za muje asibiti dan tabbatar da lafiyar abinda ke cikinki daganan zaki yarda da gaske nake."

"Ya Sadeeq ni wallahi tsoro nake ji."

"Tsoron me?"

"Haihuwa, akwai wahala fa."

Rumgumeta yayi a jikinsa yana shafa bayanta.

"Karki damu kowa da kalan nasa, insha Allah da sauki zai zo miki."

Maganganun kwantar da hankali ya dinga fad'a mata a daren ranar.


 Washe gari karfe tara suka bar bayan sunyi wanka sunyi breakfast.

Ummu shiryawa tayi cikin bakin a baya sai k'aramin gyale red da tayi rolling dashi, ba tayi wani makeup ba sai kwalli da tasa tayi lining na girarta, tayi kyau sosai, glass din da ta gani a motar ta d'auka tasa a idonta.
  Murmushi Sadeeq yayi yaci gaba da tuki, har suka iso asibitin, duk wani gwaje gwaje an mata inda aka tabbatar tana d'auke da cikin wata uku da kwanaki.

Sadeeq yayi murna sosai, ita ko Ummu kunyane da mamaki su ka kamata, bayan likita ya rubuta musu magani suka juyo gida.


Sadaukarwa ga Ummu Aishat.

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


  SANADIN HA'DUWARMU

    ©Pharty BB


   Wattpad @PhartyBB

30

  Sati biyu da sunan Hauwaty, Sadeeq ya samu 'kiran Abbansu, bayan yaje nan ya sanar masa da cewa Sultaan na son Laurat da aure ya shirya jibi za suje can k'auyensu dan yin magana da manya da kuma mahaifiyar yarinya.

Da murna ya dawo gidan ya fad'a Ummu, itama tayi murna sosai.

Ranar da Sadeeq zai tafi Ummu har kuka ta masa kafin ya ce ta shirya ya kaita gidan Mami.

Bata so haka ba ta shirya cikin bak'in abaya gabansa anyi zane da ash colour, hakan yasa tayi rolling kanta da gylae karami ash colour, kwalliya tayi abinta sosai tayi kyau. Bayan isarsu gidan Mami, Sadeeq ya gaishe da Mami, kan ya wuce wajen Abba da Sultaan inda suke jiransa.

Daganan suka d'au hanyar k'auyen Unguwar Liman.

Bayan tafiyarsu Ummu da Mami na zaune suna hira Mami ke tambayar Ummu ina Biebie bata zo ba ko tana da aiki a office.

Shuru Ummu tayi kanta ya d'aure, Mami bata da masaniyar cewa Biebie tayi tafiya.

Maganar Mami shi ya dawo da ita hankalinta.

"Nace miki ya Biebie ko tana office."

"Mami ai..amm..Mami ai bata nan."

"Bata nan! Ina taje?"

"Tafiya tafiya."

"Tin yaushe?"

"Kusan wata uku."

"Meye!"

Shuru Ummu tayi tana zare ido.

Mami kam mamakine ya kamata, tabbas akwai abinda ke boye kuma ba mai warwaresa sai Sadeeq.

Barin maganar tayi ganin duk Ummu ta tsorata, ta kawo mata wani hiran.


 Can bangaren Abba, Sadeeq, Sultaan, karfe sha biyu suka iso, direct gidan maigari suka yada zango, bayan sunci sun sha suka gabatar da abinda ke tafe dasu.

Mutanen gurin sunyi murna sosai daga nan aka dunguma gidansu Laurat.

Abinda suka tarar shiya tsora ltasu, Abulle ke yin wanki uban tulin kaya kuma ga dukkan alamu na Dijene, ganin mutane yasa ta bari ta dauk'o ta barmu ta shimfid'a musu, Abba da Sultaan ne da mai gari da sauran mutanen suka zauna banda Sadeeq da tsaye yayi yana k'arewa gidan kallo, Can nesa dasu Abulle ta zauna.

Mai garine ya bud'e taron da addu'a daga nan ya sanarwa Abulle abinda ke tafe dasu na Sultaan na neman auren Laurat in ta amince.

Ba shawara ba tunani cikin sauri Abulle tace.

"Na bashi ita wallahi, na basa Allah yasa matarsa har a lahira."

Kallonta mai gari yayi da kyau kamar ba a cikin hankalinta take ba.

"Karfa daga baya kice kin fasa."

"Ah a Maigari na bashi ita, ga Yayan Mahaifinta na bashi ita ya zartar da duk hukuncin da ya dace a kanta."

Fad'in Abulle na nuna Abban Sadeeq.

"To Allahamdulillah."

Fad'in Mai gari, anan Sultaan ya bada sadaki dubu hamsin da sauran kud'ad'en da ake bukata aka saka rana wata hudu in da Abba ya zama wakilin Laurat Sadeeq ya zama Wakilin Sultaan, nan aka damk'awa Abulle kud'in auren Laurat da komai da komai.

Anan Abba ya sanar mata ba anan za a d'aura auren ba acan gidansa za'a d'aura, in biki saura wata daya zai turo a d'aukota, nan ya kara bata wasu kud'aden ta rik'e a hannunta.

Kuka wiwiwi Abulle ta saka tana rokon gafararsu dan ita kad'ai tasan rayuwar da ta shiga bayan gudowar Dije daga karuwanci.


 Bayan sun gama komai suka d'auki hanyar komawa gida.

Da isarsu bayan sun huta sunyi wanka sunci sun sha, Abba ya sanar dasu an tsaida ranar d'aura aure nan da wata uku, Mami ta taya su farin ciki inda anan ta d'auki waya ta dinga k'iran yan uwa tana fad'a musu.

Har dare Ummu da Sadeeq na gidan kafin suka musu sallama zasu tafi, anan Mami ta tsare Sadeeq cewar ina Biebie.

Kansa a 'kasa da kyar ya furta.

"Na saketa Mami."

Ba Mami ba hatta Ummu sai da ta tsorata d'an cikinta ya juya.

"Saki kuma Sadeeq! Meya faru? Tukun ma saki nawa ka mata"

"Saki d'aya."

Ajiyar zuciya Mami ta sauke jin saki d'aya ya mata kan tace.

"Sadeeq in har kana nemawa kanka samun kwanciyar hankali daga wajen Abbanku gobe kaje kayi bikonta tinda saura wata d'aya ta gama Iddah."

"Mami amma..."

"Shit umarni na baka, tashi ka fitamin a d'aki."

Tashi yayi ya fita Ummu tabi bayansa sum sum, duk ta tsorata da Sadeeq.

Bayan isarsu gida daren ranar da kyar ta yarda masa gani take itama daya samu abinda yake so daga wajenta zai saketa.

Washegari haka yabi umarnin mahaifiyarsa da dare yaje bikon Biebie, inda yasha fad'a da nasiha wajen Mommynta, dan ita kanta tasan halin 'yartan.

Jin Sadeeq yazo yana nemanta a falon baki da gudu ta tashi zata fita, Mommynta ta daka mata tsawa.

"Haka zaki je masa kamar wacce aka sallamo daga gadon asibiti."

Sai lokacin ta kalli jikinta, dogon rigane sai 'karamin gyale data d'aura, tayi fari ta rame sosai dan tin lokacin da Sadeeq ya kawo mata takardar saki ta rasa isasshen lafiya har office daina zuwa tayi.

D'akinta ta wuce ta shirya cikin leshi mai kalar sararin samaniya, heavy makeup tayi ta feshe jikinta da turare ta fita.

Falon baki tayi anan ta tararshi zaune, gefe ta zauna kusa dashi kad'an dan ita yanzu tsoro yake bata.

"Ina wuni."

Tace dashi tana wuk'i wuk'i da ido.

"Lafiya, ya kwana biyu."

"Lafiya."

Shurune ya biyo baya, ganin lokaci na tafiya yasa Sadeeq mik'ewa.

"In kin shirya tafiya mu tafi ko."

Kallonsa tayi kamar za tayi kuka, amma Sadeeq ya mugun raina mata hankali.

Tashi tayi ta fita, shima fitan yayi.

Sai da tasha kukanta kafin ta shirya ta fito tama Mommynta sallama inda ta mata nasiha mai ratsa jiki ta fito.

A cikin motar ta samesa ta bud'e ta shiga yaja suka bar gidan.

Da isarsu gidansa bayan yayi parking sun shigo fakon ya tarar Ummu na zaune tana kallo, ta juya kofar shigowa baya, kusa da ita ya k'arasa ya zauna tare da rikota yana kaiwa wuyanta kiss.

"Ya kike, ya Babyna."

Murmushi tayi tana 'kara kwanciya jikinsa dan kwata-kwata bata kula da Biebie dake tsaye ba, tace.

"Lafiyarmu lau."

"Muje inyi wanka please dan yunwa nake ji."

"To Yayana."

Tace tana tashi shima ya tashi suka wuce side nnata, Biebie kam ganin abin yafi karfinta yasa ta wuce side nata tin kan su tashi.

Bayan Sadeeq yayi wanka ya nemi ta kawo masa abinci d'aki, anan suka ciyar da junansu, bayan sun gama ta fitar da plate din ta dawo itama tayi wanka tayi shirin bacci suka bi lafiyar gado.


  Sai washegari Ummu taga Biebie, anan suka gaisa har Biebie na neman gafararta akan abubuwan da ta mata, nan Ummu tace mata ba komai ta yafe.

Tin daga ranar rayuwar ma'auratan ya sauya, sun shimfid'a rayuwarsu cikin so, kauna, yarda, aminci da yardar junansu, a haka Ummu ta samu gurbin karatu a jami'a inda tske karantar Islamic History.


  Bayan wata Uku.

Yayi dai dai da ranar auren Sadeeq da Laurat, Sadeeq yana ji yana gani Ummu da Biebie suka had'a kayansu suka tafi gidan Mami.

Tin ana bikin saura wata d'aya kamar yadda Abba yace haka yayi ya tura Driver ya d'auko Abulle da yayanta Dije da Ja'afar, gaba dayasun sun nutsu sun ma kansu karatun nutsuwa, dan yanzu suna ganin sakyayyar muguntan da suka ma marainiya Ummu wacce yanzu suna ganin ishara.

Tin ran talata suka fara gabatar da shalin biki, har ranar asabar da aka d'aura aure aka mik'ata gidan mijinta.

Ummu tin da taje bata aikin komai ahlin gidan sun hanata ganin cikinta ya girma, sai dai a dafa a zubo mata taci a d'auke, wanka ke 'dagata daga inda take, ko wani lokaci Sadeeq na kiranta ya lafiyarta dana Babynsa, sai dai tayi murmushi tace, lafiyarsu lau.

Bayan angama biki kowa ya watse banda Ammin Ummu data zauna har lokacin haihuwar Ummunta.


  Wata biyu da sati biyu wata Safiyar Asabar Ummu ta tashi da nakuda, da taimakon Biebie da Sadeeq suka kaita asibiti basu dad'e da zuwa ba awa biyu ta haifo d'an ta santalele dashi sak Mahaifinsa, fari mai yalwar gashi.

Haihuwarta da awa d'aya asibitin ya cika da yan uwa da abokan arziki dan murnar zuwan jariri.

Ganin lafiyarta da abinda ta haifa yasa likita sallamarta suka koma gida.

Cikin kwanakin kafin suna taga gata da soyayya wajen mijinta da yan uwa, abinda Biebie ke mata kuwa har ya zarce tunanin mai tunani dan kowa mamaki yake, itace ta tsaya mata kan komai.

Ranar suna yaro yaci sunan baban Ummu Muhammad suna 'kiransa Safwaan, kowa yayi murna da haka musamman Ummu da Amminta harda d'an guntun hawayensu na tino musu dashi a kayi.

Watan Safwaan takwas Biebie ta haihu itama 'yarta mace taci sunan Mami suna k'iranta Afnan.

Haihuwar Biebie da wata Uku Rahma ta haihu y'a mace itama.

Ana washegari suna Biebie ta tafi zata kwana, 'kiri 'kiri Sadeeq ya hana Ummu tafiya da fushinta ranar ta kwana.

Da safe kuwa karfe takwas ta gama ayyukanta ta fito kofar falon tana jiran Sadeeq ya fito, tama Safwaan wanka ta shiryashi cikin riga da wando rigar mai layin lime da sea blue wando levender colour haka safar kafarsa lime colour.

Ita kuwa ta shirya cikin dogon riga na atamfa mai blue da brown tayi amfani da brown gyale.

Rikota ta baya Sadeeq yayi bayan ya karbi Safwaan da hannunsa na hagu ya shirya cikin yadin kashmir dark blue, yasa bakin takalmi da agogo.

"Kinga yarona ya fara hakori yana ta kokarin kai hannunsa baki."

Hannu Ummu ta kai bak'in Safwaan, cizo yasa mata duk da ba hakorin sai alamar fitowa, hakan yasa ta bud'e baki, shiko Sadeeq dariya yasa musu.  Ganin zasu bata lokaci yasa Sadeeq yin gaba, tabi bayansa suka shiga motar yaja.

A kofar gidan Rahma yayi parking ta masa sallama ta fito ta wuce cikin gidan sunan.

Anyi taro suna lafiya, an fara lafiya an gama lafiya, aka watse lafiya, Sadeeq shi yazo d'aukan matansa suka wuce gida.


 Da daren ranar gaba d'aya, Sadeeq, Ummu, Biebie, Safwaan da Afnan suna zaune yaran wasansu suke, iyayenko hira suke yi abinsu.

Nan Sadeeq ya kallo matansa yana d'aga musu gira.

"Matana yafa kamata yarannan su samu k'anne."

Tashi Biebie tayi ba shiri ta d'auki y'arta.

"Ba da ni ba haihuwa yanzu sai y'ata tayi shekara hudu."

Tana fad'ar haka ta kama hanyar side nata, kallonsa Sadeeq ya mai da kan Ummu.

"Ke fa Wife, kema sai Safwaan ya shekara hudu."

Tashi tayi ta d'auki Safwaan tana murmushi.

"Ni sai ya shekara tara a na goma na haifo masa k'ani ko 'kanwa."

Dariya Sadeeq yayi yana bin bayanta.


Asubabi ta Gari Mr and Mrs Abubakar Sadeeq.


      Taimako.

 Ka taimaki mutum ko da baka san asalinsa musammam in yana cikin tsananin bukatar hakan, ko dan gudun fadawarsa ga halaka.


 ALLAHAMDULILLAH

       TAMMAT BI HAMDULLAH.


 SADAUKARWAR NAKI NE UMMU A'ISHAT MUHAMMAD (UMMI SAFWAAN), ALLAH BAR KAUNAR DAKE TSAKANINMU, ILYSM.


  

  


PhartyBb.WordPress.com


Tags: #PhartyBb
24865
0
0
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!