Maza Da Mulki!

Written by Mrs OmarPublished on 2018-12-14 10:44:01Category FictionLittafin maza da mulki littafi ne da yake dauke da wa'azantarwa gami da nishadartarwa littafin gidan sarauta na wata kyakkyawar yariya yar sarkin katsina wada tatashi bata son talaka ko allama sai dai Allah cikin ikonsa yayi nasa.. tags: #soyayya #qauyanci #nadamaDuba was labarai »

MAZA DA MULKI

★★.   *MATA DA*  ★★

 ★.    *TAK'AMA*   ★
*بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم*


      *TSOKACI*


_wannan labarin k'irk'irre ne ba gaskiya bane nayi shine dan nishad'i da fad'akarwa, idan yazo iri d'aya da naka toh akasin haka aka samu.._       *GARGAD'I*


 _Ban yarda wani ko wata su juya min labarina ta kowace hanya ba in ba tare da sanina ba ko ince izinina ba, koda kuwa sunan jaruman da ke cikin ne, duk Wanda yayi min haka toh Allah ya isa, dan haka a kiyaye._```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION```

___________________________________


  *Story and written by*

      *_MRS UMAR_*


       *edited by*

   *_PRINCESS AMRAH_*


      *in dedication to*

    *_FIDDAUSI SODANGI_*


         ```Page 1```


      *GARIN KATSINA*~~Garin Katsina gari ne da ya tara d'umbin abubuwan ban sha'awa, Allah ya albarka cu garin Katsina da manyan masu kud'i,

 inda aka tara manyan 'yan boko, 'yan siyasa, harma da 'yan kasuwa,

uwa uba babbar Masarautarsu da ake ji da ita a duk fad'in Africa babu wanda baisan da zaman wannan masarautar ba.


  Ni dai ido kawai nake zarewa saboda yanayin garin ya bani sha'awa sosai, da yake ya kasance yanayin sanyi ne duk Wanda kagani zaka ganshi sanye da rigar sanyi a jikinshi,

ina cikin tafiya Allah ya sada ni da wata k'ofa kai na d'aga ina d'aga kai naga an rubuta ( *K'OFAR SORO*) a jikin k'ofar, harda tuntub'e naci saboda yanayin yanda akayi rubutunma kanshi abun sha'awane, anyishi da kalar golden hakan yasa ya haskaka wurin tamkar da zinari akayishi.

   Kai tsaye na danna kai cikin k'ifar duk da bansan inda zan nufa ba.

  A hankali nake tafiya yayin da naci karo da wani katafaren gida, 

dakaga gidan kasan gidan sarauta ne, gidan yasha ado anyi mashi Penti da red and white, ido na k'ara zarewa, juyowar da zanyi kenan na hango wata kyakkyawar yarinya na tafiya cikin k'asaita yayin da wasu 'yan mata na take mata baya su biyu, yanayin yanda take tafiya sai ka d'auka itace sarkin ko kuma sarauniya,

tafiya take d'aya bayan d'aya, tana jefa k'afarta kamar bata son taka k'asa, duka_duka shekarunta bazasu wuce shekara 17 ba, amma yanayin isarta da tak'ama sai ka d'auka irin babbar macen nan ce, sanye take da Gown har tana jan k'asa, jikin rigar red colour ne anyi mashi aiki da Golden, duk da rigar jikinta ta sauka har k'asa bai hana naga heel Shoes d'in da take sanye dashi ba, dogo ne kalar aikin rigar ta watau golden colour,

wani d'an siririn mayafi ta yafa a kanta tayi parking d'in gashinta, ta d'an ja mayafin baya ne shi yanuna gashin kanta wato (see me kamar yanda 'yan mata suke kiranshi), fara ce tana da tsayi bata da jiki wato siririya, sannan tana da dukiyar fulani daidai gwargwado, hancinta dogone kamar biro ko kuma ince margin biro d'in,

bakinta d'an k'arami ne kai kace teaspoon ma vmbazai iya shiga cikinshi ba, eyes d'inta manya ne k'wayar idonta bak'a ce har wani ruwa ke kwanciya a ciki.

 Chewing gum ne a bakinta a hankali take taunarsa cike da izza da tak'ama, taunar chewing gum d'inda take shi ya bayyana dimples d'in dake kwance akan kumatunta both sides.

  Duk tauna d'aya sai ta lumshe idonta kamar mai jin barci,

kafin ta k'arasa fitowa da gudu wasu motoci suka danno zuwa inda suke,

kai tsaye wajenta motocin sukayi parking, motocine na idon cin duniya kowace jikin motar an rubuta   *GIMBIYA FIDO* akai, anyi numbering nasu d'aya bayan d'aya,

 gaba d'ayansu suka fito daga motocin kamar zasu fad'i suka zube a k'asa suna kwasar gaisuwa, 

"Barka da kwana gimbiya 'yar sarki jikar sarki Allah ya d'aukaka masarautar *SODANGI,* insha Allahu sai kin gaji mahaifinki".

 Cikin isa ta wani saki murmushi ta kad'a k'wayar idonta, a hankali ta juya ta kalli Hindu da sauri Hindu tace

"Gimbiya ta amsa".

Hindu ce ta bud'e mata d'aya daga cikin motocin,

Genesis k'irar ( *2016*) ta shiga Mairo tayi saurin d'age mata rigarta, saida ta shiga suka rufe k'ofar kafin Mairo ta shiga d'ayar motar, ita kuma Hindu ta shiga inda gimbiya take watau gaba, a cikin wadda aka rubutama *FIDO 1*

 sannan matasan sukayiwa motocin key,

***

Hindu da mairo kuyangun gimbiya Fiddausi ne dukkansu bazasu wuce sa'anninta ba,

d'aya daga cikin phone d'inta yayi k'ara da sauri Hindu ta mik'a mata tana yatsina ta amsa tayi Picking,

"Hello Princess kina gida kuwa?" Wata murya tayi magana a cikin wayarta k'irar galaxy grand prime wadda har yanzu ba'ayi releasing nata ba, itama har company taje akayi mata ita,

 "No bana gida" ta bada amsa a gajarce.

   "Kinje inane?" Aka sake jefo mata tambaya,

  "Bana son yawan magana fa and You've already know that, finally, na fita yanzu zanje restaurant d'in *zamburush* ki samine a can". Ta mik'awa Hindu wayar sannan tayi hanging uo nata.

Hindu tayi murmushi tare girgiza kanta saboda a kullum tana mamakin girman kai irin na uwar d'akinta, 

duk inda suka bi sai anyi maganarsu daga mai cewa tana burgeshi sai mai zaginta, dama haka duniyar take, idan wani ya k'ika to tabbas wani sai soka komai bak'i da munin halinka.

  Kai tsaye zamburush suka nufa duka matocin uku tare sukayi parking, gaba d'aya mutanen dake wajen saida suka juya kallon motocin savoda yanayin tsarinsu ya banbanta da sauran motoci, kuma duka sabbine akayi ordering nasu saisa babu wanda ya gane cewa motocin *GIMBIYA FIDO* ne sabida kowa yasanta, ansan yanayinta ankuma san mktocinta.

   Mairo ta fito da sauri ta bud'e mata k'ofa, biyu daga cikin mazan sukayi saurin shiga cikin restaurant d'in, shima red and gold kamar adon rigar dake jikinta

sai da ta d'auki tsawan 5 minutes kafin ta fara zuro k'afarta, heel shoes d'inta da Chain d'in da ke k'afarta suka haska fuskar mutanen dake wajen, 

duk jama'ar dake wajen suka saki baki dan ganin wacece a cikin wad'annan motocin, gaba d'aya ta fito da gangar jikinta,

tana fitowa cikin yatsina ta mik'awa Hindu hannunta, da sauri Hindu ta d'aura mata glass a hannunta,

 Saida tasa glass d'in kafin Hindu da Mairo suka take mata baya.....


       *N.W.A*     _BY FATEEN SOJA_

     *MAZA DA MULKI*

★★.    _MATA DA_  ★★

 ★.     *TAK'AMA*   ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION 

______________________________


   _story and written by_

       *MRS UMAR*


       _edited by_

     *PRINCESS AMRAH*


     _in dedication to_

     *FIDDAUSI SODANGI*


          _page 2~~Suna shiga sukayi saurin goge mata kujerar da zata zauna akai, cikin yatsina ta iso wajen da sauri Hindu taja mata d'aya daga cikin kujeran ta zauna, 

matasan nan su biyu suka fara jera mata kirari,

"Barka da isowa gimbiya Fido, 

 'yar sarki jikar sarki taka lafiya dai uwar d'akinmu, gaba sallamun baya sallamun taka lafiya dai gimbiya kinyi gaba babu gimbiyar da ta kaiki saidai ta k'asanki,

  Mak'iyanki sun buga dake sun barki insha Allahu sai kin gaji mahaifinki".

 Ta wani lumshi ido ta k'ara gyara zama saboda a rayuwata tanaso taji ana mata kirari sai kanta ya k'ara girma da fashewa, alama tayi masu da hannu ma'ana zasu iya tafiya waje, jikinsu na rawa suka kama hanyar fita Mairo da Hindu suka koma bayanta suka tsaya.

"Humm baabah kana ganin yarinyar nan yanda take isa sai kace itace sarkin?". 

  "Au! ai kad'an ma kagani yarinyar nan jinta take kamar itace sarkin, yarinya k'arama da shegen girman kan tsiya,

  ko da yake mahaifinta ke da laifin yarinya k'arama ya fidda ta karatu zuwa k'asar waje". 

  "Kai baabah ina take karatun?" 

  "Naji ance wai a China take karatu". 

  "No wonder, dole ta zama haka saboda yana tunanin ita d'aya ya haifa saisa yake sangartata haka, yabi ya lalatata bata ganin kimar kowa a idonta". 

  "Dama hausawa sunce *MAZA DA MULKI MATA DA TAK'AMA,* kuma fa na gasgata hakan, wai abun mamaki sai mace ta dinga TAK'AMA kamar ita ke MULKIN saboda nan gaba yarinyar nan ta k'ara girma idonta ya kara bud'ewa toh wallahi talakawa zasuci ubansu wajenta sai kowa ya wahala".

  Duk wannan maganar wasu samari ne ke yinta sunayi suna hangen Gimbiya Fido daga nesa.

   Zamanta da kamar 10 minutes sai ga wata yarinya wadda itama bazata wuce sa'ar taba, sanye take cikin wasu english wears black Jeans da pink top, sunyi tight d'inta sai wani d'an siririn mayafi da ta yafa maganin babu, sai ga wasu mahaukatan hill shoes tasha, haka yasa duk mutanen dake wajen kallon gimbiya ya dawo wajenta, cikin isa da yatsina ta ida isa inda gimbiya take zaune, jikin table d'in dake wajen ta aje handbag d'inta cikin yatsina ta fara magana,

"Princess I don't know what is wrong with u, I called u several times but u kept rejecting it why?"

Sai da gimbiya ta murmusa kafin ta d'auki k'afarta ta d'aura kan table d'in da ke wajen, ta d'aura k'afa d'aya bisa d'aya cikin isa ta fara magana, 

tana magana tana taunar chewing gum duk magana d'aya sai ta lumshe idonta sannan ta bada k'iriss da chewing gum d'in.

"Am sorry Anum, I din't want to see ur call thats why".

Anum tayi ajiyar zuciya da sauri Mairo ta ja mata d'aya daga cikin chair d'in dake wajen, 

gimbiya ta dubeta tace 

 "Anum what do u want to eat?" 

 "Humm I like SHAWARMA yes shawarma chicken I want to eat it".

Tana rufe baki gimbiya fido ta kalli Hindu da sauri Hindu ta juya ta nufi wajen serving d'in abinci

"Kai ai wallahi sai nayiwa yarinyar can magana kaji yanda ta shiga zuciyata kuwa? 

 "Humm bazan hana kaba dan wallahi nasan girman kan yarinyar nan tana jifa kamar ita ke MULKIN garin nan". "Kai mutumin forget girman kanta kar ka manta fa duk wata mace bata min wuyar samu, komai cikar izzarta kuwa".

"Toh sai ka dawo ni kam ba dani ba, ina nan ina zuba idona dan ganin yanda zata kaya tsakanin kai da ita, dan nasan ba zakuyi rabuwar arzik'i ba",

  "Naji nidai sai naje".

 "Yana tashi ya nufa inda su gimbaya suke direct babu ko kwana kwana ko alamar shakka ya isa wurinsu....

     *KUCI GABA DA KASANCEWA DA*
     _FATEEN SOJA_


 *MAZA DA MULKI*

★★.   *MATA DA*  ★★

 ★.   *TAK'AMA*   ★


NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

________________________________


      _story and written by_

         *MRS UMAR*


          _edited by_

       *PRINCESS AMRAH*


        _in dedication to_

     *FIDDAUSI SODANGI*        _page 3_
~~"Hi princess! You are so much beautiful princess, humm am so very happy to see u a....."

   "Dan Allah dakata mallam ko ince d'an talakawa!, shin wai wama yabaka damar da zakazo kana cikawa gimbiya dodon kunne haka?" 


 Cikin zafin rai ya dubi Mairo da tayi maganar yace


"How dare u da zaki kirani d'an talakawa kinsan waye ni kuwa? Humm ko dayake bai kamata ina b'ata lokacina ina magana da kuyanga haka bah, sai mutuncina ya zube a idon jama'a".


 Yana murmushi yaja d'ayar kujera ya zauna daga gimbiya Fido har Anum ba wadda ta kalleshi, haka yaci gaba da zuba, kamar kurnar da ba dad'i,


"Oh sorry I forgot to tell u my name,

so my name is Affan Khalil, my friends also call me dogon gaye..."


 Kafin ya k'arasa rufe baki Anum ta kwashe da dariya har cup d'in da ke hannunta yana shirin fad'uwa da sauri ta ajeshi tana dariya, 

 Gimbiya Fido ta gyara zamanta sannan ta d'auki glass cup d'in kusa da ita ta kurb'i d'an Juice d'in dake ciki kad'an sannan takai dubanta ga Afran tace 


 "Mustapha Khalil Senator represented of Katsina, shine mahaifinka ko kana da wani uban wanda yafishi?,

 Ahmad Basheer SODANGI ba Wanda bai san da wannan masarautar bah,

 a duk fad'in Africa so Who is Mustapha Khalil in all Nigeria? I think he is....d 

 "Stop it Fiddausi SODANGI! Rashin kunyar taki har tabar kan talakawa ta dawo wajen iyayenmu no!! that's impossible, baki isaba wallahi kinyi kad'an, iyayena sunfi k'arfinki, na dad'e ina jin rashin kunya da rashin mutunci irin naki, to ni zan maki maganinta wa..." 

 Kafin ya rufe baki kawai ta watsa mashi juice d'in dake hannunta sai dai kawai yaji saukarshi a jikinshi haka yasa duk jama'a dake wajen suka juyo kallonsu,

 "Look at me dogon gaye kake ko wa? These gurls that you called kuyangu sunfi k'arfinka, sannan kuma sun fika daraja a wurina, dan haka close your so called mouth and leave this place before insa ayi k'asa k'asa da kai"

Cikin zafin rai idonshi yayi jajir yace 

"SODANGI u made a Mistake, ni kike fad'awa wannan maganganun? Hmm! Amma fa ki sani kin tab'owa kanki, saboda ni ba'a tab'ani a zauna lafiya, dan haka na baki bashin wannan ranar dan ba zance na yafe miki ita ba"

 "See this man, see me se wahala ooo, duk wannan abin da tayi maka baisa ka saduda ba?"

 Anum ce yanzu tayi magana shi yasa ya juya ya wurga mata harara, 

   Tsoki yayi sannan ya juya ya nufi wajen abokinshi yana zuwa yaja hannunshi suka bar wajen,

  Anum ce ta karkace ta rage murya sannan tace ma Gimbiya Fido

 "Gaskiya princess this dogon gaye is very handsome guy, bashida tsoro ko kad'an, ya burgeni sosai, haka nake son ganin namiji jarumi ba malalaci ba, duk yanda ake tsoronki a garin nan baisa ko kad'an shi yaji tsoron ba, irin yanda yake magana ma abun sha'awa ne, kuma..."

 "Anum are you mad? what is wrong with? Ina tunanin kin manta ko ni wacece ko?" 


 "No gimbiya ban manta ba" Anum ta bata amsa,


 "Just forget that stupid guy, na kula d'an rainin hankali ne, and also I don't like Nigerian guys at all, banga abunda ya burgeki ba game da wannan d'an rainin sense d'in".


Anum ce ta k'ara kwashewa da dariya harda rik'e ciki


 "Princess I don't know what is ur problem, ke ala dole bakya son 'yan Nigeria, bayan kuma all ur family suna Nigeria".


 Hararar da gimbiya ta wurgawa Anum ne yasata yin shiru ba shiri tayi maintaining.


****


Driving yake amma ji yake kamar zuciyarshi zata buga saboda tunda yake ba'a tab'a mashi irin wannan cin mutuncin ba, ko makamancinsa ba'a tab'a yi masa ba.


 "Please friend calm down mana, sai da na fad'a maka halin yarinyar nan na hanaka zuwa wurinta nake kar kaje but you refused, ga irinta nan ai ta wulak'antaka a banza".

 "Hmm Haydar don't worry, ai ba bulus taci ba, kasan halina tun asali ni ba'a tab'a ni a zauna lafiya, na d'auki alwashin sai na mata wanda yafi wannan"
        *N.W.A*


     _BY FATEEN SOJA_


 *MAZA DA MULKI'*

★★.    _MATA DA_  ★★

 ★.     *TAK'AMA*   ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

_________________________________


    _story and written by_

         *MRS UMAR*


          _edited by_

     *PRINCESS AMRAH*


     _in dedication to_

    *FIDDAUSI SODANGI*
           _page 4_

~~"Taya haka zata faru bayan kai kanka kasan halin princess yarinyar bata da kirki? yarinya ce da take jin kanta kamar itace sarkin ma, kai ko sarki baya nuna izzar da take nunawa". 

 "Humm Haydar kenan, ina zato har yanzu baka san halina bah, humm! anshe goruba hannu kuturu ba wuya bane dan haka wait and see sai na dasa mata soyayyata a zuciyarta ko ta halin yaya ne wallahi kaji na rantse".

 "Toh ba zance maka a'a bah, amma kayi a hankali ni nasan halinta baki d'aya"

 "Hmm! inaso ka bincika min school d'in da take a China because..."


 "Kafin yak'arasa maganar ya cije lips d'inshi ya girgiza kai saboda shi kad'ai yasan mugutar da zai shuka mata, a wannan lokacin ne yayi parking a Guest house d'inshi inda ya tanada domin aje 'yan Matanshi,..


   °°°°°°°°°°°°°°


Wata kyakkyawar mace nagani zaune kan bed ta buga uban tagumi sai tunani take, sanye take cikin kayan barci ta baza gashin kanta a baya da ka ganta kaga cikakkiyar bafulatana,

 duk bayan wani lokacin takan d'aga kanta ta duba agoggon dake manne a d'akin, k'ofar d'akin da aka banko ne yasata saurin d'aga kanta, tsawar da ta daka mata ne yasata tsayawa cak!


 "Dakata daga ina kike a wannan lokacin? yanzu Fiddausi a wannan lokacin zaki dinga dawowa gida? ki duba time kiga k'arfe nawa?"

 "Ido ta d'aga ta dubi agoggo taga k'arfe 11:05PM ta wane yatsina fuska ta nufi kan gado ta zauna, ko a jikinta.

 "Magana nake maki kika maidani 'yar iska tsaye tana magana"

 "Toh mommy me kike so nace maki? aidai kin san ba b'ata zanyi bah because ni ba yarinya bace, ko kina so na zauna a gida kina kallona ne?"


 "Shiru mahaifiyar tata tayi ta saki baki tana kallon d'iyarta saboda inda sabo ta saba da halinta, cikin sanyin murya ta zauna kan gado kusa da fido tace 


 "Please Fiddausi listen to me, I'm ur Mother ba zanso duk wani abinda zai kawo matsala a rayuwarki bah, burina bai wuce kizama d'iya kamar sauran yara bah, a koda yaushe ina maki addu'a Allah ya kareki a duk inda kike, inaso kizama mai tsoron Allah saboda wannan ba rayuwa bace.."

  "Oh God! Mommy u will never understand me am telling u niba yarinya bace, dan haka ki barni nayi rayuwata yanda nake so".

 "Yanzu ni kike gayawa wannan maganar Fiddausi? ina guje maki ranar da zakiyi nadama ne"

 "Mtsss"


 Bata k'ara yima mahaifiyar tata magana bah, sai dai tsokin da ta buga ta finciki towel d'in dake kan mirror ta nufi toilet,

 Mommy kasa magana tayi sai dai hawaye dake bin fuskarta cikin sanyin jiki ta mik'e ta nufi k'ofar fita, a parlour gimbiya taci karo da Hindu tana tsaye tana sallah mommy ta girgiza kai saboda tasan gimbiya ta jata zuwa yawo shiyasa bata samu damar yin sallah bah, sai yanzu cikin shashek'ar kuka ta nufi d'akin mai martaba,

Mai martaba SODANGI zaune yake kan sallaya yana lazimi k'ofar da aka turo ne yasashi saurin d'aga kanshi, yana ganinta ya gane akwai matsala, 


 "Toh me yafaru kedawa kuma?" 

 "Mai martaba kasan damuwata a kullum matsalata bata wuce akan Fiddausi ba, burina bai wuce ta zama d'iya kamar sauran yara bah, mai martaba kana sane da duk irin wulakanci da take shukawa mutane a cikin garin nan amma ka zuba ido kana kallon...."

 "Dakata...." mai martaba ya fad'i bayan ya d'agawa matarshi hannu cike da fushi yace....

  

    Aka TEEMA Lady


 *MAZA DA MULKI'* 

 ★★.   _MATA DA_  ★★

  ★.     *TAƘAMA*   ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

______________________________


     _story and written by_

         *MRS UMAR*


          _edited by_

      *PRINCESS AMRAH*


       _in dedication to_

    *FIDDAUSI SODANGI*         _page 5_

 


  Mai martaba ranshi yayi matuk'ar ɓaci, cikin zafin zuciya ya ɗaga mata hannu tare da fad'in                             "please Bahijja keep quiet i don't want to hear anything from you, because how many times I told you don't said anything to my daughter again, hmmm Bahijja i don't know what is wrong with you, ke kullum kamar bake kika haifi yarinyarnan ba?, kin ɗaura mata karan tsana, babba dake amma kin sakama yarinya ido, ko motsi tayi akan idonki"...

 Mamaki ya hanata bari ya ƙarasa, ta tari numfashinshi, "Amma mai martaba... "Dakata ban gama magana bah, shekarata nawa ina ne man haihuwa? ban samu bah sai yanzu, toh ki sani zan iya komai akan farin cikin ƴata, rashin son da kike nuna mata ko 'yar uwarki bata nuna mata shi ta d'auketa kamar ita ta haifeta, 


 Mai martaba yana magana ne cikin faɗa yayinda ta kasa magana sai hawaye da ke bin fuskarta na takaici, cikin sanyin murya ta furta

 "Allah ya huci ran mai martaba kayi hak'uri, inaji a raina nafika son Fiddausi, a kullum ina mata addu'ar zama ɗiya ta gari kamar kowa, sai dai kash mai martaba duk kana da labarin abinda take cikin garin nan ta matsawa talakawanka, da zarar ta fita jama'ar gari tsoronta suke haba mai martaba shikenan sai mu sa mata ido duniya ta zagemu?"...

 "ke duniya zata zaga ni kam ba mai zagina saboda banga abinda ƴata keyi bah, dan haka ki tashi ki koma ɗakinki kafin ki sani ciwon zuciya"..


 Cikin ban mamaki ta mik'e dukda abun ba sabo bane a wajenta ba,

 saboda a kullum indai zata kawowa mai martaba ƙarar Feedoh toh a ranar sai sunyi faɗa, ta rasa yadda zatayi dashi,

haka ta koma ɗakinta zuciyarta cike da bak'in ciki da k'unar zuciya. 


 ***************


 Washe gari! 


 Wata mata ce naga ta tura k'ofar ɗakin gimbiya Feedoh, bak'ace sannan tana da ɗan faɗin fuska, tanada jiki da alama itama matar gidance, kai tsaye ta nufi bedroom ɗin Feedoh, kwance take kan bed ɗinta yayin da ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya ga phone ɗinta rike a hannunta tana dannawa, tana ganin matar ta iso ta tashi cikin murna haɗe da murmushi, kasancewar gimbiya Feedoh ba dariya take yi bah, idan ko har tayi dariya toh ta muguntace,


 "Adda sannu da zuwa, shine bazaki bari inzo da kaina, na gaidaki ba? sai kinzo da kanki,

 "Haba dai ta hannun damana ai ke sarauniya ce zan iya miki komai dan ganin farin cikinki, saboda ni ban haihu da mahaifinki bah, amma inaji a jikina kamar nina haifeki zan iya miki komai a rayuwa.

 "Hmmm na sani Adda, but Adda i don't know what is happen to my mother because she hate me so much, bata son ganin farin cikina tafison a kullum in dinga sakarwa talakawa fuska su rainani dana fara abu zakiga ta fara min wa'azi.

 "Hmmm! My daughter don't worry am Here for you, ki daina damuwa kinsan kema dole Bahijja taso talakawa dan kuwa su suka haifeta kinga ko babu yanda za'ayi taki talaka, so dan haka shawarar da zan baki babu ruwanki da wa'azinta kici gaba da harkarki, dama y'an kuɗi na kawu maki nasan baki da kuɗi a hannunki, so ga dubu d'ari da hamsin (150k) nan ki riƙk'e kafin a kawo min kuɗi.

 "Wow! Adda thank you very much shiyasa nake ƙk'ara sonki, bari kiga in kira Anum tazo yanzu,


 Wayarta ta ɗauko ta danna numbar Anum,

 duk a binan Mum ɗinta na tsaye itada Hindu suna jinsu, hawaye ne ya fara bin fuskarta,

 "Shikenan haka zan dinga yima ɗiyata tarbiya wata na rusawa, tana lalata min tarbiyar ƴa?

 "Karki damu ranki ya daɗi akwai Allah", 


Da sauri ta dago kai saboda tayi tunani a zuciyarta take maganar, hannunta Hindu ta kama suka nufi ɗakinta..........

        *N.W.A*

      _FATEEN SOJA CE_


   *MAZA DA MULKI* 

★★.    _MATA DA_ ★★

 ★.     *TAƘAMA*  ★
```NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION```

___________________________________


     _story and written by_

        *MRS UMAR*


         _edited by_

     *PRINCESS AMRAH*


     _in dedication to_

     *FIDDAUSI SODANGI*           ```page 6```
A hankali Hindu ta kama hannunta ta zaunar da ita kan kujeran dake make a kata faren parlournta zaune take amma batasan meke mata daɗi bah, hawaye ne ke bin fuskarta ko ta ina

 bayan Hindu ta zauna kusa da ƙafarta ahankali tasa hannu tana goge mata hawayen dake fita a fuskarta cikin sanyi murya ta fara bata baki,

 "Ranki ya daɗe Allah ya huci zuciyarki ki ƙwantar da hankalinki insha Allahu abinda Adda Deeja keso ta ɗaura gimbiya a kai insha Allahu Allah bazai bata sa'a bah, karki manta kin dogara da Allah a koda yaushe shi kike kaiwa kukanki, dan haka ina mai maki albishir gimbiya sai tazamo ɗiya kamar yanda kike so ki ganta..

 "Kaiya Hindu ai hausawa sunce ice tun yana danye ake tanƙwasashi basai ya bushe bah, Fiddausi idonta yanzu ya bude bata tunanin komai sai yanda zata cutawa talakkawa, Hindu ina nadamar da Fiddausi tazamo ƴat.....

 "Kash ranki ya daɗe karki faɗi haka kefa musulmace kisan ƙaddara mai kyau da marar kyau, ki godewa Allah ma a haka..


 Mom kasa magana takarayi sai dai ido da ta kurawa Hindu tana kallonta cikin zuciyarta take cewa, 

 "Oh Allah inama ace Hindu itace ɗiyata ɗiyar da duk uwa ta gari take fata ta haifa, ɗiya kamar Hindu, Allah nagode maka.

 Dama a kullum idan suka zauna da Hindu toh tunani da zataitayi kenan, har su rabu tana ƙara son Hindu a zuciyarta a koda yaushe,


 Duk abin nan da suke Mairo na bakin ƙofa laɓe tana jinsu, direct ɗakin Adda ta nufa duk ta faɗa mata abinda suke tatauna harda su ƙari dan miya tayi daɗi, bayan fitar Mairo Adda ta ɗauko wayarta ta danna wata number warda ni kaina ban kula da sunan da yake jikin number bah, sai da tayi ring har tana shirin katsiwa kafin akayi picking, daga can ɓan garen akayi magana,


 "Hello uwar gida a gidan sarki an buga dake an barki wane mutum yaja dake ya ƙwana ƙiyama, ai ko sarkin dake yake ado, sai kin zamo ke ɗaya a gidan sai wannan yar talakkawan ta ƙwashi tsiyarta ta koma ƙauye indai mune.

 "Hahaha ƙawa ko ince 'yar uwata wallahi shiyasa nake sonki, ai in tasan wata bata san wata bah, ai so nake Fiddausi ta ɗauko masu abin kunyar da duk duniya sai ta tsanesu kai bama mai martaba kawai bah, kinga daga nan daga ita har uwar zai kora shikenan gida ya zama nawa hahaha, 

 "Wannan magana haka take ai maybe ma daga wannan bakin cikin ya faɗi ya mutu shikenan sunyi asara.

 "Wallahi dan kuwa iya kata dashi ta kaba, yanzu dai inaso ki ƙara jama Anum kunne karta kuskura ta nunawa Fiddausi ba irin halinsu ɗaya bah, saboda wallahi inaso tazamo mujiya a cikin jama'a.

 "Karki samu damuwa yaya anyi komai angama.

 "Yauwa haka nake so toh sai anjima..


 Bata tsaya bata amsa bah tayi hanging of na wayar..


 *************

 Ƙwance yake cikin swimming pool yayin da hannayenshi dukka ya fiddosu a waje kanshi a ɗage yake sama yayinda idanuwanshi ke rufe, 

 wasu matsiyatan motocine akayi parking d'insu, 

wa anan sunsha bambam dana ranar dan kuwa ko wannan su nidai a film kawai na taɓa ganinsu, cikin isa aka bude mata ƙofa, saida ta ɗauke wani lokaci kafin ta fito, yau sanyi take da black gown tayi mata matukar kyau, ahankali ta wani duka bayanshi hannunta ta ɗauka tana ɗan danna mashi hannuwanshi jiyake wani abu na shigarshi mai daɗi,

 da sauri ya fincikota ta faɗa cikin swimming pool d'in idanuwanshi na rufe bai bude subah ya hada bakinshi da nata

 ahankali yake furta

 

 "Thank you my sweetheart thank you very much , finally you come to am very happy today.....      *N.W. A*

   Fateen soja


    *MAZA DA MULKI* 

★★.    _MATA DA_  ★★

 ★.     *TAKAMA*   ★


NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

____________________________________


    _story and written by_

         *MRS UMAR*

   

            _edited by_

     *PRINCESS AMRAH*

    

     _In Dedication to_

    *FIDDAUSI SODANGI*           ```page 7```    Maganarshi ta tsaya ne saboda buɗe idonshi da yayi gaba ɗaya, cak ya tsaya dan ganin bah gimbiya Feedoh bace a gabanshi, cikin rawar murya yake furta'

“Zee what are you doing?”.

 “Why? It's me your baby ko ka manta dani ne?".


Kasa magana ya yi sai dai hannunshi da yasa ya dafe kanshi yayin da idanuwanshi ke rufe, shafashi ɗin da take ne yasa shi saurin tureta ya fito daga cikin swimming pool ɗin, direct wajen inda aka aje towel ya nufa, ya ɗauki ɗaya daga ciki yana goge jikinshi, sanye yake dagashi sai d'an guntun bossier duk wani abu dake jikinshi ana ganinsa, cikin salo na y'an duniya ta biyoshi tana mashi wani irin wasanni wanda har saida ya biye mata........


 »»»««««««««*****»»»»»»


 _After one week_

   

  Mom ce zaune gaban mai martaba tana ta faman magiya ya taimaka yasa Fiddausi kafin ta koma China taje Yola ta d'anyi kwana biyu ta gaida kakanninta saboda rabanta da zuwa tun kafin ta tafi makaranta a China, tasan ba wanda zaisa Fiddausi taje Yola sai mai martaba kawai shiyasa take magiya yayi mata magana. 


 “Shikenan Bahijja zanyi mata magana ai bazan hanata zuwa wajen y'an uwanki bah, ai bani kaɗai na haifeta bah, dama faɗan da kikaji ina miki saboda kyararta da kike ne, but don't worry i will do anything for you, bari ta dawo sai ta wuce jibe”.

 “Yauwa mai martaba nagode sai dai ina naiman alfarma?”.

 “Tame?”.

 “Dama mai martaba inaso idan zata tafi dan Allah kada a haɗata da kowa a barta su tafi daga ita sai Hindu”.


 Mai martaba yayi ɗan jim kafin ya ɗan kaɗa kanshi yace'

 “Toh shikenan idan haka kike so sai su tafi da Hindu idan yaso sai na kira aminina ya aiki direbanshi ya ɗaukesu ya kaisu ƙk'auyen, tayi kwana biyu.”

 “Toh mai martaba Allah ya ƙk'ara maka lafiya nagode".

 Mai martaba ya amsa da toh haka sukaci gaba da firarsu mai cike da so da k'auna.


*ZAMBURUSH*

 

 Gimbiya Feedoh zaune take ita da Anum basu san wainar da mai martaba da mom ke toyawa bah, dukkansu fuskokinsu daɗe suke da glass sai wani shanƙk'amshi suke, yayinda Hindu da ta haɗa ido da gimbiya sai taji takaici a zuciyarta itako Mairo ko a jikinta, Anum tasa hannu kenan zata ɗauko wataƙkwalba a cikin jikarta muryarshi ta daki dodon kunnanta.

 “Sannunku yan mata kunsan hausawa sunce masoyi baya fushi so am back again.”

 Anum ce ta kwashe da dariya yayinda gimbiya ko inda yake bata kalla bah, ballantana tasan da mutum a wajen wayarta kawai take dannawa, cikin gadara Anum ta fara jifa mashi magana, 

 "Wow dogon gaye so you back again? baka gaji da gaya maka maganan da a ke ba kenan?".

 "Stop am not talking to you".

Yana rufe baki cikin siga irinta y'an duniya kawai ya fad'i gaban gimbiya, abin mamaki duk jama'ar dake wajen sai da suka juyo kallonsu dan kuwa kowa abin mamaki ya bashi ace kamar Affan Khalil yana rok'on Mace ta soshi gaskiya ne gaba da gabanta aljani ya taka wuta,

Glass d'in dake idonta ta cire cikin murmushin mugunta ta k'ura mashi idon tana k'are mashi kallo,

 idonta ta numshi tana tunanin muguntar da zatayi mashi, 

 "Please princess say something, I love u, wallahi idan baki soni ba zan iya mutuwa saboda ke please”.

Wasu hawaye ne suka fara bin fuskarshi wanda itama kanta sai da tayi mamaki, yayinda Anum ta saki baki tana kallonshi....


    


       *N.W.A*


     *MAZA DA MULKI* 

★★.    _MATA DA_  ★★

 ★.    *TAƘAMA*    ★


NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION 

__________________________________


     _story and written by_

          *MRS UMAR*


      _in dedication to_

    *FIDDAUSI SODANGI*
         ```page 8```This page is urs my sweet *JEEDDH ALIYU* because you love me so much, yes thank you i will never forget you in my life, *FATIJIDDAH* i love u.... 


Cikin shu'umin murmushinta ta fara magana, duk magana ɗaya aiki ce a wajenta,

 "Hmm! dogon gaye, you will never understand me, look at me, and look at you, zakaga da banbanci, so I'm warning you, stay away from me, this is my last Warning, aikin banza..”

 Tana rufe baki tayi ball da table ɗin dake wajen wanda har sai da ya bigeshi ta juya ta harari su Hindu da sauri suka take mata baya, duk abin Anum kasa magana tayi sai binshi take da kallo, tanasa k'afa zata fita duk jama'ar dake wajen suka ɗauki ihu.

 "Sai gimbiya!!! wow Allah yaja da ran masarautar SODANGI".

 Murmushi ta saki mai cike da jin daɗi saboda a rayuwarta tanaso taga jama'a na bata girma, tana fita da gudu mutanenta suka buɗe mata mota tashiga da sauri, sannan sauran suka nufi tasu motar, tana cikin mota amma tana tunanin dogon gaye, ita kanta abin mamaki yake bata.


 “Gaskiya ne the guy is handsome, 

 problem ɗinshi ɗaya, shi chocolate colour ne nikuma a tsarina nafi son farin namiji, uhumm..”

 Ajiyar zuciya ta sauk'e mai ƙarfi wanda har saida Hindu ta juyo, saidai bata san abinda yasata sauke ajiyar zuciyar bah, saboda duk a cikin zuciyarta take wannan tunanin,

direct gida suka nufa da ita, yau anci sa'a saboda dogon gaye ta koma gida k'arfe 8:05pm, tana fitowa daga mota mutanen dake wajen suka dinga zubewa a ƙasa suna kwasar gaisuwa, kota kalli inda suke bare ta amsa, abin bai basu haushi bah, saboda in da sabo sun saba, kai tsaye ɗakinta ta nufa,

Tana dai dai shiga taci karo da ɗaya daga cikin ƙwarƙwarar Adda cikin ladabi ta duk'a tace

 “Barka da zuwa gimbiya dama mai Martaba yace in ƙiraki yanaso yayi magana dake yanzu.”

 Cikin isa ta juya, saida ta kusan isa ƙofar shiga bedroom ɗinta kafin tace 

 "Kice mashi ina zuwa”.

 Bata tsaya komai bah ta tashi da sauri ta fita, itako mai mulki bata nufi ƙiran mai martaba bah, har saida ta gama abinda take, har wanka sai da tayi, cikin ƙasaita ta tura ƙofa,

zaune yake a parlour yayinda fuskarshi ke ɗauke da murmushin murnar yaga ƴartashi,

 "Barka da dare.”

 “Yauwa barka dai my daughter.”

 “Dama mai Martaba naji Indo tace kana nemana ne.”

 “Eh nina aika a kiraki, dama ba wata magana bace mai tsawo, inaso ki had'a kayanki jibi zaki wuce...”


 Kafin ya k'arasa magana ta tareshi,


 “Laah! mai martaba Dubai zan tafi ne? ”

 “No zaki tafi Yola n.... 

 “What? Mai martaba Yola kuma? gaskiya ni ba zanje kauye bah".

 "what! are you mad? This is my decision i can not change my mind“.


Wani bakin ciki ne ya daki zuciyarta ji take kamar zata mutu dan haushi,

 kamarta yanzu mai Martaba yace sai taje kauye ai wannan zubar da aji ne,

 Maganar da Mai Martaba yasake yi ne yasa ta dawo daga tunanin da take. 

 

 “Toh zaki iya komawa ɗakinki zuwa gobe ki fara shirye shiryen hada kayanki dan jibi zaki wuce insha Allahu.”

 A hankali ta tashi dan tasan tunda mai martaba ya furta haka toh bazai chanza bah,

duk maganar da mai Martaba keyi da gimbiya mom na tsaye tana jinsu, taji daɗi yau sosai yanda bai goyarwa ɗiyar tashi baya bah, dan haka ta turo ƙofar tasa tashigo ita kuma gimbiya, dai dai zata fita, abin mamaki kota kalli fuskar uwartata ballantana tace mata sannu, ita dai mom ko a jikinta saboda tasamu abinda take so,

 shiyasa gimbiya ta fita jiki a sanyaye, ɗakin Adda ta nufa kai tsaye ko zuciyarta zatayi sanyi, bata tsaya komai bah ta tura ƙofar ɗakin, abinda tagani ne yasa ta tsaya cak,

muryarta na rawa ta furta.

 “k..... Toh makaranta wannan amsar taku ce, mai gimbiya ta gani ya bata mamaki a ɗakin Adda tsaya muga wa yafi ƙwaƙwalwa??????????
      Taku ce dai

  

     Fatin soja

   *MAZA DA MULKI* 

★★.   _MATA DA_   ★★

 ★.    *TAƘAMA*    ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

__________________________________     _story and written by_

         *MRS OMAR*


     _in dedication to_

    *FIDDAUSI SODANGI*       _page 9__Wannan page naku ne yan group ɗin Khalesat Haydar nagode da irin son da kuke nunawa novel ɗi na, Thank u all_   Muryarta na rawa ta furta'

 “Kai dogon gaye what are you doing in my house are you mad a...?”

 Maganarta ta tsaya ne sakamakon maganar Adda data daki dodon kunnenta. 


 “Daughter keda wa kike ta faman faɗa haka? A'a Affan yau kaine a gidan namu sannu da zuwa.”

 Gimbiya Feedoh sakin baki tayi tana kallon Adda cikin zuciyarta take faɗin 

 “Dama Adda tasan dogon gaye kenan ko yau ce ranar da ya fara zuwa wajenta no!! in yau ce ranar da ya fara zuwa wajenta ai bai kamata ta faɗi sunansa direct bah..

 “Fee! tunanin me kike haka inata magana.?”

 Da sauri ta dawo daga tunanin da take saboda maganar da Adda tayi mata da ƙk'arfi, cikin sanyin jiki ta zauna ɗaya daga cikin kujerun dake parlour, yayin da itama Adda ta zauna ɗaya daga cikin kujerar da ke fuskantar Affan tana murmushi ta kashe mashi ido ɗaya.

 “Adda dama kinsan wannan mutumin ne?”

 “Kinjiki Fee da wata magana ai Affan kamar ɗa yake a wajena, saboda ɗan ƙk'awata ne Hajiya Aisha yana yawan zuwa gidan nan gaisheni saboda yaron yana da hankali sosai, kin sanshi kenan?”.

 Da sauri gimbiya Feedoh ta kalleshi saboda duk maganar da Adda keyi idon Feedoh na kanta, shima ita yake kallo, cikin isa ta mik'e tana tafiya saida takai daidai ƙk'ofar shiga bedroom ɗin Adda tace' 

 “Bansanshi bah just yaso yayi min kama da wani Stupid boy ne..”

 Ran dogon gaye ya ɓaci dan dai babu yanda zaya yi yasa yayi shiru, Adda ta kalleshi ta fashe da dariya tace'

 “Yanzu muka fara wasan.

 Sukayi dariya dukkansu, sun daɗe suna fira kafin yayi mata sallama ya fita ita kuma ta nufi ɗakinta wajen gimbiya Feedoh koda ta shiga ta sameta tana barci,

 dai_dai lokacin da zai fita yaci ƙkaro da Hindu abin ya bata mamaki da ta ganshi ya fito daga ɗakin Adda shiko suna haɗa ido ya watsa mata harara,

 cikin zuciyarta take faɗin “Anya gimbiya tasan dogon gaye yazo wajen Adda ko naje na gaya mata, no!! nasan in na gaya mata bazata yarda dani bah, saboda yanda gimbiya ke son Adda zata iya komai a kanta, toh ko Nom zan faɗawa, no idan na gayawa mom hankalinta zai tashi sannan zata gano inda ɗiyarta ke zuwa, saboda duk uwa ta gari baza taso ɗanta na zuwa zumburash bah, ballantana ɗiya mace, oh my God ya Allah karka ba Adda sa'a akan gimbiya Feedon Allah kodan halin mahaifiyarta masu kyau..

 

 Maganar Hindu duk a zuciyarta take yinsu bata san lokacin da idanunta suka fara zubar da hawaye bah..... _After two days_


Gimbiya Feedoh a yau ji take kamar ta mutu dan haushi saboda duk hanyar da zata bi dan ta fasa tafiyar amma abin yaci tura, Mai Martaba yace dole sai taje har iya ta fada mawa watau mahaifiyar Mai Martaba, amma itama din sai bata bata goyan baya bah, shiyasa ta hakura zata tafi ba dan ranta yaso bah,....


 

  *ADAMAWA YOLA*


 Misalin ƙk'arfe 2:00pm dai_dai flight ɗinsu gimbiya ya sauka cikin airport ɗin dake cikin garin yola,

 suna isa dama already Dad yasa abokinsa ya turo dirvenshi ya daukesu ya wuce dasu k'auyen, bayan ya ƙkwashe kayansu yasa a mota sannan ya buɗe masu ƙk'ofar motar suka shiga ita dai Hindu babu ruwanta sai yanda akayi da ita,

 tafiya sukayi mai nisa kafin suka ɗauke hanyar wani kauye mai suna *WURO NYOMBE* kauye ne sosai saboda garin duk ramune da jar k'asa, haushi ne ya ƙk'ara kamata yanda motar ke zalle duk tabi ta gaji, birkin da driven ya taka ne yasasu suka tsorata ba kamar gimbiya, wani tsoho ne ke shirin ya ƙk'etare hanyar baima kula da mota bah saboda yasan ba koda yaushe mota ke bin hanyar bah, shiyasa ya tafi zai ketare babu ruwanshi da duba hanya, 

da sauri wani matashin yaro na kan Bicycle ɗinshi yayi sauri ya yarda keken ya nufi wajen tsohon, mai keken yaro ne matashi wanda shekarunshi bazasu wuce 23 bah, dogo ne fari tas yana da hanci idonshi sexy eyes ne sumar kanshi a ƙkwance take saidai an mashi irin askin nan na zamani mai suna punk bashi da kiba amma yana da fadin ƙkirji, kayan jikinshi kanana ne idan ka ganshi bazaka ɗauka ɗan kauye bane saboda ko a birni a talakkance irin kayan da zaisa kenan, 

 cikin zafin rai ya nufi motar da sauri driven ya buɗe ƙkofa zai fito gimbiya ta hanashi.

 "Kai wane irin ɗan iskan driven ne da baka kallon gabanka yanzu da ka bigeshi me zaka ce..”

 "Dan Allah kayi hakuri wallahi ban kula dashi bane am....”

Cikin zafin rai gimbaya ta fara magana

 "Karma ya hakura mana dan Allah zo kaja mota mutafi."

 Maganar gimbiya ce ta daki dodon kunanshi cikin zafin rai ya ɓalli marfin ƙkofar da take zaune.

 "Au sai yanzu nagane ba ɗan iskan driven bane ashe kece 'yar iskar.

 "Kai!! kasan koni wacece da har kake zagina toh wallahi kajawa kanka da duk wani family ɗinka bala'i saboda ubana zai iya yin komai saboda ni.

 "Toh ina ruwana waye uban naki idan har kin isa inaso yau ɗin nan naga duk matanen dake kauyen nan kinsa an gama dasu."


 Wani matashi yaro ne wanda bazai wuce sa'arshi bah yazo yana bashi hakuri.

 "Haba Balatoni ai bai kamata kana faɗa da mace bah, ɗan Allah baiwar Allah kiyi hakuri, tsaki taja ta buga ƙkofar motar yayinda driven yaja motar da sauri ita dai Hindu yunwar cikinta ma ta isheta......     *N.W.A*


   Fateen......


    *MAZA DA MULKI* 

★★.    _MATA DA_  ★★

 ★.    *TAƘAMA*   ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION 

_________________________________


     _story and written by

         *MRS OMAR*


      _in dedication to_

    *FIDDAUSI SODANGI*     _my blog name is_

www.mrsumaru.blogspot.com         _page 10_


   

_this page is for you *AUNTY MAIJIDDAH MUSA* nagode k'warai da kulawarki a gareni thank you very much_,

  Dai dai wani ƙofar gida gimbiyar tasa yayi parking duk da rabonta da garin tun bata da wayau,

toh amma bazata taɓa mantawa da gidan bah, yaran garin ne duk suka tsaya bakin motar suka yimata cha suna kallonta abinku da ƙauye idan yara suka ga 'yan birni sai suzama abin kallo,

gidan babu laifi ya ɗanyi daban dana sauran ƴan ƙauyen dan kuwa garin ƙauye ne sosai saboda ko wutar lantarki(nepa) babu, tana fitowa taga dadaɓar yaran nan a jikin mota wani baƙin ciki ne ya ƙara tun ƙarar zuciyarta ji take kamar tasa hannu a kai tayi ihu,

 yaran binta suke da kallo dan basu saba ganin mace da kaya sun matseta bah, sannan ga uban glass tasha, cikin yatsinar fuska ta nufi gidan. 

  Hindu nafitowa ta dinga masu dariya,

 sai da driven ya fiddo masu kayansu duka kafin Hindu ta tayashi ɗaukar wasu suka shiga gidan, 

bakin ƙofa suka ganta tsaye tafi ƙarfin tayi sallama ta shiga, saboda ba kowa a tsakar gidan Hindu ta kalleta ta girgiza kai kafin tayi sallama daga cikin ɗaki aka amsa sallamar, wata tsohowa ce ta fito daga ɗakin daka ganta kaga Mom.

 "Ah ah yau baƙi mukayi a gidan namu? kai maraba da mutanen katsina sanunku sanunku da zuwa.

 "Yauwa gwaggo.”

 Ita kowa gimbiya 'yar sarki tafi ƙarfin ta amsa sai dai Hindu ke amsawa yayin da itako ta kalli can ta kalli nan tana" ƙarewa gidan kallo tana ɓata fuska sai yatsina take, 

kuma taƙi cire glass ɗin dake fuskarta,

 ɗaki ta nufa dasu yayinda driven ya gama shigowa da kayansu yace

 "Toh Hajiya sai na dawo ɗaukar ku.”

 Bata amsashi bah sai dai Hindu ta amsamashi,

ɗakin take bi da kallo tana yatsina fuska kamar zatayi kuka, babu laifi ɗakin a share yake, duk da ɗakin dai ba wasu kaya bane masu yawa, akwai gadon k'arfe a kafe babu laifi amma shafe yake da suminti, daga gifen gado akwai kujeru guda biyu, ɗaya daga cikin kujeron ta zauna sannan ta dubi kakar ta ta tace 

 "Ina wuni". 

 "Lafiya k'alau Fiddausi yau kece a garin namu ai ni jinake bazaki koma zuwa ba!"

 Shiru tayi sai Hindu tace 

"Eh wallahi gwaggo kinsan makaranta shiyasa".

 "Toh masha Allah bari a kawo maku fura kusha."


 Wata ƙwarya ta ɗauko ta aje a gaban Gimbiya, Feedoh ta kalli ƙwaryar fuskarta a yatsine ta buɗe tana buɗewa taga furar har tafasa take dan tsami, ruwa ta aje masu a cup Hindu tasa hannu tajanyo ƙwaryar furar ta motsa sannan ta mikawa gimbiya cikin zafin rai ta dubeta tace 

 "Are you mad? Kina nufin ni zansha wannan sickness ɗin abin no!! never".

 "But gimbiya idan bakisha bah mezaki ci?”


 Hararar da ta watsa mata shiyasa ta kauda idonta daga gareta ta kafa kanta a ƙwaryar furar tasha sosai tana sha gimbiya na kallonta tana yatsinar fuska kamar zatayi amai, duk abin nan gwaggo bata ɗakin tafita shiyasa Hindu taji daɗin haka amma duk da haka tasan sai watarana gimbiya tayi a gabanta, bayan gwaggo ta dawo ɗakin ta dubi gimbiya tace

 "Amma Fiddausi zakiyi tafiya irin wannan ai bai kamata kisako irin waɗan nan kayan bah, saboda kinga mu nan k'auye ne sannan a al'adarmu ta fulani akwai kunya ai zaki zo ya kamata Bahijja tayi miki faɗa.”

 Sai da ta kalli jikinta sama da ƙasa kafin tace.

 "Kaji gwaggo da wata magana wannan kayan nawa mai sukayi? 

wannan fa gown ce ba wani abu bah".

 "Gawan meye haka kuma".?

 "Oh my God i forgot you are a village woman."

 Maganar da tayi ne yasa Hindu tayi saurin kallonta cikin ban mamaki.

 "Anya kuwa gimbiya nada hankali? kakarta take kira 'yar ƙauye, bayan ita ta haifi mahaifiyarta.”


 Ajiyar zuciyar ta sauke kafin ta girgiza kanta, motsinda sukaji a ƙofar ɗakin yasa suka juwa amma banda gimbiya yayin da ta d'auko wayarta tana dubawa, tsoki taja cikin fushi tace

 "Oh my God what can of village is this?"

 Ahankali ya aje kekenshi dai-dai ƙofar ɗakin gwaggo, cike da jin dad'in ganin shi tace

 "A'a Modibbo ka dawo? toh ai kam yau muna da baki a gidan namu ga 'yar uwarka tazo, da murmushinsa yaƙarasa cikin ɗakin ita dai Hindu binshi tayi da kallo yayinda yana shiga cikin ɗakin sukayi ido biyu da gimbiya, cikin ban mamaki suke kallon junansu...


       *N.W.A*     FATEEN.....

    *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_  ★★

 ★.    *TAK'AMA*   ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

__________________________________


     _story and written by_

         *MRS UMAR*      _in dedication to_

    *FIDDAUSI SODANGI*      _my blog name is

www.mrsumaru.blogspot.com        _page 11_


Wannan page naku ne mama *SADEEYA JEGAL* AND mamata *MAMAN FATEEN* Allah yakara maku basira. _Ameen_


Cikin ban mamaki suke kallon junansu wani bakin ciki ya tunkari zuciyarshi, harara ya watsa mata yayinda itama kallon sama da k'asa take mashi. Hanyar gado yanufa ya zauna a kai gwaggo tace

 "Modibbo baka ganesu bane? 'yar uwarka ce FIDDAUSI ɗiyar innarka ta Katsina, nasan rabanka da ita tun tana yarinya da suke zuwa, nasan yanzu duk zuwan da kake baka samunta saboda ubanta ya ɗaure mata gindin tayi makaranta a garin masu kananan idon nan.”

 Modibbo naso yayi dariyar gwaggo amma saboda gimbiya yak'ara daure fuska, duk wannan maganar da gwaggo keyi dashi cikin halshen fulatanci suke maganar.

 Yanzu da hausa tayi magana tace

 "Ka ganta nan wai abin kunya bata jin fulatanci sai yaren da banata ba ta ɗauka, ai ni duk nafi ganin laifin Bahijja saboda duk ita tak'ara bari ta zama haka.

 "Kai kaji min wannan tsohuwar ni dadina dake da kinga mutum ki kama mishi faɗa, toh ni ina ruwana da in iya fulatanci tunda dai na iya abinda zan iya shiga dashi ko ina.

 "Au ni kike faɗawa haka ai daɗin abin idan ta k'amarki taurin kai to wanda zaki aura yafiki dan kuwa Modibbo idan har kikace haka zakiyi mashi to zak...

 "What? gwaggo me kikace kina nufin wannan shi zan aura?

 "Eh shi zaki aura da zarar kin gama makaranta zanje na samu mahaifinki ayi magana."

 Wata dariya gimbiya ta fara ita kanta bata san ta micece ba, cikin turanci take magana

 "Never!! i will never ever marry this village man, look at me and look at this village man, no!!”

 Gwaggo ce ta ƙara magana tace 

 "Kiyi magana da yaren da zan jiki kike wani kwaranci, anya FIDDAUSI yanzu ki dube wannan yarinyar da kukazo da ita yarinya kwanin ban sha'awa wallahi FIDDAUSI ki natsu ina guje miki ranar da zakiyi nadamar wannan halin naki."

 Gimbiya feedoh taja tsaki ta wani finciki earphone tasa a kunne ta kunna waka danma kartaji abinda gwaggo ke fad'i.

 ''wani zafi ya karaji a zuciyarshi cikin zuciyarshi yake faɗin

 "Dama wannan yarinyarce gwaggo ke faɗa min zan aura yariya marar kunya mai ji da kanta zan aura? ina wannan yariyar tafi karfina."

  

 Duk abinda ake Hindu na zaune gefe guda tana sauraransu, Hindu taga alama gimbiya batada niyar gaidashi shiyasa ita tayi k'arfin halin gaidashi, saida ya lumshe idanunshi kafin ya bud'e ahankali ya amsa.

 Tana kallon Hindu hak'ik'a Hindu ta bashi sha'awa yanda yanayin shigarta kadai abin kallo ne.

 Gimbiya Feedoh da sauri ta jayo jikarta saboda yunwar da takeji, ta fara fito da wani dan kwano da cokali sannan ta fiddo robar faro watau ruwan gora duk abinda take suna kallonta, comflask ta had'a ta fara sha abinta, babu abinda yasha mata kai, cikin zafin zuciya ya bige kwanun ya fadi kasa, muryarshi na rawa ya fara magana,

 "Ke wace irin marar kunyar yarinya ce o'o zakizo kauye ke kinfi karfin kici abincinmu shiyasa kika taho da naki, toh ai danine ke da har kauyen ba zanzo bah, saboda ai na rainasu..

 "Kai dallah dakata malam,

 Stop shouting at me! oh i remember that you are village man,

 that's why you're behaving like fool.


Cikin bacin rai ya d'aga hannu zai wanka mata mari gwaggo tayi saurin rike mashi hannu, yana huci ya fara nunata da ɗan yatsa.

 "Ke karamar yar iskace, ki tambaya kiji acikin k'auye nan waye Balatoni za'a baki labarina banza mai turacin karya idan har da gaske ke marar kunya ce toh ki maimaita abinda kikace da hausa kiga yanda zanyi dake yanzu."

 Gwaggo ce ta kamashi ta fita dashi waje tana mashi faɗa da fulatanci abinda yake so ya aikata.


 "Amma gimbiya ni a tunanina kifita daga harkar bawan Allah nan saboda da alama bashi da mutunci musamu mu rabu lafiya dashi yanda mukazo la...

 "Dallah rufe min baki munafukar banza ai saboda halinki mom tace muzo tare koh?

 Toh wallahi idan shi dan iskane a garin nan to ni! kan fanka ce zan nuna mashi k'arfin mulkin mahaifina."

 Maganar gwaggo ce ta daki kunnenta tace. 

 "Ai sai ki nuna mai tunda shi uban naki bashi da hankali kamarki, to bari kiji tunda abin yazama haka ni zan samu kakarki sai ayi maganar aurenku da sauri kafin ku bamu kunya...
    mu je zuwa danjin yaya za'a ƙare da gimbiya a k'auye...
      Fateen....


    *MAZA DA MULKI* 

★★.    _MATA DA_  ★★

 ★.     *TAK'AMA*  ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

__________________________________


      _story and written by_

         *MRS OMAR*


      _in dedication to_

    *FIDDAUSI SODANGI*


  _my blog name is_

www.mrsumaru.blogspot.com         _page 12_


_Wannan page naku ne y'an NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION uwa bama da mama muna alfahari dake akoda yaushe._
  Modibbo waje ya fita amma ji yake kamar ya amaye zuciyarshi dan haushi da takaici, bakin wata bishiya ya tsaya duk illahirin jijiyoyin jikinshi suntashi dama haka yake in yayi fushi, idanunsa ya rufe sannan yasa hannunshi yana yamutsa sumar kanshi dai-dai inda ba'a aske bah, kafaɗarshi da yaji an dafa, yasashi saurin buɗe idonshi ya juya yana kallon wanda yadafashin still yaron da yabashi hak'uri d'azu shine yazo yanzu. 


 "Balatoni me yake damunka ne naga yanayinka ya canza? Wai balatoni sai yaushe zaka bar wannan zuciyar taka? kayi hak'uri ka faɗa min abinda ke damunka! kaima kasani duk garin nan baka da abokin da yakaini inazuwa nima na faɗa maka damuwata.”

 Ajiyar zuciya Modibbo ya sauke sannan ya samu wajen zama ya zauna, ya buɗe baki zaiyi magana kenan ya hango gimbiya Feedoh na tafiya itada Hindu tana take mata baya tafiya take tana yatsinar fuska kamar zata karye, sai da takusan zuwa wajensu kafin abokin ya kula da inda Modibbo ke kallo.


 "Oh nawa ashe abokiyar faɗanka kake kallo sai kace mun dama bak'owarku ce, kai amma fa yarinyar ta had'u."

 Harara Modibbo ya watsawa abokin nashi da sauri ya kauda kai, maganar tace ta da ke kunnuwansu. 

 "Aikin banza damashi dan k'auye duk yanda kayi dashi toh sai ya nuna maka shi bagidajene ni...."

 Kafin ta k'arasa magana, Modibbo har yakai wajenta wata irin fincika yayi mata, yayinda ya had'a jikinta da bishiyar da suke zaune a wajen, hannunta ya murde mata ta baya,

yana huci kamar damisa ya fara fad'in, 

 "Ke marar kunya! toh wallahi idan har tak'amarki rashin kunya toh gidanta kikazo ke har kin isa kigaya mani magana wacece ke? maikike tak'ama dashi".

 "Ubana nake tak'ama dashi saboda zai iya yimin komai dan ganin farin cikina kuma wallahi saina nuna maka k'arfin mulkin ubana, stupid village man, you are a fool, you don't know anything, i promise you i will deal with you so that you will never forget me.."

  

 Shak'ar wuyanta da yayi ne yasa maganarta ta tsaya da sauri abokinshi yasa hannu yana shirin amsarta saboda yasan idan abokinshi yayi fushi babu kyau. 

 "Haba Balatoni kai wane irin mutum ne mai bak'ar zuciya haka? mace ce fah.

 "Ali kabarni in nuna mata ita marar kunyar k'arya ce ba tana tak'ama da mulkin ubanta bah, toh sai in nuna mata babu ruwana da mulkinshi wallahi inyi mata rashin mutumci da an fara magana saita fara turacin k'arya idan harda gaske baki da kunya toh ki mamaita abinda kikace da hausa."

 Dariya tayi wadda tafi kuka ciwo kana tace, 

 "Humm kaga ko yanzu nafika saboda nayi magana bakaji abinda na faɗa bah, ko da yake banga laifinkaba dama duk yanda akayi da jaki sai yaci kara, shine za'a cewa wai kai kazama mijina! tayaya d'an k'auye kamarka zai zama mijina, in rasa wanda zan aura sai Illiterate no! never."

 Wani irin kukan kura yayi yana shirin ya fizgota Ali yayi saurin shan gabanshi, Hindu ya kalla yace. 

 "Dan Allah baiwar Allah kiyi hak'uri ki jata ku koma gida."

 Hindu ta ɗaga kai alamar toh ta nufi wajen gimbiya tana shirin kama hannunta, sai kawai taji saukar mari a fuskarta zafin da taji ne yasata saurin dafe kuncinta, cikin zafin rai Modibbo ya ingije Ali itama ya wanka mata lafiyayin mari ihu ta fasa wanda sai da Hindu tayi matuk'ar tsorata......


 Hahaha Allah sarki duniya, wai gaba da gabanta aljani ya taka wuta..       *N.W.A*


     Fateen........


    *MAZA DA MULKI* 

★★.    _MATA DA_  ★★

 ★.     *TAK'AMA*  ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

___________________________________


    _story and written by_

        *MRS OMAR*


     _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI*


    

     _my blog name is_

www.mrsumaru.blogspot.com


         _page13_ _Humm wallahi mutane kuna bani mamaki, yanzu miye na girman kai a wajen nan,sanin kanku ne in nayi typing toh zanyi post, amma wai ke har kike cewa wai dan naga anason novel ɗina shiyasa nake girman kai, gaskiya banji dad'i wannan maganar bah....._


  Cikin zafin rai yake magana jikinshi har rawa yake, 


 "Toh tinda baki da kunya ni zan nuna miki nafiki tunda abin yazama haka wallahi gwaggo koda wasa take da tacce zan aureki toh wallahi ni yanzu da gaske nake saina aureki dan in koya miki hankali, kigane duk tak'amarki da mulkin ubanki baiyi maki rana bah, dan wallahi sai kin gane shayi ruwane, hmmm dama hausawa sunyi gaskiya da sukace *MAZA DA MULKI MATA DA TAK'AMA* kina TAK'AMA sai kace ubanki ne kawai mai mulki d...."

 Cike da 6acin rai tayi kukan kura taci mai k'walar riga ta fara magana hawaye na fita a idonta.

 "Yanzu na gane kai Stupid ne inba haka bah, look at me and look at your self! zakaga da banbanci kai village man ne, ni kuma y'ar CITY! meye sunanka ma balatoni ko me, hmmm you made a mistake, wannan mari da kayi min sai na jaza maka bala'in da bazaka taɓa mantawa da gimbiya FIDDAUSI ba, y'a a wajen sarki SODANGI, wai inba k'auyanci bah, tayaya za'a dinga kiran mutum da sunan aski, mtss dan haka duk rishin kunyarka wallahi nafika because me I Hate talaka balema ace anzo ga yan k'auye..."

 Duk maganar da take idannunshi na rufe saboda yanda taci mashi k'walar riga saida yaji tsikar jikinshi ta tashi, shiyasa ya rufe ido, ahankali ya bude idonshi, ya sauke mata sexy eyes ɗinshi a kan fuskarta, murmushi yayi sannan ya cije lips ɗinshi ya cire hannuwanta daga jikinshi yace

 "Yaro baisan wuta bah sai ya taka, muje zuwa yarinya ni dake shege ya fasa indai nine sai na nuna miki kin tabka babban kuskuren zuwa wannan k'auyen."


Tsoki ya buga bai tsaya k'ara jin abinda zatace bah, ya juya abinshi yayi tafiyarsa, ita dai Hindu mutuwar tsaye tayi saboda tunda take bata taɓa ganin wanda ko da wasa yayiwa gimbiya maganar banza ba, kamar yanda balatoni yayi mata, bale ace yau harda mari!, harara gimbiya Feedoh ta watsa mata kafin ta k'ara gaba....


   *GARIN KATSINA*


  Zaune suke a babban parlourn Adda sai shewa suke yi, 

su uku ne a parlourn, Adda, Anum sai dogon gaye. Anum ta ɗauki glass cup tasa a bakinta bayan ta cire ta kalli Adda, 

 "Amma Adda kina ganin tafiyar Fee a Yola babu wata matsala karfa duk abinda mukayi wannan shegiyar tsohuwar ta rusa mana.

 "Haba Anum ai kema kinsan Feedoh yanzu babu wanda zai iya chanza mata rayuwa yanzu, saboda nariga nayi mata huɗuba koda ruwan garin kada tasha, sannan wannan dan duniyar ya tsaya sanya kamar yana jin tsoronta, inaso ka aureta saboda nasan dole sarautar gidan nan zata koma wajen mijin da zata aura, inaso tunda har ban haihu da mai Martaba bah, toh itama bazata ji daɗin rayuwarta bah,."

 Murmushi yayi ya cije lips ɗinshi sannan yace

  "Adda kenan tunda nake babu macen da ta taɓa min abinda wannan yar iskar yarinyar tayi min dan haka sai na nun...." 


 K'arar abinda sukaji ne ya faɗo yasa suka tsorata suka gano akwai wanda ya jisu, da sauri Adda ta mik'e dan ganin waye a wajen,

 

Adda na buɗe k'ofa ta sake ajiyar zuciya dan ganin bataga kowa bah, sai fanka dake juyawa, sai tayi tunanin iskan fankar ne yasa abin ya faɗi, cikin ɗakin ta koma bayan ta koma ɗakin, sai ga mai jinsu ta fito......

        *N.W.A*


        Faeen.....

   *MAZA DA MULKI* 

★★.    _MATA DA_  ★★

 ★     *TAK'AMA*   ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

___________________________________      _story and written by_

          *MRS UMAR*      _in dedication to_

      *FIDDAUSI SODANGI*     _my blog name is_

www.Mrsumaru.blogspot.com


          _page 14_
  Iya ce watau mahaifiyar mai Martaba,

ɗakinta ta nufa jiki a sanyaye tana mai jinjina maganar da su Adda keyi, dama tazo ne ta tambayeta ko sunyi waya da Fee saboda tasan kafin ta k'ira kowa sai ta kira Adda, sai gashi abinda taji suke tattaunawa, hawaye ne ya fara fita a fuskarta saboda tausayin Mom..


 Bayan sun gama k'ulle-k'ullen abinda zasu k'ulla sannan dogon gaye ya ɗauki Anum suka bar gidan,   *YOLA K'AUYE*


  Abubuwa sai k'ara k'waɓewa suke tsakanin Balatoni da gimbiya Feedoh, tak'amarta rashin kunyarta, shi kuma yanunamata yafita rashin kunya saboda ko a k'auyen ansan waye Balatoni baya ɗaukar raini ita kuma gimbiya Feedoh tanaso ta mulki kowa kamar yanda take a garin katsina. 

 Yau ta kama ranar juma'a watau kasuwar garin, inda yau su gimbiya suna da k'wana biyu da zuwa, zaune take, takaici ya isheta gashi babu service balle ta kira dady azo a ɗauketa wayarta ce rik'e a hannunta ta k'ura mata ido tunda tazo taki ta sake suyi fira da kakarta sai dai da Hindu gwaggo ke fira dama Balatoni ne abokin firarta toh yanzu saboda gimbiya baya zama, saboda ji yake idan ya zauna wata rana sai ya kusan kasheta, dan halin gimbiya kwata-kwata baiyi mashi bah, sallamar Balatoni yasata rufe ido kamar tana barci, gwaggo ta amsa fuskarta ɗauke da fara'a tace, 

 "Ah Modibbo har kashirya tafiya kasuwar toh dama inaso in faɗa maka ya kamata ku tafi tare da bak'i suga gari dama Fiddausi bata taɓa ganin yanda kasuwar ke ci bah", 

 "Amma gwaggo kinsan yadda yarinyar nan take kar muje cikin jama'a ta bani kunya".

 "Kaga Modibbo bana son gardama ku tafi tare taga gari".

 "Toh gwaggo ba damuwa su shirya tinda kince mu tafi tare."

 Gimbiya Feedoh bata so zuwa bah amma tunda taji yace kada yaje da ita tabashi kunya cikin mutane sai tayi murmushin mugunta ta cije lips ɗinta, dan ita kad'ai tasan abinda zatayi mashi.

 "Hindu kitashi kishirya sannan ki tada sarauniya itama ta shirya ku tafi tare."

 Hindu ta amsa da toh, dama yanzu sunan da gwaggo ke kiran gimbiya Fee kenan tun ranar da sukazo da daddare makuftansu suka aiko masu da tuwan dawa, dama su al'adar garin kenan akwai kara, shine fah gwaggo ta ɗauke tuwan takai masu su fara ci kafin ta gama girki ai kam Hindu na buɗe kwanun gimbiya ta fara kwara amai abin yayiwa gwaggo ciwo sosai sai dai Hindu ta ci tuwon, toh tindaga ranar gwaggo tasawa gimbiya sarauniya. Tunda tazo har yau ko ruwan garin bata taɓa shaba dama lokacin sanyi ne ba yawan shan ruwa ake bah, shiyasa ruwan da tazo dasu har yanzu basu kare bah, Hindu komai ci take duk abinda a ka bata shiyasa gwaggo taji daɗin ganin Hindu a haka.


  Bayan Hindu ta shirya gimbiya ta fito cikin wata red gown tayi mata kyau sosai duk da ba wani makeup tayi bah babu laifi tayi kyau, dan kwalin rigar ta yafa, Modibbo har ya bud'e baki yayi mata magana gwaggo tayi mashi alama da ido, Kai ya girgiza sannan ya warga mata harara tsoki taja kana ta furta,

 "Stupid that is your problem". 

 Murmushi ya sakarwa Hindu tare da fad'in, 

"Gimbiya muje koh".. 


      *Page~15.*


  Ahankali suke tafiya yayinda balatoni keta jan Hindu da fira ita kuma tana tsoron uwar gijiyarta, duk inda suka gitta mutanen gari kallonsu suke dama kunsan in y'an kauye sukaga yan birni ji suke kamarsu cinyesu, tunda suke tafiya babu wanda ya kira Balatoni da sunan Modibbo shiyasa Hindu cikin sanyin murya ta fara cewa, 

 "Wai dan Allah mai yasa duk garin nan suke kiranka da Balatoni?"

 Murmushi yayi sannan ya juya ya kalli Fee yaga ko kallon inda suke batayi bah,

 "Humm kinaso in faɗa miki?

 "Eh ina so mana".

 "Toh yanzu zan faɗa maki saboda kin chanchaci in faɗa miki, hmmm akwai wani lokaci ina yaro naje wajen inna Bahijja, toh irin nayi suma a kaina, kowa sai magana yake sai tace a ɗauke ni akaini a aske min kan toh ni kuma ina zuwa sai naga anyiwa wani irin wannan askin kaina sai nace nima irinshi nake so, sai mai askin yace toh bayan ya gama min na tambayeshi ya sunan askin sai yace min Balatoni, ni kuma bayan na dawo k'auye duk wanda yaga askin sai yayi dariya, shine fah mutane ke tambayana ya sunan wannan askin toh duk wanda na faɗawa sai yayi min dariya toh daga nan sunan Balatoni, ya bini".   "Ayya kace daga haka sunan ya bika? Amm..."

 Hararar da gimbiya ta watsa mata yasa ta had'e sauran maganarta, dai-dai lokacin suka isa kasuwa, kasuwar ba wasu kaya ke akwai bah kun san dai yanda kasuwar k'auye take suna shiga cikin kasuwar gimbiya Feedoh ta k'ara murtike fuska saboda yanda taga kasuwar, dai-dai wajen wasu matasa suka tsaya.


 "Ya balatoni yau da bak'in naka kazo kasuwa gaskiya yau kai mai sa'a ne." d'aya daga cikin matasan ya fad'a. 

 Balatoni ya amsa yana mai murmushi, wane irin yoghurt suke saidawa gashi nan dai saboda koh paper babu a jikin gorar,

gorar ce kawai zaisa ka gane yoghurt ne. haka ya ɗauko su guda uku ya mikawa Balatoni yace gashi yabawa bak'inshi babu musu ya amsa. Hindu ya fara baa ma sannan da kamar bazaiba Fee bah amma ya mik'a mata, Murmushi tayi mai cike da jin daɗi shikanshi yayi mamakin murmushin, bayan ta amsa, ta bude robar, shi kuma ya bada baya, mai zaiji sai kawai yaji saukar yoghurt ɗin a jikinshi, duk jama'ar da ke wajen sakin baki sukai suna kallon ikon Allah......
         *N. W. A*     Fateen........


 *MAZA DA MULKI* 

★★.   _MATA DA_   ★★

 ★.   *TAK'AMA*    ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

___________________________________


     _story and written by_

        *MRS UMAR*


     _in dedication to_

    *FIDDAUSI SODANGI*  my blog name is

 www.mrsumaru.blogspot.com


         _page~16._
  Cikin ɓacin rai ya ɗago kanshi ya dubi jikinshi tunda ga kanshi har zuwa jikin shi duk yoghurt ɗinne mai kamar koko, ya juya ya kalli hagunshi ya kalli damarshi yaga duk jama'ar wajen shi suke kallo, yayinda itako ko a jikinta saima chewing gum d'inta da take ta faman tauna, ta k'ura mashi ido tana kallonshi tana murmushin mugunta, shima murmushin yayi sannan ya cije lips ɗinshi ya lumshi idonshi, ahankali yake buɗesu yayinda sexy eyes ɗinshi suka canza launi, hannu yasa saman kanshi sannan ya k'waso yoghurt ɗin dake kanshi har ya zuwa wuyan rigarshi, duk yawon dake bakinshi saida ya tataro shi ya zoba akan yoghurt ɗin da ke hannunshi duk jama'ar wajen kallon ikon allah suke yi, sam gimbiya batayi tunani komai bah, shi kuwa Balatoni cike da zafin rai ya fincikota ya matseta sannan ya buɗe mata baki da k'arfi ya zuba mata wannan yoghurt ɗin hannunshi mai haɗi da yawun bakinshi, bakinta da hancinta ya tushe da hannuwan shi, mutanan gurin suka zo zasu amsheta yace da su,

 "Kar wanda yazo nan in ba haka bah wallahi kowa yasan halina a garin nan". 


  Babu shiri sukasa ido suna kallon ikon rabbu, duk wani k'ok'arin da zatayi na ganin bata haɗiye yoghurt ɗin ba tayi amma sam ta kasa saboda numfashinta na barazanar ɗaukewa yasa ta haɗiye shi ba shiri, yana ganin ta haɗiye shi ya ingijeta ta faɗi k'asa da sauri Hindu tayi kanta, nan fa tafara kakarin amai amma aman yak'i zuwa, hawaye ne ya fara fita daga fuskarta na takaici. 

 Balatoli kuwa cike da 6acin rai ya fara magana yayinda idanunshi suka canza kala suka yi jawur kamar garwashin wuta,


 "Ke k'aramar marar kunya ce saboda ke rashin kunyarki a girman kai kawai ya tsaya ni kam duk garin nan ansani ansan waye Balatoni, sannan ina mai baki shawara da ki tattara wannan shegen jikin naki mai kamada k'ura ki koma inda kika fito tun kafin in maida ki abin k'watance a idon jama'a dan wallahi abinda zan maki sai komawa garinku ya gagareki, banza mai siffar aljanu.."


 Hawaye na fita a fuskarta na takaicin abinda yayi mata ta fara fad'in, 

 "Kai ɗin banza waye kai? me kake da shi? Sa'annan me katanada inba jahilci bah, wallahi *SAI KAYI NADAMAR* abinda kayi min a yau dan sai mahaifina yaga waye ubanka a duk cikin k'auy..."

 Kafin ta k'arasa kawai taji saukar mari a fuskarta, da sauri abokanshi suka taso suka rik'e shi, huci yake kamar bak'in zaki dan yayi mugun fushi,

 "Ke in faɗa miki ubana ɗaya yake da sauran mutane, Aliyu kabarni in koyawa yarinyar nan hankali dan wallahi kafin ta koma garinsu sai na koya mata ladabi tunda bata da tarbiya, ke barima kiji wallahi wallahi kinji nayi rantsuwa wallahi saina aureki inga karshen wannan rashin kunyar taki dan in koya miki biyayya ga nagaba dake..."

 "kai ɗin banza aini ko wannan da kake kallonta a matsayin kuyangata toh wallahi tafi k'arfinka, saboda ko karnikan gidanmu sunajin turanci bare sauran dabbobi ina zato kai ko kajin gidanmu sunfi k'arfinka bareni, ni mai ilimice kai kuma jahili ne..." 

 "Ke nikike cewa jahili Aliyu dan Allah kubarni in karya yarinyar nan",

 

Hindu taga dagaske yana k'ok'arin k'wacewa daga hannunsu, yasa tayi saurin fizgo gimbiya dan subar wajen kafin yayi mata wani abun, ba musu ta bi bayan ta suka tafi, tafiya suke amma Hindu tunani take 

 "Wannan wane irin mutum ne marar tsoro tunda nake ban taba ganin wanda ya taɓa gimbiya aka zauna lafiya bah, sai wannan, yau uwa uba tasha yawon ɗan k'auye, gashi babu wanda gimbiya ta tsana irin dan k'auye..."

 Ihun da gimbiya ta fara ne ya dawo da Hindu daga tunanin da take yi.......

        *N.W.A*      FATEEN.........


   *MAZA DA MULKI* 

★★.    _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA*   ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

__________________________________     _story and written by_

           *MRS OMAR*


       _in dedication to_

      *FIDDAUSI SODANGI*   _my blog name is_

www.mrsumaru.blogspot.com*Ina kuke masoyan wannan littafi ina mai baku hak'uri a kan jina shiru kwana biyu matsalar ta faru ne akan hidimar biki da muke toh yanzu insha Allahu zaku dinga jina, saboda mun gama duk bikin, nagode masoya da wanda ya kira ni dama wanda bai samu damar kiran ba.*       _page 17_
  Ihun da ta fasa ne yasa gwaggo saurin fitowa har tana tuntuɓe .

 "Kai lafiya mai yafaru? ba dai kun nuna halin naku a cikin kasuwar bah?"

 Tambayar da gwaggo tayi ne yasata k'ara narkewa, ɗan tsayawa tayi da kukan tana tunanin karyar da zatayiwa gwaggo ko zata barta ta koma gida dan har ga Allah garin ya isheta ta tsani Balatoni tsana mafi muni tana shashshekar kuka ta fara magana,.

 "Gwaggo ba wannan Balatoni bane kawai daga yabani abu nace bansha kawai ya kamani cikin mutane suna bashi hak'uri ya k'iji shine ya buɗa bakina ya zuba min yawon bakinshi.." 

 "Modibbo ne yayi miki haka? kai nasan Modibbo da bakar zuciya amma bazai iya yin haka bah, nasan duk rashin kunyar Modibbo bazai yarda ya aikata irin wannan aikin bah,

 "Yanzu gwaggo kina nufin karya zanyi mashi? ai da yake gaban mutane yayi abin kuma wallahi sai na nuna mashi banbancin sarki da bafade! Dan wallahi sai yayi da na sanin sanina a rayuwarshi, bana barin bashin daukar fansa". 


  Gwaggo sakin baki tayi tana kallonta saboda yanda take maganar kamar tanayi da tsararta.

 

 "Haba gimbiya amma bai kamata kina ma kakarki irin wannan maganar bah, karki manta mahaifiyar mamanki ce...."

 "Keep quite stupid girl i don't want to hear anything from you, gulmammiyar banza kema wallahi zaki gane kuranki idan muka koma gida dan karshen zamanki yazo". 

 

 Cikin tashin hankali gwaggo ta kalli Feedoh saboda ta fahimci zata iya sawa a kori Hindu ita kuma har ga Allah bata son haka ta faru."


 "Kinga FIDDAUSI kinawa darajar Annabi kiyi hak'uri kàrki hukunta wadda bata da laifi a kan komai shi da yayi miki, shi yaka mata kiyiwa ba ita bah, sannan Hindu tunda bataso kina faɗa mata gaskiya ki barta duniya ce, sannan kuzo ku haɗa kayanku kutafi gida na gode haka, Allah yaso yau kasuwa akwai mota dan haka sai kuyi niya magana ta karshe daga yau kada ki saki zuwa wannan k'auyen nagodewa Allah da Allah yasa bake ɗaya bace jikata.."

 

 "Tsoki ta buga ta nufi ɗakin tana had'a kayanta, yayinda gwaggo ke binta da kallo, hawaye ya cika mata idanuwa, cikin sanyin jiki Hindu ta shiga ɗakin tana tayata haɗa kayan. 

  Balatoni ne yayi sallama, fuskar nan tashi babu fara'a ko alama, da faɗa gwaggo ta tareshi.


 "Yanzu Modibbo abinda kayi ka kyauta kenan yanzu Modibbo sai kace kai ba fillo bah, zaka kamata cikin kasuwa".

 "Amma gwaggo kinsan abinda tayi min?" 

 "Dakata banason jin komai daga bakinka tunda abin yazama haka nace su shirya su koma gida", 

 "Hmmm! Gwaggo kenan ai wallahi ko ta koma gida sai na bita wallahi sai na aureta dan inga karshen rashin kunyarta".

 "Ba sai kazo ka aure ni ba ingani, tunda ance maka ubana mahaukaci ne irinka, ina zato ajalinka ke kiranka zuwa gidanmu dan wallahi idan kafarka ta taka gidanmu toh wallahi sai dai uwarka ta sake haihuwar wani amma badai kai bah....."


Wani irin kukan kura yayi yana shirin zuwa wajenta da sauri gwaggo ta daka mashi tsawa. 

 

 "Modibbo kai wane irin yaro ne wai ba k'anwarka bace?" 

  "Toh gwaggo idan k'anwata ce sai ta zageni in sa mata ido ina kallonta, wallahi gwaggo yau ba mai rabani da yarinyar nan dan sai nayi mata maganin fitsara...... 

   Taku ce dai mrs omar       Fateen......


   *MAZA DA MULKI*

★★.    _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA*   ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

____________________________________     _story and written by_

        *MRS OMAR*       _in dedication to_

    *FIDDAUSI SODANGI*  _My blog name is_

www.mrsumaru.blogspot.com      _page 18_

  Yana shirin isa wajenta gwaggo tasha gabanshi.

 

 "Haba Modibbo kaima baka jin maganar tawa kamar yanda ita batajin maganata? ko da yake bataji maganar uwarta ba balantana taji tawa ni da nake kaka ban wuce bah, sannan zan faɗa miki wata magana ko bayan babu raina maganar zaki tuna ta ki daina wulak'anta talaka domin kuwa talakawa sune asalinki komin yaya talaka shine tushinki.

 "Hmmmm! kinji min gwaggo wai talaka shine tushena, toh ni ina ruwana da talaka ni abinda na sani ɗaya ne shine natsani talaka duk ranar da na tuna cewa mahaifiyata, talakawa ne danginta ina mai jin bak'in ciki sai ma idan na tuna cikin k'auyen da take ta kaici sai yayi kamar ya kashen..."


 Hannun da Balatoni ya ɗaga ne yana shirin marinta yasa ta haɗe sauran maganarta, gwaggo tayi saurin rik'e mashi hannu ta hanashi ya mare ta.


 "Kaga Modibbo barta taje duniya ce, sannan inaso ka kaisu su shiga mota.

 "Amma......" 

 "Kaga banson jin komai daga bakinka kayi abinda nace dakai kaji koh?."


 Kai ya daga alamar "toh" amma ji yake kamar ya kashe gimbiya dan haushi.

 sai da gwaggo ta rakaso har k'ofar gida kafin ta dawo gida zuciyarta cike da bak'in ciki irin halin gimbiya,

tafiya suke amma zuciya sai sak'a mashi take ya kamata yayi mata shegen duka amma wata zuciyar tace yabarta da halinta a haka suka isa wata 'yar k'aramar tasha da ke cikin kasuwar garin, mota ɗaya ce ta rage wadda zata shiga har cikin garin Yola sai dai motar irin jefiver ɗinan ce babu seat sai benci, suna isa Balatoni yayi tambaya aka nuna mashi motar Yola, cikin sanyin jiki ya ɗubi Hindu yace.

  "Toh ga motar Yola Hindu an samu sai dai da alama duk awaki sun ciki motar sai ku dan raɓa har ku isa."

 Cikin k'asaita gimbiya ta dubi motar sannan ta dube shi tace, 

 

 "Are you mad kana nufin kamarni gimbayar ƴa a wajen sarki SODANGI ni zan hau wannan banzar motar Allah ya kyauta."

 Murmushin takaici yayi sannan ya lumshe idonshi, saboda baiso ya k'ara yi mata magana bah, cikin zafin zuciya ya fara magana,


 "Toh tunda bazaki shiga wannan motar bah, saiki kira a kawo maki mota wadda tafi wannan, kinji koh? jikar

 ɗan karona". 


Shiru tayi tana kallonshi sai kuma tayi murmushi ta daɗe hancinta ta hau motar duk abin nan Hindu na tsaye kamar ruwa ya cita, sai da ta hau ta zauna kafin Hindu ta hau, 

har ga Allah koni ba zan iya hawan irin wannan motar bah bale ace gimbaya guda(Lol),


 "Hindu ki gaida inna Bahijja sannan ki dinga hak'uri da uwar gijiyarki...

 "Hahaha aikin banza, shi dama ɗan k'auye duk yanda akayi dashi sai ya nuna halinshi, in ba abin ɗan k'auye bah, ina kai ina faɗa dani wallahi sai kayi da na sanin zuba min yawon wannan dan iskan bakin naka mai kama da na rat wawa kaw..."


 Kafin ta k'arasa yayi kukan kura ya fizgota daga kan motar, hakan yayi dai-dai da lokacin da driven yaja motar, suka faɗi ita dashi k'asa duk jama'ar wajen sun tsorata, hatta itama taji tsoro, baiji zafin faɗuwar bah, ya mike tsaye cikin fushi ya fizgota ta mik'e tsaye ya fara magana kamar zai yi kuka.


 "Ke ba kince ke marar kunya bace toh ni zan nuna miki nafiki rashin kunya ki dubi bakina kice yana kama da na bera ai dukda ba turanci nake ji bah, nasan abinda ake kira bera da turanci, kuma wallahi yau zan kawo k'arshen wannan rashin kunyar ta ki."


 Hannu yasa ya shak'e mata wuya sannan ya matse mata hannunwa yana kukarin haɗa bakinshi da nata ido ta zaro duk jama'ar wajen kunya ta kamasu, daga mai rufe ido sai mai juyawa ya bar wajen, abinku da fulani akwai kunya....... 


 Fateen....


    *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

        *TAK'AMA* ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

__________________________________     story and written by

        *MRS OMAR*


      _in dedication to_

     *FIDDAUSI SODANGI*My blog name is

www.mrsumaru.blogspot.com


    


        Page 19
  Hankalinta ya tashi sosai ta tsorata da ganinshi haka duk wani k'okari da zatayi ta amshi kanta ta kasa bakinshi ya haɗa da nata duk yawon dake bakinshi sai da ya tattaroshi ya zoba mata a baki duk wani yunk'uri da zatayi dan kar ta haɗe yawon takasa sai da ta had'e shi,

duk ilahirin jikinta babu inda kake gani yana motsawa sai hawaye dake fita a idonta, dukan da yaji an buga mashi ne a baya ya sashi saurin juyowa cikin fushi yaga wa yakai mashi dukan, da sauri ya saki gimbiya Feedoh dan ganin Gwaggo a gabanshi sai huci take, wani kyakkyawan mari ta kai mashi mai cike da jin zafi, cikin faɗa take magana.


 "Modibbo kai wane irin mutumin banza ne? au dama abinda kake mata kenan wallahi Modibbo ka bani kunya sai kace kai ba bafulatani bah?". 

   "Amma Gwaggo kinsan abinda tayi min da har nayi mata haka?".  "Dakata mutumin banza duk abinda tayi maka bazaka hak'ura bah ba kanwarka bace?".

  "Hmmm! Gwaggo ki barshi ni ina dai-dai dashi dan haka wallahi sai yayi *da na sanin* sanina a rayuwarshi, kai bama ni bah ko mai irin sunana ka ji sai gabanka ya faɗi". 

 


"Au haka kika ce? toh bari kiga nafiki iya iskanci."

  Kukan kura da yayi ne yana shirin zuwa wajenta yasa Gwaggo saurin shan gabanshi.


 "Wai kana haukane Modibbo? toh wallahi kana taɓata ina mai k'ara wanka maka mari sha-shashan banza kawai". 


  Hannun gimbiya Gwaggo takama ta sata mota dama kamar mai motar yana jira yasa mata giya, Balatoni motar yabi da kallo yana mai jin haushin gimbiya.


Duk jijjigar da mai motar keyi gimbiya bataji bah saboda tasa kanta a cikin cinwoyinta sai kuka take na takaicin abinda Balatoni yayi mata saboda ko batayi niyar ɗaukar mataki bah ada toh yanzu ya zama dole ta ɗauka saboda tunda take a duniya babu mutumin da ya taɓa mata irin abinda Balatoni yayi mata, shiyasa tace ya zama dole ta ɗauki Action a kanshi, ahaka direba har ya isa cikin garin Yola amma gimbiya bata sani bah, sai da Hindu tace mata sun iso kafin ta ɗaga kanta, da yake mangariba ta kawo jiki shiyasa mutane nata shirin tafiya masallaci, bayan sun fito ta ɗauko ɗaya daga cikin wayoyinta ta danna number dady, babu 6ata lokaci ya ɗaga cike da murna da farin cikin jin y'ar tashi ya fara magana.

 "OH! My daughter i missing you shikenan daga an tafi ko waya inji muryarki shiru?"

  Kukanda ta fasa ne yasa mai Martaba rud'ewa cikin ruɗani yake tambayarta.


 "Me yake faruwa y'ar gatana faɗa min waya taɓa mani ke?", 

  Cikin shashshekar kuka ta fara faɗa mashi abinda ya faru da wanda ma bai faru bah,. "What? Waye shi kuma waye ubanshi a duk cikin k'auyen da har zai taɓaki a zauna lafiya?, stop crying my dear i promise to you i will deal with him. *SAI YAYI NADAMAR* saninki a rayuwarshi, i will never ever let him have peace in his life. saboda.."

 Maganar gimbiya ce tasa ya tsaya da tashi,.


 "Dady ai yaron gidan Gwaggo yake ɗan kanwar Mom ne."

  "So what in ɗan kanwarta ne, ai sai na ɗauki mumunan hukunci a kanshi, yanzu kuna ina?."

 "Dady muna cikin Yola yanzu nakeso musamu motar katsina mutaso.

 "Ina dare yayi Fee ku kama hotel idan yaso yanzu zanyi waya a samar maku ticket ɗin flight, da safe ku taso."


 Babu yanda gimbiya ta iya haka ta hak'ura suka kama hotel, shi kuma mai Martaba bayan ya kashe waya, babu inda ya nufa sai ɗakin Mom dama duk ranar da sukaga mai Martaba ya shiga ɗakinsu kai tsaye sunsan akwai matsala ba kamar in an taɓa y'ar gatanshi ba, cikin zafin zuciya ya banka ɗakin Mom...... 


      Fateen.....

    *MAZA DA MULKI* 

 ★★.    _MATA DA_ ★★

  ★.    *TAK'AMA*  ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

__________________________________     Story and written by

         *MRS OMAR*      in dedication to

   *FIDDAUSI SODANGI*My blog name is

www.Mrsumaru.blogspot.com
         Page 20


  Turo k'ofar da yayi ne yasa Mom firgita cikin ban tsoro ta ɗaga kai tana kallonshi,.

 "Lafiya mai Martaba me yake faruwa ne?."

 


Cikin zafin rai ya fara magana jikin Mom na rawa ta mik'e.

  "Bahijja dama kisan za'a ci wa ɗiyata mutumci shiyasa kika turata garinku dan a wullak'anta min ɗiya toh wallahi kisani i will never let him have peace in his life i promise you that".  "Nifa mai Martaba bansan abinda kake magana a kai bah."

  "Dama ya za'ayi kisan mai ke faruwa bayan kun kawo wani ɗan iskan ɗa yana shirin lalata min y'a".  "Wai dama mai Martaba duk akan Modibbo kake wannan maganar? Allah ya huci zuciyar mai Martaba, amma ni nasan halin Modibbo bazai taɓa yi mata abinda zai cutar da ita bah, may be akwai abinda tayi mashi shi kuma a matsayinshi na ɗan uwanta ya hukuntata.."

  "Dan Allah rufe min baki dan yana ɗan uwanta sai ya kamata ya zuba mata yawon bakinshi a bakinta,

 bakinma irin na ɗan k'àuye wanda sai ayi shekara nawa ba'asawa baki ruwa bah, da sunan za'ayi brush.."


 Cikin ban mamaki Mom ke kallon mai Martaba saboda maganar da ya faɗa tayi mata zafi sosai, bata san lokacin da hawaye ya fara fita daga idonta bah, 

shiko masifa ya ci gaba dayi har yakai aya bata k'ara ce mashi k'ala bah, bayan ya gama yasa k'afa ya fita ita kuma kuka ta dingayi gashi bata da mai bata hak'uri balantana taji sanyi dama Hindu ce mai bata hak'urin toh gashi bata nan yanzu....
*WASHE GARI*Wajen misalin k'arfe 9:05pm flight ɗinsu ya sauka cikin garin Katsina ba'a ɓata lokaci bah akazo ɗaukarsu, suna isa cikin harabar gidan bayan tafito duk wanda ya nufi gaida ita sai yayi mamaki ganin fuskar gimbiya ta kumbura dan tsananin kukan da tayi yasa fuskar ta zama haka, direct ɗakinta ta nufa Bayan ta cire kayanta ta nufi toilet, duk abinda take Hindu na ɗakin tana gyara mata kaya, bayan ta fito shi yayi dai-dai da shiguwar mai Martaba ɗakin, cikin shagwaɓa ta tareshi, cikin tashin hankali yake k'ara tambayarta, haka ta koma, jin tambayarshi yasa ta k'ara narkewa, bayan ya gama bata hak'uri akan ta yafe mashi da yasan hakane da bai turata bah, sannan ya ɗaukar mata alkawarin sai yasa an hukunta Balatoni....  *GARIN YOLA K'AUYE*  Tinda su gimbiya suka dawo gida Balatoni da ya rufe idon shi fuskarta yake kallo tana mashi rashin kunya, ya rasa dalilin haka. gashi Gwaggo na fushi dashi saboda abinda yayiwa Fee...B'angaren gimbiya ma haka da ta rufe idonta sai taga Balatoni yana haɗa bakinshi da nata, yakai ko barci take abinda take gani kenan, yau Anum tazo wajenta take bata labarin abinda duk yafaru tun zuwanta k'auye har ya zuwa dawo warta,

 shiyasa Anum ta bata shawarar.


 "Fee mai zai hana ki amshi soyayyar dogon gaye idan yaso ko zuwa sukayi daga k'auyen kinada masoyinki a hannun."Shiru gimbiya Fee tayi tana tunanin maganar Anum can ta buɗe baki zatayi magana.


"Humm Anumm....
Toh makaranta wannan littafi kash.. naso ace na gama maku wannan littafi kafin Ramadan, sai dai haka bazai samu bah, dole sai yakai bayan sallah, toh ku min hak'uri har zuwa bayan sallah zakuji yanda za'a kare tsakanin *GIMBIYA FEEDOH DA BALATONI DA KUMA DOGON GAYE* a nan ne zamu gane me yasa suke tunanin junansu.. Sannan ina son duk masoyana su tayani addu'ar cin nasara wajen exam da zan rubuta cikin wannan wata mai albarka..
Thank you very much to all my friends, 

Nice dai 

 Fateen soja take CE maku *RAMADAN MUBARAK*..... Gungiya mai albarka NAGARTA WRITER'S Association,... *MAZA DA MULKI* 

★★.   _MATA DA_  ★★

 ★.   *TAK'AMA*    ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

________________________________


 _story and written by_

      *MRS OMAR*   _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI**Ayya ina mai ba masoyana hak'uri akan rashin jina, haka ta faru ne akan exam da nake rubutawa, toh yanzu masha Allah nagama zaku dinga jina insha Allah*....         _page 21_Ɗan Shiru Feedoh tayi tana nazarin maganar Anum kafin daga bisani ta kalli k'awartata tana murmushinta wanda ya zamar mata jiki akoda yaushe tace, 

 

 "Hmmm Anum kinaga idan na aminci da soyayyar dogon gaye babu wani problem? because i don't want any problem, because you know me very well! Hmmm zan iya amincewa da soyayyar dogon gaye, amma in one condition soyayyata dashi zata tsaya na wucan gadi babu aure a tsakaninmu.."

 

 Murmushi Anum tayi sannan ta ɗan cije lips ɗinta ta lumshe ido kafin ta buɗesu a hankali tace

 "That is good my best friend, so how do you want to tell him you accepted him? because nasanki da girman kai bazaki iya samunshi da maganar kina sonshi,ko zaki iya zuwa?"

 "A you mand kina nufin ni zanje na kai mashi kaina God Forbet I will never do that".

 "Oh my dear clam down ni bance ki sameshi bah, ni nasan da kanshi zai dawo saboda ai mai nema baya fushi.

 "That is you Business."


 Tana rufe baki ta jawo phone ɗinta tana dannawa Anum taci gaba da zuba Fee bata k'ara ce mata k'ala bah, saboda ita a rayuwarta babu abinta ke mata wahala irin magana, 

da Anum ta gaji da zuba babu mai bata amsa ta tashi ta nufi ɗakin Adda, kai tsaye ta danna kai babu ko sallama dama wannan bata iyata bah, ihu ta fasa ta faɗa kan Adda tace

 "Adda congrat Adda munyi winning Fee yau ta aminci zata yi soyayya da dogon gaye kinga shikenan hak'armu zata cinma ruwa, humm Adda sai Fee tayi da na sanin zuwanta cikin wannan masarautar ta SODANGI, dan sai tazama abin kyama a idon jama'a."

 "Wannan haka yake tawa inama ace nina haifeki saboda wallahi duk halina kika gado, shiyasa nake k'ara sonki, faɗa min ya akayi ta amince?"


Sai da Anum ta gyara zama kafin ta faɗawa Adda duk yanda suka yi da feedoh bayan ta gama faɗa mata Adda ta kwashe da dariya mai cike da mugunta, a haka suka tsara yanda za'ayi dogon gaye ya koma tinkarar Fee da maganar soyayya, haka suka dinga tsara abubuwan muguntarsu itako tana ɗakinta sake da baki bata san mai ke faruwa bah.
 *B'ANGAREN DADDY*


  Mom babu abinda batayi bah, dan tashawo kan Dady amma abin yaci tura, haka mai Martaba yaci gaba da bala'in, yana shirin turawa Balatoni y'an sanda Mom ta samu iya da kuka dan tashawo kan mai Martaba da kyar tashawo kanshi da yake duk abinda yake da iya tayi mashi magana toh zai bari, ita kawai kewa mai Martaba magana ya ji,


 Duk a wannan lokacin ababuwa sun faru da dama duk a cikin satin ɗaya, >>>>>>>>>> *DOGON GAYE*>>>>>>>>>>>>>>>>


  Sanyi yake cikin shiga irinta alfarma da ka ganshi kaga had'ad'd'en gaye,

 kananan kayane yasa da kaga kayan kasan masu tsada ne indai kasan kaya,


  Zaune yake a gaban gimbiya Fee yana dariya yana wani lumshe ido, duk magana ɗaya sai ya wani tsotse lips dinshi sai kace mai shan sweet.

 "thank you princess"

 "Thanks for what?"

 "For accepting me because am waiting for this opportunity for very long time thanks alot."


 Wani Murmushi gimbiya Feedoh tayi mai haɗe da K'asaita sannan ta wani juya k'wayar idanta ta jawo glass cup ta kafa a bakinta bayan ta janye cup ɗin daga bakinta ta kalli dogon gaye taga shima ita ya k'urawa ido ko kiftawa babu, itama bata san lokacin da ta k'ura mashi nata idon bah, da kaga kallon kaga kallo mai ɗauke da almar so da k'auna, cikin sanyin murya ya fara jero mata kalaman soyayyah mai cike da yaudara. 


 "Ke kyakkyawa ce dole ne duk namijin da ya ganki ya so ki, kina da k'warjini kamar damusa, ke sarauniyar kyawawa ce duk da Allah ya yiki gidan da ake so ki kasance, a kullum bani da burin da ya wuce in dinga kallon kyakkyawar fuskarki, inaso ki kasance dani ako da yaushe, shiyasa nake da muradin aurenki...."

Takashi ɗin da Anum tayi shiya dawo dashi daga hayyacinshi, dukda haka bai kauda kai daga kallonta bah, cikin sanyin murya itama ta fara magana, muryarta mai kama da sarewa.......... 


Nice taku Fatin so.......


   *MAZA DA MULKI* 

★★    _MATA DA_  ★★

 ★.    *TAK'AMA*   ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

__________________________________


   _story and written by_

       *MRS OMAR*


    _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI* _Wannan page ɗin na sadaukar da shi ga masoyiyata *ZAHRA~B~B* ke tawa ce ni taki ce har abada Allah ya barmu tare, na gode da soyayyarki a gare ni...._

        _page 22_ 

  

  Cikin sanyin muryarta mai kama da ta sarewa ta fara bashi amsa, ita kanta bata san lokacin da ta fara bashi amsar bah, 


 "Hmmm! you are very handsome,i never see handsome man like you. zanso mu kasance tare har abada, na mallaka maka zuciyata ni takace..."

 Kafin ta k'arasa maganar dake bakinta dogon gaye ya fasa wani irin ihu ya jawo kwalbar wine ɗin dake gabanshi ya girgizata, sannan ya buɗe marfin ai kam yana buɗe marfin ta wani tashi sama duk ta wankesu,

 duk abin nan da ake ashe Hindu da Mairo na zaune a gefe ɗaya suna kallon ikon Allah, wani irin bak'in ciki ya tirnike Hindu na takaicin Feedoh ta amince da dogon gaye, hawaye ne ya fara zuba a fuskarta, da sauri tasa hannunta ta goge dan bataso Mairo ta fahimci damuwarta.


  Haka suka dinga firar soyayya kamar da gaske basu bar wajen ba sai wajen 10:00pm kafin suka bar gurin shi ma ba gida suka nufa ba, wani wajen suka nufa...  *GARIN YOLA K'AUYE!.*


  Tunda gimbiya Feedoh ta bar garin Gwaggo ta rasa gane kan Balatoni, a kullun cikin tunani yake da ya rufe idanuwanshi sai ya dinga ganin rigimar da suka yi shida ita tun baya damuwa har takai yanzu yana damuwa. 


 Yau takama ranar Monday tunda ya tashi baya jin daɗin jikinshi shiyasa Gwaggo ta tsareshi da tambaya, yau dole sai ya gaya mata damuwarshi, 


 "Modibbo ka faɗa min damuwarka ni yanzu kamar uwa nake awajenka saboda bakada kowa yanzu daga Allah sai ni, dan haka ka faɗa min matsalarka insha Allahu indai batafi k'arfina ba, toh zanyi maka maganinta."


 Sai da Balatoni ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ɗaga kai ya kalli kakar tashi ya fara magana cikin ban tausayi.

 "Gwaggo inaso kafin na fara magana kiyi min alk'awari zaki cika minshi burina shine kawai zai min maganin damuwata idan har na rasashi toh zan shiga cikin babbar matsala d...."

 Kafin ya k'arasa Gwaggo tayi saurin tarar numfashinsa.

 "Modibbo insha Allahu nayi maka alk'awari indai abun baifi karfina ba, toh zanyi makashi."


  "Hmmm! Gwaggo insha Allahu baifi karfinki bah, hasali ma ke kika fara furtawa da bakinki."

 "Toh Modibbo gashi na manta da maganar da mukai amma ka tuna mani."

 


"Gwaggo inaso kiyi min ja gora in auri Fiddausi!"...

 "Wacce Fiddausin?" Gwaggo ta fad'a tana zaro ido dan ita abin mamaki ya bata duba da irin rigimar da suka yi. 


  "Gwaggo Fiddausi y'ar wajen Innah Bahijja wallahi tunda ta tafi nike jin sonta a zuciyata, dan Allah Gwaggo ki taimaka mani."


 "Toh Modibbo ka zo da babbar magana dan wannan magana ba mai yuwa bace, taya kana talaka zaka auri ɗiyar gidan sarauta?, kaima kasan wannan magana ba mai yi yuwa bace, dan haka ka sake zance." "Hmmm! amma Gwaggo kada ki manta ke da bakinki kika furta, anyi alk'awarin had'ani aure da Fiddausi..."


  "Modibbo kenan, kanada abin dariya wallahi, 

ai ni dama wasa nake maka tayaya haka zata faru ai kowace kwarya da abokin gaminta, dan haka ka je ka samu taka dai-dai dakai..

 "Haba Gwaggo taya zakiyi min haka.? wallahi bazan iya auran ko wace mace bah inba Fuddausi b...." Cikin fushi Gwaggo ta dakatar dashi.

 "Dakata!! Modibbo kaima kasan kanka wannan maganar bazata taɓa yi yuwa bah, na tabbata mahaifin Fiddausi bazai amince Ka aure mashi ɗiya ba...


 "Aa Gwaggo taya zakice haka shi taya yazo aka bashi auran Inna Bahijja?" 


  "Uhm! Modibbo kenan yanzu ko zan baka labarin duk abinda ya faru daga haɗuwarsu har zuwa lokacin da suka yi aure......
  Toh masoyana muje zuwa dan jin labarin da Gwaggo zata ba wa Modibbo....Ni ce dai fateen so....


    *MAZA DA MULKI* 

★★.   _MATA DA_   ★★

 ★.   *TAK'AMA*    ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

___________________________________


    _story and written by_

       *MRS OMAR*    _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI* Na sadaukar da wannan page ga K'awata aminiyata abar k'aunata Maman Waleed Allah ya barki da Uncle D Soyayyar gaskiya bah....       _Page 23_
  "Ranar wata Lahadi ranar da

 bazan taɓa mantawa ba a rayuwata, a kullum kakanka yana zuwa cin kasuwanni k'auyuka, hardama kasuwar dakeci a cikin garin Yola, 

 ranar ta kama kasuwar cikin garin Yola ce, toh duk ranar da zai tafi cikin kasuwar garin yakan tafi da ita cin kasuwar domin takan tafi da tallar nono, ranar mai motar dake shiga dasu bai kaisu har cikin tasha bah, sai ya ajesu a bakin titi, bayan ya ajesu kakanka yazo zasu tsalaka titi shiyayi dai~dai da lokacin da driver mahaifin FIDDAUSI ya dannu kai, ka kanku yaga lokacin da motar zata bigeshi shiyasa ya bankaɗa Innarka a gefe ta faɗi shikuma drivern ya bigeshi, 

a lokacin da abin ya faru yazo bikin abokinshi ne haka, sannan kafin ya zama sarki yana magajin gari kenan, yana fitowa daga motar yaga halin da ka kanku yake ciki, da sauri ya ɗaukeshi ya kaishi asibiti aka bashi taimakon gaggawa da likita ya dubashi ya gani kariya ce kawai yayi, nan fa duk ya biya kuɗin da zaibiya dan yasamu lafiya! saida ya gama duk abinda ya dace yayi,

kafin ya ɗauketa ya kawota gidan ya faɗa mana abinda ya faru,, cikin tashin hankali mukaje asibitin muna zuwa mukaga da sauki,

babu yanda bamuyi dashi ba ya tafi amma yak'iya nan ya dinga zama cikin garin Yola har suka fara sabawa da ita.


Bayan wani lokacin yasamu lafiya likita ya bashi sallama muka dawo gida shikuma dama ya koma garinsu watau Katsina kenan, 

duk da haka yana zuwa ganin malam duk bayan wani lokaci a haka mukayi wani sabo dashi mai tsanani, 

nan fa yanuna yanaso ka kanka ya bashi auren Innaka, babu muso da yake malam ya yaba da hankalinshi ya amince za ya bashi aurenta, shi kuma dama yayi aure kusan shekara nawa Allah baibashi haihuwa da matarsa bah,

auransu da ita ansha rigima kafin matarshi ta barshi ya aureta,

 dan iyayensa basuda matsala, sun amince da yak'ara aure, matarshi yar bin malamai ce sosai da yake Allah yace sai anyi auren haka akayishi babu yanda ta iya, bayan aurensu ba'a dade bah Allah ya amshi ran kakanku........"


 Kuka ne yaci k'arfinta shiyasa ta tsaya daga bashi labarin,

 "Gwaggo dan Allah ki daina kuka ina tunanin wannan labarin da kika bani ya nuna min mahaifin Fiddausi mai saukin kaine, ina tunani zai amince da buk'atata insha Allahu."

 Gwaggo shiru tayi tana kallonshi kafin daga bisani ta goge hawayen dake bin fuskarta tace,


 "Toh shikenan zamuje in tambayar maka amma da sharadi."

 "Toh Gwaggo meye sharadin?"


 "Sharadin shine idan har mukaje mahaifinta bai yarda bah, toh zaka hak'ura da ita ka samu wata."


 "Hmmm! haba Gwaggo kada ki damu nasanma ba zaice a'a ba insha Allahu."

 "Toh shikenan Allah yabamu sa'a sai ka shirya gobe mubi hanya.

 "Yauwa Gwaggota Allah yabarmu tare kiyi tsawan rai."

 

Murmurshi kawai tayi bata k'ara cewa k'ala bah, saboda bata son damuwarshi shiyasa a kullum take biya mashi bukatushi, idan ya nai ma...*TA DIKKO ƊAKIN KARA* 


 Su Feedoh basu dawo bah sai wajen misalin k'arfe 1:00am kafin suka dawo, tafiya take kamar zata faɗi sai kace tasha wani abu, tsawar da aka daka mata ne yasa ta tsayawa cak,


 "Ke! daga ina kike cikin wannan tsohon daren?"


Kai ta ɗaga dan ganin wake magana tana wani lumshe ido cikin wata irin murya ta furta

 "Waye ke man magana haka? kai tsaye."

 "Ubanki ne nace maki Ubanki ne ke magana."


 Tahowa tayi tazo wajen mai maganar tana ganin mai magana tayi dariya tace,

 "Oh is you??......


 Muje zuwa dai 

    Fateen so....


   *MAZA DA MULKI* 

★★.   _MATA DA_   ★★

 ★.    *TAK'AMA*NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

___________________________________


    _story and written by_

        *MRS OMAR*

   

      _in dedication to_

     *FIDDAUSI SODANGI*_Wannan shafin nakune masoyana masu k'aunar wannan littafin nawa, hak'ik'a hausawa sunce dole kaso mai sonka, toh nima ina k'aunar masoyana a duk inda suke, bazan manta daku bah, nice MRS UMAR kuna raina....._

         


         _Page 24_

  Saukar marin da ta ji ne a fuskarta ne yasa ta saurin dafe kuncenta cikin zafin zuciya Mai Martaba ya fara magana kamar zaiyi kuka,


  "Yanzu dama FIDDAUSI duk abinda mutane ke faɗa man gaskiya ne, kina kai irin wannan daren, abinda mahaifiyarki ke gudu kenan nak'i ji, ga gaskiyarta nan yanzu ta fito." "Ohhh my God! Please Dad calm dawn look at me, am not a small baby, duk abinda nake yi da hankalina."


 "What? kinada hankali kuwa? Meyasa zakije kisha k'waya kina tafiya kamar yar gida! Hmmm! Today i regreat of having u as my daughter, a yau ina mai jin kunyar wad'annan halayyar naki."


 "Why? Dad?"


 "Don't call me your Dad, because am not you father, bari kiji in faɗa maki from today i am not your Dad." 


 " Dad!"


 "Dakata!!." 

 Tsawar da ya dakamata ne yasa duk jama'ar gidan ta shi daga baccin da suke yi kunsan idan dare yayi toh gari yana tsit, daga ne sa ma zaka iya jin abinda ke faruwa. 

Iya ce farkon fitowa daga sashenta, tana tambayarshi abinda ya faru.


 "Lafiya Basheer kake faɗa cikin wannan dare? abinda baka taɓa yi bah." 


  "Ina fa lafiya Iya! Ai dolene nayi faɗa Iya ki duba kiga abinda yarinyar nan ta ke aikatawa. Iya yau ina da na sanin kasancewata mahaifi a gareta" Mai Martaba ya fad'a zuciyar sa nayi masa k'ona sosai. Cikin ban mamakin maganar da Mai Martaba yake yi Iya ta juya ta kalli Feedoh wadda ke shirin faɗuwa Hindu ta yi saurin tarota. 

Iya bata san lokacin da hawaye ya fara bin fuskarta bah, cikin muryar kuka ta fara magana.


 "Yanzu FIDDAUSI irin rayuwar da kikasa kanki kenan? yanzu da wane ido kike so jama'a su kalli wannan masarautar mai albarka, hak'ik'a kin zubar mana da mutumci a idon jama'a." 


 "Ohh Granny kunata wani faɗa sai ka ce nayi wani babban abu ne please Dad forget tha...." 

Kafinta k'arasa maganarta Mai Martaba ya sake kai mata wani lafiyayen mari babu shiri ta faɗi k'asa, da sauri Hindu ta duk'a zata dagota Mai Martaba cikin zafin rai ya fizgi Hindu ya jefar da ita gefe ɗaya, hannu yasa zai ɗago Gimbiya kenan ta mik'e tana layi, shi ya yi dai-dai da fitowar Bahijja da Adda, aikam Bahijja na ganin halin da ɗiyarta take ciki bata san lokacin data fasa wata irin k'ara ba ta faɗi k'asa, da sauri suka yo kanta ina! kafin ace maki me nan danan jini ya fara fita ta bakinta, duk hankalinsu ya tashi amma banda Adda, Mai Martaba ya ɗagota yana girgizata, cikin layin Feedoh tayo kanta Mai Martaba ya dakamata tsawa.


 "Kada ki k'araso nan, kisani if anything happen to my wife,I will never forgive you, because of you your mother is in this condition, wallahi FIDDAUSI kin chuchi n....

 Kuka ne yaci karfinshi shiyasa ya yi shiru bai k'arasa sauran maganar ba. 


 "Basheer ba zama zakayi kana kallonta bah, asibiti ya kamata a kaita, dan cheto rayuwarta.

Cak! Mai Martaba ya ɗauketa sai mota, babu inda driver ya nufa dasu sai *RAZ SPECIALIST HOSPITAL* kasancewar ta prvt asibiti ce, da isar su direct emergency aka wuce da ita dan ce to rayuwarta.


  Gaba d'aya suka tafi asibitin amma banda Feedoh, saboda Iya tace baza'azo da ita tana cikin wannan halin bah, kusan awarsu biyu a zaune amma Dr. bai fito ba tun suna duba time har suka hak'ura sai addu'a kawai suke yi a zuciya, bayan lokacin da Dr. ya d'auka cikin sanyin jiki ya fito daga room d'in, da sauri Mai Martaba ya tareshi cikin k'aguwa yake tambayarshi.


 "Please Doctor ya jikin nata?

Shiru Dr. ya yi yana kallon Mai Martaba kafin daga bisani ya ce 

 "Ranka ya dad'e Am sorry duk wani...." Kafin ya k'arasa duk sun mik'e sunyo wajenshi, ya yinda Mai Martaba yakasa motsi daga inda yake.......

 Ku dai k'ara hak'uri ..


   Nice dai Fateen so....


   *MAZA DA MULKI* 

★★.   _MATA DA_   ★★

 ★.    *TAK'AMA*    ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

__________________________________


    _story and written by_

        *MRS OMAR*


     _in dedication to_

     *FIDDAUSI SODANGI* 

       _Page 25_
  Dukansu suka haɗa baki suna tambayarshi, 

amma banda Mai Martaba saboda jikinshi ya yi sanyi sosai, 

 "Doctor please kada dai kace mana ta rasu"


Da sauri K Dara ya juya yana kallon ma suyi ma shi tambayar, saida ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce .

 

  "Hmmm! please you people should come down, everything is normal, amma gaskiya munsha wahala kafin Allah ya bamu ikon mu cheto rayuwarta, saboda takamu da hawan jini tun da dadewa, gashi tana yawan sa kanta cikin damuwa shiya kawo wannan Matsalar saura kadan zuciyarta ta buga, gaskiya ya kamata kudinga kulawa da lafiyarta, ta daina shiga cikin damuwa saboda idan tanasa kanta a damuwa toh any time zuciyarta zata iya bugawa.."


 "Innalilahi wa'inna ilaihir raji'un! 

Abinda Iya ta furta kenan, ahankali ta sulale k'asa tana hawaye, Mai Martaba sai yanzu ya samu bakin magana ya ce 


 "Toh Doctor zamu iya shiga muganta?" 

 "Eh zaku iya shiga amma bata bukatar hayaniya."


Yana bashi amsa ya nufi office ɗinshi, su kuma suka nufi inda take, suna zuwa suka ganta k'wance da green din riga a jikinta, sannan ga oxigen ansamata ya rufemata baki da hanci, yana kawo mata numfashi, 

jiki a sanyaye Mai Martaba ya zauna dai~dai inda k'afafunta suke, hawaye ne ya fara fita a idonshi na nadama, 


"Bahijja hak'ik'a sai yanzu nagane amfanin maganar da kike faɗa min, a lokacin na rufe idona na dade kunnuwana bana jin maganar kowa sai ta yarinyar nan, gashi yanzu abinda najawa kaina, da wani ido zan kalli allummata?, Fiddausi kin chuche ni i will never forgive yo..."

 Kuka ne ya kwace mashi duk jama'ar wajen abin ya basu mamaki Mai Martaba guda yana kuka kamar k'aramin yaro hak'ik'a abin babba ne, Iya ce ta dafashi tace


"Basher ka daina kuka yanzu aikin gama yariga ya gama sai dai munemi mafita yanzu, katashi kuje gida nizan zauna da ita, 


"A'a Iya kutafi ni nazauna da ita."

Adda ce tayi magana Iya tayi murmushin takaici tace


 "Babu wanda zai zauna da ita sai ni dan haka zaku iya tafiya gidan." 


Iya tasan halin Adda shiyasa taki ta yarda ta zauna, Adda bataso ba amma haka suka koma gida.. *WASHE GARI*


Tunda safe Adda takira Anum tazo, ai kam bata ɓata lokaci ba tazo, tana zuwa ta nufi ɗakin Adda direct, dama bata tashi daga Inda take ba tana jiran ta iso, ai kam tana isowa Adda tayi shewa 


 "Adda lafiya? naga yau kina cikin nishad'i please tell me.

Sai da Adda ta kama hannunta suka nufi bedroom kafin ta zaunar da ita gefen bed tace,


 "Anum yau ina cikin farin ciki wanda bansan iya adadinsa ba, dan yau burina ya cika...

 "Please Adda tell me what is happening , na kagara ki faɗa min.

 "A'a me kike tauna na baka na zuba,

 kijira yanzu zan faɗa maki, jiya me kuka ba Feedoh tasha ne.?

 Dariya Anum ta kwashe da ita kafin ta juya kwayar idonta tace.

 "Hhhh Adda benerling ne kawai na bata tasha, kinsan yarinyar nada taurin kai dakyal tasha,

 Dariya Adda tayi sannan duk ta faɗa mata abinda yafaru jiya tsakanin Feedoh da Mai Martaba har yazuwa faɗuwar mahaifiyarta,

 

 "Kai! That is good Adda today am very happy to see Feedoh mother in this condition" 


 "Ai Anum nafiki murna saboda naso ace mutuwa tayi wallahi" 

 "Hmmm! Adda kisa ranki a ruwan sanyi dan wallahi gidan nan yakusan zama mallakinki, dan wallahi Feedoh sai ta ɗauko masu abin kunya, yanda a lokacin zatayi da na sanin sanina a rayuwarta,

 yanda daga lokacin zuciyar uwar zata buga ta mutu a banza." 


 "Kai Anum wallahi shiyasa nake k'ara sonki, kin iya bada shawara mai kyau." 


  "Yanzu Adda kitashi muje ɗakinta muga tatashi wane hali take ciki kafin muɗaura daga inda muka tsaya." 


 Suna fitowa suka nufi ɗakinta a hankali suka tura k'ofa......

 *Ina mai baku hak'uri masu cewa bana typing da yauwa, insha Allahu i will try my best.*

  nice dai Fateen ku.......

 *MAZA DA MULKI* 

★★     _MATA DA_  ★★

 ★     *TAK'AMA*   ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

__________________________________


      _story and written_

         *MRS OMAR*      _in dedication to_

     *FIDDAUSI SODANGI*
  _Wannan shafin nakune yan MRS UMAR NOVEL 1&2 nagode da k'aunarku, bazan taɓa mantawa dakuba, ni takuce har abada..._         _Page 26_


     Suna fitowa suka nufi ɗakinta a hankali suka tura k'ofar, kwance take tana barci ko kayan dake jikinta bata cire bah, bakin gado suka zauna,

zamansu yasa a hankali tafara buɗe ido, tana ganin Anum tayi saurin tashi zaune, cikin faɗa ta farama Anum magana.

 

 "Anum why do you do dis to me?why anum? kisa benelin ɗin da kika bani problem ɗin da yajawo min? sanadiyar haka tasa mahaifiyata kwanciya a Hospital, da wane ido zan kalle su yanzu?


 "OH my God! Feedoh listing to me this is small problem just calm down, so please just calm down i promise you everything will be normal m... 

 "Please Anum just keep quite because i will never listen to you again." 

 

Anum zata k'ara magana Fee ta ɗaga mata hannu babu shiri tayi shiru da bakinta, saida Adda ta sauke ajiyar zuciya kafin tace

 

 "Feedoh na wannan abu duk ba abin faɗa bane sanin kanki ne Bahijja zata iya faɗuwa kawai saboda idan kika ganta a kwance zaki iya chanza rayuwarki, amma Fee meye abin damuwa dan kinsha benelin? a tunanina duk wata rayuwa ta jin daɗi yanzu ne yakama ki samu ba sai kinyi aure bah, wallahi Feedoh na tabbata Anum bazata chutar dake ba, ko kina tunanin zata chutar dake? 

Kai Fee ta girgiza alamar a'a, Adda tana hawaye na karya tace gaba da magana 

 "Toh wallahi Fiddausi yanda na ɗaukeki kamar ɗiyar cikina bana son ganin bacin ranki, nafisan farin cikinki a kan nawa, dan haka shawarar da zan baki kici gaba da rayuwarki karki biyewa Bahijja, kinsan ita y'ar k'auye ce bata san komai ba sai wahala, sanda tazo nan kinganta kuwa? kin yarda ina sonki ko?."


  "Yes Adda na yarda nasan ke mai sona ce, but Adda my problem shine Mai Martaba yayi fushi sosai duk da jiya bana cikin kaina toh yanzu duk na tuna da abinda ya faru." 

 "Kada ki damu indai akan Mai Martaba ne nasan zai sauka daga fushin da yake dake" 

Murmushi Fee tayi sannan ta faɗa jikin Adda tana sauke ajiyar zuciya, Anum ta kashewa Adda ido ɗaya ta jinjina d'an yatsanta. 


 "Yanzu yanda za'ayi ki tashi ki watsa ruwa mufita kije ki zaɓi duk abinda kikeso na saya maki, saboda bana son ganinki cikin damuwa, idan yaso muka dawo,

 sai mubiya ki ganta a asibitin, ke kuma Anum muje kafin ta gama. Suna fitowa suka taɓa suka kwashe da dariya da sauri suka daɗe bakinsu da hannuwansu dan gudun kar wani ya ji su, sai dai aikin gama yariga ya gama, jinsu kuma na nawa duk abin nan Hindu najinsu tazo ta duba ko tatashi daga barcin da take, sai gashi duk taji maganar da suke yi , tanaji zasu fito tabar wajen da sauri, 

ta nufi ɗakinsu na kuyangu ta nufa tana zuwa ta faɗi k'asa nata kukan takaice,

 sukuma suka shige ɗakin Addar dan sake kulla wani abin.


 Tana kuka tafara magana.


 "Ho ya Allah wannan wace irin rayuwa ce? Adda keson saka gimbiya a ciki, Allah nagode maka dabakayi ni ɗiyar sarauta bah, amma yanzu zan kawo wannan k'arshen wasan na Adda, insha Allahu Allah bazai bata sa'a ba akan gimbiya, sai ta zan abin so ga kowa, toh yanzu matsalar wazai taimaka min dan shawo wannan matsalar saboda wannan babbar matsala ce.


  "Gaskiya ne wannan babbar matsala ce amma ki kwantar da hankalinki ni zan taimaka maki." 


 Da sauri Hindu ta ɗaga kai dan ganin wake magana.......
 Toh makaranta nima kaina bansan wa ya yi wannan maganar bah, amma may be ko zaku san wanda ya bata amsa, bari mugani  08021084887
 Muje zuwa nice dai Fateen so......


    *MAZA DA MULKI* 

★★.    _MATA DA_  ★★

 ★.    *TAK'AMA*   ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

___________________________________


     _story and written by_

           *MRS OMAR*


     _in dedication to_

     *FIDDAUSI SODANGI* _Wannan shafin nakune masoyan gaskiya muna godiya da irin kaunar da kuke nunawa writer's bansan iya adadinta godiyar da zan muku ba, hakika kunchanchanchi mu jinjina maku, shiyasa na sadaukar maku da wannan page din naku ne Ku kad'ai *AUNTY MAIJIDDAH AND AUNTY SISTER* wallahi *KUNA RAINA*.._


  

          _Page 27_

  "Gaskiya ne wannan babbar Matsala ce,

 amma ki kwantar da hankalinki ni zan taimaka miki, 


Da sauri Hindu ta ɗaga kai dan ganin mai magana, cikin sauri ta mike ta ambaci sunanta, 

 "Gwaggo!! yaushe kukazo waya faɗa maku Mom ba lafiya? 

 "Hmm bamusan bata da lafiya bah sai yanzu muka samu labari, muma yanzu mukazo shine Mairo ke faɗa mana duk abinda ya faru, tare mukazo da Modibbo shi yana waje", 

 "Wallahi abinda ya faru kenan Gwaggo, wannan wace irin rayuwa ce shikenan saboda abin duniya sai mutum ya saɓawa Allah'n shi,

 Adda *SON ZUCIYA* naso ya kaita da yin *DA NA SANI*, amma banni da ita *SAI TAYI NADAMA* a lokacin da batada amfani, sa'annan abinda nayi imani da shi shine *MATAR MUTUM* k'abarinsa, idan har Allah ya ce Affan shine *MASOYINTA NA HAR ABADA*, toh babu wanda ya isa yahana, na tabbata hak'uri yana da kyau a rayuwa, kamar in na tuna lokacin da Amatullah tasha wahalar *DANGIN MIJINTA* shikuma Habib ya rufe ido yanuna masu cewar *ITA D'AYA CE.*


 "Toh Gwaggo insha Allahu gimbiya sai tazama kamar yanda ake son ganin kowane ɗa yazama."


Gwaggo ido kawai ta kurawa Hindu dan maganganunta sun bata mamaki sosai, ajiyar zuciya ta sauke kafin tace


 "Hakika Hindu ke ɗiyace da ko wace uwa zatayi alfahari dake naji daɗin kasan cewarki cikin wannan masarautar nan ta SODANGI, maganganunki sun bani sha'awa sosai, sannan ki kwantar da hankalinki insha Allahu Allah na tare damu babu abinda Adda ta isa ta yiwa FIDDAUSI, ki share hawayenki muje ki kaimu asibitin muga yanda jikin nata yake."


  Hawayenta ta goge sannan suka fito, inda Gwaggo tabar Balatoni a nan ta sameshi daka ganshi kasan akwai gajiya a tare da shi.


Bayan Fee tashirya ta fito cikin wasu matsatson kaya kallo guda zakayi mata ka kauda idonka, saboda yanda tasa kayan sun kamata sosai abinka ga mai Sharp, dama ko batasa kaya matsatso ba abin sha'awace toh bale tasaka, tana fitowa ta samu su Anum da Adda allready sun fito, ga motocinta Adda tasa an wankesu, duk abin nan Mai Martaba baisan me ake ciki ba, saboda yana asibitin wajen Matarshi, mota d'aya suka shiga, 

direct *JIFATU* suka nufa,suna zuwa suka samu dogon gaye a can yana jiran su iso. 


 Su Gwaggo suna isa asibitin suka nufi ɗakin da Bahijja take, kwance take har yanzu bata farka ba. Iya da Mai Martaba sun kura mata ido duk ta fara faɗawa, Iya tana ganin su Gwaggo ta tashi tana masu oyoyo,


"A'a mutane adamawa yau a garin namu yanzu kuka iso? kai sanunku da zuwa."


 "Yauwa." Gwaggo ta amsa bayan ta zauna Mai Martaba ya duka cikin girmamawa ya gaisheta. 


"Yanzu muka iso sai muka samu mumunan labarin abinda ya faru, har yaja Sanadiyar kawota asibitin."


 "Eh wallahi fatsima ai wannan yariya tanaso ta ɓata sunan wannan masarautar ta SODANGI, kiduba yanda tasa mahaifinta cikin damuwa, mahaifiyarta na kwance bisa gadon asibiti ace ko tazo taga yanda jikin nata yake, wannan wace irin rayuwa ce? 

 "Ki kwantar da hankalinki Indo insha Allahu wannan Matsalar tazo karshe dan baza'asa ido ana kallonta ba, tajawowa mutane abin kunya. 

 

Ajiyar zuciya Iya ta sauke kafin tace 

 "Gaskiya ne wannan maganar taki."

 Shi dai Mai Martaba babu abinda ya ce daga bisani Iya ta dubi balatoni, yana tsaye bayan ya gaidasu bai kara cewa komai bah, Iya tace, 

 "Fatsima badai Modibbo bane ya girma haka?" 


 "Eh shine wallahi." 

Ana ambatar Modibbo Mai Martaba ya juya da sauri ya kalleshi....Nice dai Fateen so....


    *MAZA DA MULKI* 

★★.   _MATA DA_    ★★

 ★.   *TAK'AMA*     ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

__________________________________


     _story and written by

         *MRS OMAR*


     _in dedication to_

    *FIDDAUSI SODANGI* _Wannan shafin naki ne *KE DAYA* Sarakuwata ta kaina Balkisu Bilyamin, ba zan taba mantawa dake bah, aduk lokacin da na tuna *MATAN ALI* hakika dole na jinjina maki..._
        _page 28_
    ★Ana ambatar sunan Modibbo Mai Martaba yayi saurin juyawa ya kalleshi,

Mai Martaba ya buda baki zaiyi magana su Adda suka turo k'ofa, kai tsaye Fee ta dannu kai babu ko kunya,

ga wani uban eyeglass tasha bakin nan nata yasha jan jambaki, 

tsawar da Mai Martaba ya daka mata ne yasa ta tsaya cak!.


 "Stop!! what did i tell you? I said i don't want to see ur face again, so what are you doing here?" 


 "Please Dady why are you doing this to me? i........."


 "keep quite Fiddausi because i don't want to hear anything from you, taya zan kara yarda dake bayan bazaki tab'a chanza halinki ba, yanzu ki duba irin kayan da kike sakawa a matsayina na mai faɗa aji ace y'ata ta cikina tana irin wannan shigar." 


 "Oh my God Dad look at me, so yanzu waɗan nan kayan mai sukayi? nifa gaskiya Dad banason takur..."


 Wani wawan mari Mai Martaba ya kai mata bata san lokacin da jiri ya kwasheta ba, tana shirin faɗuwa Balatoni yayi saurin tararta, ido ta ɗaga dan gani waye ya kamata, tana ɗaga kai taga Balatoni a gabanta, cikin fushi ta tureshi.


  "How dey you Touch me, kai ubanwa ma ya baka damar zuwa garin nan? Hmmm! Balatoni you made a big Mistake , sai kayi nadamar zuwan ka wannan garin dan bakada kunya har zaka tako k'afarka cikin wannan masarautar ta SODANGI."


 Murmushin mugunta tayi sannan ta dube Adda tace

 

 "Adda nasan bani da kowa yanzu sai ke kice kawai mai sha....." 


 Maganarta ta tsaya ne sakamakon wani numfashi da Bahijja taja, dukkansu suka nufi kanta, ahankali take buɗe ido, tana buɗe idanuwanta suka sauka kan Fee, cikin rawar murya ta fara magana,

 

 "Please ku fita da ita bana son ganinta, nace ku fita da ita hamham..." 


 Numfashinta ya yi sama, da sauri Mai Martaba yaja Fee ya turata waje, duk abin nan wani daɗi ne ya mamaye zukatan su Adda, 

ganin numfashi Bahijja na barazanar ɗaukewa yasa Iya saurin zuwa kiran Dr Dara, yana zuwa ya ce su fita waje baya son ganin kowa a cikin ɗakin. 


bayan ya shawo kanta yafito yana masu faɗa.


  "Amma dai na faɗa maku bata son damuwa, saboda ciwon dake jikinta yanason hutu bata buk'atar hayaniya, idan har baku kiyayi bah, toh gaskiya zaku iya sata cikin Matsala."


 Su Gwaggo yake faɗawa cikin damuwa Iya tace 

 "Insha Allahu Doctor zamu kiyayi bazamu bari wani abu yasamita bah."


 Tana rufe baki ya juya ya nufi office ɗinshi.


Fee tana fita bayan Mai Martaba ya turata, bata damuba ko a jikinta, mota suka shiga ita da Anum suka nufi inda suke shakatawa, suna tafe suna shan kiɗa, 
*TWO DAYS LATER!!!.* jikin Bahijja ya yi sauki sosai har an basu sallama sun dawo gida, zaune suke a babban parlournta, ita da Gwaggo Iya sannan Mai Martaba. Iya tacewa Gwaggo.

 

 "Fatsima tunda kikazo bamu samu damar zama munyi magana ba sai yanzu, da fatan dai lafiya k'alau? saboda kin iso kika zamu wannan matsalar"


Ajiyar zuciya Gwaggo ta sauke kafin ta fara magana.


 "Lafiya qlau Indo dama nema wata buk'ata mukazo da ita, Modibbo ya daman dole sai nazo.


 "Toh da fatan dai ba wata matsala bace tataso."

 

 Numfashi ta sauke kafin ta gyara zama, tace

 "Lafiya Indo sai dai muna tare da buk'ata... munzo akan naimawa Modibbo auren FIDDAUSI ne.....


 "What! auren ƴata that is impossible, taya ƴata zata auren ɗan kauye ina!!" Mai Martaba ya faɗa cikin fushi, Iya ce ta dakatar dashi da cewa,


 "Dakata Basheer wannan ba magana bace kake."


 "Iya taya zaki faɗi haka bayan....." 

Nice dai Fateen so.


    *MAZA DA MULKI* 

★★.    _MATA DA_  ★★

 ★.     *TAK'AMA*   ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

___________________________________


       _story and written_

          *MRS OMAR*


       _in dedication to_

     *FIDDAUSI SODANGI*          _Page 29_

"Dakata Basher ai wannan ba magana bace kake"

 "Iya, taya ya zaki faɗi haka bayan kin san bani da wani farin ciki da ya wuce na wannan yarinyar."

 "Au haka za kace bayan kana gani saboda irin son da kake nuna mata yana so ya kai ka da yin da nasani, toh wallahi tun wuri ka chanza ra'ayinka."

 "Iya a gaskiya nayi alk'awarin ba zan taɓa yiwa ɗiyata auren dole ba, yanzu abinda nasan zan iyayi shine ɗaya idan har FIDDAUSI tana da wanda take so toh zan bata wanda take so idan kuma babu toh zaku iya bata Modibbon, dan ni kam ba zanyiwa ɗiyata auren dole bah."

  "Haba Mai Martaba wannan wace irin rayuwa ce kake son samu ciki?"


 Bahijja ce yanzu tayi magana, cikin fushi ya mik'e tsaye yace.


 "Bahijja this is my choice because i will never change my choice."


 Yana kai karshen maganarshi ya juya yabar ɗakin, Gwaggo ta kasa koda motsi saboda abin Mai Martaba ya bata mamaki, ahankali Iya ta kama hannunta tace.


 "Fatsima taso muje akwai maganar da nake so muyi dake."


  Babu musu Gwaggo ta tashi suka nufi ɗakinta inda suka sauk'a, ahankali suke magana ni kaina bansan mai suke faɗa ba...


  

  Balatoni tunda yazo tun ranar da suka haɗu da Fee a asibiti har yau bai 'kara sata a ido bah, saboda duk sanda ya tashi toh ita tana barci sanda zata fita shikuma yana tare da Hindu, gashi in ta fita bata dawowa sai cikin dare, shi kuma a lokaci yayi bacci.


 Cikin sanyi jiki Iya ta fita a ɗakinsu Gwaggo, tana fita babu daɗewa Balatoni ya shigo, yanda yaga Gwaggo tayi shiru yasa shi saurin k'arasawa wajanta yana tambayarta.


  "Gwaggo meke faruwa, ya naga jikinki duk yayi sanyi ba dai jikin Inna Bahijja bane ya dawo?"

 Gwaggo ta ɗago jajayin idanunta ta kura mashi ido, sai daga bisani ta sauke ajiyar zuciya tace.

 "Humm Modibbo! Kenan ai dama na faɗa maka kazo da babbar magana na tabbata indai Basher na raye toh bazai taɓa bari ka aure ɗiyarsa ba, sai dai wani abin Allah, dan haka shawarar da zan baka kayi hakuri mu koma gida kasamu wata yarinyar dai dai da kai, kaji ko?"


 Cikin firgita ya mike tsaye zufa na bin fuskarshi yace.

 "Haba Gwaggo taya zakuyi min haka bayan ni duk duniya babu yarinyar da nake so bayan FIDDAUSI, wallahi bazan taɓa auren wata yarinya in ba FIDDAUSI ba."

  "Toh ni dai Modibbo abinda ubanta ya faɗa kenan dan haka babu abinda zan iya akai."

 Tana rufe baki ta juya tabar ɗakin, shikuma inda yake yayi mutuwar tsaye..   *AROUND 1:00PM*


  MAI MARTABA ya aika a k'ira mashi Fee, mai hali baya fasa halinsa sai da tagama abinda take zata fita kafin ta biya wajenshi, zaune ta sameshi bisa kujerarshi ta alfarma, yau cikin sanyin jiki ta shiga kamar duka kenan.


  "Sallamu alaikum."

  "Wa'alaikis Salam."

 Ya amsa ba tare da ya kalleta ba, bayan ta gaidashi ya amsa ba kamar kullum ba.

  "Toh da fatan kinsan dalilin da yasa na aika aka kiraki?

  "A'a Mai Martaba."

   "Toh ba wata magana bace mai tsayo ina so na faɗa maki daga yau kin bar makaranta, aure nake so nayi maki."

 Cikin firgita ta ɗaga kai ta dubeshi, ba tayi magana ba shiyasa yaci gaba da magana.

 "Kinsan alk'awarin da na ɗauka bazan yiwa ɗiyata auren dole ba, dan haka idan kina da wanda ki ke so toh ki turo manshi inganshi, dan na gaji da wannan sakarcin naki, kina da tsayayyene?"

 Kai ta girgiza alamar babu, yace.

 "Toh masha Allah tunda baki dashi toh mahaifiyarki na dashi sai a haɗaku aure dashi fatanmu Allah yabaku zaman lafiya."

  "Mai Martaba wayeshi?"

  "Modibbo shi....."

  'What! Dad Modibbo? that's impossible....."  Mrs Umar


    *MAZA DA MULKI* 

★★.    _MATA DA_   ★★

 ★.     *TAK'AMA*    ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

____________________________________      _story and written by_

         *MRS OMAR*


      _in dedication to_

     *FIDDAUSI SODANGI* _wannan page ɗin naki ne tawa my sweetheart, abar k'auna hak'ika idan nace ina da kamarki nayi k'arya, ke tawa ce ni ɗaya banda kamar ki, ina maki fatan Allah ya saukike lafiya ya nuna mani naje sunah a kebbi, *KE DAYA CE*my JEDDAH ALIYU_       Page 30"What? Dady, no That's impossible, i will never marry that village man, haba Dad tayaya zakayi min haka? karasa da wanda zaka had'ani aure dashi sai da wannan d'an k'auyen d'an k'auyen ma, illiterate no Dady i will never marry him.."


 Hawaye ne ya fara fita daga idanunta shiyasa maganarta ta tsaya. Mai Martaba saida yayi gyaran murya sannan ya gyara zamanshi sosai yana fuskantar ta, itama shi take kallo, cikin k'asaita ya fara magana a natse.

  "Toh ni dai har ga Allah bani da niyar yimaƴy'ata auren dole, saboda nasan ilarsa saida na tambayiki kinada wanda kike so kikace babu,toh dan haka tunda baki dashi kinga kuwa dole ki aure wanda ke akwai yanzu....

 "Ina dashi Dady.

 "Kina dashi? toh masha Allah tunda kinadashi waye shi?"


 Shiru tayi tana tunani saboda ita kanta bata san lokacin data furta haka ba, Mai Martaba ne ya katsemata tunaninta ta hanyar sake tambayarta,

  

  "Hmmm! inajinki ke nake jira kibani amsa,

  "Eh Dad dama wanine toh ba wani dadewa mukayi dashi bah, shiyasa ban faɗa maka bah."

  "Toh tunda kina da wanda kikeso babu wani dogon bayani zaki iya turo munshi muyi magana kafin ya turo magabatanshi,dan bana son abin ya ɗauki lokaci, zaki iya tafiya."


  Cikin sanyin jiki ta meke tana tafiya, cike da ban mamakin abin da Mai Martaba yake shirinyi mata, hak'ik'a ta yarda Mai Martaba ya gaji da ita, tana fitowa Allah yasa taci karo da Balatoni, bata san lokacin da tasha gabanshi bah, 

  "Kai ɗan k'auye!!"

 Wani irin kallon sama da k'asa yayi mata yaja tsaki, abinka da dan iskan k'auye, cikin faɗa taci gaba dayi mashi magana,

 "Stupid village man, you are a fool, you don't know anything i promise you i will deal with you so that you will never forget me, kadube ni kace wai ni zaka aura ko kunya bakaji bah?"

 

 Wata irin dariya ya kwashe da ita kafin yace.

 "Na faɗa maki ke k'aramar yar iska ce idan har kin isa to ki maimaita abin da kikace da hausa,wallahi kiga yanda zanyi dake a wajen nan saboda ni bana jin kunyar mu kwashi yan kallo a wajan nan."

 "To ai kai baka isa ba har in tsaya inayin musayar yawo a wajanka bah, saboda kaga wancan karan yafika mahim'manci a wajena..."


 Hannnu ya ɗaga zai kai mata mari sai kuma ya tsaya ya cije lips ɗinshi ya ce.

 "Kinci sa'a ɗaya wallahi da sai kin gane shayi ruwa ne,."

  "Aikin banza,"


 Tana rufe baki taja tsaki kawai ta kara gaba abinta, shi kuma yabita da kallo, saboda yanda yaga mazaunanta na juyawa, kamar ana juya masa, 

jiyake kamar ya kamota, itako batasan ma yanayi ba, ɗakin Adda ta nufa direct zuciyarta cike da bak'in ciki, tana zuwa ta faɗa jikin Adda tana kuka. 


  "Adda nashiga uku Mai Martaba zaiyimun auren dole."

 "What? aure kuma tayaya haka zata faru bayan burina bai cikaba."

 "Adda wane irin burinki?

 "Hmmm! ina nufin burina bai cika ba na son ki kammala karatunki, naso kizama abin da duk jama'a zasu dinga kwatance dake."

  

 Yaro yaro ne. Adda so take ta kai Fee ta baro, ita ala dole Adda masoyiyarta ce,

  "Hmmm! Adda ai nasan ke mai sona ce, Mai Martaba baya sona yanzu, idan har yana sona bai kamata yayi min aure yanzu ba, please Adda look at me am still a Small girl, ban isa aure ba."

  "Nasani Feedoh! amma yanzu wace shawara kika yanke? 

 "Adda na yanke shawarar auren Affan duk da ba ajina bane. 

  "Toh she Affan din........     Kashhh! naso nayi maku typing ɗin da yafi haka sai dai abinku da marar lafiya sai a slow, ku kara hak'uri muje zuwa.
Nice dai Fateen so.......


   *MAZA DA MULKI* 

★★.    _MATA DA_   ★★

 ★.    *TAK'AMA*     ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

___________________________________


      _story and written by_

        *MRS OMAR*


 

    _in dedication to_

    *FIDDAUSI SODANGI*


     

    

*OH MY GOD AM VERY HAPPY TO SEE THIS TIME* 

Am so happy , dis day is my 10 years in marriage i pray dat God will continued bless my home,

I will never forget this time, nayi murna da zagayuwar wannan rana sai dai kash... No just forget ba sai na furta abin da ke zuciya ta bah, wannan rana nayi murna sosai ta kara tunu min da rayuwata ta baya, hak'ika aure rahama ne, dani da mijina AHMEED UMAR AND FATIMA UMAR muke maku fatan alkairi, thank you very much to all my Fans.      Page 31
"Toh shi Affan ɗin kina da tabbacin zai aureki?"

 " Adda kenan toh ai ni a tunanina babu namijin da zai gani ya kasa aurena, Adda ba wannan bace damuwata, yanzu babu abin da zakiyi dan kada ayi wannan auren."

 

 Ajiyar zuciya Adda ta sauke kafin daga bisani tayi murmushin mugunta ta ce.

 "Humm Feedoh niko ke da yanda za'ayi dan kada kiyi aure yanzu indai har zaki bani haɗin kai?

  "Haba Adda i promise you i will do anything you say." 

 "Yauwa kawo kunnuwanki kiji."


Kunanta ta kangawa Adda kafin daga baya ta ɗago kanta ido ta zaro da sauri ta rufe bakinta da hannunta ta ce.

 "Adda kinaga idan nayi haka babu wani problem?" 

  "OH! my dear don't worry i promise you babu abin da zai faru kidai kibani goyan baya,

  "Adda kenan kisan duk duniyar nan banda kamarki saboda nasan bazaki cutar dani bah" 

 "Haka ne yasa nake k'ara sonki a zuciyata." 


 Murmushi ta yiwa Adda wanda har sai da ya nuna dimple d'inta.

 "Adda ni zan fita kuma ni ɗaya zan fita da mota because i don't want sa ido." 


Dariya Adda tayi kana ta ce 

 "Kina da gaskiya ai yanzu idan zakibi ta mutane to ko fita bazakiyi ba dan haka kici gaba da abin da kike babu ruwanki da kowa."


 Duniya kenan! Wani daɗi taji a zuciyarta da Adda ta bata wannan shawarar, kafin ta mike tayiwa Adda kiss a goshi ta fita. Adda ta kwashe da muguwar dariya ta ce


 _"Humm yaro baisan wuta ba sai ya taka, sai nan gaba za ki san koni wacece, a lokacin da za kiyi kuka da idanunki yarinya, sannan zan zuba ruwa k'asa insha dan murna...._"

"Toh hatsabibiya insha Allahu Allah bazai baki wannan sa'ar bah."

 "Cikin firgita Adda ta mik'e bakinta na rawa ta fara kiran sunanta

 "Iya! ... Hmmmm! sannu da zuwa." 

 "Rufa min baki ke dai Hauwa har yanzu baki barin wannan halin na ki, wannan wace irin rayuwa ce kika sa kanki a ciki? shikenan dan ba ki haihuwa sai ki lalata ɗan wani, toh wallahi kiji tsoron Allah tun wuri kafin lokacin nadama ya k'ure maki."


 Borin kunya ta fara yi shiyasa Iya ta juya abinta tabar mata ɗakinta..


 ***

 Balatoni tun da ya koma ɗakinsu da ya rufe ido Feedoh yake gani, yanda take mashi tsiwa da yanda take tafiya, wani irin daɗi yakeji sai yaji sonta na k'ara shiga zuciyarshi, murmushi yayi kafin ya tashi ya ɗauro alwala ya nufi masallaci duk abin Balatoni sallah bata wuce shi..  Bayan ta fito taja mota babu inda ta nufa sai gidan dogon gaye.

 abin mamaki ya fito toilet dagashi sai towel a ɗaure, yayinda Anum ke zaune gaban mirror tana gyara Make'up d'inta, gaban mirror ya k'arasa ya ɗan duko da kanshi ya ce.

 "Ya dai har kin shirya kenan?"

 Kai ta ɗaga ma shi, taɗan lumshe idonta, ya juya kenan zai nufi wajan bed, sukaji ana knocking da sauri ya juya ya kalleta itama ta k'ura mashi ido.....
 Toh Readers kenan akwai wani abu a tsakanin dogon gaye da Anum ta ɓoyewa Adda.? wannan amsar ku zaku ba kankuNice dai Fateen so......


    *MAZA DA MULKI* 

★★.   _MATA DA_    ★★

 ★.    *TAK'AMA*     ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

___________________________________


     _story and written by_

        *MRS OMAR*     _in dedication to_

     *FIDDAUSI SODANGI*       _Page 32_
  Knocking ɗin da suka ji ne yasa su saurin ɗaga ido suka kalli junansu, cikin rawar jikin Dogon gaye ya nufi parlour dan ya duba mai masu knocking, yana laikawa yaga Fee ce a tsaye, cikin hanzari ya koma bedroom ya ce.

 "OH! my God Anum yau asirinmu zai tonu Feedoh ce a waje.

 "What Fee? munshiga uku, so what are you doing now?

 Kafin ace miki me Anum jikinta ya ɗauki rawa, Affan shiyayi ta maza ya ɗauko gyalenta ya jefa mata ya mika mata Handback ɗinta sannan ya kama hannunta ya ce.

 "Please Anum calm down, haka da kike shi zai nuna mata akwai wani abu a tsakaninmu kikwantar da hankalinki i promise you babu wani wanda zai gane akwai wani abu a tsakaninmu, yanzu abin da nake so dake kije ki buɗe mata kofa kada ki yarda ta gane komai kinji koh?"


  

 Cikin sanye jiki take tafiya dai-dai taje parlour Fee ta kara knocking ɗin kofa, ahankali ta karasa ta buɗe kofar, 


  "A'a so is you Feedoh? ayya am sorry naji ana knocking toh yana ciki wallahi bansan ke bace, nima yanzu na kirashi a waya sai ya ce min na biyo ta nan zamuje wajanki."


 Fee batayi mata magana ba kawai ta wuce abinta, tana shiga tabi parlour da kallo saboda bata taɓa zuwa ba yau ne zuwanta na farko gidan, abin da ya kara bata mamaki bai wuce ganin photonan ta a parlour ba, wani murmushi ta saki mai ɗauke da jindaɗi ta ce.


  "Wow Anum ina Affan ya samu pic ɗina haka? kinga yanda suka yi kyau, gaskiya na yarda Affan na sona."


 Wata irin ajiyar zuciya Anum ta sauke mai sauti saboda ita a tunaninta gimbiya Fee ta gane gaskiya, sai yanzu Anum ta samu damar rufe k'ofa ta k'araso wajenta ta dafata ta ce.  "Fee nima na yarda da haka tun da na shigo gidan nan yau, hak'ika Affan namiji ne da kowace mace zata so shi.

 "Yes haka ne, ina yake ne?

 "Au yana wanka yace in jirashi ya gama ne.

 "OK."

 

 Tana rufe baki ta zauna ɗaya daga cikin kujerun parlour, phone ɗinta ta fara dannawa,

 yayin da Anum ke murmushin mugunta ta bita da kallo, k'amshin turaren da tajine yasata saurin ɗaga kanta, sanye yake cikin suit sun mashi bala'in kyau, binshi tayi da kallo yana isowa ya nufi wajanta ya zauna seat ɗin da take a kanshi, ɗan dukowa yayi har suna jin numfashin junan su ya ce


 "Hey my princess how are you? wow today you are so beautiful looking pretty ."

  Murmushi ta sakar ma shi haɗe da juya kwaryar idanunta ta ce

 "just like you dear ."


Zamanshi ya gyara kafin ya kashewa Anum ido ɗaya ya jinjina mata ɗan yatsenshi, kafin ya juya ya kalli Fee ya ce.


 "Wallahi my princess a kullum sonki yana k'ara shiga zuciyata Hajiya? idan ban same ki ba zan iya rasa rayuwata, Fee inaji a jikina kamar wani na shirin rabani dake hak'ik'a duk ranar da haka ta faru zan kashe kaina.."


 Hannunta tasa da sauri ta rufe ma shi baki kamar zatayi kuka ta fara magana.

 "Why are you saying this ? ko kanaso zuciyata ta buga har kana tunani wani zai iya samun zuciyata, ni a tunanina babu shi, ban taɓa son wani namiji ba bayan kai kuma babu wanda ya isa ya rabamu.

 "Are you sure ?

 "Yes am very sure ."


 Ihu yayi ya kama hannunta da ta rufe ma shi baki ya manna mata kiss ya ce

 "Kai my princess I'm very happy, na yarda kina sona."

 Shiru tayi ta dan bata fuska cikin sanyi muryarshi ta yaudarar 'yan mata ya ce

 "Baby what is wrong are you oK?"

Ɗan jum kadan tayi kafin ta ce.

 "Affan akwai matsala babba.

 "Matsala princess what is the problem?"

Idanunta ta lumshe kafin ahankali ta fara bud'esu ta ɗan cije lips ɗinta tace.

 "Affan Mai Martaba ya ce in fitar da mijin aure, bazan ci gaba da karatu bah.." 

 "What?.....


 

 Mrs umar na godiya da kaunarku a gare ta masoyana...


    *MAZA DA MULKI* 

★★.     _MATA DA_  ★★

 ★.     *TAK'AMA*   ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

___________________________________


      _story and written by_

         *MRS OMAR*       _in dedication to_

     *FIDDAUSI SODANGI*  _wannan shafin naku ne masoyan yan NAGARTA mungode da irin k'aunar da kuke nuna mana, hak'ika yanzu muka gane kuna kaunarmu, sannan Feedoh duk taga sak'onku tana godiya sosai, Allah yajikan mama ya kai haski kabarinta.._
        _Page 33_

  "Affan Mai Martaba ya ce in fitar da mijin aure bazan cigaba da karatu bah.

  "What? to ke yanzu wace shawara kika yanke?"


 Numfashe ta sauke kafin daga bisani ta kara fuskantarshi sosai ta furta

 "Hmmm! yanzu na yanke shawarar kai zan aura.."

 Da sauri Affan yakai dubansa ga Anum, alama da ido tayi ma shi shiyasa Gimbiya bata gane komai ba a fuskarshi, 

cikin sanyen muryarta mai kama da sarewa ta ce

 "Affan will you marry me?

 "Yes my princess i will marry you, ai duk duniya babu wanda ya dace ki aura sai ni, dan haka gobe Dad d'ina zai dawo daga Dubai yana dawo zan sameshi da maganar, kin kusa ki zama tawa ni ɗaya."


 Murmushi tayi ta juya kwayar idonta, mikewa tayi tsaye tana shirin tafiya da sauri ya riko hannunta ya ce.

 "Ina zaki tafi koma bayan ban gaji da kallon kyakkyawar fuskarki bah?

 "Time na tafiya kutaso mutafi." 

 "OK hannunta yasaki ya ɗauki wayoyinshi, sannan suka fita ranar bai ɗauki motarsa bah, motarta ya shiga shida kanshi yake driving, yayinda Anum ita kuma tashiga tata motar,ta tafi su kuma shida ita suna cin soyayyarsu a mota, Fee yau duk girman kan nan nata ta sauke shi.... **************


  *AFTER TWO DAYS*


Mai Martaba an kwana biyu bai kara ganin gimbiya bah, kuma duk sanda zai aika a kirawota to sai a tanda har tafita, dan haka yau ya aika tun da safe ya ce yana son ganinsu wajan karfe 1:30pm..

 zaune suke a babban parlournsa dukkansu amma banda Modibboh, gyaran murya mai Martaba yayi sannan ya fara magana.


 "Toh da fatan dai kowa yasan dalilin da yasa na taraku a wajan nan?"


 Shiru suka yi ba wanda ya bashi amsa, magana yaci gaba dayi yace.

 "Kwana biyu da suka wuce na aika aka kirayo man ke akan kifitar da mijin aure, kika ce kinada wanda kike so, toh naga maganar taki ba gaskiya bace dan haka na yanke shawarar haɗaki da Modibboh...

 "What!!!! Dad Modibboh? Dad na faɗa maka wallahi inada wanda nake so, Dad ɗinsa ne yaje Dubai jiya ya dawo amma inasha Allahu nasan gobe zaizo,.

 "Wannan matsalarki ce, Fiddausi kinaso a ɗauke ni a tsohon banza ni kuma bazanso sunana ya ɓace a idon jama'a ba.

 "Dad dan Allah kayi hak'uri ka bani nan da gobe i promise idan har baizo ba to na yarda zan aure Modibboh."


 Shiru yayi yana kallonta kafin yace

 "OK na baki nan da gobe amma idan har ya wuce gobe to aurenki da Modibboh babu fashi...

 "Amma Mai Martaba ni a tunanina bai kamata kayiwa y'arka haka ba, ai Feedoh ta wuce ajin Modibboh mai zai hana ka haɗashi aure da Hindu...

 "Hindu!!? tayaya haka zata faru, ina."

 Iya ce da Gwaggo suka tari Adda gaba ɗaya suka haɗa baki, Adda shiru tayi tana kallonsu cike da ban mamakin haɗa bakinsu, mai Martaba yace.

  "Wannan shawara ta rage wajanku nidai na gama magana saboda ba zan bari saboda ita ba sunana ya lalace a idon jama'ata ba,dan haka zaku iya tafiya."


 Tashi suka yi suka fita bayan fitarsu Adda taja Fedoh suka nufi ɗakinta.

 "Fee yanzu abinda nake so dake kije kisamu Affan kifaɗa mashi yanda kukayi da Mai Martaba.

 "Nima abin da nake tunani kenan zanyi.

 "Yauwa kije yanzu kishirya."


 Kai ta gyada kafin tafita daga ɗaki, tana fita Adda ta danna number Dogon gaye, saida suka ɗauki kusan awa ɗaya suna magana.


 ★★★★★★★★


 Wajan karfe uku ta fito tayi kwalliya babu laifi, daga nisa ta hango wani kyakkyawan sauraye, tsaye cikin kananan kaya ne a jikinshi, sannan yasha aski ga sajinshi ya fito sosai ga wani uban eye glass yasha, yayi kyau sosai ga farinshi ya bayana, da ka ganshi kaga haɗaden gaye, ita kanta bata san lokacin da ta dinga kallonsa bah, ahankali take tafiya har tazo dai-dai inda yake tsaye, ido ta zaro bata san lokacin da takwashe da dariyar da bata taɓa yin irinta bah ta ce.


 "Wallahi Hausawa sunyi gaskiya, dama sunce ɗan k'auye idan yazo birni yafin ɗan gari iya iskanci, hahaha kai ko kunya bakaji ba, wai nan kayi kwalliya hahaha."


  Dariya yayi sannan yayi mik'e ya cire glass ɗin dake fuskarshi, ya dube ta sosai ya k'ura mata manya idonshi ya ce,

  "Hahaha Allah abin godiya Allah nagode maka da nima dai uwata daga kauye tafito, kenan ɗan kauye ya wuce in rainashi, gashi kuma zan haɗa zuri'a da ɗan kauye.."


 Wane kukan kura takai mashi taci mashi kwallar riga ta ce.

 "Kai har ka isa ka gaya min magana.....


Fatin so....


 *MAZA DA MULKI* 

★★.    _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA*  ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

________________________________


    _story and written by_

        *MRS OMAR*


      _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI*
  _wannan page nakune yan group ɗinmu MRS UMAR AND JIDDAH ALIYU hak'ika muna godiya da irin yanda kuke nunawa group ɗinmu so muma muna kaunarku._
         _page 34_


  Wani irin kukan kura takai mashi a take taci mashi kwallar riga, sai wani irin haki take kamar wadda tayi gudu cikin fushi ta fara magana.


  "Kai har ka isa ka gaya min magana, to bari kaji in faɗa maka wani abu da baka sa ni ba, idan ma ba'a faɗa maka ba ni zan faɗa maka, tun dare baimaku ba kutattara kayanku ku koma k'auyenku dan nasan abinda ya kawoku k'unci ya isheku haka, saboda nasan ba'a saba cin daɗi ba, tun kafin ku fara zawo gara ku koma k'auye aje aci abinda aka saba ci.

  "Hahaha wallahi FIDDAUSI daɗina dake kina da abin dariya, kada ki manta tun da har daɗi baisa wadda takawo ni duniya ba, toh ai ina tunani nima kuwa bazai sani zawo ba, saboda itama a sannu ta saba, kinga kuwa dole na girmama dan k'auye saboda shine sanadiyar zuwana duniya."

  

  "Wani bak'in ciki ne ya kara tun karar zuciyarta, kwalar rigarshi ta k'ara matsewa, Balatoni har yana jin saukar numfashinta.

  "Are you mad? kai har ka isa ka haɗa uwata daku wallahi uwata tafi karfinku, sunan kawai an haifeta a k'auye ne amma ta wuce ajenku."

   "Hmmm! Ni ai ba kiji na anbace sunan kowa a nan ba, nadai faɗa miki gaskiya ne, dan kisan ɗan k'auye nada daraja a wajanki, saboda ko yanzu na yarda da haka kedai ki faɗi gaskiya, kice dai kinaso kitaɓani kin rasa yanda zakiyi shiyasa kika fara burin kunya, gashi yanzu kin taɓa ni kina jin dad'i ..."

  Rasa amsar da zata bashi tayi shiyasa tayi mashi wata irin ingiza dan haushi jitake kamar tasa wuka ta daɓa mashi, kasa magana tayi da gudu ta koma cikin gida, shiko wani irin daɗi yakeji, duk abinda suke Hindu na kallonsu ahankali ta karaso wajanshi, yana ganinta ya tsaya da dariyar da yake.


 "Amma Ya Modibboh kanaga wannan abun da kakewa gimbiya babu wata matsala? saboda nasan hali gimbiya babu mai taɓata a zauna lafiya, idan bakai ba abin har mamaki yake bani.

  "Hindu kenan kada ki damu babu wata matsala insha Allahu, ni a yanzu burina bai wuce na aure taba, badan komai nake son aurenta ba, sai dan in nuna mata darajar da ɗan k'auye yake da ita, hak'ika na yarda *HAR A ZUCI* FIDDAUSI bata son 'yan k'auye, Hindu damuwata ɗaya da mai Martaba bai aminci dana aure FIDDAUSI bah, amma nayi alkawarin bazan koma Yola ba zan tsaya in dinga fadawa Allah na tabbata addu'a bata faɗuwa kasa banza, idan kuma Allah ya ce ba matata bace zan hak'ura.."


  Muryarshi ce tayi sanyi kamar zaiyi kuka shiyasa ya tsaya da magana.

 "Ya Modibboh ka k'ara hak'uri kada kamanta da abinda Allah ya faɗa ya ce Innallaha ma'assabirin dukan mai hak'uri yana tare da samu.

 "Haka ne Hindu nagode a kullum idan muna tare dake nakanji daɗin kalamanki a zuciyata."

.

 Murmushi tayi a haka sukaci gaba da hira har Balatoni ya manta da abinda ya faru.


gimbiya ɗakinta ta nufa dagudu ta faɗa kan gado zuciyarta kamar zata fashe, idanunta ta rufe tana rufewa taji sautin kalaman da Balatoni ke faɗa mata suna dawowa a kunnanta, da sauri ta tashi zaune amma bata daina jin muryar tashi ba, tsaye ta tashi ta dinga watsar da kayan ɗakin kamar zatayi hauka,tanufi madubi tana ɗaukar kayan sama tana jifa dasu.


 "Balatoni i hate you na tsaneka bana sonka wallahi *SAI KAYI NADAMAR* shigowa rayuwata, sai na mai da kai abin kallo a idon jama'a."


 Kwalba ta ɗauka zata fasa glass d'in madubin shi yayi dai_dai da lokacin da Adda shigo ita da Anum, da sauri suka rik'e hannunta,


  "Haba Fee mai yayi zafi haka?"

 Adda ce tayi mata tambayar, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba,

 "Please my princess stop crying kisan banason ganin hawayenki ko kinaso nima na fara?"

 Kai ta girgiza mata alamar a'a." 

 "Yauwa to faɗa min meke faruwa?"

 Dan shiru tayi da kukan kafin daga bisani ta faɗa mata duk yanda sukayi da Balatoni, ajiyar zuciya Anum da Adda suka yi kamar duka kenan, kafin Adda taci gaba da magana.


 "Wallahi Feedoh har kinsa hankalina ya tashi jinake wani abu ya faru, ashe saboda wannan ɗan k'auyen kike wannan abin to meye dan ya ce Bahijja itama daga k'auye take ai gaskiya ya faɗa, kidaina damuwa dashi kada ya rainaki saboda naga alama Bahijja tafi son shi a kanki.

 "Nima Adda nasan da haka but Adda bana son ganinshi a gidan nan.

  "Kadaki damu my dear i promise you insha Allahu i will try my best, sai yabar gidan nan tun da bana ubansa bane.

  "Yauwa Adda thank you very much i will never forget you, i love you.

  Rungumuta tayi zuciyarta ciki da farin ciki, Anum ta taɓe fuska kafin ta ce

 "Toh ya isa haka kun barni zaune ina kallonku, Fee na faɗa maki a duk lokacin da kikaji damuwa irin wannan ga abinda zakisha kinasha zakiji kin manta da abinda ke damunki."

  Anum na fitar da kwalbar gimbiya ta zaro ido waje........
  Nice dai fateen so..... *MAZA DA MULK*

★★.    _MATA DA_ ★★

 ★.     *TAK'AMA* ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

_____________________________________


   _story and written by_

       *MRS OMAR*


    _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI*  _Na sadaukar da wannan page ɗin ga AMINNAN JUNA masoyan gaskiya masu k'aunar junansu dan Allah *@(RAZ)* hak'ika yanda kuke k'aunar junanku kuna bani sha'awa, ina maku fatan Allah ya baku mazaje na gari, ni kuma Allah ya barni da abar k'aunata Jiddah ta..._


       _Page 35_


 Anum na fitar da kwalbar gimbiya ta zaro ido waje.


  "Haba Anum kada ki manta irin matsalar da nasamu ranar da nasha abin nan, sanadiyar shi ne yasa mai Martaba fushi har yayi ik'irarin zai min aure, hak'ira tun daga ranar nayi nadamar sa ni da ku kayi na sha." 


 "But Fee amma..." 


 "Please Anum dakata! just keep quite because i don't want to hear anything from you today, kinsan irin problem ɗin da na shiga ranar kuwa? a lokacin da akwai karar kwana da mahaifiyata ta rasa ranta duk a sanadiyata.." 


 "Amma ni a tunani Fee wannan duk ba matsala bace zaki iya shan abinki.."


 Wata irin tsawa gimbiya ta dakawa Anum, tasa hannu ta bugar da kwalbar ta faɗi a kasa ta fashe, Anum zatayi magana Adda tayi mata alama da ido tayi shiru, ganin ranta ya ɓace sosai yasa suka bar ɗakin, hawaye ne yaci gaba da sauka a idonta na takaicin abin da Balatoni ke mata. Gashi yanzu babu halin ta samu mai Martaba ta faɗa mashi damuwarta, ranar haka ta wuni bata fita ba..


   *********


  Zaune yake a babban parlourn mahaifinshi shi da abokinshi Haydar suna jira ya fito, bai wani ɓata lokaci ba sai gashi ya fito daga bedroom ɗinshi, sanye yake da jallabiya a jikinshi, bayan ya zauna suka fara gaidashi.


  "Barka da fituwa." 


  "Yauwa barka dai maike tafe daku? nasan da na ganku ku biyu to akwai matsala me ke faruwa?" 

 "Haydar faɗa ma shi." 

 "A'a kai ka faɗa ma shi mana." 

  "Kunga bana san shirmen banza ku faɗa min abin da ya kawo ku .

  "Dady dama! Affan ne yasamu yariyar da yake so to shiyasa mukace bari mu faɗa maka yanzu haka iyayenta sunce ya turo." 


  "Kai masha Allah ai abin da nake so kenan, yar inace waye mahaifinta?.

  "Dad yar gidan mai Martaba sarki Basher SODANGI ce.

  "To ai wannan abu duk mai sauki ne, ai Basher abokina ne sosai bari ma na kirashi yanzu, kai masha Allah gaskiya ka iya zaɓe."


  Phone ɗinshi ya ɗauko ya danna number Mai Martaba, sai da ta kusan katsawa kafin k'wark'warashi ta ɗauka

  "Hello dawa nake magana?.

 "Kibawa mai wayar inason magana da shi.

  "Sorry sir sai ka gabatarmin da kanka kafin na ba shi wayar, idan yanaso yayi magana dakai."


 Cikin fushi ya furta.


 "Ki faɗa mashi senator Mustapha Khalil ne ke son magana da shi." 


  Cikin ladabi ta faɗa mashi, take ya amshi wayar mahaifin Affan shiya fara magana.


 "Barka da dare rankaya daɗe Allah ya ɗaukaka masarautar SODANGI." 


  "Yauwa abokina kwana da yawa?" 

 "Wallahi kuwa Mai Martaba kasan yanayin aikin namu bamu samun zama."


 "Haka ne to Allah ya bada sa'a." 


 "Amin! to dama Mai Martaba yaron waje nane yazo min da magana auran ɗiyarka ya ce ka ce ya turo iyayenshi, shiyasa nace bari na kiraka da kaina naji." 


 "Gaskiya ya faɗa, ni nayi mata magana na ce ta ce dashi ya turo iyayenshi amma bansan yaron wajanka bane, amma yanzu komai yazo da sauki ai ɗanka ɗanane kada ka samu damuwa na ba shi.

  "Kai nagode Allah yabar zumunci." 

 "Amin."


 Sun ɗan daɗe suna hira kafin suka yi bankwana bayan ya kashe wayar suka ci gaba da tatauna maganar auren shi dasu har suka tsaida gobe za'a kai kuɗin naiman aure da sadaki.

  


  Duk abin da suka tatauna k'wark'warar Bahijja tajisu da sauri taje ta faɗa mata duk yanda ta ji suna tattaunawa , Mum tayi bakin ciki sosai da ba Balatoni zai aure ta ba, daga baya kuma ta godewa Allah da Allah yasa zatayi aure ko sun huta ko hankalinta zai kwanta....


   N.W.A mune dai an buga damu an barmu, mu kabewar kan kabari ne bamu fito ba saida muka shirya, yaro ana babbakar giwa wazai juyo kamshin zomu, mu munfi karfin yaro sai dai babba.

  Muje zuwa..  Mrs umar


    *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA*  ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

__________________________________


    _story and written by_

       *MRS OMAR*    _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI*


 

  _Wannan page ɗin naki ne Khadija Aliyu ( Dijeena ) kinfi kowa son wannan littafin nawa.._

  


        _page 36_
  Bayan mahaifin Affan da yan uwansa sun samu Mai Martaba, nan aka tsaida ranar auransu nan da wata biyu masu zuwa saboda basu son a ɓata lokaci,

 tun da Modibboh yasamu labarin an sakawa gimbiya ranar aure hankalinsa ya tashi sosai, kwance yake a ɗakin dasuke hawaye ne ke bin fuskarshi kota ina jiyake kamar ya haɗi zuciya ya mutu dan haushi. Gwaggo dake kusa dashi ta k'ura masa ido tana kallonsa itama ji take kamar ta tayashi kukan cikin sanyin murya ta fara magana.


  "Haba Modibboh kada ka manta kaifa musulmi ne, ana son musulmi da ɗaukar k'addara mai kyau ko marar kyau, na tabbata akwai abin da Allah yake nufi da yin haka, dan haka inaso kayi hak'uri kazo mu koma gida ka yarda da k'addara haka Allah ya nufa FIDDAUSI ba matarka bace.


  "Hmmm! Gwaggo kenan wallahi ni kaina bansan lokacin da hawayen nan ke fita daga idona bah, Gwaggo inaji a jikina a duk lokacin da aka ɗaurawa FIDDAUSI aure da wani to a lokacin zan rasa rayuwata..." 


  "Ya salam kana haukane Modibboh? ko ka manta da matsayinka ne kada ka manta kai talaka ne ita koma yar masu kuɗi ce, a cikin masu halin ma, ita a masarauta take, ni dama na tabbata wannan babban al'amari ne kazo dashi saboda FIDDAUSI ba matar auranka bace, dan haka mu koma gida kasamu yarinya dai-dai dakai."

  "Gwaggo na tabbata bazaki taɓa gane abin da nakeji ba saboda tun da nake ban taɓa son wata yarinya ba inba FIDDAUSI ba, hak'ika rayuwata na cikin hats...."

  

  Kuka ne yaci k'arfinshi Gwaggo itama bata san lokacin da hawaye ya fara bin fuskarta ba, haka suka dinga kuka ba mai ba wani hak'uri, da sauri nima nabar ɗakin dan nima ina gab da kukan...


  *******

  "Haba Affan kasan wannan abin daka aikata babbar matsala ce tayaya zaka amince da auren Fee bayan akwai alkawari mai karfi a tsakaninmu, munyi sharad'i dakai bazaka aureta ba, sai dai kawai mu lalata mata rayuwarta to tayaya yanzu zaka amince da aurenta?"

  "Haba baby please listen to me, wallahi bani da laifi Adda ce ta kirani ta ce dani na amince da maganar auranta, saboda idan ta aure wannan ɗan iskan k'auyen to akwai matsala babu yanda na iya shiyasa na amince dan bana so ta gane akwai wani abu a tsakaninmu, wallahi baby i promise you kona aureta muna tare.

  "Hmmm! Affan kenan look at me i am not a small girl, so i don't want to hear anything from you, saboda na san yaudararka tun ba yau ba." 


  "Haba babyna kada kimin haka mana."


 Tsaki ta buga tasa hannu zata buɗe k'ofar mota da sauri ya fincikota ta faɗa jikinshi, wani irin kallo sukaci gaba da yiwa junansu mai cike da sha'awa, hannu yasa ya tallabe kanta ya kanga kanshi kenan a bakinta bai k'arasa ba phone ɗinshi tayi k'ara tsaki yayi ya ɗauko yana dubawa yaga sunan Dad ya bayyana a screen ɗin wayarsa, da sauri ya ɗauka ya d'ora a kunnanshi.


  "Hello Dad barka da wuni?.

 "Yauwa Affan ina fatan kana kusa da gida?." 

 "Yes Dad.

 "Yauwa kazo yanzu inason ganinka."

  

 Dad na rufe baki ya kashe wayarshi, cikin sanyin jiki ya dube Anum ya ce

 "Baby am very sorry Dad ɗina ne ya kirani, yana son ganina yanzu kiyi hak'uri zan kiraki."

 Yana rufe baki bai tsaya jin amsarta ba ya buɗe k'ofar mota yafita dama cikin motarta suke,

bai wani ɓata lokaci ba ya isa kiran Dad ɗin na sa, zaune ya sameshi yana kallon news, shima ɗaya daga cikin kujerun parlourn ya zauna. 


 "Dad gani da fatan badai wata matsala bace?

 "Babu wata matsala kawai dai na kiraka ne dan in faɗa maka an tsayar da ranar auranka nan da wata biyu masu zuwa." 

  "Kai Dad amma naji daɗi thank you very much." 


  "Sai dai ba'a kawo min sarakuwar tawa na gani ba, ko kana rowarta ne?." 

  "A'a Dad kawai dai naga baka yauwan zamane." 

 "To ko a photo abani ita nagani."

 Murmushi Affan yayi kafin ya danna wayarshi, can ya bude wani photo nata da tayi da pink and gulden gashi ta ɗanyi murmushi dimple ɗinta ya fito, wayar ya mikawa Dad, yana mika mashi da sauri ya tashi tsaye yana faɗin.

 "What kana nufin wannan yarinyar ita zaka aura?

 "Eh Dad itace ko akwai matsala?" 

 "Affan ai wannan yarinyar ba matar yara bace matar manya ce ina zaka da wannan tsaleliyar yarinyar?.

  "Dad kamar ya ban gane mai kake nufi bah." 

  "Affan kenan ai wannan yarinya......  To masu karatu tirk'ashi!! Akwai abu fa.....
  Ni ce dai Fateen so....   *MAZA DA MULKI*

★★.    _MATA DA_ ★★

 ★.     *TAK'AMA* ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

___________________________________


   _story and written by_

        *MRS OMAR*


      _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI*       _page 37_
  "What kana nufin wannan Yariyar ita za ka aura?."


 "Eh Dad itace ko akwai matsala?"


  "Affan ai wannan yarinyar ba matar yara bace matar manya ce ina za ka da wannan tsaleliyar budurwa?." 


 "Dad kamar ya? ban gane mai kake nufi ba.?"


  "Affan kenan bazaka gane ba ai wannan yarinyar ba irin matar da ya dace ka aura bace." 


 "Saboda me Dad? Please Dad i don't understand what you mean kayi min magana ta yanda zan gane."

  

 Wajan da yake zaune ya koma ya zauna kafin ya gyara muryarsa ya fuskance ɗan nasa yaci gaba da magana.


 "Affan ina nufin mizai hana tun da kaga mahaifiyarka ba zama take ba kullum tana wacan kasar gobe tana wacan..."


 Shiru Dad yayi ya kasa karasa maganar, 

tun da ya fara magana Affan ya k'ura masa ido yana kallonsa ya ji abin da zai fito daga bakinshi.

 

 "Dad inajinka ka yi shiru kuma." 


 "Hmmm! Affan ina nufin mai zai hana tun da dama inaso na k'ara aure ban samu yarinyar da nake so ba, to yanzu naga yariyar nan sai naji ta kwanta min mai zai hana ka bar min it...."


 "What??? Dad wace irin magana ce kake yi haka? ya kana maganar abin da bazai taba yuwa ba." 

 "Please Affan ka fahimce ni wallahi nayi maka alkawarin duk abinda kake so ni zan maka." 


  "Hmmm! Dady kenan, wallahi a kullun idan kana wani abin mamaki kake bani, toh bari kaji wallahi bazan hak'ura da FIDDAUSI ba, kai ko banyi niyar auranta ba to yanzu saina aureta.." 


  "Please Affan katsaya kada ka tafi mu fahimce juna."


 Ina kafin ya k'arasa magana, Affan har yabar parlourn wajan motarsa ya nufa ya shiga yayi mata key, yanda yaja motar yasa mai gadin gidan tsorata dashi, da sauri ya buɗe masa get dan yasan halin bala'insa, saboda bazai taɓa mantawa da marin da yayi masa ba, cikin fushi yake driven direct gidansu gimbiya ya nufa, wani irin brake ya taka dai-dai k'ofar gidan, hannunsa ya buga a steering motar, ahankali ya rufe idanunsa.


  "Haba Affan meye abin fushi bayan ba sonta kake ba, kada fa ka manta Dad mahaifinka ne zaka iya sadaukar masa da soyayyarka barema ba sonta kake ba." 

   "Ina! ai bazai yuba tayaya zan sadaukar masa da soyayyarta bayan ban cika burina ba a kanta, bantaba ganin abin da yaban sha'awa ba ban lasa zumarsa ba, dan haka wallahi sai na lasa zumar Fee koda zan barta."


 Duk a cikin zuciyarsa yake wannan maganar, wayarsa ya ɗauko ya danna number Adda bansan me suka faɗa ba daga baya ya kashi wayar, ya buɗe k'ofar motar ya nufe cikin gidan

yana zuwa ya sameta a parlour zaune shi take jira, bayan sungaisa duk ya faɗa mata abin da ya faru shi da Dad, d'an shiru tayi tana tunanin maganar kafin daga baya ta gyara zamanta sosai, sannan ta fara magana ahankali dan bata son wani yaji abin da suke tattaunawa.


  "Hmmm! Affan wannan fa babbar magana ce mahaifinka yazo da ita, idan har ka hak'ura kabar masa Fee ya aura to duk wani Plan namu zai rushe, burinmu bazai taɓa cika ba, Affan na faɗa maka idan har kayi abin da nace maka ka aikata to basai ka aureta ba, idan kuma baka aikata ba to dole kai zaka aureta saboda banason naga Fee da mahaifiyarta a cikin farin ciki nafinson na gansu suna kuka da idanunsu, dan haka inaso yau ka gayya ce Fee zuwa gidanka, ka kirata a waya yanzu kada ka nuna mata kana gidan nan ka faɗa mata baka da lafiya sannan kada ta faɗawa kowa koda Anum ce."

 

 Kai ya girgiza kafin ya ɗauko waya ya danna numberta, cikin murya k'asa-k'asa yake magana dan ta ɗauka da gaske bashi da lafiya, yana kashe wayar tajinjina masa hannu kafin ta ce  


 "Kayi sauri ka koma gida, bayan ya fita taci gaba da dariyar mugunta" 


 "Bahijja kin kusan ki bakunci lahira dan wannan karan da kin faɗi sai dai makabarta wallahi hhhhh." 

    *NWA*
 Fateen so...


   *MAZA DA MULK*

★★.    _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA*  ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

__________________________________


   _story and written by_

       *MRS OMAR*


     _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI*  _wannan page ɗin sadaukarwa ne ga duk wata members dake group ɗin Benazir Omar watau *ZAUREN KATATU*_       _page 38_
  Zaune take a bayan mota yau ba itake tuk'a motar ba drivernta ne, ita ko kwata-kwata hankalinta baya jikinta, breke ɗinda yatakane haɗe da horn duk a lokaci ɗaya, yasata saurin ɗaga kai dan ganin abin da ke faruwa,

 wani tsoho ne yana dogara sanda da alama titin yakeso ya tsallaka amma ya k'asa, da sauri drivern nata yayi parking yafito ya ma manta suna tare da ita.

  "Sannu baba da fatan dai bakaji ciwo ba?" 


 "Eh yaro banji ciwo ba." 


 Gimbiya wani irin haushi ne ya kamata da sauri ta 6alle marfin motar tafito.


 "Nuhu wannan wane irin iskanci ne? ina cikin mota zaka fita ka barni."


 Da sauri Nuhu ya tashi daga kan tsohon yana faɗin.


 "Sorry maa naga nakusan bankeshi ne shiyasa na tsaya domin na dubashi."


  "What?? Are u mad? to ni ina ruwana that is your business is not my, dan haka bani key ɗin motata." 


 "Gimbiya dan Allah kiyi hak'uri wallahi gani nayi tsoho ne kada mutafi mubarsa shiyasa na tsaya." 


 "Nuhu ka bani key ɗin motata na ce, idan kuma da kudin ubanka aka saya to sai ka rik'e." 


 "Haba baiwar Allah kiyi hak'uri kada ki koreshi saboda ni dan Allah." 


  "Malam bada kai nake magana ba, kanaji koh?" 


  "Amma ni a tunanina bai kamata kina wallakanta ɗan adam ba kadafa ki manta mahaifinki shike mulkin garin nan bake bah." 


 "Hmmm! au dama kasan koni wacece? naji daɗin da kasan haka ni ba sa'ar talakawa bace." 

 "Allah ya shirye ki amma wannan ba hali bane mai kyau kina TAK'AMA da mulkin mahaifinki kina wullakanta talakawa, ko da yake ba kanki aka fara ba, dama ance *MAZA DA MULKI MATA DA TAK'AMA*, ba zanyi maki baki ba sai dai nayi maki fatan shiriya."

 

 Tsaki taja kafin ta juya ga Nuhu wata irin gigitarciya tsawa ta daka ma shi, jikinshi na rawa ya bata key ɗin motar.


 "Aikin banza daga nan ka wuce gida har sai lokacin da na neme ka."


 Bata tsaya jin amsarsa ba ta shige mota taja da sauri, 

 bayan ta isa gidan Affan tayi parking tafito, ta nufi parlournsa tana zuwa taga bata ganshi a parlour ba da sauri ta nufi bedroom ɗinsa, tana zuwa ta ganshi kwance da sauri ta karasa wajansa bakin gadon ta zauna tana faɗin.


 "Babyna lafiya meya sameka?" 


 "Hmmm! wallahi princess ciwon sonki ne ya dame ni na rasa inda zansa kaina" 


 "Ban gane ba ta ya ya ciwon sona zai kamaka bayan na mallaka maka zuciyata?."


 Tashi zaune yayi ahankali ya kama hannunta yana wasa da yatsenta, kasa magana tayi sai dai manyan idanunta da ta k'ura masa.


 "Princess bansan mizan faɗa miki ba bansan yaya zan kwatanta miki yanda nake jinki a zuciyata ba, wallahi a kullum idan na tuna yanda surar jikinki take ina jin sha'awarki na shiga zuciyata."


 Affan yana magana yana lumshe ido kamar mai jin bacci, hannunsa ya sake d'aurawa a saman cinyarta, sai k'ara shiga jikinta yake yanzu har yakai suna jin numfashin junansu cigaba yayi da magana.


   "Fee kinsan ni zan aureki ko?"


 Kai ta daga masa alamar "Eh!." 


  "Yauwa na san duk abin da nake so wajanki nasan bazaki hanani ba, Fee inaso yau ki mallakamin kanki." 


   "Affan ban gane me kake nufiba saboda kasan hausar tawa sai a slow ka fito fili kayi min bayani ta yanda zan gane."


 Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya maida hannunsa a kan kafaɗarta ya kanga bakinsa a kunnanta ya raɗa mata.

  "Fee yau so nake ki mallaka min kanki muzama kamar miji da mata kin.....    *NWA*
   Mrs so....    *MAZA DA MULK*

★★.    _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA*  ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

__________________________________


    _story and written by_

       *MRS OMAR*


    _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI*   _Wannan shafin sadaukar wane ga ALHAJI SANIN BABINDO FAMILY Allah ya albarka ce wannan family mai albarka_      _page 39_
  Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya mai da hannunsa a kan kafaɗarta ya kanga bakinsa a kunnanta ya raɗa mata.

   "Please Fee yau so nake ki mallaka min kanki muzama kamar Miji da mata, kinsa ni dai zan aureki wallahi bazan iya jure har sai munyi aure ba."


 Jikiinta na rawa ta tashi tsaye tana ja da baya da baya shima tashi yayi yana binta.

  "Please stop Affan don't touch me."

  Ina ai wanda yayi nisa baya jin kira, binta yake har sai da ta kure wa bango, idanunta ta runtse saboda tasan karyarta ta kare ya kure mata, k'asa-k-asa yake magana kamar wanda yasha wani abu, sai da ya shige jikinta sosai.


  "Haba Baby please don't do this to me kina so yau saboda sha'awarki in mutu? please baby help me is just once ba wanda zai gane." 

  "Affan wannan wane irin iskanci ne na faɗa maka kada ka taɓa ni."

  Hannu yasa zai fincikota batasan lokacin da wani karfi yazo mata ba ta ingijeshi ya faɗi kasa, da sauri ta buɗe k'ofa tabar ɗakin, kafin ya tashi yabita har taja motar, wani irin haushi ne ya kamashi, kanshi ya dafe saboda yanda yake ji yana juyawa, kasa zaune yayi yajuya nan yajuya can, shawara ya yanke kawai bari ya kira Anum yasan ita bazata bashi kunya ba. 


Fee tun da ta isa gida ta faɗa kan gado take kukan abin da yayi mata, sak'on da taji ya shigo a wayarta ne yasata tashi zaune, sunan Affan tagani a sakon ya bayyana da sauri ta buɗe dan gani abin da ya rubutu mata.  _"Am sorry my princess kada kiyi min wani mumunar fahimta kice ni ɗan iskane bazaki aure ni ba, babyna ni ba dan iska bane kawai dai nagwada ki ne, saboda irin maganganun da mutane keyi a kanki ne, shiyasa nace bari na gwadaki naga da gaske ne, sai gashi ba haka bane please princess kiyi hak'uri, kisani ni masoyinki ne na gaskiya, wallahi bazan iya rayuwa ba idan babu ke a kosa dani, ke tawa ce ni ɗaya, nagode daga mai sonki, F.A.."_

  

 Wani irin murmushi ta saki da sauri ta rungumi wayar a jikinta.


  "Ayya babyna nayi maka mummunar fahimta, ashe ba haka bane, to me Affan yake nufi da F.A? au yana nufin f amatsyin FIDDAUSI take A kuma a matsyin Affan, yesss."

  Ihu ta fasa ta cigaba da k'ara duba sakon, bayan ta gama ta lumshe idanunta, murmushi take saboda shi kawai take tunawa a lokacin da yake mata maganar yau,

 "Affan na yarda da kai Kaine *MASOYINA NA HAR ABADA* bazan taɓa rabuwa dakai ba."

  


  _Bangaren Balatoni_


Rayuwa tayi masa zafi duniya ta zamo masa tamkar ruwan zafi, idan ya buɗe idanunsa babu abin da yake gani sai duhu, yau iya ta haɗa kayansu domin su koma Yola. 


  "Gwaggo yanzu kina nufin haka zan tafi ba tare da na aure FIDDAUSI ba, Gwaggo kitausaya min kada na rasa rayuwata.

 "Nidai Modibboh babu abin da zan iyayi dan haka kazo kawai mukoma gida."


  Tashi yayi tsaye kawai lum yayi zai faɗi da sauri Gwaggo ta kamashi ta zaunar, sallamar Bahijja ce yasa su ɗaga kai.

  

 "Gwaggo ina tunanin bai kamata ku tafi dashi cikin wannan halin ba, ya kamata aje asibiti kafin ku wuce.

 "Kada ki damu gara mu tafi gida kawai saboda idan yana nan to hankalinsa bazai taɓa kwanciya ba, idan ko mukaje gida na tabbata wata rana zai manta da FIDDAUSI har abada."


 Hawaye ne ya fara fita a idon Bahijja, cikin muryar kuka ta fara magana.

  "Modibboh kayi hak'uri wallahi dan banida yanda zanyi ne shiyasa har bazaka aureta ba, Gwaggo ina neman gafararki.

  "Nayafi maki balle ma baki taɓa min komi ba."


 Haka abubuwa suka dinga faruwa har kwanakin bikin nata zuwa, Affan kuwa da Anum nata sheke ayarsu, duk Fee da Adda ba su san meke faruwa ba....    *N.W.A*

    _Feen so_


   *MAZA DA MULKI*

★★.    _MATA DA_ ★★

 ★.     *TAK'AMA* ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

________________________________   _story and written by_

       *MRS OMAR*  _in dedication to_

  *FIDDAUSI SODANGI*  _Wannan page din naki ne aminiyar arziki bata...., *KHADIJA CANDY* ina mai tayaki murnar cin nasarar wannan gasa ubangiji Allah ya kara basira,_        _Page 40_
      *SATIN BIKI*

  

 Tun ana saura wata ɗaya bikin

 Fee aka fara mata d'inka, jikin nan nata yayi gwanin ban sha'awa idan ka ganta sai mutum ya ɗauka aljanna ce, tayi wani irin bala'in kyau, duk inda ta zauna k'amshin turarenta ke tashi, idan ta zauna a waje sai wajan yayi awa biyar(5)kamshin turaren jikinta baibar wajan ba.

Duk inda kabi a cikin garin Katsina zakaga symbol ɗin bikinsu an rubuta kamar haka 


_THE LONG AWAITING JOURNEY HAS COME TO AN END_

***********AS***********

  *GIMBIYA FIDDAUSI MUHAMMAD BASHIR SODANGI*

         _AND_

*AFFAN MUSTAPHA KHALIL ( DOGON GAYE)*

Ga wani pic ɗinsu an saka sun d'an rungomi junansu,

sunyi matuk'ar kyau ga wani murmushi mai k'ayatarwa wanda shi ya kara fito masu da kyansu, duk inda kaje zakaji labarin bikin ake, yau ta kama ranar kamu har gida aka kira mai Make-up tazo tayi mata, ya salam,

kunga yanda tayi kyau kuwa duk lokacin da Anum ta kalleta sai taji bak'in ciki a zuciyarta, itako wani irin daɗi takeji saboda yanzu son Dogon gaye ya kara shiga zuciyarta, motocine aka Parker na idon cin duniya duk cikin motocin babu wadda take k'asa da million ashirin(20)duk wanda yaga motocin yasan bikin yar gatan SODANGI ake, da yake ba wasu kawaye gareta ba shiyasa kawayenta su biyar ne suma duk ba yan cikin garin Katsina ba ne, duk wad'anda sukayi makaranta ne a China, kawayen na ta sunyi ankon cotlace mai kyau da tsada, red ne sai black ɗin d'an kwalli suma babu laifi sunyi kyau, gimbiya sanye take cikin wasu kaya na idon cin duniya ni kaina bazan iya faɗin kuɗin kayan ba, ahankali take tafiya k'awayenta na take mata baya, gasu Hindu na watsa mata wani jan fure, amma duk wanda ya kalli fuskar Hindu yasan tana cikin damuwa, wajen wata hadad'ɗiyar mota aka nufa da ita motar tasha ado ana buɗe k'ofar mota Dogon gaye yasa hannu ya kamota, Tana shiga ya wani lumshe ido yaja iskan kamshin turaren da yake jikinta.


  "Tsarki ya tabbata ga wanda yayi wannan kyakkyawar halintar, tunda nake, i never see beautiful woman like you in my life."


 Murmushi tayi saboda jin daɗin maganar da yayi mata, hannunta ya kama ya ɗaura saman cinyarshi yana wasa da yan hannunta.

 "My F.A yau baza kiyi min kalaman ki masu sanyaya min zuciya ba, wallahi a kullun idan ina tare dake inaji kamar bani bane,kece HASKEN IDANIYATA, ni makahune aduk lokacin da bana tare dake idanuwana sukan rufe, bana ganin komai har sai lokacin da na ganki.


  "Are you sure?" 


 "Very sure, na taɓa faɗa miki karya?" 


 "No na yarda da kai dan haka nima ina sonka kamar yanda kake sona."


 Suna gama magana Affan yayi murmushi ya cije Lips ɗinshi, sannan ya kara jawota jikinshi har suka isa hall ɗin da suka kama, duka motocin a tare suka isa filin sun d'an ɗauki wani lokaci a cikin motar sai da duk jama'ar wajen suka shiga hall ɗin kafin aka buɗe masu, cikin kasaita suke tafiya har suka isa mazauninsu, hall ɗin yasha ado irin na gargajiya, kunsan dai yanda ake decoration ɗin kamu, ba'a wani ɓata lokaci ba MC ya fito ya fara magana da halshen turanci.


 "Ladies and gentleman,for the first time I want to evert the bride Best friend babbar kawar Amarya... Anum umar."

 Tafiya take kamar zata kare ga kayan jikinta sun wani kamata, idon Affan na kanta kai bama shiba duk jama'ar wajen idanuwansu na kanta, bayan Anum ta gama jawabi nan fa akaci gaba da abin da ake duk abin nan Bahijja kin zuwa tayi sai dai su Adda uwar Amarya sune a gaba-gaba, sai wajen 11:00pm suka tashi washe gari daren biki akayi shirin zuwa dinner.


 Duk abin nan ban kara jin labarin Balatoni ba. 


  Nice dai.....Fateen so.


  *MAZA DA MULKI*

★★.    _MATA DA_ ★★

 ★.   *TAK'AMA*   ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

____________________________________


    _story and written by_

       *MSR OMAR*   _in dedication to_

  *FIDDAUSI SODANGI*      _page 41_

Kowa yayi shirin zuwa dinner,

 kwalliyar yau itace k'arshe duk wadda ka gani zakaga ya kure adakarshi babu mai shigar banza a ciki. kayan da gimbiya Fiddausi tasaka yau sai mutum ya ɗauka zenari wato gold ne, tundaga ne sa kayan ke haskawa,

hall ɗin da aka kama jiya to yau bashi bane wani daban ne wanda yaci uban wancan, bayan ango da Amarya sun zauna M.C ya fara koro bayani ne, wata mata naga ta nufu wajan da ango da Amarya ke zaune cikin k'asaita ta ɗan doko kanta wajan Fee.


 "Amarya kenan ya kike ina fatan kinsan ko ni wacece ko?"


 Fee ta wani yatsina fuska kafin ta girgiza kai saboda tafi karfin ta bata amsa, murmushi matar tayi kafin takai dubanta ga Affan taci gaba da magana.


 "My son kenan baka taɓa nuna mata pic ɗina ba ko dan kana fushi dani banzo bikinka da wuri bah?" 


 "A'a mom ba haka bane kinsan kaina yayi zafi amma ya za'ayi nayi fishi dake, My F.A she is my mom, bata zama a kasar nan ne shiyasa baki santa ba."


 Fee murmushi kawai tayi bata bashi amsa ba, maman tashi kai kawai ta girgiza ta nufi seat din da take zaune, bayan M.C ya gama duk abin da za'ayi anyi addu'a sannan ya ce yana so ango da Amarya su fito filin yanzu,

 Affan hannunta ya kama suka mike tsaye ya wani fincikota ta faɗa jikinshi babu kunya yasa hannu ya ɗauketa cak kamar baby ya nufa filin da ita duk jama'a wajen ihu suka fasa, da yake wajan ya cika da jama'a da wanda aka gayata da wadda ma ba'a gayata ba duk sunzo, sai da ya ajeta suka fara rawa kafin k'awayen Amarya suka shiga da abokan ango Haydar shi duk inda Anum tayi biye yake da ita, kawayen Amarya kunga yanda suke chashewa UMMI AISHA, MAMAN SHAKUR, LUBIEE harda kwasar shoki ita kam KHALISAT HAYDAR tana mane da mijinta, su RAZ ai ba'a magana kwasar rawarsu kawai suke, kai anyi ɓarin naira duk wanda yazo filin babu mai zuba dubu hamsin sai dai sama da haka, bayan an gama rawa M.C ya ce su fito su yanka cake bayan sun fito sun tsaya wajan cake ɗin sannan M.C yaci gaba da musu bayani.


 "Yauwa ango da Amarya yanzu zaku yanka cake d'in nan amma sai na kirga biyar kafin ku yanka, 1.2.3.4.....5, kai jama'a ku taɓa masu, yanzu zamuga ango da Amarya zasu iya ciyar da kansu, ango zaka ɗauki cake ɗin nan kabawa Amaryarka kema haka."


 Fee ta fara saka mashi a baki kafin ya ɗako zai saka mata, data buɗe baki sai ya kauce hannunsa na karshen ya saka mata amma ya ɗan ɓata mata lips ɗinta, baki yasa ya lashe wadda ya bata mata lips, kai ranar jama'a sunga abu, yau ba'a tashi ba sai wajan 1:30am kafin aka tashi.**********


 *RANAR ƊAURIN AURE*


Yau ta kama ranar ɗaurin aure gidan ya cika da jama'a ko ta ina, hankalin Anum bai kara tashi ba sai da taga yau ɗaurin aure gashi lokaci ya kusa da yake ɗaurin auren 12:00pm ne, Iya ce ta kira Bahijja a gife da yake ta fahimce tana cikin damuwa.


 "Bahijja meke damunki na lura kina cikin damuwa ki faɗa min matsalarki."


 Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta dubi Iya cikin sanyen jiki ta fara magana.


  "Iya damuwata ɗaya ce naso ace duk wannan abin mahaifiyata nanan za'ayishi sai dai kash haka bai samu ba, wallahi da akwai yanda zanyi da nayi dan Modibbo ya auri yariyar nan amma babu yanda na iya." 


 "Bahijja ya ya zamuyi da lamarin ubangiji haka Allah ya nufa, dan haka kiyi hakuri kicigaba da abin da kike sannan shikuma mutayashi addu'a Allah yabashi mata ta gari, kinji ko?" 


 "Naji Iya insha Allahu zanyi abin da kika ce."


 Bayan sun koma cikin gida kowa yaci gaba da hidimarsa, ita kuma Fee na ɗakinta da kawayen ta, duk surutun Anum yau bakinta ya mutu anrasa abin da ke damunta. 

Suna cikin surutu wata tsohowa ta shigo tayi guɗa.


 "Yau dai an ɗaura auren GIMBIYA FIDDAUSI DA AFFAN lakadan ba ajalan ba, kai masha Allah, in Allah yayarda sai munzo suna, ga jama'a nan yan ɗaurin aure duk sun dawo, gida ya cika da jama'a."


 Murmushi Fee tayi kafin ta ciro kuɗi masu yawa tabawa matar, 


Kai yau ma ansha bidi'a sosai har dare yayi ana shirin ɗaukar Amarya kafin aka fara watsewa... Kuyi hak'uri da wannan typing.


Nice dai Mrs umar....


   *MAZA DA MULKI*

★★.  _MATA DA_  ★★

 ★.   *TAK'AMA*   ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

__________________________________


   _story and written by_

       *MRS OMAR*    _in dedication to_

  *FIDDAUSI SODANGI* _Wow am very happy today my best friend JIDDAH ALIYU ta haihu lafiya      _page 42_

  Dare yayi ana shirin ɗaukar Amarya amma anguna basuzo ba, har 9:00pm yayi amma shiru kakeji jakadiyar Mai Martaba ce ta shigo ɗakin gimbiya da sauri ta duk'a a gabanta.


 "Allah ya taimaki gimbiya Mai Martaba nason ganinki yanzu."


Yatsina fuska tayi kafin ta ce 

 "Hindu ki tambayeta kiran me yake min."


 "Allah ya baki nasara duk Amarya idan zatayi aure iyaye sukan mata nasiha." Cewar Hindu. Kai ta girgiza kafin ta yiwa jakadiya alama da hannu zata iya tafiya, k'in tashi tayi sai da k'awayenta suka matsa mata kafin ta tafi, tana tafiya Hindu da mairo na take mata baya dai-dai zata shiga parlour su kuma suka dawo, tana buɗe k'ofar parlour tayi tsaye saboda abin ya bata mamaki yanda taga parlour cike da mutanen gidan, duk sun k'uro mata ido.


 "Ke k'araso ba na kiraki bane dan kiwa mutane tsaye a kai." Mai Martaba ne yayi maganar fuskar nan tasa a ɗaure kamar bai taɓa yin fara'a ba, cikin sanyin jiki ta k'arasa ta zauna saboda taga yanda mahaifin nata ke magana, bayan ta zauna ya kai dubansa ga Bahijja ya ce


 "Bahijja!" 


  "Na'am" Ta amsa masa atak'aice. 


"Ina wannan yaron Modibbo? sannan ina Gwaggo ban ganta a nan ba." 


  "Dama...." 


Wata irin tsawa ya daka mata wadda yasa y'an parlourn tsorata.


 "Dama me? tambayarki nake kina cemin dama." 


 "Allah ya huci zuciyar Mai Martaba, dama Modibbo bashi da lafiya yau sati uku kenan an kwantar dashi a *RAZ SPECIALIST HOSPITAL.*" 


 "What? So bashi da lafiya and you didn't tell me, maza kisa driver ya ɗaukosu yanzu shida Gwaggo inason magana dasu." 


 "Amma mai Martaba bashida lafiya." 


 "Nasani ko mutuwa yake yana dawo akawoshi yanzu nan."


Bahijja ba musu ta tashi cikin sanyin jiki, duk mutanen parlourn abin ya basu mamaki sosai, k'irjin Adda sai dukan uku-uku yake. 

Iya ce tayi karfin hali cikin ɗaurewar fuska ta ce 

 "Wai kai Basher meke faruwa duk ka taramu anan?." 


 "Allah ya baki hak'uri Iya magana ce mai mahimmanci amma bari su iso."


Shiru tayi bata k'ara magana ba bayan Bahijja ta tura a ɗaukosu ita kuma ta dawo ɗakin, driver bai wani ɓata lokaci ba ya isa asibitin ya ɗakosu da yake tsakanin asibitin da masarautar babu nisa titi ne kawai ya rabasu, driver shi ya kama hannun Balatoni yasa a kafaɗarshi suna tafiya a hankali har suka iso parlour ita dai Gwaggo biye kawai take dasu, bayan driver ya zaunar dashi a jikin kujera shi kuma ya fita abin sa, parlourn yayi shiru maganar Mai Martaba kawai ake jira, gyaran murya yayi kafin ya fara magana.


 "Sannu da zuwa Gwaggo ya mai jikin?" 


 "Mai jiki da sauki." 


 "Allah yabashi lafiya." 


 "Amin" 


 "Nasan dukanku baku san dalilin da yasa nataraku ba, to da farko dai inaso dukanku ku bani hankalinku a nan musamman ke." Ya nuna gimbiya da hannunsa.


 "Allah shine mai yanda yaso dama hausawa sunce *MATAR MUTUM* K'ABARINSA, shiyasa nayi abin da ya dace da ɗiyata, niba mutuman banza bane bale in bada y'ata ga mutanan banza, yau na bada y'ata ga wanda ya dace, FIDDAUSI ashe mutanan da kika kawo min ba mutanan kirki bane?"


 Cikin sauri takai dubanta ga mahaifin nata saboda duk maganar da yake bata fahimci me yake nufi ba.


 "Ko k'arya nayi maki? kika dube ni da sauri, wai kamar ni Mustapha zaizo min da wata magana wai yana nai man alfarma d'aurin auran nan kada a daura da ɗansa a ɗaura dashi, wannan wane irin wawanci ne? ai ko a shirin film ba'a taɓa irin wannan ba, toh shiyasa gaba ɗaya nace duka auran an fasa dan kada a fasa kwata kwata nace a ɗaura da Modibbo!!...


 "What Dad Modibbo? no that is dream is impossible."


 Hannunta tasa tana goge idanunta Mai Martaba ya daka mata tsawa.


  "Ke bansan shirmin banza ki bude idanunki gaskiya nake faɗi yau kin zama matar Modibbo."


 Balatoni baisan lokacin da ya tashi zaune ba dan murna sai yaji duk ciwon jikinshi ya warke, hawaye ne ya fara fita a idonta ta bude baki ta fara magana.

  

 "Dad na shiga uku yanzu ka rasa da wanda zaka had'ani sai da wannan village m..." 


 Lumm tayi kawai ta faɗi a sume, Balatoni zai nufi kanta da sauri Mai Martaba ya dakatar dashi.


 "Dakata Modibbo ka barta dan ubanta."


 Gorar ruwan dake gabansa Mai Martaba ya ɗauka ya kwara mata a jiki, da sauri ta ta shi. 


 "FIDDAUSI ki sani idan mutuwa zakiyi sai dai ki mutu amma babu uban da ya isa ya warware wannan auran naki....

Nice dai............


  *MAZA DA MULKI*

★★    _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA*  ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

__________________________________    _story and written by_

       *MRS OMAR*      _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI*  _this page is for you my Ashnur Allah ya k'ara tsare min ke ._      _page 43_


       ********"FIDDAUSI ki sa ni idan mutuwa za ki yi sai dai ki mutu amma babu uban da ya isa ya warware wannan auren na ki, ni za ki ɗauka mutumin banza to baki isa ba ki sa ni nike MULKIN garin nan bake ba duk ina da labarin iskancin da kuke yi ke da k'awarki, dan haka yau ba sai gobe ba za'a kaiki gidanki na riga nagama duk tsara inda za'a ajeki, shiyasa na hana kowa ya faɗa muku ba da wannan dan iskan yaron aka ɗaura ba, sannan idan za'a kaita bana son taron mata, daga Iya sai Gwaggo zasu kaita."


"Amma Mai Martaba ka naga abin da kayi ka yiwa y'ar ka adalci? yanzu fa an daina auren dole wanda ka haɗata dashi kwata-kwata bai da...."


  "Dakata bana son shirmen banza."


 "Amma Mai..." 


 "I said keep quite i don't want to hear anything form you, FIDDAUSI is my daughter dan haka kada na k'ara jin bakinki a maganar y'ata."


 Kuka Adda ta fashe dashi wai Mai Martaba yayi mata gorin haihuwa, abin ma dariya ya bawa su Iya sai da taci kukanta babu wanda ya ce mata tayi hak'uri kafin ta ta shi da gudu tabar parlourn. FIDDAUSI tana kuka ta k'arasa wajen mahaifinta ta kama k' afarsa cikin kuka take magana.


 "Please Dad i beg you don't do this to me. Wallahi Dad idan har na zauna da wannan d'an kauyen mutuwa zanyi, please Dad kada kayi min haka ni ce fa y'ar ka FIDDAUSI.."

 

Saboda kada ta k'arya ma shi zuciya yasa hannu ya tureta ta faɗi k'asa taci gaba da kuka, sannan Mai Martaba yaci gaba da magana cikin zafin rai.


 "Kisani wannan aure an riga anyishi babu mai warwareshi, kuma dole ki zauna da shi this is my order idan har kikace bazaki zauna dashi ba to wallahi daga yau jama'ar ɗakin nan zasu shaida babu ni babu ke sannan kada ki k'ara amsa sunanki da sunana, wannan itace magana ta ta karshe."


Iya ce ta ɗagata tana goge mata hawaye hannunta ta kama suka nufi ɗakinta, suna zuwa suka samu kawayen nata na hira da sauri suka haɗa baki suna tambayarta lafiya amma bata basu amsa ba, mayafinta Iya ta yafa mata kafin suka fita,k'awayen na ta sun taso Iya ta dakatar dasu


 "Kuyi zaman ku dan mahaifinta ya ce baya son yaga kowa ya kaita, yanda take cikin wannan halin zaku iya zugata tunda ba'a aura mata wanda take so ba.."


 "Iya kina nufin bada Affan aka ɗaura ba?"


 Anum ce tayi tambayar wanda tun safe ta kasa magana sai yanzu an rasa meke damunta, gaba d'aya k'awayen na su suka kai duba wajanta, dan kada sugane abin da take nufi tayi saurin gyara maganarta 


 "Allah dai yasa ba'a fasa ba yanda suke son junansu ace an fasa."


 Su dai k'awayen shiru suka yi babu wadda ta bata amsa. 

Iya na rik'e da hannunta har suka isa wajen motar da za'a kaita dama Mai Martaba yace harda Modibbo zasu wuce sannan kuma mota ɗaya zasu ɗauka, koda suka isa wajan motar Gwaggo da Balatoni sun riga sun shiga, gaban motar yake zaune sai Gwaggo na baya, suna tafiya Bahijja ta shiga toilet ta ɗauro alwala tana mai yiwa Allah godiya,


 Ɗaya daga cikin gidajen Mai Martaba ne ya basu guda a cikin wata unguwa da ake kira modoje, gidane na idon cin duniya, bayan driver yayi parking sun fito suka shiga cikin babban parlourn gidan masha Allah koshi abin kallo ne, a parlour suka zauna kafin Iya ta fara bata baki.


 "To FIDDAUSI babu yanda mutun ya iya da hukuncin ubangiji Allah ya ce dama Modibbo shi ne majinki dan haka kiyi hak'uri ki ɗauki kaddara.."


 "What? kaddara Iya this is not kaddara da gangan akayi wannan abin kuma wallahi wannan village man d'in ba zai ta6a zama mijina ba."


 "Kiyi hak'uri FIDDAUSI haka Allah yaso." 


 "Dakata Gwaggo ai abin da kukayi niya ne kuka aikata, hmm! amma sai dai ina mai sanar maku sai kuyi dana sanin haɗa wannan auran."


 Gwaggo da Iya zasu kara magana Balatoni ya hanasu, tashi suka yi suka koma gida, suna fita kamar jira FIDDAUSI keyi su fita ta fara ruwan bala'i. Duk naji sakonku kudai kara hak'uri komi yazo karshe.Mrs umar


   *MAZA DA MULKI*

★★    _MATA DA_ ★★

 ★.   *TAK'AMA*  ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

___________________________________


  

    _story and written by_

      *MRS OMAR*     _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI*       _page 44_

  Wata irin shak'a takai ma shi tana faɗin 

 "Wallahi sai ka sake ni bazan zauna dakai ba na tsaneka tsanar da ban taɓa yiwa wani ba wallahi sai ka sakeni."


 Idanunsa ya runtse saboda yanda takai ma shi shak'ar gaba ɗayan jikinta na jikinshi na shanunta suna gogarshi bakinsa ya cije saboda cikin lokaci ɗaya tanaso ta tada ma shi hankali, idonsa ya buɗe ya sauke su akan kyakkyawar fuskarta, yana kallon yanda take magana idon nan nasa sun chanza kala sunyi jajir, murmushi tayi ta kara shak'arshi.


 "Yaro wallahi idan har baka sakeni ba to kadan kafara gani yanda idonka sukayi ja ɗin nan to akwai ranar da zaka fara kuka da idonka."


 Murmushi mugunta yayi kafin ya kanga bakinshi a kunnanta ya raɗa mata.


 "Bazaki gane ba wallahi ko haka muka tsaya ya isheni saboda bakiji wani daɗi da nakeji ba, duk sha'awarki ta mamaye zuciyata."


 Ido ta zaro tana shirin sakinshi ya damke mata hannuwa, gaba ɗaya ya juyata a kan kujera yana kokarin haɗa bakin shi da nata jiyake wani irin karfi yazo mashi duk ciwon da yakeji a jikinshi babu, bakinta da idanuwanta ta matse gam, hannunsa ɗaya yake kokarin turawa cikin nashanunta shiyasa ta fasa ihu.


 "Wayyo jama'a na shiga uku kwarto zai min fayde please help me wayyo Allah, wallahi baka isa ka haɗa jikinka da nawa ba, dan wannan jikin nawa mutum ɗaya zan iya bawashi, wayyo Allah kwarto jama'a."


 Balatoni yanda take magana sai abin ya bashi dariya, kin fitar da dariyar yayi waje sai ya kara haɗe fuska.


 "Ke ba kince bakida kunya ba ashe ke marar kunyar karya ce, toh yau sai na nuna miki ɗan kauye nada mahinman ci a gareki."


 "Please Yaya Balatoni karufa min asiri kada kayi min fayde."


 Balatoni jikinshi yayi sanyi yanda ta karaya da sauri haka, duk da haka bai barta ba, kokarin haɗa bakinsa yake da nata amma taki bari saboda yanda take juye juye da kanta, bata san lokacin da karfi yazo mata ba ta kai mashi duka a kirji da sauri ya sake ta, dagudu ta haura sama. 


 "Idan ka isa ka biyoni nan kaga yanda zan maka."


Murmushi yayi ya lumshe idonsa saboda yanda takai mashi dukan yaji zafi sosai, tashi yayi yana karewa parlour kallo, sama shima ya haura ya tura wani ɗaki yana turawa ya buɗe shiga yayi ya fara isa parlour kafin yaga wata kofa ya shiga bedroom ne shi ya nuna masa ɗakinsa ne kenan tunda bai ganta a ciki ba. 


Ita kuwa gimbiya zuciyarta wani irin k'una take mata, phone ɗinta ta ɗauko ta danna number Dogon Gaye amma is not available, hawaye ne yaci gaba da fita a idonta, na takaicin rabata da masoyinta, har barci yayi gaba da ita,

 

*****


Washe gari


Balatoni tunda yayi sallah asuba ya dawo babban parlour ya zauna yana jira ta fito amma shiru, har 11:30 tayi babu ita babu dalilinta, kitchen ya dinga nema har yagano shi, amma yana shiga yayi tsaye saboda bai iya kuna gas ba, parlour ya dawo ya zauna yana tunanin mafita, har 1:00 tayi can sai gata ta sauko itama da alamar yunwan ya sauko da ita, ɗaya daga cikin kujerun ta zauna, shikuma yana kare mata kallo, bama tasan yanayi ba wayarta kawai take dannawa tana kaɗa kafa, zamanta babu daɗewa akayi nocking da sauri ta nufi kofar, order abincin da tayi ne aka kawo mata, ya meka mata take away a cikin wani abu, bayan ta amsa ta dawo parlour ta zauna ta buɗe take away ɗin, wani irin kamshe ne ya mamaye parlour, da gangan ta fara ci dan tasan bai karya ba, yawu Balatoni ya fara haɗewa saboda yanda yaga abincin......

    Muje zuwa 


Nice dai mrs umar


   *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

 ★.   *TAK'AMA*  ★


_NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

_________________________________


   _story and written by_

      *MRS OMAR*   _in dedication to_

  *FIDDAUSI SODANGI* _this page is for you Mariya Aliyu na gode da son da kike nuna ma wannan novel nawa_        _page 45_   *D*agangan take ma shi wannan iskanci saboda tasan bai karya ba, gashi Balatoni bashida hak'urin yunwa k'arfin hali yayi ya murtik'e fuska ya ce

 

 "Ke ina nawa abinci ko haka aka koya maki?, Ba kisan sai mata ta fara bawa mijinta ba kafin taci nata."


Shiru tayi, taci gaba da danna phone ɗinta kamar bazata kulasa ba, kafin daga bisani ta ɗauki fork ta d'ebo abincin ta kura mashi ido ta tabe baki ta ce


 "A k'auyenku ka iya cin irin wannan abincin ne?"


 Har ya bud'a baki zai bata amsa sai kuma yayi shiru yana kallonta, wayarta taci gaba da latsawa duk hankalinta ya tafi kan wayar, ahankali yazo ya ɗauke robar take away ɗin ya fara ci duk bata san abin da yake ba, kamar ance ta juya, taga ba roba da sauri ta juya ta kalleshi taga yana shirin sa abincin a bakinshi, cikin zafin zuciya ta nufi wajansa, yanaganin ta nufushi ya ga da gaske take kawai sai ya tofa yayu aciki yasa cokakin ya motse abincin, idonta ta zaro waje saboda tunda take bata taɓa ganin irin wannan k'azantar ba, ta ke cikinta ya juya sai amai ta dinga k'warawa, juyawa yayi ya kalleta tana aman ko a jikinsa yaci gaba da cin abin shi, duk abincin da tafara ci sai da ta amayar duka a parlourn, idonta sunyi jajir ta ɗaga kai tana kallon yanda yake cin abincin hankalinsa kwance, fuska ta ɓata saboda idan taci gaba da kallonsa ta tabbata sai an kaita asibiti, suna haɗa ido ya kashe mata ido ɗaya ya ce


 "Baby ya ko zakici? naga wanda kikaci duk kin amayar da shi."


 Wani irin bak'in ciki ne ya k'ara tunkarar zuciyarta ji take kamar ta kasheshi ta huta, tashi yayi ya nufi wajan Water distensal yayi mika.


 "Kai shege balatoni kaifa kazamo k'adangaran bakin tulo akasheka akashe tulo abarka ka ɓata ruwa."


Dariya yayi kafin ya ɗauki cup yaga wani malatsi ya danna gani yayi kamar suraci na fita daga cup ɗin shiyasa ya tara hannunsa yaji ko sanyi ruwan yayi da yawa, ai kam yanasa hannunsa bai san lokacin da ya sake cup ɗin ba ya fasa ihu.


 "Wayyo Allah hannuna ya toye."


Fee bata san lokacin da ta kwashe da dariya ba, dama ita idan kaga tayi dariya mai karfi to ta mugunta ce.


 "Hahaha that is good tsiyar d'an kauye kenan duk yanda akayi dashi sai yaci kara, idan ba abinka ba inakai Ina ni ai wannan babban kuskure ne ka tafka a rayuwarka, wallahi nayi alk'awarin sai najaza maka abin da zaya zaman maka nadamar aurena.


 "Hmmm! yaro yaro ne ai kisani babu ranar da zanyi nadamar auranki sai dai ke kiyi nadama amma badai niba." 


 "Wallahi k'arya kake d'an talakawa nafi k'arfinka." 


 "Ke kuma yar matsiyata ko?"


 Fee bataji zafin abin da ta faɗa mashi ba sai wanda ya faɗa mata, jiyayi kawai ta kaimashi shaka saboda maganar ta ɓata mata rai kamarta zai kira yar matsiyata,


 "How dear you to call me y'ar matsiyata har ka isa ka kirani da y'ar matsiyata look at me and look at you nida kai waye yayi kama da ɗan matsiyata....


 Maganarta ta tsaya ne saboda jin bakinsa a cikin nata, kokuwa suka fara nan fa ya jefata cikin aman da tayi yabi kanta duk abinta ta kasa amshe bakinta daga nashi, cigaba yayi da tsotsar bakinta kamar sweet har yana wani lumshe ido, duk jikinta ya ɗauki rawa saboda ta rasa yanda zatayi dashi sai hawaye ne kawai da ke bin fuskarta,

k'ofar da aka turo ne yasa shi saurin ɗaga kanshi dan ganin suwaye da sauri ya tashi daga kanta..
 Ina mai ba masu son littafin nan daga farko hak'uri, duk wanda yaga ban turo masa ba, bani dashi ne daga farko yanzu, amma duk maiso zai iya zuwa shafin group din Khaleesat Haydar novel zai samu a can, nagode da soyayyarku... 
Nice dai.......


    *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA*  ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

___________________________________


   _story and written by_

      *MRS OMAR*   _in dedication to_

  *FIDDAUSI SODANGI*   

       _page 46_
     *D*a sauri ya ɗago kanshi dan ganin suwaye, Hindu ce da wasu yan mata su biyu sai namiji ɗaya, da sauri Balatoni ya tashi yana sosa k'eya saboda yaji kunya yanda suka samesu, Hindu tayi mamakin ganin parlour haka cikin ladabi suka zube kasa, 


 "Barka da kwana gimbiya."


 Shiru tayi bata amsamasu ba, cikin sanyin murya Hindu taci gaba da magana,

 "Allah ya taimakeki dama Mai Martabane ya turo mu yace muzauna dake ga kuma kuku wannan kuma yan aiki ne.

 "Au har yana tunanin zan zauna shiyasa ya turo ku, mtsss"


 Tana jan tsaki ta juya ta haura sama kai Hindu ta girgiza kafin ta nuna masu duk yanda zasuyi babu ɓata lokaci suka fara gyara parlourn, bayan sun gama duk abinda zasuyi ta nufi sama dan tambayar abinda take so kukun ya dafa mata, ahankali Hindu ta tura k'ofar ɗakin tana shiga parlour ita kuma tafito daga bedroom taci wata irin shegiyar kwalliya kamar wanda zata gasar kyau.

  "Rankishi daɗe dama nazo na tambayeki ko kina da bukatar kuku ya dafa miki wani abu ne?

 "Banda bukata.

 "Rankishi dade naga kamar fita zakiyi?"


 Gimbiya bata ba ta amsa ba saidai phone ɗinta da ta kanga akune.


 "Hello Anum how far."

Daga can ɓangarin Anum ta amsa da.

 "Am fine?

 "Why are you not picking my calls.

 "I don't see your calls.

 "OK kina gida ne? Anum tun jiya nake kiran Affan amma wayarshi a rufe, Anum wallahi idan har banga Affan yau ɗin nan ba zan iya rasa rayuwata saboda bakiji yanda zuciyata ke bugawa ba."


Wani irin kishine ya tun kari zuciyar Anum.


 "Zaki iya zuwa gidan sa ai kinsan hanyar gidan shi."

 Anum bata tsaya jin amsar Fee ba ta kashe wayar, gimbiya ta danyi mamakin haka sai kuma tayi tunanin ko network ne yasa ta kashe wayar, cikin sanyin murya Hindu kamar zatayi kuka ta fara mata magana.

 

 "Gimbiya amma ni a tunani na bai kamata kije gidan Affan, ki sameshi saboda ke yanzu matar aure ce wani abu zai iya faruwa kinsan sharin shiɗan yan......"

 Bata karasa ba taji saukar mari a fuskarta.

 "Are you mad ke har kin isa ki gaya min yanda zanyi da rayuwata who are you?"


Hindu fuskarta ta rike hawaye na bin fuskarta ko ta ina, tsaki gimbiya tayi ta kara gaba abinta, tana zuwa ta samu mota biyu su Hindu sukazo da ita key ta amsa hannun driver ban, 

karar tada motar da Balatoni yaji ne yasashi saurin lekowa yana dubawa yaga itace zata fita da mota, da sauri ya sauko kasa kafin ya iso har ta fita

parlour ya dawo ya zauna yana tunani ina ta tafi? to ko guduwa tayi?, itako driving take ahankali har ta isa gidan Dogon Gaye, bayan tayi parking ta fito nocking tayi zuciyarta sai bugawa take,

 takai wasu yan lokutta kafin ya buɗe, yana ganin itace ya murtuke fuska.


 "Meya kawoki gidana?

 "Please baby listen to me, Wallahi i don't ........

 "FIDDAUSI please just get out of my house."

 Yana rufe baki ya juya ya barta tsaye amma bai rufe k'ofar ba, da gudu taje ta rungumeshi ta baya, wani irin shock yaji ya kamashi, cikin muryar kuka ta fara magana.

  

 "Please baby am sorry Wallahi ba laifina bane bansan komi a kai ba, Baby Wallahi ba zan iya zama da kowane namiji ba idan ba kai ba, idan na rasaka mutuwa zanyi i promise you wannan ɗan kauyen ba zai taɓa samun zuciyata ba."


 Kuka ta fashe dashi, ahankali ya juyo da ita gabanshi yana kalllonta ido cikin ido, sai yaga ta kara masa wani irin kyau goshinshi ya haɗa da nata sannan ya fara magana .

 "Kina nufin yanzu baki san abinda mahaifinki ya shirya yimin ba?"

 Kai ta ɗaga alamar eh, kai ya girgiza kafin ya zaunar da ita kan kujera shikuma ya nufi bedroom ɗinshi, bai wani ɓata lokaci ba ya fito cikin shirin shi, hannunta ya kama suka fita, 


 Ranar haka suka wuni yawo cikin gari yana jan ta da soyayya iri iri, bata dawo gida ba sai 12:00pm dai dai na dare, tana zuwa taga parlour an kashe wuta hankalinta kwance ta kunna wutar phone ɗinta, tana kunnawa shiyayi daidai da kunna wutar parlour, cak ta tsaya.....


👸🏼 *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA*  ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

____________________________________  _story and written by_

      *MRS OMAR*
   _in dedication to_

  *FIDDAUSI SODANGI*

 _this page is for you Feedo Yar Ficika happy birthday to you, Allah ya albarkaci rayuwarki ya nuna min auranki musha shokie_
       _page 47_         *C*ak ta tsaya saboda ganin Mai Martaba tsaye a gabanta, kafin kace menene, kawai sai taji saukar mari ya wanka mata, tangal-tangal tayi kamar zata faɗi ya fizgota ya kara mata wani mari, ihu ta fasa saboda tunda take ba'a taɓa mata irin wannan marin ba, Mai Martaba jikinshi na rawa muryarshi kamar zaiyi kuka ya fara magana,


 "FIDDAUSI kin cuceni,kin nunawa duniya cewa ke ba jinina bace, idan har ke jinina ce bazaki aikata abinda kikayi a yau ba, FIDDAUSI wannan abun da kika aikata, I will never forgive you".

 "Haba Dad because of dis village man you slap me, da..."

 "Keep quite stupid girl kawai!, kina kuma kara magana ina karyaki a wajan nan, wacce bata san ciwon kanta ba, Modibbo dama na faɗa maka ba guduwa tayi ba, nasan komin dare zata dawo gashi ta dawo yanzu, Modibbo dan Allah ina rokonka da karufa min asiri ka zauna da FIDDAUSI kayi hakuri da duk abinda zatayi maka, idan yaso ka kirani ka faɗa min duk abinda tayima, kuma daga yau kada ka sake barinta ta fita inba tare zaku fita ba."

 "Naji Mai Martaba insha Allahu zanyi yanda ka umarce ni da nayi."

 "Yauwa Modibbo Allah yayi maka albarka, tashi marar mutumci kije kibashi hakuri tun kafin nayi kasa-kasa dake a wajan nan."


Da taga babu sarki sai Allah,

da gaske Mai Martaba shirin sake dukanta yakeyi, yasa ta tashi jikinta na rawa, gaban Balatoni ta duka.

 "To kayi hakuri."

 "Haka ake ba miji hakuri dan ubanki."

 Hannu ya ɗaga zai kara kai mata mari da sauri Balatoni ya zube kasa yana ba Mai Martaba hakuri saboda ta bashi tausayi.

Mai martaba ya zauna sannan yaci gaba da yi mata nasiha mai shiga jiki, bayan ya gama yayi masu ban kwana ya tafi abinsa.

 Fitarsa keda wuya Balatoni ya kwashe da dariya harda rike ciki.


 "Kai duniya ashe duk iskan cina akwai wanda nake tsoro, ashe dai gaba da gabanta Aljanni ya taka wuta, mutum ya fita in kara kiran Mai Martaba yazo ya murje abinsa...."

 "Idan ka isa yanzu ka kirashi ko kana tunani wannan nasihar da yayi min tashiga zuciyata ne? to Wallahi bata shiga ba,

 da wannan maganar tasa da busa duk ɗaya na ɗauke su, barima kaga na kira wanda naje wajanshi ɗin idan yaso kayi abinda ka isa kayi."

 Phone ɗinta ta danna number Dogon Gaye, bugu ɗaya ya ɗaga kafin tayi magana shi ya fara yi.


 "Hello babyna ya har kin isa gida ne? wallahi tunda muka rabu nake tunani ki inaso akoda yaushe ina jin kamshin turarenki a kusa dani babu abinda nike buri inbanda na ji dimin jikinki a jikina b....."

 Bai karasa ba Balatoni yayi kukan kura ya fizgi wayar ya bugata da kasa, jikinshi na rawa ya fincikota ya shaki wuyarta ya haɗata da kujera.


 "Ke har kin isa ki kira wani kato a gabana to bari in faɗa miki ni ba irin wawayen mazan nan bane, au dimin jikinki yace yakeso yaji ko? to kafin yaji dimin jikinki ni zan rigashi ji yau zan kawo karshen wannan wasan naki, da auran nawa a kanki zakije kina kula wani namiji to wallahi baki isa ba."

 Kokowa suka fara yanaso ya zage mata zip ɗin riga da tsiya, ihu ta fara da kuka mai karfi ko Allah zaisa su Hindu su fito, 

batayi zato ba kawai taji bakinsa a nata, harshe yasa yana wasa da bakin nata, harshen ta kama ta sakar mashi wani mayan cizo baisan lokacin da ya saketa ba, da gudu ta haura sama, bakinshi ya rike yana gunji saboda zafi , duk a tanuninshi ma harshen nasa ya fita ne, ga azaba, 


 Tana shiga ɗaki ta faɗa kan gado tana kuka mai cin rai, itako sai yanzu take da nasanin dawowarta Nigeria dama da aka basu hutu tayi zamanta a China bata dawo ba.


  *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA*  ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

___________________________________


   _story and written by_

      *MRS OMAR*  _in dedication to_

  *FIDDAUSI SODANGI*


      _page 48_

    Washe gari 
  *T*unda safe gimbiya ta tashi, abin har ya ba Hindu mamaki domin bata saba ganin hakan ba, parlour ta koma ta zauna ta ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya, tace Hindu ta haɗa mata omo da ruwa cikin bokiti takawo mata, babu musu Hindu tayi abinda ta umurceta.

Tashi tayi tana zuba ruwan omon akan matakalar bene, duk abinda take Hindu na kallonta, bayan ta dawo ta zauna can sai ga Balatoni yana shirin saukowa, tashi tsaye tayi tana juyawa duk dan ta ɗauke mashi hankali saboda kayan dake jikinta na barci ne, ai kam daga nesa ya hangota gaba ɗaya hankalinshi ya tafi wajanta, kafarsa ɗaya da zai fara sakawa kawai yaji santsi ya kwasheshi, tun daga kan benan yake murgina har zuwa k'asa, kanshi ya bigi dinning Table. Hindu ta ɗaura hannuwanta a saman kanta, da gudu tayi kanshi, tsawar da gimbiya ta daka mata ne yasa ta tsaya cak!.

 

 "Stop don't even touch my husband, kina hauka mijin nawa zaki taɓa dan baki da hankali."

 Hindu sakin baki tayi tana kallonta saboda abin ya bata mamaki.

 Dai-dai kanshi taje ta ɗago dashi, ya mik'e zaune, rik'e kan nashi yayi saboda azabar da yakejin kan namasa, cikin isa ta fara magana.


 "Balatoni! Kenan, 

ya kaji wannan sakon safen nawa? tun kafin ka karya kayi breakfast da abinda na fara tanadar maka, humm kada ka damu wannan shine kaɗan daga cikin abinda na tanadar maka har sai lokacin da ka sake ni kafin na barka ka huta."

 Murmushi yayi wanda yafi kuka ciwo. 

Ya buɗe baki zai mata magana amma ya kasa, juyawa tayi ta haura sama abinta, 

ita kuwa Hindu na tsaye hawaye nata bin fuskarta, tashi tsaye yayi niyar yi amma ya kasa, da sauri Hindu ta kira kukunsu dan ya taimaka masa, ɗakinshi,yasa aka kaishi nan Hindu ta bashi magani yasha, saboda kan nashi baiji ciwo ba, cikin muryar kuka take magana.


 "Amma ranka shi daɗe ni a tunanina da kayi hakuri da soyayyar gimbiya dan samawa kanka saukin bala'inta."

 Baki ya cije haɗe da rufe ido kafin ya amsa mata, murya kasa kasa yake magana. 

 "Hindu kada ki damu zanyi hakuri da duk abinda zata zo min dashi, ni nasan akwai lokacin da zata gane ni masoyinta ne na har abada."

 "Anya kuwa wannan ranar zata zo rankashi daɗe?"

 "Zatazo Hindu insha Allahu kadafa kimanta mu musulmai ne, sannan daga yau kada ki kara kirana da ranka shi daɗe, ki kirani da sunan da kike kirana da."

 "Insha Allahu daga yau na daina."

 Murmushi yayi sannan ta tashi ta fita taja mashi k'ofar,

 Gimbiya tunda ta koma ɗaki take cizon ɗan yatsa tana mamakin kiran Balatoni da tayi a matsayin mijinta,

 bayan angama breakfast Hindu ta kawo mashi har ɗaki yana ci suna hira, a lokacin zafin kan nashi ya fara tafiya, haka suka wuni tana kula dashi amma duk gimbiya bata sani ba.
*********


 *ƁB'angaran Affan da Anum*


 Kwance take saman cinyarshi cikin parlour suke zaune, sunata wasannin banza, daka ganta kasan ta juma a gidan nasa saboda towel ne kawai a jikinta, magana ya fara mata cikin zolaya...


 "So baby you're now happy ?"


 "Happy because of what?"

 "Saboda an fasa aurena da Fee mana, naga abinda baki taɓa min ba, amma yau kinyi minshi."

 Dariya tayi takai mashi duka a kirji.

 "To ya kakeso nayi ko kana sonta ne dama?"

 Ido ya zaro waje sannan ya girgiza mata kanshi alamar A'a.

 "Kasan wani abu ai Wallahi ji nake da ka auri Fee, to Wallahi da mutuwa zanyi saboda bazan iya ganinku a tare ba."


 "Ko?"


 "Eh mana, saboda kai duk macen da ta sameka idan ta rabu dakai gaskiya tayi asarar gwarzon namiji."

 Dariya yayi harda muntsilinta, wayarta ce tayi kara tsoki taja dan ganin number Adda ce ke yawo a wayar.


 "Hello Anum ina kikaje? kin manta da maganar da mukayi zamuje wajan bokan nan yau, kinsan ya kamata mu koma a faɗa mashi duk abinda ya faru

 "To Adda...... Muje dai zuwa Nice dai.....


   *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

 ★.   *TAK'AMA*  ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

_____________________________________


   


  _story and written by_

     *MRS OMAR*    _in dedication to_

  *FIDDAUSI SODANGI*
      _page 49_

   *W*ayar ta kashe sannan ta dubi dogon gaye ta ce

 "Baby Adda ce ta kira ni wai tanaso mu koma wajan bokan nan, Wallahi baby nifa na fara gajiya da aikin nan na Adda."

 "Saboda me kikace haka?

 kada fa ki manta bai kamata mubar Fee haka kawai ba,

ya kamata mucika burinmu a kanta, idan yaso sai mugudu mubar k'asar, muje wani wajan muyi Aure abinmu."

 "Anya wannan shawarar taka tayi?"

 "Tayi mana ko kina shakka ne?"

 "No bana shakkarka, amma problem ɗina ɗaya ne, ban yarda kai kayi wannan aikin ba, saidai kasamu wani, saboda ina kishinka sosai."

 Dariya yayi sannan yaja karan hancinta.


 "Don't worry my sweet baby, I can do anything for you, kinsan ina bala'in sonki zan iya miki komai a rayuwata."

Murmushi tayi tace "Yauwa baby shiyasa nike k'ara sonka wallahi."


 Tashi tayi ta nufi bedroom ɗinshi ta saka kayanta sannan ta fito, kiss tayi mashi a goshi sukayi ban kwana da niyar da sun dawo zata zo ta faɗa mashi duk yanda sukayi, bayan ta fita yabi bayanta da harara ya ce


 "Aikin banza wawuya kawai kina tunani duk wannan ɓata lokacin da nake yi duk a banza nayi shi?

To ba haka bane dan in samu biyan bukata akam Fee nayi, dan haka bazan tashi a banza ba, yarinya wannan sabo kike, ai Wallahi tunda yawu na yabiya a kanta to sai na lasa, kamar yanda na lasa naki haka itama zan lasa nata, mtsss aikin banza kawai."

 Ya tashi ya nufi bedroom din shi.


 ************


 Wani k'auye ne mai nisa su Adda suka nufa, ana kiran k'auyen da suna *SABUWA* duk garin babu wanda bai san da zaman wannan bokan ba, ya gagari kowa a gari duk macen da ta amsa sunanta a harkan hatsabi-banci tasan da zaman wannan bokan, inda yake zaune ya fita daga cikin garin sabuwan, cikin wani daji yake, suna zuwa Adda ta tsaya jikin wata bishiyar kuka ta fara kirari.


 "Ina kake boka kabutu gani nazo kafito shege ɗan shegiya, wannan lokaci aikinka baiyi ba komi ya ruguje..."

 Kafin ta rufe baki sai gashi ya fito.


 "Kai ku gafara dan kutimar.......,"

ya yanko wani irin zagi mara dadin ji,

"sai ni boka kabutu, nine kisa, kishiya ta mutu in raba uba da uwa da 'yayansu, nike sawa a kai mutum lahira dan kutimar........,

Ya sake d'uro wasu ashar din.

"Ni yau boka kabutu har nayi aiki ace aikin baiyi ba kawai karya ne."


 "Shedanu su baka nasara boka Wallahi ni kaina nayi mamakin wannan abu."

 "Tayaya kika bari har aka ɗaura aure da wannan ɗan iskan yaron?"

 "Boka Wallahi nima bansan haka zata faru ba."

 "To gaskiya kin kusan ki tafka babban kuskure, domin wannan yaron da ta Aura shege ne kamar uwarta, amma kada ki damu aikin bazai bamu wahala ba, saidai matsala ɗaya ne yanzu a gabanmu, Anum tana so ta watsa mana wannan aikin."

 Kirjin Anum ne ya buga saboda taga asirinta na shirin tonuwa.

 "Ki kwantar da hankalinki Anum duk nasan abinda kike aikatawa inaso ki sani kada ki yarda a samu matsala a wajanki dan ni bani da imani zan iya rabaki da duniya baki ɗaya, dan haka ki kiyaye, ke kuma ga wannan zan baki a tabbatar an zubawa FIDDAUSI a abincin da take ci, wannan kuma a ruwan wankanta za'a dinga zubawa,kinaji ko?"

 "Naji boka, amma me Anum tayi?

 "Kada ki damu ita tasan abinda ta aikita, sannan kina yawan sallah shiyasa aikin nan baya tafiya, ya kamata ki aje sallah har sai lokacin da zamu gama aikin"

 "Toh boka zanyi duk abinda kace indai zan samu abinda nake so."  Anum hankalinta ya tashi sosai sai zufa, ke keto mata ta ko'ina, saboda jin maganar da boka yayi tasan zai iya aikata komai dan ganin yayi nasara, jikinta yayi matukar sanyi, suka fito daga wajanshi.

Suna kan hanya Adda ta fara tuhumarta akan ta faɗa mata abinda boka ke nufi da maganar da ya gaya mata amma tace itama batasan abinda yake nufi ba, haka Adda ta hakura ta barta, suna motar suka fara tunanin yanda zasuyi da maganin da boka yabasu, gashi ba gida ɗaya suke da Fee ba yanzu, Anum tabawa Adda shawarar akan subawa mairo kuɗi masu yawa sun san zata iya aikatawa, idan yaso sai su kira gimbiya su faɗa mata ya kamata Mairo ta koma wajanta, saboda sunsan Hindu bazatayi ba, a haka suka tsayar da magana.....


  *MAZA DA MULKI*

★★.    _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA* ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

____________________________________


 

 _story and written by_

    *MRS OMAR*   _in dedication to_

 *FIDDAUSI SODANGI*
_Wannan page na sadaukar dashi ga masoyan wannan litttafin nawa, hak'ika naga irin soyayyar da kuke nuna masa shiya kara mani kwarin gwaiwa, nagode kwarai da gaske thank you very much_       _page 50_
  *S*una komawa gia,Adda ta kira gimbiya, nan fa ta cikata daɗin baki, har ya zama ta amince da Mairo ta koma wajanta, amma duk gidan babu wanda yasa ni sai ita.

yau Gwaggo ta haɗa kayanta duka zata koma Yola, a tsaye suke ita da Iya.

 "To Fadima tunda kinki ki zauna damu shikenan, amma dan Allah ki ɗinga zuwa kina ganin yanayin zaman FIDDAUSI da Modibbo wallahi hankalina har yanzu bai kwanta ba da zamansu."

 "Kada ki damu insha Allahu babu abinda zai faru a kullum muna addu'a akan Allah ya basu zaman lafiya, insha Allahu zan dinga 

zuwa lokaci-lokaci."


 "To Allah shi yarda."


 "Amin."

 

Ana ciki haka saiga Bahijja ta fito fuskar nan tata kamar anyi mata mutuwa, da ka kalleta kasan bata so mahaifiyar tata ta tafine.

Haka nan dai sukayi bankwana, driver dinsu shiya ɗauketa har zuwa garin Yola.


 Modibbo da Fee kuwa babu abinda ya sauya wajan faɗansu, sai ma abinda yayi gaba.


 ********
 *AFTER ONE MONTH*


 Tana zaune cikin falo, kwatsam! kamar a wacce aka tsikara, sai ta mike tsaye tana kiran sunan dogon Gaye, cikin rawar jiki ta nufi hanyar fita waje, jikin nata sai rawa yake.

 Hindu tabi ta da gudu tana faɗin.


 "Gimbiya lafiya ina zaki kuma,mai ya faru?"

 Ina ta riga tayi nisa ko mota bata ɗauka ba haka ta fita da gudu, Hindu dawowa tayi da sauri-saurin ta, sama hau dan fadama Balatoni abinda ke faruwa.

Amma abin mamaki data sanar dashi ko wani damuwa bai nuna ba, sai cewa ma yayj 

 "To Hindu mai kike so in mata? kina kallon yanda muke zaune da ita a cikin gidan nan, babu ranar da bama faɗa da, jiya fa maganin zawo tasa min a abincina nai ta shiga kewaye,da ace da karar kwana da na mutu".

Yadan tsagaita


 sannan ya cigaba

"Hindu ki barta kawai taje duk inda zata nasan zata dawo."

 "Amma ya Modibbo kana ganin haka shine mafita."

 "Hindu shine mafita, saboda a kullum idan ina tare dake, sai naji duk wani bakin cikin da tasani ciki na nemeshi na rasa, gaskiya Hindu keta dabance kafin asamu mai irin halinki za'a sha wahala a rayuwar nan."


 Murmushi tayi bata bashi amsa ba ta fita abinta,

 driver ya bita da mota da gudu amma ina taki tsayawa, duk wanda ya ganta sai yayi mamaki, domin ya wancin mutanan gari sun santa saboda pic ɗin aurensu da aka mammanna ita da Dogon Gaye wancan lokacin. Sa'ar ta d'aya ma unguwar da suke babu mutane dan ba cikin gari bane sosai.

Bata tsaya ko ina ba sai gidan Dogon Gaye, jikinta na b'ari ta shiga bugon k'ofa amma ba'a buɗe ba.

 Wani waje ta samu ta zauna hawaye na bin fuskarta, ta kasa gane duniyar da take ciki.


 "Baby wai meke damunki? naga tun lokacin da Adda ta kiraki kuka koma wajan bokan nan na rasa gane kanki gabad'aya, yanzu baki yarda dani, kuma kinsan dai babu yarinyar da nake nema inba keba".

"Please tell me what is wrong with you?"


 "Nothing" atakaice ta bashi amsa, sannan ta cigaba "kawai dai inaso na saba zama da rashin kane, saboda zan koma school."


 "Humm wannan ba hujja bace, dan zaki koma school sai ki guje ni?"

 "Ba haka bane."

 "To naji,

tunda haka ne muje gidana yanzu kin san nayi missing dinki da yawa."

 "Gaskiya kayi hakuri babu inda zani saboda yanzu ma da kaganni Adda ce ke jirana."


 Affan babu yanda bayyi da Anum ba amma taki binsa, hakanan ya hakura ya nufi gida jikinshi a sanyaye, yana shiga da motar tundaga nesa ya hango Fee zaune tana kuka, da sauri yayi parking ya nufi inda take.

 Tana ganinshi ta ruga da gudu ta faɗa jikinshi sai kuka, kara sata jikinshi yayi kafin ya buɗe parlour suka shiga...
 Nice dai....


  *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA*  ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

________________________________


   _story and written by_

      *MRS OMAR*     _in dedication to_

  *FIDDAUSI SODANGI*  _This page is for you AISHAT MUHAMMAD ( MAMAN SHAKUR) kawata ta kaina Allah ya barmu tare._      _page 51_
   *K*an kujera ya zaunar da ita, zaya juya ta k'ara rik'o hannunshi tana hawaye kan kujerar shima ya koma ya zauna kafin ya kama hannunta cikin murya mai daɗi taji yana tambayarta.


 "Baby what is happening to you? please tell me."


  Kuka ta k'ara fashewa dashi kafin ta fa ɗa jikinshi tana cigaba da kuka.


 "Please baby stop crying am here with you, waya taɓa min ke?"

 Fuskarta ta ɗago hawaye na bin fuskar, tasa hannunta duka biyu ta tallabo fuskarshi sannan ta fara magana.


 "Please Affan mu gudu mutafi wani waje can muyi aure, wallahi daga jiya zuwa yanzu bana ganin kowa sai kai wallahi idan har narasaka na tabbata mutuwa zanyi, please kataimaka min kada na rasa rayuwata, wallahi ina sonka bazan taɓa rayuwa da ko wane namiji ba a duniya.."


 Faɗawa jikinshi ta sakeyi tana cigaba da kuka hannu yasa yana shafa sumar kanta.


 "Please Baby is ok don't worry i will do anything for you."

 Dariya yayi kafin ya cije lips ɗinshi ya girgiza kai.

 "Affan wannan ce dama ta k'arshe a gurinka ya kamata kayi amfani da wannan damar ka biyawa kanka bukata saboda yarinyar nan bata cikin hayyacinta, asirin bokan nan yayi tasiri a kanta yanzu zaka iya yin komi da ita."

 "Yes wannan haka take."

  Duk a cikin zuciyarshi yake wannan maganar, kara sata jikinshi yayi yana shafata yana wani lumshe ido.


****


 Bayan ta fita Mairo ta kira Adda ta faɗa mata aiki yayi fa cikin farin ciki da murna Adda tace tazo ta amshi kuɗin da sukayi mata alk'awari, tana isa gidan ta samu Anum har ta rigata isa. 


 "Kai Mairo gaskiya ke abin a amince maki ne gaskiya naji daɗi sosai idan abin da muke so ya faru nayi miki alk'awari zan baki gida da mota sannan idan kin samu mijin aure ni zanyi miki komi."


 Murmushi tayi mai cike da jin daɗin maganar da Adda tayi mata.

 "Nagode ranki ya daɗe insha Allahu wannan lokacin karshen matsalarki tazo dan sai kin zama tauraruwa a gidan nan ke kawai ke haskawa, dan Wallahi ni kaina bana son yariyar nan ba kamar uwarta da kayi abu sai ta fara maka wa'azi Allah ya ce Annabi ya ce, shiyasa babu ruwana da ita."


 "Toh ai Mairo nan gaba kaɗan zataga karshen wa'azi dan sai ɗiyarta ta ɗauko mata abin da zatayi kuka da idonta, sannan idan yaso mijin ya saketa, nan kuwa na tabbata Mai Martaba bazaya bari ta zauna mashi a gida ba."

 "Kai gaskiya ranki ya daɗe ke babba ce, sai ke uwar gida a gidan Mai Martaba idan kikaga wata to Wallahi kwartowa ce, dan babu wata matar da ta dace dashi in ba ke ba."


 Wani juyi tayi ta gyara zama saboda taji Mairo nata fasa mata kai, dubanta takai ga Anum wadda keta danna wayarta, duk maganar da suke bata saka masu baki ba.

  

 "Anum kinaji muna magana amma kinyi banza damu nifa Anum ban gane kanki ba."


 Murmushin karfin hali ta kakaro saboda kada Adda ta gane damuwarta, bataso ta rasa rayuwarta saboda Affan, hak'ik'a tasan halin boka shiyasa ta hak'ura da soyayyarshi a zuciyarta.

 

 "Humm Adda ba haka bane naga kina magana da Mairo ne kuma bana son saka maku baki ne, amma sanin kanki ne nafi kuwa son wannan aikin yayi dan haka ki kwantar da hankalinki aiki yayi, sai dai mu zauna cikin masu dariya."


 Wani daɗi ne ya kara ziyarta zuciyar Adda saboda sun kara mata k'warin gwaiwa, hira sukaci gaba dayi kafin daga baya tabawa Mairo kuɗi masu yawa tace ta koma gidan gimbiya taga abin da ke tafiya... _B'angaren Affan da Fee_


 Shafata yake yana wani k'ara lumshe idanuwa hankalinshi gaba ɗaya ya fara tashi, mekiwa tsaye yayi sannan ya kamota yasata jikinshi yana wasanni da ita hannu yasa ya fara zage mata zip ɗin riga, itako sai k'ara shiga jikinshi take.......Kashh na so yafi haka amma ku k'ara hak'uri. 


Nice dai........


  *MAZA DA MULKI*

 ★★.   _MATA DA_ ★★

  ★.    *TAK'AMA*  ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

__________________________________


  _story and written by_

     *MRS OMAR*    _in dedication to_

  *FIDDAUSI SODANGI*  _Wannan shafin nakune ku kadai ZAUREN BIEBIE ISAH nagode da soyayar da kuke nuna min_      _Page 52_


   *I*tako sai k'ara shiga jikinshi take, wani irin daɗi yake ji saboda yau burinshi zai cika, hannu yasa yana shirin ɗaukarta cak, sai kawai yaji an banko k'ofa da karfi, da sauri ya ɗaga kanshi dan ganin waye, Balatoni ne jikinshi na rawa yayi kanshi, itako kara shiga jikinshi tayi ta rike shi gam, Balatoni ya fincikota da k'arfi ya jefata kan kujera sannan ya shaki Dogon Gaye.


 "Kai har ka isa da auran nawa ka taɓa min mata kai ɗin banza wallahi yau sai na ji dalilin da yasa ka hana matata zaman aure."


 Murmushi Affan yayi kafin ya yatsina fuska ya ce

  "Wai dama wannan ɗan k'auyen shine mijinki? wanda ko ɗan wankin mota bai kaiba, gaskiya baby Mai Martaba ya cuce ki, da ya haɗa ki da wannan illiterate ɗin." 


A tak'aice Balatoni ya bashi amsa da 


 "Gara ni ɗan k'auye ne amma kuma kada ka manta ni ba mazinaci bane dan bana neman mata, bale har nayi tunanin neman matar aure."


 Maganar da Balatoni ya faɗa mashi tayi masa zafi sosai dambe suka fara wannan ya kaiwa wannan duka, amma ina karfin Balatoni da Affan ba ɗaya ba, saboda kafin Affan yakaiwa Balatoni duka ɗaya shi ya kai masa biyu, gani tayi Balatoni na shirin fin karfin Affan yasa tayi saurin shiga gaban Affan ta tare dukan da Balatoni zai kai masa.


 "Wai kai wane irin maye ne? nace ban sonka ban k'aunar ka mai k'aunar ka ma ban k'aunarsa, kuma wallahi babu gidan ubanda zani ina nan saboda na tabbata idan na koma gidan nan yau mutuwa zanyi."


 Wata irin shak'a Balatoni yayi mata yana janta da k'arfi amma tana cijewa, dariya Dogon Gaye yayi mai karfi harda taba hannuwa, kafin yabita da kalamai masu daɗin gaske.


 "Oh my baby please just go i promise you i will come visit you time to time."


 "Muna fukin banza idan ka isa ka maimaita maganar da hausa kaga yadda zanyi dakai karamin ɗan iska."

 Fincikarta yayi ya ɗauketa cak sai mota Hindu na zaune a bayan mota ya jefata kusa da Hindu sannan driver ya tada Mota,

suna isa gida ya fizgota daga motar yana janta kasa gashi Balatoni bai iya fushi ba idan yayi fushi ba kyau, yana isa parlour ya jefata kan kujera yana huci kamar maciji, Hindu ya duba da jajayen idonshi ya fara magana kamar zaiyi kuka.


 "Hindu nagode da kika nuna min ilar barinta ta fita ita d'aya, yanzu da baki matsa min naje gidan wannan dan iskan ba da wani abu ya faru da matata yau....

  

 Maganarshi ta tsaya ne saboda tsawar da ta dakawa Hindu.

 "To muna fika! Au dama ke kika fad'a masa inda na tafi, hmm! wallahi baki burgeniba tunda ke baki bashi kanki b...."


 Marin da Balatoni ya sakar mata ne yasa maganarta tsayawa.


 "An fad'a maki itama dabba ce kamarki Hindu da kike gani yarinya ce mai tarbiya ba irinki ba da kika zamu ballagaza." 


 "Saboda wannan baiwar tawa zaka mare ni? har kana had'ani da ita."


 "Na mareki ko zaki rama? Hmmm! wannan baiwar da kike gani tafiki daraja a ido."


 "Karya kake d'an kauye me zaka iya min me kake dashi waye kai?, me ka tanada kuma naga ubanda ya isa ya rabani da masoyina." 


 Kanta yayi yana shirin kamata da sauri Hindu tasha gabanshi, ita kuma baya tayi da gudu, abinma dariya ya bashi.


 "Karamar yar iska da kitsaya na nuna maki nafiki zama dan tasha, zanga gidan ubanda za ki k'ara fita."


 Bayan ta nufi d'akinta shi kuma ya zauna a parlour yana kallon Hindu tana hawaye.


 "Kiyi hak'uri Hindu bansan haka zata faru ba, da ban ambaci sunanki ba."


 "Kada ka damu Ya Modibbo ba ina kukan abin da gimbiya tayi min bane, a'a ina kukan yanda zamanku yake ne, amma ina da wata shawara da zan baka kuma insha Allahu na tabbata wannan shawarar zatayi maka amfani." 


 "To Hindu inajinki insha Allahu zanyi amfani da ita."


 Ajiyar zuciya tayi kafin ta fad'a ma shi abin da zaiyi, murmushi yayi kafin ya k'ara kura mata ido sosai.


 "Hindu kina ganin wannan shawarar taki tayi.?

 "Insha Allahu Ya Modibbo tayi, wannan shawarar itace zaisa gimbiya ta so ka."

 Godiya yayi mata saboda irin kulawar da take dashi kafin ya nufi d'akinshi.... _After two week_


 Gimbiya duk ta fita hayyacinta ga shi Hindu da Balatoni idan suka fita basa dawowa sai dare, idan ta kira Dogon Gaye tace zatazo sai yace kada tazo shi zaizo saboda baya so ana ganinta a gidansu, yau ta kirashi tana kuka shiyasa yazo har gidan.....
Nice dai......


   *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

 ★.   *TAK'AMA*  ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

_________________________________  _story and written by_

       *MRS OMAR*    _in dedication to_

  *FIDDAUSI SODANGI*
      _page 53_

 *T*un kafin ya iso tasa kuku yayi masa abinci iri daban-daban, dama gidan yau ita kaɗai ce Balatoni sun fita shida Hindu in suka fita basa dawo sai wajan magarib fitarsu bata damunta, yana isowa harabar gidan ya k'irata a waya da gudu tazo suka shiga cikin gida, bayan ya zauna a parlour ya dinga binta da kallo saboda kayan da tasaka sun kamata sosai ga abin da idan ya kalla suke k'ara rikitashi yake jin sha'awarta, juyawa tayi zata nufi kitchen, cikin kasalallar murya ya k'ira sunanta.


 "Baby ina za ki kuma?"

 "Ina zuwa my sweetheart just 2 minutes(Minti biyu)."


 Kai ya girgiza tare da cewa 


 "A'a ban yarda ba ki dawo ba na son kiyi nisa dani saboda ban gaji da kallonki ba."


 Murmushi tayi kafin tazo dai-dai kan hannun kujerar da yake zaune ta zauna, tashi tsaye yayi ya ɗagota ya zaunar da ita kan kujerar da yake zaune sannan shi kuma ya durk'usa dai-dai k'afafunta ya ɗaura hannunsa a kan ciyarta yana kare mata kallo.

  

 "Yanzu Baby haka zanci gaba da kallon ki a gidan wani kina irin wannan shigar yana kallan man surarki? gaskiya bazan amince wani k'ato ya dinga kallan man jikinki ba."


 "To sweet ya zanyi? duk wani abu da zanyi ma shi nayi ma shi duk dan yayi zuciya ya sake ni amma yaki sweet I don't known what am going to do to make him divorce me?"


 "Please Baby kiyi wani abu a kai gaskiya bazanci gaba da ganinki kina zama a gidan wani ba, *KE TAWA CE* u are only mine ."


 Magana yake kamar da gaske saboda nunawa yayi kamar zaiyi kuka, hawaye ne suka fara sauka a idanunta na tausayinshi.

  

 "Wallahi sweet nasan kana sona nasan babu namijin da zai soni kamar yanda kake sona, amma don't worry i promise you yau sai wannan dan k'auyen ya sake ni, idan yaso ko Mai Martaba bai amince ba sai muje can wata k'asa muyi auren mu."


 "Wow! Baby are you sure yau zaki dawo gare ni?"

 "Yes"


 Ihu yayi kafin ya rungumuta jikinshi cikin murya k'asa-k'asa yayi mata raɗa


 "Baby kinki amincewa dani Wallahi a kullum idan muna tare bakiji yanda sha'awarki ke mun yawo cikin jiki ba."


 Yanda yayi maganar sai kirjin ta ya halba dakewa tayi, saboda ji take a yanzu bata iya ma shi maganar da zai ɓata ma shi rai, cikin murya mai daɗi itama ta bashi amsa.


 "Don't worry sweet mun kusa mu zama anta da jini a koda yaushe muna tare sai abin da kaga damar yi dani, amma yanzu kayi hak'uri har lokacin ya zo."


 Tashi yayi kafin ya koma kan kujera ya zauna ya ɗaga kanshi sama yayinda ya rumtse idonsa, ahankali ya buɗesu kafin ya kara dubanta.

 "Kina nufin haka zamu dinga zama har sai lokacin da ku ka rabu?"

 Bata bashi amsa ba sai dai kai da ta ɗaga mashi alamar eh, remote ya ɗauka ya danna tashar *MBC BOLLYWOOD* yana buɗewa dai-dai lokacin da suke maimaita wani film na India mai suna *TASHAN*, tare suka dinga kallo bayan film ɗin ya kare ya juya ya kalleta ya ce

 "Baby kinaga abin da Yariyar nan tayi ma wannan gayen tayi mashi adalci?"


 Kai ta girgiza.


 "Kinga irin soyayyar da yake nuna mata amma taje ta aure wani daban, gaskiya Baby ina tsoro kema kada daga baya ki dawo kina son wannan ɗan k'auyen nan."


 "What? Allah ya kyauta never bazan taɓa son shi ba."


 Dariya yayi kafin ya kashe mata ido ɗaya.


 "To ya me kika tanadar min mai daɗi?" 

 Murmushi tayi kafin ta kama hannunshi suka nufi dinning table kujera taja ma shi ya zauna kafin ta shiga buɗe kuloli gaba ɗaya kamshin abincin ya baɗe parlour iskan abincin ya shak'a.


 "Wow! Amazing so delicious."


 Gira ta ɗaga ma shi kafin ta zuba ma shi ya fara ci yana ci suna hira, sai da ya gama kafin ya duba time da sauri ya dube ta.


 "Baby time ya tafi ni zan tafi gida sai na dawo naga yanzu 5:00pm nasan yanzu wannan ɗan k'auyen na hanyar dawowa."

 Nunawa tayi kamar zatayi kuka amma ya dinga rarrashinta har ta hak'ura sai da ta kawoshi har wajan motarshi kafin sukayi bankwana yana fita daga get ɗin gidan motar su Balatoni na dannu kai....Nice dai........


  *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA*  ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

___________________________________   _story and written by_

       *MRS OMAR*     _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI*
      _page 54_

  *Y*ana fita daga get ɗin gidan kenan motarsu Balatoni na dannu kai, kafin su iso get ɗin gidan har ya riga ya wuce shiyasa basu haɗu ba don ba hanya ɗaya sukabi ba,

 Dogon Gaye na tafiya ta koma ɗakinta dama yanzu bata fitowa parlour ta zauna, su Balatoni suna isowa parlour idanuwansu suka sauka kan dinning table, wajan dinning ɗin suka karasa, abin da ya basu mamaki abincin da suka gani iri-iri, dariya Hindu tayi kafin ta fara ma shi magana cikin wasa.


 "Kai Ya Modibbo wannan irin delicious abincin haka duk kai ɗaya? gaskiya inaga GIMBIYA ta sauko."

  

 Harara ya watsa mata kafin yaja tsaki mai k'arfi.


 "Mtsss Hindu kenan kinsan kema da wuya wai gurguwa da auren nesa, mai hali baya taɓa sake halinsa, baki ga ni abincin ancishi kinga kenan bani akayiwa ba."


  Dan kada ya zargi wani abu yasa Hindu saurin juya maganar.


 "Hahaha wasa nake maka dama jiya naji tana waya da Anum zatazo to may be tazo kenan."

 Baki ya taɓe sannan yaja ɗaya daga cikin kujerin dinning ɗin ya zauna.


 "Ita dai ta sa ni, bari kiga ko badan ni akayi abincin nan ba sai na ci dan wata irin yunwa nakeji, kinsan yau nagaji da yawa."


 D'an shiru Hindu tayi kafin daga baya itama ta zauna tana fuskantarshi, sai da ta sauke ajiyar zuciya mai k'arfi kafin cikin sanyin murya mai daɗi ta fara magana.


  "Uhmm Ya Modibbo a kullum ina jin tsoron wannan fitar da muke tare kada ta kawo matsala saboda ni kaga daga baiwa ban wuce ba, abin kunya ne ace ina fita da mijin uwar gijiyata, gaskiya ni dai banason abin da zan samu matsala a rayuwata."


 "Hindu kenan wallahi kina da abin dariya kada ki manta itafa bata ɗauke ni a matsayin miji ba, a matsayin ɗan k'auye ta ɗauke ni wanda baisan komi ba, kada kiyi min haka Hindu kada ki manta da alkawarin da kiyayi min, wallahi Hindu nayi maki alkawarin duk ranar da FIDDAUSI ta dawo tana min kallon mijinta to daga ranar zan miki kallon abin da kike so."

  

 Murmushi tayi ta daga ma shi kai, a haka suka cigaba da fira, mai cike da farin ciki.


  Fee kwance take a saman gadonta (bed) yayin da kanta ke sama tana kallon silin din ɗakin, murmushi take tana kaɗa kafafuwanta da alama tunanin Sahibinta take, text ne ya shigo a wayarta da sauri ta tashi zaune sunan Affan ta gani a jikin sakon da sauri ta buɗe ta fara karantawa kamar haka.


 "Hy Baby how are you?, please baby do something idan har baki aure ni ba zan iya mutuwa, baby kiyi abin da zaisa mutumin nan yayi zuciya ya sa keki , magana ta karshe idan har bakiyi abin da zai sa kike ba, to zan hak'ura dake sannan za ki rasani kwata-kwata....."

  

 "No Affan i will do anything please don't leave me." Abin da ta ce da k'arfi kenan. 

 Text ɗin ta dinga bi da kallo, number d'in shi ta shiga kira.


********

 Around 6:30pm


 Bayan sun gama cin abincin da Affan ya rage shi da Hindu suka yi bankwana shiya nufi ɗakinshi itama ta nufi na su, yana zuwa toilet ya nufa direct dan yayi alwala ya tafi masallaci, buta ya ɗauka dan shi dama baya alwala a tap(Fanfo) shiyasa da suka fita da Hindu ya sawo butarshi, ɗaukar butar yayi da niyar ya kama ruwa, daga shigar shi cikin toilet ɗin babu daɗewa ya fasa wani irin ihu na fitar hankali.


  "Wayyo na shiga uku nayi tsarki da barkono. wayyo Allah."

 Da gudu Hindu ta hauro saman dan jin ihunshi zata nufi bedroom ɗinshi sai kawai taga Fee tsaye a bakin k'ofar tana dariyar mugunta harda rike ciki, tsayawa tayi sake da baki tana kallon ta.    

Nice dai........


   *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA*  ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

__________________________________


   _story and written by_

       *MRS OMAR*
  _in dedication to_

 *FIDDAUSI SODANGI*
 *Hak'ika mai sonka shike ganin kayi kuskure ya fito fili ya faɗa maka, wanda bai sonka kuwa zaiga kayi kuskure mai makon ya faɗa maka dan ka gyara to bazai faɗa maka ba, sai dai ya dinga kokarin k'ara ingizaka ka k'ara aikatawa, to dan haka duk wadda akayiwa gyara dan Allah muyi hakuri mu danne zuciya koda kuwa gyaran bai maka daɗi ba, saboda akwai wani hadisi Manzon Allah ( S.W.A) wani sahabi yazo wajan Manzon Allah yace ya rasulillahi nazo ni inason kamin nasiha, Manzon Allah yace to kada kayi fushi har sau uku, to ashe ko nasiha nada kyau ayi maka, ɗan Allah ba dan ni ba duk writer's ɗin da akayiwa nasiha mu dinga ɗauka, ba cin fuska bane idan mutum yayi ba daidai ba aka faɗa mashi, Allah kasa mudace amin*
     _page 55_

  " *W*ayyo na shiga uku nayi tsarki da barkono wayyo Allah na!."

 Da gudu Hindu ta hauro saman dan jin ihunshi zata nufi bedroom ɗinshi sai kawai taga Fee tsaye a bakin k'ofar tana dariyar mugunta harda rik'e ciki tsayawa tayi, sake da baki tana kallonta, zuciyar Hindu cike da bak'in ciki ta juya abinta saboda gudun matsala amma dan babu yanda zatayi ne yasa ta juya abinta, dariya take mai sauti yadda zai jita da kyau, a daddafe ya fito daga toilet ɗin saboda azabar zafin da yake ji jikin fan(Fanka) ya nufa sai da ya kure number fan ɗin duka ga sanyin A.C dake ɗakin amma duk da haka zafin barkonon yake ji yana shigarshi wata irin zufa ke ketumasa, idonshi ya rufe gam duk wata jijiya dake jikinshi sai da ta bayyana, ahankali yake jin sautin dariyar Fee ta shiga kunnanshi ji yake kamar a mafarki, idanunshi ya fara buɗewa ahankali k'ofar parlournshi ya k'orawa ido yayinda idonshi sukayi jajir kamar gauta, 'yan maza sunyi fushi duk zafin barkono da yakeji bai hana shi gane muryar Fee ba.


  "FIDDAUSI! ita ta aikita min wannan mumunan abin? Hmmm! Kinyi kuskure *FIDDAUSI SODANGI!!*" 


  Murmushi yayi wanda da ka ganshi kasan bai kai zuci ba, cikin fushi ya nufi k'ofar, itako duk bata san ya taho wajanta ba jingine take a jikin k'ofar hankalinta kwance, hannu yasa ya fizgo ta baki ɗaya ta fad'o tare da k'ofar, shirin faɗuwa take hannu yasa ya tarota ta ke ta tsaya cak tana ɗaga ido tayi ido biyu da Balatoni da sauri ta fasa wata irin k'ara ta rufe idonta da hannunta ɗaya saboda yadda ta ganshi, hannu yasa ya kama hannun da ta rufe idonta da shi yana janta.


 "Please Modibbo leave my hand, please! i promise ba zan k'ara maka irin haka ba."


 Ina ai ko jinta baiyi kan gado ya jefata yayinda idanunta ke rufe har yanzu sai hawaye ne kawai da ke bin fuskar ta bata so ta k'ara buɗe ido ta ganshi haka.


 "Ke k'aramar 'yar iska ce, shine har za ki ɗauki barkono ki saka min cikin butar da nake alwala, dan kinga na saka miki ido ko? kina yadda kika ga dama to zan nuna maki ni Balatoni na fi ki zama cikakken ɗan iska, yau sai dai wannan azabar barkono muji shi tare dake."


  Nan danan jikinta ya fara rawa, kan gadon ya hau cikin jarumta ya fizgota da karfi, kuka taci gaba dayi tana bashi hak'uri, saboda tasan yau kashinta ya bushe babu mai kwatarta sai Allah, kafin ace maka me har ya cire mata riga duk da akwai bra a jikinta bai hanashi jin kasala ba sai yaji duk zafin barkono da yakeji ya daina ji , ahankali ya lumshe idonsa.


 "A'a Modibbo kada ka aikata abinda kake shirin yi yanzu kada ka manta alk'awarin da ka ɗauka akan bazaka tab'a kusantarta ba har sai lokacin da ta amince dakai ta ɗauke ka a matsayin Mijinta."


 "To ya zanyi da rayuwata wannan hanyarce kawai zanbi dan in rama abinda ta aikata min yau."


 "Wannan ba hujja bace akwai hanyoyi da yawa da zaka iya ramawa, amma shawarar da nake baka kada ka sa6a alk'awarin da ka ɗauka kayi tunani."


 Duk wannan maganar shi da zuciyarshi suke ahankali ya buɗe idanunshi ya sauke su kan fuskar Fee har yanzu idanunta rufe suke, ahankali yaji wani irin sonta na k'ara shiga zuciyarshi saboda yadda hawaye ke fita daga fuskarta ba k'aramin kyau yaga ta k'ara mishi ba, hannu yasa yana maida mata rigarta bayan ya maida mata shi kuma ya jawo jallabiyar da ke kusa dashi ya saka, 

abin yabata mamaki da taji yana maida mata riga amma duk da haka baisa ta buɗe idonta ba, 


 "Ki buɗe idonki babu abin da zan maki."

 Hannu tasa ta k'ara rufe idonta, wata irin gigitarciyar tsawa ya daka mata.


  "Ki buɗe idonki nace idan kuma ba haka ba zan miki abin da nayi niya."


 Ahankali ta fara buɗe idonta saboda bata son ta sake ganinshi kamar yadda ta ganshi d'azu, ido ɗaya ta fara buɗewa ganinshi da jallabiya yasata ida buɗe ɗayan dariya ma ta kusan bashi amma ya sake ɗaure fuska, hannunta ya kama ya jata sai da ya kaita bakin k'ofa kafin ya turata waje.


  "K'aramar marar kunya na baki bashin wannan ranar saboda ganin tsorata dani da kikayi."


 Baki ta murguda mashi kafin tayi magana ciki ciki.

 "Hannu yaro kai d'in banza har ka isa inji tsoranka."


 Duk a tunaninta baiji abin da tace ba.

 "Me kikace k'aramar marar kunya ki k'ara maimaita abin da kikace mana."

 "To ni magana ka ji na yi?."


 Binta yayi da gudu ta nufi ɗakinta Allah ya bata sa'a ta rufe ɗakin ahankali ta dinga sauke a jiyar zuciya......

Nice dai..........


    *MAZA DA MULKI

 ★★.   _MATA DA_ ★★

  ★.    *TAK'AMA*  ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

_________________________________


   _story and written by_

      *MRS OMAR*     _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI*

 _This page is for you *AUNTY MAIJIDDA MUSA* thank you very much_       _page 56_

  *AFTER SIX MONTH*


 *A*bubuwa duk sun taro sun dame Adda saboda ganin yadda har yanzu aikin Boka baiyi tasiri akan Fee ba, zaune suke a babban parlournta su hud'u ita Anum Dogon Gaye da Mairo, cikin zafin zuciya Adda ta ta shi ta wankawa Mairo lafiyayyen mari.


 "K'arya kike Mairo kice duk abin da muka baki kin zubawa FIDDAUSI idan da kin aikata haka da yanzu komi ya zo k'arshe wata nawa kenan yanzu? da zuwanmu wajan Boka amma har yanzu babu abin da ya canza."


 Hawaye na zuba a fuskar Mairo ta fara magana.


 "Allah ya baki hak'uri ranki ya daɗe wallahi duk abin da kika faɗa min nayishi dai-dai sai dai bansani ba kodai an samu matsalar bane daga wajan mai gidan."


 Ta nuna Affan da hannunta, cikin fushi Affan yayi kanta danjin tana shirin ɗaura mashi laifi, da sauri Adda ta tsayar dashi.

 "Dakata Affan gaskiya ta faɗa mana laifinka ne sai kace ba namiji ba, baza kayi mata ta k'arfin tsiya ba?"

 "Adda tayaya zan mata ta k'arfin bayan kinsan ta ɗauke ni a masoyin gaskiya."


 "Ta ɗaukeka a masoyi na gaskiya to ni ina ruwana ni dai burina kawai buk'atata ta biya."


 Sai yanzu Anum tayi magana.

 "Ni a tunanina duk wannan maganar mu barta kawai dukkanmu ku tashi gaba ɗayanmu mu kuma wajan boka."


 "Wannan shawarar taki tayi." Cewar Mairo. 


Gaba ɗayansu suka tashi suka nufi wajan boka, itako Bahijja na ɗaki batasan wainar da suke tuyawa ba.


*******


 Yau satin Balatoni ɗaya da tafiya k'auye babu yadda baiyi da Fee su tafi tare ba amma tace babu inda zataje, haka ya hak'ura ya tafi shi ɗaya, tunda ya tafi Hindu ta shiga damuwa ita kanta tana mamakin kanta, saboda yanzu Balatoni ya zamemata abokin hira a koda yaushe, 

  

Ta b'angarenshi kuwa shima tunda yaje k'auye yake tunaninta, Gwaggo har tana tunanin ko tunanin matarshi yake, idan ya gaji da zama sai ya tafi wajan abokinshi Ali suyi hira dukda haka yana tunanin ta, 'yan k'auye ba k' aramin mamaki suka yi da suka ganshi ba, dama shi can ma'a bucin wanka ne...


  


****


Sune basu isa k'auyen da Boka yake ba sai wajen 5:00pm kafin suka isa, da isarsu Boka ya fito kamar yanda Adda ta saba mashi kirari haka yauma tayi mashi Mairo da Affan sun tsorata da ganin shi."


 "Hahaha toh muguwa yau kuma da wacce muguntar kike tafe?" Boka ya ce da ita cikin muyar shi marar dad'in sauraro. 


 "Boka kafi ni sanin da wadda nake tafe."


 "Haka ne na sa ni, amma uwar yarinyar nan shegiya ce duk abin da muka k'ulla ita ke wargaza mana shi saboda k'arfin addu'ar da take yawanyi mata."


 "To Boka yanzu babu wani abin da za'ayi akai?"


 "Hahaha muke da abinyi kuwa. Hannunshi ya d'aga sama saiga wani garin magani a hannunshi, Affan ya mik'awa.


 "Ga wannan ka amsa kai zaka rike a hannunka idan kaje gidanta ka tabbatar ka zuba mata a abin sha tasha idan tasha a take hankalinta zai fita jikinta, sannan zaka iya duk abin da kaga dama da ita."

 Jikin Affan na rawa yasa hannu ya amshi garin maganin.


 "Ku tabbatar wannan aikin anyishi kamar yadda mukace saboda rafane sunce idan har wannan aikin baiyi ba to daga yau sungama yi maki aikin."

 "Boka kada ka ji komi yanda kace haka za'ayi."


 "Hahaha." Dariya yayi kafin ya b'ace daga wajen, da sauri Affan da Mairo suka yi gaba dan tsananin tsoron da ya kamasu,


 Bayan sun isa gida suka k'ara tataunawa a kan gobe Affan zaije gidan Fee tunda Mairo ta faɗa masu Balatoni yayi tafiya, bayan sun gama abin da suke Affan yace Anum ta taso zai sauketa gida, a hanyarsu ta tafiya suka tsaya suna magana.


 "Baby naga duk yanayinki ya canza kodai baki so nayi Wannan aikin ne?"

 Murmushi ta kirkiro kafin ta ce.

 "No problem kada ka damu wannan aikin important ne a wajanmu zan iya sadaukarwa Adda da komi nawa, dan haka kada kaji komi muna tare kai dai ka aikata abin da Boka ya ce da kai."


 "Zanyi amma me zai hana mu wuce gidana ki kwana?" 


 D'an shiru tayi tana tunani can ta tuna da maganar Boka.


 "A'a kada ka damu yau Dad ɗina na gida kuma ka san gobe zan koma China makaranta."


 Hannunta ya kama yana kare mata kallo wani irin abu taji tundaga tsakiyar kanta har zuwa kafarta da sauri ta k'wace hannunta daga nashi ta buɗe k'ofar motar ta fita.....

Nice dai......


 *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA* ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

_________________________________


  _story and written by_

     *MRS OMAR*    _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI*


 

  _"Wannan page ɗin na sadaukar dashi ga masoyan *BALATONI* gabaki dayanku"_

     _Page 57_

  *H*annunta ya kama yana kare mata kallo wani irin abu taji tun daga tsakiyar kanta har izuwa k'afafuwanta, cikin sauri ta kwace hannunta daga nashi ta buɗe k'ofar motar ta fita da sauri, murmushi yayi kafin ya tayar da motarsa ya k'ara gaba.


 

 *Washe gari*


 Tunda wuri Fee ta tashi abin har yana bawa Hindu mamaki,

 gidan tasa suka gyara gabaki ɗaya yayi gwanin ban sha'awa, sannan tasa kuku ya dafa abinci mai rai da lafiya, bayan sun gama duk abinda zasuyi mata, sannan tace taso su tafi can gidansu saboda zatayi bak'i kuma bata son takura.

 Hindu tadai amsane kawai da toh amma hankalinta bai kwanta ba kwata_kwata.

Mairo kuwa wani irin daɗi takeji yana ziyartar zuciyarta saboda yau alkawarin da Adda tayi mata zai cika, suna fita ko,

 ta haura sama tayi wanka sannan ta dawo gaban dressing mirror ta zauna kwalliya ta shafa wannan ta murza wancan haka ta dingayi saida fuskar nan tata ta koma kamar ta baby ba k'aramin kyau tayi ba.

Sipp ta nufa ta shiga duba kayan da zata saka, wasu English wears ta jawo black Jeans sai red top ta saka sunyi matukar mata kyau saidai bai dace wannan kayan ta sakawa wanda ba muharraminta ba, domin kayan sun fitar mata da shape ɗinta sosai, ko ɗan kwali bata ɗaura ba saidai kawai tayi parking ɗin sumarta, murmushi tayi kafin ta lumshe idonta ahankali saboda wani irin daɗi da takeji yau cikin zuciyarta. Nocking ɗin da taji ne yasata buɗe ido da sauri, cikin hanzari ta nufi k'ofar da sauri ta buɗe masa k'ofar, tsaye yake ya ɗaura hannunsa a kan k'irjinsa idanunsa suka sauka kan kyakkyawar fuskarta, binta ya dingayi da kallo tun daga fuskarta har zuwa k'afafunta, shima babu laifi yayi kyau sosai, bayan ya shigo sannan ta tura k'ofar parlourn.

 Kan kujera ya zauna yayin da fuskarshi ke ɗauke da murmushi.


 "Wow Baby look at u!,

U look so beautiful Queen."


 Murmushi tayi kafin ta ɗan yatsina fuska.


 "A inda ba kyau ba, ka kalli fuskarka kuwa kaga yanda kayi kyau?"

 Lips ɗinshi ya dan tabe kafin yasake kai dubansa gareta ya ce


 "Baby yau fa da kishirwa nazo gidan nan nace bazansha komai ba sai nazo gidanki, dan haka ki kawo min wani drinks mai sanyi da cup biyu."

 Murmushi ta sakar mashi kafin ta tashi tana fadin

 

 "OK Sir."


 Kitchen ta nufa kafin daga baya ta fito da cup biyu a hannunta sai kwalbar wine, gabansa ta aje a kan table ɗan shiru yayi yana tunanin ta yanda zai saka mata maganin da Bokan ya basa ba tare da ta gani ba, murmushi yayi kafin ya dubeta cikin irin salonshi na yaudara ya ce.

 

 "Baby ina phone ɗinki?"

 "Tana bedroom ɗina garin saurin in tareka yasa na barta a can."

 "OK please idan ba damuwa kidan ɗauko min ita inaso na duba wani abu."


 "Har sai ka roke ni ka manta abuna nakane."


 Tashi tayi ta nufi saman, shi kuma da sauri ya buɗe kwalbar wine ɗin nan ya zuba a cikin cups ɗin da sauri ya kwance magani ya zuba cikin ɗayan cup ɗin, ɗan yatsanshi yasa ya motsa saboda babu cokali a kusa dashi da sauri ya maida maganin a aljihunshi yayi kamar bai zuba mata komi ba. Fuskarta ɗauke da murmushi ta mika mashi wayar bayan ta zauna ya mika mata cup ɗin gabanshi hannu tasa ta amsa hankalinta kwance, ahankali takesha yayinda ya kura mata ido yana kallonta shi kadai yasan abinda yake sak'awa.


 "Yaro baisan wuta ba saiya taka yarinya yau ce damata ta k'arshe a gareki maybe bazaki sake ganina ba har abada."


 "Sweet wai yau lafiya naga fuskarka ɗauke da murmushi?"

 

 Da sauri ya dawo daga tunanin da yake saboda tambayar da ta jefeshi da ita.


 "Lafiya lau Baby ba dole ki ganni cikin fara'a ba saboda ina tare dake kinsan *KE CE HASKEN ZUCIYATA* a koda yaushe idan ina tare dake inajin nishaɗi koke baki jin haka a zuciyarki?"


 Cikin murya kamar ta mararsa lafiya ta bashi amsa.


 "Inaji m.."


Ina ai kafin ace maka me har ta zube kan kujera, wata irin dariya yayi mai sauti.


 "Wayyo duniya! Sorry Baby bazan iya ganin wannan kyakkyawar surar taki ba kuma in tafi in barki haka ba tare da na bar maki tabona ba."


 Tashi yayi ya nufi kanta yayinda yake k'ara kare mata kallo wani irin abu yakeji na shigarshi mai daɗi hannu yasa ya ɗauketa cak! Sai bedroom ɗinta, kan gadon ya sauketa yayinda ya haura da sauri jikinshi na rawa, cikin zafi_zafi ya dinga aika mata da sakonni iri_iri, yayinda bata san duniyar da take ba, ɗakin na baro saboda bazan iya ganin wannan aika-aikar ba...


 *

Yau tunda garin Allah ya waye Bahijja ta kejin bata jin daɗin jikinta, sai wata irin faɗuwar gaba da takeji ita kanta batasan meke damunta ba, hankalinta ya k'ara tashi sosai saboda jin faɗuwar gaba ta yanzu tafi na da, addu'a ta shigayi dan samin sauki kafin daga bisani ta tashi ta nufi toilet ɗinta dan ɗauro alwala dama duk lokacin da taji irin wannan yanayin babu abinda take taji sauki a zuciyarta irin ibada. **

 *Around 6:0pm*

 

 Tun lokacin da Affan ya bata maganin nan tasha, Fee barci kawai take bata san inda kanta yake ba sai yanzu ta fara motsawa, ahankali take buɗe idanunta wani irin masifaffen zafi ne ta dinga ji daga gabanta wanda bata taba jin irinsa ba, saboda tasan yanda take jin zafi idan zatayi mestriation amma sai taji wannan zafin ya babanta da wancan k'okarin tashi take amma ina sai taji zafin k'ara shigarta yake ahankali ta lumshe idanunta, abinda ya faru tundaga zuwan Affan har zuwa yanzu ya dinga dawo mata, hawaye ne suka fara sauka a fuskarta yayinda ta jingina kanta a kan gado.


**


 _"To masu karatu hawaye murna ne Fee keyi ko name?_"
 Nice dai.....


  *MAZA DA MULKI*

 ★★.   _MATA DA_ ★★

  ★.    *TAK'AMA*  ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

________________________________


   _story and written by_

      *MRS OMAR*   _in dedication to_

  *FIDDAUSI SODANGI*      _page 58_
  *I*danuwanta ta lumshe kafin daga bisani duk abubuwan da suka faru suka dinga dawo mata sabo fil!, Bedsheet ɗin da take lullub'e dashi ne ta ɗan d'aga yanayin da taganta ne yasata saurin kauda kai, hawaye suka fara sauka a fuskarta tayi saurin jingina da kanta a kan gado.


 "Affan why did you this to me? I love so much because you are my heart, meyasa bazaka hakura ba sai munyi aure yanzu da wani ido zan kalli Mijina? Me Zan......"

 

 Bata k'arasa ba tayi shiru domin shesshekar kukan da yaci karfinta phone ɗinta tajawo ahankali ta danna number Affan amma abin mamaki sai tajita a kashe, jifa tayi da wayar zuciyarta cikeda bakin ciki, k'okarin tashi take amma ta kasa saboda wata irin azaba da takeji na k'ara shigarta.


 "No FIDDAUSI try your best kada ki yarda su Hindu su dawo su same ki a cikin wannan halin zaki shiga cikin babbar matsala sunanki zai b'ace a idon jama'a."


 Duk zuciyarta ce ke bata wannan shawarar k'arfin hali tayi kamar zata tashi amma ina azabar da takeji ba zaisa ta iya tashi ba, ido ta rumtse kafin ta fara rarrafe har ta isa k'ofar toilet ɗinta tana shiga tayi sa'ar akwai ruwan zafi a toilet ɗin, duk da rarrafe ta haɗa ruwan shima dan ta daure ne, shiga tayi ciki tana shiga ta saki wata k'ara nan danan zufa ta fara karyo mata, hawaye yaci gaba da fita daga idanunta, saida ta ɗauki wani lokaci a cikin ruwan kafin tayi wanka ta fito.

 Ta ɗanji daɗin jikinta saboda zafin yaɗan rage mata, bedsheet ɗin gadon ta samu ta cire saboda yanda ya lalace bata son a gane, a washing mashin ta saka shi. Tafiya take amma ita da kanta tasan tafiyarta ta sauya, wani irin jiri takeji yana ɗibanta da sauri ta dawo kan gado ta kwanta yayinda ta dafe kanta da hannunta duk biyun.


 "Humm Affan duk da wannan abin da kayi min bazan daina sonka ba, saboda nasan kaima kana sona."

 Ido ta lumshe tayi kamar tana barci nan ko wani irin zafin zazzabi ne takeji..


 **


 Adda ce kange da phone ɗinta a kunnanta kafin daga bisani ta cire wayar sannan ta kalli Mairo ta kwashe da dariya.


 "Kai Boka aikinka yayi nasamu abinda nake so yau zanyi barci harda munshari, wasu ko suyi kwanan bakin ciki......."

 

Bata kaiga k'arasawa ba Mairo ta tari numfashinta.


 "Allah ya baki nasara badai komi ya tafi dai-dai ba?"


 "Humm Mairo komi ya tafi dai-dai, yanzu Affan ne yakirani yacemin ya kama hanyar India, yayinda Anum ita kuma ta wuce China makaranta."


 "Kai Adda saike! kuto-kuto mugun ice kin zama kadangaren bakin tulu a kasheki a kashe tulu a barki ki b'ata ruwa."


 Murmushi tayi kafin ta jawo kuɗaɗe masu yawa ta mikawa Mairo.


 "Humm Mairo kenan ai duk sunan da zaki kirani dashi na wuce haka, kinga ga alkawarin mu yau na cika maki dan haka bana son kuma ganinki a cikin gidan nan ga makulli mota zansa driver ya kaiki har gidan dana saya maki."


 Faɗuwa k'asa tayi tana kwasar godiya harda kukan munafinci.


 "Bakomi Mairo ai kin wuce haka, dan haka kitashi kutafi kafin dare yayi."


 Haka Mairo ta tashi tayi tafiyarta zuciyarta cike da farin ciki, bayan fitanta Adda ta danna wata number ta kanga a kunnanta daga b'angaran da ta kira aka fara magana.


 "Allah ya taimaki uwar gida a gidan Mai Martaba SODANGI da girman kujerarki."

 "Yauwa gwagwa, aiki ne ya taso yanzu nake so kuyi shi, kuma bana son asab'a."

 "Haba dai rankiya dade ai ko Mai Martaba kike so a gama dashi yanzu zamu gama masa aiki."

 "A'a bashi bane wata yarinya ce nasa ɗan ladi ya kawota wajanku suna zuwa ku gama mata aiki saboda yarinyar tasan duk wani sirri nawa, yarinyar nada son kuɗi zata iya yin komi dan ta samu kuɗi dan haka suna zuwa ku gama da ita akwai kuɗi a hannunta na aikinku ne."

 "Angama rankiya daɗe."


 Wayar ta kashe kafin taci gaba da dariya.


 "Mairo!! Sorry kin tafka babban kuskure da kikayi saurin amincewa da Adda..."


 Tashi tayi ta nufi bedroom ɗinta tana ci gaba da dariya.**


 Hindu taga har dare ya farayi Fee bata kirata ba kuma tace idan bak'in sun tafi zata kirata amma shiru tashi tayi ta kirasu dan su koma amma ba taga Mairo ba, abin bai dame ta ba, sawa tayi driver ya maida su, suna zuwa sukaga parlour babu kowa saman ta nufa Hindu dan ta fad'a mata sun dawo kwance ta sameta tana rawar jiki, da sauri ta k'arasa wajanta.


 "Lafiya gimbiya meke damunki?"


 Bakinta na rawa ta firta.


 "Hindu banda lafiya."

 "To ko mutafi asibiti?"


 Kai ta girgiza alamar a'a.


 "To kinsha magani?"

  "A'a."


 Da sauri Hindu ta nufi inda suke ajiyar magani ta ɗauko, sannan ta bata cup ɗin ruwa ta d'agata dan shan maganin, bayan ta kwantar da ita ta dawo parlour, wajan dinning table ta nufa saidai abin mamaki yanda suka bar abincin haka suka same shi,

 duk maganin da Hindu ta bata tasha amma ta kasa barci sai juyi take a kan gado, da ta rufe ido saita ɗinga ganin abinda ya faru tsakaninta da Affan.....


   *MAZA DA MULKI*

★★.    _MATA DA_ ★★

 ★.     *TAK'AMA*  ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

_________________________________


  _story and written by_

       *MRS OMAR*    _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI*
 _Wannan page ɗin na sadaukar dashi ga yan group ɗin Maman Abdushakur *NOVEL WORLD* nagode sosai_
      _page 59_

*A*hankali take buɗe idanunta,

jitake wani irin sabon zafi ke k'ara shigarta jitake kamar yanzu abin ya faru duk illahirin jikinta yayi mata nauyi jikinta yayi mata tsami, idanunta ta sake rumtsiwa cikin jarumta had'i da kuzari tatashi ahankali a dadafe ta nufi toilet ɗinta, ruwan zafi ta sake haɗawa wanda sukafi na jiya zafi ta shiga tanajin zafi sosai amma ta daure, ta ɗan bata lokaci a ciki kafin ta fito daga toilet ɗin, bayan ta fito kaya kawai ta chanza sannan tasamu dakyar tayi sallah tana gamawa ta jawo wayarta number Affan ta sake trying amma bata chanza zani ba yanda dai ake faɗa mata yanzu ma haka akace mata, wani irin bakin ciki taji yaziyarci zuciyarta da sauri cikin fushi ta ɗauki makullin motarta, tama manta da zafin da takeji, tafiya take harma batasan inda take sa k'afarta ba, a parlour su Hindu suke ita tana zaune yayinda masu aiki ke gyaran parlour daga nisa ta hangota da sauri ta mike tsaye saida ta iso gab dasu kafin Hindu takai gaisu.


 "Barka da tashi gimbiya ya karfin jikin naki?"


 Fee kota juya ta kalli inda Hindu take balle Hindu tayi tunanin zata amsa gaisuwar tata, abin yaba Hindu mamaki ganin yanda gimbiya ta fita cikin sauri kai kawai Hindu ta girgiza kafin tace gaba da abinda take, motar da Fee taja ne har saida mai gadi ya tsorata.


 "To gimbiya ko lafiya taja mota haka to Allah yasa dai lafiya gashi mai gida yayi tafi balle yabita."


 Cewar mai gadi, gudu take babu tsayawa Allah ya taimaka ta hanyar babu motoci shiyasa taji daɗin yin gudu, babu inda ta tsaya sai get ɗin gidan Affan tana zuwa tayi horn da sauki mai gadi yazo ya buɗe, tana k'okarin shiga da kan motarta mai gadin yayi saurin dakatar da ita.


 "Dakata rankiya daɗe mai gida baya nan yayi tafiya zuwa India ya..."


 Kafin ya k'arasa maganar da sauri tatari lumfashinshi, saboda wata irin faɗuwar gaba da taji ta ziyarceta.


 "What India? please don't tell me nonsense, tayaya zai tafi India ya barni please ka fad'a min gaskiya."

 Ajiyar zuciya mai gadi ya sauke kafin ya sake kai dubansa gareta ya ce.

 "Hajiya abinda yace dani kawai idan kinzo na baki sakon da ya bani in baki saboda yasan dole zakizo nemansa dan haka ina zuwa bari na ɗauko maki sakon."


Yana rufe baki ya koma ciki ɗan ɗakinshi ya shiga bai wani ɓata lokaci ba ya fito da envelope a hannunshi yana zuwa ya mika mata.


 "Rankiya daɗe gashi abinda yace na baki."

 Jikin Fee na rawa tasa hannu ta amsa, bayan ta amsa ya koma cikin ya rufe get ɗin, ahankali take buɗe envelope ɗin har tayi nasarar fitar da takardar dake ciki, jikinta babu k'arfi ta buɗe takardar murmushin da ta fara ganine yasata saurin k'ora idonta, ga abinda ya rubuta a jiki. _"Hummm Aslm da fatan kina cikin koshin lafiya baki wahala ba my dear amma a baya ba yanzu ba, Fee gaskiya yanzu na tabbatar da bakida hankali a haka kike TAK'AMA ke yar gida MULKI ce bayan baki da wayon zama a gidan mulki TAK'AMA ce kawai taki amma baki iya zama da mutane ba, dama hausawa sunce *MAZA DA MULKI MATA DA TAK'AMA*, ke tak'amar ce kawai taki, nayi amfani da soyayyarki ne kawai amma ni ba sonki nake ba, kawarki nakeso Anum! tun ba yanzu ba muke tare da ita yanzu haka auranta ma zanyi, sorry dear kada fa zuciyarki ta buga gara kiyi hakuri ki rumgume village man ɗinki dan shine dai _ dai dake dan ni yanzu nayi maki nisa,Baby I know that you won't forget me in your life, but whenever you think about me just assume I came into your life for a little while, then make your life miserable am so sorry bae but I have to leave and be with my first love bye._

    

  *AFFAN (Dogon Gaye)*

      ******


 Jitayi numfashinta na barazanar ɗaukewa da sauri ta buga hannunta bisa steering motar bata san lokacin da bakinta ya fara furta.


 "Innalillahi wa'inna illahi rajun."

 Hawaye taji kawai suna sauka a fuskarta zuciyarta na mata wani irin zafi, idanunta ta lumshe ahankali ta fara furta.


 "Oh! My God AFFAN you deceived me? What did I do deserved this from you? I love you, I even disobeyed my father's orders just because of 

you,and the worst part is that ANUM was your love but you guys didn't even let me know? Oh my God am a fool indeed a fool"

 Ahankali taci gaba da hawaye ta rasa meke mata daɗi, dakyar ta samu ta fara dai_daita kanta kafin ta tayar da motarta tafiya take amma hawayen da ke sauka a idonta sunki tsayawa, a haka ta isa harabar gidanta bayan tayi parking ta fito ji tayi jiri na ɗibanta da sauri ta dafe kanta a haka ta isa parlour.


 "Dakata daga ina kike yanzu?"

 Cak ta tsaya da jin muryar balatoni a kunnanta......


 *MAZA DA MULKI*

★★.   *MATA DA* ★★

 ★.     *TAK'AMA* ★NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

________________________________


  _story and written by_

      *MRS OMAR*    _in dedication to_

  *FIDDAUSI SODANGI* _to masoya wannana Littafi duk ina ganin sak'onku da wanda na samu damar amsamawa da wanda ma ban samu ba, kalmar dai ɗaya ce kuce gaba da bin wannan Littafi zaku samu abinda kuke so, da masu cewa na ɓata shi da masu cewa na ci mutumcin aure duk kuyi hakuri shi Littafi ana son k'aruwa ne ba nishad'i kawai ba nice dai *MRS OMAR* ɗinku_     _page 60_

  " *D*akata daga ina kike yanzu na dawo bakya gida "


 Cak ta tsaya danjin muryar Balatoni a kunnanta, 

 "Tambayarki nake daga ina kike?"

 Cikin sanyin jiki ta juya ta k'ora mashi jajayen idanunta saboda bata san amsar da zata bashi ba, da sauri ya ɗauke kanshi daga dubanta.

 "Matsalarki ce Fiddausi koma me zakiyi ga fili ga mai doki."

 Yana rufe baki ya kai dubansa ga Hindu sukaci gaba da magana, juyawa tayi ta fara tafiya, juyowa yayi ya kalle ta yanayin yanda take tafiyar ne yasashi k'ara k'ora mata ido take yaji wani abu ya soki zuciyarshi da sauri ya dafe k'irjinshi da hannunshi, cikin sanyin murya yake tambayar Hindu abinda ya samita.

 

  "Hindu meke faruwa ne bayan tafiyata naga Fiddausi duk yana yinta ya chanza?"


 Ajiyar zuciya Hindu ta sauke kafin ta k'ak'aro murmushin k'arfin hali ta ce

 "Humm wallahi bata jin daɗi ne jiya ma da zazzab'e ta kwana to amma ina tunanin yau da sauki tunda har ta iya fita."

 "To shikenan Allah ya kyauta, ya kamata ki tashi ki shirya mufita."

 A tak'ace ta bashi amsa

 "Kaida yanzu ka dawo ai ya kamata ka huta."


 Dariya yayi kafin ya bata amsa.

 "Kada ki damu Hindu kuma kada ki ɓeye abinda ke zuciyarki, kinga ba wata duguwar magana zamu tsayayi ba tashi ki shirya kafin wannan yar bala'in ta fito gara mu bar mata gidan."


 Dariya kawai Hindu tayi sannan tayi mashi alama da kai watau toh tashi yayi ya nufa ɗakinshi, sannan itama ta tashi ta nufi nata ɗakin,


***


 Yau masarautar Mai Martaba SODANGI cike take da jama'a anata jimamin ganin gawar Mairo, gawar Mairo ce kwance a k'asa duk wanda yazo sai yayi mamakin kisan da akayi mata, kisane na fitar hankali kisane na zalinci da kaga kisan kasan babu imani ga wadda yayishi, yankan rago ne akayi mata, Mai Martaba kanshi da yaga gawar Mairo saida ya zubar da hawaye, Bahijja kuwa ta kasa ganin gawar saboda tausayi, Adda kuwa kuka take na fitar rai tana faɗin.


 "Wayyo Mairo waye ya aikata maki wannan mumunan aikin, yariya mai hankali babu ruwanta Mairo me kikayi masu, suka rabaki da rayuwarki wayyo Allah."


Nan fa ta faɗi tana kuka Mai Martaba yasa aka kamata cikin fishi Mai Martaba ya fara magana.


 "Koma waye ya aikata wannan aiki to wallahi duk ranar da yazo hannu to bazan taɓa barin saba dan sai ya gane ya taɓa masarautar SODANGI, duk wanda ya aikata wannan abun da biyu yayishi kuma na tabbata akwai sa hannun wani a masarautar nan."


 Adda jitayi k'irjinta ya buga kadadai Mai Martaba ya zurfaffa bincike asirinta ya tonu, haka yaci gaba da faɗa daga baya ya bada umarnin aje ayiwa Mairo surura a kaita gidanta na gaskiya, ranar nan haka masarautar ta yini cikin jimanin mutuwar Mairo.

  


 ****


Fee na ɗakinta bata san abinda ke faruwa ba ma, ita dai kawai abinda ke damuta ya isheta tunda ta dawo daga gidan Affan take aikin kuka ta rasa ina zatasa kanta wayarta ta k'orawa ido kawai tana kuka saboda tayi try number Anum itama tajita a kashe.


 "Nashiga uku yanzu ina zansa kaina yanzu da Anum za'a haɗa kai a chuce ni, to Adda fa itama tasan komai kenan? no that's impossible nasan Adda baza tayi min haka ba Adda mai sona ce, to me zai hana na kirata na faɗa mata duk abinda ya faru."


 Number Adda ta shiga dubawa.....


  *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA* ★
NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

___________________________________


  _story and written by_

      *MRS OMAR*


   _in dedication to_

  *FIDDAUSI SODANGI*
_Zan rayu dakai, zan mutu dakai,Abdullah *ABADAN* dani dakai zamu zauna! idan nace ni ina nufin kai, idan nace kai ina nufin ni, nice fa Maryam, Maryam ɗinka... Abadan dani da kai zamu zauna wannan page na sadaukar dashi ga *SAFIYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* hak'ika kinyi namijin k'okarin wajan wannan Littafin naki naji daɗinshi sosai Allah ya k'ara basira amin_
       _page 61_

 *N*o Fee kada ki aikata kuskuren da yafi na baya, kinaso asirinki ya tonu ne? kiyi hakuri ki barma zuciyarki komi Affan ya riga yagama dake Fee."

 

 Duk zuciyarta ce ke bata wannan shawarar, kuka ta k'ara fashewa dashi saboda batasan wazata kaiwa kukanta ba yanzu, kanta ta sake kifawa akan pillow tana maida lumfashi sama_sama, ita kadai tasan irin zafi da kunar da zuciyarta ke mata, magana taci gaba dayi harma batasan abinda bakinta ke faɗa ba.


 "Oh my God yanzu da wane ido zan kalli Modibbo ya auranmu yake? ya zanyi da rayuwata idan ya gane gaskiya, da wane ido zan kalli Mai Martaba na faɗa mashi bani da laifi, Affan ka chuce ni i promise to my self i will never forgive you, please God help me.."

 Kuka ta k'ara fashewa dashi, wunin ranar nan ko ruwa batasa a bakinta ba, kuka ne kawai abincinta,


 ****

 Adda burinta yacika an kashe Mairo saboda gudun kada ta tona mata asiri, abinka ga ɗan duniya duk wata hanya da zaisa a gano dasa hannunta wajan kisan Mairo ta tosheta, babu wanda zayayi tunanin dasa hannunta saboda duk jimamin dake na mutuwar duk da ita ake, ta nuna tafi kowa jin mutar Mairon ma, Mai Martaba duk yasa an baza yan sanda cikin garin Katsina da ance maka 7:30pm tayi to zakaga duk mutane sun fara haramar zuwa gida, Mai Martaba SODANGI akwai tausayin talakawa balle har gida akazo aka taɓa jama'arshi, haka abubuwa suka dinga faruwa yanzu babu abinda take jira irin taji Fee ta dawo gida amma har yanzu shiru takeji, ta ɗauri aniyar duk wata hanya da zatabi sai tabi dan Modibbo ya saki Fee sannan Mai Martaba ya tsaneta, ita dai Bahijja a kullum sallah da addu'a sune abokanta, gashi tunda Fee taje gidan Balatoni bata taɓa kirata a waya sun gaisa ba, wannan duk ba damuwarta bace itadai damuwarta ɗaya shine su zauna lafiya,


 *****

 Kwanan Fee biyu a ɗaki babu ci babu sha sai kuka, gashi babu wanda ya shigo ya dubata ko lafiya idan kaga ta tashi to sallah ce kawai saboda yanzu taji uwar bari sallah bata wuce ta, yunwa ce taji tana shirin kasheta yasa ta fito parlour, a parlourn babu kowa sai ɗaya daga cikin mai aiki, cikin sanyin murya take tambayarta ba kamar kullum ba da take masu magana cikin isa da TAK'AMA ko gaisheta sukayi kafin ta amsa aiki ne, ita kanta mai aikin abin ya bata mamaki saboda yanda taga ta chanza duk ta faɗa.


 "Talatu ina Hindu take kwana biyu najita shiru?"

 Da sauri ta yak'e hak'oranta tana bata amsa.

 "Allah ya baki nasara ai ta fita ita da rankaya dade, ai kwanan nan biyu basa zama a gida da gari ya waye suke fita basa dawowa sai lokaci barc...."

 Talatu bata k'arasa ba Fee ta dakatar da ita ta hanyar ɗaga mata hannu saboda bazata iya jin sauran maganar ba ita kanta bata san dalili ba, taji wani abu kawai ya soke ta a zuciya, dakyar ta iya k'ara magana. 


 "Ki faɗawa Emma ya haɗa min tea ba madara ya kawo min yanzu."

 "To rankiya daɗe "

 Da sauri ta nufi kitchen dan ta faɗa mashi, wajan zama Fee ta samu saman kujera ta zauna yayinda ta kwantar da kanta a sama, idanunta ta lumshe tana maida lumfashi sama_sama ita kawai tasan abinda ke damunta yanzu.


  *MAZA DA MULKI*

★★.   *MATA DA* ★★

 ★.    *TAK'AMA*  ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

____________________________________


  _story and written by_

      *MRS OMAR*   _in dedication to_ 

  *FIDDAUSI SODANGI*
      _page 62_  _this page is for you my Tawa Aisha Aliyu_

  *T*un ranar da Balatoni ya dawo daga tafiya da suka haɗu da Fee bata k'ara sashi a ido ba shida Hindu, saboda da gari ya waye suke fita fitarsu bata damunta ita dai damuwarta ɗaya ce kada ya gano abinda ya faru ita da Affan, a kullum idan tayi sallah tanayiwa Affan mummunar addu'a.


***

  

 *BAYAN WATA UKU*


 Duk wanda ya kalli Fee yasan ta chanza ta rame amma batayi baki ba haskenta ya k'ara haskawa, ita kanta tasan yanayinta ya sauya a kullum tana yawan jin kasala a jikinta, duk wannan iyayin da isarta ta daina ita kanta mamakin kanta take, yau tunda ta tashi take jin indomie kawai take son ci Allah Allah take ta gama sallar safe hijabinta kawai ta cire ko kayan barci ma bata chanza ba, bayan ta sauko k'asa parlour ta nufa direct babu kowa har ta juya zata nufi kitchen saiga Emma ya fito, yana ganinta ya duka cikin girmamawa ya gaisheta bayan ta amsa ta bashi umarnin abinda zayayi mata.


 "Yauwa Emma indomie zaka dafa min ɗaya bana son a sa komi a cikinta sai maginta kawai."

 "To HAJIYA an gama."


Tashi yayi da sauri ya nufi kitchen ita kuma ta koma parlour ta zauna, *DSTV* ta kunna yayinda ta danna tashar *ZEE WORLD* tana dannawa shi yayi dai_dai da lokacin da suka saka wani film mai suna *LOVE OH LOVE* tana cikin kallo kawai taji hawaye sun fara sauka a idonta saboda an taɓo mata tsohon rauninta da Affan ya barmata, kai ta girgiza kafin ta ce.


 "No Avni don't risks your life,I made the same mistake in my life. gashi yanzu najama kaina."

 

Ji tayi bazata iya ci gaba da kallon film ɗin ba yasa ta kashe dstvn sai taji damuwarta ta dawo sabuwa, tana cikin wannan tunanin ne taji motsi a kan dinning table da sauri ta juya, ido biyu tayi da Hindu yanayin da ta ganta ne yasata saurin ɗauke kanta take taji wani abu ya soketa a zuciya, gani tayi Hindu tayi kyau kamar ba ita ba ga wata kwalliya da tasha.


 "Hajiya ga indomie a nan zan aje ko a dinning?"

 Batayi magana ba hannu kawai tasa ta amsa, shi kuma ya juya, cikin girmamawa Hindu ta gaisheta, banza tayi da ita tayi kamar bata jita ba, jiki a sanyaye Hindu ta koma wajan dinning, ahankali yake saukowa daga bisa matattakalar benen yayinda idanunsa daga nisa ya kafesu a kan Fee, duk yana kallonta ta jawo indomie ta saka cokali tana kaiwa a baki bai kai mata cikin wuya ba ta fara kwara amai, baisan lokacin da ya k'araso gabanta ba ya riketa,

Jijigata ya fara kamar zaiyi kuka.


 "Fiddausi meya sameki dama baki da lafiya Hindu me yasameta baki faɗa min ba?"

 "Yaya nima Wallahi bansan batada lafiya ba."


 Abinka da ba komi a cikin sai ruwa kawai take amayarwa idanunta ne ya fara ganin sun fara yin sama, da sauri ya ɗauketa cak ya fita da ita da gudu, yasa Hindu ta ɗauko mashi makullin motarshi da hijabinta, bayan yasakata yayinda Hindu ta shiga gaban motar shiyaja motar ni kaina saida ya bani mamaki, gudu yake bakin k'okarinshi babu inda ya nufa da ita sai asibitin *KALEEESAT HAYDAR* suna zuwa sukayi sa'a tana office da sauri aka kirata, bata wani ɓata lokaci ba tashi ga duba Fee duk wani gwaje_gwaje saida akayi mata, Balatoni da Hindu na tsaye suna jira ta fito, saida suka ɗauke kusan awa uku a wajan kafin doctor Khaleesar ta fito fuskar nan tata ɗauke da murmushi, 


 "Doctor ya jikin nata?"

 "Da sauki muje office ɗina inason magana dakai."

 A sanyaye Balatoni ya take mata baya, yayinda suka bar Hindu tsaye a wajan, bayan sun zauna doctor Khaleesar ta gyara zamanta sosai sannan ta cire glass ɗin dake fuskar, cikin sakin fuska ta ce


 "Congratulation matarka na ɗauke da ciki har na tsawon wata uku.."

 "Ciki?"


  *MAZA DA MULKI*

★★.    _MATA DA_ ★★

 ★.     *TAK'AMA* ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

__________________________________


  


   _story and written by_

         *MRS OMAR*     _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI*
 _Wannan page sadaukar wane ga yan group d'in *KHALEESAR HAYDAR* Facebook nagode da irin goyan bayan da kuke bani_


 

       _page 63_  *C*ongratulation matarka na ɗauke da ciki har na kimanin wata uku."

 "Ciki?"

 A firgice Balatoni ya tambayi doctor Khaleesar, kai ta ɗaga mashi cikin isa irin ta likitoci ta ce.

 

 "Ko baka murna ne kaima kana ɗaya daga cikin mazan nan da basa son haihuwa ne?"

 Murmushin yak'e ya k'irk'iro kafin ahankali ya fara dai_daita kanshi, cikin sanyin murya ya ce.

 "Ina so mana doctor akwai wanda dama baya son karuwa."


 Dan gudun kada ta sake mashi wata maganar daban yasa ya ce.


 "To doctor ya jikin nata?"

 "Jikinta da sauki sosai dan yanzu ma haka na bata magani da allura ta dawo dai_dai zaku iya komawa gida da ita, sannan tana yawan sa kanta a damuwa gaskiya ka dinga kulla da ita."

 "To shikenan doctor nagode."


 Kafin ta bashi amsa har ya fita, yana fita yaga wata nurse ta fito da ita da alama doctor Khaleesar tasa a fito da ita, juyawa yayi ya kalli Hindu dake tsaye tuni tana jiransu ya ce.


 "Hindu ki tafi zan sameki a wajen."

 Kai ta d'aga mashi kafin ta juya ta fara tafiya abinta, shi kuma ya kama hannun Fee daga wajan nurse ɗin yayi mata godiya yana zuwa ya buɗe mota ya sakata tana kallonshi ya fara driving, kamar yanda sukazo a guje yanzu ma haka, sai gudu yake da motar, babu inda ya tsaya sai harabar gidansu, cikin fishi yayi parking fuskar nan tashi babu alamar murmushi ko alama, hannunta ya sake jawowa daga cikin motar ita dai binsa kawai take babu inda ya nufa da ita sai ɗakinta yana zuwa ya jefata kan gadonta da sauri ta ɗaga idonta tana kallon shi.


 "Kina kallona ko baki san abinda kikayi ba ne?"


 Kai ta ɗaga mashi 


 Lips ɗinshi ya cije kafin yazo daf da ita idanunsa sun chanza kala, da sauri ta sadda kanta k'asa hannu yasa ya ɗago kanta suna kallon juna ido cikin ido ya ce.

 "Doctor Khaleesar tace kina ɗauke da ciki har na kimanin wata uku.."

 "Cak taji lumfashinta na bara zanar ɗaukewa, kafin kace me hawaye har sun fara fita daga idonta, sakinta yayi ya koma jikin bango ya tsaya ya k'ora mata ido."

 "Ke nake jira ki bani ba'asi."

 Ɗagowa tayi ta kalleshi fuskarta cike da hawaye cikin muryar kuka ta ce.

 

 "Please Modibbo listen to me i promise you I will tell you the truth i don't know anything Wallahi b..."


 Bata karasa ba ya dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu, gabanta ya sake zuwa, cikin muryar da bata taɓa jin yana da irinta ba ya fara bata amsa.


 "Fee just keep quite because today i don't want to hear anything from you,I just realize that you have done what your heart wanted you to do since from the beginning,thanks may Allah grant you quick recovery."


 "Take Fee tayi mutuwar zaune dan jin Balatoni na watso mata turanci, juyawa yayi zai fita bata san lokacin da tasha gabanshi ba,ta faɗi k'asa tana kuka.

 "Please save my life please Modibbo........"


 Da sauri ya katseta .


 "Fee dole sai Mai Martaba ya san da wannan zancen ko da zanyi wani abu a kai".

 "Please Modibbo ka tausaya min i promise duk abinda zakayi min zan ɗauka amma banda faɗawa Mai Martaba."

 Kuka ta k'ara fashewa dashi yayinda ta kama kafarshi ta rike, ɗan shiru yayi yana kallonta kafin daga baya ya ce.


 "Alright! Alright!! Alright!!! but on one condition........."

Kafin ya rufe baki ta bashi amsa."

 "Zan amince koma meye amma banda faɗawa Mai Martaba."

 D'an shiru yayi yana kallonta kafin daga baya ya yatsina fuska yace 

 "Alright! zan hakura na barki bazan faɗawa kuwa ba amma dole ne na k'ara aure..."

 "What aure fa kace?"

 "Yes aure."

 Cikin muryar kuka ta ce."

 "Aure to wacece zaka aura?"

 "Umm ba kowa bace kin santa, Hindu c......


  *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA*  ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

____________________________________   _story and written by_

      *MRS OMAR*    _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI* 

 _Tafiya da gwaninka akwai daɗi maganar ciki zata fito fili ki rik'o da gaske da santsi ni daga ke bazan kula kowa ba, my *Jiddah Aliyu* kina raina wannan page naki ne TAWA KE ƊAYA CE_
       _Page 64_


   *C*ikin muryar kuka ta ce .


 "Aure kuma to wacece zaka aura?"

 Murmushi yayi kafin ya taɓe fuska ya juya k'wayar idonshi kafin ya ce.

 "Uhmm ba kowa bace kin santa Hindu ce."

 "What Hindu fa kace? kasan abinda kake faɗa Hindu fa baiwata ce taya zanyi kishi da ita no never."


 Baki ya taɓe kafin ya ɗaga kafad'arshi cikin irin salon nan na masu aji.

 "OK no problem because this is my decision tunda baki amince ba zan iya zuwa na faɗawa Mai Martaba idan yaso sai ya ɗauki action da kanshi."


 Wayyo Allah ji tayi kamar ta fasa ihu dan haushi mi kewa tsaye tayi ahankali ta fara goge hawayen da ke fita a idonta sannan takai dubanta ga Balatoni cikin dusashewar murya tace.

  

 "Ok i accept your decision I know this is my destiny, amma kasani bazan tab...."

 Ɗan yatsansa yasa da sauri ya daɗe mata baki."

 "Shhh! please just shut up your mouth bana son yawan magana yanzu, iyakar maganar da zan iyayi dake kenan, hope you understand?"

 

 Kai ta ɗaga mashi kafin ta koma saman gado ta zauna jiki a sanyaye, dubansa yakai gareta kafin ya girgiza kai ya juya abinsa ya fita, yana fita ta fashe da wani saban kuka irin mai cin ran nan, ta faɗi kwance tana kuka. 


 "Affan ka cuce ni karaba ni da mutumcina,

yanzu zan haife abinda jama'a zasu dinga mashi kallon ɗan shege."


 Dan shiru tayi tana tunani yau salon da taga Balatoni yazo mata dashi wanda bata taɓa ganinshi da irin salon ba.


 "Dama Modibbo najin turanci ne ya nuna min kamar bayaji ko yanzu ya koya? oh my God! Modibbo taya zaka auri Hindu na zauna da ita a matsayin kishiya bayan ita baiwata ce, Modibbo why do you do this to me? meyasa baka fito fili ka nuna min ainahin kanka ba, wayyo Allah, na cuce kaina."


 Kuka ta k'ara fashewa dashi lumfashinta kamar zai ɗauke.


 *****


 Tun bayan dawowar Balatoni Gwaggo take jin kewarsa shiyasa kawai ta yanke shawarar biyo shi tunda dama ita kadai ce yanzu a gidan, tunda ta iso gidan Mai Martaba Bahijja ke murnar ganin mahaifiyar tata sai taji duk wata damuwarta ta kau, zaune suke ita da Iya da Gwaggon a parlourn Iya suna hira mai cike da nishad'i, Gwaggo ta dube Bahijja ta ce.


 "Wai meke damunki ne naga kin chanza ko har yanzu akwai matsala tsakaninki da bishir ɗin ne?"


Murmushi tayi mai cike da kauda duk wata damuwa sannan ta d'ago kanta tana fuskantar gwaggo.


 "A'a Gwaggo babu komai ina cikin farin ciki a koda yaushe."

 "Humm Fatsima kema kinfi kuwa sanin halin Bahijja ko tana cikin damuwa bazata faɗa ba, tun kafin kizo nake fama da ita ta faɗa min damuwarta amma taki ta faɗa min."

  

  Murmushi ta sakeyi wanda a koda yaushe yake k'ara fitar mata da k'yaunta, Gwaggo ce ta k'ara magana yanzu.


 "To babban abinda ya k'ara kawoni garin nan akwai wani sirri da muke ɓoye maki babu wanda yasan da maganar dagani sai Dijee."


 Ta nuna iya da hannunta


 "Shiyasa nace ya kamata mu faɗa maki saboda halin rai kafin ta Allah ta kasance."

  

 Da sauri Iya takai dubanta ga Gwaggo, ta dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu


  "A'a Fatsima karkiyi haka har yanzu da sauran lokaci bai kamata mu fallasa al'amarin nan yanzu ba har yanzu da sauran lokaci."

  "To amma Dijee idan bayan bama raye fa, yaya za'ayi bayan babu wanda yasan da lamarin nan dagani sai ke sai Allah sai ko...."

 Kafin Gwaggo ta k'arasa maganarta Iya tayi saurin tararta dan jin zata kira wani sunan.


 "Dan Allah Fatsima kiyi hakuri abar maganar nan."


 Shiru tayi da bakinta tana kallonta, yayinda suka saka Bahijja a cikin duhu.


 "Sirri kuma to wani sirri ne wannan suke boye min basa son kuwa ya sani, har yanzu akwai lokaci to wannan wane irin sirri ne?" ***


 Ni kaina ina tunani wane sirri ne wannan? maybe Readers ne kawai zasu bamu wannan amsar....
Ni ce dai


 *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA*  ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

____________________________________   _story and written by_

       *MRS OMAR*     _in dedication to_

  *FIDDAUSI SODANGI*  _Wannan page sadaukar wane ga yan group ɗin Mum ɗina ta kaina MUM FATI *MATAR K'ABILA* Allah yabarmu tare...._
        _Page 65_66  *D*uk a cikin zuciyarta take wannan tunanin, ɗakin shiru ya ɗauka na wasu yan minutes duk kansu akwai abinda kuwanensu ke sak'awa a zuciyarshi, shirun da Bahijja taga yayi yawa ne yasata tashi ta nufi k'ofar fita, kura mata ido sukayi suna kallonta har ta fita daga ɗakin.


 "Watau Fatsima ga dukan alamu munsa Bahijja a cikin tunani sirrin da muke ɓoye mata, amma duk da haka bai kamata mu faɗa mata ba har yanzu akwai sauran lokaci."


 Ajiyar zuciya Gwaggo ta sauke wanda tun da Iya ta fara magana take kallonta.

 "Shi kenan Dijee bani da tacewa tunda tun farko mun ɗaukarwa junanmu alkawarin rike wannan sirrin har sai lokacin da yadace zamu faɗeshi."

 Dariya Iya tayi sannan ta kama Gwaggo.


 "Yauwa Fatsima ko kefa."

 Hira sukaci gaba dayi sunayi suna raha gwanin ban sha'awa.


 ***


 Bayan Fee ta ci kuka ta gaji babu wanda yace taci kanta hakan yasa tatashi ta dawo parlour ta zauna, zaune take a babban parlournsu ga wasu kaya a gabanta ta tula, duk bayan mentina takan ɗaga kai ta kalli agogon parlour, tanayi tana jan tsoki horn ɗin da taji yanyi ne ya tabbatar mata da su Balatoni ne suka dawo, gyara zama tayi tana jiran su iso a tare suka shigo shida Hindu fuskokinsu ɗauke da nishaɗi, basu masan tana parlourn ba Hindu ta gita zata nufi ɗakinta Fee ta daka mata tsawa.


 "Dakata Hindu ina zaki?"

 Cikin girmamawa Hindu ta nufi wajan Fee.

 "Kiyi hakuri gimbiya wallahi bansan kina nan ba, yajikin nake?"


Fuska Fee ta k'ara ɗaurewa cikin faɗa ta fara bata amsa.


 "Bansani ba Hindu, ke bari ma na tambaye ki nan gidan ubanki ne?"

 Cak Balatoni ya tsaya da tafiyar da yake dan jin zagin da gimbiya tayiwa Hindu.


 "Tambayarki nake Hindu ko masautar SODANGI da danginku akayi ta?"

 Kai ta girgiza alamar A'a take idanunta suka cika da hawaye.

 "Good, tunda ba da danginku akayi taba to yau zaki bar masarautar SODANGI kuma kada na k'ara ganin k'afarki ko nasamu labarin kinzo."

 "Babu inda zata tana nan zama daram."


Cewar Balatoni da sauri ta ɗaga kai tana dubansa, 


 "Amma Modibbo karfa ka manta ni keda iko da su zan iya canza su a duk lokacin da nake so, dan haka yau sai Hindu tabar gidan nan."

 "OK so you have started again? i can see that you have forget about my decision OK then do as you like."

 "Modibbo because of this girl shine zaka tozartani."

 "Yes saboda tafiki mutumci a wajena."

 "Abinda zaka faɗa kenan to wallahi sai tabar gidan nan tunda bana ubanta bane."

 "Humm wallahi kina bani mamaki Fee ko kin manta matsayinta ne a zuciyata, yanzu na k'ara faɗa maki, sannan kuma abinda bakiso ya faru shi zai faru yanzu nan Mai Martaba zai samu labari."

 "Amma Modibbo.."

 "Fee I said keep quite."


 Hannu ya ɗaga mata baki ta saki tana kallonshi, sannan ya umarci Hindu da tatafi ɗakinta ita kuma suka barta a tsaye kamar ice, kuka ta fashe dashi ta nufi ɗakinta da gudu tana kuka, 


 "Fee shawara ɗaya da zan baki itace kawai mafita kije ki zubar da cikin nan, dan samun kwanciyar hankalinki maybe mijinki ya soki."

  "No i can no do this, laifi zaiyi yawa laifi biyu ga laifin abinda na aikata ga laifin zubar da ciki no I can never do this."

 "Fee kiyi tunani wannan damar ce kawai zaisa Modibbo ya soki, idan yaso sai ki nemi gafara wajan ubangiji."


 Duk zuciyarta ce ke bata wannan shawarar shiru tayi tana tunanin shawarar da zuciyarta ke bata, daga baya ta sauke ajiyar zuciya ta ce.

 

  "Ok i will do anything indai har zaisa Modibbo ya soni ya janye maganar auranshi da Hindu......"


 *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA*  ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

___________________________________    _story and written by_

        *MRS OMAR*

 


     _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI*
       _page 67_
     *WASHE GARI*Balatoni ne da Hindu zaune a saman dinning table ,

 ga abinci nan a gabansu sai fama yake da ita amma taki ta kulashi ahankali hawaye ya fara bin fuskarta.


 "Ya salam haba Hindu meye abin kuka a nan daga magana."

Cikin muryar kuka ta fara magana.

 "Ya Modibbo dole nayi kuka kasan ko wacece gimbiya a wajena ni baiwarta ce bai kamata ace a sanadiyata zata dinga zubar da hawayenta ba, bayan ni baiwarta ce bani da wata daraja a gareta."

 Ɗan shiru tayi da maganar da takeyi yayin da suka kurawa junansu ido suna kallon juna, murmushi Balatoni yayi kafin ya cije lips ɗinshi.


 "Humm sanin kanki ne Hindu banida wata mafita da ta wuce yin haka please Hindu ki daure ki ida cika min alkawarin da kika ɗaukar min ba danni ba Dan Allah zaki cika min."

 Shiru tayi tana tunanin kafin daga baya ta ɗaga kanta.

 "Alright zan ida cika maka amma wallahi ina tsoron abinda zai biyo baya."

 "Humm ki cire duk wani tsoro a zuciyarki babu abinda zai faru."


 Murmushi tayi mashi mai cike da gamsuwa, Fee ce ke sakowa daga sama a hankali kamar mai tsoron taka k'asa, hijabi ne a jikinta yau har k'asa daga nesa ta hango su take ta ɗaure fuska kamar mai shirin kuka, a haka har ta isa wajansu cikin girmamawa Hindu ta gaisheta, fuska ta yatsina kafin ta dubi Balatoni cikin murya mai daɗi ta gaidashi.

  

 "Ina Kwana?

 Ko ya kalli inda take saidai ya amsa mata a takaice.

 "Lafiya"

Jiki a sanyaye ta fara magana dan jin amsawar da yayi mata.

 "Dama! Dama ina so zan fita ne zanje..."


 Bata k'arasa ba ya ɗago kai yana kallonta ganin haka yasa tayi shiru tana kallonshi, juyawa yayi yaci gaba da cin abincinshi cikin salo na masu aji, saida yakai cokalin abinci a bakinshi kafin ya kalleta ya yatsina fuska ya ce.

 

 "Alright you can go anywhere you wish to go because da dakike fita kina tambayan izinane? so yanzu ma kina iya tafiya wish you safe journey" 

 Sakin baki tayi tana kallonshi take hawaye ya fara fita a idanunta cikin sanyi murya ta fara magana.

 "Modibbo why are you doing this to me? did I deserved this from you?ya kamata ka fahimci cewa wannan kaddara ce agareni ka taimaka min badan ni ba kayi hakuri ko dan cikin da yake jikina." 


Murmushin takaici yayi kafin ya girgiza kanshi alamar jin haushin maganar da tayi mashi, cikin zafin zuciya ya fara bata amsa.

 "Wow! so you called this destiny? wannan ba kaddara bace ra'ayin ki ne to meye halak'ata da cikin da ke jikinki?"

 "Modibbo please listen to me."

 Cikin ɗaga murya ya daka mata tsawa.

 "Stop Fee just keep quite because i don't want to hear anything from you, I have already told that I must marry Hindu so why are you still disturbing, and this my last word to you I Modibbo will marry Hindu....."


Cak ya tsaya da maganarsa saboda ganin Adda da yayi a gabansu gaba ɗayansu jikinsu ya ɗauki rawa ba kamar Fee data tabbatar da Adda taji komai da suke faɗa.

 

 "Adda sannu da zuwa dama zakizo shine baki faɗa min ba."


 Tsaki Adda tayi kafin ta juya da sauri ta fita daga parlourn, take Fee ta sulali k'asa ta fasa wani irin kuka mai cin rai.


 "Na shiga uku shi kenan yau asirina da yake rufe zai tonu da wane ido zan kalli Mai Martaba?"


 Take taba Hindu tausayi duk da tasan itama tana cikin matsalar da tafi ta Fee ɗin dama Adda ba sonta take ba, ahankali ta iso wajan Fee tana shirin kamata da sauri ta ɗaga mata hannu da niyar dakatar da ita.

 

 "Dakata!!! Hindu kada ki kuskura wannan dattin hannun naki yayi gigin taɓa jikina."

 Harara Balatoni ya watsa mata kafin ya ce.

 "That is your problem, kadan ma kika gani yarinya." 


 Shiru tayi tana kallonsu dan ganin kwata,kwata ya rufe ido sai rashin mutumci yake mata.


 *AFTER 1 HOUR* 

 

Fee kuka take har yanzu Balatoni ko yace taci kanta bai ce ba, wayarshi kawai yake dannawa cikin kwanciyar hankali da alama kukan nata daɗi yake mashi, cak ya tsaya da danna wayar da yake dan ganin sunan Mai Martaba na yawo a screen ɗin wayar kamar yanda yayi saving sunan, ahankali ya ɗaga k'iran ko gaisawa basuyi ba Mai Martaba ya faɗi abinda zai faɗa mashi.

 "Modibbo kome kuke yanzu kuzo ku dukka ina son ganinku yanzu nan."


 Modibbo bai bashi amsa ba yaji kawai ya kashe wayarshi, take ya faɗa masu abinda Mai Martaba ya umarce shi da yayi yanzu, turkashi saura kaɗan Fee tayi mutuwar zaune, saboda tasan Adda ta faɗawa Mai Martaba duk abinda ya faru shiyasa yace suzo, tashi sukayi suka kama hanya yayinda Fee da Hindu jikinsu ke rawa saboda Hindu tasan yau abincin ta ya k'are a gidan, bayan sun shiga motar yaja da gudu basu wani ɓata lokaci ba suka isa masarautar SODANGI.

 Babban parlour Mai Martaba suka nufa suna zuwa suka ga kowa zaune a parlour da alamun su kadai ake jira, bayan sun gaisa Mai Martaba yayi gyaran murya kafin ya dubi Balatoni ya fara magana.


 "Modibbo duk naji abinda ke faruwa tsakaninka da FIDDAUSI shiyasa na tara wannan taron dan kowa yaji da kunnansa naji kana shirin auran Hindu to masha Allah bazan hanaka ba amma....."

 "Innalillahi wainna illahi rajun."

 Salatin da Gwaggo da Iya suka ɗauka shiyasa Mai Martaba yayi shiru yana kallonsu.

 "Fatsima shi kenan yau asiri zai tuno dole yau zamu buɗe wannan *ƁOYAYYEN AL'AMARIN* tun kafin abinda bamuso ya faru."

 "Dole ne Dijee yau mu tona wannan asirin."


 Gaba ɗayansu suka juya suna kallonsu Iya dan jin abinda zasu faɗi, Mai Martaba ne yayi magana a takaice.

 "Gwaggo Iya meke faruwa wane irin sirrine wannan ? zaku faɗi ai yakamata ku bari mu gama da wannan matsalar kafin nan sai ku faɗi abinda zaku faɗa."

 "Basher wannan sirrin shine keda alaka da wannan maganar dan yau dole sai mun tonashi."


 Cewar Gwaggo, Iya ta ce.

 

  "Gaskiya ne domin kuwa Hindu da Modibbo babu aure a tsakanunsu.."

 Take ɗakin yayi kamar an ɗauke wuta gaba ɗayansu suka zaro idanuwansu a waje ba kamar Hindu, Modibbo da Bahijja......


 *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA*  ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

____________________________________  _story and written by_

       *MRS OMAR*
     _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI*  


        _Page 68_


*HAUSAWA SUNCE RANAR WANKA..* *I*ya ta gyara zamanta kafin ta ce.


 "Basheer yau dole zamu faɗa maka abinda muka daɗe muna ɓoyewa hausawa sunce ranar wanka ba'a boyon cibi dan, haka yau zamu tona wannan sirrin da muka daɗe muna ɓoyonshi koka yarda ko karka yarda ya zama dole mu faɗeshi yau."

 

 Duk maganar da take yana fuskantar mahaifiyar tasa yayinda duk jama'ar ɗakin suka baza kunne suna jiran suji abinda zata faɗa.  

 *1986*


 _"lokacin da bazan tabba mantawa a rayuwata ba a lokacin da Bahijja na ɗauke da cikinta na farko, wanda duk jama'a dake masarautar nan sunyi murnar samun cikin, babu kamar Mai Martaba SODANGI sannan yana raye, yayi murna sosai da ganin Bahijja ta samu cikin, wanda a sanadiyar haka ne yasa Mai Martaba SODANGI ya k'ara son Bahijja, tunda Nana ta kyalla ido taga Bahijja na ɗauke da ciki ta kasa zaune ta kasa tsaye babu inda bataje ba dan ganin cikin ya fita amma bai fita ba, ranar da nagano abinda take ciki hankalina ya tashi sosai take nazo nasamu Basheer na faɗa mashi gashi _ gashi abinda naji Nana na shirin aikatawa amma da yake bai cikin haiyacinshi sai yaki yarda da maganar da na faɗa mashi, ya amsa ne kawai da to saboda a matsayina na mahaifiyarshi amma baiyi wani abu akai ba, tunda na gano haka na matsawa Bahijja tasa a kawo mahaifiyarta watau Fatsima domin ta dinga kulawa da ita, bayan Fatsima tazo duk na faɗa mata abinda ke tafiya ta tsorata sosai da jin haka amma na bata hakuri ta hakura, duk inda Nana zata shiga saida ta shiga domin cikin Bahijja ya fita amma cikin hukuncin ubangiji yaki fita, ana haka cikin Bahijja har ya shiga wata tara watau watan haihuwarta, tunda Nana ta tabbatar da Bahijja cikinta ya shiga wata tara hankalinta yasake tashi take kaiwa tana kawowa, wata rana na fito daga ɗakin Fatsima mungama hira zan koma ɗakina kawai naji Nana na waya bansan da wa take wayar ba abinda kawai naji tana faɗa mashi shine, idan ta haihu ka tabbatar da duk yanda zakuyi kuyi dan ku kashe abinda ta haifa bana son abinda ta haifa ya rayu, nima ban haihu ba to babu wadda ta isa tazo ta haihu a masarautar SODANGI. Abinda naji tana fada kenan, tunda naji haka hankalina ya sake tashi, take na koma na faɗama Fatsima duk abinda naji tana faɗa, bayan anyi wannan ya wuce da sati ɗaya Bahijja ta fara nakuda haka muka ɗauketa muka kaita asibitin *F.M.C* muna zuwa bata wani ɓata lokaci ba Allah yasauketa lafiya, dama tun kafin akawota asibitin na kira doctor Abdul na faɗa mashi duk abinda ya faru sannan shi yatsara mana duk abinda za'ayi, bayan ta haihu doctor Abdul ya fito ya faɗa mana ga baki ɗayanmu harda ku, cewar Bahijja ta haihu da namiji saidai baizo da raiba, babu wanda baiji mutuwar ɗan nan ba, sannan mai Martaba SODANGI yace kawai a rufeshi nan cikin asibitin basai an kawoshi gida ba, dagamu har doctor munji daɗin hakan da yace, bayan mun koma gida muka sake dawowa nida Fatsima sannan doctor Abdul ya nuna mana abinda Bahijja ta haifa munyi murna sosai sannan muka yanke shawarar zamu bada rainonshi idan yakai shekara biyu sai mu amsai, haka ko akayi doctor Abdul shiya amsheshi ya kaiwa kanwarsa shi yabashi suna da *MUHAMMAD* saida ya cika shekara biyu sannan Fatsima tazo mukaje muka amsai muka yanke shawarar Fatsima ita zata ɗaukeshi sannan duk wanda ya tambayeta ɗan waye tace ɗan wata yar uwarta ce dake Cameron ta ɗauko, sannan Fatsima ta bashi suna da Modibbo saboda sunan Mai Martaba SODANGI ne aka bashi._


 "Modibbo dama ɗan sarki ne!!!!"

 Gaba ɗayansu suka haɗa bakin cikin tashin hankali, Gwaggo yanzu ita ta amshi maganar ta ce.


 "Tabbas Modibbo shi ɗan basheer ne."

 Duk ɗakin jikinsu yayi sanyi dan jin wannan maganar amma banda Adda daketa raba ido, cikin sanyin murya Mai Martaba ya ce 

 "To kunce tsakanin Hindu da Modibbo babu aure ko zaku faɗa min dalilin?"

 "Dole ko zamu faɗa maka domin kuwa abinda ya faru shine...."

 Da sauri Gwaggo ta tsaida Iya ta hanyar ɗaga mata hannu.

 "Dakata Dijee ni yakamata na bada wannan labarin.

 "To Fatsima."


 Duka ɗakin yayi shiru suna jira suji abinda Gwaggo zata faɗa. _"Tun bayan haihuwar Bahijja bata k'ara haihuwa ba har kusan shekara goma, hankalinta ya tashi sosai bama ita kadai ba dukka jama'ar masarautar nan, har ana tunanin bazata k'ara haihuwa ba, saida ta cika shekara goma sha biyu, kwatsam rana ɗaya Bahijja ta waye gari bata da lafiya bayan an kaita asibiti doctor Abdul ya tabbatar da tana ɗauke da ciki, murna ba kaɗan ba akayi saidai a lokacin Mai Martaba SODANGI Allah yayi mashi rasuwa, aikam tunda Nana ta samu labarin Bahijja ta samu ciki hankalinta ya sake tashi sosai, burinta kawai taya zata samu ta nakasa Bahijja saidai tunda Bahijja ta samu cikin bata da lafiya kullum laulayi take, haka yasa na sake zuwa na zauna da ita, lokacin da Bahijja tafara nakuda mukaje muka k'ara samun likita dan mukara yin irin na Modibbo saidai wannan kara doctor Abdul ya ce bazai yuwuba, saboda Bahijja na ɗauke da ciwon zuciya idan har aka k'ara cemata cikin dake jikinta baizo da raiba zata iya zamun matsala ana iya rasata baki ɗaya, tunda mukaji haka muke neman mafita ranar da akakai Bahijja asibiti haihuwa ranar aka kai Kanwar doctor Abdul watau wanda ta raini Modibbo saidai ta riga Bahijja haihuwa tana haihuwa Allah yayi mata rasuwa, munyi jimamin mutuwarta sosai ba'a daɗe ba Bahijja ta haihu lokacin da ta haihu doctor Abdul ya kawo shawara a masanya Yaran tunda duka mata suka haifa mukace mashi babu matsala yace ba wata matsala, daga baya yace dole yace yarinya marigayiya ta rasu domin a samu yarinyar Bahijja itama ta girma cikin masarautar mahaifinta, amma dole a kaita a gidan marayu idan tayi wayo a amsota, haka aka sauya FIDDAUSI a matsayin ɗiyar Bahijja Hindu ta dawo a matsayin baiwa bayan ta cika shekara biyu muka amso Hindu a gidan marayu, Hindu itace diyar Bahijja ba FIDDAUSI ba..."_


 "Innallahi wainna illaihi rajun.!!!"

 Gaba ɗayansu suka ɗauki salati.


 "Wannan wane irin *B'OYAYYAN AL'AMARI NE*? mai cike da rikitarwa yanzu dama FIDDAUSI ba ita bace ɗiyata? ɗiyar Kanwar doctor Abdul ce ya salam."

 Cewar Mai Martaba take duk jama'a dake ɗakin jikinsu yayi sanyi hawaye keta zuba fuskar Hindu,Fiddausi, Modibbo, Mai Martaba ya ce.

 "Yanzu kenan FIDDAUSI itama babu aure tsakanunsu?"

 "Akwai auri tsakanunsu mana Ko kamanta."

 Da sauri suka ɗago kai suna kallon mai maganar.

 "Yauwa doctor Abdul gara da kazo ayi wannan maganar da kai."


 Cewar Gwaggo.


 "Dama nasan wannan ranar zatazo, Mai Martaba ka manta tun lokacin da Bahijja ta haihu kwata_kwata ruwan nononta ya ɗauke babu irin maganin da bamu bata ba amma yaki zuwa haka yasa muka hakura muka dinga bata madara tana ba babyn, a haka FIDDAUSI har ta isa yaye amma FIDDAUSI batasha nonon Bahijja ba ko sau ɗaya."

 "Alhamdullilahi!!!!"

Gaba ɗaya ɗakin ya ɗauka

 "Wannan ai maganar banza ce wallahi k'arya kuke baku isa ba."

 Adda ce ta tashi tana borin kunya yayinda mai Martaba ya wanka mata lafiyayen mari.

 "Mahaifan nawa kike cewa suna maki k'arya?"

 "Eh nace domin kuwa cikin dake jikinta ba nashi bane shege n..."

 Bata karasa ba Modibbo ya tashi cikin fushi yana huci yace

 "Adda don't you dare call my unborn child shege,did you get it?........


 *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

 ★.   *TAK'AMA*  ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

________________________________


  _story and written by_

      *MRS OMAR*   _in dedication to_

 *FIDDAUSI SODANGI* _ina mai ba masoyan wannan Littafi hakuri akan mistake ɗin da aka samu na number 66 akan zan rubuta number 66 sai na rubuta number 67 nayi tsallakin number ɗaya kenan a gafarce ni_
       _page 69_

   *M*odibbo na huci kamar zai duke Adda yaci gaba da gaya mata magana.


 "Abinda kika so ya faru Adda bai faru ba da yake kinsan Allah baya barci, humm wallahi Adda nayi mamakin wannan halin naki ashe dama har yanzu akan samun masu hali irin naki?"

 "Modibbo wai meke faru wane?"


 Cewar Mai Martaba, Modibbo ya juya ya kalli mahaifin nasa kafin ya koma inda yake zaune ya zauna, cikin sanyin murya kamar zaiyi kuka ya fara basu sharhin abinda ya faru.


 _"Tun ranar da aka ɗaura min aure da Fiddausi ba mu taɓa zaman lafiya da ita ba koda na sakan ɗaya ne, kullum acikin faɗa muke babu ranar da bamu faɗa, wata rana Hindu ta fuskanci faɗan namu yayi yawa sai ta same ni har ɗakina take ban shawarar mezai hana na koma makaranta tunda abinda yasa Fiddausi ke min haka duk dan taga banyi karatu bane sosai, da Hindu ta bani wannan shawarar na zauna nayi tunani sai naga ai wannan shawara ce mai kyau tunda dama nayi makaranta a k'auyenmu har secondary school na gama saidai kunsan karatun k'auye ba wani turanci ake koyawa ba saidai wanda ba'a rasa ba, Hindu itace tasa ni a gaba da taimakonta tasamamin admission a Yar'aduwa university, naji daɗi sosai da yake inada saurin ɗaukar abu komawa karantun bansha wata wahala ba, haka yasa nasa Hindu ta ɗaukar min alkawarin bazata faɗawa kowa ba har sai lokaci da na kammala kafin wani ya sani, sannan a koda yaushe tare zamu dinga fita ko Allah zaisa Fiddausi ta fara kishin fitar da muke, amma da yake bata cikin haiyacinta shiyasa kwata _ kwata bata jin haushi fitar da mukeba, wani lokaci an bamu hutu na sati biyu da naga na samu lokaci sai nace bari kawai na shirya na tafi Yola tunda dama na kwana biyu banje ba, haka nazo na samu Fiddausi daniyar itama ta shirya mu tafi tare amma tace min ita bazata ba haka na hakura na tafi ni ɗaya, tunda na isa hankalina yak'i kwanciya kullum tunanin dawowa nake, ranar da nacika sati ɗaya da tafiya ranar hankali ya k'ara tashi sosai da yamma nacewa Gwaggo nidai zan koma gida babu yanda batayi dani ba akan na bari sai gobe amma nace a'a haka ta hakura ta barni na kama hanya, abin mamaki ina isowa cikin garin Yola kawai sai ga wata bakowar number an kira ni da ita bayan na ɗaga tace min ai Anum ce kawar Fiddausi nayi mamakin ganin kiranta daga nan nake tambayar lafiya dai ko?, babu abinda Anum ta ɓoye min gami da zuwansu gidan Boka da abinda suke so ya faru tsakanin Fiddausi da Affan ita kuma abinda yasa kawai tace gara ta faɗa min saboda mafarkin da take yawanyi na ban tsoro, gashi Boka ya gano tana tare da Affan, shiyasa yayi ikirarin zai kasheta to ita gara Boka ya kasheta a bisa abinda take gani, nan ta faɗa min duk yanda Boka yace suyi tun daga farko har ya zuwa maganin da yaba Affan ya saka mata ga abin sha, bayan ta gama faɗa min nace mata ina hanya idan na iso zan kirata, haka ko akayi ban iso garin nan ba sai da safe wajan goma ina isowa na k'irata ta same ni muka tsara duk yanda ya dace, bayan Affan yaba Fiddausi maganin tasha ya ɗauketa ya kaita ɗakinta saidai ya manta bai rufe k'ofa ba, shiyasa ina zuwa na tura k'ofar ta buɗe, yana k'okarin cire mata kaya na isa gabansa yana ganina hankalinshi ya tashi sosai, nayi niyyar kai mashi duka sai wata zuciyar tace kada nayi haka, cikin ilimina da Allah ya bani na zaunar dashi na dinga mashi nasiha da yake Allah ya kawo karshen abin haka jikin Affan yayi sanyi daga baya ya duka har k'asa ya bani hakuri sannan ya ɗaukar min alkawarin zai bar k'asar kwata _ kwata kuma bazai k'ara k'iran Fiddausi ba, ya ɗaukar min alkawarin zai auri Anum da zarar ta gama karatu, a ranar Affan ya haɗa kayansa ya wuce India, bayan ya tafi na dinga tunani to me zanyi yanzu wanda Fiddausi zata manta da Affan har Abada taji ta tsaneshi a rayuwarta, can wata zuciyar tace ga abinda ya kamata kayi babu muso na ɗauki shawarar da zuciyata ta bani, a haka tana kwance batasan inda kanta yake ba nashigeta, bayan na gama abinda nake da ita dan ta tabbatar da Affan yayi mata wannan aikin na tashi na bar gidan na tafi gidan abokina wanda muke makaranta ɗaya dashi, a can gidan nasa na rubuta letter na kaiwa mai gadin gidan Affan nace idan kinzo ya baki yace inji Affan kada ya nuna maki nina bashi haka ko akayi, bayan na dawo washe gari nasan halin da kike ciki amma na nuna bansan komi ba, yanayin tafiyar da naga kinayi kin bani tausayi sosai saidai nace bari nima na rama abinda kike min kema kiji da daɗi, Hindu kuma da kike tunanin zan aureta to wallahi ba auranta zanyi ba duka duk yana cikin plan din da na tsara,amma babu komi tsakanina da Hindu kawai dai ina mata son yan uwantaka ne, to duk kunji abinda ya faru._ "Munafiki k'arya kake wannan cikin ba naka bane Affan da kansa ya k'irani yace aiki yayi...."

 "Ba gaskiya bane nayi hakane kawai dan ki fita harkar Fiddausi sannan nasan zaki tsaya da zuwa wajan Boka saboda yace idan har muka saba aikin to Fiddausi zata dawo haiyacinta ni kam yanzu na tuba da abinda nake."

 

 Da gudu tayi kan Affan taci mashi kwallar riga tana faɗin.

 "Ni zaka ci amanata to wallahi sai naga bayanka idan yaso sai ka kwaci kanka idan na koma wajan bokan."

 Mai Martaba ya tashi da sauri cikin fushi ya fincikota ya wanka mata mari take hawaye ya fara fita a idanunsa yana magana yana nunata da yatsa.

 "Wallahi kin bani mamaki kin cuci kanki dan karshen zamanki gidan nan yazo a tarihin masarautar nan babu matar da aka taɓa saki amma ni yau zan fara a kanki, dan haka na sakeki saki uku! sakin da bazaki taɓa dawowa ba har abada."


 Cak tayi mutuwar tsaye take maganar da Boka ya faɗa mata ta dinga dawo mata a kunne.


 "Kada ki bari aikin nan bayyi ba idan har aka kuskure wannan aikin akwai matsala duk ranar da mijinki ya gane gaskiya ya sakeki to daga ranar zaki fara hauka a haka zaki k'are rayuwarki a hauka."


 Dariya ta kwashe da ita tana faɗin.


 "Kasake ni? kai wallahi ban saku ba hhhhhh wai kunji ya sake ni, har fa Mairo na kashe duk dan kada ta tona min asiri kunji wai ya sake ni."


 Ɗan kwalinta tacire tayi jifa dashi tana shirin guduwa Mai Martaba yasa su Balatoni su riketa dukda sun gano ta haukace, wayarshi ya jawo ya danna number yan sanda, ba'a wani ɓata lokaci ba suka iso cikin parlour nasa, take ya basu umarnin sukamata yace masu itace ta kashe Mairo sannan yanaso ta k'are rayuwarta a gidan yari, haka ko aka tafi da ita Mai Martaba ya bada umarni.

  

 "Na godewa Allah da Allah yasa inda magaji ashe dama Modibbo ɗana ne na cikina Hindu kema ɗiyata ce ashe?"


 "Shiru yayi yana kallon Fee yayinda hawaye keta safa da marwar fita a idonta kai Mai Martaba ya girgiza kai kafin ya ce.

 "Fiddausi ki daina zubar da hawayenki wallahi har yanzu kina a matsayin da kike har yanzu ke ba sarakuwa ta bace ke y'ata ce, masha Allah mungodewa Allah da yakawo karshen wannan al'amari, sannan Hindu daga yau ta dawo gidansu bazata k'ara komawa gidanku ba Modibbo ka ɗauki matarka ku koma gida Allah yayi maku albarka, na kuma godewa Allah da ya azurtani da iyaye na gari kamarku Gwaggo."


 Dariya sukayi kafin daga baya aka rufe taron da addu'a, yayinda Mai Martaba yacewa Modibbo su tashi su koma gida tunda suka shiga mota Fee take kuka yayinda kanta ke k'asa, saida suka isa gidansu yayi parking kafin yasa hannu ya jawota jikinshi a hankali yake raɗa mata.


 "Haba *MRS SODANGI* why are you crying? please stop crying kinsan bana son ganin hawayenki."

 Da sauri ta ɗago kai tana kallonshi, take ya kashe mata ido ɗaya ya sa hannuwansa ya tallaɓo fuskar tata yana kallonta ido cikin ido take yasa harshe yana lashe hawayen dake fita idonta........


  *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA* ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

________________________________


  _story and written by_

       *MRS OMAR*  

    _in dedication to_

  *FIDDAUSI SODANGI*

      _Page 70_

 

*B*aki ta saki tana kallonshi ɗauke da mamakin yanda yake lashe hawayenta da bakinsa, fuskarta ta juya da sauri gefe ɗaya hannu yasa ya k'ara jawota jikinshi yayinda suna jin saukar lumfashin junansu, cikin murya mai daɗin gaske ya fara raɗa mata.

  

 "Baby ko har yanzu zuciyarki bata amince dani ba ne? please Baby Accept me as your husband, ya kamata yanzu ki gane komi ya wuce yanzu muyi sabuwar rayuwa ba kamar na baya ba."

Shiru tayi bata bashi amsa ba yayinda take sauke lumfashi ahankali, shi kuma fuskarshi ya ɗaura a kan k'irjinta yayinda hancinshi ke tsakankanin na shanunta yana shakar k'amshin turaren da yake jikinta, ahankali ya lumshe idannunsa yana k'ara shakar kamshin turaren jikin nata, Fee da taji shirun yayi yawa yasa tayi saurin zame jikinta daga nashi ta buɗe k'ofar mota zata fita da sauri ya ruko hannunta cak ta tsaya yayinda taji wani abu na mata yawo a jiki, sakinta yayi ya fito daga cikin motar ya zagayo wajanta cak taji ya ɗauketa.


 "Daga yau bazan k'ara bari a dinga wahalar min da Baby ba dan haka ni zan dinga ɗaukarki duk inda zaki."

Ido ta zaro take ya kashe mata ido ɗaya haɗi da ɗaga gira ɗaya, babu inda Balatoni ya sauke Fee sai bedroom ɗinta, yana sauketa ya juya zai bar ɗakin da sauri ta gudu ta rumgomushi ta baya, kuka ta fashe dashi cikin muryar kuka ta fara magana.


 "Am sorry ya Modibbo please don't live me i promise you daga yau bazan k'ara maka duk abinda na diga yimaka a baya ba, na yarda na amince *KAINE SIRRINA* ka cancaci duk wata mace da ta soka kai namijin nan ne da ko wace mace zatayi alfahari dakai, nagodewa Allah da Allah yasa ban *TAFKA BABBAN KUSKURE* ba da *NAYI NADAMA* babba a rayuwata, please Yaya Modibbo kayi min alkawarin komai wuya muna tare kamar yanda *HALEESA* ta ɗaukarwa *YAYA HABEEB* alkawari nima inaso ka ɗaukar min wannan alkawarin."


 Wani irin daɗi ne Balatoni yaji ya ziyarce shi sai yaji gaba ɗaya ta sakar mashi kasala, ahankali yasa hannunsa ya juyo da ita a gabanshi yana kare mata kallo take ranar farko da ya kusance ta ya dinga tunowa, da sauri ya jawota jikinshi ya rungometa yana maida lumfashi ahankali.

 

 "Baby na amince maki karki manta ke *JININ JIKINA CE* duk ranar da ɗayanmu ya kauce to daga ranar nasan za'a samu matsala, akoda yaushe burina shine ki amince dani to nagodewa Allah da ya nuna min wannan ranar Baby na ɗaukar maki alkawarin komin wuya muna tare ke kuda kuwa *BAN SAN ASALINKIBA* bale muna tare HAR ABADA, nima ina so ki ɗaukar min alkawarin zaki ban zumar da nasha ranar nan kina barci."


 Wata irin kunya taji ta kamata, k'ara shigiwa tayi cikin k'irjinshi tana dariya ahankali, hannu yasa ya ɗagota ahankali ta lumshe ido sai taji wata irin kunyarshi takeji yanzu.


 "A! yau kuma kunyata akeji bayan an gama yimin rashin kunya a baya."

 Kuka ta fara yin mai irin na shagwaɓa tana dira kafa ido ya zaro waje ya ce.

 "Bakin ciki kike min da Babyna shiyasa kikeso ki bashi wahala ko?"

Dariya tayi taga ya k'ara bata wata kunyar da sauri ta juya tana shirin barmashi ɗakin yasha gabanta ya k'ara fincikota jikinshi, ahankali ya raɗa mata.

 

 "Ina zaki Maman Biyu ko bakya son jin dimin mijinki ne a kusa dake, kinga yanzu yunwa nakeji ki shirya muje restaurant muci abinci wajan nada kyau can muke tsayawa muci abinci nida tsohuwar budurwata Hindu."

 Muntsili takai mai saboda tasan zaulayarta yake, shima cikin irin wasan nan yace 

 "Wash."

 Dakyal Fee ta samu ta zame jikinta daga nashi ta gudu ta nufi toilet, dariya yayi ya girgiza kanshi kafin shima ya nufi k'ofar fita ɗakinshi ya nufa.******************


Mai Martaba ji yake kamar ya goya Hindu saman bayanshi dan murna saidai yana tausayawa Fiddausi, Bahijja kanta tayi murna sosai sai yanzu ta gane ashe Hindu ba tausayinta take ba aduk lokacin da ta ganta cikin damuwa hankalinta ya tashi, ashe sone Hindu ke mata irin na ɗa da yake nunawa uwarshi, bayan sun fito daga parlour Mai Martaba, ɗakin Bahijja suka sake nufa yayinda suka dasa wata sabuwar hira, Bahijja ta ce


 "Nagodewa Allah da Allah ya bani ɗiya kamar Hindu, ɗiyace da ko wace uwa zatayi alfahari da ita."

 "Gaskiya ne maganarki Bahijja."

Cewar Gwaggo da Iya, hawaye ne suka fara sauka fuskar Hindu da sauri Bahijja ta jawota jikinta tana tambayarta.

 

 "Haba Hindu me yayi zafi badai wannan maganar da nayi bace ta ɓata maki rai?"

 Kai Hindu ta girgiza alamar a'a.

 "Mom ba abinda yasani kuka kenan ba, ina tunanin halin da Fee take ciki, da tasamu wannan labarin, Mom inaso ki ɗaukar min alkawarin har yanzu Fee na a matsayin ɗiyarki kamar da babu abinda ya sauya."

Ajiyar zuciya Bahijja ta sauke, kafin ta ɗago y'ar tata tana kallonta ta ce.

 "Hindu wallahi har cikin zuciyata har yanzu Fiddausi nanan a matsayin da take babu abinda ya sauya, dole naso Fiddausi domin kuwa yanzu bata da, kowa inba doctor Abdul ba mahaifiyarta da mahaifinta dukkansu basa duniya bata san ko ɗaya a cikinsu ba, mu ta sani tun tana yarinya dan haka kisaka a ranki Fiddausi y'ata ce."

Dariya Hindu tayi sannan ta godewa Allah da yabata uwa kamar Bahijja, haka sukaci gaba da hira cikin kwanciyar hankali.


 ***

 

Balatoni da Fee basu dawo gida ba sai dare suna can suna yawon shakatawa, suna dawowa ɗakinshi ya nufa da ita bata so ba amma babu yanda ta iya haka ta hakura, suna shiga ɗakin ya bata umarnin da tashiga toilet ɗinshi ta watsa ruwa sannan ta ɗauro alwala daga can, da zata fara gardama ya ɓata fuska dole tatashi tayi abinda yace da ita, bayan ta fito ya aje mata ɗaya daga cikin rigar barcin da suka saya yace ta saka, shi kuma ya nufi toilet babu musu ta ɗauki rigar ta saka a jiki babu laifi dukda tana rigar barci tayi mata kyau, bayan Balatoni ya fito daga toilet suka tada sallah bayan sun gama yayi masu addu'ar samun zaman lafiya, dama already sunci abinci kafin su dawo gida yana gamawa babu wata_wata ya ɗauketa babu inda ya sauketa sai kan bed ɗinshi, take jikinta ya fara rawa sai ta ɗinga tuno zafin da ta ɗinga ji na ranar farko dukda bata cikin haiyacinta yayi amma taji zafi da ta farka, bayan ya kwantar da ita saman gado sannan shima ya cire jalabiyar dake jikinshi ya haura saman gadon, ido ta lumshe da sauri murmushi yayi sannan ya kashe wutar ɗakin ya jawota jikinshi, cikin zafi_zafi ya fara shafata har jikinshi na rawa, nan danan hankalin Fee ya fara tashi sai ta fara kuka cikin sanyin murya ya fara bata hakuri.

 

 "Haba Baby please help me just one's, ko kina so na fara neman matan banza ne?"

 Kai ta girgiza dukda ya kashe wutar ɗakinkin amma ya gane saboda kanta da yake jingine da kirjinshi.

 "Yauwa Baby wallahi bazan iya hakuri ina kallonku haka ba, a baya ma hakuri kawai nake ina dakewa ne, amma tun ranar da nasanki a ɗiya mace nakejin wani irin sonki na k'ara shiga zuciyata, please ki amince min Baby kin amince Baby?"

 Kai ta ɗaga mashi alamar eh, hamdalah yayi kafin ya fara wasa da sassan jikinta,saida ya ɗauki mintina yana wasanni da ita kafin daga baya yatafi... Fee ita kawai tasan azabar da take ji tun tana kukan zuci har ya fito fili, Balatoni sai yaji yau tafi ranar farko, haka Balatoni ya dinga bata wahala yama manta tanada ciki, Balatoni ya kai awa uku kafin yabar Fee ta huta ahankali yake maida lumfashi yayinda ita kuma hawaye keta fita idonta, bayan ya huta ya ɗauketa cak ya nufi toilet da ita ruwa masu zafi ya sakata aciki kafin daga baya yayi mata wanka bayan ya gama mata yayima kanshi ya fito da ita ya kwantar da ita saman bed shima ya kwanta yaja masu bedsheets.


 *****


 *BAYAN WASU LOKUTA*


Haka rayuwar Balatoni da Fee ta zama gwanin sha'awa duk inda ka gansu tare, dukda Balatoni Allah yayoshi irin mazan nan ne masu yawan sha'awa amma Fee takanyi k'okarin bashi hak'inshi.....


   *MAZA DA MULKI*

★★.   _MATA DA_ ★★

 ★.    *TAK'AMA*  ★

NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

___________________________________   _story and written by_

       *MRS OMAR*     _in dedication to_

   *FIDDAUSI SODANGI*     


   _*THE LAST PAGE*_O

 *AFTER SIX MOMENT* *F*amily ɗin masarautar SODANGI ne gaba ɗayansu tsaye a asibitin doctor Abdul duk wanda ka ganshi baki a buɗe yana murna, doctor Abdul ne ya faɗa masu cewa Allah ya sauki Fee lafiya ta haifi yan biyu mace da namiji, murna wajan Balatoni ba'a cewa komi kamar ya taka kan jariri, basu wani daɗe a asibitin ba doctor Abdul yabasu Salama suka koma gida yayinda Mai Martaba ya wuce gida da jama'arshi, Gwaggo da Iya cewa sukayi babu inda zasu suna wajan mai jigo har sai anyi suna kafin su wuce, Balatoni ko kunyarsu Iya bayayi koda yaushe yana lik'e da matarshi, tun Fee najin kunya har itama ta fara biye mishi, Hindu kuwa tun komawarta gida Mai Martaba ya ce ta maye gorbin Fee ta wuce makaranta China bataso zuwa ba amma haka ta hakura ta tafi, tasamu labarin haihuwar Fee tayi murna sosai taso tazo saidai suna exam haka ta hakura saidai waya kawai da suke da mai jigon,

yau takama ranar suna yara sunci sunayen kakaninsu BAHIJJA ana kiranta da AMEERA sai uwa uba mai Martaba watau BASHEER ana kiranshi da AMEER, suna ake na gani na faɗa shagali ake sai wanda ya gani dan kuwa gidan har ba masaka tsinke ko ina jama'a ne doctor Abdul da matarshi Affan da amaryarshi Anum duk sunzo, haka akayi suna na gani na faɗa, bayan taro ya watse Affan da Anum sukazo suka k'ara basu hakuri abinda ya faru a baya....


******


 *BAYAN SHEKARA DAYA*


Rayuwa tayi daɗi duk gidajen da kaje suna cikin murna da farin cikin, banda Adda da take ta fama da hauka a gidan yari tun 'yan uwanta na zuwa dubata har suma suka gaji suka daina zuwa,

 Balatoni ne da Fee kwance a ɗakin da yaransu sun k'ura masu ido suna kallonsu yayinda yaran ke barci abinsu, Balatoni yayi murmushi ya jawo Fee jikinshi yana rada mata.

 "Do you know something Fee?

" No dear"

"I think I almost made a great mistake in my life and that mistake is losing you in my life, Fee I love you and I will keep loving you till the end of my life"

Murmushi tayi itama kafin ta k'ara shigewa cikin kirjinshi.

"Thanks mijina I love you too,inaso wannan soyayyar tamu ta zagaya dukka duniya, a koda yaushe ina mai godewa Allah da yabani miji nagari kamarka."

Dariya yayi cike da jin daɗin maganar da tayi masa ya k'ara rungomota jikinshi yana kiss dinta ta ko ina,da sauri na bar masu ɗakinsu nayo waje abuna...
*ALHAMDULILLAHI*Toh makaranta littafin *MAZA DA MULKI MATA DA TAK'AMA* anan nakawo k'arshen wannan littafin mai suna *MAZA DA MULKI MATA DA TAK'AMA*, idan nayi kuskure a cikinsa ubangiji Allah ka gafarta min, idan kuma na fad'a dai dai toh Allah kabani lada!!!


Thank u very much to all my "FANS" I Luv all


*JINJINA* ga 'yan group d'ina Facebook & WhatsApp MRS UMAR HAUSA NOVELS ina alfahari daku..


_UWA MABA MAMA JINJINA GAREKI K'UNGIYARMU MAI TAKEN *NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION,* gaskiya kuna k'ok'ari a garemu, mungode sosai_


Gaisuwa ga abun alfaharina:-

Munay

Zarah bb

Mamu

Queen Meemi

Sdy jegal

Fido Yar ficika

Ayshat one

Feenat Ja'afar

Maryam Abdul

Fati Bb

Ashnur 

Mom fatu

Zahra bukar

Da duk wanda ban samu na kira sunansu bah, wallahi kuna raina,


Gaisuwarku ta dabance aminan arzik'i

SADEEY S ADAM

BEEBAH LUV

AUNTY SIS

AUNTY MAIJIDA MUSA


hummm ai ke taki ta dabance my sweetheart *JIDDA ALIYU* hak'ika yanzu kin wuce k'awa sai dai na kiraki 'yar uwa, saboda banda bakin yimiki godiya sai dai nayi maki fatan alkairi thank u very much sweet i will never ever forget you in my life,


ina kike k'awalita wannan novel naki ne KE D'AYA watau *FIDDAUSI SODANGI* ina alfahari dake tawa,


'Yan uwana masoyana Khadija Umar Aisha Ibrahim maman lukman maman ummi maman jine saratu Ali bukar Maman Na'im ina gaisuwa


 ai ko gaisuwarku ta dabance kawayen kirki idan nace ina da kamarku a 35bn army barrack nayi karya ku kawaye ne na amana shiyasa na baku kyautar wannan page din

SAMIRA UNCLE D 

MAMAN AFFAN

MAMAN DADDY

AYSHAT MUSA BAJI

Allah ya barmu tareSai kuma kun jini a sabon littafina mai suna *DA BANSAN ASALINTA BA*zaizo maku nan bada jimawa ba,


Masoyana dan K'arin bayani ko kuma k'orafi, zaku iya nema na number kamar haka


*08021084887*


Tags: #soyayya #qauyanci #nadama
19246
0
1
2
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!