Matacciya!

Written by Queen MermuePublished on 2018-12-14 23:26:06Category HorrorMatacciya. Irin yanayin nan da d'an adam mai mai numfashi yake shiga a sa'adda ruwan jini suka yi aniyar dulmiyar dashi... Zumunci bai yi tasiri ba, bai hana cin amana ba bai hana cutarwa tsakani ba. Ina laifin Madina dan ta kasance Matacciyar da ta d'auki alkawarin daukar fansa, ba wa ita ba, wa Mahaifanta biyu da akayi wa Kisan Izgili, rashin cikar burin ya sanya Zahara ajjiye alak'ar da take tsakaninta da Ayusher ta zama annoba, Matacciya mai yawo acikin jini da warin gawa har sai da ta kawar da masu cutar da zumunta a doron k'asa. tags: #queenMermue #horor #fatalwaDuba was labarai »

[:23PM, 10/13/2017] : *_MATACCIYA_*


*Na*

*QueenMermue*


*Babi Na d'aya*


_NI Madina_

*"Na kasance mai yawan Kallacce-kallacen horo films, haka zalika ina matuk'ar son abani labarin aljanu kowani al'amari mai ban tsoro.*

*da yawa mahaifina Idan yadawo ya tarar dani a gaban TV mafi yawa irin 11to 12am zaiyi fada sosai yace banida hankali ganin hakan yasa na matsa aka siya mun TV a daki Na, a kalla zan Kai 3am ina kallon horo, Amma Sam hakan bai raunana ibada ta ba"*

***

Sanye take da doguwar Riga ta uniform wadda bata wuce guiwukan ta ba k'afafunwan ta d'aure da sandal sai doguwar safa da ta rufe k'orikan ta, gashin kanta an d'aure shi da madauri. 

Da sauri da sauri take tafiyar yayin da take faman waige waigen bayan ta, 

Garin sai duhuwa yake karayi sanadiyar hadarin da yayi bak'i kirin ga tsawa da walk'iya daakeyi gabanin ruwa ya sauka. 

Jakar makaranta da ke bayan ta take faman zakud'awa, da kaganta kasan akwai farga ko tsoro a tattare da ita, sai faman numfashi take sama_Sama,

Da kyar ta ga ta shigo harabar kwatas din, sai da ta kai bakin get din gidan nasu kana ta kara gyara zaman Jakar ta ta juyo, 

Hankalin ta ya kwanta ganin mai bibiyar tata bai bayayyana ba,

K'ara juyawa tayi dan ta shige gidan, da sauri tare da tsinkewar zuciya ta K'ara juyo wa. 

"k'at k'at k'at! " hakoran ta suka shiga kakkaurawa da juna, 

Nan take cikin ta ya fara kuka,

Abinda idanun ta suka gano mata ne a gindin bishiyar yasanya ta wannan mummunan hali, 

"Ma...... Madihdihdi! "

Maganar ta kasa k'arasa fitowa, 

Wata irin tsawa mai firgitarwa akayi tare da sakin ruwa masu mugun k'arfi.

"Zarahhhhh! Kizo anan Muyi labari"

Zarah da tagama rikicewa da karfi ta shiga tura Get din gidan, ihu take iya karfin ta. 

"wayyo Allah na! Wayyo Daddy! Mummyyyyy!!! Dan girman Allah kuzo ku bud'e k'ofar!"

Madina dake zaune a gindin bishiyar Sanye da uniform irin shigar Zahra sai ita nata uniform dauke suke da fenti ja wanda yafi dacewa da akira shi da jini shar! Gashin kanta an raba shi gida biyu, gefen fuskar ta dauke da sabon ciwo wanda da alama yankan wuk'a ne ko wani abu mai kaifi, haka Ma gefen damtsen hannun ta dauke da sabon yankan jini danye shar a ciwon, duka kafafuwan ta jini ne kamar wadda tayi barin tsohon ciki.

Dariya tayi wadda ta bayayyana harshen ta da aka yanke ta gefe.

Mik'ewa tayi a tsaye tana mik'owa Zahra hannuwan ta biyu, 

"Zarah na Kizo ki rika ni zanyi fitsari, "

Ganin ta tunkaro ta ne yasa ta K'ara k'aimin ihun ta, 

"wayyo Dan Allah ki barni kada Kizo anan. "

Wata irin tsawa da walk'iya da aka tafka ne yasa ta K'ara sakin ihun da bubbuga get din da iya k'arfin ta, 

Daidai nan aka bud'e k'ofar get din tare da hasko fitila a fuskar Zarah, a gigice take k'ok'arin shiga gidan batare da ta tsaya ganin wanda ya bud'e ba ta afka a guje, 

Daddy dake rik'e da lema ya kamota da sauri ita K'ara janye jikinta tana ihu, 

"Zarah!!!me kikeyi haka? "

Da karfi yake Maganar sanadiyar ruwan da suka tsananta, jin muryar Daddy yasa tayi saurin k'amkameshi, 

"Daddy Madina ce gata can Zata biyoni wayyo daddy ka boye ni, "

Daddy da bai gama gane zancen ta ba ya haska fitila a waje nan take aka kwankwatsa wata Irin tsawa mai dauke da walk'iya mai kamar zata tsaga Sama cikin lokaci d'aya, Nan take torchlight din ta mutu, Zarah kam tuni kanta ya riga k'afafuwan ta isa falon gidan, Daddy ganin ba kowa a wajen yasa yayo cikin gidan tare da bubbuga fitilar.

Zarah tana ji Daddy yana knocking k'ofar dakin ta amma tak'i bud'ewa,

Kai kawo take a tsakiyar dakin da jikakkin uniform din ta ko jikar ta kasa cirewa sai naushin hannun ta takeyi, 

K'ara bugun k'ofar akayi da sauri tayi k'ofar cikin matuk'ar bacin rai 

"Daddy nace ka tafi kawai katafi nace! "

Shiru tayi lokacin da tayi arba da Yah Hisham a tsaye bakin ko k'ofar, 

Kauda kanta tayi tare komawa bakin gado ta zauna.

A hankali ya shigo dakin 

"Zarah meye haka Kin zauna da kaya da sanyi? "

"zan cire! "

Ta fad'a a tak'aice

"Zarah! Ajin karatun ki d'aya da Madina, Ranar da Madina ta bata ya akayi baki san da fitar ta ba?"

Cikin wani irin yanayin tsoro da bakin ciki ta juyo ta kalleshi, 

"dole Idan Zata fita sai nasani? An cemaka Dan kanta ya bata meye Na wani dogon bincike? "

Dan murmushi yayi,"Zarah ance tare kuka fita taya zakice haka kuma? "

A hasale ta mike tsaye, "Madina banida masaniya da Abinda ya sameta, ranar ko magana ba muyi akan mummunan Abinda ta aikata, "

Tana kaiwa nan ta shige toilet,

Shikam fita yayi cikin daurewar kai. 

Saida taji fitar sa sannan ta fito ta rufe k'ofar ta, jinginawa tayi a bangon dakin tare da sakin wani irin kuka, 

"Na shiga ukku ni Zarah! Madina meyasa ban kasan ce miki gata ba? Meyasa ban zame maki k'awa, uwa uba 'yar uwa ba? Laifi nane ko? Eh laifi nane wallahi da baki zama Matacciya ba"

Kuka take sosai, dorowar ta ta jawo tare da ciro wani photo dukan su biyu sunyi Dariya tare da rungume juna. 


_NI ZARAH,_

"nakasance......


*Duk wanda ya karanta ra ayinsa ne, tabbas akwai taba zuciya da kad'awar Hanta aciki 😐 mai tashin dare kasani fatalwa Na yawo a gari*_Ni Madina_


_"Kafin Na kasance Gawa kuma Matacciya wadda ruhi da numfashin ta suka bar gangar jikinta Nakasan ce wahalalliya a gidan Mahaifina bayan zamantowarsa Gawa yayinda Mahaifiyata ta kasance Matacciya!hmm bakuji komai ba nasan Bayan babu ni Zarah zata baku labarin irin tsanar da tsangwama da nake samu ta ko'ina"_


*BABI NA BIYU*

β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…


"Madina 'yar uwata ce kuma k'awata, ya kasance yarinyar da kowa bayaso Akan yawan laifukan ta, Amma ni kuwa sai na ta'allak'a hakan da yawan muzan tata da akeyi, 

Makarantar mu d'aya wadda ta kasance mallakin Familyn muce, karamar makaranta ce ta 'ya'yan Manya, yayin da ta kasance ta Jinsin maza da mata,

Ni Zarah nakasance tauraruwa a makarantar akan hazak'a ta, duka makarantar aji hudu Zuwa biyar ne a wannan lokacin muna aji Na biyar, yayinda babbar yayar mu Aisha takasance aji shida, Madina ta kasance muguwar dak'ikiyace, principal din mu ta tsaneta sosai, tun lokacin da ta zuba mata ruwan Lipton a jiki, Matsalar Madina ba anan ta Kare ba, Aunty Ayusha itace yayata, Duk fadin duniyar Nan Babu wanda ta tsana kamar Madina, nidai bazan iya cewa ga dalili ba saidai ina ta allaka hakan da son zuciya irin na Yaya Ayisha, da yake makarantar duk fada ake a wurin ta kasancewar mahaifin mu yafi son ta da kowa a makarantar,yanayin rayuwar makaranta mu abin haushi dan kuwa malamai su suke tsoron dalibai basu da karfin iko na tilastawa dalibi, Aunty Ayusha kuwa Malamin da tasaka aka kora basu da iyaka kasancewar principal ma fada yake a wurin ta.

Yah Hisham shine dan babban yayan su daddy wanda ya rasu tun yana karami Daddyn Madina ya dauke shi, tun Madina tana jss 1 yake son ta yayinda Aunty Ayusha take mutuwar son shi, wannan son da yake yiwa Madina yayi bala'in tasiri a kiyayyar da Ayusha take yiwa Madina, saidai ni a yanda na dauka Madina bata son alakar su tafi son ya auri Ayusha, hakan na matukar bani haushi.

Jameel kuwa yayan mune nida Ayusha, lalataccen gaske ne sosai tun yana Jss yake biyar mata, Madeena ta tsole masa ido.

Salees shine babban gayen makarantar yana aji shida a lokacin aji daya da Aunty Aisha, shine saurayin Madina wanda yasha wahala kafin ta aminta dashi, ya kasance matashi wanda ko wace budurwa so take a school din, frnd ne a wajen Aunty Ayusha sosai ganin yanda Ayusha ke walakanta Madina yasa yakasance mai tausayin Madina duk fadin makarantar shine mai kyautata mata har soyayya ta shiga tsakanin su wadda ni nasan yaudara kawai zaiyi, dan kuwa nasha jin suna waya da Ayusha suna dariya akan yadda yake shirin walakanta ta, ita kuwa Madina idan na fada mata ba yarda take ba,

Hakan yakansa muyi fada da ita dan mugun haushi abin yake bani,

Mu yan aji biyar karfe shida muke zuwa gida yayin da yan aji shida suke kwana anan ga mai bukata dan karatowar exams dinsu ana so suyi karatu sosai.

Aunty Ayusha a hostel ta tare amma ko jakar ta sai Madina ta kai mata hakan yasa bata dawowa gida sai karfe 8.

Yau ma kamar kullum ina parking jaka ta zan wuce gida dan an tashi daga makaranta ita kuwa madina tana a sit din baya tana sharban baccin ta,

Shigowar Ayusha ne da wasu daliban yasa na dago kaina, bukitin ruwa ne a hannun su ai kuwa suna zuwa Ayusha tasa aka wanka mata su.

"Dan Ubanki an tashi daga school kin barni da jaka?"

Da sauri ta mike tana jan numfashi akan ruwan da suka sarke ta.

"Yi hakuri dan Allah,"

Wani wawan mari ta banka mata tare da zube mata bukiti 

Daya tayi tsaki ta wuce yan korenta suka mara mata baya.

Rawar d'ari ta fara da yake sanyin maraice ya sauka, jika ta na bude na jefa mata towel dake ciki,

"Malama yi sauri ki canja kayan ki bani towel dina zan wuce gida tun da kin riga da kin zama jaka,"

Cikin bacin rai nayi maganar kamar ni akayi wa, murmushi tayi tace,

"Nagode Zarah, duk duniya bani da kamar ki kinfi kowa sona bakya son acuta mun ni kaina bana son kaina kamar yadda kike so na"

Guntun tsaki nayi na fice,

Da yake akwai wurin da muke canjin kaya kowa da drower ta a wurin dan kala biyu ko ukku muke zuwa dasu wani sa'in anan muke barin sport wears din mu.

Shiru-shiru bangan ta ba har duhu ya fara sauka hakan yasa na fito dan nufi dakin kaya,

Dai-dai shiga Girls room din na hango Ayusha da Salees suna kissing din junan su a cikin other room, mugun tsaki na saki dan ba yau ne na farko da nagansu ba suna wannan iskancin,

"Allah yasa waccan shashashar kada ta ganesu"

Abinda na fada kenan kana na fita na kama hanya zuwa gida,

Abinda bansani ba kuwa shine ashe Madina ta riskesu acikin wannan halin, haka ta shiga ta samesu nan ta fashe da kuka su kuwa daga Salees har Ayusha din dariya suka saka mata, cikin haushi da bakin ciki Madina tace,"Salees dama haka kake?"

Dariya ya karayi yaci gaba da kissing din Ayusha,

"Yarinya kike sosai Madee, Ayusha ce masoyiyata yayinda na kasance masoyinki"

Wata irin dariya suka kara saka mata,

Cikin haushi ta fita, ni kuwa acan bakin get na hadu da ita ta takure a gefe tana kuka hakan ya tabbatar min da ta gansu,

"Mtss dan Allah ki bani towel dina sakarya, akan banzaye kike kuka idan an gaya maki gaskiya kice hakuri hakuri,"

Murmushi tayi kana tace,"Yi Hakuri Zarah baki san irin damuwata bane,"

"Menene damuwar taki?"

"Yi hakuri basai kinji ba nafiso na rike abi ta,"

Tsaki nayi a bayyane,

"Kiyi ta zama da damuwa in kin iya ki haukata tunda ke kam haka Allah yayoki a matsayin sauna"

Ina kaiwa nan na wucewata zuwa gida.

Ina cike da bakin cikin abinda akeyiwa Yar uwata Madina,


Daddy na ya kasance makiyi a wajen Madina, sam baya son ta kullum cikin hantarar ta da zagin ubanta, nidai a yanda naji gulma cewa yana bakin cikin Madina ne dan itace mai ga do.


_NI MADEENA_


_"Ranar bak'ar rana ce! Ina cike da farin cikin dawowar mu daga kauyen mahaifiyata,_ _kwatsam akan hanyar mu Allah ya aiko mana da_ _mummunan hatsari, nidai bansan ya akayi ba sai a asibiti na ganni,_ _mahaifiyata ta rasu nan take yayinda mahaifina yake kwance akan gadon asibiti cikin mawuyacin hali, bayan na farfado ya bukaci gani na da kuma kanen sa wato Daddyn Zarah, kuka nake sosai jin cewa wasiya yake barmana_

_"Jameel ka rike Madeena amana kamar yadda zaka rike yayanka, duk da naga take taken ka amma ina so ka kauda komai a zuciyar ka, gado na kuwa ku biyu na bawa gadon mahaifiyar ta kuwa ya kasance mallakin ta dama mahaifiyarta batada magadi bayan ta,_ _dan Allah ka rike amana kada ka bari matar ka tayi nasara akan ka"_

_Yana kaiwa nan likitoci suka fitar damu ganin numfashin yayi nisa, Rai yayi halinsa Gawa biyu aka jera rana daya,_ _yayinda babu digon bakin ciki ko kadan a zuciyar Daddyn Zarah, Abinda zarah bata sani ba shine,_

Dalilin da yasa _Mahaifinta baya sona kasancewar dukiyar da yake tak'ama da ita tawace ni kadai, nashi gadon da aka bashi na mahaifana tuni matar shi ta cinye, dulmiya dulmiya yake da dukiyata dan duniya ta dauki cewa tashi ce,_

_Ni kadai nake zama a bangaren mahaifi na sai halayena daga lokacin na koma wata halitta ta daban."_


*BABI NA UKKU*

β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…


Bayan na dawo gida na fitar da uniforms dina dan a wankemun,

Haka kawai naji ina son karbo na Madeena a wanke mata dan nasan yau zata kwana tana bakin ciki haka zalika zata tafi makaranta gobe cikin datti.

Ni ba mai yawan shiga part din bace dan kuwa mahaifiyar mu ta hana mu, dan haka na bari har Mummy tayi bacci ko idan ta wuce dakin Daddy.

10:10 na kwankwasa kofar, jin a bude take yasa na fara shiga ciki,

Gidan ko ina datti da kura ne tsawon shekara biyar baiga shara ba,

"Madeee! Madeee!"

Daga falon kasa nake kiranta yayinda nake toshe hanci akan kurar da tayi yawa a falon.

Karar Tv na dinga jiyowa acan ciki dan haka na nufi ainahin dakin Daddyn Madee,

A falon na tsaya ina kallon tv dake aiki hankali na bai nuna min Madee zaune akan kujera ba, karasowa nayi ido na akan Tv,

"Eh shi ruhin Matacciya ne da Aka kashe ta shekaru dari da suka wuce har yanzu an kasa kwanatar da ita,"

"Mrs smith ya zamuyi a yanzu? Mu biyu ne acikin gidan nan yanzu haka ina jiyo takun fatalawar a falon kasa,"

Da gudu suka shige bayi suna shiga suka rufe,

Takun suke jiyowa yana gab da shigowa dakin,

Yayinda ko wannen su dauke da abun bugu,

Bil bil bil bil, fitilar bayin ta dinga daukewa da kawowa yayin ta dinga motsi kamar an mata lilo. Bil aka dauke wutar gaba daya,

Hakan yasa nayi saurin ajiyar zuciya dan azahirin gaskiya na tsorata kuma dama can ni ba gwana bace a fagen kallace kallacen horo,

"Maad!"

Numfashi na ya dauke lokacin da na hango mutum ya tsareni da ido,

"Wayyoh Allah, innalill....."

Cak ta rike hannayena yayinda ni kuma na durkushe a wajen dan dai nasan in ma fatalwar ce gudu na bazai tsiratar dani ba,

"Zarah meye?"

Jin muryar Madee yasa na dago kaina daga kareshi da nayi da hannaye na,

A jiyar zuciya nayi sosai kana in harareta nace,"ke kam wallahi kin ga bone kin tsare tv da kallon horo da karatu kikayi zai fiye maki ko tsoro bakyaji ke kadai a wannan gidan,"

"Yi hakuri"

Abinda ta fada kenan tsaki nayi a bayyane"nidai zo ki bani uniforms dinki idan zaki iya,"

Daki ta wuce na bi bayanta, abinda ya firrgitani shine ganin duka dakin zanen fuskokin mutane ne a bangon dakin,

A hankali na taka zuwa takardar fuskar mahaifinta ce zane, na juya daya ta mahaifiyar ta dukan su suna murmushi,

Dayan gefen fuska tace tare da Madee duka dariya muke,

Acan gefe na hango an makala takarda ukku mahaifiyata mahaifina Jameel yayana, dukan su a siffa mafi muni tayi zanen su, sun hade rai matuka,

Da sauri na juya bangon hagu, Hisham ne yayi smiling dayar kuwa Ayusha ce rike da jaka fuskar ta baka kirin kamar mai dauke da sakon mutuwa,

Gabana naji ya fadi akan gadon kuwa duka papers ne a ajiye, Salees take zanawa a yanzu, juyowar da zanyi na tambaye ta me hakan ke nufi naji numfashin mu ya sarke sanadiyar ashe tana baya na gab dani, ina juyowa na ganta a hakan saida na dan ja da baya,

Ni kaina nasan Madee nada ban tsoro wani lokacin hardai idan ta ware idanun ta,

Tambayar na fasa na karbi kayan da ta miko min na fice da sauri,

Ina kaiwa falon kasa difff wutar gidan ta dauke,

Da mugun gudu na fita.

Haka na kwana ina tambayar me zanukan fuskokin mu yake nufi? Wasu da murmushi acikin sifa mafi kyau wasu kuwa da mummunar siffa.


Da safe akan kofar gidan na hango ta tana jiran kayan ta dan haka na aika mata,

Bamu hadu sai a makaranta da ta shigo ajin a makare, banyi mamaki ba dan kuwa kullum zata rigani fitowa amma kaf makarantar sai kowa ya riga ta shigowa classes,

 Bayan an tashi breakfast ne na jata muka je kafteria acan mukaci abincin, wata studen aka aiko kiran Madee ko ban tambaya ba nasa Ayusha ce dan haka nayi zama na,

Saida na kare abinda nake na nufi ajinmu,

"Tunda tsirara kike so na fito shiyasa baki zo kikayimin wanki ba toh a yau ke zaki fita tsirara, shegiya banza cire rigar nan,"

Tsawa nayi ina kallon Ayusha da yan korenta suna kokarin maida Madee a tsiraraa, nasan zasu iya dan ba imani suke da ba dan haka na nufi wurin cikin bacin rai,

"Wai alAyusha meye haka? Rigar tata zaki cire?"

Na tambaye ta cikin bacin rai,

"Zarah zanci gidan ku! Kesan na haneki da shiga sabgata ko?"

"Ohk toh ki cire mata ai yau Yah Hisham zai dawo,"

Nace mata hakan ina hararar ta yayinda na kalle Madee da tayi tsaye kamar gumki"ke kuma sai ki jira amaidaki tsirarar sakarya,"

Ina kaiwa nan na nufi sit dina,

Ayusha kuwa jin na ambaci Hisham yasa ta fice da sauri rabin ranta zai dawo kuma tasan muddin ta aikata hakan sai ya cimata mutunci.


_NI MADEENA_

_"Yah Hisham ina matukar son shi tun ina yarinya hakan yasa nake murnar naji ance zai dawo, amma a wannan lokacin tsoro da farga suke darsuwa a kirji na aduk lokacin da naji ance zai dawo, ina son sa amma zuciya ta bata aminta da hakan ba yayinda ruhi na yake tabbar da bazai iya rayuwa mai dadi ba muddin ba Hisham a rayuwa ta, Aunty Ayusha! Eh itace tasa nake karfafa wa_ _zuciyata da cewa bana son Hisham, bayan shekaru ta fito da tsirfar cewa shi take so haka duka familyn sun goya mata baya dukda da sun san cewa mahaifina yabar wasiyar aure tsakanina da Hisham,_

_Wani tashin hankali da na shiga bai wuce irin yadda Jameel yasani a gaba yana neman lalata_ dani,

_"Aunty Ayusha ni bana son Hisham kuma ke zai aura dan Allah kiyi hakuri kada ki cuceni,"_

_Shine abinda nake yawan ce mata duk lokacin da ta rutsani da zancen Hisham,"_


*Babi na Hudu*.


β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…


"Kuka Madeena ta shiga yi, nasan bakomai bane sai irin wahalar da zata sha acikin satin nan domin duk Yah Hisham ya dawo azabar da take sha ta daban ce amma fa a abayan idon sa haka zalika koya tambaye ta bazata fada ba nice mai kaudin fada masa,amma da Ayusha takaini kara a wajen Daddy hakan yasa na tsame kai na a al'amarin su, amma fa kullum nakan zuga Madee da cewa kada ta yarda ta cewa Hisham bata son shi,

Da murna na shiga falon jin hayaniya a falon dan nasan kuwa har ya iso, Ayusha ma ashe ta baro hostel tayo nan gida, farin ciki ake sosai shekaru ukku kenan da tafiyar shi sai a yau ya dawo,

Mummy ta jani gefe muka rabe gashin kai na ta kama,

"Ke nasan munafika ce, toh kinga yar uwarki Hisham take so dan haka Dole waccan tayi hakuri nasan kece mai zuga ta, yanzu kice ta shiryo ta dawo part dinku dan kar ya gano wani abu,"

Da ba uwata bace da na shake ta wallahi, amma ina uwa tafi gaban raini koda kuwa batada hankali ne, cikin bakin ciki na kira Madee dakin Mummy Muka wuce,

"Mummy gani"

Inji Madee lokacin da duka, Mummy ta taso ta kama kunnen ta,

"Yayanku ya dawo, to ki dawo nan da zama saura ki dinga munafici kiga yanda zan hallaka ki acikin gidan nan, ki tashi ki fice mun ke kuma Zarah ki bata kayanki,"

Harare hararen da nake yasa Mummy ta kaimin rankwashi akai da sauri naja Madeena muka fice,

Dakina muka shiga nan tayi wanka nan nabata sabbin kaya na tasa,

"Saura idan Yah Hisham ya tambayeki maatsalarki kice ba komai,"

Cikin takaici nayi maganar,

Murmushi tayi ta kwanta gefen gado,

Ayusha kuwa ta tuburewa su Daddy Hisham take so hardai yanzu da ta ganshi ya kara wani mugum kyau, Da taje masa da zancen kuwa cewa yayi tayi hakuri shi Madee ce Matar shi,

Hakan yasa ta rufe Madee a daki tayi mata mugun duka,

Hisham kuwa daga kallon Madee yasan tana tare da matsala hakan yasa ya nemi Daddy da cewa zaije course na wata biyu a US yana so da ya dawo a daura aurensu in yaso acan in zai koma su tafi tare, Daddy kam zufa ta yanke masa dan yasan Madee zata nemi dukiyar ta kamar yadda mahaifinta ya bar wasiya cewa abawa mijin ta Hisham yasan lokacin ya rike hankalin kansa dan haka zai rike ta amana.

Daddy bai nuna masa komai ba kuma ya karbi bukatar Hisham,

Ranar da zai wuce ya nemi ganin Madee, Madee kam kuka tayi ta mishi har yayi zancen sa ya kare bata ce komai ba in banda kuka,

"Madee zan tafi kar ki damu auren mu nan da wata biyu da nadawo damuwar ki ta kare, Ki tashi ki tafi,"

"Yahh Hisham Ina sonka!"

Abinda ta fada kenan yayinda take kallom shi ido cikin ido,

Tsigar jikinsa yaji ta tashi dan bata taba cemasa hakan ba hasali ma har yayi zance ya kare ko dago kanta bazatayi ba,

Daga haka Yah Hisham ya tafi,

Ayusha da taji labarin auren kulle kanta tayi a daki daga karshe ta nemi kashe kanta,

Daddy da Mummy hankalin su ya tashi hakan yasa suka nemi hanya mafi sauki garesu,

Da na nemi Madee ta cigaba da zama waje na sam taki yarda hakan yasa mukayi fada da ita,

Yau an tashi daga makaranta Ayusha ta aiko kiran Madee, 

 Banji shigowar Madee gida ba har nayu bacci,


Da safe ina shiga get din makaranta naga kowa yana kallo na kamar yadda ake kallon takardun da naga an lika a ko'ina, da yake ana tsoro na sosai a makarantar babu wanda ya tunkaroni har nakai a class, 

Ayusha ta jefoni da takarda daya abakin class din,

Durkusawa nayi na dauka na fara ware takardar,

Gabana ya bala'in faduwa ganin poster din,

Ayusha tayi tattaki izuwa gabana,

"Ayusha wane irin kazafi ne hakan?"

Na fada cikin murya mai amon bakin ciki,

Wayar ta ta miko min wani short vedio ta nuna min tare da wasu pics masu muni,

Durkushewa nayi a wurin ina kukan bakin ciki.


_NI MADEENA_

_tashin hankali yayimin yawa alokacin da na zauna na tsawon sati daya a part din su Zarah, daga Mahaifiyar su har Ayusha da Yayanta Jameela dake neman lalatani kota ina, danaga abun yayi yawa nakai kuka na a wajen DaddynZarah"D'ana ba lalalatacce bani, ki hada naki da naki kibar min gida,"_

_Wannan maganar tayi min zafi matuka bansa lokacin da nace"Daddy ammma ai wannan gidan da makarantar kaf duk suka acikin gado na,_ _sa'annan idan ban manta ba Daddy yace idan zanyi aure abani dukiyar Mummy da kuma nashi gadon nawa, Yah Hisham zan bawa rabi kai kuma ka dauki rabi."_

_Marin da ya rufeni dashine yasa jini ya balle a hanci na,_

_"Tsinanniya har kin isa? Ko ubanki ya isa ne? Toh bari kiji nida kaina nasa aka banye birkin motar Yayana dan naci gadon sa tun ni Allah yaki bani arziki, naso har ke ki mutu alokacin amma da kike aljana kika rayu, to bari kiji dukiya tawa ce kuma Hisham keda auren sa sai alahira,"_

_Karfa kuyi tunanin mu biyu ne alokacin da yake maganar, a'a Matar shi na nan, haka suka korani,_

_Ayusha ta aiko kirana bayan mun tashi makaranta, ba tare da bata lokaci ba na sameta a bakin get cikin mota, ina zuwa tace na shigo,_

_Babu gardama na shigo duk da naji gabana yana faduwa bansan wane irin mummunan abu zata aikata mun ba,_

_Bakin wani karamin gida muka tsaya nan ta umurceni da na shiga ciki,_

_Hankali na ya bace bansan me yafaru ba, a gida na ganni ina barci a falo._

_Tashin da nayi ne naji banida lafiya ko kadan jiki na yana matukar ciwo,_

_Da kyar nake tafiya har na isa makaranta,_

_Postocin akayi ta jifa na dasu tun abakin get kowa ya tsareni da ido,_

_Gabana ya shiga dukan uku uku ganin photo na a tsiraice tare da wani saurayin wanda ba a nuna fuskar shi ba saidai ni da nake akan kirjinsa,_

_Hankali na ya bala'in tashi ta ko'ina sai yanzu na fahimci abinda ya faru dani a daren jiya, sam bazan iya tuna wa saidai nasan a windon gidan na hango Jameel yana lekon mu kafin mu karaso aciki,_

_Kuka nake sosai dalibai kuwa sai hantara ta suke da jifa na wasu yawu suke zuba min,_

_Ina shiga class na hangi Zarah durkushe akan benci ko ba'a fada ba kuka takeyi,_


_Malamai suke rufeni da tambayoyin abinda na aikata acikin office din principal, kuka na shiga yi sosai nan suka koroni bayan naci duka mai tsanani, suka ce zasu zauna da Uncle dina._

_Ana tashi school Ayusha ta shigo tare da kawayenta,_

_Mikewa nayi a hasale lokacin da take nunamin vedion, nice ake tozaltawa ajikin vedion tsirara haihuwar uwata, Ayusha dariya suka yi tare da tambayata ashe na amarce?_

_Wani wawan mari na bata har saida ta kai kasa._


*BABI NA BIYAR*

β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…


"Bayan Ayusha ta wuce na tashi a hasale na wuce disfiln commitee nan na bada umurni duk wata poster a cire ta haka vedion da ake ta share na sa aka karbe wayoyin su duka tare da goge komai, haka nayi ta yawo a makaranta ina bala'i da teachers da daliban duka,

Rai na yana kuna sosai,

Lokacin da Madee ta shigo ajin ko kallon ta banyi ba,

Littafin da nake karatu na ajiye da naji hayaniyar tayi yawa a wajen,

Ashe Madee ce ta mari Ayusha har saida ta fadi kasa, a hasale ta mike ta kama gashin kan Madee, 

Janta sukayi izuwa dogon hall,

Ina son nayi karatu amma hayaniyar su da kukan Madee da nake jiyowa yayi yawa dan haka na hada nawa da nawa na fito zuwa gida,

Madee turmushe acikin kasa Suna dukan ta, 

Ko kallon su banyi ba dan daga ita har Ayushar haushi suke bani,

Banida abinda zanyi wa Madee dan haka na gifta ta wajen ta zan wuce,

Kuka mai karfi take rike da marar ta, 

"Zarah zoki rakani zanyi fitsari,"

Ban kalleta ba naci gaba da tafiya,

"Zarah dan Allah kada ki barni zasu kasheni, kizo ki tafi dani, Zarahhh kawata."

Wannan shine kalma ta karshe da naji abakin ta.

Da safe ina fita naga polices a bakin get din mu,

Daddy na hango yana matsar fuska,

Hankali na a tashe na nufi wajen, cikin part din Madee na shiga,

'Yan sanda sunata hanani shiga, a guje na isa dakin Daddyn Madee,

 A firgice na fasa mugun ihu daidai nan police suka dinga ja na,

"Madeeenah!!!! Madeeeeennnnnnnahhhh! Wayyo Madeeena mekike a haka? Ki tashi nace ki tashi ki tashi"

Duk wannan sumbatun cikin rashin hankali nake maganar, kunsan me nagani?

Madee ce kwance cikin jini shar, yankan yuk'a a fuskar ta damtsenta, cikin ta kuwa an huda shi da yuk'a har ciki zaka iya ganowa, kafafuwanta kuwa jina jina dasu.

A lokacin da aka fitar dani somewa nayi ajikin Daddy.


_NI MADEE_


_wannnan marin da nayi wa Ayusha sai da nayi da nasanin zuwa na duniya ga baki d'aya._

_na wahaltu matuk'a ga irin mugun dukan da sukayi min, ciki na da suka luguda ko ba'a fad'a ba nasan nasamu mummunan rauni a wajen, da kyar na samu naja k'afa ta izuwa gida yayinda tuni idanuna sun fara zubar da ruwan jini, a get din gidan na had'u da Daddyn Zarah, da gudu nayi kanshi ina kukan fitar numfashi,_

_"Daddy Amana ce ni akan ka Daddy ka cuci Daddy ka kalleni kaga abinda yake faruwa akai na,"_

_hmmm kunsan me ya faru? Wani irin azzalumin mari ya daukeni dashi dai-dai nan Ayusha ta fito zata koma hostel tare suka fito da Jameel,_

_"tsinanniya ni bansan laifin da nayi wa Allah ba ya hadani zama da ubanki har kika zo duniya shegiya mai gyambom talauci,"_

_Jameel da Ayusha dariya sukayi sosai, "kai Daddy aini na samu abinda nake so da za'a barmin ita dan hutawa"_ 

_Jameel ne mai maganar, duka Ayusha ta kai masa, har zata wuce nayi hanzari na shak'o wuyan ta, "Sai duk na kashe ku, kai! Ke! Ku! Har ni duk zaku mutu nida kaina zan kashe ku makiya Allah maciya amana, Daddy banyafe Allah zai isar min."_

_dukan su mamaki na basu dan a iya sanin su magana wuya take mum sai gashi na haukace musu harda barazanar kisa_

_a iya lokacin da na shiga falon gida na ko mai bana iya gani, jini ne ke zuba a ido na sosai, da kyar nake lalabawa har na fad'a kan kujera,_


_da kyar numfashi na yake fita ga ciki na da yake azabar ciwo, Bacci mai tsanani ya daukeni, nidai iya abinda nasani shine naji saukar wani abu mai kafin gaske a damtse na, da sauri na kyalla ihu hakan yasa naji an danne ni sosai kusan mutum biyu ne, k'ok'arin ihun da nake yi ne naji wani irin mugun rad'ad'i a harshe na, daga lokacin kuma na kasa koma d'aga harshe na, "Ta Mutu muje kawai"_

_Shine abu na k'arshe da naji sai wani irin rad'ad'i da na dinga jiyo tun daga kan yatsa ta har izuwa tsakiyar kai na, hak'ik'a Mutuwa abu abuce mai ciwo da tsanani dukan ku nasan zaku d'an d'aneta kamar yadda naji ta, amma fa ku sani babu wani mahaluki da ya isa ya sanar daku azabar mutuwa har sai lokacin da ta riske ku._


*BABI NA SHIDA*

β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…


"Ban san me ya wakana ba har na tsawon sati d'aya, bayan tashi nane na dinga tuno abunda ya faru, Madeena ta zama Matacciya?? Hmm bak'in cikin da nayi ba abu bane na wasa ba, k'awayen Ayusha har party su kayi Jameel ne da Salees kan gaba, Wallahi-Wallahi nasan kashe Madeena akayi, ko duniya zata nad'e bazan yarda cewa ita ta kashe kanta ba, Daddy yayi min horo mai tsanai kamar yadda na tsane kowa nawa, haka naci gaba da rayuwar k'unci, Yah Hisham gwanin ban tausayi da aka shirya masa karya, basu barshi ya koma ba har saida aka daura auren sa da Ayusha,wannan dawowar da yayi itace ta biyu tun bayan rasuwar Madeena, kabarin ta yana acikin gidan na mu daga can bayan inda aka rufe mahaifinta da mahaifiyarta haka Mahaifin Yah Hisham wurin dai ya zama mak'abarta dan kusan kushewa goma ne a jere."


β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…

*cigaban labari*


Bata a hama ba da wannan tunanin da takeyi har tufafin jikin ta suka bushe kamar ba dukan ruwa ta sha ba,

Tsam ta mike ta nufi tsohon d'akin Ayusha,tsohuwar wayar ta ta dauko wadda tun aurenta ta ajiyeta.

19/9/2016 Wayar da Ayusha tayi da Jameel ta kai a ofishi dan a gano mata me suka tattauna a ranar, tabbas ranar anyi waya da mutum shida da sim din,na farko shine Jameel anyi waya dashi na har sau bakwai, Sai Salees sau hud'u, ukku kuwa kuwa wata Num ce da ba tada suna, sai na karshe a ranar shine Daddy.

Nan take a nemo record din duka Zarah ta had'a,

*19/9/2016,*

Wayoyi ne barkatai da Ayusha tayi,

Mafi yawa da Daddy ne,

Nan take Zarah ta gano komai shiri ne,

Fyad'en da akayi wa Madee da sa hannun Salees da Jameel had'i da Mummy karan kanta, babbar shirin itace Ayusha.

Abinda ya k'ara daurewa Zarah kai sai wayar da Ayusha tayi da Daddy a ranar *20/9/2016.*


A yanzu kam Zarah ta fahimce meye silar mutuwar Madeena.

 A hasale ta shigo gidan, kuka take sosai nan take ta fara magana acikin masifa da daga murya yayinda Daddy and Mummy da kuma Ayusha dake dauke da tsohon ciki suka jiyo cikin firgita.

"Kun kashe ta ko! Nasani dama aikin ku ne shiyasa kuka sani nayi shiru da baki na, to ku kalli wannan"

Tarkadun ta watsa musu tare da nuna musu wayar Ayusha nan take suka zaro ido su duka,

"Kee! Kinada hankali kuwa? Kinsan inda kike magana?" Acewar Daddy cikin daure fuska, ma tsowa tayi gab dashi,

"Eh Daddy ba!kuma makiyin Allah maki amana makashin Madeena!"

Wani mugun wawan mari ya kwashe ta dashi yayinda Mumy ta taso ta rike hannun shi.

Ko gezau Zarah batayi illa murmushi da tayi,

"Ayusha kin aure Hisham hankalin ki ya kwanta! Jameel ka yi lalata da Madeena hankalin ka ya kwanta! Mummy da Daddy, dukiyar ta ishe ku a ayanzu ko kuna bukatar karin wata?"

Hard'e hannayenta tayi taci gaba da zagayar su,

"Zaku ga mai zai faru, kotu zata karb'e ku hannu biyu sai naga karyar shaidan da zai fitar daku, dukan ku masu hannu ne a kisan kai idan kotu bata hukunta ku ba duk sai na kashe ku."

Hmmm kuzo kuga falon kamar ba kowa aciki dukan su sunnyi shiru suna mamakin Zarah, daga haka ta fice daga falon,

Ayusha da taji cikin ta yana mird'awa ta kalli Daddy cikin tsananin tsoro,

"Daddyyyy! Zata aikata jiki na ya bani zamu mutu kayi wani abu akan Zarah,"

"Daddy zufa ya shiga sharewa ya fice falon haka ma Mummy tayi d'aki, Ayusha na ganin haka ta figi motar ta zuwa gidan ta.


Zarah da ta fita bata dawo ba sai karfe sha d'aya na dare,

*20/9/2016.*


_RUHIN MATATTU_

_Hmmm!!!! Matacce shine wanda aka zare ransa daga gangar jikinsa haka a ka raba rai tsakaninsa da ruhi._

_fatalwa tana barin k'abarinta tazo duniya ne yayinda ta kwanta dauke da wani babban burin da bata cika shi ba ko kuma aka kashe ta ba tare da hakkinta ba ko idan lokacinta baiyi ba,_

_masana tarihin fatale sunce_

_shi gangar jiki yayinda ya kwanta kabari, akwai wasu mugayen aljanu da suke bibiyarsa muddin suka riske zuciyar sa da buri, hakan yasa suke tada gangar jikin su dawo da ruhin su shiga aciki_.


~a ina ake samun fatale?~

~next chapie~

*ina jin dad'in comments dinku sosai sune suke k'aramin k'arfin guiwa, nagode da k'aunarku sosai Allah ya biyaku, Ku maida hankali sosai akan wannan babin nafi so ku barshi zuwa 10:30 na dare ku karanta, duk kauna ce.*


*BABI NA BAKWAI*


"Suna na Salees, kuma nasan kun sanni a matsayin saurayin Ayusha da Madee,

Kamar yadda kuka sani na kammala secondary ne tare dasu Ayusha to yanzu haka ina jami'a ne aji d'aya, kamar kullum na dawo daga school ina cikin tafiya ne na hangi wata had'addiyar yarinya first class, 

Yawu na suka biya na lashe leb'en baki na, a hankali na gangara mota ta izuwa wajen ta, ko kallo na batayi ba hakan yasa na sauke glass,

"Wow a rayuwata ban tab'a ganin halitta mai kyau kamar ki ba, Dan Allah amma dai kin hada jini da saraki ko? Wai kinga tsayin ki ma irin na big babies dinnan ke ni ko a novels banji an lisafa irin naki kyau ba,"

Wani murmushi tayi min da ya k'ayatar dani, saidai abinda ya bani mamaki shine tun kafin nayi mata iso na tashigo motar ta bude murfin ta shigo, wani k'amshin ta ya dake ni kai dagani zatayi dad'i,

Lasar lebe na shiga yi kana na juyo na kalleta lokacin da nake murza sitiyarin motar,

"Baby mud'an je mu huta ko? Ko ya kika gani?"

Murmushi tayi tare da d'aga kai,

Cikin salon samun b'agas nace "bae ya sunan naki?"dariya tayi ta rufe fuskar ta hakan ya k'ara burgeni na kara kaimin gudun motar tawa,

*holewa d'adi Allah k'aro kud'i muji dad'in mata*

Abinda na fad'a a raina kenan lallai wannan yarinyar anyi gaula nan take na shiga kiran aboki na Jameel shima yazo mu huta a jikinta,

Ina kiransa ya d'auka kuwa,

"Maza!"

Daga can yace "yh Maza!"

Dariya nayi na dan kalleta da gefen ido ganin titi take kallo yasa na ci gaba da wayar"Maza sabon kamu sabuwar zuma mai kyau ko zaka d'ana dan dagani bishiyar ta iya rik'o"

Daga can Jameel yayan Ayusha ya shek'e da dariya,

"Ana Maza wlh zan zo, amma dai kazo nan gidan gonar Daddy dake a nan bayan gidan mu,"

"Ohk toh bari na juyo nan"

Daga haka na katse wayar dama tun da jimawa tun muna secondary idan muka samu na latsawa acan muke labewa da yake gidan gonar yana nan cikin Makarantar tamu amma shi acan baya yake, haka ma yamzu har kwana muke aciki mata sai kalar da muka kai.

"Hmmm Baby sanyin zuciya ni duk na kalleki sai naga kin k'ara kyau matuk'a gashi ko magana kinki kiyimun,"

Cikin kashe ido tare da dan rungumota nayi maganar har wa yau dai murmushi tayi mai kyaun gaske.

Tuni na matse dan jin nake kamar na parka motar naji dadi na dan haka muna isa bakin get din gidan gonar na kira Jameel inda ya shaidamun da cewa yana ciki tare da Safee baby,(k'awar Ayusha cikin masu take mata baya)

Dama itama 'yar hannu ce muna hutu da ita sosai,

A falo na sauke kyakkyawar Babyn tawa da yake an fara magrib alokacin, wanka na shiga yi kafin nayi mata iso zuwa d'aki yayinda Jameel suke daki daya,

"Baby ko zakiyi wanka ne?"

Na tambayeta ina daura towel a jiki na,

D'aga kanta tayi alamar eh,

Ni kuma dama yunwa nake ji dan haka na ce ta shiga bari inzo,

Tufafi nasa da sauri na ja key din mota,

Koda na fita hadari yayi bak'i sosai sai walk'iya da ake da tswa dukda ba a fara ruwan ba,

 Da kyar na iya lallabawa na dawo sanadiyar ruwan da aka fara,

Direct d'akin na wuce ina shiga na same ta zaune da yake babu wuta sai wayata da na kunna dan haka na ajiye wayar a mirrow nazo na jawota jikina dan muci kajin da na siyo,

Baki na da nata na had'a nashiga yi mata kiss na yan duniya lamba d'aya, a iya sanina duk macen da na fara kiss da ita sai ta nemi shid'ewa amma ita wannan ko gezau dan haka naso cire baki na akan nata,

Amma ina dagani hajira ta, mak'aleni tayi tun ina hak'uri har na dinga tura ta baya amma na kasa komai, numfashi na yayi k'asa sosai dan haka da k'arfin gaske na ingije ta yayin naja gefe ina maida numfashi,

Ido na zaro tare da mik'ewa tsaye lokacin da naga jikin ta duk jini ne,

"Innalill....."

Kasa k'arasawa nayi lokacin da aka tarwatsa wata irin kwatsatsa,


Da sauri naja wayata na nufi hanyar waje da gudun tsiya,

"Jameellll!" Wayyo wayyo Allah kuzo ku ganni lokacin da na bud'e dakin su Jameel, banga kowa ba sai Jina da nayi santsi ya jani, fitilar waya ta na haska ganina acikin jini tsumdum ya k'ara firgitani,

Mik'ewa nayi da sauri naja da baya,

A bangon gini na jingina ina fidda numfashi,

 Fad'owar wani abu daga sama yasani fad'uwa zaune wanwar, kunsan meye? Jameel ne aka rataye daga sama shine yake janjalinbo a silin din dakin, k'afafuwansa a daure sama, tsirara haihuwar uwarsa,

A halin yanzu banida karfin rike wayata dan haka can gefe take cikin jini,

Kuka mai karfi ya kwace mun lokacin da na fuskanci mutuwace tazo min,


"Wacece ke? Me mukayi miki?"

Cikin raunin murya nake maganar aikuwa sai ta bayyana a gabana,

_"Saleees yaro kake har yanzu"_

Wannan muryar nasan mallakinta kafin nayi wani yunk'uri ta bace batt,

Ai kuwa naja k'afa a guje, ruwa tsawa da walkiya alokacin basu gaba na, hanya mafi sauk'i na biya,

Saida ashe da shiri tayi min hakan,

Ina kaiwa bakin k'ofar da zata sadani da falon gidan aka fincikoni,

Acikin mummunar siffar ta ta bayyana,

Zara~zaran faratan ta tasa masu kama da tsinake ta kamo gabana,

Tale tale tayimin duk irin gunjin kukan da nake yi amma tsawar da ake ta hana ajiyoni,

Al'aurata ta cire gaba d'aya yayinda ta tsaga cikina izuwa bayana.

Jinin ta diba ta shafa ajikin ta.

Daga haka na rufe ido na na kasance *MATACCE*.

_k'idan tasoshi_


_Aunty queen wallahi wannan ya faru da gaske, dan Allah ki fadawa duniya cewa fatalwa gaskiya ce a garin mu ya faru._


_"mun kasance masu jin haushin 'yar uwar mu akan dukiyar da Allah ya bata, kowa jiran yake ta mutu yaci gado, kowa addu'ar mutuwar ta yake bawai dan tayi mana komai ba, haka zalika ta kasance mai saida abinci, wani rikici ya taba hada mu akan kwanukan abinci, nayi tsaye nace kwanuka nane alhali nata ne, abin ya matukar yi mata ciwo ba'afi sati ba Allah yayi mata rasuwa._

_da dare ne ta rasu dan haka akayi mata wanka aka kira wasu tsofi guda biyu akace su kwana da ita har safe a binne ta, tsofin nan suka zauna sai d'aya ta fara angajen bacci ita kuwa daya tana tashin ta, can bacci barawo duk ya kwashe su har carbin su ya fadi,_

_d'aya biyu! Yagga tawa ce wagga tawace, daya biyu ukku hudu, tasoshin nawa ne,_


_matacciyar ce ta mike acikin likkafanin ta ta nufi gun jeren dakin ta ta na kidayar tasoshin ta,_

_tsofin nan dayar da batayi saurin bacci ba tana falkawa ta hango Matcciyar na kidayar dukiyar ta ai nan take ta zauce a wajen dayar kuwa dogon suma tayi koda safiya ta waye daga su har gawar duk a kwance,_

_bayan an tashe su suka dau kuka saida sukayi sati biyu basa magana, nida mukayi fada akan kwanuka , ina bacci naji ana nishi, da yake bana jin me ake fada na kara saurara,_

_wagga tawa ce, wagga ma, ke Wance bani kwanuka na zan kwanta_

_saida nayi sati goma babu lafiya karshe daga nawa kwanukan har nata na hada nakai gidan su._

_kinji me ya faru Aunty queen ance mai daga baya kowa yaci gadon ta sai take zuwa tana basu tsoro daga karshe mai mutum ya haukace saida aka bada komai nata a sadaka sa'annan ta daina tasowa_.


_Fatale akan same su acikin daji ko kuma mak'abarta ko gindin bishiyar kuka._


*BABI NA TAKWAS*


β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…


*"Hmm suna na Zainab, nasan baku sanni ba amma dai nasan kunsan Ayusha ko? Yawwa toh k'awata ce sosai kuma nice mai bata shawara"*

Baifi awa biyu ba da mukayi waya da Ayusha ba,dan haka ganin Isha'i tayi naji bazan iya zuwa gidan ta ba kamar yadda ta buk'ata, 

Hankali na ba a kwance yake ba daga labarin da Ayusha ta fara gayamin, haka

Bacci mai dad'i na shiga yi ko sallar isha banyi ba, bayan karfe 8:00pm ta gota, a hankali na dinga jiyo haushin karnuka yana tashi, ga ciki na da naji yana mird'awa, da yake ni kad'ai ce acikin gidan sai 'yan aikin gidan mu dan kuwa Mama ta yi tafiya saida safe zata dawo.

Hmm wai kunsan kashin dare yana dad'i kuwa? Akan masai na zauna ina abina sai naji wani dad'i yana shiga ta,

Tabbas akace idan kayi mantuwa toh kada ka wahalar da kanka wajen tunowa jeka akan masai ko ka kabbarta Sallah,

Ina tsakiyar kashin wani mummunan tunani ya zomin, 

Abinda na tuna shine lokacin da mukeyiwa Madeena mugun duka a hall din makaranta, dariya nayi nace "Allahu akbar rayuwar makaranta mai dad'i"

Shabiyu daidai ina cikin toilet din daidai nan aka dauke wuta, wayata na kunna torch light, 

"Waih! Kwana na biyu banyi kashi ba kenan"

_"da gaske?"_

Zaro ido nayi jin kamar an yi magana a bayin, fitilar na haska a gefe da gefe banga komai ba,

_"Zainab"_ wata irin tabbatattar murya ce da nasani take kirana.

Wai kun tab'a had'uwa da wannan firgicin? Kina cikin toilet a kira ki da sunanki?

"Wahh wah! Waye anan?"

Da sauri da sauri na wanke kashin ko sabulu bansa ba na fito daga bayin, 

"Sadi!"

Na shiga kwalawa mai aikin mu kira,

Tana zuwa taga yadda jiki na yake rawa ta tambayeni meye,"kije ki kunna min jen yanzun nan"

Da sauri ta fita zuwa waje ni kuma daki na nakoma duk da hankali a tashe yake,

Bayan ta kunna ne na kwanta ina so nayi bacci dan kar na kara jiyo abinda naji, rufe ido na nayi tam dan nayi saurin bacci, uhrhhurhhh! Wani irin nishi na dinga jiyowa da gurnani mai tsananin gaske, rawa jiki na ya fara but still naki bude ido na, _"waaaahwuhhwuhwhu, yeeeyahha yeeeeeahhh iyauuuuuuuuuuuu!"_

"Wayyoh wayyoh wayyyyyyyyoh la'ilahha subh wa iyaz," muguwar hirgita nayu lokacin da naji wannan at dsm tym ina bude ido wutar dakin ta mutu,

"Innnah Sare! Inna Sare Mamma kuzo ku ceceni"

Wai kunsan waye Inna Sare? Mai aikin mu ce da har marinta na taba yi akan bata kirani Aunty ba yau nice da kiranta Inna, a zamanin da idan aka kira mutum da inna gani nake kazanta ce amma ayau sai naga salihanci ne,

A guje na fice falo nayi sa'a jaka ta na wajen, dan mugun ta maimakon na sanar da Sare me ke faruwa dan tasamu tsira inaaaa! Sai na fice a guje tashin mota ta kawai kila zata ji,

"Heeh heeh!" Haka nake ajiyar zuciya yayinda nake lalaben wayata na kira Ayusha,

Kwatsam naga bettery shutdown, jefar da wayar nayi naci gaba da gabza gudu,

Baifi 12ms ba na isa unguwar,

Ina shiga harabar kafin na isa gidan naji motsi bayan mota ta,

_zainabu abu, gel gel gel_

Zaro ido nayi yayinda na hangota ta madubi,

"Wah wah wah wwwwaaaye ke meeena nannan miki?"

_Madeeeeee! Ayusha ca kike wa wannan kallon?_

Wannan itace kalamar da nake amfani da ita duk lokacinda naso Ayusha taci uban Madeena,

Wai kunsan me?

Ta windown motar na fito yayinda najiwa kaina mummuman ciwo,

"Dan girman Allah dan girman Allah kiyi hakuri walllah ke san Allah? Wayyo ya zan miki ki yafeni? Na shiga ukk"

K'afa me naci ban baki ba?

Ganin banida ta cewa na wazga aguje na nufi get din gidan duk irin tsawar da ake da ruwan da ake tafkwa baji ba gani nake wazga gudun,

Ina kaiwa bakin get din saura kiris na afka cikin wani hangamin ramen da ya bayyana a gaba na,

Banida ta yi dan ramen kamar rijiya yake ruwan jini ne ke juyi aciki kundum ga sassan jikin mutane da nake hangowa,

_Zainabu? Zainabu? Hahhahahahahaha wooooooohhhh!_

Wata irin tsawa aka tafka da walkiya, tusssss kaji fashewar abu,

Kunsan meye? Kai nane ta fasa kamar yadda ake fasa Kankana a kan floor,

Kai na ya tarwatse yayinda kwayar idanuna suka zazzago inaji ina gani ta ingizani acikin ramen *MATATTU* yayinda na isa a matsayin *MATACCIYA*.


_*Uhum wai dai Madeee ce mai wannan fansar ko yah?*_*BABI NA TARA*


β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…

*MUMMY DA DADDYN ZARAH*


"Cikin rashin kwanciyar hankali muke kwance akan gadon, tun da aka fara ruwa da tsawa na tsuwar mu ta gushe, barin ma rashin ganin Zarah da bamuyi, hakan ya k'ara tada hankalin mu, Jameel kuwa munyi kiran wayar sa har mun gaji ba'a picking, nidai jin rashin nutsuwar tayi min yawa yasa na mik'e daga kwancen da nake,"

"Daddyn Zarah,ya kamata mu kira Ayusha muji ko Zarah tana gidan ta, irin wadannnan ruwan zasu iya illata ta,"

Daddy kam tsaki yayi ya k'ara juyi,

"Ban tare ki ba ai, ni kidaina damuna da zancen wata Zarah uban wa yace ta fita bayan ta ga hadarin nan,"

Cikin damuwa na kalle shi,"Haba Jameel Daddyn Jameel, yanzu fisabilillahi dan Laifin da Zara tayi bazaka iya yafe mata ba?"

Cikin fushi ya taso,"wai kesan me kike magana? Ai kina ganin yarinyar nan shaidu ne take tattarawa dan taga an makamu kotu wanda kuma tasan hukuncin kisa ne zai rataya akan mu duka,"

"Haba dai! cika baki kawai ne mana amma ina Zarah ina wani iya shiga kotu, dan Allah ka taso muje duba ta, ko k'ila tana bangaren can(da nufin bangaren Madeena dan jiya acan ta kwana) wata kila can ta zauna,"

Mik'ewa yayi tsaye cikin bacin rai,

"Ba inda zani, in ta iya ta mutu ai ita taja..."

Bai k'arasa zancen ba ya fad'a kan gadon a guje tare da kankame ni, nima abinda nayi kenan sanadiyar wata irin walk'iya da ta gitta ko ba'a fad'a mun san ta fad'o a gidan mu,

"Innalillahi! Daddyn Zarah zamu mutu tsawa ya fad'o mana, wayyo na shiga ukku"

Shiru mukayi jin ta lafa,

"Ke wai wace irin shasha sha ce,wannan tsawar kike ma ihu? Sakeni dan Allah sakarya kawai,"

Mikewa yayi daga yanda ya had'a kansa da bargo, sam bamuji bude k'ofar dakin ba Sai Zarah da muka gani a tsaye,

Dukan mu mun firgita ainun, da sauri nazo na rungume ta,

"Zarah ina kikaje ana ruwan nan haka?"

Kauda kanta tayi kana ta juya baya,"ina wajen Madeena!"

"Madeenah!?"

Muka fad'a a tare cikin muguwar tsorata,

"Eh Madeena, menene na firgita haka?"

Tassss Daddy ya kwashe ta da wani irin gigitaccen mari amma ko gezau batayi ba,

"Ke dan Ubanki mu zakiyi wasa da hankali? Madeenar gidan ubanwa kika gani?"

Wani irin hot smile ta bamu, "Madeenar gidan ubana!"

Ta bamu amsa babu ko tsoro a tattare da ita, mukam tsaye mun kayi kamar wasu samudawa, saida ta kai bakin k'ofa ta juyo,

"Muna tare da ita yanzu haka a gidan nan, tazo ta kashe ni ne, amma bana tsoron kisa a yanzu,!"

Wata irin mummunar kwatsatsa aka saki nan take rabin bangon d'akin ya tsage yayinda wuta mai k'arfi ta gifta tare da tafiya da bangon,

Nan take d'akin ya zama abin tsoro bangon ya fad'i kana iya hango harabar gidan ta baya, Nikam da Daddy tuni mun zata mun rasu ne,

A guje na nufi stairs zuwa k'asa, Daddy kuwa ganin Zarah tana mik'a hannun ta izuwa inda bangon ya tsage yasa cikin hanzari ya finciko ta wanda baifi saura taku d'aya ba ta fad'a,

"Madeena me nayi maki zaki kashe ni? Dan ban fad'i gaskiyar lamarin ba? To idan na fad'a wazai tsaya maki?"

Cikin kuka take maganar tana turjewa da janta da Daddy yakeyi,

Da kyar yajata suka iso falon k'asa nikam tuni na fara suntiri ina jiyo k'amshin mutuwa,

Daddy tsoro ne ya kamashi matuk'ar gaske,

Had'e kan mu mukayi dani dashi a firgice yayinda Zarah take tsaye k'aik'am,

Wata irin mummunar inuwa ta fara giggittawa a falon,kamar mutum sanye da dogon Hijabi,

Nan take wata iska tazo mai k'arfi tare da tsawa mai gumzar gaske,

"K'at k'at k'ar'" hak'orana suka shiga had'ewa,

_Daddyyyyy_

Wata irin murya mai k'arfin gaske ta fad'a nan take Madina ta bayyana a gaban mu cikin shigar ta ta Uniforms,

"La'ilahailallahu, Ya k'ussu! Zuljalali wal ikram,"

Abinda baki na ya iya kamowa kenan tare da wani irin fitsari mai zafin gaske,

Daddy kuwa rungume ni yayi yayinda ya turani a tsakiyar k'afafun shi, kan sa kuwa yayi k'okarin saka shi cikin budaddiyar rigar bacci na,jin ina addu'a yasa shi samun karfin guiwar karanto zazzafar addu'a"fiji jiha habulun min...,fiji jiha habulun min....,inni sulaimanu inni masu inni sulaimanu inni musa ya fir'auna"

Nikaina sai na jinjina masa nan take na saki tawa addu'ar na kama tashi, tare muka ci gaba da fad'a yayinda muka runtse idanun mu sosai," fiji jiha,inni sulaimanu inni musa, inni sulaimanu innni masu ya fir'auna wa k'aruna,"

_Zuciyar tahhhh!_

Abind ata fad'a kenen kana ta bace kamar an hura mata iska,

Cikin hanzari muka saki juna nan take muka kara firgita rashin ganin Zarah a wajen,

"Wayyo mun shiga ukku,Jameelu ka janyo muna bala'i Allah ya isa, wallahi sai ka nemomin diya ta ko kaima na kashe ka,"

Cikin kuka naci kwalar rigar sa ina rusa ihu,

Wani mugun bugu ya kaimin a baya,

"Na rantse Jameela ke kika ci amana ta koma me na aikata kece sila shegiya d'iyar matsiyata mai matsiyatan 'ya'ya, bani da kamar Madeena duk duniya,"

Yana fad'a yana kuka nikam mamakinsa ya k'ara rufeni wai bashida kamar Madeena,

Mik'ewa yayu tsaye nabi bayan shi, cikin hanzari na shak'o wuyan shi,

"Mugu azzalumi kai ka kashe ta, Allah ya isar mata, nidai Allah ya gani badani ba,kuma wallahi sai ka nemonin 'ya'ya na,"

Bangajeni yayi ya fita waje ana ruwa da komai amma baya ji baya gani, saidai muna fita muka ci karo da abinda ya k'ara firgita mu,

Gawa ukku muka gani a jere,ta farkon dai ko babu tantama mun gano Jameel ne,

Wani irin uban ihu na saki na juya aguje cikin gida, saidai nauyin da nak'ara ne ya firgita ni, sai alokacin da na isa d'aki na fahimci ashe Daddyn Zarah ne ya haye baya na, duk wannan gudun da na lafta yana goye a bayana,

"Wayyo Allah na shiga uku! Madeena kizo ayi ba'asi, dan Allah ki fito wallahi gaskiya zan fad'a maki!"

*"Daddyyyyy!"*

Muryar Zarah ce muka jiyo cikin wani matsanacin hali,

Da sauri Daddynta ya fita yayinda na maida d'akin na kulle,

Rakub'ewa nayi k'arshen gadon ina rawar dari,

Bud'ewar k'ofar yasani sakin yani abu mai zafi a cikin zane na dan ko panta babu a jiki na,

Tsaye take da k'aton k'arfe a hannun ta,

Hannu wana a had'e na fadi a some, saida nayi nadamar suman dan kuwa tana bugamin wannan k'arfe na farka yayinda kaina da ido na suka shiga juya kansu da kansu.

_Nawa ne sauran ki a account?, Mummy tashi tashi tashi, tashi kada ki mutu bari na kashe mijinki,_

Nidai ba iya fahimtar zancen nake a sosai ba dan idanuna kawai ne a bud'e amma tuni nayi k'amshin mutuwa.

Bud'ewar k'ofar tasa na bude idanuna da jini ke bi ta cikin su, Daddyn Zarah ne ya shigo a hirgice, yana ganin halin da nake ciki ya juya a guje,

Wata irin muguwar dariya naji inuwar nayi nan take ta k'ara makamin wannan k'arfe"tussss!" Fashewar kankana, daga haka taja k'afa ta yayinda idanuna suka rufe dan kuwa har kwanya ta ana iya ganowa watse, *MATACCIYA*maraba da zuwa cikin *MATACCI*.


_NI AYUSHA_

_Cikin tsananin damuwa da firgita na koma gida, kalaman Zarah k'anwata sun firgita ni, nan take na dauko wayata na kira Zainab, bugu daya ta dauka lokacin da take shan sauti,"ke banza, wai kinsan Zarah ta haukace?"_

_Daga can ra rage sautin cikin rashin fahimta tace,"bangane ba? Zarah k'anwar ki?"_

_"Eh ita, wallahi Zainabu ina cikin tashin hankali, aljanun Madeena sun shafeta yau dinanna ta had'a duk wani record zata bawa Hisham Allah yasoni baya gari sai gobe zai dawo,"_

_Cikin rashin damuwa Zainab tace,"kisa ayi mata duka kuma a karbe komai mana,"_

_"Duka? Wai kinsan me tacewa Daddy? Wallahi cewa tayi sai ta kashe mu muddin kotu bata hukun tamu ba,"_

_nan take Zainab ta maida hankalin ta,"toh Ayusha, a kawar da ita mana, kinsan akwaita da taurin kai tunda ta furta zata iya aikatawa,"_

_cikin tsoro da rashin daukar maganar nace" insa a kashe kike nufi fa? A'a gaskiya ina son ta bazan iya ba"_

_"Toh me kike so nace maki? Ki barta ai in baki kashe ta ba ita zata kasheki kuma ta rabaki da Hisham din, nidai sai anjima zan raka mummy airpot"_

_tana kaiwa nan ta kashe wayar, ni kuma na zauna ina tunani tare da jujjuya waya ta, shigowar kiran Hisham ne ya katseni, da sauri na daga kiran,"Am Ayusha zan dawo gobe Zara ta kirani tace na dawo amma taki ta gayamin me yake faruwa na zata ko kin haihu ne?"_

_cikin firgici da in iniya nace"eh Nice!"_

_"kece me? Kin haihu?"_

_sai lokacin na gano me nace,"a'ah ban haihu ba amma dai bani da lafiya ne,"_

_"Allah ya sauwak'a gobe zan shigo Insha'Allah."_

_"kutt!" Na had'i wasu miyau masi dacin gaske nan take naji mara ta ta murd'a sosai._


*BABI NA GOMA*

β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…


*DADDY(DAN BATSULA INJI AUNTY QUEEN)*

Cikin hanzari na nufi bangare na da tsawar bata tab'a, cikin wadrobe na bud'e na shige ina ta addu'ata ta inni musa.

A hankali na dinga jiyo tafiyar ta tare da jan wani karfe a k'asa, tsakanin hanta, da tumbi na had'i da hanjin ciki na bansan wa yafi wani karfin kokuwa ba, wani irin hautsinewa sukayi wanda yasani kara jiyo kamshin *MATACCIYA* Jin taja ta tsaya da k'arfen ta yasani k'ara karfin addu'a Allah yasa kada ta ganni.

"Inni musa"

_"inni Matacciya"_

Wani irin zaro ido nayi da jin wani irin nishi a kusa dani, 

Ina jiyowa ta sakar min wani murmushi wanda ya bayyana hak'oranta da suka fad'i yayinda gashin kanta yake a tsaye wata irin inuwa yana fita aciki,

Murmushin na maida mata wanda yafi kama da na Matattu,

"Innu musa"

Na fad'a ina yak'e baki tare da k'ok'arin tura k'ofar wadrobe din cikin dubara.

_"lah lah lah lah Daddy! Ana Matacciya!"_

"Wayyo na shiga ukku, ya Musa ya sulaimana wayyo, Allah na ka ceceni, "

Da gudun masifa na fita saidai ban kai ko'ina ba naji an jawo ni da k'arfi,

Akan kujera ta zaunar dani, inuwa d'aya ta saki acikin inuwowin da suke tattare da ita nan take inuwar nan ta daure ni tamau,

Wani irin langa-langa ne a hannun ta nan take ta shiga yayanka min shi a jiki,"

Kuka na baya fita lokacin da ta cakamin shi a ciki,

Ya tsunta ta dora akan saitin zuciya ta nan take zara-zaran faracen ta suka shige a ciki, ciro zuciyar tayi nan take bugun ta ya tsaya.

_"Zuciyar ka ba tada amfani._

_"cikin mintuna k'alilan zaka mutu yayin da zan kashe kowa naka"_


Nidai kam daga haka inuwar ta bace min sai kuma na kasance *MATACCE*.


_ZARAH D'IN KU CE_

_Nasan da yawa bazaku so ace Madeena ta kashe ni ba, nima bana fatar hakan, saidai abin da nayi Mamaki shine taso na fad'o daga kan bene lokacin da tsawa ya tsaga bangon ginin Su Mummy wannan ne sanadin da ta dinga mik'omin hannayen ta nazo, wanda na tabbata da ba dan Daddy ba da na fad'a,_

_bayan Mutuwar Daddy da Mummy acikin gidan, yayinda gawar Jameel, Zainab da Salees suke jere abakin k'ofa, hakan yasani barin gidan dan na nufi gidan su Ayusha, saidai ina fitowa harabar gidan inuwar Madeena ta zagayeni, cikin sauri nake tafiyar yayinda nake hango inuwar tana biye dani, a guje na malala da gudu saidai na kasa dogon tafiyar, tsayawa nayi cak ina fidda numfashi,"ki fito! Me nayi maki kike biya ta? Ko zaki iya kashe nine?"_

_cikin ihu nake maganar daga can na ganta tsaye tana kallo na, "Zarahhhhhhhh! Zan tsaida ke."_


_idan mai karatu bai manta ba, a shafi na shida mun tsaya a inda Zarah takeyiwa 'yan uwan nata barazanar kisa, yayin da a shafi na goma Ayusha ta Koma gida a hargitse cikin tsananin tsoro yayin da ta Kira k'awarta Zainab dan neman mafita_.


*BABI NA SHA D'AYA*


β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…

Wannan shawarar da Zainab ta bani ce acikin rai na, sam nakasa zama nakasa tsayi Sai kai da kawo wa nake

Wayar dake hannuna ta dauki ruri wanda hakan ya bala'in sani na firgita, da kyar na dai-daita kai na nadauki wayar, Yah Hisham ne da kyar na amsa Sallamar da yake mun, 

"Am Zarah ta kirani tace duk abin da nakeyi na barshi nazo gobe, meya faru halan ko kece ba lafiya? "

Da a kusa dani yake da zai iya jiyo k'ugin da ciki na yayi "Ehhh.. Eh"

"Eh? tun yaushe ne baki sanar dani ba? "

Ni sai alokacin na tuna amsar da nabashi nan take nayi saurin Cewa, "a'a lafiya ta kalau bansan me take neman ka ba, "

Shiru ya danyi kana yace, "Ohk gobe zan taso"

Yana kaiwa nan na tsinke Wayar dan yanda zuciya ta take bugawa da k'arfi da k'arfi, 

Mummy na kira saida tayi ta ringing bata dauka ba, 

Can ta kirani na dauka "Hello Aisha kina jina? Ina cikin taro ne yanzu tafiya ta kamamu nida Baban ki, sai dare sosai zamu dawo, "

"ohk Mummy Zarah fa? "

"Zarah tana nan gida inaga ciwon hauka ya kamata ko aljanun Madee suka kamata amma kada ki damu da zancen ta da mun dawo zamu san matakin da zamu dauka"

"toh Mumy sai kun dawo, "

Daga haka ta tsinke wayar, nikam zuciya ta bata yi sanyi ba hakan yasa na kira Zarah din,

Cikin sanyi na fara magana lokacin da tadauki wayar, 

"ya kin kirani kuma kinyi shiru?"

Cikin rashin mutunci take maganar

"Zarah"

"Ina jinki"

A jiyar zuciya nasaki cikin wani irin hali na fara magana,

"Zarah kin dai san abinda kike shirin yi kamar tarwatsa zuri'ar ki ne, dan Allah dan girman Allah kada ki nunawa Hisham wadan nan takardun wallahi nayi nadamar abin da na aikata kema kan ki kingani Hisham walak'an tani yake wannan cikin ne nawa yasa ya fara kulawa dani, Dan Allah kibar maganar nan"

Na karashe maganar cikin matsanacin kuka, a tunani na jikin ta zaiyi sanyi saidai wata irin dariya da tayi yasani katse kuka na,"Hmm Ayusha kenan, wallahi wallahi sai na tone a sirin ku idan kuma banyi nasara akan hakan ba duk abinda ya biyo ba ku kuka jawa kan ku"

"Zarah!"na katse ta cikin kuka nan take ta canja murya wadda kana jin ta kasan tsantsar tsana ce,

"Wallahi Ayusha ba abinda zai tsaidani sai nasa an kashe ki an kashe Daddy ta hanyar da ta dace daku yayin da Jameel da duk wani da ya shiga rayuwar Madeena zai mutu yana danasani, Ina da abinyi kada ki kara kira na sai mun had'u kotu."

Tana kaiwa nan ta katse kiran tuni fitsarin da nake matsewa ya fara fitowa,

Tsoro ne k'arara a fuska ta cikin karfafa zuciya ta na dannan kiran Zarlie, ringing d'aya biyu, ya dauka,

Cikin fargaba na shaida ma Zarlie aikin da nake so ya kaddamar kafin dawowar su Daddy,

Zarlie shine dan ta'addan Daddy sune suka lalata motar Baban Madeena hakazalika sune suka kashe Madeena,

Yasan duk wani sirri na gidan kamar yadda yake zuwa duk lokacin da yaga dama,

Ba'afi 30ms ba ya tabbatar min ya isa gidan,

Babu inda bai shiga ba amma babu Zarah,

Bangaren Madeena ya nufa, kafin ya shiga ciki ya hango mutum tsaye acan cikin mak'abar tar gidan,

Hakan ya tabbatar masa da ita ce,


Doguwar tafiya yayi sosai kafin ya isa a wajen,

"Wannan alk'awari ne Madeena, koda kuwa bayan na aikata zanyi da nasani nidai nasan ban shiga hakkin musulunci ba, mahaifana basu da kirki sassaucin azabar Allah nake nema musu"

Jin taku a bayan ta yasa

Cikin tsoro Zarah dake tsaye ta juyo dan ganin waye.

Wani irin tsoro ya ziryace zuciyar ta ganin Zarlie ne,

"Mememe kazo yi anan?"

Dariya yayi ganij rudewar da tayi,

"Ashe haka kike da kafiya? Kin buk'aci ki mutu da kiji dadin duniya? Hhh koda yake baki da zuri'a tagari dan yanzu haka Yayar ki tasani na kashe ki,"

Ja da baya ta fara yi tuni hawaye sun wanke mata fuska,

"Dan Allah dan Annabi kada ka kashe ni"

"Zaki kawo duka shaidar? Kuma zakiyi shiru da bakin ki?"

Jin buk'atar sa yasa ta tsaya cak!

"Bazan bayar ba, koma wace irin barazana Ayusha zatayi min bazan bada ba,"

Wata irin muguwar dariya yayi,"amma kuwa zakiyi asara idan kikayi tunanij wasa ya kawo ni anan, zaki bani ko bazaki bani ba?"

Jin ya maida muryar sa ta maras imani yasa ta ja da baya har ta fara takin k'aburbura,

Ganin tana neman tserewa yasa shi saurin damko hijabin ta ya hade ta da bishiyar tsamiya dake a wajen,

Kokari take ta kufce amma ina yafi karfin ta,

wajen ta kwacu kan ta ya bala'in gaura kan ta bishiyar,

Shak'eta yayi sosai tun tana turje turjen k'afafu har jini ya maye gurbin idanun ta,

Ganij ta tsaya cak yasa yayi jifa da ita gefe,

Wayar Ayusha ya kira jin yana fitar da numfashi yasani fashewa da wani irin matsanacin kuka,

Kafin yayi magana na katse wayar a kan gado na koma ina kuka "anya bazanyi ladamar abinda na aikata ba?"

Cikin wani irin tsoro da ya ziyarce ni na kira wayar Daddy,

Cikin tashin hankali ya fara magana jin ina kuka?

"Ayusha? Waya tabaki?"

"Daddy Zarahhh!"

"Zarah?me tayi maki? Ina zaran take?"

Kuka sosai nake nayi saurin katse wayar,

Nan take mara na ya fara wani irin murd'a haka na dinga kiran wayar Zarlie amma a kashe.

Har safe ban rumtsa ba da Daddy ya dawo har gida na suka zo,

Babu tambayar da baiyimin ba nayi shiru,

Abinda yasani rud'ani shine bayan su Daddy sun koma gida sai ga shi ya kirani har ya bawa Zarah mukayi magana yayin da ta jefeni da mummunan kalamai da shaidamin tana nan akan bakar ta hakan ya janjo Daddy yayi mata mugun

 duka tare da shaida mata zai harbe ta idan ta kara tada maganar.


Wannan kenan!_AYUSHER_

_Rashin d'aga waya ta da su Zarlae basuyi ba ya bala'in d'aga min hankali, kai da kawo nake a d'akin, magrib tayi sosai amma shiru babu labarin su, "ku yaudara ta zasuyi ne?"na tambayi kai na nan take kuma na gano amsar;"da yaudara ta sukayi da sun zo karb'an kud'i amma shiru tun jiya,"_

_A tsorace nake da na kira 'yan gidan mu dan ina jin tsoron mummunan labari, da kyar na daga wayar Jameel na kira, ringing biyu ya dauka,"hello"_

_"Ya akayi Ayusher?"_

_Cikin annushuwa naji muryar sa babu wani tashin hankali hakan yasa na hadiye wasu yawu masu daci,"am Jameel Zara fa? Tana ina?"_

_"Eh d'azu dai na ganta but yanzu ina gidan gona ki kira wayar ta ko na Mum"_

"Ohk bye"_

_Daga haka na katse wayar zuciya ta tashiga bugawa,_

_Da kyar na daga wayar da Hisham yake mun, nan yake shaidamun zuwa 12am zasu iso gida,_

_Ina so na kira Mum amma bansan tambayar da zan mata ba haka yasa na kira Zainab nan nashaida mata fa Zarah na nan._


*BABI NA SHA BIYU*

β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…


*SUNANA AYUSHER NASAN KUN TSANE NI KO? HMM RAYUWA CE DA YAWA MUN KASANCE MASU SON ZUCIYA WANDA HAKAN YAKAN JANYO KOMA MENENE ZAMU IYA AIKATA SHI DOMIN BAWA ZUCIYAR MU ABINDA TAKE MURADA SAI DA DAGA KARSHE MUYI DA NASANI*

a matuk'ar tsorace nake, Mara ta baya na da k'afafuna suna min bala'in ciwo, ko ba'a fad'a ba nasan nak'ud'a ce ta kamani,

Tun magrib nake kiran Mummy anki a dauki wayar haka ma Daddy Jameel ma shiru ga kawata zee danaji shiru ita ma, ga ruwa da ake tafkawa a garin ga tsananin tsoro da ya addabi zuciya ta, kai da kawo nake a falon ina faman rik'e ciki, na rasa meye mafita nasan ko na fita bazan iya kai kai na asibiti ba hakan yasa na daure ina jiran zuwan Yah Hisham,

Ganin yawon bashi bane mafita nazo na durk'usa a falon tare da jingina kai na a jikin kujera, ji nake kamar abin da zan haifa zai fito sai kuma naji ya koma, baccin mai nak'ud'a na shiga yi sai na fara naji an cije Mara na na bude ido a hanzarce, haka dai nayi ta fama har sha d'aya na dare,

Can cikin bacci naji ana tashi na, a tunani na ko Yah Hisham ne ya dawo amma sai naga ba kowa a falon, hakan yasa na koma durkushe kai na akan kujera,

Kafin baccin ya k'ara dauka ta naji an buga k'afa ta a iya tunani na duk ciwon labour ne kesa hakan amma abinda nagani lokacin da na dago kai nane yasani mantawa da wani labour,

Shadows(inuwowi) nagani a jere kamar na mutum mutume a falon suna yawo,

Cikin tsananin firgita na mike tsaye yayinda hakan ya haddasa ma abinda yake ciki na wani irin juyi da sai da na durk'ushe a wajen,

"Waye anan? Yah ne?"

Jin shiru gashi shadow din sun bata yasa na mike a hanzarce na wuce d'aki tare da kulle k'ofar d'akin,

Ina shiga dakin na durkushe abakin toilet ina wani irin ihun gaske,

_"Aunty Ayush! Nice ungozumar ki Mummy tana jiran ki acan!"_

"Innalillahi......wayyo"cikin rashin sa'a nakasa idashen addu'ar sai ihu da na dinga kwararawa,

Wani irin matsanacin tsoro ne da firgici a tattare dani gani ko wacece mai wannan maganar!

"Zarah!menayi miki kike so ki tsoro tani?"

Wata irin mahaukaciyar dariya ta bushe da ita nan take ta yaye kyallen dake daure a goshin ta,

Wata irin kara na saki tare da fashewa da kuka,

_"Baki da labari ne? Hmm Ayusha kenan,nazo nan ne nayi maki albishir da cewa na kashe Mummy na kashe ubanki na kashe yayanki haka zalika zan kashe ki na kashe mijin ki na dauki abin da zaki haifa na maidashi shed'ani kamar ni!"_

Hak'ora na sun kasa rabewa da juna wani irin daukewar numfashi naji ya zomin,

Nan take na fad'i a some,

Iskan bakin ta ta hura min nan take kuma na dawo hayyaci na,

Ganin tana takowa izuwa waje na yasa na mike a hanzarce na shige bayi tare da datse k'ofar,

Waya ta na shiga danna nan take na lalabo wayar Hisham na kira shi,

"Yah Yahh...!"

Numfashi na ya sark'e lokacin da na ga Madeena a gaba na,

Wani fitsari mai zafi yazo min wanda saida ya sauka k'asa na gano ruwan haihuwa ne suka zomin

_"Aunty Ayusha! Bana iya tsaida Zarah daga abin da zata aikata amma zan miki jagora ki tsaida ta, nayi iya k'okari na lokacin da ruhin ta yasame nawa da na hane ta saida nata yafi nawa k'arfin gaske, Fansa take d'auke ke kuma zuciyar ta zaki dauka!"_

Nan take wani iska yazo ya shige gaba na,

Tare da bude kofar bayin,

A iya wannan lokacin zan iya cewa zuciya ta ita take sarrafa jiki na dan ni kaina bansan me nake aikatawa bale nasan me yake faruwa ba,

Cikin yarda da maganar *Matacciya* na nufi kitchen har wa yau hasken bibiya ta yake,

Zantaleliyar yuk'a ta na dauko na fice daga gidan a guje,

Keys da na rarumo a falon na shiga motar dan na samu mafita kafin wannan hasken ya bata,

Abinda ban sani ba shime ina fitowa Hisham ya shigo ganin na fita da mota ne yasa yabi baya na,

Gudu nake tamkar zararriya,

Da kyar na ganni a bakin get din gidan,

Nan take hankali na ya tashi lokacin da hasken ya bata nan take na tsinkayo bangon da ya fado a gidan sanadiyar wata muguwar walk'iya da akayi,

Turus! Naci birki a bakin kofar ganin *MATATTU* a jere kamar matuware,

Nan take wata irin bak'ar guguwa ta tashi a wajen,

Da gudu na bi jeji, gudu nake ina nak'uda kamar in shid'e na mutu,

Jin kan jariri na ya kusa fitowa yasa na rabe gidin bishiyar mangoro ina wani irin gurnani,

Tuni jini ya wanke, gab da fitowar jaririn wannan bak'ar inuwar ta bayyana a gaba na,

_"Hahhhahahaha"_

Wata irin mahaukaciyar dariya ta shiga yi nan take aka saki wat irin tsawa.

Cikin karfin zuciya na mike tsaye tana isowa waje na na luma mata wannan wuk'ar a gefen ciki,

A tsammanina naga ta fadi wani abun mamaki sai cire wuk'ar tayi tana murmushi mai ban tsoro.

_"sau nawa kike so na mutu ne? Kin kashe ni jiya ni kuma zan kashe ki a yau zaki tafi inda na tafi zan kara samun ki acan na wahalda ke na kara kashe ki dan nafiki matsayi acan,go to hell!"_

Nan take ta cire hannu na daya wanda banji cirewar shi ba sai ganin shi nayi a k'asa.

_"Zarahhh! Zarahhhh zan tsaida ki anan, Zarahhhhhh!"_

Madeena ce bayyane a wajen nan take Zarah ta zuba mata wata harara,

_" Madee! Ki tafi ki tafi ki tafi! Sai na dauki fansa!"


 *MATACCIYA*


*MATSORATAN BUK DINA*

*AND DUK WANI MAI SON MATACCIYA WANNAN GAISUWA CE BABBA MATACCIYA TACE A MIKO MUKU, MAI BUK'ATA ZATA KAWO MUSHI ZIYARA*

*NAGODE NAGODE*.


_ZARAH_

_"Wallahi ban tab'a zaton Ayusha zata iya kashe ni ba, ban tab'a zaton Daddy zai goyi bayan ta ba, anci amanata an hanani mutuwar salama!"_


*_BAK'AR DUHUWA MAI AIKATA BARNA_*

_"a gindin bishiyar ra fad'i a kwance wanda duk abinda ya faru akan ido na aka aikata"_

_" na kasance ina bibiyar Madeena tun daga wata rana da nasemeta tsakar talatainin dare tana kallon wani shirin ban tsoro, hakan ya birgeni na dinga bibiyar ta,_"

_" bana bayyanar kai na a wajen ta saidai nakan gwada bata tsoro acikin hangon gidan ta amma ko d'ar bazata ji ba hakan ya tabbatar min da ajinin ta yake_

_ni bak'ar duhuwar aljana ce ma kasance a jinsin bak'ake masu sanyin hali amma idan aka kai mu bango muna aikata aikin tashin duniya,_


_nakasan ce ina ziyartar mak'abar ta gidan kamar yadda muka saba da 'yan uwa na haka zalika bishiyar da aka shuka mana anan muke tad'in dare_

_Allah ya doramin son Madeena hakan yasa bana iya cutar ta amma sai gashi akan ido na aka hallakata,_

_daga lokacin naso na tagayyara gidan nayi musu kare dangi da izinin Allah amma yan uwa na suka hana ni_


_Bibiyar tawa ta koma kan Zarah lokacin da Na fahimci burin ta yafi na Madeena k'arfi!_


_iya wannan lokacin da aka kashe Zarah Tura takai bango nan nagane cewa wasu bil adaman sun fiye son kai da burin duniya_


_wannan ne dalilin da na kasance bak'ar duhuwa na shiga Ruhin Zarah na siffantu da gangar jikin ta._


_nice mai aikata kisan nice nan! Sai naga bayan su dayan bayan daya."_


*BABI NA SHA UKKU*

β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…


_THE END_


Wata irin mahaukaciyar dariya ta bushe da ita lokacin da ta dinga tsotsar jinin da yake fitowa akan gangar hannu na da ta fizge,

Wannan jinin da tasha nan take ta canja kama daga kan Zarah izuwa mummunar Aljana,

"Wayyo Madeena! Madeena zoki taimaka mun."

Ihu nake ina neman ina ma na suma ko na mutu da wannan azabar,

Wadda nake kira a matsayin Madeena tuni ta bace a wajen,

Wannan mummunnar bak'ar duhuwar tazo ta raba k'afafu na biyu daidai lokacin da jariri na yake kunno kai zuwa duniya,

Nan take tasa zara-zaran faratan ta ta tura shi ya koma,

Wata irin azaba naji wadda na tabbatar har hanji na ta tab'a,

Hannuwan ta ta tura acikin gaba na ta kamo hanjin ciki na tare da jaririn da mahaifa nan take ta dora bakin ta ta fara tsutsar wajen,

Ina ji ina gani rai na yake batun fita a jiki na,

Matuk'ar azaba naji ta tun anan duniya,

Tabbas cuta illa ce,

Najawa kai na na jawa miji na najawa d'ana mai zuwa duniya.


Daga haka nake muku bankwana daga wannan duniyar!


β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…


Hisham da ya shigo jejin a firgice fitilar shi sai billin billin take,

Nan take ya hango wannan guguwar,

Tsoro ne k'arara a fuskar shi,

"Innalillahi wa inna alaihir raji'un!"

Abun da ya ambata kenan hakan ya janyo hankalin bak'ar duhuwar nan,

A siffar ta,

Bak'in hayaki ne kawai zaka gani kamar hijabi,

Amma abin mamaki zaka iya gano jajayen idanu acikin bak'in hayak'in haka zalika zaka iya hango faratan ta da hak'oran ta harshen ta kuwa kamar harshen tsari ko na maciji,

Jini ne a bakin ta yayin da ta tallafo jaririn yana azabar kuka.

Cikin juriya da karfin zuciya Hisham ya fara karanto ayatul kursiyu.

_" hahaha! Zan raini wannan jaririn zan rada masa suna *Zaramadee*_ _zan maidashi babban shed'ani da zai addabi mutanen duniya masu hali irin na uwara sa"_

Hisham bai daina karatun da yake ba haka yaki sauraron ta hakan yasa ta fara ja da baya,

Addu'ar yake sosai nan take wannan hasken ya bayyan har izuwa gida hud'u

Ganin hasken bai sashi ya daina karatun ba nan take wani Mutum ya bayyana zaune akan wata kujera,

Sai namiji da mace a gefen sa,

Wannan bak'ar duhuwar na ganin hakan ta yarda jaririn da yake hannun ta Hisham yayi karfin hali dauke shi har wa yau bakin sa dauke da addu'a

_" kin kauce k'a'ida ta! A matsayi na na sarki mai adalci har na barki kika rayu a yanki na,yau zan yanke maki hukuncin da ya dace dake shine ki kasance *MATACCIYA*_

_Wannan bawan Allah kayi hakuri da izinin Allah ba abinda zai same ka_"

Yana kaiwa nan wannan bak'ar duhuwar ta dinga wata irin kururuwa wanda ya janyo daukewar ruwan saman da ake!

Nan take ta kama da wuta.


β˜…β˜…β˜…β˜…


Gawawwakin ajere ras!

Nan take aka sallace su aka binne su acikin gidan wanda hisham yasa a ka k'ona komai na gidan,

Makarantar aka rufe ta.

Aka maida wajen mak'abarta.


Hisham saida ya shekara kwance a gadon asibitin mahaukata,

Ganin babu dama aka maidashi gun malamai,

Ya samy taimako kwarai kafin ya dawo hayyacin sa,

β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…β˜…

Bayan nan na daukoka daga gidan marayu na raine ka, saida na shafe shekaru da dama kana na aure Sadiya,

Wannan shine dalilin da yasa har kullum kake gani ina dai-daita ka da k'anen ka, haka zalika na guje maka auren Zakiya na baka Sarat, Mutum mai son kai ko mai yawan mummunan furucu ba abun so bane,

Ke kuma Madeena shiyasa kikaga na hane ki da kallon Horro films a dare na tsaisheki da raya dare da nafilfili,

Zaid, Rilwan Sagir Madeena, Fateema kun ji Abinda ya faru da zuri'a ta duk akan son ka da biyewa zuciya,Allah ya kiyayemu gabaki daya,ku tashi ku tafi Allah ya albarkace ku ya k'ara muku son juna.


*ALHAMDULILLAHI*


*DUK KUSKUREN DA NAYI ACIKI ALLAH YA YAFEMUN.*


Tags: #queenMermue #horor #fatalwa
2187
1
6
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

Maryama Sokoto2019-01-04 11:29:24πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚Aysha kin bani dariya

Aysha Samarou2018-12-27 15:39:32wai Allah wannan buk ai sai kutum yamutu a zaune