Makirci Ko Asiri!

Written by Firdausi JeebohPublished on 2018-12-13 14:44:23Category FictionSuna zaman Amana da matarshi babu wanda ya taba jin kansu, daga shigowar Mufeedah gidan ta wargaza masu zama ta raba kan ma auratan ya tsani Ramlah ko sunanta bai san a fada gabanshi. tags: #asiri #aure #kishiyaDuba was labarai »

: MAKIRCI KO ASIRI


   ©Rubutawa

        Yar_ficika 
BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM Ban yarda wani ko wata ya juyaman labari ta wata siga ba batare da izinina ba..


Banyi wannan labarin dan cin fuskar wani ba duk wanda labarin yayi daidai da halinshi to yayi hakuri nidai nawa fad'akarwa ne....Wannan labarin na sadaukar dashi ga Anty Maijidda Musa (Mama)Littafin tukuici ne gareki Anty Amina KauraNow I know why you always asked me to be strong… because you knew that one day I would need the strength to bear your loss. I miss you Maama may Allah grant you jannatul firdausi 💔😭
21 September 

Birthdays are nature's way of telling us to eat more cake. Birthdays are like boogers. The more you have the harder it is to breathe. Another year older, none the wiser. Birthdays are just finger posts on the road of getting old… I was born with a gift, the gift of awesomeness I'm not just a year older I'm also a year better and prettier. I know you're jealous. I'd like to thank my mom and dad for making this miracle possible. ITS MY BIRTHDAY🎂🎉


Boom! Yes, today is my birthday, Therefore I will be treated like a Queen👑💃Wattpad @yar_ficika

Blog www.phirdauceejeebo.blogspot.com


Instagram: yar_ficika 

Snapchat: phirdauceejeeb5

Twitter: Feedoh Deedoh

Skype: phirdaucee Jeeboh 

Facebook: phirdaucee Jeeboh 


®NWABABI NA D'AYA


  Shimfida

  Gidan Malam Bahaushe...

Idan akace gidan Malam Bahaushe gidane da kyar kasamu matar aure d'aya zaka iya samun sama da d'aya ga yara wasu zamansu lafiya da kishiyoyi wasu kuma zaka samu akasin haka...
  Zaune yake palour cikin lallausar kujera tagumi yayi gaba d'aya hankalinshi bai tare dashi, d'agowa tayi ta kalleshi girgiza kai tayi ta cigaba da shirya yaranta da zasu wuce islamiyya, tana gama shiryasu tabi kowaye ne da peck a kunci kallon babbar tayi tace

"Princess ki kula da k'annenki kinji ko?"

"To Ammi zan kula dasu"

"Kuje kar ku makara driver yana jiranku."

  Tafiya suka yi suna

"Daddy mun tafi."

 Amma hankalinshi bai jikinshi.

  Mik'ewa tayi tsaye kayan dake jikinta sun bayyanar da cikar sura da zatin halittarta. Doguwa ce tana da d'an jiki sai dai ba sosai ba amma gabanta cike yake da dukiyar fulani bak'ace amma ba wulik ba idanuwanta farare ne gata da hips komai nata daidai ita.

  Matsawa tayi kusa dashi ta zauna, hannunshi ta janye daga tagumin da yayi d'agowa yayi ya kalleta tare da sakar mata murmushi kawar da kanta tayi gefe tace

"Tun yaushe nake binka ka gayaman damuwarka amma kak'i fad'aman shin ka mance matarka nake uwar yayanka ko kuma ban isa na san damuwarka ba?"

 Dasauri ya kalleta yace

"Ba haka bane ba bansan ya zaki d'auki abun bane ba"

 Tashi tayi taje gabanshi ta duk'a hannunshi ta kamo tace

"Ka fad'aman damuwarka kai tsaye ni kuma nayi alk'awarin zan baka goyon baya"


  D'agota yayi ya zaunar da ita kan cinyarshi,

"RAMLAH"

 Ya kira sunanta jikinta sanyaye ta amsa da

"Naam"

"Kiyi hak'uri akan abinda za kiji daga bakina banyi haka dan in b'ata maki ba ko kuma kin rageni da wani abu tsawon shekarun da mukayi tare wallahi baki tab'ayi man laifi ba duk abinda na umurceki shi kikeman tabbas samun irinki a wannan zamanin sai an bincika."

  Murmushi tayi tace

"Nagode kwarai da yabon ka a kaina mijina."

"Ramlah"

D'agowa tayi ta kalleshi batare da ta amsa ba sai kuma ta saukar da kanta ganin yanayin daya shiga, 

"Aure nakesan na k'ara. Da sauri ta d'ago

"AURE?"

"Eh aure."

Ajiyar zuciya tayi ta saukar da kanta k'asa.

  Cikin kanta taji yana cewa

"Banyi niyar k'ara auren nan ba dan cin fuska ko kin rageni da wani abu ah ah kawai zan iya kiran wannan auren da auren k'addara dan Allah ki fahimci mi nake nufi."

 Kallonshi tayi ta sakar mashi murmushi tace

"Yanzu dan zaka k'ara aure shine ka kasa gayaman, haba Imran kaifa mijina ne kuma ay Allah ya hallata maka k'arin aure, muddin zakayi adalci a tsakaninmu wallahi ni banda matsala fatana dai ka kasance mai adalci Allah yasa ta gari zaka auro Allah kuma ya had'a arzik'inmu."

  Tun kafin ta k'are ya k'ank'ameta,

"Tabbas Ramlah ke Alheri ce (Biebee'n Feedoh) duk namijin daya sameki wallahi yayi sa'ar mata Allah ya saka da alheri ance Aljannar mace tana k'ark'ashin k'afar mijinta to nikam na d'aga maki k'afata."

  Dariya tayi tare da sauka k'asa tace

"Nagode mijina. A ina k'anwar tawa take? Kuma miye sunanta?"

"Nan garin take a nan goruba road kuma sunanta Mufeedah"

 Murmushi tayi wanda ita kanta batasan na miye ba. Tashi yayi yace

"Zan fita"

Mik'ewa tayi tsaye tace

"Sai kadawo Allah ya kiyaye hanya"

Tana kaiwa nan ta wuce dan batasan ya gane halin da take ciki.


   Tana shiga d'aki ta banko k'ofa fad'awa tayi kan gado ta fashe da kuka sai da tayi mai isarta taga ba maganin da zai mata ta mik'e ta nufi toilet alwalla tayi ta fito tayi raka'a biyu tare da neman Allah ya bata juriya da dangana akan auren da mijinta zaiyi. Ta dad'e tana adua daga k'arshe ta shafa ta tashi ta nufi kitchen danyin girki kafin pikins d'inta su dawo.

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI 


      Rubutawa

        Yar_ficika 


®NWA


Wattpad @yar_ficika 

Blog 

Phirdauceejeebo.blogspot.comThe one thing that I am forever thankful for is that you never forget my special day and always greet me a happy birthday right on time, thank you! Nd i love y'll♥


BABI NA BIYU


  Girki take amma hankalinta bai tare da ita da haka harta gama, k'arfe shida da rabi yaranta suka dawo da gudu suka shigo 

"Ammi mun dawo" abinda suke cewa kenan, 

parlour suka had'u da ita gaba d'aya sukayi kanta suna dariya had'asu tayi gaba d'aya ta rungume, da sauri ta goge hawayen da suka gangaro daga fuskarta tayi....

  Sun kai kusan minti biyar a haka kana ta sakesu, kallonta babbar tayi tace 

"Ammi kuka?" 

Girgiza mata kai tayi 

ba kuka nayi ba princess, murmushi tayi tace 

"Ammi kuka kikayi mana ga idonki nan yayi ja" 

jawota tayi jikinta tace 

"nace maki ba kuka nayi ba abu ne ya fad'a man a ido kuma na cire." 

  Amm amma Ammi.... 

Haneefa jeki cire kayanki bansan yawan surutu 

oya my pikins kuzo muje a cire kaya kafin a kira sallah, gaba d'aya suka rufama mata baya...


  Suna shiga d'akin ta canja masu kaya, duk abinda takeyi idon Haneefa na kanta tana gama canja masu kaya tace

"Kuje kuyi alwalla"

Amsa mata sukayi da "to"

Sukabar d'akin....

Zama Haneefa tayi kusa da ita tace

"Ammi tunda muka dawo nagane kina cikin damuwa amma kin kasa fad'aman karki manta fa ni diyarki ce"

Kallonta tayi ta mata murmushi

"Karki damu princess na gaya maki abu ya fad'aman a ido kuma ayna cire karki damu kanki kinji" 

d'aga mata kai tayi alamar

"To"

"Yauwa my baby tashi kije kema kiyi alwalla nima gani nan fitowa.."


  Saida sukayi isha kana suka hau dainning table dan cin abinci, da kanta tayi serving yaranta sai da taga sun k'oshi kana tace

"Kowa ya d'auko assignment d'inshi"

Tashi sukayi sukaje suka kawo, d'aya bayan d'aya ta masu inda ta masu assignment d'in nan sukayi bacci..

  Kwashe su tayi takai su d'aki ta masu ad'ua ta rufesu da blanket ta ja masu k'ofa...

 Tana shiga d'aki ta fad'a toilet, ta dad'e tana wanka daga baya ta fito gaban mirror ta tsaya tayi kwalliya tana gamawa ta mulke jikinta da oil perfume ta d'auko kayan bacci masu kyau ta saka feshe jikinta tayi da turaren tom ford, tana gamawa ta koma parlour ta zauna ta kunna tv tana kallon mbc max..

  11:00pm daidai ya danna door bell a yangance ta tashi taje ta bud'e mashi, tana bud'ewa ya ware hannunwanshi da gudu ta ida isa wajenshi, k'ank'ameta yayi kamar wani zai kwace mashi sun kusa minti biyar a haka kana ya saketa murmushi ya sakar mata

"Angel kinga yanda kikayi kyau kuwa?" 

"Bawani kyau hayatee"

Rufe mata bakinta yayi da hannuwanta yace

"Waya gaya maki baki kyau ba?"

"Ni ay nasan banyi kyau ba" tana magana tana zumb'ure baki..

"Ya salam"

Abinda ya fad'a kenan gaba d'aya duk ta hargitsa mashi lissafi

Kafin ta k'ara magana ya sunkuce ta baki d'aya ya shiga ciki da ita da k'afa ya tura k'ofan, bai ajeta ko ina ba sai saman 3seater..


  Zama yayi kusa da ita yana haki

"Haka kika k'ara nauyi? Wai mi kikeci idan na fita?"

Dariya tayi tace

"Nikam mizanci"

"Kedai fad'a gaskiya"

Allah bancin komi fa" 

"To na yarda"

Kallonshi tayi

"Yanzu mi zaka farayi cin abinci ko wanka?"

"Duk abinda Angel tace inyi shi zanyi"

 Fari tayi da idanu tace

"To wanka zaka farayi"

"Your wish is my command.."


  Murmushi tayi tace

"Ina zuwa" 

Binta yayi da ido tsananin tausanta ya kamashi shi kanshi yarasa dalilin da yasa yakesan k'ara mata kishiya dan Ramlat ba ta cancanci ay mata kishiya ba, bai gama tunaninshi ba yaji hannunta ciki sumarshi..

 D'agowa yayi yace 

"Yadai?"

"Muje ga ruwan wanka can na had'a maka"

Tashi yayi yabi bayanta har suka isa d'akinshi suna shiga ta mik'a mashi towel karb'a yayi ya mata peck kana ya fad'a toilet...

  Kayan bacci ta fito mai dasu ta feshesu da turare kana ta aje mashi su kan gado...

 Fita tayi ta koma parlour dan had'a mashi abinci...


Dont forget to vote comments nd share

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI 

         

       Rubutawa

           Yar_ficika 


®NWA 


Wattpad @yar_ficika

Blog

Phirdauceejeebo.blogspot.com


BABI NA UKU


   Koda ya fito wanka bai ganta ba, shiryawa yayi cikin kayan da ta aje mashi yana gama shiryawa ya feshe jikinshi da turaren BOSS ORANGE. Parlour ya fito dam yasan can zai sameta, ta baya ya rufe mata idanuwa murmushi tayi 

"Hayatee"

Dariya yayi yace

"Shine kika gudu kika barni?" Daidai yana juyo da ita...

"Abinci nazo na had'a maka fa"

"Kedai wayo kikaman kika gudo kika barni."

  Murmushi ta sakar mashi tace

"Am sorry"

Hancinta yaja yace

"Issokay"


  Hannunshi ta kama ta zaunar dashi

"Mizaka faraci?"

"Duk abinda Angel tabani"

 Murmushi ta zuba mashi tuwon shinkafa da miyar agushi, tura mashi plate d'in tayi, kallonta yayi yace

"Ya haka?"

"Kaci mana"

"Dama da kaina nake cin abinci?"

"Gara kasaba tun yanzu kasan nakusa samun k'anwa"

  Kallo ya tsareta dashi har saida taji kunyar yin maganar da tayi, jawota yayi jikinshi yace

"Aure na ba abinda zai rageki daga kula dani haka nima bai rageni daga kula dake da yarana ko kin manta kune rayuwata?"

Sunne kanta tayi cikin jikinshi tana share kwalla wanda bai san tana yinsu ba...

"Tashi kibani abinci inci" abinda taji yace kenan, ba musu ta tashi tafara bashi abinci yanaci suna fira har saida ta tabbatar da ya k'oshi, kayan ta kwashe takai kitchen saida ta wanke su kana tadawo parlour...

  Kallonta yayi yace

"Hajiya nifa bacci nakeji"

Dariya tayi tace 

"Jeka kwanta saida safe"

"Aww inje in kwanta kikace ko?"

"Eh"

Bata ankaraba taji ya sungumeta niyar kwace kanta takeyi amma ta kasa haka ta hak'ura bai dire ta ko ina ba sai bisa gado, side lamp ya kashe masu yaja masu bargo ya rufe.....


      *********

  zaune suke biyar mata uku sai namiji biyu cikin d'akin shisha pot ce gabansu suna sha hankalinsu kwance ga wak'ar wizkid ta DADIYO na tashi...

"Yanzu Mufeedah dagaske aure zakiyi kibarni?" 

Cewar wani saurayi dake zaune gefen ta..

  Hayakin shisha ta busar ta taso ta k'araso inda yake kanshi ta shafa tace

"Aure na ba abinda zai rageka dashi asalima kasan sanadiyar yin auren nawa so karka tada hankalinka baby nah"

Haka ta dinga kwantar mashi da hankali...  A hankali ta zare jikinta, toilet ta fad'a tayi wanka tana fitowa ta tarda ya tashi murmushi ta sakar mashi shima murmushin ya sakar mata yace 

"Shine kika tashi kika barni ko?" K'arasowa tayi inda yake tace 

"Bansan na tasheka daga bacci ne shiyasa" 

girgiza kai yayi ya mik'e ya fad'a toilet...

  Yana fitowa ta taimaka mashi ya shirya tsaf, hannunta yaja ya zaunar da ita bisa gado yace 

"Ramlah inasan ki lissafaman duk abinda kike buk'ata na baki kudin cz next month ne bikin" murmshi tayi tace 

"Ko nawa kaban bakomai Allah ya sa masu albarka kaida ke da hidima minene kuma sai kaman" 

k'ura mata ido yayi kamar mai karantar wani abu. Ajiyan zuciya yayi ya kamo hannunta yace

"Hakk'in kine na maki dan haka karkiji komai kedai ki abinda nace" 

murmshi ta mashi tace

"Shikenan in shaa Allah kafin kadawo nagama komai".

Rungomata yayi 

"Allah ya maki albarka yabani ikon faranta maki kamar yanda kike faranta man nima" 

"Amin"

Tabashi amsa..

"Break fast is ready fa" 

Kashe mata ido yayi yace

"Zokiji"

Dariya tayi ta ruga tace 

"Naki wayon"

Girgiza kanshi yayi ya tashi ya bita yana jin k'ara san matarshi hannu ya d'aga ya nama Allah godia daya bashi Ramlah a matsayin mata...

  Parlour ya tarda ta tana had'a mashi abinci, hannunta yajawo 

"Yanzu wana kama?"

Dariya tayi bata bashi amsa ba...

  Zaunar dashi tayi ta dinga bashi abinci kamar wani taro har sai da ya k'oshi kana ta kyaleshi....

  Jikarshi ta d'auko ta rik'o mashi hannu ta rakashi har gaban mota. Duk'awa tayi ta bashi jikar

"Allah ya kiyaye hanya ya kaika lafiya ya maidoka lafiya alkairin dake tattare da ranar nan Allah ya had'aka dashi sharrin dake cikinta kuma Allah ya nisanta kadashi ka kuma tabbata halak d'inka zaka kawo mana"

"Amin ya Allah"

Abinda yace kenan yana murmushi saboda irin aduar nan ta riga data zamar mashi jiki muddi zai fita saita mashi ita shiyasa yakejin duk duniya babu wanda yakaishi sa'ar mata..

  Kanta ya shafa yace "a kullum ina alfahari dake Allah ya bani abinda zan faranta maki"

Motar ta bud'e mashi peck ya mata kana ya shiga

"Kigaidaman yarana idan sun dawo yau na makara bamu gaisa ba har suka tafi makaranta"

  Murmshi tayi tace 

"In shaa Allah zan gaya masu.."

Motar yama key ya fita d'aga mashi hannu takeyi har saida taga ya fita daga gate d'in gidan kana ta juya ta koma cikin gida.....

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI 


      Rubutawa

        Yar_ficika 


®NWA


Wattpad @yar_ficika 

Blog

Phirdauceejeebo.blogspot.com


BABI NA HUD'U  Kan kujera ta fad'a hawaye suka cigaba da sintiri kan fuskarta, dafa ta taji anyi da sauri ta d'ago fuskarta ganin waye ya dafata..

  "Lafiya kike? Tunda na shigo nake sallama amma baki amsa ba sai ma kuka da kikeyi" 

cewar wata mata dake tsaye

 Murmushi tayi ta share hawayenta

"Bakomai"

Zama matar tayi tare da murmushi wanda iya karshi labb'a

"Ba maganar ba komai gashi kina kuka sai dai in ban isa nasan damuwarki ba neba"..

Hawaye ta share

"Dama Imran ne zai k'ara aure"

Tashi tsaye matar tayi 

"what?"

"Aure" 

"Shi Imran d'inne zai k'ara aure?"..

   Kamo hannunta tayi ta zaunar da ita tace

"Eh aure zaiyi"

"Laifin mi kika mashi ne? Nidai iya sanina ban tab'ajin tsakaninku ba bare har yace zai k'ara aure"

 Nisawa tayi tace

"Dama sai kama namiji laifi zai k'ara aure? Ai namiji duk sanda ya buk'aci k'ara aure to komi kake mashi sai ya k'ara sai dai fatan Allah ya sa wanda za'a auro ta gari ce.."

"To ke yanzu wane mataki kika d'auka?"

"Mataki kuma?"

"Eh kina nufin hakanan zaki zauna? Wallahi gara ki tashi tsaye kinsan wadda za'a kawo maki? Kinsan dami zata shigo gidanki? Gara kisan matakin da zaki d'auka ki shirya ina da wajen malamin da zan kaiki sha yanzu magani yanzu ke ina tabbatar maki ko auren baza'ayi ba.."

  D'agowa da sauri Ramlah tayi ta kalle ta

"Anya Zainab kina da lafiya kuwa? Kinsan mi kike fad'a wajen malami fa"

"Eh malami keni kin ganni nan wallahi mijina bai isa yace zai k'ara aure ba cz hannuna yake sai yanda nayi dashi.."

"Wa iya zubillah Allah kamana tsari da irinku Zainab da ina ganinki mai hankali ashe baki da hankali, to bari kiji wallahi ko da zan zama abun tausayi bazan iya zuwa wajen malami ba da sunan a hana mijina aure ba'a aure ni aka aure ni? Kuma miye hukuncin wanda ya haramta abinda Allah ya halasta? Allah ne yace suyi aure idan zasuyi adalci, Idan har bazan tashi da dare ba inkai ma Allah kuka na to kada Allah yaban ikon zuwa wajen wani malami Kuma idan kinsan saboda irin haka zaki dinga zuwa gidana karki k'ara zuwa nayi dana sanin k'awance dake amma ina neman maki shiriya Allah ya ganar dake"

Mik'ewa tsaye Zainab tayi tace

"Ko bakice ba ban k'ara zuwa kuma indai namiji ne gayacan ya gasaki sarkin biyayya" 

tawani shek'e da dariya ta fita tabar gidan...

     **********

   Haneefa ce tare da k'annenta suka shigo da sallama yarinya yar kimanin shekara bakwai, k'arasowa sukayi inda take zaune, zare mata hannu tayi daga tagumin da tayi d'agowa tayi ta kallesu tana murmushi

"Har kun dawo? Banji shigowarku ba?"

  Murmushi tayi ta kalli k'anneta tace 

"kuje d'aki ku cire kaya sai muyi wanka muzo muci abinci muyi shirin Islamiyya"

Ba musu suka nufi d'aki..


  Zama tayi kusa da Ramlah tace 

"Ammi akwai abinda ke damunki amma baki fad'aman" 

Ita kanta tana mamakin irin wayon Haneefa da hankalinta

 Jawota tayi jikinta tace

" bakomai kinji my babe kedai ki rink'a man adua kinji ko"

"In shaa Allah Ammi"

"Allah ya maki albarka"

"Amin"

Mik'ewa tayi ta nufi d'akin dan itama ta cire kayanta...

  Binta tayi da kallo tana k'arajin k'aunar d'iyarta a ranta duk yanda take b'oye damuwa amma Haneefa tana ganewa..

  Suna fitowa suka wuce dainning dan cin abinci da kanta tayi serving yaranta suna gama ci suka wuce islamiyya..  Da sallama ya shigo ga maigadi na ta shigowa da akwatina, bai ganta parlour ba yasan bata wuce d'aki.

  D'akinta ya lek'a zaune take bisa sallaya tana azkar, wuri ya samu ya zauna sai da tagama tsaf ta d'ago da murmushi ta kalleshi shima murmushin ya mayar mata

"Sannu da zuwa "

"Yauwa"

Ya amsa mata...


  Tashi tayi ta nufi toilet dan had'a mashi ruwan wanka, tana fitowa ta kalleshi tace

"Ga ruwan wanka can"

Mik'ewa yayi ya kamo hannunta suka nufi parlour baice mata komai ba..

  Zaunar da ita yayi ya kalleta yace

"Ga akwatina nan set biyu ki zab'i daya ki barma Amarya d'aya duk abinda ke nan akwai shi nan sai dai kayan kowane da kalarsu wad'an can kuma nasu Haneefa"

  Murmushi tayi tace

"Mungode Allah ya k'ara bud'i"

"Amin ya rabb"

Set guda ta d'auka ta duba komai na ciki ya mata tana cikin dubawa yace

"In akwai abinda bai maki ba saiki fad'a"

D'agowa tayi da murmushi tace komai yayi Allah ya k'ara rufa asiri...

"Amin"

Ya amsa tare da mik'ewa

"Gobe masu fenti zasuzo"

Yana fad'ar haka ya wuce d'aki dan yin wanka

"Allah ya kawosu lafiya"

Ta bashi amsa..

   Fitowa yayi shirye cikin k'ana nan kaya, tana kallonshi tace 

"Har kafara kyallin agonci"

Dariya yayi yace

"Zaki fara ko?"

Wuri yasamu ya zauna da taimakonta yaci abinci bayan ya gama ta kwashe kayan ta kai kitchen dawowa tayi ta 

zauna k'asa tana matsa mashi k'afafuwa, kud'i ya zaro ya mik'a mata "ga wannan dubu d'ari biyu ne idan akwai abinda zakiyi"

Murmushi tayi tace

"Wallahi ba abinda zanyi kaman komai dan haka ka barsu"

Tsura mata ido yayi yana kallonta, kanta ta saukar k'asa tana wasa da yan yatsunshi..

"Ramlah"

Ya kira sunanta d'agowa tayi ta kalleshi yace

"Nina baki wannan kud'in ko bazaki komai dasu ba ki aje wajenki"

  Hannu biyu tasa ta karb'a tace

"Nagode Allah yasaka da alkairi ya k'ara buri"

"Amin"

Ya amsa mata...

  Tashi tayi tace 

"Ina zuwa"

Jim kad'an ta dawo da wata leda bud'ewa tayi ta fito da wata shedda getzner fara tasha dinki da babbar riga tace

"Ga tawa gudumuwar inasan mijina ya sata ranan d'aurin aure"

Karb'a yayi ya k'ura mata ido

"Ina kika sameta?"

Order ta nayi a YML fashion design sukace na tura mejoment d'inka na masu sending shine yau suka kawo man"

Ay tun kafin ta k'arasa ya rungumeta

"Tabbas samun mata kamarki sai an bincika a kullum ina godema Allah da yabanke a matsayin mata uwar yayana"

Dariya tayi tace

"Ganinka cikin farin ciki yafi man komai a rayuwa.."

 K'ank'ameta yayi yana k'ara jin san matarshi kwallan da suka gangaro mata ta share dan batasan ya gane halin da take ciki...


Don't forget to vote comments nd share it really means alot to me. I love y'all my sweetos

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI 

         

       Rubutawa

           Yar_ficika 


®NWA 


Wattpad @yar_ficika

Blog

Phirdauceejeebo.blogspot.comBABI NA BIYAR


   "Ammi Ammi Ammi"

Haneefa ce ke kwalamata kira da sauri ta fito daga kitchen tace

"Haneefa lafiya?"

"Lafiya lau Ammi"

Ta bata amsa..

  B'ata fuska tayi tace

"Ji yanda kika d'agaman hankali da kira"

Dariya tayi tace

"Yi hak'uri"

"Inasu Haneef?" 

Suna d'aki..

"Yauwa Ammi akwatina nagani d'akinki na waye?"

"Dama nasan wannan kiran da kike akwai wani abu"

Namune Daddynku ya kawo mana d'azu"

Ido ta zaro tace

"Namu ne muduka Ammi? Lallai Daddy naji damu"

Ta dinga tsalle tana murna, ita dai Ramlah binta tayi da ido tana girgiza kai.

"Amma Ammi miyasa ya siyo manasu?"

Kanta ta shafa tace

"Aunty zai kawo maku shine yamana d'inkin biki"

"Aunty?"

"Eh Aunty"

Ta bata amsa, bata k'ara cewa komai ba ta janye jikinta ta nufi d'akinsu, kallonta Ramlah tayi ta girgiza kai, ta koma kitchen...


  Saida ta gama aikin da take kana ta nufi d'akin yaran, ganinsu tayi zaune sunyi tagumi kallonsu tayi tace

"My pikins ya kukayi tagumi?"

"Bakomai" 

Haneef ya bata amsa

B'ata fuska tayi tace

"Akwai abinda ke damunku"

Numfasawa Haneefa tayi tace

"Ammi miyasa Daddy zai k'aro mana Aunty? Ina tsoro saboda gidansu Sadeeya kinga basu zaman kafiya kullum cikin dambe da fad'a kullum sai Sadeeya taban labarin irin fad'an da ake gidansu, Ammi ina tsoro kar itama ta dinga nemanki da fad'a"

Shiru Ramlah tayi 

Yanzu kamar Haneefa tasan irin wannan matsalolin?"

Takowa tayi ta k'araso inda suke zaune ta sakar masu murmushi tace

"Haneefa ba kowane gida baneba basu zaman lafiya wani gidan idan kikaje zaki tunanin babu kishiya kisa aranki ta gari Daddy zai kawo kudai ku cigaba da adu'a kunji yarana.."

   D'aga mata kai sukayi sukace

"In shaa Allah Ammi zamu cigaba da adua"

D'aya bayan d'aya ta bisu ta masu peck tace 

"Allah ya maku albarka"

"Amin"

Suka amsa...


       ************

 Gidan yau cike yake da mutane anata hidimar biki, duk wanda yaga Ramlah bai cewa itace za'ama kishiya ba, yanda take fara'a kowa sai mamakin irin halinta yakeyi...

  D'aki ta tardashi ya fito wanka tana ganinshi ta saki murmushi kaga

"Angon Mufeedah"

K'arasowa yayi inda take ya rungumeta yace

"Ramlah wace irin matace ke wai? Miyasa abu bai b'ata maki rai?"

  Kwalla ta share ta d'ago tace 

"Bayan da zanyi da abinda Allah ya rubuta to kaga tada hankalin bashi da amfani nidai fatana dakai Allah ya baka ikon yin adalci.."

K'ara rungumeta yayi yace

"Ramlah ance Aljanar mace na k'ark'ashin k'afar mijinta ko?"

"Eh"

"Toh na d'aga maki"

Murmushi tayi tace

"Nagode"

 Hannunshi taja tace 

"Muje ka shirya kada ka makara...."


  Da taimakon Ramlah Imran ya shirya tana shirya shi tana tsokanar shi

"Kaga yanda kayi kyau? Gaskiya baka tab'a kyau irin haka ba"

Murmshi yayi yace

"Nagode.."

  Tana gama shiryashi ta feshe shi da turaren BOSS ORANGE wani k'amshi ke tashi mai sanya zukatan masoya..

  Tana gamawa ta kalleshi tace

"Allah yabada sa'a Allah yasa abokiyar arzikinka ce zaka auro Allah ya had'a kanmu Allah ya baka ikon yi mana adalci."

Tunda tafara maganar yake kallon bakinta tabbas yasan maganar nan har zuciyarta suke..

  Rungumeta yayi yace

"Nagode mata tagari ked'in daban ce acikin mata.."

  Hannunshi taja har gaban k'ofa kana ta kalleshi tace

"Allah ya kiyaye"

Juyawa tayi da sauri kar yagane halin da ta shiga, har yafita yadawo hugging d'inta yayi ta bayya yace

"Nasan yanda kikeji Allah ya maki albarka"

Murmushi tayi ta juyo tace

"Amin"

Peck ya manna mata a kunci ya fita..

  Yana fita ta fad'a kan gado ta saki kuka mai tsuma rai, saida tayi mai isarta kana ta tashi tayi wanka ta fita cikin mutane aka cigaba da hidima...


       *********

  K'arfe shida aka shigo da amarya gud'a kake taji ta ko ina sai habaici ke tashi Maryam k'awar Ramlah zatayi magana Ramlah ta hanata, haka suka k'araci habaicinsu babu wanda ya tanka masu, babu wanda yayi tunanin ya kawo amarya wajen uwargida..

  Abin ya k'ona ran k'awayen Ramlah amma tahana suyi magana, wata daga cikinsu tace

"Gaskia Ramlah hak'urinki yayi yawa"

Murmushi tayi tace

"Hak'uri ay baya yawa"

Haka suka dinga mita amma bata biye masu ba...


   K'arfe goma aka rako ango, bayan yan rakiya sun tafi ya tara matanshi dan ya masu nasiha...

  Nasiha ya masu mai ratsa jiki yace

"Mufeedah kece k'arama ya zama dole kibi Ramlah banda matsala da ita dan haka indai kina sona to dole kiso uwar yayana bazan so wani ya wulak'anta taba. Kema Ramlah ki kama girmanki ki bata girmanta na k'awarki nasan banda matsala dake.."

Murmushi Ramlah tayi tace

"In shaa Allah bazaka samu matsala dani ba"

"Allah ya maki albarka" 

Ya fad'a..

Mufeeda tace

"Nima banda matsala sai dai ban d'aukar raini.."

Kallonta Imran yayi yace

"Indai dan Ramlah za'ayi fad'a to baza'ayi shi ba nasan halinta."

Tab'e baki tayi, ita dai Ramlah ido ne nata...

 "Honey tashi muje mu kwanta kasan nagaji"

Murmushin yak'e yayi 

Dariya Ramlah tayi tace

"Ya kamata kam kuje ku kwanta.."

Mik'ewa tsaye yayi yace

"Saida safe Hayatie"

"Allah ya kaimu.."

Ta amsa

 Juyawa sukayi suka fita, Mufeeda ce ta dawo da sauri ta kalli Ramlah tace

"Ke matar kirki ko? Ana wani yabonki ana kod'aki hmmm soon zan maki illa sai na rabaki da mijin da kike tak'ama dashi ke gidan ma zan rabaki dashi sai na tarwatsa kanku inga ta yabonki.."

 Tana kaiwa nan tayi tsoki ta juya ta tafi....


Hmmmm ana wata ga wata, anya Mufeedah zatayi galaba akan wannan ma'auratan da suke san junansu? Kudai biyo Phirdaucee Jeeboh danjin wannan badak'ala....


#Team MKA


Vote

Comments

Nd

Share

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI 

         

       Rubutawa

           Yar_ficika 


®NWA 


Wattpad @yar_ficika

Blog

Phirdauceejeebo.blogspot.com
BABI NA SHIDAWANNAN BABIN NAKINE ASHNUR PYAR INAJIN DAD'IN YANDA KIKE AJEMAN COMMENTS ALLAH YASAKA DA ALKAIRI YA BARMU TARE♥ #Ilove #Team MKA  Da kyar ta ja k'afanta ta nufi d'akinta, bisa gado ta fad'a rajab tagumi tayi wasu hawaye suka dinga sintiri kan fuskarta.

"Me matar nan take nufi da maganganunta mike shirin faruwa dani? Kodai na kira k'awata na shaida mata halin danake ciki ne?"

Wata zuciyar tace mata karki saki kifara fad'ama kowa damuwarki saboda wata k'awar tafi guba zata iya kaiki ga halaka kuma wannan ay sirrinki ne adu'a zaki dage dashi in shaa Allah bazata tab'a nasara akanki ba....

  Hannunta ta d'aga sama tace

"Allah kada kaba wannan baiwar taka yin galaba akanmu Allah ka kare man mijina da yarana da ni daga sharrinta" shafawa tayi tare da yin tagumi..

  Saurin mik'ewa tayi ta fad'a toilet Alwalla ta d'auro tazo ta kabbara sallah tana idarwa tahau adu'a neman kariya bata bar kan dadumarta ba sai da tayi sallar asuba kana ta koma kan gado ba jimawa bacci mai nauyi ya d'auketa...


   K'arfe goma ta diro daga kan kado toilet ta fad'a saida tayi wanka kana tafito tana fitowa ta shirya cikin doguwar rigan atamfa purple d'inki yayi matuk'ar karb'anta a jikinta ba wata kwaliya tayi ba asalima ba kwalliya take ba turare ta fashe jikinta dashi kana ta nufi d'akin yaranta koda taje ta tarda sun tashi da gudu suka k'araso gurinta

"Good morning Ammi"

Murmushi tayi tace 

"Morning my pikins hope kun tashi lafiya?"

"Lafiya Lau"

Suka amsa mata

  Toilet ta shiga ta had'a masu ruwan wanka d'aya bayan d'aya tama yaranta wanka sai da ta gama da mazan kans tace ma Haneefa taje tayi itama ta shiryasu tsaf kana tace 

"Muje parlour"

Suna isa parlour ta kunna masu cartoon ta nufi kitchen dan shirya breakfast...

           ******

  Zaune yake kan gado yayi tagumi shidai yasan ba cikakkiyar mace ya sami Mufeedah ba amma kuma yakasa tsanarta, k'ofar toilet aka bud'e fitowa tayi da wani shu'umin murmushi yana ganinta yafara dariya ya ware mata hannu da gudu ta k'arasa wajenshi ya rungumeta kamar wani zai kwace mashi ita..

  K'arfe shad'aya suka fito daga d'aki ganin su Ramlah parlour yasa Mufeedah k'ara shige mashi, shiko kunya duk ta kamashi saboda yanda Haneefa ke kallonsu, k'arasowa yayi wajensu ya kalli Ramlah yace

"Morning Angel"

Murmushi tayi tace

"Ango kun tashi lafiya?"

Had'a hannuwanta yayi yace 

"Lafiya lau"

Juyowa yayi ya kalli yaranshi gaba d'aya sukace

"Morning Daddy"

Murmushi ya sakar masu ya rungumesu tare da yima kowa peck ...

  Duk abinda akeyi Mufeedah na tsaye tsanar Ramlah da yaranta ta k'araji a zuciyanta 

"Soon zan tarwatsa wannan family"

Abinda tace a zuciyarta kenan 

  Imrah yace 

"Bakiga Angel ba? Banga kin gaidata ba"

Wani takaici ya kamata tace 

"Hmm zanyi maganinku"

A zahiri kuma tace

"Naga kuna magana shiyasa"

  Bai k'ara magana ba ta zube k'asa tace

"Anty ina kwana?" 

Da far'anta ta amsa 

"Da lafiya lau antashi lafiya ya kwanan bak'unta?"

"Lafiya lau ta amsa"

  Juyawa tayi kan yaran kafin tayi magana sun gaidata, banda Haneefa data cika ta batse

  A hankali Ramlah tace 

"Princess baki gaida Mammy ba?"

Da kyar ta bud'e baki ta gaidata 

"Zakici ubanki yarinya"

A zahiri ta amsa cikin sakin fuska tace

"Babyn tawa miskilace"

Hameef yayi sauri yace

"Haka take Mammy batasan yin magana"

Kafin su k'ara magana Ramlah ta kallesu tace

"Breakfast is ready"

Gaba d'ayansu suka nufi dainning danyin kalaci..


  Abinci sukeci suna fira banda Haneefa wanda ta had'e rai abincin ma da kyar take taunashi..

  "Yarinyar nan zatayi taurin kai amma zan gyara mata zama"

A zahiri kuma tace

"Babynah yana ga baki cin abincin?"

Banza tayi da ita ta kyale sanin halinta da Ramlah tayi bazata tanka ba tace 

"Haneefa bakijin Mammy na magana?"

 D'agowa tayi da runanun idanuwanta tace

"Banjin dad'ine"

  Nanfa Imran ya rud'e dan duk duniya bai had'a yaranshi da kowa ba

"Babyna mike damunki gayaman kinji"

Dariya tayi tace

"Calm down Daddy ciwon kai ne kuma yayi sauk'i" 

Ajiyar zuciya yayi yace

"Har naji sanyi "

Tab'e baki Ramlah tayi dan dama tasan k'arya Haneefa takeyi dan tasan lafiyarta lau. Murmshin takaici Mufeeda tayi a ranta tace

"Wannan rawan kan da yakeyi kanku nan bada jimawa ba zai tsaneku tsanar da ko hanya yaganku bazai nuna ya sanku ba...

  Haka suka k'arasa cin abincin suka dawo parlour....


   Imaran yace

"Mufeedah ga yara na nan wannan sunanta Haneefa shekaranta gona tana primary 5 shikuma mai bita shekaranshi bakwai yana primary 3 nd sai d'an Auta Mukhtar shekaranshi hud'u yana primary 1 duka suna school a Hope intenational school i hope zaki rik'esu kamar yaranki.."

  "Mufeda?"

Ni zai kira da Mufeeda gabana yake kiran shegiyar matarshi Angel amma ni Mufeeda zakuyi danasani ku duka..

  Zahiri kuma tace

"Allah ya masu albarka in shaa Allah zan rik'esu kamar yarana"

Murmushi yayi yace

"Nagode"

Ya juyo kan yaran yace

"Mufeeda kece babba dan haka ga Mammy nan kamar yanda naji Amminku tace ku kirata kuyi mata biyayya kamar yanda zakuyima Ammi kece babba duk abinda kikayi shi k'annenki zasuyi thou banda matsala daku I trust you yarana nasan zaku mata biyayya.."

  Itadai Haneefa batace komai ba haka kuma bata d'aga kai ta kallesu ba dan gaskia tun da taga Mufeedah taji ta tsaneta bata kwanta mata ba....

  A hankali ta d'ago tace

"In shaa Allah Daddy zamu kwatanta"

"Allah ya maku albarka"

Suka amsa da

"AMIN"...Dont forget to vote comments nd share

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI 

         

       Rubutawa

           Yar_ficika 


®NWA 


Wattpad @yar_ficika

Blog

Phirdauceejeebo.blogspot.comBABI NA BAKWAI


  Kallonshi Mufeedah tayi tace

"Honey muje mud'an huta ko?"

Dariya yayi yana sosa kai yana kallon Ramlah murmushi tayi tamashi alama da ido alamun sutafi...

  Kyam idon Mufeedah akansu, wani malalacin murmushi ta saki ta k'ara narke murya 

"Honey pls tashi muje wallahi nagaji kasan jiya kaban wahala"

Dum yaji abu har cikin ranshi 

"Wannan wace irin mata ce haka? Shin bata ganin yaranshi take wannan maganana"

Amma a zahiri murmushi yayi ya mik'e tun kafin ta k'ara sako wata maganar...

Ita dai Ramlah bata ce komai ba sai ma murmushi da ta sakar masu..


  Har sun kai bakin k'ofa ta juyo ta masu wani kallon kun kusa zama abun tausai kana ta shige d'aki...

  Hankalinta Ramlah ta maido kan yaranta tace

"Kuje d'aki ku kunna tv amma ke Haneefa ki tsaya zanyi magana dake.."

  Ba musu suka mik'e suka nufi d'akinsu, sai data ga sun shige kana ta maido hankalinta wajen Haneefa..

"Miyasa kikamata haka? Shin tarbiyar da muka baki kenan?"

Cikin rashin fahimta Haneefa tace

"Wake nan?"

Murmushi Ramlah tayi dan tasani sarai ta gane watake magana amma tasan miskilancin ta bazai bari ta nuna ta gane ba..

"Mammy nake magana miyasa zaki mata haka? Itamafa mamarkice saboda Babanki ya auro ta kingako ay tazama Uwa wajenku.."

D'agowa Haneefa tayi tace

"Ammi baki lura da yanayin matar ba? Nikam gaskia bataman ba"

Bige bakinta tayi tace

"Karna sake ji kince bata maki ba kimata biyayya kamar yanda zakiman kinajina?"

D'aga kai tayi murya sanyaye tace

"Naji Ammi"

Allah ya maki albarka tashi kije kiyi muraji'a kafin lokacin Islamiyya yayi. Tashi tayi ta nufi d'aki a ranta tana sak'a yanda zata ma matar nan dan muddin bata bari taci zarafin Amminta kuma da alamu matar zatayi rashin mutunci...

           ******

  "Gaskia banji dad'i yanda kike maganganu gabansu Haneefa ba yara nefa mikike so su d'auka?"

Imran ne kema Mufeedah magana..

  Turo baki tayi tace

"Minayi? Ina cewa da mijina nake magana"

Tana magana tana cika tana batsewa, ganin tana fushi yasa duk ya daburce ya shiga lallashinta da kyar ya samu ta sauko..

 Ajiyan zuciya yayi yace

"Nagode"

Murmushi tayi ta fara shafoshi ganin abinda take shirinyi yasa ya mik'e yace

"Bari naje naga abokina"

Bai jira mi zata ce ba yayi waje..

  Kitchen ya sameta da sand'a ya shiga idonta ya rufe kamshin turarenshi yasa ta saki murmushi tace

"Hayatee"

Kwantar da kanshi yayi a bayanta ya kai minti 5 a haka baice komai ba.

"Yadai?"

Abinda tace kenan, ajiyan zuciya yayi yace

"Nothing"

Juyowa tayi ta suna kallon juna murmushi ta sakar mashi tace

"Ina baccin?"

Hancinta yaja yace 

"Zanga Ahmad ne"

"Ok"

Hugging d'inta yayi tare da mata peck a kunci yace

"Saina dawo"

"Allah ya dawo dakai lafiya "

Ta bashi amsa, kai yasa ya fita a bakin kitchen yaci karo da Mufeedah murmushi ta sakar mashi sosa kai yayi yace

"Ya akai kika fito?"

Dariya tayi tace

"Nazo taya Anty aiki ne"

Dad'i yaji ya mata peck yasa kai ya fita, cikin kitchen d'in ta k'arasa 

"Ke k'aramar karuwa"

Da sauri Ramlah ta juyo tana kallonta

"Eh dake nake ubanmi ya had'aki da mijina? Ai kinsan daga nan har tsawon kwana bakwai yana tare dani amma shine dan munafunci saida kikasan yanda kikayi kika jawoshi jikinki wallahi zaki gane kurenki saina dasa mashi tsanarki dagake har shaggun yaran da kike tak'ama dasu...."

  Tun da take magana Ramlah bata ce mata komai ba har tagama, juyawar da zatayi taga Haneefa tsaye tana mata kallon tsana 

"How dare you zaki dinga kiran Mahaifiyata da munanan kalamai haka? Miki keji dashi ne kodan kinga tana hak'uri kwana d'aya da zuwanki kina neman tarwatsa mana gida mikike tak'am......"

 Tsawar da Ramlah ta matane yasa tayi shiru da bakinta..

  "Dake take? Ko kuwa sa'arkice ita?"

Duk'a ki bata hak'uri, turo baki Mufeedah tayi tace

"Kiyi hak'uri"

Murmushi tayi ta dafa kanta tace

"Karki damu yantama da sannu zan maidaku abun tausai dake da uwartaki.."

Tana fad'ar haka tayi d'akinta..

  K'arasowa Haneefa tayi cikin kitchen tace

"Ammi saikin aje hak'urin ki indai baso kike matar nan tayi galaba akanki ba.."

Tana fad'ar haka ta juya tayi d'akinsu cike da takaici....


Don't forget to Vote Comments nd share

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI 

         

       Rubutawa

           Yar_ficika 


®NWA 


Wattpad @yar_ficika

Blog

Phirdauceejeebo.blogspot.com


BABI NA TAKWAS  Shiru Ramlah tayi dan tabbas tasan Haneefa gaskia take fad'a mata dole ta tashi tsaye da adu'a dan matar nan da alamun batazo da zaman lafiya ba, ita har mamakin Haneefa takeyi a iya shekarunta amma tasan ama wani abinda bai dace ba....

  Tana shiga d'aki tajawo waya ringing biyu aka d'auka 

"Hello Lash kina ina?"

Banji mi akace ba,

"Ok kizo gidana yanzu ina san ganinki", tana fad'ar haka ta datse call d'in, tashi tayi ta dinga zurga zurga cikin d'akin

"Hmmm Ramlah zaki raina kanki dake da marar kunyar d'iyarkin nan zaku san wacece Mufeedah yar ruwan zafi baka tab'ani bama na k'ona ka bare ka tab'ani da nayi niyar in d'an barku amma naga d'iyarki tsaye take to dole zanyi maganinku da wuri sai na mai daku abun tausai a gari...

  Haka ta dinga zagaye d'aki tana sabbatu ita kadai..

            *******

   Banko k'ofa tayi ta shigo ko sallama babu

"Lafiya Mufeedah?"

Sai a sannan ta juyo, murmushi tayi taja hannunta suka zauna bakin gado...

  "Ina jinki fad'aman ko hankalina ya kwanta"

Dafa kafad'arta tayi tace

"Akwai matsala"

"Matsala?"

"Eh matsala"

"To matsalarmi ke da aka kawo jiya wace irin matsala kenan kodai ya gane ba budurwa ya sameki ba ya maki wulakanci?"

Dariya tayi tace 

"Tabbas ya gane ba cikakka nake ba sai dai kinsan baida hurumin ya man maganar ko ya canjaman saboda boka yaman aiki akan haka..."

 Numfasawa tayi tace 

"To kodai kin had'u da hatsabibiyar kishiya wadda tafiki MAKIRCI?"

Wata dariya ta saki tace

"Kina tunani akwai wadda zata fini makirci kuwa? Toh in gaya maki ba haka Ramlah take ba in gaya maki kwana d'aya nayi da ita amma nasan wacece ita mace ce mai hak'uri da kawaici."

  Kallo ta bita dashi tace

"Ramlah ki fitoman a mutum ban san inda kika nufa ba..."

  Gyara zama tayi tace 

matsalar daga d'iyarshi ne"

"D'iyarshi?"

"Eh"

"Dama yana da d'iya babba ne?"

  Girgiza kai tayi tace

Bazata wuce shekara goma ba"

Dasauri Lash ta mik'e tace 

"Shekara 10?"

"Eh"

"Ke ko wace lalacewa tazo maki da yarinyar cikinki zata tada maki hankali?"..


  Zaunar da ita tayi tace

"Kinfi kowa sanin wacece Mufeedah yar ruwan zafi ban da tsoro ko kad'an baka tab'ani ba na k'onaka bare ka tab'ani, kinfi kowa sanin dalilin dayasa na shigo rayuwar Imran na shigone dan na rabashi da farin ciki in tarwatsa gidanshi, da nayi niyar in d'an d'aga masu k'afa amma wannan mara kunyar yarinyar tasa dole zanyi maganinsu da wuri...."

 Ajiyan zuciya tayi tace

"Naji amma mi yarinyar ta maki?"

  Zama ta gyara ta kwashe komai duk abinda ya faru ta gaya mata...

  Dariya Lash tayi tace

"To yanzu miye abinyi?"

   Murmushi tayi tace 

"Yauwa yar gari yanzu kikayi magana, wajen boka nake san kije ki gaya mashi komai karki rage komai kice nace so nake ya tarwatsasu ya hana masu farin ciki ya dasa masu bak'in ciki har k'arshen rayuwarsu kingani yanzu babu yanda za'ayi na fita tun da jiya kuka kawoni.."

  (Wa iya zu billahi mi mutane suka d'auki duniya? Shin ko sun manta ana mutuwa ne? Idan ka hana wani farin ciki ribar mi kaci? Kar mu manta akwai ranar sakayya ko Allah bai saka ma wanda ka cuta duniya ba wallahi sai ya saka mashi ranan gobe k'iya, Allah kasa mufi k'arfin zukatanmu..)

  Wata irin dariya Lash tayi tace

"Buk'atarki ta biya, sai dai kinsan saikin kashe kud'i ko?"

Dariya tayi tace

"Kud'i ba matsala ta bace ba ke kin sani"

 Tana gama fad'an haka ta mik'e ta nufi wardrobe d'inta kud'i ta d'auko rapper 1k guda biyu ta wurga matasu tace

"Nasan zasu isheki"

Dariya tayi tace

"Harda canji ma kuwa.. "

   Shewa sukayi suka tab'a...Don't forget to vote comments share nd follow it really means a lot to me..

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI 

         

       Rubutawa

           Yar_ficika 


®NWA 


Wattpad @yar_ficika

Blog

Phirdauceejeebo.blogspot.comBABI NA TARAWannan BABIN nakune Ramlah Yusuf Ayagi Mufeedah Abubakar Dijah Waziri da Raheena Mamoudou #1love♥ #TEAM MKA


  Kallonta Lash tayi tace

"Bari na wuce kinsan da safe ake kamun fara dan haka yanzu daga nan can na nufa.."

 Rungemata Mufeedah tayi tace

"Shiyasa nake sanki Aminiyata samunki a rayuwata babban alkairi ne...

  Jakarta ta d'auka suka fito bakin kitchen suka had'u da Ramlah tana ganinsu ta washe baki kallon Mufeedah lash tayi tace

"Kar dai kiceman wannan ce kishiyar taki?"

  Tab'e baki tayi tace 

"Itace"

Dariya Lash tayi tace

"Bakida kishiya wannan ay bata da maraba da mai aiki"

Shewa sukayi suka tab'a

  Lash takai dubanta ga Ramlah tace

"Hajiya ina fatan kin shirya kishi damu danmu kishi damu sai mutum ya shirya..." 

Tana fad'an haka suka wurga mata harara suka fita..

 Jiki sanyaye Ramlah taja jiki ta koma kitchen..

  Suna fita ta kalli Ramlah tace

"Amma matar nan akwai kyau"

Tab'e baki tayi tace

"Tana da kyau"

 Dariya tayi tace

"Dakyar na iya kallonta na gaya mata magana dan kwarjini taman wallahi"

  Harararta tayi tace

"Malama ki wuce dan ki dawo da wuri"

  sallama ta mata tayi gaba....

             ********

  Tafiya takeyi ciki k'urmin daji ba gida gaba ba gida baya sai da tayi tafiya sosai kana ta iso bakin wata bukka, ita kad'ai ce bukka a wajen.

 "Gafaranku dai"

Abinda tace kenan

  Shigo daga ciki, shiga tayi tana kirari, takai minti goma da shiga kana ya mata izinin zama, waje tasamu ta zauna..

  "Allah ya taimaki boka"

Mutum ne bak'ik'irin idanuwanshi jajaye ya daka mata tsawa yace

"Ba'a kira mana Allah anan ko kin mance dokar wannan bukar ne?"

 Jiki na kyarma tace 

"Aiman afuwa boka na mance ne"

 Kai ya d'aga mata batare da yayi magana ba..

 "Mike tafe dake?"

Zama ta gyara tace 

"Boka ba zuwan kaina bane ba zuwan Mufeedah ne.."

Hak'oranshi ya washe wanda sukayi jawur yace

 "Amarya zakice man lafiya take ko?"

Dariya tayi tace

"Lafiya lau"

Dama boka so take... ta kwashe komai ta gaya mashi...

  Wata irin dariya ya kwashe da ita yace

"Aikinta mai sauk'i ne ita kuma Haneefa ba zamu kasheta yanzu ba sai sun d'and'ani wahalar rayuwa kana daga baya zamu kaudasu d'aya bayan d'aya.."

 Baki Lash ta lashe tace

"Godiya muke boka"

  Wani magani ya d'auko a wata kwarya yace 

"Kice mata wannan ta wanke gabanta dashi idan ta wanke ruwan ta mashi girki ta tabbata daidai shi tayi girkin dan ba'a buk'atar wani yaci girkin sai shi idan tayi yanda mukace to sai yanda tayi dashi, wata kwarya ya d'auko yace wannan kuma kwaryan ta saka a k'ark'ashin gadonshi to zai tsani Matarshi da yaranshi zaiji bai san ganinsu.."

  Godiya Lash ta mashi ta karb'a ta aje mashi rapper 1k guda yana gani ya washe jajawur d'in hak'oranshi..

  Sallama ta mashi ta fita, saida tayi tafiyar awa guda kana ta iso bakin titi mai napep ta tsaida tace 

 "Katsina zaka kaini"

Kallonta yayi yace

"Hajiya katsina fa maimakon ki hau mota ko kin manta daga inda kike in kin manta bari na tuna maki charanci kike kuma da alama daga k'auyen d'an turu kike"

  Dariya tayi tace

"Ka kaini in baka dubu biyar.."

Baki ya washe yace

"Shigo muje.."

Shiga tayi suka tafi....

  Sai da yahau titi sosai ya juyo ya kalleta yace

"Amma malama mi yakaiki k'auyen d'an turu? Nidai a sanina babu gidaje sai bukkar boka dumbus kuma da alamu ke macen arzik'i ce nayi mamakin dana ganki kin fito daga k'auyen"

 Tsawa ta daka mashi tace

"Idan tambayoyi zakaman ajeni in sami wata.."

"Allah ya baki hak'uri"

Abinda yace kenan yaja bakinshi yayi shiru....Ana wata ga wata shin Mufeedah zatayi nasaran raba Ramlah da farin cikinta? Dagaske Imran zai juyama Ramlah baya da yaran da yafiso a rayuwa? Ya makomar Mufeedah daga k'arshe? Ku cigaba da yar mutan katsinawa dan jin amsoshinku...Don't forget to vote comments nd share tnx y'all

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI 

         

       Rubutawa

           Yar_ficika 


®NWA 


Wattpad @yar_ficika

Blog

Phirdauceejeebo.blogspot.comBABI NA GOMA


Wannan BABIN na kune yan DANDALIN FEEDOH DEEDOH nagode da yanda kuke ban hadin kai akan MKA comments d'inku na k'araman kwarin guiwa Allah yabarmu tare♥ #1love😍 #team MKA😘  Yamma lik'is ta iso gidan Mufeedah, da sallama ta shiga gidan ganin ba kowa parlour ya bata damar fad'awa d'akin Mufeedah, fad'awa tayi kan gado tana 

"Wash" 

dai dai Mufeedah ta fito daga wani d'an d'aki dake cikin d'akinta. Kayan jikinta ya bayyanar da sururta doguwa ce gaban nan nata ba komai sai tudun bra hips d'inma babushi bak'a ce amma ba sosai ba kan nan nata yasha attach tsaye dai take kamar sanda. Nikaina dana kalleta sai danayi mamakin mai mata kamar Ramlah mi zaiyi da Mufeedah..

  Dasauri ta k'araso wajen Lash tana washe baki, itama Lash d'in dariyar takeyi cikin k'aguwa Mufeedah tace

"Anyi nasara?"

  Dariya tayi tace

"Aikin san kullum muke da sa'a.."

  Tana fad'an haka suka tab'a tare da sakin dariyar yan bariki..

  Mik'a mata magungunan tayi ta mata bayani yanda boka yace, kallonta tayi tace

"Mufeedah abubuwanan suna da had'ari sai kin kiyaye dan karmu samu matsala."

  Dariya tayi tace

"Kinsan yanda nake bin dokar boka ko ta maifiyata banabi so karki sa damuwa ba wata matsalar da za'a samu saboda ni kullum mai sa'a ce..."

  Jinjina kai Lash tayi dan tasan makircin Mufeedah duk abinda tasa gaba to sai tayi nasara, a kullum ita mainasarace...

  Jakarta ta d'auka tace

"Bari na wuce gida kar dare yayi.."

  Tare suka fito, parlour sukaci karo da Imran na shigowa daidai Ramlah na jera abinci a dainning, dasauri Mufeedah ta isa wajen Ramlah tace

"Haba Anty da kin barshi na k'arasa jerawa ai bak'uwar ba dad'ewa zatayi ba"

Mamakine ya kama Ramlah 

"Tabbas duk inda Makira takai yarinyar nan takai."

A zahiri kuma tace

"Kibarshi na k'arasa kinsan ke amarya ce.."

  Dariya sukayi baki d'aya dai dai Imran na k'arasowa wajensu tare da washe baki ganin yanda Mufeedah kesan Ramlah...

  "Sannunku da gida"

"Yauwa suka amsa dashi"

 Kitchen ta nufa da sauri ta d'auko sauran warmers d'in, ta aje a dainning, binta da ido Ramlah tayi tana mamakin yanda take rawan kai kamar ba ita ke gasa mata magana ba, da kyar tace

"K'awarki na jiranki"

 Juyawa tayi inda Lash ke tsaye ta kashe mata ido, Lash kuwa ta daskare dan mamaki tace

"Harna manta da ita"

Tana fad'an haka ta k'arasa wajen Lash taja hannunta suka fita....

 Suna fita Lash ta kalleta 

"Mihakan ke nufi? Nasan dai wani sabon abun ne zakiyi"

Dariya Mufeedah tayi tace

"Dad'ina dake saurin ganewa dole sai na had'a da kissa da MAKIRCI ai asiri kad'ai bazaiyi tasiri ba dole sai na had'a danawa to gaban idan mijin zan nuna nafisan su akaina kinga bayan shi in gasasu yanda raina keso ko fad'a mai tayi bazai yarda ba..."

 Dariya Lash tayi tace

"Nikaina ina tsoronki"

Tafawa sukayi ta mata sallama ta tafi ita kuma ta koma cikin gida....

  Tana shiga parlour idanta yakai kansu, rungume take jikinshi yana shafa kanta, wani bak'in ciki ya taso mata amma ba yanda zatayi

 "Nan da wasu yan lokaci zan maidaki abin tausai zai tsaneki fiye da komai a duniya..."

 K'arasawa tayi ciki da sallama, saurin sakin Ramlah yayi ya juyo yana mata murmushi, itama murmushin takeyi ta isa wajen Ramlah tace

"Anty baki buk'atar komai?"

 Daskarewa Ramlah tayi da kyar ta tattaro kalaman bakinta ta had'a tace

"Bani buk'atar komai nagode"...

 Imran ya kalli matanshi yace 

"Nagode sosai yanda kuka had'a kanku Allah ya maku albarka"

"Amin"

Mufeedah ta amsa, ita dai Ramlah ta zama yar kallo..

 "Kuje kuyi sallah nima masallaci zan wuce"

 Yana fad'an haka ya juya ya fita 

  Kallonta Mufeedah tayi tace

"Kin kusa raina kanki a gidannan sai na zame maki k'adangaren bakin tulu" 

Tana fad'an haka ta buga mata tsaki ta wuce d'akinta....

  Kai Ramlah ta girgiza tace

"Allah ya fiki"

Tana fad'an haka ta shige d'akin yaranta...

  Tana shiga suka taso da gudu sukayi kanta, rungumesu tayi wasu kwalla na gangaro mata, Haneefa na kallonta, sallah da aka kira ne yasa ta sakesu tace

"Kuje kuyi alwalla kubi Daddynku masallaci Haneefa ke kuma ki tashi kije kiyi alwalla..."

 Ba musu suka tashi sukayi alwalla suka fita dan tafiya masallaci..

 Juyawa tayi zata nufi d'akinta 

"Ammi"

Haneefa ta kirata

  Juyowa tayo da fara'arta tace

"Yadai princess?"

  Takowa tayi ta k'araso wajenta tace

"Ammi kina cikin damuwa ki dage da adua in shaa Allah, Allah na tare damu.."

  Duk'awa tayi ta rik'o hannunta tace

"Ina alfahari da samunki a matsayin d'iyata Allah ya maki albarka.."

"Amin"

  Tace ta wuce ta tada sallah..

  D'akinta ta nufa tana shiga ta fad'a toilet tayo alwala tana fitowa ta tada sallah tana idawa ta d'aga hannunta sama tana adu'a bata tashi daga kan carpet ba sai da tayi sallah isha kana ta tashi ta ninnike abin sallah...

             *******

  Parlour suka had'u gaba d'aya suka nufi dainning table suka zauna su Haneef suka gaida ko da kyar Haneefa ta iya gaida Mufeedah, Ramlah ta mik'e zata zuba masu abinci dasauri Mufeedah ta amshe serving spoon d'in tace

"Anty gani zakiyi aiki"

 Binta da ido Ramlah tayi dan yanzu abun nata ya daina bata mamaki, yak'e tayi ta zauna, da kanta ta zuzuba masu kowa ta aje mashi gabanshi, abinci suka faraci bamai magana har saida suka gama, Haneefa ta mik'e zata wuce, hannunta ya rik'e yace

"Princess anya kina da lafiya?"

  Yak'e tayi tace

"Daddy lafiya lau"

 Murmushi yayi ya saketa...

 "Amm Anty kibari gobe zanma Baban Haneefa abinci da kaina so ke sai kiyi namu kar abun ya maki yawa.."

  Bata kawo komai a ranta ba tace

"Shikenan Allah ya kaimu.."

  Wani farin ciki ne ya lullubeta na samun nasara..

  Kallonshi tayi tace

"Honey bari naje nayi wanka kafin ka shigo"

 Tana kaiwa nan ta tashi tabar parlour'n..

  Dasauri ta isa d'akinta ta d'auki kwarya ta d'an corridor tabi ta shiga d'akinshi, saida ta saka key a k'ofar kana ta dawo ta d'aga katifan da kyar ta iya d'agata ta saka kwaryan ta mai da katifan, ta gyara gadon kamar ba'ayi komai ba, ta lallab'a ta bud'e k'ofan kana ta wuce d'akinta tsalle ta buga na samun nasara tace

  "Saura kaci abincin gobe.."

  Juyi tayi tace

"Kullum ni mainasara ce kuma zan cigaba dayin nasara, Ramlah namaki alk'awarin tarwatsa farin cikinki kuma nasan nike da nasara..."

 Haka ta dunga surutanta tana murna ganin ta kusa nasara....
Vote

Comments 

Nd

Share

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI 

         

       Rubutawa

           Yar_ficika 


®NWA 


Wattpad @yar_ficika

Blog

Phirdauceejeebo.blogspot.comBABI NA SHA D'AYA


  K'arfe bakwai ta tashi ta nufi d'akinta, tana shiga ta wuce inda ta aje maganin d'auka tayi ta nufi toilet wanke gabanta tayi tas kana ta d'auki ruwan maganin ta nufi kitchen dashi, tana isa k'ofar kitchen taci karo da Ramlah na shirya breakfast, wani takaici taji, komawa tayi d'akinta ta adana ruwan, saida ta tabbatar Ramlah ta gama ta koma wajen yaranta dan suyi shirin makaranta, da sauri ta nufi kitchen ta d'ora taliya dan danan ta had'a taliya, tuni kitchen ya d'auki k'amshi dan ta saka kayan k'amshi sosai yanda bazai gane akwai wani abu....

  Mintuna kad'an ta juye taliyan cikin warmers ta ta had'a mashi tea da yaji kayan k'amshi shima tea sai data zuba ruwan tsarkinta, komai na mutum guda tayi kana ta kwasa ta nufi d'akinshi dashi tana mai neman Allah ya bata nasara yaci abincin nan...


  Tana shiga d'aki ta tar da yana bacci, a hankali ta yaye blanket d'in daya rufa, iska take hura mashi a gashin kanshi har sai daya bud'e idonshi, idonshi bisa fuskarta tana sakar mashi murmushi, shima murmushin yake mata, hannu ta mik'a mashi ba musu ya mik'o mata ta kamashi, bakin toilet ta kaishi ta kalleshi tace 

"Kayi wanka kazo ga breakfast d'inka yau girkina zakaci.."

  Tana magana tana kashe mashi ido..

 "Angama amaryata"

Ya fad'a yana dariya...


      Fitowa yayi yana tsane jikinshi da towel k'arasowa tayi ta k'arba ta tayashi gogewa, da taimakonta Imran ya shirya, yana gama shiri tace

"Ga abinci"

  Kallonta yayi da mamaki yace

"Abinci kuma? Ayba nan nake cin abinci ba"

 "Nasani amma yau nan zakaci"

Ta fad'a tana b'ata rai, babu yanda ya iya illa yabi umurninta...

  Zama yayi ta zuba mashi taliya, ta had'a mashi tea ta mik'a mashi gabanshi, ba musu ya faracin abincin yanaci yana zuba mata santi saida ya cinye tas ya sha tea, wani irin farin ciki Mufeedah take ciki wanda bata iya misaltashi...

  Yana gama cin abinci yaji kanshi yayi nauyi jikinshi duk ya mutu kallonta yayi yace

"Bari nad'an kwanta"

Kafin ta amsashi har ya fad'a kan gado..


  Mik'ewa tayi tazo wajenshi ta tab'ashi amma ina yayi nisa, tsalle tayi tana rawa tace

"Yau zan fara aikina da alama maganin nan yayi aiki.."

               *******

  K'arfe shida ya tashi ji yake jikinshi duk ya mashi wani iri toilet ya shiga yayi wanka ya d'auro alwalla, zuwa yayi ya tada sallah sai da yayi azahar kana ya maida la'asar, shigowa tayi cikin k'ana nan kaya riga da wando (kamar sanda ta sa wando lolzz), yana ganinta yaji duk k'uncin da yake ciki ya yaye, ware mata hannu yayi da yar kisisinarta ta isa wajenshi rungumeta yayi tare da a jiyar zuciya..

"Shine baki tadani nayi sallah ba"

Cewar Imran yana d'ago Mufeedah daga k'irjinshi

  Fari ta mashi da ido tace

"Kasan idan mutum na bacci ba'a ta dashi"

 (Niko nace inji wane malamin ya gaya mata haka ai sallah na gaba da komai..)

 "Bari naje naga Ahmad"

Shagwab'ewa tayi tace

"Nidai ba inda zaka"

  Jawota yayi yace

"Ba dad'ewa zanyi ba yanzu zan dawo kinji my babe.."

 D'aga mashi kai tayi...


 A tare suka fito a parlour suka had'u dasu Ramlah ji yayi gabanshi ya fad'i wani irin tsanarta yaji da yaran kwatakwata bai san ganinsu, d'auke kanshi yayi daga inda suke..

"Sannu da fitowa"

 Cewar Ramlah

Shiru yayi bai tanka ba kuma bai kalli inda suke ba, murmushi Mufeedah tayi tace

"Baby ana magana fa"

Naji abinda yace kenan

  Mukhtar ne ya ruga wajenshi ya rungume shi yana Daddy, jefar dashi yayi kan carpet har saida kanshi ya fashe yana huci...

  Dasauri Ramlah ta k'araso tace

"Imran lafiyarka kuwa?"

Harara ya wurga mata yace

"Natsaneku dagake har shegun yaranki, ki gaya masu su daina shiga harkata kuma kada ubanda ya k'ara kirana Daddy Wallahi na tsani ganinku gidannan ji nake kamar in bud'e idona inga kun mutu.."

  Wani irin kuka Ramlah ta saki tare da rungume Mukhtar shima kukan yake, ganin haka yasa Haneef fashewa da kuka..


  K'arasowa Haneefa tayi tace

"Daddy mikake shirinyi? Kamanta suwaye mu? Yaranka ne dakafi k'auna sai kuma Ammi da duk duniya kake cewa baka da kamart...."

 Tsawar daya daka matane yasa sauran maganar tamak'ale..

"Nace na tsaneku bansan ganinku ko bakiji bane ba?"

  Gabanshi Mufeedah ta k'araso tace 

"Calm down my baby abun duk bai kai haka ba, kayi hak'uri inma wani laifin suka maka kayafe masu..."

 Hararta yayi yaja hannunta suka fita suka bar parlour'n, rungume yaranta Ramlah tayi tana kuka suma kukan sukeyi banda Haneefa da idonta yayi ja kamar garwashi saboda tsananin b'acin rai....


Dont forget to Vote Comments nd share

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI 

         

       Rubutawa

           Yar_ficika 


®NWA 


Wattpad @yar_ficika

Blog

Phirdauceejeebo.blogspot.comBABI NA SHA BIYUThis page is for you Miemie waziri thnx for d love care support nd courage♥ #1love #MKA  Hannunta ta fizge tace

"Miye haka kakeyi? Mi suka maka idan wani laifin suka maka ai ba haka zaka hukun tasu ba ji yanda ka fashema Mukhtar kai.."

 Baki ya tab'e yace

"Ni basuyi man komai ba kawai natsanesu bank'i in bud'e idona inga basu gidannan ba.."


"To ka saketa mana basai su barma gidan ba"

 Ido ya zaro yace

"Ban iya sakinta bansan miyasa ba amma bansan ganinta.."


 "Ina da aiki gabana"

Abinda ta fad'a a ranta kenan, murmushi ta mashi tace 

"Ya kamata ka tafi kada ya dinga jiranka.."

  Ba musu ya mata peck ya juya ya tafi, ita kuma ta koma cikin gida...

  Shiga tayi tana wak'e wak'e wuce su tayi takai k'ofar d'akinta ta dawo duk'awa tayi gaban Ramlah

"Dama nace zaki raina kanki kad'an kika gani daga aikin Mufeedah yar ruwan zafi kinga wannan gidan da kike tak'ama dashi sai kin fita kin barshi.."

 Tana fad'an haka ta mik'e tana dariyar mugunta..


  "Ke baki isa ki mana abinda Allah bai mana ba kuma gidan da kike tak'ama zamu bari ke zaki barshi da izinin Allah muda Allah muka dogara kuma shi zai mana maganinki cikin ruwan sanyi.."

Haneefa ce ke magana tana huci...

 Juyowa tayi ta kalleta tace

" kina burgeni saboda kwazonki amma kwanannan zanyi maganinki dan na lura kece matsalata.."

 D'agowa Ramlah tayi ta kalleta sannan tayi magana

"Baki isa ki mata abinda Allah bai mata ba da Allah muka dogara kuma yana tare damu..."

 Dariya ta kwashe da ita tace

"Zan gani ni daku wanda zaiyi nasara"

 Tana kaiwa nan ta shige d'akinta...


  Rungume yaranta tayi ta fashe da kuka..

"Ammi yanzu ba lokacin kuka baneba lokacin da zaki kwaci gidanki ne da martabarki idan kikace kuka zakiyi bazai amfana mana komai ba muna gani zatayi galaba akanmu kamar yanda ta fad'a.."

  Tana kaiwa nan ta mik'e ta wuce d'akin Amminta..

 "Tabbas maganar Haneefa gaskiya ne yanzu ba lokacin da zanyi kuka baneba lokacin da zan dawo da martaban gidana da mijina ne hannuna amma taya?" 

Duk a zuciya take wannan tunanin..

 Haneefa ce ta fito da first aid box ta gyarama Mukhtar inda yaji ciwo, ta kwashe kayan da tayi amfani dasu ta maida d'akin Ammi..


 Tana shiga d'aki ta dinga zagaye zagaye

"Dole nad'auki mataki kan Haneefa dan zata kawoman cikas.."

  Wayarta ta jawo ta kira Lash, saida ta kusa tsinkewa kana ta d'auka

"Hello Lash akwai matsala"

 Banji mitace mata ba tace

  "Inasan ki koma wajen Boka Dumbus a kauda man da Haneefa daga duniya saboda tana kawoman matsala yariyar na tsaneta kawai ya kasheta..."

 Tana gama fad'ar haka ta katse wayar ta cigaba da zagaye d'aki burinta kawai taga Haneefa tabar duniya to komi zaizo mata dasauki...

            ******

 Rungume take da Mukhtar wanda yayi baccin wahala gefe Haneef ne shima yayi bacci, zuwa Haneefa tayi ta kwashesu ta kaisu d'aki ta kwantar dasu, kitchen taje ta had'oma Ramlah tea ta kawo mata tace

"Ammi gashi kisha"

  Karb'a tayi ta mata yak'en da yafi kuka ciwo

"Nagode Allah ya maki albarka ya rabaku da sharrin mutum da Aljan Allah ya karemanku.."

"Amin"

 Haneefa ta amsa


 Kafa cup d'in tayi bata ajeba saida ta shanye tayi hamdala, juyowa tayi wajen Haneefa ta rik'e hannunta tace

"Haneefa kidaina ma Mufeedah rashin kunya ina tsoron karta maki wani abu kinji kalamanta bansan yanda ta rabamu da Imran ta maki illa kema dan Allah kidaina shiga harkanta duk abinda zatayi kidaina tanka mata ina tsoron ta illatamanke bansan ta rabani dake kune farin cikina yanzu.."

 Kukan da yaci k'arfinta ne yafito. Dakyar Haneefa ta lallasheta tayi shiru..


  "Ammi kidaina sakawa a ranki zataman wani abu Wallahi babu abinda zataman duk abinda kika ga ya sameni to dama can Allah ya rubuta zai sameni, kedai ki cigaba da mana adu'a saboda adu'arki takobi ce ga duk mai binmu da sharri.."

  Rungumota Ramlah tayi ta k'ank'ameta kamar wani zai kwace mata ita, sabon kuka ta fashe dashi mai tsananin damuwa, duk dauriyan Haneefa saida tayi kuka itama sun dad'e haka kana Ramlah ta saketa ta tashi ta nufi d'akinta...


 Tana fita ta had'u da Imran yadawo sauri yayi ya k'auda kanshi.

"Sannu da zuwa"

 Shiru yayi ya cigaba da tafiya, sauri tayi tasha gabanshi tace

"Dan Allah idan laifi na maka kayi hak'uri kada ka hukunta ni da abinda bansan na aikata ba kuma laifina bai kamata ya shafi yaranka ba kaga yanda kajima Mukhtar ciwo yaro ne baisan komai ba.."

 Hannu ya d'aga mata

"Ba abinda kuka man kawai na tsaneku da zaki taimaka keda yaranki kun fita harkana ko gaidani kada ku sakeyi Wallahi na tsani ganinku.."

 Yana fad'an haka ya rab'ata ya wuce, duk'ewa tayi k'asa tana kuka ganin kukan ba maganin da zai mata yasa taja ka'afafuwanta ta wuce d'akinta...


 Duk abinda yafaru kan idon Mufeedah murmushi tayi mai k'unshe da ma'ana kala kala kafin ta koma d'aki...Vote

Comments 

Nd 

Share

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI 

         

       Rubutawa

           Yar_ficika 


®NWA 


Wattpad @yar_ficika

Blog

Phirdauceejeebo.blogspot.comBABI NA SHA HUD'U


  Dariya yayi mai isarshi yace

"Wannan aikin mai sauki ne amma bari na duba nagani.."

  Dariya tayi dan dama tasan duk idan tazo nan to buk'atarta ko wace iri ce zata biya...

  Duk'ufa yayi yana bincike tunda ya duk'a bai d'ago ba sai k'asa da yake bugu yakai kusan minti talatin yana abu guda duk ya had'a zufa...


  D'agowa yayi dasauri ya kalleta yace 

"Akwai matsala"

 Dubanshi tayi da alamar firgici a ranta tace

"Bangane mi kake fad'a ba.."


  Zama ya gyara yace

"Gaskiya kashe Haneefa zaiyi matuk'ar wahala saboda duk abinda nayi sai inga wani haske na binta kiyi hak'uri kasheta zai iya zama barazana akanmu...."

  Shiru tayi a ranta tana cewa

"Wannan wace irin yarinya ce haka?"

  A sanyaye ta kalleshi tace

"To raba auren Ramlah da Imran fa?"

  K'asa ya cigaba da bugawa dasauri ya kalleta yace

"Wannan wane irin aiki ne kika kawoman? To bari kiji auren Ramlah da Imran bazan iya kasheshi ba saboda tafimu bata bacci ita da d'iyarta suna kaima Allah kukansu idan har na matsa to nidake zamu rasa ranmu na gaya maki..."

  Cikin tsananin firgici tace

"Katai makeni kasan dakai na dogara ko nawane zan biyaka indai buk'atata zata biya.."


 Tsawar daya daka matane saida ta kusa sakin fitsari yace

"Bakiji mi nace maki ba? Idan muka matsa zamu iya rasa ranmu, basu barci kullum suna kaima Allah kukansu, shima Imran abinda yasa mukayi galaba akan shi saboda bai damu dayin azkar ba dan haka tashi kiban wuri ni inasan rayuwata...."

  Kallonshi tayi da b'acin rai tace

"Kaban kunya ashe akwai abinda zai gagareka to in kai ya gagareka ni bazai gagareni ba namaka alk'awarin saina kashe Haneefa da hannuna na raba auren Imran da Ramlah..."

  Tana kaiwa nan ta mik'e ta fita rai b'ace....

               ******

 Yamma lik'is ta shigo gidan, bata tarda kowa parlour ba dan haka d'akinta ta nufa tana shiga tai wurgi da jikar hannunta ta fad'a kan gado, bata damu da tayi sallah ba, haka ta dinga juyi kan gado tana neman mafita dan gaskiya barin Haneefa a duniya ba babbar barazana bace ba a rayuwata...


 Aiki suke ita da Haneefa a kitchen, dan yau zata karb'i girki suna aiki suna fira..

"Ammi mi zamu dafa ne yau?"

 Murmushi tayi tace

"Favourite food din babanki"

  Tab'e baki tayi tace

"Jallof rice ryt?"

Murmushi tayi tace

"Eh Mamana"


  "D'auko kaza a fridge ki gyara kiyi pepper chicken"

 Kazar ta d'auko ta wanke tasa a wuta, suna girki suna fira, dama kullum idan Haneefa tana gida to tare suke shiga kitchen dan tana koya mata abinci...

  Guava juice suka had'a dayake fav drink din Imran d'in kenan, kafin kice mi gidan ya d'auki k'amshi, suna gamawa Haneefa ta jera komai a dainning table, shafa kanta Ramlah tayi tace

"Allah ya maki albarka"

"Amin"

  Ta bata amsa...

   "Bari naje nayi wanka"

Cewar Ramlah tana fad'an haka ta nufi d'akinta itama Haneefa d'akinsu ta nufa....


  K'arfe takwas daidai ya shigo gida da sallama, tashi tayi da sauri taje ta tareshi da fara'a shiko ganinta ji yayi kamar an buga mashi guduma a k'irji...

"Sannu da zuwa Hayatee"

  Yauwa ya fad'a kanshi gefe, jakar hannunshi zata karb'a ya dakatar da ita..

 "Bawai na hanaki shiga harkata ba?"

"Kayi hak'uri" 

  Cewar Ramlah


  "Mizaka farayi wanka ko abinci?"

 Tsawa ya daka mata yace

"Waike dak'ik'iyar inace? Bakiji mi nace ba? Nace maki natsaneki bansan ganinki.."


  "Kayi hak'uri naga yau aiki nane"

 "Eh aikinki ne amma ki sani bazanci abincin naki ba..."


  Zuciyarta wata k'una takeyi, daurewa takeyi take magana dan gab take da fashewa da kuka..

  Duk'awa tayi ta rik'e k'afafuwanshi tace

"Dan Allah idan laifi na maka kayi hak'uri bazan iya d'aukar hukuncin daka yanke akai na ba yaman tsauri Imran.."

 Tana fad'an haka ta fashe da kuka..

  Hankad'eta yayi sai da kanta ya bugi tiles d'in parlour'n yace

"Ramlah ki fita harkana natsaneki bansan ganinki..."

  Yana fad'an haka ya rab'ata ya wuce, ya nufi wajen Mufeedah wadda tun da Imran ya dawo ta fito, yana isowa wajenta ya rungumeta yace 

"I miss you my babe"

  Rungumeshi tayi tace

"Miss you more honey"


 "Mi kika dafaman? Yunwa nakeji"

  Tab'e baki tayi tace

"Ba abinda na dafa dan gaskiya bazan juri yin girki ba dan bashi nazoyi ba..."


  Rungumeta yayi yace

"My babe duk yanda kikeso haka za'ayi, yanzu muje ki shirya muje muci abinci a restaurant .."


  Da tsallenta ta shiga d'aki, binta yayi d'akin, can suka fito cikin shirin riga da wando, Mufeedah ta zubo gashin attach d'inta kai ko d'an kwalli, rab'a Ramlah sukayi suka wuce suna rungume da juna..

  Har sun wuce Mufeedah ta dawo ta duk'a gabanta...

"Yakamata ki sassauta ma kanki ki kwashe kayanki kibar gidannan dan mai gidan yatsaneki.."

 Murmushi Ramlah tayi tace

"Burinki kenan ko? To bazaki tab'a yin nasara ba in shaa Allah.."

  Tana fad'an haka ta mik'e ta nufi d'akinta, k'afafuwanta Mufeedah taja tabi bayan Imran dake tsaye bakin mota yana jiranta....Don't forget to vote comments nd share

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI 

         

       Rubutawa

           Yar_ficika 


®NWA 


Wattpad @yar_ficika

Blog

Phirdauceejeebo.blogspot.comBABIN NA SHA UKU


  K'arasowa wajenshi tayi yana ganinta ya saki murmushi, rungumeta yayi ya saki ajiyar zuciya, janshi tayi ta kaishi d'aki.

"Had'aman ruwan wanka"

 Cewar Imran yana kallon Mufeedah

  Turo baki tayi tace

"Gaskiya nagaji kawai kaje ka had'a nifa bazan iya yan had'e had'en ruwan wankan nan"

 Babu yanda ya iya ya tashi ya nufi toilet...


  Fitowa yayi ko inda yake bata kalla ba sai cika take tana batsewa haka ya shirya kanshi yazo ya zauna kusa da ita

"Miyafaru ne?"

  Naga kamar kina cikin damuwa, fashewa tayi da kuka tace

"Bayan ka fita Ramlah da Haneefa suka tusani gaba suna zagi kamar ni nace ka tsanesu Ramlah harda marina ita kuma Haneefa tana cewa wai karuwace ni har ciki na zubar kana nazo na aure ka.."

  Bata k'arasaba ya tashi yana huci ya nufi d'akin Ramlah


  "Ramlah! Ramlah!! Ramlah!!"

  Kwalamata kira yakeyi kamar zai tada gidan, k'arasowa tayi dasauri tace

"Lafiya Imran?"

 Saukar mari taji a kuncinta kafin ta ankara ya k'ara kwasheta da mari sai da ta saki k'ara d'agowa tayi tace

"Imran mina maka?"

 "Aww baki masan mi kikayi ba?"

D'aga kai tayi alamar bata sani ba

"Ubanwa yace ku zagar man mata keda d'iyarki? Har d'iyarki na kiranta karuwa to sai dai idan kece karuwa"

 Dasauri ta kalli inda Mufeedah ke tsaye ta hard'e hannuwa tana murmushi, kashe mata ido Mufeedah tayi tana dariyan mugunta. Girgiza kai tayi tace

"Wallahi ba abinda mukayi mata"

"Aww k'arya zata maki lallai Ramlah kin cika annamimiya.."

 Hawaye suka kwararo mata tace

"Iya gaskiyata na fad'a maka.."

Cakumota yayi ya d'aga hannu zai k'ara marinta

  "Daddy" 

jin muryan Haneefa yasa ya kasa k'arasa marin Ramlah wanda takai k'asa sanadiyar hankad'ata da yayi...


 K'arasowa tayi inda yake tsaye yana huci, kallonshi tayi tace

"Daddy ka canja ba haka ka saba mana ba baka tab'a yima Ammi fad'a a gabanmu ba, yau gashi kan wata ta nuna Mufeedah tace ka d'auki hannu ka mareta ka jefeta da munanan kalamai akan abinda bata sani ba shin baka gudun Allah ya mata sakayya?" Wallahi Daddy Ammi bata tab'a d'aga ido ta kalli matarka ba da sunan cin fuska amma yau an gaya maka magana ba bincike ka d'aga hannu ka mareta ka aibata ta wanda kafi kowa sanin halin matarka kasan abinda zata iya, ka d'auki hannu ka mareta duk akan wannan munafukar matar taka..."

 D'agowa yayi da sauri zai kai ma Haneefa mari sai kuma ya fasa dan duk cikin yaranshi yafisan Haneefa bai san abinda zai tab'ata..

  Murmushi tayi tace

"Ni yaka mata ka mara ba Ammi ba saboda Ammi bata da laifi nike gayama matarka magana a yayinda taci fuskar mahaifiyata kuma kasan duk d'an halak bazai bari aci mutuncin mahaifiyarshi ba kuma ban tab'a kiran matarka da karuwa ba kafi kowa sanin irin tarbiyan da kuka bamu..."

 Tana fad'an haka ta d'aga Ammi dake ta hawaye suka wuce har sun kai bakin k'ofa ta saki Ammi ta juyo wajen Imran ta duk'a tace

"Daddy idan maganganun dana maka sun b'ata maka rai dan Allah kayafeman, idan wani laifi muka maka muda mahaifiyarmu dan Allah kayi hak'uri kuma da kace baka sanmu ka tsanemu Wallahi mu munasanka muna fatan kadawo Daddynmu nada mai wasa damu mai maida damuwarmu damuwarshi wanda yafi sanmu a kanshi wanda bai iya cin abinci sai muna gabanshi, juyawa tayi wajen Mufeedah tace kinyi nasara amma kijira ranan sakamako Wallahi k'arshenki bazaiyi kyau ba..."

  Tana gama fad'an haka ta mik'e takama mahaifiyarta ta kaita d'aki...


  Huci Mufeedah keyi tace

"Kanajin yanda d'iyarka ke gayaman magana amma ka kasa d'aukar mataki"

 Kallon ta yayi yace

"Bansan miyasa bazan iya bugun Haneefa ba bazan iya aibatata ba Haneefa d'iyatace bazan iya yi mata komai ba kawai dai nasan natsanesu amma bazan iya dukanta ba.."

 Harararshi tayi ta buga tsaki ta nufi d'akinta binta yayi yana kira amma bata tanka ba tana shiga ta maida k'ofa ta rufe tanaji yana magiya yana rok'onta amma tak'i kulashi....

 K'afafuwanshi yaja ya nufi d'akinshi yana zuwa ya fad'a kan gado yana juyi shi kanshi yasan akwai abinda ke damunshi amma bai sani ba haka ya dinga juyi har bacci ya d'aukeshi..


 B'an garen Haneefa kuwa suna shiga d'aki ta fad'a kan Ramlah tana kuka cikin kuka tace

"Ammi kinga abinda nake gaya maki ko? Nace maki matar nan ba matar arziki baceba amma kika kasa yarda da maganata to wallahi idan baki tashi da adua ba nan gaba gidan zata rabaki dashi kamar yanda take ikirari kinaji kina gani zata rabaki da gidanki.."

 Jawota Ramlah tayi jikinta suka cigaba da kuka saida sukayi mai isarsu kana sukayi alwalla sukazo suka fara sallah suna kaima Allah kukansu....


 Mufeedah na shiga d'aki ta saki uban kuka tace

"Yau ni Mufeedah yar ruwan zafi ake gaya ma magana ban d'auki mataki ba dole in kauda Haneefa daga duniya dan itace babbar matsalata yanzu.."

  Haka ta dinga sak'awa da warwarewa daga baya bacci yayi gaba da ita....


BAYAN KWANA UKU

 Zaune take gaban boka dumbus tana gaya mashi matsalolinta saida ta gama kaf yayi dariya ya d'ago yace

 Mufeedah amarya yanzu mi kikeso ayi masu ne?"

 Zama ta gyara tare da jin dad'in yin nasara tace

"Boka so nake ka kauda Haneefa daga duniya ita kuma Ramlah ka saka Imran ya saketa ya koreta ita da yaranta subi duniya daganan gida ya zama nawa nikadai sai yanda nayi..

  D'agowa boka dumbus yayi ya kalleta sai kuma ya fashe da wata irin dariya, wadda koni bansan ma'anarta ba...
 Wait is like some of my wattpadders basu karanta littafin nan dan basu tab'a wannan yar tauraruwar, while kullum sai na tuna maku kodai labarin baiyin dadi ne na canja wani? Dan abinda kukeso shi nakeso in kuma yana maku dadi pls show me some love, ta danna yar tauraruwar nan thnx y'all❤

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI 

         

       Rubutawa

           Yar_ficika 


®NWA 


Wattpad @yar_ficika

Blog

Phirdauceejeebo.blogspot.com


BABI NA SHA BIYARWannan page d'in na kune yan Team d'in Ramlah, Ramlah na godiya sosai da irin k'aunar da kuke mata, ana tare♥ #1love #team MKA


  Sha d'aya da rabi (11:30pm) suka shigo gida, ratsowa sukayi cikin parlour yana rungume da ita, basu lura da wanda take zaune ba jin maganar da sukayi, yasa suka tsaya..

"Sannunku da dawowa"

  Ramlah ta fad'a tare da k'arasowa gabansu

  "Yauwa"

 Mufeedah ta fad'a tare da tab'e baki shiko Imran inda take bai kalla ba sai guntun tsakin da ya saki...


  Murmushin takaici Ramlah tayi ta k'arasa gaban Imran kallonshi tayi sama da k'asa duk ya canja ba Imran d'in da tasani da bane, mai tausanta mai san ganinta cikin farin ciki mai san ganinta kusa dashi yau shine ya tsaneta ya tsani ganinta kusa dashi, wasu hawaye taji zasu zubo mata tayi saurin mai dasu tare da jin wani k'arfi da ya taso mata dan yau ko yane sai ta karb'i yancinta...

  "Lafiya kikazo gabana kikaman tsaye"

Cewar Imran yana cika ya batsewa

  D'agowa tayi ta kalleshi tace

"Yanzu abinda kayi ka kyauta? Baka gudun Allah yaman sakayya ko ka manta yau aiki nane? Ka d'auketa kafita da ita mikake nufi da hakan? Abinci na maka amma ko inda yake baka kalla ba sai jifana da kayi da k'ana nan maganganu dami wannan kucakar tafini? Wallahi bata fini da komai ba ka kalleta ka kalleni wallahi nafita komai dubi kanta kagani gashin doki ne fa bisa kanta"

 D'an kwalinta ta warware ta girgiza kanta gashin ta ya zubo har gadon baya juyi tayi tace

"Ka kalleni ka kalleta dami ta fini, ko baka fad'a ba nasan kasan nafita da komai..."

 Tsaye yayi ya daskare ya kasa koda motsa hannunshi ne...


 Ihu Mufeedah ta saki tayi kan Ramlah, d'aga hannu tayi zata mareta rik'e hannun tayi tace

"Kada ki soma gigin wannan mummunan hannun naki zai tab'a fuskata, duk abinda zai man zan d'auka saboda miji nane Aljanna nake nema wajenshi amma ke baki isa kice zaki d'ora hannunki kaina ba duk randa ko kikayi gigin aikata haka wallahi sai kinyi danasani..."

  Tana gama fad'an haka ta jefar da hannun Mufeedah....


 Kallonshi tayi sama da k'asa tace

"Ka guji had'uwarka da Allah duk randa hakkina dana yaranka ya tashi kamaka wallahi sai ka tsani kanka..."

  Tana fad'in haka tayi gaba, ji tayi ya fizgota da k'arfi sai da ta fad'a k'irjinshi....


 "Ubanwa kike gayama magana?"

D'agowa tayi ta kalleshi tace

"Ba magana na gaya makaba na tunatar da kaine dan naga kamar ka manta miye adalci shiyasa nake tunatar da kai dan kasan mi kake ciki tun kafin lokaci ya k'ure ma..."

 D'aga hannu yayi zai mareta, da sauri ta kalleshi tace

"Kada kasake wannan kuskuren na cewa zaka mareni, kada kaga ka mareni ban cema komai ba amma duk randa ka sake wannan mistake d'in sai ka gane kurenka.."

Tana fad'in haka ta fizge tayi d'akin yaranta.....


  Ihu Mufeedah keyi tana zagin Ramlah ita ko bata juyo ba bare tasan da ita take..

  Tsaye yayi kamar an dasa shi mamaki cike da ranshi tun da yake da Ramlah bata tab'a mashi gardama ba amma yau gashi ta tsaya gabanshi ta k'are mashi cin mutunci....


  Harara Mufeedah ta watsa mashi tace

"Burinka ya cika matarka taman cin mutunci amma ka kasa d'aukar mataki"

 "Kiyi hak'uri baby zanyi maganinta"

 Tsawa ta daka mashi tace

"Rufe man baki kafin ka d'auki mataki ni zan d'auka.."

  Tana fad'an haka ta ruga d'akinta binta yayi yana kira kafin ya k'arasa ta shige d'akin tare da rufe k'ofar ba yanda ya iya dole ya juya ya nufi d'akinshi cike da k'unar rai....


 Tana shiga d'akin yaranta, ganin su kwance suna bacci, hawayen da suka gangaro mata ta goge, adu'a ta masu kana ta juya ta nufi d'akinta tana kai bakin k'ofa..

"Ammi"

  Dasauri ta juyo ganin Haneefa da alamun ba bacci takeyi ba..

  Dawowa tayi tace

"Miya hanaki bacci?"


  "Taya zanyi bacci iyayena na cikin wani hali"

  "Amma Haneefa kinsan fa dare yayi 12 fa kuma gobe kuna da makaranta"

  Murmushi tayi tace

"Nasani Ammi, a yanzu ne ya kamata mukaima Allah kukanmu ba mu kwanta muna bacci ba.."

 D'aga kanta tayi dan tasan gaskiya d'iyarta ta fad'a


  Mik'ewa Haneefa tayi ta nufi toilet tana kai bakin kewaye ta juyo ta dubi Ramlah tace

"Ammi ki tashi kije ki gana da mahaliccinmu kinsan irin wannan lokacin da kanshi yake saukowa yana cewa ina masu neman biyan buk'ata in biya masu..."

  Tana fad'in haka ta shige ban d'aki, kwarin guiwa Ramlah taji ta tashi ta nufi d'akinta tana shiga itama Alwalla tayi tazo ta tada sallah...Hmmmmm in yan team d'in Ramlah nasan kunji dad'i akan yanda tayi k'ok'arin karb'an yancinta... dan haka one word about this chappy thnx y'all♥Don't forget to vote comments nd share it really means a lot to me Nagode #ana tare #Team MKA

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI 

         

       Rubutawa

           Yar_ficika 


®NWA 


Wattpad @yar_ficika

Blog

Phirdauceejeebo.blogspot.com


BABI NA SHA SHIDA


 K'arfe bakwai dai dai tagama shirya yaranta suka mata sallama suka wuce school....

 D'akinta ta shige tana shiga ta wuce toilet ta dad'e tana wanka kana ta fito...

 Tsintar kanta tayi da sha'awar yin kwalliya ta b'ata lokaci wajen yin kwalliya tana gamawa ta wuce wardrobe, red super ta d'auko doguwar riga, ta saka rigar d'is ta zauna jikinta ta kafa d'aurin d'an kwali kai kace gwargwaro ne ta nad'a, feshe jikinta tayi da turararuka kala kala, ga sanyin AC, sai ya bada wani k'amshi mai sanyaya zuciya....

 Kanta ta kalla a madubi murmushi ta saki wanda ita kanta tasan tayi kyau, (Nikaina sai da na firgita ganin kyan da tayi sai kace wata balaraba...), parlour ta nufa tana isa ta zauna kan 1seater ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya tana kallon MBC Bollywood....  K'arfe tara ya fito cikin shirin shi na tafiya office dai dai Mufeedah itama ta fito daga d'akinta murmushi ya sakar mata yace

"Good morning baby"

  Inda yake bata kalla ba bare yasa ran zata amsa..

Yana d'agowa suka had'a ido da Ramlah, murmushi ta sakar mashi kauda kanshi yayi amma a ranshi yana yaba kyan da tayi

"Ina kwana"

  Muryanta ta katse mashi tunanin da yakeyi

 A tak'aice ya bata amsa da

"Lafiya"


  Kallonta Mufeedah tayi, saida ta kusa fad'uwa ganin irin kyan da Ramlah tayi, kanta ta duba gani tayi Ramlah tafita komai ta mata tazara nesa ba kusa ba ji tayi kamar ta d'aura hannu bisa kai tasa ihu saboda takaici, harara ta bankama Ramlah tayi tsoki ta koma d'akinta...

"Your breakfast is ready"

 Ya tsinkayo muryan Ramlah, bai tanka mata ba ya nufi dainning table, k'arasawa tayi dan tayi serving d'inshi, soyayyen dankali ne sai tea ta had'a mashi wanda yasha kayan yaji..

 Tura mashi tayi gabanshi tace

"Ranka yadade gashi nan nasan kayi missing abinci na."

 Tana fad'an haka ta kashe mashi ido tare da sakin murmushi, harara ya wurga mata tare da tsoki ya fara cin abinci, yana gamawa yayi hamdala, ya mik'e ya nufi d'akin Mufeefah...


 Da sallama ya shiga d'akin, zaune take bakin gado tayi tagumi, bata amsa ba haka ba kuma ta d'ago ba..

 Takowa yayi yazo gabanta hannunta ya cire, kwacewa tayi ta buga mashi tsoki..

  Jawota yayi ya had'ata da k'irjinshi, kuka ta sakar mashi , gaba d'aya hankalinshi ya tashi

"Minene Baby kinsan bansan ganin kukanki.."

 Hawaye ta share tace

"Kana gani jiya matarka taciman mutunci amma ka gagara rama man.."

 Bayanta ya dunga bubbugawa yana bata hak'uri shi kanshi ya rasa ya akayi ya kasa hukunta Ramlah jiya da dare...

  Hak'uri ya dinga bata da kyar ya samu tayi shiru, wasanni ta fara mashi daga nan komai ya canja...


 Wanka ya fito yana tsane kanshi, hararta yayi yace

"Idan kikasa aka koran aiki yau sai kisan ya zakiyi damu.."

  Dariya tayi tace

"Bama mai korarka.."

  Shiryawa yayi ya fito dan wucewa aiki tare suka fito shida Mufeedah tana manne a k'irjinshi, parlour suka tarda Ramlah zaune tana jiran fitowarshi, wucewa sukayi inda take bai kalla ba, itako Mufeedah sai shigewa take jikinshi tana cewa

"Baby Allah kamar mu koma nifa ban gaji ba.."

 Ta kalli inda Ramlah take ta kashe mata ido tana murmushin mugunta..

 Hancinta yaja yace

"Idan na biye maki yau baki barina fita..."


 Ramlah ji tayi kamar ta fashe da kuka, wannan wane irin bala'i ne haka aikinta ne fa amma yaje ya nemi wata, kukan dake neman kubce mata ta maidasu dan bata san Mufeedah ta gane halin da take ciki tayi dariya..

  Murmushi ta k'ak'aro tace

"Harka fito?"

"Eh"

 Ya bata amsa a tak'aice...


 Kallon Mufeedah yayi yace

"Baby sai nadawo ko?"

 Rungumeshi tayi tace

"Ka kabiyoman da shawarma"

"An gama"

 Yace mata ya juya ya tafi..


 Yakai bakin k'ofar fita parlour ya juyo muryanta tana cewa

"Allah ya kiyaye hanya ya baka sa'a ya had'aka da alkairin da ke cikin wannan ranar sharrin dake cikinta Allah ya nisanta ka dashi, ka tabbata halak d'inka zaka kawo mana idan baka samo ba ka dawo zamu hak'ura.."

 Juyowa yayi ya kalleta, murmushi ta sakar mashi

"Nagode"

 Yafad'a a hankali yana fad'a ya juya ya fice...


 Juyawar da zatayi taga Mufeedah zata zuba abinci, dasauri ta k'arasa wajen ta d'auke warmer din tace

"Akanmi zaki tab'aman abinci?"

 D'agowa Mufeedah tayi ta watsa mata harara tace

"Bangane ba?"

"Bazaki gane ba ai"

"Naga abinci kuma inajin yunwa mi zai hana bazan ciba.."

  Dariya Ramlah tayi tace

"To naga bake na dafa mawa ba mijina na dafa mawa akanmi zakici"

 Iya k'ulewa Mufeedah ta k'ule tace

"Kiban abinci inci"

"Bazan bada ba aikema macece ki shiga ki dafa da kanki"

 Zagi ta maka mata tace

"Miye amfaninki gidan dama dan ki dafa mana abinci zakiban ko kuwa"

 Shek'ek'e Ramla ta kalleta tace

"Bazan bada ba idan kin isa kizo ki karb'a"

  Tana fad'an haka ra juya ta tafi, zagi Mufeedah ta dinga jifar Ramlah dashi, ko juyowa ba tayi ba bare ta tanka ta..

 Haka ta k'araci masifarta taja k'afa ta koma d'aki dan yunwa takeji sosai...Dan Allah kuna danna d'an star dinnan kuma ku shiga d'an akwatin nan ku aje ra'ayinku, wallah ra'ayinku shike k'ara mana k'arfin cigaba da typing idan kuma kukayi shiru sai muga kamar labarin bai maku dad'i... thnx y'all my sweetos❤

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI


   Rubutawa 

       Yar_ficika


®NWA

Wattpad yar_ficika


BABI NA SHA TAKWAS  Inda tasha tea nan tabar cup din da sauran bread ta koma kan gado, wayarta ta jawo ta kira Lash, ringing biyu Lash ta dauka.. 

"Hello Lash"

  Banji mi Lash tace ba, ajiyan zuciya tayi tace "Lash akwai matsala fa komai na niyar kwance man" nan ta kwashe komai ta gaya mata..

  D'ayan b'angaren Lash tace 

    "To ko boka zamu canja?"

Tsoki tayi tace 

   "Ba abinda boka zai mana tun da boka na kan tudu ya kasa to babu wanda zai man wannan aikin illa ma suci kudina.."

 "To yanzu ya kenan?" Cewa Lash

Ajiyan zuciya tayi tace

   "Karki damu nasan mizanyi" 

Tana gama fadan haka ta kashe wayar bata jira taji mi Lash zata ce mata ba ta yarda wayan bisa gado ta kwanta rigingine tana tunanin miza tama Ramlah...


  Kitchen ta fito dan ta shirya lunch dan yaranta 2:00pm suke dawowa daga school, jellof rice tayi sai ferfesun kayan ciki, kafin kicemi k'amshi ya cika gidan, tana gama abinci ta kwashesu cikin warmers takai d'akinta dan tayi alk'awarin ta gama dafa abinci Mufeedah taci idan bazata iya dafawa ba da kanta ta bari...

  Jin k'amshi ya cika mata ciki taji wata kasallar yunwa ta taso mata dan tasan tea ba abinda zai mata, mik'ewa tayi ta nufi kitchen dan yunwa takeji sosai, da saurinta ta isa kitchen ta bud'e tukunya ganin tuk'unyar wayam ba komai sai k'anzo k'anzo ji tayi kamar ta d'ora hannu bisa kai ta rushe da kuka dan takaici..

  Dakyar take jan k'afafuwanta tayi d'akin Ramlah, bako sallama ta banka mata d'aki, zaune take tana kallo tana cin abinci, wasu miyau Mufeedah ta had'iye dan dagajin k'amshi, abincin zaiyi dadi. Inda take Ramlah bata kalla ba balle tasan akwai mutum wajen...

  "Ina abinci na?"

Banza tayi ta kyaleta kamar ba da ita take magana ba.

   "Ramlah Ina abincina?"

Sai sannan ta d'ago ta kalleta tace

"Ajiyan abinci kikaban?"

Itama kallonta tayi ta ya mutsa fuska tace 

  "Wanda kika dafa.."

Dariya Ramlah tayi ta kalleta sama da k'asa tace

  "Ban dafa dake ba"

  "Saboda mi?"

  "Saboda ba Yar aikinki nake?, beside haka aka koya maki gidanku shiga d'akin mutane ba sallama? Ko dayake ba laifinki bane ba islamiyya ce ba'a je ba, bama wannan ba ay mace kike kema kuma aure kikeyi mizai hana bazaki shiga kitchen ki dafa da kanki ba? Ko kuma ance maki ni yar aikinki ce, ko dan in dafa maki abinci nake zaune gidan, zaman aure nakeyi kamar yanda kikeyi, dan haka idan zaki dafa abinci da kanki ki dafa kici idan bazaki dafa ba wallahi nagama baki abinci kin iya kwanciya da miji amma baki iya dafa abinci ba, to nima bazan kara dafawa ba idan kinga nayi abinci gidannan nawane da 'ya'yana sai kuma mijina..."

  Tana gama fad'an haka ta cigaba da cin abincinta..

   Ji tayi kamar ta fashe da kuka dan Ramlah ta gama da ita, da kyar taja k'afafuwanta ta nufi d'akinta dan idan ta k'ara minti d'aya d'akin Ramlah sai tayi kuka wanda kuma aganinta raini ne....

  Tana fita Ramlah ta bita da harara ta cigaba da cin abincinta hankali kwance....


  D'aki ta koma tana shiga ta fad'a kan gado, rigingine tayi tana kallon silin, wulakancin da Ramlah ta mata ya dawo mata, dole ta d'auki mataki sai tama Ramlah illah., haka ta cigaba da surutunta ita kadai....


  K'arfe biyu da minti goma yaranta suka shigo gida, da sallamarsu, ganin ba kowa parlour yasa suka wuce d'akin Amminsu, dan yanzu zaman parlour ba kullum akeyinshi ba sab'anin da. Da kullum suna parlour tare da iyayensu cikin k'auna da aminci...

  "Assalamu Alaikum" 

Cewar Haneefa dake gaba..

 Amsawa tayi da 

"Amin wa'alaikum salam " 

Shiga sukayi cikin d'akin, da fara'a ta tarbesu 

"Har kun dawo?"

"Eh Ammi"

Suka bata amsa, ware masu hannuwa tayi suka k'arasa wajenta ta had'asu duka ta rungume, Banda Haneefa da tayi tsaye tana kallonsu....

  "Kallonta tayi tace

"Princess baki zuwa ki hugging Ammi?"

Dariya tayi tace

  "Wad'annan sojojin naki sun makaleki Ina zan iya zuwa"

Dariya sukayi tace 

 "Come on princess zoki hugging Ammi.."

K'arasawa tayi wajenta ta had'asu duka ta rungume, tana k'arajin k'aunar yaranta a cikin ranta...


 Takai minti biyar rungume dasu kana ta sakesu, kallonsu tayi tace

"Kuje ku cire unifoam kuzo kuci abinci"

"A d'aki zamu ci abincin?"

Cewar Haneefa, d'aga mata kai tayi, alamar 

   "eh"

 Ba musu suka nufi d'akinsu, jim kad'an suka dawo d'akinta da sallama, suna shiga suka samu wuri suka zauna. Warmers ta d'auko ta bud'e da kanta tayi serving d'insu kowane ta tura mashi gabanshi..


  "Ammi miyasa zamuci abinci a d'aki yau?" 

Cewar Haneef, 

murmushi tayi tace 

  "Kawai inasan yau muci abinci a d'aki ne ko bakuso mu koma parlour?"

  Da sauri Mukhtar yace

"Munaso Ammi ki barmu nan.."

 Shafa kanshi tayi tana murmushi, ita dai Haneefa ba tace komai ba illa abincinta da take ci.. suna gama cin abinci Mukhtar ya kwashe plate d'in ya kai kitchen.

 "Ammi tun d'azu nake fad'uwar gaba" 

Haneef ya fad'a cikin damuwa, kallonshi tayi cikin kulawa, jawoshi tayi jikinta tace

"Ka dinga karanta innalillahi wa'inna ilahir raj'un in shaa Allah zai daina"...

  D'aga mata kai yayi alamar to, hira ta dinga jansu dashi, har lokacin islamiyya yayi, kallonsu tayi tace 

   "Kuje kuyi shirin Islamiyya"

Ba musu suka mik'e suka nufi d'akinsu dan shiryawa....

  Cikin shirinsu na islammiya suka fito, daidai itama ta fito daga d'aki.

"Har kun shirya?"

"Eh"

Suka bata amsa.

Tace "to kuje kada ku makara, Allah ya bada sa'a ku maida hankali kunji..."

  Amsawa sukayi da "Ameen"...

Banda Haneef da kwatakwata bai ciki walwala, hannunshi ta kamo tace 

"Soja nah ya dai?"

Tab'e baki yayi kamar zaiyi kuka Ammi wani abu mummuna zai faru dani"

 Da sauri ta rufe mashi baki tace 

"Pls stop saying that Haneef nothing will happen to you (bari fad'in haka Haneef ba abinda zai faru da kai)" fad'uwan gaba ne kuma in shaa Allah zai daina...

 D'aga mata kai yayi, "Haneefa Kuje, pls take care of them for me (Haneefa ki kularman dasu)"

  "In shaa Allah l'll.."

  Kama hannunsu Haneefa tayi suka tafi, yakai bakin k'ofa ya dawo da sauri ji tayi an rungumeta ta baya, juyowa tayi taga Haneef k'arfin hali tayi ta duk'a tace 

 "Soja yadai?"

K'ura mata ido yayi yana kallonta, sai da ta girgizashi kana ya dawo hayyacinshi...

"Haneef mike damunka?"

 Rungumeta yayi yace 

"I love you so much Ammi"

Ita ma k'ank'ameshi tayi tace 

"Love you more Haneef" 

  Sakinta yayi ya juya ya tafi, yakai bakin k'ofa ya juyo ya d'aga mata hannu, itama hannun ta d'aga mashi yana fita ta sauke hannunta tare da share kwallan da suka zubo mata? Hannu ta d'aga tana adu'a wajen Allah kan ya kare mata yaranta duk inda suke....

  D'aki ta koma jiki ba kwari duk tausan d'anta ya kamata, komawa tayi kan gado ta kwanta lum tana tunanin halin da yaronta yake ciki dan tunda ta haifeshi bata tab'a ganinshi cikin wannan halin ba, da kyar ta samu tayi sallah ta koma kan gado ta kwanta dan yau ko abincin dare batajin zata iya idan sun dawo ko indomie ce ta dafa masu.... 


6:00pm

  K'aran tsayawar motar Imran taji, gabanta ne ya yanke ya fad'i tuna yanda sukayi da Mufeedah yau tayi tasan Allah kadai yasan irin sharrin da zata mata yau....


   Shigowa yayi yana kwalama Mufeedah kira, itako tana jinshi taki amsawa sai ma kuka da ta fashe dashi, d'akinta ya k'arasa yana kiranta, ganin tana kuka yasa hankalinshi ya tashi, da sauri ya k'arasa inda take...

  "Lafiya?"

 Ya tambayeta tare da jawota jikinshi, tureshi tayi tace

 "Ka kyaleni"

A rud'e ya kalleta yace

  "Miyafaru? Please tell me"

 Kuka ta fashe dashi hankalinshi idan yayi dubu ya tashi, lalashinta ya fara dan in akwai abinda ya tsana kukan Mufeedah ne.....

 Da kyar ya samu tayi shiru yace 

"Miyafaru?"

  "Kana fita Ramlah tafara zagina tana zagar man iyaye wai ni karuwa ce, kaima sai da kagama lalata dani kana ka aureni ay kaima dan iskane irina babu abinda bakasha babu matan banzan da baka bi, ta tara yaranta tana gaya masu suna man dariya, wani kukan munafuncin ta fashe dashi, mik'ewa yayi tsaye yana huci kamar zaki har wani bak'i bak'i yake gani gabanshi, haka ya fita yana hard'e k'afafuwa...


 "Ramlah! Ramlah!! Ramlah!!!"

  Tun daga d'akin Mufeedah yake kwala mata kira, gabanta ne yaci gaba da fad'uwa dan tasan dama za'ayi haka, fitowa tayi da sauri inda yake tsaye, kafin tayi magana taji saukar Mari? Marinta yake ta ko Ina sai da yaga takai k'asa kana ya cire belt ya fara dukanta dashi.....

  Dukanta yake ta ko Ina tun tana Iya kuka har yakai bata kuka, tsaye tayi ta hard'e hannu tana kallonshi tana murmushi...

  Shigowa yayi da sallama yana kiran Ammi, da gudu ya k'araso ganin Imran na dukanta, kamashi yayi 

  "Yana Daddy ka daina dukanta mita maka?" 

Wurgi yayi dashi ya cigaba da dukanta, tashi yayi zai koma Mufeedah ta kamashi ta je far dashi bisa tiles kanshi ya bugu, daidai shigowar Haneefa da Mukhtar wata irin k'ara yayi daga nan bai sake motsi ba, da gudu Haneefa ta k'arasa wajenshi tana kiran 

"Haneef"

  Jin k'arar da tayi yasa ta ingijeshi ta nufi inda Haneef yake kwance kanshi ya fashe, kuka ta saki sosai tana jinjigashi, dagoshi tayi ta rungume tana kiranshi ganin bai motsi yasa ta d'aukeshi su Haneefah suka bi bayanta suna kuka....

  Hanyar fita tayi maigadi na tambayarta bata tsaya bashi amsa ba ta fice tana fita tayi sa'a mini jeep (napep) ta aje wasu fad'a wa tayi tace Alheri clinic zaka kaimu...

  Mai napep yaja suka tafi kuka takeyi sosai suma su Haneefa kuka sukeyi, gani tayi kamar mai napep din bai gudu tace

"Malam dan Allah ka kai motar ka k'arshe kada yarona ya mutu.."

  Tausayi ta bashi dan tunda suka fito yaga halin da suke ciki, gudu yake amma bata gani saboda rud'e take......


  Suna isa bata bari ya ida tsayawa ba ta fito, ganin haka shima bai jira kar b'an kud'inshi ba ya wuce. Da gudu ta fad'a cikin asibitin tana kiran nurse, wata nurse ce ta tashi ta karb'i Haneef tayi emergency dashi....

 Tazo shiga aka hanata, fashewa tayi da kuka ganin tana kuka ya saka Haneefa da Mukhtar kuka, rungumesu tayi ta cigaba da kuka kamar ranta zai fita.........Ana wata ga wata one word about dis chappy, shin Ramlah zata yarda idan wani abu yasamu yaronta? Imran zai d'auki mataki irin yanda Mufeedah ta jefar da Haneef har kanshi ya fashe? Amsoshinku na chapter ta gaba, yawan votes dinku da comments dinku shi zai bani k'arfin guiwan yi maku typing next page💃🏻 

  Dan Allah kada ku manta ku danna d'an tauraron nan na gefen haggu, sai kuma d'an akwatin nan shima ku shiga ku aje ra'ayoyinku. Thnx y'all I love you from d bottom of my heart ♥ 

#Team MKA

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI


   Rubutawa 

       Yar_ficika


®NWA

Wattpad yar_ficika


BABI NA SHA TARAThe great thing about new friends is that they bring new energy to your soul." This Page is for you ummu Bassam (mummyn admin), thnx for d support courage nd kia you mean so much to me, I love you to d moon nd back Ganin kukan da suke ba abinda zai masu yasa ta kama yaranta ta zaunar dasu, "Ammi ya Hafeen ba zai mutu ya barmu ba ko?" Cewar Mukhtar, hawaye ta share tace 

 "In shaa Allah zai tashi bazai mutu ya barmu ba...."

  Jawo Haneefa tayi jikinta tace

  "Princess kuka bazaiyi magani ba please stop crying adua zaki dingayi in shaa Allah he will be olryt okay?"

  Hawaye ta share tace 

  "Ammi na tsanesu I hate dem both wallahi ta kashe man k'ani l'll kill her nima.."

  Rufe mata baki tayi "please stop saying dat Haneefa ita bata isa ta kashe Haneef ba sai dai idan kwananshi sun kare, kuma ki daina cewa kin tsanesu bare ta kaiki da cewa sai kin kasheta I kwn it's hurt amma muyi hakuri, duk abinda Imran yayi ba yanda zakiyi mahaifinki ne ita kuma matar shi ce dole ki bata respect kamar yanda zaki bani, kuyi hakuri nasan Imran bai mana adalci amma ba laifinshi bane kunsan irin sanda yake mana dan haka duk abinda kuka ga yana faruwa ba laifinshi bane kedai kawai keep praying, in shaa Allah komai zai koma daidai...." 

  Haka ta cigaba da lallashin Haneefa tana bata baki...

  Bayan awa guda aka fito da Haneef daga emergency, yana cikin gadon asibiti kanshi d'aure da bandage tashi sukayi da sauri suka nufi inda suke, "doctor ya jikinshi?" Cewar Ramlah, murmushi doctor yayi yace 

   "Dasauki yanzu za akaishi d'aki,"

   "Alhamdulillah" gaba d'ayansu suka fada..,

  "kece mamarshi?"

  "Eh nice "

  "Kisameni office inasan magana dake"

   Bai jira amsawarta ba yayi gaba....


  Kallon Haneefa tayi tace

"Bari naje yanzu zan dawo"

"Daga mata kai tayi, hanyar da taga doctor yabi ita ta nufa, da sallama ta shiga office d'in d'agowa yayi ya kalleta 

    "Have a seat"

 Ba musu ta samu wuri ta zauna. Rubuce rubuce yayi yakai minti goma kafin ya d'ago ya kalleta, har ta k'osa da zaman da takeyi

  "Ke kika haifeshi?"

Maganarshi taji cikin kwanyar kanta, d'agowa tayi ta kalleshi tace

  "Eh ni nahaifeshi"

   "Ina babanshi?"

"Bai nan yayi tafiya" 

Haka kawai ta tsinci kanta da mashi karya wanda ita kanta bata san dalilin yinta ba....


  "Garinya akai yaronki ya fad'i haka?"

Gabanta ne ya fad'i dan bata san mi zatace ba ko zata gaya mashi kishiryata ne ta mashi haka no bazan iya ba zaiga sakaci na kuma kamar na tona asirin gidan mijinane ...

  "Toilet ya shiga kawai sai dai naji karanshi, Ina shiga na ganshi kwance kanshi ya fashe nafi ganinta ga faduwa yayi"

 Haka kawai ta tsinci kanta da gaya mashi haka...

  Kallonta yayi ido cikin ido, Har sai da gabanta ya fad'i "kodai ya gane k'arya na mashi?"

  "Wani irin sakaci ne iyaye kukeyi yanzu d'anki yaji ciwo irin haka baki san tak'amaimai abinda yaji mashi ciwo ba? Shin ko kin manta yaranki amanane Allah ya baki? Amma kike sakaci dasu haka, well ba wa'azi zan maki ba, yaronki kanshi ya bugu sosai dan har jini sun taru amma munyi aiki mun cire kuma zai samu sauki in shaa Allah yanzu dai mun bashi gado Sai ya warware sosai zamu sallameshi...."

  Kanta duk'e yake tunda ya fara magana, sai da ya gama ta d'ago tace 

  "Nagode likita in shaa Allah bazan karayin wasa da lafiyan yarana ba zan kula dasu sosai..."

  Murmushi yayi yace

  "Zaki iya tafiya.."

   Sallama ta mashi ta tashi jiki sanye ta fita, inda ta barsu Haneefa nan ta iskesu kamasu tayi suka nufa d'akin da aka kwantar da Haneef, tura k'ofan sukayi suka shiga, bakaji motsin komai sai k'aran AC, gaban gadonshi suka k'arasa kwance yake yana fitar da numfashi daya bayan daya, kanshi ta dafa 

  "Allah ya baka lafiya Haneef forgive ur Daddy kaji?" 

  Hannunta ta janye ta share hawayen da suka gangaro mata, Haneefa ta kalla tace

  "Bari naje gida na d'auko abinda muke bukata"

"To Ammi saikin dawo"

  "Take care of your self nd my pikin kinji ko?"

  "In shaa Allah Ammi"

  Peck ta ma Haneef a kunci tace

   "Get well soon my Baby", kamar yaji mi tace yayi murmushi, "princess sai nadawo" tana fad'an haka ta fita daga d'akin.....


  K'arasawa wajen gadonshi Haneefa tayi ta k'ura mashi ido, hawaye suka zubo mata Mukhtar ne ya matso kusa da ita yace 

  "Adda Haneefa stop crying please"

  Hawaye ta share ta rungume Mukhar 

 "Karka damu nadaina kuka" d'agowa yayi ya share mata hawaye daga nan babu wanda ya kara magana....


  Tana shiga gidan babu kowa parlour haka ta shige d'akinta ta d'auki abinda zata buk'ata taje d'akin yaranta kowa ta d'aukar mashi abun buk'ata takai mota, dawowa tayi ta d'auki wayarta da ATM card dinta ta saka a hand bag ta fito ta rufe d'akinta, harta kai k'ofar fita ta dawo tabi wani corridor, ta shiga d'akin Imran, sallama tayi ba'a amsa ba, shiga tayi cikin d'akin zaune yake ya had'a kai da hannuwa, kallo ta k'are mashi duk ya fita hayyacinshi sai kace ba Imran d'inta ba d'an gayu kamili Maiji da kanshi...

  "An kwantar da Haneef asibiti"

Abinda ta iya fad'a kenan d'agowa yayi ya kalleta baice komai ba, itama kuma batayi expecting zaice wani abuba...

  Juyawa tayi zata tafi, "wane asibiti yake?"

  Abinda taji yace kenan

   "Alheri clinic " 

  Ta bashi amsa a tak'aice

   "Allah ya bashi lafiya"

   "Amin"

   Ta saka kai ta fita, tana fita maigadi ya taso yace

"Hajiya lafiya?"

 Murmushi tayi tace

 "Haneef ne ba lafiya amma yanzu da sauki"

"Allah ya bashi lafiya"

"Amin"

"Yana wane asibitin?"

"Alheri clinic"

"Allah ya sawak'e"

"Bud'eman gate Baba"

  Ba musu ya wangale mata gate wuta ta ba motarta ta fita daga haraban gidan, d'aga mata hannu mai gadi yayi har saida yaga k'ulewarta kana ya rufe gate d'in ya koma bakin aikin shi......


  Tafiya take tana tunani tabbas sai ta d'auki mataki dan idan ta kyale Mufeedah sai ta gama illata mata yara kuma da alama Imran bazai d'auki mataki ba, da haka harta iso asibiti, d'akin da Haneef yake ta nufa, sallama tayi ta shiga, zaune suke babu mai ma wani magana, murmushi k'arfin hali ta masu tace

  "Yara na yadai?"

Mukhtar ne yace 

"Bakomai Ammi"

"Princess are sure ba abinda ke damunku?"

Sai sannan tayi magana tace 

"Ammi ba abinda ke damunmu sai ciwon Haneef"

 K'arasawa tayi wajensu tace

"Karki damu in shaa Allah Haneef zai warke"

   "Ammi idan ya Haneef ya warke karmu koma gidan Daddy please "

Jawoshi tayi tace 

  "Can zamu koma"

"Saboda mi?"

"Saboda babu inda yafiye mana nan nanne gidanmu gidan mahaifinku nikuma gidan mijinane dan haka bamu da inda yafi nan kaji ko?"

  D'aga kanshi yayi alamar yaji.....


  Wayanta ta zaro ta kira Ahmad ringing biyu ya d'auka 

"Hello Ahmad Ina wuni"

"Lafiya lau Ramlah ya kuke dasu princess?"

 "Lafiya lau muke dama zan gaya maka Haneef baida lafiya muna kwance asibiti"

"Subahannallah miyasa meshi?"

 "Maganar na da tsawo sai kazo"

"Okay to in shaa Allah nan da minti talatin zanzo wane asibiti ne?"

"Alheri clinic" ta bashi amsa 

  "To shikenan in shaa Allah gani nan zuwa.....
           *************

  Wayan ta ne yayi k'ara tana dubawa taga Ahmad d'auka tayi, 

"gani na shigo"

"Okay muna room3 private room"

Kashe wayan yayi dan yanama kusa da d'akin, sallama yayi ya shigo, da gudu Mukhtar ya k'arasa wajenshi yace

"Uncle Ahmad ya Haneef kanshi ya fashe, kuma Anty Mufeedah ce ta jefar dashi sai da kanshi ya fashe."

  Kallon Ramlah yayi yana neman k'arin bayani, kamo hannun Mukhtar tayi tace

"Princess kuje daga waje kinji"

 Hannunshi Haneefa ta kama suka fita waje....


"Ina wuni?"

"Lafiya lau "

Ya bata amsa a tak'aice, "maganar da Mukhtar ya gayaman gaskia ne?"

D'aga kanta tayi alamar "Eh"

   "Garinya haka ta faru inashi Imran din yake?"

"Yana nan"

"Yana na?" Cikin tsoro ya sake tambayarta

"Eh yana nan" ta bashi amsa, Ramlah mike faruwa daku? Karki b'oyeman komai ki fad'aman komai...


 Wuri ta samu ta zauna ta share hawaye da suka gangaro mata, tun bayan Auren Imran da Mufeedah.......... nan ta kwashe komai ta gaya mashi babu abinda ta rage mashi, gumi ne ya karyo mashi 

"Innalillahi wa'inna ilaihir raj'un" kawai yake ta maimaitawa....

  Gaban gadon Haneef ya k'arasa kanshi ya Shafa yace 

 "Allah ya baka lafiya my boy"

  Yana fad'an haka ya juya ya fita, sai da yakai bakin k'ofa kana ya juyo ya kalleta yace

"Zanje in dawo"

  Bai jira amsarta ba yayi gaba....


  Yana fita babu inda ya wuce sai gidan Imran, horn ya dingayi kamar zai b'alle gate d'in gidan da gudu mai gadi ya wangale mashi gate, cinna kan motarshi yayi cikin haraban gidan, bai ida ko parking ba ya fito yayi hanyar shiga cikin gidan, tunda ga bakin k'ofa yake kwalama Imran kira, Har ya shiga parlour, da sauri Imran ya fito d'akinshi dan gane muryan waye ke kiranshi, itama fitowa tayi dan taga wakema mijinta wannan kiran...

  "Ahmad lafiya kuwa?"

Cewar Imran da ya k'araso inda yake, kallonshi Ahmad yayi sama da k'asa yace

  "Kai zan tambaya lafiyarka kasan mi kake yi kuwa? Kasan wutar da ka kunna ma gidanka da kanka?"

"Ban fahimci mi kake nufi ba fa"

"Ina zaka fahimta an juya maka kwakwalwa sai da nace karkayi auren nan ba alkairi baneba ka dage Sai kayi gashi nan irin abinda ka aura. Wallahi kaji tsoron Allah Imran kasan mi kake ciki saboda sai Allah ya tambayeka irin rik'on da kama iyalanka, yanzu Haneef na asibiti kuma matarka ce silar komai amma banganka asibiti ba kuma banga ka d'auki wani mataki ba, Anya hakkin yaran nan da mamarsu bazai tambayeka ba.."

   Harara ya wurga mata yace

"Ke kuma kiyi duk abinda kika iya lokacin kine kuma zakiyi nadama a lokacin da wuri ya k'ure maki." Yana gama fad'an haka ya juya ya tafi, harara ta bishi dashi tace 

  "Zanyi maganinka kaima daga kaina kagama shishigi gidan wasu.....


                  Asibiti

  Kanshi ya dafe yana k'ok'arin yin kuka da gudu suka k'arasa wajenshi, kamashi Ammi tayi tana mashi sannu, 

"Bari naje na kira likita"

  Cewar Ammi dake k'ok'arin fita, hannunta ya rik'e gama, a hankali ya fara bud'e idanshi, fes ya ajiye idonshi kan Ammi, murmushi ta mashi, shima murmushin yayi, juyawa yayi ya kalli su Haneefa dake gefenshi, suma murmushi ya masu..

  "Bari naje na kira doctor "

Girgiza kai yayi

 "Ki barshi Ammi naji sauk'i, ki zauna dani bansan kiyi nisa dani.."

Kujera ta jawo ta zauna, tayi ta gumi d'ayan hannun na rik'e da hannun Haneef, cire mata tagumi yayi yace

"Ammi bakin ce tagumi ba kyau ba?"

"Eh ba kyau my boy"

"To miyasa kikayi?"

"Bakomai nadaina"

  Girgiza kanshi yayi, ya k'ura mata ido.

"Ammi"

  D'agowa tayi ta dubeshi jikinta duk ya mutu, 

"Yadai?"

"Ammi forgive me please kaina zafi yakeman"

 "Haneef please ka daina karyaman zuciya in shaa Allah zakaji sauki."

  Juyawa yayi ya kalli Haneefa yace 

"Adda forgive me, zan tafi in barku ki kulaman da Ammi da my little bro, i knw its difficult amma nasan zaki iya ki cigaba da taya Ammi da adu'a komai zaizo maku dasauki, nd finally kice ma daddy ya yafeman, naso in ganshi, amma baizo ba,"

 gaba d'ayansu kuka suke, "Ammi stop crying"

 Kamo Mukhtar yayi yace 

"Lil bro bazanyi doguwan rayuwa tare daku ba amma kasani ina k'aunarku, zan barku cikin k'unci a yanzu amma gaba zakuyi dariya."

  Fad'awa Haneefa tayi jikinshi tana kuka, d'agota yayi yace 

"Kidaina kuka Adda nasanki da juriya please stop crying be strong, be strong for me kinji" d'aga mashi kai tayi, d'agowa yayi a hankali ya mata peck, "take care of my Ammi nd my lil bro" hannunshi ya kai kan fuskan Ramlah yace ki daina kuka kinji, now bless me kinji" d'agowa tayi ta share hawayenta tace 

"Allah shi maka albarka"

Amsawa yayi da amin, peck yama kowa a kunci ya koma ya kwanta tare da had'a hannuwansu cikin nashi.....

  Ji tayi wurin yayi shiru, da sauri ta d'ago ta kalli inda yake, hannunta ta kai kan k'irjinshi idan ba mafarki take ba Haneef bai numfashi, jijjigashi ta farayi tana kiran sunan shi amma ina Allah yayi nashi ikon kan Haneef fashewa tayi da kuka mai tsuma rai, kuka takeyi Haneefa ma kuka takeyi, 

  "Ammi mi yasamu Ya Haneef "

Cewar Mukhtar da bai fahimci komai ba, kamoshi tayi tace 

"Haneef he's gone, he's gone forever" daidai shigowar Imran da Ahmad.

"What?"

  Gaba d'aya suka juya ganin jin muryan waye, da sauri ya k'araso inda Haneef yake kwance yayi zai tab'ashi.

"Don't touch him, don't touch my son komi ya sameshi kune sila, now matarka ta kasheman yaro sai ku zuba ruwa k'asa kusha, amma kasani bazan tab'a yafe maka ba kaida matarka."

  Kanshi k'asa ya kasa magana ya kuma rasa abinda ke damunshi, yasan dai wani abu na damushi amma shi kanshi baisan ko miye ba...

  "Calm down Ramlah yanzu ba lokacin da zamuyi magana baneba nan bari inje in sami doctor" Cewar Ahmad, fita yayi dan kiran likita.....Gaskia ina ga zan tsaya da typing dan ku nakeyi amma naga labarin kamar bai maku dad'i, voting fa kawai nace kuyi Sai comments amma bakuyi #cry, natafi hutu sai kunyi biko, yawan votes dinku yawan typing dinku. Duk da haka dai Ina sanku, I love you ya'all, Allah ya barni daku♥

#team MKA

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI


   Rubutawa 

       Yar_ficika


®NWA

Wattpad yar_ficikaBABI NA ASHIRIN  The beautiful memories of the times we've spent together make me smile, only until the moment when they eventually remind me that you're no longer here. I miss you Maama,💔😭 I dedicated this page to my one nd only, my lovely, my everything Mom♥ may Allah bring peace in ur grave nd make aljannah firdausi ur permanent home🙏🏼😭 Maama ur Auta loves you so much, l'll never stop crying for loosing you😭😭 I love you Hajiya Maama ♥


   Yana fita ta d'ora kanta jikin Haneef tana kuka, gaba d'aya yaran kuka sukeyi, babu mai lallashin wani, tsaye yake kamar gunki ya kasa motsi zuciyanshi wani irin zafi yake mashi, duk da yasan yanzu yaran basu gabanshi, amma ya ji mutuwa Haneef saboda yaron ya shiga ranshi sosai..

  Ahmad ne ya dawo da sallama yana gaba doctor na biye dashi, gaban gadon doctor ya k'araso gwaje gwaje yayi yakai minti goma yana gwaje gwaje, daga k'arshe da ya d'ago yace

  "Sai dai muyi hak'uri Allah ya karb'i abunshi."

Kuka ne ya kufce mata, ta k'arasa wajen gadon Haneef da gudu tana kuka, 

  "Haneef katashi dan Allah ka tashi munasanka ni dasu Adda dan Allah Haneef ka tashi"

Babu wanda baiyi kuka ba, harta likitan saida yayi kwalla.

  Haneefa ce ta k'arasa wajenta ta kamo ta tace

"Ammi kiyi hak'uri Haneef ya tafi ya barmu adu'a zamu dinga mashi amma kinsan bazai dawo ba da ana mutuwa a dawo da babu wanda zai bari nashi ya mutu bai maidoshi ba, ki godema Allah ya ronki ya rasu yana neman yafiyarki dama gashi yaro bai balaga ba kiyi ta wakkali Allah bazai barki haka ba sai kinga sakamakonki nan gaba, kima gode ma Allah ya rasu ya huta da wannan rayuwan da muke ciki..."

  Sakin baki likita yayi yana kallonta "dama akwai yara masu irin wannan baiwar? Lallai kowa da baiwar da Allah ya mashi.." ciki zuciya yake wannan tunani...

   "Likita muje office kabamu bill d'inmu mutafi dashi dan yau za'a mashi sutura gobe in shaa Allah akaishi gidanshi.."

  Ahmad ne ke fad'ama likita haka, fita likita yayi Ahmad ya bishi baya dan yayi clearing komai, su tafi gida da gawan Haneef. Saida Ahmad ya gama da asibiti ya biya bill d'in da aka mashi yadawo d'akin inda ya tarda wasu nurse sun shirya Haneef d'aukarshi akayi aka sashi mota, suka nufi gida......


                ***********

  Abinda ya faru, Ahmad na fita daga cikin gidan, Imran ya biyoshi baya, harya tada mota zai tafi, yaji an bud'e gaban mota an shiga, bai tanka mashi ba ya ja mota yabar haraban gidan, saida ya tabbatar da ya hau titi, ya juyo ya kalli Imran, kauda kanshi yayi yace

  " Ina zan kaika? Danni asibiti zan koma"

"Nima asibitin zani, inasan in ganshi inga halin da yake ciki.."

  Juyowa Ahmad yayi ya kalleshi daga nan ya kauda kanshi bai k'ara mashi magana ba har suka iso asibiti......


                ************

  Daidai bakin gate d'in gidan Imran, Ahmad yayi horn maigadi ya lek'o ganin motan Ahmad ne yasa ya koma da sauri ya bud'e masu gate, shiga yayi cikin gidan ya samu wuri yayi parking, suna fitowa mai gadi na k'arasowa 

   "Hajiya ya jikin Haneef? Ko an sallameshi ne?"

Ya fad'a yana kallon Ramlah, gaba tayi dan bata iya bashi amsa...

  Ahmad ne ya bashi amsa da 

"Allah yayi ma Haneef rasuwa"

  Tun kafin ya ida Baba maigadi ya fara salati yana sharan kwalla, gaba d'ayansu sukayi cikin gida banda Baba maigadi da aka bari tsaye yana hawaye....


  Suna shiga Ramlah ta saka hannu ta amsheshi daga wajen Ahmad tayi d'akinta dashi, zaune suke parlour Ahmad da Imran sunyi jugum jugum, babu mai ma wani magana. Da karairaya ta fito parlour bako sallama ta samu wuri kusa da Imran ta zauna, hannunshi ta zare daga tagumi tace

  "Baby kadawo kenan? Wai inama kaje?"

   "Asibiti naje"

      Ya bata amsa.

"Aww hakane fa ya mai jikin?"

D'agowa yayi jiki ba kwari yace

"Yarasu"

  Tab'e baki tayi tace

"Allah ya jikan nusulmi"

Amsawa yayi da 

"Ameen"

  Duk abinda ya faru idon Ahmad na kasu wani mamakine ya rufe shi,

"Anya matar nan kuwa tasan Allah? Duk abinda yafaru ita ce sila amma yanzu kalli yanda ta nuna abun bai dameta ba, zanyi maganinki..."

  Cikin zuciya yake maganarshi, tana d'agowa suka had'a ido da Ahmad, wata harara ya watsa mata sai da gabanta ya fad'i...


  Tashi tayi tace

"Baby natafi in kwanta sai ka taho"

Tana fad'in haka ta juya ta nufi d'akinta, Imran na d'agowa idanuwansu suka had'u waje guda shida Ahmad, harara Ahmad ya wurga mashi..

  "Katashi kaje d'akin Ramlah ku zauna da gawan, ni zan zauna nan"

"Bazan iya zuwa ni kad'ai ba please muje tare sai mu kwana da gawan ita idan yaso sai ta tafi d'aki da yaran.."

"Akanmi zamu rabata da d'anta sai dai kai ku zauna tare da ita" marairaice mashi yayi yace 

"Ban iya zama da ita kusa dani"

"Why?"

"I hate her, na tsaneta na tsani na ganta kusa dani duk idan tazo kusa dani daurewa nakeyi, wallahi bazan iya zama kusa da ita ba har mu kwana zan iya mutuwa nima.." Galala Ahmad ya saki baki yana kallonshi, dan tabbas baccin yasan waye Imran da sai yace shaye shayen zamani yafara, amma wannan ko ba'a fad'a ba kasan bayin kanshi bane ba, saboda irin san da Imran ke ma Ramlah kowa yana mamaki amma yanzu yana fad'in ya tsaneta....

  Banza Ahmad yayi dashi, kamar ba dashi yake magana ba, kwanciya yayi bisa kujeran da yake zaune yayi, shima Imran d'in kwanciya yayi, alamun bazaije d'akin Ramlah shi kad'ai ba....

  Ganin da gaske yake Ahmad ya mik'e yace 

"Muje"

  Ba musu kuwa yabi bayanshi, da sallama suka shiga d'akin zaune take k'asa ta kunna karatun qur'ani, ta d'aura kan Mukhtar bisa ciyarta da alama yayi bacci, Haneefa na gefenta tayi tagumi...

  "Ramlah kuje d'akinsu Haneefa kubarmu zamu kwana da gawan"

Ta bud'a baki zatayi magana yace

"Ah ah karki man gardama kiyi yanda nace baki ganin Mukhtar yayi bacci kuje can d'in mu muna nan.."

   Ba yanda ta iya dole ta tashi ta d'auki Mukhtar taja hannun Haneefa sukabar d'akin.....


                ****

 Tana shiga d'aki fad'awa tayi kan gado tana murna, wayarta ta jawo ta danna kira, har wayan ta tsinke ba'a d'auka ba, k'ara dailling number tayi, saida ta kusa tsinkewa kana aka d'auka.

  "Hello Mufeedah lafiya kike kirana cikin dare haka?"

Murmushi tayi tace 

  "Kiyi hak'uri Lash Ban iya bari sai da safe ban maki albishir ba."

"Miyafaru? Ina jinki"

"Haneef ya rasu"

"Wane Haneef?"

"Yaron Ramlah mana."

  "Miyafaru? Gayaman dan nasan koma miye kece sila."

  Dariya tayi sosai tace

"Kamar kin sani." Nan ta kwashe komai ta gaya mata, shewa sukayi gaba d'aya,. "Gaskia Mufeedah baki da kyau"

  Ajiyan zuciya tayi tace

"Ay dama nace ni zanyi komai da kaina, sai dai bashi naso ya mutu ba wannan marar kunyar yarinyar naso ta mutu, dan Haneef ya d'an shiga raina...

  Dariya Lash tayi tace

"Itama bani kokonto zaki gama da ita soon." Dariya suka saka, haka suka cigaba da hira kamar wani abu bai faru ba daga k'arshe sukayi sallama kowa ya kwanta.....


                 9:00am

   K'arfe tara daidai aka shirya Haneef dan kaishi gidanshi na gaskia. Fitowa akayi dashi za'a tafi dashi, tashi Ramlah tayi ta rik'e gawan tana kuka ganin haka yasa Haneefa kuka ita da Mukhtar duk wanda ke parlour babu wanda baiyi kuka ba, sai Mufeedah dake latse latsen waya.....

  Dak'yar aka janye Ramlah daga jikin Haneef, tanaji tana gani aka wuce da Haneef makwancinshi na gaskia, ana fita dashi ta fad'i k'asa sumamma, da gudu mutane sukayi kanta, ruwa aka dinga yayyafa mata dakyar aka samu ta farfad'o. Tana farfad'owa ta had'a Haneefa da Mukhtar ta rungume tana kuka, babu wanda bai masu kuka ba, duk rashin imaninka sai kayi kuka......
Inama duk d'an team d'in Ramlah ta'aziyan rasuwan Haneef, nasan duk kuna team d'in Ramlah. To ni gaskia zan koma team din Mufeedah, lolzz wasa nake nima Ina nan team d'in Ramlah... Dan Allah karku manta kud'an danna tauraro nan na hannun hagunku, sai kuma ku shiga akwatin nan ku aje ra'ayoyinku, nagode Allah ya barni daku ni daku k'auna ce wadda bata da k'arshe idan babu ku babu feedoh, kusani Ina k'aunarku each nd every second♥ I love y'all my hayatiees😘

#team MKA

#1love

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI


   Rubutawa 

       Yar_ficika


®NWA

Wattpad yar_ficika
BABI NA ASHIRIN DA D'AYA  Haka aka cigaba da zaman karb'an gaisuwan Haneef, duk wanda yasan Ramlah da ya ganta yanzu sai yaga canji, wasu suna zaton mutuwar Haneef ce ta mayarda ita haka...

  Bayan sadakan bakwai, Ahmad ne zaune parlourn Imran, gaba d'aya ya tara Imran da Ramlah dan yanasan magana dasu, kallon Imran yayi yace 

"Ina matarka?"

"Taje unguwa" 

Ya bashi amsa. Ajiyan zuciya yayi yace

"Dama maganar da zanyi bata shafeta ba, zanyi magana ne akan kai da Ramlah da irin zaman da kukeyi..."

  Kallon Imran yayi yace

"Da kai zan fara saboda kaine namiji kuma ikon gidanka yana hannunka, gaskia nayi mamakin irin sakacin da kayi akan iyalenka idan wani yace zakayi haka wallahi ni zan fara k'aryatawa amma gashi bawani yabani labari ba ni nagani yanda ka maida gidanka, duk da ba laifinka amma akwai sakaci ka kuma san ba ruwan Allah sai ya kama ka da laifin daka aikata, a gabanka matarka ta zama silar rasa d'anka amma baka d'auki mataki ba kuma nasan bazaka d'auka ba bance kuma ka d'auka ba dan nasan bazaka d'auka ba, amma duk bawani abu ya jawo maka haka ba rashin dagewa da azkar, numfasawa yayi, ya cigaba kaji tsoron Allah ka dawo hayyacinka kayi adalci tsakanin matanka iyakar shawara da zan baka kenan..."

  Ramlah ya kalla yace

"Nasan ba amaki adalci ba amma ki dubi irin sanda mijinki yake maki ke da yaranki a da dakuma juyawar da ya maku yanzu kinsan ba laifinshi baneba kiyi hak'uri ki dage da ibada in shaa Allah komai zai koma kamar ba'ayi ba, kuma kiyi hak'uri da d'aukan mataki akan rasuwan Haneef kibar ma Allah ya saka maki karki manta Haneef bazai wuce ranan ba kawai dai Mufeedah ta zama sila, kiyi hak'uri nasan kinayi to ki k'ara akan wanda kikeyi..."


  Kanta k'asa tace

"In shaa Allah zan cigaba da adua kuma nabar maganar"

"Alhamdulillah"

  Abinda Ahmad ya furta kenan, kallon Imran yayi ko zaiyi magana amma baiyi ba kuma da alamu bashi da niyar yin magana, girgiza kanshi Ahmad yayi yace

 "Akwai wani malami daura da akaman maganarshi adu'a yakeyi in shaa Allah zanje wajenshi zuwa jibi komi zaizo k'arshe.."

  "Allah shi yarda"

Cewar Ramlah., sallama ta yima Ahmad ta tashi ta koma d'aki, kallon Imran yayi yace

"Ranka ya dade zan wuce gida"

  Tashi yayi dan ya rakashi, suna isa k'ofar fita parlour sukaci karo da Mufeedah ta dawo, kallonta Ahmad yayi sama da k'asa, ya wurga mata harara. Gabanta ya fad'i ta rasa dalilin da yasa da taganshi take fad'uwan gaba, rab'asu tayi ta wuce.

  Imran ne ya washe baki

"Baby sannu da dawowa"

Inda yake bata kalla ba bare yasa ran zata amsa maahi. Tab'e baki Ahmad yayi ya wuce, suna fita haraban gidan, Ahmad ya dubeshi yace

"Yanzu haka matarka ke fita Imran? Wani irin freedom kaba yarinyar nan? Kalli yanda ta fita riga da wando ne fa jikinta amma kabarta ta fita haka anya Imran kwakwalwanka bai tabu ba?".

  B'ata fuska yayi dan baisan maganar. Murmushin takaici Ahmad yayi yace

  "Na tab'a maka yar gwal ko? Shiyasa kake b'ata fuska?"

  Shiru yayi bai bashi amsa ba, shima bai k'ara cewa komai ba ya isa gaban motarshi, ya shiga ya tada mota yabar haraban gidan ba tare da ya kalli inda Imran yake ba....


  Komawa yayi cikin gida, d'akin Mufeedah ya nufa, yana zuwa ya murd'a k'ofa, cikin rashin sa'a kulle ya tarda k'ofan, buga k'ofan yakeyi amma tak'i bud'e wa haka ya hak'ura ya koma d'akinshi....         BAYAN KWANA BIYU

 Ahmad ne ya shigo cikin gidan da sallama ba kowa parlour, waya ya zaro ya kira Ramlah bugu biyu ta d'auka. 

"Gani parlour"

  Abinda yace kenan ya kashe waya, daga kitchen ta fito rik'e da flask d'in ruwan zafi.

"Ashe kina kitchen?"

Murmushi tayi tare da gaidashi, amsawa yayi fuska sake yace

"Ina Imran d'in?"

"Yana d'akin Mufeedah"

Tabashi amsa, waya ya zaro ya kira sai da ta kusa tsinkewa kana aka d'auka.

"Ina parlour"

 Yana fad'in haka ya kashe wayarshi, Jim kad'an sai gashi ya fito, da fara'a suka gaisa, inda Ramlah take bai kalla ba inda sabo ta riga da ta saba...

 "Ramlah zanje daura kamar yanda na gaya maku dan haka shiyasa nazo In sanar daku."

Haka kawai taji gabanta ya fad'i, jikinta sanyaye tace

"Allah ya maidoka lafiya"

Ta juya ta nufi d'akinta, amsawa yayi da 

"Ameen"

   Hannun Imran yaja suka fita, saida suka isa bakin mota yace

Imran zan tafi kuma kasani tafiyan nan zanyi ta ne dan kai, inajin jikina ba dad'i amma daurewa zanyi in tafi saboda nasa raina da wannan tafiyan kuma inasan ka koma Imran d'inka na da, Ina san ka saka wannan a zuciyar ka Ramlah bata da kowa saini ni kad'ai na rage mata gashi nima zan tafi ba lallai baneba in dawo inasan kaman alk'awarin duk runtsi bazaka rabu da Ramlah ba, a lokacin da na barku Ramlah bata da kowa sai kai inaso kayi hak'uri ka rik'eta matsayin mata kuma matsayin k'anwa, dan nasan ko bayan raina watarana sai gaskia tayi halinta sai ka koma Imran d'inka na da, kaman alk'awarin zaka rik'e Ramlah da yaranta..."

  Jiki sanyaye ya d'ago ya kalleshi yace

"Na maka alk'awarin bazan rabu dasu ba zan zauna dasu duk da a yanzu babu wanda nafi tsana irinsu amma zan zauna dasu, kuma zakaje lafiya kadawo lafiya.."

  Hawayen dake mak'ale kan fuskan Imran suka gangaro, rungume juna sukayi sun kai minti biyar kana suka saki juna, shiga mota Ahmad yayi ya tada, lek'owa yayi ta window yace

 "Kace ma Princess, koda ban dawo ba ta cigaba daga inda na tsaya I know zata iya, I trust her..."

D'aga mashi kai yayi alamar "to", motarshi yama wuta ya bar haraban gidan, d'aga mashi hannu Imran ya dingayi har sai da yaga ya bar gidan kana ya sauke hannunshi ya koma cikin gida, jikinshi duk babu kwari......

  Haka Ahmad ya hau hanyar daura sai fatan Allah ya kaishi lafiya ya mai doshi lafiya...          FLASH BACK

 Imran Sadeeq haiffen d'an katsina ne, a unguwar saulawa, maihaifiyar Imran ta haifi mata biyar amma babu wanda ya tsaya, suna da shekara uku suke fara wasu k'uraje daga nan sai su mutu, tun da tasamu cikin Imran take rok'on Allah yasa ya tsaya harta haifeshi bata daina rok'on Allah cikin Imran na da wata biyar mahaifinshin ya kwanta ya rasu sanadiyar rashin lafiya da yayi, Imran har ya girma ya wuce shekarun da yaranta ke mutuwa, San duniya ta d'aukeshi ta d'aura akan Imran amma duk da haka bata fasa bashi tarbiya ba, kuma ta bashi ilimin boko da na Allah. K'awancen Ahmad da Imran ya samo a saline tun suna yara unguwa d'aya suke, haka makaranta d'aya sukayi tun daga primary har zuwa jami'a dake cikin garin katsina...

 Ahmad d'an k'anin baban Ramlah ne Alhaji Habeebu, iyayenshi sun rasu sanadiyar gobara da sukayi cikin dare lokacin Ahmad yana gidan yayan babanshi, a lokacin baisan mutuwa ba shiyasa mutuwar bata dameshi ba. Bayan rasuwan iyayenshi gaba d'aya rik'onshi ya koma wajen yayan babanshi, ba abinda ya nema ya rasa na rayuwa shiyasa bai San minene maraici ba...

  Suna aji hud'u primary school shida Imran, Aisha matar Alhaji Habeebu ta haifi d'iyarta kyakyawa, wadda taci suna Ramlah tunda Imran ya ga Ramlah yace ya samu mata, duk idan ya dawo daga makaranta yana nan mak'ale da Ramlah bacci kawai ke rabashi da ita, shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakanin Ramlah da Imran ko hannun wa take da taga Imran ta dinga kuka kenan sai an sauke ta ta tafi wajenshi. haka Ramlah ta taso cikin so da k'auna kowa santa yake saboda Ramlah nada shiga rai, duk abinda Imran ya samo ramlah yake kawo mawa. tana girma shak'uwa na k'ara shiga tsakanin ta da Imran....

  Imran na aji biyu jami'a lokacin Ramlah na ss2 lokacin gaba d'aya komai na budurwa ya gama fito mata, gakuma samari da suke kawo Mata hari, ganin haka yasa hankalin Imran ya tashi, samun Ahmad yayi ciki damuwa shi dai zai gaya ma Ramlah yana santa, dan gani ya keyi kamar za'a kwace mashi ita. Dariya Ahmad yayi har yana kama ciki yace

"Ai sai da nace ka gaya mata kace kafisan sai ta gama makaranta to yanzu ay gashi nan kanaji kana gani zata zama rabon wani.."

  Bugu ya kai mashi Ahmad ya goce yana dariya.

"Ramlah ta wace ni kad'ai babu wanda ya isa ya mallaketa sai ni dan haka kasa a ranka yau zan gaya mata abinda ke cikin zuciya"

Dafashi Imran yayi yace

"Abinda ya kamata kayi kenan dan haka ina bayan ka d'ari bisa d'ari.."

Rungume juna sukayi suna dariya cikin so da k'auna.....


             *********

  Kwance take d'aki wayarta tayi ringing, yi tayi kamar bazata d'auka ba sai da wayan ya kusa tsinkewa kana ta d'auka ganin wanda ke kiranta ne yasa ta fad'ad'a murmushin ta d'auka tayi cikin shagwab'a tace

"Ya Imran Ina ka shige duk yau banga ka ba?"

Wani irin murmushi ya saki wanda shi kad'ai yasan fassaranshi yace

"Yi hak'uri angel mun fita ne da Ahmad amma after magrib zamu dawo so ki shirya ina da maganan da zan gaya maki.."

  Bai jira mi tace ba ya kashe wayanshi, kan gado ta fad'a tare da sakin murmushi mai tarin ma'ana kala kala ita kanta tasan idan tana tare da Imran Wani irin yanayi take tsintar kanta dashi, wanda ita kanta batasa ma'anar shiba kawai ta barshi akan shak'uwa dake tsaninsu ne. Haka ta dinga juyi bisa gado tana murmushi da haka har bacci yayi gaba da ita.....Don't forget to vote comments nd follow thnx y'all

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI


   Rubutawa 

       Yar_ficika


®NWA

Wattpad yar_ficikaBABI NA ASHIRIN DA BIYU


  Bata tashi daga bacci ba sai k'arfe shidda na dare, da sauri ta diro daga kan gado ta nufi toilet wanka tayi tare da alwalla sai da ta gabatar da sallah la'asar kana ta nufi dressing mirror, kwalliya ta tsantsara kana ta nufi gaban wardrobe atamfa ta d'auko holland lemon green ta saka, d'inkin doguwar riga ya zauna d'as a jikinta. D'aurin d'an kwali ta kata kamar ta nad'a gwargwaro k'ara feshe kanta tayi da turaruka kala kala, kallon kanta tayi cikin madubi Wani irin murmushi ta saki wanda ita kanta bata san ta iyashi ba....

  Zaune take bakin gado aka kira sallah magrib tashi tayi ta kabbara sallah, tana gamawa tayi adu'onta ta Shafa tana nan bisa carpet wayarta tayi ringing alaman sak'o ya shigo. Bud'awa tayi dan tasan daga inda sak'on ya fito.

"Ina d'akin Ahmad"

  Abinda yace kenan, tashi tayi ta d'auki mayafinta ta nufi d'akin Ahmad, a corridor suka had'u da Ahmad kallonta yayi sama da k'asa yace 

"Wannan kwaliyan fa? Duk Imran aka mawa?"

Zumb'uro baki tayi tace

  "Wallahi yaya Ahmad ni bashi namawa ba kaina namawa"

Dariya yayi tare da Jan hancinta yace

"Wuce kije amma nasan karya kikeyi"

Dariya tayi ta yi gaba. Tana isa k'ofar d'akin Ahmad taji gabanta yana fad'uwa daurewa tayi ta shiga da sallama, juyowa yayi tare da amsa mata sallama yana jifarta da wani murmushi..

  Ji tayi k'afafuwanta sun kasa d'aukarta dan wani kyau da kwarjini da ya mata yau bata tab'a tunanin yana dashi ba.

 A b'an garenshi shima gani yayi ta canza ta mashi kyau fiye da sauran lokutan da yake ganinta. K'arasowa yayi inda take tsaye, iska ya hura mata a hankali tayi Ajiyan zuciya tare da kallon k'asa..

 "Irin wannan kyau haka da kikayi"

Cikin kwanyar kanta ta jiyo muryanshi yana magana. D'agowa tayi ta turo baki kamar zatayi kuka, hannunta yaja ya zaunar da ita saman kujera dan bai iya jure shagwab'an da zata mashi. Kusa da ita ya samu ya zauna, sun kai kusan minti biyar babu wanda yayi magana. A hankali ya kira sunanta

"Ramlah"

Wani iri taji har cikin zuciyanta ji tayi babu wanda ya iya kiran sunanta irin Imran ko dan bai tab'a kiranta da sunan ta ba sai dai angel. Kasa d'agowa tayi ta kalleshi bare kuma ta amsa. Sake kiranta yayi d'agowa tayi suka had'a ido ganin yanayin da yake ciki yasa tayi sauri tayi k'asa da idonta. Bai damu ba ya cigaba da magana

 "Ramlah tun randa aka haifeki Allah yasa man sanki a lokacin bansan miye so ba amma nasan dai Ina sanki, Ina girma sanki na k'ara girma na d'auka shak'uwa ce da mukayi sai daga baya na gane sanki nake kece mahad'in rayuwata a yanzu na gane bazan iya rayuwa babu ke ba, Allah ya kawoki duniyata danni kad'ai a yau zan gaya maki abinda ke raina Ramlah Ina sanki san da bazan iya misalta shi ba Ramlah kece rayuwata kece komai nawa inasan ki taimaka ki zama abokiyar rayuwata."

 Tunda ya fara magana kanta yake k'asa tabbas itama sai a yanzu tasan bata iya rayuwa babu Imran kusa da ita duniyarta bazata zama daidai ba sai tare da taimakon Imran.

  Jin tayi shiru bata ce komai ba yasa ya kira sunanta nan ma shiru tayi bata amsa ba, jikinshi yayi sanyi yana tunanin kodai Ramlah bazata amince dashi ba. D'agota yayi yace

"Kiyi magana please"

  A sanyaye tace

"Kaban lokaci zanyi shawara"

  Murmushi yayi wanda bai kai ciki ba yace

"A iya sanina ba kida abokin shawara sai ni? Dan haka gani kiyi shawara dani"

Zumb'uro baki tayi

"Ni dai gaskia sai nayi shawara yanzu ba zanyi shawara da kai ba"

 Dariya yayi yace

"A yau nake san naji matsayina wajen angel."

  Tashi tayi tsaye ta kalleshi

"Ya Imran duk abinda kake ji dashi game dani haka nima nake ji game da kai kasani zuciyan Ramlah ba kowa sai kai kaine sarki cikin zuciyan Ramlah na baka ita kayi duk yanda ka gadama da ita a yau na tabbatar ma kaina bazan iya rayuwa ba batare da kai ba ya Imran I love you more than you love me (ya Imran Ina sanka fiye da yanda kake sona)." Tana gama fad'in haka ta ruga da gudu cikin gida, karo sukayi da Ahmad yana daidai shigowa har ta yarda mashi tray d'in da ke hannunshi, bata ko tsaya bi ta kanshi ba bare tasan ta mashi barna.....

  Girgiza kai yayi ya kwashi tray d'inshi ya kutsa kai cikin d'aki, yana shiga ya samu Imran yana surutu shi kad'ai

"Ramlah Ina sanki kamar yanda uwa ke san d'anta Ina sanki fiye da komai a duniyar nan a yau nasan nafi kowa sa'a a duniya tabbas zan zama fitilar da zaki dinga gani a duniyarki." Haka ya dinga surutai shi kad'ai

  Zama Ahmad yayi kusa dashi, dafashi yayi tare da cewa

"Yadai malam Imran? Kodai ka tab'u ne?"

  Bugu ya kai mashi yace

"Akan Ramlah abinda yafi tab'uwa ma zanyi"

 Tab'e baki yayi yace

"Ai naga duk kun tab'u ita kanta ban kad'eni tayi bata ko tsaya ba bare taga b'arnar da taman."

 Dariya Imran yayi yace 

"Malam bazaka gane miye so ba sai ka fad'a tarkonshi, a yanzu gani nake nafi kowa sa'a a duniyar nan."

"Aiko kafi kowa sa'a dan abincinmu da na d'auko Ramlah ta kifar dashi kuma wallah sai dai yunwar da kakeji ta kashe ka dan bazan koma kitchen ba."

"Dariya Imran yayi yace 

"Kafin inga angel nake Jin yunwa amma wallahi yanzu ganinta yasa na k'oshi"

  Tab'e baki Ahmad yayi yace kunji dashi ni kaga natafi masallaci, tare suka mik'e suka nufi masallaci..

  Tana fita ta nufi d'akin mamarta fad'awa tayi kan cinyarta, d'agota tayi tace 

"Ramlah karki karyani"

K'ara shiga jikinta tayi tana dariya, murmushi tayi tace 

"Miya saki farin ciki haka? Kodai kyauta Imran ya maki?"

 Sunne kanta tayi jikin Mamarta tana dariya, d'agota tayi tace gayaman mana, kafin ta bata amsa Ahmad ya shigo da sallama. Tashi tayi daga jikin mamanta tace

"Please big bro don't say anything (dan Allah babban yaya karka ce komai)"

  Harara ya b'alla mata yace 

"Sai na fad'a"

   Murmushi maman tayi tace

"Son mike faruwa?"

"Mama yarinyar nan tana ganin yanda muke jin yunwa ta taho da gudu kamar mahaukaciya ta b'are mana abinci kuma ko ta tsaya sai ma kai da tasa tayi gaba."

 Kallonta tayi tace

"Garin ya haka ta faru?"

 Turo baki tayi tace 

"Bangani ba fa Mama"

"Eh nasan baki gani ba amma miye saki gudu"

"Bakomai"

  Zaro ido yayi yace 

"Bakomai?"

  Shiru tayi, dariya yayi yace Mama ni zan gaya maki komai kuwa, marairaicewa tayi, dariya yayi yace

"Wallahi sai na fad'i"

  Zama ya gyara, kafin ya fara magana sukaji ance

"Nima Bari in shigo ayi dani"

Ganin Alhaji Habeebu yasa Ramlah ta tashi ta ruga d'akinta.

  Zama Alhaji ya gyara yace

"Son mike faruwa?"

  Murmushi yayi ya kwashe komai ya gaya masu, ba abun mamaki baneba dan ganin yanda shak'uwa mai k'arfi ta shiga tsakanin Ramlah da Imran, dukansu sunyi murna da jin wannan maganar dan sun San Imran yana da halin kwarai kuma sun San ko bayan ransu zai rik'e masu Ramlah...


             **********

Soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin Ramlah da Imran kowa burinshi ya kyautata ma d'an uwanshi yake, tsaftatacciyar soyayya sukeyi babu mai San yaga d'aya cikin damuwa, soyayyan Imran da Ramlah ta zagaye dangi babu wanda bai san da wannan soyayya ba....


  Imran na aji uku jami'a Allah yayi ma mahaifiyarshi rasuwa, yayi kuka kamar ranshi zai fita, ya daina cin abinci sai idan Ramlah ta tsareshi watarana ma sai ta sa mashi kuka kana yakeci, bayan bakwai Alhaji Habeebu ya nemi Imran da ya dawo gidanshi tunda dama bacci kawai ke baiyi gidan, bai musa ba haka ya tattaro ya dawo gidan Alhaji Habeebu, tun da ya dawo gidan gaba d'aya komai na Imran Ramlah ke mashi, kullum cikin yi mata gori ahmad yake, idan ya ishesu sai Mama tace

"Kaima ka samo mata"

  Da an fara fad'a mashi haka sai yayi shiru saboda tsoron mata yakeyi shi gani yake soyayya b'ata lokaci ne....


            ********

Su Imran sun k'are karatu cikin sa'a bayan result ya fito Alhaji Habeebu ya samo masu aiki a company d'inshi. Tun da Imran ya fara aiki, ya fara maganar aure anso ya bari sai Ramlah ta shiga aji uku dan A lokacin tana aji d'aya jami'a Amma ya dage shi dai lokacin yakeso ayi komai, bayan da Alhaji Habeebu ya iya dole yasa aka saka biki, anso a had'a da na Imran to shi ko budurwa bai da ita.

  Alhaji Habeebu shi yayi komai b'angaren ango da amarya dan yace "shima Imran d'anshi ne, haka akayi biki aka gama cikin jin dad'i, inda amarya ta tare a gidanta dake barhim...

  Zaune suke cikin so da k'aunar juna babu maisan yaga ran d'an uwanshi ya b'aci, randa suka cika shekara da aure ranan Ramlah ta haihu ta samu d'iyarta mace, zo kaga murna wajen Imran, ranan suna yarinya taci sunan maman Imran Ameena amma suna kiranta da Haneefa....


   Haihuwar Haneefa da wata uku Allah yama mahaifan Ramlah rasuwa, sakamakon had'arin Jirgin sama da sukayi. Tayi kuka kamar ranta zai fita, daga k'arshe ta dangana, tun daga lokacin Imran ya k'ara jin tausayinta dan gani yakeyi yanzu bata da kowa sai shi mijinta Sai kuma d'an uwanta Ahmad...
Vote

Comments 

Share 

Nd 

Follow 

"Team MKA

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI


   Rubutawa 

       Yar_ficika


®NWA

Wattpad yar_ficika
This page is for you matar Aminina Maryam kwaiseh (Inna Maryama) my personal person, my partner in crime, my annoying babe, my idiot😡 you knw I love you amma kad'an fa🙅🏼‍♀ nasan zaki tsaneni a wannan page din don't mind me next page zakiji dad'i sai kinyi dariya😇 I love you babe♥BABI NA ASHIRIN DA UKU


 Haka zaman Imran da Ramlah ya kasance cikin so da k'aunar juna, kullum tattalinta yakeyi, duk abinda Ramlah keso shi Imran keyi baiso ko kad'an ya ganta cikin damuwa. Shekaran Haneefa uku Allah ya k'ara azurta Ramlah da haihuwa inda ta samu namiji, ranan suna yaci suna Alhaji Habeebu amma suna kiranshi da Haneef, haka suka cigaba da kula da yaransu sun basu tarbiya daidai gwargwado, Haneef na da shekara biyu ramlah ta haifi Mukhtar murna waje Imran ba'a magana, yaso ya saka sunan Ahmad sai Ahmad yace mukhtar za'a sa mashi saboda sunan babanshi ne kuma baza'a b'oye mashi ba.

  Haka yaran suka taso cikin so da k'aunar iyayensu, duk abinda suke so iyayensu zasuyi masu muddin bai kauce ma fad'ar Allah ba. Kullum cikin yima Ahmad gori Imran yake dan yayi aure, sai dai yayi murmushi yace

  "Ina ga matata bata duniya"

    Tun rashin auren Ahmad na damun Imran da Ramlah har suka hak'ura suka sa mashi ido, idan Imran ya matsa mashi da cewa ko dan ka haihu ya kamata kayi aure sai yayi dariya yace

"Tunda kai da Ramlah kun haifaman Ai kamar ni na haifesu ne."

  Dan dole suka sa mashi ido suka daina mashi maganar aure sai dai kullum suna mashi adu'a Allah ya bashi mata ta gari.. 


              ************

  Zaune suke parlour suna fira, Mukhtar na saman cinyarta yayi bacci Haneefa da Haneef suna kallon cartoon, kallonshi tayi tace

"Hayatee yau zamu je yawo after isha"

 "Ina zamu je?"

  Abinda yace mata kenan, murmushi tayi tace

"Wait and see (tsaya ka gani)" girgiza kanshi yayi alamar "to..."

   Shirya yaranta tayi cikin shigar k'ananan kaya, Itama shiryawa tayi cikin bak'ar abaya, parlour suka fito inda yake zaune, kallonsu yayi da mamaki

"Wai dagaske kike fita zamuyi?"

  Zumb'uro baki tayi tace 

"Bana gaya maka ba"

  Murmushi yayi ya tashi zuwa yayi daf da ita, ya kama bakin ya murd'e yace 

"Sai yaushe zaki san kin girma harda yara uku? Amma kullum k'ara shagwab'a kike"

K'ara ta saki dan bakin har zafi yake mata, sakinta yayi yana dariyan mugunta ya wuce d'aki da gudu ta bishi, suna shiga ya janyo ta da k'arfi ta fad'o jikinshi, marairacewa ta farayi tana ta tuba. Hancinta yaja yace

  "Matsoraciyya"

Ita ta taimaka mashi ya shirya shima cikin k'ananan kaya. A jere suka fito kamar sabbin aure, k'arasowa sukayi parlour d'aukar Mukhtar tayi shikuma ya d'aukar mata handbag d'inta ya kama hannun Haneef suka fita. 

  Suna isa parking space ya bud'e mota Haneef da Haneefa suka shiga mik'a mashi Mukhtar tayi tace

"Bani key"

  Ba musu ya karb'i Mukhtar ya mik'a mata key ya shiga mota itama shiga tayi tama motar wuta suka bae haraban gidan....

  Basu tsaya ko Ina ba sai wajen salah, suna zuwa tayi parking duk suka fito, sukayi ciki suna isa aka kawo masu menu mik'ama Haneefa tayi ta zab'i abinda zataci, shawarma ta zab'a shima Haneef shi ya zab'a. Kallon Imran tayi tace

  "Kai kuma sai abinda na zab'ar maka."

Murmushi yayi yace

"An gama madam"

   Dariya tayi ta zab'ar mashi fried rice nd coslow sai ferfesun cow leg, itama shi ta zab'a ta bada order, jim kad'an aka kawo masu suka faraci suna ci suna fira kai da kagansu kasan akwai soyayya mai k'arfi tsakanin wannan familyn. Suna gama ci aka mata bill ta biya tashi sukayi suka fita...

  Tunda suka iso hankalinta gaba d'aya ya koma kansu, duk Abinda sukeyi akan idonta gaba d'aya sun gama tafiya da imanin ta ,duniya ji tayi babu wanda ya mata irin Imran lokaci guda kuma taji ta tsani matarshi zata iya komai dan ta rabasu ita kuma ta samu shiga, suna tashi ta tashi ta bisu, daga nesa ta dai dai ta camera d'inta tayi zooming ta d'auki number motar hoto ta koma ciki....

  Tana shiga ciki, k'awarta tace 

"Mufeedah Ina kikaje?"

Dariya tayi tace

"Sabon kamu nayi"

 "Sabon kamu?"

   Ta tambayeta dan bata gane maganarta ba. Dariya tayi tace

"Haka nace"

"Ayna kenan? Nidai naga muna nan kuma babu wanda yazo wajenmu."

  Murmushi tayi tace

"Baki ga wanda suka zauna nan ba?"

"Nagani"

"To shi naji inaso kuma san da zan iya kauda ko waye ya nemi hanani tarayya dashi.."

  Ido ta zaro tace

"Ba gaskia bane ba akwai dai abinda kika hango a wajenshi."

  Dariya tayi tace

"Kina da ganewa gaskia ne daga ganinshi yana da abun hannunshi ni kuma kinsan duk hannu mai maik'o shi nake bi.."

"Amma Mufeedah kina ganin zaki samu shiga wajen shi? Jifa yanda yake tarairayan matarshi da d'iyanta."

  Dariya tayi tace

"Lash kin manta wacece Mufeedah kenan kin manta Ban tab'a neman abu na rasa ba, Bari in gaya maki tunda na kalli matarshi naji na tsaneta dan haka ko ta halin k'ak'a Sai na shiga gidan mutumin nan sai na tarwatsa gidanshi na dasa masu bak'in ciki daga nan nikuma in kwashe kud'inshi in k'ara gaba, shiyasa na bisu na d'auki number motarshi hoto dan gobe asuba gurin boka na kan dumbus zataman.."

  Dariya Lash tayi tace

"Nasan zakiyi fiye da haka akan abinda kikeso to banda shakku akanki."

Tab'awa sukayi suna dariya....


           *********

  Tunda asuba ta tashi dan tafiya wajen boka, k'arfe bakwai dai dai tana zaune gaban boka Dumbus, tana mashi bayani. Dariya yayi yace

"Tun kafin kizo nan an man bayanin zuwan Ki."

  Wata kwarya ya jawo gabanshi yayi siddabarunshi kallonta yayi yace

"Matso nan"

 Tana matsawa ta kai fuskan ta wajen kwaryan da sauri ta d'ago dan ganin wanda Ke jikin kwaryan.

"Imran ne jikin kwaryan."

   Wata irin dariya boka ya saki yace

"Ko bashi bane?"

  D'aga kai tayi alama shine, dariya boka ya saki yace

"Daga yau ki fara d'aukar kanki a matsayin matar Imran, kuma idan kika bi abinda nace to sai yanda kikayi dashi, wani abu ya d'auko d'aure yace kisan yanda zakiyi kin saka wannan layar cikin gidanshi idan kika saka to bazai tab'a maki gardama ba akan aurenki ke sai yanda ma kikayi dashi."

  Zaro ido tayi tace

"Boka Taya nida ko sunanshi bakinka naji bare har nasan gidanshi."

 Hak'oranshi ya washe yace

"Da kanki kuma zaki saka akwai ruwan maganin da zan baki da kin kusa shiga gari ki shafashi ki kira sunanshi sau uku kije titin barhim da k'arfe shida zaki had'u dashi."

Murmushi ta saki dan tasan halin boka zaiyi fiye da haka, kud'i ta aje mashi ta mashi ban kwana ta fito....              ***********

  Biyar da rabi ta isa cikin garin katsina, ruwan maganin ta d'auko ta shafa tayi duk yanda boka yace mata.

  "Titin Barhim zaka kaini"

Abinda tace ma mai napep ke nan, titin barhim ya kaita ya ajeta, ta kusan minti sha biyar tsaye ba taga alaman Imran zai zo ba har ta fara sarewa. Daga nesa ta hango motarshi wata Ajiyan zuciya ta saki dan ko mafarki ta tashi zata gane number motar. Yana k'arasowa daidai wajenta, juya kai tayi kamar bata san ya iso ba..

"I found my missing rib"

  Abinda taji yace kenan, shiru tayi kamar ba taji shi ba, k'arasowa yayi kusa da ita yace

"Malama ina magana"

  Kallonshi tayi sama da k'asa ta watsar.

"Wow Allah yayi halitta nan"

  Kallon kanta tayi dan tasan ya dai fad'a ne amma bawani kyau ne da ita ba....

  "Dan Allah kiman magana ko naji sanyi"

Kallonshi tayi tace

Mizance maka?"

"Komai ma kifad'a"

"Ni dai sunana Imran"

  Abun ba k'aramin mamaki ya bata ba dan tun tana wajen boka ya gaya mata sunan shi, amma wani lokacin tasan boka Dumbus zaiyi abinda yafi haka.

"Ina magana kinyi shiru"

  Ajiyan zuciya tayi ranta fes ta ya tsina fuska tace 

"Mizance?"

"Komai ma kice

"Sunana mufeedah"

"What a nice name"

  Murmushi tayi da bai kai ciki ba, yace

"Muje in kaiki inda zaki "

"Karka damu ka barshi"

   Haka ya dinga mata magiya amma ta kafe, dan dole ya hak'ura amma sai da sukayi exchanging phone number. Yana tafiya ta tsaida napep cema mai napep tayi ya dinga binsa a baya amma a hankali karya gane suna binshi, haka kuwa akayi suka dinga binshi har suka iso gidan, tana ganin gidan yasa tayi dariya ta cema mai napep su tafi....


   K'arfe 8:00pm dai-dai ta dawo k'ofar gidan Imran, knocking tayi mai gadi ya lek'o gaidashi tayi tace

"Nazo wajen matar gidan ne, mu bak'i ne bayansu muke shine nake shiga muna gaisawa.."

  Mai gadi najin haka ya bud'e mata gate ta kutsa kai cikin gidan.

  Wata hanya ta gani, hanyar tabi cikin ikon Allah tana isa taga wani d'an wuri da k'asa tona wurin tayi ta binne layar ba tare da wani ya ganta ba, tana gamawa ta mik'e cikin farin ciki ta nufi hanyar fita, bankwana tama mai gadi ta fita ranta fes da tabbacin zatayi nasara...  Tun randa Mufeedah ta binne laya, Imran ya kasa zaune ya kasa tsaye burinshi dai ya auri Mufeedah, ita kuma sai yawo take mashi da hankali, da kyar ya samu ta amince zata aureshi....

  Ahmad ya samu da maganar k'ara aure ba k'aramin tashin hankali Ahmad ya shiga ba sakamakon bincike da yayi akan wacece Mufeedah, da kuma irin rayuwar da takeyi, koda ya zoma Imran da maganar ya janye auren Mufeedah saboda ba d'iyar kirki bace ba bama a gidan iyayenta take zaune ba wajen saurayinta take zaune. Ba k'aramin fad'a sukayi ba dan Imran cewa yayi sharri ne ake mata amma mufeedah natsattsa ce. Da yaga ba yanda ya iya dole ya saka mashi ido dan Imran baijin maganar kowa akan auren Mufeedah. Haka akayi bikin Imran da Mufeedah babu wani danginta sai abokanta yan bariki. Ba yanda Ahmad ya iya haka ya shiga cikin hidima dole aka dinga komai dashi....
            CIGABAN LABARI

   Tafe yake yana tuk'i cikin kwanciyar hankali, bakajin komai sai k'arar karatun al qur'ani. K'arfe shida (6:00pm) ya isa daura da kwatance ya gane gidan Malam Andu. Zaune yake k'ofar gida yana karatu.

  Sallama ya mashi, d'agowa malam Audu yayi da fara'arsa ya amsa tare da mik'a mashi hannu sukayi musabaha....

"Malam wajenka nazo"

"Bismillah ka zauna to"

  Wuri ya samu ya zauna tare da tan kwashe k'afa.

"Malam mike tafe dakai?"

  Zama ya gyara yace

"Ni dai sunana ahmad kuma wani bawan Allah ne yaman kwatancenka saboda Ina cikin matsala yace idan nazo wajenka in shaa Allah komai zai zo da sauki, to shine nazo yau danni mutumin katsina ne.."

"Allah sarki"

  Abinda malam yace kenan 

"To malam Ahmad Ina jinka mike tafe dakai?"

  Zama Ahmad ya gyara ya warware ma malam komai tun daga farko har yanzu ba abinda Ahmad ya rage ma malam...

  Shiru malam yayi na d'an wani lokaci kana ya maida dubanshi ga Ahmad yace 

"Ina zuwa"

  Tashi yayi ya shiga gida, jim kad'an ya fito daga gidan...

  Zama yayi yana mai kallon Ahmad yace

"Gaskia asiri ne aka mashi kuma muddin ba a karya asirin ba to bazai tab'a komawa daidai ba kuma wadda ta mashi asirin bata aure shi dan tana sanshi bane ba ta aure shi ne dan ta rabashi da iyalanshi kuma ta cinye mashi dukiya, kuma asirin da aka mashi yana nan cikin gidan ba wani wuri aka kai shi ba cikin gidan aka binne koma miye, dan haka sai kun tashi tsaye kun cire komai kana, Kuma duk ruwan shanshi ya zama akwai adu'o'i ciki to in shaa Allah za'ayi nasara kuma dole sai ya dage da yin azakar saboda akwai sakacin Adu'a tare dashi, amma in shaa Allah komai yazo k'arshe, yanzu akwai wani ruwan magani da zan baka sau uku zai wanke fuskarshi dashi sai kuma ya kurb'a ma'ana na kwana uku he duk sanda zai wanke fuskanshin ya kurb'i ruwan to duk wani sammu da aka mashi wanda yaci zai karye idan akayi wannan kuma aka cire layun dake cikin gidan to komai yazo k'arshe dan zai dawo cikin hayyacinshi"

  Tashi malam yayi yaje ya kawo ruwan magani ya ba Ahmad, godia Ahmad ya mashi tare da aje malam rapper 200. Godiya malam ya ma Ahmad.

  Sai da sukayi sallah magrib kana Ahmad yama malam bankwana ya kamo hanyar katsina...


  Tafiya yake yana tunanin ta Ina zai fara baisan ta inda zai fara neman layun ba amma koma dai yane in shaa Allah sai yayi iya k'ok'arinshi ya karya asirin nan ko dan k'anwarshi da amininshi su koma masoyansu nada, Sai da yay tafiya mai nisa kana ya kira Imran dan Sai da ya kusa shiga katsina kana ya kiranshi, bugu uku ya d'auka gaisawa sukayi Ahmad yace

"Ina kan hanya zan dawo yanzu"

"Allah ya maidoka lafiya d'an uwana"

 Kashe wayar yayi sakamakon kanshi da yaji yana juya mashi, ji yayi idonshi na rufewa alamar yana jin bacci, ga kuma kanshi da ke sara mashi kamar zai b'are biyu..

  Gani yayi wani abu ya gifta mashi kamar mashi, gaba d'aya ya saki sitiyarin yayi cikin daji wani icce ya buga sai da motar ta lotsa....

  Wasu ne dake gefen titin sukayo kanshi da gudu, dan duk abinda faru akan idonsu ya faru.

  Dakyar suka jawoshi daga cikin mota, ganin baya numfashi yasa suka tsaida wata motar suka kwashi abubuwanshi masu amfani suka nufi cikin gari dashi dan kaishi asibiti....Hmmmm nasan dayawa baza kuji dad'in Page d'innan ba amma kuyi hak'uri next page zakijini dad'i trust me bazan baku kunya ba, thnx y'all nd I love you from the bottom of my heart ♥ 

  Don't forget to vote comments follow nd share it mean a lot to me❤

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI


   Rubutawa 

       Yar_ficika


®NWA

Wattpad yar_ficika
BABI NA ASHIRIN DA HUD'U  Medical center suka nufa dashi, suna zuwa akayi emergency dashi. Likitoci uku ne kanshi da kyar suka ceto numfashinshi ya koma daidai. Allura aka mashi aka d'aura mashi k'arin ruwa, ga kanshi da aka d'aure saboda jini dake zuba....

  Zaune yake yayi tagumi ya rasa Abinda ke mashi dad'i. Haka b'angaren Ramlah abun yake, tun da marece take jin gabanta na fad'uwa ta rasa dalili.

  Wayar Imran ne tayi ringing kamar jira yake da sauri ya duba ganin waye ya kira yasa ya saki numfashi.

"Hello dan Allah Imran ne?"

"Eh shine ya amsa da kyar gabanshi sai fad'uwa yakeyi."

"Dama mai wayar nan ne yayi accident yana medical center nan emergency, mun duba munga kaine mutum na k'arshe da kukayi waya da shi shine muka kiraka."

"What?"

  Ya mik'e tsaye ga zufa na karyo mashi.

"Ai na yayi accident d'in?"

  Basu bashi amsa ba suka kashe waya, dai-dai Ramlah ta fito daga d'aki.

"Imran lafiya?" 

Ta tambaya, baiko kalli inda take ba haka bai bata amsa ba yasa kai ya wuce, sai da ya kai bakin k'ofa kana yace mata

"Ahmad ne yayi accident yana medical center a nan emergency."

  Yana fad'ar haka yayi waje..

  Kuka ta fashe dashi tayi d'akinta da gudu, hijab ta d'auko da key d'in mota tayi waje, tana shiga ta tada motar horn ta dinga ma maigadi kamar zata b'alle gate d'in da sauri ya wangale mata gate tayi waje. Gudu take sosai kamar zata tashi sama, Allah ne kawai ya kaita asibiti lafiya...

  Kusan tare suka isa asibitin ita da Imran, a tare suka shiga emergency Amma babu wanda kema d'an uwarshi magana. Basu sha wahala ba suka gane inda yake, kallo d'aya zaka mashi kasan yana jin jiki, k'arasawa sukayi wajenshi gaba d'ayansu. Hawaye Imran yakeyi

"D'an uwana haka ka koma? Duk dan kasama man farin ciki miyasa ban hanaka tafiya ba a lokacin da kace man zaka tafi miyasa ban bika ba miyasa kullum burinka ka faranta man koda kai zaka k'untata."

  Haka ya dinga surutu yana kuka, fad'awa Ramlah tayi jikinshi tana kuka sosai.

"Ya Ahmad please ka tashi kada Kaima ka tafi kamar yanda Mama da Baba da Haneef suka tafi dan Allah ka tashi kai kad'ai kaman saura kaine gata na idan ka tafi bansan inda zan saka kaina ba ya Ahmad ka tashi nasan kana jina, na yafe zan zauna da Imran cikin k'unci basai ya kulani ba indai zan dinga ganinka kusa dani yafi man komai.."

  Kuka take tana sabbatu kamar zararra, Imran ne yazo kusa da ita ya janyeta fizgewa tayi ta koma jikin ahmad tana kuka. K'ara ta kowa yayi yazo ya janyeta ya k'ank'ameta jikinshi, ji yayi wani abu na mashi yawo cikin kanshi da sauri ya ingijeta gefe guda yana huci..

  Fashewa tayi da sabon kuka ita kad'ai tasan halin da take ciki, tabbas tasan tayi missing d'in mijinta har dai yau da ya had'a jikinta da nashi, ita kanta tasan tana kewarshi...

  Ganin kuka bai mata ta shiga toilet ta d'auro alwalla zuwa tayi ta kabbara sallah tana neman ma Ahmad sauk'i. Shiko Imran yana kusa dashi zaune ya kama hannunshi ya rik'e kamar wani zai kwace shi...

  Tana nan zaune bisa sallaya har aka kira sallar asuba tashi tayi ta gabatar da sallah, shima Imran masallacin dake cikin asibitin ya tafi...


  K'arfe bakwai ya dawo in da Ahmad yake, tana nan zaune inda ya barta, kallon gefen da Ahmad yake yayi

"Yakamata kije gida"

  Batace mashi k'ala ba ta tashi ta d'auki jikarta ta fita.....

  Cikin gida ta nufa bakowa parlour d'akin yaranta ta nufa zaune ta gansu sunyi tagumi, d'agowa sukayi dan suga waye zai shigo suna ganinta gaba d'aya sukayi kanta.

"Ammi Ina kikaje?"

  Cewar Haneefa data rik'e hannunta, shiru tayi taja hannun Mukhtar suka zauna.

"Ammi talk to me please (Ammi kiman magana dan Allah)." Hawaye ta share tace uncle Ahmad ne yayi accident yana asibiti. Dasauri Haneefa ta mik'e

"Ammi tun yaushe?"

"Jiya ne "

  Tashi tayi tace

"Kima Mukhtar wanka kema kiyi zanje na had'a breakfast mukoma asibiti."

  Tana fita ta nufi kichen dan shirya kalaci. K'arfe tara dai-dai suka gama shirinsu, basu tsaya kalaci ba suka nufi asibiti cikin motar ba mai magana sai karatun alqur'ani dake tashi k'ira'ar sudais. Koda suka shiga asibitin basu tsaya ko Ina ba sai d'akin da Ahmad yake, da sallama suka shiga. Amsawa yayi batare da ya kalli inda suke ba.

  K'arasawa Haneefa tayi wajen Imran tace

"Daddy Ina kwana?"

"Lafiya"

  Ya bata amsa, shima mukhtar gaidashi yayi ya amsa ba yabo ba fallasa. Gaidashi Ramlah tayi a dak'ile ya amsa, wuri suka samu suka zauna.....


   A hankali ya fara bud'e idonshi har ya gama bud'esu gaba d'aya. Tuna Abinda ya faru dashi jiya yayi, dafe kanshi yayi tare da fad'in 

"Wash"

  Dasauri Ramlah tayi inda yake, shima haka Imran ya tashi ya nufi bakin gadon, sannu suka fara mashi. Murmushi ya masu tare da karkad'a masu kai...

  Kallon Imran yayi ya fara magana

"Imran ga Ramlah nan amana kasani daga randa zan barku daga rannan ta koma bata da kowa sai kai ka tuna halaccin da iyayenta sukayi mana ka rik'e ta amana, naso na ida aiki na akanka amma Allah bai nufa ba, nasani ko da na mutu a yau nasan akwai wanda zai ida abinda na fara dan Allah ka dage da adu'a."

  Hawaye ne suka fara sintiri fuskan Imran tare da rufe mashi baki.

"Ka daina fad'an haka d'an uwana zaka tashi zakaji sauk'i ciwo ba mutuwa ba."

  Girgiza kai yayi yana cije leb'e, hannunshi Ramlah ta damk'e tana kuka.

"Dan Allah ya Ahmad ka daina magana irin haka, kasani bani da kowa sai kai kasani na rasa iyaye na na rasa d'ana na rasa farin cikin mijina na rasa komai nawa k'unci yaman yawa kai ne uwata kaine ubana gashi kaima kana niyar barina dan Allah kayi hak'uri ka tsaya dani zuciyana zata iya tarwatsewa a yayin da naga babu kai kusa dani kaine gatana yanzu.."

  Rik'e mata hannu yayi

"Naso in zauna daku naso in sama maki farin ciki kamar yanda iyayenki suka bani farin ciki amma hakan bazai samu ba, baki rasa komai ba ni nasani Imran na sanki kuma kema kinsan haka daga randa nabar duniya daga rannan za'a cigaba daga inda na tsaya ki dage da adua a yanzu mijinki adu'arki yake nema In shaa Allah watara sai kunyi dariya.."

  Kuka take sosai, Haneefa da Mukhtar suna gefensu Mukhtar kuka yake yayin da Haneefa ta kasa kukan sai dai idonta da yayi ja kamar tarugu. Hannu ya mik'a ma Mukhtar yace

"Babana zo nan"

  Ba musu mukhtar yaje gabanshi shafa kanshi yayi yace 

"Allah ya raya ka kaji babana kasani ina sanku sosai."

Hawaye ya share 

"Muma muna sanka Papa."

  A hankali ya d'ago ya kallesu

"Kubani wuri ina san inyi magana da princess"

Ba musu suka fita, mik'a mata hannu yayi ta k'arasa kusa dashi....

  Murmushi ya sakar mata

"Shekarar ki nawa yanzu?"

"Sha biyar"

  Ta bashi amsa, gyad'a kai yayi yace

"Nasan kinyi k'ank'anta amma sanin da na maki zaki iya nasan zaki iya aiki zan baki naso inyi da kaina amma hakan bazai samu ba, nasan ke kad'ai zaki ida man shi, Haneefa sai kin daure sai kinyi hak'uri aikin akwai wuya Amma nasan zaki iya Allah na tare dake."

  Nan ya kwashe duk yanda sukayi da malam ya gaya mata ya k'ara da cewa

"Amma sai kinbi a hankali saboda Mufeedah ta wuce yanda muka d'auketa, inasan ki tone duk wani asiri da ta binne a cikin gidan nan inasan ruwan Imran na sha ya zamana akwai adu'a ciki, a mota na da nayi accident nasan za'a d'auko ta akwai ruwan magani ya wanke fuskanshi sau uku ya kuma sha, rana uku kenan, ki taimakeni ki ci kaman buri na ki dawo da farin cikin iyayenki nasan zasuyi alfahari dake..."

  Hawaye ta share tare da fad'in

"In shaa Allah Papa zan cika maka burinka duk wuyarshi I want you to be proud of me Papa, zan dawo da farin cikin iyayena no matter how long it will take me, sai na cika maka burinka sai kayi dariya zan daure duk wahalarshi na maka alk'awari."

  Murmushi yayi 

"I trust you my princess kuma inasan abun nan ya zama sirri har sai kin gama aikinki saboda bansan kema a halakaki."

"D'aga mashi kai tayi alamar to, hannunta ya rik'e yana dariya, motsi bakinshi ya farayi yana salati daga baya kuma yayi shiru. Bata kawo komai a ranta ba ta d'auka bacci ya samu....


  Lura tayi kamar baya numfashi, kanta ta kai wajen k'irjinshi Amma da alamu baya numfashi, da gudu ta fita ta nufi waje dai-dai likita na tahowa rik'eta yayi tare da tambayar 

"Lafiya?"

D'akin ta dinga nuna mashi da hannu dan bata iya magana shiga yayi cikin d'akin, ganin haka yasa Imran da Ramlah suka bi doctor d'akin. K'arasawa doctor yayi tare dayi mashi aune aunen, d'agowa doctor yayi ya kallesu

"Am sorry to say he's gone"

"What?"

  Cewar Imran tare da shak'e doctor 

"K'arya kake bai rasu ba bamuyi dashi zai rasu yanzu ba munyi dashi zamu rayu tare taya zai mutu yabarni." 

Da kyar doctor ya kwace kanshi wajen Imran.

  Kanshi Ramlah tayi da gudu tana fad'in

"Ya Ahmad katashi please kada kaman haka kada ka mutu kabarni taya zaka barni cikin Wannan duniyar mai cik'e da rud'ani dan Allah ka tashi ka tausayaman kaine gatana bayan na rasa mahaifana Ina kakeso in saka kaina? Mutuwa Taya zaki man haka wane irin jarabawa ne wannan mai wuyar cinyewa."

  Kuka take tana surutu, Haneefa ce tazo kusa da ita ta janyeta, ita kanta kukan takeyi ta kasa magana sai kuka.

  Imran kuwa kusan zarewa yayi gaba d'aya kuka suke babu mai ba wani hak'uri....


  Ganin kukan bai mashi yasa yaje ya biya Bill aka bashi gawan Ahmad sukayo gida da ita, kafin kace mi mutuwar Ahmad ta zagaye dangi da yan unguwa da abokin arziki, gidan Imran tun kafin ya baro asibiti yafara cika, wanka akama Ahmad aka shiryashi aka d'auke shi aka nufi dashi gidan shi na gaskia, sai dai muyi mashi fatan Allah yasa ya huta...

  Duk wanda ke gidan Imran sai da ya zubda ma Ramlah Hawaye ganin yanda ta koma ta lalace ta fita hayyacinta.. 

  Kowa na zaune parlour ana karb'an gaisuwa ban da Mufeedah da tunda taji labarin mutuwa ta koma d'aki bata fito ba...
         ABINDA YA FARU

  Shigowar ta gida kenan taji Ahmad nama Imran magana akan magani, komawa tayi da baya dan ta gama razana tabbas tasan idan tayi sake Ahmad sai ya ruguza mata shirinta. Ita kuma duk wanda yayi yin k'urin b'ata mata shiri sai ta ga bayanshi...

  Tana shiga d'akinta ta fara zarya cikin d'aki. Boka Dumbus tayi tunanin zuwa wajenshi, tuna yanda sukayi dashi ta tuna tasan ba halin komawa dan bazai saurareta ba. Waya ta jawo ta kira Lash bugu d'aya ta d'auka

"Lash Ina cikin matsala"

  Cewar Mufeedah dake had'a gumi.

"Lafiya Mufeedah?"

  Kwashe komai tayi ta gaya mata ta k'ara da cewa

"Lash idan Ahmad yaje daura komai nawa zai warware inna ce komai Ina nufin komai da kika sani duk shiri na wallahi zai lalace, kuma kinsan yanda mukayi da boka Dumbus bazan iya komawa ba zuwan Ahmad daura barazana ne daga dukkan komai nawa, kuma duk wanda yayi yunk'urin tsaida man aiki na sai na halakashi, dan haka ki samo mana mafita.."

  Numfasawa Lash tayi 

"Karki damu Mufeedah k'arya Ahmad yake yace zai b'ata mana shiri, yanzu ki shirya gobe akwai wani boka dake malumfashi kuma shima aikinshi kamar yankan wuk'a yake sai muje.."

  Sai a sannan Mufeedah ta samu d'an kwanciyar hankali dan tasan Lash da kutse kutse....


  K'arfe goma bukkan boka ta masu, gurfana tayi gaban boka ta warware mashi komai, ta k'ara da cewa

"Boka so nake a kasheshi inasan a datse mashi numfashi dan muddin yana numfashi to zai b'ataman aiki nikuma alk'awari nayi duk wanda ya nemi b'ataman aiki sai na kaseshi..."

  Dariya boka ya saki yace 

"Tashi kuje aikinki ya biya"

kallon boka tayi da mamaki tana neman k'arin bayani. Dariya yayi yace

"Kina tunanin abinda Zanyi ko? To aljani zan tura mashi idan yana hanya shi zaiyi komai kedai ki saurara zakiji ance maki ya rasu.."

  Godiya sukayi ta ajema boka kud'i suka tashi suka bar wajenshi, Lash na k'ara kuranta mata boka....

  Tunda Ahmad yayi tafiya take sauraran taji ance ya rasu, tana mak'ale bakin k'ofa taji wayar Imran tayi ringing da kuma amsar da Imran yaba Ramlah ba k'aramin dad'i taji ba..

 Komawa d'aki tayi da gudu ta d'auki waya ta kira Lash, ta gaya mata komai nan suka shiga murna. Koda aka shigo da gawan Ahmad wani irin dad'i ne ya rufe ta ganin wanda ke neman kawo mata cikas ta kaudashi. Sai dai Mufeedah ta manta da tayi tuya ta manta da albasa.....


  Bayan kwana biyu, Haneefa ce zaune d'akinta tayi tagumi ta rasa taya zata fara aikinta da ta d'aukar ma Papa Alk'awari tabbas tasan aikin akwai wahala amma sai ta cika mashi burinshi tasan zakiji dad'i ko da yana kabari ne, amma ta rasa ta Ina zata fara. Ramlah ce ta shigo da sallama, Haneefa bata san shigowarta ba. Hannunta ta janye daga tagumi ta samu wuri ta zauna kusa da ita. Murmushi tayi tare da fad'in

"Ammi yaushe kika shigo?"

"Ina zaki san nashigo kin tsunduma cikin tunani"

  Dariya tayi tace 

"Wallahi ina tunanin Papa ne "

"Kina tunani Papa ko kina tunanin maganar da kukayi dashi? Wai miye ya ce maki ne ko Allah yasa ina da abinda zan taimaka maki nima dashi.."

 Dariya tayi tace

"Wannan yak'i nane Ammi, and I have to fight it alone, kedai ki tayani da adua, sai na dawo maki da farin cikin ki koda zan rasa nawa farin cikin I want you to be proud of me Ammi."

 Shafa kanta Ramlah tayi tace

"Ina alfahari dake d'iyata kuma In shaa Allah zakiyi nasara kuma adua ta tana binki koda yaushe, kedai kiyi a hankali bansan kema in rasaki, kamar yanda na rasa d'an uwana da D'ana.."

"Kisa a ranki ba zaki rasa ni ba Ammi In shaa Allah.."

  Jawo ta Ramlah tayi ta rungumeta tana k'arajin k'aunar d'iyarta har cikin ranta....
Ana wata ga wata, shin Haneefa zatayi nasara akan Mufeedah Ko kuma Mufeedah zata hallaka Haneefa kamar yanda ta hallaka Ahmad? Duka amsoshinku suna tare dani kudai ku cigaba da bina kuma da bani had'in kai wajen danna Yar tauraruwar nan da kuma shiga d'an akwatin nan dan aje ra'ayoyinku, inasan inga comment yau 1k shi zai saka inji dad'in maku typing har kuzo inda kukeso azo.... thnx y'all....

[13/12 12:35] yar ficika: MAKIRCI KO ASIRI


   Rubutawa 

       Yar_ficika


®NWA

Wattpad yar_ficika
BABI NA ASHIRIN DA BIYAR
BAYAN KWANA BIYU

  Zaune take d'aki tayi ta gumi duk abin duniya ya isheta ta rasa taya zata fara aikin da Papa ya sakata, ita kanta kwakwalwanta ta cunkushe. 

"Anya zan iya kuwa?" 

Tambayar da tama kanta kenan. "Zaki iya kisa a ranki zaki iya kin d'aukar ma Papa alk'awarin zaki iya komai dan kiga burinshi ya cika, kuma ko ba komai zaki dawo da soyayyar iyayenki wanda suka gina tun da dad'ewa rana guda aka tarwatsasu."

  Wata zuciya ce ke fad'a mata haka. Mik'ewa tayi da sauri tare da fad'in 

"Zanyi komai akan Ammi da Daddy dan ganin nadawo masu da farin cikinsu koda kuwa haka na nufin rasa nawa farin cikin..."

  Tashi tayi ta dinga kai komo cikin d'aki ita kad'ai tana sak'awa da warwarewa, k'arasawa tayi jikin window ta yaye labulen window d'in...

"Akwai ruwan magani a mota na inasan Imran yasha ya kuma wanke fuskanshi na kwana uku ne ki taimakeni ki ci kaman burina ki dawo da farin cikin iyayenki nasan zasuyi alfahari dake" tunawa tayi da maganar Ahmad yayi mata da ta ga motarshi anyi parking d'inta...

  Da gudu ta nufi waje, cikin ikon Allah bata tarda kowa ba. Tana bud'e k'ofar motar taji ta bud'e shiga tayi inda direba ke zama ta fara dubawa ba taga komai ba haka ta dinga bin motar tana dubawa amma ba taga komai ba takai kusan minti ashirin tana dubawa amma ba abinda tagani, a kasalance ta fito jikinta duk ya mutu, hawayen da suke mak'ale da ita suka gangaro mata. Goge hawayen tayi cikin kuka take furta.

"Kayafeman Papa na kasa cika maka alk'awari bansan ta ina zan fara ba abun nan yafi k'arfina naso kana raye da komai yanzu yazo k'arshe."

  Kuka takeyi sosai tana surutu.

Magana taji ta rasa ta in maganar ke fitowa duba wa tayi ko ina amma bataga mai maganar ba sai dai ko mafarki ta tashi bazata mance muryan Papa ba.

"Kiyi hak'uri nasan zaki iya nasan akwai wahala amma nasan ke zaki iya ke kad'ai nasan zakiman yanda nakeso ki taimakeni ki dawo da farin cikin ma'auratan nan.."

  Wani k'arfi taji yazo mata, adu'a tayi ta juya ta nufi gida taku biyu tayi ta juyo, cikin motar ta koma ta fara dubawa a hankali. Wata leda taji a k'ark'ashin sit d'in kusa da direba jawota tayi a hankali tana fito da ita, ta bud'e ta ruwa tagani cikin kwalba, ko tantama baza tayi ba tasan wannan sune ruwan da Papa yake nufi.

  Fitowa tayi tana mai hamdala ga Allah ta nufi cikin gida, d'akinta ta nufa ta b'oye ruwan maganin tana ma Allah godiya....


  Fitowa tayi parlour abinda ta tarda bai bata mamaki ba dan ba sabon abu baneba

"Ramlah wallahi na tsaneki na tsani ganinki da zan iya rabuwa dake dana rabu dake dan Allah ki taimaka ki tattara kayanki ki koma BQ Idan na daina ganinki kusa dani zan daina jin rad'ad'in dake damuna.."

Magana yake yana huci, Mufeedah zaune bisa kujera ta d'aura k'afa d'aya kan d'aya tana murnushi.

 Hawayen da suka gangaro mata ta share tare da fad'in

"Karka damu indai ganina ne ke sa kanajin wani iri a rayuwanka zaka daina ganina Daga yau wallahi da zaka sakeni dana fi buk'atan haka dan yanzu nafisan nayi rayuwa ni kad'ai."

"Darling ka saketa mana tunda ta buk'aci sakin da kanta.."

"Wallahi da zan iya sakinta dana saketa to sakinta wani baraza nane ga rayuwata amma ta tattara tabar cikin gidan nan bana buk'atar ganinta.."

 K'arasowa Haneefa tayi inda Ramlah take duk'e tana kuka, kamata tayi ta tashi, dubanta ta kai wajen Mufeedah tace

"Ki guji randa asirinki zai tonu nayi alk'awarin sai na tona duk wani asiri naki..."

  Tana gama fad'in haka taja mahaifiyarta suka bar parlourn, mik'ewa Mufeedah tayi kamar zaki tayi hanyar d'akinta tana shiga ta lailayo ashariya ta d'urama haneefa 

"Kafin kiga bayana ni zan ga bayanki yarinyar nan kin zak'e da yawa amma zanyi maganinki zaki raina kanki wallahi namaki alk'awarin kema sai naga bayanki..."

  Haka ta dinga surutai ita kad'ai...


  Suna shiga d'aki ta share hawaye tace

"Ki fara had'a kayanku zamu koma BQ"

"Akanmi?"

"Hakan mahaifinku ke buk'ata"

"Wannan ba hujja baneba babu inda zamu"

 Dafa kafad'arta tayi tace

"Dole muyi biyayya ga Imran gaba d'aya nidaku k'ark'ashinshi muke dan haka dole muyi abinda yake so.."

 Tana gama fad'an haka ta tashi tafara tattara duk abinda take buk'ata ba yanda Haneefa ta iya itama tashi tayi ta nufi d'akinsu ta had'a masu kayan buk'ata. Da taimakon Haneefa Ramlah ta gama shirya kayansu a BQ dan dama BQ d'in akwai komai d'aki biyu ne kowane d'aki a kwai toilet kuma akwai gado sai parlour mai d'auke da set d'in kujeru da kayan kallo, sai kitchen haka dai suka gama shirya ko ina yayi tsaf.....        BAYAN SATI D'AYA

Tun da Ramlah tabar cikin gidan yaji kamar an sauke mashi wani dutse dake kanshi, duk abin buk'ata na game da abinci ya aje mata shi a BQ sai dai duk hanyar da zata had'asu ya toshe ta dan yanzu rayuwarshi yake hankali kwance shida Mufeedah, har mancewa yake da Ramlah. 

  Itama b'an garenta hakane duk wata hanya da zata had'asu ta toshe ta dan ganinta shike saka shi damuwa ita kuma tayi alk'awarin ya gama ganinta dan ya dawwama cikin farin ciki, sai dai kullum tana adua Allah ya dawo dashi hayyacinshi...


           ****************

  A hankali ta shiga parlourn dubawa tayi ko ina taga ba kowa, Jin shirun ya tabbatar mata da Mufeedah ta fita kamar yanda taji tana waya d'azu da take lab'e, k'arasawa tayi d'akin Ahmad tana tura k'ofa taji ta bud'e hamdala tayi tare da fad'ad'a murmushinta alamar cin nasara. Fridge d'in dake d'akin ta nufa bud'e waa tayi duk ruwan dake ciki sai da ta bud'e ta tofesu da adu'a kana ta rufe ta maida fridge tare da fitowa, kitchen ta nufa nan ma ruwan dake cikin fridge d'in haka ta tofesu da adu'o'i. Tana gamawa ta fito fuskan ta cike da murna tare da yima Allah godia yanda ta fara aikinta batare da tasamu tan gard'a ba...

  Tana shiga cikin BQ da sallama Ammi ta gani tare da Mukhtar suna fira, wuri ta samu ta zauna kusa da Mukhtar. K'ura mara ido Ammi tayi can ta nisa tare da fad'in 

"Daga Ina kike?"

"Cikin gida naje"

  Ta bata amsa, ido ta zaro 

"Mi kika je yi cikin gida? Kinga Haneefa bansan d'aukar magana kibar ma Allah komai shi zai mana maganin duk wani abu dake damunmu indai maganar da kukayi da Papa ne nikam na yafe nafisan mu zauna haka da kema In rasaki."

  Dafa kafad'arta tayi ta sakar mata murmushi

"Bazaki tab'a rasani ba In shaa Allah kedai ki bini da adua"

Tana fad'in haka ta mik'e ta nufi cikin d'akin Ammi....


  Da sallama ya shiga cikin gida ganin ba kowa yasa kai ya nufi d'akinshi, fridge ya bud'e buttle water ya d'auko ya bud'e d'aga kai yayi bai aje ba sai da ya shanye gaba d'aya ya ajiye roban ji yayi wata natsuwa ta diran mashi, k'ara d'auko wata roban yayi ya bud'e rabi yasha kana ya maida a fridge tare da rufewa...".

  Haraban gidan ya fito yana fitowa yaci karo da Haneefa rik'e da cup. Murmushi ta sakar mashi, shima kuma murmushin ya mata dan gaskia yan san yaranshi har dai Haneefa .

"Ina wuni"

Muryanta ya tsinkaya tana gaidashi. Amsawa yayi da 

"Lafiya lau" 

Yana mata murmushi...

Cup ta mik'a mashi tana fad'in 

"Gashi kayi bismillah kasha sai ka rage d'an kad'an ka wanke fuskanka dashi."

  Kallonta yayi ya kalli cup d'in yace

"Nasha ruwa cikin gida banjin zan k'ara shan wani abu yanzu."

  Murmushi tayi da taji yace ya sha ruwa kuma ta tabbata ruwan da yasha akwai adu'o'i ciki.

 Tab'e baki tayi tana fad'in

"Wancan ruwan da kasha daban wannan kuma daban dan haka Daddy ka karb'a please kasha ko yanzu in maka kuka.,"

 Ba yanda ya iya dole ya karb'i cup d'in yayi bismillah yasha ya rage ya wanke fuska, tsalle tayi tare da fad'awa kanshi tace

"Allah ya bani ikon k'arasa abinda nayi niyya.."

Kanta ya Shafa yana maijin nishad'i kasancewar yaji jininshi a jikinshi...

 Duk abin nan da ya faru akan idon Ramlah, hawayen da suka zubo mata ta goge tare da wani farin ciki ko ba komai tasan Haneefa zata dawo mata da martabanta gidan mijinta, a yau yafi mata komai dad'i yanda taga Imran ya nama Haneefa dariya har ya rugumeta koba komai yau ta kasance rana mai tarin abubuwa da dama wanda bazata iya manta dasu ba. Dasauri ta juya ta nufi cikin gida dan kar Imran ya ganta ranshi ya b'aci ta salwanta mashi farin cikin shi...          WASHE GARI

  Fitowa yayi zai tafi wajen aiki, hannunshi rik'e da jaka d'ayan hannun kuma Mufeedah ya d'an rungumo jikinshi har suka iso bakin mota, sakinta yayi ya bud'e mota ya saka jikarshi, juyowa yayi ya kalleta tare da sakar mata murmushi yace

"Dan Allah ki daure yau ki mana girki nagaji da sayen abincin waje."

  Murgud'a baki tayi tace

"Wallahi bazan girka maka abinci ba dan banma iya ba ka kuma sani kawai ka tsaya ka mana take away."

  Tana fad'an haka ta juya ta nufi cikin gida tana gunguni. Girgiza kai yayi tare da shiga mota.

  Inda ta b'oye ta fito da sauri wajenshi ta k'arasa yana k'ok'arin tada mota, kwankwasa mashi glass tayi, ganin wacece yasa ya bud'e yana dariya.

"Good morning Daddy"

Good morning princess "

 Murmushi tayi ta mik'a mashi cup d'in ba musu ya karb'a yayi yanda yayi jiya, yana gamasha yaji wata natsuwa ta sauko mashi. Mik'a mata cup d'in yayi ta karb'a.

"Miya hanaki zuwa makaranta?"

"WAEC mukeyi kuma yau banda paper"

  Girgiza kanshi yayi tare da wata kunya da ta sauko mashi dan baisan yaranshi ko aji nawa suke ba a makaranta.

"Allah ya bada sa'a"

  Ta tsinkayi muryanshi yana fad'a jiki sanyaye.

"Ameen Daddy"

Ta amsa, kud'i ya zaro cikin Aljihu ya mik'a mata, hannu biyu ta saka ta karb'a tana mai godiya, motarshi ya tada ya bar haraban gidan, d'aga mashi hannu ta dingayi har sai da taga yabar gidan kana ta nufi BQ da gudu tana kwalama Ammi kira...


  Dasauri Ammi ta tare ta tana tambayarta

"Lafiya?"

Dariya tayi taja hannunta suka zauna, ta gaya mata duk yanda sukayi da Imran ta bata kud'in. Rungumeta tayi tace

"A kodayaushe Ina alfahari dake ina k'ara godema Allah da yabani ke a matsayin d'iya, Allah ya k'ara taimakonki adu'ata tana biye dake ke dai kiyi a hankali ina tare dake In shaa Allah."

"Ameen Ammi"

 Ta fad'a ta tashi ta nufi d'akinta..


  Tun safe take lab'e dan taga fitowar Imran amma har yanzu shiru, agogon hannunta ta kalla taga 12 saura d'an guntun tsaki taja tare da juyawa zata nufi BQ. Muryanshi ta juyo yana waya da sauri ta juyo, ganin shine ya sa ta saki murmushi wanda itama bata san tayi shi ba.

  K'arasawa tayi gabanshi da cup a hannu, tun kafin tayi magana ya gane mi take nufi karb'an cup d'in yayi kamar yanda yakeyi kullum haka yauma yayi. Yana gamawa ya mik'a mata cup d'in tare da murmushi.

"Nagode duk sanda na sha ruwan nan ina samun natsuwa."

Fad'awa tayi jikinshi tana fad'in

"Zanyi komai dan ka samu farin ciki Daddy idan ruwan fridge d'inka ya k'are kaman magana zan kawo maka wasu amma inasan ya zama sirri bansan matarka tasani."

 Dariya yayi yace

"Angama zanyi duk yanda kika ce"

  Haka kawai yaji ya bata amsa batare da ya mata gardama ba, kuma kullum idan yana ganin Haneefa yana k'arajin k'aunar ta da sabuwar natsuwa da ke kamashi. A haka ya mata sallama ya fita, da murna ta koma cikin gida, duk abinnan da akeyi Mufeedah bata sani ba a tunaninta ta gama dasu tun da ya Koresu daga cikin gidan nan gaba kad'an ma zai rabasu da gidan, alk'awari ne da ta d'aukar ma kanta. kuma shima bai gaya mata Haneefa na bashi ruwa ba. Tana shiga d'aki ta fad'a kan gado.

"Na gama wannan cikin nasara Allah ka bani ikon aikata sauran suma cikin nasara batare da wata matsala ba."

 Ji tayi An karb'a da 

"Ameen"

  Juyawa tayi Ammi taga ni tsaye da gudu ta tashi ta rungumeta tana dariya. Itama rungume d'iyarta tayi tana shi mata albarka.


          BAYAN SATI BIYU

  Zirga zirga ta keyi cikin d'aki ta rasa abinda za tayi tafara komai a sa'a amma tana ganin abun kamar ba zaizo mata da sauk'i ba, tun da ta gama ba Imran ruwan magani ta rasa abinyi, sai dai tayi imani ruwan shanshi akwai ayoyin Allah wanda ita da kanta take mashi kuma ta tabbata yana sha dan ta fara ganin canji daga gareshi. Sai dai ta rasa ta ina zata fara bincike cikin gidan har ta gano asirin da ta binne. Haka ta dinga zirga zirga cikin d'aki tana tunani, wata zuciya taji tana k'arfafa mata guiwa akan zata iya kuma komai zai zo mata da sauki.

 Dasauri ta zuri hijab d'inta tayi hanyar fita, a bakin k'ofa sukayi karo da Mukhtar yana daidai shigowa

"Adda Haneefa Ina zaki haka kike sauri?"

 Murmushi tayi ta duk'a daf dashi, dafa kafad'unshi tayi tare da fad'in

"Zanje in ida aikin da Papa ya sani kaji, Kai dai kawai ka bini da adu'a"

 Tana gama fad'in haka ta tashi tayi hanyar fita. Muryanshi ta juyo yana mata adu'a

"Adda Allah ya baki sa'a ya tsareki ya kare mana ke."

  Juyowa tayi tana murmushi

"Ameen Auta nagode kaji"

  Tana fad'in haka ta juya ta nufi hanyar fita....


  Tana fita tayi hanyar lambu, magana taji ta window Mufeedah lab'e wa tayi dan taji maganar mi takeyi.

"Lash Ina cikin matsala"

"Matsalar mi?"

"Imran ya fara canjawa ban isa in sakama Imran doka yanzu ya biba na d'auka na gama da matsalata tun da ya raba Ramlah da cikin gidan kuma na kauda Ahmad dake kawo man matsala, sai gashi wata matsalar babba na neman faruwa, kodai asirin da nayi yafara karewa ne. wallahi Lash a yanzu san Imran nake dagaske amma yana neman ya canja man bansan ya zanyi ba ki taimakeni kiban shawara."

  Numfasawa Lash tayi tana fad'in 

"Hanya d'aya ce zamu bi shine mu koma wajen boka Dumbus shi zai warware mana komai."

"Zuwa wajen boka bashi bane mafita ke kanki kinsan yanda mukayi dashi last zuwan da mukayi dan haka komawa wajenshi ba shi bane ba solution."

"To yanzu ya zamuyi?"

  Tsoki Mufeedah tayi tace

"Kibar komai a hannuna zanyi maganin komai da kaina."


  Murmushi Haneefa tayi cikin ranta tana fad'in.

"Asirinki ya gama tonuwa duk wani shiri da kikayi ni zan b'ata maki shiri daga yanzu zan fara bibiyarki dan nasan bazaki zauna haka ba."

  Duk a zuciya take magana, b'angare d'aya kuma kuka take da yau taji wacece dalilin mutuwar mutumin da tafi k'auna bayan iyayenta dan haka tama kanta alk'awari sai taga bayan Mufeedah kamar yanda taga bayan Ahmad."

  Hawaye ta share ta nufi cikin lambu.


  Wuri ta samu ta zauna tayi ta gumi, babu abinda ka keji sai kukan tsuntsaye, hawaye suka dinga gangaro mata sakamakon tuna kalaman Mufeedah da taji tana ba k'awarta labari. Hannu ta d'aga sama tana rok'on Allah

"Allah kaban ikon tona duk wani asiri da wannan baiwar taka tayi."

 Shafawa tayi, tare da d'aukar wani d'an icce tana wasa dashi wani tudu ta gani ji tayi bata yarda dashi ba, tashi tayi ta matsa wajenshi iccen hannunta ta fara tona wurin amma yak'i tono abinda ke wurin. Tashi tayi ta fara waige waige, wani k'arfe ta hango dasauri ta d'aukoshi, duk'awa tayi da bismillah ta fara tona ramin, a hankali take tonashi har tazo k'arshe cigaba da tonawa tayi tauri taji bismillah tayi ta saka hannunta da zumar ta zaro koma miye. Iska ne ya taso mai k'arfi d'aukar ta yayi ya wurgi da ita, adu'a ta farayi cikin ikon Allah iskan nan yayi sauki. Tashi tayi ta koma wajen ramin adu'a tayi sosai kana ta saka hannunta cikin ramin, wani bak'ar leda ta d'auko tashi tayi da sauri ta matsa gefe warware ledan tayi wani hayaki ya dinga tashi adu'a tayi sosai kana hayak'in ya daina fita, layu ta gani cikin ledar warware tayi sunan Ramlah da Imran ta gani sai Allura 99. Hamdala tayi ma Allah ta maida k'asa ta rufe kamar yanda taga wurin dan kar a gane, kwashe layun tayi ta nufi hanyar cikin gidansu. Ganin ba kowa parlour yasa ta nufi kitchen, ashana ta d'auka ta kunna ma layun, ci suka dingayi tare da wani irin kuka da akeyi wanda bai tsoratata ba sai ma k'arfin guiwa da ta samu tare da adu'o'i, sai da wutar nan ta cinye layun nan tas kana ta daina jin kukan da akeyi.

  Hamdala ta yima Allah ta juya zata koma cikin d'aki, juyawar da zatayi sukaci karo da Ramlah da gudu ta k'arasa gurinta ta rungume

"Ammi...."

  Rufe mata baki tayi tare da murmushi tace

"Naga komai Allah ya maki albarka ya k'ara baki nasara abinda nakesan ki dashi yanzu ki k'ara kula kiyi a hankali kibi komai a sannu.."

"In shaa Allah Ammi ke dai ki cigaba da yimana adu'a."     Tafe yake cikin mota, kanshi yaji ya sara mashi dafe kanshi yayi yana fad'in wash kaina, ganin idanuwanshi sun fara rufewa ya samu da kyar yayi parking gefen titi. Kanshi ya d'ora kan sitiyari da kyar ya fara adu'an neman d'auki a hankali yaji sarawan kan tana ragewa. K'ok'ari yake ya tuna wani abu da yafaru dashi amma ya kasa tunawa, haka ya tada mota yayi hanyar gida jiki a mace.

  Yana shiga bai ko yi parking dai dai ba ya fito ya nufi cikin gida ba tare da sallama ba.

  Dasauri ta tareshi

"Imran lafiya ka shigo cikin gida ba tare da kayi sallama ba?"

"Hannun ya d'aga mata alamar bai san magana, k'arasowa tayi inda yake tace

"Magana nake da kai"

  D'ago idonshi yayi da suka canja kala yace

"Dan Allah Mufeedah ki rabu dani bansan surutu kuma ban ce ki shigo inda nake ba dan bana buk'atar kowa kusa dani a yanzu."

  Yana gama fad'in haka ya juya yayi d'akinshi, tsaye tayi sake da baki ga wani bak'in ciki da ya hanata magana. D'aki ta nufa da gudu tana kuka.

  Yana shiga d'aki ya bud'e fridge buttle water ya d'auko ya bud'e ya kafa kai, bai aje roban ba sai da ya shanye kana yaji natsuwa ta sameshi. Bisa gado ya fad'a yayi rub da ciki yana tunani a haka bacci yayi gaba dashi.


           BAYAN KWANA UKU


   A gurguce, abubuwa sun faru da yawa cikin kwana uku ciki harda sauyawar Imran, kwata kwata bai shiga harkan mufeedah kuma idan ta ishe shi da surutu tashi yake ya bata wuri, ko ya bar mata gidan. Ba k'aramin d'aga hankali Mufeedah tayi ba duk hanyar da zata bi tabi dan ta juyo da hankalin Imran ya dawo kanta amma kwata kwata bata gabanshi, babu yanda ta iya illah ta koma wajen boka nakan Tudu ta bashi hak'uri ya sake mata sabon shiri akan Imran. Da wannan shawaran Mufeedah ta natsu akan idan gobe tayi zata shirya ta tafi wajen boka. Haka take a b'angare Imran duk abubuwa sun mashi yawa yana san ya tuna wani abu da ya manta amma ya kasa tuna komai. Duk halin da Mufeedah ke ciki Haneefa na sane dashi dan tana bibiyarta sosai ba tare da ta sani ba, harta zuwan ta wajen boka ta sani, Sai dai tayi alk'awari sai ta b'ata mata duk wani shiri da takeyi da wanda zatayi nan gaba.            2:30am

 Sanye yake da fararen kaya sunyi mashi kyau sosai, ta kowa yakeyi wajenta murmushi yake mata itama murmushin ta mashi k'arasowa yayi kusa da ita ya zauna yana mai k'ara sakar mata murmushi, Itama murmushin take mashi. sun kusa minti goma ba wanda yayi ma d'an uwanshi magana sai dai murmushi, ganin shirun yayi yawa yasa ta yanke shirun tare da fad'in 

"Papa ka k'ara kyau"

Dariya yayi wanda ya bayyana fararen hak'oranshi tare da fad'in

"Kema kinyi kin k'ara girma ga kyau da kikeyi."

  Murmushi tayi ta kauda kanta gefe guda. Hannunta ya rik'o juyowa tayi ta kalleshi, shima ita yake kallo.

"Nagode kwarai da yanda kika cikaman burina naji dad'i sosai da kikeso ki maido da martaban iyayenki tabbas haneefa kin cika d'iya, d'iyar da kowa zaiyi alfahari da ita bayan ya sameki, kinyi k'ok'ari sosai Sai dai har yanzu akwai sauran aiki a gabanmu."

  Dasauri ta juyo tana fad'in

"Aiki?"

"Eh aiki"

"Wane irin aiki? Wallahi nagaji papa bazan iya ba"

"Zaki iya dan nasan zaki iya shiyasa na sakaki aikin da zakiyi yanzu yafi ko wane muhimmanci amma yafi kowane had'ari idan kikayi shi to ina tabbatar maki mahaifinki zai dawo cikin hayyacinshi ki daure ki k'arasa Haneefa."

 Ajiyan zuciya tayi tana fad'in 

"Taya zan fara?"

  Murmushi yayi tare da shafa kanta 

"Allah ya maki albarka"

"Ameen"

"Akwai wani asiri da Mufeedah ta saka a d'akin Imran wanda idan kika cireshi kin gama da komai nata sai dai bansan inda yake ba amma nasana cikin d'akin yake shiyasa nace maki yafi sauran wahala amma nasan zaki iya."

"Bazan iya ba"

"Zaki iya ni nasan zaki iya, ki taimaka ki dawo da farin cikin iyayenki ke kad'ai yanzu zaki iya basu farin ciki sanadiyar tona duk wani asiri da aka masu, idan har kika kasa to yana nufin iyayenki zasu cigaba da zama basu k'aunar junasu, kuma ni nasan zaki fisan farin cikin iyayenki akan naki nasan zaki iya dawowa da farin cikinsu koda hakan na nufin rasa naki farin ciki."

  Yana gama fad'in haka ya tashi ya tafi, kira ta dinga kwala mashi amma bai juyo ba.

  A firgice ta farka ta fara juye juye, tabbas mafarki ne tayi kuma da Ahmad. Maganganun su suka dawo mata a kwakwalwa, hannu ta d'aga sama tana mai neman Allah ya taimaka mata. Tagumi tayi tana tunanin ta ina zata fara, ganin shirun ba abinda zai mata ta tashi ta d'auro alwalla tazo ta kabbara sallah tana mai neman Allah ya bata sa'a akan abinda ta saka gaba. Bata tashi akan sallaya ba sai k'arfe bakwai na Safiya kana ta koma kan gado, tana kwanciya bacci mai nauyi yayi gaba da ita..  Bata farka ba sai k'arfe sha d'aya, dasauri ta diro daga kan gado tayi hanyar toilet, tana fitowa wanka ko mai bata shafa ba ta saka turare ta zura doguwan riga ta fita, a parlour suka had'u da Ammi. Gaida Ammi tayi, cikin sakin fuska ta amsa.

"Ina last born?"

"Ya tafi makaranta"

"Allah sarki Auta kwana biyu bamu had'uwa"

"Shi kanshi rigiman da ya dingayi kenan yau wai bazai tafi school ba sai ya tadaki ko ya jira sai kin tashi dan yana mssn d'inki dakyar na lallabashi ya tafi ga exams sun fara."

 Langwab'e fuska tayi tana fad'in

"Wayyo Auta nima nayi mssn d'inshi amma yau in shaa Allah zamu had'u d'akin mu ma zai kwanta ba wurinki ba yau."

  Tab'e baki tayi tace

"Kyaji dashi."

  Mik'ewa tayi tace

"Ammi bari naje lambu"

"Kalacin fa?"

"Kin manta yau Thursday ina azumi "

"Hakane fa na tuna"

  Waje tayi dan tanasan yau ta fara aikinta akan cikin gidan Imran. 

"Amma Taya?"

 Tambayar da tama kanta kenan, kafin ta samo amsa taji hannunshi cikin nata, d'agota tayi ta kalleshi murmushi ya sakar mata.

"Tunanin mi kike princess ?"

"Bakomai Daddy Ina kwana?"

"Lafiya lau ya bata amsa"

"Ina zakije ne?"

"Zanje lambu"

  "Dan zan fita da na rakaki."

    Murmushi tayi tana fad'in 

"Ina Anty? Banga motar taba"

  Tab'e baki yayi yace

"Ohon mata inaga tafita dan tun safe nima ban ganta ba."

  Wani murmushi ta saki tace

"Bari na shiga d'akin ka na gyara nasan yayi k'ura."

"Kamar kin sani ki wanke harda toilet"

 Amsa mashi tayi da 

"To" 

  Tayi gaba cikin farin ciki. Shima wajen da ake fakin d'in mota ya nufa. Motarshi yama wuta yabar haraban gidan....


  Da murnanta ta fad'a cikin gidan, kai tsaye d'akin Imran ta nufa, tana shiga taji gabanta ya fad'i adu'o'in neman tsari ta karanto kana ta nufi cikin d'akin, kai tsaye toilet ta nufa duk abind ke toilet sai da ta fito dashi duk wani sak'o da lungu sai da ta duba amma bata ga komai ba, wanke toilet d'in tayi ta maida komai wajen shi ta kunna turaren wuta, tsaf toilet d'in yayi kamar ba'a tab'a amfani dashi ba. Fitowa tayi bed room ta zauna bisa gado tayi tagumi.

  Hawaye suka gangaro mata, duk iya tuninta ya k're kan toilet zata ga komai sai gashi ta duba ko ina amma babu alamun wani abu da yayi kama da asiri, kuma Papa ya tabbatar mata koma miye yana cikin d'akin Daddy.

"Allah ka taimakeni"

  Abinda ta fad'a kenan, tashi tayi ta fara tattara d'akin dan gadon a gyare yake shara tayi da goge goge harta mopping sai da tayi sai da ta ga komai yayi daidai kana ta nufi hanyar fita, juyawa tayi ta kalli d'akin, ji tayi tanasan ta juya katifan saboda taga kamar tayi k'asa kuma zata iya saka mutum ciwon baya, dasauri ta koma ta yaye zanin gadon, da kyar ta cire katifan tana neman juyawa datti tagani k'ark'ashin gadon, ajiye katifan tayi gefe guda ta d'auko tsintsiya, katakan gadon ta cire. Abinda tagani ne ya d'aga mata hankali kwarya ce da wani ruwa tsutsotsi na sha, adu'a tayi ta rufe ido ta ciro kwaryan ta aje gefe da sauri ta maida komai ta shimfid'a zanin gado ta d'auki kwaryan tayi hanyar fita dashi, can baya wajen lambu ta nufa, daidai fitowar Ramlah daga BQ ganin Haneefa da kwarya tayi hanyar lambu yasa tabi bayanta...


  Tana aje kwaryan ta fara adu'o'i ta dad'e tana adu'a kana ta d'aga kwaryan sama ta saki wuta tafara ci wajen sai wani kuka da akeyi. Daidai Mufeedah na k'arasowa wajen da gudu dan tana shigowa gidan zata shiga cikin gida kenan ta juyo muryan Haneefa na karatu, zuwan da tayi dan ta ja mata kunne karta k'ara mata karatu kusa da d'aki kwaryan da ta gani hannun Haneefa ne ya d'aga mata hamkali amma kafin ta k'araso Haneefa ta fasa kwaryan. ta nufi Haneefa zata shak'e Ina k'afarta ta rik'e wasu k'urajene suka fara fito mata. Ja da baya Haneefa tayi ta nufi wajen Ammi dake tsaye ta kasa tab'uka komai

  Hawaye Mufeedah ta farayi tana fad'in

"Kinyi nasara akaina dama boka ya gayaman na d'auka zan iya gamawa dake sai gashi kafin In an kara kin gama dani Haneefa lallai d'an hakkin da ka raina shike tsone maka ido ban tab'a d'aukan ke zaki gama dani ba."

  Dariya Haneefa ta tuntsire da ita tace

"Sai kuma gashi na gama dake ko? Dama na maki alk'awarin sai na kawo k'arshen ki to yau gashi kuma na cika maki alk'awari, sauran hukunci kuma sai Daddy yazo.."

  Tana gama fad'in haka taja hannun Ammi sukayi cikin gida, sai a lokacin Hawaye suka zubo ma Ramlah, hannu Mufeedah ta d'ora akai tace 

"na cuci kaina Allah ka kawo man d'auki."

  Nikam nace sai a yanzu kika san Allah?  Jiri ne yaji yana d'iban shi ga kanshi yana sarawa dafe kanshi yayi amma jiri bai daina d'ibanshi ba gaba d'aya kamaninshi ya canja.

"Kaina"

  Abinda yake fad'a kenan, k'ara ya saki ya fad'i sumamme daidai Haneefa da Ramlah na k'arasowa da gudu sukayi kanshi, da taimakon mai gadi suka kaishi cikin gida. Ruwa Ramlah ta dinga yayyafa mashi ko motsi baiyi ba, kuka ta fashe dashi hannunta Haneefa taja ta zaunar da ita, komawa tayi kusa dashi ta fara mashi karatun alqur'ani an d'auki lokaci ya fara motsi da hannun shi a hankali ya dinga bud'e idonshi har ya gama bud'e su bai sauke idonshi ba sai kan ramlah, wadda tayi bak'i ta rame kamar ba Ramlah ba. Dasauri ya tashi sai dai jikinshi ba k'arfi komawa yayi ya kwanta yana mata nuni da hannu da tazo gareshi, kuka ne yaci k'arfinta ta tashi ta nufi d'aki da gudu tana kuka. Kallon Haneefa yayi da alamomin tambaya, murmushi tayi ta kamashi ya zauna, ruwa ta d'auko a cup ta mashi adu'a kana ta bashi ba musu ya karb'a, duk abin an da akeyi maigadi na tsaye shi kanshi kuka yakeyi dan duk abinda yake faruwa gidan babu abinda bai sani ba..

"Mike faruwa da nine princess?"

  Tambayar Haneefa yayi yana mai dubanta, itama shi take duba da idanuwanta suka rine sukayi ja dan da wuya kaga kukanta.

"Daddy........ nan ta kwashe komai ta gaya mashi har yanda taji mutuwar Ahmad sai da ta gaya mashi."

  Kuka ya fashe dashi mai tsuma rai yace

"Na cuci kaina na auro wadda ta rabani da farin cikina a dalilin auren da nayi ta rabani da d'an uwana da duk duniya banda kamar shi ta rabashi da numfashinshi ta kumayi sanadiyar rasa d'ana danayi Allah kayafeman." 

 Kuka yakeyi sosai yana sabbatu, tashi yayi ya nufi d'akin Ramlah, Haneefa ba tayi yunk'urin binshi ba dan tasan suna buk'atar privacy.


  Yana shiga d'akin ya zube kan k'afafuwanshi yana mai fuskantanta k'afarta ya kama yana kuka.

"Gani gabanki ni mai laifine ta sanadiyar auren da nayi kika rasa d'anki da d'an uwanki bazan iya baki hak'uri ba, ki yanke man hukuncin da kika san ya dace dani wallahi zan karb'i ko wane irin hukunci ne amma banda na rabuwa dake.."

  Itama kuka takeyi sosai, d'agoshi tayi tace

"Duk abinda ya faru baka da laifi duk abinda kayi kayishi cikin rashin sani ne saboda an kauda maka hankalinka dan haka na yafe maka komai dama can ban rik'e ka ba."

  Kafin ta ida magana ya rungumota, suduka kuka sukeyi mai tsuma rai sun dad'e a haka kana yaja hannunta suka fita. Ganin su da Haneefa tayi haka ba k'aramin dad'i taji ba sai a sannan Hawaye suka gangaro mata, ko a yanzu tasan ta cikama Papa burinshi wanda ya dad'e yanaso yaga ya cika.

  "Ina Mufeedah?"

Muryan Imran taji ya fad'a rai b'ace.

"Tana lambu"

  Tabashi amsa, jan Ramlah yayi suka fita, binsu a baya Haneefa da maigadi sukayi. Inda suka barta tana nan zaune, Amma duk wanda yasan Mufeedah idan ya ganta yanzu bazai gane ta ba, saboda gaba d'aya halirtanta ta canja, gaba d'aya k'uraje sun fito mata masu k'ak'ayi duk inda ta sosa sai su fashe ga kuma wari da sukeyi. Suna isowa suka toshe hanci dan gaba d'aya wari takeyi ga k'uraje har a fuskanta.


  Kallon takaici Imran ya mata yace

"Ko a haka aka barki kinga darasi ai da nayi niyar kasheki kamar yanda kika kasheman d'an uwa na da d'ana amma na fasa saboda nafisan kisha a zaba ki d'and'ani a zaba a duniya kafin kije lahira ki iske wadda Allah ya tanadarma irinku. Kiga yanda kika koma wannan ya isheki ishara dake da duk wani mai hali irin naki, Mufeedah na sakeki saki uku."

  Hannu ta d'ora bisa kai ta fasa uban ihu

"Nashiga uku Imran dan Allah kuyafeman Ramlah ke na cuta dan Allah ki yafeman ko nasamu sassauci daga wajen Allah wallahi jikina zafi yakeyi kamar ana huraman wuta, kuyafeman dan Allah yanzu haka daga wajen boka nake yabani magani in saka maka a abinci da kaci kaga ganin kowa sai ni sai dai kafin na saka Allah yayi ikonshi a kaina. Imran na cuceka kai da Ramlah duk abinda ya shiga tsakanin ku nice sila...." komai ta kwashe ta gaya mashi tun daga randa ta fara ganinsu da irin asirin da ta masu sai da ta tona.

  Kallonta Imran yayi yana huci

"Allah ya isa tsakaninmu dake wallahi bazan iya yafe maki ba.."

  Dubanta ta kai kan Ramlah tace

"Ramlah ki yafeman nasan ke mai hak'uri ce dan Allah ki yafeman ko nasamu sauk'in azabae da nakeji.."

  Allah sarki Ramlah mai zuciyar imani kuka ta fashe dashi, ta bud'e baki zatayi magana, Imran ya rufe bakin tare da janta. Dan yasan da tayi magana to zata yafe mata ne shikuma abinda baiso kenan gara duniya ta mata hankali..

  Hannun Ramlah da Haneefa ya kama suka nufi cikin gida suna kuka, dan bak'aramin tausanta Ramlah keji ba har dai yanda taga lokaci guda Allah ya canjata lallai mutum ba a bakin komai yake ba.


  "Dan Allah maigadi bani wayarka in kira Lash"

Ba gardama ya mik'a mata, number Lash ta kira sai da ta kusa tsinkewa kana aka d'auka

"Hello Lash"

"Ba ita baceba Allah yama Lash rasuwa d'azu sakamakon had'arin mota da suka samu yanzu ma aka dawo daga rufeta."

  Ihu ta saki tana fad'in 

"Nashiga uku na lalace Ina zan saka kaina Lash ta rasu."

  Wayarshi maigadi ya karb'a yace

"Hajiya ki tashi ki tafi kar maigida ya zagayo yazo ya tardaki dan raina sai yafi naki b'aci."

 Bata da zab'i dole ta lallab'a ta tashi da kyar take taka k'afarta dan idan ta takata ji take kamar ranta zai fita saboda zafi da suke mata, haka ta fita daga cikin gidan, juyowa tayi ta kalli gidan hawayen da suka mak'ale mata suka gangaro, tafiya takeyi ita kanta batasan ina ta nufa ba...  Tunda suka shiga cikin gida ya had'a kan iyalanshi, dan a lokacin Mukhtar ya dawo daga school, kuka yakeyi sosai yana neman yafiyarsu da kyar suka samu yayi shiru, had'asu yayi gaba d'aya ya rungume kamar wani zai kwacesu.

 Haneefa ce tayi gyaran muryan tace

"Nasan duk kunasan kusan ya akayi nasan komai, har dai kai Daddy dan Ammi tasan wasu abubuwa saidai itama ba komai ta sani ba to...........nan ta kwashe duk yanda sukayi da Ahmad a asibiti ta gaya masu har mafarkin da tayi da ya gaya mata akwai asiri d'aki Imran babu abin da ta rage."

  Kuka Imran da Ramlah keyi sosai. Imran yace

"Allah sarki Ahmad ta sanadiyar farin cikin mu ya rasa nashi farin cikin Allah ya jik'anka da rahma."

"Ameen"

 Gaba d'aya suka amsa. Kallon Haneefa yayi yace

"Tabbas samunki a rayuwa ba k'aramin alkairi ba ne nagode ma Allah da ya mallakaman ke a matsayin d'iya Ina alfahari dake kuma zan cigaba da alfahari dake har k'arshen rayuwata Allah ya maki albark."

 Fad'awa tayi kanshi tana fad'in

"Ameen Daddy, Zanyi komai dan inga kun dawwama cikin farin ciki, ganinku cikin farin ciki yafi man komai a rayuwa ko a yanzu nasan Papa yana cikin farin ciki saboda burinshi ya cika Allah ya jik'anshi da rahma."

  Gaba d'aya suka amsa da

"Ameen"

 Gaba d'aya ya k'ara had'asu ya rungume yana k'ara godema Allah da yafarkar, dashi akan had'arin da ya fad'a...             A GURGUJE


  Bayan kwana biyu, cikin kwana biyu komai ya koma daidai gidan Imran, duk idan ka gansu zakayi tunanin basu tab'a shiga halin k'unci ba, kullum k'ok'arinshi yaga ya kyautatama iyalanshi, a kullum sai yayi kuka ya rok'i Allah gafara akan ya yafe mashi abinda ya aikata, kuma kullum sai yama Ahmad da Haneef adu'a samun Aljanna. Ita kanta Ramlah kullum k'ok'ari take ta mantar dashi Abinda ya wuce saboda ba yin kanshi bane be..


  Kwance take cikin bola gaba d'aya jikinta tsutsa yake fitarwa, tayi bak'i ta rame ga gabanta wasu ruwa masu wari da yake fitarwa babu wanda zai iya gane mufeedah ce cikin wannan halin. 

 Tafe yake da gudu bisa mashin sakamakon hanyar babu abun hawa sosai, gaba d'aya mashin d'in ya kwace mashi neman birki yake ya taka amma ya kasa, bai an kara ba sai dai yaji k'ara, dubawar da zaiyi yaga ya takata gaba d'aya k'afafuwanta suka kare, ga jini dake fita, ganin ba kowa yaja mashin d'inshi yayi gaba ya barta nan cikin azaba.. kuka take tana neman d'auki amma babu wanda yazo bare ya taimaka mata, fizge fizge ta fara tana cire gashin gabanta, a haka har Allah ya karb'i ran Mufeedah cikin wannan halin...


  Gaba d'ayansu suna parlour zaune, shigowa yayi da sallama, tashi tayi taje wajenshi, tana k'arasawa ya kamata ya rungume yana mata peck a goshi, sunne kanta tayi cikin k'irjin shi tana mashi magana

"Baka ganin haneefa da Mukhtar?"

  Dariya yayi yace

"Nagansu, dan suna wajen sai na fasa rungumar matata, beside Haneefa ma kwana nawa ya rage nayi suruki tunda gashi ta gama SSCE d'inta yau."

  Dariya tayi ta d'ago daga k'irjinshi taja hannunshi suka k'arasa cikin parlour.

"Daddy sannu da zuwa"

 Gaba d'aya suka fad'a. Amsawa yayi da murmushi ya zauna cikinsu, kallon Haneefa yayi ya mik'a mata hannu sukayi shaking yace

"Congratz Allah amfana abinda kika karanta, my baby is grow up now."

 Dariya tayi tace

"Thnx Daddy"

  Waya ya mik'o mata IPhone X yace

"Ga gift d'ina"

  Ihu ta saki tare da fad'awa kan Imran tana murna

"Karki karyaman miji"

  Cewar Ramlah dake tsaye

  Dariya tayi tace

"Bazan karya maki tsohon mijinki ba"

 Duka ta kai mata ta goce tana Dariya, suma Dariyan sukeyi.

"Daddy na gode Allah ya k'ara rufa asiri"

"Ameen princess"

"Daddy ni Ina nawa wayan?"

Mukhtar ne ke magana kamar zaiyi kuka, Dariya Ramlah tayi tace

"Kyalesu soja na ni zan sai maka wanda tafi na Adda kyau kaji."

  Murna ya dingayi za'a sai mashi wayan da yafi na Adda.

"Miji za'a fito dashi ko kuwa karatu za'a cigaba?"

  Cewar Imran da ya zuba mata ido yana kallonta.

"Zumb'uro baki tayi tace

"Daddy karatu dai kasanfa jamb d'iya 209 naci beside Ina san na cikama Papa burinshi na In zama doctor, kasan dama yace ni medicine zanyi."

  Dariya Imran yayi yace

"Hakane nima wasa nake maki ay babu gatan da zan baku yanzu da ya wuce ilimi, amma kisani karatu bai hana aure idan miji ya zo maki wanda hankali na ya kwanta dashi zai rik'eman ke da amana to zan aurar dake."

  Sai a sannan Ramlah ta zauna kusa da Mukhtar tace

"Dama ko kasan yaron Alhaji Najeeb ya ganta yanaso nine na dakatar dashi nace ya bari sai ta k'are secondary school, to d'azu sai gashi ya turo Mamansu wai ya maganar tunda yanzu ta gama school."

  Da murmushi yace

"Wane Alhaji Najeeb ba dai makwabcinmu ba?"

"Shifa"

"Wane yaron nashi daga ciki?"

"Naufal, kasan germany yake aiki, to sun hana ya koma sai yayi aure kaga idan sun daidaita kansu bayan biki basai tayi karatunta can ba?"

  Dariya Imran yayi sosai yace

"Wannan shawara tayi, amma sai naji daga gareta kinsan bazan yimata dole ba, in tana sanshi shikenan."

 Kallonta yayi yace

"Princess kina sanshi? Karkiji komai ki gayaman abinda ke ranki duk abinda kikeso shi nakeso bazan maki dole ba."

 K'asa tayi da kanta tana murmushi, dan gaskia ta dad'e tanasan Naufal dan guy ne wanda mata ke kwakwar samun irinshi kullum inta ganshi sai taji wani abu ya ratsata bata tab'a tunanin ya santa ba bare har yace yana santa dan ko kallon mutane bayayi dan Naufal miskili ne.

"Kinyi shiru ana tambayarki"

  Cewar Ammi da taga bata da alaman yin magana.

  D'agowa tayi ta kallesu tace

"Daddy Ammi idan kun yarda da natsuwarshi da tarbiyanshi na amince."

"Allah ya maki albarka Haneefa, tabbas kinyi miji dan kowa yasan yaran gidan Alhaji Najeeb daidai gwargwado suna da tarbiya."

  D'agowar da zatayi suka had'a ido dashi wani murmushi ya sakar mata, wanda yasa jikinta yayi sanyi. Ya dad'e tsaye yana jinsu dama shigowar Imran ya gani shine yaje ya sami babanshi akan zaizo ya mashi magana, yanasan Haneefa, shine babanshi yace mashi yazo.

  Sallama yayi ya k'arasa cikin parlourn, gaba d'aya suka amsa mashi suna mashi murmushi, Banda Haneefa da ta duk'ar da kanta tana jin kunya. Wuri ya samu k'asa ya zauna gaidasu yayi cikin Ladabi, amsawa sukayi cikin sakin fuska, nan ya gaya masu buk'atarshi, Imran kuma ya amsa mashi ya kuma k'ara bashi tabbacin cewa gobe ya turo mashi magabatanshi dan su tsaida maganar aure.


  Magabatan Naufal sunzo akan neman ma d'an su auren Haneefa an kuma basu, an saka ranan aure sati d'aya saboda hutun Naufal zai k'are kuma yanasan ya tafi da matarshi, sun biya sadaki dubu d'ari, Sai dai jiran ranan d'aura aure.

  Soyayya tsaftatacciya akeyi tsakanin Naufal da Hanefa kowa Yana burin kyautatama d'an uwanshi, dan dukansu Wannan ne soyayyarsu ta farko dan haka duk abu na kyautatawa shi sukeyi. Kallonta yayi yace

"Princess Visa d'inki tafito yau zanje na karb'o."

"Inzo In rakaka?"

"Ah ah ki zaman ki randa mukaje kiga yanda maza ke kallonki sai da nace masu matata ce nidai bazanje dake ba."

  Dariya tayi tace

"Sai kadawo."

 Peck ya mata ya juya ya tafi.

   A yau aka d'aura auren Naufal Najeeb da Haneefa Imran inda dubban mutane suka shaida, kuma a yau jirginsu zai d'aga Zuwa germany, bayan d'aurin aure aka kai amarya wajen iyayenta suyi mata fad'a dan za'a wuce da ita Abuja ta nan zasu tashi, gaba d'aya kuka sukeyi sosai, da kyar Imran yace

"Kiyi biyayya ga mijinki hak'urinki da juriyar da nasanki da ita ki cigaba Allah ya maki albarka."

  Yana gama fad'an haka yayi cikin d'aki, fad'awa tayi kan Ramlah tana kuka ita kanta Ramlah kuka takeyi sun dad'e a haka kana Ramlah ta janye ta daga jikinta ta mata adu'o'i ta tashi da kanta ta mik'a ma Naufal ita tana murmushi tace

"Ga amanar yar uwarka nan Allah ya maku albarka."

  Amsawa yayi da 

"Ameen"

  D'akinta ta nufa tana kuka, hannun Haneefa yaja suka shiga mota inda mota uku ce zata rakasu Abuja daga can kuma su wuce Germany. Sai muyi masu fatan alkairi, Allah ya bada zaman lafiya da zuri'a d'ayyaba.


  Zaune take parlour ita kad'ai yan biki kowa ya tafi, Mukhtar kuma yayi bacci. Shigowa yayi da sallama, amsa mashi tayi jiki ba kwari, k'arasowa yayi wajenta yace

"Angel lafiya?"

 Fad'awa tayi jikinshi tana kuka, bubbuga mata baya ya farayi yace

"Kina mssn princess ryt?"

 D'aga mashi kai tayi alamar 

"Eh"

  Dariya yayi yace 

"Princess tama manta dake tana can ta kama mijinta Ke kuma zaki saki naki mijin kodai In k'aro maki abokiyar zama?"

 Fad'awa tayi jikinshi tana mashi dukan wasa, shikuma yana janta, sai da yaga ta sake tana dariya kana ya kyaleta, rungumota yayi ya mata rad'a 

"Ya kamata na baki ajiyar Lil Ahmad cikin Daren nan dan gidan nan yana buk'atar yara tunda princess tayi aure."

 Dariya ta fara tana neman kwace kanta, rik'e ta yayi sosai yanda bazata iya kwacewa ba a haka ya dinga aikamata da sak'onni kala kala, tun tana zillewa har tafara maida mashi, tashi yayi ya kamata suka nufi d'aki....

  Nikuma zan dasa aya daga nan...Alhamdulillah anan na kawo k'arshen makirci ko Asiri, kuskuren da nayi Allah ya yafeman, alkairin dana rubuta Allah yakai ladan a kabarin mahaifiyata.


Jinjina ga nagarta writers association, nagode da irin gudumuwar da kuka bani, kusani Feedoh na alfahari daku kuma zan cigaba da Alfahari daku har k'arshen rayuwata.


Wannan littafin sadaukarwa ne ga Anty Maijidda Musa (Maama) nagode da irin shawarwarin da kike bani, Allah yaja kwana.


Littafin nan tukuicine gareki Anty Amina k'aura


Wannan labarin nawa goro ne gareku yan DANDALIN FEEDOH DEEDOH da my wattpad readers Allah ya bar k'auna .


Ban manta dake ba maman Hanan, nagode da irin k'aunar da kike man nida littatafaina, nima Ina k'aunar ki sosai...


Sai mun had'u daku cikin sabon littafina bayan sallah idan Allah ya kaimu.


Thank you y'all, I love you to the moon and back♥


Tags: #asiri #aure #kishiya
5175
0
2
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

2019-09-10 18:55:21