Mafarin So!

Written by Rabiatu Mashi SkPublished on 2018-12-12 16:02:48Category Romance Ƙaddara ce take yawan haɗasu, sai dai duk sanda suka haɗu sai sunyi faɗa a tsakaninsu, har tsautsayin da yayi silar aurensu yaa faru cike da ƙiyayyar juna, koya zaman nasu zai kasance? tags: #Ahmad #Rabi’atu #mafarinsoDuba was labarai »

[3/17, 19:13] Sisinah: ♡♡MAFARIN SO♡♡

  ♡♡♡♡♡♡♡♡    

     ♡♡♡♡♡

        1-5


©Rabiatu sk mashi

     ®NWA


Rerbeeart_sk @wattpad


www.babymsh.blogspot.com


Tafiya take cikin nutsuwa, burgewa, da takun Isa, Sanye take cikin doguwan rigan material, kalan brown da milk, saita yafa k'aramin mayafi akai, tana rik'e da wasu littafai a hannunta.

   Bata ankara ba sai dai taji abu ya dakar mata goshi harta kusa faɗuwa, kafin ta ɗago kanta kawai taji an kwashe da dariya, cikin k'unar zuciya ta ɗago da kanta tana k'arema wurin kallo, gaba ɗaya cike wurin yake da ɗaliban jami'ar kuma kusan duka hankalinsu na akanta. Dariyarshi tafi shigar mata kunne, juyawa tayi ta watsa mishi harara.

  Dariya yayi irinta gogaggun en iskannan, 

  "zo mana" ya kirata da hannu, yana zaune saman motah da en korenshi zagaye dashi, taso ace zata iya komawa ta sauke mishi duk masifan dake ranta, anma jin kanta da tak'ama bazai taɓa barinta ba, kuma shi bai kai ajin da zata tsaya gaban mutane tana maida magana dashi ba. Juyawanta kawai tayi taci gaba da tafiyanta,

   Batasan sanda ya diro daga saman motan ba, sai dai kawai taji yana neman rik'o hannunta, cikin zafin nama ta juyo ta wankeshi da marin da yazo mishi a bazata, ɗaga kanshi yayi yana kallon mutanen da sukayi cincirindo suna kallonsu, sannan kowa ya fara k'ok'arin riƙe dariyanshi don babu wanda baisan halin Abdallah ba.

    "Ni kika mara?"

   "an mareka ɗin, wannan shine gargaɗin dazan maka na ƙarshe akan shiga harkata da kake"

    "ke kinsan waye Abdallah, wallahi sai kinyi dana sanin marina da kikai"

   "Anma bakasan wacece Rabi'ah ba, kuma ina mai baka shawaran karka zaƙe akan saika sani ɗin"

   Nunata yayi da ɗan yasha, "zan ramane a inda zaifi miki ciwo, kuma ki sani ban taɓa son abu na rasa ba, ko bakiso dole kiyi soyayya dani"

  Tofar da yawu tayi a k'asa, "Allah ya kiyayemun soyayya da ɗan shaye-shaye" ta juya ta barshi wurin a tsaye yana huci yama kasa maida mata magana, ya watsa ma mutanen wurin kallo ba shiri kowa ya ɓace, ya shige motanshi ya jata a guje.


Hankalinta kwance ta gama lecturenta suka fito tare da Aminiyarta Amrah, hannunta taja suka koma gefe,

   "Faɗamin Rabi'ah meye gaskiyar abinda naji wai kin mari Abdallah"

   "toh meye naga duk kin wani ruɗe kaman wani babban abune ya faru?"

  "haba Rabi'ah, naga hankalinki kwance kaman bakisan halin Abdallah ba"

  "ni mamaki kike bani wallahi, siyasa ne kawai zai nunamun, anma kuɗi kam har ke kinsan Yayana yafi mahaifinshi sosae, don haka duk abunda zaiyi nima zan iya, ban taɓayin abunda nayi dana sani ba"

   "hakane fa, anma ni dai duk a tsorace nake"

   "kinma warware,"


Tun daga bakin gate, ma'aikatan gidan ke kawo mishi gaisuwa anma ko kallo basu isheshi ba, ganin motoci da yawa ya tabbatar mishi Daddyn nashi na a ciki, don haka kai tsaye falon Mai girma mataimakin Governor ya wuce, 

   Zaune yake yana amsa waya, bodyguards nashi zagaye dashi, yana ganin yanayin da Abdallah ya shigo dashi, ba tare da yaa gama ba ya katse wayan.

   "Yadai Son?" cikin sham ƙamshi ya kalli bodyguards ɗin, sannan ya maida kallonshi kan Dad din nashi, alama ya musu da su fito, cikin bin Umarni duk suka fita.

   "waye kuma ya taɓomin kai?"

  Saida ya ƙara ɓata fuska sannan ya fara magana, "Haba Dad! Ni bansan me yasa baka damu da abinda nakeso ba, ba ruwanka dani sai harkan siyasarka kawai"

   "akwai abinda ka taɓa nuna kanaso banyi maka bane?"

   "A'ah kawai dai wannan ne nake tunanin bazan samu ba"

  "babushi, indai Kuɗi da Mulki na iyayin komai a duniya babu abinda zaka nema bazanyi maka ba"

   "I know Dad, but uh should promise me"

   "promise"

  "thank you Dad, i love you"

Sannan ya fara fara'a, jinsa yake wasai kaman yama riga da yaa rama abinda Rabi'ah ta mishi.


Follow me On wattpad @Rerbeeart_sk


©Rabiatu sk msh

[3/17, 19:13] Sisinah: ♡♡MAFARIN SO♡♡

  ♡♡♡♡♡♡♡♡    

     ♡♡♡♡♡

        6-10


©Rabiatu sk mashi

     ®NWA


Rerbeeart_sk @wattpad


www.babymsh.blogspot.com


Hankalinta kwance ta k'arasa gidan, tama manta da wani abunda ya faru tsakaninta da Abdallah,

  Kai tsaye ɗakin ƴaƴan yayan nata ta wuce, en biyune mace da namiji Hayra da Hayran, hankalinsu duk yana kan laptop saboda Game ɗin da suke.

  Tsaye tayi tana kallonsu, da taga dai basusan da shigowanta ba ta musu gyaran murya duk suka juyo a tare, har suna rige-rigen zuwa mata Oyoyo,

   "har an gama Home work ne, aka zauna ana Game?"

  Hayra tace "nidai na gama nawa"

  "ni nama rigata gamawa Auntie"

  "Awwah Gud, bara in dawo nima ayi Game ɗin dani"

   "Awwah Auntie, daman sai cheating yakemun"

   "itace bata iya bafa, tun ɗazu nake kasheta"

  "mortal combat ne? Bara in dawo in muka fara kasheka ko motsi bazaka iya ba"

  

   "Kai kai, waye zai kashemun ɗa?" sai dai suka jiyo muryan Matar yayansu tana hargowa,

   "Momie a Game ne fa" inji Hayrah

  "ke yimun shiru, tun yanzu za'a fara koya muku maganar kisa?"

  Murmushi kawai Rabi'ah tayi, don indai akwai sabo 

ta saba da halin matar yayan nata, "Aunty deejah Sannu da gida"

    "yauwa" tana taɓe baki,

   Ta raɓa ta gefenta kawai ta shige, ɗakinta ta shiga, sai da ta watsa ruwa sannan ta saka kaya mararsa nauyi, ta haye gado saboda gajiyar da takeji.


Rabi'ah kenan, er gatan Yayanta Alhaji Ibraheem Naira, su biyu ne a wurin iyayensu, an mishi aure ba daɗewa Allah ya amshi rayuwansu, shiyasa ya maida ita gidanshi yana kula da ita da karatunta, akwai shaƙuwa sosae da soyayyar juna a tsakaninsu, bai haɗata da kowa ba shiyasa matarshi ma take kishi da ita, shine ya zama uwa da Uba a wurinta, saboda yanda yake tausaya mata da rashin iyayensu.

   Rabi'ah yarinyace mai son gayu da nuna harkar girma, babu abinda tafi so a duniya kaman yayanta, babu kuma abunda tafi tsana kaman soyayya, shiru-shiru ce ga wanda bai santa ba, anma masifaffiyace ga wanda ya taɓota ko kaɗan bata jiran saita kwana.


Tun ranar data mari Abdallah ya daina shiga harkarta, ko a makaranta ma ta daina ganinshi, ita daman bashi gabanta, sai murna takeyi taa koya mishi hankali.

  Suna tare a ɗakin Haiyran tana nuna musu Home work wayanta tayi ringing, tana ganin mai kiran tayi saurin ɗagawa,

   "Hallow sis, ya naji ki shiru fa"

   "maganar me fa?"

     "kin manta zamuje a mana lallen bikin Stylish ne?"

  Tayi dariya, "wallahi fa sis, nina ɗauka zata zo gidane ta mana"

  "idan tayi mana lallen a gida, gyaran jiki da gashin fa?"

    "komai sai tayi mana, ko nawane basai mu biyata ba, kinga ni banson jirannan"

  "kinga ni sai kinzo" ta kashe wayanta,

  A shirye take, mayafi kawai ta ɗauko a ɗaki da mukullin mota ta fito, ɗakin Matar yayanta ta shiga mata sallama,

   "Aunty deejah na tafi wurin lalle"

  Ta taɓe baki tana kallon gefe, "aifa, abunda kika iya kenan, kullum kina hanyar makaranta, in kun dawo kuma babu zama sai shegen yawo, shi kuma ya saka miki ido"

   Murmushi tayi murya k'asa-k'asa tace, "amfanin ilmin kenan ai, babu mai sanin daɗin karatu sai wanda yayishi" (ita daman deejah iyakanta secondry, ta mak'alewa Yayan Rabi'ah saida akai auren, da yake shima ba baya ba wurin kyau da gayu, ga kuma Naira)


  "me kikace, daman ba tun yau ba nasan kin gama rainani"

  "bance komai ba" ta fito ta biyo bayanta, su Hayra na tsaye suna jiran fitowarta,

   "Auntie nima za'amun lallen" inji Hayra

  Hayran yace "nima zan raka ki Auntie"

  "tohh kuje ku shirya"

  "bazasu je ba, ku wuce ɗakinku binto ta kunna muku kallo" ta daka musu tsawa, ba shiri suka wuce. 

  Rabi'ah ta ɗaga kafaɗa, ta juya tayi tafiyanta.


©Rabiatu sk msh

[3/17, 19:13] Sisinah: ♡♡MAFARIN SO♡♡

  ♡♡♡♡♡♡♡♡    

     ♡♡♡♡♡

        11-15


©Rabiatu sk mashi

     ®NWA


Rerbeeart_sk @wattpad


www.babymsh.blogspot.com


  A hankali take tafiya, ta kunna wak'an Zara larsson (So Good) ta k'ure ƙaran sosai tana bin waƙan cikin jin daɗi, tana cikin tafiya wayanta ta sake ringing, ta duba Zahran dai ce, ba tare da taa rage k'aran wak'an ba ta ɗaga da yake hanyan ba mutane sosae.

   "Hey sis" sai magana take bataji sannan ta saka hannu zata rage k'aran,

   "ke kinga nama kusan gidan, bara na k'ara taka motan" ta faɗi tana k'ara gudu ba tare da tana kallon gabanta ba, sai dai taji an take wani wawan burki, ae batasan sanda ta saki wayan ba tayi gefe da motanta saura kaɗan su buga ma juna,

  Sunyi tsaye da motan sai maida numfashi take tayi matuƙar tsorata, saida ta gama dawowa hayyacinta taga shiru mai motan yaƙi ya janye gashi dole saiya matsar da motar zata wuce.

  Sai cika take ranta yayi matuƙar ɓaci, gashi bata ganin ko waye a cikin motan an rufeta da (tin tet), saida taja tsoki cikin ɓacin rai ta fara matsa horn, anma ko gezau baiyi ba, ranta ya k'ara ɓaci,

  Kusan fiye da 30mnts suka kwashe a haka, gashi jin kanta ya hanata fita ta mishi magana, tana ganin kiran Zahra na shigowa taƙi ta ɗauka, saima ta jefar da wayar cikin ɓacin rai tace,

   "anma fasa lallen, bazanyi ba" ta kwantar da kujera tana karkaɗa kafa, awa huɗu suka kwashe a haka, saida taga magriba na niyyar mata a wurin, da alama kuma idan ta biyewa mai motan sai su kwana a wurin, ta buɗe mota kaman zata fita, kuma sai ta fasa, tayi haka yakai sau biyar sannan dai ta fita, 

  Dai dai motan nashi taje, sannan ta ƙwankwasa, tana riƙe da ƙugu taa juyar da fuskarta donma karsu haɗa ido damai motan ta sassauta daga masifan data rik'o,

   

   Tana jin an buɗe motan daddaɗan ƙamshin turaren da taji ne ya tabbatar mata da fitowanshi, sannan ta jiyo da fuskarta cike da masifa,

   "wannan wane irin wulak'an.....?" kasa ƙarasawa tayi saboda cin karo da tayi da kyakkyawar fuskarshi mai cike da ƙwarjini, ɗauke da kyakkyawan murmushin daya k'arawa fuskarshi kyau, 

  "Handsome" ta faɗa a ranta,

   Ɗaga mata gira yayi cikin wani irin salo daya k'ara fito da haɗuwanshi, ya nuna mata hannu alaman, "Yadai?"

   Da sauri ta girgiza kai, cikin ranta tace “A'ah Rabi'ah ba abinda ya fito dake ba kenan” ta k'ara haɗe rai, a fili tace,

  "miye yasa bazaka matsar da motanka?"

   "bakice bane"

 Lallaima mutumin nan ya gama raina mata hankali, 

  "yanzu nace, yi sauri matsar mun da motannan" tana kaɗa hannu,

  "Awk" kawai yace, sannan ya koma zai shiga motan, 

  Haushi yazo mata iyakan wuya yanda yake maida mata magana kai tsaye, yatsunta biyu ta sake kaɗa mishi, ya juyo suka haɗa ido,

   "waye zai bani hak'urin asarar daka kusa yimin?" ba tare da yayi magana ba yake kallonta yana neman k'arin bayani, kaman ta haɗiyi zuciya ta huta,

   "Motana daka kusan bugawa"

   "na bugane?"

  "sai kaa buga zaka bada hak'uri kenan"

   "Yi hak'uri" ya koma zai shiga motan, ta sake mishi magana,

   "hak'uri kawai? Kasan ko motan nawace da zakana bani hak'uri cikin rashin kulawa"

   Murmushi yayi, "masu kuɗi babu ruwansu da ko nawa ne suka siya abu, koda ya lalace zasu siya wani ne" ya shige motanshi ya barta nan tsaye baki buɗe,


  Cikin jin haushi ta kwashi k'asa ta watsa ma motanshi data riga ta wuce ma, "Na tsaneka" ta faɗa, jin tsanarshi take fiye da duk wani abu dake duniyar nan, don ko Abdallah bata tsana haka ba, gani take tsanar ma matsayine da ita, kuma idan ka tsani mutum dole ne zai tsaya maka a rai, anma Abdallah baida wannan matsayin da zata tsaneshi, ko kaɗan bai dameta ba.

   Anma wannan tunda take ba'a taɓa ɓata mata rai irin haka ba, lallai duk sanda ta k'ara ganinshi koda a mafarkine sai ya raina kanshi.....


Domin samun Postn cikin lokaci, maza garzaya kuyi liking page ɗina a facebook

@Rabiatu sk novels

  Ko kuma kuyi follown ta wattpad, @Rerbeeart_sk, plz dont forget to Vote©Rabiatu sk msh

[3/17, 19:14] Sisinah: ♡♡MAFARIN SO♡♡

  ♡♡♡♡♡♡♡♡    

     ♡♡♡♡♡

       16-20


©Rabiatu sk mashi

     ®NWA


Rerbeeart_sk @wattpad


Ina kishiyar wani? Nima ga tawa SADEEY S ADAM (SaNaz) mai kirki da halin girma, ga hak'uri da yawan fara'a, tabbas kishiyatah dabance a cikin kishiyoyi, kuma qawahce da babu kamarta, bansan ta inda zan fara gode miki ba, akan littafin da kika sadaukarmun, TUN RANAR BIRTHDAY ƊINTA, nayi matuk'ar murna da ganin wannan littafi, har bansan ta yanda zan bayyana miki farin ciki na ba, ko kunsan littafinta na HUZNUL HAYAT ma nita sadaukar mawa? Tabbas tsakanina dake yafi k'arfin godia, sai dai addu'ar Allah yabar zumunci da kuma Zaman tare, Allah ya k'ara basira da ɗaukaka, ya kareki da dukkan wani sharri, ina rok'on masoyana a duk inda suke, nikam koda baku karanta wannan page ɗin ba plz ku tayani da yima kishiyata addu'ah, Allah ya saka mata da mafificin Alkhairi😍 #One luv


www.babymsh.blogspot.com


Lokacin data isa gida har an gama Sallahn Magrib, idanunta cike da ɓacin rai ta shiga gidan, a babban falo taci karo da Yayanta su Hayrah sun zagayeshi.

    Idanunshi na kan k'ofar da zata shigo, nan da nan tayi saurin kauda damuwarta, ta faɗaɗa fara'arta da gudu ta tareshi.

   "Oyoyo Yayana" sai kuma ta ɗan ɓata rai ta juya gefe,

   "ni namayi fushi, kawai koma ka faɗamun yau zaka dawo, kuma fa ko da safe munyi waya"

  Murmushi yayi yana ɗago da fuskanta, "bara inga k'anwar dake fushi da yayanta"

    Dariya tayi kawai, "Baki duba wayanki ba halan? Tun ɗazu nake kiranki harna daina k'irga missed calls yanzu haka zaman jiranki nake anan"

  Sai sannan ma ta tuna da wayanta, batasan ma inda ta shige ba, "Ayyah! Sorry yayana, U did'nt told me yau zaka zaka dawone, da bazan fita ba"

    "kawai naso nayi Suprising naki ne"


Fitowan Aunty Deejah ne ya katse musu firan, "ka ganta nan ba, kullum ina faɗa maka tana fita gantalinta in baka k'asar anma kak'i ka yarda, yau kaa gani da idonka ba"

  Cikin takaici take kallonta, "Aunty deejah gantali kuma?"

   "eeh gantali, idan ba can ba ina kikaje?"

   "na taɓa fita ban faɗa miki ba? Yauma aena faɗa miki inda naje"

   "kincemun zakije lalle dai, idan da gaskene ina lallen?"

  Cikin bak'ar magana tace "tun a gantalin ya goge"

  "ni zaki faɗama bak'ar magana? Kana jinta take maidamun magana son ranta?"

   

  Ɗaga kanshi yayi tana kallonta, "kinfi kowa sanin banson Hayaniya, daga dawowana zakimun tsaye akai, ko tarbar kirki ban samu daga wurinki ba"

   "shikenan, daman ya za'ayi tayi laifi wurinka? Sai kacemun gatanan in ringa kula da ita, toh ni daga yau na fidda hannuna a kanta, don karma ta lalace a ga laifina"

  "Subhanallahi, Allah ma ya kyauta mata da lalacewa" bata tsaya saurarenshi ba ta juya ɗakinta tana kumburi,

    Girgiza kai yayi sannan ya juyar da kanshi daga binta da kallon da yayi, murmushi Rabi'ah tayi, "Bara nayi Sallah Yayana, me za'a girka maka?"

   "haba nasan kin gaji da yawa, zan fita inci k'anwata"

  "kwana nawa kana cin na wajen? Nidai faɗamun"

  "komai k'anwata ta girkamun zanci, anma fa mai sauk'i"

  "an gama Yayana" ta wuce ɗakinta tayi Sallah.


Tana idar da Sallah ta shiga kitchen ɗin falon daman ita tafi amfani dashi indai yayanta na gari, daman Deejah babu ruwanta da cinshi, ita dai in en aiki sun girka taci kawai, kitchen ɗin tsaf da yake kullum sai an gyarashi, ta ɗauka tukunya ta ɗauraye nan da nan ta ɗaura girki, Cocunut rice ta girka mishi, da miyan kaji sai k'amshi ke tashi, ta markaɗa fruits ta mishi drink dashi, ta ɗauka a tire sai ɗakinshi, ta shiga bayan ya amsa mata sallama,

   Tana ajewa ta kama hannunsu Hayran, "ku taso muje muci namu, kun cika Daddy da surutu"

   "ina zakuje? Ku zaunanan muci tare"

   "A'ah Yayana, ka dawo da gajia, ka huta sai da safe"

  Yayi murmushi "tohm Allah ya kaimu"

   "Ameen"

 Suma suka mishi "Good nyt" sannan suka tafi. Sai da ta tabbatar sunyi Sallah, sannan ta raka kowannensu ɗakinshi, ta kunna musu kallon Tom and Jerry,

   "idan anji barci a kashe, kar kuma a manta da Addu'a"

  "tohm Auntie" itama ta dawo ta wuce ɗakinta, 

  Tana kwanciya kaman a T.V, hotanshi ya ringa dawo mata, yanda yake mata kyakkyawan murmushinshi, cikin Izzah da nuna isa, da yanda yake bata amsa da idanu kawai ko da hannu, ta ringa jan tsoki kawai tana juye-juye, tsawon lokaci sannan barci ya ɗauketa.


  Yayan nata na gama cin girkin, yayi shirin barci, bai zame ko ina ba sai ɗakin Deejah, ya ɗan k'wank'wasa shiru ba magana yama ɗauka tayi barci, sai da ya murɗa k'ofan ya shiga, can ya hangota gefen gado ta bashi baya, shi sai lokacin ma ya tuna da wai laifi aka mata,

  Girgiza kai yayi, Deejah ko rigima, hakanan ya k'arasa kutsa kanshi cikin ɗaki yana tunanin ta inda zai fara rarrashi.


©Rabiatu sk msh

[3/17, 19:14] Sisinah: ♡♡MAFARIN SO♡♡

  ♡♡♡♡♡♡♡♡    

     ♡♡♡♡♡

        21-25


©Rabiatu sk mashi

     ®NWA


Rerbeeart_sk @wattpad


SO NE MAFARIN K'AUNA, inji (Nura M Inuwa), niko nace Shi SOn miye MAFARIN shi??


www.babymsh.blogspot.com


Washe gari tana duba wayanta, misscalls 99+, da messages ɗin Zahra duk dai tana mata mitar rashin zuwan da tayi ne, kaɗan kaɗan zata daki Zuciyanta, saboda anan ne takejin Zafin abunda ya mata, koda second ɗaya ta kasa mantawa dashi, kyakkyawan murmushinshi sai yawo yake mata a k'walwa, 

   "I hate him" ta faɗa da k'arfi, ko breakfast ta kasayi har kusan 1pm. Sai da yayanta yayi kiranta sannan ta fito daga ɗakinta ta nufi sashenshi,

  Bayan sun gaisa ya nuna mata wata haɗaɗɗiyar k'atuwar jikka mai kyau,

   "ko kinma manta da sak'onki ne?"

   "Ina fa? Kawai nabar Yayana ya gama hutawa ne" ta fara buɗa jikkar cikin farin ciki.

   "Wow Yayana duk wannan nawane? gaskia Yayana ngde...."

   "Shhht!! Idan ban miki ba wazan mawa? Duk duniya kina da wanda ya fini ne?" murmushi tayi, taɗanyi hugging nashi,

   "Allah yabarmun kai Yayana"

  Ta ɗauka tsarabanta, a bakin k'ofa suka haɗu da Deejah sai shan k'anshi take, tana duban jikkan hannunta taja tsoki, murmushi kawai Rabi'ah ta mayar mata,

   "Aunty deejah An tashi lafiya??"

  "eeeh" kawai tace da ita, bata k'ara cewa komai ba itama ta wuce.

  Kayan da zata saka wurin Dinner ne na yau, anko ne komai kalan da za'a saka, anma nata is more expensive, sai da ya haɗo mata da er k'aramar jikka mai ɗaukan ido, da takalminsu da agogonsu mai haɗe da necklace da earrings nasu, komai dai da zata buk'ata masu tsada sosae.

   

A ɗakin Yayanta, Aunty deejah ce ta haɗe ranta wuri ɗaya sai cika take, da yayi kaman ya mata banza don yasan k'orafinta bai wuce kan Rabi'ah, sai kuma ya ɗago kai,

   "Yadai deejahna na ganki cikin farin ciki?"

   "na maka kama da wadda take farin ciki ne?"

   Saida yayi k'asa da murya sannan yace "toh aike kullum ma haka kike"

   "me kace? Yanzu idan nayi magana kace na cika tsegumi, anma kuma ko kaɗan kasan baka kyautamun"

  "Yau kuma me nayi?"

    "tun jiya nace ka nunamun tsaraban Rabi'ah kaqi, sai yanzu ka bata saboda kasan nata yafi nawa ko?"

   "Cikin dare ko hutawa bazaki barni nayi ba zanta faman nuna miki tsaraba? Saboda Allah deejah miye bana miki? Anma gaba ɗaya kin saka idonki akan er k'anwarki"

   "Naji babu abunda bakamun, anma ai kana banbantani da ita"

  "itafa k'anwatahce, ke kuma matata, kinga kuwa akwai banbanci sosae a tsakaninku, kina dasu Umma da Abba, kina dasu Hayrah da Hayran, gani nima naki ne, anma itafa Rabi'ah ni kaɗai take da, meyasa zamu barta tayi kukan maraici?"

   "nidai koma......" ɗaga mata hannu yayi, "don Allah ya isa haka Deejah, ki barni na k'arasa aikin lissafinnan gobe nake son fara fita aiki"

   "kenanma daga zuwa na harna isheka?" dafe kanshi kawai yayi, yama rasa mezaice mata. Ko kaɗan baison Hayani da yawan magana, anma deejah abunda tafi iyawa kenan fiye da kula da miji.


  Waya suke da Amrah tana bata labarin guy ɗin data gani, ita kam sai dariya take mata, 

    "idan kin gama dariyan kinmun waya"

   "Srry dear, na daina" 

  "ke ɗince wlhy, hw many times shld i tell uh dis? Dnt start a fight dat uh ddnt knw hw it will end"

   "yama k'are insha Allah, coz all i wish is not to saw him again"

    "da alama bakinki na faɗin abinda ba shine a zuciyarki ba"

  "har a zuciyana hakanne"

   "nikam daman nice na ganshi, don yanda kike faɗan haɗuwarshi..."

   "da kinsha kayan haushi kam, don ɗan rainin hankaline na qarshe" suna gama waya, ta koma barcinta, ba ita tashi ba saida aka kira la'asar.


  Da wuri ta shirya tafiya wurin dinner tun duhu baiyi ba, sai da tayi Sallama ya amsa mata sannan ta shiga, sai kuma tayi baya zata fito.

   "Yadai?"

  "ba komai naga kana aiki ne"

     "idan ina aiki ba'amun bankwana?"

   "Sorry Yaya, na tafi"

  "haka zaki tafi babu kuɗin lik'o?"

   "ba komai Yaya, akwai kuɗi wurina"

  "idan ya qare fa? Kinga ni zoki amsa" ta shiga tana murmushi.

  Bandir na 1k ya bata guda biyar, ta amshe ta saka jikka, "sun isa ko a k'aro?"

  "sunmayi Yawa Yaya, kaga jikkar ma ta cika sai dai na rik'e wayoyina a hannu, Allah dai ya k'ara buɗi"

   "Ameen Ya rabbi, a dawo lafiya"

  Tayi tsaye tana gyara zaman mayafinta, ya ɗago yana murmushi yasan akwai magana,

   "ehheen!"

  "daman keys ɗin motarnan"

   "ba kinsan inda suke ba?"

  "wannan bak'ar fa"

  "tohm ki ɗauka mana"

    "sabuwarnan fa Yaya"

  "ita ɗin, idan kinji daɗinta ki rik'e kawai"

   "Da gaske Yaya? Wayyo daɗi," ta faɗa jikinshi tana murna, "thank uh so much Yaya" ya ɓata rai,

   "bana hana godiyarnan ba?"

   "Sorry broz, saina dawo"

  "tohm a dawo lafiya, kar dai kiyi dare sosai"

   "Insha Allah, bye" ta biya tama su hayran Sallama, sannan ta wuce gidansu Zahra, a can ta iske Amra ana musu makeup, ana gamawa itama aka mata, anan suka shirya, wurin 10 suka wuce wurin dinner kai tsaye.


  Suna isa wurin kallo ya koma sama, don kowacce ba k'aramin haɗuwa tayi ba, ga wani taku da suke a tare na burgewa, suna sanye da pink ɗin riga, da mini-skirt baqi, ankon da kowacce ta saka wurin, sannan suka zubo dogon gashinsu bak'i mai santsi, sai Zarah da tayi k'ananun kalba mai kyau, ba k'aramin haɗewa sukai ba, wurin da aka bari musanman donsu suka zauna, daman already an fara suka shigo.

   Ko kaɗan Rabi'ah bata ɗaga fuskanta ta kalli inda su Zahra keta firan wani haɗaɗɗen guy ba, da alaman duk samarin wurin babu wanda ya haska kamanshi, shine Babban abokin ango zaune a hightable, ita kam haushin wanda ya dameta kawai ya isheta,

   Sama-sama take jiyo daddaɗar muryar Abokin Ango yanda yake bada tarihin Ango cikin yaren Hindi, kaman ba indiyen Asali, cikin taushi yake magana sosae ya burge mutanen wurin, sai da ya gama sannan yayi da turanci yanda kowa zai fahimta, cikin barkwanci yake magana.

  Tananan tana tunani har aka kira Amarya da Angonta su taka, sannan aka kira k'awayenta da nashi suma suyi rawan, Amrah sarkin son rawa kusan ta riga kowa mik'ewa, Rabi'ah tace "nidai liƙi kawai zanyi" suka jera a tare zuwa filin.

  Taja tsoki, "kunsan da zanga mutuminnan a wurinnan zan shak'eshine kawai in huta da haushinshi"

   Har suna haɗa baki "wa kenan?" su sunma mnta

  "guy ɗin dana baku labari mana"

   "da alama ya dameki da yawa" inji Amrah

   "bazaki gane yanda nakejin tsanarshi bne"

   Zahra tace  "want another reason to hate him?" kafin ta maida ma Zahra amsa sai dai taji ta taka abu suna dai dai isa filin rawan, ta zame ta tafi suuuu tana niyyar faɗuwa sai dai taji tayi karo da mutum, da sauri ya rik'ota ta faɗa k'irjinshi.

  Yanayi biyu ne ya ziyarceta, na farko faɗuwar gaban ta kusa faɗuwa, na biyu kuma k'irjinta ne ya buga, wani irin yanayi da bata taɓaji ba sanadiyyar haɗuwan jikinsu, kunya ta sanya ta kasa ɗaga kai ta kalleshi, tayi kwance saman lallausan k'irjinshi, tama manta duniyar da take.

   Tafin da aka farayi a wurinne ya dawo da ita, da sauri ta ɗaga kai suka haɗa ido, ta waro dukkan idanunta cikin kaɗuwa da mamakin ganin kowaye,

    "kaine?" ya ɗaga mata girarshi, cikin salon dayake saurin rikitata.

   Ko waye Rabi'ah ta gani??


©Rabiatu sk msh

[3/17, 19:15] Sisinah: ♡♡MAFARIN SO♡♡

  ♡♡♡♡♡♡♡♡    

     ♡♡♡♡♡

        26-30


©Rabiatu sk mashi

     ®NWA


Rerbeeart_sk @wattpad 


Lokuta da dama Abota (friendship) ke zama MAFARIN SO, ta wani ɓangaren kuma, Shaƙuwah ne kesa a fara SOn juna, Anmafa ƘIYAYYA ma tana rikiɗewa ta koma SOYAYYA, kaman yanda Kishiyah ta faɗa, ko a ciki menene nasu MAFARIN SOn?🤔


www.babymsh.blogspot.com


Sai kallonshi take ta kasa ko k'ifta ido, guy ɗinnan ne da suka haɗu zataje wurin lalle, guy ɗin da take iƙirarin duk dunia babu wanda ta tsana kamanshi, yau sai gata kwance male-male a ƙirjinshi, wannan wanne irin baƙar rana ne take gani?.

   A hankali yaɗan hura mata iska a idonta, ta dawo daga tunanin da take har lokacin idanunta na kanshi, da idanunshi ya kalla inda ta rirriƙeshi da hannu ta kasa saki, sannan ya sake kallonta, alaman yana mata tuni da riƙon data mishi kenan.

  Da sauri ta sakeshi tana gyara tsayuwarta, ta juya gaba ɗaya mutanen wuri su suke kallo, ɗan matsowa yayi dab da ita, ya raɗa mata a kunne,

   "Kinsan kuwa ko rigan nawa ne kika cukuikuye?", ta buɗe baki zatai magana ya dakatar da ita, a hankali ya sake furta mata wata maganar, da sauri ta tureshi yana dariya, juyawa tayi tabar hall ɗin ko su Zahra batai ma bankwana ba,

   Koda ta isa gidama, ɗakinta kawai ta wuce, ta rufe wayanta ta jefar ta kwanta ko kaya bata canja ba, tunani ta ringayi kala-kala, haushinshi da tsanarshi na k'ara yawa a zuciyarta, wata zuciyar tace 'taimakonki fa yayi, da ƙasa kika faɗa da kinji jiki', taja tsoki, 'aeni yamafimun in faɗi k'asan da rikon da yamun' haka dai ita kaɗai ta ringa zancen zuci, ranar kam don barci na ɓarawo ne kawai ya iya saceta,


Daman bata kwana da niyyar ƙara zuwa wani Shiri na bikin ba, sai kai Amarya kawai, don haka yau kodata farka, ƙin fitowa tayi, daman taga text ɗin yayanta ya tafi aiki, tananan ɗaki sai dai su Hayran suka shigo tayata fira, da taga zasu damewa ta kunna musu tarihi suna kallo ta shigewanta, 

   Tana cikin tunani sai ga Hayrah ta shigo ɗakin, sai dai taji an taɓata har saida ta firgita, "Aunty Rabi'ah me akai miki?"

  Murmushi tayi, "Ba komai Hayrah me kika gani?"

   "Duk yau baki fita ba, kuma baki zauna munyi kallo tare ba"

  "Ai nace ku fara zanzo"

  "Um-um nidai Auntie kallon babu daɗi ba bakinan"

  Hayran ya shigo da gudu, "Auntie ya ƙare, zamuje siyen chocolate ɗin?"

   "A'ah ku bari sai gobe"

  "gobe fa akwai tahfiz, please Auntie, please, please!!!"

   "Naji toh! Kuje ku shirya" da gudu suka fita suna Murna, sannan ta tashi itama ta shirya, tana gamawa sai gasu,

    "Kun faɗa ma Momie?"

  "A'ah, zata hanamu ne"

    "bazata hanaku ba, muje a faɗa mata" ta kamo hannunsu suka fito, suna ganin tayi hanyar bangaren Aunty deejah duk suka saki hannunta, suka rigata fita wurin motar"

   Ita kaɗai ta shiga, "Auntie deejah mun fita dasu Hayran Shopping"

   "wanne irin shopping kuma? Salon dai ki koya musu yawo irin naki da kullum baki zaman gida, toh babu inda zasuje komai suna dashi, inma suna buƙata zanyi wayane a kawo musu"

   "haba Auntie ai sun ɗan fita suga gari, daga makaranta sai makaranta, kowanne yaro fa yanason wasa, kuma idan sun fitan zasuji daɗi"

   "oho! Nace dai bazasuje dake ba"

  Taɓe baki tayi, "saimun dawo" ta juya ta barta.

  Ta ƙwala murya tana faɗin, "awh! Tafiyar zakiyi dasu? Ni daga yau in zaki fita gantalinki ƙarama ki daina faɗamun, tunda ko nayi magana ba jina kike ba, kuma bari yayan naki ya dawo, nidai na gaji da wannan abu" ta ringa faɗa ita kaɗai cikin gida.

 

   Wuraren wasannin yara da yawa ta kaisu, ita kanta ta ɗanji sauƙi a zuciyarta, sai da sukasha yawo sosae, Yamma liƙis sukaje wani babban Shopping mall a garin katsinar, siyayyan kayan zaƙi sukayi sosai masu tsada, tana riƙe da ledojin a hannunta suka fito,

  Sun kusa fita daga wurin, Hayrah yace "Auntie kawo na riƙe nima"

   "A'ah, ae babu nauyi" ta duƙa tana mishi magana, ɗagowan da zatayi sai dai taji tayi karo da mutum, gaba ɗaya ledojin hannunta sun faɗi, komai ya zube.


  Ɗagowa tayi da niyyar fara faɗa, suka ƙara haɗa ido da wannan guy ɗin dai data tsana wanda ko sunanshi bata sani ba, girgiza kai yayi yana kallonta, yau ko murmushin bai tsaya yi mata ba sai dai kallon mamakin daya bita dashi,

   "kedai baki taɓa duba gabanki idan kina tafiya?"

   "ni dakai dai, ai kaine ya kamata kana kaucewa"

  Ta kamo hannun Hayran daya duƙa yana tsince sweets ɗin, ta kamo hannunshi, "ka barsu anan ka tashi mu tafi"

   Ya miƙe, Guy ɗinma ya riƙo hannunshi harta juya zata tafi ta tsaya, 

   "sake mishi hannu"

  Ɗaga kafaɗa yayi, sannan ya girgiza kai, ta ƙara jan hannun Hayran zata fizgeshi ta kasa, ta juyo tana hararanshi, ya sakar mata murmushi yana ɗaga gira, ya cema Hayran,

  "Abokinah muje nima ka rakani" suka wuce, ta bisu da harara, sannan taja hannun Hayrah suka bar wurin a zuciye.


Sun daɗe a mota tana jiran Hayran, harta fara ƙosawa da jiran duk ranta ya gama ɓaci, sai shawaran ta tafi take, wata zuciyar na hanata, idan ta koma gida babu Hayran kam tasan ko ya dawo, Aunty deejah sai tayi sati tana aikin masifa, ba tsoranta takeji ba, anma bazata ita barishi ba, tananan zaune a mota sai saƙar zuciyah take, ta hangosu yana riƙe da hannunshi, suna labari suna dariya harda tafawa.

  Siyayya yayima Hayran sosae, harma tafi wadda sukayi a farko, ya kawoshi har wurin motar ya buɗe mishi ya shiga ya rufe, su Rabi'ah sai kumburi take,

    Ta tada motan zata tafi, "Sai Anjima Auntie Rabi'ah" ko kallon inda yake batayi ba, ta fizgi motan ta tafi,

    Tana tafiya Hayran sai bata labarinshi yake, wani irin tsawa ta daka mishi har saida ya tsorata, don tunda suke ko faɗa bata taɓa musu ba,

   "na tambayeka labarinshi ne? Watau bakajin magana ta sai tashi ko, nace karka bishi harda juyawa da binshi"

   Kaman zaiyi kuka yace "yi haƙuri Auntie, ke kikace muna yin abunda manyanmu sukace"

   "kasanshi ne? Idan ya sayar dakai fa? Kuma wayace ma ka faɗa mishi sunana?"

  Duk ya tsure da yaji tace zai iya siyar dashi, "Tambayana yayi, kuma naga yana da kirki....."

   "kaimun shiru nace" nan ya kame bakinshi yayi shiru, sai da suka kusan ƙarasawa gidan yace "Anma dai Auntie ba mai siyar da mutane bane ko? Kirkine dashi sai fira yakemun"

    "ai wayau yake makane, yanda zaiji daɗin kaika a cire kan" aifa nan take idanunshi har sun kawo ƙwalla, Hayrah ma jikinta har ɓari yake ta rirriƙe ɗan uwanta,

  Ita kam Rabi'ah fuska tayi, duk da sunso su bata dariya, anma ta dake don guy ɗinnan ya gama bata haushi.

  Da suka isa gidan, suka biyota da ledojin siyayyan har ɗakinta,

   "Auntie ga kayannan"

 "kuna so kuci ku ɓace ko? Ku kaima Baba mai gadi, in kukaci babu ruwana"

  "nidai bazanci komai ba Auntie"

  "nima ba ruwana" suka juya da kayan, itama bin kayan tayi da harara, 'ko wayace yana bukatar siyayyanshi?'


©Rabiatu sk msh

[3/17, 19:16] Sisinah: ♡♡MAFARIN SO♡♡

  ♡♡♡♡♡♡♡♡    

     ♡♡♡♡♡

        36-40


©Rabiatu sk mashi

     ®NWA

And


©Ruksad

     ®EWF


Rerbeeart_sk @wattpad


www.babymsh.blogspot.com


   Rabi'ah ce zaune abakin gadonta sai cika take tana batsewa, tama rasa wane irin wulakanci ne guy dinnan ya mata, ita zaya maidawa siyayyar underwears, ina ma yanzu ta fita ta ganshi aida tamasa wulakancin kare dangi, 

  Wayar tace ta ɗau ruri alamun kira yashigo tana dubawa taga Amrah ce, 

  "Hello" tafada murya ba alamar walwalah, 

  Amrah tace "Haba wai miyasa koda yaushe kikeson ɓata mana lokaci yanzu gashi ke muke jira kuma kinsan zuwa anjima zamu tafi kai amarya," 

   "Kibarni kawai Bestie yau irin ɓacin ran danake ciki tunda aka haifeni ban taɓa shiga irinshi ba, banajin zan iya zuwa koda ƙofar gida ne,"

   "Miya faru kawata" inji Amrah

  Rabi'ah tace, "menene ma bai faruba? kinsan gayen nan rashin mutuncin da ya Shukamin kuwa,?"

   "kekam a ina kika ƙara ganinshi? Naga jiya bakizo kamu ba"

   "a shopping Mall mana, wai ni zaya sayawa Underwears," 

  Daria sosai takama Amrah, Anma ta dake saboda sanin halin ƙawar tata, tace 

  "har yaushe Soyayyar ku tayi girman da zai saya mikin irin wanan kayan kuma?"


Wani baƙin ciki ne yadaki zuciyar Rabi'ah "Siya nayi, mukayi karo komai ya zube nabar mishi na tafi, shine fa ya riƙe Hayran saida ya sake mana wani siyayyan"

   "kema da laifinki, tunda kinsan akwaisu cikin siyayyan ai da kosu kaɗaine kin ɗauke"

  "Hmm ni ɓacin rai ma yaa barni na tuna?"

  Rabi'ah ta kara nisawa sannan tace "Natsane shi, bana sonshi, da zanganshi dana nuna masa kuskuransa na farko a rayuwa," kamar zautatta take fadin wadan nan kalaman,

  Amrah tace, "kiyi haƙuri kawai kizo muje kai amarya, kinsan bamu kyautawa stylish ba idan bamuje ba" 

  Sai a lokacin Rabi'ah ta tuna da taganshi wajen dinner, "Yauwa ƙawata ganinan zuwa"

  Amrah cewa tayi "Allah ya kawoki lafiya"


Toilet Rabi'ah ta shiga tayi wanka ta ɗauro Alwala tana fitowa da ɗauko sallaya da kayan Sallarta ta gabatar da Sallan La'asar, sannan ta dauko lallausar Man shafawarta ta shafa, Rabi'ah akwai son gayu, wata tsadadiyar Material ta ɗauko kalar Golden da maroon wacce ɗinkinta yayi masifar kyau da tsaruwa, tasaka ɗinki yayi ɗas ajikinta kamar dan ita, yar ƙaramar sarƙar zinari tasaka da ɗan kunne, da awarwaro, ta ciro gale golden da takalmi golden, ta ajiye gefen gadon ta, ta nufi inda kayan shafe shafenta suke hoda da kwalli da lip's kawai tasaka, sannan ta dauko ɗan kwalinta ta dauran naɗin zamani, Har takusa mantawa da ɗaukar fansa zata je, Turarenta mai ƙamshi ta feshe jikinta dashi.


Tayi kyau sosai, ta fito ta nufi ɗakin Yayanta,    

  "Hayran! Hayrah!!" kuna ina ta faɗa

  "gamu anan" suka fito daga inda suka buya suna daria , Hayrah tace

  "kinyi kyau Auntie" Hayran yace "Eeh wallahi Auntie,"

  Kama Hannunsu tayi, "Kuzo muje wajen daddy in mishi bankwana zanje kai amarya"

   "To Auntie" suka faɗa a tare,

  Ta jasu zuwa hanyar ɗakin daddynsu Hayrah,


  Da sallama suka shiga, Ya Amsa sallamar sannan ya ajiye wayar shi akan ɗan karamin table ɗin da ke cikin palon da Alama waya ya gama 

  Rabi'ah tace "ina wuni yayana"

    "lafiya lau kanwar ina zuwa haka?"

  "Kaa manta kai Amaryan da mukayi magana"

  "Ohh! Inane na za'a kai amaryar?"

   Rabi'ah tace "A kano ne Yaya,"

  "toh kar kiyi dare sosai kinji ƙanwata, kinga ba kwana zaki ba dakin ga gidan ki dawo da wuri"

  "tohh Yaya insha Allah"

    "Kuɗi fa? Nawa zasu isheki zuba Mai?"

   "Ina da mai, kuɗin liƙin rannan ma banyi amfani dasu ba"

  "Tohm shikenan, sai ki canja mota tunda tafiya zaki mai nisa," 

  Daman tunda Aunty deejah taga tayi Hanyar ɗakin yayanta ta biyota da sauri, daga inda take laɓe ta fito tace "ka bata sabuwar mota mana taje tayi karyar data saba cikin ƙawaye sukuwa suna binta kamar wata sarauniya," 

  Daria ce takama Rabi'ah anma ta dake, ta cewa Yayanta ya musu Pictures ita da su Hayrah, wayar shi ya ɗauko ya dinga daukarsu photo sunyi kyau sosai sannan suka dauka ita da Yayanta, Anty deejah kuwa ta kawo iyah wuya,

  A haka ta barsu ta wuce gidansu Amrah.


©Rabiatu sk msh

©Ruksad Mum Siyama

[3/17, 19:16] Sisinah: ♡♡MAFARIN SO♡♡

  ♡♡♡♡♡♡♡♡    

     ♡♡♡♡♡

        31-35


©Rabiatu sk mashi

     ®NWA

And


©Ruksad

     ®EWF


 


Yar gatana taken naki nada banne kin wuce kawa kin wuce aminiya kin zama yar uwa kuma gudan jini *My Amnoor Allah ya kara mana donkon zumunci da kaunar juna😘*

  

   Cikin jin haushi tace, "ko wayace yana bukatar siyayyanshi?'

Ta koma kan gado ta kwanta cike da takaicin wannan gayen aranta tace "dama wanka masa mari nayi"

   Hayran ne tsaye a bakin kofar dakin Rabi'ah, ya jinginar da ledojin jikin bango dan a tsorace yake da kayan, tunda Antynshi tace za'a cire masa kai,

Anty deejah ce ta fito neman Hayran din, dan taga Hayrah adakinsu tana Game, tana hangoshi tace, "kai tsayuwar me kake anan? "

  "Bakomi", yabata amsa 

"To muje ka kiyi wanka ka kwanta" 

  "To momie ya fada yana kokarin kare ledojin dan kar tagani,"

 Bata kulah dasu ba tayi gaba abinta, shima Hayran ya tafi dakinsu,


  Washe Rabi'ah ta fito zata shiga kitchen saboda yunwar da takeji, gashi kuma tanason yima yayanta girki, Abakin kofa taci karo da kayan da dan rainin hankalin guy ɗinnan nan ya bama Hayran Sunan da ta raɗa masa kenan, a zuciya tace 'kenan Hayran bai kaiwa Baba megadi wannan tarkacen ba ko,' ta ƙwafa ta wuce,

  Kitchen din ta nufa tabar kayan nan A inda suke, kunun alkama tayi, da ƙosan dankalin turawa wanda yaji nama a ciki, ta hada da ruwan zafi ko zaisha tea, 

    A tire ta jera komai, bayan taa gyara wurin data ɓata, sannan takai ma yayanta nashi, ta fito da nata a falo ta zauna tana ci,

   Anty deejah ce ta wuce taga ban Rabi'ah kaɗan ya rage ta ɓarar mata da abinci, 

   Rabi'ah kaman bazata tankata ba, ganin tana sane yasa tace, "ashe gidan namu harda makafi. 

   "Anty deejah tace yayanki ne makaho kuma ya aje makauniya", 

Abin daria ya bama Rabi'ah azuciyarta tace 'daman nasan jira kike na tanka", 

  Azahiri kuma cewa tayi "Lahh! Aunty deejah ce kiyi hakuri ban kula ke bace shiyasa" banza ta mata sai harare-harare take, Rabi'ah na riƙe dariyar da take ta sake cewa.  

  "bismillah ga break fast,"

Mamaki yakama Anty deejah takasa cewa komi wai Rabi'ah ce ke bata hkr kode gamo Rabi'ah tayi, 


  Taɓe baki Aunty deejah tayi, sannan tace "naki na haƙuran, wani salon rashin mutuncine zaki fitomin dashi ko dan kinga yayanki na gida," 

  Rabi'ah batasan tabiyewa deejah ne dan karta ƙara hauda mata wata damuwa bayan wacce gayen nan yasakata, Kayan da taci abinci ta haɗa ta kai kitchen tabar Anty deejah a palon, itama deejah tanata faman masifa tabar palon, 


Tana fitowa daga kitchen ɗin ɗakinta tanufa, sai alokacin ta kula da wata karamar takarda manne jinki lodojin dayan an rubuta (this is for uh Aunty Rabi'ah) dayar kuma ansa (and this one is for my kids)

   Dayar tatace dayar kuma ta su Hayran ce, 

Kawai taji zuciyarta nason sanin mike cikin ledojin, sau biyu tana kai hannunta za ta dau ledojin sai ta fasa, A na uku ne ta daure ta daukesu ta nufi dakinta da su, na su Hayran ta fara dubawa taga chocolate kala kala, kayan wasa niƙi-niƙi, kayan ya jibgo masu su dayawa, A ranta kuwa cewa tayi wannan mutumin akwai ɗan rainin hankali, ya gama ɗagamun kai harda wani siyayya zai musu, ta kwashi kayan tanufi hanyar dakinsu hayran, zata kaimasu, abakin ƙofar dakin su ta tsaya to idan suka tambayeta idan sunci baza su mutu bafa ko kansu ya fita, ta bata lokaci tana tunanin me zata fada masu kafin ta shiga dakin, ta tura kofar da sallama, da gudu suka taso suka tareta, "morning Auntie" 

  "Morning, Ya kuka tashi?"

  "lafiya lau"

  "yauwah naji daɗi, ga siyayyan kunan kusaka kowane inda ake ajiyeshi, ga kayan wasa kuma gasu chocolate," Ai fafurur suka ki daukar kayan wai kar acire masu kai tasha wuya kafin su yarda bazasu zama doya ba idan sunci, Hayra kuwa cewa tayi zata fadama Abbanta koda anga tazama doya to Uncle ne ya saida ita, daria sosai Rabi'ah take, tace "hayra kenan kinaso Daddy yamun fada ko"

  "A'a Auntie" Hayra ta fada,"

  "kar kifada ma Abbanku" tace,

  "To Anty bazan fada ba, Hayran kuwa har ya fara shan dadinshi, ta tayasu suka jere kayansu sannan ta koma dakinta, 


Tana shiga ta buda dayar ledar daman duk ta ƙagu dason taga wacce siyayyarne aciki, ta fara ciro manyan turaruku masu tsadar gaske kala biyar, 

   "lallai ma mutuminnan, an faɗa mishi na rasa turaren dazan shafane?" ta fada a zuciyanta, sannan mayuka masu kyau sosai da kwantar da fata, sannan kayan Make Up masu tsada sosai ya siyamata, ta kara ciro wata leda daga cikin ledar da take dubawa, tace "nan kuma miye?" Yage ledar tayi dan taga Meke ciki abinda tagani yasakata suman zaune (Pants, brezia, cutton), ita tama manta data siyesu a cikin siyayyar da sukayi, a fili tace, "Anma mutuminnan ya gama dani, ɗan iska kawai, ɗan rainin hankali" har hawaye ya fara zubo mata tsabar jin kunyar kanta,

  


 Kun jini shiru, kumin uzuri plz abubuwanne da yawa, anma yanzu nida sistona ne RUQSAD, Insha Allah zakuna jinmu akan lokaci


©Rabiatu sk msh

     And 

©Ruksad Mom siyama

[3/17, 19:17] Sisinah: ♡♡MAFARIN SO♡♡

  ♡♡♡♡♡♡♡♡    

     ♡♡♡♡♡

        41-45


©Rabiatu sk mashi

     ®NWA

And 


Ruksad

    EWF


Rerbeeart_sk @wattpad


www.babymsh.blogspot.com


Tana tafiya a mota tana tunanin guyn nan da batasan ko sunanshi ba, da sauri take tafiya da motan don ta isa da wuri, ba tafi mintuna 15 ba ta isa gidansu Amrah, bata ko zauna ba akace ta tafi gidan biki, ta gaishe dasu Mamansu kawai ta juya zuwa gidan bikin.

  Tana zuwa ta tarar da 

Amrah ta rako wata ƙawarta bakin ƙofar gidan tana fira da saurayinta, da Alama sabon kamune tayi cikin Abokan ango, 

   Amrah na ganin Rabi'ah ta ƙaraso wajenta tana faɗin "sai yanzu kikaga damar zuwa,"

  "Rabi'ah tace naji dai mikike a ƙofar gida?" Amrah ta mata nuni da wace take firah,

  tace "kice takin baya kika fito toni na na shiga da ga ciki idan tagama kun sameni aciki," da "Ok" Amrah ta amsa sannan


  Rabi'ah ta wuce cikin gida tana zuwa babban palon inda amarya take, zata bude kofar taji an turo ƙofar, ƙofar ta datse mata dan yatsa na ƙafa,

   Wata razananniyar ƙara tasaki cikin muryar kuka, hakan yasa wannan ya buɗe ƙofar saurin fitowa dan yaga mike faruwa, karo yaci da ita ta duƙar da kanta ƙasa ta riƙe ƙafa, shima ganin ƙafar ya sashi saurin riƙe kafar yana mata sannu.  

  "kiyi haƙuri wlh bansan kin tafo bane," duk ya nuna damuwarshi, Jin muryarshi yasa gabanta yayi munmunar faɗuwa, anma tadage ta ɗago da kanta 

  tace "eeh lallai rainin hankalinka, da rashin kunyarka bai isheka ba, yanzu har neman kashe ni kake ko?"

  Sai lokacin ya lura da itace, sakin ƙafar nata yayi ya miƙe, 

  Yace "Uhm ashe kam farko da nayi tunanin kece banyi kuskure ba? Ana faɗin mata wurin natsuwa in suna tafiya, anma ke sam bakya duba gabanki, ko ko dai nine kike bi duk inda nayi ne?"

  "Oh! Aeni ban ɗauka kana da bakin magana ba, kajimun ciwo a ƙafa kuma kana mun hayaniya akai?"


   Abokan Angon da suka tafo bayanshi ne ke tambayansu "Meya faru ne?"

  "Ku tambayeshi mai laifin" ta saka takalminta zata wuce, ae yana gogar wurin sai da ta ƙara sakin ƙara, a haka dai tana ɗingisawa ta wucesu, binta kawai yayi da kallo yana murmushi, ba ƙaramin kyau ta mishi ba, hakanan yaji yana tausaya mata bugewan da tayi.

  Tana shiga suka ringa gaisawa da ƙawayensu, kowa ce mata yake tayi kyau, sai dai tayi fari da ido cikin jin daɗi tace, "Na gode" daman an gama shirin zuwa kai Amarya, suka fito anata shiga mota,

  Wata ƙawarta Mai suna Sadeeya ta ƙaraso inda take, "Ƙawata nikam in tambayeki mana"

   "Tohm ina jinki"

  "Don Allah miye tsakaninki da wancan babban Abokin Angon?"

  "Wa kenan?" 

 "wancan kyakkyawan mana" ta nunashi da Hannu, juyawa tayi don taga ko wayene, dai-dai lokacin shima ita yake kallo, ya ɗago mata hannu alaman "Yadai?"

  Harara ta sakar mishi sannan ta juya, "Babu abinda ke tsakanina dashi"

  "Haba Rabi'ah, koda numbernshi ne kawai ki bani, zan kula da sauran"

  Cikin ƙulewa tace "Bani da ita, gaki gashinan ae sai kije ki amsa"

  "Allah ya baki hak'uri, ai bansan Saurayinki bane"

   "Saurayina? Allah ya kiyayemun" lokacin Sadeeya ma tayi tafiyanta, su Zahra da Amrah kuma sun k'araso,

   "wai bazamu tafi bane? An riga da an tafi da Amarya fa kowa ya kusa tafiya"

  "toh muje mana, ta juya tana nufar wurin motarta"

  "Ina kuma zakije?"

    "Bada Motana zamu tafi ba?"

  "A'ah muma duk anan zamu bar namu, tafiya mai nisa ce fa, akwai wadatattun motoci"

  Ba don ranta yaso ba, suka shiga ɗaya daga cikin motocin Abokan Angon, jinta take duk a takure bata saba zaman bayan mota ba, tana jinsu Amrah na firansu, wani lokacin Abokin Angom ya saka musu baki, anma tayi shiru kaman ba ita ba.


©Rabiatu sk msh

©RukSad Mum Siyama

[3/17, 19:19] Sisinah: ♡♡MAFARIN SO♡♡

  ♡♡♡♡♡♡♡♡    

     ♡♡♡♡♡

        46-50


©Rabiatu sk mashi

     ®NWA

And


©Ruksad

     ®EWF


Rerbeeart_sk @wattpad


www.babymsh.blogspot.com


  A haka suka isa Kano, A gidan amarya suka tsaya gaba ɗaya,

  Anyi adu'a sosai dan samun ɗorewar zaman lfy, wa ma auratan.

  Sannan wasu daga cikin abokan angon sukaje siyan Abincin da za suci kafin masu komawa katsina su dau hanyan, wata restaurant suka nufa, sukasa aka hada masu abinci kalah kalah, dan kowa yazabi kalar daya keci, dan tafiyar tazama ba mutun daya ba, 

Angama haɗa masu komai sannan suka shiga wani kayatancen mall, suka sayi drinks kala-kala da ice cream, sannan suka koma gidan Amarya, 

  A palo suka ajiye abincin sannan suka kira ƙawayan amarya da sufito suci, duk suka fito kowace ta ɗauki kalar abinda takeson ci, Rabi'ah kuwa tace sakwaran doya takeso, Abba ne cikin abokan angon yace, 

  "kin ci Sa'a kuwa dan bamu sawo sakwaran doya, bamu jira ba abinda ke akwai dai mukace abamu, shiyasa muka taho ba mu tsaya ansaba,"

  "Anma mun bar *Ahmad* acen Allah yasa ba iya cikinchi zai sawoba,"

 suka Amsa da "Ameen"

 Rabi'ah kuwa cewa tayi "Allah nidai ina son cin sakwaran idan ya siyo iya cikinsa saide ya hakura da ita ni naci,"

 daria suka samata dan tabasu daria, Abba yace,  "ina laifin dai kuci tare anma kice sede chi ya hakura, kinsan shimafa ita kadai yakeson ci,"

  tace "To kuci abincinku ni zansha Ice cream kafin yazo," ta ɗauki roba guda ta koma inda take zaune ta fara sha, "Assalamu alaikum" wata cikakkiyar murya Me cike da haiba, da kwarjini, ta fada gaban Rabi'ah ne ya fara dukan tara-tara, jin muryar Me sallama, Abba ne yace "yauwa Rabi'ah ga *Ahmad* ɗinnan yazo, kitaso kuci"

 

  Ahmad yace "lafiya malam daga zuwana zaka faramin gayata?, kuma kasan iya cikina nace zan siyo ko? Abba

  yace "yi hakuri Rabi'ah ce takasa cin komai sai sakwara kuma naga kaima ai itace kasawo ko, kaga sai kuci tare"

   "Ah OK na fahimta Ahmad ya faɗa" yana murmushin mugunta

  "to ta taso muci ko, dan ni yunwa nakeji, kuma idan tasa jan aji wlh zan cinye, dan bana jure yunwa ni,"   

   Abba yace da Rabi'ah  

  "kitashi kici mana" 

  "A'ah", kawai ta iya fada dan ganin guy din jitayi komai ma yafita ranta,   

  Amrah tace "miye kuma haka bestie? kije kuci abincin mana yanzu fa zaki koma katsina kinasan yunwa tamiki illah kafin kikai gida ko,"

  Abba sarkin surutu yace da Ahmad "Aboki kaɗan matsa mana kuci karka cinye ka kyaleta" harda wani kashe mishi ido, Alamar yaje kawai, 


  Ahmad ya ɗauki plate ɗin abinci ya ajiye gaban Rabi'ah yace "to bismillah muci ko" yana mata wani irin kallon da bata aminta da shiba duk se taji ta takura, kuma bazata iya musa mishi ba, ta ɗauki cokali tasa cikin plate ɗin ta ɗebo zatakai baki yace, 

   "wato gulma na ma kike masu ko,"

  kasa kai abinci tayi bakinta kuma ta kasa ce mashi komai sai uwar harara da take zuba mashi, 

  Kashe mata ido yayi can ƙasa yace, 

  "wannan kallon son fa? Ƙwalelenki dai" ta buɗa baki kenan zatayi magana yace wa Abba "Aboki ka sakani nadawo wajenta gashi ma takasa cin abincin," 

  Abba yace "kici abinci Rabi'ah dan zai iya gamawa da shi idan baki ciba,"

   "To" tace wa Abba dan tanajin maganarshi sosai, Ta sake kai cokalin bakinta, Ahmad yace 

  "Kinga ni banson kinibibi, kina sona anma kin kasa faɗamun, kiyi bayani ko zan iya taimakawa na amsa soyayyarki"

  Rabi'ah ta kawo iya wuya plate ɗin ta dauka ta juye masashi akai, nan take miyar ta bata masa fararan kayanchi, kowa ya zabura yana kallonsu, ta sunkuya dai-dai kunnuwanshi

  tace, "bari kaji na faɗa maka ko ba maza duniya ba abinda zanyi dakai,"


©Rabiatu sk msh

    And 

©Ruksad Mom siyama

[3/17, 19:20] Sisinah: ♡♡MAFARIN SO♡♡

  ♡♡♡♡♡♡♡♡    

     ♡♡♡♡♡

        51-55


©Rabiatu sk mashi

     ®NWA

And


©Ruksad

     ®EWF


Rerbeeart_sk @wattpad


www.babymsh.blogspot.com


    "Da fatan kajini da kyau" Rabi'ah ta faɗa, bai iya cewa komai ba dan kar ya buɗe ido barkono ya shiga ya kama idon ya rufe ruf, 

  Amrah tace, "haba bestie miye haka wannan ai wulakanci ne,"

  Abba ne yace da sauran jama'ar wajen "ku ƙyale su wannan faɗan da kuke gani na masoya ne,"

  wata kawar amarya ce tace da Abba "Kace faɗan na manya ne, fadan masoya wanda ya shiga shi keda kunya, anjima zakaga sun dawo dai-dai" 


  Abba yace da Rabi'ah   

   "a taimaka mishi ya wanke mana, ko sai ya makance?"

  taja ƙwafa tace "Ai ko damun huta",   

  "wanne hutu kuma keda zaki koma jagora?"

   "Tabɗijan" ta faɗa, , Abba da yaga da gaske take yace, "bari dai nakai miki shi, anma ke zaki zuba mishi ruwa ya wanke"

   "Wa? Badai ni ba"

  Amrah tace "Kinga Malama, kefa kika zuba mishi miyarnan, tashi zaki ki wanke mishi"

  Ta ansa sabulu tabi bayansu tana kumburi,

Abba ne ya kaishi har toilet yana riƙe da hannunshi sai lalube yake kaman sabon makaho, famfo ya kunna mishi yanda zai wanke, ya wanke da ruwa sannan ya ce wa Abba 

   "ina sabulu?" Abba yace "yana hannun kawar ka," sannan yayi tafiyanshi, ya barsu Sabulun yace ta bashi,  

  "Tab ni zan ma baka sabulo ko? to gashinan a ƙasa idan kaji zaka iya ɗauka ka dauka idan kuma baza ka iyaba ruwanka dan ni kaga tafiya ta,"

  "Au tafiya zakiyi ma ko" ya faɗa, 

  tace "A'a wanka zan tsaya inyi maka,"

  "Saurin me kike?" ya faɗa, "ai akwai lokacin da zakiyi mun wankanma, ko yanzu kikeso ki fara?" duk da idanunshi a rufe saida ya kashe mata ɗaya,

   tsaki taja, tayi hanyar fita da sauri, lallai ta tabbata mutuminnan ɗan iskane, jin alaman tafiyanta yasa yace, "bikiji ba" 

  Ta tsaya kawai,  

  "in kinje ki cewa Abba ya dauki key ɗin mota na yaje ciki akwai fararen kayana ya ɗaukomun"  

  "To Oga" ta faɗa "ga yar aikin ka ko? Zan faɗa mishi"

   "Yauwah, kiyi sauri jiranki nake" tayi er dariya kawai ta wuce, don ita kaɗai tasan meta shirya mishi,


Tana zuwa wuri ta nema tayi zamanta, Abba yace "ina kika baro mutumin naki?"

   "Ohon mishi, yace inzo ne yana zuwa" ba wanda ya ƙara tambayarta kawai sukaci gaba da firarsu, har kusan Awa ɗaya,

  Wayanta ce tayi ringing, ta fito da ita kiran yayanta ne harya katse, sannan taga shine misscall na 22, gabanta saida ya faɗi da sauri ta duba lokaci, saiga kiranshi ya sake shigowa da sauri ta ɗauka, ya sauke sanyayyar ajiyar zuwa,

   "Hello! Ƙanwana?"

  "Naam yayanah"

  "Haba Rabi'ah! Kin manta da yayanki bazaki kira ki faɗamun yanda kuka isa ba?"

  "lafiya lau Yayana, wallahi hayaniya, kayi haƙuri plz"

   "Yanzu kam hankalina ya kwanta, ina fatan dai kina hanya kin kusa isowa?"

   "Eeh Yayah insha Allahu yanzu zamu taho"

   "Zaku taho fa kikace? Kinsan kuwa ko ƙarfe nawa?"

  "eeh Yaya zamu iso yanzu insha Allah"

  "Yauwah ƙanwana, ki tashi yanzu maza ki taho, bazanyi barci ba har sai kin dawo"

  "Tohh Yaya" harma ya kashe wayan, 

  

 Ta kallesu,

  "Wai yaushene za'a fara maida waɗanda bazasu kwana ba?"

   Khaleed yace "wanne wanda basu kwanan? Ai an gama maida kowa, duk wanda kika gani anan kwana zasuyi, muma daganan hotel mukayi"

   "Na Shiga Uku! Ya akai ba'a faɗamun ba?"

  "ai tun zuwanku anan suka juya"

  Zahra tace "Sis ai yanzu darema yayi, ki kwana anan kawai"

  Kaman zatayi kuka, "Haba sis, kaman bakisan Yayana bane? Bance mishi zan kwana ba, kuma dai kinsan bai taɓa barina na kwana a wani wuri ba"

   "ki buga ki tambayeshi mana"

  "A'ah nifa gida zan koma, duk dare a katsina zan kwana"

  Kaman zatayi kuka duk ta damu, 

   "duk ku kuka hanani tahowa da motana, dana tafiyana kawai"

  "cikin darennan zaki koma ke kaɗai?"

   "eeh mana" tana magana kaman ta fasa kuka, duk sun tausaya mata, kawai gani sukai Abba ya fara dariya, duk suka tsira mishi ido suna tambayarshi lafiya? Dariya ma ya hanashi faɗi,

  "Haba Abba, bafa abun dariya bane" ta faɗa cikin jin haushin dariyar,

   "tohh ai bakusan abun dariyar ba"

  Har suna haɗa baki, "Menene? Faɗa mana"

   Daƙyar ya iya faɗin, "Ahmad ne kawai zai koma katsina yanzu, don shima ya faɗamun bazai iya kwana kano ba" aikam gaba ɗaya suka kama dariya,

   Ta zaro ido cikin tashin hankali, sai yanzu ta tuna data baroshi toilet da jiƙaƙƙun kaya, Anya kuwa zai kaita? Itama tunanin ta yanda zata fara binshi take cikin darennan.


©Rabiatu sk msh

©Ruƙayya Maman siyama

[3/17, 19:22] Sisinah: ♡♡MAFARIN SO♡♡

  ♡♡♡♡♡♡♡♡    

     ♡♡♡♡♡

        55-60


©Rabiatu sk mashi

     ®NWA

And


©Ruksad

     ®EWF


Rerbeeart_sk @wattpad


www.babymsh.blogspot.com

*Assalama Alaikum masoya muna masu baku hakuri sakamakon rashin jin mu da kukayi kwana biyu hakan ya faru ne sakamakon wasu uzurinrika dasuka sha kanmu anma bi'iznillahi yanzu komi yazo normal muna tare daku kuma muna kaunarku dare da ranna dan da bazarku muke rawa*


Kishiyatah SADEEY S ADAM, Ina tayaki murnar kammala littafanki (TUN A RANAR BIRTHDAY ƊINTA, da kuma MENENE AIBUNA?) Allah ya baki ladan faɗakarwa, ya ƙara basira da hazaƙa, bani da bakin godia akan sadaukarmun littafin da kikai, tabbas yafi ƙarfin godia, kamar ko yaushe ina miki fatan Alkhairi.  Jiki a sanyaye Rabi'ah tace ma Abba "namanta Ahmad yace ka ɗauko mishi kayanshi a mota,"

  Abba yace " Badai yana bayi ba tun ɗazu?" Kai kawai ta iya ɗaga mashi, dan tama rasa abinyi tana tunanin yayanta kuma tana tunanin wannan Ahmad ɗin ƙwaƙwalwarta duk ta ɗau caji, 


  Abba kuwa yaje ya daukoma Ahmed kayanshi, ya kaimashi toilet ɗin Abba ya ƙwanƙwasa ƙofar toilet ɗin Ahmad yace "waye ne?"  

  Abba yace "Nine Aboki ga kayanka," Wata nauyanyar ajiyar zuciya Ahmad yasaki kafin ya ce " To" 

Ya bude ƙofar da jiƙaƙƙun kayanshi harsun fara bushewa, sannan yace "kaga yadace abunda kamun tsawan lokacin da nace ka ɗaukomin kayana shine kashareni anan ko? Ya maka kyau ba damuwa nagode," Cikin bacin rai yake magana,

Abbah yace "haba Aboki miye na daukar zafi haka bayan baka da tabbacin saƙonka yazo gareni ko baizo ba, ka fara zubamin ruwan masifa,"

  Sai a lokacin ya tuna da wacce yabawa sakon ta fadawa Abokin nashi, 

"Hmm bakomi ya fada ni zataiwa ɗanyen rashin mutunci ko"

  Abba yace "bakamasan wani abu ba Aboki kasan fa yanzu zata koma katsina,"

  "Ah haba dan Allah" Ahmad ya faɗa, 

 Abba yace "da gaske makuwa,"

   "ita dawa zata tafi? Kuma naga kaman bada mota tazo ba"

   "waye zai koma bayan kai?"

  Wani guntun murmushin mugunta Ahmad ya saki, sannan Abba ya bashi wuri ya canja kaya, kayan sun karɓe shi sosai, har sunfi wanda ya cire yi mishi kyau, tare suka koma cikin palo inda su Rabi'ah suke.


  Sallama sukayi sannan suka shiga.

  A tsaye suka tarar da Rabi'ah ta matsawa Amrah akan lallai sai sun rakata tasha tahau motar haya,

Amrah ko magiya take mata akan takira yayanta tace dashi zata kwana a Kano in yaso washe gari sai suyi asubanci suje katsinan idan Allah ya yarda,

  Rabi'ah tace "kibar ni kawai besty idan bazaki rakani ba ni kinga tafiya ta dan haka saduwar Alkairi,"

  Ahmad ne yace "to ainima yanzu zan wuce katsinan,"

  Abba yace "yawwa Aboki to dan Allah kabiya da ita mana kaga yanda mukazo dasu amana ne awajen mu dan haka ga amana nan mun damƙa a hannunka ka kula da ita sosai kaji,"

  Rabi'ah tace, "Allah ya tsare da nabi wannan dan rainin hankalin"

  Ahmad yace "waye zai tafi da wannan shugabar en ji da kan?"

 Abbah yace "kunga ku taimaka ku aje wannan Alayin soyayyar taku, dare yakeyi kuma kunga hanya zaku dauka,"

 Amrah tace "Dan Allah Besty kije mana ku tafi kinsan fa Yaya yana jiranki," Hankalin Rabi'ah yakara tashi gashi ita bata hau motar hayar ba kuma ga wannan ɗan dandalin yana ɓata mata lokaci,

  Ahmad yace "to nidai natafi kumin fatan Alkairi, 

  Abba yace da Rabi'ah "kitafi kuje mana," a sanyaye tace "to,"


 Ahmad yace "waye zai biya kudin motar dan ban tsara da zan dauki kowa a motata ba?" 

  Abba yace "naji zan biya ko nawane", Rabi'ah kuwa a zuciyar ta cewa tayi kowace balagazar mota ce dashi har yake ma mutane iya yi, bayanshi tabi suka fita Abba da Amrah ne suka rakasu har bakin get sannan suka masu fatan sauka lafiya,        

  Dai-dai saitin Ahmad, Abba ya duƙa a hankali yace mishi "wlh Aboki kowa zai dauka matarka ce dan kunyi masifar da cewa, ya kamata tazama takafa,"


Daria Ahmad yayi tare da fadin "wannam ai gulmane da sa ido"

  "ba wannan maganar Aboki"

 Sannan sukayi bankwana dasu.


  Motar shi fara kirar (Audi) irin motocin nan da ake kira masu numfashi, Da bisminllah ta chiga sannan ta fara karanto addu'ar hawa abin hawa 

(Subhanan lazi sakara lana haza wama kunnan lahu mu'ouridun wa'in,na illah Rabina lamun'kalibun) Sannan ta hada da Lakad ja'akum rasulun......


Ta tofa ta shafe jikinta duka, shima addu'a yayi sannan ya dauki hanyar zuwa katsina sunfi kusan muntina sha biyar ba Wanda yace da wani ƙalah, 

 Ahmad ne ya gaji da rashin maganar tata, kuma yana gudun shi ya mata maganar taji dadin kara jan aji, 

Hakanan ya daure "yace wai ke kurma ce?

  Bata ko kalli inda yake ba tayi banza dashi kamar ma ba da ita yake ba 

  Ya sake cewa " Ja aji kitsufa gidan ku An mata" 


  Da tayi kamar bazata mishi magana ba, kuma sai tace tana taɓe baki, ba tare data ko kalleshi ba.    

  "daɗinta dai a gidan namu zan tsufah ba gidan wasu balle aji dadin yimin gori kuma aji ai sai cikakkiyar mace," taja karamin tsaki 

  "Waye cikkakiyar macen anan?"

  "gata a gabanka"

  "da wuri haka har kin faramin tallar kanki"

  Tsaki taja sannan tace "da ma wani cikakken namiji kace"

  "Tabdijan ni zaki fadawa wannan maganan" 

  "Eh an faɗa maka idan kana da abinda zakayi ai sai kayi ko"

  "Eh niko nake da abinyi bari ki..." Kasa ƙarasawa yayi sanadiyar karo da motar ta kusayi da wata bishiya

  Rabi'ah kuwa Inna lillahi... Kawai take ta nanatawa abakinta dan tasare da rayuwa.


©Rabiatu sk mashi 

     And 

©Ruksad Mom siyama

[3/17, 19:23] Sisinah: ♡♡MAFARIN SO♡♡

  ♡♡♡♡♡♡♡♡    

     ♡♡♡♡♡

        61


©Rabiatu sk mashi

     ®NWA

And


©Ruksad

     ®EWF


Rerbeeart_sk @wattpad


www.babymsh.blogspot.com


  Rabi'ah ba ƙaramin kaɗuwa tayi ba har saida en cikinta suka kaɗa, duk ta dunƙule wuri ɗaya tana kalmatus shahada, 

  Shikam daya samu ya tsaida motan cikin ikon Allah basu kaima iccen karo ba, yana kallonta me zaiyi ba dariya ba harda riƙe ciki. Can ta fara jiyo dariyarshi, ta ɓata rai ta ɗago da fuskanta, sannan ta fahimci meke faruwa.

  "me abun dariya anan?"

  Ya ƙara kyalƙyacewa da dariyan yana kallonta, "ki barshi kawai ke bazaki gane ba"

  Ta ƙara tunzura, "jakkar Ajinmu nake, ƙarewar rashin ganewa, tashin hankalin daka sakani harka samu abun dariya?"

   "kika sakamu dai, duk waye ya kusa ja mana idan bake ba?"

  "watau laifina ma kake gani kenan?"

  "toh dafa? Kinga kuwa yanda kika maƙure ashe dai kina tsoran mutuwa?"

   hararanshi tayi, "so kayi ka ƙarasani kenan?"

  Anan wani faɗan yaci gaba, gashi su biyu babu mai rabawa, sun ɓata lokaci sosai a haka, kafin yace mata,

  "Yanzu masifar zakici gaba ko zaki barni mu fita daga dajinnan? Don ni ina da abunyi a katsina in ke baki da"

   "Waye masifaffiyar? Nayi maka kama da marar abunyi ne?"

  "toh malama mai abunyi muje" ya tada mota suka tafi,


Wannan karon a hankali yake tafiya sosae, ko mai tafiya a ƙasa zai iya rigansu ƙarasawa inda zaije, tasan duk son ta kulashi ne, tayi mishi banza kawai, yana en waƙe-waƙenshi na india, (waƙan cikin Tevar, Hey listen baby, baby i will do anything for uh, Nah M just jocking......).

  Ta shareshi kawai ta kwantar da kujerar zata jingina, da sauri ya tareta.

   "ɗan tsaya man," ta ɗaga ido tana kallonshi baki buɗe,

  "kuɗin motar da aka biya miki, na zamane kawai banda kwancia"

  Dogon numfashi taja, sannan tayi sama da idonta ta sauke, "idan duka kuɗin motar kake buƙata, ka faɗamun zan siya, saboda wannan ƙarfen da yayi kaɗan a kirashi mota sai wani ɗaga kai kake"

   "yaushene nace miki zan siyar da motana? Kawai dai kwanciya ne na hana"

  "sai inga ta yanda zaka hana ɗin" ta gyara wuri ta kwanta tana murguɗa baki, murmushi kawai yayi yana riƙe baki cikin tunani,

   "Yauwah, nikam ɗazu naji kina magana akan kina na qarshe a aji, ya baki taɓa faɗamun ba?" ya ƙarasa magana yana ƙoƙarin riƙe dariyarsa,

  Wannan karon yafi ƙarfin ta maida da baki, kusa da ita ta duba, babu abun duka, cire gyalenta tayi ta ƙudundune ta fara dukanshi, sai karewa yake yana dariya.

   "kinga karki ƙara sakawa muyi na ɗazu"

   Ko saurarshi batayi ba da yake taga a hankali yake tafiyan, saida taga yana ƙoƙarin riƙota ne, gashi motar ta fara tangal-tangal sannan ta haƙura ta koma ta kwanta tana maida numfashi.


Motance ta tsaya, a dai dai sun kusa isa garin Ingawa, ta tashi zaune,

  "me kuma ka tsayayi?"

 Buɗewa kawai yayi ya fita ba tare da yace da ita komi ba, ta buɗe itama ta bishi,

   "ina zakaje ka barni cikin tsohon darennan kuma ko faɗamun bazakayi ba?"

   Gaban Motar ya buɗe, ya ɗanyi taɓe-taɓenshi ya rufe ya koma ciki, ta bishi da sauri.

   "Dakai fa nake magana"

 Ya sake tadawa duk batayi ba, ya dafe kanshi, duk ya haɗa zufa, ya sake fita yana ɗan tafiya, tasha gabanshi.

   "malam magana nake maka fa, ka kama ka kashe mota, kaje mu tafi"

   "mu tafi ina? Nasan kinajin yunwane na fita in duba ko akwai restaurant anan, kici abincin"

  Duk bata gane baƙar magana ne ya mata ba, "an faɗa maka a gidanmu babu abincinne? Idan bazaka tafi ba nizan iya tafiya" tun kafin ta ƙarasa magana ya miƙa mata mukullin, ta saki baki tana mamaki, ta anshe ta shiga motar, tadawa ta shigayi anma mota taƙi tashi, duk da haka taƙi haƙura don kar yaga gazawarta, sai data gaji don kanta ta daina, ya duƙo da kanshi ta glass ɗin motar.

   "Yadai? Taƙi tashi ba? Kin ɗauka da gangan na kashe motan don kawai inason sauraren masifarki?"

  "Na shiga Uku, mota ta lalace mana a dajinnan?"

   "kin gane kenan"

  Ɗaura hannu tayi akai zata fara rusar kuka.


©Rabiatu sk msh

©Ruƙayya Mom siyama

[3/17, 19:24] Sisinah: ♡♡MAFARIN SO♡♡

  ♡♡♡♡♡♡♡♡    

     ♡♡♡♡♡

        66


©Rabiatu sk mashi

     ®NWA

And


©Ruksad

     ®EWF


Rerbeeart_sk @wattpad


www.babymsh.blogspot.com
  Ahmad ya riƙe baki, 

  'kajimin er rainin hankali wato kukama zakiyi bazaki tsaya mu nemi mafita ba, bayan kuma kece silar komai,"

  A harzuƙe ta taso masa "wato nima zakace, da gani daman ka saba wahala da wannan tsohuwar motar taka, zakawani laƙamin sharri,  

 Tun wuri ma gyara kasan abinyi dan Allah bazaka barni a dokar da jin nan ba"

 Har tayi shiru ta ƙara kallonshi, "Kuma dole mu isa katsina a yau saboda wlh bazan ɓatawa yayana rai ba saboda da kai" 

  Ahmad yace "dole mu kwana a katsina yau? saboda ke keda iko da komai ko, bazaki ce insha Allah ba"

  "To ai dama komai sai da yardar Allah muke yinshi" Rabi'ah ta faɗa,

 "Da wannan masifar da kike da ma tunanin mafita kika mana da yafi miki," Rabi'ah tace "aikai kataho dani sai kasan yanda zakayi dani dan Wlh bazan kwana a jejin nan ba, koka manta kuɗin mota aka biyamun?, ka kira makanike yazo ya duba mana motar ko masan inda dare ya mana"

  "Wato saboda bashi da aikin yi shi makanikan sai hidimar mota ko? to ki duba Lokaci karfe nawa yanzu, idan mijinki ne kinji daɗi ya fito yabarki cikin tsohon daren nan don ya gyarawa wani mota ba hatsari ba, ba komaiba balle ace ceton rai ya fito,

Mota kuma tanshin kinkine yasa battery yayi sanyi dan haka dole saida safe idan Allah ya kaimu an chager shi saimu wuce gida , kingane?" ya faɗa tare da kashe mata ido ɗaya.


Rabi'ah kuwa ta cika tayi fam tunanin Yayan ta ya faɗo mata, motar ta buɗa zata ɗauka wayanta a jakarta, don ta sanar dashi halin da ake ciki. Kawai ta duba ko sama ko ƙasa babu ita, sai lokacin ta tuna taa barota a gidan Amarya, haƙura tayi kawai da neman ganin babu yanda zatayi.

  Ahmad kuwa jira yake yaji kuma da wane bala'in zata fara zazaga mashi, 

 Anma abin mamaki sai yaga ta juyo ta kalleshi jiki a sanyaye da Alamun nadama a fuskarta,

Azuciyarshi kuma cewa yayi 'nasan wani munafuncin takeson ƙullawa chine tayi kalar tausayi...

 Maganarta ce ta katse shi da cewa "Dan Allah ka bani Aron wayarka zanyi kira"

 "Awwh! babu credit a naki wayan?" ya faɗa,

  "A'a na bar jakar ne a gidan Amarya, nasan su Zahra zasu tafomun da ita"

  "saurayinki zaki kira yazo ya ɗaukeki ko?"


A zuciyarta tace 'dan na tambayeka ne zakamin rainin hankali ko ni badan yayana ba ka isa na karɓi wayanka'

  A zahiri kuwa cewa tayi "A'ah Yayana zan kira na faɗa mishi dan kada hankalinshi ya tashi"

  Ahmad yace "dan mi bazaki kira ummanki ki faɗa mata ba? Ai hankalinta zaifi na yayan naki tashi"

 Maganarshi tasa jikinta yayi sanyi sosai wasu siraran hawaye ne suka fara bin kuncinta kawai tunanin iyayanta ya faɗo mata a rai ashe marainiyace ita, ko soyayyar yayanta gareta yasa tamanta da mairaicin da take ciki ƙafafuwanta sun kasa riƙeta dole ta jasu hakanan takoma cikin mota ta zauna hawaye kawai take wasu nabin wasu,

  Ganin halin data shiga ne yasa Ahmad cikin damuwa shima binta yayi motar yace "dan Allah kiyi hakuri bansan zan ɓata miki raiba, kinji pls m so sorry wlh banason ɓatawa wani rai wannan ma bansan ranki zai ɓace ba dan Allah ki yafeni"

  "Bakomai" ta faɗa, "kawai ka tunamin ne da maraici na, Yayana shine Uwa da Uba a waje na ya maye min gurbinsu domin mun rasasu gaba ɗaya"

  Jikin Ahmad ya mutu sosai Wani tausayinta ne ya shiga ƙoƙon zuciyarshi, jiyake ina ma ace zai iya rungumeta ya rarrasheta sai dai ba hali anma ya ƙudurta azuciyarchi, bazai iya barinta ba koda kuwa zaya shiga matsalane, ya rasa mema yakeji a jikinsa tausayinta ne duk yabi ya mamayeshi

 "Allah sarki kiyi hkr dama duk mai rai mamaci ne, sannu kinji ba kukanki suke bukata ba addu'arki ce mafi soyuwa a wajensu" hkr yabata sosai cikin Wata sassanyar muryar da batasan daga ina ya samota ba sai da yaga ta nustu sosai sannan ya bata wayarshi ta karɓa sannan tasaka number Yayanta anma takasa samu Busy kawai ake ce mata, gashi wayan Ahmad ɗinma Charge ya kusa ya ƙare, tayi kira yafi a ƙirga anma Busy kakeji yaƙi shiga, tasan ita yake nema, A dole ta haƙura akan idan ya daina kira zata kirashi, gashi wayanta silent ballantana Amrah taji ƙararta ta ɗaga kiran.


 A ɓangaren Yayanta kuwa ya kasa sukuni domun kwata-kwata hankalinshi a tashe yake ya kira Rabi'ah yafi a ƙirga anma taƙi ta ɗaga, tunaninshi ba lafiya ba Aunty deeja kuwa cewa tayi "kabi duk kadamu da ita bayan ita ɗin bata damu da kai ba tanacen tana sheƙe ayarta ita da abokan shashancinta, dama ya lafiyar kura bare tayi hauka, tana garin nan ma a tare da mu tayi balle garin da ba idanunmu aiko sai abinda Allah yayi, idan ina faɗa maka ai ƙin yarda kakeyi, gashi nan ka gani da kanka, tun ɗazu kayi waya ance maka ta taho, shin ko wani abu ya faru ai dole za'a samu wanda zai ɗaga kiran, ka daina damun kanka ma, kananan zakaga ta dawo sanda taga dama"


©Rabiatu sk mashi 

     And

Ruksad Mom siyama

[3/17, 19:24] Sisinah: ♡♡MAFARIN SO♡♡

  ♡♡♡♡♡♡♡♡    

     ♡♡♡♡♡

        67


©Rabiatu sk mashi

     ®NWA

And


©Ruksad

     ®EWF


Rerbeeart_sk @wattpad


www.babymsh.blogspot.com


   "Dan Allah muje ka kwanta ka huta in yaso sanda ta dawo ai sai kaji inda ta shige ko,"

  Baiko kalleta ba, yanata zarya tsakar falon yace "kije ki kwanta kawai in zaki iya,"

  tace "to mezai hanani iya bacci ni kuwa? kai ma ai dan ka saka kankane shiyasa tana can tana sheƙe ayarta dan haka ni saida safe, bacci ya kama ido na sosai kabiya ta dakin su Hayrah Kai masu addu'a sai kashigo daga ciki kaji"

   "OK" kawai ya iya faɗa ita kuwa Anty deejah dakinta ta nufa sam babu abinda ke damunta game da rashin dawowar Rabi'ah gida.


  Ta ɓangaransu Rabi'ah kuwa sunga dare yaja sosai Ahmad ne yace da ita "wai ke a ina zamu kwana kinsan baza muyi bacci Annan mukadai ba KO kuma ni banga Alamun hotel anan ba"  

  Rabi'ah tace "ai dama duk mazan takar da kake nunawa ta banzace bazaka iya kwana a dokar daji ba, hmm to ai kai zaka nemi mafita dan ni hannun direba aka bayar da amanata dan haka haƙƙin driver ne ya nemamin gurin kwana"

  Agogon hannunshi ya duba yaga dare yayi sosai shiyasa bai kulata ba dan yasan idan ya biye mata Wata sabuwar rigimar zasu shiga kawai shiya fito daga motar ya nufi wani dan guri daya ke ganin haske haske kamar alamar gidane awajen. 

 Rabi'ah ko ganin ya mike hanya yana tafiya yasata fitowa da sauri daga motar tare dabin bayanshi cikin sassarfa har ta isa gurinshi. 

  Jin kamar tafiya bayanshi ya sashi waigowa ganinta dayayi bayanshi ya bashi mamaki, yaushe tabiyoshi,

Yace "wato biyoni ma kikayi ko"

  "Au nufinka in tsaya acen ko wato ka gama cinikin kaina Wanda ka saidawa suzo sutafi dani shine ka faki idona kataho ko? to naganka shiyasa na biyoka inyaso sai su ɗauki motar taka badai kaina ba"

  Daria sosai tabashi wato tsoro ya hanata zama ita kadai kenan shiyasa ta biyoshi 

Bari kiji na faɗa maki wannan guntun Kan naki ba zaki bada abinda akeso ba koda sai dashi akai, sai na bari lokacin da mukayi aure na ciyar dake sosai kan yayi girma lokacin sai in sai dashi matsoraciya kawai, anma dazu harda cemin ba namiji ba miyasa yanzu ke kikaki komawa namijin?"

  "Hmm, Kenan ma kaji ƙyaleni ne kayi"

  "Idan ban ƙyaleki ba biyeki Zani Kenan, kina zuba mani hauka ina ɗauka"

  "Wato ma A layin mahaukata ka sakani Kenan to aide Nafi.."

   "Wlh kimin shuru anan idan zakije ki wuce mu tafi idan kuma bazaki ba ki koma mota", yayi gaba ya ƙyaleta, bayanshi tabi sunata tafiya sunyi tafiya mai nisa sannan suka isa wajen da yaga hasken ga mamakinshi mutun biyu ya iske a ƙofar gidan da alama magidan ci ne da matarshi.


Sallama ya masu cike da tsoro suka amsa mutumin yace "Mutun ko Aljan", gashi dai su duka kyawunsu bai kasa bayyana a cikin hasken ba, abunda ya ƙara tsorata masu gidan kenan,

  Ahmad yace "baba mutane ne, ina wuni", ya gaishe su, Rabi'ah ma sunkuyawa tayi ta gaishe su, sannan Ahmad yace "kan hanya ne muke zamuje katsina shine motar mu ta tsaya, Alfarma muke nema ko mun samu wurin kwanciya kafin gari ya waye musami makanike" 

 Maigidan ne yace "ba laifi ɗaki biyu ne dama gidan namu sai ku shiga ɗayan ku kwanta" ya umarci matarshi data tashi ta masu iso zuwa ɗakin

  Tashi tayi ta rakasu har cikin dakin ɗakin a tsabtace ta kunnamasu wuta tace "asuba ta gari"


  Ahmad ne ya tsaida ita yace "dan Allah zan samu ruwa a buta?" tace "ba matsalah bari na kawo maka" ta fita, ta kawo mishi ruwa sannan ya karɓa yayi alwalah,

  Rabi'ah na zaune daga bakin gado tana mamakin karamcin waɗannan mutane, sun basu masauki cikin darennan ba tare da ko sunayensu sun sani ba, tohm anma a ɗaki ɗaya zasu kwana?

  Yana gama alwalan, ya faɗa kan ɗan ƙaramin gadon ƙarfen dake ɗakin inda Rabi'ah take zaune,

  Ta saki baki tana kallonshi, irin kallon kama rainamun hankalinnan, tace, "me kake nufi ne da zaka kwanta kan gado bayan ga tabarma nan a ƙasa?"

   "Taɓdijan, na miki kama da wanda ya saba kwana a tabarma da zakice wai ga tabarma, ai ke ya kamata ki kwanta kan tabarmar ko"

  "Ni zaka kalla kace na kwana a tabarma, anma wlh ka rainawa kanka hankalima, ka dubeni da kyau Malan dan haka tun wurima ka sauka daga gadon nan tun kafin raina ma ya ɓace" Rabi'ah ta faɗa. 

  "Wato dukana zakiyi idan ban sauko ba ko, to bismillah ran naki idan yayi dubu ya daɗe bai ɓaci ba, kisamo bulalah dan kiji dadin dukana da kyau"


  Kallanshi take sosai anma hankalinta ba wajen shi yake bâ, tunani take ita dai bazata iya bacci bisa tabarma ba kuma gadon gashi kwancin mutun biyu ne, biyun ma sai mata da miji domin jikin su ma yana goga juna to ita ya zatayi?

  Ahmad ɗago yana kallonta, "kinmun zaune a gado malama, ko so kike ince kizo mu kwanta tare? Ba haka nake ba, ki sauka a ƙasa kiyi tunaninki"

  Murmushi tayi, saboda muguntar data tuna, ta kalleshi, "ai tunaninma ya ƙare, kaa kawo shawara, bazaka sauka ba ko?"

   Yace "eeh ɗin, bazan kwanta a ƙas ba"

  Ta ware hannu, "nima haka, mafita ɗaya kawai ta rage mana kenan"

  "me kenan?"

Gyarawa tayi ta kwanta saman gadon, anma ba tare data taɓoshi ba, da sauri ya tashi zaune, "ke me kikeyi haka? Nifa ustazu ne"

  "kai kasan wannan, nidai nayi wurin kwanciya" harararta yayi, yasan don ya sauka tayi hakan, a ranshi yace 'aikam bazan bari yarinyarnan tayi nasara kaina ba, idan taga na kwanta naƙi sauka, ita zata sauka ne' ya koma ya kwanta can gefe ya maƙure.


Rabiatu Sk mashi 

     And

Ruksad Mom siyama

[3/17, 19:24] Sisinah: ♡♡MAFARIN SO♡♡

  ♡♡♡♡♡♡♡♡    

     ♡♡♡♡♡

        68


©Rabiatu sk mashi

     ®NWA

And


©Ruksad

     ®EWF


Rerbeeart_sk @wattpad


www.babymsh.blogspot.com


  Shiru-shiru ta jira bai tashi ba, miƙa ta farayi hannunta ya kusa taɓoshi da sauri ya wuntsila,

   "ke wai me kike nufi ne?"

  "oho maka! Kaji na tankaka ne?"

  Ta saka hannu kaman zata cire kayanta 

  "kaa ganninan, ban saba kwanciya da kaya ba, Yauwah ina fatan dai bazaka damu ba don wani ya ɗaura maka ƙafa a barci, ehen da munshari ma, fatan bazai hanaka barci ba"

   "ke wai wacce irin magana kike? Nifa bazan sauka ba"

  "na ƙara cewa ka sauka ne? Kwanciyar dare ɗaya kam ae ba matsala bne"

  "in don kwanciyar dare ɗaya nima banda matsala donna kwana a tabarma, an bar miki gadon"

   Dariya sosai ta kama mishi, "ke meye abun dariya? Kin bani tausayi ne kawai yarnya"

  "eeh naji dai"

 Ya koma saman tabarma ya kwanta, ya barta a gadon tana mishi dariya, har barci ya kwashesu.

  Har tayi barci wayarshi na a hannunta, sai dai tunda suka shiga wurin network ɗin wayar tashi ya ɗauke, hakanan ta haƙura ta kwanta tayi barci.

  Washe gari sanyin Asuba ne ya tasheta daƙyar saboda gajiya, ga kuma daɗewar da tayi bata kwanta ba, donma ta saba da tashi sallahn, saman tabarman da yake kwance ta duba babushi, a hankali ta sauka ta fita daga ɗakin, matar mai gidan ce ta gani tana ƙoƙarin hura wutar girki, ta ɗago ta kalleta, 

  "barka da tashi"

    "Yauwah sannu da aiki" ta kawo buta gabanta

  "ga ruwan Alwala"

    "Na gode"

 Ta amsa, tayi alwala har tayi sallah bataji ya shigo ba, gari ya fara wayewa shiru Rabi'ah bataji koda motsin Ahmad ba.

  Da taji shirun ya mata yawa, ta tashi ta fita matar gidan na wanke-wanke ta kama mata, da yake daman a gida tana taimakawa en aikinsu idan bata komai, suka gama zatayi shara shima ta amsa ta mata, Rabi'ah da bakinta bai shiru tanayi tana bata labarin bikin da sukaje da yanda sukai ta motarsu, saida suka gama sun zauna gari harya fara haske, gabanta sai fargaba yake to ina ya shiga ya barta?

  Ta kalli matar tace "waini wancan mutumin bai faɗa miki inda ya tafi ba?"

  "wanne mutumi? Mijina ne fa sarar itace ya shiga daji"

   "A'ah bashi ba, wannan saurayin da mukazo tare"

  "Awwh mijinki kenan, sanda ya tafi ina sallah gaskia"

  "na shiga uku, badai guduwa yayi ya barni a wurinnan ba" 

  "guduwa kuma kaman yaya? Ba mijinki bane? Haba ya za'ae ya tafi ya barki?" sai tambayoyi take mata, ita kam Rabi'ah hankalinta a tashe, sai gashi sun hangoshi yana tafe, fararen kayannan nashi duk sun ɓaci da baƙi, fuskarta cike da masifa take kallonshi, anma ganin matarnan ya hanata magana.

   "harkin tashi kenan? Ina can wurin gyaran mota sai yanzu aka kammala, zamu wuce ko?"

  Sai sannan ta sauke ajiyar zuciyah, "bara in ɗauko mayafina"

  "zaku wuce da safennan? Kun tsaya dai ko kalaci kuyi ko, gashi mai gidan ma bai dawo ba" inji matar gidan.

   "haba ba wani abu, ae munga wuri insha Allah zamu dawo, ƙara mu isa gidan da wuri don nasan duk hankalinsu ya tashi"

  "tohm Allah ya kiyaye hanya, Allah ya kaiku gida lafiya"

  "Ameen mun gde fa, Allah ya saka da Alkhairi"

  "Ameen"

 Suka kama hanya, har zuwa wurin da motarsu take, suka kama hanyar katsina, da yake cikin ƙaguwa take su isa gida ko hankalinta zai kwanta, sai tayi shiru ba taƙalen masifa, shima ya maida hankalinshi akan tuƙi.    


  Yayanta da ko runtsawa baiyi ba a ranar, tsabar fargabar inda Rabi'ah ta shige, ya tasa ƙofa da wayarshi a gaba, ko nan da can bai zuwa don gani yake kamar yana tafiya za'azo nemanshi da maganar Rabi'ah ko kuma a mishi waya bai kusa, gidajen radio kam da duk kafafen yaɗa labarai, ga ofisoshin en sanda tun daga kano har katsina babu inda bai sa anyi sanarwa ba, gidan tunda safe harya fara cika da en uwansu ana jajantawa juna, shikam duk hankalinshi ba'a jikinshi yake ba.

  Ita dai Auntie deejah bakinta ya kasa shiru, sai maganganu take, ita da take zaune da Rabi'ah ita tasan halinta, ta fita sanda taga dama tayo kwanakinta sannan ta dawo, bata jin maganarta kullum yawo cikin gari, samari kala-kala take tarawa, su fita yawo sai dai saurayi ya ajeta, maganganu dai gasunan tanayi tana ƙara ƙirkirowa, wasu sun yarda wasu kam basu yarda Rabi'ah zatayi haka ba.


©Rabiatu sk msh

©Ruksad Mom siyama

[3/17, 19:25] Sisinah: [8/23, 09:22] Rabiatu Sk Msh: ♡♡MAFARIN SO♡♡

  ♡♡♡♡♡♡♡♡    

     ♡♡♡♡♡

       69-70


©Rabiatu sk mashi

     ®NWA

And


©Ruksad

     ®EWF


Rerbeeart_sk @wattpad


www.babymsh.blogspot.com


Suna tafiya a hanya, Ahmad ya lura da Rabi'ah duk taa damu, fuskarta babu walwala, 

   "ke lafiyanki kuwa?"

  "ina cikin tashin hankali, nasan Yayana dole ya damu da rashin komawa na gida jiya, anma bansan wacce irin tarba zaimun ba, bansan mezance mishi ba"

   Sai daya nisa sannan yace "cikin abubuwan da suka faru jiya, akwai abunda bazaki iya faɗa ma yayanki bane?"

   "A'ah"

 "Yayanki ya yarda dake ba?"

    "eeh"

  "tohm ki faɗa mishi gaskiyar abunda ya faru, zai fahimceki"

  "tohm anma don Allah zakamun abu ɗaya?"

  Kallon Rabi'ah kawai yake, a ɗan lokacin daya santa, bai taɓa ganin wannan yanayin a tare da ita ba, lallai Yayanta nada muhimmanci a wurinta.


[11/6, 13:57] Rabiatu Sk Msh: "ki faɗi kawai"

  "don Allah muje gidanmu a tare, ka ƙarama Yayana bayani"

  "haba! Amanarki fa aka bani, ai dolene in kaiki har gida insha Allah"

  Jinjina kai kawai tayi taci gaba da kallon titi, lokacin sun isa cikin garin katsina, tana mishi kwatance da sannu har ƙofar makeken gidansu.


Tunda aka buɗe gidan taga alamar da mutane gabanta ya fara faɗuwa, mai gadi na ganin itace ai ya danƙara a guje faɗama yayanta, ta fito daga motan tace Ahmad ya gyara parking ya shigo.

  Kusan ƙofar shiga falon sukaci karo da Yayanta, Auntie deejah na biye dashi, kwantar da kanta tayi a kafaɗarshi ta fara kuka,

  Shikam Yayan nata duk a ruɗe yake yama rasa mezaice mata, cikin tsawa Auntie deejah tace,

  "Ya zaki wani fasawa mutane kuka bayan tashin hankalin da kika sakamu?"

  Hannu ya saka ya dakatar da ita, "banson jin komai yanzu, share hawayenki Ƙanwatah, idan kinyi wanka kin shirya kya faɗamun abunda ya faru"

   ajiyar zuciyah ta sauke, yayanta akwai sanyin hali da fahimta


 "kamanya tayi wanka ta shirya? Duk hana idonka barcin da kayi badon kaji abunda ya tsaida ita bane?"

   "badon inji abunda ya tsaida ita bane, don insan halin da take ciki"

  Wani ƙanin babansu ne da yake cikin garin yace "bai yiwuwa, ƙara dai ta faɗa mana inda ta kwana"

  Gabanta ya ƙara faɗuwa, anma da yake ta yarda da gaskiyarta, ta buɗe baki ta fara musu bayani.

  "lokacin da mukayi waya na taho, to a hanyane motan ta lalace"

  Cikin tashin hankali yayan nata yace "motah ta lalace miki cikin dare? Ya kikayi kenan? Ina motar taki?"

  "ba'a motatah bane, bani kaɗai bace"

   "keda wayene?"

  "nida shine"

    Ta nuna Ahmad da ke dai-dai shigowa, kowa ɗakin tsit yayi saboda wutan data ɗauke musu.

  Sai Aunty deejah dake ta faman tafa hannu,

   "Alhamdulillahi, yau dai gashi gaskiyata ta fita a gaban kowa"

  Girgiza kai kawai yake cikin jimami, "da motanki kika fita a gidannan, anma bada motanki kika dawo ba, kuma ta lalace muku a hanya ke dashi, a tare kuka kwana kenan?"

  "eeh Yayana, anma...."

 Kafin ta ƙarasa ya kwasheta da wani wawan mari, da sauri ta saka hannu ta dafe, tana taɓo kunnanta da take tunanin ya faɗa ciki🤣.

  Idanunshi jawur yake kallanta, ya tafi kaman zai faɗi da sauri ya riƙe kujera, juyawa yayi zai bar falon.

   "don Allah Yaya kayi haƙuri ka saurareni"

  "ba yanzu ba Rabi'ah, na saurari duk abunda nakeson ji daga gareki, kin riga da kin shafe duk wata yarda dake tsakaninmu"

  Zaro idanu tayi tana kallonshi, "ƙwarai ma kuwa, kinci amanata, kin cuci kanki, Allah ya gani tun tasowarki nake ƙoƙarin kare miki mutuncinki, duk wani gata na duniya na nuna miki shi, na soki fiye da yaran dana haifa, na fifita soyayyarki fiye da yanda nake son kaina, da abunda zaki sakamun kenan?"

  Kuka kawai take tana girgiza kai, ta rasa kalmomin da zatayi amfani dasu wurin kare kanta, ga Ahmad tsaye sai zufa yake ko kaɗan bai ɗauka Al'amarin zaiyi zafi haka ba.

  "ji yanda kika tsayamun a wuri, Rabi'a wa kike tunani zai kalleki a wannan abun da kika aikata ya aureki? Wazai auri macen data kwana da wani namijin a waje?"

   "ni zan auri Rabi'ah"

 Gaba ɗaya kallo saiya koma kan Ahmad da baisan sanda ya furta hakan ba, kallonshi yayan nata yake da rinannun idanunshi ko ƙiftawa baiyi.

  Ahmad yaɗan fara inda-inda, "ina nufin idan ka amince, zanso ka bani auren Rabi'ah"

  Ba tare da wani shawara ba Yayan nata yace "ka shirya nan da sati ɗaya" ya miƙe yabar falon ko kallon Rabi'ah baiyi ba da zuciyarta ta kusa bugawa.


Alhamdulillahi

Kuci gaba da haƙuri damu dai masoya, karkuji shirun yayi yawa, shiyasa zamu ɗan dakata anan, insha Allah zakujimu a cigaban MAFARINSO, wanda muka canja ma suna zuwa MATAR AHMAD, ku kasance damu a ranar farko ta sabuwar shekara donjin cigaban wannan labari.

  Akwai fa rikici da yawa a gaba.

  Shin Rabi'ah zata amince da Auren Ahmad? Ahmad yanason Rabi'ah kuwa? Ya rayuwar aurensu zai kasance idan kuka tuna kullum cikin faɗa suke? Gaskia zata fito kuwa? Shin wanene Ahmad ma? Ina fatan dai baku manta da labarin Abdullahi ba.... Domin jin amsoshin tambayoyinnan saiku kasance damu a cikin littafin MATAR AHMAD


Rabiatu sk msh

Ruksad mom siyama

Tags: #Ahmad #Rabi’atu #mafarinso
3422
1
7
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

2019-09-05 11:54:52

2019-08-19 20:36:32

2019-06-14 19:04:49

2019-04-22 23:42:50mafarin so 2