Rayuwarmu A Yau! (Year 2015)

Written by Aisha Adamu SadiqPublished on 2019-01-03 23:56:43Category Mystery/ThrillerLabari ne da aka gina shi bisa ga la'akari da rayuwarmu a yau. Labari ne da ya tabo bangarori da dama na rayuwar mutane, kama daga rayuwar auratayya, tarbiyya da abubuwan da suka kunshi rayuwa da sakacin iyaye akan yaransu. Labarin ya faru a gaske. Sai dai kwaskwarima da ya samu ta wasu fannoni. tags: Family #Love #Relationships #Betrayal #Rape #Northern NigeriaDuba was labarai »

RAYUWARMU A YAU

 

Hakkin Mallaka 

©Jam33lerh & ChuchunGaye 

 

K'ark'ashin jagorancin 

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION ?? 

 

ARASHI 

Wannan k'agaggen labari ne, ba'a yi dan rayuwar wani ko wata ba idan har labarin yayi kamamceceniya da na wani ko wata akasi aka samu.. 

 

GARGADI 

Ba mu yarda wani ko wata ba ya sarrafa wannan labari ta wata siga ba tare izinin ma su hakkin mallaka ba, hakan ya sa6a ma kudin doka, dan haka a KIYAYE... 

 

{1}

 

Tafe suke su biyu suna tafiya cikin hanzari dauke da farin bokiti a kai irin wanda ma su talla ke d'orawa,kallo d'aya za'a ma su a tantance rashin wadataccen ilimin boko da na addini a tattare da su saboda rashin natsuwar su a wajen tafiyar kanta.. Ba su wuce shekaru 10 ba.. 

 

Can mu ka tsinkayi muryar wani na cewa "Salima! Salima !! Salima!!!", sai suka k'ara azama, ya sake cewa "wai ba za ku tsaya, siya fa zanyi Allah".. Sannan suka tsaya ya k'araso wajen su.. Wadda aka kira Salima ta daure fuska tare da juyar da kai gefe guda, ya kalle ta yayi dariya yace" na ma fasa siyan awarar taki gun Saddik'a zan siya".. Murguda baki tayi tare da ta6e bakin, yasa hannu ya safke ma su bokitan wanda na Salima awara ne sai na Saddik'a doya da kwai.. Ya mik'o ma su naira hamsin yace "kowacce ta samun na naira ashirin da biyar (N25).. Ba musu suka zuba ma shi, Salima tayi saurin daukar bokitinta tayi gaba, sannan Saddik'a ta biyo ta a baya.. 

Suna tafe suna firar su kafin su isa gida har sun siyar da sauran kayan tallar su.. 

 

Wani gida suka dosa, da sallamar su suka shiga gidan inda k'arar dakan ke tashi tinkwal! Tinkwal!! Tinkwal!!! Sai da suka ida shigowa gidan, matan da ke dakan daure da zani da riga daban-daban .. 

 

Suka washe baki tare da fad'in "har kun dawo?" Saddik'a tace "Eh Inna yau munyi saurin siyarwa".. Matar da ke bakin murhu tace" ai kun kyauta".. 

 

Salima tace "Inna ina abincin mu?", tace "gashi can daki saman cabet d'ina na rufe da faifai".. Ta wuce cikin dakin ta dauko ma su abincin su ita da Saddik'a suka zauna,faten tsakin masara ne fari kwal be ji isasshen mai ba, sai ganyen zogale da ke ciki, haka suke ta turawa daga gani dan yunwa suke cin wannan faten ba dan marmari ba.. 

 

Haka suke rayuwa hannu baka hannu kwarya, cikin talauci da jahilci.. 

 

Ana idar da sallar maghriba sauran yaran gidan su ka shigo, iyayen su mata nata karakaina wajen zuba abincin dare, tuwo ne zagabu wanda ko surfa masarar ba'a yi ba, ga miyar kuka koriya shar! 

 

Ak'alla yaran gidan sun tasar ma ashirin da takwas,kowanne rukunin da kwanon su da yake yaran kai da kai abin dai ba'a magana... Suna gama ci suka hau wasannin su na guje-guje, daga gefe Saddik'a da Salima ne ke carafke.. Gaba daya gidan ya kaure da hayaniya da ashar, Babu mai kwaba ma wani cikin su kowa harkar gaban shi yake.. 

 

Wajen k'arfe 10pm, mai gidan ya shigo 'yan manyan cikin su kadai suka gaida shi, sauran nata harkokin gaban su... 

 

Matan gidan ne suka fito daga d'akunansu suna ma mai gida sannu da zuwa, duk daurin k'irji a jikin su.. Suna ma shi sannu da zuwa fuska d'aure ya amsa ma su, daya daga cikin su da mu ke zaton ita ce da maigida tace "malam a kawo maka abincin ka?".. Kad'a kai yayi tare da furta" a ah na k'oshi".. 

 

Daga can gefe yara ne da basu wuce shekaru takwas ba suna wasa tare da rera wad'annan baitocin:"Jan janje Jan jan je.. 

Jan jan je da gidan gwauro.. 

Ban amsa ba ina tsoro.. 

Tsoron mi? Tsoron mi? Tsoron wani abu jan baki, jan baki sari hoto, hoton gidan baraje.. 

Barajen dawa yake? Mik'o hannu mu je mu, mu je mu wace rana? Ranar tashin Balele.. 

Balele barbashin kuka tinkwal makad'i tinkwal kwal kwal"... 

 

Baitin na tsayawa akan gwiwar wata yarinya muka ga ta tankwashe k'afa guda.. Haka sukai ta wasan su har lokacin kwanciyar su yayi...

RAYUWAR MU A YAU 

 

NA 

 

©JAM33LERH 

CHUCHUNGAYE 

 

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION ?? 

 

{2}

ASALIN JAMA'AR GIDAN

 

Malam Amadu Bature mutumin Kofar Kona ne dake cikin garin Zazzau (Zaria), mutum ne da ya gaji sana'ar noma da rini tun iyaye da kakanni.. 

 

Su biyar ne wajen mahaifin su Malam Bature mai rini, sai mahaifiyar su mai suna Abu.. Suna da ya'ya kamar haka : 

Baba Sa'adu mai mata biyu da ya'ya goma sha biyu. 

Baba Muntaka mai mata daya da ya'ya bakwai.. 

Gwaggo Hassu tana aure a Birnin Gwari da ya'ya bakwai.. 

Gwaggo Sarai tana aure a Fambeguwa tana da ya'ya shida.. 

Sai autan su Amadu dake da mata uku da ya'ya goma sha tara. 

 

Matan shi ta farko da ake kira da Inna Habiba tana da ya'ya takwas,Abubakar, Lawal, Saude, Lubabatu, Ayuba, Yakubu,Salima da Kabiru.. 

 

Sai Mairo da suka kira Inna amarya mai ya'ya bakwai, Suwaiba, Sabi'u, Habibu,Saddiqa, Rakiya, Adama da Aliyu. 

 

Sai Hajara da suke kira da Amarya tana da ya'ya hudu, Jafaru, Sa'adatu, Hamisu da Ahmad da suke kira da Babangida.. 

 

Duk yawan wadannan iyalan gabadaya suna zaune a gida daya ne wato GIDAN GANDU.. 

 

Dakunan gidan a wargatse suke kowanne da dakunan su, sai kakannin su a gefe guda.. Yawanci matan gidan yan yara a dakin Gwaggo suke kwana wato kakar su Abu.. Gida ne gidan yawa da kowanne 'yan daki ke fafutukar ganin sun nemi na kan su.. Shiyasa kowacce mata dake gidan ba'a rasa ta' yar sana'ar da zata rufa ma kan ta asiri.. 

 

Cikin ya'ya sha takwas da Malam Amadu ke da su ya aurar da guda guda biyar wato Suwaiba, Lubabatu, Saude, da Lawal.. Lawal duk a cikin sashen Mal. Amadu yake ke da matar shi harda ya'ya.. 

 

Saboda rashin kula na masu gidan wato mazajen, iyakar su su ajiye hatsi ya rage ma su iyaye matan su sarrafa wannan hatsi zuwa nau'ika na abinci.. Suna rayuwa ne cikin mawuyacin hali, saboda haka iyayen su mata basu zama lafiya da junan su burin su da yarinyar su ta tasa su aurar da ita ga duk wanda ya zo ba ruwan su da halin mijin da zasu aurar da diyar su gare shi su dai sun yadda kwallon mangwaro sun huta da kud'a.. 

 

CIGABAN LABARIN 

La'asar sakaliya suna zaune a tsakar gida Inna amarya wadda ke da girki nata fama da dakan dawa da zata yi garin tuwo, Adama na taya ta da hura wuta ta d'ora ruwan miya.. 

Sauran matan na zaune bakin kofar dakunan su da daurin k' irji jikinsu butu butu alamun ko wanka basu yi ba... 

 

Salima ce ta fito wanka, tana ta shafa.. Karaf ta ji yaro ya shigo gidan yace "ana sallama da Salima a waje".. Inna dake zaune bakin kofar dakin ta tace "gata nan zuwa".." ke Salima yi sauri ki fito ko sai ya tafi".. 

 

Tace "toh Inna gani nan tafe"... Ta fito taci gayunta daidai gwargwado ita 'yan mata.. Haka ta tsallake su ta fita. 

 

Cikin zauren gidan ta iske shi, dan saurayi ne shima irin 'yan chaburos din nan ne.. Nan sukai ta firar cike da rashin kunya..

RAYUWAR MU A YAU

 

NA

 

© CHUCHUNGAYE

JAM33LERH 

 

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION ?? 

 

{3} 

Hango babansu da tayi tafe yasa ta komawa gida a guje ta fad'a dakin gwaggo. Ganin gwaggon a hargitse tana neme-neme yasa tayi turus tana kallonta da mamaki, tace "gwaggo lafiya? Meya faru haka?".. 

 

Cike da damuwa gwaggo ta cigaba da hankad'a katifarta tana fiddo kwanuka sannan daga bisani ta juyo tace "wallahi kudi ne Saratu ta kawo min ajiya akan gobe za taje Kano sayayyar kaya, to yanzu na nema na rasa".. Ta qarasa maganar a raunane. 

 

Cikin nuna halin ko in kula Salima ta mik'e tace "yanzu haka wani wurin kika jefar zaki ishi mutane da mita" tana fadin haka ta fice. Bangarensu ta wuce ta tarar da iyayen nasu a tsakar gida suna hirar la'asar da d'aurin k'irjin nan dai, mahaifiyarta na hangota ta washe baki tace "yar albarka har ya tafi ne? naga kinyi saurin dawowa". Wucewarta tayi ta shige dakinsu ba tare da ta kula Innar ba. 

 

Inna zata qara magana suka jiyo muryar gwaggo daga sassan ta alamun tana fada. Sukayi tsaki suka cigaba da harkokinsu. Ba'a jima ba gwaggo ta karaso inda suke tana kuka tana kwalama Duduwa matar baba Sa'adu kira. Duduwa ta amsa da "gani lafiya gwaggo?" Gwaggo cikin hargowa tace "Kun haifi barayi ba dama in aje kudi sai dai in nema in rasa to wallahi ba ku isa ba na gaji da daukar asara"... 

 

Duduwa tace "gwaggo har yanzu ban fahimci inda maganar ki ta dosa ba", gwaggo tace "eh dole kice haka mana kudi na aje danki Isma'il yabi dare ya sace..." Kafin goggo ta rufe wurin ya dauki salati. 

 

Duduwa ta hade rai tace "gaskiya gwaggo karki lak'a ma d'ana sata ban haifi barawo ba,ai ba shi kadaine a gidanba ga sauran yara nan sai shi za'a sa ma ido wallahi ba zan yarda ba".. 

 

Gwaggo ta fashe da kuka "zagina zakiyi? nice za ki ce nayi ma d'anki sharri? Bari mijin naki yazo ya sameni idan shi ya baki damar min rashin kunya". Daidai nan baba Muntaka ya shigo zai wuce su ya shige dakinshi don tun kofar gida yake jiyo hayaniyarsu wanda ba bak'on abu bane a gidan, amma ganin gwaggo a wurin ya sanya shi tsayawa. Yace

"Goggo meke faruwa ne?" 

 

Nan fa goggo ta kwashe ta sanar masa da yanda ta gano Isma'il ne tana daddaga kayan ya dawo neman zoben shi kuma inda ta aje kudin zoben ya fad'i". 

 

Isma'il ya fashe da kuka yana rantse-rantse wallahi baba ban daukar mata kud'i ba, jiya a dakinta na kwana wurin barci zoben ya fad'i wallahi baba ba ni bane", Duduwa tace "to gashi nan dai yaro ya fad'i gaskiya yanzu haka gigin tsufar tane ta jefar wani wurin ta manta". 

 

Baba Muntaka ya daka mata tsawa "kar ki k'ara fada ma gwaggo irin wadannan maganganun ba uwar mijinki bace? Kai kuma zo nan" ya jawo wuyan rigar Isma'il suka fita gwaggo ma ta koma sashenta. 

 

Da fitarsu tsakar gidan ya k'ara hargitsewa kowa da abinda yake fada k'arshe dai har dambe ya kusa kaurewa jin shigowar baba Sa'adu yasa su watsewa domin sun san halinshi bashi da wasa kaf gidan tsoron shi suke...

RAYUWARMU A YAU 

 

NA 

 

©CHUCHUNGAYE

JAM33LERH 

 

®NAGARTA WRITERS ASSOCIATION ?? 

 

{4} 

 

Da sanyin safiya mutanen gidan kowa ka gani harkokinsa yake masu had'a abin kari nayi, masu hira nayi, gefe kuma yarane maza da mata da basu wuce shekara 6-7 ba suke ta guje gujensu gefe kuma k'ark'ashin bishiya matasan 'yan mata ne ke yar carafke da duwatsu. 

 

Baba Amadu ya shigo gidan da sallama yana rik'e da buta ya zauna a wani dakali dake gefe a tsakar gidan yana k'are masu kallo sai hayaniya suke inda kasan gidan biki kamar ba zai yi magana ba can dai yace "wai yau duk ba mai zuwa makaranta ne kun cika gida da surutu?",duk cikin yaran ba wanda ya tanka har yan mazan dake kaiwa da komowa. Sai matarsa Mairo ce tace "ka manta an koro su ne? Yace "af haka akayi,har yanzu baki dumama tuwon bane?" wani kallo ta sakar masa ta k'ara gaba,ya bita da kallo sannan ya maida idonshi wurin Hajara dake tsefa ma diyar ta kai yace "Hajara yunwa fa nakeji",ita ma ta masa shiru. Inna Habiba da ba ita ya tambaya ba tace "kaji Malam da wani zance ka kawo abincin ne da har kake tambaya yaushe rabonka da bamu abinci ga mu nan sai hamma muke mun rasa na kaiwa bakin salati".. 

 

Share zancen nata yayi ya kwala ma Anas dake wanki kira (d'an baba Muntak'a ne) Anas ya dago ba tare da ya amsa ba,baba Amadu yace" Anas zo mana". 

 

Daga duk'en Anas yace "baba gaskiya ni wanki nake kuma kana ganin yanda nake sauri-sauri in gama don inada wurin zuwa", baba Amadu yayi shiru don ya san a rina yace "Habiba ina Ayuba ne? Inna Habiba ta tabe baki tace" ni ina nasan inda yake inaga yau ba a gida ya kwana ba in aike za kayi ga yara nan dake wasa".. Acikin su ya kira wani yaron ya mik'a masa kudi yace "ga wata ashirin nan ka sayo min koko maza kaji" yaron ya karba ya fita yana gunguni. 

 

Ko da aka sayo masa kokon iyalinsa suna kallo ya shanye tas k'ananan cikinsu suka zagaye shi kowanne yana "baba zan sha", amma yayi biris dasu ya gama sha ya karkade babbar rigarshi ya fita.

 

Nan fa yara suka dasa kuka don tun wayewar garin ba abinda suka sa ma bakinsu hatta ruwa tsada yake saboda rashin na famfo sai sun siya, rijiyar gida kuwa daga damina sai damina suke samun ruwa... 

 

Haka dai suka gaji da kukan suka cigaba da wasanninsu har dai wajejen misalin 11 na safe matar baba Sa'adu ta fito da sauran tuwo zata zubar inna amarya tayi maza ta tare ta tace "yauwa Asiya dan Allah ki bamu idan zubarwa zakiyi" Asiya ta kalleta a sheke tace "ban gane in baki ba to mijina bai bani izini ba meya hana mugun mijin naku ciyar daku?" Inna amarya ta fara rokonta gami da hadata da Allah sannan da kyar ta yarda ta dangwara mata kwanon a jikinta tayi wucewarta. Aifa yaran suna ganin abincin da rige-rige suka fada ma abincin manyansu su ma suka taso a guje harda 'yan matan haka dai da fad'a suka gama ci. 

 

Iyayen na gefe kowacce kofar dakinta kace-kace ba tsafta hatta tsakar gidan sai yayi sati basu share ba don duk cikar su kowacce bazata sanya danta yayi ba. 

 

Hiransu kawai suke harda yaransu suna fad'a 'ya'yan na tsoma baki a haka har lokacin tafiyarsu talla yayi babu zancen sallah bare wanka suka sunkuci bokitansu suka fita. 

 

A zaure Saddik'a taja tunga tace "Salima ki tafi kawai zanzo in sameki". Salima tace "me zakiyi?" Tace "ke dai ki tafi nace zanzo", tana ganin tafiyar Salima ta fad'a wani d'aki dake zauren. 

 

Yana kwance a kasa kan yagaggiyar ledar dake dakin yana jin muryarta ya tashi da sauri yana murmushi irin na 'yan duniya "kin barni inata jira inace kun wuce ne" tace "tabdi yaushe zan tafi yunwa fa nike ji dolema inzo ko na samu nacin alale a hanya". 

 

Ya washe hak'ora tare da janyota jikinshi yana mutsittsikata yana dan nishi sun shagala sosai suka ji murya ana k'wala masa kira. "Anas kana ciki ne?" a tsorace ya saketa ya tashi ya fita ya isko baba Muntak'a yace "baba ina ciki ai barci ne ke neman dauke ni" ya fad'i yana murza ido. 

 

Baban yace "to ai sai ka tashi ka fita don nayi bak'o zan masa addu'a", a take jikinshi ya dauki rawa cikin in ina yace baba yanzu zaku shigo ne?" Yace "eh bari inje in kirashi ina ce d'akin a kulle yake ne ai", yana fadin haka ya juya ya fita Saddik'a najin komawarshi ta fita da saurin ta, tace "yaya bani kud'in in wuce dan Allah", ya shafa gemu yana lalubar aljihu yace "kije anjima zan baki idan kun dawo". 

 

Ta marairaice kamar zatayi kuka tana rokonshi har baban da bak'on suka samesu baba yace "wani kud'i ne kike magana ya baki bashinki yaci halan?" Da sauri tace " eh baba" jikinta ya dauki rawa. 

 

Baba Muntaka ya soma yi ma Anas fad'a ya bata kud'inta yace "baba nace zan bata in suka dawo yanzu bani dashi" . Bak'on ganin za'a bata masa lokaci ya zaro gudar dubu d'aya ya mik'a mata da hanzarinta ta fisge ta k'ara gaba babu godiya. 

 

Anas ya bita a baya "malama ki kawo kud'in nan mu raba a sanadiyyata kika same su", ta k'ara kalmashe kud'in a lalitarta tare da daga k'afa tana zuba sauri. Ya bita da sauri yana k'ok'arin janyota a haka hannunshi ya kai k'irjinta ta saki dariya tare da juyowa tace "yaya ga kango can ka ga dama bamu gama ba" ta kama hanyar kangon ya bita a baya...

RAYUWAR MU A YAU 

 

 

©JAM33LERH 

CHUCHUNGAYE 

 

®NWA

 

 

 

{5}

Dan kango Saddik'a da Anas suka shige sai da ya gama lalu6e ta, sannan ya tafi ita kuma ta wuce wajen tallar ta.. 

 

A lokacinne ta tuna da Salima, ta duba hanya bata ga Salimar ba, ta dauki bokitin doya da k'wan tata tayi gaba.. Tana tsakar tafiya ta ji an ce "keeee".. A tsorace ta waigo, sannan ta fad'ad'a fara'arta tace" har ka ban tsoro Kabiru".. Murmushi yayi tare da kanne ido irin na gogaggun 'yan bariki yace "kwana biyu mun bar had'uwa ina ta kewar ki", tace "nima na yi kewar ka".. Yace" da gaske bebi?", ta ware idanunta tare da yin fari da su.. Yace "biyo ni muje kiga gyaran da nayi ma dakina".. Tace" kaga Kabiru talla na fito ka bari gobe zan biyo in gani har kallo sai ka kunna mani".. Yace "muje zan biya kudin doyar nawa ne?", tace "dubu d'aya da d'ari uku ne", yace "ba matsala mu je".. A tare suka isa har shagon Kabiru, yace" yi sauri ki shiga kada wani ya hango ki".. Tana shiga ya duba ya ga ba kowa sannan shi ma ya fad'a ciki ya sa sakata.. 

Ya zauna kusa da Saddik'a yana murmushi tare da rik'e hannunta yana murza yatsunta.. Tayi saurin janyewa tace "ba ni kudina tukunna", yasa hannu cikin aljihun wandon shi ya zaro duba d'aya da d'ari biyar (N1,500)ya mik'a ma ta, sannu a hankali har ya kai su ga tanbada ba kunya ba tsoron Allah... 

 

************************************

Zaune suke a d'aki suna magana su biyu, Inna Amarya tace "Salima ki taimake ni ki rufa man asiri ki auri wannan bawan Allah tun da dai yana son ki, in samu in kauda ke kina ganin dai irin rayuwar da muke ciki mahaifin ku ba ruwan shi da cin mu kowa tashi ta fishshe shi, dan haka tun da dai yaron nan na da abin hannun shi shikenan kakar mu ta yanke sak'a kema kin huta, matarshi karta tsorata ki ita d'in banza".. Sa'a ta murmusa tace " har da 'ya' ya fa gareshi, gashi jibgege yayi 3 na bak'ik'irin dashi ragowar samudawa", " ke shashasha ina ruwanki da wad'an nan yarinya indai zaki samu wurin da zaki huta nima in huta ai magana ta k'are duk ki kauda wannan a ranki, ko kinfi so ki k'ara fad'awa gidan laka na sawa baka ya gagareki? Meye amfanin haka kin tashi a wahalce ki k'are rayuwar a wahalce ". Tace "toh shikenan Inna", ta washe baki tace "yauwa Salima".. 

 

Tun da Isiyaku ya aiko gidan su Salima maganar aure, babu bincike babu komi aka ba Isiyaku Salima . Aka saka ranar biki wata biyu kacal. 

Hakan ya tad'a ma Inna amarya hankali ganin Salima zata yi aure ta bar Saddik'a.. Ba arzik'i Saddik'a ta fiddo wani saurayin ta kabiru kurtun soja .. Haka iyaye mata suka soma tara dan abinda zasu kai ya'yan su gidan miji. Wanda al'adar gidan ce iyaye maza ba abinda ya shalle su da hak'k'in matan su da ya'yan su sun sakar ma mata ragamar gidan gabadaya shiyasa tarbiyya tayi ma su karanci.. 

 

********************

Dare ne ya tsala kowanne dan Adam na kwance a makwancin sa domin hutawa kamar yadda aka ce "dare mahutar bawa".. Duk wani mutumin kirki na kwance, inda shaid'anun aljanu da mutane ke karakaina wajen yad'a fasadi a doron k'asa.. 

Hakan ne ta kasance ga ahalin gidan su Salima.. Sad'af! Sad'af!! Sad'af!!! Ya shige dakin, cikin rad'a tayi magana ta ce "ba dai ka had'u da kowa ba?". Ya ce "babu kowa". Tashi ta yi ta nufi bakin k'ofar d'akin ta sa sakata..

Ta ce "Muntaka taho muyi abinda za mu yi kafin asuba ta yi 'yan sa ido su zo".. Yayi murmushi ya ce " ai dole na, dan wajen ki kadai ni ke samun kwanciyar hankali Hajara".. 

Sai gab da asuba ya bar d'akin tare da mik'a ma Inna amarya naira d'ari biyar.. Hakan ya fad'ad'a fara'arta tana murnar 'yan canji da ta samu.

‬: RAYUWAR MU A YAU 

 

©JAM33LERH 

CHUCHUNGAYE 

 

®NWA?? 

 

{6}

Haka rayuwar gidan su Salima ta ke tafiya kamar rayuwar dabbobi, babu tayi ma su katutu ta yi ma su dabaibayi hakan yasa sam babu Allah a gaban su burin su samu abin saka ma bakin salati, Idanun su a rufe suke in dai magana ce ta kudi babu abinda ba za su iya yi ba.

Bikin Saddiqa da Salima ya zo, iyayen su na ta tara taro da kobo dan ganin sun tara abinda za su fita kunyar ya'yan su. Gabadaya hankalin Saddiqa a tashe yake tunanin in da za ta samu kudi ita ma ta yi irin siyayyar da akai ma Salima, sai yawo da 'yan tukwanen da kulolin da Salima ta siyo ake a d'akunan gidan.. 

Wajajen Isha'i Saddiqa ta fakaici idanun jama'ar gidan da ke ta safa da marwa,sad'af ta shige dakin baban su (baba Amadu), kayan sawar shi ta ke ta bincikewa cikin aljihan rigunan da wanduna har ta ji hannun ta ya damk'o kudi, tsab ta k'ilga kudin sun tasar ma dubu shida (N6,000). Murmushin jin dadi ta yi tuno yanda amarya ke ta ma baban su magiya akan ya bada kudin kalaci ya ce

"kwandala baya maganin ta", Saddiqa ta cusa kudin a rigar mama ta lalla6a ta fita ba tare da wani ya gan ta ba. 

 

Malam Amadu ya shigo gidan hannun shi rike da leda ya shige d'akin shi ya zauna kan tabarma ya bude ledar,tsire ne k'ullin guda ya cinye su tas, ya bude randar ruwa yasha yayi k'at. Hannu ya saka cikin aljihun rigar shi ya ji wayam ya hau zazzage kayan shi ba amo ba labari. 

Ya fito tsakar gidan ya ce

"Mutanen gidan nan ku zo nan dan uban ku, uban wa ya daukar man kudi cikin kayana?"

Mutanen gidan su ka hau cece-kuce, Inna ta rangad'a guda ta ce "Allah ne ya toni asirin ka", Inna amarya ta ca6e tace "kowa ya dauki kudin nan sun mani dai-dai dama wanda beyi sharar masallaci ba zayyi ta kasuwa".. 

Bak'in ciki ya addabi Mal. Amadu amma saboda tijarar jama'ar gidan haka ya hak'ura.. 

 

Salima ta shiga d'akinsu da sauri tana jawo kaya cikin kullin kayansu da ke cunkushe wuri d'aya banda wari babu abinda ke tashi wurin. Ta yatsina fuska 

"Su fa shegun yaran nan k'azanta tayi masu yawa al'qur'an, inna kinji wani hamami wurin nan ga daud'ar tsiya"

Innar ta dake tsince shinkafa tace "au don zaki auri me kudi har kin fara k'yamar kannenki, kema ai har yanzu cikinsu kike don tunda bikin nan ya kusa ina lura dake saidai kiyi kwaskwarima ki fita dama kuma ba damuwa da wankan kika yi ba har kina da bakin zagin wasu". 

Bata ce komai ba ta cigaba da bincika kayan da bisa ga alama basa samun wanki saidai a cire a mayar wurin. 

 

Innar tace " yauwa Salima kinga bikin nan k'ara matsowa yake ko abincin da 'yan biki zasuci ban tanada ba bare kayan da ni da k' annenki zamusa muci biki, dan Allah ki kawo wani abu cikin kud'in da Alhajinki ya baki in samu in toshe wata kafar". 

Wani irin zagi ta sakar ma uwar tace "nifa Inna na lura tunda na shigo da kud'in nan ki ke masu wani gani gani, saboda haka ne ma na kai a boye min don nasan hali, ba k'aramin abu bane a gidan nan in nema in rasa kuma ba yanda na iya saidai inyi Allah ya isa" 

Innar ta aje shinkafar da take gyarawa ta tausasa murya "Haba mai k'ashin arziki duk ina zaki kai dubu 30 a hidimar biki, shi ma dama yasan bamu da shi shi yasa kika ga ya baki da auki saboda muna ki sammana ki rufa min asiri kar in tozarta ki bani ko dubu 10 ne". 

Wani ashar din ta kuma saki ta ma uwar kallon raini mai nufin baki ma da hankali ta ce "lallai ma Inna had'amarki tayi yawa, to wallahi kwandala bazan baki ba nima ba isata zasuyi ba, ba naga kin shiga adashi ba kedai kisan yanda zakiyi amma kima daina hangen wad'annan kudaden". Ta janyo wani hijab da ya sha gwagwarmayar duniya duk daud'a jikinsa ta saka ta fice tana k'unk'uni tana fad'in

"Yanzu ma da kika ga ina saurin nan kasuwa zani ban gama siyayya ba".

Ta bar uwar da baki a sake ta marairaice fuska tana kallonta.

 

RAYUWARMU A YAU

 

©CHUCHUNGAYE

® NWA

 

JAM33LERH

 

{7}

********************

Rana ba ta k'arya..... Hakan ta faru ga Saddiqa da Salima ya'ya ga Mal. Amadu an daura ma su aure.. An daura auran Saddiqa da Kabiru, Salima da Isiyaku... 

 

Babu wasu jama'a wadanda za'a nuna ace dangin mazajen su Salima ne, sai wadanda suka zo a matsayin waliyan su. Ba laifi iyayen su mata sun dan had'a ma su iya abinda za su iya. 

Da dare aka kai kowacce gidan mijin ta. Aka bar su daga su sai halayen su.

 

Kwanaki sun zama satittika, satittika sun zama watannin.. 

 

GIDAN SADDIQA

Duk'e ta ke tana tankad'e, tafiya ta ji ta waigo ta ce "sannu da zuwa", be ko kalli in da ta ke ba, ya shige daki.. Can ta ji ya kwala ma ta kira ya ce "Saddiqa ina abinci na?", jikinta na kyarma ta fad'o d'akin ta ce "kayi hak'uri ka san fa ba ka bar komi ba ka fita sai da aka kawo wanki na samu na siyo garin masara". Ba ta ida magana ba ya kwashe ta da mari ya ce "kar ki fad'i man maganar banza, sakaryar banza wadda tayi gadon tsiya ki fad'i man sau nawa uban ki ya ajiye hatsin abinci tun da ki ka taso sai ni da ki ka raina ma wayau".. Shiru ta yi ya gama sababin shi ya fita gidan.. 

Ladidi ta fito ta lek'o d'akin (makwabciyar Saddiqa ce da yake gidan haya su ke zaune), ta ce "Saddiqa har yanzu baki da wayau ki zauna Kabiru na zagin ki da iyayenki ke ba wa ta tsiya ya ke tsinana ma ki ba". Saddiqa ta ce "auren shine rufin asiri na".. Nan Ladidi ta bude kwanon dambu ta ce " ina kwarya". Cikin sauri kamar an hankad'o ta, ta zauna kan tabarmar su ka ci dambun da Ladidi ta kawo..

 

RAYUWARMU A YAU 

 

©CHUCHUNGAYE 

JAM33LERH 

 

®NWA

 

{8}

Tana zaune a d'aki ta had'a tagumi hannu bibbiyu cikin duhu tana jiran dawowar mijinta Kabiru . Tun fitarshi da safe bai sake waiwayo gida ba bare ya kawo mata abinda zata sanya ma bakinta, ga cikinta dake ta faman k'ugin yunwa. 

 

Lokaci lokaci takan saki sautin tsaki, gashi ba waya ko agogo bare ta duba lokaci.

K'ok'ari take tayi barci kar ya rinjayeta, amma duhu da tsit d'in da wurin yayi ga rashin abinyi tana zaune wuri d'aya na dad'a sanya mata kasala. 

 

A hakan yanda yake mata dawowar dare idan yazo yaga duhu sai ya ritsata da fad'a wai mugunta ce ta hanata kunna kyandir nan kuwa ko naira biyar bata magani. 

'Dan kishingid'a tayi gefen gadon katakon da aka siya mata a kamacha da yar yaloluwar katifa. Kamar jira take tuni barci yayi awon gaba da ita. 

Tayi nisa cikin mafarkin wani na binta yana tangad'i tana ja da baya har ya samu nasarar fad'owa jikinta ta matsa ya fad'i gefe. A zahiri kuma sai taji kamar fad'uwar abu, a firgice ta farka kunnenta ya kwaso mata nishin mutum a gefenta. Ta fara lalube har hannuta ta isa ga jikinsa sai akayi sa'a ta dora daidai aljihunsa inda wayarsa take.

Ta dauko ta danna haske ya bayyana ta haska fuskarsa tayi tozali da mijinta cikin mummunan yanayi rabin jikinsa a gado rabi a kasa. 

 

Bata san lkcn da kuka ya subuce mata ba ta d'ora kanta jikin gadon tana rerawa. Cikin mayen ya d'aga k'afa tare da 'yan surutai yaja jikinshi k'afarshi ta sauka a gadon bayanta. Ta dauki kafar ta maka jikin gadon duk bai ma san tana yi ba.

RAYUWARMU A YAU 

 

©CHUCHUNGAYE 

®NWA

 

JAM33LERH 

 

{9-10}

Tun safe da ta tashi ta ke hamma, cikinta na kiran ciroma. Ta kai kallonta ga mijinta Kabiru da tun jiya da ya shigo da dare ya kwanta be tashi ba. 

Tsaki ta ja ta fito daga d'akin, k'amshi ta ke ji yana tashi a gidan na su. Nan take cikinta ya bada wata irin k'ara "k'ululu", wanda idan mutum na cikin ma su kyakkyawan ji kunnuwanshi za su jiyo ma shi. 

Ladidi ta hango a bakin k'ofar d'akinta zaune da risho (kerosene stove) ta na soya wainar kwai a cikin kasko (frying pan). Ta had'iyi yawu, ta ce "yau kuma Ladidi d'ad'i ake son ci". 

Ladidi ta galla ma ta harara dan i zuwa yanzu ta gaji da halin rok'o na Saddiqa. Kujera ta jawo 'yar tsugunne ta zauna ta na washe yaleyen hak'o ranta da su ka jima ba su ga man goge baki ba, tun na cikin lefenta da ya k'are Kabiru be sake siyen wa ni ba.

Haushi ya kama Ladidi ta ce "wai ke Saddiqa haka za ki ta zama da k'azanta a jikin ki, ko ni dai da miji na ke d'ad'ewa be zo ba ina gyara jikina". 

Saddiqa ta ce "Uhmmm to ina naga sabulun wankan ma, ai wallahi da inma Kabiru kwalliya gara in zauna haka". Ladidi ta ce "tab ki na fama da daud'a kam bare yanzu da ake zafin nan". 

Saddiqa ta ce "Ni dai ki taimaka ki sammani abinda ki ka dafa ko yaya ne wallahi yunwa ni ke ji". Haka Ladidi ta gutsuro biredi da kwai ta mik'a ma Saddiqa ta had'a ma ta da ruwan shayi. Cikin d'an k'ank'anin lokaci ta shanye tas harda sud'e sauran da su ka mak'ale jikin kofin kamar tsohuwar mayya. Ta na gama sha ta fad'a d'akin, sannan sha d'aya saura, ta bubbuga k'afar Kabiru ya fara mitstsika ido ya na fad'in "har asuba ta yi?",ba ta tanka ma shi ba, har sai da ya bud'e idanunshi ya hango hasken rana da ya shigo d'akin. 

Saddiqa ta ce" an dai ji kunya ace mutum tun baccin jiya sai yanzu zai tashi ba sallah ba salati". Kabiru ya ce "ai gara ni yanzu na tashi wa ta kuwa tashin wurinta be tsinana ma ta komi ba d'an ita ma ba sallar ta ke ba". 

Murguda baki ta yi ta ce "ai sai ka tashi ka nemo mana abinda za mu ci, tunda gara ta ta k'are baka sake kawo abinci gidan nan ba". Ya ce "ashe ma jira ki ke in kawo ma ki abinci, yanda uwar ki ke neman na sakama bakin salati ke ma ki nema tunda ubanki be ajiye a gidanku ba". 

Kuka ta rushe da shi ta hau zagin shi uwa da uba, wani wawan mari ya kwasa ma ta ya yi kwallo da ita ya fita ya bar gidan. 

 

GIDAN SALIMA 

Da gudu ta fito daga d'akinta amai ta ke shek'awa ba k'ak'k'autawa, har sai da ta gama amayar da komi na cikinta, ta yi zaune dabar ta nna maida numfashi. 

Fitowarshi daga d'akin kenan ya bita da harara, ta yi azamar tashi ta na layi kamar mashayiya ta ce "Isyaku za ka fita ba ka bani kud'in da za ni asibitin ba". 

Ya ce "da yake ubanki ya bani ajiya ba, kud'i na ki ka ga ni iyayenki su ka tilasta dole in aure ki dan haka duk kud'in da na kashe ma ki sai kin yi aman su". Hawaye su ka zubo ma ta, ta ce "Allah ya isa tsakani na da kai banza azzalumi kawai kana fama da muni", be ce da ita kanzil ba ya ja dattin k'afafuwanshi ya bar gidan, wanda ta san sai ya dau sati be dawo ba. 

Takaicinta d'aya tunda su ka yi aure ba ta taba ganin wasu dangin shi ba, babban bak'in cikinta yana da mata d'aya da yara a yanda ya fad'i ma ta ba ta san in da su ke ba. 

Haka ta shi tabar aman a wajen ba tare da ta gyara ba, ta fad'a d'akinta ta kwanta. 

Nan muka bi gidan da kallo, d'aki d'aya ne ciki da falo, sai makewayi . Cikin d'akin ko cili (ceiling) ba be sai ledar biskit da aka rufe saman saboda zafin rana. Bango kuwa babu pilasta, k'asan kuwa gurji-gurjin zagaryar siminti ne da aka ahad'a da yashi. 

Kwata (gutter) ce a tsakar gidan da ke wari saboda kazanta na matar gidan. 

 

Ta gama sak'a da warwara abinda zata yi dan taci abinci. Ta mik'e da hanzari ta bud'e akwatin ta ta dauko atamfofi biyu ruba-ruba da wakas cikin kayan lefenta. Ta suri hijabinta da ya yi dik'i-d'ik'i ta rufe gidan da kuba ta k'ara ma bujenta iska. 

Wajen ma su kayan koli ta nufa ta sayar da kayan aka ba ta dubu d'aya da dari biyar (N1,500), ta sak'e abinta a cikin rigar mama tayi. 

 

Da wannan kud'in ta ke sayen abinci irin su dambu, d'an wake, alale suma sau d'aya a rana sai ta d'addaki ruwa ta kwanta. Haka ta ke rayuwa hannu baka hannu kwarya. Sam mijinta be san cinta ba, bare shanta.

 

RAYUWARMU A YAU

 

© CHUCHUNGAYE

JAM33LERH

 

® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

 

{11}

GIDAN SADDIK'A

Da hargowa ta shigo gidan ta isko Ladidi dake zaune a tsakar gidan tare da yaranta suna shan iska. Ladidi tace "ke dawa haka nake ta jin surutai?" 

Ta cire daud'ataccen hijab dinta ta cukwuikuye shi ta aje a kasa bisa siminti ta zauna kanshi, tace "wallahi maman Sani ce zata wuce na tsaya muke hira, nace ma ta kwana biyu ta k'aurace mana in don wannan maganarce ai ta wuce a wurinki ko?". 

Ladidi ta basar da zancen ta hanyar sunkutar buta ta shige bayi. Ganin haka itama Saddik'a ta tashi tana soshe-soshe ta shige dakinta. Turus ta tsaya tana masa wani kallo yana daga kwance tsakar d'aki ta yatsina fuska "me nake gani haka? Me kakeyi a gida?", idonshi a lumshe yace "zazzabi nake ji ta sani dawowa dole". Ya ja dogon numfashi ya cigaba da cewa "daga ina kike?". 

Ta zauna dabas a kasa tace "makwafta na shiga hira zaman gidan ya isheni". Yayi murmushi kawai tare da fad'in "Allah ya kyauta". Ta fara kici kicin cire riga dake warin rana ta ja zanin ta d'aure a k'irjinta sannan ta cire brassiere duk ta watsar a tsakar d'akin. 

Daga inda take zaune ta zura masa ido sai faman rawar d'ari yake a ranta tace "lallai ba k'aramin ciwo ne ba, mutumin da ke k'osawa gari ya waye ya bar gida" ta tab'e baki. Ta cigaba da kallonsa can ta ce "ni fa gidan Salima nake son zuwa gobe ance batada lafiya, nasan ka da sammako sai ka fice ban sani ba don haka ka bani kudin mota tun yanzu".

Biris yayi da ita ya k'ara jan zani ya rufe jikinshi da bai bar rawa ba tace "da kai fa nake ka min shiru, ba sai goben kace min baka da kud'i ba ahtoh don ba yarda zanyi ba" . 

Shidai bai ce mata komai ba yana fama da kanshi, ita kad'ai tayi ta bambaminta har ta gaji tayi shiru.

: RAYUWARMU A YAU 

 

© CHUCHUNGAYE 

® NWA

 

JAM33LERH 

 

{12} 

 

Washegari tun da sassafe ta tashi tayi ayyukan da zatayi, Ta je rijiya ta d'ebo ruwa ta zauna bakin k'ofarta da soso da sabulu tayi kwaskwarima ta koma d'aki tayi shafa. Ta mik'a hannu saman gadonsu da nufin d'aukar bra d'inta wacce tsabar kazanta baka bambance kalarta anan hannunta ya shafi jikin Kabiru dake kwance da sauri ta janye hannunta ta ce "wai wai wai me nakeji haka kamar garwashi ka ji jikinka kuwa tabdi". 

Ta tab'e baki ta koma cikin kabet dinta ta d'auko wata jar atampha ta saka, ita kad'ai ta rage mata sabuwa cikin k'irgaggun kayan lefen. 

Ta koma gefen gadon daidai saitin kanshi tana fad'in "Kabiru! Kabiru!! Ta bubbugashi "Kabiru!!! Magana fa nake kuma nasan idon ka biyu, to na shirya zan tafi ka bani kud'in hawa". 

Da k'yar ya bud'e idanunshi da suka rine zuwa ja ya k'are mata kallo duk ta cab'e fuska da kwalliya a hankali yace "ke wace irin jaka ce? baki ganin halin da nake ciki ne? Inace jiya kina jina yanda nake ta juyi cikin rad'ad'in ciwo, sannu bata had'ani da ke ba, shine kuma don rashin sanin ciwon kai kike tambaya ta kud'in abin hawa, to ko na abin zama bani da shi wawiya kawai sokuwa". 

Ta harareshi "ai dama nasan ba ciwo kake ba langab'ewa kawai kayi don kar ince ka bani abinci, munafiki to wallahi ko baka bani kud'in ba sai na tafi, tun da akayi aurenmu na tab'a zuwa gidanta ne?". Ta janyo hijabi cikin shirgin kayanta da bata ninkewa ta saka ta kama hanyar fita tana sababi.

Ya girgiza kai yana mai takaici tare da fad'in "yarinya da ba ciwo nake ba da kin gane kurenki da kirana munafiki"

Tana fita ta fad'a d'akin ladidi babu ko sallama sukayi kicibis da mijinta yana zaune da singileti da gajeran wando. Ladidi ta daka mata tsawa, ba shiri ta koma da baya taja tunga a bakin k'ofa. Ganin alamun Ladidi bata da niyyar fitowa ya sa ta d'aga murya tace Ladidi dan Allah ki fito ina son magana da ke ne shiru ba amsa ta k'ara d'aga murya dan Allah kiyi sauri ba don halina ba nan ma wani shirun ya biyo baya sai da ta k'ara magana sannan daga ciki Ladidi ta ce "meye Saddik'a?", tace " dan darajar iyayenki kud'i zaki aramin kafin anjima ko a wurin baban Umma in zan samu ba don halina ba". 

Ladidi zatayi magana mijin ya dakatar da ita ya d'aga filo ya ciro kud'i ya bata tare da fad'in "je ki kai mata in ba haka ba bazata barmu sukuni ba da nacin tsiya, karki ce komai" . Haka nan ta tashi ba don ranta yaso ba taje ta watsama Saddik'a ta juya, ita bata ma damu ba ta kwasa da murnarta ta fice daga gidan.

 

chuchungaye.wordpress.com

 

RAYUWARMU A YAU 

 

©JAM33LERH

CHUCHUNGAYE 

 

® NWA 

 

{13 }

 

Da kwatance da tambaya ta isa gidan Salima dake Anguwan iya . Ta shiga da fara'arta tana k'wala mata kira Salimar ta fito daga kicin tana amsawa da k'yar tace "Saddik'a ce yau gidan". 

Saddik'a ta washe baki "ai kuwa sai yau Allah yayi, ina ne d'akin? Ta fad'a tana k'are ma gidan kallo sannan ta bi inda taga Salima ta shiga. 

Ta zauna bisa kujerun falon tana yaba d'akin tace "naga kujerunki har sun fi nawa aminci, baki ga yanda nawa ya koma ba d'inkin duk ya fara warwarewa", ta cire hijab d'inta "wai gaskiya d'akin nan akwai ni'ima ba kamar gidanmu ba". Ta kai dubanta ga Salima wacce ta tsura ma tv ido kamar ba da ita take magana ba. 

Saddik'a tace "shegiya irin ke kin zama Hajiya din nan , to in zakiyi isar taki har damu ma na gida da muka san sirrin juna". Salima ta kalleta ta wutsiyar ido ita warin da ke fita jikinta ke damunta gaba daya d'akin ya d'auki d'oyi da k'yar take jan numfashi. Ta mik'e tsaye tare da fad'in "ya maigidan naki? Ta shiga cikin bedroom. 

Saddik'a tace "yana nan lafiya, can na baro shi kwance malalacin, ke ni ba wannan ba taimaka min da abinci naga kamar daga kicin kike". Ta saurara tana jiran taga Salima ta fito ko kuma ta amsa ta amma taji akasin haka. Tace "ko d'akin nada zurfi ne Salima! Kinji me nace? Ta tashi ta kutsa kai d'akin Salimar na zaune gefen gad'o, ta k'arasa ciki tana bin d'akin da kallo. Salima ta mik'e zumbur ta janyo hannunta zuwa falo tace "ke baki da hankali ne? Miji na fa na cikin band'aki yana wanka yanzu idan ya fito fa?. 

Saddik'a ta tab'e baki "sannu mai miji, ke ni naga fa tunda kika auri mai kud'i kika canza to wa zaki nuna ma arzik'i muma Allah ya bamu". Ta k'arasa magana a fusace. Salima ta murmusa kad'an tace "zo muje kicin d'in in baki abinci", Saddik'a ta b'ata rai "ni duk abinda za'a wulakanta ni ba sonshi nake ba, don ma na taimaka nazo gidanki". 

Salimar ta fita tana dariya take fadin "dama ai ba kiranki nayi ba". Minti kad'an bayan fitarta Saddik'a ta bi bayanta zuwa kicin d'in ta tarar da ita tana kwashe abincin a flask Salima ta d'an kalleta tayi murmushi ta d'auke kai. 

Saddik'a ta k'arasa ciki "yar iska dama kinsan d'an wake ne kika barni zanyi ma kaina bak'in ciki watso min shi nan kiga", ta d'auko plate a cikin kwando ta mik'a mata. Salima tace "ah ah ba kince kin fasa ci ba har ina murna abinci na ya k'ara auki". Cikin nuna k'osawa ta fara k'ok'arin tsunbula hannunta cikin flask d'in ta d'ebo d'anwaken da sauri Salima ta rik'e hannun "ah aha a ah me zan gani? ba dai k'azamtaccen hannun nan naki zaki saka min a abinci ba? kinga tsaya in zuba miki". Ta sanya serving spoon ta zuba mata ta karba tana tab'e baki "iyayi karyar banza danwaken ne za'a wani sa cokali tab, ni bani kiga" ta karb'e plate d'in ta zauna a k'asa anan kicin d'in ta tsoma hannunta ta kama ci. 

Salima tace "bazaki wanke hannun ba? Ni mijina idan yaga haka bazai ci ba don yanada tsantseni kar kiga kamar takura miki nake ni kaina har yau na kasa sabawa da wannan k'ak'alen banzan". Saddik'a kam bata tanka ta ba hankalinta naga abinci ci take hannu baka hannu kwarya tana nanik'e da plate d'in tamkar za'a kwace. Salima dai ta fita ta barta nan. 

 

{14}

 

Wuni tayi a gidan Salima har mijin ya fita ya barsu. Har dare bata da niyyar tafiya sai k'wak'ulo hira take Salimar kuwa daurewa kawai take tana amsa ta, duk ta k'osa ta tafi domin bata so mijin ya dawo Saddik'ar na nan bata so ta fahimci zaman da suke shiyasa ma ko gaisawa bata bari sunyi ba. Lokacin da ya fita Saddik'ar na kicin ko da ta fito saida ta mata mita.

Ta k'wak'ulo hammar k'arya tare da duban agogo "kai har k'arfe 9 ke ko Salima baki tsoron hanya ga dare mijinki ma ai ya'ce ko bazaki dawo bane". Saddik'a ta k'ara gyara zama "k'yale banzan wlh ni har banson tuna gidan nan mtswww, ke kam ai kinyi sa'a rayuwarki gaki cikin daula ga kwanciyar hankali uwa uba gidan kanku kuke". 

Salima tayi murmushi tana tuno yanda wani yazo d'azu yana masu tijara wai su tashi su bar masa gidansa, tana ma mijin tsiya Saddik'a ta shigo shiyasa ma yanzu duk ta k'osa ta tafi kafin ya dawo don yau za'ayi wacce za'ayi sai ya fad'a mata yanda akayi ya zama gidan wani". Tayi k'wafa tana girgiza kai. 

Saddik'a ta dube ta "lafiya kike kwafa ", tace "lafiya ba komai, kinga kizo ki tafi gaskiya ina ji maki tsoron hanya barinma yanda garin nan ya baci". Ta d'auko rigarta ta mik'a mata "ungo sa ko har yanzu zafin ne? Ta karba tana sakawa tace

"ai ni bana jure zafin nan har na saba a gida in daura zani abuna iska na shiga ta". 

Har k'ofar gida ta rakata sukayi sallama Saddik'a na rok'onta ta bata wani abu ta mik'a mata naira 100 tace ta hau mashin. Ta rufe gidanta ta koma ciki tana jiran mijinta. 

Bata dad'e zaune ba ya shigo gidan ko zama baiyi ba ta fara fad'in "maci amana munafiki dama jiranka nake so nake yau ka warware min wannan munafurcin dakake boye... Mari ya sauke mata lafiyayye. 

Idonta a warwaje take kallonshi ta hasken kyandir don batayi tsammanin marin ba. A fusace yace "kisan irin maganganun da zaki rik'a fad'a min wawiya kawai mara tarbiyya, ai ba tsoronki nake ba da zan kasa fad'a miki cewa nan gidan haya ne sbd haka gobe goben nan ki had'a kayanmu zan maida ke gidan da matata take dama d'akin ki ne ban gama gyarawa ba, da kuma matata da ban fad'a mata na k'ara aure ba, yanzu ma daga can nake sai da na lallab'a aba ta sannan na taho". Daga haka yayi shigewarshi d'aki ya barta tsaye tana huci. 

Maganganunsa sun mata bak'inciki ita da take murna a tunaninta k'arya yake da yace mata yanada mata tanace gwadata yake, taga har wata 6 da aurensu bata ga ko k'eyar wani nashi ba, shine yanzu zai ma had'a su har da fad'a mata yaje ya lallab'a matarshi. 

Wani abu yazo ya tokare mata a wuya tayi kukan kura ta fad'a d'akin ta cigaba da zazzaga masa rashin kunya.

 

chuchungaye.wordpress.com

 

RAYUWARMU A YAU 

 

©CHUCHUNGAYE 

®NWA 

 

JAM33LERH 

 

{15}

BABBAN GIDA 

'Yan matan gidan ne kwance a d'akin Gwaggo su na bacci hankalinsu kwance. Kamar daga sama Rakiya ta ji ana shafa k'afarta, za ta fasa ihu ta ji an toshe bakinta. Kokari ta ke ta ceci kanta saboda ba ta sa dogon wando ba amma ina, k' arfinta da na namiji ba d'aya ba. 

Ta na ji tana gani ya gama shafe ta, sannan ya fita. Wannan ba sabon abu bane dan idan da sabo sun saba da halayyar mazan gidan. Matuk'ar dare ya yi to fa haka za su ji ana shafar su, shiyasa su ke saka dogon wando a ciki. 

 

Gari ya yi haske tangararau amma ba alamar za'a dora tukunya a babban gida. Kowa harkar gabanshi ya ke.

Gwaggo ce ta kwad'a ma Babangida (dan Amarya) kira dake gara taya a tsakar gidan ta ce "Babangida zo ka siyo man koko da kosai na N50".

Da yake aikin abinci ne ba musu ya zo, ya amshi kud'in. Yana zuwa zaure Sabi'u (dan Inna amarya) ya kwace kud'in da ke hannun Babangida ya ruga. 

Da kukan shi Babangida ya shigo gidan, Gwaggo ta ce" ba dai har ka dawo ba?". 

Ya ce "ba Sabi'u ba ne ya kwace kud'in". 

Gwaggo ta rafka salati, buguzum-buguzum ta yi d'akin Inna Amarya ta ce "Mairo fito ki biyani kud'ina barawon d'anki ya ma Babangida fashi". 

Inna Amarya ba ta ko kalli Gwaggo ba, ta fito tsakar gida tana wak'ar ta.

Nan Gwaggo ta hau tijara, shigowar Baba Muntaka ya sa tayi shiru da ta ji yana tambayar ba'asi. Nan ya fiddo naira dari ya bata, ya shige d'akin matarshi.

Baba Amadu dake zaune kan tabarmar da ke k'ark'ashin bishiyar bedi, ya k'ad'a kai ya ta'be baki, duk abin nan yana kallo amma bai ce komai ba, ya bud'e ledar dake gabanshi ya hau cin biredi da kosai yana korawa da ruwan shayi . K'ananan yaran suka baibaye shi, amma ko kallonsu be yi ba. Sai da ya yi k'at. Ya kalle su ya ce "kowa yaje uwar shi ta ba shi abin karin kumallo". 

Ya kishingid'a yana sauraran radio sansanyar iskar bishiyar tana kad'a shi tare da sanya masa nishad'i. Inna Habi ta fito daga d'akinta ta zauna bisa wani dutse dake fuskantar mijin nata ta shiru da tagumi hannu biyu tana kokawa da kalmomin da ke cinta a rai can ta nisa tace "yanzu Malam abinda kake mana shine daidai a gareka ka wofintar da hakk'inmu na ciyarwa da ke wuyanka, ai inace inmu matanka bazaka ci damu ba yaranka tilas d'inka ne haba Malam ka rik'a tuna lahira".

Ya tashi daga kishingid'en ya zauna ya fuskance ta da kyau yace " to Abu kin idar ko in karyo miki icce ki shige ni?". Ta rik'e baki "Malam me ya kawo Gwoggo cikin zancen nan?" ta yunk'ura da nufin tashi "uhnn Allah ya baka hak'uri". 

Inna Amarya tace "ai kema Habi maganinki kenan kamar yau kika fara sanin wannan azzalumin? Ai inda sabo yaci ace mun saba da halayyarsa bare ke me shekaru ashirin da 'yan kai tare dashi, ai saidai muce Allah ya saka mana". Inna Habi ta zauna kusa da ita suka cigaba da maida maganar. Amarya ma daga d'akinta tana tayasu.

Ganin zancen nasu yak'i k'arewa ya daka musu tsawa "kai! ya ishe ku haka , kaji min makirai da tsakar rana ba kunya ba tsoron Allah a gabana kuna antayo min sharri! Irin haka ne in bak'o ya ji sai ya d'auka bana tsinana muku komai". Inna Amarya ta bud'e baki da niyyar magana amma kafin nata ya fito nashi ya riga nata 

"Inace yau kusan wata 6 kenan da aurar da tsinannun yaran nan amma babu figaggiyar da ta tako k'afarta gidan nan , ah ah kar kice komai ina lissafe sarai , su basuzo ba bare mazajensu har insa ran su kawo min ihisani sai dai ku a k'ullo a kawo muku, ko kunace bana hankalta da shige da ficen da ya k'aru a d'akunanku?" ya jawo takalmanshi ya hankad'asu gaba sannan ya saka ya mik'e yana fad'in

"Don haka na daina wahalar banza, kud'ina sun huta babu mai k'ara cin sisina, ba wayau kuka fini ba ai" ya kad'a kanshi ya fita .

Inna Amarya ta bishi da fad'in "karka k'ara tsine ma yaranmu ehe, munji basu baka d'inba azzalumi kawai."

 

chuchungaye.wordpress.com

 

RAYUWARMU A YAU

 

©

CHUCHUNGAYE 

®NWA

&

JAM33LERH

 

{16}

 

Bayan kwanaki da wannan, aka samu k'aruwar 'ya'ya biyu a babban gida. Haihuwar da tazo da hatsaniya da tsegunguma duk da haife haife ba sabon abu bane a gidan, don basu yayewa suke d'aukar wani cikin. Wannan karon Hajara (matar Amadu) da uwargidan Baba sa'adu ne suka haifi 'yan maza tserar su kwana d'aya. 

Tsegumin kuwa akan jaririn da Hajara ta haifa ne yaron da yazo da bak'uwar halitta da basu saba gani ba. Sabanin munanan bak'ak'en yaran da Amarya ta saba haifa shi wannan sai Allah ya albarkaceta da kyakkyawa, babu ta inda yaron ya d'auko kamannin uwar ko uban. Abinda yafi tsayama mutane kuwa haihuwarsa da akayi da hak'ori hakan ya janyo cece kuce a gidan da waje. 

Mutane har a gaban mejegon fad'i suke " wannan karon dai Hajara tayi farar haihuwa jiba yaro tubarkallah ke ni duk gidan nan ai yaran Malam Amadu ne munana inaga wannan kamannin a dangi ya samo, ko ya biyo Mumtak'a shi da ake cewa kamar balarabe don kamannin sak har yaso finshi ma. 

Wata dake tare da mai maganar tace "ke ta kamanni ma kike, jaririnfa da hak'ori yazo ". Matar ta fiddo ido dà fargaba "ke don Allah wani irin hakori kamar a tatsuniya ".

Mai bada labarin ta bud'a bakin yaron don ta tabbatar mata sai ga hakora biyu a kasa. Nan sukayi ta alhinin abin. Hajara na daga uward'aka tana jiyo su ba damar magana. Domin ita kanta abin ya dameta harta Gwoggo surukarsu sai da tayi mata gori tace "ko dai mugun abu kike aikatawa Allah ya aiko miki ishara?. Inda ta sami sassauci ma da Malam d'in ya fad'a mata wannan ayar Allah ne karta damu.

Da ranar suna ta zagayo su Salima suka dira a gidan zuwansu na farko tun aurensu. Babu wani d'oki ko zumud'in zuwa gida a fuskokinsu irin na sauran amare. 'Dakunan iyayensu suka shige sai mutane ke biyo d'akin su gansu . D'akin Inna Habi mahaifiyar Salima nan akafi tururu domin tunanin da sukeyi na tana auren mai kud'i watak'ila tayi musu kyauta. Ita kuwa tana zaune ta mimmik'e k'afa tana yatsina fuska Innar nata kaiwa da kawowa tana k'ok'arin sa ma mata abinci, sauran mutanen da ke fadanci sai rawar jikin tambayarta mai zataci sukeyi.

Ana haka Saddik'a ta shiga d'akin tashe da cikinta da ya soma fitowa . Kallo d'aya zaka mata ka fahimci rashin wadata da kwanciyar hankali a tattare da ita . Tana shiga ta washe baki Hajiya Salima ai tuni nake taso in shigo mu gaisa Inna ta tsareni da surutu ta nema ma kanta wurin zama a kusa da Salimar yayind'àa ita kuma ta 'bata fuska had'e da kauda kai tace "da kin bari kun gama gaisawa ai".

Saddik'a tace "d'okin ganinki ina zai barni, ai ke kam hira zamu kwana yi" . Salima ta zaro ido "kwana! A ina? A wannan gidan? Tabdi ai gida na zan koma sai kace daga wani gari na zo".

Mutanen dake d'akin sukace "kaji Saddik'a da shirme ita da ta saba kwana a bulo da bulo na'ura na hura ta , gidan nan ai sai mu bari mu, baku wuri ku zanta". Daga nan duk suka watse .

Kamar jira take su fita ta fisgo kwanon da kannenta ke cin abinci ta fara zura loma nan yaran suka hau ihu da koke koke . Inna ta fito daga uward'aki tana tambayar "lafiya, meya faru?" gaba daya yaran suka had'a baki wurin fad'a mata "Salima ce ta kwace mana abinci".

Inna ta kalle ta "haba Salima ya haka? nan fa kikaji ina tambayarki me zakici ki bada kud'i a sayo miki, don nasan ynx ba zaki iya cin shinkafar hausa ba, kuma ita aka dafa na sunan". Ba tare da ta kalli innar ba tana cigaba da cin abincin tace "na manto kud'in bisa gadona jakarce kawai, amma ba ko sisi ciki ". 

Duk suka zubo mata ido harda Saddik'a wacce annurin fuskarta ya gushe a lokaci guda tace "kambu ni da nake murna yau zan kwashi ganima ya zaki sace min gwuiwa tun ban fara rattabo miki matsalolina ba". Dogon dariya ta saki harda k'walla

"su ganima manya" inji Salima.

 

RAYUWARMU A YAU

 

©

CHUCHUNGAYE

® NWA

&

JAM33LERH

 

{17}

Sai da ta tasar da kwanon nan tas ba tare da damuwa da k'ugin kukan da yaran ke yi ba, ta sud'e hannunta ta jawo ruwa ta kora , Su kam mamaki ne ya ishesu. Inna ta sauke ajiyar zuciya "ni ko ba don kar kice na miki shisshigi ba da sai ince yanda kike cin abincin nan tamkar wacce ta kwana bata ci ba, a irin mijin da kika aura ban tsammaci ganin haka daga gareki ba". 

Ta had'e rai tace "ni fa sa ido ne bana so , nasan dai 'yan kudin da kika sa ran zan baki ne kike wannan k'ulafucin, saidai kiyi hakuri ki tari gaba wannan kuwa ya wuce". Saddik'a tace "uhm to Innarki ma kenan bare ni bari inyi ta kaina ni dai" ta yunk'ura ta fice .

Salima ta maida hankalinta wurin Innar ta cigaba " ni fa kallon kud'i kawai ku ke min amma ba haka bane rayuwar maneji ce kawai so kike in fad'a dumiya ta ji nasanki ba'a sirri dake". A lokacin da ta kai k'arshen maganar kuwa har ta isa bakin k'ofa . Innar tace "ai da kin min bayani tun fari, aa da gaskiyarki 'yar nan ko ni bazanso asan halin da kike ciki ba bare ga mahassada cike da gida".

Ta juya kan yaran kuyi min shiru shegen sai kun tara min jama'a in abinci ne bari inje in samo ku da zakuji dad'i ma sha'ani ake ba zaku kwana da yunwa ba", wani mai wadan matashi cikinsu yace "Inna daga zuwanta fa ta cinye mana abinci alhalin ko zuwa gidanta mukayi kullum a rufe bazata bud'e ba".

Ta buga masa robar hannunta a kansa "rufa min baki shak'iyi mara ta ido, bata bud'e din ba, gayyar gidan nan in biyewa zatayi ai can za'a tare mata".

A tsakar gida mutane ne zazzaune kasancewar gidan da fad'i ga inuwa yalwatacciya kowa ya nema ma iansa mazauni a inuwar rukuni rukuni. Hakan ta kasance ga Saddik'a wacce tayi d'aid'ai sai d'aurin kirji suna hira da Salima . Inda Salimar ke cewa "gidan nan dai duk shekarun da mutum zaiyi bai zo ba ranar da ya dawo kuwa abinda ya bari zai taras", Saddik'a tace "shiyasa ko sha'awar zuwa ban tab'a yi ba, gidan mijina ya fiye min nan duk wahalar da zansha kuwa , to ko abincin da mutum zaici ma ai gagara zaiyi nan ma fa wai don ana sha'ani ne".

"Ah ah 'yan albarka ashe kuna tafe ina ta zuba ido ina tsumayen zuwanka ashe kun hallaro". Malam Amadu ke maganar da fara'arsa ya nemi wuri gefen bishiyar ya zauna duk ga mata amma baiji kunya ba.

 

{18}

Yaran suka gaishesa ya tambayi mazajensu suka amsa da "lafiya lau". Ya rage murya "to me kuka kawo mana ne gidan namu a bushe yake kasuwar yanzu tayi k'asa wallahi, nayi ta zuba nace yaran nan ko zasu sa mazansu su tallafeni tunda kunsan yanayin garin gwagurawa kawai mukeyi".

Suka kalli junansu suka sadda kai Saddik'a tace "baba ni dai mijina kasan bashi da shi watarana ma ko abinci babu, dama inada niyyar in tambayka idan da hatsi a taimakamin ". Ya kalleta a wulakance wannan shine ka saida akuya ta dawo tana ci maka danga kawai dai kice min bani da rabo kanki". Tace 

"Baba ai duk da haka na tara 'yar 500 dita zan raba muku kai da Inna" ta fiddo kud'in. Nan take ya fisge ya saka a aljihun babbar rigarsa me zatayi da kud'i nida ke wahalar kula dasu", ya washe baki "to ke kuma fa d'iyar arziki yana fad'a yana kallon Salima dake wasa da ta d'ago d'auke da murmushi bayan ta sami tabbaci daga zuciyarta kan abinda zata fad'a "Baba ni garin sauri na manto jakata a gado na aika yaro tun d'azu ya d'auko min Allah yasa kar ya min wasa".

Ya gyara zama "auho ai da har zuciyata ta tsinke inace kema da naki kukan ne, mai hankali dai kika aika ko don ba'a wasa da kud'i". Ta amsa da "eh" yace ke baki da cikinne ?". 

Ta rufe fuska cike da kunya ta lallab'a ta tashi ta shige d'akinsu . Innarsu na ganin haka ta bita ko da ta shiga tana d'auke da jakarta da alamar shirin tafiya .

Inna ta tsaya turus "yar nan me zan gani ba dai tafi ba" tace "Inna tafiya kuwa dole kafin Baba yaci min mutunci a bainar jama'a, nidai ga 500 nan ki bashi bazan iya bashi da kaina ba, yanzu ma hak'ura zanyi da kud'in mota in taka da k'afa". 

Inna tace "oh Malam gashi ya korar min ke ko hirar yaushe gamo bamuyi ba ta kwanto kud'i daga k'ullin zaninta ungo nan d'ari ce ki hau mota amma rance na baki kya aiko min da shi" ta karba tare da aje ma Innar turmin atamfa ta fic tana fad'in "Allah bamu alheri, ba sai kin rakani ba banso asan tafiya ta".

 

RAYUWARMU A YAU

 

©

CHUCHUNGAYE

®NWA

&

JAM33LERH

 

{19}

K'irjinta keta dukan 3 - 3 yayinda ta kusanto gidan mijinta bata san kuma mai zata tarar ba yanzu . Tun maidota da mijinta yayi gidan da kishiryarta take bata k'ara samun kwanciyar hankali ba , da ace tare da kishiyar ta fara zama watak'ila babu abinda zata karas dangane da rayuwar amarci. Uk'uba kawai take sha a gidan nan ba ga kishiyar ba bare 'ya'yanta da basu ganinta da k'ima. Allah ya gani ba don gidansu ma wani tarin tashin hankalin bane da tuni ta kashe auren ta huta . Ga miji sai lokaci lokaci take ganinsa wannan shine rana zafi inuwa k'una. 

Muryar mai a daidaitan ne ya maido ta daga tunanin da ta dulmiya yace 

"Hajiya inata magana shiru tun dazu na tsaya ki mik'o min kud'i abu ya gagara". Ta mik'a masa 100 sannan ta sauka ta tsaya .

Ganin yana k'okarin tada mota tace

"ya haka canji fa ?" yace 

"ai kud'inki kenan". 

Fuskarta a raunane tace 

"Haba malama daga 'kofar kona' zuwa nan "karauka' ne zakace naira 100..." bai jirayi ta karashe zancenta ba ya ja motarshi yayi gaba. 

Ta dad'e tana shawara da zuciyarta wurin shiga gidan gann bata da mafita gashi tana ta share lokaci a titi tayi k'arfn hali ta fad'a gidan . Kishiyarta Gaje ta fito daga kicin 

" 'yar dangi karfe 3 har an gama sunan? Ko dai marmarin gani na kike baki gaji dani ba?". 

Jikinta a sanyaye ta cire mayafin jikinta ta rataya jikin k'yaure(kofa) "an watse ne, kinsan dayike bana fari bane hidimomin basu k'arewa shiyasa Babanmu yace muzo mu koma gidajenmu".

"Lah Mama kiji wai gidajensu, har da nan gidan ma gidanku ne? Cewar wani yaro da bazai wuce shekara 8 ba. 

"Shine nima nake jira inga k'arshen k'arfin hali Ameer, kai ma yaro kenan ka lura, dallah kinmin tsaye a kai wuce ki karik'e min girkin can". Gaje ta fad'a tana harararta. Salima ta k'arisa kicin d'in kamar wacce aka cire ma laka. 

 

*************** ******** 

 

{20}

 

Kamar yanda ya saba shigo mata haka ya fad'o d'akin, barcinta kawai take shak'a don yanzu ta daina jiransa k'ofar ma ta bar kullewa saboda sanin mijin nata fataken dare ne. 

Ya shigo yana malangaran a tsakar d'aki had'e da surutai shi kad'ai. Ya k'are mata kallo tayi d'aid'ai zanin kanshi ya bar jikinta , skirt dinma ya hankad'e sai mazaunan muraratan, Ya saki murmushi yana murza ido. Idonshi ya sauka kan jakar ledarta dake gefen gado yashe tare da mayafinta da takalmi bisa ga dukkan alamu bata dad'e da dawowa ba gajiyace ta kada ita barcin dole. Kai tsaye ya isa wurin ledar ya zazzage ya tsince kud'ad'en dake ciki ya soka cikin wandonsa.

Ya fara cire kayan jikinsa da d'ai d'ai sai wandon ya adana sa da kyau daga nan ya afka mata, da ihu ta farka suka k'arisa sunnar da kokawa.

BAYAN KWANA BIYU

A jigace taketa zagaye d'akin da ta hargitsa, bakinta kuma bai bar furta. 

"Allah ya isa tsinanne".

Gaba d'aya ta fita hayyacinta taci kuka harta gode ma Allah 'yan kud'ad'en da ta samo wurin mahaifiyarta yabi ya d'auke yanzu bata da abinda zataci . Ga wata azababbiyar yunwa da ke k'wak'ularta da d'an cikinta da ke wani irin juyi kamar hanjin zasu fito da yaron ciki.

Tun dawowarta suna gidansu bata tashi tuna kud'in da Innarta ta bata ba sai yau da ta rasa abinci a d'akin, tun da ta yasar da ledar a tsakar d'aki bata k'ara bi ta kanshi ba bare tayi tunani kaudawa ta kimtsa d'akin. Tana da tabbacin Kabiru ne ya d'auka. A bayyane tace

"Tsinanne d'an tasha, Allah ya isa". Fuskarta d'auke da damuwa mai tsanani.

Ta kwanta a tsakar d'akin tun tana kuka k'asa k'asa har ta koma rerawa. Mak'ociyarta Ladidi dake tsakar gida tana aikace aikace ta rik'a jiyo gunjin kuka, kamar bazata je ba wata zuciyar dai ta raya ma ta tashi ta nufi d'akin . 

Ta firgita da ganin halin da Saddik'a ke ciki " Saddik'a lafiyarki kuwa ko nak'uda ce", ta bud'e baki zatayi magana ya mak'ale . Ladidi ta k'ara rud'ewa tana jijjigata ita kuwa Saddik'a sai nuna mata cikinta take, da taga Ladidi ta gagara ganewa ta koma nuna mata bakinta .

A guje ta fita ta samo mata abinci ta tallabota, tana bata ya dawo, nan tayita shek'a amai ga cikin ba abinci sai majina ke fita. Ranar dai Saddik'a ta jigata kamar ranta zai fita, da taimakon Ladidi ta d'umama cikinta ta dawo hayyacinta. Har lokacin kuwa bata fasa tsinewa Kabiru ba.

 

RAYUWARMU A YAU 

©

CHUCHUNGAYE

®NWA

&

JAM33LERH

 

{21}

Haka rayuwa tacigaba da mirginawa a wurin Saddik'a. Bayan wasu kwanaki suna zaune a tsakar gida ita da Ladidi suna shan hantsi. Ladidi tace "wai ke ko Saddiqa haka zakiyita zama ba awo ba ganin likita ga ciki na dad'a tsufa". Murya a raunane tace "to ya na iya, ni yanzu ba ta wani zuwa asibiti nake ba ta abinda zanci har d'an cikina ya amfana nake, ke ma d'in wani lokacin kina min abu kamar ba mace ba wani sa'in sai ki kauda kai ki mance da tausayi ki hanani".

Ladidi ta d'an dara "har kisa ni dariyar da ban shirya ba kina magana kamar ni na aje ki, ni zan zauna inyita ci da ke ne mijinki aikin me yake?, ke ko yar sana'a kink'i yi kin jab'e wuri guda aiko zakiga zaunau", "ni kinga bari inje in shirya anguwa zani na tsaya zuba".

Saddik'a ta lallab'a ta shige d'aki don bata da aikinyi illa ta kwanta ta tashi duk irin aikace aikacen gida ba yinsu take ba dama wanke kwano d'aya da taci abinci cikinsa ne kawai aikin shima sai yayi kwana 3 ko fiye kafin ta wanke".

Bayan kwana biyu da maganar da Ladidi, tun da sassafe ta farka saboda ta samu ganin Kabiru don ya saba fita tana barci ba kasafai suke had'uwa ba duk da kwana d'aki d'aya da sukeyi.

Bakin gado ta zauna tana jiran tashinsa sai sak'e sak'e take a zuci tana k'are ma d'akin kallo, a hankali duk ta gama sayarda duk wata kadara dake d'akin illa gado da sif kawai, a watanni 10 da suke da aure d'akin ya zamanto kamar an share masallaci. Tana wannan tunanin kuwa ya farka yayi mik'a ya sauka gadon ya fita ya wanko fuska ya dawo . Ya d'auki rigarsa da ya cire zai mayar . Tace

"Kabiru dama magana nake so muyi"

Ya mata kallon k'askanci daga sama har k'asa banda hamami babu abinda takeyi duk ta kod'e kodayike duk d'aya suke, ya kauda wannan tunanin yace "maganar ta zama ce ko kuwa?.

Tace "da ka zauna zaifi armashi".

"to hanzarta kiyi maganarki, ina saurare"

"dama awo nake son fara zuwa kana gani dai ciki na wata bakwai kenan, daidai da panadol baka tab'a kawo min ba da sunan rigakafi".

Yace "af to awo ko? To ban sanshi ba ,idan ma na sani to banida da halinshi". "ai dama haka zakace mai hali ai baya canza halinsa mugu azzalumi tun bayan amarci baka kuma nuna damuwa kan halin da nake ciki ba, haka zaman aure? yake ko ci dani bakayi k'iri k'iri na koma ci da kaina kamar mai zaman kanta, saidai ma idan kaga nawa ka d'auke,".

"ai shikenan sai ki nema ma kanki mafita in kin gaji" ya fad'a cikin halin ko in kula ya tashi ya fita . 

"amma in fitinarka ta tashi ai kasan hanyar zuwa ka kore k'ishirwarka lokacin nake da amfani". Ta fad'a a hankali, ashe maganar ta iskoshi wanda ita kanta bata san haka ba ya dawo da baya ya cafko bakinta ya murd'e da karfi don azaba har fitsari ta saki sannan ya gwab'e bakin da hancinta

"ki kiyayeni niba sa'anki bane"

yana kaiwa nan ya fice. 

 

chuchungaye.wordpress.com

 

RAYUWARMU A YAU

 

©

CHUCHUNGAYE

®NWA

&

JAM33LERH

 

{22}

Ruwan da taji k'afafuwanta cikinsu ne ya sanya ta duba k'asa inda ta ganta tsamo tsamo cikin ruwa da ya malale ledar d'akin . Ta ja dogon tsaki 

"Banzan ji yanda ya jik'a min d'aki, mtswww wawa kawai".

 

Ta mik'a hannu bayanta ta jawo yamutsattsen zaninta da ke bisa gadon ta jefo shi saman ruwan ta sa k'afarta tana dannawa tana bin ruwan har zuwa inda bokitin da ruwan ya zube yake ta d'agashi tare da ware ido

"La la la dama wannan bokitin ya shure? 'Dan ruwan da nake tattalawa ina sha, bala'i to wallahi da sake, bai d'ebo min ba amma ya iya min ta'adi zaka dawo ka sameni ne mashayin wofi".

Ta k'arasa fad'a kamar zatayi kuka.

 

'Yar yarinya ce ta fad'o d'akin a guje har suka kusa karo ta sa hannunta ta tura yarinyar tace "Ke ke dallah tsaya can ji yanda ke kuma kika jagula min d'aki da k'asar k'afarki". Ta fad'a ranta a bace. Ta ja tsaki tare da jefar da zanin gefen gado tace

 

"Na ma fasa yayi ta zama haka da wanne zanji"

 

Daga waje Ladidi ta rik'a kwalo ma 'yar kira har ta shigo d'akin duk ya jagule da tabo ta kauda kanta daga kallon ledar "um ni fa zan wuce sunan kince zaki bini, kin sanarwa Kabiru kuwa? Don ni dai na shirya banso rana tayi min don inta kyanyare fitar bazata yiwu ba".

Kafin Ladidi ta k'arasa zancenta har Saddik'a ta jawo mayafinta a saman k'ofa tana k'ok'arin sa wa. Ladiddi tace 

 

"a aha, wai kice cikin shirinki ma kike, amma dai ba cikin wannan daud'ar zaki bini ba ko?".

Ta kalli jikinta

"Kai Ladidi da cin fuska to ni bani da wankakken zani sai dai in zaki ara min kayanki".

 

Da sauri Ladidi tace "Muje kawai hakan ma kinyi kyau". Ta juya ta fita Saddik'a ta bita a baya ta kullo k'ofarta ta dauko kariya samn windonta, tana dannewa tace

 

"Kwad'o ma zan daure in sayo saboda wannan wawan, yanzu sai ya faki fitata ya lalube min d'aki". 

 

* * * * * *

Da k'afa suka isa gidan sunan kasancewar ba nisa. Sunyi wa maijego barka sannan Ladidi ta mik'a abin suna da ta rik'o. Saddik'a tace "Oh su Ladidi an iya sirri da yaushe kikayo wannan siyayya banda labari? Sai kace mugun abu, amma ni komai na sayo sai na nuna miki".

Kunya duk ta lullub'e Ladidi ta fara waige waige tana kallon fuskokin mutanen da ke d'akin tana k'ok'arin karantar fuskokinsu. Saddik'a tacigaba

 

"Abin mamaki ma wai dangin miji kikayo ma wannan hidima"

 

Ta jawo ledar da Ladidi ta mik'ama mejego, ta fiddo kayan ciki. Ta zare ido. 

"Ke Ladidi ji wannan d'and'asheshiyar atamfa", ta fad'a tana juya atamfar fuskarta d'auke da mamaki

"amma kud'inta zaiyi nawa?", Ta d'aga rigunan jariri "Oh ke kam ai kin sadaukarwa miji da danginsa rayuwarki, a k'arshe sune masu zugin a miki kishiya, ni da kin nemi shawarata yaushe zan barki kiyi wannan asara". Ta fad'a tana k'ara jujjuya kayan.

Duk mutanen d'akin sun tattara hankulansu a kanta sun zuba mata ido yayinda ita kuma ta dage wurin sharhin kayan da Ladidi ta kawo, hankalinta kwance take maganganunta. Daga bisani ta maida kayan cikin ledar sannan ta jefasu gefen maijegon 

 

"Amma dai kayan nan kin kashe yayu dubu biyar ko?", ta ta'be baki "Ni ko Kabirun bazan iya kashe masa naira biyar ba ma bare wasu danginsa can kema d'in neman sunan ya kaiki".

 

Ladidi bata iya bata amsa ba illa tashi da tayi kanta k'asa kunya kamar ta nutse k'asa ta fita d'akin. Mutanen d'akin ma an rasa mai magana mamaki da al'ajabi duk ya cikasu.

 

chuchungaye.wordpress.com

 

RAYUWARMU A YAU

 

©

CHUCHUNGAYE

®NWA

&

JAM33LERH

 

{23}

 

Tsawon lokaci d'akin shiru ko tari bakaji kowanne da abinda yake kissimawa a rai. Saddik'a na zaune gefen gado tana binsu da kallo jefi jefi kuma takan kalli cooler abinci da ba'a dad'e da shigo dashi ba.

Kasa jure had'iyar yawun da ta dade tanayi take, barin ma da hancinta yake kwaso mata kamshin abincin sai cikinta ya amsa da wani irin k'ara kulululu. Ta muskuta ta gyara zamanta yanda cikinta zai fito da kyau ko Allah zai sa wata mai hangen nesa cikinsu ta lura da lalurar cikin da take d'auke dashi ta mik'o mata abincin nan, tunda su taga basu da niyyar ci. A ranta duk take wannan tunanin.

Bayan d'an gajeren lokaci hak'urinta ya yanke ta mik'e tsam ta isa wurin kular ta jawo filet ta zuba abincin ta cika taf har yayi tsini, ba tare da ta rufe kular ba ta d'auki abincinta ta fita. 

Cikin inuwa ta nema ma kanta mazauni jikinta har rawa yake yayinda take aika abincin bakinta kamar tsohuwar mayya. 

A tsakar gidan kowa harkokinsa yake ba wanda ya lura da zamanta har sai da masu idon gane gane sukayi kicibis da wata irin mace cikin mummunar shiga busu busu da tulin abinci gabanta cin mutum 3 ko fiye. Abinka da mata a hankali kallo ya koma kanta da maganganu k'asa k'asa, yayinda ita bata ma san suna yi ba. Su kuma sun sa ido ne suga yanda wannan mata zata k'arar da wannan abinci.

Bisa ga mamakinsu cikin yan lokuta ta tayar da abincin. Sai a lokacin ta dago kai, ta numfasa sannan ta yafito wani yaro had'e da sakin gyatsa mai sauti. Fuskokin mutanen bai 'boye al'ajabin halayyar wannan mata ba.

Bayan ya kawo mata, ta karba ta sha tare da sakin gyatsa a karo na biyu tana share gumi. Ta ture filet d'in gabanta yanda zataji dad'in mik'e k'afa ba tare da ta damu da bisa abincin da ta zuzzubar ta d'aura k'afarta ba. 

Ladidi tazo kanta tana hushi ranta a bace tace

"Tunda nake ban taba ganin shashasha ballagaza irinki ba, ban taba tabbatar da rashin tarbiyyarki ba sai yau". Ta katse Ladidi 

"Me akayi ne wani abu ya faru ne?" kallonta Ladidi tayi da bacin rai kamar ta bugeta "To wallahi bazaki had'ani da dangin miji na ba, yau irin kunyar da kika sa ni ciki ai yawa gareta".

Saddik'a ta tab'e baki "Niko nasan dangin mijinki ba mutanen kirki bane", Ladidi ta ware ido ta rik'e baki

"au iyye".

"Don ma na nuna kawaici amma mutane marasa tunani da halin girma basu dubi halin da nake ciki ba na cikin dake jiki na ba ina ganin abinci ba wanda yayi tunanin min tayi". Saddik'a ta fad'a bakinta na fidda kumfa.

Lokaci kad'an magana k'arama ta fara zama babba har Ladidi ta cira hannu da nufin marinta wata dattijuwa ta rik'eta. Mutanen wurin duk suka taso suna fad'in "Gwaggo ki barta ta koya mata hankali".

"A'a baza'ayi haka ba, ku barta da halinta ta dai tattara ta bar gidan nan yanzu yanzu".

 

{24}

 

Tun daga nan Saddik'a bata k'ara magana ba, haka kuma bata bar gidan ba amma fuskarta akwai damuwa sosai. Daga bisani tace " Ladidi sai anjima zamu tafi gida ne?".

Maganarta ba kadan ta shayar dasu mamaki ba 

"Lallai Saddik'a ta cika jaka maras zuciya", inji wasu daga cikinsu.

Dattijuwar d'azu tace "shashanci ne ke damunta, wannan mijinta na ganin ayyuka yana hak'uri, don naga alama sauna ce", ta k'are ma Saddik'a kallo wacce ke zaune da'bas a k'asa tana wuri wuri da ido. Dattijuwar ta girgiza kai 

"Ke Ladidi anya kina sauke hak'k'in makotaka kuwa, baki fad'a mata gaskiya halan?, wannan k'azanta ta kai intaha ni wannan gwamutsa numfashi da ita ai sai mutum ya daure". 

Wata daga gefe bayan ta gumtse dariyarta tace "Allah Gwaggo ba shak'iyanci ba d'azu haraswa ne kawai banyi ba a d'akin nan shiyasa ma na fita". Nan gaba d'ayansu suka kwashe da dariya .

Ladidi tace "Abin ai sai wanda ya gani, watarana ma ita da mijin ai yi suke kamar zasuyi dambe, nid'an ba k'ara in kuma zuwa wani wuri da ita ta kunyata ni

Cin mutunci iri iri sukayi ma Saddik'a a wannan rana, bare fushinsu na d'azu ba sauka yayi ba ta k'ara musu wani. Amma hakan bai sa ta bar gidan ba, sai da Ladidi ta gama cin sunan sai gab da magriba tukunna suka tafi gida da guzurin abinci da Saddik'a tayo a leda.

 

Allah ya kyauta tsuntsun da ya jawo ruwa shi ruwa kan duka.

 

* * * * * * * * * * * * * * * * *

 

chuchungaye.wordpress.com

 

RAYUWARMU A YAU 

 

©JAM33LERH 

CHUCHUNGAYE 

®NWA ?? 

 

{25}

 

Salima ce zaune a d'akinta ta rafka tagumi ta rasa tunanin da take, kamar daga sama ta ji sallamar shi, yaran shi na fad'in "Oyoyo ga baba". 

Ta lek'o ta labulen d'akinta, ta yi saurin komawa d'akin ta fad'a kan gado ta kwanta. Ba wanda ya tuna da ita saboda ba ita ke da miji ba. 

Hawaye ma su zafi suka zubo ma ta, ta na tunanin ta huta da wahalar gidansu ashe ba'a rabu da bukar ba an haifi habu. Amma duk da mawuyacin halin da take ciki da wulak'antacciyar rayuwar gidansu gara gidan mijinta. 

Da haka bacci barawo ya yi gaba da ita. 

Washegari da safe ta na tashi a gurguje ta yi sallah dan ba sanin muhimmancinta ta yi ba. Tsakar gidan ta fito ta hau kaye-kaye sai da ta share tsakar gidan tsaf, ta shiga madafi ta daura ruwa sannan matar gidan ta fito, ta bi Salima da kallon tara saura kwata. Jikin Salima na kyarma ta ce "Maman Ameer Ina kwana?", bata amsa ma ta ba tayi tsaki ta ce "yar gidan talakawa kin dai daura ruwan wankan su Ahmad dai ko?". 

Salima ta gyada kai kamar k'adangaruwa. Abinda ba ta saba ba a gidansu shi take yi yanzu ba dan komi ba sai dan ta zauna lafiya. 

 

Haka rayuwar gidan Salima ta ke kowacce rana da irin izayar da take ci, hakan be sa ta taba marmarin zuwa gidansu ba. 

 

Kamar a mafarki ta ji muryar shi yana tada ta, ta mik'e tare da yin hamma ya ware idanunta akan mijinta Isyaku. 

Tsaki ya yi tare da murtuke fuska ya ce "miye nan a hannuna?". Ta kalli hannunshi ta gani ta ce "kud'i ne", ya ce "na ki ne amma da sharadi". 

Ta kwalalo idanu ta ce "na ji ko wane irin sharadi ne". 

Ya ce "kin ga kud'in nan, Jari ne na baki Naira dubu goma ba dan komi ba sai dan ki tallafawa kan ki ki samu na biya ma kan ki bukatu, na gaji da bani bani da kike damuna dashi kullum, kuma kar ma kiyi tunanin kin ci bulus ne". 

Da hanzarinta baki na rawa ta ce "toh mai gida nagode". Ya wurga ma ta kud'in tare da k'arin kashedi, yana fita ta buga uban tsalle tana murna. 

Tun daga wannan rana Salima ta warware ta hau busha-busha da kud'in da aka bata ta yi sana'a. Sayi banza sayi wofi haka ta ke ma kud'in. 

Kishiyarta Gaje kuwa sana'a take a cikin gidan irin kayan koli su dankunne, da dai sauran k'ananan kayan kwalliya na mata ma su sauk'in kud'in da kayan dandano na abinci. 

Mal. Isyaku ma'aikaci ne na gwamnati a makarantar firamare. Aurenshi hud'u Gaje ce ta biyu sauran ukun sun fita kuma kowacce nan ta bar 'ya'yanta Ak'alla yaran gidan sun tasar ma 12 guda 7 na Gaje. Ciyarwa, sutura da shayarwa kacokam ya na kan matar shi ne, ba abinda ya dame shi da cin su da shan su, matuk'ar ya ajiye muhimman kayan abinci toh kayan had'in su sai dai Gaje ta yi. Kula da makarantar ya'yansu ma a wuyanta ya rataya, albashin mijin sam be amfana ma su komi. Tun abin na damunta har ta saba ta fita harkar shi. 

Sanda zai auri Salima ya yi ma ta karyar kud'i inda ta yi tunanin ta samu gidan hutu haka ma jama'ar gidansu ke ma ta kallo, ashe duk burga ce harda mata da ya'ya gare shi. 

 

A tsakar gidansu ta zauna ta baje gammon kifin da ta je ta siyo a kasan layinsu, ta na ci tana dangwala yaji. 

Gaje ta fito ta bi ta da harara daga baya kuma ta kyalkyale da dariya ta na habaici tana rero wak'ar marigayiya Barmani Choge a cikin wak'ar ta na "Mu kama sana'a mata, macen da ba ta sana'a ta bani lale maraba da ke zinariya". 

Salima ba ta tanka ba dan ta san sauran. 

Sam habaicin Gaje be dame ta ba, burinta ta ci d'ad'i tasan idan kud'in suka k'are Isyaku zai karo ma ta wasu, haka dai take kulla wannan wasikar jakan ba tare da tayi koyi da kishiyarta ba. 

 

************

Hamma ta saki wanda sai da ta dauki ak'alla ta dau minti d'aya bakinta a bude tana wannan hammar. Cikinta ne ya bada wata k'ara "k'ululu". 

Yunwa take ji kamar za ta yi kuka ta rasa inda za ta sa ranta. 

K'amshi ta ji ya bad'e gidan, ta fito tana kallon Gaje da ke dafuwa a kitchen d'in gidan. 

Shigowar mijinsu ya sa ta komawa d'akinta, zuciyarta cike da takaicin irin abinda ake ma ta a gidan. 

Gaje tai ma shi sannu da zuwa, ya kalle ta ya washe baki ya ce "uwargida sarautar mata". Murmushi ta yi, tana jin d'ad'in kirarin da yake ma ta ko dan Salima ta ji. 

Ya ce "Ina Salima ta ke ne?", bata tanka ma shi ba dan bata son yana maganar Salima. 

D'akin Salima ya nufa ya na shiga, ta yi saurin tashi ta gaida shi. Ya amsa fuska a turbune, ta ce "Baban Ameer dama akwai maganar da zamu yi". 

Ya ce "Ina Jin ki". Ta ce "dama kud'in da ka bani ne suka k'are shi ne nike son ka k'ara mun wasu sai in ja jarin". 

Wani wawan mari ya watsa ma ta wanda ta rufe idanunta tana hango wani haske kamar walk'iya saboda tsabar shigar ta da marin yayi. 

Bai bi ta kanta ba, ya fita daga d'akin yana bambami, wanda Gaje da ke labe hakan ya faranta ma ta. 

chuchungaye.wordpress.com

 

RAYUWARMU A YAU

 

©CHUCHUNGAYE

®NWA

 

&

JAM33LERH

 

{26}

 

Ko da ya shiga d'akin gaje da fara'arta ta tarbeshi ta d'auko masa farfesun naman kasuwa(naman Sa) da zafinsa yana turiri, da damammiyar fura da yayi kyawun damu ga ra'ba jikin kwanon, wani irin farinciki ya ziyarceshi, domin kuwa yanada bukatar abu mai sanyin, ya zauna yana sha tana masa hira. 

A 'bangaren Salima kuwa tagumi ta kafa tana tunani duk zuluncin Babanmu bai ta'ba dukan matanshi ba, ji yanda Alhaji Isyaku ke lalla'bani lokacin da yake neman aure kai Namiji! Nami... Kalmar ta mak'ale sanadiyyar kitan da taji yana mata daga tsakar gida. Sai da ta 'bata lokaci sannan ta fita .

Ya bita da kallon k'ask'anci "Sannu isassa wato sai da kika mula kika ga dama ko?".

Ta tsareshi da idanuwa bata ko k'iftawa.

Yacigaba "Inace yau ke kike da girki amma banga alamar kin d'aura ba, me kike nufi? yayi shiru yana jiran amsarta, bata tanka ba kuma bata fasa kallonsa ba.

"Kina nufin yara na idan suka dawo makaranta suci babu kenan?". 

Ya juya wurin Gaje da ke zaune bakin rijiya "Ba dai iskancin da take shimfid'a miki kenan ba? Gaje ta sassauta fuskarta zuwa ta wadda aka zalunta 

"Gani nayi amarya ce, inyi magana ace bani da hak'uri gwara da ka gani da idonka". Ta d'auki shinkafar da ta wanke ta nufo inda suke tana cigaba da magana. 

"Kullum nike wahala a gidan nan, dama ace yara na ne kawai gidan da abin yazo da sauk'i amma ga na kishiyoyi marasa tarbiyya ka ta'ba su ace mugunta ai ni kam abin ya min yawa", ta raunana fuskarta tana kallon Salima wacce ta daskare da jin wannan k'arya.

"Ita kuma kullum tana mak'ale a d'aki ba damar inyi magana sai ta nemi zagina gwara tun wuri asan abinyi".

A lokacin da ta kai k'arshen maganarta ransa ya k'ai k'arshe wurin 'baci don haka ba tsammani ya koma d'aki ya zaro belt ya dawo kan Salima ya jibgeta duka ba na wasa ba sannan ya k'ara da cewa

"daga yanzu duk ayyukan gidan a maidasu kanta tunda bata da mutunci bata gaji arziki ba".

Wannan hukunci ba k'adan yayi ma Gaje dad'i ba har bata iya b'oyewa ba bayan fitarsa tayi juyi. A gaban Salima wacce ke durkushe tana kuka tace 

"Yarinya kad'an ma kika gani, ba dai kince gidan Baban Ameer ba" tayi k'wafa. 

"Za ki bada labari". 

Tayi shewa ta shige d'aki tana k'ara jaddada mata ta hanzarta d'aura ma yaranta girki.

 

A wannan lokaci Salima ta ga rayuwa a gidan nan yayinda halayyar mijinta ke k'ara bayyana gareta, a lokacin ne ta fahimci watanni 4 da sukayi gidan haya lallab'ata yayi saboda tana amarya yanzu kuwa har da shi a masu son ganin ta k'untata a gidan.

A dawowarta ne ta kuma fahimta wayeshi ta fannin harkokinsa duk da karantarwar da yakeyi, ta kwana 2 ce kawai yake zuwa sauran 5 d'in kuwa balaguro yake gari gari a cewarsa yana business a garuruwa, ga wasu irin mutane dake musu zarya a gida maza da mata yana basu bashi mai riba cikinta. 

Tashin farko taji abin bai kwanta a rai ba tana kokonto kansa "to me kenan hakan ke nufi?" tayi ma kanta tambayar da bata da amsarta.

Bata gushe ba wani zuwa da tayi gida tayi ma babansu maganar yayi mata shiru har ta cire rai da samun amsarsa, sai can ya murmusa har yalayen hak'oransa suka fito yace

"Kar ki damu duk cikin neman kud'i ne, 'yan bana bakwai da basu son wani da cigaba su ke kiranshi ma da wai BASHI DA RUWA tsabar k'eta da bakinciki, ai mijinki yayi dabara gwara a raba k'afa, yanzu ba'a zama dole a nemi kud'i ko ta wace hanya, don haka ke dai kiyi ta kwantar da kai ki bisa sau da k'afa ki yagi rabonki". 

Da wannan ta sami natsuwa ta share zancen ta cigaba da harkokinta na yi ma kishiya bauta. 

 

RAYUWARMU A YAU

 

©CHUCHUNGAYE

®NWA

&

JAM33LERH

 

{27}

Tana kicin taji yana k'walo mata kira, da hanzarinta ta fito daga hayak'in tana fyace majina da gefen zaninta, a lokaci guda kuma tana amsa kiran, idanuwanta sunyi jawur ga zufa ko ta ina, tayi yarkace yarkace.

Kallo d'aya ya mata ya kauda kai ya mik'a mata ledar dake hannunsa .

"ungo kifin nan"

Tasa hannu ta kar'ba tana jiran k'arin bayani ya cigaba akwai ragowar shinkafar gwamnatin nan ko?". "Eh akwai, amma ina ga bai wuce gwangwani 3 ba, lallaba ta muke kamar yanda kace". Gaje da ba ita aka tambaya ba ta bada amsa tana fitowa d'aki hannunta rik'e da d'ankwali tana k'ok'arin d'aurawa.

"Yauwa kun kyauta", amma kuma bazai ishesu ba". Ya fad'a yana rik'e da k'ugunsa yana tunanin mafita. 

Gaje ta washe baki "Yau dad'i zamuci ne Baban Ameer? Naga an sayo kifi himili guda". Ta karbi ledar daga hannun Salima.

Yayi d'an tsaki "Bak'i fa zanyi, wani alhaji ne zai d'aukeni a kasuwancinsa na sayar da siminti kinsan ana samu sosai, mutumin shegen wayo ne dashi da rashin yarda, shine fa wai bazai bani ba har sai yaga inda na ke zaune da kuma iyalina ya tabbatar da gaskiyata kar in gudu watarana".

Duka su biyu matan fuskarsu d'auke da fara'a da jindad'in wannan cigaba da zai samesu "ah kace mun warke dad'i zai samemu" cewar Gaje.

Ya share zancen nata da fad'in "Yanzu dai abinda za'ayi ke Gaje ki tayata ku kama aikin sosai don a gama da wuri kafin su iso, ku d'ebo gwangwani d'aya cikin shinkafar hausar nan ku gauraya ai inaga bazasu gane ba" har ya juya zai fita ya tsaya

"Af kifi nan kar a mutsikashi a barshi su hangoshi luk'a luk'a".

Gaje tace "Haba Baban Ameer yanda kace mai kud'i ne zaizo shine zaka sayo kifi a sanya masa a abinci idan baya ci fa? tayi tsaki "wannan abin kunya da mai tayi kama, kuma da kake fad'in a dafa gwangwani 4 rabin mudu akace maka gayya zaiyo, ko kuma aure zaizo nema wurinka, da za'a dafa abinci haka dayawa". Kai matsolo dai baiyi ba". 

"Babu abinda ya shafeki na fad'a miki, ku dai kuyi abinda na sanyaku kawai, Kuma saura inga ba daidai ba, ko a cinye d'an kifin". Ya sa kai ya fita.

Gaje tace "Allah dai ya kyauta maka, ta juya ta kalli Salima a inda take tsaye ta yatsina fuska ta kauda kai "ni in banda raina ya biya da kifin ko hannu zan saka ne, aikin banza aikin wofi, ni wuce muje kin tsare da ido" 

Suna cikin girki ya aiko da jolly juice a had'a ma bak'i lemu. Gaje ta karb'a tana had'awa tana zazzagama yaranta da ita kanta suna sha, dama kuma zama tayi kawai a kicin d'in ba aikin da takeyi illa hantarar Salima yayinda kifin ke gabanta tana tsakura tana ci tana fad'in "ya je ma ya kwaso abu duk k'aya". Ta gutsiro dan mitsitsi ta mik'ama Salima wacce keta had'iyar yawu.

Bayan yan awowi ya shigo da saurinsa fuskar d'auke da murmushi "Da fatan komai ya kammala? Don gashi nan ya kirani yana layin nan na masa kwatance ku mik'o min in jera a falo na kafin su karaso".

Ta mika masa ya bubbud'a yana tona kifin "kai kai kai kifin dari 200 ne ya dawo haka?, ya na ga ya rage auki?". Salima ta kalli Gaje. Gaje tace "ya zaki kalleni inace tare muke nan yara dake ta kuka a basu na fincina musu". Ya zabura tare da fiddo ido "Ubanwa yace kiba su? Wad'annan masu tsinannen kwadayin da ko guba suka gani sai sunci, ba sai ki k'yalesu suyi su gama ba da suna ci ne?". Ya ja dogon tsaki mai nuna takaicinsa. Ya d'auki tiren abincin 

"Mata dai baku da amana wallahi, kuma Allah ya isa idan kifina ya wuce kan yara don nasan ba iya su ya tsaya ba". Ya fita yana cigaba da sababi.

 

RAYUWARMU A YAU

©Jam33lerh

&

© Chuchungaye

® NWA

 

{28}

 

Bayan an jima kusan awa guda, suna nan zaune yara duk sun cika gida da koke ya shigo a fusace, ya daka masu tsawa mai firgitarwa "Ku min shiru don iyayenku, mutuwa aka muku zaku cika ma mutane kunne da kukan banza". Nan da nan natsuwa ta shigesu baka jin tarin kowa sai na muciya a kicin da Salima ke tuk'a tuwo. Ya d'auke kai daga muzuran da yake ma yaran ya koma ya kwaso abincin da akayi ma bak'in ya diresu a kasa tare da janyo kujera yar tsuguno ya zauna, sai binshi da ido suke. 

Ya jawo kular ya bud'e ya ja wani mummunan tsaki "Amma wannan mutumi anyi shege, to ce masa nayi bani da yanda zanyi da abincin zai min haka?. Ya sake jan tsaki a karo na biyu fuskarsa murtuke babu sassauci.

Salima daga kicin tace "Baban Ameer lafiya kake ta sababi kai kadai?. Yayi shiru kamar bazai amsata ba har sai da Gaje tace "Shisshigi ba kwarjini". Ya kalli Gaje 

"Ai kuna jina ina magana ba wacce ta tanka, ke kuma kina neman k'ara bata min rai kan wanda nake ciki".

"To ka zo ta tasa mutane da muzurai kana ta fad'a kai kadai, ba sai musa maka ido kaje can kaji da damuwarka ba". 

Yayi k'wafa "Wai ashe mutumin nan su biyu zasu zo nayi barnar abinci haka k'arshe ma ana bude abincin ya fara kakarin amai wai baya son kifi, sai wanda sukazo tare ne ya tasa shi gaba da ci ba dama in hanasa, wai ni nan kar ya cinye na tashi da wayau na kira almajirai, nufina suyi bara yana basu in k'wace, matsiyaci yaci kadan ya kwashe duk kifin ciki ya basu abincin, anan falon suka dira kan kular matsiyata mayunwata, Allah dai ya isa, ni kaina hamma nake tayi amma na hana kaina saboda bak'onka annabinka" ya marairaice fuska kamar zaiyi kuka. "Ba abinda yafi min bak'inciki irin abincina da nayi asara inda na aje muku ba na huta ba kuyi ta lalla'bashi yayi muku sati".

Gaje ta kwashe da dariya Amma bak'o ya iya tsiya", ta k'ara darawa "Gashi nan baka ci da iyalinka ba ka kaiwa dawa, har da cewa mu ci tuwo kar a k'ara taba shinkafa, to ai gashi nan, kuma tuwon iya mu kawai nasa tayi don ba kwanonka, nasan zakaci mai dad'i wurin bak'i". 

A yayin da take maganar kuwa jikinsa ba inda baya rawa ya zazzaro ido.

"Ko tunanin ido guba bakayi ba haka ka kwashe tas munata hadiyar yawu, har gwara mai girkin k'ila ita tayi sud'i". 

"Wai kina nufin anyi tuwon?

"Me za'a fasa Baban Ameer zamuci shiru ne? Ke yi ki zubo ma yaran nan kinaji tun dazu suke ihun yunwa". 

"Kambu asara biyu? ya fada yana kara jaddadawa 

"To wallahi kanku zata k'are, abincin kwana biyu kenan zaku rasa". 

Haka ya wuni yana fad'a a gidan kamar zai ari baki, ko miya yaga yaran sun zubar wurin cin abincin sai ya rufesu da duka a cewar suna masa almubazzaranci.

Bayan kwana biyu suna tsakar gida dukkansu harda yaran, masu d'an girma cikinsu suna wanki tare da Salima, yayin da uwargida ke gefe tana sauraron radio. Ya fito daga d'akin Salima cikin shiri rataye da jaka yana murmushi 

"Mutan gida to ni fa tafiya ta tashi, Alhaji ya neme ni zamu tafi abeokuta wurin kasuwanci zai had'ani da yaransa mu tafi".

Ya karkace ya zaro kud'i daga aljihunsa "Ga dubu biyu nan ku rik'e, sai ayi min addu'a sai Allah ya dawo damu".

Salima ta saki wankin ta bishi "Baban Ameer zaku kai kwana nawa? Yace "kwana? kusan wata ma zamu yi inaga",

"To nawa kudin fa?

"Duk gashi can kuyi fincincinawa, ni na tafi". 

Daga Gaje har sauran yaran ba wanda ya tanka sai k'ananan ne sukace

"Baba ka siyo mana minti".

 

RAYUWARMU A YAU 

 

©Jam33lerh 

©Ayeesh Chuchu 

®NWA 

 

{29}

 

Tun bayan tafiyar Isyaku garin Abeokuta, Salima ta shiga halin ha'ula'i wanda ta gwammace mijinta na gida. Tsakaninta da Gaje sai hantara ba ta samun abinci sai wanda Gaje ta rage da ya'yanta. Sauran yaran ma da iyayen su suka tafi suka barsu izaya su ke sha. 

Kwance take ta ji cikinta ya hautsina amai na niyyar zubowa, da gudu ta fita ta nufi band'aki ta dinga shek'a amai kamar za ta amayar da 'yan cikinta babu komi ciki sai ruwa. Sai da ta gama haraswa ta kwara ruwa ta kuskure bakinta da ruwan da ke cikin bokiti ta fito duk ta galabaita. 

D'aki ta koma ta kwanta yunwa na azalzalarta, hawayen bak'in ciki na kwarara a idanuwanta tana tunanin tafiyar mijinta sati daya kenan ta fara galabaita saboda rashin abinci. 

Gaje da ke tsaye bakin k'ofar d'akinta ta yi murmushin mugunta tare da furta "kowacce shegiya ta zo sai ta saki mara tai ta zubo ya'ya kamar kanya, mijin da be damu da ya'yan ba ma". Ta yi shewa tare da komawa d'akinta. 

Salima ta dafe kirji jin kalaman da ke fitowa daga bakin Gaje, tabbas ciki gare ta dan wancan watan ba ta ga al'adarta ba. Sannan akwai sauyin da ta gani a tattare da ita na cikar k'irjinta. Tunanin makomar ya'yan da za ta haifa ta ke, ba ta san sanda kuka ya kwace ma ta ba. 

**********

Kwanaki sun ja, Saddik'a zaune a tsakar gidansu tare da Ladidi tana taya Ladidi tsince wake ko ta samu na sakawa bakin salati. 

Daurin kirji ne a jikinta da turtsetsen ciki jikinta yau ko gobé haihuwa. Duk wanda ya santa a da zayyi tunanin ba ita ba ce saboda muni da ta k'ara dan tsabar kazanta irin ta ta. 

Ladidi da ta kalli Saddik'a a kaskance ta ce "wai ke Saddik'a ba za ki yi wanka ba ne ki aske gashin jikin ki, kin ga dai kin kusa haihuwa kuma kina jin irin wulakancin da malaman asibiti ke ma mata a asibiti dan babu mai amsar haihuwar ki kina wannan d'oyin". 

Maimakon maganar ta bak'anta ma ta sai ta washe baki ta ce "sai suyi ta yi ni banda kud'in da zan siyi reza bare sabulu". 

Ladidi ta girgiza kai cike da takaicin hali irin na Saddik'a. 

Mik'ewa ta yi ta amshi waken ta shiga cikin d'akinta, sai ga ta ta fito da sinkin sabulun giv ta mik'a ma Saddik'a ta ce "sai ki tashi ki je ki yi wanka da aski dan ni tashin zuciya ki ke sani idan kina zaune kusa gare ni". 

Dakinta ta shiga ta datsa sabulun biyu da wuka ta tura sauran k'ark'ashin gado, sannan ta nufi band'aki. 

Fitowarta wanka zai tabbatar da irin daud'ar da ke dankare a jikin Saddik'a wadda da alama ma ba ta gama fita ba, amma ba laifi ta danyi haske. 

Ta ce "kai Ladidi kin ji yanda iska ke shiga ta ko ta Ina, ji ni ke kamar ba jikina ba". Ladidi bata tanka ma Saddik'a ba har ta karaci maganarta ta shige d'akinta. 

Cikin dare ta ji ana buga ma ta kofa, tsoro ya kamata kamar ta saki fitsari, ta k'ara jin bugun k'ofar, can ta tsinkayi muryar shi ya ce "Saddik'a ki bude ni ne". Jin muryar mijinta ya sa ta tashi da kyar saboda jin k'ugunta ya rike. 

Ta isa bakin k'ofar ta zare sakatar, ya yi dai-dai da jin lema nabin k'afafunta. Ta ji an tsikarar ma ta ciki, wani azababben ciwo ta ji ya taso ma ta tun daga kwakwalwarta har zuwa 'yan yatsun k'afarta. Ihu ta kurma tare da zubewa k'asa wanda yayi dai-dai da shigowar Kabiru d'akin.

RAYUWARMU A YAU 

 

©Jam33lerh 

©Ayeesh Chuchu 

®NWA 

 

{30}

Kallo ya bi ta da shi sai murkususu take a k'asa saboda azabar da take ji. Haka ya tsallake ta ya ajiye kayan shi ya kwanta. 

Can ta ji kamar an cire ma ta k'aya a jiki ta tashi ta haye gado, sannan ta hau bubbuga Kabiru. 

Ta ce "munafuki saboda tsabar wulakanci ka dawo ka ga ban lafiya amma ko kallo ban isheka ba, to Allah ya isa ban yafe ba. Idan mutuwa ma zanyi in yi kenan". 

Budar bakinshi sai cewa ya yi "ki mutu mana dan zama da irin ki idan ba kaddara ba mai iya zama da shashasha irin ki". 

Wani k'ululu ya taso ma ta, ba ta da yanda za ta yi da shi ta kwanta bacci. Asubar fari cikinta ya k'ara tsikarinta, firgigi ta farka ta fad'in "wayyo". 

Kabiru ya tashi yana kallonta tana ihu, tana fad'in "wayyo Allah mutuwa zan yi, bayana zai balle". 

Fitowa ya yi ya kwankwasa ma Ladidi ta fito tana tambayar lafiya?. Kabiru ya ce "Saddik'a ce ba ta lafiya". 

Ladidi ta ce "Ina ga haihuwar ce ka je ka samo mota". 

Yana fita ya je ya dawo da direban taxi, Ladidi ta taimaka aka saka Saddik'a ciki. Za ta shiga Kabiru ya ce "ki koma ciki Ladidi idan ta haihu zan zo in kira ki". Ta koma cikin gidan. Shi kuma ya gama k'issima abinda zai aikata. 

Unguwar su Saddik'a yai ma direba kwatance, har suka iso gidan su Saddik'a a sannan an tada sallar asuba a masallacin unguwar.

Ya kamo Saddik'a ya ce ma direba "ka jira ni in dawo". Zauren gidan ya ajiye ta bayan ta gama galabaita. 

Ya juya ya fita daga zauren zuciyarshi k'al kamar farar takarda. Dawowar su daga masallaci ne suka ji nishin mutum a zauren, Baba Muttak'a ne ya haska tocila, suka rafka salati ganin Saddik'a kwance a zauren. 

Da azama mahaifin Saddik'a ya shigo gidan ya tada Inna amarya, da gudu ta fito ganin Saddik'a cikin wannan halin ya firgita ta. Sauran matan gidan su ka fito aka kaita d'aki ba maganar zuwa asibiti. 

Ba'a yi minti talatin ba cikin ikon Allah Saddik'a ta haihu. Ba maganar gode ma Allah sai guda da ake rangadawa. 

Ruwa aka daura bisa al'ada akai ma mai jego wankan jego, aka wanke jaririya tas. 

Bayan komi ya nutsa sai kuma k'ananan maganganu dake tashi a cikin gidan na ganin Saddik'a a zauren gidan, dama gutsiri tsoma al'adar gidan ce. 

Inna amarya ta kalli Saddik'a dake rakube jikin gado ta ce "wai ya aka yi ki ka zo gidan nan?". Cikin halin nuna takaici ta ce "Kabiru ya kawo ni ya ajiye". Innar ta rafka salati ta ce "yanzu tabbataccen yaron nan abinda ya yi kenan? Zai zo ya same ni".

RAYUWARMU A YAU

 

©Jam33lerh 

&

© Ayeesh chuchu

® NWA

 

{31}

Har akayi kwana uku kabiru bai waiwayo gidan ba. Mutanen gidan suka taso Saddik'a da Innarta gaba da gulma da habaici duk inda aka zauna sai anyi. A na gobe suna iyayenta maza suka gaza hakuri suka tafi nemansa a gida. A can d'in Ladidi suka taras take labarta musu 

"Ai tunda ya d'auki Saddik'a a mota ba'a jima ba ya dawo ina tsaye ina taraddadin halin da take ciki, haka ya wuce ni ya shige d'aka, nan ma bai dade ba ya fita, kunji rabonmu da shi kenan". 

Jiki a Salu'be su Baba Sa'adu suka juyo gida inda suka bar Ladidi da al'ajabi 

"ashe gida ya kai Saddik'a", ta jinjina kai

"kai jama'a wannan aure nasu, uhuhm Allah dai ya kyauta".

Da wannan mummunan labari suka dawo gida dukkansu ransu a bace da wannan tozarci. Saddik'a taci kuka kamar ranta zai fita mutanen gida na ta lallashinta na ganin ido daga bisa suka watsar suka cigaba da harkokinsu ransu wasai. 

A ranar Baba muntak'a yayi ma jaririyar hud'uba da sunan gwaggo wato zainab. Inna Amarya hau ta dire sam bata yarda da wannan zabi ba tun kafin Baba Muntak'a ya bar d'akin. ya dubeta da mamaki 

"sunan uwar tamu kike cewa baki yarda ba? Haba mairo kawaici fa d'abi'ar bahaushe ce amma naga ke kin rasa shi, to ko zaki mutu sai yarinyar nan ta amsa sunan Zainab". Ya fita ya barta da bacin rai tana bala'i ita kad'ai.

Bikin sunan ma babu wani armashi don babu wani bare da yazo sai tsirarun dangin Inna amarya, mafi yawanci bataliyar gidan ce da sauran 'ya'yansu mata da suka aurar suma da tasu gayyar yaran. Kowacce ka duba furgai furgai a bushe kamar wad'anda aka k'watosu daga yak'i. 

Abincin da za'a ci ma gagara taso yi, da k'yar don a fita kunya gwaggo ta bada tsakin masara akayi fate fari fat babu kayan had'i sai kabewa haka kuwa suka rufu kanshi kan kace me babu ko d'igo. Don Innarta cewa tayi sisinta baza tayi asararshi kan wannan gantalallen haihuwar ba. 

Da karo karo 'yanuwa suka hada turmi 5 da rigar jaririya guda 9 suka bata baki har kunne rabonta da sabon kaya tun na lefe. Salima ma ta gwangwaje ta da atamfar dubu 3000 da riga jaririya guda aka wuni yawo dasu d'aki d'aki ana nunawa "ai gudunmawar Salima ce".

* * * * *

Kwanci tashi Saddik'a ta d'au hanyar kwana ashirin a gidansu amma babu Kabiru ba labarinsa. Maimakon aga mai jego tana haske 'bul'bul ita da jaririyarta, nata sai yazo a hargitse cike da rashin kwanciyar hankali da wadata. Abin ya tarun mata da kewar miji hakan ya haifar mata wani mummunan rama. 

Idan tana shayar da d'iyarta sai ta d'au fiye da awa yarinyar bata k'oshi ba, har taraddadi takeyi taji yarinyar na kuka inda Allah ya taimaketa d'iyar hak'urarra ce.

Kwatsam wasu irin kuraje suka fito mata a nononta d'aya masu azabar zafi da k'aik'ayi, haka take zama tayi ta susa a hankali suka fashe suka fara zagaye nonon yayi rami duk yayi ca'ba ca'ba babu kyawun gani. Ba k'aramar wahala take sha kanshi ba ko barci bata iyawa don azaba. 

Babu wanda yayi tunanin kaita asibiti sai magungunan gargijiya sukayi ta karbo mata amma ba'ayi sa'a ba. Da abu ya ishi mahaifiyarta ta aika aka kirawo wata mai maganin a gwada sa'a.

 

RAYUWARMU A YAU

 

© Jam33lerh

&

© Ayeesh chuchu

®NWA

 

{32}

Suna zaune a k'azamtaccen tsakar gidansu suna hira yara nata guje guje suka tsinkayi sallamar wata zazzak'ar murya. Duk suka zuba ma had'add'iyar budurwar ido cike da yabawa. Ta zube tana gaishesu, kunya ta ishesu mace haka yar gayu ke gaishesu har k'asa, don haka da d'an tsoro suke amsawa. 

Tayi dariya ganin basu ganeta ba tace

"Aisha ce fa d'iyar Ruk'ayyar katsina". 

Gaba d'aya suka yanyameta "kece kika zama haka ? idonki kenan? Ashe rai kanga rai?" Ita dai murmushi take binsu dashi.

 

Aisha d'iyar Baba Sa'adu ce, mahaifiyarta Rukayya yar asalin garin katsina ce iyayenta suna da rufin asiri. K'addara da rabon 'ya'ya ta zauna a gidan zaman hak'uri da ukuba ta haifi 'ya'ya biyu mace da namiji. Amma zaman bai wani d'ore ba suka rabu, ta tafi da macen 'yar shekara biyu ta bar namijin. 

Tun da ta tafi babu wanda ya waiwayeta bare su tambayi lafiyar 'yar su, haushin wannan ya sa da zata sake wani auren ta dawo musu da 'yar tayi tafiyar ta bata sake waiwayo ba har wasu shekaru. 

Da kukanta ta sami yayyinta akan tana yawan mafarkin yaranta su taimaketa su dauko mata su daga wannan mugun gida kar a lalata mata tarbiyyar yara. Yayyinta masu zumunci sukayita bata baki sannan suka d'au hanyar zaria. 

Hankalinsu yayi matuk'ar tashi da ganin Aisha yarinya ta lalace ta yamushe an mayar da ita 'yar tsakar gida da kowa ke da hurumin bautar da ita babu kwa'ba, ga wasu manyan zagi a bankinta kamar bamagujiya. Namijin kuwa basu sami gaminshi ba wai karen mota yakeyi motar tirela suna zuwa legaa suka sanar musu sai bayan sati zai dawo.

Ransu yayi matukar baci "wai yaro dan shekara 7 aka tura wannan uwa duniya", saboda haka suka nemi a basu Aisha shi kuma Umar din zasu dawo su dauke shi daga baya. Babu musu aka basu suka tafi da ita katsina sati na zagayowa yayan Rukayyan ya dawo ya tafi da Umar ya rik'esu duka ya saka a makaranta. Tun wannan tafiyar dangin ubansu babu wanda ya neme su haka su ma basu kawo su ba.

Lokaci ya ja ta gama secondary har ta fara jami'a tana aji daya shi kuma Uwar ya gama yana aiki a portharcourt. Wannan karon Kawunta yayi tunanin tazo taga iyayenta idan su basa buk'atarta to ita sun zame mata dole, dole ta nemesu a duk inda suke. 

'Dakin Gwaggo ta sauka domin d'akin matan Babanta ba zai zaunu mata ba, tun da can ma basu aje ta d'akunansu ba bare yanzu. 

Sai dare suka samu ke'bewa da Gwaggo suna hira. Gwaggo tace "to ya labarin aure ince dai sallama kika zo mana ko?" ta fad'a da fara'arta tana 'balla goro. Tayi murmushi a kunyace

"A'a Gwaggo yanzu fa na fara karatu, sai na kai kamar aji biyu haka..."

Tun kafin ta k'arasa maganar Gwaggo ke rafka salati tana k'arawa tsoro da firgici k'arara a fuskarta 

"kema kin zama bayahudiyar?" Muryarta a raunane

"Allah ya tsine ma bokon, yanzu ke har boko ya fiye miki aure? ohh Innalillahi wa innahir rajiun iyayenki sun so su ja mana bala'i".

Ita kuwa da mamaki take kallon Gwaggo abun sai yayi mata wani iri "to mye aibun bokon?" Bata dai furta ba taja bakinta tayi shiru don yanda Gwaggo ke wannan hak'ilon fad'an ko me za'a fad'a mata ba zai gamsheta ba. 

Ta gyara wuri tayi kwanciyarta. Da kad'an kad'an yaran gidan sukayi ta shigowa suna kwanciya, nan da nan d'akin ya cike da hayaniya. 

Karad'insu ba kad'an ya dami Aisha ba kamar ta fasa ihu don ita bata saba da hayaniya haka ba. Ga sababin Gwaggo da bata fasa tsine ma boko ba ga surutun yaran sun cika mata kwanya, sai juyi take a katifa ta dade a haka a hankali kuma surutun ke raguwa alamun sun fara barci Gwaggo kuwa tuni ta hangame baki tayi barci. Sai lokacin barawon ya sace ta itama.

 

RAYUWARMU A YAU

 

©Ayeesh chuchu

®NWA

&

©Jam33lerh

{33}

Washegari Gwaggo ta tara mazan gidan da kukanta take sanar musu "muna nan mun hangame baki an kashe yarinyar nan, ku dubeta gansamemiya da ita wai ba yanzu zatayi aure ba, to wallahi bazan lamunta ba, ba dai a zuri'a ta ba karatun boko ta wuce aji uku ai ba kanta, yanzu in aka bibiya ma ko na arabi basu saka ta ba don haka nan kusa kai Sa'adu ka samo mata miji ka bashi Allah ya rufa asiri". 

Aisha da ke uwar daka bata san lokacin da ta saki ihu ba duk suka firgita suka nufi ciki sai ganinta sukayi tana kuka. Gwaggo tayi tsaki 

"ki mutu ma, amma babu inda zaki koma kinzo gida kenan a nan kuma zamu sa ma miki miji kiyi auren ki, karatu kuma Allah ya karba". Suka had'a baki wurin fad'in "hakane Gwaggo maganarki gaskiya ce". 

Baba Amadu dayike duk yafisu zafi yace "duba fa sa'anninta su Saddik'a kowacce ta kammala gidan mijinta cikin rufin asiri gashi har sun fara aje iyali, Ba zamu sa miki ido ki zama uwar mata ai bake kika haifemu ba", ya juya wurin Gwaggo

"ai kar ku damu ni zan samo mata miji ko sadaka ne a bada ita a huta itama ta nasu wuri daya". 

Baba Muntak'a ya tare " shikenan ma haka za'ayi, ke kuma cire rai da wani boko can, inba 'yan iska ba wa kike gani a jami'a?, ya buga tsaki "mu da yaranmu da bamuyi ba kinga mun kasa jin dadin rayuwa?. 

Baba Sa'adu da ranshi ya gama baci yace "ai ni bansan turbar yahudu suka d'aura min 'ya'ya ba", ya fad'a hana harararta

"shi marik'in nata daya kawota yace in ya dawo daga Kaduna yau zai biyo muyi sallama, kai tsaye ma zan fada masa tazo kenan kuma aurar da ita zanyi da gaggawa".

A firgice take kallonsu duka, dama ba wani soyayya da shakuwa tsakaninsu don haka take jin tsanarsu na d'arsuwa a ranta "Wannan wace irin rayuwa ce daga zuwanta zata fara fuskantar matsaloli? to meye aibun bokon da suke tada jijiyoyin wuya kansa".

Muryar Gwaggo ta tsinkaya cikin murna take shi ma yaran albarka sannan ta sallame su ta dauki mayafinta da kwano ta fita. Aisha ta koma ta jingina da bango tana tunanin mafita.

Da gaggawa ta jawo wayarta ta tura ma kawunta text ta sanar masa dukkan abinda ya faru tare da rokonshi ya taimaketa kar a kashe mata rayuwa.

 

{34}

Wuraren azahar yaro ya shigo gidan yace "wai wani Alhaji a katuwar mota yana sallama da mazan gidan yace ace kawun Aisha ne..." Kafin yaron ya dire Baba Amadu ya shura takalmanshi da sauri ya fita.

Da fara'a ya tare shi ya masa jagora d'akin zaure suka gaisa suka taba hira. Baba Amadu yace "Alhaji wallahi naji dadin ganinka inda kasan an min albishir da aljanna". Alhajin yace "toh da matsala kenan? ka fad'i ko meye ina saurarenka". 

Baba Amadu ya wage baki tare da gyara zama 

"um uhm dama matsaloli ne suka tarun min wallahi Alhaji babu tayi min dabaibayi abincin da za'aci a gida na kanshi ya gagara, kaga gidan nan inaga nafi kowa iyali. Alhaji ywyi dariya sosai daga bisani yayi shiru. Shi kuma ya cigaba 

"kasan kuma mutum da gane gane a wannan halin na gano wata bazawara can fambeguwa gidan da kanwarmu ke aure, tsakani da Allah rai na ya biya har nayi magana ma an sa rana, ranar juma'ar nan za'a daura aure". Yayi shiru yana kallon Alhaji kasa kasa.

Yace "cigaba ina jin ka". 

"Dama nace Dan Allah ka taimaka min Allah ya gani..." ya bude masa aljihunsa "ka ga wallahi bani da ko kobo ban aje ba ban ba wani ajiya ba bani da halin biyan sadaki bare aje ga maganar lefe Alhaji ka taimakeni yanda Allah ya rufa maka asiri, shiyasa ake ganin kullum ina k'arewa ga rama kamar wanda ake miyar biki dashi, to iyali sun taso ka gaba kusan rai 16 a kasa na". Ya k'arashe maganar murya a raunane.

Alhaji yayi dariya irin ta manya "Amadu kenan to baka da kudi kake tunanin karin aure fisabilillahi, yaranka nawa kace? 

Ya jinjina kai alamar tunani "gaskia ina ga kiris ya rage su cike ashirin duk da wadanda muka rabu da iyayensu suka tafi dasu".

Alhaji ya girgiza kai cike da takaici kamar ba zai magana ba dai yace "to amma ka duba ga 17 gabanka ka kasa kula da su kuma kake kokarin rakito wani auren? Duk kayi yaya dasu?

Ya d'an bata rai "Annabi yace in kaga ka auri daya bakayi kudi ba ka kara, ni ko nayi kusan 6 kenan har yau ba sa'a". 

Alhaji ya yamutsa fuska alamar maganar ta fara gundurarshi "daman fa haka kuke fakewa da maganar annabi ku fassara abinda yace da son ranku, Allah ya ganar da ku". Ya karkace ya zaro kudi ya mika masa yace "kiramin 'yan uwanka sauri nake, banso ma dadewa haka ba". 

Jikinshi na rawa ya karba yana godiya "k'yale su Alhaji ganinsu ma wani bata lokacin ne muje in raka ka". Ya mike daga durk'uson da yayi suka fita yanata zuba godiya har da bude masa mota. ya rusunar da kai Alhaji 

"to dan Allah ka taimakeni da naira dari inyi ma iyali cefane, wannan sai in biya sadakin da sauran hidimomi". 

Key din da yake kokarin sawa jikin mota ya su'buce masa ya kalleshi da kyau yana son tabbatarwa shin da gaske daga bakin Amadu maganar ta fito ko kunnenshi ne? bisa ga mamakinsa bai fasa zuba masa addu'a da kirari ba kamar tsohon maroki. 

Bai ce komai ba don ya na masa tunanin ta'buwar hankali ya k'ara zaro wasu kudin ya mika masa "to dan Allah ga amanar Aisha nan kar inji wani mummunan labari, kuma in hutunsu ya k'are a barta ta dawo dan Allah". 

"Ai Alhaji Usman karka damu in ma ta kama da kaina zan tasota gaba in dawo da ita don na fara jin wani kishin daga 'yanuwa na wanda ni ban lamunta ba". Yayi murmushi ya daga masa hannu ya wuce ya barshi da godiya kamar zai kwanta masa. 

Tunani da al'ajabi fal zuciyarshi "Mutum diya 17 mata 3 yana maular naira dari kuma yana hangen wani aure, kai Allah yayi mana magani".

RAYUWARMU A YAU

 

© Ayeesh Chuchu

®NWA

&

© Jam33lerh

 

{35}

Bayan ya koma gida ya kira Aisha ya labarta mata yanda sukayi. Sukayi ta dariya gami da al'ajabin abin daga bisani yayi mata nasiha sosai sukayi sallama.

Aisha akwai saurin sabo saidai miskilanci bata da hayaniya magana bata dameta ba. Cikin k'ank'anin lokaci ta saba da mutanen gidan tana k'ok'arin shiga cikinsu suyi hira har ta tayasu aikace aikacen gida su yita mamaki don basu saba ba yaransu sam basu san taya iyaye aiki ba sunfi gane suyi hira da wasa.

Suna zaune ita da Saddik'a a bakin k'ofar dakinsu. Aisha na rik'e da jaririyar 'yar firit tana juya kai da k'yar hannu a baki tana tsotsa. Tausayin 'yar ya kamata ta k'ara rungumeta "wai Saddik'a ko madara baki ba ta ne? Tunda ruwan nonon kince ba isarta yake ba gashi yanzu ya koma bangare daya". Saddik'a tayi murmushi iya lebe "ana ta neman kafiya da abinda za'a wa ke ta madara kema neman zance kawai kike".

Aisha tayi shiru tana nazari tun da tazo fa ta lura gidan kowa ci da kanshi yake ba iyayen ba ba yaran ba, ita kanta yanzu ita ke siya ma kanta da Gwaggo, a hakane ake zanxen aurar da ita a nan, tab Allah ya tsareni" ta fada a fili. Ta k'ara duban yarinyar dake barci numfashin na fita da k'yar tausayinta ya k'ara kamata. Ta yafito yaro ta ciro kudi daga k'ugunta ta bashi tace yayi maza ya siyo mata madarar yara ta kuma mika masa naira goma daban tace ta bashi. Da gudun shi ya fita yana murna.

Saddik'a tayi dariya tana firfita ciwon "yaran gidan nan sun koya miki hankali ko? Ta kasa kallonta wani irin tashin zuciya take ji ta mike tana fadin

"wallahi fa".

 

* * * * * * * * * * * * 

"Ku matsa, ku matsa nan, yauwa to ku shigo dasu, kuyi hankali mana karku bubbugesu". 

Baba Amadu ya shigo tare da wasu k'artin maza d'auke da katakai gado da sif ya nuna musu d'aki suka saka ya ciro kudi ya basu suka fita.

Matanshi duk suka taso suna tambaya "lafiya malam? tun jiya kake ta gyare gyare cikin dak'in nan sai kace dakin mace ko dai aure zaka k'ara ne bamu da labari? Cewar Amarya. Ya kalle a kaikaice

"Idan ma auren zan k'ara laifine?

"Au dama aure zakayi shine kabi duk ka rage mana fadin dakuna? Ta fada a raunane.

"Eh to idan ban ragi d'akunan na nema mata daki ba ina zan kaita? kaji min ja'ira". 

Amarya ta fashe da kuka "amma malam baka kyauta mana a gidan nan mu kanmu da muke tare da kai baka iyar mana ba ka jajibo wata kuma? Yayi dariyar cikin nuna ko in kula "to albishirinku, gobe amarya zata tare sai ku fara shirye shirye".

Inna Habi wacce tunda aka fara maganar bata tanka ba tace "shiri kai ta kama kai me abu, mu kuwa ko a gefen zaninmu itama da kaga tana kuka sa kanta tayi, mu yau muke da kai? aure irin naka ai sai dai fara ma amarya k'irgen kwanaki".

" Aniyarki ta biki munafuka algumguma bakinki ya sari d'anyen kashi, wannan ba farar kafa gareta irin taku ba don na hango sa'a ba kadan ba, ni da kaina na duba auren nan alheri za'a k'ulla kuma zaku sha mamaki".

Tace "wannan kuma kai ka jiyo, mu 'yan kallo ne".

"Ai malam kai kai d'in nan sai kaci wutar Allah annamimi, ai ido na sa maka nan ka gama zage su Alhaji Usman amma yana zuwa kabi ka kanainayeshi ka kwashi gara kayi ma 'yan uwanka buk'ulu ka kalmashe kudi ka ta tafi neman aure alhalin ga babban hakk'i a gidanka ka kasa saukewa, malam an dai ji kunya". Inna amarya ta koro masa wannan jawabi tana nuna masa yatsanta.

Ya fara hargagin borin kunya a hankali ya sulale ya bar gidan. 

RAYUWARMU A YAU

 

©Jam33lerh

&

©Chuchu

®NWA

 

{36}

Washegari juma'a aka daura auren Amadu da Mariya shekara kusan goma da mutuwar aurenta kuma bata taba haihuwa ba. Da kanshi yaje ya dauko ta, mutanen gida saboda tsabar gulma har hira dare suka dasa don kawai suga zuwan amarya. Sai gasu sun shigo tare idonta kyar, suka sa shewa 

"ashe ma tanada abin gori, mun sa ido dai muga kamun ludayinta"

Basu kula su ba suka shige d'aki ya sa sakata daga nan duk suka watse.

Dare ya tsala yaran suna kwance d'akin Gwaggo gaba dayansu barci ya kwashesu. Kamar a mafarki taji hannu na tafiya a tsakanin kafafuwanta tayi lamo tana son ta gasgata shin abinda takeji aljanin dare da ake fada ne ko kuwa mafarki take yi?. Jin abin na neman wuce gona da iri tana ji za'a keta mata haddi bata da alhaki, ta dan motsa domin taji alamar saukar numfashin mutum daf da ita. Ta sake motsawa a karo na biyu ko zai hankalta, ina sai ma kokarin shafo kirjinta yake.

Da sauri ta cafki hannun tare da fasa ihu, ya danne bakinta da karfi yana kici kicin danneta. Da karsashi ta gantsara masa cizo iyakar karfinta ya sakeshi ba shiri, ya fita a guje. Ta lalubo wayarta ta haska d'akin taga wasunsu sun farka amma ba wanda ya tanka tace "idonku biyu ne? Wani ne ya shigo yana neman mim lalata".

Sautin tsaki taji saidai bazata iya shaida kowaye ba, mai tsakin tace "dallah in zaki kwanta ki mana shiru ki kwanta muna barcinmu kin katsemu da ihu". Ta sake buga tsaki. Dakin ya kara daukar tsit can kuma taji sautin minsharinsu.

Ta koma ta kwanta jikinta ba inda baya rawa tana mai cike da bakin cikin kasancewarta wannan gida. Bata mantawa wata rana da daddare Gwaggo ta matsa mata ta fita ta siyo mata ashana a hanyar dawowa cikin zaure cikin duhu taji an cafkota, tayi k'okarin haska shi da wayar ta kuma shaida fuskarshi Sabi'u ne yaron Inna habi ya rike mata hannu yana zayyana mata maganganun banza. Ita al'ajabi ne ya daskarar da ita a wurin. Tayi kici kicin kwacewa don ta wuce salin alin ba tare da kowa yaji ba, amma sai k'ok'arin rungumota yake, sai da ta watsa masa mari ta zageshi tsaf sannan ya bata hanya. Har yau d'innan kuwa kunyar had'a ido da ita yake a fili tace "to ko shi ne?

Ta share hawayen da suka taru a idonta, ta rintse idon hoton abinda ta gani d'azu yana mata yawo a kai. Gab da la'asar kowa na daki ita ta fito zata shiga bayi, tana dunfaro kofar taji sautin nishi da sambatu ta sake saurarawa don ta gasgata ilai kuwa sautin kala biyu mabambanta. 

Ta k'udurta ma ranta ita kuwa sai taga ko waye da wannan d'anyen aiki, ta koma da baya da sauri ta labe a kofar sasan Gwaggo yanda zata iya hango hanyar bayin da kyau. Bayan dogon lokaci har kafafunta sun soma zafi sai taga an turo kofar a hankali kan namiji ya lek'o ya duba ko'ina sannan ya fito yana zare ido had'e da share gumi can kuma macen ta fito itama d'auke da fargaba tana tafiya cikin sand'a.

Sulalewa tayi wurin ta zauna domin idanunta sun hangota mata babban al'amari, Baba Muntaka da Amarya matar Baba Amadu wato kenan sune taji suna aikata masha'a "Innalillahi wa inna ilaihir rajiun". 

Haka ta wunin yau bata da karsashi. Shine kuma yanzu ake neman a dorar mata da damuwar da neman keta mata rigar mutunci. Anya mutanen gidan nan suna tsoron Allah kuwa shin basu gudun had'uwarsu da ubangiji? tab gaskiya al'amarinsu akwai gyara ba kadan ba, ni kuma lokacin bari na gidan ya zo tun da sauran damata". 

Wani zazzafan kuka yazo mata, ta rufe rufe bakinta ta hanashi fitowa sai na fuskarta dake ta zuba bisa kuncinta. Kafin tazo tayi d'okin zuwa ganin dangin Babanta ba kadan ba duk da basu nemeta ba marikanta basu taba nuna mata rashin kirkinsu ba saidai nasihar su bisu a duk inda suke. Allah sarki Yaya gwara da bakazo ba bare ka ga wannan kwamacalar rayuwa. 

Bata sake komawa barci ba don tsorace take sosai, motsi kadan zata haska d'akin.

RAYUWARMU A YAU

 

©Jam33lerh

&

©Ayeesh Chuchu

®NWA

 

{37}

Washegari ta tashi idanunta suntum Gwaggo babu tambayar da batayi mata ba duk kuwa da taji abinda ya faru jiya sai ce mata tayi "in don abin jiya ne ai sai da na fada miki ki rik'a kwana da dogon wando 'yan mata gidan nan basa kwanciya haka". Bata ce mata komai ba sai ta watsar da lamarinta tayi kokarin maida komai ba komai ba ta danne zuciyarta ta shiga cikin mutane.

Tana tafe tana gyara d'ankwalinta taji an fisgota an turata wani lungu. Zatayi ihu ya damke bakinta da iyakacin karfinsa ya k'ank'antar da ido yana mata kallon cikin ido kamar tsohon maye. Jikinta ba inda baya rawa yayi murmushin yaudara ya sassauta rik'on da yayi mata a raunane tace "Anas! 

Ya lashi lab'bansa "Baby ya akayi ne? Ashe ma kinsan sunana, ni yanzu ba wannan ba kinga dai ke wayayyiya ce da girmanki kuma kinsan inda duniya ta sa gaba kin san eh yane kin gane ai". Ya fad'a yana kanne ido d'aya da k'ok'arin shafo kumatunta ta buge hannunsa. Bai damu ba ya cigaba "kawai ki fada min ina zamu hade mu eeerh kin gane ai ko nawa kike so zan baki". Ya shafa aljihunsa yana kallonta ta kasan ido.

Takaici,bacin rai da dana sani suka cika mata zuciya. Ta kalleshi a lalace daga sama har kasa wani kazami dashi sungul hamama wanda inda yasan gatan da take dashi a bangaren mahaifiyarta ko kusa da ita akace yazo sai yayi shakka. 

Ya manna ta da bango yana kokarin kusanto fuskarshi gare, a firgice ta daka masa tsawa "me kake tunanin yi min? ya marairaice fuska yana rike cikinsa "dan girman Allah ki taimakeni zan iya mutuwa, na riga na kamu". Ya k'ask'antar da murya cikin rada yana mata magiya "ki taimakeni ko yi d'aya ne, d'iga fa nake" ta yi saurin dakatar dashi da hannunta.

Tsanarsa k'arara ta bayyana a fuskarta "yanzu kai kasan Allah? Ya kalleta a kaikaice "ina dan malam kina fada min sanin Allah, 'yan mata ki adana wa'azinki, rayuwa ce in bakiji dad'inta ba yanzu shikenan ta wuce ki, kawai ki sake kici duniyarki". 

Tayi murmushin takaici ta maido da kanta ga kallonshi tana k'ok'arin danne hamamin bakinsa da ke neman sumar da ita "Naji dadi da kasan Allah d'an malam, amma ka sani abinda kayi ma d'an wani kaima sai anyi ma naka, ko dayike gashi nan an fara aikatawa a gidan ishara gareku baku lura ba. 

Yayi k'asa da kansa a kunyace. 

"Kayi dubi zuwa ga k'annenka wad'anda bai kamata ace ko rik'e hannu su san ma'anarsa ba amma sunsan su danne junansu suji dadi hmm. Kuma kana maganar cin zamani kai kana da tabbacin zaka d'ara daga wurin nan Allah bai dauki ranka ba? me zaka ce masa a haduwarku ranar hisabi, wai ni shin gidan nan kusan cewa ku mutane ne ba dabbobi ba? Gaba daya rayuwarku kamanceceniya take da ta dabbobi. Na gode ma Allah da ban tashi a wannan forsaken house din ba. Kuma ina shawartaka ka gaggauta tuba rayuwa bata da tabbas. Rayuwar gidan nan darasi ne babba ko da yini mutum yazo sai ya fahimci halakar da kuke ciki. Tsabar masifa yayyi su hakkewa kannensu, dan uwa yaci amanar dan uwansa wace irin rayuwa ce wannan kuka dauka? 

Ta share k'wallar da ke ta ambaliya a fuskarta 

"Allah ya shirye ku".

Ta tafi ta barshi nan jiki a sanyaye yana juya maganganunta. 

RAYUWARMU A YAU

 

© Ayeesh Chuchu

®NWA

©Jam33lerh

 

{38}

Bata ƙi shiga ciki ba don in tace zata koma sasan Gwaggo darasin tofin Allah ma boko zata dasa mata. Saida ta share hawayenta ta daidaita natsuwarta sannan ta shiga. 

Mutanen gidan suna tsakar gida cikin tarkace da bola suna hirar da bata dace ba gaban yaransu, su kuma 'ya'yan su natsu kamar masu ɗaukar darasi suna sauraren zancen manya. Ta musu sannu da gida ta wuce ta shiga dakinsu Salima inda taji murya Saddik'a.

"Ah ah yau Salima ce har ina gobe zanzo gidanki"

Tayi yaƙe "ai nima bansan da zuwanki ba sai da nazo"

Suka gaisa sukayi raha kamar sun dade da sanin juna.

Ta juya tana kallon Inna habi da ke lallamin ƴarta taje mata aike ƴar matashiyar tana kumbure kumbure da faɗin "ni fa nace miki ba zani ba, ba ga Isma'il nan ba sai ni aka raina kamar mara gata kullum a aikace".

Aisha ta girgiza kai a sanyaye. Farkon zuwanta gidan idan taga irin haka tana ma yaran fada akan rashin da'arsu ga iyayensu sai taga iyayen basa son fad'an da take, ta zuba musu ido su babbake ma ba ruwanta.

Tace "wai ni ko Inna ki bani tsintsiya mana in share tsakar gidan nan ku naga baku gudun cuta sati guda yau rabon da a share fa".

Saddik'a tace "sati gudan ma don ke kika share ne ai zuwanki yayi mana rana kamar ki zauna ko Inna. Inna tayi dariya 

"Wallahi kau kinga mu yaranmu ina muke da hurumin sa su aiki ai ba zasuyi ba, ga dai yaran kirki nan da muka mora su Salima duk kyuiwarsu da zumɓure zumɓure zakiga sun mana aiki amma banda wadan nan" ta karashe maganar tana nuna yarinyar suna dariya 

"Da kiga gida kamar bolar da ta shekara, ban daki kuwa idan zaki shiga sai kin haɗa da d'aure hanci da kyalle saboda tsabar gumewa da yakeyi ke dai Allah yayi miki albarka".

Tace "amin", ta nisa 

To ai inna ku baku sani ba cutar da kanku kuke yi rashin tsaftar nan, kiga fa annabi ma da kanshi yace tsafta tana daga cikin imani bafa an faɗa ne don muji mu manta ba a'a muyi a aikace shine ingancinta. Wallahi ban kyamace ku ba, na rantse in acan ne naje gida irin haka ko ruwa bazan iya sha ba, ina mai tabbatar muku ya Umar ko kashe shi za'ayi bazai iya k'wakk'waran minti 30 nan ba. Tsafta fa ba karamar abu bace tana k'ara kima, mutunci da daraja a idon mutane. Yanzu misali Saddika yanda ta bani labarin zamanta gidan Kabiru in za'a lura ba karami raini ne tsakaninta da Ladidi ba, taya ma za'ayi mace ƴar uwata ta bude baki ta jefeni da kalmomin wari kike, bazanci abinci dake ba, bana son kina magana kusa dani bakinki sai ya sa mutum ciwon ciki, abin k'arin takaici ta ɗauki sabulu ta baki kiyi wanka me yafi wannan kalamai tozarci fisabilillahi, me ya janyo miki ƙazanta haka ke ba yara kika tara ba. 

RAYUWARMU A YAU

 

©Chuchu

®NWA

&

©Jam33lerh

 

{39}

Sukayi suguri suna saurarenta da alama maganganun nata suna ratsasu. Ko da ta duba sai taga ashe mutanen tsakar gida sun fara shigowa dakin suna sauraren jawabinta. Taja ajiyar zuciya ta cigaba

"Me zai sa miji bazai ci kasuwa kanki ba ya taka ki son ranshi kin bada kanki, ita fa mace 'yar kwalisa da gwalli ce wallahi talauci ba hauka bane, ku bar ganin babu da ya kanainaye ku inda kun iya kula da kanku ku din wasu irin mata ne da sai anyi rububin ku maza suyi ta rawar jikin yi muku hidima to amma ina tun yarinta gidan nan rayuwar 'ya'yanku ke mutuwa murus kamar misali band'aki ku. Bandaki ba karamin makami bane wurin tarwatsa rayuwarku da jindadinku".

Sukace "iyye au haba" cike da mamaki 

Ta kada musu kanta cikin tabbatarwa "kwarai kuwa kun sake shi ba gyara ba tsaftacewa, ku kuke labarta min sai yayi wata da watanni bai ga omo da sunan wanki ba ina da tabbacin hassada da kyashi sune suka taka muhimmiyar rawa a wannan bangare, kunsan me kalmar mace ke nufin? ta juya tana kallonsu fuskarta a dan kunyace.

"ku iyayena ne ba saina tsaya fasa muku ba don kun fini sanin amfaninta ga d'a namiji to kusani kwayoyin cutar da ke daskarewa a bandakunanku da k'aikayin da kuke rainawa shi ke janyo muku raini a wurin mazajenku to kun riga kun salance babu wani ragowar gardi da amfani tattare da ku ba dole namiji ya kalli tsabar idonki ya kiraki JAKA ba". Ina da tabbacin mu ukun nan idan muka fita za'a ce kun haifeni barinma ke Saddika ji jikin ya saki ki zama wata kaya da ko sadaka aka baiwa namiji a yanzu saidai ya dankaki ya kalla ke kallo ma baki isheshi ba a wannan halin dan Allah ki gyara. Kazanta ba karamar illa take wa mace ba fa. Bakar tsana take sakawa tsakaninki da miji.

Bangaren tarbiyyar gidannan ma kawai abin k'alubalanta ne, babu abinda kuke koya ma yaranku sai salon rashin albarka ga mazajensu. Suka kalleta da kaduwa. Bata damu ba tace "eh mana ai ba nufi da baki ba a'a mu'amalarku ku da iyayensu a gabansu, baku san duk wata d'iya tana koyi da mahaifiyarta bane? Ai duk abinda uwa tayi da shi 'yarta ke tashi.

Akwai maganganu dayawa a bakina game da ku amma shiru na zai fi zama alkhairi a hankali zaku fahimta, amma bazan 'boye muku ba da gaske na kyamaci duk wata halayya da zamantakewa ta gidan nan, ku gafarce ni ba niyyata tozarta ku ba kuma duk wanda na bata ma rai a zamana ya yafe min, lokacin bari na gidan ya zo gobe zan tafi.

Gaba daya an rasa mai magana ta bi ta kashe musu jiki da wad'annan magnganu nata sai gyada kai suke suna k'arawa. Barinma Saddik'a daka kallon jikinta ita kanta tasan bisa dole Innarta ke zaune da ita dakin.

Washe gari kawunta da kanshi yazo daukarta kowa gidan ranshi bai so tafiyarta ba, musamman d'an zaman da tayi na wata 2 sun k'aru da ita ba kadan ba sam abin hannunta bai rufe mata ido ba, ga ganin girma na gaba abinda yaransu suka rasa. Zata tafi ta ba Saddik'a kudi masu yawa da kayan sawa tace ta kula da kanta da 'yarta tayi kokarin gyara kanta ta nema ma kanta maganin ciwon nan itama ta dawo mace sak duk da alhamdulillahi sauk'i ya fara samuwa ciwon nata warkewa. 

Salima ma ta roketa a 'boye ta bata kudi a cewarta ko da wasa bata so 'yan gidan su san babun da take ciki. Aisha tayi kokarin mata nasiha d'aid'ai gwargwado daga bisani ta kusu sallama suna kuka tana yi ta shiga mota da alkawarin zata rik'a zuwa in ta sami hutu

 

RAYUWARMU A YAU

 

©Jam33lerh

&

© Ayeesh_Chuchu

®NWA

 

{40}

 

Sai bayan tafiyarta kewarta ke dad'a nuk'urk'usarsu, har suka d'an tabuka da yin amfani da shawararta ta bangaren tsafta kad'ai. Sun kwatanta tsaftar ta kwana biyu daga baya suka koma gidan jiya sak ma abinda ya k'aru.

* * * * *

Da sauri mai had'e da gudu ya shiga gidan yana kwala ma Saddik'a kira har yan cin karo. Amaryarsa Mariya ta kalle shi ta saki tsaki ya kalle kamar zai magana ya kauda kai kawai.

"Wai ba zaki fito bane kin barni tsaye inata shela ni kadai".

Tana daga cikin d'aki tace "gani nan Baba ina shayar da Zainabu ne".

Ya jingina da bango ya rungume hannu "in zaki taho ki tarkato har Zainabun ku zo". Yayi shiru na wasu sakwanni can yace "Wai shin Saddika sai na saba miki zaki fito ne? Shegiyar d'iyar taki da bata koshi hidimarta tafi tawa ne?. Tayi saurin fitowa ta durkusa gabanshi tana cigaba da shayar da yarinyar.

Ya kallesu ya watsar ya gyara tsayuwarsa.

"Yau Allah ya yanke min wahalata a kanku ke da yamutsattsiyar 'yarki ga mijinki can ya zo tafiya dake nima in huta hatsina ya k'ara auki". Ta dago ta kalleshi a razane 

"Kabiru? 

Ya hararta "au to ko auren maza biyu ne kanki? kina da wani mijin ne banda shi? kaji min shashasha, don haka maza tarkato komatsanku sawunki a likafa ki bi mijinki".

Matar Baba Muntak'a tace "kice Saddik'a yau lokacin tashi yayi dama jiya ina jinku da Innarki kuna gwabzawa ai gwara ki tafi d'in dai".

Yace "ah to watanni shidan nan da nayi ina wahala da ita da diyarta ba gaira ba dalili ai nayi namijin k'ok'ari", "ki tashi mana kin kafa min ido, jiranki fa yake".

Da gudunta ta tashi ta sab'a 'yarta ta shiga ciki ta kwaso kayansu a buhu, ta fito tana goye da 'yar ta tarar da Mariya na fadin "wai dama haka akeyi miji ya jingine yarinya wata shida amma daga dawowarsa ba bin ba'asi ba jan aji jeka ka dawo, za'a bashi ya tafi da ita, wannan ai rashin hankali ne da ganganci". 

Inna amrya(Innar Saddika) tace "ture ma ta jan aji ai ta zaunu ta koma d'in shi yafi amma danginsa da bamu taba gani ko jin labarinsu ba abin tamabaya ne, malam ko ya fad'a muku wani abu". Ya kallesu fuskarsa a murtuke 

"kai kar ku kawo min zancen banza dangiro nace dangiro kunji ko, tunda ya bani uzurinsa cewa aikin babbar mota ya samu a ranar da nak'udar tazo mata maigidansu ya turasu kudu tsawon lokacin nan, to in baije ba ya zauna gida ya rungume hannu mai zasuci ko da me zai kula dasu? yace dai ragon da ba'a yanka ma d'iyar ba zai yanka ko bayan shekaru nawa ne". 

Wannan kalma ita ta basu dariya duk suka kwashe da dariya banda Saddik'a da Baba Amadu da ke kallonsu a sakarce. Inna habi tace "Allah malam watarana in kayi abu inta mamaki ko dai girma ne ya riga hankali, wannan magana tasa ai ba abin kamawa bace". Ta k'ara kwashewa da dariya.

Ransa ya gama baci sosai kafin ya bude baki sallamar da akayo daga waje ta katseshi da rawar jiki ya amsa yana yafito Saddika " 'yar nema gashi can shine da wannan sallama ya gaji da jira, wuce muje". 

Tayi ma iyayenta sallama ta bishi a baya bakinta ya kasa rufuwa don murna. Mariya tace "malam to surukin namu bazai zo ya gaishemu bane? Yana tafiya yace "ke dai wallahi fitinanniya ce mtswww".

A bakin kofar d'akin zaure suka tararda shi da shirin tafiyarsa fuskarsa ba yabo ba fallasa yana rik'e da kudi hannunsa yana ganinsu ya rusuna "to baba nagode nagode ga wannan a sayi goro". jiki na rawa ya karbe ya tura aljihu yana fadin

"gata nan maza ku kama hanya Allah shi albarka".

 

RAYUWARMU A YAU

© Jam33lerh

&

©Chuchungaye

®NWA

 

{41}

 

Yana ɗakin zaure yana kasafta kuɗin da Kabiru ya bashi ya riƙa ji yo hayaniya daga cikin gida. Ya tashi ya nemi maɓuya ya adana kuɗaɗen da kyau ya ɗauki hularsa ya saka ya fita.

Tsattsaye ya gansu sun sa Gwaggo tsakiya tanata jawabi muryarta a sama tana maimaita cewa 

"wannan abu da me yayi kama". 

Ya karasa yana faɗin "Gwaggo lafiya?. 

Sauran 'yan uwanshi maza da suka shigo a tare daga waje suna tayashi tambayarta tace "Ina fa lafiya naga rashin hankali ƙiri ƙiri ya za'ayi ace yaro ya jingine yarinya da tsohon ciki wata da watanni bai waiwayeta ba, rana tsaka ya dawo an tattarata an miƙa masa babu wanda ya rakata, iyye haka akeyi? wannan abin kunya ace ba ko ɗan rakiya daga ita sai shi". 

Ta share ƙwallarta "kuma don ba'a maida ni bakin komai babu wanda yayi tunanin kaita inyi mata faa, ni dai ba'a kyauta min ba". 

Baba Sa'adu ya tareta "Gwaggo ba haka bane kinganmu nan muna waje yaron nan yazo bai nememu da maganarba sai ubanta gashi, suka shige daki suka tattauna, Muntaƙa ya tashi zai bisu na hanashi abinda ba'a sa ka ba kasa ido, muna zaune mu dai sai gani mukayi sun wuce mijin ya tasata gaba bata ce mana ba muma muka kama bakinmu".

Gwaggo ta dauki salati "Amadu me nakeji haka? Ta fashe da kuka "tun da raina zumunci ke neman lalacewa to wallahi ban yafe ba". 

Ya shiga rarrashinta hankali tashe da kyar ya lallaɓata ta koma ɗaki ya dawo kan 'yan uwansa

"inace 'yata ce ni na haifi abuna, ba ruwan kowa da harkar iyali na a samin ido kawai banson shisshigi". Ya yi musu tijara sosai ya shige ɗakin mariya.

Sai da ta ɗau lokaci sannan ta bishi yana kwance bisa gadonta ta tsaya kanshi 

"miko min kuɗin da ka samo".

Batare da ya kalleta ba yace "wanne?

"Ka fini sani, ka bani kawai". Ta fada tana kaɗa jiki.

"Bai fa bani sisi ba, wannan da kike ganinshi matsiyacine bai da komai".

Ta daka masa tsawa "sai kace yau na sanka, a banza zakayi rawa kayi kiɗi ka uzuzzura suka tafi ba tare da kowa ya shiga lamarin ba , kaga malam in kana son kanka da arziki ka bani kafin in caje ka". 

Ya tashi a sanyaye yace "ina zuwa". Ya fita. 

Tace "ni kuma ina jiraye ko zama bazan ma".

Zuciyarsa cunkushe da damuwa da tuani, tun da ya aureta kamar ta asirceshi duk wani abu da yake samu ita ke tatseshi, kullum sai ya sayo mata nama ko da maula zaiyi, ita halayyarta da tazara tsakaninta da matansa.

"na dauko ma kaina wacce tafi karfi na" ya fada lokacin da ya dauko kudin yana jujjuyawa yana tunanin ragewa, bai dai rage d'in ba ya tattarasu ya kai mata ta karba da murmushi har haƙoranta na bayyana. 

"to je ka na sallameka barci zanyi anjima ka dawo". Ya fita jiki a mace.

 

RAYUWARMU A YAU 

©Jam33lerh

Ayeesh Chuchu 

®NWA

{42} 

Da shigar su gidan ta ci karo da Ladidi da ke wanke-wanke, ta bi gidan da kallo ko'ina tsab ba kamar bolar gidansu ba. 

Sallamarsu ta dago da Ladidi, fuskarta dauke da murmushi ta ce "lale marhabin da ma su jego".

Saddiqa ta washe baki tana mamakin tsabta irin ta Ladidi. Nan suka gaisa Ladidi ta karbi yarinyar. Kabiru na bud'e d'akin ta shiga, d'akin yayi bidi-bidi kamar makwancin jakkai. 

Ba tare da ta hankalta ba, tayi zamanta bashau kan gado. Ta bi Kabiru da kallo ta ce "Kabiru wai Ina ka tafi tun da ka kai ni gida ba bayani". Ko kallonta be yi ba, bare ta sa ran zai amsa ma ta. 

Nan Ladidi ta miko ma ta d'iyar ta Zainab. Ta amsa tasa ma ta mama a baki ta cigaba da yi ma Kabiru surutu da ya ba banza ajiyarta. 

Tashi ya yi ya fita ya bar gidan. Tashi tayi ta duba d'akin kamas babu abin sakawa bakin salati. 

Fitowa tayi sabe da Zainab ta lek'a d'akin Ladidi ta ce "Ladidi ko kin rage abinci dan Allah?". Tausayi Saddiqa ta ba Ladidi, ta juye sauran abinci da ke cikin tukunya ta mik'a ma Saddiqa ta amsa ta cinye tas. 

Ladidi ta ce "ya kamata dai Saddik'a ki gyara d'akin ku tunda ya dade be ga gyara ba". Saddik'a ta ce "toh yanzun nan Dana gama cin abinci zan gyara". 

Anyi sa'a tana gama ci ta hau aikin gyara d'akin. 

 

Da dare tana kwance ita da jaririyarta ta yi nisa a bacci ta ji ana neman hakke (keta ma ta haddi), firgigi ta mik'e ya sake danne ta, zata fasa ihu ya toshe bakin. Tana ji tana gani ya biya buk'atar shi ba da san ranta ba.

 

******************

Kutsa kai ta yi cikin gidan ba tare da izinin masu gidan ba. D'akin Salima ta nufa, ta na d'aga labule. Salima zaune a falonta ta mik'e k'afafu tana kwasar shinkafa garau-garau. Da tirtsetsen ciki a jikinta ak'alla zayyi wata shida ko bakwai. 

Saddik'a ta shigo cikin falon ba tare da ta damu da yin sallama ba. 

Ganin mutum tsaye kanta yasa ta firgita, ta kai duba ga Saddik'a ta ce "yanzu tsakani da Allah Saddik'a ko sallama ba zaka yi ba zaki fad'o man d'aki". 

Saddik'a ta ce "ke mantawa nayi fa, yanzu Salima ke ma ashe kuna cin garau-garau gidan ki?". 

Salima ta ce "shi ni ke marmarin ci dai ba ni son dafaduka sam yanzu". Ba ta Ankara ba Saddik'a ta ja filet d'in gaban Salima ta fara ci kamar tsohuwar mayunwaciya. 

Salima ta bi ta da kallon takaici dan ta rasa abinda za ta ce, ita ma ba koshi tayi ba. Haka nan ta hak'ura. K'agara ta yi Saddik'a ta tafi bata son ta fahimci halin da take ciki. Da dabara ta koreta a gidan.

 

Tun da Isyaku mijin su Salima ya tafi sau d'aya ya zo, kwanan shi daya kuma ya koma Abeokuta. 

 

Kwance take a kasan ledar d'akinta tana jin sanyin siminti saboda zafin da ake tsulalawa, yan hanjin cikinta ke ta yamutsewa a sakamakon yunwar da take ji. 

Ta mik'e da kyar ta fito tsakar gidan Gaje zaune ta tasa filet cike da awara. Ta ce "Maman Ameer ki taimaka ki ban kud'i cikin kud'in da Baban Ameer ya bada banda abinda zan ci". 

Shewa Gaje ta yi ta ce "ahayye! Tsiyar fa dan talaka kenan idan ya samu wuri, banza yar gidan talakawa idan ubanki ya bada kud'in sai ki zo ki amsa". 

Salima ta ce "ba ubana ya bada ba kamar yanda ke ma ba ubanki ya bada ba, banza jaka kuma dan ubanki kud'i sai na dauka". 

Karaf a kunnen Isyaku da ke shigowa, mari ya watsa ma Salima ya ce "dan uban ki yar matsiyata ki gaya mun idan a gidan ku uban ki na bada kud'in abinci, sai anan dan kin samu waje". 

Da gudu ta fad'a d'akinta ta na kukan takaicin gorin da mijinta yai ma ta gaban kishiya.

 

RAYUWARMU A YAU

© Jam33lerh

&

©Ayeesh Chuhu

®NWA

 

{43}

Babu wanda ya nemeta har washegari itama bata fito ba sai da cikinta ya hanata sukuni da k'ugi ta lallaba ta fita ta nufi kitchen ko zata sami abin sawa a baka. Gaje ta taras tana dama koko bata kalleta ba itama bata bi ta kanta ba ta fara bubbude tukwane tana jifa da dasu, duk don Gaje ta tanka bata tanka ta d'in ba tana gama damun ta d'auki bokitin kokon ta nufi d'akinta k'ananan yaranta na biye da ita a baya. 

Salima ta harari bayanta tana tsaye wurin tana sak'a da warwara ta san dai kayan abincinsu sun k'are bare ta d'iba ta dafa ma kanta. Ranta ya biya da kokon amma tana k'yashin tambayar Gaje.

Ta duba sama da k'asa sak'o da lungu ko ina bushe cikinta kuma bai fasa neman agaji ba k'arshe zuciyarta ta yanke mata shawara da sauri ta fita kicin d'in ta nufi d'akin Gaje.

Yana kwance bisa gadon Gaje da singileti jikinsa ita kuma tana saitin kafafunsa tana kur'bar kokon yaran ma na zazzaune cike da d'aki suna sha. Ta kare musu kallo zuciyarta na suya. 

Babu wanda ya nuna ya san tsayuwarta wurin ganin haka ta had'iye bakincikin da ya tokareta tace "Gaje ina nawa kokon?

" Baki nuna za ki sha ba ai, tunda dai kinsan ba ajiyeni kikayi ba bare in fita in girka ki ci".

Haka zaki ce? Baban ameer kana jinta? 

Bai daga kansa ba bare ya nuna yaji. Ta k'ara kuluwa tayi k'wafa ta durkusa ta fara kici kicin jawo bokitin da ta hango shi k'ark'ashin gado. Gaje ta diro da sauri

"ah ah ya haka wanne irin dabbanci ne haka dallah fita min a daki"

Bazan fita ba wallahi ai nima inada hakki" Ta fisgoshi gaba daya daga k'asan gadon.

"kinga kar ki zubar min, ki bari mana". Tanaja Gaje na ja har dai ya tuntsire ya zuba a kafarta ta saki k'ara tana kokarin duk'awa, bata kai ga haka ba taji saukar mari da ya ja hankalinsu gaba daya domin ba wanda yaga saukowarshi sai sautin marin. Dakin yayi tsit gaba dayansu cikinsu ya d'uri ruwa. Sarai sun san halinsa idan yaga k'wayoyin shinkafa ma sun zuba a k'asa tashin hankali yake musu a gidan bare wannan koko rabin bokiti alhalin lokacin da Salimar ta shiga yana fada ma Gaje cewa su aje har rana su sha. 

"Wai ke wace irin dabba ce? saboda gidan tsoho ko arzikin kokon babu wato kinga na banza ko ahine har da almubazzaranci, wallahi baki isa ba wannan asarar bazata hau ni ba maza ki tattarashi ki san yanda zakiyi dashi banso inga komai wurin nan". 

Tana d'urk'ushe kukan ma yak'i zuwa. Ya daka mata tsawa "tashi mana kuma har nan da kwana biyu bata da abinci gidan nan kinaji na ko". Ya fda yana kallon Gaje. Ya ja rigarsa ya zura ya fita. 

Jiki a sanyaye Gaje ta durkusa ta tallabo Salima cikin tausayawa kokon da zafinshi sosai. Ta kalli k'afar har ta fara dagawa "muje in kaiki daki" 

"Banso". 

Ta buge mata hannu tana cije baki saboda zafin dake shigarta a hankali "ki bari in taimaka miki baki ganin yanda k'unar ta tasa" 

"ki barni nace, azzaluma bake ki sa akayi min haka ba" ta fashe da kuka ta dafa bango tana zubar k'walla ta rarrafa ta fita.

'Dakinta ta shiga ta janyo mayafi ta dauki takalminta a hannu domin taga bazai sawu mata ba a kafar nan da ke maza zugi kadan kadan. Tazo fita d'an Gaje ya shigo a guje yana haki ya shiga d'akinsu yana fadin 

"mama ga Baba can a teburin Ali mai shayi yana cin kayan dadinsa har da kwai fa da wannan taliyar" yana fada mata yana k'ara jaddadawa. Gaje tace "teburin mai shayi? lallai ma maigida shine amma yace min bazai sha koko ba ya koshi iyye kaji min zalunci..." Bata k'arasa jin sauran ba ta fita. 

Ta tsayar da kekenapep ta shiga duk da sanin da tayi bata da ko sisi. Suna isa gida ta sami yaro ta aikashi wurin innarta ya samo mata kudi. Tana ciki tana jira ta hango Anas ta k'wala masa kira, sai da ya gama jan mata aji mai motar har ya soma k'orafi ta fito ta rokeshi Allah da annabi ya taimaketa ya biya mata kud'i ya rantse ya k'ara bashi dashhi naira hamsin jal ya rage masa duniyar nan. Kamar zatayi kuka yayi tafiyarshi ya barta, yaron ma ya dawo Inna tace "bata da kwandala ma". Ta duba gabas kudu arewa babu mahalukin da zai biya mata. mai motar da ranshi ya gama 'baci ya fito ya zage ta tas yayi mata Allah ya isa yaja motarshi.

Ta d'ingisa ta shiga gida suna zazzaune yanda suka saba ta zauna bakin kofar dakin Innarta tana rike da kafarta da zugin ya karu fiye da dazu ta soma yarfe hannu. Suka baibaeta suna tambayar lafiya bata iya cewa komaiba sai k'afar ta rik'a nuna musu. Gwaggo ta ma da labari ya isketo tazo tana musu sababi bazaku bata taimakon gaggawa ba kun tsaya kanta wannan ai shashanci ne" Ta koma sasanta da sauri ta dawo d'auke da kwano ta jiko gishiri dayan hannunta kuma rike da tawada. Aka shafa mata tana ihu suka rirriketa lokaci k'afar ta kwashe abin tausayi ashe ba kadan ta k'one ba.

Cicci'barta sukayi suka kaita d'aki. Sai dare baba Amadu ya dawo aka fad'a masa yayi fad'a sosai yace "mai yasa basu mayarda ita dakin mijinta tayi jinya ba, ina samana baza'a dauro min lalura ba". 

Mariya tace "Malam jiranka muke a akaita chemist tunda ba'a san me ya baro da ita gidan mijin sai a tambayi ba'asi idan ta warware tunda ai tace mijin na gari". 

Ya langwabar da kai "Ni dai kiyi hakuri su kansu sun sani duk gidan nan ba wanda na taba kaiwa asibiti duk tsananin ciwo in ba ke ba, suma din sai dai su kai kansu in suna da kudi to ni haka Allah ya so ya ganni fak'iri bazan iya asarar kudina a asibiti ba gamu da addu'a takobin mumini" 

"au haka zakace?

Yayi shiru ya sadda kai k'asa ta kalli kishiyoyinta 

" kuna kallo yake muku zaluncin nan kuka kame bakinku tab wallahi bazan d'auka ba ku kuka yarda hu'un". 

Ba wacce ta tanka ta domin tsanin kishinta suke. Ta gaji da surutanta ta bar dakin. 

Shima har safe bai fasa nacin fad'a barin Salima da akayi a gidan ba. Washe gari tun safe ya wanke k'afa zuwa gidanta don ya sami mijinta bai tarar da shi ba ya dawo ya sauke bacinranshi kan Salimar da Innarta. Da yamma ma ya koma bai sameshi ba haka nan bai gajiya ba da dare ma ya koma ya ci sa'a ya sameshi. Isiyaku bai bari yayi magana ba ya katseshi da fadin yana da uzuri yaje zaizo gidan. Bai zo din ba sai bayan kwana biyu.

 

RAYUWARMU A YAU

©Jam33lerh 

&

©Ayeesh Chuchu

®NWA

 

{44}

Da rawar jiki Malam Amadu ya masa shimfida ya kirawo Salima k'afarta da sauk'i dai ba laifi . Tana zama ya rufeta da fad'a yana zaginta. Isiyaku bai ce kanzil ba har baban ya gaji da fad'an ya koma kan Isiyakun yana bashi hakuri yace 

"kasan mata dabbobine ba hankali suka cika ba sai ana hakuri ni kaina ka ganni nan", ya nuna kanshi "don dai Allah ya yini da tsananin hakuri ne da yaushe zaka ganni garas da lafiyata, ni kadai nasan uk'ubar da iyayensu ke shayar dani, to ya muka iya mu maza sun zame mana dole in muka taimakesu muka zauna dasu Allah zai bamu lada". 

Isyaku yayi gyaran murya babu digon surukuta sam a tattare dashi yace "Baba kana ji?

Ya yage bakinsa "eh Alhaji ina jinka"

"to kai ne mata suka zame maka dole ni kam zan iya sawwak'e mata a yanzu haka dama na gaji da ita saboda kai ne kawai..."

"lailaha illallahu kaji ba, kaji irinta ba lahaula wala kuwwata illa billahi wannan wannan tsinanniya zaki jawo min masifa yanzu in kika kashe aurenki ina zan aje ki ni Amadu ya zanyi dake sai dai ko ki nemi wani uban". Jikinshi ba inda baya rawa zufa ta ko ina

Tace "Baba kayi hakuri wallahi nima na gaji da zaman gidan nan..."

"kaji shegiya" ya fyada mata carbin hannunsa "rufa min baki matsiyaciya kinsan Allah idan kika kuskura ya sake ki tsinemiki zanyi".

Ta fasa kuka mai sauti

"In banda shed'ana da rashin ciwon kai ina zan kaiki ke da wannan tutsetsen cikin naki haihuwa yau ko gobe? wadannan sauran na gidan ma ya na k'are dasu... 

Isyaku ya katseshi "ni dai baba wannan matsalolinku ne ni dai tayi zamanta gida dama hutun take so sai mu rabu ba dole..."

"a'a a'ah haba Alhaji dan girman Allah kar muyi haka da kai yanda ka rufa min asiri ka rike min ita dan Allah ka cigaba da hakuri ka taimakeni ka agaza min wallahi in ka saketa ciwon zuciya zai iya kamani", ya juya kan Salima yana zare ido jikinshi ba inda bai rawa "bazaki bashi hakuri ba 'yar banza kawai ko yankar namanki yake baza kiyi hakuri ki zauna ba, maza durk'usa ki bashi hakuri" ya kai mata duka ta kauce. 

Da rawar murya ta fara ba Isiyaku hakuri yana basarwa da k'yar baba Amadu ya lallashe da ban hakuri kamar zai ari baki sannan ya hakuri tare da kafa mata sharudda baban yace "ko cewa kayi kullum ta kwanta ka bi ta kanta ai ya zame mata tilas ta aikata shi, maza ku tafi wuce ki bi mijinki, ko gidan bazaki koma ba bare uwarki ta zugaki".

Isiyaku ya sa kai zai fita yace "errrm bakaji ba"

"magana kake?

"eh, ke wuce ki bamu wuri kin tsaya ma mutane a ka kina wuki wuki da ido". 

Ta fita tana share k'walla. "Baba daa Allah yi maganarka sauri nake"

"Uhhm nace dan Allah babu dan wani abu da zan samu ne? kasan gidan k'amas yake Isiyaku ya masa wani kallo 

"a taimaka dai Alhaji kar a gaji damu". Ya marairaice fuska yana jan carbinsa. Isiyaku ya zaro dubu d'aya ya bashi ya fita bai saurari godiyarsa ba. 

 

RAYUWARMU A YAU

©Jam33lerh

&

©Ayeesh_Chuchu

®NWA

 

{45}

Suna fita ya miƙa mata naira hamsin fuskarsa a murtuke "gashi nan ki nemi hanyar gida ina da wurin zuwa". Ya juya yayi tafiyarsa. Ta ja ƙafarta ta nemi adaidaita ta nufi gida. Gaje ta fito ɗaki tana mata maraba tayi banza da ita ta shige ɗaki bata gaji ba ta bita ɗakin da abinci ta daɗe a tare da it tana bata baki da haƙuri sannan ta fita.

Bai nemeta ba har sai washegari da shirin tafiya ya sameta a ɗaki tana biƙin ƙafarta da ta isheta da raɗaɗi. Ya kalleta y watsar ya jefa mata kuɗi a gadonta "gashi nan gayyar matsiyata saura kuma ki cinye a sati guda, ai banyi mamakin halinki ba, ubanki ya nuna ba wanda ya kaishi kwaɗayi kai tir dai". Tace "babana kake faɗa ma magana? 

"Ƙarya nayi ba tsohon banza bane? mtswww ni na tafi" 

"Amma Baban Ameer abinda kake min adalci ne? haƙƙi na shikenan ya sha ruwa kusan wata 7 rabonka da kwana ɗakina".

Ya juya gabaɗayansa ya bita da kallo daga sama har ƙasa ta kumbura matuƙa tayi baƙi jikinta duk ya saki fatarta har wani gari gari yakeyi, bata da fasalin macentaka tsaftar jikinta kanshi bai gamsheshi ba yayi 'yar dariya "a haka zaki burgeni in baki haƙƙi? yayi dariya "to banga inda zan sauke bukatata a jikinki ba, aka ce miki ciki haukane duk kin ƙazance", yaja tsaki ya tofar da miyau "tir dai". 

Ta fashe da kuka ya taɓe baki ya miƙa mata robar ruwan dake hannunshi. "ungo nan maza kafa kai ki shanye" tayi jinkirin karɓa

"rubutu ne?

"Zan cutar dake ne?. Kamar zatayi gardama ta karɓa dai yana tsaye ta shanye ya sake miƙa mata wani goran "ki aje wannan ki riƙa sha kaɗan kaɗan kina jina? ki tabbatar kin shanye indai ke ɗiyar arziki ce, zaki ji amfaninsa a gaba". Ta gyaɗa kai, ya fita yayi tafiyarshi ya barta da ƙunar zuci.

 

* * * * * * * * * *

GIDAN SADDIƘA

Tana zaune a bisa katifa rungume da yamusasshiyar ɗiyarta tana shan mama yayinda lokaci lokaci ta kan ɗago ta kalli Kabiru dake ta lalube cikin kaya, tana sakin tsaki a hankali. 

Sai da ya gaji ya juya gareta "wai bazaki zo ki tayani nema bane? kuma na tambayeki kince baki gani ba". 

"Ji yanda kayi min biji biji da ɗaki kana gani dai sati guda nayi ina ƙoƙarin shirya kayan inda ya kamata a ajesu mtsww". "Naji dai zo ki dubamin dan Allah idan kuma kina dashi ki bani". Tayi shewa "ahayye lallai kabiru soyayyarka da sigari har ta kai haka? yau kaine da ce min dan Allah inyi haƙuri tabɗi ba don cikin bacin rai nake ba da na baka, ji wani ƙuntataccen ɗaki da ka kawo mu ciki daya fa ɗakuna gidan kanshi na laka ɗakuna kusan goma a ɗn karamin gidan nan kai ko a ina ka gano wannan kejin?

Ya kalleta a lalace "wai soba ke gaya ma dirimi nisa kin manta gidanku ne? ciki da falon ma bai isheku ba 'ya 'ya fiye da goma a cikinsa? ya gyara fuska "to ma ubanwa ya janyo aka koremu wancan, wai banda jakanci irin naki duk yanda Ladidi ke miki hidima kika nemi kashe mata ɗa da duka ba dole mai gida yaga za'a masa kisan kai ya koremu ba ga baƙar ƙazanta ai yayi hakuri ma, rashin mutunci kala kala kike masa idan yazo karbar kudi".

Ta murguɗa baki "ai duk ɗaya muke a fagen ƙazantar".

'yarta ta fara tari ta cire mata maman ta kwantar da ita

"mtswww abinda kika iya kenan ki wuni kina tura mata abu a baki amma wanda Allah ya halasta ɗin sai anyi dambe dake kike bani". 

"eh din". 

Ta miƙe zata fita zaninta ya bada kyyyaaaat ta juya ta kalli Kabiru yayi maza ya kauda kai. Ta sunkuci butar ta fita yace "kizo ki fitar da kashin nan mana". Ta masa banza. 

A tsakargidan bin 'yan gidan da kallo ta riƙayi tana mamakin yawan mutanen gidan, ƙiris ya rage su kai 'yan gidansu yawa wai nan gidan haya "tabɗijam" ta jinjina a ranta. 

Ko da ta dawo bata sameshi ɗakin ba ta nemi wuri ta kwanta can kamar an tsikareta ta tashi da sauri ta janyo ƙullin kayanta tayi ɗaiɗai dasu murya a raunane tace 

"tsinanne ya kwashe 'yan kuɗaɗen". 

 

{46}

Ta ƙarici kuka da tsine masa ta share hawayen ta fita tsakar gida da ya cika da hayaniya. Ta zauna a kofar ɗakinta tana tayasu da hirar wadda mafi yawanci ta gidajen mutane ce. Ɗaure take da zani a ƙugu da dauɗataccen breziya ba riga jikinta, mazan su nata karakaina a gidan. 

Cikin 'yan kwanaki ta fahimci kan gidan. Gida ne mai matsakaicin fili ɗauke da akuna fiye da 10 gefe da gefe suna kallon juna. Kowa na aikin gabanshi wasu na wanke wanke, girki masu daka, tankaɗe da sauran hidimomi . Yawancin matan gidan sunada sanao'i tun daga manja, mangyada, alala, shinkafa, kayan miya gasu nan dai birjik wasu har ɗinki, aikatau da wankau sukeyi.

Zaman hira da akeyi shi yafi komai yi mata daɗi a gidan, daga zaran wata ta kauce kuma za'a dasa nata hirar. Sam basu da kawaici kan 'ya'yansu duk wacce aka taba ma ɗa ko shine da laifi zagewa take tayi rashin mutunci.Da ta fahimci su ba irin Ladidi bane bazasu taba tausayinta su bata abinci ba yasa take tayasu aikace aikace daga nan suke sammata abincin ko kuma tayi suɗi a wurin wanke wanke.

 

* * * * * * * * *

Ranar wata laraba ta tashi da naƙuda Gaje na tsaye kanta da abin yafi ƙarfinta ta aika yaranta makwafta suka aro mata waya ta kira Isiyaku ta roƙeshi ya barsu suje asibiti. Kamar zai fasa wayar yace "wallahi ko nan da ƙofar gida ban amince ku fita ba asibitin banza ke duk haife haifenki ko chemist kin taɓa leƙawa? sai yanzu za'a kawo min kafiɗiri, ban yarda ba ehe". Ta marairace tana rokonshi 

"Salimar ba ƙaramar wahala take sha ba fa malam". 

"bakiji me nace bane? Lamunin kawai da zanyi ki maza gidan malam tsalha ki samo rubutu a bata tasha kinji na faɗa miki ko, na rantse idan aka fitar da ita gidan nan ban yafe ba". Ya kashe wayarshi.

Hargagin da ya mata ya tunzurata ta koma ɗakin Salima a fusace. Tana durƙushe tana ihu tayi tsaki "babu inda zani ki mutu ma haka kawai zai nemi gaya min magana". A raunane Salima tace "ki taimakeni dan Allah, wayyo Innata". Yanda take wahala ya karyar mata da zuciya ta aika yaronta gidan malam, ta sake aika wani gidansu Salima ya faɗa musu halin da ake ciki. 

Ansha artabu sunyi awowi kanta bayan ta sha rubutun ƙarfinta har ya soma ƙarewa cikin ikon Allah ta sunkuto ɗanta Namiji kamanninsa sak Isiyaku. Nan da nan Gaje ta ɗaura ruwa Gwaggo ta kimtsata ita da jaririn. Ta nemi kayan jariri sukace "babu ko pant" me Gwaggo zatayi ba faɗa ta ƙare musu tanadi kamar zata tsaga gidan da faɗanta. Ƙarshe dai gida ta koma mai goma mai ashirin aka haɗo kaya a baƙar leda harda na ƙannenta da suna jarirai aka taho dashi. 

Gwaggo bata fasa mita ba "in banda baƙin zalunci kasan ka bar mace da ciki kaƙiyin tanadin komai to a tsumma yake son yaron ya rayu kenan". 

Gaje tace "dama haka yakeyi uwar ɗa ita zata nema". Gwaggo ta riƙe baki "au iyye! Tabɗijam". Salimar tayi tsuru tsuru cike da kunyar ƙaryar da take nuna musu mijinta na wadata ta da komai. 

Wurin abinci kanshi saida akayita kai ruwa rana don Gaje sam ta hana a ƙara abinci bisa wanda suka saba dafawa ta sanar dasu hakan umurnin maigidan ne, babu yanda suka iya haka nan ake lasa abincin har da 'yan barka ba don ƙoshi ba, watarana ne ma daga gidansu ake kawo ƙanzo a sulala suci. Ga zuri'arsu dayawa kullum cika gidan suke musamman Saddiƙa nan take wuni kullum tun safe. 

RAYUWARMU A YAU

Ayeesh chuhu

NWA

&

Jam33lerh

 

{47}

Har akayi kwana bakwai Isiyaku bai dawo ba sai a waya ya sanar musu suyi ma yaron huɗuba da Musa. 

Da ranar suna ta zagayo haka nan akayi taron ba armashi domin dangin nasu jikinsu yayi sanyi da auren na Salima, da anata ɗoki tana gidan maiƙo zasu zo suna su dangwali arziki sukaga ashe ita kanta ba gwara, a nan ne aka koma tsegumi a gefe. Ba laifi maigidan yayi umurni a dafa tiya guda da rabi ta shinkafar hausa. 

Duk cikarsu daga mai bata ashirin sai hamshin ba tsoka. Aisha ma ta halarci sunan ta gwangwaje maijego da sha tara ta arziki har da saƙon kudi daga yayanta yace a ba mai jego. Ganinta da tayi ba suturar arziki ranar sunan yasa ta ciri kala biyu cikin kayan da tazo dasu da niyyar kwana ta bata taci suna.

"Wai ke kam Saddiƙa ƙazantar nan na nan? Haba dan Allah. Dubeni ki dubeki wazaice sa'anni ne mu, kin aje wata uwar tumbi, mama raɓe raɓe a cinya babu ko breziya haba fisabilillahi". Cewar Aisha

Saddiƙa tace "uhm ke dai wallahi kin cika kalen zance".

"Au kalen zance ne ma? kin maida kanki tsohuwar karfi da yaji ko kwalliya babu fuskarki kalli kayan jikinki ke da ɗiyarki kamar 'yan gudun hijira".

"To ni wa zanma kwalliya ina matar aure? da gangan kike ganin laifi na ke da kike budurwa a kasuwa kike fa", tayi 'yar dariya "ko da yike kema kin kusa shiga sahunmu kiji yanda akeji".

Takaici ya ishi Aisha ta rasa ma mai zatace mata tayi shiru kawai ta riƙa binsu da kallo dukkansu kamar wasu kurayen da suka kwana basuci ba kowacce a bushe. Hatta mai jegon ana haihuwa ayi fes banda ita fuskar nan cike da kyasbi, jikinta duk nankarwa manya manya ga wasu irin kuraje luƙa luƙa sun baibaye jikinta daga ita har jaririn alamar basu samu kulawar da ya kamata. 

"Oh Allah ni waɗanne irin dangi gareni". Ta faɗa a ranta.

Kamar ance ta waiga ta kalli Saddik'a, ta ɗaga 'yarta dake zaune jikinta ta kalli inda take zaune ta jika ma uwar zani da fitsari. Saddika ta kalleta tayi murmushi tace " 'yar banza kin jiƙani ko". Yarinyar ta tayata murmushin ta koma ta zauna a jikinta ta ɗaga rigarta tana laluben abincinta cikin nuna ko inkula ta fiddo mata ta sakeshi, ta kama tana sha ita kuma ta juya ta cigaba da hira da 'yanuwanta.

Aisha salati take tana ƙarawa a ranta wannan kwamacala haka kamar zuciyarta zata fito tace "Saddik'a kina gani fitsari ta miki bazaki tashi ki cire zanin ko ki sa mata ruwa ba? Ta taɓe baki tana kallon yarinyar

"Ƙyaleta kawai yanzu yinta na uku kenan zamanmu a nan". 

Aisha ta fiddo ido "uku? Uku naji kince? 

"Eh mana" ta ɗaga rigar yarinyar tana nuna ma Aisha babu pant jikinta.

"Haka kike barinta? lahaula wala kuwwata Saddika!". Gwaggo dake gefe tayi dariya "Saddiƙa ce fa ai kadan kika gani, kije dakinta kisha kallo, innace miki bayan gidan kwana biyu yana nan ajiye a ɗaki cikin foo karki musani". 

A guje Aisha ta fita tana kwara amai, ƙarshe kasa komawa dakin tayi tayi zamanta waje daga bisani ta yanke shawaran fasa kwana. Gab da laasar tayi musu sallama zata tafi suna faɗin "sai munzo biki" da "to" kawai take amsa musu don abin nasu na neman fin ƙarfin hakurinta.

 

RAYUWARMU A YAU

Ayeesh chuchu

NWA

&

Jam33lerh

 

{48}

 

Haka nan jegon nata ya kasance cikin garari da wahala babu kulawar kirki. Jaririn nata kullum cikin ciwo da zazzabi sai maganin gargajiya ake masa wanda Gwaggo ke jigilar karbowa daga gidansu wurin Babanta. 

Tana gab da fita jego watarana ya dira a gidan da kaya niki da niki tare da wata yarinya bazata wuce shekara 15 ba biye dashi a baya. Nan da nan ya bude d'akin da yake ajiye hatsi ya gyara shi tsaf ya shigar da kayan ciki tare da umurtar yarinyar ta shiga. Ahi kuma ya fita ya samo mata abinci taci sannan ne ya shiga wurin matansa.

D'akin Gaje ya fara shiga baiga fuska ba don haka bai dade ba ya fita ya shiga d'akin Salima Gwaggo ta fita ta basu wuri a gurguje ya duba jaririn ya koma inda yarinyar take bayan ya sanar da matan nasa su sameshi a dakin can.

Bayan duk sun hallara harda yaransa fuskarsa a sake yake fada musu aure aka bashi a wurin kasuwancinsa ubanta yaga mutunvinsa ya bashi ita don haka su riketa amana. Salima ta zare ido ta dafe kirji "aure malam aure fa? " Kwarai kuwa shi kikaji nace ko zaki hanani famuwa karara a fyskarta kirjinta na mata suya. Ya kalli Gaje "ke bakice komai ba". Tayi murmushin takaici ai ni ba sabon abu bane wuri na ka auro goma ma ina jiraye su zo mu zauna ta gama fadin haka ta tashi ta fita. Ya bita da kalo yana murmushi. 

Ya kalli amaryar kyaukkyawa kana ganinta kaga fillo ma'abociya kimshe fuska kallo daya zaka mata ka fahimci rashin walwala tattare da ita Hinde miko min jakar can" ta tashi ta mika masa har da rusunawa yayi dariya oh mutuniyar arziki kenan abinda wasu basu iya ba ba wanda ya kula shi ya fiddo kaya daga jakar ya mika ma Salima

"kayan d'anki ne kala bakwai da naki turmi uku gasu nan na haihuwarki Allah ya raya miki kije zamu gana da amarya". 

Ta tashi jiki a salube har ta kai kofa ya kirata ta dawo "yauwa ina rubutun nan dana bar miki akwai ragowa ko kin shanye? ta danyi jim kannan tace "na shanye". Ya harareta "ko baki shanye ba ai naga alama ya fara aiki jeki dallah". 

Ya kalli yaransa "kunyi tsuru tsuru kamar wasu almajirai kufice min a daki yan banza, kunzo kun tasa mutane gaba kuna kwasar rahoto". Da rige rige suka bar dakin.

Ya bakar leda ya ciro wata gora ya mika ma amarya "karbi ki rika sha a matsayin ruwan shanki kinji yanmata na tsari ne karki damu". ya fada yana washe hakora

Ko da ta koma d'aki kasa sanar ma Gwaggo tayi sai da ta isheta da tambaya sannan ta fada mata "ai sai kiyi hakuri inda zai rik'eki kuyi zamanku ke ina ruwanki? yayi ta aurenshi, da dai ki dawo mana gida ai gwara wannan damuwar, uwargida ma bata damu ba sai ke", Ta muskuta kusa da Salima nace qnya matar nan vata jinnu naga watarqna tayi kirki watarana ba wanda ya kaita rashin mutunci anya bata da matsutsai a ka?. Salima tayi mata banza itama sai ta kame bakinta.

Kwana 8 yayi dakin amarya daidai da kwana uku fitar Salima ya koma dakinta yayi kwana biyu yaje dakin Gaje yayi daya sannan ya koma dakin amarya bayan sun gama tsiya da Gaje akan yace yanzu ta tsufa ba amfanin da zata masa adalci ne ma yasa yayi mata kwana dayan. Bai sake bai sake kula masifarta ba ya shige dakin amarya daga nan ne ya koma kasuwancinsa.

RAYUWARMU A YAU

©Jam33lerh

&

©Ayeesha chuchu

®NWA

 

{49}

Bayan watanni bikin Aisha ya tashi don haka jama'ar gidan gandu sunata shirye shiryen tafiya katsina biki. Bayan dangin mamanta sun rufe musu baki da kuɗi akan su bari ayi biki a can, nan da nan Baba Amadu yayi ruwa yayi tsaki kowa ya amince. Don haka tun ana sati biyu wasu suka fara yin gaba. 

Anyi musu tarba ta mutunci an karrama su sosai, gida guda aka ware musu ta zuri'arsu don dama ƙwai da ƙwarkwata ba wanda aka bari, hatta matan dake gidajen aure. 

Su Saddiƙa ne gaba gaba wai su ƙawayen amarya, duk inda tasa ƙafa suna biye da ƙyar ta yakice su gudun su kunyatata wurin ƙawayenta yan jami'a.

Gagarumin biki suka shirya su biyu za'a aurar da ɗiyar kawunta mariƙinta. Shagalin da ake ba kaɗan yake burge 'yan babban gida ba. Sai ƙauyanci suke zubawa su kuwa dangin mamanta suyi ta kallonsu suna kwasar dariya, yayanta yayi ta musu fada abinda sukeyi. 

Events lin farko farko da akayi ba wanda ya wucesu saidai basu kame kansu matsayin dangin uba ba. Har wasu suka riƙa tunanin wai Zaria ƙauye ce? Musamman ƙawayen amarya 'yan iyayi, barin ma da Saddiƙa ke fad'a musu "ai mu uku dani Saddik'a, Salima, da Aisha sa'annin haihuwa ne, mu kanmu haihuwa ce ta sa muka manyanta da kuma talauci. Salima ta tare 

"ke ce dai talaka ni miji ai mai kuɗi ne". Ta share zancen Salimar "itama Aishar da kuka ganta haka dan tana gidan naira ne kuma ta biye ma ruɗin duniya taƙi aure, yo me za'ayi da wani boko can wahalar banza". Suka kwashe da dariya suna kallonta ƙauyanci da gidadanci zir tattare da ita tana faɗin meye amfanin boko.

Maganganun Saddik'a sun kunna Aisha kamar ta masgeta musamman kalmar talauci da take ambata wato su dai burinsu dole sai sun kunyatata sun nuna dangin ubanta faƙirai ne, dama an rainasu ɗan mutuncin da ake ganinsu dashi ya ƙarisa zubewa, kai Allah ya rabamu da jahilcin rayuwa" a ranta take wannan tunanin. 

Wata cikin ƙawayenta da ke amsa sunan Lubabatu ta katse mata tunaninta tace "a'a karfa kuga zazzagawa kamar ƙauyawa wallahi ba haka muke ba gaba da baya ni 'yar can ce karatu ne kawai ya kawoni nan, suma ɗin nasan rashin ilimin zamani ne yasa kuke ganinsu haka, amma gaskiya karku sake ku raina su". Ta faɗa fuskarta ɗaure ba alamar sassauci. Batayi shiru ba ta cigaba da zayyana musu ƙayatuwar garin duk kokarinta ta gamsar dasu ba yanda su Salima ke nunawa haka zazzau ɗin take ba, musamman ma da taga sam Aisha bata ji ɗaɗin sokoncin da Saddik'a tayi ba. 

Da akaje event din ma babu wani surutar arziki tattare dasu dukkansu a hargitse. Su kansu sai sukaji sun muzanta da sukaga ƙure a dakan da ɓangaren uwar sukayi,kowacce hamshaƙiya a motarta take zuwa, haka 'yan matan basa tururuwa wurin mota baifi kaga mace biyu zuwa uku ciki ba. Suma an basu k'ananan motoci da doguwar bus amma saida suka kusa dambe wurin shiga ƙananan motocin mata fiye da biyar ciki har da goyo wata kan wata. 

Dama sune farko farkon zuwa ba'a barsu shiga ciki ba masu tsaron wurin gani suke kamar 'yan aikin gidanne sukago gangami. Sunyi cirko cirko waje da sunga luntsumemiyar mota ta faka hadaddun mata sun fito zakaji suna fadin "alhumma arzuk'uni".

Saida yayar mamar Aisha tayi magana aka barsu suka shigada rige rige , aka nema musu wuri. Ko ina ka kalla a tsare zazzaune cikin kamewa da aji. Nasu ɓangaren kam ya hautsine da karaɗi basa ko sauraren abinda akeyi sai faman yaba mutane, wata kuma su zageta tayi shigan arna. 

Har amare suka shigo dangi da k'awaye sunata ɗauke ɗauken hotuna a manyan wayoyi. Saddik'a ta tashi ta zunkuɗa goyonta ta kama hanyar inda Aisha ke zaune da angonta, Salima na ganin haka ta bita a baya. Tana hangosu gabanta ya tsananta faɗuwa ƙawarta lubabatu tayi maza ta sha gabansu da fara'arta "ai ba'a zuwa wurin amare". 

Salima ta mata kallon gefen ido "me kike nufi? duk ga 'yan gayun nan can sun baibayesu suna d'aukar hotuna kuma munji a speaker me magana yace ƙawaye suzo a dauki hoto muma ai k'awayenta ne".

"ah to fada mata dai, mu da muke shaƙiƙanta ma za'a nuna mana wariyar launin fata".

Lubiee ta juya suka hada ido da Aisha duk ta tsure domin wadannan idan sukaje wurin can an bata show tace tabdi jan yanzu wadannan ba sai ace iyayen Aisha bane". Kafin ta ankara kawai sai tsintar su tayi gaban Aisha . Jikinta a mace kamar an cire mata laka ta isa wurin mai hoton ya juya yana daukar wasu ta jawoshi ya d'aukesu. Su kuma sun cika Aisha da surutu suna gabatar da kansu wurin ango. Da k'yar ta lallaba su suka koma wurinsu.

Suna can dambe kan abinci aka kira amarya da ango su yanka cake sunata mamakin wannan rashin kunya har aka kira Aisha. Duk suka zuba ido suka ga ta ci da angonta shima ya bata nan suka fara cece kuce suna kanbama abin an zubda albarkar aure Gwaggo kuka ta fashe dashi "shiyasa nake tsoron 'yan bokon nan bazan kara ko da minti daya wurin nan ba wad'annan mutane basu da dabi'a". Dole ba shiri ta tarkatasu duka suka fita wurin su Salima da wasu tsirarru sukayi biris da ita. Su na nan har aka tashi aka maidasu gida.

Washegari da Aisha taje gaida dasu tare da rakiyar k'awarta Lubiee Gwaggo rufe kofa tayi wai bata yarda da ita ba sai ta duba ta yanzu haka sun gama lalacewa da angon tun a waje shiyasa auren bai k'arko. "Me ake da wayewar 'yan boko ko lalacewa"

Tayi suguri tana kallon kakarta taga da gaske take cire mata skirt take kokarin yi duk da magiyar da Lubiee ke mata Aisha tace 

"Gwaggo tsaya tsaya kiji, wallahi babu wannan tsakaninmu daidai gwargwado an mini tarbiyya, gaskiya ne maganarki abinda mukayi jiya ya saba ma addini kawai dai munbi son zuciya ne mun ari zamani, amma kinji na rantse ban tqba barin shaidan yayi galaba kaina ba, mu a wurin wai haka wayewa ce ni da kaina na k'yamaci abin duk da nasan ya sab'a ma shari'a, dan Allah ki bar wannan tunani". Da haka ta lallabata ta kyale suka fita.

 

RAYUWARMU A YAU

©Jam33lerh

&

©Ayeesha chuchu

®NWA

{50}

Ana gobe daurin aure aka shirya gagarumar walima. Musamman Aisha taje bauchi ta ɗauko shahararriyar malamar nan Husna .m. inuwa don ta bada lecture kan zaman aure.

Saddik'a na maƙale da lubiee don tace duk cikin ƙawayen Aisha ta fisu mutunci gashi ta iya ɗaukar wanka tace "nagode". 

"Ai in Zainabu na ta isa yaye ke zan kawo ma ki yayeta har ki riƙemin itama ta zama yar gayu". Lubiee tayi daria kawai wannan soki burotsin ya girmi kunnenta. 

Duk yanda taso guduwar mata hakan bai samu ba dole ta haƙura da inda ya kamata ta zauna kusa da Aisha suka nemi wani wurin a gaba suka zauna. Babu abinda yafi tayar mata da hankali irin tashin da Saddiƙa ke yi kamar ba mace ba. 

Babu ɓata lokaci aka soma gudanar da walimar a katafaren filin gidan. Bayan adduo'i da gabatarwa Malama ta fara da "indai akwai yarinya a nan da bata isa aure ba a fita dasu, ku kuma iyayena kuyi haƙuri da wa'azin yau". Tayi shiru na mintuna kana ta cigaba bayan wuri ya natsa.

"Lura da yanda aure ya zama a arewacin kasar nan abin baƙinciki da tausayawa, ya sanyani ɗauko maudu'i mai matukar muhimmanci da burin kowacce zata natsu ta duba nata matsalar ta gyara",

Da farko ga tambayata gareku :

"Da zarar an yi aure sai Ango kusan duk wani abu da amarya take so cikin gaggawa zai yi.

Wani ma in ma'aikaci ne ko ɗan kasuwa har hutu ya ke ɗauka ko ya rage tsawon lokacin zamansa a kasuwa don baya son ya yi nisa da amarya. Duk fa wannan saboda ɗebewa amarya kewa ne.

Amma da zarar an samu ciki, mace ta fara laulayi, yawanci sai Ango ya fara nisa da ita musamman mai amai da yawan zubda yawu. Bayan haihuwa, ɗaya, zuwa biyu zuwa uku sai wani ya fara ganin ta TSUFA tunda ta yi yara. Mutane da dama ba su fahimtar abinda ya sa hakan ta ke faruwa.

Wasu su ce laifin Matan ne, Wasu kuma sai su ce a'a laifin daga Mazan ne".

Tayi tsam tana kallon jama'ar wurin sun cika filin maƙil.

"A ganin ku, laifin na wane ne? Kuma ta yaya za'a magance irin wannan matsalolin da su ke cikin kusan duk gidaje musamman na hausawa".

Saddiƙa ta muskuta ta ɗaga murya "Malama Allah mazanne tsinannu". Duk kowa ya juya yaga wadda tayi maganar, Lubiee kamar ta nutse wurin don kunya don kusa suke zaune kusan manne da jikinta ma Saddiƙa take. Wurin ya ɗauki hayaniya kowa na faɗin albarkacin bakinsa

Malama tace "auzubillahi haba malama tsinewa miji da bakinki subhanallahi ba kanta". 

Ta bubbuga ɗiyarta dake mutsu mutsu a baya tace

"ai malama don baki san muguntarsu bane da ƙyar wasu in zasu ketare siraɗi barinma mijina Kabiru... Malama ta dakatar da ita da hannu. Jikin Lubiee ya soma rawa wannan mata ta zare. Tayi tsam zata tashi Saddik'a ta riƙeta "ina zaki Ƙawata? Ta harareta ji take kamar ta rufeta da duka. Daidai lokacin Saddika ta kunto 'yarta daga baya dake ta tsandara kuka tayi sharkaf cikin najasa ta ajeta jikin Lubiee 

"riƙe min kiga in mata nafkin shegiyar ta fara sana'ar tata"

Malamar da yawancin mutane idonsu na kanta, yayinda Lubiee ta sunkuyar da kai cike da kunya. Saddiƙa ta fiddo ledar nafkin daga jakar leda ta karbi 'yar da banda zarni da bashi ba abinda takeyi ta saka mata tsummokara ta ɗaure. Lubiee ta faki idon na kusa dasu ta bar wurin don ta tsaftace jikinta ranta a bace. 

 

{51}

Bayan an natsa Malama ta cigaba "wato na lura ashe matsalar ma tana kusa damu:

"Tawani ɓangaren laifin matanne. Wata macen data haihu daya sai ta dinga ɗaukar kanta wai ita tashiga sawun manya, tadinga wasu abubuwa kaman tsohuwa. Wata haihuwa ɗaya batasa brezier kirki, kuganshi har tasaman bayanta wai ita a dole tahaihu. Babu gamsasshiyar tsafta tattare da ita.

Wani ɓangaren kuwa laifin nan 50 50 maza da mata su ka ɗauka saboda suma mazan haka suke ɗauka da mace ta haihu 1,2,3 to bata da sauran amfani, ita kuma sai ki ga ko dressing zatayi sai tace wannan yanxu ba nawa bane, ko kuma tace ta girmi yin kwalliya yanzu wa zanwa gayu? Daga lokacin da ki ka sake ki kaji aranki wai ke kin fara girma wasu abubuwan zaki baryin su to dga lkcn ki ka fara cutar kanki ki kasa kafa ki kai wulli da damar ki ta macentaka mutuncinki da ƙimarki ta zube gaban miji, To ku saurara kuji;

Iyayena inace sirrinku ga mazajenku a zamaninku shine haƙuri da biyayya? tsofaffi sukace 

"haka yake malama". Ta jinjina kai 

" to kusani an rasa duk wannan a tattare da matan wannan zamanin, a yanzu ne ake rasa waye sama da wani tsakanin mace da miji don shi mijinne zakiji yana tausasa murya ita kuwa nata har makwafta har kuji tana cewa (tsorona yake bana daukar raini wurin mijina)Kuji wauta. Gaba ɗaya sunyi fatali da kwalliya da gyara ga uwa uba soyayya wacce take ruhin aure da itane ake samun zuciyar maigida kisan sunnoninta da yanda zaki sace zuciyarsa. Iyayenmu zamaninsu sun riƙi bagaruwa da muhimmanci. Ita mace kullum anaso ta kasance cikin dumi kunga macen da ke rufe jikinta ku tambayi mazajensu sirrin abin suke da amsarshi amma masu tallar jikinsu ai su ne salaf ba taste. Kunga yawo ba takalmi da zama a siminti suke fara kawoma mace mishkila, shikenan fa sai ķiga an fara faɗa da miji to magunguna da aka ɗirka miki sun gama amfanin su ya fara sanin asalin wacce ke.

Mu riƙi girki da babban makami akwai girke girke na zamani da na gargajiya wanda dashi ne zaki sake maƙale zuciyar sa. Shi namiji dan shauki ne da son nishadi da tarairaye hakan kuma zai sami karɓuwa ne idan kina gyara kanki. Ki sani babu wata mace mummuna sai dai in babu gyara. Mata mu natsu mu lura da waɗannan abubuwa

* lura da kalar da ta fi miki kyau da yadda ya dace ki sa sutura, irin wacce tafi jan hankalin Maigidanki na da matuqar muhimmanci 

* karki gajiya wajen siyan kayan ado su hoda, janbaki, 'yan kunne, sarqa, zobe, awarwaro, suna kara fito da mace... Don wataqila su suka birgeshi tun kuna zance, ko baya yabawa idan kin saka karki k'osa cigaba dayi a ƙasan ransa yana jin daɗi don ba dutse bane. Ko da bazai siyan miki ba sai dai kullum yana cikin ɗinka nasa zamani ne, iyayenmu na da ba haka suke ba kar kice lallai saidai idan shi ya siyo ya baki. Haƙuri za kiyi, amfanin sana'a kenan. Tunda kina da hali to kiyi duk cikin ibadane. 

 

Yanzu iyaye sun maidashi al'ada yarinya ko budurwace in zatayi aure ayi ta ɗirka mata magunguna, baku san wasu daga ciki sunada matuƙar illa ba? Da ace mata zamu gane ma magangunan gargajiya kayan itatuwa su zaitun, habba da addini yazo mana dasu da aure ya dad'a karko don me bazaki bar 'yarki taje ma mijinta a asalin halittarta ba in yaso daga baya sai ta sha magunguna. Kayan ni'imar nan ga budurwa hatsari ne ta hakane wasu kafin a ɗaura shauki ya ɗebesu su faɗa ma halaka musamman ma lokacinnan da ake events. Mazajen ma basu bambance ainihin yanda matan nasu suke. Alhalin tun tana ƙarama ke uwa kika riga kika kashe 'yarki barinta ba wando ƙin hanata tsallake kwata da aiki mai wahala. Wasu yaran a gaban iyayensu suke wasan tsallake kwata ba'a hanasu sai aure ya tashi a cika mata ciki da magani.

Mu dinga kishin Mazajenmu mata. Mu dage da gyara kanmu da haka karuwan waje ke kwace mana su. A kullum a ko'ina suna ganin shigar sutura da kwalliya iri -iri a arha.

Bai halatta ki bayyana kankiba sai ga maigidanki. Wajibine ki rufe jikinki idan za ki haɗu da wanda ba muharraminki bane. Babbar musibar da ta ɓullo kenan musamman gidajenmu na haya a arha mazaje ke ganin matan maƙwaftansu don wata bata da kula a gaban wani gardi zata fiddo mama tana ba yaro ko kuma ta fita tsakar gida da daurin kirji da sunan shan iska. Shan iska a ina ko dai ki shaki haram. 

Mata sun natsu suna d'aukar darasi da tunanin kurakurensu musamman su Salima da Saddik'a sai sunaji kamar donsu akeyi . "Duk matar da ta faranta ran maigidanta ubangiji na yi mata gafara kuma zai sanyata cikin matan aljanna.

Shawarata ta k'arshe shine mata muji tsoron Allah mu sauke hakkin mazajen, mu bisu sau da kafa. Ku riqe mazajenku da kyau ku daina sake na waje na karbe maku su. Tarbiyar yara abune mai mahimmanci saboda yara amanane a wurinmu, yazama dole mu kula da yaranmu musan waye kawayensu, ina suke zuwa da sauransu. Zama da kishiya abune mai sauk'i idan har mace tasan kanta,mu dai zafafa kishi sai ki samu rabauta. 

 

RAYUWARMU A YAU

©Jam33lerh

&

©Ayeesha chuchu

®NWA

 

{52}

 

Ganin magriba ta gabato akayi addu'a aka tashi. Mata sai godiya suke wa Malama da nuna mata sunji daɗin lecture din, da yabon abin kowacce take barin wurin. 

Kamar yanda malama Husna tayi umurni bayan sallar isha'i a kawo mata amare, hakan akayi tare da rakiyar ƙawayensu biyu. Ashe su Saddiƙa sun faki idonsu sun bisu a baya, sai ganinsu kawai sukayi, abin ya sosa ma Aisha rai tasan yanzu ma wata taɓargazar zasu kuma yi.

Malama murmushi tayi da ta gansu "dama ko zanso mu keɓe dake baiwar Allah", ta nuna Saddika "amma kafin nan kuma ku zauna ku kwashi sirrika", Saddiƙa ta nemi kusa da Lubabatu ta zauna duk yanda take harararta shanyewa tayi.

"Ku saurareni da kyau amare kuji ƙarin bayani, a waje akwai iyaye da ƙanne so faɗar wannan magana gabansu bata yiwuwa;

"Duk namiji yana neman mata ta gari don haka ki zama ta gari, kowacce mace tanaso ta zama ƴar lelen mijinta to ai ba da kazanta da rashin kamewa zaki siyeshi ba sai kin tashi tsaye da gyara.

Cikin salo da ƙissa tamu ta mata mana, misali kuna sunna, kikaga yana taɓa inda bawai wani dadi kikeji ba, ke zaki nuna masa, to daga ranar bashi ƙara miki yadda bakiso...

Kina shan kankana kullum da madara ko babu. Kina shafa man hulba a gabanki kullum yana tsuke mace, yana ƙara ni'ima sosai, man hulba magani ne ingantacce bakowa yasan sirrin sa ba, idan kika shafa gabanki zai cicciko zai matse. Kina amfani da farin almiski don akwai sirrika da dama cikin almiski. Ki samu kaza budurwa kiyi farfesu da ita, ki zuba ruwan magarya, da dakakken kanumfari hmm ba'a magana. Kina tauna kanumfari uku xuwa biyu kullum akwai sirri acikin sa, zakiga kullum yana manne dake. 

Karki yadda miji yai wasa da dake be wanke hannuba saboda gujema ɗaukar cuta. In zaki kwanta kina shafa zuma a gabanki yayi minti talatin sai kije ki wanke d ruwan dumi, kunsan dai daɗin zuma hmm basai na karasa sauran ba. Ki riƙa gasa ƙafarki da man zaitun kiga yanda zasuyi laushi tamkar na jariri.

Karku yarda da kayan ɗa'a da mata ke yawon sayarwa ku riƙe natural abubuwa ya isar muku. Saddika tace "malama yo ke kinata maganar abin nan nifa tun da nake ban taba sanin dadin auren ba, ta ina zanso kyautata ma miji". Salima a sanyaye tace "nima fa duk ɗaya".

Malama tayi salati tayi shiru cikin tunani sannan tace "a ganina laifin daga gareku ne, dan Allah ku tayani dubar kanku kamar matan da da suka tara gajimare, ba gyara ba tsaftar bare suturar arziki haihuwarku daya kacal, ko dashike miji shi yake mayar da matarshi yanda yake son ganinta amma fa da taimakonta, amma ina tabbatar muku idan kukayi amfani da shawarwarin can nawa zakuga canji. Kuna ƙin ilimin boko ne amma alfanunsa ba kadan bane, yana sanya wayewa ke da kanki kigane darajarki, ilimin nan wata abace mai girma ko a bambancin da ke tsakaninku dasu Aisha ya isheku misali. Ba wai ina kusheku bane amma in har zaku jera da ita cewa za'ayi hadimanta ne ma'aikatanta, Haba ƙanne na kun mayar da kanku ƙauyawa da gidadanci yayi ma dabaibayi dan Allah a gyara".

Su Aisha sukayi ta zuba mata godiya, su kam sai binta da ido maganarta ta sosa musu rai. Aisha tace "Malama na kawo ƙararsu kuma ba cin fuska ba wallahi basa sallah mai yi ɗin ma Salima ce itama ɗin ba wata gamsasshiya ba". Malama ta fiddo ido, a ranta ta jinjina al'amarin waɗannan mutane "anya laifin ba tun daga gida bane kuka tashi a haka ba? tunda daɗin miji zai hanaku ibada ne idan har dama can ta ratsaku, wannan ai babbar matsalace ta ina al'amuranku zasu daidaita?. 

Saddiƙa ta kafa ma Aisha ido ranta in yayi dubu ya baci ta tashi a fusace tayi waje Salima ma ta bita a baya. Malama ta bisu da kallo "to Allah ya kyauta kuje na sallameku ku natsu kuyi nazarin maganganu na kunada wayewa ku zakufi fahimta, sa'annan kodayaushe ƙofata a buɗe take ga me neman shawara ko taimako". Suka ƙara mata godiya sosai suka fice.

Har aka watse taron biki su Salima basu ƙara bi ta kan Aisha ba, ƙin zuwa ma kaita sukayi. Ita Saddiƙa fushinta kan Aisha ya tsaya don tana kula Lubabatu sosai jin ta take a ranta ba kaɗan ba, Lubabatun ma ta cikata da abin arziki kaya kala kala ta haɗa mata ita da ɗiyarta Zainabu. Da zasu tafi Saddiƙa ta karbi numberta a takarda da alkawarin in ta koma zata nemi waya ta kirata kar zumunci ya yanke.

Sallama ta musamman dangin mahaifiyar Aisha sukayi musu harta yayanta Umar ba'a barshi a baya ba. Sun cika su da aiziki su kuma bakinsu yaƙi rufuwa sukayi ta zuba godiya sukace sai sun dawo bikin Umar. Gwaggo tace 

"Ai gida zai zo ya nemi mata". Nan take ya bar wurin yana ayyana "Allah ya tsareni, ko wani bazan masa hanyar aure cikin gidannan ba".

Bus biyu dogaye aka samo musu suka ɗuru ciki. Mariya amaryar Baba Amadu na maƙale dashi sai da sukayi nisa tace "to malam miƙo min nawa kason cikin kuɗin da naga an sunƙa maka". 

Yayi wuri wuri da ido yana waige waige "ku... ku... kuɗi wasu iri? Kinga bana son neman fitina".

"kaga malam baka isa ba fa, ai ni na ganoka, gwara tun wuri ma ka bani ba sai mun koma ka bar mu da hamma a zo ana bamu labarin an tsinceka wurin habu mai shayi kana cika ciki ba". 

Yace "haba mariya sai kace ba kanki nake ƙarar da kudade na ba ko sauran matana basa ci". 

"Ban tambayeka ba miƙo min kawai in ba haka ba kasan saura ehe". Ya juya gabas ya juya kudu arewa, yamma yana riƙe da bakin aljihu fuskarsa kimshe kamar zaiyi ihu. Haka nan ya fiddo kuɗin ya miƙa mata, ta cusa a jaka ya bita da kallo yana share gumi da gefen malun malun. 

Inna Habi daga can baya tana hangensu tace "ai mu saidai muce Allah ya saka mana". Matan su Baba Sa'adu suka saka baki suna tayata jera baƙaƙen maganganu har suka isa gida.

 

RAYUWARMU A YAU

©Ayeesha chuchu

®NWA

&

©Jam33lerh

 

{53}

 

A gida bayan dawowarsu sai suka dasa labarin katsina duk wanda yazo sai sun bashi labari "ai mutanen akwai hidimar arziki barsu dai da bidi'a da wulakanta mutane su nan sunyi karatu, yo na banza 'ya 'yansu na tambad'ewa a titi", wadda ake ba labarin tace "assha" "amma fa sun mana b'arin naira, ai mu tafiyar nan munyi garas kamar a k'ara". Ire iren hirarrakin nasu kenan.

Hakan ta kasance a wurin Saddik'a tun da ta dawo take ba mutanen gidansu labari har dasu karya, kullum labarin kenan har sun haddace kamar karatu; suka koma guje mata data fara za'a watse. 

Watarana tana cikin basu labarin wani party da akayi da dare tana farawa kowacce ta k'irk'iri hanyar fecewa suka barta. Itama ta tashi ta koma d'aki. 

Mijinta na ciki zaune yana wasa da Zainabu. Ta kalleshi ta watsar tanemi gefen katifa ta zauna ta jawo roba ta zuba miyau ta mayar, can anjima ta sake tofawa tayi har sau uku, ya dago ya dubeta

"Ke wai jakar inace tun dazu kinata min kazanta, haba da warin da kika bari ya dafar mana da d'aki zanji ko kazantarki? Ta murguda baki.

"In baka iyawa ka fita mana ko na rik'e ka? kuma ma naga ai kai ka d'irka min cikinnan 'yata ko yayeta banyi ba". 

Yayi tsaki ya maida hankalinshi wurin 'yarshi ita kuma ta ci gaba da tofe tofen tana hadawa da tauna gauta data rok'o a mak'ota. 

Can kamar an tsunguleshi yace "in banda shashasha irinki mace bata san rayuwar mijinta ba babu abinda ya shafeki sha'anin gabanki kawai kike, ko ki damu da yawan zamana a gida kwana biyu".

Cikin ko in kula tace "kai ta shafa ya wuci ka rasa kudin sayen kayan maye". Yayi murmushi 

"Allah ya kyauta miki dai gantalalliya, baki dakin wance baki gidan wance, ke kenan baki k'wakk'waran awa 2 a dakinki sai in barci ne ya danneki, inda kinsan yi da ke da suke wuni sunayi da baki k'ara bi ta kan matan nan ba", ya ja dogon tsaki. 

"To zuga zugi k'ara ma miya gishiri ko ba'ayi ba ai kace anyi mana don kaga suna bani abinci ba". Ya dubeta a lalace damuwa kwanxe a fuskarsa "baki sani bama, to tsuguni ce ta samemu na dauko ma kaina fitina, nayi shaye shaye na rotsema wani kai ya fad'i magashiyyan... Ta mike ta dafe kirji a tsorace

"yanzu dai ance yana asibiti kuma wai ni zan biya, inba haya zan bada kaina ba ina nake da kudin? shine fa suka kai k'arata wurin 'yan sanda yanzu dai neman kamani sukeyi, don haka lokacin barinmu garinnan yayi dole yanzu ko nak'i in koma mahaifata har komai ya lafa". 

"Amma kai kadai zaka tafi ko? Ta fisgo 'yarta donni wallahi ba inda zamu sai dai kasan yanda zakayi damu, ai kai ka janyo ma kanka mu bata shafemu ba". 

"Indai ko ba cewa zakiyi in sakeki ba duk inda nasa k'afa kina biye dani, ko kuma in sawwake miki a koma gaban tsoho". Ta koma yaraf ta zauna a katifa

"naji shikenan Allah ya kaimu". Ta fada a sanyaye. "Da rayuwar gidan mu ba gwara wannan uk'ubar ba ko banza gidan mijina ne". Yayi dariyar mugunta.

 

RAYUWAMU A YAU

Jam33lerh

Ayeesh chuchu

NWA

 

{54} 

Tun dare suka fara shirya kaya. Washegari asubar fari yasata tashi ta shirya suka d'auki kaya, yayi shatar mota suka kama hanyar Bauchi ba tare da sunyi sallama da kowa ba. 

Sun jigata tafiyar da suka sha ta awowi tun tana kirgawa har ta gaji, tayi barci ta farka yafi a kirga, tsina kuwa Kabiru ya shashi a mota, ga yunwa ga wahala shi yasa ko da suka isa Bauchi kamar bak'in haure sun jigata matuka. Suka shiga motar Duguri dake karamar hukumar Alkaleri, ko da suka isa dare yayi a haka kuma yake k'ara neman wata motar ta zuwa kauyensu "dogon ruwa". 

A gigice take kallonshi da yake kokarin tsayar da achaba da zai gangara da su k'auyen ga duhun dare. Ta ruk'unk'une 'yarta, yayi murmushi

"kinga kauyen nan duguri tana fa tsakanin Tafawa balewa ta jihar bauchi da kanam karamar hukuma ce a jos". Ta rik'e maratarta "ina son kama ruwa". Ta bar bayanin da ya koro yabi iska.

Yace "gwara ki rik'eshi fa, ki bari mu isa gida kinga daji muke baki tsoro? Ta kame bakinta ta tsuke. Da kyar ya sami achaba biyu, ta kalleshi gabaki daya kudadensu ya tattara a tafiyar har saida suka siyar da wani abu a hanya. 

Talatainin dare suka isa gidan zubin sa na asalin k'auye, kai tsaye suka shiga tana biye dashi tana cira k'afa da kyar har suka dangana da wani daki an sakaya, ya kutsa kai ciki matar tace "waye nan". Yace "Inna nine kabiru". 

"Wayyo Allah jama'a barawo wani Kabiru ne zaizo da tsakar daren nan". Duk mutanen gidan suka fito kasancewar dakin da duhu ba'a hango komai. Ya fita hasken farinwata.

Wata tace "Inna shine, kabiru ne". Tayi jim can ta saki tsaki ta koma d'aki, sauran ma duk suka juya. Yasan a rina don haka bai matsa ba ya fiddo zani cikin kayansu ya shimfid'a. Baiyi magana ba ya karb'i 'yar ya shimfid'e shima ya zauna.Saddika kamar zatayi ihu wannan wulakanci da tozarci. Kwanan zaune sukayi don sauro wurin basu barsu untsawa ba ga rashin wurin yada hakarkari.

Ko da gari ya waye ma ba wand yabi ta kansu har akayi abin kari a gabansu aka shanye. Sai da Babanshi ya shigo yace "ah aha wai Kabiru ne? saukar yaushe? jiya nayi ta jin sukursukur inace 'yan iskan gari ne, to zaman me kuke a waje kunyi furgai furgai haka?. 

Daga d'aki tace "ni na hana babu dan iskan da zai shigo min daki, sai da yaje ya ma karuwarshi shege iyayenta k'ila sun koreta ita kuma ta mak'ale masa shine ya san damu ya dawo". 

A firgice Saddik'a ta kalleshi ya share "Inna yasin kinji na rantse ba karuwa bace matata ce ta sunna, shekararmu biyu da aure, dan girman Allah kuyi mini aikin gafara na tuba na gane kuskurena bazan k'ara guje muku ba". Mutane suka taru kansu yana magiyar iyayensa su yafe masa. Innar tafi taurin kai shi baban tuni ya hakura sai da jama'a suka sa baki sunayi suna aibata shi sannan tace

"Naji na hakura ba don komi ba sai waccan figalalliyar da kace matarka ce gashi har da rabo ma" ta yashe baki "ni ai lokacin hutu na yazo, gani da suruka bani k'ara katabus gidannan, dama kishiyoyi sun gallabeni da habaici bani da mai tayani aiki. Matan dake tsaye wurinsukace

"hakane hakane wallahi".

"Malam a fidda tumakin can waje a basu d'akin su share su zauna".

Yace "to to an gama yanzu kuwa". Kabiru yayi ta zuba godiya ya tashi ya nufi wurin mahaifinsa yana tayashi Saddika babu abinda take sai binsu da ido ganinsu take kamar sabbin halitta. 

Kabiru shi yayi wahalar gyara wurin a lokacin rana ta kai tsakiya azahar ta kunno kai. Duk tsawon lokacin nan Saddika tana inda suka kwana ba wanda yace da ita ci kanki duk da kukan yunwan da Zainabu ke tsandarawa har muryarta ta dishe, ruwan maman ma ya k'afe domin ita kanta yunwar takeji, amma mutanen nan babu wanda yayi tunanin bi ta kansu. Shima Kabirun sai daga baya yayi magana cewa a taimaka musu da ruwa. 'Yar maganar nan Innarshi tayi ta mitar fad'a bashi da kunya "kuma baza'a basu ruwan ba ka fini sanin abinda ya dace ne? Ya kame bakinsa yayi shiru. 

A sace wata mata bata wuce sa'ar Saddika ta miko mata ruwa jawur dashi ta baiwa Zainabun itama ta kwankwad'a. Rabonsu da abinci tun jiya a mota da suka saya a tasha ya siya musu koko da kosai shine a cikinsu har yau. 

Ya sanar da Innar an gama gyara d'akin zasu iya komawa tayi banza dashi ya dade zaune sannan tace "ku je". Yayi godiya ya fita suka koma, d'aki ne ciki daya ginin laka kamar kumatu. 

Ya fita ya dawo d'auke da kwano ya dire gabanta tun kafin yayi magana ta fada kan kwanon ta shiga ci tana baiwa 'yarta, garin rogo me mai da k'uli ne. Ya zuba musu ido

"to Saddika kinga mahaifata saboda haka kiyi ma mahaifiyata biyayya ta gani ta fad'a, ina ji da ita fiye da tunaninki kar inji..."

Ta balla masa harara "au nufinka zamane ya kawo mu? tabdi jam ai billahi baka isa ba ka raboni da birni ka kawoni bakar kauyen nan, kasan Allah bazan zauna a wannan mataccen garin ba".

"Ke ke karki gayan magana mana da zaki aureni kin taba tunanin asalina ko ya nake? Ai saboda kin shirya zama dani ne a duk halin da nake ciki, sallamammun iyayenki ma basu damu da sanin waye ni ba suka aura min ke, don haka tilas dinki ki zauna, ko kasheki za'ayi bazaki san hanyar komawa gidanku ba". 

"Tab ai ka sake tunani tun wuri, bazan iya rayuwar kauyen nan kamar ta dabbobi ba. Vata ankara ba ya mauje mata baki a fusace ya tashi ya fita. Ta fashe da kuka ba mai rarrashi. 

Can jimawa Innarshi ta leko "matar bariki sannu da hanya barkanki da shigowa dangin miji, adalcin da zan miki ki huta na kwana biyu rak kwana biyu kawai daga nan zaki fita tsakar gida ki kama min aiki, ni kuma in huta kina jina? Tayi mata banza 

"au iyye lahaula wala kuwwata illa billahi ni furera mutan gida kuzo kuga min illar auren bariki, 'dan nan ya jawo mana fitina ina magana tamin banza, aiko ni ubanki zanci a gidannan". Mutanen gida suka hadu kan Saddika suna zaginta.

 

{55}

Kamar yanda ta fada kwana biyun kacal ta bata, tun asubahi ta buga musu kofa ta tasa k'eyar Saddika zuwa tsakar gida tace ta dauko bokiti maza ta bi matan gidan suje rafi debo ruwa, ta tsaya gardama Inna Fure ta rufeta da duka, ba wanda ya daga kai ya kalla ta k'araci ihunta, k'arshe kuma dolenta ta dauka sukaje rafin.

Sai da tayi sawu biyar tana dawowa ga nisan tsiya k'afafunta sai zugi, ta dangwara mata baho cike da hatsi "maza gashi nan ki surfa shi mara mutumci da idonta ya gama budewa da duniyanci kina gamawa kuma kizo a rakaki jeji kiyo itace". 

Gabanta ya fad'i "yau na boni" tunanin dukan da tasha dazu kawai ya sanya ta d'auka ta fara surfen a jigace har kusan hantsi, kuma babu wanda ya saka mata hannu. Tana gamawa ta sanyata d'umame ta gama ta kawo gabanta tana zaune tsakar gidan cikin nishadi ta tasa Zainabu a gaba dake cin kasa bata hanata ba. Saddika tasa hannu zata dauki 'yar Inna ta buge hannun "kauce min nan lalatacciyar banza, ace mata sam bata san kawaicin dan fari ba har kina neman gurb'ata min Kabiru da salon rashin kunyarki, bace min da gani". Ta fashe da kuka. 

Kallon tsana Inna ke mata yau ni naga 'ya sannu ruwa ruwa daga anyi magana sai arhar hawaye, inace ciki ne dake? wata nawa ne? Tayi shiru "ba dake nake ba? A raunane tace "nima ban sani ba". 

"Zama ki sani ne ai figaggiyar banza, to daga yau na yaye Zainabu kije kiji da na cikinki ta dawo hannuna kenan, tashi ki ban wuri". Ta tafi tana matse kwalla ta koma daki. 

Haka ta wuni aiki ba wanda ya nema mata hutu bare abin sama a baka. 

Ta kwallo mata kira "matar bariki! ta isa da sauri 

"Au bazaki durkusa ba kin tsaya min k'erere, kai wannan jaraba ta isheni ba don kinyi kama da garada wacce zata juri aiki ba ai da tuni na sa ya sakeki kin koma tushenki, mtswww, maza wuce icce zakije ki samo a daji, yanzu ya dawo aikinki kullum da safe kibi gayyar mata kuje kuyo icce ni Allah ya hutassheni rarume rarumen k'iraren had'a wuta, maza hanzarta mana". Ta tashi jiri na d'ibarta suka tafi. Da suka dawo taga 'yan itacen da ta samo fad'a ta rufe ta dashi kamar zata tsaga gidan 

"Bana son ragwanta mijinki da ragone zaki ganshi haka? Ta tura mata akushi 

"gashi nan kici".

Jikinta na 'bari ta ja kwanon ta soma ci tuwo ne gaya da mai. Turawa ta rik'ayu hannu baka hannu kwarya. Haka ta wuni cikin bauta dasu girki don ta fada mata sau biyu kawai suke girki da safe da dare watarana ma sau d'aya. Ba ita ta samu hutawa ba sai bayan isha'i bayan ta gama gurzar wanki.

Don haka ko da ta kwanta kamar matacciya gab'b'anta kamar ba nata ba. Cikin barcin ne taji Kabiru kamar yanda ya saba zuwan mata tana ihu tana komai ya hayeta.

 

RAYUWARMU A YAU

Jam33lerh

&

Ayeesh chuchu

NWA

 

{56}

 

 

Haka rayuwar Saddik'a ta cigaba da garawa a kauyen dogon ruwa cikin azabar bauta, ta koma abin tausayi duk wata tsiwa da rashin kunya sun gudu, ta zabge ta lalace tayi baki gunin tausayi ga rabata da diyarta 'yar wata 11 da Inna tayi. 

Wannan karon cikin yazo mata mai laulayi da kwadayin cin d'ata sai dai bata samu. Bata da lokacin kanta saina ayyukan Inna Fure, asubar fari zasu fita rafi suna dawowa tayi surfe su nufi daji samo itace tayi girki da wasu 'yan ayyuka da Innar ke takalowa don tsananin karta barta ta huta.

A yanda ta lura mutanen gidan kaf tsoron Inna suke don gidane na gandu, kishiyoyin Innar uku itace uwargida dukkan kishiyoyinta 'ya'yansu maza ne, mayi yawancinsu sunyi aure gidan suke zama, ita yaranta mata sunfi rinjaye namiji d'aya Kabiru shine kusan d'anta na hud'u. Kaf mutanen gidan k'ark'ashinta suke itake mulkin kowa a gidan hatta mijinsu malam Sani sai yanda tayi dasu. 

Mace d'aya ke kula Saddik'a, Rabi itama surukar gidance itace kawai take shiga sabgarta a b'oye har suyi hira idan suna aiki. A bakinta ne taji wannan labarin har take fad'a mata "mutanen waje ma har gulma sukeyi wai kai sunayen mutan gidan nan tayi gidan malam yasa ta mallake kowa, duk da kasancewarta masifaffiya wannan tsoron nata da akeyi bana hankali bane", "Kuma fa duk cikin ya'yanta tafi son Kabiru, a sangarce ya tashi itace silar lalacewarsa, tunda ya gane hanyar birni ya tafi shekararsa goma kenan sai yanzu ya waiwayo gida kuma Inna Fure ta kare babu wanda ke maganar tafiyarsa kar aga laifinsa, sai cewa takeyi kurciya aka masa, nifa dawowarku dinnan inaga kamar yanda ta fada gidan malaman ta je aka masa kiranye". 

Saddik'a ta rike baki cike da al'ajabi tsoron Inna Fure ya dad'a kamata. Rabi tace "ai ni tausayinki nake Saddik'a nasan ko kadan bazaki taba jindadin Inna ba kema ai kinzo kenan bazaki taba iya guduwa ba". Famfon hawaye ya b'alle a idanun Saddik'a, Rabi bata hanata ba tasan dole ta koka 

"mu ma da ba surukanta ba muna azabtuwa bare ke ai saidai kawai kiyi ta addu'a". 

Daidai lokacin 'yarta ta tattako tazo wurinta, ta juya taga Inna na kallonsu daga bakin k'ofarta gabanta ya fad'i wani mugun tsoronta ya dad'a tsirgata. Tayi biris da 'yar ta cigaba da aikinta zuciyarta na k'una, "kiri kiri ba dama ta rab'i diyar cikinta". 

A cikin wannan bautar cikinta yaketa girma. A wannan lokaci Inna ta tursasata ta siyar da duk wani sutura da abin kudi da ta mallaka a cewarta ta gaji da ciyar da k'atuwar mace, duk da ba abincin kirki take bata ba yawanci sud'i take ci, amma Kabiru yana dawowa gantalinsa dakinta yake wucewa ta bashi wanda taci.

Kudin kayan da aka siyar ita ta karb'e wai zata adana, ba zato kawai sai gani tayi ta raba biyu taba Kabiru rabi ita ta aje rabi. Shi kam a wurinsa duniya sabuwa, da yaga bashi da kudi zaizo ta bashi yaje yayi tatil cikin maye, ya zo ya sauke tanadinshi akan Saddika.

Wani dare barci ya k'auracewa idanunta tana tunanin rayuwarta a karo na farko.

"Tabbas babu wahalalliya irin matar mashayi", Ta zauna shiru tana tunanin yadda zata gyara rayuwarta 

"ko a ina kuskurenta yake? Duk ta gaza ganowa. Tunda aka d'aura aurenta da Kabiru k'wandala bai taba had'ata da shi ba, 

"shin dama haka auren yake? Ita dai tun tashin ta bata taba ganin an darjanta aure ba a gidansu kullum dai mace itace a k'ask'ance shiyasa suma 'yan gida burinsu kawai su girma suyi aure su bar gaban iyayensu. 

K'iri k'iri iyayensu ke saka su aiki su k'iya amma gashi a 6agas tana ma uwar wani bauta kuma bata da ikon musawa. Ta share k'wallo "kila alhaki ne".

Da wad'annan tunane tunanen barci ya sace ta. Shiyasa ma da Inna ta buga musu kofa taga kamar yanzu ta kwanta jikinta ba inda baya ciwo ga nauyin ciki.

A haka cikin wannan hali ta haihu haihuwa mafi k'ask'anci domin wannan karon nak'udar mai wahala ce, kwana tayi tana nakuda ana bata jik'e jik'e, k'arshe akayi mata yankan gishiri ta sullub'o danta a wahalce.

Aka cigaba da bata jik'e jik'en da wankan al'ada. Yaron ko kaya ba'a siya masa ba sai na Zainabu kayan mata aka rik'a sanya masa. Jegon nata yazo a gurgunce cike da rashin kulawa babu wani kumari tattare dasu. Kwananta talatin Inna ta maidota kan aikinta.

 

RAYUWARMU A YAU

©Jam33lerh

&

Ayeesh chuchu

®NWA

 

{57}

 

* * * * * * * * * 

A can Zaria kuwa ganin har sati 4 ba Saddik'a ba labarinta matar da duk sati tana gida suka damu sai suka fara cigiyarta. Ko da sukaje gidansu mutan gidan suka sanar da su su dai sun wayi gari basu gansu ba sai makullin ɗaki a jikin ƙofa sun dauka ma sun mutu ne ciki saida aka duba ba kowa. 

Hankalin iyayenta ba ƙaramin tashi yayi ba musamman mahaifiyarta. Malam Amadu yace "dallah ki kwantar da hankalinki don mata da miji sunyi layar zana ai ba abin jimami bane, kika sani ko garine yayi musu zafi, in kika kwantar da hankalinki ma muna nan zakiga sun dawo". Sauran mutanen gida ma suka yita kwantar mata da hankali.

Amma tana yawan maganar Saddiƙa (ance ɗa da mahaifi sai Allah). Har shekara ta zagayo babu su ba labarinsu ta nemi ƙara tada hankalinta malam Amadu yace "in baki bar mana zancen Saddiƙa ba, kofa bude take ki bita, kuma kar kidawo min gida". Sai ta koma tayi laƙwas.

 

GIDAN SALIMA

 

Itama zaman gareta ba wani daɗi ne dashi ba. Azababben mijinsu da muguntarshi ta ƙaru har ta kai iya abincin da yake ɗibar musu idan zai tafi in basu lallaɓa ba har ya ƙare sai dai mace tasan yanda zata cigaba da ci da kanta da ƴaƴanta. Amaryar ma har ta haihu yayi marmarinta na kwanaki, itama ya mayar da ita sahunsu. Duk iya wulakancin da zai wa mace ko yaji basayi bare neman saki.

Watanshi biyu da tafiya wannan karon yayi musu bazata ya dawo. Ɗakin Salima ya sauka. Tana zaune tsakar gida ita da ɗanta, ta zuba tagumi, domin ba dama idan yana ɗaki kema ki shiga ki zauna idan ma tsautsayi ya kaisu ɗakin ganinshi suke tashe da kayan daɗi su kuwa ya barsu da gantsarar tuwo, ƙarshe mari zai biyo baya. Gaje ce kawai wani sa'in take iya mayar masa martani.

Kayan wanki taji ya watso mata "yanzu nake son ki wankesu". Ta dago a sanyaye 

"ai ba sabulu", 

"dama ni nake bada sabulun da za'ayi min wanki?

Ta kwantar da murya "Bani da kudi ne wallahi kayi hakuri ka bayar". 

"Kici bashi mana". Ya koma ɗaki ya barta da kallon kaya tuli guda sunyi daƙa daƙa. 

Dama haka yake musu in ya tafi bazai wanke kayansa ba har sai ya dawo sannan ya basu su wanke masa babu sabulunshi saidai ke ki nema. Hakan kuwa akayi dolenta ta ciyo bashi a maƙwafta ta wanke masa, in ba haka ba ya jibgeta.

***** ****** ****

Tun dare taji jikin ɗanta Musa zafi rau kafin gari ya waye sai rawar ɗari yake hakoransa na haɗuwa. Masassara mai tsananin zafi ta kamashi har da suma. Gari na wayewa tabi Isiyaku ɗakin amarya ta sanar masa, korar kare ya mata tun kafin ta ƙarasa jawabinta. 

Ganin tana neman rasa ɗanta yasa ta ɗaukeshi ta kaishi chemist kusa dasu aka dubashi ta sanar ma mai chemist ɗin Isiyaku zai biya.

A fusace ya shigo gidan ya nufi ɗakinta tana ma Musa firfita. 

"Wato dan kin rainani kuma kina neman zubar min da mutunci shine kawai zaki kinkimi ɗanki ki kaishi chemist bada izini na ba ko? Ke tabbatacciya, to da izinin wa ma kika fita? Tayi shiru. 

"kin zaro min ido kamar tsohuwar mayya? Anya ba sai na sake sabon shiri kanki ba kuwa". Ta tashi zata fita ya daka mata tsawa.

"Don iskanci sabida kin rainani ina magana zaki tafi ki barni wato ga mahaukaci ko? 

"A'a ba haka nake nufi ba". 

"Banza 'yar iska mara tarbiyya, sai kije ki biyasu ai, donni kobo na bazaiyi ciwo ba bani na aikeki ba". Ranta ya soma ɓaci 

"Gaskiya nidai ka daina zagina".

"Au har kinada baki? Yasa ƙafa ya doketa ta haɗu da bango ya bita da duka tana ihu sai da ya gaji don kansa yana huci yace 

"Kowacce mace tana neman na kanta amma ke jakar wofi kina nan kin sanya ido akan ɗan abinda nake samu burinki ki tatseni to kinyi kaɗan bazan ɗauka ba". Ya fice ya barta, ta zube tana numfarfashi tana kuka.

Ta riƙa tunanin mafita a wannan rayuwar aure nata iyakar hangenta bata gano mafita ba. Ita dai tasan ko karen hauka ya cije ta bata isa ta tunkarin gidansu da nufin zawarci ko yaji ba, bata da mafita illa cigaba da hakuri dashi, a zahirin gaskiya ma bazata iya rabuwa da Isiyaku bane jin zaman gidan take kamar ranta.

Tana nan zube cikin rauni, taji hargaginsa da Amarya. Tayi murmushin takaici "Ya ubangiji ka kawo mana sauƙi".

 

RAYUWARMU A YAU

©Ayeesha chuchu

®NWA

&

Jam33lerh

 

{58}

 

ƘAUYEN DOGON RUWA

Cikin talatainin dare bata runtsa ba tana fama murƙususun ciwon ciki haɗe da ciwon baya mai tsanani. 

Kamar daga sama ta ga ya faɗo ɗakin maƙil cikin maye gabanta ya faɗi ganin kallon ƙasa ƙasa da yake mata yana tunkarota, tun haihuwarta wurin ke damunta ko kaɗan bata son abinda zai taɓa shi. Tun lokacin ma sau ɗaya wani abu ya haɗasu, bata kasadar kwanciya cikin ɗakin, sau ba adadi ya sha kai mata hari tana kuɓuta, tasan yau daya risketa kashinta ya bushe.

Taja jiki zuwa ƙarshen katifa tace "kayi haƙuri na tuba kuma ina cikin matsanancin yunwa". Bai fasa ƙoƙarin kamota ba yana murmushi. Matsanancin tsoro haɗe da faɗuwar gaba suka daɗa mamayeta tasan ko ya kasheta babu abinda za'ayi. 

Mugunta ya gwada mata irin ta mazan da basu san darajar mata ba, sai da yaga kamar zata mutu sannan ya barta kuka kawai take na rashin galihu tana tausayin kanta, da yana da imani da ya tausaya ma halin da take ciki, lalurar da ta sameta yana sane da ita, don yana ganin yanda take ma kanta magani da ganyayyaki da itace. 

Har gari ya waye bata bar kuka ba tana kiran mutuwa ta ɗauketa ta huta da wannan baƙinciki.

Ya shureta da ƙafa "raguwar banza tashi in kaiki gidan ubanki". Tayi lamo a katifar ya daka mata tsawa "bazaki tashi ba wai, Zaria nace miki zamu tafi yanzu". 

Tana jin ya ambaci Zaria ta nemi ciwo ta rasa tayi tsalle sai tsintar kanta tayi hanyar rijiya tayi maza ta janyo ruwa ta faɗa bayi babu soso bare sabulu. Inna Fure nata surfa mata zagi. 

Tace "ashe shiyasa Inna Fure bata nemeni ba yau da ban fito ba, ai idan na tafi sai a lahira babu ƙaddarar dazata sake maido ni dajin nan" take tunanin a ranta. A gaggauce ta riƙa komai har ta shirya ɗanta. Ta jawo cukurkuɗaɗɗen hijabinta ta saka. 

Ta sameshi a ɗakin Inna duk suka bita da kallo tana goye da ɗanta ta ƙullo 'yan kayansu a ɗankwali. Innata harareta

"Ka gani ko, dalilina kenan na ƙin tafiyar nan nasan idan na sake yarinyar nan ta bar garin nan bazata dawo ba, da sona sai kunyi shekara biyar kafin ku waiwayi Zazzau". Dukkansu suka kalleta da razana, da alama shima zaman ƙauyen kamar a ƙaya yake. Inna ta cigaba 

"Shiyasa na karɓo taimakon nan, ai na faɗa maka amfaninsa, ungo bata maza ta kur6e tas". Ya karɓa ya miƙa ma Saddiƙa ta kar6a ta kafa kai ta shanye 

"Yauwa to, yanzu hankalina zaifi kwanciya, Allah kiyaye, ku tafi har da Zainabu ma su ganta, yara sunyi 6ul 6ul abinsu". Wani sanyi ya ratsa Saddiƙa ko banza tasan bata bar komai garin ba bare idan ta tafi damuwar rashin 'yarta ya dameta. 

"Amma Inna tayi rashin azanci". Ta faɗa a ranta tana murmushi. Suka miƙe suka fita tana maimaita masa 

"Kwana biyu kawai zakuyi kaji ko, karka yarda da wani uzuri ko waye kai tsaye kace a'a", Ta dafa shi "ɗan albarka Allah dai ya tsaremin kai". Saddiƙa ta kalleta a ranta tana ayyana "in Allah ya yarda kallon ƙarshe nake miki". 

Tace "Inna mun tafi ayi mana aikin gafara". Tayi mata banza. Tayi sallama da sauran mutanen gidan suka kama hanya.

 

{59}

 

Zumuɗin da take ciki baisa ta runtsa a mota ba, illa ƙaguwa da ƙosawa ta ganta a gidansu ji take kamar ta janyo lokaci. Tsakar dare suka isa Zaria ba irin roƙon da batayi masa ba ya wuce da ita gidansu ya ƙi, baƙinciki ya isheta tace "amma ai ka iya da zan haihu, ka jefar musu dani ka ƙara gaba".

"Naji koma me zakice".

Kai tsaye wani shago suka wuce, wani tsohon shagonshi ne can take binsa zamanin 'yanmatanci suna lalata. Sai da suka shiga ya kanne mata ido guda yana zuƙar sigari "so nake mu tuna baya". Ta ja da baya tana fiddo ido "a akurkin nan? Yayi dariya sosai. 

"yanzu kikasan akurki ne? Da da kike biyoni ina baki ashirin ai baki san haka ba, ke dai kinci sa'a a gajiye nake ga yara kuma, amma akwai lokaci kiyi kwana biyun a gidanku in daukoki mu dawo nan da zama". Bata tankashi ba don tasan zai aika. 

Kasa runtsawa tayi ta ƙagu gari ya waye, ga kuma cizon da sauro da ƙwari ke gantsara musu". Gari na wayewa ta matsa masa suka tafi sai da ya gama jan mata aji, don ma ya ƙara 6ata mata rai yace takawa zasuyi har gidan, duk ta shanye domin ta gane munufarsa. 

Da gudu ta shiga gida ta saki ya'yanta. Ta rungune Innarta tana murna suka tsaya suna mata kallon rashin sani sai daga baya suka ganeta domin yanda ta kwanjame tayi baƙiƙirin ta zama ƙashi da ƙashi abin tausayi kasa ganeta sukayi. 

Innarta ta fashe da kuka Saddiƙa na tayata. Nan sukayi ta murna, har abin ya lafa ta cika cikinta ita da 'ya'yanta kamar kurayen da suka kwana basu ci ba. Abin ya ƙara ba mutan gidan tausayi. Babu zancen tsaraba yanda suka ganta a firgice barin ma da ta tuna ta barshi waje jikinta rawa ya dingayi taje bata sameshi ba hankalinta ya tashi ta rasa sukuni, Innar ta dinga mata faɗa.

Da Baban ya shigo shima bai ganeta ba sai daga baya yayi ta mamaki nan ta sanar dasu halin da ta shiga sun tausaya mata matuƙa. Baba Sa'adu yace 

"Da gani uwar mijin bata barta haka ba ta kafe ta ne, ji yanda hankalinta ya tashi rashin ganinshi da batayi ba alamun sihiri duk ya nuna a jikinta". Gwaggo cike da jimami tace

"ƴar nan ke kam kinga rayuwa a hannun mutanen nan Allah ya saka miki". Har dare sun dade suna maida yanda akayi.

Ganin dare yayi sosai Baba Amadu yace "wai mijin naki ba zaizo ɗaukarki bane? Mutan gidan suka ɗauki salati. Gwaggo tace "kanka ɗaya kuwa Amadu? 'ya'yan cikinka ka mayar dasu kamar dabbobi marasa galihu, to babu inda zata auren ma rabashi za'ayi". 

"Wallahi baza'a raba auren nan ba, kan uba! na samu ya rufa min asiri ya riƙeta za'ace ta dawo min gida zawarci, nikam bazan ta6a haihuwar zawarawa ba, ta koma tayi ta haƙuri can dama auren kenan". 

Saddiƙa ta fashe da kukan tausayin kanta, 'yan uwansa suka taso masa da faɗa. Yayi musu banza.

 

RAYUWARMU A YAU

© Jam33lerh

&

© Ayeesh chuchu

®NWA

 

{60}

 

Washegari mamakin yanda taga ana shirya abin kari a gidan ta riƙayi har sai da ta tambaya "wai meke faruwa gidannan ne? Naga komai ya canza hatta ginin ji ya yanda aka sabunta shi, jiya mune har da cin shinkafa 'yar gwamnati da nazo".

Sukayi dariya Inna amarya tace "albarkacin 'ya'ya muka soma ci yaran da shekarun baya babu wulaƙantattu kamarsu a gidannan kowa ya gujesu sune yau gatan dukkan mutanen gidan nan".

Ta dubeta da rashin fahimta. Ta cigaba "Su Umaru ne shi ya gyara gidannan ya gina shaguna a waje ya saka ƴan mazan gidan ya basu jari kowannensu da zamn banzan da sukeyi, amma dayike ba yaran rufin asiri bane gashi nan da kaɗan kaɗan suna salwantar da kuɗin, ya matsa ma su malam dole ake barin yara zuwa makaranta, sannan yake yawan yo mana aiken kayan abinci da haɗin gwuiwar 'yar uwarshi Aisha, da an kawo ake kasafta kayan abinci amma don baƙin sharri irin na Malam fakar idonmu yake ya siyar". Ta ƙare maganar da damuwa a fuskarta.

"Ya naji ana ambatar Malam ne munafurcin ya tashi ne? kinga ke! ke!! ɗin nan dama ba son zamanki gidannan nake ba yanzu sai in fatattakeki ki koma titi in ma duniya zaki shiga kin dade". Ya faɗa yana nuna Saddiƙa.

Ta sadda kai ƙasa ya cigaba da surfa mata zagi da aibatata, amaryarshi Mariya na zugashi.

Sallamarsu Aisha ta katseshi "ah aha ɗiyan kirki masu hasken goshi kun ƙaraso? Suka gaisheshi da sauran mutan gidan suka wuce ɗakin Baba Sa'adu mahaifinsu. 

Sun daɗe ciki fiye da awa har mijin Aisha ma ya shigo ya gaishe da na waje shima ya shiga ɗakin. Baba Amadu na ta sakin tsaki da faɗan ba gaira ba dalili. Da zaman ya isheshi ya ɗaga murya

"Wai shin Sa'adu kai baka da kawaici ne? ka riƙe yara tsawon lokaci, wato dai sai ka nuna mana kai ka haifesu ko, to duk abinka bazamu rabu dasu ba".

Inna Habi ta kwashe da dariya "Su Malam manya amma dai girma ya faɗi ka mance zamanin zamansu gidannan ba wanda ya fika hantararsu?.

Ya sakar mata mugun kallo "ke fa ballagazar macece, in banda rashin hankali meye na tado da zaune tsaye? salon ki sa yara su fara wani tunani na daban, to ahir dinki, na ƙara jin makamancin maganar nan sai na saɓa miki shashasha kawai". 

Ya tashi ya kakkaɓe babbar rigarsa ya leƙa ɗakin Baba Sa'adu "to ku fito haka nan nima ina son ganawa daku". 

Matar Baba Sa'adu tayi salati "yau naji ƙarfin hali wurin Malam Amadu wannan wuce gona da iri, mutum da 'ya'yansa kayi musu karan tsaye, to nufinka bazai keɓe da 'ya'yan cikinsa ba ko me?

"Ke banson rashin hankali kinji ko, kina ganin ina shiga sabgarki? 

"ah ah to naga ƙarfin halin ne yayi yawa, na tabbatar da 'ya'yanka ne, mu na gefe bazaka bari mu ɗanɗani arzikinsu ba, Allahu akbar Malam bawan Allah". 

"Kwarai kuwa maganarki haka take". Cewar Salaha matar Baba Muntaƙa.

Sai da Baba Sa'adu ya fito ya tsawatar musu sannan sukayi shiru Baba Amadu yayi ta sakar masa baƙaƙen maganganu duk ya shanye. Yace ma yaran

"kuje ku sameshi ni zan fita ina fatan zan sameku? Umar yace 

"Dama kwana biyu mukayi niyyar yi anjima kaɗan zamu koma".

"To to madallah zanyi ƙoƙari in dawo da wuri, ku fa jirani". suka amsa da

"To Baba".

Baba Amadu ya bishi da harara yace

"Sai ku biyoni magana zanyi daku". Ya wuce ɗakin Mariya yana cin magani. Mazan suka bishi, su Aisha suka zauna a tsakar gidan inda matan ke hira. 

Zaiyi magana ƴaƴan Saddiƙa suka leƙo ɗakin kamar zai cinyesu ya tashi jikinsa na rawa ya fatattakesu ya bubbuga musu takalma a kai ya dawo yana huci "shegu tsinannu masu kama da mayu".

Umar yace "ƴaƴan waye ne? Yana zazzaro ido da rawar baki yce 

"ƴaƴan Saddiƙa ne, ka gansu nan kamar karnuka duk inda suka ganni suna maƙale dani". 

Mijin Aisha yace "sun dawo ne?. 

"Jiya ya kawota dake baku lek'o gidan ba jiya shiyasa baku haɗu ba".

Ya kwashe duk yanda Saddiƙa ta basu labari ya ƙara da faɗin "amma ita shu'umar yanda take jaddada wahalar ƙauyen ban yarda da ita ba, har ana neman kawo min wani salo wai anyi mata sammu, ai kaga Sa'adu karanbaninshi yayi yawa".

Bacin ran Umar bai ɓoyu ba a fuskarshi ba, a ranshi yana faɗin "tsohon nan bashi da ta ido ko kunyar suruki baya yi".

Mijin Aisha sunkuyar da kai yayi, sukayi msa jaje da Allah kyauta yace "ina abin jaje a nan ai auren kenan". Suka masa sallama cewa zasu shiga gari kafin anjima.

 

{61}

 

A ɓangaren su Aisha tun da suka zauna take ma Saddiƙa kallon sani. Matan gidan suna lura da ita, muryar Inna amarya ta tsinkaya tana faɗin "baki ganeta ba ko?. Da sauri ta girgiza kanta 

"Saddiƙa ce fa".

Mamakin Aisha bai ɓoyu ba, kafin tayi magana Innar ta zayyane musu halin da Saddiƙa ta faɗa musu ta shiga.

A ɗage Raliya matar Umar ke kallonsu tana maganar zuci "faɗi ba'a tambayeka ba". 

Labarin bai wani girgizata ba domin ta tsammaci haka. Har mamakin Aisha takeyi yanda ta iya rungume ƴaƴan Saddiƙar. 

Aisha kuka take sosai na tausaya ma 'yar uwarta. Ta nuna jimaminta kwarai tayi ta ba Saddiƙa baki tace "ki kwantar da hankalin ki komai zaizo ƙarshe da yardar Allah, tunda kin ku6uto bazaki koma ba". 

"In dai ba ɗaukarta zakiyi ki kaita gidanki ba, ninayi rantsuwa bazata zauna min gida ba matuƙar ta kashe aurenta, ina gani ɗazu Sa'adu da iyayi ya bata addu'a ta sha a cewarshi an mata sihiri, ba wani nan ko baƙar ja6a aka mata asiri dashi sai ta koma", Cewar Baba Amadu da ya fito daga ɗakin Mariya. Ya harari Saddiƙa 

" ƴar banza daga zuwa ita da ɗiyanta an ƙara mudun abincin gidan ina zan iya".

Kallonsa suke sosai yayinda Raliya ke masa kallon ƙasƙanci, ita Aisha nata kallon na takaici ne a ranta tana ayyana "mutumin baida tunani a gaban surukarshi yake wannan taɓargaza babu kunya". 

Sai da ya fita Saddiƙa ta sami bakin magana 

"tsinnne Kabiru ya cuceni". Ta fashe da kuka mai tsuma zuciya. Itama sai da tayi ƙwalla, Aisha akwai tausayi. Tace "Inna to wane mataki kuka ɗauka game da auren?.

"Babu wani mataki, kinsan halin Malam ya jajirce kan dole ta koma ta cigaba da haƙuri".

"kuma kuka amsa masa kun amince?

"To ya muka iya Aisha mu bamu da kataɓus sai yanda yayi". 

Takaicinsu ya kamata "wai Inna dan Allah yaushe zaku farga kusan kuna da ƴanci ne? Sai ku riƙa bari mazanku na cin kashi kanku kamar bayinsu, haba dan Allah". 

Kallon da Matar Umar ke musu ya sasu shan jinin jikinsu suka gaza buɗe baki. Barin Saddiƙa ji tayi duk ta muzanta.

A ka fara jera musu abinci a sababbin kuloli. Aisha tayi yaƙe tana hankalta da yamutsa fuskan da Raliya keyi "mun ƙoshi fa Allah", A ranta kuwa tasan kazamtaccen gidansu da su kansu ne zai hanasu ko da shan ruwan gidan ne. 

Ta yafito yaran gida kuzo ku kwashe a guje suka taho ƙiris ya rage basu ɓata mata jiki ba.

Gwaggo tace "ku kuwa ƴaƴan nan a tashi ƙiƙi ƙiƙi donku ayi girki kuƙi ci". Ta dire da kallon fuskar Raliya tayi bala'in haɗe rai tana kauda fuska.

"ko dai ƙyamarmu kukeyi?. Da sauri Aisha tace "haba Gwaggo ba haka bane, da gaske mun ƙoshin ne yasa bamu ci ba". Ta shashantar da zancen aka cigaba a hira har mazn suka dawo.

Baba Amadu yana biye dasu "Kuyi tafiyarku kawai yanzu haka yayi nisan kiwo". Sukayi musu sallama bayan sun jiƙasu da kuɗi. Gaba ɗayansu suka biyosu a baya suna zuba godiya tare da mamakin yanda mijin isha ke manne da ita idonshi a kanta cike da kulawa tana takawa a hankali da ɗan cikinta da ya fara fitowa. 

Har suka bar ƙofar gidan basu fasa ɗaga musu hannu da adduar Allah ya kiyaye hanya ba. 

Basu bar garin ba sai da sukayi ma Baba Sa'adu waya ya faɗa musu inda yake suka biya sukayi sallama da shi sannan suka kama hanya kowanne da tunanin da yake, da kuma haushin halayya irinta Baba Amadu kwaɗayi da son kansa har da cewa suzo su bar garin ba dole ne sai sunyi sallama da ubansu ba. Shi duk baƙincikinshi kuɗin da yake tunanin zasu ba mahaifin nasu. 

Har suka isa katsina jefi jefi suke hira. 

 

RAYUWARMU A YAU

© Jam33lerh

&

© Ayeesh chuchu

®NWA

 

{62}

 

Sai bayan kwanaki sannan Kabiru ya waiwayo Saddiƙa. A lokacin zamanta gidan ya kaima mahaifinta maƙura, ji yake kamar kanshi take, tazame masa ƙaya a gidan tsakaninshi da ita da yaranta sai kyara da hantara. Abu kadan zasuyi ya hau tsine musu. Abinci ma da kanshi ya ƙayyade adadin da za'a riƙa basu, ga su da cin tsiya hatta na goyen ya gane ma abinci sosai. Haka nan suke lasa ko bai ishesu ba, wani lokacinne ma Innarta ke tausayinsu ta ƙara musu da nata. 

Da Kabirun yazo Baba Amadu yayi ta lallashinsa kan yayi ta hakuri dai "su mata haka suke ba cikakken hankali ne dasu ba, shiyasa aka hadasu damu mu riƙa tarosu in sun bauɗe, ka tafi da ita kuyi ta lallaɓa rayuwar har me rabawa ta raba". 

Baba Sa'adu shi ya tsaya tsayin daka tare da ƙarfafawar Gwaggo suka hana Kabirun tafiya da Saddiƙa. Babu irin cin mutunci da tijarar da Malam Amadu bai yi masa ba duk ya shanye. Sai da yatayar ma da kowa hankali a gidan, har dasu kuka yace

"anci zalina Gwaggo har dake za'a hadu don a ga bayana a gidannan ina zan kai wannan rubitin iyali? duk shekara shegun matan sai sun haihu". Gwaggo tayi masa kunnen uwar shegu domin Aisha ta aiko mata da kuɗi tace karta bari ko da wasa Saddiƙa ta koma ma mijinta, ba don hka ba itama bazata goyi bayan raba auren ba.

Tun daga nan tsangwamar Malam Amadu ta ƙaru fiyeda tunani. Da Saddiƙa taga zaman bazai mata ba ta fara wankau shima ba wani samu take ba sosai. Ita kanta haushin su Gwaggon ta riƙa ji, don zaman gidannasu ya isheta kamar a bursuna har ta fara tunanin guduwa wurin mijinta, amma inta tuna ƙauyen da ta kuɓuto da ƙyar sai jikinta yayi sanyi. 

Suna wannan zaman ne Malam Amadu ya kawo wasu tsofaffi sunji wuyar duniya yace nan da sati biyu zai aura ma ƙannensu Saddiƙa su uku 'yan mata yan shekara 15. 

Ya haɗo kan yaran yace su jeru mazan su zaɓa. Gwaggo tayi tsiya kamar ta bugeshi tace "ka rasa wa zaka haɗasu aure dasu sai su anikallahu, suna gwagwarmayar rayuwa cikin wahala, kai dai bansan wane irin yaro bane wallahi".

Duk carin da tayi masa yayi uwar shegu yace "ko bayan ranshi 'yan uwanshi su cika masa burinsa, bai yafe ba idan aka ɗaga daga sati biyunnan". Yace wa dattijan har kotu ya basu dama sukai ƙara matukar aka hanasu auren".

 

Yinin ranar wani azababben basir ya tayar masa bashi da sukuni, sai sunturin zuwa bayan gida yake jikinsa duk ya mutu. Talatainin daren ranar ɗakin Inna Habi yake, cikinsa ya juya a ruɗe ya fita ko buta bai tsaya nema ba ya faɗa bayi Inna Habi ta bishi da butar, ya daɗe ciki kafin ya fito yana numfarfashi. Ko da ya doso zai koma dakin. Sukuf yaga shigewar mutum ɗakin Hajara amaryarsa sai yayi tunanin ko sharrin dare ne zuciyarsa na masa wasiwasi yayi maza ya koma da baya, yana hangen tsakar gidan ta hasken farin wata yaga an leƙo an koma, dif aka kashe fitila ƙwai daya haske ɗakin. 

Yace "ikon Allah yau mutanen boye naci karo dasu". Baiyi ƙasa a gwuiwa ba ya tunkari ɗakin Hajara gadan gadan ko da dosowarsa kafin ya kai muryoyinsu sukayi masa maraba gabansa ya fadi, ya matsa kusa. 

"kai abin da mamaki dama ance aljannu na bude ma mutum ido ya gansu, ko dai nima haka ne bari dai inga".

Gabansa na tsananta faɗuwa tare da wani irin tsoro da ya rasa dalilinsa ya tura ƙofar a hankali ya danna kai.

"Innalilliahi wa inna ilaihir rajiun".

"Malam ba salati ba bari in haska maka da kyau ka gani". Inna Habi daga bayansa ta dallaro fitilar ƙwanta. 

"Subhanallahi haihuwar uwarsu kuwa, mutan gida ku fito yau abin kunya a cikin gida". Hankalinsa ya gushe ya rasa mai zaiyi duk ya rikice bakinciki suka dirar masa. Su kam babu ta inda zufa bata keto musu sai makyarkyata, idanuwa ƙulu ƙulu ranar tonon asiri. Ya rarumi katakon da take dogare ƙofa dashi ya buga masa. A tare suka tsandara ihu shi da ita ta runtse ido tana jiran taji saukar abu jikinta shirun da taji ta buɗe idonta ya sauka kan Muntaƙa yashe a tsakar ɗaki a sume. Ta saki kuka mai ƙarfi. Mutanen gidan duk sun firfito. Malam Amadu ya jingina kanshi da bango duniyar na juya masa.

Inna Habi nata maida ma mutanen yanda akayi. Har asalatu anata kiraye kirayen sallah ba wanda ya runtsa hankalinsu tashe ganin irin ruwan da ake ta sheƙa ma Baba Muntaƙa da ya farfaɗo ya haɗa ido da mutane sai ya koma. Ko masallaci ranar basu iya zuwa ba bare maganar hidimar gida.

Baba Amadu ganin abin na Muntaƙa har da iskanci ya cakumi wuyansa yana sakar masa maruka lafiyayyu da yaga wannan bai masa ba duk da haka yaƙi tashi ya samo dorina ya rufe ido yana zabga masa Gwaggo cikin kuka take fadin

"Amadu magidanci kake duka haka kamar ɗan cikinka ka ƙyaleshi wannan kunyar kaɗai ta isheshi".

Yayi biris da ita ya cigaba da dukan. Da yaji abin ba sauki dole ya fara ihun neman agaji don dukar fitar hankali yake masa. Da ƙyar aka riƙe Amadu aka fitar dashi ɗakin yana fadin "Tun yaushe kuke cin amanata? tun yaushe nace? Ita kuwa tana rakuɓe karshen ɗaki borin kunya da muzanta gareta ba'a magana. Suka fita ɗakin suna tir da wannan ɗanyen aiki.

Yana takure wuri guda ya dulmiya cikin tunani, tuni zawo ya kama gabansa. Ta nemi gefensa ta zauna

" Ai mu Malam wannan ba sabon abu bane garemu tun yaushe muka san sunayi shiru mukayi mukace rana dubu ta ɓarawo..."

Ya ɗago ya kalleta tashin hankalinsa baya ɓoyuwa "Yanzu kun dae da sanin ana ha'intata kuka zuba ido ina ta buju buju cikin babbar riga, ashe fanko kuke kallona duk ganin da nake na tsare ko'ina ba wanda zai min wayau ko ta wace hanya ashe ba haka bane". 

"Kai ma dai Malam, uuhm ayi sha'ani kawai ta faru ta ƙare Allah tsare gaba kuma". 

"Haka zakice? haka zakice? Hajara ta cuceni ta ci amanata ta wulaƙantani a duniya". 

Numfashin sa ya soma sarƙewa. Ta fasa kururuwa a ruɗe "ku kawo agaji jama'a". Mutane suka zo kansa ana zuba masa ruwa a hankali bakinsa ke furta

"ku kaini asibiti zuciyata zata buga, ku kaini asibiti nace, a kira min Alhaji Umar". A shashance suke masa kallon mai sambatu.

Ranar gidan ya hargitse. Baba Muntaƙa tun da ya faki ido ya fice, yayinda Hajara ke ƙulle a ɗaki ta kulle kanta. Kunyar duniya ya dabaibayeta.

A safiyar nan ya sa aka doka ma Umar kiran gaggawa. Yayi musu alkawarin su tsumaye shi zai iso da yamma. Baba Amadu ya cika gidan da zagin Hajara yana direwa da tofin Allah tsine a gareta da Muntaƙa da ahalinsa.

Garin masifarsa ya yanke jiki ya faɗi. Aka tarairayeshi aka nufi asibiti bisa umurnin Umar. Da yamma ya iso Zaria kai tsaye ya wuce asibitin shi kaɗai ya wuni sai jefi jefi mutane ke leƙowa. 

 

{63}

 

Sai dare ya tafi gidansu na gado. Yace a nemo masa samarin gidan.

"Maganar asibiti ne to wa zai kwana da Baba ne? naga ba kowa wurinsa ma". Kowannensu sai ya fara zamewa suna ƙirƙiro uzurin ƙarya. Ya lura da haka Umar akwai saurin hawa ya rufe su da faɗa sosai amma hakan bai sa sun canza ra'ayi ba. Ransa yayi matukar ɓaci musamman ma ganin iyayensu na zaune wurin suna kallo amma basu kwaɓesu ba.

Saddika ta fito "Umaru ni zan kwana dashi". Ya ɗago idanunsa jawur "zaki iya?

Tace "eh Allah zan iya". 

Yace "to dauko mayafi mu tafi". Da murna ta juya har yayi mamamakin hakan. Sai gata rungume da kaya tana goye da ɗanta ta taso macen gaba. Ya buɗe baki "meye haka me zan gani zama zakije yi ne? 

Ta juya tana satar kallon iyayenta mata. A rikice tace "err eh dama kayansa ne na ɗauko ko zai buƙaci canzawa".

"To su kuma yaran fa da kika taso a gaba kamar wacce zata yawon bara".

Cike da ƙosawa tace "Amma ai kasan zaman da nake a gidan nan nida yarana ba ƙaunarmu ake ba wa zan barma su? kawai muje kaga dare na daɗa yi". Ya kaɗa kai kawai ya musu sallama suka fita.

Ɗakin ya nuna mata ya juya ya tafi. Yana kwance magashiyyan yana shaƙar bacci an ɗaura masa drip. Gadaje biyu ne a ɗakin ta shimfide yaranta a ɗayan da ba kowa. Gefen gadon da Baban yake shaƙe da kayan tea daga ƙasa kuma su lemo da ayaba da cooler abinci. Ta jawo abincin ta shiga ci komai saida taci a wurin tayi ƙat . Ta shimfiɗa tabarma ta yada kai sai barci. 

Bata farka ba saida Dr yazo suka tasheta, Babanma ya daɗe da farkawa yanata tashinta bataji ba. Suka dubashi suka fita. Basu daɗe ba Umar ya shigo ɗauke da ledoji. Ya gaida Baba da jiki, jiya zuwa yau yayi zuru zuru.

Yace "likita yace jininka ya hau sosai, wai shin me ya faru a gidanne na ganshi a yamutse?. Ya ƙare tambayar yana kallon Saddiƙa yana nemn amsa daga gareta, ta zayyane masa koma.

Ya kaɗu sosai da rauni a muryarsa yake ba Baba haƙuri hawaye nata zarya bisa kuncinsa. Ya miƙa mata leda guda "gashi ki karya sannu da jinya Allah bada lada" . Ya gyara ma Baba kwanciya ya fara ciyar dashi.

Sun jima a asibitin duk yanda yayi da Saddika ta tafi gida ƙi tayi tace "ka bari tukunna". Bai zargi komai ba illa yana gama zamanshi yayi waya gidan a turo wani shi yanzu zai wuce yana da ɗunbin ayyuka a wurin aiki. 

Bai tsaya jiran wanda za'a turo ba a ganinshi ƴaƴanshi ma na cikinshi basu nuna kulawa kan mahaifinsu ba bare shi. Yayi masa sallama ya fita harabar asibitin yana waigen inda zaiga Saddiƙa.

Yana buɗe mota ya shiga itama ta buɗe ta tura yaranta, mamaki ƙarara fuskarsa.

"Bafa zan biya gida ba ga kuɗi dai ki hau a daidaita" Ya karkace ya zaro kuɗin.

Ta marairaice fuska "Ni fa nufina ka tafi dani katsina ne, ni bance ka kaini gidanka ba gidan Aisha zaka kaini dan Allah Yaya kayi min rai zaman gidanmu ya gagareni inje can in huta dan Allah yaya". Yanda take maganar kamar zata fashe masa da kuka ta bashi tausayi. Yayi dogon tunani watakila zuwanta ya samar mata kwanciyar hankali da natsuwa. Ya kalleta da yaranta kamar waɗannda suka kubuta daga yaƙi sunyi wujiga wujiga tsananin tausayinsu ya kamashi. Baice komai ba ya tada mota ya cilla bisa titi.

 

RAYUWARMU A YAU

© Jam33lerh

&

© Ayeesh chuchu

®NWA

 

{64}

 

Gidan Aisha ya nufa da ita duk da ba haka ranshi ya so ba sanin halin matarshi ya sanya ya kaita gidan Aisha. Bai shiga ba ya kirata a waya ya sanar da ita zuwan Saddika shi kuma ya wuce. 

Aisha tayi murna sosai ta fito cikin shiga ta alfarmar da fara'arta ta tarbeta tana fadin "Zuwan bazata haka Saddika, maraban ku muje ciki". 

Ta gabatar mata da kayan motsa baki fuskarta ba yabo ba fallasa, fargabarta guda yanda maigidan zai karbi baƙuwar tasu ta bazata. 

Suna nan zaune suna hira sama sama, tana kaiwa da kawowa tsakanin kicin da falon ta karaɗe gidn da daddaɗn kamshin abinin da tae shirya ma mijinta. Saddika ta kasa haƙuri tace "wannan ɗaukar alhaki ne Aisha ki bar ganin yanzu muka gama ci yi ki zubo mana wannan ɗin muyi mu suɗe". Aisha batyi mamaki ba dama tasan halin mutumiyar. da yaranta sun lalata mata falon da abinci. 

Har mijin nata ya dawo bai nuna komai ba illa tarba mai kyau, a gurguje ya gama abinda zaiyi ya wuce ɗakinsa, sai da ta nuna mata masauki ta wuce wurin mijinta. A can ɗin rabin hankalinta na ga baƙuwarta, ta daɗe wurinsa sannan ta fito ta tarar da ita hakimce a falo tana kallo ta ika kamar zata fashe tace 

"ah ah Saddiƙa kallo ake? Idonki ya gane miki kuma kike ƙara tambaya". Aisha ta kame baki

"toh Allah baki haƙuri halan an bata miji rai ne?. Taja mummunan tsaki "don iskanci duk salon ki nuna min kina da miji, kin wani ƙule bana ko jin ɗuriyarki ba abokin hira kina can kin ma mance kina da baƙuwa wannan ai tozarci ne". 

Aisha bata son maganar tayi tsawo don haka tace "kije ki kwanta mana dare ya tsala kihuta gajiya nima zan shige ciki". 

" Wai ni shin baƙuwa kika maida ni ne? ai na san hanya ba sai kin nuna min ba 'yar daɗi miji kije Allah tashemu". Aisha tayi murmushi ta wuce dakin mijinta. 

Kasancewar ranar weekend babu aiki basu fito da wuri ba. Saddika tun tashin safe ta tarkato yaranta suka fito falo ta kunna kallo tana tsumayen fitowar Aisha har mai aikinta ta shigo ta gyara falon ta fita babu Aisha bare mijinta. 

Zaman da kallon har suka soma gundurarta ta fara zagayen gidan tana neman inda zata ga mai aikin ko inda Aisha take. Da ƙyar ta gano mai aikin a kicin tana gyare gyare tace "wai ina Aishar ne". Tayi mamakin jin Aisha gatsau babu sakayawa tayi mata banza ta cigaba a aikinta.

"Wai babu abinci ne gidannan ko ba aikinki kenan ba, ni yunwa nake ji na gaji da jiran fitowar Aisha".

Tayi mata kallon raini haɗe "kina ƴar aiki ina ƴar aiki kina bani umurni to ban dafa ba", 

"Ke! kinsan ko ni wacece a gidan nan". Mai aikin tayi tsaki ta cigaba da abinda takeyi ta barta tsaye lokaci mai tsawo Saddiƙa na faɗa mata maganganu ta sassauta murya 

"nuna min ɗakin maigidan". 

A razane ta kalleta matar nan fa Ƙarfin halinta ya fara wuce hankali "Ban sani ba". 

Saddiƙa ta nunata da yatsa "ke na lura kanki na rawa ƙaurin talauci na sa kanki hayaki ki bari masu gidan su fito zaki gane matsayina ya isa insa su sallameki talakar banza kina wasa dani". Taja tsaki ta dungure mata kai.

Mai aikin batayi jinkiri ba ta fisgota falla mata mari lafiyyyu, ta juya baya ƙirjinta na bugawa da fargaba Allah sa bata da dangantaka da mutanen gidan, da ta boni amma suffarta da suturar jikinta bata taba ganinsu tattare da ɗunbin danginsu dake zuwa gidan ba. Ta kawar da surkullen Saddika ta cigaba da aikinta.

Jiki a sanyaye Saddika ta kma falo zuciyarta na turiri ta haɗa tagumi hannu biyu tana tunanin mai zatayi ta huce abinda mai aikin tayi mata.

Tana nan zaunee falon cikinta na kiran ciroma da neman agaji har azahar na neman yi masu gidan basu fito ba, duk wata dauriya ta nemeta ta rasa wannan baƙin wulakanci da Aisha tayi mata ya tsaya mata a rai, ba don gidan ƴan gayun ya burgeta ba da Aisha bazata fito ta tarar da ita ba da irin wannan tozarci da akayi mata. Ta koma kicin da nufin duba firij ko ta dafa abinda zataci mai aikin ta koreta har da su gori. 

Da taga ba sarki sai Allah ta koma lallamin mai aikin "ko dai sun fita gidanne? Tayi dariya "kinsan yan gayu ranar sati basu fitowa sai azahar watakila ta mance da ke ne". 

" kan uba ta mance dani, ai ko zata fito ta sameni, arziki ba hauka bane ba zan ɗauki raini ba". Ta koma ta hakimce a falon ranta ɓace tana jiransu tana ɗura ma yaranta dake koke koken yunwa zagi.

 

{65}

 

Aisha bata fito ba sai da akayi azahar. Suna haɗa ido da Saddiƙa sai da gabanta ya fadi a zahirin gaskiya ta mance sam sunyi baƙi gidan hidimar mijinta ya ɗauke mata hankali sai da tana shiri ne Saddiƙa ta faɗo mata a rai.

Tayi ƙoƙarin ƙawata fuskarta da fara'a ta ƙarasa tana ba Saddika haƙuri "hidimar dear ta shashantar dani kiyi hakuri dan Allah".

Tyi narai narai da ido "Dama haka zakice mana dama masu kuɗin nan haka kuke don kinga nazo wurinki kike neman wulaanta ni ba komai laifina ne". 

Ta zauna kusa da ita tana ɗauke numfashi sakamakon gursumetin warin da ya doki hancinta ta dafa kafaɗarta "ba haka bane... ". 

"Sweetheart shine kika taho kika barni ko, kinsan kuma bazan iya shirya kaina ba". 

Ta tashi da salo ta tarbi mijin nata ya manna mata sumba tare da tarairayota jikinsa ya manna bakinshi da nata gaba ɗaya sun shagala sun mance ba su kaɗai bane a falon. 

"Iskanci da rana tsaka". Muryar Saddika ta katsesu. Aisha ta diririce tana neman zamewa daga jikinsa. Ya matseta gam suka isa ga Saddika da ta kusa somewa a zaune take kallonsu galala. 

"Ohh baƙuwarmu kinsha zama kiyi hakuri mun sha'afa ne kina gidan", Bata tankashi shima bai damu ba "so ya baƙunta hope gajiya ta tafi? Ya sunkuya kasa yana ma yran wasa amma bai kai hannunsa ko jikinsa kusa garesu ba domin tsaftarsu bata gamsheshi ba. 

Kunya ta kama Aisha don ta tabbatar ruwa baiga jikinsu ba duk wayewar garin nan. Da wayau ta ja shi dinning inda mai aikin keta zaryar jera abinci. Ta zuzzuba masa komai ta zauna tana ciyar dashi tare da yar hira. Hakan da tayi ya tunzura Saddika ta tashi ta fisgi yaranta zuwa ɗakin da aka saukesu suna ƙara domin fisgar bata wasa bace. Suka bita da kallo.

Yayi dariya "da alama zamuyi rikici da bakuwar tamu, Kije wurinta kinji karki damu yau na ara mata da ke yau kawai fa". Tayi murmushi iya lebe ta wuce shi. 

Ƙofar dakin sukaci karo tana janye da kayanta "ah ah Saddiƙa ya haka? Tayi mata banza tana ƙokarin wuceta Aisha ta hade rai to sai ki tafi idan kinsan hanya ko kuwa bara zakiyi a titi a baki kudin mota". "Wurin mijinki zanje ya bani nasan shi ba irinki bane in ta kama ma har zaria sai kiga ya kaini amma bazan koma ba gidan Umaru zani "kiyi hakuri kinji Saddiƙa muje ciki kiji". 

Tana turjewa da noƙe noƙe da ƙyar ta lallabata suka koma. Wani fitinannen wari ya daki hancinta da sauri ta damƙe hancin "bayan gidanne ke wari haka? 

Saddika ta hade rai "ke fa saranki kenan wulakanta mutane yo meye". Ta kaɗa kanta kawai ta wuce toilet ɗin tayi flushing tana ƙare ma toilet ɗin kallo daga jiya zuwa yau Saddika ta fara sauya masa kamanni. 

Ta juya da sauri ta bar ɗakin ta dawo tare da mai aikinta ta umurceta ta wanke shi. Nan da nan ta cika umurninta. Ta koma gefen gado "Saddika ke kika kawo kanki gidan nan don haka dole ne kiyi hakuri abubuwanda zaki gani,tsakani da Allah mu ba irinku bane tsakanina da mijina akwai kyakkyawan fahimta kodayaushe muna manne bana yarda inyi nesa da shi kuma don kinzo gidan nan bazan gujeshi in barshi cikin kaɗaici ba saidai kiyi hakuri". 

"Ah lallai ba laifi dole ki tozartani tunda nazo gidanki ni zaki nuna ma son miji, namiji ɗin banza da bai wuce anjima ya narka miki saki ba". 

Aisha ta dafe kanta cike da bacin rai "yanzu wai duk baƙin da nake ja baki iya fassara shi ne? Mai aikin ta fito ta durkusa "Hajiya na gama". Hannu kawai ta ɗaga mata ta tashi ta fice.

Sun dade zaune shiru Aisha na tunanin ta inda zata fara magana can dai ta gayyato dukkan ƙarfin hali tace "Saddika na san tun wayewar garin nan baki sa ma jikinku ruwa ba anya rayuwa zata tafi haka? baki so Allah ya baki miji anan kiyi aurenki". Ta saki dariya 

"kwarai kuwa ai suna daga cikin abinda ya sa na taho nan ɗin". Tayi murmushi "to dan Allah kiyi wanka ki gyara kanki da yaranki kizo ga abinci sai mu tattauna kinji". Taje ta haɗa mata ruwan ta nuna mata yanda zatayi ta fita tana ƙara jaddada mata tayi wankan sau biyu ne in ruwan ya ɓaci ta canza wani. 

Ta koma falo wurin mijinta ta faɗa jikinsa da shagwaba shima yana biye mata. Ya tallabo haɓarta "dear na karanci rubutacciyar damuwa a fuskarki please karki ɗauki zuwan Saddiƙa gidan nan kamar takura ko wani abu, in don tani ne babu damuwa naji daɗin zuwanta ne domin ina tsananin tausayin irin rayuwar da takeyi amma kinga zuwanta wurinki ai zai taimaka matuƙa ki canza mata alƙibla ki mayar da ita mace ta sosai, karki damu kinji duk cikin zumunci ne zaki sami lada". Ta ƙanƙameshi tana cike da annushuwa samun miji gwarzo mai goya mata baya tare da ƙarfafa mata gwuiwa.

Ganin Saddika kawai sukayi kansu da ɗaurin ƙirji zuciyarsu sun sosu. Aisha ta danne nata bacin ran ta tashi tajata suka koma. Ta ciro mata kaya cikin kayanta ta bata ta sanya. Yaran dai yagaggun kayansu aka mayar musu tunda babu kamar nasu. Ta koma ta kawo musu abin kari jikinsu kamar mazari suka rufar masa. Hawaye suka taru a idonta.

Saida suka natsa suna hira tace Saddika kin duba kanki a madubi kuwa? Dubi yanda kikayi kyau ke ɗinma wata zankaɗeɗiyar macece amma rashin gyara da kula kin mayar da kanki tsohuwa, inda ace kina wanka kina kula da kanki yaushe mijinki zai wulakantaki". "Wannan tsinannen shi kanshi ma ina yayi wankan bare ya damu idan ninayi? tabɗi baki san Kabiru bane wani ƙasurgumin ƙazami ne da kike ganinshi ". 

Aisha ta fashe da dariya "kai Saddika kin iya sharri wai ƙasurgumi, ke dai ki manta da sha'anin wani Kabiru ki fuskanci rayuwarki ta gaba kinga kina son ki sami miji a nan to sufa basa son ƙazama" da kike gani fuskarta dauke da fara'a tace 

"haba? 

"Sosai kuwa, ki dage da wanka sau uku a rana ke da yaranki karki yarda ku zauna cikin ƙazanta komi ƙanƙantarsa , sannan bayan gidan can nadai nuna miki inda zaki dinga dannawa idan kunyi amfani dashi, zan sa jummai ta ria shigowa tana gyara miki ɗaki kullum".

Ta zumɓura baki "ni dai matar na batayi min ba bata da mutunci bakiga kallon uku saura kwatan da take min ba, talaka da ita ma". Aisha tayi murmushi

"Ba ruwanki da ita komai naki na hannu na kuma ki daina falo mana falo babu sallama kinga nida mijina ne gidan bakisan halin da zaki tsince mu ba".

"Ai fa aikinki kenan miji miji su mazan har wata tsiyace da zaki wani talike kanshi, Allah ya yaye miki jaraba". Tayi dariya ta share zancen, Saddika sai gyaran Allah an riga an gurɓata mata zuciya ta yanda bata ganin miji da daraja amma a hankali dai ta ƙudiri aniyar sai ta gyareta.

Da yamma ta kwashesu ita da yaranta suka tafi shago ta kwaso musu kayan sawa da ita kanta Saddikar suka biya wurin ɗinki ta basu sannan suka koma gida. 

Saddika cike da yaba yanda Aisha ke sarrafa motar tace "bazaki kaini inga gari ba nazo a bakuwa?. Idonta bisa titi tace "ki bari wannan sai na nemi izini musamman sai mu yawata amma yanzu kinga ban tambayeshi ba nan in kawai yasan zanje". 

Saddika ta taɓe baki ta juyar da kanta gefe tana ƙunƙuni "ai ni kam zansha kallo ranar da ya tashi nuna miki shi namiji ne, bari dai amfaninki ya ƙare ai kin kusa haihuwa lokacin zaki zama ke da banza duk daya". Aisha tace "Saddika kenan".

 

RAYUWARMU A YAU

© Jam33lerh

&

© Ayeesh chuchu

®NWA

 

{66}

 

Zaman Saddiƙa katsina wani bahagon zamane cike da haƙuri a bangaren Aisha. Ayyikata kamar ai taɓin hankali bata da kunya da kawaici ba dama Aisha da mijinta su zauna falo atazo taui mus bake bakee bata damuwa kna da higar da zatayi. Ta'adi kuwa tayi mata ba kaɗan ba, tayi mata asarar kaya sosai sabida tsananin karanbaninta. 

Ta sha fama da ita kafin ta fara wanka. Sai da sukayi kwana 4 ta gane basa wanka. 

Ta daɗe tana mamaki yanda akayi bashin da sukeyi bai rabu da jikinsu ba alhalin ta tanadar musu kayan ƙamshi na wanka dana fesa ma jiki sai da wata rana ta shiga ɗakin Saddiƙar daidai lokacin ta fito wanka ta juya baya tana zaɓa kayan sawa a na Aisha ta hango bayanta danƙare da datti ta matsa kusa da ita tabbas dauɗa har murjewa take a jikinta.

Ta dafe kai "Saddika meke damunki ne fisabillillahi? wanka ma babba dake sai anyi fama da ke? Jikinta a sanyaye ta juyo 

"To banson yin ɓarnar ruwan ne idan ya ƙare fa? Yanda kike sani kullum danna abin kashin can ai sai ruwan ya ƙare watarana sai mu rasa na tsarki ma". 

Duk da bacin ran data sanyata saida ta murmusa "Saddika manyan gari ni me zan miki ne ki riƙa fahimtar magana". A nan tayi mata bayanin komai yayinda tausayi ya kamata wato ta saba da rayuwar maneji su a wurinsu ruwa ma da ƙyar ake samu wani sa'in sai an siya. Rayuwa kenan. 

 

Satin Saddiƙa guda a gidan Umar ya ziyarce su. Sai da suka keɓe da Aisha yake jinjina mata namijin ƙoƙarin da takeyi na zama da Saddiƙa "mata kamar mahaukaciya". Tayi dariya 

"Ai jininmu ne ba yanda zamuyi da su". Yace "hakane gidana yakamata ace ta sauka amma baƙin kishi irin na Raliya da rashin haƙuri bazasu daidaita ba, tana ƙara sati zanzo in mayar da ita kafin t jao miki magana gidan aurenki". 

Ta gyara zama "wai ta fara bani labarin daya girgizani bamu ƙarasa ba, ina taso in kira ka bansamu dama ba wai da gaske ne an kamasu tare? Ya girgiza kai annurin fuskarsa ta ɗauke 

"ai ke dai kawai Allah ya kawo sauki, gidan nan kwata kwata ba gidan da zakayi alfaharin nuna su bane, kinsan mutumin nan iyalinsa ko ciwon mutuwa zasuyi ko chemist baya kaisu saidai su kai kansu amma kiji hawan jini na kayar dashi yasa aka kirani wai akaishi asibiti sukayita masa habaici, shi kuwa ko a jikinsa in taƙaici miki tsirfa iri iri ya dingayi, ina nan aketa min waya yace a siyo kaza a siyo kaza kuma nasan harda na ƙarya kawai dai na biye masa ne a rabu lafiya". Aisha ta katseshi

"Inda kana Portharcourt ɗin ina ma zasu ganka bare". Yayi kwafa "ai inaga wani transfer ɗin zan sake nema can garin inyamurai inga ta tsiya". Ta katseshi da 'yar dariya 

"a'a kai kuwa haka nan dai za'ayita haƙuri sakayyace muke gani ka mance izayar da sukayi mana a gidan?

"Hakane, shekaranjiya naje an sallameshi, wai zai shigar da ƙara kotu wai in tsaya masa, kai tsaye nace a'a bazan yi ba dukkanku iyayena ne shine fa yaji haushi yayi ta sirfa min zagi a waya kamar ubana, da na tuntumi Baba da maganar cewa yayi in janye jiki na ba ruwana kuma naji dalin haka, Babu inda nasan mutanen nan basu da tunani ba wanda yayi zancen Saddiƙa sai fa a shekaranjiya, Ina yaron nan Sabi'u da akace ya zama ɗan daba",

Tayi jim cikin tunani bazata mantashi ba kuwa wanda yayi ƙoƙarin yi mata lalata zuwanta na farko da sauri ta gyaɗa kai "na gane na ganeshi".

"Wai can wurin daban su sukayi faɗa da wani murus ya kashe yaron har lahira, yana ganin haka ya arce ya bar gari, iyayen basu sani ba basu ƙara jin ɗuriyarshi ba kuma basu nemeshi ba sai a shekaranjiya 'yan sanda sukazo tafiya dashi a sannan ne suka faɗa musu su sun ma mance rabon da su sashi a ido, yanxu dai maganar na kotu".

Aisha ta shiga salallami jiki har rawa yake ta kasa magana. Ya cigaba "wai kinsan Baba komawarshi gida ya shiga tsine ma Sabi'u wai ya sallamashi ya tsameshi daga zuri'arshi ba zai goga masa bala'i ba, maimakon addu'ar shiriya, ranar kuma mijin Saddiƙa ya sake dawowa ya tafi da matar shi tsabar rashin tunani lokaci ne suka tuna da ita wai sun zaci ta gudu wurinshi ne kiji hauka fa". 

Ita dai banda kaɗa kai ba abinda takeyi al'amarinsu ya wuce hangenta

"yace shi bataje masa ba bai ganta ba, wai saiga mutane hankalinsu tashe suna son sanin halin da take ciki, ni baƙinciki ma ya hanani magana, shi kuma jakin ya saka bala'i boyeta sukayi sufito masa da matarshi da 'ya'yansa kiji ƙarfin hali wai ko a biyashi kuɗaen da ya kashe mata tun suna samartaka har aurensu kinji fa kamar a wasan kwaikwayo takaici ya sani damƙo wuyan matsiyaci na zuba masa maruka na koreshi, ba saiga Baba Amadu ya bishi fa har ƙasa yana roƙonshi yayi haƙuri na rantse kiris ne ban haiyi zuciya ba".

Aisha tayi dariya sosai "kai Yaya haɗiyar zuciya kamar haɗiyar panadol". Ya harareta "ke fa wani lokacin baki iya cin ribar zance ba nufin ki ƙarya nake rattabowa ko me? 

Tana cigaba da dariya tana bashi hakuri da hannu "sorry ba haka nake nufi ba ina jinka yaya na". Yayi tsaki 

"dan banza da yaga ya kuɓuta hannuna a zaure yake cema Baban wai ya basu kwana biyu su fito masa da ita in ba haka ba kome yayi su suka ja, shi kwa sohon majadu ya natsu surukinsa na faɗa masa magana son ranshi". Ta riƙe baki

"Babnka ne fa Yaya bai kamata ba gaskiya".

Ya ɓagarar da zncen ta "ina faɗa miki gida na can a hautsine, ita Hajarar ya korata gidansu, Baba Muntaƙa ma tunda ya ari na kare ba wanda ya ƙarajin luriyarshi iyalinsa baki ga yanda suka koma ba abin tausayi ko fitowa waje basayi, komai nake faɗa miki ya cakue musu ga ɓatan Saddika don ban fada musu tana nan ba, in banda jahilci a gana ma ɗiyarka irin wannan izayar ta dawo da ƙyar suna fatan mayar masa da ita,

Kinsan Baba Amadu da zagi kamar ya haɗa dangi da maguzawa tsina da zagi bansan adadin da yayi akan Saddiƙa ba, ya koma kamar zararre baki ga yanda ya zabge ba fitintunun rayuwa sun gallabeshi. 

Aisha ta rausayar da kai "Allah sarki na tausaya masa abubuwan sun masa yawa ga kuma kotun da aka makasu na rigimar Sabi'u ga rigingimun liyanshi mata suma a gidajen mazajensu zaman ba daɗi, to ai sai ya haƙura da kai Baba Muntaka yaji da wannan ma in banda abinshi ma shari'a da ɗan uwanshi ai kamar kanshi ya daɓa ma wuƙa, amma abu baiyi daɗi ba wannan irin cin amana har ina ni Aisha".

"Ki bari kawai abin nan ya tsaya min a rai, bakiji bama, matanshi sun zugeshi wai autanta ɗin nan data yaye basu yarda an shi bane". 

Ta zaro ido "kuma?.

"Ai ke dai kawai Allah ya kyauta ni canza layi ma zanyi suje can su ƙarata banji ba ban gani ba bazan sa kaina a fitintininsu ba, ubana bai lauko min magana ba sai wai can". 

Aisha ta shiga tausarshi "ai ba'a haka yaya ka riƙesu duk daya watarana sai labari".

Suna cikin hirar Saddiƙa ta ɓullo taci riga da skirt na atamfa kamar ba ita ba, saboda matsawar da Aisha ke mata kan tsafta har ta fara canzawa. Ta washe baki

"ashe baka tafi ba ina can ina kallo". 

Da sigar zolaya yace "muna shirye shiryen komawarki zaria ne gobe zanzo in mayar dake". Ta daka wani uban tsalle sai gata bakin kofa "yasin ba inda zani haka kawai ina cikin daula a datse min ni kam naga wurin zama". 

Ya gimtse dariyarsa "mijinki ya zo tafiya dake ne ai".

"Ko uwarshi ya ɗauko tazo biko na ba inda zani", ta fashe da kuka "ni fa buri na in sami miji anan inyi aurena baki alaikum". Suka yita dariyar maganganun Saddika har mijin Aisha ya dawo ya iskoshi akacigaba da hirar dashi.

 

{67}

 

Bayan kwana biyu Aisha ta ɗauketa suka tafi gidan Lubiee, tun zuwanta take mata zancenta, tund ta faɗa mata tayi aure itama anan Katsina shikenan ta hura wuta sai ta kaita, dole Aisha tasa rana musammn domin ziyarar ƙawarta. Zumuɗi ya cika Saddiƙa domin bata mance da karamcin Lubiee a gareta ba.

Tafiyar yan mintuna ya kaisu gidan mijinta. Tarba ta musamman tayi musu dama tasan da zuwansu ta riƙa ina zata saka da Saddika hakan ya ƙara dasa mata son Lubiee. Bata nuna baƙunta ba sam har taso fin Aisha zama yar gida su dai saidai suyi ta dariyar wautarta. 

Sai dare suka fara haramar tafiya dawowar mijin Lubiee ya tsayar dasu tunda suka ƙule ciki bata fito ba. Saddika kam ta daina mamakin wannan rawar ƙafa da sukeyi akan mazajensu tana dariyar mugunta a zuciyarta tana ƙissima dariyar da zata musu ranar da mazajensu suka tashi juya musu baya a tunaninta.

A fili kuwa sai cewa tayi "ku dai kun bani wallahi mata ba aji kuyita wani rawar jikin akan namiji zaku sani ai ina nan". Aisha tayi dariya 

"Zakiji alheri kuwa insha Allahu". Saddika tayi dariyar mugunta 

"ha yarinya bazaki gane karatun nawa ba don yanzu kuke amare shiyasa mu mun dade a harkar munsan komai zaku gani kuma". Aisha tayi mata shiru domin wannan mugun fata da take musu ya fara ɓata mata rai.

Sai da ta haɗa da kiran Lubiee a waya sannan ta fito tana dariya take basu hakuri. Ta miƙa ma Saddika leda shaƙe da kaya tayi ta zuba godiya. 

Har sun kai bkin ƙofa ta tsaya ta juyo "ni kuwa mai zai hana in kwana? Gabansu ya fadi a tare sukace

"kwana! Aisha ta kara da cewa "a ina?

Kafin tayi magana ta fisgi hannunta suka fita tana cema Lubiee "sai munyi waya kawai".

A mota faɗa ta rufe Aisha dashi "ke na lura duk hanyar ƙaruwa toshe min kikeyi to meye don na kwana gidanta, mata tana nuna min ƙauna kamar jininta, ji hidimar arzikin da tayi min, kika sani ma ko an uwanta in suna zuwa gidan wani ya ganni ya ƙyasa", tayi kwafa ranta bace "wallahi baki kyauta min ba tsakani da Allah". 

Kallo daya Aisha tayi mata ta kauda kai a ganinta mai cikakken hankali ake ba amsa.

 

*RAYUWAR MU A YAU*

 

©Jam33lerh 

Ayeesh Chuchu 

 

®NWA 

 

69

Zaman Saddik'a a gidan Aysha yasa ta dan san wasu abubuwan na rayuwa, ta dan fara tsabta ita da yaranta wanda kullum faɗansu da Aisha kenan. Rashin tsabtar Saddik'a. 

Aisha zaune da tsirtsetsen cikinta yau ko gobe haihuwa ta mik'e kafa tana kallon tashar _African Health Tv_ suna tattaunawa akan abubuwan da suka shafi masu juna biyu. Saddik'a ta shigo falon sanye da ɗaurin kirji. Tana saɓe da ɗanta Lawal, Zainab yar shekara uku na biye da ita a baya. 

Aisha tace "haba Saddik'a yanzu duk kayan da na baki babu na sawa a ciki zaki fito da ɗaurin kirji falo?". 

Saddik'a tace "ba zan iya sa wadannan kayan a cikin gida ba ai na zuwa unguwa ne". Takaici ya kama Aisha tace "Wallahi matukar ba zaki daina gidadanci da rashin tsabta zan kira Yaya Umar ya zo ya maida ke Zarian tunda dama har yanzu Kabiru be sake ki ba na gaji kullum baki na sai yayi tsawo dan magana , ya isa ace idan karatu ne kin haddace shi haka". 

Saddik'a tace "ki rufa man asiri duk yanda kika ce zanyi, ni wallahi ba zan koma Zaria ba, kusan yanda zaku amso min takardar saki na wajen Kabiru". 

Aisha tace "in dai kin natsu mi zai hana Saddik'a". 

Sannan ta samu Saddik'a ta koma ta sanya kaya jikinta. 

Haka Aisha ke hakuri da fama da muguwar dabi'ar Saddik'a.

Dawowar Al-Ameen mijin Aisha yasa ta tashi ta shige ɗakin da aka ba su. Aisha da ta mike da kyar, yayi saurin dakatar da ita, ya ce "Baby na hana ki wahala da kina ganin kinyi nauyi sosai kina wahalar mun da kan ki, na yafe duk wani abu sai Allah ya sauke ki lafiya". Murmushi tayi na jin ɗaɗin irin yanda yake tarairayarta. Mikewa yayi yace "bari kiga in dai ina gida ko tafiya bance kiyi ba". Aisha ta marairaice ta ce "haba Sweetu kasan fa _exercise_ nada muhimmancin gaske wajen mace mai ciki. Yace" Naji amma dai na riga na faɗi ". Cak ya dauke ta haɗe da brief case din shi. Karaf akan idon Saddik'a, tayi tsaki ta ce" ýan iska wannan ai lalata ce". Dariya ta suɓuce ma Al-Ameen, be kula ta ba har sai da ya dire Aisha akan _sofa bed_ dake ɗakin shi. 

 

Yayi wanka ya kintsa duk tana kwance ya zo yana matsa ma ta kafafunta da suka kumbura. Ya ce "Baby ina ga ya kamata asa ɗiyar Saddik'a _school_ ta isa ta fara shiga aji".

Aisha tace" ni Saddik'ar ma ni ke so asa a islamiyya da makarantar yaki da jahilci dan abubuwan da take yi hadda rashin ilimi da gogayya da wayayyun mutane". Yace "kin kawo shawara kam, zuwa gobe sai ki tuna man tunda farkon _first term_ ake yanzu. Tace" nagode Sweetu Allah shi kara arziki mai amfani, ya kuma bar mu tare ". Y a ce" amin, tare da kai ma ta _peck_ a kunci.

Washegari da safe bayan sun yi _breakfast_ da yake _weekend_ ne, Aisha ta tuntubi Saddik'a da maganar ta ce "Saddik'a ya kamata dai yanzu asa Zainab makaranta, kema ki koma islamiyya da kuma yaki da jahilci dan ki ceto kan ki daga halaka". Budar bakin Saddik'a tace "lallai ma Aisha yanzu gamsamemiya da ni zan koma makaranta ai da kunya. Ita Zainab nawa take duka duka bata fi shekara uku ba wannan sata maka ai asarar kuɗi ne". 

Baki Aisha ta saki tana kallon wawanci irin na Saddik'a. Tace "Har yanzu Saddik'a da sauran ki, nida ke son ceto rayuwar ki, ki natsu ki gane babu mai auren ki koda ansa Kabiru ya sake ki anan Katsina, ke ko yaron gidan nan Salele ba iya auren ki zayyi ba dan kiji da kyau, a hakan zaki samu miji kina gidadanci. Zainab da kike cewa bata isa sawa makaranta ba to har yan shekara biyu ake sawa, kiga yaro ya taso da kwazo. Shiyasa nike son ta fara zuwa, makarantar da za'a sa ta haɗe take da islamiyya kinga da Lawal ya dan tasa sai shi ma a sa shi ". Saddik'a ta kaɗa kai cike da gamsuwa da bayanin Aisha. 

 

Cikin yarda Allah aka sa Zainab ɗiyar Saddik'a makaranta, ita ma Saddik'a ta fara zuwa islamiyya ta matan aure da ke unguwar. Sannan tana zuwa makarantar yaki da jahilci Asabar da Lahadi tun safe karfe 8am sai 4pm suke dawowa.

 

chuchungaye.wordpress.com

*RAYUWAR MU A YAU*

 

©Jam33lerh 

Ayeesh Chuchu 

 

®NWA. 

 

70

 

*BABBAN GIDA*

Rigima ce babba da ta kunno kai a gidan, wanda gaba daya zaman lafiya yayi karanci a gidan. Dama yaya lafiyar kura... 

Hankalin Gwaggo ya matukar ɓaci, saboda rarrabuwar kawuna da aka samu a gidan sakamakon kama Baba Muntaka da aka yi da Amarya Hajara matar Baba Amadu. Duk inda mutum ya kutsa a gidan maganar ake tun bayan dawowar Baba Amadu daga asibiti. 

Fitowar shi daga bayi kenan yayi sashen Gwaggo, bayan sun gaisa yace "Gwaggo ni fa maganar Muntaka kotu zan kai dan bazan iya zama da ɗan uwan da zai ci amanata, yana haik'e matata". 

Gwaggo ta ce "yanzu Amadu a taru a rufa ma juna asiri ka gwammace ka je ka yi tonon silili kowa yaji abinda ke faruwa". 

Yace "Gwaggo zuwa kotu fa ba fashi, saboda wannan abu har jini na sai da ya hau". 

 

Suna cikin maganar suka ji Sallama daga bakin kofa. Gwaggo ta washe baki tace "marhabin lale da Alhaji Ummaru". Murmushi yayi ya duka yana kokarin cire _cover shoes_ dake kafarshi. 

Baba Amadu yace "ka shigo da takalmanka dan yanzu sai ka nema ka rasa". 

Ya shigo ya duka har kasa ya gaida su. Bayan sun gaisa Baba Amadu yace "Naji ɗaɗin zuwan ka Ummaru dama kotu zan kai karar Muntaka Kaga sai ka shige mun gaba". 

Umar yace "haba baba wannan maganar fa bata kuto bace, kamata yayi a zauna a gida a warware wannan matsalar, zuwa kotu zai iya jawo wata rigimar wadda sai ta shafi kowa a gidan nan, saboda yanayin tsarin zamantakewar gidan ma akwai gyara sosai a ciki". Gwaggo ta ce "Yauwa Ummaru maganar da mu ke kenan". 

Umar yace "taya zan raka ka kotu baba bayan duk ɗaya kuke a waje na kai da Baba Muntaka". 

Da kyar da suɗin goshi baba Amadu ya amince da barin shigar da kara kotu.

Yace "toh yanzu dai sakin Hajara zan yi dan bazan iya zama da ita ba". Umar yace "ka jira baba wannan abun bana gaggawa bane, sai abinda addini ya tanadar za'a yi, dan haka zan dan kwana biyu a nan kafin in tafi komi zai warware In Shaa Allah". 

 

_BAYAN KWANA BIYU_

 

Umar ya je gun babban limamin masallacin da ke unguwar, fitaccen malamin addini ne da ya shahara wajen bada fatawa. Bayan sun gaisa Umar ya kwashe duk abin da ke faruwa a babban gida ya faɗi ma malamin. 

Malamin ya ɗaɗe ko motsi be yi ba, tana ta'ajjibin abinda Umar ya faɗi ma shi dangane da rayuwar da mutan gidan ke yi. Yayi ta jimami da irin halayyarsu. 

Yace "Malam Umar ya zama dole mu je wannan gida ko dan a ceto rayuwar mutan wannan gida daga halakar da suka faɗa". Umar yace "nagode kwarai Malam Allah shi saka da mafificin Alkhairi". 

 

Kamar yadda Malam ya alkawarta washegari ya iso babba gida bisa ga jagorancin Umar. A sashen Gwaggo mutanen gidan suka taru, yara da manyan su. 

 

Malam ya fara da korar shedan a zaman su, ya fara bayani akan hakikanin mi Zina ke nufi kamar haka :" Lafazin ZINA a shari'ance yana nufin saduwa da mace ba tare da an yi aure ba ko an mallake ta. Haka nan akan yi amfani da lafazin zina akan abin da ba

kai saduwa ba, kamar yadda ya zo a hadisin Abu Huraira (R.A) Manzon Allah (S.A.W) ya ce: "An rubuta wa dan Adam rabonsa na zina babu makawa sai ya

same shi,zinar idanu ita ce gani, zinar kunnuwa ita ce ji,zinar harshe ita ce magana,zinar hannu ita ce damqa,zinar qafa ita ce taku, zuciya kuwa tana

kwadayi tana fata,farji kuma shi yakegaskata haka ko ya qaryata" Muslim.

A cikin wannan hadisi zamu ga

yadda Manzon Allah (S.A.W) ya nuna cewa kowane dan Adam an rubuta masa rabonsa na zina, kuma zai sami wannan rabo babu makawa, sai dai ba

za a kama shi da laifi ba har sai idan ya gasgata abin da idonsa ko kunnensa ko hannunsa ko qafarsa suka jiyar da shi,ta hanyar yin amfani da farjinsa don biyan buqatar wadannan gabbai, wannan shi ne ma'anar faɗin Manzon

Allah a qarshen hadisin da ya ce, "farji shi yake gasgata haka ko ya qaryata" (Duba Sharhi Sahih Muslim Na ImamNawawi ).

Sannan wannan hadisi yana

nuna mana cewa ana amfanin da lafazin zina akan abin da bai kai gasaduwa ba, amma duk da haka ba a bashi hukuncin zina na jifa ko bulala.

 

*Hukuncin Zina A Musulunci*

 

Zina haramun ce a addinin musulunci,Allah madaukaki Sarki ya haramta ta in da yake cewa "Ka da ku kusanci zina,domin ita alfasha ce kuma tafarki ne

mummuna" (Isra'i : 32). Malamai suna cewa fadin Allah ka da ku kusanci zina,ya kai matuqa wajen hana ta, don ya fi a ce "kada ku yi zina".

Sheikh Abdur-Rahman Assa'idiy

yana cewa : "Hani ga a kusanci zina ya fi kai matuqa akan hana yin ta, saboda cewa kada a kusance ta ya hada hana

dukkan yin abubuwan da suke

gabatarta kuma suke kawo yin ta,domin kuwa duk wanda ya yi kiwo a gefen shinge to ko yana daf da fadawa cikinsa, musamman ma akan irin wannan lamari,wanda da yawa daga cikin zukata suna dauke da abin da yake sa wa a afka masa. Sannan Allah ya siffata zina da cewa alfasha ce,ma'ana zina wata aba ce da shari'a da hankali suke ganin muninta, saboda ta keta alfarmar Ubangiji, da shiga haqqin macen,da haqqin danginta,da mijinta, kuma batawa mijin ta

shimfiɗarsa,da cakuɗa dangantaka da makamancin haka". (Tafsirin Assa'idiy ).

A wani wurin a cikin Alqur'ani mai tsarki Allah madaukaki sarki ya siffata bayinsa muminai da cewa su ne

wadanda ba sa zina, in da ya

ce,"Wadanda ba sa kiran ko bautawa wani a tare da Allah, ba sa kashe ran da Allah ya haramta sai da haqqi, kuma ba

sa zina, duk wanda ya aikata haka zai gamu da azaba" (Suratul Alfurqan : 78).

Ya tabbata a cikin hadisi an

tambayi Annabi (S.A.W) akan wane zunubi ne ya fi girma, sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, "Shirka da Allah alhali shi

ne ya halicce ka" sai aka ce sai wanne?

Sai ya ce, "Sannan kashe ɗanka don kada ya ci tare da kai" sai aka ce "sannan sai wanne? Sai ya ce, "Ka yivzina da matar maqocinka" (Bukhari). Kun ga kenan wannan maganar ta fado akan Muntaka da Hajara. Haka kuma Allah madaukaki sarki ya sanya hukuncin wanda duk ya yi zina kuma

ya taba aure da a jefe shi, namiji ko mace,idan kuwa bai taba aure ba, sai a yi masa bulala ɗari sannan a baquntar shi a wani gari daban tsawon shekara guda.

Duk wanda ya kalli haddin zina

zai ga yadda Allah ya keɓance shi da wasu abubuwa saboda munin zina din,daga cikin wadannan abubuwa akwai: Kausasawa wajen uqubar

mazinaci, ta hanyar jefewa. Ko

kuma bulala da baquntarwa

shekara guda.

Hana jin tausayin mazinaci ko

mazinaciya yayin da ake musu uquba.

Allah ya ce:"Mazinaciya da mazinaci ku yima kowane daya daga cikinsu bulala ɗari, kada ku ji tausayinsu a cikin addinin

Allah in dai kun yi imani da Allah da ranar qarshe".

Yi musu uquba a gaban

mutane, ba a yarda a yi

musu a ɓoye ba, Allah ya ce

Wasu bangare na muminai su halarci wajen yi musu uquba (haddi)" (Suratul Annur:2).

Duk wadannan abubuwa suna

nuna mana munin zina da rashin kyanta a musulunci. Imamul Bukhari ya kawo a cikin ingantaccen littafinsa daga

Maimun Al-audiy ya ce, "A lokacin jahiliyya na taba ganin wani biri da ya yi zina da wata biranya, sai sauran birran suka taro suka jefe su". Ku duba kuga dabba ma kenan. 

Mafi munin zina ita ce wadda

mutum zai yi da mahaifiyarsa, sai da muharramarsa, sai wadda zai yi da matar maqocinsa. Allah ya kare mu.

 

*ILLOLIN ZINA*

 

Babu ko shakka ga duk mai hankali yasan cewa zina tana tattare da illoli masu yawa, wadanda suke shafar mazinacin

ko mazinaciyar, ko su shafi al'umma gaba daya, ga wasu daga cikin illolinta :

1. Zubar da mutunci da jawo wa

kai Kaskanci : domin duk matar

da ta yi zina to ta jawo wa kanta da danginta da mijinta kaskanci,ta kuma zubar musu da mutunci a idon duniya. Idan kuwa ta yi

zina ta sami ciki sannan ta kashe dan, to ta hada laifi biyu, laifin zina da laifin kisan kai, in kuma ta bar shi to kuma ta shigar wa mijinta ko danginta wanda ba ya cikinsu. Idan kuwa mai zinar namiji ne to ya lalata mace, ya jawo mata lalacewa da tabewa, wanda hakan lalata duniya ce gaba daya.

2. Zina ta hada dukkan sharri

gaba daya : saboda a cikin zina

akwai, rashin tsoron Allah, da

rashin kunya, da tsantseni, da

rashin cika alqawari, da qarya,

da butulci da sauransu.

3. Zina tana haifar da cututtuka,

da mutuwar zuciya, da sanya ta

bakikkirin, da samun kai cikin

damuwa da rashin kwanciyar

hankali da nutsuwa a ko yaushe.

Bincike ya tabbatar da cewa cutar kanjamau ta fi yaduwa ta hanyar zina da fiye da kowace hanya da ake iya daukar cutar daga ita, sannan ta hanyar cuta akan kamu da muggan cututtuka masu mungun hadari.

4. Zina tana haifar da talauci da

musiba a bayan kasa, saboda da

duk namijin da yake mazinaci to ba ya iya tattali,kullum kudinsa suna wajen matan banza, kuma Allah ya kan zare masa albarka, don haka duk abin da zai samu ba zai amfanu da shi ba yadda ya dace, a banza zai tafi. Hakanan

duk matar da take mazinaciya

duk abin da ta samu yana qare

wa ne wajen yadda zata janyo

hankalin maza zuwa gare ta,

kuma Allah zai zare wa dukiyarta albarka.

5. Zina tana kawo qiyayya da gaba tsakanin masu yin ta da sauran mutane,Allah madaukakin sarki yana cire musu kwarjini da girma daga idon mutane, saboda haka ne zaka ga qaramin yaro

yana fada da sa'an kakansa a

wurin neman mata, saboda ba ya qaunarsa ballantana ya girmama shi.

6. Zina tana jawo rashin

amincewa da mai yin ta, kowa

yana mai kallon maha'inci,mayaudari.

7. Zina tana haifar da wari daga

cikin mai yinta, ba wanda yake

jin wannan wari sai mutanen qwarai. 

8. Zina tana jawo azaba mai

tsanani ga mai yin ta idan bai

tuba a duniya da lahira . A

duniya jefewa ko bulala da

bakuntarwa, a lahira kuwa

makomarsa wuta. Allah ya kare

mu.

9. Zina tana kawo rugujewar gida da ɗaiɗacewar iyali, sannan tana kawo lalacewar tarbiyya.

10. A cikin zina akwai tozartar da dangantaka, da sanya cin dukiyar mutane ba da haqqi ba, domin kuwa duk ɗan da aka samu ta hanyar zina abin da zai gada ba haqqinsa ba ne.".

: *RAYUWAR MU A YAU*

 

©Jam33lerh 

Ayeesh Chuchu 

 

®NWA 

 

 

71

Duk su kai jigum-jigum suna sauraron Malam. Tabbas maganganun shi sun ratsa su, yanda suka yi shiru kamar ba mutane a wajen. 

Malam yace "yanzu tunda har magana ta fasu kowa ya san abinda Muntaka da Hajara ke aikatawa, kuma sun amince da abinda aka ce sun yi hukunci zai hau kan su. Wanda bani zan yanke wannan hukunci ba kotu ce. 

Ya kalli Hajara yace" tsakanin ki da Allah abinda aka ce kuna aikatawa hakane ko kuwa kage ne?". 

Hajara da hawaye suka zubo ma ta, tace "Malam maganar gaskiya hakane sharrin shaidan ne da kuma haqqin mu da ya rataya a wuyan mai gida be yi shi ya jefa ni wannan hali, ya'ya uku duk bana Amadu bane na Muntaka ne". Ta karashe maganar tana kuka. 

Malam yace "Muntaka mi zaka ce?". Yace "Malam duk abinda aka fada daidai ne". 

 

Malam yace "a gaskiya akwai gibi babba a gidan nan fanni rashin tarbiyya, sannan ku maza baku sauke haqqin matan ku. Wanda hakan ba karamar azaba ku ke janyo ma kanku ba, matukar kuka mutu a haka hakika azabar Allah ta tabbata gare ku. Kadan daga cikin hakkin mata da Zan baku su ne : " 1. Ya kyautata Dangantakarsa da ita. Ta hanyar sakin fuska da

kyautatawa.

2. Ya jure da halayenta irin nasu na mata. Domin ita an halicceta ne daga Qashin hakarkari karkatacce.

3. Yayi mata afuwa abisa laifuffukanta. Kar ya riketa azuciyarsa.

4. Idan zai yi mata fada,yayi mata daga shi sai ita. Ba agaban yara ba,kuma ba a tsakar gida

ba.

5. Wajibi ne ya sanar da ita dukkan iliman da take bukatuwa izuwa garesu.Kamar hukunce-hukuncen Tsarki da

sallah dana azumi, dana Jinin Haila dana biki. Da sauran su.

6. Wajibi ne ya ciyar da ita ya shayar da ita, ya tufatar da ita daga dukiya ta HALAL.

7. Kar ya kallafa mata hidimomi masu yawa alokaci guda. Idan yana da damar rage mata ayyukan gida, ko kuma dauko mata 'yar aiki, to babu laifi.

8. Kar ya rika aikata wasu abubuwa domin Muzguna mata, ko takura mata.

9. Wajibi ne ya rika yin Ado da tsafta musamman domin matarsa ta kalla.... Kamar yadda shima yakeso matarsa ta rika yi masa ado don ya kalla yaji dadi.

10. Kar ya dauki dogon lokaci bai kwanta da ita ba, domin yin haka zai iya jefata acikin matsananciyar bukata.

11. Wajibi ne ya rika nuna kishinsa akanta. Ya rika mutunta ta. Amatsayinta na matarsa.

12. Wajibi ne ya mutunta iyayenta da 'yan uwanta kamar

yadda shima yake so ta mutunta masa nasa.

13. Wajibi ne ya kula da dukkan hakkokinta, kar ya zalunceta. Domin ita Amanar Allah ce ahannunsa.

14. Wajibi ne ya gyarabmata tarbiyyarta, banda tsinuwa banda bakaken maganganu, domin ita ce Babbar Malamar 'ya'yansa, ita ce mai basu tarbiyya.

Yanzu ku faɗi man wanne daga ciki ku ke ma matan ku na tabbatar da kyar idan kuna 2 daga ciki. Hakan ba karamar musiba bace, shiyasa Sam duk abin da zaku nema ba zai albarka ba, tunda baku sauke hakkin matan ku. Dole ku mike tsaye wajen gyara tarbiyyar ya'ya, dukka kun riga kun rusa ginin. Shi kuma icce tun yana ɗanye ake tankwara shi idan ya bushe sai dai ya balle. Dan haka sai dai kuyi taka-tsantsan, ya'yan ku amana ne a gare ku sai Allah ya tambaye ku amanar da ya baku, mi zaku ce da shi bayan kun banzatar da wannan amanar. Ya kamata ku farka tun kafin dare yayi maku ku san mi duniya ke ciki. Tarbiyya sha'ani ne mai wuyar gaske sai da taimakon Allah a ciki".

 

Jikin su yayi matukar yin sanyi jin wannan jawabi daga bakin Malam. Yayi masu nasihohi masu ratsa jiki dangane da tarbiyya a musulunci da kuma irin rayuwar da suke, ya kuma zaburar dasu akan irin azabar da Allah ya tanadar ga masu irin halin su. 

 

Bayan Malam ya tafi, Umar ya dora da na shi bayanin. Hajara da Muntaka nata kuka suna neman yafiyar jama'ar gidan. 

 

Da Umar zai tafi ya wadatasu da duk wani kayan masarufi, da kudi da zasu ja jali. Ya sha albarka a ranar. Baba Sa'adu yana ta kwararo addu'a. Lallai Umar da Aisha alkhairi ne babba a gidan su.

*RAYUWAR MU A YAU*

 

©Jam33lerh 

Ayeesh Chuchu 

 

®NWA 

 

72

_GIDAN SALIMA_

 

Kukan yara ne ke ta tashi a tsakar gidan, kowa da irin salon na shi kukan. A fusace ya fito daga uwar ɗaka, yace "kukan uban mi kuke ma mutane da uwar sahiyar nan?". 

Gaje dake zaune bakin kofar dakinta ta ce "ba dole suyi kuka ba Malam tsakani da Allah jiya basu ci abincin dare ba, yau ma ga babu na safe ko babba ai dole yayi kuka bare yaro".. 

Ya ce" suyi kukan jini ma in dai abinci ne, ku bar ni inji da musibar da ni ke ciki mana, kuna ganin dai kudin da ni ke takama dasu wannan tsinannen mutumin daga rance ya gudu ". 

Salima dake daki tayi saurin fitowa tace" alhakin mu ya fara kama ka". Yayo kanta da gudu yace "ina jin dai gara ni da matsiyacin uban ki da ko kwanon shinkafa be taba ajiyewa ba". 

Ya kalli amaryar shi Sahura yace "munafuka duk ke ce sila, daga zuwan ki gida musiba ke ta afko man saboda shegiyar farar kafarki". 

Duk sai kallon shi suke, ya zama kamar wani taɓaɓɓe. 

Gaje ta ce "malam ka kawo kudin abinci kana ganin dai yanda yara ke ta kuka, saboda auri sakin ka, ka jawo mana bala'i yara makil da gida". 

Ya ce "kowacce ta ciyar da kanta da ya'yanta". 

Gaje ta rafka guɗa tace "tafi nono fari". 

Salima ta jawo yaranta gaba ta tasa su, hawayen bakin ciki na zuba daga idanunta. Danta Musa na ta cewa "mama yunwa ni ke ji". Tayi shiru tana tunanin inda zata samu kudi, ta gama tunaninta bata samo mafita ba. Tashi tayi ta saɓa Firdausi a baya tana jijjiga ta har tayi bacci.

Daga fitar shi be zame ko ina ba sai gidan wani malamin zaure. Bayan sun gaisa yace "Malam dama na zo ne a duba man akan salwantar dukiya ta, ko wani ne ya samun hannu. Kwanakin baya duk abinda na taɓa sai ya salwanta, har ya kai kudin da suka rage man na ba wani mutumi bashi har yau babu labarin shi" . 

Malam ya gyara zama, ya buga kasa tare da yin zane a sama, ya dau tsayin wasu mintoci. Daga bisani yace "Mal. Isyaku alal hakika dukiyar ka gurbatacciya ce shiyasa kake fuskantar wannan matsala babu wani da ya sama hannu".. 

Mal. Isyaku yace" dalla rufe man baki ai dama ku malaman nan shegiyar karya ce daku, to ni jikina ya bani samun hannu aka yi ". Ya gama bambaminshi ya tafi. 

 

Kullum Mal. Isyaku beda aikin yi sai bin malamai dan a buga ma shi kasa, kamar sun hada baki duk maganar daya ce. Har ya gaji ya dawo zaman gida baya ko fita. 

 

Gabadaya Salima ta fige fiye da zaton mai karatu, babu sisin kobo da ke shigo ma ta a hannu. Tun da gari ya waye take saka da warwarar abinda ya kamata tayi dan ta ceci rayuwar ta. Ganin kowa takanshi yake a gidan. Gaje da ke dan taimaka mata itama babu. 

A hankali ta sadaddafa ta fita waje hannunta rike da Musa, ta goya Firdausi a baya. Tayi tunanin zuwa gidan su. Haka sukai ta tafiya har zuwa unguwar su a kafa. Tana shiga gidan bako sallama ta fada dakin innarta. Gidan tsit kamar ba kowa. Abinci ta gani cikin _food flask_ an ajiye ta bude, ido ta zaro ganin dafa-dukan taliya da wake harda dan kifi a sama. Bata tsaya bata lokaci ba ta hau kaima cikinta, bayan ta zuba ma Musa a murfin _food flask_ din. Tana Ci tana ba Firdausi. 

Nan da nan Salima ta gama cinye abincin tas, harda suɗi.. Rabon da ta ci abinci haka har ta manta. Mamaki take na sauyin da aka samu a gidan. Ruwa ta kora da shi ta kwanta saman ledar kasa da ke dakin, sai bacci. 

 

Cikin bacci ta ji hayaniya alamar mutan gidan ne suka dawo, shigowar Innarta yasa ta bude ido. Innar ta ce "sai yau ake ganin idonki Salima". Ta zauna bakin gado, Salima ta mike tana hamma bata rufe baki ba. Innar ta harare ta. 

Salima tace "daga ina kuke haka Inna? Nafi awa biyu a gidan nan ba kowa". Innar tace "muna sashen Gwaggo ana koya mana karatu". 

Salima ta dafe kirji ta ce "karatu kuma? Tsofai-tsofai daku". Inna tayi murmushi ta ce "ai ba'a tsufa da karatu Salima, mike damun ki naga duk Kin kara lalacewa haka?". 

Hawaye suka zubo mata taba Innarta labarin halin da suke ciki.

Tsakanin uwa da da sai Allah, Innar tace "miyasa tun farko baki zo ba Salima, ni sam ba son auren nan nike ba, kina ganin Saddik'a na can Katsina cikin jin dadi taki komawa gidan mijin ta, dan Naji Ummaru na cewa zai karbo takardar sakin ta wajen Kabiru". 

Salima ta ce "Inna ina son mijina, ki taimaka ki bani abinda zan samu na rika ciyar da kaina".

*RAYUWAR MU A YAU*

 

©Jam33lerh 

Ayeesh Chuchu

 

®NWA 

 

73

Salati Inna ta saka tace "Salima duk wahalar da kike ciki kin gwammace ki zauna haka, shikenan ai. Kinga ga dubu biyar nan cikin kudin sana'a ta ne ki je kija jali ko irin kayan miya kina saidawa yafi zaman haka, kinga mu yanzu gidan nan Alhamdulillahi abubuwa sun fara daidaita, yaron nan Ummaru na iya bakin kokarin shi". 

_Food flask_ din abinci ta jawo ta ji shafal ta ce "Salima ba dai ke kika cinye abincin ciki ba?". 

Salima tace "da yunwa na shigo gidan ne Inna". Takaici ya hana Inna cigaba da magana. 

 

Zaune yake a masallaci, bayan an gama sallar La'asar ya kwanta. Wadanda ke majalisi a cikin masallacin suka fara karatun su, inda Malamin yake karanto hadisai daga cikin littafin *BULUGUL MARAMI*, inda suke cikin babin riba. Yana magana akan hadisin Jabir R. T akan cewa Manzo S. A. W ya la'anci mai cin riba. 

Mal. Isyaku ya tashi daga kwance yana sauraron su, har suka kammala da babin inda malam ya cigaba da bayani aka ita RIBA kamar haka : " Riba shi ne siyar da wani abu

tare da amsar makwafinsa amma da kari,kamar mutum ya siyar da mudun masaravbiyu amma a bashi mudun masara biyu da rabi. Ko ya bada bashin duba daya, idan an maido ma shi a bada duba daya da dari biyu. Kun ga a nan abin da aka kara akai din nan shi ne RIBA. 

 

Hukuncin Riba a cikin Addinin Musulunci

 

Haramun ne ci da kuma amsar riba, kuma Allah SWT ya la'anci wanda yaci riba ko ya zama sanadin samun ta. Akwai hujjojin haramcin ta kamar yadda suka zo a cikin Alkur'ani da hadisan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata gareshi da iyalan gidansa. 

Ayoyi 7 ne suka yi magana akan haramcin Riba a cikin

Alkur'ani mai girma amma ga wasu daga cikin su. 

A cikin suratul Ali Imran aya ta 130 Allah madaukakin Sarki yana cewa "Ya ku wadanda kuka bada gaskiya kada kuci riba ninkin ba ninkin kuma kuji tsoron Allah don ku rabauta".

Acikin suratul bakara aya ta 276

Allah madaukakin sarki yana cewa "All yana shafe albarkar riba yana kara ladan sadaka kuma Allah baya son duk wani mai yawan butulci mai yawan saɓo". 

Ita dukiya ta riba bata albarka kwata-kwata saboda hakkin mutane da ke ciki. Sannan akwai azaba ta musamman da Allah ya tanadar ma da mai cin riba matukar be tuba ba, tun anan duniya zai fara ganin illolinta a tare da shi".

Malam Isyaku yayi shiru, shedan na ziga shi akan kada ya yarda da batun da aka yi magana. Komawa yayi ya kwanta ya fada duniyar tunani yana tuna irin asarar da tabka duk a sanadiyyar riba. Tabbas ya yarda RIBA ce ta kai shi ga fadawa wannan mummunan hali. Yayi alkawalin ya tuba, ko dan talaucin da yake ciki ya isa ya zama IZNA a gareshi.

: *RAYUWAR MU A YAU*

 

©Jam33lerh 

Ayeesh Chuchu 

 

®NWA 

 

74

 

*BAYAN SHEKARA BIYU*

 

Saddik'a ce rike da dan da Aisha, mai suna Ibrahim suna ce da shi Abul Khair dan shekara biyu. Aisha ta ce "Saddik'a barka fa, nan da yan kwanaki kin amarce da Salele, abin kamar wasa. Kinga dai yanzu da da ba daya bane Saddik'a, tsabtar nan ki dage da yin ta duk da dai har yanzu da sauran ki kin ki ki saki jikin ki ki saba da tsabta. Gidadanci da kazanta duk ba naki bane yanzu. Kina dai ganin yanda Salele ke da tsabta duk da cewa namiji ne, kuma kinga yanda nike zaune da mijina lafiya duk da na haihu hakan be sa ya wulakanta ni ba, bari kiji duk wani wulakanci da ɗa namiji zai ma mace ita ce ke siya da kudin ta ". 

Saddik'a tace" na fahimta Aisha da gani nike wahalar banza kike yanda kike tarairayar baban Abul Khair, na dauke ki sakarya ashe nice babbar sakarya. Aure na da Kabiru shi ya kara wargaza rayuwa ta, rashin ilimi babban giɓi ne a rayuwar dan Adam ". 

Aisha tayi murmushi ta ce" nagode ma Allah da yasa kika fahimta da kan ki Saddik'a yanzu ya rage gare ki ki gyara rayuwar auren da zaki yi, idan kika cigaba da irin halin da kike ada wuya zaki ji, jin dadin ki daya wancan _boys quarters_ din zaku zauna, gaki ga ya'yan ki. Saddik'a ki basu ingantacciyar tarbiyya duk abin da zan fada kin riga kin ji shi a makarantar da kike zuwa saura aiki da abinda kika ji ya rage ". 

 

Sun dade suna tattauna batutuwa da suka shafi rayuwa. 

 

*BABBAN GIDA*

Rayuwa ce mai tsabta dake gudana acikin gidan sakamakon sauyin rayuwa da suka samu. 

Yaran dake tasowa a gidan suna samun tarbiyya dai-dai gwargwado, inda suka fita daban da sauran yayyensu a fannoni da dama na halayya da ilimi. 

Baba Sa'adu, Baba Amadu suna zaune lafiya da matayensu. Budi nata samuwa a hankali, duk abin da suka san zasu iya na dangane da ciyarwa suna yi daidai gwargwadon karfin su. Haka ma matayensu basu zauna hakanan ba, suna sana'oinsu dan su dogara da kan su.

Tunda da akai maganar zuwa kuto kai Baba Muntaka da Hajara aka nemi baba Muntaka sama ko kasa ya gudu. Hajara ma ta bi dare ta gudu kauyen su, dama baba Amadu ya sake ta. 

Ya'yan ta Dana baba Muntaka duk baba Sa'adu ya rike su. 

 

*GIDAN SALIMA*

 

Zaune take tana kulla sukari a lada, tana debowa daga cikin buhu tana kullawa Gaje ce ta leqo dakin tace "Hajiya Salima ana ta sana'ar ne?". Murmushi ta yi tace "ba dole na ba, zaman banza Be ganni ba SANA'A SA'A". Dariya Gaje tayi tace "da kika ji uwar bari ko". 

Salima tace "nayi wauta ada bani fatar sake maimaita ta, rashin sana'a ba abinda Be haifarwa". 

Gaje tace "kwarai kuwa kina ganin dai yanzu malam babu kudi ko da can da yake da su bayi yake ba, amma yanzu muna da rufin asirin mu, zamu yi duk wata hidima daidai halinmu ba tare da mun jira shi ba". 

Salima tace "sosai ma Yaya ai ni yanzu ban jin zan iya zama babu sana'a ka saba duk rana ta Allah canji zai shigo maka". Gaje tace "bari kawai, Allah dai shi kara rufa mana asiri duniya da lahira".

 

Tammat Bi hamdullah! 

 

Anan zamu dasa aya sai Allah mai kowa mai komi ya nufe mu da sake saduwa da ku a cikin wani sabon labarin. 

Dafatan wannan takaitaccen labari zai zama darasi a rayuwar al'umma. Ire-iren wadannan mutane na nan birjik a cikin al'ummarmu. Fatanmu a kullum mu kawo gyara a cikin rayuwar al'umma aka fannin rubutu. 

 

Mune naku 

Jam33lerh da Ayeesh Chuchu ke maku fatan alkhairi. 

Dan kawo gyara ko tsokaci sai a tuntuɓe mu ta wannan Layin Jam33lerh +2348147830740

Ayeesh Chuchu +2348068069242

 

 


Tags: Family #Love #Relationships #Betrayal #Rape #Northern Nigeria
6700
0
0
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!