Kunya Adon Mace!

Written by Firdausi JeebohPublished on 2018-12-17 23:00:02Category Non-fictionTsaye take a gaban faculty of law, a NILE UNIVERSITY ABUJA, wristwatches d'in hannunta ta kalla mai tambarin appl tsaki tasaki alaman kamar an takura mata. wata budurwa ce ta nufota tana washe baki d'aure fuska tayi, murmushu tayi data k'araso wajenta, tace   "am sorry nasan na b'atamaki lokaci wlhi natsaya summiting assignment ne." tab'e baki tayi tace "Hamida kin b'ataman rai dakin tarar da nayi tafiyana akanmi zaki b'ataman lokaci kinsan dana gama lecture burina naje naga Ammi nah." Dariya tayi tace "Aysaah yar gidan Ammi yanzu dai mutafi.." Wajen motarta ta nufa mai k'irar BMW i3 . tags: #kunya #Ado #feedohDuba was labarai »

KUNYA ADON MACE


  Phirdaucee Jeeboh 


BABI NA UKU


  Zaune take tana ta shafan wayanta tana murmushi, takai 20mnts tsaye amma batasan tana wurinba tsaki tayi ta fizge wayan d'agowa tayi da masifa tace

“Hanifa miye haka? ina ruwanki da wayana?.”

hanifa tayi tsaki

“ke dai Aysaah sai kin gyara tun yaushe nake wurinnan amma bakisan nazo ba gaba d'aya hankalinki yana kan photo ina amfanin haka Allah idan bazaki gyara ba sai na gayama Ammi.”

Jin an ambaci ammi tace

“Haba my bestie miye kuma har sai kin gaya ma Ammi kina san asirina ya tonu.”

Murmushi Hanifa tayi ta samu wuri ta zauna dafa ta tayi tare da fad’in

 “Aysaah ina da shawaran da zanbaki.”

Gyara zama Aysaah tayi tana fad’in

“Ina jinki bestie.”

“Why not kisame shi ki gaya mashi kina sanshi.”

Zaro ido Aysaah tayi

“ in fad'a mashi fa kikace?”

D’aga kai Hanifa tayi tace 

“I mean it.”

Girgiza kai Aysaah tayi

“Kada Allah ya kawo ran da zance ina san namiji shin kin mance karin maganan hausawa da suke cewa KUNYA ADON MACE yanzu na sameshi nace ina sanshi taya zai d'aukeni banda kunya kenan, zan cigaba da dakon sonshi har sai ran da, da kanshi yace yana sona amma nikam I can't idan ma ammi nah taji saita yi fushi dani.”

Tab’e baki Hanifa tayi

“Shikenan dama shawara ce nabaki tunda kink'i d'auka muje kawai.”


    Tsaye take kitchen tana d'auraye kayan da tayi girki dasu wani k'amshi taji wanda bazata iya mantawa da shi ba aranta tace

“Ya salman har nafara mafarkin turarenka.”

 Takowa akayi akazo bayanta jin k'amshin yak'a k'aruwa yasa ta juya ganin wanda yake tsaye yana mata murmushi yasa ta saki baki idanuwanta ta murza kana ta bud'e ganin ba mafarki baneba yasa taje da gudu ta fad'a jikinshi shiko ya rungumeta cikin siririyan muryanta tace 

“Ya Salman kaine?”

Murmushi ya yi 

“Nine my baby doll.”

shagwab'a ta farayi mashi

“Ni gaskia nayi fushi, shine kak'i gaya muna yaushe zaka dawo.”

 Salman yace 

?Sorry my baby doll so nake nayi surprise d'inku shiyasa amma on mah kneels bazan k'araba.”

za tayi magana ya d'aura hannunshi kan lab'b'anta yace 

shhhhhhh don't say anything.”

murmushi tayi yaja hannunta sukayi d'akin Ammi..

          

 Suna shiga d'akin Ammi Aysaah ta fara ihu duk tabi ta cika gidan tafiya tayi ta fad'a kan Ammi 

“my babe karki karyani.”

 zumb'uro baki Aysaah tayi tace 

“Ammi nah duka nawa nake.”

dariya Dalman yayi

 “Kunfi kusa.”

Abinda yace kenan, 

“Aysaah shiyasa kuke fad'a da Mummynzarah saboda ihunki.”

zumb'uro baki tayi tace 

Ammi kinajinshi.”

“ Salman ka kiyayeni ka dawo kenan zaka saman baby gaba duk yanda tayi missn d'inka amma daga dawowan ka zakasa tarame.”

 Murmushi yayi yana fad’in 

“Ayi hak'uri Ammi nd mummy's pet.”

Dariya Ammi tayi su kaci gaba da hira Aysaah tace 

“Ya Salman ina tsarabana?”

Salman yace

 “Tsarabanki na nan my baby doll.”

Haka dai sukaci gaba da fira, Salman na basu labarin rayuwan school na dariya suyi dariya na tausayawa su tausaya, basu ta shiba sai da aka kira magrib kana kowa ya mik'e dan gabatar da farali..


  Sun had'u daining suna cin abinci Mummy ta duba ba taga Salman ba Mummynzarah tace 

“Zaah tashi ki kira yayanku yazo yaci abinci.”

Kafin ta tashi Salman yace 

“Mummynah gani nan.”

murmushi tayi tace 

“naga banganka bane ba.”

Wuri ya samu ya zauna da kanta Mummynzarah ke serving d'in Salman sai data zuba mashi wadatacce kana ta koma ta zauna, Salman yace 

Thank you so much my mummy.”

murmushi tayi tace 

“Your welcum my son.”

Suna gama cin abinci Salman yace 

“Nifa zan afi na kwanta bacci na keji.”

Mummynzarah tace 

“ay yakamata.”

Dayake daddy yayi tafiya, Aysaah tayi narai narai da fuska tace 

“Bro tsarabana fa?”

Mummynzarah tace 

“sai kizo ki kwata.”

Murmushi ya yi Ya shafa kanta yace 

“afuwan my baby gobe zan baki kinji.”

d'aga kai tayi alaman 

“to.”

Harara Muummynzarah ta wurga mata jawota Ammi tayi jikinta tace 

“kyalesu my babe su suka sani.”

dariya yayi yawuce d'akinshi...


Yana tafiya itama ta kwashi wayoyinta tama Ammi saida safe, Ammi tace 

“Allah ya kaimu my baby u make sure kinyi adua kinji.”

d'aga kanta tayi ta wuce ko kallon inda Mummynzarah take bata yiba dan tasan suna had'a ido zata wurga mata harara tana hayewa sama tayi shirin kwanciya kit d'inta tajawo ta d'auko hoton tana dubawa murmushi ta keyi tace 

“Inama zakasan irin sanda nake maka da ka tausayaman inama kazama uban yayana da nafi kowa murna.”

Hawaye ne suka wanke mata fuska share hawayen tayi ta mai da hoton ta kwanta tayi lamo har bacci ya d'auketa.


Nasan masu karatu sun matsu suji waye wannan da Aysaah ta mutu kanshi dan da Alama shi baima san tana yiba to nima dai har yanzu nakasa samo amsar amma kudai cigaba da bina zakuji waye wannan saurayin....

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


  Phirdaucee Jeeboh 

 

BABI NA BIYU


  Suna isa gida ana kiran magrib ko da suka shiga parlor ba kowa sama suka haye kowa tayi d'akinta Aysaah na shiga d'aki tayada jikkarta kit d'in naga ta d'auko ta bud'e pic d'in ta d'auko tana kallo tana murmushi yanda tadamu da hoton nan ko kanta bata damu dashi ba da sauri tayi hanyar toilet, Alwalla tayo ta gabatar da magrib tana gamawa tafara karatun alk'urani cikin muryanta mai dad'in sauraro bata tashiba sai da tayi isha wanda dama al'adanta ne idan tayi sallahn magrib bata tashi saitayi ishaaa.


K'asa ta nufa wajen iyayenta daining area tasamesu da murmushi ta isa wajen. wani dattijo naga ta nufa wajenshi tana murmushi peack tamashi tana fad’in

“papa i miss u.”

rungumota yayi yace 

“I miss u more my baby.”


Hararanta Mummyn Zarah ta farayi kumbure fuska tayi tace 

“Papa Ammi na kunga mummyn Zarah na harara na?”

 Dariya Ammi tayi tace 

“come here my babe kyale Mummyn zarah.”

papa yace 

“Waimi yasa kikesan matsama dota ne?”

Tab'e baki Mummyn Zarah tayi tace

“ ai naaga tab'aran yarinyar nan sai k'ara gaba yakeyi.”

murmushi Ammi tayi tace 

“haka dai kika gani.”

kujera Aysaah taja ta zauna Ammi ce ta zuba mata tuwon shinkafa miyan agushi, saikuma pepper soup d'in kayan ciki Aysaah tace 

Thank you so much my Ammi.”

kumatunta Ammi taja tace 

“Your welcum my babe.”


Tana gama cin abinci tama iyayenta saida safe ta haye sama sai da tayi shirin bacci kana tajawo wayanta tafara chrtn tana chrtn tana murmushi da alamun tanajin dad'in firan datakeyi 10:30pm ta aje wayanta adu'o tayi kana taja bargo.

Aysaah bata farka ba sai asuba tana yin sallan Asuba tayi azkar ta koma ta kwanta, bacci take mai dad'i bata farka ba sai 12:00pm da yake yau weekends ne tana tashi ta shiga toilet tayi wanka light makeup tayi taje gaban wardrop abaya ta d'auko maroon ta saka ita kanta tasan tayi kyau tana gama shiryawa tayi hanyar parlor.


Tana sauka wata kyakyawar yarinya ta taho da gudu ta rungumeta duk'awa tayi ta mata peack tace 

“Basma nah kintashi lafiya?”

Basma tace 

“lafiya lau unty.”

aysaah tace 

“Inasu zarah?.”

“Suna d'aki”

 Gyad'a kai tayi ta tashi tayi hanyar d'akin Mummyn Zarah, da sallama ta shiga amsa mata akayi zama tayi nesa da ita ta gaishe ta 

“Mummyn Zarah ina kwana”

A dak'ile ta amsa da

“Lafiya.”

Abun bai dameta ba tun da dama haka take amsa mata....


Tashi tayi ta nufa d'akin Ammi da gudu ta shiga fad'awa tayi kanta d'agota Ammi tayi tace 

“Zanso naga sanda zaki hankali k'ila saina maki aure.”

Dariya 

“Haba Ammi nah kingaji dani kenan?”

Murmushi ammi tayi 

 “Ina zangaji da baby nah”

gaidata Aysaah tayi amsawa tayi cikin kulawa fira suke yi cikin so da k'auna Ammi ta kalli Aysaah 

“Dota nah bataci abinci ba oya tashi kije kici.”

Tashi tayi

“Angama my Ammi.”

 peack Ammi tamata tace 

“I lurv u my baby.”

“I love you more my Ammi.”


      Sai da taci ta k'oshi kana takoma parlor tana zama sai ga Basma tace 

“Unty assignment zaki mun.”

“ olryt.”

amma kiramun su zarah suma nasan zasuyi wasu kyawawan yanmata suka fito gaba d'aya su kace 

“Unty Yssaah good morning.”

aysaah ta amsa

“Morning.”

“Zarah Rahma Samir ku d'auko assignment d'inku.”

Tafiya sukayi suka d'auko sai da tamasu assignment su duka kana ta tashi takoma d'akin Ammi.


 Tana shiga tafad'a kan Ammi tana shagwaba itako Ammi sai biye mata ta keyi, Aysaah ta d'ago tace 

“Ammi wai yaushe Ya Salman zaidawo?”

Murmushi Ammi tayi tace 

“wlhi yak'i fad'aman wai surprise d'inmu zaiyi.”

murmushi Aysaah tayi tace 

“inaji ajikina yakusa dawowa.”

 “Yayi yar gidan Salman.”

 Dariya tayi tak'ara lafewa jikin Ammi..

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


   Phirdaucee Jeeboh 


Bismillahir rahmanir rahim


Wannan labarin yafaru ne true life story ne sai dai zan k'ara wasu abubuwan kuma zan rage wasu yanda labarin zai tafi dai-dai.


BABI NA D’AYA  Tsaye take a gaban faculty of law, a NAIL UNIVERSITY ABUJA, wristwatches d'in hannunta ta kalla mai tambarin appl tsaki tasaki alaman kamar an takura mata. wata budurwa ce ta nufota tana washe baki d'aure fuska tayi, murmushu tayi data k'araso wajenta, tace 

 “am sorry nasan na b'atamaki lokaci wlhi natsaya summiting assignment ne.”

tab'e baki tayi tace 

“Hamida kin b'ataman rai dakin tarar da nayi tafiyana akanmi zaki b'ataman lokaci kinsan dana gama lecture burina naje naga Ammi nah.”

 Dariya tayi tace 

“Aysaah yar gidan Ammi yanzu dai mutafi..”


  Wajen motarta ta nufa mai k'irar BMW i3 suna shiga tama motan key sai da suka hau titi sosai Haneefa tace 

“waini kam Aysaah yaushe Salman zaidawo?” 

wani murmushi tasaki wanda ita ka d’ai ta san ma’ana shi

“Ni kaina bansani ba amma d'azu naji suna waya da ammi maybe yakusa dawowa.” 

daga nan babu wadda tak'ara cewa komai.

Aysaah ta kalli Haneefa dake ta faman chrtn tace 

“Madam gida zaki?”

Haneefa tace 

“No maitama stores zaki ajeni daganan zan d'auki drop ya kaini gida idan nagama abinda nake.”

“Shikenan.”


Tana ajiyeta a maitama stores ta d'auki hanyar gidansu dake missippi gaban wani ash gate ta tsaya horn tayi mai gadi ya wangale mata gate hancin motanta ta saka ciki parking space tasamu tayi parking saida ta tabbatar ta kulle ko Ina kana tayi cikin gida tana kwalama Ammi kira. Ammi na dawo parlor ta samesu zaune fad'awa tayi jikin Ammi tana 

Ammi bakijina shine kika kyaleni.”

rungumeta Ammi tayi tace 

Yi hak’uri my one nd only banji ba.”

Tsaki sukaji anj Ammi tace 

hajiya lafiya?”

“inafa lafiya kalli yanda kika lalata yarinyar nan.”

Aysaah tace 

Mummyn zara waimi namaki haka?”

uwaki kikaman.”


    Dariya Ammi tayi tace 

“ai mana hak'uri hakanan, oya my dota tafi kici abinci kiyi sallah saloon zamuje nagaji da ganin kanki babu gyara.”

Dariya Aysaah tayi tana fad’in 

“Angama Ammi na.”

peack tama Ammi kana ta nufi upstairs. tanajin mummyn Zarah na masifa amma bata bi ta kanta ba..


Tana shiga d'akinta ta jefar da jikkanta wani kit naga ta jawo bud'eshi tayi ta d'auko wani envelope tana bud'ewa hoto yafad'o d'auka tayi ta kalli pic d'in tana smile, kiss tamashi kana ta tashi toilet ta fad'a shawa ta sakarma kanta sai datayi wanka kana ta d'aura alwalla tana fitowa ta tada sallah tana idarwa tayi adu'oi kana ta dawo gaban dressing mirror light makeup tayi tasaka turare, gaban wadrop taje rig da wando ta jawo black nd red sakawa tayi ta d'auko kimono ta d'aura kan Kayan Masha Allah tafito sak balaraba kallon kanta tayi ta saki murmushi dan tasan tayi kyau scarve ta d'auko tayi rolling kanta turaren rasasi ta feshe jikinta dashi gaban shoe rack d'inta taje Gucci ta jawo, black tasaka handbag d'intama ta Gucci, kallon kanta tayi murmushi tasaki kana ta nufi k'asa..


      Tana sauka sisters d'inta suka fara wow unty Aysaah kinyi kyau dariya tayi tace 

“tnx my pikins.” daining area ta nufa zama tayi taci abinci sai da ta tabbatar data k'oshi kana tanufa d'akin Ammi tana shiga tafara ihu Ammi na shirya kifito.

“ karki fasaman kunne ganinan.”

dariya tayi ta ce 

toh my Ammi of life.”


Suna isa saloon aka wanke mata kai steaming aka mata kana aka mata pedicure ana gamawa suka d'auko hanyar gida juya kan sitiyarin tayi kallonta ammi tayi

“ Ina kuma zamu?”

murmushi tayi

“Chicken capitol zamu shawarma zansiya.”

“Okay 

Suna isa tayi order basu fi minti talatin ba aka sallamesu hanyar gida suka nufa suna fira cikin so da k'auna...

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


  Phirdaucee Jeeboh BABI NA HUD’U


  Tunda tayi sallan asuba bata koma ba saboda tana da lecture 8 gashi kuma Ya Salman yana gida dan idan tana gari itake had'amashi abinci tama riga data saba, bayan tagama shirya mashi abinci ta koma d'akinta ta shiga wanka tana fitowa wanka light makeup tayi saboda batasan tarkace, abaya ta d'auko pink ta saka kana tayi rolling kanta da scarves shima pink hand bag d'inta da shoe d'inta duk na Aldo ne, gaskia Aysaah tasan gayu k'asa ta sauka a gurguje tayi break fast saboda ta kusa makara d'akin Ammi ta shiga tamata bankwana takamo hanya tafito...

       

Tana shiga d'akinshi ta iske yana waya sauri yayi ya katse wayan tasowa yayi yace 

“Wow my babe kinyi kyau.”

murmushi tayi tace 

“tnx bruh.”

“sai school?”

“eh.”

 d'aga kanshi yayi yace 

“ina abinci nah?”

“ yana kan daining kasan bazan iya fita ba ban had'ama breakfast ba.”

hancinta yaja yace

“ I knw sis datz y I lurv u.”

murmushi tayi tace 

love you more bro.”

agogonta ta kalla tace 

“Zanfa makara bari naje.”

“ ki kula da kanki kinji lil sis.”

“ l'll my bruh.”

ta juya ta tafi...


    Tunda taje school bakinta yak'i rufuwa Hanifa ta fahimci haka sai da suka gama lecture Hanifa tace 

“waini Aysaah ya dai yau naganki cikin nishad'i ko dream guy d'in naki ne yafad'a maki yana sanki?”

murmushi tayi tace 

“Da nafi kowa son haka Ya Salman ne fa yadawo.”

Hanifa tace

“ iyeh ashe shiyasa naganki cikin annashuwa fav bruh yadawo.”

murmushin ta k’ara fad’ad’awa

“ ke dai bari bestie.”

Haka dai suka gama lectures d'insu har suka dawo gida....


 Tana shiga parlor ta fara ihun nata tana Ammi nadawo parlor ta iskesu zaune fad'awa tayi kanta tace 

“Washhh my Ammi yau nagaji dayawa.”

d'agota Ammi tayi tace 

“karki karyani.”

lafewa tayi jikinta

“ Ammi dukafa 18yrz gareni taya zan karyaki.”

Tsoki Mummynzarah tayi 

“wlhi duk keke lalata yarinyar nan kullum da sabuwan iskancin da zatazo dashi.”

Ammi tace 

waini kam Mummynzarah mi yarinyata tamaki haka? Ba damar yarinya ta sake sai kifara k'orafi gaskia nagaji bansamaki idanuwa a yaranki nima kibarman yarinyata ta wala.”

Tana kaiwa nan taja hannun Aysaah su kayi cikin d'aki. Suna shiga d'aki Aysaah tace 

Ammi ina ya Salman?”

“Yaje gidan frnd d'inshi amma nasan yanzu gab yake da gida.”

Aysaah tace

“shikenan bari naje d'aki.”


    Tana shiga d'akin ta aje handbag d'inta kit ta bud'e ta d'auko hoto kallon hoton take tana shafawa a hankali ta fara magana 

“inama kanaji na inama kasan irin sanda nake maka na tabbata da kasoni Allah kasa kazama mijina uban yayana.”

hawayen da suka gangaro matane ta share sallama akayi sauri tayi ta b'oye pic d'in shigowa yayi yace 

“lilsis dama kina nan kika barni inata nemanki.”

Sorry brother mee bansan kadawo ba na tambayi Ammi nah tace kaje gidan frnd d'inka.”

zama yayi yace 

“Eh can naje.”

fira sukeyi sosai cikin firan Salman yace 

“baby doll bani labarin boyfrnd d'inki.”

 sadda kai tayi k'asa tana hawaye d'agota yayi yace 

“to miye na kuka danna ce kiban labarin surukina.”

share mata hawayen yayi yace 

“to shikenan bazan k'ara tambaya ba.”

murmushi tayi tace 

“bruh ban dashi for now amma maybe gaba nasamu.”

 “Eyyah karki damu my babe in shaa Allah ryt one na nan zuwa kinji.”

D'aga kanta tayi

“Muje kiban abinci yunwa nakeji kinji.”

d'aga kanta tayi ta tashi suka fita.....


Yana gama cin abinci ya dube ta 

“muje ki amshi tsarabanki.”

da murna ta bishi d'akinshi akwati guda Ya ajemata tana bud'ewa taga abaya da kimono dayake dama batada abun sawa sai abaya ga kuma takalma da jikka sai wata sark'a English gold fad'awa tayi kanshi tana murna

“Thank you so much bruh.”

d'agota yayi

 “Bansan godiyan sister na komi namaki kin cancanci haka kinji.”

d'aga kai tayi tamashi peack taja akwatinta tayi sashen Ammi dashi tana kwalama Ammi kira murmushi ya yi yace 

“zanso naga san da Aysaah zatayi hankali.”

tana shiga d'akin Ammi taci karo da ita zata fito Ammi tace 

“babynah lafiya kikeman wannan kiran?”

 murmushi tayi tace 

“Lafiya lau muje kiga tsarabana.”

zama Ammi tayi taga kaya Ammi tace 

“eyyeh lallai Ya Salman Ya kyauta mungode sosai.”

fad'awa tayi kan Ammi tace 

“Ammi inasanki.”

shafa kanta ammi tayi

 “Nima inasanki dota nah tashi kikai kayan d'akinki.”

tashi tayi taja akwati ta wuce d’akinta..

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


BABI NA BIYAR


  Tana shiga d'aki ta aje kayan wayanta tajawo ta shiga gallery pic d'in wani kyakywan saurayi take kallo.

“Da kasan irin sanda nake maka da kazo da sauri wajena naso ace yanda nake sanka kaima haka kake sona inama zan iya gayama abinda ke cikin raina watak'ila da kasoni saidai KUNYA ADON MACE bazan tab'a fad'ama ba har sai san da da kanka kace kana sona.”

Fad'awa tayi kan gado tana kuka sosai kamar zata fidda ranta da haka har bacci yayi gaba da ita.....

         

Koda ta farka idonta ya kumbura saboda kuka wanka ta shiga tana gamawa tayi alwalla tana fitowa ta shafa humra sai body spray jallabiya ta saka kana ta kabbara sallah bata tashi daga inda take ba sai da tayi isha tagama kaima Allah kukanta kana ta tashi ta sauka k'asa wajen iyayenta.


Ganin mahaifinta parlor ya bata mamaki da gudu ta isa wajenshi ta fad'a kanshi tana dariya 

“Papa yaushe kadawo shine bansani ba.”

Kumatunta ya shafa

“My dota tun d'azu na dawo kuma na lek'a d'akinki naga kina bacci shiyasa na kyaleki.”

duk abinnan da akeyi hankalin Ammi nakan Aysaah Ammi tace 

“My babe zo nan.”

tashi tayi taje kusa da Ammi, dubanta tayi cikin kulawa 

“kuka kikayi?”

D'agowa tayi a razane

 “Ah ah.”

Murmushi ammi tayi

 “Gashi k'arya bata dace dake ba infact bakima iya ba saboda duk kin kama kanki oya tell me the truth miya saki kuka har idonki ya kumbura karkiman k'arya.”


“Ammi cikina yayi ciwo shinefa.”

“Miyasa baki kirani a waya ba?”

 “Ammi forgive me pls bazan k'araba.”

 “Shikenan mutafi na baki magani.”

da sauri Aysaah tace 

“Nasha.”

 “shikenan. Allah ya k’ara Lafiya.”

“Ameen.

Ta amsa dashi.


Zaune suke saman dainning table suna cin abinci Pap yace 

“My boy kafa k'ara fari da kyau.”

murmushi Salman yayi

 “Pap yanayin k'asar danaje ne haka.”

Ammi tace 

“Shiyasa zan kai d'iyata can tayi masters.”

dariya akayi gaba d'aya 

Salman yace 

“Ppa inasan naje kaduna gobe.”

yana da kyau haka amma yaushe zaka dawo?”

 Banwuce 1week.”

“Allah yakaimu.”

“Ammi nah zanbi ya Salman.”

 “My baby kibar karatun naki ina?”

Kumbure fuska tayi tana kuka ita adole saita bishi jawota ya yi yana lallashi 

“Haba my baby doll kiyi hak'uri ki zauna nima fa duka sati guda zanyi kinji ni da nakesan kizama babbar lauya yanda dana jawo fad'a olrdy lil sis d'ina zata kareni.”

dariya ta dingayi haka dai suka dinga fira har lokacin bacci yayi kowa yatafi ya kwanta.....
      Tunda tayi sallan asuba takasa komawa ta rasa abinda ke mata dad'i kodan yayanta zaiyi tafiya ne oho? 9:00am ta sauko k'asa cikin shigar k'ananan kaya wanda sukayi matuk'ar karb'anta kitchen ta wuce dan had'ama ya salman breakfast tana gamawa d'akin Ammi tawuce bata sameta ba, saboda tana sashen Papa k'arfe 11:00am ya Salman ya gama komai wajen motarshi ya nufa da gudu tazo tafad'a jikinshi tana kuka, Aysaah tace 

“Dan Allah bruh karka tafi kabarni.”

d'agota yayi ya share mata hawaye 

“Kiyi hak'uri lilsis nima bada san raina zan tafi ba dan dai tafiyan yazama dol kinji my baby.”

d'aga kanta tayi yace 

“To share hawayen.”

Ba musu ta share hawayen 

“good girl.”

peack ya mata a goshi kana ya saketa ya shiga motarshi d'aga masu hannu ya keyi harya bar haraban gidan fad'awa tayi kan Ammi tana kuka janta Ammi tayi sukayi cikin gida tana aikin lallashi..Tunda suka shiga gida Ammi ke aikin lallashi da nasiha amma Aysaah kuka take yi har takai ga Ammi tamata fad'a shine fa aka samu tayi shiru rannan Aysaah sukuku tayini har dare abun yana damun Ammi sosai saboda bata san taga d'iyarta cikin damuwabyau ko abincin dare k'inci tayi tana gama sallah ishaa ta rufe d'akinta Ammi tazo tayi bugun k'ofan amma tak'i bud'ewanhoton dream guy tajawo tana kallo tana surutu ga kuma hawaye daketa bin kuncinta.......

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


BABI NA SHIDA


ASALIN LABARIN


   Alhaji Sadiq shine mahaifinsu Asalin shi d'an k'auyen katsina ne bugaje anan yayi makarantarshi firame da secondary bayan yagama ya tafi ABU zariya ya karanta civil engineering bayan yagama karatunshi yadawo gida anan iyayenshi suka aura mashi Safiyya wadda d'iyace ga liman d'in garin, daga nan yasamu aiki a abuja ya tattara iyalanshi ykoma Abuja da ita shekara shidda Allah bai bata haihuwa ba abun ya dameta sosai shiko bai damu ba saboda yasan yin Allah ne asibiti sunje kuma antabbatar masu lafiyansu lau su duka, ita tamatsamashi ya k'ara aure amma yak'i amincewa har fad'a sukayi.

Daga k'arshe dai ya amince yana wata kwangila a kaduna Allah ya had'ashi da Nafisa suka daidai ta kansu nan aka sha biki itama ta tare gidanta Abuja itama shiru shiru bako b'atan wata har aka shekara ya fara zargin kanshi da shine bai haihuwa aa cikin haka Allah yaba Safiyya ciki zo kaga murna wajen iyalan Alh Sadiq har dai Nafisa sai kace ita keda cikin saboda irin zaman lafiyan da sukeyi zaka rantse da Allah ba kishiyoyi baneba wata tara chur Safiyya ta Haifi santaleliyar d'iyarta mace san kowa k'in Wanda ya rasa zokaga murna wajen wannan family rannan suna yarinya taci sunan Aysaah bayan suna gaba d'aya renon Aysaah ya koma wajen Nafisa komai nata wajenta yake idan kaganta wajen Safiyya toh nono za tasha.


Bayan haihuwar Aysaah da shekara hud'u Allah ya sake ba Safiyya ciki ta haifi zarah, ba'ayi arba'in ba itama nafisa tasamu nata rabon wata tara ta haifi Rahma daga nan haihuwar ta bud'e mata ta k'ara haihuwar Sameer sai yar autarsu Basma daga nan babu wadda ta sake haihuwa cikinsu Alh Sadiq yaba yaranshi tarbiya da ilimi dai-dai gwargwado kasancewar Aysaah yar fari yasa Safiyya bata janta ajikinta idan ba anfad'a ma mutum cewa Safiyya ita tahaifi Aysaah zaka d’auka Nafeesah ta haifeta.


Aysaah ta sakama Safiyya Mummynzarah saboda tace bata kula da ita sai zarah take so ita kuma Nafisa Ammi dan tace Nafisa ce mamarta yanzu haka Aysaah shekararta 18 tana karatu a nail university Abuja inda take karanta law tana year 1 su kuma Zarah da Rahma na js3 sameer na js1 Basma na primary 4.

Aysaah irin matannan ne da ake kira coca cola saboda shape d'inta gata fara ga dukiyar Fulani Allah yabata sometimes mutane na danganta kyan Aysaah da rani mukraji idan Aysaah tayi dariya zaka rantse da Allah rani ce maza na kawo mata hari a school a kan hanya amma ko kallonsu batayi saboda anata cewar zuciyarta ta riga ta mallakama dream guy d'inta wanda ita kad'ai tasanshi.

       

WAYE SALMAN?

 Salman d'an sister Ammi ne su biyu ne wajen iyayensu daga mamar Salman sai Ammi tun suna yara iyayensu suka rasu sun sha wahalar duniya wajen kishiyar uwa har Allah ya kawoma mamar Salman hajia binta miji tayi aure koda tayi aure bata bar Nafisa ba da ita ta tafi acan kaduna tayi makarantartabwatan hajia binta goma da aure Allah yabata haihuwa inda tahaifi santalelen d'anta ranan suna aka sakamashi Salman.

Tun Salman yana jariri komi nashi Ammi keyin shi ko daya ya girma shak'uwa mai k'arfi tashiga tsakaninsu bai da abokiyar shawara sai Ammi daga nan hajia Binta ta sake haihuwa ta haifi d'iyarta mace aka saka mata Mufeeda.

Lokacin da Ammi za tayi aure da kyar aka raba Salman da ita sun ba kowa tausai har asibiti ya kwanta daga k'arshe dai aka tambayi mijinta yace bakomai amaidoshi shima ai mai rik'e Salman ne mafarin dawowar Salman kenan gidansu Asaah...


       Tun dawowar Salman gidansu Aysaah renonta ykoma hannunshi komai yasamo baby doll sai da ta girma tasan ba d'an gidansu bane ba amma shak'uwarsu kullum k'aruwa take lokacin da zai tafi England karatu da kyar aka rabasu tunda ya tafi tadawo shiru shiru abun har yafara damun Ammi itako Mummynzarah ba ruwanta harkanta takeyi da sauran yara dakyar Ammi tasamu Aysaah tasake.

        

Tunda Salman ya tafi karatu Aysaah take fama da tunaninshi kullum saita kalli pics d'inshi take samun sauk'i tun bata gane sanshi take ba harta gane sanshi take ran da tagane tayi kuka babu wanda yasan tana san Salman sai bestie d'inta Haneefa, kuma ta d'aukarma kanta alk'awarin bazata tab'a gaya mashi ba saboda ita macece kuma ansan mace da kunya zata dinga renon sanshi har sai ran da ya gane da kanshi idan kuma bai gane ba sai dai ta mutu da sanshi kuma baza tab'a aure ba.

Tun da Aysaah ta gane san Salman take tayi alk'awarin k'ara kyautata mashi kuma pictures d'inshi su suka zama abun kallonta safe dare da rana su kad'ai ke rage mata damuwa da kuma kewar masoyin nata.....


To masu karatu kunji wacece Aysaah kuma kunji waje dream guy d'in nata....

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


BABI NA TAKWAS


  Haka dai Haneefa ta dinga jan Aysaah da fira harta samu ta sake suna gama lectures suka nufo wajen mota wani guy ne ya kafa mata ido tunda suka fito yake kallonta sam hankalinta bai kai gashi ba amma Hanifa tana kallonshi suna isa wajen mota takowa yayi yazo wajensu sallama yamasu Hanifa ta amsa dan Aysaah ko kallonshi batai ba, murmushi yayi yace 

my name is Asad.”

murmushi hanifa tayi tace 

“Nice name”

 murmushi yayi yace 

“yanmata kufa?”

Hanifa tace 

“my name is Hanifa.”

“Nice name.”

 what of ur frnd?”

 “Aysaah”

“Wow what a nice name, amma ita bata magana ne?”


Mota tas hige tana fad’in 

“Idan kin gama surutun kizo mutafi.”


 Murmushi tayi 

“am comming pls Aysaah.”

“Amma frnd d'inna taki tamun tun da kuka taho naganta wlhi taman.”

Murmushi hanifa tayi 

“Aiki ja amma taimako d'aya zan maka ka dinga bin mu abaya dan kaga gidansu toh sauran fight d'in nakane.”


Murmushi asad yayi

 “Thank you so much sis.”


Tana shiga motan Aysaah tafara masifa ita dai batace mata komai ba Hanifa tace 

“Aysaah ki dinga sama ranki salama shin kinsan waye wannan da zaki mashi haka?”

 “To mi nayi mashi?”

 

abinda tace kenan murmushi tayi

 “Yanda yake maki magana kika shareshi toh shima masoyinki ne saboda yace sanki yake kuma ba san wasa ba.”

tab'e baki tayi tace 


“kunji dashi ku duka yanzu ina zamu?”

“mu wuce gidanku anjima natafi gida.”

Haka kuwa akayi suna tafe Asad nabin su amma bata saniba harsuka isa gida yana ganin gidansu yayi ajiyar zuciya yajuya yatafi......

         

Yana shigowa gida parlor ya iske Mammy da far'anshi ya isa wajenta kanshi ya d'ora bisa cinyarta shafa kanshi tayi tace 

“Salman yaushe zaka girma?”

 

Murmushi yayi

 “Mammy ai bazan girma ba in dai kina nan.”

shafa kanshi tayi


“Sai ran da namaka aure.”

 dariya yayi Mammy tace 

“Wai ina labarin Aysaah?”


 Dariya yayi har kumatunshi suka lotsa

 “Mammy baby doll fushi take dani tun da na taho tak'i d'aukan wayana.”

“Aysaah rigima.”


“Waini banga my love ba.”

 “Taje gidan frnd d'inta namanta dan tace kaje kad'aukota.”


“Mammy miyasa bata fita da motarta ba?”

“Nima bansaniba.”


Tsaki yayi yace 

“ga driver d'inta ko Allah mufeedah tarainani.”

dariya mammy tayi

 “Kunfi kusa nidai ga address tace na baka karb'a yayi.”

“Yanzu zan d'aukota.”

 tashi yayi yanama Mammy sai yadawo....Yana isa gaban gate d'in gidan yamata waya yace gashinan yazo minti biyar sai gashi sun fito tunda suka nufoshi yak'ura mata ido suna k'arasowa cikin siririyan muryanta ta gaidashi jiyayi baitab'ajin murya mai dad'in taba amsawa yayi cikin sakin fuska Mufeedah tace 

“Ya Sallman k'awatace sunanta Sahr.”

“Sannu Sahr.”

 “Sahr wannan shine ya Salman wanda nake baki labari one nd only bruh d'ina.”


Murmushi tayi wanda yak'ara mata kyau tace 


“nice meeting u our bruh.”


murmushi yayi yace 

“Same dear.”


Mufeedah ta kalli Sahr 

“Bestie toh mu zamu wuce.”

”kamar karku tafi.”


Dafa kafad'anta Mufeedah tayi tace 


“Dont worry bestie zan dawo.”


Salman yace 

“Sis kiban number inki dan yanzu nayi new sis.”


Murmushi tayi tace 

 “To bruh.”

Exchanging contact sukayi kana sukayi bankwana suka tafi....


BAYAN KWANA BIYU

Soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin Salman da Sahr kullum suna mak'ale a waya abin ba k'aramin d'agama Mufeedah hankali yayi ba saboda ita kanta tagano Aysaah nasan Salman sai dai bata fad'ama kowa ba dan haka itama bata fad'aba ta dai dinga tayata da adua mak'ale yake da waya suna firan soyayya Salman yace 

“Swthrt inafa da k'anwa.”


 ”Banda mufeedah?”


“Yeah akwai Aysaah she's my favorite sis inaji da ita komi take so inaso nagaya makine dan kisani karki shigo gidana kiga sabon al'amari.”


“Karka damu my Man zan tayaka san abinda kakeso.”


“Thank you so much my future wife in Shaa Allah nakoma Abuja zan had'aku.”

“shikenan my Man haka dai sukaci gaba da firan soyayya kamar karsu rabu da juna sukeji....


WACECE SAHR?

Sahr d'iyace ga senetor Basheer modibbo ita kad'aice wajen iyayenta yar gatace gaba da baya Sahr kyakywace ajin farko sai dai ko kusa bata kamo k'afan Aysaah wajen kyau ba k'awance su yasamo asaline ita da Mufeedah tun suna secondary har gashi yanzu suna jami'ah aji d'aya shekarunta bazasu wuce 17yrs ba duk family d'inta yanzu kowa yasan Salman saboda irin san da take mashi.....


TURK'ASHI

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh BABI NA TARA 


  Kwance take d'aki tana kallon pic d'in Salman ga hawaye na bin kuncinta k'arar bugun k'ofanta ne yasa tayi saurin b'oye pic d'in ta nufa bakin k'ofa tana murza ido kamar mai bacci bud'ewa tayi Ammi tagani tsaye tana murmushinrab'ata Ammi tayi ta shige d'akin biyo bayanta tayi tasamu wuri ta zauna kallonta Ammi tayi tace 

“My baby bacci kikeyi?”


D'aga mata kai tayi alamar 

“eh”

 “Tashi ki shirya kina da bak'o a parlor.”


D’ago kanta tayi ta kalli Ammi

 “Bak’o kuma Ammi?”

 D’aga mata kai tayi zumb'ure baki tayi 

“Allah ammi ni bazanje ba.”


Had’e rai tayi

“To kar kije d'in wlh kinji na rantse bakije ba bani bake munb'ata.”


Arazane tad'ago

“yes I mean it.”


Gyalenta taja fuuuuuu tayi gaba murmushi Ammi tayi tace 

“Sai dai kinje.”


Tans isa parlor wazata gani Asad ne d'aure fuska tayi tace 

“Malam lafiya miya kawo ka gidanmu ina ma kasan gidanmu?”


Murmushi yayi yace 

Relax pretty.”


Cikin muryanshi mai sanyi ya kamata ki zauna ba musu ta zauna kallonta yayi yace 

“Haba pretty fad'a banaki baneba dan baki kama da masu fad'aba ba gaskia tun randa na ganki naji kin man kuma sanki nake da aure gidanku kuma yanda akayi nasanshi binku na din gayi a baya baku saniba har naga gidanku.”


Tasowa yayi yazo kusa da ita ya d'uka 


“pretty Allah nakamu da sanki fiye da yanda kike tunani dan Allah kisoni ko zanji sauk'i.”


Hawaye ne suka dinga wanke mata fuska dan tabbas tasan zafin so saboda itama tana ciki san wani da zata iya cire Salman da tabbas taso Asad saboda shima namijine ajin farko hawayenta ya share mata 


“kiyi hak'uri pretty bana fad'a maki dan kiji haushi bane kawai dan kisan yanda nake sanki.”


kuka yaci k'arfinta tashi tayi ta nufi d'akinta da gudu tana kuka mai zafi haka dai Asad ya k'araci zaman shi ya tashi murmushi yayi yace 

“Aysaah na hango sona a idonki in shaa Allah ke rabo na ce.”


BAYAN KWANA BIYU

Zaune yake parlon bak'i Sahr ce kusa dashi tana hawaye hankalin Salman duk ya gama tashi ta sowa yayi yazo kusa da ita ya zauna hannunta yakama ya rik'e gam kamar za'a kwace mai ita.


“haba wifey ki daina kuka wlhi kukan ki yana d'agaman hankali tafiya fa ba mutuwa ba kuma kinsan ina tare dake in shaa Allah bazan dad'e ba zandawo gareki ki daina kuka kinji.”


Hawayenta ta share 

“To yanzu miyasa bazaka zauna gidanku ba kasan bansan kayi nesa dani pls kayi hak'uri da komawa Abujar nan.”


“Haba Sahr kin san dai koma wata Abuja dole ne koba dan komai ba kodan aikin da ake neman man infact ya zama dole na koma naga baby doll d'ina I miss her so much kiyi hak'uri bazan dad'e ba.”


haka dai ya dinga lallashinta da kalamai masu dad'i har ta hak'ura hannunta yakamo har wajen motanshi kallonta yayi yace 

“Zan wuce wifey ki rik'eman amanar kanki kinji?”


D’aga kanta tayi 

“I'll in shaa Allah.”


 Mota ya shigatsaye take tana d'aga mashi hannu sai data ga yabar gate d'in gidansu kana tayi cikin gida da gudu tana kuka.....

       

 Yana zuwa gida ya shirya tsaf ya d'auki jikanshi yasaka a mota dawowa yayi cikin gida d'akin Mufeedah ya nufa kwance take tana latsa waya d'agowa tayi tana murmushi 

“bruh badai harka shirya ba?”

 “Na shirya.”


Abinda yace mata kenan zama yayi kusa da ita yace 

“Lil sis kin san mina keso dake?”


girgiza kai tayi yace 

“pls ga amanar Sahr nan ki kularman da ita nasan zaki taya brother d'inki san abinda yakeso.”


Hawaye ta farayi saboda gaskia tafi san Salman da Aysaah dan tasan irin san da Susaah takema Salman, goge mata hawaye yayi yace 


“Nasan na baki aiki mai wuya amma kituna yanda k'arfin san Sahr yake gurina wlhi zaku iya rasani akanta.”


D’agowa tayi a razane tace 

“In shaa Allah bazaka mutuba kuma zanyi komai saboda farin cikinka karka damu Bro”

 “Datz my sis datz y I love.”

“I love u mre bruh.”


Rungumota yayi kana suka tashi sallama yayima iyayenshi ya d'auki hanyar abuja da zumud'in ganin fav sis d'inshi murmushi ya yi dan yasan yau akwai rigima..

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


BABI NA GOMA


  Zaune take parlor tayi d'ai d'ai tana cin popcorn sallama yayi tashi tayi da gudu ta rungumeshi sai kuma ta sakeshi ta fashe da kuka ta nufa d'akinta da gudu hankalin Salman ya tashi ganin baby doll d'inshi na kuka d'akin ya bita koda yaje kwance ya isketa kan gado tana kuka, d'agota yayi ya share mata hawaye sunanta ya kira cikin muryanshi mai sanyi kamar ta d'agowa tayi ta kalleshi 


“Miya saki kuka ko baki murnan dawowa ta ba idan baki murna ba sai in koma.”


Dasauri ta d'ago tace 

“Ahah bakai bane ba tun da katafi baka kirani ba ka mance da ni kanata harkanka.”


Murmushi yayi 

“Aysaah kenan saunawa kina ganin miskal d'ina amma baki d'aga ba nifa ya kamata nayi fushi dake amma da yake kinsan ban iya fushi dake shiyasa banyiba.”


Zumb'ure baki tayi 

“Ai ni kaima laifi kaban hak'uri.”

Kumatunta yaja yace 

”am sorry my baby doll.”


Murmushi tayi ta fad'a kanshi ya rungumeta 


“Kefa yanzu ba yarinya bace ba kin girma ya kamata ki rage shigema Salman harkina rungumarshi kin san ba muharraminki baneba keko muharraminki ne bai kamata ba saboda kinsan addininmu bai so Allah yayi hani da haka dan haka shiyasa nake k'ara jan kunnenki daki daina shigema namiji koma waye bawai Salman kad'aiba koma waye bakuma zarginku nake ba kawai saboda dukkaninku yanzu balagaggu ne.”


Maganganun Ammi ne suka dawo mata da sauri ta janye jikinta murmushi yamata yace 

“Yanaji gidan shiru inasu Mummynah da Amminki?”


Sun tafi suna su kuma su Zarah suna islamiyya, kafin yak'ara magana wayanshi tayi ringing ganin wadda ta kirashi ya sashi murmushi tashi yayi yace 


“Baby doll big bro fa yana jin yunwa dan haka anema mashi abinda zaici.”

       

Tana tashi da safe ta shirya mashi komi as usual kana ta shiryan cikin doguwar rigan material sallama ta yima Ammi ta nufi makaranta kusan tare suka shiga school da Haneefa suna ganin juna suka rungume juna Ausaah tace 

“Bestieya Salman fa ya dawo jiya.”


 Murmushi Hanifa tayi tace 

“ashe jiya munyi babban bak'o shine baki kirani nazo na tayaki had'a mashi delicious ba.”


Nurmushi tayi tace 

“Kin sanshi da surprise nima kawai ganinshi nayi.”


“bestie kinsan mi?”

Girgiza kai tayi 

“Wannan guy d'in Asad yake kowa ashe ranan binmu yadin gayi harya ga gidanmu, basai gashi ba.”


 Cikin k'aguwa Hanifa tace 

“Ya kukayi dashi?”


Kafin tabata amsa lecturer ya shigo bari muganma lecture zan fad'amaki.....


    Suna gama lectures d'insu suka nufi cafteria dan suci abinci sai da suka gama kana Haneefa tace 

“Bestie ina jinki.”


Kwashe komai Aysaah tayi ta gayama Haneefa sannan tace 


“Wallahi Hanifa baccin zuciyata na riga dana sadaukar da ita kan Salman nd kuma nama kaina alk'awarin idan ba Salman ba bazan tab'a aure ba dana saurari Asad saboda shima namijine ajin farko sai dai bazan iyaba.”


Ita dai Hanifa kallonta takeyi sai da tagama kana tayi ajiyan zuciya tace 


“Duk naji magananki ki cigaba da adua Allah yamaki zab'i mafi alkairi amma kidaina cewa wai idan baki auri Salman ba ba zaki aure ba shifa ba'ama Allah dole sai ya hanaki Salman d'in kuma kin san iyayenki bazasu samaki ido ki k'iyin aure ba, dan haka adua itace mafita wajenki.”


 Sallama sukaji akansu gaba d'aya suka d'ago Asad ne tsaye yanata masu murmushi.


Murmushi Hanifa ta mashi kana ta gaida shi amsawa yayi cikin sakin fuska kallon Aysaah yayi yace 

“Pretty can i sit?”


D'aga mashi kai tayi 

“Thank you”

Yacr yaja kujera ya zauna tashi Hanifa tayi tace


“Bestie kisameni hall.”


Kafin taji abinda za tace har tayi gaba juyowa tayi tana kallonshi murmushi yamata itama ta maida mashi martani gaidashi tayi amsawa yayi cikin jin dad'i kallonta yayi yace 

“pretty Allah dai yasa ba b'ata maki rai nayi ba ranan danaje gidanku wlhi harna koma gida ina tuhumar kaina da sanya pretty kuka.”

 “Ba ruwanka.”


Asad yace 

“Ranan namaki magana baki ceman komai ba.”


D’agowa tayi cikin sanyin murya tace 

“Asad kayi hak'uri ka bari sai gobe zan gaya maka komai da dalilin da yasa nake kuka kaga yanzu tym d'in lecture ya kusa gobe muhad'u nan wajen 11:am.”


Kallonta yayi cikin tausayawa yace 

“Allah ya kaimu tashi na rakaki.”


Har gaban hall d'insu ya kaita kana sukayi bankwana ta shig cikin lacture hall shikuma ya juya yatafi. Suna gama lecture Hanifa ta kalleta tace 

“Ya kukayi dashi?”

“gobe zamuyi maganadashi.”

Amsar data bata kenan suka wuce wajen mota dan tafiya gida..

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


BABI NA SHA D’AYA


WASHE GARI


  Suna fitowa lectures ta kalli agogon hannunta 10:55am ta gani kallon Hanifa tayi 

“Muje cafteria Hanifa.”


 Cikin rashin fahimta ta kalleta 

“Mi zamuyi?”

“Zanyi magana da Asad ne.”

“Kije kawai ni kinsameni Ana nan idan kun gama.”


D’aga kanta tayi tace 

“Issokay sai nazo.”

Juyawa tayi ta nufi hanyar cafteria, tana isa ta hangoshi in da suka zauna zuwa tayi da sallama amsawa yayi cikin sakin fuska agoginshi ya kala yace 


“Kin karya ak'awari.”


 Marairaicewa tayi sai abin ya burgeshi 

“Kayi hak'uri.”

“Shhhhh baki laifi ai pretty.”


Kujera taja ta zauna tace 

“Nagode.”


Murmushi yayi yace 

“Never mind.”


Gaidashi tayi ya amsa tare da tambayarta ya lectures amsa mashi tayi da lafiya lau, shiru ya biyo baya....


    

  Gyaran murya tayi tace 

“Idan ka shirya zan fara.”

Asad yace 

“Kafin ki fara ya kamata kisan wayeni.”

D'aga kanta tayi alamar eh..


WAYE ASAD

kamar yadda kika sani ni sunana Asad ni d'an minister of finance ne Alh jeeboh nasan zaki sanshi hajia Karima itace mahaifiyarmu mu biyu ne wajen mahaifanmu dagani sai sister na Rayhan yanzu haka tana karatu a Germany ni kuma nayi makaranta na tun daga primary har PhD d'ina a America yanzu haka ina aiki da company d'in Daddynah a nan garin yanda akayi naganki kuwa nazo school d'inku wajen wani frnd d'ina shinefa kafin yafito naganki kuma naji kin man kinji labarina da yanda akayi naganki...    Kallonshi tayi ta mashi smile 

“Wow inasan nasan wannan sistr d'in taka.”

“Karki damu pretty zan had'aku....”


   "Yanzu ke nake jira naji wacece pretty na da abinda ke sata kuka...”

        

D'agowa tayi ido rune ta kalleshi tace 

“Yanzu kuwa za kaji, kamar yadda ka sani sunana aysaah...............”


Ta kwashe komai ta gayama Asad babu abinda ta rage mashi har san da takema Salman babu abinda ta b'oye mashi.


D’agowa yayi yaja numfashi kallonta yayi yace 

“Naji komai pretty kuma na karb'i uzurinki karki damu wlhi bazan takura makiba amma dan Allah kiman taimako d'aya kid'aukeni a matsayi blood brother d'inki nikuma zan maki duk abinda yake saki farinciki....”   D'agowa tayi ta kalleshi duk sai ya bata tausayi murmushi tayi 

“Karka damu daga yau kazama brother d'ina.”


 Da murmushi ya d'ago yace 

“Dagaske?”

D'aga kai tayi tace 

“I mean it.”

“To idan hakane mik'oman hannunki mu k'ulla”


Murmushi tayi ta mik'a mashi d'an yatsa suka k'ulla. kallonshi tayi tace 

“Bro yau zanyi introducing d'inka a family na.”


Da murna yace 

“Yauwa pretty muje to.”

Tashi sukayi suka tafi suna fira.....


Haneefa na zaune ta hango Aysaah da Asad suna tafiya suna magana cikin nishad'i abin ya bata mamaki suna k'arasowa yace 

“Bestieen mu idan kingama muje ko.”


Salon baki tayi tana kallonsu dariya Aysaah tayi tace 

“Idan kin gama tunanin muje.”


Tashi tayi tace 

“Muje.”


Suna zuwa wajen mota Aysaah ta mik'amashi key karb'a yayi yace 

“Pretty mota nafa?”

“To ka biyoni baya thou ma kasan gidan.”


 Dariya yayi yafad'a motarshi itama taja mota, kan hanya tama Hanifa bayanin komai tabbas Hanifa taji dad'in haka....


     Maitama stores ta aje Hanifa sukayi bankwana kana tad'auki hanyar missippi shiko gogan naku yana biye da ita tana tafiya yana biye da ita har suka isa horn tayi maigadi ya bud'e mata cinna kan motanta tayi cikin gida shima ya rufamata baya sai da tayi parking a parking space kana tafito shima fitowa yayi kallonshi tayi tace 

“Bro muje ko.”


Kallonta yayi ya kashe mata ido 

“Muje pretty.”


Haka suka jera su kayi cikin gida suna fira, suna shiga bakowa parlor kallonshi tayi tace 

“Bro zauna bari na kiramaka su Amminah.”


 Zama yayi ita kuma ta wuce d'akin ammi tana ihu kallonta yayi harga Allah komai na Aysaah yana burgeshi kuma in shaa Allah sai ya taimaka mata burinta ya cika dan ganinta yake kamar Rayhan sister d'inshi..

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION 


BABI NA SHA UKU


 A daddafe ta kai safe saboda ko barcin kirki ba tayi ba hankalinta yana kan Asad dan ta tabbata Asad ba lafiya ba tunda har ya kasa d'aga kiranta kuma bai kirata back ba.

Tana tashi da safe ta fad'a wanka tana fitowa ta zira jallabiya tasaka turare ta d'auki key d'in mota d'akin Ammi ta shiga tana shiga ta tarar da tana toilet bata iya tsayawa tafito writing note ta aje mata bisa gado ta juya ta fita.

Parking space ta wuce motarta ta shiga ta mata key horn ta danna mai gadi ya wangale mata gate yana mata kirarin da ya saba hannu kawai ta d'aga mashi tayi gaba gudu ta dinga shararawa kamar zata tashi sama, Allah ne ya kaita gidansu Asad lafiya....


Horn ta din gayi ba tsayawa da gudu mai gadi ya zo ya wangale mata gate, shiga tayi cikin gidan tana shiga batako tsaya kulle motan ba ta fito tayi cikin gida da gudu....

       

Bako sallama ta fad'a parlor d'agowa Maah tayi taga waye Aysaah tagani tsaye tana dube dube tashi Maaah tayi ta kamo hannunta ta zaunar da ita kallonta Maaah tayi tace

“Babyn Assad ya dai kika shigo bako sallama kalli yan da duk kika firgice.”


Sai a lokacin hankalinta ya d'an dawo, ajiyan zuciya tayi tace

“Maah ina kwana.”


Amsawa tayi cikin kulawa kallonta tayi tace 

“Miyafaru naganki haka?”

Duk'ar da kanta tayi k'asa tace 

“Maaah nazo duba ya Asad ne tun jiya nake kiranshi bai d'aga ba kuma bai kira back ba shine nace bari nazo naga lafiya.”


Murmushi Maaah tayi dan tasan irin shak'uwar da take tsakanin Asad da Aysaah....


Kallonta maaah tayi tace 

“Har yanzu bai fito ba yana d'aki nasan bai tashi ba.”


Tashi tayi ta nufi hanyar d'akinshi tace 

“Yanzu kuwa zai tashi Maaah.”

       

Binta Maaah tayi da kallo tana murmushi, tana isa bakin k'ofan d'akin knocking tayi shiru murd'a murfin k'ofan tayi ta shiga d'akin da sallama amma shiru ba a amsa ba ga d'akin yayi duhu, light ta kunna dan da nan haske ya bai baye d'akin saman gado ta hangoshi k'udundune da blanket da sauri ta k'arasa bisa gadon yaye blanket d'in tayi tace 

“Ya Asad.”


Bud'e idon shi yayi ya kalleta amma yakasa magana hankalinta a tashe tace 

“Ya Asad mike damunka?”


 Sai kuma ta fad'a kanshi tana kuka da kyar ya d'agata shima tashi yayi ya kalleta girgiza mata kai yakeyi alamun tadaina kuka, cikin sheshek'an kuka tace

“Dama nasan baka da lafiya naji a jikina, dan Allah mike damunka?”

 A hankali yake magana yace 

“My pretty kaina ne keman ciwo tun jiya.”

“Kasha magani?”

Tambayar da ta mashi kenan girgiza kai yayi alamar ah ah, tashi tayi ta fita ta koma cikin gida wajen Maaah.....


In da ta bar Maaah nan ta sameta zumb'ure baki tayi tace 

“Allah Maaah sai na mai da ya Asad gidanmu tunda baki kula dashi.”


Murmushi Maaah tayi tace 

“Mikuma nayi yanzu?”

B'ata fuska tayi tace 

“Yanzu Maaah ya Asad bai lafiya yana ciwon kai shine baki sani ba haba maaah.”


Kallonta Maaah tayi cikin kulawa dan tabbas ba tasan bai lafiya ba kuma bata kyauta ba da bata dubashi yau ba dan rabonta dashi tun jiya. maah tace

“Ayi hak'uri nayi laifi.”

Murumushi tayi tace 

“Baki laifi maaah...”
   Tashi Maaah tayi ta nufi sashen Asad ita kuma Aysaah tayi kitchen dan ta had'a mashi breakfast. Indomie ta dafa mashi sai kuma tea mai kauri da ta had'a mashi, a tray ta jera su ta d'auka tayi hanyar d'akin shi dasu da sallama ta shiga kallonta Maaah tayi tana tsokanarta tace 

“Aysaah yanzu haka Asad kawai kikama girki.”


Murmushi tayi tace 

“Ai shine bai lafiya.”


Da taimakon Maaah Asad ya tashi yayi brush ta kuma had'a mashi ruwan wanka sai da ya shirya tsaf kana Aysaah ta dawo d'akin da kanta ta dinga bashi abincin ya naci suna rigima dan tace saiya cinye indomie kuma ya shanye tea d'in shi kuma yace ya k'oshi Maaah dai na gefe na masu dariya dan dole yayi yanda takeso aikam taji dad'i yana gamawa ta kwashe kayan kana ta kirasu Ammi da Salman ta gaya masu...


Su Ammi ne suka shigo da kayan marmari nik'i nik'i tashi maaah tayi ta taresu da murna dan yanzu zumunci suke sosai, zama sukayi suka gaisa Maaah ta kalli Mummynzarah tace 

“Ina d'anki salman?”


Murmushi Mmmynzarah tayi tace 

“Yana part d'in Asad.”


“Eh lallai shine yak'i zuwa ya gaidani ko?”

Ammi tace 

“Yazo fa.”


Mummynzarah tace 

“Ai mana hak'uri Maaah.”


Dariya sukayi gaba d'aya kana suka tashi sukayi sashen Asad, Salman yana ganin Maaah ya fara kame kame dariya Maah tayi tace 

“Ni rabu dani ai ka nuna d'an uwanka yafi mamanka.”


 Dariya ya yi yace 

“Ayi hak’uri duk na rud'e ne shiyasa, nan sukama Asad ya jiki sai marece kana sukabar gidan itako madam Aysaah gaba d'aya nan tadawo saboda tace Maaah bata kula da Adad yanda ya kamata. 


Kwananta hud'u Asad ya warware kamar bashi ba, kana ta had'a kayanta tayi gida.

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION 


BABI NA SHA BIYU


  Tana shiga d'akin Ammi ta tarar da ita zaune bisa gado fad'awa tayi kanta tace 

“Wash Ammi na bakiji ina kiranki ba?”


D’agowa ammi tayi tace 

“Banji ba my dota kin dawo lafiya?”

“lafiya lau na dawo Ammi na.”

D’ago ta tayi tace 

“Ya dai my dota naga kina dariya kamar akwai magana bakin ki.”


 Fad'ad'a dariyan ta tayi tace 

“Akwai Ammi na Papa yana gida?”

“eh"

Ammi tace 

“Yauwa Ammi na ga yamashi yana da guess a parlor.”


Kallonta Ammi tayi d'aga mata kai tayi alamar eh waya tajawo takira Papa tagaya mashi sak'on Aysaah tana gamawa tace

“Yauwa Ammi tashi muje.”


Ba musu Ammi ta d'auki gyalenta ta bita har parlor, suna zuwa parlor dai dai Papa da Mummynzarah suma sun shigo parlon, suna shiga parlon kowa ya aamu wuri ya zauna.


Asad ne ya sauka k'asa ya gaidasu amsawa sukayi cikin sakin fuska, kallon rashin sani suka din gayi mashi dariya Aysaah tayi tace 

“Nasan baku san shiba amma yanzu zaku sanshi.”


Salman ne yayi sallama da gudu taje ta kamo hannunshi tace 

“Yauwa Bro gara kai ma daka na nan.”


Murmushi ya mata yace 

“Tasamu ne my baby.”


Dariya tayi zama yayi ya gaida su Papa mik'ama Asad hannu yayi suka gaisa..

        

“Papa nasan baku san waye ba, sunanshi Asad yaron minister of finance ne Alh Jeeboh mun had'u dashi last week shine yace yana san nazama sister d'inshi saboda ina mashi kama da sistr d'inshi Rayhan shine nace to bari nayi introducing d'inshi wajenku.”


Jinjina kai Papa ya yi yace 

Tabbas Asad mahaifinka aboki nane kuma mutumin arzik'ine naji dad'in yanda ka nuna kulawarka akan my dota kuma ka d'auka nan gidanku ne baka da matsala da kowa.”


“Nagode Papa Allah yak'ara girma.”


Ammi tace 

“Gaskia nafi kowa farin ciki da d'iyata ta samu d’an uwa dama an had'e mata kai cikin gida.”


 Dariya akayi Mummynzarah tace 

“Sai dai kayi hankali saboda wautanta yayi yawa idan tayi shirme kadinga zaneta.”


Zumb'ure baki tayi tace 

“Ammi kinaji?”


Jawota Ammi tayi tace 

“Ba mai dukanki ai yayanki ne.”

 Aysaah ta kalli Salman tace 

“Ga d'an uwa namaka, Asad wanan kuma shine Salman d'in da nake baka labari.”


murmushi yayi 

“Ina ganin shi na ganeshi, haka dai suka cigaba da fira tashi su Papa sukayi sukabarsu sunata fira sai marece sosai kana Asad yabar gidan tare da farin ciki fal aranshi na karamcin da yasamu gidansu AYSAAH....


Wata dattijuwa ce zaune parlor tana kallon zee world sallama yayi ya shiga amsa mashi tayi tare da sakin fuska yana zuwa inda take, d'ora kanshi yayi kan cinyarta shafa kan tayi tace 

“My son yau ina katafi kabarni ni kad'ai kasan bansan kana nesa dani ba.”


 D’agowa yayi ya kalleta 

“Maaah ina gidansu AYSAAH.”


murmushi Maaah tayi tace 

“Hope dai kun daidaita.”


Gigiza kai yayi yace 

“Maaah yanzu Aysaah matsayin sistrna na d'auketa matsayi d'aya suke ita da Rayhan.”


Maaah dai sakin baki tayi tana kallonshi saboda ranan da ya fara ganinta kamar zaiyi hauka amma yanzu gashi ya canja magana kallonta yayi yace 

“Maaah nasan zaki mamaki Aysaah akwai wanda takeso.”


Kwashe komai yayi ya gayama Maaah yace 

“Kuma nayi alk'awarin zan ta yata fighting akan abinda takeso kuma sai naga tasamu abinda takeso.”


Kallonshi Maaah tayi tace

“Kaifa?”

Murmushi yayi yace 

“Shiyasa nace maki yanzu ta zama k'anwata pls Maaah ina san kid'auki Aysaah kamarni da Rayhan dan Allah.”


Shafa kanshi tayi tace 

“Karka damu in shaa Allah zan d'auketa kamar ni na haifeta.”


Rungumeta yayi yace 

“Nagodai Maaah kin masan wani abu babanta abokin Daddy ne.”


Maaah tace 

“Ashe d'iya ta mace yanzu yaushe za'a akawo man ita?”

“Maaah karki damu sai kin gaji da ganin Aysaah.”

“Shikenan my son.”


Haka dai rayuwa ta ciga da tafiya kullum Aysaah kamar ana k'ara mata son Salman shikuwa soyayya mai k'arfin ta k'ara shiga tsakaninshi da Sahr yanzu Asad ke kai Aysaah school ya kuma d'auko su watarana Asad da Salman sun fita sai yaji Salman yana waya sai da ya gama yace 

“Dawa kake waya?”


Dariya yayi yace 

“Da matata.”


 Kallonshi Asad yayi yace 

“Wce irin mata kuma?”


Murmushi yayi yace 

“Matar da zan aura mana sunanta Sahr.”

 Sai da wutar Asad ta d'auke ga zufa da ya farayi saboda jin maganan kallonshi salman yayi yace 

“Yadai?”


Murmushi ya k'ak'aro yace 

“Aysaah tasani kuwa?”


 Girgiza kai Salman yayi yace 

“Har yanzu ban gayamata ba bari nayi sai munje kaduna kawai nayi surprise d'inta.”


Girgiza kai Asad yayi yace 

“Shikenan.”


Haka suka koma gida jikin Asad duk a mace ga tausayin Aysaah daya cika mashi rai, haka dai ranan ya kwana kamar bai lafiya, Aysaah ta dinga kiran wayan Asad amma ank'i d'agawa hankalinta ya tashi gashi wajen 11:pm bare taje gidansu taga ko lafiya.

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATIONBABI NA SHA BIYAR


 Tana shiga d'aki ta maida k'ofa ta rufe fad'awa tayi kan gado ta saka sabon kuka kamar wadda aka cirema rai, Ammi tazo ta dinga bugun k'ofa da kyar ta tashi ta bud'e mata, shigowa Ammi tayi cikin d'akin hannunta ta kamo ta zaunar da ita itama zama tayi kiran sunan ta tayi d'agowa tayi ta kalleta 

“Aysaah kiban hankalinki magana nakeso nayi dake.”

D’aga mata kai tayi tana share hawaye

“Aysaah.”

Sunanta Ammi ta kira, amsawa tayi 

“Daa naam.”

“Aysaah miye sa kike haka shin kin fisan kullum kina d'agaman hankali ne? Kinsan babu abinda na tsana naga damuwarki amma ke kullum sai kin d'agaman hankali tafiyan Asad baya nufin kun rabu ba kenan zai dawo, kuma kin san bazai k'i bin umurnin mahaifansa ba saboda ke dan haka wake up ki daina kuka ki daina sa damuwa cikin zuciyanki idan kina san mu shirya.”


“Ammi kiyi hak'uri m in shaa Allah na daina kuka bazan sake d'aga maki hankali ba.”

Murmushi Ammi tayi tace 

“Gud gal Allah yamaki albarka.”

 Amsawa tayi da amin, tashi Ammi tayi tabar d'akin..

        

Tana bud'e kit d'in english gold ne tagani sark'a da d'an kunne sai zobe shima da ban tana d'auko wa ta ga wata takarda tana budewa taga wata yar k'aramar ta karda ta fad'o da writing note

D’auka tayi ta duba ga abinda tagani, 

“pretty nasan zaki mamakin ganin abinda kika gani so ba abin mamaki bane ba saboda komi nasamu na kine, wannan english gold d'in nakine keda Rayhan na sai ma wa naso na baku a tare amma Allah bai nufa ba tunda zanbar gari shiyasa na baki nd takardun da kika gani na gida nane dake maitama nayi shawara da su Maaah sunce na bar maki dan haka na bar maki dunia da lahira nd pls ki daina saka damuwa kisani ni Asad ina tare dake ko da yaushe nd ki tabbatar kafin nazo ganinki komai ya daidaita ke da salman ki huta Lafiya daga yayanki mai sanki ko da yaushe.”


rungume takardan tayi tana kuka sosai, tashi tayi ta kwashi kayan ta nufa k'asa dasu parlor taci karo da su Ammi harda Papa gabansu ta zube kit d'in sai dai ta b'oye letter d'in. Bayani ta masu babu wanda baiyi mamaki ba daga k'arshe Papa ya karb'i takardun gidan yana shima Asad da albarka...


Washe gari tana tashi ta shirya atamfa ta saka red doguwan riga gaskia d'inkin ya mata kyau da yake stone work ne sark'an da Asad ya bata ne ta d'auko ta saka kallon kanta tayi a mirror ita kanta tasan sark'an yamata kyau, rolling tayi da red scarves kana ta d'aura agogonta mai tambarin apple ta d'aura a tsintsiyar hannunta, jikarta da takalmin ta duk na prada ne feshe jikinta tayi da turare, kana ta fita daining area ta iske iyayenta harda papa fad'awa kan ammi tayi tana shagwab'a d'agota ammi tayi tace

“Masha Allah yarinya na kinyi kyau.”


 Mummyn zarah ta kalli salman tace 

“Kaji yanda ake kod'a wannan mummunar.”


Dariya salman yayi yace 

“Naji.”


Papa yace 

“An ya kuwa zaku iya rik'e alk'awarin Asad kuwa?”

Dariya mummyn zarah tayi tace 

“Gaga fad'an gaskia to shikenan nida yarona mun daina magana.”

 

Haka dai suka dinga cin abinci suna fira cikin k'aunar juna gaskia zaman gidan yana burgewa kowa saboda kansu had'e yake baka tab'a gane d'an wannan inba kasani ba, Aysaah na gamawa tabi iyayenta tamasu peck harda Mummyn zarah, zata juya kenan Salman ya rik'ota yace 

“Ina nawa.”


 Murmushi tayi tamashi peck ta ruga da gudu, kallo Ammi ta bita dashi cikin sha'awa da son d'iyar tata....


Tana shiga school bata jima ba sai ga Hanifa, kallon ta Hanifa tayi ta gano damuwa k'arara a fuskarta girgiza kai tayi dan tasan damuwar Aysaah bata wuce Salman, dafata tayi firgigit ta d'ago murmushi ta mata itako Hanifa d'aure fuska tayi tace 

“Bestie bazaki daina sakama kanki damuwa ba ko? Allah kinji na rantse ko zan gayama ya Asad tun da dama kafin ya wuce sai da ya zo yaban amanarki kuma namashi alk'awarin zan rik'e amana, amma tun ba'aje ko ina ba kin fara sab'a alk'awari da kika d'aukar mashi.”


“Kiyi hak'uri bestie nasan ina saku damuwa amma Allah ba yin kaina baneba ku dai cigaba da tayani da adua amma wlhi bestie inasan Salman fiye da tunaninku kuma gashi ya Asad yace kafin ya dawo na tabbata Salman yana sona amma gashi banda wata hanya.”


Hawayen da suka gangaro mata ne Hanifa ta goge ma tace 

“Aysaah adua dai ita zance ki cigaba saboda nasan watarana zakici riban aduan ki in shaa Allah, kada ki nuna gajiyawarki wajen gayama Allah buk'atunki kinji ko.”


Fad'awa jikinta tayi tana hawaye da kyar Hanifa ta samu ta daina hawaye, a haka dai suka gama abinda suke a school ....

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION


BABI NA SHA SHIDA


BAYAN SHEKARA BIYU


 Abubuwa sun faru cikin shekara biyu ciki harda zuwan Asad nigeria wajen Aysaah tare suka zo shida Rayhan satinsu biyu kana suka koma nan ma ansha kuka dan da kyar aka raba Rayhan da Aysaah, yanzu haka Aysaah tana final year d'inta second semester ita kuma zarah an zama yanmata saboda itama tana base university tana karanta mass communication, babu abinda ya canja tsakaninta da Salman, kullum aduan ta d'aya Allah ya sa Salman ya sota shiko hankalinshi bai kanta, saboda ya riga da ya mallakama Sahr zuciyanshi kuma duk abinnan Aysaah bata san da zaman Sahr ba.


zaune take d'akin Ammi tana karatu Ammi ce ta shigo d'akin da sallama amsa mata alAysaah tayi tana murmushi da fata Ammi tayi tace 

“My baby kizo Papa yana san ganinmu.”


Haka kawai taji gabanta na fad'uwa d'agowa tayi a sanyaye tace 

“Ammi nah lafiya daiko?”


Murmushi Ammi tayi tace 

“Lafiya lau my dota kedai tashi muje.”


Mik'ewa tayi tabi bayan Ammi, parlor suka sami Mummyn zarah da Papa, zama Ammi tayi itama Aysaah wuri ta samu kusa da Amm ta zauna.


Gyaran murya Papa yayi 

“Aysaah.”

D'agowa tayi tace

“Naam papa.”

“Kinsan dalilin da yasa na kiraki?”


Girgiza kai tayi alamar ah ah, yace 

Alhamdulillah yanzu ajinki nawa?”


A sanyaye tace 

“Papa final ya nake.”


“Masha Allah kinsan abinda yasa na kiraki?”


Girgiza kai tayi yace 

So nake ki turoman wanda kikeso saboda da kin gama makaranta zan aurar dake kin ga bai yuwa kina gida gasu Zarah suna tasowa, idan kuma baki da wanda kike so to dama abokina yaman maganarki yanasan na aura ma d'anshi ke nace ya bari sai naji daga bakinki.”


“Kyarma Aysaah ta kamayi sai kuma ta fashe da kuka ta fad'a jikin Amm....

        

Tsawa Mummyn Zarah ta daka mata 

“Uwarmi aka maki daga cewa ki fiddo miji shine sai kuka ko so kike mu zauna muda ke arasa gane matan gidan.”


Ammi ta d'ago rai b'ace tace 

“Dan Allah hajia ki saura rama yarinyar nan hakanan shin dawane zataji haba mana.”


D’agowa tayi tace 

“Papa banda saurayi kuma wanda kake san kabani wallahi ban sanshi duk da bantab'a ganinshi.”


“Ni dai na gama magana nabaki nan da 3month dai dai kin gama exams d'inki da 2weeks kenan idan baki fito da wanda kikeso ni zan baki yaron abokina.”


Tashi tayi ta nufi d'aki da gudu tana kuka tana shiga ta maida k'ofa ta rufe ta fad'a kan gado tana kuka sosai hoton Salman ta jawo tafara surutai 

“Ya zakaman haka kasan duk dunia nafi kowa sanka amma ka kasa gano hakan, yanzu gashinan za'a aura man wani ba kai ba Allah ka kawoman mafita.”

Fashewa tayi da sabon kuka mai cin rai...


   Itama Ammi tashi tayi ta nufi d'aki rai b'ace dan gani take ba'ama tilon d'iyarta adalci ba...


Duk abinnan da akeyi Salman yana kd amma gobe zaidawo..


WASHE GARI

Koda Aysaah ta tashi fuskanta yayi kumburi da gani kasan taci kuka wanka ta shiga tana fitowa turare ta saka ta d'auki doguwan riga ta saka d'akin Ammi ta shiga da sallama Ammi na ganinta ta taso ta tareta zaunar da ita tayi ta had'o mata tea mai kauri ta bata ta sha saida ta tabbatar data k'oshi kana ta ajiye cup d'in, kiran sunanta ammi tayi jiki sake ta d'ago ta kalleta a sanyaye ta amsa 

”Da Naam.”


Shiru ya d'an biyo bayansu kana Ammi tace 

“So nake kiban hankalinki nan, kinsan dai bazan so abinda zai cutar dake ba ko?”


D'aga kai tayi 

“Nasan bazaki rasa wanda kike so ba to ki gaya mashi yazo yaga babanki.”


Hawaye suka fara sunturi a kuncinta kamar famfo tace 

“Allah Ammi banda saurayi banyi niyar fara soyayya yanzu ba nama zuciyana alk'awari ne.”


“Alk'awari? Wane irin alk'awari ki kayi?”


kuka kawai ta keyi

 “Nidai Aysaah bani da abinda zan gayama babanki ya fasa abinda yayi niya, ki fito da wanda ke sanki if not nasan ba abinda zai hana ya baki yaron abokinshi.”


Fashewa tayi da kuka tace 

“Pls Ammi karki bari yaban wani wlhi zaku iya rasani.”

 Sai kuma ta tashi tayi d'aki da gudu tana kuka ita dai Ammi binta tayi da ido....


   Wayanta ce yayi ringing kamar bazata d'auka ba sai ta duba sunan Ammi ne ta gani a screen d'in wayan, d'agawa tayi banji mi aka ceba sai tace gani nan tashi tayi ta d'auki gyalenta ta d'aura tayi k'asa Ammi ta gani da Mummynzarah gaidasu tayi Ammi ta bita da kallo kwana d'aya da yini d'aya duk ta fad'a.


“Ammi yana ina?”


Yana d'aki tunda ya shigo yake nemanki yace 

“ki kai mashi abincin shi.”

amsawa tayi da to ta wuce kitchen abinci ta had'a mashi bisa tray da lemu ta d'auka ta nufi d'akinshi tana isa bakin k'ofa zata murd'a kenan taji maganashi.


“Haba Sahr kiyi hak'uri ba wani dad'ewa zanyi ba zan dawo kuma kinsan yanzu ne zan tunkari iyayena da maganar auren ki tunda kin kusa gama makaranta kinga da kin ida sai ayi bikinmu.”


Banji mi taceba salman yace 

“Ai kinsan bazan tab'a son wata bayanke ba so ki kwantar da hankalinki.”


numfashinta ya nemi d'aukewa tray d'in hannunta ne ya kufce ya fad'i komai ya tarwatse k'asa, k'arar fad'uwan abu Salman yaji yasa ya nufi k'ofan da sauri............

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

  

BABI NA SHA BAKWAI


 Yana fitowa ya ci karo da ita duk'e, duk'awa yayi yace 

“Lil sis garin ya akayi haka?”


Itadai ta kasa cewa komai sai kuka takeyi, d'agota yayi yace 

“Haba baby doll miye na kuka daga kawai tsotsai ya sa kin yarda tray d'in pls stop crying.”


Hawayen ya shiga share mata hannunta ya kama yayi cikin d'akinshi da ita, zaunar da ita yayi shima ya zauna gefenta yace.

“Baby doll miye kike kuka kin san ban san kukanki oya share hawayenki zanyi surprising d'inki.”


Hawayen da suka gangaro mata ta share amma zuciyanta bai daina bugawa ba kallon ta yayi yace

“Aysaah namaki laifi amma ni a wurina ba laifi bane ba kawai ina san nayi surprising d'inki ne.”


Ita dai bata ce komai ba sunan ta ya kira 

“Aysaah.”

D’agowa tayi ta kalleshi Salman yace 

“Yau zan gabatar maki da wadda zan aura.”


 A razane ta d'ago d'aga kanshi yayi yace 

“Nasan abun zai baki mamaki amma ba abun mamaki baneba, lokacin da naje kd Allah ya had'ani da wata yarinya mai suna Sahr...”


Kwashe komai yayi ya gayama Aysaah babu abinda ya b'oye mata, in banda zufa babu abinda Aysaah keyi amma shi baima lura ba waya ya jawo zai kira Sahr murya dashe tace 

“Ya Salman banjin dad'i yanzu bari wani tym d'in mun gaisa.”


 D’aga mata kai yayi alamar toh da sauri ta bar d'akin duhu ta fara gani gabanta a haka tabi bango har ta kai d'akinta tana shiga ta maida k'ofa ta rufe tafara rera kuka..

       

Waya ta jawo tayi dialing number Haneefa ringing biyu aka d'aga muryan Aysaah ko fita ba tayi sosai tace 

“Hello bestie pls kizo yanzu gida ina san ganinki.”


Bataji amsar da zata bata ba ta kashe wayanta.


  Mintuna k'alilan taji knocking k'ofanta tashi ta bud'e Hanifa ce ta shigo d'akin da sallama, amsa mata tayi binta Hanifa tayi da kallon tambaya hannun Hanifa ta ja sukaje bisa gado suka zauna shiru sukayi can Hanifa tace 

“Bestie kin kirani kin k'iceman komai sai faman kuka kikeyi.”


Cikin sheshek'an kuka tace 

“Bestie na rasa ya Salman kunya ta sa na rasa masoyi na.”

“Ban gane kan magananki ba gara kiman bayani.”

“Salman yana da wadda yakeso sunanta Sahr yanzu haka maganan aure suke yi da ita.”


In banda innalillah wa'inna ilaihir raji'un babu abinda Hanifa ke fad'a.

“Aysaah ya akayi haka wakuma ya gaya maki ko shine ya fad'a maki?”


“Naje kaima shi abinci naji yana waya har kayan abincin suka zube, infact yaman bayanin komai da kan shi kuma ya tabbatar man da irin sanda yake mata.”


Ita kanta Hanifa kuka takeyi saboda ita kad'ai tasan irin san da Aysaah takema Salman.

“bestie ina cikin hali ga shi Papa ya ban 3month after exams d'inmu da 2weeks idan ban fitar da miji ba zai bani yaron abokinshi bestie ki taimakeni ya zanyi?”

Su duka kuka suke sosai.....


Kuka sukai mai isarsu kana Hanifa ta share ma Aysaah hawaye tace 

“Bestie ki daina kuka yanzu ba time d'in kuka bane ba adua ita zaki cigaba dayi saboda babu abinda zai gagari Allah dan haka stop crying nd keep praying kuma kidaina cewa kunya ta cuceki ta rabaki da masoyinki kefa da kanki kika nunaman darajan kunya ga d'iya mace saboda tabbas kunya ita ce adon mace kuma tunda kika rik'e kunyarki in shaa Allah za kiga ribanta nan gaba, amma ina da shawara ban sani ba ko zaki karb'eta.”


 “Inajinki.”


“Why not ki fidda Asad a matsayin mijinki dan nasan tabbas har yanzu yana sanki.”


“Bazan iyaba saboda idan namashi haka ban mashi adalci ba lokacin da ya soni na k'ishi sai yanzu da na rasa mafita zan dawo mashi Allah ban mashi adalci ba.”

Sai kuma ta fashe da kuka da kyar Hanifa ta samu tayi shiru...


“A yan da na karanto sonki cikin idon Asad ko aure ki kayi kika fito zai aure ki bare kuma ya san komai dake faruwa ke dai idan kina sanshi kimashi magana, shikuma Salman kisa a ranki dama ba mijinki bane ba, ki cigaba da d'aukanshi a matsayin wanda kuka fito ciki d'aya kamar yanda yake d'aukanki.”


 Ita dai in banda kuka ba abinda takeyi da kyar Hanifa ta samu tayi shiru ta dinga bata magana harta samu ta d'an ci abinci, sai marece Hanifa ta wuce gida..

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION 


BABI NA SHA HUD’U


 Tana shiga gida parlor ta iske yan gidansu da gudu ta isa ta fad'a kan Ammi tana dariya 

“Ammi nah i miss u so much.”


D’agota Ammi tayi 

“Nayi fushi dake.”


A shagwab'ance tace 

“kiyi hak'uri Ammi nah.”


kallonta ammi tayi

“Wasa nake maki my dota ai baki laifi.”


“Ammi nah nagode.”


“Ya mai jikin?”

“Yaji sauk’i sosai Ammi.”


Juyawa tayi tace 

“Mummyn zarah ina wuni.”


 Amsa mata tayi fuska sake abin ya bata mamaki dan tunda take bata tab'a ganin ta mata fara'a ba sai yau, katseta ammi tayi tace 

“Tashi kije d'aki kiyi wanka ki huta.”


Mik'ewa tayi tana tambayarsu “

Ammi ina su zarah?”

Mummyn zarah tace 

“Sunje saloon basma kuma sun fita da Salman.”


Murmushi Aysaah tayi 

 “Ya Salman ya bani kenan dan sai auta ta naka sa mashi aljihu.”

Dariya sukayi su duka.....


Haka dai rayuwa ta cigaba da wakana wajen Aysaah kuma babu abinda take so sai ranar da Salman zai gaya mata yana santa kullum adu'anta kenan, shiko Salman soyayya mai k'arfi ta shiga tsakaninshi da Sahr dan yanzu bai wuce 2weeks bai je kd ba, kuma duk abinnan bai gayama Aysaah yana da budurwa ba....

        

Asad ne zaune gaban iyayenshi yace 

“Daddy yanzu dole sai munkoma cairo da zama? Wlhi ban san nayi nesa da Aysaah tana buk'atar taimkona pls Daddy ni dai ku barni nan zan dunga zo maku hutu.”


Dafa kanshi yayi yace 

“Kayi hak'uri Asad ni kaina ba yanda zanyi ne kasuwanci na ya koma can kuma kaima na samo ma ka aiki can d'in kaga tafiya dakai ya zama dole kaje kafara shirye shirye nan da 3dayz zamu wuce.”


Zai k'ara magana Maaah ta d'aga mashi hannu tace 

“Ban sanka da yima mahaifanka musu ba kaje kayi abinda mahaifinka yace, kaga Rayhan itama jibi zata wuce kuma kasan bazata so ace anbarka 9ja ba tunda kasan yanda kuke kai da ita.”


Tashi yayi yana hawaye yawuce d'aki.....


Asad ne gaban Ammi yana gaya mata yana hawaye ita kanta Ammi bata san wannan tafiyan sai dai dole yabi umurnin mahaifanshi daurewa Ammi tayi tace 

“Haba Asad miye to na kuka cigaba fane kasamu kayi hak'uri in dai Aysaah ce baka da matsala zan lallasheta yanda zata fahimce ka.”


Zai k'ara magana sukaji sallamar ta amsawa Ammi tayi tana shigowa ta iske Asad zaune murmushi ta mashi tace 

“Hi bro.”

 Kasa d'agowa yayi su had’a ido.”


Kallon Ammi tayi tace ammi yadai?”

 Jawota Ammi tayi tace 

“My baby ki bud'e kunnenki ki saurari abinda zan gayamaki da kyau kinjini ko?”

D'aga kanta tayi alamar eh.

 “Dama Daddyn Asad ne d'azu ya cema Asad ya shirya nan da 3days zasu wuce cairo kuma sun koma can da zama kenan.”


“Mik'ewa tayi tsaye tace 

“No ammi wasa ya Asad ke maki.”

Sai kuma ta fashe da kuka, matsowa tayi gabanshi tace 

“Ya Asad miyasa zakaman haka kasan yanzu kaine gatana sai da kabari na saba da kai shine zaka man haka yanzu shikenan nika dai zan cigaba da rayuwa?”

sai kuma tafashe da kuka shima kukan yake, ita dai Ammi ta saka masu ido sai da su kayi mai isarsu kana Ammali ta lallashesu takuma fara yimasu nasiha harta samu suka sauko,l ranan sukuku Aysaah ta wuni ko abinci ta kasaci......


BAYAN KWANA UKKU

    Tsaye yake yana masu Amm bankwana Salman zai kai shi airport dan olrdy su Maaah sun wuce, can zai samesu airport rugowa tayi da gudu ta fad'a jikinshi tana kuka.

“Pls Ya Asad karkaman haka karka tafi kabarni kadaure ka cigaba da zama dani.”


D’agota yayi ya share mata hawaye yace 

“Haba my lilsis tafiyana baya na nufin mun rabu kenan ba ah ah zan dinga zuwa ganinki kuma zamu dinga waya ki daina kuka pls kinsan ban san kukan ki.”


Share hawayenta tayi yace

“Yau gud gal kokefa ki tabbata kafin nazo ganinki kun daidaita da suruki na saboda dana dawo aure zan maki.”

Sunne kai tayi tana dariya hannunta ya kamo yazo gabansu Ammi da ita kallon Mummynzarah yayi yace 

“Mummy nasan dama keda d'anki Salman kuke taku rama sis d'ina dan kun ga Amminmu bata magana, pls mummy ga amanarta nan na barmaku adaina mata fad'a dan Allah.”


Murmushi Mummyn zarah tayi tace 

“Idan tayi abun fad'a zan mata.”


“I trust my pretty bama zatayi ba.”


Kallon Salman yayi yace 

“Bro ga amanata nan na bar maka ka kularman da k'anwa kamar yadda kake kula da kanka, bansan tayi maraicin yaya, kasa ido a kanta kasan mi take so ka bata kuma duk abinda take so nasan bazai gagareka ba.”

Dafashi Salman yayi yace 

“Karka damu d’an uwana zanyi yanda kakeso.”


Wani akwati ya d'auko daga cikin mota ya mik'a mata yace 

“my sis karb'i.”


Amsa tayi tana kallon akwatin, agogon hannunshi ya duba yaga jirginsu ya kusa tashi, peck ya mata ya juya yamasu Ammi bankwana ya fad'a mota, shima Salman shiga yayi yama motan key suka wuce yana d'aga masu hannu, da gudu tayi cikin gida tana kuka mai tsuma rai..

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

   


BABI NA SHA TAKWAS


 Yinin ranan Aysaah bata sauko k'asa ba itama kuma Ammi bata ne meta ba dan gara ta barta ta huta, da zazzab'i mai zafi ta kwana da kyar ta iya tashi tayi sallan asuba in da tagama sallan nan tafara shek'a amai.


Ammali ce zaune tayi ta gumi kamar a tsinkureta tashi tayi da sauri tayi hanyar d'akin Aysaah tana murd'a k'ofan cikin ikon Allah taji ta bud'e shiga tayi d'akin tana sallama amma shiru can ta hangota k'asa cikin amai da sauri Ammi ta isa wajenta duk'awa tayi tana kiran sunanta amma bata iya d'aga kanta dungumarta Ammi tayi ta nufi toilet da ita wanke mata jikinta tayi tas kana ta nannad'ota cikin towel kamar wata k'araman yarinya bisa gado ta aje ta nemo doguwan riga tayi ta saka mata sai da ta gyara wurin tas kana ta kira Papa a waya ta sanar mashi halin da Aysaaah ke ciki....

       

Da sallama Papa ya shigo Mummynzarah na biye dashi, amsa masu Ammi tayi shigowa su kayi ciki 

“Mike faruwa ne?”

Cewar Papa yana kallon Ammi nan Ammi ta kwashe komai ta gaya mashi waya ya jawo ya kira Salman Salman na d'auka papa yace 

“Mu boy ka kira family doctor Aysaah ba da lafiya.”


Amsawa salman yayi da toh ajiye waya Papa yayi ya ja dogon numfashi, daga nan babu wanda ya k'ara cewa k'ala.

Salman ne ya shigo tare da doctor tashi Papa yayi ya gaisa da doctor shi kuma Salman ya nufi bisa gado yana tambayan Ammi mike damunta, kasa bashi amsa Ammi tayi saboda hankalinta yana kan Aysaah dake fidda numfashi kad'an kad'an k'arasowa doctor yayi gaban gadon dubata yayi da yan gwaje gwaje kana ya d'aura mata k'arin ruwa magunguna ya rubuta juyowa yayi ya kalli Papa yace 

“Alh fever ne da headache ke damunta amma ga wannan magungunan a siyo in shaa Allah zataji sauk'i nan ba da dad'ewa ba tunda nasa mata k'arin ruwa.”


Amsan takardan Salman yayi ya fita bankwana doctor ya masu Papa kana ya fita.....


Salman ne ya dawo da magunguna hannunshi mik'ama Ammi yayi ta amsa ta aje ya juya zai fita takira sunanshi dawowa yayi ya zauna kallonshi tayi tace 

“ina san magana da kai.”


 “To Ammi.”

“Dama ba wani abu bane ba illah kan matsalan Aysaah...”

Ammi ta kwashe komai ta gaya mashi da lokacin da Papa ya d'ibar ma Aysaah 


“Kuma abinda nake zargi shine Salman Aysaah na san wani wanda ina ga shi bai sani ba kuma bata gaya mashi ba kuma naji dad'in da bata gaya mashi ba saboda kunya itace adon mace yanzu abinda na keso da kai shine idan ta samu sauk'i ka lallab'eta ta gaya maka wa takeso saboda nasan kai zata iya gaya maka nikuma idan harta fad'a wanda takeso in shaa Allah sai na nemo matashi saboda farin cikin Aysaah shine kwanciyan hankali na.”


Numfasawa yayi yace 

“in shaa Allah Ammi zanyi yan da kike so ko dan na dawo da walwalar k'anwata da kuma ke a cikin gidannan.”


“Tashi kaje nagode Allah yamaku albarka.”

 “Amin.”


Masha Allah Aysaah ta warware sarai sai dai har yanzu ba walwala tare da ita gashi suna shirin fara exams dan monday zasu fara Salman yayi yayi ta fad'a mashi wanda takeso tace ba kowa da zaran ya matsa mata sai ta sa mashi kuka dole Ammi tace ya kyaleta, kwatakwata walwala da wasan da ta sa bayi da k'annenta ta daina kowa na gidan ya shiga k'unci idan ka fidda Mummynzarah da bata damu da halin da Aysaah ke ciki ba.


Ammi ce zaune tana tambayan Aysaah ta gaya mata damuwarta Aysaah tace Ammi karatun exams ne shiyasa kuka ganni haka da Ammi ta matsa mata sai ta sama Ammi kuka dole Ammi ta kyaleta.....


Tunda suka fara exams komi ya k'ara rikicema Aysaah dan gani take kwanakin da Papa ya bata matsowa sukeyi, hawaye suka gangaro mata hannu ta d'aga sama tace 

“Allah ka kawoman mafita shikenan na rasa Salman shima Asad ina gab da rasashi.”


Tashi tayi ta nufi d'akin Ammi tana kuka zaunar da ita Ammi tayi dan yanzu ta riga da ta saba da halin Aysaah da anyi abu kad'an sai kuka 

“Yanzu kuma miyafaru?”

 Aysaah cikin kuka tace 

“Ammi yau kusan sati kenan ina try number Asad da yan gidansu tak'i shiga Ammi yanzu ya zanyi naga Asad.”


 D'agota Ammi tayi tace 

“Bangane mi kike nufi ba? Kina nufin baki samu wayoyinsu?”


D'aga kanta tayi alamar eh, waya Ammi ta jawo ta dinga dialing numbers d'insu amma kowace kashe har data Maaah tagumi Ammi tayi tace 


“Karki damu in shaa Allah lafiya kuma kina nan Asad zai zo da kanshi.”

 “Ammi ai bai san mun dawo sabon gidannan ba dan haka gobe idan nafita zanbiya tsohon gidan inba maigadi address d'innan duk idan yazo sai ya bashi address d'in.”

Hakan ma yayi daidai.”

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

  

BABI NA SHA TARA


 Tunda su Aysaah suka fara exams take fatan Allah ya kawo mata sauk'i kuma kullum sai tayi try number Asad da yan gidansu amma stll kashe a ke cemata, duk idan kaga Aysaah sai ta baka tausayi saboda yanda ta rame kamar ba ita ba ta daina walwala kullum cikin kuka take amma duk wannan halin data shiga bai hanata karatun exams ba, saboda burinta taga tafito da papers masu kyau ta cikama Asad alk'awarinshi.

Dan bazata manta ba kafin Asad ya koma cairo watarana suna zaune yana k'ara yimata bayani akan karatunta kallonta yayi yace 

“pretty.”


D'agowa tayi da murmushi ta kalleshi shima murmushin ya mata yace 

“insan me nakeso dake?”


Girgiza kai tayi alamar ah ah asad yace 

“Pretty kiyi karatu sosai saboda ki fito da sakamako mai kyau kin san irin karatunku yana da amfani ga alummar annabi ba dan komai n kesan course d'inki ba sai dan ki taimaki wanda aka cuta kamar talaka za kiga masu kud'in mu zasu iya amfani da kud'insu su takashi tunda sun san bai da abinda zai kaisu kotu koma ya kaisu ba zaiyi nasara ba shiyasa nake san ki rik'e karatunki dan ki taimaki talaka dashi.”


D’ora hannuwanta tayi kan cinyarshi tace 

“in shaa Allah bro sai na baka mamaki zanyi duk yanda kakeso.”


Dariya yayi yace 

“Nagode sosai my pretty.”


Nan suka ci gaba da firansu....

        

Zaune take tana karatu da yake gobe za suyi last paper d'insu tana karatu tana kuka Ammi ce ta shigo d'akin da sauri Ayaah ta goge hawayenta wuri Ammi ta samu ta zauna tace 

“yanzu bakijin magana tun da har zan gaya maki magana ki tsallake kije Aysaah kiyi abinda kikeso tun da ni ban isa dake ba.”


Dasauri Aysaah ta fad'a jikin ammi tace 

“Ammi kiyi hak'uri wlhi kin isa dani ke kad'ai nakeji dad'inki duk gidannan da Allah kiyafeman.”


D’agota Ammi tayi 

“Kinasan na yafemaki?”

“Eh”

“Sai kin man Alk'awarin kin daina kuka hakanan kuma zaki dawo Aysaahr ki kamar ta da.”


 “In shaa Allah Ammi na daina daga yau kuma zan dawo Aysaah ta d'iyar Ammi.”


Rungumeta Ammi tayi tace 

“Naji dad'i sosai my babe Allah yamaki albarka.”


Yau su Aysaah su kayi last paper kowa ya fito yana murna amma banda Aysaah da tayi ta gumi tana hawaye pictures ake tayi, Hanifa ce ta juya bata ga Aysaah ba can ta hangota k'arasawa tayi wurinta ta cire mata hannun da tayi tagumi dashi d'agowa tayi ta kalleta b'ata rai tayi tace 

“Kedai aaysaah ba kijin magana, dan Allah yanzu miye na zuwa nan kiyi tagumi kowa sai ya gane halin da kike ciki, yanzu tashi mu shiga cikin mutane ayi pix d'in dake.”


Zatayi magana kenan Hanifa ta ja hannunta dole Aysaah ta mik'e ta shiga mutane anata pix da ita amma da ka ganta kasan tana cikin damuwa.......     Tunda su Aysaah suka gama exams kullum cikin tunanin mafita takeyi amma bata samu ba, tana zaune d'aki Salman ya shigo da sallama amsawa tayi wuri ya samu ya zauna kusa da ita kallonta yayi yace 

“congrats sis.”

Allah yasa kici amfanin karatun naki amsawa tayi da amin shiru ya gifta can Salman yace 

“Aysaah nayi bincike kan su Asad har can cairo d'in amma gaskia ban samu wani imformation a kansu ba sai dai kawai muciga ba da adua Allah ya bayyanar dasu.”


In ban da hawaye ba abinda Aysaah keyi tunda ya fara magananshi, lallashinta da nasiha ya shiga yimata sai da yaga tayi shiru Salman yace

“Gobe in shaa Allah zanje kd.”

 Sai da gabanta ya fad'i cikin sanyin jiki tace 

“Allah ya kiyaye hanya amsawa yayi da amin.”

        

Tunda ta tashi gabanta ke fad'uwa ko abinci ta gazaci wayanta ne yayi ringing tana dubawa taga sunan Papa nan da nan gabanta ya ciga ba da fad'uwa a sanyaye ta d'auki wayan banji mi aka ce ba.

“Gani nan zuwa.”


Tana aje wayan ta tashi tayi hanyar sauka k'asa parlor ta iske su Papa Ammi da Mummyn zarah wuri ta samu kusa da Anmi ta zauna Aysaah tace

“Papa gani.”


gyaran murya papa yayi yace 

“Aysaah yau alk'awarinmu dake ya cika amma banji kin ceman komai ba kuma na tambayi Amminki tace baki bata sak'o ba shine nace bari naji dafa gareki.”


“Papa gaskia banda wanda nakeso saboda banyi tunanin fara soyayya ina karatu ba.”


“Zab'ina zan baki kenan?”


Girgiza kai tayi 

“Kayi hak'uri Allah bansan wanda zaka bani kubar ni haka ba zanyi aure ba.”


Tsawa Mummynzarah ta daka mata tace 

“Ubanwa zai kyaleki haka shasha sakarai wadda ba tasan mi ta keyi ba to dole ko kinaso ko bakiso ki auri wanda mahaifinki zai baki yarinya duk kin lalace.”


Ran Ammi ya b'ace 

“Haba hajia mi yarinyar nan tamaki kika tsaneta haka kefa kika haifeta idan ba kija d'iyarki a jiki ba kika bata k'auna da kulawa waye zai bata amma kinbi kin tsani yarinya ko rab'owa tayi wajenki sai kin mata tsawa, kuma da kike cewa anbi an lalata yarinya ni kenan na lalata ta Allah yaga zuciyana irin tarbiyan da na bata ban bata muguwar tarbiya ba amma nagode.”

Aysaah tace

“Ammi kiman rai dan Allah.”


Tashi Ammi tayi ranta b'ace itama Aysaah mik'ewa tayi tana mik'ewa jiri yafara d'ibanta Ammi ta fara kwalama kira kafin Ammi ta juyo ta yanke jiki tafad'i da sauri Ammi ta dawo duk'awa tayi ta fara jijiga Aysaah amma Aysaah tayi nisa sai ma jini dake fitowa daga bakinta........

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

  


BABI NA ASHIRIN


 Duk'awa Ammi tayi kan Aysaah 

“Ki tashi dan Allah karki mutu ki barni.”


Sai kuma ta saka kuka da sauri Papa da Mummynzarah su kayo kan Aysaah d'aga masu hannu Ammi tayi

 “Karku k'araso wajen nan dama ai baku son kuga tana rayuwa duka Aysaah nawa take da za'ace dole sai yayi aure yanzu to gashinan ta bar maku duniyar sai ku zuba ruwa k'asa kusha kuma wlhi idan Aysaah ta mutu nagama zaman gidannan Mummynzarah burin ki ya cika kinyi sanadiyar raba d'iyarki da kika haifa da cikinki da duniya sai ku ciga ba da rayuwanku kuda wanda kukeso.”


Dukkansu jikinsu yayi sanyi tashi tayi ta je ta kira driver da taimakon driver suka saka Aysaah mota suka nufa hanyar asibiti Papa ne ya kalli mummynzarah da tayi tagumi 

“gaskia Nafisa ta fad'a mana kuma kalamanki kan yarinyar nan yayi tsauri ban san mita maki ba kin tsaneta kefa kika haifeta yanzu ba dan Allah yasa ta samu marik'iya mai tsoron Allah ba ya kika gani yakamata ki farka kija d'iyarki jikinki ki bata kulawa kamar sauran yaranki yanzu an wuce wannan zamanin k'auyancin nasan ba zata sake da ke ba kamar yadda take sakewa da Nafisa amma ki dinga bata kulawa koyane.”


Numfashi taja 

“Yanzu ba lokacin wannan maganan baneba tashi mu bisu asibitin.”

        

Suna isa asibitin da sauri Ammi ta fita taje ta samu nurses ta masu magana gadon tura marassa lafiya aka d'ora Aysaah turata akeyi Ammi na biye na sharan hawaye, ana zuwa k'ofan wani d'aki aka tsaida Ammi shiga akayi da Aysaah ciki su Papa ne suka k'araso asibitin reception suka iske Ammi ta nata safa da marwa ga hawaye suna bin kuncinta, Mummynzarah ce ta tako tazo kusa da ita dafa kafad'anta tayi 

“Ammi dan Allah kiyi hak'uri ki daina kuka tabbas na san bana kyautawa abinda na kema Aysaah amma wlhi bawai ban san ta baneba kawai ina kawaici ne akan tana d'iyata ta fari kuma kina tsaye kanta bai kamata nina dinga shiga harkanta ba kuma maganan da nayi d'azu nasan ban kyauta ba saboda irin tarbiyan da kika ba ma aysaah koni dana haifeta iyakar abinda zan mata kenan dan Allah kiyi hak'uri ki yafeman.”


D’ago idanuwanta tayi da suka rine suka zama ja saboda kuka 

“Shikenan Mummynzarah ya wuce na yafe maki Allah ya yafemana baki d'aya ita kuma Allah ya bata lafiya.”


Nan suka rungume juna suna kuka sai da Papa ya masu nuni da asibiti suke....


BAYAN AWA SHIDA

 Awan Aysaah shida cur cikin d'akin marassa lafiya amma bawani bayani tun Ammi na daurewa harta fara kuka da kyar aka samu tayi shiru. likitoci uku ke kan Aysaah dan ceto ranta amma abun yaci tura, alwallah Ammi ta tashi tayi nafila ta fara yi tana nemar ma Aysaah sauk'i....


Wani saurayi ne ya fito mai kimanin shekara talatin a dunia handglop d'in hannunshi ya cire wata nurse ya tambaya 

“Ina iyaayen patient d'innan?”


Nuna Ammi tayi k’arasowa likita yayi ya mik'ama Papa hannu yace

“Alh kar dai ace d'iyarka ce?”

 “D'iyata ce.”

Girgiza kai doctor yayi yace

 “Alh ina san ganinku office d'ina.”


Tashi su kayi suka bishi office d'inshi da sallama suka shiga amsa masu yayi kana yace su zauna....

       

Bayan sun zauna suka sake gaisawa rubuce rubuce doctor yayi kana ya d'ago kallon Papa yayi

“Alh wacece mahaifiyar yarinyar?”


Ammi ya nuna doctor ya kalleta da kyau 

“Hajiya garin ya akayi d'iyarki ta kamu da ciwon zuciya haka mai tsanani?


A razane Ammi ta d'ago 

“Ciwon zuciya?”

“Eh d'iyarki ta kamu da ciwon zuciya sakamakon akwai abinda take so bata samu ba ko kuma tana gab da rasa abun kuma gaskia idan harta rasa abinda takeso kuma ta cigaba da saka damuwa a cikin ranta to zafa ta iya rasa rayuwarta dan yanzu haka da kyar muka samu muka daidaita bugun zuciyan ta kuma aman jinin ya tsaya tunda nake amsar patient bantab'a cin karo da na irin d'iyarki ba.”


In banda kuka ba abinda Ammi keyi shiko Alh gumi yake sharewa ita kanta Mummynzarah sai da tayi kuka doctor yace 

“Alh ku kwantar da hankalinku zata samu sauk'i in shaa Allah tunda yanzu mun gano kan matsalan, amma gaskia idan ta cigaba da saka damuwa a zuciyanta to fa nan ba da dad'ewa ba zata iya rasa rayuwarta saboda zuciyanta ta raunana.”


Papa yace 

“In shaa Allah bama zata rasa ba zamuyi iyakar k'ok'arinmu.”


 “Yauwa Alhaji.”


 “Zamu iya zuwa muganta?”

 “Eh sai dai kar ayi hayaniya saboda halin da take yanzu ba tasan hayaniya.”

Godiya sikama doctor suka tashi suka fita....

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

  

BABI NA ASHIRIN DA D’AYA


KADUNA

  Salman ne gaban iyayenshi yana masu bayani, numfasawa Daddy yayi yace

“Naji komai Salman amma kaga yama iyayenka kana neman aure?”


Girgiza kai yayi da ah ah. 

“Salman ai bani ya kamata ka samu da maganan aure ka ba iyayenka ya kamata ka samu ka masu magana sune zasu nemo maka auren ni bani da hurumin da zan nemo maka aure.”

“Gaskia ne bamu zaka samu da maganan auren ka ba Ammi da Papa ya kamata kamasu magana saboda sune iyayenka su suka reneka.”

Mummy ce ke ma Salman magana 

“Hakane in shaa Allah dana koma zan masu magana.”


Mufeeda tace 

“Bro Aysaah ta sani kuwa?”


Mrmushi Salman yayi yace 

“Tasani.”

“Mitace?”

“Batace komai ba.”


“Allah sarki Aysaah da ya Salman yasan irin san da kike mashi da bai saurari wata ba Allah ya baki ikon cin jarabawanki.”

Duk azuciyaMufeeda ke wannan maganan....

     

Suna shiga d'akin suka iske tana barci duk ta rame gawani fari da tayi duk wanda yaga Aysaah sai ya mata kuka, Ammi ce ta k'arasa gaban gadon hannunta ta d'ora kan goshin Aysaah

“Haba Aysaah yanzu akwai abinda ki keso shine ban sani ba miyasa zaki man haka miyasa zaki kasa gayaman matsalanki ko dan na magance maki ita gashi yanzu kin jefa kanki cikin mawuyacin hali in shaa Allah Aysaah saina samo maki maganin matsalanki in dai bai sab'ama Allah ba sai kinyi dariya farin cikinki yadawo.”


Surutai ta keyi ita kad'ai kamar Aysaah na jinta sai kuma ta fashe da kuka Mummynzarah ce ta taso tazo ta kamota zaunar da ita tayi tana lallashinta harta samu tayi shiru.


Papa ne ya jawo waya ya kira Salman yake gaya mashi nan fa Salman ya rud'e 

“Papa gani nan zuwa.”


“Salman za kayi dare kabari sai gobe kaji my son.”


Amsawa Salman yayi da to ba wai dan yana so ba sai dan ya zama dole...


WASHE GARI

Zaune take gaban gadon ta ta rik'e hannunta kamar wani zai kwace mata ita doctor ne ya shigo da sallama amsa mashi Ammi tayi gaida Ammi yayi da tambayan ya mai jiki Ammi ta amsa da sauki.

K’arasowa yayi gaban gadon Aysaah gwaje gwaje yayi kana ya sake d'aura mata k'arin ruwa kallonshi Ammi tayi tace 

“Doctor har yanzu fa bata farka ba tun jiya.”

“Hajia karki damu dama mun fisan haka saboda zuciyanta ta samu natsuwa dan ta koma normal idan tana baccin sai tafi samun sauk'i karki damu d'iyarki zata tashi at any time.”


Godia tama doctor sosai, bankwana ya mata kana yatafi Mummynzarah ce ta shigo tashi Ammi tayi ta tare ta tare da karb'an kayan hannunta 

“Ammi ya jikinta?”

 “Dasauk'i.”

“Ya abinci nan.”

“Ban banjin yunwa.”

 “Haba Ammi daurewa zakiyi inba sokike kema abaki gadon ba.”

Dole yasa Ammi cin abinci....


12:00pm

K'arfe sha biyu su Salman da yan gidansu suka iso asibitin Papa su kama waya ya gaya masu room number d'in suna isa su kayi sallama suka shiga da murna su Ammi suka tarosu hankali Salman duk bai kansu gadon Aysaah ya matsa ganin halin da take ciki yasa Salman zubda hawaye juyowa yayi yace

“Ammi mike damun baby doll?”


Cikin hawaye Ammi ta gaya masu abinda doctor ya fad'a babu wanda bai yiwa Aysaah kuka ba Salman yace

“Haba Aysaah yanzu kina da damuwa shine baki iya gaya muna haba Aysaah why? miyasa zaki mana haka.”

D’ora kanshi yayi bisa cikinta yana kuka sosai Ammi ce tazo ta janyeshi itama tana kuka tace

“Salman yanzu ba tym d'in kuka bane ba adua zamuyi mata harta samu lafiya duk inda farin cikin Aysaah yake zan nemo matashi idan har shine zai sakata nishad'i tadawo Aysaah tada.”


 Itama kuka ta keyi da kyar aka samu su kayi shiru 

“Ni nasan miye Aysaah ke so nasan miyasa Aysaah cikin wannan halin kedai Mufeedah ba ruwanki kibari harta warke zata fad'i da kanta.”

 Duk cikin zuciya Mufeedah ke wannan maganan...

      

Daddy yace

 “Ya isa hakanan yanzu ba lokacin kuka bane ba adua zakuyi mata ba kuma bari muka gaisa ba.”

Zama su kayi suka gaisa tare da k'arin tambayan mai jiki, daddy yace 

“Papa why not afitar da Aysaah india?”

“Nima nayi tunanin haka amma kuma naga itama asibitinan na da kyau shiyasa amma mubari zuwa gaba mugani idan ba'a samu canji ba sai amasu visa su wuce kawai..”

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION


BABI NA ASHIRIN DA UKU


 Zaune take haraban asibitin tana latsa waya doctor ne yazo round yana zuwa wajen gadon Aysaah ya ga batanan.

“Ammi da tafito daga toilet ya kalleta yace

“Hajiya ina patient d'ina?”

“Ai tuni ta fita haraban asibitin wai bazata k'ara zama ba tunda ta warware dan haka sai ka sallameta.”

Dariya yayi sosai yace

“Karta damu Hajiya yau zanyi discharging d'inta.”


Ammi ce ta kirata a waya, shigowa tayi tana ihun da ta saba yi a gida bata kula da wanda ke d'akin ba ta k'araso da gudu ta fad'a kan Ammi d'agota Ammi tayi taja hancinta tace

“Naji dad'in ganin ki haka d'iyata Allah ya k'ara maki lafia.”


Kamar daga sama taji ance

“Amin.”

 juyawa tayi ta kalleshi tace

‘Ammi nah baki ceman doctor na ciki ba.”

“Idon ki ya rufe ina zaki ganni?”


 Fad'awa tayi jikin Ammi tana dariya 

 “My patient yau zan sallameki dan naga kin samu sauk'i har kina yawo ciki asibiti..”

        

Dariya Aysaah tayi tace 

“Ah ah fa kawai naje ganin yanda asibitin take.”


Takardan ya mik'oma Ammi yace

“Gashi nan na sallamar d'iyarki.”


Dariya ammi tayi tace 

“Na gode doctor da irin kulawan da kaba my one nd only dota.”


 Murmushi yayi yace

“Bakomai Ammi Aysaah ai k'anwa tace nima.”


Kallon Aysaah yayi yace 

“Rigimammar Ammi sai nazo ganin ki.”


Shigewa tayi cikin jikin Ammi tana dariya shima dariyan yakeyi.....

     

Waya Ammi ta kira Pap ta gaya mashi an sallamesu Papa ne da Salman su kazo d'aukansu tun da Salman ya shigo Aysaah ta daina fara'a shi kuma sai janta yake da wasa amma bata kulashi kallon Ammi yayi cikin damuwa yace

“Amminmu kinga dai babynki tunda ta warke ta daina kulani pls Ammi idan laifi na mata kice tayi hak'uri.”


 Dafashi Ammi tayi tace

“Karka damu my boy ba kamata komai ba kasan bata da isasan lafiya amma zaku koma normal kasan kaida ita ba'ajin kanku..”


BAYAN KWANA BIYU

 Aysaah ta warke sosai amma tunda suka dawo ta fita harkan Salman shi kuma abun na damunshi, yau ne su Mummyn Mufeedah zasu koma Salman ne ya shigo d'akin Aysaah da sallama amsa mashi tayi amma bata d'ago ta kalleshi ba zama yayi kusa da ita yace 

“Baby doll zanje kd mai da su Mummy amma 2days zanyi in dawo.”


 Shiru tayi bata ce komai ba tashi yayi ranshi b'ace ya fita yakai bakin k'ofa Aysaaah tace 

“Allah ya kiyaye ka gaida Sahr.”


 Juyowa yayi ya kalleta amma inda yake bata kalla ba. Yana fita itama ta fita zuwa tayi tai bankwana dasu Mufeedah kana ta dawo d'aki...


Ammi ce ta shigo d'akin Aysaah na ganinta ta tashi taje ta rungumeta magani Ammi ta bata tasha. Kiran sunanta tayi wanda da taji Ammi ta kirata to maganan na da muhimmanci amsawa tayi da naam 

“Magana nakeso nayi dake dan haka kiban hankalinki.”

“Waye kikeso?”


D'agowa tayi da sauri tace 

“Ammi ni?” 

“Eh ke.”

Girgiza kai tayi tace

“Ba wanda na keso fa Ammi.”


 Murmushi Ammi tayi tace 

“Kuma k'arya bata maki kyau ba tabbas nayi zargin akwai wanda kika kamu da san shi amma shi bai sani ba kuma ke KUNYA ta hanaki ki fad'a mashi sai gashi zargina ya zama gaskia saboda randa kika farfad'o kin fad'i wasu maganganu wanda ya nuna akwai wanda kikeso.”


Tashi Ammi tayi ta k'araso kusa da ita tace 

“Aysaah idan baki fad'aman damuwanki ba wa zaki fad'amawa dalilin damuwa yasa kika shiga halin da kike yanzu dan Allah ki daure ki fad'aman waye kikeso nikuma namaki alk'awarin ba kishi in dai yana da halin kwarai.”


“Ammi nifa ba wanda nakeso sai dai idan zafin ciwo ne.”


“Ninasan wanda Aysaah keso Ammi.”


 Gaba d'aya suka kalli k'ofan Hanifa ce tsaye ta had'e hannuwa k'arasowa tayi tace

“Ammi nasan wa Aysaah ke so kuma yau zan gaya makishi kodan ta fita halin da take ciki..”


Aysaah da sauri ta d'ago ta kalli Hanifa tace

“Haba bestie kar muyi haka dake pls, Allah ammi karki saurareta k'arya takeyi ni ba wanda nakeso.”


Dafata Hanifa tayi tace 

“Bestie kiyi hak'uri dole na fad'ama Ammi waye ki keso saboda nasa tana da magani matsalanki, nagaji da ganinki cikin damuwa aAyaah dole tasa zan karya alk'awarin dana d'aukar maki kodan ganin d'orewan lafiyanki.”

Kallon ammi tayi tace

“Ammi dama bawani Aysaah ke so ba illa.......”

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

  


BABI NA ASHIRIN DA BIYU


BAYAN KWANA BIYU


  Zaune suke d'akin da aka kwantar da Aysaah in banda k'aran fan ba abinda ka keji Ammi ce tayi ajiyan zuciya ta kalli Papa 

“Ni dai rashin farkawan yarinyar nan yana damuna ace kwananmu biyu yau amma ko motsi ba tayi kuma da nama likita magana sai yace zata iya farfad'owa kowane lokaci.”


Salman yace

“Ni kaina abun na damuna.”


kallonsu Papa yayi

“Haba Ammin Aysaah kin san fa likitocin nan na bakin k'ok'arinsu tun da su kace zata farka zata farka ki daina saka damuwa aranki.”


Mummynzarah tace 

“Ki daina damuwa Ammi d'iyarki ta kusa farkawa in shaa Allah kaima my boy ya kamata ka daina saka damuwa kaifa namiji ne kai da aka san namiji da zama strong amma shine kake damuwa haba my boy be a man mana.”


Girgiza kai salman yayi 

“Allah mummynah ciwon baby doll yana d'agaman hankali.”


“Nasani amma adua ita ya kamata mudin gayi yanzu ka tashi kaje zaka kai su Mummyn Mufeedah unguwa.”

     

“Ammi Karki tafi kibarni dan Allah Ammi karki tafi wlhi shi nakeso shine zab'ina Ammi kice karsu ban wani suban zab'ina.”

“Ba Ammi ba harta Papa sai da maganan Aysaah ta bashi mamaki dama akwai wanda Aysaah ke so shine ta kasa fad'a to wannan waye?”


Tambayar da babu mai amsarta sai ita, Ammi ce tace

“Aysaah lafiya?”


Bud'e idonta tayi kallo tabi Ammi dashi sai kuma ta rufe idonta Papa ne da sauri yaje ya kira doctor, yana zuwa yayi dube dube ya mata allura kallon Ammi yayi yace 

“Congrats hajia d'iyarki ta farfad'o kuma ba wata matsala yanzu sai dai d'an abinda ba'a rasa ba.”


Murmushi Ammi tayi tace

“Nagode doctor...”


D'akin cike yake da mutane yan dubiya harda Hanifa tana farkawa ta fara kiran sunan Ammi da sauri Ammi ta k'araso gabanta hannu ta mik'a mata kamata Ammi tayi ta tadata zaune kallon Ammi tayi ta mata murmushi tace

“Ammi zanyi sallah.”


Da taimakon Ammi Aysaah tayi wanka tayi alwalla zuwa tayi ta kabbara sallah sai da tabiya bashin sallan da ake binta kana ta ma Ammi alamun ta gama kamata Ammi tayi ta mai data bisa gado kowa sannu yake mata ita dai ta bisu da kallo kawai Hanifa ce da Mufeedah suka k'araso wajen gadon suna tambayanta jiki Aysaah ta ce

“Dasauk’i” 

Kallonta Hanifa tayi ta bud'e baki za tayi magana kenan Ammi ta k'araso wajen da abinci a plate..

       

Abinci take bata ta naci Salman ne ya shigo da sallama ganin Aysaah zaune tana cin abinci da sauri ya k'araso gaban gadon, kallonta yayi yace 

“My baby doll sannu.”


 kau da kanta tayi gefe guda, 

“Ammi kawo na dinga bata.”


Da sauri Aysaah tace 

“Ah ah Ammi na nike nakeso.”

 Nan fa suka fara rigima dariya kawai ake masu Mummynzarah tace 

“My boy taso kyalesu.”


Mummyn Mufeedah tace 

“Salman daga fara samun sauk'in yarinya shine har zaka fara matsa mata?”

 Kumbure fuska yayi ya fita yabar d'akin yana gunguni dariya suka bishi da ita..


Doctor ne ya shigo ganin Aysaah zaune yace

“Eyyeh my patient kin samu sauk'i fa.”


D'aga kai tayi tace 

“Eh mana ko yanzu kayi discharging nawa ma.”

 

Dariya yayi yace 

“Da sauranki yanmata ba yanzu zan sallame ki ba.”

Dubata yayi kana ya mata alluran bacci kallon Ammi yayi yace

“Yau yarinyarki tasha surutu da yawa dan haka na mata alluran bacci dan tasamu sauk'i sosai..”


Salman ne ya shigo d'akin yana had'e rai shi ala dole an mashi laifi kallonshi Mufeedah da Hanifa su kayi suka kwashe da dariya harara ya wurga masu yace 

“Besty harda ke ko?”


Murmushi tayi tace 

“Ya Salman kaine da abin dariya Allah fushi bai maka kyau dama ka daina.”

Mufeedah tace

“Tayani gaya mashi sis.”


“Ammin baby doll kina jinsu fa?”

“Gaskia suka fad'ama daga samun sauk'in yarinya na zaka fara rigima da ita doka zan sakamaku kan yarinya na bari dai mukoma gida dariya.”

Mummynzarah tayi tace 

“My boy zo nan rabu da Ammi kaji.”


Binsu mummyn Mufeedah tayi da kallon sha'awa gaskia rayuwan gidansu Aysaah na burge kowa komi nasu tare su keyi kansu had'e yake sai dai fatan Allah ya k'ara had'a kansu.

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

  

BABI NA ASHIRIN DA BAKWAI


  Tana shiga kitchen tafara had'a kayan breakfast Amaal ce ta taso da sauri tace

“Uwar d'akina ke da kanki barshi nayi.”


“Na hutar dake yau barshi zanyi komai ke dai duk abinda na b'ata ki wanke kinji ko?.”

Da sauri Amaal tace

“To uwar d'akina.”


Kafin kace wani abu gida ya d'auki k'amshin abincin Aysaah..


9:00am tagama komai jerasu tayi a daining table kana ta nufi d'akinta dan tayi wanka, tana shiga taga Hanifa na barci d'aka mata duka tayi a firgice Hanifa ta tashi tana waige waige....


Ganin Aysaah na dariya abun ya k'uleta, tasowa tayi da sauri, Aysaah naganin ta taso ta fad'a toilet tanama Haneefa dariyan mugunta.....


10:00am

K'arfe goma Aysaah da Hanifa suka sauko cikin shirinsu tsaf suna tafe suna fira duk wanda yaga yan matannan sai sun burgeshi saboda Allah yamasu kwarjini..


A daining suka iske su Ammi, da gudu Aysaah taje ta fad'a kan Ammi d'agota Ammi tayi tace 

“My baby kinyi kyau.”


“Thank you my Ammi.”

”Zo nan Hanifa.”

 Da sauri Hanifa ta isa wajen Ammi, had'asu tayi ta rungume...


Sai da suka gaida kowa kana suka faracin abinci tunda suka zauna Salman ke kallon Aysaah itama shi take kallo tana murmushi, babu wanda ya lura dasu sai Ammi kallonta Ammi tayi tace 

“Zakici abinci ko kuma zaki tsaya shirme.”

 Sunne kai tayi tana dariya...


Sai da suka gama cin abinci Papa yace gaskia Amaal ta iya abinci a shagwab'ance Aysaah tace 

“Papa nifa ce nayi ba Amaal ba ka sanfa Amaal bata iya abinci mai dad'i ba.”


Dariya yayi

“Ashe d'iyar Ammi ce tayi.”


Jawota Ammi tayi jikinta tace 

“Kyalesu my baby sun san ke kikayi santi ne sukeyi.”


Kallon Salman Papa yayi yace 

“My boy inasan magana dakai.”

A natse Salman yace 

“To Papa.”


Gyaran murya Papa yayi yace

“Salman ka girma kuma kaga k'arfina yana k'ara k'arewa ya kamata ka aje iyalai saboda ragamata hannunka zata koma kuma nan gaba kai zaka d'auki nauyi na dana iyayenka dana k'annenka dan haka na baka yan kwanaki ka fito da matar da kakeso ko wacece nikuma zan nema maka auren ta.”


Tunda aka fara maganan kan Salman k'asa yake ita kuma Aysaah sai wasa take da yan yatsu...


D'agowa Salman yayi yace 

“Papa dama ina da wadda nakeso kuma Ammi ta santa.”


Hararan shi Ammi tayi tace

“Ina nasanta idan kana mashi bayani kamashi.”


Salman yace 

“Papa dama ba wata nakeso ba illa Aysaah.”

Da sauri Aysaah ta tashi ta bar wurin tana dariya...


Da murna Papa yace

“Alhamdulillah magana ta k'are Salman na baka Aysaah duniya da lahira.”


Ammi tace 

“Oh hukunci za'ayiman da d'iyata?”

Dariya Papa yayi yace 

“ohh afuwan Ammi nayi shishigi fa.”


Mummynzarah tace 

“Ammi gamu da k'ok'on baranmu a taimaka abamu auren Aysaah...”


“Zan baku amma wit one condition kada ku dinga matsama d'iyata, ga bana ma kuna matsa mata bare na kaimaku ita yanzu.”

Dariya mummynzarah tayi

“Zamu kiyaye.”

Kallon Salman ammi tayi tace

“Kaje ka nemi so wajen Aysaah..”


“Ammi ainmun daidaita kanmu.”

papa yace


“Shikenan Allah yasama abun albarka.”

Amsawa sukayi da amin papa ya sallami Salman tashi salman yayi ya nufa d'akin Aysaahhh....

         

 Da sallama Salman ya shiga d'akin Aysaah amsawa tayi ta mashi izinin shiga...


Yana shigowa d'akin ya tarar da Aysaah zaune duk'awa yayi ya kamo hannun Aysaah yace

“Haba my wife shine kika gudo?”


Dariya tayi tace

 “Ya Salman ya za'ayi na zauna?”

 Dariya yayi ya lakuci hancinta d'agowa tayi ta kalleshi tace 

“Ya kukayi da papa?”


D'aure fuska yayi yace

“Amminki ta hana.”

marairaice fuska tayi tace 

“Miyasa Ammi zatayi hana?”

K'ara d'aure fuska yayi yace 

“Oho ki tambayeta.”


Sanda kanta tayi k'asa tana hawaye d'ago ta yayi ya goge mata hawaye yace

Miye kuka kuma? Toh wasa fa nake maki.”

da sauri ta d'ago yace 

“Eh.”

Kai mashi duka tayi, ta shi yayi yana dariya ya bar d'akin....

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION


BABI NA ASHIRIN DA HUD’U 


 Ammi ba wani Aysaah ke so ba illah Salman. Da sauri Ammi ta d'ago 

“Salman?” 

“Eh Ammi Salman duk halin da Aysaah ta shiga na son Salman ne. Ammi Aysaah ta fara san Salman tun bata san miye so ba tun ran da Aysaah ta gane tana san Salman take tayi kuka kamar ta cire ranta....” Hanifa ta kwashe komai ta gaya ma Ammi ba abinda ta rage mata.


D'agowa Ammi tayi ta kalli Aysaah dake faman kuka dafa kafad'anta tayi tace

“Tabbas kin cika yar halak kuma nayi alfahari da samunki a matsayin d'iya so da yawa ina tunanin dama ni na haifeki nasan zan yi alfahari dake.”


Fad'awa tayi kan Ammi tace

“Ammi yanzu ma zakiyi alfahari dani kumani banda wata Mama bayan ke.”


D'agota Ammi tayi ta share mata hawaye tace 

“Nagode Allah da kika rik'e kunyarki saboda KUNYA ADON MACE CE na kumaji dad'i yanda baki bari Salman ya gane shi kikeso ba, Salman da kanshi zai zo yace yana sanki. Hanifa kema nagode kin cika k'awar arzik'i Allah ya maku albarka.”


Tashi Ammi tayi tabar d'akin fad'awa Aysaah tayi kan gado tana dariya Haneefa tafara zolayanta 

“D'iyar Ammi kuka ya k'are daga yau..”

       

“Alh kaduna nakeso naje gobe amma idan na samu yanda nakeso goben zan dawo.”

Ammi ce ke fad'ama Papa kallonta yayi cikin mamaki yace 

“Kaduna kuma? Ina cewa yau yan kaduna suka tafi mi zakijeyi?”


Mumnyzarah tace 

“Ah ah Alh kabarta taje mayb akwai abinda zai kaita mai muhimmanci.”

“Shikenan Allah ya kiyaye hanya.”

“Amin.”

Suka amsa Ammi tace

“Nasan kafin Aysaah ta tashi na tafi amma dan Allah Mummyzarah kar tayi wasa da maganinta nd idan tace ina naje kuce naje minna saboda ban san tasan inda zani.”

“Shikenan Ammi in shaa Allah za'ayi yanda kikeso..”


Tunda Ammi tayi sallar asuba bata koma ba shiryawa tayi k'arfe takwas ta fito daga d'akinta daining area ta samu su Mummynzarah gaidasu tayi kana tasamu wuri ta zauna abinci sukeci suna fira sai da ta gama tsaf ta kalli Mummynzarah tace

 “Mummynzarah ga amanar d'iyata nan na yau kawai dan Allah ko tsawa kar amata.”


Papa yace 

“Bazan bari amata ba Amm Aysaah.”


Godiya tayi ta tashi har wurin mota suka rakata, juyowa tayi tace 

“Idan babynah ta tashi taci abinci tasha magani kuma idan ta tambaya inda naje ace naje minna yau zan dawo.”

“In shaa Allahu zanyi yanda kikeso.”


 Godiya tayi ta shiga mota driver yaja sai kd fatan Allah yaba Ammi sa'an abinda taje nema amin.....


Cikin shigan k'ananan kaya ta fito parlor taci karo da Mummynzarah gaida ta tayi takuma amsa cikin sakin fuska tare da tambayan ya k'arfin jiki da sauki tace tashi tayi ta nufi d'akin Ammi 

“Aysaah zonan.”

Yau ce ranan farko da Mummynxarah ta ambaci sunanta dawowa tayi ta zauna kallonta Mummynzarah tayi tace 

“Amminki taje minna amma yau zata dawo.”


Kwalla ta farayi 

“Shine bata ta dani muka tafi tare ba kallonta.”

“Bakida lafiya shiyasa itama taso tafiya dake amma ciwonki yahana amma yau zata dawo, yanzu tashi kije kici abinci kisha magani.”

Dole Aysaah ta tashi idan ta tsaya gardama yanda takema Ammi tasan ba zataji da dad'i ba.....


12:30pm

Sha biyu da rabi su Ammi suka isa horn akayi maigadi ya wangale masu gate shiga sukayi haraban gidan suka samu wuri sukayi parking, fita tayi ta nufi cikin gida da sallama Mummyn mufeedah na ganinta ta taso da sauri ta tari yar uwarta tana tambayanta lafiya? Murmushi ammi tayi tace 

“Lafiya lau anty.”

 “Hamdala Mummyn Mufeedah tayi sai da Ammi taci ta k'oshi kana ta kalli Mummyn Mufeedah da Daddy tace 

“Anty alfarma nazo nema wajenku.”

“Wace iri ce yar uwata fad'aman in dai ba tafi k'arfinmu ba zamuyi maki.”


Zama ta gyara tace 

“Anty kunsan dai Aysaah ba tada lafiya ko?”

.Eh”

sukace a tare to ba komai baneba ciwon Aysaah illa............. Ta kwashe komai ta gaya masu tasowa tayi tazo kusa dasu ta durk'usa tana hawaye tace 

Anty dan Allah ina san Salman ya auri Aysaah wlhi anty bansan ganin Aysaah cikin damuwa.”


D’agota anty tayi ta share mata hawaye gyaran murya daddy yayi yace 

“Haba Nafeesah ai kuke da hukunci da Salman wallahi duk yan da ku kayi dashi duk d'ayane ni kaina na mashi kwad'ayin Aysaah saboda kyawawan halayarta.”


Anty tace

“Haba autan Mama kinsan duk abinda kikeso shi nakeso dan haka Salman bai da wata mata bayan Aysaah.”

 Rungumeta Ammi tayi tana godiya. Daddy ne ya d'auki waya yakira Salman yazo yanzu sun asan ganinshi....


 Salman ne ya shigo da sallama ganin Ammi zaune yasa ya saki baki tashi tayi ta kamoshi tana dariya 

“My boy toh rufe bakin.”


Dariya shima yayi zama yayi ya gaidasu, daddy ya kalleshi yace 

“Mamanku dama kesan magana da kai shine tazo.”

Kallon Ammi yayi tashi Ammi tayi tazo kusa dashi tace 

“Alfarma nake nema.”

 Rufe mata baki yayi yace 

“Ammmi kifad'i abinda kike buk'ata ni kuma zan zama mai biyayya a gareki.”


Kauda kai tayi tace 

“So nake ka auri Aysaaah.”

 Da sauri ya d'ago yace

“Ammi aysaah?”

“Eh ita nakeso ka aura.”


Marairaicewa yayi yace 

“Allah Ammi bata sona ki gafa yanda ta canjaman kwana biyu.”

 Dafashi Ammi tayi 

“Ai kai zaka koya mata sanka my boy.”


Kallon iyayenshi yayi yace 

“To Mummy Daddy Sahr fa?”


Daddy yace 

“Nayi bincike kan yarinyar iyayenta ba dattawan arzik'i baneba dama yau na kesan namaka magana akanta.”

Shikanshi yasan abinda mahaifinshi ya fad'a gaskia ne iyayenta ba dattawan arzak'i baneba dan yanzu haka bat 9ja wai ta tafi london weekend kuma ita kad'ai kallon Ammi yayi yace 

“Shikenan Amminmu zanyi yanda kukeso.”

Rungumeshi Ammi tayi tana shimai albarka......


D'aki ya shiga ya rasa abinda yake mashi dad'i waya ya d'auka ya kira Sahr amma da mamaki wani namiji ya d'auka Salman yace 

“waye?”

“Saurayinta ne.”

 Abinda aka bashi amsa kenan, 

“Kum hutu ta zoman karka k'ara kiranta kabari har sai tadawo.”

Kashe wayan Salman yayi ya tura mata sak'o akan shi kam ba zai iya aurenta ba tunda dama halin da take ciki kenan da mamakinshi yaga reply d'inta da ok.... 


Kwance yake yana tunanin Aysaah komi nata ya dawo mashi a memory duk abinda ya tuna sai yayi dariya 

“Tabbas babu wadda ta dace da ta zama matata sai Aysaaah to miyasa banyi wannan tunanin ba sai yanzu?”


“Aysaah fa bata sanka kaga yanda ta canja maka.”

Hawaye suka gangaro mashi wata zuciyan tace

“Karka damu kaifa namiji ne kaizaka koya mata sanka..”


Sabon layinshi ya d'auko yamata sms kamar haka,

“Hey my wife nasan baki san waye ba to mijinki ne in shaa Allah wanda yadad'e yana dakon sonki ki saurareni gobe da misalin 8:00pm zan bayyana maki kaina. Love u so much my beautiful wife.”

sending ya mata tashi yayi ya nufa d'akin mummy Ammi ya gani da mummy kallon Ammi yayi yace

“Ammi gobe zanje ga matata dan karwani ya rugani ba Ammi ba har Mummy sai da tayi dariya.”


Ammi tace 

“Karka damu tare zamu tafi gobe, baka gaya mana ya kayi da Sahr ba.”


B’ata fuska yayi yace

“Gaskiya ba matar aure bace ba yanzu haka tana india wai vacation kuma dana kirata wani namiji ya d'auka yana man warning dana mata text akan bazan iya auren ta ba tunda haka halinta yake reply taman da ok..”

Ammi tace 

“Allah shi kyauta.”

“Dan haka Ammi na amince da zab'inku Aysaah ta zama matata.”

 Rungumeshi Ammi tayi tana shi mashi albarka....

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

  


BABI NA ASHIRIN DA BIYAR


 Wayanta taji ya yi k'ara alamun sak'o ya shigo dubawa tayi da mamakinta taga new number da kamar bazata bud'eba wata zuciyan tace

“Aysaah bud'e bakisan waye ba k'ilama Asad ne.”


Karanta sms d'in tayi tunani tafara 

“Waye wannan kuma? Kodai Salman ne ah ah ba Salman bane ba saboda ya Salman bai da wannan number toh waye wannan?”


Amsar da ta kasa samu kenan 

kibari gobe za kiga ko waye tunda yace zai bayyana maki kanshi ah ah Aysaah karki saurareshi kinga Ammi ta maki alk'awarin Salman zai kawo kanshi toh ki bari koma waye gobe zaki ganshi.”


Duk zuciyanta ce ke gaya mata haka aje wayan tayi ta cigaba da harkokinta...


Tunda ta tashi take jin wani farin ciki wanda bata tab'ajin irin shi ba duk wanda ke gidan ya gane tana cikin farin ciki, Mummynzarah ce ta kirata amsawa tayi kallonta tayi

 “Babyn Ammi ya dai naganki cikin farin ciki haka?”


Fad'ad'a dariyanta tayi tace 

“Mummyn zarah saboda Ammi na zata dawo yau ne shiyasa.”

Murmushi mummynxarah tayi tace

 “Kije ki gyara mata d'akinta.”

 Amsawa tayi da toh ta tashi....


Karfe biyar Ammi ta iso Aysaah najin horn ta tashi da gudu taje ta taro Ammi, rungumeta Ammi tayi d'agowa Aysaah tayi tana kuka 

“Ammi shine kika tafi kika barni kuma baki bari mukayi bankwana ba.”


Share mata hawaye Ammi tayi tace

 “Babynah kinfa girma yanzu ki daina kukan banza keda zanma aure kwanannan.”


Rufe fuskanta tayi tana dariya hannunta Ammi taja sukayi cikin gida tanata ma Ammi shagwab'a parlor, suka iske Mummynzarah da fara'a ta tari Ammi Mummynzarah tace

“Ammi daga dawowanki anfara maki shagwab'anko.”


“Kinsan tayi missn d'in Mamanta.”

Dariya tayi.

“Sannu da dawowa ay yanzu zaku cigaba daga in da kuka tsaya.”


Murmushi Ammi tayi tace

“Mummy kinfa sa muna ido.”

Dariya tayi tace 

“Na bari.”


Bayan Ammi taci abinci ta huta Aysaah ta bata sms d'in da aka mata ta karanta cz bata b'oyema Ammi komai, murmushi Ammi tayi saboda tasan waye, 

“Allah yakaimu 8:00pm. S'in muga waye.”


Da sauri Aysaah ta d'ago tace

“Ammi kin amince naganshi kenan?”

“Eh mana my babe ki ganshi kuma ki shirya mashi delicous d'in da kika saba had'ama yayanki kinjinko?”

“Shikenan Ammi nah zanyi yanda kikeso ur wish is my command.”

“Yauwa yar Albarka Allah yamaki albarka amarya.”

Tashi tayi da sauri tafita d'akin tana dariya.....


Waya ta d'auko ta kira Mummyn Hanifa kan tabar Hanifa tazo ta mata weekend ba wata gardama da yake Mummyn Hanifa tasan yan gidansu Aysaah har zumunci sukeyi. Ba'a jima ba Hanifa ta k'araso da gudu Aysaah taje ta tarota rungume juna sukayi suna murna, d'aki suka wuce Aysaah ta gayama Hanifa komai murmushi Hanifa tayi dan ita kanta tasan bak'on bai wuce Salman...


Kitchen suka shiga suka fara aiki suna aiki tana murmushi d'aka mata duka Hanifa tayi tace 

Murmushin mi kike?”


 Ita kanta ta rasa fara'an miye yau takeyi fried d'in couscous sukayi wanda yaji kayan had'i sannan su kayi coslow pepper meat sukayi, coconute drink suka had' ta saka a fridge bakwai daidai suka gama komai mai aikinsu ta kwalama kira tana zuwa tace gani uwar d'akina Aysaah tace 

“Zanyi bak'o k'arfe takwas da yazo ki kaimai abincinnan kafin nazo kinji.”

“Angama uwar d'akina he wishing is me kwamad.”


Dariya Aysaah tayi sosai itako Hanifa har fad'uwa tabkeyi saboda dariya tace haba

“Amaal wai yaushe zaki waye ne? Waya gaya maki haka ake cewa?”

b'ata fuska Amaal tayi tace 

“Ai saiku gyaraman.”

“Naji cewa akeyi ur wish is my command.”

Dariya Aysaah keyi harta bar kitchen d'in......

      

Tana shiga d'akinta ta fad'a kewaye wanka tayi tazo ta tsaya gaban madubi da yake tana fashin sallah tsintar kanta tayi da yin makeup light makeup tayi kana ta feshe jikinta da turaruka gaban wadrobe d'inta taje wata riga red wadda Ammi ta siyo mata ta d'auko ta saka kana ta feshe ta da turare rolling tayi da scarves kallon kanta tayi a madubi so masha Allah nikaina ita dai Hanifa ido ta sakama Aysaah saboda abun na bata mamaki, takwas dai dai sms ya shigo wayanta 

“Ina parlorn bak'i.”

Abinda aka rubuta kenan murmushi tayi

 “Lallai wannan ya cika ji da kai baima iya kirana.....”


Sauka tayi ta nufi parlorn bak'i tana isa bakin k'ofa gabanta yafara dukan uku uku sallama tayi ta shiga tsaye yake ya juya baya shiru akayi ba amsa sai da ta k'ara sallama kana ya amsa cikin husky voice d'inshi juyowa yayi ya kalleta kanta k'asa yake batama san ya juyo ba takowa yayi yazo gabanta kamar daga sama taji yace 

“Baby doll d'agowa tayi da sauri.”

Tabbas ba mafarki takeba Salman ne gabanta dama salman ne ya mata sms?”


Hannunta yaja ya zaunar da ita kallonta yayi yace

“Miye na dogon tunani nine gabanki Salman ne ur lovely broda.”

Saboda tsaban rud'ewa Aysaah ta kasa cewa komai.....


Idonta ya hura da sauri ta lumshesu kiran sunanta yayi amsawa tayi a hankali 

 “Aysaah nasan zaki mamakin ganina ko? Toh karkiyi mamaki ba abinda ya gagari Allah.”


Zuwa yayi ya duk'a kusa da ita hannunta yakamo yace

“Aysaah yau ga Salman gabanki da k'ok'on baranshi kuma sai yanda ki kayi dashi Aysaah ina sanki kuma ina san kizama mother to my unborn child.”

Hawaye suka gangaro mata saboda ko amafarki ba tayi tsammanin Salman zai so ta ba amma yau shine gabanta yana neman ta soshi share mata hawaye yayi yace 

“Yanzu ba tym d'in kuka baneba Aysaah ki taimaki d'an uwanki ki soshi na maki alk'awarin zan saki farin ciki har k'arshen rayuwata.”


D’agowa tayi ta kalleshi kashe mata ido yayi da sauri tayi k'asa da ido 

“Ya Salman naji amma kabari zanyi tunani komi kenan l'll let u knw"


“Ah ah aysaah ba tunani tsakanin mu just tell me nasamu shiga koko?”


Tashi tayi ta kalleshi tace 

“Ya Salman Aysaah ta mallakama zuciyanta sai yanda kayi da ita.”


Tana kaiwa nan ta ruga da gudu, lumshe ido yayi yace

“Masha Allah gaskia am so lucky to have as my wife.”

Zama yayi yaci abinci yayi k'at kana ya nufi d'akinshi.......

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACENAGARTA WRITERS ASSOCIATION

  

BABI NA ASHIRIN DA SHIDA


 Tana shiga d'aki ta fad'a kan HAnifa tana dariya d'agota Hanifa tayi tace

“Lafiya naganki haka?”


Murmushi tayi saikuma hawaye da suka fara gangaro mata share mata hawaye Hanifa tayi

“Miye na kuka?”


Kallon Hanifa tayi 

“Mafarki na ya zama gaskia bestie yau nice gaban ya Salman yana rok'on na soshi ban san yanda zan gaya maki irin farin cikin da na shiga ba yau.”


Kallonta Hanifa tayi tace

“To ai ba hawaye zakiyi ba godia zakima Allah.”


D'aga hannu tayi tana kwararo aduan godia ga Allah sai da ta gama Hanifa tace

“Yau kinga ranan adu'an da kikeyi ko? kinga ranan hak'urinki kuma ko?”


 D'aga kai Aysaah tayi tace

“Gaskiya ne bestie na kuma gode sosai yanda kika dinga encouraging d'ina burina d'aya ya cika saura kuma d'ayan.”


Da sauri Hanifa ta kalleta tace

“Wanene d'ayan kuma?”


Hawayen da suka mak'ale suka gangaro tace 

“Na ganin ya Asad mana inasan naga ya Asad kafin nayi aure ina san ya Asad ya halarci biki na.”


“Hakane ki cigaba da adua in shaa Allah shima kun kusa had'uwa.”

Suna cikin fira wayanta ya fara ringing tana dubawa taga Salman ne murmushi tayi ta d'auki wayan.......


Tana d'auka a shagab'e take magana Salman yace

“Baby doll shine kika gudu ko? Yau fa ne yakamata mu fahimci juna.”


“Allah ya Salman kunyarka na keji”


Murmushi yayi kamar tana ganinshi yace 

“Ai ko zan maki maganin kunyar nan.”


Haka dai suka dinga firan soyayya tsoki Hanifa tayi dan sun matsa mata pillow ta saka a fuskanta da haka har bacci ya d'auketa..


Fira sukeyi kowane yana gayama d'an uwanshi yanda yakeji dare sosai suka raba suna fira daga k'arshe sukayi bankwana ba dan sun gaji da junansu ba.....

    

Text aysaah tama Salman kamar haka 

“Com b with me wen d sun is sleepy.. you making me hold tyt my pillow like u d one. You write in oral... Ya Salman u're d sweet nd socially skilled gud nyt nd dream of me... love u so much.”

Tana gamawa tayi sending ta mai da wayanta ta kashe tana dariya adua tayi ta kwanta tana murmushin jin dad'i.....


Kwance yake yana tuna Aysaah komi nata burgeshi yakeyi sms yaji ya shigo wayanshi yana dubawa yaga Aysaah ce da murmushi ya bud'e text d'in....


Karantawa yakeyi yana sake karantawa murmushi yayi

“Ashe haka baby doll ta iya love.”

dialing number dinta yayi yaji switch off....


Murmushi yayi yamata reply 

“Sometimes ur nearnes takes my breath away & all dat i wanna say cant b expressed than bn in silence... love u so much d Apple of my eyes.”


Haka dai ya dinga juyi yana murmushi shi kad'ai har bacci b'arawo yayi gaba dashi.....


9:00am ta tashi tana kunna wayanta taga sms d'inshi karantawa tayi tana dariya aje wayan tayi ta nufid'akin Ammi.....


Tana shiga d'akin ta fad'a kan Ammi dake lazumi sai da Ammi ta gama kana ta kalleta b'ata fuska tayi tace

“Wai yaushe zaki hankali? Ina lazumi kin fad'oman.”

Marairaicewa tayi tace

“Kiyi hak'uri Ammi bazan k'ara ba..”


Ammi tace Allah yasa 

“Ya naganki haka kamar akwai magana bakinki?”

Murmushi tayi tace

“Ammi kin san waye bak'ona na jiya?”

“Ya za’ayi nasani.”


Dariya tayi ta rufe fuskanta da tafin hannunta tace

“Ammi nah ya Salman ne fa.”


Jawota Ammi tayi ta rungume tace

“Shine ki kejin kunyar gayaman harda rufe fuska?”


Dariya ta din gayi

“Alhamdulillah Allah na godema da farin ciki d'iyata ya dawo kamar da.”


Rungume Ammi Aysaah tayi tace

“Ammi nagode sosai tabbas kin ceci rayuwata Allah ya bani ikon yimaki biyayya.”

Ammi ta amsa da amin....


Kallonta Ammi tayi tace

“Ina Hanifa?”

“Tana can tana baccin banza.”


dariya ammi tayi

“Ai gara ta huta.”


Agogo Aysaah ta kalla tace

“Kai Ammi bari naje na had'ama ya Salman abinci kar ya makara.”


Tana fad'an haka ta tashi ta ruga tana dariya murmushin Ammi tayi tace 

“Allah ya shiryaki Salman ya b'ataman yarinya..”

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

 

BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS


 “Ya Salman.”

A hankali ta kirashi kamar mai jin bacci, wani iri yaji shima amsawa yayi a hankali kana ya dawo ya zauna kusa da ita shiru su kayi bamai ma wani magana....


Kallonta Salman yayi yace

“Ya dai yanmata kin kirani kin kuma yi shiru?”


Kanta k'asa tana wasa da yatsunta 

“Ya Salman Sahr fa?”


Wani iri yaji dan yanzu bai san akira mashi Sahr "ldaurewa yayi yace 

“Tana nan.”

“Mu biyu zaka aura ne?”

Maganan dariya ta bashi dan yasan kishi ne ke damun Aysaah...

“Eh haka nake tunanin had'aku ku biyu.”


Da sauri ta d'ago sai kuma taga ya tsareta da kallo k'asa tayi da kanta tana share hawaye...


Murmushi Salman yayi ya d'ago fuskanta ganin tana kuka ya b'ata rai yace

“Miye na kuka? Ke abun kuka bai maki wuya ko?”


Share hawayenta tayi

“Ni da ita wazaka fara aure?”


Tashi yayi tsaye yace

“Aysaah zan fara aura.”

Shiru tayi bata k'ara cewa komai ba har tsawon minti goma...


Takowa yayi yazo kusa da ita kallonta yayi yana murmushi yace

“Kwantar da hankalinki k’anwata ke kad'ai zan aura in shaa Allah ke kad'aice gidan Salman.”


D'agowa tayi tana murmushi har sai da kumatunta suka lotsa dariya yayi yace

“Ashe dai yarinyar tana da kishi.”

Pillow ta d'auko wurgo mashi tayi, ta shi yayi da gudu ya fita yana dariya...

         

Soyayya mai k'arfi ta shiga tsakanin Salman da Aysaah kullum a gida suna tare idan Ammi ta ishesu da masifa sai su koma suna waya dan Ammi tace Salman ya b'ata mata d'iya da rashin kunya kullum suna mak'ale da juna...


An saka ranan auren Aysaah da Salman da tagama law school da 2weeks...


Salman da Mummyn zarah sunso ayi bikin kafin ta gama amma Ammi tace bata san wannan ba sai d'iyarta ta gama tunda saura 2month ta gama idan kuma ba zasu iya jira ba ya nemi wata.

“kuji ammi da karfin hali tasan fa yanda Aysaah ta mutu kan Salman amma take haka dama yafasa muga yazatayi lolzz.”

Dole Mummynzarah ta lallashi Salman suka hak'ura..


Papa ne ya kira Daddyn Salman yace baya san komai daga gareshi zai ma Salman komai tun da dama Salman d'anshi ne Daddyn salman yayi godia sosai...


Aysaah ce zaune gaban Salman tana kuka 

Shi dai ya kasa lallashinta sai ido daya bita dashi 

“Ya Salman yanzu haka za'ayi bikina ya Asad bai nan? Ya salman inasan ganin ya Asad kafin bikinmu..”


Hawaye ya share mata yace

“Kin san bansan ganinki kina kuka ko?”

D'aga kanta tayi alamar 

“Eh.”

Salman yace 

“Share share hawayenki.”


Kallonta yayi yace

“Aysaah ina bakin k'ok'arina wajen gano Asad amma harnyanzu ba labari kiyi hak'uri mu cigaba da adua in shaa Allah Asad zai bayyana ina ji ajikina.”


kwance take jikin Ammi suna fira wayanta ta fara ringing tana d'auka taga ansaka final choice kallon Ammi tayi sai taga Ammi ba 

ita take kallo ba..


Tashi tayi za tabar d'akin Ammi tace

“Ina zaki?”

“Ammi Hanifa ce ke kirana a waya mayb ta zo ne.”


Sai da takai bakin k'ofa Ammi tace

“Hanifa ce final choice d'in?”

Dariya tayi tabar d'akin da gudu..


Ita kanta Ammin abin dariya ya bata wai Aysaah ce yau ke mata k'arya da Hanifa bayan tasan Hanifa bestie aka mata saving...


parlon bak'i ta tarar dashi da yake dama can suke fira sallama tayi, amsa mata yayi ya ware hannunshi da gudu ta k'arasa rungumeta yayi yace 

“I mmiss u my baby.”

murya can k'asa tace

“Miss you more my man..”


kamo hannunta Salman yayi suka zauna kallonta yayi yace 

“Amarya bakya laifi.”

Dariya tayi tace

“Ban dai yi ba amma nayi Mummynzarah ai sai ta zaneni.”

Dariya yayi sosai...


Wani d'an akwati ya bud'e ya zaro wani zobe hannunta ya kama ya saka mata shi ba k'aramin kyau ya mata ba peck yama hannun kana ya saketa...


Kallonshi tayi tace 

“Thank you Mijina.”

Bata ida ba ya d'ora hannunshi bisa bakinta yace 

“Na hanaki yiman godia ko amma baki bari.”

marairaicewa tayi tace 

“Na daina..


Fira sukeyi sosai hannunta ta kalla taga 11:00pm kallonshi tayi tace 

“Ya Salman dare yayi fa.”

A marairaice yace 

“Allah bangaji da ganinki ba.”

Murmushi tayi tace

“Kayi hak'uri saura kwana kad'an na koma gdanka.”


Salman yace nidai ban yarda ba. peck ta mashi a kumatu ta tashi ta ruga tana dariya. Shima dariyan yayi yarasa miyasa komai na Aysaah da ban yake da na sauran mata komai tayi burgeshi takeyi...

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

  

BABI NA ASHIRIN DA TARA


 Alhamdulillah hausawa sunce duk abinda aka sama lokaci zaizo k'arshe. Yau Aysaah ta zama cikakkiyar lawyer inda dubban mutane suke tayata murnan kammala karatunta lafiya...


Kyaututuka Aysaah ta amshe su abun tun yana burgeta har takai tana mamaki irin kyaututukan data samu..


Tsaye yake ya hard'e hannunshi bakin mota yana kallonsu ita da sauran students suna ta d'aukan pix. Takowa yayi yazo kusa da su yace

“Kuzo na maku to juyowa tayo taga Salman ne.”

Fad'awa tayi jikinshi tana dariya rungumeta yayi sauran students suka fara dariya suna ihu...


Haka dai Salman ya dinga yi masu pix sai marece sosai kana suka taho gida suka aje Hanifa kana suka d'auki hanyar gida suna tafe suna firan soyayya....


Kallonta Salman yayi yace

“Yarinya na ni miye zan bada gift?”

Murmushi tayi tace 

“Kana san na fad'a maka?”

 “Eh...”


Aysaah tace 

“To karkad'e kunnenka.”

Shiiko ya kama kunne ya karkad'e dariya ta din gayi mashi. Kallon shi tayi tace 

“Ya Salman abinda nakeso kawai ka soni har k'arshen rayuwata kayi hak'uri da duk shirme na watarana zan daina shine babban gifts d'in da zakaban..”


Jawota yayi jikinshi yace

“Kisa aranki ke kad'ai ke da zuciyan Salman sai yanda kikayi da ita, kuma ba shirme kikeyi ba yarinta ce kuma ni yarintarki burgeni ta keyi dan haka karki ji komai zan maki hallaci fiye da yanda Naufal yai ma Hudah zan soki fiye da yanda Moh yaso Nafeesarh zan k'auna ce ki fiye da yanda Hamza ya nunama Dijah k'auna.”


Rungumeshi Aysaah tayi k'am tana dariya. A haka har suka iso gida...


BAYAN SATI D'AYA

Salman ne ya kalli su Aysaah yace Hanifa

“Damu dami zakuyi?”

Haneefa tace 

“Bridal shower sai kamu sai dinner kawai..”


Atm d'inshi ya basu yace

“Gashi nan ku ciri abinda zai isheku.”


Amsa Hanifa tayi kallon Aysaah yayi yace

“Ya dai yarinya na ba wata matsala ko?”

 Dariya tayi tace 

“Babu kam.”


Aysaah da Hanifa ne ke yawon rabon iv duk gidajen k'awayensu sai da sukaje dan Hanifa tayi parking ta dawo gidansu Aysaaah sai anga ma biki..


Mai gyaran jiki Ammi ta d'aukoma Aysaah daga mai duguri ita zata mata gyaran jiki ta mata lallai kuma bata zuwa ko ina...


Salman ne ya dinga kiran Aysaah a waya yana san ganinta dan yau kwananshi ukku bai ganta ba k'in d'auka tayi dan tasan halin masifan Ammi...


Part d'in Ammi ya nufa parlor suka had'u dashi kallonshi tayi ta d'aure fuska 

“Ya dai Malama?”

Sosa k'eya yayi yace

“Dama gaidaki zanyi”

 “To nagode jeka.”

har ya juya yace

“Ammi Aysaah fa?”

“Neman mi kake mata?”

“Dama ina san ganinta ne”

“Ba yanzu ba dan yanzu gyaran jiki ake mata.”

fita yayi yana gunguni abin dariya yaba Ammi..


Yau aka kawo lefen Aysaah akwati sha biyu sai key d'in mota duk wanda yaga lefen Aysaah sai ya burgeshi..


Yan kd ma sun taho gida ya cika kamar yau ne ranan bikin...


Aysaah da Mufeedah da Hanifa ne suka kulle kansu k'uryan d'akin Ammi suna fira...


Aysaah ta kalli Mufeedah tace sis

“Ance Sahr k'awarki ce bani labari.”

 Dariya Mufeedah tayi tace

“Ai ke sis ran da ya Salman yace man Sahr yakeso har zazzab'i nayi dan na tausaya maki.”


Dariya Hanifa tayi tace 

“Sis ran da bestie ta gane ya Salman nasan wata karkiso kiga hauka.”

 Nan suka din gayi ma Aysaah dariya harta k'ule sai da sukayi mai isarsu kana suka yi shiru...


Mufeedah tace 

“Ai ta dawo wai yayi hak'uri wlhi she cant do without him waye waye, ai kam yamata spark yace shi yana da mata kuma Aysaah da yake bata labari yarinya mai hankali da tarbiya. Kuma karta k'ara kiranshi idan kuma ta cigaba da kiranshi zaiyi maganinta. Kai in tak'aice maku ta dai na yiman magana saboda ya Salman..”


Aysaah tace

“Ai ni fushi yake dani wai Ammi ta hanashi ganina kuma da amincewa ta, ya kasa gane ni kaina yanda nakeji na rashin ganinshi amma kanshi yasani.”


Kallonta su kayi suka bushe da dariya Mufeedah tace

“Aysaah Allah da gaskian Ammi Salman ya b'ataki.”

Duka ta kai mata 

“Ina ruwanku? Ai dai miji nane....”

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION


BABI NA TALATIN


 Yau aka fara bikin Aysaah da Salman inda sukayi bridal shower amarya ta sha kyau harta gaji shi kanshi angon idan ka ganshi baka gane shi sabo da kyau, ga k'awayen amarya suma sun sha kyau inda sukayi ankon red polo sai sweatpant, duk wanda yaga amarya da ango sai sun burgeshi saboda kyau... 


Sai dare aka tashi a gajiye suka dawo gida tunda suka shigo Salman ke kiran wayanta..


Tana d'agawa yace ina san ganinki bai jira mi zatace ba yakashe waya...


Tagumi tayi Hanifa ce tazo ta zare mata hannu ajiyan zuciya Aysaah tayi ta kalli Hanifa

“Allah bestie rigiman Salman tana ban mamaki.”

“Mi yayi?”

“Wai yana san ganina kamar ba yanzu muka rabu ba.”

Murmushi Hanifa tayi tace

“To sai kije..”


Zaro ido tayi 

“So kike Ammi ta balbaleni da masifa Allah ba zanje ba nasan dai fushi ne idan ya gaji ya daina.”

Tana gama magana taja blanket ta kwanta...


Tunda suka tashi suke ta faman shirye shiryen kamu 4:00 pm daidai aka fara tafiya saboda Papa yace bai san suyi dare nan ma ancashe anyi watsi da naira saidai ango na fushi da matarshi da sun had'a ido sai ya harareta ita abun ma dariya yake bata...


FRIDAY

Feedoh ce kema amarya makeup gaskia fad'in kyan da amarya tayi b'ata lokacine nabar maku masu karatu ku auna da kanku karfe 8:00pm aka fara tafiya dinner..


Amarya ce da angonta bisa high table idan ka gansu sai sun burge ka saboda irin kyan da sukayi. 


biki yayi biki kowa yaci ya k'oshi anyi rawa sosai ango shi da abokanshi sun cashe dan ango har da cire babban riga yana rawa sai 12 :00 aka tashi daga dinner kowa ka gani zaka ganshi da bag mai d'auke da hoton amarya da ango....


Hausawa sunce Rana bata k'arya saidai uwar d'iya taji kunya.

Yau asabar daidai da 22/10/2016 aka d'aura auren Aysaah da Salman akan sadaki naira dubu d'ari da hamsi inda dubban mutane suka shaida harda shugaban k'asa ya halarci d'aurin auren. Ana gama d'aurin aure aka tafi Hilton danyi reception...


Tunda aka cema Aysaah an d'aura aure ta kulle kanta k'uryan Ammi tana kuka ba kukan komi take ba yanda yau aka d'aura aurenta amma Asad baya nan..


Sai da Ammi tayi dagaske kana Aysaah ta bud'e d'akin..


Ammi na shiga d'akin ta wuce toilet tahad'ama Aysaah ruwan wanka zuwa tayi ta kama hannunta ta kaita bakin toilet amma tak'i yarda su had'a ido..


Sai da ta juyo tace

“Kiyi wanka akwai wasu magunguna na zamane ki tabbata da kin zauna su nd idan kika fito ga wasu nan a cup d'innan suma kisha su.”

Tana kaiwa nan tafita batako juyo ba...


Tana shiga toilet ta cigaba da kuka sai da tayi mai isarta kana ta fara wanka...


Tayi duk yanda Ammi ta umurce ta tayi, tana fitowa dai dai su Hanifa da Mufeedah suna shigowa, kaya su aje bisa gado

“Gashi nan inji Ammi tace ki sasu kuma ki shirya da wuri dan yan d'aukar amarya suna kan hanya.”


Suma suna fad'a suka fita dan kowace kuka takeyi...


Tana cikin shiryawa k'anwar Mummynzarah ta shigo d'akin kallon Aysaah tayi tace

“Kin gama shiryawan?”

D'aga mata kai tayi


Alkyabba ta mik'a mata ta saka kana ta kama hannunta suka fito...

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE

  

Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION


BABI NA TALATIN DA D’AYA


 Parlon Papa ta nufa da Aysaah nasiha ya mata mai ratsa jiki.

“Aysaah kibi mijinki kamar yanda Allah yace kiyi hak'uri da duk abinda zaki gani ki b'oye sirrin mijinki tashi kitafi Allah ya maki albarka.”

kuka Aysaah keyi shi kanshi Papa sai da yayi kuka...


D'akin Mummynzarah ta nufa da ita nan ma nasiha ta mata tasowa Mummyn zarah tayi tazo kusa da Aysaah ta duk'a hannunta ta kamo...


“Aysaah nasan zaki tunanin ban damu da ke ba kamar yadda na damu da k'annenki ba haka na nufin ban san ki baneba ah ah kawai dan kina d'iyar fari, kuma Ammi na iyakar bakin k’ok’arinta akanki, amma yanzu zakiji abinda kika dad’e kina so kiji Aysaah wallahi duk cikin yarana babu wanda nakeso sama dake.”

Fad'awa Aysaah tayi jikin Mummyzarah tana kuka ita kanta Mummynzarah kuka takeyi...


D'akin Ammi aka nufa da ita tana shiga ta fizge da gudu ta fad'a kan Ammi kuka suke mai tsuma rai babu wanda bai masu kuka ba...


“Aysaah kije Allah ya baki sa'a tarbiyan da kika samu wurinmu kiyi amfani da ita kinga dai yanda muke zama gidannan da kowa dan haka kiyi wanda yafishi.”

Ammi na kaiwa nan ta tashi tabar wurin tana kuka...


Kiran Ammi Aysaah keyi amma Ammi bata juyoba haka aka kama Aysaah aka nufi gidanta da ita wuse 2


Tunda suka fito gida Aysaah ke kuka har aka kawo wuse2


k'in fitowa tayi sai da aka kira Ammi a waya ban san mi Ammi tace ba tana kashe waya ta fito..


Yan kai amarya sakin baki sukayi suna ganin gida kowa ya yaba da irin kyan gidan Ayaah 3 bedroom sai 4parlor sai kitchen...

         

Yan kai amarya kowa ya kama gabanshi Hanifa da Mufeedah suka rage....


Kallonsu Aysaah tayi 

“Amma dai nan zaku kwana ko?”


Dariya Hanifa tayi 

“So kike ya Salman ya koremu?”


Kuka Aysaah ta fara 

“Miye na kuka?”

 cewar mufeedah 

“Shikenan nan zamu kwana.”

 Rungumesu tayi tana hawaye...


11:00pm

Sha d'aya ango da abokanshi suka shigo Aysaah har ta fara bacci kan cinyar Hanifa duk dan karsu tafi subarta...


wasa da dariya akayi kana abokan ango suka masu nasiha 100k suka ba su haneefa kud'in siyen baki..


Tashi sukayi zasu tafi Aysaah tace batasan wannan ba da kyar aka b'anb'areta jikin Hanifa tana kuka su kansu kukan suke....


Da gudu ta nufi bedroom ta fad'a kan gado Salman ne ya d'agota hawayen ya goge mata 

“Baby doll keda yaka mata kiyi farin ciki ba kuka zakiyi ba, yau fa ranan farin cikinmu ce kiyi hak'uri ki daina kuka nayi alk'awarin zan kula da ke kamar yadda Amminki ke maki bazan maki fad'aba.”


“Kayi alk'awarin bazaka man fad'a ba?”


Shi abun ma dariya ya bashi 

“I promise u yarinya nah.”

Dariya ta farayi har sai da kumatunta ya lotsa...


Haka ya dinga janta da fira har saida yaga ta sake..


Hannunta ya kama suka fita suna zagaya gidan gaskia tsarin gidan ya mata kyau sosai..


Wani lambu ya kaita kallonta yayi 

“Kinga inda zamu dinga wasa muda our unborn child d'inmu.”

 Dariya tayi ta b'oye cikin jikinshi....


D'aki ya nufa da ita kallonta yayi jeki alwalla kizo muyi sallah bata mashi musu ba shima alwallan yayi....


Sallah suka kabbara bayan sun gama sallah ya kama kanta ya mata adu'o'i kamar yanda annabinmu ya umurci duk wani sabon aure suyi. Tambayoyi ya mata kuma alhamdulillah ta bashi amsa..


Tashi yayi ya nufi kitchen ya d'auko plate da cups "kaji ne gasassu ya juye kamo ta yayi ya zaunar da ita bisa cinyarshi kallonshi tayi ya kashe mata ido...


K'asa tayi da kanta haka ya dinga bata a baki sai da ya tabbatar da ta k'oshi kana ya bata fresh milk shima zama yayi ya cika cikinshi kana ya kwashe kayan ya nufa kitchen dasu...


Dawowa yayi ya kalleta

“What next kuma?”

“Bacci"

“Salman yace 

“Ah ah wanka dai.”


“Tashi muje na maki.”

 Zaro ido tayi har sai da tasashi dariya, 

“Yes wanka zan maki..”


Marairaicewa tayi 

“Please Ya Salman Allah zanyi da kaina kuma zan fita sosai.”

Shi dai dariya kawai yakeyi..


Kamota yayi ya rakata bakin toilet d'in. Da gudu ta fad'a toilet d'in ta maidashi ta rufe dariya Salman yayi sosai...


Kayane ya ciro mata na bacci kana ya nufa d'akinshi dan yayi wanka...


Tana fitowa ta shirya ta d'aga kayan da ya kawo mata...


Murmushi tayi dan rigan ana ganin komai na jikinka..


Saida ya kulle ko ina kana yadawo ganinta yayi rungume da riga 

“yabaki saka rigan ba?”

“Ya salman tayi shara shara..”

“Haka kuma zaki sata”

“pls ka can jaman wata.”

“Allah ita zaki saka”

Dol ta saka rigan..


Kwanciya tayi sai da ya masu adu'a kana ya kashe wuta juyota yayi jikinshi nan fa ta fara kyarma tana kuka..


Rad'a mata yayi a kunnenta 

“stop crying ba abinda zan maki”


Amma duk da haka ta kasa daina kukan wasa Salman ya farayi da ita ko ina na jikinta sai da ya shafe kuka Aysaah keyi sosai shiko bai masan tanayi ba

Salman kasa controling kanshi yayi, ita ko Aysaah kuka takeyi tana rok'onshi amma bai san tanayi ba dan ya tafi wata sabuwar dunia...

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION


BABI NA TALATIN DA UKU


BAYAN WATA UKU


  Kwanciyan hankali da zaman lafiya ke tsakani Salman da Aysaahhh...


kullum cikin tattalin junansu suke, kowa burinshi ya kyautata tama d'an uwanshi..


Duk wanda ya ga Aysaah sai ta burgeshi saboda irin kyan da tayi ga fari sai kace ka tab'a jini ya fito....


Zaune take k'asan kafet tana gyarama Salman k'umba. Kallonta yayi

“Preety kinsan miyafaru jiya danaje kd?”


Girgiza kai tayi

“Sai ka fad'a.”


Salman yace

“Wai Mummyn Mufeedah ke cewa cikinki yakai wata biyu yanzu?”

Kallonshi Aysaah tayi tace

“Mika mata to?”

 “Cewa nayi baki da ciki..”


Girgiza kai tayi tace 

“Allah ya Salman ina san na ganni da ciki nima.”


Dariya yayi yace

“Sai mun gama cin amarcinmu yarinya duka fa 3month kenan da auren mu.”


kafin ta bashi amsa wayanta yayi ringin. Mik'o mata yayi tana d'agawa tace 

“Bestiee nayi fushi Allah.”


“kiyi hak'uri bestiee na ina nan zuwa, dama zance maki gobe za'a saka date d’in bikina da Imran.”

Wani ihu Aysaah ta saki sai da Salman yaji tsoro..


Kashe wayan tayi ta tashi ta fad'a jikin Salman tana dariya...


D'agota yayi yace 

“Yanmata ya dai irin wannan ihu haka harkin tsoratani..”


D'agowa tayi tana dariya tace 

“Ya Salman bikin bestie za'a saka gobe ita da Imran.”


Dariya Salman yayi yace

 “Kice Imran ya d'aga tuta.”

”kai dai bari ai yasha wahalanta Allah yasa rabonshi ce...”


kallon Aysaah Salman yayi yace

“Ki shirya zamuje gaida su Ammi.”

Ihu ta farayi duk ta cika gidan, tashi tayi ta nufi d'aki...


Dariyan mugunta yayi yace

“Yarinya tunda kina son kije ai sai naja maki rai...”


cikin shirinta tafito ta saka purple super riga da sket tayi kyau sosai. Tana zuwa tace

“D’an saurayi ya na ganka zaune baka shirya ba?”

“Yan mata ai sai anjima idan anyi azahar zamu.”

Ba haka taso ba amma dan dole ta hak'ura...


D'aki ta tarar dashi yana latsa computer. Dafashi tayi tace 

“Ya Salman anfayi sallah kuma naga kaima kayi pls tashi kashirya...”


Bai d'ago ba yace

“Kinga aiki na keyi bari ayi la'asar tym d'in nagama..”


Fita tayi d'akin tana gunguni dariya yayi ya cigaba da abinda yakeyi...


Parlor ya sameta tayi tagumi, hannun ya zare mata yace 

“Yan mata nah ya dai kikai tagumi?”


A shagwab'ance tace

“Ba kai bane kak'i shiryawa ba...”


Murmushi yayi yace

“Ai na shirya yanzu bari nayo sallah..”


Tsalle tayi tana murna peck ta mashi, fita yayi yana dariya...


Tunda Salman ya fita sallar la'asar bai dawo ba kad'an kad'an Aysaah ta kalli agogo...


Wajen 8:00 pm taga bai shigo ba wayanshi ta kira da mamaki ta ganta bisa gadon ta, hawaye ta share ta shiga toilet ta d'oro alwallar isha...


Tana gama sallah ta cire kayanta tasaka kayan bacci...


Salmam bai shigo gida ba sai wajen 10:00pm..


Yana shigowa ya wuce kitchen ya dafa masu indomie dan yasan yau Aysaaah sai yayi dagaske zata sauko daga fushin datayi....


Yana gamawa ya wuce d'akinshi yayi wanka...


Yana fitowa ya kulle ko ina kana ya d'auki abincin yayi d'akin Aysaah dashi...


Sallama yayi ya shiga d'akin, ciki ciki ta amsa sallamar. Aje plate d'in yayi ya dawo bisa gado wajenta....


Salman yace

“Yan mata nayi laifi ko? Kiyi hak'uri pls.”

Bata ko juyo ba bare ta amsa shi..


D'agota yayi yaga tana kuka, shi kanshi yasan bai kyauta ba kuma ta bashi tausayi share mata hawaye yayi yace

“Natuba baby doll kiyi hak'uri...”


Hawaye ta goge tace 

“Ya Salman laifin mi namaka haka? Idan laifi na maka kamata yayi ka gayaman.”

Rungumeta yayi yace

“Wallahi bakiman laifin komi ba, ni nema na maki laifi amma nagane ban kyauta ba kiyi haku'uri kinji my baby.”


Hannunta ya kamo ya sauko da ita, yakai abinci bakinta ta goce da kyar Salman ya samu ta karb'a tanaci yana bata labari har sai da yaga ta saki ranta..


Suna gama cin abinci Salman ya kwashe kayan ya nufi kitchen dasu, da wowa yayi ya kama kunnenshi yace

“Baby doll kiyi hak'uri bazan k'ara ba. Allah gobe zan kaiki wajen Ammi d'inki da safe..”


Fad'awa kanshi tayi tana dariya, rungumeta yayi sosai yana k'arajin santa na ratsa shi.

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

  

BABI NA TALATIN DA HUD’U


Tunda Aysaah tayi sallan asuba bata koma bacci ba. Aiki kawai takeyi, dariya Salman yayi yaja blanket ya cigaba da bacci...


7:00am Aysaah ta dawo d'aki, yaye blanket d'in Salman tayi. Shafa kanshi ta farayi a hankali tana hura mashi iska a fuska...


Ahankali ya fara bud'e idon shi, zaune ya ganta tana ta faman murmushi. Aysaah tace 

“Ya Salman wake up haka nan pls, kasan fa inda zamu.”

Jawota yayi ta fad'o jikinshi ya rungumeta, mutsulniya ta fara tana san kwace kanta amma ta kasa..


A kunne ya rad'a mata

“Yarinya ba yanzu zamu tafi ba sai nagama bacci na, infact sai kin ban hak'k'ina in kuma kika k'iya nafasa tafiyan.”

Zaro ido tayi, dariyan mugunta yayi

 “I mean it..”


Gunguni Aysaah ta farayi, shiko Salman dariya kawai yake mata. Ahaka ya biya buk'atanshi. Yana gamawa ya shiga toilet danyin wanka, itama tashi tayi ta nufi d'akinta ta shiga toilet...


Sha d'aya ta fito cikin shirinta cikin bak'ar kimono, daining table ta iske shi yana ganinta ya taso yayi huging nata peck ya mata a kunci 

“Baby kinyi kyau sosai fa anya zamu fitar nan kuwa?”


Marairaicewa tayi 

“Ya Salman kayi hak'uri Allah nasa ran ganin Ammi nah.”

Hancinta ya lakuta yace

“Wasa nake maki zan kai ki kiga Amminki yau.”

Dariya tayi ta mak'alk'aleshi...


Suna gama cin abinci ta kwashe kayan ta nufi kitchen dasu. Salman ne ya fito yana d'aura agogo ga hannu, amsa tayi ta d'aura mashi kallonta yayi yace

Nagode Matata.”

Murmushi aysaah tayi tace 

“Ka daina gode man is part of my duty.”


Tafe suke suna fira cikin so da k'auna, sahad store suka tsaya danyin tsaraba. Kaya suka kwasa kamar basu san darajan kud'i ba, suna gamawa suka kai aka masu bill Salman ya biya, aka kwasa kayan aka saka a mota...


Kwance take jikinshi kamar mage, sai shagwab'a take mashi kallonta yayi yace 

“Baby doll karkisa na kasa driving d'innan fa.”

Dariya tayi tace

“Sai na amsa.”

Dai dai sun iso gaban gida. Horn yayi mai gadi ya lek'o ganin Salman yasa ya wangale gate. Cinna kan motarshi yayi mai gadi ne ya biyoshi yana mashi barka da zuwa...


Baiko ida parking ba Aysaah ta bud'e murfin motan ta fita, ta nufi cikin gida da gudu tana kwalama Ammi kira. Girgiza kai Salman yayi yana daria, gaisawa sukayi da baba mai gadi Salman ya mashi kyautar da ya saba kana ya d'auko jikar Aysaah ya nufi ciki da ita....


Parlor ta tarar da su fad'awa kan Ammi tayi tana dariya, d'agota Ammi tayi tace

“Aysaah kece?”

sai kuma ta rungumeta tana hawaye. Itama Aysaah hawaye takeyi, tsaye yake ya hard'e hannuwa yana kallon ikon Allah. Papa yace

“To yanzu miye kuma kuke kuka?”

Mummynzarah tace

“Salan tace my boy yana mata laifi ko?”

Dariya Ammi tayi tace

“Mu dai bamuce ba.”


Zama Salman yayi tare da gaida su Mummynzarah amsawa sukayi cikin sakin fuska, itama Aysaah gaida su tayi nan aka shiga tsokanan Aysaah mik'amata bag d'inta Salman yayi. Aysah tace

“Ammi inasu zarah?”

“Sun je kd jiya.”

Zumb'ure baki Aysaah tayi 

“Shine ba suzo mukaje tare ba.”


Hararanta Salman yayi yace

“Waye zai barki kije?”

Hararshi Ammi tayi tace

“Marar kunya kai zaka barta.”


Dariya akayi gaba d'aya. Baba mai gadi ne yafara shigo da kayan da sukayi tsaraba. Nan Papa ya dinga shimasu albarka... Tare da k'arayi masu fad'a akan su zauna lafiya da junansu..


Ammi tace 

“D’iyata tashi mutafi d'aki kinji.”

Dariya Mummynzarah tayi tace 

“Baza'ayi gabanmu ba kenan.”

 Ammi tace

“Ya za’ayi muyi sirri gaban uwar miji.”

Gaba d’aya dariya suke yi kama hannun Aysaah tayi suka bar parlor 


Mummynzarah taji dad'in ganin Aysaah cikin jin dad'i, sai dai kunya tasa ta kasa nunawa..


Suna shiga d'aki Ammi ta kalli Aysaah ita kanta taji dad'in ganinta cikin kwanciyan hankali

“Aysaah ba dai wata matsala tsakanin ku ko?”

“Babu Ammi yana k'ok'arin kyautataman.”

“Alhamdulillah” 

“Yanzu cikinki watanshi nawa?”


Kanta ta sadda k'asa tace

“Ammi har yanzu banda ciki.”


D’agota Ammi tayi tace

“Karki damu baby nah in shaa Allahu , Allah zai baki kinji, karna sake naga kin tada hankalinki.”

“in shaa Allah Ammi zanyi yanda kikace.”

shafa kanta Ammi tayi tace

“Good gal Allah ya maki albarka.”

“Amin”

ta amsa...


Sai dare su Aysaah suka bar gida cike da kewar iyayenta.

          

Tunda aka fara bikin Hanifa Aysaah bata zauna ba, kullum ta fita sai dare take dawowa...


Salman ne keta faman yima Aysaah rigima 

“Nifa Aysaah nagaji tunda aka fara bikin nan baki da tym d'ina kullum kina kan hanya.”


shafa sumarshi tayi tace

“Haba ya Salman ai Hanifa tafi k'arfin komai wajenmu kaga fa bikinmu gida ta dawo gaba d'aya inkayi hak'uri ai gobe ake gama bikin.”


Rungumota yayi yace

“Shikenan princess Allah yabasu zaman lafiya ki d'auki 100k kibata gudumuwa ta.”

Rungumeshi Aysaah tayi tana mashi godia...


Angama bikin Hanifa lafiya, ankai amarya minna kuka Hanifa tayi sosai da Aysaah zata dawo ita kanta harta iso abuja tana kuka...


Salman ne ya shigo da sallamarshi rungumeta yayi ta baya, yace 

“Your welcum habeebty.”

“Thank you.”


Juyota yayi yaga tana kuka murmushi yayi yace

“Dama nasan za'ayi haka.”


Murmushi tayi tace 

“Allah ya Salman duk dauriya na sai da Hanifa ta sani kuka.”

Hannunshi ya d'ora bisa bakinta yace

“Ai dama dole sai kunyi kuka bare yanzu kunyi nisa da juna”

 Kafin ta k'ara magana ya sungumeta yayi ciki da ita tana tsalle tsalle amma ta kasa kwace kanta.


“Baby pls ka kyaleni Allah nagaji.”

Dariya yayi yace

“Allah yarinya baki isa ba.”

Bayan da ta iya dole ta kyaleshi...

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

  


BABI NA TALATIN DA BIYU


 Kwance take bisa gado tana kuka matsowa yayi kusa da ita 

“Please Aysaah ki daina kuka Allah bazan k'ara ba.”


Harara ta wurga mashi

“Wama zai k'ara yarda da kai in dai haka ake aure ni dai ka maidani wajen Ammi nah...”


Shi maganan ma dariya ta bashi amma ba halin yi, matsowa yayi kusa da ita ya dafa mata kai zafi sosai yaji ta bashi tausai, bige mashi hannu tayi...


Tashi yayi yaje toilet ya had'a mata ruwan zafi ya saka dettol ciki, d'akin yadawo dan tai maka mata...


“Kije ki wanka zakiji k'arfin jikinki.”

Hannunta ya kamo ta goce..


Tashi tayi da sauri sai kuma ta fasa k'ara ka mata yayi ya mik’ar da ita tsaye.


Da taimakon Salman Aysaah tayi kamo ta yayi ya fito da ita bisa gado ya ajiye ta.


Kayan bacci ya d'auko ya saka mata ya bata magani ta sha kana ya kwantar da ita...


Tashi yayi shima ya shiga toilet yayi wanka..


Bayan sunyi sallar asuba Salman ya d'aga hannu yana ma Allah godia da ya bashi kamilar mace..


Yagama adu'o'i ya juyo yaga Aysaah kwance tana bacci..


Tausayinta ya kamashi dan shi kanshi jiya yasan yaba Aysaah wahala...


cire mata hijab d'in yayi ya d'auketa ya mai da ita bisa gado. Yana rungume da ita har bacci yayi gaba dashi cikin nishad'i...


Sha biyu daidai Salman ya zare jikinshi daga jikin Aysaah. D'akinshi ya nufa toilet ya fad'a yayi wanka...


Cikin shirin k'ananan kaya ya dawo d'akin Aysaah..


Haryanzu bacci take samun wuri yayi ya zauna ya k'ura mata ido yana murmushi...


A hankali Aysaah ta fara bud'e idonta tana salati kallon Salman tayi dake ta faman washe mata baki. Murgud'a mashi baki tayi ta juya baya..


Kwantowa yayi bisa bayanta 

“Haba baby doll nifa mijinki ne bai kamata kina fushi dani ba akan abinda Allah ya halarta man kuma namaki alk'awarin bazan k'ara yimaki da zafi ba..”


Tausayin Salman ya kamata juyowa tayi ta shafi kuncin shi tana murmushi. Rugumeta yayi yace 

“Kin daina fushi dani ko?”

D'aga mashi kai tayi peck ya mata yace 

“Thank you my baby...”


Hannu ta mik'a mashi kamata yayi ta tashi ta shiga toilet....

        

Tana fitowa daga wanka ta iske Salman ya aje mata kaya dariya tayi taje gaban mirror..


Light makeup tayi ta mulke jikinta da turaruka masu tsada da k'amshi...


Kayan da Salman ya aje mata ta d'auka ta saka k'ana nan kaya ne rigan iyakarta cibi sai wandon bai kai gwuiwa ba...


Tana sakawa tadawo gaban madubi ta kalli kanta ita kanta tasan tayi kyau ga gashinta da ta raba hud'u ta saka ribom sai ta fito baby doll d'in sak


Parlor ta iske Salman yana ganinta yace 

“Wow.”

Duk'ar da kanta tayi tana dariya.


Duk'awa tayi k'asa ta gaishe amsawa yayi ya kamota ya zaunar da ita kusa dashi yana murmushi..


Kallonta yayi yace 

“Babynah kinyi kyau.”

 “Thank you Hubby.”

“Yanzu Amminki ta aiko mana da abinci ga wannan ma tace abaki.”

Yar guntuwar takarda ce ya ba Aysaah..


Duba letter tayi tana karantawa tana murmushi lek'owa Salman yayi ta b'oye fizge ta yayi ya tashi ya ruga binshi tayi yana gudu yana karantawa. Dole ta zauna saboda zafin da takeji...


yana gama karantawa ya wurga mata yana dariya...


Turo baki tayi 

“Shine ka karanta man sirri?”

Kama kunnenshi yayi yace 

“On my kneels d'iyan ammi baxan k'ara ba..”


Kusa da ita ya za gayo ya zauna hannunta ya kama yace

“Ammi fa na nuna sankai ki jifa abinda tace wai ga abinci nan basai kin wahalan girkawa ba kuma tayi missn d'inki. Ke kad'ai tayi mssn banda ni kenan...”


Dariya Aysaah tayi tace 

“Ai kasan tsakanin Mama da d’iya.”

Dun gurinta yayi yana dariya...


Hannunta ya kama suka tafi daining table da kanshi ya dinga ba Aysaah abinci sai da yaga ta kusa amai kana ya kyaleta. Shima ci ya farayi yana ci suna fira..


Suna gamawa Aysaah ta kwashe kayan ta nufi kitchen sai da ta wanke su kana ta dawo parlor...


Tana zuwa Salman ya rufe mata fuska da kyalle yaja hannunta suka nufi haraban gidan...


Bud'e mata fuska yayi a hankali ta dinga bud'e fuskanta kallonshi tayi tana murmushi...


Makulli ya mik'amata Aysaah

 “Na miye?”

Mota ya nuna mata..


Zare ido tayi sai kuma ta ruga wajen motan tana dariya..


Juyowa tayi tace 

“Ya Salman da gaske wannan mota tace? Marcedes AMG E43 ce fa nake gani, my fav car..”


Takowa yayi yazo kusa da ita sak'ala hannunshi yayi a k'ungunta yace 

“Yes motarki ce Aysaah gift d’ina kenan na kammala karatun ki da kuma gudumuwata na auren ki.”


Duk'awa tayi k'asa tace 

“Naa gode ya Salman Allah yabani ikon yimaka biyayya har k'arshen rayuwata...”


D'agota yayi ya rungume yace

“Kin fi haka, nike da godia da kika rik'eman mutunciki da darajanki dole nayi duk abinda zai faranta ranki, kamar yanda kika faranta raina jiya...”

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE Phirdaucee Jeeboh NAGARTA WRITERS ASSOCIATIONBABI NA TALATIN DA SHIDA


  A hankali ta fara furta 

“Ya Asad dama zan k'ara ganinka?" 

Saikuma ta fashe da kuka, zama tayi tana kuka sosai a yayinda Salman yazo kusa da ita yana lallashinta, shiko Asad mutuwar tsaye yayi danko a mafarki beyi tunanin sake ganin Aysaah ba.

   Takowa yayi yazo kusa da ita ya duk'a yana kallonta tare da yin murmushi yace, 

“Haba Preety miye na kuka? Kiga fa halin da kike ciki amma kina kuka kidaina pls."

Kallon Salman yayi yana murmushi yace, 

“d'an uwa ashe da rabon zamu sake had'uwa?"

Dariya Salman yayi yace, 

“ikon Allah kenan!" 

Rungume juna sukayi suna murnan ganin junansu.


  Aysaah tace, 

“Ya Asad wai me yafaru dakai ne? Kuma yaushe kayi aure? Dagaske Little d'iyarka ce?" 

Gaba d'aya parlorn aka fara dariya, Asad yace


"Preety duk ni zan amsa questions d'innan?" 

D'aga kai tayi alamar 'eh.' Dariya yayi yace, 

“zan amsa amma sai gabansu Ammi dan haka kushirya mutafi can."


   Kallon Hanan yayi yace, 

“dear yau burina ya cika naga second family nah." Murmushi Hanan tayi tace, 

“congrats Hubby" Asad ya kalli Little ya kirata da, "zo nan Little" 

da gudu Little taje wajen Asad ta fad'a jikinshi tana dariya, kumatunta ya shafa yace, 

“Little kinga wannan?" 

ya nuna Aysaah, d'aga kai tayi tace, 

“ai itace Antynah danake baka labari Daddy" murmushi yayi yace, 

“toh Antynki ce dagaske 'cause she's my sis, shikuma uncle Salman shima d'an uwa na ne" 

tsalle Little ta fara tana murna da gudu taje kan Aysaaah tana dariya. Rungumeta Aysaah tayi tana hawaye, Asad yace, 

“kutashi mu wuce gidansu Ammi" 

duk suka mik'e. 


  Suna isa gidan basu ida parking ba Aysaah ta fita da gudu tana k'wala ma Ammi kira, kallon Salman Asad yayi yace, 

“dama haryanzu Aysaah bata daina wannan guje gujen ba?" 

Girgiza kai Salman yayi yace, 

“wallahi bata daina bafa" 

Hanan tace, 

“ashe Little nan ta gado guje guje da ihu" 

dariya sukayi suka wuce cikin gidan.

   Shiga ciki Aysaah tayi tana k'walama Ammi kira a yayinda ta tardasu su duka a parlour. Da gudu ta fad'a jikin Ammi inda Ammi tayi saurin d'agota tana tambayarta ko lafiya cike da tashin hankali. Dariya Aysaah tayi tace, 

“lafiya lau dama-"

  katseta Ammi tayi da fad'a tace, 

“dama me? Waike yaushe za kiyi hankali? Bakisan abinda ke cikin ki ba amma har yanzu kina wawanci toh wallahi ba ruwana idan wani abu ya sami abinda ke cikin ki keda kakar yaron, aikinsan ko wacece ita."


Marairaicewa Aysaah tayi tace, 

“Ammi Allah abin farin cikine-" 

Bata ida magana ba sukaji sallama.

  Amsawa sukayi Ammi tace, 

“ashe tare kuke?" Salman yace, 

“eh Ammi" 

Kafin ta k'ara magana sai ga Asad ya shigo da su Hanan. Zumbur! Ammi ta mik'e tana nuna Asad, kallon inda take nunawa Mummyn Zarah tayi itama ta mik'e lokaci d'aya, atare sukace 

“Asad kaine?!" 

Murmushi yayi ya k'araso kusa dasu ya zauna yace, "nine" 

waya Ammi ta d'auka takira Papa ta gaya mashi ga Asad nan da murna Papa yace gashi nan zuwa.


  Nan fa aka fara gaisuwa yaushe rabo kowa na murnan ganin Asad. 

  Asad ya kalli Mummyn Zarah yace, 

“Mummy haka Zarah ta zama budurwa ashe na kusa yin suruki" 

Dariya akayi itako sunne kai k'asa tayi tana wasa da yatsunta a yayinda tun shigowarsu Little ke jikin Ammi tana ta wasa.

  Bayan 'yan mintuna Papa ya shigo da sallamanshi a yayinda Asad ya mik'e yaje wajen Papa ya rungumeshi cike da jin dad'i, sosai Papa yayi murnan ganinshi. Bayan nan Papa ya zauna suka gaisa dasu Asad, gaidashi Hanan tayi amsawa yayi cikin sakin fuska.

   Aysaah tace, 

“Papa surukar ka cefah" 

Papa yace, 

“to Alhamdulillah." 

Little ce ta taso tazo wajen Papa ya d'auketa yana mata wasa. Mummyn Zarah ake kallonsu tace, "gabanmu zaka d'auki kishiyarmu?" 

Dariya akayi Salman yace, 

“ai dayake Aysaah ce"

  Papa yace, 

“sunanta kenan?" 

Asad yace, 

“Eh”

“Papa yar k'anwata nama takwara." 

Sai da akaci aka k'oshi kana suka dawo parlour dukan su, lokacin Little tayi bacci karb'anta Aysaah tayi daga hannun Papa tayi d'akin su Rahma da ita. Dawowa parlon tayi ta zauna. Binsu da kallo Papa yayi yace, 

“Salman ina kuka gano d'an uwanku?" 

Gyara zama Salman yayi yace, 

“Papa munje chicken capitol ne..." 

Nan ya kwashe komai ya gaya masu harda zuwa gidans hi da sunkayi duk ya gaya masu. Cike da mamaki Papa yace, 

“ikon Allah sai kallo!" 

Ya cigaba, 

“Asad miya faru ne muka daina jinku? Kuma munyi bincike amma shiru." 

Gyara zama Asad yayi yace, 

“abinda yafaru shi ne..."


MUJE ZUWA DANJIN MIYAFARU DA ASAD...

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION


BABI NA TALATIN DA BIYAR
BAYAN SHEKARA BIYU

  Aysaah ce tsaye gaban Salman ta rik'e k'ugu ga k'aton cikin ta, d'agowa yayi ya kalleta ya kwashe da dariya. Salman yace

“Ya dai maman babys kika kama man k'ugu kamar mai shirin dambe.”

Tab’e baki tayi

“Kaga tashi ka kaini chicken capitol shawarman can nakesan ci..”


Zaro ido Salman yayi yace 

“Yanzu fa kika gamacin burger.”


Aysaah tace 

“Allah shawarman chicken capitol nakeso idan kuma ba zaka kaini ba ka gayaman kawai.”

Dariya Salman yayi yace

“Ni na isa jirani na d'auko key d'in mota mutafi...”


Suna kan hanya Salman ya kalli Aysaah, yace 

“Baby doll d'azu Ammi ta kirani wai tunda cikinki ya shiga 8month na mai daki gida ki haihu.”


Kallonshi tayi

“Mikace mata to?”

“Ban bata amsa ba cz gaskia ban san ki koma gida nafisan ki haihu gidanki.”


Murmushi Aysaah ta cigaba dayi, kallonta yayi 

“Ya bakice komai ba?”

“Ya Salman mi kakeso nace duk yanda kukayi daidai ne ay.”

Daidai sun isa gate d’in chicken capitol 


Suna shiga Salman yaje yayi mata order , kana ya dawo wajenta ya zauna. basu fi minti talatin da zuwa ba aka kawo masu..


Kallonta Salman yayi yace 

“Madam tashi mutafi.”

”Ina? Ay anan zanci.”

Zaro ido yayi 

“Eh nan zanci.”

 mik'amata yayi ya bita da murmushi.


Sai da ta gamaci ta kalli Salman tace 

“Bro lets go.”

Dariya yayi ya mik'e, jitayi an rik'eta ta baya ana “mammy! mammy!! Mammy!!! " 

Juyowa tayi dan taga wanda ya rik'eta. Wata yar k'aramar yarinya ce wadda baza tafi shekara hud'u ba ta mak'alk'aleta. Tabbas yarinyar ta burge Aysaah, duk'awa tayi ta shafi kuncin yarinyar, tace where is your Mammy?.”

Kallonta babyn tayi tace 

“I don't knw.”


Rik'e hannun yarinyar tayi kamar ta santa, kallonta Salman yayi yace 

“Hajia nah sakarta mutafi mana.”

Murmushi tayi ta girgiza kai 

“Ya za'ayi mu tafi mubarta mutsaya muga zuwan mammy d'inta..”


" Wata yar kyakyawar mace ce wadda batafi sa'an Aysaah ba tak'araso wajen, sallama tamasu amsawa Aysaah tayi saukowa yarinyar tayi daga jikin Aysaah ta ruga wajen matar nan tana 

“Mammy Ina kika shiga?”

D'aga ta sama tayi tace 

“little ke zan tambaya daga naje na maki order saiki b'ace..”


Matuk'a sun burge Aysaaah, kallon mammy little tayi tace 

“Mammy meet my anty tana da kirki.”


Dariya tayi ta mik'ama Aysaah hannu tace 

“my name is Hanan,”

murmushi aysaah tayi tace 

“nice meeting u.”

Hanan tace 

“Same”


Aysaah tace 

“Miye real name d'in little?”

Hanan tace 

“AYSAAH”

wani juyowa Salman yayi ya kalli yarinyar da aka kira Aysaah. Itako Aysaah mutuwan tsaye tayi, Hanan tace

“Ya dai antyn little?”

Murmushi tayi tace notin..


kallon ta Salman yayi ya mik'ama little hannu, da gudu ta sauka taje wajenshi rungumeta yayi sosai, ya kalli Hanan yace

“Sunan antyn Little kenan Aysaah.”


Ita kanta Hanan abun ya bata mamaki. murmushi kawai tayi tace

“Shiyasa su kaji suna son juna.”

Dariya salman yayi...


   Nan fa suka fara fira, harda exchanging contact. Aysaah ce ta shafi kuncin little tace 

“My baby ina nan zanzo d'aukarki kiman weekend kallon Hanan tayi tace hpe za'abani?”

Murmushi tayi tace 

“Sai kin zo amma zakiyi fama da daddynta kafin ya yarda cz bai san yayi nesa da ita.”

Aysaah tace 

“in shaa Allah zai yarda”

Nan sukayi bankwana kowa ya tafi...


BAYAN KWANA BIYU

Aysaah ce ta fito cikin shirin ta na doguwar riga da yake yanzu kayanta duk dogaye ne saboda ciki, zama tayi kusa da Salman tace 

“Dan saurayi nafa shirya tashi ka kaini naga my little Allah yarinyar ta shiga raina da yawa fa.”

Kuncinta ya shafa yace

“Nasani tashi mutafi.”


Address d'in suka bi har suka isa gidan da ke area 11, gaban gidan suka tsaya sukayi horn. Gate man ne yazo ya bud'e masu shiga sukayi cikin gidan.


   little ce ke wasa da ball, ganin mota ya tsaya tabi motan da kallo Aysaah na fitowa little ta tafi da gudu tana 

“Anty.”

Ware hannu Aysaah tayi da gudu little ta k'arasa wajen Aysaah Rungumeta Aysaaah tayi sosai.


D'agota Aysaah tayi tace 

“I miss u so much my baby.”


Murmushi little tayi tace

 “Missed u more my anty.”


Shidai Salman binsu yayi da kallo yana dariya 

“Anty naba daddynah labarinki yace yana san yaga anty nah.”

Aysaah tace 

“my little dadynki zai ganni yau amma ga uncle can jeki gaidashi.”


Da gudu ta fad'a jikin Salman tana 

“Uncle am sorry banganka baneba.”

 Murmushi yayi ya shafa kanta yace 

“Dama ya za'ayi kiganni kina tare da antynki..”


Dariya little tayi ta k'ara sunne kanta jikin Salman..


Hannun Aysaah little taja suka shiga cikin gida tana kwalama mammy kira, Fitowa mammy tayi tace 

“Ya dai?”

Bata k'arasa ba taga Aysaah tsaye rungume juna sukayi suna murnan ganin juna ..


Hanan tace 

“Maman twinse ina uncle salman?”

Dariya tayi tace 

“Yana mota Hanan”

”kika barshi waje? Oya little jeki ce uncle d'inki ya shigo..”


Salman ne ya shigo da sallama yana rik'e da hannun little wuri ya samu ya zauna. Gaisawa su kayi da Hanan, masu aiki ne suka cika gaban su Aysaah da kayan ciye ciye kala kala Hanan tace

“Kun ko ci sa'a daddyn little yana nan bari namashi magana..”


Dawowa tayi parlorn tace gashinan zuwa. Fira sukeyi sosai shi kuwa Salman hankalinshi yana wajen little dake ta mashi surutu...


Da sallama ya shigo parlorn amsawa Salman yayi, d'aga kan da Aysaah za tayi suka had'a ido dai dai shima Salman ya kalleshi, a tare suka mik'e tsaye Aysaah ke nunashi da yasa.

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATIONBABI NA TALATIN DA BAKWAI


  “Zaune muke a parlor nida Daddy, ita kuma Maaah na kitchen. Kuka muka fara ji a d'akin Rayhan, da gudu muka isa d'akin muka tarar da ita kwance tana hawaye, Daddy ne ya d'agota ayayin da Maama ta shigo d'akin."

    Kallonta Daddy yayi yace, 

“Rayhan mike damunki?" 

Kasa magana tayi sai kuka da takeyi, ga numfashinta na fita ba daidai ba. Maah tace, 

“yanzu ba lokacin tambaya bane ba, mu d'auketa muyi asibiti da ita."


   “Mota na d'auko su Maah suka sakata ciki, asibiti muka nufa da ita. Muna shiga asibitin nurses suka karb'eta sukayi ciki da ita.”

    “Kusan minti talatin sai ga Doctor ya fito daga d'akinta. Kallon Papa yayi yace, ina san ganinku. Gaba d'aya" 

“Atare muka nufi office doctor, da sallama muka shiga. Amsawa yayi yamana izinin zama, saida yagama yan rubuce rubucen shi kana ya kalli Daddy da murmushi .”

“Alh dama tana da Athma ne?" 

“Girgiza kai Daddy yayi yace,”

“gaskia bata da Athma."

  Doctor yace, 

“toh gaskia Athma ce ke damunta, amma yanzu da sauk'i mun yi mata allura kuma tasamu bacci."

Godia Daddy yayi yace, 

“doctor zamu iya ganinta?" 

Doctor yace, 

“eh" 

nan muka tashi muka nufi d'akin da Rayhan take. Kwance take tana bacci amma numfashinta ya koma normal.


   Zumbur Maah ta mik'e tsaye, kallonta Daddy yayi yace, 

“lafiya?" 

  "Wallahi nabar gas kunne" 

ta amsa.

  Da sauri na mik'e Papa yace, 

“garin ya haka?" 

Kallon Papa nayi nace, 

“yanzu ba tym d'in tambaya bane ba bari naje gidan." 

Maaah tace, 

“jirani Asad muje tare" 

girgiza kai nayi nace, "

“Maah bari naje in shaa Allah ba abinda zai faru."

     

Ina isa layin gidan mu na fara ganin hayak'i, amma nakasa yarda gidanmu ne. Saida na isa 

“tabbas gidan mu ne abinda nake fad'a kenan, mutane nagani tsaye harma an kashe wutan.  

   Aljihuna na laluba na d'auko waya dan na kira Daddy amma da mamaki banjita ba, tunawa nayi dana barta gida, dole na juya asibiti dan na gayama su Daddy. Ina shiga d'akin Maaah ta mik'e tana tambaya na.”

“Asad miyafaru?"

 Kasa magana nayi saida Daddy yaman magana. Kallonsu nayi nace, 

“gidan ya k'one komai na gidan ya zama toka.

“Salati Daddy keyi, sai da ya natsu kana yace, 

“muje na gani."


  “Bayan kwana biyu aka sallami Rayhan. Kallon Daddy Maaah tayi tace, 

“yanzu ina zamu?" 

Murmushi Daddy yayi yace, 

“ai tuni na sama mana gida, har ma an saka kaya." 

Murmushi Maaama tayi tace, 

“shikenan." 


  Tun da muka koma gida nake neman hanyar da zata had'ani daku ban samu ba, gashi gabad'aya wayoyinmu sun k'one.

    Su Daddy na tarar da parlor shida Maamah, na zauna. Kallo na Daddy yayi yace, 

“Yadai akwai magana bakink" 

Murmushi nayi nace 

“Eh”

“daddy dama ina san naje Nigeria ne saboda su Aysaah nasan zasu nememu." 

Daddy yace, 

“nima nayi tunanin haka dan haka sai kayi arranging komai zuwa jibi saika tafi"

   Godiya nama Daddy na mik'e cikin murna. Da murna na, na iso Nigeria, ina sauka airport na d'auki drop na gaya mashi inda zai kaini, abin mamakin muna isa bakin gate na tambayi mai gadi yace man gaskia shi bak'one. Nace dan Allah ya taimaka yaman magana da masu gidan. Jim kad'an wani saurayi ya fito cikin sakin fuska muka gaisa, na mashi bayani, ceman yayi gaskia kun tashi, dan Babanshi ne ya siya gidan. Nace mashi ko yasan inda kuka koma? Yace gaskia baisani ba, kuma tsohon maigadin bai dad'e da daina aiki ba.

   Haka na dinga yawon neman ku a gari amma bansamu ba, dole na hak'ura na koma Cairo cikin bak'in ciki.”


  Kullum cikin hanyar bincike muke ko zamu ganku, amma shiru har na hak'ura. Wata rana naje na samu Daddy akan inason ya barni na dawo Nigeria da zama ko Allah yasa na ganku, Daddy yace zai amince amma sai nayi aure, nace, 

“daddy nikam banda wadda nakeso amma idan kana da wadda tamaka ka had'ani da ita." 

Murmsuhi Daddy yayi yace, 

“Ina da ita zan had'aka da d'iyar abokina kuma tana da hankali sosai."


  Ba'a d'auki wani lokaci ba akayi bikinmu da Hanan, bayan biki muka dawo Nigeria da zama. Kullum cikin yawon neman ku nakeyi amma Allah baisa na ganku ba sai yau sanadiyar little."


Babu wanda baiji tausayin Asad ba, ita ko Aysaah harda kuka tayi.. Papa yace, 

“Alhamdulillah dama haka Allah ya tsara abinshi kuma gashi daga k'arshe mun sake had'uwa." 


  Waya Asad ya jawo ya kira Daddy ringing biyu Daddy ya d'auka. Da murna Asad ke gaya mashi ya gasu Papa, murna sosai Daddy yayi yace abawa Papa, gaisawa sukayi sosai da murnan k'ara ganin juna, Daddy yace, 

“Alhaji muna nan zuwa next week muganku." 

Papa yace, 

“kubarshi sai Allah ya sauki Aysaah lafiya sai kuzo."


  Sai dare su Asad suka bar gida, 

“Salman ne ya kalli Aysah yace, 

“Madam mutafi ko?" 

Ammi tace, 

“ina? Ai tazo kenan yaro saita kuma haihu cikinta ya shiga wata tara ba inda zata, dan haka ka kwaso mata kayanta" 

tashi Salman yayi yana gunguni, Haka yafita.


 Washe gari suna zaune parlor sai ganin sukayi ana shigo da kaya. Salman ne ya shigo da sallama, amsawa sukayi wuri ya samu ya zauna gaidasu yayi, Ammi tace, 

“malam yadai? Naga kaya haka da yawa." 

Murmushi yayi yace, 

“ai Ammi mun dawo kenan sai randa kika maida man matata."

Yana kai wa nan ya mik'e ya fita, dariya Mummyn Zarah tayi tace, 

“ai ga irinta nan kin hana yaro matar shi" 

tab'e baki Ammi tayi tace, 

“Sai dai yadawo amma Aysaah sai ta haihu ko tana komawa."

[15/12 23:05] yar ficika: KUNYA ADON MACE


 Phirdaucee Jeeboh 


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION


BABI NA TALATIN DA TAKWAS


BAYAN SATI BIYU

    Aysaah ce kwance bayan Ammi ji tayi cikinta yana ciwo Mik'ewa tayi zaune. Farkawa Ammi tayi ta ganta zaune Ammi tace, 

“my Baby lafiya?" 

Murmushi Aysaah tayi tace, 

“nothing Ammi"

“To koma ki kwanta.”

Kwanciya tayi ta rufe idonta kamar tana bacci, amma ba barci takeyi ba..

   Can taji cikinta ya k'ara murd'awa, Ammi ta fara kwalama kira da sauri Ammi ta farka tace, 

“Aysaah miye?" 

Kasa magana tayi sai cikinta da take gwadama Ammi, tashi Ammi tayi ta fita da sauri, shigowa sukayi ita dasu Mummynzarah da Salman. Kama Aysaah akayi aka sa kata a mota, in banda salati ba abinda Aysaah keyi..


    Suna isa asibiti aka shiga da Aysaah labour room. Ammi ce ke zagaye zagaye tana ta adua, yayin da Salman ke hawaye, Dafashi Papa yayi yace, 

“Haba Salman be a Man mana, akanmi zaka dinga kuka a yanzu Aysaah adur'amu take nema ba kuka ba, dan haka share hawayenka". 

Hawayen shi ya share.

   Kusan awa guda tunda aka shiga da Aysaah ba wani labari. Ammi ce ta kalli Papa tace, 

“gaskia nikam abin nan na bani tsoro ace haryanzu shiru." 

Murmushi Papa yayi yace, 

“karki ce haka kowa da yanda yake haihuwan shi kedai kawai mucigaba da yimata adua."

   Likita ne ya fito yana cire handgloves d'inshi, gaba d'aya suka mik'e sukace, 

“Likita ta haihu?"

binsu yayi da kallo yana murmushi, mik'ama Salman hannu yayi yace, 

“congrats my man matarka ta sauka lafiya kuma ta samu d'iya mace". 

Nan aka fara murna kowa da abinda yake cewa..


   Suna Shiga d'akin sukaga Aysaah kwance, ita kuma babyn na gadon jarirai, har rige rigen d'aukan baby'n akeyi tsakanin Ammi da Salman, ita kuwa Mummyn Zarah ta zama yar kallo. Papa ne ya karb'i d'iyar ya mata adu'a. mik'ama Salman yayi yace, 

“sai kai mata hud'uba" 

wajen gadon Aysaah Salman ya matsa peck ya mata a kunci yace, 

“Nagode sosai my baby doll da kika haifaman mace mai kama dake, dan haka yanzu na baki zab'i ki fad'i sunan da kikeso a saka mata." 

Murmushi tayi tace, 

“Nagode sosai matso na gaya maka.”

Matsawa yayi ta mashi rad'a murmushi yayi yace

“Angama hajia nah." 

Sudai iyayen binsu sukayi da kallo suna murmushi.


   Tun cikin daren aka fara fad'ama mutane Aysaah ta haihu.

   Washe gari Likita ya sallami Aysaah da yake ba wata matsala, koda suka isa gida cike suka tarar dashi da mutane kowa na murna. Asad da Hanan ma sunzo. Tunda Little taga Baby shi kenan ta koma wajen Aysaah ko fita batayi.


   Haihuwa da kwana uku yan Cairo suka iso, kowa 

yayi murnan ganin d'an uwanshi, gida ya cika yan Kaduna suma sunzo.


  Yau monday daidai da 07/11/2016 akayi suna, inda yarinya taci sunan Ammi, Nafeesa amma za'a dinga kiranta da ASBAN Ammi taji dad'i sosai dan har kuka saida tayi kowa yayi murna da aka sama baby sunan Ammi.

   K'arfe hud'u na hango Aysaah taci ado cikin super red, d'inkin ya karb'eta, shiga ta din gayi cikin mutane ana gaisawa kowa da gifts d'in da yake bata.

yan NAGARTA na hango

sun shigo gidan sunan cikin shiga ta alfarma, Aysaah na hangosu taje tayi hugging d'insu, ciki tayi dasu tana nuna ma Ammi ga yan groups d'insu. Sha tara ta arzik'i k'ungiyar Albarka NAGARTA tayima Aysaah, taji dad'i sosai itama ta bisu da tukuici.

Sai dare aka gama taron suna, kowa ya koma gida cikin farin ciki.


  Aysaah ce zaune parlon Ammi tana cirema Asban pampers. Salman ne ya shigo parlon, Ammi na ganinshi ta d'aure fuska tace, 

“Ranka yadad'e lafiya?" 

Duk'ar da kanshi k'asa yayi yace, 

“Ammi nazo ganin sune." 

Abin dariya yaba Ammi, tashi tayi tace, 

“Na baka 20mnt tana kaiwa nan ta fita."

   Zama yayi yana gunguni, dariya abin yaba Aysaah amma ba halinyi. Kallonta yayi yace, 

“yarinya komawa gida zakiyi basai kin gama wanka ba, dan wannan takuran ya isheni."

Dariya tayi ta fad'a jikinshi, d'agowa Aysaah tayi tace, 

“Salman kullum ina alfahari dakai da ka zama uban 'ya'yana Allah ya k'ara had'a kanmu." 

Rungumeta yayi yace, 

“Aysaah a yanzu kin zama wani abu daga cikin jikina." 

D'aga hannu sama yayi yace, 

“Allah na rok'eka ka raya Aysaah da abinda zata haifa kabani abinda zan ciyar dasu na halak.”

Aysaah ta amsa da Amin, had'asu yayi ya rungume ita da Asban yana murmushi....


Anan zan aje biro na...


Godia ga Allah subahanu wata'ala da yabani ikon gama wannan littafin. Kura kuren dake cikinshi Allah ka yafeman...


Godia ta gareku bata da iyaka NAGARTA WRITERS ASSOCIATION, mungode sosai yanda kuke had'a kanmu, Allah yabar k'auna. luv y'all..."Wannan littafin goro ne ga duk masoyana wanda na sa ni da wanda bansani ba, na gode da irin soyayyarku gareni Feedoh loves u my sweetos.


Tags: #kunya #Ado #feedoh
5659
2
6
4
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

fatima isha2019-01-03 17:41:39matsa Allah haka ake so

ahx2019-01-01 23:15:07labarin yayi dadi