Mahabu!

Written by Maman Ja’afarPublished on 2018-12-12 17:59:12Category FictionYana magana ne akan hadarirrikan dake faruwa ga mazaje masu tafiya kasashen waje na rasa rayukka da dai sauransu Ga kuma uwa uba halinda matayensu da suka baro gida suke fadawa ta dalilin rasshinsu a kusa tags: #Maman Ja’afar #rayuwaDuba was labarai »

[4/21, 10:12 PM] Maman Ja"afar: 🌻MAHABU🌻


      1 Daga Alkalamin

Maman Ja'afar✍*GODIYA*


_Ina farawa da godiya ga Allah (S.W.A) mai kowa mai komai daya bani dama da kuma ikon fara wannan littafi na Mahabu lafiya, ina rok'onsa kuma yabani ikon kammalasa lafiya batare da ansamu wata tangard'a ba_


_Da wannan zanyi amfani wajen bawa masoyana hak'uri, kasancewar ba kullum zaku dinga samun Mahabu ba domin nasha fad'a maku dama typing ga mai iyali yanada matuk'ar wahala, amma dukda haka dai zanyi iya bakin k'ok'arina wajen ganin abinda ya turewa buzu nad'i_


_Da banyi niyar fara tura maku ba har sai na kammala, to amma sai naga yin hakan kamar zai d'aukeni tsawon lokaci, shiyasa naga gara inayi ina tura maku a hankali yanda zai kasance harma na kammalasa batare dana ankara ba_


_Masu neman nasakasu a group da masu sakani ina fita, ina mai baku hak'uri wallahi bana yin group kuma banida group amma badan bana so ba sai dan wani dalili na daban_


_Hakan nema yasa nake saka lambata a k'arshen littafin nawa saboda mai buk'atar ci gabansa_


_Ina masu cewa bana saka soyayya a cikin books dina ko kuma bana canza salon rubutuna? Kuyi hak'uri dukda har yanzu ni d'aliba ce acikin rubutu amma na fahimci cewa dukkan wani marubuci yakanyi rubutu ne akan abinda yake damunsa kuma yakeda ilimi akansa domin yaji dadin isar da sakon da yakeso ya isar, to nima ta wannan bangaren nake da ilimi kuma matsalar da nake yin rubutu akai itace tafi damuna a cikin zuciyata_


_Taya zanyi maku rubutu akan abinda banida ilimi akansa? Ina fatan zaku fahimceni?_


_Nagode da irin k'aunar da kuke nuna mani ko nace kuke cikin nuna mani, ni kuma insha Allahu bazan baku kunya ba_👏 *SADAUKARWA*_Wannan littafin Sadaukarwa ne ga K'asashe guda 2 wato Nageria da Nijar_


_Ina rokon Allah ya k'ara had'a kanmu ya kuma ha6ako mana da tattalin arzikinmu kana ya kawo mana zaman lafiya da kuma kwanciyar hankali a cikin K'asashenmu da sauran K'asashen musulmi baki d'aya_


_Muje zuwa cikin Mahabu gadan-gadan._*Mahabu*


Malam Audu ne zaune acikin d'akinsa yayinda ya saka 'yarsa Indo a gaba yana yi mata nasiha gami da jan hankali akan sa6alli-kitar da takeso ta aikata da sunan soyayya


"Yanzu Uwata yin wannan auren kina ganin bazai haifar mana da d'a marar ido ba? Nida zaki bi ta tawa wallahi da Hashimu kika aura d'an gidan sarkin noma, amma ina amfanin ki auri mutum ko gama cin amarci bakuyi ba ya kama hanya ya tafi wata uwa duniya? Uwata kodai Hashimun ne baiyi maki ba?"


Ya k'arashe maganar tasa cikin alamu na lallashi, dayake sunan Mahaifiyarsa aka sakawa Indo d'in shiyasa yake kiranta da Uwata


Shuru Indo tayi na d'an wani lokaci, kasancewar duk wani abu da zai fito bakinta sa6anin abinda Mahaifin nata yake buk'ata ne shiyasa ta rasama abin cewa


"Uwata ki bani amsa mana kinyi shuru" ya sake maimaitawa karo na ba adadi 


"Baba nidai gaskiya da son samu ne da Mahabu d'in kuka barni na aura domin yafi kwanta mani a acikin rai, amma Idan kunce Hashimun kukeso babu komai Baba sai na hak'ura da Mahabu d'in akwai"

Ta fad'a muryarta na sassark'ewa ga dukkan alamu dai inaga kuka take shirin yi


"Malam kaddai maganar nan da muka gama yi da kai d'azu itace kake maimaitawa yarinyar nan?"


Abinda Mahaifiyar Indo Inna Rabi kenan ta fad'a cikin alamu na fusata bayan ta d'aga labulen d'akin mai gidan nata Malam Audu, kana ta k'ara da cewa


"Ni banga illar auren wannan yaro Mahabu ba da kaketa k'ok'arin dak'ilewa, ai ni a ganina abin murna ne kuma abin farin ciki ne ace yau ga 'yarka ta cikinka tana auren d'an Libi (dayake haka ake kiran hausawanmu maza mazauna kasar ta Libiya)


Ta k'ara da cewa 


"Malam indai ba so kakeyi na sakaka a cikin layin masu yi mana bak'in ciki ba dan Ya rasulullahi ka daina tada maganar nan ya isa haka, Indo dai Mahabu takeso shima Hashimun Allah ya bashi wadda ke sonshi ba shikenan ba?"


Tana gama fad'ar wa'yannan bak'ak'en magan-ganun nata ta saki labulen ta wuce abinta band'aki domin dama can ta nufa ta jiyo magan-ganun Malam d'in yayinda tazo giftawa ta k'ofar d'akin nasa.

****

Yau jumma'a da misalin kusan k'arfe takwas na dare a k'ofar wani gida mai farin fenti na hango dandazon 'yan mata da samari kowa yaci kwalliya ya k'ure adaka abinsa sai hidimar gabansu sukeyi, wasu na fira da 'yan matansu, wasu kuma samrin gabzar rake kawai sukeyi, yayinda wasu kuma sigari suketa faman busawa, kowa dai da kiwon da ya kar6eshi wai mak'wabcin mai Akuya ya sayi Kura.


Ga dukkan alamu dai ina tsammanin wani gagarumin biki ne suke gudanarwa a cikin wannan K'auyen nasu na Mayi wanda yake cikin K'asar Nijar


A irin haka ne na hango wasu matasa guda biyu kyawawa kuma ajin farko


D'an bakin shine Mahabu yayinda Abokinsa Mamman shi kuma ya kasance fari, dukkansu ina tsammanin shekarunsu bazasu gaza Ashirin da biyar biyar ba, inma zasu haura hakan to da kad'an ne nakega.


 Zaune a gefe guda bisa wani dakali suna d'an ta6a fira jefi-jefi, a 6angare guda kuma suna jiran k'arasowar Indo wacce ta kasance budurwa ga Mahabu kuma nan bada dad'ewa ba suma ake shirye-shiryen gudanar da nasu shagalin


A tsammanina zamansu anan su kad'ai yasamo asali ne na rashin hayaniya da basa so domin a kullum su basa yiwa kansu kallon yan K'auye, kullum su gani sukeyi hakan tamkar wani k'ask'anci ne agaresu.


"Kasan miye Mahabu?" Mamman ya tambaya tare da duban fuskar babban Aminin nasa cikin kulawa 


"Ina kuwa zan sani tunda ba fad'a mani kayi ba"

Ya fad'a a tak'aice kuma cikin alamu na nuna basarwa


"Wallahi da ace nikeda budurwa zankad'ed'iyar zankad'aziya mai sona da k'aunata kamar Indo wallahi da babu abinda zai kaini yin wata tafiya koda kuwa nanda Yamai ne neman kud'i bare kuma wai har nayi tunanin haurawa wata uwa duniya wai ita LIBIYA, anan kam gaskiya ina ganin wautarka abokina"


Murmushi Mahabu yayi, kana cikin isa da tak'ama na yabon masoyiyarsa da akayi yace 


"Kace da ace kaine ko?"


Gyad'a kai Mamman yayi alamun amsawa


"To kuma sai akayi sa'a ba kai d'in bane ni ne, kaga kenan bai kamata ace kana damun kanka akan wannan ba ko?" Ya fad'a shek'ek'e cikin nuna alamu na ko in kula, kana ya k'ara da cewa 


"Kai Abokina har yanzu baka gane halin mata ba ne? Wallahi duk sanda mace takeyi maka idan dai bakada kud'i wallahi a banza ne, kana ji kana gani zata gujeka ta tafi gurin mai kud'in, ka fahimceni abokina? kud'i ba k'aramin k'arawa soyayya dank'o da k'arko sukeyi ba, saboda haka gaye ka nemi kud'i kawai kaga yanda mata zasu ringa bika, a lokacinma har yanga zaka dinga yi masu. 


Cikin sanyi jiki Mamman ya dubi abokin nasa domin ya fahimci Mahabu yayi nisa kuma ga dukkan alamu ba jin kira zaiyi ba 


"To nidai shawara ta k'arshe da zan baka itace, kawai ka hak'ura da auren yarinyar mutane tunda tafiya zakayi, kaga duk sadda kadawo sai kayi auren ka, karka fitar da yarinya cikin sahun 'yan mata kuma bata shiga layin matan aure ba bare kuma a sakata layin zaw...


Katseshi Mahabu yayi domin ba jin dad'in zancen nasa yakeyi ba


"Babu abinda za'a fasa daga cikinsu insha Allahu, nanda wata 2 zan auri Indo kuma nanda wata 3 zan tafi Libie" Ya fad'a tare da wurgawa Mamman wata uwar harara 


"Ka tafi d'in, sakarai kawai banza, ni kuma ina mai tabbatar maka indai katafi Wabillahillazi ganima zamu kwasa dani da sauran masu rabo" Ya fad'a yayinda yake yiwa abokin nasa dariyar k'eta 


Jijjiga kai Mahabu yayi tare da ciza le6e, kana yace 


"Aiko da sai naci kut...


Kafin ya k'arasa ashar d'in da ya lailayo ne sukaji sallamar Indo a cikin zazzak'ar muryarta mai kama da ana busa sarewa


Mahabu ne ya rik'e baki tare da dukan bakin nasa lokaci guda"Shege baki mai yanka wuya, zaija mani masifa ina zaman zamana, Allah yasa dai bataji firar tamu ba kasan k'arya na shek'a mata akan cewa na fasa yin tafiyar"


Ya fad'a murya can k'asa-k'asa domin gudun kada masoyiyar tasa Indo tajiyo abinda yake fad'a dan dab take dasu


"Ko shanya ce aka shanya anan ai yaci ace ta bushe wannan zamanda mukayi anan" Abinda Mamman ya fad'a kenan yayinda ya mik'e tsaye yana dubanta tare da kakka6e k'urarada rigarsa ta kwasa a gurin


"Dan Allan kuyi h'akuri wallahi yanzunma da k'yar na samu na fito, kunsan babbar k'awa ita da Baranya koda yaushe anaso su kasance ne manne da amarya"


Ta fad'a yayinda ta langa6ar da kai alamun ban hak'uri tattare a fuskarta da kuma nadama sai kace wacce ta tabka wani babban kuskure 


Murmushi Mahabu yayi irin na masoyan da suka dad'e da macewa akan so da k'aunar junansu


"Nidai bani da matsala ta 6angarena domin kinsan bakya laifi a gurina, idanma kinyi laifin nakanyi sauri ne na d'auko yafiya gami da afuwa na ajiyesu a mazaunin da kikayi mani laifin, mita da k'ananan magan-ganun ai sai su o'i sai kace wata mace"


Ya fad'a yayinda yake duban fuskar abokin nasa Mamman gami da yi masa gwalo a kaikaice 


Shi dai Mamman baiyi yunk'urin mayar masa da wata amsa ba saima k'arawa gaba da yayi abinsa domin neman tasa masoyiyar Binta 


"To ya gajiyar biki" ya fad'a yayinda ya tattaro hankalinsa zuwa gareta


"Alhamdulillahi" ta fad'a a tak'aice


"Amma dai ai daga yau kun gama bikin naku tunda amarya ta iso gida ko?"


Zaro ido tayi cikin alamu na mamaki ta dubesa

"Inafa aka gama? Ka manta gobe ne zamu fara fita Gudun San Doki?"


"Gudun San Doki kuma? Mi ake nufi da ita wannan kalmar kuma ta gudun san doki?"Ku biyoni domin jin ko menen gudun san doki, nasan da yawanku 'yan burni baku san wannan kalmar ba ko?Bara naga Comment dinku kun yaba da Mahabu ko kuwa dai bai gamsar da ku ba kamar sauran?👂


  Nice taku

 Maman Ja'afar

+966592551785

[4/21, 10:12 PM] Maman Ja"afar: 🌻MAHABU🌻


      2


Daga Alkalamin 

Maman Ja'afar✍
Gudun San Doki wata al'ada ce ta 6uya da amare kanyi suda k'awayensu yayinda aka kaisu gidan mazajensu


Sukan tafi ne gidajen tsofi su 6uya a k'ark'ashin gadonsu ko kuma cikin Rumbu da garken awakai ko mak'abartu da cikin gonaki da sauran dai guraren 6oyo inda baza ayi tsammanin suna nan ba


Yayinda su kuma dangin ango zasu bazama nemansu babu ji babu gani, wani lokacin su ganosu wani lokacin kuma har sai sun bayar da cin hanci a wasu daga cikin k'awayen amaryar su nuna masu inda suke suje su d'auko amaryarsu su dawo da ita

Sukanyi kamar kwana 5 zuwa sati suna wannan guje-gujen, idan an ganosu nan su koma can idan an gano can d'inma su k'ara yin gaba.

****

Langa6ar da kai tayi kana cikin zun6uro baki tace"Kai Mahabu yanzu tsabar gudun k'auyen da kakeyi har yasa ka fara mantawa da al'adunmu kuma?"


"No ba haka bane Indo kinsan tun tasowata ban cika zaman gida ba, nine bani Yamai bani Maradi bani Agadas wata ran kuma ina Nageria, sannan duk sadda zanzo gida cikin Damina nake zuwa kuma ke kanki kinsan ba aure akeyi ba cikin Damina ko?"


Sai yanzu tayi murmushi da ya bata hujjojinshi gamsassu, saboda ita a tsarinta ta tsani taji wata magana makamanciyar ta raini ga k'auyen nasu na Mayi 


"Wannan gudun na 6uya da akeyi idan aka kai...


D'aga mata hannu yayi alamun dakatarwa cikin murmushi


"Ba sai kin k'arasa ba nama tuna, amma dai ai idan akayi bikinmu bazaki bisu wannan gudun haukan ba ko? Ko baki matsu ki ganni a matsayin mijinki ba kamar yanda ni na matsu ki zamo mallakina?"


Rufe fuskarta tayi da d'an yalolon mayafinta alamun kunya tare da yin murmushi 


"Kenan kanaso a sakani a gad'a kenan ana terere dani nakai kaina gidan miji ko?"


"Hakanefa kuma, na tuna har wata wak'a kuke yiwa wacce batayi ba ko? Um..Um.. yama wak'ar?"


Yayi shuru alamar tunani, zuwa can yayi tsalle cikin murna sai kace wani d'an k'aramin yaro ya amsa tambaya dai-dai a makarantarsu

"Yauwa wallahi na tuna"


_*Ayye wance tayi abin kunya*_


_*Gudun san dokinma batajeshi ba*_


_*Ayye tayi abin kunya*_


_*Jaraba ce koko rashin kunya tayi*_


_*Ayye tayi abin kunya*_


_*Kodama fanko ce bamu lura ba*_


*Ayye.....*


"Dan Allah Mahabu wak'ar ta isa haka karka sa cikina ya k'ulle dan dariya"


Ta fad'a yayinda taketa faman k'yak'yata dariya harda dafe ciki


Shima dai cikin dariyar yace"To shikenan na daina, ai bazanso na k'ullarwa da masoyiyata ciki ba, wallahi Indo kullum haka nakeso naita ganinki cikin farin ciki da annashuwa, shiyasa nake k'ok'arin faranta maki duk ta hanyar da zan iya tunda Allah baiyoni mai kud'i ba"


B'ata rai tayi kana ta dubesa ido cikin ido "kafara ba"


"Allah ya huci ran gimbiya na daina"


Cikin farin ciki da annashuwa suka gama firarsu irin ta masoya sukayi sallama kowa ya kama gabansa Indo ta koma ciki gurin amarya yayinda shi kuma Mahabu ya nufi Majalissarsu domin shan Ataye


Ataye wani shayi ne mai d'an karan dad'i da mutanen K'asar Nijar sukeyi, yana korar bacci kuma yana k'ara k'arfin jiki, amma dukda haka su Mahabu sai sun k'ara Alabukum a ciki ko kuma dai wata k'waya mai sa aji garau

*****

"Kai!Kai! Mahabu zo nan, ina zaka kaketa faman yin wani sand'a sai kace 6arawo? Kai a tunaninka nayi bacci tun d'azu ko? To idona biyu kuma badan komai nak'i yin baccin ba sai dan naga iya gudun ruwanka"


Cewar dattijo Malam Shehu kenan yayinda yake duban d'an nasa cikin 6acin rai


Sosa k'eya nayi yayinda nake sissinar da kai alamun rashin gaskiya, domin a zahirin maganar gaskiya banyi tsammanin zan tarar da wani mahaluk'i idonsa 2 a cikin gidan nan ba, musamman ma idan akayi la'akari da kusan k'arfe sha biyu na dare yanzu, watak'ilma harda 'yan mintina


"Wato ashe tun yamma da nace kabawa Tumakan can abinci k'in jin maganata kayi kasa k'afa kayi ficewarka ko? Shiyasa nace bazanyi bacci ba komin dare zakazo ka sameni kuma sai ka basu abincin sunci"


"Dan Allah Affa kayi hak'uri, wallahi bazan iya shiga wancen k'azamin garken ba duk ca6i yayi yawafa aciki" Na fad'a yayinda nake zuzzun6uro baki


"Ba ca6i ba ko kwata ce yau sai ka shiga, yau inaso na gane ko wane ne uban tsakanina da kai" Ya fad'a rai a 6ace


"Allah ya baka hak'uri" na fad'a a tak'aice tare da tattare sabon wandona na shige cikin garken


Nan dai bada dad'ewa ba zan huta da wannan wahalar insha Allahu, ina amfani mutum yana zaune a gari K'adago ma wannan ta gagaresa (Nera ashirin) mutum bazai samu kud'i ba har sai kaka tayi angama d'ebe amfanin gona, kome kakeso sai kaje kayi 'yar murya kana a baka, ni wallahi ma har na matsu a gama bikin nan nawa nasan inda dare yayi mani.


Ina nan inata faman surutai na na zuci har nagama bawa tumakan abinci da ruwa na share gurin batare dana ankara ba.


Gun Karhi (randa) na nufa na d'ebo ruwa na shiga kewaye na wawwanke jikina kana na nufi d'akina domin kwanciya.


*Bayan wata biyu*


Dandazon mutane ne na hango a k'ofar gidansu Indo mata da maza yara da tsofi sai faman turereniya sukeyi domin ganin wani abu, wa'yandama tsawonsu bai kai ba har d'orasu naga anayi a kafad'a domin suma su ganewa idanuwansu....


Gaskiya kaina ya kulle, wai mike faruwa ne haka?


Kuyi hakuri da kadan👏


  Nice taku 

 Maman Ja'afar

+966592551785

[4/21, 10:12 PM] Maman Ja"afar: 🌻MAHABU🌻


      3


Daga Alkalamin 

Maman Ja'afar✍
Mutane ne na hango dank'am sun cika sun batse, kowa soyake ya ganewa idanuwanshi abinda ke faruwa a gurin


Can cikin gidan na k'ara hangawa, Indo ce na gani zaune tsakar gida akan d'an k'aramin turmi daga ita sai 'yar shime da d'an kamfai sai faman rabsa kuka takeyi tamkar ranta zai fita


Yayinda na hango wata 'yar tsohuwa mai kimanin kusan shekaru sittin a duniya rik'e da wata k'warya sai ya6a mata lalle takeyi ta ko ina, tana yi tana had'awa da 'yan wak'e-wak'ensu irin na sakun lalle


*Dangani daure d'iyar Nana*

*Dangani daure d'iyar Nana*

*Aure ba mutuwa bane*

*Shi kuma ba yak'i ne ba..*


Yayinda su kuma k'awayen amarya da sauran 'yan kallo sukeyi mata amshi.


And'au kusan minti ar'ba'in ana yin wannan wanka a bainar jama'a kana daga bisani aka kammala amarya ta nufi d'aki domin ta saya jikinta.


Mahabu ne zaune akan k'atuwar tabarmar kaba dashi da abokinsa Mamman , kowa yaci kwalliya ya k'ure adaka da k'ananun kaya har wani tokewa da zanzaro sukayi


Suma dai nan 6angaren angon gabatar da nasu shagul-gulan bikin sukeyi, sai dai su Inga tsiyar dangi suke gudanarwa yau, ga dukkan alamu an dad'e da sawa ango lalle ta 6angarensu, sa6anin gidansu Indo da akeyin sakun lalle yau.


Inga tsiyar dangi itama wata al'ada ce da akeyi tsakanin duka gidajen guda 2 sai dai kowa da ranar da yake gudanar da nasa inga tsiyar 


Tabarmar kaba k'atuwa ake shinfid'awa a tsakar gida, yayinda ango ko amarya zasu zazzauna dasu da makusantansu guda d'aya ko biyu, 'yan'uwa da abokan arziki kuma kowa zaizo ya ajiye gudunmuwarsa a wannan tabarmar, yayinda mai shela shi kuma zai d'inga d'aga sauti yana fad'awa jama'a adadin kud'in da kowa ya bayar domin ango ya hardace saboda ranar mayarwa.


Sai zubawa Mahabu kud'i akeyi amma a yanda na fahimta kwata-kwata shi hankalin sam bama akan kud'in yake ba


Cikin damuwa Mahabu ya dubi Mamman tare da yin K'asa-k'asa da muryarshi domin gurin dank'am yake da cukowar jama'a 


"Mamman yanzu hakafa k'artin banza suna can suna kalle mani matar da za'a kawo mani gobe ko?"


Harararsa yayi cikin wasa domin indai da sabo yaci ace Mamman ya saba da 'yan k'orafe-k'orafen Mahabu


"Matarka ita kad'aice mata? Sauran matan da akeyiwa fa? Kosu ba mata bane?Karka manta tun kamin a haifemu akeyin irin wannan al'adar kaga ko dolenka ko kanaso ko bakaso a gane maka mata tunda an saba anayin abu baka isa kazo rana tsaka kace kai ba za'a ayi maka ba, duka matar takama a nawa take? Shekara sha biyar ta wuce wanka ne a tsakar gida?"


Mintsininsa yayi ta yanda jama'a bazasu ganshi ba


"Kaifa wani lokaci mahaukaci ne, bansanma me ya kaini fad'a maka damuwata ba"


Murmushin k'eta Mamman yayi "To kai abokina me ya hana ka fad'awa iyayenta tun farko bakason ayi mata wanka?"


Bai ce masa komai ba saima duk'ar da kansa da yayi k'asa na d'an wani lokaci, kana daga bisani yayi k'wafa 


"Allah dai ya tsinewa wannan shegiyar al'adar ya nuna mana ranar da za'a dainata" Ya fad'a a bayyane 


Dariya Mamman ya bisa da ita


"Yekuwa jama'a! Tanimu wanzan abokin ango ya bada jaka biyar" Cewar marok'in kenan yayinda yake d'aga kud'in sama domin nunawa jama'a kowa ya gani


Da wannan suka maido hankullansu gurin inga tsiyar dangin da ake gudanarwa


"Ammafa mutumina Tanimu ya k'ok'arta ba laifi fa" 


"Dayake kyauta ya bani ba, ko ka manta ga bikinsa jaka hud'u na saka mashi a inga tsiyar dangi?" Ya fad'a rai a 6ace


"Allah ya huci zuciyar ango, maida wuk'aken domin nidai muna nan tare dakai tun d'azu bare ko kayi tunanin nima naje kallon sakun lallen ne da kaketa faman yi mani muzurai"


Yana gama fad'ar haka ya mik'e tsaye yana lalubar aljuhunsa domin bayar da tashi gudunmuwar shima.

*****

*Washe gari da daddare*


Indo ce goye a bayan wata tsohuwa tayi luf sai kace wata 'yar k'aramar yarinya, yayinda 'yan rakiyarsu suke biye dasu a baya suna tafiya suna raira 'yan wak'ok'insu irin na rakiyar amarya d'akin mijinta

Su kuma 'yan rakiyar amaryar suna biye dasu abaya suna amsawa


A haka har suka iso k'ofar gidan na Malam Shehu tsohuwar ta sauketa a k'ofar gidan aka mik'a mata tsintsiyar laushi a hannun dama hannun hagun kuma aka bata Sahwani ta rik'e (buta) kana daga bisani aka bata umarni da tayi bisimillah kana ta fara shiga da k'afarta ta dama.


Kamin kace me gidan anguna ya kaure da gud'a ta ko ina, kowa ka kalla a wannan lokacin fuskarsa na cikin farin ciki da annashuwa, sai 'yan d'ai-d'aikun mutane da ba'a rasa ba daga 6angaren su Hashimu.

****

*Washe gari*

Akayiwa amarya jerenta mai d'an karen kyau, Samiru kusan saiti ashirin aka jejjera mata a cikin kwabet d'inta, yayinda su kuma K'waraye aka jejjera matasu a can saman kwabet d'in, sai 'yan fanteku da kuma languna nacin abincin yau da kullum


Gado kuwa guda biyu akayi mata dan gata, da babba mai rumfa sai kuma d'an madaidaici a K'asa, tabarmin roba ma har uku aka kai mata, ta kaba kuma guda d'aya, d'aki dai ya had'u iya had'uwa sai fatan su Indo Allah ya bada zaman lafiya da kuma zuri'a d'ayyiba.

*****

Washe gari akayi tuwon uwar d'iya tare da unbande(kayanda ake rabawa ango da 'yan'uwansa daga gidansu amarya)da daddare kuma k'awayen amarya sukayi da huwarsu ta 6arna inda komai suka zubashi oba, suna ci man shanu na bin hannayensu


"Yanzu Lantu a ina zamu fara zuwa 6oyon kenan?" Cewar d'aya daga cikin k'awayen amaryar kenan yayinda dafa dukan shinkafa ya kai mata karo


Wacce aka kira da Lantu shuru tayi alamun nazari kana daga bisani kuma tace

"Ina ganin kawai mu fara ta gidan gwaggo, kunsan ta tsufa sosai ba gani takeyi garau ba barema idan anzo nemanmu har tayi tunanin fallasamu"


Da wannan shawarar 'yan matan amarayar sukayi sauri suka gama abinda sukeyi suka fice daga gidan a lokacin kusan k'arfe sha biyu na dare


Inna Fure maihaifiya kenan ga ango, tsohuwa yar kimanin shekaru hamsin abduniya ta fito zata zagaya ta gansu suna sand'a d'aya bayan d'aya suna ficewa daga gidan batare da yin ko k'wak'waran motsi ba


Batayi tunanin ce masu komai ba saima murmushi da tayi ta wuce band'aki abinta.

 *****

Gudun san dokinsu Indo bai wani d'au lokaci ba suka gamasa kasancewar ba wani goyon bayan kirki amaryar ke basu ba, a k'arshema ita tabada shawarar aje 6uya gidan Yayar Mahabu, batare da 6ata lokaci ba kuwa aka ganosu a can aka mayar da amarya d'akin mijinta 


Badan komai Indo tayi hakan ba sai dan sanin kanta ne Mahabu ba san wa'yannan 'yan guje-gujen yakeyi ba, itako ta tsani abinda zai 6ata ran Mahabu duk k'ank'antarsa kuwa.

******

*Bayan sati uku*


Mahabu ne zaune a

gaban Indo sai faman dibi-dibi yakeyi, yanaso ya fad'a mata maganar tafiyarsa Libiya nanda sati d'aya kuma yana jin tsoron abinda ka iya biyo bayan furta zancen nasa da yaketa faman 6oyewa domin tun kamin d'aura aurensu ya tabbatar mata da yafasa yin wannan tafiyar, shiyasama ta saki jiki sosai dashi


"Mahabu lafiya kuwa ka tasani a gaba sai faman kallo kake? Tun d'azun nace maka na zuba surfen tsaba (gero) a turmi, yanzu hakama ya kusan jik'ewa, kai baka barni naje nayi surfen ba kuma kai baka fad'a mun abinda kakeso ka fada mani ba, ko so kake nayi daren tuwo ne yau?"


Sosa k'eya yayi kana daga bisani yayi k'arfin hali ya daure yayi ta maza ya dubeta jiki a sanyaye


"Dama..kan maganar tafiyata..Libei ne nakeso na fad'a maki..ina ganinma indai tafiyar ta tabbata ran kasuwar tasawa nake ganin zamu wuce (ranar lahadi kenan) Yana magana yana inda-inda sai kace wani marar gaskiya


Duk'wa tayi a gabansa ta d'auki k'waryar furarda ke gabansa wacce ya shanye furar tun d'azun amma bai daina juya ludayin a cikin k'waryar ba saboda jimamin magan-ganun dake shirin fitowa daga bakinsa


Saida tayi murmushi kana ta nufi bakin k'ofar d'akin, d'aga labulen d'akin tayi kana ta waiwayo ta dubeshi


"Yau kuma zaulayar ta wannan 6angaren ta motsa maka? To a canza wani salon wasan domin wannan wasan bai gamsar dani ba....Har yanzu dai shinfid'a mukeyi domin bamu shigo cikin labarin Mahabu gadan-gadan ba


  Nice taku 

 Maman Ja'afar

 +966592551785

[4/21, 10:12 PM] Maman Ja"afar: [23/03, 6:36 a.m.]

🌻MAHABU🌻


      5


Daga Alkalamin 

Maman Ja'afar✍
Malam Audu yaci gaba da banbamin fad'ansa


"Tun farko saida nayi k'ok'arin tunatar dake irin wannan ranar tana zuwa amma kikayi kunnen uwar shegu da magana ke ga 'yar sarkin masu soyayya, saboda haka tun wuri ina mai gargad'inki tun kamin na zuciya na 6a66ala maki k'afafuwa garama ki bar gidan nan tun wuri, kije can soyayyar taki tayi maki maganin matsalarki"


Yana gama fad'ar wannan maganar ya shige d'aki abinsa ko kallon inda matar tasama take baiyi ba


Cikin d'aga sauti Inna Rabi ta bisa da "Aiko babu inda zata tafi batare da anzo anyi bikonta ba, ehe"


Kana ta juyo kan d'iyar tata


Cikin siga ta lallashi ta dube ta tare da yin kasa-kasa da murya


"Keko Indo me ya kaiki dawowa gida da sunan yin yaji bayan bikinki duka-duka ko wata d'aya bai cika ba? A gaban idonki dai idan aka kai amarya wata saita shekare cur bata fita ko nan da can ba, mai d'an sauk'in kunya ce zata fita bayan wata shidda, so kike ki jamana abin magana ne a gari? Ki dubafa ki gani yayunki Hansatu da Rakiya yau kusan shekarunsu hud'u-hud'u a d'akin miji amma babu wacce kika ta6a ganin ta lek'o gidan nan da sunan yin yaji, sai ke da suke ganin kamar nafi fifitaki akansu ace an fara samun 6araka daga gareki? Haba Auta a dinga hak'uri mana"


"Inna idan ya tafi fa sai yayi shekara da shekaru bai dawo ba ni shine damuwata fa" ta fad'a tare da zuzzun6uro baki harda wani harba k'afafuwa


"Idan kikayi hak'uri kuma Indo ai shekarar kamar kwana ce, kuma nasan dai yanda Mahabu yake matuk'ar k'auanarki na tabbata bazai wuce shekara d'aya zuwa biyu ba zai dawo gida"


"Inna to idan ya tafi ni miye matsayina kenan?"


Cikin alamu na 6acin rai uwar ta dakatar da ita


"Ni kam Indo matsalata dake shegen tambayoyin bin k'wakk'wafin tsiya, ke inma baya ga wauta dake damunki tafiyar tasa ba gata bane agareki? Ki duba kiganifa duk wa'yanda mazajensu suke Libei zaki gansu sunsha banban da sauran mata, saboda kusan duk wata d'aya biyu sai sunyo masu aiken kud'i atamfofi sabullai mayuka, ke har turarema aiko masu sukeyi, to me yafi wannan jin dad'in duniya? Bakiga wasu matanma har bak'in ciki sukeyi maki ba dan kin auri wanda zaya Libei? Dan Allah Indo ki kwantar da hankalinki ki bashi goyon baya d'ari bisa d'ari yayi wannan tafiyar kinji Auta? Wannan tafiyar fa idan yayi bake ba harma mu iyayenki sai mun amfana da ita, ko dai nakison ganinmu cikin farin ciki ne?"


Murmushin yak'e tayi wanda naji hausawa suna yi masa kirari da kafi kuka ciwo


"To Inna babu komai na amince Allah ya kaishi lafiya ya dawo mana dashi lafiya"


"Yauwa to koke fa 'yar albarka? Shiga d'akina akwai Hura na nan a saman Ragaya ki d'auko kisha yanzun nan na gama damata kuma taji kindirmo sosai harma mai zaki gani a samanta ya d'an kwanta, irin damunki ne nayi yanda kikasan dama kin sanar dani zakizo"


Dayake Indo masoyiya ce ga hura wacce taji nono sosai shiyasa da gudu ta shiga d'akin ta sauko hurar daga kan ragaya inda aka d'orata ta zauna k'asa dirshan ta fara kwankwad'ar furar abinta.


Da wannan uwar ta samu ta lalla6a ta shawo kan 'yar tata har zuwa dare lokacin da 'yan biko sukazo aka basu ita suka d'auketa suka mayar da ita d'akin mijinta.

****

Tun daga wannan lokacin Indo ta daina nuna damuwarta akan tafiyar da Mahabu zaiyi

Sai dai hakan bawai yana nufin da ta daina damuwar bane kwata-kwata, a'a damuwa na nan dank'are a cikin zuciyarta dandai kawai bata da mai share mata hawayene shiyasa ta bar abin iya ranta, dan hakanema duk ta wani rame ta fige ta lalace dama gata ba wata k'ibar kirki ba, kuma sai gashi damuwa tazo tayi mata yawa ga kuma alamun shigar sabon ciki a jikinta na kusan wata d'aya

Ana dara ga dare yayi.

****

Tafiyar Mahabu ta rage saura kwana 3 Mahaifinsa ya basa umarni da yashiga runbu ya d'ebo wake kimanin buhu uku yaje kasuwar Isawan ya siyar domin k'arin guzurin tafiyarsa


Itama Mahaifiyar Mahabu ba a barta a baya ba domin k'aton d'an marak'inta ta kwance ta siyar ta mik'awa Mahabu kud'in domin ya k'ara yayi guzurin tafiyar da ke gabansa.

****

Yau mun wayi gari ranar Alhamis wanda gobe Jumma'a kenan mukesa ran tafiyar Mahabu ta kama


Har Indo tayi nisa a cikin baccinta taji Mahabu na tashinta


"Indo tashi muyi magana kinji?"


Dak'yar ta samu ta wartsake daga nannauyan baccinda yayi awon gaba da ita, cikin layi irin na mai jin bacci ta dubesa


"Lafiya dai Mahabu ko?"


"Lafiya lau Indo, kinsan gobe ne zan tafi ko?'


"Eh" ta fad'a a tak'aice 


"Dan Allah Indo ki cire damuwa a cikin ranki, insha Allahu kamar yau ne zakiga nadawo munci gaba da zamanmu cikin so da k'aunar juna kamar yanda muka fara kinji?"


Duk da k'ok'arin da tayi wajen takawa kukanda ke yunk'uro mata birki amma hakan bai yiyu ba saida kukan ya kubce mata ya fito


Yarfa hannuwa yayi kana yace


"Kinga irinta ba? Shiaysa hankalina ya kasa kwanciya wallahi, saboda kullum tunani nakeyi da zarar na sa k'afa na tafi baki da wanda zaki mayar abokinki face kuka, dan Allah Indo ki daina kada kije garin kuka wani kije wani ciwoma yazo ya sameki"


D'ankwalinta tasa tana goge hawayenda keta faman shatata a fuskarta


"Indo so nake kiyi mani alk'awarin bazakiyi kuka ba ko bayan na tafi, kiyi mani alk'awarin zakici gaba da mu'amalolinki tamkar ina nan kinji? Ni idan kikayi mani haka kin gama mani komai"


Ya fad'a yayinda ya rungumeta a jikishi yana mai dadda6ar bayanta alamun rarrashi


Cikin shesshek'a tace"insha Allahu bazanyi ba, amma Mahabu idan ka tafi sai yaushe zaka dawo kenan? K'ilanma har sai na haihu yaron ya girma baka dawo bako?"


Jikinsa yayi sanyi matuk'a da jin wannan kalamin nata


"Nidai kwanciyar hankalinki kawai shine damuwata Indo, amma maganar dawowata ai ba dad'ewa zanyi ba, kika sanima ko ina can na aiko kud'i a d'auko mani ke?" Ya k'arashe maganr tasa cikin murmushi


Itama dai murmushin ta mayar masa dashi, kana yaci gaba da cewa


"Ko bayan na tafi idan kina da buk'atar wani abu ki nemi Mamman zai baki, domin akwai kud'in da nabashi dan kawai kula dake, saboda nasan idan na bawa Inna ba lallai ta bakisu a sadda kike buk'ata ba, har kud'in ragoma duk na bar masa suna hannunshi, addu'a kawai ta rage mana, muyi fatan Allah ya kaini lafiya ke kuma Allah ya saukeki lafiya koba haka ba?"


A ranar dukkansu babu wanda yayi wani baccin kirki, kawai dai sun kwanta ne amma kowa da tunaninda ya addabi zuciyarshi.

*****

■Washe gari■


Tun safe Mahabu ya gama kimtsa komai nasa Amalanke kawai yake jira


 Mamman da Tanimu ne sukazo da Amalanke, batare da 6ata loakci ba suka d'ebi Mahabu dashi da Mahaifinsa da kuma mahaifiyarsa


Indo dai bata samu damar zuwa yin rakiyar ba saboda tun cikin dare ta tashi da wani matsanancin zazza6i.


Har zuwa cikin garin tasawa 'yan rakiyar suka kaisa, tunda dama tsakanin Mayi da tasawa indai a amalanke ne tafiyar batafi ta mintin arba'in zuwa awa d'aya ba.....


A garin tasawa ne tushen labarin tafiyar Mahabu K'asar Libei ya fara Maman Ja'afar

+966592551785

[4/21, 10:12 PM] Maman Ja"afar: 🌻MAHABU🌻


      4


Daga Alkalamin 

Maman Ja'afar✍
"Kinga Indo dawo dan Allah ki zauna magana ce zamuyi ta fahimta, karki damu da jik'ewar hatsi ai a kwai wani a runbu idan ya jik'e sai a d'ebo wani"


Da jin wannan kalamin nasa jikinta yayi sanyi, hakanan a sanyaye ta dawo d'akin ta zauna dab dashi tayi tagumi da hannayenta duka biyun, ga dukkan alamu shi take sauraro


"Indo dan Allah idan na fad'a maki kada kiyi mani mummunar fahimta kinji?"


"Uhm ina jinka Mahabu fad'a mani abinda kakeson fad'a mani kawai basai ka tsaya yin wani dogon sharhi ba"


Baiji dad'in ganin yanda yanayinta ya sauya lokaci guda ba, amma sai dai bashida mafitar da ta wuce ya sanar mata d'in, domin ko bata sani ba yanzu dolen sa dai ranar da zaiyi tafiya sai yayi mata bankwana 


"Maganar tafiya Libei ce dama nakeso nayi maki kin mayar da ita wasa, wallahi fa da gaske nakeyi rana yata yau zan tafi insha Allahu"


Fad'uwar gaba taji likaci guda tare da zubar wasu zafafan hawaye batare da ta ankara ba


"Yanzu Mahabu hakan da kayi mani yaudara za'a kirashi ko kuma rashin adalci? Kasan kuwa irin yak'inda nayi kafin na zamo matarka? Haba Mahabu dan Allah karka yi mani haka mana wallahi zanji kunya agurin Affana idan ya samu wannan labarin"


Ta fad'a yayinda ta rungumesa tare da sakin wani tsanancin kuka mai ban tausayi sai kace wacce aka aikowa da sak'on mutuwa


"Haba Indo ki fahimceni mana, tafiyar nanfa da zanyi badan buk'atuna kawai zanyita ba ni kad'ai a'a harda naki buk'atun da kuma na yaran da zamu haifa nan gaba, ni a ganina tafiyar tamkar wani rufin asiri ne agaremu dagani harke baki d'aya, kina ganifa idan akace maki garin Allah ya waye ko Biye(Nera ashirin) da zan baki ki siyi 'yar tsala(wainar cikin mai)bani da ita sai kinje gurin Affa ya baki, banida ikon cin abinda nakeso a gidana sai wanda akaga dama aka girka, ko salla tazo Affa ne keyi mani kayan salla, idan kin ganni cikin kud'i to kaka ce tayi an gama kammala amfanin gona zan dinga d'iba ina sayarwa domin saka canjin a aljihuna, yanzu inba dan rashin kud'in ba taya zan zauna gida d'aya da iyayena Indo? Maganar gaskiya Aisha sai dai ki sawa ranki hak'uri amma tafiya kam babu fashi"


Da gama jin wannan dogon sharhin nasa wanda ya tabbatar mata da cewa lallai bata isa ta hanashi yin wannan tafiyar ba ta k'ara rushewa da wani uban kuka tamkar ana yayyanka naman jikinta


"Yanzu Mahabu kana nufin kaima idan ka tafi sai nayi shekara da shekaru ban ganka ba kenan? Haba Mahabu kaji tausayina mana karkasa duniya tayi mana dariya, Mahabu ka tuna so da k'aunar da ke tsakaninmu mana, ko har ka manta ne? Wai Mahabu kodai har kafara gajiya dani ne tun yanzu? dan naji dama wasu matan suna cewa wai amarcin yanzu dama na wata d'aya ne, har a lokacin ina k'aryatasu ina cewa nidai namu amarcin dani da kai na har abada ne insha Allahu, kaddai kace mani maganarsu ce ke shirin tabbatuwa akanmu?"


Jawota yayi ya k'ara rungumiwa a jikinsa yana bubbugar bayanta alamun rarrashi, domin ga dukkan alamu wa'yannan sabbatun da takeyi sun kusan fitar da ita daga cikin hayyacinta


Ba shakka yarinyar ta basa tausayi, sai dai da zama cikin irin wannan k'asurgumin talaucin ya gwammace ya jure tausayin nata nad'an wani lokaci, domin nanda gaba kad'an saita fi kowa murna da yin wannan tafiyar insha Allahu.


"Mahabu lafiya kuwa nake jiyo wani abu kamar tashin kuka daga d'akinku?"

Cewar mahaifiyarsa kenan yayain da ta raka6e daga bakin k'ofar d'akin tare da jimamin abinda ke faruwa a cikin d'akin 


"Ina Indo d'in take ne ko itace mai yin kukan?"


"Inna babu komai fa, kilanma kukan D'an marak'i(Sa)ne kikaji kike tsammanin kukan mutum ne" ya fad'a yayinda yake yiwa Indo nuni data goge hawayenta domin kada Inna ta fahimci abinda ke faruwa


"To shikenan"

"Indo! Dan Allah zo ki tayani sissika kinji? tun d'azun naketa famanyi amma har yanzu dawar tak'i k'arewa sai kace k'arota akeyi"


Simi-simi Indo ta fito daga cikin d'akin ido jawur sai kace anyi mata feshin barkono


"Ja'irin Yaro, kace mani ba a d'akinku nake jiyo tashin kukan ba? Ga idanuwan yarinya nan sunyi jajir sai kace wadda aka bad'awa tasshi(yaji) kodai kaima irin mazan nan ne masu dukan matayensu?"


"Haba Inna, Allah ya sauwak'e na d'aga hannuna da sunan zan daki mace barema matar da nake aure, kawai kan maganar tafiyata Libei ne danayi mata maganar shine take kuka" Ya fad'a yayinda yake shirin fitowa daga d'akin


"Wai da gaske haka ne Indo?"


D'aga mata kai tayi alamun amsawa 


Nan take tsohuwar ta d'aure fuska tamau tamkar ba ita bace ta gama duban Indo da sigar tausayi d'azu ba


"Inma zaki daina wannan kukan shagwa6ar garama tin wuri ki daina domin dagani har babanshi babuwanda bai amince masa yayi wannan tafiyar ba, sai ke rana tsaka zakizo mana da wani kinibibi?"


Rik'e baki tsohuwar tayi kana ta k'ara da cewa


"Ni tunda nakema nata6a ganin jarababbiyar yarinya irinki Indo? 'Yar mitsitsiyar yarinya dake amma kullum kina nane da miji? harda wani iya yin wai bakiso ya tafi nema? Wannan zamani! Allah dai ya fitar damu lafiya daga cikinshi"


"Inna ayi mata a hankali har yanzu Indo yarinya ce fa" ya fad'a cikin yanayi na 6acin rai, dan dai ba yanda ya iya ne amma da yanada iko da ya dakatar da Mahaifiyar tasa wad'annan 'yan magan-ganun da takeyiwa abar k'aunarsa


"To tantabara sarkin aure ai sai kazo ka dakeni sabida na ta6a maka 'yar lele ko?


Indo dai bata tsaya ta ida jin k'arshen maganar tata ba, ta kaikaita ta shige d'akinta tare da d'auko mayafi ta yafa ta kama hanyar gidansu, tana tafiya hawaye na bin fuskarta


"Ke Indo zo mana, ina zakije ne haka kina kuka? Dan Allah dawo karkije kiyi mani bak'in fenti a wajen iyayenki" Mahabu ne mai fad'ar haka yayinda yake binta a baya


"Barta ta tafi mana ai bamu kad'ai za'a zaga ba harda ita, ace aure ko wata guda baiyi ba har ta fara yin yaji"


Bai bi ta kan uwar ba saima k'ara azama da yayi wajen k'ok'arin dakatar da Indo d'in abinda take shirin aiwatarwa.


 ****

Inna Rabi ce na hango k'ark'ashin bishiyar da ke tsakar gidan d'aure da d'aurin k'irji, kan nata kuwa ko d'ankwali babu, tana daka cikin k'warewa tana tilla ta6aryarta tana cafewa cikin nishad'i abinta, wani lokacin ma harda 'yan wake-wakenta na habauci take had'awa


Tana cikin haka ne ta hangi tahowar Indo ta bayan zanar da aka kewaye gidan da ita, dayake zanar ba wani tsayin kirki ne da ita ba shiyasa wani lokacinma zaka iya hangen mai wucewa ta k'ofar gidan, musamman ma dogaye irinsu Indo


Da shigowar Indo ta sake rushewa da wani sabon kukan


Cikin tashin hankali uwar ta tarota da sauri"Indo lafiya dai ko? Ko mutuwa akayine a gidan naku? Kai ina tsammanin ba mutuwa bace domin da ace mutuwa ce na tabbata koke-kokenda za'ayi a gidan naku muma zamu iya jiyowa daga nan tunda ba wani nisan kirki ne a tsakaninmu ba"


Uwar sai faman jero mata tambayoyi take amma Indo babu abinda takeyi face rabsar kukanta


Saida uwar ta daka mata tsawa da k'arfi tukunna ta dawo hayyacinta 


"Dama Inna ashe wai Mahabu bai fasa yin tafiya Libei d'in ba k'arya yayi mun yace yafasa? wai sai d'azu ne yake shaida mani wai wai yau saura sati d'aya ya taf...


"Shine ke kuma kika kwaso tsumman k'afarki da nufin yin yaji ko kuma kawo k'ararsa gurinmu ko?"


Cewar Malam Audu kenan Wanda shigowarsa gidan kenan yanzu....


 Maman Ja'afar 

+966592551785

[4/21, 10:12 PM] Maman Ja"afar: 🌻MAHABU🌻


      6


Daga Alkalamin 

Maman Ja'afar✍Cikin jimami gami da kewar juna sukayi sallama yayinda su Mamman suka nufi hanyar komawa gida shi kuma Mahabu ya k'ara nausawa cikin tasha domin neman motar da zata sadashi da Damagaran


Bai wani 6ata lokaci ba gurin samun motar "Dan Allah wannan motar Damagaran zata tafi?"

Ya tambayi wani d'an saurayi wanda yake jingine a bayan wata rakwa6a66iyar mota


"Eh can zata tafi saidai ba yanzu take tashi ba"


"Kamar ya? bayan naga kuma motar a cike?" Ya fad'a cikin alamun mamaki


"Kai karka dameni da tambayoyi mana, to ba yanzu take tashi ba sai bayan sallar juma'a, shikenan ko?"

Da gama fad'ar haka saurayin ya zagaya ya shige cikin motar abinsa ya zauna


Shima dai Mahabu bai tsaya k'ara neman ba'asi ba ya d'auki jakarshi gari yayi zafi shima ya shiga cikin motar ya zauna.


Kamar kuwa yanda karen motar ya fad'a, ana tasowa daga sallar juma'a motarsu Mahabu ta tashi, kamin wannan lokacin dama ta riga ta gama cika da mutane.


*****

"Inna har kun dawo daga rakiyar 'yan Libei d'in?" Cewar Indo kenan wacce tun tafiyarsu take kwance a bakin k'ofar d'akinta sai faman murk'ususu takeyi


"Eh wallahi, ke dai bari 'yar nan abin gwanin tausayi, yanda kikasan ince yafasa yin tafiyar nan mu dawo gida tare"


Da jin wannan maganar aiko sai hawaye shar-shar tamkar dama jira takeyi


"A'a kaddai kice mani zazza6in ne har yanzu bai sakeki ba?"


"Eh amma da d'an sauk'i yanzu" ta fad'a a tak'aice


"To sannu, shiga d'aki kid'an mik'e ko kya samu kiji d'an dama-dama kamin Affanku ya dawo daga daji na jik'a maki hararra6i da sabara dama kamin ya tafi na bashi sallahunsu(Sako)


"To Inna"


Da k'yar ta samu ta rarrafa ta shiga d'akin, tana shiga kuwa batai wata-wata ba ta fara sana'ar tata wato kuka.


******


Dukda motar da su Mahabu suka shiga rakwa6a66iya ce amma hakan bai hanasu tsula gudu a hanya ba


Sunyi nisa sosai a cikin tafiyar tasu suka hango Jandarmomi tsaitsaye akan hanya (Gate)


"Ina masu karti? (Takardar zaman k'asa) kuyi sauri ku fiddo kamin mu k'arasa gunsu"


Cikin sauri kowa ya firfitar da takardar daga aljihunshi, banda Mahabu wanda ya baro tashi gida a tsammaninshi takardar batada wani amfanin kirki akan hanyar Libei d'in


Suna k'arasowa dab dasu Jandarmonin basu nemi wani k'arin bayani ba sai neman takardun kamar dai yanda dama direban ya fad'a masu tun abaya


Masu takardu suka babbayar suko su Mahabu da basu da ita aka cajesu jaka d'aya- d'aya(jaka d'aya ta nijar kimanin dari biyu kenan koda hamsin amma yanzu bansani ba tunda nerar tamu har yanzu batada tsayayyen farashi)


Da isarsu cikin garin Damagaram basu wani tsaya 6ata lokaci ba suka nemi masallaci sukayi sallar la'asar, amma shi Mahabu harda azahar ya had'a yayi dayake dama a tasawa bai tsaya ya sallaci jumma'a ba


Da gama sallarsu suka nufi wurin mai abinci aka zubo masu farar shinka da miyar yakuwa (abinci mafi soyuwa kenan ga mutanen garin) suka shararra6i abinsu, suka k'ara nausawa tasha domin neman motar da zata kaisu garin Adarbiso


Basu sha waa wahala sosai ba wajen samun motar Adarbiso d'in, shima d'an zagayen da sukayi cikin tasha dandai basu san cikin garin bane ba shiyasa.


"Adarbiso! Adarbiso! Saura mutum hud'u ta cika" cewar wani k'aren mota kenan yayinda yaketa faman safa da marwa a tsakanin motocin


Dayake dama su uku ne kad'ai zasu shiga motar Adarbiso d'in sauran mutanen duk iya Damagaran dama tafiyarsu ta tsaya


Wasu sunzo neman kudi, yayinda wasu kuma zumunci ne ya kawosu garin na Damagaran d'in. 


"To kai Kare mu nan mu uku ne ya za'ayi? Zaku jamu mu wuce Adarbiso d'in ne ko kuwa a dole sai kun sami cikon mutum d'ayan?"


Cewar Sa'adu kenan d'aya daga cikin abokan tafiyar na Mahabu


Ko kallon inda sukema baiyi ba saima ci gaba da neman fasinjansa da yaci gaba dayi


"Bawan Allah maganafa mukeyi maka ka mayar damu wasu dutsina" cewar Mahabu kenan bayan ya dafa Karen motar


"To ai ji nayi yace kare! Ni kuma na tabbata duk nan cikinmu babu kare inba shiba shiyasa na ajeshi a jerin mahaukata naci gaba da abinda ya dameni tunda ni inada aikin yi"


"Allah ya baka hakuri, yanzu ma iya shiga mu zauna daga ciki ko kuwa?" Cewar Abashe kenan cikon na ukun wanda zasu wuce Adarbiso d'in tare


"Kwa iya shiga, amma dai kai yakamata kaje ka koyo magana dan na lura ba iyata kayi sosai ba" ya fad'a tare da duban fuskar Sa'adu wacce tayi bak'i ta rine dan tsabar shan sigari.


Koda shigarsu mai motar bai tsaya ida jiran mutum d'ayan ba ya tada motarsa suka lula.


******


"Ummaru! Ummaru! Indo ce kwance a tsakar d'akinta tana kiran d'aya daga cikin yaran gidan nasu, da yake gidan nasu babban gida ne amma kowa da nasa 6angaren ita kad'aice aka ajiye dab da Inna wato sirikarta kenan


Da gudu yaron d'an kimanin shekaru shidda yazo, domin yasan indai ya shigo 6angaren Indo bazai rasa d'an abin sakawa a bakin salatinsa ba


"Dan Allah Ummaru jeka yi sauri ka kira mani Mamman kaji?"


Dayake yaron yasan Mamman d'in saboda yana yawan shigowa gidan shiyasa bai 6ata lokaci wajen tambayarta ko wanne Mamman take nufi ba.


Can k'ark'ashin wata bishiya ya hangoshi zaune sunata fira suna korawa da ataye cikin nishad'i shida abokansa


"Mamman wai Indo tace kazo" abinda yaron ya fad'a kenan bayan ya isa inda suke


Cikin mamaki Mamman ya dubesa "lafiya kuwa Indo ke nemana yanzu?"


"Nima ban sani ba" ya fad'a a tak'aice 


Sallama yayiwa abokan nasa kana yabi Ummaru suka juya


Da isarsa ko 6angaren Inna bai lek'a ba ya wuce kai tsaye 6angaren su Mahabu


"Yanzu Ummaru yazo yake cemani wai nazo kina nemana lafiya kuwa?" Cewar Mamman kenan bayan ya samarwa kansa matsugunni a cikin d'akin


"Lafiya za'ace, amma dai ba lau ba, zazza6i ne ke damuna sosai wallahi shiyasa nace yayi mun l kiranka ko zaka taimaka ka siyo mun magani wajen Iliya mai tireda"


"Assha! Ashe bakiji dad'i ba?"


Tasowa yayi yazo dab da inda take kwance ya kai hannunsa zuwa ga jikinta


Cikin alamu na tausayawa ya dubeta


"Gashi nan kuwa jikin zafi rau sai kace garwashi"


Taso ta taka masa birki tun lokacin da ta lura da so yakeyi yakai hannunsa zuwa gareta, amma kuma sai ta tsinci kanta tana mai jin dad'in hakan


Saboda ita wata mace ce da Allah yayita mai tsananin buk'ata, shiyasa tayi k'ok'arin nusar da iyayenta da kuma Mahabu wannan matsalar amma kowa ya kasa fahimtar ta.


Cikin wannan tunanin Mamman ya barta ya nufi gun Iliya mai tireda domin siyo mata maganin.


Sai yanzu ne da ya dawo sukayi kici6is da Inna


"A'a Mamman ne? Kace har ka fara kewar aminin naka tun yanzu?"


"Ya za'ayi Inna ai sai hak'uri, yanzunma wai magani ne nasiyo Indo tana zazza6i shine zan mik'a mata na wuce"


"Wallahi kuwa tun safe take fama da zazza6in nan, yarinya duk tabi ta sakawa kanta damuwa ina dalili ina d'an mafari? shiga tana ciki" ta fad'a tare da shigewa nata 6angaren..._Har yanzufa wayar ba daina suma tayiba, dana fara typing sai dai naga tayi Luuuuuum_

_Kuma nace maku kuyo mani karo-karo ko ba mai tsada ba 'yar ta dubu dar'i biyu ma ta isheni, sai ku had'a kud'in jirgi ku bawa d'aya daga cikin ku ya kawo mani amma naji shuru har yanzu_😭😭😭😭 Maman Ja'afar 

+966592551785

[4/21, 10:12 PM] Maman Ja"afar: 🌻MAHABU🌻


       7


Daga Alkalamin

Maman Ja'afar✍Sai cikin dare su Mahabu suka samu isowa garin Adarbiso d'in, amma duk da hakan basuyi tunanin tsayawa su kwana a hanya ba, a cikin daren dai suka nemi motar da zata sadasu daTanik.


Sunsha wahala mat'uk'a kamin su sami motar Tanik d'in, sai daga bisani suka samu, saidai a dole shatarta suka dauka su ukun tunda yanzu cikin dare ne ba wasu fasinja za'a samu masu zuwa ba.


Daga Adarbiso zuwa Tanik ba wata tafiya mai nisa bace domin tafiyar 'yan mintina kad'an ce zata kaika


********


Da shigar Mamman d'akin baiyi wata-wata ba ya nufi bayan k'yaure ya d'auko mod'a ya d'ebo ruwa a cikin karhi, kana ya taimaka mata ta tashi tasha maganin da ya kawo, kana daga bisani ta koma ta kwanta tunani fal a cikin zuciyarta 


Shima dai Mamman a nasa 6anagaren hakan take, domin shima tunanin Indo d'in ne ya addabi zuciyar tashi


"Shege Abokina ashe dai yasan abinda ya hango ajikin yarinyar nan shiyasa mukaga ya nanik'e mata"


Abinda yaketa faman fad'a kenan a cikin zuciyarshi

*****

Dab da shiga garin Tanik nanma su Mahabu suka had'u da hukumomin masu tsaron gate, suma dai kamar na bayan, mai takarda ya huta wanda ko bashida ita jaka biyu ce zata rabaku dasu.


Bayan sun gama daidaitawa da hukumomin ne suka umarce su da su tsaya anan su kwana inyaso da safe sai su ida shiga cikin garin Tanik d'in tunda yanzu dare ne


Haka kuwa akayi, nan gindin motarsu kowa ya shimfid'a 'yar rigarsa ya kwanta, kusan tafiyar maza dama ba wasu kayan kirki suke rik'owa ba.


■Washe gari■


Bayan sun gabatar da sallar asuba hukumomin suka basu d'an abin ta6awa suka lallasa badan ank'oshi ba, bayan sun natsu direba yajasu har cikin garin na Tanik.


Garin Tanik ba wani gari bane mai girman gaske, hakan nema yasa indai mutum Libei yakeson tafiya baya tsayawa a garin domin kwana.


Da dai su Mahabu suka samu suka cika tankin cikinsu basuyi wata-wata ba suka natsa cikin tasha domin neman motar da zata kaisu garin Agadas.


*****


Indo ce na hango tsugunne a Makewaya jini sai faman kwarara yakeyi daga jikinta, ga dukkan alamu dai ina tsammanin 6ari ne tayi, tun tana nuk'u-nuk'u ita kad'ai tana 6oyewa har ta kai ciwon yayi tsananinda baza'a iya 6oyeshi ba


"Inna! Inna! Da k'arfi Indo take k'walawa Surukar tata kira


"Kina ina ne Indo? Kamar naji kira kuma ga d'akin nata babu kowa"cewar Inna d'in kenan yayinda take 'yan waige-waigenta


"Gani nan a Kewaye"


"Subhanallahi! Lafiya dai ko Indo?" Abinda tsohuwar keta faman fad'a kenan yayinda take tunkarar magewayar


"Subhanallahi! Indo haka abu ya faru kuma? Gaskiya zubar jinin nan yayi yawa ina ganin bama jin 'yan jik'e-jik'e zaiyi ba, kawai a nemo Mamman ya d'auro mana Amalanke akaiki Likita (Assibiti) kona Kanan Bakashe ne"


Ai kuwa batare da 6ata lokaci ba Mamman yazo da Amalanke suka wuce.


"Saidai kuyi hak'uri domin cikinda ke jikinta ya zube" Abinda likitar ta fad'a kenan bayan ta gama duddubata


Jiki a sukwane suka dawo gida bayan anyi mata alluran tsayar da jini, an kuma bata 'yan magun-guna.


Koda Mamman ya saukesu a gida bai zame ko ina ba sai wajen Mati mai balango ya siyo mata na dala d'ari, harda awara da zo6o ya biya bakin gari duk ya siyo mata kana ya dawo gidansu Mahabu d'in


Ba k'aramin jin dad'i tayi da irin wannan karamci da Mamman ya nuna mata ba, hakan nema yasa take rayawa a cikin ranta wannan kulawar inama ace Mahabu ne yakeyi mata ita?


******


Tafiyar kwana d'aya da wuni d'aya ce ta kawo su Mahabu cikin garin Agadas.


Garin Agadas babban gari ne mai tarin Sahara, mai d'auke da mata farare kuma kyawawa, gashin nan nasu kuwa har gadon baya


Mazanma a gurin kyawu ba'a barsu a baya ba domin suma farare ne gashin nan kuwa bak'ikk'irin akansu yayi luf tamkar larabawan Saudia

Saidai duk namijin da ka kalla indai ya kai munzalin zama saurayi zakaga kanshi nad'e da bak'in rawani, harma da way'anda basu kai samarin ba dan karanbani sakawa sukeyi tunda yin hakan a wajensu tamkar wani ado ne na musamman


Idanuwansu da kuma bakinsu ne kawai zaka gani a waje amma komai na fuskarsu a lullu6e yake da wannan bak'in rawanin.


A wannan garin su Mahabu suka yada zango sukayi kwana 2 a cikin garin batare da samun wani masaukin kirki ba


A kwana na ukun ne suka nausa a cikin gari domin harhad'a kayan guzuri wanda da wannan guzurin ne suke saka ran zasu d'auki hanyar Libei.


Duk abinda sukasan zasu buk'ata a hanya saida suka sayeshi, kama daga garin kwaki, madara, suga, tafiyoka biskit da dai sauran abubuwa marasa nauyi wanda sukasan matafiyi zai iya buk'ata


Ruwa kuwa saida kowa daga cikinsu ya sayi irin k'atuwar jarkar nan ta masu ga ruwa d'aya-d'aya, domin a hanyar Libiya babu babbar matsalar da ta wuce ace ruwan mutum ya k'are a, idan kuwa hakan ta faru komai na iya faruwa.


Saida suka k'ara yin kwana d'aya a garin na Agadas kana suka samu hawa motar Libei d'in kai tsaye, sun k'ara kwana ne saboda rashin cika da wasu motocin nasu basuyi ba


Dayake motoci ne masu yawa ak'alla zasu kai kusan ashirin ko kuma sama da haka, kuma a jere akeso su tashi kuma a rana d'aya


Manya-manya ne irin na d'aukar shanu d'in nan koko nace maku irin na d'aukar itace.


Saida kowannensu ya bayar da jaka goma goma kud'in hukuma bayan wanda suka bayar na mota, kana motocin suka samu lulawa.


Tun asuba motar su Mahabu ta d'au hanya, babu abinda direban yakeyi face sharara gudu.


*****


Tunda Indo tayi 6ari Mamman keta faman yin zarya a gidan da nufin wai yana zuwa ganin jikinta ne, kuma duk sadda zaizo baya zuwa hannu biyu sai ya sami wani d'an abin ta6awa ya taho mata dashi.


Yauma kamar kullum, bayan sun gaisa da Inna shashin Indo d'in ya wuce kai tsaye dayake dama bashida wani shamaki a ko ina na cikin gidan.


"A'a! Alhamdulillahi jiki yayi sauk'i kenan tunda har gashi naga anata faman goge-gogen kayan d'aki"


Ya fad'a bayan ya k'araso ya zauna akan tabarmar robar da ke shinfid'e a tsakar d'akin 


Da murmushi ta dubesa


"Jiki kam Alhamdulillahi yayi sak'i sosai d'an yauma da safe har bayan gari naje na tsinko Kalgo na gasa, yanzuma da ka ganni nan ban dad'e da dawowa daga rijiya ba nayi wannan wanke-wanken, shine fa kaga ina gogewa" ta k'arashe maganar tata cikin murmushin dai


"Ai haka akeso, Allah ya k'ara sauki"


"Ameen" ta fad'a a tak'aice, kana ta k'ara da cewa 


"Nafa gode sosai da irin d'awainiyar da kayitayi dani, Allah ya bada ladar zumunci"


"Babu komai Indo, ai kinfi k'arfin komai a gurina, kuma duk abinda nayi maki ai ban fad'i ba, dan wallahi jinki nakeyi tamkar matar da nake aure kinga ko kome mutum yayiwa matarsa ai bai fad'i ba ko?"


Bata bashi amsa ba saima murmushi nan dai data saba ta bishi dashi


"Wallahi ina mamakin Mahabu da yayi watsi da irin duk baiwar da Allah yayi mashi na samun mata kyakkyawa mai hankali da natsuwa irinki, inda ace nine mijinki.. Aradu da k'yar ma idan zan iya fita ko nan da waje gurin abokainaina, ai kullum ina d'aki ina lalla6a kayana koba haka ba?"Ya fad'a tare da rungume hannayensa a k'irji


Maganarsa ba k'aramin fami tayiwa Indo ba, domin sai yanzu ne take jin haushin abinda Mahabu yayi mata, wanda a yanzu ne take buk'atar kulawarsa sosai da sosai


Murmushin k'arfin hali tayi kana tace "Kaima Allah ya baka kamata ko kumama wacce ta fini komai"


"Ai Indo baza'a samu kamar ki d'in bama bare kuma wacce ta fikin, me za'ayi da Binta wacce ko wankan kirkima bayi takeyi ba, amma ke duk sadda na ra6eki wani k'amshi mai d'ad'i nake jin yana ratsa mani har cikin kwanyata"

Ya fad'a tare da matsawa dab da jikinta, waishi a dole k'amshinta yake sansanowa...


 *Maman Ja'afar*

 +966592551785

[4/21, 10:12 PM] Maman Ja"afar: [27/03, 3:35 a.m.]

🌻MAHABU🌻


      8


Daga Alkalamin 

Maman Ja'afar✍
Motocinsu Mahabu gudu sukeyi ba kakkautawa, har zuwa lokacin da suka samu isowa wani gari mai suna *Kwarin Kantana*


Wani k'aton kwari ne mai tsananin yashi da kuma k'ura, wanda tsananin k'urar dake cikin kwarin ko idanuwan mutum bazaka iya gani ba, k'ura ce mai tsananin gaske wadda zata rufeku ruruf


Gari ne Kwarin Kantana amma ba wani garin kirki ba tunda babu wasu gidaje sosai a cikinsa duk daji ne, saifa 'yan bukkaye da wasu Buzaye sukayi, ina tsammanin sunyisu ne domin su dinga yada zango a gurin


To shinefa mutanen Nageria suke d'an ra6awa a cikin bukkunan suna yin abinci suna sayarwa matafiya da tsada tsugugu(Dayake kunsan kud'in Nijar sunfi na Nageria daraja, a Saifa kad'an sai abaka nerori masu yawa idan ka canza)


Anan su Mahabu suka tsaya suka shisshiga Bukkunan domin cin abinci


"Nifa Sa'adu wallahi ba ganin gabana nakeyi sosai ba, nikad'ai wannan matsalar ta sama ne ko kuwa har ku?"


Cewar Mahabu kenan yayinda yaketa faman murzar idanuwa


"Kaima Mahabu da neman magana kake wallahi, wane kai kad'ai kuma bayan kana ganin tare mukayo wannan tafiyar"


Shiko Abashe babu abinda yakeyi face murzar idanuwa da gefen rigarsa, wanda a hakanma ba wani sauk'i yakeji ba, dan tamkarma ank'aro mashi azaba a idanuwan nasa yakeji.


A haka su Mahabu suka gama cin abincinsu mai shegiyar tsada kuma suka k'ara sayen ruwa jarka-jarka suma ruwan mau duk domin k'arin guzuri dana kada ruwa su k'are masu a hanya


Bayan sun d'an natsu ne suka kokkoma cikin motocinsu suka d'au hanya.


A wannan k'ungurmin dajin haka sukaita wuce namomin daji kala-kala wanda tunda sukema a rayuwarsu basu ta6a ganin irinsu ido da ido ba sai dai ko a cikin Tele(TV) idan ana fina-finan ban tsoro irin na namun dawa.


Basu k'ara tsayawa a ko ina ba sai a cikin K'auyen Turayya a Turayya nanma sun had'u da Gate d'in Jandarmomi, inda Jandarmomin suka tsaitsayar dasu


"Yauwa Direba ku sassauko kubi layi" Cewar wani Jandarma kenan yayinda yake lellek'a cikin motar


Haka sukabi su Mahabu d'aya bayan d'aya suna k'ar6ar jaka-jaka a hannunsu, da mai takardar da wanda bashida takardar kowa sai da ya bayar da jaka jaka kana daga bisani kuma Jandarmomin suka umarcesu da su tsaya su kwana domin dare yayi washe gari sai su wuce.


Wan shekare(Washe gari)Motar su Mahabu ce a gaba shiyasa sahiya nayi sukaja sukayi gaba yayinda sauran motocin suma suka rufa masu baya.


******


"Haba Mamman d'an matsa mana, baka tunanin Inna zata iya fad'owa a kowane lokaci cikin d'akin nan?" Ta fad'a yayinda take ja da baya da baya


"Karki damu Indo babu wata Inna da zata shigo yanzu, dan shigowata d'in nan naganta tayi arwallar Lisha ta shige K'ofarta"


B'ata rai tayi kana ta sake cewa"A'a nidai gaskiya ka matsa wallahi tsoro nakeji"


K'ara matsawa yayi dab da ita har jikinsu yana gogar juna


"Wane tsoro Indo? Wallahi babu wanda zai shigo, ina mai tabbatar maki koda wani abu zai faru a tsakaninmu babu mai sani wallahi, idan kuma baki yadda ba bari na k'ara lek'awa tsakar gidan naga inda wani a kusa"


Da gama fad'ar haka ya nufi tsakar gidan yana duddubawa, kamar kuwa yanda tsammata babu kowa a tsakar gidan, domin duk sun nufi sashinsu dan gabatar da sallar Isha


"Kin gani ko? Wallahi babu kowa a tsakar gidan barema kiyi tunanin ko wani zai iya shigowa ya ganmu"


Ya fad'a bayan ya dawo cikin d'akin, inda ya tsaya dab da ita jikinsa har gugan nata yakeyi


"Amma to Mahabu fa?" Ta fad'a yayinda gabanta ke ci gaba da dukan tara-tara


"Manta da Mahabu dan Allah, inda yana sonki har ya kama hanya ya tafi wata uwa duniya ya barki ba tare da tunanin halinda zaki iya shiga ba? Ko an gaya masa dutsi ya ajiye a gidan ne?"


Magan-ganunsa ba k'aramin tasiri sukayi a zuciyar Indo ba, domin dama a matse take wata 'yar dama kawai take jira ta samu


"Amma dai a rufe k'ofa ko?" Ta fad'a cikin murya mai tattare da shagwa6a


"Ai yanda kikeso haka za'ayi amaryata"Ya k'arashe maganar tasa tare da nufar k'ofar d'akin


"Amaryar Mahabu dai zakace ko?" Itama ta fad'a cikin murmushi


"Dan Allah manta da wannan bahon" Ya fad'a tare da rungumota a jikinsa.


_Gaskiyar Allah (S.W.A) daya fara ambatar mace gurin aikata zina kana ya ambaci namiji saboda anan mace itace jagora domin itace mai bada k'ofa, a gurin Sata kuma sai ya fara ambatar namijin kana ya ambaci mace dayake a wannan gurin aikin k'arfi ne.Ya Allah ka tsare mana zukatanmu daga bin hud'ubobin shaid'an la'anannen Ubangiji_


Nidai ban tsaya na ida ganin k'arshen wannan ta'asar da ake shirin aikatawa ba na gudu daji abina zuwa wajensu Mahabu.


******


Daga Turayya su Mahabu basu k'ara tsaya a ko ina ba hanya kawai suke kwasa


 Kusan kwanansu hud'u a hanya suna tafiya a cikin wannan saharar mai d'auke da matsanancin zafi da tarin rairayi, wannan dalilin nema yasa duk ruwan wasu daga cikin matafiyan ya k'akk'are saboda zafin rana da kuma tsananin k'ishirwarda ke kama mutum a wannan hanyar


Suma su Mahabu da sauran way'anda ruwan nasu bai k'are ba badan wai k'ishirwar tasu ta mutu ba suke daina shan ruwan nasu, a'a suna barin ruwan ne kawai domin gudun kada suma ruwan nasu ya k'are mai afkuwa ta afku, saboda indai ka yadda ruwanka ya k'are a wannan hanyar to sai dai abinda Allah yayi da kai kawai.


Da yake motoci ne masu yawa suka d'auki hanyar ta Libei d'in shiyasa mutanen da suka mutu dalilin k'ishirwa suka yawaita dan sunfi a k'irga.


Da mutum ya mutu a hanya ba'a tsayawa wani 6ata lokaci domin binnesa sai dai kawai daga cikin motar a tillosa waje, kuma mintina kad'an yashi ya rufesa ruf ko d'an yatsansa bazaka iya gani ba


Idan kuma ta baya mutum yayi ya fad'i daga cikin motar inma da rai inma matacce shima haka za'a wuce a barsa a gurin har k'asa ta rufesa ruf shima


"Kasan miye Abashe?" Mahabu ya fad'a tare da dafa kafad'ar Abashen


"A'a sai ka fad'a Mahabu"


"Wallahi duk yanda nake jin Malamai suna kwatanta mana tashin alk'iyama ban ta6a yadda da maganarsu haka take ba sai a wannan tafiyar tamu ta zuwa Libei, wallahi wannan tashin hankalinda nake gani a yanzu tunda uwata ta haifeni ban ta6a ganin irinsa ba"


"Kai kaga tashin hankali ko ni? Yo nifa tunda nake a rayuwata ban ta6a ganin gawar mutum ido da ido ba sai a wannan tafiyar, kaga dai yanda ake watanda da gawarwakin mutane sai kace wasu gawarwakin 'yan tsaki" Abashen ya fad'a tare da duban fuskar Sa'aduCikin Sanyin jiki da kuma jimamin abin Sa'adun yace"Kawai dai muyi fatan Allah ya kaimu lafiya domin muma bamu da tabbacin zamu ida isa Libei d'in lafiya ko kuwa mumu a hanya za'a yada gawarwakinmu kamar sauran?" Ya fad'a yayinda hawaye ke bin fuskarsa shar-shar sai kace wata mace


"Wayyo Allah jama'a! Wayyo mak'oshina zai tsage! Ku taimaka mani da ruwa ko yaya yake dan Yarasululluhi, ku taima mani dan Allah kada nima na rasa rayuwata, wayyo Allahna! Shikenan nima mutuwa zanyi"


Abinda wani matashi d'an kimanin kusan shekaru 30 yake ta faman maimaitawa kenan daga cikin motar da su Mahabu d'in suke


"Bari na bashi ko a tafin hannu ne, dan shimafa inaga mutuwar yake shirin yi"


Cewar Mahabu kenan yayinda yake lalubar jarkar ruwansa


Zaro ido Abashe yayi kana ya dubesa cikin 6acin rai


"Ka bashi? To bashi d'in kaima kuma ka mutu kamar yanda shima yake shirin mutuwa ba"


Abinda Abashe ya fad'a kenan yayinda ya k'ara matse yar jarkar ruwansa data kusan k'arewa a tsakan-kanin cinyoyinsa


Shiko Sa'adu d'an Saurayinma ko kallon tsiya bai ishe shi ba, domin a wannan tafiyar nafsi-nafsi ne kawai, idan jifa ta wuce kanka to kan kowama ta fad'a kai bakada matsala....
*Maman Ja'afar*

+966592551785

[4/21, 10:12 PM] Maman Ja"afar: 🌻MAHABU🌻


      9


Daga Alkalamin 

Maman Ja'afar✍Tun daga wannan lokacin Mamman ya mayar da Indo tamkar wata matarsa ta sunna, duk dare sai yazo mata, kodai ya shigo ta k'ofar gida ko kuma wataran ya hauro ta katanga.


******


Tafiya takeyi a hanya sai faman surutai take ta faman yi ita kad'ai sai kace wata zararriya


"Oni 'yasu! Wannan irn cin amana dame yayi kama?"


Har ta shigo gida bata daina 'yan surutan da takeyi ba


Da yake yau rana ake zabgawa mai d'an karan zafi shiyasa kowa na gidan ya kasance a tsakar gida k'ark'ashin bishiya suna d'an jin iskanda ya ke busowa kad'an-kad'an


"Inna lafiya kuwa naga kin shigo kamar ranki a 6ace, kodai yauma a gun shari'ar taku ba'a dace bane ba kamar kullum?"


Indo ce ta d'ago da kai daga yankan akaifar(k'unba ko farce) da take yi ta fad'i hakan yayinda take duban fuskar sirikar tata


Dayake tun bayan rasuwar Mahaifin su Inna Furen taketa tabka shari'a tsakaninta da yayanta wanda yake k'ok'arin handame mata nata gadon Shanun da kuma Gonakin da mahaifin nasu ya rasu ya bari, to yanzunma ga dukkan alamu daga gun shari'ar ta fito


Girgiza kai tayi cikin jimamin abinda zai fito daga bakinta


"Wai ashe lalacewarda duniya tayi yanzu har ya kai haka? Yoni Indo tashin hankalindama nagani a gidan Kashen (Sarki) ai yafi wanda na tafi dashi"


Matar Bala K'anin mijin Inna Fure ce ta mik'e tsaye tare da gyara d'aurin zaninta da alamun tambayoyi tattare a fuskarta


"Wai Fure mike faruwa ne haka? har yanzu dai baki fad'a mana abinda kika gani a gidan Kashen ba"


Ajiyar zuciya tayi kana ta dubesu


"Wato wasu maza ne nagani a gidan Kashen kusan su uku, kuma kowannensu wai k'arar matarsa ya kawo, kunsan me matan sukayi?"


Ta fad'a yayinda take duban fuskokin matannda ke zazzaune a tsakar gidan


Jijjiga kai sukayi alamun basu sani ba amsarta kawai suke jira


"Waifa a cewar mazajen nasu tafiya sukayi zuwa Libei, ko shekara nawa sukayi a can? Oho! Wallahi na manta ko nawa suka ce"


"Muna jinki dai Inna Fure" Cewar d'aya daga cikin matan da ke gurin kenan


"Tofa shine bayan sun dawo daga Libei din suka tarar da matayen nasu wasu da ciki wasu kuma da goyo, kai intak'aice maku labari watama har yara biyu mijin ya dawo ya sameta dasu"


Salallami matan suka farayi tare da tofin Allah tsine ga matayen da suka aita hakan


Yayinda ita kuma Indo tayi wani fik'i-fik'i sai rarraba idanuwa takeyi a tsakaninsu sai kace wacce aka kama tayiwa sarki k'arya


"Wannan abin kunya dame yayi kama haka?" Cewar d'aya daga cikin matan kenan


"To Inna Fure shi kuma Kashen yaya zaiyi ya taro kan wannan shari'ar kenan?"


Cewar wata mata kenan wacce ta lek'o ta katanga tana sauraren firar tasu


"Ina kuwa zan sani tunda ba tsayawa nayi na ida jiyo k'arshen shari'ar ba"


"Nifa dama ba yau na fara jin wannan labarin ba, nasha ji yafi a k'irga kuma a cikin garin nan, wasuma matan tare muke yin mu'amala dasu, dan dai kawai baka kama suna ba tsoron kar a kiraka sheda a gaban Kashe"


Cewar Laure kenan d'aya daga cikin matan gidan


"To ai ke Laure in baya ga abinki idan 6era da sata to ai daudawa ma tanada nata warin, saboda haka ni ban ware kowa ba acikin mazan da matan, inda kashe zaibi ta tawa dukkansu kamata yayi ayi masu hukunci"


Cewar matar K'anin mijin Furen kenan


Ita dai Indo bata tsaya ta ida jin k'arshen firar tasu ba ta tashi sumui-sumui ta shige d'aki abinta


******


Suna ji suna gani wannan d'an saurayin ya shid'e ya mutu batare da kowa yayi tunanin taimaka masa ba.


Wata Inyamura tana gefe itama tanata faman murk'ususun k'ishirwa, koda taga abinda ya faru da wannan saurayin batayi wata-wata ba ta d'auko kofinta ta tsugunna tayi fitsari aciki ta kwankwad'e kayanta(Wuya koda magani ba dad'i)


Dariya Abashe yayi kana ya dubi sauran abokan nasa


"Ammafa 'yar inyamurar can tayi dabara, kaga shima wannan da haka yayi k'ilan da ya kai labari" Ya fad'a yayinda yake duban gawar wannan saurayin


Muskutawa Mahabu yayi

"To ya za'ayi da k'aran kwana? Dama Allah ya k'addara badashi zamu ida isa Libei d'in ba"


*****

Saida su Mahabu suka k'ara kwana da wuni kana suka samu isowa Rijiya Mai Tol


A lokacin ruwan mutane da dama ya k'are a hanya, sai dai Allah yayi da sauran kwanan wasu a gaba basu riga sun mutu ba amma dai sun jigata sosai


Rijiya Mai Tol wani guri ne da yafi ko ina Sahara a hanyar ta Libiya, domin idan ka hanga sosai zaka iya hango nisan da ya kai kusan tsakanin Katsina da Kano


Domin tsabar saharar da ke gurin ko bishiya d'aya babu bare kuma duwatsu ko kuma gidaje


Kuma indai dare yayi maku a wannan gurin akeso ku kwana kamin zuwa safiya ku k'ara gaba


Akwai wata Rijiya a gefe guda wacce itace ake kira da Rijiya Mai Tol, kuma a wannan Rijiyar ne wasu masu motocin sukan zuba mutanen da suka mace masu a hanya (Masu d'an sauran imanin kenan)


Kuma dai har wa yau a wannan Rijiyar wad'anda ruwansu ya k'are a hanya suke shan ruwa


Idan Allah ya k'addara kanada sauran rayuwa agaba idan kasha ruwan ka tashi, idan kuma dama kwananka ya riga ya k'are tofa da kasha wannan ruwa ko miniti biyar bazaka k'ara ba zaka shid'e, kuma a dole kasha d'in domin a wannan lokacin k'ishirwar da ke tattare da kai ko ruwan guba ne aka baka da sauri zaka kar6a ka kwankwad'e.


"To jama'a nanfa zamu yada zango saboda dare yayi, dan idan mukace zamu wuce k'arshenta muyi 6atan kai a hanya" Cewar direban su Mahabu kenan


A wannan filin Allahn ta'ala matafiyan suka rarra6a domin yin bacci, yayinda su Mahabu da Sa'adu da kuma Abashe suka ra6a guri guda su kad'ai, saboda tunda suka had'u a hanya suka jone suka zama tamkar 'yan'uwan juna


"Nikam wani mugun wari nakejifa a nan kusa dani, hancina ne ko kuwa dai kuma kun jiyo shi?" Cewar Abashe kenan yayinda yake toshe hanci


Tocila Sa'adu ya fiddo daga cikin aljihunshi ya fara hahhaskawa


"Wallahi gawa ce a gurin, kuma ga dukkan alamu sabuwa ce" Abinda Sa'adun ya fad'a kenan yayinda yake duddubawa


"Gaskiya ku tashi mu canza wuri dan nagaji da ganin gawarwakin nan hakanan, wannan ai sai imanin mutum ya ida fita gaba d'aya" Cewar Mahabu kenan yayinda ya mik'e tsaye ko kallon inda suke nuna masan ma baiyi ba


Suma sauran ba tare da 6ata lokaci ba suka rufa masa baya


■Washe gari ■


Tun dugu-dugu kowa ya nufi hanyar motarsu, dama ba maganar salla akeyi ba a wannan lokacin 


Anan d'inma saida suka bar wasu mutanen a kwakkwance suka wuce, wasu sun mutu, wasu kuma na shirin mutuwar, ga dukkan alamu dai inaganin wad'anda sukasha ruwan Rijiya Mai Tol ne....
Wannna bala'in da nake baku labari na hanyar Libiya ni Maman Ja'afar ina mai tabbatar maku da babu k'arya a cikin zancena


Domin har rantsuwa zan iya yi maku akan hakan, saboda a nawa tsarin bana baku labarin da ban tabbatar da sahihancinsa ba


Tabbas hakan ke faruwa kuma hakan keci gaba da faruwa


Ina mai shirin tafiya Libiya? To ka shirya tarbar wannan Bala'in kaima.Muje zuwa Mahabu Number 10


*Maman Ja'afar*

 +966592551785

[4/21, 10:12 PM] Maman Ja"afar: [31/03, 4:51 a.m.]

🌻MAHABU🌻      10


Daga Alkalamin

Maman Ja'afar✍Daga rijiya mai tol su Mahabu basu sake yada zango a ko ina ba sai a wani d'an k'aramin gari mai suna DURKU adaidai inda hukumomi suke


Durku gari ne sai dai ba wani garin kirki ba, dan dai kawai gurin akwai 'yan duwatsu kuma babu sahara sosai shiyasa wasu 'yan tsirarun mutane sukazo suka kakkafa 'yan gidajensu a gurin


"Ina masu takardu" Cewar Jandarmomin kenan yayinda suke fitar dasu Mahabu daga cikin motar daya-bayan daya


Direban ne ya umarci masu takardu da su ware gefe guda, marasa takardunma haka


Masu takardu jaka goma-goma Ikon (hukuma) suka kakkar6a a hannunsu, marasa takardu kuma jaka sha biyar-biyar


Wanda kuma bashi da takarda kuma bashi da kud'i a dai-dai nan Iko zasu rik'eshi su mayar dashi baya, ma'ana ya koma inda yafito, waccen wahalar da yayi ta tashi a banza


Idan kuma dama tun a Agadas iya kud'in motar Durku ka biya, to sai a ajiyeka anan kayi ka biya Iko kud'insu kana ka zauna anan kayi neman kud'i, irin wanki da guga, noma, gini, da saida ruwa na 'yan watanni kana ka ida haurawa Libei d'in(Koko nace kusa da Libei din)


Daga garin Durku tafiyar da su Mahabu sukayi batafi ta 'yan awanni ba suka sami isowa wani d'an k'aramin gari na Buzaye mai suna LATTAI


Basu dad'e da wuce garin Lattai ba dare yayi masu a hanya, kuma dama ak'a'idar tafiyar ba'aso ana yinta da daddare saboda tsoron 6ata a hanya, saboda indai kuka yarda motar ku ta 6ata a hanya to saidai kuyita gararanba, baku Chadi baku Algeria har ruwanku ya k'are a hanya ku mutu ku duka.


Daidai wasu duwatsu motocinsu Mahabu suka faffaka, kowa ya firfita domin mik'e hak'ark'arinsa kamin safiya a d'ora daga inda aka tsaya


Cikin way'annan duwatsun suka shisshiga domin kwanciya kamin safe


Idan lokacin zafi ne duwatsun sukanyi tsananin zafi ne tamkar garwashin wuta, idan kuma lokacin sanyi ne nanma duwatsun sukanyi tsananin sanyi ne tamkar K'ank'ara, koma dai yaya ne abin ba wani sauk'i ne dashi ba


A haka su Mahabu suka rarra6a acikin duwatsun nan


"Wai!wai!wai! Wannan irin zafi ai sai mutum ya k'one, gaskiya bazan iya kwana a nan ba, gara na kwanta a saman yashin nan k'ilan ya d'anfi sauk'i-sak'in azaba"

Cewar Sa'adu kenan yayinda zafin dutsen ya kusan toya mashi k'afa


"To in baya ga abinka ai babu wani banbancin azaba tsakanin yashin da kuma dutsin, nanfa inda ka ganni tsaye rigata ce na cire na d'ora a k'asan takalman nawa dan naji yar dama-dama"


Cewar Mahabu kenan yayinda yake d'aga k'afa d'aya yana ajiye dayar duk dan ya samu sauk'i-sauk'i 


Abashe ko rugawa da gudu yayi ya d'ale motar da suka baro


"Nikam gara na kwana anan dana kwana acikin wannan azabar, dan har naji mak'oshina ya fara bushewa wallahi, inama ruwan nawa yake?"


Ya fad'a yayinda yake 'yan dube-dubensa a cikin motar


Wata uwar ashar ya lailayo ya sauke, kana da k'arfinsa yake fad'ar


"Shi kenan wallahi sun kasheni, sun sace mani ruwana kuma nasan ba mayar mani za'ayi ba dama y'an kad'an ne suka rage mani"


Yana magana muryarsa na rawa tamkar mai shirin yin kuka, domin babu abinda yake tunawa sai irin yanda mutane sukaita mutuwa a hanya dalilin k'ishirwa


"Mahabu kaji abinda Abashe yake fad'a kuwa?"


Sa'adun ya fad'a tare da kallon fuskar Mahabu wacce ta jik'e sharkab da zufa saboda tsananin zafinda ke gurin


"Naji mana, kai ya kake ganin za'ayi?" Ya k'arashe maganar tasa yana kallon fuskar Sa'adun domin jin amsar da zai mayar masa


"Ya kuwa za'ayi? Kawai hak'uri zaiyi ya bar mana wasiyya idan mun samu saduwa da 'yan'uwanshi mu fad'a masu, domin ya kusan zama gawa shima, inkuma zaka sammashi naka ruwan ne ban hanaka ba"Ya fad'a yayinda shima ya haura gurin motar domin samun sauk'i-sauk'i 


Jiki a sanyaye shima Mahabu ya shiga motar ya zauna


"Dan Allah 'yan'uwana kud'an yi mani karo-karo mana"Ya fad'a yayinda hawaye ke bin fuskarsa


"Nikam bazan baka ruwana muyi mutuwar kasko gaba d'ayanmu ba, saboda daga nan bansan iya nisan da zai kaimu Libei d'in ba, gara dai d'aya ya rayu d'aya kuma ya mutu kada asarar rayukkan tayi yawa"


Cewar Sa'adu kenan fuska a d'aure sai kace dama can bai ta6a sanin Abashen ba


Jiki a sanyaye Abashen ya juyo wajen Mahabu"Kaima Mahabu bazaka taimaka mani ba ko?" Ya fad'a murya na rawa


"Nima dai gaskiya Abashe sai dai nace kayi hak'uri dan ban shirya mutuwa yanzu ba, ko amarci bamu gama ci da Indo ba na hak'ura na barota gida domin neman abinda zamu rufawa kanmu asiri, haka kawai sai dai aje mata da labarin na mutu? Ina! Kawai kayi hak'uri Abokina kaita yin kalmar shahada kurun tunda dama ba wasu iyali ne da kai ba"


Bai k'ara ce masu komai ba ya samu guri ya kwanta abinsa.


Sai kusan Asuba rahama ta fara mamaye gurin, daga bisani kuma sanyi mai tsanani ya maye gurbin wannan tsananin zafin, tsabar sanyin gurinma har kyarma zakaga mutane sunayi.


****

Daga wannan gurin su Mahabu basu k'ara tsayawa a ko ina ba sai a wani gari waishi SIGIDIM, a Sigidim ma saida Iko suka kakkar6i jaka-biyu-biyu a hannunsu kana suka barsu suka wuce


Tun daga wannan lokacin kuma motocinsu Mahabu suka fara gudu baji ba gani, basu k'ara fakawa a ko ina ba sai a wani daji gindin wata tsohuwar rijiya


Danma dare yayi masu ne suka tsaya a nan d'in badan haka ba da sai inda mai ya k'are(Inda direba ya gaji)


"Ina way'anda ruwansu ya k'are? Ku firfito ga wata rijiya a can kuje kusha"Cewar direban kenan yayinda yake sank'amar biredinsa yana korawa da ruwa


Cikin murna Mahabu ya bugi kafad'ar Abashe"Abokina gafa ruwa can ansamu, yi sauri kaje kasha kafin mutane su cika wajen"


Ga mamakinsa sai ya ga Abashe ya 6ingire, cikin kid'ima yake jijjigashi

"Abashe! Kaddai ace kaima mutuwa kayi?"


"Subhanallahi, badai ya mutu ba?" Abinda Sa'adu ya fad'a kenan yayinda ya k'araso gurin


"Wallahi ya mutu, ashe shiyasa tun d'azun naketa faman bashi labarin Indo naji shuru? Ni wallahi na zacima fushi yakeyi damu ashe rai har yayi halinsa?"


Cikin jimami suka kinkimesa zuwa bayan wasu duwatsu suka yada shi a can


*Washe gari*


Da suka d'au hanyafa basu k'ara tsayawa a ko ina ba sai wani gari MADAMA kafin shiga garin Madama d'inma saida Iko suka tsayar dasu suka kakkar6i na abinci kana suka ida shigowa cikin garin


Garin Madama babban gari ne ba laifi, wanda ko ananma mutum ya tsaya zai iya yin neman kud'insa


A wannan garin su Mahabu suka canzar da kud'insu daga kud'in Nijar zuwa kud'in Libiya, kuma dai har wayau kwana d'aya sukayi a Madaman suka wuce gaba


Saida sukayi tafiya mai nisan gaske inda babu hukumar Nijar bare ta Libiya kana suka samu isowa wani k'ungurmin daji


A cikin wannan dajin ne kuma suka tarar da wasu motoci manya-manya masu yawan gaske a gurin


Direban su Mahabu ne ya fara fita yayi magana da d'aya daga cikin masu motocinda suka tarar kana ya dawo bayan mota inda su Mahabu suke zazzaune


"Yauwa ku fito ga motar da zaku koma can, itace zata ida shiga daku cikin gari har kusa da Libei"


Ya fad'a yayinda yake nuna masu inda motar take


Batare da 6ata lokaci ba suka koma cikin motar da ya nuna masun


Haka suma sauran motocin sukayi kamar yanda direban nasu Mahabu yayi.


Dayake motocin na y'an asalin cikin garin Libei d'in ne shiyasa tun daga cikin wannan dajin babu 6arauniyar hanyar da basu sani ba wacce zata iya sadasu da garin Libei din


(Su kuma irin sana'ar da sukeyi kenan suna samun y'an canjinsu suna sakawa a aljihu)


Tunda suka fara tafiya basu samu damar tsayawa ba har saida suka iso gurin hukuma


Wanda a tsammaninsu basu zaci zasuga hukuma ba a gurin domin ta 6arauniyar hanya suka biyo


Nanfa suka fara wasan tsere tsakaninsu da hukumomi, da harbi da komai amma saida suka 6acema hukumomin dayake kunsan ance dama da d'an gari akanci gari


Saida sukayi zagaye sosai kana suka dawo hanya kai tsaye saboda gudun koda za'a biyo sawun motar tasu


Sai cikin dare sosai su Mahabu suka iso wani gari waishi GATURAN dayake dama direbobin y'an gari ne shiyasa basu sha wata wahala ba wajen samun gidan da zasu 6oye fasinjojin nasu ba.


Gidane mai girman gaske, mai d'auke da wata doguwar katanga sai kace gidan yari (Shima a iya kiransa da gidan yarin) wanda ina ganin dama anyisa ne domin saukar bak'i irinsu Mahabu.


Saida suka samu natsuwa kana direban nasu ya fita ya kawo masu shayi da biredi


"Allah sarki Abashe, dafa yanzu dashi muke shan shayin nan ko?" Cewar Mahabu kenan yayinda ya sur6i shayin


"Nima tunanin da ke cikin raina kenan ka rigani furtawa"


Anan dai su Mahabu suka samu sukayi wanka suka d'an wanke kayansu duk a cikin wannan daren


*Washe gari*


"Ga motoci can a k'ofar gida na abokanmu zasu wuce daku SUBAHA yanzun nan, saboda haka kowa ya bada kud'in motarsa" Cewar mutumin kenan wanda yake magana fuska a d'aure ko alamun fara'a babu


Anan su Mahabu suka harhad'a masa kud'in motarsu suka mik'a mashi


Batare da 6ata lokaci ba ya kaisu gurin motocin suka shisshiga shi kuma ya dawo masauki abinsa.


Basuyi nisa sosai ba shima wannan direban ya k'ara juyesu a wata mota, nanma saida suka biya wani sabon kud'in, a haka saida akayi masu canjin mota kusan guda hud'u kuma kowacce sai sun bayar da kud'i kana suka samu isowa garin Sabaha d'in


Garin Sabaha koko nace k'auyen Sabaha mai d'an girma ne babu laifi, anan ne kud'in su Mahabu kuma suka k'are suka zauna domin yin aikatau na d'an wani lokaci.


Duk wani aikin k'arfi da akeyi cikin wannan garin saida su Mahabu sukayishi, wanda mafi yawancinshi ma Noman abincin dabbobi ne.


Saida sukayi kusan wata 4 a wannan garin kana suka samu kud'in haurawa a hakanma dan yan garin suna dan k'wakk'wace masu kud'in nasu ne badan haka ba da bazasu kai tsawon wannann lokacin ba a wannan garin


Wani lokaci azo har gida ayi masu satar tunda ansan su duka bak'i ne, yayinda wani lokacin kuma a hanya nema za'a taresu da wuk'a koda bindiga ayi masu k'wacen kud'in.


*****


"Shin waini Laure kun lura da yan canje-canjen da Indo takeyi acikin gidan nan kuwa? Itace batason warin wancen abin, batason k'amshin wancen abin, ga wani uban shan yaji data tarka sai kace 'yar gidan Alai (Mayu)


Lauren katse Kilima tayi

"Nifa ran nan naje kar6ar kanwa a d'akin ta naje na sameta tanata kakarin amai"


Zaro idanuwa Kilima tayi gami da rike baki alamun mamaki fal a fuskarta "Kai haba dan Allah Laure"


Buga hannayenta tayi a cinya "Fad'i da ihu k'ara da wayyo Allah, tabbas na gani da wad'an nan idanuwan nawa ba wani ya bani labari ba" ta fad'a yayin da take nunawa Kilimar idanuwan nata da yatsa


"Aiko indai hakane bamuga ta zama ba, dole muje mu samu Inna Fure da wannan maganar"


Dafe k'irji tayi kana tace "Wa? badani ba wai gad'a a Mak'abartu, baza'aji mutuwar sarki a bakina ba"


"Aikoni za'aji mutuwar uban sarkinma a bakina, kinmaga tafiyata" Tana gama fad'ar hakan ta nufi sashen Inna Furen

****

"Inna! sallama ashe kikeyi?"Abinda Lauren ta fad'a kenan bayan ta samarwa kanta matsugunni a cikin d'akin


Sallame sallar tayi kana ta fuskanci Lauren


"Nama sallame daga raka'a biyu idan muka gama maganar na k'arsa sauran raka'a biyun daga baya, tunda nasan ke tauraruwa mai wutsiya ce ganinki ba alheri ba, dame kuma akazo mani?"


Ta fad'a yayinda take duban Matar D'an d'an Bala Kanin mijinta kenan wacce zamuce kusan matsayinta d'aya da Indo a gurinta


(Nidai Maman Ja'afar tunda na fara zuwa islamiyya ban ta6a jin Malamai sunce akwai wata Mazhabar da tace ana iya sallame salla daga raka'a d'aya ko biyu daga baya a ida sauran ba, ban sani ba ko ku masu karatu kun san da wannan)


"Inna kin kuwa san Indo tana d'auke da juna biyu?" Ta fad'a murya k'asa-k'asa gudun kar wani yazo wucewa ya jiyota


Wani rugugin aradu Inna Furen taji ya sauko mata ak'irji har saida tayi k'ok'arin dafe k'irjin nata gudun kada kirjin ya tarwatse...Muje zuwa Number 11_Kuyi mani afuwa koda nayi kuskure a cikin rubutun nawa, domin yanzu haka kaina namun tsananin ciwo nakeyi maku wannan typing d'in saboda naji kunata tambaya ni kuma banaso na 6atawa masoyana rai_😭👏Maman Ja'afar ce 

 +966592551785

[4/21, 10:12 PM] Maman Ja"afar: 🌻MAHABU🌻     11Daga Alkalamin

Maman Ja'afar✍
Zaune take a tsakar d'akinta ta tasa kwanon kwad'on yakuwa a gaba wanda yasha had'in daudawa da magi da yaji sai faman zak'a takeyi tana zare ido tana fyace hanci ga gumi nata bin fukarta sai kace wacce aka matsawa adole sai taci


Muryar Inna ce taji cikin d'aga sauti sai banbami take, kuma ga dukkan alamu ba ita kad'ai bace kuma nan k'ofar tata suke k'ok'arin tunkarowa


"Ina Indon take? Fito nan munafukar banza munafukar wofi, ashe dama cin amanar d'ana kikeyi ban sani ba?"


Da jin wannan furucin nata Indo ta firgice ta gigice harma tana neman fita hayyacinta


Dayake babu riga a jikinta sai d'aurin gaba shiyasa batayi wata-wata ba ta jawo rigar Mahabu dake rataye a jikin k'usa ta zura, a zuwan wai ita nan rigarta ce ta saka, a sakun rigarma gaba baya ta saka dayake duk a rud'e take


Babban fatan da takeyi Allah yasa dai ba wani ne yaga Mamman lokacinda yake hauro ta katanga ba ya fad'a masu


Fitowa tayi daga cikin d'akin nata tayi tsaye a bakin k'ofa tana jimamin abinda ka iya zuwa ya dawo, a lokacinma har sun riga sun k'araso k'ofar tata


Da zuwan Inna batayi wata-wata ba ta kamo hannun Indo tana duddubawa, tana girgiza kai ta gwale idon Indon ta dudduba, kana daga bisani ta duba tafin k'afarta


Tana gama y'an dube-dubenta ta rushe da wani matsananci kuka tana fad'in


"Indo kin cucemu kin cuci rayuwarmu, kin ja mana abin kunyar da har y'ay'a da jikoki za'a dinga goranta mana, cikin shege a wannan gidan? Allah dai ya isa tsakaninmu dake Indo"


Babu abinda Indo take maimaitawa a cikin zuciyarta face kalmar cikin shege


"Hakan na nufin wai ina d'auke da cikin Mamman kenan a jikina?"


Nan take itama ta fara rusar kuka kamar yanda sauran matan gidan suma suketa faman yi gami da yi mata tofin Allah wadarai


Ana cikin wannan yanayin ne mahaifin Mahabu ya shigo gidan domin yin sallar magariba


Inda yaji koke-koken na fitowa can ya tunkara kai tsaye cikin yanayi na rashin sanini takamaimen abinda ke faruwa a gidan nashi a daidai wannan lokacin


Shi a tsammaninshi ma Indo d'in ce ta mutu, saida yaga Indon a durk'ushe tanata faman rizgar kuka kana ya musanta tunanin nasa


"Wai mike faruwa ne a cikin gidan naga sai faman kuka kukeyi ku duka? Kodai cikin yaran gidan ne wani ya rasu?"


Ya tambaya yayinda yake kallon fuskarsu d'aya bayan d'aya 


"Babu wanda ya mutu Affa Indo ce taje tayo cikin shege" Lauren ta fad'a cikin disashewar murya irinta wanda yaci kuka ya gaji


Salallami tsohon ya fara tare da rik'e baki alamun mamaki k'arara a fuskarsa


"Ai kuwa bazamu zauna dake da wannan d'ingimemen abin kunyar ba a cikin gidan nan, dolenki ki bar mana gida yanzu-yanzun nan dan haka kawai bazaki ja mana abin zagi ba a gari" Cewar Affa kenan


Kilima ce tayi farat"Ni ina ganin kawai Affa ka saketa sai taje can taci gaba da iskancin da ta sabayi"


_Wata sabuwa inji yan caca_

_Wani da sakin matar wani koya wannan lamarin yake?_


Affa baiyi wata-wata ba ya dubi Indo


"Kinga yarinya ji nan, ba kuka zaki tsaya kina yi mana ba jeki gidanku na sakeki saki d'aya" Yana gama fad'ar haka ya baza babbar rigarsa ya fice daga gidan rai a 6ace


Inna tana share hawaye tace "Inama ace uku yayi maki gaba d'aya? Dan zama da irinki ai tamkar zama da annoba ne, amma na tabbata idan Mahabu ya sami wannan labarin sai ya ida cikata maki biyun"


"Inna to ai bata fad'a mana wanda yayi mata cikin ba ko?" Cewar Laure kenan


"Ubanki ne yayi mata, ni ina ruwana da wanda yayi mata ciki da zakice na tambayeta? Kema munafukar Allah ta'ala" Da gama fad'ar haka ta wuce sashinta cikin matsanancin 6acin rai


Sumui-sumui Laure ta wuce sashinta itama jiki a sanyaye


Suma sauran kowa ya nufi nasa 6angaren suka bar Indo anan durk'ushe ita kad'ai sai faman rizgar kuka takeyi tamkar ranta zai fita...._Jiya nayi maku kad'an yau kuma nayi maku da yawa ko? Karku damu halin yau da gobe ne_


 *Maman Ja'afar*

 +966592551785

[4/21, 10:12 PM] Maman Ja"afar: [01/04, 10:52 p.m.]

 🌻MAHABU🌻      12Daga Alkalamin

Maman Ja'afar✍
Su Mahabu kusan su 6 suka fito neman motar BARAK CHADI daga nan cikin garin Sabaha


Wani Balarabe ne yazo dab da inda suke tsaye ya faka da motarsa "Barak Chadi zaku tafi ne?" Ya fad'a da harshen larabci


Basuji abinda yake fad'a ba amma ga dukkan alamu sun fahimci abinda yake nufi domin daga masa kai sukayi suduka alamar "Eh"


Umarni ya basu da su shigo cikin motar, suko batare da 6ata lokaci ko wani dogon tunani ba suka shisshiga cikin motar suka zauna.


Balaraben nan bai zame dasu ko ina ba sai a k'ofar wani gida mai gate, umarni ya basu da su biyosa a baya zuwa cikin gidan


Sudai zungum-zungum suke biye dashi domin dukkan su wannan shine zuwansu na farko Libei shiyasa bawani sanin halin larabawan sukayiba bare har su san abinda ke shirin faruwa dasu yanzu.


Gidan k'aton gidane koko nace fili domin fili ne kawai aka d'iba aka zagayeshi da doguwar katanga ta yanda mutum bazai iya haurawa ba aka saka mashi gate

****

Mutane suka gani dank'am a cikin gidan farare da jajaye, hausawa y'an Nageria da y'an Ghana y'an Chadi da sauran k'asashen da dai mutane suke yawan fita ci rani


Wasu daga cikinsu nata faman ayyuka wasu kuma dukansu akeyi, wasu ana tsattsaga masu jiki da reza yayinda wasu kuma cikin nishad'i suke abinsu, abin dai babu kyan gani


_(Kamar dai wannan gidan da aka kai su Murjanatu na Yeman a cikin littafina Idan Kunne yaji)_ 


Cikin kid'ima Sa'adu ya dubi Mahabu"MAhabu wai mike shirin faruwa damu ne kuma anan?"


"To ai nima tambayar da nakeso nayi maka kenan"


Suko sauran wad'an da suka shigo tare dasu Mahabu d'in hanyar k'ofar gida suka nufa domin k'ok'arin barin gidan


Wasu yarbawa ne k'atti majiya k'arfi suka dawo dasu baya, saboda naushinda suka kaiwa d'aya daga cikinsu a hak'ark'ari saida ya duk'e dan tsananin azaba 


Sunaji suna gani wannan Balaraben da ya kawosu ya kar6i kud'i a gurin Ogan gidan ya juya ya fice daga gidan abinsa


"Sa'adu anya mutumin nan ba sayar damu yayi ba kuwa? Kaga dai har wasu kud'i ya kar6a a hannunsu kana ya fita"


"Ina ganin mumafa namu kwanan ne ya kusan k'arewa, sai dai muyita addu'a kawai"Cewar Sa'adu kenan yayinda hawayen danasani ke bin fuskarsa.

*****

Wannan gidan ba wani gida bane face gidan da ake kasuwancin mutane, tamkar dai yanda ake Kasuwancin Bayi a zamanin da ya gabata


Idan kanada buk'atar mai yi maka aikin gida ko aikin gona ko kuma wanda zaka dingayin Luwad'i dashi idan kai mai yin Luwad'in ne, ko macen da take buk'atr lafiyayyen namiji kala kaza da kaza duk a wannan gidan zakazo ka cake kud'inka ka siya


Bazaka ta6a ku6ukata daga wannan gidan ba har saidai idan wanda ya sayekan yayi sakaci ka gudu daga hannunsa


Gidan ga tsananin yunwa da k'ishirwa, domin a kullum ta Allah biredi biyu ne ake baku, d'aya da safe d'aya kuma da daddare


Mutane da yawa suna mutuwa a cikin wannan gidan saboda tsananin azabar da akeyi masu ko kuma yunwa, saidai da ka mutu a cikin wannan gidan ba'ayin wata maganar yi maka wanka ko salla bare a binneka, yanda dai kukasan mushen Jaki ya mutu ana kaiwa bayan gari a yar, to haka kaima za'a kaika bayan gari a yar

*****

Kwanansu Mahabu arba'in a wannan gidan Mahabu yayi sa'a wani Balarabe yazo ya siye shi a zuwan zaije ya dinga yi masa Noman rani


Sunyi matuk'ar shak'uwa da Sa'adu shiyasa a lokacin da Mahabu zai tafi har kuka sukayi na rabuwa da juna, wanda ba mamakima daga wannan rabuwar mai yiyuwa bazasu sake had'uwa ba kuma har abada.


Da wannan damar Mahabu ya samu ya sulale daga hannun wannan Balaraben bayan yayi masa aiki na tsawon sati biyu


Batare da 6ata lokaci ba ya nemi motar BARAK CHADI, amma a gurin shiga motar saida yayi taka tsantsan sosai gudun kada a sake maimaita abinda ya faru a baya

*****

Tafiyar kwana d'aya ce ta kawo su Mahabu Barak Chadi daga nan kuma ya nemi motar zuwa QA'D'DAHIYA


Daga Qaddahiya motar GULULEK suka nema saboda tun a Barak Chadi ya samu abokan tafiya


Kwanansu Mahabu biyu a Gululek suka hau motar Shanu domin wucewa ZILLETAN


Shinfid'u ne direban yayi a bayan motar tamkar masu shirin yin bacci ba masu shirin yin tafiya ba


Cikin mamaki Mahabu ya dubi Qadiri d'aya daga cikin abokan tafiyar tasa kenan wanda shima ya kasance haifaffen k'asar ta Nijar


"Wai mai motar nan kodai shirin rena mana hankali yakeyi tunda kud'inmu sun riga sun shiga hannunshi? Dan ni yanzu na daina yarda da jajayen nan"


"Kaidai ka tsaya ka gama ganin sarautar Allah mana" Ya fad'a a tak'aice 


Koda gama wannan shinfid'ar direban ya umarcesu da su shisshiga su kwakkwanta a ciki


"Ita dama motar taka ta kwanciya ce bata zama ba?" Cewar Mahabu kenan


"Baka ta6a bi ta wannan hanyar bane?" Cewar direban kenan


"Eh" Ya fad'a a tak'aice 


"To saboda tsoron hukuma ake kwanciya domin hukumar Libiya bata buk'atar bak'i a cikin k'asartata, shiyasa suke d'aukar k'wakk'waran mataki akan hakan, shiga idan zaka shiga, idan kuma motar zama kake nema zauna nan kaita jiranta kaji?" Yana gama fad'ar haka ya shigewarsa gaban motar yayi zamansa


Kamar yanda direban ya umarcesu haka kuwa sukayi


Kowa ya kwakkwanta akan wannan shinfid'ar daga bisani kuma aka kawo manyan Barguna aka lullu6esu, kana daga nan kuma aka samo Ganyayyakin Ciyawa aka d'odd'ora asamansu, a zuwan abincin dabbobi ne aka d'ebo daga Daji


******


"A'a Indo lafiya kuwa naga kin shigo mana da wannan irin kuka haka? Kefa matsalata dake kukan sakalci wallahi, ko duk kukan rashin Mahabu d'in ne ba'a gama ba har yanzu?"


Cewar Mahaifiyar Indo d'in kenan yayinda ta dakata daga wura wutar tuwon daren da takeyi ta kamo hannun y'ar lelen tata zuwa d'aki, dayake mahaifin Indo din yana gida kuma uwar baso takeyi yaji abinda zasu tattauna ba shiyasa taja y'ar tata zuwa d'akin.


Cikin kuka Indo ke labartama uwar abinda ya faru, tun daga farko har zuwa inda Affa yayi mata saki d'aya, abu d'aya ne kawai ta 6oyewa uwar wato sunan wanda yayi mata cikin


Itama uwar kuka ta saki mai tsananin gaske yazamana da uwar da d'iyar babu mai bawa wani hak'uri


"Indai auren d'an Libei ne kad'an ma kuka gani daga irin matsalolinda yake haifarwa, dama ai na fad'a maku wanda baiji bariba dolensa wata rana yaji Wohoho"


Cewar mahifin Indo d'in kenan wanda ya kasance a bakin k'ofar d'akin tun lokacin da suka fara maganar


Cikin hanzari ya koma d'akin sa ya d'auko wata tsaohuwar shar6e6iyar wuk'arsa data dad'e a ajiye


"Kodai ki fad'a mani wanda yayi maki wannan cikin ko kuma na kasheki na huta da bak'in cikin da kika dad'e kina dasa mani a cikin zuciyata, inyaso nima a kasheni na mutu gaba d'aya sai kowama ya huta" Yana magana hawaye na bin fuskarsa


"Mamm..man ne" ta fad'a cikin sassark'ewar murya


"Badai Mamman aminin Mahabu ba?" Uwar ta tambaya cikin kid'ima


Shuru y'ar tayi wanda hakan ya tabbatar masu da lallai shid'in dai take nufi


"Aiko wannan abin kunyar badai a wannan gidan ba wallahi sai dai ki san inda zaki nufa" Tsohon yana magana hawaye na bin fuskarsa abin tausayi......Muje zuwa 13 domin jin chakwakiyar da ke gaba*MAMAN JA'AFAR*

 +966592551785

[4/21, 10:12 PM] Maman Ja"afar: [04/04, 6:54 a.m.]

🌻MAHABU🌻     13Daga Alkalamin 

Maman Ja'afar✍
Mai motar nan bai zame dasu Mahabu ako ina ba sai a wani gari MUSRATA a k'ofar wani k'aton gida kamar dai yanda sukayi masa kwatance


Inda ya kasance matattara ne ga bak'in dake zuwa garin musamman masu son shiga cikin K'asar ta Libiya da kuma sauran mutane masu son haurawa Italiya ta jirgin ruwa


_(Ko a cikin satin nanma naji labarin ance wajen jirgin ruwa hud'u ne ya nitse a cikin ruwa na masu son haurawa kasar ta Italiya, wanda a dalilin hakan nema ya jawo asarar rayukkan mutane sama da dubu uku.)_


_(Haba jama'a wai me muka dauki rayukkanmu ne? Na rasa gane mai laifin daga cikinmu, shin laifin na masu yin tafiyar ne ko kuwa na gwamnatocin da suka kasa sauke hakkinda ke kansu na al'umar kasarsu ne?_


Babban gida ne koko nace babban gari saboda girmansa yafi k'arfin a kirasa da gida ko wata unguwa saidai kawai akirasa da gari guda


Bene ne hawa d'aya a saman gidan kuma dai girman saman tamkar girman k'asan ne


Duk girman wannan gidan k'ofa biyu ne dashi, data shiga sai kuma ta fita


A cikinsa babu abinda ba'a sayarwa na buk'atun rayuwa shiyasama idan ka shigosa ba maganar fita, inama kaga hanyar da zaka fita d'in masu gadi tako ina?


Kuma duk girmansa da irin dinbin mutanenda ke rayuwa a cikinsa Band'aki 2 ne kacal a cikinsa.


Anan d'inma kasuwancin mutane akeyi aciki tamkar dai wancen gida dasu Mahabu suka baro


Sai dai wannan cinikin ya banbanta da wancen ta 6angare da dama


Misali dama tun farko kamin ka baro k'asarku zaka samu lambar wani d'an'uwanka ko kuma abokinka wanda ke zaune a K'asar ta Libiya kuyi yarjejeniya dashi idan kazo wannan gida zai fansheka daga hannunsu inyaso daga baya idan ka nema ka biyashi inma riba yake buk'ata sai ka k'ara mashi, duk dai kuyita dawajewa tun kamin ka taso daga gida


To da kazo wanann gida sai ka bada lambarshi suyi magana asakaka a mota a kaika har inda yake su kar6o kud'insu su dawo


Suma wannan ne kasuwancinsu kuma da wannan zalincin suke cin abinci.


******


"Qadiri kadai zo da lambar wani naka ko?"Mahabu ya tambayesa bayan shigowarsu da sukaga irin azabar da ake ganawa mutane a cikin gidan


"Alhamdulillahi nazo da ita, banida rabon wannan wahalar za'a shata dani, kaifa?" Ya tambaya yayinda yake duban fuskar ta Mahabu


Dafa kafad'ar Qadirin yayi tare da cewa


"Nima dai ka tayani murna nazo da ita, da harfa mantawa nayi da ita a k'asan katifa sadda zan taho Indo ce ta taimakeni ta tuna mani badan haka ba da ina ganin nan gidan ne ajalina tunda dama k'arfina duk ya riga ya gama k'arewa a hanya"


Wani k'akk'arfan matashi ne yazo inda suke, dayake Bayarabe ne cikin gwarancin hausarsa yake tambayarsu lambobin waya


Lambobin ya kakkar6a kana daga bisani aka umarceshi da ya kakkawo masu abinci


Cikin mamaki Mahabu ya dubi abokin nasa"Wato Qadiri indai mutum yana duniya zai dinga ganin abin mamaki kala-kala"


"Saboda mi kace haka?"


"Kallafa iya ganinka duk inda ka waiga jama'a ne dank'am y'an k'asashe daban-daban, wasu iyakarsu Libei wasuma Allah ne kad'ai yasan inda zasu tsaya, babban abindama yake d'aure mani kai Qadiri Kallafa mata da k'ananan yara ko ina birjik yanda kasan ba hanyarda na biyo mai had'arin nan suma suka biyo ba"


Yana magana yana waiwaigensa domin bawa idanuwanshi abinci a cikin gidan


Wani tsoho ne ya zo dab dasu ya zauna, wanda tun fara firar tasu yake gefe yana saurarensu


"Ai Malamai nanma kad'an kenan kuka gani tunda a kullum ta Allah ana d'ibar wasu ana kaiwa gun yan'uwansu, inda jibgewa akeyi ai duk girman gurin nan da kuke gani yayi mana kad'an sab....


Mahabu ne ya katsesa

"Amma bawan Allah su kuma way'an nan matan da k'ananan yara me sukeyi anan su kuma?"


"Eto wasu dai daga cikinsu mazajensu suka biyo, wasu kuma Karuwanci sukazoyi, musamman ma irin wad'ancan arnan" Ya fada yayinda yake nuna masu inda arnan suke


"Wallahi duk daga Kudancin Nageria suke fitowa, wasu iyakarsu nan Libei wasu kuma karuwancin zasuyi su samu kud'in haurawa Italiya"


Ya k'ara da cewa


"Yo shuwagabannin K'asar tamu ne duk gasu nan dai abin sai addu'a kawai, saboda basu kishinmu bare kuma kishin rayukkanmu, kaga idan akace maka K'asar Nijar Nageria Ghana Chadi Kamaru Benin da dai sauransu...babu inda aka tattara 6arayin gwamnati marasa kishin k'asa da kuma cigaban K'asar irin way'an nan k'asashen dana lissafa maku, shiyasa kullum mu bama gida muna kan hanyar bin K'asashen da suka samu cigaba neman arziki ta yanda zamu rufawa kanmu asiri da kuma iyalanmu, wanda inda za'a baje abin a faifai wallahi tallahi ina mai tabbatar maku babu abinda K'asar Saudia ko Sudan ko Libiya zasu nuna mana barema har muyi tunanin tafiya K'asashensu neman kud'i muita rasa rayukkanmu a banza a wofi, wallahi ina mai tabbatar maku da sai dai azo nema a k'asarmu badai mu muje nema a k'asar wasu ba"


_Mutumin yana magana hawaye na bin fuskarsa abin gwanin tausayi Tamkar dai ni Maman Ja'afar da nake zubar da hawayena a lokacinda nakeyi maku wannan typing d'in_


Qadiri ne ya numfasa"Kabar ma maganar Nijar, dama kowa yasan mu haka muke kullum jiya i yau, ni babu ma irin mulkinda ke ci mani tuwo a k'warya kamar mulkin mak'wabciyarmu Nageria, sunyi sa'a Allah ya basu shuga nagari wanda wasu ke neman irinshi ruwa ajallo basu samu ba, amma su Allah ya basu sai faman wulak'antawa suke, gafa shugaba na gari amma y'an hana ruwa gudu sai dak'ile masa aikinsa sukeyi, kullum yana tubka su kuma suna warware, inko a na haka ai babu ranar da zamu daina fita ci rani kenan K'asashen wasu?"


"Allah dai ya kawo mana agajin gaugawa a cikin wannan lamarin" Cewar Mahabu kenan


******


"Haba haba Malam, idan kace Indo ta bar gidan nan ina kakeso ta nufa sabida Allah? Ai yin hakan tamkar k'arin wani abin kunya ne agaremu, yanzu ba kowane ya san da wannan maganar ba amma barinta gidan nan shine zai jawo hankalin mutane zuwa garemu, wanda yin hakan kuma ba k'aramin gore-gore da habaici zaija mana a cikin garin nan ba, k'arshentama nan gaba kad'an ko fita nanda k'ofar gida ya gagaremu dagani har kai"


Itama dai kamar Malam d'in tana magana hawaye na bin fuskarta


"Abin kunya kuma na nawa Rabi? Ai saidai kar a kuma"


Mai da wuk'ar yayi cikin kubenta ya fara wasu yan dibi-dibi na rashin takamaimen abinyi, ga dukkan alamu tsohon a rud'e yake, can dai ya numfasa yace


"Rabi bata gyale ta yafa muje gidan Kashe"


"Me kuma zakuyi a gidan Kashe wanda ya wuce tonon siriri Malam?"


"Ada ne kamin tayi wannan aika-aikar a sirinmu yake a rufe amma yanzu kam ai tamkar anbazashi a Faifai ne kowa ya d'auka"


Badan taso ba ta d'auko gyalen ta mik'awa Indo, itama nata gyalen ta d'auko ta d'ora a ka, danko tsayawa yafashima batayi ba tabi bayansu zungui-zungui


*****


Babban mutum ne d'an kimanin shekaru kusan hamsin a duniya


Kashe kenan zaune a fadarshi fadawa duk sun zagaye shi tako ina


Ya hango su Indo na tunkaro inda yake gadan-gadan


Yafito d'aya daga cikin fadawan nasa yayi, fuskar nan tasa tamke babu wani alamun wal-wala acikinta domin ya gaji da irin k'ararrakin da ake kawo masa a cikin y'an shekarun nan


"Na Amma gafa wata yarinya can iyayenta sun tasota agaba, Allah yasa dai ba irin k'arar matanda suka tashi d'azu ba suma suka kawo mani?"


Kan Bafaden a k'asa saboda tsananin girmamawa yace


"Allah ya taimakeka ai saidai aita hak'uri da yan tafiya Libei d'in nan domin ba dainawa zasuyi ba"


"Ai kuwa indai abinda nake tunani akansu ya tabbata wallahi nasan matakinda zan d'auka, mataki ne zan d'auka k'wakk'wara wanda bazaiyiwa kowa dad'i acikin garin nan ba, inyaso...


Kamin ya k'asa maganar tasa ne su Malam Audu sukayi sallama a cikin fadar


Bayan Fadawan sun amsa masu ne suka basu umarni da su zazzauna


"Meke tafe daku Malamai?"

Cewar Kashen kenan ransa a 6ace


"Ranka ya dad'e k'ara ce na kawo" Ya fad'a tare da duban Indo


"Wato ranka ya dad'e wannan yarinyar da kake gani bayan bikinta da wata d'aya ne mijinta yasa kai ya tafi Libei, to bayan tafiyar tasa ne aka samu wani tsinannen Abokinsa ya d'ika mata ciki, to shine nakeso ranka ya dad'e a taimaka a bi mani hakkina agun azzalumin yaron da yayi mata cikin saboda ya zalincemu sosai dan yanzu hakama sirikin nata har ya saketa saki d'aya" Yana magana muryarsa na sassark'ewa alamun yaci kuka har ya gaji


Wannnan bayani na Malam Audu ba k'aramin kara 6atawa Kashe rai yayi ba, domin dama ran nasa a 6acen yake


"Malam Audu kana jina?"


"Ina jinka ranka ya dad'e"


"Kuyi hak'uri ku koma gida insha Allahu gobe goben nan zan d'auki mataki na k'arshe akan wad'an nan matsalolin da suke faruwa a cikin wannan garin nawa"


Fadawan nasa ya duba d'aya bayan d'aya idanuwan nan nasa sunyi jajir sai kace garwashin wuta saboda tsananin 6acin rai


"Inaso a tara mani mutanen garin nan dukkansu gobe i wara haka anan gurin, kuna jina ko baku jina?"


"Munaji ranka ya dad'e Allah ya kaimu goben lafiya" Suka amsa kusan a tare cikin ladabi....


MAMMAN JA'AFAR

+966592551785

[4/21, 10:12 PM] Maman Ja"afar: 🌻MAHABU🌻      14Daga Alkalamin

Maman Ja'afar✍Kamar kuwa yanda Kashe ya buk'ata washe gari tun misalin k'arfe hud'u da rabi na yamma kowa ya hallara a gabansa, babu wanda aka bari a gida sai yara k'ananu da kuma tsofi marasa lafiya way'anda bazasu iya tashi ba.


 Saida dogarai suka tsawatar sosai akan hayaniyar da jama'a keyi kana suka d'an saurara Kashe ya fara bayaninsa kamar haka


"Assalamu alaikum jama'a"


Cikin hayaniyar tasu suka amsa sallamar kana kuma daga bisani aka tsawatar masu sukayi shuru


"Ba komai bane yasa na taraku anan sai wata k'wakk'warar doka danake son kafa maku, duk wanda ya bita ya tsira wanda kuma yabi akasin hakan zai kuka da kanshi, domin tarar da zan d'orawa mutum ina tsammanin sai ya sayar da dukkan gonakinsa da kuma garkunansa kana ya biya, mai yiyiwama a hakan sai na biyoshi bashi"


Da jin wannan lafazi na Kashe nan take jikin kowa yayi sanyi, domin duk abinda Kashe ya fad'a babu makawa sai ya aikata dan irin hakan ta ta6a faruwa dasu a wani lokaci da garin suka samu albarkatun gona da yawa har suka rasa yanda zasuyi dashi mutanen birni sukaita zuwa suna banzatar masu dashi a arha, domin a lokacin bana mantawa har nera 30 suke sayar da tiyar wake, saida Kashe ya tsawatar masu ya nuna masu illar abin da kuma saka tara mai tsanani ga wanda ya aikata hakan kana suka daddara suka daina sayarwa


Kashe ne ya katse masu tunanin nasu da cewa


"Doka ce mai tsanani zan saka ga dukkan wasu masu tafiya Libei ko suke shirin tafiya Libei, kai bama Libei kad'ai ba harda sauran K'asashe da mutanenmu suke zuwa ci rani, kuma dokar ba akansu kad'ai zata tsaya ba, a'a zatayi aiki ne har akan iyayensu maza da mata"


Shuru yayi na d'an wani lokaci kana yaci gaba da bayaninsa


"Daga rana mai kama data yau duk wanda yayi tafiya zuwa wata K'asa yadawo ya tarar da matarsa da ciki ko kuma da goyo, to babu wata maganar jayayya ko saki ko kuma wata kawo k'ara gurina, cikin nan daya tarar ko kuma goyo ni Kashe Sumaila na mallaka masashi halak malak, kuma ko yanaso ko bayaso dole ya kar6a kuma ya rik'e a mutunce tunda ba uban wani ne ya tilasta masa cewa wannan tafiyar ala dole sai yayita ba"


Numfasawa yayi kana yaci gaba da cewa


"Kuma maganar ya aiko da takardar saki daga wata K'asa ko kuma ya saka mahaifinsa ya saketa koshi mahaifin ganin damar kansa ya saketa babu ita, na rushe wannan daga yau"


K'ara gyara babbar rigarsa yayi kana cikin tsananin fushi yaci gaba da cewa


"Da wannan nake bada umarni duk wata mata da mijinta ya saketa ko mahaifin mijinta ya saka indai ba saki uku uku bane ni Kashe nace ta koma gidan mijinta, inga ubanda ya isa ya sa6a maganata kuma"


Zama yayi akan kujerar katakonsa kana yaci gaba da cewa


"Kuma duk wadda ta koma gidan mijin nata akayi mata bak'ar magana ko habaici ko gori ko wani kallon banza k'ofata a bud'e take a koda yaushe tayi gaggawar zuwa ta sanar dani ni kuma zakuga irin matakinda zan d'auka"


D'ora k'afa yayi d'aya akan d'aya kana yaci gaba da cewa


"Wacce kuma akayiwa saki uku ina mai bata hak'uri tayi hak'uri ta zauna a gidan iyayenta amma duk ranar da mijin nata ya dawo tazo tayi gaggawar sanar dani domin ganin irin matakin da zan d'auka akanshi"


Numfasawa yayi kana yace


"Nagama maganata daga nan duk wadda ta san ansaketa ta wuce d'akinta kai tsaye"


Da wannan taron ya watse kowa ya kama gabansa, yayinda sakakkun irinsu Indo kowacce ta nufi d'akin mijinta cikin isa da tak'ama domin Kashe Sumaila ya d'aure masu gindi. 

*****

Wannan nema yasa Indo bata fuskanci wata tsangwama ko takurawa ba a wajen iyayen mijin nata da kuma danginsa, sai dai dukda haka babu mai shiga sabgar wani tsakaninta dasu.


*******


*MAHABU*


"Waye Mahabu a cikinku?" Cewar wannan Bayaraben kenan wanda yake kula da 6angaren shiga da ficen su Mahabu


"Gani ya" fad'a a tak'aice


Alamu yayi masa da ya biyosa a baya


A gaggauce sukayi sallama da Qadiri domin rabuwa ce ta ba lallai su sake had'uwa ba har abada.


Gurin su goma aka d'iba zuwa gurin wata Tasi, saboda dama gurin tamkar irin ace an ajiye mutum a Lagos ne wani zai tafi Kano, wani Katsina, wani Abuja, wani Mai Duguri.


Shiyasa sai a d'ebi kamar mutum 5 ko 10 cikin k'aramar mota wad'anda tafiyarsu tazo d'aya aje akaisu, kuma hukumomi bazasu fahimci komai ba tunda ba gayyar jama'a sukaga ankwaso ba .


*****


"Allah sarki Mahabu ashe rai kanga rai" Cewar Yusha'u kenan wanda ya kasance amini ga Mahabun tun suna yara bayan ya kar6osa gurin masu motar nan sun shigo gida sun zauna suna hutawa


"Wallahi ka cuceni, ka zalunceni iya zalunta Yusha'u"


Cewar Mahabu d'in kenan


Dariya matashin yayi sosai harda k'yak'yatawa wanda shekarunsa bazasu gaza na Mahabu d'in ba


"Da ace sadda kace mani zakazo na hanaka zuwa, ko kuma na fad'a maka gaskiyar matsalolinda ke akan hanyar, wallahi ko zan had'iyi qur'ani ina rantse maka da matsala ba yarda zakayi ba, shiyasa muna fara jayya da kai na sakar maka nace kataho d'in, yanzu ba gashi nan kagani da idanuwanka ba? Ni wallahi nazacima sak'on mutuwarka ne zai iso kunnuwana ba kai d'in ne zaka iso gareni ba"


Yana magana yana dariya abinsa, kana ya tsagaita da dariyar tasa yace


"Kudai kawai kuga mutu a wata K'asa indai tafiyar k'afa akace maku yayi har ya isa gareta, domin bakusan irin iya wahalarda ya sha ba kamin ya iso, ku matsalarku da kunga mutum yanata turo kud'i gida sai ku d'auka tamkar abin ba wata wahala ne dashi ba, yanzu ai gashi nan ka gani da idanuwanka nan gaba idan kaji wani yace maka zaizo Libei sai kasan irin amsar da zaka bashi"


Dukan bayansa Mahabu yayi cikin wasa


"Banza mugu kawai, nidai kira mun Tanimu a waya ya had'ani da Indona dan nasan wancen sakaran Mamman waya ba wani zama takeyi a hannunsa ba, ba wuya ya siya kuma ba wahala ya sayar....


Muje zuwa shafin k'arshe


*Maman Ja'afar*

[4/21, 10:12 PM] Maman Ja"afar: [04/04, 12:17 a.m.]

🌻MAHABU🌻


     15


   K'arsheDaga Alkalamin

Maman Ja'afar✍A lokacinda Mahabu yake k'ok'arin kiran Tanimu a waya a kuma daidai lokacin ne Tanimun yake k'ok'arin had'a Amalanke domin kai Indo assibiti, ina tsammanin k'ilan haihuwar ce ta taso (Domin Mamman tunda labari ya bazu a gari aka nemesa sama ko k'asa ka rasa) 


Wurin kwanansu uku a assibitin anata fama amma haihuwar tak'i zuwa, a cikon kwana na hud'un ne Allah ya taimaketa ta suntumo d'anta namiji kamarsa da Mamman kuwa harta 6aci domin tamkar an tsaga kara ne an ajiye kamannin nasa da uban


Sai dai abin farin ciki zance koko abin bak'in ciki yaron baizo da rai ba, domin a cewar likitocin wai watanninsa basu kai na haihuwa ba.


*****


Satin Indo uku ta samu lafiya ta dawo garau abinta tamakar ba itace ta haihu ba, a lokacin kuwa Mahabu har ya fara aiki a wani kamfani na gyaram motoci inda Yusha'u yake aiki


******


"Mahabu aradu wayar Tanimu ta shiga" Yusha'un yana magana wayar na a kunnensa ga dukkan alamu dama ya dad'e yana neman lambar


Cikin murna ya diro daga kan k'atuwar katifar mai kama da gado


"Da gaske? Banishi dan Allah" cikin sauri Mahabu ya kar6e wayar


A daidai wannan lokacin kuma Tanimun ya d'aga wayar


"Banza baho bokiti kawai, anata nemanka a waya amma kullum a kashe?"


Saida Tanimu yayi wani ihu gami da tsallen murna kana yace"Dan Allah abokina kayi hak'uri wallahi abubuwa ne sukayi yawa, kuma kasan dai ba wata wutace damu ba, kullum sai mutum ya bayar da kud'i anyi masa cajin waya, kud'in kuma basu ke akwai ba, ai nima gani nan zuwa gareku, yaushe zaka turo mani kud'i nima na taho?"


Wata muguwar dariya ce ta kunbcewa Mahabu, daidai kunnensa Yusha'u yazo yake rad'a masa "Karka fad'a masa barshi shima yazo ya d'and'ana yaji abinda muma mukaji a hanyar"


Baibi takan wannan zancen ba ya canza akalar firar tasu


"Tanimu ina Indona take? Muryarta kawai nakeson ji na fad'a mata na sauka lafiya naji irin farin cikinda zatayi"


Shuru Tanimu yayi nad'an lokaci, kana dai daga bisani yace "Yusha'u bai fad'a maka komai game da ita ba?"


"Bai fad'a mani ba, kaddai kace mani gurin haihuwa Indon tawa ta mutu?" Cikin rud'ewa yake fad'a wannan maganar


"A'a ba mutuwa tayi ba sai dai wani abu mai kama da mutuwar ya faru da ita, kai bama ita kad'ai ba kowama abin ya shafeshi..


Cikin rud'ewa Mahabu yake kallon Yusha'u duk da wayar da ke hannunshi


"Yusha'u wai meke faruwa da Indo ne kuketa faman yi mani k'unbiya-k'unbiya?"


"Saurari wayar dai Tanimun ya fad'a maka, amma ni kam wannan labarin k'wad'on bakajishi a bakina ba"Ya fad'a yayinda yake nuna masa wayarda ke hannushi


Da k'yar dai Tanimu ya kwashe labarin komai ya sanar dashi, tun bayan tafiyarsa har zuwa haihuwarda Indon tayi d'an baizo da rai ba


Bai k'arasa jin sauran bayanin daga bakin Tanimun ba yaga wani duhu-duhu ya rufe masa idanuwa, nan take ya sulale ya fad'i k'asa a sume


Dama tun farko abinda Yusha'u ya guda kenan shiyasa bai tunkaresa da wannan mummunan labarin ba


Da k'yar Yusha'u ya samu Mahabu ya dawo hayyacinshi tare da taimakon wasu y'an garin nasu


"Mamman ka cuceni, kaci amanata, ka lalata mani rayuwa, ka kafa mani tarihinda zai dinga bibiyata har y'ay'a da jikoki"


Sabbatunda Mahabu keta famanyi kenan, sauran jama'a nata rarrashinsa gami da ban hak'uri


"Dama saida Indo tace kar nafi kar nafi, nayi biris da ita, yarinyar nan har kwanciya rashin lafiya tayi saboda tafiyar da zanyi na rufe ido nak'i tausaya mata bayan nasanta sarai nasan tafi son kusanci dani fiye da komai a rayuwarta, wani lokacima idan dare yayi har fad'a mukeyi inace mata nida nagaji bazan....


Yusha'u ne ya dad'e masa baki saboda lura da yayi da abokin nasa yana neman fita cikin hayyacinsa


"Yusha'u wallahi komawa gida zanyi, zanje nabawa Indona hak'uri domin kome ya faru da ita nafi kowa sanin nine sila, wallahi tallahi ko duniya zan samu da abinda ke cikinta wannan bak'in cikinda Indo da Mamman suka k'unsa mani nasan bazai ta6a goguwa a cikin zuciyata ba, saboda haka na hak'ura da neman kud'in, zan koma gida idan talauci na kashe mutane nima ya kasheni"


Da k'yar dai suka samu suka shawo kansa ya daina sabbatunda yakeyi.


******


Washe gari tun safe yake damun Yusha'u akan ya kira masa Tanimu a waya 


"Nifa ba waya ce bana son baka ba, banaso kaita jin labarai marasa dad'i ne a gida shiyasa"


"Kaidai bani dan Allah" Cikin zak'uwa yake maganar


Zaro wayar yayi daga aljihunsa jiki a sanyaye ya mik'a mashi


Bai dad'e yana daddannawa ba wayar ta shiga


"Yauwa Tanimu kaiwa Indo waya"Abinda ya fad'a kenan bayan ya daga wayar


"Au har yanzu dai baka daina yarda da abokai akan iyalanka ba ko?"


Ajiyar zuciya yayi kana daga bisani yace"Wane abokai kuma? Ai aikin gama ya riga ya gama kaima idan kanada wata k'ulalliya a cikin ranka ai gaka ga ta nan" Ya fad'a cikin 6acin rai


"Allah ya huci zuciyarka bara na ruga na kai mata"


******


Indo tana k'ofarta tana sana'arta da ta saba wato kuka taji sallamar Tanimu


Cikin sauri ta d'auko hijabinta ta saka domin abinda ya faru agareta ba k'aramin darasi ya koyar da ita ba, shiyasama tad'aukarwa kanta alk'warin insha Allahu har abada abokin miji ko hak'orinta bazai ta6a gani ba bare kuma har a kai ga...


"Indo fito ga waya Mahabu ya bugo maki"


Wani fad'uwar gaba taji lokaci guda har saida ta dafe k'irjin nata


Jiki na kyarma ta k'ar6i wayar, bata samu damar ko yin sallama ba saima wani matsanancin kuka daya kubce mata


"Dan Allah Mahabu kayi mun rai, dan girman Allah karka sakeni, wallahi tallahi har yanzu banida tamkarka a cikin zuciyata, sharrin shaid'an ne kayi mani aikin gafar...


"Kinga yi shuru daina kukan ya isa haka kinji? Share hawayenki"


Kamar kuwa tana kallonsa tasaka gefen hijabinta ta share hawayen nata


"A cikin abinda ya faru kowa yanada nasa laifin daga cikinmu, amma nawa laifin yafi na kowa yawa, karki damu Indo na yafe maki, kuma aurenmu yana nan nidake mutu ka raba insha Allahu"


Numfasawa yayi kana yaci gaba da cewa


"Da wannan labarin ya riskeni naso dawowa gida, to amma sai su Yusha'u suka bani shawarar akan na tsaya ko neman shekara d'aya ne nayi nasamu kud'in da zan hawo jirgi na dawo ta sama, kiyi hak'uri, ki k'ara hak'uri insha Allahu bad'i kamar yanzu Indo na tare da mijinta, gatanta kuma uban y'ay'anta"


Yana magana hawaye nabin fuskarsa, dukkan abokansu way'anda ke zazzaune a cikin d'akin saida suka tausaya mashi, kuma suka jinjinawa wannan k'arfin soyayya dake tsakaninshi da Indo.


Suko mutanen gidansu Indo har rige-rige sukeyi wajen sauraron irin hukuncin da Mahabu zai d'auka akan Indon, a ciki kuwa harda surukarta Inna Fure


Da suka fahimci masoyan suna k'ok'arin sasanta junansu ne sai kowa ya dinga sulalewa da d'ai d'ai da d'ai d'ai gudun karsu furta wani abu akan Indon Kashe ya d'au mataki akansu kamar yanda ya ambata.


******


_BAYAN SHEKARA D'AYA DA Y'AN WATANNI_


Mahabu ne na hango zaune akan babban hadonsu a d'akin uwar gidansa kuma amarya wato Indo, sunata faman fira abinsu cikin nishad'i da walwala tamkar dai dama can babu wani abu marar dad'i daya ta6a faruwa a tsakaninsu


Amma dukda hakan Indo bata saki jikinta ba sai faman wani nonnok'e fuska taketayi sai kace wata tsohuwar munafuka


"Waini Indo dan Allah yaushe zaki daina jin wannan kunyar tawa ne? Haba kullum abu yak'i ci yak'i cinyewa sai kace cin K'wan Makauniya?"


Ita dai murmushi tayi gami da k'ara jawo mayafinta ta rufe fuskarta


"To shikenan tunda har yanzu kin k'i sakin jiki dani bara kiga nayi abinda zai fissheni"


Saukowa yayi daga kan gadon nasu mai runfa ya fara rausayawa a hankali yana tafa hannuwansa duka biyun yana dukan cinyarsa yana raira wak'arsa kamar haka


_*Ayye wance tayi abin kunya*_


_*Gudun san dokinma batajeshi ba*_


_*Ayye tayi abin kunya*_


_*Jaraba ce koko rashin kunya tayi*_


_*Ayye tayi abin kunya*_


_*Kodama fanko ce bamu lura ba*_


_*Ayye tayi abin kunya*_


Dariya ce ta k'wacewa Indo taci gaba da k'yak'yatawa harma batasan lokacin da mayafin nata ya fad'o daga kan nata ba.K'arshe


Tammat Bi HamdullahKuyi mani hakuri banida lafiya ne shiyasa na d'an takaita maku labarin kunsan komai saida lafiya._Allah sarki_

_Soyayya babu yafiya babu mantu babu afuwa bai kamata mu kirata da sunan soyayya ba. inji ni Maman Ja'afar__Idan da za'a sami wanda zai tambayeni yace mani Zulaihatu miye babban burinki a duniya?_


_Zan amsa masa da cewa_


_Babban burina a duniya bai wuce ace mutanen Karkara sun samu cigaba a rayuwarsu ba, musamman ta 6angaren ilimin addini dana zamani_


_A sama masu assibito da kuma k'wararon likitici domin kula da lafiyarsu_


_Sannan kuma asama masu Kwarirrika ajawo masu ruwa ta ko ina, ta yanda ko babu noman damina zasu dingayin noman rani, wanda hakan ba k'aramin aiki zai samawa mafi yawancinsu ba, a haka har asamu rarraguwar masu fita k'asashen waje nema suna mutuwa a banza a wofi_


_Idan har wannan burin nawa yacika to kuwa bani da sauran wani burin da ya wuce ace na samu cikawa da imani_
*GODIYA*


   1


_Godiya da yabo da jinjina sun tabbata ga Allah (S.W.A) mai kowa mai komai da ya nufeni da fara wannan littafin lafiya har gashi cikin ikonsa da kuma yardarsa na kammalasa lafiya batare da ansamu wata tangarda ba_


 _Ina rokonsa ladarda yake cikin wannan d'an sakon nawa yasa muyi tarayya dani daku a ciki, kuskurenda kuma nayi ya gafarta mani_  *GODIYA*


     2


_Ina mik'a godiyata ta musamman ga Malamata acikin wannan tafiyar wato *SADIYA JEGAL* da taimakonki da shawarwarinki na fara wannan rubutun har gashi cikin ikon Allah na kammmala litattafai har guda 3 lafiya kuma Alhamdulillahi dukkansu sun samu karbuwa a gurin al'umma_


_Nagode sosai Malamata Allah ya kara girma da daukaka ya bar so da kaunar da ke tsakaninmu_*GODIYA*


   3


_Ina godiya marar iyaka a gareku Yan'uwana wato *TANIMU* da kuma *SULEMAN* dake K'asar Libiya_


_Kun bani gudunmuwa sosai a cikin wannan tafiyar bansan ma da bakinda zan iya gode maku ba, sai dai nace Allah ya saka da alkhairi ya kara dankon zumunci a tsakaninmu kana ya dawo mana daku gida lafiya_*GODIYA*


   4


_Ina mika godiyata ga masoyana masu bin litattafaina maza da mata musamman ma wadan da suka juri bina tun daga littafina na farko Kalubale sukaita bina har littafina na 2 Idan kunne yaji, gashi kuma sun juri bina tun daga farkon MAHABU har zuwa karshensa, kai godiyata bazata misaltu agareku ba_


_Sai dai nace nagode nagode Allah ya bar so da kaunar da ke tsakaninmu da ku_


_Da wannan zanyi amfani wajen neman afuwa agareku ga wanda na batawa ko nayiwa ba daidai ba, ina fatan zaku yafe mani? Nidai dama bakuyi mani komai ba kuma babu wanda na rike a cikin zuciyata, idanma kunyi mani to na yafewa kowa_


_Sai kuma Allah ya sake hadamu a cikin wani littafi na daban mai dauke da labarin wata kasar kuma ta daban idan munada rai da lafiya_
*TAMBAYAYOYI*_Shin littafin MAHABU a naku ganin wane sako yake son isarwa ga al'umma?_


_Mekuka karu dashi acikin wannan d'an takaitaccen littafin na Mahabu?_


_Shin sabon salon rubutun da nazo maku dashi na tafiye-tafiye da kuma zak'ulo maku wasu matsalolinda suke addabarmu yayi maku naci gaba da yin irinsa ko kuwa dai na canza wani salon na daban kamar yanda wasunku suka bukata?__Shin acikin litattafan da nayi guda uku_ *_KALUBALE_*


*_IDAN KUNNE YAJI_*


*_MAHABU_*


_Wanne yafi kayatar daku?_
_Bani wadannan amsoshin masoyana shine zai tabbatar mani da cewa lallai kuna tare dani dari bisa dari a cikin wannan tafiyar__SAI NAJI DAGA GAREKU MASOYANA_
🏵Y'AR GHANA🏵


        1


Daga Alkalamin 

Maman Ja'afar✍
"Azumi! Azumi! Daga tsakar gida uwar taketa faman k'wala mata kira


"Iye Ammah" y'ar ta amsa daga can cikin band'aki inda take k'ok'arin yin wanka


"So nawa zan fad'a maki bana son wannan wankan naki da kika tsira a cikin Makewaya iye? Duka dukanki a nawa kike? Shekarunki fa basu wuce 14 ba amma ke har kinsan ki wani shiga makewaya kice zakiyi wanka, kodai so kike asakaki a bakin duniya ne ana cewa kin matsu kema ki zama budurwa?" Cikin matsanancin 6acin rai uwar takeyiwa y'ar tata fad'a "Haba Ammah haba Ammah, nifa wallahi kunyar yin wanka nakeyi a tsakar gida, dan Allah kidinga barina inayi a Makewaya d'in kawai" tana magana tana had'awa da y'an dire-direnta murya na rawa tamkar mai shirin yin kuka


"To way'anda suka fikima anan tsakar gida sukeyin wanka bare keda kika fara k'irgar dangi yanzu, zaki fito daga Makewayar nan ko sai nazo na bad'a maki tankwa a gabanki?" (Barkono)


Da gudu y'ar ta sa6o bokitin wankan nata tayo waje, domin har yau bata manta tankwan da Ammah ta bad'a mata ba sadda ta aiketa yin nik'a takai gurin k'arfe goman dare bata dawo ba


"Haba! Yarinya tun kina k'ank'anuwanki (k'arama)sai shegen kinibibin tsiya, ina kuma ga kin girma?"


Itadai Azumi wankanta taci gaba dayi tana rurrufe k'irjin nata da soso saboda kunyar da takeji kar agani 


Har ta gama wankan nata uwar data baje a bakin k'ofar d'aki bata daina y'an surutanta ba.


Bayan Azumi ta gama y'an shafe-shafenta ne ta dauko riga da zani zata saka wanda yayarta Baraka ta kawo mata daga Nageria, harta ware zanin uwar ta lek'o ta gani


"Azumi! Bana hanaki saka zanin nan ba ne wai? Wai meyasa kikeson rayuwa irinta manyan mata ne? Idan mutane suka ganki da zani ai sai suyi maki dariya, maza ajiye zanin nan d'auko riga da wandonki da kika saba sakawa kisaka"


Cikin k'unk'uni y'ar ta d'auko dogon wando


"Bashi zaki saka ba, mayar d'auko gajeren"


A haka badan tanaso ba ta d'auko wata y'ar fingilar riga ta saka gami da d'an guntun wando, ta d'auko hularta hana salla ta d'ora akanta, tadaiyi shiga tamkar dai yanda mahaifiyar tata ta buk'ata


K'aton tire d'in biredinta ta d'auko ta d'ora aka wanda yake ajiya a gefe guda na cikin d'akin


"Ammah na tafi sai na dawo" Y'ar ta fad'a a tak'aice 


"Saura kuma ki dawo mani baki sayar ba, Ciiiiii Lalado"(Banza kawai sakarya)Y'AR GHANA KENANZaizo maku nan bada dad'ewa ba idan Allah ya bani lafiya*NICE DAI TAKU*

*HAR KULLUM* 

*MAMAN JA'AFAR*

+966592551785

Tags: #Maman Ja’afar #rayuwa
1426
0
2
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!