[30/08, 18:05] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR* *AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M* ✍🏻
*1* ~*2*
*BISMILLAHIR* *RAHAMANIRRAHIM*
*DA* *SUNAN* *ALLAH* *MAI RAHAMA* *MAI JIN'KAI* *DUKKAN* *YABO* *DA* *GODIYA* *SUN TABBATA* *GA* *UBANGIJI* *WANDA* *YA BANI* *DAMAR* *RUBUTA* *WANNAN* *LITTAFIN* *ALLAH* *KASA* *NA GAMA* *LAFIYA* *AMEEN*
*IDAN* *NAYI* *KUSKURE* *A CIKI* *ALLAH* *KA YAFE* *MIN*
~~~~~~BABIN FARKO
Tuqi take akan titin cikin kwanciyar hankali da nutsuwa motar ta mai qiran passat. Ahankali take tafiya kamar wacce batason tuqawa.. Duk da kuwa yanda motoci suke kara kaina akan titin hakan bai hanata tafiyar ta ahankali ba..
" Kanta tadan kwantar a jikin kujeran motar tana sauraron karatun al qur'ani mai girma muryan al sudais wanda da dukkan alamu idan kaganta zakasan cewa tanajin daďin karatun,,
" Matashiyar budurwa ce wacce aqalla shekarunta bazasu wuce 18 ba """ Sanye take cikin baqar abaya wadda babu wani ado ajiki illa dan stons da aka zagaye hannuntà dashi gyalen abayan tayafa a kanta,
" Kyakkyawar budurwace ta gaske fara Amma bacan ba kuma ba ruwan tarwaďa ba farinta daidai misali wanda kallo daya zakayi mata kasan cewa ruwa biyu taďauko"" Tanada dogon hanci Amma ba sosai ba sai dan qaramin bakinta madaidaici tadan shafa mishi jambaki kadan sai idonta da tasa masa gaxal sai yaqara mata kyau sosai
Cigaba tayi da tuqin motar duk ta miķa hankalin ta kan titin tana kallon yanda motoci keta gilmawa masu mita sunayi masu kallon ta suna kallon ta..
" Phone dintane yafara ringing tajuya tamika hannu cikin qaramin jakanta madaidaici taďauka dan duba wake qiran ta ""
" Ya salam tafada tare da dafe kanta sanadiyar sunan wanda tagani a fuskar wayan..
" Daidaita kanta tayi kafin ta amsa wayar,
Jikin ta na bari tace Hello yaa mahmud tana dan wuri wiri da ido kamar marar gaskiya,,
" Ji tayi yace mata Dan qaniyarki wayabaki izinin daukar min mota kifita da ita bansani ba ?""
"Shiru tayi masa batace komiba jikin ta kuwa cigaba yayi da bari dan ita kam harga Allah ta mance motor shi ce ta ďauka'
" Tsawan da taji yadaka mata ne ya sanya har wayan hannun ta yafaďi qasa saura kadan tuqin da takeyi ya kubuce yabar hannun ta.
Saurin daidai tawa tayi akan titin kafin ta sunkuya taďauki wayar tamayar dashi kunnen ta""
Ji tayi yaqara cewa badake nake magana ba kinyi ma mutane shiru wato mahaukaci kika mayar dani ?
" Girgiza masa kanta tayi kamar tana gabanshi
" takwabe fuska Tace aiyya yaa mahmud wlh nazo nefa fita da motar mummy sai naga babu dana tambaye ta sai tace min kafita dashi shine tabani naka tace inje dashi..
Meyasa bazaki qira ki fada min ba,?? Da kike cewa mummy ce tabaki izinin ďauka Motar tawace ko nata ?' Ya tambaye ta
" Nanma shirun tayi masa batace komai ba
"Yace badake nake magana ba kinyi shiru ga dan iska kenan ko ?
" A a tafada tana girgiza kanta..
"To bari kiji in fada miki wlh wlh kinji na rantse idan kika kuskura kika bari wani abu yasamu mota na Allah sai nayi mugun saba miki naraba ki da wannan shegen ķafar mai son yawon tsiya kuma kiyi hanzari ki dawo min da mota na tun kafin raina ya gama baci kinji nagaya miki tunda ke halinki ďaukar abun mutane ne basu sani ba Yana kaiwa nan taji ya kashe wayar qit,
Ajiyan zuciya ta sauķe tare dayin hamdala ta mayar da wayar cikin jakan ta.
Cigaba da tuqin motar tayi a hankali da yake ta shigo layin da babu motoci dayawa hakan yasa taqara rage dugun motar""
Ohh ďan masifa da bala'l akan an ďauki motar ka shine kaketa wani balbale mutane da masifa kamar ran ka aka ďauka bayan kaima motar wani ka ďauka harda wani yima mutune mummunar fata than gud motar ma takace bata wani ba koda wani abun ya sameta bakin ka ne yajawo' tafada tana dan yamutsa fuska,
"A'uzubillahi minashshedanirrajim tafada tare da dafe qirji, Saurin taka Burkin tayi dan karta bugu da motar da taga yasha gabanta yayi mata over taking bata saniba..
Amma inaa duk saurin taka birkin da tayi hakan bai sa ya hanata buguwa da motar ba" Zare ido tayi tare dayin salati ta daura hannu a ka,
"Cigaba da salati tayi tare da ďaura kan ta a string motar tana fadin shikenan nashiga uku na lalace yanzu meye haka wannan mutumin ya min ?"
Can taji an wani irin qwan qwasa mata windo kamar za'a fasa ana qoqarin bude murfin motar' Dago kanta tayi dan ganin wanne mahaukacin ne yake mata irin wannan iskanci..
Wani Kyakkyawan gaye tagani, Fari ne sosai dan ya fita haske sanye yake cikin farin shadda kaftan wanda yasha zubi mai kyau da hulan sa dinkin bama "" Gani tayi ya harďe hannayensa bisa ķirjin sa yana mata wani irin kallo.
'Windon motar ta sauke kafin ta ďaga idon ta wanda ya ďanyi jaa dan tsabar ruďewa, Kallon shi tayi tare da cewa Malam lafiya?
Wato dan rainin hankali tambaya ma kike lafiya kamar bakisan abunda kikayi ba kina tuqi a hankali kamar kin samu kwaltan gidan ku' Matashin saurayin yafada yana dan jingina da jikin motar.
Ajiyan zuciya ta sauke tare da cewa kayi haquri dan Allah nima banso hakan yafaru ba..
Dama ku yayan adam haka kuke sai kuyiwa mutum laifi bai isa yayi magana ba zaku danga nashi da kalmar haquri kamar ku kukayi ta" Yafada yana cigaba da kallon ta,,
" dafe kanta tayi tace Ohh ya rabbi yau ina ganin ikon ka, Bude motar tayi ta fita ta ďaga idon ta kalle shi da kyau kafin ta zagaya gaban motar tana fadi a ranta Allah yasa baiji ciwo sosai ba..
"Hamdala tayi tare da sauke ajiyan zuciya sanadiyar ganin motar bata lotse sosai ba dan a tunaninta zataga yaji ciwo ne sosai..
Barin jikin motar nata yayi yadawo inda take' kingama ikon naki kenan ya tambayeta yana kallon ta ?
Jiyowa tayi ta kalle shi sosai cikin idon ta kafin tace' Haba malam wannan wani irin hali ne kake dashi haka ??ya zaka bata min mota kakasa bani haquri ni dana baka haqurin akan ka amsa sai ka tsaya kana fada min ďacin magana da mitan tsiya haka ai bai dace ba "
Duban ta ya qara yi sosai tare da ďaura hannun sa akan ķirjin shi" Yace sannu uwar magana ni bakiga ciwon da kikaji wa tawa motar ba kenan, kina tafiya akan titi saikace kin samu titin unguwar ku.
" To shikenan tunda haka kace banson dogon surutu dan inada abun yi agaba na nabar ka lafiya Allah ya saka min tafada tare da juyawa dan barin gurin,
Bata an kara ba taji anjanye gyalen data yafa akan ta hakan yayi sanadiyar bayyanar gashin kanta waje wanda yake kyalli dan tsaban gyaran da ya samu""" Jiyo da kanta tayi dan duba wanda yayi mata wannan tijaran..
Shi din dai tagani tsaye yana kallon gefen ta kamar bashi ya cire ba hannun sa riqe da gyalen nata"" Fuska ta ďaure ta fisge gyalen daga hannun sa tamayar dashi kanta ta rufe gashin ta, tukun ta ďaga ido ta kalle shi da kyau tace wannan wani irin iskanci ne zaka yaye wa mutum gashi akan hanya kowa yana kallo, dan Allah ni ďauke min motar ka a gaba na nawuce duk kabi ka bata min lokaci halan ka qara jawo min magana kuma Allah ya isa na ban yafe ba bude min kai da kayi a kan titi'" Tana magana tana zumbura baki ,,
Ďaga kansa yayi ya kalle ta sosai " yace bakiga iskanci ba Amma yanzu zan nuna miki yanda ake iskanci kuma ki tabbata duk wannan rashin kunyar da kika min da lotsa mota ta da kikayi duk sai na rama"
Harara ta watsa mishi tace inka fasa kaqi Allah,ta wuce motar ta dan ba qaramin haushi yabata ba,
Motar sa shima ya koma mai qiran G L 450 4MATIC ya bude ķofar ya shiga ya tada motar,
Da taga ya tada motar sai ta ďauka matsawa zaiyi ya bata waje dan tasamu ta wuce"" Amma sai taga sabanin hakan Qara gyara tsayuwar motar yayi a gaban ta yayi ķememe ta yanda koda tace zata wuce sai tadan ji jiki, Kwantar da kujeran sa yayi ya ciro iPhone 6 din shi daga aljihu yafara latsawa yana kallon ta ta ķasan ido dan yaga yanda zatayi,,
Dogon tsaki taja tare da sawa motar key tayi baya sosai kafin ta karya kan motar ta wuce ta bayan shi tana qunquni..
Murmushi yayi yace zagi gamu dani yarinya da ni kike wasa"" Daga nan ya tashar da nashi motar yabar wajan bayan ya gama ďaukar number motar nata,
"Batafi minti biyar ba ta isa inda zataje"" waje ta nema mai kyau tayi pakin, ta bude motar ta fita..
Saida ta buga ķofar kusan sau biyar kafin taga an bude mata,
Dalla ni malama bani gu na wuce kin wani kulle ķofar gida da ranan Allah saikace wani saceku za 'ayi bayan kuma na sanar miki ina hanyar gidanku kin barni sai bugun ķofa nake kamar wata sabon kamu" .
Baki Amina ta riqe tana salati, Tace to sannu almasifatu yau yan masifan suna kusa kenan, Wai ma tsaya waya bata miki rai haka kikeso ki sauķe shi a kaina banci ba ban sha ba??
Dogon tsaki taja ta dubi Amina,Tace wlh wani dan iskan mutum ne nashigo wannan layin bayan ku da babu motoci dayawa kawai ina cikin tuqi naji ya sha gaba na da mota,hakan yasa na bugu dashi,
Ido ta zaro waje tace ya salam ina fatan dai bai lotsa miki motar ba?
Kibar dan iska ya lotsa mana kuma dan girman kai na damun shi ya kasa bani haquri ni dana bashin kuma ya tsaya yana gaya min ďacin magana bayan shine mai laifi, ni damuwa ta ma daya ne motar yaa mahmud na ďauka bata mummy ba..
To Allah dai ya kyauta haquri zakiyi kinsan wasu ba a iya musu, Hala ma ko gamo kikayi mu huta da yan tasha a ķofar gida,Amina tafada ta fuskar zolaya
"Allah ya tsareni wlh bakin ki ya sari guntun kashi,Idan nayi miji da wannan ai na shiga uku baza'a kwana ba zaku gan ni da a kwatina na dawo gida..
Amina ta kwashe da dariya tace kai Humaira wlh baki da sauķi" Kedai Allah ya kawo mana na gari fatan da zamuyi kenan,
Yauwa ko kefa yanzu kikayi magana mai kyau""
Wlh kedai Ameena bakida Kirki kinbarni tsaye saizuba nakeyi kamar kanyarda bazakii gashi nakwaso gajiya kintitseni da shegen surutu bazakice inwuceba
Ameena tayi dariya tace yihakuri Kawata mushigato tare suka jera zuwa ciki'a tsakar gidan tasamu ummar Ameena tagaisheta ta amsa cikin sakin fuska tana tambayarta momynta"" tace qalau take tacema nagaisheki
Ina amsawa dakin Ameena suka wuce kaitsaye saman gadon humaira tazube tanacire mayafinta Ameena tadibomata ruwa tasha sukasoma firan komawa skull.....
*HaneeSat*✍🏻
[30/08, 18:06] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*3~4*
***Misalin k'arfe Biyar na Yamma ta tashi. Kallon Ameena tayi tukun tace "ni zan koma gida yamma yayi, kuma inaso na tsaya a wurin makaniki ya d'an gyara min inda mota ta lotse don nasan ba K'aramin bala'i zan sha ba idan mai ita ya gani a haka domin Sai da yayi min garga'di."
" Kai haba mana ke kuwa kin cika hanzarin tsiya daga zuwa tun bamu gama hirar tamu ba zaki wani ce tafiya za kiyi Sai kace korar ki akeyi, kibari dan Allah idan munyi sallan magariba sai ki koma tunda ba wani Nisa bane damu", Cewar Amina,"
Harara Humaira ta watsa mata tukun tace" Amma lallai ba kida godia Allah jiya fa a gidan nan na yini yauma tun uku fa nake gidan nan kin san kuma fa'da za'a min idan na kai dare, idan kina da wata maganar sai ki min waya kawai. "
" Shikenan malama uwar bayani naji, tashi na Rana ki bakin Mota"Cewar Amina,"
Gyale Humaira ta d'auko taje gaban madubin ta yasa shi da kyau a kanta ta d'an gyara fuskan ta duk da bawai ya b'aci bane tukun ta juyo tace da ita muje ko kawata ha'de da watsa mata murmushi da yake k'ara mata kyau.
A tare suka jera suka fito Umma suka gani a parlon ita da zarah k'anwar Ameena. Humaira ta je gunsu ta d'an rusuna tace umma ni zan koma gida,"
"A a tun yanzu zaki koma? Baza ki jira kici abinci ba gashi ya kusa dahuwa" Cewar Umman Amina, Domin duk cikin k'awayen Amina tafi ganin hankalin Humaira baya ga haka mahaifiyar ta Aminiyar tace, shiyasa take Jin da'din k'awancen su,"
" Umma ba damuwa wallahi banajin yunwa kuma yamma tayi gwara na koma gida da wuri kafin Garin ya gama duhu", Humaira tace tare da mi'kewa.
"To ki gaida gida ki cewa mummyn ki zan kira ta", Cewar Umman Amina.
"To Umma insha Allahu zan sanar ma ta", Humaira ta fa'da a hanzarce ta kama hannun Ameena suka fice.
Har gun mota Amina ta Raka ta,Humaira ta bu'de ta shiga Sannan Amina tace " to besty a kula da hanya Allah ya tsare sai munyi waya" .
Hannu humaira ta ďaga mata tare da cewa "sai na ganki dai bawai sai munyi waya ba", ta ja motar ta tafi.
Murmushi Amena tayi tare da girgiza tashige cikin gida abun ta,
" Amena bature ķawar humaira ce sosai tare suka yi secondary har suka kammala "" yanzu haka suna university of Africa wanda ke cikin garin Khartoum a qatsar Sudan" hutu ne ya dawo dasu gida kusan wata shine suke shirye shiryen komawa dan saura musu sati daya hutun yaqare"
Sanadiyar haduwar su lokacin da su humaira suka dawo abuja da zama bayan sun daidaita komi sai suka nema mata karanta dan taci gaba da karatun ta a lokacin ta gama primary kenan zata shiga 1secondry
Akaci sa'a suka samu makaranta mai kyau Fu'ad Lababibi wanda ke zone 3" Haďe yake da islamiya dan haka in sun tashi 4:00 bata barin makarantan sai 6:00pm kafin ta dawo gida,
Wata rana humaira na zaune a class bayan an tashi break, taji a lamun mutum kusa da ita"" ďago kai tayi sukayi ido huďu da Amena wacce ke sakar mata murmushi" sallama tamata "" humaira ta amsa mata cikin sakin fuska""
Ameena "" tana kallonta tace ke kuwa yar uwa bazaki kici wani abu ko kisha iska ba kafin break ya qare kin zauna kedai a class?" dan ta kula da ita tunda ta shigo makarantan haka take idan an tashi break bata fita saidai tayi zaman ta a class tana duba karatun da akeyi musu hakan ba qaramin burge Amena yake ba shiyasa ta yanke shawaran yin qawance da ita!
Murmushi humaira ta sakar mata tace bakomai yar uwa bana sha awar fitane kawai "" wlh"
Ameena tace ""shikenan zan iyah zama akusa dake??? Tayi nuni da kujerar da humaira take zaune,"
"Matsawa tayi tace zauna mana aiba matsala"" ameena tazauna suka gaisa"" sunana Ameena bature " Amman idan badamuwa kozan iyah sanin sunanki???
Humaira tasake kallonta akaro nabiyu da murmushi akan fuskarta tace Aisha Ali girema sunana Amman zaki iyah kirana da humairah"" ""
Ameena tagyada kai suna mai dadi"" idan ba matsala zamu iya ķulla qawance? dan gaskiya na yaba da halin ki Amena ta tambaye ta.
Lahh ai ba matsala wlh" Dan itama ta kula duk cikin class din tafi ganin hankalin Amenar,
humaiya tace niyar maiduguri ce bamu daďe da dawowa abuja ba,
Kice kunyi gudun hijira kenan Amena tafaďa ta fuskar zolaya,
Dariya humaira tayi tace wlh a a zuwan mu daban ne ba gudun hijira mukayi ba!
""Itama dariyar tayi tace wasa nake miki, Mu mazauna ķatsina ne Amma mun daďe da dawowa Abuja don a nan ma na gama primary na,
Murmushi Humaira tayi tace "sunanki mai da'di kuwa"
"Daga nan K'awance mai k'arfin gaske ya ķ'ullu tsakanin Humaira da Amina, Abun gwanin ban sha'awa komin su tare suke yi hakan ba K'aramin burge mutanan makarantar yake ba. Dalilin hakan ya sanya iyayensu suke mutunci sosai,"
"Tayi nisa sosai cikin tafiyar da take yi tana sa'ke sa'ke a zuciyar ta na bala'in da zata je ta tarar a gida idan yaga abunda ya samu motar sa,don ita ta mance da tsayawa a gun makaniki ya gyara har saida ta shigo cikin unguwar su ta tuna gashi. Babu yanda zatayi fatan ta ďaya Allah yasa baya gida taje ta ajiye ta yanda idan ba ido yasa ba bazai gani ba,"
"Wani babban gida na hango mai kyawun gaske gidan sama da qasa ne wanda duk cikin unguwar ire iren gidajan ne babu na k'ananan mutane,Nan Humaira ta Nufa.
"Hon ta danna mai gadi yazo da sauri ya le'ka yana ganin ta ya koma ciki ya bu'de mata makeken gate d'in ta shiga kai tsaye pakin space ta nufa tayi pakin motar kafin ta fita gun mai gadin ta koma suka gaisa ta tambaye shi ko Mahmud yana gida? don taga motar mummy a pakin space hakan yasa jikin ta ya fara karkarwa take tsoron gamuwa dashi.
"A a yace da ita, ya dawo d'azu bai daďe ba sai kuma abokin shi yazo suka k'ara ficewa tare.
Ajiyan zuciya ta sauke tare da cewa maigadin "shikenan" daga nan ta juya ta shige cikin gidan.
"Can na hango wata Kyakkyawar mata zubin y'an fulani wanda kallo d'aya zaka mata ka ga kamannin su ďaya da Humaira, zaune take akan darduma a tsakiyan filin gidan.
Dattijiwa ce wanda a k'alla zata kai shekaru hamsin a duniya sai wani da na hango d'an Kyakkyawa wanda shima yayi talatin da wani abu sai dan yaro karami a gefe yana wasa abinsa cikin kwanciyar hankali.
Nufowa gun tayi da murmushi a fuskar ta, ba ta ankara Ba ta Ankara ba taji Annur yazo ya fa'do mata yana cewa "oyoyo anty"..
D'aga shi sama tayi tana dariya tace, "Annur kaine yau a gidan namu" tana mishi wasa yana dariya ta qarasa gun su mummy.
Zama tayi kusa da mummyn ta zaunar da Annur akan cinyar ta ta juya tace" Yaya Musty ina wuni sai yau kuka ga damar zuwa mana koh.
Kallon ta yayi yace "Sannu uwar fita unguwa yawo kamar kin ci k'afar kare,jiya ma na shigo gidan nan na tambaye ki akace min kinje gidan su k'awarki yau ma haka. yanzu kuma kinzo kina cewa sai yau naga daman zuwa, Na kula tunda kika dawo daga makaranta bakya iya zaman gida sai kin fita don tsaban son yawo ", cewar yaya Musty.
"Kwashewa tayi da dariya Har da tafa hannu tace," Kai haba dai yaa musty da ka amsa min gaisuwar ma tukun ka fara k'orafin naka, kuma fa ni bana fita a gidan nan saida da dalilin da uzuri ".
Harara ya cilla mata yace ba wani uziri tsaban yawo dai Mahmud ne maganin ki ai.
Cak ta tsaya da dariyar da take,dan tasan wanne laifi tayi mishi'
Dariya yakwashe dashi yace matsoraciya an qira miki sunan dodo ba,
Dazun nan yagama mita akan an baki motar sa bayan ko ķwarewa bakiyi ba halan ki lotsa mai mota inafatan dai baki lotsa ba?" Musty ya tambaye ta yana duban ta
Wlh ina cikin tafiya na wani mutum ya buga min shi Amma bai lotse sosai ba tafaďa tana sauķar da ajiyan zuciya.
Musty yace zakisha bala'i Allah dai ya tsare gaba.
Mummy ce tace Amin tukun tace bakya tafiya a hankali ba dole ba" Girgiza kai humaira tayi tace wlh mummy a hankali fa nake tuqin shine dai yasha gabana da motar sa,
" Himm mummy kinga kar na mance umman Amina tana gaishe ki tace zata kira ki.".
"Ina amsawa saida na hanaki yin yamma nace miki ki dawo da wuri Amma Don tsabar bakya ji shine baki tashi dawowa ba sai yanzu ai da kwana kika yi", mummyn ta fa'da tana mata wani irin kallo me cike da tuhuma.
"Ayya mummy na kiyi ha'kuri wallahi tun biyar na bar gidan su tafiyar ne na keyi a hankali", ta f'ada tana langwa'bar da kanta a kafaďar mummyn.
Musty ne ya juyo ya kalle ta yace sannu yar shagwa'ba kullum kamar bakya girma, Aurar dake zamuyi ai koma huta da wannan shagwa'bar.
Kanta ta ďaga daga kafaďar mummyn ta zumbura baki tukun tace "kai haba mana yaya musty mai name tare muku ne zaku ce aure zaku min, nifa har yanzu yarinya ce fa Sai watan gobe ne fa tukun zan shiga shekara Sha Tara, Ni Wallahi ku daina min maganar aure yanzu don sai na kai shekara ashirin da biyar zanyi aure" Tana gama fad'in haka ta sauke Annur dake cinyar ta ta zari gyalen ta wanda tana shigowa gidan ta cire shi akan ta da k'aramar Jakarta ta shige ďakin ta.
Girgiza kai yayi yace Humaira kenan Allah dai ya nuna mana auran naki.
Tana shiga ďakin na ta ta cire kayan jikinta ta ďauki tawul ta wuce toilet don yin wanka.
Tana gamawa ta ďauro alwala don taji Kiran sallan magariba,
Kayan barci ta saka ta zaro hijabin ta ta shimfiďa sallaya ta fara sallah.
HaneeSat📚
[30/08, 18:06] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR* *AURENA* 🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M* ✍🏻
*5* ~ *6*
*Hawy* *zan* *iya* *cewa*wannan👈 *page* *ďin* *naki* *ne* *duk* *abinda* *kikagani* *kiyi* *haquri* *ki* *rungumi* *ķaddara*😜😜
****Misalin karfe goma na safe Kwance take bisa gadon ďakin wanda aka ķawata shi da kayan alatu. Mirgina wa tayi akan gadon ta juya ďaya gefen tare da janyo bargon ta mai laushin gaske ta rufe jikin ta dashi daga dukkan alamu tanajin dadin kwanciyar nan,""
kasancewar jiya kwana akayi ana zurfa ruwan sama cikin garin abuja kamar abakin bakin ķwarya hakan ya sanya garin ya ďauki bala'in sanyi mai ratsa ko wanne sashi na jikin ďan adam..
"buďe idanun nata tayi suka sauka kan a gogon dake manne a bangon ďakin.gwalalo ido tayi waje tare da murza idon taga gaskiya ne idon ta yayi mata ko ķarya ne, dan tunda ta idar da sallar asuba tayi azkar ďin safe ta koma tayi kwanciyar ta akan takwas zata tashi tayi musu karin kumullo""Ganin da gaske har goma ta gota ya sanya ta tashi a hanzarce.
" Ya salam ta furta tare da dafe kanta, ya akayi na makara ni da zan tashi tun takwas nice har goma.
Ķaramin hijabi ta zara ta wanda ke gefen ta jiya bayan tazo kwanciya ta cire shi,zira shi tayi akan kayan baccin dake jikin ta duk da sanyin da takeji hakan baisa ta tsaya qara sa wani kayan sanyi ba, ficewa tayi daga ďakin cikin sauri kai tsaye kitchen ďin ta nufa,
Can ta hango Mumy tsaye dafda gass hannun ta riqe da ludayi da alama girki takeyi .
Ķarasowa gun tayi tare da cewa Ina kwana Mumy" ďago da kai mumyn tayi ta kalle ta tukun tace lafiya Sai yanzu baccin naki ya qare? tafaďa tana ci gaba da juya kazar dake cikin tukunya,
Waiyyo Allah mumy kiyi haquri wlh yau makara nayi tun ďazu naso tashi Amma sanyi ya hanani bansan goma har tayi ba, Kawo zan qarasa kije kiyi zaman ki Humaira tafaďa tana shirin ansar ludayin dake hannun mumyn.
" Barshi nagama ai ke zan tsaya jira ki tashi a bacci ga doya can cikin kula ki ďauka ki kai dining daga nan ki wuce bàngaran Abban ki kice masa an kammala Mumy tafaďa tana sauķar da tukunyar kazar.,
"To humaira tace tare da ďaukar kular doyan ta fice daga kitchen ďin,
"Kai tsaye dining ta zarce ta ajiye kular kafin ta wuce,
Bàngaran Abba ta tura ķofar tare da yin sallama ta shiga, hango shi tayi a kishigiďe hannun sa riqe da New paper da alama karantawa yake,
"A a Mamana ya kin tsaya qaraso ciki mana, taji Abban ya faďa ďauke da murmushi a fuskan sa. Qarasawa ciki tayi ta sukunya a agaban shi cikin girmamawa tace,Abba ina kwana..
Lafiya lau Mamana kin tashi lfy ya tambaye ta yana kaiwan Tea bakin sa wanda Mumy ta kawo masa kafin ta kammala breakfast ďin
" Kan ta a qasa tace lafiya Abba, Mumy tace in sanar maka angama breakfast din, to Mamana tashi muje ko,Abban yafaďa yana tashi daga kishingiďe da yake,
Tashi tayi suka fice, kai tsaye dining suka nufa , Mumy suka tarar tana zaman jiran fitowar su,"
"Kujera Abba yaja ya zauna humaira ma kujeran taja tayi zaman ta mummy ce tafara zubawa Abba Soyayyen doya da qwai kafin ta zuba masa danderun kazar wanda inbanda ķanshi babu abinda ke tashi duk ya gauraye dining room ďin da ķàmshi
,
"Tana gama zuba mishi ta zuba nata tukun ta miqawa humaira itama ta ďiba, Ansa tayi ta zuba kaďan yanda zata iya ci ta rufe sauran ta ajiye. " Suna tsaka da cin abincin sukaji an turo glass ďin dake tsakanina dining room da parlon dan gudun shigan warin abinci cikin parlon,
" Mahmud ne ya shigo ďauke da sallama a bakin sa ya qarasa ciki, Ansa masa sukayi yaja ďaya daga cikin kujerun ya zauna kafin ya gaishe da Abba da mummy cikin sakin fuska suka amsa masa Abba ya tambaye shi kana gida ashe baka fita ba?
"Eh wlh Abba yanzu ma sauri nake in fice yau sanyin da akeyi yasa na makara ban tashi da wuri ba, Mahmud yafaďa yana zuba abincin,
" Ya mahmud ina kwana, humaira tafaďa can cikin maķoshin ta tana ďan satan kallon sa kamar dole aka sata gaisuwar dan tun isowar sa gun jikin ta yafara karkar na lefin da tayi masa jiya da alama baigani ba da itakam yau nata yaqare Allah Allah take a zuciyar ta kar Allah ya nuna mai..
" Harara ya tafkamata kafin yace lfy shi din ma dan yaga idon Abba ne ya Amsa mata,"
"Sama sama suke jefa fira gwanin ban sha'awa Amma banda mahmud dake tacin magani shi kaďai saikace dole aka sa shi cin abincin, Mummy ce ta kula da haka Amma ta basar dan tasan shi sarai da mitan tsiya hakan yasa bata kula shi ba
"Abba mum ni zan wuce na makara sosai wlh dan gashi har shaďaya ya zarta ina ban fita ba, Mahmud ya dasu yana tashi daga kujeran tare da gyara a gogon dake hannun sa"
"A a tun yanzu zaka fice ko abincin baka kammala ciba Mummy tafaďa tana duban sa,
A a mum wlh yanzu ma na makara bari na wuce sai na dawo anjima,
To a dawo lafiya Allah ya tsare yabada sa'a,
Amin mum nagode yafaďa ya fice daga dining room ďin,cikin hanzari dan ba qaramin makara yayi ba,
Abba ne ya miķè shima yana goge hannun sa bayan ya wanke, kasancewar ya kammala da cin abincin, Parlou ya koma ya zauna Ya kunna tv tashan N T A yasa yafara kallon labare.
"Ya rage saura Mumy da humaira wacce ke kai abincin bakin ta kamar dole aka sata ci,
Idan kin kammala ki tattare gun kisa turaren wuta Mummy tace da humaira bayan ta miķè, dan zuwa parlou wajan Abba.
Tattare wajan humaira ta soma yi dan itama ta kammala cin nata abincin,"
"Kambun uba shegiyar yarinya Ni zaki rainawa hankali, Zakici kwal ubanki wlh a gidan nan Mahmud yafaďa sanadiyar lotsewar motar sa da yaga tayi kuma yasan babu wanda ya aikata masa haka sai Humaira dan itace ķàrshen fita da motar sa jiya Yana huci saikace tsohon zaki ya koma cikin gidan,
"Fitowar ta kenan hannun ta riqe da da kulan abinci zata shige kitchen ta hango shi yana nufowa inda take kamar sama zai tashi,
" Tuni
tasha ruwan jikin ta" idon ta ya kawo kwalla ta ďaura hannu ďaya aka Nashiga ukuna yau tawa taqare a gidan nan idon ta duk yayi zuru zuru tun kan taji bala'in da zai sauķè mata," Juya kai tayi da niyar komawa ciki, taji yace wlh kika kuskura kika ďaga ķàfar ki anan sai na kakkarya ki,
Cak ta tsaya jikin ta na rawa duk tabi ta daburce dan mugun tsoron shi takeji,
Zo nan dan ubanki yafaďa bayan ya qaraso inda take,
Jikin ta ne ke karkarwa kamar taga mutuwa
Kasa mosawa tayi ko kaďan,
Wani mugun tsawa ya daka mata hakan yayi sanadiyar faďiwar kular dake hannun ta,
Badake nakeba kin min banza,
Jiya banyi miki kashedi kan karki bari wani abu ya samu mota naba?" Ya tambaya ta tare da harďe hannayen sa bisa ķirjin sa yana mata kallon tuhuma,"
"Nan ma shirun tai takasa bashi amsa.
Mugun kallo ya watsa mata Yace zaki ban amsa ko sai na kakkarya ki yanzun nan,
Kayi haquri wlh bani nayi ba wani ne ya buge ni da tasa motar.
Bai bari ta qarashe maganar ba ya kai mata wani gigitaccan mari a fuska ta,
Shegiya ni zaki renawa hankali ina ruwana da wanda ya buge ki zaki tsaya kina gaya min maganar banza stupid kawai bàce min da gani kona qara miki shegiya kawai,
"Kuncin ta'ta riqe take hawaye yayi mata facafaca a fuska dan mugun mari yayi mata jiki na rawa ta koma ciki tabar kular a wajan,
"Kan cinyar Mummy ta zube tana rusan kuka" Hankali tashe Abba ya shiga tamyar ta lafiya Mamana waya tabàki haka kike kuka?
Cigaba da kukan tayi ta kasa cewa komi ,Mummy ce ta ďago kanta tace ke bamu son sakarcin banza kin shigo da gudu cikin kuka kuma an tambayeki kinyi banza da mutane Tayaya zamu san abunda ya sameki.
A a ke kuwa bita a hankali mana,
Mamana gaya min wanda yasaki kuka
Hawayen da yayi facafaca a fuskan ta tashiga sharewa Tace ba Ya mahmud bane Ya mare ni dan na lotsa masa motar sa bansani ba,
Ina shi Mahmud din yake Cewar Abba bayan ya tashi da niyar zuwa ya sameshi,""" yana waje ta bashi amsa, tanaci gaba da shafa kuncin ta dan ba qaramin zugi yake mata ba,
*
"Cikin bàcin rai ya koma motar sa hannu yasa a aljihun sa dan ciro phone ďinsa sai yaji babu, Tsaki yaja ya koma cikin gidan dan ya tuna a dining ya mance wayar,
" Karo sukaci da Abba a bakin ķofar parloun,
" Abba yace kai zo nan dan uwaka wanne dalilin yasa zaka daketa saikace kasamu jaka?
" Mota na ta bàta min kuma dan ta raina min hankali taqi faďa min kenan in gani da ido, Mahmud yafaďa yana watsa ma humaira harara wacce keta faman haki idon nan yayi zutumzutum kamar bashi ba,
Dan tajima motar ka jiyo shine kakeso ka nakasa ta kai gashi an tabà rayuwar ka ko.To buďe kunnen ka kaji da kyau wlh wlh idan ka kuskura ka sake ďaga hannu ka mare ta sai nayi mummunar sabà maka sakaren banza wanda baisan girma yake ba, Abba yace dashi yana masa mugun kallo"
'"To shikenan kuma Abba tayi lefi baza a hukunta ta ba halan gobe ma tasake Yarinya inbanda rawan kan tsiya yawo na cin ķàfar ta ina ita ina tuqi yanzu dama ina sane da ita tunda tadawo hutu bata zaman gida saikace mintsinin ta ake,
Nidai wlh karta kuma gigin ďaukar min mota dan wlh zan iya bàbbàlla ta tunda ba kuďin ta bane ya siya min Yana kaiwa nan ya shige dining ya ďauki wayar sa ya ficewar sa daga parlon ransa in yayi dubu ya bàci ,"
" Girgiza kai Abba yayi akaro na biyu ya koma parlon yace da Humaira kiyi shiru mamana nan gaba duk inda zaki karki kuma ďaukar mishi mota kiyi amfani dana momyn ki insha Allahu kina gamaa karatun ki kema zan siya miki mota kinga kin huta da wannan ja'irin yaron'
Tashi tsaye tayi tana goggoge fuskan nata Tace to Abba nagode bazan kuma ba insha Allahu daga nan tashige ďakin ta ta kwanta dan yanda takejin tsananin ciwon kai,
Tattare dining ďin da bata qarasa ba kenan," "Mummy kam shiru tayi bace qala ba dan bazata iya da bala'in mahmud ba, duk da itace ta bata motar,
ķarshe sai mai aikin su hawy ce wacce ke musu shara wanke wanke da dai sauran su ta qarasa tattare wa tasaka turaren wutan,"
🌾🍃🌾🍃🌾🍃🌾
****A a ya haka kuma Abdulmalik kasan fa fita zamuyi Amman kayi rashewar ka kana banzan tunanin gashi har biyar na shirin yi bamu fita ba, kasan kuma inada abunyi, gwara ai mu hanzarta muje mu dawo tunkan rana ta faďa," cewar wani guy bayan ya iso gun ya zauna kan ďaya daga cikin kujerun parlon,"
Wanda aka qira da Abdulmalik ďin ne ya lumshe idon sa ya buďe da murmushi kwance akan fuskan sa ya ďago daga kwance da yake ya sauķe ajiyan zuciya tare da busar da iska ta bakin sa ya shafa sajen sa mai sheqi wanda ya kwanta luf a Kyakkyawar fuskar sa, Yace bazaka gane bane haisam nayi ganganci a lokacin dana gamu da ita, kallo ďaya nayi mata wlh nakasa gane kaina gashi bansan sunan ta ba bansan wanne unguwa take ba,
Naso ace na kuma haďuwa da ita ,
Jinjina kai Haisam yayi yana mamakin sauyawar abokin nasa tun jiya da yadawo gida ya lura da lamarin sa, dakewa yayi akaro na biyu yace wacece ita haka wacce har tayi nasaran satar zuciyar ka a lokaci ďaya bayan kai ba shiga safgar ýàn mata kake ba , gaskiya wannan bari nayi gaggawar sanar da Maraqishiya tun yanzu tafara shiri tarbàn kishiya dan ga mijin tanan yana shirin qara aure,
Dukan wasa abdulmalik ya kai masa tare da watsa mai harara yace Allah zanyi maka rashin mutunci banson maganar banza,
Dariya haisam yayi masa bayan ya kaucewa dukan, Yace ayi min afuwa aboki na bazan kuma ba duk da gaskiya nafaďa..Yanzu dai a bar zancan tashi mutafi mu duba bawan Allah nan kar yaga rashin mutincin mu,"
Tashi daga kujeran yayi tare da gyara rigan shaddar sa ruwan toka wanda yasha zubin farin zare yayi matukar ķarbàn jikin sa," Yace da haisam muje,
Haraban gidan suka fito suka nufi mota mazaunin driver Abdulmalik ya zauna ya tada motar shi kuma Haisam ya zagaya gefe ďayan ya shiga suka Fice daga gidan suka hau titin da zai sada su da inda zasu..
******
Suna isowa asibitin Abdulmalik ya soma fita kafin haisam," Har ya soma takawa kamar ance masa ya juya yaga motar a gefen sa a pake, ido ya buďe da kyau ya qara murzasu akaro na biyu yaga tabbas motar da yake nema ďin ne,
Murmushi ne ya kubùce masa bai ankara ba,
Haisam ya dawo baya da yake shi har yayi nisa kaďan," Yace abokina lfy ka tsaya muda muke sauri?
Lafiyar ce ta kawo haka Abdulmalik ya bashi ansa yace kaga motar ta nan na tabbata duk yanda akayi tana cikin asbitin nan," Haisam yace ai motar kagani ba ita ba hala ma idon kane ke maka gizo dan haka muje dan Allah muyi abinda ya kawo mu, yarinya saikace ďiyar aljanu tana shirin susuta ka a lokaci ďaya,
Harara ya watsa masa yace kaifa ka cika zancan banza uban wa yace dakai sonta nake kawai dai neman ta nake na rama rashin kunyar da ta min dan naga alama batasan girman mutane ba Amman zan koya mata hankalin,
"Yana kaiwa nan yayi gaba yabar haisam nan tsaye yana masa dariya dan ya gano sa burin kunya yake sauķewa,"
****
Cikin gaggawa suka duba abokin nasu suka fito Abdulmalik ne duk yabi ya kaďawa haisam hankali kamar duniyar zai bari haka yake ta Allah Allah a zuciyar sa kardai ta tafi,
Bai gama ida addu'ar tasa ba ya hango motar yana ficewa daga haraban asbitin.." cikin sauri ya ďaga ķafar sa ya iso ga motar sa yace da haisam ya shiga sutafi, batare da ya tsaya bata lokaci ba ,"
Girgiza kai haisam yayi yau yana ganin ikon Allah kodai abokin sa gamo yayi da yar aljanu ?,"A zuciyar sa yake zancan bayan ya shiga sunbi bayan motar......
📚📚
[30/08, 18:06] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR* *AURENA*🥀🥀 🥀
*NA*
*HAFSAT M* ✍🏻
*7*~ *8*
A hankali suke bibiyar motar batare da mai shi ya fahimci binsa ake ba, kasancewar cikin dabara yake taka masa baya haka nan suketa ratsa kyawawan gidaje dake jere a cikin unguwar, A wani babban gida sukaga tsayawar motar mai gadi ya buďe masa ya shiga,"
Ganin haka yasa shi jan nashi motar zuwa gefen kwaltan dake layin yayi parkin ďin motar nasa , kafin ya, kwantar da kan sa ajikin kujeran yayi matashi da hannayen sa duka biyu ya lumshe idon sa murmushi sauķe a fuskan sa yana hango ta cikin kwakwalwar sa sanda take masa tsiwa da ďan madaidaicin bakin ta, qara gyara zaman nasa yayi akaro na biyu murmushi ta ķubùce masa da hango Kyakkyawar gashin kanta mai sheqi baki siďik da yayi ,"kallo ďaya tak zaka masa ka fahimci cewa yana cikin nishaďi," muryan haisam yaji kamar daga sama shi dayawo dashi daga duniyar da ya wula,"
Kutuma ķur'anin Allah Abdulmalik kamayar dani ďan iska, sanin kanka ne inada inda zanje Amma ka kama ka ďauko mu inda ba'a san da ķurar ka ba, to billahil azim wannan gadaran ta isheni nabar ka lfy zan qarasa gida da taxi, idan kagama banzan tunanin da ya kawo ka kasame ni a gida, yana kaiwa nan ya buďe motar yayi ficewar sa, ran sa in yayi dubu ya bàci dan tun suna bibiyar motar yake masa mita Amma yayi banza dashi shiyasa yaga idan ya biyesa sai ayi magariba basu bar unguwar ba,
Ajiyan zuciya ya sauķe tare da shafo sajen fuskar sa, bayan yagama sauraron ķorafin haisam, Murmushi yasaki tare da girgiza kai ya tada motar yabi bayan shi,,""" Hango sa yayi ya tsaida taxi zai shiga hakan ya sanya yayi gaggawar isa gareshi..glss ďin motar ya sauķe, ya ďago kai ya kalle shi,yace,"
Haba abokina miye na zuciya akan wani abu qalilan kamar ba dangin mazaje ba hakan na nuna ragwanci nefa Abdulmalik yace da haisam ta fuskan zolaya tare da kinne masa ido ďaya yana masa dariya dan yanda yaga ya takura fuska,"
Tsaki yaja tare da buďe motar ya shiga kafin yace ai kai zan cewa ragon namiji wlh Abdulmalik kabani kunya wlh mace guda ďaya tilo ta susutaka harda biyo ta unguwar su saikace asirce ka tayi duk kabi ka ďaga hankalin ka akanta wlh ko Maraqishiya ni banga kayi wannan ruwan ķafa haka akan ta ba,,ai ko mayya ce ta kamaka iya kaci kenan,"cikin bàcin rai yake maganar,,"
Ganin mitar nasa bana qarewa bane, hakan yasa Abdulmalik girgiza kai baice dashi uffan ba dan yaga alama ransa ya matukar bàci sosai tada motar yayi sukabar unguwar
*************
Zaune take a parlou ita ďaya kasancewar yau gidan nasu ba kowa Abba ya fita office yau tun safe mahmud kuma yaje gun aikin sa mumy ma fita tayi bayan gari yagama waye wa gidan aminiyarta hajiya fatema, kan maganar walimar auran ďanta sufiyan wanda za'a gabatar gobe, tayi tayi da humaira ta rakata dan ta gaishe da hajiya fateman da yake kullum idan sun haďu saita tambaye ta, Amman fur taqi,
Ita kuwa ba qaramin tsanan zuwa gidan tayi ba sakamakon maganganun da sufiyan ďin ke mata tun wani lokaci da mumy ta aike gidan da yake unguwa ďayasuke ," tun a nesa ya ķallara ido akan yaji gaba ďaya ta tafi da nutsuwar shi,"tunda daga lokacin yaji bazai iya rayuwa ba ita ba shidai yasan yana ganin ýan mata iri iri Amman wannan daban take, hakan yasa yabi diddigi ya gano cewa ashe ma ýar gidan aminiyar mahaifiyar shi ce,"
Daga nan yasamu ya sanar da mahaifiyar tashi, ranan yaga murna a gunta zai iya cewa rabon da yaga farin ciki haka qarara a furkan ta ya manta,,"
Batare da bàta lokaci ba ta nasar da qawar tata itama mumy taji daďin zancan ta amince bayan ta sanar da Abba yace mata shifa baison abunda zai kawo masa bàcin rai dan haka sai ya tabbata idan yarinya tana so tukun zai amince, mumy kuwa batace mishi ķala ba, ta sanar da hajiya fatema abinda Abban ya faďa,"" hakan yasa ta samu ďan ta sufiyan tagaya masa,"
Shi kuwa daga ranar ya hanata sakat a layin duk inda zataje sai ya tare ta da surutu ,
wai shi ala dole sonta yake zai aure ta, bala'in haushin sa takeji duk lokacin da yaganta wani irin mayun kallo yake binta dashi saikace sakare, wannan idan ta sake ta aure shi ai ta zalunci kanta, ta inama zataji daďin RAYUWAR AURE, dashi mutum kullum yana nan sakakam yau ta ganshi da waccen yarinya gobe ma ta ganshi da wata daban duk haďuwar da zatayi dashi tare da mace zata ganshi saikace na mamajo,'"
Hakan ya sanya ta tsani zuwa gidan nasu tun mumy na mita kan tun yanzu tasamu yaro mai hankali yana sonta Amma ta tsaya tana iskancin da taga dama sai taga uban wa zataso bayan wannan, dan ita dai bataga lefin sa ba idan kyawun nema ai yanada shi ba lefi ga sana'ar sa yana yi to meye aibun sa,""
"Ita dai qala batace mata idan tana mitar dan gani take kamar asirce ta yayi ko dan yaron aminiyar tane, ohho ko tace mata ba sonshi take ba sai tace ai shi so ba matsala bane lokaci ďaya zakiji kinason mutum!, ganin da gaske taqi yarda dashi, ya sanya tun daga lokacin tabar harkan ta!!
Ba qaramin murna tayi ba ranar da taji labarin zaiyi aure ji take kamar ta zuba ruwa a qasa tasha ranan farin cikin ta baya misaltuwa kwana tayi tana godiyar Allah da yaraba ta da alaqaqai,,"" Shiyasa yau da mumy ta nema suje taqi binta, gwara tayi zaman ta a gida ita ďaya kuma gobe ma ko tace suje walimar bazataje ba dan bason haďa ido dashi take ba,""
ďaukan kibiya tayi tafara tsefe kanta bayan ta kammala da girkin abincin rana da duk wani aikin cikin gidan da yakamata ace tayi, "cikin sauri take tsifan kan da yake saura kaďan ya rage mata Allah Allah take tagama ta huta dan ba qaramin takura ta gashin yayi ba jitake kamar ta ďauki almakashi ta aske shi kotaji sukuni," Jifa jifa take kai kanta ga tv dake manne a bangon parlon tana kallon tashar Zee world ,'"
***
Sallamar mumy da taji ne yasa ta da ďago da kai daga tsifan da take, amsa mata tayi tace, sannu da zuwa har kin dawo da wuri haka, ai nazaci zaki kai la'asar,,"" Harara ta kaimata tace da ita da ban dawo ba kwana zanyi , fuskan ta a ďaure tayi maganar dan yau ta bata haushi qin binta da tayi dan ta gaishe da aminiyar nata, ko yau da taje saida ta tambayeta," yaukam kasa bòyewa tayi tace tana gida nayi nayi da ita mu taho tare Amma taqiya,"murmushi hajiya fatema tayi batace komi dan ta gano dalilin rashin son zuwan ta, to in banda abin ta ai komi ya wuce tunda dai gashi wanda take gudun aure zaiyi,"
Ganin ranta a bàce yake yasa ta gimtse dariyar ta tayi shiru taci gaba da tsifar ta tasan idan ta qara magana zata iya balbale ta da faďa,"
"Wai ke meyasa bakijin magana ne tun jiya na kula kikeso ki tsefe kan nan na hanaki Amma da yake taurin kaine dake ina fita kika zauna tsefewa kwata kwata ma yaushe akayi qitson da har zaki tsafe shi,tunda abin naki yazama iskanci to maza gama tsifar kije a daďa miki wani ķitson kuma naga kin qara zaman tsefewa sai nayi mugun sabà miki, Mummy tace da ita bayan ta cire mayafin dake jikinta ta zauna akan ďaya daga cikin kujerun dage mamaye a parlon,"
Tura baki tayi tana qunquni dan ita dai harga Allah babu abunda ta tsana kamar taga tayi zaman ķitso baya ga haka ta gwammace kanta ya lalace indai har sai tayi ķitso zaiyi kyau,"
Haka tana qunquni taci gaba da tsifan kan,,""qaran buďe ķofar parlon sukaji anyi tare da sallama,,"" Tsalle humaira ta daka saka makon waýanda tagani batama san kibiyar hannun ta ya faďi ba cikin murana ta isa garesu dayake kullum sai tayi maganar zuwa musu kafin hutun ta ya qare,"
Oyoyo mama na sannun ku da zuwa wlh kullum kuna raina ko jiya saida nayi niyar inje muku sai bansamu dama ba," ashe kuma kuna tafe kuyi min afuwa, tana maganar tare da haďa hannayen ta kamar tana neman gafara,"
"Wacce ta qira da maman ta watsa mata harara tace karya kike ja'ira uwar bayani tunda kika dawo daga makaranta ko sunan unguwar mu nasan baki kamaba balle muga ķàfar ki, kauce min daga hanya ni," tana kaiwa nan ta ratsa ta wuce gun mummy wacce keta binta da ganin murna ta zauna suka shiga gaisawa",
ku kuma miye haka kun titsiye mutum agaba kuna masa dariyar muna furci saikace wasu sabbin kamu nasan duk kune kuka haďa ni faďa da ita ai humaira tace da wasu ýan mata wanda suka shigo tare da mamar, dan tunda mama tafara mata maga suke mata dariyar mugunta",
Dariya suka kuma kwashewa dashi ďayar tace kinga malam mufa ba rigima bane ya kawo mu dan haka bamu gu mu wuce kiyi lefi kuma kizo kina sauķe mana borin kunya rukky shigo mu qarasa gun mummy idan muka biyar wannan yar rigimar sai mu kwana a tsaye
," wacece aka qira da rukky ne keta gimtse dariyar ta dan yanda taga tayi kicinkicin da rai tana musu wani irin kallo, wai ita ala dole ranta ya bàci,"
Gun su mummy suka qarasa sukafara gaishe da ita cikin sakin fuska Mumy ta Amsa musu, take tambayar su ya karatu? alhmdla suka bata amsa kafin suka juya ga humaira wacce keta binsu da harara bayan ta iso gun nasu ďauke da abun motsa baki a hannun ta dire shi a gaban mama ta dawo gunsu ta zauna batace dasu ķala ba fuskan nan a ďaure,"
Haba malam kallon banzan ya isa haka ai sai wani ciccin magani kikeyi kamar meso faďa fadila tace da ita bayan ta zunguri kanta tana mata dariya,"
Harara ta watsa mata tace wlh zan miki rashin mutunci banson iskancin banza da wofi kinji na faďa miki ,"
Wai ma ina sadeeq ne ko bashine ya kawo kuba? ta tambaye su tana duban ķofa tunda tasan kullum shi ke kawo su idan yana gida
kice dai ina ďan bala'i mutum kullum cikin ďaure fuska yake saikace baķin Arne, ni wlh haushi yake bani idan yana wani abun, rukky taba ta amsa tana yayya mutsa fuska,
Himm kema kenan ai duk zuriyar su ďaya da wannan shahararran mugun mutumin waisu basu san raini ga shegen zagi saikace katsinawa kinga yaa mahmud indai yana cikin gida to bakai basakewa,,ko jiya saida ya balbale ni da bala'i akan wata akwalar motar sa dako....
Maganar ce ta maķalemata can cikin maķoshin ta sanadiyar shigowar sa parlon shida sadeeq, kame bakinta tai tayi shiru tana fatan Allah yasa bai jiyo ta ba dan tafi kowa sanin halin shi yanzu sai ya iya fasa mata baki idan yajita,"
Shi kuwa kota kansu baiyi ba yasamu ďaya daga cikin kujerun parlon ya zauna sadeeq ma zama yayi kusa dashi kafin ya gaishe da Mumy, cikin sakin fuska ta amsa masa tace Ashe tare kuke tafe dasu?,"yace eh wlh tare muke na tsaya a waje ne dan tun a bakin get ya hango mahmud hakan yasa yana sauķe su shi kuma ya tsaya tare dashi sai yanzu suka shigo gidan ,"
Mama ce tayi magana tace ni kuwa mahmud ya maganr aure ne har yanzu banji kanayi ba gashi qannan bayanka saiyi suke ai gwara kayi ka gaggauta cire mana surika musha biki idan baka samu wacce ta maka bane shikenan kazo munada wacce zamu baka ga ko raihana sai a haďa ku da ita tunda dama tana sonka kaine kake mata wasa da hankali,
Murmushi yayi ya saukar da kansa qasa yace habadai mama ina ni ina ajiye mace yanzu balle wata raihana nifa kota kan budurwa banbi dan bàta lokaci ne su masuyi ďin ma basuda aikin yi ne,"
Kai kai wlh yaa mahmud gaskiya ka iya zuba ka manta duk tulin yàn matan da kakeda shi yanzu kuma kace babu dan neman mafita, akwai ďayar ma wacce da alama ita kafiso kullum sai kasa hoton ta a storyn ka na Snapchat,, Azban ko Asban nema ohho ni sunan nata ma wahala yake bani cewar fadila tana riqe baki dan maganar tasa yabata mamaki,"
Wani irin mugun kallo ya tafka mata bayan ya jefeta da pllow dake kusa dashi yace shegunaye yan iskan yara masu zubin aljanu dama nasan gulmar munafurce ke saku following mutum, "Wlh wlh kunji na rantse duk wata yar iskar da taqara kallon story na sai na babbàlla ta magulmata, kullum sai anyi blocking naku Amma dan jaraba sai kun biyo mutum, nan gaba zanyi maganin ďan iska wani ya kuma bibiyata yagani, yana kaiwa nan ya ciro wayar sa a ajihun sa yafara latsawa,"
Dariya ne ya kubùce wa sadeeq ya girgiza kansa yace indai waýnà nan yaran ne ai saidai kayi ka gaji dan wlh ko mayu nan ya gansu ya barsu barsu,"
Fadeela tace au hakama zakace mune mayun kenan dan kai bamu faďi nakaba, ko mancewa kayi munsan ta duk cikin wayar ka in an bincika hoton ta ke yawo aciki hatta kan screen ďin wayar ka itace gashi ko kyau ma batada shi gwara ma waccan ta farin naka Aina'u wanda karabu da ita...
Katseta yayi fuska a damķe yace wlh kika sake kika qara magana a nan sai na miki ba daďi magulmaciya yar sa idon banza,,
Shikenan yau asirin wasu ya tonu bara nima nafaďi abinda nasani, humaira tafaďa tana dariya tare da tafa hannun dan dama hanyar magana take nema sai gashi yau ta samu dan ita tafi kowa sanin sa da ýan mata,duk sanda Abba ko mumy suka aike bàngaran sa sai taji yana waya da budurwa kamar a bola yake kwasan kuďin sai sushafe a wanni suna hira tun tana jiran sa ya ida wayar har tagaji taje tadawo still saidai taga ya yanke wayar idan ya karbì sakon ta sai yaci gaba taso ta haďa shi da Abba Amman ta basar,"
"
Harara ya watsa mata bayan ya ďago kansa daga latsa wayar da yake rai a bàce fuskan nan babu alamun wasa yace billahil azim idan kika kuskura kikace wani abu a kaina to ki tabbata da karyayyen qafa zaki koma makaranta shegiyar yarinya,ke gaki mai dogon baki ko to bisimillah,
Yana kaiwa nan ya kau da kansa yaci gaba da abinda yakeyi,
Baki ta murguďa masa a ranta tace kaidai wlh kaji jiki bana kaiwa asbiti ba mutum ace baida aikin yi sai na masifa Allah yasa kagamu da masifaffiyar mace wacce zata koya maka hankali sai ka rainawa kanka mugu kawai, maganar mumy taji , tace,"
kai bamuson sakarcin banza da wofi ya ishemu haka shikenan ku bakusan kun girma ba kullum cikin yi kuke da ķannan ku saikace sa'annin ku idan anyi magana kuce sun raina ku bayan ku kuka siya ,"" ku kuma ta juya ga su humaira tace marasa kunya kar na kuma jin wani yayi magana ja'ire kawai maza ku wuce ku fitar da kayan abinci dining tunkan na sabà muku fuskan ta a damķe tayi maganar dan ta kula idan ba burki ta taka musu ba ýan mazan nan zasu iya musu rauni,"
Tashi sukayi sumsum fuskan nasu duk a ďaure suna qunquni suka nufi kitchen dan ciro abincin badan ran su yaso ba,"
*****
🌾🍃🌾🍃🌾🍃🌾
Gida ne madaidaici mai ďauke da parlou dining sai ďakuna biyu ko wannen su tare yake da banďaki sai ďan kitchen wanda ke manne da sto," Idan kayi la'akari da gidajen dake jere a unguwar zakaga komin su iri ďaya yake babu banbanci hatta fenti,"
Zaune yake kan ďaya daga cikin kujerun parlon wanda yake fesfes ko ina an gyara an goge yayi tas dashi , hannun sa riqe da takardu da alama rubutu yakeyi,""
Yana cikin rubutun ne ya duba yaga babu ďaya daga cikin su hakan yasa yashiga binciken ko ina na parlon dan muhimmin takarda ne gobe yakeson gabatar dasu,""
"yana tsaka da bincike ne ya tuno da jakan office ďin sa ya tabbata yana ciki, dogon tsaki yaja tare da shafo kansa da yake ya mance a gidan haisam shekaran jiya bayan ya shigo gari a gidansa ya sauķa kafin a shashshare masa gidan sa wanda ya siya musamman dan yana yawan shigowa abuja,"
Tashi yayi bayan ya kammala da takardun gaban nasa ya nufi toilet ďin dake cikin parloun ya ďauro alwala, dan yaji anata qiraye qirayen sallah la'asar' yana fitowa ya tada hiqama dan gabatar da sallah,"
Bayan ya ida sallah yayi azkar tare da addu'oi ya shafa kafin ya tashi ya ya zari makullin motar sa yabar gidan cikin hanzari dan zuwa ďauko jakan nasa,"
***
Shigowar su kenan cikin parloun bayan sunyi ma su fadela rakiya sun koma gida, humaira tace,""
Mummy dan Allah ranta min motar inje suparmaket inaso inyo shopping kayan makaranta, Abba yabani kuďin jiya kinga jibi ne tafiyar tamu,"
Meyasa baki bi su fadila ba tunda hanya ďaya ne basai su ajiye kiba," "A a mumy nafiso natafi da kaina idan sun ajiye ni wa zai dawo dani ","kinsan sadeeq ba kawo ni zaiyi ba sai ya walaqanta ni, ni kuwa harga Allah na tsani walaqanci, na gwammace banje ba,""
Makullin motar ta jefa mata kafin tace, kin kyauta ai saura ki wuce yawon banza da wofi, ko gidan su Amena ban laminta ki tsaya ba kina kammalawa ki juya kidawo gida wlh idan kika kai magariba baki dawo ba sai nabàta miki rai narabaki da ķafa ďaya,"
A a mummy baza muyi haka dake ba wlh da wuri zan dawo idan kika rabani da ķafa ďaya ai tawa ta qare, nifa ku kuke ganin nacika yawo Amman banda haka ai bana fita ko ina saida dalili,,"
tana maganar ne tana dariya dan yanda taga mumyn da gasken ta take,"
Ďaki ta shige ta canzo kayan jikin ta zuwa baķar Abaya,"taďan gyara fuskar ta ta feshe jikinta da turaruka masu ķàmshi ta naďe kanta da gyalen abayan, kafin ta fito tayi ma mumy sallama ta fice ta nufi mota,"
"Tada motar tayi mai gadi yazo yana ďaga mata hannu alaman gaisuwa ya buďe mata get ta fita bayan ta gaisa da shi,,""
Bata jima sosai akan hanya ba ta isa shopping mould ďin,""pakin tayi ta shiga ciki tafara dudduba abubuwan da take buka ta, turaruka tafara ďaukawa da su man shafawa da dai sauran su,""
Tana kammalawa ta nufi gun biyan kuďi a gaggauce ta biya ta fice dan komawa gida cikin sauri take tafiyar dan ganin har shida tayi kafin ta isa gida za'a iya qiran magariba,""
*
Isowar sa kenan cikin shopping mould ďin bayan ya tashi daga gidan haisam ya jiyo nan dan siyan wasu abubuwan da zai bukata kafin yabar garin,"" Hango ta yayi tana zuba sauri kamar zata tashi sama, hannuwan ta riqe da ledojin, ido ya zuba mata yana kallon ta yanda ko ina na jikin ta ke motsawa dan saurin da takeyi" ,girgiza kai yayi tare da murmushi yaci gaba da kallon ta kamar zai cinye ta,""
Ta iso ga motar ta kenan cikin sauri take tafiyar kanta a sama, bata ankara ba taji ta wani irin buguwa da k'aton dutse a gaban ta yatafi da ita tabaya luuuu zata faďi, wata yar ķara tasake tare da runtse idon ta sosai zuciyan ta na dukan uku tafara Ambaton Allah tunawa da ķaton ramin dake bayan ta tasan idan tafaďa cikin wannan wangamemen ramin, itakam nata ya qare, sai yanda rabbi yayi da ita ta riga da ta gama saddakarwa saidai a ďauki gawanta aciki...
📚📚
[30/08, 18:06] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR* *AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*9*~*10*
Har yanzu idon ta a runtse yake takasa buďe su zuciyan ta naci gaba da bugawa yana harbawa kamar zaibar ķirjin ta, bakin ta kuwa har yanzu bai daina Ambaton Allah ba, jira kawai take taji tayi masauķi cikin wannan wangamemen ramin,""
Jin shirun yayi yawa kuma ga wani daddaďan ķàmshi dake bugan hancin ta duk yabi ya addabe ta ji take idan bata mance ba kamar ta tabàjin wannan ķàmshin jikin wani,,hakan yasa tayi karfin halin buďe idon nata dan taga gatan da ubangiji yayi mata dan ita dai tasan fitowar ta daga cikin shopping mould ďin bataga kowa a kusa da wajen ba balle tasamu mai taimaka mata,"
Buďe idanun ta farayi ahankali kamar sabuwar waraka daga makanta," tana gama buďewa caraf suka sauķa cikin ķwayar fararen idanuwan shi wanda yakafe ta dashi kamar zai cinye ta murmushi ďauke a fuskar sa,""
Cikin hanzari tayi ķoķarin kwacewa daga riķon da yayi mata hakan yasa ta qara tafiya baya zata faďi," cikin azama ya qara tamķota, wannan karon kam dan gana tayi,dan in tayi wasa qarasawa zatayi ciki,"
Wlh zan iya sakin ki ki faďa ciki idan baki tsaya ba, taji ya faďa yana ďan buďe idon sa kamar da gaske,"baki ta murguďa masa bayan ta kawar da ķwayar idonta daga nashi,"
Tsallaka ramin yayi kafin ya ďagota ta tsaya da ķafar ta," fuskan ta har yanzu a tamķe yake ta juya batace dashi ķala ba ta ta kwashi ledojin ta wanda suka zube qasa ta buďe motar ta dan barin gurin,"
Ji tayi anyiwa hannun ta wani irin riqo,hakan yasa ta jiyo da kanta sukayi ido huďu da shi,cikin sauri ta kawar da nata dan bazata iya juran kallon idon sa ba, fisge hannun ta tayi daga nashi,"kafin tace, meye haka zaka wani riqe min hannu saikace kasamu matar ka,tana maganar ne cikin haďa rai,tamkar bata tabàyin dariya ba,"
" Abun nata ma dariya yaso bashi ganin karfin hali irin nata,"wai ace an taimakawa mutum daga jin ciwo,akan yayi maka godiya saima ya tsaya yi maka rashin kunya," juya kai yayi ya nufi shopping mould ďin batare da yafaďa mata abinda yayi niya ba,"
"Thank u yaji tafaďa can cikin qasan maķoshin ta kamar an maqure mata wuya,"
"Murmushi ya ķubùce masa baice da ita ķala ba yayi gaba a ran shi yace kiyi duk abunda kikaso zaki shiga hannu na watarana ,"
Ganin kota kanta baiyi ba gashi tuni har an soma ruwan sama jikin ta yafara jiķewa yasa ta buďe nata motar ta shige jikin ta duk yayi sanyi tabar shopping mould ďin zuciyan ta tunkushe da abubuwa iri iri,"gani take sam bata kyauta masa ba, ji take tamkar ta koma tayi masa godiya sosai, dan ba qaramin taimaka mata yayi ba tayi mamaki matuka ganin wannan karon ya sauya mata kamar bashi kece mata zai rama abinda tayi masa ba, haďuwan su ta farko,"
Ajiyan zuciya ta sauķe tare da yafo gyalen ta da ya warware a kanta lokacin da zata faďi ,"
"Wani daddaďan ķàmshin turaren sa ne taji ya doki hancin ta hakan yasa ta saki yar murmushi ta lumshe ido tare da kaiwan gyalen bisa hancin ta tana sinsinawa kamar kare,"
Ajiyan zuciya ta kuma sauķewa a karo na biyu," take cewa inama a ce wannan bawan Allahn zai sota da tafi kowa farin ciki, dan duk wani abu da za'a ce mace taso a jikin namiji to duk ya mallake su saidai kyawun hali ne bata sani ba Amman ga dukkan alamu idan ka dubi ya nayin shi bashida matsala gani take duk abinda yayi mata na rashin kyautata wa itace sila,"
Qara gudun motar tayi kaďan dan ganin garin ya ďauki duhu ga ruwa saman da ake har yanzu kar yayi karfi kafin ta isa gida," murmushi ne sauķe a fuskan ta tana addu'ah a ranta Allah ya kuma haďa ta dashi tayi masa godiya tabashi haquri kafin tabar ķasar,"
**
Ana qiraye qirayen sallah ta isa gida, cikin sauri tayi pakin ta kwashi ledojin ta tabuďe motar ta tafita,"
"Bataga kowa cikin parloun ba hakan ya tabbatar da sun shige yin sallah ne,"ďakin ta tashige kai tsaye toilet ta nufa ta ďauro alwala kafin ta cire kayan jikinta da ya jike,ta zura wani dogon rigan shan iska tare da hijabi ta tada sallan ta cikin nutsuwa,"
BAYAN KWANA BIYU
Humaira ce zaune a ďakin ta sai faman haďa kayan ta take cikin a kwatin ta mai kyawun gaske, cikin hanzari take haďa kayan, " ji tayi an turo ķofar ďakin an shigo," Mahmud tagani fuskar sa a tamķe, yace, wai mai kika tsaya yine tun ďazu ina jira kifito, dan kinsamu ma zan kai ki, zaki mayar dani ďan iska, wlh idan bakiyi sauri ba zan iya fasawa kya nemi wanda zai ki, airport ďin,"yana kaiwa nan ya juya yafice,"
Hararar ķofar tayi bayan ya fice, tace to kada Allah yasa ka kaini mana tafi nono fari, ta qarasa haďa sauran kayan kafin ta ďauki wayar ta taqira Amena tana amsawa, tace mata ta shirya gasu zuwa su ďauke ta," kashe wayar tayi tasaka shi cikin jakan ta qarami bayan ta gama," taja a kwatin ta tafice daga ďakin,"
Kai tsaye parlou ta wuce, mumy da Abba da yaya musty ta tarar," Abba ne ya soma mata nasiha mai shiga jiki kafin ya samata albarka rungume shi tayi batare da tace komai ba ji take da zai iyu da ta fasa komawa ," mumy ma nasihar tayi mata tasa mata albarka tare da yi mata Allah ya kiyaye hanya,"
Amin tace idon ta duk ya ciko da ruwa," ta rungumi mummyn tana sharan hawaye," kafin ta rungumi yaya musty tana ce mishi ya gaishe mata da Annur tunda yaqi zuwa dashi,"
Murmushi yayi yace ki daina kuka kina abu kullum kamar ýar bording school,ke bazaki girma ba kenan," dariya tayi batace komai ba, dan ita kaďai tasan kewar su da zatayi,"
Har zuwa mota suka rakota yaya musty ya buďe mata gaba ta shiga bayan ya saka mata a kwatin ta a baya,"" tana ďaga musu hannu, mahmud ya tada motar suka fita,"" saida suka biya suka ďauki Amena a gidan su kafin suka hau hanyar airport ,"
**
Zaune yake cikin airport kan ďaya daga cikin kujerun da aka tanadawa yan tafiya ya gama komi yana jiran haisam ya kawo masa wasu mahimmun takardun sa, wanda ya manta su kafin ayi bording,"
" phone ďin sa ne ya soma ringing daga aljihun sa,cirowa yayi yaga haisam ne, murmushi yayi kafin ya qara a kunnen sa, yace hello abokina har ka iso ne ? ," eh aka yabashi masa ta cikin wayar,"
Tashi yayi ya fita waje bayan ya kashe wayar," Haisam ya hango a ďan gaba ya qarasa gunsa yabashi hannu suka tafa tare da karbàn takardun da ya kawo masa, yace ,"
How far abokina tun ďazu nake zaman jiran ka na ďauka kafasa zuwan ne ai ,"Hararan wasa haisam ya kai masa kafin yace,
ďan rashin mutunci da badan takardun nan ba tafiya zakayi bamu haďu ba kenan?,"
A habadai ni na isa wlh aikin gaggawa ne ya taso min shiyasa nakeso nakoma a yau," zan dawo ai bayan kwana biyu kasan ni da abuja kullum ina kan hanya ,'"muje ciki yanzu za'ayi bording, Abdulmalik yace da haisam,"Jerawa sukayi suka fara tafiya suna hira,"
Ba su wani daďe akan hanya ba suka isa airport ďin da yake ba nisa tsakanin su,"
pakin space ya nema yayi parkin , kafin kowa ya sauķa daga motar cikin sauri suka jajja a kwatinan nasu suka nufo ciki," A gogon hannun ta ta duba tace, kai gaskiya Amina yau ďin nan mun makara sosai muyi sauri,
Amina tace barkan mu ďaya ma angama mana komi sai tafiya kinga mun huta da bin layi,"
Suna cikin tafiyar ne hankalin su duk yatafi ga saurin da suke, humaira ce taji ta bugu da mutum ta kafaďa, hakan yasa takardun dake hannayen sa zubewa qasa,"
Aiyya sorry dan Allah Malam ban kula bane, Humaira tace dashi bayan ta kai qasa dan kwashe masa takardun,"" kaiwa qasan yayi kafin yace mata,""No bakomai karki damu bar su kawai zan kwashe ,"
Kamar daga sama taji muryan nashi da take fatan sake haďuwa dashi, ya doki dodon kunnen ta,"
Ďagowa tayi da niyar tashi dan ganin shine ko kuma farki take," akayi rashin sa'a shima ya ďago kenan da niyar tashi basu an karaba goshin su ya bugu da juna,"
Washhh Allah suka furta a lokaci ďaya tare da dafe goshin suna murza wajan bayan sun ďago da kan su, tayi mugun jin zafin goshin nata Amman ta basar, tace,,"
Kayi Haquri dan Allah fuskan ta ďauke da murmushin da batasan na meye ba, tace am sorry ina cikin sauri ne bansani ba na bige ka," kuma nagode fa sosai da taimakon da kayi min shekaran jiya nasan da Allah bai kawo ka wajen ba da saidai a ďau gawa na aciki , pls am sorry, ta qara faďa tare da miķa masa takardun sa wanda ta kwashe,""
Bakomi yace da ita fuskar sa ďauke da murmushi, yana kallon shigar dake jikin ta yauma bakin abaya ne tayi rolin kanta da gyalen abayan," yace ai komi ya wuce ki daina faďin haka duk inda bawa yake Allah yana tare dashi,,,"
Murmushi ta qarayi tace haka ne nagode sosai bari na tafi kar ayi bording ni suke jira," Ina zaku ne haka? ya tambaye ta fuskar sa ďauke da murmushi,"" wlh makaranta zan koma Sudan,tabashi amsa tana shirin tafiya,"
Am ji mana yace da ita ko zan iya sanin sunanki, idan ba damuwa"
Sunana Aisha Amman da Humaira ake qira na, tabashi amsa a gurguje "" jinjina kai yayi yace ni kuma sunana Abdulmalik, ko zan iya samun number ki tunda yanzu mun shira an daina min tsiwa kinga sai muna gaisawa,""murmushi tayi tace ba matsala bani taka idan na sauka zan nemeka insha Allahu,"
Ganin sun tsaya wani hiran daban hakan yasa Amena jan a kwatinan tabi bayan mahmud wanda shi tuni yayi gaba, tabar su nan tsaye,"
Number wayar shi yabata bayan ya mata kashedin kar ta manta fa bayan ta sauķa," bazan manta ba wlh tace dashi tare da ce mishi sai anjima, ta juya da niyar shigewa,"
Karo taci da mahmud, da sauri taja da baya tana ďan kame kame kamar marar gaskiya ," kallon banza ya mata kafin, yace hira da saurayi ne ya kawo ki ko? kinsan yanzu zaku tashi?," Amma da yake jaraba na damun ki a airport ďin ma sai kinyi hira da saurayi," idan baki daina tsayawa da wani katon namiji ba billahillazi zanyi mugun sabà miki, in banda jaraba ina ke ina saurayi keda kike karatu,,"
Dalla malam wuce karna ji miki jiwo yanzun nan stupid kawai kinsan ba jiranki z'ayi ba dan iskanci zaki tsaya sakarcin banza da wofi,"cikin sauri ta shige tana waiwayan sa,"
wani irin kallo yayiwa Abdulmalik kafin yabi bayan ta,"
Girgiza kai yayi yace da haisam wanda ke tsaye yana kallon lamarin abokin sa," yace mushiga kar a tashi ina nan tsaye bansani ba," har inda jirgin yake haisam ya rakashi sukayi sallama kafin shi ya jiyo dan komawa gun aikin sa, dama yana tsakiya da aikin ne, Abdulmalik ya qirashi a waya yace masa ya sameshi a airport tafiyan gaggawa ya iske shi zai koma ķatsina,"
Bording fars ďin ta yabata kafin yace Allah ya kai ku lfy," Amin tace mishi duk jikin ta yayi sanyi ji take ajikin ta zatayi kewar yayan ta kodan faďan da take dashi kullum,"" har ta juya zasu tafi sai ta dawo baya ta rungume shi , tace yaa mahmud pls kayi haquri da duk abinda nayi maka pls ka daina faďa dani banajin daďi wlh ," tana maganar ne Amma muryan ta na sarkewa dan kukan da taji yataso mata,"
Jikin sa ne yayi sanyi matuka harga Allah yanajin son qanwar shi a ran sa zaiyi kewar ta sosai," ďago da kanta yayi daga jikin shi yace," haba Humaira kinsan dai ke qanwata ce inasonki fiya da yanda kike tunani, kije kar a tafi a bar ku Allah ya kaiku lfy , yana share mata hawayen yace daina kuka kinji kuna isa kiyi mana waya, kafin ya ďaga mata hannu zuciyar sa tunkushe da ķaunar qanwar sa tun dawowar ta hutu yasan shi ke takura mata baya sake mata fuska ji yake duk bai kyauta mata ba,"
Itama hannun ta ďaga masa tana murmushi takama hannun Amena wacce ke kallon su suka nufi ciki,"
**
Ko acikin jirgin ma humaira shiru tayi tana zancan zuci sai taji tana kewar ýan gidan su sosai, " gefe ďaya na zuciyar ta kuwa tunanin abdulmalik take sai yanzu ta tabbata da maganar mumy da take ce mata a lokaci ďaya mutum yake kamuwa da so gashi kuwa yafaru da ita, ji take zuciyar ta bazata iya jure rashin sa ba addu'ah take Allah yasa ya sota yazama mijin ta na aure,"
Murmushi tayi sosai tana tuna farkon haďuwar su da lokacin da ya taimaka mata sanda zata faďa cikin rami," murmushi ta kuma yi, tare da lumshe idon ta ita kaďai tasan mai takeji a yanzu ,"
ke meye hakane wai sai faman murmushi kike tayi ke ďaya saikace kin soma tabùwa kodai mutumin ne ya miki illa? kisanar dani dan daga alama zai kawo wuta," Amena tace da ita bayan ta zunguri kanta tana kallon tare da yi mata dariya ,"
ajiyan zuciya ta sauķe kafin tace kedai qawata zakisha lbr bari mu sauka ," Allah ya kaimu lfy Amena ta faďa bayan ta maida hankalin ta ga bayanan da ma aikatan jirgin suke,"
🌾🍃🌾🍃🌾🍃🌾
Sai wuraren karfe uku na yamma jirgin su ya sauka, kai tsaye gun motar sa ya nufa da yake tunkan su tashi ya qira driver sa ya sanar dashi yana hanya," office ďin sa yace ya kaishi bayan sun gaisa cikin girmamawa, batare da bàta lokaci ba yaja motar sukabar airport ďin ,""
**
Sai daf da magariba ya kammala da aikin gabansa, take ya har haďa takardun da yagama dasu ya saka cikin jaka kafin ya kulle office ďin ya fice dan komawa gida ji yake duk jikin sa ya gaji hutu kawai yake bukata a yanzu ga wani irin yunwa da cikin sa keji Allah Allah yake yaga ya isa gida,"
Saida ya tsaya a masallacin dake unguwar su yayi sallah magariba tare da yin addu'oin sa," yana nan zaune har saida aka qira isha yagabatar kafin ya wuce gida kai tsaye,"
Yana shiga cikin gidan bàngaran sa ya nufa," toilet ya shige yayi wanka ya fito ya goge jikin sa kafin ya saka farar jallabiya ya feshe jikin sa da turaruka masu ķ'àmshi yafito ya wuce dining dan yanda yake jin cikin sa na kukan yunwa rabon sa da abinci tun safe ,"
Yayi matukar mamaki ganin babu ko tasa ďaya akan dining ďin yana surutai shi ďaya yace to ita kuma wannan mai yahana ta dafa abinci," dawowa yayi ya zauna kan ďaya daga cikin kujerun parlon ,"
Mtsee yaja wani dogon tsaki," ya tashi yayi hanyar ďakin ta ransa a bàce,"
kwance take kan lutsetsen gadon ta tana sharar bacci harda minshari cikin kwanciyar hankali ko kayan jikin ta bata cire ba sai gyalen ta da jakar ta da takalmi wanda ta watsar dasu a filin ďakin," kallo ďaya zaka mata kasan cewa ba qaramin gajiya ta kwaso ba,"
Turo ķofar ďakin yayi ya shigo yana qiran sunan ta ," Maraqishiya, Maraqishiya," shiru yaji ko motsi batayi ba,"" ganin yanda ta watsar da kayoyakin ta a filin ďakin ya tabbata masa bata yini a gida ba,"
Qarasawa gaban gadon yayi, yaga yanda take sharar bacci saikace jaka," dogon tsaki yaja kafin ya juya yabar ďakin yana bambami," kitchen ya shige ya haďo Tea madara da milo, ya dawo parlou ya zauna yafara sha ,"
Ran sa inyayi dubu ya bàci," ya dafe kan sa yace mutum yanada mata Amma goro ma yafishi jin daďi da kwanciyar hankali, inbanda iskanci saida na sanar mata zan dawo yau da daddare ta haďa min abinci da yake ta rainani ko ruwa bata ajiye min ba bare abinci saima sharar bacci da ta kwanta yi," zaki gamu dani tunda kin nuna min ban isa dake ba," cikin bàcin rai yake maganar ji yake kamar yaje ya tasheta ya mata faďa Amma babu amfanin yin hakan, gashi baison fita waje yaci abinci, haka ya haqura,"
ďakin sa ya tashi ya shiga bayan ya kammala da shan Tea ďin, gado ya hau ya kwanta rigingine fuskar sa na kallon saman silin ya rufe idon sa,"
Har wajan misalin karfe 12 idon sa yana nan lumshe kamar mai yin bacci,"
wayar sa ce tasoma ringing, ya buďe idon sa tare da miqa hannu gefen gadon ya ďauka ya duba mai qiran sa, sabon number yagani da alama bata nigeria bace," kallon number yayi da kyau kafin ya ansa yakai wayar kunnen sa,"
Assalama alaikum yaji tafaďa cikin sanyin muryan ta mai daďin sauraro,"
Wa'alaikumussalam ya amsa mata cikin murya qasa qasa tare da gyara kwanciya fuskar sa ďauke da murmushin jin daďin neman sa da tayi,"
Jin yayi shiru baice komi ba yasa tayi gyaran murya tace Humaira ce ke magana, dama naqira dan in cika alqawarin dana ďauka ne,"
Murmushi ya kuma yi tare da shafo sajen fuskar sa, yace nagane ki ai ba Humaira yar rigima ba?",
Fuska ta kwabè tace, yauwa ďan ayi zaka fara ko?
A a malama nifa babu abinda nace dan nace yar rigima ai gaskiya nafaďa, cikin zolaya yake mata maganar,kamar suna waje ďaya,"
To ai sai kayi kai ďaya saida safe tunda kai baka hutu da neman faďa cikin dare,"
Dariya ne ya ķubùce masa jin da gasken ta tayi maganar,," yace,
Haba mana madam yi haquri bazan kuma ba ai yanzu mun daina faďa ko?,"
Him nidai saida safe tunda na cika alqawari,"
To shikenan naji ya kike kun sauka lfy?
Lfy lau tafaďa a takaice,"
To yayi barka tunda kun isa lfy,"
Shiru tayi masa bata kuma cewa komi ba,"
Haba mana sarauniya dan nace yar rigima shine kikabi kika kame fuska ko magana ma anqi aiyi min gashi inada muhimmin abu da zan faďa miki banda hakama ai nabada haquri ko?," kamar mai neman agaji taji yayi maganar, hakan yaso bata dariya Amman takame tace,"
Him kafaďa to bacci nakeji ko kabari, gobe mayi waya dare yayi saida safe,"
Kekam badamuwa tunda bacci kikeji kibini bashi gobe zan sanar miki, saida safe,"
Allah ya kaimu lfy tafaďa tare da kashe wayar ta ajiye shi gefen gadon ta ta gyara kwanciyar ta tare da rufe jikin ta da bargo har kanta idon ta ta rufe dan yin bacci tana tunanin maganar da yace zai sanar mata gobe Allah yasa taji mai daďi tace a zuciyan ta tana murmushi,"
To malama a dai yi ahankali kar a faďa rijiya garin zumudi, taji muryan Amena wacce ke sauraron su tun ďazu da yake ďaki ďaya suke ga gadon ta gana Amena,"
Bargon fuskan ta tayaye tayi mata kallon tuhuma,
"Tace bangane maganar ki ba mai kike nufi da hakan?
bana nufin komi uwar bala'i kafin ki sauķe a kaina banci ba ban shaba,
share ta tayi ta rufe idon ta da niyar bacci ji take batason wani magana a yanzu,""
Tana zancan zuci bacci ya kwashe ta bata saniba,"
Yana nan kwance yana shirya maganganun da zai gaya mata gobe na sirrin zuciyar shi, ji yake yazama dole ya sanar da mahaifin Shi yanaso ya qara aure,'
Saida ya tabbatar yagama shirya saqon da zai tura mata gobe dan yanaga haka zaifi, masa sauki, kafin bacci ya kwashe sa zuciyar sa fal tunani iri iri na yanda zata karbì batun sa..
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:06] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR* *AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT_M_S* ✍🏻
🌺🌸🌺🌸🌺 *ABADAN* 🌸 *ABADAN* 🌺 *ABADAN* 🌸🌺🌸🌺🌺🌺 *SAFIYYA* *MUSA* *ABDULLAH* *HUGUMA* 🌺🌺🌺🌸🌺🌸 *QAWATA AMINIYATA* *TA* *KWARAI* 🌺🌸🌺🌺🌸 *BARI* *NAYI* *AMFANI* *DA* *WANNAN* *DAMAR* *WAJAN* *JINJINA* *MIKI* *KAN* *KAMMALA* *LITTAFIN* *ABADAN* *DA* *KIKAYI* 🌺🌺🌸🌺🌺🌺 *ALLAHU* *YA* *SANYA* *ALKHAIRI* 🌺🌺🌸🌺 *HAKIKA* *KIN* *KOYAR* *DAMU* *DARASI* *MASU* *YAWAN* *GASKE* *MUNA* *ALFAHARI* *DAKE* *DA* *KIKA* *KASANCE* *HAKA* *AGAREMU CIKIN YANAR GIZO ALLAH YABAR MU TARE CIKIN AMINCIN DA KAUNAR JUNA* 🌸🌺🌸🌺 *GA* *KAĎAN* *CIKIN* *TAYAKI* *MURNA* *SAURAN* *SAI* *MUNYI* *WAYA🌺🌸🌺 HAFSAT MAI SHERIFF ĎINKI KE MIKI FATANALKHAIRI*😘😘😘😘
*11~12*
~~~Qiran sallah asuban fari ya buďe ido yayi miqa tare da salati a bakin sa,"
addu'ar tashi daga bacci yayi kafin ya tashi ya shiga toilet ya ďauro alwala yafice yayi bàngaren ta,"
ķofar ďakin ta ya tura ya shiga dan ya tashe ta sallah,"
Yaqarasa ciki ya tsaya a kanta, yana mamakin ganin har yanzu bacci take mai nauyin gaske, anata qiraye qirayen sallah, Amman ko ji batayi ba bare tayi azaman tashi,"
Tashin ta ya soma yi yana qiran sunan ta, dan yasan in yabari ta tashi da kanta zata makara ,"
Kamar a mafarki taji muryan sa yana qiran sunan ta, hakan yasa tayi juyi ta amsa masa da himm, tana qara gyara kwanciya,"
Tashi kiyi sallah yace da ita atakaice, ya juya yabar ďakin,"
Masallaci,ya wuce akayi sallah dash yana nan zaune yana tasbihi bayan an idar ,"
Saida garin yayi haske kafin ya dawo gida,"
Ďakin ta yaqara shiga dan ganin tayi sallar koyaya,"
Har yanzu tana nan kwance yanda yabar ta da alama ko motsi batayi ba bayan ya tashe ta, ransa a bàce haka ya daure zuciyar sa yaqara tashin ta,"
Miqa tayi sosai tana hamma kamar mayya ta buďe qananan idanuwan ta tana mirqisasu suka sauķa a nashi,"
wani irin kallo yayi mata na bàcin rai kafin ya juya yabar ďakin,"
Idanuwan ta takai kan a gogon dake manne a bangon ďakin karfe bakwai saura tagani, bashiri ta gwale ido tare da miqewa tana salati ganin ko sallah batayi ba har fitowar rana,"
saida tayi alwala tare da yin brosh tafito ta gabatar da sallah,"
tana idawa tafice a ďakin kai tsaye hanyar ďakin sa tayi,"
cikin sanďa tabuďe ķofar ta shiga a hankali kamar marar gaskiya,"
can ta hango sa a tsaye gaban madubi yana gyara sumar kansa da alama yanzu fitowar sa a wanka,"
daurewa tayi ta qarasa inda yake ta rungume shi ta baya tana faďin barka da safiya mijina abin alfaharina katashi lfy?
Banza yayi da ita kamar baiji ta ba yaci gaba da taje sumar sa, hakan yasa ta ďago da kanta ta zagayo dashi ta gaban fuskar sa tare da sakin murmushi tace,"
Haba mana dear kayi haquri nasan nayi lefi Amman wlh na ďau kafasa zuwan ne shiyasa nayi kwanciya ta gashi nagaji sosai, am sorry pls dear, kabar wannan fushin, kaji? karya wuya tayi irin namasu neman agaji,"
Shiru yayi baice da ita komi ba ya ajiye com ďin dake hannun sa yabar gaban madubin,"
kayan sa yasaka shadda ruwan madara mai zubin farin zare, ya ďauki hukar sa kalan shaddar yasaka yadawo gaban gado ya zauna yana gyara a gogon hannun sa,"
Tana nan tsaye inda yabar ta, tana neman kalmar da zata karbì kanta, dan yanda taga ya bàta rai duk haqurin da tabashi yaqi kulata,"
karfin hali tayi taqarasa inda yake ta kai gwaiwar ta qasa tare da faďin,"
Baby nabaka haquri fa pls mana am sorry bazan sake ba,"
Ajiyan zuciya ya sauķe ya ďago kansa ya kalle ta da kyau kafin yafara magana yace,"
Maraqishiya, ya qira sunan ta yana duban ta," Na am ta amsa masa idon ta na kallon nashi, yace,"
Meyasa kikeso ki koyi halin da ba naki ba?" meyasa kikeson canzawa daga yanda kike?,"" jiya da zan shigo saida nasanar miki dan kiyi abunda yadace Amman da yake kin nuna min ina mijinki ban isa dake ba kika ďauki ķafa kikabar gidan, banda hakama da kika gama yawon kika dawo dafa abincin ma shima ya gagareki saima sharar baccin da kika zube kinayi nufin ki inna dawo kaina zanci ko meye ?,"
Shiru tayi tanajin sa batace komai ba,
dake nake magana kin min shiru kuma waya baki izinin fita baki sanar dani ba?,"
Hannun sa ta kamo ta haďa da nata, cikin qasa qasa da murya tace yi haquri dear ai bazan zake ba kuma sanda ka min waya ma wlh bana gida dana dawo kuma a gajiye nake naga dare yayi bakya dawo ba shine nace hala fasawa kayi shiyasa banyi komi ba,"
Hannun sa ya cire a nata ya tashi tsaye yana gyara hular kansa ya zari wayoyin sa kafin yace kin kyauta ai ni bani waje na wuce sai nadawo inyaso ki ďau ķafa kifita kema tunda yawo kikasa gaba," yana gama fadin haka yayi ficewar sa yabar ta nan zaune,"
ajiyan zuciya ta sauķe ta tashi tsaye tafara gyaran ďakin sama sama kafin ta fice tayi ďakin ta,"
Yana fita motar sa ya nufa ya buďe ya shiga tare da bismillah kafin ya tashar da motar mai gadi ya buďe masa get ya fita,"
kai tsaye gidan su ya wuce bai wani jima a kan hanya ba ya iso ya danna hoon aka buďe masa ya shiga yasamu pakin space yayi pakin motar ya fito ya kulle ya nufi cikin gidan bayan sun gaisa da baba mai gadi,"
Bàngaran mahaifin yafara shiga ya buďe ķofar parlon tare da yin sallama,"" wani dattijon mutum ne kishingiďe a filin parloun yayi matashi da pllow ya ďaugo da kai tare da amsa masa sallaman," wanda kallo daya zaka masa ka hango tsantsan kamanni shida Abdulmalik,"
Qaraso mana babana ya ka tsaya kuma dattijon yace dashi cikin sakin fuska,""" qarasowa ciki yayi ya zauna a gaban sa kansa a qasa yace,"
ina kwana Abba?
Lfy lau babana ashe ka dawo ?
Eh jiya shigowa na gari yace da Abban har yanzu kansa na qasa
To madalla ya yakabaro aikin naka da kuma iyalin naka lfy dai ko?
Lfy lau yabashi amsa kafin yace Abba bari nashiga na gaishe da umma zan wuce office yanzu,""" To babana a dawo lfy,
Allah yasa yafaďa ya fice a parloun Abban yayi bàngaren mahaifiyar sa,"
karo yaci da ita hannun ta riqe da kular abinci da alama daga kitchen ta fito,""" rusunawa yayi qasa yace barka da safiya umma nasameku lfy,"
Yauwa barka Abdul kadawo kenan?
Eh jiya na dawo ya bata amsa bayan ya ďaugo daga rusunawar, yace umma yunwa ina fatan akwai abinci,"
Yauwa ďan nasaba shegiyar matar taka haka tabarka kafito da yunwa abincin ma kasa dafa maka tayi hala ma ko farkawa batayi? ,"
A a umma sauri nake zan fita shiyasa ban tsaya naci a gida ba,
Haka ai zakace tunda ta mallake ka baka ganin lefin ta in ance ka kara aure sai kaga kai takura ka za'ayi ga matar kirki na baka Amman kaqi amsa, sai kaje kayi ta zama hakanan mace tana maka iskancin ranta har zuwa randa zata shanye ka kahuta,"
Haba umma ya kike faďin hakane bazama ta shanye niba, nidai yanzu kibar wannan maganar idan na koshi naje office nadawo ma qarasa,"
Wani irin kallo tayi masa tace dawa zaka qarasa? in kayi min tsiya sai in hanaka abinci inga yanda zakayi marar zuciya kawai, tana gama faďin haka tayi wucewar ta tabar shi nan tsaye yana mamakin umman tashi kodan in da sabo ma yaci ace yasaba da korafin ta,"
ajiyan zuciya ya sauķe yabi bayan ta, zuwa parlon Abba nan ya zauna sukayi karin kumullon,"
saida ya tabbatar da cikin sa ya koshi ya haďa Tea ya kora akai kafin ya tashi yana gyaran shaddar jikin sa, yace,"
To Abba ni zan wuce sai nashigo anjima,"" adawo lfy Abba yace dashi yana kaiwan tea bakin sa,"
umma na wuce, to tace dashi a takaice, tanaci gaba da cin abincin ta,"
saida ya biya gefen Inna mahaifiyar Abba ya gashe cikin girmamawa, Amsa masa tayi cikin sakin fuska tace A a maleeku yaushe yadawo?," jiya yabata amsa yana shirin fita yace kinga inna nifa wlh kibar lalata min suna dan ba shiryawa zamuyi ba,
Ja'irin kawai yaji tace baza' a bar lalata sunan ba,"
Sai kiyi kuma ai,"
ga abinci fa an kammala bazakaci ba kafin ka wuce naga kamar sauri kake,
karki samu damuwa yanzu naci agun Abba kawai ki ajiye min na anjima in na tashi a office zan wuco nan inci kafin naje gida, kinsan ba iya barin abincin zanyi ba, yar tsohuwa ta yace da ita yana mata dariya,"
To shikenan ba matsala sai kadawo ďin tace dashi cikin sakin fuska tanajin kaunar ďan jikanta a ranta,"
Amin ya amsa mata yace, ya yau gidan naku shiru ina yan matan suke?," ka mance yau akwai karatu shiyasa gidan yayi daďi ai,
Kai inna bakida dama wl nidai natafi sai anjima ,dariya tayi tace adawo lfy,"
Yana fita a gidan bai wuce ko ina ba sai gun aikin sa," cikin minti ishirin ya isa ya danna hoon aka aka buďe masa get ya shiga yayi parkin cikin sauri ya nufi office ďin bayan ya kulle motar nasa,"
**
yana nan zaune kan kujera bayan yagama da aikin gaban sa hannun sa riqe da waya yana latsawa hankalin sa kaf yana kan abinda yakeyi,"
Saida ya shafe kusan rabin lokaci yana tsara maganganun da zai faďa mata na sirrin zuciyar sa,' kafin ya tura mata yana fatan Allah yasa ta karbì batun sa karta guje shi dan a yanzu ya riga da yagama tabbatar wa da irin sonda yake mata,"
🌾🍃🌾🍃🌾🍃🌾
Agajiye ta shigo cikin ďakin bayan sun tashi a makaranta," kai tsaye toilet ta wuce tayi wanka tare da ďauro alwalar la'asar dan har an fito a masallaci, godon kaya ta zura ta feshe jikin ta da turaruka kafin ta tashar da sallah bayan ta saka dogon hijabin ta,"
Tana idarwa ciro wayar ta bayan tashafa addu'oin ta," tashiga duba saqon da taji ya shigo mata,"
zuciyar tane yafara bugawa yana dukan uku uku kamar a mafarki takeji murza idanuwan ta tayi da kyau taqara kallon saqon a karo na biyu tana zarkin anya ba idon ta bane ke mata gizo cikin mamaki da fargaba tafara karantawa tana murmushin farin cikin,"
Turo ķofar ďakin Amena tayi tashigo tare da sallama, ta qaraso inda Humairan take," ganin batasan ma ta shigo ba yasa ta ďan bigi kanta kaďan tana faďin,"
Ke kuwa lfy kike ta wani abu kamar tabàbbìya?"""", tsalle humaira tayi tare da rungume Amena tana dariyar farin ciki tace,"
Waiyyo Allah qawata ki tayani murna tarko na yakama tsuntsu,"
cikin rashin fahimta Amena tace kinga malama tsaya ki nitsu ki min bayani dallah dallah kin sakani a duhu,"
Him tace da ita har yanzu fuskar ta ďauke da murmushin jin daďi ai bazaki gane ba gashi ki gani da idon ki, ta miqa mata wayar tana zagaye cikin ďakin dan murna,"
amsan wayar tayi tafara karantawa tare da sakin baki anya kuwa da gaske mutumin nan yake kwata kwata yaushe yafara ganin ta,'
qawata ya kikagani taji muryan humaira wacce har yanzu dariya take,"""" him Amena tace da ita kin tabbatar da zancan sa ?
zama tayi a bakin gado kafin tace Eh to kinsan komai daga Allah ne nidai Allah ya kalli zuciya ta wlh na kamu da son shi kuma so na haqiqa nake masa Amman meye ribar sa idan yaudara ta zaiyi ?"
hakane fatan mu Allah ya sanya alkhairi ya tabbatar da soyayyar ku cikin aminci,
Amin qawata nagode humaira tace tare da kwanciya tana tsara amsar da zata bashi,"
tana gama rubuta amsar ta nunawa Amena tare da tambayar ta ko yayi? ,"" jinjina kai tayi tace yayi tura masa,"
Tura masa tayi zuciyar fal tsantsan farin ciki, da tunani iri iri,"
Fitowar sa daga office kenan zai shiga motar sa dan komawa gida da yake tuni ya kammala da aikin gaban sa,
qaran shigan tes wayar shi yaji yakan yasa ya buďe ķofar motar ya shiga kafin ya ciro wayar a haljihun sa yashiga duba saqon,"
Wani tsantsan farin ciki ne ya ziyarci zuciyar sa ganin amsar da tabashi kan bukatar sa yana murmushin jin daďi ya danna number ta ya qira,"' saida ya kusa tsinkewa kafin ta ďauka tare da yin sallama cikin sanyayyar murya,"
Amsa mata yayi tare da faďin Amarya bakya lefi ko kin kashe ďan masu gida,"
Dariya ne ya kubuce mata tace tofa abun ma haka ya koma?
Hakane mana tunda dai kin amshi soyayya ta yanzu kinga ina tashi wajan Abba zan wuce nayi masa maganar auran mu,"
Murmushi tayi tace wa yace maka na aminci da soyayyar ka? kaga nifa bance zan aureka ba dan haka gwara ka kamayar da murnan ka ciki?
Himm haka kikace Amarya to waya rubuta amsar? ya tambaye ta kamar suna waje ďaya ,"
Bansan wanda yayi ba ta bashi amsa,a takaice,"
To naji zan kamaki ne bari in nakoma gida zan qiraki yace da ita yana shirin kashe wayar,""" ok sai anjima tafaďa tare da kashe wayar ta ďaura shi kan ķirjin ta tanajin wani irin son shi na daďa shiga ruhin ta,"
*********
Tun daga wannan lokacin soyayya ce mai karfin gaske ta ķullu tsakanin su kullum suna makale da waya a kunne tun Amena nayi mata mita har tagaji ta barta da kanta,""" Yau saura musu wata ďaya su dawo Nigeria kullum Humaira Allah Allah take taga sun koma gida dan tana muradin ganin masoyin ta,"
lokacin da tasanar dashi sun kusa dawowa yayi matukar murna ba kaďan ba bai bàta lokaci ba yace da ita zai sanar da Abban shi kan maganar auran su,""" tsantsan farin cikin ta bai misaltuwa da jin maganar da yafaďa,"
haka sukaci gaba da soyayyar su cikin tsari da kamala,"
**
Yau yana tashi gun aiki bai wuce ko ina ba kai tsaye gidan su ya nufa ya wuce bàngaran Abban shi, zaune ya sameshi yana kallon TV tashan labare,"
Cikin girmamawa ya rusuna ya gaishe dashi, fuskan sa a sake Abba ya amsa yace babana ya akayi naga kamar a kwai magana a bakin ka, kansa ya ďan sosa yafara kame kame kamar baida gaskiya,
Abba yace lfy kake kuwa faďa min mana meke tafe da kai?
Dama Abba.. sai kuma yayi shiru zuciyar sa fal tunanin yanda Abban zan karbì maganar,""" dama meye kayi magana mana Abba yace dashi yana duban sa,"
Abba dama aure nakeso naqara shine nace bari na sanar maka, kansa a qasa har yanzu, bai ďago ba yake maganar,
Kamar daga sama sukaji muryan umma tana nufowa inda suke tace Auran gidan uban ka zaka qara ?...
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:06] Ameena Group Aysha Kn: *🥀🥀🥀RAYUWAR AURENA🥀🥀🥀*
*NA*
*HAFSAT M* ✍🏻
*page*
*13*
*ASSALAMA ALAIKUM Yaku yan uwa musulmai bari nayi amfani da wannan damar wajan tunatar daku falala mai girma ta salatin Annabi (saw) Watarana mala'iku guda huďu sukazo wajan manzon Allah (saw), mala'ika JIBIRILU yacewa Annabi duk wanda yayi maka salati goma 10 to ni zan kama hannun sa na ketare dashi akan siraďi ranar tashin Alķiyama,mala'ika MIKA'ILU yace ni kuma zan shayar dashi ruwan Alkausar, mala'ika ISRA'FILU yace ni kuma zanyi sujjada gaban Alllah bazan tasoba har sai Allah yagafarta masa mala'ika AZARA'ILU yace ni kuma zan zare masa ransa cikin sauki kamar yanda nake zare na Annabawa ,Allahu Akbar Allahu Akbar Allahu Akbar ya Allah ka ķarawa Annabi daraja da ďaukaka da matsayi a ranar tashin Alķiyama Allahumma salli wasallim ala khatimil Anbiya'i wa imamul mursalina.*🙏🏿🙏🏿🙏🏿
Zuciyar sane yafara dukan uku uku dama kamar yasan za'ayi haka,"
Nace auran gidan uban ka zaka qara? Umma taqara maimaitawa bayan ta iso inda suke,"""
shiru yayi ya rasa amsar daa zai bata,"
badakai nake magana ka min shiru,"
Kansa ya ďago ya kalle ta yace haba Umma kefa kike cewa in qara aure kullum bakida wata magana sai na in qara aure yanzu kuma nace zanyi auran kuma kinaso ki nuna bakisan da zancan ba,"
kallon banza tayi mishi tace Eh nasan nice mai ce maka ka qara aure Amman yanzu na fasa, tunda ba wacce nakeso zaka aura ba,
Abba ne yayi gyaran murya yace ke bara'atu wannan wani irin sakarci kikeson nunawa?,"" dole ne sai ya auri wanda kikeso?," ko kece zaki zauna masa da ita?"" to buďe kunnen ki ki saurareni tun wuri kibar yaron nan ya auri wacce yakeso tunda ba'a kanki zasu zauna ba, kinji nagaya miki,"
Haba alhaji ya zakace haka indai wacce yakeso ne ai nabar shi ya aura, in banda walaqanci irin nashi ga mace kamila tana son shi Amman ya tsaya yana ruwan ķafa akan wasu yan iska,"
Idan ma rashin karatu ne ai gashi tanayi yanzu," to nidai harga Allah bazan laminta wannan karon ma ya watsa min qasa a ido ba, ko ya auri suwaiba ko kuma na hanashi auran wata, nayi haquri a wancan lokacin Amman yanzu haquri na ya qare dole ne ya auri suwaiba ko afasa auran gaba ďaya,"""tana gama faďin haka ta juyar da kanta gefe tana girgiza ķafa ďaya alaman ranta yabàci,"
Abba yace to shikenan bara'au kiyita jayayya dani, yayi miki kyau," kafin ya juya gun Abdulmalik yace babana faďa min yar gidan wanene kuma daga ina take,"
Ajiyan zuciya ya sauķe tare da kai kanshi qasa yace Abba sunan ta Aisha humaira mahaifin ta alhaji Ali girema ďan siyasa ne a maiduguri Amman dai abuja suke zama,"
Umma ta jiyo da kai tace Amman Abdulmalik bakada hankali, yanzu ace duk yan matan nan da suke cikin faďin garin katsina karasa wacce idon ka zai kalla yaso sai yar maiduguri?",
Hannu ta ďaga ta nuna shi da yatsa tace to bari kaji wlh wlh kaji dai na rantse maka auran yar maiduguri ba'a cikin dangin nan ba, kuma bazanyi kaffara ba," tana kaiwa nan ta kabè zanin ta tabar parlon tana bambami ita ďaya har ta isa bàngaran ta,"
Nauyayyan numfashi Abba sauķe yana mamakin masifa irin nata," dakewa yayi yace da Abdulmalik, babana karka samu damuwa akan maganganun mahaifiyar ka barni da ita, insha Allahu da kaina zan tafi abuja na nema maka auran ta in har na yaba da halin ta, tashi katafi abunka,"
Tashi yayi jikin sa babu ķwari yana ma Abban nashi godiya yabar parloun, yau kam ko ďakin inna bai leqa ba dan ji yake gaba ďaya maganganu umma ta ruďashi, meyasa takeso tayi mishi wannan hukuncin tana nufin kenan har mata uku zaiyi, kai inaa da sake daga humaira sai humaira babu wani mahaluķin da zai mallake min gurbin ta a zuciya na, haka yaci gaba da surutan sa shi ďaya har ya fice a gidan zuciyar sa tunkushe da abubuwa iri iri,"
koda ya isa gida ďakin sa ya wuce yayi wanka tare da ďauro alwalar magariba ya wuce masallaci,"
Saida yajira akayi sallan isha kafin ya dawo bayan yayi addu'oi sosai kan lamarin umma,""" ďakin sa yaqara komawa tare da hawa kan gado ya zaro wayar sa ya danna qiran abar kaunar sa ko zai samu sassauci cikin zuciyar sa,"
Yana fara ringing ta ďauka da yake wayar tana kusa da ita, cikin muryan ta mai sanyi tayi masa sallama ya amsa mata cikin kasala, tunda taji muryan sa tasan akwai abinda ke damunsa bata bàta lokaci ba ta shiga tambayar sa meke faru?," shiru yayi yace da ita babu komi, ganin ba gaya mata zaiyi ba hakan yasa tayi dabaran faranta masa rai da kalamai masu ratsa zuciya har ta mantar dashi damuwar dake ransa saida ta tabbatar zuciyar sa yayi fayau kafin sukayi sallama kowa ya kwanta cikin kaunar juna,"
Ana cikin haka Abba ya samu ďan uwansa malam kabeer da mahaifiyar sa inna ya sanar dasu abinda ke tafiya suka goyi bayan maganar tunda yaro yana so ai sai abarshi ya aura cewar malam kabeer, Umma tanajin haka ta hau kanshi da habaici tana gaggaya masa magana masu ďaci ai dama da hannun ka aciki inbanda shishshigi ina ruwanka da wannan maganar tunda dai yaro bana ka bane ni na haife shi, a cikina," shidai malam kabeer baice da ita komai ba dan inda sabone yaci ace ya saba da halin ta dan bayau ta soma ba,""
bayan kwana biyu Abba ya shirya da kansa shida ďan uwan sa malam kabeer da Abdulmalik shine jagoran su suka kama hanyar abuja,""
Basu suka isa ba sai wuraren karfe huďu da yake fitan safe sukayi lokacin ko wanne masallaci an fito daga sallan la'asar,""" Har ķofar gidan Abdulmalik ya kaisu kafin ya danna hoon mai gadi ya leqo yaga ko suwaye ne, cikin girmamawa ya iso gun motar nasu yafara tambayan su daga ina suke bayan sun gaisa,"" Abdulmalik ne ya tambaye shi ko mai gidan yana nan' eh bashi amsa, yace kaje kace mishi yayi baķi daga ķatsina,"
To yace dashi tare da komawa cikin gidan,""" Yana shiga ya rusuna har qasa ya gaishe da mai gidan nasa kafin ya nasar dashi baķin da yayi,
Cikin mamaki Abba yace a shigo dasu parlon tarar baķi , gashi nan zuwa,"""
fita mai gadin yayi a parloun yaje ya buďe musu get kafin yayi musu jagora zuwa inda ake taran baķin,
Abba yana tashi yaje yasamu Mumy ya nasar da ita baķin da sukayi daga ķatsina yace ta haďa musu abinci da abun mosa baki, kafin ya wuce inda baķin suke",
Cikin girmamawa Abba ya isa parlon fuskar sa ďauke da murmushi ganin abokin shi Alhaji Sulaman ne yau a gidan shi,
Ba qaramin mamaki bane ya bayyan fuskan Abban Abdulmalik yana riqe da baki yace ďan uwa ashe rai kanga rai?," cikin farin ciki suka rungume juna, Abba ya ďago yace haba Alhaji Sulaman haka ake rayuwa yau rabona da kai kusan shekara nawa,'
Dariya alhaji Sulaiman yayi yace yanzu dai ba wannan ba zauna mu gaisa magana mai mahimmanci ne ke tafe damu,"
Babu musu ya zauna yace Allah yasa alkhairi ne suka fara gaisuwar yaushe gamo,
Abdulmalik kam danqarewa yayi inda yake yana ganin ikon Allah kenan dama sunsan junane ko meye? yake tambayar kansa, rasa mai bashi amsa yayi ya dago da kansa tare da gaishe da Abba cikin girmamawa,""" fuska a sake ya amsa masa yana tambayar sa sun dawo lfy,"
Lfy kalau ya amsa masa kansa a qasa yana wasa da ďan ya tsunsa,"
Mummy ce ta shigo parlon hannun ta riqe da abun mosa baki ta ajiye a gaban su kafin ta shiga gaisawa dasu,"
Saida ta kawo musu kayan abinci kala kala Abba yasa su sukaci sosai bayan sunyi sallan la'asar kafin, alhaji Sulaiman ya sanar dashi abunda ke tafe dasu kan yar wajan shi Humaira ,da ďan wajan sa,
Farin ciki sosai Abba ya shiga yace Ai babu matsala tunda suna son junan su banda hakama Ai Abdulmalik ďa ne a gareni na yaba dashi nasan bazai cutar da ķanwar sa ba," kaga sai ayi tuwo na mai na wannan ba qaramin dankon zuminci zai qara mana ba,
Alhaji Sulaman yaji daďi sosai yace saidai wani hanzari ba gudu ba yanada mata haifuwa ne dai Allah bai basu ba,
Lahh meye abun damuwa Idan kishiya ce ai kai mijin mata huďu ne fatan mu dai Allah yabasu zaman lfy Abba yafaďa cikin sakin fuska,"
Cikin jin kunya Abdulmalik ya shiga ma Abba godiya kansa a qasa, zuciyar fal murna"
Abba yace karka damu ai kai ďan gida Humaira ķanwa ce a gareka yau idan bama raye na tabbata kana tare da ita," dan haka tun yanzu kasa a zuciyar ka nabaka Humaira a matsayin matar aure har abada ku zauna cikin Amana da kaunar juna
Godiya sosai alhaji Sulaiman yayi yana mai farin cikin karramawar da suka samu gun sa,"
Basu sukabar gidan ba sai bayan magariba bayan sun gama maganar komai idan ya rinya ta dawo za'a yanka rana abada sadaki," Abba yayi yayi dasu su kwana tunda a kwai a waje Amman sukaqi kan cewa zasu kama hotel gobe zasu koma bai kamata su duka ace su zube mishi a gida ba,"
ganin sunqi kwana haka ya haqura ya musu rakiya har get kafin ya dawo cikin gida yasamu Mumy ya sanar mata abinda ke tafe dasu,""
Bataqi ba tunda ya rinya tanaso ai shikenan Allah ya sanya alkhairi tafaďa, tana jimamin yanda yarta mace ďaya tilo zatayi RAYUWAR AUREN ta da kishiya,"
Ji yake zuciyar sa fayau yana ta godiyar Allah suna isa hotel bai tsaya yin komai ba bayan sun kama ďakin kwana kowa ďaďďaya," ya zari waya ya qira ta ya sanar da ita duk abunda yafaru yau da yake dama yafaďa mata yau zasu shigo abuja shida magabatan sa gun Abban ta batun auran su,'"
Tayi matukar mamaki jin wai Abban ta da Abban shi sun san juna," ranar kwanan farin ciki sukayi jin daďi fal zuciyar ko wannan su,"
Tun daga wannan lokacin Abdulmalik yaketa faman damun ta yaushe zata dawo shifa gaba ďaya ya masu yaga anyi wannan auran",
Dan Allah kuyi haquri da wannan 🙏🏿🙏🏿
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:06] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M✍🏻
*page*
*14*
*YA YAN UWA NA MUSULMAI GAWATA YAR GARABÀSA KAĎAN, Watarana manzon Allah (SAW)yafita zagaya gari shida sayyidina Abubabar (R.A), sukazo wucewa kusada wata rijiya sai Annabi (SAW)yacema sayyidina Abubakar "ďauki dutse ďaya kajefa acikin wannan rijiyar" Haka kuwa akayi yaďauuki dutse karami yajefa acikin rijiyar, sai manzon(SAW),yace mutafi sukatafi abunsu sai ranarda dutsen yacika shekara ďaya da jefawa Annabi (SAW),yasake ďaukar sa suka tafi wajan wannan rijiyar bayan sun isa sai sayyidina Abubakar yaji karar faďawar abu acikin rijiyar sai Annabi (SAW) ,yacemaAbubakar kokasan menene yafaďa sai Abubakar yace a'a. sai Annabi (SAW),yace dutsen daka jefa wancan lokacin damu kazo yau shekara ďaya kenan sai yanzu yakai ķarshen rijiyan,kuma wlh babu wanda zaishiga aljannah har sai ladarsa tacika wannan rijiyar, Hankalin Abubakar yayi matukar tashi yazo yasami sauran sahabbai azaune yace mekukeyi azaune ai wlh zama bai samemuba sai yagaya musu yanda Annabi yace Suma hankalin su yatashi sukaje suka tunkari Annabi (SAW) sukace Ya RASULILLAH mukam a ina zamu iya aikin dazai cika wannan rijiyar?Sai Annabi (SAW)"yace ku kwantar da hankalin ku akwai aiki ďaya wanda idan ďayanku ya aika tashi to zai samu lada wacce tafi wannan rijiyar yawa, Annabi (SAW) yace idan ďayan ku ya furta kalmar LAILAHA ILLALLAH a asirce kuma yana mai kaskantarda kansa zuwa ga Allah zai bashi lada wacce taninka zurfin wannan rijiyar sau uku.Yan uwa kuji falalar dake cikin wannan kalmar Ya Allah kabamu ikon faďar wannan kalmar TA LAILAHA ILLALLAH 🙏🏿🙏🏿🙏🏿*
Zaune take a gaban madubin ďakin su tana shafa mai a jikin ta da alama fitowar ta a wanka, doguwar riga ta atamface a jikin ta, sama sama tayi kwalliya bayan tagama shafa man ta mai ķàmshi, tafara feshe jikin ta da turaruka,"
Ganin batada niyar gamawa, gashi lokaci na wucewa yasa Amena ta tashi tsaye taje inda take tace,"
Kinga malama wlh banason walaqanci idan fa bazakije ba zanyi tafiya ta, nagaji tun ďazu nagama shiri nake zaman jiran ki Amman kin tsaya kina kwalliya kamar ance miki wajan gatsar kyau zamuje, indai fa bakida abun siya kifaďa min zanyi tafiya tace da ita tana kakkame fuska dan tagaji da jiran ta,"
Tashi tayi a gaban madubin ta zari mayafin ta kalan atamfar jikin ta da jakar yar qarama, ta juya tace to uwar korafi sai kizo mutafi ai ko?,""
banza tayi mata bace komai ba suka jera suka fita,"" shopping mould dake kusa dasu suka taka suka shiga kowa yafara ďaukan abinda ya kawo shi,""
Tana tsaka da zabàn kaya ta iso gun agoguna masu masifar kyau da tsada, harta wuce sai kuma ta dawo baya, fuskan ta ďauke da murmushi ta zabì agogo guda ďaya mai kyau kalan baki, kafin ta juya tabar wajan,
Gun Amena ta wuce tace idan kin gama mutafi ba? nagama ta bata amsa sukaje gun biya kowa yabiya nashi suka fito dan komawa hostel,"
Suna tafiya suna taďi Humaira tana bama Amena lbrn yanda komai yatafi cikin sauki tsakanin ta da Abdulmalik," cikin jin daďi Amena ta rungume ta tace kai qawata gaskiya na tayaki murna Allah ya sanya alkhairi, yanzu yaushe ne auran naku musha biki ?," dariya tayi tace kefa kinga matsala ta dake kenan kin cika zumuďi, to ba'a dai saka rana ba Abba yace sai na dawo za'a sa,
Yoo meye ya rage ai da an saka yaune fa komawar tamu nifa wlh duk kin gigitani ji nake kamar ace yaune ma auran Amena tafaďa tana mata dariya,"""harara ta kai mata tace to sannu uwata uwar hanzari yanzu ma zaki iya aurar dani ai, tunda na takura miki,"
Kedai kikasani Amarya gidan Abdulmalik",
Himm kawai tace sukaci gaba da tafiya, Amena dai bata fasa ba sai zolayar take,"
Har sun iso bakin get ďin shiga hostel ďin Humaira taji an warce ledar dake hannun ta hakan yasa ta juya taga ko waye ne mai yi mata wannan ďanyar aikin,"
wani matashin saurayi ta gani ďan kykkyawa ba lefi sanye cikin qana nan kaya gashin kansa yasha gyara irin na yan zamani" , yana yi mata murmushi tare da zuba mata ido yana kallon ta hannun sa riqe da ledar kayan ta daya warce,"
gyara tsayiwar ta mai kyau tayi tana mishi kallon tuhuma, tace malam lfy kuwa meye haka kawai ina tafiya zaka kwace min abun hannu na kamar wanda nayi maka sata,"" murmushi yayi har saida hakoran sa suka fito yace dama bakisan tun ba yauba kika min sata? yanzuma biyo ki nayi na amshi abuna, da kika sace,"
Cikin rashin fahimta tace yaushe ka taba ganina da har zakace nasaci kayan ka? banda hakama meye naka wanda nasata da har zaisa ka tare ni akan hanya kamar kaga yar iska?,"
Zuciya ta kika sace min taji yafaďa a takaice, yace tun lokacin da nafara ganin ki naji kin kwanta min a rai, kuma da gaske nakeson ki ba yaudarar ki zanyi ba, idan zaki amince dani har auran ki zanyi kizama matata,"
Wani irin kallon sama da qasa tayi masa kafin tace kaga malam nifa ba irin yan iskan yan matan nan ne da suke yawo a kan titi kuke taran su kara zube suke baku abinda kukeso bane, idan kana tunanin haka nake to zuciyar ka tayi maka karya," dan haka ina gargaďin ka daga yau kafita harka ta babu ruwanka dani," tana gama faďin haka ta warce ledar ta a hannun sa ta juya tace da Amena mutafi wacce ta sake baki tana ganin ikon Allah, shi ko wannan dame yazo,"
Ransa a bàce yace lallai yarinyar nan ni zaki kalla ki gaya min ďacin magana dan ma kinsamu ance ana sonki, kalle ni dakyau ni ba irin wannan samarin nan bane masu jure walaqancin yan mata, karkice wannan rashin kunyar da kika min kinci bulus, ina nan ina bibiyar ki, kiguji gamuwa ta dake bazai miki daďi ba,""" yana kawai nan ya juya yabar wajan yana aiyya na abunda zaiyi mata duk sanda ta shiga hannun shi, dan bazai qyale ta banza ba yanzun ma sa'a taci akwai idon mutane da shi kaďai yasan rashin mutuncin da zaiyi mata,"
kota kansa batayi ba ta shige cikin hostel ranta a bàce,""
bayan ta Amena tabi ta sameta a zaune a bakin gado, tashiga yi mata gargaďi tace wlh Humaira kiyi hankali da irin samarin nan sam basu da mutunci idan kinyi ma wani ya qyale ki wani ba barin ki zaiyi ba,"""ita dai kala batace ba dan gaba ďaya yagama batashi haushi,"
Kayan shopping ďin da sukayi suka fara jerawa cikin akwati bayan sun gama suka shirya suka nufi airport tun wuri dan jirgin su ya kusa tashi,"
Basu wani jima sosai da zama ba akayi bording bayan sun tura kayan su sunyi duk abunda yakamata suka shiga cikin jirgi,
ba'afi mintina ishirin ba jirgin su ya ďaga,"
********
Bayan kwana biyu da dawowar ta gida tana zaune a ďakin tana hira da masoyin ta yanata mata korafin meyasa bata barshi yazo ya ďauke a airport ba, haquri take bashi tace bataso ta wahalar dashi ne shiyasa, fuska ya kwabè mata kamar tana kallon shi yace ni nayi fushi ba ruwana dake,"
dariya abun nashi ya bata ganin yana mata shagwaba kamar wani ďan karamin yaro,"" Mummy ce ta turo kofar ďakin ta shigo tace da ita kije Abban ki yana qiranki, to ta bata amsa tare da ce mishi sai anjima ta kashe wayar," tashi tayi ta zari hijabin ta tafita tayi bàngaran Abba, yana zaune ta same shi ta qarasa gaban sa bayan tayi sallama ta zauna kanta a qara tace barka da hutawa Abba,"
Yauwa mama na ya gajiyar hanya?"" lfy tafaďa batare da ta ďago ba,"" Abba yace da farko dai maganar Abdulmalik zanyi miki yazo da magabatan sa kan maganar auran ku, yace kun riga da kun sasanta tsakanin ku," ina fatan dai kin amince kina sonshi? dan bazan so kije inda bakya so ba,"" kai ta ďaga cikin jin kunya alaman Eh tanaso,"
Murmushi Abba yayi tare da sa mata albarka yace kafin ta koma makaranta za'a sa rana ayi auran idan yaso ta qarasa a can gidan mijin ta tunda darajar ýa mace gidan miji gwara ayi yanzu,"" Mummy dai jin su take batace komai ba dan ita tunda taji ance yanada mata hankalin ta yaqi kwanciya,"
Tashi kije yazo yana jiranki a parloun baķi Abba yace da ita,"""
cikin mamaki ta kalli Abba tace yaushe yazo?
tun ďazu shigowar sa Abba yabata amsa, yace tashi kije kar yaga an barshi shi ďaya,"
Tashi tayi sum sum tana mamakin sa a zuciyar ta tace abu yanzu muka gama waya dashi Amman ko yace min yazo," girgiza kai tayi alaman zanyi maganin ka, ta wuce ďakin ta ta qara feshe jikin ta da turare kafin ta wuce parlon baķin,"
Tura ķofar tayi ta shiga tare da yin sallama,"" yana zaune ta hango sa kan ďaya daga cikin kujerun parlon yana magana da alama waya yake, qarasawa tayi ta zauna ďan nesa dashi tana kallon sa ta qasan ido yanda bakin sa ke motsawa wani irin kwarji taga yayi mata fiya dana da, shigar kayan jikin sa ta kalla, sanye yake cikin farar yadi ďinki babbar riga ya sha farar hula a kansa sai ķàmshi yake zubawa, kamar wanda ya tashi daga ďaurin aure,"
Idan kin koshi da kallon nawa sai mu gaisa, taji muryan shi fuskar sa ďauke da murmushi,yana kallon ta,"
Saurin kawar da ķwayar idan ta, tayi tace sannu da zuwa, kamar dole aka sata"""
yauwa yafaďa yana kallon ta har yanzu yanda ta sunne kai qasa kamar ba ita ba,, jin tayi shiru yasa yace yadai Amarya ba magana ne?"" Babu tafaďa batare da ta kalle shi ba,"
Meke faru ne yau naga sai wani ciccin magani kikeyi ke ďaya wani abun nayi miki? ya tambaye ta yanda yaga ta kame fuska,"
Tashi tayi tsaye tace sai anjima ni natafi tunda ba waje na kazo ba idan kagama ka rufe ķofar,"
kallon rashin fahimta yayi mata tare da tasowa ya yaqaso inda take , ya tsaya a bayan ta daf da ita ya harďe hannayen sa ta baya tare da kai kansa gefen kanta yana shaqar ķàmshin turaren ta yana murmushi,,"""jin alamun numfashin mutum yana sauķa ta gefen kunnen yasa, ta jiyo da fuskan ta, batasani ba ta gware da nashi fuskar,"" dafe fuskan ta tayi cikin jin zafi tafara baya da niyar zama taqara buguwa da tebur ďin dake bayanta tare da zamewa zata faďi,""" cikin zafin nama yayi saurin ta rota yana cewa kiyi a hankali ina idonki ya tafi ne,"
Ni karabu dani tace dashi tare da kwacewa daga riķon da yayi mata ta koma ta zauna kan kujera,"" komawa shima yayi ya zauna yace lallai mutumiyar yau mutanan suna kusa kenan?,"
shiru tayi masa tayi batace komiba"",
ganin yau a kumbure take yana mata magana ma tana kakkame fuska yasa yashiga lallamata da kalamai masu daďi har ta sake fuska suka fara hira",
Suna cikin hiran su mai daďi ya ďago yace, mai nayi ne yau kiketa fishi dani haka sarauniya ta har kike jima kanki jiyo,?"
fuska taqara kamewa tace ai kasan abinda kayi ďazu fa muka gama waya dakai baka sanar dani kazo ba kawai sai ji nayi Abba yace wai inzo kana jirana a parloun baķi,""
To sake fuskar mana dan Allah yanzu akan wannan ne kiketa cin magani dan nayi miki zuwan bazata," to sorry Amarya bazan kuma ba kinji?," yafaďa yana karya wuya,"
Dariya ne ya kubuce mata tace naji zan rama ai nima kabini bashi, dan ni ba'ayi min in qyale,""
To kiyi ma mijin ki sassauci yace da ita yana kallon cikin kwayar idon ta wanda yasha kwalli yaqarawa fuskan ta kyau,"
Ba matsala tace tana girgiza kai tare da murmushi,"
Tashi yayi yana gyara hular kansa yace to madam ni zan wuce sai naqara shigowa kafin na koma,""
Aiyya mana tun yanzu zaka tafi yaushe ma kazo dan Allah" cikin kwabèwar fuska tayi maganar,"
Dariya yayi yace kedai kinada abu iri iri wlh yanzu kika gama ďaure min fuska dan nazo ban sanar dake ba, nace zan tafi kuma kina min korafi ,"" Amman dai karki damu zan qara shigowa ai kafin na tafi tunda an damu dani yanzu,"
To tabashi amsa tare da miqewa tace muje nayi maka rakiya, dan tagane neman nayi yake,""
kafin sukai ga fita aka buďe ķofar parlon," Mahmud ne shida abokin sa suka shigo suna hira," tsayawa yayi da hiran da yake yana kallon su yace a zuciyar sa ita kuma wannan yarin yar nan mai takeyi da ķaton gardi cikin parlou?..
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:06] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M* ✍🏻
*Page*
*15*
*Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace.. duk mutumin dakafi so aduniya ,to dashi za'a tashe ka ranar gobe kiyama ,ya Allah ka tashe mu tareda Annabinka da iyalen gidan sa tsarkaka Allah ka karemu da son yahudawa Amin*🙏🏿🙏🏿
*Qawata Maryem Abdool karki sa rai cikin wannan shafin dan ba mallaka miki zanyi ba*😜😜
Sannu da shigowa ya mahmud tafaďa batare da ta kalle shi ba,"" yauwa yabata amsa yana mata kallon tuhuma, tare da miqawa Abdulmalik hannu suka gaisa kamar an sashi dole,""
Wani irin mayun kallo taga abokin mahmud ďin yana yi mata, hakan yasa tafara tsarguwa da kanta tana duba shigar da tayi, tace to shi kuma wannan wani irin mayene sai kallo na yake kamar yasamu TV,""muje ko? taji muryan Abdulmalik yana shirin fita bayan yagama gaisawa dasu mahmud," bayan shi tabi suka fita har zuwa gun motar sa ta rako sa, tace to Yaya Abdool sai anjima Allah ya tsare,""
kallon ta yayi bayan ya buďe motar ya shiga yace,"""bangane ba wannan sunan fa daga ina kika samo shi?,"
Murmushi tayi tace daga ruhinka mana,"
A a kidai canza dan bazan dauka ba ina mijinki Amman kina qirana da sunana kai tsaye, babu ko sirki banda hakama ai Abdool daban Abdulmalik daban,"
To ni shi yafi min daďi kuma dashi zan ina qiranka tace da shi tare da rufe mishi ķofar,"
kunna motar, yayi yana shirin ficewa, yace kidai gyara "
Tana dariya tace to yaya Abdool zanyi kokarin gyarawa tunda baso kakeba,
Au qarawa ma kike, ya miki kyau ni na wuce yace mata yana ďaga mata hannu,""" itama hannun ta ďaga masa tare da juyawa ta koma cikin gida zuciyar ta fal murnan zuwan shi da yayi,"
Faisal ne keta safa da marwa cikin parlon yana magana shi ďaya ya kasa zaune ya kasa tsaye,"""gajiya mahmud yayi da kallon sa yace wai meyake damunka ne faisal naga tunda muka shigo ka kasa zaune ka kasa tsaye wani abun ne yafaru?" ya tambaye shi yana duban sa"
kujera yasamu ya zauna tare da dafe kansa yace abokina dan Allah, ka taimaka min wlh nayi sake,"
kallon sa mahmud yayi da kyau yace bangane maganar ka bafa , kayi min bayani yanda zan fahimta,"
Shiru faisal yayi na ďan dakiku kafin yace qanwar ka humaira, da alama ta kubùce min,"
Ajiyan zuciya mahmud ya sauķe yace dama akan humaira ne kabi ka ďaga hankalin ka ? waima tsaya tukun kana nufin har yau ka kasa sanar da ita kana son ta?"
kai ya girgiza masa alaman Eh yace wlh lokacin da ka turo min ita kasa faďa mata nayi shiyasa nadamu ka faďa mata da kan ka tunda qanwar kace,"
To ka hutawa rayuwar ka ai dan ni babu abinda zan iya maka a yanzu,"
Haba mana abokina karka min haka dan Allah ka shige min gaba cikin wannan maganar, faisal yace da mahmud tare da tasowa yazo kujeran da yake,"
Shikenan ba matsala zanyi mata magana. ya bashi amsa tare da cewa kazo mu shiga wajan Abba daga nan sai nayi mishi maganar,""""yauwa abokina kokai fa yanzu naji dama dama a zuciya ta da saura kaďan ta buga wlh,""" ai da ya buga ďin da mun huta kuwa, Mahmud yace masa bayan sun fita a parloun suka nufi wajan Abba,"
Shida mummy suka tarar zaune suna hira, sukayi musu sallama tare da qarasawa cikin girmamawa faisal ya gaishe dasu suka amsa masa cikin sakin fuska kafin ya fice yabar mahmud a gun dan ya gabatar musu da bukatar sa,"
gyara zama mahmud yayi tare da yi maya Abba bayanin son da abokin sa faisal yake ma humaira,"" yace to ai ya makara mai yasa tuntuni bai fito ya faďa ba sai yanzu da yarinya ta kawo wanda takeso kuma har magabatan sa sunzo angama magana saidai yayi haquri Abba yafaďa,"
mamaki ne ya cika zuciyar sa yace to yaushe duk akayi wanna aika aikan a cikin gidan nan baiji lbr ba,"" haka yatashi ya fita ya samu faisal a waje ya sanar dashi komai Abinda Abba yafaďa,""" danasani da baķin ciki qarara a furkan sa yana wadaran zuciyar sa da takasa barin ya furta mata kalmar so, gashi yanzu yayi sake wani ya riga shi,"" jiki babu kwari yayi sallama da mahmud ya wuce gida cikin nadama,""
Bayan sati ďaya da dawowar ta magabatan Abdulmalik suka qara zuwa suka bada sadakin sisin gwal tare da yanka rana wata ďaya dan yanda Abdulmalik ďin ya dami Abban shi so yake yaga anyi wannan auran," Abba har mamakin shi yake yace kana abu kamar wani gauro wanda bashida mata, shidai kala baice mishi dan shi kaďai yasan irin zaman da yake a cikin gidan sa yanada yaqinin cewa Humaira zata maye masa gurbin bàcin ran da yake ciki,"
****** ********
Biki yakan kama yau saura sati ďaya a ďaura aure Amarya tasha gyaran jiki musamman Mummy ta ďauke ta sukaje maiduguri akayi mata dilke da halawa har na tsawon sati uku kafin suka dawo," kyawu kam tasha fatar jikin ta yaqara taushi da tsantsi sai wani sheqi takeyi fukar nan inka ganshi yaqara kyau da haske,"
Jiya alhamis aka gabatar da walima tare da gayyato babban malami yayi musu wa'azi mai shiga jiki,""yau jumma'a da daddare za'ayi wushe wushe an shirya amrya cikin a tamfa ďan ubansu wanda samu ďinki mai kyawun gaske riga da siket akayi mata lifaya hannayen ta nan yasamu kunshi tsararre gashin kan ta akayi mata qitson kla yakku na kanure aka waso mata shi gaban goshin ta kai yau idan ka ganta sai ka rantse ba ita bace gabaki ďaya ta sauya,""
Bayan sun gama shirya ta suka fito da ita filin gidan da aka gyara shi aka zuba gujeru na zaman mutane da yake a nan za'a gabatar da wushe wushen,"
Amarya tana fitowa mai qirari ya soma qirari bayan ya gama gabatar da yan ganga kura mata da maza sukayi rawan ganga kura kafin mai qirari yazo yagabar da yana mai tsada ta soma yin waka cikin kanuri haka yan uwa da abokan arziki suka fito suna takawa," Amarya da ango na zaune suna kallon yanda komai yake wakana bayan sun fito sun ďan taka,""
Saida aka shafe lokaci ana hidima har karfe goma sha biyu kafin aka rufe taro da addu'ah kowa ya watse,"
kasa sakin hannun ta Abdulmalik yayi ji yake kamar ya hadiye ta dan ba qaramin kyau yaga tayi masa ba," saida haisam yazo ya sashi gaba da surutun dare yayi su tafi, kafin ya rabu da ita dakyar itama ta shige cikin gida,"
🌾🍃🌾🍃🌾🍃🌾
Umma ce a ďaki ita ďaya sai safa da marwa take, gaba ďaya ta rasa mai yake mata daďi, zama tayi a bakin gado ta riqe habàr ta tana nazarin mai yakama tayi akan wannan auran, can ta kuma miqewa tsaye tace inaa, da sake wlh, bazan tabà laminta ba tunda dai har suka iya hanaka auran suwaiba to wlh sai na kunno musu bala'i da masifa zaku san ďana kuka mallake tsinannu,"
Turo ķofar ďakin akayi Batula ce ta shigo qanwar Abdulmalik,," Umma kina lfy kuwa kin shigo ďaki kinbar jama'a sai nemanki ake, tace da ita tana kallon yanda duk tafi ta canza,"
Too mai zanyi musu ko nice na gayyace su duk wani ďan talikin da ya nemeni kice musu bana nan dan babu yawu na cikin wannan auran,""
Haba umma meyasa kike faďin haka, Abdulmalik nefa ďanki na cikin da kike nuna mishi so da kauna,"
kinci kutumar ki batula, kutumar ki nace, ďan hanji nane bana ciki na ba," Umma tafaďa tare da kai mata daķuwa,"""tace dallah ďauko min wayar nan ki qira min number tsinanniyar ďayar matar tashi, in fara a kanta,"
Allah ya huci zuciyar ki batula tace tare da ďaukar wayar ta danna qiran number dan tagane wa take nufi,"
Zaune take kan ďaya daga cikin kujerun da aka tanadawa yan hidimar biki ita da sauran qawayan ta, gurin cike yake da jama'a anata tashewa babu abinda ke tashi sai kiďa, hannun ta riqe da jus tana sha wanda idan ka kalli gaban su duk ancike musu da abinci iri iri,"
qaran wayar ta taji yana ringing, ajiye jus ďin hannun tayi tare da kallon mai qiran nata,"" dogon tsaki taja tana yamutsa fuska tace ita kuma wannan matar mai ya motsata taza qira mutum da daddaren Allah in banda fitina,""
Amsa wayar tayi tare da kaiwa kunnen ta tace Assalama alaikum Umma ina wuni,""riqe gaisuwar ki taji tafaďa atakaice tace wai ina kike ne haka sai kiďar waqa nake ji yana tashi kamar gidan karuwai?",
Ya mutsa fuska tayi najin haushin tambayar nata tace, Haba umma ina wajan bikin qawata ne," ni kuwa mai zai kaini gidan karuwai ina matar aure?",
To ina nasani ko kin fara, nidai bashi bane dalilin qirana ba," "idan kin kammala da hidimar bikin qawar taki sai ki dawo kiyi na mijinki,"
Cikin rashin fahimtar inda maganar ummar ya dosa tace bangane bafa mai kikeso ki gaya min ne umma?
Yoo ina zaki gane kuwa kullum bakida aikin yi sai nayawon banza,," to abinda nake nufi shine duk lokacin da kika gama sakarcin naki sai ki dawo ki tari kishiya dan gobe zata tare,,"" tana gama faďar haka ta miqawa batula wayar tace gashi kashe nagama aikin yau saura na gobe kuma,""
Himm umma kenan wai wanne irin gobara kike shirin kunnawa ne a gidan yaya??
Batula batula umma tace tana dariya kedai zuba min ido kiga mai nakeyi idan zaki tayani to shigo daga ciki dan bazan zauna kara zube ba,""
kai umma ķur'anin Allah wani abun sai ke,, yanzu dai kifito yan uwa sunata cikiyar ki,""" jeki ina zuwa umma tace da ita bayan ta miqe tana gyaran ďaurin zanin ta, zuciyar ta fayau takeji tasan ba qaramin abu tayi ba""
Car uba billahil lazi yau za'ayi bura uaban da ba'a tabà yiba cikin faďin duniyar nan,, Maraqishiya tafaďa cikin ďaga murya tare da miqewa tsaye tana kwasan jakar ta da takalmi,""
ďaya daga cikin qawayan ta ne ta miqe tace ke kuwa lfy kiketa wannan bambamin kodai wani abun Ummar tagaya miki??
Himmm shiwari bazaki gane ba wai ni Abdulmalik zaiyiwa kishiya dan rashin mutunci inan ina zaman bikin wata ashe nima ana can anayi min, to wlh da sake, ķur'anin Allah bazan jure ba, kunga tafiya ta,"
Salati qawayan ta suka fara tare da mamaki, shiwari takamo hannun ta tace dawo qawata, ki zauna nufin ki komawa ķatsina zakiyi cikin daran nan?? inaa kema kinsan bazai iyu ba," bari zakiyi gobe idan gari ya waye sai kiyi sammako kinji Amman yanzu dare yayi koni bazan barki ki kama hanya ba,""
Kuka ta fashe dashi tare da zama tace ni wlh kubar ni natafi yanzu,, zuciya ta bazata iya jurewa ba har zuwa gobe fuskan ta yayi shabè shabè da hawaye tana sharan majina,"
Girgiza kai shiwari tayi ta shiga lallashin tare da bata baki tace karki ďaga hankalin ki qawata muna tare dake cikin wannan batun kiyi shiru ya isa haka, tana shafan ta taci gaba da bata baki har tayi shiru fuskan ta yayi zutu zutu idanuwan ta yayi jazur kamar garwashi,, haka shiwari ta kwashe suka bar wajan, dinner da ba'a gama dasu ba kenan,""
**** *****
Yau Asabar rana ce ta farin ciki gurin Humaira da Abdulmalik ko wannen cikin Annashuwa yake,,"" misalin karfe goma na safe jama'a babu iyaka gaban ķofar masallacin dake kusa da gidan alhaji Ali girema," yan uwa da abokan arziki duk sun ha latta," can gefe guda ango ne da abokanan sa inka ganshi kasan yana cikin farin ciki da Annashuwa,""
Tana ďakin a zaune gefen ta Amena da matar yaya musty anty fati, Amena sai zolayar ta take, Amman ta share ta,,Fadeela ce ta shigo ďakin da gudun ta tana dariya tace shikenan Humaira yau Babu kin tashi daga budurwa kin koma matar aure yanzu Abba ya shigo yace an gama ďaurin aure,"" kuma yace idan kin gama shiryawa ki sameshi a parloun shi,,
Zuciyar tane taji ya buga dum tafara farga Amman ta rasa dalili tunda fadeela tace mata an ďaura aure, ta rasa mai yake mata daďi, tashi tayi ta wuce gun Abban dan dama ashirye take,"""" A zaune ta sameshi da mummy kusa dashi, tayi sallama tare da qarasawa inda suke ta zauna kusa da mummy kanta a qasa,""Abba ne ya soma yi mata nasiha mai shiga jiki sosai ya sama Albarka bayan yagama,"" Mummy ma nasihan tayi mata tare da Addu'ah irin ta uwa da fatan alkhairi,""
Bayan sun gama mata nasiha Abba da kanshi ya rakota har mota ta shiga tana kuka sosai na barin gida dakyar tarabu da jikin mummy itama karfin hali tayi tana tausayin yarta,"
Shiga motar sukayi suma yan rakiya Amena da anty fati da fadeela,"" Mahmud ne yaja su a motar sai airport dan Abba duk ya biya musu kuďin jirgi, yace basai anyi gayya ba su uku ma ya isa" bayan sun isa airport ďin basu daďe ba jirgin su ya tashi sai cikin garin katsina,""
Suna isa dama driver yana jiran su ya kwashe su bayan sun fito,, bai tsaya dasu ko ina ba sai gidan Alhaji Sulaman mahaifin Abdulmalik dan gabatar da buďan kai,"" dama ashirye suke, saukowa sukayi daga motar suka shige cikin gidan Amena na riqe da ita ta gefe fadeela ma na gefe sai anty fati dake bin bayan su,"" guďa jama'ar gidan ketayi ga Amarya tana shigowa,, Har parloun Umma aka shigar dasu wanda ke ďauke da mutane suna zaman jiran Amarya ta iso ayi buďan kai,,""Umma na zaune kan kujera da kame fuska tare da ďaura ķafa ďaya kan ďaya tana girgizawa, ita ďaya tasan mai takeji dama dole aka sata fitowa,""
Basu sukabar gidan sai wuraren karfe goma na dare bayan an kammala da buďan kai,"" kai tsaye gidan Abdulmalik driver yayi parkin aka sauķo da Amarya aka shiga da ita,,,,kallon yanda gidan ya tsaru suka tsaya yi, parlou ne babba da kujeru masu masifar kyau da tsada,"" ďakin ta suka shige da ita wanda yasha gyara sosai akayi mishi jere nagani na faďa,, basu tsaya bàta lokaci ba suka shiga qara gyara Amarya tare da saka turaren wuta,, gidan duk yabi ya ďauki ķàmshi,,
cikin qasaita ya shigo gidan shida haisam da sauran abokanan sa sukayi hanyar ďakin Amarya ,, a zaune suka tarar dasu bayan sunyi sallama suka qarasa ciki,, waje suka samu suka zauna suna faďin Amarya bakya lefi ko kin kashe ďan masu gida,, Abdulmalik ne yayi magana yace to nagode muku saida safe idan mun haďu,, dariya haisam yayi yace tofa abun ma harda kora ne, barka dai duka mu nan munada mata dan haka sai anjima,, tashi sukayi suka fita bayan sun gama mishi tsiya,,"" su Anty fati ma tashi sukayi suka fice bayan sunyi musu saida safe tare da ja musu ķofar ďakin suka wuce ma sauķin su,,
Tashi yayi daga inda yake ya tako wajan ta ya zauna a bakin gadon yace Amarya ta sarauniya ta a ďan buďe min fuskar mana na kallah ko nima rowar za'ayi min ina maigida?,"
shiru tayi masa tana sharan hawaye,"" Hannun sa ya kai da niyar ďaga mayafin da aka rufe kan nata dashi fuskar sa ďauke da murmushin jin daďi,, baikai ga buďewa ba sukaji An banko ķofar ďakin da karfin gaske an shigo.....
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:07] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA* 🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M* ✍🏻
*Page*
*16*
*MUSIBAR MUTUWAR ANNABI ITA CE MAFI GIRMAN MUSIBA A GURIN MUSULMI:*
Musibar mutuwar Annabi tsira da amincin Allah ita ce musiba mafi girma a gurin dukkan wani mumini ba wai mutuwar Sayyidina Husaini ko mutuwar wanin sa ba. Wannan shi ne abin da Shari'ar Musulunci ta zo da shi ta ingantacciyar hanya.. Malamai da dama sun
rawaito cikin hadisai da dama cewa *Manzon Allah* tsira da amincin *Allah* su tabbata a gareshi yace.
(( ﺍﺫﺍ ﺃﺻﻴﺐ ﺍﺣﺪﻛﻢ ﺑﻤﺼﻴﺒﺔ ﻓﻠﻴﺬﻛﺮ ﻣﺼﻴﺒﺘﻪ ﺑﻲ ﻓﺈﻧﻬﺎ ﺍﻋﻈﻢ ﺍﻟﻤﺼﺎﻳﺐ ﻋﻨﺪﻩ )).
*Ma'ana:* ((Idan aka samu dayan ku da wata musiba to ya tuna da musibar da ta same shi ta dalilina (mutuwata); lalle ita ce mafi girman musiba a gurin sa))._
*Allah* muke roko da Ya taimaka wa al'ummarmu Ya cusa musu kin dukkan wata bidi'ah..Amin🙏🏿🙏🏿
~~Huci take sosai tamkar tsohuwar zaki ta fara takowa inda suke,"
Cak hannun sa ya tsaya da buďe mata fuskar zuciyar shi ya tsinke shi gaba ďaya kaf ya mance da batun ta sai yanzu da ya ganta ya tuna da lamarin ta," to wai ma waye ya sanar da ita yayi aure shidai yasan ko zama da ita na arziki beyi ba bare ya sanar da ita,"
Wuyan humaira ta cikumo ta saukar da ita daga kan gadon bayan ta yaye mayafin dake rufe da fuskan ta", har yanzu huci take ranta a bàce ta wanke ta da lafiyayyun mari, masu shiga jiki"",,
Sosai ta riqe kuncin ta idanuwan ta yafara zubar da hawaye tanajin zafin yanda ta matso wuyan rigan ta kallon ta tayi da idon ta wanda har yayi ja dan azaba, a zuciyar ta tace to ita kuma wannan wacece haka?,,,, ganin da gaske wani dukan zata kai mata yasa shi tasowa daga inda yake tare da kwace wuyan ta a hannun ta, yaja ta baya yace, Bakida hankali ne wanne irin hauka ne ke damun,ki, meye tayi miki da zaki mareta kamar kin samu jaka?
kaga malam bada kai nazo yi ba kabari nagama da ita kafin na iso kan ka, qara nufo ta tayi da niyar kamata,, cikin zafin nama ya damķo hannu ya jefar da ita gefe har saida ta bugu da kujera a bayan ta,,, Hannun sa ya ďaga ran sa in yayi dubu ya bàci ya nuna da ďan yatsa yace," wlh wlh Maraqishiya kishiga hankali zanyi miki ba daďi wannan wani irin sakarci ne ko kin haukace ne?
Hauka hauka fa kace Abdulmalik ni zaka kalla kace min ko na haukace to bakaga hauka ba yanzu zan nuna maka cikekken yanda ake hauka, ďan kwalin kanta ta cire ta ďaura a ķugun ta tana huci ta buga ķirji tace, Ni zakaciwa Amana ni ni nan zakayi ma kishiya dan munafurci shiyasa da nace maka zani bikin qawata ko musu baka min bare ka hanani dan kasan makircin da ka haďa,,to Billahil lazi la'ilaha'illahuwa,, bazan tabà zama da kishiya a cikin gidan nan ba, kodai ka saketa ta koma gidan uban ta data fito kodai ta rasa kwanciyar hankali, sai ta gwammace da batayi auran nan ba",
Hannayen sa ya harďe bisa ķirjin sa yana ganin yanda ta zage take gaya mishi ďacin magana ko ta manta shi wanene, Ajiyan zuciya ya sauķe yace bisimillah kiyi abunda zakiyi, indai saki ne saidai ke ki saku Amman ba Ita muna nan da ita a cikin gidan tunda ke kin nuna bazaman lfy kikeso ba,"
Haka kace ko? to mu zuba nida ku zaka ranar mahaukaci yahau kura, wai ni zakayi ma walaqanci a gaban wata shegiya,' to Billahil lazi zakaga tashin hankalin da baka tabà tsammani ba,, ke kuma ta juya ga Humaira wacce ke tsaye inda take takasa motsawa,tace dan ubanki zakisan kin shigo kabari ki ďauka daga yau kin rasa zaman lfy har abada indai ina numfashi a doron qasa, ķur'anin Allah bazanyi kaffara ba sai nayi sanadiyar lalata *RAYUWAR AURAN KI*sai kinyi nadamar shigowa gidan nan tunda har kika zabì auran mijin wani,"" tana kaiwa nan ta juya da niyar fita..sai kuma ta dawo baya ta ďauki ledar kazar da tagani a gefen su, tace saidai kuci kanku Amma ba wannan kazar ba, fuu tafice tana bambami ta sai ďakin tare da rufe ķofar da karfi ta faďa gado tana huci sosai.,"
Ajiyar zuciya ya sauķe tare da juyawa ya tako inda take tsaye har yanzu tana sheshsheqar kuka, kamo hannun ta yayi da niyar janta jikin shi dan ya lallashe ta," warce hannun nata tayi atakaice tace kabani takarda ta in tafi,," dum yaji zuciyar shi ta buga, yace kinsan mai kike furtawa kuwa? idan har zan iya sakin ki to meye ribata na auran ki?,"
Cikin kunar zuciya ta ďago da jajayen idanuwan ta wanda sukayi lubùlubu ta qara cewa kabani takarda ta in koma gidan iyaye na banason wani dogon bayani,"" har cikin ran shi nakejin kalamar sakin nan, nauyayyan numfashi ya kuma sauķewa akaro na biyu ya qara kamo hannayen ta duka biyu yana kallon cikin kwayar idon ta yafara cewa, haba Humaira dan Allah kiyi haquri nasan ban kyauta miki ba, wlh badan naci zalinki na bòye miki, ba Dan Allah ki fahimce ni kibar ambaton wannan kalmar zuciya bazata iya jurewa ba, kamar yayi kuka yakeji gaba ďaya hankalin sa baya jikin sa,""
Hannayenta ta zare daga cikin nashi ta durkushe qasa a wajan tare da fashewa da kuka sosai mai tsuma zuciyar mai sauraro,"""cikin sarkewar murya ta soma magana, meyasa zaka min haka Abdulmalik? meyasa kaqi sanar dani kanada aure? meyasa ka zabì kaci Amanar mu biyu a lokaci ďaya? meyasa meyasa meyasa Abdulmalik? ," kukan ne yaci karfin ta sosai takasa cigaba da maganar,"
Duk ilahirin gabòbìn jikin sa yayi matukar sanyi da jin tambayoyin data jefo mishi a lokaci ďaya,"" durķusowa shima yayi zuwa qasa yana kallon yanda take zubar da hawaye kamar a bakin kwarya, idanun sa ya runtse yasan shine musabbabi yana jin tausayin ta a ran shi yasan ba qaramin abu ya bòye mata," sai yanzu yake nadamar kuskuren rashi sanar da ita da baiyi ba," idanun sa ya buďe tare da jawo ta jikin shi sosai ya rungume ta tsam, yafara bata haquri, yace dan Allah ki yafe min matata ki daina wannan kukan da kike wlh baso nake ba,kinji my angel plss Am sorry," shiru tayi masa tayi luf a faffaďar ķirjin sa tana shaqar daddaďar ķàmshi turaren sa,""
ganin tafara tsagaita kukar yasa ya ďago da kanta tare da miqar da ita yana kallon ķwayar idon ta yafara yaye mata mayafin dake jikin ta," hannayen sa ta riqe cikin tsarkewar murya tace kabar ni zan cire da kaina,, murmushi yayi har saida hakoran sa suka bayyana ganin yanda jikin ta ke rawa yace matsoraciya ki nutsu babu abinda zanyi miki, kayan jikin ki kawai zan rage miki sai ki kwanta ki huta,, bata hana shiba yaci gaba da yaye mata mayafin....
*Da ace kasan kanada aiyyuka agaban ka ko zuwa makaranta ko zana jarrabawa ko wasu abubuwan da zai hanaka yin typing kayi ma makaranta posting akan lokaci yafi ace baka fara littafin ba har zuwa lokacin da kakeda free idan kuma kafarane wani abun yazo maka to yana da kyau ace ko kaďan kaďan ne ka samu kana typing koda kuwa read more ďaya ne yafi kajin kirta masu karantawa har tsawon sati buyu ko uku yazamo har an soma mantawa dashi*.
Dan Allah kuyi haquri da wannan naso nayi dogon page Amman hakan bata samu ba," kuma ina neman uzirin ku yanzu ba dogon page zakuna samu ba, Amma insha Allahu zan ina iya kokari na ganin nayi muku posting kullum,🙏🏿🙏🏿
Taku har a kullum,,
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:07] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA* 🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M* ✍🏻
*Page*
*17*
*Kafin na wuce inaso nayi amfani da wannan damar wajan yi muku godiya kan yanda kuke nuna min kulawa inafarin cikin kasance wata daku,*👇
Babbar yayata sweet Anty fauzy
Maman nana
Maman zee
Maman khady
Hanee
*Ina miqa muku gaisuwa ta fatan Allaha yabar zuminci da kaunar juna Amin*🙏🏿🙏🏿
_Baheera karfa kisa rai aciki_ 😜😜
~Ahankali yake yaye mata lifayar cikin nutsuwa tare da bin surar jikin ta da kallo yanajin wani irin a ran shi,""Alhamdulillahillazi bini'imatihi tatimmussalihat,,, Tabarakallahu masha Allah,,ya furta bayan yagama yaye mayafin, ya rungume ta tsam ajikin shi yanajin wani irin sanyin ni'ima yana sauķa mi shi cikin zuciya, daure wa yayi ya kai hannun sa kan zif ďin riganta yafara zugewa, cak ta riqe hannun sa tare da ķoķarin zame jikin ta a nashi ta buďe baki da muryar ta wanda ya dashe dan kuka tace,, meye haka kake min kabar min kayana,,"dariyane sosai ya ķubùce masa ganin yanda tayi maganar kamar wata yar yaye, ya buďi baki yace,,"
Kinga malama ki kwantar da hankalinki nifa babu wani abunda zan miki kawai dai so nake na taimaka miki,da wannan kayan zafin,"
zamewa tayi gaba ďaya daga jikin shi kanta a qasa takasa ďago da kai ji take idon ta bai iya jure kallon na shi ba," atakaice tace karabu dani bana bukatar taimakon ka,""
"Cak ya ďauke ta fuskan sa ďauke da murmushi yace shikenan gimbiya nabari muje ki kwanta, kinji ? yana murmushi," kawar da kanta tayi gefe taqi haďa ido dashi""a kan gado ya dire ta ya gyara mata pllow tare da kwantar da ita yaja mata bargo ya rufe ta," tsayawa yayi yana kallon yanda ta lumshe idanuwan ta kamar mai bacci,, lumshe idon sa shima yayi tare da buďewa ya sauķe nauyayan Ajiyan zuciya,"
kinyi sallah kuwa? ya tambaye ta, yana kallon ta,"" ďaga masa kai tayi alaman Eh,""To tashi muci abinci kafin kiyi bacci,"
Banajin yunwa tace dashi cikin qasa da murya,
ban yarda ba nidai taso muje muci kinji my angel yana shafan kanta, yana ganin kyawun fuskan ta"""Bazanci abincin ba ni karabu dani dole ne, cike da takaici tayi maganar ji take bata bukatar komai a yanzu duk da irin yunwan da takeji,Amman bazata iya cin komai ba""ďauke hannun sa yayi daga kanta ya tashi tsaye, ganin har yanzu bata huce ba kuma batada niyar hucewa, yace to shikenan na qyale ki kiyi baccin ki saida safe ya juya yabar ďakin, zuciyar sa cike da abu iri iri yana takaicin wannan daran sam beji daďin shiba,, ďakin sa ya nufa ya shige toilet yayi wanka ya fito tare da goge jikin sa ya shafa mai ya ďauko farar jallabiya mai kyau ya saka tare da feshe jikin da turaruka masu ķàmshi yaja ķofar ďakin ya rufe bayan ya fice, yayi lungun ďakin ta ya tura ķofar ya buďe""
Tsaye ya ganta tana ta jeka ka dawo duk tabi ta tashi hankalin ta bata cikin nutsuwa," duban ta yayi da ido ganin yanda ta birkice kanta ko ďan kwali babu gashin ta yayi cibiri cibiri dashi ita kaďai ta haďa uban zufa ďan tsaban masifa nacin ta kamar mai neman nayi,,""girgiza kan sa yayi ya qarasa shigowa cike da mamakin ta, yake tambayar zuciyar wai yanzu zafin kishi ne ya hanata kwanciyar hankali ko kuma bàtan kai ne ?,"shidai bai tabà sanin ta da irin hakaba saida yayi wannan auran yaga haukanta,""
Mai kuma kazo yi a ďaki na? yaji ta tambaye shi tana kai masa harara,""" kota kanta baiyi ba ya ďauki abinda ya kawo shi ya fice,daga ďakin,"
Harara taqara bin sa dashi tace munafukin mutum kawai ai bakaga tashin hankali ba tukun muje zuwa, tana girgiza kai take maganar cike da masifa," qaran wayar ta taji ta ďauka tasa a kunne,"
Hello qawata yane mai ake ciki da gaskene yayi aure?,"shiwari ta tambaye ta tacikin wayar,"" himm shiwari kenan ai kibari wlh matar nan ba qaramin taimaka min tayi ba maganar ta gaskiya ne naga cin Amana wajan namiji ai ban qyale su saida na nuna musu rashin hankali na kafin nabar ďakin ," tsaf ta zayyane mata irin tashin hankalin da ta musu,"" cike da takaici Shiwari ta shiga mata faďa tare da bata shawarar yanda zata billoma lamarin," saida tagam sauraran ta kafin takashe wayar bayan sunyi sallama zuciyar ta cike da jin daďin shawarar da shiwari ta bata haka ta haura gado ta kwanta ita ďaya tana murmushin mugunta,""
Yana barin ďakin ta ya shige na Humaira," har yanzu tana nan yanda yabar ta Amman da alamun tayi bacci,""kan gadon yahau bayan ya maqala wayar sa a charge,""
A hankali cikin dabara yaye bargon da ya rufe ta dashi, wani irin yarr sokar jikin sa yayi ya lumshe idanun sa ya qara buďe su suka sauķa kan bayan ta wanda yafara zuge mata zif ďin riganta,,hannun sa ďaya yakai yaqarasa zugewa ganin bacci mai nauyi takeyi tana sauķar da nauyayan numfashi, idan ka ganta kasan cewa kuka tasha sosai ba kaďan ba "shafan bayan ta ya soma cikin dabara da nutsuwa yanajin yanda fatar jikinta ke tsantsi da fitar da daddaďar ķàmshi akaro na biyu ya kuma lumshe idanuwan sa ya buďe yanajin wani shauķi a ran sa haka har yayi nasaran cire mata rigan jikin ta ya zubawa surar ta kallo a zuciyar sa yana qara godewa Allah da ya mallaka masa wannan hallitan nashi a matsayin matar sa ta aure,""
Jawo ta jikinsa yayi ya rungume ta sosai a faffaďar ķirjin sa ya gyara kwanciyar sa tare da jawo musu bargo ya rufe su ya lumshe idon sa, zuciyar sa cike da tunani iri iri har bacci yayi nasaran ďaukan sa yana nan rungume da ita....
A dai qara yimin afuwa makaranta nagode🙏🏿🙏🏿
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:07] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA* 🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*Page*
*18*
Qiran sallah asuba ne ya farkar dashi cikin daddaďar baccin da yakeyi, buďe idanun sa yayi tare da kaiwan hannun sa gefen gadon ya ďauki wayar sa wanda ya naqala a charge, ya duba a gogo yaga karfe biyar da mintina," ajiye wayar yayi yakai idanuwan sa kanta bacci mai nauyi takeyi har yanzu tana sauķar numfashi, a hankali" fuskar sa ďauke da murmushi yafara zareta daga jikin shi a hankali yana tsoron karta farka,,"
Tashi yayi bayan ya gama zareta ya gyara mata kwanciyar ta ya shige toilet ya ďauro alwala ya dawo gaban gadon yafara tashin ta,"" buďe idanunwan tafara a hankali suka sauķa cikin nashi wanda ya zuba mata su,yana kallon ta"" kawar da idanuwan tayi ta rufe su,gam"" tashi kiyi sallah asuba tayi yace da ita ganin bason haďa ido dashi take ba,,"" banza tayi masa bata kulashi ba har yanzu idon ta a rufe taqi buďe su,"" girgiza kai yayi ya fice daga ďakin cikin sauri dan yanaso yasamu jam'i ko hanyar ďakin Maraqishiya baiyi ba ya wuce masallaci,""
Jin shiru bata kuma jin maganar sa ba hakan ya tabbatar mata da ya fice,," buďe idanun ta tayi tare da miqewa zaune bayan tagama karanto addu'ar tashi a bacci, tare da dogon hamma wani mugun yunwa cikin ta keji"" hankalin tane sosai ya tashi ganin babu rigan jikin ta, cike da mamaki take tunano daran jiya lifaya kaďai tasan ya cire mata daga haka bata barshi ya cire mata kaya ba tadai san da riga ta kwanta, har bacci ya ďauke ta," cike da al'ajabi ta sauķa a gadon ta ďauki rigar ta wanda tagani can gefen gadon ta inda ya kwanta," tace to kodai zagayan ďan wake ya min, bansani ba"" sakawa tayi ta shige toilet ta ďauro alwala ta fito ta tayar da sallah,""
Addu'oi sosai tayi kafin tayi sallama kan sabon rayuwar da ta shigo tana tunanin yanda zata fara rayuwar auran ta da kishiya, ita sam cikin tsarin ta idan tayi aure bata tabà saka kanta cikin layin masu zama da kishi ba, sai gashi yanzu wai itace zatayi rayuwa da kishiya, zuciyar ta cike da fargan Kalaman ta Allah masanin abinda zatayi mata,"" saida tayi tasbihi sosai kafin ta tashi ta tubè kayan jikin ta tashige toilet, ganin garin yayi haske,""
Wanka tayi da ruwan zafi tare da yin brosh ta fito ďaure da towel iya cinyar ta,tana goggoge jikinta, taje gaban mirror ta zauna tana kallon fuskan ta ta kai hannun inda jiya tasha mari tana shafawa har yanzu tanajin yana mata raďadi,," cream ta ďauka mai ķàmshi ta soma bin jikinta dashi,,"bayan tagama ta tashi ta feshe jikin ta da turare ta juya da niyar ďaukan kayan ta a kwati wanda zata saka,,"" karo taci dashi dawowar sa daga masallaci, sosai goshin su ya buge dana juna,"" dafe wajan tayi da hannun ta cikin jin zafi tace,"
Washhh Allah na,' ta ďago idon ta ta kalle shi cike da tsiwa tace wai miye hakane dan Allah kullum sai ka buge min goshi na da naka?,"
Yana riqe da nashi dan shima yaji zafin buguwan yace kedai zanyima wannan tambayar koda yaushe kina cikin buge min goshi kalan kifasa min shi ki huta, cike da zulaya yayi maganar yana kallon surar jikin ta,""ganin yana nema ya mayar da abin wasa yasa ta share shi ta wuce ta gaban shi, tafara tafiya," Hannun ta taji ya kamo ya dawo da ita ya zagaye ta da hannayen sa ya rungume ta tabaya yana shaķar ķàmshi jinta yace,"
Haba mana babynah wai meyasa kin cika saurin fushi ne kuma bakya hucewa da wuri tun jiya fa naketa biye dake ki yafe min na tafka babban kuskure nasan ban kyauta miki ba, Amman kinqi hucewa babynah pls mana," yana gogan gefen fuskan ta da nashi yake maganar yanajin yanda take fitar da numfashi,," lumshe idanun ta tayi zuciyan ta na bugawa tanajin zafin wajan marin da yake goga mata nashi fuskan,"" Hannayen ta takai kan nashi wanda ya riqe mata ķugu dashi ta cire tare da zamewa batace masa komai ba ta zari hijabin da tayi sallah dashi ta saka ta fice a ďakin, tabar shi nan tsaye yana kallon ta,""dafe kansa yayi ya zauna a bakin gado yana mamakin fushi irin nata duk da yasan bai kyauta mata ba Amman yaci ace yanzu ta huce," ajiyan zuciya ya sauķe ya miqe ya shiga banďaki danyin wanka,""
Tana fita tayi ďakin inda su Amena suka sauka,"" cikin kuka ta shiga ďakin, taga, Anty fati zaune a bakin gado tana waya da alama da yaya musty take," fadeela da Amena kuma sunyi wanka suna shiryawa dan yau zasu koma,""kan cinyar Anty fati ta faďa tare da qara rushewa da kuka mai tsuma zuciya, tafara magana tace Abdulmalik ya yaudare ni ya cuce ni yaci Amana ta wlh bazan zauna dashi ba a mtsayin matar aure ba koya sakeni kona koma gida da auran shi a kaina ďan wlh bazan iya *RAYUWAR AURENA* da kishiya ba, kuka take sosai babu gaggautawa , abin tausayi,""
Cikin tashin hankali suka dube ta suna salati, Anty fati ta ďago da kanta tana kallon cikin idanun ta tace kina cikin hankalin ki kuwa kinsan meye kike faďa Humaira?,"
Inada hankali na wlh nidai komawa gida zanyi saidai na dawwama da auran sa a kaina idan bazai sakeni ba," Amena tace duk irin sonda kike mishi akan yanada mata shine zaki rabu dashi to wlh tun wuri ki gyara bakin ki karkiyi danasi nan gaba," cike da takaicin maganar nata ta watsa mata harara da idanunwan ta wanda sukayi jazur dan kuka tace kiyi min shiru ke kuma bana bukatar ki,""dariya Amena tayi taci gaba da shiryawan ta, dan tasan idan ta biye ta zata iya sauķe wannan fushin akan ta,""
Lallashin ta anty fati ta shiga yi tana bata baki kan tayi haquri ta rungumi ķadddara ai bakin alķalamin ya bushe tunda an ďaura aure,," lallashin ta tayi sosa tana tausaya mata tare da bata shawarari mai kyau na yanda zata zauna da kishiya,,"" Sosai ta gamsu da maganar ta kuma ta ďauki shawaran ta tafara share hawayan da ya wanke mata fuska, tace shikenan naji zan zauna dashi kuma zan yafe mishi Amman sai nagwada yin wasa da zuciyar shi na auna irin sonda yake min dan bazan zauna haka ba," dariya ne ya kubuce musu sukace, kedai dama kina son abunki kikazo kika tashar mana da hankali,," himm kawai tace tana saqa irin abunda zatayi mishi a zuciyar ta,""
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:07] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA* 🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*Page*
*19*
🇵🇰🇳🇫🇳🇫🇳🇫🇵🇰
*Abdulmajeed🇳🇫🇵🇰🇳🇫🇳🇫🇳🇫🇳🇫Abdulmajeed💄💄💄💄💄💄Qawata aminiya ta yar uwata my beasty💄💄💄💄💄Marmem Abdool Mai jambaki💄💄💄💄💄💄Ina tayaki murnan kammala littafin Abdulmajeeda🇳🇫🇵🇰🇳🇫🇳🇫🇳🇫🇳🇫🇵🇰🇵🇰🇵🇰 Haqiqa kinyi namijin qoqari wajan isar damu darasin da kikeson isar mana kuma mun ďauka da izin Allah mungode sosai qawata Allah yaqara basira Allah ya biyaki ladan abinda kika isar, Am soo happy for u dear Allah yabar zuminci da kaunar juna,na ji daďin littafin nan banso yaqare ba i will miss u a lot my Abdool and ramlat soo much, Hafsat mai shariff namiki fatan alkhairi sai mun jiki a littafi nagaba mai suna HAFSAT saura naji....🤣*
Tashi tayi tsaye tayi ta dubi Anty fati tace dan Allah duk abunda kukaga inayi ku goya min baya karku nuna baku san da zancan ba, tana gama faďin haka ta fice, bata jira taji na bakin su ba,"" Miqewa Anty faty tayi tana nazarin meye humaira take shirin yi, koma meye dai zamu gani tafaďa a ranta,,"shirri tafara yi tace da su Amena kuyi sauri mu fice dan gashi lokaci yana tafiya kar muyi missing plight, amsa mata sukayi sukaci gaba da shiryawa,"
Tana barin ďakin su Anty fati tayi hanyar nata cikin sauri kamar ana korar ta ķafafuwar suna harďewa har tana tuntubè ta isa," ta tura ķofar ďakin ta shiga", tsaye ta ganshi shi gaban mirror yana taje sumar kansa baķi siďik yana sheqi sanye yake cikin gogaggiyar shadda kaftan ruwan blue, wanda yayi masifar ķarbàn jikin sa,"idanuwan ta a lumshe ta buďe su suka qara sauķa akan sa fuskar ta ďauke da murmushi, taci gaba da kallon yanda yakebi yana tajar sumar cikin nutsuwa,"" ajiye comp ďin yayi bayan ya gama ya jiyo da kan sa ,"" ido huďu sukayi da ita,""tayi saurin kawar da kanta ta haďe rai kamar baķin hadari ta wuce tafara abinda ya kawo ta kamar ba ita ke kallon shi ba,,"Murmushi ne ďauke a fuskar sa ya zuba mata idanuwan sa cike da kauna yana kallon abinda takeyi, ya harďe hannayensa bisa ķirjin sa yaga ta, buďe, akwatin ta ta ďauki kayan sawan ta ta shige toilet,,"yana tsaye inda yake ko motsawa baiyi ba yana jiran fitowar ta,"" sanye da baķar abaya ta fito wanda akayi masa ado da jan stones ta gaba aka zagaye hannayen dashi, yayi masifar mata kyau ajiki,'""koda yaushe idan idanun sa suka sauķa kanta godiya yake da Allah ya mallaka masa ita a matsayin matar aure,,"gyalen abayar ta yafa akan ta ta rufe a kwatin tare da miqewa ta ďauki jakar ta taja a kwatin takama hanyar fita,"" cike da al'ajabi yake kallon ta ya kasa motsi zuciyar sa na raya masa abu iri iri, yace to meye ya rinyar nan take shirin, aikatawa ne? tana nufin har yanzu bata haqura da ķungirin ta ko meye? ganin tsayiwan da yayi bàta lokaci ne yayi saurin rufa mata baya, ya fice a ďakin,, karo yaci da su Anty fati suna ta howa da jakan kayan su a hannun su, tsaya wa yayi yafara gaisawa dasu cikin nutsuwa, yace yanaga kun fito da jaka a hannu,lfy ?," murmushi anty fati tayi, tace lfy lau zamu koma ne, yanzu ma sauri muke jirgin mu tara zai tashi,," aiyya tun yanzu zaku koma baza kuyi mana ko kwana biyu ba?," murmushi Anty fati tayi tace, haba dai ai bazai iyu ba daga rakiyar Amarya sai yaza ansamu wajan zama, kaga mudai zamu wuce munayi muku fatan alkhairi a riqe Amanan juna", insha Allahu yace da ita gashi ku tsaya kunyu karya ba yanzu za'a kawo," badamuwa tace mishi suka fice," bayan su yabi ya suka fito haraban gidan yana biye dasu yana kallon ta tana jan a kwati baice mata qala ba ya zuba mata ido yaga gudun ruwan ta,ita kuwa ko ido taqi bari su haďa, bare yasamu damar ta," Har gun mota suka iso yayi ma isiyaku driver magana ya kaisu airport, cike da girmamawa ya ansa masa, tare da buďe masu ķofar motar Anty fati da Amena suka shige baya fadeela kuma ta shiga gaba,, buďe ďayan ķofar gefen tayi, da niyar shiga har ta saqala ďayan ķafar ta, taji ya riqo hannun ta sosai taji riqon ya shige ta ta juyo da kai suka haďa da nayi wanda ya canca launi, ya buďi bakin sa yace, ina zakije?," rai ta haďe tare da fitowa daga motar tana ķoķarin kwace hannun ta daga riqon da yayi mata Amman ta kasa kwacewa dan ba riqon wasa yayi mata ba, idanuwan ta ďaga fuskan ta a haďe har yanzu alamun ba wasa, tace ka sakar hannu babu ruwanka da inda zanje, ta juyar da kanta kamar ba ita tayi maganar ba" marairai cewa yayi da fuska abar tausayi, yace haba Humaira meyasa kikeso ki kasance cikin masu fushin da basa hucewa ne?, tun jiya nake cikin baki haquri nasan banyi miki daidai ba ban kyauta miki ba naji na karbì lefina Amman meyasa bazaki yafe min ba kibar kugirin ki kidawo mu shifiďar rayuwar auran cikin soyayya da kaunar juna meyasa humaira? meyasa kikeson zakani ciwon zuciya? shiru yayi yana jiran amsar ta,"" Kanta na gefe taqi ďagowa ji take gabaki ďaya yabata tausayi, kamar ta rungume shi takeji ta faranta masa rai, ajiyan zuciya ta sauķe tace karabu dani nace bana bukatar haqurin ka gidan mu zan koma nabarka kaje ka ķarata da matar kuma idan saki ne ka riqe shi duk lokacin da ka gaji da dakon shi sai ka turo min, zuciyar ta babu daďi take maganar kamar dole ake sata,," Hannun ta ya sake yana kallon ta da idanuwan sa wanda suka canza launi sukayi jazir dan jin furucin ta zuciyar sa na dukan uku uku, ya buďi baki a sanyaye yace shikenan Humaira taji bukatar ki tunda kinqi yafe kije ba matsala da kaina zan kawo miki takardar ki Allah ya kiyaye hanya, yana kaiwa nan ya juya jiki babu kwari ya nufi wajan motar sa ya buďe ya shiga ya tayar mai gadi ya buďe masa get ya fice a gidan zuciyar sa tunkushe da abubuwa iri iri yayi hanyar gidan su cikin kunar da rai,"" Sosai jikin ta yayi sanyi ta juya ta kalli su Anty fati wanda suka zuba mata na mujiya suna kallon shirin da take,"" rufe masu ķofar motar tayi ta sunkuyo ta window tana yar murmushi tace musu to Allah ya kiyaye hanya nagama abunda zanyi, tukun tace isiyaku ya ciro mata a kwatin ta wanda yasa a bayan mota,"" cire mata yayi ya koma ya tayar da motar suka fice suna ďaga mata hannu,," cike da kewar ýan uwan ta tashige ciki tayi ďakin ta,,"
Tsaye take tun ďazu a bakin ķofar parloun fitowan a ďaki taga wucewar su taje tana leqar draman da suke, zuciyar ta fall,,""wani irin qaluluwa ne taji ya tokare mata zuciyar ta cike da takaici tace shegiyar ya rinya meye kuma ya hanata tafiya?," Amana muje zuwa sai kin gwammace da gidan ubanki kika koma tsinanniya bàrauniya, ďakin ta ta kowa cike da kunci tana shirya abinda da zata fara kunno mata, dan ji take baza iya jure ķara koda yini ne batare da tayi shirya wani abu ba,""
****** ******
Tana nan kwance tana tunanin wanne shiri zatayi mishi wanda zai wanke masa zuciyar sa daga takaicin data jefashi, tashi tayi daga kwancen da take ganin har huďu yana shirin yi, wanka ta shiga tayi ta fito bayan ta goge jikin ta ta buďe a kwatin ta ta zari atamfa haďaďďiya ďinkin riga da siket ta saka ďinki yabi jikin ta sosai duk wani halittan ta ya bayyana ya karbì jikin ta," gaban mirror taje ta zauna tafara kwalliya cike da nishaďi tayi ma fuskan ta kwalliya tayi masifar kyau kamar ba ita ba, dawowa tayi bakin gado ta zauna tana jiran dawowar sa, tana tsaďan wayar ta,""a kasalance ya shigo gidan tun bayan fitan sa ya kasa zuwa ko ina abubuwa sun tunkushe masa zuciya ya rasa mafita haka ya yini yanata zagaye gari,""kai tsaye ďakin sa ya wuce ya shige toilet yayi wanka jikin sa kamar babu jini haka ya shirya cikin qananan kaya tare da feshe jikin sa da turaruka, kafin ya fice zuwa parlou ya zauna ya zabga tagumi shi ďaya yasan mai yake cin zuciyar sa,""
Yana nan zaune har sawon wani lokaci, kamar an tsokare sa ya miqe yayi hanyar ďakin zuciyar sa na bugawa, ya tura ķofar ya shiga,,"" cike da mamaki ya zuba mata ido yana kallon ta tare da murzawa anya kuwa itace ba geza idon sa ke masa ba," hannayen sa ya ďaga ya nunata da yatsa yace Humaira,"murmushi mai sanyaya zuciya ta sakar masa tana takowa inda yake, tayi masa fari da idanuwan ta, ta kai hannayen ta ta zagayo dashi ta wiyan sa tayi daf da shi jikin su na gogan juna tayi masa fari da idanuwan ta tace nice mijina abin alfaharina," lumshe idanun sa yayi yanajin wani irin shauķi a zuciyar sa da farin ciki, kiss ta kai masa gefen fuskan sa tare da sakar masa murmushin kauna tace, cikin sanyayyar muryan ta tace buďe idon ka kalle ni mana my dear nice Hamaira ba mafarki kakeyi ba," wani irin sanyi yaji ya ziyarci zuciyar shi, a hankali ya buďe su suka sauķa cikin nata, " fuskar dauke da murmushin farin ciki,zaiyi magana ta rufe masa baki da zarazaran yatsunta, tace shiii karkace komai mijina na yafe maka komai ya wuce wlh har a raina,," cike da jin daďin kalaman ta ya rungume ta sosai tsam ajikin sa yana shaķar ķàmshin ta , yana gode ma Allah da yasa ta yafe masa ta dawo gare shi,""qara gyara kwanciya tayi a faffaďar ķirjin sa tanaji kaunar sa a acikin zuciyar ta, taqara matse shi kamar taza shige cikin sa,""
Sun ďauki sawon lokaci suna rungume da juna kafin ya daugo ta yafara kai mata kiss a wiyan yana sinsinar ta tare da bin ko wanne lungu da saqo na jikin ta yana shafawa yanajin soyayyar ta sosai yana karuwa cikin zuciyar sa," cigaba da shafan tayi yana kissing ďin ta sosai," tanajin yanda yake murzata Amman bata hana shi ba duk da yanda tsoro ya cikata ganin ya rikice mata jikin yana rawa sosai zuciyan ta na bugawa, ta daure batace masa komai ba,," tsayiwar ne ya gare shi ya ďaga cak a hannayen sa yana kallon da idanuwan sa wanda suka sauya launi suka kankance,"" kan gado ya dire ta ya mata rufa da ķirjin sa yafara aika mata rikitattun saqonni masu wiyan misaltuwa,"" gani yana nema ya wuce gona da iri ga tsoro ya gama mamaye mata zuciya yasa tafara masa magana,ya isa haka. bata qarasa ba ya toshe mata baki da nashi yana tsotsa babu gaggauta wa, Sosai ya fice a hankalin sa jinsa yake a duniyar da bai tabà zuwa ba,,"" kamar a mafarki sukaji muryan umma na kwala masa qira shi yadawo dashi daga duniyar da ya tafi, jiki babu karfi yaja gefe ya kwanta rigingine yana sauķar da numfashi, ji yayi ta qara cewa, cikin ďaga murya Kuna ina ne yan iska baza kufito ba kosai na shigo har ciki na sameku....
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:07] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*●HAFSAT M●*
*Page*
*20*
_Assalama alaikum Makaranta dan Allah kuyi min alfarma da kurakuran da kuka gani apage 19 wlh ban samu damar yin editing bane shiyasa dan Allah duk kuskuran da kuka gani kuyi min afuwa rashin gyara ne nagode_ 🙏🏿
TUNATARWA 👌🏿
*Hadisi daga bakin fiyayyan halitta manzon Allah (Saw)*
*An karbò daga Anas ďan malik Allah yaqara masa yarda yace, lallai manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace, kada kuyi qaita atsakanin ku, kada kuyi hassada da junan ku, kada ku juyama junan ku baya, ku kasance bayin Allah yan uwan juna, bai halatta mutum musulmi ya ķaura cewa ďan uwan sa fiya da kwana bakwai ba*
*Bukhari ne yara waito*
_Ya Allah ka haďa kawunan mu Amen_🙏🏿
Cike da takaici Maraqishiya ta fito daga ďakin ta tana kunkuni tare da dogon Hmma kamar zataci mutum, bacci ne yafara ďaukan ta taji muryan Umma daga parlou ta surutai," bayan ta iso inda Ummar ke tsaye tana jiran fitowar su," tace sannu da zuwa umma Ashe kece ke tafe??" kaďa ķafa take cike da masifa tayi mata banzan kallo ta haďe rai, tace, A a uwarki ce ke tafe bani ba, wato dan iskanci da rainin wayo tuntuni nake cikin gidan nan babu ďan talikin da yafito ya tareni dan ga yar jaraba ta iso ko, to mu zuba nida ku zakusha mamaki,,"
murmushin yaķe tayi tace Allah yabaki haquri umma wlh bacci ne ya soma ďauka na shiyasa kikaga ban fito ba,,"" gogon tsaki taja cikin ďaga murya tace aikin banza aikin wofi ,Aikin ki kenan Maraqishiya bakida da wani amfani a cikin gidan nan koda yaushe sai aikin bacci sakace jaka idan kin tashi kici mai daďi ki qoshi kije banďaki ki zazzzagar dan albazaranci, yau shekarar ki nawa a gidan nan Amman kin kasa iya koda bàri ne bare ki iya ďaukan ciki da yau ke watace da kin ijiye uku ko fiya da haka, dan munafurci kuma kin hanashi auran wacce zata haifa masa kin barsa ko ohho,"
Ranta ne ya sosu matuka taji maganar Ummar ya shige ta ya mata ďaci a zuciya Amman tabasar ďan tagane matsalar ta ďaya ne zata iya shawo kanta nan bada jimawa ba," dakewa tayi tace Umma kiyi haquri insha Allahu zamu haifa karki samu damuwa, yanzu dai ga guri ki zauna karki gaji bari na kawo maki abin motsa baki",mugun kallo ta watsa mata tare da nuna ta da yatsa tace, ke ki shiga hankalin ki wlh bana ciki da sakarcin banza zaman ma kece zaki sakani, to banga damar zaman ba tana dube dube ta qara da cewa, ina ita waccer shegiyar yar uwar taki, tana nufin inje in sameta ne ko meye?,"
bakin cikine taji yana addabar zuciyar ta da takaicin maganganun ta, sarai tagane wacce take nufi Amaman ta kawar da kai gefe tana ya tsinan fuska tace wacce yar uwata kuma?,"
Au bakima santa ba kike nufi ko kuma rai nin hankali? tace da ita tana mata kallon tuhuma," idan Amaryar daya auro jiya kike nufi bansan inda take ba hala ko tana ďakin ta," atakaice ta bata amsar dan idan da sabo ne yaci ace yanzu ta saba da bala'in ta Amma na yau daban ne ta rasa wanne bala'in ne ya ďauko ta ya kawo ta da yamman Allah," ina ďakin yake?taji ta tambaye ta tana yawo da idanu tana neman hanyar ďakin," gashi can ta nuna mata da yatsa tana nan tsaye tana ganin gudun ruwan ta koda mai tazo yau kuma,,
A fusace tayi hanyar ďakin tana gyaran ďaurin zanin ta daya fara sincewa tare da surutai, har ta iso bakin ķofar ta murďa taji a kulle, buga ķofar ta shiga yi da karfin ta tana kwala musu qira kamar za'ayi tashin duniya,,"
Yana nan kwance riginginen da yake sauķar numfashin sa yafara raguwa, ita kuwa tana gefe kuda ta kasa jiyo da kanta su haďa ido ji take gabaki ďaya kunyar sa takeji, bugun da Umma kewiwa ďakin ne ya tashar dashi zaune ya miqe yana mamakin ita kuma meye ya kawo ta da yamma ko wani abu ne yafaru", kallon Humaira yayi ganin ta makure waje ďaya ta kasa buďe idanunwan qitson da akayi ma gaban goshin ya rufe mata fuska",a hankali ya tako gefen da take kwance luf yakai bakin sa kan furkan ya hura mata iska mai sanyi yana lumshe ido, yace Matar tashi muje wajan Umma mu gaishe ta sai mu dawo muci gaba da gashi dan yau sai naga abunda ya turewa buzu naďi,
Yana murmushi yake mata maganar cike da zolaya yana so yaji mai zatace, dan yana jinta ďazu take neman hana sa jin daďin sa Amman ya basar da ita yaso ace yau ya samu abinda bai samu ba jiya Amman Umma tazo ta katse mishi jin daďin sa,, buga ķofar da ta qarayi ne yasa ya kamo hannayen ta ya ďaga ta daga kwancen da take ya miqar da ita kanta a qasa tana watsa da ya tsunta, yana kallon yanda ta canza mishi kamar ba ita bace wacce yanzu ta shigar dashi ni'ima ba, Matar wai kina nufin kice kunya ta kikeji ya? tambaya yana cigaba da kallon ta," shiru tayi masa kamar bataji shi ba,"" ganin ba Amsa zata bashi ba, yace, to shikenan baby muje mu gaishe da umma mu dawo kafin ta bàlla kofar dan a yau sai nacire miki kunyar nan dan bazan laminta mu zauna cikin kunya ba kamar dangin fulani ba, maganar tashi ne yaso bata dariya tayi saurin dannewa tace mishi muje bayan ta zari hijabin tasa, yana riqe da hannun ta ya buďe ķofar da niyar fita," karo sukaci da Umma wacce tayi kicinkicin da rai tana girgiza ķafa ita ďaya dan har tagaji da bugun kofar, ta sai suka buďe," cike da masifa tabi Humaira da harara ta dawo kan Abdul malik wanda ya zuba mata ido yana kallon ta, tace, meye kuke nufi ķofar ďakin ma rufe shi zakuyi? harda kai Abdul kana cikin ďaki kana jina ina kwala maka qira da yake daga zuwan ta harta zuba maka guba kasha yasa ka kasa fitowa saida tasake ka ko to yayi maka kyau ?," hannu yakai kansa yana shafawa yace kiyi haquri umma bamuji bane shiyasa,'hararar sa tayi tana masa mukun kallo, tace ina kuwa zakaji kana can ka maqale a gindin da babu arziki bare riba ai sa'a naci da yanzu ma kafito,,"
Jiikin ta yana dar dar zuciyar ta na sinkewa a ranta tace ,wannan bala'in da me yayi kama",, fitowa tayi daga bayan shi ta rusuna har qasa tace ina wuni umma,,"
Dan uwaki riqe gaisuwar ki bana bukatar ta, umma tace da ita tare da kai mata daķuwa a fuskar ta tace shegiyar ya rinya kina nan simisimi dake kamar mutumiyar arziki, harda wani rusunawa ina wuni umma dan munafurci, to dan ubanki da ban yini ba zaki gani ne, ta nuna da yatsa ta qara da cewa ke wannan da kin daďe da shigowa gidan nan na tabbata zaki iya ganin baya na munafuka tashi min a gaba na,"tashi tayi ta koma gefe ta tsaya kamar sanda idanun sun fara kawo ruwa,"
Runtse idanun sa sosai yayi yaji maganar ta shige shi ya rasa meye dalilin ta na tsanar yarinyar da yanzu ne shigowar ta gidan, ajiyan zuciya ya sauķe, yana kallon yanda take huci ita ďaya yace, Umma dan Allah kiyi haquri wai meye akayi miki ne yau kikeson huce mana?," daķuwa shima ta kai mishi da hannu tace kaci kutumar Abdul uwarka aka min, ka zauna gindin yan iska suna juya ka yanda sukeso, kuma ina nan kan bakata babu fashi karkaga wai nabar ka kayi wannan auran billahil lazi ban haqura ba ka zauna da shire ina nan tafe", ta juya ga Humaira wacce ke tsaye takasa ďago kanta bare taga kamannin ta," cike da masifa, tace ke kuma muje zuwa nida ke sai kinyi dana sani a rayuwar ki shegiya annamimiya kawai" ,tana bambami ta kaďa zanin ta tayi gaba tare da watsawa Maraqishiya harara ta fice daga parloun,"
Daďi taji ya ziyarci zuciyar ta cike da murna tabi bayan ta da sauri, tana qiran sunan ta umma umma tsaya kiji,"" har takai bakin get ta dawo da baya tana duban ta cike da gadara, tace faďi bukatar ki meke tafe dake sauri nake zan tafi karki bàta min lokaci,""dariyar karfin hali tayi tace Umma babu komai dama godiya zanyi miki kin taimaka min sosai ranar da kikasar dani maganar auran nan nagode matuka a gaskiya kin cika sirika ta gari Allah yaqara girma,," Himmm tayi tana murmushin da ko baki bai iso ba tace, Maraqishiya kenan wani sa'in hankalin ki kaďan ne wlh ki zauna nan kisa ido wanan masu zubin yan wutan ta kwance miki gida, ķur'anin Allah kina ganin ta simisimi kamar saliha to wlh ba yar arziki bace, ba gida kaďai mijin ki ma sai ta hanaki ganin sa zauna wasa yarinya,"
Murna fal ranra tayi shu'umin murmushi, tace Umma idan kina tare dani ai saidai mu muga bayan ta Amma ba ita ba, nifa wlh tunda idanuwa na suka sauķa kanta naji mugun tsanar ya shige ni ai ranar saida na wanke ta da mari lafiyayyu biyu da badan ya tare ta ba da saina kakkarya ta wlh,,"
kinyi min daidai umma ta faďa tana mugun murmushi tare da dafa kafaďar ta tace kici gaba karki fasa nima ina nan nima da kanta zata kwashi tsinannun qafafun ta tabar gidan," tana kaiwa nan ta juya ta fice a",, yatsan ta saka a baki tana girgiza kai tare da murmushin mugun ta ita kaďai tasan me zai faru nan gaba yanzu aka fara yaķi tunda Umma ma ta goya mata baya yanzu komai zai taho mata da sauki ta ďauka ita ďaya ce ashe fa.. kaďa kai tayi ta zagaya bayan gidan taqi bi ta parlou bare ta haďu dasu ta wuce kitchen neman abinci dan wani mugun yunwa da taji cikin ta naji,"
Jiyowa yayi ya kalle ta ya tako wajan ta tana zubar da hawaye inda take tsaye tun fitar Umma takasa yin ķaķkawan motsi zuciyar ta sosai yake bugawa tana fargan zaman da zatayi a gidan nan tun yanzu tafara cikin karo da tashin hankali inaga in anyi gaba sosai hawayen ta ke zuba cikin kunar rai",, kamo hannayen ta duka biyu yayi yana kallon ta tare da kai hannun sa ďaya yana share mata fuskar ta, yasan me takewa wannan hawayan, yace haba matar meye na kuka, dan Allah ki daina bàta min hawayan ki kan maganar umma babu abinda zata miki kawai dai ta faďa ne ni nasan ta, dan haka kiyi shiru kinji zo muje ciki," shiru tayi masa batace komai ba, ya ďauke ta kamar yar baby ya shige da ita ďaki ya dire ta ta tsaya da ķafafun ta daf da shi ya zagaya da hannayen sa zuwa bayan ta yana sinsinar ta yafara zuge mata zif ďin riganta yana lumshe idanun sa fuskar sa ďauke da murmushi,,"
Ganin abinda yake shirin yi yasa ta riqe hannayen sa ta ďago da kanta ta kalle shi har yafara canza ya nayi," shagwabè masa fuska tayi tare dakai hannayen sa kan cikin ta tace yunwa pls wlh rabo na da abinci tunda na shigo gidan nan bazan iya komai ba karfi na yaqare," cikin shagwaba tayi maganar kamar yarinya qarama,,"
Mamaki ne ya cika shi matuka ya shafi cikin ta shamilak dashi kamar fanko yace babyna meye ya hanaki cin abincin ba' a kawo bane?," kai ta girgiza masa alaman Eh tace tun fitan ka banga an kawo komai ba,," cike da takaici, yaji haushi dan yasan saida yasa a gida ayi abinci akawo tunda akwai baki, to meye yahasu kawowa gashi sun bar mishi mata da yunwa," ajiyan zuciya ya sauķe yace,," shikenan jiyo in rufe miki zif ďin sai muje muci a waje,,ba musu ta juya masa baya ya rufe mata, tana kallon sa tace ka nuna min kitchen in shiga in dafa basai muci a waje ba ji take baza iya jure har suje waje suci ba", A a ďauki mayafin muje yaushe zaki dafa da wuri kici yanda naga yunwa ya shige ki? fito muje kawai", bata masa musu ba ta shige toilet ta canzo kayan ta zuwa baķar abaya ta yafa gyalen ta fito," yana gyara a gogon hannun sa ta sameshi a hankali tace na shirya," kallon ta yayi sosai ganin shigar tayi masa kyau matuka, cike da zolaya yace ke shikenan koda yaushe kina cikin bakin kaya saikace balarabiya," murmushi tayi ta wuce gaban madubi ta tsaya gyara fuskan ta wanda ya canza dan kukan da tayi," sama sama tayi kwalliya ta feshe jikin ta da turare,,"yana ganin ta, yace nifa abinci nace muje muci, Amman kin tsaya kwalliya kamar mai shirin zuwa wajan biki Allah ki goge kwalliyar nan kona fasa," dariya tayi masa tace to haka kakeso na fita da fuska na babu kyan gani? A a to waye ya isa ya gane min ke, shiyasa banso kiyi kwalliya dan haka goge tun wuri kafin nayi da kaina,"
Fuska ta canza ta ďan murmushi tace cikin muryan ta mai sanyi nifa harga Allah qara min yunwar nan kakeyi muje ni karna sume maka yanzu,", dariyar sa me kyau yayi yace nasan kuwa zaki aikata muje sai in mun dawo ma qarasa,"
Gwanin ban sha'awa suka jera suka fito suna hira cikin nishaďi,""Maraqishiya suka gani tana kwasan lomar indomie tana kaiwa bakin ta kamar wanda ance mata za'a ďauke abincin,,"tafiyar su sukaci gaba dayi yana kallon ta baice mata komai ba har suka fice",, tashi tayi tsaye ta ture indomie tabi bayan su da gudun ta same su har sun shige mota yana shirin tayar wa,""
Kanta ta leķo ta glass ďin motar tace, meye ma'anar ka? kina nufin fita zaku kubar ni inci kaina kenan?, to wlh baku isa ba ko katafi dani duk inda zaka da ita kona hanaku fitan kasan zan iya ba qaramin aiki na bane", mugun kallo yayi mata cikin zafin rai yace bàtsa kibani waje kona kaďai ki anan," ďaga kanta tayi tana haďa rai tace, jirani ina zuwa wlh dani zaka tafi," ciki ta koma dan ďauko mayafin ta," yana ganin ta shige ya tashar da motar mai gadi ya buďe masa get ya fice Humaira tace masa ai da kajira ta mun tafi tari hakan ba daďi", bai bata amsa ba yaci gaba da tuqin sa ran sa abàce,"da sauri ta shige ďaki ta ďauki mayafin ta fito haraban gidan inda ta barsu tana rarraba idanu bata gansu ba," cike da jin haushi tana kaďa kai ta koma ciki tasa makulli ta dantse ķofar parloun dashi tace, zakusan ni kukayi ma wannan iskanci inga ta inda zaku shigo idan kun gama yawon shashancin naku...
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:08] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA* 🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT_M_S* ✍🏻
*Page*
*21*
*Sadaukarwa ga qawata Aminiya ta Aisha gentle lady Abar kauna ta akoda yaushe*😘😘
_Waiyyo Allah tawan ki agaza mana kar hawan ruwan mu yatashi agan mu a asbiti dan Allah Anwar ya dawo salma taga azaban duniya ya ishe ta haka pls_ 😭😭
Tuqin motar yake cikin gudu ya ďauki hanyar da zai kaisu, City Restaurant, yana sauri yaga sun isa dan yanda yaga yunwa ya shige jikin ta sosai, ransa yayi matukar bàci,"dogon tsaki yaja, tare da dafe kan sa," tunani iri iri fal a ransa ya rasa gane dalilin da yasa ba'a aiko da abinci ba bayan ya sanar dasu tsaki ya kuma yaja akaro na biyu", gani yake gaba ki ďaya wajan ya masa nisa, hakan ya sanya yaqara gudun motar kamar zai tashi sama,,,,sosai yana yin ta ya canza ganin shi baya cikin walwala, tasan yayi haquri da juriya ba iyaka yana matsayin angon da ya tare jiya," can cikin maqoshin ta ta sauķe numfashi ta jiyo da kanta ta kalle shi,"" hankalin sa yana kan tuqin da yakeyi," Hannunta ta ďaga takai kan kafaďar sa, ya jiyo da idanun sa da suka canza launi dan bàcin rai, ya kalle ta,,,sanyanyar murmushi ta sakar masa tana shafan kafaďar sa ta buďe bakin ta a hankali tace,""
Pls habibty ka rage gudun motar tayi yawa," murmushin shima ya qiqiro ya sakar mata yanaci gaba da tuqin, yace kin manta yunwa ne sosai yake cin jikin matata ai bani ba kwanciyar hankali?,," dariya tayi har saida fararan hakwaran ta suka bayyana da jin daďin furucin sa,"kwantar da hankalin ka tace dashi, ai ta daina jin yunwar yanzu,"
"Yana karya kan motar cikin sigar wasa yana kallon gaban sa yace," A a ban yarda ba nidai karki yaudare ni, gashi ma mun iso pls tayi haquri,""murmushi kawai tayi ta kawar da kanta gefe tare da ďauke hannun ta daga kafaďar sa,,"
Parkin space ya samu yayi parkin tare da kashe motar, ya jiyo ya dube ta yace, muje ko?,"kai kawai ta ďaga masa ta buďe ķofar ta sauķa,"" sauķa shima yayi, ya zagayo inda take ya kamo hannun ta, yana murmushi yace sorry fa matar," kawar da kai tayi tace kaifa ka cika surutu dayawa tana haďa fuska cikin wasa,"" dariya yayi yana riqe da ita suka shige yaja mata,"
City Restaurant wajan cin abinci ne dake cikin garin katsina haďaďďe nagani nafaďa, ya tsaru iya tsaruwa, kana gani kasan namasu hali ne bana qananan mutane ba,"" kujerun da aka tanadar wa masu zuwa cin abinci, sukaje yaja mata ďaya ta zauna, shima ya zauna kan wanda yake kallon nata,"" ďaya daga cikin ma aikan wajan ne yazo inda suke, ya gashe su cikin girmamawa, tare da tambayar mai za'a kawo musu?,, "lafiyayyan abinci yasa aka kawo musu," a hankali ta soma kaiwa bakin ta tana ci tana taunswa kamar magani," kalon yana yin ta yayi, ya ďauki loma ďaya daga spoon ďin hannun sa ya tura mata bakinta", bata an karaba ta ďago idanunta ta kalle shi, tana haďa fuska tace, meye haka mutane suna kallon muf....bai bari ta qarasa maganar ba ya qara tura mata wani, yana dariya yace maza cinye in qara miki wani ,"kicinkicin tayi da rai ta zumbura masa bakin ta wanda ya cika mata da abinci, tanaso tayi magana Amman ta kasa, haka ta daure tana taunawa har ta haďye shi,," wani ya kuma kaiwa bakin ta da niyar tura mata," tayi saurin kawar da kanta gefe, tace dan Allah ka daina,,murmushi yayi ya kai abincin bakin sa yana kallon ta, yace, yadai matar kici mana zaiyi sanyi fa,"" naqoshi tace masa tana ture plet ďin gefe guda,"" ci gaba da kallon ta yayi, yace, ko kici da kanki kona baki da kaina har ki cinye dan bazan barki ki koma gida da yunwa ba,""yana shirin kai mata bakin ta yayi maganar," ganin da gaske tura bata zaiyi yasa tayi saurin qiqiro murmushin dole tace kabari zanci da kaina,"" qyale ta yayi tafara ci yana kallon ta da idanun sa yanda take cin abincin..
Cike da nutsuwa takeci har ta kammala, idon sa na kanta, ya zuba mata su, yana kallon ta" da yake shi ya gama da cin nashi ,," hannun ta takai kusa da fuskan sa ta kaďa tace lfy malam yada kallo haka fa??," murmushi yayi ya fuzar da iska ta bakin sa, yace, dan ina kallon matar nawa ma shine sai an tuhume ni? himm nidai tashi mutafi magariba tayi, tafaďa bayan ta miqe tsaye,"
Ma aikacin wajan wanda ya kawo musu abincin ya qira ya bashi kuďin abunda sukaci, tare da miqewa suka jera suka fito haraban restauran ďin inda yayi parkin motar sa,," buďe mata ķofar yayi ta shiga shima ya zagayo ma zaunin sa ya shiga ya tada motar suka bar wajan...
Basu wani daďe ba suka iso gida dan yanda yake sharara gudu kamar zaibar duniya, tun tana korafi har tagaji ta rabu dashi, wai shi yasaba bai iya tuqi a hankali ba kamar mai koyo "" hoon ya danna mai gadi ya buďe masa ya shiga yayi parkin tare da kashe motar ya sauķo,"" itama sauķa tayi suka nufi ciki,," murďa ķofar parlon yayi yaji a kulle, bugar ķofar yayi yafi a irga yaji shiru bata buďe ba," hakan yasa ya shiga bugawa da karfin sa kamar zai bàlla,"" tana kwance a ďakin ta a gado tanajin yanda yake buga ķofar, dariyar mugunta tayi a ranta tace, cigaba dayi malam kaďan ma kagani dani kuke wasa,,,, mamaki ne ya ishe shi matuka,"ya juya wajan mai gadi ya tambaye sa ko ta fita ne?," A a ya bashi amsa da cewa shidai tun fitan su baiga ta fita ba, dawowa yayi yace gaba da buga ķofar yana kwala mata qira tsit kakeji taki buďewa", dafa shi humaira tayi tace, kayi a hankali karka karya ķofar hala ko bacci takeyi," ba wani baccin da takeyi idon ta biyu, yafaďa yana cigaba da bugawa,"
"To bakada wani ma kullin ne a wajan ka? ta tambaye sa tana duban sa," dafe kansa yayi da hannun sa yaja godon tsaki, shi gabaki ďaya kaf ya mance yanada wani ma kullin a gunsa ya tsaya yana shan wannan wahalar ,"" motar sa ya koma ya shiga ya ďauko tare da rufe motar ya dawo yasa ya buďe musu suka shiga,," kai tsaye hanyar ďakin ta yayi da niyar yaje ya sameta," humaira tayi saurin ta rosa tana girgiza masa kai alamar a a tace,"
Dan Allah ka rabu da ita kasan ko barci ne ya ďauke ta yasa bataji ba,"" cike da bàcin rai ya dakata da tafiyar, yace wanne irin bacci ne wanda zaisa bazata ji wannan bugun ba, ai ko mutuwa tayi yaci ace ta motsa,"" murmushi tayi masa ganin yanda yake maganar cikin faďa, tace sorry kayi haquri mu shiga ciki kaga ana qiran sallah karka makara masallaci,"ba musu taja hannun sa suka shiga cikin ďakin ta,,
Tana leqan su ta jikin ķofar ďakin ta tanajin duk abunda suke faďa har suka shige, tana leqan su, girgiza kai tayi tana cizan lebàn bakinta na qasa ta rasara ta ina ya samu makulli har yayi nasaran budè musu ta ďau alwashin, da yau saidai suyi kwanan waje, Amman aikin ta baiyi kyau, bakin gado ta dawo ta zauna a zuciyar ta tana haďa shirin ta na gaba wanda zata aiwatar dan su da zama lfy kam yaqare har abada,,"
Toilet ya shige yafara ďauro alwala ya fito itama ta shiga dan ďauro nata alwalar,," fitowa tayi bayan tagama ta same shi yana shirin fita, ya ďaga kai ya kalle ta, yace to matar ni na wuce masallaci sai nadawo tare da kai mata kiss gefen kumatun ta ya fice yana sauri dan kar yayi missing sallah,"" kai ta girgiza fuskar ta da murmushi ta zari hijabinta tasa ta tada sallah,,
**
Yana nan zaune bayan an idar da magariba yana karatun alķur'ani mai girma suratul baqara,,,bai bar masallacin ba saida ya jira akayi isha'i dashi, ya zauna gefe yana tasbihi," Sai wuraren karfe tara yabaro masallacin ya shigo gida,, kai tsaye ďakin ta ya wuce,ya shiga bai ganta ba yaji motsin ruwa a toilet alamun wanka takeyi," murďa ķofar toilet ďin yayi yaji a buďe yana murmushi ya tura ya shiga,"" jikin ta har fuskar ta ta mulke shi da kumfar sabulu," tsayawa yayi ya zuba mata idanuwan sa tare da harďe hannayen sa a bayan sa yana kallon surar jikin ta," Tabarakallahu masha Allah ya furta can cikin maqoshin sa," wankan ta take hankali kwance ta juya masa baya hakan yasa batasan a kwai mutum a bayan ta ba,," kayan jikin sa ya cire batare da yabari tasani ba ,"daga shi sai bes da gajeran wando ya rage masa, a hankali ya soma takawa har yakai inda take, yasa hannayen sa duka biyu ya zagaye ta dashi tare da maqala kansa jikin kafaďar ta yana sinsinar wiyar ta,"" a razane ta jiyo da fuskan ta sukayi ido huďu dashi, ya sakar mata da lausassar murmushi cikin sigar wasa, yace,"
Haba babynah yanzu kin kyauta kenan, zaki shigo wanka bazaki jira in dawo muyi tare ba?,"yunqurin kwace jikin ta tayi daga nashi kunya duk ya ishe ta Amma ta kasa dan runguma mai kyau yayi mata," fuska ta haďe tayi kicinkicin da rai, tace meye haka ne dan Allah zaka shigowa mutum toilet yana wanka?,," dariya yayi yace, ni da matar tawa ma sai an tuhume ni?, to bari kigani tare zamuyi wanka sai inga wanda ya isa ya hanani," sakin ta yayi yafara cire bes ďin jikin sa ya saura masa gajeran wando," hannun sa yasa da niyar cirewa yana kallon ta yana dariya," runtse idanun ta tayi ta durqushe qasa a wajan tana kare jikin ta da hannayen ta, ta budè baki tace, Waiyyo dan Allah ka daina wannan abun kafita kabar ni banaso,,"
Tsayawa yayi da cire wandon yana dariyan jin yanda tayi maganar, yakai qasa inda take durqushe, ya hura mata iska ta bakin sa yace, haba mana matar mijin kine fa kike cewa ya fita..shafan gashin kanta yayi cikin qasa da murya yakai bakinsa kunnen ta yaqara cewa pls angel kibari muyi tare mu raya sunnar manzon Allah mana,"lumshe idanuwan ta tayi tanajin yanda yake shafar gashin kanta, zuciyar ta na bugawa, ta kasa Kyakkyawar motsi,,"a hankali ya ďago ta ya juyo da ita, yana kallon yanda ta maqure jikin ta da hannayen ta tana kakkare ķirjin ta," murmushi yayi yaqara duban fuskan ta, yace kin amince matar in shigo muyi tare?,"
Shiru tayi masa takasa haďa idanu dashi dan wani irin mugun kunyar sa daji ya shige mata zuciya", jin tayi shiru batace komai ba, yasa ya shiga bahon wankan, a hankali ya rungume ta tsam ajikin sa, yana sauķar da wani irin numfashi A hankali,"" luf tayi cikin faffaďar ķirjin sa bata motsa ba, har na sawon wani lokaci, kafin ya ďago da kanta yana kallon cikin kwayar idon ta ya ďauki sabulu, cikin salon soyayya yakai qaramin bakin sa kan nata yafara tsotsa idanun sa ya lumshe cike da nutsuwa yake bin duk jikin ta da hannayen sa yana shafan ta da sabulun yana jin wani irin shauķi a cikin zuciyar sa...
Zaman ďakin ne taji ya ishe ta ta dawo parlou tana kallon ķofar ďakin Humaira, takasa zaune takasa tsaye sai safa da marwa takeyi ita ďaya," qaramin yatsan hannun ta tasa a baki ta ciza ta kasa zama, ji take zuciyar ta bazai tabà jurewar mijin ta ya kwana da wata mace ta qyale ba",, nemar mafita take ido rufe takasa samu idan ta tuna wannan sai taga beyi mata ba haka har ta gaji da tsayuwa ta samu kujera ta zauna ta ďaura ķafa ďaya kan ďaya tana girgizawa, can ta miqe tsaye tayi hanyar ďakin Humaira ta murďa taji a rufe, kaďa kai tayi ta wuce kitchen, tana aiyya na abu iri iri a ran ta..
Saida yagama mulke ta tas da sabulu shima yayi ma kansa tare da kunna musu ruwan shower a kansu ya ďauraye musu jikin su yana shafan ta, kafin ya kashe ruwan ya fito daga cikin bahon wankan itama ya fitar da ita kanta a qasa takasa haďa idanu dashi gabaki ďaya kunyar sa take ji yana mamaye ta," babban towel ya ďauka ya nannaďe ta dashi shima ya ďaura towel a kunkumin sa yana kallon ta ya ďaga ciďak kamar ýar beby yafito dasu ya ajiye ta a bakin gado, ya kwantar da ita shima ya hau gefen ta daf da ita yajata jikinsa yafara warware mata towel ďin da ya ďaura mata, duk tana jinsa Amman batayi yunqurin hanasa ba, dan itama ya riga da yagama rikita mata lissafi, duk wani tsoro da fargaba da takeyi ta danne shi," sosai jikin ta ya ďauki rawa da jin rikitattun saqon da yake aika mata, sosai ya fice a hayyacin sa yau kam ya ďau al washin samun abinda da tunda akayi wannan auran bai samu ba..
Tabàrya ta ďauko a kitchen ďin ta dawo ta fara dukan ķofar ďakin zata bàlla kamar wata sabuwar kamu tana huci ji take duk abinda suke zuciyar ta bazatayi haquri ta qyale su suci amanar ta ba bayan tana numfashi a doron qasa,"
A hankali ta tsayar dashi da abinda yake cikin kasalalliyar murya tace masa wani yana buga ķofa,, ajiyan zuciya ya sauķe ya koma gefe badan yaso ba yana saukar da nauyayan numfashi, da yake shima yaji", bugun ķofar ne yaqara razanar dashi ya tashi zaune ya duba a gogon gefen yaga karfe goma har ta gota cike da mamaki ya miqe tsaye ya zari jallabiyar sa dake gefe yafara sawa,,"" banko ķofar ďakin tayi ta shigo hannun ta riqe da tabàrya tana huci ďan kwalin kanta ta ďaure shi a kunkumin ta cike da masifa take bin ko wannen su da idanu....
*Hafsat_Moh* ✍🏻📚📚
[30/08, 18:08] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA* 🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M* ✍🏻
*Page*
*22*
*Sadaukarwa ga qawata Aminiya ta Aisha gentle lady abar kauna ta*😘
Assalama alaikum yan uwa kuyi haquri da rashin jina da kukayi jiya wlh saida nagama editing kafin nayi posting ina kunna data nayi losing wanda nayi editing shiyasa kukaji shiru jiya ga aiki ya min yawa bare nayi wani😭😭😭
Dan Allah ina neman tayin Addu'ar ku wlh my lovely brother bashida lfy sosai yanzu haka an riqe shi a asbiti wannan shine dalilin da yasa bansamu damar yin posting da wuri plss I need ur du'ah thanks 🙏🏿🙏🏿
_Tunatarwa ce_👌🏿
*An karbò daga Abdullahi ďan abbas Allah yaqara musu yarda yace: Manzon Allah tsirada amincin Allah sut abbata agareshi yace: duk mai komawa kyautar sa kamar kare ne yayi amai sannan yakoma ya lashe aman sa*
*Bukhari da Musulim ne suka rawaito,,, Allah yasa mudace Amen* 🙏🏿🙏🏿
Cikin kiďimewa take binta da ido tana kallon ta tare da kakkare jikin ta tana dukunkunewa cikin bargo tana neman hanyar tashi tasa kaya Amma babu hali, haka ta maqale inda take tana cigaba da binta da ido gabaki ďaya kanta ya kulle zuciyar ta yakasa tantance mata wanda take gani"" binta da kallo yake zuciyar sa na raya masa abubuwa iri iri shin wai wannan matar shi da yasani ne tafara hauka?,,,can yanisa yana ci gaba da binta da ido ya buďe baki yace, ke meye haka lfy kike me ya shige miki kwakwalwa zaki ballawa mutane ķofa ki shigo kamar mahaukaciya??
qarasa shigowa tayi tana binsu da mugun kallo,"" ita ko sai qara jan bargon take tana rufuwa da yake ba riga a jikin ta,"" kallon shi da kyau tayi cikin ďaga murya ta qira shi da sunan shi tana kaďa jiki, tace Abdul malik kenan ai idan haukane na ďade da haukacewa, Amman bazaka gane ba a yanzu,," tabàryan dake hannunta ta ďaga tayi setin Humaira dashi, tana zare ido, ke kuma karuwar banza karuwar wofi, yar iska muje ni dake, zakisan ba'a shiga gona ta, karki yaudari kanki kice kinyi nasaran auran mijina, to ķur'anin Allah zakiyi kuka da kanki duk wani mai hali irin naki saiya shafawa kansa ruwa,, kibar tunanin ina numfashi a doron qasa zan iya bari karuwancinki da kisisinar ki yayi tasiri akan mijina, Sam wlh tun wuri ki canza shawara yanda kikasan ake zaman makabarta to shi zakiyi a gidan nan dan kanki idan kinji azaba zaki nemi inda dare ya miki,, zungurin goshinta tayi da tabàryan,, shegiya baķar aljana yar isk....kunnunwansa kasa iya jure kalaman ta yayi, taji ya kame mata bakin ta da hannun sa, ransa a bàce,, cikin zafin rai, yace wlh idan kika kuskura kika qara buďe bakin ki da niyar zagin ta to ina mai tabbatar miki bazaki gane kamannin ki ba,idan kin musa kuma bisimillah, tabàryan ya warce daga hannu ta ya cilla shi gefe tare da yi mata nuni da yatsan hannun sa alamun ta baçè masa da gani ,"
dariya ta kwashe dashi kamar ta bàbbiya tana shewa yanda ya nuna zagewar sa,, tace inaga saidai ka bàtar min da kammanni na, Amman indai akan wannan shegiyar nan ne bazanyi shiru wata yar iska karuwan layi taci galaba a kaina ba saidai idan na mutu,,,harzuqashi kalaman ta suka qarayi cikin zafin nama yaja hannun ta ya fitar da ita a ďakin," kwace hannun takeyi daga riqon da yayi mata, cikin masifa take tana dirdirjewa, yayi banza da ita, kai tsaye ďakin ta ya wuce da ita kafin ya sake ta ransa a bàce ya juya ya fice a ďakin baice mata qala ba,,,zage zage take tana surutai marasa daďi billahillazi la'ilaha'illahuwa zakaga tashin hankalin da baka tabà gani ba wai har ni zakayi ma walaqanci kan wata yar iska karuwan...shiru tayi cikin kunar rai tayi zaman dirshem a filin ďakin,,,ji take kamar tayi hauka ko kuka,hala taji sauķin bakin cikin da take a yanzu, hannun ta ta murza akanta tana yamutsa gashin, ta ta rasa ta ina zata bòllowa lamarin nan duk abinda tasoyi gani take baya mata aiki,,""
dawowa ďakin yayi zuciyar sa babu daďi ya qaraso inda take ya zauna a bakin gadon, tana kwance idonta a lumshe kamar mai bacci," hannun sa yakai goshin ta yana shafawa a hankali ta buďe idon wanda ya cika da ruwa suka sauķa cikin nashi so take tayi kuka Amman ta danne batason ďaga masa hankali," murmushi ya sakar mata yana mai bata haquri cikin sanyayyar murya kiyi haquri dan Allah, kinji matar am sorry,, murmushin..bakinsa ta kame da hannun ta alaman yayi ta qiqiro murmushin yaķe da baikai gefen baki ba, ta miqe tsaye tare da ďaure jikin da bargon batace masa qala ba, tayi hanyar akwatin ta ta ďauki dogon riga na bacci ta shige toilet, duk yana ganin ta yarasa mai zaice mata tagumi yayi da hannayen duka biyu yana shafan sajen sa, tare da busar da iska ta bakin sa, zuciyar sa nayi masa zafi,, haka ta fito ta sameshi, da kayan baccin ta a jikinta ta qaraso inda yake, tana kallon sa yanda ya shiga damuwa ta sakar masa da kayataccan murmushi tace,"
Dan Allah karkasa kanka a damuwa, nifa banyi fishi ba, komi ya wuce pls kazo mu kwanta saida safe ta haura gadon,"" nauyayan ajiyan zuciya ya sauķe, ya yana zancan zuci ta wanne hanya zai bùllowa lamarin nan, sai lokacin da yagama fita hayyacin sa sha'awar sa tagama tashi yana dafda ya sauķe sa, za'a shigo masa da tashin hankali," godon ya haura ya kwanta kafin ya lumshe idonsa yana saqe saqen neman mafita inda zaije ya sadu da matar sa cikin kwanciyar hankali batare da wani yamusu cikas ba,,"a nutse ta mirgino gefen sa tayi matashi da ķirjin sa tanajin yanda numfashin sa yake sauķa,,a hankali ya buďe idon sa yana kallonta yasa hannayen ya rungume ta tayi luf ajikinsa tanajin wani iri a ilahirin jikin sosai yagama ďaga mata hankali,,," haka suka rufe ido da niyar bacci kowa da abinda yake saqawa a ransa,,"
"Ji tayi zaman da tayi ba karbèta zaiyi ba zumbur tayi saurin tashi zuciyar ta na ayyana mata munanan abubuwa idan ba komawa tayi ba zuci gaba da abinda bazata iya jure ganin mijin ta yanayi da wata mace ba a doron duniya, bata tsaya bata lokaci ba, ta qara komawa ďakin har tana tuntubè dan sauri,,,ganin su manne da juna yaqara tashar mata da hankalin ta ba kaďan ba ji take kamar numfashin zai ďauke, idan ta qyale su a haka," cikin ďakin ta qarasa shiga," cike da zafin rai tasa hannu ta janye ta da karfi taraba ta dashi,har zuwa qasa kafin ta dire ta, tahaye gadon ts manne da jikin sa,,,cikin mamaki yake binta da kallo, itama shi take kallo ta haďe fuska, kamar bakin hadari tayi banza dashi tana girgiza ķafa ďaya,,,,kasa magana yayi ya miqe zaune tare da dafe kansa a hankali ya furta ya salam, damuwa fal a zuciyar sa ya rasa me zaice da ita, gani yake kamar hauka ya tabà mata kwakwalwa tunda yake bai taba saninta da haka ba,"
Runtse idonta tayi sosai tanajin wani irin baķin ciki yana shige mata zuciya,,take taji kuka ya taho mata mai zafi wannan karon kam kasa dannewa tayi, tabarshi,, sosai take kuka tanajin takaici da wannan tashin hankalin, meye take nema da ita? meye ta tare mata da zaisa ta hanata kwanciyar hankali? hasalima yaushe ta shigo gidan? kuka take sosai mai tsuma zuciya ta rasa mai bata amsa,,ganin zaman ta bashida amfani yasa ta miqe tana shashsheqar kuka ta fice a ďakin ko kallon inda suke batayi ba,,,
har cikin ranshi yake jin kukanta,, jiki babu kwari ya tashi da niyar bin bayanta, yaji an damķe jallabiyar jikin sa ta baya,,, ransa a bàce ya jiyo ya dubeta, tana masa kallon tuhuma, tace meye ma'anar ka? binta zakayi kabarni a ďakin? to wlh baka isaba bawata shegiyar da zan bari kabi,,, fisge rigansa yayi ransa in yayi dubu ya bàci,,, yatsan sa ya nunata dashi da niyar mata faďa, yaga ba amfanin hakan tunda ba' acikin hankalinta takeba,,qyale ta yayi ya fice a ďakin batare ta yatsaya ya sauraren surutan taba,,"
kwance ya sameta kan doguwar kujera tana sharan hawaye,,ya iso inda take yasa hannu yana share mata fuskar tare da girgiza mata kai alamun tayi shiru bayaso,,kukan taji ya qaru mata,, na takaici sosai hankalin ya tashi yajata jikinsa yana bubbuga bayanta,,"
fitowa itama tayi tabar ďakin tana girgiza kai wato ni suka mayar yar iska, fitinanniya ko? to muje zuwa,,a parlon ta tarar dashi, yana aikin lallashi..wani shu'umin murmushi tayi na mugunta, shegiya baķar yar iska yanzu kika soma kuka ai idan nine,,,a takaice dai yanasu kwanciyar hankali tayi cikin wannan daran, ransa ya bàce sosai, ya zazzage da masifa Amma duk a banza haka yagaji dan kansa ya qyale ta,, ķarshe haka suka kwana a parlon har asuba tayi humaira ta kasa rumtsa idonta dan tashin hankali, shima kusan idon sa biyu garin ya waye dan damuwa,, haka ya fice masallaci, itama ďakin ta ta koma ta shige toilet ta ďauro alwala ta fito kafin ta tayar da sallah haka sukabar ta nan kwance tana sharan bacci,,
Sai wuraran karfe tara da rabi ya shigo gidan hannun sa riqe da abun karin kumullo,, a nan parlon ya tarar da Maraqishiya tana sharar bacci da alama ko tashi sallah batayi ba,, girgiza kai yayi yana wadari da wannan halin da fara,, kafin ya wuce ďakin humaira,,, samun ta yayi zaune a gaban madubi tana ďaura ďankwali tana sanye cikin ďinkin riga da siket na atamfa mai ruwan jaa,, sosai ya zauna a jikinta daram yamata kyau,,,a bakin gado ya zauna ya juya yana dubanta fuskan sa ďauke da murmushi yace Matar yauma wankan kikayi ke kaďai baki jira nadawo munyi tare ba?,,
tana jinsa ta kawar da kai gefe ta taso ta rusuna har qasa ta gaishe shi cikin daddaďan muryan ta,,amsa mata yayi da lfy kafin yace zauna muyi karya, babu musu ta gyara zama ya buďe musu soyayyan dankali da egg,,cikin mamaki take bin dankalin da kallo to a ina ya samo wannan abici kodai gidansu yaje ya kawo.. shiru tayi tafara kaiwa bakinta tanaci,, sama sama yake jefa mata hiran soyayya yanaso ya mantar da ita baçin rainda take ciki...
Da sallama shiwari ta turo ķofar parlounta shigo tana dube dube, masu gidan musunan ne?,,, hango ta shabè shabè zube tayi tana sharar bacci kamar wanda tayi aikin noma ta gaji baki riqe take mata kallon mamaki, ta shiga tashin ta tana qiran sunan ta,,,a firgice ta buďe ido tare da miqewa tana dogon hamma,,ke kuma shiwari yaushe kika shigo bansani ba?, Yoo ina kuwa zakisani bayan kin zube filin parlou kina sharar bacci saikace jaka,,,Himm kedai bari kawai wlh bansamu bacci bane jiya shiyasa kika ganni haka,,cike da rashin fahimta take binta da ido, bangane bakisamu bacci ba mai yahanaki yi?? ke shiwari baganewa zaki zo mushiga ciki nayi miki bayani,,, ďakin suka shige Maraqishiya tayi hanyar toilet ta ďauro alwala tare dayin brosh kafin ta fito ta gabatar da sallah,,,,mamaki yagama cikata,, wai sallahn me kikeyi ne war haka??
Asuba mana wani abu ne? tace da ita tare da dawowa bakin gadon ta zauna kusa da ita,,, a a gani nayi ai asuba ta wuce, yanzu fa goma ake nema,,kinga malama dan Allah ya isa wannan tuhumar taki muyi abunda ya kawo ki,,,Murmushi shiwari tayi tace, ai kema kinsani idan a shirye kike kawai taso muje gun wannan malamin kinsan aikin sa ba makawa,,,Dan manzon Allah kibar maganar nan shiwari idan kinada wata shawara daban kawo inaso Amma banda harkan malamai ko bokaye,,,,To ai sai kizauna nan sanķarau ya kashe ki wata shegiyar yarinya tayi miki rufin da babu ruwa,
dama nasan ba amincewa zakiyi ba kinga tafiya kayi abunda kikaga yafi miki,,,jakanta ta ďauka ta zari mayafin ta da tacire tayi hanyar fita,,"
Yi haquri dan Allah dawo qawata baza'a ji kanmu ba ai, tace da ita tana jan hannun ta ta zaunar da ita,,,yanzu dai kawo wata shawara, kinga jiya ma hanasu kwanciyar hankali nayi firr dan rainin wayo zai ďauke ta yafita da ita ni gani yar shegiya ba'a san da qurata ba, ko gidan uban wa sukaje ma ohho,,, wani shu'umin murmushi tayi tace qawata ke ďin mai kyau ce wani lokacin, kinyi daidai wannan kaďan kikagani sai kin tashi tsaye,, Amman wani hanzari ba gudu ba, kawo kunnan ki kiji wata shawara kafin kin amince da zuwa wajan malamin,,matsowa tayi ta raďa mata a kunne,,, cike dajin ďadin shawarar ta kwashe da mugun dariya,, gaskiya zan kawo haske idan ina tare dake,,,cigaba da hira sukayi suna shewa,,Maraqishiya ta fita kitchen ta dafo musu indomie da egg ta kawo suka faraci suna kulle kulle,"
****** *******
🌾🍃🌾🍃🌾🍃🌾
Kuka take sosai tana shashsheqa fuskan nan duk ya bàci da hawaye da majina sanye take da rigar atamfa daban zani daban irin na yan kauye sai jeka ka dawo take tana zuba kurmatsan kayanta cikin jaka,,, Umma ta turo kofar ďakin ta shigo, cikin tashin hankali ta shiga tambayar ta, ke kuma Suwaiba ina zaki kike harhaďa kaya cikin jaka, ko wani abun aka miki ??,, kai ta kawar taqi kulata taci gaba da tusa kayanta cikin jaka, tana gamawa taja zif ďin ta zuge tare da saka guntun hijabi ta ďauki jakar ta tayi hanyar fita,,, ganin ficewa zatayi da gaske yasa umma saurin damqo hannunta tana kallonta cikin ruďewa, tace haba Suwaiba kiyi haquri kisanar dani ďan iskan mutumin da ya tabàki kinji?,, kuka taqara fashewa dashi tace ni bana bukatar wata magana ki rabu dani na koma kauyan mu yafi min kwanciyar hankali kullum sai kice min zaki aura min Abdulmalik Amman kikabar shi ya auri wata yarinya daban ba ni ba, bayan kinsan irin sonda nake mishi zan iya rasa raina akansa kika kasayin komai,"
Himm suwaiba kenan yanzu akan Abdulmalik ďin ne kike wannan kukan harda komawa gida? kin mance nine na ďauko ki da kaina kuma ni nayi miki alqawarin auran sa? ďana ne ni ďauki cikinsa har na tsawon wata tara, ni nakeda iko akan sa karkiga wannan auran da yayi zaiyi sanadiyar hanaki shiga gidan sa, Sam ko kusa share fuskar ki kibiyo ni,,
Tana sharan hawayan fuskan ta tabi bayanta suka fice,,,karo sukaci da Batula, a parlou tana tahowa baki riqe take kallon su, tace Umma lfy dai ina zuwa haka da wannan ranan?? inda kika aike ni bata amsa a takaici ta wuce ďakin ta ďauko mayafi kafin ta fito, ta dubi suwaiba tace biyo ni muje,,,
Umma badai kina nufin gidan Yaya zakije ba wannan karon ma? gidan uwaki zanje uwar tambaya,,, Amman, kin manta da masifan da Abba yayi miki ran nan da kikaje?,,, mugun kallo ta watsa mata tace, ke Batula fita idona in rufe banson sakarcin banza, idan kinga ba tayani zakiyi ba karki kuma shiga safgata, kinji na gaya miki duk abunda kikaga inayi zuba min ido ba ruwanki a ciki tunda ba tayani zakiyi ba,,,Umma Abba ya hanaki fa,, kinci Kutumar ki batula yanzu ma yana parlon sa zaki iya zuwa kinasar dashi tunda ke kin zama munafuka yarinya,,,,Ke kuma taho mutafi tace da Suwaiba ta fice daga parloun,, bayanta tabi Batula tana mata magana ta shareta ta ko kallon inda take batayi ba ta fice,,,girgiza tayi ta wuce ďakin su tana mamakin abunda umma keyi kamar ba mahaifiya ba,,,
A hankali suke takawa tana tsoron kar Abba yaga fitan su,,,kamar marar gaskiya, ta buďe ķofar get ďin suka fice,,,har bakin titi suka taka kafin suka samu mai adaidaita sahu suka shiga tace mishi ya kaisu unguwar Layout,,,
Ba tare da bàta lokaci ba yaja su har ķofar gidan ta kwatanta masa ya sauķe su kafin ta biyashi kuďin shi tafara buga ķofar get yafi a riga kafin baba mai gadi buďe musu bayan ya leqa yaka ko suwaye ne,,,cikin haďa fuska ta dube shi yana gaisheta,, wato dan rainin hankali ni da gidan ďan nawa ma sai anga dama za'a buďe min ko?, haquri ya soma bata yana rusunawa, yace wlh na zaga bayine yi haquri hajiya,,, bata saurare shiba taja hannun Suwaiba suka nufi ciki,,
Zaune yake parlou kan doguwar kujera yana latsa wayar sa, Humaira na kusa dashi ta zabga uban tagumi abun duniya ya ishe ta sama sama yake jefa mata hira jinsa kawai take batan mai yake faďa ba,,banko ķofar parlon tayi ta shigo batare da tayi sallama ba, suwaiba na biye da ita a baya,,Turus ta tsaya tana binsu da kallo ta rire habàr ta tare da zabga salati yau taga wayewar yan duniya, ta qarasa shigowa,,,
"kallon kallo suka tsaya binta dashi, a ransa ya furta ya salam yana dafe kai yau kuma dame tazo ganin ta tare da yarinyar da beson gani,,ya ďago kansa yace Umma daga ina haka da ranan Allah?,,,,daga gidan uwaka nake ta bashi amsa tana hararan sa,,,kafin tasamu kujera ta zauna suwaiba ta zauna kusa da ita,,, shiru yayi bai kuma cewa komi ba sai ido da suke binta dashi har yanzu,,, To ku cinye ni ďanya ku huta kunji mayo? harda kai ka zuba min na mujiya saikace yau katabà ganina,"
Saukar da kanta qasa tayi kafin ta sauqo daga kan kujeran, tace sannu da rana Umma,,,,Ke dakata ta nuna ta da yatsa banson munafurcin banza kinji ko? simisimi kamar mutumiyar arziki wai barka da rana, to riqe ta bana bukata, kuma daga yau sai yau karki kuma gaishe dani kinji nagaya miki ko a hanya kika ganni to bakisani ba,,,,,Kai kuma ďan gidan masu mace yanzu da yake bakada kunya da tsoron idon mutane zaka zauna waje ďaya da ita ga ķugunta ga naka kuna gogan juna, ka nunawa duniya kai jarababbe kenan?.......
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:09] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*Page*
*23*
Dedicated to my besty
*AISHA GENTLE LADY*💃
🤡🤡 *Hanjin Mijina akwai naci akwai na zubarwa* 🤡🤡
*Na*
*Babbar marubuciyar mu yayata Billy galadanci* 😘 *Haqiqa kinyi namijin qoqari wajan faďakar damu littafin sosai ya faďakar ya nishaďantar naji daďin sa babu makawa fatan Allah yaqara miki basira da karfin ido yasa kifi haka Billy na najinjina miki na tayaki murnan kammalawa lfy kamar, yanda kikace kinason takwarata Hafsat ilham tabbas ni dai inasonta ko a ina take duk bawan da ďan adam yaso shi to ba shakka wannan yana tabbatar dacewa Allah ne yaso shi fatan Allah yabar zuminci da kaunar juna ina miki fatan alkhairi sister Billy na natayaki murna matuqa Ana tare* 😘😘
Kuďin daban kuke a gareni na gaisheku da babban murya
qawata Maryem abdool
My Saffyya musa huguma
My Phartiemarhk
My Namesy sawwamat
Maman zee
Maman Nana
Sister Aisha
Sister Lieey
Sister Heenar
Nagoge muku sosai da kulawar ku gareni da duk sauran masu min addu'o'i kan rashin lfyar qanina jiki Alhamdulillah yaji sauki sosai nagoge Allah yabar zuminci da kaunar juna 🙏🏿🙏🏿
*Nazo gareki siater Smasher HBD to u dear 🎂🎂 Allah yaqaro shekaru masu Albarka lokacin kine kiyi duk abinda kikeso wishing u sister Smasher* 😘😘😘
Shiru yayi ya rasa wanne amsa zai bata Sam kwana kin nan tunda yaqara wannan auran yakasa gane kan mahaifiyar shi gabaki ďaya ta ďauki tsana ta ďaura shi kan Humaira ya rasa meye dalilin ta na tsanar ta kodan yaqi auran wacce takeso ne shi kuma harga Allah bayason haďa koda hanya ďaya ne da ita Sam yarinyan bata cikin muradin shi gashi yanzu Umma ta kaso tazo masa gida da ita zuciyar sa tana fargaban dame tazo",,
jin sunyi mata shiru babu wanda ya tanka mata yaqara tunzura ta cikin faďa ta dube su tace, Au ni zaku mayar tabàbbìya kenan ina magana kun shareni kun mayar dani shara ko??
Ajiyan zuciya ya sauķe yana kallon yanda ta ďaure fuska yace Allah ya huci zuciyar ki umma ai tambayar takice wani iri ko kin mance matata ce humaira?,,,hararar sa tayi tace,
A a ka mance qanwar mahaifiyar kace, ja'irin yaro kawai ina magana idon ka akaina kana min rashin kunya kai gaka mai mace to wlh kashiga hankalin ka idan kayi wasa sai in iya rabaka da ita gaba ďaya inga yanda zakayi tunda ba tsinana min da komai zatayi ba dan haka ni ba wannan iya shegen naka bane ya kawo ni kaga wannan ta masa nuni da suwaiba wacce ta zuba masa na mujiya tana kallon sa kamar zata haďiye shi ji tayi mata kwarjini sosai a ido fiya da yanda ta saba ganin sa a baya, tace ka shirya nanda kwanaki kaďan nakeso za'a haďa auran ku da ita itama ta shigo sahum matan gidan, kuma umarni ne nabaka ba neman shawaran ka nakeba da kanka nakeso zuwa gobe kaje kasamu mahaifin naka kace masa zaka aure ta tunda shine dama mai ďaure maka gindi yana maka duk abinda ka nema kamar kai kaďai gareshi,,"
Cikin gigicewa ya ďago da kai ya kalle ta itama shi ďin take kallo tace, kanada nacewa ne kana kallo na haka saikace ran ka za'a ďauka??,,shiru yayi bece mata komai ba illa maganar zuci da yake meye nufin umma tana kan bakanta kenan, ina shi ina auran wata suwaiba shi sam bata cikin tsarin sa ina zai sakata idan ya aureta wannan yazama masa tilas yasamu Abba yasanar masa tunkan lokaci ya kùre masa yazo yarasa mafita,,"
Manne take bakin ķofar kitchen tun shigowar umma gidan ganin ta tare da suwaiba yasa ta rakubè tanajin duk abunda take faďa,,sosai hankalin ta ya tashi jin abinda ya kawota wannan yazama mata dole ta tashi tsaye tayi wani abu a kai idan tayi wasa za'a qara yi mata rufin da babu ruwa, yanda taga umma ta zage har yanzu tana kan bakanta tilas ba makawa zata iya sa shi auren wannan yar ķauyen,,,mafita iri iri take nema wanda zaisa Umma tabar maganar nan, zuciyar ta bazata iya jure mata zama da kishiyoyi har biyu a gaban ta ba wannan tabbas tayi wani abu akai idan ba hakaba nan gaba kaďan zata iya komawa abun tausayi,,,,zagaye kitchen ďin ta somayi tana safa da marwa duk ta gigice jitake kamar tayi hauka ta rasa ta wanne hanya zata iya bùllowa wanda zaiyi mata aiki a yanzu batare da an bàta lokacin ba,,tana cikin tunane tunane ta tuno da qawar ta shiwari ta tabbatar da cewa itace kaďai wanda zata iya kawo mata ko wanne irin mafita take bukata,,,ciro wayar ta data cusa shi a ķugunta tayi tare da danna number shiwari tana girgiza kai ita kaďai tasan mai takeji a yanzu cikin zuciyar ta",,
Har wayar ta tsinke bata ďauka ba, ta qara qira shiru saida tayi ta qira yafi so a irga, kafin ta ďauka,, lokacin har babu tagama fusata, cikin faďa tafara mata magana,,haba shiwari kefa wani sa'in waya batada amfani a gurin ki tuntuni naketa qiranki Amman kin watsar dani kinqi ďagawa kikasan meke tafe dani,,,,shiru tayi tana sauraran korafin ta, saida taji ta tsagaita daga bisani ta bata haquri tare da cewa wanka nashiga shiyasa banji ba Amman lfy kike min wannan qira haka saikace za'ayi tashin duniya duk kinbi kin ďaga min hankali da qiran waya kodai wannan yar iskar kishiyar taki tayi miki wani abun??,
Nan taji ta taqara tono mata abunda keci mata tuwo a qwarya, taja kujeran dake kitchen ďin ta zauna tana sauķe numfashi tace, kedai bari qawata ina kuwa lafiya ai gwara ayi tashin duniya akan wannan bala'in dake shirin tunkaro ni ina nan zaune ban gama da tagaba na ba za'a qaro min wata asani hawan jini lokaci na beyi ba,,,,,cike da mamakin jin maganar ta taqara kasa kunne sosai tace banagane hausar da kike ba Maraqishiya fito fili kiyi min bayani dalla dalla yanda zangane kinsani a duhu fa,,,, dafe kanta tayi da hannu tana busar da iska ta bakin ta tace wlh Wannan matar ne ke jaza min kai Sam alaman ta ya nuna batason zaman lfy,, nan ta kwashe komi ta faďa mata kan kudirin ta na auran suwaiba,,,
Shiru shiwari tayi tana nazarin yanda zata fara bata shawaran yanda zatayi can ta nisa tace qawata ai babu matsala wannan duk mai sauki ne buďe kunnenki da kyau ki saurare ni kiji abinda zan faďa miki matukar kikayi amfani dashi na tabbata zaki warke daga cutar dake damunki, ai bamuga ta zamaba, yanzu abinda zakiyi shine kinsan halin mijinki kin zauna dashi kusan sama da shekara uku, kinsan abunda yakeso kinsan wanda bayaso dan haka kafin maganar umma yayi tasiri sai kifara korar wannan tagaban naki idan nazo ko gobe zamu qarasa sauran maganar, inafatan kinfara aiki da shawarar da nabaki?,,,,kai ta girgiza mata kamar tana kallon ta tace, yanzu zanyi dan har nagama haďa abincin ma idan na kai sai nayi sauran,,"
yauwa to shikenan ki tabbatar komi yatafi daidai yanda ya tsara miki hakan shi zai kawo mana sauki wajan aiwatar da sauran aikin mu nagaba, ita kuma Umma kibar ta batun ta zamuyi kanta daga baya kinji ko??,, kai ta girgiza tace Eh qawata naji sai kinzo kawai nagode tafaďa tare da kashe wayar bayan sunyi sallama,,"
Cike dajin daďi tana yar waqanta zuciyar ta fayau ta kammala haďa abincin,,, juye su tayi cikin kula ta haďe su kan babban tire kai tsaye dining ta nufa ta jera su, kafin tayi hanyar parlouta dan zuwa sanar dasu suzo suci abinci,,"
Tana murmushin yaķe da baikai baki ba ta qaraso inda su umma suke ta kai har qasa dakyar kamar an sakata dole tace, sannu da zuwa Umma ina wuni.......
*Dan Allah masoya na masu karanta littafina kuyi haquri da wannan kunsan muna fama da maral lfy ga aiki wlh yarufe min ido banida lokacin zama ko kaďan Amma insha Allahu komi yakusa daidaita zakuna samun dogon page kamar yanda kuke samu abaya nagode*🙏🏿
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:09] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*Page*
*24*
Dedicated to my besty
*AISHA GENTLE LADY*💃
*Sister Lieey,*
*Sister Lieey*
*Sister Lieey*
Karkiga naqira sunanki haka kin cancanta ne shiyasa ina miqa miki gaisuwa ta matuka ako ina kike da akwai hali dana mallaka miki wannan page, Amma Karki samu damuwa insha Allahu nest time😁Allah yabar zuminci da kaunar juna ana tare🙏🏿
🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂 *Sister Smasher karkiga naqara miki HBD badan komai bane illah dan kin cancanta ne keďin daban ne lokacin ki bai qure ba kina cikin watan haifuwar ki bazan daina miki fatan alkhairi ba Allah ya albarkaci rayuwar ki yasa kigama da duniya lfy wannan kirkin naki kiqara riqe shi dakyau karki bari shine jigon rayuwa HBD Sister Smasher 🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂 again and again am wishing u a long life*😘
*My Safiyya musa huguma Ana tare a riqe zuminci da kyau banda rabewa ina miqa miki gaisuwata sai kin ganni Safiyyu na*😜😜
Cikin sakin fuska ba yabo ba fallasa ta amsa mata gaisuwar tace, ya nashigo banganki ba ina kikayi?,,,,Eh wlh umma ina kitchen ina haďa mana abinci,,"
Kallon rashin fahimta tayi mata kafin tace bangane kina haďa muku abinci ba, ita wannan ďin fa tayi nuni da humaira meye amfanin ta a gidan da bazata dafa muku ba sai ke ba itace qasa dake??,,Himm kawai tace ai bata fara girki ba tukunna umma,"
"Tun yaushe aka auro ta zakice bata soma girki ba, dan taci mai daďi tasha mai daďi taje banďaki ta zazzagar aka kawo ta gidan kenan ko? ta tambaye ta tana mata wani irin kallo,,,,,zata fara ai umma duk mun zama ďaya fa yanzu, idan nice nadafa ma ai ba matsala bace itama watarana zatayi mana zaman tare ne ai,,"
Hannu ta ďaga mata tace kinga dakata uwar bayani yaushe kika sauķo haka bansani ba, harda wani kun zama ďaya?faďa min inajinki,,"Umma dan Allah kibar wannan zancan komai ya wuce ni a wajena,"
To shikenan Maraqishiya naji nabari damuwar kice batawa ba nasan dama dole za'ayi haka duk zuriyar ku ďaya mota ďaya ta kwaso ku dan haka kuje ku qarata, kuma duk abinda yabàci miki akan wannan shegiyar yarinyan kiyi kuka da kanki zakice nagaya miki,,,kai kuma kanajina ko? aure kaida suwaiba dole ne ba makawa har indai ina numfashi a duniya to sai anyi shi,,,tana kaiwa nan ta miqe tsaye tace ke tashi mutafi nagama abinda yakawo ni sai gobe kuma,,,tashi suwaiba tayi babu musu zuciyar ta fayau takeji kamar ta daka tsalle dan murna itama nan da kwanaki kaďan zata zama hajiya sai abinda taso zatayi waiyyo Allah nuna min wannan lokakin,,"
Umma ku tsaya muci abinci mana ya nuna fa,,harara ta watsa mata tace karki kuma ce min umma munafuka kawai kina nan kamar zakiyi wani abun arziki ashe ba hakaba sai kuje ku cinye abincin ku inadashi a gida na,,"
Shiru tayi bata qara magana ba saida taga sun fice daga parlon, kafin ta tashi da sauri tana faďin bari naje naba Umma haquri naga ranta yabàci sosai ina zuwa, daga Abdulmalik ďin har humaira babu wanda ya tanka mata illah mamakin canzawan ta da sukaga tayi ba zato ba tsammani,,"
Baba mai gadi ya buďe musu ķofar get ďin zasu fice kenan ta fito da gudun ta har tana tuntubè taďaga murya tace Umma dan Allah tsaya kiji abinda zancan mana,,,tsayawa tayi tare da jiyo da kai tana mata kallon bàcin rai tace, lfy zaki tsayar dani?,,,,tana sauke numfashi alamun ďan gudun da tayi ya shige mata jiki tace,,"
Umma karfa kice zakiyi fishi da abunda kikaji yanzu nafaďa wlh siyasa nayi musu cikin dabara zan aiwatar da duk wani shirin dana kulla mata batare da yagano bakin zaran ba kinga kenan suwaiba na shigowa ita kuma tana fita koya kikace da wannan shirin??,,,jinjina kai tayi tana washe baki tayi dariya tace ba shakka na gamsu da shirinki Maraqishiya wani lokacin kinada kaifin kwakwalwa har kike iya haďa munafurcin da koni bazan iyaba, sai yanzu naji wasai a raina kinga kafin nan idan itama suwaibar ta shigo sai ta tayaki kuyi tare,, ni natafi sai gobe idan nashigo kuma ma qarasa sauran,,"
To umma gobe ma zuwa zakuyi??
Har ta saqala ķafar ta waje ta jiyo tana mata kallon banza tace zaki hanani ne?,,
"Murmushin dole ta qiqiro tana ďan sosa kanta tace A a umma nidai na isa kawai dai na tambaya ne in tabbata dan in haďa muku wani abun kafin kuzo,,
""karki damu idan nashigo goben kya haďa koma meye,,"
To umma agaida gida nagode sosai,,gida zaiji kawai tace mata tare da jan hannun Suwaiba suka fice daga gidan,,koda suka taka zuwa bakin titi sun kusa cin rabin lokaci dakay kafin suka samu adaidaita sahun da zai mayar dasu gida,,"
Tana yar waqe waqen ta na jin daďi ta koma ciki, a nan parlon ta tarar dashi kwance kan doguwar kujera, wayar sa a hannun sa yana latsawa,, kujeran dake kallon nasa ta zauna tareda kai kai dubanta kansa tana murmushi tace dear, muje muci abinci na kammala fa,,saida ya kalle ta dakyau ita ďince haka kafin ya tashi tsaye yamayar da wayar sa cikin aljihu baice mata qala ba ya huce kan dining,,,bayan sa tabi taje taja masa kujera ya zauna kafin ta zuba masa farar shinkafa da miya da slat iya yanda zai iya ci tana kallon sa tace dear ina humaira ne banganta ba?,, yana kaiwan loma ďaya bakin sa ya ďaugo ya kalle ta yace meye zaki mata wani tashin hankali zakije ki qara mata?
Kashe murya tayi cike da kisisina tace haba mana dear meyasa zakace haka nifa yanzu nagane kuskure na nasan abuda nayi a baya bai tace dani ace nayi ba kawai dai neman ta nake tazo muci abinci mu sasanta kanmu ai kishiya ba abokiyar faďa bace,,"
"To idan da gaske kike har cikin zuciyar ki kije ki qirata tana dakin ta yace da ita batare da yasake kallon ta ba yaci gaba da cin abincin sa, shi kanshi da zata ajiye wannan tashin hankalin da take kunno musu kullum a zauna lfy da yafi kowa fari ciki Amman yayi mamakin ganin canzawan ta lokaci ďaya harda haďa musu girkin da rabon da yaga ta dafa masa yaci har ya mance saidai idan yaje gida in sun dafa yaci Amma ba'a gidan sa ba,,"
Tana barin wajen nasa ta nufi ďakin Humaira ta murďa ķofar a hankali bakinta ďauke da sallama ta shiga,,,,zaune ta hango bakin gado tana magana da alama waya takeyi, tsayawa tayi fuskan ta ďauke da murmushi tace, qanwata idan kin kammala da wayar ki samemu a dining table muci abinci,,,cike da mamakin jin furucinta ta ďaga mata kai itama tana mayar mata da murmushin tace ok ina zuwa ku fara ci,,,,fita maraqishiya tayi a ďakin ta koma dining table taja kujera ta zauna kusa da nashi tareda da zuba abincin iya wanda zataci ta rufe sauran,,ganin ita kaďai ta fito yasa yace ina humairan take bazataci bane??
Tana zuwa waya takeyi tabashi amsa tana kaiwan abincin bakinta,,"bai kuma cewa komai ba yaci gaba dacin nashi abincin,,"
Tana nan zaune bakin gado inda ta barta har yanzu tana waya kafin daga bisani tayi sallama tare da kashe wayar,,har zata fice sai kuma ta fasa ta lalubò number mummy ta qira tana kewar jin muryan mummyn ta,, saida ya kusa tsinkewa kafin aka ďaga,, cikin zumuďi tace salama alaikum mummy na ina wuni kwana biyu kina lafy?,"
"lafiya lau ďiyata kefa kina lfy?,,
"Saida ta haďa fuska kafin tace eh mummy duk lfy muke Amma kika shareni daga ke har Abba duk kun daina qirana bare kuji ya lafiya ta take,,"
Haba Humaira mu mun isa mu mance dake kina gidan mijinki ai bai kamata ace kullum muna qiranki a wayaba bayan munsan kina lfy,,"
"himm mummy kenan shikenan ina ya mahmud ne? shima tun rabuwa na dashi bamuyi wayaba,"
"yana gun aikin sa yau tun safe ya fita,,,Abba fa mummy shima baya nan ko? Eh ta bata amsa tare da cewa ya abokiyar zaman taki ba wata matsala ko??,,
Murmushin kirfin hali tayi tace, himm mummy na kenan karki damu wlh ba wata matsala muna zaman mu kamar ya da qanwa idan kin ganmu, saidai nifa bangane wani abu ba mummy duk fa banga kayan kitchen ďina ba ko a ina su Anty fati suka jera bansani ba,,To bari zan qirata in tambaya miki ita Allah yabaku zaman lfy ki kula da mijinki karkiyi wasa da nasihan da Abban ki yayi miki Allah yamuku albarka sai anjima,,
To mummy insha Allahu zanyi amfani dashi ki gaishe min da Abba na kice nayi kewar sa sosai sai naqira shi yanzu suna jirana inje muci abinci kar suga ban fitoba suji ba daďi,,
"Su waye suke jiranki??
Abdulmalik ne da ita abokiyar zaman tawa,,
To sai anjima ki gaishe dasu,, to mummy zasuji tace tare da kashe wayar,, ta maqala shi a charge ta fice daga ďakin ta nufi dining inda suke,,,iske su tayi har sun kusa kammalawa taja kujera ta zauna ďan nesa da nasu tana murmushi cikin qasa da murya tace kuyi haquri dan Allah ban fito da wuri ba ina waya da mummy tace tana gaisheku,,muna amsa Abdulmalik yafaďa tare da tambayar ta suna lfy, Eh tabashi amsa taja plete ta ďibi abincin kadan ta rufe sauran,,"
Shegiyar yarinya la'ananniya mai kama da aljanun ruwa da karki fito mana dan kin samu ma an dafa miki himmmm bakisan mai nashirya miki ba nan gaba kici dakyau yar iska harda wani kashe murya wai kuyi haquri waya nake zakigane kuranki ai, cikin zuciyar ta take maganar tana girgiza kafa ita kaidai tasan mai zebiyo baya nan gaba kaďan,,"
Tashi yayi bayan ya gama cin nashi yasha suwa kafin ya koma parlou ya zauna kallon TV tashan labare,,itama tashi tayi ta dawo inda yake ta kai har qasa ta rusuna a gaban sa tana duban sa tace dan girman Allah mijina kayi haquri ka gaficeni da duk wani tashin hankalin da nasaka cikin kwanakin nan wlh ba har cikin zuciyata nayi saba sharrin sheďan ne shi yake zugani duk nayi muku wannan tashin hankalin Amma yanzu kam harga Allah nagane kuskure na ka yafe min daga yau bazan qarayin wani abu makamancin hakaba zan riqe ta kamar qanwata ciki ďaya mu zauna lfy bazaka qara jin kanmu ba nayi wannan alqawarin......
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:09] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*Page*
*25*
Dedicated to my besty
*AISHA GENTLE LADY*💃 _Daga ni sa ike_
*Yan zauren Biebie isa gaisuwar wannan shafin gabaki ďaya takuce Aminan juna yan mutunci* 👇
_Shukrah Cute_
_Auntie jamiey_
_Meenarh Parrot_
_Amal BaibiiAna mugun tare iya wiya_🤝🏿
Shukura ina miki barka da murna na kammala littafin Ranar suna da kikayi fatan alkhairi Allah yaqara basira na jinjina miki matuqa sai munjiki ana gaba kuma Ranar wanka 😜
*Zan iya cewa taki gaisuwar daban take ďiyata Meela Adeel fatan Allah yabar zaman tare karki samu damuwa autana bazan zauna ina gani wata Neesah takwace miki Adeel ba, kece kaďai kika cancanta da Adeel kinji ďiyata*😁
Ido ya zura mata yana kallon ta gabaki ďaya ya tattara hankalin sa yamar dashi kanta ganin yanda ta harďe hannayen ta duk biyu waje ďaya idon ta na zubar da kwalla alamun nadama qarara a fuskan ta,,,ajiyan zuciya ya sauķe yana cigaba da duban ta sosai kamar mai nazari kafin daga bisani yasa hannayen sa duk biyu ya dafa kafaďun ta tare da ďago da ita ya zaunar ta kusa dashi yana kallon cikin kwayar idanun ta ya buďi bakin sa ya qira sunanta a hankali yana riqe da hannayen ta cikin nashi yace,,"
Maraqishiya, na'am ta amsa masa cikin qasa da murya batare da ta ďago ta kalle shi ba,
kinsan dai inasonki ko? auran soyayya mukayi nida ke ba auran haďi ba, dan ina matukar kaunar kine yasa na auro ki badan komai ba ke kanki kinsan a iya zamana dake ban tabà tauye miki wani hakki naki ba ban kuma tabà nuna miki rashin kyautatawa ko gajiya dake ba ko kin tabà ganin sauyi daga gareni a iya shekarun da mukayi dake?? kai ta girgiza masa alaman A a, yaci gaba da cewa to meyasa kike tunanin auran dana qara kamar nayi ne ďan na daina sonki ne ko kuma nayi tane da wani manufa har yasa kike abu kamar hauka? shiru nan ma tayi tanajin sa yace kibani amsa mana inajinki,,"
"Kanta ta ďago suka haďa ido dashi tana qara tamqe hannun sa cikin nata tayi qasa da murya kafin tace nidai kayi haquri dan Allah mijina ka mance da duk wani abunda yafaru a baya nagane kuskurena irin haka bazai tabà qara faruwa ba daga yau zan riqeta Amana zamuyi zama tamkar ya da qanwa nidai kayafe min kawai nasan nagaya maka maganganu masu ďaci marasa kan gado wanda ban tabà gaya maka irin makamancin su ba cikin bàcin raine wlh duk sharrin sheďan ne da huďubar sa pls dear nayi alqawari bazan kuma ba, kanta ta kifa kan kafaďun sa idonta na cigaba da zubar da kwalla tana shashsheqar kuka,,,hannayensa duk biyu yasa ya zagayo ta yana lallashin tare da bubbuga bayanta kafin daga bisani ya ďago da kanta yana share mata hawayen fuskan nata yace,,"
kiyi shiru kukan ya isa haka na yafe miki, komai ya wuce fatan bazaki qara maimai makamancin irin hakaba? kai ta girgiza masa tana murmushi,,jin daďi,, shima sakar mata da murmushin yayi cike da kauna ya ďaga kansa ya kalli humaira ya sakar mata da qayaraccan murmushi a ran sa yake faďin ohh kishi kumullon mata ganin yanda tayi kicinkicin da fuska ta zuba musu ido tunda suka fara magana take binsu da kallo ko ķeftawa babu,,saurin kawar da nata idon tayi dan bataso ta haďa da nashi tana wasa da spone ďin hannunta tana jujjuya abincin dake gabanta ji tayi duk abincin ma yafice a ranta, qasa qasa yayi dariya yadawo da duban sa kan Maraqishiya yayi mata nuni da taje ta bata haquri su sasanta junan su tunda duk wani tashin hankalin da tayi ma itane dalilin an auro tane badan komai ba,,"miqewa Maraqishiya tayi tana ďan murmushin dako baki bai iso ba dan dole takeyin wannan abun badan tanaso ba Amma ya zatayi tunda babu tafara isa gareta tayi ta zauna kan kujerun dake kusa da ita,,tana kallon cikin idonta ta kamo hannayenta ta haďe da nata cike da iya magana tafara tacewa,,"
Humaira kiyi haquri dan Allah kema ki yafe min abubuwan da nayi miki nasan ban kyauta miki tun ranar farkon ki a gidan nan na hanaki kwanciyar hankali na ruguza miki farin cikin ki na daran farkon ki wanda za'ace ko wacce ýa mace takeyin alfahari dashi na lalata miki Amman baki tabà buďan baki kince min qala ba ko ki rama abunda nayi miki ba wannan ya tabbatar da cewa ke ďin alkhairi ce insha Allahu daga yanzu na ďauke ki matsayin yar uwata kiyi haquri ki mance da duk abunda yafaru abaya mudawo muyi zaman lfy tare da kwantar wa da mai gidanmu hankali batare da kowa yaji kan mu ba, maganar take Amman ita kaďai tasan mai take shiryawa cikin zuciyar ta dan ta ďau alwashin muddun tana raye a doron qasa sai tasan yanda tayi tafitar da ita daga cikin rayuwar mijinta kota halin qaqa koda kuwa zata rasa ranta ne ta rantse bazatayi kaffara ba,"
"Bazaki iya yafe min bako humaira?tafaďa tana qara kallon ta akaro na biyu jin tayi shiru ko kai bata ďago ba bare su haďa ido,,,,Ajiyan zuciya ta sauķe ta ďaugo da kanta tana kallon gefe guda tace karki damu komai ya wuce ban tabà riqe ki cikin zuciya taba baki min komai ba idan kinyi ma nayafe miki,,tana kaiwa nan ta miqe tsaye ta kwashe kayan abincin da suka kammala fuskan ta ba yabo ba fallasa tace inane wajan wanke wanke inaso in ďauraye kwanikan,"
"A a ai baza'ayi hakaba kina Amarya ace kinyi wanke wanke barsu zan wanke su je kiyi hutunki mun zama ďaya ai yanzu,"kedai kawai muje ki nuna min zan wanke tafaďa a takaice,,,dariya tayi ta miqe ta ďauki sauran kayan abincin tace muje to tunda kinqi bari tun yanzu zaki fara min gardama bayan nice gaba dake cike da zolaya tayi maganar batare da ta kalle taba, murmushi kawai humaira tayi bata qara magana ba,,tana gaba itama tana biye da ita a baya suka zagaya bayan gidan inda ake wanke wanke, gani tayi filin gidan yayi mata matuqar kyau ya tsaru iya tsaruwa flowers ne jere tako ina masu masifar kyau gefe guda an shimfiďa grass binsu take da kallo ba qaramin sha'awa yayi mata ba ga wani daddaďan iskan bishiya dake kaďawa yana busar da iska mai ratsa jiki kamar ta kwanta a wajan takeji dan ni'imar dake tashi ,"
Cikin limana suka fara wanke kwanikan a tare tas suka kammala wankewa tana jefa mata fira sama sama itadai humaira jinta kawai take bata cewa komai dan ji take har yanzu zuciyar ta bai gama gamsuwa da maganganun taba fatan ta Allah ya kareta duk wani shrarrin da zai biyo baya har zuwa nan gaba bazata tabà mancewa da munanan kalaman ta akanta ba,,kitchen suka kai kayan humaira ta tayata suka gyara shi fes ko ina yayi kyau bayan sun kammala,,suka fito daga kitchen ďin, basu tarar dashi a parlon ba sai tv dake aiki shi ďaya da alama ya fice masallaci dan jin anata qiraye qirayen sallahn la'asar,,,jiki a sanyaye tayi hanyar ďakin ta,,,hannunta Maraqishiya ta riqo tana duban ta tace haba qanwata ina zakije kuma har yanzu naga kin kasa sakewa dani kodai baki yafe min bane kina tantama akaina da gaske nakefa wlh banzan miki komai ba cikin langabè kai tayi maganar,,"
Murmushin yaqe ta qiqiro tace komai fa ya wuce wlh kawai dai ciki nakeso in shiga kinga lokacin sallah yayi kar ya wuce mu,,,cikin sigar wasa tana dariya tace to matar kulle kullum shikenan ke sai zaman ďaki idan sallah ne ai ko a parlou basai muyi ba ga toilet ko ďakina ma to nidai idan kin idar da sallahn ki sameni a parlou muje in zagayar dake cikin gidan in nuna miki kiga yanda yake nasan har yanzu bakisan ya abubuwa da tsarin gidan sukeba, to antyna tafaďa tana yar murmushi tare da shigewa ďakinta,,, shegiyar aljana harda wani to Antyna dan tsaban munafurci banza bakisan koni waye bane Amman nan kaďan bada jimawa ba zakici kol ubanki wlh yar uwar shi dangi ďaya ma ban qyale ba bare ke wata ďangin da babu iya bare na baba,,"
Tana idar da sallahn ta bayan tayi tasbihi ta kishingiďa da jikin gado tunani iri iri fal a zuciyar ta addu'ah sosai takeyi na neman taimakon Allah da neman agaji zaman da zatayi da maraqishiya dan ita a iya saninta duk faďin duniyar nan idan ka bincika ba ko wacce ýa mace bace mai iya ďaukan kishiya a matsayin abokiyar zama ba koda kuwa ta ďauka to dole asamu wani tsabàni yau da gobe tana tsaka da zancan zuci, wayar ta dake maqale a charge ya ďauki ruri ta yunqura ta duba taga sunan Mummy hakan yasa tasakar da murmushi himmm uwata kenan har an soma kewata bayan bai jima ba muka gaisa tafaďa bayan takai wayar kan kunnen ta jitayi mummy tace,, ba wani kewar ki da muka farayi mantawa nayi ďazu ban tambaye kiba shin kin fara aika abinci gidan mahaifiyar tashi kuwa??"tsuru tsuru tayi da ido ta furta ya salam a hankali tana dafe kai ita Sam gabaki ďaya ta mance da batun aika wannan abincin abu tun shigowar ta gidan ma ba zaman lfy suka barta tayi ba bare harta soma girkk ,, kinyi shiru fa kodai baki fara aikawan bane har yanzu?,,Waiyyo mummy kiyi haquri wlh na mance ma kwata kwata kibar maganar kawai tayaya ma zan soma yin girki irin wannan ni kaďai ai dako fadeela kinbar min ni ta tayani gaskiya ni bazan iyaba mummy kawai tunda ba sanin wannan al'adar sukayi ba ashare wlh zai min yawa ni kaďai fa gashi da alama sunada ďan yawa a gidan nasu bare nayi kaďan cikin shagwaba tayi maganar dan itakam harga Allah bazata iya ďawainiyar dafa abinci har na sawon sati ďaya ita kaďai ba,,
"cike da bacin rai mummy tafara mata faďa tace ke kinga banison sakarcin banza kinji ko idan bakece zakiyi ba to waye kikeso ya miki kinaji dai anan Abban ki yahana kar a taru musu a gida dan haka maza tunkafin na sabà miki daga gobe kifara saura kuma naji bakiyi ba sai ranki ya mugun baci kinaji na ko?kai ta girgiza tace Eh mummy naji insha Allahu zanyi kiyi haquri, yafi miki taji tafaďa tare da kashe wayar kit,,nauyayan numfashi ta sauķe ranta babu daďi yanzu ta ina zata soma wannan baķar al'adar kai kanuri basuyi ba wlh ko minsu daban dana mutane cikin zuciyar ta take maganar tana yamutsa fuska to inbanda abun Abba a ina aka tabà yin haka da zai hana kowa tayata zama ai ba Amarya bace take wannan girkin abincin mutane ake kawowa suyi suna aikawa Amma ita gashi ko mutum ďaya ba'a bar mata ba bare ya tayata kuma dole sai tayi waiyyo Allah na ta furta cikin ďaga murya kafin ta gyara zaman ta,, tananan kishingiďe ta lumshe ido kamar mai bacci, Maraqishiya ta turo ķofar ďakin ta shigo tare da sallama ganin tun ďazu tana jiranta bata fito ba tana murmushin yaķe tace, qanwata yanajiki shiru fa muje mana ke naketa jira fa naji shiru lfy dai ko ?,,buďe idon ta tayi tasakar mata da murmushi batare da tabata amsa ba ta miqe ba musu tabi bayan ta suka fice cikin hikima sukafara zagaye cikin gidan tana nuna mata abubuwa da yanda take aiwatar da komai nata,,"
******* ******
Cikin ďan kwanaki biyun da sukayi da ita ba shakka taga canji sosai a gareta komai ita takeyi musu hatta girki dakyar take bari ta taya suyi tare haka Maraqishiya ta dauke ta tamkar yar uwar ta ciki ďaya sosai tasake da ita suke aiwatar da komai nasu a tare batare da kowa yaji kansu ba ko wani tashin hankalin ba kullum Umma sai ta tako ķafar ta gidan maganar ta baya wuce na auran suwaiba tunda ita wannan shegiyar da take zaton zata iya aiwatar da komai ashe ba hakaba sai gani take tana shigar da ita jikin ta idan tayi mata magana sai tace duk acikin shirine saura kaďan ta kammala shi kuwa idan tayi masa maganar amsa mata kawai yake ya lallamata har ta koma gida lokaci yakeso yasamu yasar da mahaifin sa tun kafin ta qara ingiza shi,,"
ganin komai yana tafiya daidai batare da wanin tashin hankalin ba hakan yasa yau da daddare bayan sun kammala da cin abinci suna zaune a parlou duk su uku Maraqishiya tana kusa dashi kan kujera humaira kuma tana qasa a gefe guda yayi da ita ta hau kujera Amman fur taqi tace tafinson zaman qasa haka ya haqura ya rabu da ita,,gyara zaman sa yayi yana kallon ko wannan su yayi gyaran murya tare da qiran sunayan su,, amsa masa sukayi suna kallon shi suna jiran suji abunda zai faďa,,a hankali ya soma magana yafara da godiya ga Allah yace,,"
Alhamdulillah na godewa Allah da nuna min wannan rana ahaqiqanin gaskiya nayi farin ciki sosai da kika gane kuskuren ki kika yarda zaki zauna da ita lfy amatsayin yar uwa, ke Maraqishiya kece babba da ita kinga dole wani abun sai kin nuna mata inaso kamar yanda kuka haďa kanku a yanzu karku bari naji ko nagani wani tashin hankali ku zauna lfy dukan ku nan sonku nake shiyasa na auro ku badan komai ba inafatan kun fahimci magana kuma zaku kiyaye? kai suka girgiza alaman Eh, Maraqishiya tace insha Allahu daga yau karka samu damuwa zamu kiyaye kuma zamu zauna lfy bazakaji kan mu ba, humaira dai qala batace illa saukar da kant qasa da tayi,, jinjina kai yayi yaji ďaďin canzawan ta matuka daga nan cikin hikima yaqara musu nahiha kafin daga bisani yaraba musu kwana ko wacce kwana biyu, daga gobe,addu'ah yayi musu yasha kafin ya miqe ya shiga ďakin kai tsaye ya wuce toilet dan yin wanka,,"
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:09] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*Page*
*26*
Dedicated to my besty *AISHA GENTLE LADY*💃 _Daga ni sai ke tawan_
_Nidai yau najarabtu da abun takaici yafi kusan biyar ina editing yana gogewa bansan meyasaba wlh har nagaji dayi tunjiya nake abu ďaya Amma ina kusan gamawa sai wayar ta mutu dakanta ta kunnu idan nashiga sai naga yagoge min gyran dana yi wlh har nagaji kukane kawai yarage min_🤧🤧
*Gaisuwar wannan page ďin gabaki ďayan sa takice my sister HAUWA SAMASHER keďin daban kike cikin mutane bazan bòye miki ba ina mai farin cikin kasancewata nice mawallafiyar littafin KADDA KO SAKACi nagode sosai SMASHER fatan Allah yaqara hazaqa kina haske akoda yaushe muna tare*🤞🏿
🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂
*HAPPY BIRTHDAY 2 U MY QAWALLI HANEEFA USMAN FATAN ALLAH YAQARO MIKI SHEKARU MASU TARIN ALBARKA CIKIN ADDININ MUSULUNCI AM SO HAPPY FOR U DEAR*🎂🎂🎂🎂🎂
*HBD again and again is ur time hanefuna ana mugun tare babu rabewa*😘
🌲 *YAYI SAKE*🌲
*NA AISHA A'MUHD*
Ban mance dake ba wlh
*JINJINAR BAN GIRMA GAREKI YAR UWA BA SHAKKA KINYI NAMIJIN KOKARI MUNGA SAKON DA KIKA ISAR MANA TABBAS YAYI SAKE YA FAĎAKAR YA NISHAĎANTAR FATAN ALLAH YAQARA BASIRA DA HAZAQA, DUK WANDA YABARI BAI KARANTA BA AYANZU TO BA SHAKKA ZAIYI SAKE KO INCE YAYI SAKE* 😜 *SAI MUN JIKI ASABON LITTAFIN KI NAGABA MADAM AISHU, MAI SHERIFF KE MIKI FATAN ALKHAIRI*🙏🏿
Yau tunda asuba bayan ta idar da sallah tayi azkar tare dayin addu'oi sosai tana nan zaune tana tasbihi har garin yasoma hasken rana,,dogon hamma ne yazo mata idonta yana rufewa alaman baccin bai isheta ba, tashi tayi ta haďe sallayan tare da ninke hijabin bayan ta cire ta ajiye su a mazaunin su tana tangal tangal kamar zata faďi taqara hayewa kan gado taja bargo ta rufe duk jikinta idanunta a rufe sabon bacci mai nauyi yasake ďaukanta,,"
Har wajan misalin karfe goma bata farka ba, lokacin tuni har sun kammala da karin safe jin shiru baiga fitowar taba gashi office zai wuce yasa yayi hanyar ďakinta dan ganin ko lfy take, a hankali ya tura ķofar ďakin ya shiga yana sanye cikin farar shadda kaftan kansa sanye da hula ďinkin bama kansa da hula ďinkin bama sai ķàmshi ke fita a ajikin sa, kwance ya hangota dukunkune cikin bargo da alamun sanyin A C yana shiga jikinta sosai tamkar dole aka sata kwanciya cikin sanyi, kai ya girgiza ya qarasa bakin gadon ya zauna bayan ya kashe mata A C lausassar hannun sa yakai bisa gashin kanta wanda ya kwanta mata luf a gaban goshinta ya kawar mata ganin zai iya shige mata duk sanda ta farka, a hankali yakai ďan madaidaicin bakinsa kan nata ya sumbace ta fuskar sa ďauke da murmushi yashafi kanta abu dayawa yake sakawa cikin ran sa shi ďaya yasan me yakeji tattare da ita saida yaqara sunbatan ta a gefen fuskanta kafin daga bisani ya miqe ķàmshin daddaďan turaren jikinsa duk ya gauraye cikin dakin ya fice yaja mata ķofar ya rufe kai tsaye bai tsaya yin komai ba ya fice haraban gidan ya nufi inda motar sa yake ya shiga tare da tasharwa baba mai gadi ya buďe masa get ya yafice,,"
Ba ita ta farkaba sai wajan wuraren karfe goma sha ďaya, a hankali ta buďe idon ta tana murzawa tare dayin miqa bakinta ďauke da salati ita kanta tasan tayi bacci sosai yaukam ba kaďan ba murmushi ne ya bayyana a fuskan ta jin kamshin turaren sa ya gauraye cikin ďakin ko ba'a faďa mata hakan ya tabbatar mata da cewa ya shigo cikin ďakin, ganin yanda lokaci yatafi sosai gashi aiki ne sosai da ita yasa tayi gaggawan tashi tsaye ta shige toilet, wanka tayi tare dayin brosh kafin ta fito ďaure da babban towel ta goge jikinta cikin sauri ta shafa mai kafin tafeshe jikinta da turaruka ta zari dogon riga nashan iska ta saka ta ďaure kanta da ďan kwalin sa, bata tsaya bata lokaci ba ta gyare ko ina na ďakin nata yayi fesfes dashi ta wuce toilet ta gyara abunda yakamata ta gyara da yake jiya ta wanke shi hakan yasa babu datti sai ďan abunda baza'a rasaba,, tana kammalawa ta fice a ďakin tareda jan ķofar ta rufe,,"
fitan ta daga ďakin ta nufi ķofar da zai sadata da bayan gidan, karo taci da Maraqishiya daidai ķofar fitan hannunta riqe da waya a kunne tana sheqa dariya, baya taja ta tsaya dan su gaisa,, tsagaitawa tayi da dariyan tayi saurin kashe wayar dan gudun kar taji abunda shiwari take gaya mata, dole yasa ta murmushin yaķe ta kalle ta kafin tace yau ina kika shige ne tun safe har mukayi karin kumullo baki fitoba ina fatan lfy dai? lafiya lau ta bata amsa a takaice wlh bacci ne yau sosai ya rufe min ido shiyasa, Aiyya ai naji shiru ne har zan leqa kuma sai natsaya nace bari in jira fitowar warki tunda lfy kike shikenan daman fita zanyi yanzu halan sai yamma zan dawo yau kece da girki naso in zauna natayaki but inada abunyi mai mahimmanci Amma gobe da izinin Allah ina gida zan tayaki cikin sakin fuska ďauke da fara'a take maganar tana dafe da kafaďar ta,,
"murmushi kaďan humaira tayi tace laah bakomi fa wlh Anty zan iyayi ni kaďai ai nagode sosai a dawo lfy, Allah yasa tace da ita ta wuce zuciyar ta tunkushe da abubuwa iri iri Allah Allah take taje ta dawo daga gidan shiwari tazo ta aiwatar da abunda ta shirya mata a yau tana dariyar mugunta taje ďakin ta tagama shiryawa kafin ta fice a gidan da motar ta,"
Koda ta fito bayan gidan kitchen ďinta ta nufa wanda Abdulmalik yasa aka haďa mata shi madaidaici tare da store a manne dashi tsayawa tayi tana kallon kitchen ďin yanda taga tsaruwan shi iya tsaruwa an zagaye shi da drowes ruwan toka da baki sosai cloun ya burgeta ya mata kyau matuka tana nan ta zubawa kitchen ďin ido tana nazarin ta ina zata soma ganin lokaci na daďa kurewa ya sanya ta cikin hanzari ta fiffito da kayoyakin ta wanda aka tara su cikin store tafara jerasu ko wanne ta ijiye shi inda yadace ya zauna lokaci qalilan ya ďauketa ta kammala jera kulolin zuba abinci kyawawa wanda mummy tasa aka siyo mata daga dubai,, kayan abincin da Abdulmalik ya cefano musu kowa da nashi komai ya siya hatta ďanyen kaya bai bari saida yasa aka kawo musu da yake yanada yan kasuwa wanda ya sansu,,bata zauna wani hutu ba ta ďauki ďaya daga cikin tukunyanta masu sabo fil ta wankesu tas ta ďaura kan gase naman rago ta cirota ta wanke ta jefa cikin tukunyar Albasa manya manya mai yawa ta kwaso ta zauna bakin kitchen ďin tare da fara yankawa,, kuka yasakata sosai idanun yayi jazir tanayi tana share hawaye, cikin sauri ta kammala yankawa ta juye shi kan naman tare da kirbà kayan miyanta ta zuba akai tare da zuba kanwa kaďan dan yasashi narkewa da wuri kafin ta rufe tukunyar, bata tsaya bata lokaci ba ta ďaura ruwan farar shinkafa ta rufe kafin ya tafasa ta ďaura kaza tukun taci gaba da haďa sauran kayan haďin abincin,,"
Bayan ta kammala haďa komai taja kujeran dage tsakiyan kitchen ďin ta zauna jiran dafuwan sa tare da faďin Washhh Allah tana dafe kanta duk tabi ta haďa zufa tana sharewa Allah Allah take tayi ta kammala wannan girkin taje tayi wanka ta huta ji take ta jima rabon da tayi aiki dayawa irin na yau har ta mance,,jin anata qiraye qirayen sallahn Azahar yasata miqewa ta fice daga kitchen bayan ta duba girkin ta,,"kai tsaye ďakinta ta nufa ta shige toilet ta ďauro alwala ta fito kafin ta tayar da sallah,,"
idarwan keda wiya bayan tayi azikar tare dayin addu'oi ta miqe ta fice a ďakin ta koma kitchen taci gaba da haďa sauran abubuwan da suka rage mata,,"
Sai wuraren karfe uku kafin ta kammala haďa komai taciro sabbin kulolin ta masu masifar kyau kala biyu jaa ďayan kuma ruwan madara,, saida ta ďauraye su kafin tafara raba Abincin,, jan kulan ta zubawa Abdulmalik kafin ta juyewa su Umma sauran ta rage saura ta samu ďan madaidaicin kula ta juyewa Baba mai gadi,,cikin sauri ta kammala rarrabawa ta jera su a dining kafin ta zura hijabin ta dogo har qasa wanda ta ajiye kusa da ita koda wani zai shigo fita waje tayi ta miqawa baba mai gadi nashi bayan sun gaisa,, daďin karrama shi da takeyi yakeji shi tunda yake aikin gadi cikin gidan nan in banda ogansa matar gidan ba girmamashi takeba bare har na kula tabashi abinci mai rai da lfy cike da murna yayi mata godiya yana mata fatan alhairi,,bayan ta miqa mishi ta dawo ciki kai tsaye ta wuce ďakin sa dan ta gyara masa , tsayawa tayi tana rarraba idanu ta rasa ta ina ma zata fara ďaki ne gashi babba dashi yasha kayan jere masu masifar kyau da tsada komai nashi Fari ne da baki hatta carpet ďin dake shimfiďe tsakiyan ďakin fari ne da baki sosai taga colurn ďakin ya mata kyau ya burgeta saidai rashin samun fasali da beyi ba komai a hargitse yake ba inda yakamata su zauna yakeba yasa dattin ďakin yafito ,ganin tsayuwan da tayi qara bàta mata lokaci yakeyi ya sanya cikin hanzari ta soma tattare kayan da suke zube filin ďakin da Alama bayan fitan shi Maraqishiya bata tsaya gyara ďakin ba ta fice Unguwa,,"
Saida ta gyara ďakin yayi kyau komai ta ajiye su inda yadace ya zauna kafin ta nufi yake adana kayan sawan sa,, mamaki ne ya isheta ganin kayan duk a hargitse suke komai a haďe kamar tunda aka ajiyesu ba'a tabà sa hannu da sunan gyarawa ba, ajiyan zuciya ta sauke duk da ta gaji sosai yau ďin nan Amman dole ta gyara masa bazata iya tana ganin su haka ta qyale ba,, qara ďaga jiki tayi ta shiga gyarawa, bai ďauke lokaci dayawa ba ta kammala kafin ta shige toilet, bata tsaya kallon komai ba ta shiga wankewa ganin shima dattin ne dashi har sosai ya soma dafewa abunka da farin abu,,"
Sosai tasa karfinta ta wanke shi yafita yayi fari tas dashi kamar bashi ba, bayan ta gama ne taja masa ďaikn ta rufe kafin ta shiga nata,, wanka sosai da ruwan zafi tayi tare da ďauro alwala jin anqira sallahn la'asar,, tana fitowa ta nufi wajan kayan sawan ta, ta ciro atumfa mai kyau ďinkin riga da skirt,, sakawa tayi bayan ta goge jikinta ta shafa mai ķàmshi tare da feshe ko wanne lungu da sako jikinta da turaruka masu ķàmshi, sama sama tayi kwalliya ba sosai ba, ta zari hijabi ta gabatar da sallah kafin ta dawo gaban madubin tayi ďaurin ďan kwalin ta goggoro mai kyau, ta juya ta fice daga ďakin,,"
Kitchen ta koma ta kunna garwashi ta raba shi kwasko uku dawo tafara saka turaren wutan da Mummy tasa musamman aka haďa mata a maiduguri da jimawa tun batakai girman yanzu ba ko wanne turare mai ķàmshi daban ta zuba ďaya takai ďakin sa ďaya takai ďakinta ďayan kuma tabari a nan parlon,,kujera ta samu ta zauna dan jiran dawowar sa ta maida hankalin ta ga TV tana kallon tashar zee wold,,"
Bashi ya dawo gida ba sai wajan karfe shida na yamma lokacin har bacci sama sama,, bakinsa ďauke da sallama ya shiga ciki, daddaďan ķàmshi ne wanda tunda yake cikin rayuwan sa bai tabà jin irin saba ga wani sanyin A C mai kunshe da daddaďan ni'ima dake ratsa masa gabòbìn jikinsa, tsayawa yayi inda yake yakasa qarasawa shi kanshi yasan yasan yayi dacen mace wanda zata kula dashi ta jiyar sa abunda yarasa bai samu ba kamar yanda mazaje suke samu gun matan auran su,, kamar daga mafarki taji sallamar sa hakan yasa tayi saurin miqewa, a hankali ta iso gareshi tana murmushi takai har qasa tace sannu da zuwa cikin qasa da murya tamkar batason yin magana, hannun sa yasa ya ďagota yasakar mata da kayataccan murmushi tare da rungume ta tsam cikin faffaďar ķirjin sa yana shaķar ķàmshin jikinta ya buďi bakin sa kamar mai raďa yace mata,,"
"Haba babynah haka zakiwa mijinki sannu da zuwa? idanuwanta ta lumshe batace masa komai ba tanajin daďin yanda yake mata maganar cikin sanyayyar muryansa mai mata daďin sauraro,, qara matseta yayi har saida tayi yar qara kaďan bata shirya tace dan Allah ka daina zaka iya ji min ciyo fa,,to kibani amsa yafaďa yana mata dariya bayan ya ďaugo da kanta yana kallon cikin kwayar idon ta,, saukar da nata idon tayi tace Himm nidai yanzu ba wannan ba muje ka watsa ruwa ajikin ka sai kafito kaci abinci, tana gama faďa masa ta zare jikinta daga nashi ta juya da niyar tafiya,,hannun yakamo yadawo da ita baya ya zagayeta duk hannayen sa biyu yana sinsinar wiyar ta yace to matar ai baki bari nagama abinda zanyi ba gaggawan meye kike kiyi shiru kawai idan nagama zan miki magana sai muje ki min wankan,,buďe baki tayi da niyar masa magana Maraqishiya ta turo ķofar parloun ta shigo kanta a sama kaďan ta mangaje su kafin tadawo baya,, tayi mutuwar tsaye idonta akansu takasa koda kekkyawan motsi zuciyar ta sosai yake mata kuna tamkar karwashi yana sokan kirjin ta ganin su manne da juna ba qaramin tada mata da hankali yayi ba,,"
Jin alamun akwai mutum abayan su ya sanya ta zare jikinta daga nashi ta jiyo taga ko waye,,ganinta tsaye har yanzu idonta akan nasu ko keftawa batayi ba Amma yayi jazir dashi kamar gauta dum dum takejin buguwar zuciyar ta, murmushi humaira ta sakar mata tace sannu da dawowa sai yanzu? wani irin mugun kallo ta watsa mata cike da takaici ta mangajeta a kafaďa ta wuce ko kallon inda yake batayi ba ta shige ďakin ta tare watsar da jakan dake hannun ta yaye mayafin dake kanta ta rufzu kan gado ita kaďai tasan irin raďaďin zafin da zuciyar ta yake mata a yanzu tamkar tacire daga ķirjinta takeji ta huta,,"
Jiki a sanyaye humaira ta kamo hannun sa tace muje ko nasan ka gaji dayama, baice mata komai ba suka jera kai tsaye ďakin sa suka shige tana kallon sa tace kashiga wankan kafin zanje nabawa driver abincin su Umma yakai musu dare yanayi,,Aiyya yauma kenan bazaki min wankan dakan ki ba ni kaďai zanyi kike nufi cike da kashe murya yake mata maganar kamar ďan qara min yaro,, murmushi tayi masa tace karka damu kabini bashi gobe tafice cikin sauri ganin yana shirin cafko ta,, kai ya girgiza kafin ya shige toilet ďin,,"
Tana fita daga ďakin tayi kicibìs da Maraqishiya tana barin wajan dining, cike da fargaba ta bòye hannunta ta baya tana qiqiro murmushi tace qanwata sannu da aiki fa kin aikatu gaskiya,,, rasa abun faďa humaira tayi cike da mamaki take binta da kallo ganin yannda tayi tsurutsuru saikace marar gaskiya tana bòye hannunta ta baya banda haka da fishi ta dawo harda mangaje ta Amma yanzu kamar ba itaba,, murmushin kawai ta mayar mata tace Eh to ya za'ayi ai dole ne,, to ni zan shiga ciki naga maigidan naki yana nan kar natakura muku sai anjima idan kun gama na fito,, bazaki zo muci abincin ba? murmushi ta qarayi tace karki damu qanwata a koshe nake hala dai ko anjima, to Allah ya kaimu tace da ita sai kin fito tana gama faďan haka ta wuce zuwa kitchen, Driver tagani tsaye yana jiran fitowar ta, saida suka gaisa cikin girmamawa kafin ta miqa masa kayan abincin tace yakai gidan su Umma mahaifiyar Abdulmalik tana gama basa ta dawo ciki a dining ta hangosa yana latsa wayar sa, nufowa tayi inda yake tasa hannayenta ta dafa kafaďar sa tare da sakar masa yar murmushi sorry nabarka da yunwa ko bari na zuba maka,, bata tsaya jin mai zaice ba ta dawo ta zauna kan kujeran dake kusa dashi tafara zuba masa,, lafiyayyan farar shinkafar ta soma zubawa kafin ta zuba masa jar miyan akai ta buďe kular kazar ma ta zuba masa duk ya watsa mata idanun shi akanta yana ganin yanda take ďiba masa abincin cike da nutsuwa,, kaďai masa idon tayi da hannu tace mai kuma yacika maka idon haka kake tunani har nagama zubawa bakasani ba? kece kikeso ki min illah yafaďa a takaice yana cakulan kumatunta bayan ya ajiye wayar dake hannun sa,, nidai karka min sharri kafara ci karyayi sanyi yana dariya ya ďauki loma ďaya na abincin yakai bakinsa da bisimillah.....
_Afuwan da jin kirin dana ďauka kafin nayi typing_🙏🏿🙏🏿
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:09] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*Page*
*27*
Dedicated to my *AISHA GENTLE LADY*💃 _Daga ni sai ke tawan
🙏🏿🙏🏿🙏🏿🙏🏿🙏🏿🙏🏿🙏🏿
*Qawata HAUWA NA YAYA (UMMU ARIF) mai yasa bazaki amince dani ba?wannan hukuncin da kika yanke min baqara min illah tayi min ba sosai wlh kullum cikin bugun zuciya nake dan Allah ki taimaka ki agaza min qawalli ta* 😭😭😭😭😭😭😭
*Wannan shafin bata kowa bace illah taki ďiyata sister FEEDOHM ina mai jinjina miki ina tayaki murna kan kammala littafin ZAN RAYU DAKE, ahakikanin gaskiya kinyi namijin kokari posting 2 pages kullum fatan Allah yaqara miki hazaqa da kaifin ido FEEDOHM kina haskawa koda yaushe ban mance ba ina daďa godiya da mallaka mana littafin ABINDA KE BOYE da kikayi keďin daban ce FEEDOHM Allah yabar zuminci da kaunar juna iya wiya ana mugun tare*🤞🏿
_TUNATAR WACE_👌🏿
_Ingantacciyar hadisi daga bakin fiyayyan halitta Manzon Allah (SAW)_
*An karbò daga baban hurairah-Allah yaqara masa yarda-yace: Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yace:-"Babu mai shiga aljanna har sai kunyi imani. baza kuyi imani ba har sai kun so junan ku. Ashe bazan nuna muku wani abuba wanda idan kukayi shi? ku yaďa sallama atsakanin ku zaku so junanku*
*Muslim ne ya rawaito, Allah yasa muso junanmu so na gaskiya*🙏🏿
Kafin yakai ga sawa abakin sa ya dubeta ganin bata da niyar ci yace bangane ba ke bazakici bane kin tura min ni kaďai incinye dan ni gani rumbu?, dariya ne yaso ķubùce mata ganin yanda yadake yayi maganar fuskar sa a haďe, danne dariyar tayi tana yar murmushi tace kaidai fara ci ina nan tafe zanci ai gaggawar mi kakeyi haka?, kansa ya girgiza yace to sai kinzo madam nidai bazan iya jiranki ba,,"
Abincin yakai bakinsa, tare da kafeta da ido yana sakar mata da murmushi Allah Allah yake yaga yaci abincin yanda yaji fitinan nan ķàmshin sa da ya mamaye duk cikin gidan tamkar yanzu ne ake girkawa,,"
bai kai ga fara tauna abincinba ba shiri ya dawo dashi tari sosai yakama shi sakamakon wani irin gigitaccan yajin da yaji kame masa baki, neman abinda zai sha yakore masa azababban barkonon da yake kona masa baki tamkar wutan karwashi aka watsa masa duk yabi ya rikice,,"
Cikin tashin hankali ta miqe ta iyo kanshi tana ambaton sunan Allah ta dafe kafaďar kafin ta shiga tambayar sa, lfy kuma me sameka haka faďa min dan Allah,,"
Rikicewa tayi ganin yanda yabi ya galabaita gabaki ďaya yasara meke masa daďi, cikin sauri ta ďauki ruwan sanyin da ta ajiye kusa dasu ta buďe masa tana masa sannu,"
Ba shiri ya karbà daga hannun ta ya kafa kai yana kwankwaďa tamkar zai haďe da rubber ya shanye,,"
Saida ya shanye ruwan tas yayi jifa da rubber kafin ya jinginar da kansa jikin kujeran yana saukar da wahalallan numfashi har lokacin bakinsa raďaďi yake masa bai dena jin zafin ba,,kitchen ta koma ta ďauko rubber zuma cikin sauri take har tana tuntubè ta dawo tabashi a hannun sa tare da ce masa yasha zaiji saukin zafin da yakeji,,"
karbà yayi ya kafa rubber duka a bakinsa yafara kwankwaďa tamkar yana shan ruwa,, warta tayi daga hannun sa ganin yana neman shanyewa sannu ta kuma faďa masa tana duban sa har lokacin yana fifita bakinsa da hannu ya rufe ido,,"
kallon sa ta kumayi akaro na biyu tace dear minene kaji acikin abincin har yasa ka rikicewa haka yaji ne yayi yawa ko meye ?,,"idon sa ya buďe ya sauķe su anata cikin iriyar murya yace,,"
Wani irin tambayan rainin hankali ne wannan? kina nufin bakisan meye kika zuba yayi yawa ba? to idan sani ne bakiyi ba har abada kada Allah yasa kisani nima bansani ba ga abincin nan yabaki amsa, yana kaiwa nan ya miqe tsaye fuskar sa ahaďe ya ďauki rubber ruwa ďaya ko kallon inda take baiyi ba yafice daga gidan,,"
Mutuwar tsaye ne ya kamata zuciyar ta na bugawa jikinta har bari yake ta shiga tunani iri iri mamaki ne ya isheta wai shin mafarki take koko?,, tana nan tsaye inda yabar ta takasa koda motsawa,,qiran sallan magariba ne daya daki kunnen ta yadawo da ita daga tunanin da tafaďa,,"
Ajiyan zuciya ta sauķe a hankali ta ďibi abincin da yabari takai bakinta tare da yin bismillah tafara taunawa,,"
Bashiri itama ta dawo dashi tana tari sosai take ta buďe rubber ruwa ta shanye, ganin zafin qaruwa yake yasa ta shan zuman da takawo masa,, bata cire daga bakinta ba saida taji dama dama kafin taja kujera ta zauna tana sauķar da numfashi sama sama tunda take a rayuwar ta bata tabà cin abincin mai fitinan nan yaji irin na yauba,,"
Tambayar kanta ta shiga yi wai shin itace da kanda ta girka abinci mai a zababban yaji haka? ita dai tasan sanda ta gama haďa komai ta tabà taji yayi daidai babu abunda ya kauce koya gaza Amma to tambayar ta ďaya a nan shine ya akayi abincin yayi yaji dayawa tunda tasan lfy lau tabar shi?,,"
Ganin ba mai bata amsa zata samu ba yasata miqewa tsaye ta kwashi kayan abincin duka tamayar kitchen kafin ta wuce ďakin ta dan gabatar da sallah,,"
Rakubè jikin ķofar ďakin ta take duk abunda ke faruwa akan idanun ta tana kallon su ba abunda ya wuce ta,, ganin aikinta yafara yin kyau a yau kaďai har ya soma gaya mata ďacin magana, girgiza kai tayi tare da kwashewa da wani irin mugun dariya wanda yasa har tanajin hanjin cikinta na kullewa, kamewa tayi ta durkushe a gurin tana ci gaba da dariya sosai kafin daga bisani ta tsagaita ta miqe tsaye tana kallon ķofar ďakin Humaira tace shegiya masu zubin yan wutan jahannama kaďan ma kikagani yarinya yanzu ma nafara aiwatar da aikina akanki, zakisan da waye kike zaman kishiya muje zuwa, tana kaiwa nan ta kuma kwashe da dariya ta shige ďakin ta tare da ďaukan wayar ta tashiga lalumo number Shiwari,,"
baifi ringing biyu ba Shiwari ta ďauka tana faďin qawata yane har kin isa kenan?,, dariya da take dannewa ya ķubùce mata ba shiri ta zube kan gado ta shiga yi babu gaggautawa , shiru shiwari tayi tana mamakin qawar tata ko meye yasata dariya haka?,,"
Sanda tayi mai isar ta kafin ta tsagaita tace Shiwari buďe kunnenki da kyau ki saurare aminiyar ki yau tayi abun arziki,,bangane inda kika dosa ba Maraqishiya kiyi min bayani da kyau ko zan fahimta,, girgiza kai tayi tace kefa shiwari wani lokacin bake bace bakya zuwa gana wlh sauki salak bayan kuma kece jagorata,,ina kuwa zan gane me kike nufi kinzo sai dariya kiketayi saikace sabuwar tabùwa,,murmushi Maraqishiya tayi kafin daga bisani tace barin in baki lbr,,"
Tafara da cewa kinsan ina barin gidan ki nace miki zan wuce wani waje to sai Allah ya taimake ni nafasa wani abu yace in koma gida kawai,,ajiyan zuciya ta sauķe kafin tace qawata kinsan meye idanuna suka gane min?,,kai shiwari ta girgiza alaman a a tace sai kin faďa,,"
Himm taci gaba da cewa shigana cikin parloun idanuna ya sauka akan Abdulmalik mijina da wannan shegiya yar iskar yarinyan manne da juna ya rungume ta baya suna zuba soyayya basu ma san na shigo ba,, ķur'anin Allah shiwari bakiji yanda zuciya ta tashiga min kuna tamkar wutan karwashi ake watsa min duk wani kishin da nasan indashi da wanda bansani ba wlh saida suka tashi a wannan lokakin naso na nuna musu bala'i na a lokacin Amma na danne zuciya ta na wuce ďaki banbi ta kansu ba, tsagaitawa tayi jin shiru yasa tace,"
kinaji na kuwa shiwari? inajinki qawata kici gaba,,"ci gaba da bata lbrn tayi tace kafin inkai ga shiga ďaki idanuna suka min tozali da kayan abincin da ta haďa da alama babu wanda ya taba bayan na shige ďaki na kwanta kaďan zuciya ta sosai take min kuna shiwari tamkar zata bàlla min kirjina ta fito waje,, tashi nayi bayan mintina kaďan na leqa ta ķofar ďaki na naga babu kowa sunbar parloun hakan ya sanya cikin sanďa nafita na nufi kitchen cikin sauri na kwashi attarugu wanda bansan adadunsu ba na kirbà shi tare da ďiban wannan jan barkonon na haďe su waje guda,,"
Ke atakaice dai ina gaya miki qawata haka na kwashi wannan yajin gabaki ďaya na garwaye su cikin haďaďďan jan miyar da kazan da ta dafa ni kaina billahillazi kinji na rantse miki wlh karfin yajin ba qaramin min addaba na yayi ba, Amma ta kusa cafkeni kafin na waske na wuce, nabarta a nan,,"
kekam qawata atakaice dai ina gaya miki bayan yafito ya soma cin abincin sosai yasha wuya dan azaba rikicewa tayi cikin sauri ta taimaka masa inajinta tana masa sannu, karshe dai ďacin magana ya gaggaya mata ransa abaçe haka ya kade ta ya fice yabar gidan, ina rakubè jikin ķofar ďakina ina leqan su, tana kuma sheqa dariya taqare maganar da cewa kai yau qawata zuciya ta wasai nake jinta tamkar in zuba ruwa aqasa insha dan farinciki,,"
katseta Shiwari tayi ranta a bàce tace kingama koda raura? na gama ta bata amsa atakaice tana jiran taji me zatace,,"
To sai anjima tunda kingama ni na ďauka wani lbrn arziki zakibani ashe ba hakaba akan wannan ďan kankanin makircin da bai taka kara yakarya ba tun ďazu zaki bàta min lokaci ko sallah banyi ba na tsaya nabaki lokaci na, taci gaba da cewa wlh da nasan wannan ne da ban tsaya na saurareki ba idan zaki haďa makircin da babu kyau ba qarami zakiyi ba sai kin nemi babba wanda kikega yafi komai illah yafi komai yawan zunubi kafin kiyi shi dan haka idan bazaki ďauki shawarata ba karki kuma lalata min lokaci na irin haka, tana gama faďin haka kit ta kashe wayar bata jira taji ta cewar taba,,"
Jiki a sanyaye Maraqishiya ta ajiye wayar tana nazarin maganganun shiwarin ita aga ninta tayi abu mai kyau harda zumuďin sanar da ita ashe gwaleta zatayi? saida ta gama nazarinta har lokacin kafin daga bisani ta tashi ta shige toilet dan ganin yanda garin yayi duhu sosai gashi ko sallahn magariba batayi ba,,"
🌾🍃🌾🍃🌾🍃🌾
Umma ce zaune filin tsakiyar parlou ta zubawa kulolin abincin da Humaira ta aiko wanda tunda driver ya dire su a parloun suke gurin ko yunquri tabawa batayi ba bare tasan meyene aciki, ita kaďai tasan me take saqawa cikin ranta,,Batula ce ta shigo cikin parloun ita da suwaiba suna fira guri suka samu suka zauna Batula ta kalli kulolin dake jere a tsakiyar parlon tace Umma waye ya aiko wanna kyawawan kulolin abincin gaskiya sunyi min kyau ba karya bari muga meyene aciki,,"
Tasowa tayi daga inda take ta buďe kulan miyar da kazan taji wani irin fitinan nan ķàmshi ya doki hancinta ba shiri ta miqe tsaye tana faďin wlh ko waye ya kawo abincin nan sai naci dan daga gani shiga zaiyi, bayan ta suwaiba tabi tace ai bake kaďai ba wlh harda ni, plete da cokali suka ďauko daga kitchen suka dawo har lokacin Umma ta zuba musu ido tana kallon su bata ce musu qala ba,, sun gama ďiba abincin kenan zasu soma kaiwa bakin su, rai abàce cikin faďa umma ta ďaga musu tsawa tace dan ubanku bakuda hankali ne kwaďayayyon banza da wofi kunsan ko wanne irin guba tayi amfani dashi cikin abincin?....
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:09] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT_M*✍🏻
*Page*
*28*
Dedicated to my *AISHA GENTLE LADY*💃 _Daga ni sai ke tawan_
🎂🎂🎂🎂🎂🎂
*HAPPY BIRTHDAY 2 U MY QAWALLI UMMU ARIF😍 FATAN ALLAH YAQARO MIKI SHEKARU MASU AL BARKA CIKIN ADDININ MUSULUNCI ke ďin daban ce Allah yabaki lfy da karfin jiki ya sauķe ki lfy kifitar min da takwara hafsy 😉 AM SO HAPPY DEAR Qawata HAUWA NA YAYA (UMMU ARIF)kaina aqasa dai* ☹
_My FEEDOHM_🙋🏿
Basu kaiga sa awa cikin bakin na suba suka dawo da abincin duk suka zubawa Umma idanu suna kallon ta jin furucin da tayi,,ajiye cokalin Batula tayi tare da faďin umma meyasa zaki hanamu ci? kuma ya kike faďin ta zuba guba aciki? wai ma tukun wayene ya aiko abincin wanda yasa hankalin ki yaqi ďaukan sa har kike wannan kalaman?,duk wannan tambayar tsareta tayi da ido tana jiran taji amsar da zata bata,,"
Muguwar harara ta watsa mata tare da kai mata daķuwa da hannu cikin faďa tace kinci gidanku Batula shegiya uwar tambaya to qanwar uwaki ce ta aiko da abincin kwaďayayyar yarinya idan naga kun kuskura kunci abincin nan wlh sai naci zarafin ko waccen ku a gidan nan masu zubin mayu kawai, tana kaiwa nan tace maza ku tashi ku kwashe min shi agabana bana bukatar ganin sa,,"
Shiru tayi bata kuma cewa komai ba tasan yanzu idan ta qarayin magana zagi da faďan da yafi wannan zata balbale ta dashi hakan yasata tashi tsaye tace da suwaiba su kwashe sukai kitchen ďin badan ranta yaso ba Amman ko ba'afaďa mataba tasan daga gidan yaya aka akawo kuma wannan faďan nata ba zai wuce kan Humaira bane,,"
Ďauka sukayi kowa sukayi hanyar fita, karo sukaci da Abba da inna a ķofar suna shigowa, kallon tuhuma inna tabisu dashi ďaya bayan ďaya tace ina kuma zaku kai abincin nida nazo ci?, kitchen zamu kai batula ta bata amsa atakaice tare da rabèwa ta gefen zata wuce, kamo ta Inna tayi ta dawo da ita baya tare da haďe fuska tace,,"
dawo dashi marar kunya idan na gama ci kya mayar kitchen ďin,,ba musu ta dawo dashi abun nema yasamu matar driver ta haifi taya dubun su goma ya huta dama itama so take taci umma ta hanasu tunda yanzu Inna ma ci zatayi kuma Abba ya shigo ai bata isa ta hanasu ba,,"
Qarawa tayi akan wanda ta ďiba ďazun, kafin sufara ci umma cike da masifa tana nuna su da yatsa tace ķur'anin Allah duk wani abunda yasameku ta dalilin wannan abincin to kuyi kuka da kanku tunda nahanaku ku nuna min ku yan dangin sune to bisimillah gashi nan sai kuci ai,,"
Basubi ta kanta ba suka soma kaiwa bakin su kowa yana sauri yaga yaci, hannu inna tasa cikin plete ďin ta cika tare da yin bismillah takai bakinta,,A lokaci ďaya suka dawo da abincin tari sosai ya kamasu yi suke babu kakkautawa duk sunbi sun rikice suna neman agaji, Amai ne yakama inna a lokaci ďaya tafara kwararawa tana tari sosai tamkar zata amayar da kayan cikin ta,,"
cikin tashin hankali Umma da Abba suka iyo kansu babu abunda Abba ke ambatawa sai sunan Allah yana tambayar me yasamesu, hannu umma ta ďaura aka tana zabga salati cikin ďaga murya tace shikenan billahillazi ta kashe su shegiyar mayya mai bakar aniya dama kamar nasan za'ayi haka saida nace muku karkuci wannan shegen abincin Amman kuka min kunnan uwar shegu to garinta nan ai yanzu gashi tana neman hanyar hallakar daku ,,"
Wani irin mugun kallo Abba yayi mata ganin yanda duk sukabi suka galabaita daga gani yajine ya shaqesu ita kuma tazo tana kawo musu banzan magana hakan ya sanya shi cikin ďaga murya ransa a bàce yace ke bara'atu banason zancan banza da wofi maza wuce ki kawo musu ruwan sanyi da zuma,,Alhaji wlh kar muyi asaran ruwan mu wannan ba yaji bane wlh guba ta zuba aciki gwara muyi gaggawar kaisu asibiti tun kafin su qarasa mutuwa dan wannan tarin kam bana tunanin zasu tashi,,"
Ganin irin kallon da ya kuma binta dashi ya sanya ta wucewa aiken da yayi mata tana zagezage tare da tsinewa humaira taje kitchen ďin ta ďauko rubber zuma da ruwan sanyi ta dawo har lokacin Abba na riqe da Inna yana mata sannu tare da bubbuga bayanta damuwa qarara a fuskar sa ya rasa wanne irin fitinan yaji ne haka wanda har yake neman hallaka masa uwa da yara,,"
Amsar ruwan da zuman yayi daga hannun ta ya buďe yasa abakin ta tasha ruwan sosai tare da bata zuman shima tasha kafin ya miqawa batula da suwaiba sauran dan susha ko zai rage musu azaban da sukeji a yanzu,,"
Ďaga inna yayi yamar da ita kan kujera yanaci gaba dayi mata sannu,,wahalallan numfashi ta sauķe tana fifita bakin nata da hannu har lokacin bata dena jin zafin yajin ba sosai ta galabaita ji take zuciyar ta yana mata kuna tamkar gasa shi ake da wutan karwashi,,"
Safa da marwa umma ta somayi cikin tsakiyar parloun tana nazari tare da dantse karamin yatsanta abaki tana kaďa kai tace ķur'anin Allah bazan barki ki zauna lfy ba Allah ya kaimu gobe sai kinyi danasin yun kurin kashe mu da kikayi,,kai Abba ya ďago ya dubeta kafin yace, wlh bara'atu kinji na rantse miki idan kika kuskura kika ďauki ķafa kika fita da sunan zuwa wani waje to wlh zakiga bacin raina idan kuma kin musa ki gwada zuwa kigani, yana kaiwa nan ya ďauki inna ya wuce da ita ďakin ta ya kwantar da ita tare da bata magani kafin yaja mata ķofar ya nufi bàgaren sa,,"
Kai ta kaďa batace masa qala ba azuciyar ta kuwa ta ďauki alwashin cewa dole tayi sammako taje gidan koda kuwa zaiyi faďan da bai tabàyi bane ta gwammace yayi Amma bazata iya haquri ta zauna tana kallo wata shegiya taso kashe mata yara ba kuma ace an hanata ďaukar fansa, jiyo da kai tayi ta watsa wa batula da suwaiba harara kafin tace to dangin kwaďayayyu ga irinta nan ai kungani gobe ma kuci kuma wlh karku kuskura kubar min parlou na haka maza ku gara shi tas wannan shegen abincin kuwa ku tabbatar kun zubar dashi a bola karnaga koda kwalli ďayane tana gama faďin haka ta shige ďakin ta tana bambami,,"
Tashi sukayi suka soma tattare wajan har lokacin bakinsu yana raďaďin zafin yaji bai daina ba haka suka daure suka kammala kwashe kayan abincin tare da goge inda Inna tayi amai, zaman parloun da basuyi ba kenan suka koma ďaki duk kanin su suna danasani da basuci ba ai da bazusha wannan fitinanniyar azaban yajin da yaso kashesu ba,,'"
zaune take kan abar sallah tana tasbihi kallo ďaya zakayi mata kayi zaton bacci take kasancewar lumshe idanunta suke ta jinginar da kanta jikin gado zuciyar ta na tunani iri iri ta rasa ya akayi yaji yayi mata yawa cikin abincin ta damuwar ta ďaya yanzu batasan ya su Umma zasuji nasu ba, kamar an cokareta ta miqe tsaye tare da nannaďe abar sallah bayan ta cire hijabin ta ďaure kanta da ďan kwalin rigan jikin ta kafin ta fice daga ďakin,,"
Zaune ta hango sa a parlou ya miqa hankalin sa ga TV yana kallon tashan rabare,,zuciyar na bugawa ta danne kafin ta qarasa wajan sa, kusa dashi ta zauna tare da riqo hannun sa cikin nata kafin ta ďago da kanta tana kallon sa cikin qara da murya ta soma magana tace,,"
Dan Allah kayi haquri wlh bansan ya akayi haka ta kasance ba Amman insha Allahu zan qara kula hakan bazata kuma faruba, duban sa ta kumayi akaro na biyu kafin tace bari inje in haďo maka wani abu, batajira taji me zaice ba ta miqe tare da sakin hannun sa ta wuce kitchen,,"
Hankalin tane Sam bai kwanta ba sauran miyar da ta rage ackin tukunyar ta buďe ta ďana abakin ta tana fargaban zafin yajin da zataji, idonta a rumtse ga mamakinta salam taji miyar yanda ta haďa shi babu wannan yajin, kaďa kai tayi tare da qara ďiban miyar ta kai bakinta wani farinciki ne ya ziyarci zuciyar ta ido ta lumshe ta kumw buďe su tare da sakin murmushi ta ďaga hannayen ta duk biyu sama tana godewa Allah sosai dama ita tasan bata zuba wannan yajin hakaba Amman koma waye yayi mata wannan aika aikan fatan ta Allah yasaka mata tunda batan shiba,,"
Cike da farinciki tasa shinkafar da miyar da haďaďďan kazan nata sukayi zafi sosai bayan taqara tabà ko wannen su taji basu da wata matsala kafin ta samu qananar kuloli ta juyesu aciki ta haďe su kan babban tire tareda sa plate da cokali ta ciro sobò mai sanyi wanda ta haďa kafin ta ďauki tiran tabar kitchen ďin zuciyar fayau takejinta bata da sauran wata fargaba a yanzu,,"
Nan ta tarar dashi inda ta barshi har lokacin idanun sa sunakan TV,qarasowa tayi wajansa fuskan ta ďauke da murmushi ta ajiye abincin agaban sa itama ta zauna kusa dashi kafin ta dube shi tace,,"
To sauqo kaci abincin nagama, shiru yayi mata baice komai ba kuma bai ďagoba, ganin bashida niyar saukowa yasata qara magana tace, haba mana dan Allah kadaina wannan fishin mana nabaka haquri fa kuma ai gashi na haďo maka wani abincin, cike da shagwaba tayi maganar tamkar zatayi kuka,,"
Saida ďauki mintina kusan biyu kafin ya sauķe ajiyar zuciya ya sauko qasan carpet ďin ya zauna har lokacin bai buďi baki yace mata komai ba illama qara haďe fuka da yake qarayi,, haka zuciyar ta babu daďi ta soma ďiba masa shinkafar ta zuba miyar tare da zuba kazar a gefe taja sauran ta rufe,,qara haďe fuska yayi ganin irin abincin ďazun da yazo kashe shi ne ta qara kawo masa, kawar da plate ďin gefe yayi batare da ya kalleta ba yace,,"
Yanzun ma kasheni kikeso kiyi kenan kin ďauka bazan gane bane zaki kawo abincin ďazu kuma kice min yanzu kika haďa wani,,cikin rashin fahimta ta dube shi sosai kafin daga bisani ta danne zuciyarta duk da bataji daďin maganar da yayi mata ba Amman ta basar tace, dan Allah kabar irin wannan maganar tayaya kake zaton zan iya kashe ka wancan ďin ma ai kuskure akasamu Amma kaci wannan kaji wlh babu komai aciki idan bazaka yarda dani bama kuma bari nafara ci kagani,,"
Bata jira komi ta ďiba abincin takai bakinta tare da yin bismillah ta cinye ta qara wani saida tayi kusan cokali huďu kafin tace masa to gashi naci kuma lfy ta qalau pls kaci kar yunwa ta gama shiga jikinka,,"
To mai kuma yara rage ai babu tariga da tagama cinye min gangan jikina saidai kar a kuma,, basar dashi tayi bata kuma yin magana ba ta saki fuskan ta da kanta ta fara bashi abaki, nan ďin ma saida yayi mata waine waine kafin ya yarda tabashi abaki,,"
Karbàn cokalin yayi daga hannun yace kinga malama barni zanci da kaina ai ni ba yaro bane da zakisani a gaba kamar ďanki kina bani abinci abaki,,"
Yo ai gwara yaro ansan shi yaro akan kai tafaďa tana dariya,"
Allah ki iya bakin yau idan kika shiga hannu na zaki gane kuranki dan ba barinki zanyi ba gwarama kibini a hankali,"
Shiru tayi takawar da zancan da yake tagane inda ya dosa,,sosai abincin yayi masa daďi cikin kwanciyar hankali ya kammala ci yana santi ya dauki sobò mai sanyin da ta zuba mishi a cop yashanye tas kafin ya ďago kansa ya kalleta cike da zolaya yace,,"
Abincin ma ko daďi babu ďauke kayanki bana bukatar sa,,"
Haka zakace ai tunda cikinka yagama cika kana santi bakasan har kacinye ba, yanzu kazo kana burin kunya, tana maganar ne tare da tattare kayan abincin ta mayar kitchen, saida ta tsaya ta wanke kwanukan ta gyara kitchen ďin sauran abincin da yarage ta qira baba mai gadi ta miqa masa kafin ta dawo parloun, wayam taga ba bayanan hakan yasa tayi zaton ko ya shige ďakinsa ne, kashe TV da wutan parloun tayi tare da karaton Ayatul kursiyyu kafin tayi hanyar ďakin ta dan yau ji take saidai tayi kwanan ita kaďai Amman bazataje ďakinsa ba,,"
Batakai ga shiga ďakin ba taji mutum ya ďaga ciďak ba shiri ta buďe baki da niyar kwala ihu tana wintsila ķafafun ta baiyi wata wata ba ya toshe mata bakin ta da nashi bai direta ko ina ba sai cikin ďakin shi...
📚📚📚
[30/08, 18:09] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*Page*
*29*
Dedicated to my
*AISHA GENTLE LADY*💃 _Daga ni sai ke tawan_
My Sister *HAUWA SMASHER* ina nan tafe gareki 😁
Dan Allah ayi min afuwa wlh tun jiya nakeso nayi posting Amman bansamu time nayi editing ba wannan fitinannun yan gidan namu suka hanani sakat ina zaman yin editing sai naji anqirani wlh haka har saida dare ya tsula suka barni ni kaďai saikace idan bani ba bazasu iyaba rayuwa ba🙄🙄
_TUNATAR WACE_👌🏿
_Ingantacciyar hadisi daga bakin fiyayyan halitta Manzon Allah (SAW)_
*Ankarbò daga sahlin ďan sa'adis sa'idiyu Allah yaqara masa yarda yace: yazo wajan manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agare shi sai yace: ya manzon Allah kanuna min wani aiki wanda idan nayi shi Allah zai soni kuma mutane ma su soni, sai Annabi yace: kaguji abun duniya sai Allah ya soka, kuma kaguji abun hannun mutane sai mutane su soka".*
*Ibnu maajah ne ya rawaito. Allah yasa mudace Amen*🙏🏿🙏🏿
Tura ķofar ďakin yayi da ķafar sa ya rufe har lokacin bakinsa yans cikin nata saida ya tabbatar ya tsotsi bakinta sosai iya son ranshi kafin ya saki bakin tare da qara rungume ta tsam ajikin sa yana sinsinar wiyar ta yarafa zuge mata zif ďin riganta har zuwa lokacin bata iya cewa komai ba illah bugun da zuciyar ta keyi sosai yana harbawa",,
Jin abunda yake shirin aikatawa yasa jikinta ďaukan rawa tafara yunkurin kwace kanta daga gareshi ita kam harga Allah bata shirya karban sa yau a wannan lokakin ba,,"
Baikai ga qarasa zuge zif ďin ba yadakata ganin da gasken ta take raba jikinta da nashi,,ďago da kanta yayi yana kallon cikin kwayar idanunta tare da shafa gefen fuskanta da hannayen sa cikin iriyar muryar sa wacce ta soma dashewa dan shi tuni hankalinsa a tashe yake ya soma barin jikinsa babu abunda yake bukata a wannan lokakin kamar ya rakubì matarsa lumshe idon sa yayi ya buďe su yana ciki gaba da kallon ta a hankali yace,,"
Matar meyene kuma yafaru kike neman hanani hakkina karfa ki mance tunda akayi bikin mu bamu tabà samun lokaci mun farantawa junanmu rai ba wanda a duk sanda nasamu nafara jin daďin ďumin jikin ki hankali na yasoma barin jikina a lokacin ne wata matsala zata kunno kai hakan yasa nayi haquri na danne zuciya ta dakyar na iya kawowa har zuwa yanzu,dan haka karkiyi yunkurin hanani kibar mu raya sunnar Manzon Allah a wannan daran ranar mu farantawa zuciyoyin mu da ruhinmu rai mubawa gangan jikin mu hakkinsu kar mutoye musu abunda suka ďau tsawon lokaci suna muradin sa,,"
Shiru yayi yana ci gaba da kallon ta har zuwa lokacin idonta yana qasa bata iya ďagowa ta kalle shi ba zuciyar ta sosai yake bugawa ita kanta a zuwa yanzu tasan ba qaramin haquri yayi ba duk da itama a duk lokacin da gangan jikin sa yarabè da nata jikin takan shiga wani irin yanayi mai wiyan misaltuwa wanda bata tabà tsintan kanta aciki ba tana bukatar sa sosai Amatsayin sa na mijinta Amman tsoro da fargaba ya hanata sukuni batasan tayaya zata fara karban wannan baqon lamarin ba,,"
Jin tayi masa shiru batayi magana ba yasashi qarasa zuge mata zif ďin rigan yana faďin dan Allah karki min gardama matata kibani haďin kai a wannan daran haka yaraba ta da rigan nan take kirjinta ya bayyana waje,, lumshe idanun sa yayi ya buďe tare da zubawa suran jikinta kallo yana murmushi,, baiyi wata wata ba yaci gaba da shafan ta yana bin ko ina na jikinta duk yabi ya gigice mata gabaki ďaya cikin qanqanin lokaci ya fice a hayyacin sa yana fitar da numfashi sama sama jikinsa har rawa yake yaci gaba da bin ta yaraba da skirt ďin jikinta,,"
Tsayuwar ce ta gagareshi yasa hannayen sa duk biyu ya ďauke ta kamar yar baby dakyar yake takawa ya dire ta kan gado kafin ya cire kayan jikinsa shima ya haura ya mata ruba da faffaďar ķirjin sa kafin yaci gaba da aika mata da wasu irin rikitattun saqonni masu wiyan misaltuwa,,"
Jikinta rawa sosai yake duk yanda taso tayi yunkurin hanasa abun ya faskar saima gara cigaba da yake ganin yanda gabaki ďaya ya fice a hayyacin sa baisan ma tanayi ba yasa jikinta yayi sanyi sosai tasakar masa da duk wani karfi nata tana sauķar da nauyayan numfashi,,"
Salon ne taji ya canza mata ba shiri ta buďe baki ta kwala wani irin gigitaccan ihu sosai tana rumtse idanun ta tare da yunkurin tashi zaune sakamakon wani azababban zafin da taji a qasanta ya shige ta wanda tunda take a rayuwar ta bata tabà jin azaba kamacinsa ba sosai ta galabaita duk wani sauran karfi na jikinta da yarage mata ta nemeshi ta rasa tun tana iya jurewa abunda yake aika mata har yakai ga inbanda zubar da hawaye ba abunda ke fita cikin idanunta tana sauķar da wahalallan numfashi duk ta haďa zufa dan wahala,,"
Hannu Maraqishiya ta aza akai tare da zabga salati ta durkushe a wajan warwas tayi zaman dirsham wanda fitan ta kenan daga ďakin ta zata shige kitchen dan neman abinci ganin duk an kashe wutan parloun yayi duhu yasata kunnawa tana kunkuni har zata shige kitchen ďin sai kuma tafasa tamkar ance mata taje ta duba ko mai sukeyi a wannan daran dan ji take bazata iya jure ganin mijin da wata mace ba,,"
kai tsaye tayi hanyar ďakin sa zuciyar ta sosai ya soma ingiza jin motsin su ba qaramin tashin hankali ya shigar da ita ba hakan yasa takasa barin bakin ķofar ďakin ta rakubè sosai takasa kunnuwan ta tana jiyo duk wani motsin da sukeyi,,"
Tamkar tayi hauka takeji a hankali tafara magana cikin ranta tace shikenan ni Maraqishiya na shiga uku na lalace tawa ta qare a cikin gidan nam kamar ta tashi ta tura ķofar ďakin ta shiga takeji gani take baza iya cigaba da bin wannan mummunar shawaran da shiwari taba ta ba ta gwammace ta nuna musu haukan ta su san cewa basu ba zaman lfy akan tacigaba da aiwatar da shirin ta batare da sun sane ba a hakikanin gaskiya bazata iya cigaba da juriyar ganin mijinta yana tarayyan aure da wata yar iska daban ba ya zame mata dole ta nemi wata hanyar daban Amman ba wannan ba idan taci gaba da zama ahaka akoda yaushe tana kallon mijinta yana haďa shimfiďar sa da wata matar daban tsabanin ita to ba shakka wani lokacin za'a iya kwasan gawanta matacciya,,"
Dafe kanta tayi da duk hannayen ta biyu zuciyar ta sosai yake mata kuna tashin hankali qarara tattare da ita, batasan lokacin da hawaye ya soma kwaranya daga idanunta ba jazir ya koma tamkar garwashi, ganin zaman a bakin ķofar ďakin ba komai yake qara mata illah ma jininta da takeji yana shirin hawa idan ba wajan tabari ba to lallai ba makawa ciwon zuciya zai iya kamata bataci bata shaba,,"
Haka ta rarrafa tana jan ķafa tamkar gurguwa har ta isa cikin ďakinta ta tura ķofar da karfin gaske ta rufe tare da zubewa a kan gado Abincin da tafasa ci kenan ji tayi duk yafita a ranta ta daina jin yunwar sai fitar da numfashi sama sama da takeyi ita kaďai tasan irin zugin da zuciyar ta keyi a wannan lokakin daran da yake naman hanyar hallakata lokacin ta baiyi ba,,"
Bashi ya sarara mata ba saida yajisa ya gamsu sosai hankalin sa yafara dawowa jikinsa kafin yaja gefenta ya kwanta rigingine tare da lumshe idanun sa yana fitar da numfashi, saida ya ďauki tsawon mintuna yana kwance wani irin farin ciki yakeji yana ziyartar zuciyar sa mace macece ko wacce da irin ni'imar da Allah yayi mata, fuskar sa ďauke da murmushi cikin ransa yana qara godewa Allah Da yahaďa shi da humaira amatsayin matar auran sa,,"
Buďe idanunsa yayi ya jiyo da kansa zuwa gareta yana qarewa kirjinta kallo wanda yake a cike tam tamkar mai shayarwa,, hannun sa yakai kan fuskan ta yashafa tare da gangarowa kan ķirjin ta yanajin yanda zuciyar ta ke bugawa a hankali ya ďago daga kwancan da yake yaqara duban fuskan ta akaro na biyu ayayin da idanuwanta suke a rufe tamkar wacce take bacci mai nauyi,,"
Ďago da kanta yayi ya rungume ta cikin faffaďar ķirjin sa yana shafan bayan ta ganin yanda duk tabi ta galabaita shi kansa yasan baiyi mata da sauki ba kafin ya buďi bakin sa tamkar mai raďa yafara cewa,,"
Pls am sorry matata nasan banyi miki da sauki ba Amman kiyi haquri pls my angel ke ďin daban kike cikin mata Allah yayi miki albarka cikin rayuwar ki yatabbatar mana da soyayyar mu da kaunar juna a tsakanin mu nagode sosai matata da kikawo min budurcinki gareni, sosai yakejin sonta yana qara dasuwa masa cikin qasan ķoķon zuciyar sa ba babu abunda yake qara nanatawa cikin ransa inbanda godiya ga Allah ma mallakin sarki,,"
Yafi kusan mintina biyar yana rungume da ita a ķirjin sa kafin daga bisani ya ďago ta jin shirun yayi yawa batayi magana ba illah zufan dake keto mata cikin jikinta hakan yasashi yafara tashinta a zatonsa wahala ne yasata bacci haka , ba qaramin tashi hankalin sa yayi ba ganin ko numfashi bata fitarwa bare tayi motsi, cikin ruďewa yake qiran sunanta tare da ďaukan rubber ruwan da ke kusa dashi yafara yayyafa mata kafin ya tallafota yana cigaba da qiran sunanta duk yabi ya rikice ya rasa wanne taimako zaiyi mata ta tashi duk wata basira ta kwakwalwar sa dashewa yakeyi tsam ya kuma manne ta ajikinsa yana girgiza ta cikin tashin hankali,,"
Ya ďau tsawon lokaci yana manne da ita cikin ķirjin sa har zuwa lokacin bai daina girgiza yana qiran sunan ta ba,, wani iri wahalallan ajiyar zuciya ta sauķe tana fitar da numfashi sama sama tare da buďe idanunta a hankali wanda suka rine suka qanqance suka sauķa cikin nashi wanda shima har zuwa lokacin idanunsa na kanta duk yabi ya rikice ganin ta buďe idanunta yasa yashiga murna ba kaďan ba yaqara janta jikin shi ya rungume ta tsam yana qara sa mata albarka,,"
ita kuwa inbanda wahalallan numfashi babu abunda take saukewa fuskan ta shabè shabè da hawaye ga wani irin fitinan nan yunwa da cikinta keji sai kurwa yake mata idan bata mance ba rabon da taci abinci tun jiya ko yau data tashi da safe blacktea cop ďaya kawai tasha hakan ya sanya ta a hankali ta soma raba jikinta da nashi tanajin azababban zafi sosai wanda ya ďaure mata duk ķafafun ta shirin miqewa tsaye take Amman hakan ya faskara saima qara zubewa a jikin sa da tayi tana sauķar da nauyayan ajiyan zuciya wannan wani irin azaba ne haka gaskiya idan haka raya aure yake akwai matsala,,"
Ganin tashi takeso tayi ta kasa yasa shi a hankali ya ďago da kanta yana duban fuskan ta tare da tallafota cikin qasa da murya tamkar mai raďa yafara cewa,,"
Sorry my angel naji miki jiyo sosai ko? am sorry kinji my dear nest time I promised zanyi miki a hankali bazanji miki ciwo ba, duban ta ya kuma yi akaro na biyu ya furta tashi kikeso kiyi?,,kai kawai ta samu daman girgiza masa alaman Eh tanaci gaba da sauķar da ajiyan zuciya,,"
Mai zakiyi idan kin tashi? ya tambaye ta yana riqe da fuskan ta a iyayin da idanuwanta ke kallon qasa batare da tabari sun haďa ido ba ta buďi bakin ta Cikin da shashshiyar muryan ta tabashi amsa a takaice tace,,"
Abinci nakeso naci yunwa nakeji sosai ko karin safe banyi ba,, cike da mamaki yake kallonta kafin yace, haba babynah me yasa kikeson barin kanki da yunwa ne? akwai abinci bawai babu ba Amma sai ki kasa ci, meyasa?, shiru tayi batace masa komai ba illah qara yunkurin tashin da takeyi,,"
Sakinta yayi a hankali ya miqe ya sauķa daga kan gadon tare da ďaukan kayansa ya mayar jikinsa kafin ya dubeta yace zauna ina zuwa bazaki iya tashi ba kar ki motsa kinji?, toilet ya shige ya haďa mata ruwan wanka mai zafi ya fito tana nan zaune inda ya barta hannun sa yasa ya ďaga ta ta tsaya da ķafafun ta dakyar ya shige da ita toilet ďin kafin ya shigar da ita cikin bawon wanka wani irin azababban zafi taji ya shige ta wanda yasata sakin yar qara tana yarfe hannu tare da kankame shi dan azaba,,"
Da kansa ya gasata da ruwan zafin tare da yi mata wanka tas kafin ya qyaleta tayi wankan sallah shi ďin ma dakyar tanayi yana taimaka mata har ta kammala,,"
Babban towel ya ďauka ya nannaďe ta dashi tare da taimaka mata suka fito daga toilet ďin idanunta a rumtse tamkar mai bacci takasa buďewa su haďa koda ido wani irin kunyan shine taji yana shige mata jiki idan ba yazame mata dole ba da bazata iya barin shi yayi mata wanka ba,,"
Zaunar da ita yayi bisa gado kafin ya fice a ďakin ya shige ďakin ta ya nufi inda kayan sawanta suke ya duba ya ďauko mata wata yar qaramar kayan bacci mai tsantsi wanda tsayin sa bazai wuce iya gwaiwa ba hannun sa na shimi,,"
Dawo wa yayi ďakin ya tarar da ita inda yabar ta har lokacin kanta yana qasa a hankali ya qaraso gareta ya saka mata kayan sosai ya karbì jikinta man shafawan sa da turarukan sa ya ďauko ya shafa mata tare da fesheta da turarukan masu ķàmshi yana qara duban ta yace,,"
My dear pls bari nima nayi wanka zanfi jin daďin zama nabaki abincin da sauri zanyi bazan bàta lokaci ba kinji my dear,, yana maganar ne tare da tallafo fuskan ta, bata iya ta buďi baki tayi masa magana ba illah kanta kawai data gyada masa alaman to duk da yanda takeji yunwan yana qara kwakule mata ciki bazata iya tashi taje koda nan da canba dan yanda jikinta yayi tsami sosai,,"
Bai tsaya bata lokaci ba ya shige toilet ďin yayi wanka cikin qanqanin lokaci yafito ya sameta har yanzun tana zaune bata motsa ba, goge jikinsa yaye ya shafa mai kafin ya nufi inda kayansa yake ya ďauka farar doguwar jallabiya yasaka tare da feshe jikin sa da turare, saida yaqara kallon ta ya furta am sorry fa my angel kafin yafice a ďakin cikin sauri yafita inda kitchen ďin ta yake da kanshi ganin ba ko wanne abincin da faffe yasa shi ďaukan indomie ya ďaura mata dakyar ya iya kunna wutan baici wani lokaci dayawa ba ya kammala girka mata ya kashe komai kafin yabaro kitchen ďin yadawo ďaki,,"
A gaban ta ya ajiye yana duban ta yafara ďiban indomie yakai bakin tare dayin bisimillah yafara bata a hankali take buďe bakinta yake sa mata har ya kammala bata ya ďauki plate ďin ya mayar kitchen yadawo,,"
Sauķe ta yayi qasa ya cire zanin gadon ya wuce yakai toilet yazo ya canza wani kafin yaqara ďaukan ta ya mayar da ita tare da kwantar da ita, ya wuce ya kashe wutan ďakin ya dawo ya haura gadon ya kwanta daf da ita tare da janta zuwa jikinsa ya rungume ta idanun sa a lumshe yana shafan bayanta duk tanajin sa Amman bata iya ta tanka masa ita kaďai tasan irin wahalan da tasha duk da gasata da yayi cikin ruwan zafin ta ďanji zafin ya ragu Amman har zuwa yanzu tanajin wajan yana mata raďaďi sosai, yana ci gaba da shafan bayan ta har bacci ya kwashe su,,"
_Ranar kice yau Humaira Amman shawara ta gareki karfa kice zaki sake masa jikin ki dayawa gwara kiyi takatsantsan kar watarana ta bàci miki_ 😜
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:09] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*Page*
*30*
Dedicated to my *AISHA GENTLE LADY💃*_Daga ni sai ke tawan_
😥My dear *Feedohm*sannu da haquri da juriyar rashin da akayi miki saifa kin daure banda kuka addu'ar mu shi take bukata a wannan lokakin kiyi haquri ki danne zuciyarki fatan mu gareta Allah ya gafarta mata yayi mata rahama yasa wannan mutuwar hutune agareta muma idan namu yazo Allah yasa mucika da imani Amen summa Amin🙏🏿🙏🏿
*Jinjinar ban girma gareki sister Hauwa Smasher ina daďa godiya kan mallaka min littafin KADDARA KO SAKACI da kikayi hakika kin cancanti komai fatan alkhairi agareki yar uwa Allah yabar zuminci ana mugun tare
Misalin karfe biyar saura na asuba wanda lokacin ko wanne gefe na masallacan dake cikin unguwar qaran qiran sallah kakeji ke tashi wanda shine yayi sadiyar farkar dashi daga baccin da yake yana rungume da ita a ķirjin sa,,"
Buďe idanunsa yayi a hankali yafara zareta daga jikin sa dan gudun karta farka, yana gama zareta daga jikin nashi ya tashi ya shige toilet ya ďauro alwala kafin ya fito, ganin bacci mai nauyi takeyi har zuwa yanzu hakan yasa shi qyale ta ya wuce masallaci batare da ya tashe ba idan,,"
Sanin yabarta bata da karfin da zata iya tashi har ta iya yin sallah hakan yasa shi bayan sun idar da sallah tare dayin azkar bai tsaya jiran fitowar ranaba yabaro masallacin yadawo gida,,"
Wannan karon kam idanuwan ta a buďe suke ya tarar da ita tana shirin tashi dakyar da sauri ya qarasa gareta yana mata sannu tare da taimaka mata ta miqe tsaye tana harharďe ķafafun ta dan har yanzu tanajin zafin wajan tamkar tsagata da wuqa ake,,"
Yana riqe da ita ya shigar da ita toilet ďin tare da taimaka mata tayi sarki dakyar sam tace sai yafita kafin zatayi Amman fur ya mata qememe atafur babu inda zaije saidai kar tayi, ganin irin gardamar da yakeyi mata yaqi koda juya bayansa yayi sai ma cewa da yake shine zaiyi mata tsarkin idan tayi masa wasa gashi lokaci dake qara tafiya garin yana shirin yafara haske ko sallah batayi ba hakan yasa ta daurewa takawar da kanta gefe guda dakyar ta iyayin tsarkin ya taimaka mata ta miqe tare dayin alwala kafin ya fito da ita, mamaki abun nashi yake bata jifa jifa take satan kallon sa yanda taga duk yabi yazage sai narnar yake da ita tamkar wata yar qaramar yarinya,,"
Zaunar ta bakin gadon yayi yazo ya shimfiďa mata abar sallah, yana kallon ta yanda ta sauķar da kai qasa ya sakar mata da kayataccan murmushi kafin yace,,"
Matar jirani bari naje ďakin ki nakawo miki hijabin sallah, bai jira amsar taba yafice a ďakin kai tsaye nata ďakin ya nufa baisha wahalan neman hijabin ba da yake ta ninke shi kan sallaya a gefe guda,,"
ďauka yayi ya dawo ďakin ya sameta da kansa yasa mata hijabin yatashar da ita kafin ya koma gefe ya ďauki al ķur'anin sa mai girma ya soma karatu yana jiran idarwan ta, jifa jifa yake kai idanun sa kanta dakyar ta iya idar da sallahn taja gefe ta zauna tana tasbihi tare da jinginar da kanta jikin gado tana rufe ido,,"
Ta ďan ďauki lokaci kaďan tana tasbihin kafin taji bacci sosai ya taro mata cikin kwayar idanunta sai hamma take hakan yasata cire hijabin dake jikin ta tare dakai dubanta gareshi har zuwa lokacin ķur'anin ne a hannun sa yana karantawa cikin muryan sa wanda yake mata daďin sauraro,,"
Kanta a qasa cikin sanyin murya ta furta ina kwana tana ďan wasa da yatsan hannun ta bare da ta ďago da kanta ta kalle shi ba dakatawa yayi da karatun da yake yakai dubansa gareta yana murmushi ya amsa mata da lfy bata kuma cewa komai ba ta lallaba ta haura kan gado dan yanda taji baccin na rufe mata idanu idan ba yin shi tayi ba koda na lokaci kaďan ba zai iya damunta,,
Cikin qanqanin lokaci ba wiya baccin yayi awun gaba da ita a hankali take sauķar da numfashi, a iyayin da shi kuma ganin wani baccin ta koma yi hakan ya sanya shi ci gaba da karatun sa har kusan misalin karfe bakwai kafin daga bisani ya rufe ķur'anin tare da miqewa ya shige toilet dan yin wanka, bai ďauki lokaci ba yafito cikin sauri ya goge jikinsa tare da shafa mai ya feshe jikin sa da turane kafin ya nufi inda kayansa suke ya zaro shadda kaftan ruwan green ya saka kafin yashiga gyara sumar kansa yana gamawa ya juyar da kansa zuwa inda take kwance har zuwa lokacin Bacci take sosai duk mutsuniyar da yaketa yi bataji saba, makullin motar sa ya ďauka daga gefen gado ta inda ya kwanta kafin yadawo ta gefenta yakai kansa bisa goshin ta ya sumbaceta tare da shafan gefen kumatun ta fuskar sa ďauke da murmushi a hankali ya furta sai nadawo ya fice a ďakin,,"
Saida yabi ta ďakin Maraqishiya ganin itama baccin take yasashi yaja mata ķofar ďakin kai tsaye ya fice a gidan yana sauri tamkar zai tashi sama da yake yanada muhimmin takardun da yakeso yagama cikasu kafin azo a karbà,,"
🌾🍃🌾🍃🌾🍃🌾
A hankali ta buďe ķofar dakin ta ta fito cikin sanďa take takawa ta ďibi takalman ta a hannu dan bata bukatar kowa yaga fitan ta bare Abba da yayi mata gargaďin kada ta yadda yaga ta fice daga gidan a sunan zuwa gidan Abdulmalik koda bai saniba za'a sanar dashi ita kuwa ta ďauki alwashin sai fa dole taje dan bazata iya juriyar zuba idananu kan wata shegiyar daban tazo ta kashe su da ran su basuci ba basu shaba, hakan ya sanya ta tunda ta idar da sallah bata taqi komawa bacci tana zaman jiran garin ya ďanyi haske dan taji daďin samun Adaidaita sahun dazai kaita har zuwa ķofar gidan batare da tasha wahala ba,,"
Fitowar Batula daga ďakin su kenan taza shiga kitchen tana hamma dan ji take bacci bai isheta ba Amman ya zame mata dole tafito ďaura karin safe tunda tana gida, idanunta ne ya hango mata Umma tamkar wacce ta saci wani abu daga ganin yanayin ta koda ba'afaďa mata ba babu shakka tasan daga nan wannan fitan nata da zatayi bazai wuce gidan zataje ba cikin mamaki take binta da ido har tafice daga parlon,, girgiza kai tayi ta wuce inda zata tana mamakin mahaifiyar tasu yanda tafi ta canza sosai ta dalilin waannan auran da Abdulmalik yayi koda lokacin da ya auri Maraqishiya baita taso ya aura ba Amman batayi masifa makamincin irin haka ba ta rasa meye dalilin ta na tsanar yar mutane tukda dai tasan taso ya auri suwaiba matsayin mace ta biyu Amman ya jajirce mata hakan bazai sa tayiwa yar mutane tsana irin hakaba batare da wani kwakkwarar shaida ba, itadai harga Allah tun ranar farkon sata a idanu da tayi taji ta shige mata rai daga ganin yanayin ta dan bataga aibunta ba,,"
Koda ta fito haraban gidan tana waige waige ta iso bakin gate ďin tasa mai gadi ya buďe mata ķofa bayan tayi masa gargaďi sosai kada yasanar da Abba ko wani daga gidan ta fita kafin ta fice ta kama hanyar tafiya da kafa ta isa bakin titi,, batasha wahala sosai ba tasamu Adaidaita sahu ta masa kwatancan inda zai kaita, da yake garin safe ne babu motoci dayawa masu kaikawo dan yanzu nema rana ta soma fitowa hakan ya sanya babu bata lokaci ya isa da ita har ķofar gidan kafin ya sauķe ta,,
Tana hanzarin taga taje ta aiwatar da abunda yakawo ta kafin rana tayi yasa bata tsaya biyan sa kuďin sa ba ta isa bakin gate ďin tafara bugawa da karfi yanda taji shi a kulle, ganin an buďe mata ķofar zata shiga bata biyasa kuďin sa ba yasa shi sauka da sauri yana faďin hajiya baki bani kuďina ba zaki tafi ko kin manta ne? jiyo da kai tayi ta dube shi tare da dafe kanta tafara laluman jikinta dan tabiya sa kuďin tare da faďin kayi haquri mancewa nayi,,dogo tsaki taja sosai ganin Ashe ta mance garin sauri bata ďauki ko sisi ba bare kabon da zata iya biyansa kuďin sa hakan yasa tace dashi yayi haquri idan ta shiga zata miqo masa kuďin,, tsayawa yayi yana jiran fitowar ta a iyayin da ita kuma ta qarasa shigewa cikin gidan bate da ta tsaya sauraran gaisuwar da baba mai gadi yake mata ba,,"
Tura ķofar parloun tayi ta shiga a zaton ta zataji ķofar a kulle sai taga tsabanin haka, cike da ďagun murya tamkar za'ayi tashin duniya ta shiga kwalawa ko waccen su qira babu kakkautawa tana bin ko ina na parlon da kallo taga inda zata fito ranta sosai in yayi dubu ya bàci ganin babu wanda ya yafito duk irin ďaga muryan da tayi tasan dole ne sujita koda kuwa duk irin nisan baccin da suke, a fusace tayi hanyar ďakin da tasan na Humaira ne wanda a lokacin ne ita kuma take fitowa gada ďakin cikin sauri tana kiciniyar saka hijabi da yake tun tana toilet tana wanka take jiyo muryan ta wanda hakan yasata saurin ďaureye jikinta ta fito batare da ta ankara ba taji ta gware sosai da mutum agaban ta hakan yasata riqe kanta da duk hannayen ta biyu tana faďin Washhh ta ďago da kanta sukayi ido huďu da Umma wacce ke tsaye tayi kame kame ta harďe hannu a kirji tana kaďa kai inbanda harara ba abunda take aika mata a lokacin,,"
har qasa takai cikin girmamawa ta gaisheta tare da bata haqurin bigeta da tayi,,"
Qara tunzura ta gaisuwar yayi cike da masifa tace tashi a gabana munafukar yarinya dangin matsafa ba gaisuwar ki bace ta kawo ni ba nazo ne nayi miki gargaďin koda wasa kaga ki kuskura ki qara aiko mana da shegen guban abinkin gida bama bukatar sa kinji dai naga miki idan kuma kika kumayi wani daga cikin yarana yaci yamutu to wlh ki tabbatar saidai kema iyayenki suzo su ďauki gawarki tunda sune munafukan idan kunne yaji gangan jiki ya tsira.....
_Dan Allah kuyi min haquri da wannan nidai nasan narubuta _ _Amman bahaka naso ba aikine yamin yawa Amman nest week insha Allah zakuna jina akai akai_
📚📚
[30/08, 18:10] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*Page*
*31*
Dedicated to my
*AISHA GENTLE LADY*💃
*Gareki Shatuwa na wannan shafin bata kowa bace illah taki ke ďaya AISHA ĎAN SABO LEMO ahaqiqanin gaskiya bazan boye miki ba wlh naji daďin littafin HAMAL sosai wlh yani shaďantar dani ba iyaka duk da nice HAFSAT muguwar cikin sa bazanyi fishi ba😉 domin ya ilimantar yafaďakar wlh Shatuwa kinyi namijin kokori posting akai akai kullum 2 page gaskiya ba kamar ki Aishu fatan Allah yaqara miki baseera da kaifin idanu da hazaka keďin daban kike kina haskawa akoda yaushe muna nan muna jiranki har zuwa nan da sabuwar shekara fatan Alkhairi agareki Shatutu mugun tare muke wlh*😚
_Maryam Abdool Mai jambaki na ina miki fatan alkhairi ya Allah yabaki lfy da karfin jiki yasa kaffarace Amen ya Allah sorry_😥
*HANEEFA USMAN*
*AMEENA BATURE* wlh harga Allah banida kamarku😍
_TUNATAR WACE_👌🏿
_Ingantacciyar hadisi daga bakin fiyayyan halitta Manzon Allah (SAW)_
*Ankarbò Suhaiben ďan sinanirrumiyya_ Allah yaqara masa yarda- yace: Manzon Allah tsira da amincin Allah sutabba tagare shi yace-: Abun mamaki ga Al amarin mumini, Lallai dukkan al amuran sa Alkhairi ne, Kuma babu wanda yakeda wannan sai mumuni Idan abun fariciki yasame shi sai yayi godiya hakan zai zama alkhairi agare shi idan abun bakin ciki yasameshi sai yayi haquri da juriya hakan zai zama alkhairi agare shi".*
*Akhrajahu Musulimu* Allah yasa mudace 🙏🏿
Tashi tsaye tayi cikin sanyi jikin ta yana ďar ďar kanta a qasa ta kasa koda ďago da kai ne suyi ido huďu zuciyar ta sosai yake dukan uku uku jin irin furucin dake fita daga bakinta gashi ba daman tayi magana taqara haurawa kanta hakan yasata jan bakinta tayi shiru tamkar kurma taja gefe guda batace qala ba illah sauraron abunda zata kuma cewa,,"
Cikin magagin bacci tareda yin miqa ta fito daga ďakin ta tana murzan idanunta tare dayin dogon hamma fuskan ta a ďan kumbure irin na masu baccin da bai gama isar suba dan cikin bakin ciki ta kwana jiya, cike da takaici tana taho ta soma faďin wanne tsinannen mahaukacin ne zai shigowa mutane cikin gida da safiyar Allah saikace gidan uban shi yazo yana mana ihu dan iskan.....cak maganar ta makale mata can qasan maķoshin ta ba shiri ta cafke bakinta da hannayen ta biyu tana zare ido da kyau taga dai Umman ce tsaye a gaban ta ba wani mutumin na daban ba hakan yasa cikin tsarkewar murya a hankali tana muzurai da kai tamkar wacce akebi bashin Kuďi bata biya ba tace, au Umma Ashe kece ke tafe war haka ai bansani ba wlh da yake yanzu farkawa ta daga bacci banyin zaton ke bace,,"
dakata tayi mata nuni da hannu cikin haďe fuska tace qanwar jatimar kice bani ba marasa kunyar banza nufinki nice mahaukaciya tsinanniyar ko? to ki tabbatar yana kan jatimar ki,,"
Aiyya mana Umma Sam fa ba haka nake nufi ba kiyi haquri dan Allah tana ďan rusunar da kanta take maganar iyakar bakinta ya tsaya can qasan zuciyar ta ita kaďai tasan mai take aiyyanawa, baki ta buďe da niyar qara wata maganar sallamar baba mai gadi yakatse ta hakan yasata dakatawa jin da ita yake maganar cikin bada girma kansa aqasa yace Hajiya kinbar mai Adaidaita sahu fa a waje yana jiran kuďin sa, qara haďe fuska tayi tamkar bakin hadari tare da dubansa tace to gulma ce takawo yanzu kasanar da duniya ban biya kuďin mai Adaidaita sahu ba ko kuwa shi ďan marasa haqurin ne ya aiko ka? Allah ya huci zuciyar ki hajiya aiko ni yayi ya bata amsa jikinsa yana rawa bata kuma qara ce masa qala ba ta juyo da kanta tabisu da kallo ďaya bayan ďaya gameda cewa cikin ku wani yabiya sa kuďin sa a takaice tayi maganar cikin bada umarni dan aganin ta kuďin ďanta ne a gidan sa suke zaune idan wanin su yayi gangancin ce mata bashida kuďi ma to yayi karya aqalla tasan babu makawa dolene duk sanda zai fita yabarwa ko waccen su kuďi a hannun ta dan haka basu da hujjar da zasuce mata basu dashi,,"
Ayayin da jin abunda Ummar tafaďa yasa Maraqishiya sake gyara tsayuwa tana neman qarin bayani a ranta take faďin meye ma'anar matar nan kenan nufin ta ko biyan mai Adaidaita sahun da yakawo ta batayi ba kenan mune masu kuďin da zamu biya? dantse harcanta tayi kaďan tace ai kuwa ķur'anin Allah saidai tasan yanda zatayi dan ko sisi na bare kwandala ta bazan bayarba inama dalilin zuwanta da sassafen nan yashafi qaruwata da sai nabiya Amman haka kawai bazanyi asaran kuďi naba saidai ko ita wacce ďin zata iya biya mata ,,"
Ba qaramin haushi shirun nasu yaqa sata ba ganin babu wanda ya motsa daga inda yake tsaye illah ma banza da ita da sukayi tamkar basuji mai tace dasu ba akaro na biyu ta kuma duban su cikin ďaga sauti wanda yayi sanadiyar dawo da Humaira nisan tunanin da tafaďa, tace ba daku nake magana ba kun mayar dani shashasha, salon sabon wata rashin kunyar kenan zaku nuna min? Umma ai maganar taki ce bamu ganeba kuďin mai kikeso mu biya? Maraqishiya tafaďa tana kawar dakai gefe guda ayayin da Humaira jiki babu kwari ta juya da niyar shigewa ďakinta dan ji tayi bazata iya juriyar cikaba da sauraron bala'in taba a yanda takejin yanayin ta a yanzu bata bukatan tashin hankali,,"
Kee dakata ina zaki taji Ummar tafaďa cikin ďaga murya gameda binta da mugun kallo hakan ya sanya ta fasa shiga ďakin tadawo da baya badan ranta yaso ba dan jin mai kuma takeso taqara cewa tayi tsaye batare da ta kalle taba wanda a wannan lokakin Abdulmalik ya sako da kansa cikin parloun tare da bin Umma da kallo yana mamakin ganin ta kenan itace tabar mai Adaidaita sahu yana jiran takawo masa kuďin Abunda ya ďaure masa kai yake tambayar zuciyar sa toma wanne dalilin ne yakawo ta da safen nan?maganar tane ya katse masa zancen zucin da yake tana duban sa tace yauwa dama kai nake nema, To ai gani nan Umm mai yafaru yau kuma kikayi mana sammako war haka wanda wasu ma bacci suke a wannan lokakin basu farka ba Allah dai yasa lfy ? yace da ita yana qarasowa inda take tsaye,"
Ina kuwa lfy ai ba qaramin kokari nayi ba daba kuganni tsakiyar dare ba shima albarkacin mahaifin kane da tun a lokacin zaku ganni komin dare dan.. bata qarasa maganar ba ya katse ta da cewa to meye akayi haka wanda yanaki haquri? kaga kalle ta nan ta nuna Humaira da yatsan hannun ta tare da jifanta da mugun kallo tace wannan la'ananniyar matar taka masu zubin yan wuta dagin baqaqen aljanu ita take neman hanyar kashe mu nida yara na ta zuba mana guba cikin abincin yanzu haka ga Inna can rai a hannun Allah idan munci sa'a tarayu idan kuwa mukayi rashin sa'a ta mutu shikenan an huta,,"
Innalillahi ya furta cikin nuna tashin hankali yace mai ya sami Inna kuma jikinta ne yatashi komai tun yaushe haka baku sanar dani ba? damuwa qarara a furkan sa ya jero mata tambayoyin a lokaci ďaya yana jiran yaji amsar ta dan gabaki ďaya maganganun ta ďaure masa kai sukayi bai gane abunda take nufi na guba ba, Umma kiyi magana mana meye ya sami Inna wanne irin guba taci yaqara tambayar ta cikin damuwa sosai yanda yakejin son yar tsohuwar kakar sa a ransa ,,"
Kasan meye nakeso kayi min a yanzu? a a yafaďa yana girgiza kansa, rubuta mata takardar saki uku tace dashi a takaice tare da tsare shi da ido ayayin da damuwar sa sosai ta kuma qaruwa jin irin mummunar furucin dake fita daga bakinta, cikin qasa da murya yace Umma waye kike nufi zan saka kinsan mai kike faďa kuwa umma kodai? kodai meye kaga banison sakarcin tsiya karka sake ka kawo min zancen banza ai kafini sanin wacce nake nufi ba shaye nake ba cike da bacin rai take masa maganar, yace to meye tayi miki zakice in saketa Umma kwata kwata yaushe ma akayi auran ko cikekken wata ďaya fa ba'ayi ba idan kika umarce ni da aika wannan mummunar aikin ai sai naza abun nunawa da zagi cikin faďin garin nan bayan bansan meye dalilin hakan ba gaskiya nikam umma saidai kiyi haquri Amman wlh harga Allah bazan iya aikata wannan abunda kikeso in aiwatar ba,,"
To shikenan Abdulmalik ka kyautawa rayuwar ka kayi min gardama tunda kaine ubana kai ka haifeni har kake iya gaya min irin wannan maganar agaban wa ýannan shegun yan iskan masu lalataccan mahaifa, saidai inaso kasan wani abu hanzari ba gudu ba umarni nake baka ba neman shawaran ka nakeba a matsayina ta mahaifiyar ka wacce ta iya ďaukan cikin ka tayi ďawainiyar sa harna tsawon wata tara da rabi nashayar dakai nonon da ayau kake rayuwa cikinsa wanda ko kai waye baka isa ka iya biyana shiba dan haka kuma a yanzu agabana nakeso inga ka aiwatar kuma idan katashi ka haďa da waccan mannanniyar cingam ďin ka sakesu a lokaci ďaya itama haquri na yaqare akanta duk subar gidan idan wata mace kakeso kake bukata wannan ba matsala bace dama inada wacce zan baka mai kyawun mahaifa wacce zata kawo mana haske cikin zuri'yar mu..
tsagaitawa tayi da maganar tasamu kujera ta zauna tana kaďa ķafa ďaya ta qara da cewa dakai nake magana fa kayi min qememe saikace sandar itace kosai ka kuma bata min rai kafin? tsare shi da ido tayi sosai a yayin da ya saukar da ajiyan zuciya ganin yau ba zaman lfy take nema ba illah ma tashin hankalin da takeson sakashi ciki yaga gwara yayi gaggawan ficewa daga gidan tun kafin tasa shi aika abunda baiyi niya ba cikin safiyan Allah kallon ta ya kumayi akaro na biyu yace,,"
To shikenan Umma dan Allah ki kwantar da hankalin ki zanyi abunda kikeso bari inje mota in ďauko abun rubutu, bai jira jin mai zata ceba ya juya yafe a parloun cikin hanzari yana gudun karta tsayar dashi, kai tsaye yafice waje inda yayi parkin motar sa da yake sauri yake daman ďaukan wasu takardu ne yadawo dashi yatarar da wannan tashin hankalin, cikin sauri yafigi motar yabar unguwar zuciyar sa tunkushe da al ajabi kan mahaifiyar shi,,"
Ta ďauki tsawon mintuna kusan ishirin tana zaman jiran dawowar sa har tagaji da zaman ta miqe tsaye gameda cillawa Maraqishiya harara wacce ke tsaye takasa zaune ji take duk abun duniyar ma ya isheta wanda tuni Humaira ganin bala'in bana qarewa bane tayi dabaran shigewa ďakinta batare da tasani ba,,bayansa tabi ranta a bàce haka ta zagaye duk gidan bataga koda motar tasa ba bare shi da kanshi ranta ba qaramin mugun baci yaqara yi ba ta tambayi baba mai gadi ina mai Adaidaita sahun da tabari yace mata ai mai gidan yabiyashi tuni yatafi hakan yasata komowa cikin parloun tasamu Maraqishiya zaune ta zabga uban tagumi sosai tayi nisa cikin tunani tana neman hanyar zata mullowa wannan lamarin dan yazame mata dole tayi wani abu akan Umma idan ba hakaba saidai aganta akan layi da akwati a hannun,ke tunanin me kike inata magana kinyi min banza taji muryan umma tamkar saukan aradu tana tsaye akanta tace,,"
Kiyi haquri Umma wlh banji bane me kikeso kuďin mota zaki bani ta bata amsa a takaice gameda cewa shi ďan rainin hankalin tafiyar sa yayi yabarni ina zaman jiransa dan ya mayar dani abokiyar wasan shi Amman ba komi tunda shi bazaiyi abunda nasashi ba ni kuwa zanyi da kaina, ajiyan zuciya ta sauķe tareda cewa bari nakawo miki kuďin tana kaiwa nan ta kawar da kanta ta wuce ta gabanta,,"
Kuďin takawo mata batare da ta kalle taba tace Umma gashi sai anjima ki gaida yan gida tare da komawa ďakin ranta a bàce sosai bata bukatar jin wani abun dan gabaki ďaya ma haushin ta sosai taji yaqara dasuwa mata a rai ita kaďai tasan wanne shiri zatayi nan gaba.....
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:10] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*Page*
*32*
Dedicated to my
*AISHA GENTLE LADY*💃Ana mugun tare
*Gareki Babbar AUNTY NA SISI gaisuwar wannan shafin da ita shafin da kanta gabaki ďayan sa takice bata kowa ba AUNTY SISI ke ďin daban kike cikin duniyar whatsapp wannan maganar tawa haqqun take kowa da kowa ya sanda wannan zancan babu kamar ki wajan mutunci a yanar gizo AUNTY SISI fatan Alkhairi gareki iya wiya ana mugun tare ba makawa*😚
Fitan ta daga gidan cikin hanzari tana fatan Allah yasa babu wanda yafarka bare yaga shigowan ta, haka taka da kafarta har zuwa bakin titi anan tasamu mai Adaidaita sahu dakyar ya ďauketa ya mayar da ita gida, saukan ta keda wiya bayan ta biyasa kuďin sa ta juya da niyar shiga cikin gidan ta hango motar Abdulmalik an buďe masa get yana fita,binsa tayi da kallo yayi tamkar bai ganta ba yaqawa motar gudu har ya baçe mata da gani,kafin ta kaďa kai a zuciyar ta tace dani kake wasa yaron nan bakasanni ba Amman nasan mai zanyi,,shiga cikin gidan tayi tana bambami ita ďaya bata ankara ba tayi kicibus da Abba tsaye bakin shiga ķofar parlon bangaran ta, ya harďe hannayensa bisa ķirjin sa tare da jifanta da kallon tuhuma fuskan sa a haďe yace,,"
Daga ina kike da sasafen nan? bari jikinta ya soma bataso yagane fita tayi ba Amman tasan koda shi baiga ficewar ta daga gidan ba ta tabbata zuwan da Abdulmalik yayi bana banza bane dole yasanar dashi gidan sa taje, tambayar ki nake kinyi min shiru, taji muryan shi ya sinkayo ta ta ďago da kai tana kallon gefe guda ta soma kame kame tace babu inda naje kawai dai na ďan shiga gidan makociyar mun nan ne anyi mata haifuwa shine naje inyi mata barka, ni kike nema kiyiwa rainin hankali Bara'atu duk irin gargaďin da nayi miki na yanaki kar naga kin fita ashe nuna zakiyi ban isa dake ba, kin ďauka bazan san fitan ki bane ko kin ďauka bansan inda kikaje bane?ya tambaye ta yana qara duban ta yace yanzu bisabidillahi duba lokaci yayi mata nuni da a gogon hannun sa yaci gaba da cewa ko ke agareki ba babban abun kunya bane ki kwashi ķafa da safen Allah kije gidan surukar ki ko tashi a bacci ma basuyi ba kinje kina zubar da girman ki da qimarki kina mataayin uwa ahaka kuma kikeso su kalli girmanki,,"
To inaso kisan wani abu bara'atu hanzari ba gudu ba wlh kinji nayi miki rantsuwa duk lokacin da naji lbr ko nagani da idona wani abu yasaki ďiban ķafafun ki da niyar zuwa gidan surukanki to ki tabbatar da cewa zakiga bàcin raina wanda baki taba gani ba tunda ke kin nuna ba zaman lafiyan ne sam bakyason shi,,"
Tsagaitawa yayi da maganar ransa a bàce yana mata wani irin kallo yace bani waje in wuce in yaso gobe ma kije gidan tunda ke bakisan girman kanki ba, matsawa tayi tabashi hanya ya wuce tana jinsa ya shige bangaran sa, haka tana kunkuni ta qarasa shiga parloun ta samu kujera ta zauna tare da cire hijabin jikin ta tayi jifa dashi sosai takejin bakin ciki aranta babu shakka idan tayi wasa tabiye gargaďin da yakeyi mata nan gaba kaďan zata koma abun magana cikin mutane,,"
Tagumi tayi tana nazarin ta inda zatayi taga ta gyara gidan ďanta batare da wani yasa mata ido ba koshi yagane taba dan a iya zuwa yanzu bazata ce zata qara wani zaman haquri ba yazame mata tilas ta miqe tsaye tayi abunda batayi shi ba ada, tashi tayi daga parlon ta wuce ďakin cikkn zuciyar ta ta kulla wancan ta kulka wannan,,"
******* ********
Bayan wasu ďan kwanaki abubuwa da dama sun faru cikin zaman auran da takeyi, wanda a kullum ya kasance idan ranar kwanan ďakinta yazo takan zagewa taga tayi girke girke iri da kala masu rai da lfy ta gyare ko ina lungu da sako na cikin gidan yayi fesfes dashi ta saka turanen wuta ko ina yakama da kamsh saidai wani abunda dake ďaure mata kai akoda yashe idan yazamana tayi girki sai takan samun matsala cikin abincin da ta dafa kullum yana cikin mata korafi kenan,,"
Daga yau yace mata gishiri yayi yawa gobe yace mata yaji har baya iya cin abincin saidai ta girka masa ko indomie cikin qanqanin lokaci idan itama ta taba taji takan mamaki to tayaya hakan yake kasancewa da ita a halin ba'a gidan ta soma girki ba, hakan yazamana ba qaramin tashin hankali yake sakata ba dan har tafara ganin canji daga garesa hakan na damunta matuka sosai,,"
Yauma Kamar kullum itace da girkin hakan yasata tun wuri ta shige ďakinsa ta gyare masa ko ina tare da wanke toilet ďin da idan ta lura ba'a wanke sa saidai ita ta wanke, fas tagama gyara masa taja ķofar ta fice, kai tsaye kitchen ta nufa ta ďaura tuwon shinkafa da miyar yakuwa sosai yabaďa cikin gidan da kamshi, tanayi tana gyara kitchen ďin har tasamu ta kammala cikin qanqanin lokacin ta juye komai cikin kula ta haďa plate dasu cokala,,"
Barin su tayi a kitchen ďin ta fita tare da wucewa ďakinta tayi wanka tasamu kayanta na atumfa tasaka riga da zani sosai ya karbì jikinta, tayi kwalliya sama sama ba sosai ba gameda feshe ko ina na jikinta da turare kafin ta fita taje tasa turaren wuta bayan tagama ne ta koma daķin ta ta kwanta rigingine tana kallon saman ďakin cikin zuciyar ta tunani iri iri ta faďa tayi nisa sosai kallo ďaya zakayi mata kasan cewa hankalin ta baya tattare da ita,,"
Wuraren misalin karfe biyar na yamma ta dawo daga gidan shiwari tana gama parkin ďin motar ta tafita tareda rufe motar ta zagaya ta bayan gidan dama da shirin ta tazo tayi alqawarin yauma sai ta lalata mata girkin ta saidai idan batayi ba tunda taga yanzu sun fara samun matsala tsakanin su, hakan ya sanya cikin sanďa tamkar sabuwar barauniya tana leqe ganin ķofar kitchen ďin rufe yake hakan ya tabbatar ma da cewa bata ciki fatan ta ďaya Allah yasa bata shigar da abincin kan dining ba dan a kitchen ďin ne zatafi jin daďin aiwatar da abunda tayi niya,,"
Cikin sa'a kuwa ta hango su ajiye cikin kitchen ďin ganin su ba qaramin daďi yayi mata ba tana wani irin shu'umin murmushi na mugunta ta buďe kular taga miyar yakuwa ce ďayan kuma tuwon shinkafa tana yamutsa fuska ta ďibi ruwa cikin cop biyu ta juye su cikin wannan miyar tasa cokali ta garwaya taga yazama tamkar ruwan kogi kafin ta rufe kular ta gyra inda ya bàci a hankali taja ķofar kitchen kamar yanda yake ta fita, kai tsaye bayan ta shiga parloun babu kowa sai daddaďan kamshin turaren wuta dake tashi cikin ranta take faďin shegiya bakar aljana kafin dai ki kashemu da wannan mugun hayakin naki ni zanyi gaggawar fitar dake daga gidan,,"
Tana toshe da hancinta ta shige cikin ďakin dan batajin zata iya ci gaba da shakar wannan shegen fitinannan hayakin a kullum,,"
A gajiye yadawo gida yau tilis yakejin sa dan gajiya ga wani irin bala'in yunwa dake rarike masa cikin kokon cikin sa ji yake gabaki ďaya idan ba samu yayi yacika cikin sa da abinci ba bazai iyayin komai a wannan lokakin hakan yasa yana shiga parloun ďakinta ya nufa kwance ya tarar da ita idanunta lumshe tamkar wacce take bacci, yaqarasa cikin ďakin ya tsaya akanta gameda qiran sunan ta kusan sau uku kafin tajisa a hankali ta buďe idon ta suka sauka cikin nashi da sauri ta miqe zaune tana kallon sa tace sannu da zuwa har kadawo?, yauwa yafaďa a takaice yace ina abinci yunwa nakeji, muje in zuba maka tafaďa tare da tashi suka fita, kitchen ďin ta wuce ta ďauko kulan abincin da abun ďibawa yana zaune kan dining yana zaman jiranta ta tarar dashi, tana ďan murmushi ta ajiye abincin tana faďin lailla yau ba qaramin yunwa ka kwaso ba yanda ko wanka bakayi ba zakaci abinci dan tasan al adar sace kullun idan yadawo daga aiki idan ba wanka yayi ya canza kayaba bayajin daďin zama yaci abinci hankali kwance,,"
Buďe abincin tayi zata zuba masa yana kallon ta yace bani in zuba da kaina bakya sauri kafin nan kije ki ďauko min charger phone ďina a ďaki, ba musu ta basa abun ďiba abincin tana masa dariya ta wuce dan zuwa aiken da yayi mata,,"
Bayan ya ďauki tuwom malmala ďaya tare da buďe kular miyar zai ďiba cikin jin daďi ya lumshe idanunsa ya buďe su yana qara shakar daddaďan kamshin miyar dake tashi yana shige masa cikin hanci, a iyayin da yasaka ludayin cikin miyar ya ďiba yana zubawa kan plate ďin tamkar sinkekkiyar ruwa tsala yake zubawa,,"
Atake yanayin fuskan sa ya canza wannan abun ba qaramin bashi haushi yayi ba cikin bàcin rai sosai ya shiga kwala mata qira cikin ďaga murya wanda yayi sanadiyar sinkar mata da zuciya sosai jin irin yanda ya qira sunanta ba shiri cikin tana rawan jiki ta fito daga ďakin hannun ta riqe da chargen daya aiketa, tunda ta qaraso inda yake tsayen taga yanayin sa yanda yabi ya canza ta tabbatarwa da kanta ba lfy ba dan a yanda suke zaune shi da ita bai taba mata irin wannan mugun qiran hakaba bare yayi mata irin wannan mummunar kallon da yanzu taga yake binta dashi.....
_Masoyana makaranta littafina dan Allah kudai qara min haquri nakusa samum hutu insha Allahu nagode_🙏🏿
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:10] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*Page*
*33*
Dedicated to my
*AISHA GENTLE LADY*💃Ana mugun tare
Wannan wanne irin iskanci ne, ke shikenan a rayuwarki bazaki iyayin girki yayi kyau ba kullum cikin asara da abinci kike kodan bakisan zafin zuwa aiki a nema bane na lura tunda kikafara girki cikin gidan nan baki tabà yin abincin da ba shida wata matsala ba, hannayen sa ya harďe kan ķirjin sa yana mata kallon bàcin rai yaci gaba da cewa, waima wanne irin abune yake yawo cikin kwakwalwar kanki wanda bazai iya barki ki ajiye kanki da hankalinki waje ďaya kiyi girki mai kyau ba why humaira menene matsalar ki?meye damuwar ki?,,"
tsare ta da idanun sa yayi cike da bàcin rai yake jero mata wannan maganganu marasa daďin ji daga gare ta wanda yayi sanadiyar bugun zuciyar ta yaqaru cikin kiďimewa ta ďaga kwayar idanunta ta kalle shi damuwa qarara kwance bisa fuskan ta sam takasa fahimtar inda maganganun nasa suka dosa duk ya ďaure mata kanta da igiyoyi a iya sanin ta yau lfy lau suka rabu kuma lfy kalau ya shigo cikin gidan saida yanzu da zaici abincin ransa zai bàci bayan tasan babu wata matsala cikin abincin ta na yau saidai daga yanayin jin irin maganganun da yake firfitowa daga cikin bakin sa hakan ya tabbatar mata da cewa yauma wani abun yaji wanda har yafi nada,,"
Dan duk irin yanda zataga ransa yayi mugun baci bai tabà mata irin na yauba, muryan sa taji tamkar sauķar aradu wanda yayi sanadin ďawo da ita daga zancan zucin da take yace, dake nake magana kin min shiru tambayar ki nake meye damuwar ki humaira wanda yake hanaki nutsuwa kiyi abu mai kyau akoda yaushe?,"
To ai bansan meye nayi ba ka fahimtar dani ko zan gane lefina,bazaki tabà sanin abunda kikayi ba sai na nuna miki tunda ba idanu bane dake, ludayin yasaka cikin miyar ya ďiba gameda tsiyayar da ita cikin kular miyar yana mata nuni dashi yace duba kigani wannan wani irin walaqanci da abinci ne yanzu shikenan yazama asara banza, to wlh daga yanzu haquri na yazo karshe bazan iya ďaukar wannan albazarancin ba inaso ki buďe kunnenki da kyau kiji gargaďin da zan miki daga yau sai yau karki kuma karki sake dafa min abinci har idan kinsan bazaki ajiye nutsuwar ki kiyi abu daidai ba dan haka ga jagwalgwalon ki sai kisan yanda zakiyi dashi dan nidai bansan ta wanne hanya zan iya soma cin wannan abincin ba, cike da ďagun murya tamkar za'ayi tashin duniya yake mata faďan,,"
cikin bàcin rai ya kawar da kular miyar wanda har yayi sanadiyar zubewar miyar yayi kacakaca kan dining ďin gameda jan wani irin mugun dogon tsaki wanda zai tabbatar maka da cewa ransa ba qaramin mugun baci yayi ba, tana tsaye kanta na kallon qasa tana jinsa yagama bambamin sa yafice daga parlon gameda shigewa motar sa ya masa kay ya fice daga gidan gabaki ďaya, a iyayin da ta kuwa ta sauķar da nauyayan ajiyan zuciya gameda rufe idanuwan ta ta buďe su cikin kasalanci sam ji take ko wanne sashi na jikinta tamkar laka aka zuba mata batada sauran wani guzari zuciyar ta a tunkushe wannan karon kam batasan mai zatayi ba ji take tamkar ta durkushe a wajan tayi kuka sosai ko zataji saukin zafin da cikin zuciyar ta keyi a yayin da idanun ta suka sauka kan miyar dake kwance malale bisa dining table ďin,,"
tamkar kace ba miyar yakuwa bace dan yanda ruwan yayi masa mugun yawa sosai ganyan yakuwar daban ruwan miyan daban,,haka tasa hannayen ta biyu tafara kwashe kayan abincin gameda mayar dasu kitchen kafin tadawo ta gyara inda ya zubar da miyar tana kammala gyare wajan ta juya ta shige ďakin ta zuciyar ta babu daďi,,"
wanda a wannan lokakin ita kuwa ta kwashe da wani irin mugun dariya da yake dama tuni tana leqan su dan taga ya zasu kwashe har ji take cikinta na kullewa tasa hannunta ta kame tanaci gaba da dariya cikin qasa da murya ta kaďa hannun tace shegiya munafuka yarinya ai yanzu kika soma ganin kaidina bazakisan ni ďin banida kyauba Amman nan gaba kaďan zakisan ni ba qaramar shaiďaniya bace muje zuwa nida ke, tana kaiwa nan ta juya ta shige ďakin ta gameda kaďa jiki tana juyi irin na yau tayi nasara aikin ta yayi kyau hakan na tabbatar mata da cewa wanda zata haďo nan gaba saidai ya rubuto mata da takardar saki uku,,"
tare da yi mata kora tamkar karai dan a wannan lokakin kam tasan haqurin sa yagama qarewa,,Tun bayan fitan sa daga gidan ganin magariba ta doso kai wasu masallacan ma an soma qiran sallah hakan ya sanya shi bai zarce ko ina ba sai masallaci yasamu gu yayi alwala gameda zama jiran ayi sallah, bayan an idar da sallahn magariban yana nan zaune gefe guda azahiri saikace tasbihi yake Amman cikin kokon zuciyar sa tunkushe yake da bàcin rai magana yake cikin ransa yace shikenan shi dai a rayuwa bazaiyi sa'an mace ba kenan, ita wancan ba zama zatayi tayi masa girki ba,,"
itama ďayar wacce zata zauna ďin ba iya girkin tayi ba kullum indai har kwanan ďakinta yake to bazai iya cin abincin gidan sa ba saidai ya kwashi kafar sa yaje gidan su shima cikin dabara dan duk a lokacin da yabari Umma ta kalle shi yana cin abinci to yashiga cikin magana a wannan lokakin ne yake tsokono mata da inda yake mata qaiqayi ta rinqa surutai kenan sa'an shi ďaya idan Abba yana nan a wannan lokakin yake samun sararawa daga maganganun ta, haka yauma a irin yanda ya kwaso gajiya ga yunwa dakeji yana rarike masa ciki, ya sanya shi miqewa da sauri yanajin yanda cikin sa ke masa kukan yunwa ya fice daga masallacin cikin hanzari, yafigi motar sa kai tsaye bai zarce ko ina ba sai gidan su ya dosa yana isa yayi parkin a waje kafin ya sauka ya shiga cikin gidan,,"
tamkar wanda bashi da gaskiya yake takawa har ya shige bangaran Abba yana Allah Allah kar yasa ta hango sa har sai ya kammala da baiwa cikinsa hakkin sa dan a yanayin yanda yakeji a yanzu bazai iya ďaukan korafai korafen taba, Allah yasa yaci sa'a yana shiga parloun ya hango Abba shi ďaya kishingiďe qasan carpet ďin idanun sa na,,"
kan TV yana kallon tashan labare a yayin da kulolin abincin ne jere agaban ga dukkan alamu nan gaba zai soma cin abincin, ba qaramin nishaďi yaji ya shige masa zuciyar sa ba cikin murmushi yaqarasa gaban Abban gameda rusunawa har qasa ya gaishe da shi bayan ya amsa masa yace Abba ina Umma ina fatan tana gefen ta,Eh yabashi amsa yana kallon yanayin sa yace Babana hala yunwa ce ta koro ka hama? cikin jin kunya yace eh wlh naga kafin naqarasa gida yunwar zata gama min illah shiyasa na shigo nan, to ai ga abinci nan matso muci tare yanzu aka kawo shi Abban yafaďa yana tashi daga kishingiďen da yake , tamkar dama jira yake cikin sauri ya ďiba ko jiran Abban bai tsaya yi ba ya soma ci yana saurin yaga ya kammala dan gudun karta shigo ta samesa,,"
yana cikin ci ta shigo cikin parlou tana magana cikin waya ganinsa yasata kashe wayar bayan tace tana zuwa a lokaci ďaya tabishi da mugun kallo bayan gameda qarasowa inda suke cikin magana tamkar mai habaici tace sannu ďan zama gindin bishiyoyin da basu da amfani namiji goro wanda bashida mace ma yafika samun kulawa gashi ka kasa ďaukan mataki ai abun kunya ne wlh ace kanada mata fiye da ďaya Amman kullum sai a gidan iyayenka zagana cin abinci,,"
Allah dai ya wadaran na wani ya lalace dan nikam nawa babu ya riga da yagama lalacewa nan gaba kaďan zakasan ni mai nema maka alkhairi ce, tana kawai nan ta juyar da kai gameda komawa ta fice daga parloun dan tasan idan yanzu ta tsaya bazataji dakyau ba, shi kuwa dama ko hankalin sa baikai gareta ba har ya kammala da cin abincin ya tashi ya kaďe rigar sa yana duban Abba yace ni zan wuce Abba mutashi lfy, har zaka wuce kenan yau babu hira ne Baba na, Eh wlh Abba yau ďin agajiye nake saidai ko gobe, to shikenan ka gaida yan gidan Allah ya kaimu Abba yace dashi a yayin da shi kuma bayan ya amsa masa da Amen ya fice,,"
daga gidan, ganin lokacin sallahn isha'i ya kusa yasa shi tsayawa a masallaci ya jira akayi isha'i dashi kafin ya fito yadawo gida yana parkin ya kashe motar ya nufi cikin parloun Maraqishiya kaďai ya hando kwance kan doguwar kujera tana waya, ganin sa yasata kashe wayar ba tare da da cewa wanda suke wayar tana zuwa ba, tana wuri wuri da ido gameda miqewa zaune tana ďan sakar masa da murmushi tace sannu da shigowa dear sai yanzu? yauwa yace da ita a takaice, kai tsaye ďakin sa ya wuce ba tare da ya tsaya ya saurareta ba,,"
saida ya shige toilet ya watsa ruwa a jikinsa ya zura doguwar farar jallabiya kafin daga bisani ya haura kan gado ya kwanta rigingine tare da rufe idanuwan sa,,"
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:10] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*Page*
*35*
Dedicated to my
*AISHA GENTLE LADY*💃Ana mugun tare
_TUNATAR WACE_👌🏿
_Ingantacciyar Hadisi daga bakin fiyayyan halitta Manzo Allah (SAW)_
*Ankarbò daga Abdullahi ďan Amru ďan As Allah yaqara musu yarda yace: Manzon Allah (S.A.W) yace:" hakika mafificin Azumi a wajan Allah shine Azumin Dawud, mafificiyar sallah a wajan Allah: sallar Dawud ya kasance yana yin barci rabin dare, sai ya tashi a ďaya bisa ukunsa, sai yayi barci a ďaya bisa shida, ya kasance yana yin Azumi yau ya ci gobe""*
_Allah kasa mu dace Ameen_🙏🏿🙏🏿
Ďago da kanta tayi gameda miqewa tsaye wanda har i zuwa lokacin hannun ta yana kan kirjinta tana riqe dashi sanadin zafin da takeji yana qaruwa mata tamkar ta balle shi takeji cikin bàcin rai ta ďago da idanunta,,"
""wanda suka soma canza launi tareda sauķar dashi bisa kansa ganin fuskan sa ba qaramin mugun bàcin rai ya kuma jefata ba gameda qara murtuke fuska tana masa mugun kallo,,"
"Ta buďi baki dakyar da niyar masa magana tanajin tamkar Aman fitowa waje zayi hakan ya sanya ta fasa abunda tayi niyar faďa,"
"Tasa ķafar ta zata koma cikin motar taji yace,,"
"Kiyi magana masa sarkin rashin kunya idan yau ďinma kinada baki,hakan da taji ya faďa ne yaqara tunzura ta bataso tanka masa cike da bàcin rai ta dawo da baya zuwa inda yake tsaye yana harďe da hannayen kan ķirjin sa gameda zuba mata na mujiya yana jiran yaji mai zatace, idanunta tar akansa ta danne abunda takeji,,"
"cikin zuciyar ta tare da qara haďe fuska ta ďago hannunta tayi setin fuskan sa da yatsan ta kafin tace,,"
"Gaga malam wlh tallahi kafita a harkata banason iskancin banza kanaji na ko? wlh ko tafiya nake ka ganni to ka canza hanya ko kayi kwanan layi ko kuma ka juya baya dan wlh banida kyau bana ďaukan zancen banza da wofi irin naku na yan tasha masu zaman kashe wando bakuda wani aiki inbanda saka idanunku kan matan mutane bakusan komai ba duk wacce tazo wucewa da ruwanku, to nidai inaso kasan wani abu tamkar yanda kasan nayi maka gargaďi abaya wannan karon ma shi zanyi maka kafita harkata karka kuma bi takai na dan ni ba tsarar ka bace kaji nagaya maka,,"
"Idan kunne yaji to ba shakka gangan jiki ya tsira..keee ya dakatar da ita da hannun sa cikin jin zafin kalaman ta yace, wlh kibar ganina haka ni ba'a takani da ķafa kai tsaye a wuce inaso kisan cewa billahillazi la'ilaha'illahuwa kinji da sunan rabbi na rantse miki ba iblis ba wlh na ďauki alwashin sai kinyi dana sanin wannan munanan qazaman kalaman naki a kaina ki tabbatar da cewa bake ba zaman lfy ko ina kike zan nema nasani,,"
"Mitsee taja dogon tsaki tace in kafasa kaqi Allah a niyar ka tabika wlh nafi karfin ka, tana kaiwa nan ta juya zata shige mota tayi kicibus da shi ba shiri ta dawo baya yana mata kallon tuhuma,,"
"A takaice ya tambaye ta yace keda waye wannan kuke magana??
"Nima bansan shiba kawai ganina yayi ya tsaya yana gaya min zancen banza,,au baki sanni bako zakice? badamuwa ya rinya akwai lokaci nan gaba kaďan zakisan koni waye, yana gama faďin haka ya kaďa kansa gameda da shigewa cikin super market ďin ransa in yayi dubu ya bàci,,"
""A yayin da itama ta shiga motar ranta a jagule har ta zauna sai kuma Aman data danne shi ya taro mata cikin baki batasan lokacin da ta fito daga cikin motar ba ta soma kwara Aman sosai babu kakkautawa wanda ganin hakan ba qaramin mugun hankali ya tashar masa ba,,"
"Cikin kiďimewa har ya shiga mazaunin sa yafito ya zagayo gareta inda take yasa hannayen sa duk biyu ya riqe kafaďunta yana mata sannu gameda da tambayar ta me yasameta haka?a yayin da inbanda wahalallan numfashi babu abunda take saukewa tanajin wani Aman yana soma fito mata sosai ta galabaita,,"
""Idanunta sunyi jazir tamkar jan garwashi dan wahala tanaji kamar harda yayan hanjin cikinta zasu fito saida tayi sosai yazamana sai yawo ke fita kafin taji dama dama tafara jan gefe guda, a iyayin da iya ruďewa yagama ruďewa har zuwa lokacin bai daina furta mata sannu ba gameda ďago da ita tsaye ya jinginar ta jikin sa kafin cikin taku a hankali,,"
"ya shigar da ita cikin motar wanda a wannan lokakin har masu gadin wajan da wasu mutane haka sun zo zuna mata sannu tareda tausaya mata ganin yanda tabi ta wahalu,,"
"A yayin da cike da bugun zuciya ta rasa wanne tunani zatayi, tayi wannan taga ba shiba tayi wannan taga ba shiba takasa koda kwakkwaran motsi tanaso tafita tabi bayan wannan saurayin Amman tsoron abunda tagani takasa shigowar sa cikin motar ya dawo da ita cikin tunanin da tafaďa ba shiri tasa hannunta ta buďe ķofar motar,,"
"ta fice cike da sauri ko tsayawa rufe ķofar batayi ba tanajin sa yana tambayar ta ina zataje su da zasu tafi Amman tayi banza dashi ta shige cikin super market ďin ta soma raba idanuwan ta gameda ragare cikin kota ina zata hango wannan saurayin yanzu kafin ya biyo ta dan tasan dolene ya biyo bayanta idan yaji shiru wanda cikin sa'a kuwa ta hango sa tsaye wanjan turaruka yana zaba,,"
"Hakan ba qaramin mugun daďi taji ya darsu mata cikin rai ba tana saukar da ajiyan zuciya ta qaraso gareshi fuskan ta ďauke da murmushi tayi masa sallama ya amsa mata batare da yabar ďaukan turaren da yake ba yace ya akayi malama ko lfy?,"
"Lafiyar ce takawo haka tambayar wani abu zanyi dama nakeso nayi,"
"To inajinki Allah dai yasa nasani yafaďa gameda dakawo hankalin sa gareta tace, dama nace ko kasan wannan yarinya ne wacce yanzu naga kuna magana da ita a waje?,"
"Eh yabata amsa a takaice yaci gaba da cewa sonta nake Amman tana min walaqanci dan batasan koni waye ba tun ganinta na farko da nayi na bita na bayyana mata sirrin zuciya ta cikin kwarin jiki Amman dan tsaban ita batagaji mutunci ba wai har ni, ni nan ya nuni da kansa da hannun sa yana dokan ķirjin sa yace ni zatagani ta furta rashin so agareni har tana gaggaya min zancen banza dan batasan koni waye ba, Amman ķur'anin Allah tafaru taqare,,"
"daga yau na ďauki alwashin rama walaqancin da tayi min sai tayi nadama a rayuwar ta a wannan lokakin ne zatasan ni ba irin mutanan da za'a taka in qyale bane...
"Kai malam dan Allah dakata tace dashi ya isa haka wannan lbrn naka bakasan sauri nake bane akan ķafa nake yanzu abunda za'ayi phone number ka zaka bani idan na zauna I will call u dan akwai wani mahimmin aikin dana keso muyi tare dakai nan gaba kaďan har indai zakabi ta hanyar da zanbi dakai to ba babu makawa zaka aure ta har ka gaji da ita ka watsar idan fa kaso kenan,,"
""Dan Allah ko zaki iya min bayani dalla dalla kifitardani cikin duhu kozan gane ina maganar taki ya dosa? kaidai bani phone number ka nace banison wani surutun tsiya har idan ka amince ka hanzarta sauri nake zakaji komai daga baya,,"
"To ai babu matsala yafaďa yana ďan sosa qeyar sa tareda fitar da murmushi ta gefen baki kafin ya irgo mata phone number sa ta ďauka cikin wayar ta gameda ce masa sai kaji call ďina, tana gama faďin haka ta juya ta fice daga cikin super market ďin wanda a wannan lokakin shi kuma yake shigowa sukayi karo dashi cikin haďe fuska yake binta da kallon tuhuma yace,,"
"Me kika shiga yi tun ďazu inata jiranki saikace wani driver gidanku bayan kinsan kuma ba daďi takeji ba, toni ina ruwana da rashin lfyr ta? indai harni lfy kalau nake ai badamuwa ta bace, nama gama abunda yashigar dani sai kazo mutafi inda zaka kaimu,"
"Cike da rashin kunya take mayar masa da maganar a sanda ta wuce ta gabansa ta shige cikin motar kanta a sama ko sannu bata juya tayi mata ba illah haďe haďe da ta somayi cikin ranta ita kaďai tasan mai zata shirya nan gaba kaďan,dawowa cikin motar yayi yasa mata kay sukabar wajan,,"
"Basu ďauki tsawon lokaci ba suka isa har zuwa bakin ķofar gidan mai gadi yana hango sa ya taho da saurin sa ya buďe masa get ďin ya shiga gameda kwasan gaisuwa, yasamu waje yayi parkin ya fito yasa hannunsa ya buďe mata itama ta fito cikin kasalanci ko ina na jikinta a sanyaye takejin sa domin tunda taga sun doso cikin gidan zuciyar ta ya qara tsananta bugu ita ďaya tasan me takeji, haka suka jera suka soma shiga,,"
" bàngaran Abba Maraqishiya na biye dasu a baya tana yayya mutsa fuska, yana zune a parlou suka tarar dashi da qaninsa suna hira,,"
Cikin girmamawa suka rusuna har qasa suka gaishar dasu Abba yana tambayar su ya suke komai lfy? lfy lau suka bashi amsa kafin ya tashi yace dasu su shiga bàngaran umma, sukayi ma Abba sai anjima kafin suka fice sukayi nata gefen, suka shiga zaune suka tarar dasu cikin parloun, gabaki ďayan su suna hira harda Inna suna kwasan dariya gefensu kulolin abincin ne a ajiye wanda wannan lokakin buguwar zuciyar ta ya qara tsananta fiya da naďazu ganin irin kallon da Umma ke binta dashi tasan bana zaman lfy bane Amman ya ta iya dole tazo tunda bayin kanta bane,,"
"Cikin ďarďar ta buďi bakin ta na rawa qasa da murya tace Ina wuni Umma? kinga dakata tace da ita tana mata mugun kallon taci gaba,,"
"Amman kamar natabà miki gargaďin bana bukatar gaisuwar ko? ko akan hanya nace kika kalle ni bance ki gaisheni ba bana bukatar sa kinji dai naga miki simisimi dake saikace mutumiyar arziki harda wani wai Umma ina wuni to karki kuma banaso daga yau,,"
"Kai, kai, kai, Umma wai meyasa kike hakane wai? shikenan ke kullum cikin tsanar yar mutane kike tun kafin kisan wacece ita har zuwa yanzu Amman kin kasa ďaukan ta kamar yanda kika ďauki sauran surukan ki, kin ware ta daban tamkar ba auran ďanki take ba ai haka bai dace ba gaskiya wlh Umma ki sake wani tunanin daban, Batula, Na am, Batula, na am, Batula na am Umma inajinki ai,,"
"Kinci kutumar gidanku shegiyar yarinya fuska saikace an dama taiba wlh banason saurin idanu zan iya ci miki zarafi kinji ko? banason shashencin banza da wofi ki daina shiga
zance na,"
"Yo ai Umma gaskiya nafaďa miki, ki min shiru nace batula tunkan na tsabà miki,,to ai shikenan nayi shiru tafaďa cikin ranta gameda tashi cikin haďa fuska ta dawo inda Humaira ke zaune itama tayi mazauni a kusa da ita tasa hannunta kamo nata tana sakar mata da murmushi tace Anty Humaira sannu fa kinga nikam sai yau nayi miki kallon mai kyau koda ranar buďan kai ma kallon ki bai isheni ba,,"
" Amman yau dai nasan zaki barni nayi miki kallo mai isata har sai in nine nace ya isheni ko Auntyna? kai ta girgiza mata cike da kunya tana ďan murmushin yake,,"
"A yayinda Zaliha wacce ke kusa da Umma baki sake take binsu da idanuwa tanajin wani irin sabon abu dake faruwa cikin sakin fuska tana dariya ta dawo da dubanta kansa tace babban yayanmu kana nan ashe ko gaisawa bamuyi ba rabona dakai tun ranar bikinka shikenan, wlh fa kedai bari kawai Zaliha abubuwa ne sai aslow ina shi mijin naki har yanzu bazai dawo bane ko bai gama bane? dan nikam na kwana biyu rabona dashi,,,"
"Aiyya ai shima yafaďa Amman ya kusa dawowa kwanan, to Allah ya kawo sa lfy yace da ita ina Amal banji muryan taba ko bakizo da ita bane? A a da ita nazo bacci take Amman nasan ma yanzu tana dafda tashi..bata idisa maganar ba sai gata cikin magagin bacci ta fito daga cikin ďakin Umma tana hango sa ta taho da gudu tana dariya tafaďa jikinsa tace,,"
"Oyoyo my uncle nayi missing ďinka yanzu ka daina sona ko? tana duban fuskan sa tayi maganar cike da shagwaba,yana ďan jan kumatun ta yace haba mana my baby girl taya zakice uncle ďinki ya daina sonki? ina nan dake baby kinji kiyi haquri, to uncle na haqura tafaďa tana dariya tace uncle ina Aunty sabuwa da kayi mana nifa ban tabà ganinta ba, gatanan ai nazo miki da ita yayi mata nuni da Humaira wacce kanta ke qasa tana sauraron su cikin gudu tazo gareta tana dariya tace Aunty sabuwa ina wuni, lfy ta amsa mata cikin sanyin murya ta zaunar da ita kan cinyar ta kafin ta soma tambayar ta sunanta da ya school ďinta,,"
Wanda hakan nanda nan cikin qaramin lokaci tasaki jiki da ita sunata hiran su Batula ma nasa musu baki,,,"
"Sunci lokacin kaďan suna hira Maraqishiya na gefen Umma da Zaliha suna nasu hiran Inna kuma ta shige cikin su humaira anayi da ita ganin babu sarki sai Allah yasa itama suwaiba ta shigo cikin su, wanda shi kuwa ya dake gefe guda yana latsan wayansa,,"
Can ďan bayan wasu lokaci Umma tace da Batula suje su kawo abun zuba abinci aci abincin da Zaliha ta kawo, musu suka fita kitchen suka ďauko plate da cokala da kulan da za'a sakawa Abba nashi suka dawo Umma ta karba ta buďe kulolin Abincin ta tana zubawa dafeffen tuwon semo da miyar ganye wanda ķàmshin kifi ke tashi cikin sa duk ya garwaye parlonu,,"
"A yayin da ta toshe bakinta da hancinta ta miqe tsaye da gudu ta fice waje kafin ta qarasa waje mai qasa ta soma kwarara ruwan Amai zalla sosai tamkar zata Amayar da hanjin cikinta da gudu suka fito daga cikin parloun duk suka iyo kanta suna mata sannu banda Umma da Maraqishiya dake sake da baki sun rasa na cewa saida tayi sosai tana saukar da numfashi sama sama kafin ta ďago dakyar yana riqe da ita sai sannu yake mata gameda mata duba mai kyau yace nikam meke damunki ne da wannan sau biyu kenan kikeyin Amai anya lfy kike kuwa kodai wani abune bakyaso? kasa koda girgiza masa kai tayi illa numfashin da take fitarwa tana rufe idanuwan ta,,"
"Wanda ganin hakan yasa shi yin salla dasu Umma ya shigar da ita gaban motar yace da Maraqishiya ta ďauko jakanta ta shige baya sutafi tana gumbura fuska taje ta ďauko tadawo ta shiga yatashar da motar sukabar gidan Inna dai sai sannu take faďi tana Allah sarki yar arziki ko me yake damunda a sanda Umma kam ta rasa wanne tunani zatayi a ranta tace kodai yarinyar ciki take ďauke dashi? haka tana zance cikin ranta suka koma cikin parloun kowa da abuda ke qakawa cikin ransa,,"
" Ko acikin motar ma sai sannu yake mata yana kaiwan hannun sa kan goshinta yaji zafi cikin nuna damuwar sa yaqarawa motar gudu, cikin qanqanin lokaci ya isa cikin Asibitin yasamu waje yayi parkin gameda sauqowa ya zagayo inda take tana shirin fitowa yasa hannunsa ya riqe nata suka shige ciki,,"
"Sanadiyar wani tunani da taji yashige mata zuciya yasata sauka daga motar batare da tayi niya ba tabi bayansu cikin sauri ta iso inda suke,,"
Suna cikin tafiya suka haďu da wata Nurse ta tsaya suka gaisa yana kallon Humaira yacewa Nurse ďin Dr Nake nema inaso a duba ta yau sai Amai take sosai bansan meke damunta ba,,"
"Haba dai alhaji ai kawai murna zakayi daga ganin wannan matar taka kallo ďaya zaka mata kasan cewa ciki ne da ita,,"
"Wanda hakan da taji ya sanya taji wani karfi yazo mata batasan lokacin da ta dafe kirji ba gameda da zaro idanunta wanda suka rine waje ta buďi baki tace nurse kinsan mai kikecewa kuwa? ciki fa kikace nake ďauke dashi bayan ko dubani bakiba zaki yanke min hukuncin ranki kice wai cike ne dani......
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:10] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT_M_S*✍🏻
*Page*
*34*
Dedicated to my
*AISHA GENTLE LADY*💃Ana mugun tare
*HAUWA M JABÒ*sannu da hanya 🙋🏿
A hankalin cikin sanyin jiki batajin ko wani irin kuzari tattare da ita ta tura ķofar ďakin ta shiga zuciyar na bugawa sosai tana tsoron qarasawa inda yake gameda da tunanin ta inda zata soma basa haquri ganin idanuwan sa a rufe tamkar wanda yayi nisa cikin bacci hakan yasa tayi zaton bacci yake har ta juya da niyar komawa taji muryan sa yace,,"
"lfy?hakan yasata tafasawa ta dawo da baya ta qarasa gareshi gameda da durkushewa qasa kan gwaiwowin ta tana duban sa ta buďi bakin ta cikin sanyin murya ta soma magana, tare da haďe hannayen ta waje ďaya tamkar zatayi kuka idanun ta sun soma kaďawa tace,,"
"Am so sorry mijina dan Allah kayi haquri ka yafe min wlh bansan tayaya haka yake faruwa dani nidai nasan a iya sanina wlh komai na daidai nakeyi Amman bansan tayaya abinci na yake lalacewa ba akoda yaushe idan nayi girki, but Am sorry again insha Allahu zanga nayi kokari na gyara kuskure na zan ina kula bazaka taba qara samun wata matsalar ba,,"
"Bari inje in haďo maka wani abu kaci,miqewa tayi jiki babu kwari da niyar fita daga ďakin taji muryan sa yace,"
"Kibari banajin yunwa a takaice yayi maganar tamkar dole gemeda juya kansa gefe ďayan a iyayin da ta dawo baya gareshi cikin nuna rashin fahimta ta kuma duban sa akaro na biyu dukda bataji daďin juya mata bayan da yayi ba hakan baiyi nasaran hanata yin wata maganar ba tace,,"
"kamarya bakyajin yunwa ko kaci abincin ne a waje?,,"
"Wannan kuma ba damuwar ki bace nace miki ki rabu dani banajin yunwar ko dole ne sai naci?
A a tafaďa gameda girgiza kanta,, yace to dan Allah kibar ni na huta saida safe,,"
Allah ya huci zuciyar ka mutashi lfy,"
Dakyar ta iya qarasa maganar cikin jin zafin zuciya ta fice tare da ja masa kofar ďakin kai tsaye ta shige nata ďakin gameda zubewa bisa gado cikin kunar rai batasan lokacin da idanuwan ta suka soma zubar da zafafan hawaye ba,,"
"Sosai taji kukan ya shaqeta ba shiri tashiga yi tana shashsheqa cikin kunar zuciya takasa koda motsawa bare ta canza kayan jikinta zuwa na kwanciya haka har baccin barawo yayi nasaran kwasan ta batare da tasani ba,,"
Asuban fari ta buďe idanunta cikin kasalanci jikin yayi tsami sosai tamkar wacce akayiwa dukan tsiya ji take sosai kanta ya kame yana mata azababban ciwo, a hankali ta miqe tsaye bayan tayi addu'ar tashi daga bacci tana riqe da kanta wanda takeji ya ďaure sosai yana sarawa tamkar guduma ake kwala mata tana dafe dashi, ta shige toilet ta ďauro alwala tafito tayi raka'atul fajiri kafin tayi sallahn asuba bayan ta idar ne ta zauna tana tasbihi gameda yin Addu'ah sosai,,"
"tana rokon Allah ya nuna mata wanda yake lalatar mata da abincin ta idan tayi dan a iya sanin ta bata tabàyin girki a gidan su ance mata yau ga wani abu yayi yawa ba ko yayi ruwa ba sai a gidan nan abun ba qaramin damunta yake ba, sosai tayi addu'ah harda zubar da kwalla sanadin idan ta tuna da babu wani lokaci guda ďaya wanda za'a ce gashi yaci abincin hannun ta lafiyayye ba kullum sai an samu matsala,,tana nan zaune tana wuridi gyangyaďi yana ďiban ta,,"
"bataso bacci ya kuma ďiban taba,
ba ita ta farkaba sai wuraren karfe bakwai da ďan mintuna, salati ďauke abakin tayi miqa gameda tashi tsaye ta shige toilet tayi wanka tare dayin brush kafin ta fito, ta shirya cikin doguwar riga ta atumfa mai ruwan kore ta shafa cream da turare a jikinta kafin ta shiga gyaran ďakin dukda ba wani datti bane dashi kafin taja ķofar ta fice kai tsaye kitchen ta nufa cikin hanzari ta ciro kaza daga freezer,,"
da yake a yanke a wanke yake yasata jefa shi cikin tunkunya tayi mishi haďin dafuwan danderu yayi rigijif dashi ya farfashe tamkar kace ba kaza bace gefe guda kuma ta tafasar da dankalin turawa ta soya shi gameda da haďe shi da albasa da green pepper da magi kaďan ta garwaye shi yayi kyau,tana kammalawa ta ďauko kula tafara juye su cike da nutsuwa,,"
"Wanda a wannan lokakin ya turo ķofar kitchen ďin ya shigo neman ta, tsaye ya hango ta cikin sanďa ya taka a hankali ya isa gareta dameda saka hannayen sa duk biyu ya kamo kwankwason ta a iyayin da ya zagareta dashi,,"
"Wanda yayi sanadiyar tsoratar da ita ba shiri tabar abunda take gameda da jiyo da kanta sukayi idanu huďu da nashi, saukar da nata idanun tayi batare da tayi magana ba ta jiyo da kanta tare da maido da hankalin ta kan aikin da takeyi,lumshe idanun sa yayi ya kuma buďe su gameda da shakar daddaďan kamshin abincin dake shige masa cikin hanci sa,,"
"Wanda baisan lokacin da yaqara tusa kansa tsakanin wiyan ta da kafaďun ta ba, cikin qasa da murya ya buďi bakin sa ya soma magana yace,,"
Amarya bakya lefi koda kuwa kin kashe ďan masu gida,,"
"Himm Allah ya tsare in gwada kashewa mana wanda idan nima ba'a kashe ni ba nan take batare da bata lokaci ba,,"
"Haba mana matar wai fishi kike dani ne haka? to waima in tambaye ki me nayi miki wanda ya hanaki zuwa ďakina mu kwana jiya kika barni ni ďaya tamkar kace goro wanda bashi da mata haka inata juyi har bacci ya ďaukeni batare da nasani ba nidai gaskiya kinci hakkina na jiya baki kyauta min ba Amman zan haďa da nayau duka a lokaci ďaya kuma baki isa ki hanani ba,,"
"Amman dai kayi baccin ko? ta tambaye shi bayan ta zare hannayen sa daga riqon da yayi ma kwankwason ta,,"
haba mana matar meye kinata wani harhaďa min rai ne, idan abunda yafaru jiya ne ai babu ya wuce ki mance dashi raina ne ya bàci sosai jiya shiyasa but ai gashi yanzu naga kina dafa mana mai daďi,"
"pls my angel I can wait muje muci yunwa nakeji karki bari ya min illah, tamkar mai shagwaba yake maganar yana kwabe fuska,,"
"To muje nagama ai tace dashi batare da ta kalle shi ba tana danne dariyan da taji ya taso mata,"
"Yauwa muje yafaďa tareda taya ta ďaukan wasu kayan tana tafe yana biye da ita har suka shigo wajan dining, nan ya ajiye kan table ďin gameda da jan kujera ya zauna, ajiye na hannunta tayi kafin ta dube shi fuskan ta a sake,,"
"tace bari inje in qira Aunty tazo muci tare,,"
"A a rabu da ita zauna muyi karin mu zata fito ai,,"
"Haba mana babu daďi ai ta fito taga munacin abincin batare da mun qirata ba bayan ita koda yaushe iadan tayi abinci sai ta nemeni munci tare kaga kuwa ai banyi mata adalci ba,,"
Gardama zakayi min kenan abunda baki tabà min ba?
"A a tafaďa gameda girgiza kanta, yace to zauna kizuba muci,,"
"zama tayi ba musu kan kujeran dake kusa da nasa kafin tafara zuba masa tazo zata zuba nata taji ya riqe mata hannun ta yana kallon cikin kwayar idanunta yace tare zamuci basai kin dibi naki daban ba, hakan yasata ďaukan fork ta miqasa masa itama ta ďauka suka fara ci, santi ne sosai ya ďibe shi yanaci yana girgiza kai alamun ba qaramin mugun jin daďin girkin yayi ba,,"
"Wanda cike da zolaya yana ďan murmushin gefen baki ya dube ta yace,,"
"Ashe dai daman kin iya dafa abincin mai daďi irin wannan Amman bakya iya zama kiyi?,"
"Himmm kaidai kaci banason wata magana,,"
"Dama Ai bazakiso ba,
"nidai pls kina saka hankalin ki wajan girkin kinayi mai kyau kinji?,,"
"Naji insha Allahu kar samu damuwa tafaďa tanaci gaba da kaiwan abincin bakinta yaqara da cewa yauwa kinga tunda yau Saturday ne bani da inda zanje ku shirya yau muje gida gun su Umma kekam baki tabà zuwa bama kinga yakamata muje kar suyi fishi ko?,,"
"Eh tabashi amsa a takaice a yayin da takejin zuciyar ta ya soma dukan uku uku tamkar tace ita bazataje ba takeji dan ahaqiqanin gaskiya tun yanzu ta soma tsorata da Umma batasan yau kuma idan taje gidan mai zata tarar ba bayan ba tabà zuwa tayi ba,,"
"Washh Allah na tafaďi cikin ranta gameda da dafe kanta batare da tasan maganar yafito fili ba,,"
"Lfy kike kuwa kina riqe kai kodai kanki ne ke miki ciwo?
"Eh Amman nasha magani kar damu tafaďa tana ďan sakar masa murmushi, wanda a wannan lokakin Maraqishiya ta fito daga cikin dakin ta cikin shirin ta na fita unguwa taci uban kwalliya tamkar wacce gidan biki zata, cikin takun ta na qasaita tana yamutsa fuska gameda binsu da mugun harara batare da tabi ta kansu ba dan wani mugun haushi da taji a take ya darsu mata cikin qoqon zuciyar ta, har takai bakin ķofar parloun ta buďe zata fita tajiyo muryan sa yace ina zakije?,,"
Fita zanyi tabashi amsa a takaice gameda dawowa baya tana kallon su,,"
Duba lokaci kigani kwata kwata ko goma ma batayi da safen Allah zakice min fita,,"
"To meye zan tsaya nayi maka tunda bani bace da girki banda hakama ai gidan Shiwari zanje ba wani wajen daban ba shi ďin ma dan kayan mu sun shigo ne,maganar take cike da haďe fuska tamkar dole aka sakata, a iyayin da yace to dawo babu inda zaki idan kuma ban isa dake bane sai ki nuna min in gani,,"
"yana kaiwa nan ya miqe tsaye gameda da wucewa ďakin sa, a iyayin da ta dawo ta zauna kan ďaya daga cikin kujerun parloun gameda bin humaira da mugun harara sanda take ce mata Aunty ga kari fa kizo muci,,"
"kinga wlh banason munafurcin banza idan kinada niyar bani inci ai da har ďaki na zakije ki qirani Amman dan tsaban munafurci saida kukaci kuka rage yagama yin sanyi zaki wani buďe baki kice min ga kari saikace ance miki ni yar gidan aci a rage ne,,"
"Allah ya huci zuciyar ki ba nufi naba kenan wlh tafaďa gameda da miqewa ta soma tattare wajan tanajin ta taja dogon tsaki bata kuma cewa komai ba tagama tattarewa ta shige ďakin ta dan shiryawa,,"
Around 12:30pm ya fito daga dakinsa cikin shirin sa na qananan kaya yana gyaran a gogon hannun sa ya dubi Maraqishiya wanda ke zaune a parloun tun zamanta na ďazun bata motsa ba ta kumbure fuska dan gabaki ďaya ma haushin sa takeji,,"
"Tashi mutafi taji yace da ita,,"
"Bangane ba ina zamu kuma bayan kasan inada abunyi mai mahimmanci ka hanani fita yanzu kuma kazo kace min muje, to nidai harga Allah babu inda zani,,"
"Ba shawaran ki nake nema ba umarni nabaki dan haka ki sameni a mota, yana kaiwa nan yaje yayi ma humaira magana ta fito cikin shirinta na bakar Abaya tamkar balarabiya tayi kyau sosai ta nannaďe kanta da gyalan sa, yana tafe tana binsa a baya suka fito haraban gidan inda yayi parkin motar sa shi shige mazaunin driver,,"
"ita kuma ta buďe na gefen sa zata shiga Maraqishiya ta fito cikin saurin bayan rufe ķofar parloun, harda ďan gudun ta gameda damke hannun ta tace wannan baiyi miki kama da wajan zamanki ba dan haka ki koma baya, ba musu tasake ķofar motar ta dawo baya suka shiga ya tayar da motar mai gadi ya buďe masu gate suka fita, a iyayin da cikin motar ya ďauki shiru tamkar kace kurmaye ne cikin motar tsit kakeji,,"
"Har ya isa dasu bakin wani super market Kalamu waheed, yasamu parkin space yayi parkin gameda da jiyowa ya dube su yace ku jirani ina zuwa, kafin ya fice ya shige ciki,wanda a wannan lokacin bayan wasu mintuna kaďan taji a take cikin qanqanin lokaci gabaki ďaya zaman cikin motar ya isheta yana dunguran ta ga wani irin tashin zuciya da Amai Amai da takeji yana tokare mata cikin zuciyar ta tamkar zai fasa mata kirji yafito waje takeji,,"
"ba shiri tasa hannunta ta buďe ķofar motar tana toshe da bakinta ta fita waje gameda da durkushewa qasa a filin wajan tana saukar da wahalallan numfashi dan ba qaramin mugun damunta yake ba sai danne kirjin ta take da hannayen ta ko zataji sassaucin raďaďin da yake mata,,
"A iyayin da wani matashin saurayi yazo zai wuce ta wajan ya hangota durkushe qasa, ganin yagane fuskan ta yasa shi tsayawa a kanta dan har yau bazai tabà mancewa da walaqancin da tayi masa ba,,"
tamkar saukan aradu taji muryan sa ya sauka bisa tsakoyan kanta yace tun yanzu kin soma ganin duniya kin soma nadama kenan???......
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:10] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*Page*
*36*
Dedicated to my
*AISHA GENTLE LADY*💃Ana mugun tare
Dafa kafaďan ta Nurse ďin tayi gameda da sakar mata da yar murmushi tana duban yanayin ta yanda tabi gabaki ďaya tagama ruďewa tace, Haba dai yar uwa wani abunne idan ance kina ďauke da ciki? ai ni aganina murna zakiyi abun farin ciki nefa,,"
"kinga Nurse ya isa haka dan Allah ni muje ki duba ni kafin ki tabbatar min da cewa cikin ne gareni,,"
"Humaira taji sa ya qira sunanta cikin iriyar murya wanda hakan ya sanya ta ďago da kanta, ta kalle shi da idanunta gameda cewa na am,,"
"Bangane abunda kike nufi ba, cikin ne bakiso ki ďauka ko meye ma'anar ki? Aiyya mana dan Allah, nifa ba cikin bane banason ďaukà kawai dai gani nayi kwatakwata yaushe nema mukayi aure dahar za'a ce na ďauki ciki, banda hakama karatu fa zan koma saura min shekara ďaya in kammala, yanzu idan cikin ne gareni, da rainon ciki zanji ko kuma da faman yin karatu?
"Ni shine kawai abunda nake dubawa Amman ba...Amman ba miye ba? me kike nufi da haka humaira so kike kice min bazaki ďauki ciki a yanzu ba sai bayan kingama da karatun ki?,'
"Daga baya kenan idan kinga ba iya rainon cikin sa zakiyi ba, sai ki zubar dashi ingani, cikin nuna bacin ransa yake maganar bayan yasaki hannunta daga nashi batare da ya kalleta yakai dubansa ga Nurse ďin dake tsaye ta saki baki tana kallon abun mamaki,,"
"Yace dan Allah gata nan kije da ita ki dubata yanzun nan inajiran result ďin,"
"Karka samu damuwa yallabe, ba matsala yanzu kuwa za'ayi sai kaje ka yanki katin kafin, cewar Nurse ďin, tana maganar takama hannun humaira tace muje ko? ba musu tabi bayanta tana zunbure zunbure itadai harga Allah bataso ďaukan ciki a wannan lokakin ba, niyar ta sai ta kammala da karatun kafin, ta tamkar tayi kuka takeji,,"
"Cikin zuciyar ta tanata Allah Allah a ranta yasa ba ciki bane da ita, dan batasan ta ina zata soma haďa rainon ciki da karatu ba a lokaci ďaya, tana zancen zuci har aka ďibi jinin ta akaje wajan gwaji nurse ďin ta dawo da ita inda yake zaune yana jiran saka mako banda Maraqishiya dake tsaye ta kasa zaune ta kasa tsaye sai zirga zirga take tsoronta ďaya kardau ace ciki ne ďauke da ita dan babu makawa watan mutuwar tane zai kama a wannan lokakin,,"
"Yana hango tahowar su ya mike tsaye cikin zumuďin jin albishr ďin, yace nurse ya akayi me kikagani cikin ne? insha Allahu cikin ne yallabe, yanzu dai mun ďibi jininta zaku iya komawa gida zuwa gobe sai ka dawo ka karbi sakamakon,,"
"Bazai iyu mujira abamu yanzu ba? a a saidai zuwa gobe,,"
"To ba matsala yace da ita nagode sai nazo gobe ďin, bayan yagama faďan hakan ne yakai dubansa garesu yace sai kuzo mutafi ko?,,"
"Bin bayansa sukayi ko wannan su da abunda yake sakawa cikin ransa kowa yana fatan Allah yasa dai ba ciki bane, haka har suka fito haraban Asibitin humaira kam dan haushi ma ko gigin zaman gaba batayi ba, tashige gidan baya a yayin da Maraqishiya kuma ta shige gidan gaba ya tayar da motar suka bar Asibitin, zuciyar kowa da zancen da yake babu wanda yace da juna koda uffan cikin motar tayi tsit tamkar kace kurmaye ne ke ciki,,"
"Wuraren misalin karfe biyu ya isa dasu gida mai gadi ya buďe masa get ya shiga, ko gama parkin baiyi ba humaira ta buďe nata ķofar ta fice, bayan ya gama daidaita kan motar Maraqishiya ta fito tazo ta buďe musu ķofar parloun batare da takai dubanta gareta ba, dan ji take tamkar ta mangaje ta da hannu, ta zube watse nan wajan, idan yaso koda cikin ne da ita sai yayi sanadiyar zubewar sa, a wannan lokakin zata samu sassauci cikin tsakiyar zuciyar ta,,, shi kuwa yana ganin shigar su ya juyar da kai ya fita zuwa masallaci dan gabatar da sallan azahar,,"
"Dakin ta Humaira ta wuce dan gabatar da sallah, tanajin wani iri cikin ko ina na jikinta yana shigan ta, tun sanda taji batun ciki ne ďauke da ita,,, Maraqishiya kuwa kai tsaye kitchen ďinta ta nufa dan neman abinci da yake ko karin safe batayi ba dama a nufinta idan taje gidan shiwari ne, zata nemi wani abun taci sai kuma yazo yamata cikas bayaga haka ga abinci lafiyayye tana kallo gidan Umma, yayi mugun shiga ranta basuci ba sukabar gidan hakan shike qara tunzurar cikin zuciyarta, dan haushi tana kunkuni ta gama dafa indomie ta dawo ďaķinta ta zauna fara ci gameda da lalumo number wayar shiwari ta qira tana ďauka ta shiga bata labarin komai abunda yafaru a yau,,"
"Gado tasamu ta kwanta bayan ta idar da sallah tana tasbihi cikin zuciyar ta, gameda lumshe idanunta tanajin wani irin kasala naqara shige mata jiki, haka har bacci ya ďibeta, koda ya dawo cikin digan ďakin ta ya soma shiga ganin bacci take yasa shi fitowa ya wuce ďakinsa ya ďauki abunda zai ďauka ya kuma ficewa daga gidan, batare da Maraqishiya taga shigowar sa ba bare fitan sa tana can tana zubawa shiwari lbr suna haďeďen yanda zasu bullowa lamarin,,"
** **
Washegarin gobe Sunday da safe kusan misalin karfe takwas, ya farka daga baccin da ya koma bayan yayi sallan asuba,, ya tashi daga kwancen da yake ya juya gefen sa ya hangi Maraqishiya wanda ke sharan bacci hankali kwance da yake itace da kwanansa,, bai tsaya yabi ta kanta ba ya miqe ya shige toilet yayi wanka ya fito bayan ya goge jikinsa ya zaro shaddar sa kaftan yasaka tareda feshe jikinsa da turare,har ya kammala shiryawan sa, tana nan kwance tana bacci bataji koda motsin sa ba ya fice yabar mata ďakin,,"
Zaune ya hango Humaira can daga tsakiyar parloun, sanye cikin doguwar riga ta atumfa kanta tayi ďaurin ture kaga tsiya da ďankwalin atumfar,, tana shan black Tea da lemun tsami aciki, hankalin ta kwance ba qaramin jin daďin sa takeba jifa jifa take kai idonta ga tv tana kallon tashan rabaren da ake,,"
"A hankalin cikin sanďa da dabara, ya iso gareta batasani ba ya durkusa ta bayanta, sai jin hannun mutum tayi ya kame mata kunkumi yana tusa kansa tsakanin kafaďanta, wanda hakan ya sanya ta jiyo dakai sukayi idanu huďu dashi yana sakar mata da qayaraccan murmushi ya buďi bakin sa yace,,"
"Shikenan kuma sai akace ki zauna ke ďaya kina shan tea batare da kin nemi mijinki bako? kin kyauta kenan matar?kodai small babynah ne ya tashar dake da wuri ya saki shan Tea da wannan safiyar? shiru tayi masa batace komai ba illah cup ďin tea da take shirin kaiwa bakinta, bata ankara ba ya karbà daga hannunta, yace ina magana akan kice min gashi insha nima, Amman sai kika min banza,,"
"To ni zan shanye wannan ďin saidai ki ďibi wani, yana kallon ta yakai shayin bakinsa, bayan yasa hannunsa ya anshi cup ďin ya kurbi kaďan sai kuma yadawo da cup ďin, yana qara kallon ta a karo na biyu yace shayin yayi daďi but kamar kinsa lemun tsami ko? Eh tabashi amsa,, bayan ya ije cup ďin yace,,"
Haba mana humaira wai so kike kiyiwa kanki illah ne? bayan kinsan yanzu ciki ne ďauke dake, bakisan wannan tsamin da kikesha illah ce ba a gareki, zai iya haifar miki da matsala babba cikin mahaifar ki yayi sanadiyar zubewar cikin dake jikinki ba?,,"
"Yi haquri bansani ba, but ai yanzun ba cike akace maka nake ďauke da shi ba, dan haka ai zan iya shan kayana,,,"
Wayace miki? ya tambaye yana qara duban ta yaci gaba da cewa yanzu ma wannan shirin nawa da kikegani Asibitin zanje in karbò result ďin, kinga kuwa ai zancen ciki ya tabbata kenan, sai nadawo ma nikam zan qarasa shan wannan shayin dan yayi min daďi yafi wanda kike min,, Amman dan Allah ina rokon wata alfarma karfa kici gaba shan wannan lemun tsamin Allah zai iya miki illah kinji?,,"
"Naji mai gida ran gida adawo lfy Allah yasa atafi a sa'a adawo da mai kyau, saidai kuma bakaci komai ba, banda hakama ai yayi safiya sosai yanzun,"
"Yauwa matar haka nakeson ji bye karki damu sai nadawo zanci, kuma zan tsaya a office ne kafin in wuce asibitin, nidai ki kular min da kanki, yana gyaran hular kansa da ďan murmushin sa yake maganar tabishi da Allah ya kiyaye hanya,,"
"Cikin zuciyar ta na ďarďar fatan ta ďaya kuma shine bazata dena ba,,"
Koda ya fice daga gidan office ďinsa dan dubu wasu takardu, yana nan zaune ya duba a gogon dake maqale kan hannunsa ganin har ana neman shiga shaďaya ya sanya shi miqewa ya kulle office ďin ya fice zuwa Asbitin,,"
"Yana shiga ciki, yayi sa'a ya haango nurse ďin da suka haďu jiya ya isa gareta cikin fara'a suka gaisa, ganin sa ya tabbatar mata da cewa Resut ďin yazo karba, cikin minti kaďan taje takawo masa,,"
"Fuskan ta ďauke da murmushi tace, yallabe ina tayaka murya matuka, matar ka na ďauke da cikin wata ďaya ga sakamakon nan..
"Bai bari ta qarasa maganar bakinta ba,, cike da murna ya karbì takarkan daga hannunta, farin ciki qarara kwance bisa fuskan sa, cikin zuciyar sa yana yiwa Allah godiya da yasa shima zaiga ďan cikin sa,,"
Sosai ya godewa Allah ya ďago da kansa ya kalli nurse gameda da yimata godiya ya yace shi ya wuce, ya juya zai tafi ta tsayar dashi gameda miqa masa paper hannunta tace,,"
"Yallabe ga magungunan nan, shi za'a siya tanasha zai taimaka mata wajan Aman da takeyi sai a kula sosai dan Allah tanasha akan lokaci kuma a tabbatar da tana samun kulawa dan samun lfyn abunda ke cikin ta,,"
"Insha Allahu za'a kula nagode yace da ita har zai tafi ta kuma cewa yauwa yallabe jiya naji matar taka ta nuna batason cikin lfy take kuwa? dan abun farin ciki ne nagani,,"
"Lafiyar ta lau tsorata tayi Amman ba wata matsala,,"
"To shikenan Allah ya sauke ta lfy, a dai kula,,insha Allahu yace da ita cikin sauri ya fice daga Asibitin ya shiga motar sa ya masa kay, yana Allah Allah yaga ya isa gida zuciyar sa fal farin ciki da annashuwa, a ransa yake faďin shikenan nima nakusa zama uba, na kusa komawa mahaifi nan gaba kaďan ďan ciki na, zaina qiran sunana da Abba,,"
"Wani irin ķayataccan murmushi ne ya sauķa bisa fuskan sa, yasa hannunsa yana shafan sajen dake kwance kan fuskan sa gameda da qarawa motar gudu, gani yake tamkar bata gudu,,"
"Dan tsantsan irin mugun farin cikin da yake cin tsakiyar zuciyar sa, ya sanya shi zarcewa gidan su kai tsaye dan ji yake dole ne ya sanar dasu a yanda yakejin sa,, yana isa ķofar gidan yayi parkin a waje batare da ya shiga ba,,"
"Bàngaran Abba ya soma shiga, yaga babu kowa, ya fito ya shiga bàngaran Umma,,"
"Zaune ya hango ta, ita da qanwarta hajiya zulai suna hira, yana murmushi ya isa garesu, cikin girmamawa ya gaishe dasu,,"
"Haquri Umma takasa yi, tana duban yanayin fuskan sa ga dukkan alamu yau acikin Annashuwa yake, tace,,"
"Abdullah lfy yau kake naga sai wani irin murmushi ne ke fita cikin fuskan ka wani albishir ďin ne aka maka?,,"
"Umma ai bari kawai yau ďin nan ta gefen dama natashi cikin ni'ima,,"
"Tofa faďa muji mana kodai figaggun matan gidan naka ne akaci sa'a yau suka maka abun arziki?, dan na kwana biyu rabon da naga dariyar ka haka,,"
"Kai, Kai Umma, zaki soma ba? nifa bashine ya kawo ba, abunda ya kawoni daban ne, to faďi muji mana ja'irin yaro ka shanyar damu kana mana zancen banza,,"
"Cewar hajiya zulai cikin ďaga sauti dan gabaki ďaya ta gama ķosuwa taji meke tafe dashi,,"
"Gashi yace da Umma yana miqa mata takardar, tasa hannunta ta karbà gameda tambayar sa wannan kumafa takardan miye ce?,,"
"Umma kedai duba mana hanzarin me kikeyi, zakiga komai aciki ai, Yoo ai rubutun naku ne banaganewa, anshi ke zulai ko zakisan me ake cewa,,"
"Umma kawo in karanta muku,,cewar Batula da tafito daga ďaki cikin shirinta na zuwa makaranta,, ta karbà takardan daga hannun Umma ta soma buďewa, tana cewa ku wlh wani lokacin Inna kaka ma tafiku lfiyar ido..
""Ganin abunda ke rubuce kan takardan ne yayi sanadiyar rufe mata baki, batasan lokacin da ta durkushe qasa a wajan ba,,"
cikin tsantsan farin ciki ta buďi bakin ta muryan ta na sarķewa a hankali ta furta ya salam Allah abun godiya, shikenan nakusa tashi daga suna Batula in koma Aunty Batula,,"
"Tana dariya takai dubanta zuwa ga Umma da hajiya zulai wanda suka zuba mata na mujiya baki sake tamkar kace mi, tace,,"
"Umma shikenan kema daga yanzu burinki babu yagama cika, sunanki ya tashi daga Umma ya koma grand mother bakin ki daga yanzu ya huta da surutu,,"
"Aunty zulai ke kuma kin koma grand small mother...
"Ke Batula bamuson shashencin banza da wofi kinji ko? cewar Umma zaki mana bayanin abunda idanunki sukagani ne, ko kuwa zaki tsaya yi mana sakarcin banza?,,"
""Kaiyya Umma ai bari kiji matar yaya ce ke ďauke da cikin wata ďaya, kinga kuwa ai babu zancen banza a nan..
""bata bare tagama rufe bakinta ba, ta warce takardan daga hannunta bayan ta miqe tsaye, cikin nuna tsantsan murna , bakinta ya kasa rufuwa dan tsaban farin cikin da takeji yana ziyartar cikin qatsan zuciyar ta, tace,,"
"Wacce ce aciki mai ďauke da cikin? Maraqishiya ce ko wa?,,"
"Umma ba ita bace, Humaira ce, bakiga Aisha Ali girema neba a rubuce ba?,,"
""Mtsee taja mugun dogon tsaki, nan take taji murnanta da farin cikin ta ya kuma ciki, batasan lokacin yasar da takardan dake hannunta a qasa ba,, bayan ta murkushe shi ta koma ta zauna,,"
"Tana faďin, zancen banza zancen wofi, wlh duk kin lalata min Annashuwar da nakeji ayau......
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:10] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*Page*
*38*
Dedicated to my
*AISHA GENTLE LADY*💃Ana mugun tare
"Zama shiwari ta gyara dakyau, a karo na biyu ta kuma kaiwan dubanta gareta, tace, meke faruwa ne, kin sakani a duhu sam ni bansan me kike nufi da haka ba, cikin waye kike iqirarin zaki zubar har kike irin wannan rantsuwar a kansa,?"
"Sauķe hannunta tayi daga tagumin da tayi gameda da sauķar nauyayan ajiyan zuciya, ta dawo da dubanta kan shiwari, damuwa qarara kwance bisa fuskanta, cikin iriyar murya, tace."
"Humaira" tana ďauke da ciki shiwari ya zanyi da raina, komai nawa rugujewa zaiyi."Ya salam shiwari tafaďa nan take ta zaro idanu waje tamkar wacce aka aiko mata da zancen muta, ta dafe kirji, bakinta yana ambaton salati, tace wanne ďan tashan ne yayi miki wannan mummunar zancen wanda ko daďin ji babu kodai mafarki kike.?"
"Da idanun na, da kunnuwa na, shiwari dani akaje asibiti, a gabana Nurse ta tabbatar mana da wannan zancen, yanzu haka, dalilin da yakawo ni gidan ki kenan, yanzu yakawo mata result ďin tabbatacin cikin ne ďauke da ita, inajin sa ya sanar da ita, wlh ba mafarki nake ba, ba kuma faďa min akayi ba, da idanuna wlh shiwari." cikin dashewar murya take maganar, gameda jinginar da kanta jikin kujeran da take zaune, tana fitar da numfashi."
"Wanda hakan ya sanya shiwari qara gyara zama, batare da ta qara wata maganar ba, har na tsawon wasu mintuna kaďan, kafin daga bisani, ta sauķar da ajiyan zuciya, a hankali cikin sassauta murya, tace, qawata matso kusa, inaso ki tattaro min da hankalin ki waje ďaya kiji abunda zan faďa miki."
"Inajinki shiwari, wlh na tattara miki hankali na, faďi inji ko wacce irin shawara ce zan ďauka idan har zai fitar dani daga cikin damuwar da nakeji yana cin cikin zuciya ta."
"To saurare ni kiji dakyau, shiwari tace da ita, a hankali zamu fara tafiya tamkar tafiyar maciji, har mu samu mu aiwatar da aikin mu." taci gaba da cewa, kamar yanda kike barazanar babu makawa sai kin zubar mata da ciki, to shawarar ta itace, ba'a yanzu zaki zubar dashi ba, idan har kinaso taji raďaďin zubewar cikin, to yazama dole ne mubata lokaci koda kuwa kaďan ne, dan yaron cikin nata yafara tsira, idan yaso kafin wannan lokakin kinga wannan saurayin naki da kika samo shi, sai ki nemo masa phone number ta na tabbata baki da ita, sauran abunda zai biyo baya kuma nasan kun gane ko me nake nufi basai nayi bayani ba."
"Ya salam shiwari" kin ceci rayuwata da faďawa mummunar hali, wlh ke abokiyar tafiya ce, tunda nake ban tabà irin wannan tunanin ba, nagane komai abunda kike nufi, shima nasan babu shakka ya tafi gana, yanzu ina komawa gida, zan san yanda zanyi in ďauki phone number ta, sai in tura masa, kinga shikenan farin cikin da narasa zai dawo gareni, in koma yanda nake a da, ya kake da suna tashi mutafi, bukata na tabiya, shiwari sai kinji ni, zan qiraki duk yanda akayi zakiji."
"Cike da wani irin farin ciki take maganar, tana washe haqora, tamkar wacce akayi mata kyautar wasu maqudan kuďi, jinta take kamar tayi tsuntsuwa a yanzu taga kanta a gida." tana gama gyaran mayafin dake kanta, ta zari jakanta, gameda yin hanyar fita, har zuwa lokacin bata daina dariya ba, ita kaďai tasan irin mugun farin cikin da takeji yana ziyartar cikin zuciyarta." A yayin da wannan saurayin ya miqe tsaye, cikin nuna rashin fahimtar abunda suke shirin aikatawa, yana kallon ko wanne su yafara magana, wanda hakan shi ya dakatar da ita daga fitan da zatayi, gameda da kawo duban ta zuwa gareshi, yace."
"Da farko dai kafin nafaďi abunda nakeso nace muku zan fara gaya muku koni waye, ni sunana zaid, ni haifaffan ďañ garin nan ne, dalilin da yasa na amince da maganar da kika kawo min shine, dan insamu hanyar da zan rama rashin mutuncin da ya rinyar nan ta min ne, saidai kuma wani abu guda ďaya da nakasa fahimta shine, wannan maganganun da kukeyi, idan kuma na fahimta, so kuke kuce min ya rinyar da kuke magana akai itace wacce nakeso, ma'ana tanada aure kenan har take ďauke da ciki,?"
"Zauna a wajan shanye tamkar kayan wanki, wacce kakeso tayi maka rashin mutunci, to da ita muke, itace ke ďauke da ciki, kuma sai na zubar dashi babu makawa."
" Tana nuna kanta da hannunta, taci gaba da cewa, Karkace, a banza da wofi nake wannan maganar, sam babu ko ďaya inada dalili, ni wannan da kake gani kishiyar tace, ina zaman zamana ni ďaya a gidana ta shigo ta aure min miji, kuma bazan tabà yin kaffara ba kamar yanda nake ni ďaya da mijina haka zata fita tabar min gida ni ďaya, ina fatan yanzu ka fahimci magana ta, kuma zaka bani goyon baya har nacima burira kaima kaci ma naka,?"
"Jin maganganun tane ya sanya shi saukar da ajiyan zuciya, yana mamaki, gameda yin wata iriyar murmushi, na wanda zai tabbatar maka da cewa shi cikekken ďan duniya ne, kafin yace, yanzu nagane komai idan hakane kuwa kun sameni a daidai." yana shirin fita daga parlon, ya qara cewa muje ki mayar dani inda kika ďauko ni, inada abunyi, kina komawa gida sai ki turo min phone number ta ďin, sauran kuma ni nasan abunda zanyi."
"Fita sukayi gabaki ďayan su daga parlonu suna qara tattaunawa, kafin sukai ga fita daga cikin gidan, mijin Shiwari ya turo ķofa ya shigo, ya tsaya yanabin ko wanne su da wani irin kallo, musamman zaid wanda yake neman hanyar fita Amman baiga hanya ba, wanda cikin rauwan jiki da tsoro duk ya gama cikata ta matso kusa dashi tana qiqiro murmushin dole, tace, dear sannu da zuwa ya kadawo da wuri haka bayan kace min sai dare zaka dawo,?"
"Dan nace miki sai dare zan dawo shine kika samu lasisin kawo min wannan qawar taki ko, banda hakama harda kawo min katon gardi cikin gida, yazo ya ďauke ku fice kenan, duk irin gargaďin da nake miki bakyaji sai kinci gaba ko,?" to shikenan kici gaba dayi ďin muna nan tare dake." bai tsaya ya saurareta ba ya wuce cikin gidan ransa a bàce, bayan yabisu da wani irin kallo."
"A sannan Maraqishiya ta matso kusa da ita, cikin damuwa da tsoro tace, shiwari meye haka nake gani, bake bace kikace min baya nan ba, ya akayi kuma na ganshi yanzu bayan kinsan bason ganin mu a tare yake ba,?" ai dama ba tafiya nace miki yayi ba, ya dai fita ne kawai, kuma saida ya tabbatar min da cewa sai dare zai dawo shiyasa, ni kaina banyi tsammanin zai dawo gida a yanzu ba."
"Himm shikenan nidai mun tafi sai anjima, idan munyi waya, tace da ita gameda ficewa daga gidan, zaid yana biye da ita sukayi sallama da shiwari kafin suka shige cikin motar sukabar gidan, ita kuma ta koma cikin gida, zuciyar ta yana dukan uku uku, tana fargaban yanda zata shiga ta tarar dashi, dan tasan babu makawa dole ne ya tuhumeta akan wannan saurayin da yagani, tunda dama kullum yana cikin mata ja mata kunne da irin yawon da suke ita da Maraqishiya."
"Koda suka kama hanya, saida ta jiye shi a unguwar da ta ďauke shi, kafin ta dawo gida wanda a wannan lokakin har yamma tayi rana tagama faďawa, ana neman magariba, bayan mai gadi ya buďe mata get ta shiga tayi parkin motar ta a parkin space, kafin ta fito daga cikin motar ta nufi ciki, zuciyar ta wasai batajin ko wanne irin damuwa."
"Tasa hannu ta tura ķofar parloun ta shiga, idanuwanta suka sauka a kansa zaune qasan filin parloun, yana cin abinci, Humaira na kusa dashi tana masa hira cikin kwanciyar hankali, ga dukkan alamu idan ka kalle su hakan zai tabbatar maka da cewa ta saukar dashi daga fishin da yake da ita."
"Wanda ganin su hakan da tayi a tare ba qaramin baķin ciki ya kuma shigar da ita ba, duk wani walwalan da take ciki ya gusar mata dashi." cikin haďe fuska, tayi hanyar dakinta zata shige batare da ta qara kai dubanta garesu ba, taji muryan sa ya tambaye ta, yace."
"Daga ina kike,?"
"Daga gidan shiwari, tabashi amsa a takaice, bayan ya maido da dubansa gareta ya qara cewa waye kika tambaya da zaki fita, banda hakama, ban hanaki wannan shegen fitan da kikeyi ba, kina nuna min ni ban isa dake ba kenan, duk lokacin da kike da ra'ayin fita zaki ďauki qafa kifita kai tsaye da yake zaman kanki kike ko,?"
"Jiyowa yayi da kansa ya ďibi abincin sa da yake ci zai kai bakinsa ya qara cewa, kije kici gaba da abunda kikeyi tunda hakan shine kikega yafi miki daidai a rayuwarki." yana gama faďin hakan yaci gaba da cin abincin sa, hankali kwance yana santi, a iyayin da itama batare da tace masa qala ba ta shige cikin dakinta tana zancen zuci ta faďa kan gado tana fitar da numfashi qasa qasa."
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:10] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*Page*
*40*
Dedicated to my
*AISHA GENTLE LADY* 💃
Sosai takejin zuciyar ta yana bugawa, cikin rawan jiki, taja a hankali ta koma kan kujera ta zauna, gameda zabga uban, tagumi, nan take abubuwan da yafaru tsakanin ta dashi yafara dawo mata cikin kwakwalwar ta." runtse idanunta tayi akaro na biyu ta kuma buďe su, tareda qara tunowa da munanan kalaman sa akanta tun farkon haďuwan su, mamakin ta ďaya shine a ina ya samu phone number ta,?" tambayar zuciyar ta take, waye ya samu har ya bashi phone number ta,?"
"Ganin irin yanda tabi ta ruďe, da alamu wata duniyar daban na tunani ta faďa, wanda har zuwa wannan lokakin wayar tana jefe a qasa, tun yana magana shi kaďai yaji shiru har yagaji ya tsinke wayar." A hankali yakai zuwa qasa yasa hannunsa ya ďauki wayar yana qarewa number kallo, kafin daga bisani ya ďago da idanunsa gameda kaiwan dubansa gareta, kafin yace, keda wayene, wa ya qiraki,?"
"Tsik taji zuciyar ta ya qara tsinkewa, wanda ganin irin kallon tuhumar da binta dashi ya qara haifar mata da wani faďiwar gaban, cikin rawan jiki ta sauķar da nauyayan ajiyan zuciya, ta qara runtse idanunta, tana shafan fuskan ta da tafin hannunta." sam ta rasa wanne amsar zata basa, batasan me zatace masa ba." cikin sanyin jiki, ta buďi bakin ta a hankali tace, bansan ko waye bane, halan haďin number yayi."
"Kamar ya zakice baki sani ba haďin number ne,?" cikin nuna rashin fahimta ya tambaye ta, wanda ya sanya ta qara faďin, wani ne nace maka bansan shiba."cikin rawan murya tayi maganar tamkar wacce batada gaskiya." tana faďin hakan ta miqe tsaye tasa hannunta ta ďauki wayar ta, wanda ya ajiye kusa dashi, ta haďa da plate ďin da yagama cin abincin, ta wuce zuwa kitchen kai tsaye, batare da ta tsaya sauraran me zai kuma cewa ba."
"Kujeran dake ajiye cikin kitchen ďin wanda yake a tanade domin zama, shi taja ta zauna, tare dayin wani tagumin, sam ji take duk jikinta yayi sanyi, tambayar ta a nan shine, meye wannan mutumin yake nufi da masoyin tane,?" bayan ita koda lokacin da ya tare ta a kan hanya, ba fuska tabashi ba, illah ma gargaďin da tayi masa na kada ya qara bi ta hanyar ta, to meye yake nema tattare da ita tunda ba soyayya suka tabà yi ba." can ta saukar da ajiyan zuciya, cikin ranta tana rokon Allah da ya mata tsari tsakanin ta dashi, dan batasan ya zatayi ba, idan yaci gaba da bibiyar ta, bayan kuma aure ne da ita a yanzu."
"Haka tayi zaman ta a kitchen ďin batare da ta koma wajan sa ba, har zuwa bayan wasu mintina kaďan, taji qaran motar sa an buďe masa get, hakan ya tabbatar mata da cewa ya fice daga gidan." dawowa tayi zuwa cikin parloun, ta haďu da Maraqishiya hannunta riqe da plate ďin indomie." cikin sakin fuska ta gashe ta, wanda ita kuma tamkar dole akasa ta amsa gaisuwar." bata qara ce mata komai ba ta wuce ta kammala kwashe sauran kayan abincin takai zuwa kitchen, kafin ta dawo ta wuce cikin ďakinta, gameda faďawa, kan gado, ita kaďai tasan me takeji, cikin ranta, tana sauķar da numfashi qasa qasa, tamkar wacce ta aikatu da wasu aiyyukan tayi luf a kan gadon."
******* *******
BAYAN WATA BIYU
"Wanda a zuwa wannan lokacin cikin dake jikinta ya shiga wata uku, yafara bayyana, hakam take kokarin juriyar wahalan da yake bata, ga yawan amai dake sata, mafi yawancin kwanaki cikin kasalanci take wuni, gashi babu abunda take marmari take sha'awa kamar taga tanashan farin qasa, akodayaushe, mafi yawancin ranaku batula ce ke hanyar zuwa mata ita take siyo mata farin qasan dayawa, sai ta boye shi tanasha a boye batare da tabari ya sani ba."
"Tunda haka wani lokacin yakan kamata tanasha, sam bayason ganinta tashan wannan farin qasan, Amman takasa hanuwa, da yake shi ranta keso, ji take yafi mata cin abinci sau dubu, Umma kam dama ko sau ďaya tunda taji batun cewa tana ďauke da ciki bata kuma zuwa gidan da sunan wata maganar auran suwaiba ba, ko wani tashin hankalin." Haka babu laifi cikin wata biyun da sukayi babu wata matsala tsakanin ta da Maraqishiya, idan sun haďu zasu gaisa, Amman ta daina mata tayin komai koda kuwa abinci ne ko shiga harkanta, dan ganin ba sake mata fuska take ba gashi mafi ya wancin kwanaki bata wuni a gida, kamar dama jira take, tana ganin fitan sa, itama zata zari mayafi ta fice a gidan, bazata dawo ba sai goshin magariba, wani lokacin ma idan ba ita bace da girki takan kaiwa har zuwa sha'i kafin ta dawo gida."
Hakan shine ya sanya ta kame kanta, sam batajin daďin zaman kaďaici, ita ďaya kullum tamkar mayya takeji, sai duk lokacin da batula tazo gidan, cikin nishaďi zata wuni idan ta tafi kuma shikenan sai ita ďaya, sai idan shi ya dawo daga wajan aiki takan qara samun sakewa." saidai wani tashin hankalin dake damunta a yanzu, wanda ko wahalan da cikin ta ke bata, bataji kamar sa, shine, har zuwa yanzu zaid bai daina qiranta a waya ba, kullum cikin qiran wayar ta yake, wani lokacin ta amsa, ta gaggaya masa ďacin maganganu, wanda yaci ace idan wani me zuciya ne ya rabu da ita, Amman shi kullum baya fasawa sai yaqira, wani abun bakin cikin dake qara damunta shine, mafi yawancin lokutan da yake qiran ta, suna tare da Abdulmalik, idan qaran wayar ta ishe sa, sai ya tambaye ta, wayene ke yawan qiranta, kuma meyasa bata ďauka,?"
"Hakan cikin dauriyar zuciya, zata qiqiro masa karya ta faďa masa dan su kwana lfy, dukda itama bason yin wannan karyan take ba, Amman gani take ya zame mata dole a yanzu dan batasan ko zai yarda da ita ba idan ta sanar dashi gaskiya."
"Haka yauma kamar koda yaushe, suna cikin ďakinsa suna hira, da yake kwananta ne yau, ta haďa masa Blacktea wanda yasha kayan kamshi na shayi, da basbusa a gefen, bayan tayi wankan ta, tare dayin shirin ta na kwanciya kafin ta shigo ďakin sa."
"Yana zaune bisa carpet a filin ďakin, ya jingina bayansa da jikin gadon, yana kaiwan shayin bakinsa, wanda ita kuma a wannan lokakin tana saman sa a kan gado ta kwanta luf tamkar wacce take bacci, jikinta duk babu karfi takeji sam, dakyar tayi girki yau, so take taga tayi baccin Amman fur yaqi zuwa mata, gashi shima sai jifanta da hira yake, hakan ya sanya ta ba yanda ta iya takan amsa masa ciki ciki, saikace dole aka sata."
"Phone ďinta wanda ke ajiye kusa da ita ne ya soma ringing." a hankali ta miqa hannu ta ďauki wayar, idanunta suka sauka mata kan wannan number, wanda hakan yayi sanadiyar canzawan fuskan ta." cikin bacin rai ta danna number busy, gameda mayar da wayan ta ajiye, tana fargaban, kada ya tambaye ta waye ya qirata, dama idan zata shigo ďakin sa, takan sa wayar a silent." sam ta mance yau bata wayar a silent ba." can ta leqe sa ta gefen ido, ganin shayin sa yake sha hankali kwance yana kaiwan basbusan bakinsa da alama baima kula da qaran wayar ba, hakan ya sanya ta sauķar da numfashi a hankali." kafin takai ga rufe idanuwan ta, taji wayar ta qara ďaukan ruri, wanda wannan lokakin kam saida ya jiyo gareta, gameda tsareta idanu, yace."
"Waye ne yauma yake qiran ki da wannan daren,?"
"Shiru tayi masa takasa basa amsa, tamkar tayi yaya, takeji, itakam harga Allah batasan wanne karyan zatayi masa yauba." cigaba da ringing wayar tayi, wanda hakan ya sanya shi ce mata ta amsa wayar, babu yanda ta iya, dan batada hujjar masa gardama, dan zai iya cewa batada gaskiya." cikin rawan jiki tasa hannu ta ďauki wayar, gameda da qarawa a kunnenta, tayi shitu, tamkar kurma." yana ci gaba da kallon yanayin ta yace, saka wayar a speaker, hakan da taji yafaďa ne ya qara haifar mata da wani faďiwar gaban." a hankali ta cire wayar daga kunnenta, gameda da sawa a speaker kamar yanda yace, wanda a wannan lokakin shi kuma cikin muryan sa yake faďin."
"Hello gimbiya sarautar mata bakyaji nane,?" meyasa kike danna min number busy idan na qiraki,?" wani lokacin kuma bakya amsawa sai kibar ni inata qiranki." shiru yayi can kaďan, kafin yaqa cewa, kiyi magana mana kinyi shiru, pls baby..... kit ya kashe wayar batare da yaci gaba da sauraran sa ba." cikin bàcin rai, ya cilla mata wayar a kan gado, yana dubanta yafara magana yace, wato shine ke miki waya a koda yaushe, idan na tambaye ki sai kice min bakisani ba dan baso kike insan abunda kikeyi ba, to nidai abunda nakeso kisan dashi shine, aure ne dake kuma ciki ne ďauke dake a yanzu, dan haka sai ki samu kisanar dashi, dan bani bukatan qara ganin qiran wayar sa a gida na musamman idan muna tare."yana kaiwa nan ya miqe tsaye, zuwa wajan ma kunnin wuta ya kashe, kafin ya dawo ya kwanta ďan nesa da ita gameda juya mata baya, yana zancan zuci, tambayar sa itace to waye shi wannan saurayin da har yakewa matar sa irin wannan maganganun kuma meye tsakanin sa da ita?."
"Wanda a zuwa lokacin ita kuwa inbanda bugun zuciya babu abunda take, har zuwa lokacin bata daina rawan jiki ba, tamkar tayi kuka takeji, cikin zuciyar ta sai tsine masa take, dama abunda take gudu kenan gashi saida yafaru mata yau."
"Jikinta na ďar ďar, ta tashi tsaye, ta kunna hasken wutar wayar ta kafin takai qasa a hankali ta ďauki kayan shayin da yagama sha, gameda ficewa daga dakin." yana jinta taja masa kofar baice mata qala ba." kai tsaye kitchen ta wuce ta ajiye kayan shayin, gameda da mayar da sauran basbusan da yarage cikin freezer, kafin ta kashe duk wutan kitchen ďin, ta dawo zuwa parlou ma ta kashe kafin." har zata shige cikin ďakin sa, sai kuma tafasa ta shige nata, ta samu bakin gado ta zauna, gameda da danna qiran number zaid ďin." yana fara ringing ya ďauka tamkar dama qiran wayar ta yake jira."
"Cikin iriyar muryan sa na yan duniya ya soma magana yace, baby how far, sai yanzu aka samu lokaci na kenan,?" dakata ta furta masa cikin ďagun murya da bàcin rai, tamkar a gaban yake, taci gaba da cewa, wlh wlh, kaji nayi maka rantsuwa da sunan Allah, billahillazi idan har baka fita a harkata ba, ka daina damuna a waya ba, to ina me tabbatar maka da cewa gamuwa ta dakai bazatayi maka kyau ba, dan bazan laminci wannan iskancin da rainin hankalin ba, ina cikin zamana lfy zaka jaza min bala'i da masifa, to wlh kada ka kuma qara qirana a waya, kaji nagaya maka, tun yanzu ka kama gaban ka kasan inda dare yayi maka."
"Batare da ta tsaya jin zancen da yake furtawa ba, ta kashe wayar, cikin bàcin rai zuciyar ta, naci gaba da bugawa har zuwa wannan lokakin....
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:10] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSATM*✍🏻
*Page*
*41*
Dedicated to my
*AISHA GENTLE LDY*💃
Tashi tsaye tayi daga zaunan da take gameda kaiwan idanunta kan agogon dake manne jikin bangon dakin, ya nuna mata har shaďaya ta zarta."cikin ranta take faďin, yanzu inbanda ďan iskan mutum yana neman hanyar raba mini aure ba, sai dare lokacin da duk yawancin mutane sun kwanta bacci, kafin zai qirani halan ya jaza min bala'i." qara sauke numfashi tayi a hankali tanaci gaba da neman tsarin Allah tsakanin ta dashi."
"Ficewa tayi daga ďakin bayan ta kashe wutan gameda rufe ķofar, ta nufi nasa ďakin, cikin ranta tana Allah Allah yasa bacci ya ďauke sa dan gudun kaga ya jero mata tambayoyin da batada amsar su a wannan lokakin."
"Bayan tashiga cikin ďakin, ta maida ķofar ta rufe, tare da kunna hasken wayar ta, ta qarasa zuwa gadon inda yake, yana nan kwance yanda ta barsa, bai canza ba, hakan tayi tsammanin yayi bacci." A hankali ta haura kan gadon ta kwanta gameda juya masa baya kamar yanda shima ya juya mata."idanunta a rufe, bayan ta karato addu'oin bacci, ta shiga zancen zucin da yakeson zama mata wajibi akoda yaushe idan tasamu nutsuwa."
"Inafatan dai kin sanar dashi abunda nafaďa miki,?" tamkar saukan aradu taji tambayar tasa ya doki dodon kunnenta, wanda hakan shi ya dakadar mata da zancen zucin da take, ta buďe idanunta a hankali ta jiyo da kanta garesa tana kallon bayan sa,kafin ta soma cewa."
"Nasanar dashi wlh batun yauba, tun sanda ya soma bibiyata na gargaďe sa da yarabu dani, ya daina qirana a waya, Amman hakan ya faskara kullum cikin qiran waya na yake bansan meye dalili ba." tamkar wacce takeson yin kuka take maganar, cikin qasa da murya taci gaba da cewa, dan Allah karka bari sheďan yayi tasiri a zuciyar ka, har kashiga zargina akan abunda ba hakaba, wlh babu komai tsakanina dashi, bansan shiba, pls karka zargeni..ya isa haka taji yafaďa cikin muryan sa batare da yabari taqarasa maganar da take ba, yaqa cewa, tambayar ki nayi, kuma kin bani amsa shikenan bana bukatar wani dogon bayani a yanzu, kiyi baccin ki kawai saida safe."
"Hakan da taji yafaďa ne ya sanya ta runtse idanunta, Kafin ta buďe, a hankali cikin sanyin jiki ta masa zuwa jikinsa tayi dafda dashi ta zagaye shi da hannunta tare da sakala kanta ta tsakanin wuyar." yana jin ta duk abunda take masa baice da ita qala ba, illah ma rufe idanunsa da yayi dan yin bacci."
"Haka tana manne dashi a jikinsa ta baya, har bacci yayi awun gaba da ita, wanda shima a wannan lokakin bacci ya ďauke sa."
"Koda asuba tayi bayan ya fita masallaci akayi sallah dashi, kafin ya dawo gida wanda itama a wannan lokakin har ta idar da nata sallan ta koma ta kwanta bayan tayi zikiri da addu'oin ta." shima komawa yayi ya kwanta, wani sabon baccin ya kuma daukar sa."
Wajan misalin karfe takwas saura ta buďe idanunta, gameda kai dubanta garesa, ganin baccin sa yake hankali kwance, yasa a hankali batare da yaji motsinta ba ta fice a ďakin zuwa nata, kai tsaye wanka tayi tare dayin brush, kafin ta fito, ta shirya cikin doguwar riga ta atumfa, wanda bazai takura mata ba, Amman ďinkin yayi ma jikinta kyau." bayan ta fesa turare ta shafa me, ta fito kai tsaye ta wuce kitchen, dan ďaura musu karin safe." kifi tarwaďa ta ďaura dafuwa haka rigijif, da soyayyan dankali, gefe kuda kuma blacktea ta ďaura da kuma shayi me madara shima daban wanda yasha kayan kamshi na shayi."
"Wajan misalin karfe tara ta kammala dafawa, ta juye ko wannen su cikin kula, kafin takawo ta jerasu kan dining table, tana gamawa ganin har zuwa wannan lokacin bai fito ba ya sanya ta, komawa ďakinta taqara watsa ruwa a jikinta, tasake wani sabon shirin tare da qara fesa turare masu daďi ajikinta, tayi kwalliya sama sama ba sosai ba, kafin ta fice daga ďakin ta nufi nasa."
"A hankalin ta tura ķofar ďakin ta shiga, taga baya nan." can taji motsin ruwa cikin toilet hakan ya tabbatar mata da cewa wanka yake." kafin ya fito tashiga gyaran dakin dukda ba wani datti bane dashi."
"Fai fito ba har tagama gyaran ďakin ta zauna a bakin gadon tana jiran fitowar sa," bayan wasu mintuna kaďan, ya fito daga toilet ďin ďaure da farin towel babba, tana kallon sa ta miqe tsaye daga zaunen da take, gameda qarasowa garesa, fuskan ta cikin murmushi ta gaishesa ya amsa mata batare da yaqara fadin komai ba, yaci gaba da goge ruwan dake jikinsa."
"Sam bataji daďin ganin irin yanda ya amsa mata gaisuwar, tamkar bayaso, hakan ya sanya jikinta yin sanyi, cikin ranta take faďin, yanzu shikenan abunda take guduwa ya afku mata, duk yanda zatayi ta sanar masa da gaskiyan ta ba yarda da ita."
"Cikin zuciyar ta sam babu daďi." batare da ta qara faďin masa komai ba, ta tsaya jiransa har ya kammala shiryawan sa cikin blue shadda kaftan, wanda yasha zubin farin zare." sosai yayi kyau cikin kayan."
"Fitowa sukayi daga cikin ďakin a tare zuwa dining table, yaja kujera ya zauna, itama taja wanda yake kusa dashi ta zauna bayan ta zuba masa a kan plate iya yanda zai iya ci, tare da zuba masa ido tana kallon sa yanda yake cikin abincin, cikin zuciyar ta kuwa tana haďe haďen yanda zata fahimtar dashi, dan yabar wannan fishin da yake da ta."
"A hankali ta saukar da numfashi tare da ďaukan cup guda biyu ta tsiyaya blacktea aciki ta ajiye masa ďaya kusa dashi, itama ta soman shan ďayan." jifa jifa take satan kallon sa ta gefen idanunta, har ya kammala da cin abincin sa ya miqe baiyi magana ba, ya ďauki wayar sa dake kusa dashi ya zura cikin aljihu, kafin ya ďauki hanyar fita, wanda ganin da gaske fitan zaiyi har zuwa lokacin bace mata qala ba, ya sanya ta, tashi da sauri daga zaunen da take, bayan ta ajiye cup ďin shayin dake hannunta ta, har ya isa bakin ķofar parloun zai fita, cikin ďaga kafa ta qaraso garesa, batare da yasani ba, tasa hannayen ta duk biyu ta rungume sa ta baya, wanda hakan yayi daidai da fitowar ta daga dakinta tana murzan fuska, idanunta karaf a kansu."
"Cikin bugun zuciya, taqara gyara tsayuwar ta gameda zuba musu idanu tana kallon su, tamkar yau ta soma ganin su, cikin ranta take faďin, wannan wani irin mutane ne, wanda duk wata hanyar da nabi dan inga sun samu tsabani a tsakanin su, abun faskara yake saikace aljanu..shiru tayi daga zancen da take, tare da kasa kunne dan jiyo abunda take faďa masa dukda tsakanin su da ita akwai ďan taku, ba lallai bane taji ba, saidai idan cikin ďagun murya suke maganar."
"A hankali tana manne dashi cikin sanyin murya ta soma magana tace, haba mijina wannan wani irin hali kakeson jefa ni, tunjiya nakasa gane kanka, pls dear ka yarda dani wlh bazan tabà cikin amanar kaba koda kuwa a mafarki ne, kane mijina me sona uban yara na, sonka da nake yarda dakai da nayi shi ya sanya ni zamtowa matar ka a yanzu, dan Allah karka bari sheďan ya sanya ka zargina a hanlin ba hakaba, pls mijina, tana qara tusa kanta jikin bayan sa take maganar a yayinda yasa hannunsa ya riqe nata tare da juyo da ita suna kallon juna......
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:10] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*Page*
*42*
Dedicated to my
*AISHA GENTLE LDY*💃
"Kayataccan murmushi kwance bisa fuskan sa, yanaci gaba da kallon ta, ya saki hannunta daga riqon da yayi mata, tare da tallafo nata fuskan, cikin qasa da murya ya soma cewa."
"Sam bana fushi dake Maman baby, waye yace miki zan tabà iyayin fushi dake, sam, ni mijinki bazanyi fishi dake ba, domin kina ķàrķàshin kulawa tane, ki daina tunanin haka kinji Maman baby."
"Babu shakka batayi tsammanin jin haka daga bakinsa ba matuka, a zaton ta zai ciga da canza mata, ya nuna rashin yardan sa da ita, shiyasa take ta sake saken ta yanda zata karbì kanta idan ya tunkare ta zancen." saukar da idanunta tayi daga kan nashi kafin ta buďi baki a hankali tamkar me shagwabà tace."
"Tunjiya rabona dakai mijina, ka shareni akan abu qalilan, kabarni na wayi gari da fargaba cikin zuciya ta, sam jikina banji daďin sa ba kaurace min da kayi sai yanzu da naga ka saurareni na samu sassauci cikin raina."
"Amman dai yanzu kin samu nutsuwar ko Maman baby,?" ya tambaye ta yana qara tallafan fuskan ta, tace Eh Amman ai da yanzu ban tsayar dakai nayi maka magana ba da tafiyar ka zakayi ka barni cikin tunani...shiiii yace da ita bayan ya ďaura yatsan sa ďaya akan labèn bakinta, yace."
"Ya isa haka wannan korafin komai ya wuce ai, dama gwada ki nayi ingani ko har in fita zaki bini kiyi min magana ko barina zakiyi in tafi cikin fushi, sai gashi naga ashe matar tawa ta damu dani bazata iya bari na cikin fishi har na tsawon lokaci ba." yana murmushi yake mata maganar, cikin sigar wasa takai masa duka kan ķirjin sa, ta qara faďin."
"To kaji ďaďi ai tunda yanzu ka gane gaskiya ni ďin meson farin cikin kane a koda yaushe."
"Nasani kuwa Maman baby kuma na qara tabbatawa a yanzu ke ďin daban ce." yana maganar yakai duban sa kan gogon dake maqale a hannunsa yaqara cewa, yanzu dai barni in tafi kar rana tayi sosai kinga har shaďaya ake nema, gwara in hanzarta ko,?"
"Hakane a dawo lfy baban baby." fuska ya canza jin irin sunan da ta qira sa dashi, cikin zolaya yace, wannan sunan fa daga ina yazo,?"
"Ramawa nayi tafaďa tana dariya, ya qara cewa, to canza min shi banaso."
"To me kakeso in qira ka dashi bayan ka kusa zama uaban yara."
"Yauwa anzo wajan, yace da ita yana yaqa dubanta, tace kamar ya anzo wajan me kaji,?'
"Abban yara zakina qira na nest time kinji,?"
"Haba dai kai kuwa Amman gaskiya ka zuzuta dayawa, kaida ko ďaya baka samu ba a halin yanzu kana ambaton dayawa." wayace miki,?" ya tambaye ta yana riqo hannunta cikin nashi ya qara cewa, nidai shi nakeso dan haka dole ayi abunda nakeso."
"To ba matsala yanzu dai a tafi sai an dawo, tafaďa tana murmushi bayan ta cire hannunta daga riqon da yayi mata kafin ya juya ta qara cewa, pls idan badamuwa inaso in koma makaranta kaga tuni an daďe da komawa ni kuma har yanzu shiru ban koma ba."
"Dubanta yayi da kyau cikin ido kafin yace zaki koma Amman ba yanzu ba sai bayan kin haufu, wanda wannan furicin da taji ya fito daga bakinsa ya sanya ta gwale idanu waje tamkar zasu faďo qasa, gameda dafe kirji, cikin rawan murya, zatayi magana ya dakatar da ita, yace bari sai na dawo zamuyi maganar yanzu rana tanayi."shiru tayi babu yanda ta iya haka ta rabu dashi badan ranta yaso ba, ya kai mata kiss a goshin ta gameda shafan cikin ta, kafin yayi mata bye bye ya juya ya fice haraban gidan." tana kallon sa jikinta babu kwari har ya shige motar sa me gadi ya buďe masa get ya fice."
"Ta ďauki tsawon mintuna a wajan tana jingine da jikin ķofar parloun, tunane tunane iri iri fal cikin ranta, fatan ta ďaya Allah yasa kar hanata komawa makarantar nan, dan batasan ya zatayi ba idan ya hanata saidai kuwa idan bijire masa zatayi, dukda tasan hakan ba me iyuwa bane."
"Ganin tsayuwar da tayi ba me amfani bane a gareta, hakan ya sanya ta juyawa zata koma ciki wanda a wannan lokakin itama cikin sauri dan gudun kar ta kalle ta su haďa ido har tayi tunanin wani abu." juyawan da zatayi batasani ba sai ji tayi goshin ta ya bugu da bangon ķofar ďakin, ba shiri ta ďan saki qara kaďan tasa hannunta duk biyu tana shafan wajan, wanda wannan qaran da tayi shi ya janyo da hankali humaira, cikin sauri ta qarasa zuwa gareta tana faďin sannu tasa hannunta biyu zata riqe ta, cikin takaici ta juyo da kanta tasa hannu ta mangaje ta, gameda da watsa mata magun harara, batare da tayi magana ba ta kaďa kai ta shige cikin ďakin ranta a bàce tana kunkuni ta zauna a bakin gado tana murzan goshin ta, sosai takejin wajan yana mata raďaďi."
"Cike da takaici taja mugun dogon tsaki, ta soma faďin, duk kasa kunnuwan da nayi dan inji me suke fadi banji ba illah ma jin ciwon da nayi, mtsee ta kuma jan wani tsakin a karo na biyu taci gaba da cewa, ga dukkan alamu matsalar zaid bayayin tasiri a tsakanin su, akan inga suna faďa saidai inga tsabanin haka, ohh rabbi ka dubeni, tafaďa tana riqe da wajan, cikin jin haushi ta mike ta isa gaban madubi gameda kurawa goshin nata ido sosai har ya soma tashi dan buguwan da tayi." zafin wajan takeji dan haka ta ďauki sabo rob ta shafa a wajan ta rufe ta mayar dashi kafin ta fice daga ďakin ta nufi kitchen ďin ta dan neman abinci, wanda ita kuma a wannan lokakin tuni ganin irin mangaje ta da tayi cikin bàcin rai tamkar itace sanadin buguwar da tayi, hakan ya sanya ta shigewa ďakin da bayan ta tattare wajan da yaci abincin ta wanke na wankewa."
**
Da rana wajan misalin karfe biyu lokacin duk ko wanne masallaci an idar da sallan azahar, ya dawo gida bayan mai gadi ya buďe masa get ya shiga, yana gama parkin motar, yaga babu motar Maraqishiya a wajan, ko ba'a faďa masa tabbas yasan fita tayi, tunda haka saida ya tambayi baba mai gadi yace masa ai yana fita itama bata jima ba ta fice daga gidan."
"Ransa a bàce ya nufi ciki, ya buďe ķofar parloun ya shiga, babu kowa, hakan yasa shi yin hanyar dakinta, yasa hannunsa ya tura ķofar idanunsa suka sauka a kanta tana kwance idanunta a rufe ga dukkan alamu bacci take, a hankali ya taka ya isa zuwa gareta, tare da zama a bakin gadon dafda ita, yasa tafin hannunsa yana shafan kanta zuwa fuskanta, ya soma faďin."
"Maman baby bacci kike ne haka pls tashi zamu fita, kodai bakyajin daďi ne,?" shi kaďai yake maganar yanaci gaba da shafan fuskanta yana mata yawo a hankali tamkar maciji, wanda hakan shi yayi sanadiyar buďe idanunta a hankali da yake baccin nata baiyi nauyi ba, tasa hannunta tana murzan idanunta."
"Ganin sa zaune kusa da ita yana sakar mata da murmushi ya sanya ta tashi zaune, bayan tayi hamma tare dayin salati tana miqa, takai idanunta garesa ta dubesa cikin qasa da murya tace ya kadawo da wuri haka, karfe biyu fa yanzu kodai mantuwa kayi,?"
"A a ba mantuwa nayi ba shiryawa zakiyi yanzu zamuje gida, shiyasa na dawo da wuri." yana maganar ne tare da miqewa tsaye, ya qara faďin pls shira da wuri kafin in watsa ruwa, yana gama faďin haka ya fice daga ďakin ya nufi nasa, wanda jin inda yace zasuje ya sanya ta mutuwar zaune, itakam harga Allah bason zuwa gidan nan takeba sam bata sakewa a koda yaushe idan sukaje, sai idan batula da inna suna nan takan samun sakewa, Amman babu yanda ta iya tunda shine ya umarce ta ba yin kanta ba, indai dan itane kam sai ta shekara bataje gidan ba saidai kuwa idan hakan zai zame mata abun magana ta gwammace akan taje gidan da aka tsaneta."
"Jiki a sanyaye ta miqe tsaye ta shige toilet ta wanke fuskan ta tare da yin brush kafin ta fito zuwa inda kayan sawanta suke ta zaro doguwar jan abaya, wanda aka masa ado da farin stone." tana tura baki ta canza kayan."
"Cif kayan ya zauna mata a jiki tayi kyau sosai cikin ta ya ďan fito ďan qarami dashi cikin abayan." bata tsaya yin kwalliya ba ta yafa gyalen abayan a kanta tasa kwalli kaďai da hoder tare da shafa turanen mai me kamshi, ta ďauki jakanta da wayar ta fice a ďakin gameda jan ķofar ta kulle."
"Ganin bai fito ba har ta gama shiryawa yasa ta zama a parlou, kafin ya fito ta ďauki wayar ta ta qira number wayar mummyn ta, yana fara ringing ta ďauka kamar dama jiran qiran nata take, cikin jin daďi suka shiga gaisawa tana dariya ita ďaya tace mummy wlh inayin kewar ku sosai kullum tamkar inyi tsuntsuwa in dawo gida nakeji mummy wlh ina missing ďinku." sosai ta nuna son zuwa ta kalle su, bayan sun gama hiran da zasuyi ta sanar da mummy kan cewa tanaso tazo ta koma makaranta tunda hutu ya qare bata koma ba har yanzu gashi suna cikin shekaran karshe." Mummy tace da ita bari idan Abban ta ya dawo zasuyi maganar idan yaso itama sai ta nemi izinin mijinta." jin abunda da mummyn tafaďa na cewa ta nemi izinin mijinta ya sata sanyin jiki dan zuciyar ta na bata cewa idan ba sune da kansu sukayi masa maganar ba, ba lallai bane ya amince dan zai iya cewa sai ta haifu ita kuwa a wannan lokakin babu amfanin komawar ta makaranta tunda lokaci ya kure."
"Bayan sun gama maganar da zasuyi tace ta gaishe mata da Abba da yaa mahmud dasu ya musty kafin ta qira su, sukayi sallama da mummyn ta kashe wayar tare da gyara zama tayi tagumi tana zancen zuci, wanda a wannan lokakin shima ya fito daga ďakin sa cikin wani sabon shiri, yayi mata magana da ta tashi su tafi, haka ta miqe suka fita haraban gidan bayan taja ķofar parloun ta kulle tunda ba kowa, ta shiga gaban motar kusa dashi, baba mai gadi ya buďe musu get suka fice."
"Yana cikin tukin motar ya ďauki wayar sa ya qiran number wayar Maraqishiya." saida ya kusa tsinkewa kafin ta ďauka, bai tsaya ya saurari me take faďi ba yace da ita."
"A takaice idan kin tashi daga yawon naki ki sameni a gidan su Umma." kitt ya kashe wayar ya ajiye ta gefen sa kusa dashi, cikin zuciyar sa yake cewa, nikam wannan wacce irin macece dani meson shegen yawon tsiya a koda yaushe idan garin Allah ya waye, bata iya zama cikin gidan ta tamkar mintsinin ta ake da allura zata kwashi kafa ta fice, Himm ya furta a hankali ya sauķar da ajiyan zuciya, wanda hakan ya sanya ta jiyo da kanta gareshi tana dubansa tace yadai dear lfy kuwa,?"
"Lfy lau nake maman baby, kawai dai ina ďan tunanin wani abu ne." bata kuma qara tambayar sa ba jin yace mata babu komai, Amman ga dukkan alamu yanda taga yanayin sa tasan da abunda yake sakawa cikin ransa."
"Jifa jifa suke ďan hira har suka isa gidan, yayi parking a waje batare da ya shigar da motar ba." bayan ya daidaita ta buďe nata ķofar ta fita, shima ya buďe nasa bayan ya kashe motar ya fita." yana tafe tana binsa a baya suka shige cikin gidan." tunda ta kalli haraban gidan yanda takalmomi suke baje bakin ķofar parloun ya tabbatar da mata cewan yau akwai mutane sosai." suna dafda shiga cikin parloun Amal ta fito da gudun ta ta faďa jikinsa cikin dariya take faďin, oyoyo my uncle."
"Oyoyo my dear how a u, yafaďa yana jan hancin ya ďaga ta sama, tace am 5n uncle dady na ya dawo yana ciki." haba dai to muje muga dadyn ki, to uncle yau ina aunty humaira bata biyo ka bane,?"
"Ta biyo ni tare mukazo da ita gata nan yafaďa yana juya bayansa yaga wayam babu kowa." cikin mamaki ya soma dube dube shidai yasan tare suka shigo da ita, to ina kuma tayi,?" ya duba gefen kwanan sa ďayan yaga bata nan, itama sai dube duben take tana faďin uncle kodai wayo kake min bakazo da ita ba,?"
"Haba dai nazo da ita wlh bàcewa tay... kafin ya idisa rufe baķin sa daga maganar da yake, ta bùllo ta ďaya kwanan tana dariya tace gani ba bàcewa nayi ba." cike da jin daďi ta sauka daga hannunsa, ta ďale jikinta tana dariya tace Aunty wlh na ďauka shine yake min wayo Ashema kece."
"Nice babynah tafaďa tana mata dariya suka bi bayansa zuwa cikin parloun, qasa qasa takebin yan parlon da kallo, jikinta a kame sam bataso zuwa gidan nan ba musamman da tasan akwai mutane haka har fiya da waďan da tasani da ko rashin lfyar karya ta kwanta dolen sa ya qyale ta, sam bason shiga cikin mutane irin haka takeba."
📚📚📚
[30/08, 18:11] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*Page*
*43*
Dedicated to my
*AISHA GENTLE LDY*💃
Zaman family gabaki ďayan su sukayi a cikin parloun kowa da kowa yana nan banda Abba da shi yake nasa bàngaran." Umma ce zaune saman kan kujera, sai najeeb ďanta na biyu wanda yake bin bayan Abdulmalik yana zaune shima kan kujeran da Umma take, qasan gefen sa kuwa matar sa ce zaliha mahaifiyar Amal, siyama qanwar su ta uku wanda daga najeeb sai ita sai batula ce auta."
"Latsan wayar ta take hankali kwance batasan ma hiran me suke ba da yake jiya dawowar ta daga makaranta tazo gida yin weekend, sam ji take sun isheta da surutun, dan bason irin hayaniya haka takeba, Inna da suwaiba da batula duk suma suna qasan filin parloun a zaune sai raha suke suna kwashewa da dariya cikin nishaďi."
"Cikin su Abdulmalik ya qarasa, fuskan sa cikin murmushin jin daďin ganin familyn sa haka cikin walwala." waje ya samu ya zauna kan kujeran da siyama take." kafin, ya shiga gaisawa dasu Umma."
"A hankali ta qarasa cikin su tana riqe da Amal a hannunta, ta samu ďan nesa dasu ta zauna." murya a sanyaye ta gaishe dasu, Zaliha tana murmushin yaķe ta amsa mata tare da zolayar ta, duk da tasan idan ta gaishe da Umma ba amsa mata zatayi ba illama ta rufe da faďan da babu gaira babu dalili, Amman hakan baisa ta qin gaisheta ba." cikin qasa da murya ta gaishe ta." babu laifi ta Amsa mata gaisuwar fuskan ta babu yabo babu fallasa." najeeb yace, sabuwar Amarya sannu da zuwa." yauwa tafaďa cikin jin kunya sam ta kasa sakewa a cikin su." cikin su Batula ta shigo da ita, sunayi tanajin su bata cewa komai illah himm idan sun ta bòta, wani abunda ke ďaure mata kai wanda ta kula dashi a yanzu tunda suka shigo cikin parloun, siyama ke jifanta da wani irin kallo wanda takasa gane wani irin kallo ne wannan, gashi ko sanda take gaishesu, kowa ya amsa Amman banda siyama, dan ko kallon kirki batayi mata ba bare harta gasheta."
"Sun jima suna zaune a parloun har zuwa lokacin sallan la'asar kafin duk suka tashi dan yin sallah."
"Qara fitowa parlon sukayi bayan sun idar da sallan banda humaira da tayi zaman ta cikin ďakin su Batula, tayi tagumi tana nazari cikin zuciyar ta." batula ce ta shigo cikin ďakin ta samu waje ta zauna kusa da ita gameda kai dubanta gareta tace, Aunty humaira lfy kike kuwa yau,?" naga duk kin canza kin kasa sakewa idan Umma ce ma ai ta sauko yanzu."
"Lfy lau wlh." tafaďa tana kallon ta ta qara cewa ina cikin matsala ne wlh batula, Amman karki damu lfy nake, saidai inaso pls zan baki kuďi ko mai gadi ki bawa ya siyo min sabon SIM na mtn."cikin kallon tuhuma batula tace, karna zuzuta tambayar tawa da sai ince meyasa kike neman sabon layi, but ba matsala inada ma sabo wanda ban soma amfani dashi ba, bari in baki shi ďin kawai basai kin siya ba." tana maganar ta miqe tsaye ta isa zuwa inda jakan ta ke rataye, ta ďauko mata sim ďin ta dawo."
"A nan ta canza layin tare da ďaukan duk numbers ďin da take bukata ta mayar dasu cikin sabon layin." cikin zuciyar ta tana qara tsine masa tare da qara neman tsarin Allah tsakanin ta dashi, dan a qalla yau tunda gari yawaye yaketa fafitikan qiran wayar ta, Amman taqi ďauka illama number busy da take danna masa, hakan baisa ya fasa qira ba, ko yanzu kafin ta canza sim ďin saida ya qirata ta kashe wayar."
"Bacci ne taji ya soma zuwa mata tana gyangyaďi, taja dogon hamma." ganin baccin takeson yi yasa batula tashi tsaye tayi mata nuni da ta hau gado ta kwanta, Amman fur taqi, hakan yasa ta rabu da ita, dan ta samu tayi baccin ta fice daga ďakin tare da ja mata ķofar**
🌾🍃🌾🍃🌾🍃🌾
Da yamma wajan karfe shida saura lokacin rana tafaďa ana neman magariba, wanda sai a wannan lokakin suka kammala da abunda zasuyi ita da shiwari." gyalan ta ta ďauka ta yafashi jikin wiyar ta, tare da ďaukan jakanta, shiwari ta rakota suka fito har zuwa inda tayi parking motar ta."
"Buďe motar tayi tasa kai ta shiga, tana riqe da habàr ta ta ďago da kanta, kamar me nazarin wani abu tace nikam shiwari sai yaushe kike ganin zamu zubar da wannan shegen cikin ne,?"
"Tana kaďa ķafa ďaya taci gaba da cewa, ķur'anin Allah kinji nayi miki rantsuwa shiwari wlh wannan cikin dake jikinta ba qaramin dungura na yake ba kullum akoda yashe idan idanuwa na sukayi tozali dashi rasa sukuni nake shiwari gaskiya ya isa haka wannan bada lokacin pls mu ďauki mataki ko a yanzu ma dan wannan ďan iskan zaid ďin kam babu wani abunda yake tsinanawa kullum manne suke tamkar cumgom babu wata matsala tsakanin su, dan haka dole ne in tashi tsaye....
"Ya isa haka." shiwari ta dakatar da ita daga maganar da take ganin yanda ta zage, tace kiyi haquri qawata kwantar da hankalin lokaci yayi da zamu aiwatar da duk wani shiri namu, yanzu dai abunda nakeso dake, gida zaki koma, gobe ko jibi duk sanda kikaga ba wata matsala shima kince kinji yana cewa zaiyi tafiya to kinga kuwa faďiwa tazo mana daidai da zama, ina jiran call ďinki da shirina zan taho."
"Tana daban kafaďarta ta qara cewa, qawata ina me tabbatar miki da cewa a wannan ranar a gadon asibiti zata kwana, kedai sai naji call ďinki."
"Ya Allah tafaďa cikin dariya tace kai qawata Allah yabar mu tare wlh bazan bòye miki ba ke ďin abokiyar tafiya ce kece hasken rayuwa ta, sai kinji call ďina tafaďa gameda rufe ķofar motar, tayi sallama da ita, tasawa motar kay kafin ta soma tafiya shiwari tana dariya cikin zolaya tace da ita, yanzu daga nan sai gidan nasu kenan ko,?"
"Wa ni,?" tafaďa cikin buďe ido tace ai wlh haram kiga ķafa ta a gidan su, kingan ni nan ina barin nan wlh gida zan wuce kai tsaye, saidai idan ya dawo mu kwashe dashi Amman wlh bazani ba, nifa harga Allah shiwari bazan bòye miki ba yasin bason familyn sa nakeba sam wlh tamkar in gama dasu a lokaki ďaya nakeji idan da hali musamman wannan fitinanniyar mahaifiyar tasa wlh kullum shiga min hanci da kudindini take, billahillazi da wannan shegiyar yarinyar nan da ita da ďan da yaron dake cikin ta sunyi min qameqame a gabana ba, shiwari wlh da ita zan soma kawar wa, dan bazan.... ke ya isa mana haka da'ala uwar surutu."
"Shiwari tace da ita, daga tambaya shikenan sai kiyi ta zuzutawa kamar parrot babu ko stop."
"Tana dariya tace ai bari qawata wlh a wiya na suke gabaki ďayan su duk sun hanani fitar da numfashi shiyasa, kedai bari in tafi sai kinji ni." to tafaďa kafin tayi mata sallama ta ja motar tabar gidan, itama shiwari ta koma ciki, tana barka da har yanzu mijinta bai dawo ya gansu a tare ba har ta tafi."
_Dan Allah kuyi min haquri da wannan kaďan ďin, wlh aiki ne yamin yawa, sam yau yini nayi inata aiki kamar inji babu stop pls a lallama da wannan, naso nayi dayawa Amman ba kanta_ 🙏🏿
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:11] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*✍🏻
*Page*
*44*
Dedicated to my
*AISHA GENTLE LDY*💃
*ZUWA GAREKI QAWATA AMINIYATA, TA ASALI, AISHA IBRAHIM GENTLE LADY, MARUBUCIYAR SO KO ZURFIN CIKI DA LITTAFIN WIYA BATA KISA (SAI KWANA TAQARE) AKODA YAUSHE INA ALFARI DAKE, KE ĎIN DABAN KIKE AGARENI MUTUMIYATA INA SO KISAN CEWA WANNAN LITTAFIN RAYUWAR AURENA DUNGURUGUN NAKINE MALLAKAN KINE KEĎA YABA TAREDA WANI BA, INA FARIN CIKIN SADAUKAR MIN DA LITTAFIN SO KO ZURFIN CIKI DA KIKAYI, THANK U MY DEAR ALLAH YABAR ZAMAN TARE DA AMANA, IYA WIYA ANA MUGUN TARE AISHU NA, KINA HASKAWA AKO DA YAUSHE LITTAFEN KI AKWAI FAĎAKAR WA*😘
Baccin ta take sosai me nisa hankalin ta kwance bata farka ba har aka qira sallan magariba aka idar tana bacci, tamkar wacce ake binta bashin bacci." batula ce ta turo ķofar ďakin ta shigo dan duba ko lfy take haka har zuwa yanzu bata fito ba gashi duk kowa yayi sallah an zuba abincin za'a aci kowa yana wajan banda ita."
"A hankali ta qarasa shiga cikin ďakin, tare da zama a gabanta tasa hannu a kafaďar ta kafin ta soma tashin ta a hankali tana qiran sunan ta." kamar a mafarki taji ana qiran sunan ta, cikin magagin bacci ta buďe idanunta ya sauka kan fuska batula, ganin itace ke tashin ta ya sanya ta tashi zaune tana hamma tayi miqa tare dayin salati." tana sakar mata da murmushi tace Aunty tashi kiyi sallah lokaci tayi idan kin idar sai ki same mu a parlou zamuci abincin ke ake tambaya, kinata bacci tun ďazu."
"Batayi magana ba illah kai kawai da ta gyaďa mata alaman to, ta miqe tsaye ta shige cikin toilet ďin su dake cikin dakin, batula kuma ta fice ta dawo parlou inda suke har sun soma cin abincin, Abdulmalik ya tambaye ta yace ina humaira har yanzu baccin take,?" A a tabasa amsa da cewa yanzu na tasheta, tayi sallah zata fito idan ta idar." bai kuma faďin komai ba yaci gaba da cin abincin sa, najeeb dake gefen sa yana kaiwan loman abinci bakinsa, bayan ya gama haďiyewa yace, nikam meke damun Amaryar tamu ne haka, naga tunda kukazo bata cikin kuzari saima bacci da tafaďa yi, ina fatan dai lfy take,?" ya qarashe maganar yana duban Abdulmalik wanda ya miqa hankalin sa ga abincin da yakeci."
"Zaiyi magana batula ta tari baķin sa da cewa, yaa najeeb kana ina muka samu wannan babban rabon baka saniba, na ďauka ma wlh dan tsaban farin ciki shine zai soma baka lbr ashe ba hakaba da alama nice me rabo." tana dariya tare da gyara zama ta qara cewa, yanzu dai Allah yasa nice zanyi maka albishir dan haka yarjejeniya zamuyi, idan nafaďa maka to tabbas ba makawa zaka cika min alqawarin da kayi min na sabon waya, basai har nagama school ba, ka amince da haka,?" tana kallon sa tayi masa tambayar, wanda shi kuma hakan da yaji tana faďa ya sanya shi dawo da hankalin sa gareta da yake ya kammala da cin nashi abincin ya kawar da plate ďin gefe kafin yace."
"Naji na yarda saidai kuma kiyi sauri ki sanar dani, tun kafin in gane da kaina, dan idan na canki albishir ďin da kaina, shikenan kinga kinyi asaran sabon waya, Ina ai baza'ayi hakaba, tafaďa tana ci gaba da dariya tace to bari kaji amaryar yaya dai aunty humaira ciki ne ďauke da ita, aqalla yau wata uku kenan muke ciki..
"Zataci gaba da magana ya katseta da cewa, tsaya batula daga nan ya isa haka, bama irin wannan wasan dake, kifaďa min gaskiya, wlh tallahi yaa najeeb kasan dai baka bina bashin rantsuwa wlh ciki ne ďauke da ita, kuma idan ma yarda ne bakayi ba ga yaya nan ka tambaye shi, zakaji daga bakinsa ko su Umma zaka iya tambaya duk zasu faďa maka." bai kuma bi ta kanta ba ya kai dubansa ga Umma gameda tambayar ta ko maganar ta gaskiya ne," banza tayi masa tamkar wacce ba da ita yakeba illahma kawar dakan ta gafe da tayi."ganin taqi kula sa saikace batasan me suke magana akai ba, hakan yasa ya rabu da ita yadawo da duban sa ga Abdulmalik wanda yaja gefe daga wajan abincin da yake shima ya kammala da cin abincin yace, Abdullah dan Allah wai haka zancen yake,?"." kai ya gyaďa masa alaman eh hakane batare da ya kalle sa ba."
"Wanda tabbatar masa da hakan da yayi ba qaramin farin ciki ya jefasa ba marar misaltuwa matuka ya taya yayan sa murna, sosai yake godewa Allah, cikin nuna farin cikin sa qarara ya matsa kusa da Umma yasa hannayensa ya yakamo nata hannun cikin nasa, yace Umma yanzu dama wannan albishir ďin ne kika qi sanar dani ina tambayar kima kika min shiru Umma abunda kikeso kike burin gani jikan ki daga gurin ďanki abunda muka jima muna tsimaye..
"Zai qara wata maganar ta dakatar dashi tare da ďaga masa ďayan hannun ta." cikin haďa fuska tamkar bakin hadari ta soma cewa, kaga kayi min shiru banason jin wata zancen banza daga cikin bakin ka, tunda ni ban sanar maka ba ai ita waccan mai shegen bakin akun ta faďa maka, kuma kaji gaskiyar magana daga bakinsa, to me kuma kakeson ji daga gareni wanda ya wuce wannan,?" tsare shi da idanu tayi tana masa wani irin kallon da yakasa ganewa, hakan ya sanya shi sauke nashi idanun daga gareta gameda sakin hannunta da ya riqe cikin nashi, yaja ya koma inda yake ya zauna."
"Cike da takaicin ganin yanda Umma takeyi a duk lokacin da aka qira sunan abu da Humaira ta rasa miye dalilin ta na tsanar yar mutane har haka , itakam harga Allah bataga illan yarinyar nan ba."bazata iyayin haqurin shiru ba sai tayi magana." tana kallon gafe guda ta buďi baki tace, gaskiya Umma abunda kikeyi akan humaira sam babu kyau wlh ki gyara Allah zai iya tambayar ki dalilin wannan tsanar da kikayi mata da babu gaira babu dalili..ingo naqi tayi mata dakuwa da hannu batare da tabari ta qarasa maganar da take ba tace wlh idan baki fita a idanuna na rufe ba batula zan iya ci miki zarafi kinji ko, banison shashencin banza, yarinya sai shegen tsaurin idon tsiya, ina magana kina tareni da zamcen banza."
"Cikin nuna bacin ranta take mata faďan, ta dawo da kallon ta garesu tare da qara haďe fuska tace, kunga wannan shegen zaman banzan da kukayi min a gabana ya isheni haka duk ku kwashe matan ku, ku barmin gida na, nagaji." Umma me yayi zafi haka zakiyi mana kora da hali,?" cewar najeeb dake mata kallon mamaki yana riqe da baki, tace kadai ji abunda nafaďa kai ba kurma bane dan haka zaka tashin ko zaka tsaya yi min tsaurin ido, kai gaka me bakin magana, to tashi kubar min gida saida safe." zai kuma yin wata maganar Zaliha tayi saurin dakatar dashi tana girgiza masa kai alaman yayi shiru kawai, tasa hannu ta ďauki jakanta da gyalenta tare da riqo hannun Amal dake gefen ta tayi kicinkicin da fuska jin ana maganar Auntyn ta." tana dubanta tare da murmushi bayan sun miqe tsaye tace, Umma sai da safe bari mutafi, sam ita hakan beci mata rai ba dan a iya zuwa yanzu kam tagane ta ko wannan koran da tayi musu tayi ne dan humaira tabar gidan Amman badan harda su ba."
"Tashi najeeb ďin yayi shima beko ce mata qala ba ganin sai qara haďe rai take ita ďaya, yayi ma Abdulmalik magana dasu tafi wanda shi tuni dama jin inda maganar ya dosa, ya miqe tsaye yana gyaran a gogon hannunsa, ya ďago da kansa ya dubi batula da ta qira masa humaira su tafi..kafin ya idisa rufe baķin sa ta buďe ķofar dakin ta fito kanta a qasa ko gigin ďaga kai ta kalli inda Umman take batayi ba, dama tana idar da sallah bayan tayi azikar ta tashi taje gaban madubi ta nannaďe kanta da gyalan abayanta kafin tazo zata fito zuwa parloun inda suke, harta fara buďe ķofar ďakin zata fita, kunnuwan ta ya jiyo mata zancen da suke, hakan ya sanya ta tsayawa a bakin ķofar ďakin tana sauraran su har zuwa yanzu da taji yace a qira ta, ta fito dan itama Allah Allah take taga sun tafi sunbar gidan, tamkar akan qaya take haka takeji."
"Inna dai rasa abun faďa tayi sai Allah ya wadarai take cikin zuciyar ta da masu hali irin na Umma saikace ita ba zaman auren takeba bayan ita ba'a gillaza mata ba Amman ita tana gillazawa matan yaranta." tashi tayi dan tayi musu rakiya da yake duk sun kammala da cin abincin, suwaiba dake zama kusa da itama ta miqe tana Ala ture qeya dan ba qaramin farin ciki takeji ba a duk lokacin da taga yanda Umma take nuna tsantsan tsanar ta ga humaira." siyama dai nata kallo ne tana jinsu duk irin maganganun da suke bata tanka musu ba, Amman dai harga Allah cikin ranta tayi ma yayan ta murnan cikin da matar sa tasamu saidai fa tafison ace Maraqishiya ce keda wannan cikin."
"Tamkar yaran kaji haka Umma tasaka su agaba tana biye dasu abaya dan musu rakiya itadai so take taga tafiyar su dan sun isheta." A hankali take tafiya tana takawa kafar yana harďe mata, jikinta duk a kame tamkar tayi tsuntsuwa ta riga duk kanin su fiewa daga gidan takeji, da yake duk suna gabanta itace karshe Umma tana bin bayanta sai takeji kamar zatayi mata wani abun."
"Ya nayin yanda take tafiyar ķafar ta na harďewa, tazo daidai dakalin dake ķofar parloun, ta sakala ďayan ķafar ta waje, zata daga ďayan bata ankara ba Ashe ta take qasan Abayan da ďayan ķafar nata da yake yanada tsayi ďinkin nasa har qasa yake."ďagawan da zatayi tsantsin sa ya kwasheta, zuwa baya zata faďi, Umma dake tafe a bayanta tasa hannayenta duk biyu ta tareta tana salati, cikin faďiwar gaba tasaki yar qara wanda ya janyo da hankalin su zuwa gareta duk sun tsorata da sauri suka dawo baya zuwa inda take, idanunta a rumtse a zaton ta barinta zatayi ta faďi ďan tasan tana bayanta sai kuma taga tsabanin haka, a hankali ta buďe idanunta, sukayi tozali da nata cikin qara haďe fuska, ta buďi baki tace, yar bakin cikin tsiya wlh sai in iya sakin ki ki qarasa faďiwa kiji ciwo, sa'ar ki ďaya idan nabari kika qarasa faďiwa nice da asara, kinga saura miki watanni kaďan lokacin ki yayi kina haifo min da jikana dake maqale a mahaifar ki, to ba faďiwa a nan ba kinsan nisan da rijiya yake dashi ko, idan kin samu wanda yafisa zurfi ko ruwan maliya zaki iya fadawa ciki ki nitse babu ruwana, ya rage naki bani bace da asara, tashi min a jikina, tafaďa tana mata mugun kallo, cikin rawan jiki, ta soma zarewa daga riqon da tayi mata, Abdulmalik wanda ya qaraso gareta yasa hannunsa ya riqe nata tare da taimaka mata ta miqe tsaye, batare da ya kalli Umman ba yaja ta suka soma tafiya, sam beji daďin irin maganganun dake fita daga bakinta akan matar sa wacce ta zama itace uwar yaransa."
"Bàngaran Abba ya wuce da ita a nan cikin parloun sa suka tarar dashi yana cin abinci tv yana aiki." cikin girmamawa suka gaishe dashi ya amsa masu yana murnan ganin su tareda saka musu albarka yana musu fatan alkhairi, da fatan Allah ya sauketa lfy da yake shima yaji batun cikin da take ďauke dashi dan aranar da yazo yasanar dasu, yana dawowa gida batula dama tana jiran dawowar sa, cikin zumuďi tayi masa albishir ďin, yaji daďi kwarai da gaske kuma ya nuna farin cikin sa a fili, sosai yayiwa Allah godiya da wannan kyautar da yayi musu."
"Bayan sun gama gaishesa, sukayi masa sallama suka fito haraban gidan a nan suka tarar dasu najeeb ďin wanda yake cikin motar sa zaliha tana gefensa agaba sai Amal dake kujeran bayan motar ta sakalo da kanta tsakanin nasu kujerun tana musu surutu." cikin ďaga murya tana dariya tace Aunty bye bye saida safe gobe Abba na yace zai kawoni gidanki har mu kwana, pls kiyi min abu masu daďi kinji Aunty,?" To Amal naji zanyi miki duk abunda kikeso, sai kinzo gobe ďin."murmushi kwance a fuskan ta take mata maganar, kafin sukayi sallama, batula da inna na biye dasu, suka fice waje zuwa inda yayi parking motar bayan an buďe get najeeb ya fita da nashi motar, yana ďaga musu hannu."
"Saida safe batula da inna sukayi musu." suna nan tsaye har ya tashar da motar sukabar unguwar, kafin suma suka koma cikin gida, Umma kam dama tuni ta shige ďakinta ita da siyama sai suwaiba suka tarar a parloun ta kurawa tv idanu tana kallo tamkar wacce yau ne ta soma sanin TV a duniya."
"cikin daki inna ta wuce kai tsaye, Batula kuma ta tsaya a kan suwaiba tana mata kallon raini, cikin haďe fuska tayi mata magana da ta tashi su tattare wajan da akaci abincin tunda idan ba gaya mata akayi ba batasan abunda ya dace ba, dole ta miqe suka shiga kwashe kayan abincin, tanajin haushin ta katse mata kallon TV da takeyi."
Koda suka isa gida, bayan mai gadi ya buďe masa get ya shiga, yasamu wajan da yake parking, ya daidaita kan motar, kafin ta buďe nata gefen ta fita, shima ya buďe nasa ya fice bayan ya kashe motar." A tare suka jera zuwa ciki, wanda idanun su yaci karo da Maraqishiya tsaye bakin ķofar shiga parloun, ganin shigowar motar su ya sanya ta tashi tsaye tana safa da marwa sai cije labèn bakinta take." ko kallon inda take baiyi ba tamkar baima san akwai mutum a wajan ba, humaira tasa hannu cikin jakanta ta zaro makullin ķofar ta buďe."shi yafara shiga ita kuma tana biye dashi a baya, tanajin abunda take cewa, Amman bata tanka mata ba tayi shigewar ta ďaki kai tsaye dan tasamu tayi wanka ko zataji sanyi cikin jikinta."
"Kitchen maraqishiya ta shige dan neman abincin da zataci yanda taji cikinta na mata kukan yunwa ya zame mata dole ko indomie ma ta dafa, cikin ranta tana danasin dawowa gida da wuri da tayi da tasani tayi zamanta a gidan shiwari taci abincin ta a can idan yaso bayan tayi sallan isha'i ta dawo gida tunda suma gashi sai yanzu suka dawo, kuma sun kulle mata ķofar sun tafi da kay tuntuni tana zaman jiran dawowar su a waje tamkar wata almajira mai yin bara."
Wajan misalin karfe goma na dare ta shigo ďakin sa, bayan tayi wankan ta tare da yin sallan isha'i." cikin shirin ta na kayan bacci, hannunta riqe da tray na shayi da samosa a gefen sa, yana zaune bakin gado yana dube duben wasu takardu, ta qarasa zuwa garesa, cikin murmushi ta ajiye tray a gabansa kafin ta zauna kusa dashi, tayi masa sannu da aiki." yanaci gaba da dube duben sa, ya amsa mata da yauwa yana faďin har kin gama kin shigo,?" Eh tace dashi tana kallon sa ya qara cewa, ina fatan dai kinci abinci da muka dawo,?"
"Shiru tayi masa batace komai ba, kamar bataji me yace mata ba." jin shirun da tayi masa hakan ya tabbatar masa da cewan bataci ba kenan, kuma dole ne taji yunwa dan yasan koda suke gidan Umma an kawo abinci kowa yanaci Amman banda ita da ko fitowa a dakin batayi ba. "
"Dakatawa yayi da abunda yake yadawo da duban sa gareta, cikin kallon tuhuma, yace meyasa da munaci a gida baki fito munci ba, kuma meyasa da kikadawo bazaki dafa koda indomie ne kici ba, bayan kinsan yanzu bake kadai bace,?"
"Zanci ai tafaďa tana kallon qasa ta qara cewa, wlh miyar kuka ke raina kuma gashi dare yayi ni kuma gaskiya harga Allah bazan iya girkawa a yanzu ba shiyasa na haqura ko zuwa gobe nadafa inci idan kafin nan bai fita a raina ba, idan yaso yanzu zanci samosa da blacktea ya isheni."
"Aiyya Maman baby kenan, yace yana dariya ya qara cewa gashi kuwa tuwo da miyar kukan mukaci, da kinfito munci tare kinga da kin mayar da marmarin ki."
"Yo ai ni banacin tuwo da miyar kuka sai da couse couse nakeci...
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:11] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSATM*
*Page*
*45*
Dedicated to my
*AISHA GENTLE LADY*💃🏻
Ya mutsa fuska yayi tare da tsuke baki alamun jin irin kalar abincin yayi masa jagwalgwalo, yana kallon ta yace tayaya zaki iya cin miyar kuka da cous couse ana zaman lfy,?" zan iya ci mana, tafaďa tana dariya, taci gaba da cewa, kaga nifa ko a gidan mu bamusan cin wani tuwo da miyar kuka ba saida cous couse kasamu ka haďa shi da gashashshen kifi karfasa da man shano, duk family mu hakane, musamman Abban shi kam bashida wani abinci wanda ya wuce wannan, indai har kanaso kaga yaci wani kalan abinci, to kada ka tambaye sa me zaka dafa masa, dan idan ka kuskura ka tambaye sa wanne irin abinci zaici, to miyar kuka da cous couse zaice maka kullum baya gajiya da ci, so all gidan mu gaskiya munaso..
"Sai yayana mahmud shine kaďai daban a cikin mu wanda bayaci a duk lokacin da yadawo gida daga wajan aiki yaga nadafa wannan abincin, to a ranar babu makawa akaina zai sauke duk wata bala'in shi da masifar sa sai idan Abba yana nan yake raga min, har gargaďi yake min cewa wai idan har nasan wannan shegen abincin zan dafa to in tabbata nayi masa wani abincin daban Amman ba wannan ba."
"Tana haďe fuska ta qara cewa, kaji fa dan Allah saikace wani ubana ko yasamu wata yar aikin sa harda jera min qa'ida."
"Sosai maganar nata yabashi dariya, yana dariyar yace to ai idan ba uban ki bane kinsan dai cewa is ur brother yanada right a akan, dan haka ko nima ina bayan sa wlh inaji ina gani bazan zauna inci wannan jagwalgwalon abincin naku ba."
"Ci gaba da duba takardun sa yayi bayan ya ajiye cup ďin shayin dake hannunsa, ya qara cewa, kinga malama nifa wannan surutun naki ya isheni haka inada aiki agaba na dayawa, daga tambaya shikenan sai kikafaďa zuba min lbr saikace BBC hausa, babu ko full stop."
"Haďe fuska tayi jin abunda yafaďa kamar yar yarinya ta cura masa baki kafin tace, au hakama zakace ko, to shikenan ai gashi kayi ma kanka buqulu dama gobe nake da niyar dafawa in haďa shi da kifi na da man shano." tsuke bakin ta taqarayi tareda haďiyan yawu, kafin tace, kaga kuwa inaci kana kallo na ko tayi bazanyi maka ba kwalelen ka."
"Ai baki isa ba, yace da ita yana murmushi ya qara cewa kinsan idan nayi niyyan ci inaso basai kinyi min tayi ba zanci, Amman dole kiyi wannan kifin da rabona, kin ma tuna min insha Allahu gobe zan tafi abuja akwai aikin da zanje inyi, bazan wuce sati ďaya ba, pls sai ki kula da kanki banda fita, nasan ma ba fita kikeba but ki kiyaye."
"Zan kiyaye tafaďa tana kallon sa, cikin qara qasa da murya tace pls mutafi tare mana, inaso in koma school ďin nan zaman gidan da nake ya isa haka, , dan Allah karkace a a idan mukaje abujan ko Abba zai shirya min komi wlh ga Ameena qawata tare muke zata kula dani pls."
"Zaki tafi Maman baby Amman ki qara haquri idan nadawo da kaina zan shirya miki komi sai kitafi, idan yasoma in rakaki da kaina muje tare kinsan yanzu a qarqashin kulawa ta kike dole nine wanda zan biya kitafi ba Abban ki ba."
"Runtse idanunta tayi, tanajin wani irin zugi cikin zuciyar ta, sam bataji daďin maganar tasa ba na cewa bazai tafi da ita ba, a halin shi da kansa yasan yakamata ace ta koma makaranta yanzu, Amman yana mata waine waine, akan tana ďauke da ciki saikace akansa aka soma ďaukan ciki, dalilin da yasa bataso ace ta ďauki ciki a yanzu ba har sai bayan ta kammala karatun ta, kash tafaďa cikin ranta shiyasa batayi murnan sa ba a lokacin da taji wannan lbrn cikin, dukda kyauta ce ta ubangiji bataqi sa ba..
"Wasu ma neman sa suke idanu rufe tamkar makafai akan haifuwa, saidai kuma Allah nabayar wa wanda yaso ne a lokacin da yaso, Amman gashi abunda take guduwa ya afku mata da alama dole ta tashi tsaye idan ba hakaba akan wannan cikin da yake masa kallon babu kamar sa a yanzu zai iya jenyo mata asara tayi biyu babu, domin idan kulawa ne sai tasamu fiya da wanda yanzu take samu daga garesa."
"Sauķe idanunta qasa tayi daga garesa, ta kawar dakan ta gefe, tanajin yanda zuciyar ta ke mata zugi kamar zatayi kuka takeji, cikin rashin kuzari ta miqe jiki a sanyaye, batare da takai dubanta garesa ba, ta soma cewa, shikenan bakomi na haqura da zancen nabari daman nasan dole za'a rina insha Allahu ni kuwa daga yanzu nidai abakina bazakaji nayi maka zancen komawa ta ba, duk lokacin da katashi kayi niyar bani izini a shirye nake, saidai inason kasan cewa... shiru tayi tareda rufe idanunta ta buďe su, wanda har zuwa lokacin nasa idanun yana kanta.," qasa qasa take sauķe numfashi tamkar wacce batada lfy, ita kanta tasan tunda sukayi aure bata tabà ďaga muryan ta akansa tayi masa magana ba sai yau, tanaso taci gaba da maganar dan suna nan maqale cikin ranta, Amman ganin yanda ya kura mata idanunsa yana kallon ta tamkar yaune ya soma ganinta babu keftawa, yasa jikinta yin sanyi, bata kuma faďin komai ba ta zagaya ďayan gefen gadon ta kwanta abunta gameda rufe idanunta, tana jiran taji ko zaice wani abu."
"Wanda shi kuma a wannan lokakin ya sauķar da ajiyan zuciya, cikin ransa sam yasan baiyi mata adalci ba idan har yahanata komawa ci gaba da karatunta, bayan tana shekaran karshe, saidai tunawa da tana ďauke da cikin sa ajikinta shi ke sake masa jiki gashi zatayi nisa dashi har zuwa wata qasar da ba nan ba, inama da a nan ne bazai damu sosai ba Amman sunyi nisa."
"Yana zence cikin zuciyar sa yasa hannunsa ya tattare takardun dake gaban sa yamayar dasu cikin jaka kafin ya tashi zuwa inda ma kunnin wuta yake ya kashe yadawo kan gadon ya kwanta a hankali ya juya yana kallon bayanta tare da matsawa zuwa jikinta dafda ita yasa hannunsa yaja musu bargo ya rufe su, yanayin yanda sanyin A C ya cike ďakin, ya rungume ta tabaya tare da sakale kansa tsakanin wiyan ta yana sinsinar ta tare da bin jikinta da hannunsa yana mata tafiyar tsutsa."
"Qara runtse idanunta tayi sosai tanajin sa duk irin abunda yake mata Amman tayi masa banza tamkar batasan yanayi ba saima qara damqe jikinta da takeyi daga garesa tana kamewa kamar me tsoron faruwan wani abu."
"Ci gaba da bibiyar jikinta yayi, ganin ba saike masa zatayi ba duk yanda yayi mata, alamun ranta babu daďi yau dan tunda suke bata tabà masa hakaba a duk lokacin da suke a tare." haqura yayi yana manne da ita, cikin zancen zuci batare da yasani ba bacci ya kwashe sa wanda itama a wannan lokakin tayi bacci."
"Koda gari ya waye bayan ta gama haďa karin safe yafito yana ci, tamkar babu abunda yafaru tsakanin su jiya haka tasake masa, har sai wajan karfe goma sha ďaya kafin ya fice daga gidan, wanda ganin yafice ya sanya ta shiga gyare gyaren gidan duk inda yakeda datti ta gyara tare da kunna garwashin turaren wuta tasaka tana zagaye gidan dashi daddaďan kamshi ke tashi ga sanyin A C dake ratsa cikin parloun yana fitar da wani irin ni'ima."
"Cikin ďakinta ta shige da turaren wutan bayan tagama zagaye cikin parloun dashi tasaka a ďakinsa wanda ta gyare masa shi tamkar bashi ba, batare da ta rufe nata ķofar ďakin ba ta isa zuwa bakin gado ta zauna tareda ďaukan wayarta wanda ta maqala shi ajikin charge, tana murmushi ta danna qiran phone number Amena, saida yakusa tsinkewa kafin ta ďauka, suka shiga gaisawa, kafin suka soma fira irin ta tsakanin qawaye Amena take tambayar ta kan cewa sai yaushe zata dawo school gashi sai karatu ake ana wuce ta."
"Rasa me zatace mata tayi, tana tunani cikin ranta karshe dai tasanar mata kan cewa tana ďauke da ciki ne ba kullum takejin daďi ba Amman insha Allahu zatayi kokari ta dawo verry soon."
"Murna Amena tayi mata sosai da nuna farin cikin ta, tareda yi mata korafin meyasa bata sanar mata ba tuntuni da zancen yakeda zafi zafin sa ba sai yanzu da yayi tsami dan haka tayi fishi." haquri ta soma bata tana faďin ko agida wajan su mummy da Abba babu wanda yasani, daga nan sukaci gaba da hiran su sukayi cikin nishaďi tana Amena nabata lbr tana dariya."
"Tamkar daga sama tajiyo muryan mutum cikin parlou ana kwaďa sallama gameda faďin ko babu kowane a gidan,?" Ina zuwa tacewa Amena kafin takashe wayar ta ajiye a baķin gadon, ta tashi dan zuwa duba wanda yake sallamar, wanda har yanzun ba'a daina ba." tana mamakin ko waye haka, ta isa dafda bakin ķofar ďakin nata zuwa cikin parloun tace ina zuwa wayene,?"
"Qanwar uwarki ce taji anfaďa cikin ďaga murya wanda hakan shi ya sanya ta ďaga kwayar idanunta dan ganin wanda ya ďura mata irin wannan zagin haka kai tsaye ko kara babu." qarasa fitowa tayi idanunta suka sauka kanta taga kamar wannan fuskan tagani jiya da sukaje gidan Umma Amman batasann ko wacece ba saidai duk yanda akayi yar uwar su ce jini ďaya dan ga kammanni qarara tanagani." cikin sanyi tace baiwar Allah yada zagi haka lfy,?"
"Cikin qara haďe fuska tace lfyr ce takawo haka." tana nuna kirjin ta da hannu ta qara cewa ni zaki kalla da ido kice min wai wayene, kina nufin kice bakisanni ba ko meye, to idan sanina ne bakiyi ba ko kuma dai nuna sabon iskanci zanyi miki alfarma ki sanni a yanzu dan gudun haďuwar nan gaba, sunana siyama Ibrahim qanwar Abdulmalik wanda yake mijin ki kenan uwa ďaya uba ďaya muke, inafatan yanzu kinsan koni wacece, dan haka ki kiyaye nest time."
"Tana kaiwa nan ta kaďa kai ta shige ta gaban ta zuwa ďakin Maraqishiya, bayan ta zabga mata uban harara tamkar idanunta zasu fice waje, A nan baķin ķofar ďakin, tana dafda shiga taci karo da Maraqishiya tana dogon hamma tareda yin miqa."
"Ganinta ya sanya ta yin murmushi tace A a wanake gani haka su siyama manyan mata, ashedai kece najiyo muryan ki ina bacci nace ko keda waye haka nakejin murya, yaushe kikazo yar makaranta,?"
"Kedai bari Aunty shekaran jiya dawowa ta da yamma, jiya yaya yaje gida inazaton zan ganki sai kuma ashe baki biyo su ba, shine nace kafin in koma bari in dubaki nazo yanzu inata kwaďa sallama wannan matar taku ta fito take tambaya na wai waye ne wannan,?" tana ya mutse fuska tace kijifa dan Allah wani irin tambayar rainin hankali saikace gidan ubanta, ni kuwa dana fita iskanci na bata amsa da cewa qanwar uwar tace, kinga anyi daidai ai."
"Himm tafaďa cikin ranta ta juya tayi mata mugun kallo kafin ta dawo da dubanta zuwa ga siyama tace, idan wannan ne zata aikata fiya da hakama zo mushiga daga ciki kafin ta addasa miki ciwon zuciya."
"Wa, ni,?" siyama tafaďa tana gwale idanu tace, Allah ya tsare ni ai saidai ta addasawa kanta Amman bani ba dan nafi karfin ta wlh ." tana maganar ne tare da shigewa cikin dakin tana toshe hancinta tace gashi duk an murtuke ku cikin garin hayaki saikace wata yar gidan matsafai." bayanta Maraqishiya tabi tare da cillawa humaira harara fuska a haďe tamkar bakin hadari tana cewa ai haka take kullum cikin baďe mu da hayakin tsafi a qarqashin ubangijin mu muke shiyasa kika ganmu a raye har zuwa yanzu da tuni sun daďe da tsotse mu lokacin mu baiyi ba."
"Itakam mamakin su take cikin ranta take faďin daman akwai mutane irin haka masu maka tsana babu dalili,?" Himm tafaďa cikin ranta, tareda girgiza kanta ta koma daķin ta, kai tsaye gado tafaďa dan wani irin bacci da takeji, Allah Allah take taga ta kammala aiyukan dake gaban ta ta kwanta bacci ga wani irin kasala da ya addabe ta yau ko wannan aikin da tayi cikin dauriya ne Amman bawai dan tanajin daďi ba."
"Bata ďauki tsawon lokacin ba bacci me nauyi ya kwashe ta hankali kwance take sauķe numfashi....
✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:11] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*46*
Dedicated to my
*AISHA GENTLE LADY*💃🏻
"Darana wajan misalin karfe biyu, yana zaune kan kujeran dake cikin office ďin sa yana danne dannen computer."
"Barin abunda yake yayi gameda kaiwan hannunsa gefen sa ya ďauki phone ďinsa, yashiga cikin nombobi ya qira number wayar Humaira yaji sa akashe, yaqara qira still akashe yajisa, mamaki yake cikin ransa ya akayi yau wayar ta yake akashe bazai zama ace mutuwa tayi ba babu charger ba dan yawanci akoda yaushe phone ďinta yana maqale a wuta yake gani."
"Ganin ba samunta zaiyi ba kuma gashi time na wucewa ko wanne lokaci abokan sa da yake jira zasu iya zuwa suje gidan sa suci abinci, hakan ya sanya shi qiran wayar Maraqishiya lokacin tana nan zaune a dakinta ita da siyama suna hira, plate ďin indomie ajiye agaban su da alamun shi suka gama ci yanzu."
"Yana ringing biyu ta ďauka tana mamakin ganin qiran wayar sa iwar haka da ranar Allah." hello tafaďa cikin muryan ta kamar da gaske ta gaishe dashi ya amsa mata tare da bata saqon sa na kancewa ta gayawa humaira ta haďa musu abinci yana tare da mutane around 4:00pm zasu dawo ko itama tayi musu idan ita humaira batajin daďi sanin yau da kullum abunka da me ciki dan yayi ta qiran phone ďinta yaji akashe ."
"Haďe fuska tayi tamkar tana gabansa jin abunda yafaďa a nan take tace masa wlh bazanyi ba tunda ba nice da girki ba alfarma ta ďaya wanda zan iyayi shine zan sanar da ita Amman bawai inyi aikin da yake nata ba, kitt taji ya kashe wayar dan idan yaci gaba da sauraran rashin kunyar ta ransa ne zai iya bàci dan haka yafi masa ya rabu da ita."
"Cikin yamutse fuska tana jan dogon tsaki tayi jifa da wayar a kan gado, siyama tana ganin haka daga jin yanda take maganar ta gane da yayanta take waya, tana kallon ta tace Aunty ya akayi kina haďa rai wani abun ne yaya yace miki,?"
"Dawo da dubanta kan siyama tayi tace kedai bari sister wai ace girkin wannan shegiyar ne yau Amman wai ni inyi mata da kaina, dama ace wata matar ce daban zan iyayi shima dan yana matsayin mijina Amman dan ita wlh idan zanyi ma to ba me kyau ba, kinga kuwa gudun kar ayi kar a soma." tana bude ido take maganar siyama tace gaskiyan kine wlh dukda brother yake a gareni ina bayanki indai har akan wannan bakar aljanar ce masu zubin yan wuta zan iyayin komai, dan haka ga wata shawara ta karfe nawa yace miki zasu dawo,?" karfe huďu naji yafada, cewar Maraqishiya da take washe haqora tana tsumayan jin wanne irin shawara zata bata, Siyama tace to kada ki kuskura ki sanar da ita a yanzu kibari sai zuwa kamar karfe uku ko kuma uku da rabi, huďu zasu dawo sai muga tayaya zata iya haďa a abinci a wannan qwarar ran lokacin ya kike gani,?"dariya sosai Maraqishiya tayi tace Allah yabar min ke siyama keďin haske ce." daga nan suna dariya sukaci gaba da hiran su, bayan wasu mintuna kamar rabin lokaci siyama ta miqe tsaye tare da ďaukan mayafin ta da jakan ta, tace da Maraqishiya ni zan tafi inaso daga nan in wuce gidan yaa najeeb kafin yamma tayi, fuska Maraqishiya ta sake tana kallon ta tace tun yanzu siyama bazaki tsaya kiga lbr ba,?"
"A a Aunty, siyama tafaďa tana dariya tace duk yanda akayi kekam kibani lbr ta waya, tana kaiwa nan ta fice a ďakin Maraqishiya ta rakota har bakin get kafin ta komo cikin gida ta rashe kan ďaya daga cikin kujerun parloun gameda yin tagumi tamkar wacce aka aiko mata da zancen mutuwa, cikin zuciyar ta tunanin ta ďaya na wanda zata jaza mata bala'i musamman bashi kaďai zai dawo ba yau akwai lbr, dole tayi wani abu akai." tana nan zaune a parloun ta jima tana sake sake, can ta ďaga kanta idanunta suka sauka kan agogon dake manne jikin bangon parloun ya nuna mata karfe uku da minti goma, tana shu'umin dariya gameda kaďa kai alamun yau tana cikin rana me ďauke da daďi."
"Tashi tayi ta nufi zuwa ďakin humaira ko sallama batayi ba ta shige ciki kai tsaye tamkar cikin ďakin ta, ta tsaya dube dube tana magana taga alamun babu kowa aciki, hakan ya sanya ta ficewa daga ďakin ta fita bayan gida zuwa inda kitchen dinta yake ko tana can, hango ta tsaye tayi tana yankan albasa sai jan hanci take idanunta duk sun ciko da hawaye dan azaban zafi, mamaki ne ya isheta ganin abinci take dafawa cikin ranta tace to kodai ya samu ya sanar mata ne,?" can tayi nazari tace hala dan yau itace da girki shiyasa, himm itadai tasani koma meye." tana ya mutse fuska tayi gyaran murya wanda yasa humaira jiyo da kai dan ganin waye, atakaice tana mata wani irin kallo tace inji me gidan yace ki haďa masa abinci yana nan zuwa karfe huďu shida mutane."
"Cikin nuna rashin fahimta humaira ta kalle da kwayar idanunta tace a yanzu zan haďa musu abinci bayan karfe huďun ma tayi,?" Wannan kuma can ta matse miki lallai a tsuliya idan yarda ce bakiyi ba kinada phone u can call him kiji daga garesa nidai bada saqo ce tawa kuma nabada dan haka sauran ya rage naki kiyi ko kar kiyi badamuwa ta bace." tana harhaďe fuska take maganar tana kaiwa nan ta ta juya tabar ta nan cikin kitchen ďin tsaye daskar tayi mutuwar tsaye ita bama maganganun nata bane yaci mata zuciya tunanin ta ďaya shine a wannan qanqanin lokacin da befi rabin lokaci ba tayaya zata iya haďa abincin cin fiya da mutum biyu inama ko su biyu ne wannan abincin da tahaďa masa zai iya isar su."
"Tana cikin maganar zuci ganin tsayuwar da tayi ma qara bàta mata lokaci yake ya sanya ta duba a gogon wayar ta dake ajiye kan freezar taga karfe uku da minti ishirin da alamun idan tayi sauri zata iya qara dafa wani cours couse ďin sai ta qara vegetable soup ďin da tayi aqalla kafin huďun yacika su dawo zata iya kammalawa, sa'an ta ďaya dama babu ta gasa kifin ta guda biyu nufin ta ita ta ďauki ďaya shima ta haďa masa ďayan da da nashi abincin."
"Batare da bàta lokaci ba ta ďaura ruwa kaďan na wanda zai isa dafa cous couse kafin ya tafasa ta qara daka tattasan ta da attarugu ta qara yanka albasa, a yayin da ruwan da ta ďaura ya tafasa cikin sauri ta zuba mai da gishiri kaďan tareda buďe cous couse leather biyu ta zuba cikin ruwan dake tafasa ta rage masa karfin wutan kafin taci gaba da gyara miyar tanayi tana duban time fatan ta ďaya shine Allah yasa ta kammala har tayi sallah da wanka kafin su zo dan batasan ya zatayi ba yasata aiki a qaramin lokaci."
"Cikin qanqanin lokaci kuwa Allah ya taimake ta karfe huďun cif ta kammala haďa komai ta juye su cikin kulolin da ya dace duk takaisu kan dining ta jerasu tare da haďa plate da cokala da fork da ruwan sanyi na sha dama tanada haďaďďan sobòn ta da kunun ayan ta wanda ta haďa tun ďazu kafin ta soma girki duk ta ajiye kan dining ďin tana kammala jerawa ta wuce cikin ďakin ta kai tsaye dan tasamu tayi wanka da sallah ya nayin da take tana sharan zufa idan ba wankan tasamu tayi bazataji daďin jikinta ba , wanda a wannan lokakin Maraqishiya dake zaune a parloun duk tana ganin ikon Allah gani take yarinya sai jera abubuwa take, tambayar zuciyar ta take to wai dama tanada su dafeffe ne ko kuwa acikin qanqanin lokacin ne duk ta haďa wannan abincin,?"
"Ganin bamai bata amsa zata samuba yasata miqewa tsaye ta isa zuwa bakin ķofar parloun tasaka kay ta kulle kafin ta dawo ta tsaya kan dining ďin tabi duka kulolin abincin tana bude su tana kallon su cikin kwayar ido daga kan farin cous couse ďin har zuwa kan vegetable soup ďin da gasheshshen kifin, babu shakka ita kanta wannan abincin da sukayi tsurutsuru suna kallon ta ba qaramin shiga ranta yayi ba da zata samu babu makawa ci zatayi tamkar babu gobe." mayar da murafen su tayi ta rufe tabar wajan ta wuce zuwa cikin ďakinta, tana shiga ta soma safa da marwa tana cije baki tana neman mafita kala kala tana tunani kafin su dawo taje ta aiwatar da abunda zatayi."
"Can tunanin ta ya tsaya cikin sauri ta isa bakin ķofar toilet inda roban zuba bola yake ta shiga bincikawa taci karo da curarran gashin kanta wanda ďazu data taje kanta guntun gashin da yafita ta jefa shi cikin bolan." tana murmushi ta kaďa kai bayan ta ďauki gashin a hannunta ta fice daga ďakin tareda wucewa kitchen ďinta ta ďauki roban kalanzir da cokali ta dawo wajan dining ďin tana leqe leqe tayi sauri ta buďe kulan cous couse ďin ta yaryaďa wannan kalanzir ďin dake hannunta a ciki ta garwaye shi ya koma sai warin kalanzir ne ke tashi cikin sa haka ta bude na kifin ma ta yaryaďa masa shima, kafin ta mayar ta rufe su, tana kaďa kai ta buďe kulan miyar tana zuruzuru da ido ta warware wannan qananan gashin dake hannunta ta cikin miyar tasa cokali ta garwaye ta mayar da nashi murfin ta rufe, cikin sauri tabar wajan ta koma ta buďe ķofar parloun da tasawa kay ta dawo kai tsaye ta shige cikin dakinta tana shu'umin dariyar mugunta."
"Wanda a wannan lokacin Abdulmalik ya turo ķofar parloun ya shigo shida abokanan sa su huďu, sukayi sallama tareda qarasowa cikin parloun ķàmshin turaren wuta da sanyin A C sukaji yana dokan hancin su su kansu sunga banbanci da dayake da mace ďaya da yanzu kuma da yakeda guda biyu a yanzu dan ya wanci idan sukazo gidan sa irin haka gaskiya zasu iya cewa basu tabà jin ni'ima irin hakaba."
"Bayan sun samu kujera sun zauna Abdulmalik yace dasu bari in shiga ciki in watsa ruwa yanzu zan fito." Yana maganar ya wuce ďakin sa kai tsaye ya shige toilet ya watsa ruwa a jikinsa kafin yafito cikin sauri ya sake sabon shiri cikin farar shadda da garin sa tamkar me shirin zuwa ďaurin aure bayan ya feshe jikinsa da turare ya daidaita hulan kansa ya dauki wayoyin sa da duk wani abunda zai tafi dashi dan yana kammala cin abincin zai wuce dan ganin yanda time ke tafiya dole sai yayi sauri idan ba hakaba zai iya missing plight.?"
"Cikin parloun yadawo yasamesu zaune suna hira, ya musu tayin abinci duk kannin su suka miqe suka isa zuwa dining table ďin kowa ya zauna kan kujera, Abdulmalik ya buďe musu kololin abincin suka soma ďiba ďaya bayan ďaya sunaci gaba da surutun su irin ta abokane, saidai wani abu ďaya da suka kasa ganewa tunda suka soma diban Abincin sukejin warin kalanzir na tashi cikinsa....
*HAFSYSY*✍🏼 📚📚📚
[30/08, 18:11] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*49*
Dedicated to my
*AISHA GENTLE LADY*💃🏻
Tana cikin dube dube ta hango nurse ďin da ta tabbatar musu da cewa ciki ne ďauke da humaira, Cikin sauri ta qarasa gareta, bayan sun gaisa tayi mata bayanin abunda ke tafe da ita, bayan ta Nurse tabi zuwa waje haraban asbitin inda shiwari tayi parking motar, ta tayasu suka ďauke ta sukayi cikin asibin da ita, Nurse ďin tayi musu nuni da wani dakin da babu kowa suka shigar da ita, bayan sun kwantar da ita a sannan Nurse ďin ta dawo da hankalin ta kan Maraqishiya tace, baiwar Allah meke damunta ne haka me ya sameta naga sai jini take zubarwa,?"
"Tsik taji zuciyar ta ya tsinke daman tambayar da take guduwan ji kenan batasan wanne karyan zatayi ba, tana tunani cikin ranta, ta kai dubanta kan shiwari tana daga mata gira alaman me zatace mata, jin tayi shiru batace komai ba sai kalle kallen juna da suke suna wiriwiri da idanu tamkar marasa gaskiya, hakan yasa Nurse ďin gyaran murya ta qara cewa kuyi sauri kusanar dani abunda ke damunta mana dan asamu abata taimakon gaggawa kafin lokaci ya wuce."
"Ajiyan zuciya Shiwari ta sauke kafin tace nurse dan Allah kiyi abunda zaku iyayi akai daga baya sai muyi muku bayanin abunda ke damunta, kinga yanzu tana bukatar taimako."
"To idan bakuyi mana bayanin abunda ke damunta ba ta ina kukeson mu fara bata taimako,?" cewar nurse ďin tana kallon su ta qara cewa, Idan kuma ba gaya min meke damunta zakuyi ba shikenan ga gata nan sai kusan tayi danni inada abunyi yanzun ma dan naga naganeta ne kuma da alama tana bukatar taimako shiyasa na tsaya har nake tambayar ku, Amman kun kasa yi min bayani kamar marasa gaskiya."
"Cike da kaďuwa Maraqishiya ta kai dubanta kan nurse ďin jin abunda tafaďa ya sanya ta tsarguwa, tana tunanin wanne karyan zatayi wanda bazai ruguza musu shirinsu ba, ganin nurse ďin da gasken ta takeyi tafiya zatayi, ya sanya ta cikin sauri ta shige gaban ta, muryan ta na harďewa ta soma cewa."
"Bakomai bane ke damunta illah bari da tayi cikin dake jikinta ya zube" Ya salam, Nurse ďin tafaďa tareda yin salati jin cewar bari tayi, cikin nuna damuwar ta akan hakan tace, garin yaya haka tafaru, faďiwa tayi ko yaya,?"
"Himm kedai kibar zancan nurse wlh babu daďin ji, ba faďiwa tayi ba, kinsan ai dama tun farkon zuwan mu wannan asibitin da kikace mata ciki ne ďauke da ita, batayi farin cikin sa ba,?" kai nurse ďin ta girgiza mata alaman Eh, Maraqishiya taci gaba da cewa, to shine fa tun daga wannan lokakin take nuna tsantsan tsanar ta akansa duk hanyar da zatayi taga cikin nan ya zube to shi takeyi, tun ina mata magana kan cewa hakan da takeyi babu kyau zai iya mata illah Amman bataji har nagaji narabu da ita, yauma Allah yasa ina gida ne da saidai a dauki gawar ta matacciya wlh, dan wani irin ruwan itace da nagani a hannunta baķi ķirin a ruba, lokacin da mukaji ihun ta muka taso dan ganin me yafaru da ita, kinga kuwa ga dukkan alamu maganin zubar da cikin tasha."
kai nurse ďin ta girgiza tana riqe da habàr ta, mamaki duk ya isheta da jin wannan, lbrin tace to ina shi mijin nata yake bai sani bane,?"
"Ina kuwa yasani Maraqishiya, taba ta amsa tana tabè baki ta qara cewa, yanzu haka da nake gaya miki baya gari so baima san meke faruwa ba."
"Ajiyan zuciya Nurse ta sauke tace to Allah dai kyauta Amman gaskiya banji daďi ba sam wlh, bari dai inje in samu doctor inyi masa bayani dan abata taimako cikin gaggawa yanda naga sai bleeding take, but before that u have to call him kisanar dashi dan yasan me yake tafiya dan wannan dole ne ayi mata wankin ciki" Tana kaiwa nan ta buďe ķofar dakin tafice, Shiwari tana kallon fitar ta ďaga dakin ta matso kusa da Maraqishiya tana dariya, a hankali ta soma cewa, Amman dai gaskiya qawata wani lokacin ke makirace, irin wannan zuba karya haka saikace baķar boka, koni wlh banyi tunanin irin wannan karyar taki ba."
"Qasa qasa ta kwashe da dariya tana faďin kedai bari qawata abun ba daga nan yakeba dakyar na iya haďo wannan karyar yanda naga nurse ďin nan tasamu gaba kamar wacce tagano wani abu daga garemu, shima yanzu zan zazzaga masa karyar a waya, dan haka zo mufita waje kafin doctor ďin yazo dubata, fatana kuma shine Allah yasa tarabu da wannan shegen cikin har abada." Murmushi shiwari tayi tana girgiza kai, kafin suka fice daga ďakin, can ďan nesa da ďakin suka samu kujera suka zauna" Maraqishiya ta soma danne danne cikin wayar ta, tana haďa saqon da zata tura masa, dan a ganinta idan qiran sa tayi a waya zai iya fara jero mata wasu qabilun tambayoyi dan haka taga gwara ta tura masa ta message zaifi mata sauqi dan ba iya amsa masa wata tambayar zatayi ba idan ya ďaure ta."
"Suna nan zaune a wajan suka hango Nurse ďin ta taho tareda da wani doctor sun shige ďakin da humaira take kwance dan bata taimako, Ganin hakan ya sanya shiwari tashi tsaye tace da Maraqishiya ni zan koma gida tunda dai yanzu komai ya lafa an samu doctor da zai dubata, idan ba komawa gida nayi da wuri ba har mijinta yadawo bana nan zan iya fuskantar bàcin ransa tunda dama dakyar yabar ni na fita." Miqewa tsaye Maraqishiya tayi tana gyaran mayafin dake jikinta, tace muje ki sauķe ni nima gida zan koma tunda nayi mata nawa taimakon sauran kuma ya rage nata idan ma mutuwa tayi banida matsala a yanzu" Dariya shiwari tayi, bayan sun soma tafiya dan barin asibitin tace, qawata kenan gaki da tsoron tsiya ga kuma shegen mugunta, ďazu kika gama nuna tashin hankalin ki wai dan karta mutu ki shiga uku yanzu kuma kince idan mutuwa ma tayi bakida matsala."
"Dariyar suka kuma kwashewa a tare har suka fice haraban asibitin inda shiwari tayi parking motar ta" Shiga sukayi shiwari tayi driving nasu sukabar asibitin."
"Bayan ďan wani lokaci qalilan doctor ya gama dubata tareda cewa Nurse su gyra mata jikinta kafin a jona mata ruwa" Fita nurse ďin tayi daga cikin ďakin ta duba inda ta hango su zaune ďazu bata gansu ba, tayi zaton ko sun ďan zagaya ne, haka ta shiga neman su tana duban inda suke har tagaji ta dawo ta nemi wasu Nurse's yan uwanta suka shiga dakin da humaira take, suka gyara mata jikinta tareda sauya mata wani kaaya zuwa rigan asibiti, bayan sun gama doctor ya dawo ya jona mata ruwa tareda yi mata wasu dube dube wanda har izuwa wannan lokakin idanunta a rufe suke bata farfaďo ba."
"Ficewa sukayi daga dakin tareda ja mata ķofar suka rufe dan tasamu hutawa kafin ta farfaďo."
🌾🍃🌾🍃🌾🍃🌾
*ABUJA*
Tuqin motar yake a hankali cikin nutsuwa tamkar bayason yin tuqin, Haisam dake kujeran kusa dashi, sai mita yake masa kan cewa yana tuqin mota saikace wani ďan koyo baya gudu, gashi yayi yayi da yabashi motar zai tuqasu Amman yaqi har dana sani yake da yabiyo sa, da yasan irin wannan tafiyar zaiyi, haka ya haqura yarabu dashi ganin ba kulasa zaiyi ba saima qara rage gudun motar da yake."
"Yanda yaga ran abokin nasa yabaci duk ya haďe fuska tamkar hadari, hakan ya sanya shi yin murmushin gefen baki tareda qarawa motar gudu, Cikin mintuna kaďan suka isa gidan haisam dake cikin unguwar katamfe, bayan sun shiga cikin Estate ďin yasamu waje yayi parking motar" Tun kafin ya kashe motar haisam ya buďe nasa ķofar yafita, kai tsaye yayi cikin gida."
"Girgiza kansa Abdulmalik yayi gameda yin murmushi ya buďe nasa ķofar ya fice, bayan ya kulle motar yabi bayan haisam, cikin ransa yake faďin kai abokina Allah yamaka sauki bakada haquri wajan yunwa, da yake dama tun suna hanyar su ta dawowa yake masa complain, shifa yunwa yakeji sosai zai koma gida" tura ķofar parloun yayi ya shiga ciki A nan ya tarar da haisam ya fito daga toilet jikinsa da ruwa da alamun alwala ya ďauro" Ganin sallah zai tashar ya sanya Abdulmalik dakatar dashi da yajira sa suyi sallan tare tunda shima bayi yayi ba."
"Bayan yafito haisam yajasu suka soma sallah suna idarwa sukayi azikar, Nuwaira matar haisam ta kawo musu abincin a nan parlon ta ajiye musu bayan sun gaisa da Abdulmalik tabasu guri dan su samu suci abincin."
"Farar shinkafa ce da jar miya, Abdulmalik ya ďiba kaďan yanda yakega zai iya turawa, Haisam ma ya dibi nashi yanda zai ishen sa" Suna cikin cin abincin Abdulmalik ya ciro wayar sa daga cikin aljihun sa dan duba saqon da yaji ya shigo masa tun yana tuqi, ya shiga dubawa ganin sunan Maraqishiya ya sanya shi shiga ciki batare da ya tsallake number nataba, ya shiga karanta saqon da ta turo masa ganin yanada dan yawa" A hankali yake bin rubutun yana karantawa, cikin bugun zuciya ya miqe tsaye yana ci gaba da karanta saqon, baisan lokacin da wayar ta subùle daga hannunsa ta faďi zuwa qasaba jin wannan mummunar saqon ba qaramin ďaga masa hankali yayi ba, Zuciyar sa naci gaba da buguwa ya soma karanto Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un, yana maimaitawa" Ganin irin halin tashin hankalin da yashiga ya sanya haisam barin cin abincin da yake, ya taso tsaye tareda matsowa kusa dashi, yasa hannu ya dafa kafaďar sa yana masa kallon sa yace abokina lfy kuwa, meke faruwa, me kagani haka wanda yatashar maka da hankali,?"
"Shiru yayi yakasa basa amsa saima qara ci gaba da Innalillahi da yayi, yaja da baya yayi saman dirsham bisa ďaya daga cikin kujerun parloun, yana shafan kansa, cikin wani irin kuna da yaji zuciyar sa nayi masa, A hankali ya soma faďin, karya ne humaira karki min haka, kada ki hukunta ni da irin wannan mummunar tashin hankalin bazan iya ďauka ba....shiru yayi daga zancen da yake, ya rasa meke masa daďi gani yake sam wannan lbrn karyane, zuciyar sa takasa aminta da hakan, gani yake humaira bazata zubar masa da cikin sa ba, ita kanta tasan irin yanda yake kaunar abarsa, bazatayi masa hakaba"
"Ganin duk irin yanda yake jero masa tambayoyi Amman yakasa basa amsa saima qara ci gaba da maimaita lahaula da yake da alamun baya cikin nutsuwar sa, hakan ya sanya haisam kaiwan hannunsa ya ďauki wayar sa dake qasa a jefe kafin ya ďago yakai duban sa kan Abdulmalik wanda ya zabga uban tagumi."
"A hankali ya soma bin saqon yana karantawa, cikin nuna tashin hankalin sa, bayan yagama karanta saqon ya soma salati, sam ya rasa me zaice abun ya ďaure masa kai, ya za'ace mutum yanada auran sa da mijinsa ace ya zubar da cikin dake jikinsa saikace cikin shege, karyata zancen yayi sam yakasa yarda da hakan gani yake saidai wani tsabànin aka samu, Amman humaira da yake gani sam bazata aikata hakaba, a iya kallon mai hankali da nutsuwa da yake mata koda kuwa ace cikin shege ne tayi albarka."
"Hankalin sa ne yaqara tashi ba shiri ya miqe tsaye, tunawa da yayi tun lokacin da tasamu wannan cikin take nuna masa rashin son wannan cikin sanadiyar ita makaranta takeson komawa bataso ta ďauki ciki a yanzu ba har sai bayan ta kammala da karatunta" Cikin hanzari ya karbì phone ďinsa dake hannun haisam tareda ya masa sallama kan cewa zai kama hanyar ķatsina sai ya qira shi a waya, Cike da kaďuwa haisam ya dube shi kafin yace haba mana a yanzu kana ganin yamma ta soma yi ina neman karfe huďu shine zakace hanya zaka hau, kasan kuma ba qaramar tafiya zakayi ba ai gwara ma kabari gobe da safe idan yaso ko jirgin safe sai kafi, Amman yanzu zakayi dare a hanya" Kansa ya girgiza shi kaďai yasan yanda yakeji, batare da yace masa qala ba ya fice daga parloun ya sauka qasa inda yayi parking motar sa" shiga yayi yana tashar da motar haisam ya biyo bayansa tareda yi masa maganar yabari gobe, fur yaqi yace dashi bazan iya zamaba hankali na bazai kwanta ba idan har ba zuwa nayi naga lfyr yarona ba, tuk da bawai na gama abunda yakawo ni bane, But I have to go now, sai nadawo kawai." Rabuwa dashi haisam yayi tareda yi masa Allah ya kiyaye da fatan ganin alkhairi, bayan sunyi sallama yaja motar sa cikin gudu ya yabar wajan, Haisam ya koma cikin gida yana zancen zuci sam kansa ya kulle masa fatan sa ďaya shine Allah yasa wannan lamarin ba haka yakeba."
"Koda ya komo cikin parloun karo yaci da matar sa Nuwaira ganin sa cikin damuwa ya sanya ta tambayar sa meke faruwa haka naga Abdulmalik ya fice da sauri ko abincin nasa baici inafatan dai lfy,?"
"Lfy yace da ita tareda bata lbrn abunda yafitar dashi da sauri, cikin mamaki ta kallesa gameda yin salati yanda taji maganar cikin zuciyar ta tace, wasu suna neman haifuwa idanu rufe wasu kuma suna zubarwa, Himm ta sauke numfashi a hankali tace wannan zancen da mamaki yake Allah dai ya kyauta ya rufa mana asiri" Amin yafaďa tareda gyara zaman sa akan kujeran da yake ya shiga zance cikin zuciyar sa."
"Wajan da sukaci abincin tashiga kwashewa bayan ta tambaye sa ko zai qarasa cin abincin yace mata A a, dan gabaki ďaya ji yayi ya koshi duk irin yanda cikin sa kejin yunwa bazai iya qara zaman cin abinci ba."
**
Da daddare wajan misalin karfe shaďaya saura ya shiga cikin garin ķatsina, tamkar zaiyi tsuntsuwa ya tashi sama haka qara gudun motar Allah Allah yake yaga ya qarasa gida ko zaiji kwanciyar hankali" Yanayin yanda yake guduwa da motar akan titi yasa har mutane suke magana masu zagi suna nunashi da hannu sunayi masu binsa da ido sunayi, shi kuwa baisan ma sunayi ba ko takansu baibi yaci gaba da sharara gudun sa, haka har ya isa gida yayi parking motar a waje kafin ya fito ya fara kwankwasa ķofar get ďin baba mai gadi gadi ya leqo da kansa dan duba ki wane wane, Ganin ogan sa ne ke buga ķofar ya sanya shi cikin hanzari ya buďe masa get ďin tareda kwasan gaisuwa yana mamakin ganin dawowar sa da wannan daran shida yasan abuja yatafi."
"Hannunsa kawai ya iya ďaga masa batare da yabi ta kansa ba ya shige cikin gidan, yana tura ķofar parloun kai tsaye ya wuce ďakin humaira ya duba duk cikin ďakin har toilet bata nan baiganta ba, baiyi wata wata ba ya fice daga cikin ďakin ya nufi na Maraqishiya" Kwance ya hango ta bisa gado idanunta a rufe da alamun bacci take" zuwa gabanta ya qarasa ya shiga qiran sunan ta tareda tambayar ta ina humaira take,?" Cikiin jin haushin tashinta da yayi daga baccin da ta soma yi mai daďi ta miqe zaune daga kwancen da take ta zumburo masa baki tace meye haka kawai ina bacci na zaka tashe ni kana jero min tambayar da bata shafeni ba,?"
"Haďe fuskan sa yayi yana mata kallon bàcin rai yace zaki bani amsar tambayar da nayi miki ne ko kuwa rashin kunya zaki tsaya min,?" Kanta ta kawar gefe guda ciki ciki da murya tace masa kamar yanda kagani a saqon da natura maka hakane yanzu haka tana asibitin da kake ta lokacin da batada lfy idan kaje zaka sameta, dan haka ni karabu dani bacci nakeji" Zai qara mata wani maganar sai kuma yafasa ganin idan yabiye mata rashin kunya zataci gaba dayi ta bàta masa lokaci hakan ya sanya shi ficewa daga ďakin nata batare da yaqara bi ta kanta ba" Kai tsaye ya fice waje inda yayi parking motar sa ya shiga ya tashar da motar yabar wajan, Baba mai gadi yana ďaga masa hannu tareda faďin Allah ya kiyaye hanya ganin yanda yafigi motar tamkar zai tashi sama."
"Cikin ďan mintuna ya isa cikin Asibitin yanayin yanda yake sharara gudu akan titin" Bayan yayi parking motar ya nufi cikin asibitin, shiru yake babu mutane sosai sai ďaďďaya da yake garin dare ya soma yi" Yana cikin tafiya yaci karo da wata ďaya daga cikin Nurse ďin da suka gyara mata jiki" Bayan sun gaisa ne ya shiga tambayar ta marar lfyr da aka kawo ďazu tareda faďa mata sunanta" Kan ta girgiza tayi shiru kaďan kamar mai narazin wani abu kafin, tace gaskiya alhaji marasa lfyr dayawa suke saidai akwai wata wanda take cikin matsalar daka faďa yanzu Amman bari in haďaka da Nurse ďin da ta karbè ta idan yaso saita kaika kagani ko itace" Amsa mata yayi da to yabi bayanta takaisa wajan nurse ďin, ganin tagane fuskar sa ya sanya ta cikin murmushi suka gaisa dashi tareda yi masa jajan abunda yafaru."
"Jin irin maganar da yake fita daga bakin nurse ďin ya sanya shi maganar zuciya, Runtse idanunsa yayi gameda buďe su, cikin wani irin yanayi ya yace da ita ta nuna masa ďakin da aka Kwantar da ita, batare da bàta lokaci ba takaisa har zuwa bakin ķofar ďakin kafin tace masa tun ďazu ma ta farfaďo tana bukatar kulawa Amman babu kowa nata wanda suka kawo ta sun koma har yanzu basu dawo ba sai nice nake zuwa dubata akai akai ."
"A hankali ya tura ķofar ďakin ya shiga idanunsa suka sauka a akanta kwance cikin rigan asibiti ruwan blue wanda ake sakawa marasa lfy."
"Cak ķafafun sa suka tsaya a jikin ķofar ganin ta kwance lakwas har ta soma faďawa dan wahala hakan shi yaqara tashar masa da hankalin sa, zuciyar sa na bugawa sosai tamkar ya malle ta yakeji dan yanda yake masa raďaďin kuna, cikin iriyar muryan sa wacce ta soma canzawa tsantsan fargaba, ya buďi bakinsa yafara magana yace, Humaira karkice wannan mummunar lbrn da gaskene, pls humaira ki karyatar dasu kice ba hakaba bane, ki karyatar da abunda idanuna suke gani, bana zaton ko a mafarki zaki iya gigin zubar min da cikin da nafi son sa a yanzu.....
✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:11] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*50*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY* 💃🏾
Sosai cikin ta ke murďawa tasa hannu tana kamewa cikin jin azaba ga wasu irin maganganun sa da taji ya doki kunnuwan ta wanda bazata iya fassara su ba sun ďaure mata kanta sam ta rasa inda maganganun nasa suka nufa."
"Takowa yayi a hankali zuwa gareta ya zauna a bakin gadon da take kwance tareda kamo hannunta ya riqe cikin nasa yana murza ya tsunta, yakai dubansa gareta a lokacin ta jiyo da kanta zuwa setin fuskan shi suka haďa idanu da nasa, cikin jin zafin kullewar da cikin ta keyi ta runtse idanunta tareda buďe su, takasa iya qara haďa idanu dashi, ganin yanda yanayin ya sauya tasan da abunda ke cin zuciyar sa dukda surutan da yake a ďazu bata gane komai a cikin saba" Hannunsa ďayan yakai kan cikinta yafara shafawa har zuwa lokacin idanunsa yana kanta a hankali ya soma faďin, Humaira dan Allah kisanar dani gaskiya ina babynah yake, pls ki karyatar da abunda hannuna sukajiye min humaira babu komai acikin ki....shiru yayi ya dakata daga zancen da yake jin yanda ta riqe masa hannunsa gam dake kan cikinta yana shafawa."
A hankali ta buďi baki ta soma magana cikin qasa da murya tace, dear bangane ta ina maganganun ka suka dosa ba, me kake nufi da haka, ina zan kai maka babyn ka, pls kayi min bayani ka sakani a duhu, kodai wani abun ne yasamu ďan cikina bansani ba, dan Allah kafaďa min wlh irin maganganun da naji kanayi sun gama tsoratar dani nakasa iya fassara su....shiru tayi tana rumtse idanunta takasa qarasa maganar da take" sosai takejin murďan cikin kamar tayi yaya, wanda hakan ya sanya ta kasa daurewa cikin jin azaba tasaki ďan qara tareda damqe cikin ta sosai da hannayen ta duk biyu hawaye na zuba bisa kuncinta" Ganin yanda tabi ta dunkule waje ďaya tana fitar da numfashi sama sama hakan ya qara tashar masa da hankalin sa, cikin damuwa ya taso daga zaunan da yake ya matso zuwa kanta gemeda sa hannu ajikinta yana girgiza ta" Tambayar ta yake Amman takasa basa amsa sai murďewa da takeyi."
"Ganin wahalan da takesha har ta soma galabaita ya sanya shi sakinta, yakama hanyar fita daga ďakin, cikin sa'a yaci karo da doctor Ibrahim wanda ya duba ta jiya, yana shigowa dakin tareda norse kusa dashi" A tare suka Qarasa gareta doctor yashiga dubata, bayan yayi gwaje gwajen sa yace da Abdulmalik ya biyo sa office akwai maganar dazai tattauna dashi."
"Bayan doctor Ibrahim ďin yabi suka fice daga ďakin zuwa office ďin a yayin da nurse ďin ta tsaya dan bata kulawa."
"Bayan sun shiga cikin office ďin, Doctor Ibrahim yayi masa nuni da kujeran dake kallon nasa ya zauna, kafin ya soma yi masa bayani yace, a gaskiya alhaji wannan matar taka taji rauni sosai a cikin ta dole ne sai anyi mata wankin ciki da sauran su banda haka kuma mahaifan ta yasamu matsala zaiyi wuya tasamu wani cikin domin ba qarafin ciyo taji ba wajan zubewan cikin kasancewar cikin ya soma girma halittan dake cikin ta ya fita daga matsayin gudan jini ya soma zama mutum, so gaskiya saidai wani ikon Allah, dan haka yanzu kai muke jira musanar dakai kafin ayi mata wankin cikin" Shiru doctor Ibrahim ďin yayi bayan yagama maganar yana jiran yaji amsar sa a yayin da inbanda zufa babu abunda ke keto masa, tsantsan tashin hankali ya shiga zuciyar sa na masa zafi da wani irin kuna tamkar yayi kuka me sauti yakeji ko zai samu sassauci daga cikin zuciyar sa."
"Humaira kin cuceni kin cuci kanki kin aika babban kuskure a rayuwar ki" Cikin zuciyar sa yake maganar yaqara faďin Innalillahi wa inna ilaihi raji'un yana shafan kansa zuwa fuskan sa, damuwa qarara kwance bisa fuskan sa." Ganin da alamun baya cikin nutsuwar sa yashiga damuwa matuka hakan ya sanya Doctor Ibrahim tasowa daga nashi kujenan ya zagayo garesa yasa hannu biyu ya dafa kafaďun sa a hankali ya soma masa magana, yace, haquri zakayi alhaji Allah da yabaka wannan cikin kuma shi ya amshi abunsa, dan haka haquri zakayi ka rungumi Kaddara ka dogara dashi har zuwa wani lokacin da zai baka wani haifuwar, yanzu tashi muje asamu ayi mata wannan aikin tun kafin lokaci ya kure."
"Jikinsa babu kwari ko kaďan dakyar ya iya tashi tsaye suka fice daga office ďin, doctor yayi masa nunu da wani kujera dake kallon ďakin da take kwance, shi kuma ya wuce zuwa ďakin tareda da saka nurses Aka canza mata wani dakin wanda har lokacin tana cikin murďan cikin ta."
"Haka yaci gaba da zama a wajan yashiga tsantsan tahin hankali sosai ya rasa me yake masa daďi, a gogon hannunsa ya duba yaga karfe shabiyu ta wuce ana neman karfe ďaya" dan irin takaicin da yake ciki baiso ya kwana a asibitin ba Amman ba yanda ya iya dan ko wanne irin lokaci doctor zai iya neman sa yanayin condition ďin da take ciki."
"Bayan wasu lokaci bacci ne sama sama ya ďauke sa yana jingine da kujeran da yake kai doctor yazo ya samesa dan yayi masa magana ganin alamun bacci yake hakan ya sanya shi barin sa batare da ya tashe sa ba yasamu norse ďin da suke tare yayi mata umar nin da tana shiga mintuna mintuna tana dubo ta karta farka neman wani abun ba'a saniba tunda bacci take yanzu."
"Koda asuba tayi wajan karfe biyar, qiraye qirayen sallan da ake ya tashar dashi dukda bawai daďin baccin yaji ba ga sauro ga rashin daďin kwanciyar wajan ga tarin gajiya da yataru masa ajiki" Miqewa tsaye yayi ya fice dan yin alwala, bayan yasamu yayi alwala ya wuce masallaci."
"A nan ya zauna bayan an idar da sallan har garin tayi haske rana ta soma fitowa lokacin ana neman karfe bakwai" Barin masallaci yayi ya koma cikin asibitin" ďakin da take ya shiga ya hango ta idanunta a rufe da alamun bacci take har zuwa yanzu, hakan ya sanya shi barin ďakin bayan yaja mata ķofar ya rufe kai tsaye ya fice daga cikin asibitin tareda shigewa motar sa ya ďauki hanyar gidansu, zuciyar sa tunkushe da tunani iri iri damuwa fal a ransa tayi masa yawa, haka yaci gaba da tukin motar har ya isa gidan ya danna hon kusan so biyar a lokaci ďaya" cikin hanzari mai gadi ya taho ya buďe masa get ďin bayan ya leqa yaga ko waye."
"Yana shiga da motar yayi parking ďinta a tsakiyar filin gidan, bayan ya kashe motar tareda cire kay ďin kafin ya fice ya nufi bàngaran Abban sa kai tsaye" Yana dafda shiga parloun yaci karo da Batula tana fitowa cikin shirin ta na zuwa makaranta."
"Oyoyo yaya, tafaďa tana dariya ta qara cewa yaya yaushe agari ina Aunty humaira kwana biyu ma yau bansamu na leqa ta ba hope dai tana lfy,?" Mugun kallo ya watsa mata tareda binta da harara, yace ke riqe surutun ki bashine ya kawoni ba idan har kin damu kinason sanin lfyr ta kije ki dubata mana bawai ki tsareni a hanya kina tambaya taba kamar yar darija. "
"Yana kaiwa nan ya qarasa shigewa cikin parloun itama tabi bayansa tana zunbura baki" Abba ya tarar zaune qasan carpet ďin hannunsa riqe da news paper yana shan shayi Umma na zaune kusa dashi, ganin sa ya sanya ta sakin murmushi tana faďin a a ďan abuja yaushe agari haka,?" Shiru yayi mata baibi ta kanta ba a hankali ya qarasa ciki ya zauna kusa da jikin Abba tareda kifa kansa akan kujera yana saukar da numfashi."
"Cup ďin shayin dake hannunsa Abba ya ajiye tareda kawo dubansa garesa yasa hannu ya dafa kafaďar sa kafin ya soma magana cikin nutsuwa yace, babana ya akayi meke damunka haka naga ka shigo ba walwala tattare dakai ina fatan dai gidan lfy kabaro su,?"
"Abba, Humaira ta cuceni ta cuci rayuwa ta, tayi min irin abunda bazan tabà mancewa dashi ba har karshen rayuwa ta" Cikin wani irin yanayi mai wiyan misaltuwa yake maganar muryan sa a dashe tamkar mai shirin yin kuka, yaci gaba da cewa, Abba ka taimakeni ka tayani tambayar ta meye nayi mata a faďin duniyar nan meye na tabàyi mata nida yaro na kwalli ďaya tak wanda zai sanya ta yanke mana irin wannan mummunar hukuncin meye dalilin ta na aikata min haka,?"
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:11] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*51*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY* 💃🏾
"Cike da rashin fahimtar inda maganganun nasa suka nufa Abba yaqara dubansa a karo na biyu ya kuma cewa, Abdullah wai me yake damunka ne, kayi mana bayanin abunda ke faruwa mana ka saka mu a duhu, meye ita humairan tayi maka haka wanda ya shigar dakai irin wannan tashin hankalin,?"
"Abba, Humaira ce Wlh, itace ta cuceni ta zalunci rayuwa ta, wlh Abba bazan tabà yafe mata ba....cikin sauri Abba ya toshe masa bakinsa da hannun sa hakan ya katse shi daga maganganun da yake fitarwa cikin bakin sa" Abba ya soma faďin Innalillahi wainnailaiaihi raji'un Babana meye kake shirin yi haka, karkayi saurin yanke hukunci irin haka, a duk irin girman lefin da tayi maka haquri zakayi kasawa zuciyar ka ruwan sanyi, Allah ma munayi mishi lefi idan mun nemi gafara kuma ya yafe mana batareda yanke mana hukunci ba, bare ace ďan adam ajizi kullum yana cikin aikata zunubi, dan haka ka nutsu Babana, kasanar damu abunda tayi maka."
"Rufe idanunsa yayi wanda suka soma rinewa ya buďe su tareda sauķar da nauyayan ajiyan zuciya ya ďago da kansa wanda ya kifa jikin kujera kafin yakai dubansa kan Abba wanda yake kallon sa ya kura masa idanu har zuwa lokacin yana jiran yaji abunda zaice tayi masa."
"Cikin iriyar murya ya soma cewa, Abba humaira tayi min babban illah a cikin zuciya ta, ta cuceni Abba, Humaira ta zubar min da cikin da nafi son sa a yanzu wanda na ďauki tsawon lokaci ina jiran Allah yabani shi, gashi yabani Amman ta zubar min dashi Abba ta cuceni bansan meye nayi mata ba""Innalillahi Abba yaqara furtawa a hankali, a yayinda batula tayi mutuwar tsaye da jin wannan lbrn, wanda hakan shi yayi sanadiyar idanunta suka cika da kwalla."
"Cikin wani irin yanayi na fusata, Umma ta miqe tsaye tana tafa hannayenta, tareda zabga salati, abunda taji yafaďa ba qaramin tashar mata da hankali yayi ba, cikin ďaga sauti ta soma cewa."
"Shikenan ai tafaru ta qare ya rinya ta cuce mu ta zalunce mu, ni dama wlh kamar nasan za'ayi haka, yanda naga dama bata kula da wannan cikin nasan da abunda ta kulla a cikin cikinta kar nayi saurin magana kuce min tsanar ta da nayi ne, Amman wlh kallo ďaya tak nayi mata nasan cewa munafuka ce yar kisan kai ce, shegiyar yarinya, wlh bazan tabà yafe mata ba, jikina da ta zubar min, sai Allah yayi mana hisabi wlh a ranar gobe qiyama.... Shiru tayi tana huci ta koma ta zauna kan kujera takai idanunta kan Abdulmalik dake zaune yayi shiru abun yana ci masa ransa, cikin ďaga sauti tana nuna shi da yatsar hannunta taci gaba da cewa, ai wlh ba ita bace da lefi kaine jarababbe mai shegen kwashe kwashen yan matan tsiya ko wacce aljanar ya rinyar da idanun ka suka gani sai kace kanaso zaka aura saikace na mamajo haifaffan ďan garin zariya ga yan matan arziki na Allah da manzon sa yan gidan mutunci wanda suka san waye Allah meye hukuncin addini an baka su kasa kafa ka tsallake su dan tsabagen ruwan idon tsiya, shikenan ai ga irinta nan wai anyiwa mai zani ďaya sata, gashi yanzu wa gari ya waya, ta shigar dakai cikin asara, gobe ma idan ance maka ga haske ka tsallake kace duhu zaka shiga wanda a wannan lokakin kuwa saidai ka kalli fankon gawar ka a barzagu, kuma wlh inaso kasan cewa yanzu kam haquri na yaqare akan wannan yar iskar auran subaiba wajibi ne dolene, kuma saki uku shima dole ne kayi ma wannan shaiďaniyar dan.....
"Tsawan da taji Abba ya ďaga matane yayi sanadiyar dakatar da ita daga maganar da takeyi."
"Cike da fusata yashiga mata faďa cikin masifa yace waike meke damunki ne, zakibar yaro yaji da abunda da damuwar da yake cin sa ne ko kuwa zaki tsaya kina qara rura masa wani damuwar, to wlh bara'atu inason ki ajiye min hankalin ki kibar ganin inayin shiru kinayi abunda kikaga dama idan raina ya bàci bazakiji daďi ba dan haka kiyi shiru karna kumajin kin kuma cewa komai tunda ke bakin ki baisan ambaton alkhairi ba."
"Kanta ta kawar gefe guda tana gunagune tareda ďaura ķafa ďaya kan ďaya tana girgizawa ita kaďai tasan mai zata shirya cikin zuciyar ta dan ya zame mata dole ne ta ďauki kwakkwaran mataki akan wannan lamarin idan ba
hakaba nan gaba kaďan saidai ta kashe mata ďanta kwalli ďaya tanaji tana gani."
Dawo da dubansan kan Abdulmalik, Abba yayi, cikin lumana yashiga lallashin sa tareda faďa masa kalamai masu kwantar da hankali" Saida ya tabbatar da nutsuwar ta dawo jikin sa kafin ya miqe tsaye yana gyaran rigar jikinsa dan zuwa suje su duba lfyr ta, tunda ko bakomai kamar ďiya take agareshi tunda kusan abokai shida mahaifin ta suke banda hakama auran ďansa take surukace a garesa, duk irin lefin da tayi baici ace shima ya juya mata baya ba idan yayi haka baiyi ma mahaifin ta adalci ba."
"Dakyar yayi convincing Abdulmalik akan da ya tashi yakai su wajan ta tunda su basanin wanne asbitin take ba da kuma ďakin da aka Kwantar da ita sukayi ba" Haka badan yaso ba ya tashi suka fice tare da Abba, Batula ma tabi bayan su zuciyar ta babu daďi ita sam takasa amincewa da humaira zata zubar da cikin ta da gangan saidai ace wani hatsarin ne ya afku mata, zuciyar ta yakasa aminta da wannan zancen dukda tasan tana maganar kan cewa zuwan cikin nan yayi sanadiyar rashin komawar ta makaranta hakan bazai iya sanya ta aikata wannan babban zunubin ba, dan itakam tana mata kallon mai hankali da ilimin addini saidai ta hana wani ma Amman ba wai Ita tayi da kanta ba."
"Umma tanajin qaran motar su suka fice daga gidan ko gigin binsu batayi ba, sanin ba binsu zatayi ba ya sanya Abba kinqi kulata baice da ita su tafi ba" daman ita tun farko ta tsaneta bare kuma da yanzu ta aikata musu wannan mummunar abu hakan yaqara rura mata wutar tsanar ta a cikin zuciyar ta."
"A zaune take akan kujenan Amman ji take tamkar anbi qasan kujenan da allure suna cokin ta, kasa zaman tayi ta miqe tsaye ta soma safa da marwa cikin parloun tunani iri iri fal cikin ranta, ta ďauki alwashin ko shi yayi mata saki uku a lokaci ďaya tabar gidan ko kuwa ita tayi mata nata sakin tayi mata korar kare a wannan lokakin dole ya auri ya rinyar da takeso babu makawa tunda sun rabu da shegiya."
"Cak tunanin ta suka tsaya mata cikin ranta, tana girgiza kai alamun hakan da zatayi shine kaďai mafita a gareta, haka ta fice a parloun tayi nata bàngaran kai tsaye ta shige kitchen dan haďa musu karin kumullo kafin su dawo tunda itama Batulan kwasan ķafa tayi ta bisu ita kuwa suwaiba na cikin ďaki tana sharar baccin ta, daman bawai kwarewa a dafa abincin batayi ba bare ace ita tayi musu idan ma anbarta tayi saidai a wannan ranar aci kwabàbbàn abinci."
"Koda suka isa cikin asibitin bayan yasamu waje yayi parking motar kafin suka sauka suka nufi ciki, yana tafe a gaban su yayi musu jagora har zuwa ďakin da aka kwantar da ita."
"Tana nan kwance har zuwa wannan lokacin idanunta suna rufe da alamun ko farkawa batayi ba daga baccin da take" A hankali Abba ya qarasa zuwa gareta Batula na biye dashi a baya ya tsaya dafda kanta tareda aza hannun sa bisa koshin ta, cikin sauri ya ďauke hannunsa, sanadiyar wani irin mugun zafi tamkar wutan garwashi da yaji daga kan koshin ta ya ďane masa hannu" Subuhanallah ya furta cikin bakin sa a hankali gameda karanto mata addu'ar marasa lfy sosai tausayin ta ya sauķa masa a cikin zuciyar sa matuqa ganin irin yanda tabi duk tafaďa ciki ta rame sosai fuskanta fayau dashi bakin nan har ya bushe tamkar wanda ta shekara batasamu shan wani abu ruwa ko cin abinci ba."
"Kujeran dake cikin ďakin wanda aka tanada shi dan zaman masu dubiya, shi Abba yaja baya ya zauna akai yana saukar da ajiyan zuciya mamaki ya ishi zuciyar sa na kan cewa wai humaira ce ta zubar da cikin ta, to idan hakane ma meye hujjar ta akan hakan, sam cikin ransa yakasa gasgata wannan maganar, dukda kuwa ko wanne ďan adam ajizi ne a koda yaushe zai iya aikata lefi, wanda bakayi tunanin zai aikata mummunar abu ba shine zakaga ya aikata, wanda kuma kake tunanin zai aikata mummunar abu shine zakaga bai aikata ba."
"Zama a bakin gadon Batula tayi gameda dafan hannunta tana shafawa a hankali, ji take tausayin tsantsa ya mamaye mata cikin zuciya, tamkar tayi kuka takeji a halin yanzu."
"Sun dauki ďan tsawon lokaci suna cikin ďakin a zaune wanda a lokacin shima Abdulmalik yagaji da tsayuwa ya matsa kusa da kujeran da Abba ke kai ya zauna gameda da zabga tagumi har izuwa lokacin yanajin zuciyar sa tana masa kuna."
"Ganin garin rana ta gama fitowa lokacin ana neman karfe taran safe, kuma bata farka ba har yanzu baccin take, hakan ya sanya Abba tashi tsaye yace da Abdulmalik ya mayar dasu gida tunda bata farka ba har yanzu idan yaso ko anjima ya kuma zuwa ya dubata."
"Ganin idan sun tafi ita kaďai zasu bari a ďakin babu wani na kusa da ita wanda zai kula da ita a halin yanzu idan ta farka, hakan ya sanya Batula cewa Abba su tafi ita zata zauna da ita tana duba lfyr ta har zuwa lokacin da zata farka" Barin ta Abba yayi shi yafice daga ďakin Abdulmalik yabi bayan sa dan mayar dashi gida idan yaso shima ya koma nashi gidan dan yasamu yayi wanka ya huta gajiyar dake jikinsa dukda bawai daďin yanayin da jikinsa yake ciki yakeji ba" Haka batula ta zauna kusa da ita tareda zabga tagumi ta kura mata idanu tamkar yau ta soma saninta, tana jiran ganin farkawanta
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:11] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*52*
"Ta ďauki tsawon lokaci babu lefi tana wannan baccin har kusan wajan karfe shabiyu da mintuna wanda a wannan time ďin ana neman karfe ďaya wasu masallacan ma an soma qiraye qirayen sallan azahar" Har izuwa lokacin Batula ce zaune kusa da ita a kan kujera tana jiran ganin farkawan ta" A hankali ta soma buďe idanunta tamkar makauiya take buďe su, tun tana ganin dishi dishi har ta soma kallo mai kyau" a hankali ta jiyo da idanunta wanda suka qanqance dan wahala ta sauķe su kan na Batula, a yayinda dan tsaban farin cikin ganin ta farka ya sanya Batula washe baki tana dariya gameda godewa Allah tasa hannunta cikin nata ta riqe gam a lokacin da humaira ta saķar mata da murmushin karfin hali tareda lumshe idanunta ta buďe su, cikin qasa da murya ta soma magana a hankali tace, Batula meye yasamu cikin dake jikina, meye naji yayanki yana magana akan cewa na cuce shi na zalince shi ""Dan Allah ki sanar dani abunda ke faruwa, maganganun sa sun gama tsoratar min da zuciya ta bansan me yake nufi da hakaba."
"Qara dantse hannunta cikin na humaira tayi tareda zuba mata ido tanayi mata kallon tausayi ganin yanda ta jero mata da tambayoyin tamkar me shirin yin kuka" a hankali ta sauķar da ajiyan zuciya tana runtse idanunta ta soma cewa."
"Aunty humaira ni dama nasan saidai ayi miki sharri Amman bazaki aikata wannan mummunar abunda yaya yazo mana dashi ba na cewa wai kin cuceshi kin zubar masa da cikin sa, na tabbata tsabàni aka samu but i know humaira u can never do something like that, na aminta dake ďari bisa ďari dan haka ki kwantar da hankalin ki ki sanar dani tayaya hakan tafaru har kika rasa kyautar da Allah yabaki."
"Wasu irin zafafan hawaye ne taji ya gangaro mata bisa kuncin ta, ba shiri ta shiga yin kuka me cin zuciyar mai sauraro, babu tagama qaddamarwa a ranta shikenan cikin ta ya zube ta rasa kyautar da Allah yabata" Cikin muryan kuka ta soma cewa, Batula ban zubar da cikin dake jikina da gangan ba, wlh ko kasheni za'ayi bazan tabà iya zubar da kyautar da Allah yabani, I know I can remember farkon lokacin da Allah yabani wannan cikin banyi farin cikin zuwan sa ba dan ina tunanin zai iya hanani ci gaba da karatuna, but not now da ya ďauki tsawon kusan four months ina renonsa soyayyar sa ya shige min cikin zuciya ta na shakaqu dashi matuka ace kuma wai yanzu rana tsaka dare ďaya na zubar dashi tamkar wacce banida imani bansan Allah ba."
"Cikin kuka sosai take maganar tana shashsheqa taci gaba da cewa, Batula duk rashin tsoron ubangiji na bazan tabà iya kashe ran koda dabba ba bare ace na mutum jariri wanda ko gama zama cikekken halitta baiyi ba ace na kashe shi, Sam bazan iya aikata irin makamancin hakaba, idan zan iya tunawa lokacin dana kammala haďa abincin da zanci I was very hungry a wannan time ďin nazo zan shigo cikin parlou ban kula da gabana ba tsantsin wani abu ya kwashe bansan kona meye ba sosai nafaďi akan cikina matuka ba makawa naji ciyo sosai tun ina iya juyawa ina murqususu gameda ķoķarin naga natashi Amman abun ya farkara har karfina ya kare daga nan ban kuma sanin inda kaina yakeba saida na ganni kwance bisa gadon asibiti da wasu irin rikitattun maganganun da naji yana fitowa daga bakinsa, bansan meye akace masa ba game dani har yake ganin zan iya kashe masa jininsa......
"Shiru tayi ta kasa cigaba da maganganun da take, a yayinda idanun Batula sun gama cikewa da hawaye tsantsan tausayin ta, ita dama tasan saidai wani abun Amman sam bata yarda kan cewa humaira zata aikata irin hakaba" a hankali ta ďaura hannunta kan fuskan humaira bayan ta saki nata cikin hannun ta soma share mata hawayen da suka wanke mata fuska tana faďin, kiyi shiru ya isa haka wannan kukan kisa Allah a zuciyar ki idan ma mai wannan aika aikan yayi hakane dan ya shiga tsakanin ki da mijinki ya rabaki da shi to da izinin Allah saidai sharrin sa ya koma kansa Amman bazai tabàyin tasiri a kanki ba, dan haka stop crying pls kinji Allah zai mayar maki da wani mafi alkhairi."
"Kanta ta daura jikin na humaira tanajin ta tana shashsheqar kuka har zuwa iyanzu
taci gaba da lallashin ta, wanda a wannan lokakin yana jingine da jikin ķofar ďakin ya buďe zai shigo kenan maganganun da suke ya sauķa cikin tsakiyar kunnuwan sa hakan ya sanya shi fasa shigowa yayi tsayuwar sa bakin ķofar yana sauraran duk abunda suke cewa."
"Nauyayyan ajiyan zuciya ya sauķe yaqarasa shiga cikin ďakin a hankali ya taka zuwa garesu, jin alamun motsin mutum cikin ďakin ya sanya ta buďe raunannun idanunta ta sauke su kan nashi, cikin sauri ta mayar da idanunta gefe guda tana kallon qasa zuciyar ta yana bugawa sosai cikin ranta take faďin Allah yasa ya amince da ita ya yarda kan cewa ita baza cucesa ba har qarshen raguwar ta, bazata tabà gigin zubar masa da cikin sa dake qunshe ajikinta ba."
"Kanta Batula ta ďago wanda ta kifa shi jikin humaira, ganin sa tsaye a kansu ya sanya ta saurin miqewa daga kan kujeran gameda matsa masa kaďan daga wajan dan ya zauna, tana goge hawayen dake fuskanta tace sannu yaya har ka dawo,?"
"Kansa kawai ya girgiza mata alaman Eh yaja kujeran da ta tashi akai ya zauna gameda zubawa humaira idanunsa yana kallon ta tamkar sabuwar abu yake gani ta canza masa matuqa tayi fayau da ita sai qashin wiyar ta da yaqara fitowa dama tana dashi kaďan bare yanzu da bata da lfy raman da tayi yaqara fitar dashi waje."
"Hannunsa ya ďaga yakai kan goshin ta yana shafawa har zuwa wiyar ta yaji rau zafi sosai da alamun zazzabi ne ya rufeta, jin hannunsa jikin wiyar ta da tayi ya sanyar mata da jiki a hankali ta ďago da idanunta ta shigar dashi cikin nashi tana kallon sa ta soma magana tace pls ka aminta dani ban zubar maka da cikin ka dake jikina ba wlh ban..... toshe mata bakinta yayi da hannunsa yace mata shiiiiiit alamun tayi masa shiru bayason jin wata magana, hakan shi ya hanata qarasa maganar da takeyi."
"Yana kallon cikin kwayar idanunta yace da ita, yauwa to sannu aljazeera zakifara surutun da kika kwana biyu bakiyi ba kenan, yanzu ma bakida lfy surutun yana cinki sai kinyi shi ina kuma da kin samu lfy kin gama warwarewa.. yaya a wannan lokakin kam inaga saidai mu toshe kunnuwan mu idan ba hakaba zata iya lalata mana dodon kunne."" Cewar batula dake kallon su tana dariya, Humaira ta jiyo da kanta ta cilla mata harara cikin haďe rai hakan ya sanya Batula gimtse dariyar ta."
"Yana kanta yana zaune jin anata qiraye qirayen sallan azahar ya sanya shi cewa Batula da taje gida ta haďo ma humaira abinci shi zai fita yayi sallah daga nan sai ya wuce wajan likita ya amso mata magunguna ganin yanda zazzabì ya rufeta" amsa masa batula tayi da to kafin ta fice a ďakin shima yabi bayan ta tareda yajan ķofar ďakin ya rufe."
**
Sanda Batula ta isa gida kai tsaye kitchen ta shige dan ta haďa abincin cikin sa'a tasamu har an kammala dafa abincin rana ko ba'a faďa mata ba tasan Umma ce ta girka, ganin farar shinkafa ce da jar miya hakan ya sanya ta ďaukar kula madaidaici ta ďiba, bayan ta kammala ďibawa ta sakasu cikin basket, dama jiya da daddare ta siya balangun ta akan zataci sai kuma bataci ba ta kawo ta ajije a freezer, hakan yasa yanzu ta ďauka ta juye shi cikin tukunya yayi zafi kafin ta samu abu qarami ta zuba aciki ta haďa da su plate da cokala da ruwan sha duka cikin basket ďaya, bayan ta gama haďawa ta fice daga kitchen ta wuce ďaki dan yin sallah" Suwaiba tagani kwance sai sharar bacci take tana munshari tamkar wacce tayi aiki ta gaji" kai batula ta girgiza ta shige toilet ta ďauro alwala kafin ta fito ta gabatar da sallah" Bayan ta idar da sallan ta zari mayafin ta tareda ďaukan basket ďin tafice cikin sauri daga dakin, har ta kammala komi tafita, Suwaiba bataji motsin taba tanata sharan baccinta hankali kwance."
"Koda tafita daga parloun tana dafda ficewa daga get ďin gidan tajiyo muryan Umma ta bayanta tafito daga bàgaren Abba" cikin tsawa bayan ta qaraso inda take tsaye tace mata dakata ja'irar yarinya mai shegen yawo tsiya saikace kinci ķafar kare ina zaki qara zuwa bayan fitan da kikayi ďazu kuma miye wannan hannunki,?"
"Kumbura fuska batula tayi cikin takaici, ta jiyo ta kalli Umma yanda ta kura mata idanu, tace kai haba mana umma bafa ko ina zanje ba yaya ne ya aiko ni yace nazo na kaiwa humaira abincin tunda ta farka.....bata barta taqara maganar ba ta katse ta da tsawa cikin nuna bàcin rai tace kutuma bani abinci na" Tasa hannu ta warce basket ďin dake riqe a hannunta kafin ta qara jefar ta da mugun kallo a karo na biyu tace, Batula bakida hankali wlh na kula bason zaman lfy kikeba neman tashin hankali na kike, da yake ni kuka ajiye boyiboyin ku a gidan shegu yan iska ke kin ďauki ķafa kin tafi gantalin banza da wofi inda bai shafeki ba, ita kuma suwaiban asararriya yarinya tana can tana sharan baccin asara, batasan ma meye duniyar take ciki ba, natashi da kaina na ďaura girki ke gaki mai tsaurin idon tsiya kenan marar kunya har kinda karfin halin da zaki shigo min kitchen ki ďibi abincin da na girka kice wani wai yaya ne yace kizo ki kaiwa wata shegiyar daban abinci, to ba yaya ba yayo."
"Cikin qara ďagun murya ta qara cewa to bari ma kiji wlh abinci ba'a gidan nan ba, sam bazata sadu ba allura a ruwa, yanada gida yanada kayan abinci tunda ke kinga zaki iya ďaukar wannan wahalan zaki iya zuwa can gidan nasa ki girka mata Amman ba'a gida na ba kuma ba'a abincin da na girka ba" tana kaiwan nan daga maganar da take ta juya da niyar komawa ciki tana qara faďin shegiyar yarinya kawai ja'ira......
"Cak ķafafun ta suka tsaya tayi shiru da baķin ta sanadiyar Abba da tagani yana qarasowa garesu cikin haďa fuska" Batula tana kallon sa tayi saurin zuwa wajan sa, cikin fushi da fuska tace, yauwa Abba gwarama da kafito wlh kaga Umma kawai dan na ďauki abincin zan kaiwa humaira ta farka, shine ta warce abincin wai bazan kaiba, dan Allah Abba kayi mata magana wlh ni yaya yake jira tuntuni ta farka"" cike da shagwabè fuska ta qarashe maganar a yayinda Abba ya qarasa inda Umma ke tsaye rai a haďe yace bani abincin" Ba musu ta miqa masa tana gunagune ta shige ciki yana jinta tana cewa wlh saidai ka zauna da yunwa dan rabon ka kabasu."
"Baice da ita qalaba har ta shige tana surutai, cikin takaici da irin hali nata ya girgiza kansa kafin yazo ya miqawa Batula basket ďin abincin yace da ita ta gaishe da humaira shima yana nan tafe anjima idan yamma tayi rana tayi sanyi." amsar basket ďin tayi daga hannunsa gameda amsa masa da to kafin ta fice a gidan shi kuma ya koma ciki."
"Koda ta isa asbitin bayan ta kwankwasan ķofar ďakin kafin ta shiga tareda yin sallama" zaune kan kujera ta hango sa yana latsar wayar sa dake riqe a hannunsa, Humaira kuma na kwance har zuwa lokacin ta juya masa baya" ganin ta ne ya dakatar da shi daga latsa wayar da yake ya mayar cikin aljihun sa gameda da yi mata umarnin da ta zuba mata abincin ta taci."
"kan ďan wani table ta samu ta ajiye basket ďin kafin ta ďauki plate ta zuba farar shinkafar kaďan ta zuba jar miyar ma akai tareda zuba balangun a gefen abincin ta mayar da sauran ta rufe kafin ta qarasa kusa da ita gameda qiran sunan ta ta miqe dakyar ta jinginu da jikin bango numfashin ta na fita sama sama wahaye na zubo mata A fuska dan yanda takejin zazzabìn yana cin jikinta."
"Dakyar batula ta lallashe ta taci abincin ďan kaďan shima saida yasa baki kafin ta iya ci a dole suka bata magungunan tasha dakyar shima tana sha tana ķoķarin yin amai" Bayan sun gama da bata magungunan, Batula ta gyara mata kwanciyar ta kafin ta ďauke plate ďin a wajan, shi kuma ya fice a ďakin yace mata zaije dawo anjima kafin ta koma gida."
****** ******
"Haka humaira tayi jinyar kusan sati ďaya da wasu kwanaki a wannan asibitin duk batula ce ke kwana da ita tana bata duk wani kulawa da marasa lfy suke bukata, sam bata komawa gida sai idan Abdulmalik yazo takan tafiya gida tayi wanka ta ďauka musu abunda zasu bukata dukda shima bawai zuwa yake akai akai yana wuni ba saidai ya leqo yaga yanda take ya fice shi ďin ma yana yin hakan ne dan tunawa da yayi hakkinta dake kansa bai kamata ya juya mata baya ba a halin da take ciki a yanzu Amman cikin zuciyar sa sam ya kasa amincewa da cewa da tayi bata zubar da cikin nan ba faďiwa tayi, shi kuma ya rasa gane wannan wani irin mugun faďiwa tayi da har zaiyi sanadiyar zubewar yaron sa, sam hankalin sa ta kasa ďaukar wannan zancen, saqon da yaga Maraqishiya ta tura masa shi zuciyar sa tafi aminta dashi tunda dama tun farko yasan bason cikin takeyi ba makaranta takeson ta koma, kawai dai ta zauna dashi ne a matsayin dole dan ya jajirce mata....
✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:11] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*53*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*
"Abba ma haka yakan zuwa dubata akai akai dan yaga yaya jikin nata yake, kullum idan zai zo asibitin sai ya tabbatar da yayi mata siyayyar kayan ciye ciye dasu fruits"" Umma kam dama ba'a maganar ta domin tunda hakan yafaru inbanda tura saqon tsinuwa babu abunda take aikawa humaira domin kuwa a wannan lokakin ne taji tsantsan tsanar ta yaqara dasuwa cikin zuciyar ta wanda bata tabà yima wani mahaluqin ďan adam mutum irin hakaba, ji take yanda abun ke ci mata a rai idan ba samu tayi ta amayar dashi ba zai iya haddasa mata ciwon zuciya dukda hakan ma wani rana saida taje gidan Abdulmalik ďin ta tarar da Maraqishiya ita ďaya a gidan tamkar mayya, dukda itama dai ba sonta take ba cikin zuciyar ta Amman gani take tafi mata akan humaira."
"Abun nema yasamu matar driver ta haifi taya dubun su goma ya huta, haka shine yafaru da Maraqishiya a lokacin da taga umma acikin yanda taga yanayin fuskan ta tagane cewa ba lfy, cikin makirci irin nata kuwa tasamu kan Umma ta zazzaga mata karya da gaskiya akan zubewar cikin humaira, babu abunda ke fita a bakinta tamkar tsinuwa da ďaukan alwashin cewa kota halin qaqa sai tayi mata korar kare a cikin gidan tareda cusa tsanar ta a cikin zuciyar Abdulmalik, hakan da Maraqishiya taji Ummar tafaďa ba qaramin farin ciki yaqara jefata ba, bayan Umma tabar gidan ta ďauki wayar ta gameda qiran shiwari ta zazzaga mata yanda sukayi da Umma a yanzu."
"Hankalin ta sam yakasa kwanciya saida tabi tana ta yaďa abunda shegiyar matar ďanta tayi, tasamu qanwarta hajiya zulai ta bata lbrn abunda yafaru, hajiya zulai tayi baķin cikin jin hakan matuqa, hakan ba qaramin ingiza mata rai yayi ba" koda najeeb da matar sa Zaliha sukaji lbrn hakan sunyi matuqar tausayawa Abdulmalik domin sun san yanda yakeson haifuwa shima yaga yaron sa wanda ya haifa Amman gashi hakan bai iyuba, dukda suna mamakin jin cewa wai humaira da gangan ta zubar da cikin, hakan bai hana najeeb zuwa asibitin yaga ya takeba dukda bawai shaquwa sukayi da ita ba amatsayin matar yayan shi Amman ya yaba da halinta zuciyar sa takasa aminta da hakan" Zaliha kam a dole take binshi suje asibitin badan ranta yaso ba dan dama jininta sam bai ďauki na humaira ba dan aqalla zata iya cewa duk lokacin da suka haďu a gidan umma hira bata shiga tsakanin su, dan haka yanzu ma da taji hakan baki ta cura cikin zuciyar ta tace dama zata aikata ance idan kaga mutum ďan adam to kabarshi a yanda yake dan da zakaji abunda za'ace maka gashi ya aikata wani abu ko kuma yana aikatawa, zaka iya musawa."
"Koda doctor ya tabbatar da cewa tasamu lfy sosai kuma zazzabìn da ya rufeta shima yabarta a yanzu ta ware ba wani waje nata dake ciwo, hakan ya sanya shi rubuta musu takardar sallama yabasu" a lokacin da aka sallameta Batula ce tareda da ita yauma kamar kullum sai Abdulmalik" cikin hanzari batula duk ta harhaďa musu kayan su, suka fice a ďakin, suka iso zuwa haraban asibitin inda yayi parking motar."
"Mazaunin bayan motar Humaira ta buďe ta shiga batula kuma ta shige mazaunin gaba Amman badan ranta yaso hakan ba, dan ita anata taso humaira ta zauna a gidan gaba dan yanda taga tsakanin su babu sakin fuska har yanzu musamman shi Abdulmalik da bakasafai ma yake mata magana ba, idan yayi maganar ma takama sane Amman badan yanada niyar yi ba, aqalla idan ta duba zata iya irga iya maganar da tashiga tsakanin su."
"Koda suka shige cikin motar Abdulmalik ya figi motar yayi hanyar gida dasu" suna isa bayan mai gadi ya buďe masa get ya shiga, yasamu waje yayi parking kafin suka fito daga cikin motar, Humaira jiki a sanyaye batayi magana ba ta qarasa zuwa cikin parloun tana riqe da wasu kayan a hannunta, Batula ma ta tsaya ta kwashi sauran kayan da sukazo dashi kafin tabi bayan ta."
Tun daga baķin ķofar parloun sukayi harba'a da muryan Maraqishiya cikin parloun tana kwasan dariya tamkar kace zararriya tazama, ga dukkan alamu yanda sukaji ta sunsan hira take a waya dan bakajin muryan kowa sai nata dukda kuwa ga qaran muryan TV natashi wanda ya kure cikin parloun Amman hakan be hana muryan ta fitowa sosai ba."
"Ganin haka ya sanya humaira qarasa shigewa a hankali kanta a qasa tamkar batasan akwai mutum cikin parloun ba ta qarasa zuwa baķin ķofar ďakin ta gameda tsimayar qararowar batula dan tabuďe mata ķofar da yake sanda take kwance bisa asibiti itace tazo ta kulle mata ďakin, tareda ďauko mata phone ďinta ta kai mata kitchen kam dama tun ranar da tayi wannan faďiwar ta kulle shi saidai kawai makullin da shima yafaďi a wajan, shine take zaton ko yana wajan Maraqishiya tunda itace a gidan."
"Ba komai bane ya hana humaira kula Maraqishiya ba illah tunawa da tayi, itace sanadiyar mijinta yayi tafiya da tsantsan fishinta a zuciyar sa, akan ace yatafi cikin walwala da nishaďi, hakan shi ya haddasa mata baķin ciki a zuciyar ta, dan aqalla idan ta tuna ba qaramin cutar ta tayi ba saidai kawai Allah ya saka mata itama kuma tasa hankali akan komai nata nan gaba dan babu tagama aiyyanawa a ranta zama tsakanin su zai zama da zargi dan ba yarda zata qarayi da ita ba."
"Haka Batula ma tayi wucewar ta a parloun tazo ta iske humaira a bakin ķofar bateda ta ďaga ido ta kalli inda Maraqishiya ke zaune ba dan mugun haushin ta da takeji."
Tana mata murmushi ta buďe musu ķofar suka shige tareda rufo ķofar, a yayinda idanun Maraqishiya ke kan ķofar ďakin dama tunda taga shigowar su take binsu da muguwar harara wacce zaka kasa gane irinsa tamkar abokan gaba musamman tsakanin ta da batula dama basa shiri tunda ta auri yayanta Abdulmalik jinin su bai ďauki na juna ba duk cikin su saidai siyama da take babba sama da batula itace wacce ke shigewa qarqashin Maraqishiya ganin irin halayyar ta suna burgeta hakan yasa da Aunty ma take qiranta kullum idan bawai a makaranta takeba idan tana gida to akoda yaushe tana tareda Maraqishiya."
"Suna shiga cikin ďakin humaira kai tsaye ta shige cikin toilet dan tasamu ta watsawa jikinta ruwa mai zafi ko zataji daďin sa, ganin haka ya sanya Batula ajiye kayan da tashigo dashi a hannunta ta fice a ďakin tayi bayan gidan zuwa inda kitchen ďin humaira yake."
Buďe ta tarar da ķofar an maqala makullin ajiki, mamaki ne matuka yakamata ta shiga tambayar zuciyar ta shin humaira ce ta mance makullin ajiki tabar ķofar abuďe har tsawon kusan sati biyu ko yaya"?
"Can tayi shiru tana nazari cikin zuciyar ta ganin bamai bata amsa zata samu ba ya sanya ta qarasa shigewa kitchen ďin, batare da bàta lokaci ba ta girka musu jalof ďin supargeti haďaďďai sai ķàmshi ke tashi cikin sa" Bayan ta kammala juyewa cikin kula ta tsaya ta gyara kitchen ďin inda yabàci kafin ta ďauki plate da fork ta fice a kitchen ďin ta nufi ciki bayan da ta tabbatar da ta kulle ķofar ta zare makullin ajiki."
"Koda ta dawo cikin ďakin humaira ta tarar zaune bisa sallaya alamun sallah tayi jin anata qiraye qirayen sallah ta ko ina na la'asa, cikin zolaya batula ta qarasa gareta tana faďin, To matar malam ustaziya ai sai kicire hijabin naki ki matso muci abinci dan nasan kinajin yunwa matuqa" Murmushi humaira tayi cikin sakin fuskan ta wanda yake a ďan rame har izuwa yanzu, batareda tace komai ba ta matso kusa da ita bayan ta cire hijamin dake jikinta."
Sanadiyar batula ita ba sallan takeyiba tana cikin hutu yasa ta zuba musu a plate ďaya suka soma ci cikin nishaďi sama sama suke tabà hiran su suna dariya."
"Suna tsaka da cin abincin ne Abdulmalik ya turo ķofar ďakin ya shigo bakinsa ďauke da sallama, suka amsa masa ya qarasa garesu inda suke zaune shima ya zauna dama yunwa yakeji yana tunanin zuwa gida yaci abinci can tunda ita Maraqishiya ta jajirce masa bazataci daba dayin aikin wahala ba tunda ba ita bace da girki yau, wanda tayi masa a baya ma taimaka masa tayi dan haka tunda yanzu ta dawo sai taci gaba da aikinta"" batareda yayiwa ko wannan su magana ba ya ďauki plate ya ďiba abincin kafin ya ďauka ya fice a ďakin, Humaira da batula suka bishi da idanu, ganin tamkar shi yadafa abincin kawai yazo yasa musu hannu ya ďiba babu ko magana."
Ajiyan zuciya humaira ta sauke gameda ci gaba da cin abincin ta tana maganar zuci."
"Bayan sun kammala da cin abincin ne batula ta tattare wajan gameda kaiwa kayan zuwa kitchen ta ďauraye su kafin ta dawo ďakin inda humaira ke kwance bisa gado fuskan ta da alamun damuwa qarara, ganin irin halin da tashiga ne ya sanya Batula taji tausayin ta yaqara shigar mata zuciya tasan ba komai bane ya shgar da ita wannan damuwar face fishin da Abdulmalik keyi da ita akan zubewar wannan cikin."
"Cike da sanyin jiki ta qarasa zuwa gareta ta zauna a bakin gadon tareda dafa kafaďar ta tashiga lallashin ta tana gaya mata tausasan maganganun da zasu kwantar mata da hankali tareda bata shawarwari akan yanda zatayi ta dawo da hankalin sa gareta har ya amince da ita akaro na biyu."
"Saida Batula ta tabbatar da hankalin ta ya kwanta tasamu nutsuwa kafin tayi mata sallama ta koma gida akan cewa gobe insha Allahu idan ta tashi a school zata biyo mata dan taqara duban lfyr ta da yanda take."
****** ******
"Kamar yanda batula tabata sharwari akan yanda zatayi hakan tayi, kullum sai tayi iya qoqarin ta na ganin ya aminta da ita Amman abun ya faskara acikin kwanakin da suka ďauka suna tare agidan sam baya sake mata fuska akoda yaushe idan tazo ta zauna a kusa dashi dan su fuskanci juna, tana soma magana saidai taga yatashi yabar mata wajan batareda ya kulata ba, wani lokacin kuwa tsawan gaske yake ďaga mata tamkar yasamu yar qanwar sa akan ta tashi tabar masa guri idan baso take taga bàcin ransa ba."
"Haka jiki a sanyaye babu guzari zata bar masa wajan batareda tace masa qala ba"" idan kwanan ďakinta ne kuwa yazo, ranar acikin baķin ciki da zafin zuciya take kwana dan kuwa koda abinci ta girka masa bayabi takanta barema har ya zauna yaci, dama tun a hanyar sa ta dawowa yake wucewa gidansu yaci abinci tareda Abba a wannan lokakin cikin surutan Umma marasa daďin ji yake kammala cin abincin har yabar gidan kafin yake samun sukuni...
✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:11] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*54*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*
"Yau lahadi ya kasance itace da karbàn girki, ganin irin yanda har izuwa wannan lokakin bayan faruwan wannan lamarin yana cikin fishi da ita bai daina ba baya sakar mata da fuska saima a duk lokacin da ta tun kareshi tamkar qara ingiza shi akeyi akanta sai ya haura mata da bambami tamkar bashi ba idan ya soma mata faďa, dan haka yasa yau ta ďauki alwashin cewa saidai suyita taqare yau ko ita ko shi dan tagaji da zaman haquri irin wannan."
"Tun safe bayan ta tashi daga baccin da ta koma bayan sallan asuba ta shiga yin gyare gyaren ta da tasaba yi dan yanda takejin jikinta yanzu yagama warkewa wasai takejin kanta tamkar ba ita bace tayi kwanciyar kusan sati biyu a gadon asibiti ba."
"Haka tayi ta aikin ta ita ďaya ba ruwan ta da shiga safgar Maraqishiya ko hanya bata bari sun haďa ba bare har wani yace ma wani qala." bayan ta kammala da duk abunda zatayi ne tasamu gado ta kwanta bayan tayi sallan azahar dan yanda taji bacci na rufe mata ido tamkar wacce ta kwana batayi bacci ba."
"Kafin baccin ya ďauketa ne ta ďauki wayar ta dake ajiye kusa da ita, tashiga qiran Mummyn ta, baifi ringing biyu ba taji mummy ta amsa wayar" cikin murmushi ta qara wayar bisa kunnenta, suka shiga gaisawa."
"Saida ta dauki tsawon lokacin tana hira ita da mummy Amman ko kaďan har yau batayi gigin sanar da mummy abunda yafaru da ita ba, dama tasan basusan tanada ciki ba tunda ita babu wanda tasanar wa inbanda Amina."
"Bayan tayi sallama da mummy taqira Abbanta shima suka gaisa yana mai tambayar lfyr ta, ta amsa masa da lfy lau."
"Suna gama gaisawa tayi mishi sallama kafin ta kashe wayar taqira na Yaa mahmud shima suka shiga gaisawa."
"Baccin takeji sosai Amman Haka tabi duk wayancin yan uwanta wanda suka kwana biyu basuyi waya ba ta gaggaisa dasu a qarshe taqira Ameena."
"Bayan ta kammala da wayan ne ta ajiye shi a gefen ta tareda rufe idanunta cikin zuciyar ta tana haďe haďen yanda zata fuskance shi zuwa anjima idan ya dawo,"
"Tana cikin zancen zuci bacci mai nauyi ya kwashe ta bata sani ba sai wajan karfe biyar ta farka tana miqa tareda karanto salati" kwalalo idanu waje tayi cikin firgici tamkar wacce taga baķin dodo sanadiyar ganin agogo da tayi har yamma tayi batayi sallah ba."
"Cikin hanzari batare da bàta lokaci ba ta miqe tsaye ta shige toilet ta ďauro alwala ta tashar da sallah, bayan ta idar ne ta gyara zaman ta a wajan tana tasbihi ta shige cikin duniyar tunanin ta da baya qarewa dan ba abinci zata ďaura bats ."
**
Da daddare wajan misalin karfe tara ya shigo cikin gidan a gajiye kai tsaye ďakin sa ya wuce, bai tsaya yin komai ba ya shiga toilet ya watsa ruwa ya fito ďaure da towel a kunkumin sa" Yana cikin tsane ruwan dake jikinsa ta turo ķofar ďakin ta shigo baķinta dauke da sallama cikin shigar kayan bacci wanda ya mata kyau ajiki, daddaďan ķàmshin turare na tashi ajikinta, hannunta riqe da tray na shayi da samosa a gefen sa" cikin qasa da murya taji ya amsa mata sallaman yanaci gaba da goge ruwan dake jikinsa batare da ya kalle ta ba dama batayi zaton hakan daga garesa ba."
"A hankali bayan ta ajiye abunda ke hannunta cikin sanďa ta tako da ķafafun ta zuwa garesa zuciyar ta na bugawa dum dum tasa hannayenta duk biyu ta rungume shi ta baya tsam ajikinta ta runtse idanunta gam."
"Tsigar jikinsa ne yaji ya tashi yanda yaji ta matse shi tamkar wanda aka za'a kwace mata shi yanajin sauķar numfashin ta tabayan sa, ba makawa tabbas yayi kewar ta sosai yana begen ta cikin ransa saidai zuciyar sa yakasa yarda da ita, a duk lokacin da yafara saukowa yanaso ya manta da abunda yafaru sai abun ya faskara da zaran ya tuna da babynsa sai yaji yaqara shiga tsantsan baķin ciki marar misaltuwa, Allah yagani yanason haifuwa Amman gashi bai samuba."
"Cikin qasa da murya ta soma magana tace, pls ka aminta da zance na amatsayi na matar ka wanda ka yarda da ita wlh ban aikata abunda kake tunanin nayi ba, Allah ne yabamu wannan cikin kuma gashi ya amshi abunsa fatan da zamuyi shine Allah yabamu wani mafi alkhairi, Haqiqa nima inason wannan cikin har cikin qasan zuciya ta but banida yanda zanyi tunda Allah ya amsa kayansa, Mijina am telling u d true wlh ban zubar da ciki na ba tsautsayi ne ya afku min pls ka yarda dani ya isa wannan juya min bayan da kakeyi wlh banajin daďi sam kullum cikin kunar zuciya nake kwana a duk sanda na buďe idanuna bangan ka kusa dani ba, dan Allah ka daina fishi dani kadawo gareni muci gaba da zaman mu yanda muke ada kar hakan yajanyo min ciwon zuciya.... shiru tayi batare da ta qarasa maganar da take ba, har zuwa lokacin baice da ita qala ba yanajin buguwar zuciyar ta tamkar ana buga shi da gukuma."
"Hannayensa taji akan nata ya riqe a hankali ya jiyo da ita zuwa gaban shi ya daidaita tsayuwar sa tareda sauķar da ajiyan zuciya suna facing juna, hannayensa yana riqe da nata cikin qasa da muryan sa tamkar mai raďa ya soma cewa."
"Naji duk bayanan ki tunba yauba kuma suna nan maqale cikin kwakwalwa ta, but inason kisan wani abu humaira tayaya kike tunanin zuciya ta zata aminta da kalaman ki bayan nasan cewa bason wannan cikin kikeyi ba school kikeso ki koma keda kanki kika faďa min, dan haka a wannan bàngaran kinyi karya da kike faďin cewa har cikin zuciyar ki kikeson wannan cikin, ki gyara kalaman ki don't deceive ur self kina faďan abunda babu shi a ranki indai a kaina ne, I know that na daďe inason haifuwa bansamu ba sai yanzu Allah yabani Amman kuma da yake ba rabona bane sai ya karbì abunsa, na yarda da cewa a duk lokacin da Allah yatashi zai iya bani wani haifuwar tareda wata matar basai lallai dake ba, dan haka bazan takura miki ba a halin yanzu tunda bason haifuwar kike ba bakida bukatan kizo har ďakina dan mu kwanta tare yakamata kisan hakan ki saka shi aranki bakida bukatar kwanciya dani."
"Sakin hannunta yayi wanda yake cikin nata bayan ya gama maganar da yake yabar ta tsaye a wajan idanuwan ta duk sun gama cika da kwalla batasan lokacin da hawayen baķin ciki ya soma zuba a fuskan ta ba, sam bataji daďin irin wannan kalaman nasa akanta ba, ba abun ta buďi baki itama tagaya masa ďacin magana kamar yanda yanzu ya yagama gaya mata ba Amman yanda takejin zuciyar ta yana mata kuna koda tafara bazata iya qarasawa ba."
"Tana nan tsaye a wajan da take kanta a qasa takasa koda kakkyawan motsi har ya kammala saka kayan baccin sa ya feshe jikinsa da turare, batareda yaqara kai dubansa gareta ba ya haura kan gado ya kwanta ya kunna A C tareda juya mata baya ya rufe idanunsa da niyyar yin bacci Amman yanajin wani iri a zuciyar sa wanda baisan ko na meye ba,"
"Jikinta yayi sanyi sosai har zuwa lokacin bata daina zubar da hawaye ba saima yazamana tamkar qara ingiza ta akeyi, ganin tsayuwar ta a ďakin ba karbàn ta zaiyi ba saima yaqara mata wani baķin cikin dan haka taja ķafafun ta tabar masa ďakin batareda ta kalli gadon inda yake kwance ba" Yanajin rufewar ķofar da tayi yagane cewa tafice a ďakin hakan ya sanya shi gyara kwanciyar sa yayi rigingine tareda faďawa cikin maganar zuci idanunsa yana kallon saman dakin."
"Bayan tabar ďakin sa kai tsaye nata ďakin ta shiga ta faďa kan gado a wannan lokakin taji wani kuka mai karfin gaske ya taho mata bashiri tashiga yinsa har yana fitar da sauti tanajin zuciyar ta yana tsantsan zafi tamkar tacire shi waje takeji ta huta."
"Ba ita ta daina kuka ba har saida ta tabbatar da tayi mai isar ta kafin tayi shiru tana shashsheqar kuka tareda sauķar da nauyayan ajiyan zuciya har bacci yayi nasaran kwasanta batareda tasani ba."
"Cikin dare wajan misalin karfe uku tafarka cikin nauyayan baccin da take, Ahankali ta buďe raunannun idanunta wanda sukayi jazir tamkar jan garwashi dan tsaban kukan da tasha har zuwa lokacin tanajan ajiyan zuciya" Miqewa tsaye tayi da yake wutan ďakin a kunne yake bacci ya ďibeta, ta kai dubanta kan a gogon dake manne ajikin bangon ďakin taga karfe uku da mintuna azaton ta asuba tayi sai taga tsabanin sa, hakan yasa ta shige toilet kai tsaye ta ďauro alwala tafito tada sallah."
"Saida tayi sallama uku ko wannan su sai tayi addu'ah sosai cikin sujjada, acikin sallama na ukun ne bayan tagama karanto tahiya da salatin Annabi gameda karanto addu'ar dujal ta zauna ta ďaga hannayenta guda biyu sama tafara wata sabuwar addu'ar tana shirin yin kuka."
"Mirginawa yayi daga baccin da yake ya buďe danunsa sam ya kasa gane meyasa baccin sa yaqi yayi daďi tun yana haquri yana juye juye har yagaji ya buďe idanun sa, tamkar wanda ake cokaran sa da kibiya, cikin kasalanci ya miqe tsaye ganin karfe uku harda rabi ta wuce ana neman karfe huďu, hakan yasa ya shiga toilet ya ďauro alwala ya fito" wani irin bala'in sanyin ďakin ne yaji yana ratsa gangan jikinsa da yake A C a kunne yake tamkar ruwan qanqara ake watsa masa, yana kakkame jikinsa ya ďauki sallaya da ķur'ani ya fice a ďakin dan yanda yakejin sanyin ya masa yauwa bazai iyayin sallah acikin sa ba koda kuwa ya kashe A C kafin sanyin ya ragu zai iya sanya shi mura."
"Yazo daidai da ķofar ďakinta kenan zai wuce parlou sai ya tsaya cak ya kalli ķofar da kyau kafin yasa hannunsa ya tura ķofar tareda sa kansa zai shiga ya hango ta zaune bisa sallaya hannayenta ďage a sama tana kuka sosai cikin dashewar muryan ta yaji tana cewa, Ya Allah kaine gata na kai kasan abunda zan iya aikatawa da wanda bazan iya ba, ya Allah kaine sheda ta akan wannan lamarin idan nice nayi kana kallo na, ina mai roqon ka da kacire ni acikin wannan tashin hankalin kasa mijina ya amince dani yasan cewa ban zubar masa da cikin sa ba ya Allah.... shiru tayi takasa ci gaba da addu'ar sanadiyar kukan da yaqa cin karfin ta, batasan lokacin da ta kifa kanta ajikin gado ba tashiga rairawa tana shashsheqa tareda sauķar da nauyayan ajiyan zuciya tanajan numfashi, fuskan ta yayi facafaca da hawaye idanunta sun kaďa sunyi jazur tamkar garwashi."
"Tausayin tane sosai yaji ya mamaye cikin zuciyar sa jikinsa yayi mugun sanyi sosai tamkar ya qarasa zuwa gareta ya rungume ta tsam ajikinsa yakeji, Amman yakasa musamman da ya tuna da abunda tayi masa kawai yaja mata ķofar yabar wajan zuciyar sa tunkushe take da wasi wasi iri iri."
"Fasa yin sallah a parloun yayi ya koma cikin ďakin sa ya shimfiďa sallayan kafin ya tada sallah bayan ya kashe A C na ďakin dake ta faman aiki."
"Sama sama taji bacci ya ďauke ta a wajan har zuwa lokacin kanajin ajiyar zuciyar ta."
"Qiran sallan asuban da ake shi yafarkar da ita, cikin nauyin jiki ta miqe tsaye ta shige toilet taqara ďauro alwala kafin tazo ta gabatar da sallah."
"Bayan ta idar ne ta koma ta kwanta tana riqe da kanta sosai takejin yana sara mata tamkar zai fashe gashi duk jikinta yayi mata tsami."
✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:11] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*55*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*
koda gari yagama wayewa tun safe ya shirya ya fice yabar gidan batare da yayiwa koda ďayan su magana ba dan a gurin sa baiga amfanin su a gidan."
"Wuraren wajan karfe goma na safen lokacin ta farka jikinta babu daďi sam takeji kamar zazzabi ne ke shirin rufe ta ga tsantsan ciwon kan dake damunta har yanzu bai daina ba, ji take kamar ana kwala mata guduma, haka ta miqe tsaye dakyar ta shige toilet tayi wanka da ruwan ďumi tareda yin brush ta fito ta shirya cikin doguwar riga ta atumfa yayi mata kyau sosai ajikinta" turare ta ďauka masu ďaďin gaske tafesa a duk jikinta tashafa mai kafin tazo ta ďaura kwalin kayan akanta, bayan ta gama ne ta fice a ďakin dan ďora shayi, breakfast kam bataga amfanin yin ba tunda kullum idan tayi bayaci saita nemeshi a gidan ta rasa shi."
"Dukda a daran jiya bataji daďin abunda yafaru tsakanin ta dashi ba irin ďacin maganar da ya yagaya mata hakan bai hanata leqa dakinsa ba, Amman kuma sai taga baya nan alamun ma yafita a gidan"
"Himm tafaďa cikin ranta tana girgiza kai ta fita zuwa kitchen ďinta ta ďora shayi yana tafasa ta juye shi a plas ta dawo ďakin ta zauna a qasa ta jingina bayanta da jikin gado tana fitar da numfashi a hankali tana rufe idanuwan ta tana buďe su tunani iri iri fal a zuciyar ta,"
"Haka ta wuni zaune a cikin ďakin batareda ta motsa ba daga inda take ko abinci takasa zuwa ta dafa taci tun safe illah shayin dage gabanta kawai da ta iya sha har yaqare, Sallan azahar ne kawai ya tasheta bayan tayi taci gaba da zama a wajan" Qiran sallan la'asar da tajine yaqara miqar da ita dakyar ta ďauro alwala tagabatar da sallah tana idarwa ta kokwarta ta fice zuwa kitchen ta kunno garwashi ganin tun gyaran safen da tayi yana nan babu inda bàci hakan yasa ta soma saka turaren wuta ta kunna A C da yake akwai wutan nefa sai ya haďe da daddaďan ķàmshin turaren wutan ya mamaye cikin parloun yana fitar da wata irin ni'ima."
"A gidan su Abdulmalik Umma ce sanye da mayafi ajikinta ta rataya baķar jaka a kafaďar ta kallo ďaya tak zakayi mata ganewa cewa tana jikin damuwa domin takasa zaune takasa tsaye sai zirgazirga take cikin tsakiyar parloun tana jiran fitowar siyama ta shirya sutafi kafin yan gidan su dawo dan gashi magariba ta kusa" musamman dama ta qira ta daga makaranta ta dawo gida dan ta taya ta aikin da takeson aiwatarwa dan aganin ta yan iskan yaran nan Batula da suwaiba babu abunda zasu tsinana mata face su ruguza mata abunda tayi niyyar yi musamman batula da batason taga an faďi wani ďacin magana akan humaira anan zatafara karanto mata kabili da ba'adi tana qira mata sunan Allah, ita kuwa suwaiba dolancin tama yafi karfin ta ba tuqin ta iya ba bare ta tuqa sutafi, ko a fannan rubutun ma ba iyashi tayi ba wasa tasaka agaba takasa bawa karatu muhimmanci shiyasa gashi har zuwa yanzu takasa ci gaba a karatu sai baya da take komawa."
"ko jiya da Abba yaga siyama tadawo gida kuma wai kwana zatayi abun yabasa mamaki saida ya sata agaba yana tambayar ta mai yadawo da ita gida ahalin yasan ba hutu suke ba" Tsuru tsuru da idanu tayi ta rasa wanne amsa zata basa, sanin halinsa ne idan batayi hankali ba zai iya cewa ta koma a yanzu dan bayason shashanci ita kuwa harga Allah taďauki alwashin cewa sai tabi Umma sunyi mata taron walaqanci dan lokacin da Umma tasanar da ita lbrn humaira ta zubewar da cikin ta ba qaramin bàcin rai yasata ba tamkar tayi tsuntsuwa tadawo gida takeji, tsanar ta yaqa daďuwa cikin ranta dama ita sam jinin su baizo ďaya ba" kafin Abba yace da ita wani abu tayi saurin qiqiro masa da karyan cewa lfy ce batada shi shiyasa ta dawo Amman jibi zata koma idan tasamu lfy"" Shiru yayi naďan wani lokaci yana magana a zuciyar sa alamun yana tantama da zanceta dan baiga alaman rashin lfy tattare da ita ba, saidai kawai ya tabbatar da takoma jibi kamar yanda tace dan haka yace da ita ta tashi tabar gadansa."
"Tashi tayi tabar wajansa tana tunanin ko yagane tane karya take masa dan yanda taga yana binta da wani irin kallo alamun bai yarda da ita ba,"
"Mintuna mintuna Umma take kai dubanta kan a gogon dake manne jikin bangon parlon, ganin karfe biyar da rabi har ta zarta, ya sanya ta cikin bàcin rai ta nufi ďakin su Batula" kwance ta hango siyama bisa gado tayi rufda ciki tana magana qasa qasa murmushi kwance a fuskan ta, ga dukkan alamu idan ka kalle ta zaka gane cewa waya take da saurayi dan yanda take kakkashe murya tamkar tana gabansa suna tare waje ďaya."
"Cike da takaici Umma ta isa gareta batare da tayi mata magana ba, ta ďaga hannunta cikin zafin nama ta zabga mata uban dundu mai zafin gaske abayan ta wanda hakan yayi sanadiyar sata kwala ihu da karfi ta miqe zaune batasan lokacin da wayar ya sulale qasa ba tasa hannu abayanta cikin jin raďaďin zafi, tafara murza wajan ganin Umma ce tsaye akanta ta murtuke fuska tamkar batasan akwai wani abu dariya aduniya ba, hakan ya sanya Siyama cura baki tana faďin washhh Allah na zafi sosai Umma meye nayi miki dan Allah zaki min wannan uban dukan haka bansani ba"?
"Uwaki kika kakiyi min shegiyar yarinya fuska saikace an dama taiba, cewar Umma tana kai mata daquwa da hannu tareda watsa mata mugun harara cikin bàcin rai ta qara cewa, dan iskancin banza na damunki zaki shanya ni a parlou tsaye tamkar mayya ina jiranki ashe ke kina nan kwance kina waya da qaton gardi bayan kuma kinsan idan ba sauri mukayi ba har ubanku yadawo muna nan to basamun fita zamuyi ba koda kuwa motar sa ya dawo ya tarar babu dole yayi magana, Amman da yake ba tunani bane dake kin mance da abunda yadawo dake zaki kwanta kina shashancin banza da wani qato, To wlh kinji na rantse miki tun kafin ki ruguza min wannan ranan kitashi mutafi idan kuma kinfasa bazakije ba ga hanya nan yanzun nan sai ki koma cikin makarantan da kikabaro ni kaďai ma zan iya aiki na basai wanin ku ya samin hannu ba tunda ku yanzu kun gama zama yan iska bakuda aikin yi inbanda hira da gardaye suna gaya muku zancen banza."
"Tana kaiwa nan a faďan da takeyi ta fice daga ďakin cikin bàcin rai batareda ta tsaya jin guna gunan da siyama takeyi ba tana cura baki har zuwa lokacin tana murza wajan dan raďaďin da yake mata babu shakka wannan dukan ya shige ta sosai" Ganin idan ba tashi tayi tabi bayanta ba tafiya zatayi tabar ta dan ba qaramin aikinta bane, hakan ya sanya ta miqewa cikin sauri ta ďauki makullin motar dake kusa da ita tareda kaiwa qasa ta ďauki wayar ta wanda yafaďi qasa tazo ta zari yar qaramar gyalan ta wanda dashi da babu duk ďaya ne tafice a ďakin cikin hanzari har ķafafun ta suna harďewa."
"Saida ta duba cikin parloun kaf da ďakin Ummar taga batanan hakan ya tabbatar mata da cewa ta tafi kenan, bata tsaya bata lokaci ba tabi bayanta, Ganin bata haraban gidan hakan yasa ta wuce inda motar yake ta shiga mai gadi ya buďe mata get ďin ta fita tana dube duben hanya inda zataga Umma"" Can ta hango ta tsaye bakin titi tana taran a daidaita saho."
"Kai siyama ta girgiza tareda qarasawa bakin titin inda take tsaye tana danna mata hon" Jiyo da kanta Umma tayi ta dubeta suka haďa ido Amman sai ta kawar dakai gefe guda taci gaba da taran adaidaita saho tamkar bata ga mutum a wajan ba" Ganin haka ya sanya Siyama girgiza kai ta sauka a motar cikin ranta tace kai kai Umma na akwai saurin fishi wlh bakida dama."
"Tsayawa a gabanta tayi tana duban yanayin fuskanta tace, Haba mana Umma wai fishi kikayi ne, ai gashi na fito da motar sai kizo mutafi ko"? Wani irin muguwar harara Umma ta watsa mata kafin ta mangaje ta ta shige motar tana faďin shegiyar yarinya ai da kin rabu dani tafiya ta zanyi da kaina" A dai yi haquri uwata tuba nake, Siyama, tafaďa tana dariya ta shige motar sukabar bakin titin" Yanda tahau kan titin tana sharara uban gudu kai kace ba mace bace mai tuqa motar na mijine."
"Koda suka iso ķofar gidan a waje Umma tayi mata umarnin da tayi parking motar a nan basai sun shiga ciki ba" bayan Siyama ta daidaita kan motar ne suka sauka mai gati ya buďe musu ķofar suka shiga ganin mahaifiyar mai gidan sane ya sanya shi cike da girmamawa ya tsaya yana kwasan gaisuwar ta" Ciki ciki ta amsa masa gaisuwar fuskan ta ba yabo ba fallasa ta ciro kuďi cikin jakar dake hannunta ta miqa masa tace maza jeka can ko bakin kasuwa koma dai inane ka anso min ganyan yakuwa da alaiyahu zan tafi dashi gida."
"Cike da rusunawa Amsa kuďin yace da ita to ya fice a gidan cikin ďaga qafa dan yayi sauri ya kawo mata tunda tace masa dashi zata tafi gida."
"Suna cikin tafiya zasu shiga parloun Siyama ta tsayar da Umma takai idubanta gareta kafin tace, nifa Umma bangane miki ba, yanzu fa muka wuce wajan masu siyar da ganye kina kallon su Amman bakice mu tsaya mu siya ba sai yanzu da mukazo zaki aiki baba mai gadi ya siyo miki, banda hakama mai zakiyi da yakuwa tunda saida muka haďa abinci kafin muka fito"" Himm Umma tayi tana murmushin gefen baki tace, bazaki ganeba yar nan riga kafi nayi ai, dan bazan koreta a gabansa ba domin da zaran wannan mayan matan yadawo ya duba gidan yaga bata nan, to ina mai tabbatar miki da cewa dole ya tambaye sa ina tayi shi kuma yafaďa masa gaskiya, kinga idan ba haka nayi ba ai sai ya fallashe mu yace yaga munfita da ita kinga kuwa ai babu kwanciyar hankali dan ubanku ma ba barina zaiyi ba shiyasa nakeso tun kafin sun dawo gida muyi sauri mu koma."
"Jinjina kai Siyama tayi tana dariya tace, Ummata kenan bakida sauķi wlh Amman kumafa gaskiya kikafaďa dan nima kinga jiya Abba tsareni yayi da tambaya wai mai yadawo dani gida bayan ba hutu mukeba, Ni kuwa nace masa banida lfy ne Amman jibi zan koma kinga ai na kwaci kaina."
"Gizgiza mata kai Umma tayi tace eh kin kwaci kanki uwar karya babanki ma baki bari ba sai da kika zuqa masa" dariya Siyama tayi akaro na biyu tace to ai kece sanadi Umma idan ba karyan nayi ba ai bazan kwaci kaina ba kema kuma kinsan halin Abba zai iya mayar dani"" Shiru Umma tayi bata qara ce mata komai ba suka qarasa shiga cikin parloun."
"Wayam suka gani babu kowa a cikin parloun sai TV dake aiki shi kaďai ga wani daddaďan ķàmshin turaren wuta yana tasowa tareda fitar da sanyin A C mai ni'imar gaske ko ina a gyare fesfes babu inda yakeda datti" kan ďaya daga cikin kujerun Siyama tafaďa ta zauna tana lumshe idanunta tace, kai kai wlh wannan matar shaiďaniya ce sai shegen iya tsaftan tsiya idan ta gyara waje dan ni'imar sa saikace aljanna ne, nidai ban tabàjin ni'ima irin haka ba a gidan yaya saida ya auro ta, Wannan ai idan bacci ya kwashe ni a nan sai in kwana biyu ban tashi b.....Maganar ce ta maqale a maķoshin ta batareda da qarasa ba ta miqe tsaye ganin Umma tana shirin kai mata duka tace, shegiya yar kauyan banza da wofi tashi da'ala muyi abunda yakawo mu banison shashancin banza."
"Dariya Siyama tayi tace wlh parloun ne ya min daďi ga ķàmshi da sanyin A C sai dukana yake har wani abu yana ce min kar mu koreta domin ko bakomai tanada amfani ta wani fannin" Ke kikasan wannan kuma Umma tace da ita tana watsa mata harara ta wuce ďakin da tasan shine na humaira kai tsaye babu sallama ta bankaďe ķofar ta shiga Siyama na biye da ita ta tsaya tana bin cikin ďakin da wani irin kallo tana ya mutsa fuska a yayinda Humaira ta zabura ta miqe zaune tana kallon wanda ya bangaďe mata ķofar ďaki ya shigo babu ko sallama" Mamaki ne sosai ya kamata ganin Umma ce tsaye riqe kunkumi tamkar mai shirin yin faďa gefenta kuma Siyama ce tana yay yamutsa fuska saikace taga kashi, ba shiri tashiga zancen zuci, can kuma ta sauke numfashi qasa qasa a hankali tace Sannu da zuwa Umma ga waje ku zauna" Tana musu nuni da baķin gado ta qarashe maganar a yayinda Umma ta watso mata muguwar harara wanda ya sanya hancin cikin ta kaďawa tayi saurin sauķar da kanta qasa tana wasa da yatsun hannunta."
"Wani takarda Umma ta ciro cikin jakan dake rataye a hannunta ta jefawa Humaira shi ajikinta tace, To munafuka gashi takardar saki ne inji mijinki wanda kike taqama dashi yanzu yace kar yadawo yaganki a gidansa, dan haka ga hanya nan sai ki fice masa babu wata doguwar magana" Tana kaiwa nan ta juya ta kalli Siyama tace ke kuma biyoni, kinga idan nace zan tsaya ita ta ďauki kayanta da kanta bàta min lokaci zatayi dan haka gwara muyi da kanmu."
"Cikin inda Humaira ke ajiye kayanta suka buďe Siyama ta hango wani bagco ta buďe taga ba komai acikin sa kafin ta miqawa Umma tafara zuba kayan aciki batareda ta duba komai take kwasa ba itadai duk abunda ya shigo cikin hannunta ďauka take ta tusa acikin bagcon."
"Ganin sai yi take kayan baya qarewa ya sanya ta miqewa tsaye ta riqe kunkumi tana share zufan da tahaďa tace da Siyama kinga na gaji rufe bagcon haka ya isheta daga baya Uwar ta ko ubanta sa turo a kwashe mata sauran kayan idan sunada bukatar sa."
✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:11] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*56*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*
"Tunda idanuwan ta suka sauka akan takardar da Umma ta jefeta dashi, Jikinta yashiga mugun yin rawa zuciyar ta yana tsantsan bugawa sosai, a hankali takai zuwa qasa tasa hannu ta ďauki takardar hannunta yana karkarwa ta warware shi a hankali take binsa da kallo tana karantawa, idanuwanta suka cika da kwalla batasan lokacin da hawaye mai zafin gaske ya soma bin kuncinta ba."
"Tsantsan firgita da abuda idanunta suka gani shi ya sanya ta durkushewa qasa a wajan tana qara maimaita abunda ke rubuce a takardar cikin kunar zuciyar ta soma faďin Innalillahi wainnailaiaihi, tana runtse idanunta taqara cewa, Abdulmalik meye nayi maka haka zakayi min irin wannan sakin walaqanci har saki uku"? meye nayi maka dan Allah bayan nafaďa maka gaskiya ta....
"Shiru tayi tana kuka sosai takasa qarasa maganar da take, Bata ankara ba taji an jefeta da abu ajikinta, Hakan shi ya sanya ta cikin mutuwar jiki ta ďago da jajayen idanuwan ta wanda suka soma kumbura dan kukan da tayi."
"Ido huďu sukayi da Umma wacce ke tsaye a kanta tana mata mugun kallon da ya sanya ta sauķar da nata idanun qasa."
"Cike da zafin nama Umma ta fisgi hannunta ta riqe gam ta soma janta daga ďakin suka fice Siyama na riqe da bagcon da suka tusa kayanta aciki tabi bayansu."
"A cikin parlou sukaci karo da Maraqishiya hannunta riqe da plate ďin abinci zata shiga kitchen da alamun yanzu ta kammala cin abincin" Ganin Umma riqe da humaira tana jan hannunta, ga Siyama na biye dasu riqe da bagco ya sanya ta ajiye plate ďin a qasa ta dawo zuwa garesu cike da mamaki tace, Umma lafiya dai naganki haka da yamman nan halan wani abun ne yafaru,?"
"Kawar da kai gefe tayi tanajan dogon tsaki ta daidaita tsayuwar ta kafin tace, kefa Maraqishiya wani lokacin kin cika tambayar rainin hankali wlh, kinaso kice min bakigane abunda zanyi bane ko meye,?" To idan ma ganewa ne bakiyi ba zan ganar dake, Abunda kika kasa yi tuntuni shi zanyi yanzu, Tana mata nuni da humaira wacce kanta ke qasa inbanda hawayen baķin ciki babu abunda take zubdawa, Umma taci gaba da cewa kinga wannan ja'iran matar ita zan kora yanzu tayi hanyar gidansu tasan inda dare yayi mata dan bazan iya cigaba da kallon wannan shegen muguwar baķin fuskan nan a matsayin surikata ba tazo daga baya muma ta ďauki adda ta kashemu ďaya bayan ďaya tunda har ta iya kashe jaririn da ko gama zama cikekken halitta baiyi ba...
"Dan haka abunda nakeso dake yanzu shine, maza babu bàta lokaci ki samu abun rubutu ki tsara gaskiya da karya ki rubuta kemadai kinsan sauran, kuma dan nace gaskiya bawai ina nufin ki rubuta mu muka koreta ba, a a ita ta kori kanta yanzu a tashar mota zamu sauketa daga nan sai mu koma gida idan kin gama tsara rubutun saiki ajiye a inda kika tabbata zai gani da kansa kuma idan ya tambaye ki ko kinsan inda take kice masa bakisani ba yanzu haka na aiki sani mai gadi kinga shima kenan baisan meke tafiya ba, kuma idan yakawo min saqona ki ajiye min ban yarda kiyi amfani dashi ba."
"Tana kaiwa nan taqara kallon Maraqishiya da kyau akaro na biyu taqarashe maganar da cewa ina fatan dai kingane menake nufi, kuma zaki kiyaye,?"
"Gizgiza mata kai tayi alamun Eh tagane komai, Umma ta girgiza kai tace yauwa yar nan haka nakeson ji yanzu abunda zamuyi shine samo min wani qalle ki rufe min idanuwan ta ruf sosai domin ko hanyar da mukabi da ita baniso tagani bare tayi gigin dawowa" Babu musu Maraqishiya tacire ďaurin ďan kwalin dake kanta tazo dafda su ta ďaure idon Humaira dashi gam dan mugunta zuciyar ta wasai har saida tasaki yar qara tana kama ďan kwalin, Bayan tagama ďaura mata ne Umma taja hannun humaira da karfin ta Siyama tabi bayan su suka fice daga parloun kai tsaye waje suka nufa inda motar take parke suka shiga Umma tashiga gidan baya tareda Humaira dan gudun karta kunce ďan kwalin basu sani ba."
"Har zuwa lokacin idanunta suna zubar da hawaye zuciyar ta yana mata zafi makuqa wani gefe na zuciyar kuma yana mata zugi akan tayi musu gardama dan tasan zata iya karbàn kanta saidai idan batayi niya ba, Amman kuma batada kuzari sam tunda har shine ya rubuta mata takardar saki har uku koda tace zatayi musu gardama hakan bashida amfani gwara ta koma gidan su kota samu kwanciyar hankali a can."Tanaji Siyama ta tashi motar ta hau kan hanya dasu cikin gudu."
"Lokacin da su Umma suka fice sukabar Maraqishiya tsaye tana jinjina abun acikin ranta" Waje tasamu ta zauna tamkar ta zuba ruwan sanyi aqasa tasha haka takeji, dan tsantsan farin cikin da take ciki a yanzu takasa sukuni, Miqewa tayi daga zaunan da take kai tsaye ta wuce ďakin ta ta ďauki paper da biro ta soma tsara abunda zata rubuta wanda kota halin qaqa bazai karyata saqon ba yace Humaira bazatayi haka ba, Sauri take tagama tagama rubutawa dan tasamu ta labartawa shiwari lfy dan ba'ayi wannan draman bataji lbr ba."
"Sun isa tashar mota lokacin anata qiraye qirayen sallan magariba dare ya soma ratsa cikin garin, tashar cike take makil da hayaniyar mutane sai tashi yake kowa yana harkan gaban sa ba ruwan sa da wani, yan tallah na shirin komawa gida masu shaguna da drebobi suna hanzari dan su samu sallah."
"Babu tausayi ko tunanin idan yanzu sun ajiye ta anan ta ina zata soma neman hanyar tafiya ba, haka suka saukar da ita acikin tashar tareda jefa mata bagcon kayan ta kafin subar wajan Umma ta kalleta da kyau cikin buďe ido tamkar na mujiya tace, To malama ala qaqai mayyar mata ga tashar motoci nan na taimaka nakawo ki dan haka sauran ya rage naki idan sata zakiyi ki samu kuďin mota ma ohho komadai ya zakiyi ke kikasan wannan matsalar, ke tashafa nidai nayi nawa qoqari ko a wajan Allah ansan na taimaka miki."
"Tana kaiwa nan ta juya ta shige mota Siyama tashiga mazaunin driver tafigi motar sukabar tashan bayan itama tagama binta da tazagi iri iri tareda yi mata gwalo."
"Tunda suka tafi suka barta a tsakiyar tashan kanta yayi mugun ďaurewa gani tayi wajan gabaki ďayan sa yayi mata girma sosai, Tana bin cikin tashar da kallo ta soma magana a zuciyar ta tace, Yanzu ya Allah ta ina zan soma tafiya, Na ďaya ba kuďi bane a hannu na wanda zan biya mai mota dashi na biyu gashi babu wanda nasani acikin faďin garin ķatsina face gidan aurena shi kuma gashi an haramta min zuwansa barema ince zan koma" Runtse idanunta tayi wasu zafafan hawaye suka qara zubo mata akaro na biyu, cikin kunar zuciya ta rasa yanda zatayi tunda ba sanin kan tasha tayi ba domin ita zata iya irga sau saunawa tashigo cikin tashar mota tunda aka haifeta bazai fi sau biyu ba shi ďin ma karbàn saqon Mummy ne idan ta aike ta shi ma a baķin get ďin tashar suke haďuwa da mutumin ta karbà, tafiya kuwa dama basayi a motar kasuwa mafi yawancin tafiyar da sukeyi a girgi ne saidai wani lokacin idan garin bamai nisa bane sukan yin shi a motar gida."
"Nauyayyan ajiyar zuciyar ta sauķe tasa hannu tashare hawayen dake kwance a fuskan ta, Tunawa da tayi tafito wayar ta hakan yasa ta shiga qiran wayar Batula domin itace kaďai tasan wacce zata iya karbàn ta, Qirar wayar tayi yafi so a irga Amman bata ďauka ba ganin haka yasa tace bari taqira na Ameena ta samo mata wani ďan uwanta yakaita gidan su dake cikin garin ķatsina idan yaso ko acan ta kwana gobe da safe takama hanya tunda ba iya qiran su mummy zatayi ba a yanzu domin karta tashar musu da hankalin su sushiga cikin damuwa."
"Wani abun baķin cikin da ya sanyata tsaki shine wayar Ameena taqi shida akashe take gabaki ďaya, Cike da takaici ta yarfe hannu tana dafe goshin ta dake sara mata har zuwa lokacin."
"Cikin rashin kuzari ta yanqe a zuciyar ta cewa bari tasiyar da wayar dake hannunta kawai shi zaifi mata sauki domin ta tabbatar da kuďin sa zai isheta tasamu koda hotel ne ta kwana kuma tayi kuďin mota har tayi komai ma dashi, a hankali ta soma takawa tana tafiya tareda da dube duben inda zataga shagon masu waya."
"Ganin duk inda ta duba bataga shagon masu waya ba gashi garin ya ďauki duhu dare yashiga domin har masallace sun idar da sallah hakan ya sanya ta yanke hukuncin tasamu wani wanda yasani ya nuna mata dan idan ba hakan tayi ba darene zaiyi mata sosai."
"Hango wasu mutane tayi zaune akan benchi su biyu suna shan rake tun daga nesa suna ganin tahowar ta garesu suka soma binta da wani irin kallo da yake akwai hasken wutar nefa da yamamaye cikin tashar, Tun daga qasan kafafun ta yanda take tafiyar har zuwa saman ta, kamar haďin baki suka kalli juna a tare sukace kai kai abokina kaga wannan halittar kuwa,?"
"Gingina kai sukayi suna shu'umin dariya ďayan yace, ķur'anin Allah abokina yarinyar zata kawo wuta kalli fa yanda hijabinta ke bin jikinta komi na sururar ta yana bayyana tamkar babu wani abu kaya ajikinta... Zai qara watar maganar sai yayi shiru ganin ta qaraso zuwa garesu tayi musu sallama cikin muryan ta wanda ya dashe dan irin kukan da tasha."
"Amsa mata sallamar sukayi tamkar basu suka qare mata kallo ba, ďayan wanda yagama maganar ta yanzu kafin ta qaraso ya dubeta yace, Malama ya akayi wani abu kike nema ne,?"
"Kai ta girgiza masa alaman eh tace dan Allah shagon da ake siyar da waya nake nema ko zaku taimaka ku nuna min" Gin tambayar da tayi musu ya sanya su Kallon juna a tare cikin zuciyar su suna ayyana cewa shikenan sun samu mace domin daga ganin ta suka gane cewa baquwa ce a garin nan dan haka zasu iya ďaukar ta suyi sha'anin su da ita su more rayuwar su yanda sukeso batareda wani yasani ba."
"Kashewa junan su ido sukayi a tare suka miqe tsaye ďayan yace muje mu nuna miki yar uwa ai gwara da kikazo nan kika tambaye mu domin inamai tabbatar miki saidai ki gama zagaye cikin tashar nan kaf batareda kin samu shagon masu waya ba dan ba'a nan suke zama ba sai kin fita can waje kin ďanyi tafiya kaďan kafin ki samu, Amman karki samu damuwa zamu nuna miki yanzu kinzo gidan sauķi ai mu masu taimako ne."
"Suna cikin tafiyar ne yake mata duk wannan surutun tanajin sa bata tanka masa ba, saidai zuciyar yana mata wasi wasi yanda taji yana maganar ya ďaure mata kai Amman sai tabasar ganin acikin jama'a suke koda zasuyi mata wani abun bazata rasa mai taimakon ta ba
✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:11] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*57*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*
"Fita sukayi daga cikin tashar suna tafe tana binsu a baya minti minti suke juyowa da kansu suga ko tana binyu idan sun haďa ido sai taga sun sakar mata da shu'umin murmushi wanda take kasa ganewa, Ganin dare sai qarayi mata yakeyi dan gashi har an soma qiran sallan isha'i hakan ya sanya ta dakatar dasu acikin tafiyar tace dasu, dan Allah har yanzu bamuzo shagon bane,?"
"Ama
sa ďayan yabata da Eh tareda qara faďin shagon da yakama mukai ki ďin ne a rufe yake Amman akwai wani mutum mai siyan waya a nan bayan layi na tabbata za'a sameshi" Kanta kawai ta girgiza bata qara cewa komai ba sukaci gaba da tafiya."
"Gani tayi sun shiga da ita wani dogon layi mai ďan duhu wanda cikin sa babu hasken wuta sosai, haka zalika baka kallon mutane dayawa sai ďaďďaya hakan shi ya haifar da shiru a layin tamkar babu ďan adam aciki."
"Tsoro ne ya soma mamaye cikin zuciyar ta ganin yanda yanayin layin yake ta soma dana sanin da bata biyo su ba domin gashi sun qara shigar da ita inda batasani ba, Dube dube tafarayi tana rarraba idanu tana shirin komawa baya dan tagama yankewa a ranta bazataci gaba da binsu ba suje suyi mata abunda batayi tsammani ba tunda dama zuciyar ta ba gama gamsuwa tayi da bayanan su ba kawai dai rashin sanin waje ne ya sanya ta binsu."
"Sun iso daidai bakin wani qaramin gida suka tsaya wanda cikin sa kwata kwata idan ka gani bazai wuce ďakuna biyu ba,
"Tattaunawa sukayi a tsakanin suna dariya ganin ta tsaya a baya tana raba idanu yasa sukayi zaton kota gane me suke nufi da ita, hakan yasa suka yanke shawaran ďauke ta su shiga da ita ciki dan karta kawo musu cikas tunda babu mai kallon su."
"Batareda da tace dasu komai ba ta juya baya tayi hanyar da suka biyo da ita ta soma tafiya batare da tasan inda zata nufa ba, Bata ankara ba taji hannun mutum a bakinta an toshe mata shi yanda bazata iya kwakkwaran ihun da mutane zasuji ba" Ďaga ta sukayi ďayan ya riqe jakar kayan ta, tana witsl witsl da ķafafunta tana ķoķarin kwacewa daga riqon da sukayi mata Amman takasa domin ba qaramin riqo sukayi mata ba. yanayin yanda suka toshe mata baki da hanci yasa duk irin ihun da takeyi baya iya fitowa waje ga numfashin ta da takeji yana shirin ďaukewa."
"Cikin wannan gidan suka shiga da ita suka nufi cikin ďaya daga dakuna biyun dake jere a gidan suka kunna wutan ya haska komai na cikin ďakin."
"Madaidaicin ďaki ne irin na samarin zamani babu wani tarkace dayawa acikin sa" Shimfiďe yake da yar kwoďaďďiyar leda a tsakiyar dakin sai katifa dake shimfiďe da pllow akai gefe guda kuma ďan karamin TV ne ajiye da DVD akansa sai tarkacen kwanukan abinci wanda sukaci suka bari da kofinan shayi masu datti"
"Direta sukayi kan lotsats tsiyar katifar kafin suka saki bakinta wanda suka toshe mata shi" Numfashi take saukarwa wahalalle tana haki sosai tamkar wacce tayi mugun gudu, Bayan tadawo daidai tashiga raba idanu ganin inda suka shigo da ita ya sanya ta miqewa tsaye tana waige waige tsoro yagama cika mata zuciya sosai, Cikin dauriya da karfin hali. muryan ta yana harďewa ta soma ce musu, Meye kuke nufi dani, meye nayi muku daga neman taimako zaku kawo ni wannan dakin,?"
"Dariya sosai maganar nata ya sanya su suka shiga yinsa babu kakkautawa."
"Saida sukayi mai isar su kafin suka tsagaita dariyar suna mata kallon sha'awa ďayan yafara takowa gabanta a lokacin da take takawa baya a hankali yana girgiza kai tareda murmushi irin na yan iska" Bayan ya kureta yakai hannunsa zuwa kan fuskan ta da niyar shafan ta, Ganin abunda yake shirin yi mata yasa cikin sauri ta kaucewa hannunsa tana masa mugun kallo, duk da cewa a tsorace take Amman hakan bai yanata yin magana ba."
"Cikin karfin hali ranta a bàce tana nuna shi da yatsar hannunta ta soma cewa, Wannan wanne irin iskanci ne kakeson yi min, ko ance maka ni yar iskace da har zaka ďaga hannu kace zaka tabà ni saikace kasamu matar auran ka, To bari kaji in gaya maka idan kasaba yima wasu suna qyale ka to ni ba irin su bace idan kasan wata to kabasan wata ba, inamai gargaďin ka kada ka kuskura kayi gigin rabàn jiki na domin wlh bazaiyi maka kyau ba kuma kuyi gaggawar fitar dani daga wannan shegen kazamin gidan tun kafin yabàci muku idan kunne yaji gangan jiki ya tsira."
"Shiru tayi bayan tagama maganar zuciyar ta yana tsantsan bugawa sosai tamkar zai malle yabar kirjinta dan karfin hali ne kawai yasa ta iya gaya masa wannan maganar, Idanunsa yana kanta tunda ta soma magana yake kallon cikin kwayar idanunta ba qaramin basa haushi tayi ba hakan yaqara harzuqa zuciyar sa Bazato ba tsammani taji yayi mata muguwar shaqa ta wiya ya riqo hijabin dake jikin ta wanda hakan yayi sanadiyar firgitar da ita tana wuri wuri da ido dan jin azaba tareda qoqarin kwace kanta daga riqon da yayi ma wiyanta."
"Cike da zafin nama yaqara maqure wiyan hijabinta numfashin ta yana fita sama sama dan tsantsan jin zafi, yana zare mata ido ya soma cewa, Ke karamar kwaro wlh wlh baki isa kice zaki kawo min raini ba ke asuwa dahar zaki nuna min yatsa kina min rashin kunya, to bari kiji idan ma keba yar iska karuwa bace yau ďin nan zaki zama yar iska zakisan kuma da uban yan iska kika haďu."
"Yana kaiwa nan daga maganar da yake ya fisge hijabin dake jikin ta ya cire shi tareda kamo hannunta da karfi ya cilla ta kan katifa yana huci ya iyo kanta zai afka mata ayayinda inbanda hawaye babu abunda takeyi, zuciyar ta yagama karaya cike da tsananin tsoro take matsawa baya tana haki sosai..
"Ganin da gaske afka mata zaiyi ya sanya ďayan abokin nasa yayi saurin riqo hannunsa yaja sa gefe guda kafin ya soma cewa, Haba mana, Haba mana baaba. karka bani kunya dan Allah akan wannan figeggiyar yarinyar nan wacce bata wuce cikin tafin hannunka ba, pls ka kwantar da hankalin ka karabu da ita dan batasan mu ko suwaye bane shiyasa take mana rashin kunya Amman zata gane kuran ta zatasan ruwa ba sa'an kwando bane domin ba'a tabà mu a zauna lfy. Dan haka abunda nakeso dakai bani kunnenka kaji wani abu."
"Miqa masa kunnen yayi ya raďa masa wata magana wanda ya sanya shi sheqewa da muguwar dariya yana faďin, kai nasir kaifa shege ne wlh kashiga gari dayawa."
"Shima dariyar yayi ciki ciki yaja hannun abokin nasa suka fice daga ďakin. wanda aka qira da Baaba yaja ķofar da karfi ya rufe ya danna masa kwaďo kafin sukabar gidan suna hiran su irin ta abokanai."
"Tun lokacin da ya cilla ta kan katifa take haqi sosai jikinta yana muguwar rawa domin a rayuwar ta bata tabà shiga irin wannan mummunar hali hakaba sai yau, Kuka ne yaci karfin ta bashiri tashiga yi sosai ta kifa kanta tsakanin guiwar ta har zuwa yanzu cikin buguwar zuciya take bai daina ba."
"Saida tasha kuka sosai tayi mai isar ta kafin ta tsagaita kukan tana haki ta ďago da kanta ta miqe tsaye a hankali ta soma bin cikin ďakin da kallo tana takawa har tazo baķin ķofar tasa hannu zata buďe taji gam a kulle yaqi buďuwa" bubbuga ķofar tashiga yi sosai har tagaji tabari da kanta hawayen fuskan ta suna qara gangarowa tana goge shi da bayan hannunta."
"Wajan katifar ta koma ta ďauki wayar ta wanda yafaďi a qasa ta duba agogo taga har karfe tara saura zuciyar ta yaqara bugawa sosai gashi ko sallan magariba batayi ba bare isha'i, Ganin babu wanda ya qira ta yasa ta qara qiran wayar Batula yayita ringing bata ďauka ba, Cikin jin haushi ta ajiye wayar tana takakcin irin wannan ranan da kake bukatar mutane Amman baka samun su."
"Saida ta ďauki tsawon lokaci kaďan tana zaune kafin ta miqe ta shiga binciken ďakin tana neman inda zata samu ruwa ko qasa tayi alwala dan ta gabatar da sallah" Cikin sa'a ta hango ledar ruwa guda biyu a ajiye kusan da wannan kwanuka masu dattin, ba bàta lokaci ta ďauka taje can wani gefe guda inda taga da qasa tayi alwalan ta a wajan tazo tafara gabatar da sallan da yawuce ta."
"Sai wuraren wajan karfe goma na daran ranar Abdulmalik yadawo gida a gajiye kai tsaye ďakinsa ya wuce yayi wanka bayan ya shirya cikin kayan bacci ya kwanta tareda lumshe idanunsa da niyyar yin bacci Amman saiji yayi yakasa runtsawa tunawa da humaira da yayi sai yaga sam baiyi mata adalci ba koda kuwa da gangan ta zubar da cikin sa baici ace ya juya mata baya ba har irin haka ba" Maganar zuci yashiga yi yaka yakasa sukuni, Ganin hankalin sa yakasa kwanciya yasa ya miqe zai fita da niyar yaje ya dubata su shirya."
"Har ya buďe ķofar zai fita sai kuma yafasa yadawo da baya ya kwanta abunsa ya runtse idanunsa sosai ya yanke a ransa cewa zai bari har zuwa lokacin da zata qara zuwa neman gafaran shi tunda kullum sai tayi masa magiya akan ya yafe mata."
***** *******
Bayan kwana biyu da faruwan hakan yau laraba da safe Humaira na zaune akan lotsats tsiyar katifar ďakin ta zabga uban tagumi abun duniya ya ishe ta tun tana iya kuka tana zubar da hawaye har yazo ya gagareta ta komayin kukan zuciya mai cin rai, Kallo ďaya zakayi mata ka kalli rama qarara kwance ajikinta idanunta sun faďa sosai akoda yaushe suna kawo mata abinci da ruwan sha Amman ko kallo bai isheta ba bare harta iya ci domin damuwa kaďai yagama cika mata ciki babu abunda take bukata a yanzu face taga ta fice a wannan kurgumin ďakin da suka jefo ta, a kwana biyun da tayi aciki cikin tashin hankali da rashin nutsuwa take domin akoda wanne lokaci suna iya faďo mata dan suyi lalata da Amman cikin ikon Allah duk wani karfi nata da tasan tanada shi zata shiga yin kokuwa dasu duk abunda yazo hannunta kwala musu take tana shuran su da ķafafunta iya karfin ta take ihu..
"Ganin ihun da take da kokuwan da takeyi dasu zai iya janyo musu fallasa jama'an dake waje su san abunda ke tafiya ko kuma taji musu ciyo hakan yasa suka rabu da ita gameda yanke shawaran cewa kwayar da zai bugar da ita ya sanya ta bacci sosai zasu bata idan yaso sai suyi duk irin lalatar da sukeso suyi da ita, Da yake a cikin ďakin sukayi maganar dukda qasa qasa sukayi dan gudun kar taji mai suke cewa Amman ta tsargu takasa yarda dasu babu shakka akwai abunda suke nufi da ita hakan yasa yau ta kwana idanunta biyu takasa runtsawa duk motsin da taji sai takai hankalin ta ga ķofa taga ko sune"
"Tunda tayi sallan asuba take zaune a wajan tana tunanin hanyar da zatabi taga tafice daga gidan..
✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:11] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*58*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*
Tana cikin tunanin yanda zatayi ta fita ne wani dabara yafaďo mata cikin kanta, ganin idan har Allah ya yarda dabaran ta yayi aiki zata iya kubùta daga hannun su yasa ta miqe tsaye da sauri ta soma bincika kayan dake cikin ďakin taga ko zata samu wani abu."
"Can ta hango wani daďaďdan tsohon murfin kwano na samisa ajiye da maskito da ashana akai da alamun aciki suke kunna maskiton, kura duk ya mamaye sa haka tasa hannu ta ďauka ta karkaďe kuran da maganin sauron aqasa kafin ta dawo ta ďauki bagcon kayan ta da wayar ta ta tsaya abayan ķofar ďakin tana jiran zuwan su, zuciyar ta yana bugawa matuka tana tsoron abunda zata aikata saidai kuma idan ba hakan tayi ba sai yanda kuma Allah yayi da ita."
"A daidai lokacin bayan ta tsaya kaďan a bayan ķofar taji motsin mutum ana buďe ķofar, Cikin tsoro jikinta yafara karkarwa zuciyar ta yanaci gaba da dukan uku uku, ta qara riqe murfin kwanon da kyau a yayinda Baaba ya turo ķofar ya shigo shi kaďai yans yar wakan sa yaga ďakin kamar bakowa."
"Cike da mamaki ya soma waige waige da kansa yana tambayar cikin zuciyar sa to ina yarinyar nan ta shiga da safen Allan nan bayan ķofar a kulle take" Baiyi zato ba baiyi tsammani ba yaji an buga masa abu akan sa, cikin jin azaba ya riqe wajan yanaja da baya ya jiyo da kansa yanaso yaga meye ya buge masa kai haka."
"Ganin buguwar kamar bai shigesa sosai ba bare yafaďi qasa tasamu hanyar fita ya sanya ta kafin yagama jiyo da kansa su haďa ido dashi tayi saurin qara buga masa murfin kwanon tareda shuresa da ķafa bashiri ya rufzu aqasa yafaďi yana riqe da kansa wanda yafashe jini yana zuba."
"Har zuwa lokacin jikinta rawa yake sosai dakyar ta iya aikata hakan dan shine kaďai dabaran da yafaďo kanta wanda takega zai iya kubutar da ita daga hannun su, Bata tsaya bata lokaci ba ta ďauki kayanta ta fice a ďakin bayan taqara mangaje shi da ķafa yana shure shure gameda ķoķarin ya miqe ya cafko ta Amman ya kasa yanaji yana gani ta fita daga cikin gidan bashida halin da zai iya kamota dan yaji azaban zafi sosai."
"Tafiya takeyi cikin sauri tamkar zatayi tsuntsuwa ta tashi sama batareda tasan inda ķafafunta suka nufa ba, Allah Allah take a ranta kawai ta kalli kanta acikin tashar mota Amman abun ya faskara domin kuwa gani tayi garin yayi mata mugun girma sosai dukda tasan ta shiga qasasai wanda sukafi wannan girma Amman saida taga tamkar babu garin da yakai wannan faďi da girma kodan shekaran jiya ana magariba ne yasa bataga girman sa ba sai yanzu da yake garin safiya ce rana ta fito kana kallon komai da ko ina ba."
"Haka taci gaba da tafiya tana dube duben bayanta taga ko yasamu damar fitowa yana binta sai taga bakowa hakan yake take qara godewa Allah"
" Yanayin yanda take tafiyar cikin sauri da ďaga kafa tamkar kace wata zararriya mai shirin haukacewa dan yanda ķafafunta da jikinta ya ďauki ķuran qasan wanjan sakamakon sanyin da akeyi aciki garin ķatsina ya sanya taron hazo asama wanda idan ba ido sosai ka buďe bama bazaka iya gane abunda ke can gaban kaba."
"Cikin hikimar Allah tana cikin tafiyar ta hango wani shagon masu waya a gabanta batasan lokacin da tasaki murmushin farin ciki ba tana godewa Allah acikin zuciyar ta da yasa tasamu shagon da take nema" Tana sauri ta qarasa wajan shagon tashiga bayan tayiwa mai shagon sallama suka gaisa yabar aikin goge kuran da yake yadawo da hankalin sa gareta, ga dukkan alamu shima yanzu ne ya buďe shagon."
"Wayar ta Samsung galaxy S6 mai kyawun gaske da tsada ta nuna masa suka shiga yin ciniki yace sam saidai yabata dubu hamsin dan wayar ta ďan sha ruwa, Sun ďauki tsawon lokaci suna cinikin ganin bàta mata lokaci yakeyi gashi garin rana tafarayi sosai yasa ta cire Sim card ďinta da memory ta miqa wayar tace yaba hakan ta amince" Karbà yayi ya ajiye gameda irgo mata daidai kuďin yabata."
"Batareda ta tsaya irgawa taga yacika ko bai cika ba ta ďauki bagcon ta tafice ta soma tafiya."
"A daidaita sahu tagani ta tsayar dashi tashiga kafin tace dashi yakaita tashar mota" Cikin mintuna kaďan ya isa da ita cikin tsakiyar tashar, Bayan ta biyasa kuďin sa ne ta tambaye sa da ya nuna mata inda ake lodin yan abuja, Nuna mata yayi ďan nesa kaďan da inda suke tsaye."
"Godiya tayi masa sosai kafin ta nufi wajan masu lodin fasinjoji" Cikin sa'a Allah ya taimake ta tasamu motar da take lodin yan abuja ya cika saura mutum ďaya ya rage"
"Shiga tayi bayan sun faďa mata daidai kuďin motar ta biya.
"driver ya tashar da motar yakama hanyar abuja cikin gudu tamkar mai shirin tashi sama."
"Acan bàngaran Baaba kuwa tun lokacin da ta buge masa kansa ta shure sa yafaďi qasa dakyar ya iya tashi zaune ya jinginu da jikin bangon ďakin yana sauķe numfashi qasa qasa tareda tsuke fuska yana jan dogon tsaki dan tsananin zafin wajan da yakeji, hannunsa yana kansa yana murzawa dan wajan har ya soma kumbura" Abokin sa Nasir ya shigo cikin tafiya irin ta kasaita tamkar bayason taka qasan"
"Murmushi ne kwance a fuskan sa wanda kana gani kasan na magunta ne bana arziki ba, hannunsa riqe yake da drink a leda ya shigo dakin yana faďin Baaba kana inane gani nadawo fa..Maganar ce ta maqale masa a maķoshin sa sakamakon abunda idanunsa suka gani."
"Cike da mamaki ya qarasa inda Baaba ke jingine ya ajiye ledar dake hannunsa kafin ya dafa shi yana faďin, Ya salam abokina meke faruwa haka, waye yayi maka wannan aika aikan"? Kuma ina yarinyar take ya banganta ba" Ta gudu, ya bashi amsa a hankali ya qara cewa kwala min abu tayi akaina bansani ba ta shureni nafaďi qasa cikin jin zafi kafin in yinkura nakamo ta tayi sauri tafi...
"Katse shi Nasir yayi cike da takaici yace, Haba mana wannan wani irin magana ce Shine kuma dan tagudu ka kasa binta kenan, koka manta mace ce karfin ta baikai koda rabin naka ba, duk irin gudun ta kai namiji kota halin qaqa zaka iya cimmata."
"Wani irin muguwar harara Baaba ya cilla masa kafin yace lallai Nasir sai yanzu nakula da cewa qaramar kwakwalwa ce dakai, inbanda rashin hankali irin naka dubi fa irin ciwon da taji min akaina duk baka tausaya min ba saima rufeni da surutu da kayi wai meyasa ban bita ba, waima koka mance yanzu safiya ce akwai jama'a so kake in kwana a police station ko"? To idan kuwa hakane ga hanya zaka binta ka kamota kayi duk abunda kakeso da ita idan an kamaka kuwa wlh bakasanni ba dan hanya ta daban naka daban domin kaina ma da tafasa min ya isheni inyi jinyar sa."
"Yana kaiwa nan daga maganar da yake ya kawar da kansa gefe yana shirin miqewa tsaye a yayinda Nasir yayi shiru yana jinjina kai shima ya miqe tsaye yana faďin, Gaskiyar kane abokina naji kayi haquri kazo yanzu muje wajan mansur yasa maka spirit tun kafin jinin jikin ka yaqare ka wula lahira in shiga uku, Gashi yanzu ma abun haushi wannan shegiyar yarinyar ta sanya munyi asaran ďan guntun canjin da muke dashi gashi bamu cimma burun mu akanta ba, ķur'anin Allah da zan ganta yanzu idan ta cafke ta bazata gane kammanin taba dan sai nayi kaca kaca da jikinta."
"Yo ai yanzu aikin gama yagama bakin alqalami yabushe tunda dai ta gudu, Bari kaga in ďauki drink ďin nan insha kar muyi asara biyu, ba ita ba ba kuďin muba."
"Dariya Nasir yayi suka fice daga gidan Baaba yasa kwaďo ya kulle suka nufi pharmacy dake kusa dasu."
"Wajan wuraren karfe biyar saura na yamma motar su ta isa cikin garin abuja ta sauke su a tasha, a nan ta nemi taxxi tayi masa kwatancen unguwar su har ķofar gida ya kaita, Bayan ta biyasa kuďin sa ta sauķa daga cikin motar a lokacin ne kuma tunanin yanda zatayi ta fuskanci yan gidan su a yanda take haka riqe da bagco a hannu jikinta duk kura kamar yar farauta domin kuwa tasan ba makawa dolene su sata agaba su tambaye ta mai yafaru ita haka tazo buya buya bazato ba tsammani."
"Saida ta ďauki mintuna kaďan tana tsaye a wajan tana neman karyan da zatayi ya karbè ta dan ba iya faďa musu gaskiyar abunda yafaru da ita zatayi ba "Ganin bàta lokacin ta takeyi a wajan gashi takasa samun mafita duk karyan da tahaďa sai taga baiyi ba za'a iya gano ta hakan yasa ta yanke shawaran cewa bari tashiga kawai cikin sanďa ta shige kai tsaye idan Allah yasa babu wanda yaganta sai tashiga ta ďakin ta ta gyara jikinta ta tsaftace shi kafin taje ta fuskance su dan ba qaramin mugun datti tayi ba, ji take ko ina na jikinta tsami yake, kawai ba yanda ta iya ne Amman da bazata iya jure wannan qazantar ba, Dan da tafi kwana biyu kam a wannan shegen ďakin da suka sata saidai azo a ďauke ta rubàbbìya dan datti tunda kulle ta kuruf sukayi a ciki bata samun iska sosai koda kuwa shiga toilet ne ya kamata tana gaba suna binta a baya tamkar wasu bodyguard ďinta har tayi ta fito kuma su qara kulle ta ba halin tace zatayi wanka bata sani ba su afka mata."
"Saidai kuma wani lokacin idan akwai wutan nefa takan jin dama dama da yake akwai fanka a saman daķin."
"Qaramar ķofar dake jikin babban get ďin gidan nasu tashiga kwankwa sawa, Cikin sauri mai gadi yazo ya buďe mata gameda tsayawa ya tare ķofar yana mata kallon sama da qasa, gani yayi kamar hajiyar sa humaira ce saidai kuma wannan tayi baka sosai tayi rama bakamar tasu humairan da yasani ba duk da itama tanada ďan duhu Amman wannan tafita duhu da rama."
"Katse shi tayi daga zancen zucin da yake tana kallon sa cikin damuwa tace, Meye hakane Malam musa zaka matsa kabani waje in shiga ne ko kuwa zaka tsaya kasani agaba kana kallo na saikace kasamu TV....
✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:11] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*59*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*
Yi haquri hajiya ai bangane ki bane shiyasa kikaga ban baki hanya ba" Haushi maganar tasa yabata cike da takaici tace Haba malam musa ni Humairan ne zakace baka gane ni ba kodai kawai neman magana kake"?
"Allahu akbar ya salam ranki ya daďe ki gafarce ni wlh fuskar takice ta canza min wani iri shiyasa bangane ki ba, bisimillah ga hanya ki shigo kawo jakar taki, Cike da rusunawa yake mata maganar yabata hanya dan ta wuce yana miqa mata hannu dan ya karbì bacgon dake hannunta, fuskan sa cike da mamaki yana tambayar zuciyar sa to meye yasamu hajiya humaira haka ta lalace tamkar ba yar gata ba."
"Batareda ta kuma bi ta kansa ba tasa kai cikin gidan tana faďin bar min kayana zan iya shiga dashi basai ka karbà ba kuma kada kasanar da Abba ina gida idan yadawo" Kai ya girgiza mata ba musu ta shige abunta, yana tsaye yana binta da kallon al'ajabi ta baya domin shi ganin ta cikin irin wannan yanayin ba qaramin mamaki ya jefa shi ba dan ko amafarki akace masa wannan humaira ce ta koma haka dakyar zai yarda bare yanzu azahiri."
"Da yake cikin gidan nasu babban gida ne yana ďauke da babban fili, An mamaye shi da flawers masu kyawun gaske ya sanya gidan yin bala'in kyau da tsari."
"Tana cikin tafiyar ne tadawo da baya zuwa inda malam musa ke tsaye yana riqe da habàr sa har zuwa lokacin idanunsa yana kanta, Ganin ta dawo inda yake ne yasa ya maido da hankalin sa gareta, Cikin qasa da murya tace Suwaye da waye ne agida, Abba yana nan"?
"Kai ya girgiza mata alaman a a kafin yace, Abban ki dai baya nan bai dawo ba Amman nasan duk yanda akayi yanzu yana hanya yayanki kuma gaskiya shikam zuwan sa zai iya kaiwa dare Amman dai Hajiya tana ciki ba inda taje....
"Kai ta kaďa ta shige cikin gidan batareda tsaya ciki gaba da sauraran tambayar da tayi masa ba dan ganin bàta mata lokaci yakeyi daga tambaya ďaya da tayi masa yakama jero mata bayanai."
"A hankali take taka ķafar ta tamkar kace marar gaskiya tana tafiya tana waige waige, cikin zuciyar ta tana fatan Allah yasa tashiga ciki kai tsaye har ďakinta batareda Mummy ta kalleta ba."
"Tana dafda shiga cikin parloun nasu tajiyo motsi daga kitchen alamun ana tabà plates" Zuciyar tane sosai yafaďi sakamakon ďaga kai da tayi ta hango Mummy tsaye kusa da gas ta juya bayan ta da yake window kitchen ďin babba ne yasa ta iya hango ta sosai."
"Numfasawa tayi a hankali ganin alamun hankalin Mummyn yana kan aikin da take ya sanya tasa hannu ajikin ķofar parloun a hankali ta buďe ta shiga."
"Cike da sauri ta haura saman beni ta nufi ďakin ta batareda tsaya bàta lokaci ba tana fata a ranta Allah yasa ķofar a buďe take basu kulle ba tunda yanzu bata gidan domin a nan take ganin zatafi sakewa har tagaba shirin ta batareda wani ya shigo ya ganta ba."
"Hamdala tayi a ranta tana murmushin jin daďi sanadiyar samun ķofar da tayi a bude" kutsa kai tayi ta shiga tareda mayar da ķofar ta rufe tasa masa key ta ciki kafin ta qarara bakin gado ta zauna tanabin cikin ďakin da kallo, Sosai taga ya canza mata tamkar ba shiba ga wani irin ni'imataccan ķàmshin turaren wuta dake tashi a ciki tareda sanyi sanyi mai ratsa kankan jiki."
"Ajiyan zuciya ta sauķe tareda buzar da iska ta bakinta, cikin wani irin farin ciki ta kwanta rigingine akan gadon tana lumshe idanunta fuskan ta ďauke da lautsatstsar murmushi najin daďi a ranta tana faďin ohh finally now i have came back to my home thank u ya rabbi...
"Saida ta ďauki mintuna tana kwance kafin ta miqe tsaye cikin hanzari tamkar an cokareta ta shige toilet kai tsaye dan tayi wanka ta tsaftace dattin dake jikinta."
"Ta ďauki tsawon lokaci sosai tana wanka da ruwan ďumi kafin ta kammala tayi brush gameda ďauro alwala ta fito daga toilet ďin."
"Bayan ta tsane ruwan dake jikinta ne ta isa zuwa inda cupboard ďin kayan sawanta yake ta zaro doguwar riga ta material mai kyau ruwan baki da fari wanda akayi masa ďinkin bubu" Sakawa tayi ta ďaura baķin gyale akanta kafin ta nufi gaban madubin ďakin nata tashafa mai tareda feshe jikinta da turare masu daďi."
"Bayan ta kammala da kintsawan da takeyi ne tayi sallan la'asar da ake binta dan shine basu tsaya a hanya sunyi ba kafin tafice a ďakin nata a sannan tafara zagaye cikin parloun da kallo tsaf yake ko ina agyare babu datti sai daddaďan ķamshin turaren wutan dake tashi a cikin sa yahaďu da sanyin A C dake kunne a parloun."
"Ta dining table ta nufa tafice zuwa kitchen" Tun daga baķin ķofar ta hango Mummy wannan karon kam zaune take kan kujerar dake tanade a kitchen ďin tana danna wayar ta" a hankali Humaira ta qarasa zuwa gareta ta baya tasa hannu a fuskanta ta rufe tana danne dariyar dake cin cikinta."
"Riqe hannun nata Mummy tayi tana faďin ohh ni ýasu waye wannan yazo ya rufe min idanu haka...Shiru tayi batareda ta qarashe maganar ba, cike da mamaki kasancewar ķàmshin turaren humaira wanda tafison amfani dashi taji ya doke mata hanci hakan ne ya sanya ta miqewa a hankali ta cire hannun daga kan fuskan ta kafin ta jiyo da kanta sukayi idanu huďu da yar autar yarta wacce take kewar ta sosai"
"Dariya humaira ta kwashe dashi tareda faďawa jikin Mummy tana faďin surprise my lovely Mum I really really miss u so much wlh."
"Cike da nuna farin ciki Mummy ma ta rungume ta tsam ajikinta tana mamakin ganin ta" Sun lokaci suna rungume da juna kafin Mummy ta ďago da kanta tana kallon ta sosai cikin ido ta soma cewa,
"Humaira kece nake gani haka agabana, yaushe kikazo bamu sani ba babu wanda kika fadawa banda hakama meye ya sameki naga kin rame kinyi duhu inafatan lfy dai"?
"A lokaci ďaya duk ta jero mata tambayoyin wanda hakan ya sanya Humaira sauķar da idanunta qasa wanda suka soma cika da wahaye tunawa da abubuwan da suka faru da ita tun sanda ta tare tabar garin su gidan su zuwa gidan mijinta ta sara farin ciki da kwanciyar hankali."
"Danne kukan dake shirin ķubùce mata tayi cikin zuciyar ta, A hankali ta ďago da idanunta ta qara kallon Mummy akaro na biyu tana qiqiro murmushin karfin hali tace..
"Lfy ta lau Mummy na wlh nadawo dan in koma makaranta ne, karki damu naqi sanar daku zuwana ne dan inaso nayi muku surprise kuma gashi nayi naji daďi dan haka idan Abba da yaa Mahmud sun dawo karkice masu nadawo dan so nake kawai su kalle ni agaban su, Dan haka yanzu muje inga mai kika girka mana yau wlh yunwa nakeji sosai gashi nayi missing ďin girkin hannunki Mummy na."
"Cikin shagwabà ta qarashe maganar tana karya wiya a yayinda take jan hannun ta tana qara faďin, Nikam ina Hawy ne tunda nazo banganta ba"?
"Amsa Mummy ta bata da cewa, Hawy na aike ta bata dawo ba, Sai kuma meye ya mayar dake haka Humaira baki faďa min ba"?
"Wayyo Mummy ya hakane, dan Allah ya isa wannan tambayar pls ki yarda dani lfy ta lau kawai dai na ďanyi zazzabì ne shiyasa kikaga narame dan haka muje kibani abinci inci wlh yunwa cinye min cikina yake."
"Kai ta jinjina kawai tana raya abun a ranta dan tanaji ajikinta da abuda humaira ke bòye mata saidai kuma bazata tilassa mata ba a hankali zatabi tagane koma miye take bòyewa."
"Qarasa haďa Abincin sukayi a tare Humaira takai dining table ta jerasu bayan ta ďibi nata a plate domin irin jin yunwar da takeyi bazai iya bari tajira zuwan su Abba har zuci tare ba" Ďakinta tashiga da abincin cike da plate tamkar kace mutane biyu ne zasuci, ita kanta tasan ta ďiba abincin dayawa irin yanda bata bàta yi ba ko Mummy saida tayi mamakin ganin irin yawan abincin da ta ďiba bayan kuma tasan tun farko ďiyar ta bamai cin abinci dayawa bane itadai abarta da shayi kullum tanasha kamar buzuwa."
"Abba ne yadawo gidan wanda a lokacin dare ya soma shiga dan har an idar da sallan magariba ana neman isha'i" Gefensa ya shiga kai tsaye ya watsa ruwa a jikinsa ya shirya cikin farar jallabiya ya fesa turaruka kafin yabaro bàngaran nasa zuwa dining dan sawa cikin sa abinci."
"Mummy ne tazo ta sameshi zaune a kan ďaya daga cikin kujerun dining table ďin yana shirin ďiba abinci" Bayan tayi mishi sannu da zuwa ya amsa kafin ta ďiba masa abincin daidai yanda zai iya ci tareda zuba nata a ďaya plate ta mayar da murfin kulan ta rufe."
"Sunacin abincin suna jefa hira sama sama cikin nishaďi gwanin bansha'awa Amman ko kaďan Mummy bata gwada masa cewa Humaira ta dawo gida ba tunda tace mata tanaso tayi masa surprise da kanta yasa bata sanar dashi ba tayi shiru" A lokacin ne Humaira ta baro ďakinta dama tun daga window bayan ta idar da sallah tana leqe ta hango zuwan shi hakan yasa ta sauķo daga saman beni ta nufi inda dining table ďin yake a hankali tana takawa har ta iso garesu da yake zaman kujeran da Abba yayi ya juya ma ķofar dining ďin baya bazaisan wanda yake zuwa a bayansa ba sai Mummy dake kallon ķofar ita tayi ido huďu da Humaira wacce ke shirin rungume Abba ta baya batareda yasani ba."
"Kai Mummy ta girgiza tana murmushi taci gaba da cin abincin ta a yayinda Humaira tasa hannu ta rungume Abba ta baya tsam ajikinta cikin dariya take faďin, Surprise my Abba yau ga autar ka tadawo."
"Cike da tsananin farin ciki da mamakin muryan wacce yaji yasa yadakata da cin abincin da yake, ya miqe tsaye ba shiri, baki sake yana binta da kallo wanda yake na farin ciki da mamaki."
Rungume sa taqara yi akaro na biyu tanajin wani irin daďi a ranta yau gata ga Abban ta wanda ta ďauki tsawon lokaci tana kewar su" Cikin shagwabè fuska tana tura baki tace."
"Haba mana Abba na yanaga saikace bakayin farin ciki da zuwana kodai na koma inda nabaro ne"?
"A a, yafaďa yana girgiza mata kansa yasa hannunsa ya rungume ta shima kafin ya ďago da kanta yana kallon cikin kwayar idanunta da kyau yace, Humaira wai kece nake gani agaba na, Yaushe kikazo bamu sani ba kuma meyasa baki sanar damu ba akan kina hanya"?
"Ohh Abba na ai yanzu wannan tambayar ta wuce tunda dai gani nan nazo lfy."
"Kai ya gyaďa mata yace hakane Mamana saidai ya naga kin rame bakida lfy ne"?
"Yana shafa kanta yayi maganar a yayinda ta sauķe numfashi a hankali tana murmushin karfin hali tace, my Abba lfy lau wlh nake kawai dai missing ďinku ne ya ramar dani but now nadawo zuwa gareku nasan ba makawa nan da kwana kaďan zan koma yar lukuta lukuta."
"Dariya maganar nata ya sanya shi harda Mummy dake cin abincin ta saida tayi murmushi tana girgiza, Abba yakamo hannunta ya zaunar da ita kan kujerar dake dafda nashi ya matso da plate ďin abincin sa zuwa gabanta yace, To Mamana naji maza sa hannu muci abincin tare dan inaso tun yanzu infara mayar dake lukuta kamar yanda kikace dan nasan ke ďin ba gwanar cin abinci bane zaki iya min wayo."
"Dariya tayi tace, Haba dai Abba bazanyi maka wayo ba wlh ai yanzu hakama a koshe nake dan ina dirowa gida na ďiba nawa abincin naci dayawa domin yunwar da naji yasa nakasa jiran dawowar ka muci tare."
"To shikenan Mamana bari in kammala da cin nawa abincin sai mu koma zuwa parlou kibani lbrn yan ķatsina ko da yanda kikabar su mijin naki."
"Shiru tayi bata kuma cewa komai ba illah murmushin da ta sakar masa gameda jiransa har ya kammala da cin abincin ta kwashe wajan ta qara saka turanen wuta bayan ta ďan buďe windows ķàmshin Abincin yafita wanda a lokacin su Abba sun koma parlou."
"Bayan ta kammala sawa ta nufi zuwa parloun inda suke ta zauna kusa da Abba suka shiga yin hiran yaushe rabo."
✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:11] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*60*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*
"Suna zaune a parloun suna hira har zuwa lokacin wayar Mummy ya soma ruri tasa hannu ta ďaga ganin Mahmud ne ke qiran ta."
"Cikin kashe murya bayan ya gaisheta yace Mummy pls kisa Hawy ta miqo min abinci na wlh nagaji dayawa bazan iya qarasowa ciki ba."
"Mitse, Mummy taja dogon tsaki cikin ďaga murya tace, Wai Mahmud meyasa bakajin magana ne, yaushe katsiri irin wannan iskancin, meye kazama da zakace abinci ma saidai a miqo maka gefen ka kai bazaka iya zuwa ba saikace ďan gidan shugaban qasa, To bari kaji wlh daga yau sai yau bazan kuma aika maka abinci ba idan yunwar yana damunka zaka iya zuwa kaci idan kuma baya damunka shikenan, dan haka ka shigo abincin ka yana kitchen idan kanada niyya dan babu wata Hawyn da zan aika maka, Ja'irin yaro kawai."
"Kashe wayar tayi cikin haďa fuska bayan tagama masa maganar Humaira ta ďago da kanta tace Mummy keda Yaa mahmud ne ko, To bari in kai mishi tunda har zuwa yanzu yakasa daina halin nashi, kingama nasamu hanyar mishi surprise ďin kenan."
"Tana maganar ne tareda miqewa tsaye tace Abba karfa katafi bacci kajirani yanzu zan kai masa nadawo dan hiran tamu bata qare ba."
"Kai ya gyaďa mata yana murmushi ta wuce zuwa kitchen ta haďa abincin akan tray ďaya ta nufi bàngaran sa."
"Koda ta buďe ķofar parloun ta shiga wayam ba kowa tagani hakan ya sanya ta ajiye abincin akan table ďin dake tsakiyar madaidaicin parloun kafin ta nufi ďakin sa kai tsaye."
"Har tasa hannu zatayi knocking tashiga da sallama sai kuma tafasa Ta tura ķofar a hankali ta shiga ďakin tana leqe da kanta, Kwance ta hango bisa gado yayi rigingine fuskan sa yana kallon sama Amman idanunsa a rufe suke tamkar mai bacci."
"Kai ta jinjina tana murmushi ta qarasa zuwa garesa a hankali tafaďa kansa ta gefen gadon tana dariya tace, Surprise My lovely brother."
"Hakan da tayi ne ya sanya shi miqewa a firgice sosai yana salati, Ganin Humaira ce a gaban sa ya sanya shi sakin baki yana mata wani irin kallo da yake bayyana alamun tambaya."
"Fuska ta kwabè cike da shagwabà ta qara rungume sa akaro na biyu tana faďin, Haba mana Yaa Mahmud, Wannan firgita haka saikace kaga baķin dodo, kodai Bakayi marhaban da zuwana bane naga kana min wani irin kallo"?
"Ya salam yafaďa a hankali ya ďago da kanta suna kallon juna yafara binta da idanu sama da qasa, Mamaki ne ya ishe sa matuqa ganinta haka a rame gashi tayi baka domin kuwa kayan dake jikinta yanzu yasan lokacin da take sakashi yayi mata daidai ajikinta, But now sai yaga tayi yar frit acikin kayan tamkar aron shi aka bata."
"Numfashi ya sauķe a hankali ya miqar da ita tsaye yana qara kallon ta akaro na biyu yace, Humaira yaushe kika dawo cikin garin nan baki sanar damu ba, kuma meye ya sameki kika lalace irin haka"?
"Jin irin tambayar da yayi mata ne yayi sanadiyar sanya sauķar da idanunta jikinta yayi sanyi sosai domin kuwa a haqiqanin gaskiya tasan cewa yayanta yana mugun sonta sosai har a zuciyar sa kuma yana damuwa da ita da lfyr ta koda da suke yawan faďa kullum sanda take gida kafin tayi aure yana cikin dukanta tasan cewa itace batajin magana duk abunda tasan zai iya bàta masa rai shi takeyi shi kuwa zafin zuciyar sa tafi karfin sa dan bayason rainin hankali ko kaďan idan zaka bashi girma zaku zauna lfy idan kuwa kace kai tauri qiqi ne marar kunya to zaka fuskanci fushinsa."
"Numfasawa tayi a hankali ta sauķar da ajiyan zuciya tana riqe da hannayen sa biyu cikin nata ta soma cewa."
"Aiyya my lovely brother pls kwantar da hankalin ka lfy ta kalau just na ďanyi zazzabì kaďan ne but now am well" Ajiyan zuciya ya sauķar tareda tallafo fuskan ta yana murmushin farin cikin ganinta yace, Alhamdulillah qanwata naji daďin ganin ki, ya hanya ya kikabaro ķatsina"?
"Lfy lau yake fatan kaima lfy na sameka"?
"Garau nake my sisi ya jikin naki hope ba wata matsalar dake damunki"?
"Ohho Yaa Mahmud, Yasin kafiye tambaya dayawa saikace sabon lawyer nace maka nasamu sauki kuma banida wata matsala pls muje nakawo abincin naka kaci kaji"? kar yunwa yayi sanadiyar cinye min cikin my lovely bro,"
"Dariya yayi sosai bayan ya cakuli hancin ta yaja hannunta suka fice daga ďakin".
"Itace ta zuba masa abincin daidai yanda zai iya ci, yayi yayi da tasa hannu suci tare sam taqi tace a koshe take hakan yasa yarabu da ita yaci gaba da cin abincin sa tana masa hira yana amsa mata cikin nishaďi."
*Ķatsina*
"A wannan daran ranar wajan misalin karfe goma ya shigo gida kai tsaye ya shige ďakin sa zuwa toilet yayi wanka ya fito ya shirya cikin doguwar jallabiya ruwan toka ya feshe turare ajikinsa ya isa kan gado ya zauna ya buďe wayar sa yaga miss call ďin Haisam."
"Qiran sa yayi suka shiga gaisawa, suna cikin hira ne Haisam yake tambayar sa ina Humaira da Maraqishiya"? Kai Abdulmalik ya dafe yace ya salma abokina lfy suke but ina zuwa zan qiraka anjima" Yana kaiwa nan ya kashe wayar yana dafe kansa da ya ďaure masa qam."
"Bakomai bane ya shigar dashi wannan halin face tunawa da yayi da Humaira sam kwana biyun nan da yake aiki yamasa yawa ya rufe masa idanu sam ko hutun zama baya samu, gari yana wayewa tun safe kafin kowa yatashi zaiyi wanka yafita batareda yayi karin safe ba haka zai wuni sai dare wajan su karfe goma zaishigo gida wanda a wannan lokakin kuwa da yake Maraqishiya ce keda kwanan sa ya sanya bai damu da rashin motsinta da bayaji ba."
"Mamaki ne ya ishe sa a ransa yace lfy kuwa yarinyar nan take kodai batan nadawo bane"?
" Miqewa tsaye yayi dan yaje ya dubota domin yariga da yasan cewa duk ranan da yake natane tanajin motsin dawowar sa zatazo ta tareshi ko fishin da yake da ita baya damunta sai tazo gareshi Amman yanzu da ya lura tun daran shekaran jiya da tazo tana bashi haquri yagaya mata maganganu masu ďaci wanda shi kansa yasan yaci ranta to tun a ranar bata kuma kusontowa garesa ba har yau da rashin ganinta ya damesa."
"Koda yabaro ďakin sa kai tsaye nata ďakin ya nufa yasa hannu ya tura ķofar yashiga" ganin ďakin yayi yamasa tsit alamun babu mutum mai numfashi aciki, baiyi qasa a gwaiwa ba ya qarasa gaban ķofar shiga toilet yakasa kunnensa ko zaiji motsinta aciki Amman sai yaji tsamanin haka."
"Fita daga ďakin yayi bayan yaja ya rufe ya nufi kitchen ďin ta a tunanin sa ko tana can, Saidai kuma wani abunda yaqara ďauŕe masa kai ķofar ma a kulle take da key."
"Hankalin sane sosai yayi mugun tashi tsantsa yana tambayar zuciyar sa to ina ta tafi da daddaran Allah batare da nasani ba"?
"Ganin bamai basa amsa zai samu ba yasa ya nufi ďakin Maraqishiya yana kwala mata qira cikin muryan damuwa wanda wannan ďaga muryan da yake yana qiran sunanta shi yayi sanadiyar farkar da ita daga baccin da ta somayi mai daďin gaske domin ba qaramin mugun gajiya takwaso ajikita ba ko ina ciwo takeji yake mata dan yinin ranar yau gabaki ďayan sa a gidan suna tayi shi ita da shiwari na wata qawar su da haifu sune qirjin biki hakan yasa tayi mugun gajiya."
"Tana cikin murza idanunta da yake cike da magagin bacci ya turo ķofar ya shigo batareda ya tsaya ya kula da murzan idon da take ba yace."
"Ina Humaira take"?
"Ohho ya rabbi, tafaďa tana dafe kanta cikin bàcin rai da takaici taja tsaki tareda komawa ta kwanta taja bargo ta rufe jikinta tana faďin."
"Yanzu dama akan wannan matar ne zaka zo ka raba min bacci na mai daďi da nakeyi, To bansan inda take ba tunda ba shiga harkanta nake ba kuma ai ba ajiyan ta aka bani ba da zai zama ace nasan inda take ko take zuwa."
"Fuskan ta yana rufe cikin bargo take maganar a yayinda ya yinquro cikin bàcin rai da niyyar ya finciko ta sai yaga kuma babu amfanin hakan ya fice yabar mata ďakin domin kuwa wani haushin zata qara shigar dashi akan damuwar da take damunsa."
"Ficewa yayi haraban gidan kai tsaye yana kwalawa baba mai gadi qira cikin ďaga murya" A gurguje baba mai gadi yafito daga ďan madaidaicin ďakin sa yaqaroso gaban sa ya rusunar da kansa qasa yana faďin."
"Sannu da hutawa ranka shidaďe gani me za'ayi maka"?
"Bakomai Humaira nake nema banganta ba ko kaga fitan yau da gare ya waye"?
"Allah ya taimake ka yallabai wlh banga hajiya ba bare fitan ta daga gidan nan yau kwana biyu kenan ana neman na uku ko abincin da tasaba bani kullum yanzu banga tana bani ba har nima nake cewa ko lfy take haka."
"Ya salam, ya furta a bakin sa a hankali cikin tsananin tashin hankali ya koma cikin gida bayan yace da baba mai gadin shikenan ya koma yayi kwanciyar sa zai gwada qiran layin wayar ta yaji ko ina tayi."
"Kamar yanda yace ďin haka yayi yana nufar ďakin nasa ya ďauki wayar sa yashiga qiran phone ďinta Amman meye sai yajita akashe, baiyi qasa a gwaiwa ba yaci gaba da qira Amman inaaa akashe take, Haka ya haqura yana tunani cikin zuciyar sa To ina tashiga kuma takashe wayar ta."
"Yana cikin zancen zuci ne ya tuna da tana shiri da Batula zai iya iyuwa tasan inda take" Qiran wayar Batula yayi bata ďauka ba saida yakusa tsinkewa kafin ta ďauka tace."
"Hello Yaaya ina wuni"?
"Lfy, ya amsa mata kai tsaye yace, Ina Humaira take ko kinsan inda tayi dan bata gida kuma naqira phone ďinta akashe"?
"Aiyya Yaaya wlh bansani ba bata sanar dani ko zataje wani waje ba kuma nima shekaran jiya ranar talata da safe naga miss call ďinta Amman da naqira naji akashe ko yau saida naqara qira but still akashe har nake cewa gobe zan shigo na duba ta naga ko......
"Qit ya kashe wayar batareda yagama jin maganar da takeba yanajan dogon tsaki yace, kaji min yarinya yar gidan surutun tsiya daga tambayar ki abu ďaya shikenan sai ki zarce da dogon bayani saikace ance miki lokacin kine dani."
"Tashi yayi yabar ďakin nasa ya nufi nata a karo na biyu ya soma zagaye cikin ďakin da kallo tamkar sabon gani yana qara tambayar kansa ina tashiga ta kashe wayar batareda yasani ba."
"Waje yasamu yasamu ya zauna a bakin gadon ďakin yanajin ķàmshin turaren wuta yana dokan hancin sa yasa hannayen sa duk biyu yana shafar sajen fuskan sa gameda fuza iska a hankali yarasa meke masa daďi tunanin sa ďaya shine yanzu ta ina zai soma neman ta a cikin faďin garin nan bayan yasan ba ko ina tasani ba face gidan su Umma tunda ba yawo takeba bare yace tasan wasu mutanan."
"Ajiyan zuciya ya sauķe mai nauyin gaske cikin tsantsan damuwa da rashin sanin abunyi ya miqe tsaye da niyyar komawa daķin sa ya qira Haisam yasanar dashi abunda ke faruwa ko zai iya taimaka masa."
"Idanun sa ne suka sauka kan wata yar takarda wacce take a dunkule kan drawer kusan da gadon ďakin inda yake tsaye."
"Hannun sa yake zuwa kan drawern ya ďauki takardar ya warware shi yana binsa da kallon mamaki" Ganin irin doguwar rubutun dake zane ajikin takardar ne ya sanya shi daidaita tsayuwar da kyau kafin ya soma karanta takardar kamar haka.......
✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:12] Ameena Group Aysha Kn: RAYUWAR AURENA
*Page*
*61*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*
"Assalama alaikum ya masoyina abun alfari na, Nasan cewa abunda idanuwan ka zasu gani yanzu ajikin wannan takardar ba qaramin mamaki zai shigar dakai ba ko tashin hankali."
"Yau inaso in sanar dakai abunda bakasani abaya, Ya kai mijina kasan cewa Allah ma munayi masa laifi kuma ya yafe mana idan mun nemi gafaran sa, nayi maka laifi na nemi gafarar ka Amman kaqi yafe min kaqi fuskantar halin da nake ciki narashin ka."
"To yanzu komai yazo ķarshe zan bar maka gidan ka yau in koma gidan iyayena idan kadawo baka sameni ba karka shiga damuwa dan nayi maka nisa a wannan lokacin kuma inajiran takardan saki naraba aure tsakani na dakai domin kuwa bazan iya cigaba da rayuwa dakai a wannan hali na rashin jituwa ba."
"Karkace idan nafita daga gidan ka narasa wanda zai aure ni kenan, Sam ko kusa inada samari masu sona da aure."
"Nasan cewa a zamana nida kai abubuwa da dama sun faru a tsakanin mu na rashin jituwa har zuwa yanzu da nabar gidan ka."
"A zamana nida kai nan gaba bazu tabà jin daďin zama ba tunda har zargi yayi nasaran shiga zuciyar ka."
"Dan girman Allah inamai rokon ka da kacireni a zuciyar ka kashafe sunana a bakin ka yazamana baka tabà sanin mai wata irin suna Humaira ba domin yanzu nayi maka nisa bazaka sake qara ganina ba koda kuwa a mafarki ne inaso lbr na yazama tarihi a gareka..
"Nima kuwa daga yanzu nashafe ka a rayuwata" Dan haka daga nan nake maka fatan alkhairi da fatan samun zuri'a tagari."
"Wanna saqon yana fitowa ne daga cikin baķin Tsohuwar matarka Humaira ina fatan zai isa zuwa cikin birnin zuciyar ka dan tasamu lasisin wanke shafin rayuwata batareda tabaka walaba."
"A nan nake maka fatan alkhairi Yaa Abdulmalik bissalam sai mun sake saduwa ranar gobe kiyama."
"Tunda ya soma karanta takardar yayi mutuwar tsaye, zufa duk ta wanke masa fuskan sa baisan lokacin da ya zauna a bakin gadon ďakin ba yana qara juya takardar a hannunsa."
""Zuciyar sa a jagule take sosai ya rasa wanne irin tunani zaiyi ganin abun yake tamkar a cikin mafarki domin kuwa a iya zaman sa da ita bai tabà yin zaton haka daga gareta ba" Ajiyan zuciya ya sauķe mai nauyin gaske yana shafan sajan fuskan sa."
"Ya shafi tsawon lokaci yana zaune a ďakin har zuwa lokacin yana maganar zuci domin ba qaramin ďaure masa kai yayi ba" tambayar kansa yake shin anya Humaira ce"?.. Shiru yayi tamkar an cokaresa ya miqe tsaye ya cura takardar ya dunkule ta tareda wurgar dashi a filin ďakin ya fice kai tsaye zuwa ďakin sa ya kwanta rigingine bisa gado gameda rufe idanuwan sa yana buďewa har izuwa lokacin zuciyar sa yana cikin wasi wasi."
****** *******
🌾🍃🌾🍃🌾🍃🌾
*Abuja*
Abba, Abba, Pls inaso ka siya min sabon phone kaga gobe ne zan koma makaranta dole in tafi da waya a hannuna dan ina qiran Abba na da mummy na inajin muryan su."
"Humaira ce ke wannan maganar cikin nishaďi da walwala, fuskan ta ďauke da murmushi wanda ya sanya bayyanar fararan hakoranta" cike da zolaya ta qarashe maganar tana kallon fuskan Yaa Mahmud ta witsiyar idanunta a yayinda ya ďago da nasa idanun ya cilla mata harara yana haďe fuska yace."
"To sannu yar autan Abba da Mummyn ta wato ma su kaďai kikasani su kaďai kikeson jin muryan su, ba komi zaki gamu dani wataran inga kin qirani kashewa zanyi dan nima a lokacin bansan koke waye ba, Kuma saura naga kinzo kina kashe min murya cewa kinaso nabaki wani abun maujeki zanyi."
"Kai Yaya na, Miye haka yayi zafi na wannan dogon bayanin, wasa fa nake maka kasan nida kai ai hanta da jini ne duk faďan da zamuyi bama rabewa, da wuri muke shiryawa abun mu dan haka yanzu ma nake shirin roqon ka cewa zaka kaini gidan su Fadila da Ummar Amena in gaishesu nasan zaka zamuje ai ko kuma kabani aron motar ka."
"Tana cikin dariya ta qarashe maganar, Mahmud Ya qara cilla mata harara yana kaďa kai Abba ya dawo da duban sa kanta yace."
"Mamana maiyasamu wayar taki kikeson a siya miki wata"?
"Abba faďiwa qasa tayi warwas tafashe."
"A takaice tayi maganar tana kaiwan loman abinci bakinta da yake dama a dining table suke dukan su da Mummy suna karin safe."
"Ya salam Abba, yafaďa yana salati yaqara cewa, ina wayar take kawo in gani."
"Dum taji zuciyar ta ya buga ita zaton ta karyan da tayi zai karbè ta ashe fa ba hakaba."
"Mamana ina wayar take kinyi shi, kodai kin barota a can katsinar ne"?
"Eh Abba, Tafaďa cikin gyaďa kai tana muzurai da idanuwanta wanda kana kallo zaka iya gane alamun rashin gaskiya tattare da ita."
"To shikenan bari yanzu zan bawa Mahmud kuďi sai kuje dashi ki zabì wanda kikeso."
"Yauwa Papa na thank u so much but kabamu kuďin dayawa dan IPhone 6+ nakeso da kuma qaramar waya extra."
"To sannu yar gidan masu kuďi, acikin siyar wayar ma harda Extra, da yake ance miki a shara ake kwasan Kuďin ba"?
"Mummy ce ke wannan maganar tana watsa mata harara a yayinda Humaira ta kwabè fuska tace, Haba mana Mummy karki min haka mana abu shi Abba wanda zai bayar da kuďin ma baiyi complain ba sai ke, To nidai gaskiya biyu nakeso babba da qarami, Ko Abba zaka saya min ai ko"?
"Tana langabàr da kanta ta qarashe maganar."
"Himm Mamana kenan kedai kuje ko duk wayar shagon gabaki ďayan sa kikeso zan iya siya miki har indai inada halin yin hakan dan haka karki samu damuwa kije ki ďauki duk wanda kikaga yayi miki a ranki ."
"Tashi tayi tsaye daga kujeran da take zaune cikin dariyar farin ciki ta rungume Abba ta baya tana faďin, Yauwa my lovely Dad shiyasa nake qara sonka a raina thank u so much Allah yabar min kai har zuwa tsawon rayuwa ta."
"Amin Amin ya Allah Humaira."
"Cewar Abba yana dariyan shima a yayinda Mummy ta dawo da dubanta zuwa garesa tace."
"Wato gaskiya Alhaji ba kowa ke bàta yarinyar nan ba face kai, yanzu fisabidillahi yaza'ace yarinyar nan zata riqe waya har biyu bayan gashi ko ďayan ma ba iya kula dashi tayi ba."
"Dawo da dubanta ga humaira tayi tana hararan ta kafin ta qara cewa, kodan ai kece da lefin sai shegen kinibibin tsiya girma kikeyi Amman ko kaďan bakisan kina girma ba, to zanga a gidan da zaki riqe waya har biyu ja'iran yarinya kawai."
"Mummy rabu da ita iskanci ke damun ta bani bane zan kaita ta siya wayar, to zanga ta inda zata ďauki har biyu idan kuma ta ďauka saidai ta biya da kuďin tunda yanzu ita yar familyn wasu ce ba namu ba."
"Cewar Mahmud, bayan ya miqe tsaye yana gyaran rigar jikinsa wanda a wannan lokakin Humaira ta kumbura fuska tana zunbura baki tace, Haba mana Yaa mahmud ya zaka biye wa mummy kana min haka ka mance kai waya uku ne tare dakai kana amfani dasu, ba gwara ni bama da natsaya a guda biyu."
"Yunqurowa kanta yayi da niyyar ya mauje mata bakinta tayi saurin bùya a bayan Abba tana dariya tareda yi masa gwalo."
"Harara ya watsa mata tareda cewa, shegiyar yarinya yar rainin hankali ance miki ni ďin sa'an wasanki ne, To wlh kishiga hankalin ki kibar ganin kinyi aure yanzu kice kinfi karfin duka, To nikam zan iya nakasa ki wlh inyi miki dukan tsiya marar kunya kawai....
"Kai Mahmud ya isheka haka nan banison jin wata maganar banza maza wuce ka kaita ta ďauki duk wayar da takeso ko nawa ne kabayar tunda bada kuďin ka zaka siya mata ba Kuďi nane, Kuma daga nan ka wuce da ita gidajan da takeson zuwa ta gaishai su saura kuma inji lbrn cewa baka kaita ba saina sabà maka."
"Abba ne ya katse shi cikin ďaga murya."
"Kansa Mahmud ya kaďa fuskan sa a haďe yakama hanyar fita daga parlon yana gunanai ciki ciki yace, zanga uban wanda zai iya lalata lokacin sa akan wannan zirga zirgan dan nikam bazanyi ba tunda ba drivern ta bane ni."
"Abba yanajin sa yana guna gunan, Ya murmusa yace Mamana shirya kibi bayan sa kuma duk abunda yace bazaiyi miki ba idan kin dawo kisanar dani."
"To Abba na ashirye nakema thank u sai nadawo kawai bye."
"To ďiyata Allah ye yakilewaro sadi,( To ďiyata Allah ya kaiki lfy)
"Yana maganar ne tareda miqewa tsaye yana shirin fita daga parlon shima dan zuwa office Mummy nabin bayansa dan ta raka shi wajan mota tace, Amman dai gaskiya alhaji ka rage shagwabàr da yarinyar nan da kakeyi wlh shi yake sakata bata ganin kan kowa da gashi."
"Murmushi Abba yayi yana girgiza kansa yace, Mumyn Humaira kenan Amman dai kinsan cewa ďiyar tamu batada rashin kunya da raini ko, saidai idan an tsokalo ta, idan ma tsakanin ta da Mahmud ne kema kinsan shine bashida hali inda zai bita a hankali to zasufi kowa zaman lfy babu faďa, dan haka kibar ganin lefin ta."
"Himm Mummy tafaďa a ranta batareda takuma cewa komai ba ta rakashi zuwa get ta dawo cikin parloun ta qira hawy suka tattare wajan abincin bayan ta buďe Windows ķàmshin abincin yagama fita lafin suka saka turaren wuta ko ina na cikin gidan ya ďauki ķàmshi."
"Washegarin ranar da la'asar Mahmud yakai Humaira zuwa airport ta shiga jirgin su ya ďaga sama zuwa qasar sudan, Dama ta qira Ameena ta sanar da ita cewa zatazo dan haka ta shirya mata komai kuma ta nema mata uziri daga gurin teachers nasu masu tambayar ta....
🌾🍃🌾🍃🌾🍃🌾
A katsina kuwa Abdulmalik ne zaune a parloun Abba ya harďe hannayensa bisa ķirjin sa kansa yana jingine da jikin kujera ya lumshe idanunsa, Tunani ne kaca kaca tayi masa yawa a zuciyar sa sam yakasa samun mafita" kuma wannan tunanin ba ko wacce bace face ta damuwar maganar Umma akan auran Suwaiba, domin kuwa a idan shi baizo gida ba to ita zata bishi har nashi gidan da maganar."
"Damuwar sa ďaya shine idan har ya kuskura ya auri suwaiba ya haďa su zama da Maraqishiya to ya tabbatar da cewa zasu iya tashar masa da bom a gidan sa, domin a ganin sa Suwaiba yar kauye ce ba gama wayewa tayi ba ita kuwa Maraqishiya wayewar nata da hauka har yana nema yaci karfin ta dan idan ya tuna sanda ya auri Humaira ba qaramin wahala yashaba kafin ta sauķo akafarazaman lfy, To yanzu kuma ina ga an haďa ta da Suwaiba ai sai abunda Allah yayi, Banda hakama gashi har yau wajan tsawon sati biyu kenan Amman ko kaďan yakasa samu yasanar da su Abba cewa tabar masa gidan sa, saidai kuma ganin Abba bai tabà tun karansa da maganar ba yasa yace a ransa to hala itama batasanar dasu iyayen ta ba kenan domin idan har tasanar dasu to babu shakka zasu qira Abban sa."
"Ajiyan zuciya ya sauķe ya buďe idanunsa yakai kan Umma wacce keta masa magana cikin haďa fuska tun ďazu Amman ko kaďan baisan ma mai take cewa ba."
"Marar kunyar yaro badakai nake magana ba ko so kake kace min bakasan ma mai nake faďa ba"?
"Yi haquri inajin ki Umma mai kikeso nayi miki"?
"Uwaka zaka min ja'irin yaro, wato mahaukaciya kamayar dani tun ďazu sai zuba magana nake saikace BBC dan iskanci yanzu kace min bakama san meye nake faďa ba, To bari kaji abunda zan qara gaya maka ka shirya asabar mai zuwa auran ku da Suwaiba faqat babu makawa wannan shine qarshen magana ta koka yarda kokar yarda ya rage naka nidai zan tura maka matarka ana gama ďaurin aure."
"To sannu zuciyar sa kin gama yanke masa hukunci sai kiyi mugani."
"Cewar Abba yana binta da kallon bàcin rai a yayinda Abdulmalik ya miqe tsaye cike da takaici yace."
"Abba dan Allah yanzu kam karabu da wannan maganar nahaqura nima banida abunda zance, dan ni Mata yanzu basa gaba na domin duk basu da amfani a gareni, dan haka ba suwaiba ba ko matan duniyar baki ďaya za'a aura min banida lokaci na akan su da zan basu."
"Yana kaiwa nan ya ďauki hular sa da wayar sa dake kan kujera yasaka akan sa kafin ya fice daga parloun yabar Abba yana binsa da kallo a ransa yace to mai yake damun yaron nawa haka yake irin wannan maganar"? Numfashi ya sauķe bayan wani lokaci yana qara cewa kodan mahaifiyar sace tasaka shi agaba dole yayi irin wannan maganar ba lefin sa bane."
"Umma kam murmushi tayi a ranta tace, ja'irin yaro ai dole ma ka aureta kodan kasamu kwanciyar hankali nima nasamu nawa ya kwanta."
***** ******
A kwana a tashi ba wiya a wajan Allah domin kuwa yau ne akaa wayi gari ta kasance rana ta asabar an ďaura auran Abdulmalik da Suwaiba an gayyaci yan uwa da abokan arziki"
"Tun da aka daidaita maganar auran yan uwa sunji sun aminta a cewar su tunda yaro ya amince su basu da matsalar komai."
"To tun a wannan lokacin Umma tashiga shirye shiryen gyaran Amarya itace gyara nan itace gyara can domin kuwa itace ta kasance mahaifiya ga Amarya itace qawa dan suwaiba kam ko harkan su bata shiga tamkar batasan ma abunda ke gudana ba a gidan illa karatun ta da tabawa himma dan ba qaramin haushi suke bata ba , Siyama kam dama tana makaranta batasan wainar da suke soyawa ba."
"A daran ranar ne aka shirya Amarya akaita zuwa gidan mijinta Abdulmalik, Umma da kanta tashiga cikin yan kai Amarya sukaje suka dawo bayan tayi mata irin nata huďubar da maikyau da marar kyau."
✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:12] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*62*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*
"Suwaiba ce tsaye a filin ďakin Abdulmalik da aka shigo da ita kan cewa shine ďakin ta domin Umma ko kaďan bata nuna tasan da barin humaira gidan ba kuma shima bai nuna mata komai ba duk abunda tace zatayi baya tanka mata dan a ganin sa bashida lokacin su, Hakan shiyasa tace to Suwaiba ta tare a dakinsa kafin ya kammala haďa gidan sa wanda bai gama kammaluwa ba."
"Badan komai tayi hakan ba bace dan ta nuna tamkar batasan abunda ke faruwa ba duk da ace taso ta tare a dakin humaira Amman hakan bai samuba dan baso take a gano tanada hannu aciki ba tunda har yanzu shi yakasa buďan baki ya sanar musu to itama ta gwammace a zauna a haka har zuwa lokacin da abu zaiyi tsami kowa yaji domin tasan kobadaďe ko a juma dole ne watarana asiri ya tonu dukda bazataso hakan ba idan yafaru."
"Babu abunda takeyi a cikin ďakin face safa da marwa tana riqe da kunkumin ta tarasa abunda ke mata daďi a ranta kallo ďaya tak zakayi mata ka fahimci tsantsan damuwa tattare da ita, jifa jifa takan kai duban kan a gogon dake manne jikin bangon ďakin Amman sai gani take dare yana qara tsulawa Amman ko motsin sa bataji ba bare har tagansa ya shigo ďakin da take amatsayin ta na sabuwar Amaryar sa."
"Faďi take a acikin zuciyar ta wannan wani irin aure ne da ita tayi wai ance an kawo Amarya gidan ta Amman miji ya shanya ta yakasa dawowa gida bare ya shigo suci amarcin su" Numfashi ta sauķe a hankali tanaci gaba da zagaye cikin ďakin."
"Ji tayi an murďa ķofar ďakin za'a shigo cikin sauri ta koma kan gadon ta zauna tareda mayar da mayafinta ta rufe kanta da fuskan ta tana wuri wuri da ido acikin mayafin domin a zaton ta Abdulmalik ne ya shigo cikin ďakin."
"Muryar wacce taji ne ya sanya ta ďago ta kanta gameda yaye mayafin dake rufe da fuskan ta" Maraqishiya tagani tsaye tana sakar mata da murmushin karfin hali tace,
"Sannu da hutawa dai Amarya ya gajiyan biki"?
"Lfy, Tabata amsa a takaice tana tsuke baki tamkar dole aka sata."
"Maraqishiya ta qara cewa, To sannu bari in koma daman ina zaune ni ďaya ne tun ďazu naga Mai gidan bai shigo ba har yanzu shine nace to bari in ďan leqo mu gaisa kafin ya dawo."
"Aiyya nagode sosai,"
"To saida safe nikam zan kwanta hala shima wani abun ne ya tsayar dashi haka har dare" Eh inaga hakan ne."
"Cike da takaici taqarashe maganar ji take tamkar ta kurma uban ihu dan baķin ciki, wannan wani irin walaqanci ne ace mutum yana Amarya Amman ace ango yakasa shigowa gida, Waiyyo Allah na, Tafaďa cikin qasa da murya tana murza kanta ta miqe akan gadon ta kwanta tana zancen zuci."
"A sanda Maraqishiya tabar ďakin da suwaiba ke ciki kai tsaye nata ďakin ta nufa ta zauna abakin gado gameda zaro wayar ta wanda ke cokare a kugunta ta danna number wayar shiwari."
"Saida ya kusa tsinkewa kafin ta ďauka, Maraqishiya tace,
"Sannu matar fastor, kina can kina jin daďin ki ke ďaya babu mai tashar miki da hankali ni kinbar ni cikin damuwa."
"Dariya shiwari tayi tace, Yo ai keďin da akazo aka ďaga miki naki hankalin ke kikaso dan kinga zaki iya ďauka ne Amman kinga ni da bazan iya ďauka ba ai ba'ayi min ba."
"Himm shiwari kenan bazaki gane bane wlh abun ne yanzu ya soma fin karfi na miji ne da uwar miji Allah yabani jarababbu kinga ai sai ahankali yanzu haka fitowa ta daga ďakin wannan tsinanniyar yar kauyen wai ita amarya badan komai ba sai dan gudun magana kinsan wannan jinin Umma ce dole na inbin abun da dabara inzo musu ta bayan ķofa dan ban isa ince zanyi mata irin na humaira lokacin da ta tare ba domin kuwa idan na kuskura nayi garajan yin haka wannan jarabbiyar matar bazata min da sauki ba dan haka kinga dole kizo mushirya yanda zamu fitar da ita tun kafin suci nasaran ďauke numfashi na a gidan nan gwara ni inyi nasara akan su."
"Numfasawa Shiwari tayi a hankali tamkar suna gu ďaya ta soma magana tace, Naji komai qawata kuma nasan damuwar ki abunda nakeso dake shine kibisu a hankali ayi zaman lfy har zuwa lokacin da zamuyi na qatqat wancan da ba dangin iya bare na baba itama bamu bari ba bare su, dan haka saida safe yanzu ogan nawa ya shigo ya iskeni ya tsareni da shegen tambaya kamar shi ya ajiye ni dan haka mutashi lfy."
Kafin ta ajiye wayar ne Maraqishiya, tayi dariya tace, kaji min shegiyar mata idan bashi ne ya ajye ki ba to uban waye ne"?
"Kekam saida safe dare nayi mu qarasa gobe."
"Kashe wayar tayi bayan sunyi sallama tayi miqa a kan gadon tana murmusawa a ranta gameda wasu irin tunani na neman mafita."
"Wuraran wajan misalin karfe shaďaya ya shigo cikin gidan ya nufi hanyar ďakinsa da niyyar yaje ya wasta ruwa ya huta gajiyar dake jikinsa" Tunawa da yayi a ďakinsa aka sauķe Suwaiba hakan sai ya sanya shi dakatawa yafasa qarasawa ya shiga dan ba komai zata qarasa shiba face bàcin rai."
"Ďakin Humaira ya nufa kai tsaye yasa hannunsa da niyyar buďe ķofar Amman cikin mamakin sa sai yajita a kulle qam da key, Cike mamaki ya shiga zancen zuci yace, Nidai nasan wannan ķofar a buďe take lokacin da tabar gidan, to waye yazo har ya rufe baisani ba"?...Shiru yayi yanaci gaba da raya abun a ransa yace to kodai Maraqishiya ce ta rufe, Amman ai ita kanta tace batasan da barin ta gidan ba bare har ta rufe mata ķofar daga baya, kodan zai iya iyuwa itace tunda shidai baiga shigowar wani ba zai zama tabbas itace."
"Dakin ta ya nufa yana dafda shiga ya tsaya tunawa da haukan ta da yayi yanzu haka baici ba bai shaba zata tasar masa da hankali hakan ya sanya shi haqura ya nufi nasa ďakin ya shiga a hankali yana zagaye sa da kallo inda zaiga Amaryar."
"Kwance ya hango ta bisa gadon baccin sa tayi rufda ciki, yanajin jan numfashin ta da fitar munshari tamkar kace jaka."
"Girgiza kansa yayi cikin takaici yaja tsaki a ransa ya wuce cikin toilet, zuciyar sa a jagule da damuwa yace Allah ya wadaran naka ya lalace mutum ya baje da bacci da munshari saikace kare....
"Wanka yayi ya fito ya shirya cikin kayan baccin sa ya feshe jikinsa da turare duk motsin da yakeyi batasan ma da mutum a ďakin ba illah qara jan munshari da takeyi, haka yagama shirinsa ya kwashi wayoyin sa ya fice a ďakin."
"Kan doguwar kujeran dake cikin parloun yahau ya kwanta rigingine ya rufu da bargon da yafito dashi kansa yana kallon sama gameda rufe idanuwan sa yana buďe su yashiga tunani cikin zuciyar sa har bacci ya kwashe sa batareda ya ankara ba."
"Koda asuba tayi qiran sallan farko ya tashi ya shiga toilet ďin dake cikin parloun ya ďauro alwala yafito ya wuce masallaci."
"Ba shi yadawo gida ba sai wajan karfe bakwai na safe a wannan lokakin rana ta fito ta soma haska garin."
"Har izuwa lokacin bacci take shara ya shigo ya sameta a ďakin, Kansa kawai yaqara girgizawa ya shige toilet yayi wanka ya fito yayi shirin zuwa office, ganin har ya kammala shirin bata farka ba saima qara juyi da takeyi tana gyra kwanciyar ta hakan yasa ya bigi gefen gadon kusa da ita da karfin sa wanda hakan da yayi ya firgitar da ita arazane ta miqe zaune tana wuri wuri da idonta wanda ya ďan rine dan baccin da tasha."
"Mugun harara ya watsa mata yace, ke wacce irin yarinya ne, ace tun karfe biyar aketa qiran sallan asuba Amman kin kasa tashi ki gabatar da sallah saikace wata kafura har rana tafito kina jifge kina sharan baccin banza, to bari kiji wlh wlh Allah wannan shegen ďabi'ar taki ba'a gidana ba bare a ďakina idan zaki gyara rayuwar ki to gwara ki gaggauta gyarawa dan bazan iya ďaukan wannan baďalan a gidana ba."
"Cikin faďa da haushi, fuskan sa a murtuke yake mata maganar yana zuwa qarshe a zancen sa ya ďibi jakansa da wayar sa ya fice a ďakin yana qara faďin wawiyar ya rinya kawai marar tarbiya ace duk arasa Matar da mahaifiyar ka zataso ka haďa zuriya da ita sai wannan gujagar,
"Mtsee, yaja dogon tsaki bayan ya iso ga motar sa ya shiga mai gadi ya buďe masa gate ya fice."
"Kanta Suwaiba, ta kame tana haďa fuska tace waiyyo Allah na miye haka nayi, Mtsee, taja tsaki ta miqe tsaye ta nufi toilet ta ďauro alwala ta gabatar da sallah."
***** *****
Bayan kwana biyu da hidimar bikin suwaiba, Tana zaune a ďakin da take ta zabga tagumi da hannayen ta duk biyu ta rasa abunda ke mata daďi a ranta, sam takasa gane kansa a cikin wannan kwanaki biyun da sukayi ko kusa da inda take bayason takowar ķafar sa bare har yaso yahaďa idanu da ita a duk sanda tayi gangancin tunkaran sa ko yabar inda take ko ya daka mata tsawa dan tabar wajansa jiki a sabule zatabar wajan tana ya mutsa fuska dukda kuwa ba zama yake a gidan ba idan yafita tun safe bata sanin ya fita sai cikin dare tana zune tana jiran dawowar sa kafin zata gansa ."
"Gajiya tayi da zaman ďakin ta duba a gogon dake manne jikin bangon ďakin taga karfe biyar saura hakan yasa ta miqe tsaye ta fice a cikin ďakin zuwa haraban gidan tana zagaye cikin gidan gabaki ďaya ganin sa tayi yaqara mata mugun kyau tamkar ba kamar sa a faďin garin ķatsina haka takeji, Murmushi ta sakar a hankali tace, Inama ace nice kaďai matar auran sa a gidan nan in sakala in wala....
"Shiru tayi har yanzun tana Murmushi, Tana cikin zagayen gidan taji anyi hon baba mai gadi ya buďe gate an shigo."
"Shi ta hango ta glass ďin motar idanun sa sanye da baķin glass, Murmushin tane taji yaqara faďaďa ganin irin kwarjinin da taga yayi mata"
"bayan yayi parking ya sauķo ya nufi ciki tamkar bai ganta ba, bin bayan sa tayi tana faďin sannu da dawowa.
"Hannunsa ďaya kawai ya ďaga mata batareda ya kalleta ba ya shige cikin parloun ya nufi ďakin Maraqishiya da take kwance kan gado tayi rufda ciki idanunta a rufe tamkar wacce take bacci."
"Motsin sa ne ya sanya ta buďe idanunta ta miqe zaune tana kallon sa cikin murmushi da fuska tace, Barka da dawowa ya aikin"?
"Yauwa sannu, Yafaďa bayan ya zauna a bakin gadon ya qara cewa, pls jeki ďakina ki ďauko min jallabiya da gajeren wando inaso in watsa ruwa daga nan ki shigo min da abinci na yunwa nakeji."
"Amsa masa da To, tayi ta fice a ďakin dan zuwa aiken da yayi mata a lokacin da takejin wani irin daddaďan farin ciki a zuciyar ta ganin tun ranar da aka kawo suwaiba yaqi sake mata fuska bare tasamu wajan zama a gidan."
"Kayan ta ďauko masa tareda abincin ta nufi ďakin nata, har ta ďauki komi Amman bataga idon suwaiba ba, badan komi takeson ganinta ba kawai dan taga yanda ta koma da rashin kulawar da baya bata."
"Ganin bai fito a toilet ďin ba har ta dawo ya sanya ta ajiye kayan da abincin ta zauna jiran fitowar sa" Bayan mintuna kaďan ya fito daga toilet ďin sanye da babban towel ďinta na wanka da ďaya a hannun sa yana tsane ruwan dake jikinsa."
"Tashi tayi ta miqa masa kayan bayan ya kammala tsane ruwan dake jikinsa ya karbì jallabiyan da wandon ya shirya ta miqo turaren fesawan ta da man shafawa ya fesa ya shafa, duk tana kallon sa yana shirin batace komai ba Amman dai taji daďi a ranta matuqa ganinsa a ďakin ta da kansa yana komai aciki, badan komi take cikin jin daďi ba face tun lokacin da Humaira ta shigo cikin rayuwar su ta rasa duk wani kulawa nasa da take samu abaya lokacin da suke su biyu ne a gidan."
"Numfashi ta sauķe a hankali tana murmushi tazo ta gabansa suna kallon juna tasa hannunta a wiyar sa ta rungume sa tana fitar da numfashi qasa qasa tana shafan bayansa tace, wlh I really miss u mijina pls kadawo zuwa gareni muci gaba da raruwar mu kamar yanda mukeyin sa a baya, kaurace min da rashin kulawar ka a gareni ba qaramin illah yake min ba, pls am so sorry da duk lefin da nakeyi maka nasan inayi maka rashin kunya sosai but ba lefina bane wlh kishin ka da nakeyi ne ya haifar min da haka, pls am sorry again zanyi kokari inga na daina daga yanzu."
"Lumshe idanunsa yayi ya buďe su a hankali ya ďago da kanta yana tallafe da kumatun ta ya sakar mata da lausassar murmushi yace, karki damu matata na nayafe miki komai ya wuce ki mantar kawai kamar bai faruba, kinsan cewa inason ki dan haka banaso naga kina cikin damuwa."
"I really love u my lovely husband thank u Allah yabar mu tare."
"Amin ya matata,"
"Cikin nuna farin cikin ta ta qara rungume sa akaro na biyu a yayinda yake kai mata kiss a witan domin shi kansa yasan tayi juriyar rashin kulawar sa a gareta."
"Suwaiba ce ta buďe ķofar ďakin ta shigo batareda tayi musu knoking ba, Abunda idanunta suka gani ne yayi sanadiyar daskarewar ta a bakin ķofar takasa motsawa illah zuciyar ta da taji yana mugun bugawa tamkar zai fasa kirjin ta ya fito dan tsantsan kishi da taji ya mamaye duk ilahirin gangan jikinta."
"Magana ta somayi a hankali muryan ta na rawa tamkar mai shirin yin kuka tace, Yanzu harga Allah irin adalcin da kakeyi yayi daidai kenan, Ni Amarya ce a gidan nan shekaran jiya tarewa ta Amman duk irin ni'imar da amare suke samu a daran auran su ni ko nawa idon mijin bangani ba bare ace nima ya shayar dani abunda amare sukeji a wajan mazajan su, Abdulmalik babu kyau abuda kake shirin aikatawa koda kuwa baka sona yakamata kasani ni yar uwar kace ta jini dangin ka bai cancanta kayi min haka ba kodan albarkacin mahaifiyar ka."
"Irin Maganganun da takeyi ne ya janyo da hankalin su gareta duk suka zuba mata ido suna kallon ta har zuwa lokacin da takawo qarshe a maganar ta fice a ďakin cikin ďaci da kunar zuciya
✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:12] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*63*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*
"Ajiyan zuciya ya sauķe a hankali yace muje ki zuba min abincin inci."
"To muje"
"Wajan da ta ajiye abincin suka zauna ta zuba masa a plate, ganin irin kalan abincin ne ya sanya shi canza fuska yana kallon tareda nuna abincin da hannu yace, Haba Maraqishiya wannan wani irin abune, ace ke shikenan bazaki iya girka abincin kirki ba kullum daga jalop na taliya sai makaroni saikace babu wani kalan abinci a gidan, dan Allah ki daina kina bada lokacin ki kina abincin kirki dan nikam na soma gajiya."
"Aiyya mijina pls karka gaji wlh zanyi kokari kamar yanda kace daga yanzu komai ya canza dan haka kayi haquri kaci wannan ďin."
Kansa kawai ya kaďa batare da yaqara cewa da ita komai ba ya soma cin abincin tana jansa da hira yana ci har yaci kaďan yace da ita ya koshi ta ďauke sauran kafin ya miqe tsaye yace bari in fice masallaci magariba ta doso ki min shayi mai daďi pls sai nayi sallan isha'i zan shigo."
"To insha Allahu adawo lfy."
"Allah yasa yace da ita ya fice daga ďakin ita kuma ta tattare kayan abincin ta fitar zuwa kitchen."
"Around 9 o'clock ya shigo cikin gidan ya miqe ya kwanta a kan ďaya daga cikin dogayan kujerun parloun tareda kunna TV yasa tashan labare ya soma kallo."
"Azahiri idan kayi masa kallo ďaya tak sai ka ďauka cewa hankalin sa akan labaran da akeyi yake domin idanun sa suna kan TV Amman a can cikin qasar zuciyar sa sam baima san me akeyin labare akansa ba sanadiyar faďawa tunanin Humaira da yayi tsantsan kewar ta ke masa yawo a ilahirin ajikinsa, tamkar yaje garin abuja zuwa gareta su fuskanci juna haka yakeji, akoda yaushe idan ya dawo gida daga wajan aiki yana fara shiga cikin parloun kewar ta ke soma addabar sa wajan ķàmshin turaren wuta da sanyi A C dake tashi yana ratsa masa jiki tsabànin yanzu da tabar gidan sosai yana ganin banbanci kota wajan abincin da tsantsan kulawa baya samu kamar yanda yake samu a gareta lokacin da take nan."
"Yayi matuqar nisa cikin tunanin da yakeyi a yayinda Maraqishiya ta nufo parloun zuwa garesa hannunta ďaya riqe da kayan shayi ďayan hannun kuma cup ne guda ďaya tazo ta ajiye agaban sa tana qiran sunan sa."
"Qiran sunan nasa takeyi idanunta suna kan nashi idanun da ya kurawa TV kallo" Ganin sai magana takeyi Amman a banza dan ko qifta idanun bayayi bare yasan akwai mutum dake magana agaban sa hakan ba qaramin mamaki ya shigar da itaba tana tambayar cikin ranta tasa hannu a kan nasa hannun ta ďan bige sa kaďan tana qara qiran sunan sa akaro na biyu wanda hakan shi ya ďan firgita shi ya dawo daga cikin tunanin da yayi nisa."
"Miqewa yayi zaune itama ta zauna kusa dashi ta soma tsiyaya masa shayin bayan tasa top tea ďaya da suger acikin cup ďin tana faďin, Nikam my dear wacce duniyar ka lula ne haka na taho gaban ka tuntuni inata qiran sunan ka Amman bakaji ni ba saida na ďan tabà ka"?
"Mtsee, yaja tsaki a hankali yana shafan fuskan sa yace, bari kawai bakomi wlh aikine yasha min kai."
"Aiyya dear sannu Allah ya huce gajiya"
"Amin, yafaďa tana miqa masa cup ďin shayin ya karbà yakafa a baķin sa ya soma kurbà."
"Cike da ya mutsa fuska yadawo da cup ďin ya ajiye a qasa yana tsuke baķin sa tareda jan qaramar tsaki tamkar wanda ya tauna kashi."
"Dear lfy kuwa naga ka ajiye cup ďin"?
"Batare da yakai dubansa gareta ba ya miqe tsaye yana gyaran jallabiyar jikinsa yace, Lfyr ce takawo haka ace shayi kal bazaki iya haďa shi yayi daďi ba ai da matsala babba."
"Tsaye ta miqe itama tana duban sa tace, Haba mana Abdulmalik wannan wani irin cin rai ne kakeson kayi min, ko ka mance lokacin da ka auro ni irin wannan shayin nakeyi maka akoda yaushe kuma kakesha sai yanzu dan ka auro mata fiya da ďaya ka ďanďana irin nasu shine kake nema kaci zarafi na kakeso kace bakasan da irin shayin hannu na ba"?
"Shikenan yayi kyau kuma nagode insha Allahu daga yanzu bazan kuma qarayi maka shayi ba koda kuwa kasa kani saidai kaje wajan masu shayi kasha idan kuma akwai wacce kasaba shan nata bisimillah zaka iya ci gaba da zuwa kasha."
"Cikin fushi da jin haushi take maganar tareda huci tamkar mai shirin yin tambe, Tana zaunawa a zancen da takeyi ta kwashi kayan shayin ta wuce ta gabansa batare da ta kalli inda yake ba."
"Kansa kawai ya girgiza gameda jan tsaki ya kama hanyar shiga ďakin sa yana faďin, shashencin banza kawai shayi kal ma ace mutum bazai iya dafawa ba dan asara tayi masa yawa."
Bayan ya shiga cikin ďakin ya hango Suwaiba zaune a baķin gado tayi tagumi, batareda yace da ita qala ba ya buďe drower na kusa da gefen da yake kwanciya yasa hannu ya kwaso wasu makullen kofofi dayawa ya ajiye a kan gadon kafin ya shiga duba wanda yake nema, Yana samu yamayar da sauran yakama hanyar fita daga ďakin har zuwa lokacin bai kuma kallon inda take ba Amman ita sai binsa take da kallon tausayi a zaton ta maganganun da tagaya masa ďazun ne yayi tasiri akansa har ya sanya shi shigo mata yanzu saidai kuma taga tsabanin hakan dan yanda yayi tamkar baisan ma akwai mutum acikin ďakin ba."
"Yana dafda baķin ķofar ďakin kafin yakaiga ficewa gaba ďaya Cikin takun sauri Suwaiba ta iso garesa ta rungume sa qam batareda ya ankara tamkar kace kwace mata shi za'ayi tana runtse idanunta sosai gameda jin wani irin sanyi a ranta sakamakon jikinta ya rabù da nasa gangan jikin sai takeji a ranta inama ace sun dawwama a haka batareda sun rabe da juna ba, a hankali ta soma magana cikin ďarďar da murya tana sauķe numfashi qasa qasa tace, Haba mana ango na nayau da kullum meyasa kakeson walaqanta nine bayan kasan cewa ina mutuqar sonka har cikin zuciya ta saboda dalilin meye ni bazaka bani hakkina ba a matsayina na matar auran ka wlh ba qaramin shaukin ka nakeyi ba dan Allah nima katareraye ni da zumar soyayyar ka kamar yanda kake tarairayan sauran matan ka yanda suke muradin ka a ransu haka nima nake muradin ka dan girman Allah kazo zuwa shimfiďa ta ko zan samu sauķi a cikin zuciya ta....
"Shiru tayi daga zancen da take har zuwa lokacin kanajin sauķar numfashin ta a sanda Ransa yayi dubu ya mugun bàci jin yanda ta kame masa jiki qam batada niyyar sakin sa hakan ya sanya shi cikin takaici ya kama hannayen ta da nasa hannun ya rabata da jikin sa dakyar gameda jiyo da dubansa zuwa gareta cikin wani irin mugun kallon da ya ďan tsorata ta, fuskan sa a murtuke ya soma magana yana nunata da yatsan hannun sa yace, Ke kishiga hankalin ki wlh banason rainin tarbiya wannan wani irin sabon iskanci ne da karuwanci zaki riqe ni saikace kin samu abonkin wasan ki, to bari kiji billahillazi zan iya tattaka ki inyi miki rashin mutuncin da bakiyi zato ba idan har bakibar shiga harkata ba, indai har rabàn jikin masa kikeson yi ki fita kan layi baķin titi mana ai gasu nan barkatai zaki samu duk wanda kikaga yayi miki arai basai kinzo kinashan wahala wajan shiga hurumin da banaki ba ni nan da kike gani jikina yafi karfin ya haďa wajan kwanciya dake bare har in rabè ki, dan haka inamai ja miki kunne idan har kinada bukatar lfyr jikin ki kibar shiga harkata tun kafin in miki ba daďi."
"Cikin qara ďagun murya ya qarashe maganar a yayinda yana kaiwan qarshe ya juya ya fice daga ďakin ransa a mugun bàce yana karkaďai jikinsa da hannayen sa ta inda ta rungume sa dan ba qaramin qyanqyamin duk jikinta yakeba tamkar ya koreta a cikin gidan sa yakeji kawai dai dan ba hali ne Amman koba daďe ko a juma ya ďauki alwashin watarana sai yayi waje da ita."
"Innalillahi, Tafaďa dameda dafe kanta tana yamutsawa cikin wani irin tsantsan takaici ta durkushe a wajan da yabar ta tsaye tana wasu irin surutai marasa kan gado tamkar tayi hauka takeji, wannan baķin cikin da meye yayi kama ace kana matuqar son mutum kamar ranka zai fita akan sa Amman shi ko kaďan basan kanayi ba saima ya tsaya gaggaya maka munanan maganganu masu ďacin ji saikace baisan zafin so ba, waiyyo ya rabbi ko kwatan rabin zuciyar sa ne ka mallaka min kar nayi biyu babu...
"Kallo ďaya zakayi mata kayi tsammanin zaucewa ta somayi a lokacin da ta tsagaita daga surutan da taketayi ta miqe tsaye dakyar ta faďa kan gado tana sauķar da ajiyan zuciya na baķin ciki da takaici a sanda take aiyyanawa a cikin ranta ya zame mata dole takai qaransa wajan Umma idan ba hakaba bazata iya zaman haquri dashi a irin wannan mugun tsanar da yake nuna mata ba har yake mata kallon ita yar iska ce."
"A lokacin da yabar ďakin nasa cikin bàcin rai kai tsaye ďakin Humaira ya nufa ya sanya kye ďin dake riqe a hannunsa ya buďe tareda sanya ķafafun sa a ciki a yayinda da wani irin ni'imataccan ķàmshin turaren wutan da ya ďauki tsawon lokaci tun barin ta gidan ya daina jinsa shine yanzu ya doki can cikin hancinsa tamkar yanzu ne ta saka shi yanda ķàmshin ya taso tareda ďan sanyi sanyi."
"Lumshe idanunsa yayi batareda ya sani ba, fuskan sa ďauke da lautsatstsar murmushin jin daďi ya buďe idanunsa a hankali ya taka zuwa kan daddaďan gadon ta gefen da take kwanciya bayan ya mayar da ķofar ďakin ya rufe da key dan kar ko wacce mace acikin su tazo ta ruguza masa samun natsuwar da shiga a yanzu."
"Ďaura kansa yayi bisa pllown ta ya kwanta ta gefen hannun dama tareda kunna wayar sa yashiga cikin gallery zuwa kan hotunan ta ya kura musu idanuwan sa yana kallo batareda ya qefta ba wani ita kaďai wani ita dashi bayan sunyi aure wani kuma sanda suka fito daga cikin toilet sunyi wanka ďaure da towel babba ďaya ya matse ta ajikinsa yace sam sai sun ďauki hoto a haka."
"Murmushin sane ke qara faďaďawa a sanda yake tunowa da irin soyayyar da suka gudanar a tsakanin su da tsantsan kulawar da take basa wanda bai tabà sanin akwai saba tsakanin mace da namiji dan ko Maraqishiya a lokacin da yake auran ta ita ďaya har zuwa iyanzu saidai shi ya nuna mata kulawar Amman bawai ita ta nuna masa ba."
"Murmushin sane ya koma can cikin qasan zuciyar sa ya kifa wayar akan ķirjinsa yana runtse idanunsa ta sakamakon tunawa da yayi da irin tsabànin da ya shiga tsakanin su na rashin jituwa da zubar masa cikin sa da tayi kwalli ďaya tak wanda ya kwarrafa ransa akai tarabasa dashi."
"Tunanin nata yaci gaba da yinsa a cikin zuciyar sa har bacci mai daďi da nauyi ya kwashe sa batareda yasani ba."
"Gari na wayewa wajan misalin karfe bakwai na safen lokacin Suwaiba tayi sammako ta kwashi kafar tafice a gidan ta tari a daidaita sahu yakaita zuwa gidan Umma batareda Abdulmalik yasan da fitan ta ba."
"Tana isowa gidan tayi bàngaran Umma cikin sauri ta shiga cikin parloun tana barka da tasamu ķofar a buďe, Jin motsi daga kitchen ya sanya ta nufar sa kai tsaye a lokacin da ta hango Umma hannun ta riqe da wuqa Batula na gefen ta suna fafutikan haďin karin kumullo."
"Gudu ta kwasa tana shirin yin kuka tafaďa jikin Umma ta baya batereda ta ankara ba wanda hakan ya sanya Umma firgicewa da takaici tana faďin, wannan wani irin mahaukacin ne zai haye min kan baya saikace yasamu jakar sa idan hakan yasa na yanke hannu na da wuqa fa"?
"Cikin faďa take maganar a sanda ta juyo da dubanta ganin Suwaiba ce ta faďa jikinta irin haka tana kwasan kuka ya sanya ta fadin, ya Subuhanallahi, Suwaiba meyake damunki haka, mai yafaru dake kike cikin wannan tashin hankalin"?
"Umma dan Allah dan son Annabi idan har kina kauna ta ki raba aurena da Abdulmalik daga yau har zuwa nan gaba har abada na daina son shi wlh koda kuwa mutuwa zanyi idan har soyayyar sa batabar cikin zuciya ta ba na gwammace in rasa rayuwata akan inyi zama cikin irin wannan tsantsan tsanar da yake nuna min.....
✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:12] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*64*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*
Innalillahi wainnailaiaihi raji'un, Umma keta maimaitawa a cikin zuciyar ta a yayinda Batula ta tabar abunda takeyi ta maido da hankalin ta garesu a ranta tana Allah gwandama munafuka kaďan ma kikagani."
A hankali ta ďago da kanta tana kallon cikin kwayar idanunta ta soma share mata hawayen da ya cika mata fuska kacakaca tace,
"Suwaiba ďiyata, ko zaki iya sanar dani irin lefin da yayi miki har kike irin wannan maganar"?
"Umma, Abdulmalik baya sona baya kaunata kokaďan a ransa bazan iya ci gaba da zama dashi a matsayin dole yana nuna min tsana da walaqanci ba, dan haka nikam nahaqura da zaman auaran sa wlh dan Allah ki raba mu Umma tunda dama kece kika haďa mu wannan auran."
"Ya salam, Umma, Tafaďa tareda da dafe kanta cike takaici bayan tasake ta ta soma magana tace, Wai ke wannan wani irin iskanci ne ke damunki, ko so kike kiyi wasa da hankali na,
"Tuntuni naketa faman tambayar ki meye yayi miki dukan ki yayi ko meye Amman kinyi banza dani sai qara tashar min da hankali kike kina faďin in rabaki da shi kingaji da zaman auaran sa, to bari kiji ni kina lalata min lokaci na idan har ba sanar dani zaki ba to gwara ki koma inda kika baro ki rabu dani inyi aikin dake gabana banason shashencin tsiya da asara."
"Cikin faďa take mata maganar bayan tazo qarshe a zancen nata ta juya ta maida hankali kan aikin da takeyi tana jan qaramar tsaki dan yanda abun yabata mugun haushi."
"Jikin Suwaiba ne yayi sanyi matuqa a hankali ta matsa gafda jikin Umma tasa hannu a kafaďar ta tadafe ta kafin ta soma magana cikin muryan kuka tace."
"Dan Allah Umma na kiyi haquri kar ranki yabàci akaina, bakomai yayi min ba face tun lokacin da kuka kaini gidan sa amatsayin matar sa Umma har ila yau bansan meye daďin aure ba domin hatta daran farko na a cikin baķin ciki da kunar zuciya na kwana dan ko dawowar sa gidan banji ba bare har inga kwayar idanunsa harma nayi tsammanin tarairayan da amarya take samu a daran farkon ta,
"Umma hatta jiya da natare shi da maganar bani hakkina da bayayi kawai sai yashiga zagina wai ni karuwace yar iska idan maza nakeso infita kan titi zan samu duk wanda yayi min, Waiyyo Allah na wlh yaci min zuciya da wannan munanan maganar Umma kinga ai gwara ya sakeni in mutum akan son sa bawai inyita zama yanaci min rai da tsanar sa agareni ba....
"Kambu Shi Abdulmalik ďin ne yayi miki irin wannan tijaran"?
"Kai suwaiba ta gyaďa mata alaman Eh tana qara faďin, Umma nice amaryar sa Amman sai ganin sa nayi da Maraqishiya suna nunawa junan su soyayya dan rashin adalci ni kuma ko ohho."
"Ran Umma ne ya kuma sosuwa da jin wannan lbrn, cike da takaici da zafin rai tabar aikin da takeyi ta ďauki hijabin ta dake rataye jikin ķofar shiga kitchen ta zura shi ajikin ta tareda kamo hannun Suwaiba tace biyo ni muje in nuna masa shi bai isa yaci zarafi naba yayi kaďan wlh."
"Tana maganar ne tareda ďaukan hanyar ficewa ganin hakan ya sanya Batula dake tsaye har izuwa lokacin faďin, Umma ina kike nufin zakije da safiyar Allah akan wannan maķaryaciyar yarinyar tazo tazuba miki karya da gaskiya tasaki zaki ďibi ķafa da safen nan kije ki ďagawa ďanki hankali."
"Qaniyar ki Batula, Cewar Umma fuska a murtuke tana mata daķuwa da hannu tace, Gidan Ubanki zanje shegiya munafukar yarinya ai nasan dama duk bakin ku ďaya kawai dai shiru nayi naqyale, kuma wlh idan nadawo naji lbrn kin kai gulma gun Abbn ki cewa ga inda najeba, Himm zakici gidanku sai na tabbatar da nacire miki labèn baķin ki ďaya."
"Shiru Batula tayi tana tabè baki batareda ta tanka mata ba har takawo qarshe a zancen ta taja hannun Suwaiba suka fice, A sannan batula ta sauķar da numfashi tana surutai a ranta taci gaba da haďin karin kumullon da sukeyi."
"A sanda suka iso gidan a nan parlou Umma tayi tsaye ta riqe kunkumi tana kaďa kai tace, ke Suwaiba wuce ki samo min shi..."kafin takai ga rufe baķin ta sai gashi ya fito daga ďakin sa cikin shirin sa na zuwa office yana gyaran baķar agogon dake maqale a jikin hannunsa wanda a wannan lokacin ana neman karfe takwas na safe."
"Ganin wacce idanunsa yayi harba'a da ita ya sanya shi dakatawa da gyaran agogon da yake, Cike da tsantsan mamaki ya tsaya yana zancen zuci saidai kuma ganin Suwaiba zaune kan ďaya daga cikin kujerun parloun ya sanya shi haďe fuska batareda ya shirya ba domin ko ba'a faďa masa yasan cewa zuwan Umma da wannan safiyar da biyu..
"Sannu ja'irin yaro marar kunyar banza ďan gidan asara zaka qaraso ne koso kake ni in qaraso gareka da kaina"?
"Umma ce tayi maganar cike da ďaga murya fuskan ta a murtuke wanda hakan shi yasan sa shiru a zancen zucin da yakeyi ya tako a hankali zuwa inda take tsaye kansa a sunkuye yace, Barka da safiya Umma kin tashi lfy"?
"Mugun harara ta watsa masa gameda masa nuni da hannu tana faďin, Kai dakata riqe gaisuwar ka bana bukatar sa dan ba shine yakawo ni ba."
Allah ya huci zuciyar ki inafatan dai lfy"?
"Ai babu lafiya sam Abdulmalik baka ďibo hanyar zama lfy ba inbanda asara da rashin godiya ace Allah yabaka matar aure saliha yar gidan arziki wacce zaku hayayyafa ku tara zuri'a ďayyaba da ita Amman kana neman kasa qafa ka shure, To bari kaji wlh idan har wannan girman kan naka baka ajiye shi a gefe kasan inda yake maka ciyo ba zakayi mugun ganin bàcin raina wanda baka tabà gani ba dan haka gata nan maza ko yanzu ko anjima itama ka bata abunda kake bawa sauran yan iskan matan naka masu lalataccun mahaifa saura kuma inji ko in gani bakayi abunda nace ba, Himmm kasan mai zai biyo baya basai nafaďa ba."
"Umma Amman kinsan meye kike faďa kuwa, ta yayama kike zaton zan iya janta a jikina har in haifu da ita wlh bazan iyaba gwarama tun wuri tasan inda dare yayi mata dan ba karbùwa zatayi a wajena ba."
"Ransa a muguwar baçe yayi maganar yana tsuke baki a yayinda Umma ta kuma harzuqa cikin zafin rai taqara faďin,
"To dan ubanka da uwarka zaka haifu idan baka haifu da ita ba"?
"A'uzubillah Umma wai meye hakane dan Allah kibarni in huta mana Aure ne kince tilas sai nayi kuma gashi nan nayi ba shikenan ba, dan haka pls kirabu dani wlh Umma na soma gajiya nikam kuma wlh idan ba hankali tayi ba saidai taga kanta a waje mayyar ya rinya kawai."
"Baki sake take binsa da idanunta a sanda yazo shi qarshe a zancen sa ya fice fuu a parloun ransa a jagule yabarsu tsaye har zuwa lokacin idanun su akansa har ya bàce ma ganin su sunajin qaran motar sa da buďe gate suka gane alamun ya fice."
"A hankali Umma ta sauķar da ajiyan zuciya tareda zama kan kujeran dake kusa da ita tana jinjina abun a ranta har na tsawon wasu mintuna kafin ta miqe tsaye cikin sanyin jiki batareda ta kalle taba tace, Suwaiba zan koma gida rana tayi yanzu nabar komai daga hannunki ki tabbatar da cewa koma meye zakiyi da ina zaki shiga to kidawo da hankalin sa gareki har Allah yasa a dace idan naji shiru kuma babu lbr to akan zan faďa kinsan halina banida sauki domin ke mace ce akwai hanyoyi dayawa da zakibi ki shawo kansa dan haka mu yini lfy."
"To Umma karki samu damuwa nagode zanyi kokarin yin hakan dukda nasan dakyar ne yadawo gareni saidai kuma karkiga lefina Umma Yaya sai ahankali wani irin juyin kaine dashi" Qarashe maganar tayi tana lankabàr da kanta a yayinda Umma takama hanyar fita tana faďin, ke kuma kikasan wannan bai shafeni ba...
"Tanajin ta batareda da tayi magana ba tayi mata rakiya har zuwa waje tasamu Adaidaita sahu tahu ya ďauketa hanyar komawa gida a sannan itama suwaiba ta shige ciki kai tsaye zuwa ďaki tana qarasa haďa zancen a ranta."
"Maraqishiya ce rakubè jikin ķofar ďakinta tana leqen su tun lokacin tanajin duk irin abunda ke gudana a tsakanin su, Dariya ne ya ķubùce mata sosai batareda tashirya ba ta koma kan gado tafaďa tanaci gaba da dariya a ranta tace, shegun mutane ai saidai a niyar ku tabiku wlh nafi karfin ku kai Allah na gode maka...
*Bayan wata uku*
Abubuwa ne da dama kan faruwa tsakanin Umma da lamarin gidan Abdulmalik da matan sa domin kuwa sam takasa kwantar da hankalin ta akansu itadai damuwar ta shine taga an haifu an kawo mata ďan jikanta ta riqe shi a hannu wannan yasa ko wanne bayan kwana biyu sai taje gidan dan taji ansamu lbr mai daďin ji ko yaya."
"Abba kam dama yabar shiga harkan ta ganin tazama tamkar wata zautacciya tanayin abubuwa batasan da ta girma ba."
"Haka zalika yauma kamar koda yaushe zaune take a qasan filin parloun bàngaren ta tasa TV a gaba yanata faman aiki Amman badan kallon sa takeba illah hankalin da yake kan abunda take kullawa a cikin ranta "Batula ce zaune a saman ta tanayi mata tsifar kai Inna na zaune itama sanye da hijabi ajikin ta kan qaramar layyan ta tanajan dogon carbi ga dukkan alamu salla ta idar dan kanajin wasu masallacen ma a wannan lokacin suke tada qiran sallan la'asar."
"A zaune take Amman ji takeyi tamkar cokarin ta akeyi da qusa hakan yasa ta miqe tsaye kamar wacce ta tuna da wani abu
_Dan Allah masoyana masu bibiyar littafina pls kuyi haquri zaku jini kusan sati ďaya ko fiye da hakan banyi posting ba, dan Allaha yimin uziri idan nadawo babu fashi insha Allahu nagode_👏🏿
✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:12] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M S*
(HaneeSat)
*Page*
*65*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*
Sakin baki Batula tayi cikin mamaki ta kalle ta tace
"Umma yadai! lfy kika tashi bamu kammala tsifar ba?"
"Ina zuwa kijirani idan nadawo kya k'arasa min".
"Cewar Umma a sanda ta saka hijabi a jikinta ta ďauki hanya zata fice Inna ta dakatar da ita da faďin
"To sarauniyar yawo sai ina kuma kenan?"
"Ya salam". Umma tafaďa tana dafe kanta da hannu bayan ta juyo da dubanta zuwa ga Inna tace
"Haba mana inna saikace wata wacce taci k'afan kare dan nace zan fita, kudai kawai sai na dawo ai ba nisa zanyi ba".
"To ai sai kitafi adawo lfy".
"Yauwa to Allah yasa".
Tana gama faďin haka ta juya ta fice a yayinda Batula ta kaďa kai tareda kai dubanta kan Inna tace
"Himm Inna kinsan daga nan Umma gidan Yaya zataje ko ba'a faďa ba wallahi na gano ta, halan wani bala'in nata ne ya tashi shine zataje ta sauk'e musu".
"Himm". Inna tafaďa tana tabè baki tace
"Ai halin wannan Uwar taku wane mutum saidai Allah ne zai iya da ita".
Dariya Batula tayi bayan ta miqe ta nufi hanyar ďakinsu tana faďin
"Kai Inna kin iya magana wlh".
Bayan fitan Umma kai tsaye gidan Abdulmalik ta nufa, cikin sa'a ta tarar da shi zaune a tsakiyar parlou yana cin Abinci
Maraqishiya na kusa da shi tana jefan sa da hira cikin raha, a yayinda Suwaiba ke zaune can gefe guda tayi sanyi da jiki, kallo guda zakayi mata ka fahimci cewa ba'a cikin jin jin dad'i da kwanciyar hankali take ba,
domin kuwa ita kaďai ne tasan irin zaman da takeyi dan har zuwa yanzu ba samun sakewar fuskarsa take gani ba, kullum akoda yaushe yana cikin ďaure mata fuska tamkar wanda bai tab'a yin dariya ba, haka yana faruwa ne lokacin da yayi idanu hud'u da ita.
"Idanun Suwaiba ne ya soma harba'a da Umma wacce ke tsaye d'an nesa dasu batare da ta k'araso garesu ba.
Tashi tsaye tayi tana d'an murmushin yak'e wanda kwatakwatan sa bai wuce gefen baki ba.
"Umma sannu da zuwa ina wuni?" Tafad'a bayan ta iso gareta.
Jin an kama sunan Umma ya sanya su d'ago da idanuwansu a lokaci d'aya a yayinda Umma ta k'araso inda suke zaune sunyi tsurutsuru suna kallon ta, fuskan ta a murtuke batare da ta amsa gaisuwar da Suwaiba tayi mata ba illah hararan gefen ido da ta watsa mata wanda har ya shigar da Suwaiba zancen zuci gameda mamakin ganin irin hararan data watsa mata.
"Barka da zuwa Umma". Maraqishiya ta fad'a cikin ya tsine fuska yanda ba ganeta za'ayi ba, a yayinda Abdulmalik ya dakata da cin Abincin da yakeyi cike da mamakin ganin ta yauma a cikin gidan sa, kuma ga dukkan alamu ganin yanayin yanda fuskanta ya sauya ya shaida masa cewa yauma wani tashin hankalin ta kawo masa.
"To sannu mai idanu saikace na mayu, kazuba min su a kaina sai kallo na kake dan nazamo maka bakuwar fuska ko?" To maza d'auke min idonka a kaina dan ba shine ya kawo ni ba, abunda ya kawo ni shine maza a yanzu nake son naga ka irgawa wad'an nan 'yan iskan matan naka saki uku uku a take a gabana, dan so nake naga ko wacce shegiyar mace ta kwashi rub'ab'b'un k'afafuwanta ta bar wannan gidan, kuma umarni nake baka ba shawarar ka nake nema ba".
Bayan tasamu kujera ta zauna dafda shi take maganar tana nuna su da yatsar hannun ta gameda bud'e masa ido alamun babu wasa tattare da maganganun ta.
A sanda tazo k'arshe a zancen nata ta zuba masa ido tana jiran taji ya cika umarnin da ta basa wanda a wannan lokakin ko wannen su yayi mutuwar tsaye dajin irin furucin da tayi dan ba k'aramin girgiza zuciyoyinsu yayi ba, musamman Suwaiba wacce a iya tunanin ta bata tab'a zaton haka daga wajan Umma ba, saidai kuma a irin halin da take ciki a yanzu gwarama ya sake ta d'in ta koma gida dan nan zatafi samun kwanciyar hankali."
"Ganin yanda duk kanin su suke k'ara kallon ta a karo na biyu d'aya bayan d'aya hakan ya sanya ta sake had'e fuska bayan ta kura masa ido tace
"Dakai nake magana d'an asara, zakayi ne ko zaka tsaya raina min hankali, kayi banza dani dan gani mahaukaciya ko?"
Kansa ya girgiza mata kawai alamun a'a tareda mik'ewa tsaye batare da yace da ita komai ba yakama hanya ya fice a parloun yabar ta tana ta kwala masa k'ira tareda barazanar zata tsine masa idan har yafice bai cika umarnin da ta bashi ba, yanajin ta bai tanka ta ba har yafito haraban gidan ya shiga motar sa mai gadi yabud'e masa gate ya fice ya d'auki hanya badan ya yanke inda zaije ba, wanda a sannan zuciyar sa ta tunkushe da wani irin bak'in ciki gameda halin mahaifiyar sa...
"Tashin hankali! Umma ta fad'a cikin d'aga murya da nuna b'cin rai, bayan ta miqe tsaye tana gyaran d'aurin zaninta a sanda take huci tamkar mai shirin yin dame da wani a bokin gaba.
Hannu ta d'aga tana nuna Maraqishiya da Suwaiba da d'an yatsanta tace
"Wato ni mijin naku zai nema ya rainawa hankali dan kun asirce shi da shegen tsafin ku na tsiya, sai kuna sauk'ar min da kai simisimi saikace yaran arziki, to aniyar ku tabiku domin kuwa duk nasan halin ko waccen ku a tafin hannu na take, kuma tunda shi d'an iskan ba iya sakin ku zaiyi ba to maza ko wacce shegiya ta kwashi tsummo karanta ta bar gidan nan tunkafin ku fuskanci tashin hankalin da bakuyi tsammani daga gareni ba".
"Cike da tsananin b'acin rai ta k'arashe maganar.
A sannan Suwaiba ta tako zuwa gareta jiki a mace tana kallon ta cikin mamaki tace
"Umma lfy kike kuwa!? Meye kike nufin da ya sake mu, nice fa Suwaiba d'iyar ki, kenan nufin ki harda ni za'a saka?"
"Eh mana". Umma tace da ita tareda d'an bud'e mata idanu ta k'ara cewa
"Harda ke za'a saka Suwaiba dan bakida amfani sam a cikin gidan nan ko kad'an, gwara kema kifita a hakalin in samo masa wata mai k'ashin arzikin amman ba ke ba, dan haka kibar mamaki na maza ki wuce ki d'ibo kayanki mu koma gida a tare".
"Numfashi ta sauk'ar k'asa k'asa kafin tace
"To shi ke nan Umma idan hakan kikega yafi miki banida matsala, dan nima nagaji da wannan zaman gidan da ake nuna min k'iyayya, aurena akayi kamar yanda ake auren ko wacce mace amman ace hatta girkin Abinci saidai idan Abokiyar zamana ta dafa tabani, shi ke nan ni banida kitchen d'in da zanyi girkin kaina, dan haka gwara in koma gida daman abunda nake shirin yi kenan domin kuwa a iya zamana dashi ya koyar dani wani darasi na son wani koshin wahala idan har kace zaka shiga cikin zuciyar wani mahaluk'in da shi tashi zuciyar bakai yake so ba saima tasanar ka dayayi to babu shakka kuwa zaka gamu da tsananin wahala da azaba, idan ma hakan baiyi sanadiyar d'aura maka ciyon zuciya ba... Ke! Suwaiba ya isheki haka". Umma tafad'a cikin tsawa ta k'ara cewa
"Kinga rufe min bakin ki banason k'ara jin wata magana daga gareki, maza ki wuce ki d'bo kayanki mu koma gida".
"K'arashe maganar tayi tana fad'in
"Shegiyar yarinya me bakin rashin kunya, da ba kece kike neman haukacewa akan son shi ba, sai yanzu zaki tsaya kinama mutune cacan bakin banza da wofi".
Batare da ta kuma yin magana ba ta wuce cikin d'akin Abdulmalik a cikin d'an k'ank'anin lokaci ta kwaso duk kayan sawan ta tafito zuwa parlou inda Umma ke tsaye tana faman jiran fitowar ta, a yayinda Maraqishiya tuni tabar cikin parloun ta nufi d'akin ta domin zuciyar ta kasa iya jure munanan maganganun da take zuba musu ba.
"Mutafi Umma gani nagama d'iban kayan". Suwaiba ce tayi maganar cikin tura baki.
A sannan Umma ta nufi d'akin Maraqishiya ta bud'e gameda d'an tsak'ala kai ta hango ta kwance bisa gado tasa waya a kunne alamun magana take da wani.
Umma tace
"To magajiya saura ke karki kuskura ki bari na dawo natarar dake a cikin gidan nan dan sai nayi miki korar walak'ancin da yafi na 'yar uwarki, kema kinsan wacce nake nufi basai na ambaci sunanta ba".
Murya a d'age ta k'arashe maganar sannan taja k'ofar da karfin gaske suka bar gidan ita da Suwaiba.
**
"A washe garin ranar da Umma taje ta dawo da Suwaiba koda Abdulmalik yadawo a daran Maraqishiya ta sanar dashi a binda yafaru bayan barin sa gidan, baice komai ba face hamdala da yayi da bar masa gidan sa da tayi, domin ko Umma bata dauke ta sun tafi ba shi da kansa yake shirin fitar da ita daga cikin rayuwar sa.
Zaune take a tsakiyar gadon d'akinta ta mik'e k'afafunta, a yayinda Shiwari take kusa da ita suna tattauna a binda yakamata su aiwatar akan matsalar da Umma ke kawowa ako wannne wayewar gari.
Nauyayyan ajiyar zuciya Maraqishiya ta sauk'e tana shafan fuskanta da tafukan hannunta cikin tsananin damuwa da takaici ta soma magana tace
"Shiwari a gaskiya
ya zame min dole in d'auki tsatstsauran mataki akan Umma, dan gaskiya ba k'aramin shiga min hanci da k'udindini takeyi ba,
kinga ko Suwaiba da take a matsayin kishiya ta bata d'aga min hankali tamkar yanda Umma take d'aga min ba, duk da cewa itama a d'an zaman da mukayi cikin d'an watannin nan tayi min a binda yaso lalata zaman aurena tsak'anina da Abdulmalik, amman nayi saurin taka mata burki dan a ranar data k'ulla min muna furci nashiga tsantsan damuwa Shiwari dakyar samu na shawo kansa ya hak'ura,
dan haka kinga tunkan daga ita har wannan tsohuwar banzan suci nasaran lalata min rayuwar aurena gwara inyi sauri in tashi tsaye dan insan a binda nake ciki, kinsan masu iya magana sunce duk a binda ka shuka shi zaka girba, alkhairi ko mugunta, to kinga kuma gashi na soma girba tunda abunda nayiwa tawa kishiyar shine wata takeyi min.
"Dan haka kafin in k'arasa girban abinda na shuka gwara inyi gaggawar kammala shukawa dan idan natashi girba in girbe su a lokaci d'aya".
Numfashi ta sauk'ar k'asa k'asa akaro na biyu tanaci gaba da kallon Shiwari kafin ta k'ara cewa "Koyaya kikace k'awata?"
"Hakane kam". Shiwari tafad'a a sanda take kad'a kanta tace
"Ai kuwa kinyi tunani sosai a nan, dan a binda kikayiwa Humaira kad'ai ya isheki girbewa, domin kece silar barinta wannan gidan, kece ke kulla mata duk wani sharri har kika rabata da kyautar da Allah yabata, nidai nasan nawa taimako ne na samo yanda za'ayi cikin ya zube, amman k'uduri nakine dan haka zaki fini girban mai tsoka".
"Dariya ne yakama Marak'ishiya sosai, saida tayi mai isar ta kafin tace
"Kai k'awata k'ur'anin Allah bakida sauk'i...Cak maganar ta mak'ale mata can k'asan mak'oshi batare da ta shirya ba ta soma had'iyan yawo tana ware idanuwanta a yayinda cikin zuciyar ta ke mugun bugawa sosai tamkar zai b'alle biyu yabar k'irjin ta.
"Ganin yanda duk tabi ta susuce a lokaci d'aya ya sanya Shiwari binta da Kallon mamaki ta kad'a mata hannunta a kan fuska gameda cewa
"Ke! dalla malama lfy?"
Meye haka kin daburce a lokaci d'aya saikace wacce taga wani abun firgitarwa?"
Bata iya ta bud'i bakinta tace k'ala ba illah nuni da idanunta da tayi zuwa setin k'ofar d'akin tanayi mata a lamun ta juya bayan ta.
Juyawa tayi batare da wata farga ba.
Idanuwanta ne suka tsaya cak ba shiri ta dawo da duban ta kan Marak'ishiya cikin zare idanu a sanda zuciyar ta ya shiga tsantsan bugawa gameda ambaton sunan Allah tana d'aura hannayen ta aka, a hankali muryan ta na rawa k'asa k'asa tace
"Ya salam! Innalillahi mun shiga uku...
*Haneefsat*✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:12] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAPHSAH M*
*Page*
*66*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*
Tsaye yake dai-dai k'ofar d'akin ya hard'e hannayensa duk biyu bisa k'irjin sa, a yayin da idanuwansa ke kan su yana binsu da wani irin mugun kallo na nuna b'acin rai.
Zuciyarsa ce ta shiga tsananin mamaki da a binda kunnuwansa suka jiye masa.
Tambayar cikin ransa yakeyi. "Shin mafarki nakeyi ko kuwa a zahiri ne?"
Ganin ya kasa amsa tambayar da yake yiwa zuciyarsa hakan ya sanya shi takowa cikin d'akin ya k'araso zuwa garesu inda sukayi tsuru tsuru da idanuwansu a sanda kansu ke sunkuye sun gagara d'agowa bare harsu had'a ido da nasa.
Bud'an baki yayi da niyyar magana sai kuma yayi shiru, a takaice yace
"Ku same ni a mota".
Yana kaiwa nan ya fice daga cikin d'akin, har zuwa lokacin ransa a jagule yake.
Dum! dum! zuciyar ko waccensu ke mugun buguwa, tsoro da fargaba ya sanya su rud'ewa, jiki na rawa suka bar d'akin bayan sun d'auki mayafinsu da wayoyinsu.
A haraban gidan suka iske shi zaune cikin motarsa yana jiran dawowarsu, a sanda yake sak'e sak'e a ransa na shi kad'ai yasan irin hukuncin da zai yanke musu, dan sun cuce sa a rayuwa sun gama dashi matuk'a.
Tada motar yayi bayan sun shiga baba mai gadi ya bud'e masa gate ya fice, bai zarce ko ina ba sai gidansu.
A wajan gidan yayi parking motar kafin ya nufi ciki a yayin da suke biye dashi a baya jiki a sab'ule tamkar suyi tsuntsuwa su b'ace sukeji, haka ya nufi b'angaran Abba a bakin k'ofar parloun sukaci karo dashi cikin shirin sa da alamun fita zaiyi.
"A'a Babana kane tafe war haka bakaje wajan aiki bane!?" Cike da mamaki yayi masa tambayar ganin su Marak'ishiya tafe a bayansa.
Kansa kawai ya girgiza masa tareda fad'in "Abba pls inaso inyi magana dakai mai muhimmanci".
"To mu k'arasa ciki babana, fatan dai komai lafiya?"
"Lafiya". Ya fad'a a takaice, a yayin da ya k'arasa shigewa cikin parloun.
Dawowa cikin parloun Abba yayi bayan ya amsa gaisuwar da su Shiwari sukeyi masa.
"Abba, zanyi magana ne yanzu a gaban ka in ai watar da a binda nake shirin ai watarwa badan komai ba face dan ka zame min shaida wani lokacin, ko kuma karkaji lbr daga baya kace me yasa ban sanar maka ba, duk da kuwa nasan akwai a binda na b'oye maka shi kusan watanni baka san dashi ba, amman insha Allahu yanzu zakaji komai da ya dad'e yana faruwa a cikin gidana ba tareda kasani ba".
Tun a sanda ya soma maganar cikin su babu wanda ya iya cewa uffan, illah Abba da ya tattaro da hankalin sa zuwa kansa.
A yayin da yazo k'arshe a zancen sa yakai dubansa kan Marak'ishiya gameda k'iran sunanta cikin iriyar murya yace
"Kije na sake ki saki biyu daga baya zan cikata miki d'ayan, ke kuma! yayi nuni da Shiwari murya a d'age yace
"Ki k'ira min mijinki yanzu a waya kiyi masa kwatancen inda kike yazo ya same mu".
Cikin sanyin jiki kamar yanda ya umurce ta dashi hakan ta ai watar ba tareda yin musu ba.
A lokacin da zuciyar Marak'ishiya ya tsananta buguwa jin kalmar saki daga bakin sa bama d'aya ba har biyu, gashi yana ik'irarin cewa daga baya zai cikata mata d'ayan wanda da zaran yayi shi ke nan tsakanin ta dashi babu ko wanne irin aure face idan ba wani auran tayi aka saketa ba.
Hakan da ta tuna ne ya shigar da ita cikin tsananin tashin hankali da nadamar a binda ta aikata a sanda idanuwanta suka cika da kwalla ta d'ago dasu tana kallonsa murya a raunane ta soma cewa.
"Dan Allah Abdulmalik karka yanke min irin wannan mummunar hukuncin wlh ba lefina bane, bani kad'ai na aikata abinda kaji...
Shiru tayi ba tareda taci gaba da maganar ba a sanadiyar ganin irin mugun kallon daya watso mata ba shiri ta kawar da kanta gefe guda tana sauk'e numfashi.
Duka maganganun da sukeyi Abba yana sauraran su baice dasu k'ala ba, ganin duk sunyi shiru hakan ya sanya shi sauk'ar da nauyayar ajiyar zuciya gameda gyara zaman sa ya dubi Abdulmalik yace.
"Abdullah, naji duk a binda ka fad'a da kuma d'anyar hukuncin da ka zartar a kan matarka wacce kuka d'auki tsawon shekaru kuna zaune da ita ba tareda anji kanku ba sai yanzu kwasam, dan haka inaso ka sake min bayanin matsalar dake wakana a cikin gidanka har tsawon watanni amman bansani ba.
Kawar da kansa gefe yayi cike da b'acin rai yana nunata da d'an yatsar hannun sa yace.
"Abba! kaga wannan matar munafuka ce muguwa bansani ba nake zaune da ita, Abba itace sanadiyar zubewar ciki na wanda Humaira ke d'auke dashi, itace silar barin ta gidana ba ita ta kori kanta ba.
"Abba meye zanyi da ita, meye zanyi da matar da zata iya kashe hallitar Allah da hannunta ba tareda tsoro ko fargaba ba jariri wanda ko kammala zama tsoka baiyi ba.
"Kin cuceni Marak'ishiya bazan tab'a yafe miki ba har k'arshen numfashi na, matuk'ar zan iya d'aga idanuwana in sauk'ar a kanki to ina mai tabbatar miki da cewa baza kiji dad'i ba.
K'arashe maganar yayi yana fad'in Innalillahi wainnailaiaihi, a sannan ya koma ya jinginu da jikin kujerar da yake zaune gameda runtse idanuwansa yana jin wani irin k'una a cikin zuciyarsa tamkar yayi kuka yakeji ko zai samu sassauci cikin irin damuwar da yake ciki a yanzu.
"Subuhanallah!".
Abba ya fad'a yana jinjina a bun a ransa yace.
"Yanzu kana nufin kace duk wannan wutar dake ruruwa a cikin gidanka kasani amman baka sanar damu ba, kuma har Humaira tabar gidanka ta koma gidan iyayen ta bansani ba, sai yanzu zaka zo kana bani lbr, wannan da wani irin ido kakeso in kalli su Abdulmalik?"
"Kayi hak'uri Abba ka gafirce ni muje ka tayani bikon ta, dan nima kaina bansan a binda ke faruwa ba kenan sai yau da naji suna maganar ashe duk sune suke had'a mata ko wanne irin makirci suka zubar min da yarona dan su rabani da ita, a sanda nagane cewa tabar gidan da kuma irin sak'on da tabar min ya sanya ni k'ara jin haushin ta, dalilin haka yasa banyi bikonta ba kuma banga amfanin sanar maka ba tunda itace tazab'i hakan, Kayi hak'uri Abba kayi min bikonta, wlh bazan tab'a gafartawa kaina ba idan har Humaira bata dawo zuwa gareni ba.
K'arashe maganar yayi yana fad'in
"Marak'shiya ta cuceni tunda ta kunna wannan gobar a cikin gidana bansani ba.
"Dan girman Allah Abdulmalik ka daina fad'in na cuceka na ha'ince ka, wlh tallahi kaji nayi maka rantsuwa da sunan Allah ba nice silar duk wannan a binda kake fad'a anyiwa Humaira ba, na amince da nice sanadiyar zubewar cikin dake jikinta, kuma nice nake had'a mata duk wani sharri wanda zai shiga tsakaninta dakai, nice nake lalata mata girkinta a koda yaushe idan tayi, amman wlh banice na koreta a gidanka ba, dukda cewa nice silar faruwan hakan amman ban koreta ba Umma ce tayi mata koran walak'anci ita da Siyama suka kaita tashar mota bayan ta sanya ni rubuta maka sak'on k'arya wanda zai nuna cewa Humaira ce ta rubuta da kanta.
"Inaso kasan cewa inason ka bazan iya zama babu kaiba, nasan nice silar duk a binda yafaru amman wlh rabin sa Umma ce bani kad'ai ba.
Marak'ishiya ce ke maganar cikin muryan kuka da nadama tanajan numfashi.
Innalillahi wainnailaiaihi raji'un!". Umma take nanatawa gameda tafa hannayenta tana salati bayan ta k'arasa shigowa cikin parloun dan duk irin maganar da Marak'ishiya keyi a kunnuwanta suka sauk'a, hakan ba k'aramin takaici ya shigar da ita ba.
Ranta a mugun b'ace ta nuna ta da yatsarta kafin tace
"Sannu munafuka annamimiya, ashe dama ke 'yar maciji ce, azzaluma mai iya kashe jaririn da ko gama fita daga gudan jini baiyi ba, kin cuceni wlh Marak'ishiya bazan tab'a yafe miki ba matuk'ar ina numfashi a doron k'asa, muguwar mace kawai ni da nasan cewa kece annamimiya wacce ta watsar min da d'an jikana ai da ke zanyiwa korar walak'anci ba ita ba, gashi dan irin bak'in halin ku da ke da wannan shegiyar k'awar taki yasa kun gagara d'aukar cikin bare ku sake yaro, amman dan tsaban mugun hali irin naku sai kace dangin fir'auna yasa yau kusan tsawon shekaru kuna zaune da rub'ab'b'un mahaifa.
"Astagafirulla!". Tafurta a hankali cikin tsananin takaici da nadamar irin a binda tayi, sannan ta kuma fad'in
"Astagafirulla! a karo na biyu kafin taci gaba da cewa
"Waiyyo Humaira! nasan cewa nayi mugun tsanarki amman inason jikana wlh, dukda cewa a farko na nuna rashin k'aunar sa kasancewar a cikinki yafito amman daga baya naji ina k'aunar sa, da nasan cewa bake kika zubar da cikin nan ba da ban koreki ba wlh".
"Umma!".
taji ya k'ira sunan ta cikin iriyar murya a dashe ya k'ara cewa
"Kina nufin kece kika kori Humaira daga gidana bansani ba? "Meye tayi miki Umma, meye illar Humaira dan Allah, tun kafin in auri yarinyar nan kika d'auki tsanar duniya kika d'aura mata, yanzu gashi kin koreta kin rabani da ita kika sani auran wata k'azamiya, meye amfanin haka?"
Kai! kaci gidanku, bansson shashencin banza, dan kaji dad'i an rabaka da annuba shine kake nema ka kawo min k'abili da ba'adi, to na koreta d'in idan kanada abun yi sai kayi ingani, kuma wlh baka isa kace dan ka gano gaskiya zakaje kayi bikonta ba, karya kake wlh ban baka wannan damar ba".
"Ke Bara'atu!". Abba ya daga mata tsawa cikin tsananin b'acin rai yace.
"Wlh idan kika kuskura kika bari raina ya gama b'aci to wlh baza kiga da kyau ba, kin bani mamaki Bara'atu! Wannan wani irin muguwar hali ne dake, kina aikata a bubuwa irin na yara marasa kan gado, kin zubar da girmanki sam baki san ciwon kanki ba, wlh wlh kinji na rantse miki idan har yarinyar nan bata yarda ta dawo garesa ba to ina mai tabbatar miki da cewa kema barin wannan gidan zakiyi in sallame ki tunda kedai ba macen arziki bace, kin haifi yara kusan hud'u amman baki san inda ke miki ciwo ba, ki rasa wad'anda zakiyi fad'a dasu sai surukanki matan yaranki! Allah yawadarai da masu lalataccan hali irin naki, kinji kunya wlh".
Tun a sanda Abba ya soma mata fad'an takasa bud'an baki tace k'ala illah kanta da takawar gefe guda tana hucin takaici, ita tama rasa haushin meye takeji a yanzu, Marak'ishiya da tazubar mata da jikanta ko kuma fad'an da Abba yasata a gaba yanayi mata ko kuma fallasan da akayi?"
Shiru ne ya ratsa cikin parloun na d'an dak'ik'u, cikin su babu wanda yace komai kowa da a binda yake sakawa a cikin ransa, suna nan zaune mijin Shiwari yayi mata waya kan cewa gashi nan yazo yana k'ofar gida.
Tashi tayi da niyyar taje ta shigo dashi Abdulmalik ya dakatar da ita, shi da kansa ya fice waje bakin gate ya shigo dashi har zuwa cikin parloun Abba suka zauna.
Bayan sun gaggaisa ne mijin Shiwari yayi gyaran murya sannan yace.
"Ina fatan komai lafiya dai?"
"Lafiya k'alau". Abdulmalik ya bashi amsa tareda zayyano masa a binda ya jima yana faruwa basu sani ba.
Ya salam!" Mijin Shiwari ya furta a hankali yana karanto salati a cikin zuciyar sa gameda shanfan kansa ransa ya b'aci sosai ba kad'an ba, cike da takaici ya d'aga hannun sa ya nuna Shiwari da yatsa yace
"Kinji dad'in rayuwar ki Shiwari, dama ni tuni nagaji da zama dake dan bakida amfani ko kad'an a gareni, dan haka kije nasake ki saki d'aya, kije ki huta a gidan iayayen ki tunda hakan kikafi so".
Mik'ewa tsaye yayi bayan yakai k'arshe a zancen sa yayi sallama dasu Abba ya fice daga parloun ransa a b'ace.
"Cikin nadama da tashin hankali Shiwari ta d'aura hannunta akanta tace.
"Waiyyo Allah! wannan abu ya same mani jalli joga, nashiga ukuna, daga taimako sai abu yadawo kanka?"
Tashi tayi tsaye jiki a sab'ule ta d'auki hanyar ficewa daga parloun, ganin haka ya sanya Marak'ishiya tashi tabi bayan ta ba tareda tace da 'yan parloun komai ba suka fice a tare.
Ajiyan zuciya Abdulmalik ya sauk'ar a hankali ya matso kusa da inda Abba ke zaune, murya a raunane yace.
"Abba, dan Allah ka taimaka min yanzu ka k'ira Abban Humaira kaji ina take, pls Abba idan kai ne zasufi jin maganarka, dan nikam bansan ta yaya zan soma bata hak'uri ta amince ta dawo gareni ba, inason Humaira sosai Abba bansan ya akayi na watsar da ita a sanda take tare dani tana min kukan batayi a binda ake cewa tayi ba...
Shiru yayi a sanadiyar mak'ale masa da maganar yayi a can mak'oshin sa yana dana sanin irin a bubuwan da yayi mata a cikin zaman auransu.
Kafad'ar sa Abba ya dafa cikin tsananin tausayawa yace.
"Kayi shiru Babana, karkasa damuwa a ranka, yanzu zan k'ira su muji gada garesu.
Hakan da yaji ne ya sanya zuciyarsa yin sanyi ya koma gefe guda ya zauna, yana kallo Abba ya d'auki waya ya k'ira wayar Abban Humaira, yana soma ringing ya d'auka bakinsa d'auke da sallama.
Bayan sun gaisa cikin girmama juna Abba ya soma bawa Abban Humaira a binda ke faruwa a tsakanin ta da Abdulmalik bayan ya tambaya yaji Humaira tazo gida yanzu haka tana makaranta.
Mamaki ne sosai yakama Abban Humaira, jin irin a bubuwan da yafaru kuma ko kad'an bata nuna musu hakan ba, duk da cewa yayi zargin wani abu tattare da ita amman sanin ba k'arya ta saba yi masa ba ya sanya shi yarda da ita bai tsaya binciken meke damunta ba.
"Numfasawa sannan yace
"Karka damu alhaji insha takusa dawowa daga makaranta, idan yaso zamu samu a sasanta komai ta dawo gidan mijinta.
Ba k'aramin dad'i Abba yaji ba da wannan furucin, a nan sukayi sallama da juna Abba ya kashe wayar tareda kawo dubansa kan Abdulmalik yace
"Kwantar da hankalin ka Babana, ance ta koma gida yanzu haka tana makaranta ta kusa dawowa, idan ta dawo sai muje can Abujan a sasanta komai, dan haka karka saka damuwa a ranka komai zaizo da sauk'i".
Kansa ya girgiza yana tunanin ta a cikin zuciyarsa ya mik'e yayi sallama da Abba ya fice a daga gidan ya nufi hanyar office zuciyar sa cike da tunanin ta.
✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:12] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAPHSAH_M*
*Page*
*67*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*
Umma kam dan takaici kasa magana tayi, ganin duk kowa dake cikin parloun sun watse daga ita sai Abba, hakan yasa itama ta fice a parloun tana gunagune a cikin zuciyarta, a sannan Abba ya mik'e gameda ficewa daga parloun yana jinjina a bun a ransa.
***** *****
Kwance take rigingine bisa gado idanuwanta lumshe tamkar mai bacci,
a sanda take tunanin zamanta da Abdulmalik wanda ya juya mata baya a lokacin da take bukatarsa.
Runtse iduwanta tayi sosai ta bud'e su a yayinda suka ciko da k'wallah tasa hannunta ta goge gameda sauk'ar da numfashi, jin phone d'inta dake kusa da ita ya d'auki ruri ya sanya ta tashi zaune ta dai-daita nutsuwarta kafin ta amsa wayar cikin muryanta ganin Abba ne ke k'iran ta.
"Assalama alaikum Abba na!".
"Wa'alaikumussalam Mamana". Abba ya amsa mata gameda fad'in
"Kina lafiya, ya karatun?"
lafiya lau Abba sai hamdala".
"To yayi kyau". Yace da ita gameda k'ara fad'in meyene ya shiga tsakaninki da Abdulmalik?"
A takaice yayi mata tambayar wanda yayi sanadiyar tsinkewar zuciyarta ya shiga bugawa tana amton sunan Allah a ranta tace
"Nashiga uku ya rabbi a binda banaso ya tonu gashi ya tonu, waye ya sanar dashi damuwar da nake b'oyewa?"
"Kinyi shiru Mamana bakice komai". Taji ya fad'a.
"Abba, bakomi fa tsakani na dashi lafiya lau na dawo".
"Kar kice zaki min k'arya Humaira nasan komai, dan haka so nake yanzu inji daga bakinki".
"Runtse iduwanta tayi tanajin wani iri a cikin ranta kafin tace
"Bani da a binda zance maka a yanzu Abba please kabar maganar bata waya bace, idan na dawo gida sai muyi".
"To shi ke nan Mamana ki dawo lafiya".
"Allah yasa". Tafad'a a takaice sannan tayi saurin kashe wayar tana sauk'ar da numfashi k'asa k'asa.
"Ya salam! Na shiga uku meke faruwa, waye ya sanar da Abba a binda ya faru tsakanina da Abdulmalik?"
Ohh ya rabbi ka taimaka min".
"Ke! malama lafiyarki kuwa ke kad'ai kin daburce meyene ya faru?"
Amena ce tayi mata tambayar gameda kafe ta da ido, dama shigowar ta cikin d'akin kenan taci karo da ita a rikice tana salati.
"Amena shi ke nan a binda na d'auki tsawon lokaci ban sanar da kowa ba na bari yana cin raina shine yanzu Abba ya k'ira yake min magana a kai, narasa taya a kayi ya sani".
Guri Amena ta samu kusa da ita ta zauna gameda dafa kafad'arta sannan tace
"Kin sakani a duhu Humaira! Meyene shi wannan a sirin da kike b'oyewa wanda ya d'aga miki hankali?"
Ajiyar zuciya ta sauk'ar a hankali ta jiyo da dubanta kan Amena kafin ta soma bata lbrn irin a bubuwan da yayi ta
wakana a zaman auranta ita da Abdulmalik.
Salati Amena tayi tana tafa hannu tace
"Yanzu Humaira duk wannan abun ya faru amman ko kad'an baki sanar dani ba!?" Ai a lokacin da kinyi min waya na sanar a gidanmu anzo an d'auke ki, kinga da baki shiga hannun mugayan mutanan nan ba".
Cike da takaici Humaira ta watsa mata harara cikin murtuke fuska tace
"Dalla malama rufe min baki! A lokacin na k'ira ki wayarki a kashe sai kace wata 'yar siyasa tayaya kike tunanin zan sameki?"
"Kinga baki da a binda zakice min, dan haka kiyi shiru kawai, a sanda mutum yake cikin damuwa da tashin hankali yana neman taimakonku a lokacin ne zaku kashe wayoyi yayita nemanku bazai sameku ba, idan mutuwa nema sai dai ya mutu a banza".
Ranta a b'ace take maganar a sanda ta mik'e tsaye ta d'auki kud'i da mayafinta ta fice daga d'akin ba tareda ta kuma kallon inda Amena take ba, sanadiyar abin ba k'aramin haushi da takaici ya sanya ta ba.
Ganin irin yanda ta fice ranta a b'ace ya sanya Amena tashi tabi bayan ta cikin hanzari tana bata hak'uri.
Shagon da ake siyar da kati ta nufa Amena na biye da ita tana mata magana amman tayi banza da ita tamkar bata san da ita take ba.
Bayan ta siya katin ne ta jiyo da niyyar ficewa daga cikin shagon taji taci karo da mutum a gabanta tayi saurin matsawa baya tana fad'in
"Sorry dan Allah ban...
Maganar ce ta mak'ale mata a wiya ya sanya ta murtuke fuska ganin Zaid ne ke binta da mayen kallo yana shu'umin murmushi.
Ratsawa tayi ta gefensa zata wuce taji ya kamo hannunta ya dawo da ida baya wanda hakan ya bata haushi ta d'aga hannu ta wanka masa mari tana hucin takaici tace
"Kai! wallahi wallahi bari kaji bana son iskancin banza da wofi, wato kayi iya sharrin da zakayi kaga bai gama tasiri a kaina ba shine yanzu ma ka biyo ni nan dan ka nuna min kalan karuwancinka, to billahillazi idan har baka kama kanka kasan inda dare yayi maka ba ina mai tabbatar maka da cewa zakaga tashin hankalin da bazaka iya d'aukar sa ba, idan kuma ka musa mu zuba ni da kai sai kasan cewa shayi ma ruwa ne".
Tana kaiwa k'arshe a zancen da take ta mangaje shi ta wuce Amena tabi bayanta a yayinda yake rik'e da kuncin sa yana goga wanjan dan yaji zafin marin da tayi masa ba kad'an ba, saidai kuma ya d'auki alwashin kota halin k'ak'a sai ya samu yaci mutuncinta dan bazai k'ale ta haka banza ba wanda koda wasa baza tayi gigin walak'anta wani daban ba.
Bayan sun shiga cikin d'akinsu Amena tashiga mata fad'a tana ja mata kunne akan tayi hankali da irin wad'an nan samarin, dan ba mutunci bane dasu.
Shiru tayi ba tace da ita k'ala ba illah zancen zucin da tashiga yi tana tunanin yanda zasu kwashe da Abba idan ta koma gida, dan ita a yanzu ba matsalar Zaid bane a gabanta...
****** ******
*Bayan watanni hud'u*
Alhamdulillah yau Humaira ta kammala da karatunta suna zaune a Airport ita da Amena kan d'aya daga cikin kujerun da aka tanadarwa masu tafiya.
Ba d'auki tsawon lokaci ba bayan sunyi bording jirgin ya tashi sama dasu.
Kasancewar tashin safe sukayi ya sanya da yamma suka iso garin abuja, dama Mahmud yazo yana jiran sauk'ar jirginsu.
Bayan sun kammala kwasan kayansu suka shiga mota Mahmud yajasu suka kama hanyar gida, sai da suka sauk'ar da Amena a gidansu kafin suka kamo hanyar nasu gidan, cikin mintuna kad'an suka isa Mahmud ya danna horn malam Musa ya bud'e masa gate ya shiga, bayan yayi parking motar Humaira ta sauk'o rik'e da jakanta a hannu ta nufi cikin gidan Mahmud na biye da ita malam Musa ya kwaso mata kayanta ya nufi ciki dasu.
Tana shiga cikin parloun taci karo da Mummy na shirin fitowa, fuskanta d'auke da murmushin farin ciki Mummy tayi saurin zuwa ta rungume ta gameda fad'in
"Humaira kina lafiya kuwa! Yanzu a binda kikayi yayi miki dai-dai a cikin rayuwarki kenan?" Har zaki d'auki ciki Humaira ya zube kusan kullum muna waya dake amman ko kad'an baki tab'a sanar dani ba, bayan haka irin matsalolin da kika yita fuskanta amman bakiyi gigin sanar mana ba, meye dalilinki na hakan?"
Tunda Mummy ta soma jero mata wad'an nan tambayoyin yayi sanadiyar tsinka mata zuciya, jikinta yayi mugun sanyi sosai tana runtse idanunta da suka soma cika da kwalla ta d'ago da kanta a hankali ta dubi Mummy dake kallonta cikin damuwa tace
"Dan Allah kiyi hak'uri Mummy! Nasan nayi babban kuskure da rashin sanar daku da banyi ba, but bana son tashin hankalinku ne ya sanya na rik'e abun ni kad'ai a raina".
"Amman kinyi kuskure Humaira, karki kuma aikata irin haka, mu iyayenki ne munada ikon da zamu san a binda ke gudana a cikin rayuwarki da kikeyi a ko ina".
Kanta ta girgiza tana murmushi tareda goge hawayen da taji ya gangaro mata tace
"Insha Allahu Mummy bazan kuma ba, zan ina k'ok'ari inga na sanar daku komai".
Murmushi itama Mummy tayi kafin taja hannunta suka k'arasa cikin parloun inda Abba ke zaune yana kallonsu.
Kusa da Abba ta zauna, bayan sun gaisa shima yayi mata fad'a akan halin da tashiga amman bata sanar dasu ba.
Kanta a langab'e tabashi hak'uri tareda fad'in bazata sake ba kafin ta mik'e tsaye ta haura sama zuwa d'akinta dan ta samu tayi wanka taci abinci ta huce gajiyar dake jikinta.
****** ******
Bayan kwana biyu da dawowar ta daga makaranta tana kwance bisa gadon d'akinta Mummy ta shigo tace da ita Abban ta na k'iran ta ta same su a parloun taran bak'i.
Cike da mamaki ta mik'e gameda ficewa daga d'akin tana sak'e sak'e a can zuciyarta tace
"Ko lafiya Abba ke nema na kuma a parloun taran bak'i!? To Allah dai yasa ba maganar Abdulmalik zaiyi min ba".
Tana tsuke baki ta k'arashe maganar a yayinda ta iso dai-dai k'ofar parloun tayi Ar'ba da takallama fiya dana mutum d'aya.
Bata kawo komai a cikin zuciyarta ba ta k'usa kai ta shiga cikin parloun bakinta d'auke da sallama...
"Kasa k'arasa sallamar tayi baki sake, batasan a sanda tayi mutuwar tsaye ba zuciyarta ya shiga tsananin bugawa.
Bakomai ya shigar da ita cikin wannan halin ba face Abdulmalik da Abbansa da tagani zaune tareda Abbanta sai Mummy dake zaune kan d'aya daga cikin kujerun parloun tayi tagumi tana tunanin wani abun daban.
"K'araso ciki ki zauna mana Mamana". Abba ya fad'a yana mata nuni da kusa dashi.
Har izuwa lokacin zuciyarta bai daina bugawa ba, a hankali jiki babu k'wari ta k'arasa kusa da Abban ta zauna ba tareda ta kuma kallon gefen da Abdulmalik ke zaune ba, illah ma sauk'ar da kanta k'asa da tayi tana wasa da yatsar hannunta bayan ta gaishe da Abbansa ya amsa mata cikin sakin fuska.
Gyaran murya Abba yayi gameda dai-daita zamansa sannan yakai dubansa kan Humaira yace
"To Mamana, ga mijinki nan yazo bikonki, ya sanar damu komai a bubuwan da yasha faruwa a tsakaninki da shi, shine mukace bari ki dawo daga makaranta tunda kin kusa kammalawa idan yaso sai ku sasanta ki koma gidan mijinki, tunda har yanzu da auransa a kanki, idan kuma bakida abin fad'a shi ke nan sai ki shirya gobe ku kama hanya, dan abinda yariga yafaru ya wuce sai fatan alkhairi Allah ya gyara zamanku yakau da shaid'an a tsakaninku".
K'arashe maganar yayi yana k'ara dubanta a karo na biyu dan yaji mai za tace.
Sun d'auki kusan mintuna uku duk sun zuba mata ido suna jiran mai za tace amman tayi shiru ta kasa fad'in komai.
Ganin shirun yayi yawa da alamun bata da niyyar cewa komai, hakan ya sanya Abba fad'in
"Kinyi shiru Mamana! kiyi magana mana, dukka nin mu nan ke muke sauraro".
Runtse iduwanta tayi gameda sauk'ar da numfashi a hankali ta d'ago da kanta ta dubi Abba da idanunta wanda suka cike da ruwan hawaye tace
"Abba, nasan inda kasan irin halin da nashiga bayan Umma ta koreni, da kai da kanka za kace baka yarda in koma wancan garin ba.
"Abba nashiga tsananin tashin hankali da damuwa marar misaltuwa a sanda na kasance a garin da bani da kowa da zai taimaka min a cikin mummunar halin da na tsinci kaina, wanda da badan Allah ya taimaka min yaji k'aina ba da sai dai kuji labarin na mutu ko kuma na salwanta cikin mummunar hali...
Kuka ne yaci k'arfin ta, ya hana ta ci gaba da zancen da takeyi.
Tashi Mummy tayi daga kujeran da take zaune ta matso kusa da ita gameda dafa kafad'arta cikin tausayin d'iyarta duk da bawai tasan irin halin da ta shiga bane amman Hakan yasa ta cikin damuwa.
"Humaira!". Mummy ta k'ira sunanta sannan tace
"Kiyi shiru kibar wannan kukan ki fad'a mana a binda ya faru dake kin shigar damu cikin fargaba".
Ajiyar zuciya take sauk'arwa a hankali tana share hawayen dake malale bisa kunta taci gaba da cewa
"Abba, a lokacin da Umma da siyama suka fitar dani daga cikin gidan, da kansu suka kaini bakin tashar shiga mota cikin goshin magariba kanaji ko ina ana k'iraye k'irayen sallah haka suka jefa min jakar bacgon da suka tusa min kayana aciki suka barni yashe a bakin tasha ina kallonsu suka b'acewa gani na.
"Sanin kanku ne ba kowa nasani cikin garin k'atsina ba, ba ko ina nake zuwa ba bare insan wani waje, haka bayan na k'ira wayar Batula in sanar da ita halin da nake ciki amman bata d'auka ba har nagaji da k'ira nazo na gwada na Amena Bature kasancewar ta su 'yan katsina ne na tabbata koda wani d'an uwanta ne zata samo min, kash sai dai kuma wani abin takaici ita kuma nata wayar a kashe, ni kuma na saka a raina bazan k'ira ku na d'aga mugu hankali ba gwara in nemi wata hanyar.
"Ganin haka yasa nabazu ina zagaya cikin tashar ko zan samo inda zan siyar da wayar tawa idan yaso inyi kud'in mota dashi tunda shine kad'ai Allah ya taimaka min zan fito dashi sanadiyar ba barina sukayi in d'auki komai ba shima sa'a naci yana hannuna cikin hijabi basu kula dashi ba da sai sun karb'a.
"Bansamu shagon siyar da waya ba gashi sai dare ne keyi ganin haka yasa na yanke shawaran tambayar wasu mutane biyu da nagi zaune ko zasu nuna min.
"Danasan hannun 'yan iska zan shiga da banje koda kusa dasu ba, domin kuwa cewa sukayi zasu nuna min amman suka shigar dani wani unguwa mai ban tsoro ba tareda nasani ba sai ji nayi sun d'aukeni sun shiga cikin wani gida dani zuwa wani d'aki suka sauk'ar dani.
"Haka na kasance a cikin wannan kurgurmin d'akin har na tsawon kwana biyu ba tareda ci ba bare sha, dukda kuwa suna kawo min jagwalgwalon abincinsu amman bazan iya ci ba dan bansan wanne mugun abu suka watsa min aciki ba, tunda ba mutanan arziki bane, so suke burinsu ya cika a kaina su lalata min rayuwata amman hakan ya gagare su, domin kuwa a koda yaushe idan d'ayan su ya shigo cikin d'akin sai ya tunkare ni da mugun nufi cikin taimakon Allah duk abinda nagani kusa dani rad'a musu nakeyi ina kokuwa dasu da duk iya k'arfi na,
ganin haka ya sanya su yanke shawaran bani k'waya kota halin k'ak'a idan nabugu sai su samu subiya bukatarsu.
"Tun a daran ranar da naji haka bacci ya k'aurace min dukda bawai baccin nake ba daman, har zuwa asuba idona biyu bayan na samu na gabatar da sallah kafin gari yagama yin haske Allah yafad'o min da wata dabara,
na samu wani murfin samira na d'auki bacgon kayana da wayana na rakub'e bayan k'ofar d'akin ina jiran isowar ko wannan su.
"A sanda d'ayan su shi kad'ai ya bud'e k'ofar d'akin ya shigo ni kuma na rad'a masa murfin samiran akansa sau biyu na shure sa yafad'i k'asa ba tareda ya ankara ba nafice daga d'akin a yayinda yake k'ok'arin cafko ni yana rik'e da kansa wanda ya soma zubar da jini sanadiyar bugun da nayi masa..
✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:12] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*68*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*
"Bayan na samu na kub'uta daga hannunsu ina cikin tafiya ba tareda nasan inda na dosa ba na hango wani shagon masu waya na shiga na sayar da wayar, ina fitowa na samu mai adai-dai ta sahu nace ya kaini tashar mota.
Bayan ya kaini ya nuna min motar da ake lodin 'yan Abuja, kasancewar wajan mutum d'aya ne ya rage, hakan yasa ina shiga muka kamo hanya har muka iso cikin Abuja na samu mai taxxi ya kawo ni har k'ofar gida".
"Runtse iduwanta tayi a karo na biyu wasu zafafan hawaye suna k'ara zubo mata, a hankali ta d'ago da jajan idanunta da suka yi jazir sosai dan kuka ta dubi Mummy da Abba kafin tace
"Yanzu duk irin wannan mawiyancin halin da na shiga idan nace zan koma wancan garin zaku yarda in koma?"
"A'a".
Mummy ta fad'a tana girgiza kanta hawaye na gangaro mata a fuskanta tace
"Humaira! kinyi babban kuskure da rashin k'iran mu da bakiyi ba, yanzu da sun lalata miki rayuwa daga k'arshe sun kashe ki waye da a sara?"
Mune ba kowa ba, dan Allah ki daina irin wannan halin ba'a b'oye mummunar abu idan ana cikin neman taimako".
Jikinta ta shiga dubawa tana k'ara fad'in
"Ina fatan dai basu samu damar cin galaba a kanki ba har Allah ya kub'utar dake?"
"Mummy lafiyata lau na dawo, ki kwantar da hankalinki ai babu wanda yayi na saran biyan buk'atarsa".
Tana murmushin k'arfin hali ta k'arashe maganar a yayinda Mummy tayi hamdala a ranta tana godewa Allah da ya kare ma d'iyarta mutuncinta.
Shiru ne ya ratsa cikin parloun na d'an dak'ik'u, babu wanda ya iya fad'in komai sai sautin sauk'ar numfashita dake tashi, ba Abdulmalik kad'ai ba har Abba sai da suka tausaya mata, lallai kuwa ta auna arziki, da ba dan kariyar Allah ba da sai yanda sukayi da ita.
Abban Abdulmalik ne ya katse shirun da cewa
"To d'iyata, munji duk abinda ya faru dake, a gaskiya kin auna arziki, fatan Allah ya kiyaye gaba ya rufa asiri, dan ba k'aramin mugun hannu kika fad'a ba, sai dai kuma mun godewa Allah ubangiji da yasa basu samu damar aiwatar da mummunar nufinsu a kanki ba.
"Dan haka a yanzu bani da abinda zan iya cewa cikin wannan lamarin, dukda cewa mijinki bashi da laifi sosai a ciki amman kuma hakan ya faru ne a rashin baki yarda da amincewa da baiyi ba, ya biyewa zuciyarsa ya d'auki irin hud'ubar da take basa.
Kinga kuwa yanzu ya rage a tsakaninku, idan kinga zaki iya binsa ku k'ara shimfid'a rayuwar auranku ingattacciya to bisimillah gashi nan sai ku sulhunta tsakaninku, idan kuma kinga baza ki iya ci gaba da zaman aure dashi ba, shi ke nan kina da ikon kanki a cikin wannan lamarin".
Tsantsan tashin hankali ba kad'an ba Abdulmalik ya shiga jin irin furucin da Abbansa yayi ya sanya bai san a sanda ya d'ago da kansa ba cikin muryan tausayi yana duban Abbansa yace
"Haba mana Abba!, dan Allah karka min haka, dan Allah karka cire kanka a cikin wannan maganar, nasan cewa ina da nawa lefin nine silan komai, amman na tuba na gane kuskurena yanzu bazan kuma juya mata baya ba".
Cikin k'asa da murya ya k'arashe maganar a yayinda tausayin sa ya shiga cikin zuciyar Abban Humaira yasa hannunsa ya dafe kafad'un sa yace
"Kayi shiru Abdallah insha Allahu zata dawo gareka kuyi zamanku cikin k'oshin lafiya, ni nayi maka wannan alk'awarin zan dawo maka da ita.
Dan haka kwantar da hankalinka, ka cire damuwa a ranka zata yafe maka, kasan yarinya ce komai sai a hankali".
"Nagode Abba, Allah yak'ara girma".
"Amin Abdallah". Abba yace dashi fuskarsa cikin murmushi.
"Abba! Amman ko kasan cewa kota halin k'ak'a bazai iyu in koma gidansa ba?"
Cikin nuna damuwa tayi maganar ganin da gaske Abba zai iya sata ta koma gidan.
"Saboda meye Mamana?" Abba ya tambayeta yana dubanta.
"Ina zuwa". Ta basa amsa a sanda ta mik'e ta fice daga cikin parloun.
Cikin mintuna biyu taje ta dawo ta same su hannunta rik'e da wata takarda.
Mik'awa Abba takardar tayi kafin ta zauna a k'asa kusa da Mummy.
"Ya salam!" Abba ya furta cikin tsarkewar murya yace
"Meye wannan kuma nake gani Abdullah?"
Takardar sake daga gareka, kuma kake so ta koma gidanka?"
"Saki kuma Abba! wallahi a'a, bani na rubuta ba wallahi ban san dashi ba.
Cike da tsananin mamaki yake maganar tareda zaro ido a ransa yana wadarai da irin wannan masifar da Umma ta shigar dashi, tambayarsa itace, ta yaya zai fahimtar dasu cewa bai san da wannan takardar sakin ba ko kad'an, hasali ma shima rubutun k'aryan sukayi masa dan ya tabbatar da zancen.
Gyaran murya Abbansa yayi kafin yace
"Zai iya iyuwa bashi ya rubuta takardar ba mahaifiyar sa ce, insha Allahu kuma yanzu idan na koma zan k'ara bincika yanda lamarin yake, idan yaso daga baya idan yarinya ta amince ta hak'ura sai ta dawo suci gaba da zamansu.
Kai Abba ya jinjina alamun ya gamsu da zancen sannan suka yi sallama suka watse a parloun.
D'akinta tashigo ta fad'a bisa gado tana sauk'ar da numfashi sama-sama, dan ita a yanzu ba son komawa gidansa take ba, duk da kuwa tana k'aunarsa har cikin ranta, kuma tana son kasancewa dashi, amman baza taso ta k'ara fad'awa cikin makamancin halin da ta fad'a a baya ba.
**** ******
A washe garin ranar tun safe misalin k'arfe goma shad'aya bayan ta kammala da duk wani aikin da zata yi ta shirya taje gidansu Amina ta wuni har yamma wajan k'arfe biyar sannan ta kamo hanyar dawowa gida.
Ta shawo kwanan layin gidansu kenan wata farar mota tasha gabanta, cikin tsinkewar zuciya tayi saurin taka birki tana fitar da salati a bakinta.
Ganin wanda ya fito daga cikin motar ne ya sanya ta had'a rai cikin takaici ta bud'e k'ofar motar ta fito game da nufowa inda mutumin ke tsaye jikin motarsa yana kad'a key.
"Haba Sufiyan! wannan wani irin nuna isa da mallaka ne? "Ya ina cikin tuk'i zaka zo kasha gabana da yanzu na bugu da mota sai kace meye?"
"Sai ince sorry mana". Yafad'a a takaice yana sakar mata da murmushi.
"Mtsee". Taja tsaki tace
"Sai kayi ai ni dai bani da lokacin ka".
"Ke kuwa kike da lokaci na". Yafad'a a sanda ya shige gabanta ganin tafiya zata yi.
"Wai meye hakane Sufiyan!?"
"Magana nakeso nayi dake amman kuma kina ja min aji, karki mance ni d'in mai sonki ne har yanzu ban daina ba.
Dan haka shawaran da zan baki shine, akan wannan auran da kika yi babu riba gwara ki dawo zuwa gareni muyi auranmu cikin so da k'auna, tunda gashi dan ba dad'in zaman auran kikeji ba kin dawo gida kusan tsawon watanni, kodai ya sake ki ne bamu sani ba?"
Yayi mata tambayar yana bud'e mata ido.
"Ya salam!". Tafad'a cikin haush da takaici game da jin irin banzan maganganun da yake jero mata.
Hannu ta d'aga tana nuna shi da yatsa tace
"wlh Sufiyan kashiga hankalinka banason zancen banza, karka ganni haka ni ba tsararka bace, kabar harka na kasan inda dare yayi maka, dan haka bani waje in wuce matar da ka aura ma ta ishe ka zama".
Ranta a mugun b'ace ta k'arashe maganar a yayinda ta ratsa ta gefensa ta wuce zuwa motarta tana jan dogon tsaki.
Kad'a makullin dake hannunsa yayi a sanda ta figi motarta tana watsa masa harara tabar wajan.
Jan nashi motar shima yayi yabar wajan yana aiyyana wasu abubuwa a cikin ransa, domin kuwa shi har ila yau bai daina sonta ba, da zata yarda dashi da tuni sunyi auransu sun mance.
Zaune yake cikin motarsa ya jingina kansa a jikin kujerar a yayinda idanuwansa ke kansu yana kallon abinda ke wakana a tsakaninsu, kasancewar tunda ta kamo hanya daga gidansu Amina ya hango ta yake biye da ita a baya ba tareda da ta lura da hakan ba.
Ajiyar zuciya ya sauk'e a sannan ya tashar da motarsa ya nufi gidan nasu a cewar zai nemi izinin fita da ita idan yaso zai san yanda zaiyi ya shawo kanta har ta hak'ura ta ta dawo zuwa garesa, dan hakan shine hanyar da yaga zai iya samun fita da ita ba tareda yasha wahala ba.
Shiga cikin gidan yayi bayan mai gadi ya bud'e masa gate ya shiga a sannan ya tura sa ciki dan yaje ya k'irawo masa ita.
Cikin girmamawa ya nufi cikin gidan a parlou ya tarar da ita kwance bisa kujera idanuwanta a lumshe a sanda fuskarta ke d'auke da 'yar murmushi wanda ya nuna alamun tunanin wani abun farin ciki take.
Mummy na zaune kusa da ita Mahmud na k'asa yana cin abinci cikin had'e fuska tamkar dole aka saka shi, sanadiyar yauma kalar abincin da baya so suka girka, wato couscous da miyar kuka.
"Assalama alaikum, ranki shidad'e mai gidanki yana miki magana yana filin gida".
Yafad'a cikin surunawa.
Tashi zaune tayi tana ya mutsa fuska tace
"Wanne mai gidan nawa kenan?"
Harara Mummy ta watsa mata game da fad'in
"Ja'ira yarinya, wannan wani irin banzan tambaya ne haka, halan mazaje dayawa gareki?"
"Mummy yo ni ai nasan a yanzu bani da wani mutum a sunan mijina shiyasa".
"Tashi kije idan kinga wanda yake neman naki zaki san cewa baki da miji".
"Nifa Allah Mummy a gajiye nake babu wajan wanda zani da yamman nan, dan haka kaje kace masa bana gidan ma gaba d'aya na fita".
Rai a had'e ta k'arashe maganar tareda komawa ta kwanta tana rufe idanunta.
Ganin idan ba zare mata ido tayi ba da gaske take ba zuwa zata yi ba, saidai ta k'yale sa shanye, hakan ya sanya Mummy mauje ta da hannu tana fad'in
"Maza tashi fice min a parlou tunkan ranki ya b'aci, saura inji bakije wajan nasa ba kiga abinda zanyi miki".
Tashi tayi ba dan ranta yaso ba ta fice daga parloun.
"To Mummy nikam idan ba dole bane a barta mana tunda bason koma masa take ba, naga dai ba kowa bane ya sata auransa ba a baya, dan haka bai kamata a matsa mata dole sai taje k'iran da yayi mata ba, tunda shine yayi sakacin hakan ya janyowa kansa, banda hakama ga mazaje dayawa binta suke suna son ta kinga ai sai ta zab'i d'aya daga cikinsu, dan har yanzu hakama abokina bai daina sonta ba wallahi".
Mahmud ne yayi maganar a sanda yake fuskantar Mummy da ta zura masa ido tana masa wani irin kallo.
"Ka gama maganar taka?" Mummy ta tambayesa a takaice.
Kansa kawai ya girgiza mata sannan tace
To ai kaima Yayanta ne zaka iya aura mata wani mijin wanda kaga yayi maka, tunda a naka fasalin ana aure kan wani aure".
Tana gama fad'in haka ta tashi ta bar sa shi kad'ai a parloun yana kad'a kai.
Tana zumbura baki ta iso haraban gidan inda yake zaune cikin motarsa ya jingina kansa a sanda idanuwansa ke rufe.
Sarai ya gane da isowarta amman sai ya dake tamkar bai san da mutum tsaye a kansa ba.
"Kaga malam! Tafad'a cikin had'e rai ta kuma cewa
"Nifa ba sauraran shirunka bane ya fito dani ba, idan kana da abin cewa inajin ka kayi sauri dan inada aikin yi ba tsayuwa nazo yi ba.
"Ki shigo cikin motar sai muyi maganar". Ya fad'a a sanda ya bud'e idanunsa yana kallonta.
"Wa! Ni?". Ta fad'a cikin zare ido tace
"Babu inda zan shiga bari kaji, idan dama hakane ya kawo ka kaga tafiya ta sai anjima".
Juyawa tayi da niyyar komawa ciki, ganin haka ya sanya shi saurin fitowa daga motar ya kamo hannunta cikin zafin nama a yayinda take fisgewa ya shigar da ita gaban motar kafin tayi yunk'urin bud'ewa dan ta fice yayi saurin shiga nashi gefen tareda sanya key ya kulle motar, baice da ita k'ala ba ya tada motar ya fice daga gidan a yayinda ta murtuke fuska tana masa kallon tuhuma tace
"Meye haka zaka shigar dani motar ka a dole?"
Banda hakama ina zaka kai ni bada amincewata ba?"
Sace ki nayi zan kaiki gidan 'yan yankan kai, kuma ni ban shigar dake a dole ba kece kika ga damar shiga.
Dan haka tun yanzu kiyi min shiru da bakin ki tunkan in soma fed'e ki".
Cikin nuna isa da iko yayi maganar yana ci gaba da tuk'a motar ba tareda ya dubi gefenta ba.
"Baki ta murkud'a masa bata kuma ce dashi komai ba ta juya kanta gefe tana kallon titi, a yayinda take tambayar cikin zuciyar ta, to ina wannan mutumin yake shirin kai ni?"
"Kibar yin doguwar tunani kina yarinya kar ya janyo miki ciwon zuciya".
"Cikin sigar wasa yayi maganar ba tareda ya kalleta ba a sanda ya iso dai-dai k'ofar gidan yayi parking motar.
Sauk'a yayi ya sak'alo da kansa ta window yace da ita
"Bisimillah sauk'o mu shiga".
Had'e rai ta kuma yi akaro na biyu tace
"Wai meye kake nufi dani ne?"
Ya zaka kawo ni hotel da mutuncina kace min inzo mu shiga ciki, ko ance maka 'yar isa na zama ne?"
To wlh babu inda zani idan zaka mayar dani gida gwara tun wuri ka mayar dani tunkan magariba tayi a soma nema na".
Tana murk'ud'a bakinta ta k'arashe maganar a yayinda ya sakar mata da lausassar murmushi yana lumshe idanunsa yace
"Himm sannu al'masifatu uwar masifa, kin mance cewa ni mijinki ne har ila yau?" Dan haka ba hotel na kawo ki ba, gidanki ne kizo mu shiga ki gani, idan su Abba kike tsoro kuma zan k'ira in sanar dasu muna tare kar su damu".
K'arashe maganar yayi yana kashe mata ido d'aya ya k'ara cewa
"Ki same ni a ciki ni na shige".
Yana kaiwa nan ya nufi cikin gidan.
Ganin batada sarki sai Allah ya sanya ta fita daga motar tabi bayan sa dan babu yanda ta iya, domin ko wayarta bata fito dashi ba bare kud'in da zata iya taran taxxi ta koma gida.
Kwance ta iske shi kan d'aya daga cikin dogayen kujerun dake zagaye a cikin parloun yana kallon TV.
"Zauna mana". Yace da ita yana duban ta.
Zama tayi kan kujerar dake nesa da nashi wanda har lokacin cikin fushi take fuskanta a had'e.
"Tashi yayi daga kwancen da yake ya dawo zuwa nata kujerar da yake mazaunin mutum d'aya, ya zauna kusa da ita suka matse juna a kan kujerar.
Yunk'urawa tayi zata mik'e yayi saurin dawo da ita ta zauna tana sauk'ar da numfashi.
*HaneeSat*✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:12] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*69*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*
"Ina kike tunanin zaki je?". Ya fad'a yana kallonta.
Juya kanta tayi ba tare da ta kula sa ba.
A hankali ya sak'ala hannayensa biyu bisa k'ugunta ya zagaye ta dashi zuwa tunbinta ya matse ta sosai wanda ya sanya ta sakin k'ara kad'an sannan yace
"Please Humaira ki tattaro min da hankalinki ina so muyi magana ta fahimtar juna, wannan guje min d'in da kikeyi wlh yana shigar dani tsantsan damuwa, dan Allah my lovely wife ki bani hankalinki".
Cikin kashe murya ya k'arashe maganar, a yayin da ya langab'ar da kansa tsakanin wiyarta.
"Ina jinka kayi maganar da zakayi".Ta fad'a a takaice ba tare da ta kallesa ba.
Ajiyar zuciya ya sauk'ar a hankali ya soma fad'in
"Kiyi hak'uri dan Allah Humaira da irin abubuwan da nayi miki a iya zamana dake, nasan nayi miki ba dad'i, haka zalika na juya miki baya a yayin da kike buk'atar kulawata, Am so sorry Humaira, please kiyi hak'uri ki yafe min kura kurena ki dawo zuwa gareni mu shimfid'a sabuwar rayuwa mai d'auke tsafta, mu mance da duk wani abinda ya faru a baya mu fuskanci na gaba, dan Allah ba dan ni ba kinji".
Ya k'arashe maganar cikin k'asa da murya tamkar mai shagwab'a.
Zamanta ta gyara game da kawo dubanta garesa sannan tace
"Haba mana Abdool, me yesa kake b'ata bakin ka akan abinda kasan ba iyuwa zaiyi ba?"
Kasan bazan iya d'aukar k'afafuna da sunan komawa gidanka ba, sam an wuce wajan, ko a mafarki bana tunanin hakan bare kuma a zahiri, dan haka idan kasan wannan maganar ne zaka yi min to ka bar lalata bakinka, dan ba koma maka zan yi ba".
Matso ta sosai ya kuma yi a karo na biyu wanda yafi na farko, hakan yasa cikin jin zafin rik'on da yayi mata ta sak'i k'ara game da runtse idanunta tace
"Wai meye hakane dan Allah!? "Kasheni kake so kayi?"
"Idan na kasheki ai nine da a sara". Ya fad'a cikin iriyar murya.
"Dan Allah ka sassauta min rik'on nan wlh akwai zafi, ko ka mance ina da ciwon ciki ne?"
Sakinta yayi cikin sauri ya jiyo da kanta game da tallafo fuskanta yace
"Wanne irin ciwon ciki kenan?"
Sauk'ar da idanunta k'asa tayi a hankali tace
"Ban sani ba nima amman ya wancin rana ku yana min ciwo".
"Aiyya sannu, amman kinje Asibiti an duba ko menene?"
Kanta ta girgiza alaman a'a.
Had'e fuska yayi sannan yace
"Bana son irin haka fa, ya baki da lafiya amman ki kasa zuwa Asibiti, to maza tashi idan nayi sallah sai muje a duba min ke, dan ba zan k'yale ki haka ba".
K'arashe maganar yayi a sanda ya mik'e tsaye itama ya mik'ar da ita yana k'ara fad'in
"Yanzu bari inyi sallah kema kiyi idan kina yi tunda an k'ira magariba, idan yaso sai muje Asibiti a duba ki daga nan in mayar dake gida bayan mun tsaya munci wani abu".
Had'e rai tayi tana masa wani irin kallo tace
"Meye nufin ka da idan ina yi?" Kuma nace maka ina bukatar zuwa Asibiti ne ko yunwa nace ma ina ji?"
Kinga Malama bana son jin wannan surutun naki, dan haka kiyi abinda nasa ki mutafi".
Fuska ta ya tsina ciki-ciki tace
"Nidai wallahi gida zaka mayar dani dan babu Asibitin da zanje, harda wani bani umarni sai kace wata matarka".
"Yana jin ta baiyi magana ba illa kad'a kai yana murmushi ya wuce band'aki ya d'auro alwala ya fito ya fara sallah.
Har ya idar da sallar tana tsaye bata a inda take bata motsa ba.
"Matar! Wai baza kiyi sallar bane?, kodai da gaske kina hutu ne?".
Ya tambaye ta bayan ya juyo da kansa gareta.
Kai ta kawar gefe guda ba tare da tace dashi komai ba, a ranta tace
"Wai yanzu a ce mutum babu abinda ya sani sai zancen banza, ka yita ta k'are ai ni dai bazan tanka maka ba".
"Himm, zan kama ki ne yarinya dani kike zancen, idan ba sallar zaki yi ba ni ki same ni a mota sai mu tafi, kuma ki kulle k'ofar gidan naki kar wani b'arawo ya shigo miki".
Yana maganar ne cikin sigar zolaya fuskarsa d'auke da murmushi a sanda yake d'aukar wayarsa da makullin motar.
Ficewa yayi bai kuma cewa da ita komai ba, ganin hakan ya sanya ta kulle k'ofar gidan sannan tabi bayansa.
A cikin motar ta iske shi yana zaune ya lumshe idanunsa, a zahiri sai kayi zaton bacci ne sama-sama ya d'auke sa, amman sam ba haka bane, tunani yake a cikin ransa yanda a bubuwa suka kasance masa a halin yanzu.
Bud'e gidan baya tayi ta shiga tare da rufe k'ofar da d'an k'arfi wanda hakan shi yayi sanadiyar dawo dashi daga tunanin da ya keyi, bud'e idanunsa yayi ya juyo da kansa ya kalleta sosai yana murmusawa sannan ya mai do da kansa yana kallon gabansa ya gyara zama alamun bashi da niyyar jan motar su tafi.
Had'e rai tayi sosai cike da takaici tace
"Ya ka tsayar damu a cikin mota sai kace gunki?" Dare fa yi yake, kasan kuma Abba zai min fad'a idan ya dawo bana gida".
"Ai sai dai yayi miki fad'ar ya had'a da duka ma, indai har a bayan mota zaki zauna inyi driving d'inki sai kace madam, to kuwa zaki dad'e yarinya indai haka ne nufinki".
"Amman dai kasan cewa abinda kake yi babu kyau ko"?
"Haka zalika kema abinda kike yi babu kyau, indai nima bana yin mai kyau to kema bakya yin mai kyau".
Maganar yake amman har zuwa lokacin bai juyo da kansa ya kalleta ba, illa dariyar da ta rik'e masa wiya tana neman kub'ucewa.
Ganin da gaske yake idan ta biye nashi haka zasu zauna har dare yayi sosai, hakan ya sanya ta fitowa daga bayan motar ta dawo gidan gaba a sanda take k'ara zumbura baki ta rufe k'ofar da k'arfin gaske wanda yafi na farko.
"Ni dai ayi a hankali kar b'alla min murfin mota a bar ni da a sara". Ya fad'a a sanda ya tashar da motar suka hau kan hanya.
Ita dai tana jinsa bata ce dashi k'ala ba har sukayi nisa, ganinsa ya nufo dasu Asibiti ya sanya ta yin magana a takaice cikin mamaki tace
"Meye zamu yi a Asibiti kuma!?"
Kedai zuba min ido mana ina ruwanki". Ya fad'a a sanda ya samu waje yayi parking motar.
"Fito muje ko?"
"Ina kenan?"
Kinga, ni nifa bana son yawan surutu da tsaurin ido, idan zaki fito muje to bisimillah". Yayi maganar a sanda yake kallonta.
"Ai ba shigar zanyi ba shiyasa". Ta bashi amsa a takaice.
"Saboda meye kenan?"
"Saboda lafiyata k'alau".
Ta bashi amsa a takaice.
"To Shi ke nen". Yafad'a k'asa k'asa a sanda ya tashar da motar suka bar cikin Asibitin ba dan komai ba sai dan ganin yau tana ji da wani irin masifa, ko dan tana al'ada ne! ohho." Ya fad'a a cikin ransa, dan idan ba rabuwa da ita yayi ba ta rink'a masa tsiwa kenan, hakan yasa bai tsaya tilasta mata ba.
Bashi ya mayar da ita gida ba har sai wajan k'arfe tara na dare, dan tuk'in yake yi a hankali son ransa duk dan ya jawo maganarta amman sam tak'i tanka masa, kasancewar ta gane nufinsa.
Yana dai-dai ta kan motar kamar jira take ta bud'e k'ofar ta fita bayan ta jefa masa makullin gidansa dake hannunta wanda ta kulle da zata fito.
Ciki ta zarce kai tsaye yana kallon shigewarta ya girgiza kansa yana murmushi game da danna horn malam musa ya bud'e masa gate ya fice yana masa sai da safe.
A parlou ta iske Abba da Mummy suna hira ta isa garesu kusa da Abba ta gaishe sa sannan yace
"Mamana kenan! Har an shirya da mai gidan naki saura komawa ko?"
Fuska ta canza a sanda ta mik'e tsaye tana shirin barin wajan tace
"Himm, Abba nifa babu shirin da zamu yi dashi bare har in koma gidansa".
Tana kaiwa nan ta wuce sama cikin sauri dan gudun kar ya kuma jefo mata wata maganar, dan ba son yin sa take ba.
Kai Mummy ta kad'a sannan tace
"Alhaji, kawai abinda za'ayi shine, mu samu mu had'a yarinyar nan kawai ta koma gidan mijinta, tunda tana son shi yana son ta, dan haka banga amfanin barin ta a gida kullum yana zuwa bikonta ba, duk da dai ban so hakan ba, amman babu yanda na iya, dan mai faruwa ya faru sai dai Allah ya kiyaye gaba".
Numfasawa Abba yayi yana girgiza kansa yace
"Hakane kam abunda ya dace a yi kenan, tunda dai da auransa a kanta shi yace bai sake ta ba, kuma Abbansa ma ya tabbatar mana da hakan, kinga a cikin kwana biyun nan sai a sulhunta komai ta koma gidanta, tunda dai karatun da take shima ta kammala sai kuma sauran ta yi su a can".
"Hakan yayi dai-dai". Cewar Mummy daga nan suka ci gaba da hiransu.
***** ******
A cikin kwanaki kad'an aka sasanta komai Humaira ta koma katsina gidan mijinta, duk da kuwa dakyar aka tura ta dan ta dirje da gaskenta tace sam ba zata koma gidansa amatsayin matar auransa ba, duk da yace shi fa bai sake ta ba to ya sake ta a yanzu tunda ba ciwon kanta ya sani ba bare har ya bata girma da amincewa, domin shi zaman aure tsakanin mutane biyu a na bukatar aminta da juna kada a bari zargi ya shiga tsakani, dan da zaran zargi ya shiga tsakani to shi ke nan aure ya lalace tun a wannan lokakin, domin babu yanda za'ayi ku k'ara yarda da juna ko amincewa.
Haka dai babu yanda ta iya ganin iyayenta suna son komawar nata, hakan yasa ta amince ta koma gidansa bayan ta k'ara yin gyaran jiki anyi mata dilke da halawa tayi fas da ita sai shek'i takeyi tamkar sabuwar Amarya, dan hatta hannayenta da k'afafuwanta duk sai da a kayi mata lallai ubansu wanda yayi mata muguwar kyau.
*HaneeSat*✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:12] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT M*
*Page*
*70*
Sadaukarwa ga k'awata
*AISHA GENTLE LADY*
GARIN KATSINA
Misalin k'arfe tara na dare da wasu d'aurin mintuna, tana
kwance bisa gadonta dake shimfid'e a tsakiyar d'akin tayi rufda ciki a sanda wayarta ke hannunta tana latsawa.
K'ofar d'akin taji an murd'a ana shirin bu'dewa, jin hakan yasa tayi saurin kashe wayar ta ajiye shi sannan ta rufe idanunta tamkar mai baccin gaske a cewarta k'ofar a bud'e take, ta ma mance da ta kulle k'ofar da makulli hakan yasa take tsimayar shigowarsa.
Jin yana ta murd'a k'ofar game da k'wank'wasawa yasa ta mik'e zaune ta d'auki wayarta ta kunna tana dafe kanta game da jan k'aramin tsaki tace
"Wash! kaina, wallahi na ma mance da na kulle k'ofar ba ta inda zai iya shigowa idan ba nice na bud'e masa ba, bare ma bazan bud'e ba sai dai kayi ka gaji, idan yaso ka hak'ura ka tafi".
Ci gaba da latsar wayarta tayi hankali kwance a sanda murmushi ke shimfid'e bisa lausassar fuskarta, shirun da taji na an daina buga k'ofar d'akin yasa ta kuma murmusawa a karo na biyu ta bud'i baki tace
"Himm, ka yita ta k'are amman bazan bud'e k'ofar n..."
Ba ta kai ga iya k'arasa maganar ba ya mak'ale mata a can k'asar mak'oshinta, sanadiyar ganin fuskarsa da tayi yasa ta kawar da kanta gefe taci gaba da latsar wayarta kamar ba ta san mutum ya shigo cikin d'akin ba, sai dai kuma mamaki take a cikin ranta a ina ya samu irin makullin d'akinta har ya bud'e Ya shigo? "ko dan gidansa ne a nan na iske shi". Ta fad'i hakan a cikin zuciyarta tana tab'e baki.
"Yanzu dama kina cikin d'akin nan nazo nayi ta bugawa ina k'iran sunanki ki bud'e min k'ofa amman kika yi banza dani sai yi nake kamar tab'ab'b'e! Da bani da wani makullin da shi ke nan sai dai in hak'ura kenan?". Yayi maganar cikin sigar mamaki a yayin da ya iso gareta yayi tsaye yana kallonta.
Shiru tayi masa tamkar ba taji abunda yace ba, illa ma zama da ta gyara a sanda idanunta ke kan fuskar wayarta sai kayi zato wani abu mai muhimmanci take yi.
Da ke fa nake magana matar!" Ya k'ara fad'a cikin dakiyar murya mai cike da tsantsan mamaki.
Wannan karon ma shiru tayi masa tana ci gaba da latsar wayarta, ganin da gaske ba niyyar kula sa take dashi ba hakan yasa ya zauna a bakin gadon daf da ita yana murmushi ya kalleta daga saman fuskarta har zuwa k'asar k'afar ta, a sanda take cikin tsararran shiri tana sanye da inglish wears wanda ya zauna mata a jikinta yayi mata kyau sosai, a yayin da kuma gashin kanta ke cikin gyara ta mishi tufka d'aya sai shek'i yake mai, ban da haka ga daddad'an k'amshin turaren wuta dake tashi a cikin d'akin, sai ya zo ya had'u da sanyin A C yake fitar da dad'in ni'ima.
Idanunsa ya lumshe sannan ya bud'e su yana jin wani irin tsantsan kewarta a cikin zuciyarsa, zama yayi a bakin gadon daf da ita yana murmushi, a hankali ya d'aura hannunsa kan tausasshiyar k'afarta ya soma murza yatsunta yana mai kallonta yanda tsarinta yake, dan ba k'aramin kyawu yaga tayi masa ba, gani yake taba tab'a yin kyau irin na yau ba,
Numfasawa yayi a sanda yake fad'ad'a murmushinsa yace
"Matar, mu je ki bani abincin da zan ci ya toshe min yunwar da ke cin cikina, dan naga alamun yau kina ji da shan k'amshi, ni da nake mijinki ma sai ja min aji kike, dan haka ni dai yanzu muje ki bani abincina inci da sauran hakkina dake kanki, idan yaso sai kina kwana ke kad'ai kullum kina shan k'amshinki, amman fa sai bayan kin gama bani ko wanne irin hakkina gaba d'aya sannan". Ya k'arashe maganar cikin sigar wasa.
K'afarta ta zare daga cikin hannunsa ba tare da ta kallesa ba tace
"Kaga, nifa abincin ne ban dafa ba bare kayi tsammanin zan baka, kuma bani da wata hakkinka a kaina da kake fad'i, dan haka ka rabu dani bacci na keji". Ta k'arashe maganar tana mai mik'ewa a kan gado game da juya masa baya ta rufe idanunta tana mai jin maganar da tayi masa yayi mata wani irin d'aci a cikin zuciyarta.
Mamakinta tsantsa ya shiga cikin zuciyarsa, ganinta yake tamkar ba Humaira matarsa wacce ya sani ba, dan jin kalaman nata yay barkatai ba kan gado.
"Anya kuwa! Ko dai wani lefin nayi mata ban sani ba take shirin yanke min hukunci ta hanya mafi tsauri a gareni?". Yayi tambayar a cikin zuciyarsa yana mai ci gaba da kallonta.
Numfasawa yayi game da sauk'ar da numfashi a hankali sannan yace
"Humaira, dan Allah idan wasa kike da wannan kalaman naki to please ki daina, idan kuma wani abun aka yi miki ban sani ba ko nine nayi miki lefi ki sanar dani, amman bawai ki juya min baya kina fad'a min kalamai marasa dad'in ji a sanda nazo gareki ba".
"Dan girman Allah ka rabu dani nace! Bana son takura, abinci ne dai ban girka ba, sannan kuma a yanzu bani da wani abu a sunan lokacinka, fak'at, dan haka ga k'ofa nan zaka iya ficewa, ina da bukatar kasancewa ni kad'ai, ina tunin gidanka nema, kasan yanda tsarin komai yake da inda kitchen yake, kaga kenan zaka iya girkawa kanka wani abun, idan har fa yunwar ta matseka kenan".
Maganar take yi masa a sanda ta juyo da dubanta kan Kyakkyawar fuskarsa wanda ya sauya nau'i, sannan ta k'arashe maganar cikin d'aga sauti game da bud'e masa idanunta tana nuna masa tafukan hannunta wanda hakan yake nuna yanayinta da gaske take babu sirkin wasa a ciki.
Mamakinta ne shimfid'e k'arara a kan fuskarsa, idan da labari aka basa zai musa da hakan, sai kuma gashi da idonsa ya gani, sannan ya rasa meye haka ya canza ta kwatsam a lokaci d'aya, bayan shi bai tab'a saninta da wannan halin ba.
Tashi yayi daga bakin gadon ba tare da ya k'ara cewa da ita komai ba ya fice daga d'akin a yayin da ko wanne gab'a na gangar jikinsa yayi sanyin gaske yana mai k'ara jadda da yanayinta a cikin zuciyarsa, domin kuwa sam bai ji dad'in furicinta a garesa ba, sai dai kuma yana tunanin duk yanda aka yi a kwai wani abun da ke damunta yasa ta juya masa baya a yayin da ya zo gareta, dan ba irin haka ta tab'a yi masa ba a cikin zamantakewar auransu, hakan ya sanya zuciyarsa kokonto da kalar da ya ci karo da ita a yau.
Babu yanda ya iya da wannan rana wacce ta kasance masa sabuwar yanayin da ko mafarkin hakan bai tab'a yi ba bare har yayi tsammaninsa, a sanda zuciyarsa ta kasa gaskata yanayinta, yunwar da ke rarike masa can cikin cikinsa yasa ya kasa hak'uri da juriya ya shige kitchen d'inta kai tsaye wanda ya sha gyaran gaske, duk wani k'ura da yanar gizo da ya mamaye kitchen d'in duk ta gyare su ta goge ko ina ta sake masa sabuwar jere.
Indomie ya bincika ya samu ya dafa ya fito daga kitchen d'in, bayan ya kashe duk wutan gidan ya kulle k'ofofi sannan ya wuce zuwa d'akinsa dan zaman cin wannan indomie ya zama ya bawa cikinsa hakkita, sai dai kuma har a sannan zuciyarsa tana masa cikin wasi-wasi, da na sani yake a ransa da gidansu ya wuce yaci abinci inda har ya san haka zata kasance masa a yau.
Bayan da ya kammala da cin abincin ne sannan ya ture plate d'in gefe guda ya haura saman gado ya kwanta ya rufe idanunsa da niyyar yin bacci, a kan cewa gobe ya fitar da plate d'in idan gari ya waye.
Cikin k'asar zuciyarsa sam ba ta cikin walwala da annashuwa haka har ya wayi gari wajan k'arfe tara na safe ya shirya ya fice wajan aiki, ganin ko k'ofar d'aki bata lek'o ba bare yayi tsammanin samun karin safe daga gareta ko wani kulawar ta musamman.
Ko da ta tashi daga bacci wanka kawai tayi ta shirya cikin tsararran atumfa riga da siket d'inki yabi jikinta tamau yay mata kyau.
Bayan ta kammala gyare ko ina na gidan ta saka turaran wuta daddad'an k'amshi duk ya mamaye gidan ya had'u da sanyin A C sai yake fitar da ni'ima mai ratsa sashen jiki.
Bak'in shayi wanda ya sha kayan k'amshi da citta ta dafa ta wuce d'akinta dashi tana sha tana latsar wayarta dake rik'e a hannunta, sai dai kuma wayar take latsawa idanunta suna saman fuskar wayar, amman sam hankalinta yana wani waje daban a sanda zuciyarta take tunanin irin abunda tayi masa a jiya kad'ai sam hankalinta ya kasa kwanciya, domin kuwa tana k'aunarsa ji take ba zata iya ci gaba da aikata masa irin haka ba a yayin da ya zo gareta yana muradinta a cikin zuciyarsa.
Da rana misalin k'arfe sha biyu da rabi Batula tayi sallama ta shigo cikin d'akin kai tsaye a yayin da murmushin farin ciki yake bayyana a kan fuskarta.
Oyoyo Auntyna!". Cewar Batula bayan ta k'araso kusa da ita ta zauna tana mai k'ara fad'ad'a murmushinta.
Dariya Humaira tayi cikin nuna jin dad'i suka rungume juna sannan suka soma gaisuwar yaushe gamo.
Yi ni su ka yi suna hiransu cikin nishad'i da annashuwa, Humaira ta girko musu abinci lafiyayye suka ci, sai wajan karfe biyar na yamma sannan Batula tayi mata sallama ta koma gida, a cewarta bari ta bar ta zata yiwa yayanta girki dan ya kusa dawowa, jinta kawai take amman ita kad'ai tasan mai take gasa masa, dan kuwa ta d'auki alwashin rama irin juya mata baya da yayi a sanda take bibiyarsa tana buk'atar kulawarsa.
Ba shi ya dawo gidan ba sai bayan yayi sallar isha'i, tana zaune a kan d'aya daga cikin kujerun parloun tana kallon indian tashar Zee world ya same ta cikin wata sabuwar shiri wanda ya matuk'ar tafiya da hankalinsa, har ya soma mancewa da irin abunda tayi masa jiya, sai yake tunanin koma dai meye ne ta sauk'o a yanzu zai iya tunkaranta.
Yana murmushi ya k'arasa gareta a sanda zuciyarsa take kwad'ayin kasancewa da ita a halin yanda yake ciki.
Kusa da ita ya zauna yana mai k'ara fad'ad'a murmushisa a yayin da ya kai hannunsa yana shirin kamo nata hannun, sai dai kuma a mamakinsa ya ga tayi saurin tashi daga kan kujeran tayi hanyar d'akinta ba tare da ta bari ya kama hannunta ba.
Baki sake idanuwansa a kanta yana kallonta har ta b'acewa ganinsa ta shige cikin d'akinta, a sanda k'aran kulle k'ofar ya doki kunnuwansa.
Tagumi yayi yana raya abun a ransa, tamkar a gidan kallo yake ganin abun, sam hankalinsa ya kasa kwanciya da irin abunda ya ga tana yi masa.
Ya d'auki kusan tsawon mintuna zaune a wajan jikinsa yayi mugun sanyi, sannan ya mik'e ganin zamar ba haifar masa da komai zai yi ba face tunani, hakan yasa ya duba ko ta girka abinci amman sam bai ga komai ba, bai yi mamakin ganin hakan ba, sai dai ransa babu dad'i yauma, haka ya shige kitchen d'inta ya girko indomie sannan ya wuce zuwa d'akinsa, yana ci ne yana shiga cikinsa amman ba dan yana jin dad'insa ba.
Haka dai yauma a wannan daran ya kasance cikin tunanin da mamaki.
*HaneeSat*✍🏼📚📚📚
[30/08, 18:12] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT_M*
*Page*
*71*
Sadaukarwa ga qawata
*AISHA GENTLE LADY*
Sun d'auki kusan tsawon sati d'aya suna irin wannan zaman, wanda a lokacin ya gama tsorata da lamarinta, dan yayi iya bincikensa amman ya kasa gano komai game da ita, ya rasa gane me ya canzata haka.
Ganin duk hanyar da ya bi na ganin sun fuskanci juna toshe hanyar ta ke yi, ko ido bata bari ta yarda su had'a bare har ya kusanceta, hakan ya sanya shi yanke shawaran k'ara tukaranta, ko Allah zai sa ya dace, dan irin halin da ta ke nuna masa yana k'ara shigar da shi cikin mawiyancin halin da shi ba zai iya magancesa ba, dole sai ita.
Wajan misalin k'arfe goman dare, ya shigo gidan kai tsaye ya wuce zuwa d'akinsa yayi wanka ya tufata jikinsa da doguwar jallabiya fara, ya feshe ko ina na jikinsa da turaruka masu dad'in k'amshi, sannan ya fice daga d'akin ya nufi nata kai tsaye, a sanda zuciyarsa ta ke masa wasi-wasi na ba lallai yau ta amince masa ba.
Cikin sa'a ya samu k'ofar d'akin nata a bud'e ba ta sa makulli ta kulle sa ba kamar yanda ta saba kullewa da.
Kansa ya k'usa ciki ya shiga zuciyarsa tana d'ar-d'ar, dan tsoron kar yau ma ta gasa masa maganganun da zai masa mugun d'aci a ransa, wanda zai iya d'aukan tsawon lokaci bai mance da shi ba.
Kwance ya tarar da ita ta juya bayanta da alamun bacci ta ke, hakan yasa ya haura saman gadon ta bayanta ya kwanta daf da ita, a yayin da ya ke jin sauk'ar numfashinta k'asa-k'asa yana fita.
A hankali ya sanya hannunsa ta baya bisa k'ugunta ya zagayeta da shi, a sanda ya sak'ala kansa tsakanin wiyarta da kafad'arta yana mai sinsinar daddad'an k'amshin turarenta da ke dokar cikin hancinsa, wanda a ko da yaushe yake da murad'in kasancewa da ita cikin irin wannan k'amshin da sai a jikinta kad'ai ya ke ji.
Wasa ya soma aika mata cikin jin shauk'inta a cikin zuciyarsa, wanda duk irin wasannin da ya ke yi mata tana jinsa amman ta rufe idanunta ruf ta rabu da shi wanda shi a nasa zaton bacci ta ke bata san da ya shigo cikin d'akin ba.
Barinsa tayi yaci gaba da shafar ko wacce sashi na jikinta, har ya zamto da tana gyara kwanciyarta dan ya samu yanda yake so, duk da cewa itama tana jin tsananin kewarsa a ranta, amman babu ta yiwa zuciyarta alk'awarin sai ta d'an wahalar da shi ko da rabin wahalar da ya bata ne sannan ta amince da shi, amman dole sai ta d'aurewa zuciyarta, dan irin son sa da k'aunarsa da ta ke yasa zuciyarta yake karaya da irin halin da ta ke jifan sa da shi.
Ya shagala sosai ya kai mak'ura wajan wasan da yake da ita jikinta, wanda har hankalinsa ya soma gushewa daga jikinsa, ji ya ke ba zai iya hak'ura ba sai ya samu ya biya buk'atarsa sannan zai samu sauk'in sha'awarta da ke damunsa a zuciya.
Ganin idan ba dakatar da shi tayi daga abun da taga yana shirin aika mata ba zai iya karya mata zuciya ta amince da muradinsa har ya samu nasaran biyar buk'atarsa, wanda hakan kuma zai lalata mata shirinta a kansa, hakan yasa tayi saurin ture sa gefe guda ta raba shi da jikinta a sannan tayi baya tana sauk'ar da numfashi sama-sama ta sauk'a daga saman gadon ta tsaya da k'afafunta.
"Kaga! Ni fa wallahi bana son irin haka, wannan wani irin abu ne kawai ina kwance zaka zo ka haura min ba tare da amincewata ba, sai kace turo ka aka yi, to wallahi tallahi ka ji dai nayi maka rsantuwa, kar ka kuskura ka ce zaka kusanceni, ban baka wannan damar ba, sannan kuma bazan laminta da irin haka ba!".
Maganar ta ke yi masa cikin fad'a da nuna b'acin ranta a sanda ta ke nuna sa da yatsar hannunta, sannan ta k'arashe maganar cikin nuna isa da gadara, wanda zai tabbatar maka da cewa ba k'aramin takaici da haushi abun da yayi mata ya shigar da ita ba.
Mamakinta ya gama cika masa zuciya, wanda tun a sanda ta ture sa gefe bai iya ya motsa ba, domin halin da yake ciki bashi da wata kuzari tattare da shi, sauk'ar numfashinsa kawai ke ji yana tashi, cikin rashin k'arfi ya mik'e tsaye da kyar a hankali ya soma takowa zuwa inda ta ke, a yayin da ta ke matsawa da baya cikin zafin rai tana k'ara murtuke fuska ta ke juya masa kai alamun ka da ya kuskura ya k'araso gareta dan ba zai ji dad'insa ba.
Tsayawa yayi ba tare da ya k'arasa gareta ba ya ba da d'an tazara a tsakaninsu, a sannan ya d'aga hannunsa ya d'aura bisa k'irjinsa yana mai mata nunu da zuciyarsa ya soma bud'an bakinsa cikin wani irin yanayi na ban tausayi, alamun yana cikin tsaka da buk'atarta, sannan ya soma k'iran sunanta cikin dak'iyar murya idanunsa sun canza launi zuwa kalar ja yace
"Haba mana Humaira, meye nayi miki haka kike neman hanyar illatani?, bayan ban tab'a saninki da irin wannan d'abi'ar ba, ki sani cewa ni fa mijinki ne na sunnah, auranki na ke Humaira ba ba zaman banza na ke da ke ba, dan Allah ki a gaza ki tausayawa zuciyata, ki daina guje min domin bazan iya jure haka ba..."
Shiru yayi daga zancen da yake yana mai rufe idanunsa cikin wani irin a zababban yanayi ya k'ara bud'an bakinsa a karo na biyu a yayin da ya gama sauya kala ya k'arashe maganar da fad'in
"Dan Allah Humaira ki taimaka min, ki taimakawa zuciyarta, domin ta kasa gano lefin da ta yi miki kike a zaftar da shi haka ta wannan hanyar".
Takaici ne ya kamata a lokaci d'aya, tana kawar da kanta gefe guda ba tare da ta kai dubanta kan fuskarsa ba ta koma saman gado ta zauna a sanda murmushin takaici yake bayyana kansa a bisa fuskarta sannan ta bud'i baki tace
"Himmm! Abdulmalik kenan, dole ka ce haka, baka yi min komai ba na tozarta a rayuwa, dan haka kana da gaskiya ta wannan fannin, baka cancanti haka ba, sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, zan so in tunatar da kai abun da ka mance ko kayi fuska ka nuna ka mance da shi, ko ince a wajanka baka d'aukesa wani abun tozarta ba".
Ajiyar zuciya ta sauk'ar a hankali tana mai runtse idanunta sannan ta bud'e su tana mai jin wani irin k'una can k'asar zuciyarta, wanda dalilin hakan shi ne tunawa da irin kalamansa a kanta, a sanda ta ke basa hak'uri kan cewa ba ita ta yi lefin da yake zarginta da shi ba, sai dai yayi watsi da lamuranta yana gasa mata d'acin maganar da ba zata tab'a mancewa da su a cikin ranta ba.
"Abdulmalik!".
Ya ji ta k'ira sunansa cikin iriyar murya wanda yayi sanadiyar sa shi d'ago da idanunsa ya d'aurasu a kan nata yana mai kallon cikin kwayar idanunta a sanda tsananin damuwa ya ke dad'a fad'ad'a a kan fuskarsa.
"Kasan cewa na shiga mawiyancin hali a sanadiyarka, na sinci kaina cikin muguwar halin da ya so min illah a cikin zuciyata, ni mai k'aunarka ce Abdulmalik, duk wiya duk runtsi zan iya kasancewa da kai, tsab'anin kai da ba zaka iya kasancewa da ni ba a cikin ko wanne halin da zan sinci kaina ko aka jefe ni ba, domin tun a zamana da kai na baya na gama gano hakan.
"Cikina da ke jikina wanda Allah yayi min kyautarsa, shi aka zubar min aka raba ni da shi, sannan aka min sharri da cewa ni ne na zubar da gangan dan ina son komawa makaranta zai iya takura min, ina yawan yin girki tun a gidanmu, ba'a tab'a samun matsala ba sai da ka auroni na shigo cikin gidanka, nayi iya k'ok'arina na ganin ka fahimceni amman abun ya faskara, duk yanda zanyi in kula da abincina ina yi, sai dai masu iya magana sun ce, mugu bashi da gama, sai in rasa wanda yake min wannan d'anyar aikin, a sanda kai kuma ka kasa fahimta ta, idan kayi min uziri yau gobe ba zaka yi min ba, sai dai ka furta min munanar kalamai masu d'acin gaske, wanda su ke sosa min zuciyata tana min k'una..."
Numfasawa tayi a sanda ta sauk'ar da ajiyar zuciya tana mai tuno da abubuwan da suka faru a cikin ranta, a sannan taci gaba da cewa
"Wasu kalamanka a kaina da suka fi k'ona min zuciyata shine, a lokacin da ka shigo da abokanka cikin gidan nan dan cin abinci, sai aka samu tsab'ani, haka ka rufe idanuwanka ka ka yi min fad'a son ranka sannan ka zazzaga min kalamai munana marasa dad'in ji a gareni, wanda yay mugun k'ona min zuciya, na san ba zan iya mancewa da wad'an nan abubuwan ba, domin har ila yau ina jin su a can k'asar zuciyata".
K'arashe maganar tayi a hankali cikin k'asa da murya a yayin da ta ke sauk'ar da kanta k'asa, hawayen da ke cike a cikin kwayar idonta ya soma gangarowa kan kuncinta.
Kansa ya dafe da tafukan hannunsa a sanda ya runtse idanunsa sai ya ji duk wata gab'a ta jikinsa ya sake yayi muguwar sanyi, dan maganganunta yasa shi tunowa da irin abubuwan da yayi mata a baya, wanda idan ba tsantsan hak'uri bane da kai ba zaka iya d'aukarsu ba, sai dai ku kwasa tare.
Kasa furta komai yayi sannan ya kasa dosan inda ta ke, haka ya ja k'afarsa jikinsa a sanyaye ya juya ya fice a d'akin, a sanda zuciyarsa ta kasance cikin damuwa, sam ya kasa jin dad'insa, sai ya ke ji tana masa wani irin zafin da shi kansa ba zai iya d'auka ba, domin kuwa a hak'ik'anin gaskiya shi da kansa ya san cewa bai kyauta mata ba, haka zalika bai yi ma soyayyar da ke tsakaninsu adalci ba.
Ganin ya fice daga d'akin bai iya cewa komai ba, hakan yasa ta mik'e tsaye ta isa bak'in k'ofar d'akin ta tura ta kulle shi da makulli sannan ta dawo gado ta kwanta game da rufe idanunta, cikin zuciyarta tana rok'on Allah da ya yafe mata wahalar da ta ke bawa mijinta, a yayin da jikinta ita ma yayi mugun sanyi, yin hakan ta ke amman ba dan ranta yana so ba.
Ko da ya baro b'angaranta na shi d'akin ya nufa, kai tsaye ya wuce band'aki ya k'ara wasa ruwa a jikinsa tare da yin wankan janaba, a sannan ya fito ya sake sabon shiri, har zuwa lokacin baya jin dad'in jikinsa, haka ya haura gado ya kwanta amman ba dan yana tunanin bacci zai iya d'aukarsa ba, sai dai kuma da baccin ya d'aukesa da a sannan ne zai samu sauk'i a cikin zuciyarsa kafin gari ya waye.
Sai da ya kai tsakiyar dare idanunsa biyu yana tunanin yanda aka yi abubuwa suka kwab'e masa, bayan yayi nafila da addu'oi sosai ya dawo gado ya kwanta, sannan bacci mai cike da damuwa ta d'aukesa ba tare da ya sani ba.
A washe garin ranar da yamma bayan sallar la'asar misalin k'arfe biyar da 'yan d'ori, yana zaune ne bisa kujerar da ke tanade cikin office d'insa, ya zabga tagumi ji ya ke abun duniya ta ishesa, domin irin damuwar da ke k'unshe cikin k'asar zuciyarsa tana nema tayi masa illa.
K'ofar office d'in Haisam ya turo game da k'uso kansa ciki ya shiga a sanda murmushi ke bayyana saman fuskarsa, sai dai kuma a take wannan murmushin nasa ya gushe sakamakon ganin halin da abokinsa ke ciki, yanayinsa ya matuk'ar sauyawa, ba kamar yanda ya san shi a baya ba.
"Yane abokina kana lafiya kuwa na ganka haka?".
Haisam yayi masa tambayar bayan ya zauna kan kujerar da ke kallon nasa.
Ji yayi ya masa shiru ya kasa amsa masa tambayar da yayi masa, sai ma yayi tamkar bai san da mutum ya shigo cikin office d'in ba, lura da hakan ya sanya Haisam k'ara tambayarsa a karo na biyu yace
"Abdulmalik da kai na ke magana fa kayi min shiru, meke damunka ne!? Alamunka ya bayyana cewa akwai wata matsala, meke faruwa ne?"
Ya k'arashe maganar a yayin da ya ke duban cikin idanunsa yana k'arewa yanayinsa kallo.
"Na tafka babban kuskure a cikin rayuwata, nayi irin abunda mai cikekken hankali bazai yi irinsa ba, a sanda na ke yi ban san ina hankalina ya gushe ba, gashi yanzu ina fuskantar matsala, na shiga halin da na shigar da ita a baya".
Maganar yake yi ba tare da ya motsa ko ya k'afta idanunsa ba, a yayin da tsananin damuwa da tashin hankali ya gama bayyana akan fuskarsa, bayan ya sauk'ar da nauyayar ajiyar zuciya yana mai numfasawa sannan ya k'ara cewa...
*HaneeSat*✍🏻📚📚📚
[30/08, 18:12] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT_M*
*Page*
*72*
Sadaukarwa ga k'awata
*AISHA GENTLE LADY*
_KAINA AK'ASA MASOYANA, AGAFARCINI TSAWON LOKACIN DANA D'AUKA, AYIMIN UZIRI MATSALA AKA SAMU, SAI KUMA YA HAD'U DA ZUWAN AZUMI, AMMAN YANZU KAM NA DAWO BABU JA DA BAYA, YANZU HAKA NA KAMMALA LITTAFIN, POSTING KAWAI YARAGE MIN, KENAN KULLUM ZAKUNA GANIN POSTING D'INA, NAGODE ASHA KARATU LAFIYA_
"Humaira wahalar dani ta k...". Ba tare da ya k'arasa maganar da ya soma ba, Haisam yayi saurin rufe masa baki yana girgiza kai, alaman kada ya ce haka.
"Abdulmalik". Ya k'ira sunansa cike da sassauta murya bayan ya d'auke hannunsa da ke kan bakinshi, sannan ya ce "Ina so ka sanar dani abunda ke faruwa tsakaninka da Humaira, dan insan abin yi, bawai ka sani a gaba kana min wasu irin zaututtukar da ba ganewa zanyi ba, bare har in samo maka mafita".
Kai ya d'an sauk'ar k'asa a hankali yana shafar fuskarshi da tafukan hannunsa, sannan ya soma fad'a masa duk irin abubuwan da ya shiga tsakaninsa da ita, tun a sanda suke cin abinci Marak'ishiya ta turo masa sak'on zubewar cikin Humaira, har zuwa yanzu da ya ke cikin mawiyancin hali, wanda ba kowa ya shigarsa ba face Humaira.
Yasan cewa a zaman takewarsu shi da ita bai kyauta mata ba sam, ya juya mata baya a ya yinda take tsananin buk'atar goyon bayansa, amman yayi watsi da lamuranta, sai yanzu ya ke nadamar abinda yayi mata, wanda hakan kuma sam ba lefinta bane.
Numfashi Haisam ya busar ta bakinsa game da sauk'ar da ajiyar zuciya, a sanda ya ke jinjina al'amarin a cikin ransa, dan kuwa ya mutuk'ar d'aure masa kai, ya kuma shigar dashi cikin tsananin mamaki.
"To naji duk abubuwan da ka fad'a min, fad'ana a nan shine, a gaskiya kana da babban lefi a cikin wannan lamarin, ka shigar da rayuwar yarinyar mutane cikin hatsari babba, wanda da ba dan kariyar Allah ba da rayuwarta ya salwanta".
"Dan haka a yanzu bani da abin fad'a illa in baka wata shawara d'aya, wacce ina tunanin za'a dace, tunda tana tsananin sonka, dan na gano cewa kawai tana maka hakane dan kaima ka d'and'ana irin wahalar da ta sha a baya, amman ba wai tana yi dan bata sonka ba".
Jinjina kai yayi cike da tunani iri-iri cikin ransa, tabbas maganar da Haisam yayi hakane, domin kuwa shi karan kansa yana da tabbacin cewa Humaira mai tsananin k'aunarsa ce a koda yaushe, duk wata irin wahalar da zata ba shi sai dai ta yisa cikin dalili, wanda shi sam baiyi tunanin haka ba, sai yanzu da Haisam yayi wannan maganar sannan tunaninsa ya je.
"Wato ba, kana da gaskiya Haisam, maganarka hakk'un, sai yanzu na fahimci hakan, dan haka ina sauraranka, ka bani shawarar da kace zaka bani, fatan Allah yasa ta amince daga yau, ta daina wahalar dani haka ya isa, domin kuwa ba k'aramin bak'ar wahala nake sha ba wajan rashinta".
D'an k'aramar dariya Haisam yayi wanda hakan ya sanya Abdulmalik had'e fuskarsa yana jifarshi da wani irin kallo ta sigar wasa.
"Au dariya ma kake min ko?". Ya fad'a cike da k'ara had'e rai.
"Ba komai ba lefinka bane, lefina ne da nake fad'a maka ko wacce irin matsalata idan ta taso min".
Wata dariyar ce ta tsark'ewa Haisam, sai da yayi mai isarsa sannan ya tsagaita yana mai kad'a kansa yace,
"Inbanda abinka Abokina, idan baka sanar dani matsalarka ba waye zaka sanarwa? Amman dai mu bar wannan maganar in baka shawararka in koma gida, dan dama ba zama ne ya kawoni ba".
Himmm kawai ya fad'a a cikin ransa, a sanda ya mai da hankalinsa waje d'aya dan ya saurari maganar Haisam d'in da kyau, domin ba yaso ya samu matsala.
D'an kusa da kunnenshi Haisam ya matsar da bakinsa, bayan ya mik'e daga na shi kujerar zuwa nasa.
Rad'a masa a kunnensa yayi sannan ya d'ago da kansa yana fad'in,
"Ka jarraba da wannan, idan Allah ya nufa an dace to".
"Insha Allah za'a dace Abokina nagode ka gaida gida, sai munyi waya". Ya fad'a yana mai jinjinawa a cikin ransa.
Kai kawai Haisam ya gyada masa sannan ya fice daga cikin office d'in, ya bar Abdulmalik shi d'aya yana tunanin yanda abun zai kasance, fatansa d'aya Allah yasa ta saurareshi, kada yayi wahalar banza.
**
Da daddare misalin k'arfe goma na dare.
Tsaye take cikin kitchen gaban gas tana had'a shayi da samosa, sanadiyar cikinta da ta ji yana k'ullewa alamun yunwa, yasa ta shigo kitchen d'in babu shiri, dan rabuwanta da abinci tun na safe da ta ci indomie, sai bak'in shayi da ta wuni tana sha sai kace buzuwa.
Bayan ta kammmala ne ta kashe wutan kitchen d'in game da kulle k'ofar sannan ta shigo falo zata wuce zuwa d'akinta.
'K'aran fad'iwar wani abu ta ji alamun glass ya doki cikin kunnenta, wanda yasa ta d'an firgita kad'an, ba shiri ta juyar da kanta tana kallon k'ofar d'akin da ta tabbatar da cewa a ciki wannan k'aran ya fito.
Kamar kar ta je ta ga me ya fashe, har ta kama hanya zata wuce d'akinta, sai zuciyarta ya raya mata cewa, gwara ta je taga meye ne tunda tasan baya gidan, kada wani abun ne ya faru.
A hankali ta sanya hannunta jikin k'ofar d'akin da niyyar turawa ta bud'e, bayan ta ajiye abunda ke hannunta a falo, sai dai ga mamakinta sai ta jisa a bud'e, duk da dai dama bawai yana kullewa bane idan zai fita, amman yanzu wayan ta iskar da k'ofar, ko dan akwai labule ne ya rufe k'ofar d'akin yasa bata gane a bud'e yake ba.
Kutsa kanta ciki tayi ba tare da tunanin komai a cikin ranta ba, bakinta d'auke da sallama wanda ta furtasa a hankali tana waige-waigen cikin d'akin da kanta dan neman k'aran abunda ta ji ya fad'i ya fashe.
Karo ta ci da shi kwance a tsakiyar d'akin shane-shane cikin kwanciyar rigingine, idanunsa a runtse kansa na kallon sama, a ya yinda ya kame cikinsa da hannunsa na hagu yana jujjuyawa cikin tsananin a zaba, gefensa na hannun dama fasheshshen glass ne a watse kan jini.
Turus ta yi ta tsaya ta kasa motsawa daga inda take, illa rawa da jikinta ya d'auka tana mai mamakin ganinsa cikin wannan mummunar halin, yaushe ma ya shigo cikin gidan?Tambayar da take yiwa zuciyarta kenan, domin a nata zaton sam bai dawo cikin gidan ba, dan ba jin motsin shigowarsa tayi ba.
Zura masa idanu ta yi tamkar yau ta soma sanya shi cikin idanunta, dan kuwa ganinsa hakan ya matuk'ar d'aure mata kai. "To meye ya faru da shi haka?". Ta fad'a a cikin ranta.
Ganin yana matuk'ar buk'atar taimako yasa ta isa zuwa garesa, a hankali tasa hannayenta duk biyu ta tallafo da kansa tana fad'in,
"Meye ya faru da kai haka Abdulmalik? Meke damunka dan Allah? Ina da tabbacin cewa lafiyarka k'alau ka fita ka bar gidan nan, amman yanzu a ce ka dawo cikin wannan halin! Ohho ya Rabb".
Maganar take yi cikin iriyar murya, wanda zai nuna maka damuwa ta gama rufe mata fuskanta, sannan ta k'arashe tana mai runtse idanuwanta cikin jin zafi a zuciyarta, domin ganinsa cikin wannan halin ya sanya duk ilahirin jikinta yin sanyi.
Tari ne sosai ya hard'e masa wiya, ya shiga yinsa yana mai tamk'e kan zuciyarsa da d'ayan hannunshi na hagu.
Tashin hankali ne sosai ya bazama kan fuskanta, ganin irin tarin da yake yi yana rik'e kan zuciyarsa, hakan yasa tayi saurin tashi jiki na rawa ta d'auko masa ruwa ta kai zuwa k'asa da k'afafunta, sannan ta soma basa ruwan cikin nutsuwa.
Kad'an ya iya shan ruwan yana mai kallonta ta k'asar idanunsa, yanda tabi ta kid'ime a kansa ya sanya shi murmusawa a cikin zuciyarsa, dan kuwa hakan ya k'ara tabbatar masa da k'aunarta a garesa.
Tallafa masa tayi ya mik'e zaune ta jinginar da shi a jikin gado, cikin sauri ta samo kayan da zata gyara masa jikinsa.
Haka yana jinta ta goge masa hannunsa wanda ke d'igar da jini, bayan ta kammmala gyara masa hannun ta tallafa masa ya hau gado ta kwantar da shi a kan filo, sannan ta zauna a gefensa tana mai kallonsa cikin wani irin yanayi na tausayawa.
"Me ka keso ka ci in dafo maka dan ka samu ka sha magani?". Ta tambayesa cikin raunanniyar murya.
Kai ya girgiza mata ba tare da ya bud'i bakinsa ba, sai dai hakan ya nuna mata ba yason komai.
Sanin idan zata ci gaba da tambayarsa mai zai ci zai iya mata taurin kai, hakan yasa ba ta k'ara cewa da shi k'ala ba ta mik'e tsaye ta bar d'akin.
Kitchen ta nufa ta dafo masa indomie da k'wai ta dawo d'akin, bayan ta kashe wutan kitchen d'in gameda kulle k'ofar.
Yana kwance ta tarar shi inda ta bar shi bai motsa ba, a hankali cikin nutsuwa ta zauna kusa da shi bayan ta d'an d'aga masa kansa yanda zai iya cin abincin ba tare da ya k'warar da shi ba, sannan ta soma basa kad'an-kad'an yana ci dakyar, sai kace mai cin magani.
Bayan ta kammmala ba sa abincin ya ci ya rag'e kad'an, ta ba shi ruwa ya sha kafin ta mai da plate d'in kitchen ta dawo da tsintsiya da tsumma ta gyara wajan da glass d'in ya fashe, tana gama gyara wajan ta dawo ta zauna a bakin gadon daf da shi.
Idanunta na kansa tana kallon cikin k'wayar idanunsa da ya kafeta dasu, cikin tausassiyar murya ta soma magana tace,
"Meye yake damunka Abdulmalik? Ka fad'a min dan insan wanne irin magani zan samo maka, tunda ka samu ka ci abinci".
"Ke ce rashin lafiyata, ke ce damuwar dake cin cikin zuciyata, haka zalika ke ce wacce maganin da zan sha ke wajanta, in samu lafiya a lokaci d'aya".
*Sheriff*📚📚📚
[30/08, 18:12] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT_M*
*Page*
*73*
Sadaukarwa ga k'awata
*AISHA GENTLE LADY*
A hankali yake maganar cikin wata iriyar murya, wacce tayi shige da na marasa lafiya.
Cike da mamaki ta kalli cikin k'wayar idanunsa a karo na biyu, ta saki baki ta kasa fad'in komai.
"Baki yarda cewa haka bane ko?".Muryansa ya tsinkayota. "Humaira, ke ce silar rashin lafiyata, haka zalika maganin da zan sha in samu waraka yana tattare da ke. Dan Allah ki tausaya min matata, ki bani in sha ko zan samu waraka a cikin zuciyata wacce take min tsananin rad'ad'i a kan rashinki, dan Allah ba dan ni ba".
Maganar ya k'arashe yana mai k'ara k'ask'antar da muryansa.
"Ta yaya za'a ce nice silar rashin lafiyarka Abdulmalik? Meye nayi maka wanda zai sanya ka rashin lafiya?". Ta fad'a a sanda idanunta ke kallon nasa har zuwa lokacin bata k'efta ba.
"Nasan na yi miki lefi, sosai na yi miki babban lefi Humaira, sai dai kuma na gane kuskurena wallahi, na nemi gafararki ki yafe min, amman kina ta wahalar min da zuciyata Humaira".
"Dama a kan hakane ka kwanta rashin lafiyar k'arya? Nufinka zan yafe maka duk abinda ka min, to tun wuri ka cire wannan mafarkin da kake a cikin ranka, dan ba mai tabbatuwa bane".
Tayi maganar cikin d'aga sauti, bayan ta mik'e tana shirin barin d'akin.
Hannunta ya kamo cikin na shi lausassar hannun, ya bud'i bakinsa da niyyar k'ara yin magana, ya ji ta fizge hannunta cikin zafin nama ta soma barin d'akin.
Tana daf da ficewa ta ji tari ya sark'esa, yi yake yi babu kakkautawa. Cikin tashin hankali ta koma garesa tana rirrik'esa game da tambayarsa.
"Meye kuma haka Abdulmalik! Mutuwa zaka yi? Dan Allah ka daina irin wannan tarin yana d'aga min hankalina.
Cikin rud'ewa teke masa tambayar, ganin yanda tarin ya sha k'arfinsa.
"Wallahi har indai a kaina ne komai ya wuce, na yafe maka, ba zan kuma juya maka baya ba, na yafe komai daga yanzu muci gaba da zamanmu, mu gina rayuwarmu cikin inganci da rik'on amana, amman dan Allah kada ka mutu yanzu Abdulmalik, ban gaji da zama da kai ba, ina k'aunarka har cikin zuciyata, daman ina yi maka hakane dan kaima ka ji abinda nima na ji a baya, amman tunda hakane wallahi na ajiye k'udirina a kanka, na yafe har cikin zuciyata".
Maganar ta k'arashe a sanda muryanta yake k'ara raunanewa, tana mai ci gaba da girgizasa, tashin hankali k'arara ya kammmala rufe mata fuska, wanda a lokacin ya ji wani irin tsananin farin ciki marar misaltuwa ya mayaye cikin zuciyarsa, rabuwansa da wannan farin cikin tun rabuwarsa da ita.
"Da gaske kike wannan maganar Humaira ba mafarki nake ba! Kin yafe min har cikin zuciyarki kamar yanda na ji bakinki ya furta?". Ya yi maganar cikin wata irin murya, wanda zai tabbatar maka da cewa ba k'aramin farin ciki bane ya mayaye zuciyarsa.
"Da gaske nake na yafe maka mijina, ba mafarki kake ba a zahiri ne". Ta fad'a cikin murmusawa tana mai kad'a masa kanta.
"A hankali ta taimaka masa ya mik'e zaune, idanuwansu na kallon na juna cikin tsantsan farin ciki.
"Please zan iya yin wanka ko zan ji dad'in jikina?". Yayi mata tambayar yana mai shagwab'ar da muryansa.
"Tambayana ma kake yi ko zaka iya yin wanka! To ba zaka yi ba shi ke nan?". Ta fad'a tana d'an bud'e masa idanunta.
"Ayi hak'uri a barni na yi wankan yanzu gimbiyata, tuba nake ba zan kuma ba, ko muje ki yi min da kanki ne matar?". Ya yi maganar cikin sigar wasa, yana mai kashe mata idanuwansa wanda suke kan nata ya k'asa d'aukewa.
"Himm, ni kam ba dani ba gad'a a kotu, ka je ka yi wakanka kawai ina nan ina jiranka".
"Haka za'ayi ko matar?". Ya fad'a yana sakar mata da murmushi.
Kai kawai ta girgiza masa ba tare da tace k'ala ba.
"To ki taimaka min mana zuwa band'akin, dan kar jiri ya d'ibeni in fad'i ya barki da asara".
Kallonsa ta yi tana murmusawa ta taimaka masa zuwa band'akin, yana binta da wani irin kallo na nuna tsantsan kewarsa a gareta, ya shiga band'akin dan yin wankan.
Kafin ya fito daga wanka taje ta kulle k'ofar d'akinta, sannan ta d'auko shayinta da samosa wanda ta ajiye a falo.
Bai d'auki tsawon lokaci ba ya fito daga band'akin, d'aure da babban towel a kunkuminsa, sai wani k'arami dake d'auke a hannunsa yana tsane sauran na jikinsa wanda ke d'iga, tana can bisa gado tana zaman jiransa, ganinsa cikin wannan yanayin ya sanyata sauk'ar da idanunta k'asa.
Lausassar murmushi ya sakar mata, yana mai jinta a cikin ransa, bata d'ago ta k'ara kallonsa ba har ya kammmala shirin, k'amshin turarensa da take ji yana dokar hancinta, duk ya gama mamaye cikin d'akin.
"Matar na kammmala shirin, meye aka kawo min mai dad'i?". Ya fad'a bayan yayi mazauni a kusa da ita, yana mai sakar mata da lausassar murmushi, mai cike da tsantsan k'auna da soyayya.
"Shayi ne da samosa idan zaka ci". Ta ba shi amsa a sanda itama take sakar masa da nata murmushin k'aunar, mai cike da kewarsa.
"Kin cika min cikina da indomie, ba zan iya k'ara cin wani abu ba, amman gaskiya zan sha wannan shayin, domin ba k'aramin kewarsa nayi ba, rabona da shi tun a sanda kika d'auki k'afa kika bar gidan nan, kinga ai nayi k'ok'ari sosai ba kad'an ba, ko Matar?".
"Hakane, amman da yanzu ka bar wannan surutun naka ka samu magani ka sha". Ta ce da shi, a ya yinda ta tsiyaya masa shayin a cup ta mik'a masa, ita kuma ta soma cin samosanta.
"Na samu lafiya ai yanzu, daman tari ne ya rik'e min mak'ogorona, amman ya daina baya ciyo, kada ki damu". Ba tace da shi k'ala ba, suka soma gudanar da hirarsu ta soyayya cikin annashuwa, haka har suka kammmala ta matsar da kayan gefe, kafin ta haura gado ta kwanta shima ya kwanta a bayanta game da rungumota tsam a jikinsa.
A hankali yake bin ko ina na jikinta yana shafawa, tana jinsa amman ba ta yi gigin hanasa ba, dan kuwa tasan yayi kewar rashinta ba kad'an ba, jin yanda yake mata sunbatu yasa ta juyo da kanta zuwa gareshi, da taimakonta ya samu damar gamsuwa da ita sosai yaji dad'inta, tamkar sabuwar amarya wacce aka kawo masa ita yau, haka ya jita a wannan daran.
Ba su koma sun kwanta ba, sai da suka shiga band'aki suka gabatar da wankan janaba, sannan suka dawo sukayi kwanciyarsu manne da juna, cikin shauk'in so da tsantsan k'auna.
*****
Washe gari da misalin k'arfe sha biyu, kasancewar rana ce ta asabar, ba shi da zuwa office, yasa ba su tashi da wuri ba, bayan sun yi karin safe yasa ta shirya suka fita zuwa gidansu Umma.
Suna cikin tafiya a motar, ta jiyo da tubanta garesa, sannan tace "Wai da gaske ne ka auri Suwaiba?".
"Eh". Ya ba ta amsa a takaici, sunan Suwaiban da ta kama, sai yayi sanadiyar tuno masa baya, kama da zaman da suka yi, tsanarta da ya soma mancewa yaji ya taso masa a rai.
"Aiyya amman ya ban ganta a gidan ba?".
"Ba zaki ganta ba, dan tana gida, amman yau ma nake da niyyar mik'a mata takardarta, dan ba iya zama da ita zan yi ba, sam yarinyar ba ta cikin tsarina, gashi ma duba ki gani". Ya mik'a mata wata farar fefa, tasa hannu ta karb'a.
"Ohho ya Rabb!". Ta furta a hankali game da dafe kanta.
"Haba mana mijina, kada kace zaka yanke wannan d'anyar hukuncin, aure fa sunnah ce ta Manzo, ba fa abin wasa bane".
"To ya kike so in yi, ni dai ace sonta kam sam bana yi, ko kad'an babu a cikin zuciyata, kinga akan ace na barta da aurena a kanta, ba tare da na zauna da ita ba, kinga ai yafi in sawwak'e mata, in zauna lafiya itama Allah ya ba ta wani mijin wanda yake sonta, ko ya kika gani?". Ya tambayeta yana mai ci gaba da tuk'in motar.
"Hakane kana da gaskiya, sai dai kuma ai ita tana sonka, kuma tana k'aunar zama da kai, ka yi duba da hakan".
"Ki bar maganar ni kam ta isheni, yafi ki kawo mana wani hira mai dad'i, wanda zai sanyaya mana zuciya, amman ba irin wannan ba, dan shi kam bak'anta min rai yake". Ya yi maganar ba tare da ya dubeta ba.
Dariya kad'an ta yi a cikin ranta tace "ka yi ta yi ai, ni dai ka taimaka kada ka saki yarinyar mutane, dan ba dad'i ne da shi ba sam, akwai cin zuciya sosai".
"Kin ce wani abu ne Matar?". Ya tambayeta yana kallonta. Amsa ta ba shi da a-a, lokacin sun iso gidan an bud'e musu gate ya shiga da motar.
Zuciyarta ne ta ji ya soma bugu, tunawa da wacece Umma da ta yi, da irin tsanar da take nuna mata. "Ohho ya Rabbi taimakeni!" Ta furta a can k'asan ranta, damuwa na bayyana kansa bisa fuskanta.
"Ya naga canji akan fuskarki Matar? Dan Allah ki bar damuwa, ki cire komai a zuciyarki, babu abinda Umma zata miki". Kanta kawai ta iya girgiza masa, ba tace komai ba ta bud'e k'ofar ta fita, fita shima ya yi bayan ya rufe motar suka nufi b'angaran Abba.
"Yana kishingid'e suka tadda shi, Batula na zaune a gefensa, sallamarsu yasa Batula d'ago da kanta.
"Lahhh Aunty Humaira oyoyo, ke nake gani haka!?" Ta fad'a bayan ta rungumeta.
"Ni ce, ya kike ya Makaranta?". Lafiya lau wallahi sai hamdala. Suna murmushi suka k'arasa wajan Abba suka gaishesa, suna cikin hira gwanin ban sha'awa, sai ga shigowar Umma da Siyama.
Ganin wanda idanunsu ya gane musu, hakan ya sanya fuskokinsu had'ewa tamkar hadari, dakyar cikin k'asaita Umma ta amsa gaisuwar Humaira, wannan ma dan Abba na wajan ne, da ko kallo bata isheta ba.
Basu wani jima a gidan ba, ganin yanda ta takuru dayawa, ta kasa sakewa, hakan yasa ya d'auketa suka bar gidan. Ba su suka koma gida ba, sai da ya biya da ita gidan k'aninsa Najeeb, bayan sun tashi ya wuce da ita suka siya shawarma da ice-cream, a lokacin har magariba ta yi.
Bayan sun dawo gida sunyi sallah, sannan suka watsa ruwa game da sabon shiri na kayan bacci...
*SHERIF*📚📚📚📚
[30/08, 18:12] Ameena Group Aysha Kn: 🥀🥀🥀 *RAYUWAR AURENA*🥀🥀🥀
*NA*
*HAFSAT_M*
*Page*
*74*
Sadaukarwa ga k'awata
*AISHA GENTLE LADY*
A falo suka yada zango, inda TV keta faman aikinsa shi kad'ai, a lokacin ana neman k'arfe taran dare. Yana zaune bisa doguwar kujera, tayi matashi da cinyarsa, ko wan-nansu yana cikin shirinsa na kayan bacci, hannunsa dake kan gashinta yana shafawa a hankali.
"Matar, ni kam yaushe za'a d'an min dakon babynah ne?". Cikin sigar zolaya ya yi mata tambayar, bayan ya d'auki wayarsa yana latsawa.
"Himm! Me kake ci nabaka na zuba? Ai Kada ka damu indai wannan zancen ne, ko gobe ma zan iy d'auka, ai ba abu mai bak'ar wahala bane".
"Haba! Da gaske?".
"Da gaske mana, tunda nice zan bawa kaina". Ta mayar masa da amsar tambayansa, game da jefa masa harara ta sigar wasa.
"Ya dai kamata ki hanzarta, dan gaskiya ina k'aunar ganin yarona".
"Ai fa! Kai kam ka bar damuwa, kawai zuwa gobe kasa tsammani, zaka ji..." Ta kashe masa idanunta d'aya, had'e da d'age gashin saman giranta.
"To shi ke nan, Allah yasa hakan, duk da dai nasan kina fa fad'a min ne cikin sigar wasa, domin ban mance da bayanin Doctor Ibrahim ba, na cewa mahaifarki ta samu matsala, haifuwa yanzu dakyar ne, sai in kuma wani ikon Allah".
Maganar tasa tayi matuk'ar sosa mata rai, amman gudun jan wata magana yasa ta basar, kasancewar tasan silar faruwar hakan, ba zata musa masa ba, dan ba k'aramin rauni suka ji mata a ciki ba.
"Yoo kuma kasan da wannan zancen amman kake irin tambayar nan?" Ta fad'a tana mai kallonsa. "Eh, amman ai Allah yana amfani ne da abinda ke aiki a cikin zukatarmu, so kinga ko gobe kamar yanda kika ce, ko hala yau ma, zaki iya d'auka".
"To na ji, yanzu dai a bar zancen, ni bacci ma nake ji, sai da safe". Ta k'arashe maganar a ya yinda take mik'ewa tsaye.
Tashi ya yi shima yace baccin zaiyi, su shiga su kwanta, bayan su kashe komai na falon, sannan suka wuce d'akinsu na bacci.
Washe gari da safe, suna zaune a dining table suna karin kumullo cikin raha.
Shi ne ya soma gama cin abincin sannan ita, kafin ta kwashe wajan ya wuce d'akinsa ya yi shirin fita.
"Fita zaka yi ne?". Ta tambayesa. "Eh wallahi akwai wani abunda zanje inyi a office ne, amman ba zan jima ba zan dawo, dan kinsan yau Lahadi rana ce ta hutu".
"Hakane kam ranka shi dad'e a dawo cikin k'oshin lafiya".
"Amen-Amen ya Rabb". Ya amsa mata yana mai shirin ficewa, yana daf da bakin k'ofar falon da zai sada shi da haraban gidan, ya dawo da baya zuwa gareta, a hankali taga yasa hannunsa bisa kan idonta na gefen dama, ya wangale shi yana duba cikinsa, ba tace da shi k'ala ba ya kai hannunsa kan d'ayan idon, shima ya wangale yana duba cikinsa, sannan ya dawo kan tafukan hannunta yana dubawa, kai ta kad'a cike da mamakinsa tace
"Haba! Meye shi haka kake ta min dube-dube a jikina? Sai kace wani sabon likita".
"Dubawa nake inga ko yau kin d'auki cikin, ko hakan da na yi nada lefi?".
"A-a babu, ba ka da lefi Doctor Abdool, tunda ce maka akayi ina d'auke da ciki".
"Shi ke nan, wannan sunan da kika sa min ta yi". Ya fad'a yana dariya.
"Dan Allah ka tafi haka-nan, ya isa wannan was..." Ba ta iya ta k'arashe maganar ba, ta ji wani irin hajijiya ya d'ibeta, kad'an ta fad'i k'asa yayi gaggawar cafketa, cikin damuwa ya shiga jijjigata yana tambayarta meke damunta, ganin ta gagara basa amsa, hakan yasa ya fita da ita harabar gidan ya shigarta cikin Mota, sannan ya dawo d'aki ya d'auka mata hijabi ya kulle k'ofar falon, kafin ya dawo Motar ya sameta tana sauk'ar da numfashi.
Ba tare da b'ata lokaci ba ya figi Motar suka d'auki hanya sai Asibiti, a nan ya samu aka duba ta da sauran gwaje-gwaje, aka tabbatar masa da cewa ciki ne da ita.
Iya mamaki ya yi da jin wannan babban kyautar da Allah ya ba shi, domin sanin samun cikinta yanzu zai yi wahala, sai dai kuma tunawa da ikon Allah da ya yi, sai ya murmusa a cikin zuciyarsa yana mai jin tsananin farin ciki da annashuwa.
Haka dai yake ta nuna mata kulawa da abinda ke cikinta, komai take so zaiyi mata, ko da Batula ta zo wajan Humaira, da jin labari ta kwasa ta kaiwa su Umma, sun ji dad'in labarin sosai, ba k'aramin murna da tsananin farin ciki bane ya ziyarci sukatansu, domin a yanzu kam Umma zuciyarta yayi sanyi a kan k'udirinta na tsanar Humaira, sanadiyar hakan kuwa shine, batun cikin da ta ji yasa ta aje duk wasu mak'amanta, sanda ya sanarwa Haisam, murna ba kad'an ba ya tayasa.
******** ******
A kwana a tashi babu wiya wajan Allah, yau an wayi gari Humaira ta tashi da matsanancin ciwon ciki, nak'uda ne ya afko mata a lokaci d'aya, babu b'ata lokaci Abdulmalik ya d'auketa sai Asibiti, tare da Batula kusa da ita, kasancewar su biyun nan basa barinta suyi nisa, shi ya kwantarwa da Mummynta ma hankali, na cewa kada su sanya damuwa a ransu tana samun kulawa sosai, fiye da yanda basa zato, dan Umma ma yanzu ta karb'eta a matsayin suruka, tana yawan zuwa taga lafiyarta.
Cikin ikon Allah ta haifo yaronta santalele, wanda ya d'auki kaman-nin babansa, masha Allah da shi, son koya k'in wanda ya rasa.
Haka suka dawo gida cikin murna da farin ciki, a nan aka soma sanarwa 'yan uwa da abokan arziki, inda Mummy dasu Fadila da wasu cikin 'yan uwanta duk sun zo.
Ranar suna yaro yaci sunan kakansa, mahaifin Babansa, suna aka yi nagani na fad'a, gidan nan ya cika makil da mutane, sai ci ake ana sha gwanin ban sha'awa.
Bayan suna su Mummy suka dawo da ita gida Abuja, dan yin wankan arba'in.
***
Marak'ishiya! Marak'ishiya!! Marak'ishiya!!!" Mahaifiyarta dake girki a kitchen ita keta faman k'iranta, jin shirun yayi yawa tun d'azu take kwala mata k'ira amman tak'i fitowa, hakan yasa ta shigo har cikin falon ta sameta zaune ta zabga uban tagumi, idanunta na tsiyayar da waye, wanda sukayi shige da na nadama.
"Wai ke yanzu dan iskancin banza na damunki, kina jina ina kwala miki k'ira amman kika min kunnen uwar shegu, kalan sabon rashin kunya ko!? To bari kiji in gaya miki, wannan kukan da kike yi kece da kanki kika jawowa kanki, ba wani ba, wai ke idan an tuhumeki kice kishi ne, kishi ko hauka, kin biyewa k'awaye na yanzu sun zuga ki kin aikata abunda ko kasheki za'a yi ba zaki aikata ba, sai kuma gashi kece kika tashi da asara, dan haka ni taso ki min aikin da na sakaki, kukanki ba abunda ya shafeni bane".
Cikin zafin rai da takaici take mata fad'an, a ya yinda ta zauna a zancenta ta juya ta bar falon, kukan k'unci mai k'ona zuciya ya kamata, ita kanta tasan tana son mijinta, tana matuk'ar k'aunarsa, amman tashi d'aya akan kishi da biyewa shawarar k'awa, yaje ya shigar da ita wannan halin, ya rabata da abar k'aunarta.
Sallamar Shiwari shi ya dawo da ita, daga duniyar tunanin da ta jefa kanta.
"Me kuma ya kawoki gidanmu?". Ta yi mata tambayar a takaice, cikin had'e fuska.
"Haba k'awata! Dan wannan abun ya faru shine kike neman hanyar raba k'awancen dake tsakaninmu? Kada ki mance fa, dalilinki nima aurena ya rabu, ba ke kad'ai bace, bai kamata kina had'a fishinki harda ni ba, kamata yayi mu zauna mu sasanta, musan ta yanda zamu tafi da rayuwarmu".
"Bari kawai Shiwari ba zaki gane ba, ina cikin tsananin damuwa, raina a b'ace yake, yanzu haka labari naji wai har ta dawo gidan, bama wannan bane abun tashin hankalin, waifa har ta samu ciki ta haifu, duk irin ciwon da muka ji mata".
Ya salam!". Ta furta cikin nuna damuwarta da jin wannan labarin.
"To k'awata kuma shine kika yi zaune sai kace shegiya! Ba zaki tashi tsaye ba, ai ko hak'uri kyaje ki ba shi ko zai yarda ki koma gidansa, tunda ba saki uku ya yi miki ba, har yanzu akwai aure a tsakaninku".
"Hakane Shiwari, nima shawarar da na yanke a raina kenan, sai dai kuma naji baya ma gari yana Abuja, shima ya bita can, kuma da alama sai ta kammmala arba'in d'inta zasu dawo, zan bari kawai sai in sun dawo d'in".
"To shi ke nan Allah ya kaimu lokacin". Shiwari tace haka, daga nan suka shiga hirarsu ta duniya, da irin abubuwan dake cikinta.
******** *********
Humaira ta kammmala arba'in d'inta cikin k'oshin lafiya, a lokacin kuma yasa an k'arasa gina masa gidansa na Abuja, duk wasu abubuwan da zata buk'ata, da wasu kayanta na Katsina, duk ya dawo mata dasu nan, a nan ta tare da ita da Yaronta, suna aiwatar da rayuwarsu ta hanyar da ta dace, kullum Marak'ishiya tana hanyar gidansa na Katsina, amman cikin rashin sa'a bata samunsa, har ta gashi ta yanke hukuncin k'iransa a waya, ko zai saurareta, amman kuma da sabon number, dan tasan ba d'aukar numberta zai yi ba.
Da daddare misalin k'arfe tara, suna zaune a falo bisa doguwar kujera, Abdulmalik na rik'e da babynsa a hannu yana masa wasa, Humaira kuma ta d'an yi matashi da kafad'arsa, fuskanta d'auke da murmushin jin dad'i, wayarsa ce ta soma ruri, yasa hannunsa ya d'auka, sai yaga bak'uwar number, har ya ajiye ba zai d'aga ba, amman Humaira tasa shi ya d'aga, acewarta ko waninsa ke nemansa.
"Sallama aka yi masa ta cikin wayar ya amsa cikin d'ari-d'ari da murya, dan kuwa ya gano ko muryan wacece, jin magiyan da ta soma mi shi tana basa hak'uri akan abunda ya faru, hakan yasa ransa b'aciwa, cikin takaici da ya d'aga muryansa yace
"Kinga! Daga yau sai yau, kada ki kuskura ki sake k'iran wayana, idan ba haka ba kuma, duk abunda na yi miki kece kika jawa kanki, da kinsan kina son zaman auran amman kika aikata abunda ko mahaukaci ba zai yi ba, iskancin banza kawai!".
Ya katse wayar ransa a b'ace, game da jan 'yar k'aramar tsaki.
"Kai da waye ne haka kake ta fad'a?". Ta tambayesa tana mai d'ago da kanta, wanda ke jikin kafad'arsa.
"Waye in banda wannan mahaukaciyar Marak'ishiya!".
"Aiyya, dan Allah kada ka d'aga hankalinka a kanta, daman nima ina ganin da yana da kyau ka dawo da Suwaiba d'akinta, a hankali komai zai dai-dai ta, insha Allah, tunda tana k'aunarka".
"Kinga fa na hanaki kawo min hiran wad'an-nan mutanan, amman bakya ji, ko kin mance na tafi mata da takardarta kwanaki? To na bawa Umma ta bata, dan ba zan iya d'aurawa kaina abunda ba zan iya ba".
"To shi ke nan mijina, Allah ya hucar min da zuciyarka, insha Allah na daina daga yanzu".
"Yauwa ko ke fa Matata, ai rayuwata yanzu na mu biyu ne, babu wata a ciki, Ya fad'a tare da rungumota a jikinsa, ya matseta sosai da ita da babynsa, gameda kai musu kiss a goshi, suna dariyar farin ciki itama ta kai masa kiss kan saman leb'en bakinsa, ya sakar mata da lausassar murmushi mai cike da tsantsan so da k'auna.
*TAMMMAT BIHAMDU LIllAH*
A nan na kawo k'arshen littafina, abunda nayi ba dai-dai Allah ya yafe min. Sai kunji ni a littafina na gaba, wanda zai zo muku da abubuwa daban-daban, nagode masoyana, ina gaishe daku baki d'aya.
Body
Name
No comment!!