Matata Ce!

Written by Rabiatu Mashi SkPublished on 2018-12-12 15:02:15Category FictionBautar ƙasa ne ya kaishi ƙauyensu, aka bashi aurenta cikin rashin gata saboda iyayen riƙonta sun ƙosa da ita, sunyi rayuwar aure harna wani lokaci yana bata farin ciki, kafin ya gama bautar ƙasar sa ya gudu ya barta da cikin ƴarsa. Aikatau ta samu a birni, a gidansu tsohon mijinta a lokacin da shi harya sake wani auren yabar ƙasar shi da matarshi, soyayya ce mai tsanani ta shiga tsakaninta da ƙanenshi daya karbeta a matsayin ƴar ƙauye kuma bazawara, ga kuma igiyoyin auren yayanshi a kanta, Yaseer yace MATATAH CE, Najib ma yace SAUDE MATATAH CE, shin matar waye a cikinsu?? tags: #matatace #Najib #saude #yaseerDuba was labarai »

Copied By

HAYATU BABA ZUBAIRU

    (admin

  Arewa hausa novels 

    Novels villa

   Duniyan novels 

  Hayat hausa novels

Hausa novels and fashion

     And 

Cool novel, makeup and cooking) 


   WHATSAPP NO:

  +2347039625239

[3/7, 12:04 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

        1-5


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


GODIYA

  Ta tabbata ga ubangiji mahaliccin sammai da k'assai, daya bani ikon fara rubuta littafinnan, ya Allah ka bani ikon gamashi lafiya, ka yafemun kuraren dake ciki, Ameen ya Rabbi


www.babymsh.blogspot.com


  Kuka takeyi tun bayan da en tsirarun mutanen da suka rakota suka tafi, kuka take wanda tunda aka haifeta bata taɓa yin irinshi ba, duk da tunda tayi wayau bata taɓa tsallake rana ɗaya ba ba tare data zubda hawayen bak'in ciki ba, yau kukan nata har yaso ya k'arar da hawayen nata, ga wani irin shesshek'a da takeyi,

  Sallamar da yayi ne ya sanyata tsagaita kukan, a hankali ta fara k'ok'arin share hawayen nata duk da kukan yak'i tsayawa,

  "Har yanzu dai kukannan kike Saude?" ta share hawayenta cikin murya kuka tace "na daina fa"

  "Yauwah ko kefa, ay saiki saka kanki yayi ciwo, ga gajiyar hidimar biki kuma"

 "Idan banyi kuka ba Uncle Yasseer waya kamata yayi?"

  "kina kuka don an haɗaki aure da mak'iyinki ko?" da sauri ta fara girgiza kai "A'ah wlhy ba haka bane, kawai dai abunne na k'onamun zuciyah, ban tunanin duk duniya akwai macen da aka taɓa ma wulak'antaccen aure irin nawa, kayi hak'uri nasan kaima ba sona kake ba lik'a makani kawai akayi, don babu ta inda muka dace"

  "Who said so? Ke kyakkyawah ce saude, kina da kyawawan halaye, Ina sonki saude, fiye da yanda kowa zai soki a duniyarnan, kuma ban tunanin akwai macen dana dace da ita bayanke, idan kuma kina ganin akwai inda bamu dace ba ki faɗa mun sai in gyara"


  "Akwai babban banbanci fa tsakaninmu, ni ina er k'auye, kai kuma ɗan birni kuma ɗan gayu" shiru yayi yana k'ara mamakinta, maganganun saude, wayonta da zurfin tunaninta sunfi k'arfin shekarunta, ya nisa sannan ya fara bata amsa,

  "Tohh yanzu ba gani a k'auyen ba? Kinga mun zama ɗaya kenan, kuma idanna gama bautar k'asana ai dake zan tafi birnin, kema ki zama er birni, ki daina tunanin akwai banbanci a tsakaninmu, babu wanda yafi wani a wurin Allah, sai wanda yafi tsoronshi" ɗaga kanta tayi tana share hawaye, maganganunshi sunyi tasiri sosae a zuciyarta, 


Hannu ya saka yana tayata share hawayen "kin daina kuka daga yau Saude, bai miki kyau, hawayen farin ciki kawai nakeson gani a fuskarki" ya jawota zai rungume a k'irjinshi, ta fara togewa tana tureshi, duk da jikinta yayi sanyi tun sanda ya fara share mata hawaye,

  "bakison in taɓaki?" ta ɗaga mishi kai,

 "Ai ba wani abu an miki ba kinji ki saki jikinki dani kinji, duk sanda kike cikin damuwa, anan ne ya kamata ki kwanta kiyi kukanki, duk da bazan taɓa bari ki shiga damuwa ba" ta ɗago tana kallonshi yana nuna mata k'irjinshi da hannu, ya k'ara jawota zai haɗata da jikinshi, ta mak'ale kafaɗa duk ta takure, ya saketa kawai "shikenan tashi kiyi alwala muyi sallah, nima bara inyo"

  "nayi sallah fa" 

 "wannan ta musammance zamuyi, domin mik'a godia ga Ubangiji, da kuma neman albarka a cikin auren namu" kai kawai ta ɗaga mishi, ya tashi ya fara fita, maida kai tayi ta jinginar tana tunanin rayuwarta ta baya, da kuma haɗuwarta da Uncle Yasseer.


****

Wata rana matar k'anin mahaifinta Gwaggo Bilki, taa aiketa ebo ruwa rafi, tafiyah take a gajiye ga yunwa tun asuba take aiki ko tsugunawa batayi ballantana ta samu damar zaunawa ta huta, tana tafiya tana haɗa hanya har tazo dai dai wata bishiyar magwaro da wasu yara biyu keta faman jefa dutsi yak'i ya faɗo, ɗaya daga cikin yaran ya k'wala mata kira,

  "Saude don Allah kizo ki ciro mana mangwaronnan"

 Taja ta tsaya tana tunani a ranta, ko a kan lokaci ta koma gida sai gwaggo bilki tayi mata faɗa, ballantana ta tsaya hanya,

  "A'ah kabiruwa, ɗebo ruwa nake idanna tsaya gwaggo zatamun faɗa, kayi hak'uri kaji"

  "Dan Allah nace fa saude, ni sai in ɗebo miki ruwan" ya taho yana k'ok'arin amsar tulun a hannunta,

  "shikenan anma kuyi sauri fa,"

  "Tohh anma fa da yawa zaki ɗebo mana"

  "naji nace" ta tafi ta fara k'ok'arin hawan bishiyar, duk da ba wani iyawa tayi ba, anma duk k'auyen su kabiruwa na ɗaya daga cikin yaran da basu mata rashin kunya.


 Saida ta gama, jefo mangwarorin a k'asa, taa fara k'ok'arin saukowa, taji k'afarta taa zamo, da sauri ta rik'e wani reshe, anma kasancewar baida k'wari taji ya fara ɓallowa gashi har lokacin su kabiruwa basu dawo ba, ta rink'a kuka ta rasa yanda zatayi, saidai taji taa faɗa k'asa tim saman wani abu.


©Rabiatu sk msh

[3/7, 12:10 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

      6-10


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


 Saman mutum taji ta faɗo, ya tafi zai rik'ota, anma saida suka faɗi tare, k'afarta ta dama ta bugi wani k'aton dutsi, ta saki wata irin k'ara, 

  Ya tafi inda take da sauri zai rik'ota sai kuma ya fasa, 

  "Sannu kinji, kema in banda halinku na en k'auye meya kaiki hawan bishiya kina mace?" sai sannan ta ɗago fuskarta wacce tayi kaca-kaca da hawaye, ta tsagaita da kukan da take jin daddaɗar muryarshi a kunnenta, yana magana cikin natsuwa, da zazzak'ar muryarshi mai daɗin sauraro,

  Wannan kyakkyawan ɗan gayunne da ake labari duk k'auyen, Ɗan bautar k'asar da yazo musu, sunanshi ma na en gayu ko rik'e sunan batayi,


  Ya hure mata manyan idanuwanta data tsura mishi tana kallonshi, tayi saurin sadda kai cikin jin kunya,

  "Halan kin daina jin zafinne kika tsuramun ido haka kina kallo?" ba tace mishi komi ba, ta rumtse idonta kawai tanajin yanda k'afarta keta mata raɗaɗin ciwo, dai-dai lokacin su kabiruwa suka dawo, suna hangota tsugune suka nufi inda take a guje, wurin gudu suka yarda tulun nan a hanya ya fashe gaba ɗaya ruwan ya tsiyaye,


  Ta k'ara ɗaura hannu akai, "na shiga Ukuna! Kabiruwa kun kasheni"

  "sannu Saude, bamusan zaki faɗo ba da bamu rok'ek'i ki ciro mana ba" ya faɗa yana matse k'walla ganin yanda k'afarta ta fara kumbura, anma ita ta tuluntama take, taasan yau Allah ne kawai mai rabata da azabar gwaggo bilki,

  "nima bansan zaku fasa tulunnan ba da ban baku ba, shikenan yau kasheni kawai zatayi, in tafi can inda babana da mamana suke" cikin tausayawa yace "wacece zata kasheki?"

  "Matar k'anen mahaifina mana, kullum sai tamun kashedi akan tulunnan, ko gurjewa yayi saita dokeni" ba k'aramin tausayi ta bashi ba, ganin yanda take kuka, ga kuma ciwon da k'afarta ke mata,

  "ina ake siyarwa? Basai kije mata da wani ba"

 "Ba'a siyarwa a k'yauyennan fa, sai cikin gari (birni), nidai na shiga uku na"

 "Ki daina ihunnan, kije gidan sai kice mata faɗuwa kikayi, tunda ga shaida nan a k'afarki" shiru tayi kawai tana mishi kallon bazaka gane bane, ita kaɗai tasan bala'in da take ciki,


  Ta fara k'ok'arin tashi, anma har k'afarta tayi tsami, ta kusan faɗuwa da sauri taje zata rik'oshi, ta kuma fasa gaba ɗaya ta kasa taka k'afar, sai dai ta tsaya da k'afa ɗaya,

  "Sannu" yace mata ganin yanda taketa cijar leɓe, su kabiru na can gefe suna kuka, yaje zai kamata ganin ta kasa taka k'afar ta matsa da sauri, bai saurareta ba, ganin ɓata mishi lokaci take bazata iya tafiya da ita ba, ya sungumeta kawai ya nufi cikin k'auyen da ita, su kabiru suka bi bayansu suna nuna mishi hanya har k'ofar gidansu,

  Tun kafin isarsu labari ya kaima gwaggo bilki da kawu Ado, ga Saude can ta faɗi tulunta ya fashe, ɗan bautar k'asarnan ya ɗaukota zai kawota gida, tun kafin su iso taketa kumfar baki tana masifa, kamar ta haɗiye kawu Ado ɗanye, gajiyar da yayi da saurarenta ya sakashi mik'ewa ya nufi hanyar fita, sai gashi sun haɗu da Saude Yasseer na niyyar shiga da ita gidan kamar ya ɗauka en tsana,

  Cikin zafin rai kawu Ado ya mik'a hannu zai cakumota, Yasseer ya matsa da ita da sauri, ta fara k'ok'arin sauka, ya duk'a ya ajiyeta,

  "Yanzu Saude wulak'ancin naki har yakai haka? Ki faɗi da gangan ki kashema bilki tulu, yauko zakici ubanki a gidannan, Gobe ko mutuwa ce tazo muki kinyi k'ok'arin kare tulun bawai faɗuwa ba, in banda tsabar bak'in ciki ma inji da Ci dake mana, anma saikin janyo mana asara? Wallahi baki isa ba" baba Ado ne keta faman banko mata masifarnan, tunita takure wuri ɗaya, ji take inama mutuwa tazo ta ɗauketa ta huta da bala'in da zata shiga yau, shi bama ta ciwon da taji yake ba, duk da ganin saida aka ɗaukota aka kawota gida, ya saka hannu ya jawota, ta fasa wani uban ihun azaba,

  Yasseer bazai iya kallon wannan rashin tausayin ba, cikin muryar tausayawa yace "Haba baba, yanzu ko baka tausayama halin da take ciki ba, ay kaa saurara mata saboda ciwon dake k'afarta, marainiya? Baka gudun hak'k'inta a kanka, saboda abin duniya saika jikkata ta? Wannan fa k'addara ne, don Allah kayi hak'uri ka tausayama halin da take ciki," 

  Shiru kawu Ado yayi yana saurarenshi, duk jikinshi ya fara sanyi, ya kalli k'afar tata da tayi wani suntum, ga wani ciwon da taji, sai ga Gwaggo Bilki,

  "Malam tsayawa kayi kana saurarenshi? Kama manta da asarar da tamun kenan, tunda ba uban wani zai biyani ba wlhy yau sai jikinta ya gaya mata"

  "nawane kuɗin?" Yasser ya tambayeta,

  "jikka biyu da rabi (500)"

 Ya zaro mik'ak'k'ar dubu ɗaya a aljihu ya mik'a mata, cikin zalama ta saka hannu ta warce, sannan ta ɗaureta a zani, saida ta tabbatar ta ɓoye sannan ta jawo Saude, k'ii tana ihu duk ta fita hayyacinta saboda azaba,

  "tahonan, ko an biyani kuɗin ay baza'a maido min tuluna ba, kema sai kinji a jikinki asarar da nayi," ta shiga da ita cikin gidan, tana janta a k'asa sai ihu take, ga ciwon k'afa, ta dinga dukanta da wani iccen girki har k'afar take bugowa duk inda ta samu,

  Kasa jurewa Yasseer yayi, ya fita yabar gidan yanajin k'unci a zuciyarshi, hakanan Allah ya ɗaura mishi tausayin yarinyarnan. Shima kawu ado sai fitar yayi


©Rabiatu sk msh

[3/7, 12:11 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

     11-15


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


   Saida Gwaggo ta gama dukanta son ranta, ta farfasa mata jiki ko ina zafi yake mata, tun tana ihu har tayi shiru kawai sai dai ajiyar zuciyah, anan ta barta tana jiyyar kanta ta wuce ɗaki tana ci gaba da faɗa, can kuma ta lek'o,

  "Saude! Jira kike sai nace ki tashi ki ɗaura girkinnan? Ko wani kika ajje dazai miki wanke wanke da sharar," 

   k'ara fashewa tayi da kuka, yanzu banda gajiyar da tayi, ga dukan da tasha, da kuma yunwar da takeji tun safe har bayan sallahr la'asar bataci komi ba, kuma duk ita tayi girkin safe da ranar, kuma yanzu wani aikin zatayi, ta yunk'ura zata tashi, ta kasa, k'afarta ma dak'yar take motsata,

  Cikin muryar kuka tace "Gwaggo ina abincina?" 

  


   A harzuk'e ta yaye zanin da tayi labule dashi ta fito,

  "Kikace me?" tayi k'asa da kanta, "Ban ajje miki ba, tunda ba ajiya kika bani ba, Shi matsiyacin uban naki daya tashi mutuwa meya bar miki? In banda wahalarki daya bar mana, yarinya sai shegen bak'in jini," tayi shiru tanajin yanda gwaggo ke balbalo mata masifa, harta gaji don kanta ta wuce ɗaki,

  "Kuma karki tashi kiyi aikinnan har in fito in sameki"

   Tana kuka ta tashi da jan jiki ta tafi ta ɗauko tsintsiyar, daga zaune haka ta dinga sharar tana hawaye harta gama don batason taka k'afarta saboda yanda take mata zugi, haka wanke wanke ma a zaune ta yishi, tanayi tana jan k'afa taje ta duba sanwa harta gama, saida akayi sallahr isha'i sannan ta samu ta huta, abincinma ba'a bata ba sai dai tabi dare taci k'amzo duk da gwaggo Bilki ta zuba mishi ruwa, shima bawai don ya isheta ba.


  Daren ranar kasa barci tayi, ko ina jikinta na mata ciwo, ga k'afarta ko matsata batasonyi, sai juyi take a k'asa inda ta shimfiɗa tsammokaran kayanta, sai dai taji saukar ruwan sanyi a jikinta, ta murgina a firgice, tana zazzaro ido sai dai ganin Gwaggo tayi tsaye saman kanta, ta jefa mata bokitin dake hannunta.

   "Tashi maza ki ɗebo mana ruwan Girki, tunda ke kullum sai ance kiyi" tayi tsaye tak'i tafiya, saida ta tabbatar Saude ta tashi, tanabin bango tana hawaye ta fito daga gidan, kamar mai koyon tafiya, dak'yar ta isa rafin tana haɗa hanya har gari ya fara wayewa, anan tayi sallah sannan ta ɗebo ruwan, duk yanda taso kaasa ɗauka tayi, ta samu wuri ta zauna tana kuka, ga yunwa har wani dishi-dishi take gani.


  Ji tayi an dafa kafaɗarta, a hankali ta ɗago daga duk'ar da kan da tayi, suka haɗa ido ya zuba mata shanyayyun idanuwanshi dake k'ara kashe mata jiki,

   "Ina kwana"

 "Lafiya lau, har jikin naki ya warke ne kika fito da safennan?" ta girgiza kai tana k'ok'arin fara wani sabon kuka,

  "Gaskia marik'anki basu da imani Saude ko kaɗan, kinci abinci?" ta girgiza mishi kai, kallonta kawai yake cikin tausayi,

  Laida ya mik'a mata da madara da biredi a ciki,

  "Ga wannan idan kinje gida saiki haɗa" tun kafin ya ida mik'o mata ta anshe daga hannunshi saboda matsananciyar yunwar da takeji, da taga laidar ma zata mata wahalar kuncewa, sai dai ta yageta kawai taci gaba daci, ya saka hannu ya share hawayen da suka zubo mishi.

  Ya ɗaukar mata bokitin ruwan, "tashi mu tafi in rakaki" ta mik'e anma ta kasa tashi, "Sannu kinji, bara inzo" ya tafi cikin hanzari ya tafi cikin gari, da tambaya aka nuna mishi gidan wani mai kamu suka taho dashi, har inda take tananan yanda ya barta,

  "tashi zaune kinji Saude a kama miki k'afarnan zakifi jin daɗinta"

 Tace "tohh" tana k'ok'arin tashi zaune, mai kamun ma kanshi saida yayi mamakinta, ganin batayi gardama ba, ya ɗaga kai yana kallon Yasseer,

  "Anma fa sai an samu mai rik'eta"

  "Ba matsala, bara in rik'eta" ya zagaya inda take, ya kamota ya rik'e sosae sannan aka fara mata kamun,


  Wani irin yanayi ta tsinci kanta a ciki saboda rik'on daya mata, gaba ɗaya ta k'arasa rasa kuzarinta, ko kukan zafin ciwon ma kasa yi tayi, sai k'ara shigar da kanta take a jikinshi tana jin wani irin nishaɗi, ji take daman ta k'arar da rayuwarta a haka,

  Shima kwatankwacin halin data shiga, gaba ɗaya ta dagula mishi lissafi er mitsilniyar da takeyi a jikinshi, kaɗan-kaɗan zaice "Baba ba'a gama ba?" da wata irin kasalalliyar murya, shi kuma duk ya ɗauka tausayinta ne yake,

  Dubu ɗaya ya bama wanda ya mata kamun, ya dinga mishi godia harya tafi, sannan ya kalli saude,

  "Kiyi zamanki nan ki huta, kinga dai baki lafiya" cikin sanyayyar maganarta tace "dukana zatayi idanna daɗe"

  "Ay kin riga da kin daɗe, ko yanzu kika koma zata dakeki ne, kinga nima yau bazanje inda nake koyarwa ba don dai in tayaki zama" ta ɗaga mishi kai, don itama hakanan ta tsinci kanta da son zama dashi, wani irin farin ciki takeji da tun zuwanta duniya bata taɓa jin kamarshi ba,

  "Kallon ya isa haka, idan kin huta akwai maganar da nakeso muyi dake" ta maida kallonta gefe cikin jin kunya,


©Rabiatu sk msh

[3/7, 12:12 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

     16-20


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


  Yaseer ya kalli Saude data tattara hankalinta wuri ɗaya tana saurarenshi,

  "Kince iyayenki sun rasu ko?" ta ɗaga mishi kai,

  "Da gaske kawu Ado k'anin mahaifinki ne uwa ɗaya uba ɗaya?" ta k'ara ɗaga mishi kai,

  "Banson ɗaga kannan, magana nakeso muyi kinji"

  "tohh"

  "Bayan rasuwar mahaifanki duk danginki babu wanda ya amsa rik'onki sai su?"

  "eeh, saboda kawu Ado bai taɓa haihuwa ba, kuma dangin mahaifiyatah suna gudun rik'ona wai hidima zan zamar musu, kuma idan aka tashi aurena dole sai sunmin kaya ɗaki da duk abunda akeyi, shiyasa ma ko zuwa inda nake basuyi, don kar baba Ado yace zai haɗasu dani"

 Ya jinjina kai, "Kenan sunsan halin da kike ciki?"

  "eeh mana labari yana je musu, anma babu wanda ya taɓa zuwa tun bayan rasuwar mahaifana"

  "to meyasa bazaki koma wurin kakanninki ba?"


Duk'ar da kanta tayi ta k'ara fashewa da kuka,

  "Babu ko ɗaya, kawu Adon fa shine kawai ya ragemun"

 "Ayyah sannu kinji, yi hak'uri daina kuka, Allah yaji k'ansu"

 Ya dafe kanshi yana sauraren kukan nata, hakanan yaji yanason ya taimaka mata, anma ta yaya?

 Ta mik'e tsaye, "k'afar babu zafi yanzu, bara in tafi gida, ngde sosae da taimakon da kaimun"

  "A'ah ni nake da Godia" ya faɗa shima yana mik'ewa tsaye,

  "Sabodame?" ta tambayeshi cikin mamaki,

  "Saboda kin bani dama na taimakeki mana, harna samu lada" ta ɗanyi daria, 

 Ya ɗaukar mata bokitin ruwan, tare suka jera suka tafi, duk da tasan abunda zata iske gida, anma yau sai taji hankalinta bai wani tashi ba, idan har tana tare dashi bata da wani fargaba,


 Suna tafiya, sun kusa shiga gari, rana tayi sosae ana kiran sallahr azahar, ya katse musu shirun da sukai da cewa,

  "naga a k'auyenku auren wuri kuke, ya akai har ynzu ke bakiyi ba?"

  "lokaci ne baiyi ba, anma duk sa'anni na an musu aure harma da wanda suka haihu"

  "Hmm hakane, aina ɗauka kece bakya kula samarin"

  Tayi daria, "A'ah fa, kawai dai kawu Ado ne bai yarda ba har yanzu, anma kaga ɗan gidan sarkin noma ya daɗe yana naci, da ɗan gidan Alh musa duk garinnan babu mai kuɗinshi, harma da manyan mutane, kaga Yayan Kabiruwa ma mun daɗe muna soyayya, ynzu yama tafi birni neman kuɗi, anma kawu Ado yace bai tashi aurar dani ba, kuma nima bansan dalili ba"

  "A'a'ahh, tohh kicemun k'anwar tawa farin jini ne da ita" tayi saurin saka hannayenta biyu ta rufe idonta tana dariya, 


Kallonta yaci gaba dayi, Saude yarinyace anma ba sosai ba zata kai 15yrs, jikinta ɗan k'arami, anma tana da diri komai nata a cike yake dai-dai, farace tas, kuma duk da a k'auye take tana da tsafta, ga hankali da nutsuwa duk da ba ilmine da ita ba, bata cikin duhun jahilci, tana da kaifin tunani da iya magana, 

  Shi kaɗai ke tunaninnan a zuci har kawu Ado ya wucesu da k'aton ice a hannu yana muzurai ya nufi rafi, don tsabar masifa ma, bai lura dasu ba harya wuce, har k'ofar gida ya ajiye mata ruwan, sannan ya mata sallama ya tafi,


Bayan sati ɗaya...

Kullum Yasseer cikin tunanin yanda zai ceto Saude daga halin da take ciki yake, ko kaɗan baida wani nutsuwa ko wurin aiki yaje, gaba ɗaya tausayinta ke kamashi idan yana tuna halin da take ciki,

  Yau ya shirya ya tafi gidan, tun daga soro yake jiyo ihun kukanta, ba shiri ya ɓurma cikin gidan, canya hangota wurin murhu, Gwaggo Bilki na k'ok'arin saka hannunta cikin wutan, sai kuka take tana son janyewa, ganinshi ya sanyata dakatawa,

 Ranshi ya ɓaci, ga saude nan duk'e tana zubar da hawaye, suka jiyo sallamar kawu Ado daga waje,

  Tun kafin yaji abunda tayi, ya daddage ya kwaɗa mata mari, "Shegiya wahalalliyar banza, ai tunda ba wani ya bamu ajiyarki ba, baki gaji da shan azaba ba"

 Yasseer ya rumtse idanunshi, yanajin kamar shine aka mara, kawu Ado ma baisan da zuwanshi ba, tunda ba shiga gidan yake ba,

  Bai san sanda bakinshi ya suɓuce mishi ba, sai dai ya tsinci kanshi da cewa "Baba zaka bani auren Saude?" su duka suka maida kallansu kanshi, ba kamar Saude data buɗa baki cikin mamaki, shi kanshi saida yayi maganar sannan ya gano wautarshi,

  Gwaggo bilki tayi wani malalacin murmushi, don tasan yanda yake ɗan birninnan iyayenshi bazasu taɓa amincewa da Saude ba, "Mizaisa mu hanaka aurenta kuwa? Aymu jin daɗinmu nema zaka rabamu da jaraba, ko Malam?"

  Ya kalleta da mamaki, ganin yanda ta amince da wuri haka duk da yaron ɗan birni ne, "eeh, eeh mana, duk sanda ka tashi ka turo iyayenka kawai"


 Shiru yayi, tayaya ma zai iya kaima iyayenshi maganar auren er k'auye daga zuwa bautar k'asa? Yasan bazasu taɓa amincewa bama, 

  "Tohh Baba nagode," sannan ya juya ya tafi jikinshi a sanyaye, Kawu Ado ya juya yana kallonta,

  "tayaya zaki saurin amincewa dashi? Bayan bamusan danginshi ba, bamusan asalinshi ba"

  "tohh ina ruwanmu da wani asalinshi? Ya tafi da ita birnin mana a yanke mata kai, ai dai mun huta, ni wallahi na gaji da ganin yarinyar nan"

  "Hakane kuma, harma mun huta" 

  Tace "eeh mna," Saude dai na duk'e tana jinsu, hakanan ta kasa gane farin ciki ne take koko mamaki, anma dai tashin hankali yafi mata yawa,


Sai bayan kwana biyu da maganar ya k'ara dawowa gidan, ya faɗa musu iyayenshi bazasu samu zuwa ba, bazasu ma amince da auren ba, 

  Kawu Ado yace "Toh mu ina ruwanmu da sai sunzo? Nidai na baka auren Saude, kuma nasan kai kayan ɗaki ba damunka zasuyi ba, indai ka samu inda zaka ajjeta, kazo kawai a ɗaura aure"

  "k'waraima kuwa, sadaki ai shine aure," inji gwaggo Bilki,

  Jikinshi duk yayi sanyi, ya musu sallama ya tafi,


  Wani ɗan k'aramin gida da yafi kama da bukka, ya samu ya kama haya, katifarshi da kayan girkinshi, komai dai nashi ya kwaso ya maida a gidan, Cikin sati ɗaya aka ɗaura aure, ba tare da sanin iyayenshi ba, babu wanda yasan daga inda yazo, babu wani bincike, duk don SANADIN K'IYAYYAR da Gwaggo bilki, da kawu Ado suke mata,

  Ranar ɗaurin aurenma tsirarun mutanene suka taru aka ɗaurashi, wani Abokin kawu Ado ya samu yayi ma Yasseer ɗin waliyyanci, anma fa shagali sosae gwaggo Bilki tayi kodan ta samu kuɗi safga, da dare aka ɗauka Saude aka kaita gidanta, ko abunda basu so basu haɗata dashi ba,


****

K'arar Vibrating ɗin wayarshi ne ya dawo da ita daga tunanin da take, duk ta jik'a fuskarta da hawaye, ta zabura ta koma wuri ɗaya ta dunk'ule , tana kuka jikinta sai kyarma yake,

  Daga can waje yace "lafiyarki kuwa?" Kasa magana tayi saboda tashin hankalin data shiga jin katifa na girgizawa saima ta k'ara 'karfin kukan,

    "Meya faru dake Saude? Kimun magana mana" tayi shiru dai duk ta haɗa zufa ju take kamar ginin ɗakin zai faɗo mata, kuma tsabar tsoro ya hanata ta tashi ta gudu, gashi da katifar taa ɗan daina girgizawa sai taci gaba,

  jin kukan nata yak'i k'arewa ne ya sanyashi tahowa ɗakin.


©Rabiatu sk msh

[3/7, 12:13 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

     21-25


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


  Da gudunshi ya shiga ɗakin, harya kusan tuntuɓe, can ya hangota rakuɓe k'arshen katifa sai haɗa zufa take, ya haye inda take,

  "Meya faru wai?"

 Duk a tsorace take ta nuna mishi inda vibrating ɗin ke tahowa, lokacin an sake kira, wani abu ya tokare mishi zuciyah, bak'auyen mutum ma baiyi ba,

  "Wayatah ce aka kira Saude, Mamana ce ke kira" yana niyyar mata kashedin idan ya ɗauka waya karta yi magana yaga ta duk'a duk taa tattara nutsuwarta wuri ɗaya,

  "Mama ina wuni," sakin baki kawai yayi yana kallonta, ita a gaske gaishe da surukarta takeyi, "Zauna kinji, ina zuwa"

 "Alwalan zanyo"

 "tohm jeki dawo inanan ina jiranki" ta tashi ta fita, sannan ya kira Maman tashi,


 Bayan ya jasu Sallahr, suka gama ya kwararo musu addu'o'i sosai suka shafa, sannan ya juyo ya fara mata tambayoyi akan addininta, ba laifi tasan wasu abubuwa, tunda tana ɗan zuwa makarantar Allo, in dake da gyara yaɗan gyara mata, sannan ya jawo musu ledar kaza,

  "Nasan kinajin yunwa, taho kici"

  "A'ah na k'oshi" duk da a ranta tana so, anma cikin zuciyarta tace 'taɓ! Wazaici maka kazar? Ay su hinde suna bani lbr indai naci kazar nan kaima saika rama,

  Ya katse mata zancen zucinta da cewa "meyasa bazakici ba? Nasan dai bakici komi ba"

  "Nifa na k'oshi dai" lallashinta ya shigayi yasan tanajin yunwa, anma ta nace bazataci ba, ya ɗebar mata farar tsoka, ya nufi bakinta dashi, ta duk'e, ya matsa gaf da inda take har tana jiyo numfashinshi. ta ɗan matsa shima ya k'ara matsawa,

  "ka koma inda kake"

 "Sai kince sannan"

   "Nifa na k'oshi"

  "Naji wannan ay baa abinci bane, ki buɗa bakinki" da taga dai baida niyyar matsawa, gashi duk yaa takura mata, ta buɗa bakin ya saka mata,

  "Yauwah ko kefa, tohh saka hannu kici da kanki, ko ni zan baki" a kunyace ta saka hannu ta faraci, gabanta sai faɗuwa yake, don dai ba yanda zatayi ne, duk da harta manta rabon da taci nama, bataci da yawa ba ta tashi ta koma gefe,

    "Barci?" ta ɗaga mishi kai, sannan tayi kwanciyarta k'asa, shima bai daɗe ba ya gama, ya fita ya wanko hannu sannan ya dawo ya kwanta,


  "tashi ki dawonan Saude"

 "A'ah, a gidanmu ma k'asa nake kwana"

   "Tohh ai nan gidanki ne,"

  "Nidai A'ah" ya gyara zama yana kallon ikon Allah,

  "dawonan, ni sai in kwanta a k'asa"

    "A'ah"

  Bazai iya da rigimarta ba, ya tashi ya sungumeta ya ɗaura saman katifar, can jikin bango yanda bazata iya sauka ba,

  "kiyi kwanciyarki, ba abinda zan miki" tayi shiru tana saurarenshi, duk taa takure wuri ɗaya, ya juya mata baya kawai,


  Shi tun farko tausayin Saude ne ya sakashi aurenta, bawai don so ba, ko kuma don yana sha'awarta, to mezaiyi sha'awah ma a wurin er k'auye? Shi yarintarta ma yake gani, anma hakan data nuna ya sanyi shi tunanin tasan ALAK'Ar (Littafin ililee mai zuwa) dake tsakaninsu kenan? Bazai iya saita kanshi ba gaskiya, tunda dai taa zama halaliyarshi, kuma shi cikakken mutum ne mai lafiya,

    "Saude" Yasseer ya kira sunanta, anma bata amsa ba, hakan ya tabbatar mishi da tayi barci, yasa hasken wayarshi ya hasketa, idanunta a rufe tana barcinta cikin kwanciyar hankali, ta baje saman katifa, ɗan zanin data ɗaura yayi gefe, rigarta taa ɗan yage (da yake tsaffin kayanta ne ta saka ba'a mata sabo ba), k'irjinta yaa ɗan fito, baisan sanda yakai hannunshi ba,

  Da yake barcin yayi mata nisa, ji take kamar a mafarkine, sai shafata yake hankalinshi ya fara tafiya, ganin bata farka ba, ya sanya ya fara jagwalgwalata yanda yakeso,

  Shesshek'ar kukanta ya fara jiyowa can k'asa, ya fara lalubar fuskarta yaji koda gaske kukan take, hawaye ya jiyo,

  "In daina bakiso?" tayi shiru, jin babu amsa sai ci gaba da tayi da kukanta ya sakashi juyawa kawai ya k'yaleta,

  "Kayi hak'uri akwai zafi ne" 

 Sai sannan ma hankalinshi yakai, yanda yake mata dolene ma zataji zafi, ya manta k'aramar yarinya ce

   "Shikenan ki kwanta ki barcinki" 

 Ta k'ara murginawa can k'arshe, bata daɗewa ba wani barcin ya kwasheta, shikam dai kusan ido biyu ya kwana,


©Rabiatu sk msh

[3/7, 12:13 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

      31-35


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


 Yasseer ya sake kallonta,

   "Ki tashi ki dawonan, magana zamuyi" ta tashi a hankali kamar bataso, ta koma kusa dashi, zata zauna ya jawota ta faɗa jikinshi,

  "tahonan mu kwanta kiyi barci kafin lokacin Sallah" shiru tayi tana lafewa jikinshi, "yau ranarki ce, babu inda zanje, don haka fira zamuyi," 

  "kina zuwa makarantar Allo ba?" ta ɗaga kai,

  "an taɓa faɗa muku hak'k'ok'in miji akan matarsa?" tayi shiru tana tunani,

  "na manta, sai dai na mata akan mijinta"

  "lallai k'anwata wannan son kai ne, shikenan ni kin manta da hakk'ina a kanki?" ta sunnar dakai jikinshi tana daria,

  "koda yake, ba mantawa kikai ba, don a ɗan zaman da mukai dake, zan iya shaidarki a ko inane, kinamun biyayya sosae, kuma kina kyautatamun"


 Shiru suka k'arayi yama rasa ta inda zai fara mata magana, sai dai kawai ya share,

  "Meyasa bakiyi makarantar boko ba?"

 "Daa inayi, baba Ado ne ya hana wai ina barin gwaggo da aiki, daman ba kullum nake zuwa ba"

  "Aji nawa kika tsaya?"

 "Na manta"

   "Kinason karatun?"

  "Da sauri ta ɗaga kai"

   "Tohh shknan zanna koya miki," ta washe baki sai murna take sosai.


 A gida ya yini ranar, bai fita ko ina ba, shinkafa da wake ta musu da rana, shi taa iya, kuma daman abincin dayafi so ne, har dare shi sukaci,

  Da dare ma kamar jiya, yana fara taɓata ta saki kuka, haka ya hak'ura ya juya kawai yaci gaba da barcinsa,

  Washe gari monday, ya shirya ya tafi wurin aiki, daga can gari ya wuce ya musu siyayyan kayan abincin da yasan su ta iya girkawa, dai dai k'arfinshi, da duk abinda yasan zata buk'ata, sai marece sosae ya dawo harta fara damuwa da rashin dawowarshi,

 Tashi tayi tana mishi sannu da zuwa, ta duk'a har k'asa sannan ta mik'a hannu ta rage mishi kayan daya shigo dasu, sannan tabi bayanshi suka shiga ɗaki,

   "Sannu da dawowa"

  "yauwah Saude ya gidan?"

    "Alhamdulillah, ya hanya?"

  "lafiya lau, kin jini shiru, daga can gari na wuce"

  "Buɗa ki gani kayan abincine, idan akwai abinda babu"

 Tace "Angode Allah ya k'ara arzik'i"

  "Ameen Saude, buɗa wannan ma kiga ko zasu miki" ta ansa tana kunce laidar.


  Kayan sakawa ne a ciki anma na Gwanjo masu kyau, ta fara ɗagawa tana murna, rigunan duk masu kyau da buje shima dai dai ita, wani wando ta ɗaga shima mai kyau, ta ɗaga kai ta kalleshi cikin farin ciki suka haɗa ido, ya sakar mata k'ayataccen murmushinshi, ya ɗauka ma ko bazata iya sakawa ba, yace "Kinaso?"

 Ta ɗaga kai duk tamafi murna dashi, "Eeh yayi iri ɗaya da wanda Hanne ta taɓa bani, Gwaggo bilki ta saidashi, amma wannan ma yafi kyau"

  "Aikam ga wanda ya fishi kyau kin samu, zaki saka ko?"

 Ta ɗaga kai tana daria,

  "Yauwah anma nawa ne ni kaɗai, bazaki fita dashi ba"

  "ni ay babu ma inda zanje"

 "Yauwah k'anwata, yanzu maidasu a ledar, idan kin samu ruwa mai ɗan zafi ki jik'a kinji, kafin inje garinmu in sawo miki wasu, naga bakizo da kaya bane kuma dai bani da isassun kuɗin siya miki Sabbi"

  "wannan ma sunyi, Allah ya k'ara buɗi," 

   "Ameen" ta fara tattara kayan ta kwashe tayi waje dasu, nan take ta tafasa ruwa, saita sirkashi yayi ɗumi ta jik'asu da dare ta wanke, daman kala ɗaya ne jikinta tun wanda aka kaita dasu,

 Harta kwanta tana mishi Godia, taji daɗin kayan sosae, shima kwanciyarshi kawai yayi, don baison ta mishi kukan data saba.


 Bayan kwana biyu, suna zaune yana cin abincin rana bayan ya dawo daga wajen aiki, itama kuma tana can tana sharar tsakar gida, na uku kenan tayi sharar a ranar, k'wala mata kira yayi, da sauri ta taho, ta duk'a a gabanshi

  "Yanzu muka gama magana da mamanah" ya ɗanyi shiru, itama tayi shiru tana saurarenshi ya k'arasa faɗi,

 "Ina ganin wannan satin zanje gida, kinga wata na uku kenan da zuwa banje ba" tayi shiru duk fuskarta tayi alamun damuwa, a ranta tace 'kuma ko sati bakayi da aure ba zaka tafi ba', sai tunani dai take, duk zuciyarta bata mata daɗi ba,

  "Kinyi shiru ko kar in tafi?"

 "A'ah nina isa in hana ka"

 Cikin sigar zolaya yace "in tafi kenan kin gaji da gani na?" ta ɗago tana daria.

   "A'ah nifa ba haka nake nufi ba"

  "Hakane mana, kullum dare ina takura miki" hannu ta saka tana rufe fuska, ta tashi zata fita,

  "Ki dawo mana" ta dawo ta zauna ba tare data buɗa fuskar ba, ɗan matsawa yayi inda take, ya fara mata raɗa a kunne, nidai gani nake kawai tana daria kota ɗaga kai,

  "yanzu tohh faɗamun abubuwan da kike buk'ata, kafin in tafi sai in siyo miki"

  "Komai akwai"

    "Kin tabbata?" ta ɗaga mishi kai,

  "tohh shikenan ai zan gani da kaina" ta mik'e tayi waje, indai yananan bata cika son zama ɗakin ba,


  Da dare suna kwance kamar yanda suka saba, kowanne ya kalli wuri daban, duk dare sai zuciyar Yasseer ta cika da haushi, daman haka masu auren sukeji? Auren er k'auye ma sai a hankali, shi kaɗai yake tunani yana can tsoki cikin zuci, duk da ba son Saude yake ba, tausayinta ne kawai ya sakashi aurenta, anma ai shi ba katako bane, kuma duk inda mace da namiji sun haɗu sai sunji wani abu a ransu, ballanta shi da take matarshi,

  "Saude" ya kira sunanta, a hankali ta amsa,

  "Ya maganarmu ta ɗazu?" tayi shiru babu amsa,

  "Kina jina fa" gabanta sai faɗuwa yake tace "Duk sanda kakeso"

  "Ko yanzu ma?"

    "Banda yanzu"

   "anjima kenan"

  "A'ah ba yau ba"

 "in hak'ura dai, jibi fa zan tafi" shiru tayi, shima sai bai k'ara mata magana ba, ya k'yaleta, duk da yau cikin buk'atarta yake sosae, anma baiso ya mata dole,

  "Na yarda tohh"

   "Da gaske?"

      "eeh"


  Tsabar farin ciki ɗaukota yayi ya ɗaura samanshi, ya fara haɗa bakinshi da nata don abunda yafiso kenan, shiyasa kullum yake nuna mata tsabtar baki, tsotsarshi yake kamar zai ciro mata harshe, yana shafa ko ina a jikinta, ita dai duk yanda yayi da ita bi take, tanajin yanayinda bata taɓaji ba, 

  Ji da tayi yaa sauka k'asa, batasan sanda ta saki kuka ba, ta rirrik'eshi, ya dakata kawai, duk da yanayin daya shiga.

  Cikin wata irin murya tace "Kayi hak'uri don Allah na daina kukan, Allah bansan sanda yazomun ba"

  "Tohh anma kiyi duk abunda nace kinji ko"

  Tace "tohh" murya a shak'e,


  Hakan kuwa ya k'ara rikitashi, shima lokacinshi na farko ne don haka baimasan yanda zai lallaɓata, yana jintama tana kukan da ihun, anma bai tsaya saurararta ba, har duka take kai mishi, iyayenta kam sunsha kira, harta da kawu Ado da Gwaggo bilki sunsha kira duk da tasan ko cutarwa ne bazasu kawo mata agaji ba, tsabar ruɗewa dai kawai.


  Sai da hankalinshi ya fara dawowa ya kalla gefen da take, tana kwance ko motsi bata iya yi, a ruɗe ya fara jijjigata, ya ɗauka ko suma tayi, ta buɗa idanu dakyar tana kallonshi, hankalinshi ya tashi sosae, ya fita yama rasa yanda zaiyi mata, gashi a k'auyen babu asibiti,


©Rabiatu sk msh

[3/7, 12:13 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

     26-30


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


Wannan shafin naki ne Aunty khadija, (Maman Majeeda), lol naaga en RAZ NOVELLA sun fara fiddo ido kamar Yasseer yaga dahuwar indomie,😄 daman Maman Majeeda na group ɗinnan muke ta bama Majeeda rashin gaskia? @Haramtaccen Zama, hhhh duk taa jiku fa😜


www.babymsh.blogspot.com


  Washe gari tunda Yasseer yadawo daga masallaci, ya koma ya kwanta, bai farka ba sai wurin 11 saboda k'arancin barcin daya samu da dare, ya duba inda Saude take batanan, ya mik'e ya fita wajen ɗakin, can ya hangota tana kwashe shara, daga inda yake yanata kallonta tana aiki.

   "Sannu k'anwata, aiki kikasha?"

 Juyowa tayi anma bata yarda sun haɗa ido ba, har k'asa ta durk'usa,

  "Ina kwana"

  "lapia lau ina gajia?"

    "Alhmdlh, babu"

  "Haba duk wannan aikin da kikasha, waya faɗa miki amarya na aiki?"

  "uhm" tace, ta wuceshi zuwa ɗakin daya tashi,

 Shima gyaranshi ta shigayi, komai tsaf, daman gyaran katifar ya rage mata da shara, tana cikinyi ta jiyoshi yana kiranta, ta tafi da hanzarinta sai gashi sun haɗu a hanya,

  "Saude ina muka samu ruwa? Naaga ko ina a cike"

  "Nice na ɗeboshi da asuba"

 Da mamakinshi yace "ke kuma? Dagayin auren saiki fita ɗebo ruwa?"

 Ta k'ara k'asa da kanta, "babu ruwan da zanyi amfanine, kuma sanda na fita ma harna dawo babu mutane"

  "idan fa wani abu ya sameki? Banson ɗebo ruwannan daga yau, zan dinga sawa a ɗauko miki"

  "tohm bazan k'ara ba"

  "Yauwah, bara in samo mana abun kalaci, nasan kina jin yunwa"


  Harya juya tace "Nayi girki fa"

  "Kuma dai Saude? A ina kika samu abinda kika girka?"

  "Cikin kayanka"

    "Kinci abinci kenan?"

  "A'ah fa"

    "tohh kawomun in gani" ya koma ɗakin, tabi bayanshi, tukunyar abincin ta ɗauko, ta ajje mishi, sannan ta kawo mishi kwano da cokali,

  "sannu Saude, mantawa nayi ince miki basai kinyi girki ba, kinga ni bani ma iya break fast idan ba da tea ba" ta ɗaga kai tana kallonshi, don ba duka maganarshi ta gane ba,

  "zubamun inci tunda ke kika girka," tace "tohh" sannan ta buɗa tukunyar zata zuba mishi, ya k'walalo ido yana kallon cikin tukunyar,

  "menene kika girka?" donshi yamafi mishi kama da tuwon da yayi ruwa, sai kallo yake yaa rasa gane menene, ga k'amshin daudawa kuma yanaji, kodai jallof ɗin tuwo ne?😉

  "taliyarnan ce ta cikin leda?" ta bashi amsa,

  "taliya kuma?" ya tambayeta da mamaki don duk cikin kayan abincinshi babu taliya,

  "ɗaukomun in gani," ta tafi da sauri ta kwaso mishi ledojin indomie, yana gani ya maida kallonshi cikin tukunyar, ta wani dafe, gashi taa huce harta sandare,

  "Yanzu wannan taliyarce kikama dahuwar haka?"

 Ta ɗaga mishi kai tana murmushin, "eeh mana tafi daɗi idan aka mata dahuwar daudawa"

  "nina gani kam, bara in fita in samo bread"

   "Abincin fa?"

  "kici kawai, anjima zanci"

   "Tohh a dawo lafiya"


 Yana fita ta zuba indomie ɗinta, ta faraci, itadai tayi mata daɗi, sai da taci sosae taji cikinta ya ɗauka, sannan ta koma ɗaki, ba abinda zatayi, anma bata saba zama hakanan sai tayi ta neman aikin da zatayi.

  Bai daɗe ba ya dawo da bread da kayan tea, yace ta ɗaura mishi ruwan zafi, ta haɗa icce ta dafa ta kawo mishi, ya haɗa musu cup biyu,

  "tohm taho ki ɗauka naki"

  "naci abinci cikina ya cika"

  "tohh taho ko tean kisha"

  "A'ah na k'oshi"

    "Gardama ko Saude?"

   "Da gaske Allah"

  "tohh shknan",

     Saida ya gamasha ya k'oshi, ya koma saman katifan ya kishingiɗa, tana can gefe taa zauna wurin k'ofa, su duka sunyi shiru,

  "taso kizo nan Saude" cikin bin umarni ta tashi har inda yake ta tsuguna, 

  "nan zaki zauna" ta kalli inda yake nuna mata, sannan ta sadda kai bata tashi ba,


©Rabiatu sk msh

[3/7, 12:13 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

      36-40


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


 Duk ya ruɗe ya rasa yanda zaiyi da ita, sai girgiza jikinta yake yana cewa "tashi Saude, na daina fa" ita kam kukanma ya daina zuwa,

  Sai can ya tuna da ruwan zafi fa ake shiga a wanke jiki, da sauri ya tafi ya duba babu ko wanda babu sanyi sosai, haka ya ɗaura ruwa cikin darennan, ya haɗa sannan ya ɗauketa ya shiga kewayen da ita, bayan ya gasa mata ko ina, har wankan soso ya mata ya wanketa tass, sannan ya taimaka mata tayi wankan tsarki, ya fito da ita ya kwantar da ita saman katifa, tana kwanciya sai barci,

  Washe gari cikin nishaɗi ya farka, sai yau ma yake jinshi kamar Angon, sai wani annuri yake fita a fuskarshi, bai tasheta daga barcin da take ba, shiya haɗa mata break fast, da duk abunda zata buk'ata ya ajiye mata, yakai hannu ya shafi fuskarta, zazzaɓi harya sauko mata, gashi baison ya tasheta, ya ajje mata magani inda zata gani sanda zai fita, har yakai k'ofa yana waiwayenta, taa k'ara yi mishi kyau sosae, don dolene kawai zaije wurin aikinnan, anma idan sonshi ne ya zauna kawai yayi jiyyarta.


 Tana jin yaa fita ta buɗa idonta, daman taa daɗe da farkawa kunyarshi ce ta hanata buɗa ido, ga yunwa tanaji anma bazata iya cin abinci ba, maganin daya aje mata ta gani, ta ɗauka tasha, sannan tayi kwanciyarta.

  Duk da babu inda ke mata daɗi a jikinta, haka ta tashi da taga rana tayi, ta ɗaura mishi girki, tun kafin ta gama ta fara jin k'arfin jikinta, sai dai zafinda bata daina ji ba, tana gamawa sai gashi, yau da wuri yazo, tana gyara inda tayi girki, baima kula da ita ba saida ta amsa sallamarshi.

 Ya juya yana kallonta abun mamakin Saude bai k'arewa, sai kallonta yake yace "Saude maiya fito dake kuma?" da sauri ta bar abunda take, a inda take ta durk'usa tana kallon k'asa,

  "Sannu da dawowa"

   "Yauwah ya gida" a can ciki ta amsa, duk ta takura da kallon da yake mata,

  "Bana hana yawan aikinnan ba Saude? Keda bakijin daɗi ai kamata yayi ki kwanta ki huta"

  "Ai naji sauk'i"

 "Ban yarda ba, ki ajje aikinnan muje ki huta" tace "tohh" ta mik'e tana sauri ta k'arasa aikin, zuwa yayi ya kamo hannunta ta mik'e tsaya, yana rik'e da ita har cikin ɗakin, sai k'asa take dakai, kamar k'asa ta buɗe ta shige kawai, wani irin kunyarshi takeji,


 Saida ya Zaunar da ita, sannan ya buɗe laidar daya shigo da ita, fresh milk ne da naman balango mai zafi sai k'amshi yake,

  "Ki zauna kici, naga bakiyi break fast ba, zan tashi in watsa ruwa kinji"

  "tohh abincin fa?"

   "a ina aka samu?"

  "Girkawa nayi,"

 Rasa me mezaice mata yayi, "yanzu dai a k'oshe nake, k'ila anjima" ta gyaɗa kai, yana fita ta fara cin namanta, saida taci sosae har taji ba wuri, sannan ta kora da fresh milk ɗinta. 

  Ba laifi Saude ta samu kulawa daga wurin Yasseer a ranar, duk da bai wani san yanda zai tarairayeta ba, yana zaune gida, anma sai yawan yi mishi waya ake, duk dai maganar tafiyarshi ce,

  Tun cikin dare yake haɗa kayanshi, ita dai har tayi barci bai kwanta ba, duk ta shiga damuwa, batason ya tafi ya barta, ita da tanada damar hanashi ma bazata bari yayi tafiyar ba, sai dai kawai k'ok'arin dannewa da take,


  Da asuba bayan tayi Sallah ta kwanta, tana jiyoshi ya dawo daga masallaci toilet ya shiga yayo wanka sannan ya shigo ɗakin, tana jinshi yana shiri, saida ya gama ya fara tashinta, ta buɗe ido kamar mai barci, 

  "Yi hak'uri naa tasheki, yanzu zan wucene"

 Batasan sanda tace "tun yanzu?"

  Tsadajjen murmushinshi ya sakar mata, "Tohh ai garinmu ne da nisa, shiyasa zan tafi yanzu k'ila in isa kafin magrib"

  "Tohh Allah ya yarda"

    "Ameen"

Ta mik'e zata ɗaukar mishi jakar kayanshi ta rakashi, ya kama mata suka fito har soro, har lokacin gari da sauran duhunshi,

 Suna tsaye sai wasa take da yatsun hannunta, ya sunkuyo dai dai fuskarta, ta lumshe ido, "Yadai?"

 Idanunta a rufe tace "ni bansan mezan baka bane, idan ka tafi ka ringa tunawa dani"

  "Saude kenan, tafiyar kwana biyun? Ai abinda kika bani ma ya isa har k'arshen rayuwatah bazan manta dake ba" da sauri ta juya jikin bangon tana ɓoye fuskarta,

  "tohm baka faɗamun sunan garinku ba"

 Cikin wasa yace, "tsoro kikeji kar in gudu in barki?"

  "A'ah inason sani kawai" ta faɗa tana dariya,

 Har yanzu cikin zolaya yake mata magana "A k'asar katsina nake"

  "Uhmn nasan ai ba jaharmu ɗaya ba"

 "Hakane fa, garinmu yana can hanyar wani gari, idan anje kusa da wani gari, anma dai muna kusa da babban birnin tarayya, garinmu babban birni ne,"

  Shiru tayi dai duk bata fahimci maganarshi ba, ita tunda take banda k'auyensu babu inda ta taɓa zuwa, ko k'auyukan mak'wabtansu bata sani ba.

 Wayanshi ce tayo ringing, ya katse kiran sannan yace "lokaci nata wucewa, karna rasa mota, ko zaki rakani gari saiki dawo?"

  "A'ah za'aita yimun surutun na fara fita ai, Allah ya kaika lafiya ya maido dakai lafiya"

  "Ameen saina dawo" ya juya ya tafi, har yayi nisa tana mishi addu'a, sai k'ok'arin shanye kukanta take, tana daina ganinshi kau ta duk'e wurin ta fara kukan da babu mai rarrashinta.


BIRNI

Da marece sosae Yasser ya isa garin nasu, kai tsaye gidansu ya wuce, babban gidane, mai kyau da tsari, duk yanda kyanshi yazo muku a rai, ya wuce nan, idan kaa shiga bazaka taɓa tunawa a k'asarnan kake ba

  Daman zaman jiranshi suke, sosae suke nuna farin ciki da zuwanshi, sai da ya nutsu ya zauna sannan suka k'ara gaisawa da momiensa,

 Husna data kasa sakin jikkarshi duk ta rirrik'e tace "Yaya tsarabanah fa?"

  Momie tace, "In banda abunki Asma'u wanne tsaraba ne a k'auye?"

  "nidai inaso momie, ai shine yamun alk'awari"

  "indai tsaraba ne gaki gashinan, inda abunda zaki iya ci"

  "zanci indai bazai ɓatamun ciki ba"

  "kin daiji dashi" yace mata

 Kiran wayarshi da akayine ya sakashi mik'ewa,

  "Bara in shiga in shiga ciki momie, idan Daddy ya shigo a kirani plz" yana kallon husna ya k'arasa maganar,

 Dariya take rik'ewa da yayi hanyar ɗakinshi, "tohh yaya, abincinka nananma, yaa daɗe yana jiranka"

  "Yauwah k'anwar"


Yana tafiya ya ɗauka kiran, muryarta ta sauka a cikin kunnanshi,

  "Hakanan jikina ya bani yau Masoyina ya dawo"

  Yasseer ya saki murmushi kamar tana ganinshi, "Kin canka dai dai, yanzunnan ban daɗe da dawowa ba"

  "Aina sani, kuma shine baka faɗamun ba?"

  "Yi hak'uri Masoyiyah, nayi laifi"

  "Zan hak'ura anma sai kaazo na ganka"

  "Insha Allah gobe zaki ganni"

 "Ban yarda ba, nidai yau zan ganka"

  "Kinsan na shawo gajia fa, gashi dare yayi, goben idan nazo har saikin gaji dani"

   "nidai A'ah, wata uku fa ban saka ka a idanuna ba"

  "tunda kinyi hak'urin wata uku, ki k'aramin en awanninnan mana, nima fa naso in ganki"

  Suna cikin maganar ya isa ɗakinshi, duhu yaa fara ta ko ina yakai hannu zai kunna fitila, sai kawai ya jiyo an rungumoshi ta baya, zai juyo ta saka hannu ta rufe mishi fuska.


©Rabiatu sk msh

[3/7, 12:13 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

      41-45


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


  Rik'e hannuwanta yayi yana shafawa, sannan yayi murmushi,

  "Rabi'ah?" sautin dariyarta ne ya fita sannan ta sakeshi, bayan sun katse wayan.

  "Haba ko baki rufemun ido ba, ina shigowa gidannan jikina ya bani kina ciki"

  "Hhm ba waninnan, kaida kace bazakaje ka ganni ba, ni kaɗaice na damu da ganinka ma"

  "A'ah ai don nasan kina gidanne"

  "Hhm ka cika wayau"

   "Faɗin Gaskia dai"

 Sannan takai hannu ta kunna hasken,

  "Da alama kaa gaji Masoyi, bara in jiraka a fallo ka watsa ruwa"

  "aini nama manta da wani gajia fa tunda na ganki"

  "hhm tohh shknan, kayi sauri dai banso ka zauna da yunwa"

  Yayi daria "tohh ko zaki tayani?"

 Sai data tsaya tana ɗan tunani, sannan ta ware ido "I wish i could, anma ai akwai lokaci" tana mayar mishi da murmushinshi

   

Rabi'ah kenan, k'awar Husna ce tun suna sckul, harsun zama tamkar en uwa, suna gari ɗaya anma har kwana tanayi a gidansu Husna saboda Yasseer, tunma kafin su fara soyayya, har yaji shima tayi mishi ya bayyana mata sirrin zuciyarshi, ba wani ɓata lokaci ta amince mishi, yanzu haka babu wanda baisan da maganar soyayyarsu ba, itace ma wacce zai aura.


  Cikin mintuna kaɗan ya gama wankan ya fito, sannan ya zura kaya, zaune ya tardata saman carpet ta jera abincin tana jiranshi, lokacin an kira Sallahr Magrib, ya wuce masallaci itama ta shiga toilet ɗinshi tayo alwala.

 Bayan yaa dawo anan suka baje falo, tana zuba mishi abinci, ya kalleta sannan yace,

  "Da alama akwai magana bakinki"

  "Kuma akwai damuwa a zuciyana ba"

  "Duk meya kawo hakan?"

 Ta k'ara ɓata fuska, da alama abun na damunta sosae,

  "k'auyen can mana, Allah banison zamanka k'auyennan, daga bazaka daɗe ba, harfa cewa kayi bazaka zauna ba, anma shine kayi daɗewarnan"

  "to ai gashi naa dawo, duka wata nawa ya ragemun in gama duka?"

  "Hakane anma nidai don kak'i, anma wallahi tun farko da nayima Abba magana an barka nan"

  "A'ah ni nafison inyi bautar k'asarnan inda aka turani"

 "Saboda ka ringa ganin en matah ba"

 Ita maganarshi ma dariya ta bata, "K'auyene fa Rabi'ah"

  "k'auyen basu da idanune? Na tabbata ko duk makafine ka wuce ta inda suke dolema suji sunason mallakarka, kana dakyau Yayanmu, ka mallaki duk wani abu da mace zataso a wurin namiji, en k'auyen daka raina nasan suma rububinka suke"

 Har yanzu dariyar yake mata "kedai kin cika kishine kawai, anma plz ki daina wahalar da kanki akan en matan k'auye, ina laifi ma kiyi kishi da wayayyu en birni?"

  "Indai a kanka ne ban raina kishi da kowa ba, ina sonka da yawa ne, ni kaina bansan kalar son da nake maka ba dahar nakejin idanna rasaka zan iya rasa raina, kuma da inyi kishi da wata a kanka, k'aramun in rasaka, don bansan kuma halin dazan shiga ba"

  Mummunar faɗuwar gabane tazo mishi, shi sai yanzu ma ya tuna da yana da wata mata, yaya kenan idan Rabi'ah tasan shifa yanzu mai aurene? Gaba ɗaya jikinshi yayi sanyi, zufa duk taa jik'a mishi riga, bai iya bata amsa ba, sai dai yayi shiru kawai yana tura abincin dak'yar.


  Washe gari kowa yaa hallara a dinning suna break fast, Momie, Daddy, Husna, da Rabi'ar Yasseer, suna cin abinci sai satar kallonshi take, tana so su haɗa ido, anma ko kallonta baiyi ba, ganewa ne kawai Rabiah batayi ba anma tun jiya Yasseer cikin damuwa yake, ta k'asa ta sanya k'afa tana zunguroshi, ya ɗaga kai suka haɗa ido, murmushi ta sakar mishi, da sauri ya maida kanshi yana ci gaba da wasa da cokali,

  Murmushin mugunta tayi, sannan ta haɗa yatsunta biyu na k'afa, ta kamo yatsarshi ɗaya ta matse, har saida yaso yayi k'ara, ya ɗago kanshi da sauri ta tuntsure da daria, Husna naa lura dasu, daria take ciki-ciki, sannan ta shanye tace,

   "Wai yaya har yau naji shiru, nifa na k'ara biki yazo musha shagali, Gani k'anwar Ango kuma k'awar Amarya"

 Wani kallo ya watsa mata, "Ke! Ina wasa dake?"

   Can ciki tace "to ni ba k'awar budurwarka bace"

  "Kika ce?"

 "Ba komai, kawai ina tunanin Yaya Najib ne"

  "ai saiki bishi makarantar" 

 Ta turo baki zata k'ara magana Daddy ya katsesu, "Ya isa hakanan!" ya kalla momie, "Daman maganar da nace miki inasonyi dashi kenan idan yaa dawo, tunda dai bautar k'asar ake jira ya k'are, sai a saka lokaci wata ɗaya bayan yaa gama"

  "Hakanma yayi Alhaji, Allah ya kaimu"

  Daɗine ya kama Rabi'ah, da gudu ta tashi ta tafi ɗakin Husna cikin jin kunya, 

   "Ameen, kinga tare dana Husna kenan" itama tashi tayi tabar wurin, Daddy ya ɗaga kai yana kallon Yasseer daya haɗiye abincin daya saka baki dak'yar,

  "Bakace komi ba, hakan yaa maka dai-dai?"

  "eeh yayi"

   "Yauwah toh abinda nakeso ka gane, yarinyarnan tana sonka sosai, amanah ce a wurinka, don haka kaci gaba da rik'e amanarta, ban yarda da abinda zakai mata ka ɓata mata rai ba"

  Momie tace "Gaskia ne Alhaji, an riga an tsayar da magana a tsakaninku, ban yarda da wata doguwar magana ba daga baya, kowanne zama ɗan hak'uri ne, don haka komai ya faru tsakaninku, kuna dai daitashi basai kowa yaji ba"

  "Insha Allah Momie, Daddy zan kiyaye" ya faɗa dak'yar, yana k'ok'arin ɓoye tashin hankalin daya shiga. Robar ruwan Faro mai sanyi ya ɗauka ya kafa a baki, saida ya shanyeshi tas baima sani ba sannan ya sauke robar, ko kan abincin bai k'ara bi ba ya wuce ɗakinshi yana tunani,

  Saude MATATAH CE, anma ko kaɗan banijin sonta a raina, Rabi'ah itace Masoyiyatah, kuma wacce ta dace dani, itace nake burin na k'are rayuwata da ita, anma abunda zai faru idanta gano ina da wata matar bamai kyau bane, banson na rasa Rabiah, itace burin zuciyatah, anma ya zanyi da auren Saude?


K'AUYE

 Daren Ranar da Yasseer ya tafi, dak'yar Saude ta iya barci ita kaɗai, sai rungumar filo take, tunaninshi kawai ya hanata ta runtsa, ji take daman yana tare da ita, ta k'ara lumshe ido tana rik'e da filo kamar yana tare da ita,

  "harda wani cewa kake 'Saude abunda kika bani ma ya isa har k'arshen rayuwatah bazan manta dake ba' Hmm ni kuma saika bani yanayin da bazan taɓa iya rayuwa babu kai ba, ka daure ka dawo da wuri, ina buk'atarka" tayi murmushi, ita kaɗai tasan yanda takeji akan Yasseer, cikin kewarshi barci ya ɗauketa,


  Tunda Safe bugun gidan da ake ya tasheta, ana dukan k'ofar kamar za'a ɓallata har saida ta tsorata, ta mik'e ta tafi tana tunanin ko waye? Tambaya tayi "Waye?"

  "Uwaki ce" saida gabanta ya faɗi da taji muryar Gwaggo Bilki, ko tunawa da itama batason yi, jikinta na kyarma ta bangajeta ta shiga gidan,

  "Lallai, kin samu wuri ko tunawa bakiyi damu, duk yacce zakiyi dai baki da kamarmu, shegiya mai bak'in hali," ita dai bin bayanta kawai tayi suka shiga gidan, ko gaisuwarta ma bata amsa ba, ta shige ɗakin,

  "naji ance mijinki yayi tafiya, abunda ya bar muki zaki ɗauko ki bani"

  "ai ba daɗewa zaiyi ba, babu abunda ya barmun"

  "k'arya kike! ni zakima k'arya? Tun kafin kiyi wayau muke ciyar dake, ke kinyi gidan miji zaki gujemu ko" sai faɗa take tana ɗage ɗage duk ta watsa en kayan dake cikin ɗakin, ta hankaɗa katifa bata samu komi ba, da taga dai babu kuɗin da take nema, ta buɗa kwalayen da kayan abinci suke ta kwashi son ranta,

  "idan kin hana kuɗi ai bazaki hana wannan ba" bata tanka mata ba, ta ɗauka hartaa fita ta dawo data tuna bata duba k'asan laida ba, tana ɗagawa kuwa sai ga kuɗi, ta ɗago tana kallon Saude,

  "Hinyeh! Munafuka, ni zakima k'arya ko?" takai mata rank'washi, sannan ta k'irga kuɗin,

  "Duk dubu Ukun ma zan tafi dasu, tunda ba daɗewa zaiyi ba kin gane" ta kalleta k'walla suka zubo mata, ta k'ara kai mata bugu "kin tsuramun k'attan idanunki kina kallona, muna fuka" ta gama zazzaga mata, sannan ta kaɗa buje tai gaba,


©Rabiatu sk msh

[3/7, 12:13 AM] ‪+234 703 962 5239‬: ♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

     46-50


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


 Kwana biyun da Yasseer ya mata alk'awari, bai k'ara ba ranar sunday da dare harma ta fidda rai da dawowarshi taa kwanta, ta jiyo bugun gidanshi da sauri ta tafi ta buɗe,

  Tsayawa tayi tana kallonshi cikin hasken farin wata, er tafiyarnan da yayo harya k'ara komawa ɗan gayun fiye da daa, kyanshi yaa k'ara fitowa, ga wani haske daya k'arayi, tama rasa ta inda zata bayyana mishi farin cikin da taji da dawowarshi, kamar ta rungumeshi takeji sai kallonshi take tana washe baki,

  Shima tsayawa yayi yana kallonta, wai nan mijintane ya dawo anma batasan yanda zata tarbeshi, Rabiah ya tuna dako igiyar shanya bata taɓa shiga tsakaninsu ba ballantana ta aure, anma data ganshi zata rungumeshi cikin farin ciki tana faɗa mishi daɗaɗan kalamai, anma ita da take matarshi batasan yanda zata tarbeshi ba, wani haushinta ma ya fara ji, tun farko meya kaishi aurenta? Er k'auye da ita duk taa canja mishi lissafi,

  "Sannu da dawowa"

   "Yauwah sannu da gida" ya wuceta ya shiga cikin gidan, tabi bayanshi yana zama ta kawo mishi abinci ta ajje.

   "A'ah na k'oshi da abincinnan, a gajiye nake kwanciya ma zanyi"

  Tace "tohh" sannan ta koma gefe ta zauna, ya gama rage kaya ya tashi ya shiga ya watsa ruwa, sannan ya dawo ya saka kaya mararsa nauyi duk tana zaune tana jiranshi, ya haye gado ya kwanta, itama bata matsa mishi ba ta raɓa gefe itama ta kwanta babu wani dogon magana a tsakaninsu.

 Washe gari ma tunda wuri ya fice, bayan ya bata kayan tsarabarta, da abubuwan daya sawo mata, yana fita ta fara buɗawa tana murna, ɗinkuna ne masu kyau kalar na birni dai dai jikinta, kala biyar da hijabbai harda takalma, ita kaɗai ta ɗinga murna a gida.

 Ta buɗa sauran kayan mayukan shafawa da kayan wanke kai, harda kayan abinci, tsarabar birni kala-kala, babu ma wanda tasan amfaninshi,


  Saida ya kusan dawowa ta shiga wanka bayan ta gama aikin gidan, cikin kayan Gwanjon daya sai mata ta zaɓi wanda tafiso a ciki ta saka, sannan ta zauna shafa, tana cikin shafa mai yayi sallama ya shigo, ta amsa.

  Yana yaye labulen yayi tsaye yana kallonta,

  "Menene kike shafawa Saude?"

 "Man shafawan daka kawomun ne"

 Ya k'arasa shigowa ɗakin duk takaici yaa cika mishi zuciya, "Yanzu Saude blue band ɗinne man shafawa? Abun da akecin bread ne fa"

  Ya duk'a yana shinshina kanta jin warin Shampoo da takeyi, k'amas babu ruwa a jiki, duk taa tsorata ganin yanda ranshi ya ɓaci, ya kama hannunta yana shinshinawa,

  "Dame kikayi wanka?"

  "Wannan sabulun mai ruwa"

 "wanne irin sabulu kuma?"

Tashi tayi daga inda take ta ɗauko mishi shampoo ta mik'a mishi ya saki baki yana kallonta, duk ta marairaice da ita,

  "Saida naji k'amshin sabulu gareshi nasan wanka za'ayi dashi, kuma kumfa gareshi sosae har saida na k'ara watsa wani botikin ruwan sannan kumfan ya fita"

  Tana k'arasa maganar ya kwashe da dariya, donshi dariyama ta bashi, saida yayi mai isarshi sannan yace ta ɗauko kayan ya fara nuna mata yanda zatayi amfani dasu.


Bayan Wata Biyar.

Saura wata ɗaya ya gama bautar k'asa, zamansu ba yabo ba fallasa, tana matuk'ar girmamashi, shima yana k'ok'arin kyautata mata, yanzu yaa daina daɗewa baije gida ba, kuma duk sanda zai dawo da sabuwar damuwa yake zuwa, gashi yanzu ya kusan gama bautan k'asa, baisan yanda zaiyi da Saude ba, don bama zai iya tunkarar gidansu da ita ba,

  Cikin watan ne ta fara laulayin ciki, wahala yake bata sosae, ya koma kusan komai ma shi yake mata, duk tayi yaushi ta rame, abunda ke k'ara mishi damuwa kenan, 


  Sauran sati ɗaya ya gama bautar k'asa ya ɗauketa suka tafi gidan Kawu Ado, daman daga ganinsu shida Gwaggon suka ɓata rai, ko shimfiɗar tabarma ba'a musu ba, saidai suka tsuguna kan k'afafunsu suna gaishesu, babu wanda yayi amsawar kirki a cikinsu,

  Yasseer ne yayi magana "baba dama zuwa nayi in faɗa muku na kusan komawa gida insha Allah"

  "tohh naji, sai akayi yaya?"

 "maganar Saude ce, zata zauna anan tunda har yanzu iyayena basu san da auren ba, idan na samu lokaci zan dawo insha Allah"

 Tunda ya fara magana take kallonshi, ita batasan da maganar zai tafi ya barta ba,

  "Idan ka barta anan sai yaushene zasu san da auren naku? Ni duk wannan bai shafeni ba, Saude dai na samu na aurar da ita, don haka babu sauran wani abu tsakanina da ita, duk yanda kaso kayi da ita, anma karka sake ka kawomun ita nan"

  Hularshi ya cire saboda zufar data karyo mishi, "Akwai matsala ne idan naje da ita Baba"

  "Aini nafison a samu matsalan idan kunje, anma bazaka bar Saude anan ba, ka ɗauka matarka ku fice, idan zasu saka wuk'a su gutsuttsura ta bai dameni ba, babu sauran alak'a tsakanina da ita, don haka banma ce ku k'ara zuwa inda nake ba"

  Su duka kasa motsi sukayi, anma Saude daɗi taji sosae da Kawu yace da ita Yasseer zai tafi,

  "ku tashi ku tafi nace" kawu ya k'ara daka musu tsawa, jiki a sanyaye Yasseer yayi hanyar fita, itama ta tashi ta bishi.


 Tun daga ranar itama ta fara shirin tafiya, kullum cikin zumuɗin tafiyar take, saboda murnar tafiya birni ma ko lura da fushin da yake da ita batayi ba, ko kaɗan ya daina sakar mata fuska, bala'in haushinta yakeji, gashi kullum bata lafiya,

  Ana gobe zai tafi tana kwance tana barci, yayi tagumi yana tunanin wannan k'addararren aure, bazai iya sakin Saude ba, kuma bazai iya tafiya da ita ba, bai tanaji kalmomin dazaiyima iyayenshi, iyayen Rabiah da itama Rabiahr bayanin matsayin Saude a wurinshi, Saude Matarshi ce kuma harda ɗanshi a cikinta, ta yayama zasu tsaya harya musu bayanin er k'auyen daya aura daga zuwa bautar k'asa?.

  Yana Zaune har akayi kiran Sallahr farko, ya kalli inda take kwance tana sharar barci, kallonta yake cikin tausayawa a fili yace,

  "Kiyi hak'uri Saude, ki yafemun anma bazan iya zuwa gaban iyayena dake ba, bani da zaɓi ne bayan wannan, kiyi hak'uri ki raini ɗanmu har girmanshi, bazan taɓa mantawa da zaman da mukai ba" jin da Yasseer yayi hawaye nason zubo mishi, ya mik'e da sauri ya ɗauka jikkarshi ta tafiya, a hankali ya buɗe gidan ya fita cikin duhun Asuba.


****

Cikin mafarki ta ganta cikin daji, gudu take iyakar k'arfinta, tana tafiya tana waiwayen baya, gaba ɗaya duhu take gani ta ko ina, batasan sanda k'afarta ta faɗa cikin wani zurmemen rami ba, ta k'walla ihu.

  Cikin ramin wani tsananin rayuwah ne ya baibayeta, ta ko ina ji take rayuwar ta juya mata baya, sai kuka take tana neman agaji daga Mahaliccinmu, tana hawaye tana rok'on Allah ya kawo mafa ɗauki.

 A hankali taga haske ya fara bayyana ta cikin ramin data faɗa, har wurin yayi haske sosae, ta ɗaga kanta tana kallon wajen ramin, idonta yayi tozali da kyakkyawar fuskar Yasseer yana mata murmushi, hannu ya mik'a mata alamar ta taho, da sauri ta tashi cikin farin ciki ta mik'a mishi hannun ya rik'e gam, wani farin ciki da bata taɓa ji ba ya ziyarceta, sai murmushi take tana murna,

  Yana cikin fiddota daga ramin data faɗa tana cikin jin daɗi, sai kuma taji ya saki hannunta ta koma ciki, tana shiga duhun ya k'ara lulluɓeta. A firgice ta farka tana Addu'ah a ranta, ta duba inda Yasseer yake kwance babushi ba alamarshi.


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

       51


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


 Cikin tashin hankali Saude ta tashi ta fara waigen ɗakin bata ga Yasseer ba, a ruɗe ta tafi k'ofar toilet ko yana ciki anma bata jiyoshi ba, kamar kaɗangaruwa ta ringa bin bango harta lek'a ciki bainan, tsananin tashin hankali batasanma sanda ta fita daga gidanba, tafiya mai nisa tana nemanshi har wurin masallaci duk da ba'a shiga ba, haka ta daure ta dawo gida, 

   Sai lokacinma ta duba duk kayan Yasseer bai bar komi ba, katifarnan kawai ya bar mata da kayan amfani, tana ɗaga filo sai gaa mak'udan kuɗi nan yaa bar mata, sai lokacin ta ida yarda lallai Yasseer yaa barta, wani irin kuka ne yazo mata na tausayin kanta.

 Ta saka hannu tana shafa cikin jikinta cikin muryar kuka tace "Shikenan mahaifinka yaa tafi ya barmu, ya tafiyanshi, ya gudu ya barni dakai kaɗai" ta k'ara fashewa da wani kuka,

  "Lallai sai yau na k'ara yarda ni marainiyah ce, kayi kuskure Yasseer, kayi kuskure daka shigo rayuwatah ka cutar da wannan raunanniyar zuciyar tawa, kaa riga kaa gama da zuciyatah, tunda ka koyar dani yanda zan soka, kuma ka gudu ba tare daka nunan hanyar dazan daina ba" kuka yaci k'arfinta, tana dukan bango tana kuka, komai na duniyar gaba ɗaya yaa daina mata daɗi.


  Gari naa fara haske ta zari mahafi sai gidan Kawu Ado, shi ɗinne dai komai zai mata bata da inda zata kai kukanta daya wuce can, idanunta duk sun kumbura, duk da rufe fuskar da take en k'auyen sai binta suke da kallo. Harta isa gidan da sallamarta ta shiga, sunyi shimfiɗa tsakar gida suna cin ɗumame, duk suka saki baki suna kallonta.

 Tun kafin tayi magana Gwaggo bilki ta mata tsawa "Yau kuma da wacce tsiyar kikazo mana? Halan kinyi bak'in halin da mijin naki ya fasa tafiya dake?"

 Munanan tambayoyin da suka dira kunnanta kenan daga bakin Gwaggo, anma da yake hankalinta a tashe yake saita k'ara fashewa da wani sabon kukan, "Guduwa yayi, yaa gudu yaa barni"

  "Tohm yanzu waya aika kiranki anan da kikazo kina faɗa mana? Ko sakinki yayi?"

  "A'ah Gwaggo bai sakeni ba, don Allah ku taimakeni"

  Sai yanzu baba Ado yayi Magana "Taimakon k'aniyarki? Lallai duk shekararnan ba'a rainamun hankali ba irin haka, mu ga yaranki ko, mu ringa zagaye gari gari muna nemo mikishi ko ya kikeso ayi? Yaron da bamu taɓa ganin kowa nashi ba bamusan daga inda ya fito ba, koko so kike ki dawo mana nan da zama?"

  Yayi shiru yana mata wani irin kallo, "Tohh ko ɗaya bazai yiwu ba, shi kanshi bazai iya da bak'in halinki bane shiyasa ya gudu ya barki, don haka tunda muma mun samu kinyi nesa damu ki kiyaye ni, aradu na k'ara ganin ko sawunki ne hanyar gidannan sai naayi bala'in saɓa miki"

 Gwaggo tace "k'warai kuwa malam, don kokai kaa yarda ta zauna ni bazan k'ara zama da ita ba, mijinta ma yaa gujeta ballantana mu"

  Wani irin kuka ta fashe dashi tana rok'arsu, "Don Allah Kawu ka taimakeni, kai kaɗai ka rage gatana, bani da kowa a duniya sai kai"

  "ni ɗinma fiddani a lissafinki, indai ni kike kallo a matsayin gatanki tohh bakki dashi, don haka ki tashi ki ficemun nace"

  Kuka taci gaba dayi tana rok'arshi anma yayi biris da ita, da yaga bata da niyyar tafiya ma icce ya ɗauko ya rakata har waje a guje, ya tsaya yana ci gaba da masifa, tsabar kuka Saude har sik'ewa take, dak'yar ta iya kai kanta gida.


  Lallai babu mai laifi a cikin rayuwar data tsinci kanta kamar kawu Ado, yana sane da cewa basu san asalin Yasseer ba, basusan kowa nashi ba suka bashi aurenta don tsanar da suka mata, da sun samu wani wanda yake garin komai talaucinshi komai nakasunshi yafi mata wannan auren k'addarar da suka ɗora mata, maganar Yasseer ce ta ringa dawowa mata kullum ta tambayeshi garin da yake,

  "Kina tsoran kar in gudu in barki ne?" sai yanzu ne ya tabbatar mata da abunda yake nufi, duk da yarda dashi da tayi bata taɓa sakawa taa kawo hakan a ranta ba.


Bayan wata bakwai...

Rayuwar Saude har tafi ta daa muni, tana gida ita kaɗai sai abunda ke cikinta, ko waje batason lek'awa don da an ganta ne za'a fara mata wak'a irin tasu ta k'auye, ana sakar mata habaici, har yara gulmanta suke idan zata wuce, mijinta yaa gudu yaa barta, ita kam kullum cikin saka ran dawowar Yasseer take, don shine yasan inda take, tana saka ran duk daɗewa zai nemeta.

  Wata rana tana zaune ita kaɗai tayi tagumi cikin watan haihuwarta, cikinta ne ya fara murɗawa, nak'uda tazo mata gadan-gadan, gashi babu kowa gidan sai ita kaɗai, daman babu mai zuwa inda take, ta dinga ihu tana neman agaji, tayi matuk'ar galabaita,

  Cikin sa'a saiga k'awarta Hanne zata wuce ta shiga gidan, daman ita kaɗaice koda tana gidansu Gwaggo takejin tausayinta, ba ɓata lokaci ta tafi tazo da unguwar zoma, lokacin harta fara fita hayyacinta, ita ta taimaka mata harta haifo k'atuwar yarinyarta jajir kamar babanta. Farine kawai ta ɗauko na Babanta anma komai nata na mamantane, kamarsu ɗaya da Saude kamar tayi khaki.

  Unguwar zoma da Hinde ne suka taimaka mata suka gyarata da jaririyar tata, zata tafi ta ɗauko kuɗin sallama ta bada ta tafi tana ta godia, Hinde ita ta samo maiyi ma Saude wanka da erta, idanta samu lokaci tana zagayota, da en tsirarun en k'auyen masu zuwa su bama idonsu abinci, su gwaggo dai ko lek'e har akayi suna.

  Cikin kuɗin da Yasseer ya bar mata ne, ta saima yarinyar kayan sakawa, tasa aka yanka ma yarinyar ragon suna, taaci suna Hafsat, saboda yanda takeson sunan, kuma babu dai wanda zai zaɓa ma er tata suna bayan ita.


  Kwanci tashi babu wuya wurin Allah, Hafsat ta fara girma, taayi wayau ita ta zama abokiyar firar Saude, ita take ɗebe mata kewar mahaifinta, ko wasanta take da Saude tayi shiru tana tunani zata rarrafo ta tafi inda take, tana ɗaukarta tayi ta wangale baki.

  Zara dai bata barin dame, hafsat nada kusan shekara biyu komai ya fara fin k'arfin Saude, duk kuɗin dake hannunta sun k'are tunda daman ba juyasu take ba, harta fara siyarda kayan amfanin gidan, rayuwar hafsa take tausayamawa, batason ta tashi cikin k'uncin rayuwa ta saba da babu da yunwa, idanma ta zauna a haka ai saidai yunwa tayi ajalinsu tunda babu mai taimaka mata, sannan kuma wacce amsa ma zata bama hafsat idan taa girma ta tashi tambayarta waye mahaifinta? Taa rasa sana'ar da zatayi, gashi k'auyen ba kowane ke bada aikatau ba, kowa baison fidda kuɗi.


  Wata matar dake ɗaukar en aiki takai birni taje ta samu ta faɗa mata buk'atarta nason ta samar mata gidan aiki inda za'a dinga biyanta koda abincin da zataci ne,

 Baba haja ta nisa tace "Anya Saude zaki iya kuwa? Nifa banan kusa nake kai en aiki ba, can birnin Abuja nake zuwa"

  "koma a inane zan iya zuwa wallahi baba Haja, wake gareni a k'auyen da bazan iya tafiya ba? Ai yin nesan ma shine zaifimun Alkhairi"

  "tohh Allah yasa hakan, daman akwai wata Amaryah ce don ko haihuwa batayi ba, tace in samo mata er aiki, Allah yasa ta amsheki don basu cikason en aiki yara ba"

  "Ameen baba, ni indai zata amince wallahi aikinta ko yakai girman me zan iya mata"

  "Tohh ai shikenan, sai kije ki fara shirye-shirye idanna tashi tafiya zan nemeki"

 Tayi ma baba Haja Godia sosae sannan ta tashi ta tafi.


  Tana shirin tafiya tana tunanin yanda Yasseer ya mata, saida ta gama shiri ya tafi ya barta, ita yanzu tama fidda rai da dawowarshi, don indai bai manta da ita ba tsawon lokacinnan yaa isa ya nemeta.

  Ko sati biyu ba'ayi ba, baba Haja ta aiko mata tafiya taa tashi, en kayanta da suka rage daman duk taa sayar, ta tattara en kuɗinta suka tafi, bayan taje tayima mai gidan hayar da suke godia, don daman cewa yayi kuɗin da Yasseer ya biyashi ko zata shekara biyar a ciki bazasu k'are ba, ta bar mishi dai ta tafi.

  Wa yaga Saude a Abuja😄 ita da ko k'auyensu bata taɓa bari ba, nima dai naa tafi in shirya don dani za'aje Abujar nan😃👯👯


©Rabiatu sk msh

Copied By

HAYATU BABA ZUBAIRU

    (admin

  Arewa hausa novels 

    Novels villa

   Duniyan novels 

  Hayat hausa novels

Hausa novels and fashion

     And 

Cool novel, makeup and cooking) 


   WHATSAPP NO:

  +2347039625239

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

       51


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


 Cikin tashin hankali Saude ta tashi ta fara waigen ɗakin bata ga Yasseer ba, a ruɗe ta tafi k'ofar toilet ko yana ciki anma bata jiyoshi ba, kamar kaɗangaruwa ta ringa bin bango harta lek'a ciki bainan, tsananin tashin hankali batasanma sanda ta fita daga gidanba, tafiya mai nisa tana nemanshi har wurin masallaci duk da ba'a shiga ba, haka ta daure ta dawo gida, 

   Sai lokacinma ta duba duk kayan Yasseer bai bar komi ba, katifarnan kawai ya bar mata da kayan amfani, tana ɗaga filo sai gaa mak'udan kuɗi nan yaa bar mata, sai lokacin ta ida yarda lallai Yasseer yaa barta, wani irin kuka ne yazo mata na tausayin kanta.

 Ta saka hannu tana shafa cikin jikinta cikin muryar kuka tace "Shikenan mahaifinka yaa tafi ya barmu, ya tafiyanshi, ya gudu ya barni dakai kaɗai" ta k'ara fashewa da wani kuka,

  "Lallai sai yau na k'ara yarda ni marainiyah ce, kayi kuskure Yasseer, kayi kuskure daka shigo rayuwatah ka cutar da wannan raunanniyar zuciyar tawa, kaa riga kaa gama da zuciyatah, tunda ka koyar dani yanda zan soka, kuma ka gudu ba tare daka nunan hanyar dazan daina ba" kuka yaci k'arfinta, tana dukan bango tana kuka, komai na duniyar gaba ɗaya yaa daina mata daɗi.


  Gari naa fara haske ta zari mahafi sai gidan Kawu Ado, shi ɗinne dai komai zai mata bata da inda zata kai kukanta daya wuce can, idanunta duk sun kumbura, duk da rufe fuskar da take en k'auyen sai binta suke da kallo. Harta isa gidan da sallamarta ta shiga, sunyi shimfiɗa tsakar gida suna cin ɗumame, duk suka saki baki suna kallonta.

 Tun kafin tayi magana Gwaggo bilki ta mata tsawa "Yau kuma da wacce tsiyar kikazo mana? Halan kinyi bak'in halin da mijin naki ya fasa tafiya dake?"

 Munanan tambayoyin da suka dira kunnanta kenan daga bakin Gwaggo, anma da yake hankalinta a tashe yake saita k'ara fashewa da wani sabon kukan, "Guduwa yayi, yaa gudu yaa barni"

  "Tohm yanzu waya aika kiranki anan da kikazo kina faɗa mana? Ko sakinki yayi?"

  "A'ah Gwaggo bai sakeni ba, don Allah ku taimakeni"

  Sai yanzu baba Ado yayi Magana "Taimakon k'aniyarki? Lallai duk shekararnan ba'a rainamun hankali ba irin haka, mu ga yaranki ko, mu ringa zagaye gari gari muna nemo mikishi ko ya kikeso ayi? Yaron da bamu taɓa ganin kowa nashi ba bamusan daga inda ya fito ba, koko so kike ki dawo mana nan da zama?"

  Yayi shiru yana mata wani irin kallo, "Tohh ko ɗaya bazai yiwu ba, shi kanshi bazai iya da bak'in halinki bane shiyasa ya gudu ya barki, don haka tunda muma mun samu kinyi nesa damu ki kiyaye ni, aradu na k'ara ganin ko sawunki ne hanyar gidannan sai naayi bala'in saɓa miki"

 Gwaggo tace "k'warai kuwa malam, don kokai kaa yarda ta zauna ni bazan k'ara zama da ita ba, mijinta ma yaa gujeta ballantana mu"

  Wani irin kuka ta fashe dashi tana rok'arsu, "Don Allah Kawu ka taimakeni, kai kaɗai ka rage gatana, bani da kowa a duniya sai kai"

  "ni ɗinma fiddani a lissafinki, indai ni kike kallo a matsayin gatanki tohh bakki dashi, don haka ki tashi ki ficemun nace"

  Kuka taci gaba dayi tana rok'arshi anma yayi biris da ita, da yaga bata da niyyar tafiya ma icce ya ɗauko ya rakata har waje a guje, ya tsaya yana ci gaba da masifa, tsabar kuka Saude har sik'ewa take, dak'yar ta iya kai kanta gida.


  Lallai babu mai laifi a cikin rayuwar data tsinci kanta kamar kawu Ado, yana sane da cewa basu san asalin Yasseer ba, basusan kowa nashi ba suka bashi aurenta don tsanar da suka mata, da sun samu wani wanda yake garin komai talaucinshi komai nakasunshi yafi mata wannan auren k'addarar da suka ɗora mata, maganar Yasseer ce ta ringa dawowa mata kullum ta tambayeshi garin da yake,

  "Kina tsoran kar in gudu in barki ne?" sai yanzu ne ya tabbatar mata da abunda yake nufi, duk da yarda dashi da tayi bata taɓa sakawa taa kawo hakan a ranta ba.


Bayan wata bakwai...

Rayuwar Saude har tafi ta daa muni, tana gida ita kaɗai sai abunda ke cikinta, ko waje batason lek'awa don da an ganta ne za'a fara mata wak'a irin tasu ta k'auye, ana sakar mata habaici, har yara gulmanta suke idan zata wuce, mijinta yaa gudu yaa barta, ita kam kullum cikin saka ran dawowar Yasseer take, don shine yasan inda take, tana saka ran duk daɗewa zai nemeta.

  Wata rana tana zaune ita kaɗai tayi tagumi cikin watan haihuwarta, cikinta ne ya fara murɗawa, nak'uda tazo mata gadan-gadan, gashi babu kowa gidan sai ita kaɗai, daman babu mai zuwa inda take, ta dinga ihu tana neman agaji, tayi matuk'ar galabaita,

  Cikin sa'a saiga k'awarta Hanne zata wuce ta shiga gidan, daman ita kaɗaice koda tana gidansu Gwaggo takejin tausayinta, ba ɓata lokaci ta tafi tazo da unguwar zoma, lokacin harta fara fita hayyacinta, ita ta taimaka mata harta haifo k'atuwar yarinyarta jajir kamar babanta. Farine kawai ta ɗauko na Babanta anma komai nata na mamantane, kamarsu ɗaya da Saude kamar tayi khaki.

  Unguwar zoma da Hinde ne suka taimaka mata suka gyarata da jaririyar tata, zata tafi ta ɗauko kuɗin sallama ta bada ta tafi tana ta godia, Hinde ita ta samo maiyi ma Saude wanka da erta, idanta samu lokaci tana zagayota, da en tsirarun en k'auyen masu zuwa su bama idonsu abinci, su gwaggo dai ko lek'e har akayi suna.

  Cikin kuɗin da Yasseer ya bar mata ne, ta saima yarinyar kayan sakawa, tasa aka yanka ma yarinyar ragon suna, taaci suna Hafsat, saboda yanda takeson sunan, kuma babu dai wanda zai zaɓa ma er tata suna bayan ita.


  Kwanci tashi babu wuya wurin Allah, Hafsat ta fara girma, taayi wayau ita ta zama abokiyar firar Saude, ita take ɗebe mata kewar mahaifinta, ko wasanta take da Saude tayi shiru tana tunani zata rarrafo ta tafi inda take, tana ɗaukarta tayi ta wangale baki.

  Zara dai bata barin dame, hafsat nada kusan shekara biyu komai ya fara fin k'arfin Saude, duk kuɗin dake hannunta sun k'are tunda daman ba juyasu take ba, harta fara siyarda kayan amfanin gidan, rayuwar hafsa take tausayamawa, batason ta tashi cikin k'uncin rayuwa ta saba da babu da yunwa, idanma ta zauna a haka ai saidai yunwa tayi ajalinsu tunda babu mai taimaka mata, sannan kuma wacce amsa ma zata bama hafsat idan taa girma ta tashi tambayarta waye mahaifinta? Taa rasa sana'ar da zatayi, gashi k'auyen ba kowane ke bada aikatau ba, kowa baison fidda kuɗi.


  Wata matar dake ɗaukar en aiki takai birni taje ta samu ta faɗa mata buk'atarta nason ta samar mata gidan aiki inda za'a dinga biyanta koda abincin da zataci ne,

 Baba haja ta nisa tace "Anya Saude zaki iya kuwa? Nifa banan kusa nake kai en aiki ba, can birnin Abuja nake zuwa"

  "koma a inane zan iya zuwa wallahi baba Haja, wake gareni a k'auyen da bazan iya tafiya ba? Ai yin nesan ma shine zaifimun Alkhairi"

  "tohh Allah yasa hakan, daman akwai wata Amaryah ce don ko haihuwa batayi ba, tace in samo mata er aiki, Allah yasa ta amsheki don basu cikason en aiki yara ba"

  "Ameen baba, ni indai zata amince wallahi aikinta ko yakai girman me zan iya mata"

  "Tohh ai shikenan, sai kije ki fara shirye-shirye idanna tashi tafiya zan nemeki"

 Tayi ma baba Haja Godia sosae sannan ta tashi ta tafi.


  Tana shirin tafiya tana tunanin yanda Yasseer ya mata, saida ta gama shiri ya tafi ya barta, ita yanzu tama fidda rai da dawowarshi, don indai bai manta da ita ba tsawon lokacinnan yaa isa ya nemeta.

  Ko sati biyu ba'ayi ba, baba Haja ta aiko mata tafiya taa tashi, en kayanta da suka rage daman duk taa sayar, ta tattara en kuɗinta suka tafi, bayan taje tayima mai gidan hayar da suke godia, don daman cewa yayi kuɗin da Yasseer ya biyashi ko zata shekara biyar a ciki bazasu k'are ba, ta bar mishi dai ta tafi.

  Wa yaga Saude a Abuja😄 ita da ko k'auyensu bata taɓa bari ba, nima dai naa tafi in shirya don dani za'aje Abujar nan😃👯👯


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

       52


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


 Ina matuk'ar baku haqurin rashin jina kwana biyu, wasu na faɗa musu uzuri na rashin charge, anma komai yaa dai daita zakuna jina insha Allah, Nogode sosae da soyayyarku ga wannan littafin.❤

  Masu tambayana daga farko, na samu naa sakashi a blog, zaku iya samunshi a can harma da wanda aka wuce👇🏻😊


www.babymsh.blogspot.com


 Da marece sosae suka isa garin, sai da aka gama kai kowa sannan ta tafi kai Saude gidan da zatayi aiki, sai kalle-kalle take ta dai daure tace, "Baba haja wai duk nan garine?"

   "eeh mana, babban birnin tarayya kenan da kikeji"

  "Aini ban ɗauka yakai girman haka ba, wannan ai sai dai a kirashi k'asa guda"

  "A'ah shima garine, ai bakiga komi ba a girman garin Abuja,"

  "Taɓ! Gaskiya ne Baba haja, kowah da garinsu"

 Baba haja na mata daria tace "hakane kam"

 Suna tafiya ta k'ara ganin wani ginin bene, shima dai kasa shiru tayi tace "Yanzu baba wannan ma mutanene suka ginashi?"

  "tohh saude kin taɓa ganin Aljanu sunyi gini?"

  "A'ah baba, anma dai yana faɗowa ko?"

   "A'ah ko zaki hau ne?" Baba Haja ta tambayeta cikin tsokana, da sauri ta girgiza kai, "A'ah ni bazan hau ba ya zurma dani ciki"

  Baba Haja na mata daria tace "ai bazaki zurma bafa"

  "A'ah nidai Baaba"


  Ana kiran Sallahr Magrib suka isa gidan da Saude zatayi aiki, Babban gidane sosae anan ma saida Saude ta cika Baba Haja da tambaya, ta ware ido sosae tana kallo, sai tayi tuntuɓe take ɗan kallon hanya sannan taci gaba.

  Saman carpet suka zauna bayan an tafi musu iso, sai faman shafawa take tanajin laushi har mai gidan ta fito da fara'arta da yake tasan baba Haja, suka gaisa cikin mutuntawa, Saude ma ta gaisheta, sannan Baba haja ta gabatar mata Saude a matsayin er aikin data nema, saida ta gama k'are ma Saude kallo sannan,

  tace, "Baba haja mantawa nayi ban faɗa miki ba, banda en matah indai an samu dattijuwa dai ita nakeso"

  "Ai duk ɗayane uwargidanah, duk aikin da dattijuwa zata miki itama zata iya"

  "Ba aikin ba ai Baba haja, ina tsoran budurwa da aiki ne"

  "tohh ai ita ba budurwa bace, gashi dai harda Goyonta"

 Dariya tayi "Haba Baba, wannan ai sai dai ko k'aninta, anma er yarinya da ita da goyo? A daiyi hak'uri a samo dattijuwar Baba, anma dai wannan batayi ba"

  "Tohh ai shikenan" Baba ta faɗa a sanyaye, ita kam Saude tuni ta lulluɓe fuskarta a mayafi, tana ta kukanta marar sauti, yanzu aikinma taga samu taga rashi.

  Abinci aka kawo musu da drinks, bata wani ci da yawa ba dai duk Baba na lura da damuwar data shiga, ana isha'i suka fito gidan.


 Suna fitowa Saude ta fashe da kuka, Baba haja ta kalleta,

   "karki kuka Saude, insha Allah zaki samu inda zaki aiki"

  "A ina Baba Haja? Nidai Saude naaga rayuwa"

  "Haba Saude, ki daina mana, ki barni inyi tunanin gidan da suka sakani neman er aiki"

 Shiru tayi sun samu wuri cikin duhun daren sun zauna, Baba haja na tunani ita dai sai shesshek'ar kuka take.

  "tohh ni Saude ina zan kaiki yanzu?"

  "ki taimakeni Baba don Allah karmu koma garinnan"

  "Yanzu tashi muje gidan Hajia, nasan ko bazata ɗaukeki aiki ba zata taimaka miki" da sauri kau Saude ta maida goyon Hafsat, ta saɓi kayanta suka tafi. Tana Addu'ah a ranta Allah yasa ta dace.


  Gabanta naa faɗuwa suka isa gidan Hajiyar, harma yafi na inda suka fara zuwa girma, ga motocinan da ma'aikata birjik, duk da darene ko ina Haske yake da fitilu masu launuka sun haska gwanin kyau duk hanyar da zasu bi, tafiya sukayi mai ɗan nisa sannan suka isa hanyar da zata sada su da cikin Gidan, gabanta na faɗuwa sukayi sallama suka shiga.

  Dattijuwar macece fara tas kyakkyawar gaske, da jin daɗi da hutu suka ɓoye shekarunta, tana zaune a falo taa gama sallamar bak'i, ta tari su da fara'arta, tana nuna musu kujera su Zauna, Baba Haja ce kawai ta zauna, anma Saude kasa zama tayi.

  "Haja Sai yau muke ganinku?" dattijuwar ta faɗa tana murmushi,

  "Hajia abubuwanne da yawa, yanzu ma en aiki ne nazo kawowa"

  "Ayyah! Wannan ta wajenki ce?"

  Tayi dariya "Ta gida daice, anma itama aikin na kawota, ba'a dace ba nace bara muzo ko kina da buk'ata"

  "tohh wannan er yarinya ina zata iya da aikin gidannan? Kuma Gaskia ban daɗe da ɗaukar en aiki ba"

  "tohh Hajia a duba dai, taimakon da kika saba"

    "tohh ai gaskia...." tayi shiru tana tunani, Saude batasan sanda kukan da take rik'ewa ya kubce mata ba,

  "tohh ɗiyata lafiya kike kuka?"

 Cikin tausayawa Baba Haja tace "Hajia nasan ke kaɗaice zaki iya taimaka mata, rayuwarta tana buk'atar taimako, batasan iyayenta ba tun kafin tayi wayau Allah ya ansa abinshi, gashi babu miji, sai musgunawar dangin mahaifi" nan Baba Haja ta fara bama hajiyar tarihin Saude komai ta faɗa mata sai dai taa ɓoye mata cewar Mijin Saude mutuwa yayi bata da aure, daman Saude taa rok'eta karta faɗa mijinta guduwa yayi ya barta, duk daman Baba Hajar bata sanshi ba.


  Tsabar tausayawar da hajia tayi mata har saida ta zubda hawaye, kuka sosai tayi daman macece mai tausayi bama kamar ga mata, "Sannu kinji Saude, gaskia naa tausaya miki, rashin iyaye ba k'aramin rashi bane, Ga na miji kuma, ni naasan zafin rasuwar miji don har yau inajin ta maigidana, shekararshi ɗaya kenan da rasuwa,"

  "Allah sarki, Allah yaji k'anshi" inji Saude

  "Ameen tare da naki, ai ke keda rashi, da k'uruciyarki babu miji babu iyaye, wallahi na tausaya miki sosai"

  Maganganun hajia kuka suke k'arama Saude,

  Ta share hawayenta cikin son kauda ma Saude damuwa, 

   "Ina tsohuwar take? Kawomun itanan in ganta Allah sarki itama tayi rashin mahaifi" Saude ta kwanto Hafsa a goye, cikin tsaftar ta duk da kayanta a koɗe suke, an wanke tas babu k'azanta, kuma bata barinta tayi fitsari a wando.

  "Ya sunanta?" hajia ta tambaya tun kafin a mik'a mata ita,

  Baba Haja ce tace "Hafsat"

  "A'a'ahh ashe takwarah ce, zonan Hafsatul kiram" ta ansheta tana fara'a, itama hafsat ɗin sai washe mata bak'i take.

  Cak ta tsaya tana k'are ma Hafsat kallo, yanda take daria da sauran Abubuwa kallonta kawai take, ta kasa hak'uri dai tace "Baba Haja abun mamaki bai k'arewa a duniya"

   "Hajia wani abun ya faru?"

  "Ke baki gani ba Haja? Wallahi yanayin yarinyarnan Sak na Daddy lokacin yana k'arami, ko zuwan duk da yana babba anma yanayin fara'arsu da dariyarsu ɗaya, ke ni duk yanayinsu ɗaya ma wallahi"

  "aikau hajia nima saida kikayi magana na lura, abun mamaki kam da yawa yake, tunda nazo daman ban tambayi mutumin nawa ba, ina mai sunan Baba?"

  "Aikam saɓani kuka samu Daddy yau ya koma wurin aiki"

  "Allah sarki, mun kwana biyu bamu gaisa ba" Hafsat ta kamo fuskarta tana ta k'iriniyarta a samanta kamar sun saba, itama sosae ta fara jin yarinyar a ranta.

  Baba Haja ma kallonta take "Gaskia duk da basu kama, anma yanayin harya ɓaci"

  Hajia tace "ai daman hakane, sai kiga wani yaa haifa maka ɗa"

  "Hakane fa, kama dai komai na babarta ta ɗauko"

  

 Hajia ta nisa bayan duk sunyi Shiru, "Zan ɗaukeki aiki Saude, anma ina da sharaɗi"

  Harta farajin daɗi, kafin hajia ta k'arasa maganarta, sai kuma murnarta ta koma ciki, "ki faɗi sharaɗin Hajia, insha Allah ko menene zanyi"

  "kin tabbata?"

  Ta ɗaga kai gabanta na ci gaba da faɗuwa, "Indai zaki zauna anan, sai dai ki zauna a matsayin ɗiyata" wani farin ciki ne ya kama Saude da Baba Haja ko wannensu sai murna yake,

   "Nagode! Nagode Hajia! Allah ya saka da mafificin Alkhairi" abunda Saude kawai ke cewa kenan, tama rasa abun cewa saboda murna,

  "Ba komai Saude, hakanan tausayinki ta ɗarsu a raina, zan rik'eki amana, kema ki rik'e amana, zan zame miki gatan da kika rasa, zan baki duk abunda zaki nema a rayuwa indai Allah ya horemun ina dashi, zan baki duk wani farin ciki da zaki buk'atah"

  "Na gode Hajia, ki bani iyayen dana rasa ma yafimun komai, na miki alk'awarin bazan taɓa baki dalilin da zaki koka da halina ba"

  "Naji daɗi sosai Saude, ki saki jikinki kamar gidanku, ni kaɗaice a yanzu, bara a nuna miki ɗakin yayarki da tayi aure anan zaki zauna"

 Ta fara k'wala ma mai aikinta kira, sai gata da sauri ta mata umurnin akai Saude ɗakin ɗiyarta da tayi aure, dare yayi ta huta, hafsat ɗinma cewa tayi ta barta zata bama wacce zata kula da ita tunda an yayeta, Baba Haja ma ɗakin bak'i aka kaita ta kwanta.


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

       53


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


Ga Shafinku nan na jiya Masoya littafinnan, ```KISAN KANKI GRP```😜❤ gareku RAZ NOVELLA 1&2 I really appreaciated soyayyar da kuke nunama littafinnan, Rabiat na k'aunarku har k'asan zuciyatah😍


www.babymsh.blogspot.com


 Wani k'ayataccen ɗaki aka shiga da Saude, ɗaki ɗayane anma babba sosae, akwai kujeru masu kyau da babban Gado saiti, komai na ɗakin a tsare kalan skye blue, ba k'aramin k'ayatuwa yayi ba, a ciki harda toilet shima babu abunda babu a ciki kamar ansan da zuwan Saude, 

  Wuri ta samu ta zauna gefen gadon saman lumtsumemiyar katifarta, wai wannan k'ayataccen ɗakin duk nata ne, duk kayan dake cikin ɗakinnan na mutum ɗaya ne, lallai en gayu sunji daɗinsu, 

  Mai aikince ta dawo mata da abinci sannan ta faɗa mata tanaso tayi sallah, ta rakata toilet ta nuna mata yanda zatayi, ananma duk tasha k'auyanci, dak'yar ta gama kalle-kallenta tayi alwala ta fito.

  Tunda tayi sallah ta kwanta barci ya ɗauketa, ko juyi batayi saman luntsumemiyar katifar, sai da asuba aka k'wank'wasa mata k'ofa, dak'yar ta tashi tayi sallah saboda barcin dake idonta, tana idarwa ta kwanta saman carpet ɗin taci gaba da barcin.


  Sanda ta farka ta fito har Baba Haja ta tafi, bataji daɗi ba taso suyi bankwana ta mata godiya sosae, er aikin Hajiya ce ta rakata har ɗakin da hajiyar take tace tun ɗazu take nemanta, da Sallama ta shiga ɗakin, ta amsa mata duk da tana kan waya ne, ta ɗan tsaya bata shiga ba.

  "shigo mana Saude, ina waya da ɗan uwanki ne"

 Allah sarki hajia har yaranta sun zama en uwan Saude, saman cinyarta ta iske Hafsat tana ta wasanta, tana ganinta ta k'ara washe baki tana mik'a mata hannu, anma kunya ta hanata ɗaukarta ta nema wuri k'asa ta zauna tana jiran Hajia ta gama magana.

 Cikin nishaɗi take wayar cike da soyayyar ɗa da uwa, 

  "Yanzu haka kaa gantanan hannuna, sai kallonta nake tana ɗebemun kewarka da kana yaro" bataji mai akace ba ɗayan ɓangaren sai dai hajiyar ta k'ara magana,

  "nifa ba kama kuke ba, ita ai kyakkyawah ce kamar mahaifiyarta" dariya ta k'arayi bayan taa gama magana.

  "kana dashi, anma dai takwarah ta taa fika kyau"

 Tana dariya ta gama wayan "Hmm shak'iyin yaro kawai" 


  Saude tayi murmushi, "Ina kwana hajia"

  "lafiya lau Saude ya kika tashi? ya bak'unta?"

  "Alhmdlh"

   "gaskia kinsha gajia, har Baba Haja ta tafi kinata barci, nina hana a tasheki gara a barki ki huta"

  "uhum" kawai tace,

 "Daddy ne muke waya inata bashi labarin Hafsat, yarinya mai saurin sabo, wai harya k'agu weekend yayi yazo yaga childhood image ɗinshi"

   "Allah ya dawo dashi lafiya" 

  "Ameen, ya dawo yaga k'anwar dana mishi" murmushi dai kawai Saude take, taso ta tambaya Hajia sunanshi na gaskia, anma kunya ta hanata, da alama Hajia tanaji dashi sosae.

  "kinyi wanka?" ta katse mata zancen zucin da take, girgiza kai tayi

  "karin kumallo/kalaci fa?"

    "A'ah"

  "Har yanzu? Aikam mun tashi ɓatawa, banison bak'untarnan Saude kije kitchen talatu ta haɗa miki abunda zakici, idan kinyi wanka ki buɗa ma'ajiyar kayan sawa akwai na yayarki nanan kafin tayi aure, k'ila suyi miki kafin in fita ayi miki wasu" 

  "tohh Hajia nagode"

  "kuma dai? Idan zakimun Godia duk abunda zan miki a rana dubu nawa zakimun? Kamar mahaifiyarki nake babu godia tsakaninmu, don haka ki ringa kirana da Momie kamar sauran Yayunki"

  "Tohh momie Na..." sannan kuma tayi shiru ganin Momie ta ɗago tana kallonta, ta sakar mata murmushi sannan ta fita wurin talatu, cikin sa'a a falo ta ganta, daman tana tunanin inda zata gano kitchen ɗin.


 Zaman Saude cikin gidan tana daɗa samun kwanciyar hankali, duk da babu inda take fita kuma shigarta da komai nata na k'auye nanan, sai dai jikinta dake k'ara murmurewa yana kyau ta ɗanyi k'iba jikinta ya fara kyau alaman hutu, kullum Momie zata kirata su zauna tana mata fira, tana k'ara janta a jiki, tsakaninta da Hafsat kuma sai kallo ko idan Momie taa fita ta ɗauketa, koda yaushe tana hannun Momie sai barci take bada ta wurin mai kula da ita, kayan yara masu na mata data gani zata zoma Hafsat dasu, ta washe sosai daman Gata kyakkyawa, kamar ba'a k'yauye aka haifeta ba, ta k'ara zama abun sha'awa ga kowa. Soyayya sosae take nuna musu kamar ita ta haifa Saude.

  Kwananta biyar da zuwa gidan ko tsakar gida bata taɓa fita ba, aka fara shirye-shiryen dawowan yaron Momie, kullum sai momie tayima Saude firan Daddy, shima har gajia yake da labarinta da momie ke bashi, yamafi son firar Hafsat har waya suke tayi ta yi mishi gwarancinta.

  Daren Ranar dazai dawo basu kwanta da wuri ba, soye-soye aka dinga mishi kamar ba mutum ɗaya ne zaizo ba, yanda Saude ta dage tana aiki duk da daman kullum bata zama, yasa momie take ta faman ce mata taje ta huta, anma bata tafi ba har aka gama.


 Washe garin ranar dazai dawo friday, tunda safe suka farka aka fara girke-girke, momie sai faman kiranshi take tun safe, kaɗan-kaɗan taa cema Saude, ko mantawa take da tayi mata maganar?

  "Kinga k'azamin yaronnan yak'i ya dinga barin mukullanshi a mishi gyaran ɗaki, kullum yafison zama cikin k'azanta"

  Sai dai kawai tayi murmushi "ai haka ɗakin mazan yake Momie"

  "Haba k'azamai dai, koda Husna nanan sun dinga faɗa kenan idan taa mishi gyara bai sani ba, wai tana zubda mishi takardu masu amfani"

  "Allah sarki, ai basu cikason hakan ba"

 "Hhm bakisan k'azantar Yayannan naki bane, saiya buɗa ɗakin nashi zakiga jibji" dariya tayi sosae, momie ma ta tashi tana dariyar jibjin da tace.

  Har marece ana jiranshi baizo ba, momie sai kiranshi take a kashe sai marece sosai ta sameshi.

  "wai meya tsaida kai har yanzu baka dawo ba?" ta ɗanyi shiru tana saurarenshi.

  "A'ah kasan banson tafiyar darennan, kayi zamanka kai aikinka wani satin kaazo"

  "A'ah nace, duka yaushe ka tafi? Ka zauna ka gama duk abunda kake fa"

  "Yauwah tohh zan kashe saimun sake maganar" ta sauke wayar fuskarta da alamar rashin jin daɗi.

 "kin ganshi ashe aiki ya tsaidashi, wannan satin bazai samu zuwa ba"

  "Allah sarki, ai kamar gobene"

 "Hakane Allah ya kaimu"

   "Ameeen"


 Da dare momie ta kirashi tana k'ara tambayarshi aikin, duk yaa lura bataji daɗin rashin zuwanshi ba, Momie taa damu dashi sosae, sai dai yaci gaba da kwantar mata da hankali da firar da zata sakata daria irinna ɗa da mahaifiya harta ware, sannan sukai sallama, lokacin Saude ta shigo mata saida safe, tana kan cewa ya rik'e wayan su gaisa da k'anwarshi harya kashe, ta mata bankwana ta koma ɗakinta.

  Washe gari da wuri Momie ta fita, har Hafsat ta saka aka shirya mata ita ta tafi da ita Saude na can tana barci, sai k'arfe 10 ta farka da wata matsananciyar yunwa, ta sauko daga Gadon sannan ta jawo zani ta ɗaurin k'irji dashi saman doguwar rigar barcin jikinta, ta tsira ɗan kwalinta irin style ɗin da suke a k'auye shigarsu dai ta en k'auye, kai tsaye kitchen ta nufa.

  Talatu ce kaɗai a kitchen ɗin ta fara aikin rana, ta gaisheta cikin girmamawa, sannan tace "Momie fa?"

  "sun fita ita da takwararta"

  "Yau safko sukayi kenan"

   "aikam da wuri ta fita"

 Suna ɗan taɓa firarta tana haɗa break fast, doya da k'wai sai ruwan tea ta ɗauka ta fito tana cema talatu bara tayi break fast ta dawo.

  "ai naga alama barcinnan bai isheki ba, yunwah ce kawai ta tasheki"

  "wallahi fa, ai hakanan dai zan barshi" ta faɗa tana murza ido da hannun data rik'e tean, bayan taa cika baki da doya. Dai-dai lokacin tana wucewa ta k'ofar da zata shigo da mutum falon.

  Ji tayi ta kaima mutum karo, gaba ɗaya tean dake hannunta ya kwarare mishi a jiki, da sauri tayi k'asa dakai ba tare dasun haɗa ido ba, jikinta ya fara kyarma ganin yanda ta mishi a jiki tama kasa bashi hak'uri.


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

      54


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


 Ko kallon inda take duk'e baiyi ba, ya wuce ta kawai ya shiga falon, wata hanyar yabi daban, saida taji yaa wuce sannan ta ɗago tana kallonshi bata ga fuskarshi ba, anma a jiki ma ba k'aramin haɗuwa yayi ba, shigarshi kanta ta dabance, ga k'amshin turaren daya bar mata nan mai daɗin k'amshi.

  Sauke ajiyar zuciyah tayi bayan yaa shige, take tambayar kanta shi kuma wannan daga ina? Anma ganin yanda ya shiga gidan kai tsaye ya sanyata gano shine yaron Momie da suke sanya ran dawowarshi jiya. Yasseer ta tuna, da ko dak'ik'a ɗaya bata taɓayi ba tare da tunaninshi ba, hakanan wani lokacin sai dai ta shige ɗaki tayi ta kuka har sai k'uncin ranta yaɗan rage, don wani lokacin kuka ma yana maganin damuwa.

  Break fast ɗinma kitchen ta koma dashi tayi, hakanan sukuku ta ringa taya Talatu girkin, har Momie suka dawo bata sani ba tana can suna aiki, sai dai ta aiko ma Talatu kalolin Abincin da za'ama Daddy,

  Talatu tace "ashe dai Daddy yaa dawo? Yanzu girkin gidannan zai k'aru"

  "cin abinci ne dashi sosae kenan?" Saude ta tambayeta,

  "A'a zaki sha mamakin kalolin abincikan da za'a haɗa mishi, anma sai yaga dama zaiyi cokali biyar"

  Sadeey tace "tohhh"

 "sosai fa, kuma duk ma'aikatannan gidannan idan yazo ni kaɗai nake girki yaci, donshi bai son abincin en aiki"

  "Allah sarki, wasu ai k'azantane basu so"

 "kamar kin sani kuwa shima haka yake, don ɗan gayune na gaske, ubangidana akwai tsafta, anma idan kika shiga ɗakinshi...."

 Tun kafin talatu ta k'arasa Saude ta kwashe da dariya tuna abunda momie tace jiya, 

  "tunma kafin kiga ɗakin nashi kin fara dariya kenan" ta faɗa taa ɗauka ita take ma dariya, talatu akwai labari koba komai firar da take mata tana rage mata wani tunanin,

  "kinga yanzu tayani zakiyi mu ɗaura girkin nashi, rana nayi gashi kuma wannan ban kusa gamawa ba"

  "tohh" tace sannan ta tashi ta fara k'ok'arin ɗaurawa, da yake tana koyo a wurin talatu kusan duk girkinma ita tayishi, har suka gama suka jerashi a dinning.


  Ɗakin Momie ta shiga, tayi mata sannu da dawowa, harta mik'e zata tafi, Momie da fara'arta tace "Yayanki yaa dawo fa, yanzunnan ya fita dakun gaisa" shiru tayi data tuna abunda ta mishi saida taji tashin hankali, jiki ba k'wari tace, "Barka momie ya iso lafiya"

  "Yauwah Saude, kije kiyi wankan kun gama girki ko?"

  "eeh an ajje komai Momie"

 "yauwah tohh idan kinyi wankan kimun magana"

  "tohm momie"


  Bayan ta fito daga wankan, mai kawai ta shafa ta saka kayanta, milk atamfa ce mai kwalliyan ja a jiki, ɗinkin riga da zani yayi kyau sosae, tayi ɗaurin k'irji da zanin can sama ta tattareshi, ta cukuikuye ɗan kwalin ta ɗaureshi tsakiyar kai, ta fito daga ɗakin ta fara biyawa ɗakin Momie, tare suka fito bayan taa kira Daddy a waya.

   Da sauri Saude ta jama Momie kujera ta zauna, ta zuba mata abinci ta duba bata ɗauko miya ba, 

  "Momie ban ɗauki miyanki ba bara inzo"

  Tace "tohh" tana k'ara kiran Daddy a waya ko meya tsaidashi? Da sauri ta ɗauko miyan tana sauri ta kawo ma Momie wurin shiga dinning ɗin sukaci karo shima yana sauri momie tayi kiranshi, kamar ɗazu dai gaba ɗaya ta juye mar miyar a jikin fararen kayanshi. Da sauri ta ɗaura hannu akai a razane.

  Wannan karon ta k'ure hak'urinshi da rashin maganarshi, wata irin tsawa ya daka mata "ke jahilan wacce gari ce da bakya kallon gabanki tsabar k'auyanci"

  Duk taa tsure hawayene ke bin fuskanta, "Kayi hak'uri"

  "Dallah rufamun bakinki, hak'urin banza, wannan ma ai tsabar raini ne, kinga ɗazun ban miki ba kawai kuda kunfison mutum yana ɗaga muku murya"

  "kinyi shiru malama saina faɗa miki ki gyara ɓarnar da kikayi?" da sauri duk ta ruɗe ta kamo rigarshi ta fara k'ok'arin gogewa duk wurin ya k'ara damewa, wani tsawar ya k'ara mata,

   "ke! Miye haka?" duk ta tsorata taja baya, tama rasa me zatayi, Momie daga can tana jiyo su, cikin faɗa-faɗa tace "Haba Daddy banfason zafin rannan, tunda taa baka hak'uri kaje ka cire kayan mana" ya buɗa baki zaiyi ma momie magana kuma ya fasa, a zafafe yabar wurin bayan ya sakar ma Saude wani dogon tsoki, baiko kalla inda take ba.


  Wata miyar taje ta kawo ma Momie, sannan ta gyara wurin duk jikinta a sanyaye, muryarshi nata yawo a k'walwanta, sosae take ratsa mata dukka sassan jikinta, ko kaɗan bataji daɗin abunda tayi ma ɗan lelen Momie ba.

  Momie ta kirata bayan ta gama gyara wurin, 

  "Kinga zauna kici abincinki, ki manta da wannan Yayan naki Zafin rai ne dashi, kina hak'uri da faɗanshi kinji"

  "babu komai fa Momie aini na mishi laifi"

  "Yauwah tohh zuba abincinki kici" ta zuba kaɗan, tana zama taa gama zubawa sai gashi ya dawo da wasu kayan da alama wankama ya canja.


  Bayan yaa zauna Momie tace Saude ta zuba mishi abincin, Momie tace "Me zakaci?" baiko ɗago kai ba ya bata amsa sannan yaci gaba da danna wayarshi, lallai mutuminnan miskili ne, ko magana bai cikason yi ba.

  Data gama zuba mishin ma ya daɗe sannan ya ɗauka ya fara ci, yana ci yana danne-dannenshi a waya, sai dai yakai cokali yaji babu komi yaa cinye plate ɗaya, Momie na lura dashi tace "Da alama girkinnan dai yayi maka daɗi" cikin zolaya

  "Gaskia ne Momie, talatu bata taɓa girki mai daɗin na yau ba"

  "Daman ya za'ayi Talatu tayi girki mai daɗi haka? K'anwarka ce tayi maka"

  "K'anwatah kuma?"

  "eeh mana, idonka ya rufe da faɗa ko gaisawa bakuyi ba,"

  Ranshi ne ya ɓaci, waida wannan cikakkiyar bak'auyarce Sauden da Momie ke bashi labari? Duk da baiga fuskarta ba, shigarta ya nuna ko hasken birni bata saba gani ba. Ajje cokalin kawai yayi ya mik'e zai bar wurin.

  "Koma ka zauna nace" inji momie, yaɗan tsaya anma bai tafi ba, ta k'ara cewa "Idan ba so kake raina ya ɓaci ba" da sauri ya koma ya zauna don baison ɓacin ranta.

   "Saude baki gaishe da yayan naki ba" a hankali tace "ina wuni"  

   "Lafiya" ya amsa a tak'aice kaman dole,

  "Ya hanya an dawo lafiya?" tsoki ya saki kawai, sai da Momie ta mishi wani kallo sannan ya amsa, har lokacin hankalinshi nakan waya.

   "Banson halinnan Daddy k'anwarka ce, ka ɗauketa kamar Husna, banson k'ara ganin wani banbanci"

  "naji Momie"

    "Yauwah Babanah, Saude tashi ki k'ara mishi abincinnan", don dai abincin ya mishi daɗi, anma kamar yace karta zuba duk da ya k'oshi sai yace "farfesun en cikin kawai" daman shi kaɗai ne baici ba, sai lokacin ta ɗaga kai ta kalleshi.

  A tare shima ya ɗaga ido yana kallonta, wani irin faɗuwar gaba taji, da batasan dalilinshi ba, tama kasa ɗauke ido daga kallonshi duk taa zuba mishi manyan idanunta, duk yanda ake cewa suna yanayi da Hafsat bata ɗauka yakai haka ba, har yanayin kallonsu ɗaya, shima kallonta yake ko k'iftawa baiyi, bak'auyah ce, anma ba irin k'auyawan daya saba gani ba, kallonta kawai yake yana k'are mata kallo, 

  Ya rigata ɗauke ido, gaba ɗaya rikitashi take da manyan idanunta, "ke kallonma k'auyanci kike mishi?" da sauri ta sauke idanunta tana zuba mishi girkin, Momie tayi dariya kawai lokacin taa gama nata launch ɗin.

  Ta mik'e zata tafi yace "Momie wai yaa maganar kiwon da nace miki zan fara?"

 Tana dariyarta ciki-ciki tace "Kiwon en ciki?" aikam sun bama Saude dariya, shima dariyar yayi, "Nifa Momie ba santi nake ba"

  "ai bance ba, daɗin girkin Saude ne kawai kakeji" ta tafi tana dariya, ta barshi daga shi sai Saude a wurin, waya taji an kira shi, abinda kawai taji yace "Eeh Najib ne"

  A hankali ta sake maimaita sunan nashi "NAJIBULLAHI" suna mai daɗi.


  ©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

       55


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


Wannan shafin sadaukarwane gareki sis AL'EEMAN, naga sak'onki, kuma naji daɗin soyayyar da kikema littafina, nagode sosae da Addu'arki gareni, Allah yabar zumunci, Ameen


www.babymsh.blogspot.com


  Tunda ya fara magana a waya ta zuba mishi manyan idanunta tana kallonshi ko k'iftawa batayi, maganarshi cikin nutsuwa hankali kwance yake fitar da ita ɗaya bayan ɗaya, yana cikin magana ya ɗago yaga shi take kallo, wani banzan kallo ya watsa mata, batasan ma yanayi ba, saida ya gama wayan har zai mata magana ya fasa, sai dai yaja dogon tsoki, aikam da sauri ta dawo hankalinta, bata tsaya ganin kallon da yake watsa mata ba tabar wurin.

  Abinda ta lura ga Najib (Daddy) baison yawan magana, kuma bai cikason a shiga harkarshi ba, ita kaɗai ke zancen zuci harta isa amsa kiran Momie.

  Bayan ta duk'a har k'asa tace "Gani Momie"

  "Yauwah ki shirya yanzu Daddy zai ajjeki gidan Husna, yanzu taimun waya batajin daɗi kiɗan rage mata ayyukan gidan"

  "tohh Momie" ta tashi zata tafi Momie ta fara magana, "itama dai Husna, tak'i yarda a ɗaukar mata er aiki, yanzu aida taa samu maiyi mata gyaran gidan" Saude ta fita ta barta tana faɗa, daman Momie tana bata labarin Husna itace er Autar ta tana bima Najib (Daddy) shine na biyu, sai kuma babban yayansu yana Moscow shida Matarshi, yaranta uku daman.


  Kayan jikinta mayafi kawai ta ɗaura akai, sannan ta dawo ta faɗama Momie taa shirya, ba k'aramin ɓata rai yayi ba da Momie tace ya kaita gidan Husna kawai don bazai iya mata musu bane, wani irin kallo yakai mata sannan ya kalli zanin data ɗage can sama (alaman ta saukeshi) donshi yafi aika sak'o da kallo bai cikason magana ba, bata gane mai yake nufi ba, sai tayi saurin kauda kai.

  "A haka zaki fita da wannan zanin?" ɗaga kai tayi bata fahimceshi ba,

  "da Allah saukeshi nace" da sauri ta saukeshi, anma still dai saman ciki, kaɗa kai kawai yayi ya wuce gaba ta bishi, yau ne fitarta ta farko harabar, sai kalle kalle take daman an fiddo mishi da mota a wanke sai k'yalli take, ya buɗe ya shiga ya barta tsaye, taa rasa inda zata shiga, batasanma yanda zata buɗe ba, 

  Tsoki ya k'ara ja saboda yanda take ɓata mishi lokaci, daga ciki ya buɗe mata, da sauri ta tafi ta shiga, ta zauna kamar mai koyon zama, wani sak'on ya k'ara aika mata da kallo, anma duk bata gane ba, sai ta k'ara gyara zama ta rirrik'e kujerar data zauna a gaba,

   "Motar ma nizan rufe miki?"

  "yi hak'uri" sannan ta saka motar ta jawo motar a hankali ta rufe kamar tana tsoran karta ɓalle,

  "bata rufu ba" yace da ita, ta k'ara sanya hannu ta jawota, girgiza kai yayi sai magana take sakashi, "matsanan" ta kwanta sosae jikin kujerar, yakai hannu zai rufe duk da haka saida ya taɓa jikinta, da sauri ya ɗauke hannunshi saboda wani yanayi daya ziyarceshi, 

Itama wani abune ya ratsa mata har tsakiyar kanta, ba shine na farko ba, anma bata taɓajin yanayin da taji yanzu ba, kodan an kwana biyu ba Yasseer😉.


  Gidan da suka fara zuwa da baba Haja nemar mata aiki taga an buɗe mishi ya shiga da motan, gani yayi sai kokawar buɗewa take, ya shareta kawai ya fita ya barta, a ranshi yace 'sai dai ki kwana a ciki ni ba ɗan buɗe miki k'ofa bane' kamar tayi kuka haka ta dinga kiciniyar buɗewa duk ta haɗa zufa ko ina a rufe, sai mai ban ruwan fulawane ya buɗe mata ta fito tana maida numfashi, ta mishi godia sannan ta shiga gidan, da yake tasan hanya.

   Zaune ta iskeshi suna fira da dariya kamar ba shi ba, Husna ta kalleta tanaso ta tuna, ta nunata da hannu "kece Saude?" da sauri ta ɗaga kai,

  "Allah sarki, kamar kece kukazo da baba Haja darennan ko?"

  "eeh nice"

 "Anma dai naji daɗin kasancewarki gaban Momie, kiyi hak'uri da wannan ranar kinji"

  "ba komai fa"

   "Yauwah" sannan suka gaisa, ta mik'e sukaje tana nuna mata abubuwan da zatayi, share-share ne kawai da goge-goge, tana fita taci gaba da aiki, shima tun shigarsu ya tashi yabar gidan.


  Sai dare ta gama mata dukkan ayyukanta, ta haɗo mata mayuka masu kyau na gyaran jiki dana kai, da turaruka masu k'amshi ta bata, Saude ta amsa tana ta mata godia.

   "haba banson godiyarnan Saude, ai mun zama ɗaya"

  "Tohh Aunty Allah ya saka da Alkhairi"

  "Ameen" sai kuma ta kalleta,

  "Saude kenan, gaki a birni anma har yanzu k'yauye tak'i barinki"

    "Ban gane ba Aunty husna"

  "gani nayi har yanzu shigarki nanan ta k'yauye, baki ganin yanda en matan birni keyi? Ki canja shigarnan kinji" ɗaga mata kai tayi har lokacin bata dai fahimtan ba, driver aka saka ya kaita har gida.

  A harabar gidan ta iske motan da suka fita da ita tare da Najib, an bubbuɗeta da alamar wanketa akayi, ta zagayeta ta wuce cikin gidan kai tsaye ɗakin momie ta shiga, muryarta ta jiyo da alama faɗa take,

  "Yanzu saboda kaa ɗauka k'anwarka a mota ne kake wanketa Daddy?"

  "nifa momie wallahi da gaske ta ɓatamun mota, ni kunyama nayita ji kar wanda ya sanni a ganni da ita cikin motah"

  "Hinyehh! Ai da cemun kayi bazakaje da ita ba kawai, sai insan yanzu kaa daina jin maganata"

  "kiyi hak'uri Momie" 

Saida ta share hawayenta sannan tayi sallama cikin ɗakin momie duk yanayinta ya canja, tunda take bata taɓajin zafin kasancewarta er k'auye ba irin yau.

  Momie ta nemo fara'a tanajin sallamar Saude "Sannunki da dawowa"

  "yauwah momie Sannu da gida" ta zube mata kayan da Husna ta bata a gado,

  "Gashi ta bani, tace a gaishe dake"

 "Ina amsawa, an gode ma Auntynki Husna, naa gani ki adana"

 "tohh" ta tashi zata tafi, Momie duk bata yarda da yanayinta ba tace "kodai wani abu ta miki naga yanayinki yaa canja?"

  "A'ah Momie, Aunty tana da kirki sosae, er gajia ce kawai"

 Momie ta sauke ajiyar zuciya data tabbatar Saude bataji maganar su ba, tace "Sannu kinji, kije ki kwanta da wuri"

 Tace "tohm Momie"

 Idanunta k'asa k'asa ta kalla inda Najib yake, yana rungume da Hafsat tayi barci a jikinshi.


 Washe gari saboda gajia taa daɗe bata tashi ba, sanda ta tashi Talatu harta kusan gama ayyukanta, ta kama mata dai suka k'arasa, duk sai taji ba daɗi kuma ta zauna bata aiki, ta shiga ɗakin Momie ta mata gyaran kaya, ta k'ara gyara ɗakin.

 Ɗakinta ta koma duk batason zaman hakanan, da marece kafin su fara girkin dare ta tashi ta fara zagaya gidan, hanyar ɗakin Najib tabi hakanan taji tanaso taje taga inda ɗakin yake, cikin Sanɗa ta k'arasa cikin Sa'a kuwa a buɗe yake, ta dinga lek'en falon ba k'aramin kyau yayi ba, komai a tsare sai dai kuma ko ina yayi datti, bataga alamunshi a falonba, hakan ya bata k'warin gwiwar shiga bedroom ɗin shima ta labule ta lek'a anma bataga alamunshi ba, shima duk yayi kaca-kaca kamar ba mutum ke zama a ciki ba, saida ta tabbatar bai cikin gidan sannan ta gyara shirinta ta fara aiki, gyaran ɗakin ta shigayi ko ina take kakkaɓewa tana kauda kayayyaki.

  Cikin lokaci kaɗan ta gama gyaran ɗakin, ko ina yayi fes yayi kyau fiye da daa, har zanin gadon ta cire ta canja mishi wani, toilet ɗinshi ma ta wanke mar duk da baiyi wani datti ba, ta saka turaren wuta mai k'amshi ta turare ko ina. Ita kaɗai ta tsaya tana kallon ɗakin, ita ma kanta yaa burgeta sosai, yanzu momie zata daina damuwa da dattin ɗakin Najib, ta faɗa a zuciyarta.

 A hanzarce ta gama ta fito, a hanyar da zata fiddata gaba ɗaya bangaren nashi ta haɗu dashi yana niyyar shiga, a ruɗe ta k'ara sauri tabar wurin, binta yayi da kallo kamar ya mata magana kuma ya fasa, ya wuce ɗakinshi.


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

      56


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


  Tun a hanya yake jiyo tashin daddaɗan k'amshi daga ɗakinshi, bai ida yarda a ɗakinshi bane saida ya shiga, tsayawa yayi yana mamaki fitarshi har an gyara ɗakinnan yayi kyau haka, tohh waya shigar mishi ɗaki? Dubawa yayi duk wani takardunshi daya ajje inda zai ɗauka baiso su rikice mar, da kayanshi dayake ajjewa inda zai buk'ata, duk dai wani abu mai amfani bai gani ba, ranshi ya ɓaci ya juya kai tsaye ɗakin Momie ya shiga.

  Tun bakin k'ofa yace "Momie kin saka aimun gyaran ɗaki ne?"

  "A'ah kaida kace bakaso a shigar maka ɗaki kuma"

 Saude ta faɗo mishi rai yaga tana fitowa, lallai itace ta mishi shisshiginnan, Momie tace "Lafiya meya faru?"

  "Ba komi Momie" ya juya da hanzari yabar ɗakin, dubata ya shigayi har kitchen bai ganta ba, can ya hangota tana tafiya ita kaɗai, da sauri ya tardata ya kama kunnanta sosai, ya ruɗe ta juyo harta buɗa baki zata kurma ihu, ya saka hannu ya rufe bakin.

  A kunne ya raɗa mata "idan kika sake kikamin ihu kunnan naki zan cire" aikam ta nutsu don ba k'aramin rik'o ya mata ba, idanunta sunyi jajir don azaba kamar tayi kuka.


 A tsakiyar falon ya tsaya da ita, anma bai saketa ba cikin kakkausar murya yace "waye yace kizo kimun gyaran ɗaki?"

  "ba kowa"

   "Dakyau isassa, idan baki maidamun duk kayana inda suke ba sai kinyi mugun shan wahala" kai ta ɗaga mishi, itadai Addu'anta Allah yasa ya saketa, yana sakinta ta fara tafiya inda ta ajje takardunshi, kamar wacce tayi harda kowanne saida ta ajje inda ta ɗauka cikin tsari,

    "Na gama" ta juya zata tafi, "Dawonan" ya tsayar da ita sannan ya tafi ya fara dubawa, ko takarda ɗaya batayi kuskuren ajjewa ba, yasha mamaki sosae, sai yama rasa mezaice mata.

  "Tohh maidasu inda suke" yace ba tare daya kalleta ba, ta maida kowanne tana mishi bayanin inda yake, tana gamawa ta k'ara juyawa zata bar ɗakin duk a takure take.

  "Wannan ya zama na k'arshe da zakimun shisshigi a abunda ya shafeni, zanfi jin daɗin zaman ɗakina yanda yake da, don yanzu k'yank'yaminshi ma nake da kika shiga cikinshi, Momie ta kawoki gidannan, don haka indai zuciyar mutanene a jikinki karki k'ara nunamin fuskarki" ɗaga kai kawai tayi ba tare data ce komi ba, ta tafi kawai tana hawaye, sai yanzu taga wautarta ma na shige mishin da takeyi.


  Tunda ta shiga ɗakin bata fito ba, ranar monday tunda safe yabar garin ya wuce Kaduna inda yake aiki, saida ta fito Momie take faɗa mata yayanta ya tafi basuyi bankwana ba, murmushi dai kawai ta mata. Saida ya tafi ta fara samun sakewa a cikin gidan, Hafsat kullum da gwarancinta saita tambaya ina Daddy, saboda shak'uwah ce sosae tsakaninsu, yanaji da Hafsat sosai kamar shi ya haifeta.

 A wurin aiki kullum Najib ba sukuni, ko yaushe cikin tunanin Saude komai yake fuskarta ce ke mishi yawo, hakanan inya tuna wani abun da tayi shi kaɗai yayita murmushi, saiya gane tunanin Saude ne fa yake yayita jin haushin kanshi, duk yanda yaso ya yakice tunaninta a ranshi ya kasa.

  Abokinshi Ahmad ne ya k'wank'wansa mishi kujerar da yake, ya dawo a ɗan razane, "Yadai?" ya tambayeshi, "Dai-dai, naga alamun kwana biyunnan tunani yaa aureka"

  "ba wani tunani, abubuwanne da yawa"

 "Ka faɗama abokinka hakan, bawai Amininka ba daya gama sanin duk wani motsi naka"

  "kuma laifi ne idan mutum yayi tunani?"

 "babu laifi, anma kamar kana da damuwa kuma kak'i ka faɗamun"

   "nifa babu abunda ke damuna"

  "Ok daman shigowa nayi, naga an tashi ko anan zaka kwana?"

  Dariya yayi, "A'ah yanzu nake shirin fitowa" ya mik'e bayan yaa gama tattara takardun gabanshi, "ban baka labarin Saude ba? Da tana wurinnan zaka ga yanda zata tattara takardunnan bazakace batayi makaranta ba"

  "Saude er k'yauye?"

    "ita fa"

  "kai kam kana son labarinnan Saudennan"

  "Haba ni mezai sakani maganarta" 

  "Muje ko?" suka jera a tare suka fito, kowa ya shiga motarshi suka tafi.


  Da dare Ahmad yaje ɗaukoshi gida zasu fita restaurant da yake shima baida aure, ya buɗe motan ya shiga, ya jawo zai rufe kenan ya fara dariya harda rik'e ciki, 

  Ahmad ya fasa tada motan ya tsaya yana kallonshi, donshi kanshi wani lokacin mamakinshi yake idan yana dariya don bai saba gani ba,

  "wai kai lafiyanka?" bai tankashi ba yaci gaba da dariyanshi "dakai nake fa, kai daman indai anga kana dariya mugunta ne, Allah ya taimakeka bani kake mawa ba"

 "nida bak'yauyarnan mana, idan kaaga yanda tayi zata rufe mota randa zan kaita gidan sista Husna, naa tabbata saika fini dariyarnan"

  "Sauden dai?" Ahmad ya faɗa da cikin fara k'osawa da zancenta da Najib ke mishi,

    "ita mana" kaɗa kai kawai Ahmad yayi yaja mota suka tafi don haushi ma ko magana bai k'ara mishi ba.


 Suna cin abinci anma shi dak'yarma yayi cokali Uku ya ajje, sai zancen zuci yake, yadai fito fili yace "kuma kasanme?" Ahmad ya girgiza kai, "wlhy zakasha mamaki idan kaci girkin da er k'yauyennan tayi, ko a restaurent ban taɓa cin mai daɗinshi ba"

  Ahmad yace "Ita Sauden ba?"

 "Kaa canka dai dai" inji Najib.

   "Yanzu kana da magana ne bayan tata? Tunda labarinta ne kam yanzu za'a fara jinka kana dogon surutu"

  "Kamar yaya?"

    "kamar yanda kake shirin bani kunya mana, duk haɗaɗɗun babies ɗin da suka rikice ma soyayyarka, ka rasa wacce zaka so sai wata er k'yauye can Saude, kullum kana cika bakin bakaga macen da ajinka zai kai ka sota ba"

  "Haba! Banson iskanci fa, er k'yauye fa kuma zawara, ta inama kake tunanin dacewarmu?"

  "kai ke wannan tunanin, anma a yaren So shi babu ruwanshi da wani dacewa"

   "ni don Allah daina tayarmun da zuciyah, tayaya ma zanso wannan yarinyar? Ko kaɗan bata dace dani ba wallahi"

  "ka daina yaudarar kanka, don tuni zuciyarka ta faɗama soyayyar Saude"

  "nida nake da zuciyar ban sani ba sai kai?"

  "ka taɓa sanin alamomin So?"

  "Na taɓayin Soyayya ne dazan wani san alamomin so?"

 "kaji matsalan, bakasan yanda akeji idan an fara soyayya ba shiyasa ka kasa yarda da kanason Saude, uku kawai zan faɗa maka ka yarda da abunda nake faɗa" shirun da Najib yayine ya bama Ahmad damar ci gaba da magana.

  "Kana yawan tunanun Saude ba?" ya ɗan tsaya yana tunani, Ahmad yace "ka cemun eeh kawai" 

 "tohh eeh ina jinka"

   "kullum kana yawan yimun maganarta, baka da zance dai saina Saude tun sanda ka dawo, na biyu kenan"

  Najib ya gyara zama, tabbas sai yanzu ya fahimci duk maganganun Ahmad hakane,

  "Na Ukun fa?"

    "Na fahimci Saude duk abunda tayi a baya, burgeka yake yanzu ba?" baki buɗe Najib ke kallonshi yana murmushi yama rasa bakin magana "kuma naa tabbata komai kake kanajin daman Saude na kusa dakai ko babu wani dalili"

  Najib na dariya yace "tohh malamin soyayya, darasi yayi daɗi har kaa faɗi huɗu baka sani ba"

  "Na biyarma zan faɗa maka yanzu, sai wani murmushin jin daɗi kake ina maka firarta, wannan ma babban alaman kana sonta ne"

  Dariya yayi sosae ya bashi hannu suka tafa "Tohh aini malami na dukkaa rikitani ma"

  "Hahhah bafa ajin maths muke ba, maganar soyayyah ce"

  "ai wani lokacin yaren mathematics ɗinma sai yafi na So sauk'in ganewa"

  "ba kamar ga sabon shiga ba"

 "hakane, anma fa ni har yanzu ban yarda inason Saude ba, baka ganta bafa, ni haushin shigarta ma nake"

  "kana son Saude fa, ka daina yaudarar kanka, kawai ka maida ita kalar macen da kakeso"

 "Kayi magana ananma zanyi tunani akai"

  "Yauwah kokai fa"


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

      57


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


❣Page ɗin yau dai yayi tsawo, musamman don sadaukarwa ne ga Auntiena ```Asma'u musa barah msh``` (Husna a nvl ɗinnan😉) fatan Alkhairi a duk inda kike.


www.babymsh.blogspot.com


  Tun bayan tafiyar Najib sai Saude taji gidanma yafi mata daɗi a haka, Hajia na ɗan aikata gidan Husna harsun saba sosae, hankalinta yanzu kwance har mantawa take da wani Najib, tunanin Yasseer ma kullum k'ok'arin yakiceshi take.

  Ranar friday sati uku da tafiyar Najib, da aiki suka tashi gidan kamar za'ayi wani manyan bak'i, kuma taa lura Momie na cikin farin ciki fiye da kullum, sai dai bata tambayeta dalili ba don bata faɗa mata ba, 

  Sai bayan saukowar masallaci suka kammala, a gajiye Saude ta fito daga kitchen ɗin batama jira an gyara wurin da ita ba, tafiya kawai take bata kallon gabanta sai dai ta jiyo sallamar mutum, idanunta akan hanyar shigowarshi, harta buɗe baki zata amsa mishi sallamar ta tuna maganarshi daya faɗa mata.

  "Idan har zuciyan mutanene a jikinki, karki k'ara nunamun fuskarki!!!" maganar taa shigeta sosae, kafin ya shigo ta lallaɓa ta koma can jikin bango ta laɓe bayan ta amsa sallamar can cikin mak'oshinta, tana hangenshi ya shigo ya wuce, ya k'arayi mata kyau sosae, anma kamar yaa ɗanyi rama.

  Saida ta tabbatar ya shige ɗakin Momie, sannan ta fito tabar wurin, ɗakinta ta shige, bata k'ara marmarin fitowa ba.


  Tun shigarshi gidan yaketa hangen inda zaiga Saude anma bai ganta ba, shiyasa ma kai tsaye ya wuce ɗakin Momie yasan zai sameta a can, anma bai ganta ba, Momie ita kaɗai ke maganar ta anma tunanin ta inda Saude zata fito yake. Dubara tazo mishi na tambayan Momie,

  "Nifa tun zuwana banga Hafsat ba ko tana wurin Mamanta?"

  "A'ah tana wurin lesson ne" shiru yayi donshi ba amsar da yaso ta bashi ba kenan, 

  "Aina ɗauka tana wurin Mamanta" 

  "A'ah" kawai Momie tace mishi, baiso hakanba, sai kuma yaga wannan kamar dama ne dazai fara yima Momie tuni akan hakk'in Saude.

  "Momie itafa Sauden yaushene zata fara zuwa makarantar?"

  "Haba Saude fa, ai ita yanzu tayi girma da zuwa makaranta, nasan bazata so ma tana shiga aji da k'annanta ba"

  "A'ah Momie, shi karatu ai baida babba babu yaro, idan har tanaso ko inane zata iya, in kuma bataso sai mu k'yale andai fita hakk'inta"

  "Hakane, anma tunda gaka kazo saika nema mata makarantar daya dace"

  "tohm shikenan Momie, tana ina?" ya samu dai ya tambayeta.

 "k'ila tana ɗakinta ko, gajiyar aiki nasan tana hutawane, tun asuba bata zauna ba" wani irin daɗine yazo mishi,

   "Momie Saude ita tayi girki?"

  "Kusan ita tayi fa, don yanzu Talatun ma ita ke tayata" fara'arshi saita k'aru yau zaici girkin Saude, har k'agara yayi su tafi dinning cin abinci, anma kuma shiru babu Saude, kuma yaji Momie batayi maganarta ba, sai yanda Momie zatayi maganarta yake anma bata kula ba.

  Haka duk ranshi ba daɗi ya yini a ɗakin Momie, sallah kawai ke fitar dashi don karma ya fita Saude ta shigo bainan, har dai Momie da taga dare ya kusa bai fita ba tace "yau kuma bazaka fita ba?"

  "A'ah Momie, yau ranarki ce babu inda zanje nan zamuyi ta fira" aikam taji daɗi sosae da maganarshi, ta ɗauka daga sallahn isha'i ma zai wuce ya kwanta, sai gashi har 10:30, yana jiran Saude tazo mata saida safe.

  "Naga alaman yau anan zaka kwana, kaga ni tashi barci nake ji"

  "Momie yau kuma korata ake?"

  "Ya zanyi na kori Babana, barci nakeji gobe ka dawo muyi firan"

 "Tohm mu kwana lafia" ya tashi ya tafi yanajin haushin barcin wurinnan na Momie yau, duk da haka a falo ya zauna yana hangen hanyar da zata fito yana kallon dole.

 Saude da taga haka saita fasa fitowarma, ta koma ɗaki ta kwanta ko kaɗan bataji daɗin rashinma Momie saida safe ba, barcin k'arya ta ringayi duk sanda ta aika kiranta da rana don batason fita, saida dare ya raba tsakiya sannan ya hak'ura ya kwanta.


  Washe gari da asuba taje gaisheta tana gama sallah tasan bai dawo masallaci ba, da yake yaa daɗe baiyi barci ba, sai bai farka da wuri ba sanda ya tashi harsun gama break fast, ta koma ɗaki, yinin ranar ma wasan ɓuya suka ringayi, kota fito bata bari su haɗu.

 Ranar asabar kenan haka har dare basu haɗu ba, gashi lahadi yakeson komawa, kusanma haushin kanshi ya fara ji, kenan maganar Ahmad gaskiyane yana son Saude? Shiyasama duk ya damu ya ganta, miye ma a jikin Sauden da zaiso ya gani? Tunaninta ya matsa mishi har baison zama shi kaɗai, tashi yayi yabar ɗakin Momie yama fasa son ganinta.

  Lokacin ita kuma Hafsat na wurinta ta matsa sai dai ita zata rakata ta kwanta, ta rik'o hannunta suka fito, tana ganinshi ta juya tun kafin ya gansu anma ta makara saida Hafsat ta mishi magana tanata so ta k'wace hannunta taje wurinshi.

  Tsura mata ido yayi duk da yaji daɗin ganinta a zuciyarshi, amma saiya kauda kai, ta saki hannun Hafsat kawai, ta juya tabar wurin, yabi bayanta da kallo harta shige.

  Hafsat ce ta kamo hannunshi, sannan ya maida hankalinshi kanta.

  "Uncle ina sweets ɗina?"

 "Sorry Hafsat kinga yau ban fita ba, gobe zamuje in siyo miki"

  Ta washe baki, "gobe zaka fita dani yawo ko?"

  "eeh mana"

 Harda tsallenta "Yauwah gashi babu ckul"

  Ya ɗaga mata gira "Hakane fa, tohh kije ki kwanta da wuri"

 "tohm uncle Good night"

   "bye karki manta da addu'ah" tun daga nan ta fara kware baki tanayi donma yaji bata manta ba, murmushi kawai yayi, shi yanzu harya daina mamakin surutun Hafsat, shekarunta biyu anma labari kam kamar mai sauke hadda, wayau ne da ita sosae shiyasa tun wuri aka kaita prep.


  Yau bai fito ba, break fast ma sai dai yayi ma Momie waya aka kai mishi, na rana ma shiru bai fito ba, Momie ta aika aka mata kiran Saude,

  "Shiru bakici abinci ba, yayanki ma bai fito ba duk yau"

 "Naci a kitchen Momie"

 "Bana hana ba Saude? Ɗauki na Yayanki kikai mishi"

  "tohh Momie?"

 Bata iya musa mata, anma da akwai yanda zatayi bazata je ba, cikin sanyin jiki ta harhaɗa mishi, ta kwasa ta tafi gabanta na faɗuwa har ta shiga.


  Yana kwance abubuwa sun mishi yawa, duk zuciyarshi cunkushe take, haushin kanshi kawai yakeji, tunanin Saude, Soyayyarta, da kuma son ganinta sun rikita mar k'walwa, ya ɗauke wayanshi ya kira Ahmad.

  "Masoya! Ananan da Saude an manta damu"

 "wace Saude? Bazan iya ba Ahmad, gaba ɗaya na fara tsanar kaina, ita zuciyar daman haka take? Bazatayi shawara dani ba akan wacce ya kamata taso ba sai Saude"

  Ahmad na mishi magana Saude ta shiga ɗakin, a falo ta aje mishi saman centre table, sai kuma taga kamar bazai san an kawo ba, ta tafi ta faɗa mishi, ta jiyoshi yana magana.

  "Haba Ahmad baka ganta ba, bak'yauyah ce ta k'arshe, ko ɗaurin zane bata ita ba ballantana ɗan kwali, sai afkin wanka anma babu wayewa, ni wallahi haushinma ganinta a haka nake" dafe k'irjinta tayi tuni hawaye suka wanke mata fuska,

  "bak'yauyen mutum fa Ahmad duk yanda zaka mishi yananan dai da duhun k'yauyenshi, duk inda zai shiga kuwa...." abunda ta iya saurara kenan, da gudu ta tafi zata bar ɗakin, wurin sauri k'afarta harta zame ta faɗi, ba k'aramin zafi taji ba haka ta daure da sauri tabar wurin.

 K'arar faɗuwar mutum da yaji ne ya fito dashi, anma baiga kowa ba sai dai girkin da aka aje mishi, bayanta yabi anma harya fito baiga kowa ba, Momie ya gani da shirin fita ta fito,

  "Sai yanzu ka fito?"

  "eeh, fita zakuyi ne?"

    "eeh anma bazan daɗe ba, Saude takai maka abinci ko"

 Ya samu amsar tambayarshi kenan itace ta shiga ɗakinshi, "eeh Momie" rage tsawonshi yayi inda Hafsat take,

  "Ba magana don za'aje anguwa?"

  "A'ah akwai"

 "tohh ina mamanki?"

   "tana ɗakinta"

  "muje ki rakani" yanda Momie bazata ji ba yayi maganar, ya kama hannunta.

  "Momie muna zuwa plz"

    "owk ta sameni a mota" tayi gaba su kuma suka tafi.


  Hafsat taa rigashi shiga ɗakin da Saude take, da murnarta donta faɗa mata tare suke da Najib sai kuma taga tana kuka.

  "Mama kuka kike?"

   Ta share hawayenta tana k'ak'aro murmushi, "waya faɗa miki kuka nake?"

  "nina gani da kaina Momie, kuma kin hana kukan rigima"

  Kuka ne ta k'ara fashewa dashi, a k'alla ta samu damar da zata faɗi damuwarta ko zata samu sauk'in zuciyarta, duk da tasan Hafsat bazata fahimci komi ba,

  "ba kukan rigima nake ba Hafsat, inayi ne don in rage bak'in cikin zuciyatah, miye don an haifeni a k'yauye? Ni bani da kyau ne? Ko kuma wani mugun abunne k'yauyenci? Mutane da yawa sun gujeni silarshi, harda babanki Hafsat, nasan shima dalilinshi kenan na barina, Uncle ɗinki Najib ma abinda ya sanyashi tsangwama ta kenan, Momie kaɗai ke sona Hafsat, kawuna ma ya tsaneni saboda maraicina, babu fa wanda na ɗaurama kaina, ko kinsan inda k'yauyencinnan yake a jikina in cireshi in huta?"

 Kamar tasan me tace, ta girgiza mata kai, murmushi tayi, "Naji daɗi da baki tashi a k'yauye ba Hafsat....."

 Muryar Momie suka jiyo tana k'wala ma Hafsat kira, harta tafi da gudu kuma ta dawo, hannu ta saka ta share mata hawaye, sannan ta koma ta gudu.


  Murmushi tayi tabi Hafsat da kallo, kawai sai taga mutum tsaye a bakin k'ofa ya harɗe hannuwanshi biyu yana kallonta, jikinta na kyarma ta tashi tayi hanyar fita don taa rasa inda zata shige a ɗakin, ya k'ara mamammake k'ofar yanda babu wurin fita, ta kasa haɗa ido dashi a hankali tace,

  "Kayi hak'uri"

   "Dame fa?" ya tambayeta cikin wani irin salo.

 "Na saka kaa k'ara ganina" 

 Ita har yanzu bata manta da wannan maganar ba kenan? Ya shareta kawai.

  "menene damuwarki?" ta ɗan ware idanunta duk da bata ɗago fuskarta ba,

  "ba komi" ta juya da sauri zata koma, saboda hawayen dake k'ok'arin zubo mata.

  "meyasa kike kuka?"

 Muryarta na rawa alaman kuka yaci k'arfinta tace "kaina kemun ciwo" ta bashi amsa duk taa matsu yabar ɗakin.

  Tohh meya shigo dashi shida yace baison k'ara ganinta? Ko kuma wani wulak'ancinne zai k'ara mata.


  "Sanya mayafinki kizo muje" ya katse mata tunani, ta k'asan ido take son kallonshi donta tabbatar koda ita yake magana,

  "Dake nake, ki sameni a waje" ya fita kawai ya barta, sannan ta sauke ajiyar zuciyah, ta k'arema ɗakin kallo babu wata sai ita dashi, anma tana gudun ta fita ya mata faɗa ko bada ita yake ba, ko kuma tak'i zuwa tayi laifi.

  Saida ya gaji da jira ya dawo don kanshi, yace taje su tafi, ta tashi ta bishi zuciyarta na mugun bugawa, harta shiga motan, tunani kawai take a ranta ina zai kaita?.


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

       58


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


I wish to give so much more than a page to uh ```Aunty maijiddah``` thank uh 4 ur support and care, thank uh a million times over❣


www.babymsh.blogspot.com


 Tafiya kawai suke babu wanda kema wani magana, duk a takure take, shikam ko a jikinshi kamar baisan tana a motan ba.

  Dai dai wurin wani babban wuri taga yayi parking da batasan ko ina bane, ya fita ya barta a motan, bai daɗe ba saiga wata kyakkyawar budurwa ta fito wurin tana ta karairaya tasha Makeup harya mata yawa.

  Tana daga ciki suke maganarsu har suka gama, sai dai ya buɗe mata yace ta fito, kallonsu dai kawai take, budurwan ta kalleshi tana wani lumshe ido.

  "zan maka waya idan an gama, don zai ɗauka lokaci gaskia"

 "ba komai, idan an gama inanan ina jira"

  "owk, muje ko Saude?" ta kalleta tana murmushi, maida kallonta tayi kan Najib duk a tsorace take, ya ɗaga mata kai, sannan ta juya ta bita.

    

   Hannunta ta sak'ala cikin nata, suka shiga wurin tana binta a baya sai da taga mata da yawa wurin hankalinta ya kwanta, wasu ana musu kitso, wasu gyaran gashi, wasu Make up, wasu gyaran fuska, kowa dai da abunda ake mata.

    Wurin mai gyaran jiki takai ta, wani ɗaki ana ma wata an kusan gama,

   "Aunty Nainah sannu da zuwa, keda kanki kuma?"

 Bata tsaya bata amsa ba tace "ko waye a layi, dakin gama wanda kikema ga sistatah, ki mata gyaran jiki mai kyau so nake idanna dawo bazan ganeta ba"

  "tohm shikenan Aunty an gama" Saude tana zaune kamar tayi tsalle don murna, duk ta matsu a gama itama ai mata, sai bin mutanen wurin take da kallo tana murmushi.


  Gyaran jiki, fata, k'afa, fuska, gashi, baki, wuya komai lungu da sak'o na jikinta babu wanda ba'a gyara ba, wata haɗaɗɗiyar doguwar rigane red colour, Aunty Nainah ta kawo mata, ta shiga ta saka, sannan aka mata Makeup, ita da kanta ta naɗa mata gyalen rigar, sannan taja hannunta,

  "Zo muje" tabi bayanta har gaban Mirror, tsayawa kawai tayi baki buɗe tana kallon kanta, wai itace nan a haka? Kamar wata jinsin larabawa masu masifan kyaunnan, ita kanta saida tayi k'ok'ari wurin gane kanta, Maganar da Yasseer ke faɗa mata kullum itace ta faɗo mata a rai.

   "Saude ke mai kyau ce" jin maganarshi kawai take a matsayin yabo, ko kuma yana faɗi don ya sakata farin ciki, inama ace yau yana tare da ita yaga yanda Saudenshi ta koma? Tsananta tunaninshi da tayi ne kawai hawaye suka fara zuba a idanunta.

 Aunty Nainah ce ta dafa kafaɗarta "Yadai Saude?" share hawayenta tayi duk da bata iya ɓoye damuwan dake fuskarta ba,

  "Ba komai Aunty, Na gode miki sosai"

  "Bani badai, Najib shiya biyamu kuɗaɗe da yawa donmu muki gyarannan, bansan yanda kuke dashi ba, anma Allah yasa yana da muhimmanci a gurinki kamar yanda kike wurinshi"

  Maganarta taa ɗaure mata kai, harma ta rasa me zata ce mata, hannunta ta sake rik'ewa.

  "Muje yana jiranki tun ɗazu" suka tafi har kusa da wurin ta rakata, sannan ta mata bankwana don tafiso ta k'arasa ita kaɗai.


  Shi kaɗai harya gaji da jira, anma bai nuna alaman k'osawa ba, ta daɗe a tsaye, bai buɗe ba hankalinshi ma sam bai kanta, ta saka hannu taɗan k'wank'wasa k'ofan, sauke glass ɗin yayi kaɗan, ya kalleta yana sauraren k'arin bayani.

  "Daman an gama ne" tace tana wasa da yatsun hannunta, ya taɓe baki donshi tsakaninshi da Allah bai ganeta ba.

  "an gama me?"

    "Aunty Nainah ce ta rakoni" sannan ya ɗaga kanshi yana kallonta sosai, donshi ko kallan mata bai cika yi ba, sai kuma ya ware ido bakinshi ɗauke da murmushi.

  "Saude??" ta saka hannu biyu ta rufe fuskanta tana daria, "Naam" ai saiya buɗe mota ya fito, hannu ya saka ya janye mata hannun data rufe fuska dashi, yana k'arema kyakkyawar fuskarta kallo.

  "I cant believe dis Saude kece kika koma haka?" dariya kawai take, ya ɗaura hannunshi saman kafaɗarta.

  "Kinyi kyau, kinyi kyau Saude, ke mai kyauce"

 Gabanta ne yayi mummunar faɗuwa, duk fara'ar da take ta kauce saboda k'ara tuna mata Yasseer da yayi, ta kalli kafaɗarta inda ya ɗaura hannunshi, ya ɗauka abunda ya ɓata mata rai kenan da saurinshi ya janye.

  "Meya faru kuma?"

   "ba komai" ta k'ak'aro murmushi, yace "Selfie?" yana ɗaga mata gira cikin wani irin salo mai burgewa.

 Batasan me yake nufi ba, sai dai ya janyo waya, kusa da ita ya tsaya anma bai taɓata ba, ya dinga musu pics masu kyau, sannan itama ya mata, mutane sai kallansu suke ba k'aramin burgewa sukai ba,


 Daganan wani k'aton boutique ya kaita, ya dinga jidar mata dogayen riguna masu kyau da masu wando, harda kayan barci duk wanda ya burgeshi ɗauka yake ya zuba kawai, kamar mai shirin buɗe kanti, kuɗi masu yawa taga ya zaro ya mik'a.

  Basu gama ba har dare yana yawo da ita, wuraren shak'atawa ya dinga kaita, sunsha yawo sosai, wani iri takejin ranar daban da sauran ranakun da tayi a baya, duk da ba wani magana suke a tsakaninsu ba, shi miskili ita kuma sarkin kunya, saima ta maida fuskarta gefe tana shak'ar sanyayyar iska da yake glass ɗin a sauke yake, wani irin farin ciki na k'ara shigarta, ga wani kiɗa mai taushi dake tashi.

  Kaɗan kaɗan zata waiwaya ta kalleshi, tanason mishi magana anma kunyarshi taa hana, hankalinshi gaba ɗaya yanakan tuk'i, shima wani irin nishaɗi yake ciki, wak'ar koredo bello ne yake bi a bakinshi kamar shine ya rairata, yana lura da duk wani motsinta.

  "Ina zamuje?" ta tambayeshi cikin fargaba, batasanma yaji ba saida ya bata amsa,

  "Gida, ko akwai inda kikeson zuwa?"

 Ta k'ara k'asa da kanta tana wasa da hannunta, kallonta yake anma tak'i magana.

  "kinyi shiru, karki goge zanen lallen mana"

 Da sauri ta ɓoye hannunta tana dariya, "Daman..." kuma sai tayi shiru.

  "ehen..."

    "Zamuje gidan Aunty Husna?"

  "Me zakiyo?"

    "ba komai"

 Ya duk'o da kanshi yana kallon fuskarta,

  "zaki nuna mata kwalliyar ne?" ta girgiza kai duk ta takure jikin k'ofa, shi kuma ya wani shige mata.

  "eeh mana kedai faɗamun" wani irin zaro ido tayi tana nuna mishi gabanshi, 

   "Gabanka yaya Najib" da sauri ya koma kan tuk'unshi baiga komai ba, ya kalleta sai dariya take mishi.

  Ya ɓata rai "kekoh" itama duk saita marairaice fuska ta ɗauka haushi yaji.

   "yi hak'uri"

  Sai sannan shima ya fara dariya sosae, "kinfi kyau a haka" kallonshi kawai take.

  

  Mutum mai faɗa da birkitaccen hali idan baka fahimceshi ba, anma mai sauk'in kai da son mutane, ga wanda suka zauna dashi, ya iya zama da mutane sosae ba tare da yaa ɓata musu ba, matsalanshi kawai kar a mishi katsalandan.

  Sanda suka isa gidan har Momie ta dawo tana shirin kwanciya, suka shiga ɗakin da kaya niki-niki, ba k'aramin daɗi taji ganin Saude a haka ba, ta dinga saka musu albarka, ita da kanta ta dinga mishi godia, ta mishi addu'ah sosae.

 Shiya ɗaukarma Saude kayan har ɗakinta, tana tsaye jikin madubi don bata gajia da kallon kanta, sai murmushi take ita kaɗai, daga bayanta ya tsaya tana kallonshi ta cikin madubin, sai kuma taji kunya da sauri ta rufe idanunta.

  Saitin kunnanta yake mata magana "bansan me nake tunani ba Saude, anma yau ranace ta musanman a gareni, naji daɗin kasancewarki cikin farin ciki" yasan bazatayi magana ba, yana gama faɗa ya fita sannan ta buɗe idanunta,

  "Nagode sosai ta sabuwar rayuwarnan daka bani Yaya Najib" ta faɗa kamar yanajinta, bayan taji fitarshi


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

       59


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


  Ranar Monday kenan washe gari da wuri ta farka, barcinta kaɗanne, ta kasa mantawa da abubuwan da suka faru, kayanda ya kawo mata ta dinga ɗagawa tana gani, taji daɗinsu sosae.

  Tunawa tayi da yau fa zai koma, gashi har rana tayi k'ilama ya tafi, dirowa tayi daga saman gadon tayi hanyar ɗakin Momie, tama manta da riga da wandon kayan barci ne a jikinta, tana sauri ta koma ta saka hijabi sannan ta tafi.

  Da yake sauri take saida ta faɗa ciki ma sannan tayi sallama yana Zaune da Momie suna magana, shima jallabiyace a jikinshi da alama ko shirin tafiya baiyi ba.

  Kasa magana tayi tana tsaye dai tana kallonshi, komai ya sakama kyau yake mishi, idan ta ganshi cikin k'ananan kaya saita ɗauka duk sunfi mishi kyau, idanta ganshi a manyan kaya ma haka, yau da ta ganshi da jallabiya ma ba k'aramin kyau ya mata ba, ta manta ma da Momie a wurin. Saida ta tuna a kunyace ta gaisheta, tace 

  "kinyi mamakin ganin yayanki bai koma ba ko?"

  "eeh Momie, meyasa?"

    "saboda ke" ya riga momie bata amsa, waro ido tayi tana daria, sannan ta kalla Momie.

  Ɗaga mata kai tayi "nima dai haka yacemun"

  "Daddy so yake ya sakaki a makaranta, kinason karatu?"

  "eeh inaso sosae"

   "Yauwa ki shirya yanzu ya kaiki, daman a garinku ai kina makaranta ko?"

  "A'ah banyi nisa ba, anma dai...." kuma sai tayi shiru idanunta ya kawo k'walla.

 Momie cikin tausayawa tace "kawu Ado ko?"

  Girgiza kai tayi, "Mijina dai yana koyamun a gida"

   "ki daina kuka Saude idan kin tunashi, addu'ah zakina mishi, abinda mamaci ke buk'ata kenan"

 Share hawayenta tayi "Insha Allah Momie" Najib tashi yayi ya fita kawai, Momie tace "tohh yi sauri kije ki shirya, sai kizo ki break fast"

   

  Da wuri suka isa makarantar, tsadajjiyar makaranta ce a garin Abuja, sai yaran wane ne ke a ckul ɗin, akwai ɓangaren nursery, primary, junior and senior secondry ckul. Kai tsaye ɓangaren shugaban k'aramar makarantar suka wuce (junior), cikin girmamawa ya amshesu, bayan sun gaisa Najib ya mishi bayanin daya kawosu.

  Kallon saude yayi ta cikin gilashin daya saka, "what's ur name?"

  "My name is Saude" ta bashi amsa cikin wani dadaɗan turanci kamar wata baturiya, yaci gaba da mata en k'ananun tambayoyi na en primary duk kusan taa haye, na sec ɗin daine take cewa batasan wannan ba, wanda ta sani kuma ta bashi amsa.

  "congratulations Mr. Zamu ɗauka Saude a aji uku (J.s3) duk da yayi mata girma, anma nasan insha Allah karatun bazai mata wahala ba don da alama tana ganewa, sai dai kuma a samu wanda zaina koya mata a gida"

  "Insha Allah, wannan ba damuwa bane, nagode sosae"

  "jin daɗinmu ne"


  "Saude wa za'a rubuta mata jikin admission ɗin?"

  Kallonta yayi, "ya sunan babanki?"

  "Saude Yasseer za'a sakamun"

 Yamutsa fuska yayi, "Yasseer ba sunan baban Hafsat bane?" ta ɗaga mishi kai, wani irin haushinta yaji, cikin muryar ɓacin rai yace,

  "sunan babanki nace ki faɗamun" duk sai taji ba daɗi da yanayinshi ya canja,

  "Muhammad"

    "Saudat Muhammad za'a saka mata" saida ya tabbatar an gama mata komai daya dace, ya biya kudaɗe da yawa, sannan suka tafi ko kallan inda take baiyi, wani irin haushinta yakeji. Anan ckul ɗin aka bata unifoam da littafai, suka wuce gida washe gari zata fara zuwa.


  Har sukaje gida yana fushi da ita, yanayin parking da sauri ta buɗe ta fita, don karma ta k'ara ɓata mishi rai, sauri take taa kusan shiga ɗakinta taji taji ya kira sunanta.

  "Saudat!!" saida ko ina ya amsa sunan cikin kanta, har k'asan zuciyarta takejinshi da kuma yanayin daya faɗa, bata taɓa sanin haka sunanta yake da daɗi ba sai yau daya k'ayatar dashi, saida ta rumtse ido tama kasa juyawa, ta kasa ci gaba da tafiya sai dai ta tsaya wuri ɗaya.

  "Saudat!" ya k'ara kiran sunanta, still dai bata waiwaya ba, ya ɗanyi tafiya gab da inda take, magana yake mata yanda ita kaɗai zataji.

   "Yau zan tafi, ko kaɗanne kina sakani cikin tunaninki, plz a sanmin wurinda za'a dinga tunawa dani cikin inda ake tuna baban Hafsat"

 Jinshi gaf da ita ya saka ta jawo mayafinta ta rufe fuska, ta kasa bashi amsa tana jiran ya tafi, zagayawa yayi inda take yana lek'en fuskarta ta cikin mayafin da sauri da rufe wurin, ya juya ɗaya bangaren nanma ta rufe, haka suka dingayi saida taji kamar ya tafi ta buɗe fuska, da sauri ta zaro ido data ganshi gaf da ita.

   "Zan tafi ko damuwa bazaki ba ko?" girgiza mishi kai tayi, 

  "banda amsa ko?" shiru ya juya zai tafi, a hankali tace "Yaya Najib" ya juyo yana kallonta, "Allah ya dawo dakai lafiya"

  Ya sakar mata murmushi, "Ameen".

   A ranar ya wuce kaduna, bayan ya tabbatar da ya samar mata mai lesson da drivern dazai kaita ya ɗaukota.

 

  

Page ɗin yau yayi kaɗan na sani, plz kumin uzuri donma banso ku jini shirune, na gaisheda duk wani Masoyan littafinnan, k'aunarku da nake batta da iyaka❤


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

       60


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


 Su Saude, Aww Saudat😄 anci gaba da zuwa makaranta, kullum mai mata lesson yana zuwa bata gajia da karatu, tanason ckul d'inta sosai, a can kowa so take tayi k'awance da ita, gashi ba iya shiga mutane tayi ba ko k'awar kirkima bata da ita.

   Ahmad ne rik'e da wayar Najib hannunshi yana kallon hoto duk ya yamutsa fuska, hotan Saude yake gani wanda tana er k'yauyentane sosai.

   "Waida wannan ce Sauden? Gaskia Abokina ka badani, haba idan kana cemun er k'yauyece duk ban d'auka taakai haka ba, gaskia wannan bata dace dakai ba, inaa wannan in mukazo biki ma ai sai abokanmu suna mana dariya"

 Yana cikin maganganunshi, Najib ya gano mishi wanda tayi a er birninta,

  "Tohm ga Saudat kuma"

    "wacece Saudat d'in?"

   "Gani da kanka"

 "wow Aboki, wannan irin had'uwa haka, ashe daman abunda ka dad'e kana b'oyemun kenan, kullum maganarka baka tashi soyayya yanzu ba, ashe kasan tanajin da kayi, ita kuma wannan ina ka samota?"

   "Saude ce"

 Coffee daya kurb'ane a bakinshi ya furzar dashi har yana k'warewa,

  "Saudence ta koma haka?" ya d'aga mishi kai fuskarshi d'auke da murmushi.

  Hotanta na k'yauye da wannan ya ringa comparing, donshi duk bai yarda ba, ya ringa kallon hotan.

   "Kai Matan Aurece fa kake mata irin wannan kallon"

  "hhh ni kuma abokin mijinta ne"

  "wallahi ita d'ince fa, gashinan komai iri d'aya, sai yanzu na lura ana k'yauyenma ashe kyaune da ita sosae, kai Aboki kaayi babban kamu fa, ashe akwai abinda ka gano a bazawarar er k'yauyennan"

   "Kaa cika surutu"

  "aina kasa tsaida maganata ne, plz indai kaa fasa by any chance, let me know"

  "Kayi me dan U***ka, kaifa Namamajo ne"


  "Indai na samu kamar wannan aina daina kula kowacce mace, nasan kana son Saudat, anma dai zan k'ara fad'a maka ka rik'eta amana, karka cutar da zuciyarta ta kowanne hanya"

  "ina son Saude da yawa Aboki, Soyayyar da ko kaina banayi mawa, ko wani ya b'ata mata rai sai nawa yafi b'aci, Soyayyarta bazata tab'a bari na mata wani abu da zataji ba dad'i ba, Idan harna rasa Saude bani da sauran jin dad'in rayuwa, ita na fara so, kuma da ita nake burin k'are rayuwatah".

  "Allah yasa ta soka kamar yanda kakesonta, sai yaushene zaka fad'a mata?"

  "saita fara sona"


  MOSCOW

Yasseer ne kwance yana barcin rana, wani irin mafarkin Saude yake mai razanarwa, a firgice ya farka yana fad'in.

  "MATATAH CE! MATATAH CE!! MATATAH CE!!!" duk ya Had'a zufa don ba k'aramin firgita yayi da mafarkin ba, ada idan yana mafarkin Saude cikin kuka take zo mishi tana neman taimakonshi, anma yanzu cikin farin ciki yake ganinta wani na neman k'wace mishi ita. 

  Ana gobe zasu tafi moscow saida yaje k'yauyensu Saude cikin dare ya isa da niyyar da safe zai d'aukota ya maida birni ko bada sanin danginshi ba, baije gidan ba saida safe don yaga kalan murnar da zatayi idanta ganshi, sai kuma ya had'u da bak'in labari wai a safiyarnan tabar garin, yasha nemanta harya gaji, ya hak'ura dai ya koma gida kuma a ranar yabar k'asar da maraice, ita kuma a daren ta isa gidansu Yasseer d'in.

   

 Ta bayanshi ta kwanto tana sumbatar wuyanshi ta ko ina, rumtse hannunta yayi cikin nashi ya d'an juyo da fuskarshi yana lumshe ido, muryarta a sark'e tace "waye yace Rabi'ah ba matarka bace? Ni taka ce, sai dai ka k'ara jaddada musu"

  Ta had'a bakinta da nashi tana sumbatarshi hannunta akan k'irjinshi, duk taa fara rikitashi, dak'yar yakai hannu ya shafi cikinta a kunne ya rad'a mata,

  "Yaushe ne zamu sama baby? Inason yara Rabi'ah"

 Buge hannunnashi tayi, "Ba yanzu ba, duka yaushene auren namu? Kuma ko ckul ban fara ba, saina gama gaskia, raino wahala"

  Ya jawota jikinshi, "Plz Rabi'ah" tureshi tayi, ta mik'e zata tafi,

  "Zan kawo wacce zata haifamun idan ke yana miki wahala" da sauri ta dawo tana huci, ta nunashi da yatsa

  "karma ka fara, kai nawane ni kad'ai, babu macen data isa ta rabani dakai" shi dariyama take bashi idan tana nuna kishinnan,

  "bazan b'oye miki ba Rabi'ah, hak'urina ya fara k'arewa, inason yara" maganar taa fara gundurarta, ta mik'e ta bashi wuri, yabi bayanta da murmushi kawai.

 Rabiah rigima, matsalanshi da ita kawai rashin haihuwa, anma in akazo b'angaren abun ko gajia batayi, kuma yana samun kulawa sosae daga gareta.


 Saude ce ta fad'o mishi rai da yaron cikin daya barta dashi, ko wanne hali suke ciki? Dukan k'irjinshi ya shiga yi, ko zaiji sauk'in bugawar da zuciyarshi take mishi, shi kanshi yasan bai kyauta ba, kuma kullum zuciyarshi cikin azabtuwa take da rashinta, 'Ya Allah ka nunamin Saude, da abundata haifa, ya Allah kasa tana tunawa dani kamar yacce koda yaushe take cikin tunani nah'


  Tunawa yayi da Rabi'ah fa fushi tayi, yaja tsoki ita abun b'acin rai bai mata wahala, kitchen ya tafi ya sameta, ya kwanto ta bayanta.

   "Me ake girka mana duk k'amshi ya cikamun hanci" tureshi tayi ba tare da tace komai ba, ya k'ara kwantotah, ta k'ara tureshi, 

  "Shikenan, ni daman duk sona da kike cewa nasan ba haka bane tunda kina fushi dani" ya juya kamar zai tafi, da gudu ta tafi ta fad'a mishi tana kuka.

   "Plz hniee ka dainamin maganar kishiyarnan, Ina sonka da yawa karka saka zuciyatah ta fashe"

  D'ago da fuskarta yayi "ke miye na kuka? Nifa wasa nake miki, banson ganin hawayennan plz" ya saka hannu ya fara share mata, tayi murmushi, "tohm kaima ka daina"

  "na daina, bara inje wanka" ta d'aga mishi kai.


  Suna zaune dinning ta zuba mishi abinci yanaci, cokalin farko kawai yakai tunanin Saude ne kawai ke dawo mishi, ko tana ina? Wanne hali take ciki? Ita tamaci abincin kuwa? Ji yayi bazai iya ci gaba da ci ba, a yanzu tunanin Saude duk yafi damunshi, ya ajje cokalin kawai ya tashi zai tafi, ta kalleshi duk ta marairaice fuska.

  "Bazaka ci abincin ba?"

   "zanci sai anjima"

  "kodai bai maka dad'i ba?"

  "kawai banjin ci ne" yana fad'ar haka ya wuce zuwa d'akinshi, har dare baida wani sukuni, baima k'ara fita ba a ranar, da wuri yayi shirin barci ya kwanta.

  Saida ta gama duk abunda take ta shigo d'akin, ta kunne haske idonshi biyu anma da alama tunani yake, ta kashe sannan itama ta haye gadon, shiru bataji ya tanka mata ba kamar baisan da shigowarta ba, ta matsa inda yake ta saka hannu ta fara yawo dashi wurin wuyanshi, jin bai hanata ba ya sanyata komawa samanshi wani fitinannan kiss da dinga binshi dashi, tana aika mishi sak'onni, anma ko motsi baiyi ba, ita kad'ai ke kid'inta da rawarta, wani irin haushinshi taji, takai mishi duka a k'irji.

  "koba komai ai saika fad'amun u're not in d mood" jin baiyi magana ba ta k'ara kai mishi wani dukan, ko a jikinshi, tashi tayi ma tabar mishi d'akin.

  "Plz Saude ki dawo rayuwatah hakanan, kece farin ciki na"


 Yau da gobe a kwana a tashi su Saudat har lokacin fara jarawa (J.S.C.E/J.L.S) yayi, kullum bata da lokaci saina karatu, bataso ta bama Najib kunya, sai dai kuma yawan tunani dake damunta, kullum cikin tunani.

  Ranar laraba suka fara exam, tunda wuri take shiri bayan ta gama duk aikin da zatayi, cikin hanzari ta shirya ta tafi makarantar, lokacin da taje har an shiga, ta ajje littafinta harta tafi ta dawo ta k'ara dubawa sannan ta tafi da gudu ta shiga, malamin dake dubasu ne ya tsayar da ita.

   "Saudat muhammad! Sai yanzu kike zuwa exam d'in don baki d'auketa serious ba?"

  "M srry sir" ta tafi zata wuce sumi-sumi, ya k'ara kiranta.

  "ki jira anan, yanda bakizo da wuri ba bazaki fara da wuri ba" idonta kamar zatayi kuka tace "pls sir" hannunshi ya d'aura saman bakinshi, sannan ya nuna mata inda zata tsaya, duk ranta ba dad'i.

  Saida suka dad'e da farawa sannan ya mata alamar taje ta zauna, cikin dubara ta share hawayenta taje ta zauna, lokacin daya rage baida yawa, aka mik'a mata question paper ta fara dubawa, amsar data sani baida yawa a ciki nanta fara k'ok'arin tuna hardar da tayi anma kamar wacce akama satar k'walwa, komai ta kasa tunawa, bata rubuta komai a takardarta ba har aka amsa takardar, tun anan ta fara kuka.


 Da gudu ta shiga falon Momie ta tare ta,

   "Lafiyanki?"

 Ta duk'e gabanta tana wani irin kuka, Momie ta dafa kafad'arta tana lallashinta,

  "meya faru dake a makarantarne, kukanme kike?"

 Ta k'ara fashewa da kuka,

  "Nayi karatu Momie, wallahi nayi karatu sosai"

  "ni kaina shaidace, fad'amun meya faru?"

 Cikin kuka ta bata labarin duk abunda ya faru a wurin exam, sannan ta k'ara da cewa "wallahi nayi karatu momie"

  "ki kwantar da hankalinki kinji, yanzu yaushene zaku k'ara wata?"

   "friday"

  "kinga kina da lokacin karatu sosai, ki daina damuwa nasan zaki iya, nasan bazaki bamu kunya ba"

 Ita dai duk hankalinta bai kwanta ba, ta tashi d'akinta tana kuka.


Da Najib ya kira waya Momie ta fad'a mishi, yace a bama Saude wayar, shima kuka kawai ta saka mishi ya ringa lallashinta dak'yar ya samu tayi shiru, sannan ya tambayeta,

  "Baki gane lesson d'in da ake miki ne?"

  "nifa nayi karatu, komai saida na hardace ina zuwa na manta"

 "nasan kinyi karatu, anma daman waya kaiki harda? Indai kika maida hankali kika gane basaikin harda ba kinji ko" 

   "tohm"

 "Yauwah zan dawo gobe, sai in tayaki karatun"

  Sannan tayi dariya, "Da gaske gobe zaka dawo?"

 "ai naji ko murna bakiyi, nama fasa"

  "A'ah dad'inne har yamun yawa, Allah ya kawoka lafiya"

  "Ameen k'anwata"

    "Ina Hafsat?"

  "ta tafi tahfiz"

    "tohm bani labari"

  "labarin me?"

    "komai ma, bani na kanki dai, yau me kika saka? Nasan kinyi kyau sosae"

   "umm"

    "umm kuma? Fad'amun zakiyi" Momie ta kalla, ba kallonta take ba anma tasan da tayi magana zataji.

   "mezan girka maka gobe?"

  "kunyar Momie ta hanaki bani amsa ko? Ni saikin fad'amun" 

  Tashi tayi daga d'akin Momien sukaci gaba da waya, bai k'yaleta ba saida ya tabbatar hankalinta ya kwanta bata da sauran damu, sannan ya yarda ta ajje wayar.


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

       61


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


  Kamar yanda ya mata alk'awari, goben nayi sai gashi da wuri, tayi murna sosae da ganinshi saboda ba k'aramin kewanshi tayi ba, yanzu akwai shak'uwa sosae a tsakaninsu. Abinci kawai ta barshi yaci ta kwaso littafanta ta zube mishi.

  Cikin sauk'i yanda zata gane ya dinga mata bayani, ba k'aramin burgeta yayi ba yanda yake mata bayani daya bayan daya, rik'e take da littafin anma shi kawai take kallo hankalinta ma ba saurarenshi take ba, saida taji yayi shiru tace "Kayi shiru"

  "kina kallona ne"

   "sorry na daina"

  Yaci gaba da koya mata sosae takejin dadin karatun, Sallah kawai ke tadasu, saida ya tabbatar ta gane sannan ya barta taci gaba da karatun inda bata gane ba ta tambayeshi, har dare ko motsin kirki batasonyi, ta saka littafi tana ta karatu ko abinci tak'i taci.


  "wai bakyajin barci?"

   "zan kwanta, gobe fa ne exam d'in"

  "tohm ai karatun ya isa haka, ga abincinki tun d'azu kink'i kici"

  "ni nafa k'oshi ma, ka barni in k'arasa karatunnan plz Yaya Najib"

  "me? Tun dawowa na banga kinci abinci ba, ajje karatunnan hakanan" rufe idanunta tayi tana maimaita abunda ta karanto, ya taso zai k'wace littafin, da gudu ta canja kujera, haka suka ringa zagaye falon tak'i yarda ya ansa littafin, tana gudu tana karatunta, saida ya gaji ya tsaya.

  Sannan ta zauna, ya d'aukar mata abincin har inda take, ta wani marairaice.

  "Plz ka barni inyi karatunnan"

 "ai ban hanaki ba," ya deb'o a cokali, ya nufi bakinta dashi.

  "bud'a bakin" ta waro kyawawan idanunta, ya d'aga mata kai, kwantar da kanta tayi tana girgazashi, ya d'an rausayar da kanshi yana mata alamar eeh da idanunshi, 

  Littafin ta saka ta kare fuskarta, ya sunkuyo ta k'asan littafin, babu yanda ta iya ta bud'a mishi ya bata a baki, "ko kefa, dana hana karatun exam d'innan" tak'i ma kallonshi taci gaba da karatunta, a haka yake bata abincin.


  Suna cikin ci ta bud'a baki zai bata kawai taji babu komai ta tauna cokali, ya kyalkyale mata da daria, ta aje littafin duk ta b'ata rai tana harararshi, sai dariya yake.

  "nama fasa cin abinci"

    "Sorry na daina"

  "nidai bazanci ba tunda hakane"

  "da gaske bazan k'ara ba" ya rik'e kunnuwanshi da hannayenshi biyu, sannan ta hak'ura yaci gaba da bata, saida ta kusan k'oshi duk hankalinta na kan littafi, taji ya cika mata baki da abinci, batasan sanda ta saka littafin ba ta fara dukanshi, shikam dariyarshi kawai yake.

   "kaje ka kwanta dukka hanani karatuna"

  "nak'i, tare zamu kwanta"

    "ni ba yanzu ba"

  Ya ware hannuwanshi, "nima haka" ya k'aro wani abincin zai bata, ta girgiza kai, "ni bazan k'ara ansa da cokali ba, da hannunka zaka bani" ya fad'ad'a fara'arshi harda nad'e hannun riga.

  "shi yafi komai sauk'i" tana mishi dariyar mugunta, yana saka mata hannun ta cijeshi, da sauri ya janye yana k'ara, ta mik'e da gudu tabar wurin tana mishi daria.

  "Saida safe"


  Haka suke karatun kullum cikin nishad'i, idan tana tare dashi mantawa ma take da wani auren Yasseer dake kanta, duk wani damuwarta kaucewa take ta bata wuri, kullum bata da wani buri daya wuce zama da Najib, idan tana tuna zamansu da Yasseer da ko abinci bata iya ci a ganshi, idan yana d'aki ita zata tsaya a wajene ko nesa dashi, bai jata a jikinshi ya nuna mata abunda yakeso ba, bai koyar da ita kalan soyayyar birni ba ballantana ta mishi a matsayinshi na mijinta, soyayyar kwanciyar aure kawai ya koyar mata yanda zata mishi, da kuma soyayyarshi daya gina a zuciyarta ya tafi ya barta da k'aton tabo, zaman shekara biyu tayi da kwanaki a k'yauye ba tare da yaa nemeta ba, kuma shine yasan inda take, ya manta da jaririn cikin daya tafi ya barta dashi, da kuma igiyoyin aurenshi dake kanta.

  Idan ta zauna ita kad'aine take tunawa dashi, sai dai tayi ta sharan k'walla kawai, bada son ranta take kuka ba idanta tunashi, don batason bama zuciyarta dalilin da zataji haushinshi, domin shine mutum na farko daya fara nuna mata soyayya da kulawa a rayuwa, shine mutum na farko daya nuna tausayinshi a kanta, ta dad'e tana mishi uzurin butulcin daya mata kasancewarshi d'an adam kuma ajizi.

  K'aran dukan k'ofan Najib ne ya fito da ita daga d'akin,

   "wai ko shirin exam d'in bakiyi ba? Halan har yanzu karatun kike"

  "A'ah unifoam kawai zan saka"

  "tohm ina jiranki" har ya juya kuma ya dawo, "kuka kikayi ko?" girgiza mishi kai tayi, "ki fad'amun gaskia"

  "Da gaske ba kuka nayi ba"

 "tohm kije ki shirya" ta juya zata tafi, ya k'ara tsayar da ita "Saudat!" cak ta tsaya,

  "bansan meye damuwarki ba, anma ina jinta har cikin zuciyatah, kullum burina ki kasance cikin farin ciki, bazan tab'a bari kiyi kuka ba inda muna tare," kai kawai ta d'aga mishi, tana toshe baki ta shige d'akinta da gudu,

  Tana shiga toilet ta k'ara fashewa da kuka, “shima haka yace, 'kindaina kuka indai muna tare, hawayen farin ciki kawai nakeson gani a fuskarki (Yasseer)' yanzu gashi ya tafi yaa barni, banda wani dalilin kuka yanzu bayanshi, shine kawai silar damuwatah!!


  Cikin lokaci kad'an ta gama shiryawa ta fito, ko littafi ma bata d'auka ba, daa ko toilet zataje da littafi, ko brush take tanayi tana dubawa har dare ya raba tana karatu, anma yanzu yaa zauna mata, data amsa question paper lokaci kad'an ta gama rubuce ta, ko wani abu ya shige mata saita tuna da lokacin da Najib ke koya mata muryarshi na dawo mata yanda yake koya mata cikin k'warewa duk yanda zata gane. Shi yake kaita exam ya d'aukota ko wurin aikinma yak'i komawa sai dai yaje ya dawo, Momie har fad'an batason zaryarnan take mishi, sai dai ya bata hak'uri ta barshi na sati d'ayane kawai.


  Gobe zata gama exam d'inta, suna d'akin Momie ita har Najib d'in, wayanta ta d'auka tana kiran wani layi, da yake hankalinta nakan karatu bataji mai take cewa ba saida ta gama ta fara fad'a.

  "Yau naaga d'an banzan yaro, kai shikenan baka da lokacin danginka baka dana Mahaifiyarka, kullum kai aiki dai, matarka dai"

  Najib yace "Momie broz ne?"

   "shi mana, shikenan kullum aka mishi waya sai yace yana busy zai kira, kuma shi bazai d'auka waya ya kira mutane ba, ya kwashi mata sun tafi k'asar turawa ya manta damunan, barni dashi azuminnan yazo bai dawo gida"

  "Momie broz Yasseer ya kusan dawowa?"

  "ai dolenshi ma ya dawo, shekaranshi nawa a can? Azumi saura wata d'aya na fad'a mishi su dawo anan za'a fara dasu, idan kunyi waya dashi ka k'ara jaddada mishi don ba k'aramin sab'a mishi zan ba ya wuce lokaci"

  "an gama momie, gaskia nayi murna da dawowarshi sosai" shi yake murnarshi, anma Momie fad'anta taci gaba dayi, ita dai Saude iyakarta saurare, ita dai ko son ganin Yasseer d'in Momien ma batayi, don tuni mai irin sunanshi ya gama b'ata damarshi a wurinta, anma dai ta lura gidan suna sonshi, Najib ma yana yawan mata firarshi.


 Ranar da zata gama exam, Najib zai kaita ckul, suna hanyarsu ta zuwa sai firarsu suke cikin nishad'i, yace "yau zaki gama junior ckul d'in, akwai maganar dazan fad'a miki anma saikin fito exam".

  "tohm shikenan kaimun addu'ah in fito lafiya"

  "Ameen dear, best ov luck"

 Tayi murmushi "tnx" sukaci gaba da firansu har suka isa.


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

      62


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


 Sun gama exam suka fito, anata bankwana kamar an tafi kenan, wasu nata hotuna, itama ta d'auko wayanta Iphone7 da Najib ya bata aro don kawai tayi pictures, nan aka dinga zuwa aro kowa sai so yake tayi dashi, daga k'arshe ma ta bar musu suyi kawai. Tana tsaye gefe wata class mate d'inta tazo inda take.

  "Alhmdlh! Saudat muhammad Allah ya taimakeni baki tafi ba"

  "tohh Allah yasa dai lafiya"

    "Da sauk'i dai, tunda ciwon daga zuciyatah ne, number Yayannan namu nakeso ki bani"

  "Yayanmu kuma? Wa kenan?" ta tambayeta kamar bata gane.

  "Plz ki gane mana, wannan kyakkyawan dake kawoki makaranta yanzu"

  "Yaya Najib ne yake kawoni, karma in tsaidake ni bani da waya"

  "haba wancan Iphone d'in fa? Nifa numbershi kawai zaki bani"

  "tashi ce ba tawa ba"

    "Yazo da sauk'i, sai ma in saka mishi tawa, in kira inga numbern"

  "ke babu fa simcard a ciki"

    "Yau ni ya zanyi? Ki jirani plz ina zuwa" ta tafi da gudu tabar wurin, Saude ta bita da kallo tana tab'e baki, tana daina ganinta ta amsa wayarta tasan yana can yana jiranta, ta kusan kaiwa wurinshi sai gata ta dawo da gudu, tana kawowa inda take ta fara tafiyar yanga.


  Takarda ta mik'a mata

  "plz ki kai mishi" hannu kawai tasa ta amsa, sannan ta wuce tana mata godia, duk taa b'ata rai ta shiga motan. Saida ya tada ta mik'a mishi.

  "Ga sak'onka fa"

    "Sak'ona kuma?"

  "wata er class d'inmu tace in kawo maka"

  "Shiyasa kike ta b'ata rai kenan?"

 Harararshi tayi, "Meye na b'ata rai kuma daga sak'o? Ni gajia nayi"

  "tohh yarda ta"

   "me? Ai tunda na amso saika karanta ta"

  "nikam bazan amsa ba, ki d'auka in kina so"

  "inaso mana, bara ma in karanta" ta bud'eta ta fara karanta.

  “zuwa ga kyakkyawan saurayin da yafi kowanne namiji kyau a doron k'asa”

  Ta k'yalk'yale da daria "wao!"

   "ke ita ta rubuta hakan?"

  “bansan meke faruwa dani ba aduk lokacin dana ganka, zuciyatah sai ta dinga bugawa da sauri, dole akwai wani abu na musanman tattare dakai dake sanyani jin hakan a koda yaushe"

  "Ciwon zuciyah ne da ita" 

  Saude ta k'ara tuntsirewa da daria, "Sirrin zuciyah dai"

 Tana dariya taci gaba da karantowa 

  “bana tunanin komai sai naka a kullum, ko yaushe cikin tunaninka nake ko abinci bana iya ci”

  "taje asibiti kota nema maganin zafi"

  "ba wani Asibiti, kai dai..."

 "me kikace?" ya amsa takardar ya cukuikuye ya jefar da ita, "komai saikin karanta kenan? Cikin jin dad'i har wani daria kike"

    "kaifa ka bani ya zaka anshe?" ta fad'a cikin dariyar.

  "ni ba ruwana da wani er ajinku,"

  "tohm shikenan na daina, saura maganar da kace zamuyi"

  "aina d'auka kin manta" ya jawo wata linkakkiyar takarda a hannunshi ya mik'a mata.


  "naga yau karatu kikeji, ki karanta wannan ma duk abinda zan fad'a miki yana rubuce a ciki"

  Ta amsa ta fara karantawa a fili.

  “You are so funny, you are so nice, 

You are the girl with whom I fell in love twice. 

The first time was love at first sight, 

The second time I feel for you was when I got to know you, 

I realized that this was love, because the feeling was completely new. 

I will never ever let you go away and leave me. 

I will hold your hand and stand by you forever, 

I will always be your Man, will leave you never! 

I love you today and for always!”


 Tana fara karantawa ta daina fad'a a fili, ya kalleta yana d'auke da wani murmushin dake tafe da wasu sak'onnin, "nasan dai yanzu kin gama karantawa, abunda ke zuciyatah ne na fad'a miki, ina fatan zuciyarki zatayi maraba dani.

  Bai lura da yanayin data shigane tun sanda ta fara karantawa, gaba d'aya ta shiga tashin hankali, anya kuwa abunda takeyi dai-dai ne? Itafa matar aurece tayama zata fara tarayya da wani? Anya ta kyautawa Najib kuwa data b'oye mishi mijinta yana a raye?

  "Ina saurarenki, Allah yasa ba lokaci zakice in baki ba, domin kuwa nayi hak'uri da yawa, bazan iya jure lokacin da zaki d'auka kina tunani ba, idan har kina sona, baki buk'atar nazari akai, ki fad'amun abunda ke zuciyarki game dani, plz ki fad'amun da sauri Saudat"

  Kamar yasan abun da zata nema kenan a wurinshi, lokacin da zatayi tunani, idan har tace batason Najib tohh tayi babbar k'arya a rayuwarta, bata da wani buri yanzu saina kasancewa dashi, anma idanta amincema soyayyarshi anya kuwa taa kyautawa auren dake kanta? Wata zuciyarce ke mata tuni da cewa wanne irin auren? Yanzu k'ilama ya gama mantawa dake, ke kad'aice kika damu dashi, ki manta da Yasseer kiyi sabuwar rayuwar dake jiranki a gaba.

 Ba tare da wani dogon nazari ba, itama takarda ta samu mai kyau ta tsara mishi rubuta ta ninketa sannan ta bashi, murmushi yayi a motan ya bud'e ya fara karantawa shima a fili, lokacin yayi parking, ta bud'e da gudu ta fita.

  “You make me feel so special every time. There is not a single moment when I am with you and I don't smile. So many lovely moments with you and so many memories that we make is all imprinted in my heart. I am so lucky that I have someone like you in my life. I love you a lot”

  Yana gama karantawa yayi murmushin jin dad'i har saida ya sumbaci takardar. Daganan nasu labarin soyayyar ya fara.


Tun daga ranar gaba d'aya Saude ta manta da Yasseer a rayuwarta ko tunashi ma ta dainayi, soyayya suke ma junansu fiye da kowanne Masoya, Momie idan tana ganinsu a haka ba k'aramin dad'i takeji ba, babu inda Najib ke kunyar nunama Saude soyayya, ko yaushe yana tare da ita, kulawa ta musammam yake bata, shiyasa gaba d'aya ta manta da duk wata damuwarta.

   Yanzu tashin hankalinta d'aya Momie tace bayan Sallah zasuje k'yauyensu ayi maganar aurensu da Najib, gaba d'aya damuwarta yanzu idan Momie taje k'yauyen aka fad'a mata cewar itafa matar aurece, mijinta nanan da ranshi guduwa kawai yayi ya barta, a wane matsayi zasu ajeta ita da Najib?.


Watan Azumi ya kama, har yayi tsakiya babu Yasseer, Momie gaba d'aya tayi fushi dashi ko kiranshi ta daina d'agawa, kullum cikin yima Najib waya yake ya tayashi bata hak'uri.

  Masoyan guda biyu Saude da Yasseer, kullum suna tare, idan ya farka zaiyi sallar tsakar dare saiya buga mata k'ofa ya tasheta, kullum asuba a falo suke zama yana k'ara mata karatun Qur'ani, shiya zama malaminta a b'angaren addini ma, yana k'ara mata sani akan sauran littafan, idan kuma suka tashi soyayyarsu sunfi kowa iyawa.

   Tare suke zuwa siyayyar sallah, komai kala d'aya yake sai musu, ko atamfane ya sai mata saiya sayi yadi kalan, kaya masu tsada ya dinga sai mata kamar baison kud'in, kowanne da takalminsu, jikka, da gyale duk kalar masu tsadar gaske, Momie ma tayi mata kayan sallah masu kyau, ita har rasa bakin godia take ga wannan mutanen.

  Anata shirye-shiryen Sallah saura kwana uku, Yasseer yama Najib waya gasunan zasu baro Moscow, koda ya fad'a ma Momie bata wani yarda da gaske yake ba don tafi kowa sani k'aryarshi kullum zaizo kuma ba zuwan yake ba, sai dai d'a da mahaifi, duk da tana fushi dashi saida tasa aka shirya musu abinci kala kala, tarba dai ta musamman.


 Suna sauka yayi ma Najib waya gasunan fa a tura musu driver, "Haba ina garin zakace driver, ganinan tafe yanzu bruz" 

  "Tohm sai kazo" daman a shirye yake yana jiran wayarshi, su Saude ma an zuba ido tanaso taga wanene wannan Yasseer d'in nasu Najib?


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

       63


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


Wannan Shafin sadaukarwa ne gareku Masoya littafinnan, Hafsat rano, hafsat faruq, hafsy hafsy, fatima sidi, mrs emir, meenert, princess da kuma bilkeesu Muhammad, Nagode sosae Allah yabar k'auna😍

  Jiya kunjini shiru ina can murna Momyn Muhseen taa biya mana Makka😊 lol, munyi fama da matsalan ntwk ne ban samu postn ba, Nagode sosai da kulawanku,  

# One Love

 

www.babymsh.blogspot.com


  Saude na zaune gefen Momie bayan ta aika kiranta, saiga Najib ya shigo yana fad'a mata su Yasseer sun sauka yanzu zaije ya d'aukoshi, tsayar dashi tayi.

  "da yanzu zan tura Saude gidan Husna da driver, anma tunda zaka fita saika wuce da ita, anma ka hanzarta tana jira"

  "Gidan Husna kuma? Me zatayi?" ya tambaya Momie cikin mamaki.

  "Wai aikin azumi ta fara, taa kasa k'arasawa kaasan yanzu tayi nauyi (cikinta ya tsufa) shine zataje ta dinga tayata"

  "kuma sai Saudat d'inne zata tayata dole?"

  "kasanta dai batason er aiki, shiyasa ta nema taimakon k'anwarta, sauri fa zakayi taa cemun girkinta nakan wuta" ya k'ara b'ata rai duk baiso ba, "yaushene zata dawo?"

  "idan ta haihu mana, nikam Daddy bansanka da haka ba"

  "ai dole in damu Momie, tunda zatayi nesa dani"


 Kunya ya bama Saude ta mik'e, "bara inje in had'a kayan dazan tafi dasu,

 Momie ta tsayar da ita, "Daddy zai kai miki daga baya, ki d'auko mayafinki dai"

  "tohh" ta tashi ta tafi, ba don yaso ba ya hak'ura ta koma gidan Husna.

 A hanya suna tafiya duk sunyi shiru, ta d'an karkad'a mishi yatsunta biyu ya jiyo.

  "wai bazakace komai ba?"

 "Nama rasa mezance Masoyiya, tunaninah kawai yanda zanyi rayuwa koda na rabin awa ne baki a kusa dani"

    "kana magana kamar wacce zata bar garin ko zata maka nisa, nasan ai duk inda nake zaka kasance tare dani"

  "Hakane fa, don yanzu zama gidan Husna ya kamamu" dariya tayi, ta bud'a baki zatayi magana dai dai lokacin sun isa gidan, ya shiga da motan yayi parking harta bud'e zata fita ya kalleta.

  "Sai sauri kike ki barni ko" da sauri ta d'aura hannunta saman leb'enta.

  "babu wannan kalmar tsakanina dakai, ni taka ce, bazan tab'a barinka ba"

  Murmushi yayi "nima duk da wasa nake miki, anma saida harshena yayi nauyin fad'a"

  "Yayanmu fa yana jiranka a airpot, kayi sauri plz"

  "Aww! Nifa ina tare dake mantawa da komai nake, saina dawo" tana murmushi take d'aga mishi hannu harya fice sannan ta shiga gidan.


 Tayi sallama sannan ta shiga gidan, Husna na zaune falo ta baje da gani ta tara gajia, ta amsa sallamar Saude.

  "Sannu Aunty Husna"

 "Yauwah Aunty Saudat" ta fad'a tana tsokanarta.

  "yau dai zan saka Matar yaya aiki"

  "Aunty Husna zolaya ko? Yanzu dai dame zan fara? Lokaci ya kusa"

  "komai yananan kitchen na fara na kasa k'arasawa"

  "Tohh Aunty bara inje" tana tafiya hanyar kitchen d'in Husna ta mata magana da d'an k'arfi yanda zataji.

  "Yaya Yasseer ya dawo kuwa?" saida gabanta ya buga yanda takeji kullum aka ambaci sunanshi.

   "A'ah yanzu dai yaa tafi ya d'aukoshi"

 "Wlhy naso aje tarbansu dani, anma dai duk jikina ba dad'i nakeji"

    "Ayyah! Aikam yaronnan yazo duniya fad'a zanyi dashi tunda yana takura Auntyna"

  "tohh bara Abbanshi yazo in fad'a mishi" tana dariya ta k'arasa shiga kitchen d'in, "ba ruwana fa wasa nake" itama Husna dariyan take. Ta shige kitchen ta fara aiki, ba wani mai yawa bane, kafin a kira Sallah taa kammala komai, ta wuce d'akin da Husna ta nuna mata ta zauna.


  Kamar ba abunda ya faru, Momie ta tarbi su Yasseer hannu biyu sai nan-nan take dasu, Rabi'ah sai wannan shisshigema Momie take ita mai suruku, sunje bud'a bakima a kusa da ita ta zauna sai fira take mata kamar ba surukarta ba ko er kunyarnan babu. Shidai Yasseer sai d'ari-d'ari yake don yasan ya b'ata ma Momie rai da yawa, sai da ta koma d'akinta yaje ya sameta jikinshi a sanyaye, ya d'uka saman gwiwoyinshi kamar zaiyi kuka.

   "Na sani ni mai laifi ne, kuyi hak'uri Momie hakan bazata sake faruwa ba, don Allah karkiyi fushi da d'anki"

  "Kaga alaman ina Fushi dakai? Damuwata na rashin zuwanka gidane daman, tunda na ganka kuma sai hankalina ya kwanta, ai babu wata uwa dake fushi da d'anta" rarrafawa yayi kusa da ita cikin farin ciki ya kwantar da kanshi saman cinyarta, "Hakan bazata k'ara faruwa ba insha Allah, nagode Momie" murmushi tayi tana shafar kanshi kamar k'aramin yaro. Magana takeson mishi akan jikokinta da bataga alamansu ba, anma taa rasa ta inda zata fara mishi.

  Rabi'ah ce ta shigo d'akin,

   "Momie ya zaki barshi kamar k'aramun yaro? Kaifa nake jira hniee"

  "Ki barni inji d'umin mahaifiyatah mana, yaushe rabon da in ganta?"

  "Oh! Tohm ai bakai kad'ai keda ita ba, nima Momien tawace" ta k'arasa shigowa d'akin itama zata kwanta cinyar Momie tana musu dariya tace "Maza dai ku k'arasa er tsohuwar tun kafin jikokina suzo", cak Rabi'ah ta tsaya duk ta b'ata rai, ta d'auka wayarta dake gefen Gadon Momie.

  "Yanzu zan wuce gida Momie, sai Allah ya kaimu"

 Baki bud'e Momie ta bita da Kallo, "Allah ya kaimu" Yasseer ya mik'e da sauri, "Bara inje in kaita Momie" sai kuma ya lura da yanayin da take ciki.

  "nima haka nake fama da ita Momie duk sanda na mata maganar haihuwa" kad'a kai kawai Momie tayi, har suka tafi.


 A tsakiyar falo suka had'u da Najib ya sab'a Hafsat a kafad'arshi, 

  "broda sai ina?" ya juyo muryar Yasseer ya tsaya sannan ya juyo, "Gidan Husna zanje"

  "Daa kuwa aron Motarka nakeso zankai Rabi'ah gida"

    "tohh ai sai in d'auka wata" yana zaro mishi mukullan a aljihu, ya saka hannu ya shafi fuskar Hafsat.

  "Ina kuma ka samu kyakkyawar babynnan?" da sauri ta fizge fuskarta daga hannun Yasseer,

  Murmushi yayi da wasa Najib yace "Tawah ce".

  "aifa da shekarun da nayi bananan sunkai shekarunta a duniya, tohm bazanyi tantama ba don kuwa komai naka ta d'auko" inji Yasseer

  Najib yace "haka aketa cewa yanayinmu d'aya, shiyasa nakeji da d'iyar Momien nan, Hafsat bazaki gaida Uncle ba?"

  Zumb'ura baki tayi ta kauda fuska gefe kamar ta sanshi, "Sunan Momie kuma kuke kiranta dashi ko sayawa bakuyi?"

  "ai Momie ta hana a b'oye sunan"

  "Mai kyau da ita, Inama kuka samota?" Najib ya bud'a baki zai bashi amsa suka jiyo muryan Rabi'ah, "Hniee kaifa nake jira" ya juya zai tafi kuma ya dawo ya mik'a mata hannu.

  "Hafsat zaki rakani?" mak'ale kafad'a tayi, Najib yace "anma dai nayi Mamaki, Hafsat bata tab'a yima wani haka ba, akwaita da sakin jiki da Mutane"

  "aini bak'one a gareta, zamu saba ko Hafsat? Hakanan ina son yarinyar sosae"

   "ai haka take da saurin shiga rai" ya juya ya tafi. Shima wasu mukullan ya d'auko sannan suka fito, cikin irin fushinta na yara ta cema Najib, "ka fad'a mishi karya k'ara tab'ani"

 Cikin mamaki yace "Sabodame Hafsat?" shiru ta mishi, har sukaje gidan yanata tambayarta tak'i ta amsa, ya k'yaleta kawai sannan ta saki jikinta. Can ta wuce cikin gidan wurinsu Husna da yake ta saba dasu sosae, har so suke tazo musu yini, Masoyan biyu kuma suna can waje ta musu shimfid'a suna fira.


  Sai da dare yayi sosai basuma sani ba, har Hafsat tayi barci, sannan sukai sallama zai tafi ya ciro sabuwar waya a kwalinta ya mik'a mata, ta amsa tana murna ta bud'a, Iphone7 ce komai irin tashi, sai murna take.

  "ni banmasan ta inda zan fara nuna maka farin cikina ba, babu abinda zan biyaka dashi da soyayyar da kake nunamin"

    "ai kin riga da kin gamamin komai tunda kika mallakamun soyayyarki, kici gaba damun Addu'ah karna rasaki Saudat"

  "bazaka rasani ba, ka kwantar da hankalinka Saudat takace"

  "zai kwanta dai, anma sai sanda kika k'arasa zama tawa d'in" murmushi tayi, "ka d'aukama na zama" ta ciro wayan daga kwalinta, a kunne take da simcard d'inta,

   "Allah yasa dai ka faramun saving numberka, don ita zan fara sakawa"

  "Abunda na fara yi kenan ranki shi dad'e"

  "gaskia nagode sosai dear" harararta yayi cikin wasa, ta rufe bakinta da hannu, "Sorry na daina, wallahi dad'ine har yamun yawa"

  "Kin rik'eni da yawa, so kike Momie tace nayi dare gobe ta hanani fitowa?"

 Yanda yayi maganar saida ta bata dariya sosae "Momie bazata hanaka ba" ta gano Camera a wayanta.

   "first selfie?" ta kanne mishi ido, ta matsa inda yake ya duk'o zasu d'auka hotan, ya d'aura yatsanshi d'aya saman yatsanta mai d'aukan hotan, sannan suka d'auka a tare su duka suna dariya.

  

 Sunyi kyau su dukansu, nan take ta mayar dashi wallpaper, "Haka zaiyi zamanshi" shima a wallpaper d'inshi ya maidashi, sunyi kyau sosae, ba don sunso ba sukai bankwana, sai da ta daina ganinshi, ita kuma ta shige gida tana nunama Husna wayanta.

  Yana mik'a Hafsat wurin mai kula da ita, kai tsaye d'akinshi ya wuce don yasan Momie tayi barci yanzu, Yasseer harya kwanta, da yake daman d'akin nasu ne su biyu

   "Big bruz harka dawo?"

  "Kasan kuwa lokaci yanzu?"

    "anma dai tashi zakayi ka bani labari, yau babu barci"

  Girgiza kai Yasseer yayi, "So nake in kwanta da wuri, gobe da safe akwai inda nakeson zuwa"

   "Haba bruz daga dawowanka? Ina zakaje kuma?"

  "K'yauyen da Naje Bautan K'asa, akwai abinda na barone mai matuk'ar mahimmanci da nakeso inje in duba, abun yana raina bazan iya k'ara lokaci banje ganinshi ba"

  "Tohh ka bari ka k'ara hutawa zuwa jibi sai muje tare, anma yanzu ga azumi ga gajia"

  "jibi daren Sallah kenan mu dawo ranar sallah? Ba komai fa kasha zamanka, namafiso inje ni kad'ai, kai dai kamun addu'ah Allah ya bani sa'ar abinda zanje nema"

   "Ameen d'an uwah, Momie dai taa barka ko?" cikin wasa yace "ai aikin lallashin ta barni zuwa nayi tun dawowatah daga gidansu Rabiah" dariya sukayi,

   "Yaka baro Saudat d'in?" Yasseer ya tambayeshi

 "ya akai kasan wurinta naje?"

 "Momie ta fad'amun mana, ko wacce mai sa'ah ce ta iya samun zuciyar little bruz har haka?"

  "Saika ganta zakasan nima mai sa'ahne sosae dana sameta"

  "kana sonta da yawa gaskia"

  "sosai kuwa bruz, ina sonta fiye da rayuwatah"

  "gaskia naso ganin wannan Saudat d'in taka, da alama Momie ma tana ji da ita, anma ai zanje ganin Husna"

  "yanzu ma bara in nuna maka hotunanta"

  "karfa in ganta tafi kyau a hoto akan zahiri" 

  Dariya yayi "Saudat ganinta ai yafi jinta" 

  Folder da yake ajje hotunanta ya shiga, sannan ya mik'a mishi wayar bayan ya gano mishi hotunanta.


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

       64


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


Ta ina zan fara? Ban sani ba sis domin kuwa kalmomi sunyi kad'an su bayyana mahimmancinki a wurina, ko yaushe kina bani k'warin gwiwa, nasan godia tayi kad'an a tsakaninmu, sai dai addu'ah Allah ya bar zumunci, wannan shafin nakine Sis ```waliyya wally```


www.babymsh.blogspot.com


  Yasseer ya mik'a hannu zai amsa wayan kenan kiran Saude ya shigo a wayan Najib, murmushi yayi,

  "Halan ita ke maka waya?"

    "itace fa, Bara inje in amsa"

 "ai naga alama kam tunda kake murna, wani lokacin naga hotan"

  "tohm shknan bruz"

 Falo Najib ya koma ya amsa kiran Saude, kusan raba dare sukai suna waya, lokacinda ya koma d'aki Yasseer har yayi barci, tunda safe kuma ya wuce k'yauyensu Saude.

  Tafiya mai nisa sosae yayi kafin ya isa k'yauyen, yasha bak'ar wahala sosai ga gajia da zaman mota, dak'yar ya iya gano gidansu Saude inda su kawu Ado suke, a waje ya tsaya aka mishi sallama dashi.

 Saiga Kawu ya fito yana washe baki, da sauri ya koma kawo mishi tabarma a soro ya shimfid'a mishi, sannan suka gaisa.

  "Sannu fa da zuwa Yaro"

    "Yauwah baba, baka ganeni ba ko?"

  "eeh tohh gaskia bangane ba"

 "Yasseer ne mijin Saude" ya fad'a yana sunne kai. Nan take Kawu Ado ya d'aure fuska.

  "toh toh, toh naji sai akai yaya?"

  "daman zuwa nayi inji kota dawo ko kuma an samu labarin inda take"

  "babu abunda ya shafemu da Saude da labarinta, tunda muka baka aurenta muka gama fita sha'aninta, yanzu wama yasan inda take? Oho! K'ilama tana can yawon karuwanci, ko kuma namun daji sun cinye namanta!"

  Cikin k'ara Yasseer yayi magana har saida ya tsorata kawu, "na rok'eka kawu karka danganta Saude da wannan maganganun naka"

  Kallonshi kawu yayi yana tab'e fuska, "da rayuwar Saude, da mutuwarta bata da wani banbanci a wurinmu, karka k'ara zo mana da maganar Saude, bamusan inda take ba, itama in tana da sauran hankali bazata nememu ba, don bazamu tab'a sonta ba"

  "zan koma, anma don Allah idanta dawo a sanar dani"

  Juya mishi baya kawu yayi bai k'ara cewa komi ba, ya zaro kud'i Aljihunshi masu yawa ya mik'a mishi, hannu ya zuro ya warce kamar yana tsoran karya maida, haka ko godia bai mishi ba harya tafi.


  En k'auyen ya shiga tambaga ko akwai wanda yasan inda Saude take, anma babu wani labari mai dad'i, gashi baba Haja bata cika zama k'yauyen ba daman babu wanda yasan takai Saude birni, har dare yana yawo k'auyen babu wani nasara.

  Duk ya gaji ga yunwa da kishirwa, sai da duhu yayi sannan ya hak'ura ya koma cikin gari, wani d'an k'aramin hotel ya kama ya kwana, washe gari ma ya koma k'auyen, babu dai labarin Saude haka ya hak'ura ya koma Abuja.


 Cikin wani irin yanayi ya isa gidansu, d'aga k'afa kawai yake anma baisan inda yake sakata ba, cikin sa'a babu kowa a falon, kai tsaye d'akinsu kawai ya wuce, kamar yanda ya zata Najib bainan, ya fad'a saman gado kawai dafe da kanshi. Momie taji shigowarshi anma shiru bata ganshi ba, duk ta damu ta ganshi daman, kuma tunda taji shiru tasan ba lafiya ba, ta tashi ta nufi d'akin nasu.

  Yana zaune ya had'a kai da gwiwa, sautin shesshek'ar kukanshi ne kawai ke tashi, ta tsaya bak'in k'ofa tana kallonshi cikin mamaki da tashin hankali, kuka yake sosae yana dukan kanshi kamar wanda yaji sak'on mutuwa, a rikice Momie ta k'arasa shiga falon ta rirrik'e mishi hannuwa.

  "ki barni Momie, ki barni don Allah in hukunta kaina akan laifin dana aikata da har yanzu nake biyan bashinshi, qila hakan zaisa na rage zugin da zuciyatah kemun, Momie na aikata laifi, wallahi na aikata babban laifi a rayuwatah" ya k'arasa maganar yana fashewa da wani kukan.

  "Subhanallahi! Yasseer wane irin laifi ne wannan dake ma farin cikinka katsalandan? Fad'amun wanne irin laifi ne wannan da har ya sakaka zubda hawaye haka"

  "Bazan iya ba Momie, lokaci ya riga ya k'uremun, yanzu fad'a mikin baida wani amfani"

  "nifa mahaifiyarka ce, kana da wacce ta fini ne?"

  "babu Momie, shiyasa nakeso ki tayani da addu'ah, don Allah karki matsa saikinsan abunda ke damuna"

  "tohh shikenan, Allah ya yaye maka"

  "Ameen Momie, kaina ciwo yakemun sosai, jikina ko ina zafi, na rasa inda zan saka raina"

  "ka sauk'ak'a zuciyarka Yasseer, komai yayi zafi, ka dage da Addu'ah, bara inma Najib waya yazo muje Asibiti"

  "A'ah zanji sauk'i Insha Allah Momie basai munje ba"

  "Tohh kasha magani dai, saika kwanta ka huta, zuwa anjima in bai bari ba sai muje asibitin"

  "tohm Momie" dak'yar yake magana, hawaye kawai ke fita a fuskarshi, saida ta tabbatar ta d'an kwantar mishi da hankali sannan ta fita ta barshi.


  Tana fitowa saiga Najib da Saudat sun shigo, sun dawo daga wurin k'unshi da gyaran gashi, ta taresu tanama Saude sannu da zuwa, har k'asa ta gaishe da Momie.

  "Ya gajiyan hidima, ya Auntynki?"

  "lafiya lau take, tace a gaisheku" taci gaba da wasa da yatsunta su duka sunyi shiru, sai Najib ne ya fad'ama "wai sannu da zuwa mukazo tayima bruz, munyi waya dashi yace yana hanya"

  "Ayyah! Aikam bai dad'e da dawowa ba, baijin dad'i ya d'an kwanta ya huta"

  "Allah sarki, Allah ya sauwak'e"

   "Ameen"

  Tsarabar Husna ta had'a mata, da kuma nata duk da bada sunanta aka siyo ba, tayi godia sosae, basu dad'e ba suka tafi don zata fara aiki, gashi daren Sallah, Momie tana ta sa mata albarka.

  Suna fita Yasseer ya fito da shirin zuwa Masallaci, jikinshi duk ba k'wari daka ganshi yana cikin damuwa.


Bayan Sallah da kwana biyu, Yasseer da Rabiah sukaje gidan Husna bankwana sun kusa komawa, tunda yazo bai ganta ba ko sallah bata iya zuwa gida ba, kamar tayi me don murna da ganinshi.

  Saude na kitchen ita da Najib, don har gidan Husna ma ko yaushe suna tare, cewa yake bai damu gidan k'anwarshi bane, ko ina yake Saudat kawai yake gani, kuma bazaiso tasha wahala ba.

  Yana jinsu ya fita falon, suka fara mishi tsiyar yanzu har aiki yakema Husna kawai don Saude na gidan.

  "ai ba don ita nake ba, Saudat nake tayawa, idan kuma aka matsa in d'auke matata mu tafi"

  Rabi'ah tace "lallai mai Matah"

  "eeh Aunty MATATAH CE Saudat, laifine don na fad'i?"

  "A'ah mamakin yanda so ya canjaka nake, kamar ba Yaya Najib d'in da ko Motsa baki wahala yake mishi ba"

  "Da kenan Matar Yayanmu"

  Husna tace "Ai kad'an kikaji indai labarin soyayyar Najib da Saudat ne"

  Yasseer na gefe sai faman duba Agogo yake, ta rik'o hannunshi, "badai tafiya ba?" ya d'aga mata kai, "kinsan dai sauri nake" a gabansu ta marairaice fuska kamar zata fad'a mishi, "nidai ka bari muyi yinin tare, saimu tafi" 

 "Zan dawo d'aukarki, nima ban gama gaisawa da sista ba"


 Husna tace "Munata fira ma Yayanmu ko ruwa bakasha ba, bara a kawo muku" ta k'wala ma Saude kira, "Aunty Saudat, a kawoma su Yayanmu drinks" Najib ya mik'e, "yanzu wannan d'inma ita zaki saka?"

   "Nikam dai Allah ya bani lafiya in huta da fad'a, ni don su gaisa da Yayan ma nasan itama har yau basu had'u ba"

  A hanyar fitowa suka had'u da Saude, ya ansa na hannunta sannan ya juya yakai musu, ruwan roba kawai Yasseer ya d'auka, "ba'a k'inshan ruwan zumunci anma a k'oshe nake"

  "Ai nasan Auntyna bata wasa da bama Yayana Abinci"

  "kamar tafiya zakayi, ka jira Saudat tazo ku gaisa plz"

 "Sauri nake, idanna dawo ma gaisa" suka fita da Najib ya rakashi, yana fita Saudat ta fito da kulolin Abinci.


Inayin read more d'aya, kukace yayi kad'an na koma biyu, shima wai yayi kad'an😭

Wani lokacin har uku nakeyi anma akwai masu cewa yayi kad'an, don Allah kuna yimun Uzuri, kullum fa nake postn, abubuwa da yawa nake bari in muku typin, don Allah kuna hak'uri da wanda ya samu👏🏻


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

      65


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


  Saudat ta gama jere ma Rabi'ah kayan ciye-ciye, Husna sai sannu take mata, sai gata ta dawo daga rakiyan Yasseer.

  "Sannunku da zuwa Aunty Rabi'ah" kallonta ta ɗanyi.

  "Saudat ko?" ta ɗaga mata kai tana murmushi, "Sannunki kinsha aiki, ya gajia?"

  "ai ba wani aiki bane"

Taje zata kama Husna dake k'ok'arin tashi dak'yar, "Sannu Aunty"

  "Yauwah Aunty Saudat"

 Rabi'ah tace "waih! Sannu kinji, gaskia kina k'ok'ari"

  "ai saima yazo kanki zaki sani" inji Husna.

  "ni? Allah ya rufamun asiri, wahalan ɗaukan ciki, haihuwa ga raino mutum ya tsofe tunda wuri"

  "Miye abun rufin Asiri? Kardai kicemun har yanzu kina da wannan Ra'ayin naki tun muna ckul, wollah garama ki canja kin sanmu dangin miji dai"

   "akwai hanyar samun yara da yawa ko ban haihu ba, yanzu dai a barni in gama cin amarcina dan Allah ki dainamun maganarnan kina kadamun gaba"

  "Baki ma da hankali wallahi, wannan ba tunani mai kyau bane, inma bazaki haifa mana ba zamu auro mai haifa mana"


 Filon kujera ta ɗauka ta jefa mata, "bakinki ya faɗama mak'iyanki, kinsan Allah ko wata naji anyi ma kishia zuciyatah tafasa take" Husna daria kawai take mata, ta k'ara ɗaure fuska, "Allah wannan ba abun dariya bane" bata saurareta ba, dariyarta kawai taci gaba dayi, yanda takeyi dariya take bata sosae.

  Da yake Saude da Najib suna waje, Rabiah da ɗan rage murya, "wai da gaske wannan ce Saudat ɗin Najib?"

  "itace mana"

 "daga ina ya samota?"

   "ɗiyar Momie ce, daga k'auye tazo"

  "lallai kice kyawawan en matah na k'auye, na birni kwalliya da wayewa zasu nuna musu kawai"

  "eeh mana, Yayanmu ma a can zamu samo mishi ta biyu"

  "Allah idan bazaki dainamun maganarnan ba yanzu zanbar miki gidanki"

 Ta rufe baki tana dariya, "yi hak'uri matar babban yaya, na daina"

  "karma ki daina ɗin"


 A gidan Husna Rabi'ah ta yini har dare, sai fira suke da Saudat kamar wanda suka saba, da yake taji ita Najib zai aura kuma dai yanzu bazata nuna mata wayewa ba, har abincikan data girka ta nemi ta koya mata, taji sun mata daɗi sosae, nan ta koya mata harma da wanda bata nema ba.

  Dare ya fara nisa Yasseer yazo ɗaukan Rabi'ah, bai shiga ciki ba yayi parking wajen gidan sannan ya mata waya ta fito, yana zaman jiranta a mota cikin duhun daren Saudat tazo wucewa, cikin tafiyarta ta nutsuwa a hankali take saka k'afafunta, ta amso ma Husna sak'o mak'waftansu.

  Hakanan yaji yanason ganin fuskar kowacece, ya bita da kallo cikin duhun darennan har lek'enta yake gashi ta juya baya, Rabi'ah na tsaye ta fito ga mota a kulle, sai k'wank'wasawa take baimasan da ita a wurin ba, gaba ɗaya taa gama k'ulewa. Saida ta dawo ta gabanshi sannan ya lura ya buɗe mata.

 A harzuk'e ta shiga ta zauna sai maida numfashi take, juyawa tayi ta fara dukan k'irjinshi, "matah kake kallo ko, bakama lura ina tsaye ba" rik'e hannuwanta yayi sai k'ok'arin k'wacewa take.

  "Waya faɗa miki mata nake kallo? Nifa ginin unguwarne suka burgeni, nake tunanin ko nan zamu gina gida idan mun dawo?"

 "mak'aryaci, wallahi saika faɗamun ko wacece kake kallo"

   "wa kikaga ina kallo nifa banmasan da wata mace a wurin ba" 

  "k'arya kake" ta k'wace hannuwanta taci gaba da dukanshi, duk ta hargitsa mishi tunani cikin motar dak'yar ya iya rik'eta, gam ya haɗata da k'irjinshi yana sumbatarta, bai saketa ba saida ta nutsu sannan, saida ta k'ara kai mishi duka a k'irji tana harara sannan ta gyara zama tana maida numfashi.


  Kwana ɗaya suka k'ara, suka ɗaga moscow bayan Momie ta mishi gargaɗin ya daina daɗewa bai dawo ba, 

  Ranar da suka tafi, da yamma a ranar Husna ta haifi jaririyarta mace, ba k'aramin murna sukai da zuwanta ba, sai Saudat hidima ta k'aru, har ranar suna itace mai hidima da bak'i ko kaɗan bata nuna gajiyawarta, yarinya taci suna Maheera, kamar Najib na jira, washe garin suna yazo ya koma da ita, aka samo mata mai kula da ita da jaririn.

  Ranar Monday ta koma makaranta SS1, gaba ɗaya hankalinta ta maidashi akan karatunta, soyayyarta da zuciyarta kuma duk ta mik'asu wurin Najib.


A moscow, tun komawar Yasseer abubuwa suka dawo mishi sabo, gaba ɗaya yanzu addu'anshi daya ɗaga hannu Allah ya nuna mishi Saude, yasan yaa cutar da rayuwarta kullum cikin nadama yake, so yake su haɗu kota yafe mishi laifin daya mata, gaba ɗaya ko wurin aiki baida sukunin yin komai, a gida ma yafison ya zauna shi kaɗai yana tunanin rayuwarsu ta baya, tohh idan Saude bata k'auyensu tana ina? Kullum tambayar da yake ma kanshi kenan.

  Rabi'ah ta shigo ɗakin da wata irin shiga mai jan hankali, a kusa dashi tayima kanta masauki, ta saka hannu ta shafi fuskarshi cikin shauk'i.

  "Yauma tunanin kake? Banson ganinka cikin damuwa, kuma kak'i faɗamun damuwarka"

  "Rabi'ah plz, inason hutu" ya faɗa idanunshi a rufe da alama damuwan ta fara fin k'arfinshi.

  "Yaushene ka fara korata a ɗakinka? Nifa damuwarka kawai na tambaya, ka faɗamin ko miye saimu zauna mu tattauna"

  "babu abunda ke damuna, don Allah ki k'yaleni hakanan"

  "bazan tafi ba, saika...."

 Wani irin tsawa ya daka mata, "kece damuwatah! Ki fita na..." yanda ta zabura ya sanyashi shiru duk baiji daɗi ba, gaba ɗaya tunanin Saude ya fara zautashi.

  Hannuwanta ya kamo ya rik'e, "don Allah Rabi'ah, ina cikin damuwa ki barni in samu kaɗaicewa kona ɗan lokaci ne" duka takai mishi, sannan ta mik'e ta fice daga ɗakin, binta yayi da kallo, ita dai dukan miji bai mata wahala, daya ɓata mata rai sai duka, Allah sarki Saude da ko magana yake mata kanta na a k'asa take saurarenshi.


  Su Saude suna samun hutu Momie ta fidda ranar zuwa k'auyensu, Najib kamar ya jawo ranar yakeji, gani yake kamar anma riga da an bashi Sauden.

  Daren ranar suna zaune a falo kamar kullum suna fira, kallon Ball yake taa biye mishi itama tana tayashi, gaba ɗaya hankalinshi na wurin.

  "wai nida ball ɗinnan waka fiso?"

 Aje remote yayi ya maida hankalinshi kanta, "karki k'ara haɗamun soyayyatah da wani abu, nafi sonki fiye da yanda nakeson kaina ma"

   "luv uh as much dear, in hakane meyasa ka k'yaleni"

  "farin ciki nakeji Saudat, wanda ban taɓayi ba, gobe zamuje k'auyenku kawu ya bani aurenki, idan harya bani ke babu sauran abunda zai min shamaki da mallakarki"

  "ka ɗauka ma ya baka fa"

  

  Fargaba ce kawai a ran Saude daren ranar, batasan yanda kawu zai amsa maganarta da Najib ba, tasan ya tsaneta komai zai iyayi don ya k'untata mata, kuskurenta tun farko data faɗa mishi Yasseer bai saketa ba ya gudu.

  Ranar batayi barcin kirki ba, cike take da fargabar yanda gobe zatazo mata. Barci bai daɗe da ɗaukarta ba aka kira Sallah, a kasalance ta tashi tayi Sallah, ta jawo Qur'an ɗinta ta fara karatu, tana gamawa dai Addu'anta kawai Allah yasa komai yazo musu da sauk'i wurin kawu.

  Bata samu komawa barci ba, Momie ta aiko mata ta fito idan taa shirya don safko zasuyi, Najib ne zai kaisu ita da Momie, da wuri suka kama hanya zuwa k'auyensu Saude.


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

       66


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


  A baya Saude ta zauna, ta koma can gefe ta rakuɓe tanata zullumi a ranta, yana drivin yana hangenta ta mirrow, k'arar shigowan message taji a wayanta, ta duba daga Najib ne.

    "Ya dai?" kallonshi tayi ta mirrow, ya ɗaga mata gira yana murmushi.

  "Meka gani?" ta mayar mishi.

 "Kinyi shiru kamar kina da damuwa, ko duk kunyar Momie ne?"

  Sai data murmusa data gama karantawa, sai ga wani text ɗin nashi ya k'ara shigowa, "wannan fuskar nakeson gani har muje, murmushi yafi miki kyau" dariya tayi kawai ta tsura mishi ido ta mirrow shima tana kallonshi, duk Momie na lura dasu, ciki-ciki take musu dariya.

 Mik'a hannu tayi ta anshe wayar tashi, "kana wannan gudun kuma bazaka maida hankali a tuk'i ba" da sauri yabi hannunta zai ansa wayan, 

 "plz momie ba wani abu nake ba, lokaci nake dubawa" 

  "kana duba na motan tohh"

 Ta cikin mirrow ta mishi gwalo tana dariya, ya harareta da wasa, bata daina mishi dariyar ba.


 Kwata-kwata ta manta da Momie a wurin, ta kwanto jikin kujerar da yake, suna kallon juna ta cikin mudubin kowanne ya kasa ɗauke idonshi, sak'on soyayyar da suka kasa furtawa a baki saboda Momie na wurin ne suke aika ma juna ta kallo.

  Garin kallo sunje shiga wani gari, bai lura da bump ba ya faɗa mishi kawai, su duka saida suka razane banda Momie da daman tana sane dashi, ta wutsiyar ido yake kallonta, saida taga abun nasu bamai k'arewa bane, ta saka hannu ta juya mirrow ɗin, su duka har saurin kai hannu suke su gyara, saida Saude ta lura Momie ce ta koma a kunyace ta zauna.

  Saida suka isa garin Katsina suka tsaya sukayi Sallah, wani restaurant sukaje sukaci suka k'oshi, sannan suka kama hanyar k'auyensu Saude.

  

 Da yake akwai nisa daga katsinarma, saida suka k'arayin tafiya mai nisa sannan suka isa k'auyen, Najib dai bin k'auyukan wurin kawai yake da kallo, wai anan Saude tayi rayuwa, nan wurin har akwai halittar dake rayuwa.

  Itama bin k'auyen kawai take da kallo, tayi kewarshi da yawa, shekara ɗaya da en watanni ko zagayoshi bata k'arayi ba, ba laifi k'auyensu an samu en canje-canje, anma bazata iya mantawa da k'auyenba, kai tsaye take nuna mishi hanyan gidan Kawu duk da k'auyen ba yawane dashi ba. Yananan inda yake, sai dai yaa k'ara lalacewa, ginin jar k'asar duk ya zaganye sai tsummuna ne aka ɗaure akayi kamar katangar dasu, suma duk sun ciccire, wurin dai babu kyaun gani, cikin zuciyarta tayi mutuk'ar tausaya musu, 

  Momie tace ta shiga ta fara sanar musu zuwansu,ta buɗa motan ta fita, tana k'ara k'arema wurin kallo.


 Cikin gidanma duk ya lalace, k'asan tayi gamsa kuka da ciyayi ko ina, ɗaki ɗaya tal ya rage a gidan, shima rufin duk ya zazzare, tana daga bakin ƙofa sai rangaɗa sallama take babu alamun kowa a gidan, harta fara gajia, saiga Gwaggo ta fito daga bayan gida, can gefen ɗakin aka zagaye wani wuri shima da tsummokara, tana ganin Saude ta washe baki.

  "A'a'aah sannu da zuwa, sannu da zuwa" duk ta rasa inda zata sakata don murna, don ko kaɗan bata ganeta ba.

 Can gefe ta tillar da gwangwanin ruwan hannunta, ta shiga ɗaki ta ɗauko tabarma da tsintsiya, ta share wuri sannan ta shimfiɗa mata tabarmar ta zauna, ita dai Saude sai binta da murmushi take ganin yanda take ta zakwaɗi tasan lalle gwaggo bata gane ta ba.

  "daga ina? Halan bak'in gidan mai gari ne? Sannu fa kunsha hanya"

  "A'ah nan gidan nazo gwaggo"

  "Gwaggo kuma? Kai gaskia badai ni ba, bansan kowa a birni ba, ki dai tuna gidan da kike nema"

  "Gidan da nake nema nazo Gwaggo bilki, gidan Kawo Ado"

 "eeh gaskia gidanne kikazo" gwaggo ta faɗa cikin sanyin jiki tana ja da baya, "Allah yasa dai ba wani abunne kikazo dashi ba baiwar Allah"

  "ki kwantar da hankalinki Gwaggo, Alkhari kawai nazo dashi"

 "tohh wacece ke?"


 Kawu Ado ne ya shigo gidan har yana tuntuɓe, yake k'walama gwaggo kira, burki yaja a tsakar gidan ganinta da bak'uwar fuska. Shima dai washe bakin yayi suka gaisa da ita, sannan yaja gwaggo can gefe.

  "Ina Mak'era aka faɗamun bak'i sun tsaya da k'atuwar mota k'ofar gidannan, nama ɗauka matsiyacin yaronnan ne"

 "bashi bane, bak'uwa ce dai mukayi daga birni"

 "gidan mai gari tazo ko gidan sarkin noma?"

  "gidannan tace tana nema, anma dai bata faɗi daga inda tazo ba"

  "tohh fa, Allah yasa ba sace mana kawuna tazo cikin k'atuwar motarnan ba"

  Suka jiyo su duka sunason tambayarta, su duka sun k'ara tsufa, kawu Ado duk gashin jikinshi ya cika da furfura.

  "baiwar Allah daga ina? Kuma wa kikazo nema?" kawu Ado ya mata tambayar.

 Tana murmushi tace, "Kawu daman Saude...."


  "Sauden K'aniya, idan ma nemanta kikazo kinzo gidan da bazaki dace bane, tunda tsohin mijinta ya gudu ya barta itama ta gama gabanta, tun kafin magana tayi nisa tsakaninmu kibar gidannan kije can kici gaba da dubata gidan karuwai"

  Rumtse idonta tayi sosai maganar ta soketa

 Gwaggo ta tari numfashinshi, "Malam anyi haka?"

 Idonta a rufe, tanajin k'una a zuciyarta tace "Sauden ce kawu"

  "Saude?" suka maimaita a tare, ta ɗaga musu kai, kunya saita kama kawu ya fara kame-kame.

  "Saude kece kika zama haka? Kin tafi birni kin manta damu, munanan muna ta addu'ah Allah ya kawoki, yasa kina cikin k'oshin lafiya, ko bilki?"

  "eeh eeh mana"

   "Alhmdlh Saude ina kika shige haka? Don bamu muka haifeki ba shikenan kika manta damu, anma dai aimu muka rik'eki har girmanki"

  "eeh mana, baki kyautaba Saude kinbar iyayenki cikin fargaba, ni banmasan ta inda zan fara bayyana farin cikin dana shiga da ganinki ba" kawu ya k'arasa maganar yana sharar k'walla.

  "kuyi hak'uri kawu, nima kuna raina"

  Nan fa suka sanyata gaba, ganin yanda ta koma lallai tayi kuɗi tana cikin jin daɗi, sunma rasa inda zasu sakata.


Saida taga sun ɗan natsa, tace "bani kaɗai nazo ba, harda hajiar da nake gidanta, da kuma ɗanta, kuma dai da maganar da sukazo da ita"

  "tare kukazo kuma bazaki shigo dasu ba? Kai Saude kinanan dai da halinki na kawaici" kawu ya faɗa, harda dariya shinan ya faɗa abun kirki.

  "tohm malam a shigo dasu bara a musu shinfiɗa"

  Gwaggo ta kwaso wasu tabarmun ta shimfiɗa musu kafin ya shigo dasu, su Kawo har kyarmar jiki ake, da hannu bibbiyu suka tarbesu, aka shimfiɗesu saman tabarma.


 Gwaggi da kanta ta saka mayafi, bashin ruwan laida mai sanyi an sakashi a randa ta anso musu, ta kawo sannan suka shiga gaisawa, en k'auyen har an fara cika gidan suna murna Saude ta dawo, ta canja ta zama er gayu. Bata k'yamacesu ba ko kaɗan, ta shiga cikinsu suna ta labari, har dare suna tare. Najib dai fita yayi ya basu wuri bayan sun gama gaisawa.

  Da yake dare yayi, kuma babu wurin da zasu kwanta a gidan, sai suka koma cikin gari babu nisa da k'auyen, a can suka samu hotel zasu kwana, banda Saude, cewa tayi a gidansu zata kwana.

 Gatan da bata taɓa tunanin samu ba su kawo suke nuna mata, don gaba ɗaya fita sukai daga ɗakin sukace ta kwanta ita zasu kwana a waje, tace su barta ta kwana inda ta saba anma sukak'i, duk yanda taso, anma a ɗakin dai suka bar mata ta kwana ita kaɗai.

 Su Momie sun tafi a zuwan sai gobe zasu dawo ayi magana.


  ©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

       67


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


  Kafinsu tashi barci, an gama haɗa musu break fast, daman da Momie zasu tafi sunsha rok'onsu su dawo nan su karya kumallo, sai gashi sun dawo tunda wuri, sabuwar tabarma aka shimfiɗama Momie ta zauna sannan aka jere mata kayan break fast kala-kala.

  Koko da k'osai, fura, ɗan wake, shinkafa da wake, alala, sabon tuwo, da shayi ruwan bunu (marar madara), Momie dai sai godiya take, "wannan kalaci duk mu kaɗai? Ai daa baku wahalar da kanku da yawa haka ba"

  Gwaggo tace "haba Hajia, ai babu komi, so muke kici ki k'oshi,"

  Ɗan waken kawai taci, don Momie akwai son ɗan wake, ta kora da ruwan koko ko kaɗan bata nuna musu k'yamata ba, zama tayi taci kamar yanda zataci a gidanta, Saude ta ɗauka na Najib ta tafi kai mishi yana cikin mota ya kasa shiga.


Ta ajje mishi, suna gama gaisawa ta tashi zata tafi, ya rik'o hannunta

  "wannan kayan break fast ɗin duk ni dawa?"

    "kai da cikinka mana"

  "wasa kike, sai dai ni dake"

    "nawa yana ciki fa yanzu zanje inyi"

  "A'ah wannan ya ishemu" ta mak'ale kafaɗa, "shikenan kwashesu ki koma dasu"

  "rigima ko?"

 Ya kashe mata ido, "mijinki na sonki kusa dashi ne"

  Jiranshi dai tayi harya gama, don a waje suka shimfiɗa tabarma, duk da ba mutane anma saita kasaci, shima Fura kawai yasha, qila itama don a gabanta ne, don gaba ɗaya tsantsamin kwanukan yake da ruwan garin, yana sha yanajin tashin zuciya dak'yar dai yasha da yawa.


 Tana maida kwanukan, ta kwashi tsarabar Hanne k'awarta ta fito, tare da Najib suka jera suka tafi shima yanaso yaga k'auyen. Nan su Gwaggo suka shiga rabon tsaraba suma, don daɗi bakunansu har kusa da kunne, wai yau sune suke fantamawa haka duk sanadin Saude da suka tsana.

  Suna tafiya tana mishi bayanin k'auyen, duk inda sukayi ana nuna su 'ga Saude can tazo da bak'on ɗan birni, Saude ce tazo daga birni taa waye, Saudece ta zama er gayu' kowah dai da abunda yake faɗa.

  "mutanen garinku fa ke kaɗai suke kallo"

  "A'ah ai kaine bak'o a wurinsu"

  Dai dai gidan da suka zauna ita da Yasseer ta tsaya tana kallo, bazata taɓa mantawa da gidan ba, abubuwa da yawa a gidan da bazata iya mantawa dasu ba.

  A gidanne aka fara ajjeta a matsayin amarya, a gidanne ta zama cikakkiyar mace, a gidanne ta samu farin cikin da bazata taɓa mantawa ba, a a gidanne ta samu bak'in cikin da har yanzu yakenan mak'ale a ranta, a gidan ta samu cikin Hafsat kuma anan ta haifeta, bazata taɓa mantawa da gidannan ba.

  Zagayowa yayi saitin fuskarta, ya ɗan kaɗa mata yatsunshi guda biyu, firgigit ta dawo daga dogon tunanin data tafi, "sau nawa zan faɗa miki banson ganin wannan fuskar a tare dake?"

  Murmushi tayi, "idan hakan ya maka mu tafi ko?"

  "Yayi anma saikin faɗamun nan inane?"

  Hawayen data daɗe tana maidawa ne suka fara kwararo mata, girgiza mata kai yayi, yasa hannu yana share mata hawayen, kama hannunta yayi sukabar wurin, 

  "ga gidan Hanne can"

    "tohm ki fito inanan ina jiranki, kuma bance kiyi sauri ba don kawai kin barni anan, zan jiraki ko yaushene"

 Murmushi tayi ta ansa ledar hannunshi. Hanne najin sallamarta da gudu ta fito ta tarbeta, har suna kusan faɗuwa.

  "sai yanzu zakizo tun jiya ake kawomun labarin Saude tazo garinnan"

 "kuma shine bakizo kin ganni ba? Wai jirama tukunna ya akai kika ganeni"

 "inafa na ganeki, yanda aketa kwatantamin kene dai"

 "wai kinga yanda kika koma kuwa? Lallai birni taa ansheki, wallahi Hajjaju komai naki ya canja fa" sai shafa jikin Saude take yanda yayi laushi tana ta surutu.

  "kemafa kin canja k'awatah, don dai bazan mantaki bane anma dak'yar na ganeki, kin zama wata babbar mace, haba duk ina gayun naki kike nema ki tsofe da wuri?"

  "Hmm Saude kenan" ta lura tana cikin matsala, kuma ita bamaison jin sirrin mata da miji bane, bazata manta taimakon da Hanne tayi mata ba, ta kawo tsarabarta ta bata, da kuɗi masu ɗan yawa tace tayi jari, godia sosai take mata har suka fito k'ofar gida.


 Wurare da yawa sukaje da Najib a k'auyen, daga k'arshe suka wuce rafi.

  "Gaskia yanayin garinnan naku da daɗi yake, bana gajia da shak'ar sanyayyar iskarnan"

  "saimu barka anan kayita zamanka ai"

  "bazan damu bafa, indai tare dake ne"

  "daman ai kawu yace indai zai baka aurena tohm sai dai mu zauna anan"

  "ke! A ina? Anma dai da wasa kike ko?"

 Babu alamun wasa a fuskanta tace "Da gaske nake mana"

  "abincin k'auyennan? In kwana cikin k'auye? Kawu ya taimakamun mana"

  Dariya tayi sosae, "Matsoraci, daman nasan duk faɗi ne kawai"

   "ba haka ba, nafison na ajeki inda zakiji daɗi ne"

  "daɗin baki ko?" ta faɗa tana dariya, sai dai taji tayi tuntuɓe har saida ta faɗa jikin Najib, da sauri ya rik'ota, ta dafe k'irjinta dake faɗuwa sannan ta tashi a jikinshi.

   Duk'awa yayi wurin k'afar tata, "Sannu, baki daiji ciwo ba ko?"

  "A'ah, bara dai a ɗauke dutsin saboda kar wani ya k'ara faɗuwa"

 Ta duk'a zata ɗauke, ya riga ya zauna wurin, kamar dutsin daya taɓa mata ciwo a k'afa sanda ta faɗo daga bishiya, da sauri ta ɗaga kanta sama, bishiyar mangwaronnan ce wacce ta faɗo daga samanta lokacin da zata ɗeboma su Kabiruwa.

  Juyawa tayi tana kallon Najib, ta k'ura mishi ido sosae ji take kamar Yasseer ne take gani, bazata manta da haɗuwarsu ta farko ba, duk abubuwan da suka faru jikin bishiyarne suke dawo mata a ranta.

  Gatanan Zaune lokacin da ake mata Kamu, tuna rik'on da Yasseer ya mata a lokacin tayi, saida duk tsikar jikinta ta tashi, gabanta ya faɗi taja wani ajiyar zuciya, maganarshi ce ta dawo mata a kunne kamar lokacin yake mata ita, lokacin data mishi godiyar taimakon daya mata.

  "ni nake da godia, da kika bani dama harna taimakeki, kuma na samu lada" 

  Najib ne ya hure mata ido, "kamar dai yau kika fara ganina" lumshe ido tayi, kamar dai Yasseer a haɗuwarsu ta farko.

  Tana murmushi mai ɗauke da damuwa ta kalla bishiyar, "wannan ne dalilin haɗuwatah da mijina na farko, ananne na ganshi, kayi hak'uri anma bazan iya tsaida tunaninshi ba duk sanda nazo wurinnan"

  "Shi kike tunani, anma ni kike gani domin nine a gabanki yanzu, bazan hanaki tunawa dashi ba, don nasan idan kika sake dawowa, nida shine zakina tunawa"

  Ɗaga mishi kai tayi, "Allah yaji k'anshi, yakai haske a kabarinshi"

  "Ameen ta amsa tana murmushi"


 Sai kusan Azahar suka koma gidan, Momie na jiransu har tayi shirin tafiya, yanayinta kawai suka gani gaba ɗaya hanjin cikinsu suka kaɗa, bama kamar Saude da gabanta ya fara faɗuwa, shikenan kawu ya gama tona mata asiri.

  Najib ne ke mata magana a ruɗe, "Meke faruwa Momie? Don Allah karkicemun zan rasa Saudat" ganin yanda duk suka tada hankalinsu, Momie ta kasa rik'e dariyarta, sannan suka sauke ajiyar zuciya.

  "mun gama magana, kawunka ya yarda zai baka auren Saude, da munje kawunanka zasu zo a saka rana, saura ka bani goran Albishir" kafin Momie ta rufe baki ya zaro komai na aljihunshi ya aje a gabanta, saida ya jiyo dariyarsu Kawu ne, ya fita daga gidan a kunyace, donshi baimasan suna wurin ba.

  A ranar sukai bankwana suka koma, duk kuɗinta da Najib ke bata harma da wanda Momie ke bata, bata kashewa ta damk'ama Kawu yayi gyaran gida, har mota ya bisu yana godia, harda en k'wallansu shida Gwaggo.

  Gaba ɗaya kuɗi sun rufe mishi ido, yama manta da wani auren Saude da Yasseer, don daman shi baida wani matsala da aurenta.


  ©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

       68


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


 Watansu shidda da komawa, suka fara zana s.s.c.e, daman tuni aka saka sunanta, sai karatu ya k'aru, kullum cikin karatu take fiye da lokacin data zana j.s.c.e, tun kafinta fara jarabawar Najib ya biya mata ta rubuta jamb.

  Karatun da take da maida hankalinta yasa komai yazo mata cikin sauk'i, babu abunda ya shige mata duhu.

  Ranar yayesu sunsha kuka, duk da bata da k'awa ɗaya anma duk ta shak'u dasu, tasha kyaututtuka ba kaɗan ba, duk da bata rik'e wani muk'ami ba, ita ta samu kyautan tsabta, kyautan biyayya, kyautan zuwa da wuri, wacce tafi kowa cin english, maths, har teacher n su mai physic da suka sanyama ido saboda mak'o saida ya mata kyauta, da aka fiddota speach yanda take zuba turanci ba k'aramin burge mutanen wurin tayi ba, en makarantarsu kamar su haɗiyeta don murna, ta samu kyautuka sosai wanda bata taɓa tunanin samu ba.


 Da dare kuma Najib ya haɗa mata nashi Partyn, duk wasu Abokanshi da yakeji dasu sun halarta a wurin, tun daga na Abuja har wanda suke aiki a Kaduna, itama ta gayyaci k'awayenta sosae har wanda bata tunani sunzo.

  Ba k'aramin haɗuwa Saude tayi a wurin ba, cikin doguwar rigarta fara tas mai kwalliyan duwatsu, duk inda ta saka k'afarta Najib na biyu da ita, sosai suka haske a wurin.

 A hankali tace mishi, "nafa lura duk en matan wurinnan kishi suke dani"

  "Saboda kinfiso kyau da iya kwalliya ba"

  Tayi dariya har hak'oranta suka fito, "Saboda ni nake da saurayin da yafi kowanne dai, kaga dole suyi kishi don nawa yafi nasu"

  "laah! Kin nusar dani ma shiyasa su Jabir keta binki da kallo ko, bakinsu ya kasa shiru sai yabawa suke da haɗuwarki, aikam partynnan an tashi hakanan"

  "Saboda me?"

    "Saboda ina matuk'ar kishinki mana, na gaji ana ganemun matah hakanan"

  "haba! Abokankane fa"

 "koda en gidanmu ne, bakisan yanda nakesonki da kishinki bane, komai zan iyayi idan wani ya raɓeki"

  Shiru tayi don yama rufe mata bakin magana, da yake da wuri aka fara Partyn dare baiyi wani nisa ba aka tashi, abokansu da yawa sunso yima Saude da Najib hotuna a wayansu, anma yak'i yarda, sukace ai indai sun dawo bazai hana suyi mata na biki ba.


  Saida aka tashi Ahmad yazo, duk Abokansu sun gama tafiya, tare suka fito da Saude tarbanshi, cikin girmamawa suka gaisa sannan tace,

   "mufa da har munyi fushi"

  "Haba Matar Aboki, keda nake cewa da zaki tayani ban hak'uri"

   "ai kamar nama fishi fushin fa"

  "tohh afuwan, wallahi abubuwa da yawa na bari na taho, don dai kawai bazan iya hak'urin nan da sati biyu biki ba sannan inga Saudat ɗinnan data sacemun abokina gaba ɗaya"

  Tayi dariya sosae "shiɗinne ma na sace duka ba zuciyarshi ba kenan?"

   "ai tunda kina da zuciyarshi, ke kikeda ragamar janshi duk inda kikeso, yanzu banda wani sauran damuwa, don naa tabbatar da abokina ya bada zuciyarshi a inda ta dace"

  "anma kinason gulma?" 

  "inasonji, anma gulma fa babu kyau"

  "an gama tunda kinason ji, sirri zan faɗa miki ba gulma ba. Kinga abokina da kike ganinshi, son matane dashi don haka kisan yanda zaki rabashi da kallon mata"

  Ta waro ido, "Na shiga daɗi" ya k'yalk'yale da dariya, "yanzu nasan kina sonshi yanda ya kamata, anma maganar gaskia wallahi tunda muka tashi ban taɓa sanin budurwar Najib ba bayanke, bai taɓa soyayya ba, a kanki ya fara, kuma yana matuk'ar sonki, yana tsoran yaudara, don Allah ki rik'eshi amana, kada ki raunana wannan jaririyar zuciyar tashi"

  "Insha Allah, kamar yanda nasan shima bazai taɓa barin soyayyatah ba"


  "Kai! Wai me kake faɗa mata ne tun ɗazu ka tsayar da matar mutane?"

  "abunda basai kaji ba, yau na fara ganinta ma baza'a barni mu gaisa ba"

  "nak'i ɗin, komai za'ace ayi gabana"

 Mik'ewa tayi, "bara in fara tafiya, barci nakeji"

  "tohm masoyiya, kiyi barci mai daɗi" Ahmad ma ya mata saida Safe, anan gidan ya kwana da Najib, washe gari tunda safe ya wuce, duk da Najib yaso ya tsaya sai bayan biki.


 Saura sati biyu biki, Momie taje babban wurin sayarda furnitures na Abuja, ta zaɓar mata fitinannun kayan ɗakin masu hegen kyau, gaba ɗaya kayan sun tasarma 3million, koda aka faɗa ma Momie ko ɗar bataji ba ta biya kuɗin. 

  Kayan kitchen ma mak'udan kuɗi ta kashe wurin haɗa mata su, jin Saude take kamar ɗiyar data haifa, gaba ɗaya taa ɗaukema su kawu duk wani hidima, komai ita takeyi.

  Haɗaɗɗen lefe Najib ya haɗoma er gatan tata, faɗan irin haɗuwar kayan da kuma kashe kuɗin ɓata lokaci ne, idan kuka tuna wanda yasai mata a tana Saudenta, akwatinan kansu abun kallone, Momie kanta ta yaba da kayan, don farko jira take kawai ya kawo ta raina saiya ƙaroma Saudenta, sai gashi ma ya wuce yanda take tunani, Saude kam har kukan murna tayi, bazata taɓa mantawa da karamcin dasu Momie suka mata ba, kullum addu'arta Allah ya bata ikon fita kunyarsu, don sun nuna mata gata sosai a rayuwah.

  Gyan jiki kam kullum cikin yi mata ake, fatarta tayi kyau sosai sai santsi take, har wani ɗaukan ido take. Ta k'ara kyau fiye da daa, kamar ba Saudat ba.


  Sauran sati ɗaya biki su Yasseer suka sauka k'asar, motoci akayi da yawa zuwa tarbansu, banda Saude da Najib suna gida yana tayata aikin tarban babban ɗan Momie. Tana gyaran kitchen bayan ta gama, yana zaune ya kasa ɗauke kallonshi daga gareta.

   "kallonnan fa ya fara yawa Masoyi" ta ɗauka plate ta kare fuskarta.

  "idan ma na kalla ai MATATAH CE, nake kallo, ki barni in kalleki, hakanan yau naji inason inyi ta kallonki"

  "nidai banson kallo fa"

 "ni kuma inason inyi ta kallon fuskarki, bazan taɓa gajia da hakan ba" ya janye plate ɗin a hannunta, jin k'arar motocine ya sakashi fita daga kitchen ɗin, ta rakashi da murmushi.


  Ɗakinta ta koma, ta sake shek'a wani wankan, ta fito ta shirya cikin wani orange ɗin atamfa, mai zanen yellow da fari, tayi kyau sosai bama kaman data zuba ɗaurin ɗan kwalinta mai kyau, ba wani Make-up tayi ba, anma tayi kyau sosai.

  Ɗakin Momie ta wuce, Rabi'ah ce kawai, ta taso da fara'arta ta tarbeta, "Sai yanzu kike fitowa? Har ina shirin zuwa ɗakinki in fito dake"

  "waceni in saka matar yaya aiki? Sannunku da zuwa"

  "yauwah Amaryarmu, kinga yanda kika k'ara kyau kuwa? Dak'yarma na ganeki"

  "ballantana ku Aunty Rabi'ah dake k'asar waje"

  "nifa da gaske nake, yanzu dai sai mun zauna kafin hidimar bikinnan ta ida haye miki za'a k'ara koyamun wasu girke-girken"

  "tohm Aunty"

 Fira suka shigayi da Rabi'ah, da yake Momie bata ɗaki, tana shirin tambayar Rabi'ah Momie sai gashi ta shigo.


 Momie tace "yanzu na aika kiranki ashe kinanan"

  "sannunku da dawowa Momie"

  "yauwah sannunki da hidima"

  Sai ga Najib da Yasseer sun shigo a tare, suna dariyansu da alama cikin farin ciki suke, Najib yace "Saudat, yau dai ga babban Yayana Yasseer" ya juya kan Yasseer, "Broda, ga MATATAH, Saude na gaji da wannan saɓanin da kuke samu"

  Yasseer yace "A'a'tohh karma sai anyi auren mu haɗu a hanya bamusan juna ba" gaba ɗaya ɗakin saida sukai dariya, kowannensu ka kalla yana cikin farin ciki.

  Hakan ya sanya Saude ta jiyo cikin ladabi ta gaishe da Yasseer, wani irin shock yaji sauraren muryarta kawai tun basu haɗa ido ba, gaba ɗaya ya kasa buɗa baki ya amsa, jin yayi shiru ya sanyata ɗago kanta, su duka saida gabansu ya faɗi, da sauri ta ɗauke kanta.

  Shikam kasa ɗauke idanunshi yayi a kanta, kallonta kawai yake kaman babu kowa a wurin.


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

       70


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


💗Whoever forgets to wish you on your birthday I will always be there to wish you.What to do if I forget? Simple come and fight with me as usual.Happy birthday I remember this time. May be we can fight next time.😜 Having you for a sister makes my life more beautiful. I hope that you know that. Happy Birthday. Sis Hauwa'u Sk Msh (Hasma) I love uh so much😍


www.babymsh.blogspot.com


  Da Yasseer yayi Sallah yaso ya koma barci abun ya gagara, wani irin azababben ciwon kai ya saukar mishi ko motsin kirki dak'yar yake da kan, gaba ɗaya ji yake kaman duniyar ne duka yake ɗauka.

  Hayaniyarsu da yake jiyowa a falonne ya k'ara hargitsashi, daganan yana jiyo dariyar Najib da Saudat, a hankali yake fita zuwa falon ya ɗaura hannuwanshi duka biyun yaa dafe, yana tafiya dak'yar.

 Sun baje I.V tana gani, ba k'aramun kyau sukai ba da gani an kashe kuɗi da yawa, ko meya haɗosu? Cikin wasan ta tilla mishi filon kujera, ya tare da hannuwanshi biyu bai sameshi ba yana mata gwalo ta k'ara jefa mishi wani sai saman k'afan Yasseer.


  Su duka suka ɗaga ido suna kallonshi, da gani yanajin azabar ciwon kan lokaci ɗaya har ya faɗa, Najib ya mik'e a ruɗe yaje inda yake.

  "lafiyanka bruhh? Meke damunka?"

 Yak'e kawai ya mishi yace "ba komai" ya raɓa gefenshi zai bar musu ɗakin, Saude ta gaisheshi, hakanan ya tsinci kanshi da sakar mata fuska.

  "lafiya lau Saudat ya kika tashi?"

   "Alhmdlh" sai kuma ya fita yanajin haushin zuciyarshi da rigimar da take shirin kunno mishi, me yasa zuciyarshi zata mishi haka? Da gani basai an faɗa ba Saudat da Najib masoyane da suke matuk'ar son junansu, tayayama zaiyi nasara?

  Yana fita Najib ya zauna jikinshi a sanyaye, damuwa ce bayyane a fuskarshi, "gaskia bruhh yana da damuwa, kuma nasan zurfin cikinshi bazai taɓa bari ya faɗamun ba, koma menene tunda kika ganshi haka yana matuk'ar damunshi da yawa, shi mutum ne da bai ajje damuwa a ranshi"

 Itama sosai ta tausayama halin da Yasseer yake, "Allah sarki, Allah yasa dai ba wani matsala bane"

  "Ameen"


 Ɗakin Momie ya shiga, tana duba zannuwan gadon data saima Saude, da ganin yanayinshi ta maida hankalinta kanshi, zaman dirshan yayi a saman carpet ya jinginar da kanshi a bango,

   Momie duk hankalinta ya tashi ta koma inda yake "Baka lafiya ne?" ya girgiza kai kuma ya ɗaga.

  "meke damunka?" wasu siraran hawayene suka gangaro mishi, cikin muryan tausayi yace "nima ban sani ba Momie" 

  "bazai yiwu ba, dole zakasan dalilin damuwarka, sai dai in yauma bazaka faɗamun ba"

  Tohh ciki waccema zai faɗa mata? Labarin Saude Matar daya aura a k'auye ya gudu ya barta da har yanzu soyayyarta da tunaninta suka hana zuciyarshi sukuni, har yanzu dana sanin abunda ya aikata yake? Ko kuma matsalar Rabi'ah ta kullum take damun k'wak'walwarshi? Bata rageshi da komai ba, duk wani soyayyar miji da mata tana nuna mishi, matsalanshi ɗaya da ita rashin son haihuwa, kuma Allah ya yishi da son yara, shima yanason yaga k'wanshi a duniya, ko kuma babban matsalan da shi kanshi kunyar kanshi yakeji, wai yanason matar da k'aninshi zai aura!

   "ban sani ba Momie, anma inajin kaman duniya gaba ɗaya ta juyamun baya"

   "meyasa kace haka?"

  "ba komai Momie, anma ina neman Alfarma a wurinku"

 "ka faɗi koma menene"

   "Don Allah Momie a taimakamun a ɗaga ranar ɗaurin aurennan"

  "saboda me?"

    "yayi shiru ya kasa bata amsa"

 "Karka damu, insha Allah kafin lokacin kaa warware, ka yawaita addu'a akan damuwarka, shi Allah maji rok'on bawansa ne, akwai wata addu'ah a cikin husnul muslim: Allaahumma 'innee 'abduka, ibnu 'abdika, ibnu 'amatika, naasiyatee biyadika, maadhin fiyya hukmuka, 'adlun fiyya qadhaa'uka, 'as'aluka bikulli ismin huwa laka, sammayta bihi nafsaka, 'aw 'anzaltahu fee kitaabika, 'aw 'allamtahu 'ahadan min khalqika, 'awista'tharta bihi fee 'ilmil-ghaybi 'indaka, 'an taj'alal-Qur'aana rabee'a qalbee, wa noora sadree, wa jalaa'a huznee, wa thahaaba hammee ."

  "fassarar addu'ar shine: Ya Allah! Ni bawanka ne, kuma ɗan bawanka, kuma ɗan baiwarka. Goshina a hannunka yake, hukuncinka zartacce ne a kai na, kuma k'addararka gareni mai adalci ce. Ina rok'onka da kowane suna naka, wana ka ambaci kanka dashi, ko ka saukar dashi a cikin littafinka, ko ka sanar dashi ga wani daga cikin halittarka, koka keɓance kanka da saninsa a cikin ilmin fake da ke wurinka, da ka sanya Al-Qur'ani ya zama kaka ga zuciyata, da haske a k'irjina, da kwaranyewa ga bak'in cikina, da kuma mai tafiyar da damuwata."

  "insha Allah zaka samu sauk'i a zuciyarka, bansan meke damunka ba, anma duk ɗan adam daka gani Allah yana jarrabarshi, kuma imanin mutum baya cika saiya yarda da k'addara mai kyau da marar kyau, komai kaga ya faru dakai k'addarane, idanma matsala tsakaninka da Rabi'ah ne kayi k'ok'arin gyarawa tun wuri, kada ka taɓa raunana zuciyar mace, kada kace zaka juya mata baya don matsalar dake tare da ita na rashin haihuwa"

  "kodai matsalan data ɗaurawa kanta?" ya faɗa a zuciyarshi, baison ya faɗama Momie tsakaninshi da Rabi'ah ne, don bazaiso ya haɗasu ta dinga ganin bak'in taba, anma dai duk yanda zaiyi da Rabi'ah batajin lallami ko shawara,

   "Na gode Momie" ya furta yana zubar da hawaye, saiga Hafsat ta shigo da gudu Najib ya biyota, baisan sanda ya mik'a hannunta tazo wurinshi ba, ta zulle ko kallanshi batayi ba ta faɗa kan Momie.

  "Guje-gujenne ko Hafsa? Bana hana ba?"

 Tana shesshek'ar gudu sai dariyarta take "Momie Daddy ne ya biyoni"

  "shine kika rugo haka ko ɗayan Daddynki bazaki gaisar ba?"

  "ni Daddy na ɗaya mai sona, ban haɗashi da kowa ba Momie"

  "Wannan ma babanki ne, ki gaisheshi nace" ta kalleshi tana tura baki, hakanan yarinya da ita gaba ɗaya haushinshi takeji, sai kuma ta ganshi yana hawaye sosai ya bata tausayi.

  Ta tafi inda yake, ta saka k'asan rigarta tana share mishi hawaye, ya ɗago yana kallonta, murmushi ta mishi, "Mamana taa hana kukan rigima, idan ta ganka kana kuka Momie zata faɗa mawa kuma Daddyna bazai kaika shan ice cream ba"

  Murmushi yayi yarinyar sai k'ara burgeshi take, inama ace tashi ce? Lallai iyayenta ba k'aramin Sa'a sukai da samunta ba.

  "na daina kuka, anma saikin yarda mun shirya bazaki k'ara guduna ba"

 Ta mak'ale kafaɗa "nina daina shiri da kowa, best frnd na ɗaya"

  "wanene?"

   "Daddy na"

 

 Najib ne ya shigo ɗakin yana nemanta, ganin Yasseer zaune gaban Momie harya juya zaiyi baya, Yasseer ya mik'e yabar ɗakin duk kalanshi ya canja.

  Momie ta kalleshi, "yayanka ya faɗa maka damuwarshi?"

  "A'ah Momie, kin sanshi dai da zurfin ciki"

  "tohm Allah ya kyauta"

    "Ameen"

 "Ina Saudat ɗin?"

   "ta wuce ɗaki tasha maganin ciwon cikinta"

  "ni wannan ciwon ciki da tak'i yarda aje asibiti"

   "ai tace da tasha magani yake tafiya"

  "Allah ya bata lafiya"

 "Ameen"


 Hidimar biki kawai ake, ranar laraba za'a fara shagulgulan, don ita Saude in yanda takeso nema baza'ayi komai ba, tunda safe take jiran Najib shiru bai fito ba, tana ta mishi waya bai ɗauka ba, ta wuce ɗakinsu a falo ta tsaya tana k'wala mishi kira, taji shiru dai saita shiga ɗakin don bataga alaman Yasseer na ciki ba.

  Najib ne kwance shi kaɗai, ganinshi da shirin fita ne ya tabbatar mata ba barci yake ba.

  "Masoyi kaifa nake jira" ya mata shiru kawai,

  "in tafiyatah bazaka kaini ba?" saima ya k'ara gyara kwanciya.

  Ta ɗan saka hannu tana buga filon da yake kwance, yanaso yayi dariya ya rufe fuskarshi da filo,

  "daman nasan ba barci kake ba" tayi dariyar mugunta, a ranta tace yanzu zaka tashi.

 Ta ɗauko wayanta ta fara mishi video, "idan kana barcinma kafi kyau, tunda bazaka kaini ba bara in maka video, wow! Kaaga yanda kayi kyau kuwa?" duk ta kashe mishi ido da flasher ya kasa rufe idon da daɗi.

  "wai da gaske videon kike?"

 "ina ruwan mai barci da abunda nake?" ya diro daga saman gado.

  "in gani inda gaske ne"


    "nak'i fa" ta tashi ya biyota da gudu, suka fara zagaye ɗakin taa hanashi ya gani.


  Suna cikin zagaye ɗakin ya samu dak'yar ya kamota ya rik'e, ɗaga wayan yayi, "kinga irin videon da zaki ɗauka nan"

  Ta fara k'ok'arin zamewa, shikam hankalinshi kwance yanata mata dariya dak'yar ta k'wace, da gudu tabar ɗakin, yace, "Matsoraciya kawai"

 Da yake ba kallon gabanta take ba, tana fita sai dai taji ta faɗa ma mutum, kwance saman k'irjinshi, wani iri takeji a jikinta, gaba ɗaya ma ta kasa ɗagowa, ko ban faɗa ba kunsan ko waye.

  Tafe yake shima gaba ɗaya komai nashi ya canja, ko tafiya yake tunani ne kawai. Zuciyarshi, ga tarin damuwa data mishi yawa.


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

       71


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


 🙋🏻kuyi hak'uri dani Masoyah, naga k'orafinku, kuma naji daɗi da gyaran da kukamun, kunsan dai ɗan adam ajizine, babu wanda yafi k'arfin kuskure, gaba ɗaya na manta na saka Saude bata gane Yasseer, wasu na cewa ya kamata ta ganeshi tunda ita a ɗan birninshi ta sanshi, maganar gaskia daman Saude bata ganeshi ba, ita da tazo Abuja ma taa canja ballantana shi daya bar k'asar, ga matarshi Rabi'ah dake kula dashi😉 kuma idan baku manta ba Saude ma tana yarinya a lokacin daya tafi ya barta, Nagode sosai da tunatarwar da kukamun, wallahi naji daɗi sosae, don Allah ko a gaba kuka k'aracin karo da wani gyaran ina maraba dashi, Nagode sosai Masoyah, Allah yabar k'auna, LYSM😍


www.babymsh.blogspot.com


 Gabantane ya shiga faɗuwa, har wani kyarma take k'afafunta suka kasa ɗaukanta, tana shirin faɗuwa ya tafi zai rik'ota, ta kauce kawai ta juya zata tafi.

  Zata ita manta kamanninshi, zata iya manta sautin muryanshi, da duk wani abu nashi anma bazata iya manta ɗumin jikinshi ba, bazata iya manta yanayin da takeji a duk sanda jikinta da nashi suka haɗu ba.

  Tana shirin tafiya ya rik'o hannunta, ta juyo suka haɗa ido, zuciyarta ce ke cewa A'ah Saudat, don yana da yanayin mijinki da kuma sunanshi ba lallai ne ya zama Yasseer ɗinki ba, kima fiddarai da sake ganinshi a rayuwanki.

  Bata taɓa tsayawa ta k'are mishi kallo ba, Yayan Najib farine sosai, yafi Najib tsayi da cikar jiki, ga wani irin k'warjini da yake tare dashi, duk da ko ranshi a ɓace yake ka kalleshi kamar yana murmushi, saɓanin Najib da ko murmushin tsadane dashi, yafi Najib sakin jiki da fira da mutane. Kyakkyawane na k'arshe harta kasa gane shida Najib wanne yafi.


  Ji yake kamar ya fito fili ya faɗa mata abun dake zuciyarshi, anma ya kasa koda buɗe bakinshi, idon yana kallonta ganinta yake kamar Saudenshi sai dai ya kasa yarda da zuciyarshi, mezai kawo Saude Abuja kuma gidansu? Kawai dai wata soyayyar ce Allah ya k'addaroma zuciyarshi, a hankali ya saki hannunta, kamar wacce take jira da gudu tabar ɗakin.

  Fitar da basuyi ba kenan. Ranar bata samu halartar partyn da Abokan Najib suka haɗa mishi ba, don gaba ɗaya ji takeyi babu abinda zata iyayi, saima ta fake da ciwon cikinta.

  Washe gari Momie tayi Mother's day, har ranar Saude bata fitowa ko k'ofan ɗakinta, wani tunanin Yasseer ne yake dawo mata sabo, ta rasa gane tsanarshi ne, haushinshi, ko kuma soyayyarsa, ga wani salon da Yayan Najib kezo mata dashi.


 Kowanne ɓangarori anata hidiman biki, su gwaggo ma ana k'yauye anata shagali sai ranar ɗaurin aure zasuzo, Najib ma duk ya damu na daina ganin Saude sai dai suyi waya, anma inya tuna ta kusan zama tashi ma gaba ɗaya sai hankalinshi ya kwanta.


 Ranar ɗaurin aure.

Tunda safe da sak'on Najib ta farka.

   "Yau burina zai cika na samunki, na tabbatar babu sauran wani garkuwa yanzu tsakanina dake, ke tawace, ni naki ne, ina sonki Masoyiyah"

 Murmushi tayi bata maida mishi ba saita kirashi, don a halin yanzu tafiso ta saurari muryarshi fiye da komai, "Masoyi an kusa zama Ango"

  "nama zama dai, waɗannan awoyinma duk zasu shuɗene bayan sun sadani da farin cikina"

  "Me kakeyi yanzu?"

    "tafiya nake"

  "Ango daman yana yawo?"

    "tohh yana iya tunda kina guduna?"

 "hhm" knockn k'ofanta taji anayi, ta sauka tana saka hijabi.

   "ana miki knockn fa"

  "Gashi zan buɗe"

 Tana buɗewa sukai ido huɗu dashi, suka sakar ma juna murmushi, "Yadai?"

  "Amaryatah nazo gani" ta tsaya jikin k'ofan bata bashi hanya ba sai so yake ya shiga.

  "ko ba'a maraba dani in koma?"

 "bak'in naka ka baro ka fito?"

  "eeh mana tunda ina son ganinki"

  Ya wuce ta ya zauna ɗaya daga cikin kujerun ɗakin.


 Dai dai lokacin Yasseer na can ɗakinsu ya rasa meke mishi daɗi, tunanin ta yanda zai dakatar da auren kawai yake, ga wani sabuwar rigimar da Rabi'ah ta ɓullo da ita, ciki ne da ita taa rantse mishi bazata haife ba, ita bata shirya haihuwa yanzu ba, dukiyarshi ma gaba ɗaya ya mata alk'awari akan ta haife mishi ɗanshi anma tak'i jin lallashi, ga damuwan zai rasa Saudat kuma.

  Meya kamata yayi? Yana kwance shi kaɗai yasan azabar da yakeji a jikinshi, yaje juyawa yaci karo da wayar Najib ɗayar daya bari, harya maida zai ajje ya hango hotanshi da Saude mak'ale a wallpaper, su duka suna dariya, wani irin daɗi yaji yana kallonta a hotan, gaba ɗaya kewanta yakeji, tunawa yayi da hotunanta da Najib ya taɓa cewa zai nuna mishi, ya shiga dubasu ba wahala sai gashi ya gansu, ya shiga yana dubawa babu wanda baiyi kyau ba, harya jawo wayanshi zai fara turawa yaci karo da wanda Najib yayi mata a tana er k'auye, wani irin zabura yayi ya tashi zaune.

  Zazzafan zazzaɓine a jikinshi, anma ji yayi lokaci ɗaya kamar an yaye mishi shi, "Saude? Lallai kuwa biri yayi kama da mutum, babu tantama wannan ce Saudenshi" wata zuciyar tace 'anma mezai kawo Saude anan? Wannan sunanta Saudat kuma matar da k'aninshi zai aura! Mezai kai Saude yin aure saman aure? Anma kuma ai ance daga k'auye tazo, gani yayi kamar yana ɓatama ma kanshi lokaci, ya diro da niyyar zuwa ya tambaya Momie, don ta bashi tabbacin abinda zuciyarshi take zargi.


  Cikin farin ciki yake tafiya kamar wanda akama bushara da gidan Aljannah, anan ya wuce abokan Najib en ɗaurin aure, ya wuce can cikin gida, duk taron matan da kema momie hidima da bak'in dake zuwa idonshi rufe ya shiga yana tambayar Momie, dak'yar ya ganota, ya jawo hannunta cikin zumuɗi, "Momie kizo kiji don Allah"

  "Meye zanji? Kai har yau kamar k'aramun yaro, bakaga abunda nake ba?"

   "plz Momie maganar nada muhimmanci ne, don Allah kizo kiji"

  "Ya zanyi da bak'in dake zuwa? Kasan en ɗaurin aurema duk yanzu zasuzo, kaje ka shirya mana"

  Rik'o hannunta yayi duk ya shagwaɓe kaman shine Autan "kizo kiji Momie bazaki daɗe ba"


 Can ya jata ɗakin da babu kowa ciki, "ki zauna kiji don Allah Momie" ta ɗanji daɗi da taga ya fara sakewa, k'ila damuwar tashice ya tashi faɗa mata, ta zauna tana saurarenshi anma duk hankalinta ya tafi ga hidimarta data baro.

  "Momie don Allah ki faɗamun ina aka samo matarnan da Najib zai aura?"

  "lafiyanka kuwa? Wai menene matsalanka da aurennan?"

 "zan faɗa miki Momie, wallahi zan faɗa miki ko menene damuwatah, anma ki fara faɗamun Momie" tayi shiru tana ɗan tunani,

  "Don Allah Momie ki faɗamun" ganin yanda yaketa gamata da Allah ya sanyata fara bashi labarin Saude kamar yanda baba Haja ta faɗa mata, komai bata rage ba harda cewa mijinta ya rasu da kuma er da tazo da ita.

  Cikin farin ciki yake tambayarta shekaran Hafsat nawa sanda sukazo? Ta faɗa mishi harma da sunanta na daa Saude, kamar ya fasa ihu don daɗi yadai daure yace "Momie ya sunan mijin nata?"

   "Yasseer" ai baisan sanda ya k'ank'ame Momie ba yana murna, ya saketa ya duk'a har k'asa yayi sujjada, "Alhamdulillahi" kawai bakinshi ke furtawa, tsananin murna ma ya hanashi cewa komi sai dai yaci gaba da zagaye ɗakin.


  Kallonshi kawai Momie keyi kaman wani zautacce, saida ya gama murnarshi take kallonshi baki buɗe, ya dawo kusa da k'afafun Momie ya zauna, "Momie ta tabbata dai Saude MATATAH CE, wallahi MATATAH CE dana biya sadaki aka ɗaura mana aure"

  Sai yanzu ta ida tsorata da Al'amarinshi, gaba ɗaya kamar k'walwarshi ta taɓu take kallonshi, tausayinshi takeji, kodai damuwar tashi ce ta fara rikita shi?

   "Matar k'aninka fa ce da za'a ɗaura musu aure yanzu ba daɗewa kake ik'irarin cewa matar kace, ba tun yanzu na gane take-taken ka ba, tun wuri ka fita idona karma ka ɗaga maganar nan wani yaji, wannan ai hanyar da zaka haddasa rigima ne tsakaninka da ɗan uwanka"

   "wallahi Momie da gaske nake, Saudat MATATAH CE, nine mijinta Yasseer, na kasa faɗa muku ne don bansan yanda zaku ɗauka maganar ba, anma k'auyensu ne nayi bautan k'asa kuma a can aka bani aurenta"

  "k'arya kake mijinta ya rasu, ka rabani da shirmennan naka ka bani hanya in wuce, sai dai in daman akwai wani abun a ranka"

  Kamar yayi hawaye yake rok'on Momie, "Don Allah Momie karki yanke hukunci a rashin sani, wannan auren wallahi gaba ɗaya bai halarta ba, nine mijinta kuma gani a raye, ki yarda dani aurene za'a ɗaura saman aure"

 

 Ita dai Momie ko maganganunshi bata fahimta, gaba ɗaya a tsorace take dashi, kallon marar lafiya take mishi, "Momie ki kirata ki tambayeta, zata faɗa miki gaskia da bakinta, idan harta musa na yarda ba Matatah bace"

  "kana cikin hankalinka kuwa? Tun wuri ka dawo da tunaninka, Matar k'anenka ce fa, idan har taji maganar nanma ai girmanka zai faɗi a idanunta, na faɗa maka ka daina maganar nan ko?" ta wuceshi zata tafi.


 Ya buɗa baki yanda zata jiyoshi, "Momie kinamun kallon mahaukaci ko" wallahi gaskiyatah nake faɗa, don Allah ki saurareni Momie, ina cikin hankalina" tsayawa tayi.

  "ki aika aka kira miki ita, idanta k'aryata abunda na faɗa na yarda da duk wani hukunci da zaku yankemun"

  Jikinta duk yayi sanyi da maganganunshi, ta dawo ta zauna, yananan zaune ta buga waya, sannan ya sauke ajiyar zuciyah.

  Najib na ɗakin Saudat Abokan wasanshi sun sanyasu gaba suna tsokanarshi, yama kasa hak'urin akai mishi ita zaizo ya mata zaune ko shirin ɗaurin auren bazai tafi yayi ba, shine ma mai k'ok'arin maida musu, don dagashi har ita babu mai yawan magana cikinsu, kiran Momie ne ya fiddasu wurin ya tafi ya rakata. Tsayawa tayi kafin su shiga ɗakin.

  "ka jirani karka biyoni kaji me Momiena zata cemun"

    "kina da sirrin daya fini ne? Ai duk wani sirrinki nawa ne, don haka daga yanzu duk inda kika sanya k'afarki ina tare dake, bazan taɓa barinki ba"

  "Gaskia na more miji dake matuk'ar k'aunatah, kaine sirrina Ya Najib, idanna zama matarka dukkan wani burina ya gama cika"


Maganan Momie sukaji, "Saudat ce anan?"

  Da sauri ta shiga, "eeh Momie gani", "keda waye?" sai gashi shima ya shiga.

  Sai lokacin suka kula da Yasseer da yayi zaman dirshan a gaban Momie, gaba ɗaya itama yanayinta ya canja, tayi niyyar korar Najib don bai kamata ayi maganar gabanshi ba, sai kuma taga ai shima ɗan uwane, 

 Cikin hikima don kar Saude tayi saurin gano yanayin da suke ciki tace "kince mijinki ya rasu ko?" Saude ta ɗaga kai ita mai gaskiyarnan, 

 Momie ta nuna Yasseer, sannan take kallon Saude cikin ido "wannan fa kin sanshi? Ki faɗamun miye tsakaninki dashi" k'walalo ido tayi tana kallon Yasseer, gaba ɗaya hankalinta ya tashi, cikin sark'ewar murya tace "Ya Yasseer, anan gidan na sanshi"

  Najib yace " Meke faruwane Momie? Wacce irin magana ce wannan?"

 Hannu ta ɗaga mishi alamun dakatarwa, "ki faɗamun gaskia" ta ɗaga kai tana kallon Yasseer, ita tsakaninta da Allah a farko gaskia ta faɗa, toh me Momie ke nufi?


Yasseer ne ya katse mata tunani, sai dai ta ganshi kawai a gabanta, 

  "ki faɗi gaskia Saude, ki faɗa musu ke MATATAH CE, nine Yasseer mijinki, nasan laifin dana miki fiye da mutuwa saiki ɗaura mun, ki faɗa musu gaskiya, ki faɗa musu mijinki ba mutuwa yayi ba"

  Najib ne ya tureshi daga gabanta cikin hucin zuciyah yace "wannan wane irin abune kakeyi bruhh? Karma ka soma, Saudat MATATAH CE, kuma munan bamusan da wani maganar aurenka ba"

  Momie ce ta mishi tsawa, yayi shiru anma sai huci yake.

  "Saude kiyi magana don Allah, karki bari ku aikata HARAMTACCEN ZAMA, nine Yasseer naki wanda naje bautan k'asa k'auyenku aka bani aurenki, wallahi nasha wahala nemanki, don Allah ki buɗa baki ki faɗa musu gaskia, kada laifin dana miki ya kaiki aikata zunubi, ni mai laifine, ki hukuntani da duk hukuncin da zaisa kiji sauk'i a zuciyarki, anma karki aikata saɓon ubangiji, karki bari a ɗaura aurennan, don har yanzu ke MATATAH CE!"

 "Ya isa haka" momie ta dakatar dashi, sannan ta kalla Saude, "ki faɗamun tsakaninki da Allah mijinki yana raye, Yasseer ɗana shine mijinki?"


 ©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

      72


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


U're de best dear, so Good to have uh in my life, I love uh My ```waliyya wally```😍


www.babymsh.blogspot.com


 A daidai wannan gab'an kam Saude baza ta iya wa momie k'ariya ba kamar yanda zuciyar ta ke zuga ta, amma toh Idan tayi na'am da wannan tambayar me ze biyo baya, wani irin kallo momie zata yi Mata? kallon maci Amana ko kuma mak'aryaciya? "Amsar ki nake jira kuma kinyi shiru Saudat" Momie ta katse mata tunanin da take. Tuni hawaye sun wake mata fuska, ta watsa wa yasseer wani kallo zuciyar ta na tsananin bugawa, Sannan cikin raunannan murya ta ce "Gskia ne momie, yasseer ya Kasan ce miji na a da can baya but not any more! ta karashe maganar da d'an k'arfi tana kallon yasseer da tuni idanun sa suka dawo jaa da jin kalaman ta na k'arshe. 


  Kafafuwan Najib ne suka kasa d'aukan sa, wani nauyi yaji kan sa na masa kamar ze fad'i yyi saurin zama dirshan akan rug carpet din dake d'akin, ya tallafo kan sa da hannayen sa biyu a hnki bakin sa na furta "innadillahi wa'inna ilaihir rajiun". Wannan shine Kalmar da momie ma ke furta wa, hankalin ta yayi dubu ya tashi ta shiga safa da marwa acikin d'akin.

"Har Yanzu ke MATATA CE Saude! matsayin ki bazai tab'a chanja wa ba agurina, Dan Allah kiyi hakuri Kar kiyi min hukunci me tsauri haka, I know I deserve even more than this but pls kiyi min aikin gafara ko Dan albarkacin 'yar mu da muka Haifa tare".

"Wace 'ya??" ta wurga masa tambayar

  "Hafsat mana, ko kina nufin hafsat ba 'ya ta bace?"

  "Ae hafsat bata da wani uba daya wuce wannan" ta nuna najib dake zube agurin

"Saboda shi ta sani kuma shine ya yi Mata rik'on mahaifi kuma ya dawo da mahaifiyar ta cikakkiyyar mutum alokacin da kaii ka guje mu" 

Yasser ze yi magana momie ta dagatar dashi cikin b'acin rae tace "Duk ku dakata! wannan bashi bane, meyasa kika boye mana wanan BOYAYYEN AL'AMARI Saudat?"

K'afan momie tazo ta Kama tana durkushe cikin muryan kuka tace "Dan Allah momie kiyi hkri, nayi gudun fad'a muku ne kuyi tunanin wani mugun halin gareni yasa miji na ya gudu ya barni, naji tsoron Kar kuki k'arba ta alokacin da bani da wani inda Zan je, shi ya......"

Najib ya katse ta "Sam! wannan ba hujja bace Saudat! I cnt bliv abunda kunne na suka jiyo min" ya Kai hannu ya d'ago ta daga durkushen da tayi suna fuskanta juna kowannen su da rinanne ido

  "Idan zaki iya b'oye wa momie then why me! I tout ni dake ayanxu mun zama d'aya da zaki iya fad'amin duk wani Abu naki tunda I'm ur soon to be husband"

  "Ya yasseer ba miji na bane ayanxu, yana da matar sa me kaunar sa haka nan nima wallahi Kai nake so ya Najib, Dan Allah karka gujeni masoyi nasan..."


 "Ni wallahi duk kun rud'a ni yaran nan, Yanzu ya kuke so mu b'ullo wa wannan sabon Al'amarin, da wani ido zamu kalli mutane kuma me kuke so nayi adaidai wannan lokaci da bai fi awa guda ba a daura aure."

  Cewar momie...

"A dakatar da auren nan momie, Dan wallahi Saudat MATATA CE, da aure na akanta har Yanzu" 

  Najib juyawa kawai yayi zai bar ɗakin, Momie na kiran shi amma ko ya saurareta, sai da Saudat ta sha gaban shi Sannan ya tsaya yana sauke ajiyan zuciya "Pls Kar ka barni masoyi! wallahi ni kai nakeso kuma Kai Zan aure"

  wani zafi yasseer yaji azuciyar sa, se alokacin yake k'ara gani wautar sa da yyi abaya.


"Ta yaya Zan aure ki bayan kuma da auren dan'uwa na akan ki, yaya ma Zan yi tunanin rayuwar aure da matar da ta Kasan ce tayi tarayya da dan'uwa na a matsayin matar sa, noo I can't! yana Kai wa nan yasa Kai ya fita momie bata Hana shi ba, ta ma rasa ta inda zata fara tackling problem d'in.

  Sai ma tashi tayi itama ta fita zuciyar ta Sam Babu dadi, tana tunanin yanda zata Fara warware wannan matsala data kunno Kai a kurarren lokaci.


Tana fita yasseer ya zube akan gwuiwoyin sa yana ba wa Saudat hakuri data yafe mishi akan kuskuren da tafka a baya, ko kallon shi bata yi ba ta cigaba da rera kukan ta yana taya ta. Gaba ɗaya jin haushin zamanshi gabanta take.

"Ka yi min raunin da bazai tab'a warkewa ba Yasseer, na jima ina jiran dawowar ka garemu ni da 'yar Dana haifan maka but u kept me waiting all dis years, Idan nace a baya ban son ka toh nayi wa zuciya ta k'arya amma wallahi tunda zuciyata ta amshi soyayyar Najib na shafe duk wani Abu da nake ji akan ka wannan yasa nayi pretending kamar ban gane ka ba tun ranar da idona ya sauk'a akan ka"

  "Plx Kar kice haka Saude nasan kina fushi Dani ne har yanzu, I know ni ki ke so ba Najib ba Dan nine Mijin ki"

  "Baka so na, kama san meye so Ya Yasseer? In har kana ma mutum soyayyan gaskia bazakaji kunyan nunashi koma a ina bane, da kana sona baza ka ji tsoron gabatar Dani ga iyayen ka ba har ka gudu ka barni kaje can ka auri wata ba"

  "Wallahi ina son ki, ina kaunar ki Saudat! ya Kai hannu ze rik'e ta, tayi saurin juya wa ta bar d'akin, Kai tsaye ta bi back door ta fita ta can wani b'angare na bayan gidan inda Bbu mutane nan ta had'a Kai da gwuiwa ta kuka na sosae...


Tana fita shima ya fice zuciyar sa na tafarfasa kamar zai fito daga k'irjin shi, Kai tsaye yyi motar sa dake can wani side na parking space d'in gidan, nan ya shiga ya fice daga harabar gidan daya cika da mutane. Ko kad'an Yasseer bai San inda ya nufa ba shi dae kawae yana zuba gudu akan titi kmr ze tashi sama, titin by pass ya dauka wato can ta bayan gari zuciyar sa na tsananin yi masa ciwo, idon sa ya chanja sosae har kamar baya gani sosae, a hnkli ya rufe idon ya sake bud'ewa Bbu abunda yake tunano wa kamar yanda Sauden shi ta chanja, ta murje zuwa had'ad'd'iyar mace me suna Saudat. Tuni yayi nisa da fad'a wa duniyar tunani, wannan yasa bae ga motar da ta sako Kai ba alokacin da yayi over taking.... 

   

  Momie ba k'aramin ruɗewa tayi da jin labarin accident ɗin Yasseer ba, gaba ɗaya kanta ya ɗaure batasanma me take faɗama taron mutanenta ba, kawai dai tace "an fasa ɗaurin auren, babban ɗanta yayi accident" mayafinta a hannu tabi driver zuwa Asibitin da aka kwantar dashi, tare da wasu en ɗaurin auren, gaba ɗaya gidan yaa rikice.


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

       73


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


 Saude na can baya tana kuka batasan meke faruwa ba, saida tayi mai isarta ta fara jiyo gidan yayi tsit, ta tashi ta koma cikin gidan bayan ta share hawayenta.

  Bataga kowa ba kamar anyi shara, babu en biki babu en gidan, babu en biki, duk da su duka babu wanda takeson haɗuwa dashi, anma saida jikinta ya bata ba lafiya ba, ta tambaya ɗaya daga cikin en aikin ta faɗa mata suna can asibiti Yasseer yayi accident.

  Komawa ɗaki tayi hannunta akai tana ci gaba da rusa kuka, gaba ɗaya abubuwa sun jagule mata, tama rasa tunanin me zatayi.


 Tana zaune tana kuka ta haɗa kai da gwiwa sai dai ta jiyo sallaman Momie a ɗakinta, wani irin kunyarta takeji, cikin muryar data gama cin kuka ta amsa, tayi shiru tana sauraren Momie.

  Ta kira sunanta "Saudat", sai da gabanta yayi mummunar faɗuwa, kasa amsawa tayi Momie taci gaba da magana,

   "Allah ya gani Saudat, na rik'e ki amana, ban rageki da komai ba tamkar er dana haifa, tun ranar zuwanki kikamun alqawarin zamui zama na amana, na yarda dake, shiyasa ban taɓa tunanin hakan daga gareki ba, tunda nake da Yasseer tun haihuwarshi bai taɓa ɓoyemun wani abu ba sai a kanki"

  Yanayin da Momie tayi maganar saida Saude ta ɗago tana kallonta, gabanta sai faɗuwa yake tana jiran hukuncin da zata yanke mata, taci gaba da magana.

  "na yarda yayi miki laifi, ya faɗamun duk abunda ya faru, na yarda da laifinshi a matsayina na mace, kuma bawai ina goyon bawanshi bane, anma laifin da kikamun na ɓoyemun ba k'aramun al'amari bane" a rikice Saude ta k'ara ɗagowa tana kallonta.

  "tabbas bazan iya ci gaba da zama dake ba, kin wargaza duk wani yarda dana miki, bazan iya haɗa jininah da mak'aryaciyah, munafukah ba, abinda kika mana kanki kika cuta" ta wurga mata takarda a inda take.


Tunda Momie ta fara magana, ko hawayen ma nema tayi ta rasa, saurarenta kawai take mamaki cike da zuciyarta, damk'e takardar tayi da hannuwanta biyu.

   "daga yau ki fita daga rayuwar ƴaƴana, don bazan taɓa bari ki rabamun kawunansu ba"

  Batasan yanda tayi ba, sai dai kawai ta ganta gaban Momie, wani razanannar kuka na k'ara tunzuro mata, "Don Allah Momie kiyi hak'uri, nasan na muku laifi, don Allah karku yankemun hukunci cikin fushi, wallahi Allah shine shaidata, ko kaɗan ban nufin iyalan gidannan da komai sai alkhairi, wallahi komai ya faru bada son raina bane"

  Wani irin kallo Momie ke watsa mata da bata taɓa ganin ko maqiyi ta yima shiba, "ai donma kar in canja tunani nah ya saka ban baro asibitinnn ba saida na tabbatar ya cikashe miki saki uku" wani irin zaro ido tayi tana kallon Momie, "don haka ya rage naki, anma bazaki taɓa lalata mana farin cikin gidannan ba" tana gama faɗar haka ta fice tabar Saude duk'e a wurin.


  Lallai yanzu ta ida yarda da ta gama rasa damarta a wurin Momie, tun farkoma meyasa ta mata k'arya? Tana magana kamar ba mace ba, bata ga laifin aurenta da Yasseer yayi ya gudu ya barta ba, ta kirata da munafuka, tama manta da shima Yasseer ɗin munafuntarsu yayi yai aure bada saninsu ba, ita dai haka rayuwanta take, duk lokacin da ta fara farin ciki sai wani k'addarar tazo ta lalatashi. Gani tayi duk tunanin bashi zai fiddata ba, ta tashi ta fara haɗa kayanta.

  Cikin mintina da basu wuce talatin ba ta gama tattara komai nata, ta fito Momie na tsaye bakin k'ofa tana ganinta ta kauda kai, a hankali take tafiya ta k'arasa inda take, har k'asa ta duk'a tana k'ok'arin rik'e kukanta.

  "Zan tafi Momie, don Allah ku yafemun duk laifin dana muku, Nagode da duk Alkhairan da kukamun, tsakanina daku sai addu'ah, bazan taɓa mantawa daku ba"

  Ko kallonta Momie batayi ba, ta mik'e gwiwa a sanye ta fice ko Hafsat bata nema ba, tunda taga Ubanta taci gaba da zaman a hannunshi kawai.


Kuyi haquri da ɗan kaɗan, A gurguje dai.


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

       74


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


 A hankali take tafiya, ko kallon gabanta batayi, harta kusan fita daga layin, tafiya kawai take tana jefa k'afa batasan inda take dosa ba, wayanta na k'ara a handbag anma batasanma tanayi ba, saida wani mai adaidaita sahu ya kusan ture ta sannan ta dawo hayyacinta, yanata faɗa ko kallonshi ma batayi.

  Duk inda take tunanin zataje, tunaninta ya gama tsayawa akan komawa k'auye, domin kuwa bata da inda yafi can, bata tsaya wani ɓata lokacin tunani ba ta wuce inda zata shiga motan Katsina, gaba ɗaya zuciyarta taa dake, kukanma nemarshi tayi ta rasa.


  Yasseer ne kwance a gadon asibiti yana kallon sama, hawayene kawai ke ratata a idanunshi, ko k'ifta idanu baya iyayi, anya kuwa ya kyautawa Saude da Hafsat? Anya kuwa hakk'in Saude zai barshi? Wannan rashin adalci har ina?

  Najib ne ya share mishi hawaye, bayan ya zauna gefenshi, "Meyasa bruz? Meyasa zakayi saurin yanke wannan ɗanyen hukuncin?"

  A hankali yace cikin zafin ciwo da kuma zafin da zuciyarshi ke mishi, "saboda ban cancanci Saude ba, ban cancanci kasancewa da ita ba, laifukana a wurinta sunfi k'arfin a lissafa, hak'urinta da kawaicinta yayi yawa, bazan iya ci gaba da tauye mata hakk'i ba, shiyasa da sauri na yarda da umurnin da Momie kemun, mezaisa naci gaba da rik'e igiyoyin aurenta bayan abubuwan dana mata a baya? Da bakinta ta faɗamun yanzu ta daina sona, kai take so"

  Ɓata rai sosai Najib yayi, "ka dainama faɗar haka bruz, babu sauran soyayya tsakanina da ita, Na tsaneta, tsanar da ba'a taɓa ma wani halitta ba, bazan taɓa bari mace ta haɗani da ɗan uwana ba"

  "ka daina faɗar haka, kuskurene tayi da babu wani ɗan Adam da yafi k'arfin yinsa, mutuniyar kirkice, kuma mace ta gari da babu kamar ta a duniyarnan"


  Mik'ewa yayi ya fita daga wajen ɗakin da aka kwantar da Yasseer, don maganar Saude ma wani bala'inne yake k'aruwa a cikin zuciyarshi, bazai taɓa iya daina sonta ba, anma abunda ta mishi bazai iya mantawa ba, cikin zafin rai ya fiddo wayanshi ya fara neman layinta, saida ta kusan katsewa ta ɗauka bata ma duba ko waye ba, ta kara a kunne, ba tare da tace komai ba, tama manta data ɗauka wani kira, sai dai ta barshi da sauraren k'aran tafiyan Mota hakan ya tabbatar mishi da har taa tafi.

  "Kin gama abunda ya kawoki kin tafi ko? Kin riga kin gama cutar da zuciyatah da soyayyarki, saida akazo wurinda bazan iya rayuwa babu ke ba zaki fitomun da asalin halinki, kin cutar dani Saudat, kin sakani nayi k'azamiyar soyayya da matar aure, kin cutar da farin cikina"

  Wani irin numfashi taja cikin sark'ewar kuka, Buɗa baki take anma ta kasa magana, saida ya gama faɗa mata duk abunda yazo bakinshi, sannan ya kashe wayan ya barta da tarin bak'in ciki.


  Lokacin data isa gidan dare yayi sosai, gaba ɗaya ta gama galabaita, dak'yar ta iya kai kanta gidan, yasha gyara yayi kyau kaman bashi ba, ta kwantar da kanta jikin k'ofar sannan ta fara k'wank'wasa, ta daɗe a haka kafin azo a buɗe, Kawu da Gwaggo ne sukazo buɗewa, ana buɗe k'ofan ta faɗa da yake jingine take a jiki, da sauri Gwaggo ta rik'ota tana sallallami.

  Kamata tayi suka shigar da ita ciki, tambayarta suke meya faru gaba ɗaya hankalinsu ya ɗaga, kasa basu amsa tayi saidai kuka kawai, ga wani irin zazzaɓi daya rufe ta, sai wani irin numfashi mai zafi take fitarwa, su duka babu wanda bai tausaya mata ba, gwaggo ce ta samu zani da ruwa tana sanya mata a jiki, a haka harta samu barci.


  Washe garima tana tashi sai kuka, idan tana tuna abubuwan da suka faru da rayuwarta ba k'aramun tausayama kanta take ba, dak'yar ta iya musu bayanin abunda ya faru ganin yanda hankulansu suka tashi.

  Su duka suka saki salati, Kawu harda kuka bilhaƙƙi ya tausayawa ma Saude, karo na farko tunda ta taso a hannunshi, cikin kuka yake cewa.

  "laifin mune, mu mukaja miki koma menene ya faru dake, bamu rik'e amanarki da kyau ba, kin rik'emu tamkar iyaye, anma muka mayar dake baiwah, muka lalata rayuwanki, mun cuceki Saude mun cutar da kanmu"

  Da sauri Saude ta rufe mishi baki, "Don Allah ku daina faɗar haka kawu, kun rik'eni na tashi a hannunku, ku kuka ciyar dani kuka tufatar dani baku taɓa korata daga gareku ba har kuka zaɓamun miji kuka aurar dani, kunmin abunda ya dace, ku daina ɗaurawa kanku laifi"

  "kayyah Saude! Tirr da hali irin nawa, dana kasa rik'e ɗiyar yayana, don Allah ki yafe mana Saude"

  "don Allah ku daina kawu, ni ban rik'eku da komai ba"


Gwaggo da itama tunda suke magana kuka take, ta bala'in tausayawa rayuwar Saude, "Anma dai mutanennnan tirr da taimako irin nasu, Allah zai saka muki abunda suka miki"

  "A'ah gwaggo karki musu Allah ya isa don Allah, mutanen kirki ne, sun rik'eni tamkar jininsu, na ɗauka abunda sukamun a matsayin ajizanci na ɗan adam"

  Kawu yace "Naji daɗi da kika baro musu er su a can, domin kuwa babu mu babu su har abada, yanzu ne zasu san kema kina da gatanki"

  Duk sai taji kamar an yaye mata kaɗan daga cikin damuwarta, daman tunaninta kawai yanda su kawu zasu amsheta, a ranar ya sanya aka gyara mata ɗaya daga cikin ɗakunan gidan da akayi da kuɗinta, donshi yanzu har sana'a yake da kuɗin data bashi, gatan da bata samu ba tana yarinya yanzu suke nuna mata, ko kaɗan basu son suga ta ɓata rai yanzu su duka zasu damu, wani kulawa sosai suke mata kamar er da suka haifa.


  Kwanciyan Yasseer Asibiti, Rabiah da Najib ne ke kula dashi, ko yaushe tana tare dashi duk da bai wani bata fuskar da zata ɓata mishi rai, hakanan ma saiya rufe ido kaman yana barci, anma hakan bai hanata kula dashi ba, don ta samu labarin duk abunda ya faru, wani k'ara sonshi ma take da taji labarin ya saki Saude.

  Satinshi biyu aka sallameshi daga asibiti, ya gama warkewa sai dai damuwa da baza'a rasa ba, tare da Rabi'ah suka koma gida Momie, tana k'ara kula dashi anma ko kaɗan bai sakar mata fuska, wani irin haushinta yakeji idan yana tuna da cikinshi da zata zubar, yasan halinta na tsayuwa akan magana ɗaya indai tace zatayi bazata fasa ba.


  Ahmad Ya kalla Najib daya gama bashi labarin duk abubuwan da suka faru, domin kuwa shi amininshi ne, bashi da abunda zai iya ɓoye mishi, don tun dawowanshi ya lura yana cikin damuwa, bayan fasa auren da akayi.

  "kana nufin yanzu ka daina son Saudat ne?"

  Wani harara Najib ya mishi, "duk labarin dana baka tambayar da zakamin kawai kenan? Bazaka faɗamun Saudat bata kyauta ba, kaman ma baka damu da abunda tamun ba"

   "indai bata kyauta maka ba, abunda aka mata ma ba'a kyauta ba, ka ɗauka kaine ita wanne irin hali zaka shiga a yanzu? Ka tausaya mata itama mana"

  "Babu tausayi tsakanina da macen da taci amanatah, sauran tsakaninsu ne, ko kana so kacemun inci gaba da son matar da yayana ya aura?"

  "Yasseer ya riga da yaa saketa, kuma a addinance aurenka da ita ba haramun bane duk kuwa da yana raye, kuna son junanku kai da Saude, ni banga wani laifi ba anan ciki"

  "ko babu sauran mace a duniya bazan iya zaman aure da Saudat ba, ballantana akwai mata da yawa a ko ina"

  "Yau kuma kaida bakinka? Kar dai kacemun kaa daina son Saudat"

  Wani wuri a hannun Ahmad Najib ya nuna, "menene wannan?"

  "tabon ciwo mana"

 "yaa warke ba?" ya ɗaga mishi kai cikin rashin fahimta.

  "kamar haka ciwon son da nake ma Saudat zai warke wata rana"


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

       75


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


  Rabi'ah ce tsaye kan Yasseer, yana kwance idanunshi a rufe anma ba barci yake ba, duk maganan da take hankalinshi ya tafi wurin tunanin halin da Saude take ciki.

  Hannu ta sanya ta shafi cikinta, "mu tafi ko? Tunda Abbanka baison ganinmu"

  Wani irin zabura yayi, "Abbansa kuma? Kina nufin kin shirya haihuwa yanzu?"

  Ɗaga mishi kai tayi tana murmushi, ta kamo hannunshi ta ɗaura saman cikinta, yaron cikin sai motsi yake, shi kuma Yasseer yanata murmushin jin daɗi.

  "tayaya zan iya cire gudan jininka daga jikina? Idan nayi haka ai koni da kaina zan iya k'aryata soyayyar da nake maka,"

  Wani irin farin ciki yakeji, ya kwantar da kanshi jikin cikinta yanajin wani irin farin ciki marar misaltuwa.

  "Don Allah ka yafemun, ka manta da duk wani abu dana taɓa maka, a shirye nake da zama duk irin macen da kakeso"

  "kin biyani Rabi'ah, kin gama biyana indai kika haifamun abunda yake cikinki, Na gode sosai"

   "naji, anma ai akwai abubuwa da yawa da nake maka wanda bakaso plx ka faɗamun in daina, kana yawan cewa Saude mace ta gari ce, anma baka taɓa cemun ba ni, plz Masoyi nima inason in zama kamarta"

   "Allah ya baki iko dear, tabbas ina yima sauran mata addu'an kasancewa na gari kamar Saudat, komai yaa wuce dear"

  Murmushi tayi "Ina tausayin Saude, wata rana zamuje neman gafararta"

  "Nagode da wannan soyayya Hniee"


  A yanzu Rabi'ah na iyakar k'ok'arinta na kauda ma Yasseer damuwa, soyayya take nuna mishi kamar jaririn goye, soyayyar da koda tana Amarya basu yita ba, sai yanzu ne yake tabbatarwa da yayi sa'ar mata, ya yardar ma kanshi kuma Soyayyarshi dai ɗayace, kuma Rabi'ah yake yimawa, tausayin Saude ne kawai mak'ale a ranshi shiyasa ya kasa mantawa da ita. Basu daɗe a gidan Momie ba suka tare a sabon gidansu da aka gama gyara musu, daman gaba ɗaya suka tattaro suka dawo Nigeria.


  Najib kam kullum babu barci, babu cin abinci sai tunanin Saude kawai, yaa kasa manta zaman da sukayi da ita, ta bar mishi abubuwan da bazai taɓa iya mantawa da ita ba, duk yabi ya rame soyayyar Saude na wahalar dashi sosai, idan kuma yana tuna abunda ta mishi duk yanda yaso yaji haushinta bazai iya ba.

  Momie tana lura dashi, ba k'aramun tausayawa ɗan nata take ba, da taa bashi ɗan lokaci tasan zai manta da Saude ne, anma har kusan 4 month kullum damuwarshi k'aruwa take.

  Ita da kanta ta tafi ɗakinshi kai mishi abinci, yana kwance rigingine 

baimasan hawaye suke zuba a idanunshi ba, tunaninshi yake da Saude a zamansu, kullum cikin nishaɗi bata yarda ta ɓata mishi rai, ranar daya fara koya mata karatu ya tuna, shi kaɗai ya dunga dariya kamar zararre fuskarta na dawo mishi tana dariya da kyawawan hak'oranta.

  Motsin mutum yaji da sauri ya share hawayenshi cikin dubara, ya ɗauko wayanshi yana latse-latse, sai ga Momie ta shigo da sauri ya tashi ya amsa kayan hannunta.

  "Momie keda kanki kuma?"

  "ai hakan kafiso ko?" Ta zauna saman gefen gadon, ya zame k'asa zai zauna, ta kalleshi "Zaunanan magana zamuyi" ya tashi ya koma gefe ya zauna.

  Kallonshi take duk ya rame ya fara fita hayyacinshi, yayi fari sosai duk ya koma sukuku dashi kamar ba Najib ɗinta ba, da alama damuwar take ranshi harta fara fin k'arfinshi.

  "Ina lura dakai duk kwanakinnan, akwai abunda kake ɓoyemun, ba halinka bane ka faɗamun ko me yake damunka"

  Ya lumshe idanunshu da duk sun faɗa, "Ba komi Momie"

  "ka faɗamun nace, har yanzu ka kasa mantawa da Saude ko?"

  "Wace Saude kuma? Nina manta da ita da daɗewa Momie, don Allah ki dainama tunamun da ita" ya k'arasa maganar cikin damuwa.

  "Naji, indai hakane tun yaushe nake maka magana daka fito da matar aure? Da dai ban sanka da saɓa ma umurnina ba"

  Yaja wani wahalallen numfashi, "Momie nifa gaba ɗaya matannan tsoro suke bani, bani da wani zaɓi sai wadda kuka zaɓamun"

  "shikenan tunda ka barmun zaɓi, Allah yayi maka albarka ya zaɓa maka ta gari"

  "Ameen Momie"

 "daga yau banson k'ara ganinka cikin damuwa, in baso kake nima ka ɗauramun damuwa ba"

  "Insha Allah momie naa daina"

  Tashi tayi ta bashi wuri, itama a ranta duk batajin daɗi, tana mutuk'ar kewar Saude, gidan duk ba daɗi da batanan, tana ɗebe mata kewa, idan tananan komai bata bari tayi da kanta, ga Hafsat kullum cikin neman mamanta take, gidan yayi kamar ba kowa tunda Saude ta tafi duk basujin daɗi.


  Najib tun ciwo na cinshi a tsaye harya kwantar dashi, gaba ɗaya ya rame sosai sai an kaishi asibiti, an maido ana tunanin ya samu sauk'i sai ciwo ya dawo sabo, gashi yak'i buɗa baki ya faɗa kome ke damunshi, idan ance mishi Saude yace ba ita ba.

   Ranar daya tashi basu tsoro basuyi tunanin zai kwana ba, suma ya ringa yi daya farfaɗo sai kiran sunan Saude, ko kaɗan bai cikin hayyacinshi, Momie har saida ta zubda mishi k'walla tayi mutuk'ar tausaya mishi.

  Yasseer ya isketa falo inda tayi tagumi tana tunani, durk'usawa yayi saman gwiwoyinshi, ya langaɓe kai irin yana neman alfarma a wurinta.

  "Momie yanzu da kika gano damuwar Najib meyasa bazaki mishi maganinta ba? Don Allah Momie karmu rasashi"

  "bansan me zanyi ba, Najib yanason Saudat anma me mutane zasu ce akan ya aura matar da yayanshi ya saki?"

  "abunda mutane zasuce zamuyi tunani ko abunda addini ya halarta? Tabbas Saudat MATATAH CE a da, anma yanzu babu wani sauran alak'a tsakaninmu da ita, na rantse da Allah babu sauran wani abu da nakeji a raina game da ita, ina mata kallone a matsayin k'anwatah, indai don nine Momie don Allah karku raba masoyannan guda biyu dake matuk'ar son junansu, tabbas munyi zaman aure da Saude, anma na k'aramin lokacine watanni kawai mukai a tare kuma babu wani shak'uwa a tsakaninmu, su kuma fa da suka yi shekaru suna gina soyayyarsu? Najib shine masoyin Saude na gaske, shi yafi cancanta da ita".

  Momie tayi shiru jikinta a sanyaye, "ni jikina duk yayi sanyi da maganganunka, ka tuna da abunda akama Saudat fa, kana tunanin zasu sauraremu?"

  "momie kefa kika fi kowa sanin kyawawan halayenta, tana da mutuk'ar kawaici da saurin yafiya, tana kuma girmama buk'atunki, sannan itama nasan har yanzu tana nan da soyayyar Najib, kinga dai dai kenan, taa gama iddarta babu sauran neman aure cikin aure"

  "hakane fa duk abunda ka faɗa a kanta, wallahi har kunyar kaina nakeji abunda na mata, yanzu da wanne ido zanje neman alfarma a wurinta?"

  "karki damu Momie, insha Allah komai zaizo da sauk'i"


  Dak'yar aka samo kan Najib, ya farfaɗo anma dai yana kwance babu k'arfi jikinshi, sai dai k'arfin hali kawai.

  Momie dai da taga taa tashi rasa ɗanta, ta tabbatar da indai ba samun Saude yayi ba shima zata iya rasashi, batayi shawara da kowa ba ta shirya tafiya garinsu Saude, daga ita sai driver da kawunnan su Najib guda biyu.

  Batasan yanda zasu amsa maganar da zataje da ita ba, tun a hanya take ta addu'ah a ranta Allah ya basu nasara ya sanya komai yazo musu a sauk'i.


©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

      76


```second to the last page```


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


  Su Momie sun isa k'auyensu Saude, kai tsaye gidansu suka wuce, Momie da kanta ta shiga gidan tun daga soro ta fara k'wala sallama.

  A tsakar gida taci karo da su Saude Gwaggo bilki na sanya mata jan lalle a k'afa, suna ta nishaɗinsu kamar basu ba, duk da Sauden ma tayi rama anma ko kaɗan babu alaman damuwa a tare da ita.

  Ita ta amsa ma Momie sallamanta, taji daɗin ganinta don murna kamar taje ta rungumeta takeji don har Abada kallon uwa take mata.

  Gwaggo ta gama saka mata laida a k'afan ta mik'e tana mata sannu da zuwa, "ku shigo daga ciki Hajia" ko kaɗan bata canja mata ba akan abunda sukama Saude

   "A'ah Gwaggo nanma yaa isa kusa da y'ata,"

  "tohh sannunku da zuwa, aikam kunsha hanya"

  "aikam dai" saida ta kawo mata ruwa mai sanyi da zoɓon da take siyarwa, sannan ta zauna suka fara gaisawa kamar daa can yanda suka saba.

  "kunyi Sa'a kuwa Mallam ɗin yana kasuwa, anma na aika yanzu za'a kirashi"

   "to ai ba komi"

  Ita da Saude dai sai er kunya, tunda ta gaisheta bata k'ara ɗagowa ba, sai wasa take da lallen hannunta, tanaso ta tambaya Momie Hafsat, anma ta kasa, da yake Gwaggo ta basu wuri sai dai ta tsinkayo muryar Momie.

   "Saude kinyi mamaki da ganinmu ko? Mun kasa samun sukuni tun bayan tahowarki, tabbas mun miki laifi, mun sani saboda kullum cikin dana sanin abunda na miki nake, kin tunasar dani akan karna yanke hukunci cikin fushi, anma nai burus nahau dokin zuciyah na miki hukuncin da yafi qarfin laifin da kika aikata, hak'ik'a ke alkhairi ce, kuma Allah kaɗai yasan abinda yake ɓoye na shigowarki rayuwarmu, gani da k'ok'on barana, ina fatan zaki yafe mana abunda muka miki nida yarana Saudat"


  "Haba Momie, kefa mahaifiyatah ce, duk abunda kika zartar a kaina dai dai ne, babu uwar da zata nema gafara a wurin er ta, ballantana ni ban taɓa rik'e iyalinnan a raina ba, kunmin abunda bazan taɓa mantawa ba, Alkharin da kukamun babu abunda zan iya saka muku dashi, tsakanina daku sai dai addu'ah"

  "nagode Saudat, kyawawan halayenki basu misaltuwa, nayi bak'in ciki da cewar ke ba 'yatah bace, anma bazan iya rasaki a matsayin suruka ba" dammn gabanta ya faɗi, ta buɗa baki tana kallon Momie kamar bata ida yarda da maganarta ta k'arshe ba.


 Bata iya cewa komai ba sai ga Kawu Ado ya shigo, da iyayen ledoji a hannunshi, Gwaggo ta tarbeshi ta amsa tana mishi sannu da zuwa, fura ce ya kawo a dama ma su Momie da nono mai yawa, harda gasassun kaji da lemuka, shima bai nuna mata wani sauyi a fuska ba suka gaisa faran-faran, sannan ta nema magana dashi suka shiga ɗaki, a saman kujeru suka zauna sannan aka k'ara gaisawa.

  "tohh Malam, gani dai da k'ok'on barana, laifine an riga an yishi, basai anyi tone-tone ba, don Allah ayi hak'uri kuskurene irinna ɗan adam"

  "haba Hajia, ai wannan magana tuni taa wuce, Allah ya yafe mana gaba ɗaya"

  "Ameen"tayi shiru kuma tana tunanin yanda zata ɓullo da sauran maganar.


  "tohm sai kuma idan babu damuwa, nazo ne ina neman alfarmar in koma da Saude a can ɗin dai"

  "Can ina Hajia? Saude kam ai tazo gida" kawu ya faɗa ba bayan ya fara rage fara'arshi.

  Rok'onshi ta shigayi, kamar ta durk'usa mishi bama kamar data faɗa mishi wai har da wakilan Najib ta taho a ɗaura aure kawai, ai kauda fuska yayi sam baisan da zancen ba. Don bazai manta da wulak'ancin da Yasseer ya musu ba har yanzu, aka tara mutane ya bashi auren Saude anma ya butulce musu a k'arshe.

  Cikin damuwa take faɗa mishi halin da Najib ɗin ya shiga, tana faɗa mishi duk tausayi ya cika mishi zuciyah, ya share zufa yana fita da hular dake saman kanshi, ba haka yaso ba anma Hajia duk taa karyar mishi da gwiwa, bazaiso ya k'ara bada Saude inda za'a wulak'antata ba, don yanzu ji yake da ita kamar tsoka ɗaya a cikin miya.

   "Shikenan Hajia, ni yanzu bani da ta cewa, sai abunda yarinya ta zaɓa, anma ni bazan tilastata akan abunda bataso ba"

  Murmushin jin daɗi Momie tayi, "Nagode Mallam Allah yabar zumunci, ni zanyi magana da Sauden"

  Tana daga waje, ba laɓe take musu ba, anma tana jiyo maganganunda suke, saida ta zubda k'walla data ji halin da Najib ya shiga, tabbas itama rayuwa bata mata daɗi da babushi, ita kaɗai zata kulle kanta a ɗaki tayi ta kuka idan ta tuna shikenan yanzu sun rabu, ba k'aramin daɗi taji ba da maganar da Momie tazo da ita ba, anma ta kanne kawai.


  A gabansu Kawu Momie ke neman amincewar Saude, kanta a k'asa bata ɗago ba cikin kunya tace "bani da wani zaɓi sai abunda Kawu yace, koma miye zanyi biyayya a kanshi"

   "karki damu Saude, banda burin k'ara tauye miki hak'k'i, don Haka zaɓinki shine nawa" inji kawu.

  Momie tace "kada ki k'wari kanki, ki fito fili ki faɗa mana abunda ke ranki, wallahi bazan taɓa ganin laifinki ba Saudat" ita duk sun ɗaureta da maganganunsu, ta jawo hijab ta lulluɓe fuskarta, Murmushi sukai su duka sun Fahimceta.


  Washe gari su Momie da wuri suka dawo aka ɗaura aure, don cewa tayi bazata tafi ko ina ba saida ɗiyarta, taron jama'a akai sosai wanda tunda ake ɗaurin aure ba'a taɓayin kamarsa ba a k'auyen, Kawu ya kashe kuɗi sosai akaci aka k'oshi harda masuyin guzuri, da wuri Momie ta ɗauka amarya suka wuce Abuja, tun kafin subar k'auyen ta fara kuka, yanzu son zama take sosai da su Kawu ko kaɗan batason rabuwa dasu. Don dai kawu yace bazai iya barin k'auyen ba, saboda shi ya saba tun kakanni anan ya tashi.


  Kai tsaye Momie gidan da Najib da Saude zasu zauna da ta wuce da ita, daman taa saka an gama gyarashi, suna zuwa mai gyara Saude na jira aka shiga gyarata, cikin ɗan lokaci ta fito tsaf Amaryarta, kafin a gama gyarata daman Momie taa wuce gida lokacin har Magriba ta kusa.

  Najib na zaune falo ya fara samun sauk'i, shida Ahmad ne yaazo dubashi suna zaune shima duk ya damu da halin daya ganshi ciki.

   Su duka suka gaisheda Momie, sannan Najib yace "Momie ina kikaje harda kwana baki faɗamun ba?"

   "neman aurenka naje, Alhmdlh dana dawo na iske ka fara samun sauk'i"

  Ya kalleta da mamaki "aurena kuma?" ta ɗaga mishi kai cikin tabbatarwa. "koka manta kaa bani zaɓine?" yayi shiru.

  Sannan ta kalla Ahmad "yauwah daman ko ban iskeka ba zan nemo ka ne, kazo ciki inason magana dakai"

   "tohh Momie" tana shiga ya mik'e yabi bayanta.

  Najib dai binsu yayi da kallo kawai, maganar Momie ma dariya ta bashi, a hakan za'a mishi aure dare ɗaya kawai?


  Bai tashi shan mamaki ba saida yaga Ahmad yazo mishi da sabbin ɗinki, ya tsareshi saida yayi wanka, ya shirya shidai dariya ma suke bashi.

    "wai kai wanne irin wasa ne wannan? Binku nake fa kawai inga inda zaku tsaya"

  "tohm ai daman ango lallaɓashi ake"


  Saude na zaune tsakiyan makeken gadonta, tana lulluɓe cikin mayafi ko ina k'amshi ne a jikinta, dare ya fara nisa duk a tsorace take, ta jiyo k'aran motoci, sannan ta saki ajiyar zuciyah.

   Tananan Zaune taji an buɗe k'ofa, Najib dai tafiya yake kawai, duk da maganganun da sukai da Momie kafin ya tafo bai k'arasa yarda wai da gaske aure aka mishi ba.

   Yana buɗe ɗakin dai-dai lokacin Saude ta yaye mayafin kanta saboda zafin da ake, ai suna haɗa ido yayo baya da gudu Ahmad na niyyar fita ya rik'oshi.

   "Saudat ce, da gaske aure akamun?"


I m Apologising wanda auren Najib Da Saude bai musu daɗi ba, anma har idan Saude bata aura Najib ba sak'on da nakeson isarwa bazai kammaluba, bincike nayi sosai kuma dai duk maganar ɗayace, Auren Saude da Najib bai haramta ba koda kuwa Yasseer yana raye, harda hakan yasa ban kashe Yasseer ba kaman yanda wasu sukaso😄 inda a gaske abun ya faru fa? Don dai karin maganar nan ta hausawa (ana barin halak don kunya) anma ba wani haramcin zama a cikin auren Saude da Yasseer, Nagode sosai gareku Masoyana. Masu cewa zasu daina karantawa! Daman page ɗaya ya rage, ko babu wanda ya karanta Alhmdlh fatana dai Allah ya bani ikon kammalawa lafiya.😄

   Inata yinshi a gurguje, kudai ci gaba da hak'uri dani plz, zan fara hidima ne, bazan samu lokacin typing ba shiyasa.


 ©Rabiatu sk msh

♡MATATAH CE♡

  ♡♡♡♡♡♡

     77-100

   K'arshe✔


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

           

      Labari....Ilileee


www.babymsh.blogspot.com


  Ahmad ya turashi, "Miye haka zaka wani faɗomun? Kaa damu mutane da Saudat! Saudat!! Saudat!!! Yanzu kuma ta zama taka da ganinta kaa wani rugo?"

  "tohh aini naa kasa yarda ne, da gaske Saudat MATATAH CE?"

  "gaka gatanan dai, sai ka tambayeta" Najib sai murna yake yama rasa inda zai saka ranshi don farin ciki, Ahmad ya k'ara zai fita yasha gabanshi,

   "ka faɗamun gaskia da gaske nayita kiran sunan Saudat?"

   "gaban Momie da Yasseer ma kuwa"

  Hannu ya saka ya toshe bakinshi, "ashe ina sonta har haka?"

  "Gashi kuwa da ganinta a gidanka harka warke"

   "hakane fa" ya faɗa bakinshi har kusa da kunne don daɗi ma ya kasa rufuwa, sai kuma ya juya ɗakin Saude da sauri ya koma don gani yake kamar zai koma ya iske batanan.


  Tananan a inda ya barta, yayi sallama, da zazzak'ar muryarta ta amsa. Ita ɗince kuwa, ya faɗa a ranshi, ta wani k'ara yi mishi kyau sosai a ido, ya kasa daina kallonta ga wani irin soyayyarta da ke fizgarshi, a hankali yayima kanshi mazauni a bakin gadon.

   "Saudat!!" ya kira sunanta, har saida tayi murmushi kyawawan hak'oranta suka fito, yaushe rabon da taji ya kira sunanta? Tayi kewar ganinshi sosai, ga tausayinshi da takeji ganin ya rame.

   "Da gaske ke ɗince kuwa? Da gaske ke MATATAH CE? don Allah karki faɗamun mafarki nake, idanma mafarki nake ki faɗa musu kar a tasheni, don ko a mafarki nake tare dake, bazanso in tashi ba har abada"

   Ganin yanda ya ruɗe saboda farin ciki, itama sai murmushin jin daɗi take, gangarawa tayi inda yake, ta ɗaura hannuwanta biyu saman k'irjinshi sannan ta kwantar da kanta, tanajin bugun zuciyarshi.

  Ajiyar zuciyah ya saki, ita ɗince kuwa, ya sak'alo hannunshi ya ida mak'ale ta a jikinshi kamar wani zai k'wace mishi.


  Ya tafi duniyar jin daɗi, yau Saudat ta zama tashi, kuma sai tunanin Yasseer ya faɗo mishi, anya kuwa yasan da aurennan? Wanne irin kallo zai mishi idan yaji yaa aura matar daya saki? Bazai iya yin abunda zai taɓa ran yayanshi ba gaskia! Zare hannunshi yayi daga jikinta. Ta ɗago kai tana kallonshi lokaci ɗaya taga yanayinshi ya canja.

   Ya mik'e zumbur, yayi hanyar fita, "ki kwanta, ina zuwa" ta kalleshi cikin rashin fahimta, yaɗan dawo ya durk'usa a gabanta shima baiji daɗin yanda ya mata ba.

  "Abunda na miki kin yafemun?"

  Hararanshi tayi da wasa, "idan kaci gaba da tuno abunda ya wuce bazan hak'ura ba"

  Murmushi yayi ya ware hannunshi, "naa daina, Meyasa ma nake mantawa da Najib baya laifi wurin Saudat?"

  Murmushi, yanzu hankalinshi ya kwanta da bata cikin damuwa, ya juya ta tafi ɗakinshi, shidai yasan suna matuk'ar son junansu shida Saudat, anma tayaya zai iya rayuwar aure da matar da yayanshi ya saki?. Ɗakin da yake a matsayin nashi ya koma, anan ya kwanta ya kwana tunani.


   Tun tana zaman jiranshi taji shiru, kaɗan kaɗan taa duba lokaci, sai taayi kaman ta kirashi a waya saita fasa, duk ta damu tana tunanin ina ya tafi, zuciyarta ce ke zugata ta k'yaleshi kawai duk inda ya tafi dai yasan yaa barta tana jiranshi ai, tana kishingiɗawa barci ya kwashe ko kaya bata canja ba.

  Da wuri ta farka duk da bata samuyin barci da wuri ba ga gajiyan tafiyan da sukasha kuma, bata nema komawa ba ta shiga kitchen da niyyar ɗaura musu girki.

  Muryanshi ta jiyo, "badai girki zaki ɗaura ba? Momie tace zata aiko dashi"

  Ta jiyo har yayi wanka yana cikin shirinshi, anan ya kwana ko gidan Momie? Bazata iya tambayanshi ba, sai dai ta gaisheshi kawai.

   "lafiya lau ya kika tashi? Ya gidan?"

  "Alhamdulillahi" sai kuma sukai shiru, shi bai tafi ba, kuma bai bata hanya ba.

  "kin jirani a jiya?" ta ɗaga mishi kai, ya wani zaro ido.

  "kindaiyi barci ko?" ta k'ara ɗaga mishi kai tana murmushi yanda ya zaro ido.


  A tare sukayi breakfast, suna gamawa yayi kamar ya fice, ya shige ɗakinshi kawai, banson yana yawaita zama kusa da ita saboda yanda soyayyarta ke fizgarshi, gashi baison fita, gani yake kamar insun haɗu da Yasseer zaice mishi bai kyauta ba.

  Haka zaman nasu yake, sai tayi da gaske, zata ganshi sau ɗaya a rana, duk yanda zata tsareshi da fira bazai zauna ba sai yayi dubara yabar inda take, kuma bai wani nuna mata a fuska, tun abun bai damunta harya fara, gashi ita ba wata k'awah ba da zata nema shawararta. Kullum Momie zata kirata taji ya suke, koda abunda take buk'ata, wani lokacin har ta haɗata da Hafsat a waya suyi fira.

  Suna wata ɗaya da aure Husna ta mata waya Rabi'ah ta haihu, ita kaɗai ta ringa tsallen murna, yanzu zata fita ta huta da zaman kaɗaici a gida.


  Saiga Najib ya fito daga ɗakinshi, yana ganinta yasan tana cikin farin ciki, "Rabi'ah ta haihu" yace mata

   "Yaushe zamuje mu gano Baby?"

  "Bazaki je ba"

     "Ganin Babyn Rabiah fa nake nufi, ina son inje plz zamuje yanzu?"

  Cikin kakkausar murya Asalin Najib ɗin data sani tunda yace "bazakije ba nace"

  Jikinta duk yayi sanyi tace "tohm" sai kuma duk baiji daɗi ba, ya ɗan rage murya anma dai cikin faɗa faɗa, "Duka yaushe akai auren da zaki fara fita? Ko so kike kowa sai yasan kin dawo?" ya ida magana duk don son ta tanka, baiji daɗin tohh ɗin data ce ba tunda ya ɓata mata rai, shiyasa yake so ya gyarota.

  "A'ah" kawai ta k'ara cewa a tak'aice, saima ta tashi ta barshi kawai, don batason ganinshi cikin ɓacin rai.


  Har daren suna, bataje ganin jaririn Rabiah ba, sai dai Husna ta tura mata da hotanshi, ko maganar ma taa daina mishi, suna zaune Husna ta k'ara mata waya.

   "Gaskia Auntie Saudat da alama gobenma Ya Najib bazai barki zuwa ba, wannan irin kulle haka?"

   "Zanzo Insha Allah Auntie, Baby dai kar yayi fushi da Auntienshi plz"

   "Mamanshi dai tace har yayi, don wannan Autien tashi bata damu dashi ba"

  "A'ah auntie Rabiah kartace haka mana, Allah inanan ina fama da hotanshi, kamar inyi tsuntsuwa inzo, ɗan kyakkyawan Babyn mu kamar bab...."

  Sai kuma tayi shiru maganar ta mak'ale mata, ganin Najib ya tsura mata indo tunda take magana yake kallonta, "Sai nazo dai Auntienah" ta katse wayan.

  "Rabiah ma tasan kina gidannan?"

  "ya bazasu sani ba? Muna waya dasu sosai" shiru yayi yana tunani, anma ya akai insun haɗu da Yasseer bai taɓa nuna mishi ba? 

   "ki shirya muje siyayyan Babyn"

  "Da gaske zamu fita?"

     "da wasa nake" ta ɗan ɓata rai duk murnarta ta koma ciki.

  "idan kina ɓata ɗai bazamuje ba" tayi dariya, da murnarta ta shirya suka fita.


  Siyayya sosai suka masa, sannan suka wuce gidan Momie, murna sosai tayi da ganinsu, bama kamar da taga Hankalin Najib a kwance, ba k'aramin murna tayi ba, saiji take dasu gaba ɗayansu.

   Hafsat ma tunda ta mak'alema Saudat tak'i barin jikinta, sai labari take mata duk wanda yazo bakinta, ita dai amsa mata kawai take saboda kunyar Momie gata er fari, Najib ya mik'a hannu zai kamota, "ni bakiyi kewata ba sai mamanki ko?"

    "kaima naayi taka, anma nafi daɗewa banga Mamanah ba"

  "ai tare zamu tafi ko? Kiyita kallon mamanki kullum bazaki k'ara kewanta ba" sai kuma ta mak'ale kafaɗa, "idanna tafi kuma chohuwarnan zatayi kewata"

   "laah! Waye chohuwan?" yace mata

Momie dai dariya take musu, "ai bama zan barki tafiya ba, su Rabi'ah ma sunyi naci sun bari, Hafsat tananan wurin tsohuwa"

   "anma dai za'ana bamu aronta ko?"

  "saina duba dai"


   Hafsat tace "Mamana wai menene soyayyan gaskia?"

  Kamar ta buge bakinta saboda kunyar data sakata, gashi Momie na wurin don ma Allah ya taimaketa kaman bataji ba, "ke ina kika taɓajin wannan maganar?"

  Yasseer dake shigowa yace "nizan baki baki amsar wannan tambayar! Soyayyar gaskia itace kaso mutum tsakaninka da Allah ba don wani abu nashi ba, ka zama mai rik'e amanarshi, duk laifin daya maka zuciyarka bazata taɓa ɗaukan laifinshi ba, kullum kuna cikin fahimtar juna, Masoyin gaskia shine wanda zai kasance dakai a kowanne hali, shine wanda bazaka iya jurar rashinshi ba na kowane lokaci, Soyayyar gaskia shine kaso mutum a duk yanda yake"

  Hannu ta ɗaga tana tafa mishi, su Saudat kam sai dai dariya kawai, "ya isheki hakanan ko kinason na baki misalin masoya na gaskia?"


  "yayanmu ashe kana kusa?"

 Saude ta katse musu firan, Najib ya kalleta da mamaki,

  "yanzu na iso, ashe rabon in gaisa da Amaryarmu,"

  "Ina wuni"

    "lafiya lau fatan duk kuna lafiya"

  "Alhmdlh, ya baby?"

    "Rabi'ah bata faɗa muku yana fushi ba?"

  "yau dai zamu goge laifi, don wannan tafiyar tashi ce shi kaɗai, ko yaya?" ta kalla Najib ya ɗaga mata kai, sannan Yasser ya mik'a mishi hannu suka gaisa, firansu sukaci gaba dayi.

  Ba Momie kaɗai ba, har Najib sunji daɗin yanda Yasseer da Saudat suka manta da baya, suka manta da komai suka rungumi k'addara.


  A gidan Rabi'ah kowa sai ji yake da Amaryan Najib, bama kamar danginshi sun hana bakinta shiru, wasu ta sansu tun wurin biki wasu kuma sai suna sukazo, cikin sakin fuska take gaisawa da kowa, kamar en uwanta, sai faɗi suke gaskia Amaryan Najib nada kirki.

  Rabi'ah taa yaba sosai da kayan da Saudat ta kawo, sai ɗaga kayan ake ana tayasu Godia, Yasseer har kamar yayima Najib faɗa, wai miye sai sunyi wani hidima, sai dare sosai suka koma gida, washe gari da wuri ta saka ya maidota suna, haka sukaita hidima har bayan suna.


  A gajiye ta dawo, suna shiga falon tayi hanyar ɗakinta, hutu kawai takeso, saida ta kusan shiga yace "inajin yunwa fa" 

   "Me zakaci?"

     "komai ma indai daga gareki ne"

  Jikka kawai ta ajje, ko kaya bata tsaya ragewa ba, ta shiga kitchen, mai sauk'i ta girka mishi, fried couscous, ta haɗo mishi da cocunut juice, yana falo ya baje yau kallo yakeji, ta ajje gabanshi ta fara zubawa.

  Ya zuba mata ido, "Momie fa ta hanamu Hafsat, Haka zamu zauna ba yara a gidannan?"

  A ranta tace 'A'ah satosu zamuyi, ko kuma insha a ruwa tunda kaa nema hak'k'inka naa hana'

  A zahiri kuma tace "ai tace zatana bamu aro ai"

  "abun aro kam an taɓa ado dashi? Kamata yayi fa muma da namu"

  "hakane" ta tak'aita zancen, tana gama zuba mishi ta wuce ɗakinta.


  Da mamakinta yana gamawa ɗakin nata ya shiga, sai da ya tadata sukayi sallahn godia ga ubangiji, suna gamawa suka kwanta, ga mamakinta ko kaɗan bai nemeta ba, ita abun nashima yanzu yaa wuce bata mamaki, har hak'urinta ya fara k'arewa.

  Hakan zaman nasu ya koma, zasu kwana a ɗaki ɗaya, anma ya bata baya kawai, da rana ma indai yana gida suna tare da juna, yana k'ok'arin sakata nishaɗi a koda yaushe, anma babu wani bayani. 

  Ta gaji da zamansu a haka, da taga da gaske yake dai, ta k'udura lallai yau zata kawo k'arshen komai.


  Wata fitinanniyar rigar barcinta ta gyarama zama, yana fara kallonshi ta rigashi tafiya kamar kullum, tun wurin wanka saida ta ɓata lokaci sosai sannan ta fito, ananma ta daɗe gaban mirrow tana shafa mayuka, turarukan da Husna ta bata kusan duka ta juye ma jikinta, duka ɗakin ya ɗauka k'amshi, maganunguna kam ta ɗuresu ingantattu wanda Husna ta haɗa da kanta ta san mata, data zura doguwan rigan ita da kanta tasan taayi kyau, milk ce mai santsi, shara-shara gata er qarama ko gwiwa bata kai ba, ta kwanshe gashinta data nannaɗe, ya zubo har wurin k'ugunta, shima yasha gyara ta ko ina k'amshi take, kashe wutan ɗakin tayi ta koma ta kwanta.

  Tana kwanciya ya shigo shima da shirin barcinshi, ya kunna wutan ɗakin, gaba ɗaya daddaɗan k'amshin dake tashi yaa cika mishi hanci, ai da sauri ya maida ya kashe yana hangota, ga wani irin kwanciya da tayi mai jan hankali.

  Ya k'ara kunna fitilan yana k'are mata kallo, anya kuwa zai iya kwana a ɗakinnan? Gaba ɗaya ganinta ya gama birkicewa, k'afafunshi dak'yar suka kaishi inda zai kwanta, duk k'amshinta ya cika mishi hanci, sai juyawa yake yana satar kallonta, anma dai k'ok'arin lallasar zuciyarshi yake, shifa ba abunda yakeso ba kenan, Sauden dai yakeso.


  Tsawon lokaci ta jishi shiru? Anya kuwa Najib lafiya yake? Yau zata gane ma dai, wani irin juyawa tayi ta k'amk'ameshi ta baya, jikinshi har kyarma yake, ba k'aramun ruɗewa yayi da jinta a jikinshi ba, ya saka hannu ya fara janyeta, cikin wata rikitacciyar murya, a hankali cikin raɗa tace "mafarkin tsoro nayi, tsoro nakeji plz karka sakeni" tuni ta k'arasa kashe mishi jiki, baija da tsawo ba, nan take labarin ya canja.

  Tun daga ranar wani son juna ya k'ara shiga tsakanin Najib da Saude, koda yaushe yana manne da ita, kullum k'ara sonta yake, koda na rabin second baison ya ganta nesa dashi, ko ina ta saka k'afarta suna a tare.

  Sanda ta fara laulayi kusan a tare sukayi, idan tana wahala kamar ya mata kuka, ganin yanda yake damuwane take k'arfin hali indai suna a tare.

  Gashi Cikin daya tashi girma sai yayi k'ato, dak'yar take tashi, hutu musanman ya ɗauka don ya ringa kula da ita, don hana Momie ma yayi a koma da ita gida.


  Sanda ta tashi haihuwa ma ba k'aramin wahala tasha ba, kwana biyu suna asibiti tana aikin nak'uda, har saida aka kawoma Najib takarda ya saka hannu za'a mata C.S, yak'i ya saka, shi babu mai yanka mishi mata, ana cikin rigima dashi nurse ta rugo tana faɗa ma likita ai kan jaririn ya fara fitowa.

  Lafiyayyun yaranta uku ta haifo, maza biyu mace ɗaya, ita ɗinma tana cikin k'oshin lafiya, a ranar ma aka sallamesu, duka iyalan suna cikin k'oshin lafiya.


   Najib sai murna yake, gashi tsakiyar yaranshi har uku, sai dai ya ɗauka wannan, ya aje ya ɗauka wannan, ya rungumo Saude a k'irjinshi, "bansan dame zan biyaki ba akan wannan kyautar da kikamun ba, Allah yayi miki albarka, Allah ya biyaki da Aljannah MATATAH"

   "Ameen"

  "wanne suna kikeso mu saka musu?

  "banda wani zaɓin daya wuce naka, sai yanda kace"

  "Muna da mai sunan Momie dai(Hafsat), su bruz sun mana wayau sunyi Daddy, tunda Maza biyu ne, sai mu saka mishi sunan su Mama da baba, Allah yaji k'ansu shi kuma ɗayan mu saka sunan bruhh"

    K'ara k'ank'ameshi tayi, tana k'ara jin soyayyar Mijinta, "Kaa biyani, wallahi ka biyani Mijina, Allah ya qara mana Soyayyar juna, mu zamu miji da mata har k'arshen rayuwarmu"

  "Ameen, Insha Allah ke MATATAH CE, har a Aljannah"


Waih😃 TAMMAT BIHAMDULILLAH.


  Anan na kawo k'arshen wannan littafinnan nawa, godia ga Allah (S.W.T) daya bani ikon kammalashi, kuskuren dake ciki Allah ya yafe mun.


Jinjina mai yawa gareka,

 Abdul'azeez ililee,

A thank you is never enough Especially for you, you have done end number of things to me, I don't know how I would be able to repay back. But, still thanks a lot for everything, you are the best.


RAZ, tsayawa faɗar matsayinku a gareni badai a wannan ɗan guntun littafinnan nawa, komai zan faɗa bazaiyi dai dai da irin matsayinku a wurina ba, hakik'ah ni Rabi'ah banda kamarku, sisinah AMRAH A. MSH da MY ZAHRA BB, Allah ya qara haɗe kanmu Ameen.


Dole kuna da fili a cikin littafinnan.

 My waliyya wally

 Kishiyatah Sadeey S Adam

Sis beely badaru

Aunty jegal

Pharty bb

Miemee bie

Kwaiseh maryama

Sistonah Zahra bukar

Autar hajia

Aneelurv

Aunty sis

Momienah didi Aneesa

Shafa'atu

Baby Amrah

Basma er lele

Basma mai sanyita

Chohuwa Candy

Kazar layyatah

Maman Adnan

Meesha lurv

Mrs Umar

My stylish

Ummiee Agos

Miss xoxo

Zeey Alk'aseem

S.A Azeez

My Inlaw Mjay 

Kdeey

Maman Haneep

Ayusha

Jiddah

Munayshat

Fiddausi sodangi

Biebie Isah

Ummul fadeela

Ashnur.

Aunty Maijidda musa

Aunty bilki Maman Sarki (Shaheed)

Aunty Asma'u musa Barah.

Ummu Zainabu (Haneesa).

Harma da wanda ban faɗa ba, bawai na manta daku bane, har kullum kuna raina.

```Fertymerh zahra``` tawa, kullum tunaninah dai INA ZANGA PHERTY? Dolene nazo ganin pherty don bazan gaji da gode miki ba, Allah ya qara basira.


My Abdul jega

Raheem jege

Abdul'azeez AAJ

Abba Gana

Gaisuwa mai yawa gareku👍🏻


En uwanah banda kamarku.

Hauwa'u sk msh

Fiddausi sk msh

Aysha sk msh


Masoyah na: Hak'ikah kune silar yin murmushina, ina ma ace zan iya lissafoku gaba ɗayanku? Tabbas banda kamarku masoyanah.

 Na gaisheku en group ɗin da nake ciki, dama duk inda littafina yake zuwa, nagode sosai masoya.

  RAZ NOVELLA 1&2, ku masoyane na hak'ika, nagode da wannan soyayya taku.


IYAYENA

Allah yaji k'anshi mahaifinmu da rahma ya gafarta mishi, Allah ya k'ara tsawon kwana momienah, Allah ya saka miki da gidan Aljannah, hak'ik'a Uwah ce ta gari, ina sonta fiye da rayuwatah!


  NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

  Ina Alfahri daku, Allah ya k'ara ɗaukaka, ya k'ara mana haɗin kai, gaisuwa ta musanman ga dukkan members na wannan k'ungiya mai Albarka.


Masu neman wannan littafin dama sauran littafaina, zasu iya ziyartar blog ɗina.

www.babymsh.blogspot.com.

  08032133670 whatsapp and imochat plz comment kawai, banda Maza👏🏻 follow me @instagram, Rerbee'art_sk, Snapchat Rerbee'at_sk


Nice dai taku Babynmashi😊

    

©Rabiatu sk msh


Tags: #matatace #Najib #saude #yaseer
24821
0
9
3
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

2019-04-14 09:04:21

2019-04-14 09:03:54

2019-04-14 08:31:13

2019-04-14 08:29:30

2019-04-14 08:28:40