Kwaiseh Maryamerh!

Written by Maryamerh AbdulPublished on 2018-12-14 23:08:58Category Historical FictionRungumeta yayi yana cewa ''nayi kewarki nima sosai'' ya cire mata hijabin jikinta da d'an kwalinta yana shinshinar gashin kanta, yace ''nayi kewar shak'ar k'amshinki'' ya shafa hannunta yace ''laushin jikinki ma duk nayi kewarsu, kuma ai ke kika hanani keb'ewa dake dan fushi dani kikeyi'' ta sauk'ar da numfashi tace ''matarka tana gidan kake son in sake dakai? Ni fah ina tsoron ta dake ni, wallahi ta fini girma da jiki''. Dariya sosai Abakar yayi sannan yace '' tunda kin hak'ura ki tashi mu tafi, nan mutane zasu iya kallon min ke kuma ina kishi'' maryamah tace ''kishi? Kishin me?'' Ya d'aga mata gira yace ''eh, ni nasan meh nake kishi, hancin nan ma...'' ya ja hancinta sannan ya cigaba ''banson ana kallonshi bare sauran jikinki'' dariya sosai Maryamah tayi sannan ta d'aura d'ankwalinta ta sa hijabi suka bar wurin tags: #shuwa #kwaiseh #romance #soyayya#qaddaraDuba was labarai »

KWAISEH MARYAMAH

 

Alk'alamin Maryamerhabdul

 

Sai da ta gama dungurawa sannan ta dauki kwaryanta ta daura akai da k'yar. Haka ta zagaye garin nan kab babu wanda ya siya ko na biyar, banda harara da tsaki babu abinda ta samu, in da sabo ta saba, dama 'yan garin ba sayan abu sukeyi agunta ba, banda yaranta ma bazata tsaya yawo ba dan babu mai saya ta sani, kullum sai dai taje k'auyensu saleh sannan ake dan mata ciniki, yau kam bata fito a sa.a ba, dan ta zagaye k'ayensu saleh ma naira ashirin ta samu. Yamma liqis sannan ta kama hanyan dawowa k'auyensu Cike da fargaba da tsoron hukuncin da za ayi mata, in tayi ciniki ma ya take k'arewa bare yau naira ashirin kawai ta samu. Tun daga nesa saleh ya hangota, da gudu ya iso gunta, ta dan firgita da ta ganshi sannan ta saukar da ajiyan zuciya. Ta gaidashi da shuwa ya ansa, ya sauqar mata da kwaryan sannan yace mata kinyi sallah kuwa? Magariba tayi fah, nima yanxu gida nakeson zuwa inyi sallah, kinga shanun mu can ya nuna mata da yatsa, ta girgiza kai hade da cewa a'a banyi ba. Yace toh barin kawo miki ruwa kiyi alwala, akwai mayafi ma sai muyi sallah anan kafin kije gida koh? Ta kada kai kaman k'adangaruwa sannan ya tashi ya tafi dan dauko mata. Ta fara alwalan kaman yanda yake koya mata, yana kallonta ko zata kuskure a wani wurin dan ya gyarata, duk wani gaba in ta wanke sai ta dakata ko zai gyarata sannan tacigaba in taga yayi shiru, kuma Alhamdulillah tayi shi daidai kaman yanda kullum yake koya mata in suna tare. Ya bata dan guntun mayafi da zai rufeta kirib sannan yace tayi sallah shima zaiyi alwala. A gun yin salla ne yaga dungurawa kawai takeyi, shi bai taba ganin tana sallah ba sai yau, dakatar da ita yayi yace ta jirashi, yayi alwala shima ya shimfida mayafi Ya ja su sallah, a bayyane yake karanto suratul fatiha sannan ya kara da wani sura da ke cikin qur'ani, in kikaji zazzak'an muryansa kya rantse ba mai kiwon shanu bane ke rero ayoyi cikin k'ira'a mai dadin sauraro, Ita kam maryamah bata san abinda yakeyi ba, in yayi sujada ta bishi haka in yayi ruku'u, kaman yanda yace tayi yanda yayi haka takeyi, ta so yin karatun da yakeyi ma ta kasa sannan tayi shiru amma bakinta na motsi, dan in yace meh yasa batayi tace tanayi a zuciyanta, wai wayo tayi masa kenan. Har suka idar da sallah yayi sallama ita ma tayi yanda yayi, ta waiga dama tayi motsi da bakinta haka ta waiga hagu tayi motsi da bakinta. Sai da ya gama tasbihi yayi azkar sannan ya shafa ita ma ta shafa. lokacin da suka idar har duhu ya fara, Ya bude kwaryanta yaga kindirmo, ya bude k'ananan duk babu wanda aka saya, ya tambayeta na nawa ne dukka ta fada masa dari shida da hansin ne, ya ciro ya mika mata sannan ya juye kindirmon a leda, haka man shanun ma ya juye a leda, cike da mamaki take kallonshi, meh zakayi dashi dukka tace, yace ina ruwanki, ya daure ledan ya daura akansa yace jira ni anan in kora shanu sai inzo in raka ki dan dare yayi

 

A hanyansu ta komawa yana rakata yana koya mata yanda ake sallah, in ya fada mata da baki yaga alaman bata gane ba sai sunje inda akwai wuta sannan ya gwada mata dan tafi dauka da kyau, har suka isa cikin gari lokacin duhu yayi sosai, tace masa ya koma anan kada a gansa aje a fadawa amty babbe, baiyi musu ba ya miqa mata kwaryanta da yasa mata kwanukanta guda uku aciki, har ya juya Ta rik'e hannunsa, juyowanda yayi dan ya fuskanceta da mamakinsa yaga hawaye a fuskanta, lafiyanki? ya tambayeta. Bata sake hannun nasa ba Daidai nan kanwar amti babbe ta yanko kwanan da suke, kuma akwai wuta kyal agurin, tana ganinsu ta koma da gudu dan kada su ganta, tafison taga komai sannan ta kai gulma wa amty babbe, daga gidanta take yanzu ma. Maryamah Kuka takeyi harda shessheka, fuskanta yayi jawur abunki da farar mace, ajiye gwiwowinsa yayi a kasa ya rik'e kafadunta yana tambayanta meh ya faru, hajje kanwar amty babbe na can tana lekensu, ta daura hannu a bakinta wai mamaki takeyi, maryamah ta zama 'yar iska. Haquri saleh yake bata sannan ta tsagaita kukan ta fara masa godiya, irin godiyan da take masa har ya wuce daidai shekarunta, mamakin irin tunani da baiwan da Allah ya mata yakeyi, kaman daga sama yaji tana cewa Allah ya kawo abinda zan iya biyanka dashi, kayi min komai kuma nagode, sai da ta gama yi masa duk addu'o'in da ta iya sannan Saleh ya sauqar da ajiyan zuciya yace babu komai maryamah, ki wuce gida yanzu dare yayi kinji, ta gyada kanta sannan sukayi sallama ya wuce ita ma ta wuce gida. Hajje da gudu ta isa gun amty babbe a cikin bukkanta har bacci ya fara dibanta taji an shigo mata da gudu, a firgice ta tashi tana kallon hajje tana cewa wa ya biyoki? Nan hajje ta zayyanewa amty babbe karya da gaskiya, tun kafin maryamah ta shigo gidan ta fara jin zagi, yarinyan nan zata raba ni a gari, da shekaruntan nan har ta fara son aure, Maryamah na shiga gida ta ga amty babbe da hajje a tsakiyan gida suna jiran isowanta, ko kwaryan bata ajiye ba taji bugu saida taji kaman k'ashin bayan ta ya karye, Haduwa sukayi su biyu suka hau ta da duka, Ammi malud mijin amty babbe yana bukkansa kaman baya jin bugun da ake yiwa maryamah, mikewa yayi akan dan karamin gadonsa yana lumshe ido ya juya wa kofan dakin baya, dukanta sukayi kaman sun samu kayan wanki amty babbe na mata Allah ya isa, sai da suka ga ko motsi batayi sannan amty babbe ta janye kudin Hannunta tana k'ullewa a bakin zani tana cewa aure kawai zan miki kafin ki ja min abin kunya, hajje tunda bikin ki ya kusa kawai sai a hada ku in huta koh? Gyalen da yake kafadanta ta gyara tana bata fuska sannan tace haka kawai a hada ni da aure da 'yar yarinyan nan, ko angumma bata kai ayi mata ba sai a hadani aure da ita bayan ni na fara shekara biyu kenan yanxu, ki bari dai ayi nawa sannan ayi nata gaskiya (Angumma style ne da 'yan mata ke yi a kansu, mace in ta kai shekara sha-daya zuwa sha-biyu zata fara angumma, yara 'yan k'anana kuma ayi musu guddiye, shi kuma raba gashin akeyi sama da kasa, sai a taro na saman a hadeshi gu daya ya zama a cunkushe a shafa masa sabulun salo ko wani abu da zai kame gashin, bayan kuma a kitsa shi kasa ko a kamasa guda daya)

 

   ''Kuma Amty kada ku had'ata da wancan yaron da na gansu, yana sonta kuma kinsan garken shanun sa?'' Ta tabe baki sannan ta cigaba ''Sadakinta zai wuce nawa kuma kinga ta fini kenan'' Amty Babbe tace ''kin kawo shawara, daga cikin kwayam din nan zamu bincika mu samo mata d'aya, basu da shanun sadaki sai k'ananan dabbobi'' Har suka gama yanke shawaran yanda zasuyi Ammi Malud bai lek'o ba da alama yayi bacci, haka ita Maryamah ko motsin kirki batayi ba har hajje ta fice daga gidan murna fal ranta. Hajje yarinya da bazata wuce shekaru goma sha uku ba, fara ce sol ga jiki, tana da kyau daidai misali dan baza a qirata mummuna ba, k'anwa ce agun Amty Babbe. Daga cikin al'adun shuwa arab, yarinya bata wuce shekara goma sha uku zuwa sha hudu batayi aure ba, shiyasa daga yarinya ta kai sha d'aya ake mata angumma dan ta zama 'yan mata, Kuma daga ta shiga shekara goma sha uku za'a nemo mata miji ba tare da sanin yarinya ba, wasu basu taba ganin juna ba ma ko a titi.

    Hajje ma hakan akayi mata, dan yanxu ana shirye shiryen biki ma bata san wanda zata aura ba, saidai taji sunan babansa kuma tasan irin shanayen da yake kiwo. Ko hanya basu hadawa da surikansu, indai surikansu suna wuri toh babu su babu zuwa wannan wuri sai sun bar wurin, haka zalika ko a titi suka zo wucewa ta hangota a nesa ko aka fada mata ga surikarta gudu zata diba sai tayi nisa yanda bazasu ga juna ba sannan ta tsaya, sai ta wuce sannan ta dawo. Duk hakan yana daga cikin d'abi'un su na nuna kunya da girmama surukai.

   Maryamah na kwance inda aka barta sai wurin k'arfe uku na dare ta iya motsawa, tayi k'ok'arin mik'ewa ta kasa ga yunwan da ya addabeta, cikinta sai kuka yake tsaban yunwa, rabon ta da abinci tun nono mai tsamin da ta samu da safe cikin kwano ta kwankwad'a babu suga, Da jikinta ta jawu wurin k'waryan kindirmon da ta shigo dashi d'azu ko zata samu na jik'a mak'oshinta, bata tunanin bacci zai d'ibeta da yunwan da takeji kaman ya kasheta. Harshenta take sawa ta lashe kindirmon da yake jikin kwaryan hawaye na zirya a fuskanta, sai da ta lashe tas sannan ta ja jiki ta rakub'e a bukkan ammi malud, in kaga kwaryan yanda ta lashe shi ka rantse ruwa aka sa aka d'auraye. Bacci mai nauyi ne ya dauketa duk da sanyin da takeji har cikin k'ashinta, haka ta daure ta duk'unk'une agu daya

 

    Garin Kaduna:- Fad'ime kyakkyawar mace ce fara tas tayi kwalliya ta sha dauri, atamfa ta sa fitted gown kalan ja, ya bala'in yi mata kyau, kwance take bisa kujera a falonta tana karatun newspaper (jarida), banda k'amshin turarenta da turaren wutan da ke tashi babu abinda zakaji a k'ayataccen falonta, falo ne da ya hadu da kayan alatu, yawancin kayan da aka k'ayatar da falon brown ne, masha Allah, murmushin da yake fuskanta shi zai tabbatar maka tana cikin nutsuwa, farinciki da kwanciyan hankali, Kaman daga sama taji an fado cikin falon ko sallama babu, d'ago kan da zatayi dan taga d'an rainin hankalin da ya shigo mata gida babu sallama sai ido hudu sukayi da surukarta uwar mijinta... Dirowa tayi k'asa tana k'irkiro murmushi kanta a k'asa tana yi mata sannu da zuwa, mama Zainaba kallon k'urilla takewa Fad'ime, daga sama har k'asa take kallonta, fuskanta bai nuna yanayin da take ciki ba, bata murna kuma bata bak'in ciki, ko ansa gaisuwan da fad'ime ke mata bata yi ba sai kallonta takeyi, fad'ime kanta a k'asa tana mamakin surikar nata yau? A ranta take cewa ''Ban tab'a ganin mama Zainaba haka ba, hasalima kullum da fara'a take zuwa kuma tana sona sosai, ko wani laifin nayi?''

    Sauk'ar da ajiyan zuciya mama Zainaba tayi sannan tace ''lallai ina da babban aiki, wai ke 'yar boko koh? Toh toh naga alaman dan ban taba miki rashin mutunci ba yasa kika raina ni kika raina maganan da nake fada wa mijinki, na tabbata yana fada miki, Tunda shi bazai iya d'aukan mataki ba na dawo kanki, shi bazai min kara ya saki ki ajiye boko ki haiho min jikoki ba ni barin sanar dake da kaina'' ''Fad'ime'' ta k'ira sunanta, Fad'ime ta ansa da ''na'am mama'' Mama Zainaba ta matso kusa da ita ta zauna kan kujera sannan tace ''jikoki nah nake son gani sun cika falo da kujeru ba kullum in na shigo in ganki ke d'aya kin hakimce akan kujera ba'' taja numfashi sannan ta cigaba ''nayi hak'uri Naga abun naki ba na hak'uri bane sai na fito fili tunda bakisan kaara ba'' Mama Zainaba taja tsaki tace ''haba, shekara bakwai ko b'ari babu, ni ina na taba ganin irin wannan auren'' Fad'ime kanta a k'asa ta kasa furta ko kalma d'aya ne, sai da taji mama tai shiru sannan tace ''kiyi hak'kuri mama, insha Allah zaki ga jikanki ba da jimawa ba''

 

   Hawayen da take karewa tuni suka zubo, ita kanta wannan rashin haihuwa nata yana damunta bare uwar miji, tabbas bata taba samun matsala da uwar mijinta har tayi mata masifa haka ba sai wannan karon, kuma bata ga laifinta ba, ba wani maganin tsare haihuwa da take sha, babu inda basu je ba ita da mijinta akan haihuwa Amma Allah bai kawo ba. Fad'ime ta sake cewa ''mama kuma maganan magani da kikace ina sha dan kada in haihu ba haka bane, hasalima ni tun da nake ban taba shan wani kwayan magani dan ya hanani haihuwa ba, lokaci ne kawai baiyi ba'' mama Zainaba ta dakatar da ita da cewa ''ya k'ara aure, in ya k'ara aure ya haihu sai ke ki jira naki lokacin bayan na samu jika'' tana gama fadan haka ta tashi ta fice fuuu kaman iska. Bata d'auki lokaci mai yawa ba sai ga ta da gingimemen akwaiti tana ja, ko kallon fad'ime da ke cewa ta bari zata shiga mata da akwatin batayi ba, dakin da take sauk'a in tazo ta shige ta buga k'ofan garau, har Fad'ime ta tsorata A ranta tace wannan k'aton akwati ba na tafiya yanxu bane kaman yanda ta saba yin sati daya zuwa biyu. Ta dage kafad'a alaman ba ruwanta sannan ta shiga kitchen dan hada mata abinci. Da ta gama hadawa ta kai mata har daki Yau ''nagode'' kawai ta samu daga gun surukarta ba kaman da da in ta kai mata abinci sai anyi mata addu'a daga ita har iyayenta ba. Fad'ime a ranta tace Allah ka bani haihuwa...

  Gidan Eng. Abakar Jidda kenan, asalin dan jihar Damaturu, a can aka haifesa yayi makarantar sakandare, bayan ya gama ya wuce A.B.U zariya. Shi kadai mahaifiyarsa ta haifa, mahaifinsa ya rasu shekaru biyar da suka wuce. Bayan ya gama degree yayi bautan kasa a garin maiduguri sannan ya wuce masters. Ya hadu da Fad'ime matarshi tun lokacin da yaje bautan k'asa maiduguri, asalinta 'yar maiduguri ce, acan tayi makarantan ta har degree inda ta karanta business admin, sai da eng. Abakar Jidda ya gama masters sannan akayi aurensu cikin jin dadi da yaddan juna. Aiki ya kawosa garin kaduna. lokacin da mahaifinsa ya rasu yaso ya dauki Mama Zainaba su dawo Kaduna amma fafur tak'i binsa, tana zuwa musu tayi sati biyu ta koma amma tak'i dawowa tare dasu gaba daya. Mama Zainaba mata ce mai hak'uri da kaara, Hakan yasa suke shiri da kowa, har surikarta zaman lafiya suke da juna, ta dauketa kaman 'yarta, duk zaman da sukayi basu taba samun sabani ba sai yanxu da take neman jika ido rufe kasancewan ita ma d'a d'aya tilo Allah ya bata shine Abakar. Wannan kenan

 

 Eng. Abakar Jidda gurfane gaban mahaifiyarsa kansa a k'asa yana sauraron fad'a da umarni da take bashi akan lallai ya k'ara aure tunda Fad'ime bata da ra'ayin haihuwa yanxu, ta inda take shiga ba ta nan take fita ba, tunda yake bai tab'a ganin bacin ran mahaifiyarsa irin yau ba, hak'uri kawai yake bata tak'i sauraron sa. Sai da tayi masa ta tas sannan tayi shiru, hak'uri ya bata sannan ya k'ara da cewa ''lokaci ne bai yi ba mama, in ba haka ba munje asibiti ba sau d'aya ba ba sau biyu ba, ita ma fad'ime na son haihuwan nan fah mama, bakiga yanda take damuwa bane, amma kiyi hak'uri insha Allah komai zai daidaita yanda kikeso'' mama Zainaba ta sauk'ar da ajiyan zuciya tace ''tunda ita Allah bai kawo mata haihuwan ba ka k'ara aure nace, ko bakaji meh nace ba?'' Ya susa kai yace ''mama ki dan k'ara min lokaci, wata k'ila Allah ya kawo mana mafita'' mama zainaba tace ''ai dama nasan da bakinka a k'in haihuwan nan, in ba haka ba matan nan har shekara bakwai babu haihuwa?'' Tayi shiru alaman tana tunani daga bisani tace ''na yadda na k'ara lokaci, amma gobe gobe kuje asibiti a sake bincikan ku, ni ban yadda lafiya k'alau ba abin naku'' haka dai suka gama magana akan gobe da safe zasu je asibiti ganin dr. Kafin ya wuce office. Sai da ya tabbatar hankalin mahaifiyarsa ya kwanta sannan ya bar d'akin yana mata sai da safe ya wuce gun matarsa Fad'ime abar k'aunarsa.

   Bude k'ofan d'akinta yayi ya shiga ba tare da ya rufe k'ofan ba, shesshek'an kukan Fad'ime ne yayi masa barka da zuwa, wutan d'akin a kashe yake babu haske ko kad'an, amma da yake k'ofan a bud'e sai haske ya hasko cikin d'akin kuma daidai inda take zaune wutan ya hasko, tana zaune a k'asa ta d'aura hannayenta bisa gwiwowinta ta d'aura kanta akai, kuka take yi sosai da alama ta jima da fara kukan, yana daga bakin k'ofa ya kasa k'arasowa gunta, ya hard'e hannayensa bisa k'irjinsa yana kallonta, yayi minti biyar a haka bai motsa ba daga bisani yayi ajiyan zuciya ya iso ta dan ya rarrasheta, ya tabbata taji maganan da sukayi da mama, dan taje d'auko masa ruwa kafin ta dawo mama ta fara masa maganan, kuma yaga inuwan ta zata shigo dakin sannan ta fasa, wato shine tazo ta zauna anan tana kuka. Ya lumshe kyawawan idanunsa a ranshi yana k'iran sunan Allah, ya isa inda take Ya zauna gefenta sannan ya janyota zuwa jikinsa, hannunsa ya d'aura saman kanta yana mayar da gashin kanta baya, ya fara shafa bayanta, sai da ta fara sauk'ar da ajiyan zuciya sannan ya fara mata magana ahankali yana rarrashinta, sosai ta nutsu tana jin kalamansa da kullum yake sata jin babu wata a duniya sama da ita, kalaman Abakar na sa ta manta duk wata damuwa da yake addabarta, kasancewan ta dashi yafi komai soyuwa a ranta, kaman a mafarki taji yana ce mata ''babu wata da zata haifa min 'ya'ya sama dake Fad'ime, ke kad'ai zuciyata ta aminta da ki haifa min yara, kuma ke kadai na yadda zaki iya bawa yarana tarbiyya yanda addini ya koyar'' ya sauk'ar da numfashi sannan ya k'ira sunanta ''Fad'ime'' ya d'agota daga jikinsa yana kallon kyakkyawan fuskanta da yayi jawur dan kuka, hannunsa yasa ya goge mata hawayen

 

  Yace kiyi hak'uri ki daina sa damuwa a ranki, ina sonki kuma babu wacce zata samu gurbi a zuciyana, zan zauna tare dake har abada. Ta d'ago rinannun idanunta ta d'aura akan fuskansa, murmushin farinciki ne ya kubce mata, shafa gefen fuskansa tayi sannan ta bashi peck (sumba) a kumatu, tace ''nagode mijinah abin alfaharina, nagode da son da kake nuna min, Allah ya bar min kai ya barmu tare'' dariya dukkansu sukayi sannan suka d'ale gado dan samun hutu.

  Fad'ime bacci mai nauyi yayi gaba da ita tana kwance bisa faffad'an k'irjin mijinta Abakar, shi kuma ya lumshe ido bacci ya gagara d'aukansa, tunanin mafita yakeyi kuma da alama bazai samo mafita ba. Bud'e idanunsa yayi ya kalli matarsa cike da tausayawa, Ya gano matsalan da yake addabansu, amma babu abinda zai iya yi akai, ya gwammace ya rik'e wannan sirrin a ransa shi kad'ai, kuma ya d'auki alk'awarin ko ta yaya bazai bata wa matarsa rai ba, zai zauna tare da ita har mutuwa, zuciyanshi ya tsinke da ya tuna mama Zainaba, ya zaiyi da umarnin da mama ta bashi na k'ara aure? a fili yace ''mama kiyi hak'uri, zanyi miki k'arya dan in Kwantar miki da hankali, ina sonki mama, kuma bana son b'acin ranki, amma babu wani hanya da zan iya bi dan kwantar da rikicin da yake shirin taso min ni da iyalina, fad'ime na da hankali, ta cancanci inyi mata komai sabida biyayya da son da take nuna min'' ya lumshe ido hawaye ya zaryo kuncinsa ya sa hannunsa ya goge sannan ya gyara kwanciya... toh fah, wane sirri ne eng. Abakar ke b'oye mana? Ku biyoni dan jin wannan sirri...

   A Garin Godil, kaman kullum Maryamah ta janyo jakinta da kwanon d'iba ruwanta har bakin Rafi dan d'ibo ruwa, duk da ciwon da jikinta yakeyi haka ta dage ta isa inda ta saba tsayawa kafin mutane su gama d'iban ruwansu, dak'yar ta iya janyo dutsi dan ta zauna, duk ilahirin jikinta yana mata ciwo, amty Babbe na dukanta amma bata tab'a shan duka irin na jiya da dare ba. Bata jima da zama ba ta hango k'awarta tilo Khajije tana tunkarota da gudu, waige waige ta fara yi dan taga ko akwai mutum a kusa, bata son a ganta tare da khajije, dan dukan Khajije Akeyi a gida in Khajije ta tsaya da ita, sauk'ar da ajiyan zuciya tayi bayan ta tabbatar da babu wanda zai iya ganinsu, Khajije da ta iso kasa magana tayi sai nishi da take sauk'ewa, gudun da tayi yasa duk ta gaji sai da ta zauna a k'asa, ta d'au minti uku sannan ta iya magana, Maryamah kallonta kawai takeyi ba tare da tace mata komai ba, Khajije tace ''jiya kinga na gudu koh? Ai naji amty Babbe na dukanki shine na gudu gida kada ta fad'awa Baba nima a dakeni'' ta cigaba da jan numfashi sannan ta cigaba ''Maryamah yanxu ki bani kwanonki, ko kuma akwai kwarya a can, kullum zan dibo miki in kawo miki nan sai ki tafi gida ko amty Babbe zata daina dukanki akan lattin kawo mata ruwa'' Maryamah ta ware ido sannan tace ''Khajije kina da hankali kuwa?'' Ta girgiza kanta sannan ta cigaba da cewa ''a'a nikam, gwanda ni na saba shan duka, ke kuma ranan da aka gano abinda kikeyi wallahi bazaki ji dad'i ba'' Khajije tace ''babu ruwanki, ni da nace zan kawo miki ai nasan yanda zanyi babu wanda zai gane'' dak'yar ta samu ta lallab'a Maryamah ta yadda, taje ta d'ibo ruwa ta kawo mata, ta tayata suka d'aura akan jaki, d'aya ta rik'e d'aya tana d'aurewa da igiya, sai kun gansu kikir-kikir yara 'yan k'anana suna d'aura ruwa kan jaki, har suka gama babu wanda ya gansu, Maryamah tayi mata godiya har da k'wallanta sannan ta wuce gida, duk da ta samo ruwa da wuri zuciyanta bai daina bugu ba, ta tabbata amty Babbe sai ta samo wani abin in har taga ta fara kawo mata ruwa da wuri, tana tunkarar gida zuciyanta na tsananta bugawa. Har ta isa bata da nutsuwa, tana shiga harabar gidan tayi ido hud'u da amty Babbe, tuwo ne a bakinta ta tsaya kallon Maryamah, ido da bakin duk a bude, bata yi tsammanin ganinta warhaka ba, ta rufe idanunta ta sake budewa ta ganta tsaye da jakin ta a baya kuma ga ruwa kan jaki, Tace ''maryamah ina kika samu ruwa?'' Zuciyanta sai da ya kusa fashewa dan batayi tunanin za a iya tambayanta ina ta samu ruwa ba? Yanxu meh zata ce, idon nan narai narai alaman bata da gaskiya, ta kasa furta ko kalma daya ne, sai da amty Babbe ta taso ta iso gunta ta sake tambayanta ''ina kika samo ruwa nace?'' Idanunta kan fuskan Maryamah tana son gano ansan tambayanta amma ta kasa ganewa

 

   Tsawan da amty Babbe tayi wa Maryamah shi ya dawo da ita daga tunanin da ta shiga na lalubo ansan da zata bata, sai da ta had'iye miyau sannan ta iya cewa ''dama... da naje.......'' Amty Babbe ta sake daka mata tsawa ''dama da kikaje meh?''

   A take taji wani courage ya zo mata tace '' Eh da naje naga babu kowa shine na d'iba kafin su zo, kuma haka zan na yi kullum dan in dawo da wuri'' kanta a k'asa zuciyanta na bugu kaman zai b'allo ya fito, amty Babbe ta tsaya kallonta, zuciyanta na bata k'arya Maryamah takeyi, ko magana bata yi mata ba ta koma kan tabarmar Kaba ta cigaba da cin tuwonta.

   Maryamah da taga haka sai da ta sauk'ar da nannauyan ajiyan zuciya sannan ta fara kunce d'aurin da sukayi wa kwanon ruwan, dak'yar ta kunce ta sauk'ar dashi a hankali dan kada tayi wa kwanon lamba a samu na duka tunda ta tsallake na lattin dawowa daga d'iban ruwa.

   Bayan ta sauk'ar ta samu tsintsiya ta share cikin gidan, ta tattara komai ta kimtsa, tun kafin ta gama Amty Babbe ta figi k'yallen kayanta ta yafa ta fice (d'inkin atamfa dama na manyan mata ana cire zani biyu, d'aya na d'aurawa d'aya na yafawa, sauran yadin kuma sai ayi riga dashi, babu styl babu shape. Kaman yanda ake kayan maza haka shima yake, mai d'an tsayi amma baya kaiwa gwiwa)

    Bata jima da fita ba suka dawo da Hajje, sai yatsina takeyi ta karb'i sak'on da aka mik'a mata acikin leda ta fita, Amty Babbe ta kalli Maryamah tace ''ki tashi muje kasuwan Yadin buni (local government na damaturu)'' ''toh'' kawai Maryamah tace mata ta d'auko takalmin roba ta sa, ta dibi ruwa a hannunta tana wanke dattin da ya mayar da bak'in takalmin fari tas, tsawa amty Babbe ta daka mata

''Dan kin dibo ruwan kuma sai kin k'arar?'' Maryamah tace ''kiyi hak'uri'' bata sake magana ba haka zalika bata sake tab'a komai ba, ta wanke d'ayan takalmi d'ayan kuma da dattinshi, a tsaye take har amty babbe ta gama shirinta ta janyo k'ofan d'akinta ta fito, ta gyara mayafin ta sannan ta kama hanyan waje, ko magana batayi wa Maryamah ba, Maryamah ta bi ta a baya.

   Tun ina gudu ina binsu a baya in sunyi min nesa har na gaji basu iso ba, ga uban sauri da suke bugawa, ta cikin daji suke bi hankalinsu a kwance. K'aya sai sossoke min k'afafu yake yi, ashe sunsan inda zasu shine suka sako k'aton danfo ni nasa 'yar flat shoe dina. Sai da mukayi kimanin tafiyan minti 40 sannan muka isa cikin kasuwan Yadin-buni. Babu alaman gajiya a tare dasu, ko shan ruwa basu tsaya sunyi ba Amty Babbe ta fara cefanenta Maryamah na binta a baya

 

A b'angaren Eng. Abakar da Fad'ime kuwa tun safe suka shirya dan bin umarnin Mama Zainaba na ganin dr., tun tashin su sallan asuba Fad'ime taga Abakar sukuku bayi da wani kuzari, ta tambayeshi meh ne yace mata babu komai. Haka ta gama breakfast (karin kumallo) ta kaiwa Mama Zainaba nata sannan suka ci tare da mijinta, Abakar duk yanda yayi dan ya b'oye damuwansa sai da ya kasa, abincin ma kasa ci yayi.

Haka suka gama shiri suka fito kowa da abinda ke ransa, Fad'ime na tunanin abinda ke damun mijinta shi kuma yana tunanin zuwa gun dr. Da zasuyi a ranshi yana addu'an ''Allah ka d'aura ni akanta kaman yanda kake bani ikon b'oye mata wannan sirri a lokuta da dama'' Tun kafin su iso asibiti dama ya sanar da dr. zuwansu ta waya da yake abokinsa ne. 

 

 

Suna isa babu b'ata lokaci office dinsa suka nufa dan an basu izini, Dr. Sulaimana yayi gwaje-gwajensa sannan yace anjima zai k'ira Eng. Abakar dan ya karb'a musu result. Fad'ime hannunta sak'ale cikin hannun mijinta suka kama hanyan waje dan tafiya gida, Eng. Abakar ya dakatar da Fad'ime yana cewa ''kinga na manta wayana a office na dr. Sulaimana'' ya ciro key na mota ya mik'a mata yana cigaba da cewa ''ki isa gun motan kafin na dawo kinji'' murmushi tayi ta karb'a tayi gaba shi kuma ya koma office din cikin sauri. Yana shiga dr. Sulaimana yace ''ai na d'auka tafiya kayi ba tare da munsan abinyi ba, nifah na gaji da b'oye abin nan eng. Anya baka ganin muna shiga hakk'in fad'ime?'' Ya fadi hakan yana kallonsa.

Eng. Abakar ya furzar da iska daga bakinsa yana mai kallon k'asa, ya juyo ya kalli Dr. Sulaimana yana cewa ''kai kad'ai kasan sirrin nan, kuma har yanxu bana son kowa yaji, shawaran da na yanke akan wannan matsalan shine matsalan da aka samu daga gun Fad'ime ya dawo kaina, ko da bazaka iya gyara cikin result d'in ba ni nasan yanda zanyi bazata ga result d'in ba, kawai ka bani goyon baya dan in kub'uta daga b'ata mata rai ko b'atawa Mama rai, in har taji matsalan daga gun Fad'ime ne aure zata sani inyi kuma fad'ime bazata ji dad'in haka ba, dan bata haihuwa bai kamata in gujeta inyi aure ba, kai kasan komai kan yanda Mama ta damu da samun jika''

Dr. Sulaiman ya kasa kifta ido tsaban mamaki, baki bud'e yake kallon eng. Abakar, anya yana cikin hankalinsa kuwa? Ya had'iye miyau yace ''ka tabbata muyi hakan babu wani matsala abokina ko da nan gaba ne?'' Eng. Abakar yace ''babu wata matsala'' haka suka gama magana suka tsara komai yanda suke so sannan sukayi sallama Eng. Abakar ya wuce gida cike da jin dad'in samun nasara

 

  Da misalin k'arfe biyu ya koma ya karb'i result, anan Dr. Sulaimana yake fad'a masa zaije Damaturu yau, sukayi sallama ya wuce gida hankalinsa a kwance dan yasan matsalarshi ta warware daga yau insha Allah, shi kuma Dr. Sulaimana ya tattara abinda zai iya d'auka sannan ya shiga mota sai hanyar Damaturu, dama da shirinsa kuma sunyi sallama da matarsa akan bazai dawo gida ba zai wuce kawai, wani aiki ne ya tsayar dashi office da tun safe zai wuce damaturu gurin meeting din da ya zama kamar dole sai ya hallara. 

 

 

A kasuwar Yadin-buni kuwa sun gaji tilis musamman Maryamah da aka tara mata kayan da aka saya a cikin buhu aka d'aura mata, kaya nik'i-nik'i kuma har lokacin basu gama sayayyansu ba, yawo suke yi a cikin kasuwa har mutane na ma Amty babbe magana akan kayan yayi wa Maryamah yawa amma sai tace musu ''ai tace zata iya d'auka shiyasa'' Maryamah kaman ta k'walla ihu tace k'arya ne amma babu dama, haka sukayi ta yawo acikin kasuwan nan in amty Babbe ta gaji ta zauna k'ark'ashin bishiya ta huta sannan su k'ara gaba.

 

 

Lokacin da suka gama suka fito bakin hanya k'arfe uku da rabi, basuyi sallahr azahar ba ga la'asar ta gabato, sai da suka ga mutane na sallah sannan suma suka samu wuri Amty Babbe ta tayata suka sauk'e kayan, suka samu ruwa cikin wani randa da suka ga mutane na d'iba sukayi alwala Suka samu buhu suka shimfid'a suka fara sallah, Maryamah wani buhu ta samu ta rufe kanta dashi tunawa da tayi Saleh yace tana sa mayafi kafin tayi sallah, har Amty Babbe ta idar bata idar da tata sallahr ba, duk da bata iya karatun sallah ba a nutse takeyi kaman yanda taga saleh jiya yayi, har tayi raka'a uku ta sallame daidai wanda jiya sukayi ita da saleh. Amty Babbe bata mata magana ba ta d'aura mata kayan suka fara bin titi dan komawa gida, saman kwalta suke bi kafin su isa layin da zasu shige dajin nasu. 

 

 

Dr. Sulaimana ya d'ibo hanya da gudu, yana so ya isa damaturu k'arfe hud'u ko da rabi, yana son ya gama abubuwan da zaiyi kafin gobe da safe su shiga meeting, gudu yakeyi kaman zai tashi sama. Tun daga nesa ya hango wata mata da yarinya an d'aura mata k'aton buhu, da gudu matar ta tsallake ta bar wannan yarinya tana fama da buhu, ahankali take tafiya dan buhun yayi mata nauyi, sai da ta iso tsakiyan kwalta buhu ya fad'i ita ma ta fad'i, Amty Babbe daga bakin kwalta ta fara salati tana tafe hannu, shi kuma Dr. Sulaimana yana ganin haka ya fara rage gudun nasa, da yazo daidai ita har yayi niyyan yanka kwana ya wuce ta sai yaga toliyanta sannan ya kai ga kallon fuskanta, hawaye takeyi tana tsince kayan da suka zubo daga cikin buhun, Kallonta da yayi kawai ya tuno da abokinsa engr. Abakar da matsalarsa, ko meh yasa oho....

Ya samu wuri gefen titi ya tsaya sannan ya fito ya fara taya ta tsince kayan suna mayarwa buhu, da yake babu wani mota nan kusa hankalinsu kwance suke kwashe kayan. Daga nesa Amty Babbe ta tsaya tana cewa ''ka barta ta kwashe yallab'ai, ai ita ta zubar'' ta fad'i hakan ne da hausan da ya bashi dariya, wai ita nan ta d'auka hausa tayi, ya kalleta ya mayar mata ansa da shuwa ''a'a yaya, ai yayi mata yawa kayan shiyasa"

 

    Baki bud'e suka tsaya kallon dr. Sulaimana, Maryamah kam tsayawa tayi ta kasa ajiye murfin roban da yake hannunta, a ranta cewa take 'yan birni dama sun iya shuwa? Amty Babbe cewa tayi ''kai shuwa ne?'' Tana murmushi ta fad'i hakan, ya ansa mata da ''eh yaya'' nan ta fara masa hira ''Ai bata ji ne Maryamah, tun safe muke kasuwan nan da tafiyanta haka har yanxu bamu koma ba'' zuba take masa shi kuwa sai dai yayi murmushi yace eh ko a'a, har suka gama ya d'aure mata buhun sannan ya tambayi inda zasu je, Amty Babbe ta fad'a masa, yace toh bari ya ajiyesu tunda ba nisa, baki bud'e Maryamah ta ware ido, tun da ya iso batayi magana ba sai yanxu da tace '' ai irin motanka baya shiga garinmu''

Juyowa yayi dan ya tabbatar da inda zazzak'an muryan ya fito, a ranshi yace ''Allah yasa engr. yaga abinda ni nake gani agun yarinyar nan'' Sai da yayi murmushin da ta gano daga d'abi'unsa ne sannan yace ''zai shiga mana'' bata yi magana ba haka shima bai sake cewa komai ba, Amty Babbe baki har kunne za'a shiga mota ba akori kura ba. In ba k'auyanci ba meh zai sa in shiga motan d'an birni dan kawai yarenmu d'aya. Ko da yake shuwa dama haka suke, indai kai yarensu ne toh ka zama nasu ko yaya kake baza'a kusheka ba sai dai a yabeka.

Ya d'auki buhun ya sa a bayan mota(boot) sannan ya bud'e ma amty Babbe baya, dak'yar ya iya gumtse dariyansa lokacin da amty Babbe take shiga mota, dan kuwa ta baya ta fara shiga, Tura d'uwawun takeyi sannan ta sake juyowa tana sa kai kaman zata shiga d'akin bukka, sai da ya rik'e hannunta ya zaunar da ita sannan ya d'aga mata k'afafun yasa a mota. Sai washe baki takeyi tana cewa ''use, Use Allah barik(nagode, nagode Allah yayi albarka)''.

Ya bud'ewa Maryamah gaba ita ma ta shiga, yanda taga ya zaunar da Amty Babbe haka ita ma ta zauna sannan ta d'aga k'afafunta ta sa cikin mota. Dr. Sulaimana har cikin ranshi ya yabi k'wak'walwa da wayonta a d'an had'uwansu na yau. Haka ya shiga mota tunani fal ransa, yana tunanin yanda zai had'a murd'ad'd'en mutum irin Abakar da 'yar daji. Wannan kenan

Haka har suka isa cikin gari Amty Babbe na masa hira, ta tambayeshi ya ansa ta haka shima in tayi maganan wani abu bai gane ba ya tambayeta, anan ne yake fad'a mata sunanshi Sulaimana kuma shi d'an Damaturu ne. A d'an hiran da sukayi ya gano takuran da Maryamah take sha gun Amty Babbe, sam bata b'oye irin haushi da tsananta da takeyi, yaso ya tambayeta dalilin wannan tsanan amma yace ba yanxu ba, zai sani in lokaci yayi kuma ya d'au alwashin kawo k'arshen matsalan da Maryamah take ciki da wanda abokinsa amininsa yake ciki, farin ciki had'e da hamdala yakeyi cikin ransa

 

 

Sun isa da misalin k'arfe hud'u da rabi, shi ya ciro buhun kayan ya shigar musu dashi, Amty Babbe ta kawo masa ruwa cikin kwano an rufe shi kirib da murfi, ta koma ciki ta d'auko k'waryan kindirmo d'an k'arami ta d'aurawa Maryamah, ko ruwa bata sha ba bare ta huta, wai nan talla zataje. Ba musu ta kama hanyan fita Dr. Sulaimana ya k'ira sunanta

''Maryamah'' ta waigo ta amsa ''na'am'' yayi mata alaman tazo da hannunsa sannan yace ''ko hutawa bata yi ba'' yana kallon Amty Babbe, tayi murmushin dole sannan tace ''ai babu yawa, yanxu zata je ta dawo'' Maryamah a ranta tace hutawa ne bakison inyi, in ba haka ba warhaka wa zai saya? Wani b'angaren zuciyan nata kuma yace gwanda ki fita ma ko zaki had'u da saleh ya koya miki karatu. Maganan Dr. Sulaimana ya dawo da ita, ruwan da aka bashi ya mik'a mata wai tasha kafin ta fita. Sai da ta ajiye k'waryan sannan ta karb'i kwanon, har ta kai baki zata fara sha ta tuna da abinda Saleh ya fad'a mata akan shan ruwa a tsaye, ce mata yayi:-

''Annabi S.A.W yace duk ruwan da kasha a tsaye mafi sauk'in abinda zaka iya yi shine ka amayar dashi, dan duk addu'a ko bismillah d'in da zakayi indai a tsaye kasha toh tabbas tare da shaid'ani kasha'' Sai da ta samu wuri ta zauna sannan ta kafa kwanon a bakinta, duk lokacin da zatayi nishi sai ta sauk'ar da kwanon tayi nishi sannan ta mayar ta cigaba da sha, sai da tasha fiye da rabi sannan ta ajiye kwanon tana sauk'ar da numfashi, duk da yunwan da yake nausan tumbinta taji d'an daidai kuma tayi hamdala. Bayan ta gama sha tayi masa godiya sannan ta fita dan zuwa talla.

Kaman kullum yawo tayi kaman yanda ta saba sannan ta wuce inda suka saba had'uwa da Saleh, yau ma shi ya juye kindirmon ya bata kud'in sannan ya koya mata abinda ya sawwak'a na daga cikin karatun Qur'ani da hadisan da zai anfaneta. A bangaren su Amty Babbe da Dr. Sulaimana kuwa bayan ya sha ruwan yace mata zai wuce, ta juye masa man shanu mai kyau da kindirmo a cikin leda dan ya kaiwa mutanensa tsaraba, har wurin mota ta rakashi. Sai da ta kori yaran da ke zagaye da motan nasa tukunna ta mik'a masa ledodin hannunta tana masa godiya da fatan Allah ya tsare.

 

 

Engr. Abakar da matarsa Fad'ime zaune gaban Mama Zainaba, kowa yayi shiru yana sauraron maganan da Engr. Abakar yace yana tafe dashi mai muhimmanci, sai da ya fara da nasiha akan yadda da k'addara, ba wai dan basu sani ba sai dai don ya tuna musu kafin ya furta musu abinda ya tabbatar zai rikita su musamman mahaifiyarsa. Sai da yayi nasihan da ya tabbatar kowa yaji a jikinsa kuma jikinsu yayi sanyi sannan yace ''naje na karb'o sakamakon gwajin da akayi mana agun Dr. Sulaimana d'azu, ban dawo gida bane sabida ina tunanin da wane fuska zan zo in sanar daku wannan mummunan labari''

Ya kalli matarsa wacce tuni fuskanta yayi ambaliya da hawaye kanta a k'asa, ya kalli Mama Zainaba sannan yace ''mama kiyi hak'uri da abinda nazo miki dashi, banso in sanar dake ba amma naga kin takura akan lallai lallai sai na k'ara aure'' ya kalli Fad'ime yace ''nasan abinda zan fad'a miki zai matuk'ar gigita ki kuma zai iya zama sanadiyyar rabuwanmu, amma dan Allah ki d'auke shi a matsayin sirrinmu, kaman yanda nake fad'a miki sirrukana wannan na d'aya daga ciki kuma na tabbata ya zarce wad'an da kika sani muhimmanci'' ya sauk'ar da numfashi sannan ya cigaba da cewa ''na jima da sanin sakamakon gwajin da aka yi mana yau, amma tsoro da rashin sanin abinda zai je ya dawo shi yasa na kasa furta miki Fad'ime, kiyi hak'uri ki gafarceni, an jima da tabbatar min bazan taba samun haihuwa ba''

kuka ya kubce masa, haka ita Fad'ime, Mama Zainaba kasa tab'uka komai tayi, tayaya bazai tab'a samun haihuwa ba? Ta d'ago kanta ta kallesa tana son tabbatar da maganansa gaskiya ne ko kuma k'arya yake mata, yanda taga yana rera kuka ya tabbatar mata d'anta gaskiya yake, nan ita ma ta fashe da nata kukan. Sai da sukayi mai isarsu babu wanda ya tanka, Fad'ime ta tashi ta bar d'akin ta wuce d'akinta, so take ta tsayar da tunaninta, zama zatayi dashi ko kuwa tafiya zatayi ta barshi tunda ba haihuwa zaiyi ba? Ita kenan har ta mutu bazata ga d'anta ba? Tunanin da yake kanta kenan

 

Mama Zainaba ta kallesa hawaye fal idonta tana cewa ''Wallahi zuciyata bata yadda da wannan magana taka ba, Abakar in ma k'arya kake min dan in janye maganan k'arin auren nan toh naji na janye, amma ka sani, Allah....'' ta nuna sama sannan ta cigaba '' yana kallonka kuma yasan ta hanyan da zaiyi ya kawo min jika ta gunka, idan kuma gaskiya kake fad'a min ina rok'on Allah ya bani juriya kuma ya sa min a zuciyana gaskiya kake fad'a min'' kuka ta cigaba da yi wanda yasa Abakar cikin rud'ani da firgici, gani yake kaman Mama Zainaba baki tayi masa da fad'an haka, toh yaya zaiyi yanzu? D'ago kansa yayi yana mai zubda hawaye yana bata hak'uri akan ta yadda da maganansa, likitoci sun tabbatar masa da haka ba sau d'aya ba, bata sake masa ba, sai cewa da tayi jibi zata koma damaturu, bazata iya zama gidan sa ba.

 

 

Bayan ya koma d'akin matarsa, zaune ya sameta kan gado tayi tagumi, a ranshi addu'a yake na Allah yasa kada tace zata barshi dan baya haihuwa. Ya samu wuri ya zauna gefenta, ya janye hannayenta da ta tallabe fuskanta, ya rik'e gam cikin hannayensa. Ita kallonsa takeyi, har yanzu ta kasa tantance abinyi, tunaninta ya cushe, ta zauna dashi ko kuma ta jira yanda Allah zaiyi da ita?

Sauk'ar da ajiyan zuciya yayi sannan ya fara da cewa ''kiyi hak'uri na b'oye miki muhimmin magana irin wannan, banso b'oye miki ba sai don banason ki barni Fad'ime, ke d'aya nakeso kuma ke kad'ai nake da, ke shaida ce akan d'unbun k'aunar da nake miki, ki gafarceni b'oye miki da nayi'' kuka ya kubce masa, ita ma kanta a k'asa hawaye ke zubowa bisa k'uncinta, a ranta tana addu'an wannan jarrabar da Allah ya sauk'o mata Allah yasa ta haye.

Dak'yar ya iya tsagaita kukan yana goge hawayensa ya k'ara da cewa ''kada kiga kukan da nakeyi ko maganan da na fad'a miki ya karya miki zuciya ki kasa yin abinda kikeso Fad'ime, ni mai sonki ne bazan so in tauye miki hak'k'inki ba, in har tafiyan kikeso feel free and tell me (ki saki jikinki ki fad'a min), ni mai yi miki duk abinda zai saki farinciki ne'' ya k'arasa maganan yana d'ago fuskanta dan ya kalli cikin idanunta, Fad'ime bata iya yi masa magana ba sai kuka da takeyi, kukan da takeyi yasa shi karaya, har ya fara cire tsammanin Fad'ime zata ce zata zauna dashi, duk da hakan ya dake ya k'ara ce mata

''Saki kikeso ko, kada ki damu, yanzu zan rubuta miki ki tafi Fad'ime'' yana fad'an haka yana tashi ta rik'o hannunsa ya koma ya zauna, ta rungumeshi sosai tana mai zubar da hawaye, shima rungumeta yayi yana zubda nasa hawayen, kuka tayi sosai yana shafa bayanta alaman rarrashi, bai tanka ta ba bare yace ta daina kuka.

Sai da tayi mai isarta sannan ta goge hawayenta tace ''akan meh zan barka mijinah? Dan kawai Allah ya jarrabemu da rashin haihuwa sai in gujeka? Idan ni Allah ya d'aurawa hakan guduna zakayi kenan? I knw (nasani) bazaka barni ba, taya zan zama butulu sweet Abakar? Ta sake sa daga rungumar da tayi masa, k'walla bai daina fitowa daga idanunta ba, ta goge da hannunta sannan ta bugesa a k'irji sai da Abakar ya d'anyi k'ara, ta turo baki tace ''wai da rubuta min takadda zakayi sai ka rabu dani? Ashe ma zaka iya rabuwa dani?'' Sauk'ar da ajiyan zuciya yayi ya d'aura kanta bisa k'irjinsa sannan yace hakkinki ne my wife (matata) ya zan tauye miki hak'k'i bayan abinda kikeso kenan?''

Tace ''wa yace maka inason barinka? I love you remember, and i will never stop loving you, i cant spend a single day without u by side (ka tuna ina sonka, kuma bazan tab'a iya daina sonka ba, bazan iya yin kwana d'aya ba tare da kai a gefena ba), taya zan iya rayuwa babu kai bare har aurenka babu shi akaina, ai mutuwa zanyi. Duka suka dara komai ya canja suka fad'a wata duniyar daban... Na tattaro nawa i nawa na k'ara gaba, So suke suce min mai sunanah ta k'ara gaba bata da masauk'i gidan Engr. Abakar. #kwafa

Yau sati biyu kenan kullum Khajije k'awar Maryamah na bata ruwa da sassafe ta koma gida, hakan ya bawa Amty Babbe daman tsiro da wasu ayyukan, in babu kuwa ta d'aura mata talla. Ba k'aramin wahala maryamah take sha ba, amma duk da haka tana jin dad'in fitan da takeyi, dan kuwa kullum tana tare da saleh suna karatu, yanxu Maryamah ta iya sallah, tasan karatun da zakayi in kana sallah, k'ananan surori na Alqur'ani d'ad'd'aya ke gagaranta. Haka zalika tasan farillan sallah da sunnoninsa, duk wani abu da ya danganci Alwala da sallah Alhamdulillah ta iya su daidai gwargwado.

  Maryamah na da k'wak'walwa sosai, duk abinda aka koya mata ba'a maimaita mata washegari, tsab in ta dawo gobe ya tambayeta zata fad'a masa, hakan yasa ya dad'a nacewa yana mata karatu. Ita ma duk ranan da suka keb'e da khajije sai ta koya mata. Khajije ma na da k'ok'ari, gaskiya da ba dan babu ilimi ko makaranta a wannan dajin ba, na tabbata za a samu hafizai da makaranta hadisai da fiqhu sosai a garin. Tabbas zama a daji yana kawo mana cikas (Allah ka bamu ilimin addini dan tsira daga fad'awa halaka... Ameen)

   Shiryen-shiryen bikin Hajje akeyi, yau saura kwana uku biki, gajiya babu wanda Maryamah batayi ba, duk wani aike ita ce. Ana washe gari biki akayi ALK'AITA(masu busa) DA GANGA-KURA(masu ganga), wasa ne ko ince kid'i wanda duk wacce ta cika 'yar gata sai anyi a bikinta, k'awayen amarya ke rawa irin na gargajiya, mayafin kayan suke rawa dashi, an rataye sa a kafad'a an rik'e kowane bakin zani a kowane hannu, yanda sautin yake tafiya haka suke d'aga hannunsu d'aya dake rik'e da bakin mayafi suke d'aurawa a k'irjinsu, in sunyi kaman minti biyu suna kad'a hannun sai su sauk'ar su d'ago dayan, kansu na juyawa suna tafiya a hankali suna bin sauti. Haka in an canja kid'i zakuga sun canja rawa, duk yara ne dan bazasu wuce shekaru goma sha uku zuwa sha hud'u ba.

   Angumma din nan sai shek'i yake dan yasha mai kuma anyi masa sabon kamu dan kwalliyan biki, kowace yarinya tasha kwalliya da sabbin kaya. Haka akayi ta rawa ana busa da ganga. Washegari aka bada sadakin aurenta, shanaye shida da awakai goma aka bada matsayin sadakin Hajje, yarinya 'yar gata kuma 'yar gaban goshin Amty Babbe da iyayenta.

   Tayi fice kuma ta zama abin kwatance, dan kuwa sadakinta abun fad'a ne dan tayi goshi. (Masu cewa ana kashe kud'i a auren shuwa, toh a zahirin gaskiya ba haka bane, hakan ya samo asali ne tun daga kakanni, hasalima basu karb'an kud'i matsayin sadaki sai dabbobi, da zamani ya canja sai suka juya zuwa sisin gold, kuma in kuka duba farashin shanu d'aya zaku ga yana da tsada, hakan yana nufin sisin gold d'aya yana nan kaman shanu d'aya''

 

 

 

Bayan an d'aura aure, aka cigaba da shan kid'a k'awaye na rawa kaman jiya, da misalin k'arfe hud'u aka tattara amarya dan a kaita gidan miji, Maryamah na tsaye a waje tana jira a fito da amarya kaman yanda duk yaran k'auyen suke tsaye, Hajje kuka takeyi tana fizge-fizge, sai da aka samu aka danneta aka ciccib'eta sai kan jaki aka d'aurata. Mutane a bayanta in zata fad'o a tareta, haka gefen jakin duk da mata dan a tarota in zata fad'o.

Maryamah da Khajije a baya suke bin 'yan kai amarya, sai dariya sukeyi suna gwada yanda Hajje takeyi da ake fito da ita daga gida, Khajije dan dariya sai da ta tsuguna taci dariya sannan ta k'ara tashi sukayi gaba. Cewa take ''yanzu kin huta, babu mai kai gulmanki gun Amty Babbe'' Maryamah tace ''eh na huta, inaga shikenan yanzu Amty zata daina musguna min sosai, dama yawancin abunda take min Hajje ke zugata, yau kam gashi nima na ganta tana kuka'' ta fashe da dariya Khajije ma haka.

Sun isa gidan Amarya a makare, dan har an tsaya bakin k'ofa ana jiran kud'in sauk'ar da amarya, basu samu cinikin ba shiyasa basu san nawa aka bayar ba, an mik'a wa k'anwar maman Hajje kud'in ta sa a cikin zaninta sannan suka cusa kai cikin gidan. Suna sa k'afansu k'awaye da dangin amarya suka fara wak'a suna tafi kamar haka:- 

 

Ani na jina, ani nal mayarum jina

 

Naddakkhan bel halud rihtal kajiji fina (ga mu munzo, gamu 'yan kawo amarya munzo, muna turare da halud(sunan turare), kamshin kajiji(shima nau'i ne na turare) a tare damu)

Mutum d'aya in ya fad'i haka sai sauran su maimaita a jam'i (in chorus), haka sukayi ta yi har suka isa d'akin da za a ajiye amarya. Daga nan kuma bayan an shiga da amarya, har na samu wuri na zauna ina nishin gajiya naji ana faman wani wak'an a waje ana tafi, ba irin wacce muka shigo da ita ba, lek'awan da zanyi naga ashe dangin ango ne ke yiwa Amarya da mukarrabanta raddi. Mutum d'aya ke bayani sauran duk amshi sukeyi suna tafi... Cewa suke ''Dambaraha jabha'' barin rubuto muku baitin kuji da kyau

 

Dambaraha jabha bel ole

 

Dambaraha jabha be samuli

 

Dambaraha jabha bel minti

 

Dambaraha jabha (d'an uwanmu ya kawota dan kayan dadi, dan uwanmu ya kawota dan biredi, dan uwanmu ya kawota dan minti)

Ma'anan wak'an a takaice, d'an uwansu ya yaudareta da minti, da biredi, da kayan dad'i, ita kuma amarya da taga dad'i sai ta yadda ta aureshi. (Dariya zai kasheni, wai biredin da minti sune abin dadin kuma su suka jata ta auresa) haka dai ranan akayi ta wak'e wak'e har dare yayi ba a hak'ura ba. Nikam ba iyawa zanyi ba dan bacci nakeji, da naga an kora Maryamah gida nabi bayanta dan in ajiye hak'ark'arina

 

 

 

Akwana a tashi ba wuya yau sati biyu da auren Hajje, babu abinda aka daina na daga tsangwama da wahala da ake bawa Maryamah, kuma had'uwanta da Saleh kullum in ta fita tallan Kindirmo da man shanu suna had'uwa, shi yake juyewa ya bata kud'in sannan suyi karatu...

Maryamah ta dawo daga aiken da Amty Babbe tayi mata da leda a hannunta taji zancen da yasa ta firgita, Amty Babbe da Ammi Malud ke hayaniya akan lallai sai an aurar da Maryamah, Ammi Malud yace baza'a a aurar da ita ba ''yaushe mata da za'a aurar da ita, wai duk abinda kike mata kin d'auka bana gani ne, dan ta zama 'yar igala sai ki wofantar da ita? Kin manta 'yar yayanki ne, dan ya rasu ya barta sai ki d'auki tsanan duniya ki d'aura mata? Nidai ban yadda da auren nan ba, in har na isa dake kuma zakiji magana nah kenan'' amty Babbe tace ''shekaranta tara, kuma in har na samo mata miji aurar da ita zanyi, ai yarinyan yayana ne dad'in abun'' Ammi Malud yayi k'wafa ya tashi ya wuce d'akinsa ya barta zaune akan tabarman da yake d'akinta

Maryamah tsoro da firgici ya bayyana a fuskanta, ita da bata fara angumma ba waye zai aureta? Gaskiya Amty Babbe bata sonta ta tsaneta, wannan wani irin tsana ne haka? Kuka ta zauna ta fara yi kaman ranta zai fita, bata san auren ba kuma bata san abinda zata samu in tayi ba, amma tasan Amty Babbe bazata nemi yi mata abinda zai mata dad'i ba, tunanin nan ya sa jikinta duk ya mutu. Fitowan amty Babbe daga d'aki ya sa ta goge hawayen fuskanta sannan ta mik'a mata ledan da ke hannunta.

Amty Babbe ta had'e rai tace ''daga yau an daina yi miki gud'd'iye, angumma zaki fara'' tana fad'an haka ta juya ta shiga d'aki, zuciyan Maryamah ya dad'a bugawa, kenan maganan da gaske ne auren za'a mata. Ranan Maryamah tayi kuka kaman ranta zai fita. Lokacin da aka bata talla, inda ta saba yin sallan azahar ta tsaya don yin sallah, tayi alwala da ruwan da ta d'iba a leda sannan ta fara sallah.

A cikin sujjadanta tayi kuka tana rok'an Allah ya kawo mata agaji. Da ta idar tayi azkar ta shafa sannan ta kama hanyan garinsu Saleh dan ta fad'a masa abinda ake shirin yi mata. Haka kuwa akayi, ranan ba'ayi karatu ba, kuka takeyi tana fad'a masa abinda taji Amty Babbe tana fad'a. Saleh bayan hak'uri da nasiha babu abinda yayi mata, sai dai ya tabbatar mata zai shawo kan al'amarin, komai zai daidaita, ta k'ara hak'uri tayi addu'a.

 

 

Yau kwana uku da yin maganan auren Maryamah, Amty Babbe ta nemi mijin da zata had'asu cikin kwayam na garin amma ta rasa, duk wanda ta tunkara da maganan sai yace mata bazai auri mayya ba, wasu kam ko ansa mata basuyi saidai su juya su tafi ko su tashi su bata wuri.

Da misalin k'arfe d'aya da rabi na rana tana kishingid'e akan tabarmar da ta shinfid'a a tsakiyan gida dan shan iska, Maryamah na zaune tana wanke mata kayan sawanta sukaji Saleh yana doka sallama a bakin k'ofa, Maryamah tana jin muryansa ta gane sa dan dama sunyi magana akan zai zo gun Amty Babbe yau. Sai da Amty Babbe ta gyara zaman ta da mayafinta sannan ta ansa ta bashi izinin shigowa, bakinta har kunne tana sunne kai k'asa dan bata gane sa ba ko ince dama bata sanshi ba. Maryamah ta mik'a masa kujera ya zauna sannan ya gaida ta, Maryamah ita ma ta gaida shi ta cigaba da wankinta bata sake kallon wurinsu ba.

Sai da suka gama gaishe-gaishe sannan ya fad'a mata ko shi waye sannan ya k'ara da cewa yazo ne akan maganan Maryamah, ''Amty in bazaki damu ba inaso in turo iyayena ayi magana tunda aure zakuyi mata, dama tuntuni ina da wannan k'udirin a raina amma ban furta ba saboda naga bata kai aure ba, kuma yanzu naji kina nema mata miji shine na kawo kaina'' salatin da Amty babbe takeyi ne ya dakatar dashi, dukkan su suka tsaya suna kallonta daga shi har Maryamah, tafi takeyi tana cewa ''yau mun shiga uku, rashin kunyan naka har ya wuce zama da yarinya a waje ya kai kazo neman aurenta da kanka?'' Ta juya ta kalli Maryamah tana cewa ''wannan kika jajubo min Maryamah wai in aura miki'' ta fad'i hakan tana nuna Saleh

Ta fashe da kuka tana cewa ''Maryamah kin cuceni kin cuci Yaya, in yana raye bansan wane mataki zai d'auka akanki ba'' ta cigaba da kuka tana rufe fuskanta da mayafinta, Saleh ya girgiza kai dan ya gano inda ta dosa, hasalima ba kuka takeyi ba, dakyar ya iya cewa kiyi hak'uri Amty, zan turo magabatana sai kuyi magana. Hannunta ta d'aga tana cewa a'a, kada ka turo su dan bazan baka Maryamah ba, ko meh zai faru saidai ya faru. Bata saurari magiyansa ba ta shige d'aki tana cewa ''Allah bazan baka Maryamah ba, kunji min mutum mara kunya, ka fice min daga gida yanzu ko ranka ya b'aci''

Maryamah da akayi komai gaban idonta hawaye suka sauk'o mata bisa kuncinta, Saleh bai tashi daga inda yake zaune ba sai kallon Maryamah yakeyi, a ranshi yana tunanin mafita. ''ya za'ayi in cire Maryamah cikin wahalan da take ciki, ko ta yaya sai na aureta, zanyi iya k'ok'arina dan ya shawo kan Amty Babbe, nayi alwashin kawo farinciki da rayuwa mai inganci cikin rayuwanki Maryamah, ina sonki tun ranan da na fara d'aura idanuna akanki, yanzu lokaci yayi da zan k'wato ki in baki 'yancinki na 'ya mace''

Bai iya yiwa Maryamah magana ba sai da ya tashi zai fita sannan ya juyo ya fuskanceta yace ''kiyi hak'uri ki daina kuka, kiyi addu'a kuma nima zan tayaki, Allah zai kawo mana mafita, insha Allahu zan shawo kan matsalan..........'' maganan Amty Babbe ya sashi dakatawa da maganan da yakeyi ''wai baka tafi bane har yanzu? Maryamah shigo nan tunda rashin kunya zaku min a tsakiyan gida'' ta lek'o tana cewa ''nace ka tafi bazan bada Maryamah ba, ka sace ta in zaka iya insan ka cika mara kunya'' ta janyo hannun Maryamah ta sata d'aki tana ta sababinta, shi kuma Saleh ya fice daga gidan jikinsa a mace

 

 

Dr. Sulaimana zaune a cikin motansa da ke harabar asibiti a wurin ajiye motoci, yanzu fitowansa daga office zai wuce gida amma ya kasa, tun ranan da ya dawo daga Damaturu yake neman hanyan da zai fad'awa Abakar k'udirinsa akan yarinyan da ya gani lokacin tafiyansa Damaturu amma ya kasa, me zai fad'a masa kuma ta ina zai fara bayan yasan abokinsa, shi ya rasa dalilin da yasa yana kallon Maryamah yaji a ransa ita ce zata kawo k'arshen matsalan Abakar, meh yasa baiyi tunanin shi ya aureta ba?

Buga siterin motan yayi yana cewa ''no way in fara tunanin ni in aureta ma, Abakar shine kad'ai ya dace da ita dan shi yake da matsalan da zata gyara masa'' Ya ja tsaki ya d'auko wayansa ya lalubo layin Abakar sannan ya k'ira, bai jima da k'ira ba aka d'aga, basuyi wani gaisuwa ba yace ''kana ina ne?'' Ya sake cewa ''toh in ka gama mu had'u a gidana mana, akwai wani muhimmin magana da nakeso muyi'' yayi shiru alaman yana sauraran abinda ake fad'a masa sannan yace ''toh ba matsala sai kazo'' sannan ya kashe wayan ya tada motansa ya wuce gida cike da fargaban abinda yake shirin aikatawa.

Abakar bayan ya fito daga meeting motansa ya wuce yana kallon agogonsa, d'an guntun tsaki ya ja ya cigaba da tafiya cikin sauri dan yayi latti, bai d'auka meeting d'in zai d'aukesu har wannan lokacin ba, gashi har k'arfe biyar da rabi. Sai da ya zauna cikin mota yasa seat belt sannan ya d'auki wayansa. Fad'ime ya k'ira ya fad'a mata bazai dawo gida da wuri ba zai tsaya gun Dr. Sulaimana, cikin damuwa take tambayansa ''lafiya dai koh?'' yace mata ''kada ki damu, ya dai ce min akwai abinda yakeson mu tattauna'' Fad'ime tace ''ba dai akan abinda ke damunka ba?'' sai da yayi murmushi sannan yace ''a'a dak'yar gaskiya, kada ki damu in na dawo zamuyi magana, take care of yourself for me (ki kula min da kanki)'' daga d'aya b'angaren tace ''no problem sir, kaima ka kula min da kanka, da zaran kaji yunwa ka dawo gida ka cika cikinka sannan ka koma kaji?'' Yayi murmushi yace ''bazan jima ba ma my wife, bye sai na iso'' ya kashe wayan yana mai tunanin son da Fad'ime take masa.

A lokaci d'aya kuma yana tunanin ya shiga hak'k'in mahaifiyarsa da shi kansa, eh mana ya shiga hak'k'in kansa, yanzu babu yanda za'ayi yaga d'ansa har ya mutu, ya haramtawa kansa ganin jininsa kenan, anya hakan zai yu? Da wuri ya gusar da tunanin yana mai cewa ''i did the right thing (nayi abinda ya dace)'' amma can ciki zuciyansa yana ganin kaman bazai iya ba, yana bala'in son ganin yara 'yan k'anana suna wasa ko suna magana.

Kuma abin kaman had'in baki, tunda ya fad'awa Mama Zainaba bazai haihu ba kullum sai yaga abokansa da yaransu, wani lokacin in ya k'ira abokinsa ko aka k'irasa sai yaji yara na magana a gefe ko b'arna ko kuma ana wani abin da yake jawo ra'ayinsa na son ganin yaran cikinsa amma babu yanda zaiyi, dole ya farantawa Fad'ime dan tayi masa halacci, da baya haihuwa da gaske haka zata zauna dashi, shi meh yasa bazai iya zama da ita ba tare da ganin nasa jinin ba. Haka har ya isa gidan Dr. Sulaimana tunanin nan ne a ransa, ya rasa yanda zaiyi duk ya takura kansa

 

 

''Engr. na samo maka wata 'yar kyakkyawar budurwa (very fine girl)ka aura, wallahi kallo d'aya na mata naji na samu nutsuwa akan ita ce zata gyara matsalan gidanka da ka d'aurawa kanka, Allah yasa ka hango abinda nake hangowa game da yarinyan nan'' Engr. Abakar dariya ya fashe da kaman zautacce da yaji maganan da Dr. Sulaimana yayi, harda tafi yana buga k'afansa a k'asa. Dr. Sulaimana bai masa magana ba sai ma d'aukan cup da yayi ya d'ibi juice d'in da matarsa ta kawo musu a falonsa ya kai baki yana kurb'a a hankali yana kallon TV. Sai da ya gama dariyansa sannan yace ''kasan meh kake cewa? Ka manta bazan tab'a haihuwa ba? Kuma ka manta meh yasa nace bazan haihu ba? Dan fah kada inyi auren ne. Kuma yanzu ka kawo min wani magana kaman baka san komai ba'' Ya ja guntun tsaki sannan ya cigaba ''sometimes in ka fad'i abu har mamaki kake bani kaman ba kai ba''

Dr. Sulaimana yace in ka gama surutunka sai ka tsaya ka saurari abinda zan fad'a maka, in kuma baka da niyyan saurarana sai in k'ara gaba in tabka maka abinda bazaka iya warwareshi ba'' Engr. Abakar yayi murmushi yace ''nasan abokina sarai, so hankalina a kwance yake dan nasan na fad'i sirrina a inda baza'a tab'a bud'e min shi ba, saidai duk da yadda da hakan bazai hanani jin tatsuniyan da kake shirin bani ba... ina jinka'' ya fad'i hakan yana kallon Dr. Sulaimana

Dr. Sulaimana yana girgiza kai yace ''hmmm, wai kai yanzu har ka mutu bakason yaro? bakason kayi wasa da naka d'an kaman yanda kake wasa da my lil Al'amin(yaron Dr. Sulaimana)?'' Engr. Abakar ya d'aga hannunsa yana dakatar dashi had'e da cewa ''look, tunda har nayi ik'irarin bazan tab'a haihuwa ba ya zama dole in hak'ura. Nasan zai yi min wahala amma akan in b'atawa Fad'ime rai gwanda in zauna babu d'a har abada''

Dr. Sulaimana ya gyara zama sannan yace ''yauwa, kai bakason Fad'ime ranta ya b'aci koh?'' Engr. Abakar ya gyad'a kai yana cewa ''yes(eh)'' sai da Dr. Ya sauk'ar da numfashi sannan yace ''shiyasa na samo maka wacce zaka aura, kuma ina mai tabbatar maka Fad'ime bazata tab'a sani ba'' da mamaki Engr. Yake kallonsa ''bazata sani ba kuma? Tayaya? Babu zaman aure kenan tsakanina da wacce zan auro, so kake in mutu in shiga wuta dan tauyewa wata hak'k'i?'' Dr. Sulaimana ya girgiza kansa alaman a'a sannan yace ''ina da plan engr. nd i know wat am saying(nasan meh nake fad'a)''

 

 

Engr. Abakar bai tanka masa ba, kansa ya d'aure, meh abokinsa yake nufi? Dr. Sulaimana ya dafa kafad'ansa yace ''trust me, inason in kawo k'arshen damuwanka, ka bani dama'' Engr. Abakar ya d'ago idanunsa da ya canja kala yana kallon aminin nasa yace ''ka fad'a min plan naka d'in in yaso sai inyi shawara, amma inaga kaman bazai yu ba Sulaimana'' ya girgiza kai yace ''ina dai jinka''

Dr. Sulaimana yace ''ba zakayi aiki anan Shika ba, zaka fara nan da one month(wata d'aya) koh? Engr. Abakar ya kad'a kai alaman a'a ya k'ara da cewa ''yanzu meeting d'in da mukayi kenan, anaso mu fara aikin nan da two weeks(sati biyu), kasan zamu jima akan aikin dan yana da yawa, zamu kai 6months(watanni shida) haka ko ma fiye'' Dr. Sulaimana ya kad'a kansa alaman gamsuwa sannan yace ''babu matsala, kaga gidana da yake can ai can zaka zauna, sai ka auri yarinyan ka ajiyeta acan, in yaso kafin ka gama aikin can zamu san yanda zamuyi''

Engr. Abakar cike da jin haushin maganan yace ''ni fah kana rikita ni, wannan tatsuniyan naka ya gundureni, taya zan auri mace bata sanni ba bata san kowa nawa ba kuma inje in ajiyeta a k'auyen can? Akwai macen da zata lamunci hakan ko iyayen da zasu bada 'yar su ba tare da na tura magabatana ba? Da kake maganan in aureta in ma ta yadda na aureta kana nufin shika zan koma da zama ina raba kwana ko zaman watanni ko shekaru kawai zamuyi mu rabu? Aure fah ba zaman kwana d'aya bane, zama ne na har abada'' bai tsaya sauraran maganan da Dr. zai sake fad'a masa ba ya tashi zai bar falon cike da b'acin rai.

Dr. Sulaimana ya dakatar dashi da fad'in ''kayi tunani akai, nasan wacce zan baka bazata tab'a k'in zama a duk inda ka ajiyeta ba'' ya taso ya tsaya a bayansa ya dafasa a kafad'a sannan ya cigaba ''in na tab'a baka gurguwar shawara na aminta ka watsar da wannan magana, in kuma ka yadda dani toh ka amince ka bani daman d'auko yarinyan in aura maka ita, bazaka tab'a da na sani ba Engr.''

Ya sauk'ar da hannunsa daga dafa sa da yayi ya d'age kafad'a had'e da tab'e baki sannan yace ''is left for you(ya rage maka) nidai na baka k'arshen gudummawa akan matsalarka, kuma babu wanda zai nuna maka so irin wanda nayi maka a yanzu, sai nan gaba zaka gane haka'' ya juya ya koma ya zauna yana shan juice d'insa hankalinsa a kwance, Engr. Abakar ya kasa tafiya ya kasa zama, yana tsaye a wurin kusan minti biyar kana ya kad'a bujensa yayi gaba cike da tunanin maganan da sukayi da Dr. Sulaimana... Meh mafita?

 

 

Bayan kwana biyu da maganan da sukayi, babu k'wak'k'waran shawara da Engr. Abakar ya yanke, hasalima bayason had'uwansa da Dr. kullum cikin kwana-kwana yakeyi, hakan da Dr. ya gani sai bai neme shi ba ya basa lokaci, a ganinsa tunani yakeyi bai gama shawara ba. A b'angaren engr. Abakar kuwa har d'an rama yayi, wani zuciyan na ce masa ya yadda wani zuciyan na kwab'arsa, ya rasa wanne zai d'auka. Duk ya canja bayi da k'uzari har Fad'ime ta fara zargin akwai abinda yake b'oye mata, ta tambayesa yace ba komai, zuba mishi ido tayi dan tasan ko ba dad'e ko ba jima sai ya fad'a mata dan bai iya b'oye mata komai nasa ba itace secret keeper(mai rik'e sirri) d'insa (wannan kam da wuya kiji sa Fad'ime)

(Mu garzaya gun Maryamah da Amty Babbe dan muji wainar da suke toyawa) Saleh da Maryamah zaune inda suka saba zama in ta fito talla, k'waryar ta na gefenta tana karanto masa addu'an da akeyi bayan an tada kabbara kafin a karanta fatiha kamar haka '' Allahu akbar kabira sau uku, Alhamdulillahi kathira sau uku, subhanallahi bukratan wa asila sau uku. A'uzu billahis sami'il aleem minash shaid'anir rajeem min hamzihi wa nafkhihi wa nafasihi, sai kace bismillahir rahmanir raheem sai suratul fatiha, hakane koh?''

Ta fad'i hakan tana kallonsa, ya tafa mata sannan yace ''kinyi k'ok'ari Maryamah dole in baki kyauta'' ta turo baki tace ''ni kyauta d'aya zaka min shine kasa Amty Babbe ta yadda, in ta yadda shikenan duk abinda kakeson in maka wallahi Allah shi zanyi, in tak'i bansan wani rayuwa zan shiga ba'' hawaye ya zubo daga idanunta yana bata hak'uri, bai san meh zai fad'a mata ba yanzu kam, yaje gun Amty Babbe yafi sau biyar amma ko saurararsa batayi, wani lokaci zagi yake samu in yayi sa'a shine tayi masa shiru ta bashi wuri tun kafin ya fara mata magana, jiya kam da yaje gunta ce masa tayi in ya sake zuwa ransa zai b'aci, yanzu ya zaiyi ma bai sani ba.

Cikin lallausar murya yake mata magana ''Maryamah kinga rayuwar nan cike yake da jarraba kala-kala, ke naki irin wanda Allah ya baki kenan, hak'uri da addu'a kad'ai zai k'wace ki Kuma nima zan tayaki dashi'' ya sauk'ar da numfashi ya rik'e hannayenta dukka biyu, kallon fuskarta yakeyi wanda ya jik'e shark'ab da hawaye yace ''Allah shaida ne na soki tsakani da Allah Maryamah, kuma ke shaida ce nayi iya k'ok'arina dan in aureki koh?'' Ta gyad'a kai alamar eh sannan ya cigaba ''yanzu alk'awari d'aya nakeson kiyi min, ai zakiyi koh?'' Cikin muryan kuka take cewa ''komai zan maka'' yayi murmushin k'arfin hali ya sake rik'e hannunta da kyau kaman za a kwace ta sannan yace

''ki daina kuka, ni banson kukanki Maryamah ko kad'an, ki min alkawarin duk rintsi bazaki manta sallah ba, akan ki zauna kiyi ta kuka kiyi alwala ki kaiwa Allah buk'atunki dan shi kad'ai ne zai iya share miki hawayenki/buk'atunki, Maryamah kuma kiyi min alk'awarin ko ba ni na aureki ba zaki nemi ilimin addini, banason ki wahala a duniya kuma kije lahira ma baki huta ba, dalilinah kenan na jajirce wurin koya miki ibadarki, ko a haka na barki Maryamah nasan kinsan yanda zaki tafiyar da rayuwanki kafin lokacin balagarki'' ya runtse idanunsa hawaye suka zubo baiyi niyyan gogewa ba ya cigaba da cewa ''Maryamah ina ji a jikina zaki zama wata, ina ji a jikina akwai wani alkhairi da ilimin da zai zo miki wanda ni bazan iya baki ba, zakiyi alfahari da rayuwan da zaki tsinci kanki, ina miki fatan alkhairi'' kuka yaci k'arfinsa

 

 

Kuka sukeyi mai cin rai babu mai rarrashi, Saleh ne ya iya daurewa ya share hawayensa ya fara bata hak'uri had'e da share mata hawayen fuskarta ''yanzu fah na gama ce miki banson kina kuka koh kwaiseh? Yi hak'uri ki daina kuka kinji'' da k'yar ya samu ya shawo kanta ta daina kuka sai sauk'ar da numfashi takeyi tana ajiyar zuciya. Murmushi ta k'ak'aro tace ''nayi alk'awarin yin duk abinda ka umarce ni Yaya Saleh, kuma insha Allah zakayi alfahari dani, a duniya babu mai sona da ya wuceka, daga kai sai Khajije sai kuma wancan da ya kawo mu gida rannan ka tuna?''

Ta fad'i hakan tana kallonsa shi kuma yayi murmushi yace ''Sulaimana?'' Ta tafa hannunta sannan ta nuna shi da yatsa d'aya tana murmushi tace ''ehhh!!! Ka tuna min Yaya Sulaimana, shima yana sona'' ta had'e rai ta turo bakinta sannan tace ''na manta abinda nakeson fad'a maka ma'' dariya Saleh yayi sannan yace ''ke kam dai wani lokacin akwai ki da shirme'' ta turo baki tace ''ai dariya nakeson kayi, in ba haka ba ni ban manta ba'' ta gyara zama tace ''yanzu kaji in fad'a maka, kaga in Amty Babbe tak'i kasan meh nakeso kayi min wanda zai tabbatar min bazaka manta ni ba ko da bamu sake had'uwa ba?''

Yace ''menene?'' Ta sauk'ar da numfashi sannan tace ''inason ka auri Khajije, tana da hankali, kuma ita ma muna karatu, duk abinda ka koya min ita ma ta sani, inason ita ma ta shiga aljannah mu had'u dukkanmu a can'' ta k'arashe maganan tana murmushi. Saleh shiru yayi bai ansa ta ba ita kuwa sai labarin Khajije take basa, hankalinsa baya gunta ya tafi duniyar tunani, sai da ta gama iya sharhinta sannan tace masa ''zaka aureta ai koh?'' Bai tanka ta ba sai da ta tab'ashi tana cewa ''baka jina ne?''

A firgice yace mata ''meh kika ce?'' Bata yi tunanin wani abu ba ta maimaita masa tambayan, murmushi kawai yayi yace ''mu bar maganan nan kinji, karatu zamuyi'' ta tab'e baki tace ''sai kace zaka aureta kamar yanda nima nayi maka alk'awari'' d'auke kansa yayi daga dubanta da yake bai ansa ta ba, ta juyo da fuskarsa da hannunta tace ''bazaka aureta ba koh? Kafison ta auri wanda bazai koya mata karatu kamar yanda kai kake koya min ba?'' Ya rik'e hannunta yana kallon cikin idonta yace ''na miki alkawari in har ban aureki ba zan auri Khajije amma sai kema kinyi karatu sannan ita ma zan koyar da ita ko insa ta a makaranta'' da murmushi a fuskarta tace ''ai zanyi ma, nagode sosai'' ya janyota kusa dashi yasa hannunsa ya zagayeta ya d'aura fuskarsa bisa kafad'anta yana rik'e da hannayenta.

Idanunsa a lumshe yana jin zafi a ransa, yana matuk'ar son Maryamah amma Amty Babbe tak'i, wata zuciyar tana ce masa ya saceta ya gudu da ita inda baza'a sake ganinsu ba bare aji labarinsu....... salati sukaji a kansu wanda yayi sanadiyyar rud'ewar Maryamah ta k'ank'ame Saleh tana cewa ''na shiga uku'' Girgizata yakeyi yana matsar da ita baya ita kuwa sai shigewa jikinsa takeyi tana kuka tana ihu, Amty Babbe da ke tsaye a kansu bata bar salatin ba baki bud'e take kallon ikon Allah, janyo Maryamah tayi ta wanke ta da mari wanda sai da Maryamah taga duhu, kwanyanta da komai nata ya tafi na wushin gadi

 

 

Saleh ya tsuguna har k'asa yana cewa ''kiyi hak'uri Amty ki dakeni tunda ni nak'i barinta kaman yanda kika ce in fita a rayuwarta bazaki bani ita ba'' tsawa Amty Babbe ta daka masa tana cewa ''ka lalata mana yarinya ba dole ba, laifina ne da nake barinta zuwa talla ashe gunka take zuwa ku shek'e ayar ku, babu komai sai ka k'ara ganinta '' ta janyo Maryamah da take kwance a kasa tana kuka.

Hanyar gida sukayi suka bar Saleh a tsaye a wurin yana da na sanin yanda ya rik'eta, shi ma baisan ya akayi haka ta faru ba yanzu ya jawo mata duka, zama yayi a wurin ya dafe kansa da yake yi masa ciwo kaman zai fashe, kuka ne mai sauti yazo masa wanda ya kasa daurewa, tsugunawa yayi a k'asa yana kuka sosai har jijiyoyin wuyansa da fuskarsa sai da suka bayyana, farar fatar nan tayi jawur, tun yana hango yanda Amty Babbe take bugun Maryamah har suka b'ace masa bai daina kuka ba.

Bayan sun isa gida Maryamah ta jibgu, suma ne kawai batayi ba amma har numfashinta yana hawa sama, tana dukanta tana cewa bazata sake zuwa talla ba kullum zaman gida zatayi tunda iskanci tasa a gaba, farin k'afan nata yasa ko miji ta kasa samu. Sai da tayi mata lilis sannnan ta tsallaketa ta wuce d'aki tana numfashi kaman wacce tayi gudu mai nisa. Ranan dai Maryamah haka ta zauna a wurin da aka jibgeta a zube kamar kayan wanki, ta sharb'i kukanta son ranta daga bisani ta koma gefe tana ajiyar zuciya har maghrib yayi ta tashi dak'yar tayi sallah.

Washegari kaman an fad'awa Dr. Sulaimana Maryamah ta jibgu sai gashi a hanyar Godil, tun safe ya kama hanya shi d'aya sai falfala gudu yakeyi kaman yanda ya saba in zaiyi tafiya mai nisa, hankalinsa a kwance sai k'ira'ar Sheikh Ahmad sulaiman ke tashi yana bi a hankali. Da misalin k'arfe sha biyu da rabi ya iso garin, gidansu Maryamah ya wuce ba tare da yasha wani wahala ba ya isa.

Yara sai bin motan sukeyi a baya manyan mutanen gari kuwa na kallon motar da ido, farar mota ce corollah x mai bala'in kyau, gashi yasha wanki sai yalk'i yakeyi kuma ga handsome guy(kyakkyawan yaro) fari tas yasha farar jamfa da bak'ar gilashi yana driving(tuk'i) sai motar ta k'ara bada ma'ana, ko ni nan ya burgeni bare wad'an da basu saba ganin mota ba sai akori kura.

Tabbas Sulaimana yana da kyau ta ko ina, shekarunsa bazasu wuce ashirin da takwas ba, abokin Engr. Abakar ne tun suna yara har suka girma sukayi makaranta d'aya kowa da abinda ya karanta, zama a kaduna kuma ra'ayinsu ne yazo d'aya suna son garin kaduna, ko suna yara in anyi hutu can suke zuwa, abotansu yasa iyayensu suka san juna, wani lokacin ma gida d'aya suke zuwa hutun, ko gidan dangin Abakar ko dangin Sulaimana. Suna mutunci sosai kuma suna girmama juna Tsakanin familynsu (danginsu)

Engr. Abakar yayi aure da shekara d'aya sannan Dr. Sulaimana yayi aure, ya auri 'yar garinsa (Damaturu) kuma danginsa mai suna Hamrah, Allah ya albarkacesu da yara biyu, na farko sunanshi Al'amin sai ta biyu mai suna Aisha suna k'iranta Ashshe.

 

 

 

Fitowar Dr. Sulaimana daga mota yayi daidai da fitowar Maryamah da gudu tana hawaye, a k'asa ta fad'i timm! sai da bakinta ya fashe jini ya fara malala, kuka takeyi mara sauti ta kasa tashi daga inda take, Amty Babbe da ta biyota waje ta koma ciki tana sababi ba tare da ta lura da Sulaimana da yake tsaye a wurin ba.

Da sauri ya isa inda take ya d'agota yana mata magana da yare ''meh ya faru Akhty(k'anwata)'' d'aga kai tayi dan taga wanda yake taimakonta, tana ganin Dr. Sulaimana kuwa ta sake wani sabon kuka mai sauti ta rik'e hannunsa gam-gam cikin kuka take cewa ''ka taimakeni, wallahi Amty bata sona kasheni zatayi'' ya zaro ido yana cewa ''subhanallahi'' d'agota yayi ta tsaya sannan yace ''mu shiga ciki sai muyi magana'' batayi musu ba ta kama hanyar cikin gida jiri ya d'ibeta ta koma luuu zata fad'i, Dr. Sulaimana da ke bayanta ya tarota ya tsayar da ita yana cewa ''Lafiya?'' ta nuna masa cikinta alamar yunwa takeji, rik'ota yayi suka shiga cikin gida bayan yayi sallama Amty Babbe ta ansa, sai washe baki takeyi tana masa sannu da zuwa, bata ma kula da halin da Maryamah ke ciki ba.

Ya samu wuri ya ajiyeta sannan ya fice ya koma mota ya d'auko ledan snacks had'e da juice sannan ya koma ciki wurin Maryamah, ajiye mata yayi agabanta sannan yace ''kije ki wanke bakin ki sai kici, yunwa koh?'' Ta gyad'a kai ta mik'e tabi bango ta d'ibi ruwa ta kurkure bakin sannan ta dawo ta zauna, ta kai hannu ledan tana bud'ewa, cake ta fara karo dashi kuma shi ta d'auka har ta kai baki ya rik'e hannun yace ''bismillahi'' da murmushi a fuskarsa, ita ma tayi murmushi sannan ta maimaita abinda ya fad'a sannan ta fara ci, rabon ta da abinci tun jiya kafin ta fita talla, yanzun ma wanki aka sata tana yi tana layi idonta yana rufuwa Amty Babbe ta d'auko tab'arya ta bita shine ta fice waje da gudu sai Allah ya kawo Dr. Sulaimana.

Amty Babbe da ta tab'e baki bata sake magana ba ta samu kujera ta kawo masa tace ya zauna, sai da ya zauna sannan ya gaisheta ta amsa cike da fara'a tana tambayan mutanen gida da kuma aiki. Sai da suka gama d'an raha sannan ya kalli Maryamah da take d'ura meatpie a baki tana kora ruwan juice ko kallonsu batayi, da alama ma hankalinta baya gunsu. Ya sauk'ar da numfashi sannan yace ''Amty meh ya faru na ganta a waje a k'asa kin biyota''

Sai da ta ja tsaki mai kyau sannan tace ''ai wannan yarinyan'' tana nuna maryamah da yatsa ''jiya kasan ina na samota?'' Bata jira amsa ba ta cigaba da cewa ''wurin wani k'aton mutum ta raku'be a jikinsa, Allah yasa jiya Hajje k'anwata ta aiko min in karb'o mata magani anan garin da ke gefenmu, da banje ba da bazan gansu ba sai ta d'uro ciki ta dawo gida ta sani kunya'' k'arya da gaskiya Amty Babbe ta tsarawa Dr. Sulaimana, shi kuwa kallon Maryamah yakeyi yana jin duk abinda Amty Babbe take fad'a yana k'iyastawa a ransa. K'arshen maganan nata take cewa ''dan bak'in hali irin nata na nemo mata miji kab garin nan daga cikin kwayam d'in nan sun k'i ta, na rasa ya zanyi da yarinyar nan''

Sai da ya gyara zama sannan yace ''gaskiya Amty aure yakamata kiyi mata kam tunda har tasan taje gun wani, kuma yanzu babu wanda kika samo mata?'' Amty Babbe ta tab'e baki ''hmm! Ai wannan yarinyar ka barta kawai'' ya had'iye miyau zuciyansa na bugawa yana addu'an samun nasara sannan yace ''ai kuwa nima akwai wani almajirina a can Damaturu Amty, inason aurar dashi dan ya isheni kuma na nema masa mata kab garin sunk'i, ko zaki bani Maryamah in aura masa ita kawai?'' Ya fad'i hakan yana kallon fuskarta.

 

 

 

Fuska Amty Babbe ta had'a kamar wacce aka fad'a mata wani abun na daban, Dr. Sulaimana bai yi k'asa a gwiwa ba ya cigaba da cewa ''kinga shima ba ya sana'an komai, a k'ark'ashina yake.......'' bai k'arasa magana ba Amty Babbe ta dakatar dashi da hannunta, kallon Maryamah tayi tace mata ''ke!!!'' A firgice Maryamah ta ansa tana had'iye meatpie d'in da ke bakinta, Amty Babbe tace mata ''ki shiga ciki'' ba tayi musu ba ta kwashi ledan snacks da kwalin juice d'in ta shige cikin d'akin Amty Babbe.

Sai da Amty Babbe ta gyara zama sannan tace ''dan ina wulak'anta yarinyar nan bai zama duk wanda yazo neman aurenta zan bashi ba, yarinyar yayanah ce kuma ina ganin kamanninshi a lik'e a fuskarta, dalili yasa na tsaneta amma kuma hakan bai nuna zan bawa wanda ban sani ba'' ta fad'i hakan tana kallon gefe, zuciyar Dr. Sulaimana ya k'ara bugawa yace a ransa ''wai nazo mata ta Almajirina ko zata yadda ashe abun ba haka bane'' yayi gyarar murya sannan yace ''Amty kina ganin zan cuceki ko zan cuci Maryamah kenan? Ai kamar k'anwa take awurina, kuma in kin aura masa ita ai a wurina zasu zauna zan sa musu ido''.

Amty Babbe tace ''kana nufin tun daga nan Godil ba Yadi za a kaita ba, ba Damaturu ba, har........'' ta juyo ta kallesa alamar tambaya a fuskarta sannan tace ''shunu ismal hille(meh sunan garin)?'' Da i'ina yace mata ''emm! Ka..... Kaduna'' tace ''yauwa Kaduna, in ka tafi da ita ina zan sake ganinta ni ba saninka nayi ba, a'a ka bari'' tana girigiza kai tace hakan, ta cigaba da cewa ''zan nemo mata anan wanda zan na ganinta ina tuna Yaya Hassan'' ta fad'i haka tana goge kwalla da mayafinta wai ta tuno yayanta.

Dr. Sulaimana yayi murmushin k'arfin hali yace ''haba Amty, ki yadda da auren nan, ni na tabbata bazakiyi da na sani ba, kuma duk wata d'aya zan zo ko kuma in kawo ta ko mijinta ya kawota, yanzu in kika ajiyeta anan babu mai aurenta, ki bari kawai nan da sati sai inzo da sadaki mu tafi koh?'' Shiru Amty Babbe tayi tana tunanin maganar nan, a ranta take cewa ''kuma gaskiya bazan samu wanda zai auri Maryamah a garin nan ba sai wannan Saleh d'in, kuma in har na yadda ta auri Saleh Hajje bazata ji dad'i ba'' a fili kuwa ta washe baki tana gyara mayafinta tana cewa ''ohh haka ne? tunda zaka kawo min ita ai shikenan''

Wangale baki Dr. Sulaimana yayi yana cewa ''kin yadda Amty in zo sati mai zuwa da komai na biki?'' Tace masa ''Eh, amma ka jira shi(kasancewar basu k'iran sunan mijinsu) ya dawo sai kuyi magana'' ya washe baki yace ''Ammi?'' Tace masa ''eh'' cike da zumud'i yake cewa ''babu matsala, zan jirasa sai muyi magana kafin in wuce kawai'' haka sukayi ta hirar yanda auren takeso ya kasance da yanda zai na kawo Maryamah bayan auren.

Har Ammi Malud ya dawo basu bar wurin ba, lokacin ne suka tashi sukayi sallar azahar, Dr. Sulaimana bayan ya idar da sallah ya fita ya bud'e bayan mota ya fara ciro tsarabar da ya kawo musu, kayan abinci masu yawa sai kayan sawa da ya sayowa Maryamah sai kuma na Amty Babbe. Yara suka taya shi d'ibar kayan suka shigar ciki sannan ya cire kud'i ya rarraba musu. Amty Babbe da Ammi Malud sai godiya suke suna k'arawa.

Maryamah da ta gama loda kayan dad'i taji cikinta ya d'auka ta fito ta koma can gefe ta cigaba da wankin da ta fara, anan ne takejin maganar auren da za'ayi mata da alamajirin Dr. Sulaimana. Da farko Ammi Malud yace bazai yu ba amma da yake d'an birni akwai wayo haka Dr. Sulaimana ya shawo hankalinsu dukka suka yadda akan ya dawo kawai a d'aura aure. Abun mamaki Maryamah bata ji haushi ko bugun zuciya game da auren da aka ce za a mata ba, sai ma farinciki da takeyi a ranta, ko dan Dr. Sulaimana ya nuna kulawarsa gareta yasa bataji haushi ba, oho mata.

 

 

 

Dr. Sulaimana bayan ya wuce garin Damaturu kwana biyu yayi ya dawo Kaduna dan suyi magana ta k'arshe da Abakar, ya iso da misalin k'arfe hud'u, wanka kawai yayi yaci abinci ya d'auki key zai fita. Hamrah ya gani a gabansa ta turo baki idonta ya ciko da hawaye, bowl(kwano) a hannunta cike da fruits tace ''fita kuma zaka sake yi daga dawowa?'' hawayen ne ya zubo kan kuncinta ba shiri, sai da yaja numfashi sannan ya janyo ta ya had'ata da jikinsa yana cewa ''kin girma fah Hamrah, yaranki biyu amma kina kuka''.

Kanta bisa k'irjinsa ta sa hannu tana bugun gefen k'irjin nasa ta sake turo bakin tana cewa ''ni ban girma ba, kuma ai kai ne yanzu bakason zama a gida, ba dole inyi kuka ba'' ta d'ago kanta ta kalli fuskarsa tace ''i missed u fah, kwana nawa kayi baka gida?'' Ta fad'i hakan tana irgawa da yatsunta, kallonta yakeyi yana jiran ta gama ta fad'a masa, yatsu biyar ta dunk'ula ta had'a da yatsu biyu na d'ayan hannun nata tana nuna masa tana cewa ''kwana haka'' dariya ta sub'uce masa yana girgiza kai ''ke d'in nan in kinayin abu kamar baby'' ta sake shigewa jikinsa tana cewa ''ai ni babynka ce, i missed you nidai kada ka fita'' fuskar tausayi tayi masa sai da ya lumshe ido dan yanda yaji maganar nata, key d'in ya mik'a mata yace ''na fasa'' haka suka koma ciki har aka dawo da yara daga islamiya suka had'u a palo suna hira yara na wasa.

Bai samu yaje gun Abakar ba sai washe gari bayan yaje office, ya k'irasa a waya amma bai d'aga ba, duk da aikin da ke gabansa bai hanasa fita ba. Office na Abakar ya wuce dan yasan lokacin ya fito daga gida yana office, yana zuwa aka barshi ya shige ba tare da an sanar da Abakar ba, da yake ansan yanda Engr. Abakar yake da Dr. Sulaimana sosai.

Engr. Abakar yana duk'ufe sai danne-danne yake akan laptop nasa, bud'e k'ofar da akayi ya jawo hankalinsa dan yaga wanda ya shigo masa office kai tsaye, ganin Dr. Sulaimana yayi a tsaye bai k'araso cikin office d'in ba, ji yayi kamar ya nutse k'asa dan kunya. Muryar Dr. Sulaimana yaji yana cewa ''in shigo ne ko in koma bakason magana dani?'' Murmushi Abakar ya k'ak'alo sannan yace ''haba my Dr., bismillah have a seat'' ya fad'a yana mai nuna masa kujerar zama sannan ya matsar da laptop nasa dan ya saurari Dr. Sulaimana da kyau. Bayan ya zauna Engr. Abakar ne ya fara cewa ''am sorry ka jini shiru koh? Wallahi ban tsaida shawara bane akan maganan nan, duk abin ya dameni na rasa na yi, har Fad'ime tambayana take ko akwai abinda ke damuna. Wallahi ka had'a min zafi''

Dariya sosai Dr. Sulaimana yayi sannan yace ''wai shine duk kayi bak'i harda guntun ramarka?'' Ya matso yana kallon fuskar Abakar shima Abakar d'in shi yake kallo yace ''magana d'aya yanzu nakeson ji, meh zuciyarka ta yanke, kada kayi tunanin wani abu bare ka kawo min uzuri, ka yadda zaka aureta? Yes or no(eh ko a'a)?

Had'iye miyau yayi sannan yace ''ka gane ne abokina, ni abun nan ya d'aure mun kai, ka k'ara min lokaci in gani'' farin ciki ya dabaibaye zuciyar Dr. Sulaimana a ranshi yace ''tunda kak'i cewa bakaso ai kana so ne kenan, wasu dalilan naka suka hanaka karb'a but i know what to do(amma nasan abun yi)'' a zahiri kuwa yace ''babu matsala, duk lokacin da ka shirya ina jiranka'' Basu jima ba Dr. Yace akwai aikin da ke jiransa a office dama maganar da ya kawosa kenan, sukayi sallama ya wuce cike da jin dad'i.

 

 

Shirye-shiryen biki Dr. Sulaimana yakeyi ba tare da kowa ya sani ba, gidanshi dake Shika wanda can za'a kai amarya yayi masa kwaskwarima, yasa akayi sabon fenti sannan ya saka kayan alatu a cikin gidan. Gida ne na bulo(block) madaidaici d'auke da d'akuna biyu da falo a tsakiya. Kowane d'aki da band'aki a ciki(toilet) sai kitchen madaidaici na mutum d'aya bazai takura ba, da tsakar gida mai kyau k'asa ne zube irin yashin nan mai dad'in shara, k'ato ne ba laifi dan motoci uku zuwa hud'u zasu iya zama a ciki, gidan yayi kyau sosai.

A b'angaren Maryamah da Amty Babbe babu wani shirye-shirye, banda wahalar da ita da take sai hanata fita gun Saleh da tayi, tun ranar da ta gansu tare har yau basu sake had'uwa ba... Yau Amty Babbe ta d'ibi kayan abinci wanda Dr. Sulaimana ya kawo a leda ta bawa Maryamah dan ta kaiwa Hajje, tun ranar da ya kawo ta ware wanda zata kai mata amma bata samu taje ba shine yau ta sa Maryamah ta kai mata. Da murna Maryamah ta bar gidan dan tsakaninsu da inda Hajje take akwai nisa sosai kuma Saleh na zuwa kiwo ta can, Allah-Allah take taje daidai inda yake zama ko zata ganshi.

Allah da ikonsa tana isa ta hangosa zaune a wani dutse kansa bisa k'afafunsa, shanayensa a gefe wasu na cin ciyayi wasu na shan ruwa a kogin da ke wurin. Har ta iso dab dashi bai san da mutum a wurinba, ta k'ira sunansa sau biyu bai ansa ba, sai da ta k'ara na uku ''Saleh'' had'e da tab'a shi sannan ya waiwayo a tsorace yana kallonta, yanda ya juyo har ita ma ta tsorata sai da ta koma baya tana kallonsa da alamar tambaya, tace ''Lafiya?'' Sai da ya sauk'ar da ajiyar zuciya sannan ya k'ak'alo murmushi yace ''lafiya k'alau kwaiseh, tunaninki nakeyi yanzu haka'' ya janyo hannunta fuskarshi da alamar tausayawa yace ''Maryamah''.

Ta amsa ''na'am'' yace kinsan halin da na shiga tun ranar da Amty Babbe ta tafi da ke gida?'' Ya kalli gefe sannan ya dawo da dubansa gareta ya cigaba da cewa ''Kwaiseh babu abinda tay miki koh?'' Murmushi tayi tace ''babu abinda tayi min, abu nakeson fad'a maka dama, ka tuna Yaya Sulaimana da ya kawo mu gida rannan?'' Ya gyada kai ba tare da ya amsa ba alamar eh sannan tace ''ai yazo sunyi magana da Amty Babbe, zai dawo ayi aurenmu da almajirinsa, wai can Kaduna zai kai ni'' ta gama maganan cike da farinciki, kallonta yakeyi baki bud'e yana cewa ''har Kaduna Kwaiseh zaki tafi shine kike murna?'' Ta turo baki tana cewa ''toh ba gwanda inje can inyi karatun da kace inyi ba akan a aura min wani anan''.

Shiru yayi yana nazarin maganar, har ransa bai so Maryamah ta tafi ba, kuma gata sai murna takeyi, guntun tsaki ya ja sannan yace ''Allah yasa shine mafi alkhairi'' yayi mata nasiha sosai tana kuka yana kuka, bayan ta tashi zata tafi hawaye a idanunta take cewa ''alk'awarin da kayi min na auran Khajije, kada ka manta'' murmushi yayi yace ''insha Allah'' sannan sukayi sallama ta wuce gun aikar da akayi mata shi kuma ya kad'a shanayensa yayi gaba.

 

 

Tun ana gobe juma'a Dr. Sulaimana ya gama duk abinda ya dace yayi na tafiya Godil, ya samu motar haya k'ato sukayi magana da mai shi suka yi ciniki, washe gari da sassafe suka kama hanyar Godil, shi da abokinsa a motarsa cikin manyar kaya farare tas fuskarsu sai annuri yake, wannan k'aton motar kuwa babu kowa a ciki, driver ne kawai da kwandasta suna bin bayan motar Dr. Sulaimana. Cikin nutsuwa suke tafiya har suka isa Godil daidai k'arfe d'aya, a lokacin mutanen garin suna shirin tafiya sallar juma'a a garin da ke kusa dasu dan babu masallaci a garin. Sai da suka sami Ammi Malud sannan suka d'ibi sauran mutanen garin sukaje masallaci dan suyi sallah sannan a d'aura aure acan ba tare da ansha wani wahala ba.

Haka kuwa akayi, an d'aura aure da sadaki naira dubu hansin kamar yanda sukayi magana da Amty Babbe. Ango bayi da labari aure ya d'auru, Dr. Sulaimana shi ya karb'i auren Ammi Malud kuma shi ya bada auren kuma ya karb'i sadaki. An shafa fatiha Maryamah ta zama amarya Engr. Abakar, kowa ya watse 'yan garin Godil suka d'uru cikin mota dan komawa gida kamar yanda suka zo. Bayan kowa ya shiga mota Dr. Sulaimana ne ya sunkuyar da kai yana gaida wasu dattijai da sukazo wucewa gefensa yaji an dafasa ta baya.

Juyowa yayi da murmushi a fuskarsa ya mik'a masa hannu sukayi musafaha. Dr. Sulaimana har ya juya zai bud'e mota mutumin ya masa magana ''magana nakeson muyi, ko ba kai bane Sulaimana?'' Da mamaki ya juyo yana kallon bak'uwar fuskar ko zai gano sa, cike da mamaki yake cewa ''sorry, ban gane ka ba, ni ne Dr. Sulaimana'' yace masa ''bazaka gane ni ba, amma zaka sanni tunda yanzu Maryamah zata zama tana kusa da kai, sunana Saleh, kuma nasan Maryamah da jimawa, alfarma nakeson nema agunka, kuma da ganinka nasan kai masani ne zaka fahimce ni. Farko da Maryamah tace min aurar da ita za'ayi a birni banso ba, amma da na ganka sai naji na samu nutsuwa kuma naji dad'in auren da tayi ma'ana auren na kusa da kai'' Dr. Sulaimana kallonsa kawai yakeyi yana jiran ya karasa zancen nasa, shi kuwa Saleh hawaye ne ya taru a idanunsa tunowa da yayi Maryamah ta zama mallakin wani, lumshe idanunsa yayi ya mayar da hawayen sannan ya cigaba da cewa.....

''Maryamah na da hankali, kuma tana da ilimi, dan Allah ka koyar da ita addininta, ko bazaka koyar da ita ba ka samo wani ko ka sata a makaranta. Kwaiseh na da baiwar da Allah kad'ai ya sani'' ya dafa kafad'ar dr. Sulaimana yace ''dan Allah ka sa ta islamiya kuma ka kula da ita dan marainiya ce, bata da gatan kowa, ka zame mata uba kuma uwa kuma yaya kamar yanda take k'iranka yaya Sulaimana'' Dr. Sulaimana yace ''duk da ban sanka ba na maka alk'awarin kare Maryamah daga dukkan sharri iya iyawana, zan kula da ita kamar k'anwata, kuma zatayi makaranta da izinin Allah, amma dan Allah kai waye, dan ban tab'a.............''

Maganar da akayi masa ya katse shi, driver ke masa horn akan yayi sauri dare zaiyi basu yi abinda ya kawo su ba, ya juyo ya kalli Saleh yace ''Saleh koh? Insha Allah zamu sake had'uwa'' ya mik'a masa hannu sannan ya shiga mota, ya tada motar ya bud'e glass ya ciro damin kud'i ya mik'a masa sannan yace ''nagode sosai, zanji labarinka agun Maryamah'' dak'yar yasa saleh ya karb'i kud'in sannan suka tafi.

 

 

Bayan sun isa ne Dr. Sulaimana ya bud'e bayan motarsa ya fara ciro akwatuna, ya ciro uku iri d'aya sannan ya ciro wani k'ato kalarsa daban, sai ghana most go shima a cike da kaya. Sai da ya gama cirowa sannan yace a shiga dasu ciki gun Amty Babbe kafin mutane su gani kamar yadda al'adarsu take, ba a kawo kayan lefe sai ranar aure ko kuma ana gobe aure, sai kud'i ko kayan tambaya da ake kawowa bayan an bada auren yarinya wanda shi Dr. Sulaimana bai bayar ba amma ya k'uduri niyyar badawa yau dan ayi komai bisa al'ada kada a tauyewa Maryamah hak'k'i.

Dr. Sulaimana da kanshi ya shiga cikin gidan dan yayi wa Amty Babbe bayanin kayan, babu mutane da yawa acikin gidan da ya shigo, tsugunawa yayi har k'asa ya gaishesu sannan ya shige d'akin Amty Babbe bayan sunce masa ya shiga tana ciki. Daga ita sai Hajje, sai wasu da alama k'awayenta ne, tabarma suka shimfid'a ya zauna suka janyo akwatunan suka ajiye masa a gabansa ya fara musu bayani ''wannan......'' ya nuna akwati kala uku iri d'ayan yace na Amarya ne, wannan kuma....'' ya nuna akwati d'aya babban yace ''kayan iyaye ne, sai kuma wannan.....'' ya nuna ghana most go sannan yace '' a rabawa k'awayenta da 'yan uwa wad'an da baza a rasa ba'' (al'ada irin ta shuwa akasari kayan tambaya ake kaiwa farko, lokacin da gemu yaga gemu aka bada aure sai akai kayan tambaya, acikin kayan tambaya zata cire abun gayyatar k'awaye, su gazal da jambaki da sauransu. Kayan lefe/aure kuwa sai ana washe gari aure ko ranar aure ake kaiwa, kayan da za'a kai kuma ya k'unshi kayan iyaye, takwara, mai mata kitso in akwai kenan mostly atamfa ake bayarwa da takalmi, sai kuma kayan Amaryan).

Hajje tayi carab tace ''ai kayan nata yayi yawa, Amty ko nawa ba kalar wannan akwatin aka bani ba'' Amty Babbe ta kashe mata ido alamar tayi shiru sannan tace ''Toh ai babu komai, mun gode, amaryar tana nan gun Khajije k'awarta, in kun shirya sai a fito da ita'' ya ansa da toh sannan ya fice. Amty Babbe ta taso ta bud'e kayan, Atamfofi da laces ta fara dubawa guda goma sha biyu, sai wad'an da aka d'inka guda shida, ta d'auki atamfa uku da laces biyu ta ajiye a gefe ta bud'e d'ayan akwatin.

Ido da baki suka bud'e suna kallon takalma daidai k'afanta dukka kamar ya auna masu shegen kyau, babu yanda zata yi da takalma guda shidan nan da ta d'auka, ta d'ibi under wears tana rabawa 'yan d'akin ta bar mata pants kawai dan sunyi k'anana shima da ta raba, babu bra bare ta kwasa, sarak'una da d'ankunnaye duk ta d'ibi wanda takeso Hajje ma ta kwashi rabonta sannan aka rufe akwati aka janyo k'aramin. kayan kwalliya ne da man shafawa da sauran tarkacen da baza a rasa ba, wasu sun sani wasu basu sani ba, sukayi ta b'arnarsu sannan suka d'ibi wanda zasu iya anfani dashi sannan suka rufe, daga baya ma suka juye kayan da yake k'aramin akwatin zuwa babban suka ajiye k'aramin wai zasuyi anfani dashi.

 

 

 

Maryamah na zaune a k'ofar d'akin Khajije idanunta na kan yaran da ke tsakar gidan suna wasa k'wak'walwarta kuma na can duniyar tunani, Khajije da ta fito daga toilet (band'aki) butar hannunta ta ajiye sannan tazo ta zauna a gefen Maryamah tana cewa ''tunanin meh kikeyi?'' Maryamah tayi murmushin takaici sannan tace ''aure fah za'a yi min yau amma ki ganni ko wanka Amty Babbe bata sani inyi ba, Khajije na k'osa in bar garin nan dan zuciyana na bijiro min da wani abu akan Amty Babbe kuma na tabbata shaid'ani ke son cutata''

Khajije tace ''Maryamah nifah banga abin tada hankali ba yau, yau fah zaki tafi kuma rayuwar ki dukka zaki canja'' Maryamah kuka ya kubce mata ta rik'e hannayen Khajije tana cewa ''shekarana goma fah kacal amma wai har an min aure? Wannan wane irin k'iyayya ne? Meh yasa Mamana ta auri Mahaifina bayan tasan shi waye'' Khajije ta rufe bakin Maryamah da hannunta tana cewa ''shhh!!! ki daina tunanin nan Maryamah, yanzu tashi kiyi wanka zanje in karb'o miki kayanki agun Amty, ki daina kukan nan'' ta share mata hawayen sannan ta tashi ta juye mata ruwar da ta d'aura a murhu dan yayi zafi, ta kai mata bucket(bokati) na ruwan toilet sannan ta fice dan ta kawo mata kayan da zata sa.

Bayan fitar Khajije sai da ta k'ara minti biyar sannan ta shiga wanka, tana cikin wankan Khajije ta dawo da kayan da ta karb'a agun Amty Babbe, daga cikin wanda aka sa mata a akwati aka d'aukosa, atamfa ce mai kalar ja da brown, d'inki mai kyau riga da skirt(siket) bayan ta fito Khajije ta shiga d'akin mamanta ta d'auko mata mai.

Maryamah tana bud'ewa taji k'amshi ya doki hancinta, mayar da murfin tayi tana cewa ''wannan mai na mama ne bakiji k'amshin da yakeyi ba'' Khajije ta ja guntun tsaki sannan tace ''ki shafa mana, ina ruwanki ke kam, kin manta Hajje k'amshin da tayi da gyaran da Amty Babbe tayi mata kafin aurenta? Ke dan kin shafa wannan wa ma zai gane?'' Ba musu ta shafa mai d'in sannan ta sa kayan d'as a jikinta, batayi kwalliya ba fuskanta mai kawai ta shafa har yalk'i yakeyi in rana ya haska, d'ankwalin kayan kuwa shi ta yafa sa ya zama gyale.

Da misalin k'arfe uku da rabi bayan kowa yayi sallahr la'asar Amty Babbe ta da muk'arrabanta suka shiga gidansu Khajije dan yiwa amarya nasiha, babu laifi ance tabi mijinta, wasu na yada magana wasu na mata dariyar batayi kyau ba kamar ba amarya ba. Amty Babbe ce ta rik'ota bayan ta yaryad'a mata turare mai k'amshin gaske a jikinta da mayafin da aka rufeta dashi, har cikin Motar bus d'in da Dr. Sulaimana yazo dashi ta kaita.

Sai da ta shigar da Hajje sannan ta sa Amaryar, ta bud'e mayafin da ya rufe fuskarta sannan tace ''Maryamah na barki a hannun Allah kuma na fita hak'k'inki tunda na aurar dake'' da mamaki Maryamah ta dago fuskarta da ya cika da hawaye ta kalli Amty Babbe, da mamakinta hawaye ta gani yana sauk'a a k'uncinta, ta ja majina ta share hawayen sannan tace ''ba dan ina sonki nake kuka ko dan zanyi kewarki ba, a'a, na tuna da yayana ne'' bata sake magana ba ta koma cikin gida tana mai zubar da hawaye, Maryamah ma kukan takeyi sosai kamar ranta zai fita.

Har mutane sun gama shiga motar sannan Khajije tazo da gudu da d'aurin kayanta a d'ankwali, ta zauna gefen Maryamah tana cewa ''an barni inje dak'yar sai da na fara musu kuka'' Gam-gam suka rik'e hannun juna sannan suka cale garin Shika gidan Amaryar Engr. Abakar

 

 

 

Da misalin k'arfe 6 suka isa garin Shika, sun isa gidan ana k'iran sallah a masallacin da ke kusa dasu. Dr. Sulaimana bayan ya shigar dasu ya nuna musu toilet da inda zasu samu ruwan alwala sannan ya wuce masallaci, da aka idar da sallah shi ya d'auki kayan Maryamah akwati kwara biyu jal bayan shi uku ya kai, babu abinda Amty Babbe ta sayo mata a matsayinta na uwar amarya, a ranshi yace ''insha Allah k'arshen matsalarki tazo Maryamah, Allah dai ya d'aura mu akan Engr.''

Sai da ya shigar har d'akin da ya ajiye domin amarya Maryamah sannan ya fito dan ya sallami driver, yace ''gobe kazo da misalin k'arfe sha-biyu ka d'aukesu ka mayar dasu, in ka dawo in akwai ciko sai ka nemeni in baka'' driver ya amsa da ''toh''.

Abokinsa ya bawa makullin mota da kud'i da k'aton foodflask(kula) dan yaje restaurant (wurin cin abinci) ya sayo wa 'yan kawo amarya abinci. Komawa yayi cikin gidan dan ya nuna musu komai na gidan, yana kan nuna musu wayarsa tayi ringing, tun kafin ya d'auko wayar daga aljihunsa yasan wacce ke k'ira dan wak'ar da wayan ke yi. sai da ya nemi izini agunsu sannan ya fita cikin gida nesa da hayaniyar matan sannan ya d'aga wayar, cewa tayi ''har yanzu baka dawo ba, lafiya?''

Murmushi yayi sannan yace ''yi hak'uri my woman, am here busy doing somthing very important(ina nan ina yin abu mai muhimmanci) zan dawo kada ki damu'' ta turo bakin kaman yana ganinta tace ''ai da ka fad'a min baza ka dawo da wuri ba, nayi abincin rana baka zo ba ga na dare, kuma ni dukka nakeson ka ci, very special dishes nayi maka'' yace ''ohh!! nayi missing girkinki kuwa, ki ajiye min dukka zanzo inci, in Al'amin baiyi bacci ba kafin in dawo nasan zai taya ni cinyewa'' cikin shagwab'a tace ''naka ne kai kad'ai sabida haka dukka zaka cinye, what time zaka dawo my one?'' Yayi murmushi sannan yace mata ''ten'' ''toh sai ka dawo, Allah ya kiyaye min kai ya tsare'' yace ''ameen'' sannan ya kashe wayar.

Ajiyar zuciya ya sauk'e sannan yace ''matar nan tana son kamo ni'' dariya yayi da ya tuna abinda tace, lokacin da taga akwati har uku a bayan motarsa, ''wai in ma kishiya zakayi ka rasa akwati nawa zaka mata sai uku'' tayi k'wafa sannan tace ''wallahi ka kawo kishiya gidan nan Allah komai nayi kada kaga laifina'' ta juya ta tafi, dak'yar ya shawo kanta ta yadda ba nasa bane. A fili yace ''yanzu in taji Fad'ime aka yiwa kishiya ai asirinmu ya tonu, yanda suke son juna d'in nan nasan zata fad'a mata, Allah dai ya kare'' sannan ya koma cikin gidan ya cigaba da nuna musu har aka kawo abinci ya musu sallama akan zai wuce, ya sallamesu dan bazasu had'u ba sannan ya wuce Kaduna.

A hanyarsa ta komawa ya k'ira Engr. Abakar, lokacin ya iso gida kenan zai fara cin abinci, Fad'ime na zaune gefensa wayarsa ta fara ringing, sai da ya kusa yankewa sannan ya d'aga yana cewa ''ina da niyyar k'iranka dama sai ga call naka'' Dr. Sulaimana yayi murmushi dan yaji dad'in maganar, ya amince da auren kenan tunda har yayi niyyar nemansa, yace ''kada ka damu, gobe zamu fita zanzo gida in d'auke ka ko bayan sallahr azahar haka''

Engr. Abakar yace ''ina zamu je?'' Dr. Sulaimana yace ''kai kam sai nazo d'in kawai, ka shirya ka sa kayan manyan mutane, ba k'ananan kaya ba dama'' Engr. Abakar yayi dariya ya kalli matarsa sannan yace ''sai madam ta bani izinin fita, dan weekend bana fita sai da izininta, kuma kasan next week zan tafi aikin nan, banson tayi missing d'ina da yawa'' ya kashe mata ido ita kuwa sai murmushi takeyi a gefe. Dr. Sulaimana yace ''whatever, nidai gobe kada inzo baka shirya ba, dan zan iya maka yaji ko kuma in baka red card kaje ka samo wani aminin ba ni ba'' engr. Abakar dariya yayi sannan yace ''zan shirya insha Allah, sai kazo kawai'' sukayi sallama sannan ya kashe wayar.

 

 

 

Washe gari tun safe Maryamah da khajije suka gyara gidan sukayi shara, Khajije ta kunce k'ullin d'an kwalinta ta ciro kasko d'an k'arami da turaren wuta a cikin leda da bazai wuce cikin hannu d'aya ba, ta kalli Maryamah ta mik'a mata tace ''gashi kina anfani dashi tunda Amty Babbe bata sa an miki ba'' godiya tayi sannan tace ''a ina kika samu?'' Ta murgud'a mata baki tace ''ina ruwanki''.

Nemo yara suka yi 'yan anguwa k'anana suka basu kaskon suje makwabta su karb'a musu garwashi zasu sa turaren wuta. Basu fi minti biyar ba suka dawo da kaskon cike da garwashi, baki har kunne Khajije ta karb'a ta zuba turaren wutan d'an kad'an, ahankali ta barshi yake fitar da hayak'in had'e da k'amshi ba tare da ta fifita shi yana kamawa bal-bal kamar yanda wasu ke yi ba.

In ya k'are ta k'ara d'an kad'an dan kada wutar ya mutu in ta zuba da yawa, tana zagaye gidan tana d'an hurawa da bakinta dan wutar kada y mutu bata gama zagaye gidan dashi ba. Bayan ta gama ta shigo d'akin ta ajiye tana cewa ''k'amshi turaren nan'' Maryamah tace ''eh, na mama kika d'iba koh?'' Khajije tace ''eh, ita ta bani harda kaskon tace in munzo musa a gidan kada mijin yazo yaji gidan baya k'amshi kamar ba amarya ba''.

Maryamah kuka ne yazo mata sosai da taji abinda Khajije tace, wato wasu ma sukayi tunanin haka amma Amty Babbe bata yi ba? Khajije tazo gefenta ta zauna sannan ta dafata, ''yanzu kin girma fah Maryamah, aure kikayi yakamata ki koyi hak'uri da juriya'' Maryamah ta rungumeta tace ''nagode sosai Khajije, saura abinda na rok'eki kiyi min na auren Saleh, shi kad'ai ya rage kiyi min wanda zai sa in sake tabbatar da d'imbin k'aunar da kike min'' Khajije ta shafa kan Maryamah tace ''duk yanda kikeso haka zanyi'' hira sukeyi sosai tsakaninsu sunayi suna zubarda hawaye, daga k'arshe kowa kusurwar d'aki ya samu ya rakub'e yana kukarsa babu mai rarrashi.

Da misalin k'arfe sha-biyu aka d'ibesu gaba d'aya babu wanda aka bari sai Maryamah da take ta sharb'ar kuka, kusan duk 'yan motar sai da sukayi hawaye da suka shiga mota, Khajije kam sai da taga motar ta fara tafiya tukunna ta rikice ta fara rabka ihu ana rik'eta tana k'iran sunan Maryamah, Maryamah kuma a bakin k'ofar gidan ta zauna tana kuka sosai har sai da tayi jawur tsaban kuka, idanunta duk sun kumbura. Sai da tayi mai isarta sannan ta tashi ta kad'e zaninta ta koma cikin gidan hawaye fal idonta.

Dr. Sulaimana ke jan motar Engr. Na gefe suna hira, tambayan duniyan nan Engr. Abakar yayi wa Dr. amma yak'i fad'a masa inda zasu je, har suka fita daga gari yana tambayarsa ''wai ina zaka kaini ne? Sayar dani zakayi kanason Fad'ime ta d'aureka koh?'' Dr. Sulaimana ya kauda kai yak'i ansa shi, da yaga baza a amsa shi ba bai sake tambaya ba, har lokacin da suka isa Dr. Sulaimana yayi parking a gidan da yake cewa zai zo ya duba in akwai gyara yayi kafin yazo aiki garin, da mamakinsa yake kallon gidan harda sabon fenti, baiyi magana ba yabi bayan Sulaimana har cikin gidan, shi kam sai kalle-kalle yakeyi dan gidan yayi masa kyau, har ya fara tunanin ya d'auko Fad'ime tunda an gyara wurin zasu iya zama tare kowane weekend suje gida har su gama wannan aikin. Sallamar da yaji Dr. Sulaimana yana dokawa a bakin k'ofar ya basa mamaki sosai, daga ciki yaji wata siririyar murya da alama kuka takeyi ta amsa sallamar.

Engr. Abakar bai gama mamaki ba sai da yasa kansa ciki falon yaga kayan da yake ciki, a ransa yace Dr. Sulaimana meh yake nufi, haya ya bada bayan yasan zai zo yayi anfani da gidan? In kud'i yakeso meh yasa bai bashi hayar ba? Dr. Sulaimana ke ce masa ''bismillah ka zauna'' babu fara'a a fuskarsa ya zauna, Maryamah ta gaishe su suka amsa, dab'as take zaune batayi tunanin kawo musu ruwa ba sai da Dr. Sulaimana yace baki kawo mana ruwa ba, tashi tayi gyalen kanta ya zame ya sauk'o kafad'anta, kanta Engr. Abakar ya gani ya ware ido yana kallon ikon Allah, saura kad'an dariya ta kubce masa amma ya gumtse ya had'iye, Dr. Sulaimana ya kula da hakan, gashin kanta ya gani wanda toliyan tsakiyan duk sunfi tsayi, gefe-gefen kuma gashi sun fara fitowa sai ya bada wani ma'ana daban. Dan ma gashin nata mai kyau ne da bazai yi kyaun gani ba.

Bayan ta fita d'ibo musu ruwa ne Dr. Sulaimana yace ''kasan wacece wannan?'' Nan ya samu yayi dariya harda buga k'afa yana cewa ''a ina ka samo wannan'' kamar daga sama yaji Dr. Sulaimana yana cewa ''malam ita ce matar da na aura maka jiya, lokacin da ka k'irani kake tambayana ina nake nace maka ina gun d'aurin aure, toh wannan ita ce matar, kuma ita ce zata kawo maka kwanciyar hankali da kuma tarzomar da ka kunnowa kanka a gidanka'' cikin tashin hankali yace ''what?'' Idanunsa har sun canja kala dan tsaban b'acin rai, ''Dr. Kana cikin hankalinka kuwa? Kasan meh kake cewa? Wannan wai ka aura min?'' Sauk'ar da numfashi yayi yana cewa ''toh ka gaggauta nemo mata miji amma ba ni ba wallahi'' waje ya fice yana huci cike da takaici.

 

 

 

Fitar sa daga d'akin waje ya wuce ba tare da yasan ina zai je ba, hankalinsa a tashe yana sake tuno yarinyar da ya gani wai ita ce matarsa? ''Meh yasa ma bai riga Dr. Sulaimana k'ira ba jiya? Shi fah dama yayi niyyan k'iransa dan yace ya yanke shawarar bazai k'ara aure ba, ashe har anyi auren ba ni da labari? Lallai Dr. ya gama da ni'' a ransa yake ta tunanin nan. Tafiya yake baisan inda yake dosa ba, sai da yayi tafiya mai nisa sannan ya ciro wayarsa a aljihu ya k'ira abokinsa mai suna Jabir.

''please kana ina ne Jabir?'' Jabir da yake driving (tuk'a mota) yace ''yanzu zan shiga Kaduna, ka manta naje Zariya tun last week?'' Engr. Abakar ya sauk'ar da numfashi yace ''dan Allah ina Shika yanzu haka, motana ya samu matsala, kazo mana ka isar dani gida'' baiyi musu ba Jabir yace ''babu matsala, nan da 30mins(minti talatin) zaka ganni''.

A b'angaren Dr. Sulaimana kuwa jikinsa yayi sanyi, ji yayi duk jikinsa yayi masa nauyi, tunaninsa ya tsaya cak ''meh Engr. Yake nufi?'' abinda yake maimaitawa a ransa kenan? Dak'yar ya iya tashi ya fice dan yaga ko Engr. yana nan, bai same shi ba hakan ya bashi damar komawa ciki.

Kitchen ya isa inda Maryamah ta shiga dan kawo musu ruwa, ita ma taje tayi zamanta kamar ita ke k'era ruwar da zata kawo musu, ganinta yayi tana kalle-kalle a kitchen d'in ko meh take nema oho. Sai da ya furzar da iska ta bakinsa sannan ya k'ak'alo murmushi yana cewa ''Maryamah me kike nema haka? Har mijin naki ya gaji da jiranki ya tafi'' sauk'ar da kanta tayi k'asa tana cewa ''ai babu kwanon da zan kawo muku ruwar, shine nake ta nema kuma ban samu ba?'' Dariya yayi sannan yace ''baki dai san kwanon ba, amma ga jug(abun sa ruwa) a gefenki'' ya fad'i hakan yana nuna mata jug da ke ajiye a gefenta da murfinsa harda kofuna guda hud'u masu kyau.

D'aukowa tayi tana juyawaa hannunta tana kallo, mai kyau dashi kuma ba k'ato ba sai dai bata ga inda zata zuba ruwar ba, wani b'uli ta gani ta sa idonta ta lek'a, Dr. Sulaimana dariya yazo masa amma ya danne, yanason yaga abinda zatayi kafin ya koya mata wasu abubuwan, bai ankara ba yaga ta fara girgizawa da k'arfinta, tana cikin girgizawa taga murfin ya fad'o k'asa, sa'a ma murfin yaci bai fashe ba, da murnarta ta tsuguna ta d'auko tana nuna masa wai nan ita ta iya bud'ewa. Dariya yayi mai isar sa sannan ya karb'a ya rufe sannan ya sake bud'e yana cewa ''haka zakiyi''.

Daga nan ya fara nuna masa kayar da yake kitchen d'in d'aya bayan d'aya, duk da ba kaya da yawa bane a kitchen d'in sai da ya nuna mata komai, ya nuna mata yanda ake anfani dasu kuma ya fad'a mata anfaninsu. Maganar abinci kuma ce mata yayi zai samo wacce zata taya ta kwana kuma tana musu girki, kafin a samo kuma zai ajiye mata kud'i tana saya a restaurant da yake kusa dasu, tayi godiya sosai sannan yayi mata sallama ya fice.

Engr. Abakar da yake zaune bakin titi shi d'aya ya shafe minti arba'in yana zaune a wurin, banda k'arar mota da yake ji fit! fit!! fit!!! baya jin komai, k'arar motar ma wani sai ya wuce ba tare da yaji ba, duniyar tunani ya fad'a da tashin hankali, akai-akai yake tsaki yana girgiza kai, wani lokacin ya bugi iska yana cewa ''why Dr. (Me yasa Dr.)'' Har Jabir ya k'irasa dan ya kwatanta masa inda yake bai dawo daidai ba. Tun da Jabir ya iso gunsa baiyi magana ba har suka isa garin Kaduna, Jabir ya kula da halin da yake ciki amma bai tambayesa ba sanin ko ya tambaya bazai samu amsa ba.

Sun isa har cikin gidan Engr. Abakar, godiya yayi ya shige gida cike da tashin hankali, Jabir tab'e baki yayi ya d'age kafad'a alamar ba ruwanshi sannan ya bar harabar gidan.

Ya shigo falon ko sallama babu ya wuce d'akinsa, Fad'ime da take zaune kan kujera ta hakimce tana kallon TV da mamaki ta mik'e tana duba lokaci ''k'arfe uku da minti ashirin da biyar kuma yace bazasu dawo da wuri ba, lafiya ya shigo warhaka kuma cikin wannan halin?'' Tashi tayi ta bishi d'aki dan jin damuwarsa.

 

 

 

Shigar ta d'akin ke da wuya ya shige toilet ko inda yake bata iso ba, zata iya cewa da gudu ya shige toilet d'in, dan sauri yayi sosai har ya tsorata ta, bata damu ba dan ta d'auka lalura ce ta kama sa, amma meh? tafi minti arba'in ko k'arar ruwa bata ji ba. Tashi ta yi ta isa k'ofar ta fara knocking (bugawa) ahankali, bai mata magana ba hakan ya bata damar yin magana ''lafiya kuwa my Engr.?'' Shiru yayi bai amsa ba.

Buga k'ofar takeyi tana tambayarsa ba tare da gajiyawa ba, shi kuma da yake tsaye yana kallon madubin da ke mak'ale a toilet d'in ya jira ta gaji amma ta k'i bari, guntun tsaki yaja sannan ya bud'e k'ofar ya fito, bai ko kalli fuskarta ba ya bi gefenta zai wuce. Rik'e hannunsa tayi tana hawaye tace ''am sorry(yi hak'uri) in ni na b'ata maka rai, bazan iya jure wannan horon ba'' sauk'ar da ajiyar zuciya yayi ya juyo ya rungumeta sosai a jikinsa, bai iya cewa komai ba sabida baisan meh zai ce ba, shi bai ma son ya kalleta dan kada su had'a ido shiyasa ya shige toilet da ta shigo, gani yake kamar zata gano ya mata kishiya da wancar 'yar yarinyar, ciki-ciki ya ja tsaki sannan yace ''a waje aka b'atan rai, kuma banson hucewa kanki shiyasa nakeson zama ni kad'ai, yi hak'uri ki daina kukar nan kinji?''

Numfashi ta sauk'ar ta goge hawayen da ke fuskarta, ta janyo shi zuwa bakin gado suka zauna sannan ta rik'e hannunsa tana kallon fuskarsa, kansa na k'asa ya kasa d'aga ido ya kalleta, gani yake kamar ya cuceta, hannunta ta sa ta d'ago fuskarsa tana cewa ''look at me(ka kalleni) muyi magana'' idonsa ya kasa d'aurawa akan fuskarta, bata damu ba ta fara cewa ''kasan banason ganinka cikin wani hali ko? Me yasa zaka yi min haka bayan kasan matsalarka matsalata ce, damuwarka damuwata ce........'' yatsunsa biyu ya d'aura kan leb'b'anta yana cewa ''sshhh!!! No need to repeat dis(babu anfanin maimaita hakan), na sani kuma ya wuce bazan sake ba. Am sorry 4evrything my wife, i olways want to see u happy, ur swt words really mek me feel special(yi hak'uri game da komai matata, inason ganinki cikin farinciki, kalmominki dad'ad'a na sani inji ni daban ne.'' Ya rungumeta yana cewa ''i love you mine, only you(ina sonki tawa, ke kad'ai)'' ita ko ta sake k'ank'amesa tana cewa ''i love you too, Allah ya huci zuciyar ka mijina''.

Yau kwana biyar da auren Engr. Abakar da Maryamah, Dr. Sulaimana kusan kullum sai yaje Shika dan jin matsalar Maryamah, acikin kwana biyar d'in nan ya samo wata dattijuwa bazawara wacce shekarunta bazasu gaza arba'in ba, tana kwana da Maryamah kuma ita ke musu girki. Haka kuma ya fara nemo mata islamiya mai kyau da zai iya sata dan cika alk'awarin Saleh.

Har ranar babu wanda ya nemi d'an uwansa acikin Dr. Sulaimana da Engr. Abakar, shi Dr. ya bar komai zuwa lokacin da Abakar zai zo Shika fara aikinsa, shi kuma Abakar bai san yanda zaiyi da wannan auren ba, kuma kwata-kwata hankalinsa bai kawo masa akan zai iya sakinta ba, bai ma yi tunanin hakan ba bare yace zaiyi ko ya huta. Matarsa Fad'ime sai shirye-shirye takeyi na abinda zata bawa mijinta ya tafi dashi Shika, snacks ne kawai batayi ba, tayi niyyar sai ana washe gari zai tafi za ta yi dan kada ya b'aci kafin ya dawo wani satin.

 

 

 

Yau Monday(litinin) yayi dai-dai da ranar da Engr. Abakar zai tafi Shika don fara aikin da aka bashi, bayar motarsa cike da kayan lashe-lashe da tand'e-tand'e, snacks(meatpie, doughnut, cake, samosa d.s) duk Fad'ime tayi masa, ta had'a masa plates na cin abinci, foodflask(kula) da spoons(cokala), hotplate da heater duk sai da ta sa masa wai wataran zaiyi anfani dasu. Hatta abincin da zai ci ranar sai da ta girka masa wai kada ya fita saye sai ya huta zuwa gobe.

Tare suka fito daga cikin gidan tana rakasa wurin mota hannunsu sak'ale da juna, kamar zatayi kuka yana bata hak'uri, bai tab'a tafiya wani aiki yayi sati ba, wannan gashi ba ma sati ba watanni zaiyi weekend kawai zai na dawo mata duk sai taji ba dad'i. Bud'e masa motar tayi ta bashi hanya, tsayawa yayi ya rik'e hannayenta yana cewa ''ni fah ki mayar da hawayen nan in ba so kike in taya ki ba'' dariya tayi shima ya taya ta sannan ya zauna wurin driver, ya sa k'afarsa d'aya a ciki d'aya a waje yana cewa ''kink'i bani kwarin gwiwar tafiya Fad'ime, duk kin b'ata rai'' ce masa tayi ''ai banson ka tafi ne, zuciyana tsinkewa yakeyi tun jiya, bansan me yasa ba''.

Zuciyarsa shima ya buga ya d'aga kai yana kallonta tana share hawayen da ya sauk'o mata, murmushi tayi sannan tace ''ina maka fatar alkhairi, Allah ya kaika lafiya ya dawo min da kai cike da samun nasara'' kafin yayi magana yaji an bud'e gate(k'ofa) hakan yasa duk suka mayar da hankalinsu kan motar da yake shigowa, Fad'ime ne tace ''kamar yasan ina mamakin zuwar da baiyi ba kwana biyu, ashe zai zo ya raka ka'' Engr. Abakar ya tab'e baki a ransa yana cewa ''ya jajubo min alak'ak'ai ai dole yak'i zuwa''.

Sallama Dr. Sulaimana yayi musu cike da fara'a ya mik'awa Engr. hannu sukayi musafaha, suka d'anyi hira da Fad'ime tana tambayar aminiyarta Hamrah kuma tayi masa k'orafin zuwan da baiyi ba kwana biyu, hak'uri ya bata sannan ya koma gun motarsa yayi parking(ajiye) gun ajiye motoci, kafin ya iso sun gama ban kwanansu shiga motar kawai yayi suka fice daga gidan, Fad'ime na d'agawa mijinta hannu.

A hanyarsu babu wanda yayi maganar Maryamah, hirar kirki ma basuyi ba dan Abakar bai sake masa fuska ba, sai wani shan k'amshi ya ke yi kamar ba Abakar d'in da ya sani ba, abun dariya ma ya basa sai dai bai dara ba dan kada Abakar ya k'ara zuciya. Sai da suka shigo garin Shika suka fara gardama, Dr. Sulaimana yace sai dai yaje gidansa shi kuma Engr. Abakar yace ''bazan je gidan ba, ai kasan da zuwa na kaje ka sa wata a ciki, na gwammace in zauna a hotel akan inje gidan can'' sai da Dr. Sulaimana ya nuna b'acin ransa sosai amma yak'i, Dr. Sulaimana cikin b'acin rai yace ''ka tsayar da motar in sauk'a''.

Abakar bai kulasa ba sai tafiya yake yi, cikin b'acin rai ya buga gaban motar yana cewa ''ka tsayar da motar in sauk'a nace'' a tsorace Abakar ya rage gudun da yakeyi ya samu gefen hanya yayi parking, kafin Dr. ya bud'e k'ofar Abakar ya kulle yana cewa ''ka tsaya ka saurare ni Sulaimana, kai kasan baka min adalci ba da ka aura min yarinyar nan, kuma ni bazan iya zama da ita matsayin matata ba gaskiya'' Dr. Abakar a ransa yace ''toh ka saketa mana, sai dai ni bazan tab'a cewa ka saketa ba dan nasan nan gaba zaka so zama da ita'' a fili kuwa gimtse fuska yayi yak'i amsawa. Sai da Engr. Abakar ya sake magana sannan yace ''in har ka yadda dani ka zauna a gidan can, ba sai kayi zaman aure da ita ba dan k'arama ce bata san komai akan aure ba, nidai kayi min wannan alfarmar kaje gidan ka zauna''.

Engr. Abakar yace ''yanzu dai sai nayi shawara, ka bari inje hotel in na gama shawara zan fad'a maka'' Dr. Sulaimana yace ''lallai Abakar, ban tab'a d'auka a rayuwa za ka yi min haka ba, ni masoyinka ne kuma taimakonka nakeson yi kai shaida ne bazan tab'a cutarka ba'' Engr. ya tab'e baki yace ''ka dai barni inyi shawarar'' Dr. Sulaimana cikin bacin rai ya bud'e k'ofar ya fita yana huci, da mamakinsa yaga Engr. ya bawa motarsa wuta ya barshi a wurin cike da takaici da mamaki.

 

 

 

Tafiya yakeyi yana nazarin sauyawar abokinsa, bai d'auka zai tafi ya barsa ba ko da wasa, shi kawai yayi hakan ne dan ya jawo hankalinsa akan ya zauna a wannan gidan amma plan nasa baiyi aiki ba, guntun tsaki yaja ya cigaba da tafiya. Kamar daga sama yaji ana masa horn, d'aga kansa yayi yaga Engr. Abakar ya sauk'ar da glass yana jiransa ya iso inda yake, tsallake kwalta yayi ya isa gunsa.

Engr. Abakar yace ''ka shigo muje'' bud'e motar yayi ya shiga ba tare da ya masa magana ba. Har suka isa babu wanda yayi wa wani magana kowa da abunda yake kimtsawa a ransa.

Bayan sun isa sun samu gidan a gyare mai kyau amma baya k'amshi baya wari, tab'e baki Engr. Abakar yayi ya samu kujera ya zauna dan babu kowa a falon. Dr. Sulaimana ya d'auko makullin k'ofar d'akin a ma'ajiyarsa ya bud'e sannan ya d'auko tsintsiya wai zai gyara masa d'akin duk dan kada Abakar yayi zuciya ya tafi. Maryamah da take d'aki tana maimaita karatun da Saleh ya koya mata kafin barinta Godil taji motsi, hakan yasa ta d'auki hijabinta ta fito falon tana kallon bak'on da ke zaune akan kujera ya lumshe ido. ''Sannu (Usek)'' tace da kalmar shuwa.

Bud'e idonsa yayi ahankali ya kalleta daga sama har k'asa, hijabi ne a jikinta bak'i, skirt d'inta kuma da yake gani ta k'asa ja da ratsin bak'i, a ransa yace ''wai ta iya sa kaya yayi matching ne ko meh? Allah dai yasa ba riga daban skirt daban take sawa ba'' a fili kuwa yace ''ya kike?'' Ta amsa da ''lafiya k'alau'' sannan ta wuce d'akin da taji alamar ana shara.

Ganin Dr. Sulaimana tayi ya nad'e hannun rigar shirt nasa yana shara, da wuri ta iso gunsa ta karb'a sannan ta gaida shi tana cewa ''me yasa baka k'irani inyi sharan ba?'' Murmushi yayi yana cewa ''baki ga mijinki bane? ko ruwa baki kai masa ba'' d'agowa tayi da mamaki tana cewa ''wai waccan shine almajirin naka?'' Hannunshi ya d'aura kan bakinsa yana cewa ''shh!! Yanzu ki kai masa ruwa zamuyi magana anjima'' ba musu tayi yanda yace sannan ta dawo ta cigaba da sharar yana taya ta goge-gogen inda yayi k'ura. Bayan sun gama yaje ya ciro kayar da suke boot na engr. Abakar ya shigo masa dasu ciki dukka sannan suka koma falo, sun riske gogan idonshi a lumshe ko meh yake nazari? oho.

Zama sukayi suka fara hira, anan ne yake fad'a mata zata fara zuwa islamiyar primary, in ta gama akwai secondary d'insa mai suna Community school for higher islamic studies Shika. Shekara shida ake gama primary haka secondary din ma shekara shida, ya cika shekara sha-biyu kenan, islamiya ne wanda yake k'ark'ashin A.B.U zaria. Yayi mata nasiha sosai akan ta kula da karatunta, ita ko tayi murna sosai harda hawayenta.

Bayan sunyi sallar azahar dawowa suka sakeyi falon, engr. Abakar shima zama yayi daga inda ya tashi ya kuma lumshe ido. Dr. Sulaimana da yaga haka sai yace wa Maryamah ''nikam baki tab'a bani labarin mama da Saleh ba, inason ji yau kam'' murmushi tayi sannan tace ''ai kai ne baka nemi kaji ba shiyasa ban fad'a maka ba, amma tunda ka nema ka sani yau zaka ji wacece Maryamah wacce ta tashi agun Amty Babbe k'anwar mahaifinta'' Dr. Sulaimana ya gyara zama ya kad'e kunne yace ''bismillah'' sai da tayi dariya sannan ta fara da cewa..........

 

 

 

''Sunana Maryamah, sunan mahaifina Hassan na mahaifiyata kuma Aisha, mahaifina ya kasance d'a na farko agun iyayensa, daga shi sai Amty Babbe, sai Ammi Hussaini sai kuma Amty Hajje, nasan ka santa dan bata jima da yin aure ba'' ya kad'a kai yace ''na gane ta'' ta cigaba da cewa ''mahaifina bai yi arabi ba bare boko, yayi karatun allo ne agun wani malami da yake garinsu can kafin su dawo Godil da zama, bayan yayi iya karatun da yaga zai iya sai ya fara tafiye-tafiye gari-gari yana kiwon shanaye wani lokacin kuma yayi saye da siyarwa.

''Haka yake yi har Allah ya kai shi wani k'auye da yake kusa da Gombe, anan ya zauna ya d'an jima kuma anan ya had'u da mahaifiyata, 'yar igala ce kuma wallahi yaya Sulaimana ba za ka tab'a gane ita igala bace sai ta fad'a maka, fara ce kuma kyakkyawa'' hawaye ya cika mata idanu ta cigaba da cewa ''bayan yayi shekara d'aya ya koma gida ya fad'awa iyayensa ya samu matar da yake so, cike da murna iyayensa su ka yi na'am ba tare da bincike ko jin a ina ya samo ba kasancewar anyi-anyi yayi aure yak'i''.

''Daga nan ya d'auki k'anin babansa da mutane biyu suka je suka nemo masa auren yarinya a can k'auyen, basu dawo ba sai da amaryar mahaifina cike da gara da kaya irin na k'auye wanda baza'a rasa ba. Sai dai tun da iyayen mahaifina suka bud'e ido suka gano wa ce ce matar d'ansu wato igala ce suka d'aura mata tsana'' ta juyo ta kalli Sulaimana tana cewa ''ai kai kasan yanda mutanen mu basu son yare irin wad'annan musamman yaren da basu sanshi sosai ba'' ya gyad'a kai yana cewa ''eh, amma dan kawai ita igala sai tsanar ya shafeki?

'' Iya sani na basu son a auro musu wata k'abila amma in an auro kuma suka ga yarinyar na da hankali tuni suke zubar da makaman yak'insu su rik'eta ta zama tasu'' Maryamah tayi murmushi da hawaye a k'uncinta, sai da ta share hawayen sannan tace ''ai abubuwa sun faru sosai hakan ya sa suka k'ara tsanar ta wanda tsanar shi yake bina har yanzu ake ta wahalar dani'' kuka ya kubce mata, sosai take kukan tana sheshshek'a Dr. Sulaimana na bata hak'uri.

Engr. Abakar da yake zaune yana jin duk abinda Maryamah take fad'a har ranshi yaji tausayinta duk da bai san wahalar da tasha ba amma yanda take kukan sai ta karya masa zuciya. Har Allah-Allah yake ta daina kukan ta cigaba da labarin.

Bayan tayi mai isarta sannan ta cigaba da cewa ''bayan anyi auren ne suka koma Godil, kuma a watar da akayi auren shanaye masu yawa na mahaifina suka b'ata, haka bayan kwanaki sun fita kiwo b'arayi suka sassareshi da k'aninsa Husaini suka kwashe shanayensa, wannan yayi sanadiyyar mutuwar Ammi Hussaini. Danginsu da mutanen gari duk suka d'aurawa mamana wai ita ce sanadi, farar k'afa ne da ita kuma mayya ce ta kashe k'anin mijinta, a yanda aka bani labari mamana ta shiga mawuyacin hali a wannan lokacin, dan jinyar mijinta ma an hanata wai kada ta karasa kashe shi, bayan ya warke mahaifina bai canja wa mahaifiyata ba dan yana sonta kuma yana da d'an guntun ilimi akan yadda da k'addara, lafiya suke zaune tsakaninsu.

''Kwatsam sai aka wayi gari mamana na da juna biyu, shikenan abu ya zama abun magana a gari, har ya kai ga mamana bata isa ta fita ko ina ba dan an dinga nunata kenan, wai tsaban rashin kunya ko shekara ba'ayi ba tayi ciki. Yaya Sulaimana in tak'aice maka babu zagi da tsangwama da zagin da mamana bata sha ba, wai rashin tarbiyya ya sata tayi ciki daga shiga d'aki'' ta juyo ta kallesa tace ''wai ai su al'adarsu mace bata haihuwa sai tayi shekara dan rashin kunya ne daga shiga ka haihu'' Dr. Sulaimana ya gyad'a kai yace ''haka ne, nima nasan hakan amma...... ko da yake ki cigaba ina jinki''.

 

 

''Kwanaki sun ja rayuwar da mahaifiyata take ciki bai sauya ba har cikinta ya shiga wata takwas, ranar sun kwanta lafiya k'alau ita da mijinta kawai washe gari da safe ta tashi amma mahaifina rai yayi halinsa, babu ciwon komai kawai ta tashi ta tashesa yayi sallah amma ko motsawa baya yi'' Dr. Sulaimana ya mik'a mata tissue ta share majinanta sannan ta cigaba da cewa ''mamana tsoro ya hanata zuwa ta fad'a dan tasan zasu k'ara d'aura mata laifin, tayi kuka har ta gode Allah amma babu wani mafita dole sai ta sanar da mutane dan ayi masa sutura akai sa gidan sa na gaskiya''

Maryama ta dakata tayi kuka iya son ranta, Dr. Sulaimana sai da ya zubar da kwalla, Engr. Abakar da yake zaune a wurin idonsa a lumshe duk sai yaji kamar ya fasa ihu dan k'uttun da yaji a mak'ogoronsa, yawu mai d'aci ya had'iye ya bud'e idonsa ya kalli Dr. Sulaimana sannan ya kai idonsa kan Maryamah yana kallon iri kukan da take yi, bai san lokacin da yace ''kiyi hak'uri ki gama mana sannan kiyi kukan bayan mun gano bakin matsalan sai musan yanda zamu taimake ki'' Dr. Sulaimana da mamaki yake kallon Engr. Abakar, murna fal ransa amma bai nuna ba, da gangan dama ya tambayi labarinta, yasan abokin nasa da shegen tausayi kuma ya tabbata in yaji labarin zai mayar da makaman yak'in nasa.

Share hawayenta tayi da hijabinta ta cigaba da cewa ''kamar yanda mamana tayi tunanin ita za'a d'aurawa alhak'in mutuwar babana hakan akayi, tsangwama da k'yara ya k'aru har aka haifo ni, ina da shekara biyu mamana ta rasu, kuma tun bayan rasuwar mahaifina bata samu taje gidan su ba dan bata da kud'in zuwa''.

''Mahaifiyata ce ta sa min suna Maryamah dan sunan da mahaifina yafi so kenan, bani da takwara, kuma ita ke k'irana da kwaiseh har ta rasu'' Dr. Sulaimana yace ''Saleh ma kwaiseh yake k'iranki'' tayi murmushi sannan tace ''eh, Saleh yasan labarina shiyasa yake k'irana da sunan'' yace ''toh shi kuma fah, ta ina kuka had'u?'' Ta sauk'ar da ajiyar zuciya tace ''Saleh dai Allah ne ya kawo shi rayuwana, ban tab'a sanin shi ba, a kogin da nake d'iban ruwa kullum yake kawo dabbobinsa shan ruwa, kuma kullum ni ce k'arshe a d'iban ruwa a garin saboda mutanen garin sun ce kada in yadda in d'iba ruwa kafin su tunda ni mayya ce kashe mutane nakeyi, kuma duk ranar da na d'iba ruwa ina gagarar d'aurawa bisa jaki nah, shi yake taimakona kuma yake koya min karatu, shi d'aya ne agun iyayensa bafulatani ne''

Dr. Sulaimana yace ''yanzu kin bar hannun Amty Babbe, komai zai koma daidai insha Allah'' Engr. Abakar yana gama jin labarin ya mik'e ya shige d'aki, Dr. Sulaimana kuma ya cigaba da hira da Maryamah, anan ne yake fad'a mata ai wannan abokinsa ne ba almajiri ba, kuma dan Amty Babbe ta yadda ta bashi aurenta ne yasa yace almajirinsa ne.

Bayan sallahr la'asar Dr. Sulaimana yayi musu bankwana zai shiga motar haya ya koma gida, yace gobe zai kawo mata uniforms nata da sauran abubuwan makaranta da zatayi anfani dashi. Har tasha Abakar ya kaisa, kafin ya fita daga motar yace ma Abakar ''Abakar na bar maka Maryamah amana, ko baka yi mata magana ba ka kula da lafiyarta dan marainiya ce, tausayinta yasa na d'auko ta daga garinsu na aura maka'' Engr. Abakar ''naji'' kawai ya iya cewa, ya sauk'esa ya koma gida.

Bayan ya koma gida ya samu Maryamah da matar da take zama da ita ta dawo daga kasuwa, gaishe ta kawai yayi ya shige d'aki.

 

 

 

A kwana a tashi ba wuya yau Maryamah na neman shekara d'aya a gidan Engr. Abakar, maganar kirki baya had'asu, kullum in ya fita aikinsa baya dawowa sai maghrib, ranar friday kuma yana tashi daga gun aiki baya dawowa gida yake wucewa Kaduna, in ya gama weekend ya dawo sunday da yamma, Dr. Sulaimana yanzu ya rage zuwa sosai dan sai yayi sati biyu bai zo ba, in yazo kuma abubuwan da zatayi anfani dasu yake kawo mata.

Lokacin da taje islamiyar aji biyar aka sata da aka mata interview, yawancin abubuwan ta iya su sosai ta dalilin Saleh, yanzu haka tana shirin shiga aji d'aya ta k'aramar secondary. Tayi k'awaye ba laifi, yanzu k'auyancin nata ba sosai ba, gashin kanta ya ciko babu alamar an tab'a yi mata gud'd'iye, sai gyarar da ba sosai yake samu ba.

Dr. Sulaimana yaje Godil ba iyaka, last zuwanshi yaji labarin Saleh zai auri Khajije har an sa rana, ya had'u da Saleh ma sunyi magana har ya bashi kyautar waya dan suna gaisawa, kuma yace zai so ya dawo kusa dashi ko sana'a zai iya basa, kuma Saleh yayi na'am da wannan shawarar. Engr. Abakar yana dawowa daga Godil ya sanar da Maryamah auren Saleh da khajije k'awarta, tayi murna sosai har da guntun hawayenta wai zataje amma Dr. yace sai dai ta tambayi mijinta.

Ita da bata san komai kan miji ba taya zata yiwa Abakar magana bayan ko sake mata fuska baya yi? haka ta hak'ura bata yi masa maganar ba. Ranar bikin sai washe baki takeyi kamar ta san abinda yake faruwa acan, nan da nan sai kiji tana cewa Inna(mai kwana da ita) ''warhaka suna yin kaza, anjima kad'an tace yanzu sun gama zasu fara kaza, Inna dai dariyar ta kawai tayi tana cewa ''baki da aiki''.

A b'angaren Hamrah matar Dr. Sulaimana ta fara zargin mijinta da zuwa gun wata, dalilinta kuwa shine, farko yana sayan turaren wuta ya sa a bayan motarsa ya kai wa Marymah, amma k'amshin baya dad'i sai ya fara karb'a agun Hamrah da sunan kyauta zaiyi dashi, tun tana bayarwa daga nata har ya zama shi yake bata kud'i ta saya ta had'a masa, danginsu humrah, turaren wuta, kulaccam da sauransu. Bayan wannan kuma ta sha ganin tarin kayan mata(atamfa, hijabai, takalma, kayan kwalliya) da sauran kayan da baza'a rasa ba na 'yan mata a boot nasa, wani lokaci a seat na motarsa na baya.

Farko tayi zargin kayan aure yake had'awa amma daga baya sai ta gano ba kayan aure bane wata yake kaiwa, hakan ya jawo gagarumin matsala. Har ta kai ga ta fad'awa k'awarta Fad'ime dan ta bata shawara. Shawarar da Fad'ime ta bata shine ''mijinki ne, babu b'oye-b'oye tsakaninku dan kun zama d'aya, me zai hana ki masa magana ku fahimci juna, wannan kumbure-kumburen naki duk bazai kawo maslaha ba dan shi bai ma san kinayi ba, namiji zai miki laifi amma sai kiga ya share ke kuma duk sai ki had'e baki da hanci kina jirar yayi miki maganar ko ya baki hak'uri sai kiji shiru, ba laifinsu bane, su a wurinsu wannan ba laifi bane amma ke a wurinki laifi ne, dole sai kin zaunar dashi, wane kayi min kaza kuma banji dad'insa ba, sai ku fahimci juna'' Hamrah tace ''ni ban k'i ya k'ara auren ba tunda yayi niyya, amma ya zai b'oye min? B'oye min da yayi shi yafi b'ata min rai'' Fad'ime tace ''kin tabbatar auren zaiyi da kike maganar ya b'oye miki?'' Tace ''ban tabbatar ba amma ai naga alamu''

Fad'ime tace ''toh kiyi masa magana first before ki yanke hukunci''....... Haka kuwa akayi, ta sameshi ta lissafa masa duk abunda take zargi, da mamakinta taga yayi murmushi yace ''akan meh zan miki k'arya in ba ke ba, wai dama akan wannan abun naga duk kin canja min?'' Tace ''eh mana, taya zaka nemi aure baka sanar dani ba?'' A tak'aice ya bata amsa ''ni ba aure zanyi ba'' rai a b'ace ta sake cewa ''toh kayan meh suke nufi? 'Yan mata kake kaiwa ko meh?'' Ce mata yayi ''kyauta na ke yi dasu, ko bani da damar inyi kyauta wa mace sai budurwa ta? In baki sani ba ma ki sani, matar aure nake taimakawa ba kowa ba dan babu aure tsakaninmu, tausayi da jin k'ai yasa nake bata'' ya juya mata baya yayi kwanciyarsa.

 

 

 

Hamrah ba k'aramin tashin hankali ta d'aurawa kanta ba, dan ita gani take mijinta ya fara bin mata, kullum sai ta ajiye shi gaba tana masa kuka, tun abun baya damunshi har ya fara damunshi yana ganin kamar yana shiga hak'k'inta.

Engr. Abakar saura sati biyu ya koma gida kaduna sanadiyyar kammala aikin da aka basu, Alhamdulillahi sun kammala ginin successfully(cikin nasara) saura paint(fenti) da akeyi wanda cikin sati biyun za su kammala komai. Ranar da Dr. Sulaimana yayi masa magana akan makomar aurensa da Maryamah cewa yayi ''ai ni ban d'auke ta mata ba'' Dr. Sulaimana yace ''toh ka saketa kawai, tunda banga anfanin taimakonka da nayi ba'' bud'ar bakin sa sai cewa yayi ''banyi niyyar sakinta ba, ka barni tunda ka aura min in lokacin da ka gama gano babu anfanin auren da kayi min sai in sauta dan kaina''.

Bai saurari maganar da zai sake masa ba ya fice ya bar masa gidan gaba d'aya. Dr. Sulaimana kad'a kanshi yayi yana cewa ''Maryamah rashin wayewa ke damunta, kuma ni bai dace kai bazan ma iya zama in koya mata yanda zata ja hankalin mijinta ba'' guntun tsaki yaja ya cigaba da neman hanyar da zai bi dan gyara wannan k'addararren auren.

Maryamah na da k'ok'ari sosai a makaranta, hakan yasa yawancin nau'i na magani na musulunci ta san su, lokacin da ta fara menstrual period bata wani sha wahala ba, kuma bata tsorata ba da taga wannan jinin dan tasan ko wani iri ne, Inna ce ta koya mata yanda ake anfani da sanitarypad(always), da kud'in da Dr. Sulaimana yake bata take saya ta ajiye sabida tsaro. Wanka da sauran abubuwan duk an koya musu a makaranta. Ga maganin da ake sha na masu menstrual pain(ciwon mara yayin al'ada):-

 

Citta

 

Kananfari

 

K'usd'ul hindi(Annabi S.A.W yace ya hore mu da anfani da itaciyar k'usd'ul hindi dan akwai waraka a ciki) ki had'esu gu d'aya ki zuba ruwa ki tafasa, bayan kin sauk'ar ki sa khal-tuffah(brown venigar) kina sha kafin ki fara al'ada.

Zaki iya samun wannan ma kiyi anfani dasu kafin lokacin period naki:-

 

Albasa

 

Citta

 

Tafarnuwa

 

K'usd'ul hindi

 

Kananfari

 

Habba

 

Soyabeans(ki markad'a ki tace) sai ki d'aura akan wuta ki zuba sauran su tafasa sai kina sha. Allah yasa mu dace.

Yau lahadi, Engr. Abakar ya gama shirin komai nasa, tun asuba ya fara ciro kayansa yana sawa a boot, da misalin k'arfe bakwai da rabi k'awayen Maryamah suka shigo gidan suna sallama, har cikin falon suka shiga d'aya ta lek'a d'aki tana cewa ''yau munzo baki gama shiri ba'' Maryamah murmushi tayi sannan tace ''na idar da sallah kawai bacci ya d'aukeni ban jima da farkawa ba, ku bani minti biyar'' k'awarta mai suna Rabi'a ta amsa da ''toh'' sannan ta koma falo.

Suna cikin hirarsu suka ga Abakar ya fito sanye da kayansa, jamfa ya saka sky blue da hularsa yayi matching da kayan sosai, ya fito yana kan d'aura agogonsa, kwata-kwata bai kula da mutanen da ke falon ba dan hankalinsa na kan d'aura agogonsa, gaishesa da sukayi ya firgita shi har sai da agogon ta fad'i, murmushi yayi da yaga uniform a jikinsu wanda ya bashi tabbacin 'yan makarantar Maryamah ne, ya amsa sannan ya tsuguna ya d'auki agogon ya fice ba tare da ya gama sawa ba.

D'aya daga cikin k'awayen nata mai suna Salma tace ''wow! Look at his smile(ku ga murmushinsa) Wannan guy d'in ya had'u, kuji k'amshin turarensa har yanzu bai tafi ba'' fauziyya ta toshe mata baki tana cewa ''kada Maryamah ta jiki, kika sani ko shi ne mijin nata'' d'aya daga cikinsu Aisha ta tab'e baki tana cewa ''wannan handsome man d'in shine zai auri Maryamah?'' K'arar takalmin Maryamah sukaji kowa yayi shiru.

 

 

 

Sanye take da uniform d'inta pink, riga dai-dai gwiwa da wando da hijabinta har k'asa, sai jakarta bak'i cike mak'il da litattafai, murmushi a fuskarta ta fito ta same su sannan tace ''mu tafi'' sukayi wa Inna da take kitchen sallama suka wuce islamiya dan da k'afa suke zuwa babu nisa. A harabar gidan suka had'u da Abakar yana gyarar boot d'insa da yake kayan sun masa yawa yak'i rufuwa. Tace musu ''ina zuwa'' tsayawa sukayi suna kallonta.

Ta isa gunsa tayi masa sallama ya amsa sannan ta gaida shi, bayan ya amsa ta juya zata tafi ya dakatar da ita da cewa ''yau zan koma gida, akwai abinda kike buk'ata'' murmushi tayi tace ''babu komai'' a tak'aice, ''bazan dawo kamar yanda na saba dawowa ba, zan d'an kwana biyu'' ya ciro makullin d'akinsa ya mik'a mata yana cewa ''in akwai wani abu ki bud'e, ki duba drawer gefen gadona zaki samu kud'i kiyi anfani dasu'' karb'ar makullin tayi tana cewa ''ai Yaya Sulaimana na bar min kud'i, zan dai rik'e maka kafin ka dawo'' tab'e baki yayi ita kuma ta juya ta barsa a wurin bayan ta sa key d'in a cikin k'aramar zip na jakanta.

A hanyarsu ta zuwa makaranta Salma ta kasa hak'uri tace ''wai Maryamah wanda muka gani a wurin motar can shine mijinki?'' Sai da tayi murmushi sannan tace ''eh shine, meh kuka gani?'' Gaba d'ayansu suka ce ''chab'!!!'' Ta kallesu d'aya bayan d'aya sannan tace ''me ne ne?'' Rabi'a tace ''babu komai'' babu wacce ta sake magana har suka isa makaranta.

Aji suka shige bayan an gama assembly, malamin da zai shiga ajin su har ya shigo aka k'irasa a waya ya fice bayan ya sanar dasu bazai samu damar dawowa ba, akwai urgent abu da zaiyi suyi muraja'a kafin wani malamin yazo. Kamar yanda 'yan ajin suka saba indai babu malami a aji kowa da group d'insa zasu zauna ayi ta hira, Maryamah ce kullum take zama a gefensu tana nazarin litattafanta.

Yau ma haka ta matsa gefe tana kan karatun ta Rabi'a tace ''Maryamah zo nan yau kam da ke za'ayi hirar nan, dan abun nan ya d'aure mun kai'' ajiye littafin tayi ta zauna a inda Rabi'a ta nuna mata, sai da ta zauna mai kyau sannan ta kai dubanta ga Rabi'a ba tare da tayi magana ba.

Rabi'a tace ''A hakan Maryamah kike zuwa gun mijinki?'' Salma ta d'aura yatsunta akan leb'b'an Maryamah tana cewa ''a hakan kike mik'awa mijinki yayi kising d'inki? Dubi lips d'inki kamar k'afar gardi duk yayi bak'i kamar baki shafa masa mai da zai gyara'' Fauziyya ta tafe hannu tana dariya sannan tace ''ku wannan kuka gani, gaskiya bazamu ce ke k'azama bace dan babu wanda jikinsa ke fitar da k'amshi irin naki a cikinmu'' ta kallesu gaba d'aya tace ''baku ga kayan da ke gaban dressing mirror nata ba, karab d'inmu babu mai kayan shafa irin nata, matsalarta bata san ya zatayi anfani dasu bane'' Aisha tace ''eh haka ne, amma kayan gabar dressing mirror d'inta zasuyi anfani ne bayan ta gyara fatarta'' ta janyo hannun Maryamah tana cewa ''ku gani fah, ga jikin sai yalk'in mai yake amma daga ganinsa kasan is dry''.

Ruk'k'ayya da ke zaune a gefe tunda aka fara maganar bata tanka ba tace ''ku ko ai fad'a mata yanda zatayi zakuyi ba wai ku ajiyeta kuna mata irin haka ba, bazata ji dad'i ba sam'' ta matso kusa da Maryamah da kanta yake k'asa kamar zatayi kuka, ta rik'e hannunta tana cewa ''kin ganni nan Maryamah, dubi lips d'inah ki gani'' Maryamah ta d'aga kai ta kalla pink dashi, kana kallonsa kaga alamar mai taushi ne, Ruk'k'aiyya tace ''abu k'anana wanda kika raina su kad'ai sun isa gyara miki leb'b'a ya dawo kamar nawa'' ta gyara zama ta kallesu dukka sannan tace ''ku ma maybe baku san sirrin ba, barin fad'a muku ko dan mu gudu mu tsira tare'' dukkansu suka sake kunne suna sauraron Ruk'k'aiya.

Tace ''ki samu kurkum da madara, duk rashin mutum bazai rasa naira d'ari ba, madara sachet d'aya zai kai ki kiyi sati kina anfani dashi in kina d'ad'a, in kika samu kurkum naki ki zuba madararki a ciki ki gauraya ki ajiyesa, duk lokacin da zakiyi anfani dashi sai ki d'iba kad'an ki sa ruwa d'an kad'an ki kwab'a, ki samu brush wanda ake goge hak'ori sai ki zuba ruwa ki goga lips naki gently kina wankewa da ruwa yanda bazaki ji wa kanki ciwo ba''.

''In kin gama ki d'auko kurkum d'in da kika dama ki shafe lips d'in dashi, ki barshi ya bushe da kansa kamar minti biyar sai ki dirzashi ya fita, ba tare da kin wanke ba zaki shafa man baki mai kyau duk wanda kikeso ko wani kala ne, ina fad'a muku duk kaushin bakinki sai ya canja, in bakinki ya koma bak'i zai dawo pink, kuma zaki ga yayi laushi sosai, ki na yin hakan safe da yamma''

Ta k'ara da cewa ''in kinyi wannan na sati zakiga kurkum din ya kame bakinki yayi yellow, kada ki damu, kamar ni in mijina baya nan nake anfani da na kurkum da madara, in naji zai dawo sai in daina, dan wannan kurkum d'in ya tafi sai in fara anfani da madara zalla, in na wanke lips da brush sai in shafa madara bayan na kwab'a sa, same procedure zaki bi kiyi wannan ma, zakiga wannan kurkum d'in ya b'ace kuma zai baki abinda kikeso''.

 

 

 

Rabi'a ta d'auko paper da takadda tace sake fad'a in rubuta nikam, sai da dukkansu sukayi dariya sannan wasu suka ce mu ma rubutawa zamuyi ciki harda Maryamah da ta d'auko littafinta da babu komai a ciki. Ruk'ayya ta sake maimaita musu suka rubuta.

Bayan kowa ya gama rubutawa Salma tace ''toh ki saurareni Maryamah, yanzu mun zama d'aya, ranar asabar duk wanda yake free zai zo wurinki ya koya miki wasu abubuwan, kafin nan bari mu fad'a miki yanda zaki gyara fatarki da abubuwa wad'an da ba masu tsada ba, kuma in kin samu lokaci kije kasuwa ki sayo sirrin mijinki a tafin hannunki, littafi ne da likitan musulunci yayi sa, duk abunda suke ciki masu kyau ne''.

Aisha tace ''akwai wani na gyarar jiki da na sani, zaku rubuta ko in fad'a muku kawai zaku rik'e? Ba wani mai wahala bane'' suka ce ''zamu rubuta dai'' Aisha tace ''toh bismillah, kinga in kika samu b'awon kwai, da kurkum sai kuma lemon tsami, zaki daka b'awon kwai yayi luk'wi sai ki had'a da kurkum ki ajiye sa, duk lokacin da zakiyi anfani dashi sai ki d'iba ki matse lemon tsami a ciki, zaki ga zai tashi a take, ki shige bayan gida ki shafe jikin ki dukka, yana bushewa sai kiyi wanka da soso, baya wuce minti biyu zai bushe, kina yin haka na kwana biyar'' tayi dariyar shak'iyanci sannan tace ''tun na farko in kina wanka ki gwada shafa jikinki kiji yanda yake laushi''.

Rabi'a tace ''wannan ai laushin jiki kawai yake sawa, kuma in ba kina cin kayan gyara jiki da mai masu kyau ba zaki ga jikinki kamar babu mai''.

Salma tace ''ni kuma wannan na fi so, rid'i d'anya da lalle, in kinaso zaki iya sa kurkum dan jikinki yayi shar d'an yalo-yalo haka, daka d'anyar rid'in zakiyi ki had'a da lalle ki ajiye, duk lokacin da zakiyi anfani dashi ki d'iba daidai yanda zai isheki sai ki kwab'a da ruwa, wayyo! kuma dama ki tabbatar kin daka sa da kyau ta yanda mai d'in rid'in zai fito. Ki shafe jikinki dukka kiyi awa d'aya sannan ki shiga wanka, ina fad'a muku zakuyi mamakin yanda zaki canja, duk dry skin d'inki wannan rid'in zai farfad'o dashi, kuma ga laushi da gyara skin, sai kun gwada zaku tabbatar''

Sukayi shewa sannan suka cigaba da hira, Maryamah dai nata kunne, har Malami ya shigo maganar da sukeyi kenan. Lokacin da aka tashi sai da suka ja mata kunne akan ta fara yin abun tun gobe tunda mijin nata baya nan. Kafin ya dawo yaga canji, tace musu ''ba matsala'' a gurguje ta dawo gida k'arfe biyu, bayan ta idar da Sallah ko abinci bata ci ba ta d'auko kud'ad'en da take ajiyewa wanda Dr. Sulaimana yake bata.

Inna ta samu ta tambayeta yaushe zata je kasuwa, Inna tace ''anjima kad'an, dama ina jiran dawowarki ne, kud'in da yayan naki ya bayar na cefane bazasu isa in sayo shinkafar ba, kinga mun manta bamu ce masa shinkafa ya k'are ba da ya kawo mana, kuma gashi ke ba wayar ne da ke ba'' Maryamah tace ''akwai kud'i a wurina, barin d'auko sai ki sayo mana, dama sak'o nake dashi a kasuwar''. Bayan ta d'auko kud'in ta bata sannan ta lissafo mata abinda zata sayo mata, harda turmin k'arfe irin k'anana d'in nan wanda zatayi dake-dakenta a d'aki asiri a rufe.

 

Rabi'a ta d'auko paper da takadda tace sake fad'a in rubuta nikam, sai da dukkansu sukayi dariya sannan wasu suka ce mu ma rubutawa zamuyi ciki harda Maryamah da ta d'auko littafinta da babu komai a ciki. Ruk'ayya ta sake maimaita musu suka rubuta.

Bayan kowa ya gama rubutawa Salma tace ''toh ki saurareni Maryamah, yanzu mun zama d'aya, ranar asabar duk wanda yake free zai zo wurinki ya koya miki wasu abubuwan, kafin nan bari mu fad'a miki yanda zaki gyara fatarki da abubuwa wad'an da ba masu tsada ba, kuma in kin samu lokaci kije kasuwa ki sayo sirrin mijinki a tafin hannunki, littafi ne da likitan musulunci yayi sa, duk abunda suke ciki masu kyau ne''.

Aisha tace ''akwai wani na gyarar jiki da na sani, zaku rubuta ko in fad'a muku kawai zaku rik'e? Ba wani mai wahala bane'' suka ce ''zamu rubuta dai'' Aisha tace ''toh bismillah, kinga in kika samu b'awon kwai, da kurkum sai kuma lemon tsami, zaki daka b'awon kwai yayi luk'wi sai ki had'a da kurkum ki ajiye sa, duk lokacin da zakiyi anfani dashi sai ki d'iba ki matse lemon tsami a ciki, zaki ga zai tashi a take, ki shige bayan gida ki shafe jikin ki dukka, yana bushewa sai kiyi wanka da soso, baya wuce minti biyu zai bushe, kina yin haka na kwana biyar'' tayi dariyar shak'iyanci sannan tace ''tun na farko in kina wanka ki gwada shafa jikinki kiji yanda yake laushi''.

Rabi'a tace ''wannan ai laushin jiki kawai yake sawa, kuma in ba kina cin kayan gyara jiki da mai masu kyau ba zaki ga jikinki kamar babu mai''.

Salma tace ''ni kuma wannan na fi so, rid'i d'anya da lalle, in kinaso zaki iya sa kurkum dan jikinki yayi shar d'an yalo-yalo haka, daka d'anyar rid'in zakiyi ki had'a da lalle ki ajiye, duk lokacin da zakiyi anfani dashi ki d'iba daidai yanda zai isheki sai ki kwab'a da ruwa, wayyo! kuma dama ki tabbatar kin daka sa da kyau ta yanda mai d'in rid'in zai fito. Ki shafe jikinki dukka kiyi awa d'aya sannan ki shiga wanka, ina fad'a muku zakuyi mamakin yanda zaki canja, duk dry skin d'inki wannan rid'in zai farfad'o dashi, kuma ga laushi da gyara skin, sai kun gwada zaku tabbatar''

Sukayi shewa sannan suka cigaba da hira, Maryamah dai nata kunne, har Malami ya shigo maganar da sukeyi kenan. Lokacin da aka tashi sai da suka ja mata kunne akan ta fara yin abun tun gobe tunda mijin nata baya nan. Kafin ya dawo yaga canji, tace musu ''ba matsala'' a gurguje ta dawo gida k'arfe biyu, bayan ta idar da Sallah ko abinci bata ci ba ta d'auko kud'ad'en da take ajiyewa wanda Dr. Sulaimana yake bata.

Inna ta samu ta tambayeta yaushe zata je kasuwa, Inna tace ''anjima kad'an, dama ina jiran dawowarki ne, kud'in da yayan naki ya bayar na cefane bazasu isa in sayo shinkafar ba, kinga mun manta bamu ce masa shinkafa ya k'are ba da ya kawo mana, kuma gashi ke ba wayar ne da ke ba'' Maryamah tace ''akwai kud'i a wurina, barin d'auko sai ki sayo mana, dama sak'o nake dashi a kasuwar''. Bayan ta d'auko kud'in ta bata sannan ta lissafo mata abinda zata sayo mata, harda turmin k'arfe irin k'anana d'in nan wanda zatayi dake-dakenta a d'aki asiri a rufe.

 

 

 

Kwanaki sun ja, rayuwa ta sauya, Maryamah ta dawo ral a idon mutane, kullum a makaranta sai sun bata lectures, tun suna yin abun su ya su har ya zama duk 'yan ajin 'yan mata da matan aure zasu had'u ayi ta fad'an abubuwan gyarar jiki, Maryamah ita dai lectures da take bayarwa akan magunguna ne, islamic medicines, littafi k'ato take dashi kuma duk ta karanta, wani lokacin ita da kanta zakiji tana cewa ''tunda wannan yana maganin kaza, wannan yana maganin kaza, in aka had'asu ai sai suyi maganin kaza koh?'' kuma da ikon Allah in ta had'a tayi sai kiga an samu lafiya.

Maryamah da shekarunta bazasu wuce sha-hud'u zuwa sha-biyar ba, tana da k'awaye manya da suka wuce ta sosai ba kad'an ba, kamar Maman k'uraish, Ruk'k'ayya, bilkisu, Asiya da Hussaina. Su Rabi'a, Zahra, Fauziyya, Salma, Aisha duk bazasu wuce ta da shekaru biyu ko uku ba.

Kamar kullum suna zaune a aji babu malami Aisha tace Maryamah fad'a min maganin infection, wanda kika tabbatar yana aiki sosai, Maryamah tace ''akwai wani wanda na karanta sai dai yana da d'an wahala'' Rabi'a ta zaro littafinta tace ''fad'i mukam zai anfane mu ko nan gaba'' Maryamah tace ''zaki samu

 

Kananfari, citta, garin hulba, garin habbatus sauda, garin k'usd'ul hindi, kowanne cokali d'aya, d'anyar citta kuma d'aya ya wadatar, ki had'asu ki zuba ruwa ki tafasa na 30mins(minti talatin). Ki sauk'ar ki raba biyu, d'aya ki sa a flask ki zuba khal tuffa(brown venigar) d'aya kisa miski(Miski kamar koko na saudi, in babu zaki iya sa kowani irin miski) ki zuba a baho ki zauna a ciki, bayan kin gama kiyi inserting misk. Wancan na flask da kika sa khal tuffa kuma kina sha''. Aisha tace ''zaiyi zafi amma'' Maryamah tace ''eh kinsan kowa da irin infection nasa, wasu har fashewa yakeyi, kinga kenan zaiyi zafi, amma miskin da zaki sa shi zai warkar da ciwon''.

Dr. Sulaimana ke zaune gaban laptop d'insa da ke d'akinsa yana aiki yaji an bud'e k'ofa babu sallama, kayan hannunta ta watsa su kan gado tana kuka tana cewa ''na gaji da ganin bak'in ciki ka mayar dani wofi kana rayuwarka da wasu a waje, bansan ina ka samo wannan halin ba Dr.'' zama tayi a gefen gadon tana rusa kuka, kayan da ta watsa kan gadon ya kai dubansa akai, kaya ne ya saya english wears zai kai wa Maryamah, a ranshi yace ''wannan kuma ta ina ta gani?'' Cike da masifa ya fara magana ''bincike kika fara min a mota ko meh? Ke ya dace in tambaya wa ya koya miki sabon halayen da kike ta tsirfa min?''.

Hamrah cike da mamaki ta d'ago fuskarta hawaye ya malale, kawar da kansa yayi daga dubanta da yakeyi, ''ni ce ke maka bincike Dr.?'' Ta kad'a kai ''Kai fah kace in d'auko maka wayarka a mota... shikenan'' ta tashi zata fice ya mik'e ya rik'e hannunta ya janyo ta ya zaunar da ita kan gado shima ya zauna. Rarrashinta ya fara yi sannan yace ''wannan abinda kike damuwa akansa Hamrah bai shafeki ba'' tace ''toh meh yasa kake b'oye min?'' Kai tsaye yace mata ''dan ya shafi k'awarki, kuma nasan zaki fad'a mata'' da mamaki take kallonsa tana cewa ''Ban gane ba''.

Sai da ya sa tayi masa alk'awarin bazata fad'a wa kowa ba sannan ya sanar da ita komai game da matsalar gidan Abokinsa ya kuma sanar da ita auren da yayi masa ba tare da izininsa da yardarsa ba, da irin zaman da sukeyi, babu abunda ya b'oye mata. Hamrah kuka tayi sosai tana tausayawa k'awarta Fad'ime, sai dai abinda yafi faranta mata rai shine k'in amincewa da Maryamah da Abakar baiyi ba, hakan shi ya k'ara bata k'arfin gwiwar b'oyewa k'awarta wannan sirrin da mijinta ya fad'a mata yanzu.

Washe gari kuwa suka shirya ita da yaranta suka bi Dr. Sulaimana Shika dan ganin Maryamah matar Abakar. Fad'ime rikicewa ne batayi ba da taga Maryamah cikin atamfarta ta sha d'auri, jikinta mai kyau gidan sai fitar da k'amshi yakeyi. Cike da wayewa ta tarbe su, ta kawo musu ruwa ta d'auki Ashshe tana wasa da ita. Har suka bar gidan ta nemi kuskuren da zata zagi Maryamah amma bata samu ba, sai dai ko rashin turanci da k'ank'antar ta, amma iya zaman da sukayi na yau ta gano tsantsar karatun addinin da take dashi. Bata tab'a d'auka zata ganta kyakkyawa haka ba, ganinta da tayi sai ya kashe mata jiki sosai.

 

 

 

Yau Maryamah ta tashi cike da nishad'i bata san dalili ba, ita kad'ai sai tayi ta murmushin da ta rasa gane dalili, kasancewar ranar Asabar ne tana gida, doguwar riga ta sa mai kyau cib-cib da jikinta, d'ankwalin nan an d'aurashi kamar fanka. Kwanciya tayi dan ta d'an huta kafin ta shiga kitchen taya Inna girkin rana. Da misalin k'arfe sha-biyu na rana ta ji dirin mota a tsakiyar gidan, idonta a lumshe har sai da taji alamar anyi parking sannan ta bud'e idon, muryar yaro taji yana kuka, tashi tayi da sauri tasan bazai wuce Ashshe da babanta bane suka zo, Dr. Sulaimana kenan.

Hijabi dogo ta sanya sannan ta nufi k'ofa, kamar a mafarki ta tsinkayi muryar da ko a mafarki batayi tsammanin zata sake ji ba tana cewa ''tana ciki koh?'', ai kuwa da gudu ta fito dan ta tabbatar da wacce taji muryarta. Tana fita kuwa taga Khajije da baby a hannun Saleh, batasan lokacin da ta saki ihun murna ta je ta k'ank'ame Khajije ba, hawaye ya fara bin kuncinta tana cewa ''ashe zan sake ganinku'' dak'yar Khajije ta shawo kanta suka shiga ciki.

Ranar sunyi hirar yaushe gamo, sunyi murna fiye da tunanin mai karatu, komai na ci na gidan sai da ta kawo wa Khajije, da yake babyn nata bai wuce wata biyu ba. Saleh da Dr. Sulaimana kuma sun fita sun barsu. Hira babu kalar wanda Khajije bata sha ba. Har bayan sallahr la'asar suna d'aki. Khajije ta tab'o cikin Maryamah tana cewa ''ni da na d'auka zanzo in ganki da k'aton ciki sai na ganki babu komai, me yake faruwa?'' Maryamah gyara zama tayi me kyau yanda labarin zai shigi Khajije da kyau, tun daga farkon rayuwarta bayan sun tafi sun bar ta har kawo yau da take zaune sai da ta sanar da ita.

Ta sanar da ita taimakon da k'awayenta suka mata na islamiyya da kuma rashin zuwan Abakar bare tayi anfani da sauran abinda k'awayen suka fad'a mata, Khajije ta furzar da iska daga bakinta ta d'auko jakarta tana cewa ''tun farko ke ce kikayi sanya, ni tun da nayi aure aka sani a makaranta ba karatun kawai nake d'auka ba, zama da k'awaye ko bakuyi magana ba zaki kwashi abinda zaki kwasa'' ta ciro kwalbar turaren wuta babba guda d'aya da k'arama d'aya, ta sake sa hannunta cikin jakar ta ciro humrah bak'a, ta juya ta kalli inda na Maryamah suke tace ''kada ki had'a wannan da wad'an can'' ta nuna na Maryamah, da mamaki Maryamah take kallon ta tace ''kamar ya? Ai duk iri d'aya ne'' Khajije tace ''ba d'aya bane, kin ga wad'annan sun zarce naki k'amshi duk da bansan k'amshinsu ba'' ta d'auko humrah tace ''wannan a cikin ruwan wanka zaki zuba kina wanka dashi'' ta d'auko na turaren wuta tace ''wannan kuma turare zaki na yi dashi'' ta janyo hannunta ta kawo daidai hancinta tace ''kamshin da wajenki ko ince tufafinki yakeyi ba shi zai anfani mijinki ba, k'amshin fatarki da k'amshin da zai fito daga jikinki lokacin da kike tare da mijinki shine k'amshi''.

Maryamah tace ''kinji Khajije da wani magana, ai duk 'yan ajinmu sun sanni da k'amshi'' Khajije ta ja guntun tsaki tace ''in kin shiga wanka kika fito kina jin k'amshin?'' Maryamah tace ''a'a, ai kowane turare dama in kayi wanka zai tafi'' Khajije ta dafe goshinta da tafin hannunta tana cewa ''wayyo!! Nikam na bone da Maryamah, kamar ba shuwa ba'' ta janyo turaren tace ''kina turare da wannan, in kin zuba a cikin wuta sai ki rufu akai bayan kin cire kayanki, ki zauna daga ke sai pant, ki turaru kamar na minti talatin in zaki iya ma awa d'aya sannan ki d'iba ruwan wanka mai d'umi ki zuba wannan humrah aciki sai kiyi wanka''.

Maryamah ta karb'a tana yatsine fuska tana cewa ''wai sai kuyi ta cewa inyi kaza inyi kaza bayan mijin da akeyi dan shi ma baya nan, nifah kunya nakeji ko yazo hijabi zan sa'' Khajije tayi dariya mai isarta sannan tace ''meh zaki b'oye masa, wad'an nan abun k'irjin naki? Kin manta ya kalli wanda yafi naki? In zaki cire kunya ki cire tun wuri dama. Kuma ki kwantar da hankalinki, ni nasan yanda za'a yi insa Yaya Sulaimana ya kawo sa ba tare da saninsa ba ma. Ke dai kawai ki tabbatar kin shirya karb'o mijinki''. Khajije bata bar gidan ba sai k'arfe tara na dare bayan Dr. Sulaimana sun dawo daga gidan da ya kama musu haya. Da yake ya bawa Saleh jari a nan Shika yake son fara sana'ansa.

Yau kwana uku da zuwar Khajije gidan Maryamah, kuma tayi duk yanda Khajije ta fad'a mata, ita da kanta taji canjin k'amshi har Inna na ce mata wani turare ta samu haka mai dad'in k'amshi tace k'awarta ce ta kawo mata. Bayan ta idar da sallahr azahar taci abinci ta aika aka karb'o mata wuta ta sa turaren wuta. Bayan ta gama ta d'auko k'ur'ani ta zauna ta lumshe idonta tana rero haddarta, dan yau an basu hutu babu islamiyya.

Engr. Abakar da yake tare da Dr. Sulaimana a cikin mota sun tsaya wurin sayar da fruits a cikin garin Kaduna, Dr. Sulaimana yana bada kud'in ya figi motarsa sai hanyar Shika, Engr. Abakar ko tanka sa baiyi ba dan dama yasan tunda yaje har gida yace zasu fita inda zai kaisa kenan, wurin wancan 'yar k'auyen can. Volume na wak'ar da suke ji ya k'ara ya kwantar da kansa jikin seat ya lumshe ido yana motsa bakinsa alamar yana bin wak'ar.

Har suka iso babu wanda yayi magana, har ciki suka shiga yayi parking motar suka fito. Dr. Sulaimana yace ''ka shiga ciki ina zuwa ka bani minti biyu''. Babu musu ya barsa a wurin motar ya nufi k'ofar shiga falo, doso k'ofar yake yana jin k'amshin d'akin na bugosa, yana k'ara gaba ya fara jin sautin muryarta tana karatun Alkur'ani, bai tabbatar da ita take karantawa ba sai da ya d'aura kunnensa jikin k'ofar, ''tabbas muryar Maryamah ce... yaushe rabon da inji Fad'ime na karatu? Wani zuciyar yace masa ba ma ita ba, kai yaushe rabonka da karatun k'ur'ani?'' Nan take zufa ya karyo masa, tun da yake a rayuwarsa bai tab'a ganin makusa a tattare da Fad'ime ba sai yau. Dr. Sulaimana a nesa ya jingina da mota yana kallon sa yana dariya ciki-ciki.

Bud'e k'ofar yayi ya shigo da sallama a k'asar muryarsa, ganinta yayi rik'e da k'ur'ani idonta a lumshe ''hadda takeyi dama?'' Ya kai dubansa ga fuskarta, ''Hasbunallah!!!'' Ya furta, ta sha hoda da man baki, lips d'in nan sai yalk'i suke ''haka yarinyar take dama ko ba ita bace?'' Sai da ta kai k'arshen ayar sannan ta bud'e idonta. Murmushi ta sake masa sannan ta mik'e tsaye tana cewa ''Sannu da zuwa''.

Kasa amsawa yayi, kallonta yakeyi tun daga k'asa har sama, fitted gown d'in da yake jikinta ya kamata sosai, duk da ba wani k'irji take dashi ba amma akwai hips. ita da taga yak'i amsawa wani zuciyar yace ''kiyi abinda 'yan ajinku suka ce, wani zuciyar na cewa a'a kada kiyi'' kamar an zungureta ta isa inda yake tsaye, sai da ta goga hannunta a hannunsa sannan ta rik'o hannunsa tana cewa ''ka tsaya a bakin k'ofa, ka shigo mana'' k'amshin da ya bugi hancinsa da laushin fatarta suka kusa sumar dashi, ko magana ya ka sa yi mata. Mamaki ya ke yi ''yaushe ta zama haka?''.

 

 

 

Janyo shi tayi ta ajiyesa kan kujerar da ta tashi, wani fari tayi da idonta sannan tace ''ina zuwa'' ta juya tayi hanyar kitchen, tafiyar nata ma wani salo na daban tana karairaya k'ugu, Abakar ido ya ware yana kallon ikon Allah. Wayarsa ta fara ringing amma ko kallon wayar baiyi ba hankalinsa na can yana tunanin ''wannan ita ya sani ko kuwa ba ita ba ce?'' Sai da wayar ta yanke aka sake k'ira sannan ya d'aga ya kara a kunne ba tare da ya duba ko wa ke k'ira ba. Daga d'ayar b'angaren aka ce ''engr. barin d'an fita ka jira ni anan please'' ''toh'' kawai ya iya cewa ya ajiye wayar.

Dr. Sulaimana da ya shige cikin mota sai da yayi dariya mai isar sa sannan ya kunna motar ya bar gidan cike da jin dad'i. Maryamah da ta shiga kitchen sai da ta kulle k'ofar ta buga tsalle tana cewa ''ashe zan iya?'' ta sauk'ar da numfashi sannan tace ''meh kuma zan sake yi?'' Ta turo baki tana cewa ''ko magana ma yak'i min ko burgeshi ma banyi ba'' wani zuciyar yace ''ke dai kiyi yanda aka koya miki kada ki basu kunya'' murmushi tayi ta had'a masa abinda zai sha akan tray ta sake gyara jikinta ta kunce d'ankwalin nata ta yafa sa akanta ba tare da ta d'aura ba.

Ta kai masa ta ajiye kusa dashi ta zauna a k'asa ta zuba masa ta mik'a masa ya karb'a ya kurb'a ya ajiye sannan ta gaida shi. Komawa tayi ta zauna ta mayar da hankalinta kan TV. Engr. Abakar yayi gyaran murya sannan yace ''wa yazo gidan nan da bana nan?'' Sai da ta danne d'ankwalinta da hannun ta sannan ta juyo dan ta samu d'an kwalin ya fad'o, tana juyawa kuwa d'an kwalin ya zame gashinta bak'i sid'ik ya bayyana, bata damu da gyarawa ba dan da gayya tayi, ta amsa shi da ''babu kowa'' sannan ta mayar da dubanta ga TV.

Yinin ranar dukka a falo suka gama shi, iyayi iri-iri babu wanda Maryamah bata yi ba, in taga zata kwabsa sai ta shige d'aki tayi dariya sannan ta sake fitowa ta ci fuska ita dan dole ba dan shi takeyi ba, kuma shi bai ma gane da gan-gan take masa ba, ya d'auka haka ta koma gaba d'aya. Duk da ba wani sakewa da ita yayi ba ya d'an yi mata hira kuma ya tambayeta abubuwa sosai akan makaranta.

Lokacin da Inna ta dawo ta same su a falo, gaishe shi kawai tayi ta shige kitchen bata sake fitowa ba sai da ta gama girki ta fice taje baya ta basu wuri. Bayan sallahr maghrib Dr. Sulaimana ya dawo, sallama yayi tun daga bakin k'ofa, engr. ya bud'e baki zai amsa sallamar Maryamah ta toshe masa baki da tafin hannunta, ta d'aura yatsarta d'aya a bakinta alamar yayi shiru sannan ta fara masa magana a hankali tana cewa ''barin shiga ciki sai ka amsa'' bata jira amsar da zai bata ba ta shige d'aki. Sallamar da bai amsa ba kenan ya tsaya kallonta da tunanin ''meh dalilin yin hakan?'' Sai da Dr. Sulaimana ya sake doka sallama yayi daidai da fitowar Maryamah daga d'aki tana amsawa shima yana amsawa. Juyowa yayi yana kallonta, hijabi ta sanya dogo wanda ya rufe kwalliyan rigar nata, ji yayi kamar yayi ihu dan dad'i ''Kwalliyar da tayi nashi ne shi kad'ai kenan?''.

Wata zuciyar tace masa ''Fad'ime kullum cikin gyale ko fita zatayi, in Dr. Sulaimana yazo ko gyallen ma bata sawa sai wasu bak'in na daban take k'ok'arin sawa'' Wata zuciyar tace ''yau kad'ai har ka fara taryo laifin Fad'ime? Ka yi wa kanka fad'a''.

Maryamah ta had'a musu abinci ta kawo musu bayan ta gaida Dr. Sulaimana, ta kawo musu ruwa da duk abinda zasu buk'ata sannan ta tashi ta shige d'aki dan su samu su sake su ci abinci. Bayan sun gama Dr. Sulaimana yace ''mu wuce koh?'' Abakar ya tashi tsaye ya na cewa ''meh zamu tsaya yi dama?'' Dr. Sulaimana yace ''mutum da matarsa kuma, in kace in barka anan zaka kwana ma ai ni bani da say'' Abakar ya kallesa yaga alamar yana gumtse dariya, ai ko ya had'e hannu ya kai masa naushi Dr. Sulaimana ya kauce, k'asa ya tsuguna dan dariya. Har ya kai bakin k'ofa zai fita Dr. Sulaimana yace ''baka shiga ka mata sallama ba''.

Ba tare da ya tanka masa ba ya koma shi kuma Dr. Sulaimana ya fice ya isa wurin mota yana jirarsa. A bakin k'ofar ya tsaya bayan ya bud'e k'ofar, zaune take a gefen gadonta ta bud'e k'afarta tana shafa mai, ko kallon inda yake batayi ba kamar bata san yana k'ofar ba. Da gangan ta d'ago kayan har cinyarta suka bayyana tana shafa musu mai, takunsa da taji yana iso inda take a tsorace ta rufe k'afafun ta tashi tsaye. Murmushi yayi yace ''matsoraciya'' sai da ya iso dab da ita kanta na k'asa sannan yace ''zan wuce nikam'' ya d'ago fuskarta yana cewa ''akwai abinda kike buk'ata?'' Kad'a kai tayi alamar a'a sannan yace ''na tafi toh'' ya juya zai bar d'akin. Bata san lokacin da ta rik'e hannunsa ba, kuma tana rik'e wa ta sake sakeshi ta juya masa baya.

Juyowa yayi yana tambayarta ''mene ne? Fad'a min ko ma meh ne'' bata juyo ba muryarta na rawa take tambayarsa ''sai yaushe kuma?'' Murmushi yayi ya juyo da ita ya rik'e hannayenta yana cewa ''kinason in dawo ne?'' Tak'i amsa shi sai ma rufe idonta da tayi. Ya kai minti biyu yana tsaye yana kallonta, ita kuma tak'i bud'e idonta. Bai mata magana ba ita ma haka, kawai ji tayi ya saketa ya fice daga d'akin.

 

 

 

Wasa-wasa wata uku ko wani asabar Abakar a Shika yake wuni, mutumin da yace baya fita a weekend sai da yaddar matarsa yau shine ko wani asabar a wurin Maryamah, tun Fad'ime bata damuwa har ta fara tambayansa ''ina kake zuwa ko wani asabar?'' Amsa d'aya yake bata kullum ''akwai aikin da nake yi''.

Kamar kullum tun safe ya tashi ya gama shirinsa cikin riga da wando, yana fesa turare Fad'ime ta shigo ta had'e rai ta zauna a gefen gado, ko kallonta baiyi ba dan ya kula kwanan nan rigima take ji, sai da ya gama komai ya d'auki wayarsa da yake gefenta ya juya zai fita. ''Ohh!!! Baza ka kula ni ba kenan? Duk kumbure-kumburen da zanyi akan fitarka ranar asabar bai dameka ba koh?'' Abakar da mamaki ya juyo yana kallonta ''Fad'ime aikin kikeso in bari in zauna miki a gida? Duk k'ok'arin da nakeyi in zauna ranar sunday bakya gani?'' Fad'ime tace ''k'ok'artawa ma kakeyi kenan?''.

Sai da ya zo ya zauna gefenta sannan ya fara rarrashinta, sosai ta sauk'o harda yi masa addu'an Allah ya bashi sa'a, a zuciyarshi kuma Allah-Allah yake ta barshi ya fita. Bata barshi ya fita ba har azahar nan ma dak'yar bayan ya sanar da ita bazai dawo da wuri ba tunda bai fita da wuri ba. A hanyarsa ta zuwa ya tsaya wani shagon sayar da waya ya sayi guda biyu masu kyau k'irar samsung had'e da sim guda d'aya. Ya sayi katin waya sannan ya kama hanyar Shika cike da farin ciki.

Ya isa gidan da misalin k'arfe biyu da rabi na rana, ledar wayar ya d'auka ya cire d'ayar ya ajiyeta sannan ya fito da d'ayar da katin ya kulle motar ya shiga cikin gidan da sallama. Kamar kullum k'amshin turare ne ya bugi hancinsa ya lumshe ido sannan ya sa kai ya shiga har tsakiyar falon. Waiwayawa yakeyi yana nemanta amma bai ganta ba kamar yanda ya saba ganinta kullum a falo. Kai tsaye ya wuce d'akinta ya bud'e sannan yayi sallama.

Ganinta yayi zaune da riga da skirt nata 'yar kanti ba d'an kwali kanta. Man baki kawai ta shafa sai hoda da ta rambad'a dai-dai kalarta. Sallamar kawai ta amsa ba tare da ta kalleshi ba, da alama fushi tayi dan ta b'ata rai. Da murmushi ya iso gunta ya ajiye ledar hannunsa a drawar gefenta sannan ya zauna kusa da ita. Tana ganin haka ta juya masa baya, rungumeta yayi ta baya yana cewa ''haba kwaiseh, fushi kikeyi da ni? Me laifina me nayi?'' Hannunshi ta cire daga jikinta sannan ta juyo tana cewa ''ba kai bane tun safe nake jiranka kak'i zuwa'' bakin nata da ta turo ya kama yana cewa ''wa ya koya miki abin nan''. Ta buge hannun nasa bata yi magana ba. Janyota yayi zai had'ata da jikinsa ta ture shi ta tashi zata bar masa d'akin.

''Maryamah yanzu meh nayi? Ki bari in miki bayani mana'' kuka mai k'arfi ne yazo mata ta zauna a k'asa ta ajiye kanta bisa cinyoyinta. ''Subhanallahi'' yace sannan ya zo kusa da ita ya d'ago fuskarta yana cewa ''wallahi indai dan banzo da wuri bane wallahi bazan sake latti ba'' kawar da fuskarta tayi tana cewa ''ina matsayin matarka na barka kake zuwa min a sati sau d'aya, hakan ma bai isheka ba sai kana min haka? Duk abinda akace in maka ina yi amma sai gwaleni kakeyi, kai ka d'auka duk abinda nakeyi yin kaina ne? Ce min akayi duk abinda mace ta yiwa mijinta yaji dadi lada take samu, ni kuma duk abinda nake maka ko dad'in bakaji bare in samu lada. Ka daina zuwa ma kawai dan kada in samu zunubi'' ta k'arashe maganar tana goge hawayen fuskarta.

Sauk'ar da numfashi yayi ya rungumeta tsam a jikinsa ba tare da yayi mata magana ba yana mayar da gashinta baya hankalinsa na can yana nemo abinda zai fad'a mata ta fahimce shi ''Maryamah is still young(har yanzu k'arama ce) ta d'auki buk'atarsa, shiyasa bai son ko da had'a jikinsa da nata dan kada ta jawo masa matsala, ashe ita abinda ta d'auka kenan baya jin dadin abinda take masa'' sai da ya d'an jima sannan yace mata ''Maryamah kiyi hak'uri, komai zai wuce kinji? Kuma ni ina jin dad'in yanda kike min, ko abincin da kike kawo min duk ranar da nazo nan ai ina jin dad'i koh? Kuma k'amshinki ma kad'ai yana sani farin ciki'' ya d'ago fuskarta yana cewa ''ki yadda da ni, ina son kasancewa tare da ke, dalili yasa kikaga bana yawan zuwa'' Rungumeshi tayi sosai tana cewa ''ina sonka'' d'auke wuta yayi ya lumshe ido ya d'ago fuskarta ya had'e bakinsa da nata.

Tuni komai ya sauya, tureshi takeyi iya k'arfinta amma ta kasa b'anb'are jikinta da nashi. Ranar dai Maryamah ta zama mallakin Abakar ba tare da yasan meh yake ciki ba, kuka babu wanda Maryamah bata yi ba.

Sai da ya dawo hayyacinsa tukunna ya tuno b'arnar da yayi, innalillahi yake furtawa sannan ya samu nutsuwa. Ya d'auki wayarsa ya k'ira Dr. Sulaimana, abu d'aya ya iya cewa ''she is just 16 kuma nayi b'arna'' Dr. Sulaimana yana jin haka yace ''taya haka ta faru? Are u mad?'' Sai cewa yayi ''meh zan mata yanzu nikam, in na ceto rayuwarta sai kayi min masifar da zaka min'' Dr. Sulaimana ya masa bayanin yanda zaiyi kuma ya aiwatar. Kuka kawai Maryamah takeyi yana aikin rarrashi.

 

 

 

K'arfe shida yayi wa Dr. Sulaimana a harabar gidan Maryamah, k'iran Engr. Abakar kawai yayi a waya yace masa yana waje. Dakyar Maryamah ta bar sa ya fito bayan ya tabbatar mata ba gida zai je ba zai dawo. Yana isa wurin motar Dr. Sulaimana ya fito ya cakume kwalar rigarsa yana cewa ''ashe baka da imani baka da tausayi ban sani ba sai yau? yau na tabbatar da k'iyayyar da kake wa Maryamah ya kai mak'ura. Why Abakar? Meh yasa baka sake ta ba lokacin da nace ka sake ta? Ashe abinda yake bak'ar zuciyarka kenan? Ka wahalar da ita? A 16year old gal(yarinya 'yar kimanin shekara goma-sha-shida)ka kusanta da girmarka da iliminka?''.

Engr. Abakar bai iya furta komai ba sai ''calm down'' da yake cewa, damk'esa Dr. Sulaimana ya sake yi yana cewa ''wallahi duk abinda ya sameta sai ranka ya mugun b'aci''. Masifa yake ta sirfawa ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba. Engr. Abakar da ya gaji da zagi da cin fuskar da yake masa ya fisge kwalar rigarsa yana mai d'aga murya yana cewa.....

''kai ba ka san ita yarinya bace ka aura min ita? Bazaka iya min uzuri ba dan na aikata abinda ko addina na bai haramta min ba'' kallo kawai Dr. Sulaimana ya bi sa dashi ya kasa furta komai. Bai sake masa magana ba ya d'auko ledar maganin da yazo dashi yayi hanyar cikin gidan, engr. Abakar yace ''ban baka damar shiga gun matata ba, she is now my wife(matata ce yanzu) ina da right akanta''.

Dr. Sulaimana yana jin haka ko taku d'aya bai k'ara ba ya juyo ya mik'a masa maganin ya shige mota. Har sai da ya tayar da motar sannan yace ''in kana son ka sake nuna min tsantsar rashin imaninka ka tafi ka barta yau, wallahi abinda zanyi maka sai kayi mamaki Abakar. Maryamah is like my blood sister(kamar k'anwata ce ta jini) i can do anything, i mean anything(zan iya yin komai, ina nufin komai) dan kawo mata 'yan cinta, try me... abotar zan ajiye gefe inyi fighting 4her ryt'' yana gama fad'ar haka ya ja motarsa ya bad'a masa k'ura ya bar gidan.

Abakar jikinsa ya gama mutuwa, ji yake kamar ya mayar da ranar ta zama safe Fad'ime ta hanashi fita, maganin cikin ledar ya bud'e ya duba sannan ya koma cikin gidan.

Shi da kanshi ya bata maganin, yayi alwala yayi sallah tana kwance, bayan ya idar ya zauna gefenta yana rik'e da hannunta yana mayar da gashin kanta baya. Bud'e ido tayi a hankali tace ''lokacin Sallah yayi koh?'' Tayi yunk'urin tashi ya d'agata ta zauna sannan tace ''kaga ko la'asar banyi ba'' runtse idonsa yayi tunawa da yayi shima baiyi la'asar d'in ba, ce mata yayi ''zaki iya yi?'' ta gyad'a kai alamar ''eh''. D'aukanta yayi cak kamar baby ya kai ta toilet tayi alwala dan ta riga da tayi wankan tsarki tuntuni. Tare suka gabatar da Sallahr la'asar, bayan sun idar ya matsa gefe dan tayi maghrib.

Tana cikin sallah wayarsa ta fara k'ara tun kafin ya d'auko wayar yasan wace ce, tsaki ya ja sannan ya d'auka ya kara a kunne. ''What time zaka dawo my one?'' A takaice yace ''zan k'iraki anjima'' bai jira amsarta ba ya kashe wayar, ta sake k'ira yak'i d'agawa daga k'arshe ma kashe wayar tasa yayi gaba d'aya ya sata a cikin drawer.

Ranar dai Fad'ime bata yi bacci ba, ko wani lokaci tana kan k'irarsa ko zai shiga, da farko tayi zargin yana gun wata ne, amma da taga k'arfe sha d'aya ta gota sai ta tabbatar da ba lafiya ba ''ko accident yayi ya b'oye mata?'' A gigice ta k'ira Dr. Sulaimana tana kuka take fad'a masa har yanzu Abakar bai dawo gida ba, ce mata yayi ''kada ki damu Fad'ime, mijinki lafiyarsa k'alau wasu 'yan matsala aka samu amma gobe da safe zaki ganshi'' dak'yar ta yadda akan lafiya k'alau amma hankalinta bai kwanta ba. Bacci b'arawo dak'yar ya iya sace ta a ranar.

Engr. Abakar da Maryamah kuwa ranar bacci sukayi suna mak'ale da juna, duk motsin da Maryamah tayi zai ce ''me ne ne?'' Ita kuwa ta samu damar shagwab'e masa duk ta rikita shi, baccin kirki bai samu yayi ba, daga tace ishi takeji zata sha ruwa sai tace ita kanta na ciwo ko kuma jikinta na ciwo, dakyar ya samu bacci mai nauyi ya d'auketa sannan shima ya samu ya runtsa.

 

 

 

Washe gari da safe bayan tayi wanka ta shafa mai ta d'auko uniform nata, yana kallonta bai mata magana ba, sai da ta d'auko rigar zata sa tukunna yace ''ina zaki je?'' K'ok'arin sa rigar take bata tanka sa ba. Sai da ta sa sannan tace ''makaranta'' d'auko wayarsa yayi yana kunnawa yace ''ban baki izinin fita ko k'ofar gida ba yau da gobe'' kafin tayi masa magana wayarsa ta fara ringing. Ficewa yayi daga d'akin sannan ya d'aga wayar, ita kuma Maryamah hawaye taji yana bin k'uncinta tana yarfe hannu tana cewa ''a hakan Khajije da 'yan ajinmu suke ta cewa inyi kaza inyi kaza?'' Tashi tayi ta cire rigar ta sa riga da skirt nata.

Da misalin k'arfe goma na safe Dr. Sulaimana yayi parking a tsakiyar gidan ya k'ira engr. Abakar a waya ''ga ni na iso''. Abakar bai wani bata lokaci ba ya fito ya samesa, hannu kawai ya mik'a masa sukayi musafaha. Ledar da ke ajiye a seat na gefensa ya d'auko ya mik'a wa Abakar yana cewa ''ba dan kai na kawo maka kayan ba, k'irana da kayi ba shi zai sa in taimaka in kawo maka kayan da zaka sa ba, kawai dan ka nuna min Maryamah ta zama wata aba a wurinka tunda har ka iya zama jinyarta, wallahi dan zaman da kayi a wurinta shiyasa na kawo maka kayan'' Abakar yayi murmushi yace ''nagode''.

Dr. Sulaimana ya sake cewa ''and ka nemo hujjar kare kanka wurin Fad'ime dan jiya kuka takeyi ta k'irani'' ajiyar zuciya Abakar ya sauk'e sannan yace ''yanzu zan koma gida nima, amma meh zan ce mata?''

Dr. Sulaimana ya hararesa sannan yace ''ka fad'a mata kazo gun yarinya 'yar k'arama ka kwana da ita'' Abakar kallon Sulaimana yakeyi yana nazarin sa, fushi yakeyi dashi sosai dan ko murmushi bai samu ba daga gunsa. Abakar yace ''Dr. ni kake basarwa haka? Abin nan fah ko ni banso ba wallahi, but......... baza ka gane ba, yanzu dai ka gafarce ni kayi hak'uri ka fad'a min yanda zanyi, wallahi bansan meh zan fad'awa Fad'ime ba''

Dr. Sulaimana yace ''k'arya zaka mata mana, in ba k'arya ba gaskiya ka ke son ka fad'a mata?'' Engr. Yace shikenan tunda bazaka bani shawara ba, ai dama yanzu kafi son Maryamah akaina, shikenan kawai'' bai jira meh Dr. Sulaimana zai ce ba ya shige ciki, shi kuma Dr. Ya bar harabar gidan.

Sai da ya gama shirinsa ya mik'a mata ledar wayar da ya shigo dashi jiya, k'in karb'a tayi ta kauda kai, dan kanshi ya ajiye mata a gefenta sannan yace ''zan wuce, ki sa wayar a caji, zan k'iraki anjima''. Bakinta ta turo kamar zata yi kuka idonta duk ya cika da hawaye, zama yayi ya rik'e hannunta yana cewa ''wai me na kukan? Ke bakisan kanki zaiyi ciwo in kina yawan kuka ba?''

Kamar jira take ta fara kukan mai sauti, ji yayi kamar yayi ihu ya fara kukan shima, d'aura kanta yayi a k'irjinsa yana cewa ''wallahi bana son kina kukan nan kwaiseh'' cikin muryar kukan take cewa ''ba kai kake sani ba, yau ka min asarar karatu kuma har gobe kace bazan je ba bayan ba zama a gida zakayi ba'' yace ''in kinason in zauna ai zama zanyi koh''.

Tashi tayi tace ''a'a ka tafi, ni kawai inason inje makaranta gobe'' yace ''toh share hawayen, in har baki sake yin kuka ba na yadda kije gobe kinji'' ta kad'a kai sannan tace ''nagode''.

Fad'ime zaune a tsakiyar falonta tayi tagumi idanunta duk sun rine sunyi ja sun kumbura dan kukar da tasha daga jiya zuwa yau, sallamar Abakar taji yasa ta mik'e da hanzari ta isa k'ofar, cin karo sukayi a hanya shi yana shigowa ita tana fita. Rungumesa tayi ta sake kuka ba tare da tayi masa magana ba.

Bai mata magana ba shima yana shafa bayanta, sai da tayi kuka mai isarta ta fara sauk'e numfashi, a lokacin ya samu damar rarrashinta har ya samu tayi shiru sannan suka wuce d'aki.

Bayan sun shiga yace mata ''jiya bayan na bar gida ina hanya sai naji cikina na ciwo sosai, hakan yasa na k'ira Dr. Sulaimana yaje ya d'auke ni muka wuce asibiti ya samu yayi min allurori. Shine ban tashi ba sai da asuba, kuma banso ya sanar dake ba tunda yace in nayi bacci na tashi zan samu lafiya'' tace ''ayya!!! Sannu, Allah ya k'ara lafiya... nidai next time ka fad'a min in abu makamancin haka ya sameka, duk na tsorata fah'' hak'uri ya bata sosai tare da alk'awarin bazai sake ba.

 

 

Yau kimanin wata biyu da faruwar hakan, rayuwa ta sauya haka lokaci ya sauya, Engr. Abakar kullum ya fita wurin aiki sai ya saci hanya yaje Shika ya dawo kawai dan duba lafiyarta duk da yana k'irarta a waya, babu wani abu da ya sake shiga tsakaninsu na rayuwar aure, kulawa dai babu wanda bata samu daga gun Abakar, kuma zuwa ya yini ko wane asabar bai fasa ba sai ma abinda ya k'aru, Fad'ime tayi masifar har ta gaji yak'i daina fita ranar asabar. Maryamah taje gidan da su Khajije ke zama ta yini musu suka sha hira sai yamma ta dawo gida. Zumunci mai k'arfi sukeyi kuma suna d'an yin waya ta layin Saleh mijin Khajije.

Kamar ko wani asabar ya kama hanyar Shika, lafiya k'alau ya isa yayi sallama ya sa kai ba tare da ya jira an amsa ba, da yake yasan Inna tunda ya fara zuwa ranar asabar ta daina yini a gidan, abincin rana ma Maryamah ke yin abunta. Shiru yaji babu alamarta a kitchen hakan yasa ya shiga d'akinta. K'ak'arin amai yaji a toilet nata da wuri ya sa kai yana tambayarta ''lafiya?'' cike da kasala ta wanke bakinta ta dafa bango tana shirin fitowa.

Cak ya d'auketa ya ajiye kan gado yana cewa ''baki da lafiya shine baki fad'a min ba? Ai tun jiya yanda naji muryarki nasan ba k'alau kike ba. Meh ke damunki?'' B'ata fuska tayi tana cewa ''nima ban sani ba, cikina sai murd'a yakeyi kuma sai inyi ta amai'' kuka ta fara masa tana cewa ''kuma babu abunda naci fah''. D'aukar wayarsa yayi ya k'ira wayar Dr. Sulaimana amma a kashe. D'aukanta kawai yayi ya sa a mota ko kulle gidan bai tsaya yayi ba ya figi motar sai cikin garin Kaduna. Bai tsaya a ko ina ba sai asibitin da Dr. Sulaimana yake aiki.

Sai da ya k'ira wayarsa bai shiga ba sannan ya k'ira Hamrah, ringing d'aya ta d'auka suka gaisa sannan yace ta bawa Sulaimana waya. Muryar bacci sulaimana yake cewa ''lafiyarka kuwa?'' K'asa-k'asa yayi da murya wai kada Hamrah taji yana cewa ''ina harabar asibiti Maryamah ba lafiya, dan Allah kazo ka dubata'' kamar an tsikare sa ya tashi yasa jallabiyarsa ko breakfast baiyi ba ya fice.

Hamrah duk ta birkice ta d'auka k'awarta ce ba lafiya, har wurin motarsa ta bishi tana tambayarsa yak'i kulata, sai da ya shiga motar har ya fara tafiya sannan ya sauk'e glass yace ''asibiti aka k'irani baya shiga shine suka k'irashi dan ya fad'a min ana nemana urgent'' sai sannan hankalinta ya kwanta ta koma cikin gida.

Bai tsaya ko ina ba sai asibiti, kai tsaye ya isa inda yaga motar Abakar ko gaisawa basuyi ba yace ''mu shiga ciki, amma me yake damunta?'' Tun da yace masa amai takeyi tun jiya jikinsa ya mutu, gwajin shigar ciki yasa akayi mata dan abinda ya fara zargi kenan.

Result aka kawo masa wanda ya bashi tabbacin Maryamah na d'auke da ciki har na wata biyu. Gumi ne ya wanke masa fuska yana furta ''innalillahi wa inna ilaihi raji'un''. Fita yayi daga office nasa yace wa Abakar ''mu koma Shika in yaso muyi maganar a can''.

Kowa motarsa ya shiga har suka isa garin Shika, Engr. Abakar ya shigar da Maryamah ya kwantar sannan ya fito ya sami Dr. Sulaimana yana tambayarsa ''me ke faruwa?'' Dr. Sulaimana yace ''me kuwa? Ciki take dashi, engr. ka cuci Maryamah, da nasan abinda zaka mata kenan da ban nuna maka ita ba sai ta k'ara girma'' Engr. Abakar cike da mamaki yake maimaita kalmar ciki, yayi guntun tsaki sannan yace ''taya zata samu ciki Dr. ban sake neman Maryamah ba tun wata biyu da suka wuce, kada ka mayar dani mara hankali ko mara tausayi mana'' Dr. Sulaimana ya ciro result d'in ya wurga masa yana cewa ''ka duba da kanka, maryamah na da ciki na wata biyu''.

Kallon result d'in yakeyi take idonshi ya koma ja, hawaye yaji sun taru masa suna barazanar sauk'owa, d'aga kansa yayi yana kallon Dr. ya sake mayar da dubansa ga result d'in. Kuka mai k'arfi ya sub'uce masa ya rik'e Dr. Sulaimana yana cewa ''am really sorry, Dr. ka zubar da cikin nan Maryamah bazata iya haihuwa ba at dis age'' buge hannayen Dr. Sulaimana yayi yana cewa ''lokacin da ka mata cikin ba ka san tayi k'arama ba sai yanzu?'' Engr. Abakar bai damu ba ya sake rik'e hannunsa yana zubar da hawaye yana cewa ''na d'auki laifin amma wallahi ina son Maryamah bana son abunda zai tab'a lafiyarta, ka taimakeni a zubar da cikin nan Dr., dan Allah ka tausaya min i really love her''.

Dr. Sulaimana ya shigar da shi mota ya zauna sannan yace masa ''na yadda zan cire cikin amma sai da yardar Maryamah'' Engr. Abakar yace ''zata yadda a cire mata in har taji illar haihuwarta yanzu, tunda ka yadda ka bar komai a hannunah zan shawo kanta tun kafin lokaci ya k'ure mana''.

 

 

 

''Nifah ban yadda a cire min cikina ba'' cewar Maryamah lokacin da Abakar ya sameta da maganar a cire mata cikin, tun yana rarrashi tana cewa ita bata yadda a cire ba har ya fara mata masifa yana cewa ko tak'i ko taso sai an cire cikin... Maryamah kuka ta sake masa mai cin rai, yana jin ta fara kuka yayi shiru, sai da yaga alamar bazata daina kukan ba sannan ya rungumeta ya fara rarrashi.

''Maryamah abinda nake guje miki da yawa akan haihuwarki yanzu, kiga yanda kika koma tun ciki na wata biyu, kuma har wata tara ake d'awainiya da ciki, kina nufin wahalar zaki yi ta sha har wata tara kuma kije haihuwa k'afarki d'aya a duniya d'aya a lahira, Maryamah barin fad'a miki gaskiya, wallahi bazan so ki wahala ba, na tsani ganinki cikin damuwa''.

Maryamah ta rufe masa baki da hannunta tana ''shh!!! Khajije bata kai ni ba ta haihu kuma lafiyarta k'alau, mutanen garinmu duk basu kai ni ba suke haihuwa, ka daina damuwa akaina, in har aka cire cikin nan kisa fah mukayi'' Abakar yace ''ba kisan da mukayi, cikin bai zama mutum ba yanzu yake wata biyu. Kuma da kike cewa yaran garinku basu kai ki ba suke haihuwa ai jahilci ke damunsu, nan birni ne kuma muna da ilimin boko''.

Maryamah tayi murmushi sannan tace ''ni kuma ilimin islama nake dashi, kuma in har ka bani dama zan samo maganin da zanyi anfani dashi dan ya rage min laulayin ciki wanda ko bature bayi dashi''. Abakar yace ''cikin nan fah sai an cireshi dan bazaki iya haihuwa ba'' Maryamah tace ''ni kuma wallahi ban yadda a cire min ciki ba'' ta tashi ta fice ta bar masa d'akin.

Wasa-wasa har sati Maryamah tak'i yadda a cire cikin, Dr. Sulaimana da kansa ya sameta akan ta yadda a cire amma fir! Tak'i. Dole suka k'yaleta suka zubawa sarautar Allah ido. Kuma ga laulayi mai wahalarwa takeyi, Abakar dan kanshi ya tambayeta maganin da tace zata sha na rage laulayin ciki dan ya sayo mata.

Lissafo masa tayi ya rubuta kamar haka:-

 

''Ganyen na'a-na'a, habbatus sauda, sai zuma. Kala biyu ne, in fad'a maka dukka zaka sayo min?'' Abakar yace ''eh mana, ai bakisan wanne ne zai miki anfani ba'' Maryamah da take kwance tace ''d'ayan kuma zaka samo min man zaitun, man habbatus sauda. Kowanne rabin lita zaka sayo''.

Abakar yace ''ya zakiyi dasu toh? Wanka ko sha?'' Maryamah harararsa tayi sannan tace ''meh anfanin fad'a maka?'' Yace ''dan insan abinda zan sayo ba mai cutarwa bane''. Sai da tayi murmushi sannan tace ''na fad'a maka malaman musulunci suka yi ittifak'i akan lallai yana rage laulayin ciki... kaga na farkon had'asu zanyi in tafasa ina sha cokali d'aya sau uku a rana. Na biyun kuma kaga mai ne, had'asu zanyi ina shan cokali......'' ta kallesa tana cewa ''yanzu cikin ya kai wata nawa ma?'' Ya tab'e baki sannan yace ''ya kusa kaiwa uku'' tace yauwa toh cokali biyu zan sha yanzu kenan, in ya kai wata shida in fara shan cokali uku, in ya kai wata takwas cokali hud'u''.

Abakar kallonta ya tsaya yi, daga baya yace ''ina mamakin ki 'yar k'arama dake kinsan irin abubuwan nan, wa ya koya miki?'' A tak'aice tace ''karantawa nayi''. Da ikon Allah yana sayowa ta fara anfani dashi kuma ta samu sassaucin laulayin sosai.

A kwana a tashi ba wuya yau Maryamah cikin ta ya shiga wata takwas, nan ko ta tsiri cin d'anyar dabino kasancewar ta karanta ance d'anyar dabino na da anfani sosai a jikin mace mai ciki. Daga Dr. Sulaimana har Abakar babu wanda baya mata guzurin d'anyar dabino in zai zo.

Tun da cikin nata ya shiga wata tara Abakar ya shiga tashin hankali, haka Dr. Sulaimana. Ranar asabar tun safe suka isa garin Shika su biyu, Abakar da Dr. Sulaimana. Sun same ta zaune akan kujera idonta a lumshe tana bin haddarta dan ta kwana biyu bata je islamiya ba.

 

 

 

Dr. Sulaimana ne ya tada maganar haihuwarta ''aka ce za'a cire cikin nan kink'i, toh haihuwa dai ta kusa, kina ga zaki iya haihuwa da kanki ko a cire miki?'' Maryamah kam abun dariya ma ya bata tace ''meh yasa ba ku gane min ne? Ni ku bar min ciki nah, in ma mutuwar kuke tsoron inyi ai kowa lokacinsa yake jira''. Abakar yace ''ai na fad'a maka ba za ta yarda ba, komai in aka ce sai ta had'a shi da addini kamar tafi kowa sanin musulunci'' ya ja tsaki.

''Yaya Sulaimana ka ganshi ko? Abinda musulunci yace ni shi zan bi, kuma ina mai tabbatar muku lafiya zan haihu, in Allah ya k'addara mutuwa zanyi dama can ko ba ta hanyar cikin ba zan mutu''. Dr. Sulaimana yace ''kin tabbata zaki haihu da kan ki bakya tsoro?''

Maryamah kai tsaye tace ''abun da ban tab'a yi ba nasan zai bani tsoro, amma addu'ar da addinin mu ya koyar mana shi yake bani k'arfin guiwa, dan cewa aka yi duk girman d'an da yake cikin ki Allah zai sauk'ak'a miki fitar d'an in kikayi addu'ar da izinin Allah, addu'ar kuwa shine:- ya Hayyu ya K'ayyum, bi rahmatika astagisu, la'ilaha illallahul azimul halim, la'ilaha illallahu rabbus samawati wal ardi wa rabbul arshil karim, Allahumma rahmatika arju wala tak'ilni ila nafsy d'arfata aynin wa aslihly sha'aniy kullah, lailaha illa anta. Allaumma la sahla illa ma ja'altahu sahla wa anta taj alul hazna iza shi'ita sahla. Allahu, Allahu, Allahu, rabbi la ushrika bihi shai'an la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minaz zalimin''.

''Bayan kin tabbatar da kina cikin alwala kuma kin karanta ayatul kursiyyu. kuma na dogara da Allah da yace mu rok'e shi zai biya mana buk'atunmu''. Abakar yace ''kina cikin nak'udan yaushe za ki yi tunanin alwala da sauran abubuwan?'' Maryamah tace ''duk da ni ba likita bace nasan ana fara jin nak'uda tun da wuri, to ana son mace da ta fara jin nak'uda tayi alwala saboda ta samu kusanci da Allah ta nisanta daga shaid'an''.

''Dalilin da yasa aka ce kiyi hakan shine:- a yayinda mace take haihuwa imma mutuwa imma rayuwa, shaid'ani na gefenki yana ingizaki fad'in maganganun marasa galihu marasa ma'ana wani lokacin a rashin sani har yasa ta kafurta, amma muddin ki ka yi alwala kika karanta ayatul kursiyyu toh aljani ko shaid'ani bazai kusanceki ba''

Dr. Sulaimana yana kad'a kai yana cewa ''Maryamah!!! Da nasan haka zaki juye mana ki dinga k'in shawararmu da ban saki makarantar nan ba'' Maryamah tace ''lallai baka sona tunda har kayi tunanin haka, karatun addini nah yafi min komai. Kuma ni ku barni in haihu da kaina''. Babu yanda suka iya dole suka barta akan bakanta sai fatar Allah ya sauk'e ta lafiya.

Bayan fitarsu daga gidan a cikin mota suke maganar yanda za ayi ta haihu a Kaduna ''Abakar lokaci yayi fah da yakamata Maryamah ta koma gidanka da zama'' cewar Dr. Sulaimana. Abakar yace ''haka ne, amma ya zanyi? Meh mafita? Fad'ime in ta gane akwai matsala Dr.''.

Dr. Sulaimana yace ''ni fah ka daina min irin haka, tun farko yanda na tsara abu na ba yanzu Maryamah zata haihu ba, kuma inada yanda zanyi bayan ta gama makarantar ta in kai maka ita har gida ba tare da Fad'ime ta b'ata rai ba in mata bayanin komai. Amma kazo ka b'ata min komai ai kai zaka nemo mana yanda zamuyi''. Abakar ya dafe kansa yana cewa ''kana k'ara min zafi Dr. Please ka daina, tunda abu ya faru kawai mafita muke nema''. Dr. Sulaimana yace ''ina da yanda zamuyi amma kada Maryamah ta kofsa mana''. Engr. Abakar yace ''mene ne? In dai Maryamah ne bana shakkunta za ta yi yanda nace'' Dr. Yace ''ka tabbata?'' Abakar yace ''na tabbata''.

 

 

 

Bayan kwana biyu da maganar, Maryamah ta tashi da matsanancin ciwon ciki, tun lokacin da ta fito gaisawa da Inna ta sanar da ita cikinta ciwo yakeyi, inna tace ''k'ira mijin naki tun wuri yazo Maryamah''.

Bata k'irasa ba har wajen k'arfe goma na safe sannan ta d'auki waya tace masa ''cikina na ciwo kuma Inna tace min nak'uda ne''. A hanzarce yace ''tun yaushe haka baki fad'a min ba? kina wasa da rayuwarki Maryamah. Gani nan zuwa''. A hanyarsa ta zuwa ya k'ira Dr. Sulaimana yace zai d'auko Maryamah nan da awa d'aya zasu iso, ''toh, sai kun iso'' kawai Dr. yace ya kashe wayar.

Ciccib'anta yayi yasa a bayan mota suka wuce asibiti. Kafin su isa nak'udar ta taso gadan-gadan, hakan yasa suna isa aka shige da ita d'akin haihuwa, abunda yafi d'agawa Abakar hankali shine Maryamah ko ihu ta kasa yi, yana ganin dai bakinta yana motsi shi a tunaninsa kalmar shahada takeyi zata mutu. Da aka shiga da ita zama yayi ya dafe kai yana zubar da hawaye tare da addu'ar Allah ya sauk'eta lafiya. Sai da suka shafe awa d'aya da kad'an sannan Dr. Ya fito murmushi a fuskarsa. Bayan ya cire kayan likitancin nasa ya isa gun Abakar da bai ma san an fito ba dan kansa na k'asa sai hawaye yakeyi.

Dafa sa yayi ya d'ago kai a firgice fuskarsa hawaye ya wanke, Dr. Sulaimana cike da farin ciki yace ''Maryamah ta samu kanta lafiya k'alau, ta samu baby girl''. Ihu Abakar ya daka sannan ya rungume Dr. yana cewa ''Thank you Dr.'' Dr. yace ''ka godewa Allah, ban tab'a d'auka Maryamah zata sauk'a lafiya k'alau ba, sai gashi ko manyan ma ba za su samu haihuwa mai sauk'i irin nata ba''. Ai ko nan take Abakar ya fara ''alhamdulillah'' kana yace ''zan iya ganinta?''

Dr. Yace ''yanzu dai ana shirya su, amma kamar yanda tace in fad'a maka, dabino d'anye takeso kamar guda bakwai haka, so ka hanzarta ka samo mata kafin ka dawo an gama komai''. Abakar yace ''Maryamah again, shi kuma meh zatayi dashi?'' Dr. Sulaimana yayi dariya sannan yace ''rannan dai da nake mata awu na bata labarin wata mata akan jinin haihuwa ya daskare mata a mahaifa, tace min da ta ci d'anyar dabino bayan ta haihu kafin taci komai zai narkar dashi ya fito ba tare da wahala ba, gashi yanzu rashin sani ya sa ta zaryar asibiti'' Abakar yace ''Allah nagode maka da ka bani Maryamah''.

Bayan an gama shiryasu Abakar yayi wa yaro addu'a sannan ya bar asibitin ya wuce gida cike da farinciki. Bai tsaya ko ina ba sai d'akin Fad'ime yana kwala mata k'ira, karo suka ci a bakin k'ofa ya rungumeta yana ihun murna, ita ma murnar ta fara yi duk da bata san me yake faruwa ba, cike da murna yake cewa ''na samu baby Girl Fad'ime'' cike da rashin fahimta ta janye jikinta daga nasa tana kallonsa, fuskarsa bai b'oye tsantsar farin cikin da yake ciki ba.

Fuskarta da alamun neman k'arin bayani, harshenta kuma ya gaza furta komai. Kallonshi kawai takeyi yana murnarsa, daga baya yace mata ''yanzu Dr. Sulaimana ya k'irani wai akwai wacce ta haihu ta rasu anan asibitinsa, kuma babu d'an uwanta ko danginta, shine ya bi duk hanyar da ya dace a bi aka bani yarinyar in rik'eta har abada'' ita ma cike da murna ta k'ank'amesa tana cewa ''Alhamdulillahi''. Shiryawa kawai tayi suka wuce asibiti cikin murna.

Maryamah da take kwance akan gadon asibiti tunani ne fal ranta, tunda aka kawota d'akin ba'a kawo mata yarinyar da ta haifa ba. Sallamar Dr. Sulaimana yayi shi ya dakatar da ita daga tunanin da ta fad'a. ''Ya jiki Maryamah?'' Ta amsa da ''Alhamdulillah'' Dr. yace ''Maryamah yanzu zamu shigo da wata da Abakar, duk abinda zamu ce ki taimake mu kada ki k'aryata mu a gabanta. zamu fad'a miki komai bayan kin bamu had'in kai''. Maryamah bata kawo komai a ranta ba ta amsa da ''toh''.

A can office na Dr. Sulaimana kuma Fad'ime ce da Abakar zaune suna jirar shigowar Dr. Sulaimana. Da murmushi a fuskarsa ya shigo office d'in yana cewa ''ai ya zo gidan sauk'i, matar da nace muku ita ma ta haihu d'an yakoma ta yadda zata shayar da ita''. Fad'ime tace ''Alhamdulillah, amma dai Dr. ka tabbata bata da wani cuta da zai iya samun babyn?'' Dr. Sulaimana yace ''sure babu komai, sai da na tabbatar sannan na fad'a muku, yarinyar nan nasan da ita, nasan komai nata, haka kawai bazan baku shawarar d'aukarta ta shayar da babyn nan ba''.

Dukkan su suka shige d'akin da Maryamah take ciki, Dr. Sulaimana yace ''gata nan yarinyar, ita ma ta haihu amma yaron ya koma'' ido Maryamah ta zare tana kallon Dr. Sulaimana da yake girgiza mata kai alamar tayi shiru, Fad'ime tace ''amma Dr. Batayi k'arama da shayar da yarinyar ba?'' Yace ''ta iya haihuwa ma bare shayarwa?'' Fad'ime tace ''toh ai ba laifi, sai ta shirya mu wuce tare koh?'' Bata jira amsar su ba ta fice ta barsu. Kuka Maryamah ta fashe dashi mai shiga rai tana cewa ''da gaske d'an da na haifa ya mutu? Yaushe ya mutu ban sani ba?'' Dr. Sulaimana yace '' 'yar ki tana nan Maryamah, ki gafarce mu bamu fad'a miki gaskiya ba tun-tuni. 'Yarki muka bawa Fad'ime matar Abakar, zaki shiga gidan ne a matsayin wacce taje shayar da 'yarta''.

Ido ta ware tana kallon Dr. Sulaimana sannan ta kai dubanta ga Abakar da kanshi yake k'asa, zufa duk ya wanke masa fuska. Kalmomin da Maryamah take fad'a shi ya janyo hankalinsa gareta har ya d'aga kai yana kallonta. Cewa take ''ni a rayuwata kenan bazan tab'a samun 'yan ci ba? Ina matsayin matarka zaka kai ni gidanka a matsayin wacce take muku hidima?'' Ta girgiza kanta tace ''na bar muku yarinyar da na haifa, na gwammace in zauna tare da Amty Babbe tana bani talla ina fita dashi, duk tsanar da take min sai na mata laifi take hukuntani. Bazan tab'a manta wannan k'ask'anci da cin zarafin da kayi min ba'' kuka mai shiga rai take yi sosai.

 

 

 

Kuka sosai ta ke yi tana gogewa da d'ankwalinta, Abakar kasa daurewa yayi shima ya fashe da kuka ya tsuguna dai-dai gadon da take zaune ba tare da yayi magana ba, Dr. Sulaimana shi yayi k'arfin halin d'aga sa ya fitar dashi waje sannan ya dawo gunta. Bata daina kukan ba sai ma k'aruwa da yayi lokacin da ya fita ''cikin da yake jikinta yake buk'ata kenan, da ya samu kuma ko magana bazata samu ba bare hak'uri da rarrashi kamar yanda ya saba mata in tana kuka'' hakan take fad'a a ranta kuma yasa kukan nata ya tsananta.

Dr. Sulaimana ya zauna a kujerar da ke gefenta yana rarrashi, ko tsagaita kukan tak'i yi hakan yasa ya fara bata labarin rayuwar Abakar, dalilin auren da kuma rashin haihuwar Fad'ime wanda Abakar ya d'aurawa kansa yak'i sanar da ita dan tausayi da soyayyar da yake tsakaninsu, sai a sannan tayi shiru tana goge hawayenta. Dr. Sulaimana yace ''na sanki kuma nasan irin zuciyarki, kina nufin har yanzu kina kan bakanki na bazaki je gidan ba saidai ki koma Godil? Kuma bazaki yafe masa ba?''.

Maryamah tace ''na tausaya mata, kuma ai da kun fad'a min tun wuri bazan yi magana irin haka ba'' ta ja majina sannan ta cigaba ''na yadda zanje gidan in zauna a matsayin wacce zata shayar da 'yar Fad'ime, amma bayan na shayar da ita komawa zanyi Shika dan makaranta na''. Dr. Sulaimana ya girgiza kai yace ''kafin ki gama shayar da ita zamu Fad'awa Fad'ime, ke dai yanzu kiyi yanda muka ce insha Allah komai yazo k'arshe''. Shi da kansa ya kaita gidan Abakar, Fad'ime ce ta nuna mata d'akin da zata zauna, babu laifi yana da kyau, yana gefen d'akin Mama Zainaba. Sai a sannan aka kawo mata yarinyarta ta ganta, har hawayen murna sai da tayi da ta d'auketa.

Yau kimanin sati uku da haihuwar Maryamah, yarinya ta ci sunan Fad'ime, in ba shayarwar ba babu abinda yake kawo Fad'ime k'arama wurin Maryamah, soyayya sosai Fad'ime ke nunawa 'yar haka zalika bata tab'a nuna k'yashi ko wulak'anta Maryamah ba. Hakan yasa Maryamah ta tausaya mata matuk'a dan kusan kullum in ta tashi sallar dare sai ta mata addu'a tana mai zubar da hawaye.

Dr. Sulaimana zaune a mota yana jirar Engr. Abakar a harabar gidan Abakar, bai b'ata lokaci ba ya iso yana cewa ''yanzu har zaka isa Damaturu kuma gobe ka kamo hanyar dawowa?'' Dr. Sulaimana yace ''toh ya na iya? Yara sun koma makaranta jibi yakamat su je'' Abakar yace ''munyi magana da Mama tace zata biyoku, dak'yar nan ma na shawo kanta'' Dr. Sulaimana yayi dariya sannan yace ''ni na wuce, dama nazo baka wasu documents ne Jamilu zai zo ya karb'a'' ya mik'a masa sukayi sallama ya wuce.

Washe-gari tun k'arfe hud'u suka shigo garin Kaduna, Mama Zainaba, Al'amin sai Ashshe a baya, Dr. Sulaimana ke driving sai Hamrah a gefensa. Mama Zainaba tayi bacci da sauran yaran, hira sukeyi tsakaninsu har suka isa gidan Engr. Abakar dan su ajiye Mama Zainaba kafin su wuce gida. Tun a hanya yayi wa Abakar text ''kada ka bari Maryamah ta had'u da Fad'ime, zata iya b'ata komai'' Abakar yana d'akinsa yaga text d'in, hakan yasa ya k'ira Maryamah, da yake ba wani shiri sukeyi ba gaisawa kawai sukayi tayi shiru, yace mata ''zamuyi bak'uwa yanzu amma bazasu jima ba, zasu ajiye mamana ne su wuce, dan Allah ki zauna a d'akinki kada ki fito kinji?'' ''Toh'' kawai tace ta kashe wayar.

Dukkansu suka shiga gidan dan ganin babyn da Fad'ime ta samu da yake tun da aka bata yarinyar Hamrah bata zo gidan ba, an dai tura mata hoton yarinyar ta gani, har take cewa Fad'ime ''da bansan bazaku iya haihuwa ba da nace yarinyar nan jinin Abakar ce, dan suna kama'' Fad'ime dariya tayi tana cewa ''da ta zama namu dai tayi shige dashi, in ba haka ba ai babu kama da sukayi''.

Sun shiga sunga baby har zasu fito Fad'ime tace ''baki ga mai shayar da ita ba, hankali yarinyar sosai, barin k'irata'' Maryamah tana ji ana k'wala mata k'ira tak'i fitowa, tana jin alamar ana doso d'akinta ta shige toilet ta sa key. Tana cikin toilet d'in taji Fad'ime na cewa ''tana toilet, tunda kuna sauri next time in kinzo sai ku gaisa'' sannan suka fice.

 

 

 

Haka sukayi ta rayuwa duk ranar da Hamrah tazo gidan sai ta b'uya, Fad'ime bata kawo komai a ranta ba amma ita Hamrah ta fara shakku, dan duk ranar da tazo gidan mai shayar da Zahra tana da uzurin da bazai yu su had'u ba. Rayuwar Maryamah na aure tsakaninta da Abakar kuwa sai dai ayi shiru, dan Fad'ime ta kasa ta tsare kuma ta toshe duk wani hanya da zai sa su keb'anta, Maryamah kullum sai tayi kuka akan irin zaman da takeyi da Abakar, kuma ga Dr. Sulaimana da yake kawo mata kayan gyara wai inji Khajije, har tana ganin wautarta in tayi anfani dasu, sai tana ganin babu anfaninsa dan ko gaisuwa sai dai in Abakar ya k'irata a waya.

Yau da misalin k'arfe sha biyu Dr. Sulaimana ya shigo gidan, suka gaisa da Fad'ime sannan yace yazo su fita da Maryamah, Fad'ime tace ina zaku?'' Dr. Sulaimana yace ''akwai wani maganin da nake son bata, shine zamu je in dubata kada in bayar ba tare da nasan yayi mata daidai ko yafi k'arfinta ba'' tace ''ohh! haka, barin k'irata, kaga Zahra ma na wurinta tana bata abinci''.

Hijabi dogo ta saka ta fito suka wuce, amma instead su wuce asibiti kamar yanda Fad'ime tace asibiti zasu je wani wuri ne da ta kasa tantance ina ne, wurin ya burgeta sosai. Parking motar yayi ya d'auki waya ''mun iso'' kawai taji yace ya kashe wayar.Bai sake magana ba sai ganin Abakar tayi yana doso su, a take annurin fuskarta ya d'auke ta d'auke kanta daga dubansa.

Bud'e mata k'ofar yayi yana murmushi ko kallon inda yake bata yi ba kuma bata da niyyar fitowa, ji tayi an d'auketa cak ta sake ihu ta fara waiwaye ko akwai mutumin da yake kallonsu, Allah da ikonsa kuma babu kowa sai Dr. Sulaimana da yake dariyar su. Ji tayi yace ''ka kawo ta asibiti in kun gama sulhun'' ya tada motarsa yayi gaba.

Kuka ta sake masa tana bugunsa a k'irji tana cewa ''da nasan nan zai kawo ni da ban bisa ba. Ni ka ajiyeni'' shi ko Abakar bai mata magana ba sai dariyar da yake mata. Bai ajiyeta ko ina ba sai kan kujerar da yake tsakiyar filin wurin.

K'asar ciyayi ne kore fatau, sai bishiyoyi da suka zagaye wurin, babu rana ko kad'an sai iska mai dad'i da yake busar su. Zama yayi kusa da ita yana cewa ''a fad'a min laifina in bada hak'uri, shareni da kikeyi yayi yawa kwaiseh'' zumb'uro bakinta tayi tana cewa ''ni ban shareka ba, ai dama baby kakeso in baka kuma na baka shine ka shareni'' ta sake masa kuka tana cewa ''ka mayar dani Shika nikam na gaji da zaman garin nan''. Ajiyar zuciya ya sauk'e sannan ya janyo ta jikinsa yana cewa ''Maryamah bazaki sake komawa Shika ba kin sani koh?'' Cikin kukan take cewa ''toh haka zanyi ta zama ina kallonka da wata, a gabana fa take kwanciya jikinka ko kunyana bakuji'' dariya abun da tace ya basa amma ya gimtse dan kada ya sake wani laifin ''yi hak'uri indai wannan ne an daina baza'a sake ba''.

Tace ''sai kuma....'' bata k'arasa ba tayi shiru, ya d'ago fuskarta yace ''me ne ne? ni banason kina kunyar fad'a min magana'' tace ''ni inason ina ganinka kullum'' Abakar yace ''ai kullum kina gani na, ke dai fad'i abun ranki, kinyi kewata ne?'' Ya fad'i hakan yana d'aga mata gira. Kunya taji ta rufe fuskarta da hannunta sannan ta ajiye bisa k'irjinsa tana dariya k'asa-k'asa.

Rungumeta yayi yana cewa ''nayi kewarki nima sosai'' ya cire mata hijabin jikinta da d'an kwalinta yana shinshinar gashin kanta, yace ''nayi kewar shak'ar k'amshinki'' ya shafa hannunta yace ''laushin jikinki ma duk nayi kewarsu, kuma ai ke kika hanani keb'ewa dake dan fushi dani kikeyi'' ta sauk'ar da numfashi tace ''matarka tana gidan kake son in sake dakai? Ni fah ina tsoron ta dake ni, wallahi ta fini girma da jiki''.

Dariya sosai Abakar yayi sannan yace '' tunda kin hak'ura ki tashi mu tafi, nan mutane zasu iya kallon min ke kuma ina kishi'' maryamah tace ''kishi? Kishin me?'' Ya d'aga mata gira yace ''eh, ni nasan meh nake kishi, hancin nan ma...'' ya ja hancinta sannan ya cigaba ''banson ana kallonshi bare sauran jikinki'' dariya sosai Maryamah tayi sannan ta d'aura d'ankwalinta ta sa hijabi suka bar wurin, babu inda ya sauk'eta sai wani k'erarren hotel suka shige.

 

 

 

Haka suka cigaba da yi, duk ranar da yakeson keb'ewa da Maryamah Dr. Sulaimana ke zuwa ya fita da ita ya ajiyeta gunsa su wuce hotel, hakan ya kawo musu fahimta da kuma soyayya mai k'arfi, wani lokacin a gaban Fad'ime zai ta kallonta ko ya kashe mata ido, Fad'ime duk bata kula da hakan ba sai Mama Zainaba da ta sa musu ido sosai tana kula dasu.

Yanda Abakar ke kallonta wani lokacin har murmushi yake sake mata ita ma ta mayar masa, Mama Zainaba duk ta damu da irin abubuwan da sukeyi hakan yasa ta k'ira Maryamah dan ta tambayeta, duk tambayar da ta mata akan suna da alak'a da Abakar k'aryatawa tayi, hakan yasa ta k'yalesu tana jiran ranar da zata gani da idonta.

Tana zaune a d'akinta ita da Abakar k'ofar a bud'e, Maryamah tazo ta wuce sanye da rigar bacci mai santsi ya kwanta jikinta, Mama Zainaba ta kalli Abakar taga idonshi na kan k'ofar, ko minti d'aya baiyi ba da wucewarta yace zai je ya kwanta, sukayi sallama ya fice.

Fad'ime ya lek'a a d'aki yaga tana bacci, ya fito ya wuce kitchen inda Maryamah take, da murmushinsa ya isa gunta yana cewa irin kayan nan zaki sa kuma kinsan bazan ganki ba? Da bana d'akin Mama da kallo ya wuce ni'' murmushi kawai tayi ta cigaba da abinda takeyi, shi ko ya rungumeta ta baya yana cewa ''rabona da in ganki da irin kayan nan har na manta. Gobe zamu fita ai koh?''

Muryar Mama Zainaba suka ji daga bakin k'ofa tana cewa ''Abakar'' a tsorace ya juyo yana kallonta, Maryamah kam kasa juyowa tayi, Mama Zainaba bata sake magana ba ta juya ta wuce d'akinta Abakar ya bi ta a baya. Lokacin da ya shigo d'akin ko kallonsa tak'i yi, sai da yace ''Maryamah matata ce fah Mama'' da mamaki take kallonsa tace ''yaushe kayi aure ban sani ba Abakar, kare kanka kakeson yi shine zaka kawo aure ciki? Abakar yaushe ka lalace haka?'' Kuka ta fara masa tana cewa ''lalacewar har ya kai ka min k'arya da aure?''.

Baisan lokacin da ya fara bata labarin abunda ya faru ba, sai da ya fad'a mata komai daga farko har k'arshe, har haihuwar da Maryamah tayi da rashin haihuwar Fad'ime, kuka mama Zainaba takeyi yana tayata, ya rok'eta da ta rufa masa asiri kada ta fad'a zai fad'awa Fad'ime da kansa amma ba yanzu ba. Kuma bata yi musu ba ta yadda da hakan, ita da kanta taje d'akin Maryamah da take ta zagaye d'aki ta kasa bacci ta mata nasiha ta bata hak'uri akan irin zaman da takeyi a gidan sannan ta bar d'akin.

Daga ranar Mama Zainaba ta tsiri aiken Maryamah kuma tace sai dai Abakar ne zai kaita, babu yanda Fad'ime zatayi saidai ta had'e rai amma ba'a fasa ba sai ma abun da yayi gaba. ita bata son mijinta yana keb'ewa da Maryamah, bata son wani abu ya shiga tsakaninsu, kishi takeji sosai in taga ya sata gaban mota wai zai kai ta aiken Mama Zainaba, ji take kamar ta mak'ure wuyar Maryamah ko zata huta.

K'iran Hamrah tayi take ce mata tazo akwai matsala, Hamrah da take gidan k'awarta bata b'ata lokaci ba ta wuce gidan Fad'ime ba tare da sanin mijinta ba. Kai tsaye ta shiga gidan ta wuce d'akin Fad'ime, ko gaisawa basuyi ba ta fara fad'a mata abinda Mama Zainaba ta fara yi ''wai Kwaiseh(da yake kwaiseh take k'iranta) take aike kuma kullum sai dai Abakar ne zai kaita, ni fah na fara gajiya da abun nan'' Hamrah tace ''kin tsaya sanya, kwaiseh zaki samu kiyi mata tas, kice in an aiketa tace zata hau taxi ba sai mijinki ya kaita ba''.

Fad'ime tace ''bazan iya ba, ina jin nauyin yarinyar'' Hamrah tayi tsaki ta harareta ta tashi fuu! Ta wuce d'akin Maryamah, ko sallama batayi ba ta bud'e k'ofar Fad'ime na binta a baya. Maryamah ce zaune tayi wanka tana shafa mai taga mutane sun shigo mata d'aki. Kallonsu kawai takeyi ta kasa musu magana. Hamrah ta juya ta kalli Fad'ime tana nuna Maryamah tana cewa ''wannan ita ce kwaiseh da kike ta fad'a min kullum'' Fad'ime tace ''ita ce, kin santa ne?'' Hamrah bata sake magana ba ta janyo hannun Fad'ime suka koma d'akinta.

Sai da suka zauna sannan take cewa ''amma an raina miki hankali Fad'ime, duk iliminki, duk wayewarki da shiga mutanen da kikayi baki gano akwai abu tsakanin wannan jakar da kika ajiye a gida da mijinki ba?'' Fad'ime tace ''kamar ya, babu komai fah tsakanin su'' Hamrah tace ''wallahi kin bani kunya, toh bari kiji, wannan yarinyar kishiyarki ce.......'' ta kwashe komai ta fad'a mata, duk abunda ta sani game da maryamah sai da ta fada mata.

Har haihuwar da Fad'ime bata yi bata b'oye mata ba dan shine abunda yasa aka auri Maryamah. Fad'ime cikin tashin hankali take girgiza kai tana cewa ''a.a. bazai tab'a yi min haka ba Abakar'' kuka ya kufce mata tana cewa ''na san Abakar bazai b'oye min komai ba'' Hamrah tace ''toh na miki k'arya. Kinga tafiya ta, in zaki d'au mataki tun wuri ki d'auka dan wallahi an raina miki hankali'' Bata jira meh zata ce ba ta fice daga d'akin ta shige motarta ta bar gidan.

 

 

 

Fad'ime tafi awa d'aya zaune inda take ta kasa motsi, hawaye kawai ke sauk'a daga idanunta, ta rasa me zatayi, tunaninta ya tsaya, k'wak'walwarta ya cushe, hawayen da ke sauk'a daga idanunta shi yake sauk'ak'a mata k'uttu da wani k'ullutu da ya mak'ale mata a mak'ogoro. Kamar an mitsine ta ta mik'e da hanzari ta wuce d'akin Abakar, duk inda tasan yana ajiye muhimman takaddunsa sai da ta bincika.

Ta barbaza ko ina na cikin d'akin bata samu abinda takeso ba, hakan yasa ta durk'ushe a k'asa tana mai zubar da hawaye, can ta sake mik'ewa da hanzari ta shiga toilet d'insa tunawa da tayi yana da d'an k'aramin save a ciki.

Neman makullin takeyi a toilet bata gani ba, da gudu ta dawo d'akin ta bud'e drawer ta fara ciro kayansa tana watsa su a k'asa, sai da ta fitar da kayan gaba d'aya sannan taga makullin a can dungu, sai da ta sauk'ar da ajiyar zuciya sannan ta d'auka ta koma toilet d'in ta bud'e, babu wasu tarkace masu yawa a ciki, daga kud'ad'e sai takaddu da kuma wani k'aton envelope an rubuta sunan asibiti a jiki, shi ta d'auko dan shi take nema dama, a cikin toilet d'in ta rufe WC ta zauna akai sannan ta fara bud'ewa.

Duk result(sakamako) na gwajin da aka musu tun na farko har na k'arshe da yace mata shine bai haihuwa duk suna ciki, tun daga farko ta fara dubawa har k'arshe, ta maimaita su yafi sau uku daga bisani ta gane gaskiya idonta yake gani, kenan ya tabbata ita ce bata haihuwa kamar yanda Hamrah ta fad'a mata? Maryamah matar Abakar ce Zahra kuma 'yarsa? Ihu sosai ta sake tana k'arawa ko zuciyarta zai daina mata zogi.

Tayi kuka kamar ranta zai fita, ko toilet d'in ta kasa bari dan dab'as ta zauna a k'asa tana mai rera kuka. Sai da tayi mai isarta sannan ta tashi ta zubar da takaddun ta wuce d'akin Maryamah.

Kai tsaye ta shiga ko sallama babu, farar fuskar nan yayi jawur idanunta duk sun kumbura. Maryamah da take zaune tana bawa Zahra abincinta a tsorace ta mik'e dan shigowar nata ya tsorata ta, kuma da ta sake kallon fuskarta sai zuciyarta ya sake tsinkewa dan ta d'auka Abakar ne ya mutu. Tun kafin ta iso gunta ta ajiye Zahra akan gado tana cewa ''lafiya?''.

Mari Fad'ime ta sauk'e mata a kuncinta mai kyau, bata jira wani abu ba ta k'ara mata sannan ta fara nemo abunda zata illata Maryamah dashi a d'akin, Maryamah rik'e da kuncinta da yayi jawur hawaye na malala daga idanunta ta kasa tab'uka komai sai kallon Fad'ime take, kamar mahaukaciya ta zama tana birkita d'akin, bata samu abun kirki ba hakan yasa tayi kukan kura ta hau kan Maryamah da duka. Fad'ime na ihu tana kuka tana cewa Maryamah ta cuceta Maryamah na kuka tana ihun tayi hak'uri.

Mama Zainaba kamar cikin mafarki take jin hayaniya, tana bud'e ido kuwa taji ihun Maryamah da Fad'ime, da gudu ta fito tana cewa ''lafiya?'' Tana shiga d'akin taga Fad'ime zaune akan Maryamah tana kan d'irka mata duka, Zahra da ke kwance kan gado ita ma sai kuka takeyi har jijiyoyinta na fitowa dan ihun da take k'walawa.

Mama Zainaba tayi iya k'ok'arinta ta raba su amma inaa, sai da taga bazata iya ba ta koma d'aki ta d'auki wayarta ta k'ira Abakar. Ringin biyu ya d'auka yana cewa ''Lafiya Mama? Gani nan kan hanya, wani abu kije buk'ata?'' cikin kuka take cewa ''kayi sauri zata kasheta'' Abakar yace ''wa za'a kashe mama?'' Mama Zainaba tace ''Fad'ime zata kashe Maryamah, kayi sauri kazo kada ayi kisan kai a gidanka Abakar''.

Bata jira cewarsa ba ta kashe wayar ta koma d'akin ta cigaba da k'ok'arin rabasu. Tun kafin ya iso ya k'ira Dr. Sulaimana yace ''kazo gidana yanzun nan akwai matsala'' bai jira amsar sa ba ya kashe wayar. Bai d'auki minti goma mai kyau ba ya iso, ya danna horn tun kafin ya iso k'ofar amma kafin mai gadi ya bud'e masa tuni ya fito daga motar ya barta a kunne kuma a bud'e ya shige gidan da gudu.

Ta inda yake jin ihun Mama Zainaba da zahra da Fad'ime yayi dan a lokacin Maryamah ko motsin kirki batayi, jibgarta Fad'ime takeyi kamar Allah ya aiko ta. Yana shigowa d'akin yaga abinda yake faruwa tuni yaji wani k'arfi yazo masa. Hannu yasa ya d'auke Fad'ime da mari mai kyau sannan ya wullata gefe ta fad'i yayi kan Maryamah yana jijjigata amma Maryamah ko motsi bata yi, fita yayi ya d'auko ruwa yazo ya watsa mata a fuskarta amma inaa, Maryamah ko motsi bata yi, rungumeta yayi yasa ihu yana cewa ''please ki tashi kada ki mutu'' sai ga hawaye daga idanunsa.

 

 

Muryar Fad'ime yaji cikin sheshshek'ar kuka tana cewa ''hakan ya tabbatar min Maryamah matarka ce kamar yanda naji'' ta tashi tsaye tana d'aura zaninta sannan tace ''wallahi tunda ka ci amanata kayi min kishiya ba tare da sani na ba ko bata mutu yanzu ba sai na kashe ta ko nan gaba ne'' ta gefensa ta bi zata wuce ya tashi ya damk'e hannunta, ya d'aga hannu zai mareta Mama Zainaba ta rik'e tana cewa ''ka mata laifi, ka barta ta huce sannan asan abun yi ba wai ka d'au mataki nan take cikin fushi ba'' janyo ta yayi ya wullata cikin d'akin ya rufe k'ofar yana cewa ''wallahi babu inda zata je sai na tabbatar Maryamah bata mutu ba''.

Durk'ushewa ya sake yi ya janyo maryamah yana hura mata iska a fuska. Ba'a k'ara minti biyar ba Sulaimana yazo, Mama Zainaba ne ta bud'e k'ofar tace ya shigo suna ciki. Ganin Maryamah yayi wanwar a k'asa kamar matacciya, da hanzari ya isa ciki yana tambayar ''lafiya?'' Babu wanda ya amsa shi sai kukan da Fad'ime da Abakar sukeyi, Zahra na hannun Mama Zainaba. Yace wa Abakar ya d'auketa su wuce asibiti kawai ba anfanin zama a gida bayan ko numfashi bata yi.

Fad'ime kawai aka bari a gida dan Mama Zainaba ta d'auki Zahra da ita suka tafi asibitin, wai kada jikarta nata a makure har lahira. Dak'yar aka samu Maryamah ta farfad'o aka mata allurar bacci aka d'aura mata ruwa sannan hankalin kowa ya kwanta.

Kwananta uku a asibiti aka sallameta, tsakanin Fad'ime da Abakar banda harara da zagi babu abinda yake had'a su, a kwana biyun nan tayi kuka har ta jeme ta rame dan tsaban rashin cin abinci da damuwa. Tun Abakar yana jin zafin dukar da tayi wa Maryamah har ya fara tausaya mata dan yasan zaiyi wuya ta fahimce shi.

Ranar da Maryamah zata dawo gida ya sameta a d'aki dan suyi magana ko zasu fahimci juna, firr! Tak'i saurararsa, goge ido tayi ta tsirfa masa rashin mutunci sannan daga baya ta sa masa kuka tana cewa ya cuceta, ya janyota jikinsa zaiyi rarrashi amma ta tureshi tana cewa ya fice mata daga d'aki bata son ganinsa ta tsanesa. Wasa-wasa Fad'ime har sati bata dawo dai-dai ba, kullum tana zaune a d'aki tana aikin kuka, ko abincin kirki bata ci, banda tea da take had'awa a d'akinta ko Abakar ya kawo mata abinci bata ci.

Maryamah ta samu sauk'i sosai, amma ko da wasa bata bin ta inda zata had'u da Fad'ime dan ta tsorata da ita sosai, Abakar d'in ma tak'i sakewa dashi dan cewa tayi ita sai dai ta koma Shika ko kuma ta koma wurin Amty Babbe. Ganin haka yasa shima ya daina shiga sabgarta dan bazai bari taje ko ina ba, ko gaishe shi tayi sai ya had'e rai yake amsawa.

Yau Dr. Sulaimana ya d'auko Hamrah dan zuwa gidan Abakar, har yanzu basu san wa ya fad'awa Fad'ime bata haihuwa ba kuma Maryamah matar Abakar ce, kamar yanda Abakar yace masa taga result din ne in yayi la'akari da yanda ta barbaza d'akin kuma yaga results d'in a cikin bayan gida. Kuma maganar Maryamah kawai tayi zargin ita matarsa ce kuma ya zama gaskiya.

Sun isa ko minti biyar basuyi ba iyayen Fad'ime da k'anwarta suka diro gidan. Duk a falo suka zauna harda Mama Zainaba da Maryamah. Abakar ne ya shiga d'akin Fad'ime dan yayi k'iranta, tun kafin yayi magana ta dakatar dashi da hannunta tana cewa ''ka fita banason ganinka Abakar'' Bai damu ba, ya zauna kusa da ita ya rik'e hannunta, bata janye ba sai fashewa da kukan da tayi, ya janyo ta jikinsa ya rungumeta, ta sauk'ar da ajiyar zuciya.

Cikin kunnenta yake cewa ''Fad'ime ki gafarce ni, nasan na miki laifi amma ki taimaka ki saurareni'' Fad'ime cikin kuka take cewa ''nasan meh yasa kayi haka, ka nuna min son da nake maka yafi wanda kai kakeyi min, shekarun da nayi da kai na zauna dakai ne matsayin wanda baya haihuwa kuma ban tab'a tunanin barin ka ba ko da nan gaba, ashe kai aure ma kayi dan bazaka iya zama ba tare da ka haihu ba'' ta ja majina tace ''ni kuma da na zauna dakai fah Abakar?'' Kuka yaci k'arfinta sosai, Abakar kuka yakeyi yana bata hak'uri kuma ya bar mata Zahra har abada, amma fir Fad'ime tace sai dai ya saketa. Da k'yar ya shawo kanta har ta yadda zata fito kamar yanda yace mata akwai wasu da suke jiransu a falo.

D'ankwali kawai ta d'aura ta shiga toilet ta wanko fuskarta suka jera suka fito tare, tana ganin mahaifiyarta ta isa gunta da gudu ta rungume tana mai zubar da hawaye, mamanta rungumeta tayi tana rarrashi tana goge k'walla ita ma. Sai da suka nutsu sannan Abakar yayi musu bayanin komai, bai b'oye musu komai ba sai dai yak'i fad'ar ba da sonshi akayi auren ba dan kada aji haushin abokinsa, hasalima cewa yayi shi yaga yarinyar yace yana so Sulaimana ya shige masa gaba har akayi auren.

Kuma ya fad'a musu dalilin k'in sanar da Fad'ime akan dan baya son ta d'aga hankalinta akan jarrabar da Allah yayi mata, shiyasa ma da Maryamah ta haihu ya bata yarinyar ko hankalinta zai kwanta. Fad'ime cikin shesshek'ar kuka tace ''nifah ban yadda da maganarka ba, wai dan farincikina kak'i fad'a min aurenka bayan Hamrah tace min har Shika taje ganin Maryamah, in har b'oye min zakayi ai bazaka fad'awa aminiyata ba dan tabbas kasan zata fad'a min kamar yanda ta fad'a min yanzu''.

Dr. Sulaimana cike da mamaki yake kallon Hamrah da kanta yake k'asa kamar munafuka, ya kai dubansa ga Fad'ime sannan yace ''Hamrah ce ta fad'a miki kenan? Kai tsaye ta amsa da ''eh, ai gata ku tambayeta mana'' cikin fushi Dr. Sulaimana ya mik'e ya finciko hannun Hamrah yayi hanyar waje, duk k'iran da suke masa yak'i juyowa hakan yasa kowa yayi shiru aka koma yiwa Fad'ime nasiha.

 

 

 

Fad'ime k'ek'eshe ido tayi tace sai dai ya saketa, babu wanda bai bata baki ba amma tace ita bazata zauna dashi ba yaci amanarta. Maryamah ce tayi gyaran murya tace ''indai dan ni kike son tafiya ni na yadda zan bar muku gidan kuma in bar muku zahra. Amma inason in fad'a miki wani abu Yaya, ki sani kowa da irin k'addararsa, wasu rashin lafiya mai muni, wasu rashin ido, wasu rashin magana da rashin ji, wasu rashin iyaye, wasu talauci, wasu Allah na d'aura musu k'addara fiye da d'aya a lokaci d'aya kuma ahakan suke rayuwa suna gode masa, ba k'in su yayi ba sai dai yayi hakan ne dan ya jarrabi imanin su, shin zasu gode masa ko zasu butulce masa, kema hakan ya hau kanki, kuma Allah yana sane dake yasan dalilin da yasa ya d'aura miki rashin haihuwa, baki rasa ci ba tun tasowarki baki rasa sha ba, haka zalika baki rasa sutura ba, har kikayi aure baki rasa soyayyar mijinki ba, zan iya cewa baki tab'a neman abu a duniya kika rasa ba, meh yasa baza ki hak'ura ki zauna da mijinki wanda yake sonki tsakani da Allah ba? mutumin da yayi komai dan ya baki farin ciki, kada ki manta duk abinda yayi dan ke yayi, acikin ni da ke in akwai wacce ya dace ta nemi saki, ni ce'' ta nuna kanta sannan ta cigaba...

''Dan ni ba auren so mukayi ba, munyi aure ne dan in haifa muku yara kuma Alhamdulillahi na haifa miki Zahra'' ta goge hawaye sannan ta cigaba ''inason kuma dan Allah ki daina d'aukan mataki cikin fushi, wallahi dukan da kika min zai iya kisa, kina tawakkali kuma ki yadda da Allah, nidai har ga Allah kunyi min komai a rayuwa, kun d'auko ni kun bani gata kun sani makaranta nayi ilimin da nake tink'aho dashi a yau'' ta ja majina sannan tace nagode sosai da kulawarku, Allah ya biyaku da mafificin alkhairi musamman Dr. Sulaimana, yayi min komai a rayuwa kuma ina masa fatan alkhairi''.

Ta juyo ta kalli Abakar da tunda ta fara magana idonshi akanta ko kiftawa baya yi tace ''ni na yadda da ka sakeni in tafi, Allah ya raya yarinyar da na haifa''. Mama Zainaba tayi carab tace ''maganar saki bai ma taso ba, kawai tunda an gane gaskiya kowa ya rik'e k'addara yayi hak'uri. Koh Madine?'' Ta juya tana kallon Maman Fad'ime, ita ma hakan tace ayi hak'uri a zauna lafiya, kuma tayi alk'awarin zata nusar da 'yarta har ta yadda ta zauna tare da mijinta da kishiyarta lafiya.

Fad'ime kuka ta ke yi sosai ta kasa magana, sai da kowa ya gama tofa albarkacin bakinsa sannan tace ''na gane kuskurena kuma na d'auki laifina, na biye wa son zuciya da kishi yasa na daki uwar 'yata tilo da Allah ya kawo min ta sanadin mijinah Abakar'' har k'asa ta isa inda Maryamah take ta nemi yafiyarta sannan ta nemi yafiyar mijinta kuma duk sun yafe wa juna. Abakar ma ya nemi afuwarta ita ma kuma ta yafe masa, kowa yayi murna sosai baban Fad'ime yayi nasiha mai shiga jiki daga k'arshe aka yi addu'a kowa ya nemi wurin hutawa kafin washegari su wuce gida.

Hamrah da take k'ok'arin k'wace hannunta daga na Sulaimana tun da suka fita daga falon ta kasa, motarshi ya wullata ya zagaya ya shige wurin driver ya figi motar sai gidansa, tun kafin su fito take kukan yayi hak'uri amma ko kallonta bai yi ba. Fitarshi daga motar yayi hanyar shiga falo ta tsuguna ta kama k'afarsa tana bashi hak'uri.

Shiru yayi yana kallonta cikin fushi, da abun ya ishe sa fizgota yayi ya shige da ita falo ya wullata bisa kujera ya fara masifa ''wallahi wallahi sai kin fad'a min uban da yake zuga ki kike k'in bin umarni nah. Kuma wai yaushe kika je kika aikata hakan bani da labari? Hamrah haka kika koma?'' Yana fad'an hakan yana kunce belt na jikinsa.

Ta kasa furta komai sai hak'uri da take basa, ciro belt d'insa yayi ya watsa mata d'aya ta saki k'ara yana cewa ''bazaki fad'a min ba sai na zane ki koh? Ai ko babu aure tskaninmu ni yayanki ne zan iya hukunta ki, wallahi in baki fada min ba na lahira sai ya fiki jin dad'i''.

Cikin shesshek'ar kuka tace ''wallahi ranar da Fad'ime ta daki Maryamah naje gidan'' ware ido yayi yana cewa ''da izinin wa kika je? Hamrah dama haka kikeyi kenan?'' Ya k'ara da ''innalillahi wa inna ilaihi raji'un, kin raina ni. Lallai duka ba shi zai hukunta ki ba, wallahi sai kin tafi gida yau, kuma in kinje ki fad'a musu laifinki''.

Yana gama fad'ar haka ya wuce d'aki ya d'auko kud'i ya fito ya watsa mata yana cewa ''ki fice ki bar min gida, in kin koyi hankali sai ki dawo'' Hamrah tana kuka tana rok'onsa amma yak'i sauraronta, shigewa yayi d'aki ya barta anan zaune tana sharb'an kuka. Bai san lokacin da ta d'ibi kayanta a jaka ta fice ta bar gidan ba. Yana zaune a d'aki yana tunanin yanda akayi Hamrah ta koma haka, basu tab'a samun matsala yace ta tafi gida ba sai wannan karon da suke da yara har biyu? Tsaki ya ja da ya tuna yaran na makaranta dole yaje ya d'auko su.

 

 

 

Bayan sati d'aya da faruwar haka:- Abakar da matansa suna zaune lafiya k'alau saidai har yanzu basu sake da juna ba, musamman Maryamah da take bala'in tsoron Fad'ime, wani lokacin har ita ke cewa ''ki saki jikinki, ai nima yayarki ce'' amma duk da hakan tsoron ta take, kuma ko da wasa bata bari Abakar yazo kusa da ita, indai Fad'ime na gidan ta dinga guje masa kenan. Dr. Sulaimana kuma yak'i d'auka k'iran wayan kowa daga gida Damaturu dan bai son ace yazo ya d'auki Hamrah.

Yafi son in ta horu ta dawo da kanta kamar yanda ya fad'awa abokinsa Abakar da yace ''bai dace ka barta ta tafi ba, ka dawo da ita indai akan Maryamah kayi haka komai ya wuce'' shi kuma yace bai yadda ba sai tayi hankali. Kallonsa kawai Abakar yayi bai sake tanka sa ba.

Yau Abakar da iyalinsa sun tashi cikin shirin zuwa Godil kasancewar Maryamah bata tab'a zuwa ba tunda akayi auren haka shima Abakar bai tab'a zuwa ba, yau kimanin shekara bakwai rabon ta da can, taci kwalliya ta ci ado ta sa hijabinta.

Tana fitowa suka ci karo da Abakar da yake shirin shigowa, komawa tayi ya rufe k'ofar yasa makulli yana kallonta, fuskar nan a had'e ba daman tayi rigima. Matsowa yakeyi kusa da ita tana komawa baya har suka isa bango sannan tace ''ni me nayi ne?'' Ya kamo hannunta ya matse sai da ta saki k'ara sannan yace ''babu inda zaki je tunda gudunah kikeyi'' hawaye ta fara zubarwa tana cewa ''ni ba gudun ka nakeyi ba tsoron matarka nakeyi'' matsowa yayi dab da ita numfashinsa na sauk'a akan fuskarta, ita kuwa ta runtse ido tana Allah-Allah ya tafi kada Fad'ime ta gansu a haka. Ji tayi yace ''in munje mun dawo raba kwana za'ayi ma kowa ya huta'' Ya cize mata hanci yana cewa ''ko in gutsire hancin nan gaba d'aya'' turo baki tayi zata yi magana ya toshe da nasa.

K'wank'wasa kofar da akeyi ya bata damar ture shi tana cewa ''ina zuwa Anty'' ta sa kai zata isa wurin k'ofar ya janyota ta fad'o jikinsa, k'ok'arin kwace kanta takeyi yak'i saketa, rantsuwa ta fara masa akan ta yadda a raba kwanan in sun dawo sannan ya k'yaleta ta fice ya bi ta a baya.

Fad'ime ce zaune a gefen mijinta, Mama Zainaba da Maryamah a baya, Zahra k'arama kuma tana gun Mama Zainaba. Maryamah ce ta nuna musu hanyar garin har suka isa k'ofar gidan da misalin k'arfe hud'u na yamma. Maryamah ce ta shiga tare da sallama da murnarta, Amty Babbe ta fara gani a tsakiyar gida tana kwance akan tabarmarta kamar yanda ta saba. Tana ganin Maryamah ta mik'e da murnarta tana cewa ''Maryamah ke ce?''.

Tuni ta fashe da kuka tana cewa ''ashe zan sake ganinki? Kwana biyu Sulaimana bai zo ba nayi ta tunanin ko lafiya ashe kina tafe?'' Ganin su Fad'ime tayi da Mama Zainaba a baya tace ''ashe da mutane kike? sannunku da zuwa sannunku'' ta d'auko tabarma a d'aki ta shimfid'a musu, Maryamah sai kallon gidan take dan ba haka ta barshi ba, abun mamaki sai gani tayi Amty Babbe ta bud'e fridge ta d'auko ruwan sanyi ta ajiye musu, a ranta tana cewa ''wannan aikin waye? Sulaimana?''.

Ta d'auke tunanin suka gaisa sannan ta fad'a mata su waye ne mama Zainaba da Fad'ime. Ita ta shigo da Abakar Amty Babbe ta mik'a masa kujera ya zauna sannan suka gaisa.

Maryamah tasha mamakin Amty Babbe dan yanda take magana kamar tasan komai, harda cewa ''ina miki murna Maryamah''. Ta fad'a musu Sulaimana ne ya sa aka buge gidan nasu aka musu na bulo, d'akuna hud'u da falo da toilet irin na zamani. Sunyi hira sosai sun zagaya gidan sun kalla sannan suka baje a tsakar gida aka cigaba da hira.

Sunyi kwana biyu anan sannan suka wuce Damaturu bayan Abakar ya musu sha-tara ta arzik'i, Amty Babbe harda hawayenta, Ammi Malud ma yayi murna sosai da ziyarar da suka kawo musu yayi musu fatan alkhairi.

Sai da sukayi sati biyu a Damaturu sannan suka tattara suka juyo Kaduna harda Hamrah ba tare da sanin Dr. Sulaimana ba. Da isar su kawai Abakar ya k'irasa a waya yace yana gidansa, shigowarsa ya gansu sun shantake a falo suna hira, gaisawa kawai sukayi Abakar yace ''mu wuce koh'' suka tashi suka fice ko rakiya Abakar yace ya hutar dasu.

Hamrah ta bada hak'uri kuma ta tabbatar masa bazata sake yin abu makamancin haka ba. Dama yayi missing d'inta tuni ya rungume abarsa komai ya sauya. Ranar ba shi ya d'auko yara daga islamiya ba sawa yayi a dawo dasu. Rayuwa mai dad'i suka bud'e cike da jin dad'i.

Kafin dawowar su Abakar ya sa an gyara d'akin da Maryamah zata zauna, ya canja wa kowa kayan d'aki dan ya k'uduri niyyar yin adalci tsakaninsu. A ranar kuwa da dare ya tara su a falonsa yayi musu nasiha sannan aka raba kwana. A wurin Fad'ime ya fara kwana bayan kwana biyu ya koma d'akin Maryamah.

BAYAN SHEKARA HUD'U, Maryamah zaune tare da Zahra tana koya mata karatun islamiya Fad'ime ta fito da yaro a hannunta tana cewa ''Kwaiseh yaron nan naki akwai rigima, wai yaro d'an wata uku har yasan hannun uwarsa, tunda na d'auke shi kuka yakeyi'' Maryamah tayi murmushi sannan ta karb'e shi tana cewa ''Abuyi Halali(babana halaliya na) kenan, ai kunzo a daidai dan mun gama saura na boko zaki koya mata''.

Zahra ta kalli Fad'ime tace ''mama me yasa Anty kwaiseh bata yi min na boko, bata iya ba koh?'' Fad'ime ta janyo ta jikinta tana cewa ''ai kowa da fannin da ya karanta, kinga ni ban iya islamiya ba ita ta iya koh?'' Zahra tace ''naji dad'ina, malamin islamiya ma yana cewa wanda yake koya min karatu malami ne nace masa a'a antyna ne kuma yace na iya sosai dan rannan abinda ya tambaya na bashi amsa wai aji biyar akeyi kuma na bada amsa'' Fad'ime tace ''toh kin gani, babanki kuma in an baki abun gini a school shi zai miki dan civil engineering ya karanta'' Zahra ta tafa hannunta tana cewa ''ni zan zo na d'aya a aji tunda kowa ya iya abunda ake mana a makaranta'' dukansu suka yi dariya. Abakar da yake danne-danne a laptop nasa cewa yayi ''in an koya miki kin iya kenan ko? Dan ba su zasu miki exams ba'' tace ''Abba ai inayi, kuma anty ta sani koh'' ta fad'i hakan tana kallon Maryamah, tace ''eh ai daughter Zahra na da ilimi'' murna ta fara yi tana cewa ''yes'' harda rawarta.

K'arshe.

Alhamdulillah, nagode Allah mai kowa mai komai da ya bani ikon kammala littafina. Inason k'ira ga 'yan uwana mata musulmai, mu rik'i addini kuma mu fifita shi akan duk wani ilimi, in mace batayi boko ba kada ku rainata ku k'ask'antar da ita, tabbas ilimin boko na da anfani a rayuwarmu ta yau amma ku sani ba sai anyi boko ake succeeding in life ba. Duk k'arancin ilimi zai anfaneka watan watarana. I dedicate dis book to all my fellow muslim sisters, i love you all, Allah ya kare mu ya d'aukaka addininmu(ameen)

Godiya ta musamman ga:-

 

Nagarta writers association

 

Na barku lafiya, with bunch of love

 

MaryamerhAbdul

Tags: #shuwa #kwaiseh #romance #soyayya#qaddara
4344
0
3
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!