Raina Kama!

Written by Noorieyyaah NoorPublished on 2018-12-14 23:51:45Category RomanceRaina kama.... Inji hausawa sukace Kaga gayyah,kirkirarren labari ne akan wani kyakkyawan saurayi mai suna Sulyman Galadanci,yakasance mutum manemin mata, amma a boye,a haka ne ya hadu da wata yarinya mai suna Amatullah Ruma wacce ta kasance ita din bebiya ce,shigowarta cikin rayuwarsa shine babban kalubale da yataba fuskanta cikin duniyar sa,hakan na nufi da canjin rayuwa da ya wanzu gareshi, kubiyo ni domin jin me ke kunshe da tasu tafiyar. tags: #Danasani, #Tausayi #Qaddara #Rayuwa #Soyayyah #Hakuri #Nooriyyah #hausanovelDuba was labarai »

RAINA KAMA...! 


By Noorieyyaah 


Kamar kullum zaune yake bisa three sitter(kujera mai cin mutum uku) din dake madaidaicinmadaidaicin falon ,duk da kasancewar falon bawani megirma bane hakan bazai hana a gane kyawu da tsaruwan falon ba,wanda komi yake a tsare kuma a tsabtace.


Sulyman dake xaune a gurin shikadai sai kuma abokiyar hirarshi dake hannunshi(wayar salula) dayake ta daddanawa da 'dan 'karfi hakan xaisa daka kalli fuskarshi xaka hango zallan jin haushi da 'kosawa a tattare da ita,ya daddage sai tsaki yake zabgawa hadi da kaiwa wayar harara jifa jifa,daga dukkan alamu wani abin yake expecting daga abokiyar taashi(waya).


Wani 'dan sauti neh mai sanyi na country music ke tashi daga cikin wayar me qirar samsung galaxyS7 edge,a 'dan qagauce yai picking call din gamida mikewa tsaye,


"Hello hajia laraba wai meye hakane kika bi kika shanya ni don kinga ina binki koh"? yafada a dan hasale. 


Daga dayan bangaren wacce aka kira da laraba ta saki wata daria irinta jiga jigan en barikin nan

Kana tace


"Hoo shegen sama,watoh duk kabi karude daga jin nace maka ansama maka er hannu kalar ka koh"


Hakan besaka ya daina harararta ba tamkar tana gabanshi,"eh nidai naji don Allah hajia kidena jamin rai,kinsan fa anfi sati rabon da asamo mun kalar tawa,kuma sanin kanki ne bazan iya harka da tsoffin hannu ba koda kuwa ayau wani yabareta a leda" 


Ya ida maganar hadi da furzar da iskar dake bakinshi alamun ranshi yafara expire ('bachi). 


Haj laraba tai shewa a karo nabiyu gamida "cewa kai kujimin dan dunia,! ni wallahi suleman iyayinka yafara isata gamida gundirata,


Tasaki tsaki sai kuma taciga ba" ace wai don tsabar iyayi mutum zaiyi iskancin sa,amman kuma don qarin feleqe da samun guri irin naka kaliqe kai kullum sai budurwa wacce bata taba sanin namji ba,haba ai wallahi kachi sa'ah ta neh don bani da yanda xanyi dakai,duk da kuwa nasan kana sane da wahalan da ake sha kafin asama maka virgins din,wallahi badon dalah dakake sakar munba kai dinnan baka isa kadinga wahalar da tsohuwar rayuwata ba"


Ta ida gamida tsaki da ajiyar zuciya wanda ke nuni da alamun tafa bala'in gajia da wannan hali na wannan dan tahaliki.


Sulaiman dinne dai ya'dan sassauta daga nashi jn haushin ha'di da cewa "haba ta wajena,bansanki da yawan complain ba,although nasan akwai gajia a wannan harka,tunda gskia nasan samun favorites dina is not an easy task,but hajajju yazakiy dani,hakuri xakiciga dayi ke kinsan da xan iya maleji da saura wallahi dana kwatanta,but wallahi bani iya nafison sabuwa dal a leda,wacce dole taimun kuka da bori,atimes ma harda suma ayayin danake bareta a ledarta,kinfi kowa sanin abinda ke sani nishadi kenan,haba hajajju me idon cin nera"yaqarasa maganar yana daria. 


Hajia laraba ta amshe gamida cewa "wallahi galadanchi bantaba ganin tsohon dan iska irinka ba,tasaki daria akaro nafarko,kai dinnan banajin in alhaki yatashi kamaka zaka wanye lahia. 


Da hanzari yakatseta," nidai don Allah kidenamun baki,sai kace wanda yasa kai gabas yake yanke yanken kawuna,dan virginity din dabe taka kara yakarya ba da ake dan taimaka musu ana hutashshe da mazaje should incase insun tashi neman hanya?" Mtsw yai tsaki ni wallahi kamata yayima azo adinga godemini,wannan aiki danake yi a bagas ba godi bare nagode" 


Ya 'karasa maganar yana daria irin tasu ta qwararrrun en dunia,sai kuma yadora toh yanxu dai ya ake ciki?Kinsan i have been longing for this for almost a week now,ai nagasu wallahi ya ida maganR hadi da dan marairaicewa.


H.Laraba tace shine dalilin kiran nawa dama sai kuma xakaimun iyayin naka da rashin hakuri daka saba,yanxu dai kashiga xuwa anjima kamar after asr prayer xuwa five haka,ajiyar ka na nan ta isa tana jiranka. 


Amman sai dai wani hanzari ba gudu ba wannan dinfa bebiya ce don bata magana,but tanaji... 


Yai saurin katseta "haba ba komi as long as za ta danyi irin ihunsu na kurame intaji maza wannan ba damuwata bace,kindai tabbatar new blood dince koh? 


Haba kaji ka kaima ta amshe,kanatacigaba" kaima kasan sai ina da confirmation ma nake fara tuntubar ka"


Yasaki wani malalacin murmushi hadi da cewa yWwa godia nake hajjaju,without you bansan yaxan dinga coping ba,kisaurareni yanxu xakiji alert na tukuicin aikin ki..Ya ida maganar yana lassan labbanshi. 


Tace to no qualms galadanchi,ina nan ina baza ido,nasan baka karya alqawari ta ida maganar tana dan dariar jin dadi. 


Atake sukai sallama tana qara jaddadamishi dayazo dai five din yatafi da er bebiyanshi, Sukai daria baki daya hadi da kashe wayoyin nasu.


Sakin ajiyar xuciya yayi hadi da shafo baqar sumar daya hade da kyakyawan sajen nashi mai qara qawata fuskar tashi maabociyar kwarjini da kamala,duk da bazaa sakoshi cikin jerin farare irin tas dinnan ba,bt kalarshi kalace me haske kuma hasken ma irin me kyau dinnan kaman irin na latin americans dinnan. 


Idanunshi ke matuqar qara mishi kyau,duk da kuwa su din ba manya bane ba sam,don xaifi kyau asanya su cikin sahun qanana,koma muce mitsimitsi irin na chanisawa da japanisawa din nan,duk da kuwa dama tsabar lumshesun dayakeyi ma bazaisa ka tantance hakan ba. 


Labbanshi kam tubarkalla masu kalan duhuwa neh kamar me shan sigari,kodayake bakama bane tunda yakan dan xuqa in yanajin tsiyar,goshinsa ko daka kalleshi kodaga nesa kake dole kahango qaton tabon sallan dayaiwa goshin nasa bake bake,hakan xaisa kaqara darajashi akaro nafarko dazaka fara dora ido akanshi,kakuma mutuntashi hadi dasakashi a jerin maza nagari koda kuwa baka shirya yin hakan ba. 


Yana da wannan advantage din akan duk wanda ya kalleshi,kwarai dagaske akwai cikar xati da kamala,hakan kuma yanaqara nasaba ne dakasancewarsa mutum dogo sosai amman ba zaaqaal ba,irin tsayin nan da dakaga mutum xaka hango tsayinshi,gakuma dan jiki dayake dashi,duk da bamu isa mukirashi da lukuti ba,but xamu iya kiranshi da irin huge dinnan. 


Tubarkallah akwai sura mai kyau kam,sabida shikanshi baya wasa da yawan motsa jiki,shiyasa tashin farko inka kalli structure dinshi xaka iya danganta shi da wannan jurumi na qasar hindi watoh john Abraham, dadin dadawa shi din ma'abocin sanyan kaftans ne a kodayashe,don inkaganshi da qananan kaya ta kattabaatar ba nisa zaiyi ba,sabida haka hakan naqara mishi qima da daraja a idon dimbin jama'ar dasuka sanshi dama wadanda basu sanshi ba sai a lokacin. 


Waneh mutum yakirashi da fasiqi mabiyin mata,ai qaryar mutum,duk kuwa dacewa shi din mutum ne mai kirki da yawan faraah ga dukkan wanda yasani nagida dana waje,amma raba kanka dashi indai ke hallitar nan ce MACE kuma ma more especially ace kinshyga hannunshi, Wayyo sunanki sorry. 


Sulyman Bello Galadanchi kenan,tuxurun saurayi mai kimanin shekaru talatin da biyar a duniya dayaqi yai aure,duk kuwa da cewa qannensa biyu dake bayanshi sundade dayin hakan,harda en cute yaransu abinsu.


Anyi mitar har angaji anxura mishi na mujia,don koh ita mahaifiyar tashi hajia binta dasuke kira da gwaggo tariga ta ta'allaka wa ranta cewa shi din beh lfya neh,shiyasa batai qasa a guiwa ba triqa amso mishi magungunan hausa wai don duk dai asamu yawarke koshima taga 'kwanshi kafin lokacinta yayi. 


Gogan naku sai dai yayi dariya a cikin xuciyarshi hadi da cewa da kunsan yanda nake punishing yaran mutane dabaku damu kanku daniba.


Shi din yakasanche architect neh,hakan yasa mostly he is self employed,kawai in akatashi sai dai abashi contract yai aikinshi,inmukai duba da tarin kudin mahaifin nasu Alh.Bello Galadanchi,kobasu nema ba akwai aqasa garesu har ma da jikokin su masu xuwa,bt still kowa agidan yanada career dinshi bawanda yasakankance da kudin mahaifin nasu. 


Duk kuwa da cewa ba yawa neh dasu ba,yayarshi daya Dr Batula,tana aure anan garin kano da 'ya' yanta hudu,sai shi din sulyman,sai qannensa buhari wanda yake shi engineer neh na civil,yayi aure da matarsa da dansu guda daya,sai auta muhammad bello amman suna kiranshi da muhammad din xallah,shikam lawyer neh,shima recently yai aure,matar har tana da juna biyu.


***

Noorieyyaah


2

 RAINA KAMA...! 


By Noorieyyaah


  04:45pm


Hudu da minti arba'in da biyar,yayi daidai da tsayawar motar sulyman a gaban gidan haj.Laraba,Wayanshi yafidda dga aljihunshi gamida da danna mata kira,na isa ina waje shine abinda yace a wayar,okay toh bari inshigo yafurta bayan yakatse wayar.


Da irin takunshi na 'kasaita yashiga get din madaidaicin gidan na haj.Laraba, direct wani corridor yabi wanda xai sada shi da falon gidan,bisa dukkan alamu yasan ko ina na gidan,falon bakowa,sai qarar t.V dake tashi,hakan yasa yasami daya dga kujerun dasuka qawata falon yazauna. 


Zamanshi keda wuya,aka turo daya daga cikin 'kofofin dake manne da falon aka shigo,macece' yar kimanin shekaru hamsin,amma inba anfada makaba sai ka 'karyata hakan,duba da gayu da hutu dasuka boye shekarun nata,tana da jiki da dantsayi,ba laifi tana da kyau daidai nata,wanda hasken fatarta yatemaka wajen' kara fiddo da kyan nata.


Da fara'ar ta taqarasa xama hadi da cewa,hoo galadanchi baka ko missing time,watoh harka bazamo koh,yasaki murmushi shi mai kara mishi kyau,hadi da cewa,kema kinsan ni din bana wasa bane,i don't play with the things i want!

Tace ni shaida ce kuwa,kai din ai bana wasa bane,taqarasa maganar da dariya,toh yanxu ya ake ciki?Kinsan da zafi xafi akan daki dutse,inaso nan da 5:30 yazamana muna gida nida madam din,,,yadage gira sama yana murmushi,

Daman yanxu nake shirin kiranta,ta ida naganar gamida kara wayanta a kunne,hello rabi,kitaho mun da yarinyar nan falon baqi,eh tachanxa kaya,tadan saurara,ohk toh kiy sauri ku qaraso,ta aje wayan gamida ce mishi afuwan gata nan fitowa,kasan bebiya ce saida lallashi.Yadan gyada kai akamun hakane,bt deep inside him ynajin yanda xaiyi coping da yarinyar,anyway nasan yanda xanyi handling nata,ya ida maganar a xuciyarshi

Turo qofan palour din da akai yayi dai dai da shigowar rabi mai aikin h.Laraba tare da wata budurwar yarinya a bayanta,wacce daga dukkan alamu bazata wuce 16-17 years ba,

Tunda suka shygo palorn yaqura mata ido,ajiyar xuciya yai gamida furta wow acikin xuciyarshi,"masha Allah she's the correct epitome of beauty"yaqara gyara xaman farin gilashin fuskarsa yana qare mata kallo.

Guri tasamu kusa da hajia laraba taxauna tana dan xaxxare idanuwa,daga dukkan alamu batasan me ke faruwaba.

Muryar h.laraba tadawo dashi dga mayataccen kallon dayakebin yarinyar dashi,yawwa toh sulyman ga amatullah nan,don Allah abi mani ita ahankali,tasake cewa basai nace ka kula da itaba nasan duk xakayi,

daga mata kai kurum yake kamar qadangare,gabadaya yarinyar tatafi da imaninshi..he just can't wait to be with her,lumshe ido yayi hadi da sakin ajiyar xuciya ahankali,haj.laraba tai dariya don duk tana lura da yanayin dayashyga tun shigowar su amatullah din,

Itakam wacce ake mganar don ita batasan ma sunayiba,binsu kawai take da kallo,especially sulyman din datake ganin wannan wani irin mayene dazai cinyeta da idanu,harara ta kaikace tasakar masa...dariya yai gamidacewa u r free to do whatever you want now sweetheart, but next time you won't b able to.

Miqewa yayi gamida cewa toh ngde hajia,sai kinji ni,i hope kayanta sun isa cikin motor din,tace mishi eh sun isa nasa rabi takai,sannan kar ka manta fa,sati daya kawai xatai kamaido mun ita,yace nasan da haka wannan ba matsala bane,

toh ama tashi kuwuce,nan fa ake daga,wacce akewa maganar ma yitai kamar batasan da ita akeba,kitashi kibishi nace haj.laraba tasake furtawa da dan tsawa,ahap ko gezau batai ba,kuma tanajinsu sarai,magana ce dai batayi.

Kallon juna sukai ita dashi, yace come on sweetheart let's go okay...harara takuma sakar mishi,wannan karon harda tukuicin murguda baki gamida maqe kafada,alamunfa ita ba inda xata.bataga dalilin dazaisa ace tabi wannan mutumin ba mai kama da maye,dadin dadawa kuma ita batasnshi ba,don mi anty laraba xatace tabishi,taqara xunbura baki gaba tana babbata rai.


Amatullah xan sabar miki fa,ya ina miki magana kinyi biris dani,kuma nasan sarai kinajina,ko sai nakira maki Haj.talatu neh xaki tashi,aibata qarasa rufe baki ba tai wuf tamiqe hadi da saurin girgiza kai alamun ah ah,gakuma idanuwanta dasukai raurau alamun son yin kuka,

H.laraba takamo mata hannu hadi da cigaba da lallashinta,karki damu kinji ama,wannan dakike gani yayanki neh,zaki saba dashi yanada kirki,ba irin adnan bane,shi baya duka sam,kiyi duk abinda yasaki kinji?ta ida maganar gamida shafa kanta alamun lallashi.

Kallon qasa qasa yake binta dashi,axuciyarshi kuma yana qissima irin dagar da zaiyi da yarinyar,bisa dukkan alamu zata bashi tough time.


3


RAINA KAMA


By Noorieyyaah 


What exactly is wrong with you Amatullah? ya furta kalmar da alamun bacin rai,zai iya tuna tun tahowarsu take faman zabga kuka,har isowansu gidan,gaba daya tagama rikitashi yarasa yanda zai yi da ita.

  Cikin sigar lallashi yaciga da lallabata tayi wanka sai sufita taci abincin kamar ynda yake tunanin cewa yunwah ce ke sanyata rigima,ko kallon inda yake taqiyi inbanda turo baki da ajiyar xuciya ba abinda take,

  Yagama iyayinshi duk tagama gano wayonsu shida da hajia,ita xa ai wa wayo?yama za ai anty laraba takawo ta wajen mutumin da bata sani ba,kuma wai har sati xatai tare dashi,lallaima!

  Tunanin datake yakatse hadi da tsandara ihu sakamakon ji datai andauketa anyi sama da ita,ihu take tana bugunshi da iya qarfinta akan ya ajeta qasa,bata taba jin takaicin rashin yin maganarta kaman yau ba,da wallahi yau irin kwandunan ashariyar daxata sauke wa mutumin nan sai yasha mamakinta.

 Direct bathroom dinshi dake manne da dakin barcin shi yanufa da ita,batai auneba kawai tatsinceta cikin ruwa tsamo tsamo,inbanda karkarwa ba abinda jikinta yake,jin yasauketa yasa taqara gyara xamanta cikin bath din,gamida dora qafa daya kan daya,kana tacigaba da hararshi cikin alamun masifa.

  Dariya ma take bashi,yanda qaramar yarinya kamar wannan ta iya masifa haka duk kuwa da cewa bada baki takeyibq,reactions dinta kadai ke isar da yanayin datake ciki.

  Yace nabaki five mins kiy wanka kifito,if not kinji narantse xanshygo inmiki,da saurinta ta gwalo ido hadi da girgiza kai,gakuma tukuicin harara dayake tasha,"dan iska kawai" tafurta hakan axuciyar ta,Allah dai yai wadaran dan iska,jibeshi don Allah kaman mutumin arziki,tacigaba dayi mishi kallon up and down bayan yajuya yafita.

  Da farko taqiyin wanka saida taga ba sarki sai Allah,sai ta daure tamaxa tayi wanka,tsaye take da towel tana tunanin yanda xatayi,domin kuwa kayanta dama already sunjiqe,tsaye tayi a tsakiyar bayin tana xare ido.

jin shirun nata yai yawana yasa yashgo bathroom din,dasauri tazuqunna hadi da runtse idanuwanta,kana tacigaba da girgixa kai alamun batason haka yafita,

    Tsaye yayi yana qarewa surarta kallo,ya Allah yafurta can qasan maqoshin shi,hadi dajin wani irin yanayi yana lullubeshi,i have to own her...i just have to!yafurta can qasan maqoshin shi,gashinta dake reto a tsakiyar bayanta yashafa,da sauri tadago kanta da alamun masifa,baiyi auneba yaji tadoke hannunshi hadi da miqewa tsaye.

Ta nuno shi da danyatsa tana wani mini mini da ido,dariya yasaki,kana yace amatullah Allah ne yarage wa aya zaqinta yasa baki magana,i wonder how your voice will sound like,nasan da zatai dadi kamar yanda kike da kyau,now come on let's go and have something to eat i'm already starving.

        ************************

   i know the chapter is short...but i hope you guys would manage with this!

   I promise a long chappy next time☺

Pls do vote and comment,that will surely be an encouragement to me.😊


4


RAINA KAMA


By Noorieyyaah 


Zaune take a kan daya daga cikin kujerun dasuka qawata madaidaicin palorn sulyman din,dawowar su kenan dga wurin cin abinci,wanda saida yasha fama kafin tayarda ma tabishi.

  Gaba daya yarinyar nabashi tough time,he wasn't expecting this kind drama daga yarinyar ba,don shi atunaninshi ma bazatai wuyar sha'ani ba sabida qarancin shekarunta,idan yayi la'akari da dimbin matan dayai mu'amala dasu abaya.

   Amman daga dukkan alamu xaa sami matsala da wannan,matsalan kuwa shine ya tabbata bazata bashi hadin kai ba,and rashin bada hadin kan nata neh zai zame maasa matsala babba,coz shi bai iya forcing yarinya a irin harkar nan,he never rape any one,duk iskancinsa sai da yarda yarinya,koda bakiso dga farko,xaiyi qoqari yasan yadda ya lallabaki har kibada kai bori ya hau.

  Moreover inyatuna sha'ani da bebaye yasan sai andaure,idan yai la'akari da irin kafiyar yarinyar yasan sai yayi dagasken gaske,coz babu abinda ya isa yahanashi kasancewa da ita,she's everything he's dying to have now.

   Wani irin xafine ya ratsa hannunshi,hakanne kuma yayi sanadin dawowarshi daga tunanin da ya lula,da alamun mamaki yake kallonta sakamakon tsayen datai mishi aka tana zumburo baki gaba,da hannu yamata alamun da menene?.Hannu tafara nunawa akan tafin hannunta tana nuna alamun rubutu,paper takeso da biro ya fahimceta.

  Mi kuma xatai da paper?Okay zomuje inbaki,yakamo hannunta suka nufi bedroom din nasa,fusge hannunta tayi da alamun jin haushi a fuskarta,itafa batason abinda mutumin nan yake mata,duk dacewa tana ganin dan girmanshi,girgiza kanshi yayi yana fadin jikin ki xai gaya miki yarinya.

   Rubutu yaga tanayi akan memo din daya bata,bayan tagamane ta miqa mishi.

  "pls take me home,i don't like staying here"

Ido yatsura mata yanason tattaro kalaman dasuka dace yafada mata.

   Why do you want to go home,bakison xama dani neh?ni ba mugu bane.Yafurta mata kalaman nashi yana qoqarin shafa sumar kanta,dasauri takuma fizgar memo din tayi rubutu,

"this is one of the reason dayasa nake son nakoma gida,nifa ba er iska bace,karka kuma tabani gaskia".

  Dariya taqwace mishi bayan yaga abinda tarubuta,nikuma dan iskanne,kuma yanxu xangwada miki iskancin nawa,nalura sainayi miki gwari gwari tukunna,oya tashi kichanxa kaya infara gwada miki halin nawa na en iska.

    Gani yai tasaka mishi kuka da iya qarfinta,tanayi tana irun shishidewar nan kaman mai shirin somewa,

Dafe kanshi yayi yanajin kukan nata naratsa jikinshi,tun asalinshi bayason kuka,kodaga wa

nne jinsi neh kuwa,,yazaiyi da yarinyar nanne?Yadafe kanshi yanajin tuquqi a zuciyar shi.

  Okay tell me what do you want?Tadago da fuskarta datai shabe shabe da hawaye da majina,kana tai rubutu acikin memo din,"nidai kamaidani gida,gidanmu a katsina nake nufi,banason komawa gidan aunty talatu"

Idan namaidaki chan shikenan?Dasauri tadaga kanta,

Toh nikuma yazakiyi dani,coz i can't live without you.Harara tasakar mishi ganin yana shirin raina mata hankali,meye hadinta dashi dazaice he can't live without her.

"Nidai kadena mun haka kawai kazo kamaidani gidanmu,Abban mu yace bakyau xama guri daya da namijin daba muharraminka ba".

Dariya yaqarayi akaro nabiyu bayan yakaranta abinda tarubuta.Yarinayar nabashi daria,okay toh yanxu yaza ayi baby na?Kiyi hkri kixauna dani,i promise you xanbaki dukkan kulawan daya dace,kitai maki yayanki kinji.

Maqe kafadanta tayi kana tacigaba da girgixa kanta alamun itafa bata yarda ba,yau gida kawai takeso.

Ganin wankin hula naneman kaishi dare yasa yamike ya ciccibeta yadorata bisa gado,take kuwa tafara xunduma ihu da iya qarfinta,hakan yabata damar yin bige bige kamar sabon kamun hauka.

 Rungemata yayi a jikin shi da sauri,yakan yasashi sakin wata bahaguwar ajiyar zuciya,gaba daya ya qanqameta yahanata motsi,hakan yabashi damar tattaro natsuwarshi gurin lallashinta.

 Calm down baby ba abinda xanmiki,bacci kawai xamuyi okay,yacigaba da lallabata jin tayi lamo tana ajiyar xuciya,

Dagowa tayi tana kallonshi don son qara tabbatar da xancen nashi na ba abinda xai mata,tsura mata ido yayi yana mata wani irin kallo,i promise ba abinda xanmiki trust me pls.Shiru tayi tanason yadda da zancen nashi.

Now let's sleep,i promise i won't hurt you kinji babyna.Tadaga kanta alamun amincewa,beyi kama da wanda yake qarya ba.

Gyara mata kwanciya yayi shima yakwanta bayan yakashe switch din dakin,duhu ya maye gurbi.

Kiyi addua kinji,good night my fragile.

       ********************


So how about this chappy?Galadanchi couldn't make it this night fa😂 despite d fact that he promised to have her by all means😂

And our stubborn amatullah is trying to prove him

wrong...

Pls your votes and comment will be appreciated!❤


5


RAINA KAMA


By Noorieyyaah


5:00 daidai alarm yayi sanadiyar tayartayar dashi daga wahalallen baccin dayasamu yakwashe shi daqyar,wanda har alokacin mamakin kanshi yake yadda ya iya hakurin qyale yarinyar,a kaf tarihin rayuwarshi wannan neh karo nafarko daya iya hakura da abinda yake tsananin muradi da bege,wanda hakan yaqara tsananta neh sakamakon kwana biyu dayayi batare da kasancewa tareda mace ba,ahar kullum yana mamakin kansa yadda yakasa tsayawa yayi aure amman ya tattare ya ta'allake a bin matan banxa,wanda a zahiri da badini yariga yasan abinda yake aikatawa din ba abu bane mai kyau,haka zalika yasan ba hanya bace mai

billewa,amman yazaiyi shikanshi bason wannan halin nasa yakeba,duk kuwa dacewa ba wanda yasan bannar dayake yi akaf xuri'ar shi,idan kacire abokinshi Kamal badaru(kb),wanda ba yanda bayayi da abokin nashi akan yadena wannan banxar halayyar tasa yayi aure,amman yaqi sai dai yabishi da toh kawai.Shikanshi yasan yana buqatar repentance idan yai la'akari da salon nashi iskancin yakere nakowa,Eh mana yakere nakowa mana,raba 'ya mace da budurcinta ai baqaramin abu bane.

   Ajiyar xuciya yayi gamida miqewa domin tafiya masjid domin gabatar da sallar asubahi,hakannan yacigaba dayiwa kanshi fatan shiriya axuciyarshi kamar kullum.

   Tana kwance chan qarshen gadon,tabi ta duqunqune jikinta hadi da takurewa guri guda,bayan yazagaye tawajen kanta neh yai qoqarin tadata domin tagabatar da tata sallar,daga mashi kai tayi alamun toh.Shikuma yawuce da dansauri yashiga bathroom domin gabatar da alwala.


         **************

Shigowarshi gidan daga masallaci yayi daidai da fara ringing din wayarshi, "Hajiyar mu" shine sunan daya bayyana a screen din wayan,da hanxari yai picking yana tunanin meyafaru da gwaggon tasu ke kiranshi da farar safiyan nan,bayan yasan kullum shike fara kiranta kafin yaje chan gidan nasu yagaishe su. 

  Sannunku gwaggo antashi lafiya,yafurta da alamun biyayya,lafiya qalau ta amsashi,yaasu abba,bamu riga mungaisa ba,tace eh nima ai maganace nake buqatar yi dakai shiyasa nakira,kuma maganar mai matuqar muhimmanci ce,kazo gidan nan da awa biyu inason ganinka,bai kawo komi aranshi ba duk da abin yadan bashi mamaki,sallama sukai bayan ya tabbatar mata da zuwan nashi nan bada jimawa ba in Allah yaso.

   

  A kicin yasameta tanata kiciniyar toasting bread,hakan yabashi damar qare mata kallo tundaga sama har qas,tana da matsakaicin tsaho,bata cika siranta ba domin kuwa bata sahun sirara,amman hakanma bazaisa kasanyata cikin jerin lukutaye ba,ma iya kiranta da chubby domin kuwa jikinta acike yake ba rama,baqāce amman ba qirin ba, irin baqin nan mai sulbi da haske,kallo daya xakai mata ka karanto baiwar kyawun da Allah yai mata,tana da wani irin sassanyan kyau mai daukar hankali,tanada siraran zane bibbiyu agefen kumatun ta dasuka qara mata kyau,.masha Allah duk da ance mutum tara yake bai cika gomaba,wannan haka yake,domin kuwa duk da irin baiwar kyau na amatullah sai Allah yayota babu baki,kodayake rashin maganar yasamo asaline tun tana qarama er shekara hudu rana daya akaji tadena magana,iyayenta sunyi qoqarin samuwar lafiyarta kafin Allah yai musu rasuwa amma Allah baiyi ba,wanda hakan yai sanadiyar riqonta yadawo hannun qanwar mahaifinta hajia talatu,dga nan aka watsar da batun nenan magani tacigaba dayi mata bauta.

         **********************

Dama kin iya girki ta tsinci muryarshi yana tambayanta,daga mishi kai tayi alamun eh,duk kuwa dacewa batasan yashygo kitchen dinba,

  Taya ta yayi yakai breakfast din data hada bisa dining table,ta kyauta masu kam datai tunanin shirya kayan kalachin,coz he have been thinking dama yanda xaiyi da ita donshi kam bai iya komiba tafannin kicin banda dafa indomi da coffee.

   Anatse takecin abincin,yayin dashikuma yakebinta da ido kamar tsohon maye,gaba daya jitai ta takura wanda shi talura hakan yazame mishi kamar dabi'ah.

  Zanje main house dinmu,sabida haka xanbarki inje indawo,bazan dade ba,kai tadaga alamun toh,sai kuma tacigaba da mishi kallon "nifa nagaji"

 Karki damu dana dawo xamui final talk,ai nafadamiki i won't hurt you,tadaga kai alamun gamsuwa,yace good xanje inyi wanka for now...Feel at home okay?.Kana yawuce domin yashirya.


6


RAINA KAMA


By Noorieyyaah


Yanxu kai kana ganin abinda kakeyi daidai neh sulyman,mahaifiyar shi tacigaba da fada,,ace kamarka ka kasa tsaya kafidda mata kayi aureh? Toh bari kaji,nagaji da xubamaka idanuwa,nalura bakasan xuru ba....Tadan numfasa kana tacigaba,sabida kamaidani abokiyar wasanka kullum saika dinga cemun inyi hkri inqara maka lokaci bincikawa kake,toh tunda binciken naka har yanxu baisamu ba ni na binciko maka, 

  Sulyman dakanshi ke sunkuye yana sauraron mahaifiyar tashi daketa banbamin fada,duk da dama dai yasaba da irin fadannan nata amman nayau kam yasha bambam,jintace ita tabinciko maa mata yasashi dan dago kai yana dan marairaicewa,

  Eh ka kalleni dakyau,nagama yanke shawara,kuma wallahi tallahi kaji narantse baka isaba wannan karon nadaga maka qafa.

Haba!Ayi mutum shi kullum girma yake amman yanacin qasa..

Tacigaba da fada,dubi qannenka kowanne yaasan abinda yataka,kai kana nan jiya iyau bansan ubanda yahanak aure ba duk kuwa dacewa kai din ba abinda karasa,,,

  Sabida haka yau dinnan ba gobe ba,kashirya katafi gidan hajia balaraba(aminiyarta) kufahimci juna kaida Laurah,

tunda tafara fadan sai yanxu yakatseta,haba gwaggo laurah fa kukace,kuyi hakuri kuqaramin lokaci wallahi xannemo mata,amma gaskia gwaggo ni laura bata cikin kalar matan danakeso,

Ungo nan!Ta aikomishi da daquwa,nace kaci gidanku,wallahi kaji narantse baka isaba,domin kuwa nagama magana,Abbankuma karkai tunanin tunkararshi domin kuwa da goyan bayanshi nake maka xancen nan,idan kuma sokake kanuna mun ban isaba sai insani,taqarashe maganar tana mishi kallon inajinka.

  Haba gwaggo yaza ai ince baku isaba,shikenan duk abinda kukeso shi za'ayi.

  Toh kokaifa,kayi qoqari kaje kufahimci juna,inafatan kafahimceni?in sha Allahu gwaggoh...Yawwah toh Allah yai maka albarka,tashi kaje.

     ********************

Kwance yake bisa cinyoyin wata er kyakkyawar tsohuwa,bisa dukkan alamu kakarshi ce,ajiyar zuciya kawai yake tun shigowarshi gidan,yayin da tsohuwa dada kecigaba da shafa kanshi ahankali da alamun lallashi.

 Hakuri xakai kayiwa iyayenka biyayya kajiko dan gidana,kuma kacigaba da adduar Allah yasa hakanne mafi alheri,amma dada ni ba'a kyautamun ba ko kadan,haba don Allah!

Amfa daina yayin auren dole ko a qauye,bareni qatoh dani xaa kama ace za aimun auren dole,yacigaba da mita yana kumbura hanci.

Gaskia dada ni kitaimakamun kiyiwa su abba magana,nasan ke kadaice hope dinah,kinji sweet granny don Allah wallahi baniyin yarinyar nan kwata kwata,da iyayinta zanji koda danbanzan girman kanta dakesa tanajin kamar tafi kowa?Mtsw yabuga tsaki,dan kyan nata cikin cokali sai yangar banxa.

  Dada takatseshi tahanyar make qeyarshi,aiko dai kuma kayi qarya,lauratu yarinya ce kyakyawa sonkowa...Barta tayi yangarta ai ta chanchanta datayi neh,haba granny kema kinso kanki,toh nikam baruwana da kyawunta don baya gabana,kuma bata cikin kalar macen danakeso atoh!

  Toh basai kafadamun in akwai wadda kakeso ba,nikuma nayimaka alqawarin shige maka gaba sai inda qarfina yaqare.

Zuru yayi yana tunani,Yasan kozaa yankashi bashi dawata yarinya dazaa nuna ace budurwarshi ce,duk kuwa da irin tarin ematan dake kawo mishi hari,amma yai qwallon tamola dasu yace beyinsu.

   Amatullah!Gabanshi ne yadan fadi sakamakon tunota dayayi,yarinyar tayi awon gaba da imaninshi ganin farko dayai mata,everything about her is wow!seeing her awoke the devil in him,thou birgeshi kawai take,he feels nothing for her than LUST!And he vow to have her by all means,even if it means marrying her!

Yes why not?Yatambayi kanshi,zai aureta ko dan yakauda masifar kwadayinta dake ranshi,bayan yakore qishin shi game da ita yabata visa takama gabanta,inyaso daga baaya ya auro wadda yakeso.

  Murmushi yayi sakamakon jin shawarar tagamsar dashi.

     ******************

Pls vote...Vote and comment☺☺


7


RAINA KAMA


By Noorieyyah


Amatullah will you MARRY ME???

Ras!_gabanta yafadi bayan tadago kanta adan razane,atake kuma tasunkuyar da kanta tana dan murmushi sakamon kallon dayatsareta dashi,batasan dalili ba duk lokacin daxata hada ido dashi take zataji kasala ta lullubeta.

   Will you be my wife,zaki aureni?yasake maimaita mata,shiru takuma yi tana naxarin maganar tashi mekama da almara,bata taba tunanin jin kalmomin nan daga bakinshi ba,ita duk kallon dan iska take mishi mai shirin lalata mata rayuwa,ashe duk bahaka bane...

  Pls answer my question,kidagamun kanki inkin amince da buqata,ya ida xancen gamida danqara matse hanneyenta dake nashi,take kunya da kasala suka qarayi mata rubdugu haka kuma jinkinta yai mata nauyi,gakuma gabanta dake ta fat,fat kamar xai faso qirjinta,shin zata amince ta auri mutumin da batasani ba?Amman kuma baiyi alamun mugu ba ko wani mai baqin hali,hasalima kwarjini yake mata sabida cikar xatinsa.

  Ki yadda ki aureshi mana,ko banxa kin huta da axabar momy talatu,uwa uba molesting dinki da adnan yake zaizo qarshe,wani bangare na xuciyarta yabata shawara...Besides the guy is breathtaking, tadanqara satar kallon shi,yahada komi da ya mace takeso ajikin da namiji.

Answer me don Allah babe,kobanyi miki bane?Girgiza kai tayi alamun ah ah,owka tell me xaki iya aurena?

Rubutu tayi a memo din dake hannunta ta miqa mishi,"karka manta fa ni bebiyace,kuma marainiyaceni,"

 Nafi kowa sanin keh bebiyace kuwa yafada axuciyar bt i have no any other option than to marry yhu matuqar inaso insameki,and to get ride of that stupid laurah.

I know babe,karki damu wannan duk bawani abu bane,nidai buqata shine kiyarda ki amince da buqatata.

"Okay i will marry you,but in one condition"

Kan uba,yafurta a hankali,bayan yakaranta abinda tarubata,ji bebiya da iyayi daga xai rufa mata asiri,har wasu conditions xatasa mishi,bakomi zaiyi maganinta.

Oakay babe tell me inajinki,what's your condition?

"Bazakaimun kishiya bah"ina tsoron kishiya"

Dariya ce taso qwace mishi,lallai samun guri!bebiya dasaka condition kaman nace inasonta!Kigodewa Allah inkika samu kika hada wata a gidana,yafurta maganar a xuciyarshi yana dariyar Kinaban takaici.

  Don wannan baawani abu babe,i promise daga keh bawata,"KEH KADAI NAKE SO"

Dadine ya lullubeta jin kalamanshi hakan yasata rufe fuskanta ba shiri tana dan dariya qasa qasa,bisa dukkan alamu zancen baqaramin Sugar yai mataba,take taji sonshi naratsa lungu da saqo na sassan jikinta,so neh irin mai matuqar wahalar nan taji xuciyar namishi don kuwa jitai bata da sairan buri a dunia baya data zama mallakinshi.

"I love you hunny"and i can't wait to have you"yacigaba da binta da kallon so,jitaayi gaba daya duniyar na zagayata don dadi,bata tabajin irin abinda takejiba yanxu!Hakan yasa taqara matse kanta cikin cinyoyinta tana qarajin sonshi na huda bargonta.

Alhamdulillah Allah yakashe yabata....Haqiqa Allah yagama mata komi daya hadata da sulyman,he's her first and he will be her last in sha Allah

 Kina ban tausayi,ya ayyana aranshi sabida lura dayayi gabadaya ta faller,i will use this opportunity to get what i want,this is the best decision tunda taqi yarda ta lalama....and i can't wait for the upcoming heartbreak in near future.

Murmushin dake qara mishi kyau yasaki kana yadago kanta gamda sanya idanuwanshi cikin nata,babe you will soon b mine... yakashe mata ido.....

        *************

Lol jama'ah kutayani yiwa amatullah jajeh,,,😩

  Pls vote!Vote!Vote! and comment....hakan xaiqaramini qwarin guiwan cigaba.

Love you all.


     8


RAINA KAMA


By Noorieyyaah


Hajia kuyi hakuri don Allah, dama akwai yarinyar danakeso bandai fada muku bane kawai.

    Wannan matsalar kace ni nagama magana!

Qara marairaice fuska yayi ganin babu alamun sassauchi a tattare da mahaifiyar tashi,

Miyasa gwaggo keson sakashi cikin wani haline?,shi yasan duk iskancin shi baya da sha'awar aje mata biyu,baitaba wannan tunanin ba kaf rayuwarshi,bayason tashin hankali shiyasama sam baya ra'ayin yin aure anan kusa.

Amma toh yazaiyi tunda zabin da'aka bashi kenan.

 Inkagama tunanin sai kasanar dani,nikaga shigata inada abun yi,ta ida xancen naata tana qoqarin tashi.

   No gwaggo kuyi hakuri naji na amince zan auresu su duka biyu din...Ya ida maganar da ladabi.

Toh kokaifa,ai dama yanda kakwana biyun nan bakai aureba mata biyun neh daidai kai..Allah yaimaka albarka.

     **********************

Hajia laraba ce tai shiru bayan tagama sauraren bayanin da sulyman din yagama yi mata,

 Shikenan sulyman zan shirya inmaida amatullah din gidansu cikin satin nan,daga nan kuma xanyi ma maman ta bayanin komi,gashi kuma kace da wuri kake son abun koh?

Yace hakane,duk da dai badaga gareni bane,daga su alhaji neh,

Toh shikenan innadawo dai xakaji yadda mukayi.

Ammm pls hajia banaso don Allah amatullah tasan su biyu xan aura coz baxataji dadin hakan ba

  Galala tayi tana kallonshi duk da dama dai har yanxu mamaki take yadda al'amura suka juya cikin kwanaki uku rak!Wai yaushe galadanchi yafara son amatullah har haka,abin na matuqar daure mata kai don tafi kowa sanin akuyancin sulyman...Allah dai yasa har xuciyarshi yakeson yarinyar ta ida tunanin gamida tabbatar mishi dacewa in sha Allah komi zai zama in order.

  

     **************

She missed him...Take taqara lumshe idonta kamar mai bacci...Yanxu wai itace xata xama matar wannan hadadden guy din...bata taba tunanin rayuwarta zata samu chanji ba cikin dan qanqanin lokaci haka.,

  Wayan da sulyman din yabata ayau kafin su rabu tasake kallo akaro na goma tun bayan rabuwarsu wanda sai da yatabbatar dayai mata subscription kana kuma yabude mata kafofin sada zumunta irin su WhatsApp da Facebook acewarshi wadannan sunfi amfani,duk dacewa kuwa shafin twitter ma nadaga cikin shafuka masu amfani,amma sanin cewa yana da wuyar sha'ani musamman ga new comers shiyasa ma bai wahalar yimata register ba.

  Message neh yashigo cikin wayar tata,take tabude sakamakon ganin "My Man" arubuce ajikin akwatin saqonnin wayar. "Ki kunna data dinki muyi hira"

Bata bata lokaci ba tukunna data din cikin doki da zakwadin sake yin hira dashi akaro na biyu tun barowarta gidan nashi.

Typing taga yanayi hakan yasa tadakata da qoqarin tura Mishi sallamar datayi niyya.

   "Seems like my baby is not missing me shey😉"

Take ta tura mishi da dan aljani mai nuna alamun jin kunya hadi dace mishi bahaka bane.

 "toh yaya neh?Kin shareni ko kiy mun text kiji yadda na isa gida koh?"

"Toh afuwan kayi hakuri i was carried away neh,nataya anty laraba girki neh"

Tamayar mishi da amsa...

"toh nhaqura baby na,now tell me are you missing me?"

 Take tasunne kai kamar yana kallonta..Sonshi naqara samun mafaka a xuciyarta.

 "daqyar ta rubuta mish yes cikin jin kunya,wanda har sai da yagane hakan.

Dolenta tasake sukayi hira sosai,wanda zallar hirar duk dga sulyman dinne aqoqarinshi nakafa dimbin sonshi a zuciyarta,shikanshi mamakin kanshi yake yadda yazage yaketa zazzaga mata qaryar sontan dayake,a inda kaf hirar yanayinta cikin cin dariyar yadda take responding wa duk wasu salon qaunar shi gareta.

  Sallama yamata bayan yasata dole ta aika mishi dasaqon emoticons na kisses acewarshi hakan zaisa yasami sauqin sonta dayake barazanar faso qirjinshi.

  Hakan koh yayi nasara wajen qara kafa soyayyarshi acikin ruhinta da gangar jikinta baki daya.

  Da tunaninshi bacci yakwasheta....Wanda har alokacin bata gusheba wajen godewa Allah daya hadata da "other half" dinta mai sonta da gaskia.


        ********

Toh asuba tagari babyn sulyman...😂

  Pls vote...Vote...And vote.

..Nagode😍

   Mrs Noor


9


Raina kama...!

      

Sannu sannu bata hana xuwa sai dai adade ba'ajeba!Cikin yardar Allah mai kowa mai komai aka daura auren Sulyman Bello Galadanchi da Amarensa Amatullah Assidiq Rumah tareda Lauratu Khalil Yakasai.A inda daurin auren yasamu halartar dimbin jama'ah na nesa dakuma kusa duk kuwa da irin qarancin lokacin da'aka sanya na gudanar da daurin auren,dakuma duk wasu rudani da tawaye dasuka so yiwa sha'anin rubdugu ta fannin shi kanshi angon dakuma bangaren amaren biyu,duba da dangin amah din dasuka daka tsalle daga farko suna mai tawaye gayiwuwar al'amarin,acewarsu bata isa aureba yanxu dadin dadawa kuma su basu san asalin ango bah sabida haka dare daya baza'a azo arabasu da 'yarsu ba,a inda xancen yazame wa amatullah wani banbaranqwai wai namiji da suna hajara,idan tayi duba da tarin tsana da chin xalin da ahalin gidan qanin mahaifin nata kemata,wanda asali shine musabbabin guduwarta kano wajen hajia laraba,wacce itadin takasance qawace ga matar qanin mahaifin nata hajia talatu,sakamakon ganin cewa itadin takasance mai sonta dayawan tausaya wa halin datake ciki aduk lokacin data kawo wa aminiyar tata ziyara anan garin katsinan.

   Da ikon Allah,dakuma qarfin iko na qanin mahaifinnata aka sasanta al'amura komi yagudana cikin kwanciyar hankali,domin kuwa yasha alwashin sagama borensu amman babu wanda ya isa yahana afkuwar lamarin,sakamakon dadewa dayayi dasanin irin tarin azabar da hajiyar da ahalinta keh yi wa marainiyar Allah.

Wannan al'amari koh yaqara fusata mommy(h.Talatu) a inda tai tsalleh tadire tahana ayiwa amarya duk wasu abubuwan al'ada dayakamata ace anyi mata din,wanda inda ason rantane ko kayan daki bazata bari ayimata ba,duk kuwa dacewa dimbin dukiyar da mahaifanta suka bar mata suna a hannun uncle din nata,toh dai komah menene mommy batasamu nasara ba,don kuwa uncle din nata yagwada mata qauna,idan mukayi la'akari da uwar dukiyar da aka kashe mata a shiryayyen gidan sulyman din dake nassarawa GRA.

   *********

Idan muka koma ta fannin laurah kuwa sai muce abin masha Allah,dominnkuwa amarya tasha gyara,gyara ba kadan ba hakan ko yasamu nasaba ne dakasantuwar mahaifiyar ta Laurah er asalin garin maradi dake jamhoniyar niger.

   Duk da dai ta fannin amarya laura ba'asami matsala ba ko kadan,idan mukayi duba dacewa abin tuwona mai nane,sai dai hakan bai hana samuwar er matsala ba daga amaryar da angon,

Aganin laura din ita bata taba ganin baudadden mutum irin nata angon ba,wanda hakan yasa takasance cikin mamakin irin halayen dyake gwada mata na ko'in kula,domin kuwa xamu iya cewa tunda aka fara maganar auren nan sau biyu yataba kawo mata xiyara nata nakanta,wanda daga bisani sai dai aminin ango (kb) yaciga da hidima da ita da qawayenta..

  Kwafa tayi bayan tagama tunano salon wulaqanchi na mijin nata,toh ko don yaga ya hadu neh qarshe shiyasa xäimata iyayi?

Toh ai taga ita dinma mai kyan ce,mai kyau kuwa tasakawa agaban mota,domin kuwa takasance fara qal mai tsayi,hancinta dabai cika tsayi ba yaqarawa round face dinta kyau,ba laifi tana da yalwatacchen gashi,gashi kuma ita din takasance macece ma'abociyar gayu da qwalisa,er gayuce ta bugawa a jarida domin kuwa duba daya xaka mata ka fahimci hakan atare da ita,dadin dadawa kuma gata er boko,domin itadin banker ce.Aqalla bazata wuce shekaru ashirin da biyar ba.

Toh koma dai menene taci alwashin sai tasauke wa mishi duk wasu wulaqancin dayakejin ya iya,aganinta mace fa take...Macen ma mai kyau da qwalisa..Toh har akwai dan abu takazan dazai raina mata class?Tace ba'ayi shiba!

duk kuwa da sonsa datake bashi xai hana tasaita shi ba,matuqar yace haka xaicigaba dayi mata halin ko inkula domin kuwa ita baxata daukaba sam. 


     **********

Ayimun hakuri chapter din baya da tsaho,i promise a long chapter next time in sha Allah..And pls don't forget to show love by voting☺

10


 Raina kama...!


Nassarawa G.R.A

08:12

      

Wai kai meyasa dan iskane kai...Kalli agogo fa just 8:12 yanxu,taya kake expecting inrakaka dakin amarya yanxu,haba ni iskancinka har isata yake, kb ya ida maganar ayayin dayake qoqarin chanza channel.

Mtsw kai nifa bani iyawa da al'adunnan,at least yakamata ace by now kowa yakama gabanshi abar mun amaryata in huta gajiya,yaqara sakin tsaki akaro na biyu,kasan Allah da 9:00 dot tayi xanqara gaba,ni banma son rakiyar taka coz lokaci xaka batamun.

   Dariya kb yasaki yana mai girgiza kai,inda sabo yasaba da halin abokin nashi.

Toh naji Allah yakaimu zuwa 9 din,garin gandokinka ma ko tunawa bakayi da er kazar amarchin dazaka riqe ba,

Dasauri sulyman din yadafe kai,hadi dacewa mhan wallahi namanta,kasan farin shyga neh ni,you have to lead me through a irin abubuwan nan,.

Kb dinne ya amshe ta hanyar cewa sabon shyga a aure ba,banda dayan don kafi dan dakon tasha sanin whazzup...Suka kwashe da dariya atare gamida tafawa.

      ***********

11:03 yayi daidai da kammala duk wasu al'adu dayakamata ace amarya da ango sunyi a irn wannan rana mai dimbin tarihi agaresu.

Hkanne yayi daidai da baqon yanayin da amah tatsinci kanta aciki,takasa ganeh miyasa takasa sukuni tun bayan tafiyar kamal bayan en barkwanci da nasihohi dayayi agaresu.

    Gaba daya takasa yadda su hada ido,inbanda sunnar da kai kamar munafuka ba abinda take,wata iriyar kunyarshi takeji duk kuwa dacewa bayau suka taba kwana adaki dayaba,wanda shi gogan naku sam baruwanshi,lallabata kawai yake tareda qoqarin ganin yacimma burin shi a daren yau din.

  Tun bayan dasukai wanka,yasata tachi abinci don dole kana kuma suka gabatar da nafila na miqa godiyar su ga mai duka daya nuna musu wannan rana,hadi dafatan Yabasu xaman lafiya mai dorewa na har abada.

  Kwance take chan qarshen gado ta takure kamar ache qyaat ta tsere,yayinda shikum yai qoqarin hawa bisa gadon hadida janyota xuwa gareshi.

  Zizzilewa tafarayi,kamar mai shirin kuka.

  Ha'an baby what's wrong?

Shiru tayi tana kallon shi qasa qasa...Ita bataso yana tabata gaskia,wani irin sanyi takeji har tsakar kanta.

  Wait zokiji ba abinda xanmiki,karatu kawai xankoya miki kinajina koh?Da mamaki takebinshi da kallo

  Wane irin karatu kuma da tsakar dare...Kamar yakaranchi xuciyar ta,taji yanacewa wani sabon karatu neh xanfara koya miki kina jina,and banason gaddama,duk abinda nayi kema shi xakiyi understand?

  Daga mishi kai tayi kamar doluwa,yayindashi kuma yacigaba dacewa toh xamfara da nan...Yakai wa goshinta wani hot peck, dasauri tai qasa dakanta gamida qara riqeshi,murmushu yayi ganin darasin shi na isar mata yanda yakeso.

 Daga nan kuma ahankali yacigaba da ribatarta da salon qaunarshi,wanda hakan yai matuqar tasiri gareta,bata raina kanta ba sai dataji yana karanto addu'ar kasancewa da iyali .

   Duka,cizo yakushi,ihu ba irin wanda baishaba,domin kuwa gogan sam baiyi la'akariba dacewa itadin sabon shyga bace,yazage ya fanshe al'amura da dama dasuka riqa kawo mishi cikas azaman dayayi da ita....Kwarai taraina kanta wanda har alokacin da komi yalafa bata fasa hawayen wuyaba,sakamakon.Muryarta data dishe kukan ma baida ikon fita da qarfi.

   Lallaashinta yaciga dayi bayan yakaita toilet yakintsata,shima kuma yakintsa,lamo tayi tana maida ajiyar xuciyar azaba,shikam sulyman qara sanyata yai ajikin shi yana aikin lallashi.

    Qura mata ido yayi yanatuna yanayin data sanyashi a daren yau din....Kaf rayuwar shi dayayj yana shashanci da neman mata baita samun nutsuwa irin wanda ita din tasanya shi ba.Lumshe ido yayi yana mai tunano irin hutawar dazaiyi da yarinyar....

Murmushi yayi gamida furta "Change of plan"

     **********

Sati sukai suna more amarchi,inda sai da yayi qoqarin koyar da ita salo salon qaunarshi,domin kuwa acikin sati dayan nan dasukayi tare yanuna mata dankaren SO! So bana wasa ba,tareda tabbatar mata da itace rayuwar shi,hakan kuma yayi matuqar tasiri agareta,tasadaukar mishi da zuciyar da dukkan jikinta baki daya,hadi da qara godewa mai duka daya bata miji mai sonta da gaskia.

  Laura fa?Bai kuma bi takanta ba dama tun bayan daurin auren dayaje ya bige mata warning nacewar karta nemeshi,domin kuwa yana wajen uwar gidanta,acewarshi duk da ba son amah yakeba,ammah tafiye mishi lauran nan sau dubu,domin kuwa gara ita amatullah din tana da advantage akanshi tunda har yakeda matuqar shaawarta,laura fa da ita ko burbushin lust din bayaji game da ita,sam bata birgeshi bare har ya yaba,duk kuwa da dimbin gayunta da iya kwalliya.

  Da sannu xanmaida rayuwarka abin kwatance...Acewar laura bayan yabar mata gidan.

    *****

So how was the chappy?

Vote pls i will appreciate that.

   Nagode


11


RAINA KAMA


Tsaye take jikin mirror tana ida goge ruwan dake jikinta,daga dukkan alamu wanka tafito.

  Da dan haanzari tashafa wa jikinta body lotion din dake bisa mirror din,bayan tagama neh tabada himma gurin dandasa wa fuskar ta make up,masha Allah don kuwa make up din ya tsantsaru tamkar kasacheta ka gudu...Yalwatacchen gashin kanta takama tasawa wasu tapka tapkan ribbons masu kyau.

 Bata dauki lokaci ba tadauki gayu cikin wani tattausan cotton les mai kalar turquoise blue,dinkin riga da skirt wanda rigar takasance high neck hakan yahana tasaka sarqa,sai dai tabi kunnuwanta da wasu silver fashion earrings masu kyau.

 Tana qoqarin fesa turare ya sanyo kanshi cikin bedroom din.

  Wow!Yafurta ahankali,hakan yasa tadan juyo tasakar mishi murmushinta mai kyau,baiyi qasa a guiwa ba ya mayar mata hadi da qarasawa kusa da ita tareda rungemata ta baya.

  Lumshe ido yayi yana shaqar qamshinta mai sanyi...Hakan yabata damar cigaba da kallonshi ta mirror din dasuke tsaye.

Mijinta mai kyau neh,tafurta hakan a xuciyarta,take kuma wata sabuwar qaunarshi na lullubeta.

  Tsinto hannunshi tayi yana shafo cikinta...

Sweetheart do you know how beautiful you look right now?Yatambayeta yana mai qara hadata da jikin shi...Murmushi kawaii tayi gamida rufe fuska.

    Bazaki daina kunyan nan bako amah?

Girgiza mishi kai tayi tana er dariya,shima din dariyar yake gamida juya da ita suna facing juna.

   Baby na kullum kyau kike qarawa...Koh babyna keh qara miki kyau...?Ya ida maganar yana qoqarin daga mata riga.

  Itakam har mamakin sulyman take,wata biyu kenan da auren su hakan kuma yayi dai dai da wata daya da sati biyu na samuwar cikin dake jikinta!

Kwarai sulyman ba abinda yakeso yakuma kwallafa wa rai irin cikin nan dake jikin amatullah,bai taba sanin haka feelings din xama baba yake ba...

Yanason cikin nan fiye da kanshi,wanda har hakan yasa yakejin zai iya zama da amah din har qarshen rayuwar shi badon komi ba sai don ta riqa haifo masa yara masu kyau irinta duk kuwa dacewa basonta yakeba.

Bt hakan bashi xai hana ya auri love of his life ba in near future... coz he believe duk inda take yakusa haduwa da ita...Yanajin hakan a jikin shi.

   Bayan yataimaka mata taqarasa shiryawa neh yai mata jagora suka fita xuwa harabar gidan nasu inda motar shi take jiransu,da'alama fita xasuyi.


         *************

Oyoyoh ga aunty amah cewar khausar,wacce ita din takasanche diya ce ga hajia batula yayar Sulyman,bazata wuce sa'ar amatullah dinba,domin itama this year tagama secondary school shiyasa tunda sukazo bikin su sulyman din bata koma ba,tazauna tareda gwaggon tana debe mata kewa.

    Bayan en gaishe gaishe,wanda ita amah din tata gaisuwar murmushi neh kawai tareda sunkuyar dakai.

Gwggon ce kehta janta a jiki,a inda itama tai qoqarin sakin jikinta da surukar tata mai tarin kirki,kausar kuwa duk da sanin cewa amah din bata iya magana hakan baisa tafasa yimata hira ba kasancewar ita din yarinyace mai surutu da saurin sabo,take kuwa suka saba da juna,wanda takai bakajin komi a palon inbanda tashin dariyar su da qaran tv.

Domin kuwa dama gwaggo ta jima da shyga daki tadan kwanta,sulyman kuwa dama yana gaisawa da gwaggonshi yafice acewarshi xaiga wani client dinshi kan wani contract daza'a bashi.

    


An Hour Later.

Qamshi kawai keh tashi daga kitchen din na gwoggo,da alama sanwa ake a madafin,kausar ce natsinto tana dariya hadi da cewa kai anty ammah,nalura kinfaye kishi!Toh yazakiyi da anty laurah?Tacigaba da dariya

Ita dinma amah din dariyar tayi gamida basar da xancen,a tunanin ta laura din wata tsohuwar budurwar mijin nata neh ada!

  Wai bakowa neh a gidan,suka tsinto wata murya mai cike da iyayi tana fada,hakan nan kuma qarar takun takalminta qwas qwas yana cigaba da dumfaro kitchen din.

 Kallon amatullah kausar tayi gamida cewa "talking of the devil" juya idanuwanta amah tayi alamun rashin fahimta.

kausar batakai ga qara magana tabude kitchen din tana kallon su up and down,da sauri kausar ta qarasa kusa ds ita gamida ceh lah anty laura kece haka da ranar nan ba unexpected? ko uncle man(sulyman) neh yakawo ki?

  Take gaban amatullah yaciga dafaduwa tun shigowar hadaddiyar matar,uncle man kuma?Toh meye hadin wannan matar da mijinta?Kodai har yanxu bata haqura bane da shi duk da bai auretaba? Atunaninta tsohuwar budurwarshi ce laurah.

  Take taji qirjinta yatokare...Hakan kuma yayi daidai da jin wata muguwar tsanar wadda aka kira da sunan laura din hakan yabata damar bjnta da kallon banxa a fakaice.

  Itama din lauran tajuya tana kallon amah din bayan tagama ba kausar amsar cewa daga bank take shine tace bari tayi branching ta gaida gwaggo.

   Qura mata ido lauran tayi tana qoqarin tuno inda tasan fuskar amah din.

Cikin kalllon banxa laura din tace wa aman do i know yhu?Itama din a wulaqance ta girgixa kai alamun "who knows"

Kausar ce tai qoqärin katse atmosphere din nasu ta hanyar sakin dariya kamar xata fadi a qas....Take kuma amah tacigaba da mata kallon.."Are you okay"?

  Tsagaita dariyar kausar tayi ta hanyar cewa kai don Allah,ni wallahi har kun ban kunyah,yanxu da awani guri kuka hadu -haka xaku wuce bakusan juna ba?Gaskia duk laifin uncle man neh,aj yakamata ace yakai ku kunga juna kobahaka ba anty laura?

Laura din ce tatabe baki da ta fahimci ko wacece amah din,hakan yasa taqará sakar mata kallon "so this trash here is my so called kishiyah"?

Take kuma ranta yafi nada baci,dama akan wannan figigiyar yarinyar mai kama da kumburarren baloon man keh wulaqanta ta?Gaskia yabata kunyah,duk feleqen nashi anan yaqare?Mtsw taja tsakki gamida cewa

So you are the "mute" girl dake daukemun hankalin miji?Ta watsa mata mugun kallo hadi da qarasowa gaban amatullah din wacce ta sandare tundaxu bayan fahimtar wacece ainihin laura din a rayuwarta,hakan yasa takasa motsi kuma kasa tabuka komi,gaba daya jikinta yayi sanyi tana mai jinjina rashin mutunci irin na da namiji.

  Miyasa zaiyi mata qarya?

   Miyasa xai munafinceta ya boye mata babban alamari irn wannan?

   Miyasa ya shammaceta?Ashe bata chanchanchi duk wasu bayani ba?Miyasa xai chi amanrta har haka?

Amatullah kike kowa?Kisaurareni da kunnen basira!

 Tatsinto muryar laura namata echoing....

Duk dayafadamun cewar keh din dundum ce hakan baxaisa nafasa magana ba tubda ancemun kinaji.

Tawatsa mata mugun kallo kana tacigaba.

   Kinyi kuskuren aurar mini miji,sabida kisani man nawa neh ni daya...Just look at yourself and take a look at me?Kinga alamun nayi kalar wacce xata iya hada mijinta da wata?Toh kisaurareni da dodadden kunnenki kiji ni...Sulyman ba ajinki bane,shi din ba kalarki bane...Idanbbanda son kai irin naki ina bebiya ina lafiyayyen namiji kamar sulyman?

  Wata fadamiki baqar mace lukuta bata sahun matan dayakeso?Yataba fada miki qananan yara sune abu naqarshe da xai iya hada shimfida da?

Da'alamu kinsan dahaka amma kikasa qafa kika shure kika liqe wa mijina...Toh bari kiji,kinyi nasarar auren mijina amma baxaki taba nasarar samun koda rabin rabin son dayake mun bah!

 Uhhhggh wai miyasama nake bata bakina neh?Bayan yariga yasanar mun dacewa taimakonki yayi sakamakon fyaden da akai miki?shi sarkin en tausai ...Toh koma dai menene inason kisa wannan at the back of your mind..!

"Mijina nawa neh nikadai,sannan kuma bayanda xa ai yayi rayuwa da dunkum mai kalar fulawa mai yeast a cikin gidanshi da ruyawar shi"he never loves yhu and never he will"

Ta wulllah mata harara ta juya cikin takunta na en gayu tafice daga kitchen din.

Kausàr wacce tunda suka fara drama din tazama statue ta hangame baki tana binsu da kallon mamaki...Gaba daya tarasa bakin magana.

   Faduwar dataji neh yamaido da ita daga firgicin data shyga gamida xunduma ihun kira sunan Amatullah din.


         **********

Your votes and comments matters to me alot

   Nagode😍


12


RAINA KAMA


Ahankali take bude idanuwan nata sakamakon nauyin da sukai mata,,,hakan yabata damar dafe kanta dake sara mata ahankali.....


Abinda yafaru dazu da yamma agidan surukan nata yafara dawo mata a kwakwalwarta hakan yasa hawayen dake maqale a idanuwänta sukacigaba da ambaliya,take kuma tacigaba da jin wani mugun bacin rai naqara ziyartar ta,hakan yasami nasara wajen taimakawa muryarta fitar da sauti na alamun kuka.


Gwaggo ce zaune gefenta tana laximi,jinn sheshsheqar kukan neh yamaido da hankalinta inda amatullah din take,wanda hakan yatabbatar mata da cewar ta farka,


Haba amah daga tashi kuma sai kuka?

Taqarasa bakin gadon tazauna gamida shafo fuskar amatullah din,kiyi hakuri kinji my daughter, kinsan dai halin dakike ciki baavika son bacin raiga mai juna biyu ba,kinga badon taimakon Allah ba da anyi asarar abinda ke jikinki.


Ta numfasa,inason kiyi hakuri mataullah,ki kauda duk wata damuwa daxata dameki,ki fawwala wa mai duka lamuranki kinji ko?


Haka gwaggo tacigaba da lallashinta don ganin ta kwantar mata da hankali,bata gusheba tana bata baki har sai da ta tabbatar da samuwar chanjin yanayi daga fuskar amatullah din..Hakan kuwa baqaramin dadi yaiwa gwaggon ba.

      *******


Khausar ce takwana da ita a asibitin,wanda har alokacin bata fasa mamaki da al'ajabin rashin bayyanuwar sulyman din ba tun kasancewarta a asibitin...Hakan kuwa yaqara assasa bacin ran datakeji game dashi.


Atunaninta kobaizo yadubata don kowaba,yazo yadibata don darajar ajiyarshi dake jikinta,tacigaba da sharar hawaye a fakaice don gujewa idanun kausar din dake daddana waya a gefenta.


Hakannan kuma bata gusheba wajen tunanin irin matakin daya kamata tadauka akan Sulyman din,duk kuwa da kasantuwar shi mutum na biyu datake matuqar so da qauna bayan mahaifanta aduk fadin duniya...Hakan bazai hana tanuna mishi kuskurenshi na abinda ya aikata mata ba.


Shin dama haka maza suke da iya yaudara kokuwa nata mijinne ya qwareh anan?har alokacin takasa gasgata wa kanta cewa Sulyman dinta neh yai mata haka...Idan tai duba ga tarin soyayyar dayake gwadata mata,wadda bakowace mace keda sa'ar samun kwatankwacinta ba.


Kaicho!Tacigabá da cizon lebe cikin jin tsananin kishin laura azuciyarta...Ko banxa lauran tasha da ita...Idan tai duba ga irin tarin baqaqen maganganun data riqa gaggasa mata a shudewar wasu awanni dasuka gabata...


Bata taba jin haushin rashin maganarta irin yau ba!

Tacigaba da share hawaye ahankali gamida rufe idanunta domin samun sassauci...Tareda fatan Allah ya bayyana wayewar gari domin ta hadu da ogan maciya amana...(sabon sunan data radawa mijin nata lol).


   **********

Da safe bayan doctor yaqara dubata yatabbatar da bata da wata damuwa yabasu sallama,bayan yabata jan kunne akan takula da abinda xai ke bata mata rai ko don lafiyar abinda ke cikinta.


Direct gidan gwaggo driver yawuce dasu,wanda yin hakan umarnin gwaggon neh,acewarta amatullah din nabuqatar hutu,wanda ita sam amatullah abin baiyi mata dadiba,tasoneh ayau suyita taqare da sulyman din,,domin tana da tarin tambayoyi akanshi.


Bayan tayi wanka ta kintsa,kana kuma gwaggon tatsareta taci abinci sosai,daga nan kuma gwaggon tasata yin baccin dole,acewarta bataso a wahalar mata da jika,kamar kuma tasan me keh ran amatullah din tace,mijinki tafiya takamashi xuwa abuja jiya ta gaggawa shiyasa baki ganshi ba,amman yasanar dani yana hanya yau da yardar Allah.


Bayan fitar Gwaggon neh tacigaba da bitar xantuttukan dake ranta,acewarta dolene suyi chatting yau...Kwaarai suna da buqatar yin chat adaren na yau...Domin kuwa tana da tarin tambayoyin da babu mai amsa mata su inbashi ba.


    *******

Cikin bacci taji ana hura mata kunneh ahankali,hakan ya tabbatar mata da kowaye,,take kuma tahada girar sama da taqasa hadida yin kicin kicin da fuska tare kuma da qoqarin tureshi daga rungumar dayai mata,,,zuru yai mata da ido yana qoqarin gano abinda ke faruwa,,,a iya sanin shi laifi daya yayi mata dayai tafiya batare daya sanar da itaba,wanda yayi qoqarin tura mata text amman baiyi delivering ba,hakan yasa yakira gwaggo yasanar mata kan cewa amatullah din takwana anan gidan inyaso inyadawo saiyayi branching yadauketa suwuce gida.


Hakan yanuna ma sam bashida masaniya akan abinda yafaru,gwaggon taboye mishi neh akan bata so yatada hankalin shi,acewarta inyadawo tayi mishi bayanin komi,haka kuma taji dalilin dayasa yaboyewa amatullah din xancen laura.


Zuru yai mata da ido yana qoqarin fahimto yanayinta,hakan yabashi damar karantar damuwa da bacin rai bisa kyakkyawar fuskar matar tashi,hakanan kuma ga wata er rama dayaga tayi mishi ayau din.


Qoqarin riqota yake xuwa jikinshi akaro na biyu domin jin musabbabin fishin nata,hakan yayi daidai da ture hannayenshi datayi gamida dirowa daga gadon,mamaki fal zuciyar shi sabida bai taba ganinta ahakaba tun bayan aurennasu.


Fizgota yayi tafado bisa qirjinshi hakan yabashi dāmar sa hannayenshu biyu yarungumeta tsam tayadda motsima gagararta yayi...Mutsu mutsu tacigaba dayi gamida sakin wani wahalallen kuka,aganinta rainin wayoh kawai yake mata,domin kuwa yanda takeji yanxu ko fuskar shi batason gani...yakasanche cikin mayaudaran maza dasuke wasa da zuciyoyin al'ummah! Eh mana yayi wasa da zuciyarta ya yaudareta yaboye mata al'amari mafi girma a rayuwar su,bayan yafi kowa sanin irin tsanar datayi wa kishiya,kodayake baisaniba amman ai tabashi clue akan qin kishiya datake!Wanda inhar bata mantaba har alqawarin bazai mata kishiyaba yayi...!


Infact miyasama xata manta,bayan akan wannan condition din tayadda ta aureshi wanda tun äwanchan lokacin batagama sanin dadin so ba,batagama sanin dadin kasanchewa da abin so din ba,haka nan bata tantance meye akewa kishin ba,meye haqiqanin auren awannan lokacin bata saniba!


Sai yanxu dare daya al'amura zasu juye ahaka...Sai datasaba dashi,yakoya mata sonshi,haka zalika tasan dadin auren sannan wannan mugun labarin zai isomata...!Take tahau dukan qirjinshi da iya qarfinta tana rusar kuka,hakan yataimaka wajen bibbige mishi fuska da dukkan qarfinta.


Cikin wata iri tsawa ya dakatar da bige bigen nata,sakamakon qoqrin dayayi naganin ta daidaitu amman hakan yaci tura....


Are you insane amatullah?Kina cikin hankalinki eyeeeh?Yacigaba da dakamata tsawa...Kinutsu banason hauka..Domin bazan lamunci duk wani abu dazai tabamun baby bah!Jibi yanda kika wahalar dani kika wahalar da kanki for God's sake...All in d name of what?Ya girgiza kai...Well i have no idea!


Yes i have no idea..bansan miyasaki wadannan abubuwan ba,if something is wrong you suppose to let me know bawai kituburemun ba kina neman kitakurawa abinda keh jikin ki...Wanda kinfi kowá sanin bazan dauki wannan shirmen ba,sabida haka compose your self and let's talk...Ya ida maganar yana zare mata idanuwanshi masu kama da namaijin bacci.


Yes let's talk....I mean sorry let's chart!

Seat down,yazaunar da ita bakin gadon kana ya dauko wayanta dake chargy ya kunna,ba'a dau lokaciba ya kunna data din wayar gamida miqa mata...Wanda har Lokacin bata fasa kuka ba da jan majina...Daya daga cikin kujerun dake facing dinta yazauna kana yacigaba da kallonta yanajiran abinda zatace.


  ********

Vote vote and vote....It really matters to me.

  Nagode😍

Noor.


13


RAINA KAMA


I'm waiting shine abinda yai mata sending ganin har awannan lokacin taqi tace mishi komi.


Jitayi gaba daya duniyar tayi mata qunci,haka zalika tsabar takaicin datakeji yahanata ta iya rubuta mishi komi,hakan yabata damar kife fuskarta akan chinyarta gamida sake rushewa da sabon kuka.


Dafe kanshi yayi cikin tsananin bacin rai...Duniya ba abinda yatsana irin kuka,kukan ma irin wannan datake tsulawa da iya qarfinta,wanda sai ka rantse da Allah naman jikinta ake yanka....Runtse idonshi yayi gamida daka mata wata irin tsawa..Wanda yayi nasarar firgitata tayi hanyar waje a sittin,hakan yayi daidai da banko qofar da kausar tayi cike da tsoro.


Karo sukayi da juna wanda dakyar kausar din tayi qoqârin riqo amatullah din ganin tayi baya zata kife aqas,ko kafin su nutsu yasake doka wata tsawar wanda yasasu qwaqume juna cikin firgici...


Wallahil azeem wani abu yasami baby nah bazan qyaleki ba,sautin muryarshi yadoki kunnuwansu,take kuma ta tsugunna qasa tana mai cigaba da burari aganinta wannan cin fuskar har ina?Itama kausar din binta qasan tayi don ganin ta lallasheta,ita tarasa wannan baqin kishi irin na amah,magana tunjia amma taqi wucewaa awajenta.


Cikin lallashi tacigaba dabata baki akan cewa tayi hakuri takoma bisa gado,haba anty amah kin manta abinda doctor yagaya miki neh?ko kinaso kijawo wakanki wata matsalar neh again...?


Mamaki yagama kasheshi azaune,meye hadinta da likita kuma?Miyasameta da har doctor keh bata dokoki?Keh xonan ya dakawa kausar din tsawa,afirgice ta rarrafa inda yake xaune yahade

girar sama data qasa,cikin daurewar fuska yace miyafaru da bana nan?


Da dan in ina tafara cewa,amm uncle man dama,dama jiyy jiyaneh anty laurah tazo gidan nan shine suka sami misunderstanding da anty amah ta zazzageta,tunda yaji ta ambaci laura jikinshi yayi sanyi...Sai yanxu yagano musabbabin fishin nata,


Bt dama ance tabarmar kunya da hauka ake nadeta,hakan yasashi sake tamke fuskar shi kai kace duniya baitaba dariya ba,and so?Sai meh yafaru? Cikin sauri kausar din tace shine shinefa anty amah din tasuma,har muka kaita asibiti nida gwaggo,dazu da safe aka sallamomu ta ida maganar cike da tsoron kawun nata,domin dai tunda take dashi bata taba ganinshi ahaka ba!


Tashi kitafi shine abinda yace mata,cikin sauri tamiqè tayi hanyar waje,wanda yayi daidai da miqewar amatullah din itama dasauri don ganin tafice mishi daga dakin....Keh dawo nan!Kar kisake kifita daga dakin nan tatsinto muryarshi yana bata order.


Kunnen uwar shegu tayi dashi tasakai tafice da saurinta,kokafin tai yunkurin dosar corridor din dazai sadaka da dakin gwaggo ya chafko ta...Daukarta yayi hadida toshe mata bakinta da nashi don ganin tana shirin wage baki ta tara mishi jama'ah,dama kausar a guje ta banka dakin dake kusa dana gwaggo.


Key yasaka ma dakin gamida tattarata ya watsa bisa gado,kokafin tai yunkurin yin wani abu yakashe switch din dakin duhu ya maye gurbin hasken,bige bige tahauyi sakamakon gane manufar shi akanta.


Lallaima namiji baida kunya,duk wannan dibar albarkar dayayi mata shune kuma yake shirin rarako wani aikin nadaban,aiko koh yau ko yafi waye naci nan xai ganta yaqyaleh,ai yanada wata matar yaje tabashi abinda yakeso.


Malama banson shirme kinutsu kibani haqqina,kan wannan shirmen kike ta kunbura kina tada jijiyoyin wuya,mtsw yaja tsaki mata kuna da matsala wallahi ya ida naganar yana qoqarin rabata da guntuwar rigar baccin dake jikinta


Batayi qasa aguiwa ba tasa qafa ta hambareshi da iya qarfinta,gamida gantsarawa hannunshi çizo,dasauri yadagata gamida sa qafafunshi ya lanqwar da ita,hakan yabashi damar banqarota gamida hada bakinshi danata a fusace...


Duk yanda takai ga wutsi wutsil saida jikinta yai laushi laqwas,wanda dole tabada kai yayi abinda yagadama da ita,komawa yayi yakwanta yana sauke numfashi bayan samun nutsuwar shi,hakan yasa ya tattaro ta ya matse a jikinshi...Itama din lamo tayi tana maida numfashi don baqaramin wahaluwa tayi ba a hannunshi....


Tanason mijinta,tana matuqar sonshi wanda hakanne yataimaka wajen assasa wutar kishinshi a xuciyarta,dolene ma yaxaba ko ita ko laura! bazata taba iya sharing dinshi da wata banza bah,taqarasa maganar tana hararshi fakaice.


   **********


Kuyi hakuri da wannan!

Nagode😍


14


RAINA KAMA


01:59am


A fusace yatashi yafita daga dakin baccin nasu sakamakon kukan da amatullah din keyi tun bayan barowarsu gidan gwaggon...


Ahaqiqanin gaskiya yafara gajia da wannan sabon iskancin datake mishi tun kwanaki ukun nan dasuka gabata....Kanta akafara kishiya dazatabi ta tada hankalin jama'ah.


Yai kwafa cin tsabar jin takaicinta a ranshi akaro na biyu...Shi yarasa wannan kafiya tata,ace mutum magana bata wucewa a gurinshi,duba da irin lallashin da mahifiyarshi tai mata,hakanan kuma tadauki laifin duka tadora akanshi,takumasa shi yabata hakuri amman duk da haka tadage akan lalai sai yazaba ko ita koh lauran.


Yasake jan tsaki gamida dafe kanshi da hannayenshi,,"bayajin xai iya sakin lauran domin jin dadinta,ko banza biyayyar datake nuna mishi da rashin nuna jin haushinshi akan wulaqancin dayake mata bazaisa yasaketa ba....Infact bayarda za ai yasaketa!Sabida yana ganin yin hakan kamar biyewa amatullah dinne da nuna chanchantar ta akan abinda takeso.


Wanda shi a iya sanin shi bata kai wannan matsayinba dazata ke sashi abu yayi...Waye ma yagaya mata sonta yake,?Aikin banxa...Batasan bata gabanshi ba sam hartake taqamar batason kishiya.


Motsin shigowarta dayan bedroom din dayake neh yadawo dashi dga tunanin da yake,hakan yasa yayi maza yahade fuska gamida nuna mata qofa.


Get out from here...Shine abinda yafara cewa tai tsaye tana kallonshi cike dason sake fashewa da kukah,i said get out koba kiji nane...? Watoh don tsabar neman magana nabaro miki chan bai ishekiba shine xakisake biyoni nan ki isheni koh?


Toh saurara dakyau baxan dauki wannan iskancin naki ba tunda nalura bakyajin lallashi,hakan ko yasa taqara sautin kukanta tana maiqoqarin hawa gadon domin tafada jikinshi,aganinta hakanne samun sauqin zuciyarta alokacin.


Karki kuskura ki matso ni,yafada da wata kakkausar murya wacce tai bala'in tsorata ta tai xuru tana kallonshi baki sake,yes!Karkisake kitabani,domin nagaji da wannan halin naki,kanki aka fara kishiya daxakibi ki hana kanki sakat?Aikin banxa kawai.


Nan take tatsugunna tariqe kafafunshi tana mai qara sakin kuka,tureta yadanyi ahankali kana yajuya yaruntse idanuwanshi,domin kuwa tabala'n kaishi qarshe,gara kawai ya yada qwallon mangoro yahuta da qudah!Haba!inbanda qaddara mixaici ma da bebiya.


Kuka take da iya qarfinta,irin kukan nan mai ban haushi hakan yasa yajuyo a fusace yadauketa da wani wawan mari wanda saida tawuntsilo daga bisa gadon,hakanan kuma bartaba yasa qafa yai ball da ita,ihu tacigaba dayi cikin tsananin gigita.


Nonsense get out from here,yarinya kinbi kinhana kanki sukuni,nima kinhanani akan dalin dabai taka kara yakarya ba,wama yace miki sonki nake daxakibi ki addabeni...Ba a aurene keh aka aureki,jibeki da Allah...Inbanda qaddara uban mixanci dake? Ko angaya miki lukutayen mata kalata neh?


Ihu take da iya qarfinta aganinta baa taba mata chin fiska irin na yau ba!Innalillahi...Yau sulyman din datake taqama yna matuqar sonta neh yaimata haka?Shin idanunta biyu ko mafarki take?


You better get back to your senses malama!Muryarshi tadawo da ita daga guntun shudewr tunanin data shyga...Yacigaba da masifa gamida turata waje cike da bacin rai,wanda ita kuma kafiya yasa tai tsaye qiqam taqi tafiya.


Wallahi albarkacin cikinnan kike chi har kika kawo iyanxu..If not datuni kîndade da tsufa a qauyenku...Haka kawai zaki hanamun sukuni kamar angaya miki keh din wata tsiyace a gurina,,,dake baki da kunya xaki kalli tsabar idona kice inxaba koke ko laurah!


Cike dason quntatat mata yacigaba da watso mata baqaqen maganganu...Inake ina hada kanki da matata?Inbanda qaddara keh kinsan ba abinda xanyi dake!Sabida haka inkinji baki iyawa kina iya qarawa gaba...Wanda yin hakan zaifaru neh bayan kinsauke ajiyata dake jikin ki.


Laqwas tayi aqasa jikinta na rawa,duniyar ce kuma tacigaba da juyamata...Hakan yasa tachusa kanta cikin qafafunta cike da dimbin tashin hankali!


Ya salam....Wannan wace iriyar muguwar ranace agareta....Shin ashe akwai irin wannan rana dazatazo wa rayuwarta?Ashe mafarkinta nasamun farincikin rayuwarta ba gaskiya bane...Ashe akwai irin wannan ranar dazata fuskanci chin mutunci daga mutumin datafiso da qauna aduk fadin rayuwarta?Ashe?Ashe haka namiji yake?


Take tasaki wani marayan kuka,cike da neman dauki,,,batare da saninta ba taji ya watsata waje gamida sa wa qofarshi key cike da tsananin jin haushinta aranshi,bayan ya watsa mata warning akan karta kuskura taqara kusanto shi inbahaka ba zai bata mamaki!

  ******

Kuyi hakuri da wanann,and pls idan kunji n shiru don Allah kuyi hakuri abubuwane suke mun yawa,bt in sha Allah zanke ganin nayi muku qoqarin koda chapter daya neh in every two days!

Nagode😍


15


RAINA KAMA


Chanjin rayuwa shine qalubalen da amah ke fuskanta agidan aurenta,hakan yafaru neh tun bayan daren da sulyman din yafito qiri qiri yafada mata matsayinta azuciyar shi.


Tabbas sanin hakan yafi komi dagula mata lissafi fiyeda duka,zagi dakuma tarin chin mutunchi da wulaqanchin dayai mata a daren,wanda hakan yayi sanadiyar ficewarta daga hayyachinta,hakanan kuma zuciyarta tai mugun shyga wani yanayi sakamakon hakan.


Chanzawar shi dga wannan mijin nata mai jinqanta da qaunarta yafi komi dga mata hankali,takan xauna tadinga tariyo danxaman dasukai tare wanda yake cike da shaquwa da tsantsar farinciki,shin dama akwai ranar dazatazo dazata fiskanchi maraichi irin wannan?Kaichonta da sakankacewa da halin da namiji.


Taruntse idanuwanta dasuka jeme suka chanxa kala sakamakon kukan dayaxame mata jiki ayanxu,hawaye masu zafi suka cigaba da gangaro mata bisa kunchinta,hakan nan kuma tachigaba da shafa cikinta da ayanxu yatasamma wata uku da kwanaki.


Shikadai neh abinda yarage mata aduk fadin duniyar nan dazata bugi qirji tace nata neh,wanda daga dukkan alamu wanda yai cikin qoqarinshi yarabata dashi da zarar tahaifeshi.


Tunanin hakan yasata sake qanqame jikinta cikin jin tsananin tashin hankali tunkafin yiwuwar hakan!

Baxata taba amincewa a rabata da danta ba,bazata taba lamuntar hakan ba har abada...Gazawarta tafannin magana bashi zaisa gazawarta tanan fannin yayiwu ba.


    ********


Malama duk wannan kukan minafinchin ba inda zai kaiki,kitashi kiwuce kije kichi abinchi da wallahi ina mai tabbatar miki wani abu yasami babyna sai munyi shari'ah dake,yadaka mata tsawar datasata tashi dasauri tanufi abinchin da yashygo mata dashi.


Duniya kenan!Yau ita sulaiman yamaida tamkar bolah acikin gidan shi...Tafara chin abinchin jikinta na rwa kasanchewar tsaye dayayi mata aka yana maijin tamkar yadoketa don haushi.


Yacigaba da balbaleta da masifa ayayin datake chusa abincin dayazame mata kamar magani,kigama kije ki wanke mun toilet, haka nan kuma kittabatar da kin gyaramun gida,sabida naga alamar kina naima kimaida mun da gida tamkar bola...Kodaye ba laifin ki bane wasan danafarayi dake tunfarko neh yajawo hakan.


Yacigaba da gindaya mata tsauraran matakai akan yanda yakeson ta tafiyar mishi da gidanshi...Acewarshi darajar cikin jikinta takechi dahar baiyi mata visa ba,wanda yasanar mata da ceqar randa tasauke ajiyar shi zai sahale mata batare data qara koda minti daya bane.


*******

Haka rayuwa tachigaba da tafiyar mata chikin dimbin wahala da hawayen xuci,domin kuwa ayanxu kukanma yaqafe daga idanuwanta sai dai na zucci,haka nan kuma ta tattara dukkan natsuwarta gurin kula da cikinta,wanda aduk bayan sati biyu sai yasata agaba yakaita awo,domin kuwa yanxu cikin yatasarwa wata bakwai...


Girman da cikin yayi yaqara taimakawa wajen karasakata kumburi,hakanan kuma jikinta yaqarayin kyau sosai duk da rashin kwanciyar hankalin datake ciki...


Gwaggo da khausar basu fasa kula da itaba,domin kuwa aduk qarshen sati sai sunxo sunganta,inda sukyman din yaimata jan ido akan chewa koda wasa kar yasake yaji tagayawa Gwaggo din wata magana data danganchi xamansu ayanxu.


Dama kuwa yadade da tarewa a gidan laura,acewarshi bazai iya rayuwa ba maceba!

Wanda shikanshi yasan bawai don chanchnatar yasa yaliqe a guntaba illah don gujewa fadawarshi wani hali,hakanan kuma don quntatawa amah din.


******

Zaune suke a gaban likitan dayake kaita awo...Bayan yagama dubata neh yabuqaci jin meke damunta neh sakamakon ganin jininta daya hau,wanda sam ba'ason mai juna biyu da hakan.


Shiru tayi gamida sunkuyar dakanta,sakamkon ganin hararar da Sulyman din ke jifanta dashi a kaikaice.Nan dai likitan yacigaba da bata shawarwari akan tarage duk wata damuwa domin ganin tasauka lafiya.


Tun a mota yake balbala mata masifa,zancen dai baiwuce xaibata mamaki intakashe mishi baby,aikin banxa dake bakisan wahalar samun yaranba shiyasa kike nema ki kashemun yaro.


Zuru tayi tana mamakin wannan ikon Allah irin na Sulyman, ita ahalin yanzu yama daina bata mamaki ikka tsoro dayafara bata,anya zata iya tsira da jaririnta daga mutumin nan?


Itadai tasan ko sama da qasa zata hade bazata taba yadda yarabata da danta ba,koda kuwa hakan xaisa tarasa ranta neh....


16


Raina kama...!


   Kamar cikin bacci taji mutum na qwaqwumarta,hakanan kuma yabi yadanneta yana shafarta cikin wani irin salo,da hanzarinta tazabura gamida wage baki da niyyar sakin ihu,ko kafin ihun yasami damar fita yasanya hannayenshi yatoshe mata baki.


Keh malama nine karki taramin mutane,jin muryarshin baisa tafasa fizge fizgen datake ba,domin kuwa jitayi zuciyarta na tafarfasa bisa ga wannan dibar akbarkar da dantahalikinga keh neman yimata da rana tsaka...Wallahi bata taba ganin mutum mara tausayiba irin Sulyman.


Duk iya qoqarinta naganin tahanashi abinda yke nema hakan baisa yahaqura yaqyaleta ba,illa qoqarin dayayi naganin ya sarrafata da dukkan iyawarshi don ganin bai takurawa babynshi dake jikintaba,kuka kam tasha shi harta godewa Allah.


Gaba daya wata iriyar tsanarshi keh ratsa jikinta,haka nan kuma ga wani axababben xafi dake fita daga qasanta,don kuwa baqaramar wuya tasha a hannunshi ba,kai kace ya shekara goma ba mata..


Baya yayi rigingine yana maida numfashi,shikanshi bazaice ga dalilin dayasa yakasa controlling kanshi ba,gaba daya yarasa mike damunshi,sam baya samun nutsuwa da laura, ganin hakan yasa yakoma harkar neman matanshi amman sam yakasa jin abinda yakeji atare da amah din.


Tsaki yayi gamida daka mata tsawa,malama karki isheni da kukan banxa,haqqinki nasauke miki bawata tsiyaba,karkuma hakan yasa kidauka keh din wata tsiyace,ya ida maganar gamida miqewa tsaye domin suturta jikinshi.


Lamo tayi bisa gadon tana maijin tausayin rayuwarta,miyasa batada sa'ah neh,tayi sauri tayi istighfari don ganin tana shirin yiwa Allah shishshigi bisa yadda yatsara rayuwarta,ahankali tacigaba da rera kuka cikin sarewa da rayuwar baki daya.


Qugunta dayake mata ciwo tun kwanaki uku dasuka wuce yacigaba da mintsininta,sannu ahankali kuma jikinta yahau rawa gamida saukar wani azababben zafi a qarqashinta,juyi tacigaba dayi gamida ambaton Allah,domin kuwa tagama sadaqarwa da lokacintane yazo.


A daddafe tasauka bisa gadon tararrafa toilet domin jin wani ruwa nabin qafafunta,haka nan kuma sai taji kamar zatayi bayan gida,inbanda gumi babu abinda take yi,kafin tasan inda kanta yake mararta tai wani irin katsawa,wanda yasata yin qasa a tsakiyar bayin tana ambaton Allah.


Nishi take da iya qarfinta don jin wani abu naturo qasanta,hakan yasa tai wani irin tsugunno tana runtse ido cikin tsananin azaba,kafin tasake sanin menene,sai tsinatar ihun kukan jariri taji aqasa,hakan kuma yayi daidai da shigowar gwoggo itada kausar cikin dakin suna mai qwala mata kira.


Ai har rige rigen shiga bayin suke donjin kukan jariri yacika dakin,mamaki fal fuskokinsu,domin kuwa sam basu kawo haihuwar yau ba,E.D.D Dinta yanuna sai next two weeks,hakan na nuna dayayi latti kenan.


Gwaggon ce tataimaka mata don ganin uwar tafito,hakanan kumâ tayanke cibin babyn dayake ta tsandara ihu gamida rarumar hannu,da'alama da yunwa yadiro duniyar tamu,koda gama yanke cibin sai ganin amatullah dintayi taqarashe sulalewa qasa gamida kwallah wata iriyar qara.


Nan fa hankalin gwaggo da kausar yatashi,gaba dayansu sunrude sun rasa abinyi,ga wannan acicin daya iso duniya yahanasu sakat da kuka,kausar dince tai qoqarin danna wa kawun nata kira.


Hello uncle man kazo gida yanxu don Allah,anty amah bata lafiya,bata jire mizaiceba takashe,gamida danno numbern matar qannin sulyman din,don ganin number din Muhammad din baya shiga.


Agaggauce tasanar da khadija matar muhammad din abinda kefaruwa,itama din arude tace gasunan zuwa gidan yanxu,sunyi qoqarin kintsa amah din duk da har a wannan lokacin batasan wake kantaba,inbanda wani irin gurnani babu abinda takeyi,hakanan kuma baby baifasa kukanshiba,duk kuwa da jijjigashi da kausar Keyi


    ********


Zaune suke gaban malamin da aka samo tunbayan ganowa da akai cewa akwai shafar jinnu cikin lamuran,domin kuwa wasu irin iface iface datake musu wandä har alokacin bata bude idontaba.


Inbanda wani irin gurnanin kuka babu abinda take,gaba daya tagalabaita wanda dole inkaganta tabaka tausayi,abin takaicin har a lokacin ba sulyman babu dalilinshi,wanda gwaggon tace arabu dashi kar asake nemanshi.


Muhammad neh yayi ta xirga xirga don ganin duk wani abinda ake buqata ya wadata,wanda hatta malaminma shawarar wani abokinshine sakamakon ganin yanayin amah din.


Malam kabir wanda yakasanche malami neh fitachche daya qwareh a fannin ruqyah,wanda tunda aka shygo da amah din yace sukwantar da ita,kana kuma yabada umarnin muhammad yatsaya sauran kuma sujirasu a waje.


Gurnaninta neh yacigaba da tashi,wanda a wannan lokacin da iya qarfinta takeyi,malam din yacigaba da fesa musu karatu cikin iyawa da qwarewa,kafin wani lokaci tafara wani irin girgiza gamida daga hannaye sama.


Dakatawa yayi da karatun domin fahimtar niyyar su tayin magana a wannan lokacin,hakan kuma yasa yaqara fahimtar cewa aljanun kurame neh.


  ******

Zaune suke gaba daya agaban malam din bayan lafawar al'amurah masu ban tausayi,a inda tu shigowar su gwaggon amatullah din tararrafa kusa da ita gamida sanya kuka ahankali.


Zuru sukayi suna mai jimamin lamarin hakan nan kuma suka baza kunnuwa domin jin abinda yake shirin fada musu,wanda har alokacin er tsohuwa dada bata fasa fyace majina ba gamida sharar kwallah don tsananin tausayin amah din,aganinta wannan yarinya taga rayuwa a yau din,ga azabar haihuwa ga azabar aljannu.


Bayan malam yabude taron da addu'ah yakuma dora da godewa Allah bisa samuwar nasara acikin aikin,yacigaba dacewa "watoh ahiqaqanin gaskiya yarinyar nan tadade tareda wadannan aljannu,domin abayanin dasukayi sunkai aqallah shekaru goma sha biyar ajikinta,a inda suka nunamin cewar taka musu da tayi alokacin har yakai ga samu nakasa a hannunshi na hagu,wanda sanadiyar haka yasa suka shigeta.


Shigarsu jikinta yasa suka dauke mata baki,ma'ana hanyar yin magana,wanda hakan yasamo asali neh kasantuwar su na su din kurame neh a jinsin nasu,amma yanxu kam alhamdulillah munyi nasarar rabata dasu,a inda kuma sukayi alqawarin barin rayuwarta har abada.


Sunanta malam din yakirah,wanda duk sunbaza kunnuwa suji mizatace,a hankali tadago kanta gida cewa naam!Wayyoh Allah karkuso kuji dadin murya gurin wannan baiwar Allah,yanxu meke miki ciwo?Malam din yacigaba da tambayarta...,anan take kuwa tace mishi,babu komi tanajin kamar ansauke mata wani nauyi a maqogwaronta.


Hamdala malam din yayi,kana yacigaba da bata shawarwari da addu'o'in dazata riqe domin samun kariya daga mutanen boye,er tsohuwa dada inbanta riqe baki babu abinda take,hakanan kuma bata fasa tsinewa wadannan aljanu ba acikin xuciyarta,aganinta suntauye wa jama'ah sauraron wannan Shigarsu jikinta yasa suka dauke mata baki,ma'ana hanyar yin magana,wanda hakan yasamo asali neh kasantuwar su na su din kurame neh a jinsin nasu,amma yanxu kam alhamdulillah munyi nasarar rabata dasu,a inda kuma sukayi alqawarin barin rayuwarta har abada.


Sunanta malam din yakirah,wanda duk sunbaza kunnuwa suji mizatace,a hankali tadago kanta gida cewa naam!Wayyoh Allah karkuso kuji dadin murya gurin wannan baiwar Allah,yanxu meke miki ciwo?Malam din yacigaba da tambayarta...,anan take kuwa tace mishi,babu komi tanajin kamar ansauke mata wani nauyi a maqogwaronta.


Hamdala malam din yayi,kana yacigaba da bata shawarwari da addu'o'in dazata riqe domin samun kariya daga mutanen boye,er tsohuwa dada inbanta riqe baki babu abinda take,hakanan kuma bata fasa tsinewa wadannan aljanu ba acikin xuciyarta,aganinta suntauye wa jama'ah sauraron wannan daddadar murya ta wannan er tahalika kamar ana busa sarewa,sabida dadinta da sanyinta.


****

Some hours later

Zaune suke itada kausar acikin dakin da aka ware mata a nan cikin gidan tsohuwa dada,acewarta babu inda yadace datayi wankan daya wuce gidan nata,acewarta ko banxa tariqa sauraren muryar amah din wacce tsabar dadinta bazakaso tayi shiru ba yayin magana.


Kausar dince keh zolayarta tahanyar cewa...Kai anty ammah har naqoasa uncle man yazo yatadda wannan abin mamakin,lord!Har bansan irin farin ciki dazaiyi ba.


Tabe bakinta tayi gmida qara rungume kyakkyàn babyn nata,wanda babu abindä yarabashi da ubanshi,kaman antsaga kara,hatta gefen kumatun slyman din dayake lobawa,shima babyn nashi haka.


Kausar dince takatseta tahanyar cewaa,anty amah miqomun yaron nan,halan sai yatsotseki kafin wayewar gari,ni narasa wannan chi na wannan yaro haba...!Ta ida maganar tana shirin daukar shi.


Aiko kaman jira yake yasake chanyara kuka,dadā ce ta shygo dakin cikin sauri har tana tuntube,wai menene ake takurawa maigidana neh?dada yaron nan yafiye chi wallahi cewar kausar din,,aiko dadan ta dalla mata harara gamida cewa bashshi yaci ubanshi yabiyo,bawanda yakai manu chin abinci alokacin yana yaro kaf gidan nan,sabida haka kusakar wa yaro mara ya shana.


Ungo maza bashi yasha,yaitasha har sai yature,tadora mata shi akan qafarta,Cikin shagwaba tace Allah ni dada nono nah xafi yake kaman xai tsinke,kigani fa...Ta ida maganar tana nunwa dada nonon nata dayai sharr gwanin sha'awah,alamun jego yakankama,dama kuma tubarkaAllah Allah yahore mata na fulani masu kyau lafiyayyu.


Rufe bakinta yayi daidai da hada idanunta da Angon qarni,wanda yai tsaye yan binta da wani irin kallo wanda ninan nakasa tantance shi,domin kuwa kallone na tsantsar "Keh nake so"


Take kuwa ta tattaro gabas da yamma,kudu da arewa ta tamke fuska,kai kace duniya ba'ataba halittar annuri da murmushi akan fuskarta ba!

*****

Vote and comment pls.

I will appreciate that.

Nagode😍17


RAINA KAMA


Ganin yanayin ama din yachanxane yasa dada saurin fuskantar qofar,ai kan kuce kwabo dada tahada rai kai kace ita akaiwa laifi!Harda su mutsi mutsi da ido alamun masifa na chinta.


Ganin hakan yasa shima gogan naku yaqaraso ckin dakin gami dasamun matsugunni akusa da madam din yana mai sakar mata murmushi,hakanan kuma yasanya hannayenshi yasunkuci danshi gamida qarewa hadadden jaririn nashi kallo.


Jibeshi da Allah ko kunya yazo gandai gandai yadauki dan da saida yagama shan azaba kafin isiwar shi dunia,amma sabida rashin imani irin naka manu sai yanzu kake ganin jininka,dada ta ida maganar gamida riqe haba.


Harara ya kaikace sakar mata gamida cewa nifa dada bansan sa ido,kikasan uzurin daya riqeni?Kema kinsan yanda nakeson iyalina ai,baa son raina hakan yafaru ba.


Kai da Allah rufe mana baki,kai däi wallahi baka da kirki,katuba kabi Allah kadena abubuwan dakake,ace jibi yarinyar nan irin gwagwarmayar data sha a yau dinnan ai abin ace kana kusa da itane,amman kana chan kana gantali agari,taqarasa zancen tana harararsa.


Shima din harararta yake gakuma haushinta dayaji yanaji ganin tanaqarawa wuta fetur instead of ta tayashi lallashi,shiyasa da hanzarinshi yajuya gamida rungoma amah din daketa chichchin magani tun shigowarshi,aganin shi yin hakan zaisa tsohuwar nan tabarshi yagana da iyalinshi da kyau.


La'ilaha'illahu yau naga abinda ya isheni,don ubanka saketa,,ta lailayo ashar...Sabida dibar Albarka zakazo kana qwaqume yarinya yau yau da haihuwa dôn baqar jaraba,,,,oh ni rakkiya yau naga abinda ya isheni...Ta miqe afusace tanufo shi.


Dama ita wadda aka qwaquma tagama sandarewa azaune,hakanan tunaninta naga yanda zatai ta gurza wa mutumin nan dibar albarka,batakai ga dire tunaninta taji hannuwanshi arigarta,sai kici kicin ciro nono yake wai danshi bai qoshi ba.


Ko kafin dada tai wani yunkurin hanashi ita tayi ta hanyar bige hannuwanshi gamida jan mugun tsaki tamiqe tafice afusace,hakan yaqarawa malam acici qara sautin kuka,,kamar zai cinye jama'ah,sai faman rarumar hannaye yake yana chanyara ihu.


Dadar ma harara taja takaikaice tawatsa mishi gamida cewa kai dai anyi girman kawai,yarinya nazan zamanta kaxo ka addabeta,toh tace batason gsninka antaba dole?Mtsw tsaki gamidayin gaba tana mita,hakanan kuma taqi kula da inya inya din da jaririn nashi ketayi,tace yaji ajikin shi shima.


Mutuminku haka yamiqe yana zagaye dakin gurin lallashin baby,shi burinshima yasamu yayi shiru koyayi masa huduba amman gogan naku acici kamar qara zigashi ake,don yanxu har wani qara mimmiqewa yake don kuka.


Hankalin emmaza fa yatashi yadugunxuma,gaba daya shima yagama rudewar yama rsa ta yanda zai cigaba da lallashin,daga qarshe afusace yafice zuwa dakin dadan don yasan bata wuce chan din,aganinnshi dontaga yana lallabata neh shiyasa hartake mishi iyayi,amman yanxu xaiyi maganin abin.


Kodaya tura qofar bedroom din khausar ce ke kwance agadon,gakuma dada chan bisa sallayah tana gabatar da sallah,tsawa yadakawa kausar din,agigice tamiqe sakamakon baccin dayafara yin awon gaba da ita,


Saida yafara galla mata harara kana yace mata ina amah din,cikeda gundira da halin kawun nata itama tace batasan inda tashigaba,keh banason shashanci bakisan inda tashigaba kamar yaya?Yafara nunota da hannu cike da bacin rai.


Dada koh dama Allah Allah take tasallame tai mishi wankin babban bargo dagashi har dan nashi dayabi yacika wa jama'ah kunnuwa,don yanxu har jinjirin ma haushinsa takeh ji aganinta dagashi har ubanshi sun takurawa baiwar Allah amah,yarinyar datasha gwagwarmayar rayuwa inji ta.


Kai dai anyi sallamamme...Yau ni naga abinda yafi qarfina,tariqe haba!Kana taciga...Yanxu dakazo kana mazurai mu muka kar zomon?Toh rataya aka bamu,haka kurum kazo zaka hana yarinya rawar gaban hantsi,naga nonon nan kaima kana dashi...Saika dauka kabashi tunda ita tace bata badawa ko antaba dole?Tai mitsi mitsi da ido tana watsa mai harara.


Shi mamakin dada yaqi yadena kashe shi,wai yaushe tafara son amah har haka datake tamishi dibar albarka tundazu,tafa fara kaishi bango,ya rama harararshi gamida yin tsaki yafice domin kuwa zazzaqar muryar baby mai amayo kuka taqi tayi shiru.


Falon yakoma yacigaba da aikin lallashi,idan ka kalli da da uban duk sun jigata sunfice hayyacin su,gaba daya dole subaka tausayi,kar ma dai baby dabaisan lallashi ba,wanda tsabar chanyara kuka muryar ma tazo kadan kadan take fita...Anci kuka anqoshi...Shima uban qiris yarage kukan bai qwace mishi ba dominnkuwa yau yaga tashin hankali qiri qiri.


  *********

Kwance take adayn dakindake gidan dadan,wanda Sulyman din sam hankalinshi bai bashi yadiba chan dinba,sabida ba amfani ake da dakin ba,sakamakon tsohon dakinshi neh zamanin yana xama da kakar tashi.


Juyi take tana jiyo kukan babyn nata har cikin ranta,gaba daya hankalinta atashe yake,tsabar tsanar ganin Sulyman din yasa bazata iya xuwa takarbi danta ba...Data rasa abinyi sai tasaka kuka,yitake cike dajin bata kyautawa babyn nata ba.


Daga qarshe dataji nononta yaqi daina zubar da ruwa,gakuma kukan dan nata datake jiyowa haray disashe sabida ihu yasa jikinta yadau rawa,hakan nan kuma tayanke shawarar taje ta amso abinta tadawo..


Cikin sanda tafito daga dakin tana dube dube,chan tahango su azaune akan Capet, yadora dan bisa kafada yana faman jijjigawa,gaba dayanshi yafice a hayyacinshi,shima babyn sai ajiyar xuciya kawai dayake hakanan kuma yasanya hannayenshi duka biyu abaki yana tsotsa gwanin ban tausayi.


Take taji hawaye ya silmiyo mata cike da tausayin babynta,hakanan kuma haushin sulyman din ya nunku azuciyarta,aganinta duk shi yajawo babynta yawahala haka.,,ko kafin kace kwabo ta sungumi abinta tayi baya da sauri bata ko waige.


Qurawa bayanta ido yayi gamida yin ajiyar xuciya,ko banxa yasan kukan danshi yazo qarshe yanxu,take kuma yaji baya fatan abunda yafaru yau,yakuma faruwa,domin kuwa jikinshi baqaramin gaya mishi yayi ba.


Yanaso yaje yagansu kafin yawuce,amman yana tsoron abinda xaibiyo baya,hakan yasa yamiqe domin ficewa daga gidan,daga dukkan alamu ahalin gidan basa buqatar ganinsa sam a kusa dasu...Gara yaiwa kanshi qiyamul laili yaqara gaba,ko banza yasamu an tafi lallashin danshi abin son shi.


Yanasa kai zaifice yajiyo muryar tsohuwa tana bige mai warning,,,agayas!Kuma kar insake ganin qafafun mutum acikin gidana ehe....Ink bahakaba nikadai nasan yanda zanyi da mutum.


Banza yayi da ita yaqarasa ficewa,domin inyatsaya biyewa dada saitasa ciwon kai yakama mutum,dama sunriga da sun sanya mishi wani,Allah yasani kuma baidama qarfin dazai iya daukar wani,abinda yasani shine bazau lamunci wulaqancin yarinyar ba,dolenta tayi yadda yakeso,domin kuwa bazai dauki raini irn na yau ba sam.!


*********

Pls kuyi hakuri da rashin ganin update dina kamar yanda nayi alqawari,wallahi bana zamane sabida project danakeyi...Sannan kuma ma kwanakin nan bani jin dadi neh,ina mai barar addu'arku don Allah duk dacewa ma nasami sauqi.

  Nagode da qaunar dakuke nunuwa #RK.

We are in this together😍


 18


RAINA KAMA. 


Aqallah sai da Sulyman yashare kwanaki hudu yana xuwa gidan batare da yasake saka amah din a idaniyanshi ba,jaririn shi kam dama har yatafi yana hannunshi babu mai hanashi,dada kuwa dama tadade dayin kunnen uwar shegu dashi aduk lokacin daya isheta da son ganin ta,duk kuwa dacewa itadin batasan meke faruwa ba tsakanin su,itama dama dalilinta baiwuce kar atakurawa baiwar Allaah ba.


Ana jibi sunah neh yakawo laurah gidan,acewarta bata lafiyane shi yahanata leqowa taga baby,tun bayan data daukeshi tai mishi kallo daya bata kuma gigin qara kallon shi ba,domin zuciyarta keta tafarfasa don ganin tsabar kyau da jinjirin kedashi,take taji dunia babu abinda take buqata irin itama taga ta haihu.


Aunty khadija matar muhammad ce tashygo dakin, bata kai ga zama ba,khausar tashygo da dan saurinta,tana qwala kiran amah din...Amah din dake zaune chan qarshen gado tana yanke akaifan qafafunta tadago gamida amsawa,domin koh dama tun shigowar laura gidan tadauke fara'ar dake fuskarta tai kichin kichin da rai,ita dai dunia bata qaunar matar nan,aganinta itace sanadiyar rushewar farin cikinta.


Kama mata hannaye tayi gamida jawo kunnuwanta tana mata rada a kunne,take suka rushe da dariya gamida tapawa!Amah dince tatsagaita dariyar datake gamida hararar kausar din cikin wasa tace,kausar kin rainani koh?Suka sake kwashewa da dariya.


Laura dake zaune tana danne danne waya sungama quleta,aganinta ita sukewa dariya,khdja dake zaune gefenta datariga tafahimci halin data ahiga neh tai qoqarin ganin auntsagaita da iya shegensu tahanyar soko musu da wani zancen.


Amah wai me qunshin nan bazata qaraso bane haka nan,kuga fa yanxu after 11 amma shiru,wallahi maman ilham nima narasa miya tsaida ta,kuma sunyi waya da khausar dazu tace nan da awah guda zata qaraso...Tabawa khadija amsar tana mai qoqarin tube kaya domin chanxa wasu.khadijan ce ta umarchi kausar data sake kiran mai lallen a waya suji miya hanata qarasowa.


Shirun dataji dakin yadauka neh yasata juyowa,riqe da towel din dake daure a qirjinta,charap suka hada ido da angon qarni yana qare mata kallo,ko kafin tasan meke nan,tanemi kausar da khadija tarasa a dakin,sai laura ce a kame bisa cushion tana danne danne a waya kai kace batasan wainar da ake toyawa ba.


Tsaki tayi gamida sake hade rai tajuya tacigaba da abinda take,qarasowa yayi ya tsaya a bayanta rungume da babyn shi akafada,sai tsotson hannu yake yana rarraba idanuwa,dama tubarkallah yadauko idanun maman shi masu shegen kyau da girma.


Karbi yaron nan kibashi abincin shi,ta tsinto muryar shi yna mata magana,kunnen uwar shegu tayi dashi kamar ba da ita yakeba,shiru yayi yana qarewa mazaunan ta kallo,gaba daya taqara kyau jikin nan yaqara zama curvy sakamakon haihuwar datayi,ko macce taganta dole tasake kallonta balle namiji irin sulyman dinta.


Matsawa yasakeyi dap da kunnuwanta kana yasaka hannayenshi yariqo qugunta da hannu daya,gamida hadata da jikinshi ta baya,take ya lumshe idanuwanshi hadi da fatan dama suka sanche ahaka har abada.


Babu zato ba tsammani yaji ansa qafa an naushe shi tabaya,gamida wata irin tsawa"dallah malam ka kama kanka banason shishshigi haba da Allah" taja mugun tsaki tajuya domin sanya doguwan rigan data fidda.


Mamaki yagama kashe shi,rainin amah din har yakai tai mishi tsaki,angaya mata itadin wata tsiyace,take yajuyo da ita gamida hadata da bango,kwata kwata ya manta da wata laurah dake xaune a dakin,batayi auneba ta tsinci bakinta cikin nashi yana watsa mata wani zafaffen kiss...Kissing dinta yake cike da mugunta,domin kuwa baqaramin tsotsa yakewa bakin nata ba.


Gaba daya takasa qwatar kanta,duk kuwa da irin mutsu mutsu din datakeyi,saida yatabbatar data galabaita kafin yasaketa,wanda alokacin tagama shiga qololuwar bacin rai,aganinta baqaramin chi mata fuska yayi ba agaban kishiya,domin kuwa sarai tana sane da ita a dakin tun dazu.


Bai qarasa maida numfashi ba yaji saukar hannayenta tas a fuskarsh ta watsa mishi mari,wanda saukar marin yayi daidai da miqewar laurah itama ta wanke amatullah din da nata mahaukachin marin,domin kuwa haushi biyu neh yahade mata,gana mugun ganin datayi gakuma na marar mata miji datayi.


Zama yayi riqe da kuncin shi cikin tsananin mamaki maras misaltuwa,faruwar al'amarin yazame masa tamkar a mafarki,what!Shi amatullah zata mara?Wannan figigiyar yarinyar ce xata mareshi?Yarinyar daya bala'in rainawa xata debi en yatsu biyar tamareshi,,,shiru yayi yana jinjina al'amarin dayazama mafi girma aduk fadin rayuwarshi.


Itama din amatullah din shiru tayi riqe danata kuncin tana watsa wa laura kallon mamaki,ina ruwanta da ita dazata mareta?Tacigaba da binta da kallon niki ka mara?Yayin da ita kuma lauran tamatsa gefe tana mata kallon ko zaki rama neh?


Laura sai kinyi dansanin sanya qazamin hannunki a fuskata cewar amah din tana nunata da yatsa,daruya tayi gamida qara tunkarota domin ganin me zata iya...Ko kafin suyi wani yunquri yadaka musu tsawa su duka.


Lauran ce kawai ta kula shi,yayinda amah din tacigaba da zazzaga masifa tana hawaye,wanda alokacin tararumi kaya tasanya hadi da nufar sulayman din domin takarbi danta tabar musu dakin,ko kafin tayi wani yunkuri ya murde hannayenta,qasa taxube cike da azaba tana hawaye.


Zuru yayi mata xuciyar shi nacigaba da azalzala mishi akan irin hukunchin dazai dauka akanta,baiyi auneba yaji saukar miyau a fuskar shi,dallah malam kasake ni banson haka...Mamakin dunia yagama hallakashi azaune...Yau shiyaga rayuwa!Shi amatullah kewa wannan chun fuskar kafin yasan miyake tasa qafa ta hambare shi.


Rai abace ya watsa mata kyakkyawan mari afuskarta wanda yasata firgicewa,ashe dazu laura shafa mata fuska tayi ba marinta tayi ba,hawayene suka fara ambaliya a fuskarta.


Nonsense ni zakiy wa iskanchi don kinga ina lallaba ki?You are very stupid...Kafin yadire tace kaima you are very stupid...Infact you are more than stupid,aikin banxa aikin wofi inka isa kadauki mataki mana.


Rainin harya kai yau tazageshi...Tana fada yana fda?Ya salam...Take ranshi yacigaba da raking bala'i,hakan yasa yamiqe domin fita daga dakin idan bahaka ba zaiyi abinda bazai musu dadi ba.


Tun kafin yakai qofa jai saukar takalmi a qeyarshi,ji kake tus yabigi qeyarshi yafado,inkacika kayi abinda zakayi sulyman natsane neka,natsaneka,nayi danasanin aurenka...Fasiqi irinka ba abokin rayuwa bane.


Kafin yasan tunanin dazaiyi sai dai tsintar bakin shi yayi da cewa kije "NASAKE KI" NASAKE KI" NASAKE KI" 

Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un suka tsinchi muryar gwaggo na ambata.


   ********

Vote and comment pls.

 Nagode😍


  19


RAINA KAMA   ....ZARAR BUNU!

Gba daya iyalan gidan galadanchin neh suka hallara a babban falon gidan sakamakon kiran gaggawan da Alhajin ya kira,wanda hakan yafaru neh sakamon afkuwar al'amari mafi muni a rayuwar gidan baki daya.


Har a lokacin amah takasa tantancewa ranta abinda kunnuwan ta suka jiyomata dga bakin tsohon mijinta,innalillahi wa inna'ilaihirraju'oun wannan wace iriyar muguwar rana ce agareta,tasake rushewa da kuka cikin tsananin tashin hankali marar adadi.


Daada kuwa dama ba'a maganarta,sabida hawayen datake ta malalarwa kamar anbude pampo!Wanda saika rantse da Allah ita aka dirka wa sakin,tun faruwar abun taketa qunduma wa sulyman din xagi,acewarta shikam dai bata taba ganin tantirin dan iska irinshi ba,hakan nan kuma tana mai Allah wadai da irin hali na sulyman din.


Oga kwata kwata kuwa ba'a magana....Kallo daya zaka ma fine face dinnan tashi yabaka tausayi,zallar nadama mai cike da dansäni kawai ke kwance bisa fuskar tashi,idanuwan nan sun kada sunyi jazuur,hakan yaba wasu jijiyoyin kanshi bayyana rangadadam!Zufa kuwa sai kwararata yake tamkar wanda ya hadiyi kunama.


Baitaba sanin yanason matarshi ba sai bayan fitar wadannan muggayen kalamai daga bakin shi!Kaichon shi....Kaicho!dama ance danasani qeya ce,,,haka zalika magana zarar bunu ce,intariga tafito bata maiduwa...Domin kuwa yau dayana da ikon maida hannun agogo baya daya maida shi tuni.


Gwaggo kuwa da sauran ahalin gidan sun rasa bakin magana,wace iriyar qaddara ce wannan ta afkawa yaran nan,ayi mutum a rayuwarsa shi sam baida haquri,yanxu wagari yawaya?Buhari da muhammad kam shiru sukai suna jinjina al'amarin yayan nasu a ransu!Saki uku ringis...Haba wane irin abune haka.


Gyaran muryan da alhajin yayine yamaido dasu tunanin dasuka lulaqa,bayan anbude taro da addu'ah neh alhajin yadora da shafin musabbabin abinda yatarasu agurin baki daya.


Dafarko ina mai jaje tareda ta'ajjabin faruwar al'amari irin wannan,haqiqanin gaskiya banjin dadin abinda yafaru ba haka kuma bantaba tunanin faruwar hakan ba,duk kuwa da gaba dayanmu anan munsan qaddara,qaddara ce wadda tariga fata,wanda kaf duniya ba wanda ya isa hana yiwuwar faruwar hakan ba.


Kai sulyman banida sauran abinda xance maka,domin kuwa mai afkuwa tariga data akfu,wanda kaf anan ba wanda baisan babu wani gyara ko kwaskwarimar daza'a iyayi wa lamarin ba,ya numfasa kana yacigaba dacewa......


Duk da bawani abinda xamu iyayi akan alamarin tunda sanin kowa neh babu gyara,ko kome cikin saki uku,amman duk da haka bazan fasa sakeyi maka tuni akan wannan bahagon hukuncin daka yanke bisa kuskure da fishi ba,baka kyauta ba sulyman,kasantuwar ka namiji na nuni da kaifin hankaki da kake dashi fiye da mace,haka kuma duba dazakayi nakasanchewarka shugaba a cikin gidanka bai kamata a tsinceka cikin maza masu yanke hukunci cikin fishi ba.


Munsani saki halas neh,amman yakasanche cikin halas din da Allah bayaso,dadin dadawa kuma ace sakin yawuce daya...Haqiqah Allah yayi hani da irin wannan sakin duk kuwa dakasancewar sa halas,duba da yadda Allah din yafada dacewa Al'arshin sa nagirgiza aduk lokacin da hakan ya afku.


Sannan kuma fadace ta Allah cewa duk mijin daya furta saki uku ga matarshi sai Allah yajarbacesu da son juna matuqaa,wanda awannan lokacin lokaci yariga da ya qure,sannan kuma babu damar gyara kuskuren da aka riga aka tafka abaya.


Ashe mutane bazasui duba da fadar Allah da manzon sa ba su kiyayi yanke hukunci cikin fishi?Meyasa inhar sakin xa'ayi baza ayi guda dayāba?Wanda shi ma dai dayan kanshi saki neh,domin kuwa matuqar miji baice yamaida matar ba,ba wanda ya isa yamaida ta,hakan nanuni dacewa tasaku kenan har abada!


Yacigaba da yi masu fada da nasihu masu ratsa jiki qwarai da gaske,wanda kaf palorn babu wanda jikinshi bai mutu ba,ba a maganar amatullah kuwa,domin kuwa tsabar kukan datake har muryar tazo bata fita,gaba daya tsanar datakeyi wa Sulyman din ce tanema tarasa!Dama tasan bacin raine yasata jin haishin sa.


Sabon sonsa ke huda bargo da qasusuwan jikinta,hakan yaqarasa ta qara sautin kukanta cikin tsananin sarewa!Domin kuwa tasan yayi mata nisa....Nisan da har abada bazaizo kusaba!Kaichonta!Miyasa xai musu haka?Tasake barkewa da kuka cike da nadamar faruwar komi atsakanin su.


Ahankali tadaga kai tasachi kallon inda yake,saida gabanta yafadi ganin yanda cikin qanqanin lokaci sulyman din yachanxa,yarame,yazabgë kai kace yashekara ne yana jinya,gaba daya yafita hayyacinshi,tunda yazauna bai motsaba a gurin,amman duk sanyin a.C din kae falon bai hana bayyanar xufaba a tako'ina a jikin shi.


Fadar irin dansanin dayake ma bata baki neh,baisan inda zaikai tashin hankalin dayake ciki ba,hakan nan har yanxu xuciyarsa takasa yarje mishi da cewa yarasa matar sa har abada...rashi kuwa na dindin!Innalillahi wa inna ilaihirraju'oun!Miya kaishi aikata wannan mummunan furuchin ga matar dayafi so kaf rayuwar shi.?


Sai yanxu ya yadda da ita dinche yakeso tun fil'azal....Itace wadda yake jiräh tun fil'azal!

Itace true love din dayake jiran bayyanuwarta shekaru da dama!Itace dai first love din daya dade yana jira,bai fahimchi hakan ba sai yanxu daya rasaata!Bai san ya tafka babban kiskure ba arayuwar shi ba saiyau!Lahaula wala quwwata illah billah....Allah kakowa mishi dauki.


Kafin kace mene,yagaza riqe tashin hankalin dayake ciki,sakamakon jiyo muryar gwaggo na tambayar inda amah din xata xauna a yanxu,domin kuwa ita kam yanxu yarinyar tagama bata tausayi gakuma kunyarta datake ji kamar me!ace qaramar yarinya kamar wannan tazama bazawara ta qarfi ta yaji,ta girgiza kai cike da jin daci a xuciyarta na rashin suruka irin wannan.


Tacigaba da zama tareda daadan kafin muzauna da kawun nata musan yanda za'ayi,maganar suna kuma acigaba da shirye shiryen yinshi,domin bana son jama'ah su fahimci abinda keh faruwa tukunna,ya furta hakan yana mai kallon gwaggon dake gefen shi.


Kaikuma yajuya ta gefen Sulyman din,ina buqatar shaidar sakin yarinyar nan arubuce domin asan miza anunwa iyayenta,kunya ce kariga da kasa munjita,wannan xai xame maka darasi,idan halinka ne gobe xaka sakeh,tashi kabani guri.


Sunkuyar dakai qaasa yayi yana maijin inama zai iya maida hannun agogo baya?Miyasa su alhaji bazasu fahimci halin dayake cikiba su tausaya mishi?Don Allah alhaji kuyi hakuri ku barmin matata wlhy hakan bazai sake faruwaba...Rabani da ita tamkar rabani da raina neh


La'ilha illalahu....Dadaa tahau tafa hannu tana sallalami,halan manu kafara shaye shaye neh?Tadiro dga bisa kujera tanufo shi afusace tana zabga masifa,mutumin bnxa mutumin wofi,ai dama nasan bakada kan gadoh!Kadirka wa yarinya saki uku sannan yanxu kana soko xancen banxa...Agidan ubanwâ zaa baka matar taka?Kai tsayama ina matar taka anan?Dan banza kasan kanasonta neh kasaketa?Aikin banza aikin wofi,sai kuma ta sake barkewa da kuka cike da jin takaichin rashin yarinya mai kyau dazaqin murya dasukayi.


Buhari neh yayi qoqarin tada sulyman din dayai tsugunne gaban abban nasu yana rusar kuka kamar qaramin yaro!Toh wai dayake sokin burutsunnan me za ayi mishi?Sabida Allah fa!


Gwaggo ce taqara buga mai tsawa akan bata buqatar sake bude idanuwanta taganshi a cikin palourn,amman hakan baisa ya motsa ba,ganin hakan yasa gwaggo ta umarchi nabila da khadija su fita da amah din daga dakin,


Jin hakan yasa kukan datake qasa qasa yasake fitowa fili,domin kuwa aganinta yau shine karo naqarshe dazata sake dora idanuwanta akan mutumin datafiso kaf rayuwarta,...Ganin hakan yasa yai qyam da ido yana binta da kallon kitausaya mun.


Ita dinma tunda suka miqe domin ficewa take waigenshi,hakan yabashi damar narka shanyayyayun idanuwansa cikin nata,wanda hakan yaqara assasa wutar qaunarta cikin qalbinshi....Haqiqa yayi rashin da har yakoma ga mahalliccinsa bazai fasa danasanin faruwar abinda yarabaashi da uwar danshi ba....Ya Allah wannan wace iriyar qaddara ce...Astagfrullah!Allah natuba yafurta hakan yayin da wasu zafafan hawaye ke cigaba da wanke fuskarsa. 


20


RAINA KAMA


Aminu kano international airport kano.

09:23pm


Ciiikin wani qasaitachchen täku irin na manyan mata take saukowa daga matattakalar benen jirgin dabai jima da dira ba,ayayinda yasauke fasinjojin daya debo daga U.K.


Baqar doguwar rigace ajikinta mai adon duwatsu na golden,hakanan kuma ta yane kanta da mayafin rigar wanda yakasanche baqi kalar abayar,kyakyawar fuskarta data kasanche fayau babu make up sai tsabar sheqi datake na zallar natural kyau ta bayyana cikin mayafin,hakan yaqarawa murmushin fuskarta tafiya da imanin mai kallonta.


Masha Allah,doguwace bachan ba,hakanan kuma bata cika qiba ba sosai,sannan kuma babu rama sam atareda ita,zamu iya sanyata cikin sahun mata masu kalar duhuwa,irin kalar nan ne mai wuyar samu mussaman anan africa,domin kuwa kallo daya zaka mata kadauka wata black american ce.


Hakanan kallo daya zaka mata kahango tsantsar wayewa da cikar xati bisa kamilalliyar fuskarta ma'abociyar fara'ah murmushi,wanda idan ka kalleta kallo daya ba lallai bane kahadata da wacchan amatullah din dakasaniba a shekaru biyar dasuka wuce,matashiyace mai kimanin shekaru ashrin da uku a duniya.


Hannunta riqe yake da wani matashin yaro fari qaal wanda bazai gaza shekaru biyar ba aduniya,ba lallai bane ka danganta shi da dantaba,sai dai ko qani domin kuwa sam basa kama,duba da yanayin fatar shi data kasanche jawuur dakuma sumar shi datasha gyara kamar tsatson larabawa.


Amatullah Assidiq ruma kenan,matashiyar er jarida da al'umma zasui matuqar alfahari da samunta,domin kuwa karatu tayi mai ciki da nutsuwa da hazaqa,dawowarta kenan daga qasar U.K sakamakon kammala karatunta na mass communication a jami'ar Greenwich dake UK.


***

Zaune take a reception da'alama jiran mai tarbansu takeyi,dago kanta tayi daga kallon siririn agogon dake tsintsiyar hannunta sakamkon jin datayi yaronta natabo ta.,ahankali tashafa kanshi kana tace sweetheart ya akayi?


Shiru yayi batareda yatankaba,hakan yasa tajuya domin kallon direction din da yaron nata yaqurawa ido...Take gabanta yafadi,hakanan kuma zuciyata tahau tseren gudu akan allon qirjinta.


Ahankali taruntse idanuwanta tana qoqarin saita hankalinta,hakan yasa ta qaqalo murmushi mai kyau ta sakaya boyayyen al'amarin dake tattare da zuciyarta....Qara kwantar da kan dan nata tayi bisa qirjinta tane mai qarewa mutumin dake tunkarosu kalloh.


Bazata taba mance fuskar nan ba,,,ma'abociin fuskar yakasanche wani bangare na rayuwarta mai wuyar fassarawa,,,ahankali ta lumshe idanuwanta sakamakon jin qamshin natacchen turararen shi dayakasance abu nafarko dake tayar mata da hankali game dashi....Ya ilahi how she missed this man!!


Sunkuyowa yayi domin rage tsawon shi kusa da rayuwaka biyu tal dasuka kasanche ababen son sa da qaunar sa....Rayuka biyu dasuka kasanche ababe biyu dazasu cika farin cikin rayuwar shi,rayuka biyu da sanadiyar su yake cigaba da addu'ar samun doguwar rayuwa,rayuka biyu dasuka sanya mishi banbance tsakanin fari da baqi,rayuka biyu dayake fatan Allah yatsawaita rayuwarshi domin ya kyautata musu...Haka zalika rayuka biyu da bazai taba kasanchewa inuwa daya tare dasuba!


Ahankali yaron yadago kanshi daga kafadar mamin tashi yana qara qarewa baquwar fuskar kallo,shafa fuskar shi yayi gamidacewa My boy how are you?Yatambayi yaron yana mai qara nutsa qwayar idanuwanshi cikin na mahaifiyar tilon danshi.


Dasauri yaron yace i'm fine thank you, domin shi dai baisan wannan mutumin ba,,,janyo yaron yayi jikin shi gamida manna mishi peck a kumatunshi yanajin inama zai iya chanza destiny din shi,mamy who is this man?Aslam din ya hankado mata tambaya.


Dasauri tadawo dga duniyar tunanin datashyga gamida daidaita fuskarta,hakan yasa tasake kallon yaron nata dake jikin mutumin data fiso kap raguwarta,sake maimaita mata tambayar yayi "Mammy who is this man?


Zuru tayi da ido tana qissima amsar daya kamata tabashi,hakan yasa tashafo kanshi gamida qara satar kallonshi,wanda shi dama duk abinda yake idonshi nakanta tun zuwanshi gurin.


Aslam he's your daddy,ta tsinci bakinta nafadi,dasauri yajuya ya ruqunqume daddyn nashi domin kuwa yajima dama yana wa mammyn tashi rigima akan shi ina daddynshi,domin yana ganin duj en class dinsu da daddies dinsu insunkawo su school,shikuwa mammyn sa kullum kadai yake gani.


Qara matseshi yayi aqirjin sa yanajin sonshi naqara ratsa zuciyarshi...Oh lord kagafarta min zunnubbai na...Yafurta hakan a xuciyarshi cike da nadamar al'amuran dasuka faru a rayuwarshi.


Dago shi yayi yana qare mishi kallo,kana yace my boy is all grown up!Take kuwa ya qyalqyale da dariya jin ance yagirma,hakan yaqarasa shi maqale baban nashi cike dajin dadi a ranshi naganin daddyn shi daya dade yana muradin gani.


Gefe ta matsa tadauke kanta tamkar batasan wainar dasuke toyawa ba,batare da saninta taji shi kusa da ita zaune,sannan kuma ga aslam bisa cinyarshi yana biyewa surutunshi na labarin abokanshi en class dinsu dayake ta bashi.


Dauke numfashinta tayi domin qamshinsa baqaramar kasala yakesakamata ba,hakan yasa tadan muskuta gefe domin sanya dan distance a tsakaninsu.


Batareda tsammani ba ta tsinto muryarshi yanacewa madam ba gaisuwa?Taso ta harareshi amman sai tafasa ganin shekaru biyar ba wasa banë yaci ace ko gaisuwa ce tahadasu kodon darajar dan dake tsakanin su.


Oh i'm sorry hankalina baya nan neh...Ina gajiya?Tafurta hakan batare data kalli inda yakeba,murmushi nan nashi yayi mai tsada,hakan yasa taqara satar kallon shi ahankali,yaqara kyau nagaske,cikar xatin nan mai fiszgar emmata akanshi na nan,sai dai wasu al'amurrah masu wuyar fassarawa data fuskanta atattare da fuskar shi wanda sam takasa fahimta.


Muna nan lafiya,ya karatu?Inafatan angama a sa'a?

Yes in sha Allah muna fatan hakan,tabashi answer ataqaiche,domin batason yadda muryarshi kesanya mata mutuwar jiki...Shiru sukayi nadan mintuna sai aslam neh daketa surutu,domin shi yau take sallah agareshi gashi ga daddynshi gakuma ammyn shi.


Inbazaku damuba muje mana na saukeku,although bansan miya tsaida su gwaggon ba dabasu iso ba har yanxu,dasauri ta girgiza kai alamun ah ha yabarshi zata jirasu...Jin atmosphere din dake tsakaninsu na neman chanzawane yasata miqewa

Domin nema wa kanta lafiya.


Tafiyata batareda kallon gabanta ba,hakan yasa tadawo hayyacinta adan firgice sakamakon ji datayi tabugi da wani abu mai dan qarfi...Tare suka hada baki wajen ambatar Allah,haka kuma alokaci guda taji anyi qoqarin tarbota sakamakon shan qasa datake shirin yi....


Da danhanzari tadire bisa qafafunta gamida qoqarin matsawa daga jikin mutumin,wanda hakan yayi sanadiyar dago kanta datayi domin ganin wanda sukayi karon battar qarfe...


Mamaki neh yakusa kasheta sakamakon ganin fuskar mutumin...Ikon Allah tafurta hakan aqasan maqoshinta,kana kuma da danhanzari taqaqalo murmushi gamida cewa pls i'm sorry towards my attitude,actually bansan miya dauke hankali naba har mukasami dan minor incidence dinnan...Pls i am sorry...


Katseta yayi ta hanyar dakatar da ita yana murmushi,,,hakanan kuma yakasa daina qura mata manyan idanuwanshi masu shegen kyau,its okay...But kiriqa pls lura kina kauda duk wani tunanin while walking...bana fatan kimin asarar kanki...Yafurta hakan batare da wata damuwaba a fuskar shi.


Galala tayi da ido da baki tana jin ikon Allah...Lallai mutumin nan abubuwan mamakin shi nada yawa...Wai kartai mishi asarar kanta!Wait is this man okay?Tasamu kanta da girgiza kai cike da mamakin shi....


Well...sweetheart we need to talk...Ya furta hakan yana qoqarin gyaaara jacket din suits dinshi dake rataye bisa kafadar shi,,hakan kuma ya karkace kai gamida langabeshi yana qare mata kallo....


Lmao...Tasaki dariya ahankali!This man is really full of dramas...Miyake nufi da sweetheart we need to talk...?Kina mun kallon majnoon koh?Ta tsinkayo muryarshi yana fadi,hakanan kuma yai mata rumfa da tsayin shi...


Dasauri tagirgiza kanta tana mai tunanin yau Allah yagamata da gamonta,gara tasamu surabu lafiya...Cikin yaqe tace okay toh, bt yanxu gaskiya i'm in a hurry...Ko kafin taqarasa yakatseta ta hanyar cewa let me drop you home... kinga dare yafarayi and i surely won't allow seeing my wife mingling around.


Ko kafin tagama dawowa daga duniyar mamakin daya antayata ya nuna mata hanya gamida fadin shall we?Kamar doluwa tadaga kai suka juya domin isa inda tabaro aslam da babanshi,garama da akai haka son kuwa dama tarasa yanda zatai tai getting ride din baban aslam din.


Atsaye suka sameshi rungume da yaronshi a qirjin sa,da alama jiranta yake tadawo sutafi,domin kuwa yagaji da ganin tilon danshi na gyangyadi kamar mara galihu,itama din baisan miyasa yake jin wani bad feeling gameda tafiyar datayi tabarsu ba.


Hangosun dayayi yasashi daure fuskar shi batareda sanin shiba,take yanemi nutsuwar shi yarasa,hakan yasa zuciyarshi tacigaba da bugawa da sauri da sauri...Wani qaton banza neh wannan yajero tareda matar shi?Kan kace kwabo jijiyoyin kanshi suntashi sambal bisa kanshi da babu hula.


Hakan yataimaka wajen sanya jikinsa daukan rawa kamar mazari...How dare her zata jero da wani qaton banza agaban idon shi?Har take masa murmushin nan nata dake qara sakashi cikin mutuwar sonta.


Qura musu idanuwa yayi cike da tantamar hukuncin daya kamata yadauka akan wannan dan shishigin,,,da'alama gayen zaiyi rawar kai...Yafurzar da iska cike da jin wani qululun kishi na faso qirjinshi.


***

M so sorry for the late update... pls you guys should bear with me,nikaina bahaka nakeso ba narashin yi muku update akan lokaci...Ina roqonku daku cigaba da hakuri dani don Allah.

Nagode da kulawarku...And i love you all.

Vote pls,i will surely appreciate that☺


21


RAINA KAMA


****

Baqaramin daurewa tayiba da irin kallon dayake jifansu dashi tun tahowarsu,hakan yasa tai mugun qarfin hali don ganin ta maze danuna halin ko inkula da halin dataga ya shiga...Besides ita tarasa wannan abu,tasan dai yafi dan dakon tasha sanin babu sauran wata alaqa data rage tsakanin su.


Shima baqon nata fuskewa yayí kamar bai lura da hararar da Sulyman din keh jifanshi dashiba,duk da ganin nashi yasa yafahimci akwai wani abu a tsakaninsu...Sannu baban aslam inajin zamu wuce yanzu,ta watsa mishi maganar tana qoqarin jan qaramin trolley din dake gefen sulyman din.


Batareda da damuwa ba baqon daba'a san sunanshiba yamiqa wa sulyman din hannu,fuskewa Sulyman din yayi kamar bai fahimci nufin shi ba,shima din basarwa yayi tamkar bai fahimci abinda sulyman din yayi ba.


Tana da niyyar mashu magana akan aslam dake hannunshi kenan wayanta yafara ringing, sunan gwaggo tagani bisa screen din,hakan yasa tadan matsa gefe domin answer call din.


Hello gwaggo nayita trying dinku baya shiga,gwaggonce ta amsa daga dayan bangaren dacewa,wallahi motor dinne yasamu matsala kinganmu nan agefen hanya muna jiran agyara,ni bansan mike damun kausar ba intariqe sitiyarin mota,gashinan taja mana ai.


Ayyah gwaggo toh bakomi bari muqaraso kawai,

Ah ah kuqara hakuri nayiwa sani,driver yazo yadauko ku naga dare nayi muma sai ya biyo yawuce damu duka gwaggon takatseta.


Lah gwaggo wlhy dama yanxu nake shirin kiranku,wani colleague dina ma yace zaiyi dropping dinmu,aslam neh yaketa bacci anan,dasauri gwaggon tace toh shikenan kuwuce gidan mahadu achan,kar sanyi yakama mun dan lele nah.


Dariya tayi gamida yin sallama da gwaggon,sannan da hanzari tajuya domin ganin sunbar airport din,tana isa gurinsu tamiqa hannu wa sulyman domin yabata aslam din suwuce,,,turus tayi ganin kallon banzan daya watsa mata.


Ha'an wai me mutumin nan keh ji dashne?Don yaga tana basarwa don arabu lafiya shine zaisami ikon raina mata wayo...Kodayake bata da lokacin shi...Batareda wani tunaniba tajuya gurin baqonta tace mishi muje kawai,hannu yasa yadauki dayan trolley din dake ta side dinta suka juya.


Batareda bata lokaciba yajuya afusace yanufi inda yai parking, kwantar da aslam din yayi ahankali abayan seat,kana yajuyaa fusace yashyga gamida yiwa motar key...Miyasa yarinyar nan taraina shi neh?Yalura da rawar kai tadawo qasar but zaisauke mata shi...(kuji mun mutum da qarfin hali)


***


Kausar ce keh tsallen ihun ganin amah din,gaba day sun cika gidan da tsallenn murnar yaushe gamo,Gwaggo ce ta dakatar da ihun gamida tambayar aslam,sai lokacin ma ta tuna da drama din dasukai da babanshi.


Kafin takai ga bata amsa,yashygo palour din dauke dashi bisa kafadar shi,hakan yasa takama bakinta ta tsuke,kallon.Mamaki gwaggon keh binshi dashi.


Kaikuma daga ina haka?Ina kasamo aslam din,saida yazauna kana yabata answer" daga airport din nake,bata gaya muku mun hadu bane?Harara gwaggon tajefeshi dashi kanatace toh angode da taimako...Miqo min yaron nan katashi katafi inda kafi wayoh.


Shiru yayi gamida jinjina irin dibar albarkar da gwaggo keh mashi a gidan nan,batareda yaqara furta wata magana ba,yatashi yamiqa mata aslam din dake ta sharar bacci hankalin sa kwance...


Kausar ce tai qoqarin ganin ta tamabyeshi ko ahada mishi abinci yáwuce dashi,don ganin datai yau tun safe yake gidan kuma a iya saninta ba abinda yaci tun xuwanshi sai ruwa da drink dayake ta bulbula wa tumbinsa.


Girgiza mata kai yayi alamun no tabarshj baya buqata,batareda yasake furta wata maganarba yaiwa gwaggon sallama yajuya yafice daga falon,kallon tausayi khausar din tabishi dashi...Yayinda gwaggo tabishi da harara.


****

Kwance suke ita da Khausaar din suna hirar yaushe gamo,yayinda aslam keh dakin gwaggo yana barza baccin gajiya...Wai qawata ya akayi neh?Waye wannan fine guy din daya kawoki dazu?Waike kinga haduwarshi kuwa?


Duka amah din takai wa khausar din gamida cewa kekam bakida "M" da sadakin khalil akanki kike yaba kyawun wani koh?Dariya khausar din tasaki gamida cewa...Yoh minene ciki,ai nasan apart frm khalil dina bawanda ya isa yasache xuciyar nan tawa...I'm just giving a compliment you know?Tadaga mata gira.


Hmm kinsan guy din mugun dan drama neh,you'd be surprise innace miki nima yau yau dinnan nafara ganinshi,keh saikinga drama din damukai dashi dazu a airport...Wai sunanshi Muhammad Ameen,ta ida maganar tana tabe baki.


Wow ga kyau ga suna mai dadi cewar khausar din tana gyra fuskantato ta,toh amma yane...Yanuna interest neh akanki?Tajefo mata tambayar...Dariya tasake saki gamida girgiza kai...Hmm keh guy dinnan fa nagayamiki dan drama neh...Kinsan miyace munne dazamui sallama?


Dasauri kausar din tagirgixa kai tana qara baza kunnuwa donjin gulma,saida tadara skamakon tuna zantuttukan muhammad amin din kafin yai mata sallama.


Waî bayan munyu exchanging phone numbers kamar yanda yabuqata,dazamui sallama sai cewa yayi toh sai yaushe kenan?Nace miahi sai randa Allah yayi!Kawai sainaga ya yayi dariya kana yacemun bazaki sake ganinaba sai amatsayin mijinki in sha Allah?


Hangame baki nayi inaji wannan qarfin hali...Itama kausar din ihu tayi gamida cewa wow!Gûrl just say yes kawai...Wallahi kunyi bala'in matching... i can't wait to sew your fine fine kids mehn.


Harararta amah dintayi gamida cewa malama kikiyayeni...Daganin sarkin fawa sai miya tai zaqi?Pls i can't deal...Takoma tabaya takwanta...Take kuma fuskar Sulyman adazu kafin tafiyarshi yafado mata...


Jitake kaman taje tarungumeshi ta lallashe shi,,.she can feel his pain,bt babu yanda zasuyi...Qaddara tariga fita...Its time she face her future...It's time she move on....She needs a new shoulder to lean on....And that shoulder is who?


Lumshe idanuwanta tayi sakamakon tuna Dan fillon saurayinta na dazu...Muhammad ameen should be that shoulder... there seems something special in him datagaza gani a dukkan mazan dasuka nuna ra'ayin son aurenta...


Its time to get really over with Sulyman Bello Galadanchi...Both physically and mentally.


***

Vote and comment pls...

Nagode😍


22


RAINA KAMA


Acikin sati daya da haduwarta da muhammd ameen sunyi shaquwa mai ban mamaki, wanda ita kanta tana mamakin muguwar shaquwar datayi dashi.... Qila hakan yana da nasaba da yanayin muhammad dinne... Kasantuwarshi mutum mai matuqar kirki da barkwanchi qwarai dagaske. 


Diba da yadda muhammad din keh matuqar gwada mata soyayyah taban mamaki yasanya mata ganin girmanshi da qimanta shi fiye da tunanin mai tunani domin kuwa shi din mutum neh daya chanchanchi dukkan wata kulawa da girmamawa daga wajenta. 


Sai dai kuma meh? Har yanxu din da'ake shirye shiryen aurenta dashi takasa jin abinda takeji akan sulyman... Tarasa wannan neman magana da xuciyarta kemata... Ko banza tana buqatar sassauchi daga irin tarin qaunar datake wa mutumin da bazaitaba zama nata ba... Idan koh har hakane lallai xuciyarta batai mata adalchi ba. 


Sai dai ko menene tayi alqawarin koyawa zuciyarta haquri tareda danne duk wata barazana da xuciyar tata keh qullo mata.... Wanda yin hakanne zaisa tabada qaimi wajen koyawa zuciyar tata son muhammad din akota halin qaqa neh... Domin kuwa shidin abin asoshi neh... Yana buqatar soyayyar tata qwarai dagaske idan tayi la'akari da kasantuwar shi maraya gaba da baya. 


Juyi tasakeyi akaro na biyar tunfara tunanin nata... Hakan yasa tacigaba da tariyo hirarta da muhammad din alokuta da dama dasuka wuce


Shi din yakasanche dan asalin garin gombe, amma yanayin aiiki yadawo da iyayenshi garin kaduna tun yana qanqani, yakasanche da namiji tilo tak agidannasu sannan kuma auta! Ya mallaki yayye mata guda hudu, wadanda biyu suna aurene anan kaduna, yayin da biyu keh aure anan birnin na kano. 


Mahaifinshi marigayi Alh sale inuwa yakasanche kwarraren injiniya neh na electrical ayayin rayuwarshi, hakan yasa yake aiki da ma'aikatar matatar man fetur, yariqe muqamai masu dimbin yawa saboda gaskiyarshi da riqon amanar shi, hakan yasa yatara arziqi mai dimbin yawa duba da kasuwanchi dayake hadawa dashi cikin harkokinshi nayau da kullum. 


Son dasuke wa muhammad din abin akalla neh a jinjina domin kuwa yakasanche da namiji tilo dasuka haifa, hakan yasa kowa da kowa nagidan keh ji da autan alhaji da hajiya,. 


Yana da kimanin shekaru goma sha biyu iyayen nashi suka hadu da hadarin mota ahanyarsu tazuwa gomben ganin gida, wanda acikin motar yakasanche da alhajinne da hajiyar dakuma muhammd din, sai kuma drivern dake tuqo su, a inda take yanke su duka ukun suka rasu saishi muhammd din da Allah yatserar batareda ko qwarzani ba. 


Kwarai dagaske yayi kuka, kuka bakadanba na rashin iyayen nashi, wanda yakejin kaf duniya bawanda akaiwa rashi irin shi din, dukkuwa dacewa ahi din baitaso cikin maraichi ba, domin kuwa babbar yayarshi hajiya kaltume ce tadaukeahi tacigaba da riqeshi tamkar iayayen nasu. 


Hakan yasa zamanshi kachokam yakoma garin kano wajen hajia kaltumen tareda maigidanta wanda yazame masa tamkar mahaifi, muhammad wanda ayanxu yakasanche matashi dan shekaru ashirin da tara aduniya, kuma saurayi sabo dal dabaitaba aureba, hasalima soyayyar ma bayinta yakeba acewarshi baishirya aureba donhaka bazai bata lokacin shi wajen batawa yayan mutane lokachi ba. 


Tashin farkon haduwarshi da amah... Yatsinchi zuciyarshi da sungumo soyayyarta, hakan yasa bai bata lokachiba take yanke ya amayar da abinda keh ranshi agareta domin kuwa ya aminta da ita atashin farko daya fara dora idanunsa akanta, dukkuwa daganin cewa shidin farin shyga neh a wannan fagen. 


Yaso ya fiskanchi dan qalubale daga yayyen nashi kasanchewar amah din bazawara kuma harda da? Aganinsu inashi ina wata bazawara diba daganin shi din ba auren yataba ba, don haka don me zaiche xaifara da bazawara? 


Hannuwa yasa yatoshe kunnuwanshi yakuma tabbatar musu dacewa shifa su qyaleshi domin kuwa ahaka yakeson abarsa koda kuwa ache aurenta yazarta goma neh... Ganin dagewar dayayi yasa suka haqura suka sanyawa abin albarka gamida cigaba da shirye ahiryen auren dan lelen autan nasu. 


*** *** ***

Dawowarsu kenan daga gurin dilka din da aketafaman yiwa amah din tun kwanaki biyar dasuka wuce, hakan yasa taqara wani mugun kyau da haske kamar kasungumeta ka tsere. 


Sauri sauri ta shiga wanka domin ta kammala shirinta kafin angonta mai shirin angwancewa nan da kwanaki kadan yaqaraso, domin kuwa shin din yakasanche tamkar saurayin kusa da gidane...jiya yazo, shekaran jiya yazo, gobe ma zaizo har sai ranar da'aka tattakura aka miqa mashi matar sa. 


Yau kam qememe yaqi yarda su zauna a palourn baqi dasuka saba zama, acewarshi hasken bulb baya isarsa waje son yadinga qare mata kallo, shiyasa yaliqe akan cewa yau aharabar gidan zasu zanta... Domin hasken Allah ta'ala yavigaba da dalle mashi kyakkyawar fiskar matarshi abin son sa. 


Dariya take qsa qasa sakamakon labarin da muhammad din keh bata nawani abokinshi daya gamu da hyperta love wanda har yakaishi ga kwanchiya asibiti du don budurwar tashi tadaka tsalle gefe guda tace bata aurenshi, tasami sabon saurayi fari qal dan qasar lebonon, hakan yasa yasami tabuwar zuciya domin kuwa baqaramin so yake wa budurwar tashi ba. 


Sun shagala sunata firar su qasa qasa, wanda hakan yasa basuji shigowar mota ba harabar gidan, sai dai tajiyo ihun aslam yana palpalowa garesu tareda kwala kiran sunan su... Mammy, uncle ameen i am back... Yaciga da nufoshi da gudun sa. 


Jiyo muryarshi yasa duk suka juya suna zuba masa murmushi, wanda tuni muhammd yayi ready din isowarshi garesu tahanyar bude hannuwanshi,. 


Itakuwa hankalintane gaba daya yakarkata akan mutumin daya sauke aslam din, bawani bane illah daddynshi.... Watso masu kallon banza yariqayi daga nesa kamar wanda yaga maqiyanshi. 


Hakan yasa yai maza tasunkuyar dakanta, gamida tunanin miya ramar dashi haka, domkn kuwa takwana biyu bata ganshi ba tun bayan tafiyar datayi taje katsina gaishe da en gidansu tadawo bata sake sanyashi a idanuwanta ba sai yau. 


Duk shirye shiryen bikin da'ake agidan baisa tachi katarin ganinsa koda sau daya bane, dukkuwa dacewa tasha haduwa da laura, wanda qwarai dagaske rashin ganin nashi yai matuqar damunta hartariqa zagin kanta azuciyarta, aganinta taciga wawiya idan har tana barin xuciyarta na damunta da mutumin dayariga dayai mata nisa. 


Sukuyar da kanta qasa tayi tana wasa dawani kyakkyawan zobe dake hannunta, hakan yasa kwata kwata tadena fahimtar surutun da aslam keyi mata. 


Emmatana miyafaru neh? Tatsinto muryar muhammd din natambayarta.. Kana kuma yanachigaba da binta da kallon tuhuma... Domin kuwa sarai yasan abinda yachanxa yanayinta yanxu yanxunnan. 


Dasauri ta daidaita fuskarta gamida qaqalo wani marayan murmushi ta qawata fuskar tata, hakan yasa tave mishi bakomi surutun aslam dinne ya isheta... 


Binta yacigaba dayi da kallo domin dai yasan qaryatake.... Hakan yasa yai murmushi gamida basar da qaryar datai mashi kasantuwar bai kasanche mutum mai son takuraba.... Saidai yai amfani da abinda tave din tahanyar lallaba aslam din akan yashiga gida yace yana gaida gwaggo sannan kuma kausar tayi mashi wanka domin yakaishi wajen daada. 


Dagudunshi ya palla yayi cikin gida saikuma yadawo baya ganin daddyn nashi zaune a mota baiwuceba.... Qarasawa yayk wajenshi d qarfin guiwarshi don yabashi labarin gurin daada da uncle ameen din zaimasa. 


Lah daddy meyafada maka a ido kake kuka? Qaramin yaron mai wayo yacigaba da tambayar majaifin nashi hade da lakato hawayen dake ta rige rigen sauka a kunchin shi. 


Da sauri yasa hanky yagoge ragowar hawayen gamida sakaya fuskarshi da yaqe duk don yakauche wa tambayoyin tilon dan nasa.... 


Wani qwarone mara tausayi yafadamani a ido aslam, amma yafitama... Kaga nadena kukan ko? Yataallabo yaron nashi jikin shi gamida sake qurawa indasu amah din keh zaune ido. 


Qwacewa yaron yayi yanufi mamyntashi yana qwala mata kira bai bata lokaciba ya daddage yajanyota yadinga janta akan tazo taga daddynshi yayi kuka, qwaro yafada mashi a ido. 


Kasa dena binshi tayi harsuka isa bakin motar tashi da dama chan yazuro qafafunshi wajene, qiqam tayi agabanshi gamida aunkuyar da kanta qasa, hakan yasa gabanta yavigaba da bugu fat fat kamar zaiyo wajen kirjinta. 


Shidinma zuru yayi mata da ido kamar marayan dayarasa uwa da uba, kana kuma alokaci guda ya langabar da kansa yana binta da wani irin fitinannen kallo.... Wanda tolas yasa tariqa jin kallon naratsa dukkan qashi da bargonta... Ya ilahi meyesa zuciyarta bata mata adalchi neh? 


Mammy kihure mashi idon kinga qwaron yaqara fada mashi a ido... Ta tsinkayo muryar aslam din nafada cike dason yin kuka, ahankali tadago kanta tasachi kallonshi... Ilai kuwa wasu hawayene suka sulmiyo tagefe gefen idanuwan shi, da'alama ma baisan suna sauka ba domin kuwa yayi mata quri da wadnnan shanyayyun idanuwan nashiasu sanya mata kasala. 


Kafin ta ankara saijin ihun kukan aslma tayi harda faduwa qasa, dasauri suduka biyun suka nufeshi domin lallashin shi.... Tsakiya suka sanya shi suna rige rigen tabashi, hakan yasanya hannayensu taba juna.... Dasauri amatullah tajanye nata domin jin irin fizgarta da al'amarin yayi, yayinda shikuma yasaki wata bayyananniyar ajiyar xuciya gamida lumshe idanunshi.... Hakan yatuna mishi da irin missing dinta dayayi. 


Hannu tasanya tana gogewa aslam din hawaye wanda har alokacin burari yake akan sai mammyn tashi tahurewa babanshi idonshi qwaron yafita, jagale tayi da ido tanajin wannan fitina ta aslam, gashi da er banzar kafiya domin kuwa matuqar batayi abinda yakesoba yau basi ba bacci, domin kuwa ba lallashi yakejiba. 


Cikin dakiya tace toh yishiru kaji sweethrt kagani nahure mashi, tadan kai bayinta wajen idanuwanshi dasuka qi daina kallonta tadan hura, qarasa zama yayi dirshan gamida jan doguwarajiyar zuciya domin kuwa baqaramin kai xuciya nesa yayiba dabai jawota ya matse aqirjinshi ba..... 


Yalumshe ido sonta nacigana da gasa zuciyarshi da gangar jikinshi.... Dariya aslam din yariqa yi ganin irin xaman dabaro din da daddyn nashi yayi, hakan yasa sukasamu yamanta da wacchan rigimar. 


Gabantane yafadi da ta tuna muhammad dake xaune achan inda tabaroshi, sanin yaga duk abubuwan dasuka faru yasa jikinta yin sanyi qalau, gamida yin tur da wannan xuciyartata dabata rabo da dauko mata magana. 


Da hanzarinta tamiqe tanufi inda tabarshi azaune, ga. Mamakinta fuskarshi sam bata sauya mata ba... Saima yajibga mata dimbin mamakinshi ta hanyar ce mata yaya inafatan qwaron yafita? 


****

Toh kuyi haquri da wannan.... Sannan kuma nagode qwarai da addu'o'inku.... Wayakuma Allah yamaida wata ma... Alhamdulillah 😊😊

We are in this together.... And pls dont forget to show love by voting... 


23


RAINA KAMA


By Noorieyyaah 


I dedicate this page to all #RK's lovers!

Inayinku😍


Ayiriririrryyyyyy wata mata mai danbanxan zaqin murya ta chanyara guda....wanda gudar yatafi neh tare da bugun xuciyar amatullah din dake bedroom din gwaggo kwanche tun wayewar garin asabar din data kasanche ranar daurin aurenta da muhammad ameen.


Take kuma hawayen datake ta qoqarin hadiyewa tun wayewar garin suka sami ikon silalowa daga idanunta....shakka babu ayau ta tabbata mata agurin wannan dan tahaliki...tuna hakan yasa tasake fashewa da wani irin marayan kuka wanda ita kanta tana turr da yin shi...sabida tasan musababbin kukan nata...tasan me takewa hawaye tareda jimami...


Tur taqarayi da wannan banxan halin nata...koma tace er banxar xuciyarta da har yau takasa yimata adalchin dena qaunar wanda bazata taba samuba....kaicho da wannan xuciya tata mai jajibo mata magana...ta ida tunanin tana mai qara rafka tagumi kamar wacce akace uwarta da ubanta sun bata.


Gwaggo ce taturo qofar bedroom din tashygo..ganin yanayin da amah dintake neh yasanyata hanxarin daure fuskar ta tamau...domin kuwa ta lura idan ba wankin babban bargo taiwa yarinyar nan ba bazata qi dauko masu maganaba.domin kuwa tadade dasanin take taken amatullah din tun filazaal....tasaki tsaki gamida daurawa amatullah din harara.


Garama kitashi daga wannan zaman dakike mara amfani,ayi yarinya sam baki da xuciya?kinbi kin ishi rayuwarki kin hana kanki sakat akan abinda kikasan samuwar shi agareki ba mai yiwuwa bane...bama haka ba...ni dunia bantaba ganin sakarai irinki ba wallahi...namiji yamani irin wulaqanchin nan wlhy ko iskar data deboshi bani qara kallo balle in tsaya ina tunanin shi...for what reason?


Itadai amma kasa takarayi da kanta tana sheahaheqar kuka ahankali...domin kuwa inda sabo yaci ache tasaba da fadan gwaggo matuqar xata kamata cikin irin wannan yanayin...ita bata taba ganin uwar da bata tausayin danta ba irin gwaggon....


Illai kuwa kaman gwaggon tasan tunanin datake tachigaba da balbala fadanta kaman ta ari baki....koda kika ga ina wannan fadan ba wai don banason shi sulyman din bane ah ah...mutunchinki da qimarki ta 'ya mace daya take nake tayaki fishi,nakuma ga nayi qoqarin kwato maki martabarki,duk da dai dama mai afkuwa tariga ta afku babu wani sauran gyara dazamu iya yi...amma duk da haka nake so ki manta dacewar ma kintaba auren wata halitta sulyman...ki godewa Allah dayabaki miji mai sonki amatullah...ki mancw da rayuwarki ta baya,ki fuskanchi sabuwar rayuwar dake kusanto ki a yanxu,basai nayi maki qarin bayani kan darajar aureba nasan kinsani...sabida haka ki mutunta aurenki ki san darajar mijin ki...haka xalika ki guji biyewa zuciya...domin kuwa tsab zata iya kaiki tabaro....


Ta numfasa kana tachigaba da xubamata nasihohi masu ratsa jiki,wanda kuwa hakan baqaramin tasiri sukai ga amatullah din ba,kanta kawai take dagawa sama alamun tana fahimtar nasihun tsohuwar uwar mijin nata...wacce tazame mata tamkar mahaifiyar data rasa ayanxu....kukan datake har yafi nada...hakan yasa itama gwggon tai hanxarin ficewa daga dakin domin muryarta data fara chanxawa alamun itama gab take da fashewa danata kukan,domin kuwa dama daurewa take bata sakeshi ba agurin...


Tabbas sulyman yayi rashi....rashi babba kuwa,domin kuwa amatullah yarinya ce mai nasibi da shyga rai...amma ya aka iya da qaddara?wacce ake cewa tariga fata!


*** *** *** ***


Amarya bakya laifi....ta tsinkayo muryar wani abokin muhammad din nafadi cike da zolaya...daga cikin mayafin ta gallaro mashi harara wacce ma iya cewa aikin banxa harara a duhu....domin kuwa basu san tanayi ba....


Tsaki taqarayi chan qasan maqoshin ta....ita wallahi bataga amfanin wannan sayen bakin ba,kamar wata budurwa...duk kuwa dama baa dade dagama dirama da kausar ba akan cewa itafa batason wannan feleqen.....kausar kuwa tace sai dai tamutu amma sukam sai sun darji siyan baki sun more kafin subar mata gidan tunda taqoasa su tafi...harara tabita dashi domin kuwa ita har ga Allah banufinta ba kenan...hmmm da kausar din tasan abinda ke ranta da batai mata wannan xargin ba....


Bayan en barkwance barkwance tsakanin abokkan ango da qawayen amarya,saikuma aka daura da nasihu ga ma'auratan,kana kuma aka rufe taro da addu'ah...wanda dama shi ango bawai jinsu yakeba....gabadayan hankalin shi naga kan amaryar tashi dataqi koda dago kaine bare kuma ai maganar dage mayafin da aka lulluba mata...


Hakan yasa yabi yaqosa sugama iface ifacensu su fice subashi guri yagana da rabin ran tashi....domin kuwa har wani langabe kai yake yana lullumshe idanuwa gamida sakin hammar qarya duk don suyi suqara gaba....


Muryar saddik yajiyo daya dga cikin abokanshi yana mashi tsiyar....toh malam ango kafin ka kai ga sanya mana kuka mu munyi nan...domin kuwa yadda ka langabe kan nan kamar wani qadangare nasan gab kake da fashewa da kuka...gaba daya falon suka dau dariya gamida yin haramar fita,bayan sunyiwa amarya sallama...duk kuwa dacewa ko kallo basu ishetaba.


Cikin en mintuna dabasu wuce homaba yadawo dga rakasu...hakan yasa da dan hanxarinshi yanufi amaryar tashi dake xaune atsakiyar gado tasanya kanta a tsakanin chinyoyinta tana sauke ajiyar xuciya...gaba daya first night dinta da sulyman keh mata yawo aka!hakan yasa ta lumshe idanuwanta tanajin baqon yanayi na ziyartarta....take kuwa hawaye suka shyga bulbulowa daga idanuwanta domin kuwa tasan wannan soyayyar daya gwada mata a wannan daren yafi gaban amantaashi....suk kuwa da cewa dimbin axabar datsha a lokachin bai xamo abin mantuwa ba agareta...amma kasantuwar shi dinne yarabata da budurchinta yafi komi yimata dadi.


Yafi mintuna biyar yana kiran sunanta ahankali,amma tayi nisa a inda ba' huruminta ba....ganin batajin shi yasa yasanya hannuyenshi yarungumota jikin shi,,,,duk kuwa da quna da xuciyar shi keyi....domin kuwa yafi kowa sanin abinda ke sanya amah din shiga irin wannan yanayin....duk kuwa dacewa baitaba tanka mata ko nuna mata bachin ranshi ba akan soyayyar datakeyi wa tsohon mijin nata ba har yanxu....


But that was then ya ambachi hakan aranshi....that was before tazama mallakinshi shiyasa baitaba nun mata da yasan abinda keh ranta ba....but for now....dolene adena mashi tunanin qaton banzaa a cikin gidanshi...


Fara janye jikinta tayi daga nashi...daalama sotake yarabu da ita tachigaba da tuanain tsohon mijinta....hakan datayi kuwa baqaramin tunxura shi tayi ba...ko kafin tasake wani tunanin sai jitayi yayi sama da ita yanufi bathroom....direta yayi cikin bath,hakan yasa tai saurin miqewa tsaye tana zare ido....


Bata sami bakin magana ba ganin yanda fskar muhammad din takoma tamkar ba wannan salihin mutumin ba,mai dimbin haquri da fara'ah...wannan dake tsaye agabanta is damn scary....domin kuwa kai kace baa taba halittar murmushi ba akan kyakkyawar fuskar shi....


Nabaki ten.minutes kiyi wanka gamida dauro alwala kisameni a bedroom dina...and dont waste my time...yanagama fadin haka yajuya yafice daga bathroom din....galala tayi da ido da hanchi harma da baki tana kallonshi....hakanan kuma sai taji kamar tsoronshi nashygarta....hakan yasa tafara hanzarin yin abinda yace din batareda taqara tunawa da tunanin sulyman din datakeyi ba some few minutes ago.


Koda tafito wata farar doguwar riga tagani da hijab dinta mai dan tsayi kadan,hakan yasa ta fahimchi nufinshi na tasanya kayan....ahanxarche ta mutsuka cream mai sauqin danqo,gamida murxa wa jikinta body sprays kala kala....domin dai daman ita gwanar bazawa jikinta turaruka ce koda kuwa ace bacci xatayi...


Ta mirror tahango shi tsaye yanade hannayenshi a qirjin shi yana qare mata kallo,gabanta neh yafadi ganin har ynxu fiskar shi na nan kaman ta dazu,hakan yasa tai hanxarin miqewa gamida kokawar sanya rigar,duk tarude kuwa,domin kuwa ko tunawa da sanya under wears batayiba.


Fahimtar yanda tarude yasa yabude mata hannayenshi.....sumi sumi ta tafi tashige cikin su....rungumeta yayi qam aqirjinshi yanajin sabon sonta na huda gabbanshi....jin tana neman karya mashi alwalar yasa yai hanxarin dagota daga kan kirjin shi sai mazurai take kamar kace kyattt taruga....dariya taso qwace mashi amman yadake...gamida riqe hannayents yanufi dakinshi da ita.


Bayan sun idar da sallah n,gamida addu'o'in dasuka kamata neh,ya umarceta data matso masu da wani madaidaichin basket din dake kan center table din dakin....kaji neh masu maiqo sai zuba qamshi suke alamun sunji gashi da hadi,gefe kuma ga wani hadadden chips nan anyi garnishing dinshi da kidney sauce,take kuwa taji miyonta yatsinke dakuma tashin tsohuwar yunwar datakeji dama tun fil'azaal....


Taso tanuna kunya taqichi,amman hakan baisamuba ba,sakamakon yanda muhammad din ya murtuke face,yariqa bata abinchin abaki baya ko barinta tayi magana....itama dama yunwa takeji hakan yasa tariqa bude maqoshi tana amshe abinchin hankalinta kwanche.


Saida sukayi qaat kana ya miqar da ita suka shiga bathroom dinshi sukayo brush,kana suka fito,,,bakin gado taje ta.maqre tana cigaba da xare ido....domin kuwa ita takasa ganewa muhammd din ayau....gaba daya yakoma mata kamar ba muhammd din datasaniba....domin kuwa har ynxu magana ta fatar baki bata hadasu ba tun bayan daya satayin wanka....


Oya come here....yafada with a commanding voice..da dan hanxarinta ta isa gareshi,hijabinta yaciremata gamida zuge zip din rigar jikinta,take kuwa rigar tayi qasa....da hanxarinta tabi rigar da niyyar danqota...


A kasalanche tajiyo muryarshi yana sake bata commnd...dont even star it...hakan yasa tai xuru a durqushe tana bobboye jikinta....idanuwanshi neh suka cigaba da hora jikin nata....domin kuwa xuru yayi kamar maye yana qare mata kallo....aranshi kam jinjina irin kyawun surar matar tashi yake....domin kuwa idan badan yasani ba dasai yace sharri ake mata da ake cemata bazawara ce...kuma ma harda da!


Kafin tasan me ake ciki sai tsinatr ta tayi ajikin shi....wanda hakan yasa taji gaba daya tsigar jikinta tamiqe sakamakon haduwar fatar su guri daya....take jikinta yahau rawa,jin shi naked datayi,domin kuwa ita batasan ma lokavin dayarabu da jallabiyar jikin shiba....


Ahankali yasauke su bisa lafiyayyen gadon shi dake tazuba qamshin sanyi hakan yasa tafunqule jikinta jin sanyin a.c din nashigarta sakamakon rashin kaya da babu a jikinta....itadai yau tanaganin qarfin hali....adakeka ahanaka kuka...tai qwafa alamun xai sani wallahi....


Rufesu yayi da blanket gamida qara mannata a qirjinshi,hakan yasa suka saki ajiyar xuciya atare,batareda da sanintaba ya lalubo bakinta yafara mata wani passionate kiss mai matuqar daukar hankali,ahankali kuma kiss din yafara chanxa salo,domin kuwa yanxu da qarfi yake tsotsan bakin nata tamkar Allah ya aiko shi,hakan yasa yafara fita daga hayuachin shi....


Itakuwa amah kuka tafara ahankali jin yana shirin cire mata baki,kana kuma yabi ya kanainayeta yahanata katabus....inbanda yamutsata babu abinda yake....jin kukanta yasa yadago daidanuwanshi dasuka chanxa launi yaxuba mata su....hakan nan bai bata lokaciba yace kiss me....in a commanding and gentle way....


Taso tayi gardama,amman ganin yanayin face dinshi yasa takamo lips dinshi tana hawaye....bai barta hakaba saida yasanyata tariqa shafashi tamkar yanda yake mata,hakan yasa dakin yaadauki shiru sai zallar zazzafar soyayyar dake gudana a tsakanin su.....


Ahankali bayan yagama tabbatar da itama kanta takamu yashiga karanta adduar saduwa da iyali,wanda Alokachin ikon Allah ne kawai ya iayasashi karanto du'a'in....domin kuwa malam muhammadu yagama kamuwa....abinka da tsohon gwauro...kuma sabon hannu!


Aikuwa amah tasha gurzaaah....gurxah ba kadan ba kuwa...domin.kuwa ko tumkuza ayau kam sai dai taganta ta kyale....hakan yasa ta dandani azabar datakejin ko rabin wacce tasha a hannun sukyman bata kaiba....dama kuka kuwa ai tasha shi harda su majina da miyau,inbanda kwandon Allh ya isa babu abinda take xubawa kausar....domin kuwa duk ita taqara jamata wannan axabar...lallai tagayawa masu garinta yau a hannun wannan gwarzo namijinn....


Lamo tayi a qirjinshi tana cigaba da barzar kuka,wand harda na tabara,shiko inbanda lallashi da jijjigata babu abinda yake.....arasnshi ko cewa yake....kai dama haka abin yake?lallai bazai fasa jin takaichin rashin yin aurenshi ba tuntuni....domin kuwa yazama dole ya hora amatullah din data jinkirta haduwarsu,domin kuwa aganin shi da tuni yadade da fara leqawa sama ta bakwai sabida nishadi da nutsuwa daya samu atattare da ita.....


Qara qanqameta yayi yanajin sonta naqra bin.lungu da saqo najikinshi....hakan nan kumaa baifasa sanya.mata albarka ba da binta da wasu kyawawan kissess a wuyanta dake bisa qirjin shi....lumshe ido yayi yana tuna yanayin dasuka tsinchi kansu a dazun......


***

Toh asuba tagari Amatullah da Aminullah!

HML to you both......inafatan fans zasuiwa amah da muhammd kara domin tayasu murnar shiga sabuwar rayuwa....blow your best wishes to them....i promise you it shall reach them😂🏃


24


RAINA KAMA


NoorieyyahZaune take a tsararren palourn gidan naata da akodayaushe ta klleshi bata fasa godewa iyalan gidan Alh bello galadanchi bisa dimbin karamchin su agreta....dukkuwa dacewa kawuntama yayi mtuqar nashi qoqarin don ganin bata rasa komiba na jin dadin rayuwa....madallah da mutanen kirki.


Tasauke numfashi tana mai qara tariyo al'amura masu wuyar mantawa dasuketa faruwa tsakaninta da mijinta,sake lumshe ido tayi tana tuna dramar dasukasha dashi da safen nan akan qin yadda daya fita dayayi ayau din....


Ba shakka muhammad namijin gaske neh,domin kuwa yayi matuqar qoqari da jajircewa wajen nuna mata tsaftachchiyar soyayyah gamida kulawar gasken gaske....hakan yataimaka qwarai wajen mantuwar wasu al'amura dasuka danganchi xuciyarta....irin su sulyman..


Tabbasa idan ba ai wasaba saita kusa tamanta da cewarma tataba wata rayuwar aure da wani chan daban,balle har akai ga tunanin shi kanshi tsohon mijin....diba da yanayin yadda muhammad din keh kifeta da kalar qaunarshi....


Murmushi tasakeyi akaro na biyu data tuna cewa,yau kusan sati biyu kenan da auren nasu amman tun daren da aka kawota gidan batasake tunawa da wani abu waishi sulyman ba...lallai muhammad ya chanchanchi lambar yabo....domin kuwa koh tunanin kanta baya bari tayi ballantana ta tuno wasu.....


Knocking din qofar falon yamaidota daga tunanin datake..hakan yasa tamiqe tana tambayr waye..domin kuwa bata expecting kowa ayau din...bude qofar yayi daidai da qanqame mata qafafuwa da akayi ana dariya....hakan yasa itama taqarasa zuqunnawa gamida qara rungume dan nata suna dariya....


Mammy i miss you....yaron yariqa fadi da qarfin shi....haka nan kuma baifasa tuttura kanshi ajikintaba...itama din cike da kewar dan nata take gayamashj irin missing dinshi datayi....


Ni kubani guri inshyge tunda ni ba ai missing dina ba....kausar tafadi gamida tura baki gaba tana shigewa ciikin palourn....tana dariya tace haba qawas kema kinsani basai nayita nanatawa ba....tunyaushe nake fama dake dakixo...but dayake keh din er dunia ce sai yau kika gadamar sake waiwayata...habawa kausar!ta ida maganar tana hararar kausar din dake nufar hanyar dining table....


Saida tazauna kana tace....keh rufani kisaya ni da mijin na naki....cewa nayi gara inbarku kugama shan amarchin kana....besides gwaggo cema qarin qarfin hanawa...wai mubarki kihuta tukunna....


Kaji gwaggo wani irin hutu kuma,taxumburo baki gaba....shiyasa kullum mukai waya nace wai yaushe xakuzo sai tace....ah ah kidai bari kisake hutawa....


Dariya kausar takwashe dashi gamida cewa...kema.kinsan ma'anar hutun da gwaggon take nufi....oya my boy zomu kwashi girkin amarya,kausar tayafito aslam dake kwanche ajikin mamanshi yana tumurmusarta....


Maqe kafada yayi alamun baizuwa....au baka zuwa koh?yaro dani kake xanchen,karma kache kasanni idan muka koma gida....ta ida maganar tana bubbude food warmers din dake jejjere bisa dining table din.


Lafewa yasakeyi ajikin mamyn tashi alamun zanchen kausar din bai dameshiba...domin kuwa shi ba binta xaiyi sukoma ba...yazo kenan!


Maida hankalinta tayi kan aslam din gamida soma lallashin shu domin ya yarda yaci abinchin,jin cewar ko a chan gidan bawani abinchin kirki yaciba duk sabida dokin zaizo yaganta....


Bakaso uncle muhammad yakaika siyo ice cream koh? Dasuari yace mammy inaso mana....kinga dama gwaggo sai taitayiwa daddyna fada wai yadena siyo mani icecream mura yake sani....ya ida maganar yana son jin mai zatace....


Ambatar daddyn nashi dayayi yasata yin xuru tana kallon shi...haka nan kuma kamar anturata ta tsinchi bakinta da tmabayar shi "aslam daddynka naxuwa neh?


Eh mana yana xuwa kullum...komin dare saiyazo yaganni,kuma gwaggo tai tayi mashi fada,nikuma banaso tanayi mashi fada,sai inyi ta kuka....yaron ya ida xanchen daalamun son yin kukan atare dashi.....


Qura mashi ido tayi tana jin wani irin abu nataso mata a qirjinta mai matuqar xafi,hakanan kuma sai taji kamar hawaye na taruwa a idanunta,


Muryar aslam din tasake dawo da ita,mammy kuma kullum idan muka fita da daddy sai yakaini wani gida mai hotunanki dayawa dayawa....anyi su babba kaman haka....yanuna window din dake manne da palourn,kinata dariya,hadda wani keda daddy kuma,ya qarasa maganar yana jin dadi.


Habawa dama dangwalolo neh....ansoso mata ciwon da dama ashe bakam yayi b warkewa yayi ba,hakan yasa zuciyarta tariqa luguden son sake ganin sukyman din koda sau daya neh akaron qarshe na rayuwarta,take kuwa hawaye suka fara rige rigen saukowa daga idanunta....


Mammy meyafada maki a ido kike kuka,daddyna ma jiya damuna kallon hotonki wani abu yafada mashi a ido...yanata kuka irin naki,ya ida maganar yana mai qura mata ido.....habawa kaman jira take ai sai tasake barkewa da wani sabon kukan mai sauti..wannan karon harda su majina,aslam dinne yafada jikinta shima yana sakin nashi kukan,duk da baisan miyasa mamin tashi kokawa hakaba.


Kausar dake chan qurya tana kwasar girki gamida latse latsen a waya tajiyo kaman shesheqar kuka,hakan yasa tachire earpiece din dake manne da kunnenta ta nufi inda suke.....galala tayi da baki tana ganin ikon Allah....toh me sukewa kuka haka?


Anty amah wai lafiya?what is happening?lafiya kike kuka haka....gashi kinsa aslam shima kukan...tazauna gamida janyo aslam xuwa jikinta,


   My boy stop crying okay?ko kanaso infadawa daddynka yadena xuwa kaika shan icecream?dasauri yaron yagirgixa kanshi gamida cewa No anty khausar nadena kukan,kingani ma...yariqa share hawayen dake bisa kumatun shi dasauri dasauri....kana kuma yace kice mammy itama tadena kuka kar daddyna yaqi siyo mata icecream...yafada yana mai kallon mammyn tashi.


Sunkuyar dakai qasa amah tayi sabida hararar da taga kausar din na wurgo mata,hakan yasan tariqa goge fuskarta gamida sauke ajiyar xuciya,hakanan kuma xuciyarta bata fasa kwadayin son sake ganin sulyman dinba....koda kuwa hakan xaixamo abu naqarshe dazatayi a rayuwarta...


  Wallahi dai kisama wa rayuwarki sauqi amah....ta tsinto muryar kausar nafada....


   I thaught wallahi kindade da rufe wannan babin a rayuwarki diba da matsayin dakike dashi yanxu....ashe mai hali baifasa halinshi?ta ida maganar tana mai qurawa amah din ido da alamun tuhuma.


  Girgiza kai amah din tayu dasauri gamida cewa,wallahi kausar tunda naxo gidan nan banqara tunawa dashiba....yanxu ma aslam neh yake bani labari....bansan ya akai nafara kuka ba...


Tafada tana mai sake goge hawayen dake sake xiraro mata,girgixa kai khausar din tasakeyi....kidai bi ahankali wallahi,kikuma riqa tuanawa da da dayanxu ba daya bane....inbahakaba keh xaki dibgar wa kanki xunnubai abanxa a wofi...

 Shiru amah din tayi tana maijin tsoron tambayar kausar din abinda takeson tambaya,amman yata iya....jitake kamar xiciyarta xata faso qirjinta inbatasan halin dayake ciiki ba....qundumbala tayi tace...


  Kausar wai miyasami daddyn aslam din...naji salam yace kullum sai gwaggo tamishi fada...


Harararta kausar din tasakeyi,amma ganin yanda idanuwan amah din suka chanxa kala yasatajin tausayin ta....wanda dama chan boyewa take,karta nunamata tasataqara kauche hanya.


Sauke numfashi kausar din tayi kanatache...."wai sakin aunty lauran yayi fa"dafe qirji amah din tayi gamida cewa...don Allah fa?meta mishi?


Daquna fuska kausar din tayi kana tace...mefa!ita dakanta tanemi sakin....acewarta tagaji da irin xaman dasuke dashi kamar ba aure sukeba ba....tundaga ranar daya sake kinnan itama tarasa kanshi....acewarta dama ta lura akbarkachinki takechi yake dan kulata ko a time din...ganin yana danne mata haqqinta yasa ta tursashi dayasaketa kota sami enchin sake samun wani farin cikin agaba....domin tayi amanna dacewa babu jinqai a tattare da auren uncle sulyman din.


Sauke numfashi amah din tayi tana maijin sabuwar qaunarshi datake tunanin ta binne nasake bijiro mata...hakanan ta tsinchi xuciyarta da jin wani irin nishadi....haka kuma saitake ganin tamkar sukyman din yacika mata wani dadadden burinta data dade da son ganin yiwuwar shi....watoh sakin laurah!


Kallonta kausar tacigaba dayi cike da tuhuma...domin kuwa tana buqatar sanin abinda yasanya amah din farin ciki a yanxu yanxun nan.....


Rausayar da kai amah din tayi tanachigaba da jin wani irin dadi aranta.....hakan yasa taji inama xata iya maida hannun agogo baya....tabbas dasun gyara kuskurensu nabaya....domin kuwa wacce taimata karan tsaye a rayuwarta da sulyman din yau babu ita.....


Hararar da kausar din keh sake wullo mata baibata haushi ba....saima tamiqe gamida jan hannun aslam suna juyawa a falon cike da nishadi.....shima yaron ganin yanda mamintashi keh wta irin dariyar jin dadi yasashi kyakyatawa yana buga tsalle jin dadi....koma menene kesa mamin tashi jin dadi har haka shima yana maraba dashi.....


Galala da ido da hanchi da baki khausar tayi tan mai cigaba da kallon wannan ikon Allah....innalillahi kardai kausar murna take da rabuwr aty laura da sulyman....


Ga alamu nan kingani...wani sashe naxuciyarta yatunasar da ita....hakan yasa taxabga uba tagumi tanajin tamkar wani babban al'amari na shiri tunkaro su.


***       ***

Vote and comment....it means alot to me.

Nagode😍


Wattpad @Noorieyyaah__


Yini guda chuur su khausar sukayi mata agidan....hakan yasa sam ta shagala da rashin dawowar muhammad din gidan da wuri...


Mammy ni nan xan xauna bazan koma wajen gwaggo ba.....yaron yacigaba da mita tare da saka qafarshi duk inda ta jefa tata.


Wallahi aslam baka da M....watoh gwaggon xakaiwa butulci koh? Cewar khausar dake tattara yanata yaanata cikin jakkarta.


Banza yayi da ita yacigaba da bin amah din cike da rigima,ganin yaqi ya sarara mata yasa tajawoshi jikinta da alamun lallashi,domin kuwa tafi kowa sanin gwggo bazata lamunchi xamanshi a tare dasu ba.....inshort rigimammen babanshi ma kadai ya ishesu jangwam.


Daqyar tasamu ta lallashe shi gamida yi mashi wayoh akan gobe xatazo tadaukeshi harda kayanshi,tunda baizo da kaya ko daya ba....daga mata kai yayi gamida doka tsallen murna.


Wai toh yanxu wazai maidaku neh?ta tambayi kausar din sanin cewar kausar din bata fito da mota ba....acewar gwaggo hannunta lalata mota yake sai dai inba ayi kuskuren miqa mata key ba.


Yoooh wakuwa?napep xamuje mushyga,tamiqe da alamun sauri,kana tacigaba...kinsan uncle Sulyman da jaraba,yanxun nan sai yahau mutum da sababi wai anje an wahalar mashi da yaro...


Ambatar sunanshi kadai saida yasanya mata nishadi....hakan yasa ta rausayar da kai gefe guda tana kallon kausar din tamkar karta dena firar sulyman din....


Tsaki kausar din tadanja gamida fadawa bedroom din amah din....domin kuwa matuqar xata kuskura tacigaba da kallon amah din za'a iya samin er gajeruwar matsala.....domin kuwa har ga Allah gab take data mangare amah din kowama ya huta....wannan jaraba har ina?


Mintuna kadan tafito saye da mayafinta asagale da alamun tagama shiri tafiya....hakan yasa amah din surar after dress din dake kan kujera tasanya ajikinta domin tai masu rakiya zuwa inda xasu shyga napep din....


Fitar su bakin gate din gidan yayi daidai da shigowar kira a wayar kausar....


Lah aslam kaga daddynka neh kirah....bata jira komiba tadaga hadi da yin sallama.


Kuna ina kawai yace....yanxun nan muke shirin tahowa uncle man....tabashi ansa asanyaye sakamakon jin yanda yake maganar akasalanche.


Tanbayanki nai kuna daidai ina yanxu?


Gamu munfito dga gidan maman aslam xamu jeh mushyga napep neh muqaraso gidan....


Wane unguwane?....saida ta kalli amah dake gefenta ta zubo mata idanuwa kana tace nan nan cikin badawa GRA ta side din Dr.grema road.


Kujirani inata arean dama....daga haka yakatse wayan batare dayaqara furta komiba.


Aslam ga daddynka nan zai zo yadaukemu....aifa jin haka yasa yaron yafara tsallen murna,,,,kana yajuya yakalli mamyn tashi yace


Mammy idan daddyna yazo kice kema yakaiki gidanshi mai qaton hotunan ki kema ki kallah....


Daga mashi kai kurum tayi kamar doluwa,domin kuwa jikinta yagama yin sanyi tun gama sauraren wayar da kausar din tayi da baban aslam din.


Kinga maman aslam kawai ki shiga gida,mu bari mudan jirashi tunda yace yana tanan baya neh....ta ida maganar tana qoqarin karbar hannun aslam dake cikin na amah din....


Amma qirir taqi sakin shi,,kana kuma tai kichinkichin da rai tana kallon gefe....hararta kausar din tayi domin kuwa tadade da fahimtar inda amah din ta dosa.....


Haba mana maman aslam miyasa kike son jawo wa kanki tashin hankali neh?yanzu dakike tsaye anan in baban aslam din yazo me xaki mashi....?


Ciki dacin rai tace me kuwa xan mashi?ganin shi zanyi....ta ida maganar tana juya kai domin bata qaunar ganin yanda fsukar kausar ke kallonta cike dajin haushi......


Kinsan Allah xankira gwaggo yanxun nan infada mata....bazan iya wannan dibar albarkar taki ba....ta ida xancen tana mai lalubo nmbr gwaggon a wayarta....


Jitayi anfizge wayar....hakan yasa taxabura da nufin karbar abinta....amma sai amah din tadanyi baya aguje tana wallahi baki isaba....haba kausar miyasa baki da tausayi neh.....


Bayan datayi yayi daidai da sanyo kan motar sulyman a layin,,,,hakan yasa bailura da itaba....yakusa gogarta da motar....


Arude tayi baya tafadi ta gefen wani dutse,hakan yayi daidai da fitowar sulyman din shima a firgice,batare da tunanin komiba yanufeta yana ambaton Allah....duk tuananinshi yadan gogeta neh taji ciwo...domi kuwa dama tunkaryo kwanar gidan gabanshi keh faduwa.....sanin dalilin dake sa gabanshu na iri wannan faduwar neh yasa ya aminta da abinda idanuwanshi keh hanga mashi akwance a qasa tana kukan shagwaba.


Tsugunnawa yayi gabanta yana qoqarin kamota,kome yatuna yayi maza yajanye hannuwanshi yana binta da wani irin kasalallen kallo.....idanuwan nan sunqara zama qanana hadi da lumshewa tamkar wanda baya samun bacci....haka nan kuma gawasu ruwanan kwance a tsakiyar idanuwan nashi dasuka xama wasu mugayen oily.....


Kiyi hakuri banlura bane....banga tahowarki ba....inafatan bakiji ciwo ba?yajero tambayoyin yana mai bin jikinta da kallo.....gaba daya taqara chanxawa,tayi wani iri kyau na gaske!kallo daya xakamata kasan wanna amaryace mai chin amarchi......


Tunanin hakan naaqara dugunxuma xuciyarshi....har yau yakasa yadda matar dayafi so nachan tareda wani namijin bashi ba.....kuma ma har suna kwanchiya shimfida guda.....runtse idanuwan sa yayi cike da jin suyar da zuciyarshi na.mishi na nunkuwa tun aranar da aka daurawa amahn shi aure....


Hakan yasa yagaza jure tsugunnon dayake yayi qasa yana dafe kanshi dayariga ya bayyanar dawasu irin jijiyoyi rada rada tamkar Ka qirga.....


Allah kakawo mun dauki....Allah natuba...ina buqatar sassauchinka....yacigaba da amabar hakan cikin ranshi.....


Sautin kukant kawai kakeji ahankali....domin kuwa ganinshi a wanna yanayin kadai yaqara jagula mata ragowar lissafinta,hakan yasa tariqa jin tamkar ta shige qirjinshi taboye inda baby wanda zai ganta bare ayi tunanin xaqulota arabata dashi.....


Kukan nata baqaramin tsumashi yakeba.....hakan nan kuma wani gefe nazuciyarshi na kwabarshi da yanayin dasuke din ayanxu wanda sam bai kamata ba.....


Amma dake xuciya bata da qashi...haka xalika igiyar soyayyah da bege na jansu,wanda har hakan yasa suka shagalu,kuma suka manta....idanuwansu suka rufe da matsayin kowannensu,suka ta'allaka wajen qoqarin baiwa xuciyoyinsu abinda suke muradi......


Batareda da wani dogon tunani ba yamiqe afirgice ya janyota jikinshi yana tambayanta da menene?jikinne?duk yarude sakamakon ihun kukan dayaji tasanya da qrfi.


Sauke ajiyar zuciya sukayi atare....hakan nan kuma jikkunansu basu fasa amsa wasu muggayen saqonni ba,qara qnqameshj tayi tana sakin ajiyar xuciya....tareda fatan inama duniya xata tsaya ahaka chak!datafi kowa farin ciki.


Da sauri yayi qoqarin rabata da jikinshi yana mai xagin kanshi axuciyarshi....wane irin abune yake shirin jawo wa kanshi....matar mutane kwanche a jikin shu tamkar halalin shi.....tunawa da kuskuren dasuka aikata yasa gabnshu faduwa da jero neman yafiyar ubangiji acikin xuciyarshi.


Qara chusa kanta takeyi ajikinshi tana mai fatan karyarabata da jikinshj daya kasanche abu nafarkk datafison kwanchiya akai....sam bata damu da matsayinta ba....bata damu da abunda hakan zai janyo ba....haka xalika bata damu da koma meye ka iya zuwa yadawo ba!ta makanche bataji bata gani.....


Idan kagama rungumar mani mata ina buqatar shiga da ita gida inbazaka damuba.....yatsinkayo wata murya mai cike da kaushi da tsantsar baqin ciki na fada.


Afirgice tadago da kanta sukayi ido hudu dashi a tsaye chan agefensu yana qare musu kallo cike da wata iriyar tsana da bala'i kwanche male make bisa fiskar shi..


Tofa dan dan dan dan dan dan dan.....


***

Best regards to nagartattun mata(Nagarta Writers Association) you guys are such an utter inspiration.😻


Raina kama...!

By Noorieyyaah


Wattpad:@Noorieyyaah__


26


Sam gabanta baifadi haka kuma bata tsinchi kanta dayin danasaniba bisa halin da mijin nata ya riskesu ba...kunya ce kadai taji tadan kamata sakamakon yanda take ganin girman muhammad din,duk kuwa da irin tuhumammen kallon da shi muhammad din keh jifansu dashi tun bayyanuwar shi a gurin.


Miqewarta yayi daidai da hada idanuwanta datayi da gwaggo agefen motar ta tana qare musu kallo...kallo neh mai cike da al'ajabi da baqin ciki,kallo neh mai tarin ma'anoni,shin me yaran nan suke so duniya ta kallesu dashi?gwaggon tachigaba da tambayar kanta...


Wuf taqarasa miqewa jikinta na bari,haka nan kuma xuciyarta bata fasa bugawa ba tamkar ta faso qirjinta,sa'an nan kuma alokachi taji wani mugun tsoro na shiga lungu da saqo na kafatanin jikinta....a inda jikinta yai sanyi laqwas tamkar wacce aka sanya a na'urar sanyaya daki,take kuma saita tsinchi bakinta da ambatar Allah....


Shikam tsugunneh yake dafe dakai yana mai fatan inama mafarki yake....domin kuwa baitaba tunanin al'amarin xai girmama har haka ba,miyasa yabari son xuciya yakaishi ga aikata wannan abin tuurr din?take yaji gabadaya komi na duniyar ya sure mashi....haka zalika yagaza dago idanuwanshi yakalli kowa dake gurin,ballantana kuma akai ga batun miqewa.


Baiji sautin tafiyaba,yadai tsinchi kunnuwanshi dajin sautin gwaggon tana ambatar sunan shi cikin kaushin murya....wanda yanayin yanda yaji sautin muryartata kawai saida yasashi faduwar gaba....akasalanche yamiqe yana maijin nauyin hada ido da mahaifiyar tashi....


Ko kafin yabude baki ya furta wani abu sai jin saukar mari yayi tasss....kafin tunanin shi yadawo yasakejin wani,kafin yasake watstsakewa yaji saukar wasu....Saranda kawai yayi tacigaba da zuba mashi tapi takowanne bangare na fuskar shi.....tun khausar dake gefe guda na qirgawa cike da tashin hankali harta gaza sabida kukan dayachi qarfinta.....hasbunallahu wani'imal wakil....yau wane tashin hankali neh haka yasamesu..?


Riqe hannunta da muhammad yayi yasanyata juyowa afusace tana harararsa,zaka sakar mani hannu ko saina saba maka?ta ida maganar tana huci....girgiza kai muhammad din yake gamida sulalewa yadamqi qafafunta cike da magiya,,,domin kuwa halshenshi yayi nauyin dabazai iya magana ba.....ashe haka gwaggo take da tsananin fishi?


Inbanda sautin kukan amah da khausar kai harma da aslam din agurin bakajin komi,sauqin tama unguwar,unguwace ta masu hannu da shuni hakan yasa ko bera bai wuceba ta gurin tun faruwar al'amarin.....


Sake juyowa tayi ta kalli sulyman din,haka zalika tadaga hannayenta ta nuna shi da yatsa tace"ayau naqara tabbatar da akuyanchinka danakejin labari.....haka zalika ayau dinnan nake danasanin baka dukkan yarda danayi,sulyman ba kanka ka wulaqantaba ni ka wulaqanta....muryarta ta fara rawa...amma bata sarara ba tacigaba da zuba maashi ruwan fada kamar ta ari baki.....


Kaji dadi ka wulaqantamu....shin irin tarbiyar damuka baka kenan ko sulyman?har gidan auren yarinya sulyman?har gida zaka biyo matar mutane ka runguma sabida kai shashasha neh marass tawakkali?idan har ita shashasha ce mara hankali kai amatsayin ka na babba ina kakai hankali naka eyeeeeh?nace ina kakai naka hankalin?


Toh bari kaji infada maka....idan har ni nahaifeka sulyman....idan har ni nahaifeka!ko bayan raina ban amince maka da auren amah ba....na haramta aurenka da amah koda wani abu zaisami auren nata....wallahi tallahi kaji na rantse bakai ba amah..!


Zufa ce kawai keh keto mashi ta kowanne lungu da saqo na jikin shi.....marukan da gwaggon ta shishshinfida mashi basu dugunxumashi kamar yanda wadannan kalmomin nata na qarshe sukayi ba....yashiga uku shikam...wace iriyar jarabtache wannan keh bibiyar shi?(yayi maza yai istighfari a zuciyarshi).


Duk da ba sakinta muhammad din yayi ba,baisan miyasa jikinshi keh bashi amah din shi takusa dawowa gareshi ba....be san miyasa yakejin abin nan dasuka aikata zai iya shafar aurenta ba....wand hakan yasa yakejin tamkar nesa ce takusa xuwa kusa.....amma sai me?mahaifiyar shi naneman sanya katangar qarfe taakanin shi da farin cikin shi......ya ilahi yadafe kanshi gamida sulalowar wasu zafafan hawaye.


Ke kuma....tajuya gamida fuskantar amah din dake ruqunqume da khausar tana gabza kuka....gabadaya fiskar nan tayi kache kache da hawaye,majina da zallar tashin hankali.....kalamen gwaggon naqarshe su sukafi komi daga mata akwatin hankali.....tashiga uku ta lalace kawai take ambato.....


Baki shiga uku ba tukunna.....har talatin xaki shiga ayayin dabaki gyara halinki ba ki fuskanchi chewa aure ba abin wasa bane....ashe baki ji dukkan nasihohina ba agareki amah?ashe dukkan abinda nake fada maki shakulatin bagaro kikai dasu?ashe nu ban isa ingaya maki magana kiji ba amah?me kike nema kimaida kanki akan son banza son wofi?bakya tsoron fishin ubangijin ki amah?ko kin dauka shida yaqaddara maki al'amuranki ahaka baida dalilin yin hakan?ashe bazaki kasanche musulma ta qwarai ba mai yadda da qaddara?shin ina iliminki yatafi?


Sautin kukan tane yaqaru tamkar maqoshinta yatsage....haka kuma wanj tsoron Allah naashigarta,takaicin kanta da kuma illar son datake wa sulyman yasa tana neman kauche hanya....yasatasake tsagewa da wani kukan.....


Bakiyi kuka ba amah.....ba baki nake maki ba,amma bakiyi kuka ba sai kin rasa mai sonki da gaskia zaki dawo hayyachinki?bakya tunanin haqqin mijinki dakike dauka....baki damu da fishin shi ba agareku duk sanadiyar so.....so dai dakike ikirarin kina wa tsohon mijinki....wanda shi yahanaki kiyi tawakkali ki rungumi qaddara koh?


Girgiza kai kurum take cike da nadama da dansani......Allah ta tuba kayafe mata....bata ko iya magana,diba daya zakai mata kahango xallar sarewa da gazawa atattare da ita.....hakan yasa gwaggon sassauto fadanta agareta tacigaba da yi mata nasihohi masu ratsa jiki....haka kuma tasanyata tabawa mijinta hakuri,takuma qara roqar shi akan dayayi hakuri yadauki komi bakomi ba da izinin Allah hakan bazai sake faruwa ba.


Alqawari yaiwa gwaggon akan komi yawuce awajenshu da yardar Allah.....kuma in sha Allah komi zai daidaita.....babu wata matsala daga bangarenshi.....


Sai lokachin hankalin gwaggon yakwanta kana ta kallo khausar dake rungume da aslam suna kallon su....idanuwan nan sunyi luhu luhu alamun sunsha kuka,bama ya aslam duk da baisan meke faruwaba,amma ganin marukan da aka shishshinfida wa daddyn shi yafi komi bashi tsoro...don shi baisan ana dukan babba ba.


Janyo aslam din tayi tana lallashin shi,shiru yayi yana zare ido....donshi kam yanxu gaba daya gwaggon tsoro take bashi...


Umartar su muhammad din tayi dasu shyga gida,dama itama gidan wata qawarta taje shine tabiyo tadauki su khausar din sanin basu fito da motaba kuma bata turo a daukosu ba....daga zuwanta ta tadda wannan tashin hankalin.....tai tsaki tana maijin tamkar ta fasa ihun takaichin sulyman din.


Riqe hannun amah din muhammad din yayi ganin tana tangadi yayin dasuka nufi inda motar su gwaggon take driver na jiransu....sai alokachin suka lura da cewar babu motar sulyman din agurin.....shiru kowa yayi yana saqe saqe aranshi.


Bayan sunshyga motar neh gwaggon taleqo da kanta ta window tacewa amahn ki kula kiriqe mijinki amah.....mutum neh mai sonki da gaskia,don Allah kar insakejin wanu abu makamanchin wannan yafaru kinji koh?Allah yabaku xaman lafiya mai dorewa har abada.


Ameen nagode gwaggo.....in sha Allahu nayi maki alqawarin gyarawa,kuma kiyi haquri kiyafe mani don Allah....taqarashe maganar tana sake sakin kuka.....


Bakomi Amah....Allah yayafe mana baki daya,kedai kije kiyta istigifari, Allah yakasanche mai yawan yafiya...ku kula da kanku sai munyi waya..


Suka wuce suna masu dagawa juna hannu.....billewar motar su gwaggon yayi daidai da sakar mata hannh da muhammad din yayi,kana bai jirayi komiba yai gaba yashige gidan batareda da yaqara kallon inda takeba.....


Shiru tayi tana mai bin bayanshi da kallo.....she thought komi yawuce awajen shi?innalillahi tafara ambato sakamakon tuna irin mugun kallon daya watsa mata kafin yashige....


Jiki a salube tabi bayanshi tana mai fatan Allah ya kawo mata dauki.


***

Best regards to NWA.

Inayinku😍(27)


Wannan shafin sadaukar wa neh ga dukkanin masoya wannan littafin, nagode da hak'urin bibiya ta da kuke a koda yaushe ba tare da nuna fishin ku, ko gajiyawar ku bisa jinkirin typing da nake ba. Hak'ik'a ina alfahari daku, domin ni nasan without you guys da bamu zo inda muke ba.

       Ana mugun tare! Irin sosai dinnan.🙌


Ina yi wa d'aukacin musulmi murnar zagayowar watan ramadhan. Allah ya amshi ibadun mu amin. 


***

"Wai menene zaki bi ki damu rayuwa ta eyeeeh? Ban san kuma me kike buk'ata ba bayan abinda nai miki a baya". Muhammad ya furta maganar cike da zallar k'osawa a muryar ta shi. 


K'ara shigewa tayi jikin shi tana kukan shagwab'a. "Don Allah hunny ka yafe mani, wannan hukuncin yayi mani tsauri" ta sake k'ank'ame shi jin yana k'ok'arin sake raba ta da jikin shi a karo na hudu. 


Shiru yayi yana k'ara hasko hoton Amatullah d'in da yayi a k'irjin mutumin da yafi tsana kaf duniyar nan, hakan yasa yaji wani sabon bacin rai na sake ziyar tar shi. "How dare him to touch his damn wife"? Yarik'a had'iye wani miyau cike da jin zafin abin a k'irjin sa tamkar yanzu abin ke faruwa. 


"I'm so sorry hunny... Don Allah ka fahimce ni" ta langab'ar da kai cike da son ya tausaya mata. Ganin yanda jijiyoyin kan shi suka bayyana yasaka ta k'ara rud'ewa domin kuwa tabbas tasan abin na nan a ransm shi bai sake shi ba. 


"Damn! Damn! Damn him". Da sauru takai hannunta ta rufe bakin shi gamida girgiza kan ta cike da nadama mabayyaniya a kan fuskar ta. "Don girman Allah hunny maganar nan ta wuce, na rantse maka da Allah nayi nadamar abinda ya faru, kuma nayi maka alk'awari da tsarkin mulkin Allah hakan ba zai sake faruwa ba in Allah yaso ya yarda, please ka yarda da ni." tasaki kuka mai tsuma zuciya.


Rubtse ido yayi yana jin kukan nata na ratsa jijiyoyin jikin shi, haka nan kuma sabon son ta na sake ninkuwa a birnin zuciyar shi, hak'ik'a kaunar Amatullah da yake daga indallahi ce, bazai taba iya dena son ta ba har qarshen numfashin sa.


Kukan nata bak'aramin tab'a zuciyar shi yake ba, hakan yasa ya kara janyo ta jikin shi gamida rarumar bakin ta. Take kuwa yaka she bakin kuka, domin kuwa tsit kake ji sai sautin sheshek'ar yanayin da suke ciki. Hak'ik'a yayi kewar matar shi! Kwana bakwai cur yana hora ta bisa laifin data yi masa, wanda horon da yake mata har da shi kan shi ya had'a, diba da irin wuya da galabaita da yayi na rashin ta a kusa dashi na wad'annan kwanakin. A inda kwanakin suka zame masa tamkar dogayen shekaru neh, amma haka nan ya jure domin nuna mata kuskuren ta ko don gaba.


Ganin yana shirin zarcewa, yasaka ta ture shi a hankali gamida nuna mashi hanyar bedroom din su. Da sassarfa ya sungumeta bridal style ya nufi makwancin su da ita, hak'ik'a yazama dole ya fanshe kwanakin da ya d'auka basa tare! Dole ne wannan.


***


Sai dai kuma ta riga da tasan cewa son Sulyman halitta neh a jikin ta, ba iyawar ta bace, haka kuma ba ikon ta bane. Ha'k'ik'a Allah shine masanin sirrin boye da ya halicci soyayyar Sulyman a zuciyar ta. 


Hakan yasa ta cigaba da boye soyayyar shi a cikin zuciyar ta da k'arfin addu'ah. Takuma dage waje ganin ta maye gurbin shi da mijin ta mai k'aunar ta da zuciya d'aya. 


Haka zalika bata gushe ba tacigaba da yiwa Sulyman din fatan alheri a duk inda yake, tare da yi mashi fatan kasancewa da wacce ta fita. 


Hawaye suka cigaba da kwararo wa daga idanuwanta. 


***


A kwana a tashi sai Allah, rayuwa tacigaba da tafiya yanda ya kamata. Domin kuwa zama neh mai cike da aminci da k'auna keh gudana a gidan Amatullah da Muhammad.


K'warai da gaske tayi namijin k'okari wajen ganin ta fidda tunanin Sulyman a zuciyar ta, haka zalika kullum tana kai wa Allah kukan ta akan ya rabata da son shi a zuciyar ta ko don ta samu rahama a gidan aurenta. 


Alhamdulillah ansamu cigaba domin kuwa addu'ah bata fad'uwa k'asa banza, diba da irin d'imbin cigaban da aka samu a lamarin, wanda a kullum bata fasa godewa Allah bisa ni'imomin shi a agareta, mussamman na bata.miji kamili mai k'aunar ta upon all her flows and imperfections!


Tabbasa Muhammad mutum neh mai daraja a idaniyan ta,zata kuma cigaba da addu'ar neman zama mai dorewa tare da shi na har abada.! Masu iya magana su kace "Wani hanin ga Allah baiwa neh". Wannan haka yake.


***

FIVE YEARS LATER.


Cike da kulawa take lallab'ashi domin yasamu koda ruwan tea d'inne ya shiga tumbin nasa da yake a tamule kuma ashafe tamkar wanda bai tab'a saka k'wayar hatsi ba a ciki.


"Gwaggo don Allah ku bar ni haka nan in mutu..." da hanzari gwaggon ta sanya hannuwan ta ta rufe mashi baki cike da dimbin kulawa da tausaya wa. Ha'k'ik'a da tana da maganin abinda ke damun Sulyman da ta yi mashi, duk kuwa da irin furucin da tayi a shekarun baya bisa bacin rai da son ganin rayuwar auren baiwar Allah bai lalace ba.


Sai dai yanda ta daidai ta rayuwar Amatullah haka ta zama jagorar tarwatsewar rayuwar nata d'an, duk a sanadin furucin da tayi domin ganin al'amura sun daidaitu. Ta sake gyara mashi bargon dake lullub'e da k'afafun shi cike da jimami da tausaya wa.


Shekaru biyar kenan yana fama da ciwon bugawar zuciya ba akan tsari ba, inda hakan yatai maka wajen kafuwar hawan jini a tare dashi, wanda tun lokacin da yakamu da ciwon bai kuma lafiya ba, sai dai yaji sauk'i lokaci-lokaci sakamakon magungunan da aka d'orashi a kai. 


Hak'ik'a bazai fasa godewa ni'imar ubangiji ba bisa bunk'sa shi da yayi da ragowar rayuwa don ganin ya gyara b'arnar da yayi a baya. 


A kullum yana mai nadamar irin rayuwar daya aikata a boye ba tare da sanin iyayen shi, tabbasam ya ha'incesu ta hanyar nuna masu shi mutumin k'warai neh bayan ba haka bane a bad'ini. 


Hakan yasa akoda yaushe yake k'ara godewa soyayyar da yake yiwa amatullah wacce ita ce tazama silar shiryiwar shi kuma sanadin canzuwar kaso mafi chasa'in na munanan dabi'un sa. 


Hak'ik'a soyayyar amah tazame mashi alkhairi da akasin hakan, domin kuwa ta taimaka wajen kafuwar sabon mutum a jikin shi, haka nan kuma ta taimaka waje tarwatsa dukkan ragowar farin cikin rayuwar shi dalilin rasa ta da yayi.... Rasawa ta har abada. 


Ita d'in alheri ce agareshi, alheri mafi soyuwa domin kuwa har yakoma ga mahalliccin sa bazai fasa godewa ni'imar shi a gare shi na bashin aron y'ar k'aramar rayuwar da ya yi tare da amatullah ba. Zau dawwama yana mai godewa Allah (S.W.T.) daya azurta shi da samun chanjin rayuwa. Allah abin godiya neh. 


Ya runtse idanun shi a yayin da bugun zuciyar shi ke tseren doki a allon k'irjin sa, hakan yasa ya dafe gefen zuciyar shi yana mai fatan samu sassaucin halin da yake ciki. 


Bai tab'a tunanin rayuwa zata iya juye wa haka ba, ya d'auka yana da ikon son abin da ya gadama da k'in abin da ya gadama, ashe ba haka rayuwar take ba. Allah shine mai ikon sanya soyayya a zuciyar wanda yaso kuma a yanayin da yaso. 


Ya kuma sanya k'iyayya a zuciyar wanda ya so da kuma yanayin da ya so. Hak'ik'a da yasan zai tsinci kan shi a irin halin nan, da tabbas ya kula da matar da ta so shi domin Allah da zuciya d'aya. 


Amma inahhh damar shi ta riga da ta wuce shi, sai dai fatan gamawa da duniya lafiya. Hak'ik'a hausawa sunyi gaskiya da suka ce RAINA KAMA... KAGA GAYYAH! Domin kuwa ya ga illar wasa da dama, haka zalika yaga illar wasa da zuciyar masoyi na hak'k'a, Tunda ga shi nan yana girbar abinda ya shuka. Allah abin godiya! 


Ya runtse idanuwan shi a yayin da wasu zafafan hawaye suka cigaba da tsartuwa bisa ramammiyar fuskar shi mai cike da k'asumba. Sa'an nan kuma a hankali yaci gaba da furta la'ilahaillahu Muhammadurrasu lullah (S. A. W). 


AHANKALI JIKIN SHI YASAKI FUSKAR SHI D'AUKE DA MURMUSHIN SASSAUCI MABAYYANI..... ALLAH AKHBAR! 


***

Alhamdulillah! 


Noorieyyaah ce ke maku fatan alheri. Tags: #Danasani, #Tausayi #Qaddara #Rayuwa #Soyayyah #Hakuri #Nooriyyah #hausanovel
30586
2
3
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

2019-11-05 13:35:30

2019-10-13 21:43:39

mardiya2019-05-19 05:01:13plss INA Neman raina kama na bilyn Abdul

Noor Amin2019-01-03 19:26:04Nagode sosai❤❤

Noor Amin2019-01-03 19:26:04Nagode sosai❤❤