Masoyina Na Har Abada!

Written by Mrs OmarPublished on 2018-12-14 10:41:03Category RomanceMasoyina Har Abada littafin ne da yake dauke da soyayya gami da yaudara wata yarinya ce samari uku suka sata a gaba ko wanne yana sonta sai dai biyu daga cikin ba soyayyar gaskiya suke mata ba akwai wani abu a ransu daya ne kawai ke mata soyayya gaskiya... tags: #yaudara #soyayya #tausayi #muguntaDuba was labarai »

*MASOYINA NA HAR ABADA*

....................®NWA................


  © *MRS UMAR*👮🏻


     Page 1_5


Kuka yake kamar ba gobe hawaye na bin fuskarshi kota ina, ahankali naji yace "please Aishat ki tausaya man karna mutu wallahi idan har na rasaki zan iya mutuwa. " wata tsohowa naji tayi magana cikin fad'a, tace " ai kam sai dai ka mutu wallahi Dan kuwa indo tafi k'arfinka, matar manya ce ita. " da sauri ya d'ago idanuwansa Wanda tuni sunyi jajir kamar wuta, yace " please Aishat I promise u, zan baki kullawa. " itama Aisha wasu hawaye ne suka zubo mata masu zafi, saboda tausayinsa, yafindo ta bud'e baki zatayi magana kenn, wata arniyar mota ta dannu kai, yafindo naga tana wani kyakkyawan murmushi, cikin isa mai motar ya k'ara so yana wani isa da takama, Aishat itama ta bisa da kallo, saboda ta san halin mutumn nata bashi da hakuri ko alama, cikin fushi ya k'ara so, yace "who are u? " da sauri ya d'ago, d'aga durkushn da yake yayi murmushi saboda yasan abinda yake nufi, ya bashi amsa da cewa "I a human being. " what do u mean? " abin da ka tambayini shi na baka amsa. " O sorry I am familiar with , Kai!! tsaya ma na tambayika kai dn gidan waye? "Humm kanaso ka San waye mahaifina? Mahaifina ALHAJI MUHAMMED ALIYU KABIR. " wow very good A.K, but acikin garin Katsina amma kana da labarina koh? ba Wanda bai son T.K bah d'a ga ALHAJI UMAR SA'AD so dan haka malam ga hanya zaka iya tafiya. " A.K ya kalleshi cikin murmushi yace " T.K kenn, ai Aishat *ALLURA CE CIKIN RUWA* mai rabo ne zai d'auka, dan haka yanzu zamuzoba muga wa Allah zai ba sa'a. " kai!!! Just keep quite, kai har ka isa kayi takara dani this is impossible T.K ya wuce haka. " T.K what do u mean? Kasan ni bahaushne. " cikin fushi yafindo tace " wai kai wane irin maye ne ance ba'a sonka toh dole ne. " yauwa yafindo gaya masa de. " ahankali Aishat ta dago jajayin idonunta tace " dan Allah kubarni in huta why, ni d'aya ce mace duk garin nan? " yafindo ta daka mata tsawa tace " uban wa yajayo bake bah, ga d'an arziki irin kudi me za'ayi da tsiya. " cikin muryar kuka Aishat ta dube T.K tace " thank u now u can leave.....

" bata tsaya jin komai bah, ta gudu cikin gida yafindo na kiranta ina ai har ta shge cikin gida....

 


 *DEDICATED TO*

  *AYSHAT MUHAMMAD*

    ( *MAMAN SHAKUR**MASOYINA NA HAR ABADA*

.....................®NWA...............


 _by_ *MRS UMAR* 👮🏻


    Page 6_10


cikin fushi yafindo ta kalle A.K tace " toh ai sai katafi koh tunda gidan ba na uban mutum bane. "Murmushi A.K yayi ya juya zai tafi, yaji tana cewa T.K " dan Allah kayi hakuri wallahi indo yarinya ce sosai sai kayi hakuri da ita. " A.K abin mamaki yake bashi saboda yanda yaga tana maganar kamar tana kuka, ahankali yaji yace " don't worry yafindo ai in dai akan Ayshat ne toh karki damu kinsan my work is better that his, kinga ko ai zan iya komai a kansa. "Yana gama maganar ya ciro kudi a mota ya bata masu yauwa ta dinga godiya, sannan ya shga mota ya tafi...


cikin kuka taji ana mata magana a kanta, jin muryar Wanda yayi maganar yasata d'ago kai da sauri, yace " haba gimbiyar Matan arewa ya kike kuka? kin san kuwa kuka ba yayi maki kyau. "Da sauri ta fad'a jikinshi tana kuka, wani Abu yaji, ya ziyarceshi tundaga kanshi har zuwa kafarsa, cikin kuka tace " yaya Mujaheed please Dan Allah ka tafi dani gidanku. " ahankali ya d'aga hannunsa yana shafa bayanta wanda tunda ta shga jikinshi hannunsa yake rawa yace " is OK please stop crying, me ya faru? please tell me. "Ta bud'e baki zatayi magana yafindo tashgo tace " toh munafiki ai dama nasan kaima kana d'aya d'aga cikin masu zigita, toh wallahi kaima baka isa bah, wai shin bah na hanaka zuwa gidan nan bah, toh bari kaji ubanka ma, da na haifa idan nace kada yasake zuwa man gida bai isa yazo bah, ballantana kai. "Ahankali ya d'ago Ayshat daga jikinshi yana share mata hawayenta, yace " sorry my sister ki share hawayenki insha Allah nine zan tsya maki a rayuwarki kinji koh!! "Kai ta d'aga masa alamar eh" yayi murmushi mai cike da damuwa, saboda yana jin haushen irin yanda yafindo ke son maida Ayshat kamar gwanjo...


Ahankali Mujaheed ya zaunar da ita saman kujerar dake falon gidan kafin ya juya ya kalli kakar tasu yace " yafindo kenn, ai Ayshat yanzu ta zama kalmar nan da hausawa ke fad'i, *ALLURA CIKIN RUWA* mai rabo ka d'auka. "Toh marrar kunya . "Tayo kansa, da gudu ya bar gidan saboda yasan halin kakartasa, itako Ayshat ci gaba tayi da kukanta, ko kallo bata isa yafindo bah, saboda tasan abinda take ma kuka ita kuma indai akan wannan ne, toh ba Wanda ya isa ya juya mata ra'ayinta....


Shiya sa take mata duk abinda take so indai na jin dadi rayuwa ne a koda yaushe tana ma Ayshat kallon matar manyan mutane.....   *DEDICATED TO*

   

    *AYSHAT MUHAMMAD*

 ( *MAMAN SHAKUR* )


© *MRS UMAR* 👮🏻


*MASOYINA NA HAR ABADA*

.........................®NWA...........


     © *MRS UMAR* 👮🏻


       Page 11_15Tana cikin kuka, ahankali naji tafurta, " I don't like him very much T.K, ni anyi nine dan namiji d'aya, wanda ko bashi da komai, zan iya zama dashi har k'arshen rayuwata. "Tana cikin haka har bacci yayi gaba da ita, itako yafindo aikin gabanta take tayi, bayan ta gama abinda takeyi, itama ta kwanta bayan jikartata...


Washe gari 

tunda safe Ayshat tayi shrin zuwa school, tunda ta tashi batacewa yafindo komai bah, sai dai fushi dama inda sabo yafindo ta saba da halin Ayshat indai aka taba abin kaunarta, toh ba zaman lafiya, cikin habaici yafindo take firta, " oho dai sai dai mutum yaci fushinsa ya gaji dan ko bani bugowa bani zagowa. "Ita dai Ayshat kota kula kakartata sai kawai ta d'auki school bag dinta tayi gaba zata fita, yafindo ta kwalla Mata kira, tace " ke!! indo. " da sauri ta juyo cikin fushi tace " yafindo am not indo, am Ayshat by name, don't call me indo again, yanzu kinsa yara har sun fara Kirana da indo. " yafindo ta zaro ido tace " toh marrar kunya sarkin turanci, dama gani nayi bakiyi kalaci bah, kuma zaki tafi makaranta. " Ayshat ta juya zata tafi sannan tace " nakoshi. " bataji amsar kakarta bah, tayi gaba abinta,

Ahankali take tafiya kasa dan yau bata tsaya ta amshi Kudin mashin bah, kanta na kasa tana tafiya abinta, saboda batason yawan kallon da mutane kemata, motace tasha gabanta ta tsaya dai dai k'afafunta, da sauri ta d'aga kai don taga waye a motar, ahankali yake zage glass din motar, ganin Wanda ke cikin yasata yin dariya, da sauri ta bud'e k'ofar motar tashiga, tana shiga ta fad'a jikinshi tana cewa " yaya Mujaheed Ashe Kaine?. "Da sauri Mujaheed ya tureta, saboda yanda ta fad'a masa saida k'irjinta ya gogeshi jikinshi dan haka yayi sauri tureta, yace " wai Ayshat meye haka, ke sai yaushe zakiyi hankali? Kefa yanzu kin girma. " baki ta turo masa tasa hannu zata bud'e k'ofar motar tafita, saboda ita a rayuwata bata son fad'a, da sauri Mujaheed ya ruko hannunta yace " ina zaki au dan nayi maki fad'a shine kikayi fushi, toh sorry my Good sister. "Ta wani turo baki tace " toh kai ba dn uwana bane? "Yayi murmushi yace " ni yayanki ne mana. " tace toh!! Kuma saika ..... "Bata karasa bah tayi shru saboda irin kallon da yake mata, Mujaheed yayi murmushi saboda shiba mai yawan dariya bane sai dai murmushi, yace " sai yanzu zakije school din? "Kai ta d'aga masa alamar eh, sannan suka kama hanya Dan zuwa school dinsu dake hanyar kwado watau ( *saldefi int'sch*,) ahankali taji yace " sister dama jiya inaso muyi wata magana dake. "Inajinka yaya. "Saida yayi ajiyar zuciya mai k'arfi kafin yace "Ayshat wace shawara kika yanke akan masu zuwa wajenki? "Hummm yaya kenn ai ni nariga nagama finda miji. "Da sauri Mujaheed yajuyo yakalleta, yace so "waye shi sister please tell me. " Ayshat tayi murmushi sannan, tace "A.K!!!! " da sauri yajuyo ya kalleta nandanan fuskashi ta sauya, ahankali tace " yaya me yafaru? "Saboda taga yanda yayan nata ya sauya sai da ya, sake dubanta ya kirkiro murmushin k'arya yace " no problem, mekika gani. "Are u sure? " sai da ya lumshe idonshi sannan yace "yes my sister....   *DEDICATED TO*


  *AYSHAT MUHAMMAD* 

   *MAMAN SHAKUR*


         ® NWA


   © *MRS UMAR* 👮🏻


*MASOYINA NA HAR ABADA*

.......................®NWA.............


    © *MRS UMAR* 👮🏻


      page 16_20


Mujaheed bai sake magana bah, har sai da suka isa school din, kafin Ayshat tayi magana, tace " yaya har mun iso gaskiya kayi sauri. " murmushi yayi mai cike da damuwa, but abunku da yarinya k'arama sai bata fahimta bah, daga murmushi nan bai sake yi mata magana bah, har saida yasamu wajen yayi parking, kafin ya ciro kudi yabada yace " ki shiga adaidaita sahu in antashi. "Tace " toh my Good Bros. " sai da tayi murmushi Wanda har dimple dinta ya lotsa sannan ta furta masa. " I Luv u my yaya!!!!

"Ajiyar zuciya yayi mai k'arfi kafin ya lumshe idonsa, ahankali yake bud'esu saboda yanda maganarta ta doki zuciyarsa, baiyi mata magana bah, sai dai murmushi da ya maida mata dashi, sannan tayi tafiyar ta kama hanyar class dinsu, binta yayi da kallo har sai da ta bace kafin ya tafi....


Ayshat basu tashi a school ba sai 2:30pm, ahankali take tafiya a hanya gashi ta gaji ga ba mai adaidaita sahu haka taci gaba da tafiya duk inda ta gita sai an kalleta, abin na bata haushi amma ba yanda ta iya sai hakuri, sai da tazo wata kwana da ba kowa a hanya, sai kawai taga motar T.K, ya tsaya a gabanta, tsaki ta buga tace " aikin banza harara cikin duhu, cikin irin isarshi ya fito, yace " a'a baby har kun tashi kenan? " baki ta murguda masa tace " bansani bah" please malam ka bani hanya na wuce kafin na tara maka mutane a nan Wallahi. " hhhhhhh baby kenn ai zanso hakan in mata ta tarawa mijinta jama'a. " Ayshat tayi tsaki sannan tace " wawa kawai. " T.K da sauri ya zabura yace ke!! Who are u calling a fool? " shru tayi tana raba idanuwa saboda taga yanda yayi mata tambayar, da k'arfin tsiya T.K ya fizguta, ya jefa mota yashiga yarufe, hannu tasa tana k'okarin bud'e k'ofar, cikin fushi ya fizguta jikinshi, kuka ta fasa tace " T.K what are u doing to me? " murmushi yayi, yace " zanyi maki maganin rashin kunya ne. " T.K I do not understand what u are saying. " T.K yaci gaba da kiss dinta ko ta ina, Ayshat tun tana ihu yar ta koma kukan zuci, sai da yagaji dan kansa ya kyaleta, sannan ya dubeta yace " don't call me that again because if u do will Dell with u, humm kinci sa'a baby, ina sonki but da yau sai kin gane shayi ruwa ne, dan Wallahi da sai na rabaki da mutincinki. " kanta ta d'ago da hawaye a fuskarta tace " T.K I I hate u ...... " ido T.K yazaro yace" ke!!!! *DEDICATED TO*


   *AYSHAT MUHAMMAD* 

  ( *MAMAN SHAKUR*

 

   ® *MRS UMAR* 👮🏻


*MASOYINA NA HAR ABADA*

.......................®NWA.............


    © *MRS UMAR* 👮🏻


     Page 21_25


T.K yace " ke!!! " sai kuma yayi shru saboda yanda yaga tana kallonsa babu alamar tsoro a fuskarta, sai yayi murmushi yace " don't worry karki damu nakusan zama mijinki sai abinda naga damar yi dake. " CIkin tsiwa ta murguda mai baki, tace " Allah ya kyauta in aure ka, " tana rife bakinta daidai lokacin da ta balle k'ofar mota ta fita da gudu, T.K dariya ma tabashi saboda yanda tafita, yana cikin dariya ya d'auki d'ayan hannunsa ya duki steering motarshi yace " AYSHAT kenn u don't known T.K am telling u no one can stop me from marry u, Ayshat am the only one that can marry u....


Ayshat tafiya take harda had'awa da gudu gudu tana waigen bayanta ko T.K ya biyota, a haka ta isa gida da yake ba nisa sosai, tana zuwa ta samu yafindo na faman aiki, Ayshat da gudu ta fad'a jikin yafindo tana kuka, cikin rudewa yafindo tace " lafiya indo meke faruwa? " Ayshat sai kuka take tana ajiyar zuciya, cikin kuka ta d'ago Kai tace " yafindo na gaya maki T.K ba mutumin arziki bane kince a'a karya nake, yanzu gashi ya tareni a hanya dakyar na samu na kwaci kaina, " cikin fushi yafindo ta cirita d'aga jikinta tace " indo kenn, nan kuma karyar taki ta koma zakiyi masa karya da shari, toh wallahi Allah baki isa bah. " Ayshat tayi murmushi takaici tana share hawayenta, tace " ai dama nasan yafindo tayaya zaki gane bayan son abin duniya ya rufe maki ido, toh wallahi nikuma wallahi da in aure T.K toh wallahi gara na mutu...... " kafin Ayshat tak'arasa maganarta yafindo ta kwasheta da kyakkyawan mari mai rai da lafiya, Ayshat tayi sauri ta rik'e kuncinta hawaye na zuba a idonta tace " yafindo yanzu saboda T.K kika mari ni? " Ayshat tana rufe bakinta ta nufi daki da gudu tana kuka, a koda yaushe tana mai bakincikin halin kakarta a haka tatashi ta shga toilet sai da tayi wanka kafin tayi alwala sannan ta fito tayi sallah, bayan ta gama tayi shrin islamiyya.....


Ahankali take tafiya kamar warda kwai ya fashe mata a ciki, ahankali taji ance sai yanzu za'a islamiyyar da sauri ta d'ago Kai dan jin muryar abin kaunarta, A.k yayi murmushi sannan ya d'an tabe fuska cikin wasa, yayi mata nuni da hannunsa alamar ga wajen zama, Ayshat ba musu tayi abinda ya umarceta, 

Ak ya kalleta yace " Ayshat ina maganarmu ta kwana ko kin amince da zabin da kakarki tayi maki? Ayshat ta d'ago idanuwanta Wanda tuni sun cika da kwalla, tace " humm har kana tunanin zan iya barinka, toh idanma mafarki kake toh ka farka, dan wallahi AYSHAT ta Aliyu Kabir ce kadai. "Ak yaji dadin maganarta amma duk da haka sai da ya sake magana, yace " Ayshat I known u Luv me so much, but I what u to promise me that Will u never ever live me.

" Ayshat ta sauki ajiyar zuciya ta fara share hawayenta sannan tayi murmushi tace " yes I promise that i will never live u for ever and ever.......


"Cak surutunsu ya tsaya saboda Wanda ta gani tsaye a gabansu.....
    *DEDICATED TO*


   *AYSHAT MUHAMMAD* 

   ( *MAMAN SHAKUR* )


   ® *MRS UMAR* 👮🏻


*MASOYINA NA HAR ABADA*

.........................®NWA...........


   © *MRS UMAR*👮🏻


      ®NWA


   Page 26_30


kallonsa takeyi kamar bata sanshiba saboda yanayin fuskarsa data gani a murtuke babu ko alamar fara'a, 


Kallonta kawai yakeyi amma acikin kasar zuciyarsa wani iriin zafi yakeji, nan take idonsa yachanza launi, da kyar ya iya daga kafarsa yana kokarin barin gurin, 

Ayshat tayi saurin karasawa wurinsa tana Murmushi, "ya mujaheed baku gaisa da A. K bah, shine nake baka labari ranar, saurayin da nakeso. " kokari take ta riko hannunsa yayi saurin kaucewa kamar bazai jiba sai kuma yayi karfi hali yakarasa gurin A.K yamika masa hannu sukayi musa haba, cikin mutunci suka gaisa, sannan yajuya yana k'okarin komawa cikin mota, 

Ayshat sai fara'a take tana kallon mujaheed har ya kusa karasa bakin motarsa ta kalla masa kira, ya Mujaheed! ! Yajuyo da idonsa sunkara ja, cike da karfin hali ya iya kirkirar Murmushi, 

Ayshat tace " kagaidamun da umma.


"Kai kawai ya kad'a mata yashige motarsa, yana shiga hawaye suka sauko akan fuskarsa, ya dora kansa akan steering sai hawaye yake, zuciyarsa cike daaa tunani kala2, yarasa sanin hanyar dazaibi ya nuna ma, Ayshat yana sonta, can kuma saiya tuna akwai kuma Wanda takeso, bazaiso ya tilasta taba akan tasoshi, dan haka zai hakura yajure duk wani zafin dazaiji a cikin zuciyarsa don kawai yafarantawa Ayshat rai, 


Ya jima yana tunani kafin ya d'ago kansa su Ayshat sunbar gurin, ajiyar zuciya yayi, sannan yashare hawayensa, jiyake jikinsa duk ba dadi kamar zazzabi nason kamashi kunna motar yayi yabar unguwar, 


Kodaa ya isa gidan jikinsa rau da zafi zazzabi yana kokarin rufesa, 


Dakyar ya iya fitowa daaga cikin motarsa yana fitowa yasoma ganin jiri, ginin gidan yariki yana dafawa har yarasa cikin falon, 


A falo ya dire saman babbar kujera duk jikinsa kyarma yakeyi wani kudun dinewa yayi a jikin kujera, 


Momnsa tana saman sallaya bayan tagama lazumi tajiyo motse a falo da sauri tafito, mujaheed tagani a kwance yana kyarma da sauri takarasso gurinsa tana tambayarsa "lafiyarka kuwa, jibi yadda kayi wani hada zufa" 

Dakya mujaheed ya iya cewa "mom banajin dadin jikina


"Subhanallah, bari nakira doctor " mom ta fad'a tana k'okari ciro wayarta, 


Mujaheed yayi karfin hali yadago kansa yace "a a umma karki kirasa kawai nidai kitaimakaman naakarasa cikin dakina" 


Tausayi yabawa mom, taje tariko hannunsa tana fadin " kaikuwa mutum ba lafiya zaice kar a kira masa doctor to mezakayi, kanada maganine a dakin naka? " kai kawai ya girgiza mata a lokacin harta mikeasa tsaye nan suka nufi dakin , 


A kan gado ta ajiyesa sannan tace "yanzu kasamu kayi bacci idan kafarka saikasha magani, saboda wannan kakkarwar da kake bayarda za'ayi cup yazauna a hannunka" 


Kakkarwar yake sosai muryarsa na rawa yace "mom sanyi nakeji, dauramun bargo a jikina" 

Mom ta lunlubeshi duk ila hirin jikiinsa da bargo sannan tabar dakin zuciyarta cike da tausayin mujaheed....   *DEDICATED TO*


   *AYSHAT MUHAMMAD* 

    *MAMAN SHAKUR* © *MRS UMAR* 👮🏻


   *MASOYINA NA HAR ABADA*

....................®NWA...............   © *MRS UMAR*👮      Page 31_35


Ayshat kuwa sai la'asar lis sannan tadawo gida, ana gaf dayin magariba, 


A zaune tasami yafindo tana figar ganyen miyar taushe, 

 

Ko kulata Ayshat bata yiba bayan sallamar datai mata, ta wuce dakinta,


Yafindo ta tabe baki "kyaji dashi amma dai auren T.K sai anyisa, yaro dan arziki irin albarka komai yasamu bani yake shikenan ke ana nuna miki hanyar arziki ke kuwa kina kaucewa, "nan fa yafindo tashiga sulalo tsiya ta inda take shiga batanan yake fita ba, 

Ayshat tana daki duk surutun datake tana jinta, kuma duk ta dameta, da tagaji tafito, "yafindo kindame mutane ana k'okarin sallah magariba, duk makwafta suna jinki, idan kindami da T.K aisaiki Kaine gidansu" Ayshat tafad'a tana juya baki, tana gama fad'a tabar gurin taje ta dora alwala, tajira ayi kira sannan ta gabatar da sallah, bayan tagama sallah tashiga kwararo addu'a, Allah yakareta daga shirin T.K, sannan kuma Allah ya cika mata burita na auren A.K, sannan ta tofa 


Haka dai suka wuni a ranar yafindo bataji dadin Ayshat ba domin ko girki kintayata tayi..


Washe gari 

Tashirya tsaf shirin zuwa school sannan tak'arasa dakin Yafindo, yanzu kam tasauko, ta gaida Yafindo 


Yafindo tace" harkin fito" 

Tace "eh nafito" 


Toh shikenan karbi wanann " yafindo tafada tare da mikawa Ayshat kudi, 


Kudin taran tane da kuma kudin mashin, Mikewa tsaye tayi tace "saina dawo " yafindo tace "a dawo lafiya" 


Nan tafita tabar gidan, dariya takeyi ciki2 ganin yadda yafindo tasauko, daman haka suke idan tayi mata laifi idan ba shareta tayiba to bazata sassautaba, 


Bata jima tana tafiyaba tasamu mai mashin, tahau yasauketa a makaranta nan tabiyashi sanann tashiga ajii.


Kamar lokacin data dawo jiya lokacin suka tashi tadawo gida, dawowar ma a mashin tadawo, 


Tana dawowa tayi wanka sannan tayi sallah, bata fitoba saida tashirya tsf sanna takarsa dakin yafindo zaune tasameta gefe gado tana Tunani, Ayshat tazauna kusa da itaa "yar tsohuwa mekike tunani? 


Yafindo tace "bakomai, kawaidai ina tunanin duniya ne, wata rana zan mutu" 


Ayshat tasaka dariya tana kallon yafindo " a'a lallai kakurs kinada tsoron mutuwa, toh kwantar da hankalinki bazaki mutuba sai kinga yarana nida A.K dina" 


Yafindo tatureta daga jikinta "dalla jamun can kekullum.maganarki A.K wannan matsuyaci" 


Ayshat tace "ahhh kakur kidaina kushenmun miji gaskiya banaso" 


Tsaki Yafindo taja jitake kamar takaiwa Ayshat duka sannan tace "ya akayi kikasan shine mijiki ai ke *ALLURA CE CIKIN RUWA* mai rabo zai dauko, kuma ina kyauta zaton T.K ne mai zabo" 


Ayshat tatabe baki "kekuma kikasan wannan, nidai mu a je wannan shirmen maganar, inaso nafita ne zanje gidansu ya mujaheed" 


Yafindo tace "Allah kiyaye hanya " Ayshat ta mike tana cewa "bazakice nagaida miki dasuba" 


Dasauri Yafindo tace "anki din " tafada cikin fad'a


Dariya Ayshat tabata tafita d'aga dakin tana fadan saina dawo....


   *DEDICATED TO*


   *AYSHAT MUHAMMAD*

    ( *MAMAN SHAKUR*) © *MRS UMAR* 👮🏻


  ®NWA


*MASOYINA NA HAR ABADA*

........................®NWA............   © _MRS UMAR_ 👮🏻        _Page 36 _40_


Kwance yake saman babban gadonsa, Wanda yaji lafiyayar katifa dukka jikinsa ya lullube da bargo saboda sanyin da yakeji, cikin wata irin murya yaji ana kiran sunnansa, muryar da akoda yaushe indan yajita yake fatan ta zama mallakinsa, har a bada, ahankali yaji ana bud'e bargon da yake ciki, hannunsa yakai da sauri, daidai inda nata yake yasa nasa, a tare suka bud'e bargon, Mujaheed yana budewa daidai lokacin da suka had'a idansu, wani lafiyayan murmushi ta sakar masa, take yaji kamshin turarenta ya dak'i hancinsa, da sauri ya lumshe idonsa saboda yanda yaji, yashigar masa kai, Ayshat takai hannunta saman goshinsa, wani irin zazzabe taji jikinsa, shiko idonsa ya bud'e yana kallonta, cikin damuwa tace "yaya what is wrong with u? Please just tell me. " Mujaheed ido kawai ya kura mata yana kallonta, nan danan hawaye ya fara fita a idonta dama indo ba wuyar kuka, da sauri Mujaheed ya tashi d'aga kwancen da yake yace " please sister stop crying, am fine "Hannunta ya kama yace " is OK sister am telling u, lafiya ta qlau kawai zazzabe ne. "Ayshat ta dube shi cikin shagwaba tace " are u sure? "Yes my dear sister. " dariya tayi sannan ta fad'a jikinsa kamar yanda ta saba, Mujaheed idonsa yasake lumshe saboda yanda tashigisa, ahankali ya d'ago ta daga jikinsa yana kallonta ido cikin ido, suna kallon junansu d'aya bayan d'aya, Mujaheed ya fara magana, yace " sister how is my kakurs? "She is, fine, so I come to said hello to u " Mujaheed yayi murmushi sannan ya koma ya jingina da gado, k'ofar d'akin sukaga an bud'e, meenat ce tashgo d'auki da fara'arta, daidai inda Ayshat take bakin gado itama nan ta zauna, tace "sister kenn yanzu mom ke fad'a min kinzo but kina d'akin yaya, shine nace bari inzo. " sister meenat kenn ba dole na fara zuwa wajen yaya bah, saboda shiya damu dani. "Humm Ayshat kema sani kanki ne inaso nazo, abinda ke hanani zuwa kawai sai fad'a yafindo. " toh shkenn sister no problem idan nayi aure ai dole ki dinga zuwa. "Hakane sister, wai yaya nifa ban gane bah, ina zazzabe ya tafi? " da sauri Mujaheed ya wurga ma meenat harara saboda yasan surutunta zata iya jayo masa ruwa a rana, Ayshat tace "yaya gaskiya ya kamata karage wannan *ZURFIN CIKIN* naka bashi da kyau. " gaskiya ne Ayshat because two days din nan ina tunani kamar, yaya ya fad'a soyayyar wata yarinya. "Ai kam indai haka ne toh Wallahi yaya I promise u duk yarinyar da kake so toh kasamu because yaya kana da duk wani Abu da mace keso kana da kyau addini ilimi, duk ka had'a, wadan nan abubuwa uku, kamar A.K dina shima duk yana da wadan nan halayen. " da sauri Mujaheed ya kalleta, sai ya lumshe idonsa saboda tabbas idan yaci gaba da jin kallamanta zata iya wargaza masa zuciya, Mujaheed yayi k'arfin hali yin magana, yace "kunga mubar wannan maganar kutashi muje falo nasan yanzu mom ta gama abinci. " dukka suka amsa da toh, sannan meenat ta dubi Ayshat tace "sister I missing u. " missing u too sister. "Gaba d'ayansu suka isa falo Dinning suka nufa direct.....


Meenat ita tazuba masu, *potatoes porridge* mom ta dafa, Mujaheed yanaci amma idonsa gaba d'aya yana kan Ayshat, itako kanta na k'asa saboda jikinta ya bata ana kallonta, Mujaheed yace " sister yaushe zaki tafi gida ko nan zaki kwana? "Ayshat ta zaro ido, tace " rufa man asiri da yafindo, inba so kake tazo yanzu bah. "Mujaheed yayi murmushi saboda shi ba mai yawan dariya bane, yace " OK no problem idan muka gama sai nayi drooping dinki. "OK yaya thank u very much, Allah yabarmu tare. " da sauri Mujaheed ya amsa da amin saboda tayi addu'a mai kyau......


  

 Toh jama'a wai suwaye Mujaheed da Ayshat shin wai akwai aure ma tskanunsu?   *DEDICATED TO*


  *AYSHAT MUHAMMAD*

   ( *MAMAN SHAKUR* )


    ® *N.W.A*


  © ~*MRS UMAR*~


*MASOYINA NA HAR ABADA*

.....................®NWA...............


     © _MRS UMAR_👮🏻

        


         _page 41 _45_


*ASALINSU*


asalinsu dai ba yan *Nigeria* bane, yan kasar *Niger* ne, watau buzayen Niger amma su ba irin buzayen nan bani na cikin daji a'a suna ciikin garin zandar, ta jahar Niger, kakansu babbban mai kudi ne babbban dan kasuwa ne Wanda akafi sani da Alhaji Ibrahim, yana da matarsa d'aya mai sunna Hajiya kulu,warda akafi kira da *yafindo* Allah ya albarkacesu da yara biyu dukka maza ne, UMAR shine babban dansu sai Abdullah, daga baya Alhaji Ibrahim harkokin kasuwancinsa ya maidoshi Nigeria inda yasayi babban gidansa a G.R.A watau cikin garin Katsina, a haka suke zaune shida matarsa da yaransa, d'aga baya, Umar ya gama secondary school dinsa, sai yasamu admission university of India, shikuma Abdullah yasamu a A.B.U Zaria, Alhaji Ibrahim yaso ace dukka yaransa sunyi makaranta a kasa d'aya saidai abun yaci tura haka ya hakura, 


Bayan shekara biyar dukka sun gama karatunsu inda Abdullah ya dawo gida shikuma Umar ya samu aiki a can kasar India inda yazama babban likita, kasar ta d'aukisa aiki, shikuma Abdullah cewa yayi kasuwanci zaiyi, bayan shekara d'aya yafindo ta matswa Alhaji da fitina dole Umar sai yadawo, a had'asu shida Abdullah ayi masu aure, shidai Abdullah da yaga yafindo ta damu sai yafitu da matar aure mai sunna Khadija yafindo tayi murna sosai haka ma Alhaji Ibrahim, bayan auransa da Khadija Allah ya albarkacesu da d'a d'aya mai sunna *MUJAHEED*, shikuma Umar baiyi aure bah, sai kosan shekara goma da haihuwar Mujaheed, inda Allah ya had'a sa da ameesha khan watau yar kasar India, yasha wahala kafin iyayensa suka aminci ya aureta, sai da yace masu musulmace sannan suka yarda,ranar daurin aure anyi shagalin biki,

Sai da suka ci amarci, kafin Allah ya albarkaci ameesha khan da cikin, inda tahaihu kyakkyawar diyarta, mai kyau abinku da ruwa biyu ga jinin India ga na buzaye, ranar sunna Alhaji Ibrahim yace " asamata *AYSHAT* da yake da tasamu ciki Nigeria ya maido daita gaban iyayensa tahaihu, 


Bayan shekara biyar Allah yayiwa Alhaji Ibrahim rasuwa, bayan su umar sunzo wajen gaisuwa shida matarsa da Ayshat yafindo ta tada bala'i dole sai an bar mata Ayshat, haka Umar ya hakura yabar mata Ayshat, ameesha tayi kuka sosai, danma yafindo naji shakar Umar, shikoma Abdullah sai harkokin kasuwanci mahaifinsa ya koma wajensa, haka Ayshat keta hakuri da yafindo, shikoma Mujaheed zaman da ake yanzu har ya kamala karatunsa aiki kawai ya rage, sai kanwarsa meenat wadda duk kusan tare aka haifesu itada Ayshat, ita kuma Ayshat d'aga ita basu sake haihuwa bah............. *DAWO LABARI*


Mujaheed yana driven yayin da Ayshat ke gaban mota, ya kunna wak'ar DA'IMAN wakar kamar haka, nayo gamo da soyayya ce da wata diya mai kyauyo Wanda banga musali..... "Bah bin wakar yake bah, sai dai kai da yake kad'awa....     *DEDICATED TO*


    *AYSHAT MUHAMMAD*

    *MAMAN SHAKUR*


   ® *N.W.A*


© _MRS UMAR_ 👮🏻


*MASOYINA NA HAR ABADA*

....................®NWA..............


     © _MRS UMAR_ 👮🏻

       


        _page 46 _50_


A haka suka isa k'ofar gidansu suna zuwa sukaci karo da motar T.K, k'irjin Ayshat ne ya buga saboda a kullum idan taga T.K tana mai jin tsoronsa, tanaji a jikinta idan har taci gaba da ma'amulla da T.K, toh a gaskiya wani Abu zai iya samunta saboda ta tabbata haduwarsu ba alkhairi bace, Mujaheed yaga yanayinta ya sauya, ahankali yace " sister what is wrong with to u "Yaya look... " Ayshat ta nuna masa T.K da dan yatsanta, Mujaheed sai da ya lumshe idonsa ahankali ya bud'e sannan yace " don't worry sister am here, ba abinda zaiyi maki. "Ayshat tayi murmushi sannan Mujaheed yasamu wajen parking yayi, shiya fara bud'e k'ofar mota yafito, kafin yazo ya bud'e mata, yana bud'e mata sai kawai ya kama hannunta ta fito, itama da biyu ta basa hannu d'an T.K yaji haushi, sai da zasu shiga cikin gida kenan T.K yasha gabansu, yana huci kamar maciji yace " why did u tourch my wife? "Mujaheed yayi murmushi takaici yace " your wife? So Ayshat is not your wife is only my. "da sauri Ayshat ta dube sa, sai kuma ta sanda kanta kasa saboda tasan yayi haka ne don kawai TK yarabu da ita, cikin zafin zuciya TK, yace ma Mujaheed " are u mad? ni kake gayawa Ayshat matarka ce? Toh Wallahi *KATAFKA BABBAN KUSKURE* kuwa, dan Wallahi *SAI KAYI NADAMA* sanina a rayuwarka..... "Kafin ya idar da maganarsa Ayshat ta daka masa tsawa tace " stop it T.K please just go I don't what to see u in my house again. "Ayshat ta juya zata tafi cikin gida T.K ya jayota da k'arfi, Mujaheed baisan lokacin da yakai ma T.K wawan dukabah, ya finciko Ayshat ta fad'a jikinsa tana kuka, saukar wani wawan mari yaji a fuskarsa Wanda bai Masan kota ina yazo bah, sai da ya bud'e idonsa sannan yaga yafindo a tsayi gabansa, tana huci kamar wadda akayiwa duka tace " mutumin banza mutumin wofi, ni zaka tunama asiri? Toh bari kaji wannan yaron a yanzu yafika a wajena Wallahi. "Mujaheed baisan lokacin da hawaye ya fara fita a idonsa bah, na takaicin hali irin na yafindo, ahankali ya d'ago kai ya dube ta yace " yafindo because of this man, zaki mare ni? "eh na Mareka koh zaka rama ne? "A'a yafindo bazan rama bah but daga yau zan kawo k'arshen wannan badakalar taki, insha Allahu. " Mujaheed yana gama magana yaja hannu Ayshat yajefata mota, ina ai kafin yafindo tazo har yasama motarsa key, fad'i taki nashiga uku " Mujaheed ina zaka kai man jika?...Toh muji dai zuwa   *DEDICATED TO*


    *AYSHAT MUHAMMAD*

    ( *MAMAN SHAKUR*)


     ® *N.W.A*


   © _MRS UMAR_ 👮🏻*MASOYINA NA HAR ABADA*

......................®NWA..............


    © _MRS UMAR_ 👮🏻

   

      


      _Page 51 _ 55_Mujaheed gudu yake da Ayshat, har bai san idan yake sa kafar motarsa bah, wani irin zafi yakeji zuciyarsa na masa kamar zata fashe, Ayshat ta lura da hakan saboda yanda taga har zufa na keto masa, ahankali ta dubesa cikin murya kasa_kasa tace please yaya come down what is wrong with to u? "Mujaheed gaba d'aya ya taka birkin motar, ya buga kansa da steering, Wanda sai da Ayshat ta tsorata, dama haka Mujaheed yake indai yayi fushi to ba kyau, ahankali Ayshat tasa hannunta, ta d'ago fuskarsa sannan ta tallabo kumatunsa, tana kallonsa ido cikin ido shima ido ya bita dashi, nan danan hawaye ya fara fita idonta, da sauri Mujaheed ya lumshe ido, sannan ya bud'e yace " is ok sister please stop crying. " Mujaheed ya zaro hank yana goge mata hawaye, ahankali take a ajiyar zuciya, yace "sister bansan mike damun yafindo bah, abin duniya yarufewa yafindo ido taki ta gane gaskiya, toh insha Allahu yau zan kawo Karshin wannan problem din. " kamar ya'ya? "Humm don't worry sister zaki gani da idonki yau, because duk abin nan dady baisan mike faruwa bah, dan haka yau zan gaya masa komai na cikina. " Mujaheed yana rife baki ya tada motarsa, ba idan ya nufa sai gidansu direct, suna zuwa abin mamaki sai suka tada yafindo da T.K sai ga dady shi da mom zaune a gife, cak Mujaheed da Ayshat suka tsaya saboda irin kallon da dady ke masa, ahankali su karaso. Mujaheed yace " dady wallahi.... "Da kata mutumin banza mutumin wofe, ni zaka tonama asiri? "Mujaheed ido ya zaro yana mamaki irin maganar da dady keyi, saboda shi baisan me yayi bah, dady yaci gaba da magana, yace " toh duk naji rashin mutumcin da kayiwa mahaifiyata, ka kyauta kayi daidai. " please dady listen to me. " keep quite Mujaheed I don't want to hear anything from u, Mujaheed ka bani kunya wallahi, so dan haka yanzu mun gama magana, nida yafindo Ayshat tana gama makaranta za'a daura mata aure ita da T.K, da sauri Mujaheed ya dube Ayshat, itama shi take kallo yayin da hawaye ya cika idonta....  *DEDICATED TO*


   *AYSHAT MUHAMMAD*

   ( *MAMAN SHAKUR* )


     ®*N.W.A*


    © _MRS UMAR_ 👮🏻*MASOYINA NA HAR ABADA*

.........................®NWA...........


    © _MRS UMAR_ 👮🏻

  


       _page 56 _ 60_Da sauri Mujaheed ya kauda idonsa daga kallon Ayshat, yayin da hawaye keta bin fuskarta, shi ko T.K sai murmushi mugunta yake,

Dady yace " au na manta ban tambayeka bah, kai d'an gidan waye a garin nan? "Humm dady kenn ni d'an gidan Alhaji Umar sa'ad ne...... " da kata!! koh Kaine T.K d'ansa? 

"Yes dady nine akwai Matsala ne? "Sai da dady ya lumfasa sannan ya lumshe idonsa ya bud'e ahankali, yafindo ya fara kallo sai yaga itama shi take kallo ta k'ura masa ido, ahankali ya k'ak'aro murmushi wanda yafi kuka ciwo yace "no problem kawai na tambayeka ne, ai nasan Alhaji Umar farin sani. " dady yana gama magana dai,dai lokacin da yake ciza lebe yana girgiza kai, Mujaheed ya lura da hakan mahaifinsa ya gano gaskiya, amma saboda kar ya batawa mahaifiyarsa rai gara ya boye gaskiya, 

Dady ne ya dawo dashi daga tunani da yakeyi, yace "so don't worry T.K tunda har yafindo tana sonka toh anyi an gama, dan haka yanzu ka d'auketa ka maidata gida, ita kuma Ayshat idan yaso gobe zan kawota, zanyi mata fad'a yafindo karki damu. "Toh naji amma kukula man da ita saboda wannan marrar kunya d'an naku. " sai yanzu mom tayi magana, tace "karki damu Wallahi nasan ba abinda zaiyi mata. " dama kyace haka mana kai tashi mutafi. "Tana rufe baki daidai lokacin da suka mek'i suka nufi hanyar k'ofar fita, Mujaheed bai tsaya yaji komai bah daga wajen mahaifinsa, sai kawai ya nufi d'akinsa, yana zuwa ya bud'e k'ofa yashiga ya maido ya rufe da k'arfi ta buga gam!!! 

Jikin mirror ya nufa yana zuwa ya watso kayan dake sama, duk sai da ya watso kayan dake sama,

Hawaye koh sai fita yake ta idanuwansa, hannunsa ya d'auka yana bugawa jikin madubin mirror yana cewa " dady why did u that, why dady!!! Ayshat *ITACE GATANA* itace rayuwata, a duk lokacin da na bud'e ido naga Ayshat bata gidana toh daga ranar zan bar duniya, saboda bazan ga an waye gari Ayshat na had'a jiki da wani bah, Ayshat *KE TAWACE* ni d'aya ba wanda zaiji kamshin jikinki sai ni d'aya. "Yana magana yana kuka ga hannunsa jini na fita,

Saboda bugawar da yadinga yi a jikin mirror,

Kan gado ya fad'a yaci gaba da buga hannayensa saman katifa...


Ayshat itama dakin meenat ta nufa, ita damuwarta tafi ta Mujaheed saboda za'a rabata da abin kaunarta A.K,kuka take kamar zata hadiye zuciyarta dan haushi, ta dubi meenat wadda tunda tashigo tana kuka ta kura Mata ido, tace " yanzu me yasa dady zai biyewa yafindo? har ya aminci da na auri T.K, bayan T.K bashi da hali mai kyau. " meenat ta sauke ajiyar zuciya sannan tace " sister please stop crying, kema sanin kanki ne dady ba zai hana yafindo abinda take sonyi bah, idan ma yayi haka toh Wallahi na tabbata tana iya cewa toh kafin ki gama school ayi maki aure... "Haka maganarki take meenat. " gaba d'ayansu kai suka d'aga dan ganin wake magana
   *DEDICATED TO* 


   *AYSHAT MUHAMMAD*

   ( *MAMAN SHAKUR*)


  

    ® *N.W.A*


    © _MRS UMAR_ 👮🏻


*MASOYINA NA HAR ABADA*

......................® NWA.............


       © _MRS UMAR_


         page 61_65Mom ce tayi magana yayin da take murmushi mai dauke da annuri, ahankali ta k'araso inda suke zaune itama ta zauna,

Yayin da ta dafa kafadar Ayshat, 

tace " Ayshat hakuri zakiyi ki rungumi kaddara,sanin kanki ne Alhaji bai isa ya hana wannan auren bah, because yafindo ba Wanda ya isa ya hanata abinda take so, dan haka Ayshat sha'awar da zan baki kirik'i T.K a matsayin mijinki na HAR ABADA. 

" mom taya zan d'auki T.K a matsayin mijina bayan T.K bashi da hali mai kyau? humm mom koda T.K yana da hali mai kyau, toh gaskiya babu soyayyarshi a zuciya ta, zuciyata ta mutum d'aya ce anyi ni ne danshi, bani da wani miji da ya wuce A.K *MASOYINA NA HAR ABADA* munyi alkawarin kasan cewa tare mom. "duk maganar da Ayshat keyi mom ta kura mata ido tana kallonta,

Hakika Ayshat ta bata tausayi but ba abinda zata iya bayan ta bata hakuri, sannan tayi mata addu'a Allah yaza6a Mata abinda yafi zama alkhairi, ahankali mom ta tallabo kanta 

Tace " please Ayshat just forget what happen stop crying I promise u, komai zaizo da sauki insha Allahu sai kin auri NAGARTA CEN miji. " cikin muryar kuka Ayshat tace " mom really? " yes my dear it's real, so dan haka yanzu ki kwanta ki huta kinji ko? "Kai ta d'aga mata alamar eh, sannan mom ta sakar mata murmushi ......Bayan fitar yafindo da T.K ba idan ya ajeta sai gida yana sauketa ya nufa wajen holewarsa, luna ya nufa direct inda karuwai suke da mashaya, 

Yana zuwa yan Matan wajen suka fara yimasa kirari ai kam ya dinga watsin naira, wajen table d'in da yasaba zama can ya nufa ya zauna, yayin da wata yarinya wadda bazata wuce shekara 16 ba tazo da rangwad'a, kayan jikinta English years ne Wanda dasu da babu duk d'aya, da kaganta kaga k'aramar karuwa, 

Ahankali ta zauna kan cinyarshi

Tana wani shafashi, shiku yana shak'ar kamshin jikinta, ahankali yake bud'e idanunshi, 

Cik ya tsaya da idonsa yayin da yasa hannu yake murza idonsa, yace " what! Wazan gani can kamar......
   *DEDICATED TO*

*AYSHAT MUHAMMAD*

  ( *MAMAN SHAKUR* )


    ® *N.W.A*

     © _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

......................® _NWA_...........


        © MRS UMAR 

        Page 66_70
Oh my God A.K a luna, so what is he doing here?. " da sauri T.K ya ture karuwarsa daga jikinshi, ya nufa wajen A.K ai kam yana zuwa yaga Ashe shine kam da gaskiya, yayin da yan Matan keta murzashi kamar kayan wanki, T.K ya kwashe da dariya mai sauti, sannan ya dinga ta6a hannunsa yana ci gaba da dariya,

Saida yayi dariyarsa mai isarshi kafin yace " Wow ALIYU Kabir that is great koko nace A.K koh? Humm Ashe dai bani kadai bane d'an iska, wow today am very happy to see u, ai ni ina tunani T.K ne kawai d'an iska, 

Ashe ba'anan gizo kesakaba, su Ayshat anyi zaben tumun dare Ashe gara ni da nafito da iskancina a fili yau zan.... "Dakata! T.K ai bata'anan na tabbata duk iskancina ban kama k'afarka bah, because duk fad'in garin nan ba Wanda bai San da zamanka bah,

Dama can ansan kai d'an iskane, hummm Ayshat kuma da kake magana ai kai kadamu da ita dan kuwa Wallahi babu sonta a raina,

Zan aureta ne kawai dan wata manufa but badan Allah bah, 

Kai barima kaji yanzu idan zakaje ka gayawa Ayshat ka ganni a Luna, bazata taba yarda dakai bah Wallahi.

" hummm A.K kenn ka gama? Toh bari kaji wani Abu, ni bawai ina son Ayshat bane har cikin zuciyata bane, ok!!! Kawai dai ina mata soyayyar sha'awa ne, so da zaran nasamu abinda nake so, 

 I Will leaves her for ever, so dan haka yanzu inaso muhadu gobe zamuyi magana.

" T.K yana gama magana yasa hannunshi cikin aljihu ya zaro kud'i, yace "so ga wannan nasan haka kazo jindadi ba dala. " T.K yana aje kud'i ya kara gaba, A.K dai ido kawai ya qura masa, hannu yasa ya d'auki kud'in yana d'auka d'an kati ya fadu kasa, ya d'auka yana dubawa number wayarshi ce, murmushi yayi sannan yasa aljihu.....


Mujaheed tunda ya rufe idonshi yak'e ya bud'e ga hannunsa har yanzu jini zuba yake saboda inda ya dinga buga hannunsa akan mirror,

Zuciyarsa wani irin zafi take na takaici ya cikashi, tayaya yafindo zata rabashi da abin kaunarsa, bayan yana tunani Ayshat itace MASOYIYARSHI TA HAR ABADA, itace uwar yayanshi sai gashi yanzu yafindo tanaso ta gina katanga a tsakaninsu,

Yafindo this is impossible tayaya zan cire son Ayshat a zuciyata?

"Duk wannan maganar Mujaheed a zuciya yake yinta, yayinda hawaye ke fita idonsa maso zafi,


Ahankali yaji ana Shafa mai fuska, 

Da sauri ya bud'e idonshi dan ganin wake shafashi,

Mom ce d'auki da murmushinta, hannu tasa ta d'ago kanshi ta daura kan cinyarta, sannan tasa hannunta na hagu tana wasa da gashin kanshi, ahankali cikin murya kasa_kasa tace "my son please just Tell me, nasan kana son ayshat ba tun yau bah, na gano haka ne tuntuni so kawai dai nabari ne ka furta da bakinka, sai dai kash!! Mujaheed kanaso kayi zurfin ciki ka beye sonda kake ma Ayshat, idan kayi haka toh wannan babbar Matsala ce kasa kanka, please my son kafito fili ka gayawa Ayshat gaskiyar magana.... " kafin mom ta gama magana,

 Mujaheed yayi sauri sa d'an yatsansa a bakinta, tashi yayi daga kan k'afarta ya gyara zama,

Sannan yayi ajiyar zuciya mai k'arfi kafin yace " mom kenn waya gaya maki ina son AYSHAT? Hummm mom kenn sanin kankine bana soyayya, so tayaya zan so Ayshat? No kawai dai naji haushin yafindo ne saboda Wanda take so tabama Ayshat bashi da hali mai kyau..... "Dakata!!! Mujaheed    *DEDICATED TO*

 *AYSHAT MUHAMMAD*

   ( *MAMAN SHAKUR*)      ® *N.W.A*


   ©  _MRS UMAR_*MASOYINA NA HAR ABADA*

.......................® _NWA_.........


          © MRS UMAR


          Page 71_75
Dakata! Mujaheed niba k'aramar yarinya bace, tun kafin na haifeka nasan meye so, dan haka yanzu zanje nasamu mahaifin..... " please mom stop it's am telling u nagaya maki ba komai a zuciyata. " yana d'aga hannunshi sai yanzu mom ta kula da jinin dake fita daga hannunshi, murmushi tayi na takaici tace " hummm gaskiya ne Mujaheed na yarda baka son Ayshat, dan kuwa gashi naga alama a hannunka. " da sauri Mujaheed ya kalli hannunshi, sannan ya k'irkiro murmushin yak'e yace " oh my mom this is nothing d'a nazo shiga toilet naji ciwon Wallahi a shawa. " da sauri mom ta kalli toilet d'in, juyowar da zatayi ta kalli mirror taga duk kayan sama a fashe, cikin fushi ta miki tsaye ta nufi k'ofar fita, Mujaheed ya gano hakan dan haka yayi saurin kiranta. " please mom am sorry. 

"Saida ta bud'e k'ofa kafin ta juyo, tace Mujaheed a kullum inayi maka addu'a Allah ya rabaka da wannan bakar zuciyar taka da kuma zurfin ciki, Mujaheed bansan wane irin hali kake dashi bah?

" tana kai karshen maganarta, taja k'ofa ta rufe, dakin dady ta nufa direct tana zuwa tasameshi saman sallaya yana lazime,

Saida tajira yagama kafin ta gaya masa abinda ya kawota, dady yayi mamakin jin wannan maganar dan haka yace su tafi dakin Mujaheed dan ya ganoma idonsa,

Inda mom ta barshi nan suka sameshi, Mujaheed yana ganin dady yayi saurin gyara zamansa yace "sannu da zuwa dady. " dakata! Ba wannan yakawoni bah, duk naji komai daga bakin Khadija, dan haka ka sani wannan Matsalarkace babu ruwana, idanma zakayi hakuri da Ayshat kayi because yafindo ta riga ta kawo wanda take so ni ban isa na chnza maganarta bah. "Haba Alhaji tayaya zamu barshi cikin wannan halin. " Khadija please just keep quite I don't want to hear anything from u, so idanma mutuwa zakayi saidai kamutu dan Wallahi bazanki bin umarnin mahaifiyataba because of u, 

Dan haka na yanke shawarar cikin week d'in nan zan saya kama form d'in army, u will leave this Katsina for ever, bazaka sake dawowa ba har sai lokacin da aka daurama Ayshat aure.

"Yana rufe baki ya kama hannu mom suka fita, saboda hawayen dake fita a idonta, mom bata da bakin magana saboda tasan halin dady baya magana biyu, 

Shiko Mujaheed kansa ya tada akan bed d'inshi yaci gaba da zubar da hawaye masu zafi, na takaici a lokacin d'aya anhada masa bakin ciki.....

    *DEDICATED TO*

  *AYSHAT MUHAMMAD*

    ( *MAMAN SHAKUR* )


      ® *N.W.A*

    

    ® _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

......................® _NWA_..........


         ©MRS UMAR


           Page 76_80
Mujaheed hawaye ke fita a idonsa ba gaggau tawa, har baisan wacce duniyar yake bah,

Tashi yayi tsaye ya nufi toilet yana zuwa ya danna shawa ya shiga cikinta yayi tsaye ruwa na dukan kanshi,

Yayinda hawaye yaci gaba da fita a idonsa harda majina, 

Hannu yasa ya doki bangon da shawar take, yace " dady why did u this to me? 

tayaya zan rasa Ayshat bayan ita nake tunani ta zama uwar yayana.

" ahankali ya sulale kasa yana ci gaba da kuka, 

Yana cikin wannan yanayin wata zuciyar tace " haba Mujaheed bai kamata kana kuka bah kaifa gwarzon namiji ne, haba karka bada maza mana, katashi kayi alwala kayi sallah ka gayawa Allah bukatunka. "Da sauri Mujaheed ya tashi tsaye danyin abinda zuciyarshi ta bashi shawara, 


Saida yayi wanka kafin yayi alwala danyin sallah,

Mujaheed saida yakai wajen awa nawa yana gayawa Allah damuwarsa kafin yayi addu'a,

Nan inda yake saman sallayar ya kasa tashi saboda ciwon da kanshi ke masa,

Ga zuciyarshi na masa k'una, 

Ahankali yaji anyi masa knocking, da sauri ya d'ago kai saboda yatada kanshi da kujera,

Cikin muryar shi mai dadi yace " yes coming. " Ayshat ce da meenat suna rik'e da hannun juna,

Mujaheed ya kura masu ido yana kallonsu ahankali Ayshat ta karaso ta zauna inda yake,

Ayshat ta d'aga kai ta kalli Mujaheed shima ita yake kallo, cikin rawar murya Ayshat tace " yaya what is wrong with u?, please tell me am here for u. "Humm Ayshat ba komai kawai kaina ne ke ciwo. " humm Yaya kenn karkasa kanka cikin damuwa dan yafindo tayi man wannan abin, 

dan kuwa yaya ga idonka nan ya nuna kayi kuka. " abinku ga farar fata idonshi yayi jajer, saida Mujaheed ya lumshe idonsa kafin ya bud'e ya k'irkiro murmushin yake Wanda yafi kuka ciwo, yace "no my lovely sister am telling u the Truth meye zai sani kuka? 


" hannu Ayshat tasa ta kama hannun Mujaheed ta rike gam,  

Tace" humm Yaya nasani ba Wanda yaso ya taimakeni sai kai, 

Yaya Na tabbata KAINE GATANA, kaso na auri wanda nake.... "Maganarta ta tsaya ne sakamakon kukan da yaci k'arfinta,

Kanta ta daura saman cinyarshi tana cigaba da kuka,

Sai da Mujaheed yayi ajiyar zuciya kafin ya d'ago hannunshi yana Shafa gashin kanta yace " please my sister stop crying, forget what happen today, everything will go normal I promise u. "Ahankali Ayshat ta d'ago kanta tace " yaya tayaya zan manta da yau ,

 bayan za'a rabani da Wanda nake tunani shine fari cikin rayuwata, yaya I Will never forget, A.K ne zabi na shine *MASOYINA NA HAR ABADA*. "tana ambatar A.K Mujaheed yaji wani Abu ya sokesa a zuciya.....
   *DEDICATED TO*

 *AYSHAT MUHAMMAD*

   ( *MAMAN SHAKUR* )
      ® *N.W.A*   ©  _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

.......................® _NWA_.........


         © *MRS UMAR*


          Page 81_85
Nan danan hawaye ya cika idonshi,

Da sauri Mujaheed ya kauda kanshi gefe saboda baya son su gani, ahankali ya lumshe idonshi cikin sanyin murya,

Yace "please meenat take Ayshat to ur room pls.ok yaya. 

"Ahankali meenat ta tada Ayshat suka nufi k'ofar fita, har suka fita Mujaheed bai bude idonshi bah,

Tunani kawai yake a zuciyarsa saboda yanzu bai San mafita bah, ya tabbata idan har yabar garin Katsina ya tafi aikin soja, toh ya rasa Ayshat kenn saboda kafin yadawo anyi mata aure,Bangaren mom da dady koh ba magana, dan kuwa mom kuka take ba gaggau tawa, yayinda dady keta bata hakuri ahankali, tace " Alhaji tayaya zanyi hakuri bayan ka fifita bare akan d'anmu na cikinmu, Alhaji kana kallon Mujaheed cikin damuwa amma bazaka share mashi hawayenshi bah, "Mom ta kara fashewa da kuka mai cin rai, 

Ahankali dady ya matso kusa da ita ya rungumeta, yace " please Khadija stop crying, sanin kanki ne Khadija nafi kowa son inga yayana cikin farin ciki,

Sai dai wannan lokani dole muyi hakuri da abinda ya faru, inba kina so mahaifiyata tayi fushi dani ba NA HAR ABADA, kina so tayi fushi dani? " mom da sauri ta d'ago kai ta gargiza mashi kai alamar a'a, murmushi yayi mai cike da jindadi yace " Khadija kiyi hakuri shikuma Mujaheed muyi masa addu'a Allah yabashi wadda tafi Ayshat,

Nima ba yanda zanyi ne dankuwa nasan mahaifin T.K farin sani,

T.K d'ane d'an ido Wanda iyayensa sun sangartashi baya ganin kowa da gashin arziki,

T.K cikkaken d'an iskane na bugawa a jarida, saboda duk wani kayan maye ba Wanda T.K baya sha, bansan me yafindo ta gani a T.K bah? "Hummm yanzu Alhaji duk kasan wannan halin nasa amma zaka bari abashi Ayshat. 

" Toh Khadija yaya zanyi kinsan halin yafindo yanzu ina furta wata magana zatace ina goyanma Mujaheed baya ne, sannan kuma tayi Fushi dani,

Ni gaskiya inaso na rabuda ita lafiya. "Mom bata sake magana bah sai dai kawai ta juya ta kwanta, shima sai kawai ya kwanta abinsa.Washe garin 

Mujaheed kwanan zaune yayi baiyi bacci bah,

Kowa ya fito wajen Dinning table amma babu Mujaheed,

Dady ya dubi mom yace " ina Mujaheed yake yau bai fito bah? "Maybe yana d'akinshi meenat jeki kirashi. " da sauri meenat ta tafi dan kiranshi,

Bata bata lokaci bah, sai gata sun fito tare amma kanshi na kasa,

Inda yasaba zama can ya nufa yaja kujerarsa ya zauna, yace " good morning dady and mom. "Morning my son. "Cikin sanyi murya Ayshat tace " ina kwana yaya " lafiya. "Ya amsa amma koya d'ago kansa, 

Kanshi na kasa meenat ta tashi ta zuba mashi abinci hannu ya d'aga mata yace " is OK I will do'it by my self. "Meenat da sauri ta koma wajenta ta zauna saboda tasan halin yayan nata da bakar zuciya,

Ruwan tea kawai ya zoba shima yakasa sha sai wasa yake da cup d'in,

Ahankali mom ta kalli dady, 

Dady yayi saurinyi Mata alama da ido tayi shiru kartayi magana,

Dady yayi gyaran murya kafin yace " Mujaheed mungama maganar komai da abokina Alhaji Aliyu nace ya samo maka form d'in Army so yace ba Matsala ansamu,

Dan haka ka fara shirya kayanka,

Nan da ranar Monday zaka wuce.

"Da sauri Ayshat tace " why dady? "Dady yayi sauri da katar da ita ta niyar d'aga mata hannu yace " just keep quite this is not ur business, dan haka kema ki shirya in zan wuce office zan tafi dake gida.

"Cikin fushi Mujaheed ya ture     cup din tea d'in, 

Sauran kad'an da ya kife kasa da sauri ya mike tsaye ,

Ya nufi d'akinshi mom zata kwala masa kira dady yayi saurin riko mata hannu, 

Meenat duk da yarinya ce amma ta fahinci akwai wani Abu dake faruwa,

Ayshat itama cikin bacin rai ta mek'e tsaye ta nufi dakin meenat,

Bata b'ata lokaci bah sai gata da hijab d'inta a hannu,

Saboda tasan ba komai yasa dady yayi hakan bah sai kawai dan yaga ya Mujaheed zai taimaketa,

   *DEDICATED TO*

  *AYSHAT MUHAMMAD*

    ( *MAMAN SHAKUR* )  

       ®  *N.W.A*


       © _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

...................® _NWA_.............


     © *MRS UMAR*


      page 86_90Dad suna zuwa suka samu yafindo zaune a tsakar gida tana gyaran wake,

Cikin ladabi dad ya gaidata itama ta amsa sannan, 

Yace " toh yafindo ga Ayshat nan na maido d'an Allah karda abarta tana yawace yawace,

Shi kuma wannan yaron da zata aura asan inda za'a dinga barinsu suna tad'i,

 Saboda kinsan yaran yanzu kahaifesu baka haifi  hali.... "Dakata Abdullah wannan yaron dakake gani d'an gidan mutunci ne yaron ne mai tarbiya, dan haka banason wata magana tashi kaje inda zaka. " toh Allah huci zuciyarki. "Amin.

  " da sauri dad ya mek'e tsaye yace "toh a huta lafiya sai anjima. "Yafindo tayi kamar bata jishi bah,

Saboda ya taba zuciyarta T.K, yana fita kamar Ayshat na jira,

  Tace " humm yafindo kenn kina nuna wannan d'an iskan T.K yafi kowa a wajenki... "Ke!! Mijin naki kike cema d'an iska dama baki da kunya. " a'a yafindo kidaina kiransa da mijina dan kuwa Wallahi bazai taba zama mijina bah, mijina na can bawan Allah amma ba wannan d'an iskan bah.

  "Toh marar kunya yaya kikayi shiru! kici gaba mana, inga kozaki d'auki kanki kikai gidanshi, batare da muna so bah, 

  Yarinya idanma zaki sawa zuciyarki ruwan sanyi kisa mata dan kuwa aure da T.K anyi angama... " Ayshat ta k'ara zuciyata nan danan idonta ya canza kala,

cikin fushi tace "yafindo!! Kenn nikuma naga yanda za'ayi na aureshi " tana rufe baki ta fad'a d'aki abinda, yafindo tace "aikin banza nasan dai yarinya bani buguwa bani zaguwa...


Bangaren Mujaheed kuwa ya saddakas dan bai San abinyi bah, sai dai kawai yayi alkawarin duk ranar da akace anwaye gari Ayshat bashi ta aura bah, toh shida aure har abada yanzu zaibi umarnin mahaifinshi...


A.k ne tsaye jikin motar T.K,

Ahankali T.K yafara magana cikin isa yace " I call u here because of Ayshat, inaso kabani hankalinka dukka kazo kaci arziki,

Business zamuyi dakai, humm A.k inaso ka barmin Ayshat zan baka naira na gugar naira, naira million d'aya,

Sannan da sharadi zakaje kasamu Ayshat kace mata baka sonta, idan har kayi haka toh kaci one million, sannan kum.... "Dakata T.K stop this act, this is impossible, tayaya zan bar maka Ayshat humm ai wannan ba magana bace. 

 "Oh friend please come down listen to me, idan kud'i sunyi ma kadan ne so I will give u more, burina kawai ka barmin Ayshat. "Humm T.K kenn ai ni, bani da burin in barwa wani Ayshat ba tare da nayi niyar abinda nasa kaina bah,

Dan haka karike kud'inka banaso. 

 " au haka kace? Humm yaro man kaza, but A.K kana da labari ba'a takara da T.K kuwa? Dan Wallahi duk Wanda yace zaija da T.K sai yazama abin kwatance a idon jama'a,

dan haka yanzu ya rage ruwanka koka amshi kud'i kokuma kabarta dan dole. "Humm T.K kenn muzuba ni dakai aga wa Allah zaiba sa'a. "A.k yana rufe baki ya kara gaba abinshi,

T.K ya bugi steering mota da hannunshi, yace yaro baisan wuta ba sai ya taka, dani kake wasa.....


Ayshat tayi shirin islamiyya tayi tsaf da ita,

Taci uwar kwalliya kamar wadda zata gasar kyau,

Sai kace ba islamiyya zata bah, 

 Yafindo tace " ke indo yanzu ba islamiyya zakije bah? Kikaci wannan uwar kwalliya. "Ayshat kota ba yafindo amsa kawai ta fizgi jakarta ta kara gaba abinta,


Tana fita ba inda tayi tsnke sai gidansu A.K
   *DEDICATED TO*

 *AYSHAT MUHAMMAD*

    ( *MAMAN SHAKUR*)


     ® *N.W.A*


      © MRS UMAR

*MASOYINA NA HAR ABADA*

......................® _NWA_..........


      © *MRS UMAR*


          page 91_95

     Tana zuwa d'akinshi ta nufa direct, dama d'akinshi na zaure ba cikin gidansu yake bah,

Ayshat bata tsaya wata wata bah, kawai ta tura k'ofar d'akin tasa kai,

Kwance yake dagashi sai boxer sai yar wata farar skeletal, wadda bazata wuce two Hundred bah,

Cikin zafin nama ya juyo da sauri,

Yace "Ayshat lafiya meke faruwa, " kamar tana jira ya tambayita ta fashe da kuka tace "A.K akwai Matsala.

" da sauri A.K ya tashi daga kwancen da yake ya nufo wajenta,

Cikin salo na yan duniya ya kama hannayenta ya zaunar da ita kan cinyayyar katifarsa yace "baby what is wrong with you? please just Tell me. " cikin shashekar kuka Ayshat,

 tace "there is problem, A.K yafindo saida ta tilastawa kanen mahaifina har ya aminci da na aure T.K.

" what!!! Oh my God' kina nufin yanzu Alhaji ya aminci da ki auri T.K? "Yes. " no baby this is impossible tayaya yafindo zatayi mana haka bayan munyi alkawarin aure dake,

Zamu rayu HAR ABADA sannan yanzu ace a'a. 

"Ayshat ta kara sautin kukanta saboda yanda taga masoyin nata yayi kamar da gaske, 

Da sauri ya fizgota, jikinshi har rawa yake,

Yasata a k'irjinshi yana shafata, cikin dakusasar murya yace " stop crying is OK. 

"Hannunshi ya d'aga yana Shafa bayanta,

Can yakai hannunsa yanaso ya zora cikin rigarta, cikin zafi nama ta buga tsalle ta mike tsaye, bakinta na rawa tace " A.K what are u doing? "Oh baby please colm down nifa mijinki ne karki manta. " humm A.K kardai kace man halinku d'aya da T.K?

idanku haka ne toh wallahi.... "Kafin ta k'arasa yayi saurin rufe mata baki yace " please baby listen to me, I'm ur husband. "Ayshat ta buga uban tsoki ta fizgi Jakarta, kafin yasha gabanta har ta bar d'akin,

Dan haka babu yanda ya iya sai kawai yadawo ya zauna, ya dafe kanshi yaso ace yau yasan Ayshat a d'iya mace,

itako sauri take kamar zata tashi sama, ita kanta bata San ina ta nufa bah,
*Ranar Monday*

Yau ta kama ranar da Mujaheed ya kamata ya tafi N.D.A,

Gidan ya koma tamkar anyi mutuwa dan kuwa duk Wanda ka kalli fuskarsa zakaga alamar yayi kuka,

Ba kamar meenat saboda ta saba da yayanta,

Zaune take bakin gadon shi kuma yana ta hada kayansa, sai da ya gama had'a bag dinshi kafin yace " toh idan kin gama kukan tashi mutafi ,

Sannan kuma karki manta da alkawarin da kika daukar man, zamu dinga waya a ko wane lokaci,

Muje dady na jirana a waje,

Suna fita suka samesu a tsaye dama dady shi kawai yake jira ya fito, mom ko tsaye take ta buga uban tagome,

Sannan Mujaheed ya k'arasa wajenta ya durkusa har kasa yace "toh mom ni zan tafi ki tayani da addu'ar samun sa'a,

 sannan idan nayi maki laifi kiyafe man.... " maganarshi ta tsaya ne sakamakon kukan da yaci k'arfinshi, itama mom kukan take,

Ahankali tasa hannayenta, ta d'agoshi tana mai share masa hawayen, tace " Mujaheed bakayi man laifin komi bah, sannan a matsayina na mahaifiyarka ako da yaushe ina maka addu'a,

Mujaheed yanzu waje ne da zakaje ba uwa ba uba daga kai sai halinka saiko abokan arziki, Dan Allah Mujaheed ka kama kanta babu ruwanka da mutanen banza,

 sannan kariki addininka banda wasa da ibada,

Kayi abinda yakaika dan Allah. "Mom I promise bazakiji wata Matsala daga gareni bah.

" yauwa my son thank u Allah yabada sa'a. "Amin mom. 

" mom tayi murmushi sannan ta shafi kumatunshi, "kinga Khadija ya isa haka kibarsa haka karkija muyi late, 

time na tafiya Kaduna ba nan bace. " toh Alhaji ba dole bah tunda ka rabani da d'ana.

"Dukkansu suka kwashe da dariya sab'anin meenat da tayi murmushi,

Yau dady shi yace zayayi driving d'in motar da kanshi, baba mai gadi ya bud'e masu get har suka fita mom da meenat na daga masu hannu,

Mujaheed yaso ace yaga Ayshat kafin yatafi amma babu yanda ya iya haka ya hakura,

Nan fa dady ya kama hanyar Kaduna......
  *DEDICATED TO*

 *AYSHAY MUHAMMAD*

   ( *MAMAN SHAKUR* )       ® *N.W.A*


      © _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

......................® _NWA_..........


         © *MRS UMAR*

  

         Page 96_100Ayshat bata ganta ko ina ba Sai k'ofar gidansu,

 tayi mamakin haka a tunaninta hanyar islamiyya take tafiya, tsoki ta buga tace "wallahi tunda nazo nan ba abinda zai maidani islamiyya yanzu. " kai tsaye ta danna kanta cikin gida,

Inda tabar yafindo nan ta sameta zaune,

Falo ta nufa kota kalli yanda yafindo take, "ke indo ina islamiyyar take? kika dawo kamar zaki tashi sama,

Au ina maki magana shine zaki shige d'aki,

lallai yarinyar nan sai na gyara maki zama. " yafindo keta faman fad'anta dan kuwa Ayshat bajinta take bah,

Kai tsaye Ayshat ta nufi bedroom tayi wurgi da Jakarta gefen bed, 

Kan gado ta fad'a ta fashe da kuka mai cin rai,

Cikin murya kuka tace "oh my God what is wrong with me? abinda zuciyata kegaya man gaskiya ne, A.K shima dan iska ne? No!!!! That's impossible, 

nasan A.K bazai man haka bah, ina ba halinsu d'aya da T.K bah..... "Maganarta ta tsaya ne sakamakon kukan da yaci k'arfinta,

Muryar yafindo taji a kanta tana cewa "ke indo meya faru kike damun mutane da kuka? Ko yanzu T.K ne yayi maki wani Abu kuma?. " kai ta girgiza mata alamar a'a. "Toh kedawa? " dama.... "No!!! Ayshat don't say anything. " da sauri Ayshat ta rufe bakinta saboda bin abinda zuciyarta ta bata shawara. "Inajinki dama me? 

" dama ba komi. "Au ba komi jindadi ne ya saki kukan? " shuru Ayshat tayi saboda batasan amsar da zataba kakar tata bah,

"Kekika sani nidai kakarki ce babu abinda zaki boye man,

 saboda yanzu ina kamar matsayin mahaifiyarki ce, dan haka nibari na gaya maki abinda ya kawo ni, bayan fitarki dazu T.K yazo yace sati mai zuwa zaya turo magabatansa. "What?!!! Yafindo zai turo kuma? "Eh ko kina da magana ne? " kai Ayshat ta girgiza alamar a'a, 

"Ai gara da kikace a'a yarinya dan kuwa aikin gama ya riga ya gama, 

Nan da wani lokaci T.K ya zama mijinki. " yafindo na rufe baki tajuya ta fita abinta, Ayshat ta kara fashewa da kuka mai cin rai.....Bangaren dady da Mujaheed sun isa garin Kaduna lafiya yayi da Mujaheed ya samu karbuwa a N.D.A,

Bayan dady ya gama komai ya kama hanyar dawowa gida sannan yayiwa d'ansa fatan alkhairi,

Mujaheed sai yanzu ya kara jin zafi rabuwa da iyayensa ga Uwa uba masoyiyarshi Ayshat...


Washe gari

 Ayshat tayi shirin zuwa school yau tayi late, ba kamar yanda ta saba tafiya bah, shiyasa take sauri, kota tsaya tayi breakfast, kud'i kawai ta amsa wajen yafindo ta kama hanyar fita waje,

Abin mamaki tana fita sai kawai taga motar T.K tayi parking a k'ofar gida ......

*DEDICATED TO*

 *AYSHAT MUHAMMAD*

   ( *MAMAN SHAKUR*)
    ® *N.W.A*

   © _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

........................® _NWN_........


         © *MRS UMAR*


          page 101_105Zaune yake cikin motarshi ya zuro kafafuwansa a waje, yana wasa da key d'in motarsa,

Ayshat tazo ta gabanshi zata wuce tayi kamar bata ganshi bah,

Da sauri yasha gabanta, "please Ayshat listen to me I want to talk to u about our marriage. " cikin fushi Ayshat ta juyo tace " u say what? Humm T.K how many times I tell u to live me a long. I don't want to see ur face again,

T.K I hate u I don't want to marry u,

Because na riga na gama fidda mijin da zan aura kai baka cikin tsarin namijin da nakeso. "Ayshat ta rufe baki ta juya zata tafi T.K yace "humm Ayshat kenn yaro yaro ne, shi wanda kike son kinsan abinda yake aikatawa a bayan ido..... "Keep quite Karka kuskura ka fad'i wata magana ga mijin da zan aura. " hhhhhhh au kina tunanin A.K har zai zama mijinki toh wannan munmunan mafarki kike gara ma ki farka da sauri kafin ya gaya miki karya. "Mtss aikin banza. "Ayshat bata tsaya jin abinda zai kara cewa ba ta k'ara gaba abinta,

T.K yayi zuciya hannunshi ya buga jikin motarsa ya ciji lebonshi, "this girl if she enter my hand I will deal with her. " yana rufe baki yashiga motarshi abinsa,

Itako Ayshat tana karawa gaba kad'an sai ga school bus dinsu Wanda a jikin bus d'in aka rubuta, 

( *saldefi international school*) bata tsaya wata wata ba ta shige bus d'in,

 saboda tana tunani ko ya biyo ta a baya,

Har suka isa school batayiwa kowa magana bah, 

Dan haka ba Wanda yayi mata magana,

Saboda mutane da yawa suna cewa tana da girman kai, tana TAK'AMA da mahaifinta dan yana zama a India, shiyasa badakowa take magana bah,

Suna isa ta fizgi school bag d'inta ta nufi class d'insu,

Kujerarta da ta saba zama can ta nufa,

Yau abokiyar zamanta batazo bah,

Tagumi ta buga tana mai tunanin halin da masoyinta yake ciki yanzu, tun bayan rabuwarsu bata kara jin muryarsa bah,

Gashi bata da waya ballantana ta kirasa, saboda yafindo har yanzu irin mutanen nan ne da bata yarda budurwa ta rike waya ba har sai tayi aure, 

Ayshat na cikin wannan tunani ne sai taji muryar kawarta mai suna UMMI AYSHA da sauri ta d'ago kanta tace " yauwa ummi Aysha dama ke nake jira wallahi, dan Allah bani aran wayarki na kira A.K. "Sai da ummi Aysha ta sauke ajiyar zuciya kafin ta zauna, tace " Ayshat kedai a kullum maganarki bata wuce ta A.K.

"Hummm ummi Aysha ba dole bah,

Kinsan kuwa yanzu anaso a hadani aure da wannan dan iskan T.K d'in nan? "Humm toh nidai Ayshat a matsayina na kawarki shawarar da zan baki kibi umarnin iyayenki, 

Because idan kina tunani T.K dan iska ne, sai kiga sanadiyar auranki Allah yashiryar dashi, auransa ya zama *WANI HASKE* agareki..... " dakata ummi Aysha nafuskanceki kema kina d'aya daga cikin mahassadanmu. "Haba Ayshat karki ce haka ni kawarki ce ta gaskiya,

Ayshat karki manta a gabanki akayi auran HABEEB LAMIDO DA HALEESA basa son junansu akayi auran wace irin wahala ce habeeb lamido baiba haleesa bah, but daga baya son da yake mata ko MADAM HINDU bayayiwa irinsa.

" ummi Aysha kenn habeeb lamido da haleesa kikace harki manta ba Ayshat kikace bah,

Habeeb lamido da ban Ayshat daban. "Humm Ayshat kenn kedai na fuskanceki idan ace maganar A.K ce toh baki hadashi da kuwa bah. "Eh mana Ai akan A.K zan iya batawa dakowa wallahi.

" humm kinga Ayshat mubar magana nan haka ta isa,

Fatana dai Allah ya zaba maki abinda yafi zama alkhairi. "Hhhhhhh Ai Allah yariga yayi man zabi saboda ga A.K nan. "Humm Ayshat kenn. 

" ummi Aysha tana rufe baki tayi shuru bata K'ara yima Ayshat magana ba dan gudun Matsala.....


*KADUNA*


masha Allah duk abinda aka koyawa Mujaheed yanayi bakin gwargwado,

Abinda yakaishi kawai yasa a gaba duk da yana tunanin Ayshat but haka bai hanashi yin abinda yakaishi bah,

Tunda Mujaheed yaje bashi da aboki sai mutum d'aya mai suna LUKMAN, shima sai da yaga kamun kansa da yawan ibadarshi kafin ya kulla abuta dashi, gaskiya bangaren Mujaheed ba wata Matsala.......
*DEDICATED TO*

 *AYSHAT MUHAMMAD*

   ( *MAMAN SHAKUR* )

     ® *N.W.A*      © _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

..................® _NWA_ .............


       © *MRS UMAR*


         page 106_110
Dady ne da mom zaune a falo, yana bata labarin abinda ya faru, 

Sai da dady ya sauke ajiyar zuciya mai k'arfi kafin, yace "humm Khadija duk wani bincike da zanyi akan yaron nan nayi,

But ba Wanda yabada shedar arziki, kowa ceman yake T.K ba mutumin arziki bane. " toh yanzu Alhaji haka za'a d'auki d'iyar abashi? "Toh Khadija yaya zanyi da rayuwata dole nabi umarnin yafindo? dan gudun Matsala. " ina Alhaji wannan ba magana bace karka manta wannan yarinyar d'iyace a wajenka duk abinda kayi mata toh zaka bari ayiwa meenat saboda duk d'aya suke a wajenka. "Khadija nasani Wallahi son da nakewa Ayshat jinake tamkar ni na haifeta,

Toh yaya kikeso nayi da rayuwata, bayan kinsan halin yafindo. " haka ne kuma maganarka Alhaji toh shi kenn mutayata da addu'a Allah yazaba abinda yafi zama alkhairi. "Toh haka kawai zamu iya cewa.

" dady da mom basu sake tada maganar bah,

Sai kawai suka ci gaba da wata firar.......*AFTER ONE WEEK*


yau iyayen T.K sukazo aka tsayar da lokaci aurensu da zarar ta gama makaranta da sati biyu za'a daura masu aure, iyayen T.K ba yanda basuyi bah akan a dawo da bikin kusa kusa in yaso sai ta ida makarantar a gidansa,

Amma dady ya cije akan sai ta gama school kafin ayi auren,

Ba yanda suka iya haka suka hakura,

Bayan sun koma gida suke gayawa T.K yanda sukayi,

Dariya yayi, kafin yace ba damuwa yasan dai yanzu nan da dan wani lokaci ta zama mallakinsa, shi d'aya.....Bangaren Ayshat kuwa, ina wuta ta saka yafindo bala'i kawai take Mata ga hawaye na bin fuskarta,

 tace "yafindo yanzu burinki Ya cika koh? Yanzu ansa ranar aure na da wannan dan iskan, toh Wallahi yafindo kisani sai dai in gawata zakukai gidansa dan Wallahi bazai taba zama mijina bah, 

 insha Allahu sai na auri A.K sai dai mahasadanmu suji kuny....... " kawauuu kararar Marin da yafindo takai mata ne ya tsayar da ita da maganar da take gayawa kakar tata, "Dama indo bakida kunya akan wannan talakan yaron zaki dinga gaya man magana,

 toh nikuma naga ubanda zai hana wannan auran indai ina duniya, marar kunyar banza.

 " cikin kuka Ayshat take magana, "why? Yafindo u hate me so much, 

a da yafindo da nasani mai sona ce mai son gani duk wani farin cikina mai kin duk wani abinda bana so, sai dai yanzu wannan yafindo halinsu ya banbanta da waccen yafindo.

"Kuka ta kara fashiwa dashi da gudu ta nufi bedroom, " aikin banza kaji min yarinya marar kunya.

"Yafindo na aiki tana ci gaba da fad'a.......


Ayshat tana fadawa kan gado taci gaba da kuka,

Saida ta d'auki wani lokaci tana kuka kafin ta saisai ta zuciyarta saboda ba mai bata hakuri,

Sai yau ta tuna da yayanta ahankali tace "Allah sarki yaya Mujaheed I missing u nasan da kana nan da duk wannan abin yazo man da sauki,

Koda zuciyata ce da ka kwantar man da ita I miss u very much,

A.K nasan kana fushi dani but gobe insha Allahu zan sameka muyi magana,

Because bazan iya zama da kowane namiji bah in ba kai bah, Kaine *MASOYINA NA HAR ABADA* I Luv u my A.K....

" kuka ne yaci k'arfinta, shiyasa maganarta ta tsaya..

    *DEDICATED TO*

   *AYSHAT MUHAMMAD*

     ( *MAMAN SHAKUR* )      ® *N.W.A*      © _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

.................® _NWN_...............


       © *MRS UMAR*


          page 111_115
.Washe gari 

Ayshat sauri take ta gama shirin school, dan kawai ta fara biyawa wajen A.K kafin ta wuce school d'in,

Tana cikin sa hijabinta ne wani yaro yayi sallama,

Da sauri yafindo ta amsa masa, yace "wai ance ana sallama da Ayshat a waje. " injiwa? "ceman yayi ince A.K ne. " jika kace bata nan. 

"Yaron har ya juya Ayshat ta fito da sauri har tana karo a k'ofa, tace " kai jekace gani nan zuwa. "Yafindo ta mik'e tsaye cikin b'acin rai tace " toh marar kunya nace bakya nan shine kika ce kina zuwa koh? Wallahi Indo ki fita daga idona tun kafin ranki ya bace. "Mtsss. "Tsoki Ayshat ta buga ta juya tayi tafiyarta. 

"Yarinya zaki ci gidanku indai nice zaki dawo gidan ki same ni,

Kuma insha Allahu T.K yaga zama mijinki, naga uban da ya isa ya haka. " haka yafindo taci gaba da fad'a yau anyi sa'a da bata bita bah..... 


Ayshat tana fita ta samesa jikin bango a tsaye ya tada kanshi da bangon, da sauri Ayshat ta k'araso wajensa tace "mutafi kafin wannan tsohowar ta fito yanzu. " tana rufe baki ta fara tafiya shi kuma ya take mata baya,

Sai da sukayi nisa da gidan ta yanda yafindo bazata biyosu bah, sannan suka tsaya,

A.K yace "please baby am sorry.... " kafin ya k'arasa Ayshat tasa dan yatsanta a bakinshi alamar yayi shiru,

Tace "A.K forget dat time, 

A.K akwai babbar Matsala. " inajinki what is the problem? 

"A.K jiya iyayen wannan dan iskan sunzo har yanyi magana aurenmu da zarar na gama school da sati biyu za'a daura mana aure. " what? aure fa kikace? "Eh. " ina, baby ke TA WACE tayaya zan waye gari bakya gidana,

Hummm T.K in kasan wata ai baka san wata bah,

dani kake zancen.

"A'a me yafaru? " humm baby don't worry kibar komai a hannuna. "Kamar yaya? " ke dai kiyi abinda na gaya miki kinji koh? "Kai Ayshat ta d'aga masa alamar gamsuwa, " yauwa baby koke fa muje na taka maki.

"Haka suna tafiya suna fira har bus d'insu tazo,

Sai da yaga ta shiga kafin ya kama hanyar dawowa gida..


*SIX MONTH LATE*


akwana a tashi babu wuya wajen Allah yau Mujaheed ya cika wata shida a N.D.A yau zasuyi passing out,

Dakaga Mujaheed ya zama cikkakin soja sanye yake cikin kamo uniform army,

Fuskarnan tashi babu alamar murmushi ko alama,

Mutanene a N.D.A ancika kota ina maza da mata babu ko matska tsnke,

Mujaheed tsaye yake a jikin wata bishiya lokaci kadan, ya kan duba watch d'in hannunsa,

ya duba sai ya buga tsaki,

Ahankali yaji daga bayanshi ana magana "conjuration on ur passing out parade my son. " Mujaheed yana juyowa yaga dady ne ke magana ya kara bata fuska.

"My son are u argy with me? " yes dady I was waiting for u many time I didn't see u.

Ahankali mom tazo takama hannunshi tace "oh my son am sorry Wallahi mun taho a hanya motar mu ta tsaya munata try phone dinka but network besy. " humm Wallahi mom har nayi fushi tun d'azo kowa yazo banda family d'in na bah.

"Dukkansu suka sa dariya, dady yace " Mujaheed sarki rigima kana nan da halinka ba abinda ya ragu. "Sai yanzu Mujaheed yaga meenat tsaye shi kawai take kallo ta kora masa ido,

Why are looking at me?don't you come and greet me? "Meenat tayi murmushi ta karaso wajenshi tace " am sorry yaya naga kana fushi ne."toh ba dole bah sister ya su yafindo Baku tafo tare bah?

"Meenat ta gane abinda yake nufi shi yasa ta basar da maganar ta cewa, " wow yaya ka ganka kuwa cikin kakin soja yanda kasan Obama, 

Gaskiya kayi kyau.

"Humm toh uwar surutu muje ga wajen zama a can...


Ansha hidima yanda kuka San biki haka wajen ya cika yayinda Mujaheed ya fito officer muk'amin second Lotternal

Bayan an gama abinda ake aka rarrabasu battalion d'in da za'a kaisu,

Shi Mujaheed Abuja aka kaishi a yar'aduwa barrack,

Yaso ace an ajiyeshi a Katsina amma haka yaci tura,

Su dady basu dawo gida bah, har sai da suka ga tashinsu yayinda meenat keta rusar kuka......

.
  *DEDICATED TO*

  *AYSHAT MUHAMMAD*

    ( *MAMAN SHAKUR* )       ® *N.W.A*


      © _MRS UMAR_


[11/6, 11:46 AM] Mrs Umar: *MASOYINA NA HAR ABADA*

.....................® _NWA_..........


        © *MRS UMAR*


           

          page 116_120
Mujaheed sun isa garin Abuja lafiya, daka ganshi kasan akwai alamar gajiya a jikinshi, yaci sa'a waje d'aya aka kaisu shi da LUKMAN,

 A pared ground motocinsu sukayi parking,

Basu sha wata wahala bah akace kowa yaje ya samu waje ya huta kafin gobe suzo office,

Da yake ba abasu gidaje bah,

 Daga mai tafiya officer mess sai mai tafiya soldiers club,

 Mujaheed yace ina shi bazai iya kwana officer mess bah,

 Sai dai suje Hotel sukwana shida Lukman,

Inyaso da safe su dawo barrack,

  Basusha wahala bah, suka samu hotel a nan wajen Abachi barrack, sun kama bed room inda zai ishesu kafin a basu gida,

Suna shiga Mujaheed bai tsaya komai ba ya nufi toilet,

Sai da ya watsa ruwa kafin yayi alwala ya fito,

Yana fitowa yasa white jallabiyarshi, 

Sannan ya shinfida sallaya, duk Lukman na kallonsa amma ba wanda yayiwa dan uwanshi magana,

Sai da Mujaheed ya tada sallah kafin Lukman shima ya nufi toilet yayi duk abinda Mujaheed yayi kafin yazo shima ya tada tashi sallah,

Bayan Mujaheed ya gama sallah yayi addu'a nan inda yake ya tada kanshi da kujerun dake room d'in,

 Lukman ya gama sallah sai bin abokinshi yake da kallo,

 ahankali yazo kusa dashi ya zauna, 

Cikin murya kasa_kasa yace "abokina I don't known what is wrong with to u, tunda su dady sukazo na rasa gane kanka,

Please abokina nasan kana cikin damuwa dukda baka fad'a man bah,

But nasan da haka, please forget everything that happen to u,

 Yanzu sabuwar rayuwa zakayi kafiskanci abinda ya kawomu.

 " ahankali Mujaheed ya sauke ajiyar zuciya sannan ya k'ak'aro murmushi k'arfin hali, yace "abokina don't worry ba abinda ke damuna but am very tired, kasan wannan aikin namu akwai gajiya. " Mujaheed kenn har yanzu kak'e fad'a man damuwarka,

Humm but no problem muje mu kwanta,

 Kasan gobe da safe zamu fita. "Mujaheed baiyi magana bah, sai dai kafad'arshi da ya d'aga,


Lukman yayi murmushi saboda yasan abokin nasa meskilin mutum ne,

Lukman ya haura kan bed ya kwanta yayinda Mujaheed ya haura kan kujera ya kwanta ,

Lukman yace " what are you doing? nothing I just want to sleep on the chair.

"Humm ok. " Lukman bai sake magana bah,

 Ya juya yayi kwanciyarshi yayi kamar yana bacci, nan ko ba bacci yake bah,

Yana tunanin halin da abokinshi yake ciki ne tun haduwarsu a N.D.A ya gano akwai abinda ke damu Mujaheed amma yak'i ya fad'a masa,

 Amma yanzu yayi alkawarin sai yagano Matsalar dake damun abokinsa yayi masa maganinta,

Indai batafi k'arfinsa bah,

Yana cikin wannan tunanin ne har bacci yayi gaba dashi,

Yayinda Mujaheed idonshi ke rufe ko bacci yake oho dai,


Washe gari


Tun misalin 5:00AM suka tashi danyin shirin tafiya office kar suyi lat saboda ba cikin barrack suke bah, sai da sukayi sallah asuba kafin sukayi dressing, Lukman ya kira da phone d'in dake room d'in ya Kira receptionist yace "a kawo mana Berkfeast zamu fita yanzu. 

"ba'a bata lokaci bah aka kawo masu....


Basu isa office bah,

Sai around 7:00am suka isa because yanda garin Abuja yake da cinkoso,

Suna zuwa kowane ya nufi office d'inshi, 

Mujaheed zaune yake kan chair tanayi tana juyashi ga sanyin A.C na shigarsa,

 But da kaganshi kasan akwai damuwa a fuskarshi,

Kujerar na cikin juyawa dashi phone d'inshi tayi k'ara,

Bai tsayawa dubawa bah,

Ya d'aga muryar Meenat yaji tace " hello yaya gata na kawo mata wayar.

"Mujaheed bayi magana bah,

Meenat ta mekawa Ayshat waya, ahankali cikin muryarta mai dadi tace " Assalamu alaikum yaya. "Da sauri Mujaheed ya rufe idonsa, ya sauke ajiyar zuciya yayinda tsikar jikinshi tatashi yarrr.......

  *DEDICATED TO*

  *AYSHAT MUHAMMAD*

    ( *MAMAN SHAKUR*
     ® *N.W.A*      © _MRS UMAR_

[11/8, 6:45 PM] Mrs Umar: *MASOYINA NA HAR ABADA*

.....................® _NWA_............


          © *MRS UMAR*


           121_125Ahankali yake bud'e idonshi yayin da yake rufesu,

Yana sauke ajiyar zuciya ahankali,

Murya Aishat ce ta dawo dashi duniya tace "hello yaya u can hear me? " yes Eshat I can hear u. "Itama Aishat da sauri ta rufe idanunta saboda bata taba jin yayanta ya kirata da wannan sunan bah, 

Yau ce rana ta farko da ya fara kiranta da wani sabon suna,

Bayan Mujaheed ya sauke ajiyar zuciya yace " sis shi kenan kin manta dani bakya tunanina koh?

Tunda natafi har Allah yasa mun gama gashi yanzu har an kawo ni Abuja.

 "Allah sarki yaya I am missing u so much, Wallahi yaya kullum da tunaninka nake kwana nake tashi,

Kasan har yanzu bani da waya yafindo tak'i bari, na rike waya har yanzu. " Eshat are u sure kinyi missing d'ina? "Yes yaya kana jin wasa ne? 

 " a'a kawai dai na tambayiki ne, toh ya kike ya school?


 "Lafiya Qlau school insha Allahu nan da 5 month na gama sai dai.... " uhmm ina jinki kinyi shuru kuma. 

 "Yaya ansa ranar aure na da T.K da zarar na gama school da sati biyu za'a daura mana aure dashi. " what saboda me su dady zasuyi haka?

"Wallahi yaya duk laifin yafindo ne, yaya yanzu yafindo bata son farin cikina sai dai duk abinda zai batamin rayuwa shi yafindo keso yanzu. 

 " oh my God, is OK sis don't worry insha Allahu komai zaizo da sauki ki kwantar da hankalinki,

INA TARE DA KE ako da yaushe kinji koh? Sannan zan dinga kiranki da wayar meenat muna magana,

Yanzu ina office bye.


"Mujaheed bai jira amsar Aishat bah,

Ya kashe wayarshi ahankali ya furta "I Luv u Eshat I really miss u, 

Insha Allahu ke *TAWA CE* ni d'aya.

 "Murmushi ya saki Sannan ya maida idonshi ya rufe kujerar naci gaba da juyashi....


 *********

Bayan Mujaheed ya kashe wayarshi Aishat ta mikawa Meenat wayarta,

 Meenat tayi murmushi tace " har kun gama kenan? "Humm eh Wallahi yace man yana office yanzu,

 Meenat wani abun ban mamaki yaya ya kira ni da yani sabon suna,

Wanda ban taba jin ya kirani da irinsa bah, kinsan wani abu kuwa Meenat? "A'a sai kin fad'a. 

  " humm Wallahi sunan yayi man dadi sai naji ina ma A.K ya kira ni da sunan da zaifi dadi.

"Humm Aishat kenn kinsan abinda na tuna kuwa? " a'a.

 "Alkawarinmu na tuna tun muna yara wanda ke kika ce insha Allahu mijin da zaki aura soja ne, ni kuma nace nawa lawyer,

 Sai dai gashi naki alkawarin bai cika bah. 

 " humm toh meenat yaya za'ayi haka Allah yaso,

 Naso na auri soja amma had'u wata da A.K sai naji na janye alkawarin.

 "Yanzu Aishat musali yaya yazo yanzu yace yana so ya aure ki zaki yarda? " hahaha Wallahi kin ban dariya meenat tayaya zan iya auren yaya bayan babu soyayya a tsakaninmu,

 Musalima haka ta faru gaskiya ba zan iya auren yaya bah,

 Saboda na daukeshi d'an uwa ciki d'aya, tabbas yaya yana da duk wani abun da mace zata so shi, sai dai ni zuciyata ta mutum d'aya ce,

watau A.K. "hahaha hakane Aishat na yarda ai musali ne nace wai ba da gaske bah.

 "Basu sake tada wannan maganar bah, 

haka sukaci gaba da firarsu da Aishat suna dariya,

 Can meenat ta fad'a tunani cikin zuciyarta tace " tabbas na yarda Aishat babu soyayyar yaya a zuciyarta,

 Zuciyarta ta mallakawa mutum d'aya ne,

 Toh tayaya yaya zai samu soyayyarta? 

 Bayan bata sonshi, kai akwai Matsala. "Sister Matsala meye? " da sauri meenat ta kalli Aishat saboda tana tunani duk maganar da take a zuciyarta tajita,
  *DEDICATED TO*

 *AYSHAT MUHAMMAD*

   ( *MAMAN SHAKUR*)       ®  *N.W.A*


 

     © _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

.........................® _NWA_............

  

         © *MRS UMAR*


          page 126_130
Meenat ta k'akaro murmushi k'arfin hali tace "no problem sister kawai am just looking for my phone,

 Naga kamar ta dauke ne. 

  " are u sure? "Yes. " OK forget that one, Meenat yanzu wacce shawara zaki bani akan wannan d'an iskan T.Kn da ake so a had'a mu?

 "Sai da Meenat ta sauke ajiyar zuciya kafin tace "humm nidai Aishat a matsayina na yar uwarki, shawarar da zan baki toh bai wuce nace kiyi hakuri kibi umarnin su yafindo bah, dan Ku rabu lafiya dasu.

 " humm Meenat kina nufin kema kina goyon bayan na auri T.K kenn? "A'a Aishat bana goyon bayan haka dan kuwa Wallahi nafiki son ki auri NAGARTACCEN namiji,

 A kullum ina maki addu'ar samun miji nagari mai hali irin na yaya Mujaheed.

 " hahaha Meenat kenan ai miji na gari na dad'e da samun miji na gari mai hali irin na yaya Mujaheed ko nace maki yaso ma yafi yaya hali na gari.

 "da sauri Meenat ta zaro ido tace " kai Aishat kar dai dadi soyayya yasa ki manta da halin yaya Mujaheed mana. 

 "Hahaha Meenat kenan how can I forget yaya, I can never forget yaya Mujaheed, 

 Yaya he is the best brother in world.

"Ummm na yarda da

,ke Aishat mubar wannan maganar,

 Naga tunda nazo kina d'aki bakije kin taya yafindo aiki bah? " mtssss wane aiki zan tayata? "Ke dakata Aishat ba dai gaba kike da ita bah? " eh mana gaba muke saboda ni yanzu ba ruwana da yafindo tunda take so ta raba ni da *MASOYINA NA HAR ABADA*,

 nayi alkawarin duk Wanda yayi yun kurin rabani dashi toh nima babu ruwana da mutun ko waye shi kuwa. 

 "Wa'iyazubillah Aishat kina da hankali kuwa? kada soyayya ta rufe maki ido ki manta da gaskiya,

 Yafindo a yanzu tana matsayin uwace a wurinki, tayi maki komai na rayuwa karki manta baya mana. 

 " Yauwa Meenat gaya mata gaskiya ai shiyasa nake sonki, kinfi d'an uwanki hankali da sanin ya kamata.

 "Maganar yafindo ce yasa duk suka juya kallon k'ofar d'akin

Tsaye take tana rike da cup a hannunta,

Cikin b'acin rai Aishat ta kalli Meenat tace "Meenat u see bah, kinsan halin yafindo da fad'a shine kika jawo mana ita koh.

 " toh marar kunya nice masifaffiyar koh?. "Cikin sanyin murya Meenat tace " a'a yafindo ba haka take nufi bah, kiyi hakuri d'an Allah,

 "Aishat ta buga uban tsoki tace " kinga muje na rakaki tunda kince gida zaki yanzu mu tafi. 

 "Meenat da sauri ta tashi tsaye gudun kar yafindo taci gaba da fad'a, tace " toh mu tafi, yafindo ni zan koma gida. "Toh Meenat ki gaida su mamantaki Allah yayi maki albarka. " oho dai muma da ba'a sa mana albarka bah, toh Allah yasa mana. "Yafindo tayo kanta da gudu ta nufi hanyar fita waje. " au da ki tsaya mana na nuna maki rashin kunyarki ta karya ce.

 "Meenat ma abinsu dariya yabata tace " Wallahi yafindo ki rabu da ita kafin ta kayar dake kasa. "Haba Meenat wane ita! ai ko ubanta bai isa bah bali ita.

 " Meenat ta kwashe da dariya tace "ni dai yafindo na tafi gida sai na sake dawowa. " toh ki gaida gida.


"Meenat tana rufe baki ta nufi hanyar k'ofar gida,

dai dai zauren gidan ta samu Aishat tsaye tana jiranta,

Murmushi tayi Sannan tace " sister baki da dama yanzu, kinja yafindo sai fad'a take.

 "Toh duk bake kika jayo bah.

 " a'a babu ruwana Wallahi. "Har suka fita waje suna gardama,

 Maganarsu ta tsaya ne sa kamakon ganin A.K tsaye a bakin k'ofar gidan malam mudi, 

Aishat kamar an sakata aljanna ta dinga washe baki,

Tace " Meenat ga A.K muje ku gaisa mana.

 Mtssss ni sauri nake babu inda zanje... "Dakata Meenat yanzu na yarda kina d'aya daga cikin mahasadanmu,

Toh ni koma Wallahi bazan rakaki bah.

 " Meenat bata tsaya bata amsa bah, sai dai tsoki da ta buga ta kara gaba abinta

Aishat ta juya ta nufi wajen A.K,

Dake tsaye yana kallonta sama da kasa,

 Ta k'arasa tana mai washe baki kamar gonar auduga,

Tace "sweetheart yaushe kazo? " humm Wallahi na dan dad'e tsaye a nan saboda ba yara yau unguwar taku.

 "Eh Wallahi duk sunje islamiyya.

 "OK dama nazo ne na gaya maki na sama mana mafita, kuma idan muka bita toh komai yazo k'arshe. " Aishat ta wane buga uban tsalle tace "da gaske kake ka sama mana mafita? kai today I am very happy, amma wacce irin mafitace? "Toh yanzu zan gaya maki mafitar...... Ina mai baku hakuri kan magana da kuke bana typing da sauri insha Allahu novel d'in yazo karshe....
  *DEDICATED TO*

 *AYSHAT MUHAMMAD*

   ( *MAMAN SHAKUR*)        ® *N.W.A*


       

       ©  _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

.....................® _NWA_..............


   

         © *MRS UMAR*


            Page 131_135A.K ya k'ara matsuwa kusa da ita cikin murya k'asa k'asa yace "please Aishat listen to me very carefully ki tsaida hankaliki ki saurare ni da kyau.

 " Aishat ta sakar masa murmushi, ta d'aga masa kanta alamar tana jinshi, yace "yauwa abinda nake so dake Ayshat,

Ki kwantar da hankalinki na saman mna mafita domin kuwa ita kadai ce mafita,kinsan ko wace irin mafita ce wannan kuwa?. 


" da sauri Aishat ta girgiza masa kanta alamar a'a, murmushi yayi mai dauke da jin dad'i, yace 

 "Aishat dole zamubi abinda zuciyarmu ta bamu shawara mu aikita shine kawai mafita a rayuwarmu,

 abinda nake so dake ki nuna a gida kin aminci da zancin auren T.K.... " dakata A.K ban gani bah kana nufin kaima ka aminci dana auri T.K kenan? 


  "Sai da A.K ya numfasa kafin ya girgiza mata kai yace " ba haka nake nufi bah, ina nufin idan kikayi haka kowa zai sakankance da kin yarda zaki aureshi, kinga sai biki ya kusa kawai sai mu gudu mu tafi wani waje muyi aurenmu su kuma nan mun dasa masu hawan jini kamar yanda suka kusan samu,


Da sauri Aishat ta zaro ido alamar tsoro, tace "no!! A.K that impossible wannan shawarar taka is not correct ta yaya zamu gudu mubar iyayenmu,

kana so suyi fushi damu kenn?

 " Kinga Aishat ba wani dogon bayani nace kiyi man bah,

Idan baki amince bah, fine zaki iya tafiya ki auri T.K d'in tunda dama kina sanshi.


"Aishat tayi raurau da ido ta fara hawaye cikin muryar kuka ta fara magana.


" why? A.K kai sanin kanka ne bana son T.K *KAI NAKE SO*, 

Saboda kai na sab'a da kowa. "Sai da ta d'ago kai ta kalleshi kafin tasa hannu ta goge hawayen dake fita a idonta tace " Shikenan idan haka shine mafitar na amince da zabin ka, but one question bazamu gudu bah, har sai na gama WAEC d'ina da neco Sannan zamu gudu. 

 "A.K ya wani lumshi idonshi Sannan yayi murmushi mugunta yace " no problem nima nafi San haka

Aishat itama ta k'ak'aro murmushin yak'e tace "toh bari na shiga cikin gida kafin yafindo ta fito ta ganmu tare tayi fad'a. " OK har kin gaji da ganina ne koh? "A'a wane ni ai a kullum bana gajiya da kallon kyakkyawar fuskarka.

 " hahaha toh Allah yasa da gaske kike. "Amin ballantana ma da gaske nake bah. " toh na yarda muje na rakaki cikin gidan. "Kam ai da yau ka shiga uku da yafindo wallahi. 

 " hahaha wasa nake maki ai nida shiga gidan nan sai ranar da muka kawowa yafindo babynmu.


 "Aishat taji kunya da sauri ta rufe fuskarta da hannuwanta ta juya da gudu ta nufi cikin gida, A.K ya bita da kallo ya wani cije leb'anshi ya girgiza kai, yayi murmushi, shi yasan abinda yake nufi da haka,

Aishat na shiga cikin gida batasamu yafindo a waje bah, dan haka ta nufi Parlour direct, zaune ta sameta kan kujera,

Yafindo ta d'ago kai ta kalleta tace "toh marar kunya har kin dawo? " bata tsaya bata amsa bah ta shige bedroom...       ***********


Haka abubuwa sukaci gaba da faruwa, amma yanzu Aishat ta chanza, haka keba yafindo mamaki chanza warta a lokaci d'aya, 

Bata San Aishat tayi hakane kawai dan bin abinda A.K yace mata bane.


B'angaren Mujaheed da dady kuwa ba'a cewa komai dan Mujaheed naso yazo gida amma dady ya hanasa zuwa,

Wannan abu ya karawa Mujaheed zafi a zuciyatshi, haka yasa damuwa ta kara yi masa yawa a zuciya kullum tunani, 

abin har ya damu Lukman, haka yasa Lukman ya gano Mujaheed soyayya yake da wata amma miskilanci ya hanashi ya nuna mata, shikuma yayi alkawarin sai ya gano ko wacce yarinya ce wannan warda ta hana abokinshi rawar gaban hantsi.....
  *DEDICATED TO*

 *AYSHAT MUHAMMAD*

    ( *MAMAN SHAKUR*)


    

       ® *N.W.A*      © _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

......................® _NWA_...........


       © *MRS UMAR*


         Page 141_145
Aishat bata tsaya ko ina bah

 Sai gidansu A.K,

 Tana zuwa d'akinshi ta nufa direct,

 Saidai kash! d'akinshi a rufe yake da kwado, jiki a sanyaye ta juya zata koma gidan,

 a dai dai bakin k'ofa taci karo da kanensa mai suna Garba,

 Yana ganinta ya washe hakora,


 Yace "A'a su Aunty Aishat yau kece a gidan namu? "Eh Wallahi Garba nice, ina yayan naka yaje? 

 " au bai fad'a maki ba yayi tafiya yace man Umma ta aikishi kauye. 

 

 "Aishat cikin mamakin, 

 Tace " kauye fa kace ai ni bai fad'a min zaiyi tafiyaba. "Hahaha kinga Aunty ki kwantar da hankalinki, bazai dad'e ba zai dawo nasan bazai wuce one week bah a can. 

  

"Ahankali Aishat ta sauke ajiyar zuciya Sannan tace " toh shikenan Garba ga numberta nan idan yazo ka bashi, please karka manta kace ya kirani. "Toh insha Allahu bazan manta bah, amma ya kamata ki shiga ki gaida Umma. " hakane Garba amma Wallahi yanzu ina sauri kace ina gaida ita insha Allahu zanzo. "Toh shikenan ki gaida gida. " toh garba nagode sai anjima


Aishat ta juya ta koma gida amma abinda A.K yayi yana bata mamaki cikin zuciyarta tace "hmm kodai A.K ya daina sona ne? ok!! that impossible nasan A.K bazai taba cin amanata bah,

*MASOYINA NA HAR ABADA* ai bazai taba bari na bah hmm.


"Duk a zuciyarta take maganar kamar warda bata da kai...


   **********************


 *TWO WEEK'S LATER GO*


Al'amarin A.K bai k'ara ba Aishat mamaki bah,

Sai yanzu da taga sauran sati d'aya aurenta da T.K amma babu A.K babu labarinshi,

Hankalinta ya tashi sosai ba kamar yau da iyayen T.K suka kawo lefe,

 akwatinane masu kyaun gaske,

dukka kayan ciki ba mai k'ara min kud'i,

 Murna kuwa wajen yafindo ba'a cewa komai,

 dan ta kasa ta tsare ita keyin komai,

 itama tana dan cikin damu da har yanzu d'anta baizo bah,

 yana India abinshi kamar auren bai sha mashi kai bah,

Mom ko da dady sun nunawa sunfi kuwa son auren haka yasa taji dad'i sosai ,

Komai da mom akeyi na harkar bikin,

 dukda dauriya kawai take an hana d'anta ya aureta gashi yanzu za'a bah, wani can daban,


 Yayin da Meenat ke tare da Aishat ita ke bata hakuri idan tana kuka, 

 Yanzu daka ganta kasan tana cikin damuwa, abin naba yafindo haushi sosai taki ta saki jikinta kwata kwata,

 Haka yasa T.K ya Kyaleta saboda taki fad'a masa abinda takeso na harkar biki, shidai ina ruwanshi saboda yanzu ya kusan samun abinda yake so


Yafindo suna zaune ita da d'anta a babban parlournta Wanda yaji kayan alatu, 

Cikin damuwa ta dubeshi tace "kaga yaron nan har yanzu bai taso bah, ga biki yazo amma har yanzu ba uban Amarya.

 " hakane yafindo kiyi hakuri ko yanzu munyi waya dashi yace man zai taso maybe jibi, hutu ne har yanzu bai samu bah.

 "Haba wannan wani irin aikine aiki yafi auren yarsa? " a'a kinsan aikin can ba irin namu na nan bane, komai can a ka'idance yake. "Toh shidai yasani kodashi ko babu Indo sai tayi aure, dan haka yanzu ka tashi kaje kaci gaba da abinda kake. " toh yafindo insha Allahu za'ayi komai.

 "Dad yana rufe baki ya tashi yayi tafiyarsa, itama yafindo taci gaba da aikin da take


 *DEDICATED TO*


  *AYSHAT MUHAMMAD*

   ( *MAMAN SHAKUR* )


     


      ® *N.W.A*       © _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

...................® _NWA_..............       © *MRS UMAR*


         Page 146_150Al'amuran Mujaheed sai K'ara gaba suke, hankalinshi yatashi sosai da ya tuna da bikin Aishat yazo da T.K,

Wanda haka yasa yake wasa da aikinshi, ranar wata Monday yaje work,

G.O.C ya kirashi yace "Mujaheed na kula dakai kwana biyu nan baka son zuwa aiki so dan haka na yanke shawarar zan turaka Co's zuwa... 

"Co's koma Sir? "Eh ko bazaka bah? A'a Sir. " OK just go to ur office, idan na gama wannan aikin i will send message for u, zakaga kasar da zakaje Co's d'in.


 "Mujaheed ya d'aga masa kai, ji yake kamar ya fasa ihu ko zai samu saukin zafin da zuciyarshi ke masa,

Yana fitowa daga office d'in G.O.C motarsa ya nufa direct dama sun tashi aiki,


Yana isa hotel d'in da suke yasamu Lukman har ya isa,

Lukman yana zaune kan kujera yana danna phone d'inshi, 

Mujaheed ya k'arasa ya zauna kan one sitter, Mujaheed kallo d'aya yayiwa Lukman ya dauke kansa, cikin zuciyarshi yace 

"Allah sarki kai ba abinda ya dameka sai ni ke cikin damuwa. " Mujaheed har kadawo ne?

 "Maganar Lukman ce ta dawo dashi daga tunanin da ya fad'a,

 Lukman yace "Humm Mujaheed wannan wacce irin rayuwa ce kasa kanka, 

kadubi yanda ka koma duk ka lalace haba. "Ahankali Mujaheed ya sauke ajiyar zuciya yace " Hakika Lukman ina cikin damuwa,

Na rasa komai a rayuwata na rasa farin cikina. "Ban gane ba Mujaheed please Tell me something. " nan fa Mujaheed yayi shuru na d'an wani lokaci kafin ya fad'a masa komai, da yafaru tundaga farko har yazowa yanzu zaman da ake komai bai sauya bah,

  

Hakika Lukman ya tausayawa abokinshi da jin halin da yake ciki yaji inama yana da wata hanya da zaya sharewa abokinshi hawayenshi,


Ahankali Lukman ya sauke ajiyar zuciya ya dub'i abokinshi,

Yace "sorry my friend hakika kana cikin damuwa, but bani da wata shawara da zanbaka, bayan kayi hakuri ka rungumi kaddara,

Allah ya baka wanda tafita. " hmmm kaiya Lukman ai ni yanzu bani da wani zabin da yawuce mutuwata, mutuwata tafi man sauki a yanzu dan Wallahi bakaji yanda zuciyata keyi bah.

"Wa'iyazubillah Mujaheed karka manta kaifa musulmi ne,

kada soyayya ta saka kayi sa6on Allah, wanda har Allah yazo yana fushi dakai.

" Mujaheed ya sauke ajiyar zuciya Sannan yace "insha Allahu bazan kara irin wannan maganar bah,

Saidai ina rokonka da katayani addu'a. "Insha Allahu Mujaheed zan tayaka.

" OK bari na shiga daga ciki. "Lukman bai sake magana bah, saidai kawai yabi abokin nasa da kallon tausayi...


 **************************

  

*AFTER FIVE DAY*


Ranar wata Friday da misalin karfe 4:30PM, na yamma Aishat suna cikin bedroom ita da Meenat tana kuka mai cin rai, 

Meenat nata aikin bata hakuri amma taki ta tsaya da kukanta, ahankali Meenat tace " sister hakuri zakiyi dan yanzu baki da wata mafita, aikin gama yariga ya gama saboda jibi kamar yanzu kin zama matar T.K.. "K'irjinta ne ya wani buga, can sai ga hawaye sharrrr a fuskarta,


" humm Meenat bazaki gane bane amma Wallahi karki tuna kiji yanda zuciyata keyi,

Meenat bazan iya zama da T.K bah, 

A matsayin mijina a rayuwata na tsani T.K *BANA SONSHI*, T.K bashi da halin mai kyau.


Meenat zata bud'e baki tayi magana kenan phone d'in Aishat yayi k'ara,

Aishat tayi kamar bataji bah, saboda tasan ba mai kiranta sai T.K, cikin sanyi murya Meenat tace "sister ana kiranki fah. " Aishat taja tsoki tace "nasan bazai wuce wannan d'an wahalar bah. " a'a sister ba'a haka please ki d'aga.


"Meenat ta dauko phone d'in zata ba Aishat taga bakuwar number ce, saida ta k'ara korawa number ido kafin ta bata,

Bayan Aishat ta dauka cikin murya kasa kasa taji ana magana kamar haka


"Yes kina jina kifito waje gani nan cikin wata bakar mota irin ta T.K ce nasan mutane za suyi tunanin shine ya daukeki, please kifito yanzu kina zuwa ki bud'e baya ki shiga.


" da sauri ya kashe wayarshi ita kuma Aishat tayi ajiyar zuciya, mai cike da jin dad'i. "Sister kedawa? "No karki damu ina zuwa yanzu zan dawo. " a'a sister muje na rakaki. "Meenat!!! Nace ki tsaya ina zuwa yanzu zan dawo, tama baya zanbi banaso yafindo tasan fitata. " OK saikin dawo.


"Da sauri Aishat taja hijabinta ta fita da sauri,

ai kam tana fita taga motar bata tsaya wasa bah, 

Ta shiga abinta, akasawa motar key da gudu akabar unguwar,


Saida sukayi nisa ba Wanda yayiwa wani magana, kafin Aishat tace " A.K ina katafi kabar zuciyata da tunaninka, kasan da yau bakazo bah zan iya rasa rayuwata akanka, birkin da taji an takane yasata d'aga kai ta zaro ido waje...........
  *DEDICATED TO*

 *AYSHAT MUHAMMAD*

   ( *MAMAN SHAKUR*)       ® *N.W.A*       © _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

.................© _NWA_................        © *MRS UMAR*


         Page 151_155
Brake da taji an takane yasata d'aga kai ta dubeshi, da sauri ta zaro ido Yaya Mujaheed dama kaine? 

"Mujaheed ya juyo ya kalleta yayin da idanuwanshi sukayi jajir kamar gauta, ita kanta ta tsorata da ganinshi haka,

 saboda duk tsawan lokacin da suka dauka da Mujaheed bata tab'a ganinshi haka bah, 

Kallon da yake mata ne ya k'ara, tsoratata cikin sanyin murya tace " yaya Mujaheed why are u look at me? "Ahankali Mujaheed ya lumshe idonsa saboda yanda yaji sautin muryarta cikin kunnensa, ya dan kwantar da kansa saman seat d'in motar, yana maida lumfashi sama sama. " yaya I'm tauking to u, kayi banza dani.


"Ahankali yake bud'e idonsa, ya sauke wata irin ajiyar zuciya,

 bud'e k'ofar motar yayi ya zagayo baya ya bud'e dai dai k'ofar da take zaune ya kamo hannunta, ita dai ido kawai ta bishi dashi, Sannan ya bud'e gaban mota yasata shi kuma ya koma inda yake zaune,

Sai da yasama motar key ya rufe ko ina kafin ya dubeta, cikin sanyin murya mai cike da tausayi,


Yace "Sis listing to me? "Kai ta d'aga mashi ahankali ya fara magana yayin da idonshi ke kan fuskarta yana kallonta,

" Sis nasan a duniya kina kallon babu saurayin da yafi sonki irin A.K, kina masa kallon shine *MASOYINKI NA HAR ABADA* Sis kinyi babban k'uskure da har kika ki gano gaskiyar MASOYINKI NA HAR ABADA, Wanda idan har babu ke a kusa dashi zai iya rasa rayuwarsa, zai iya sadaukar da komai akanki,

Saboda ke ya rasa duk wani farin cikinsa... "Dakata yaya nifa duk ban gane wannan baya nin naka bah, gara ka fito fili ka gaya man ko zan gane.

"I known it Sis nasan bazaki gane bah, because makauniyar soyayya ta rufe maki ido bazaki gane komai bah, toh bari na gaya maki ba kowa bane MASOYINKI NA HAR ABADA Aishat sai ni!! Aishat nafi kowa sonki a duniya *KECE FARIN CIKIN RAYUWATA* a duk.... " Stop it's Mujaheed this is impossible tayaya haka zata faru oh my God what is happen to me? mafarki nake ko gaske, idan ko wannan maganar gaskiya ce toh Wallahi Mujaheed ka tafka babban k'uskure, dan zuciyata, ta mutum d'aya.. "Please Aishat cold down ba mafarki kike bah, gaskiya ne ina sonki kuma insha Allahu nine mijinki. 


"Maganar banza... " kayauuu karar Marin da Mujaheed yayiwa Aishat ne yasani zaro ido waje cikin fushi yace

 "Har kin isa ki zage ni saboda wani can da baisan kinayi bah, toh naga wanda ya isa ya hana ni aurenki kuma aure dani dake anriga angama, kuma kasar zamu bari gaba d'aya dake yanzu nan yarinya. "Aishat ta zaro ido nan danan jikinta yafara rawa tasa hannu zata bud'e k'ofar motar taji a rufe, 

kuka ta fasa tace "Na shiga uku please yaya am sorry dan Allah karka rabani da A.K d'ina shine rayuwata, please yaya karka rabamu.


" Mujaheed yaja tsoki ya kunna motarshi, Aishat da taga da gaske yake yana shrin tafiya ta janyo hannunshi daga kan steering motar, nan fa ta fara dukanshi da hannunta tana cewa "I don't want to marry u, bana sonka.

" hannuwanta Mujaheed ya kamo ya matsesu da hannunshi d'aya, yaci gaba da driving da hannu d'aya,

ba inda Mujaheed ya nufa direct sai airport inda zasu tafi..........


**************************


TIME 8:30PM


Hankali yafindo ya tashi sosai tunda ta kula Aishat bata gida hankalinta ya tashi, cikin 6acin rai ta dubi Meenat tace "wai Meenat ina indo taje tun dazu bata dawo bah gashi dare nayi? " wallahi yafindo bansani bah ina tunani kamar T.K ya kirata a waya ta fita kuma bata dawo bah har yanzu.

"Ina Meenat ba T.K bane saboda na duba k'ofar gida bata waje, ki gaya man inda tatafi. " Wallahi yafindo bansani bah amma yanzu ki kira T.K kiji ko suna tare. "Toh ga wayar ganomin number shi inji yanzu nan.

"Nan danan Meenat ta gano number T.K ta buga masa, anyi sa'a kuwa ya d'aga, ko gaisawa basuyi bah yafindo tace "T K kana tare da indo kuwa? "A'a yafindo bama tare Ai banzo gidan bah duk yau... " yafindo ta rafka uban salati tace "Lailaha illallahu Muhammadun rasulinlahi, shikenan Indo ta gama tona man asiri na shiga uku ni kuluwa. "Yafindo meya faru? cewar mutane dake zaune wajen. " shikenan Indo ta gudu basa tare da TK.....
Toh jama'a wacce kasa Mujaheed zaya da Aishat? Sannan kuma ina labarin A.K ko ya chanza shawara ne ta su gudu? 


Wannan amsar taku ce makaranta littafin *MASOYINA NA HAR ABADA*
*DEDICATED TO*


*AYSHAT MUHAMMAD*

  ( *MAMAN SHAKUR*)       ® *N.W.A*       © _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

......................® _NWA_...........


    

          © *MRS UMAR*


          Page 156_160
Shikenan Indo ta gudu basu tare da T.K, asirina yagama tonuwa.

"Cikin sanyi murya mom tak'araso kusa da ita tace " yafindo ki kwanta da hankalinki insha Allahu Aishat bata gudu bah, maybe ko taje wani waje ne kada kidamu zata dawo. "Kaiya Khadija, ni nasan halin Indo tunda tace bata son T.K anyi mata dole toh na tabbata Indo guduwa tayi. " yafindo takara fashewa da kuka mai cin rai,

duk mutane dake wajen sunkasa magana sai dai kukan yafindo kawai akeji,****************************


Mujaheed suna zuwa airport sukayi sa'a flight d'insu zai tashi 7:30pm dama haka yayi buking,

Yayi yayi Aishat tafito su tafi ta kiya abin ya bashi haushi sosai, haka yasa ya fincikota daga cikin motar,

 dama kafin su isa ya kira private Musa domin ya tafi masa da motarshi, 

Aishat tana tirjewa haka yasa Mujaheed ya dauketa cak sai cikin flight, ba inda ya direta sai kan seat flight d'in, Aishat ta zabura zata gudu Mujaheed ya fincikota da k'arfi, fad'a kan k'irjinsa, hannunta ta d'aga tana dukansa akan k'irjinsa, tana fad'i I Hate u Mujaheed I don't want to marry u, I hate u so much. 

"Mujaheed kamar yana jin dad'i maganarta sai kawai ya dinga lumshe idonsa, kamar mai jin bacci ita ko sai faman kuka take, gashi garin sauri ta bar phone d'inta a gida, babu yanda zatayi yanzu,

Bayan jirginsu ya tashi Aishat tun tana kuka a waje har takai ta koma na zuci, Mujaheed yana rike da ita kam, a haka har bacci Yayi gaba da ita, duk ilahirin k'irjin Mujaheed ta jikeshi da hawaye da majina..


°°°°°°°°°§

      °°°°°°°°°°°§

             °°°°°°°°°°°°°°°°

Dady ne zaune a gaban yafindo yana aikin bata hakuri,

itako sai kuka take kamar k'aramar yarinya, cikin sanyi murya dady ya dubeta yace "hakuri zakiyi yafindo insha Allahu zata dawo, nasa a duba man ita duk inda take za'a ganta, I promise u.

"Humm ai yanzu duk inda Indo ta nufa toh tariga takai, shin wai da kaje gidansu yaron ya kukayi da iyayen shi? "Maganar gaskiya na samu mahaifiyar yaron abinda take gaya man wai ita rabanta dashi yau kusan sati uku kenn yace mata yayi tafiya, 

Haka kanansa da yan unguwa suka fad'a mana, kinga kenan bamu da shedar shiya dauketa. 

" Haba Abdullah Ai babu shegen da ya dauketa sai shi,

nasan shi ya gudu ta ita kuma Wallahi bazan barsu bah.

"Haka yafindo ta dinga kuka tana fad'a har Abdullah ya gaji.....


        ••••••••••••••••••


Aishat sai aikin bacci take a jikin Mujaheed batasan abinda ke faruwa bah, 

Yayin da take ta shashekar kuka tana ajiyar zuciya sama sama,

Har flight d'insu ya dira inda zai sauka bata sani ba tana aikin bacci. " ke!! Tashi mun iso. "Da sauri Aishat ta zabura tana raba ido Hannunta ya kama,

 ita dai ta kasa magana sai binshi take,


Abin bai k'ara bata mamaki bah, sai da suka fito taga jikin ginin airport d'in taga an rubuta *WELCOME TO HEDIRABAT INDIA* Aishat ta k'ara wage idanunta, wani dad'i ne yazai yarci zuciyarta saboda ta tabbata dady d'inta ba zayayi mata auren dole bah, 


Suna cikin tafiya d'aga kan da zatayi sai kawai ta hango Amesha khan tare da dady, da sauri ta fincike hannunta daga Mujaheed da gudu ta nufi wajensu ta fad'a jikin mahaifiyarta,Tana kuka mai cin rai ahankali Amesha khan ta d'aga hannunta tana Shafa bayan yar tata, dady yaga basu da niyar barin junansu shiyasa yace "toh ya isa haka mutafi gida kwayi a can.


" Shi dai Mujaheed ya kasa magana sai binsu yake da kallon d'aya bayan d'aya

Drive ya daukesu babu inda ya saukesu sai katafaren gidansu, gidane na idon cin duniya, 

Suna isa parlour gidan shikansa abin kallo ne, 


Sai da suka dan huta kafin dady ya dubesu yace "so ya kamata kuje kuyi wanka kuzo ga abinci nan na jiranku. "Cikin shagwaba Aishat tace " dady satoni fa yayi yafindo bata sani bah, kuma Wallahi dady ni bazan aure shi ba ina da Wanda nake so.

"Cikin fushi dady ya daka mata tsawa yace "Keep quite I don't want to hear anything from u, kiyi abinda nace daku. " yana rufe baki ya dube Amesha khan yace "chale zandagi mira. " bayan dady yatashi sun shiga ciki, Aishat ta wurgawa Mujaheed harara tace "ni kuma naga Wanda ya isa yasa na aureka. 

" Mujaheed ya sakar mata murmushi mai dauke da jin dad'i, ya shige bedroom ita ko kasa tashi tayi tana tunanin wannan wane irin al'amari ne "dama dady yasan da Mujaheed satoni yayi koh dama bakinsu d'aya kenan???
  *DEDICATED TO*

 *AYSHAT MUHAMMAD*

   ( *MAMAN SHAKUR* )     ®  *N.W.A*


   

     ©  _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

................® _NWA_..............


  

      © *MRS UMAR*        Page 161_165       *INDIA*


Mujaheed yana shiga bedroom ya cire kayanshi ya nufi toilet direct,

Ya watsa ruwa kafin yayi arwala, ya gabatar da sallar da ake abinsa,


Itako Indo da taga babu sarki sai Allah, sai kawai tatashi tashiga ciki,

itama sai da tafara watsa ruwa kafin tayi sallah,basu b'ata lokaci ba suka fito dukkansu kusan tare suka fito,


Dinning table suka nufa direct

Yayin da Aishat ke wurga mashi harara, shi dai Mujaheed ko a jikinshi,


Suna zama sai ga dady da mom sun fito, kuwanensu dauke da murmushi a fuskarshi dady yaja kujera ya zauna, yayin da Amesha khan ke tsaye tana kokarin Saving d'insu tana bud'e kular kamshin Chicken Carrot and Rice Potatoes Salt, suka doke hancinta, nan fa tasama kowa nashi yayinda Aishat naci tana wurgawa Mujaheed harara, dady ya kula da hakan,


Suna gamawa dady yace "kutashi muje parlour I want to talk to all of u. "Bayan sun zauna dukkansu sunyi shuru suna so suji abinda dady zaice dasu dady yayi ajiyar zuciya, kafin yayi gyaran murya yace " hakika Aishat naji komai dake faruwa game da wannan auren da za'ayi maki, banji dad'i jin wannan labarin bah.

"Da sauri Aishat ta d'aga kai ta kalli dady Sannan ta juya ta saci kallon Mujaheed ta saki murmushi dady yaci gaba da magana, " sannan duk naji abinda kikaso ki aikata zaki gudu keda saurayinki... "Kirjin Aishat ne ya bada daram ta zaro ido tana kallon dady cikin mamakin inda yaji maganar, "Him any way yanzu na gama magana shiyasa Mujaheed yace man zaizo Co's nace kuzo tare, dan haka na yanke shawara Mujaheed zaki aura, insha Allahu gobe idan munfito daga masallaci Babansu Amesha zai daura maku aure.. No!! Dady i will never marry yaya Mujaheed, Wallahi dady idan ban auri A.K bah mutuwa zan... "Karar mari da dady ya kaima Aishat ne yasa kowa ya tsorata a parlourn, cikin fushi dady ya fara magana" keep quite Stupid girl how day u ina magana kina magana ni zaki gayawa maganar banza, toh goben za'a daura maku auren idan yaso ki mutun.

"Ahankali Amesha tatashi tana bashi hakuri, cikin fushi ya juya ya nufi bedroom d'inshi haka Amesha ta take mashi baya sukabar daga Mujaheed sai ita Aishat a parlour, 

Mujaheed yazo dai dai kun'nanta yace " sorry babyna k'arkiyi fushi dani Wallahi I Luv u so much. "Aishat haushi ya kara kamata ta ingijeshi ta buga tsoki ta kara gaba abinta, Mujaheed yawani sauke ajiyar zuciya ya sulalo kasan kujera, yana mai cike da jin dad'i......


°°°°°°°°°°°°°§

         °°°°°°°°°°°°°°§

                  °°°°°°°°°°

      *NIGERIA*


Washe gari


Yafindo na zaune a parlournta itada Meenat

 sai ga T.K ya shigo ko sallama babu ya fara bala'i "haba tsohowa dama kice man kema ba san auren kike bah, shiyasa kikace ta gudu toh Wallahi ba zanyi asarar ko nairata bah, Wallahi sai anbiya ni komai da nakashe, ni za'a dauka dan iska toh Wallahi yau zan nuna maku ni dan Tasha ne. " haba T.K ka kwantar da hankalinka Wallahi bansan komai akai bah, nasan ba Wanda ya gudu da indo sai wannan shegin yaron A.K. "Dakata tsohowa wallahi karya ne saboda yanzu na gama waya da A.K, yana Abuja abinshi basa tare yau kusan satinshi uku kenan da tafiya, yauwa dan haka kawai ni abani matata dan wannan karyar taku tsohowa bata samu shiga ba.... " kai dakata marar kunyar karya, how day u to insulted my Granny in my House, humm yafindo kinga abinda Aishat ke fad'a maki koh kikaki yarda? "Ke Meenat ina ruwanki dashi ai yafimu gaskiya duk inda akaje.. "Mrsssss aikin banza. " yana juyawa ya fita Meenat jitake kamar tabishi, itama taci masa mutinci, "tayaya yafindo tana kallo yazo har gida yaci mana mutunci amma bata damu bah.


"Haka suka zauna a parlour ba Wanda ya k'ara cemawa dan uwan shi kala...


     ••••••••••••••••••••••••••••••


 *INDIA*

 

Bayan antaso mallaci sallah jama'a suka sheda auren Mujaheed da Aishat, 

tunda kazo ma Aishat da labarin an daura auren, take kuka mahaifiyarta ce keta aikin bata hakuri, suna cikin haka ne saiga dady sun shigo shida Mujaheed, 


Dady ya dubi Mujaheed yace "ka dauketa ga key d'in motata nan ka kaita gidan kakarta tanason magana da ita, kabi ahankali kasan India ba Nigeria bace. " toh dady. "Cikin muryar kuka Aishat tace " nifa dady banason ya kaini zan tafi da kafa... "Maganarta ta tsaya ne sa kamakon hararar da dady yayi mata ne, 

cikin sanyin jiki ta tashi suka tafi,


Ahankali suke tafiya a mota ba Wanda yayi ma dan uwansa magana, can kasan kakoshe tace " ta kabol zamubi wannan hanyar ba kyau.

"Cikin jin dad'i Mujaheed ya karya kan motarshi, 

Saida sukayi nisa Aishat taga wasu matasa zaune tayi murmushin mugunta tace " please yaya story, ka tsaya bari insayo sweet a can indawo. "A'a ban yarda bah bari inzo muje tare. " hahaha yaya nan fa India ce ba Nigeria bah, babu yanda za'ayi na gudu. "OK jekidawo kiyi sauri.

 "Aishat ta sake murmushi ta cije lips d'inta, direct wajen samarin nan ta nufa tana zuwa ta juya masu da indiyanci tace "dama wan can mutuman dake cikin motar can yake tambayar ina ake saida naman shanuwa.. " daya daga cikinsu yace "what naman shanuwa abin bautar tamu zai ci, kuzo muje mugama dashi, da gudu suka nufi wajen Mujaheed suka juyoshi daga cikin mota, juyawa yayi ya kalli Aishat sai yaga tana dariyar mugunta, tace " d'aya daga cikin aikin.......
*DEDICATED TO*

 *AYSHAT MUHAMMAD*

   ( *MAMAN SHAKUR*)
       ®  *N.W.A*      © _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

................® _NWA_....................       © *MRS UMAR*


         Page 166_170Hmm "Yaya Mujaheed kenan kad'an daga cikin abinda zan fara aikata maka kenan a rayuwarka, tunda har kayi yin k'urin rabani da masoyina, toh wallahi babu ka..... Maganarta ta tsaya ne sakamakon fizgar da yayi mata, ya had'a ta da jikin motarshi, kafin ace me ya had'a bakinshi da nata yana tsotsa. 

matasan nan dake tsaye d'aya ya kalli d'aya 

 Yace "oh my God chaloh I won't see this drama"

 Da sauri suka bar wajen yayin da Mujaheed ranshi ya b'ace sosai ya manta ma a inda suke,

 Aishat duk wani k'ok'ari da zatayi dan ta amshi kanta ta kasa

 Saboda ya had'a hannunshi da nata ya had'a a jikin motan ya rik'eta gam, ko motsawa bata iyayi a cikin zuciyarta wata dibara tazo mata...


 Da sauri ta rufe idanunta gam, 

 k'afarta ta d'aga tasa gwiwarta ta kai masa duka a gabanshi da, sauri ya saketa

 Saboda azabar zafin da yaji, nan da nan idonshi ya chanza kala ya koma red,

 ranshi ya 6aci ya k'ara fincikota ya jefata mota,

 Sannan ya shiga yasa ma motar key.


 Hankalinta ya tashi sosai saboda yanda taga ya zuciya, cikin sanyin murya kamar zatayi kuka ta furta,


 "Ni wallahi kayi parking na fita ai ba dole sai munje tare ba, Mujaheed ya juyo ya watsa mata harara, da sauri ta sadda kanta k'asa saboda yanda idonshi sukayi jajir kamar wuta, har sukayi nisa ba Wanda ya k'ara cema dan uwansa uffan, 


 Direct gidansu Ameesha khan suka nufa,watau gidan kakan Aishat kenan, hankalin Aishat bai kwanta ba sai da taga sun shiga gate d'in gidan.


30 _minutes later_


basu b'ata lokaci b

 Suka fito daga gidan yayin da Mujaheed zuciyarshi ke k'una ita dai Aishat ko a jikinta.


 Direct gida suka koma mom da daddy na zaune a parlour suna cin soyayyarsu yayinda daddy ke jin kamar yanzu aka kawo masa Amesha,

 

 Mujaheed na gaba Aishat na mara masa baya,

 Fuskar nan tashi babu alamar murmushi,

 Ya shigo parlour daddy kallo d'aya yayi masa ya d'auke kanshi saboda yaga alamar ranshi a b'ace yake,

    Mujaheed ya samu kujerar dake fuskantar dady ya zauna,

 yayin da Aishat ta ra6a ta gabansu zata wuce dady ya daka mata tsawa, "ke! zo nan gidan ubanwa zaki? ko baki ganmu bane?" 

 jikinta na rawa ta dawo baya, dady ya dube Mujaheed cikin 6acen rai yace "Mujaheed ka fad'a min komai tayi maka yanzu a gabanka zan d'auki mataki wallahi”. 

 A hankali Mujaheed ya d'ago kai ya kalli dady da jajayen idonunshi, sannan ya juya ya kalli Aishat itama shi take kallo, da sauri ya kauda kanshi daga nata, cikin sanyi murya 

 Yace "no dady is notin kawai bana jin dadin jikina ne" 

"are u sure? Mujaheed kar kayi min K'arya dan ka kareta"


 "yes dady am sure” "Ok yanzu yaushe zaka gama Co's din?" humm "two weeks ne suka bani"

 "OK toh idan ka gama zamu wuce tare idan yaso sai ayi duk wata hidima da za ayi, yanzu kuma zan kira Abdullah na gaya masa kuna nan dan hankalinsu ya kwanta”.

 "Ok dady thank u"

 Humm "don't worry duk abinda nayi maka kamar na yiwa kaina ne"

 Mujaheed yayi murmushin yak'e yayinda Aishat tsanarsa na k'ara tasiri a zuciyarta, haka suka cigaba da tattaunawa har lokacin sallah yayi suka tashi.


*NIGERIA*


Wani irin birki daya taka saida k'ura ta tashi, dan har wani k'iyyyy!! kakeji cikin fushi ya b'alle k'ofar motar ya fito kai tsaye ya shiga cikin gidan.


 Zaune suke a parlour suna jimami, labulen da sukaga an daga ne ya dawo da hankalinsu, T.K bai tsaya komai ba ya nufi wajen yafindo ya fincikota "Lafiyarka kuwa T.K ina zaka kaita? na shiga uku" Meenat tasa hannu tana so ta k'waci yafindo amma ta kasa, ita yafindo kasa magana tayi saboda yanda taga T.K tasan yasha wani abu, 

Meenat takai masa duka cikin zafin rai yakai mata wani wawan duka ta fad'i k'asa, ya juyo yace "Ke ki fad'awa ubanki na d'auki uwarsa kuma bazan bada ita bah har sai lokacin da aka fito man da matata ko kuma lokacin da aka biyani duk abinda na kashe" yafindo ta zaro ido, haka ya dinga janta har ya kaita mota, yayinda Meenat ta kasa tashi dan taji dukan da yakai mata,

dak'yar ta jayo wayarta ta danna number dady kira daya ya daga tace "hello dady akwai matsa[Truncated by Whatsapp].
*DEDICATED TO*

*AISHAT MUHAMMAD*

  ( *MAMAN SHAKUR*)     ® *N.W.A*    © _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

..............® _NWA_........................       © *MRS UMAR*


         page 171_175
Da'kyar ta jayo wayarta ta danna number dady, anci sa'a k'ira d'aya ya d'aga, cikin muryar kuka tace "hello dady, akwai matsala dady, kadawo yanzu please". Batasan lokacin da ta k'ara fashewa da kuka ba, a b'angaren dady kuwa cikin kid'ima yace "Meenat what is the problem?"


 "No dady please just come back, maganar bazatayi a waya ba".


Kafin ya bata amsa tuni ta kashe wayar ta cigaba da kuka.


T.K gudu yake da yafindo ba ji ba gani, tun tana matsar 'kwalla har ta kai tana addu'a, fad'i take "kana wa darajar Annabi Muhammad kayi ha'kuri ka maidani gida, wallahi babu hannu na a cikin guduwar Indo"


T.K ko a jikinshi, ita ke kid'inta ita ke rawarta, shidai driving d'inshi kawai yake, direct wani katafaren gida ya danna kan motarshi, cikin zafin rai yake horn yayinda maigadin yake bud'e mashi get kamar zai fad'i kasa, da gudu ya shiga kamar zai tashi sama, da sauri yayi parking ya fito cikin zafin nama ya finciko yafindo, bata san lokacin da ta fasa ihu ba, haka T.K ya dinga janta, har suka shiga parlourn gidan yana janta, suna isa ya jefata kan kujerar dake parlourn. Cikin kuka yafindo tace "Gaskiyar Indo, na tafka babban kuskure da na amince da kai, ashe kai mug..."


Maganarta ta tsaya ne sakamakon d'an yatsanshi da yasa mata a daidai lips d'inta yace "Shhhht tsohuwa humm ai bakiga komi bama acikin aikin T.K d'aga kanki kiga can.

 "D'aga kan da zatayi da sauri ta zaro ido saura kad'an da numfashinta ya dauke.....


★★★★

★ ♣ ★★★★★★★★★★★

★★★★20 _minutes later_


Cikin tashin hankali dady ya iso parlourn ganin Meenat a kwance yasashi k'arasawa wajenta,

 yana d'agota yaga jini na zoba a goshinta cikin tashin hankali yace

 "Meenat wai meke faru? " dady akwai matsala!! dady T.K yazo ya tafi da yafindo yace bazai bada itaba har sai lokacin da aka fito mashi da matarshi.

 "What? OMG yana haukane ta Yaya zaya tafida ita toh inama zai kaita? 

" Dady duk wannan tambayar yanzu ba itace mafita bah, gara asan nayi ko a kira yan sanda.

 "A'a Meenat dole yanzu na kira Yaya na sanar masa abinda ke faru kafin yaji labari.

 "Dady yana rufe bakinshi ya danna number big dady anci sa'a yana kusa ya d'aga, 

cikin ladabi dady Mujaheed ya fara magana "hello Yaya yagida ya India? "Lafiya but Abdullah meke faruwa? naji muryarka na rawa.

 " dady kamar yana jira ya fashe da kuka yace " Yaya akwai matsala babba. "Humm ina jinka. 

 " Yaya Aishat ta gudu bata gida gashi yanzu mijin da zata aura yazo ya dauki yafind..... "What ya gudu da yafindo garin yaya haka ta faru? " Yaya saboda Aishat ta gudu ne.

 "Dakata Abdullah Aishat bata gudu bah tana nan ita da Mujaheed a India yayinda yanzu haka sun zama Miji da mata. 

 " Please yaya ka daina min irin wannan wasan yanzu ba lokacin wasa bane. 

 "Humm Abdullah gaskiya na gaya mak.... "Bai san lokacin da ya dakawa yayanshi tsawa bah yace 

 "Dakata yaya kana nufin dasa hannunka cikin guduwar yarka, humm gaskiya ne toh bari kaji wallahi anything happen to my mother I will never for give u...

 "Yana rufe baki ya kashe wayarshi.

"Cikin sanyi murya Meenat ta dubeshi tace " dady lafiya naga kamar kana f'ada da big dady? "dady kasa magana yayi saidai kawai kanshi da ya dafe ya rasa mafita...


********

B'angaren dady kuwa

Shiru yayi yayinda Amesha da Mujaheed suka bishi da kallo cikin sanyi murya Mujaheed yace " dady lafiya kuwa? "Sai da dady ya sauki ajiyar zuciya kafin yace "Humm Mujaheed akwai matsala. "Nan fa dady ya gayawa Mujaheed duk abinda sukayi da dady,

Mujaheed yayi shiru yana tunani, can yayi sauri ya dakko wayarshi ya danna number mahaifinshi, dady yana d'agawa Mujaheed yace "hello dady. " Cikin fushi dady ya daka masa tsawa yace " don't u dear call me ur father because am not ur father. "Please dady listen to me. " keep quiet I will not listen to u... "Kafin Mujaheed ya kara magana dady ya kashe wayarshi....*DEDICATED TO*

AYSHAT MUHAMMAD

 ( MAMAN MAMAN )


  


       ® *N.W.A*     © _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

................ _NWA_......................        *MRS UMAR*

  

         page 176_180~~ Mujaheed ya aje wayar a susoce ba kwari a jikinshi, cikin sanyin murya dady yace

"Mujaheed nasan yanzu Abdullah ya d'auki zafi so dan haka ka barshi ya sauko kafin ka k'ara kiranshi.

"Haka ne nasan yanzu dady ya d'auki abun da zafi,

toh yanzu damuwata d'aya ce shine bamu san halin da Yafindo take ciki bah. " Humm gaskiya ne Mujaheed bamusan halin da take ciki bah,

so don't worry insha Allahu gobe zamu wuce Nigeria saboda bamuga ta zama bah, yanzu bari nasa a yankan mana biza mutum uku, idan yaso ka gama Co's d'in sai ka biyomu daga baya.

"Amma dady ai ya kamata mutafi tar.... "Dakata Mujaheed narigadana gama magana kayi abinda nace maka kana jina koh.


"Mujaheed ya d'agawa dady kai alamar eh,

dady ya k'irkiro murmushin yak'e yace " yauwa good Boy ....


*****************


*NIGERIA*


Yafindo kan da zata d'aga da sauri ta zaro ido saboda ganin wanda ke zaune cikin parlourn, ta saki baki da hanci tana mai mamakin ganinshi tana cikin haka ne taji muryar T.K a kunnanta,


"Tsohuwa kenan kina mamaki ne? oooo karkiyi mamaki dan kin ganmu a

tare, yanzu haka zaman da ake A.K baban abokina ne...

 " T.K ya d'an numfasa sannan cikin takon kasaita ya samu waje ya zauna kafin yace gaba da magana, 

"Na san zakiyi mamaki sosai, humm wannan ba abin mamaki bane,

A.K yazama abokina ne sakamakon sayar min da soyayyar Aishat ne a kan naira mai gogar naira, naira million 5 haka yasa shi mantawa da Aishat da alkawarin da suka daukarwa kansu na zasu gudu suje can wani waje suyi aure, haka yasa nace yadawo mu zauna tare dan kar mutane suyi zargin ina yasamu kud'i haka,humm dama can shima ba dan Allah yake son Aishat bah, sai dan abin duniya toh tunda na bin cika na ganu A.K mayan kud'i ne na shawo kan matsalar wajanshi, sai dai kash nayi sara ban duba bakin gatarin bah, 

ashe kema bakya son auran toh wallahi zanga uban da ya isa yasa na bada ke, sai anfito min da matata, ko kud'ina.

 "Haba abokina ai haka nan kake b'ata yayun bakinka akan wannan tsohuwar da bata san mutucin mutane bah, ai kayi mata mai sauki in nine daga gidan zan fara boll da ita wallahi. "Hahaha shegi nawa shiyasa nake sonka halinmu iri d'aya.


"Cikin kuka abin gwanin ban tausayi Yafindo tace " yanzu A.K har dakai? cikin wannan aikin duk irin son da Indo ta nuna maka abinda zaka saka mata dashi kenan,

humm T.K nasoka tamkar d'an da na haifa da cikina nayi fad'a da kuwa saboda kai sai dai kash yanzu da abinda ka saka min kenan? hakika *NAYI NADAMAR* saninka a rayuwata Allah ya is.... "Kafin Yafindo ta k'arasa maganarta A.K ya dauke ta da mari mai firgitarwa, 


°°°°°°°°°°°°°••••••••°°°°°°°°°°°°°°°


         *AIRPORT*


flight d'insu dady ya sauka garin Abuja lafiya inda basu b'ata lokaci bah, suka iso garin Katsina lafiya, direct daga airport motar Katsina suka hau shiyasa Suka isa da wuri, 

suna isa gidan Yafindo sukayi tsinke, basu samu kowa ba shi yabasu damar wucewa gidan dady, suna isa Meenat da mom suka d'auki murna anyi sa'a dady ya fita, Meenat ta kama hannun Aishat tana cewa "Sanu da zuwa Amaryar yaya kinga yanda kikayi kyau kuwa. "Aishat ta daure fuska saboda an fad'i sunan makiyinta, mom d'in Meenat ta kula da hakan shiyasa tace "Meenat kushiga daga ciki kisa Aishat tayi wanka ta huta.

"Meenat tana murmushi suka shiga daga ciki, saida suka gaisa yafin big dady yace "Khadija ina Abdullah yaje? " Humm yaya tunda wannan abin ya faru alhaji baya zama a gida, gashi har gidansu yaron anje ba'a samisa bah. "Ki kwantar da hankalinki insha Allahu tunda nazo garin nan toh sai na ganu inda mahaifiyata take. 

"bayan sun gama magana mom ta tashi ita da Amesha suka nufa d'akinta shikuma big dady ya nufi dakin dady....


°°°

Bayan su Aishat sun ci abinci sun huta misalin k'arfe 5:pm mom ta aikisu suna tafiya suna fira,

basu ankara bah suka ga mota gabansu kamar zata takaso....
*DEDICATED TO*

*AISHAT MUHAMMAD*

  ( *MAMAN SHAKUR*)         *N.W.A*        _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

................® _NWA_.................        © *MRS UMAR*


  

         page 181_185~~ Cikin ban tsoro da firgitarwa Aishat ta damke hannun Meenat, 

da sauri ya bud'e k'ofar mota ya fito Aishat bata k'ara tsorataba sai da taga A.K ne a gabanta yana huci kamar maciji,

cikin rawar murya ta furta


 "ALIYU!! dam... "Dakata yan mata ni yanzu na wuce ajinki, oho ashe kuwa maganar T.K gaskiya ne yafindo tasan da guduwarki tunda gashi yanzu da kikaji an kama kakarki kin dawo.


 "Da sauri Aishat ta k'ara d'aga manyan idanunta ta saukesu kan fuskar A.K, cikin sanyin murya tace 


"Please A.K I don't understand what u're saying? 

 "Hahaha tayaya zaki gane, let me explain to u, 

him da farko dai ina sane da irin jirana da kika dingayi dan nazo mu gudu, hahaha yan mata nasamu kud'i mai zanyi dake bayan dama saboda su zan aure ki kuma nasamu ai shikenan nagam.. "Dakata bangane ba saboda kud'i zaka aure ne bah, please A.K kadaina min irin wannan was... "Sht yan mata dadi na dake kin cika sauri kitsaya kiji mana, 

lokacin da zamu gudu dake har na yanke shawarar ranar da zamu gudu, kawai wata rana sai ga T.K yazo har gidanmu yayi min tayin na sayar mashi da soyayyarki naira million 5, himm da har nace mishi a'a sai wata zuciyar tace na amince tunda dama can ba sonki nake bah, oh kar na cikaki da surutu yanzu zaman da ake muna gida d'aya da T.K yayinda yafindo ke tare damu... "Amma wallahi A.K kabani kunya ashe dama soyayyar karya kake nuna mata, humm Aishat kinga abinda muke fada maki koh? 


"Aishat kasa magana tayi sai dai hawaye kawai da kibin fuskarta na takaici,


 "Dakata bada ke nake ba kibari sai na ambace sunanki kafinki samin baki. 


 "A.K yana rufe baki ya nufi wajen Aishat yakai hannunshi zai kamata Meenat tasha gabanshi, cikin zafin rai Meenat ta daka mashi tsawa,

 "AK me kakeso kayi karfa ka manta yanzu Aishat Matar aure ce. "Hahaha Matar aure ai ba'a riga andaura bah, yanzu dai zankai mai ita idan yaso sai yasako maku yafindo sai a daura mas... "Aishat Matar aure ce anriga an daura mata aure da Yaya Mujaheed tun a India. 

 "What aure? No that's impossible tayaya haka zata faru no!!

"Kafin A.K ya k'ara magana yan sanda sun zagayesu, 

Meenat tayi murmushin mugunta ta kashe mashi ido d'aya, A.K yajuya babu wajen guduwa dole yanaji yana gani yan sanda suka kamashi,

Meenat sai yanzu ta kula da halin da Aishat ke ciki, tsaye take ko motsi batayi sai dai hawaye da kebin fuskarta, cikin sanyi murya Meenat ta dafa kafad'arta tace " Please sis calm down karkisa kanki cikin matsala saboda wannan dan iskan, yanzu idanunki sun bude kingane mai sonki na gaskiya dan Allah badan wani abu bah kin gane yaya Mujaheed shine MASOYINKI NA HAR ABADA. 

"Da sauri Daddy ya k'araso wajensu ya kama Aishat yasata mota, gida suka nufa direct suna zuwa suka samu mom da big dady zaune a parlour Suna tattaunawa, da sauri mom ta mike tana fadin, 


 "Lafiya Alhaji mai yasamita? please Tell me. 

"Sai da Daddy yasamu waje ya zauna kafin ya fara magana,

 "Humm mungode Allah da duk abin yazo cikin sauki, harmuka gane gaskiya sannan ina mai farin ciki da Allah yasa bamu dauki Aishat mun aurar da ita ga mijin da bai dace bah, 

bayan fitarsu yanzu suka had'u da wannan dan iskan d'ayan yaron A.K ya hanasu tafiya yana k'okarin kama Aishat yatafi da ita sai Meenat tayi k'okarin kirana a waya ina dauka naji duk rigimar da suke, 

haka yasa nayi saurin kiran police har sukayi sa'ar kamashi yanzu zaman da ake yana hannunsu kuma insha Allahu zai fad'i inda T.K yakai yafindo tunda duk bakinsu d'aya.


"Har Daddy ya dasa aya big dady da mom suna kallonshi,
  *DEDICATED TO*

 AYSHAT MUHAMMAD

  ( *MAMAN SHAKUR*)
      ® *N.W.A*


   


      © _MRS UMAR_*MASOYINA NA HAR ABADA*

................... _NWA_...................         *MRS UMAR*


  

         Page 186_190~~Har Daddy ya dasa aya big dady na kallonshi, sai da big dady ya gyara zamanshi sannan yayi gyaran murya yace


"Toh masha Allah mungodewa Allah,

 da Allah yasa ka fahimci gaskiya tun yanzu kafin abu yayi nisa, hak'ika nayi tunanin T.K mutumain kirkine sai daga baya da Meenat ta kirani a waya ta fad'a min duk abinda ya faru harda zuwan Mujaheed soja da guduwar da zatayi da saurayinta, 

tunda nasamu labarin haka hankalina ya tashi sosai har nasamu mafita nasa a kai Mujaheed CO's zuwa India haka zai bada damar ya gudu da Aishat, lokacin da na kira Mujaheed na sanar dashi ga abinda zayayi har yaki amincewa sai dai na bude mashi wuta kafin ya amince suka gudu zuwa india, hakika Abdullah nafi kowa jin dadi wannan Abu da yazo da sauki har ka fahimci gaskiya. 


"Meenat tashi ku shiga daga ciki Aishat ta kwanta ta huta.

"Mom ce tayi magana yanzu, cikin sanyin jiki Meenat ta mike tsaye suka shiga daga cikin...


_55 minutes later_


A.K yaci uban duka da yaga babu sarki sai Allah yaga ana shirin kasheshi yasa dole ya fadi gaskiya, 

da inda suka kai yafindo haka yasa yanaji yana gani aka tasa shi gaba zuwa gidan,

suna shiga gidan suka sashi a gaba yayi knock d'in k'ofar, T.K na bud'e k'ofar cak ya tsaya saboda ganin yan sanda a gabanshi gashi babu damar ya gudu, 

kai tsaye suka danna kai cikin gidan parlourn gidan suka fara isa babu yafindo a ciki, direct suka nufi bedroom d'inshi ai kam suna shiga sukaga yafindo kwance kasa taci kuka ta koshi,

T.K shima yanaji yana gani suka tafi dashi, yayinda suka kai yafindo gida.... *TWO DAYS LATER*


Kwance take kan gado ta tada kanta da Pillow sai shararar kuka take,

Meenat ce zaune a bakin gadon tana aikin bata hakuri, ahankali cikin muryar kuka tana shashika tace 


 "Meenat dole nayi kuka yanzu da wane ido zan kalli Yaya Mujaheed bayan irin cin fuskar da nayi mashi, 

na nuna mishi kaitsaye bana sonshi na rufe idona na dinga masa rashin mutumci ashe duk abin nan Yaya Mujaheed ne *MASOYINA NA HAR ABADA*,

Meenat sai yanzu nayi nadamar sanin A.K a rayuwata, A.K kacucini Allah ya isa tskanina dakai bazan taba yafe maka..... "Kuka yaci karfinta da sauri meenat ta kamata tace 


" Aishat ki kwantar da hankalinki ni nasan halin Yaya Mujaheed da saukin kai,

nasan zai fahimce ki, sannan ya Mujaheed baya wasa da abinda yakeso,

kishare hawayenki sannan yanzu ne zaki nunawa Yaya Mujaheed zalla soyayyarshi,

 ki nuna masa son da kike mashi yafi wanda yake maki... "Gaskiya ne meena wannan maganar take haka take. 


" Gaba d'ayansu suka d'aga kai dan ganin wake magana!!
*DEDICATED TO*

AYSHAT MUHAMMAD

 ( *MAMAN SHAKUR*)
       ® *N.W.A*
    © _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

..................... _NWA_.................
        *MRS UMAR*


         Page 191_195
   Yafindo ce tsaye tayi maganar, ahankali tak'araso cikin fara'arta bakin gado ta zauna kafin ta fara magana,


  Hak'ika Indo ni kaina naso na *TAFKA BABBAN KUSKURE* son zuciya yaso yakaini ga dana sani

na rufe idona, na nunawa duniya nafi son farin cikin wannan shegen yaron ashe shiba haka bah, nagodewa Allah da Allah yasa auren yazo da matsala da yanzu an daura da nashiga uku dan wallahi kashe minke zaiyi,

saboda yanda naga yaron nan nata shaye shaye nasan zai iya komai a kanki wallahi, Indo dan Allah kiyi hak'uri ki d'auki Mujaheedu a matsyin mijinki kibashi girmanshi a matsyinshi namijinki kuma d'an uwanki, nasan Mujaheedu yaro ne mai hak'uri idan yadawo kada kinuna mashi wata k'iyaya ta taba faruwa tskaninku, inaso kibashi had'in kai.

   Da sauri Aishat ta d'aga kai ta kalli Yafindo cikin jin kunya Aishat bata sanda kanta k'asa tana wasa da yan yatsunta,

   Nasan nan da sati d'aya Mujaheedu na hanya, toh shiyasa na kira k'awata Hajiya Binta nace mata zakije ta gyara maki jikinki da duk sauran abubuwan da yadace,

toh dan haka kitashi kishirya yanzu Meenat ta rakaki kinji koh? 

Kai ta d'aga mata alamar eh haka suka dinga hira har Aishat tagaji ta sauko suka dingayi da Yafindo....


_AFTER ONE WEEK_


Mujaheed abubuwa sunyi dad'i inda a yau yagama Course d'inshi lafiya, yana gamawa baitsaya komai bah ya hau flight sai garin Abuja around 1:pm suka iso, 

ko Lukman bai tsaya kira ba kawai ya nufo Katsina direct, dama Allah Allah yake yazo kodan yaga sahibarshi tunda Meenat tayi mashi waya ta fad'a mashi duk abinda yafaru yake so yaga Aishat, yana tunani ko yanzu zata amince dashi amatsyin mijinta oho, yana cikin wannan tunanin ne har yashiga parlourn gidan,

babu kowa sai Mom kawai zaune tana kallo,


   Aa mutanen India dama kana hanya baka fad'a bah?

   Mujaheed yayi murmushi sannan yak'araso ya zauna a kusa da ita yace 

 "Humm wallahi Mom yau muka gama kuma nayi missing d'inku da yauwa ne shiyasa kawai na kama hanya yau." 

Haba Mujaheed ka fad'i gaskiya kai dai kace kayi missing d'in matarka ne...


   Cikin jin kunya yana Sosar k'eya yace "Haba dai Mom wane ni, yauwa mom ina su dady?" Sun fita ita kuma Yafindo tana gidanta ita da Mummynku. 

   Mom tayi shiru Mujaheed yaga bata da niyar fad'a mashi inda matarshi take, shiyasa yace "Mom Meenat fah?" Humm tana sama.


  Mujaheed bai tsaya komai ba ya haura sama ahankali ya bud'e k'ofar d'akin, zaune take a gaban mirror tana sharce kanta daga ita sai Towel kan nan nata sai wane sheki yake,

cak ya tsaya yakasa motsawa saboda wane kamshi dake tashi a dakin, ahankali ya lumshe idanunshi yana shakar kamshin,

ta cikin mirror taga mutum a tsaye da sauri ta buga k'ara sai yanzu yadawo duniya, 

ahankali yake tafiya har ya iso inda take Mikewa tsaye tayi tana shirin guduwa ya fincikota ta fad'a kirjinshi, cikin sanyi murya yana lumshi ido kamar mai jin bacci yace

  "Esh ina zaki koh har yanzu baki amince na zama mijinki bah? Esh karki manta *A DALILIN SONKI* nashiga damuwa mai yauwa please ki amince na zama uban 'ya'yanki."


  Aishat kasa magana tayi sai dai ta sanda kanta a kan kirjinshi, ahankali yasa hannunshi ya d'ago fuskarta yana kallonta da sauri ta rufe idonta,

  Please Esh open ur eyes, kin amince na zama mijinki NA HAR ABADA? 


   Ahankali ta d'aga mashi kai, ai kam baisan lokacin da ya had'a bakinshi da nataba ya dinga kissing d'inta, Kwata_kwata Mujaheed ya fita haiyacinshi yamanta a wacce duniyar yake ma, hannunshi yasa yana so yacire towel d'in da yake jikinta da sauri cikin muryar kuka ta firta, "Yaya Mujaheed karfa ka manta nan d'akin Meenat muke kuma zata iya dawowa yanzu." Da sauri ya saketa yana sosar k'eya sai da yabi jikinta da kallo kafin yace


  "Ki shirya gobe zamu wuce Abuja insha Allahu."

 Abuja kuma? yaya toh... Dakata banason gardama kiyi abinda nace maki kinji koh? Cikin sanyi jiki da fargaba tace "Toh"..


   Mujaheed ya juya ya nufi d'akinshi yana tafiya yana tunani,

Dama haka Aishat take ko ina nata a cike kai na godewa Allah da ban rasata ba a matsayin mata.


   Da wannan tunanin ya isa d'akinshi ..*WASHE GARI*


   Tunda safe Mujaheed ya gama shirinshi yayinda ya kira Meenat yace ta fad'awa Aishat tashirya da wuri zasu wuce, babu yanda ta iya dole tashirya saboda tun jiya ya fad'awa su Daddy, har Mom na cewa bashi da kunya dama matarshi yazo d'auka, cikin daren ya kaita tayi bankwana da Yafindo da Mahaifiyarta,

Mujaheed yana d'auke da box d'inshi ya iso parlourn daga Mom sai su Daddy kawai a parlourn su Meenat basu fito bah, Mujaheed ya duka har k'asa ya gaida iyayen nashi cikin girmamawa duka suka amsa,

bayan zaman Mujaheed da 5 minutes, sai ga Aishat tafito Meenat na take mata baya, 

bayan ta zauna ta gaida iyayen nata nan fa suka ci gaba dayi masu nasiha mai shiga jiki, Aishat kuka take kamar ranta zaifita yayinda taba kowa tausayi a d'aki itama Meenat kukan take,

   Toh ya isa haka kukan kutashi D'anladi najiranku zai kaiku airport kar kuyi let.

 

   Big Daddy ne yayi maganar shima kamar zaiyi kuka, Mom ita takama Aishat saida tasakata har cikin mota kafin Mujaheed ya shiga,

D'anladi yayiwa motar key ai kam Aishat tanaga suntashi ta K'ara fashewa da wani sabon kukan, har suka fita Meenat na d'aga masu hannu,


   Tun Mujaheed na bata hak'uri har yagaji ya fincikota jikinshi yana bubuga bayanta a haka suka isa airport d'in *LATE ALHAJI UMARU MUSA YAR'ADUWA* Mujaheed da kanshi ya dauki Aishat har cikin flight,

har suka isa garin Abuja Aishat na jikin Mujaheed har bacci yayi awan gaba da ita, dama kafin su isa Mujaheed ya kira Lukman yace mashi suna hanya yazo ya d'auke su..


*A BACHA BARRACK* 

 

   A can aka basu gida masha Allah gida yayi kyau sosai, bayan isarsu gidan Mujaheed ya nunawa Aishat d'akinta, shi kuma yasa Lukman ya kawo masu tekaway._AROUND 7:30PM_


   bayan sunyi sallah Lukman ya tafi gida Mujaheed ya nufi d'akin Aishat direct, kwance take kamar tana barci ahankali ya bud'e k'ofar ya shigo, saida ya kare mata kallo kafin ya haura kan gadon kwance take daga ita sai Pyjamas (rigar bacci) duka komai na jikinta kana gani, 

cikin kunnenta yace mata 

 "My Esh har kinyi barci?" Kasa magana tayi saidai jikinta da yake rawa, murmushi yayi sannan ya fincikota, cikin rawar murya tace

 "Please yaya Mujaheed kayi hakuri dan Allah kar kayi man kom...."

 Kafin ta k'arasa ya had'a bakinshi da nata, Mujaheed ya zura hannunshi cikin rigarta yana latsa dukiyar fulani yana lumshi ido, Aishat tun tana kuka har takai tana ihu Mujaheed ko a jikinshi, saida yaga yarabata da budircinta kafin yabarta, Aishat tasha wahala dan Mujaheed bai barta ba sai wajen 1: Mujaheed yasan yayi aure dan surutun da yadinga yi Allah kawai yasan yawansu yasa mata albarka sosai, ya godewa Allah da AK bai b'ata mashi ita bah, takawo mashi mutuncinta,


   cikin ban tausayi ya kalleta ko motsi bata iyayi badroom ya shiga ya gyara kanshi kafin yafito, cak ya dauketa barci har yayi awan gaba da ita, 

 saida ya hada ruwan zafi kafin yasakata ciki k'ara ta saki saboda zafi, shida kanshi yayi mata wanka kafin yafito da ita,

 ya kwantar da ita kangado yana mai bata hakurin abinda ya faru...


**************


   Cikin sati d'aya Mujaheed ya koyawa Aishat wani irin sonshi, soyayya suke baji ba gani...

*DEDICATED TO*

AYSHAT MUHAMMAD

 ( *MAMAN SHAKUR*)

        *N.W.A*
       _MRS UMAR_


*MASOYINA NA HAR ABADA*

.................. _NWA_...................


      _THE LAST PAGE_~~~ Soyayyar da Mujaheed ke nunawa Aishat ba 'yar kad'an bace, hatta office idan Mujaheed ya tafi yana rik'e da waya a kunnensa, 

 haka itama Aishat Kwata_kwata bataso yayi nisa da ita suna ba junansu wata irin kulawa,

sai yanzu Aishat ta k'ara godewa Allah da yasa Mujaheed ta aura, ita kanta tasan Mujaheed ba rago bane dan baya wasa da harka.. saboda zama dashi ya koya Mata juriya shiyasa take alfahari dashi...******************"*********


*BAYAN SHEKARA BIYAR*


Wani yaro na gani da wata yarinya yaran masu kyau masha Allah duka duka shekaran yaron bazasu wuce shekara hud'u bah, ita kuma yarinyar biyu da wani abu, 

Aishat ce ta shigo parlor hannunta rik'e da cup da gudu yaran suka fad'a mata a jiki suna kiran, "umminmu nizaki bah wallahi na rigashi cewa zansha ruwa. "Aishat tayi murmushi mai k'ara mata kyau sannan tace 

"Toh ya isa haka kuzo duk mu zauna naga wa zan fara bah.

" bayan sun zauna Aishat ta jawo yarinyar ta kafa mata cup a baki ai kam yaron yasa kuka, 


"Kai waye ya tab'a min big dady na? "Mujaheed ne yayi magana yana sanye da White jalabiya jikinshi,

"Abba ba ummi bace nace mata zansha ruwa shine taba Anisa wai sai ta fara sha kafin nasha". 

"Oh my boy! bakaga bak'uwa bace tazo maka ziyara ne kaida yakamta ka bata da kanta sai kayi kuka? ko kanaso ta tafi gida yau ne?". "A'a Abba inaso muzauna da ita". 

"Yauwa my boy, ka ringa hak'uri kaga k'anwarka ce kaji?".

  "Ehh naji abbah".


Suna cikin dariya saiga Meenat tashigo ita da Lukman suma dariyar suke Lukman yace 

"Hala tana nan ta dameku? " Aishat tace "A'a wallahi kawai suna fad'ansu ne da suka saba."


Bayan sun zauna Aishat ta dubi yaran tace "Kutafi d'akin ka big dady kuyi wasa kaji koh? "Da gudu suka fita parlor'n,

Aishat ta dubi Meenat da Lukman cikin tsokana tace "Amarya da ango badai kunzo ku d'auke min babyna bah?" Lukman yayi dariya sannan yace "Ina zamu da ita bayan yanzu da bata nan muna cikin soyayyarmu bisa tsinke."


Mujaheed ya rungumi Aishat yace mu koda yaushe cikin soyayya muke koh sweetheart? " gaskiya ne *MASOYINA NA HAR ABADA* NI TAKA CE kai d'aya". "Toh kaji fah Abban Anisa ai kaima nawa ne kai d'aya". 


"Duk sukasa dariya a parlor sannan Mujaheed yace "Toh mungodewa Allah, 

 Allah kuma yaraya mana yaranmu". "amin." Dukkansu sukace.


  Haka rayuwa taci gaba da gudana duka gidajen nan biyu cike da farin ciki, kulawa da kuma k'aunar juna.
*ALHAMDULILLAHI*Toh makaranta littafin *MASOYINA NA HAR ABADA* anan nakawo k'arshen wannan littafin mai suna *MASOYINA NA HAR ABADA*, idan nayi kuskure a cikinsa ubangiji Allah ka gafarta min, idan kuma na fad'a dai dai toh Allah kabani lada!!!


Thank u very much to all my "FANS" I Luv all


*JINJINA* ga 'yan group d'ina Facebook & WhatsApp MRS UMAR HAUSA NOVELS ina alfahari daku..


_UWA MABADA MAMA JINJINA GARIEKI K'UNGIYARMU MAI TAKEN *NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION,* gaskiya kuna k'ok'ari a garemu, mungode sosai_


Gaisuwa ga k'awayena abun alfaharina:-

Munay

Hajar

Rash kardam

Meesha Luv

Teema luff

K'urratul ayn

Rabiatu SK mash

Amrah

Xarah bb

Nana Diso

S.A.Azeez

Zahra

Autar Hajiya

Stylish bch

Baby Amrah

Nafee anka

Chuchungaye

Maman abideen

Miss XOXO 

Sdy jegal

Fido Yar ficika

Zahra bukar

Da duk wanda ban samu na kira sunansu bah, wallahi kuna raina,


Gaisuwarku ta dabance aminan arzik'i

KAUSAR LUV

FIDDAUSI SODANGI

BEEBAH LUV

HAUWA M JABO

Bilkisu chuchu 


hummm ai ke taki ta dabance my sweetheart *JIDDA ALIYU* hak'ika yanzu kin wuce k'awa sai dai na kiraki 'yar uwa, saboda banda bakin miki godiya sai dai nayi maki fatan alkairi thank u very much sweet i will never ever forget you in my life,


ina kike k'awalita wannan novel naki ne KE D'AYA watau *AYSHAT MUHAMMAD* ( MAMAN SHAKUR,) ina alfahari dake tawa,


Thank u very much my sadeey for dedicating your novel to me mai taken *A DALILIN SO*,


'Yan uwana masoyana Khadija Umar Aisha Ibrahim maman lukman maman ummi maman jine saratu Ali bukar Maman Na'im ina gaisuwa


Sai kuma kun jini a sabon littafina mai suna *MAZA DA MULKI MATA DA TAK'AMA*zaizo maku idan mun gama novel dinmu mai suna *KE D'AYA CE* insha Allahu!!!


Masoyana dan K'arin bayani ko kuma k'orafi, zaku iya nema na a


*08021084887*


Tags: #yaudara #soyayya #tausayi #mugunta
4345
1
2
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

nusaiba2019-01-09 10:04:00Masha Allah littafi yayi dadi Allah ya Kara basira

fatima isah2019-01-03 16:48:00wow