Ruwan Dare!

Written by Ashnur PyarPublished on 2018-12-14 11:44:12Category Mystery/Thriller"Hmmm!wallahi ni de ina gaya muku ku hankalta da kayan matan nan wasu ba su da inganci, nasan akwai masu kyau,amma wallahi marasa kyan sunfi yawa,haba!ba ku san dame ma ake haɗa magungunan ba,ku dai kawai a kawo muku kusha,wani ku tusa a gabanku ko tsoron ciwukan zamani ba kwa yi,duk yanda ake ta faɗakarwa akai! tags: #ashnur #queenmeemiDuba was labarai »

[23:24, 2/11/2018] 💕Luvly miemie💋: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

  *RUWAN DARE*


     *DAGA*


*MEEMI BASHIR(queen)*  

      *Aur*

     *ASHNUR PYAR*

   

   


Bissmillahir Rahmanir Raheem.Babi na ɗaya


Tafiya takeyi cikin sauri-sauri tana zancen zuci. 

"Uhmm bari inyi sauri in koma gida yau nayi dare fa gashi har duhu ya fara yi nasan yanzu baban Khadija ya dawo gida yanzun haka ma yana can yana masifar tashi daya saba".


"Haka kurum ace mutum bazai nemi na kansa ba, inba babansu ba ina na taba ji,gade hanyar samu a b'agas! Cikin kwana ɗaya sai ka tashi da naira dubu goma ko shabiyar a hannu ma banda irin su Hajiya Sa'a masu turoma ta account, adai yanda ake wahala a zamanin nan yanzu banga abinda zai hanani wannan sana'a ta saida magungunan Mata ba, domin yanzu mata nan suka fi kauri".


Da haka ta karasa cikin gidanta kamar yanda ta kintata mai gidanta ne zaune da yaran data Bari agidan wajen su uku dukansu kanana babbar zata Kai she Kara shida zuwa bakwai, mabi Mata namiji ne zaikai huɗu sai yar karamar da bata wuce biyu ba.


"Sannu malam ashe ka dawo?" bai kalleta ba sai yaran nata ke mata oyoyo. 


"Aike yaka mata a tambayi wannan bani ba, yanzu fisabilillahi har sai yaushe ne zaki daina barin yaran nan, kina tafiya harkar nan da kika ɗauka kamar ibada abu tun Rana har dare yara suci Kansu suyi duk abunda zasuyi ba ruwanki haba Sadiya. Tunda nayi-nayi kidaina fitar kinki, nace kuma duk abinda zakiyi kidaina kaiwa dare amma abu ya gagara...HMMM"."Haba malam ya kamata ace zuwa yanzu ka fahimce ni bafa yawon banza nake zuwa ba, sana'a ce fa aiyafi zaman banzan da wasu matan suke, ko so kake nima in zauna ace komai saina tambaye ka?".


"Ba zaki taɓa fahimtar abinda nake hangowa bane Sadiya, amma shikenan ki cigaba da yanda kike so".


Zama tayi a gefensa "haba malam sana'a fa nake me kake nufi nayi yanda nake so? sana 'ar nan fa na rufa mana asiri, kafin kabada kuɗin magi na fidda na saya kaima ai hutun kane,bai kyautu ace agaban yara kana yimin faɗa ba". Ta juyar dakai tana haɗe rai. Kallonta yayi yace "ALLAH ya kyauta sadiya ke kam naga yaushe zaki gane sana'a aiba dole sai ansa kafa anfita ba, gidanki ma ya isa duk maisan sayan abunki ai dole ya biyoki inda kike, ai wan nan ce sana'a me aji".


 "Malam zancen kake so wai ance da gwauro ya iyali" cike da takaici yace "atoh kiyi yanda kike so tunda ban isa dake ba kin fiso kullum kafarki na waje kina yawo kwararo-kwararo anayi dake, kiwon mutum fa ake ba dabba ba" ,taɓe baki tayi ta shige ɗaki, shikam tsaki yayi ya fice daga gidan.*************


Zaune take a faffaɗan falonta daya wadatu da kayan alatu gefe wata kanwar mijinta ce Bazawara suna hira. "Ai wallahi Maryam kayan sadiya akwai kyau aini tunda na sameta na dena siyan kowanne kayan mata agun wasu kana zaune zata kawo maka har gidanka".

 Maryam ba tayi magana ba ganin Anty Saude ta ɗau waya ta kira layin sadiya.


Bayan sun gaisa tace ta kawo mata wan nan zumar domin tata ta kare nan suka daddale zata kawo mata yanzu nan. 


Sadiya alokacin ta fito daga wani gida takai ma wata magani, da gida zata koma sai kawai ta yi hanyar gidan Anty saude.


Samari ne kimanin su biyar zaune akan benci kusa da wani shago sai ɓarar gyaɗa suke suna watsawa suna hira, dai-de lokacin sadiya tazo ta wuce ta shige gidan Anty saude, ɗaya daga cikin samarin nan yace "kai anya akwai matar da takai wan nan yawo kuwa? kullum tana tafe" wani ya cafe "kasan ran nan kuwa ina na ganta! a can wata unguwa mai nisan tsiya naganta sai sauri take" wani daga can dabe magana ba se yanzu yace

"to wai me take zuwa yi gidan nan ne?"

 ba wanda ya sake magana acikinsu sai watsa gyaɗarsu suke abaki "Wayasan mata inaga ko wani abun take sayarwa" wani ya cafe "kai wallahi nayi aure karyar matata ta dinga min yawo haka",haka dai sukai ta hira su saki waccen sukama waccen.Sadiya ce Zaune gefen kujera bayan ta shiga gidan sai bubbuɗe ledodi take. Haj saude sai murmushi take ."Wlh sadiya shiisa nake kaunar ki akwai cika aiki" dariya sadiya tayi ta kurɓi lemo "haj ai kema kina cika aiki ba bashi cas kike mikon kuɗina" ɗauko wani kulli tayi "kinga wan nan shi ake cewa BITA ZAI-ZAI ki gwada zaki bani labari" saude tace "yawwa idan kin samu sabbi ma mayi waya". Maryam dake gefe tana kallonsu tana taɓe baki nan sadiya ta gama duk abubuwan da zatayi ta tafi.Maryam tace "Hmmm Anty saude kenan, nikam wlh bansan meyasa kika sakarwa matar nan ba, harfa ɗakinki take shiga, ni ina mamakinta kullum kafartaa awaje. Allah Anty ki kiyayi kanki da irin matan nan danni yanzu shi kansa kayan matan ma tsoronsa nake. Anty nasan bakisan silar rabuwa ta da mijina bako? to ta sanadin kayan mata ne."Dariya Anty saude tayi "ai Sadiya kayanta akwai kyau kinsan ni kar nake nasan abu me kyau, kuma baza'a ninkeni bai-bai ba, na yarda da ingancinsu da ita kanta sadiyar."


"Kayya Anty kide yi baya baya da ita, duniya ta canja wai ta ina kuka haɗu ne?" Anty tace "agidan bikine takai kayan mata ana ta siya kinsan mata da san kayan mata, nan aka wawashe, to alokacin na karɓi number nata tunda ga nan take kawon nake saya" hmmm kawai marym tace.


Anty Saude dake kurɓar zumar da Sadiya ta kawo mata tace "bani labarin mutuwar auren naki ,tinda kince sanadin kayan mata ne ,kinga ni lokacin da aurenki ya mutu ina umara" tsaye maryam ta mike "zan baki Anty amma ba yauba" nan ta shige ɗaki.************


Bayan Sadiya mai maganin Mata tabar gidan Hajiya saude madadin ta nufi gida sai tace "Tunda dai naga dare be yiba bari in biya gidansu Ameera, kwana biyu ai ban leka ba kuma Ina samun kudi sosai can ma sai kuma inje gun jummai ita ma ko dubu guda ce na samo gunta ina laifi"


"Assalamu Alaikum masu gidan na nan Kuwa?"


"Wa alaikisslm a'a Sadiya ce bismilla , oyoyo oyoyo ga uwar 'yar harka ta Iso 

Shigo ciki mana kika tsaya yau me wuta-wuta ya samu kenan".


"Hehhehhe ai tunda kika ganni Ameera kema kinsan ta samu ne, yau harda ruwan zuma na uwar gida kafarki kafata in gaya miki".


 

Suka rangaɗa shewa tareda tafa hannu. "Oh kin ganmu ko ɗaki bamu shiga ba mun hau zancen abin duniya" cewar matar da Sadiya takira Ameera.


"kamawa tayi, kinsan inna ganki zuciya ta fal nake jinta da farin ciki, dan nasanki ba wasa da wurwuri kike jikan hannuna da fulusai( kuɗi) cewar sadiya.

Bayan sun shiga ɗaki Sadiya ta baje Mata kayan datazo dasu wasu kulle-kulle ne cikin Leda wasu a gora da kananan robibi farare, nan tashiga gwada Mata "kinga wannan shine mai mak'ale mata, Ina baki labari in kikayi amfani da shi babu abinda zaki nema gun oga ki rasa kuma magana sai yanda kikayi dashi yanda kika san waina acikin kasko haka zaki rika juya shi".


Wani daɗi ya kara Kama Ameera tace "yanzu kenan nawa wannan din yake?"

"Dubu biyar muke saida shi, amma tunda kece ki bada dubu huɗu"


"Haba Halimatu ke kuwa sai kace Yau mike tare kidai bar min (3500) uku da ɗari biyar kenan"


"A haba! ai inna baki haka na fad'i banfa ɗaura miki riba ba yanda na saro shi na baki, saboda yanda muke dake kuma ai aikinsa zaki duba da mahimmancinsa".


"To shikenan naji nagode aike tawa ce ina godiya da saukin da kike min"


Nan ta shige uwar ɗaki ta kirgo Mata dubu huɗu cif-cif cikin kuɗin da me gidan ta ya bata na abinci da zai yi tafiya, tana zuwa ta mik'a Mata su.

"To shikenan, Wanda zaki ɗauka ba zaki haɗa da wannan ba, in ma baki da kuɗi hannu ba matsala bane saina biki bashi ai ana tare"


Haka sadiya tayita kalallame Ameera da daɗin baki sai data sa ta ɗaukan bashin dubu biyu. Daga nan kuma suka mike don fita tsakar gida kiran sauran matan gidan suma su sayi kaya.


Dama haka ce take kasancewa in tazo sai Ameera ta gama zaɓan kayan, sannan suke kiran sauran Matan kuma kuɗin da suke biya yafi yawa kan na Ameera a haka Sadiya ke cin riba da kowannensu.


Gidan su Ameera estate house ne, mijin Ameera shi keda gidan sauran haya suke sashe uku ne cikinsa banda ɓangaren da su suke ciki,sai daga hanyar waje akayi wani ɗan daki wadatacce inda kabiru yake zama me gadi.


Fita sukai harabar tsakar gidan, nan sadiya tace da karfi "Aisha ku fito ga kayan haja" ta kalli Ameera "kode basa nan ne?" Amira ta kalli shashunan nasu tace "kinsan in kowacce ta shige part nata bakya jiyota, bande saniba ko basa nan dan yau ban leko ba sai yanzu" tana cikin magana sai gashi ɗaya daga ciki ta fito.


 Nan duk Sauran ma suka fito.Sadiya ta zauna gefen wani dakali ta kallesu "gafa haja na kawo".


 Aisha tace "Sadiya ai ina jinki kina kirana bayan kinsanni bana siyan irin kayan nan". Sadiya tace "Suɓutar baki nayi Saliha na kesan kira, amma ke kam Aisha wa ke zama haka yanzu, ai mazan nan na yanzu sai sunjiki zam- zam shine zaki zama macen gaban goshi, haba idan kana da kyau ai seka kara da wanka".


 Saliha tace "ni kinga Sadiya fito da kaya mugani bar batun Aisha"


 Ameera tace "aini har mamaki Aisha keban ko a kauye ai mata kansu ya waye wake zama haka nan duk wacce kika ga tana zama me faɗa aji gun muji to su ta rike".


Sadiya da sai yanzu tai magana tace tace "gaya mata dai" nan duk suka zauna Sadiya tana kora musu bayani ko ragi basu naima ba suka cake mata kuɗi. Sadiya tayi shewa "ai wlh Ameera, Saliha, yau mazanku sai sun muku kyauta jin-jina musamman idan kukai amfani da wan nan" ta ɗauko tana nuna musu "KARYA GADO kenan ,ta kuma zaro wata leda da wani abu aciki, "zan kuma jaddada muku wan nan na matsi ne dankar ku manta, wallahi in kukai babu magana, idan na sake waigowa nan gidan nasan sai kun nemi kari".


Suka yi shewa suka tafa "ai mukam ba haufi wake zama haka" ahaka de sadiya tayi musu sallama ta fice daga gidan.Kallonsu Aisha tayi "hmmmmm wlh nide ina gaya muku ku hankalta da kayan matan nan, wasu ba suda inganci nasan akwai masu kyau, amma wallahi marasa kyan sunfi yawa, haba bakusan dame ma ake haɗa magunan ba kude kawai a kawo muku kusha wani ku tusa agabanku ko tsoron ciwukan zamani bakwai , duk yanda ake ta faɗakarwa akai".Shewa sukai "aike Aisha kin rako mata wlh hmmmm ai komi yana son sabon taste, haba aike kam kina cutar megida da kankin kanki" cewar Ameera data turo ɗauri gaba.


 Aisha tayi dariya tace "ainima inayi ammma masu inganci komi da kaina nake haɗawa kika ɗimanci cin su kankana,kwakwa, dabino,Aya, zuma da duk wani kayan fruit wlh kin gama sune ingantattun maganin mata, dande ba zaku bari na gaya muku ba ne kunfi ganewa waɗancan" Ameera tace "rike abunki muna nan zaki zo kinacewa meye sirrin ko kuma sai an miki kishiya ki gane baki da wayau" suka kwashe da dariya kowacce ta koma shashenta.
*Ku biyo Miemie da Ashnurpyar* 👌🏻


.

[23:24, 2/11/2018] 💕Luvly miemie💋: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

  *RUWAN DARE*


     *DAGA*


*MEEMI BASHIR(queen)*       *Aur*

   *ASHNUR PYAR*

       

   Babi na biyu (2)Tunda Sadiya ta fita daga gidan su Ameera take sauri, da yake da ɗan nisa kan afita bakin titin, shiisa take zuba uban sauri ganin duhu ya fara mamaye sararin samaniya. Wani daɗi ke ratsa zuciyarta, tana tafiya tana murmushi saboda yau tafito a sa'a ak'alla ta tasamma rik'e dubu goma shabiyar (15k) cas a hannunta, bayan ta k'arasa bakin titin ta tsaya tana jiran ɗan adai-deta.
Tana nan tsaye taga me saida mangwaro yazo wucewa, nan ta tsaidashi tana son sayawa su khadija tsaraba, sun tsaya yana k'okarin zuba mata a leda ta zaro jakarta ta buɗe zata zaro kuɗin, taji an wafce jakar. 


Wani matashin saurayi ne ke ɗirkar gudu yayi gaba da jakar, ɗora hannu tayi aka "Wayyo! jaka ta".


 me mangwaron ya bishi aguje yana "kai kawo jakar nan" haka ya rink'a faɗa da k'arfi. Yaron kam ko waiwayonsa baiba, shide ya damk'e jakar yana kwasar gudu kawa,ganin yayi nisa yasa mai mangwaron ya dawo yace:


 "Hajiya, sai hak'uri zamanin ne ya ɓaci sace-sace yayi yawa yanzu kana tsaye sai a wawashe ka, musamman mata dake rik'e jaka lagajeje sai kaga an fizge ta, musaman cikin kasuwanni, kuma duk talauci ne ke damun mutane ALLAH de yayi mana me kyau."


Sadiya dake kallon mai Mangwaro baki sake!, sam bata ma gane me yake cewa, mik'a mata Mangwaron yayi.


 "Gashi ki bar kuɗin".


 Jiki asanyaye ta karɓa tayi tai mai godiya, shi kuma yayi gaba, saka Mangwaron tayi a jakar ledar da maganin matan ke ciki, nan hanunta ya taɓo alamun kuɗi. Da sauri ta zaro tabbatar sune kuɗin cinikinta ne, ta maida su tayi hamdala tace:


 "Kai ALLAH nagode maka shaf ! nama manta ma anan na aje, na ɗauka ajaka na saka, shegen ɓarawo kaje can na barka da ALLAH, bai fi dubu ɗaya dama acikin jakar ba, kai! yau na auna arziki".


 Haka ta gama magan-ganunta ta sami ɗan adaideta ta k'arasa gida.K'arfe bakwai na dare ne ya kaita gida, har an idar da sallah, tana shiga gidan tai tozali da baban khadija na zaune da yaran fuskarsa a haɗe, nan ta wayance.


 "Malam kayi hak'uri yau na auna arziki sata akai min".


Kallonta yayi yace "kaɗan ma kenan". 


 "Au haka zakace malam?"


 "Kinga Sadiya baki da abunda zaki cemun, nide ina miki fatan ALLAH yasa ki gane".


"To malam Allah ya baka hakuri" Nan ta fita da sauri taje ta ɗora ruwan girki tayo alwala.***********


Haɗaɗiyar motar Hajiya saude ce ta nufo hanyar gidanta, duk ta ɗauke hankulan samarin nan 'yan zaman banza, yau su huɗu ne zaune ɗaya yace:


"Kai! matar nan ALLAH ya bata duniya, kullum da kalar motar da zaka ganta aciki".


D'ayan yace "Mijinta ai ya tsaya mata, kaga motar nan ta ta samma miliyan biyar".

 

Wani ma yace "kai ALLAH yayi mana arziki", ɗayan kam baice komi ba, sai kallon gidan kawai yake,dai-de lokacin me gadi ya wangale mata gate ta shige ciki.Hajiya Saude na shiga gida ta tarar da Maryam afalo, nan ta zauna kan kushin ganin maryam na kallo tace.

 "Sannu da gida".


Maryamta amsa mata tana yi mata sannu da zuwa,Harda zata kira me aikinta ta ɗauko mata juice, sai kuma ta tashi ta ɗauko da kanta da kofi ahaɗe ta zauna gefen maryam.


 "Kai na gaji maryam".


 Saida ta sha juice ɗin sanyi ya sanyaya mak'oshinta, san nan ta kalli Maryam.


 "Bani labarin nan mana".


Maryam tace "kai Anty baki manta ba ashe"! dariya tayi 

"to ya zan manta" suka saka dariya gaba ɗaya, tashi tayi zaune ta fara bata labarin kamar haka:"Anty kinsan de muna zaune da mijina lafiya ko?, to mijina irin mazan nan me mabuk'ata to tun nima ban iya jurewa ba har na saba, to kinsanni akwai son harkar Social Media to akwai wani group a Whatsapp da kowa ke faɗin irin matsalolinsa, sai wata ta faɗi mtsalarta dai-de da irin tawa a kan mijinta mabuk'acine, to tana so agaya mata yanda zata gyara kanta..


 Sai nake mata comment akan cewa Ai in ta saba shikenan.To wasu daga ciki sai suka ke magana da mamaki ganin bama gyara, suka ce nan ai dole ne saida gyara, sai wacce ta kawo matsalar take tambayar kamar yaya? sai wasu sukace ai yanda mijinki ke mabuk'aci aidole sai kina gyara kanki, hakan zaisa ya daɗa jinki zam -zam, nan fa nace a bamu sirrin.


Haka fa mata kowacce sai tace kayan mata zata fara amfani da shi, nan fa abun ya zauna akaina, domin da ni sam ban damu da shan kayan mata ba saide kawai ina yawan shan fruit da wasu sinadaran.

 


Wataran na hau facebook awani group naga wata na tallan kayan mata, yanda take zuzuta kayan nata yasa naɗau Lambarta dake ajiye ak'asa,ba ɓata lokaci na buga wayarta, nace ina son kaya. Nan fa matar ta fara zayyano min irin kalolin da take dashi sunaye kala-kala akalla zasuyi kala goma, take fa muka dad-dale wajen dubu goma, domin ni nawa da yawa nake san saya.

 

Na ce mata Saidai ni gashi kano nake, ita kuma naga tasa Zamfara a hoton kayanta, ce min tayi wannan ba matsala bane in har inaso tana tura kaya ko ina, intura mata kuɗin ta account ,gobe za asa komin kayan a mota, sai na aika tasha a karɓomin.Hakan Kuwa akayi.

Washegari ta turomin da kayana, inda dama na riga na tura mata kuɗin ta cif-cif ta account.Nan fa nazo na fara amfani da kayan, ni kaina na gamsu da kayan. Dan haka da na kumai mata waya nake gaya mata take cemin ai akwai ma waɗanda sukafi wanda ta bani kyau, cikin zumuɗi nake mata bayanin ta ajemin, nan nata samma shan kayan mata haik'am, gani ina samun gamsuwa da kayan amma shi kansa mijina aɓangaren yanayin jikinsa ya canja yana jin wani iri, ran nan muna kallo yake cemin:

Wai mesa kwana biyu nake jinki idan muna mu 'amala kamar wacce keda mayen karfe,wallah abun yawa ya kemin, kode wani abun kike amfani dashi? nayi dariya nace mai bakomi, yace min kodai kayan matan nan ne da mata ke amfani dasu? Nace mai habade! basu bane, yace min inde sune ki dena wallah ,wani hali nake shiga, na taɓaji ma ana maganar cin kayan itatuwa ma kaɗai ya wadatar inma zakiyi kiyi kaɗan.


Basarwa nayi haka na cigaba da amfani da kayan matan nan hankalina kwance.


Maganin matsi kuwa, abubuwa kala- kala take bani ina yi dasu, idan wan nan bai ba saita ban wani, bana kwana biyu bansha sabon kayan maganin mata ba.


 A gaskiya bansan meye ba kwasam! sai na fara jin canji ajikina ya canja, kai-kayi agabana ga marata na ciwo haka kaɗan -kaɗan ga wani ruwa dake zuba me wari, da kyar nake iya tafiya saboda wani irin murɗawa da marartawa keyi inna tashi.


Nanfa hankalina ya tashi dana maigida. Koda muka je asibiti ganin halin da nake ne yasa aka bamu (abdomino pelvic scan)hoton ciki da mara,Sannan aka tura mu (laboratory) dan ɗiban fitsarina da ruwan dake fita a jikina mai warin tsiya.


Bayan fitowar sakamako 

binciken likita kemin bayani ina amfani da wasu sinadaran magani masu karfi. Wanda hakan har yaso taɓa mahaifata bugu da k'ari cikin magun-gunan akwai Wanda ya toshe min bakin (ovary) ɗina ya zamana ba asamin (releasing) ɗin kwan haihuwa ta yanda ya dace, kuma ya zamana k'arfin maganin yana kashe (sperm) ɗin mijina dalilin hakan ne ma yasa nakasa ɗaukar ciki.


Game da ruwan dake fita ta katsana kuma, sakamako ya nuna na wasu sinadarin magani ne nake amfani dasu, wanda suke sun sami (contamination da pathogens) (harmful microbes). Samun gurɓataccin k'wayoyin cuta,Hakan ne ya kawo Min da fitar ruwan ,kuma a kullum suna K'ara gurɓacewa ne shine dalilin jin warin ,haka nan likitar tayi tamun bayani tare cemin na kula karnaje garin neman gira na rasa ido.Haka na dawo gida na cigaba da shan magani zugi da raɗaɗin dana keji ya ragu. Amma ruwan be dena zuba ba. Nanfa mijina abun yayi mai zafi dama gashi mabuk'aci ba damar ya kusanceni ,ganin lokaci nata ja sai ya ce aure zai k'ara na tashi hankalina na ɗaga mai hankali.


Watarana daya dawo yana gayamin nan da (next week) wani satin za a tambayo aurensa, na hau masifa yace min to yaya na keso nayi? yace min aise da ya gaya min in guji kayan matan nan, gashi nan bansan dame ake yiba najama kaina, koma inayi ai se inayi da kaina ,amma kawai mata ta kawo min shirme ina siya, haka yayitamin bam-bamin faɗa,kuma yace hakurinsa ya k'are bazai iya ba.Tun daga nan zaman lafiya ya k'are, rashin kunya naita yi mai na kasa saita linzamin bakina, sam kullum cikin faɗa muke.


Wata rana muna zaune muna (breakfast),inda nake shan tea. Mijina ya kalleni yake cemin an saka rana aurensa, take naji wani daram! a k'irjina ,nan kuka ya k'wace mun ina nuna banason auren, k'arshe nace mai wallahi yayi aure bashida zama lafiya. Buɗar bakinsa sai yace min baki da wani amfani agareni yanzu,dan haka ki bini asannu.


Kamar mahaukaciya haka naita bala'i kishi ya ɗebeni na watsa mai ruwan Tea dake gabana akofi, da sauri ya mik'e cikin jin zafi yana nunan maiyasa nake hakan, ban tsaya haka ba na dinga zaginsa ina cewa ya sakeni bazan zauna da kishiya ba, haka na lailayo ashar ina aikawa iyayensa ina zagewa sam idona ya rufe.


Take ya hau huci yace na tafi na barmai gidansa ya sakeni saki ɗaya, ya fice daga gidan.


inason mijina wallahi, alokacin daya sakeni naji nadama ta shigeni, ga ciwo dake damuna haka na bar gidan na koma gidan mu,naita zaryar Asibiti da k'yar da siɗin goshi na warke, saida nayi wata bakwai ina fama har ALLAH yasa na warke sumul, to tunda ga nan na guje su kuma ina fata na koma ɗakina Anty wallah ki daina."Haj saude ta sauke numfashi tace:

 "Lallai dole ki gujesu, kinga jalala baki yi dace bane kawai, kuma bakiyi hak'uri ba, aida kinsani lallaɓa Mijinki kikayi tunda kece me lalura,k'addara dai ta riga fata. Amma kinga ni mun daɗe da sadiya nata me kyau ne ba matsala".


 Maryam tace "Anty ai badaga nan bane kinga nima fa munyi wajen shekara ɗaya ina karɓar kaya a gun matar. Anty kiyi saffa- saffa tunda akwai masu kyau, wanda akeyi da duk wani nau'in abubuwan da muka sani kuma masu amfani. Amma da yawan wasu wallahi bakya sanin dame suke yinsa, kawai kawo mana suke muna banka,haba ace ba kada wani (Natural teste) saina maganin mata. Anty gaskiya nake gaya miki".


 Anty tace "to naji zan duba."


Haka Hajia Saude tayita tunanin labarin da maryam ta bata, k'arshe ta watsar amma zata tuntuɓi Sadiyar kan magungunan.


*Ku biyo Miemie queen da Ashnurpyar* 👌🏻

t


Babi na uku (3)Sadiya ce zaune a tsakar gida sai kulla wasu saiwa take aledodi, ga Robobi da magunguna kala- kala, sallamar Magajiya da Lauratu ne ya karaɗe tsakar gidan. Sadiya tace "yau su magajiya ne agidan namu?". Gefe guda suka samu suka zauna, magajiya tace "kai lalle sadiya ciniki ya kan-kama, tana kallon kayan dake gaban sadiyar.


Bayan sun gaisa. Lauratu ta kalleta "nikam kin saro wasu kayan ne?"

Sadiya tace "Aa sonake sai na shiga kasuwa".

Magajiya tace "kin kuwa saro Wani haɗi daga Niger wlh yana da kyau, ni kinga harna haɗashi da wani ya daɗa yawa".


Sadiya tace "Au har yanzu kuna almundahanar?" Lauratu tace "yo mai za'a fasa, kece ance kina ɗan gwamutsawa kyafi samun riba da yawa". Taɓe baki tayi "A'a banaso na gwamutsa sana'a ta da cuta, a hakan ma baban khadija baya son ta, kuma ku dena haba ni kam ba ruwana".


 Lauratu tace "bafa wani abu bane kinga idan muka saro masu kyau, sai mu samo saiwoyi mu dake su luk'wi mu gauraya, sai kiga sun daɗa yawa mun daɗa samun riba".


Lauratu tace "ke nifa wataran ma bansan takamaimai wane kalan gari nake hadawa dashi ba". Suka tuntsire da dariya. Sadiya tace "kudai" Lauratu tace "ke kina nufin baki haɗawa?".


Sadiya ta rike baki "wallahi duk zuma ta da gumbata masu kyau ne, da yajin 'yargata duk da kyansu, sauran kuma ai kunsan inda muke sarowa".


"Barta batun 'yan sari Sadi, suma kansu masu bada sarin suna sirkawa, kuma kinga duk hotunan da suke mannawa jikin kwalba ko kwali, duk na Jan hankaline da neman kasuwa, sai kiga magani guda ace zaiyi aiki kusan shida, duk bogi ce mu muka san halin 'yan kayan mu, indai kika sami mai kyau kwakkwara guda saiki haɗa da ɗan sirki shine ai ribar ". Magajiya tace."Ke matan ne na yanzu fa ko kashin awaki kika daka inde matsayin maganin matane wlh siya zasuyi", suka kwashe da dariya.Lauratu ta cigaba, "Nifa ba wannan sirrin kaɗai na rik'e game da saida kayan nan ba, kunga IYA MAGANA! ta DADIN BAKI wallahi shine, kayana ko baki niyar siya ba Ina kanan-naɗe ki da zance zaki kwasa, bama irin suji kince musu wannan haɗin daga SOKOTO ko NIGER aka kawo miki su, ko kice kinga wannan karki sake kiyi amfani dashi sai lallai kin tabbatar tabbas oga na nan, karki sake kisha fa saikin san lallai za'ayi, ina zaune zaki zo kiban labari, ko kice musu wannan ai na MALLAKA ne, zaki mallake zuciyar miji sai yanda kika so dashi, to anan gun zaki ga rububi".


 Shewa sukayi gameda tafawa sadiya ta tattara kayan ta, "Aah! To lallai Nima Zan rinka ɗan sirkawan, yan'uwa yaude Kun wayar dani sosai har naji na gamsu da bayaninku".


"To da dai yafi miki wallahi" cewar lauratu. 

Suka Kalli juna ta gefe gamida kashe ido ita da magajiya, ita ko Sadiya bata gani ba.


Nan suka cigaba da bugun ruwan cikinta dan jin abinda ta taka harta fisu samun ciniki, can Sadiya tace "ni abinda nasan inayi aikin mallaka in har kinaso to sai naga kalarki Irin hajiyoyin nan masu sakin aljihu, dana caje ki dubannai kin lalemin su zan karɓi sunanki dana maigida naba Malam na tsohon gida wallahi aikinsa kamar yankan wuka, ammafa sai an caske mai nairori kuma in zaki iya bin sharuɗɗo-ɗinsa, kwana ki har ruwan tsarkin Hajiya dana mijinta ya karba".


Kallon juna sukai suka jinjina kai, daga nan suka cigaba da sauraren Sadiya na watsa musu labari.


"Hajiyan cema ta ban mamaki ko taya ta samo nashi mijin nata oho!". 

"To in ba dubunnai nagani ba banayin wannan, shiyasa ba Kowacce mace nake mawa ba, akwai wani aiki da malam yake min da tsumi ake baki ki kurkura baki kiyiwa oga juice da ruwan gade k'yama amma wallahi akwai fa aiki".


Magajiya ta cafe "Tototo! ke kuma taki dabarar kenan, kice kinada malamai masu miki aiki, haba nidai ince, shiyasa kike da customers harda Hajiyoyi"."Sosai ma ai matan ne yanzu sai da haka yawancin magungunan mallakar ne ai sai mun haɗa da malaman zaure, kuma duk abin nan wallahi duk da mijina baya son Sana'a ta nakasa ba malam yamin aiki akansa, dan nasan za'a iya ban abinda bazan iya basa yaci ba, ko ace in cusa jikina haka kawai ban san Menene ba".Lauratu tace "uhm kaji wayau ba, nikam bana wata wahalar haɗa aiki da malam in suka dameni da son na mallaka farar takarda nake samu na k'onata sai na zuba tokar acikin wata takardan, sai na kanan-naɗe da zare kamar laya, saina bada nace asa a k'ark'ashin filon oga ta can ciki kullum yarika kwanciya akai. Kunga ko! Shi kanshi takardan da ban k'onawa, watarana asirina yakusa tonuwa, awani gida matar dana Kai mawa ta buɗe layar bayan na tafi shine taga babu rubutu a jiki ,dana koma har kusan fad'a mukayi, shine dana ba shamsiya labari kinsanta ta wajen gidansu Nazirun Hajiya mai shago?"


"Eh nagane ta" cewar Sadiya. "To itafa, shine tace na rik'a sa toka gudun kota kwana sai ince tokar malam ne ya bada haka shi yasan kome yayi aciki. Ko in kika sami ɗan turarenki mai k'amshi ki basu kice na mallaka ne, ko kiba da na barbaɗe a abinci ko wanka yanzu za kiga sun sallama miki, shiyasa bana wasa da amfani da maganin rufe baki koda basu ga aiki ba basu iya tambayarka kosu fasa, A'a saidai ma gobe inkin dawo su k'ara, iyakaci ma in har kin iya cemin baki ga aiki ba, sai nace wallahi kuma yanayi sosai fa, kinsan wani namijin taurin rai garesa, wani namijin kurma ne baya nuna miki yaji abu amma ga wannan kiyi amfani dashi, Ina tabbatar miki zaki ga can ji.To duka abin fa saida 'yan dabara".


Sauke numfashi sadiya tayi tace "Lallai."

 Lauratu ta cigaba "kunga tunda na amshi maganin nan wanda ake sawa amarar kwasan tuwo da rubutu na tawada a jiki?, (MALLAKAR MARA ) ake cemai to ban sake Siyan na k'warai din sa ba, kasuwa naje na kwaso marar tuwo da yawa abina, na sai tawada na kwashe irin wancan rubutun Sannan na sanya garin magunguna na yayi kamar na wancan, haka naita saida su Ina cewa na Mallaka ne ki wanke kisha sauran kisama maigida a juice, ba tare da nasan ko fassaran mema aka rubuta ajiki ba.To inba hakan kakeyi ba, ba zaka samu fita da wani riba mai kyau ba,Allah dai ya yafe mana".Magajiya tace "inma laifi ne ai bamu kaɗai ba tunda abin harda malamai ma".


"Anya! Wanda zai bid'i waɗancan abubuwan akira shi malam Kuwa? harda ruwan tsarki fa! sai de boka". Cewar Sadiya.


"To koma dai Menene ai sunfi mu laifi Allah dai mun tuba".


Haka nan dai waɗannan mata suka cigaba da hirar sana'ar tasu gamida fallasa dabarun da Kowacce take amfani dashi wajen ganin ta samu nata rabon, gun Mata masu shayeshayen magunguna barkatai.


*(To gare ku mata sai akula ba ace shan magani kwata-kwata baida kyau ba, amma kisan wanne kike sha? Kuma gun wa kike osiya in har ke ba zaki iya zama ki haɗawa kanki maganin da zai gyara miki jiki da hannunki ba, to saiki san wacece kika mikawa yardarki. Zamanin nan yanzu ya lalace tsoron mahalicci yayi karanci, kowa burinsa yaga ya cimma buk'atar kansa ne ba tareda la'akari da duba zuwa ga hanyar da ake biba, wajen cimma bukatar zuciyoyin namu)*.


Bayan sun gama hirar ne lauratu da Magajiya sukai ma Sadiya sallama, tare da ajje batu kan cewa suma zata haɗasu da malaman dake mata aiki, dan samin cigaba cikin kasuwancin nasu. Inda itama Sadiya ta ɗauki shawarar su kan zata rik'a sirka magungunan ta da wasu abubuwan kamar yanda sauran abokan sana'ar nata keyi dan samin karin riba.


Magajiya da lauratu na fita daga gidan Sadiya suka tafa gami da dariya, domin ganin yau hak'an su ya cimma ruwa.

 (Abinda Sadiya bata sani ba shine waɗan nan mutanen sun daɗe suna mata hassada, kuma a kullum bak'in cikinsu be wuce na kayan ita Sadiyar yafi nasu inganci ba, domin da haka ne tafisu yin ciniki, sunsha bata shawara lokuta daban-daban dan ganin itama tana saka almundahana cikin kayanta yanda zasu zamo d'aya,basu taɓa cin sa'a ba sai yau.)Bugu da k'ari gashi ta bayyana masu wani sirrinta, wanda ada basu sani ba, kuma ta musu alk'awarin haɗasu da ɗaya daga cikin malaman dake mata aiki.

*Ku biyo Miemie da Ashnurpyar* 👌🏻*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*  *RUWAN DARE*


     *DAGA*


*MEEMI BASHIR(queen)*       *&*

     *ASHNUR PYAR*

       

   
Babi na huɗu (4)***********

*Wacece Sadiya*


Sadiya 'yar asalin garin zaria dake kaduna ce.

Aure ne ya kawo ta kano. Auren saurayi da budurwa sukayi itada salisu wato mijinta, wanda shi asalinsa ɗan garin kanon ne aiki ya keyi acan zaria ɗin, inda suka haɗu da sadiya har suka dai-daita kansu sukayi aure.Sadiya itace 'ya ta biyar acikin gidansu. ALLAH ya zuba mata san kuɗi tun tana budurwa hakan yasa take ɗan abubuwan siyarwa agidansu da yake basu da shi sosai.Bayan aurenta da Salisu aka kawota kano, suke zaune a unguwar gyaɗi-gyaɗi,yana da rufun asiri komi dai na jin daɗi na dai-dai iyawarsa yana yi mata ba tada wata damuwa. Salisu irin mutanen nan ne masu san wadata iyalansu, hakan ya zamanto Sadiya tayi ma sauran tsaranta zarra, duk abinda ya gani ya bashi sha'awa to Sadiya zai sayowa.Cikin ikon ALLAH ta haifi yarinyarta ta fari wato khadija, rayuwarsu gwanin sha'awa har ALLAH ya bata wani cikin ta haifi ɗanta na biyu khaleed, to kwatsam! bayan haihuwar ɗan da shekara ɗaya wani tsautsayi ya faru da salisu, inda aka koresu awajen aiki shida wasu mutane, takamai-mai basu san mai sukayi ba, sai daga baya sukaji wai sabbin ma'aikata za'a ɗauka acewarsu duk su gurɓatattune shiisa za'a ɗau sabbi, wanda su su salisu sun san kawai cutarsu akai ,haka ya dawo gida ba aikin yi kuma bai iya kasuwanci ba.Ganin zaman bazai fussheshi ba ,yasa ya ɗauki kuɗin da aka sallamesu ya shiga harkar kasuwanci a haka dai ya fara sana'ar saida kayan robobi a kasuwar k'ofar wambai yan robobi. 


Sana'ar dai da ita yake ci dasu, afarkon sana'ar ya samu kuɗin nasa wasu basu fito ba, sakamakon bashin da wasu suka karɓa na robobin,haka yaita bin su dan su bashi amma kuɗin basu fita ba, ba yanda zai iya haka ya fawwala wa ALLAH kan wan nan iftila'i daya hau kansa, kuma ya yarda da k'addara hakan dai bai ɗaukewa iyalansa komi ba haka yake k'uk'utawa yake musu.Rainuwa ce ta fara wanzuwa a gurin Sadiya komi ya kawo saita raina, ganin da suna cin daɗi, ko magana yayi mata haka zata gwasale shi ganin baida kuɗi, nan da nan sadiya ta canja hali komi masifa gani take kawai ya mak'ale kuɗinsa ne baya wadatasu,alhalin shi kam ta ɓangarensa k'arfin haline kawai, domin wataran har yaje kasuwar ya gama zamansa bai ciniki ba.Wata rana ya shigo da leda a hannu tana zaune tana jin waka. 


"Sadiya ga kayan miya nan,dama dawo wa nai na kawo kiyi miya".Buɗewa tayi taga kayan miyan k'wayoyo ne,sai nama baifi yanka biyar ba, da man gyaɗa k'ulle aleda befi gwangwani ɗaya ba, ture kayan tayi. "Yanzu saboda ALLAH! abunda muke ajewa da da yawa yau shine zaka wani kwaso ka kawo wan nan! yaya zan da naman da baifi k'waya biyar ba? kuma yankan k'anana haba! Abban khadija".


Yace Kai! Sadiya komi fa na rayuwa da kika gani a hankali ake binsa, kinsan dai da duk unguwar nan bamai gaya miki cin daɗi, na ɗauke miki komi, to ke kanki kinsan yanayin kasuwa babu ciniki yanzu, ɗan jarin nawa nake tattalawa komi fa nake danku nake yi ki godewa ALLAH wasu ma hakan suke nema".


 Tsaki tayi "naji" ta kwashi kayan.


Haka dai Rayuwar gidan Sadiya ke tafiya yau daɗi gobe ba daɗi, a haka wataran taje gidan suna taga yanda wata mata tana saida kayan mata taga an rufar mata ana saya,nan fa zuciyarta ya ɗarsu gwanda itama ta fara sana'a, tunda sana'a ba bak'onta bace,dacan kantai aure ma tanayi kota huce takaicin salisu.


 Haka akai kuwa ta samu matar nan ta gaya mata tana san fara irin sana'arta,ta karɓi lambar wayar matar akan zasuyi magana inta koma gida.Hakan matar nan ta ɗorata ahanya itama ta fara sayarwa, a wajen saro kayan ne ta haɗu da su magajiya da Laure.


Da sadiya agidan suna ko biki take sayarwa, daga baya kuma ake biyota gida ganin ba ciniki sosai take ba yasa bi gidaje tana kaiwa.


 Sam! Abban khadija baison abunda takeyi sam! sana'ar batai mai ba, yakan cemata ta canja sana'a sai tace bak'in ciki yake mata, yawon da take yi yayi mai yawa,ahakan harta haifi ɗanta na uku.Cikin k'an-k'anin lokaci akasan Sadiya mai kayan mata, sun ɗinke dasu magajiya ta watsar da matar data fara ɗora ta kan hanyar sayarda kayan.


Ana haka suka haɗu da hajiya Saude a gidan biki, ganin yanda akayi wa kayan Sadiya dafifi har suka kare. Hajiya Saude bata samu ba shine ta karɓi lambar ta,to tunda ga nan suka ɗinke take kai mata kaya, inda take samu ajikin hajiya sauden lura datai Haj saude matar mai kuɗi ce shiisa take rawar jiki da ita, kome takeyi in Hajiya ta kirata to zata ajiye taje.************


Yau ma da Sadiya ke zaune a tsakar gida tana shafawa 'ɗanta na uku mai ajiki, da yake asabar ne ba suje makarant ba yanzu shirin islamiyya sukeyi, huci kawai takeyi saboda faɗan da Abban khadija yayi mata, yana ɗaki yana jiyo ta sai tsaki take, ya rasa mai yasa Sadiya bata jin maganarsa yanzu, dai-de lokacin ta gama shirya su suka tafi islamiyya.Shiga ɗakin tayi "Abban khadija a gaskiya nikam na sare,haba! wallahi sana'a yanzu na fara" .


 Yace "ni ban hanaki sana'a ba, kowacce ma kiyi Kawai de yawon ne banaso".


 "Abban khadija in banje ba taya za'a sani?"


"Nide na gaya miki bana son yawon nan, kizauna kiyi agida inde da rabo hargida za'ana biyoki".


 Buga cinya tayi "saide kayi, mai kake bani, me kake min? komi fa da kuɗina nakeyi, to wlh sai nayi" tai fice warta.


Muryar sa ya ɗaga "kiji tsoron ALLAH, kome kike ALLAH yana gani. Sadiya ni mai son yi muku ne to ALLAH ya jarrabeni da babu kuma ahakan ban rageki da ci da sha da sutura ba, addua zaki min ALLAH ya buɗamin,yawon nan banaso wallahi da kunnena naji anayi dani a unguwar nan kan na k'yaleki kina yawo kullum rana ta ALLAH saikin fita".


Ya jin-jina kai "amma yawon da kike bada yawu na ba na gaya miki,karki manta duk matar dake fita bada izinin mijinta ba mala'iku hartaje ta dawo suna tsine mata,idan kinji to na fita hak'k'inki."Fitowa yayi daga ɗakin ya fice daga gidan.


Tsayuwa tayi jikinta yayi sanyi jin maganar da yayi tabbas tasan Abban khadija gaskiya ya faɗa, kuma tasan butulci ne irin na mata da rashin godewa ALLAH amma tasan shi maiyi ne, banda abunda ya faɗa kansa ada ya ɗauke mata komi ,tunani ta hauyi a zuciyar ta.


'To mai zaisa bazan cewa duk maison kayana ta biyoni gida ba'.

Can wata Zuciyar ta ingizata kan ta cigaba da hakan yafi.

Tsaki tayi "bazan fasa sana'ata ba,idan ba fitar naiba ba samu ake sosai ba."


Haka ta cigaba da aikace -aikace har taji wayarta na k'ara, nanfa ta ɗauka ganin sunan hajiya saude yasa tayi murmushi. Saude take sanar mata da tana san ta kawo mata gumbar mata da yajin yargata da bita zai-zai.


 Sadiya take cemata "yanzu kuwa zaki ganni" cikin rawar jiki ta kashe wayar ta faɗa wanka tasan koba komi Haj Saude nayi mata k'arin kuɗi da alkhairi kala-kala haka ta sullo wankanta ta tafi.


K'arfe sha biyu ta k'arasa gidan Saude.


Yauma 'yan sa'idon nan na zaune akan bencinsu, suna ganinta sukai shiru ita kuma ta haɗe rai nanfa suka hau gulmarta (ALLAH ya kyauta).Can cikin ɗaki suka k'ule bayan taci tasha agidan. Hajiya Saude ta tuno da labarin Maryam nan tace "yawwa Sadiya nikam dama ina son tambayar ki tun ran nan sai kuma na sha'afa,don ALLAH kayanki ki k'araimin bayani kan ingancinsu, duk da na sani suna da kyau".


 Dariya sadiya tayi "kai Haj Saude aike zaki bawa wani labari ma, kayana kinsan fa daga Sokoto sai Niger nake samowa, ke kanki shekara nawa kina amfani dasu".Saude tace "ahh! haba, bafa komi naji labari ne ana cewa akwai marasa kyau, sai nake cewa to zan gaya miki. Sadiya karki sirka naki da cuta, ko nan gaba inde kayanka me kyaune baka da haufi".


Gaban sadiya kam faɗuwa ya hauyi, domin tasan Itama nata yanzu akwai na jabu ciki, nan de ta basar suka cigaba da hira ta bata kayan ita kuma ta lale mata kuɗinta, tayi haramar tafiya ganin mijin sauden ma ya dawo Sadiya ta fice ta tafi.*Wacece Haj Saude*


Saude asalinta 'yar garin nan kanon ce, hakama mijinta ɗan nan kano ne, shahararren me kuɗi ne ɗan kasuwa ne me tashen naira ,kuma yana damawa da siyasa, ya samu kuma tana garawa dashi, suna zaune a unguwar Shagari Quaters inda tamfatse-tsen gidan sa yake, suma auren saurayi da budurwa sukai da Saude.


Saude na damawa agidan sosai, ɗanta ɗaya ɗan shekara 27 yanzu haka yana Oxford Uni yana karatu shikaɗai ALLAH ya basu,sai ɓari da Sauden tayi har yanzu de ALLAH bai k'ara basu ba.Alhaji ya sakarma hajiya kuɗi mota biyu ne mallakarta, wanda Alhaji ya saimata kuma masu ɗankaren tsada, idan ka shiga gidan akalla zakai karo da mota guda 5 haka masu tsada, idan kana gidan kamar karka fito Saboda tsari da zubi da kyau, tabbas ALLAH ya basu duniya tana gara musu.Saude irin matan nan ne 'yan fafa da san nuna fa yes! ita matar me kuɗi ce, ko gidan biki haka zaka ga tana buɗawa.


Motoci kam har na Alhaji hawa take ganin shi bai fiya hawansu duka sosai ba.


Samarin nan kuwa 'yan zaman banza sosai Saude ke tafiya da ruhinsu, ganin irin motocin da take hawa. Sadiya sosai take samu ajikin saude, saboda ita kuɗinta bai rufe mata ido ba musamman in tanayi da kai zata sakar maka.Sai wajen biyar Sadiya ta koma gida yaranta duk sunyi kaca- kaca da gidan saboda sun ci ɗumamen data rufe musu, taji ɗadi da taga Abban khadi bai dawo ba nan taji daɗi aranta.

*ku biyo Miemie da Ashnurpyar*👌🏽👌🏽


*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


  *RUWAN DARE*


     *DAGA*


*MEEMI BASHIR(queen)* 

       *Aur*

     *ASHNUR PYAR*

      


  

Shafin nan Naku ne *RUKY RUBZ, ANNURI & MOM SAHABI,MURJANATU SALEH,IKHLAS MUSTAPHA,UMMITASLIM ,AMRA* Babi na huɗu(5)


*******


A kwana a tashi Sadiya kullum kara samun customer take,har yanzu bata rage yawon kai kayan matan ba wasun har gida suke biyotan, amma hakan baisa ta dena yawon ba.


kamar wata mai lakanin sa'a duk da itama ta fara yin mixed a kayanta shawarar lauratu da Magajiya suka bata, inta saro kaya ta kanyi musu haɗi sai su K'ara yawa musamman na gari wanda ake dakawa, amma duk da haka bata yarda ta cakuɗa dayawa , a tunanin ta in customers basu ganin aiki mai kyau tofa zasu rage siya.


Wata Mata Hajiya ce itama.Hajiya Saude ta haɗa Sadiya da ita, inda matar nan ta rink'a zayyano mata matsalolinta masu girma, kuma duka wai buk'ata take abata maganin su, ita kanta Sadiya tasan lamarin yafi k'arfinta.


 Yau sukayi alk'awarin haɗuwa da matar dan har gida tace zata zo.Zuwan matar suka gama magana tace ta dawo jibi.Bayan tafiyarta Sadiya ta kama baki.


 "Oh! mu dai masu wannan sana'a muna ganin abubuwa daga zaran ance kina sai da kayan Mata shikenan sai ayita kawo miki matsaloli iri-iri da wanda kasani da wanda baka sani ba, wasu matan ma sun girme ma a shekaru amma sai su zauna suyita bayyana maka sirrin aurensu,muma ɗin muji da tamu matsalar mana,nidai matar nan matsalolinta sun wuce iyakan sani na, kawai zan haɗa aikinta da malam".Haka ko akayi matar ta dawo, tana zuwa Sadiya ta bata waɗansu magun-guna tayi mata bayanin yanda za tayi amfani dasu, a k'arshe kuma ta kawo mata shawaran tana so ta haɗata da wani malami dan yayi mata aiki, zata sami waraka sosai gami da matsalarta, bako musu cikin jin daɗi matar ta aminta da shawarar, inda a k'arshe ta ciro kuɗi yan ɗari biyar-biyar taba Sadiya, ita ko ta amsa cike da farin ciki tana murna, lallai da alama tayi babban kamu.
****** ***** *****


Matan gidansu Ameera ne zaune suna hira cikin falon saliha, dama lokaci bayan lokaci sukan haɗu a falon mutum ɗaya daga cikinsu a sha hira yanda ransu keso.


Yau ma kamar dai yanda suka saba abin a ɗakin Saliha ya faɗo, Saliha cetace:

 "Niko Ameera kwana biyu fa naga ɗan canji dana sha maganin Sadiya ba kamar daba, ko kin lura da haka kema?".


"Kai anya Kuwa! ni kuma ban Lura da hakan ba gaskiya".


"Ina tunanin ko marasa kyau ne ta bani dan banga aiki yanda nake so ba" cewar ita Saliha.


 

Ameera tace "Kai haba! bana tunanin hakan. Sadiya fa bata saida jabun kaya. Magun-gunan ta ingat-tattu ne na yarda da aikinsu".


"Hakane amma wallahi nidai kayan dana karɓa wannan Karon basu wani min yanda nake so ba, bari in kawo miki kiga kalarsu".


Nan ta shiga ɗaki ta kwaso magun-gunan data karɓa gun Sadiya. 

Ameera ta shiga dubawa tana faɗin "kuma ai naga duk kalan nawa ne, ni banga wata matsala tare da su ba kisan dama abun dace ne".Aisha tace "Oh! kude bakuda aiki kullum saina magun gunan mata, ko hira zamuyi sai kun kawo mana zancen nan".


Ameera tace "ke in zaki kibar jiran mu indai a wannan fannin ne wallahi kima kanki karatun ta natsu, zamanin nan yanzu mace ta zauna babu gyara babban matsala ne ba zaki tashi ganewa ba sai sanda oga ya kawo miki abokiyar zama, sannan zaki gane kuranki musamman ki haɗu da irinmu ".


"Ameera wallahi ba zaki gane bane, nima fa ba haka nan nake zaune ba, Ina gyara kaina mana amma ba irin naku ba, kinga in niima nake nema nakan yi amfani da Irin su kunun aya mai kwakwa da dabino ko na dafa kanumfari,citta da minannas insha da zuma ko mazark'waila ko nayi blending kankana ko zogale ɗanye insha da madara peak na ruwa, karkiyi mamaki niima da zakiyi Sannan gashi zai taimaka wajen gyara fatar jiki kayi fresh abinka, kinga riba biyu kenan an jefi tsuntsu biyu da dutse ɗaya, in matsi kuke so kuyi ga bagaruwa nan wallahi ta isheka komai zama cikin ruwan sa koyin hayaki da garinshi Kama mace yakeyi gam! ke wallahi ko ruwan ɗimi kika ɗimanci amfani dashi zakiji zam-zam ga kariya daga cutuka, Inko k'amshi da tsafta kikeso ga ganyen magarya nan ba dauɗan da bata wanke wa, shiyasa ma ake wankan gawa da ita ga samun tsari da kariya dan shaiɗanu basa sonta, in k'anshi kuke so ga miski nan Wanda sunna nema amfani dashi.


Kai in nace zan tsaya faɗa muku amfanin abubuwan nan da nake amfani dasu sai mu kwana anan bamu gama ba, ga dai kyau a addinance baka kauce hanya ba, ga kuma lafiya ajiki ban kuma bayyana sirri na da mijina ga wata ba, mai yafi wannan daɗi da riba?""Aisha kenan! ba zaki taɓa ganewa ba waye zai tsaya wahalan saiya nik'a wannan ya nik'a wancan, koya dafa wancan ya dafa wannan? gade Wanda daka tashi shane ko matsi a sauk'ak'e , in niima nema ga irinsu emergency kinasha shima ai ance da kayan marmari akeyinsa".


 

Aisha tace "ance! kenan kinga baki da tabbas akai hausawa dai suka ce gani ya kori ji.Niko da zaku ji shawarata nima da kun gwada nawa akwai litattafai masu kyau na masana gyaran jikin mace a addinance da ɓangaren lafiya.


 Da zaku saya ku rink'a dubawa da yafi muku ba tare da kun wahalar da kanku da banke-banken magunguna marasa amfani ba".


Saliha tace "to mu dake dai Kowa so yake aɗauki nasa ace yafi, in hakan be yuwa Kowa ta rike sirrintahausawa sunce Wanda yasan darajar goro shike nema masa.. ""Assalamu Alaikum"


Akayi sallama a k'ofar fakin daga waje.

 

"Wa alaikumu- salam" 


Suka amsa baki ɗaya, wata farar mata ce doguwa mai matsakaicin jiki ta shigo falon. Saliha ta mik'e cike da murna ta tare ta tana faɗin.


 "Oyoyo Aunty Zeenat oyoyo aunty, dama kin dawo ne, yaushe kika shigo garin namu?"


Murmushi tayi gamida samun wuri ta zauna.


 "Ai kya bari in zauna ko, kin ritsa ni da tambayoyi tun ban zauna ba, sai kace yar jarida". Dariya sukayi gaba ɗaya."Shekaran jiya Na shigo kano ai".


"Ikon Allah ashe baki daɗe da sauka ba".


Fridge ta buɗe ta ɗauko Mata lemo me sanyi ta tsiyaya mata a kofi. Sannan suka kara gaisawa.


Bayan sun gaisa dasu Aisha,.Ameera tasa hannu ta kwashe magun-gunan da Saliha ta baza ɗazu a tsakar fakin, sannan sukayi wa Saliha sallama.A waje bayan sun fito Aisha ta kalli Ameera suna kan tafiya sashensu tace.


 " Ni wallahi auntyn Saliha na birgeni matar akwai natsuwa ga fara'a kuma dukda Irin matsayin ta bata wulakanta mutane Sam! Kinga kwanaki shawarar nan data bamu naji daɗin amfani da ita sosai".Ameera tace "eh haka ne amma ai yau nasan Saliha zata sha fad'a, dan da wuya in bata ji kaɗan daga cikin hirar da mukeyi bagashi kuma anfito da magungunan a tsakar ɗaki ta gani, kuma kinsan ta hana Saliha sayen kayan matan nan, duk da nayi dabarar kwashe wa kamar irin nawa ne nasan saita tanka".


"Ni ai gara ma data gani kinga zata k'ara yi mata faɗa ,me yuwa tafi ɗaukar shawarar ta kan nawa, kema ki daure dan Allah ko na ɗan wani lokaci ne ki ajje magun-gunan ki, ki gwada irin nawa za kiga banbanci"."Tam naji alarammiya zan gwada".


Dariya sukayi inda Kowacce ta shige cikin ɓangarenta.
*Ku biyo Miemie da Ashnur pyar* 👌🏻👌🏻
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


  *RUWAN DARE*


     *DAGA*


*MEEMI BASHIR(queen)*  

   *ASHNUR PYAR*

       

     


 *Wan nan shafin naki ne MARYAM MUHAMMAD😍*Babi na shida(6)

Aunty Zeenat Yaya ce agun Saliha uwa ɗaya uba ɗaya suke, sai dai akwai tazara sosai a tsakaninsu dan tun bayan haihuwar ita Zeenat ɗin sai da iyayensu sukayi shekara goma sha biyu cif kafin suka k'ara haihuwa, da haihuwar ta sake zuwa sai aka haifi 

Saliha, su biyu iyayen nasu suka haifa sun taso cike da so da k'aunar junansu, akwai shak'uwa ta sosai a tsakaninsu.Aunty Zeenat ita ce ta tsaya tayi karatu sosai inda tayi karatun ta kan fannin daya shafi Mata zalla, sai data zama cikakkiyar likita a wannan ɓangaren wato (gynecologist) duk wata matsala data shafi lafiyar 'ya mace tana da ilmi akan shi.Saliha ta rigata yin aure domin ita ba tayi karatu sosai ba, aure tanuna tafi buk'ata shiyasa tana gama secondry akayi mata. Aunty zee bata yi aure ba saida ta kammala karatun ta yanzu haka shekara biyu kenan dayin aurenta, ta haifi yarinya ɗaya sunan mamansu aka asamata Zainab. Sunje wani workshop ne nasu na ma'aikatan lafiya garin Abuja bayan sun dawo shine tazo gun k'anwar tata domin bata san ma ta dawo ba, kuma dama akwai agenda ta haɗuwa tsakaninsu. Duk da Saliha ta riga yayarta aure amma ita bata taɓa haihuwa ba. Saliha tasan Auntyn ta sarai bata son hulɗa da takeyi na shaye-shayen magun-gunan Mata, saboda haka ganin su da tayi yau a falonta tasan dole sai ta sha fad'a.


Hira suke na 'yan uwan juna. Zeenat kamar ba za tayi wa k'anwarta magana akan kayan data gani ba,Saliha harta fara jin daɗi cikin zuciyar ta, k'ila Auntyn tata ta manta ne dan inba mantuwa ba tabbas ta san zatai mata magana wannan wajibi ne.Sai da suka gama duk abinda za suyi dan tama fara shiri domin tafiya, kwatsam! Saliha taji Zeenat ta jeho mata da tambayar da ta ɗauka ma ba za tayi taba, ashe tana sane.


 "Little sis wato dai har yanzu baki fasa sha da amfani da magun-gunan mata ɗin nan dana hanaki bako?".


"Laa! Kai haba Aunty ya zaki ce haka nifa tuntuni na daina".


"Taya za ayi in yarda kin bari,in har kin daina to meya kawo waɗancan magungunan dana gani ɗazu Ameera ta fita dasu cikin falon ki?"


"Laa! Aunty kawo min fa tayi dan inyi amfani dasu niko saboda sanin kin hanani yasa ban karɓa ba, ce mata nayi bana aiki dasu yanzu".


 Zeenat ta tabbatar k'anwarta ba zata fad'a mata gaskiya ba, tunda ta fara wannan yan zagaye-zagayen alhalin ita tasan abinda taji kafin ta shigo ɗakin. Sallamarta biyu ba suji taba, saboda tafiya da hankalin su yayi gun hirar da sukeyi, sai data k'ara sallama a karo na uku ne Sannan suka jita. 
Tasan Ameera ce a kullum ke k'ara saka k'anwarta a wannan hanyar, dan ko tazo tayi mata nasiha ta bari kwana biyu ita ke maida ita ruwa tsundum da munanan shawarwarin ta.

 


Taso ace alakar k'anwar tata yafi k'arfi da Aisha ba Ameera ba, dan tuni ta gane Aisha ra'ayin su be zo ɗaya dasu ba.


A kullum rok'on Allah take ya ganar da k'anwarta yasa ta daina cuta da illatar da kanta da takeyi ba tare da ta sani ba. Tana cikin wannan tunanin ne dabara ta faɗo mata tasan abinda zatayi the chines proverb said *_("If I hear, I understand. But If I do, I learned. If I see I remember"_)*

Zata nuna mata (evidence) da idanunta matuk'ar ta gani baza ta taba mancewa ba.


"Kince kin daina ko? To Ina fatan hakan ya zama gaskiya, kuma ina so ki tambayi mijinki ranar Monday kizo gidana akwai abinda zan nuna miki, ina tunanin innayi haka zaki K'ara gane matsala da illa Irin ta amfani da magun-guna barkatai, sayi wannan sayi wancan har ka kai ga cutar da kanka".


"Na sha fad'a miki cewa :

 Shifa niima da daɗi a jikin mace yake ba a magani ba, duk halittar mace ta duniya da kika sani Allah ya halicce ta da ni'imarta da daɗinta a cikin jikin ta, abinda ake so kawai ya zama ta kula da kanta yanda ya dace, ta hanyar nisanta da guje ma nau'in abinda ya shafi sanyi shiga jikin ki, taya zakiyi haka? Ki nisan ci tsarki da ruwan sanyi, shan ruwa mai tsananin sanyi a ko wane lokaci, domin yin hakan na sanyaya sinadaran dake samar da ɗumi cikin jikin ki,Ko yawan zama a k'asan siminti ko tiles ba inner wear a jikin ki, wannan tun mace na yarinya ake so mahaifiyarta tasa ido kan hakan, tare da kula da duk wani yanayi da zai sa sanyi ya shiga jikin ki na sosai to ki guje masa.


 Ki jimiri tsarki da shan ruwan ɗumi da 'ya'yan itatuwa, hakan zai sa ki kasance kina cikin ɗumi koda yaushe, wannan ne zai adana ɗumin jikin ki da ni'imarki wanda kuma shine daɗinki. Yes daɗin mace a jikinta yake".


Ta ɗan da kata, ruwan juice din dake gabanta ta kurɓa daga bisani ta cigaba."Ina fatan yanzu kin fahimci dalilin da yasa nace ni'marki da komai a jikin yake? Kiyi hak'uri kinji ina faɗo maki magana haka direct kamawa tayi, dan bana son ki da shaye-shayen magunguna barkatai ɗin nan da kike, su magungunan da kike gani ba komai suke sawa ba face (forcing ) tursasawa na'urorin jikin ki suyi aiki fiye da ka'idan yanda Allah ya halicce su suyi, mace mai yawaita shan magani dan ta sami ni'ima da wacce ke amfani da natural things don ta sami nata ni'imar, kamar misalin ace fanfon borehole ne na ruwa guda biyu, sai ace kowane lokaci fanfo guda ɗaya shi a kunne yake ruwan shi nata zuba, yayinda ɗayan shi sai ana bukatar ɗiban ruwa ake kunnashi.


 To abin a fili yake dole watan -watarana wanda ke kunne Kowa ne lokaci ruwan cikinsa ya riga na ɗayan k'afewa, to in kina shan magunguna ba bisa ka ida ba, haka zaki sa ni'iman jikin ki yayi ta fita over kafin wani lokaci zaki koma fayau, zai kasance da zaran baki yi amfani da magani ba to mijinki ba zai taɓa jin daɗin ki ba, to ina labari?".Zuwa yanzu jikin Saliha yaɗan fara sanyi domin Antyn ta yau ta fito mata ɓaro ɓaro ne. Ta gumi tayi tana dad'a cigaba da sauraran abinda ta cigaba da cewa.


"Kinga ke a yanda kike ɗin nan baki taɓa haihuwa ba to baki da buk'atar k'are kanki kan matsi, 'yan abu kalilan ne zasu wadatar dake, domin bisa ka'ida macen da bata taɓa haihuwa ba, bata buk'atar kayan matsi face ruwan ɗumi tsarki da ruwan magarya/bagaruwa, shan fruits da nau'in tsumi mai inganci da sauran su, in nace mai inganci kinsan abinda nake nufi. Saboda macen da bata taɓa haihuwa ba komai nata a rufe yake, bata da k'afofi wanda sanyi zai iya shiga jikin ta har ya raunana mata halittanta, kuma koda ace haihuwa kikayi kinga tsumi, dahuwar nama domin ciko da halittar ki amfani da ruwan ɗumi na bagaruwa, shan zuma, madara, fruit to duk bai kamata ki wuce waɗannan ba, bance waɗan nan sune iya kan gyara ga Wacce ta haihuwa ba, but they are the main ones.


 Matan wannan zamanin yanzu duk an haukace da maganin mata, musamman in kina social media ɗinnan ko ina ka taɓa Facebook, Watssp duka magana ɗaya ce MAGANIN MATA indai group ɗin mata ne, maganin mata wai shine zai sa ki mallaki mijinki shin, ko shi zai kwatar miki soyayyar ta gaskiya a gun miji taya ya?


 

Su kakannin mu iyayenmu, da suka sami so da k'auna da cikakken kulawa ta mazajen su shan magunguna Irin wannan sukayi?.


Sam! Biyayya sukayi da K'okari wajen sauke dukkan nauyin da Allah ya ɗora musu akan mazajen su tare da basu cikakken lokutansu wanda yanzu mu mata na wannan zamanin harkar waya ma bata bari aba mazaje lokutansu, sai kaga mace mijinta na zaune tana can tana latse-latsen waya musamman taji ana talla ai an kawo sabon kaya, ke sufa kansu masu sai da magun-gunan ba komai suke iya amfani dashi ma akansu ba, sai da su baku kowane kwab'an Ku sha, kuma da zaki gwada tambayar su da suke cewa ga maganin mallaka shin su ɗin sun mallaki mazajen su ne?. 


Little sis ni zan barki hakaIna fata bayanai na a wannan lokacin ya zama sun shiga kunnuwanki, maganin mata mafi yawancin su babu inda zasu kaiki face filin dana sani a k'arshe, su magun-gunan nan illolinsu yafi amfaninsu yawa, musamman in anyi amfani dasu ta hanyar data sab'a ma ubangiji misali : 


Bin malaman tsibbu ko bokaye.


Amfani da magun-gunan da basu halarta ba a addinan ce, k'ila a baki abinda yake najasa ne ace ki cusa a cikin jikin ki, wata in tayi matsi tun bayan la'asar bata wanke shi ko cire shi a haka za tayi sallah, ta dalilin magun-gunan Mata ne yanzu ake Bayyana Sirrin Rayuwar Aure wa'iyazubillahi ga Rashin biyayyan Aure.


A k'arshe kuma su kasance sun cutar da LAFIYAR ki, kinga suna kawo bushewar gaban mace ta zama in har ba maganin tasha ba to a bushe zata kasance, akan kai wani lokaci ma da ko tasha maganin ni'iman ba zai sakko ba ma'ana kin k'afe, suna zazzago da naman gaban mace ko fitar ruwa wanda in yayi k'amari yakan haifar da wari mai ɗoyi har ya jawo miki k'yama a wajen Nijnki,domin Namiji bai iya kusantar mace inhar tafara wannan warin,wai shin

to ina ranar hakan ne?".


Ta mike tsaye gamida ɗaukan jakar ta, "to nidai zan tafi in kin nemi izinin mijinki zaki sami zuwa ki sanar min, ranar Monday sai kizo akwai sauran abinda zan nuna miki ".


Godiya tayi mata tare da rakiya har bakin motar ta, sai da ta shiga motar ta, ita kuma tana ɗaga mata hannu Sannan ta dawo falon jikin ta yayi sanyi, koda bata yi karatun Aunty ta ba, amma a tunani kaɗai na me hankali tasan akwai k'amshin gaskiya a bayanan data mata.


Wani K'arin tunani ne ma yazo mata tabbas Sadiya mai kawo musu magani ita ma mijinta ba son sana'ar ta yake ba, to meyasa ita bata mallake shi ba?.
*Ku biyo Miemie da Ashnurpyar* 👌🏻
[22:29, 2/17/2018] Mumcy💯: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

  *RUWAN DARE*


     *DAGA*


*MEEMI BASHIR(queen)*         

*Aur*

     

 *ASHNUR PYAR*

     
Babi na bakwai (7)


*********


*BAYAN KWANA BIYU*Dr Zeenat ce tsaye itada wata nurse a harabar asibitin da take aiki suna hira,da yake duk sun gama abunda zasuyi zasu tafi.


 Haka suka fita dansu k'arasa motarsu, da yake zeena rage wa ɗayar hanya kallon zeenat tayi tace:

"Nikam ɗazu naso ganin patient ɗinki wan nan matar agaskiya bantaɓa Jin tashin hankali irin hakan ba ace wai silar maganin mata."


Zeenat tace "ina tunanin baki ganta ba ko?".


"Wallah sam ban gantaba kinsan yau kaina fama nai yana ciwo shiisa banje ba."


Jin-jina kai zeenat tayi ta tashi motar suka fara tafiya tace "da kinganta da saikin tausaya mata,wallah mata na rasa meke damunsu, duk sun maida hankulansu kacokan a zaman aure, sun ɗauka maganin matane Solution nasu, sai kiga mata na yiwa miji rashin biyayya da rashin ɗa'a, amma idan am mata magana sai tace ai tana iyaka k'ok'arinta, to aganinta harkar Sex shi kaɗaine hanyar zaman aure ko! shi isa mata suka raja'a wajen ganin sun zama ɗaya da ɗaya shiisa suke ɗirkar magani da cushe- cushe aganinsu hakan shi zaisa miji ya mallaka masu kansa".


Kallon maryam tayi da jimami "yanzu cases ɗinmu na mata da muke samu mafi yawa saiki ga matsalar kayan Mata ɗin nan ne"


Mariya tace "Hmmm ai ni wallahi abun matan ne sai ahankali."


Zeenat tace "kinga ma munyi magana da k'anwata Saliha, kinga yarinyar nan yanda take bankar kayan mata dana matsi kala- kala itama , kullum naje gidan nan sai nayi mata faɗa, kuma dama tun jiya monday nace tazo gidana bata samu dama ba sai gobe, dama so nake na nuna mata shaida".


Mariya tace "aikuwa to yayi hakan ALLAH yasa ta gane .


Tana komawa gida ta yiwa Saliha waya kan gobe zata biyo ta ɗauketa suje asibitin ta tambayi mijinta, nan saliha tace zata tambayeshin.Washegari k'arfe 9 tana kofar gidan Saliha, bata daɗe ba ta fito ta shiga motar suka gaisa tace "ya zeena wai me zaki nunan ne?"


 Zeenat tace "ki bari dai muje ki gani hakan nan suna tafiya suna hira har suka k'arasa.Basu jima da zuwa ba mariya ta k'araso duk suka ɗun guma. Sunje ɗakin da aka kwantar da matar suka buɗe lokacin 'yan uwanta na zaune suka gaida Dr zeenat tace su ɗan fita zasu duba matar.


Bayan fitar su Saliha sai zare ido take, zeenat ta kalli mariya "mik'on file nata nan ta mik'a mata ta duba ta kalli matar da a zaba ya isheta sai hawaye take "sannu" Dr zeenat tace mata "kan jiya da yau ya kikeji?"


Tace mata "da sauk'i yau kan jiya".


Zeenat tace "kinga wan nan" ta nuna saliha, "itama irin halinki bata da aiki sai yawan shan maganin mata da matsi barkatai dan ALLAH ki gaya mata yanda abun ya faru dake duk da komi tsautsayi ne amma hanyar lafiya abita da shekara".Matar ta kalli Saliha "wallahi 'yar uwa ki kiyaye kanki, ki kula ni kinga nina jama kaina, banida aiki sai matse -matse da cushe-cushen magunguna marasa inganci a gabana ,wanda nake saya gun wata mata, na daɗe ina amfani da su kwatsam! sai ran nan take cemin an kawo wani haɗi wai maida tsohuwa yarinya, idan nayi matsi dashi wallahi gam zan haɗe na koma tamkar budurwa. 


Jikina na rawa nace ta kawon, bayan ta kawon ne na fara amfani dashi tun safe na saka dama cewa tayi hakan zanyi sai dare na wanke da ruwan ɗimi.Tunda na saka nake jin gabana yayi wani irin dumm! haka na ɗauka duk acikin aikinsa ne, sai da nazo wankewa na kwalla ihu saboda ganin gabana yayi jaja wur kamar k'onuwa, kuma ya cakuɗe naji gaban nawa Kamar zai rufto k'asa, nayi yunkurin mikewa na kasa, kai karshe dai sai fito dani akayi daga ɓanɗakin,, ba shiri akayo dani asibitin nan" tana zuwa nan azancenta ta fashe da kuka.


"Kaicona na cuci kaina garin neman gira na rasa ido,kuma inayin hakan ne duk dande mijina ya daɗa sona kuma dan kar yayi min kishiya sai gashi na cuci kaina".


Numfashi zeenat taja ta kalli saliha da idanta ke zubda hawaye jikinta yayi sanyi.

 "sis kinga dai ko! waallah randa aka kawota kamar bazatai rai ba, koni dana zama likitar ta wallahi saida nayi kuka ganin yanda gabanta yake neman lalacewa ".


Ta juya kanta gurin matar "kinga ko! dan ALLAH mata mu kiyaye lafiyarmu ko yaushe fa mune ak'asa in komi kikeyi dan namiji to wallahi shi babu ruwansa idan kika ruɓa kanki wata zai auro to mai gari ya waya? ALLAH ya baki lafiya yasa 'yan baya su gane" nan saliha ta fita daga waje ita kuma ta kuma ta cigaba da checking ɗin matar.

 


Fitowa Dr zeenat tayi tace Saliha ta tashi,Jikin Saliha da yayi sanyi tace "ya zee agaskiya na ɗau darasi dan bakiga yanda na tsorataba wai ace gaban mutum ne ya koma haka insha ALLAH daga yau nide na dena, zan ɗau shawarki da ta Aisha Zanje ta gayan irin nata, nagode Anty zee ina alfahri dake".


Jin-jina mata kai zeenat tayi "yawwa sis bakomi ki gaida gida" nan saliha ta fita tana alwashin gaya ma su Ameera.Tunda ta koma gida take sak'e- sak'e haka duk ta ɗebo kayan matan da take dasu ta watsar ashara tana jiran Aisha su dawo dan duk basa nan har Ameera, tasha Alwashin Aisha na zuwa zatace ta koya mata yanda take dabarunta kuma zata gayawa Ameera gaskiya inta ɗauka kanta.

*Ku biyo Miemie da Ashnurpyar*   👌🏻

[22:29, 2/17/2018] Mumcy💯: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

  *RUWAN DARE*


     *DAGA*


*MEEMI BASHIR(queen)*     *&* 

   *ASHNUR PYAR*  

      

   Babi na takwas (8)**********


Wata rana da yammaci aka kawo ma Sadiya sabbin kaya daga Niger, tun safe sukayi da Hajiya zata Kai Mata kaya amma sak'on basu zo ba sai yanzu, ganin Irin kyawun kayan da aka kawo mata ne yasa tace.


 "Kai bari sai na kaiwa hajiya kayan nan a yau ɗinnan bazan bari sai gobe ba, tunda hajiya tace Alhaji ana sa ran tafiyar sa gobe ne".Babbar yarinyarta ta Kira 'yar kimanin shekara bakwai tana bar mata rikon 'yan kannenta.

 

"Kinji Khadija ga k'annen ki nan ki kula dasu ba daɗewa zanyi ba kinji ko?".


"To mama".


Yarinyar ta fad'a mata cikeda damuwa a fuskarta kamar zatayi kuka, gasu da uwa amma sun zama kamar marayu.


"Mama fita zakiyi ne?" Cewan mai bima babbar.


 

"Eh khaleed kuyi hak'uri ba daɗewa zanyi ba yanzu zan dawo, kunga ma ko Abbanku bai san Zan fita ba sauri zanyi in dawo".Kamar zai ce zai bita amma yasan in ya faɗama masifa zai sha. K'aramar ko sai kuka ta keyi mamansu tasa kai ta fita tabar gidan abinta, mai napep ta tara ta hau, a lokacin an kusa kiran sallan magriba.


Kafin minti arbain takai gidan. Sadiya ce zaune gaban Hajiya Saude ta baje magun-guna kala-kala bayan sun gaisa tayi ma Hajiya albishir da cewa yau kaya fa idan tayi amfani dasu oga zai bar mata na kashewa sosai, domin ciki harda mantuwa komi ta tambaya Alhaji zai bata.Haka nan hajiya Saude ta kwashi kaya tana murna kuɗin ta duka ta biyata.


Ta d'auki hanyar komawa gida kamar yanda ta saba ɗon tayi dare, sauri-sauri take domin gari har ya soma duhu, aka kirata awaya.


Gidan wata mata abokiyar cinikinta ta nufa Wacce take can gaba da gidan Hajiya Saude.Allah ya sani bata k'aunar zuwa gun matar nan domin daga gidanta zuwa bakin titi inda zata hau napep akwai ɗan tafiya, sai an wuce wasu bishiyoyin dake bayan layin hanyar sam ba tada kyau.


Kullum idan dai har tayi dare bata cika son biyawa gunta ba saboda tsoro, yau ma dalilin daya ya sata zuwa gidan domin tace mata kuɗi hannu, ita kuma Sadiya indai akwai naira to kukan shirya. 


Bayan ta baro gidan a yanzu har duhu yayi,tafiya take tana zancen zuci 'waɗanan bishiyoyin Allah ni tsoro suke bani, su suke k'arama hanyar nan duhu fa! amma gari da ɗan sauran haske, hanya ba haske haka ai sai ama yimaka sata ko duka ba wanda ya sani, Allah dai ka kaini.'


Tana cikin wannan zancen zucin ba zato ba tsammani Sadiya taji wani abu ya bugeta gum! Cikin razana tsabar tsoro tayi ihu, dama Sadiya akwai aukin ihu inta ga abin tsoro, Saidai ihun da tayi babu wanda yajiyo ta saboda nisan gun da bakin hanya, tayi yunk'urin juyawa kan ta farga kawai taji kamar anyi sama da ita ta faɗo! Jakarta da ledan magun-gunan dake hannunta suka zube k'asa, daga nan bata k'ara Sanin inda take ba.Can gida Kuwa har mijinta ya dawo nan ya tadda yaran su kaɗai kamar yanda ta saba barinsu indai zata fita.


Yaran suka taho suna maai oyoyo k'aramin yana faɗin "baba zan ci abinci, yunwa nake ji".


 Ranshi a ɓace yace "ina mamarku?"


 Babbar ta amsa mai da "ta fita, amma tace yanzu zata dawo ba zata daɗe ba".


Tsaki tayi ya jinjina kai 'Tafi k'arfinsa ba shida yanda zaiyi tunda dai bata jin maganarsa, zata fita ma bai da arzikin da zata sanar mai.'


Indomie ya fita ya lallaɓa ya siyama yaran suka ci, shi kuma yana zaune ,Zuciyar shi sai azalzala take

'Yau in Sadiya ta dawo zamuyi ba daɗi da ita, domin tura tafara kaiwa bango'.Shiru-Shiru yana sa ran yaga shigowarta bata shigo ba zata dawo yanzu tun yana dubawa har abin yafara bashi mamaki wajen goma na dare ake nema. Sadiya bata shigo gida ba gashi yaran har sunyi barci, wanda a al'adarta data Saba muddin tayi fitar yamma bata bari suyi barci, takan dawo musu da tsaraba suci sannan ta basu abinci kan suyi barcin,domin dama indai da yamma ta fita to suda abinci fa sai in ta dawo, kuma duk daɗewar ta bata wuce bayan isha'i, bata taɓa kai wannan lokacin ba.Tun yana fishi har yafara sakkowa inda daga k'arshe ma tsoro ya kama shi domin goma da rabi ake nema.


'Ina taje ne? Ina ta tsaya haka? Anya Kuwa lafiya! tabbas ba lafiya ba, bata taɓa kai wannan lokacin ba.' Sadiya Ina kikaje ne haka me kuma ke shirin faruwa Yau".Ya faɗa da ɗan sauti


Duk haushin ta da yake ji sai yakau kuma,ya koma tunanin abinda ya tsaida ita har wannan lokacin bata dawo gida ba, ganin har shaɗayan dare tayi ne yasa shi fita sai daya tabbatar ya rufe ko ina saboda yara sannan yabi hanya ko Allah zaisa yaga ɗuriyarta.Amma duk iya inda yake tunanin inya duba zai ganta yaje be ganta ba, abu kamar wasa har kusan k'arfe shabiyun dare mijin nata be ci sa'ar ganinta ba, ofishin 'yan sanda ya yanke shawarar zuwa dan kai musu rahoton abinda ke faruwa gashi dare yayi.Yasha wuya sosai dan bashi ya koma gida ba sai wajen biyu saura na dare.Ga uban tamabyoyin da yasha a police station, ba tambayar data fi ɓata masa rai Irin tambayar da wani ɗan sanda yayi mai "shin tun yaushe ne tabar gida?"


"Yallabai ɗazu da yamman nan ne".


"Tana da yara?"


"Eh yallabai,su uku ne"


"To dawa ta fita a cikinsu?"


"Bata fita da Kowa ba yallaɓai".


Zuwa yanzu ya fara k'osawa da tambayoyin wannan ɗan sandan sai kace yana son jin ya akayi aka haife ka.


"To dama ta saba fita Irin hakan ne? Koko yau ne rana ta farko?"


"Takan fita Irin hakan ba yau bane farko".


"To Kai kasan abinda take yine inta fita, ka taɓa binci kawa tunda kace takan fita ɗin ba yau tafara bakoko baka san ina ma?....


"Dakata yallaɓai ya isa haka Na sani nasan inda take zuwa....... ".


Sai kuma yayi Shiru ya kasa k'arasawa taya zaice musu ga abinda Sadiya take yawon siyarwa.


D'an sandan yace "sorry mai gida Inna ɓata maka rai, aikina nake Shiyasa nake ma wanɗanan tambayoyin duk cikin aikina ne".


"Ba komai yallaɓai na fahimta", nan ya zayyane musu komai saboda haka bashi da masaniya kan wasu gidaje ne matar shi ke zuwa.


Sunyi mishi alk'awarin za a bincika ta duk inda yada ce.


"Zan dawo da safe yallaɓai".


Haka ya koma gida zuciyar sa cike da damuwa bai San Ina matar sa ta shiga ba, be san a wani hali take ciki ba, ga yara duk sunyi jiran ta har sunyi bacci ,Yanda yaga Rana haka nan yaga Dare.

*Ku biyo Miemie Bashir da Ashnurpyar* 👌🏻

[22:29, 2/17/2018] Mumcy💯: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*  *RUWAN DARE*


     *DAGA* 


*MEEMI BASHIR(queen)*         &

     *ASHNUR PYAR*

       


Babi na Tara (9)************


Koda gari ya waye Salisu na Allaha-Allaha yana so ya wuce office ɗin yan sanda da wuri,nan ya nufi ɗakin yaran shi dan ganin ko sun tashi daga barci ,ga mamakinsa k'ofar ɗakin ya hango a buɗe! cikin hanzari ya k'arasa ciki suna kwance su duka amma babu Khadija ciki, da sauri ya nufi k'ofar bayi ya kwankwasa, Shiru ba amsa buɗe k'ofar yayi a hankali amma sai bai gan ta ciki ba, nan fa hankalinsa ya daɗa tashi, ya duba ko ina da ina bai ganta ba.


 'To taya akayi ta fita gidan in har fita tayi ba tare da ya jita ba, Koko shigo wa akayi aka ɗauke ta.' 


kawai sai yasa hannu aka ya fara kuka.


"Wai meke faruwa hakane! innalillahi wa inna ilaihi raji'un?".

 'To taya akayi har aka shigo cikin gida aka ɗauki ɗiyar sa be sani ba, gashi shi dai ba wani baccin kirki yayi ba, kodai Aljanu ne suka shafi Sadiya! saboda fitan dare da takeyi gashi kuma sun sace yarta yanzu'.


 sambatu yarink'ayi wani azuci wani afili,shi kansa bai san me yake faɗa ba. 'Dole yaje ya sake sanar da jami'an tsaro abinda ke faruwa.' 


Yana niyar fita Nan kuma sai yaran biyu suka tasa shi gaba da kuka, domin ya tashe su wajen K'okarin neman Khadija da yake yi,kuka suke suna kiran Mama, a dole ta sa shi kwasan su yayi gidan iyayen shi dasu. Ya bayyana masu halin da ake ciki sun shiga tashin hankali sosai.


Nan hajiya babarsa tace ya barsu nan kan aga sadiyar, ba ɓata lokaci k'aninsa yaje makarantar Allo dake gabansu ya faɗa dan ataimaka da addua. Haka salisu ya koma gidansa yayi wanka tunani yayi daya kira yan uwan matarsa ya sanar musu.


Suma daya gaya musu hankulansu ya tashi. Maman Sadiya kuwa, kuka ta saka haka kowa yana jimamin harda khadija kowaya ta'allak'a abun ga aljanu daga kanon har Zarian adduoi akeyi kawai dan neman tallafawar ALLAH.


Haka nan 'Yan sanda suka tsananta bincike ganin abun ya daɗa gaba har an sace Khadija.
*****-**--**-****--*


Can gidansu Ameera zaune su ke a falonta "Niko Sadiya mai kaya wai ko lafiya! kwana biyu Ina ta kiran lambarta amma baya shiga gashi bata zo ba kuma ina buk'atar su."Aisha tace "duk da dai bana hulɗa da ita sosai, amma Sadiya ba'a gyaɗi-gyaɗi take ba?"


 Ameera tace "eh acan take".


Aisha tace "kinsan inada k'awa a gyaɗi-gyaɗin ko? to jiya naje na kejin suna hira da kishiyarta, kan ɓatan wata mata da 'yarta ,abun yaban mamaki! naji sunce sunanta Sadiya tana saida maganin mata 'yar tata sunan ta khadija.Wai uwar aka fara sacewa daga baya aka ɗauke 'yar ba agansu ba, an neme u sama ko k'asa ba agansu ba, ba wacce ta faɗo min Sai sadiya, to tun jiyan dana dawo nakesan tambayark"


"Anya Kuwa! ban tunanin hakan, dan nima naji labarin ɓatan wata Mata ama social media nagani,amma ban kawo Sadiya bace bamma san harda 'yarta ba se yanzu, naga da girman ta da hankalin ta to ina zata shiga?".


"Lallai Ameera yanda zamanin ya lalace da sace-sacen mutane ba babba ba yaro ke har kya ce wai da hankalinta da girmanta?".


"To Allah dai shi kyauta, inma itace amma ni dai zuciya ta bata bani ba,saboda sam! nama manta sunayen yaranta, nafi rik'e de khalid bansan tana da 'ya khadija ba ,Koma wacece ALLAH dai ya sa aganta ya kuma kare mu, ni sabbin magunguna ma nake so na karɓa gunta, Saliha ko kema naki sun kare ne?""Hmmm Ameera nifa na faɗa miki na bar karɓan maganin Mata gun wata mace saboda ni nasan abinda nagani da idanuna, ki raba ni da zancen kayan nan pls, nikam na daina in Sadiya tazo ma zan fad'a mata ta daina haɗowa dani, kema ina fatan Allah yasa kiyi saurin ganewa tun kafin lokaci ya k'ure miki".


Ameera tace "me kika gani da idanuwan naki?"


"Hmmm! Ba zaki gane bane Ameera,kinsan de ranar nan nace muku zamu fita da Anty zee ko? to asubiti mukaje nan duk ta gaya musu abunda ta gani.


 "To ni tun daga lokacin ina ma dawo wa na zubar da kayan ,kuma Aisha inaso ki samu lokaci ki gayan ingantattun da kike amfani da su.

 

Ameera nide shawara nake baki atoh!, Ita kanta Sadiyar da kike zaman jiran baki san a wani halin take ba, baki da tabbacin inma ba ita ɗince ta b'ace ba,tunda yau wajen kwana nawa kina Neman layinta kince be shiga, yanda ta Saba da tafiyar yamma dare Mata a hanya Allah yasa ba gamo tayi ba,oh ni Saliha shidai maganin matan nan haka matsalolin sa keda yawa ashe".


Ran Ameera ya bƁɓaci sosai ganin Saliha yanzu ita ma tabi sahun Aisha, kushe kayan Mata take, ba tareda ta ce musu komai ba ta tashi tayi ficewarta, duk da itama jikinta yayi sanyi jin bayanin da saliha tayi,amma tabbas ta ɗarsawa ranta cewa dace ne matar kawai ba tayi ba.


***

Duk inda ya dace ya kamata ace an duba Sadiya da k'aramar yarinyar ta an bincika amma ba a same ta ba, layinta kuma kiran duniya anyi be shiga.


Haka ake wuni Neman su in dare yayi shi kuwa Salisu ya nufi gida iyayensa sunyi-sunyi kan ya bar zuwa kwana cikin gidan nasa tunda ba asan me ya ɗauke Sadiya da yarta ba.


 

Shi Kuma yaki yace lallai cikin gidansa zai kwana,kome zai faru dashi Sai-dai ya faru, ɓatan matar shi da yarinyarsa gabad'aya yasa yaji bai k'aunar kan shi ,gani yake kamar duk laifinsa ne, tunda shi ya kasa hana Sadiya fita,duk da yasan yana hanatan itace bataji.


 A rana ta uku ne da ɓatan nasu ,cikin dare kawai Salisu yajiyo motsi daga waje cikin Sauri ya tashi sanda ya ɗauka ya nufi wajen yana sanɗa sai dai ya dud-duba bai ga Kowa ba, yana dawowa falo sai ya hangi ɗakin yaran shi a buɗe, cikin farga ba ya doshiakin.


 'To ko nima dai ɗin sun zo ɗauka tane tun......'

Khadija ya hango kwance bisa gado sai sharar barcin ta take "subhanallahi ko dai gizo nake gani!".


Ya k'arasa kusa da ita taɓa ta yayi yaji mutum ce ta gaske nan ya daɗa tabbatarwa ita yake gani ba gizo ba.


Rungumeta yayi yana kuka tareda yin hamdala ga Allah mabuwayi.


Babu wata alama a jikin Khadija daya nuna ta sami wata matsala lafiyarta k'alau.

 

Labarin dawowar Khadija sai ya K'ara firgita mutane anguwar su gabad'aya Kowa ya sakan kance Sadiya tayi gamo ne da Jinni garin yawon ta da take.

Nan aka duk'ufa rok'on Allah kan itama Sadiyar Allah ya bayyanar da ita kamar yanda ya bayyana yarinyar ta.


A ɓangaren binciken da 'yan sanda keyi yanzu an tsinto ledan magun-gunan Sadiya da Jakarta da ta wurgas a hanya lokacin da aka ɗauke ta, banda waɗan nan kayan kuma anyi iya bincike akan hanyar amma ba aga wani sheda ko alama da zai nuna Sadiya ba.


B'angare guda kuma yan sanda sunyi iya tambayar da zasuyi ma Khadija dan su sami wani information amma ina abu yaci tura, anyi juyin duniya kan ta faɗi Ina ta kwana jiya Ina taje yarinya ta kafe ta cije kan cewa ita bata je ko Ina ba baccinta takeyi cikin gidansu da kannenta, da aka matsa mata da tambayoyi yarinya ta fara kuka tana tambayar Ina k'annenta da mamarsu suke akira mata su.Ganin ba za'a sami wani k'wak'waran bayani a gun ta ba sai aka ɗauke ta itama aka kaita can gidan kakaninsu inda sauran k'annenta suke.*Ku biyo QueenMiemie da Ashnurpyar* 👌🏻
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  *RUWAN DARE*


     *DAGA*


*MEEMI BASHIR(queen)*        

     *ASHNUR PYAR*Babi na goma (10)*Wan nan shafin nakune makaranta👌***************


Gyare-gyare take a falon ta tana k'ara gogewa.


"Salamu alaikum, sis har yanzu baki gama aikin nanba?".


Juyowa Aysha tayi "wallahi kuwa Saliha, yau gani nan de har yanzu ban gama ba, kinsan in oga na nan ko nan da can bai bari na mik'e har seya fita".


 Saliha tace "inyeee! lalle matar tasan kanta" .


Dariya sukai "hmmm! Saliha kenan ai ku zance keda Ameera kuda keda Sadiya tana baku kaya".


Taɓe baki tayi "ke rabani da wan nan, ai na dawo daga rakiyarsu, yanzu ma zuwa nayi ki rubutamun ki bani sirrin duk wani abu da kika san me amfanine daya dace". "To nagama bari na ɗauko takarda da biro."


Bayan taje ta ɗauko takardar ne ta zauna.


 "Kinsan ni duk abinda zanyi to saina tana di duk abubuwan kuma masu sauk'i. Na farko kinga idan k'arin Ni'ima kike so zaki iya samun:

Madara peak,Ruwan kwakwa, Zuma,Riɗi.Saiki haɗe su wuri guda, bayan kin daka riɗin yayi laushi to sai ki dinga haɗa su wuri guda kina sha, sosai yake k'arawa mace ni'imar jikinta."


Dariya saliha tayi "Kai! kuma kinga komi me sauk'i ne wajen nema, ina jinki saura wani."


Aysha tace "san nan kinga zaki iya samun:

Cucumber,Kankana,Tumatur,Mazarkwaila, Madarapeak, Kanunfari,Dabino.

Kinga idan kika samu zaki yanka kankana duka harda 'ya'yanta,haka itama Cocumber haka harda 'ya'yan ta, sai Tumatur shima kada amatse ruwan cikinsa, saiki daka kanumfari ki jik'a dabino ki cire k'wallayen, ki haɗe su guri guda ki markaɗa a Blender saiki juye a mazubi, ki saka mazarkwaila ta narke aciki, san nan ki zuba zuma ki juye madara peak gwangwani ɗaya ki rink'a sha safe da yamma hmmmm! saliha zaki sha mamaki."


Lumshe ido saliha tayi "inajinki sis ALLAH dai ya biya".


"Haka zaki iya ɗimanci shan kayan fruit sosai musamman kankan."


Saliha ta jinjina kai.


Aysha ta cigaba "kinga zaki samu kanumfari shima wani nau'in k'arin ni'ima ne da motsa sha'awa, zaki samu kaninfari ki jik'a shi shi kaɗai ki rinka sha, kina iya kuma samu kina kama ruwa da ruwan kaninfarin.."


"Masha ALLAH Aisha wan nan garaɓasa haka komi ka haɗa da kanka ba fargaba".


Aysha tace "kinsan me ki samu k'wai ɗanye da liptom ki jik'a liptom da ruwa kaɗan har sai yayi baki, saiki fasa k'wai ki kaɗa shi, saiki zuba cikin ruwan liptom ɗin,kina iya zuba madara peak saiki zuba zuma kisha, hmmmm! sosai yake kara ni'ima."Gyara zama Saliha tayi tana cigaba da ɗauke abunda Aysha ke gaya mata akanta.


"San nan zaki iya samun: Zogale ɗayanye, k'wai,Zuma,kanumfari,madara peak.ƴ

zaki gyara ɗanyen zogalenki ki wanke ki markaɗe shi sosai, kitace ki zuba garin kanumfari ki zuba madara ta ruwa da zuma ki rink'a sha safe da yamma, hmmmm! ba magana. Saliha wallh sai kince dama baki bata kuɗaɗenki abanza, kina sayen kayan da bakisan dame ma akeyi baduk da akwai masu kyau da inganci ,amma kayi da hannunka yafi bawai dan kashewa masu sai dawa kasuwa bane, Aa kawai de kasan me kakeyi ne kai karan kanka..."Saliha tace "tabbas haka nima na gane".


"San nan idan matsi kike sonyi zaki iya samun bagaruwa ki tafasa zaki iya saka ganyen magarya, bayan yaɗan wuce ki shiga ciki zaki ji dede ALLAH inkikai hakan ya wadatar kuma ruwan ɗimi ya zama na tsarkinki koyaushe, hakan zai sa kijiki ko yaushe zam -zam ni kinga abunda na gaya miki haka na keyi, akwai wasu ma kawai zan k'yaleki hakan ne ki fara da waɗan nan.


San nan zaki iya Samun Aya kina cinta sosai,ko ki yawaita kunun aya kina sha,haka su rake ɗin nan duk suna da amfani ga mace.

 

Haka zaki iya samun Dabino ki jik'ashi idan yayi taushi sai ki cire k'wallayen ,ki saka acikin firij ya samu kamar kwana uku ,saiki ɗauko ki dame shi tamkar fura saikina sha,hmmm! ba magana yar uwa".Saliha tace "kai masha ALLAH nafa gode ni kaina danaji kin gayamin wallah duk sai naji na samu nutsuwa araina".


Aisha tace "Saima kinyi amfani dasu babu illa ga lafiyarki sam! yauwa na manta bangaya miki bama ki samu:

Habbatus-sauda da Albabunaj.

Ki tafasa albabunaj da habbatus-sauda ki rink'a sha kuma zaki iya kama ruwa dashi.Yana sa sha'awa da kara ni'ima ga mace kuma zai kareta daga mazajen aljanu harya sa sha' awarta ya karu fiye da yanda take da lafiyarta,kinga dama haabbatus sauda kariya ce ga aljanu."


Saboda daɗi saliha rungume Aisha tayi "kai! masha ALLAH , sani ma nada daɗi. ALLAH ya kara ilmi nagode, kinga dama inada wasu abubuwan da kika faɗa, saide Albabunaj ne bansan ina zan samu ba?".


Aysha tace "a islamic chemis ake saidawa".


 "Nagode Aysha, yanzu kuwa zanje nayi wasu."


 Aisha tace "yawwa yar uwa".

Saliha ta tashi ta fita cike da jin daɗi aranta.
************


"Kinga Laure bafa zan hak'ura ba, saboda ALLAH dan zalinci sai ku bani abu mara kyau?".


 Wata matashiyar mata ce zata kai kimanin shekara talatin da biyar take zazzagawa laure masifa da alama awajen 'yan sanda suke."Haba Zainab! shekara nawa ina saida miki da kaya amma sai yau kice bame kyau bane haba! bai dace ba"


 "Kinga Malama saurara haka naɗau kuɗina har ddubu ashirin(20k)na damk'a miki, dan ina son magunguna da kika tashi sai kika ban jabu".


Wani sajen ne dake zaune kan kanta ya mik'e.


 "Hajiya wai meke tafe daku ne? ku ba kuzo kun faɗi meke tafe daku ba, amma kun zauna sai faɗa kuke."


Tashi sukayi suka k'arasa gaban kantar suka tsaya ''yan sanda biyu na saurarensu "munajinku" "Wallah yallaɓai wan nan matar tana saida maganin mata,to ina siya awajenta to sai Za'ai bikin K'anwata sai k'anwar tawa ta bada dubu goma, ni na bada dubu goma dan asai mata kayan da yawa wanda harma taje gidanta basu k'are ba, hakan kuwa akai nayiwa wan nan matar magana nace ta kawon magun-gunan dan amarya ta fara da wuri,hakan kuwa akai ta kawo min na damk'a mata kuɗinta, sai zuzuta kayan take harda cemin ta yarda dasu daga Niger suke inde kayan basuyi ba to na maida mata kayan ita kuma zata ban kuɗina, alokacin tayi dariya tace ninasan kayana gangariya ne ɗaya da ɗaya."


Ta tsagaita da maganar taja numfashi! san nan ta cigaba.

 

"Tun ranar data kawo dana sha cikina ya fara ciwo ina tunanin ko daga nice, saida k'anwata tasha take itama cikin nata ya fara ciwo harda gudawa.


Washegari makociyata kuwa ta shigo gidanmu, muna zaune muna maganar kayan nida k'anwata rashin kyansu, sai kuwa Makociyar tace ita tanaso mu bata haka na ɗan tsakurar mata taje gida tayi amfani dashi, wallahi yallaɓai daga sha kafin yamma ciwo ya murɗe ta saida mukaje asibiti aka ce tasha abu mara kyau ne ya rikita mata ciki,kwananta uku tana a fama sai jiya ta samu sauki ,ni kuma ganin hakanyau na kirawo ita wan matar, nace kayanta bama su kyau bane na gargaya mata duk abunda ya faru tace bata san zance ba, atafau ba zata biyamu kuɗinmu ba, ganin abun yana neman kai ga tara jama'a yasa mukazo nan."


Dan sanda yace "hajiya anyi haka?".


 Laure tai fiki -fiki da ido tace "nide bansan ya akai ba domin maganina me kyau ne".


"To wallhi kuɗina cas saikin maidomin su,ga magungunanki nan dama aikince idan basuyi ba amaido miki".

Ta wulla mata jakar magungunan.


Sajan yace yace "hajiya zaki iya kira mana waɗanda suka sha?".


Tace "tabbas kuwa bamu da nisa sosai da nan".


Take ta buga wayar k'anwarta tace zuzo ita da makociya ,suna nan zaune saiga su kuwa su 2, nan fa kofur ya tambayesu suka shaida mai gaskiya ne.


Kallon Laure yayi datai tsaurbi -tsurbi yace "hajiya zaki biyasu kuɗinsu kuma zamu sakaki acikin mutane masu saida gurɓatattun magani".


Durk'ushewa tayi ta saki kuka wiwi.

"kayi min rai wallahi bani kaɗai na saida mata ba, saida na haɗa dana Magajiya".


 "Wacece ita?" cewar Sajan".


 "Abokiyar sana'ata ne to kayan nawa ne basu cika ba iya na dubu sha biyar ne kawai, haka na buga mata nace ta kawo nata,wanda zai dede da dubu biyar, nan da nan ta kawo aka haɗa".


Sajan ya kalli kofur "kana dai rubuta komi ko?"


kofur yace "yes sir".


Nan ya maida kallon sa gun magajiya dake durk'ushe tana kuka, yace "kira ita magajiyar tazo yanzu".Haka nan Laure ta kira wo Magajiya,wajen rabun awa sai gata, itama aka tsare su aka gaya mata dalilin kiran.


Sajan yace Laure ta biya dubu goma sha biyar ,magajiya kuma dubu biyar, yace kuma zasu tsare su har kwana biyar a celll sabida kamasu da akai da saida gurɓatattun kaya wanda har yakai ga ɗaya ta kwanta ciwo. 


Sajan ya umarci Zainab dataje ta dawo gobe su karɓi kuɗinsu.


Haka sajan ya umarci kofur da wata yar sanda mace suka tasa keyar su laure kan suje kowacce ta samo kuɗi dede wanda aka gindaya mata. 


Da kyar suka haɗa dubu Ashirin cif ,suka koma station aka wullasu cell wanda sai nan da kwana biyar zasu fito, saboda saida gurɓatattun kaya.


Washegari da sassafe Zainab tazo station aka bata kuɗinta ta tafi gida,Su magajiya kam suna cell suna mai danasani wanda akace keya ce.
*ku biyo Meemi bashir(queen)& Ashnur pyar*


[20:28, 2/12/2018] 💕Anty miemie👌🏽: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

  *RUWAN DARE*


     *DAGA*


*MEEMI BASHIR(queen)*

        *Aur*

     *ASHNUR PYAR*
Babi na shaɗaya (11)************


B'angaren Sadiya Kuwa tun bayan da taji ta bige da wani abu ɗinnan, aka kuma yi sama da ita, har ta fita cikin hayyacinta ba tareda ta Kara Sanin inda take ba.


To Koda ta farka cikin wanin bak'in ɗaki ta tsinci kanta, Wanda ta kasa tantace dare ne Koko rana, saboda tsananin bak'in duhun dake cikin ɗakin, bakinta taji shi a ɗaure, hannayenta ma an haɗesu gu ɗaya an ɗaure su ta baya. 


Mutsu-mutsu ta rink'ayi tana neman yin magana amma ba hali, haka nan Sadiya ta rink'a zubda hawaye tana dana sanin halin data tsinci kanta, a dai-dai wannan lokacin magan-ganun mijinta kawai suke faɗo Mata a rai, ba Irin nasihar da be Mata ba, amma haka nan tayi kunnen uwar shegu da shi.Gashi yau a inda ta kasance wurin da bata masan ko Ina bane, bata san hannun suwa take ba.Tunanin yaranta take duk da ta kasance mara nuna cikakken kulawa a garesu saboda sana'ar ta, amma fa tana tsananin k'aunar 'ya'yanta da mijinta, yanzu duk inda suke tasan hankalin su in yayi dubu ya tashi, ba kamar mijinta da Khadija mai wayau cikin yaran.


Sai taji kamar motsin za a zo inda take sai kuma taji an koma, addua take tayi a ranta ubangiji ya kawo mata ɗauki. Gata dama ba gwanar Sanin wasu adduoi tayi ba inma ta sanin to bayi take ba. Haka tayi ta zaman jiran tsammani agun nan amma babu wanda yazo inda take.


Ga yunwa sai nuk'urk'usarta take, haka Sadiya ta kwana a wannan bak'in duhun ɗakin da bata san ko Ina ne ba. Ance dai barci ɓarawo ne to lallai dai kam ɓarawon ne domin Sadiya bata San sa'in daya ɗauke ta ba, tana cikin wannan hali na wahalan.*washegari*


Sadiya ta tashi da matsanan cin k'ishirwa ga yunw.Jikin ta kuma ta ko Ina ciwo yake, ga baki aɗaure ba halin magana.


Abinda yasa har ta iya gane safiya tayi ma, alamun ɗan haske da ta gani ya ratso ta ɗan wani ɓular rami dake jikin k'ofar ɗakin da take ciki, amma banda dalilin wannan ramin da har yanzu bata iya tantance a wani lokaci ake ciki ba.


Can ta fara jin motsi an nufo inda take, nan fa tak'ara takurewa guri ɗaya, idanunta sai zubda k'walla suke.

 'Shikenan lokacin yanka ni yayi, ni Sadiya yau nice a hannun 'yan yan kan kai'.

Haka taita tunani aranta.


Kici-kici aka shiga yi a bakin k'ofar ita dai duk ta K'ara tsurewa saboda bata San Menene ke motsi a gun ba. Kwatsam! Sai taga an buɗe k'ofar ɗakin da take ciki.


 Wani k'aton mutum ta gani tsaye a bakin k'ofa, gabad'aya jikin sa yasha bak'ak'en kaya wulik, yayinda fuskar sa kuma an rufeta da wani hula mai kamar hulan sak'a. Hular itama bak'a k'irin, idanuwan sa kawai take iya hange ta cikin hulan dake lulluɓe da fuskar tashi.


Cikin kakkausar murya yace "oga ita ɗin ce fa! ta farka kuma, a fito da itane?".


Bata ji amsar da aka bashi ba ta cikin wayar dake hannunsa, Saidai gani kawai tayi yazo ya jawo ta waje.Bak'in abu yasa ya rufe mata fuskarta itama ta yanda bata iya ganin komai, Sannan ya mik'ar da ita tsaye ya tura ta gaba yace tayi tafiya.


'Oh ni Sadiya!' sai ta fashe da kuka.

Tafiya ta farayi ba tare da ta kasance tana gani ba, tunda idanunta a rufe suke, in ta kauce hanya mutumin nan ba imani haka yake fizgota ya dawo da ita dai-dai hanya.

Daga k'arshe jawo ta ya rikayi har suka shiga wani guri.


Buɗe mata fuskarta yayi alokacin, su takwas ne acikin ɗakin amma kowannensu fuskar shi a rufe kamar na mutumin daya kawo ta gun, bata iya tantance ko su waye su, domin idanuwansu kaɗai take iya gani, haka zalika ba zata iya gane wani guri bane nan.


Babban cikinsu shine wanda ta gani zaune bisa wata farar kujera ta roba, abinda yasa tayi tunanin shine babban su shi kaɗai ke zaune a bisa kujera kuma ga sauran mutanen sun zagaye shi, gefe da gefe, mutum uku na a gefen daman shi huɗu kuma na a gefen hagunsa, sai Wanda ya kawo Sadiya shine cikon na taran su.


Umurni yayi da a k'araso da Sadiya gabansa.


Suna zuwa sai Ji tayi ya kira sunanta.


 "Malama ko hajiya Sadiya zance? Ke ce uwar ciniki iyayen nema ko, barkan ki da zuwa fada r *Dan gumurzu*".Sadiya sai zazzaro idanu take saboda bakin ta a rufe yake.


Sai ya kece da dariya sai da yayi mai Isar shi, daga bisani ya kalleta yace " kar ki ɗaga hankalin ki idan har kin bamu haɗin Kai babu abinda zamuyi miki aiki ne zaki yimana cikin ruwan sanyi zamu sake kinji ko?".'Wad'an nan Anya yan yan kan Kaine Kuwa?' Cewar Sadiya cikin zuciyar ta.


Daga nan yayi umurini da a buɗe mata bakin ta, don suyi magana.Ana buɗe ma Sadiya baki kawai sai ta hau ihu ana ta wautar wai ita ko zata samu aji a gano inda take, akawo Mata ɗauki.


Tun kafin ogan yayi magana wannan k'aton ya sake sa abu ya maida rufe bakin da yayi mata kamar a farko.


Cikin ɓacin rai ogan yace a fita da ita a maida ta inda take.


"Wannan bata ladabtu ba tukun bama ta Shirya ba ku bari in ta Shirya zamuyi magana".


Nan take k'aton nan ya ingiza ta sai wancan ɗakin da aka fiddo ta ciki ya rufe k'ofar.


Kuka sosai Sadiya take amma ba mai K'ara ba sai dai hawaye tinda bakinta rufe yake,tana dana sanin ihun da tayi.


Anan suka barta cikin d'akin nan, bata kuma K'ara jin motsin wani ba, haka yunwa yayi ta cin ta saida ya zama ko motsi bata iyga tarin salloli akanta, kishi Kuwa ji take kamar zata shiɗe.


Saida dare yayi Sannan ta sake jin anzo an buɗe kofar, k'arfin Sadiya ya riga ya kare bata iya motsawa daga inda take ba,Bata taɓa tunanin dai-dai da rana ɗaya zata iya tsintar kanta cikin kwatan-kwacin halin da take ciki yanzu ba.


Wani guntun biredi da ruwa mutumin nan ya kawo mata, ya kwance mata baki da hannu ɗaya daga ɗaurin da aka mata.Yana kwance ta ruwan ta ɗauka ta kafa kai saida ta shanye daga nan ta hau yagar biredin ba k'ak'k'autawa.


Bayan ta gama ci, rufe mata idanuwa ya sakeyi Sannan ya jata har wannan ɗakin da aka kaita ɗazu, bayan an buɗe mata idanuwanta, me Sadiya zata gani babbar 'yarta Khadija ta hango shinfide a gaban wannan mutumin daya fara mata magana ɗazu, Sadiya ta fara kuka tana rok'onsa kan Allah da Annabi kar su cutar da yarinyarta gaba ki ɗaya dukta d'ad'a rudewa.Faɗi take "wallahi zanyi muku duk abinda kuke so.Amma kada ku cutar dasu"

sai kuka take mara sauti dan tana tsoron karta kara wage baki in tayi haka bata san mai zai sake faruwa da ita ko 'yar taba, gun mutanen data lura basu da alamun imani a tattare dasu.


Gashi yarinyar sai sharar bacci mai nauyi take dan koda shugaban nasu ya karasa gun da aka kwantar da ita, hannu yasa ya bibbigi kumatun ta gefe da gefe amma bata ma san anayi ba.  Dariya shirgegen mutumin nan ya sake yi "aikin ka yayi kyau dorinar ruwa".


"Godiya nake oga". Cewar ɗaya daga cikin yaran shi.


Oga ya Kalli Sadiya yace "kina so ta tashi ko, kina so kisa ke ganin mijinki da sauran yaranki biyu?".


Cikin tsananin ruɗewa ta amsa da "Eh yallaɓai! dan Allah kada ku cutar min da yarinya dan Allah ku kyaleta, ni kaɗai na muku laifi Ku hunkuntani ni kaɗai, koda bansan me nayi muku ba".Mutumin da tunda Sadiya ta shigo ɗakin shine kaɗai yake magana da ita yace.

 "Ba zamu taɓa Kowa naki ba, ba zamu cutar dasu ba, haka zalika kema ba abunda zamu yi miki muddin kika bamu haɗin kai domin wani aiki zamu Saki".Saida ya sauke numfashi! tukun Sannan ya cigaba.


 "Idan kuma har kika sake kikayi gigin saɓama aikinmu da sharuɗɗan da zan gindaya miki ,to ko ki tabbatar kina somi-somin mafarki ne na rasa mijinki da 'ya'yan ki duka, dan ba abinda bamu sani naki ba kuma babu abinda bamu sani akanki ba".Dai-dai nan ya Kira wani da cewa "Kai RUWAN DARE".


"Na 'am oga "


Wani ya amsa cikin mutanen dake a tsai-tsaiye gefen hagun ogansu.


"Matso ka bawa Sadiya ɗan tak'aitaccen labarin ta, dan ta fahimci mu suwaye".


Nan Wanda aka Kira da *ruwan dare* ya fara bada bayanai dalla-dalla akan Sadiya sana'ar da takeyi, yawan fad'a da sukeyi da mijinta kan sana'ar Nata, zirga-zirga, shige da ficen da Sadiya take, unguwannin da take yawan zuwa da lokutan data kan koma gida duka saida ya faɗa.


Kaɗan ya rage fitsari ya zubo mata, domin yanda taji wani na bada labarin ta kamar itace ke bayarwaalhali mutumin da bata taɓa sanin ko shi wanene ba, lallai tabbas maganar mijinta gaskiya ne Mutum ake kiwo yanzu ba dabba ba.


"To Hajiya Sadiya Ina fata yanzu kin fahimci komu su waye, kuma sab'ama umarnin da Zan baki dai-dai yake da kasada ta rasa rayuwarki ko ta masoyanki". Cikin rawar jiki Sadiya ta fara magana.


"Dan Allah dan Annabi kada ku cutar min da Kowa zanyi duk abinda kuke so, kome kuka sani zanyi shi ".


"Shikenan in har kin amince yanzu zan sa a maida miki ɗiyarki gida, bisa sharaɗin in kika Saɓa ɗaya daga cikin alk'awarin da zaki ɗaukar mana, tofa ki sani yanda muka ɗauko ki muka ɗauko ta ba tare da Sanin Kowa ba,to sake yin hakan ba zai zamar mana wahala ba".


"Naji yallabai wallahi na amince a shirye nake inyi kome kuka sakani".


Haka Sadiya ta ɗaukar wa mutanen nan alk'awari ba tare da tasan ko aikin mai zasu sata tayi ba.
*Ku biyo Miemie da Ashnurpyar*  👌🏻

[17:03, 2/13/2018] 💕Anty miemie👌🏽: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*  *RUWAN DARE*


     *DAGA*


*MEEMI BASHIR(queen)*

        *Aur*

     *ASHNUR PYAR*
Babi Na sha biyu(12)********


Yau ya kama kwanan su Laure biyar a cell, acikin kwankin nan kullum cikin faɗa suke da la'antar juna musamman magajiya dake ɗora alhakin komi akan Laure, acewarta kawai cutarta tayi.


Har faɗa saida sukayi ,duk sun ya kushe fuskokinsu da faratansu,sai da akai musu duka san nan suka hak'ura.


K'arfe taran safe aka sallamesu, tunda suka fito daga harabar police station ɗin suke zazzagawa juna masifa, haka sukaita aibata junansu da tona asirin duk ha'incin da sukai, baram-baram suka rabu kowacce na danasanin cuɗanya kayansu da sukai da cuta,dan sunsan yanzu duk sun rasa costormer nasu.
****************


 Bayan Sadiya ta ɗaukarwa waɗan nan mutanen alk'awarin yin dukkan aikin da suka sanya ta, sai ta tambayesu yarinyar ta.

 Oga yace kar ta damu tuni an maida ita gida, amma Sadiya hankalin ta dai be kwanta sosai ba.


 Sai ogan cikinsu ya bada umurni aka canza mata ɗakin kwana, daga wancan mai duhun zuwa wani na daban, inda aka kawo ta yanzu ba laifi dan yafi wancan nesa ba kusa ba dan harda k'wan lantarki da fanka, abinci aka bata wannan karon akasin ɗazu da biredi taci gaya.


Ogansu yace sai ta sake kwana za'a mai data gida, Wanda bata san dalilin sa na yin hakan ba. Ita dai rok'on Allah take tayi cikin zuciyar ta kan Allah ya kuɓutar da ita lafiya daga hannun mutanen nan.Gashi sun bata aiki mai nauyi Wanda bata san ta ina zata Fara shi ba. To amma ya ta iya, ya zama dole ta amshi yarjeje-niyarsu indai har tana son cigaban kwanciyar hankalin ta dana mijinta.

 

Har zuwa yanzu bata samu ganin hak'ik'anin fuskar mutum ɗaya daga cikinsu ba, haka ginin wurin da take bata iya shaida ko Ina ne gun.


Babban burinta yanzu dai be wuce su sake ta tasamu ta koma gun mijinta da ya'yan ta ba, domin su sami kwanciyar hankali, su San tana raye ba mutuwa tayi ba.


Washegari sai da yamma tayi lik'is, Sannan oga ya bada umurni a maida Sadiya gida, bayan an kawo mata wayarta sun amshi Lambarta, nan ya sake mata kashedi na inta sake ta faɗi wani abu fa akan su ko plan dinsu, tofa ta tabbata da duk abinda ya sameta ko ita ko yaranta ko mijinta ita tajawo.


Cikin rawar murya Sadiya tace "in Allah ya yarda bama zaku taɓa jin komai ba".


Rufe mata fuska aka sakeyi amma wannan karon ba aɗaure mata hannuwa ba, amma sai da tasha kashedi muddin tayi gigin yin gudu wa to zasu mai data inda ba zata taɓa fito wa ba.


Sadiya cikin zuciyar ta faɗi take 'hmm! ni Sadiya inyi k'ok'arin gudu, inje Ina to, Haka kurum Na jawowa kaina wata sabuwa ba gara in bari su maidani da Kansu ba, tunda dai summin alk'awarin hakan'.


  

K'aran mota taji alamun yazo gaban inda take, Wanda ke kula da ita shiya ya taimaka mata ta shiga ciki.

Tafiya suke amma motar bata da k'ara sosai saida suka zo wani guri taji an tsaya, daga nan aka buɗe mata fuskarta dai-dai wajen da aka kama ta da farko nan gun suka maidota. Gari har ya soma yin duhu saboda dare ya fara yi wa.


"Sauka ki tafi, kuma in kin Kama hanya karki sake ki waigo".


"To"

Sadiya ta amsa cikin rawar murya, sauka tayi ta Kama hanya gudu-gudu take tunda ta mik'e bata waigo ba har ta ɓace, sai godiya take ma Allah daya sa suka sake ta lafiya.


Tana ɓacewa suma suka tada motar su tare da ko mawa ta wajen da suka fito.*******


Salisu mijin Sadiya na zaune bisa darduma inda ya idar da sallah be tashi ba addua yake yana lazimi, dan shi yak'i daina kwana a gidan nasu , kawai sai yaga Sadiya ta shigo cikin gidan wujiga-wujiga kallo ɗaya zakama fuskarta kasan taci bak'ar wahala.


"Sadiya! kece nake gani ko gizau ido na kemin?".

Ya fad'a tare da mik'ewa


Sadiya ta fashe da kuka ta karaso inda yake "nice Abban Khadija nice". 


Ta fadɗa, rungumeta yayi yana mik'a godiya ga sarki ALLAH, murna gurin bawan ALLAHn nan kunsan ba sai an fad'a ba, Allah ya taimake shi ya dawo mai da iyalinshi su duka.Cikin daren nan ya shaida wa iyayensa Dana Sadiyar ga Sadiya ta dawo gida da kanta.


Tunda Sadiya ta koma gida tak'i magana, in banda amsar nan data bawa mijinta da cewa ita ce, bata K'ara cewa komai ba, duk tambayar da Mijinta yayi Mata tak'i bashi amsa, haka ya kwana yana tofa Mata adduoi.


Tayi hakan ne saboda gudun kada asami wani bayani gun ta dangane da mutanen da suka saceta.Bayan gari ya waye gida ya cika da 'yan uwa da abokan arziki anata yiwa juna barka, an kawo ma Sadiya 'ya'yan ta, haka ta kwashe su tana tsananin murna da farin ciki, sai dai duk wanda ya tambayi sadiya gamida ɓatanta bata amsawa, komai aka tambayeta sai tayi Shiru bata cewa komai.


Gaba ɗaya hankulan mutane ya tafi akan cewa gamo tayi Aljanu ne dama suka so taɓa ta, saboda haka sai aka K'ara bada kaimi gun yin adduoi da sadak'a akan Allah ya buɗi bakin ta lafiya.


'Yan sanda ma sun zo sunyi iya nasu K'ok'arin domin su samu wata amsa da zata taimaka wajen binciken ɓatan nata amma basu samu wata cikakkiyar amsa ga tambayoyin da suke mata ba, k'arshe ma sai ya zama da anyi mata maganar ɓatan Nata saita fara wasu surutai tanayin bori, ganin haka mijinta ya bada shawara kan a k'yaleta kawai tunda dai an samu ta dawo lafiyamai yuwiwa fa taɓin jinni ne, akan hakan ko Kowa ya tafi.


Sadiya ko cikin zuciyar ta dama ta gama yanke ita da sana'ar saida kayan Mata kuma har abada, ɓangare guda kuma Na cikin zuciyar ta in ta tuno da alk'awarin dake tsakanin ta da mutanen nan saita fashe da kuka.


Haka mamanta Zuwanta ta dasa ta agaba tai mata Nasiha mai shiga jiki,san nan tace haka nan ta rabu da yawan yawace -yawace nan,inma wata sana'ar zata cigaba to tayi a gida,tayi mata alk'awarin duk abunda ta faɗa ta ɗauka ,san nan aka bata adduoin tsari tanayi kullum dasu rubutun sha,kuma anai mata saukar alqur ani.Bayan sati biyu da dawowar Sadiya hankalinta yaɗan kwanta ta fara mantawa,sai ga kira ya shigo cikin wayarta tana duba lambar gaban ta ya yanke ya faɗi ras!, amma ya ta iya tashi tayi ta nufi cikin banɗaki dan amsa kiran wayar sa'ar ta ɗaya ma mijinta bainan.
Tana ɗauka taji ya kece da wannan dariyar tasa ,cikin murya wanda ko cikin bacci ta tashi zata iya shaidata taji ya ce


"Sadiya yaya ne wai? Lokacin da na baki yakai fa, yanzu tsawon sati biyu kenan da komawar ki gida, ya kamata ace step1 na aikin mu yafara".Sadiya tayi k'asa-k'asa da murya gudun kada wani ya jiyota duk da yanzu ta dawo magana da Kowa, to amma abinda zata faɗi ɗinne bata so yayi tsautsayin fita.


"Yallaɓai dan Allah kayi hakuri a ɗan Karamin lokaci, wallahi wallahi tunda na komo gida ba inda naje

 ko nan da kofar gida ban lek'a ba kuma......"


Tsawa ya daka mata Wanda shi ya dakatar da ita ga barin bayanin da takeyi.


"Wannan ke ta shafa Sadiya, ni aikin dana saki kawai na sani kuma ba Zan Kara kiranki game da shi ba, sai dai idan har naga aiki bai cika ba kema kin san sauran".


" To! to!. Naji yallabai dan Allah kayi hak'uri ak'aramin Uzuri mai gidana zaiyi tafiya nan da sati ɗaya da yardan Allah yana tafiya komai zai kammalla yallaɓai ".


Sai daya yayi dariya mai isar shi tukun Sannan yace.

 "To shikenan Na miki wannan alfarmar, amma in kika sake lokaci yayi ba tareda kin cika alk'awari ba kinsan sauran".


Godiya tayi kafin daga bisa ni ya kashe wayar. 

Sadiya ta fashe da kuka

 "Yanzu saboda mijina da ya'ya na zanyi wannan ɗanyen aikin, kaico Na Sadiya kaico na duk rashin jin magana ta da fitan da nake ba tareda da izinin mijina ba shiya jamin wannan, ya Allah ka fiddani".*Bayan sati ɗaya*


Mijin Sadiya yayi tafiya zuwa Kaduna kamar yanda ta faɗa can inda aka taɓa koran su gun aiki wai yanzu kuma kwatsam! An turo da sakon ana San ganin su.


Dama sadiya tana Alla-Alla ya tafi dan ta sami damar aikata aikin da zatayi.Bayan tafiyar mijin nata ne da da kwana ɗaya, yau ta shirya aiwatarwa da yamma lik'is saida ta fakaici idon mutanen dake k'ofar gidansu duk sun tafi masallaci ta saci jiki ta fita.Bayan kamar wasu awanni da fitar Sadiya ta Kira Lambar ogan wad'an nan mutanen,wacce ya Kira ta dashi, ta sanar mai da cewa aiki ya kammala, nan take wani daɗi ya Kama sa yace zai turo mutanen sa yanzun su zo su same ta.Taje inda suka aje da ita domin haɗuwa.Tana zuwa gun ta hangi mutum biyu daga cikin mutanen nan da suka kamata ,sai dai har ila yau fuskokinsu a rufe yake ba zata iya tantance hak'ik'anin ko suwa ye su ba. 

 

Farar takardan dake hannunta ta mik'a musu inda ɗayan yace da ita.


 "Maza ki kama hanya ki tafi".Ba musu Sadiya ta juya cikin Sauri tayi gaba saida ya zamana ta ɓace ma ganin su tukunna Sannan suka juya suma.


Bayan ta koma gida taci sa'ar ba Wanda yaga fitar ta da kuma dawowar ta, dan dama mutanen dake zama wajen layin gidansu in sun tafi sallah basa dawowa.


 Can cikin dare mutumin nan ya sake kiranta yace "aikin ki na farko yayi kyau ba kuskure a ciki, saura n kuma (step2) mataki na biyu, saiki Shirya kan nan da lokacin da zamu nemeki".


Muryar ta na rawa ta amsa da "too! Yallaɓai".


Nan ya sake ke cewa da wata mahaukaciyar dariya sai da yayi mai Isar sa tukun Sannan ya kashe wayar.


Sadiya ita kuma ta fashe da kuka tace "garin yawona na janyo wa kaina masifa"
*Ku biyo QMiemie da Ashnurpyar* 👌🏻

[17:32, 2/13/2018] 💕Anty miemie👌🏽: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


  *RUWAN DARE*


     *DAGA*


*MEEMI BASHIR(queen)*

        *Aur*

     *ASHNUR PYAR*Babi na sha uku (13)
Mutanen nan da suka Kama Sadiya Irin masu satar mutane ne waɗanda aka fi sani da KIDNAPPERS, wanda idan suka sace mutum sukan faɗi kimanin wani adadi na kuɗi suce sai an biyasu kafin su sako wanda suka sace ɗin, yanzu har kan kidnapping ya zamo RUWAN DARE game duniya.


To Sadiya taci Sa'a ita ba kuɗin ta suke so ba, babban kamu suke so suyi na Hajiya Saude.Wanda Shine suke so suyi amfani da Sadiya wajen sace ta ɗin.D'aya daga cikin 'yan kidnapping ɗin Wanda ogan su ya kira da RUWAN DARE yana ɗaya daga cikin samarin nan masu zama a k'ofar shagon dake wajen gidan Hajiya saude, su biyu suke zuwa wajen su dulmiye da samarin,sun jima suna son su Kama Hajiya domin su buk'aci wasu kuɗade da za'a basu kan su sake ta kam, hanya ce ba su samu ba.Dama suna nan cikin anguwanni daban-daban suna sanya ido kan mutane ba tareda ansan ko su waye su ba.


Irin yanda saude ke damawa da Naira da take, da kuma kalan manyan motocin da take fita dasu ya daɗe yana tsone ma shugabansu idanu a duk sanda aka kawo mai labarin tamusamman in an kai mai labarin cewa yau Hajiya ta fita da mota kaza, wannan shine dalilin da yasa ogansu yasa Hajiya Saude cikin target din shi.Ya zaɓi amintaccen yaron sa *Ruwan dare* domin ya rik'a ɗauko mai rahoton shige da fice na gidan su Hajiya.


A wannan ɗan zaman da ruwan dare ya soma yi safe da yamma a unguwar su Hajiya, tareda matasan layin, a dai-dai k'ofar wan nan shagon dake gefe guda kusa da gidansu hajiyar,nan ya fahimci kusan rana ɗai-ɗaine Sadiya bata zuwa gidan hajiya, kuma da tazo babu shamaki haka ake barinta shiga cikin gidan.


Rana ta farko da yakai ma ogansu labarin Sadiya, shine ya sanya shi ya maida hankali kanta ya gano musu me take shiga yi cikin gidan, daga ina kuma take zuwa.


Wannan ne dalilin da yasa in suna hira ya rink'a tambayar Wacece Sadiya me kuma take yawan zuwa yi gidan Hajiya.Da taimakon bayanin bakin mutanen da suke hira agun ya gane sana'a ce take kaiwa gidan.

 


Daga nan kuma ya dinga bin bayan ta inta fito har yakai ga gano gidan Sadiyar,a nan ma unguwar su saida ya zauna na wani ɗan lokaci har ya samu labarin Irin sana'ar da takeyi da rashin son fitar ta da mijinta beyi, barin yara da takan yi a gida da sauran su.


Daga nan ne kuma suka shirya shirin yanda zasu Kama Sadiya, a hanyar ta na koma wa gida, bayan nan kuma suka sake ɗauko 'yarta wanda hakan ya tsorata Sadiya matuka gaya dama kuma shirin su kenan, ya zama sun tsorata ta iyakar tsoratarwa ta yanda zata amince wa buk'atar da zasu nema a gun ta cikin sauk'i.


Bayan Kama Sadiya da suka yi, sun k'ara samun duk wani bayani da suke bukata dangane da gidan Hajiya Saude.


Daga nan suka k'ulla yarjejeniya da Sadiya bayan sun mai da mata da ɗiyarta gida, kan zata taimakesu da abubuwa guda biyu wajen kama Hajiya, lokacin da Sadiya taji manufarsu na kamatan da sukayi tayi kuka sosai tare da dana Sanin wannan sana'ar da ta rink'ayi mijinta be so gashi wai yanzu da ita za'a haɗa baki wajen aikata wannan mugun aikin, lallai wannan duk alhakin mijinta ne.


Bata da yanda zatayi dole ta amince wa buk'atar su tunda suna barazanar cutar da 'ya'yan ta da mijinta wanda ita kuma ba zata bari haka ya faru ba sai iya inda k'arfinta ya k'are.Buk'ata na farko Lambar wayar mijin Hajiya suka sa Sadiya ta samo musu.

Shine abinda lokacin da mijinta yayi tafiya ta fita dan samo musu.


A lokacin da Sadiya ta bar gida da yammaci sai addua take Allah yasa ta samo abinda zataje nema.Allah ya rufa mata asiri ta sami Lambar hajiya, duk da cewa dama tasan hajiya nada sakaci da wayartatana zuwa gidan Hajiya kaman yanda ta saba a kullum ne ya kasance domin babu wani Wanda yayi mata shamaki wajen shiga gidan.


Lokacin da ta shiga cikin falon da bak'i saboda haka kai tsaye Hajiya ta shiga da ita cikin dakin ta,wanda k'anwar mijinta Maryam tasha yi mata nuni da ta daina yadda da mutum.


"Ina zuwa Sadiya ki jirani anan bari in ɗan sallami bak'in can nazo, bana so su gane me kika zomin dashi ne".


"Aaa! Haba ba komai Hajiya kije ki dawo ina jiranki". 


Tana fita Sadiya ta ɗauki wayarta dake gefen kujera Lambar mijin nata ta kwafe a jikin wani ɗan takarda bata sha wuya ba wajen gano Lambar domin hajiyar tasha faɗin sunan da take kiran mijinta dashi, agaban Sadiya, da kuma sunan da tayi saving a wayarta lambarsa kuda uku ce haka duk ta kwafe, gashi yau hakan yayi ma Sadiya amfani.


Daga hannu tayi ta gode ma Allah daya sa ta sami abinda tazo nema cikin sauk'i ba tare da an gano ta ba.


Da Hajiya ta dawo ta tambayi Sadiya lafiya kwana biyu bata zo ba tana taso ta Kira ta awaya amma bata sami dama ba.


Nan dai Sadiya ta nuna mata ba komai ai, dama taɗanyi rashin lafiya ne shine ya hanata zuwa.Nan taba Hajiya magun-gunan data kwaso Wanda bata san ma namene da mene bane, tace sauri take saboda mijin ta ya hanata fita yanzu kwata-kwata,satar jiki tayi ta fito idan ta koma gida zata mata bayaninsu.


Hajiya bata kawo komai a rai ba tayi godiya harda cewa ko an hana sadiya fita bazasu rasa hanyar da za'abi wajen amsan kaya ba, Sannan sukayi sallama.


Tana fitowa daga gidan shine akan hanyar ta na komawa ta kira ogan yan kidnapping ɗin nan kan cewa ta samo Lambar, inda shi kuma ya turo yaransa suka karɓar mai Lambarwannan kenan.

*** **** *******


Gobe ne mijin Sadiya zai sake komawa Kaduna domin maganar maidashi gun aikinsa ta kan-kama.


A ɓangare guda kuma gefen Sadiya tayi wayar karya da Hajiya inda ta neme ta da tazo su haɗu wani gida gidan k'anwarta acewarta bata da lafiya zataje duba ta,kuma tace mata bayan unguwarsu ne ganin ta samu dama shine tace bari ta gaya mata tazo ta karɓi kaya gidan tunda ita da motarta, domin bata wasu magunguna sabon kamu da aka kawo mata su daga Niger, tace magungunan sun haɗu bataso hajiya tayi rashinsa, sannan tace mijinta ba zai bari tazo gidan ta ba, kuma yayi mata ALLAH a isa kan inta kuma zuwa gidan wata mata da sunan kai kayan mata bai yafe mata ba, domin yanzu ya mata kulle gida ake zuwa a siyi magun-gunan ita kuma bata so su kare Hajiyan bata samu ba, saboda ganin kyawun kayan nema yasa ta keso ta bata da kyar da siɗin goshi ma ya barta taje duba k'anwarta tan,san nan tace zatai mata kwatancen gidan.


Saude data gama jin bayanin Sadiya tace "ina jinki gayamin kwatancen".


 Nan Sadiya ta gaya mata kwatancen,kamar dede yanda shugaban ya faɗa mata, tace gobe bayan sallahr la'asar sai hajiyar tazo, haka dai ta gama cika hajiya da daɗin baki da yan rantse-rantsen su na masu magani wanda hakan yasa Hajiya ta bata tabbacin lallai zata zo domin ta gane kwatancen, ba zata bari wannan garaɓasar ya zama ya wuce ta ba.


 Dama ita ma hajiya saude ta Saba fita bada izinin mijinta ba dan taga shi ba mazauni bane.Washegari bayan mijin Sadiya ya tafi sai ta sake kiran Hajiya dan dad'a tabbatar da yuwuwan fitowar nata, Hajiya Saude ta tabbatar mata da lallai zafa tazo karta saida kayan ta ajiye mata.Suna gama wayar Sadiya ta kira shugaban 'yan kidnapping ɗin nan ta bashi bayanin duk yanda sukayi da Hajiya.


 Yace "Yes! Aikin ki yayi kyau Sadiya, kin kusa kammala aikin ki, Anjima muma zamu zo wajen".


Sadiya ta ce "to yallaɓai dan Allah ina daɗa rok'on ka ku taimaka min ku rufamin asiri kar kubari Hajiya ko waninta ya gane dani aka haɗa baki dan sace ta, kataimake ni yallabai".

Ta karasa maganar cikin kuka.

 

Shi kuma ta can ɓangaren ya amsa da" Na riga na fad'a miki baki da matsala da wannan in har muka sami abin da muke buk'ata bama zaki sake ganin wannan Lambar da nake kiranki ba, ba zaki sake jin ɗuriyar mu ba, ke dai kawai kiyi fatan Hajiya ta shigo hannunmu".Sai da yaɗan dakata Sannan ya cigaba da cewa "alk'awari ne Nayi miki baza asan kinada hannu ciki ba, kuma innayi alk'awari bana sabawa". 

Daga faɗin haka ya kashe wayar shi, Ya bar Sadiya rik'e da waya a hannu kamar mutum-mutumi.Da yamma lik'is, ana shirye-shiryen kiran sallan magariba Hajiya ce akan hanyarta na zuwa gidan k'anwar Sadiya ,bayan sunyi waya da ita sadiyar tace hajiyar tayi sauri zo, so take ta koma gida, hajiyar tace tana kan hanya.


Bayan sun gama wayar ita kuma ta Kira ɗan gumurzu ta sanar mai.Bayan ta shiga unguwar ne, dama uguwar sam irin sababbin unguwan nin nan ce, ba mutane sosai layinma shiru sai gidaje tsilli-tsilli. Parking ɗin motar tata tayi daga gefe guda saboda motar ba zata iya shiga hanyar da zai k'arasa da ita gidan ba saboda aɗan loko yake.


Ta fito cikin motar ta fara takawa waya takeyi da Sadiya cemata take gatanan ai ta fito itama kaɗan ya rage ta k'araso kwatsam! Ba zato ba tsammani Hajiya Saude taji taci karo da wani abu tana k'ok'arin dubawa mutum ta gani tsaye a gabanta cikin bak'ak'en kaya fuskar sa ma arufe take baka iya shaida ko wanene, cikin tsananin tsoro da firgici hajiya saude ta juya da niyar komawa baya, ji tayi an fizgota ta baya gamida anshe wayar dake hannuntata buɗe baki tayi domin yin ihu, kawai sai taji an shak'a mata wani abu a hanci, daga nan kuma bata K'ara Sanin inda take ba.


*(To gare ku mata masu saye-sayen magungunan mata wallahi wannan shine abinda ke faruwa a duniyar mu yanzu, kidnappings ɗin mutane ta 

hanyar Mata masu saida kayan Mata ya zamo RUWAN DARE. Akwai wad'an da dama aiki suke tare da masu kidnapping ɗin, kina zaune cikin gida zasu miki sallama suna miki tallan kaya, da sun zo gidan ki ɗaya, biyu na uku zakiji sunce ki zo gu kaza ki karɓa, kina zuwa shikenan, akwai kuma waɗanda tursasa su akeyi basu da zaɓi kamar yanda ya faru da Sadiya saboda haka Mata sai a kula! Illolin da maganin mata yake haifarwa yawa garesu)*

*Ku biyo Miemie da Ashnurpyar* 👌🏻*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  *RUWAN DARE*


     *DAGA*


*MEEMI BASHIR(queen)*        *Aur* 

   *ASHNUR PYAR*Babi na (14)************


Bayan sun shak'a ma Haj Saude abun nan a hancinta ta some, hakan yasa suka saka ta amotar su, ɗaya daga cikin su ya shiga motar ta suka tatara suka bar wajen.Sadiya kuwa jin ta Kira wayar Hajiya Saude an katse tabbas tasan abunda ke faruwa,nan ta rik'e ciki jin yanda yake wani irin murɗawa da gudu ta aje wayar ta shige banɗaki wata irin gudawa ce ta ɓalle mata ba k'ak-k'autawa. 


Dama tana gida ba inda taje, duk kwatancen da take ma Hajiya Saude na k'arya ne.Al'amarin Hajiya Saude kuwa direct gidan da suka kai sadiya nan ita ma suka kaita, Koda ta farfaɗo gabad'aya duk rikice ganin tik'a-tik'an gardawa cikin bakaken shiga sun zagaye ta, musammn kuma ganin fuskokinsu arufe ba zata shaida kowa dake gun ba, ɗakin tajuj-juya ta kalla ba komi aciki sai kujerar oga, ga k'artin nan duk sunci bak'ak'en kaya nan ta daɗa tsorata, jikin ta sai kyarma yake, ga hannuwanta duka a ɗaure, baki kuma a rufe ansa abu mai kamar selatib an rufe ba halin tayi magana, Saidai mutsu- mutsu kamar dai yanda akayi ma sadiya. Dariyar renin hankali oga d'an gumurzu yayi, ya mik'e daga zaunen da yake yace:

 "Welcome Hajjaju saude matar Alhaji naga alamar fa kina shanawa, kuma ga alamu Alhaji yana ji dake sosai". 


Daburcewa tayi tana kallonsu da idanunta wuki-wuki mamaki take jin ya ambaci sunanta.


Tana son yin magana amma ba dama, can wayarta ta hau k'ara wacce ke hannun RUWAN DARE.Sunan Sadiya ne ɓaro -ɓaro akan screen, oga ne yayi mai alama daya mik'o mai wayar, ya amsa yace "ko wacece wannan Sadiyar da alama yar uwarki ce, dan naga ta damu dake da yawa, tunda muka ɗauko ki take kiran wayar nan, ko alk'awarin Kud'i kikai mata ne? Hajiya Saude koda yake mako........".Kafin ya k'arasa abinda yake son cewa sadiya ta K'ara kiran wayar.Daga nan yasa hannu yayi receiving call ɗin tare da sa wayar a hand free, ya zama speaker wayan ya buɗe Kowa zai iya ji.Daga can sadiya jikinta sai kyarma ya keyi domin dak'yar ta samu gudawar da takeyi ta tsaya, da harta manta da buga wayar sai ta tuno da ogan yace tabbas ta kirawo saude bayan ansaceta, hakan zaisa hankalin sauden ya kau daga zargin ita sadiyar, sauran kuma ta bar mai shiyasan abinda zai yi.Saida ta saita muryarta san nan tace "Haj saude inata jiranki gani nazo gun, amma banganki ba ,tin ɗazu ina tsaye ina jira sai bugo wayarki nake kuma baki ɗauka, ga dare nayi fa!"


Saude tana jiwo muryar Sadiya amma ba hali tayi magana bare ta fad'a mata halinda take ciki, ko zata nemo mata d'auki, sai hawaye ne kawai ke fita idanuwanta. 


Kafin Sadiya ta K'ara faɗin wani abu ya Kashe wayar dariya yayi tare da bushewa da wata mahaukaciyar dariya.


 "Hajiya kinsan meye yasa muka kamoki?".

 Girgiza kai tayi wani mummunan dariyan ya sakeyi yace "muna son kuɗi ne a wajen mijinki idan de har be fito da kuɗin da zamu gindaya mai ba, to ke da shi har abada! Saboda haka in kika bamu haɗin kai wajen amsar kuɗin to zaki sake ganin mijinki".Kuka ta saka me cin rai "dan ALLAH kuyi hkr menayi muku?".


Tsawa ya daka mata.


 "Shut up madam! atafin hannunmu kike wane irin wadak'a ne bakyayi da kuɗi don haka muma dole abamu rabonmu".


Kallon Wani gandameme yayi daya cake atsaye kamar bishiya, nan take yaja hannun Hajiya Saude tana hawaye aka sakata a ɗakin nan ya wullata ciki ya gark'ame, nanfa ta rinka mutsu-mutsu tana bubbuga k'ofar da k'afafuwanta, amma sukayi banza da ita.


*************


Da yake Alhaji baya gari shiisa ba wanda ya bibiyi saude, sai me gadi daya ga fitar ta shi keta kaikawo, Maryam da tashin ta kenan daga barci, ta dud-duba ko ina bata ga Hajiya ba, saboda haka tayi tunanin tayi fitan nata ne data Saba, shiru-shiru tana tsammanin shigowarta bata ga ta shigo ba, sai ta nufi gun mai gadi.


 Fitowar maryam take cemai "ko hajiya ta dawo ne?".


 yace "Aa".So biyu kenan tana fitowa gashi har k'arfe goman dare hankalinta ya fara tashi ganin inta buga wayar Hajiya saude bata shiga har goma ta wuce shaɗaya ta gabato kai ba hajiya, duk inda tasan hajiya na zuwa ta buga waya sai suce bata je ba ,duk da tasan hajiya na fita in Alhaji be nan amma bata fitar yamma,haka sukai curko- curko ita da megadi har shabiyu, san nan suka kulle gidan cike da zulumi.


Maryam kuka take tayi jira take safiya tayi ta bugawa Alhaji wanta, dan karta fad'a mai yanzu hankalin sa ya tashi.Washegari k'arfe shida dede maryam ta kirawo Alhji take sanar mai hankalinsa idan yayi dubu to ya tashi, yana matuk'ar san hajiya, haka ya sanar ma da maryam ɗin su jira shi yanzu zai kamo hanya ya tawo, haka fa su maryam sukaita kai-kawo. K'arfe goman safe Alhaji ya shigo kano nan take suka zarje police station yakai report sukai musu alk'awirin fara bincike.


Musaman da sukaji matar Alhaji ce sun sanshi me kuɗin gaske ne, zasu yagi rabonsu.Kan kace kwabo ko ina ya ɗauka an nemi hajiya Saude an rasa, haka 'yan uwanta da na Alhaji kowa hankalinsa ba'a kwance ba, gashi har alokacin idan an buga wayar nata, bata shiga.


********


kwanan Hajiya huɗu se yu suka fito da ita, duk tabi ta fita hayyacinta, abinci dama ba ko wani lokaci suke bata ba , tana hawaye oga ya kafa mata ido yace:

 "Hajjaju matar me kuɗi Allah ya baki duniya fa, ko yaushe da kalar motar da zaki hau hannu gwal wuya gwal".


Ya kece da dariya (haka al'adar ɗan gumurzu take magana ɗaya biyu in yayi sai ya bushe da dariya).


"kinsan nawa muke so Alhaji ya bamu?".


Ta girgiz kai yayi dariya "Munason miliyan talatin a hannun sa, yawan son da yake miki in har ya damu dake, shi zaisa ya biya ba tare da gardama ba.
Alhaji na zaune yayi tagumi shima duk ya faɗa ya rame, saboda fargaba jin wayarsa na k'ara yasa ya ɗauka ganin Private number yasa shi mik'ewa tsaye da sauri ya kara akunne.


"Rankashi daɗe ya Alhaj!" 

Yaji an fad'a ta ɗayan ɓangaren, Alhaji yace: 


"wanene?".

D'an gumurzu yayi dariya ta ɗayan ɓangaren yace " kana buk'atar sake ganin matar ka?".


Alhaji cikin rawar murya yace:


 "Wanene Kai,Ina matata take?".


" In har kana buk'atar Sanin inda matar ka take to kawai kayi yanda duk nace".

 

Dai-dai nan ya cire abinda suka toshe bakin Hajiya Saude dashi ya Kara mata wayar a kunne.


 "Alhaji" Saude ta faɗa yace 

"Saude! ina kika shiga?"


 Kuka ta fashe dashi "Alhaji ka taimaka min dan sanka da Annabi"

 

Arikice yace:


 "Kina ina ne haka saude?" 


Da sauri oga ya warce wayar yace "kai Alhaji naga kamar har yanzu baka fahimci mu suwaye ba".

 Nan fa gaban Alhaji ya faɗi oga yace


 "Mune nan muka sace matarka dan haka idan kana buk'atar matarka ka fito da kuɗi domin munsan abanza kake samun su". 


"Me nai muku meye haɗina daku ku?".


 Dariya oga yasa


 "kaga Alhaji wallahi kaji na rantse idan baka bada kuɗin da zamu gaya maka ba, to wlh kaida ita sai alahira".


 Kuka hajiya ta fasa ta ɗaga murya.Alhaji yana jiyota "ka taimaka ka biyasu abinda suke so Alhaji, nasan kana sona kodan tilon ɗan mu guda ɗaya Alhaji".


Dariya oga ya sakeyi


Alhaji yace "nawa ne kuɗin da kuke buk'ata?".


Oga yace "miliyan Ashirin mukeso kuma gobe goben nan dan munyi maka rangwame ma".


Takaici ne ya ishi Alhaji jin yace wai rangwame wani gwauran numfashi yaja "zanbiya, amma wallahi babu million ashirin a hannuna nan da gobe, sai dai zaku iya samun goma cifcif na muku alk'awari, amma kar kuyi ma matata komi".


Oga yace "To shikenan an maka lamuni kabada goman, kuma kashedin da zanyi maka ka tabbatar ka rufe bakinka karka gayawa 'yan sanda, wallahi ko alamarsu muka gani ba zamu bada itaba domin atafin ahannun mu kake". Yana zuwan nan azancensa ya datse wayar, sannan ya kashe wayar ya cire sim ɗin .Maryam dake gefe tace "yaya suwaye?" nan fa ya gaya mata take ta hau kuka.


 "Ashe masu kidnapping ne suka ɗauke Hajiya, ka biya dan ALLAH yaya ka biyasu".


 Girgiza mata kai yayi alamar zaiyi.


 'Gashi da private number aka kirashi, taya zaiyi yace musu ga kulin yanzu su sako mishi matarsa, tunda basu gama wayar ba wancan ya katse'.


 Wani zazzaɓi ne yaji na neman rufe shi. Afili yace " tunda su suka kirani, kuma Kud'i suke bukata, zasu sake kira dole".
B'angaren Sadiya kuwa, kuka sosai take na tausayin Hajiya saude tunda ta tabbatar da sun sace ta, tsoro da fargaba ne duk ya shigeta, kar asirinta ya tonu, jimamin da take yasa duk aɗan kwanakin itama ta rame. Salisu mijinta na lura da ita, amma baice mata komi ba, ta dawo shiru -shiru kullum cikin addua take ALLAH Yasa su sako hajiya ita kuma ALLAH ya kare ta.

*Ku biyo Miemie da Ashnurpyar* 👌🏻

*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*


  *RUWAN DARE*


     *DAGA*


*MEEMI BASHIR(queen)*

        *Aur*

     *ASHNUR PYAR*Babi na sha biyar (15)
Labarin kidnapping ɗin Hajiya Saude yanzu kuma shine gabaɗaya ko Ina kasa kai, baga mata ba baga maza ba, in gidan matan aure ka shiga labarin kenan zakaji anayi, matasa masu zaman banza duk wurinda kaga sunyi dan gungu to zancen kenan zakaji. Wasu na jaje wasu ko na Allah k'ara a cewarsu hakan shi yafi dacewa da irinsu Hajiya Saude.Yauma kamar kullum dandalin wasu samari ne ke hira inda ɗaya daga cikinsu ya Kalli sauran yace:

 "Nifa kunga satar hajiyan nan ba k'aramin daɗi yamin ba, domin daga ita har mijinta basu taimaka wa mutane Kansu kawai suka sani".

D'ayan ya karɓa da cewa

"wallahi kuwa Kabiru Nima kaga koda naji abinda na fad'a kenan, daga ita sai ɗanta suke cin kuɗin Alhaji, kaga yanzu haka ma ai yaron nata bayama k'asar aka ce yana waje tuntuni,kullum motar da zata hau dabance dana jiya, nifa na dade ina zargin matar nan ita ke hana Alhaji taimaka wa mutane, tunda shi da Alhaji ai ba haka yake ba yana taimakon mutane, waya sani ma ko har yanzu Alhaji na bata ɗan abin taimaka mana itace ke cinyewa".


Kabiru yace "ai Allah yakara kaga yanzu wasu zasu yagi nasu rabon a banza".


Wanda bece komai ba tunda suka fara hirar shi ne yace "Haba Naseeru Kai da kabiru ku kuwa me yasa a kullum bakin ku bai faɗan alkairi, wannan al'amari na kidnapping mutane k'iri-k'iri kaji an sace mutum, addua ya kamata mu sa gaba munayi ba dariya ba,domin kowa zai iya faruwa akansa.


Allah ya kawo mana ɗauki gwamnati kuma ya zama ta kara sa'ido kan lamarin nan, domin abun yayi tsanani satar mutane yanzu ba manya ba kuma ba k'anana ba duka sacewa ake, in yau muna jin anyi ma wasu gobe bamu sani ba ko namu za'a Kama koma mu kanmu ɗin".


Kabiru da Naseeru suka bushe da dariya,Naseeru yace:

 "Aminu nidai ban taɓa ganin mutum irinka ba, yanzu Kai saika zauna kawai wani k'ato yazo ya sace ka! kamar kai ba namiji ba".

Aminu yace "lallai Naseer to mai ka d'aukesu ne, kana karanta tunanin ka akan masu satar manyan mutanen nan, ance fa harda makaman su, mutum zai diran ma da makami ne ka shige ka ja dashi, Kama san lokacin da zasu zo ne! kuma bafa mutum ɗaya ke zuwa ba k'ungiya garesu, kafin su sace wanda suke so sai sunyi cikakken shiri akai".Kabiru yace "to kai in banda abinka Aminu me muka tara, Me muka ajiye da masu kidnapping zasu sace mu, ai irin su Hajiyan dai sune ke tsone masu ido".Aminu yace "to ce muku akayi masu kuɗin kaɗai ake sa cewa! Ai har talakawan ma ba barin mu akayi ba, kan mai uwa da wabi ne, ko kaima zata iya faɗawa kanka, al'amarin yanzu ya k'azanta wasu tsananin talauci ne ke damun su da rashin aikin yi, kawai kuma saboda rashin tunani sai ka fad'a satar mutane, wai harfa almajirai ake sacewa yanzu, kunga ko duk wanda zai Kama Almajiri yace wai yayi kidnapping kunsan lallai wannan talauci ce da rashin hankali yasa shi aikata haka.


 Saboda haka kar kuyi tunanin wai sai kun tara wani abu za a iya kidnapping naku, lamarin dai sai Addua dafatan.Allah ya tsarkake mana zukatanmu.


 Shiyasa nake k'ara baku shawara daku nemi aikin yi, ɗan garuwan nan da mukeyi muna samu cikinsa fa! amma ku kunja jiki kunce ba zakuyi ba kundaina, kunga ko dole kusa idonku akan abin wani.


Kwanaki ina ga kamar watanni biyu da suka wuce ne haka aka sace wasu Almajirai yan makarantan malam na goma"."Kai haba! Satar Almajirai fa kake ta cewa" cewar kabiru.


"Au! kun ɗauka wasa nake? Wallahi da gaske nake yi, Ina wajen layin bendelkasan shagari?".


Naseer ya amsa da "eh muna jinka wajen bus-stop ko?".


Aminu yace "eh nan fa! kasan akwai sabon makarantar Almajiran malam na goma dake gun ko, to wai in fad'a ma watarana wasu daga cikin yaran makarantar na dawowa daga aike wasu samari suka taresu ance alewa suka basu wasu since kuɗi ne, Allah dai kaɗai yasan gaskiya, shine suka jasu daga nan kuma ba ak'ara jin ɗuriyar yaran ba, wajen su biyar fa!, bayan kwana biyu ana neman yaran ba agani basai ga Kira ya shigo wayar malamin, wai in yana son yaran sa sai ya aiko da dubu goma kowane yaro guda matsayin dubu biyu".


Naseer da kabiru suka kwashe da dariya Naseer yace.

 "Amma lallai waɗannan akwai yan iskan kidnappers wai kaji dubu goma!".


Kabiru yace "wai kowane yaro matsayin dubu biyu! Allah inni ne Saidai Kowa ni ɗayansu ince Abani dubu biyar-biyar".


Aminu ya cije baki saboda jin haushin halin abokan nasa, su bama su tausaya ko su jajanta ba a'a shi kabiru tunani ma yake in shine zai amshi fiyeda haka. 

Yace "haba! Ku Kuwa, kamata yayi ace ku jajanta dan duk Wanda kaji ya saci almajiri wai yana buk'ar a bashi dubu biyu to lallai baida cikakken aikin yi nesai kuma aka taki rashin Sa'a yana da matacciyar zuciya daba imani, inba haka ba mai zaka samu dan ka sace Almajiri ! ai malamin nasu shine abinji, kunsan daya ya haɗa wannan kudin ne! saifa da akayi karo-karo da mutanen unguwar sannan aka basu kuma sai ga yara sun dawo, an tambaye su fuska since fuskokinsu arufe, anfi kyautata tunanin ma waɗan da aka sani ne, in ba haka ba ta Ina suka samo Lambar wayar malamin".


Kabiru yace "tab lallai waɗan nan sun taki sa' a, sun tashi da dubu goma cif abinsu".


Aminu yace "Kai inaga Kabiru in baka sami aikin yi ba wallahi nan da kwana biyu kaima kidnapping ɗin zaka koma".


A fusace kabiru ya nuna Aminu "Kai to malam ya isa haka, kar ka nemi ka zageni mana, ni kake kira da ɗan kidnapping, to kace ma ni na sace yaran man".


 Magana yake kamar zai duki shi Aminun."Ni dai ban cema ba, cewa nayi in har baka sami sana'ar yi ka rik'e ba kaima zaka iya satar mutane, to wai ma in ba rashin sana'ar yin ba menene damuwar ku da sa ido kan kuɗin Alhaji da facakar da Hajiya da ɗanta sukeyi, ba mijinta bane ko akwai guminka ciki ne? Kai dai naka ido".


Kabiru yace "ank'i a nemi sana'ar, kuma Allah shi k'ara bazan fasa yiwa Hajiya da Alhajin ba, kuɗi ne dama inba aba bayin Allah sunci ba ai alhaki ba zai kyalesu ba, ana zaune cikin ruwam sanyi wasu k'atti zasu ci a banza".


Ganin sa'in sar tasu yana Neman Kai ga fad'ane yasa Naseer da sauran mutane biyu waɗanda daga baya suka zo gurin, shiga tsakaninsu.*Ruwan dare* da tun farko bai sa musu baki ba cikin taɗin da suke sai yanzu yace "yo kai kabiru in banda abinka wani tabbaci kake da na cewa zasu sami nasarar amsan kuɗin, kana ganin idan har ya fad'a wa hukuma zasu samu nasara ne?".


Kabiru yace "to ai banji an fad'a musu ba gaskiya"


Naseer yace"inji waya gaya ma naji ance fa anfaɗama jami'an tsaro? dan ma suna nan suna ta bincike akai ".


Kabiru yace "yo nidai koma an fad'a ko ba a fad'a musu ba, Ina nan akan bakata, addua nake Allah yabawa barayin nan Sa'a su yagi rabonsu, komin banza sa ragi Alhaji, miliyan biyar wasa ne".


Da haka duk cikinsu babu wanda ya sake cewa komai, shi dama Aminu tun bayan da aka raba su yayi Shiru, gudun kar abin ya jawo musu matsala. 


Yana mama kin hali Irin na abokansa Ina ruwan ka da dukiyar wani, mutum shi ba D'an'uwanka ba balle kace ai ɗan uwa nane, baka taya shi nema ba, baka San taya ya tara ba, amma kace wai kasa ido akan arzikinsa da iyalinsaAllah shi kyauta".


 Ya faɗ a fili tere da mik'ewa tsaye "to yan uwa sai anjima ni zan je motsa jiki".


Naseer ma yace ai shima wuce wa zaiyi, kabiru yace zai bishi su su wuce tare.

 Nan take dai taron ya watse, inda *ruwan dare* ne ya wuce a k'arshe, yana jin daɗin ya samo amsoshin tambayar da oga *Dan gumurzu* yasa shi ya nemowa.

*Ku biyo Miemie da Ashnurpyar* 👌🏻
[00:27, 2/14/2018] 💕Anty miemie👌🏽: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  *RUWAN DARE*......
     *DAGA*
*MEEMI BASHIR(queen)*

        *Aur*

     *ASHNUR PYAR*Babi na sha shida (16)
Koda oga *Dan gumurzu* yaji labarin da *ruwan dare* yazo masa dashi, cikin ɓacin rai yasa layin waya bayan ya tabbar da ya ɓoye lamber sannan ya kira Alhaji.


Ta bangaren Alhaji ko yana ganin kira da unknown number ya shigo cikin wayarsa yayi saurin ɗauka, domin yana kyautata tunanin 'yan kidnapping nin nan ne, kamar yanda ya kintata hakan ne Kuwa ya kasance, domin yana ɗaukar waya muryar *Dan gumurzu* ta daki dodon kunnensa.


"Lallai Alhaji! da alama baka son sake yin tozali da matar ka, meyuwa dama ka soma gajiya da itane".


Alhaji ya amsa "wallahi ba haka bane, muna cikin waya dakai ta yanke baka kaiga gaya min inda za'a kawo muku kuɗaɗen ba, na kuma nemi in sake kiran ka babu Lambar, da ɓoyayyen number ka Kira ni, tun tuni nake ta tunanin ta yanda zanyi nasami yin magana daku, dan nasami baku koda....".


" Ba wannan maganar nake ba yanzu".


D'an gumurzu ya dakatar da Alhaji da kakkausan murya daga nan ya cigaba "nace kar ka sake ka sako mana da hukuma cikin maganar nan, amma shine baka ji ba kayi kunnen uwar shegu da magana ta,har ka kaima 'yan sanda labari ko? To kayi ma kanka baka sake jin kiran mu har abada, kai da matar ka kuma sai a lahira....".


Barazana yayi kamar yana shirin yanke wayar.


Cikin rawar murya Alhaji yace "Kaiwa girman Allah da Annabi kada ka kashe wayar nan, ka taimaka ka ceci rayuwa ta, wallahi tun bayan da ka kirani ranar farko ban K'ara wata magana da jami'an tsaro ba Ina....".


" Taya zaka ce baka sanar da Jami'an tsaro ba, alhali mutane na sun tabbatar min da ana bincike akan mu".

 


Alhaji yace "wallahi babu Wanda Na kuma fad'a wa Ina ga mutanen ka sun kawo ma bayani ne akan rahoton dana Kai police station tun a farkon lokacin da hajiya ta b'ata, kuma a time ɗin bamu fara waya daku ba, amma dan Allah Ku min uzuri gobe zan je police station ɗin zansa a rufe maganar case ɗin gabad'aya, yanzu abinda nake so mu sasanta daku, dan Allah ka faɗamin a ina ne Zan kawo muku kuɗadɗen naku? amma dan Allah kada ku cutar min da matata".


Sai a yanzu hankalin oga Dan gumurzu ya kwanta dan ya fahimci Alhaji ma ba zai iya yin wani abu akan su ba, shima ya tsorata dasu.


D'an gumurzu yace "to shikenan Alhaji matuk'ar kana son sake ganin matar ka to ka tabbata ka kashe case ɗin nan daka kai gun jami'an tsaro, ni kuma idan na tabbatar da hakan zan Kira ka na sanar ma inda zaka kawo mana kuɗin mu, sai na tabbatar da kuɗi sun shigo hannu sannan zan sakoma matar ka".


Bai jira ya sake jin mai Alhajin zai fad'a ba ya kashe wayar.


Alhaji yayi galala yana kallon wayar dake hannun sa 'dole ne a rufe case ɗin binciken neman Hajiya indai har yana so ta dawo garesa, dan waɗannan mutane ba imani ke garesu ba kai duniya dai tazo karshe'. 
***** ****** ******


 A gefe guda wasu dattawa ne ke hira suma dangane da sace Hajiya Saude.


"Wai yanzu satar mutane kiri-kiri ya zamo *RUWAN DARE* a wannan zamanin namu, Mlm k'aseem abin nan nafa bani mamaki da daure min kai! a sace mutum kuma a kira waya har a faɗi adadin wasu kuɗi da ake so!, amma ace hukuma ba zata iya yin komai akai ba, Gaskiya al'amarin nan akwai buk'atar gyara".


Wanda aka Kira da malam k'aseem yace "Ai malam Adamu wato in faɗama al'amarin hukumar ma ita tafi bani tsoro akan masu satar, saboda masu sace mutanen su ai duk cikin mu suke dasu muke hulɗa mukeyin komai tare, gane sune kawai bama iya yi, to amma fisabilillahi ace jami'an tsaro da aka sani su ma'aikata ne domin kare k'asa da alummar cikin ta, amma tsiraren mutane sun gagaresu Kama wa, an gagara a gano masu harkar kidnapping ɗin nan, abin sai dai ace Allah shi kyauta".


Malam sani yace "Ai duk baku sani ba".


"Muna jinka malam Sani "Suka amsa.Yace " Hausawa fa suka ce in anbi ta ɓarawo to abi ta mabi sawu, in har hukuma nada laifi to kusan laifin gwamnati yafi yawa a gani na, domin gwamnati ce ya kamata ace tasa ido sosai akan harkar tsaro, ita keda alhakin samar da ingantaccen tsaro wa mutanen k'asarta, ta hanyar tsaurara doka in an kama masu laifin ayi musu hukunci yanda ya dace, ta yanda zasu kasance misali ga duk wani mai yunk'urin aikata hali irin nasu, a samar da ingantattun kayan aiki masu kyau ga jami'an, sannan sukansu jami'an tsaron asamar da nagartattun ma'aikata wa ɗanda suka san kan aikin su, to wallahi Ina fad'a muku in akayi haka sai kuga an zauna lafiya, kidnappers ɗin me! Inda wadatattun kayan aiki tun yaushe za'a gano su, suna kiran wayar nan da sukan yi in zasu buk'aci kuɗi, za'ayi (tracing) ɗin layin wayar, wanda hakan shi zai taimaka agano har inda suke.Da haka sauran k'asashen da suka cigaba ai suka fimu.


Har ila yau ita kanta al'umar na bukatar gyara, wasu dayawa rashin aikinyi ga talauci shike jefasu ga yin sace-sace na mutanen dama sauran miyagun ayyuka, kar mu zauna muce wai komai sai gwamnati tayi mana, tabbas akwai inda gwamnati ce take da buk'atar gyarawa, amma muma ta wani b'angaren akwai namu, in baka samu aiki na gwamnati ba ai sai ka rungumi sana'oin nan namu na hannu, amma yaran mu sai suja jiki suce a'a suna ganin su ai sunyi karatu, kuma in har gwamnati bata basu aikinyi ba to baza suyi sana'ar hannun ba, to daga zaman banzan nan ne sai kaji an fada mugun aiki".


Sauran suka ce "kuma gaskiyar kafa malam sani".


Malam k'aseem ya d'ora da cewa "Inda ace akwai wannan cigaban a kasar mu, ai kwanaki da aka sace malam Usman ɗan kasuwa kace da lallai an kamasu, lafiya yabar gida fa yaje wurin kasuwancin sabawan Allah akan hanyarsa ta dawo wa kawai mutanen nan suka ɗaukeshi ni abinda ke ɗaure min kai ma shine, ta yanda akeyi su kama mutum babba guda su ɓoye har tsawon wani lokaci".


"Malam k'aseem nifa ina ganin bafa haka nan kawai suke ba". Cewar Mlm Adamu.


Shi kuma ya cigaba da labarin da yake basu.


 "Sai da akayi kwana uku ana Neman sa'a rana ta huɗu suka Kira waya, ta yanda zaka gane k'ananan ɓarayine ma 'yan unguwa, dubu ɗari biyar suka nema".


"Taya zaka ce kananun barayi malam k'aseem? dubu ɗari biyar fa kace".


"k'anana ne mana malam Adamu! akan yanzu wannan ɓarayin da suka sace Hajiya Saude, sufa miliyan biyar suka nema Alhaji ya bada".


Malam Sani yace "Ai dukansu k'ananun ɓarayi ne waɗan da suka shahara a harkar fa har miliyan talatin wallahi suna karb'a! kuma duk da haka ma sukan duba irin sana'ar da mutum yake".


Malam k'aseem ya cigaba "Tabbas kam! Wannan dai hatsi yake saidawa a kasuwa ,to ko su ɓarayin nasa kallon wani mai arziki suke mai, basu san ɗan na rufin asiri ne dashi ba, wallahi ina faɗa muku bawan Allah nan haka 'yan uwansa da iyalinsa suka tattara ɗan cinikin nasa da abinda yan uwan nashi suke dashi aka siyar aka sami cikon kuɗin kana aka ba wannan mutanen, sannan suka sake shi, gwanin tausayi koda ya dawo gida bai iya shaida mutane saida ya kwana biyu tukun ".


"To wannan al'amari dai gabad'aya Allah ya kawo mana saukinsa". Cewar malam Sani.


Inda sauran suka amsa da "Ameen" gaba d'ayansu.
*Ku biyo Miemie da Ashnurpyar* 👌🏻

[01:25, 2/14/2018] 💕Anty miemie👌🏽: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  *RUWAN DARE*


     *DAGA*


*MEEMI BASHIR(queen)*       *&* 

   *ASHNUR PYAR*  

      

   

Babi na (17)Haka dai Rayuwar ta cigaba da wanzuwa,duk inda kaje maganar sace -sacen nan daya yawaita ake ,majilusun manya da samari kowa dai maganar nande itace.


Alhaji mijin saude kuwa,duk ya faɗa ya rame saboda tunani, har ilayau bai koma Abuja ba saboda wan nan ibtila'i duk da hakan ta gefe ɗaya yasa anata addoi ALLAH ya sauk'ak'a lamarin.*******

Al'amarin gidansu Ameera kuwa, ayanzu kowacce yanzu ta koma harkar gabanta ba kamar da ba sun ɗan ja baya da juna Musamman Ameera data ɗauke musu fuska ɗif.


Musamman Ganin ta samu sabuwr k'awa datayi.


Ayanzu saliha kuwa sun game gam da aysha, tabbas tarayyarta da aysha yasa ta daɗa samun sani kala-kala.B'angaren maganin mata kuwa Agun Amira se abunda ya k'ara gaba.Tun saliha na gaya mata ta rage amfani dashi harta dena ta zuba mata ido,hakan yasa ta ja baya sa salihar, ganin ta samu sabuwar wacce ke kawo mata maganin matan sabili da sadiya yanzu tayi hannun riga da maganin mata,wato ta daina saidawa.Safar'u tsaf! irin zawara wan nan ne wanda auren su ya mutu, tunda Ameera ta sameta suka ɗinke suka k'ulle, ita safar'au gidan su na unguwar da yayar Ameera ke aure, aɗan zuwan datake can ne suka saba da safara'un, tunda tana yawan shiga gidan yayar Ameran.


Ameera nason k'awancenta da safara'u, musamman dataji tana saida maganin mata. 


Tun daga nan suka ɗinke sai take kawo mata har gidanta,haka zata bata maganin mata kala-kala ganin yanda take samun kan mijinta duk yayinda ta ɗirki kayan,hakan yasa ta daɗa janyo Safara'u jikinta Ta wani ɓangaren kuma safara'u na ɗora Ameera kan hanyoyi na rashin ɗa'a ga miji ganinta namaji saida hakan,azuwanta biyu ta gane halayyar Amerra irin shashan nan ne da komi basu da sirri ga karaɗi da surutu amma ba wayo, hakan ya bata damar cusa mata ugwayen ɗabiu.Haka Zata zauna ta kwashe kaf huɗubar da safar'au ke yi mata, acewar safara'un Namiji saida wuta ,tunda tana gyara jikinta da kayan mata tofa ta wuce zarra duk tsiyar da zata shuka mishi zai shanye.Hakafa Ameera ta faraiwa miji ɗan rashin ɗa'a ga kazanta data koya, ba biyayya falonta ko yaushe kaca -kaca ,ai aganinta ai ta gama komi tunda tana bashi abunda ya keso duk dare, samun hakan ne yasa safara'u ta buɗe wuta kullum da kalar huɗubar da zataiwa Ameera, su kuwa su saliha 'yan kallo ne.


Yauma suna zaune misalin karfe huɗu na yamma ta baza mata kayan mata safara'u tace:


"Ai Ameera wallhi kikai amfani da wan nan maganin wallahi kingama! ai ko wane irin tsiya kikai mai ta kau, saboda yasan kina kashe shi da daɗi".Shewa sukai suka tafa.


 "Ai shiisa nake sanki safara'u saboda kina ɗorani kan hanya kinga yanda adamu ke lallaɓani kuwa!"


Tafawa suka kumayii safar'u tace "to yasan zakiyi mai tijara". suka saka dariya, haka ta duk haɗa mata komi ta tafi. Saliha bayan fitar safara'u ta shiga falon Ameeran ta zauna gefen kujera.


 "Haba Ameera yanzu saboda Allah duk kin lalace kin koyi k'azanta,baki da aikin komi sai na shan magani mata haba! kingan ni nan! wlh yanzu nafi samun nutsuwa komi naturar masu inganci kayan itatuwa waɗanda na sansu na haɗa da kaina nasha.


 Amafa walh duk wan nan yaudarace safara'u take kowa, tazo tana wani gaya miki karya da gaskiya nifa nagano ta,duk tana miki huɗubar tsiya idan kinyi duba da idon basira ba bazawara bace! ita maiyasa bata zauna agidan na ta ta mallake mijin nata ba! duk bubuwan da take gaya miki duk inaji.


Kiyi tunani, ta yaya matar data kasa zama gidan mijinta ,duk da dai ansan rabuwar aure k'addara ce amma da sila, kinga kuwa tabbas halin data shuka agidan mijinta ne shine kema zatazo ta ɗora ki,Hmm! kidaiyi karatun ta nutsu atoh!, nide zaman tare muke dole na gaya miki gaskiya".

 


Ameera tace, Lallai saliha! sai kace wata uwata kinzo kina gayan abunda zanyi! to idan ba zaki gani ki kyale ba, ma'ana kiyi shiru.

Bansan sa'ido ,idan bakisan buɗe ido kiga safara'u in tazo, to kina kulle kunnuwanki da idonki.


Kallon Saliha tayi taga ranta kamar ya ɓaci sai ta basar "to wlh samun safara'u matsayin k'awa yasa dan ba kiga yanda mijina ke tarairaya ta ba! dan haka wlh yanzu na rik'e maganin mata"

 

Saliha tace "to Allah ya kyauta yasa ki gane, dama zaman tare na duba,yanzu ma zuwa nai nace miki gobe zan tafiya dan karkiji shiru".


 Amera tace "to Allah ya kaiki lafiya."Bayan Kwana biyu


**

"Yanzu saboda ALLAH! wai meyasa Ameera duk kika canja ne? ɗan girkin nan ma kindena mun sede kawai ki watsa taliya kindena zagewa kiyi me kyau, gashi kin koyi k'azanta innai magana kihau mun faɗa".


 Tashi tayi ta kaɗe riga kaga Adam! idan ba zaka iya ba sekai shiru haba! akanka zan k'are?"


 Jin-jina kai kawai yayi ya tashi ya fice.


Haka mijin Ameera ke fama yanzu da ita, se da daddare ne kawai yake samun ta dai-de, amma in bacin hakan sam! ya gaji da halayen data tsuro mai.Haka dai yake ta fama ayanzun da sabon halayen nata wata da watanni yana fama amma kullum tana karɓar kuɗinsa,daya bata kuwa maganin mata zata siya acewarta gwanda ta buɗe wuta ta toshe hanyar da wata macen ma zatai tunanin shiga gidanta.


kwatsam! yawan kaiwa aabokinsa matsalar gidansa da yake yi ne ,hakan yasa ya bashi shawarar ya k'ara aure, farko yaɗan ji tsoro saboda faɗan Ameera, amma da abokin nan yayita ɗorashi a hanya karshe yace zai fara neman aure.Ahankali ya dunga sako mai da maganar k'anwarsa take ko ya amince, da yaje ya ganta yaga tayi mai itama yayi mata, ba ɓata lokaci suka ɗinke, suka fara soyayya.


 Ameera kam ta hau kan zugar safara'u ta haukai ta zauna komi k'ara gaba yake yi.


Dan ayanzu ta tsiri ma indr zasuyi tarayya ta aure musamman intasan ta ɗirki kayan mata tofa dole saiya ajiye mata kuɗi kafin ya karɓi hak'k'insa.Bayan sati huɗuAka tsaida maganar auren mijin Ameera, tun lokacin daya gaya mata ta tashi hankalinta, me makon ta gyara, Aa sai ta daɗa birkicewa, su aysha da saliha sai bata baki suke amma taki saduda.Ba shawarar wacce take ɗauka saita safara'u, hakan taita ingizata tana hauka, mijinta yanzu baya biye mata ,ahakan lokaci ya zagayo har akayi auren amarya ta tare.

 

Abubuwa sun cakuɗewa Ameera,ga kishiyar da aka dank'ara mata, san nan yanzu kuma sam! inta sha maganin matan ba yayi mata amfani,ta dawo k'amas,tabbas tasan yanzu adam baya damuwa da ita ta ɓangaren Auratayya.

ta rasa gane meke damuwa da ita.


 Ameera tayi kuka sosai kamar ranta.Amaryar kuwa tana da kirki duk irin abunda Amira ke mata bata damuwa. 


Mijinta kuwa ya samu nitsuwa soboda ya sami mace me tsafta girki da ladabi da biyayya.Tafiya tayi tafiya Ameera ta gano gaskiya, domin ta gano kawai zugata safarau keyi ,ganin aurenta ya mitu ta keso itama ta kashe mata natan, kuma gashi duk shan magungunan nata hakan baisa mijinta k'inyi mata kishiyaba.


 Aysha da take tunanin za aiwa gashi ba aimata ba lalle ta gane maganin mata ba abunda zai tsinana mata inde batayi biyayya iya girki da tsafta.Ganin hakan yasa ameera duk ta watsar da harkar magun -gunan matan tunda ta gama yanzun baya mata amfani ko tasha abanza tarasa dalili, hakan yasa ta koma wajen su Aysha suka koya mata,daba runsu.


Sam ko zuwa safara'u tayi bata ganin fuska agun ameeran domin ta gano kawai so take ta kaita ta baro k'arshe ma tace mata tadena zuwa gidanta.


 Ameera dole ta sauko bayanda ta iya take zaune da kishiyarta lafiya ,domin ta kula adamu abu kaɗan zata yimai kota yima matarsa sai ya koreta.


Kishiyarta ta kuwa mai suna zaliha kanta awaye yake, ta iya zama da mutane,haka dai zaman lafiya ya wanzu estate ɗinsu Ameera ,sun ɗinke su huɗu abinsu suna kyautatawa juna.


 Amma har yanzu ameera na fama da rashin amfani da maganin mata ke mata ko tasha na k'arin ni'ima abanza.

ku biyo

*queen Meemi & ASHNUR pyar*👌🏽

[16:36, 2/14/2018] 💕Anty miemie👌🏽: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  *RUWAN DARE*......
     *DAGA*
*MEEMI BASHIR(queen)*

        *Aur*

     *ASHNUR PYAR*Babi na sha shida (18) B'angaren 'yan kidnapping ɗin nan Kuwa sun cigaba da rik'on Hajiya Saude ba tare da sun kira Alhaji ba, har sai da suka tabbatar da yasa anje police station an rufe case ɗin da aka buɗe na ɓatan Hajiya kan cewa za'a maida lamarin ɓatan nata gabad'aya gun ubangiji, domin adduoi za'a dage dayi har Allah ya bayyana ta.
Su Kansu jami'an tsaron sun tabbatar da hakan yafi musu sauki, domin tunda ake kawo musu cases na kidnapping ɗin nan basu taɓa cin sa'ar gano koda k'ungiya ɗaya ta masu satar mutanen ba, Saidai saboda barazana sai da suka yi 'yan mazurai wajen rufe case din, sannan suka rufe, ba tare da sun bibiyi hak'ik'anin abinda ya jawo yin hakan ba.Sai da Oga ɗan gumurzu ya tabbatar da komai daga bakin yaransa 'yan lek'en asirin sa, sannan ya sake sa layi tare da ɓoye Lambar Alhaji ya kira bugun farko ya ɗaga wayar tamkar dama su yake jira su kira shi.


"Zaka iya zuwa hanyar dogon daji dake hayin keke da Kuɗalen gobe da misalin k'arfe bakwai na yamma, idan kaje kan hanyar ka mik'eta samɓal! ɓangaren Hannunka na hagu, zaka tadda wata jaka bak'a, ka buɗe Jakar kasanya Kuɗin aciki ka juya kayi tafiyar ka. 


Idan har baka shirya ganin matar ka ba kuma to ka taho wani, idan kayi gigin aikata hakan, zan tabbatar maka da hak'ik'anin koni wanene ba kuma zaka sake jin kirana ba".Cikin rawar murya Alhaji yace "Ina sam! Ai ba zata ma kaiga haka ba, ni kadai zanzo".


D'an gumurzu ya bushe da dariya sannan yace "kana birgeni Alhaji, kai mai wayau ne, zan sanar da kai inda zaka ɗauki matar ka in har aiki ya kammala".


Daga nan bai jira jin mai Alhaji zai sake cewa ba ya kashe wayar.


Haka Alhaji ya shirya Kuɗaɗe'n da zai ba 'yan kidnapping ɗin nan cash, ya k'udiri niyar zuwa inda suka mai kwatanci gobe dan ya k'osa yasan halin da matar shi take ciki. A gefe guda ko Hajiya Saude duk tabi ta yamutse, Kallo ɗaya zakai mata ka gane cewa tana cikin mawuyacin hali, abinka da Wacce bata saba da wahala ba. Abinci ta saba sai taci ta bari amma sai gashi a 'yan kwanakin nan daga ruwa sai biredi take samu taci, shima sai sun ga dama suke bata, sai yunwar taci ta cita tukun. Hajiya Saude gaba ɗaya ta shiga kogin nadama, tabbas tasan duk yawan fitar da take ba da izinin mijinta bane,koda hakan aka barta tasan ALLAH ne nunaa mata ishara.


'Lallai ni tawa jarabawar ta kerewa na Maryam, tunda ita aure mijinta yace zai k'ara, ta mishi hauka ya sake ta, niko nawa mijin ban san mai zai faru tsakanina dashi ba, inhar ya biya mutanen nan kuɗin da suka nema dan nasan saiya tambayeni ina zani lokacin'.


Cikin zuciyar ta take wannan tunanin.


"Oh ni Saude! Yau na jawa kaina gun Alhaji bansan wani irin mataki zaiauka a kaina ba, ya Allah karka sa Alhaji yamin hukunci mai tsauri".


Ta fad'a a fili gamida fashewa da kuka.


 "Wallahi na bar k'ara harkar maganin mata har abada, saboda ta dalilin zuwan karɓa ne,ashe! Sadiya mijinta ba k'aramin K'ok'ari yayi ba kafin ya hanata fita, nima dai inna sami kaina na tuba har abada."****** ***** *******washegari*


Da yammaci misalin k'arfe bakwai na yamma Alhaji har ya isa inda zai Kai kuɗin nan, kamar yanda yamai bayani ne ko, wata k'atuwar bak'ar jaka ya hango a ajiye.


K'arasawa yayi ya bud'e Jakar ya saka Jakar kuɗin da yazo da ita.


Daga nan ya juya yayi tafiyarsa, ɗan gumurzu ko da yaran shi dama suna daga gefe guda can! Da dɗan tazara tsakaninsu da inda Jakar take, sai da suka tabbatar da Alhaji ya bar gun kuma babu alamar zai dawo,san nan sukayi saurin fitowa daga maɓoyar su, tare da ɗaukan Jakar Kud'in nan suka Kama hanyar mab'oyar su.(Dama abinda Alhaji be sani ba shine, wannan gun da Oga d'an gumurzu ya faɗa mai yakai kuɗin ajiye, kwata-kwata bai da alak'a da ainihin maɓoyarsu, yayi hakan ne gudun ko ta kwana, koda bayan sun saki Hajiya Saude Alhaji zai iya yayin tunanin Kai rahoto, dan a binciki dajin, to ba za'a sami komai nasu a gun ba).Haka ɗan gumurzu suka koma gida da yaran sa, saida suka hala 'yar k'aramar walima domin murna da farin cikin samun nasara, daren ranar Hajiya Saude ta sami abinci na musamman daga garesu.


Gari na waye wa Kuwa, Oga ɗan gumurzu ya kira Alhaji ya faɗa mai inda zai sami matar sa, yana gama faɗa mai ya cire layin wayar ya kak-karyashi.


Dama ya riga yasa an sake shak'awa Hajiya abin gusar da hankali, an kaita an yasar inda ya kwatanta ma Alhaji dan yaje ya ɗauketa, hanyar atoshe dan yanzu mutane sun daina bin ta kwata-kwata.
Alhaji na zuwa gun ya hango mutum yashe a k'asa,cikin hanzari ya k'arasa gun dan tabbatar da abinda idanunsa ke hango mai. Hajiya Saude ce kwance shame-shame a k'asa. In bacin sanin da Alhaji ya riga yayi wa Hajiya Saude matar sa, da kuma kiran da Oga ɗan gumurzu yamai ya gaya mai anan gun ne zai sami matar sa, to da zai iya cewa ba ita bace , saboda gabaki d'aya tayi baki ta rame kamar ba ita ba.


Alhaji ya kira sunan ta yaji shiru, nan ya gane cewa bata ma san inda take ba, cikin sauri-sauri ya koma ya bud'e k'ofar motarsa ya kwantar da kujerar baya, inda daga baya ya dawo ya ɗauke ta yasa ta a mota, bai zar ce da ita ko'ina ba sai asibiti domin a bata cikakkiyar kulawar data dace.*Bayan sati d'aya*


Hajiya Saude ta warware, tun bayan da aka sallamosu daga asibiti mutane sai zuwa gaisheta ake ana yi musu jaje. Ita dai duk hankalin ta ba'a kwance yake ba, dan har zuwa yanzu ba suyi wata magana da mijinta ba, babban abinda yafi damunta Sanin cewa da tayi bada izinin shi bane ta fita har aka kamata.


B'angaren Sadiya Kuwa tunda taji labarin dawowar Hajiya Saude gida, ta rink'a gode ma Allah.


Bayan wasu 'yan kwanaki Sadiya tasa waya ta Kira Hajiya amma layin bai shiga ba, domin 'yan kidnapping ɗin nan sun karɓe wayar, saboda haka wata rana ta rok'i mijinta alfarma kan ya barta taje yiwa Hajiya jaje, cikin Sa'a kuwa ya amince mata, da sharaɗin cewa kada ta daɗe kuma ta tafi da K'aramar yarinyarta, ba musu ta amince.Abinda yasa Sadiya mai maganin mata take so taje gun Hajiya Saude, dan ta dad'a tabbatar da cewa ba zarginta cikin ranta, shine hankalin ta zai fi samun natsuwa.
*Ku biyo Miemie Basheer da Ashnurpyar* 👌🏻

[17:05, 2/14/2018] 💕Anty miemie👌🏽: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
  *RUWAN DARE*......
     *DAGA*
*MEEMI BASHIR(queen)*

        *Aur*

     *ASHNUR PYAR*Babi na sha shida (19) Haka Sadiya taje gidan Hajiya Saude, bayan sun gama gaisawa tun kan Sadiyar tace wani abu Hajiya Saude ta rigata da cewa:


 "Sadiya ina fatan dai ba wani tallan magani kika kawo min bako? Dan nan da kike gani na yanzu na dawo daga rakiyar kayan mata, domin ta dalilin su na kusan cimma ajalina, Allah dai ne ya nufa da sauran kwana na a gaba."


Sadiya tace "wai! me yafaru haka ne Hajiya?".


Hajiya tace "Hmm! Ai tun ranar da mukayi waya dake kan Zan zo mu haɗu in karɓi wasu magunguna a gunki".


Sadiya tace "Eh! na tuna, ai nayi ta kiran ki ranar amma baki ɗauka ba."


Hajiya tace:


"To ai a ranar ne aka sace ni, ina kan hanyar tafiya gun da muka yi zamu haɗu dake, na fito daga mota ban fargaba kawai sai naga wani bak'in mutum a gabana, komai na jikin sa bak'i ne, ba ki ma iya tantance ko fuskar wane ne, ina fad'a miki, kafin inyi wani yinkurin komai dan guduwa naji an fizgo ni ta baya gamida shak'amin wani abu a hanci tun daga nan ban Kara sanin inda nake ba". 


 Nan dai ta cigaba da ba Sadiya labarin abinda ya faru da ita, har zuwa inda Sadiyar ta kira waya.


Tace "In zaki iya tunawa ranar da mukayi zamu haɗu ai banzo ba ,kuma kinyi ta kirana a waya ban ɗauka ba, k'arshe ma lokacin da kika sake kirana Koda aka ɗaga wayar ba'ayi magana ba ai ".


Sadiya tace "Eh! k'warai tabbas ko anyi haka, ai dana gaji da jira, naga kuma kin ɗaga waya baki ce komai ba, sai nayi tunanin ko Alhaji ya dawo ne, shiyasa baki sami halin fitowa ba, kuma kuna tare ba halin ki ɗaga wayar ki sanar min, tunanin hakan da nayi shine yasa nayi saurin komawa gida, dan nima kar nawa mijin ya dawo bai tadda ni ba".


Hajiya Saude tace "Ina! ai ba abinda ya faru ba kenan".


Nan tayi ta ba Sadiya labarin masu neman Kud'i gurin Alhaji, ita kuma sadiyar ta rinka amsa mata tamkar bata san komai da ya faru ba. A karshe ta k'ara yi mata Allah shi kyauta, ta kama hanya ta koma gida tana mai hamdala ga sarki Allah daya rufa mata asiri ya tseratar da ita daga wannan haɗarin.***" *******


B'angaren su Oga d'an gumurzu kuwa, bayan da suka jefar da Hajiya inda Alhaji yaje ya ɗauketa, bayan sun tabbatar da ya tafi sannan suka kama hanya zuwa dandalinsu, wata kwarya-k'waryar walima suka sakeyi inda daga nan Oga yace to Kowa ya matso za ayi rabon Kud'i.


Tashin farko ya ɗauki bandir din Kuɗi guda biyar, rafa ne Na dubu ɗari-ɗari yace "Kai ruwan dare ga naka, kasance war kafi sauran shan wahala ta zirga- zirga gashi kuma Kai ka fara kawo mana labarin Sadiya.mai yawan zuwa gidan Hajiya Saude, saboda haka Kai ga million ɗaya nan ka rik'e.Daga nan yabi sauran ɗaya bayan ɗaya da dubu dari biyar-biyar su bakwai million huɗu da rabi kenan in an haɗa da na ruwan dare, shi kuma yace ya ɗauki sauran tunda shine oga. Nan fa ruwan dare ya Kama murna da jin daɗi shikenan shi kakarsa ta yanke Sa'a.


D'aya daga cikin yaran ɗan gumurzu yace "Oga ni gaskiya ban yarda da wannan rabon Kud'in da akayi ba, taya za'ayi ace kason ruwan dare yafi namu! Bayan duka tare aka sha wahalar inkai Oga ne ai shi ba ogannmu bane".Wani ma yace shi bai yarda ba suda suka ɗauko Sadiyar ai su yakamata ace kason su yafi yawa bana ruwan dare ba me kawo labari, mutum uku daga ciki suka ce a'a nasu ne yakamata ace yafi yawa suda suka ɗauko Hajiya Saude har aka sami kuɗin bana Wanda suka ɗauko Sadiya ba. Nan take sai gardama ta ɓarke, Kowa da abinda yake fad'a.


Ruwan dare yace "Wai to da duk kuke ta wan nan maganar Ku ta banza naga tun yaushe ake so a tatsi kuɗin Alhaji, ba asami dama ba har sai dana fara fita dakai na, Na rink'a kawo wa Oga labarin wannan matar sadiya har aka shirya plan ɗin da akayi na sato ta, da ban kawo labarinta ba, Ku faɗa min ta inda za'a sami kudin?".


Waɗan da suka sato Hajiya Saude suka ce "Amma dai da bamu sato Hajiya mun kawo ta gurin nan ba, da ba ta yadda Alhaji zai taɓa bada Kuɗaɗen nan ba, saboda haka namu yakamata yafi yawa bana ruwan dare ba".


" Ina! k'aryane wallahi mu da muka ɗauko Sadiya dole ne namu kason yafi yawa."


Dorinar ruwa ya mik'e daga K'ok'arin kunna wuta da yake yi yace "zancen banza duk kuke, Ku kuna tunanin da ban je gidan Sadiyan na ɗauko yarinyarta ba, kuna tunanin zata bamu haɗin Kaine har akai ga sami kuɗin? Kasada fa nayi har cikin gidan su na ɗauko yarinyar. Lokacin da na mai data fa! kaɗan ya rage mijinta ya ganni kun ga ko in canccanta ne ni yafi cancanta inyi magana baku ba".


"Duk ya isa haka nace ya isah!"..


Oga ɗan gumurzu ne ya dakatar dasu da muryar shi cikin tsawa.


"Rabo ne na riga nayi kuma bazan canza ba, ruwan dare yafi Ku K'ok'ari dukanku shepherds dole kasan shi yafi naku yawa".


Nan suka watse dukkansu suna gunaguni.


Tawagar da suka kamo Hajiya Saude suka k'ulla shiri kan cewa cikin dare zasu je su kashe Oga da ruwan dare dan dama ba tun yau ba sun lura Oga yafi son shi akan su.


Dare nayi suka fito saɗaf-saɗaf cikin lambɓo da nufin zuwa sashen ogan nasu, ashe suma sauran suyi niyar yin hakan, saboda haka nan suka haɗu suka farma Oga d'an gumurzu da ruwan dare, basu san hawa ba basu san sauka ba suka ji maza sun dirar musu, nan fa aka shiga gwab zawa tsakanin mazaje Saidai hausawa sun ce sarkin yawa yafi sarkin karfi, ga rashin shiri da Oga ɗan gumurzu da ruwan dare basu dashi akan abinda ke faruwa, saboda haka sun kashe mutum biyu inda a karshe dorinar ruwa da yaran sa suka cakama d'an gumurzu da ruwan dare wuka nan take suka ɗebe kuɗin.Dorinar ruwa ya hau kujerar oga ɗan gumurzu ya bushe da dariya dama ya de yana jiran wannan lokacin.


(Kaico! D'an daba bai da amana, duk yanda zamanku ya Kai da daɗi rana daya zai iya sa kafa yayi fatali dashi kamar yanda dorinar ruwa yayi ga d'an gumurzu).


Gari na waye Dorinar ruwa yasa k'aramin cikinsu yayi musu girki sannan ya fara rabon kuɗi, ya kwashe kuɗin ruwan dare dana Oga d'an gumurzu yace duka nasa ne, su kuma sauran mutum hudu da suka rage yak'ara musu dana mutum biyu dasu Oga d'an gumurzu suka kashe, nan fa suka ce basu yarda ba dan yaso kanshi dayawa, kuma tare akayi wahalar, suka ce Kai basu ma yarda Dorinar ruwa ya zamo shugaban su ba, abu kamar wasa nan ma sai faɗa ya sake kaurewa, da Dorinar ruwa yaga shima in yayi wasa kashe shi zasuyi sai ya nemi sulhu yace su dakata to za a sake rabo , ya ɗauko sigarin dake aljihunsa ya kunna lighter, gaba ɗaya sun manta da girkin da aka ce Karamin cikinsu ya d'ora, ya bud'e gas bai riga ya kunna wuta ba ya hango sun fara rigima shima ya tafi gun, gasin yana ta fita har ya zama ya gauraye ko ina cikin dakin, gashi lokacin da Dorinar ruwa zai kunna tabar sa kusa da tukun yar gas din yake nan take huta ya Kama da gun, rigar dake jikin sa ma ta Kama cikin ruɗewa ya jawo na kusa dashi, shima ya manna me wutar ,kan kace kobo hayaki ya turnuke gun, suka Fara Neman hanyar gudu duk wani takarda Leda dake dakin su suka k'arama wutan armashi, tukun yar gas ɗin na ɗukar zafin wuta ta fashe bam! Nan wuta ta cinye su suka mutu k'urmus harda kuɗin duka, su basu ci kuɗin ba kuma babu Wanda ya rayu.

 

*(Mutum na nashi ALLAH na nasa Ta ALLAH itace gaskiya. Dama k'arshen zalunci kenan,gashi nan Alhakin Sadiya, 'yar yarinya khadija,saude da Alhaji ya kama su ɗan gumurzu sunyi baɗin baɗinahu)**Ku biyo Miemie da Ashnurpyar*👌🏻👌🏻


*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*RUWAN DARE*


    *DAGA*


*MEEMI BASHIR(queen)*     &

  *ASHNUR PYAR*

*🔚KARSHE🔚**Anty muhibba sakonki ya iso garemu minji dadi mun kuma gode da jinjina da yabo da kikai mana mun gode da kauna Allahu yabar zumunci Ameen.*
*******

Hannu biyu ta haɗa ta damk'e fuskarta da su, ba abinda ke damunta sai rashin ni'emar dake jikinta,wacce ta zamanto mata k'ak'ani kayi tsakaninta da megidanta,wanda ayanzu ta kula kacokam! ya maida hankalinsa gun amaryarsa ita kuwa ya azubar da ita a kwandon shara.Kuma tasan rashin gamsuwar da baya yi ne domin dashi da ita yanzu wahala suke sha rashin ni'emarta.Kuka ta fashe dashi "wayyo ni Amira! meyasa na cucu kaina, meyasa na biyewa safara'u! gashi yanzu takaini ta baro ga kishiya ga rashin ni'ema".Shiru tayi jin alamar za a shigo. Zaliha ce kishiyarta da sallama ta shiga murmushi tayiwa Amira itakuma cikin yak'e ta amsa mata,kula ta aje mata.


 "Gashi dama nayi d'an abun motsa baki ne na kawo miki." 


Amira tace "Nagode" ta ɗau kular, ita kuma ta fita.Bayan fitarta Amira ta tsaya tana tunani tabbas tasan kishiyarta ta bamai kwaramniya bace,ta godewa ALLAH daya yasa tayi dacen kishiya, shigewa kitchen tayi ta aje ta koma ɗaki dan tayi wanka.Misalin k'arfe 7 na dare Amera ta shiga wajen saliha ta zauna suna hira take tambayarta Dr zeenat yayarta kan tana so taje wajenta.


Saliha tace "meke damunki sis zaki wajen yaya zee?"

 Ameera tace "kedai bari! wlh abu yayi min yawa kwata- kwata banda ni'ema yanzu! ko nasha maganin baya min komi, shine nake san zuwan wajenta." Saliha tace hmmm! "ɗaya daga cikin matsalar maganin mata kenan."


Nan ta gaya mata sunan asibitin da ya zee ke aiki taimata kwatance. Ameera tace gobe zata nan sukayi sallama ta fita.*WASHEGARI*Da sassafe kuwa tafi asibitin da Dr zeenat ke aiki.

Da yake da sanayya bata daɗe ba ta samu ganin Dr ɗin.Da shigarta office ɗin ta zauna Dr zee tace "Aa! Ameera kece yau! Ameera tace "eh nice yaya.""Baki da lafiya ne?"

 Ameera tace "wlh yaya matsala nake fama da ita sam! yanzu bani da ni'ema koda nasha magun-gunan mata basayi min duk dama yanzu na dena shansu".Ajiye biron dake hannunta tayi ta kalli Ameera tace "ɗaya kenan! kunga abunda nake gaya muku kenan ko!,kinga dama su magun-gunan nan idan kuka shasu aiki sukeyi tuk'uru ta dole ni'emar take zuwa to ko injine ake yawan amfani dashi aidole yayi yaushi ya dena yin aiki yanda ya kamata.


Kinga rashin ni'emar yana samuwa ne ta hanyoyin dama dama kamar :

 Infection, Basir, ko shafar aljanu, da kuma shan magun-gunan nan matan barkatai ba bisa k'aida ba, da kuma rashin sanin kyawunsu ko ingancisu.Nan tayi mata tambayoyi a likitance ta tabbatar bata da infection da basir koda tana da su ma beyi worst da zai saka ni'emarta ta dena zuwa ba,hakan ya ta'allak'a ne ga wayan shan magun-guna barkatai shine ya janyo hakan.Nan de Anty zee duk tayi mata bayani tayi mata nasiha, k'arshe dai tayi mata bayanin ta jajirce dashan fruit da haɗin nonon rakumi da tsumin ɓaure k'arshen ta rubuta mata wani magani tace ta gwada ta gani.


Nan Amira ta tashi ta tafi.*BAYAN WATA UKU*Sadiya zaune cikin yaranta tana koya musu assingnment ita kanta yanzu tafi samun nutsuwa aranta murmushi kawai take tana hamdala aranta.


Ayanzi hankalinta akwance yake ladabi da biyayya takewa mijinta ta denai mai rashin ɗa a, yanzu sana'ar data keyi agida ake zuwa asaya bata zuwa ko ina, idan ba gaisuwa ba ko dubiya ba, rayuwarta ta dawo normal abinta. A ɓangaren maganin mata kuwa komi natural take sha yanzu duk ta watsar da waɗancan, dama ta dena sayarwa. Abangare guda Hajiya saude tunda abun nan ya faru Tana ta zuba ido Alhaji yayi Mata hukunci akan fitar da take bada izininsa ba ,tun lokacin take zuba ido akan hukuncin da zai yanke mata ,shi kuma ya zuba Mata Na mujiya kawai dama hausawa sun ce Shiru ma maganace.


Haka yanzu bata yawan fita ma, idan ma zata fitan to driver ne ke kaita,sam yanzu atsorace take tadena tuk'i da kanta saboda tsoro takejin,kuma mota ɗaya take hawa yanzu ta daina fafar kuɗi da nuna ita me kuɗin ce, haka maganin mata ta watsar da babinsu.
Gidan su Ameera kuwa, tun bayan da Amira ta karɓo maganin nan take shansa wanda Dr zee ta bata amma bata ga canji ba hakan yasa ta hak'ura, ta dage da shan fruit su zogale aya haɗeɗɗen dabino,da sauran wanda Aysha take gaya mata.


Cikin ikon ALLAH bayan k'wak'war data sha tafara samun canji dagewar datai shan su fruit kuma tana yawan shan habbat-sauda, duk da hakan ba kamar da ba, Sam yanzu ba tada wani wadataccen Ruwa ta maida kanta kamar tsohuwar data Kai shekara arbain na rashin Ruwa,ganin kwata-kwata de ba kamar da d'inba hakan yasa ko maganar maganin mata bata sonyi domin ta dalilinsu ammata kishiya.

Gashi ta rasa abu mai muhimmci atattare da ita saide dabaru.


(Su kayan Mata dama ka'ida haka suke a ɓangaren (health) indai mace ta Riga ta tsat-tsafar da ni'imarata zai wuya ya dawo)Aɓangaren Aysha kuwa su saliha Ameera da zaliha kishiyar Ameera sun bata shawarar tana saida maganin mata amma natural da kamar baza taiba sai ta ɗauka.


Hakan ta ɗau shawarar su ta fara idan mutum naso to saita haɗa mai, idan kuma kawai gaya musu zatai sai su nemo da kansu to duk yanda mutum keso amma da yawan mutanen cewa suke tai musu.


Nanda nan aka santa kuma bata zuwa ko ina agida idan mutum naso yake zuwa ya saya kuma Natural kayan mata wanda babu illa ta keyi nan tayi fice aka santa.Haka dukkan waɗan nan mutane kowa ya kama hanyar data dace mai.


Haka Ameera ɓangaren mijinta yanzu sun koma dede sun haɗe kansu itada kishiyarta.


Abangaren me shagon unguwar su hajiya saude kuwa, yaji k'ishin-k'ishin cewar hukuma sunce za'afara sa'ido kan matasa masu yin gungu -gungu Na gulma musamman wajen irin shagun nan da matasa ke taruwa ,to yaji ana tunanin irin masu satar mutane na wanzuwa adukkanin irin wuraren nan ,jin hakan yasa Ado mai shagon ya hana kowane saurayi zama wajen saide agaisa daga nesa dan ya tsorata.Al'amarin su Laure kuwa ayanzu kwata magajiya ta daina saidawa don ta tsorata, sai laurece kawai ta cigaba da saidawar amma ta cire mugunta aciki ta dena gwamutsa shi da cuta masu inganci take sayarwa masu kyau ta riga ta tuba da saida jabu.Idan muka koma baya daman munce su ruwandare sun mutu, to haka dai gawarwakinsu sukayi ta zama duk da wasu sun babbake, amma su ruwan daren hakan suka wanzu awajen ba batun suttura akaisu makwancin su kamar yanda akewa kowane mamaci musulmi,wa iyazubillah k'arshen dama irinsu kenan idan basu tuba ba. ALLAH kayi mana mekyau ka kiyayemu da yan uwanmu da rin rayuwar nan masuyi kuma ALLAH ka shiryesu.


 


*TO anan muka kawo k'arshen wan nan littafi mai suna RUWAN DARE,dukkan abinda ke cikin littfin nan gaba dayansa kusan ya faru a gaske ne saide dan kare -kare da mukai don littafin ya tafi dede. Kusan sai muce dukkan yanayin labarin ya zamo ruwandare a gaske ga al umma,musamman yanda mata suka ta'allak'a akan kayan mata kowane irin abu aka basu akace kayan mata ne to banka suke basa duba illarsa ga lafiyarsu, haka garkuwa ga mutane shima ya zame ruwan dare ba talaka ba mai kudi abun saidai du'ai ba ta yanda ba abi, kamar yanda muka kawo ya kasance ga sadiya da saude,Allah ya karemu da karewarsa,ALLAH yasa wan nan tak'aitaccen littafi namu ya zamo silar ganewar wasu,inda mukayi ba dede ba ALLAH ka yafe mana.*


*Ba zamu gajida tabo ku ba domin kun nuna kauna ga littafin Ruwandare kamar

Rubz

Lily

Ingireluma

Maryam muhammd

Maman muwadda

Ummu Adnan.

Faixa bashir

Mom fadeela

Feena manzo

 Annuri

Subz

Feenahmanzo.

Oum Jawad

Saudat idris

Mom sahabi

Maman ismael

Mrs Al ameen

Maman twins*


*Sai dukkan members na NAGARTA Allah y kara hade kanmu*


*JINJIN ga K'ungiya uwa mabada mama uwarmu maganin kukanmu wato a ɓangaren rubutu kungiya mai taken NAGARTA WRITERS ASSOCIATION ubangiji ALLAH ya ka'ra ɗaukaka ta*


*TAMMAT BIHAMDULLAH**MEEMI BASHIR & ASHNUR PYAR NE👌🏽*


Tags: #ashnur #queenmeemi
2300
0
5
1
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!