Jinnul Ashiq!

Written by Amrah Mashi APublished on 2018-12-13 15:44:33Category HorrorLabari ne da ya kunshi wata matashiyar mace wacce tun tana jinjira sakaci irin na iyaye ya sa wani kasurgumin aljani ya shiga jikinta. Bayan ta yi aure ya hana ta zama gidan mijinta. A karshe ma aka kwashe ta aka kai gidan mahaukata, a tunanin dangi da kowa nata ciwon hauka ne take yi. Ko ya abun zai kaya. Ku shigo daga ciki don jin cikakken labarin. tags: #Jinnu #Basma #Adduโ€™aDuba was labarai »

[11:45am, 6/07/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: [10:22am, 6/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    JINNUL-ASHIQ

              ๐Ÿ’€๐Ÿ’€

               ๐Ÿ’€

Page 1 to 5

Na Amrah

 ยฎNWA


Kyakkyawar ajiyar zuciya tayi tare da wata irin atishawa mai 'karfin gaske wadda ni kaina mai d'aukar rahoto sai dana tsorata.

   Hamdala mutumin yayi tare da rufe miskin dake hannun shi. Sun dad'e a haka kafin malamin yayi gyaran murya ya dubi miji da matan dake gefen shi yace "Alhamdulillah! Abun ma yazo da sau'ki Alhaji tun da sun bayyana kansu,,, sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, irin wannan JINNUN suna da wahalar fita daga jikin mace,,,, amma insha Allahu komai zai saukaka cikin iko da hikimar Allah,,,, yau da dare zanyi istahara domin tabbatar da wane irin JINNU ne take tare dashi,,,, sai mu dage da addu'ah Allah yasa dai ba JINNUL-ASHIQ bane".


   Cikin firgici matar dake kusa da mutumin tace "INNALILLAHI WA INNAA ILAIHI RAJIUN,, malan JINNUL-ASHIQ ba sune wanda suke auren mace ba? Wanda daga karshe ma har su hana ta aure?".


    Malamin yayi murmushi yace "ehh sune fa Hajiya,,, sai mu dage da adduah domin kuwa babu abunda yafi karfin Allah,,,,insha Allahu komai zai zo da sauki".


   "Tou Allah ya tabbatar da haka malan", Alhajin ya fada cikin yanayin tausayi.


    Purse matar ta bude ta zaro kudi da ban san adadin su ba ta mika wa malamin,,, yayi godiya tare da hada kayan shi yabar gidan.


   Har a lokacin budurwar da yayi wa rukiyyar bata farka ba.


ยฉPrincessAmrah๐Ÿ˜˜

ยฎNAGARTA WRITERS ASSOCIATION

[10:37am, 6/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

     JINNUL-ASHIQ

                ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                  ๐Ÿ’€

Page 6 to 10

Na Amrah

 ยฎNWA


  Bayan kimanin awa d'aya ta farka bakin ta yana furta "INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN".

   Hankalin maman ta da baban ta suka koma gare ta. Mahaifiyar ta ke fad'in "sannu Basmah! Me kike ji yanzu?",

   Bata bata answer ba sai hawaye kawai da yake gangara daga kumatun ta. Jin bata ansa mata ba yasa ta 'kara 'ko'karin sake tambayar ta. Mahaifin ta ne yace "Hajiya ki 'kyale ta ta 'kara warwarewa mana,, inaga kamar bata jin dad'in jikin ne".


    Cikin 'karfin hali ta tashi zaune da taimakon mamanta. "Ruwa" kawai ta iya furtawa.

  Da sauri Mamanta ta kawo mata ruwan maganin ta. Ba tare da Basmah ta kula ba ta fara shan ruwan.

  Wani irin ciwon ciki ta fara ji had'e da ciwon mara wanda tunda take bata ta'ba yin irin shi ba. Kuka take sosai duka hankalin su ya tashi. Ta d'auki tsawon lokaci tana magagin ciwon cikin ne sai ga amai ta fara cikin shi mai tsananin yawa. Daga 'karshe sai ga wata 'yar 'karamar laya ta fad'o.

   Tunda layar ta fad'o sai ciwon cikin ya sarara mata. Bata 'kara jin ko alamar shi ba.


   Cikin tsoro Baban ta ya d'auki layar ya fara kwancewa. Wani irin gashi ne suka gani cikin ta mai yawa sosai.

   Take kuwa ya sake kiran malamin daya tafi ya sanar dashi abnda yake faruwa. 

   Bai wani dad'e ba sai gashi ya dawo.


   "Sai mu taru mu godewa Allah. Domin kuwa JINNUN sun mata ajiya ne a marar ta wanda yake sata wannan ciwon marar har tayi wata d'aya tana zubar da jini (menstruation),,, amma tunda wannan abn ya fad'o insha Allahu komai zai tafi daidai. Wannan ba wata matsala bace sai dai ana bu'katar ta ringa shan magani koda yaushe koda kuwa taji sau'ki".


   Sosai sukayi farin ciki. Har 'kofar gida mahaifin ta ya raka malamin. Ya bashi kud'I yace "ya 'kara mai a mashin d'in shi". Godiya yayi sannan ya tafi.


Princess Amrah๐Ÿ˜˜

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

[11:50am, 6/07/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: [10:51am, 6/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    JINNUL-ASHIQ

               ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                ๐Ÿ’€

Page 11 to 15

 Na Amrah

  ยฎNWA


TUSHEN LABARI.


Alhaji Umar da Hajiya Nafeesat sune iyayen Basmah. Ta taso cikin gatan iyaye. Iyayen ta suna tsananin tausayin ta da 'kaunar ta saboda tunda ta tashi da yarintar ta bata da isasshiyar lafiya. Kullun suna kan hanyar asibiti.


    Kud'I kam kullun kashe su suke amma babu alamar sau'ki. Yau idan suka je asibiti ace tana da sickler. Gobe idan suka je ace bata da sickler amma tana da kidney problem. Wani lokacin ma cewa ake tana da ciwon zuciya.


   Har 'kasar waje sun fitar da ita amma ba'a ga komai ba. Wannan dalilin yasa kawai suka ha'kura suka barta sai dai adduah kawai da suke bin ta dashi.


   Da haka suka samu ta kammala primary School da 'kyar.

   ULUL-ALBAB secondary School suka sama mata sabida ita tace tana sonta kuma makaranatr tana da kyau sosai ta fannin boko da kuma addini.

  Sun ji dad'in yanda suka ga sun farantawa tilon 'yar su rai da suka kaita inda take so.


   A ranar da aka kaita makarantar sunyi wa principal d'in bayanin ciwon ta dan kar a ringa wahaltar da ita saboda boarding school ce. Ya gamsu da bayanin su sannan suka tafi tana yi masu bye bye.


ยฉPrincess Amrah๐Ÿ˜˜

ยฎNAGARTA WRITERS ASSOCIATION

[11:09am, 6/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    JINNUL ASHIQ

              ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

               ๐Ÿ’€

Page 16 to 20

  Na Amrah

  ยฎNWA


Direct jss 1c aka kaita. Yaran class d'in sun kula da ita sosai kamar dama sun san juna. Itama kuwa da yake wayayya ce ta iya zama da mutane dan da nan ta saba dasu. Zarah ce ta kira ta suka zauna seat d'aya. Koda aka gama classes ta raka ta office d'in principal ta d'auko kayan ta. Card d'inta ta kar'ba taga Red House ne aka kaita. Cikin jin dad'I tace "kinga kuwa room d'in mu d'aya,,dama kuma wadda muke kwana d'aya tayi transfer kinga kawai sai mu zauna tare".


   Basmah tace "ehh" kawai tayi shiru da yake ita d'in ba irin yaran nan masu hayaniya bane. Sai dai kuma ta kula Zarah mai son surutu ce da son mutane. Gata da dad'in zama. A iya zaman da sukayi tare na yini d'ayan ta fahimci halin ta.


    Satin Basmah uku a makanta ciwon ciki ya taso mata. Da yake duk an fad'awa malaimai ciwon ta yasa sukayi saurin kaita office d'in pc. Da hanzari kuwa ya kira iyayen ta aka bata permission har sai lokacin data samu lapia.


   Haka rayuwar ta taci gaba da tafiya har takai ss 1 kullum cikin komawa gida take.

   

    Ranar da suka fara jarabawa ne zasuyi ta Qur'ani aka fara data farko. Koda malamin ya jawo mata "WATTABA'U MA TATLUSH-SHAYAD'INU ALA MULKI SULAIMAN" sai naji "tiiiippppppp".

   Cikin tsoro da furgici na duba naga Basmah ce kwance hannun ta d'aya ri'ke da marar ta. D'ayan kuma ta dafe kanta. Ga wani irin ba'kin jini yana malala daga cikin wandon ta.


    Malamin bai wani damu ba saboda shi a tunanin shi ko period ne ta fara sai dai Yasa Zarah ta d'auke ta suka tafi hostel.

   Tun a hanya take tambayar ta "me ya same ta?",,, amma shiru babu answer sai hawaye kawai dake bin kumatun ta.


    Cikn tausayi Zarah ke wanke mata kayan ta. Ta kai mata ruwan wanka tasa ta tayi wanka ta bata pad ta koya mata yanda akeyi. Abnka da yarin ta duk basu kula da yanda jinin yake ba. A yinin ranar haka ta yini tana fama da ciwon mara. Tasha magani kala kala amma babu sau'ki. Zarah ma bataje evening prep ba sai 'kara tausayin babbar 'kawar ta takeyi.


ยฉPrincess Amrah๐Ÿ˜˜

ยฎNAGARTA WRITERS ASSOCIATIOM

[11:56am, 6/07/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: [11:30am, 6/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    JINNUL-ASHIQ

               ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                 ๐Ÿ’€

Page 21 to 25

 Na Amrah

  ยฎNWA


Haka Basmah ta kwana tana fama. Ba ita ba har 'yan room d'in su babu wanda ya rintsa wasu sai kuka suke mata.

    Washe gari tunda safe Zarah ta shirya ta suka tafi office d'in pc. Ganin yanayin da take yasa yayi saurin rubuta mata permission tare da kiran baban ta a waya. Har ya saba da zuwa d'aukar Basmah. Tun yana damuwa har ya daina damuwa. Sai dai kuma sakacin da sukayi basu neman maganin musulunci kuma da dama mutane suna basu shawara akan haka amma shiru basu nema.


   Da komawar ta gida ta fad'awa maman ta ciwon ta. Itakam dad'I ma taji saboda 'yarta ta fara girma tinda har gashi ta fara period.


    Kwanan ta biyar jini ya tsaya mata. Marar ta bata daina ciwo ba sai da ta 'kara kwana sannan taji sassauci. A ranar kuwa aka mayar da ita makaranta. Kowa na mamakin yawan ciwon Basmah. Gashi bata girma kullun kamar 'karamar yarin ya take dan ko breast bata fara ba har yanxu.


   Da mamaki kuma daga komawar ta jinin ya dawo mata tare da ciwon marar nan mai tsnani. 

   Zarah tace da ita a sake mayar da ita gida amma sam ta'ki saboda maman ta tace ta ringa ha'kuri da wannan ciwon marar dan akoda yaushe zata iya jin shi.

   

   Wasa wasa sai da ta kwashe kwana ishirin tana period babu wanda ya sani sai Zarah. Itakam zarah abn yana damun ta amma tayi shiru dan Basmah tace kar ta fad'awa kowa.


   Kwanci tashi babu wuya wurin Allah har su Basmah sun gama makaranta kuma duk period d'in da zatayi sai ta shafe kwanaki tana yi. Sai dai duk wata sai anyi mata 'karin jini amma baa san dalili ba daga ita sai Zarah ne suka sani. Sai kuma ni marubuciyar..lol๐Ÿ˜€.


  Duk dangin su kowa yana mamakin 'karantar Basmah. Gashi ta gama makarnata amma kamar 'yar primary school haka take.

   Bata da hayaniya bata zama inda ake hayaniya. 


    Kwana bakwai da gama makarantar su ne period yazo mata. Anan ne mahaifiyar ta ta gane lallai akwai matsala. Saboda da zaman ta tayi staining duk kayan ta suka 'baci gasu farare. Kalar jinin kawai ta gani ta tabbatar da babu lafiya.


    T ake ta fara azabbabben ciwon marar data saba yi. Cikin 'karamin lokaci mamar ta ta rikice ta kira Alahji Umar ta sanar dashi.

  

   Ranar ne kuma Basmah ta sanar dasu dalilin da yasa ake 'kara mata jini da kuma tsawon lokacin da take d'auka idan tana period.


   Ba'a kwana ba aka samo mata wannan malamin. An sanar dashi komai ya had'o mata magunguna ciki har da wani ruwa wanda zata ringa shan half cup safe da dare.

  Da kuma miski wanda shine zata mayar man shafawar ta. Haka take amfani dasu ba dan tana so ba. Kwatsam JINNUN suka taso a jikin ta wanda bata ta'bayi ba tunda take fama da ciwon.


ยฉPrincess Amrah๐Ÿ˜˜

ยฎNAGARTA WRITERS ASSOCIATION

[11:42am, 6/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    JINNUL-ASHIQ

               ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                ๐Ÿ’€

Page 26 to 30

 Na Amrah

  ยฎNWA


CIGABAN LABARI


Tun daga ranar Basmah ta samu lafiya. Duk wani ciwo da take yi babu shi. Period d'inta ya dawo daidai kuma lafiya lau tana shiga mutane.


   A ranar kuma ta kira Zarah ta sanar da ita duk abnda ya faru. Itama ta taya ta farin ciki ta kuma shaida mata cewa zata xo ta duba ta.


    Tun daga ranar Basmah tayi watsi da duk wani magani da take sha. Suma kuma iyayen ta suka 'kyale ta basa matsa mata akan tasha magani.


  (Babban kuskuren da sukayi kenan. Muna tafka babban kuskure akan shan magunguna musamman ma irin na JINNU. Saboda akwai JINNUN da suke yin lamfo a jikin mutane. Sai su nunar da sun tafi kenan amma da zarar anyi sake kuma sai suci gaba da cutar da mutane. Ita dai Basmah gashi taji sau'ki amma ganin haka yasa ta daina shan duk wani maganin da take sha daga samun sau'ki lokaci d'aya. Muna ro'kon Allah ya kare mu da kariyar sa.)


    Basmah taci gaba da jin dad'in ta da shagwa'bar iyaye sosai. Malami kuma basu sake kiran shi ba tunda wannan al'amarin ya faru.


   Ni kaina Amrah abn ya d'aure mn kai sosai. Amma babu yanda na iya dole na ha'kura na 'kyale su suyi yanda suke so. 


   Da sauri na baro gidan su da nufin zan koma daga baya. Yau take sallah dole na tafi na barsu na tafi yawon sallah nah.


Basmah mai sanyin ta dake nake. And Zara BB kema dake nake.


HAPPY SALLAH to all muslim ummah. Allah ya sa munyi karbabbiyar ibada. Allah kuma yasa muga na wata shakarar.


ยฉPrincess Amrah๐Ÿ˜˜

ยฎNAGARTA WRITERS ASSOCIATION.

[10:37am, 8/07/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: [10:09am, 8/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€  

    JINNUL-ASHIQ

                ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                 ๐Ÿ’€

Page 31 to 35

  Na Amrah

  ยฎNWA


  Kwance take kan center carpet tayi pillow da cinyar mummy. Kunnen ta sanye da ear piece tana sauraren wa'kar "My woman" ta 'kure 'karar wa'kar tana yi tana miming a hankali.


   "Basmah! Basmah!! Basmah!!!" Sau uku Mummy ta kirata bata amsa ba saboda 'karar wa'kar da take ji yasa bata ji ba.

  'Dan bubbuga ta tayi da sauri ta zare kunne d'aya tana yamutsa fuska tace "Mummy ya akayi ne?".


    Bata ansa mata ba sai nuni da tayi mata da doguwar kujerar dake gefenta.

   Ihu naji ta buga da 'karfi tare da matsawa inda yake tace "Ya Anwar yau kaine a gidan namu?", baki ta ta'be alaman shagwa'ba sannan tace "gaskiya munyi fushi ka koma".


   Mummy tayi murmushi tace "tou Anwar kaji 'kanwar taka ma bata farin ciki da zuwan ka sai ka tafi".


   "Haka zaayi Mummy barin tafi kawai tunda bata so zuwa na ba" wanda aka kira da Anwar ya fad'a sigar zolaya.


   Dire dire ta kamayi tana fad'in "mummy yau fa kwana biyu kenan da yin sallah amma sai yau yazo, kiga fa mummy".


    Rusunawa Anwar yayi yace "tou kiyi ha'kuri kinji mai sanyi nah! Wallahi wasu uzururruka ne suka hana ni zuwa shiyasa,, amma yanzu gani naxo kuma sai dare zan tafi",


   Cikin faraa tace "laah mummy kinga ya Anwar ya rusunah saboda ni, ka tashi zolayar ka fa nake",


   Murmushi ya mayar mata tare da mi'kewa ya zauna akan throw pillows dake jere 'kasan carpet yace "mummy su Ummah sunce a gaishe ku, kuma tace wai yaushe zaa kai mata Basmah su gaisa?".


    Mummy tace "Basman ne har sai an kaita? Ita dai ce bata son zuwa tunda zaman banza kawai take tunda aka fara sallah bata fita ko ina ba",


    Anwar yace "aikuwa gobe zanzo in d'auke ta in kaiwa mummy ita insha Allah".


Dedicated to Basmah mai sanyinta๐Ÿ˜œ and zarah~B~B๐Ÿ’•


ยฉPrincess Amrah๐Ÿ˜˜

ยฎNAGARTA WRITERS ASSOCIATION

[10:29am, 8/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    JINNUL-ASHIQ

               ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                ๐Ÿ’€

Page 36 to 40

 Na Amrah

  ยฎNWA


Bayan ta kawo mashi snacks da drinks ya motsa bakin shi ne Mummy tace "dama kuwa naji Dady yana neman ka Anwar",


    "Ince dai ko lafiya Mummy" Anwar ya fad'a fuskar shi kyam kan Mummy.


   "Lafiya lau Anwar, ina tunanin akan maganar karatun Basmah ne, tunda dai ta samu sau'ki shine muka yanke shawarar a siyo mata form koda na Jamb ne ta gwada idan bata samu ba sai a nema mata school of nursing",


   "Ehh Mummy nima gaskiya nayi wannan tunanin. Tunda dai yanzu ta warware sosai bai kamata tana zaman banza ba" Anwar ya fad'a tare da 'ko'karin amsa sallamar da yaji anyi.


   Dady ne yazo tun daga nesa yace "gaskiya ne abnda hajiya ta fad'a maka, gobe saturday babu aiki sai zuwa ranar monday sai kazo ka d'auke ta kayo mata duk abnda ya dace".


    Hira sosai suke yi cikin jindad'I. Wayar Basmah ce tahau ruri ta duba kan screen d'in taga an rubuta AMINIYA TA, da sauri ta d'auka tace "'kawata ya dai", daga d'ayan 'bangaren tace "ki rufe idon ki zan baki suprise ne".

  Da sauri kuwa Basmah ta rufe idon ta, kafin ta bud'e taji muryar Zarah a parlorn su tana fad'in "tou bud'e ki gani",


   Da gudu ta rungumi Zarah tana farin ciki.

   Har 'kasa zarah ta du'ka ta gaishe dasu Mummy da ya Anwar sannan suka shige d'akin Basmah, dan danan fira ta kaure tsakanin su.


   Wani ringing d'in ne taji wayar ta nayi da sauri ta d'auka. Abn mamaki sai ga kira na shigowa da mamaki sai naga suna kawai an rubuta JINNUL-ASHIQ amma babu number. Bata ko duba mai kiran ba tayi rejecting tare da fad'in "bafa zan d'auki kiran kowa ba yau, dan kar a katse mn fira ta da 'kawata".

    


   Da sauri sauri gudu gudu na baro su, dan nikam abn ba 'karamin tsorata ni yayi ba, ban tsaya ko ina ba sai gidan su sisi nah Rabiatu sk msh, nace mata "dan Allah sis ina so ki bani cikakken bayani akan wannan kalmah ta JINNUL-ASHIQ",


    Jikinta na rawa tace "ke kuwa sis miye had'in ki da wannan kalmar wadda ko dad'in ji bata da ita?",


    "Nidai kawai ki bani amsa sis",


   "JINNUL-ASHIQ shine irin mugayen aljannun nan wanda suke auren mace, idan ASHIQ ya aure ki wallahi mai rabaki dashi sai ya shirya, sis akwai bayanai sosai akan tambayar ki, amma bazan fad'a miki ba sai kin sake dawowa saboda yanxu dai kinga na shirya yawon sallah zan tafi".


   Bankwana mukayi na kama hanyar gidan mu. Nima na shirya tsaf na nufi gidan su Rash Kardam. Idan na dawo gida zan koma inci gaba da d'auko maku rahoto insha Allah.


Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œ and Zarah~B~B๐Ÿ’•


ยฉprincess Amrah๐Ÿ˜˜

ยฎNAGARTA WRITERS ASSOCIATION

[8:15am, 10/07/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: [2:14pm, 9/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    *JINNUL-ASHIQ*

                ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                 ๐Ÿ’€

Page 41-45

Na *Amrah*

 ยฎ *NWA*


Sun sha hira sosai kafin Zarah tayi mata bankwana zata tafi. Tasha kyauta wurin Basmah, dan indai wurin kyauta ne to Basmah ba daga baya ba. 

  Mummy da dady ma sun bata kud'I ta kama hanyar gidan su.


    Ita Basmah tama manta da an kira ta tayi rejecting, so sai bata ma duba wayar ba kawai ta saka a chaji ta koma parlor wurin ya Anwar. 


   Duk daren Basmah na tare dashi sai bayan isha wurin goman dare sannan ya mata bankwana cike da kewa ya tafi.


   Tana kwance a cinyar mummy can ta jiyo wayar ta na wani ringing d'in. Mummy ce tace "wai Basmah ba wayarki bace ke ringing? ".


   "Ehh itace mummy barta kawai ta gaji ta tsinke" ta fad'a ba tare data kalli mummy ba.


   Nikam da gudu na tafi d'akin domin ganiwa idona mai kiran Basmah.

   Da mamaki sai naga wannan rubutu da babban ba'ki an rubuta *JINNUL-ASHIQ*. Nikam gaskiya wannan al'amarin yana tsorata ni. Gashi kuma babu number a jiki sai suna. Naso ace na d'auko mata wayar na kai mata amma sai na barta dan nasan tana ji.


    *Bayan shekara daya*


Abubuwan da dama sun faru kamar; Basmah ta fara karatu a *UMYUK* tana karantar bsc. Ed. Biology har sun gama first semester suna shirin fara exams na second. Soyayya mai 'karfi ta shiga tsakanin ta da ya Anwar. *JINNUL-ASHIQ*Ya daina kiranta kwata kwata. Yanxu kam hankalin ta kwance bata da matsalar komai sai tsula tsiyar ta kawai take๐Ÿ˜œ.


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œand Zarah~B~B๐Ÿ’•_


ยฉ ~princess Amrah~๐Ÿ˜˜

ยฎ ~NWA~

[8:06am, 10/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    *JINNUL-ASHIQ*

               ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                 ๐Ÿ’€

Page 46-50

Na *Amrah*

ยฎ *NWA*


Tuni maganar auren su iyaye sun shiga har an saka ranar aure.


   Shirye shirye suke sosai mummy na gyara 'yar ta.


   Su Zarah sai farin ciki ake 'kawa zatayi aure.


   Ranar d'aurin aure ranar data tara manya manyan mutane tun daga 'yan siyasa, 'yan kasuwa, manyan 'yan boko da sauran su. Su Basmah sai farin ciki ake anci kwalliya abun sha'awa.


   Bayan an d'aura aure ne wayar Basmah ta hau ruri. Koda ta duba sai taga angon ta ne cikin farin ciki ta d'auka.


   "Amarya bakya laifi koda kin kashe Zarah",

   Dariya suka d'auka su duka kafin tace "tam yau dai burin mu ya cika an d'aura mana aure. Sai muyi fatan zaman lafiya mai d'orewa tare da zuri'a mai albarka",


    "Haka ne wife, Allah ya raba mu da sharrin masu sharri. Ya kawo mana zaman lafiya".


    "Allah kuma ya raba ni da kishiya" Basmah ta fad'a tana mai kallon Zarah data 'kura mata ido tana dariya.


    Sallamah sukayi tare da shaida mata cewa gasu nan zuwa daga an gama reception sai suyi selfie๐Ÿ˜œ.


   Da murna kuwa ta kashe wayar har da kiss ta manna a jikin wayar.


   Kamar ana jira ta kashe wayar sai ga wani kiran ya shigo mata. Koda takai duba ga wayar sai taga daro-daro an rubuta *JINNUL-ASHIQ*, a tsorace ta 'kara dubawa taga babu fa number a jiki. Cikin hanzari ta gwadawa Zarah da sauran 'kawayen ta da suka halarci bikin.

  Duka suka bata shawara akan ta d'auki kiran.


    "Hello" ta fad'a a hankali dan tana tsoro sosai. Tunda take bata ta'ba ganin kira babu number ba amma yau sai gashi.


   (Basmah tayi kuskure. Inda ace nice naga haka bazan d'auka kiran ba. Kuma koda ace na d'auka tou zanyi cikakkiyar bismillah a bayyane sannan inyi sallamah. Insha Allahu nasan ko waye ko miye kuma dole zai tsorata. Babban kuskuren da muke tafkawa kenan na rashin sallamah idan zamu amsa waya musamman ma idan muka ga ba'kuwar number. Wallahi ko menene ko wanene yake nufin ki da sharri da zarar kikayi sallmah sai kin tsorata shi. Ya Allah ka kare mu da kariyar ka.)


   Daga d'ayan 'bangaren naji an kwashe da dariya da 'karfin gaske kamar zai 'bare mata kunnuwa duk kan wanda ke zaune wurin sai da suka tsorata.


    Cikin wata irin magana mai firgitarwa yace "kin shigo hannu! Kin shigo hannu Basmah!! Kinyi kuskure da kika d'auki kiran nan, na dad'e ina kiran ki amma da yake bakya d'auka sai kika tsira. Duk wanda yaji zahirin muryar *JINNU* Kamar haka tou ba lallai ya tsira ba. Basmah malamin ki ya 'kona min yara na guda hud'u. Ya raunata guda biyu. Saboda haka nima sai na gama baki wahala ke da mijin ki ke har ma da yaran da zaki haifa da iyayen ki da kowa naki. Har sai naga kowa ya guje ki sannan in kashe ki".


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œ and Zarah~B~B_๐Ÿ’•


ยฉ ~princess Amrah~ ๐Ÿ˜˜

ยฎ ~NWA~

[9:41am, 11/07/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: [9:17am, 11/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    *JINNUL-ASHIQ*

                 ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                  ๐Ÿ’€

Page 51-55

Na *Amrah*

ยฎ *NWA*


   Kashe wayar yayi bayan ya gama fad'a mata abunda yake ranshi. A firgice ta kalli Zarah, Zarah ta kalle ta duk sauran 'kawayen su ma suka kalle ta. Duk da basuji maganar da yayi mata ba. Dariyar ce kawai sukaji.


   A haka suka 'karaci yinin bikin kowa baya cikin hankalin sa sosai.


    Aunty Rabi 'kanwar Mummy ce ta shigo taja amarya ta kaita wurin Mummy. Tasha naseeha sosai masu ratsa zuciya. Kafin nan Dady da kanshi ya saka ta motar shi tana ta faman kuka ya kaita gidan ta dake Sardauna Estate cikin garin Katsina.


   *Bayan sati d'aya.*


Basmah na hango kwance tana bacci Anwar ya fita. Ita kad'ai naji tana fad'in "Ash! Wash! Ka' kyale ni, akwai zafi, Innalillahi! Dan Allah ka daina".


   Da gudu ya Anwar ya 'karaso ya same ta. A tsorace ya tashe ta tayi zumbur ta tashi.


   "Me yake faruwa dake ne? Kinga jikin ki duk ya 'baci da jini Basmah, ko lokacin period d'in ki yayi ne?".


    A daburce ta kalli jikinta yanda yayi kaca-kaca da jini. A tsorace tace "Ya Anwar akwai matsala. Yau rana ta biyu kenan da ina wani mafarki wai wani aljani yana saduwa dani. Da zarar na farka sai in jini kwance cikin jini. Kaga yauma hakan ne ya kasance".


    "Subhanallah! Aikuwa wannan ba abun ayi shiru bane. Dole mu fad'awa su Dady a nemo wannan malamin da yayi miki aiki a baya. Ina ga kaman sun dawo miki ne".


    Kuka sosai Basmah keyi ta had'a kai da guiwa ta kasa fad'in komai.


    Haka suka kwana ranar Ya Anwar nata bata baki amma ta kasa yin shiru sai 'kara tuno maganar da Aljanin yayi mata lokacin daya kira ta take.


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œ and Zarah~B~B_๐Ÿ’•


ยฉ ~Princess Amrah~๐Ÿ˜˜

ยฎ ~NWA~

[9:35am, 11/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    *JINNUL-ASHIQ*

                ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                 ๐Ÿ’€

Page 56-60

Na *Amrah*

ยฎ *NWA*


Washe gari.


Tunda safe suka hau shirin zuwa gidan su Mummy. Sun shirya tsaf ta saka ba'kar after dress mai kwalliyar gold colour. Ta saka takalmi gold da jaka gold. Tayi rolling da ba'kin d'an kwalin rigar. Tayi kyau sosai amma daka ganta zaka gane tana cikin tashin hankali.


    'Ko'karin tayar da motar ya Anwar yayi amma ta'ki tashi. Yayi-yayi ta'ki. Kallon Basmah yayi yace "kinga motar ta'ki tashi. Ina tunanin ko ta lalace ne, amma kuma jiya lafiya lau na barta. Ki koma ciki zanje inzo da mai gyara sai ya duba".


    Haka nan Basmah ta shiga gida jiki ba' kwarie. Daga jiya zuwa yau duk tabi ta rame kamar ba ita ba.


     Koda ta shiga gida ya 'kara tayar da motar bugu d'aya ta tashi. Da mamaki ya 'kara kashewa ya kunna nan ma ta 'kara tashi. "Basmah! Ki dawo motar ta tashi ma" ya fad'a da 'karfi dan yasan tayi nisa.


    Dawowa tayi a hankali ta shiga ta zauna. Mutuwa motar ta 'kara yi ya kunna ta amma ta'ki tashi.


   Kallon ta yayi tsaf ya rasa abun cewa. Sun dad'e a haka babu wanda yacewa kowa komai sannan ya Anwar yace "wallahi sau biyu na tayar ta tashi babu matsalar komai amma kinga yanxu ta'ki tashi. Ina tunanin kawai mu barta muje mu hau taxi".


    Batace mashi komai ba ta fito daga motar.


   Treking sukayi har bakin gate d'in estate d'in su. Sun jira sosai sannan taxi tazo suka tsayar. A kunne take amma Basmah na hawa ta mutu. Drivern ya 'kara tayar wa amma ta'ki tashi.


   "Tou ko man ya 'kare ne?" Drivern ya fad'a shi kad'ai.


    "Tou amma kuma ai ban dad'e da zubawa ba" ya 'kara 'ko'karin tada ta sam ta'ki tashi.


   Juyawa yayi ya kalli ya Anwar sannan yace "dan Allah malan kuyi ha'kuri na d'auko ku kuma motar ta'ki tashi. Ina tunanin ko man da aka saka min mai ruwa ne cikin sa. Kuyi ha'kuri ku tari wata ni zan tura ta har in samu masu gyara su tsiyaye min wannan man".


   "Babu komai wallah" ya Anwar ya fad'a yana dariyar da bata kai zuci ba.


    Da sauri Basmah ta suri jakar ta ta nufi hanyar komawa gida. Ya Anwar na kiran ta amma ko waiwayen sa bata yi. Cikin kid'ima ya bi bayan ta har ya cimmata. Yayi juyin duniyar nan akan ta dawo su tari wata taxin amma ta'ki yarda.


    "Ya Anwar kayi ha'kuri kawai ni nasan duk matsalar daga wuri na take. Mu koma gida kawai".


    "Tou shikenan mu koma sai In kira su Mummy su suzo dan gaskiya akwai babbar matsala. Ya zama dole a d'auki mataki tun kafin abun yayi nisa"


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œ and Zarah~B~B๐Ÿ’•_


ยฉ ~Princess Amrah~๐Ÿ˜˜

ยฎ ~NWA~

[12:41pm, 13/07/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: [12:19pm, 13/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

 ๐Ÿ’€

   *JINNUL-ASHIQ*

               ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                 ๐Ÿ’€

Page 61-65

 Na *Amrah*

  ยฎ *NWA*


  Bayan sun koma gida ta nemi wuri ta zauna banda hawaye babu abun da take. Ita kanta tasan lallai akwai matsala babba musamman yanda ko wace mota ta'ki kunnuwa a dalilin ta.


    Ba'a jima ba kuwa sai ga Daddy da Mummy sun zo cikin rikici Daddy yace "Basmah! Me yake damun ki ne? Anwar ya kira mu amma bai fad'a mana komai ba yadai ce muzo akwai matsala".


   Shiru ya biyo baya bata ce masu komai ba sai wani hawayen da yake bin ta. Mummy duk ta gama rud'ewa tace "dan Allah Basmah kiyi mana bayani mana. Ko kun samu sa'bani ne da mai gidan ki?".


   Kai kawai ta gyad'a alamar a'a.


   "Tou me ya faru ina mijin naki?".


   Daidai fitowar Anwar daga d'aki yace "sannun ku da zuwa daddy".


   Wuri ya nema ya zauna ya fara basu labarin duk abunda ya faru har 'karshe.


   Ba 'karamin kid'ima sukayi ba. Dady ya d'auki wayar shi ya nemi numbern malan amma sam! Ta'ki shiga. Ya sake kira in banda switched off babu abunda ake fad'a mashi.


    Ajiyar zuciya yayi kafin yace "kiyi ha'kuri Basmah ki daina kukan nan, bana so kina yin shi. Insha Allahi na miki al'kawarin zanyi bakin 'ko'kari na ganin kin samu lafiya. Yanzu sai na kira numbern malamin da yayi miki aiki a baya amma a kashe".


   Ya dubi Mummy yace "ki zauna da ita sai muje nida Anwar gidan malamin mu taho dashi. Ina tunanin ko wayan shi babu chaji ne".


    "May be kuma ya chanja layi ne, tunda tun lokacin da Basmah taji sau'ki bamu 'kara neman shi ba". Mummy ta fad'a idon ta taf da hawaye.


    Daddy bai ce komai ba suka nufi hanyar fita shida Anwar.


    Bayan sun fita da alaman sunyi nisa sosai Basmah ta fasa wata irin 'kara da k'arfi wadda ni kaina dana tsorata sai da nayar da biro na. Da taimakon Ummul-fadeelah na gano ta a tsorace naci gaba da d'auko rahoto.


   'Kara matsawa nayi naga sai wani irin numfashi Basmah keyi da sauri-sauri had'e da ajiyar zuciya. Sai a lokacin Mummy ta diba wayar ta bata gani ba ta tuna ashe ta barta gida wurin saurin suzo.


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œ and Zarah~B~B๐Ÿ’•_


ยฉ ~Princess Amrah~

ยฎ ~NWA~

[12:34pm, 13/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    *JINNUL-ASHIQ*

                ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                 ๐Ÿ’€

Page 66-70

Na *Amrah*

 ยฎ *NWA*


Kuka sosai Mummy keyi tana neman agaji amma shiru kake ji. Dama kuma estate d'in tsakanin wani gida da wani akwai tazara. Kuma wasu duk basu dawo ba kasantuwar sabuwar estate ce.


   Kafin kace me Basmah ta koma kamar mahaukaciya. Tayi hiri hiri da gashin kanta. After dress d'in jikin ta ta cire ta cire 'karamar rigar ciki. Sai ihu da kururuwa da take yi da 'karfi kamar marar hankali. Sai data cire kayan jikin ta tsaf ya rage bra da pant ne kawai. Duk abunda yake kusa da ita ta d'auka tana ta jifan Mummy. Tun Mummy na iya ta'buka wani abu har tayi yaushi sai ajiyar zuciya take.


   Suna cikin haka sai ga su Daddy sun dawo suma jikin su a sanyaye.


   Ganin yanayin da gidan yake ciki yasa Daddy a rikice ya isa inda Mummy take. Magana ya mata amma shiru babu amsa sai rawar jiki take.


    Da 'kyar ya samu ta dawo hayyacin ta ta iya bashi labarin abun da ya faru. Basmah kuwa tana can suna dambe ita da Anwar komai ta samu ta kwad'a mashi. Da wahala ya samu ya saka mata kaya.


    Cikin rawar murya mummy tace "ina malamin yake ne?".


   Kamar Daddy zayyi kuka yace "Allah yayi mashi rasuwa. Ni yanxu damuwa na d'aya ban san inda zamu samu malami kamar marigayi ba. Kuma ya zama dole mu samo shi cikin hanzari tun kafin abun yafi haka. Ni yanzu ina ganin da mu barta haka gwara kawai mu kaita psychiatry su ajiye mana ita acan dan wallahi idan muka barta anan tsaf zata iya kashe mu".


    Mummy da ya Anwar duk suka yarda da shawarar daddy.


   Ni kuwa nace amma dai Daddy baku kyauta ba, daga fara ciwo sai ku kaita asibitin mahaukata kamar dai baku son ta? Sai a lokacin na tuno da maganar *JINNUL-ASHIQ* Lokacin daya kira Basmah a waya. Dama yace sai ya raba ta da kowa nata duk suji sun gaji da ita. Daga baya kuma ya hallaka ta.


  Sosai naji tausayin Basmah har da kuka nayi mata. Haka na raka su asibitin mahaukatan jikina babu kuzari. Sukayi mata register tare da yin yarjejeniyar idan sun samu malami zasu zo su d'auke ta. Da amincewar likitocin suka tafi nan suka barta tana ta hauka. 


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œand zarah~B~B๐Ÿ’•_


ยฉ ~Princess Amrah~

ยฎ ~NWA~

[4:15pm, 14/07/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: [12:26pm, 14/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    *JINNUL-ASHIQ*

                ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                  ๐Ÿ’€


Page 71-75

Na *Amrah*

 ยฎ *NWA*


Zaune take ta buga uban tagumi tana tunanin "a ina nake? Me ya same ni? Ya akayi na koma haka? Ina ya Anwar yake".


   Ita kanta tasan bata da amsa.


   Wata mata ce tazo wadda bazata wuce shekara 26 ba. Da sauri Basmah ta mi'ke cikin natsuwa tace "dan Allah baiwar Allah a ina nake?".


   A d'an tsorace matar tace "lallai mahaukaci mahaukacin ne, wato tun zaman ki anan yau kwana bakwai kenan duk baki san a ina kike ba, tou nan gidan mahaukata ne irin ki" tana fad'in haka ta tafi tana ci gaba da binciken daya kawo ta.


   Wata razananniyar 'kara Basmah ta saki a lokacin da matar tace mata tana gidan mahaukata ne. 'Kasa ta duke tana tunanin "wannan wace irin rayuwa ce? Me yasa su daddy zasuyi mata haka? Ko wane irin hauka take ai bai kamata su kawo ta gidan mahauhata ba, barin ma ita a tunanin ta lafiyar ta lau".


   Da wannan tunanin wani wahaltaccen bacci ya d'auke ta.


***


Daddy da mummy kuwa tun tafiyar su basu 'kara waiwayar ta ba. Duk yanda sukayi 'ko'karin zuwa wurin ta kawai sai suji baza su iya ba. Haka rayuwa taci gaba da tafiya sai ya Anwar ne kawai yake zuwa inda take. Shima kuma da zarar yaje zataci gaba da hauka ba ji ba gani wani lokacin har ta nemi illata shi. Amma kuma da zarar ya tafi sai ta dawo a hankalin ta.


   Basu kuma 'kara tunanin su nema mata wani malamin ba dan ko addu'ah suka zo yi mata sai su ringa jin kamar ana kwa'be masu baki kar suyi mata.


โ˜…โ˜… *wata uku da kai ta asibitin mahaukata*โ˜…โ˜…


Zaune take kamar kullun ta cusa kanta cikin guiwa a ranta tana 'kara tunanin halin da take ciki. 


   Dariyar da wata mahaukaciya tayi da 'karfi ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da take.


   Mahaukaciyar fuskar ta ba'ki'kirin take dariya baji ba gani. Ta d'auki kamar minti biyar tana dariya kafin ta had'e rai taci gaba da kuka kamar ba ita ba.


   Ganin haka yasa Basmah ta matso inda take tace "kodai kema lafiyar ki lau aka kawo ki nan irin nawa?".


   Baki sake mahaukaciyar tayi ajiyar zuciya tare da goge ba'kin fuskar ta ta nemi wuri ta zauna tace "kar dai kice min tun zaman ki gidan nan lafiyar ki lau?".


   Cikin mamaki Basmah tace "lafiya ta lau, sai wani lokacin kuma sai in jini bana cikin hankali nah, ke fa?",


    Dariya ta 'kara yi tace "lafiya ta lau wallahi, amma kuma ni da kai na na tsiri haukan",


   "Da kanki!?" Basmah ta fad'a cikin mamaki.


    "Da kaina kuwa, labari ne mai tsawo kuma zan baki shi da izinin Allah".


   Jin 'karar tafiya yasa d'ayar mahaukaciyar mai suna Naja'atu taci gaba da haukan ta kamar yanda ta saba.


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œ and Zarah~B~B๐Ÿ’•_

ยฉ ~princess Amrah~

ยฎ ~NWA~

[12:42pm, 14/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    *JINNUL-ASHIQ*

                ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                 ๐Ÿ’€


Page 76-80

Na *Amrah*

 ยฎ *NWA*


Wannan matar ce ta rannan tazo biye da ita mace da namiji ne.


   "Gata can tana haukan data saba, ai ni tunda nake ban ta'ba ganin mahaukaciyar da haukan ta baya sau'ki kamar Naja'atu Sulaiman Mai kud'I ba, kullun abun nata ta'azzara kawai yake yi kamar ba'a d'aukar mataki" matar mai suna Shafa ta fad'a cikin halin ko in kula.


   'Daga hannu matashin yayi kamar zai duki Shafa sai kuma ya fasa yace "kar ki kuma kiran matata da mahaukaciya. Hauka dai da kike gani ba ita ta bama kanta ba Allah ne ya d'ora mata. Kuma wallahi in banda su mama da suka matsa akan sai an kawo ta gidan nan da bazan kawo ta ba. Duk abunda zatayi a gida zan barta. Amma yanzu ma ina 'ko'karin convincing insu kuma zasu yarda da izinin Allah".


   'Dayar matar dake biye dashi ta ta'be baki tace "a haka zaka 'kare bautar mahaukaciya".


  Bai tanka mata ba sai cewa da yayi "sannu Naja'atu! Insha Allahu sau'ki ya kusa yaxo miki. Kuma halin da kike ciki ba wai dan Allah baya son ki bane. Jarrabta ce kawai".


   Ita kuwa Naja wata 'kara tayi da 'karfi tana kallon shi tana wata dariya miyau na fita daga bakin ta.


    Fita yayi dan bazai iya jure ganin matar shi kuma farin cikin shi a cikin wannan halin ba. Bin bayan shi Shafa da d'ayar budurwar sukayi suka bar Naja nata hauka.


***


Duk abunda yake faruwa akan idon Basmah ne tana mamaki.


   'Kara matsawa tayi inda take tace "ohh! Kekam miye ne haka wai? Ni ina neman wanda zai fitar dani na rasa amma ke kina 'kara jawo wa kanki hauka".


   Wani zazzafan hawaye ya futo daga idon Naja. Goge shi tayi sannan tace "baiwar Allah nasan tabbas zakiyi mamaki dama. Tou wallahi da zaman da zanyi a gida nafi son zaman gidan mahaukatan nan ma",


   Cikin mamaki Basmah tace "a haka a 'kazance? Ba'a ganin ka da kima, sai duka da hantara kullun".


    "A hakan fa wallahi nafi son zama anan. Koda kuwa zan dawwama anan har 'karshen rayuwa ta tou bazan ji komai ba matu'kar malan bai bani izinin fita ba" Naja ta fad'a ko a jikin ta.


   Ni kaina Amrah naji mamaki sosai. Tou wane irin abu ne zai sa da kanta tace tafi son zama gidan mahaukata? Hmm! Muje zuwa dai zamu ki komai insha Allahu.


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œ and Zarah~B~B_๐Ÿ’•


ยฉ ~Princess Amrah~

ยฎ ~NWA~

[4:21pm, 14/07/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: [12:56pm, 14/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

   *JINNUL-ASHIQ*

                ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                 ๐Ÿ’€

Page 81-85

Na *Amrah*

ยฎ *NWA*


  Basmah tace "nikam dama wani abu ne yake damu na kuma na rasa wanda zan tinkara da maganar",


   Cikin natsuwa Naja tace "ina sauraren ki",


   "Yau kumanin wata na uku da 'yan kwanaki a gidan nan, tou tunda nazo banyi period ba, sai kuma yanzu nake ganin mara ta tana d'an tasowa a hankali",


   Naja ta dube ta tace "kina da aure ne?",


   "Ina da aure. Sati d'aya da aure na ciwo ya same ni amma ni a tunani na shafar *JINNU* ne, iyaye na sun kasa d'aukan ko wane mataki sai suka kawo ni gidan nan. Shi yasa nake tunanin iyaye na basu sona. Nasan a halin yanzu ko na fad'a nace lafiya ta lau babu wanda zai yarda saboda dama duk inda mahaukaci yake haka yake fad'I", Basmah ta fad'a tare da share hawayen daya wanke mata kumatu.


   Cikin tausayi Naja tace "Subhanallahi! Ashe ke abunda ya faru dake kenan? Amma kuwa na tausaya miki. Sai nake tunanin kamar kina da juna biyu ne".


   Da mamaki Basmah tace "so biyu kawai miji na ya ta'ba kusanta ta da sunan aure fa, kina ganin zan iya d'aukar ciki daga wannan?",


    "Zaki iya mana" Naja ta fad'a. Taci gaba da "ko so d'aya zaki iya d'aukar ciki",


    Tagumi kawai tayi bata sake cewa komai ba sai bin cikin ta da take da kallon mamaki.


   Naja'atu ce ta katse shirun ta hanyar cewa "kar ki damu insha Allahu zan taimake ki ki fita. Tunda na shigo gidan nan ban ta'ba tunanin akwai ranar da zanyi sha'awar fita ba. Amma yanxu da naji labarin ki sai nake tunann in fita domin taimaka miki".


   Kallon mamakI kawai Basmah ke bin ta dashi a ranta tana fad'in "tou wai wacece wannan? Me ya shigo da ita gidan nan? Ta wace hanya take ganin zata iya taimako na?"


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œand Zarah~b~B๐Ÿ’•_


ยฉ ~princess Amrah~

ยฎ ~NWA~

[1:16pm, 14/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    *JINNUL-ASHIQ*

                 ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                  ๐Ÿ’€

Page 86-90

Na *Amrah*

 ยฎ *NWA*


Maganar zucin da Basmah keyi ce ta bayyana. Cikin rashin damuwa da wannan tambayoyin Naja tace "yanzu kuwa zan baki amsar tambayoyin ki".


   Gyara zama tayi kafin tace "sunana Naja'atu Sulaiman Mai kud'I, mahaifi na yaci sunan mai kud'I a dalilin dukiyar da gare shi. Babban d'an kasuwa ne da yayi suna ta hanyar smuggling d'in shinkafa. Sunyi auren soyayya shida mahaifiya ta. Shekarar su d'aya cif da aure suka haife ni, ina samun gata sosai daga wurin su. Kwatsam tafiya ta kama su ta fita China su biyun. Gidan kakana Malan Mu'awuya suka kaini a lokacin da zasu tafi nasha kuka sosai. Haka suka barni su kansu ba dan ransu yaso ba.

  A daren ranar ne sa'ko ya riske mu cewa sunyi had'arin jirgi duka sun mutu. Nasha kuka sosai kafin daga baya nasawa raina dangana na daina.


   Na samu kyakkyawar tarbiyya daga wurin malan Mu'awuya duk da shi kad'ai yake zaune matar shi ta rasu. Babban malami ne wanda yayi suna a fannin malanta. Baya shirka ko kad'an sai dai yana amfani da wasu 'boyayyun adduoi daba kowa yasan su ba. Idan kika ga yanda malan yake aiki zaki ranste yana huld'a da *JINNU* ne kuma baya yi. Yaso ya koyar dani su amma sai na'ki kasantuwar ina tsoron yanda yake yi.


   Shekara ta goma sha shida a duniya Mansur yazo ya nuna yana sona. Malan ya amince mashi daya fara neman aure na saboda ya yaba da hankalin shi.

   Ba'a d'auki dogon lokaci ba ya turo magabatan shi aka fara maganar aure.


   An d'aura aure na da Mansur cikin jin dad'I da tausayi na da yake a matsayi na na marainiya. Akwai wata 'yar uwar shi mai suna Safna, cousin sistern shi ce ashe itace taso ta aure shi sai ya'ki a dalilin rashin tarbiyyar ta. Tun daga lokacin ta tsane ni bata son gani na. Mahaifiyar Mansur na taimakon ta saboda itama bata sona. A duk lokacin da nakaiwa malan koke na sai ya bani ha'kuri yace bazai mun aiki yanzu ba sai nan gaba. Haka naci gaba da had'iyar guba na rashin son dangin miji.


   Kwatsam wata rana malan ya kira ni a waya yace yana son gani na, da sauri na tambayi Mansur ya barni na tafi. Anan ne yake shaida mn fa Safna ta kaini wurin wani boka akan za'ayi aikin da za'a kashe ni ko a haukatar dani. Na tsorata matu'ka malan yace "kar ki damu. Nayi istahara akan abun. Mugayen JINNU ne ake so a turo miki" ya bani wata adduah yace in tofa ta a jiki sannan Inyi wanka, inci gaba da haukan 'karya, wannan adduar ita zata kare ni daga *JINNU* da suka turo mn. Haukan 'karya kuma dan kar ta fahimci lafiya na lau ta sake kaini wurin wani bokan wanda zaa wahala ba'a karya aikin shi ba. Daga farko na tsorata da maganar malan sai kuma daga baya na yarda dan yace abn na lokaci ne, idan komai ya lafa zai nemi in fito".


   Har a lokacin Basmah bata daina kallon Naja ba. Kafin wani lokacin taci gaba dayi mata kuka. Dan labarin Naja ya rikita ta sosai.


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œ and Zarah~B~B_๐Ÿ’•


ยฉ ~princess Amrah~

ยฎ ~NWA~

[10:49pm, 15/07/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: [11:54am, 15/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

 ๐Ÿ’€

   *JINNUL-ASHIQ*

                ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                  ๐Ÿ’€

Page 91-95

Na *Amrah*

 ยฎ *NWA*


   Daurewa tayi cikin 'karfin hali tace "taya kike tunanin zaki fitar dani? Bayan kuma ko ina a rufe yake, babu wanda zai barmu mu fita?",


   Murmushi kawai Naja tayi kafin tace "hauka sosai zamu tayar nida ke, ai dama abunda yasa aka ware mu nan nida ke saboda haukan mu bata duka bace",


  "Kinga can" Naja ta nuna wa Basmah da yatsa,


  "Duk mahaukacin da yake a d'akin can tou ya ri'ka sosai a hauka, suma idan suka samu wuri har kashe mutun suna iya yi, tou idan mun tashi zamu tayar da namu haukan ne, dama kuma duk baza suyi tunanin haukan mu zai sa muyi attempting guduwa ba, shi isa ma suka saka mana mai gadi d'aya, kawai bubbuge shi zamuyi mu samu mu isa bakin asibitin. Da zarar mun fita sai muje bakin famfon nan mu wanke fuskokin mu mu nufi waje, a bakin gate d'in fita nasan babu wanda zayyi zargin mu mahaukata ne saboda dai gamu tsaf cikin hankalin mu, ke mu ma gaishe su dan su 'kara tabbatarwa, domin mahaukaci baya gaida mutane a cikin natsuwa".


   Cike da mamaki Basmah tace "amma fa kin iya kawo shawara, shawarar nan taki tayi",


   Zumbur Naja ta mi'ke ta fara le'ken window.


    Dawowa tayi ta zauna tace "mu bari sai zuwa magrib kafin nan kinga duhu ya fara baza'a gane fuskokin mu ba",


   Basmah tace "ehh haka ne Naja, sai mu zama cikin shiri",


   Nima kuma na zauna a shiri nah, dan ina son ganin yanda zasu gudu daga babban gidan mahaukatan da yake cike da masu tsaro (securities).


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œ and Zarah~B~B_


ยฉ ~Princess Amrah~

ยฎ ~NWA~

[10:44pm, 15/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    *JINNUL-ASHIQ*

                 ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                   ๐Ÿ’€

Page 96-100

 Na *Amrah*

  ยฎ *NWA*


A hankali suke tafiya cikin sand'a har suka isa bakin d'akin su inda mai gadin d'akin yake.


 Naushi guda Naja takai mashi ya baje 'kasa, waiwaye yafara yi yana neman ta inda aka duke shi, a 'boye Basmah ta jawo hannun shi duka biyun ta had'e su wuri d'aya ta baya.


   Nuni Naja tayi mata da ta bata 'dan k'yallen dake hannun ta, mik'a mata shi tayi ta samu ta nad'e bakin shi dashi tana mayar da ajiyar xuciya ita kanta tasan tayi namijin 'kok'arin makar datayi mashi ta farko.


 Basu bar wurin ba sai da suka tabbatar da bazai iya ta'buka komai ba sunyi mashi likis sannan suka tafi.


   A bakin famfo suka tsaya ganin babu kowa. Fuskokin su suka wanke sosai tare da barin wurin.


   Naja ta juyo ga Basmah tace "dan Allah ki cire duk wani tsoro da kike, bana so ko kad'an ki sha jinin jikin ki idan ba haka ba kuma zasu iya gane mu, mubi a hankali cikin natsuwa mu samu mu fita, idan ma zasu mana wasu tambayoyi muyi k'ok'arin basu gamsasshiyar amsa kinji?",


   Basmah batace komai ba saboda wani jiri da yake neman d'iban ta, adduoi ta fara jerowa wanda ita kanta bata san yaushe rabon ta da yin su ba.


   Tafiya suke mai cike da natsuwa har suka isa bakin babban gate d'in asibitin. Nan gaban su ya bada rass! Saboda securities d'in dake wurin duk masu ilimi ne ba irin na d'akin su ba.


  Kallon Basmah tayi tace "Action",

  Basmah ta k'yalla mata ido d'aya.


   "Tou yanzu 'kawata sai yaushe zamu 'kara xiyartar Jiddah kuma? Gaskiya haukanta yana matuk'ar tsorata ni, amma tinda dolen muce ai dole mu ringa le'ko ta akai-akai", Basmah ke maganar kamar da gaske.


   Naja tace "haka ne Salmah! Fatan mu dai Allah ya bata lafiya", "ameen" Basmah ta fad'a a daidai lokacin da wani mutumi ke kallon su. Kallon mamaki yake bin su dashi ta yanda ya gansu nagartattun matan hausawa amma suke yawo babu mayafi.


ยฉ ~Princess Amrah~

ยฎ ~NWA~

[11:15am, 16/07/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: [10:13am, 16/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

 ๐Ÿ’€

   *JINNUL-ASHIQ*

                 ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                  ๐Ÿ’€

Page 101-105

 Na *Amrah*

  ยฎ *NWA*


Ganin irin kallon da yake bin su dashi yasa sukayi saurin gaishe shi. Amsawa yayi fuskar shi d'auke da alamomin tambaya sai dai baice masu komai ba har suka fita.


   Gaban su kuwa fad'uwa kawai yake dan kar ya kira su. A haka har suka 'bule daga harabar asibitin baki d'aya.


   Adaidaita suka tsayar Naja tace "malan Rahamawa zamuje",


   "Naira saba'in saba'in zaku bayar" ya fad'a fuskar shi babu annuri.


  Basmah ta kalle ta cikin alamar tambaya sai dai bata ce mata komai ba, itakam tana mamakin halin Naja'atu, wani lokacin idan tayi abu kamar namiji take yin sa, bata da tsoro ko kad'an.


   Napep d'in suka hau har suka shiga Rahamawa, da kwatancen Naja har suka isa 'kofar gidan malan Mu'awuya.


  Sauka sukayi Naja tace "ka jira mu shiga zan kawo maka kud'in ka",


  Mai napep kuwa ya d'aure fuskar shi tam! Yace "lallai sai dai Basmah ta tsaya ita kuma Naja ta shiga ta kawo masa kud'in sa",


   Hakan kuwa tayi, koda ta shiga ta samu malan zaune tsakiyar almajiran sa suna 'daukan karatu, a firgice malan yace "Naja'atu! Lafiya? Me ya dawo dake bayan kuma bance ki dawo ba?",


   Hankalin ta kwance tace "malan duka zan amsa maka tambayoyin ka, amma ka kawo kud'in mai adaidaita yana waje yana jira na",


   "Nawa ne kud'in" ya fad'a cikin d'aurewar kai.


   "Malan mu biyu ne nida 'kawata, duka d'ari da hamsin ne",


  Karkatawa yayi ya zaro d'ari biyu yace ta kawo masa canji. Har 'kasa ta duk'a sannan ta kar'ba ta nufi waje. Can ta samu mai napep sai masifa yakewa Basmah, ita kuwa da yake bata iya fad'a ba sai ha'kuri take bashi shi kam baji ba gani yake zazzaga mata ruwan masifa.

  Naja tace "Basmah me yake faruwa ne wannan mutumin yake miki masifa ke kuma har kike wani bashi ha'kuri? Ke kam wannan halin naki 'bata mn rai yake wallahi",

  Tsoki tayi da k'arfi sannan tace "ga kud'in ka nan kai ne matsiyaci, mu munfi k'arfin d'ari da hams...". Kafin ta gama magana taji wata irin 'kara da 'karfi.


   Koda ta duba gefen da Basmah take ta ganta kwance 'kasa kamar a sume, sai wani numfashi take da sauri da sauri, bakin ta na motsi shi kad'ai. Cikin al'ajabi mai napep ya yar da kud'in a tsorace yaja napep d'in sa ya tafi.


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œand Zarah~B~B๐Ÿ’•_


ยฉ ~Princess Amrah~

ยฎ ~NWA~

[10:26am, 16/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

 ๐Ÿ’€ 

   *JINNUL-ASHIQ*

                 ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                  ๐Ÿ’€

Page 106-110

 Na *Amrah*

  ยฎ *NWA*


Cikin kid'ima Naja ta fara tunanin yanda zatayi ta shiga da Basmah cikin gidan malan, shawara ta yanke akan kawai ta shiga gidan ta fad'a masa, a k'ofar gidan taci karo dashi saboda yaji ta shiru shine ya biyo yaga ko lafiya. Ganin ta a firgice yasa shi cewa "lafiya? Ina abokiyar tafiyar taki?",


    "Malan gata can kwance ba lafiya, dama itace dalilin zuwan mu nan, acan gidan mahaukatan ne muka had'u da ita, shine take fad'a min ai ita ciwon ta bana asibiti bane, shine aka kaita can kuma lafiyar ta lau amma da zarar aka ziyarce ta sai ta koma da hauka, ni kuma jin hakan yasa na yanke hukuncin kawo ta wurin ka dan inaga kaman zaka iya mata komai ta samu lafiya",


  Cikin tausayawa Malan yace "ina zuwa, ki koma ki tsaya kusa da ita",


   Cike da tsoro Naja ta koma kusa da Basmah, malan kuwa ya shiga gida.


   Ya dad'e bai fito ba sai gashi ya fito hannun shi ri'ke da wata gorar _Swan water_da akayi wa 'yar 'bula daga saman marfin.


   K'arasowa yayi inda suke yace da Naja "matso daga baya", matsowar tayi taci gaba da kallon ikon Allah.


   Da bakin murfin gorar ta inda ya fasa yaci gaba da yayyafawa Basmah shi akai da jikin ta baki d'aya, 


   "Tashi mu shiga gida" ya fad'a da 'karfi dan koni sai dana tsorata,


   Tashi Basmah tayi tana kallon shi sai zazzare ido take tabi bayan shi, Naja ma bin bayan su tayi dan ganin ikon Allah, dama haka Malan Mu'awuya yake sarrafa aljanu ta yanda yaga dama, ko wane irin *JINNU* Suke jikin mutun da zarar anzo k'ofar gidan shi tou sai sun taso kuma tsoron shi suke yi, haka suka isa cikin gidan yana sarrafa Basmah yanda yaga dama.


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œ and Zarah~B~B๐Ÿ’•_


ยฉ ~Princess Amrah~

ยฎ ~NWA~

[11:22am, 16/07/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: [10:52am, 16/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    *JINNUL-ASHIQ*

                 ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                   ๐Ÿ’€

Page 111-115

 Na *Amrah*

  ยฎ *NWA*


*WASHE GARI*


  Zarah~B~B ce tafe cikin shigar alfarma, swith material ne background d'in shi black sai manyan flowers light blue, an mata wani rantsattsen stone works irin zanen flowers d'in material d'in, ta yafa gyalen kashka mai stones black da ratsin light blue, hannun ta ri'ke da blue hand bag irin ta zamani, takalmin ta ma blue ne, kai! Abun dai sai wanda ya gani dan nima kaina sai dana had'iyi yawu sanda na ganta.


  Sauka tayi daga adaidaita ta bashi kud'in shi. A bakin House no. 15 ta tsaya, ganin shi rufe yasa ta tababar koba gidan bane, k'ara kallon shi tayi sosai a ranta tace "tabbas nan ne gidan Basmah, tou amma ya akayi yake rufe? Ina taje? Ko ta tafi _School_ ne?",


   Wayar ta ta zaro daga jaka tace "da dai naso na baki _surprise_ ne, amma barin kira ki",


   Jin wayar a _switched off_ yasa ta k'ara nema amma _still_ a kashe.


   Da sauri tayi k'ok'arin tsayar da mai napep d'in daya kawo ta dan a tunanin ta ko tana gida ne amma har yayi nisa. Hankalin ta tashe tace "Allah dai yasa lafiya", taci gaba da tafiya har ta isa _main _gate_ na _estate_ 'din.


   Taxi ta samu ta hau ta fad'I inda za'a kaita.


   Da sallamah ta shiga gidan ta nufi side 'din Mummy. Ta samu ya Anwar zaune yana kallo hankalin shi kwance, ganin shi haka yasa hankalin ta ya d'an kwanta. Har k'asa ta duk'a ta gaishe shi ya amsa cikin girmamawa a daidai fitowar Mummy. 


   "Sannu Mummy" Zarah ta fad'a, "yauwa Zarah, ya gida yasu mama?", "lafiya lau suke, Mummy Basmah fa?",

  Hawaye Mummy ta share kafin tace "Basmah na gidan mahaukata Zarah",

   Bata gama maganar ba Zarah ta mik'e tace "Mummy gidan mahaukata!? Me ya same ta? Me yasa kuka kaita can kamar marar galihu?"


  Mummy tace "Wallahi dole ne ta kama sai an kaita, ta nemi kashe ni ne dan hauka, mu kuma kawai muka kaita da nufin idan mun samu wani malamin sai a karb'o ta, tou gaskiya bamu samu wani ba har yanzu kusan. Wata hud'u kenan tana can",


   Sosai Zarah ke kuka tace "gaskiya mummy baku kyauta ba, bakuyi wa Basmah adalci ba, saboda ciwon Basmah ba koda yaushe take hauka ba, zuwa mata yake dan dama haka ciwon *JINNU* yake, yanzu tana can cikin ri'ka'k'kun mahaukata baku gudun su tirar da ita mummy?",


   Daddy dake k'ok'arin saukowa daga bene yace "tabbas maganar ki gaskiya ne Zarah, sai yanxu nake dana sanin abunda mukayi mata, tou wai ma miye dalilin mu nak'in nema mata magani daga wurin malamn musulunci?",


   Da sauri ya Anwar dake fitar da hawaye yace "nima tambayar da nake yiwa kaina kenan, tou waima gwara ni tunda ko yaya ina xiyartar ta, amma Daddy ina tunanin tun ranar da muka kaita baku sake zuwa wurin ta ba" .


  Kuka sosai Mummy keyi tana fad'in "Allah sarki! Basmah ki yafe mana, ki yafe wa iyayen ki, 'ya d'aya da Allah ya bamu amma mun kasa kula da ita sosai, mun kasa nema mata lafiya",


   Daddy yace "kuka ba naki bane, ku tashi mu tafi _psychiatry_ d'in kawai mu kar'bo 'yar mu".


   Hakan kuwa sukayi. Su duka hud'un suka kama hanyar asibitin mahaukatan da aka kai Basmah. Nima basu barni a baya ba, biye nake dasu dan ganin yanda zasuyi idan sukaji Basmah ta gudu.


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œ and Zarah~B~B๐Ÿ’•_


ยฉ ~Princess Amrah~

ยฎ ~NWA~

[11:10am, 16/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    *JINNUL-ASHIQ*

                 ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                  ๐Ÿ’€

Page 116-120

 Na *Amrah*

  ยฎ *NWA*


Koda sukaje ba k'aramin rikicewa sukayi ba da sukaji tun jiya ake neman Basmah da k'awarta ta d'aki amma ba'a gan su ba, Zarah kamar tayi hauka mummy ma haka, dady da ya Anwar kuwa k'arfin hali kawai suke yi suna basu hak'uri.


    Tare da shugabannin gidan mahaukatan suka rankaya sai babban gidan _radio_ dake cikin garin katsina. Nan aka saka cigiyar Basmah da Naja, tare da mak'udan kud'I ga duk wanda ya gansu.


***


Ita kuwa Basmah kula sosai malan yakeyi da ita, amma har a lokacin aljanin bayyi magana ba, kwananta biyu a gidan ne malan ya had'a mata wani wani sassak'ne magani mai had'e da garin ganyen magarya, a cikin ruwa ya saka su da wani turare d'an k'arami yasa Naja tayi mata wanka dashi. Da k'yar ta yarda ake mata wankan dan jin shi take kamar ana zuba mata garwashi a jikin ta,


   A haka suka fito daga wanka Naja ta shafa mata wani mai da yake had'e da garin habbatus-sauda da mski a ciki, shima dai bata so dan dole ne yasa ta yarda ake shafa mata shi.


   Kayan sawan da malan ya siyo mata Naja ta saka mata tayi kyau abunta. Wurin malan suka tafi tace "malan gamu mun gama",


   Malan yace "tou sannun ku? Ya jikin naki?" "Jiki alhamdulillahi malan" Basmah ta fad'a.


   "Tou masha Allah, yanzu nake tunanin yanda zanyi suyi magana, saboda ko anyi Magani matuk'ar ba'aji dalilin shigar su jikin ki ba akwai matsala, saboda zasu iya su k'ara dawo Miki dan bazaki kiyayi abunda yasa suka shige ki ba saboda baki sani ba, amma barin gani",


   "Aminu!" Ya kira da k'arfi sai gashi yazo, "jeka kira su Nasiru da sauran su",


   Bai jima ba sai gashi da maza sun kai goma, nan ya fad'a masu yanda zasuyi suka d'auro alwala. Karatu suka hau yima Basmah kowane da inda yake kanrantawa cikin su, Malan kuwa yana yi yana tofa mata adduoi a kanta. Can ta fasa wata k'ara a lokacin da malan ya yayyafa mata wani ruwa.


   Take muryar ta ta canza ta koma ta maza sosai tana fad'in "zan fita! Wallahi zan fita!! Kar ku k'ona ni!! Niba musulmi bane, sunana _Solomon_, na aure ta ne tun ranar da aka d'aura auren ta da mijin ta, yanzu haka tana d'auke da ciki na wata uku".


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œ and Zarah~B~B๐Ÿ’•_


ยฉ ~Princess Amrah~

ยฎ ~NWA~

[2:57pm, 17/07/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: [11:56am, 17/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    *JINNUL-ASHIQ*

                 ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                  ๐Ÿ’€

Page 121-125

 Na *Amrah*

  ยฎ *NWA*


  Cikin kwanciyar hankali malan Mu'awuya yace "bazan 'kona kaba _Solomon_, ina so ka ajiye hankalin ka kayi min bayanin komai",


   _Solomon_yace "na shiga jikin ta ne tun ranar da aka haife ta da yamma, bayan mamanta ta shiga wanka suka ajiye ta ita kad'ai kwance tana ta tsala kuka, haka kawai nazo gittawa naji wasu yarana wanda na haifa daga cikin *JINNU* suna fad'a har d'ayan na fad'in "kai nafa riga ka, nine nace zan shige ta, kaga fa kyakkyawa da ita kuma basu nema mata tsari daga gare mu ba kafin su ajiye ta",


   D'ayan kuma yace "k'arya ne na riga ka mana, tun farko ma ai ni na gwada maka ita kafin ka ganta",


   Jin suna wannan gardamar yasa nace dasu "duk ku saurare ni, kuna magana akan waccan jinjirar bil-adama ko?",

 "Ehh" suka fad'a su duka,

Had'iyar yawu nayi sannan nace "tou ni zan raba maku gardama, ku barni na shiga jikin ta saboda ni bazan cutar da ita ba, ku kuma sai ku ringa ziyartar ta akai-akai",

  Suka jinjina kai tare da fad'in "hakan ma yayi papa",


    Nayi dariya da k'arfi saboda yarinyar babu tsari a tare da ita, cikin sauk'I na shafe ta tun daga ranar bata sake lafiya ba, kullun sai yawan kuka, asibiti babu inda basu kaita ba amma babu sau'ki. Har ta fara girma babu sau'ki bana barin ta zama a makaranta gashi ba ta wani girma sosai har suna kiran mata sickler.


   Ban tab'a bayyana ba sai wata rana ana karatu a ajin su, jin an karanto wata aya da mu *JINNU* Take k'ona mu yasa na bayyana ba shiri, amma kuma banyi magana ba.


   Tun daga nan kuma sai zubar da jini take yi ba dare ba rana, duk wata sai an mata k'arin jini.


   Bayan ta gama makaranta da wahala ne wata rana yaran nan nawa buyu sukaje jikin ta, wanda kuma ranar ne suka nemo wani malami wanda shi ya k'ona min yara, tun daga lokacin suka rasa rayukan su, nayi kuka sosai na rashin su saboda dama sune kawai gare ni gashi kuma an kashe min su, tun daga ranar na d'auki alwashin hallaka Basmah sabida a dalilin ta ne komai ya faru. Sai dai kuma duk lokacin da zanyi yunk'urin shiga jikin ta sai in tarar da ita tana amfani da wasu magani da bamu son su mu *JINNU*, hakan yasa na hak'ura na barta kafin wani lokaci.


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œ and Zarah~B~B๐Ÿ’•_


ยฉ ~Princess Amrah~

ยฎ ~NWA~

[12:13pm, 17/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€  

    *JUNNUL-ASHIQ*

                 ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                   ๐Ÿ’€

Page 126-130

 Na *Amrah*

  ยฎ *NWA*


Babban sakaci Basmah da Iyayen ta sukayi kasantuwar daina shan maganin da tayi tunda taji sauk'I, dama maganin ne ya hana ni shigar ta domin illatata sai gashi kuma ta daina, hakan yayi min dad'I sosai cikn sauk'I na koma jikin ta.


   Amma kuma na rasa hanyar da zan halaka ta saboda ko ba komai ita ma'abociyar sallah ce, hakan yasa murna ta ta koma ciki. Kwatsam na yanke shawarar kiranta a waya dan nasan da zarar taji murya ta shikenan tata ta k'are dole zata mutu. Hakan kuwa nayi sai dai nayi rashin sa'a dan bata d'auki kiran ba, haka na nace yi amma bata ma kula da kira.


   Ranar d'aurin auren ta ne abokanan ta suka bata shawara akan ta d'auki kiran duk da yake suna ne kawai babu number. Tun daga lokacin kuma na aure ta. Ranar da mijin ta ya fara kusantar tama tare dani akayi komai.


   Yanzu haka cikin jikin ta kashi biyu ne, rabi nawa rabin kuma na mijin ta, komai zai iya faruwa idan ta tashi haihuwa, dan indai abu d'aya ta haifa dole zaizo wata kalar halitta daga baya kuma ya koma hannun mu kaga sai ya zama madadin yaro na d'aya a cikin biyu. Idan kuma 'yan biyu ta haifa tou d'ayan na mijin ta ne d'ayan kuma *JINNU* ne".


   Shiru yayi daga nan kafin yaci gaba da "sai gashi kuma yau an kawo ni gurin ka, kaine mutun na farko da nake tsoro bayan rasuwar malamin daya kashe min yara, ina fatan karka k'ona ni tunda dai kaga nine da gaskiya da aka kashe min yara basu ba".


   Da k'arfi malan Mu'awuya ya daka mashi tsawa yace "ka rufe min baki! Rufe min baki nace, ku har wani gaskiya ne daku? Ka rasa cikin jinsin zama sai na bil-adama, koda aka kashe maka yara ai ku kukaja, inda ace kunyi zamanku a jinsin ku waye zai same ku har can ya kashe? Me yasa da kaji yaranka suna maganar zasu shige ta baka hana su ba? Kaga kenan kaine ka kashe yaranka da kanka, kuma wallahi matuk'ar baka tafi ba wurin sarkin *ALJANNU* zan kai k'arar ka, babu wani k'ona ka da zanyi",


   Dariya da k'arfi _Solomon_yayi kafin yace "bana tsoron kowa, dan kaga ina baka ha'kuri shine zaka ringa min wasa da hankali? Tou kayi yanda kake so d'in".


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œand Zarah~B~B๐Ÿ’•_


ยฉ ~Princess Amrah~

ยฎ ~NWA~

[3:02pm, 17/07/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: [12:29pm, 17/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

 ๐Ÿ’€

   *JINNUL-ASHIQ*

                ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                  ๐Ÿ’€

Page 131-135

 Na *Amrah*

  ยฎ *NWA*


  Matu'ka ran malan ya b'aci, cikin ranshi yace "da ina tunanin cikin sauk'I zai tafi ashe mai tsaurin ido ne, wato so yayi kawai in k'yale shi a matsayin ya tafi yaci gaba da azabtar da yarinya, munafuki kenan",


   Kafin malan yayi magana sukaji sallamah a gidan, wata mata ce rik'e da yaron ta wanda da alama ba'a jima da yaye shi ba dan baiko iya magana ba, tana zuwa nan taimako wurin malan akan babban yaron ta da yake mata sace-sace tun yana k'arami har yanzu daya girma ya shahara da sata.


   Malan ya amsa sallamar ta tare da fad'in "sannu da zuwa Ummu Abrar", (lol๐Ÿ˜€)

  "Yauwa sannu malan" ta fad'a fuskar ta da murmushi.


   Tabbas malan yaji dad'in zuwan ta dan dama tunani yake ina zai samu k'aramin yaro a wannan lokacin saboda aikin da yake so yayiwa _Solomon_ dole sai da k'aramin yaro.


  Bayan ta gaishe shi cike da girmamawa ya amsa fuska sake, yace "kamar kin san ina cikin buk'atar k'aramin yaro kuwa, irin aikin da nayiwa wata mata kwanaki da Abrar d'in ki yauma shi nake so nayi, kwatsam kuma sai gaki" ya k'ara sa maganar da murmushi.


   Matar tace "aikuwa dai malan gani kamar daga sama, ka gama sannan in fad'a maka yanda ake ciki",


   _Solomon_ dai ya hakimce kamar wani sarki shi a dole isasshe. Malan mu'awuya ya jawo alk'alamin shi da tawwada da wata farar takarda, take ya fara rubutu da ajami, nidai ban mayar da hankali na ba sai kallon ikon Allah kawai nake. Tsaf malan ya gama rubutun ya nad'e takardar shi. Adduoi yaci gaba dayi tare da wani yare wanda shi kad'ai yasan abnda suke nufi. Sai daya gama duka naga ya k'urawa wuri d'aya ido yana kallo.


   "Zonan Abrar" ya fad'a.


  Abrar kuwa daman akwai shi da son mutane, zuwa yayi wurin malan fuskar shi cike da farin ciki. 


  Mi'ka mashi takardar malan yayi tare da fad'in "kaga wancan mutumin da yake kan babbar kujerar can shi zaka ba wannan",


  Naja'atu ta tsare wurin da ido cikin tsoro amma Ita bata ga kowa ba, ummu abrar ma dai bataga kowa ba amma ita bata tsorata ba saboda kwanakin baya anyi a gabanta da Abrar.


   Cikin dariya Abrar ya dawo wurin malan, malan yace "har ka bashi ko?",


   Kai ya d'aga mashi alamar ehh.


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œ and Zarah~B~B๐Ÿ’•_


ยฉ ~Princess Amrah~

ยฎ ~NWA~

[1:40pm, 17/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€  

    *JINNUL-ASHIQ*

                ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                  ๐Ÿ’€

Page 136-140

 Na *Amrah

  ยฎ *NWA*


 Wata irin k'ara ce mai cike da ban tsoro duk gidan ya d'auka, ga wata irin jijjiga da suke ji ana yi da gidan kamar za'a zazzagar dasu duka. Adduah sosai malan yake yi yana k'ara tofawa Basmah dake ta faman ajiyar zuciya.


    Guguwa mai k'arfi ta taso cike da k'ura da iskah mai rikitarwa. Take guguwar ta cibre guri d'aya ta koma siffar babbn mutun kanshi da rawani fuskar shi cike da furfura d'auke da annuri.


    Har k'asa halittar ta tsuguna gaban malan ba tare data fad'I komai ba. Cik'in k'ank'anin lokaci kuma na nemi halittar babu ita. Komai ya natsu ya koma daidai kamar babu abunda ya faru.


   Malan Mu'awuya yace "Alhamdilillah! Da haka muke maganin *JINNU* masu taurin kai",

  Ya juya ya kalli Naja dake zaune tayi mutuwar zaune dan tunda take bata ta'ba ganin malan yayi irin haka a gabanta ba, ko zayyi tou sai yayi yanda yayi yasa ta bar gidan. Yace "Zakiyi mamaki idan na fad'a maki kome ya faru ko?",

   Cikin tsoro Naja ta d'aga kanta ba tare da tayi magana ba.

   Yace "yaron nan da kika ga na ba ma sak'o tou wurin sarkin *ALJANNU* na aike shi bayan na nemi yazo, a cikin wasi'kar na rubuta mashi duk abunda ya faru da kuma taurin kai da ya nemi ya nuna min, da yake sarki ne mai adalci kuma nasan zayyi adalcin yasa nabar komai a hannun shi.

   Yanzu wannan guguwar da kika gani inda kin kula zakiga ta koma halitta dink'ulalliya, tou sarkin ne da kanshi yazo ya bani hak'uri ya kuma shaida min da ya d'auki mummunan mataki akan _Solomon_kuma yasa an d'aure shi har k'arshen rayuwar sa, yanzu aiki ya rage namu, sai musan yanda zamuyi ta kare kanta da kanta, ina nufin ta ri'ki adhkar d'in ta saboda shine makamin mumini kuma babu wani mutun ko *ALJAN* da zai iya cutar da ita".


   Naja ta sauke ajiyar zuciya tace "Allahu Akbar! Allah mai Iko! Allah mai girma da buwaya! Allah maji 'kan bawa".


   Basmah kam baccin ta take hankali kwance kamar ba itaba.


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œ and Zarah~B~B๐Ÿ’•_


ยฉ ~Princess Amrah~

ยฎ ~NWA~

[3:06pm, 17/07/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: [1:54pm, 17/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    *JINNUL-ASHIQ*

                 ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                  ๐Ÿ’€

Page 141-145

 Na *Amrah*

  ยฎ *NWA*


  

   *BAYAN KWANA UKU*


Basmah na hango ita da Naja suna ta firar su gwanin sha'awa, Naja ta shaida mata itama malan yayi mata k'aik'ayi koma kan mashek'iya, dariya Basmah ta kwashe da ita tace "kice Safna yanxu tana can k'ila ta fara hauka",


   Naja ma dariyar tayi sosai kafin tace "anjima nake son komawa gidan ma, dan inga Mansur d'ina nasan yayi missing d'ina, in kuma shaida mashi duk abubuwan da suka faru har guduwarmu",


   Basmah tace "nima gobe nake son komawa gida, malan ne yace in jira akwai maganin da zai had'o min anjima da dare, da kuma addu'ar da zai bani in tafi da ita", ta kwantar da kai tace "Naja'atu ban san da wane baki zan gode maku ba, hak'ik'a kun taimake ni a lokacin da nake bu'katar taimako, Allah ya saka maku da alkhauri Allah kuma yaji k'an magabata",


  Malan dake k'ok'aron shigowa yace "Ameen Basmah, Allah kuma ya k'are mu da lafiya, ga wannan maganin ki cakud'a shi cikin man da zaki ringa shafawa, wannan kuma garin ki zuba shi a zuma kullun ki ringa shan cokali uku safe rana dare, shi zaiyi maganin ko wane irin abu yake cikin ki dan nasan komai zai iya faruwa saboda dashen *JINNU* ne, wannan kuma ruwan a ruwan wankan ki zaki ringa had'awa, na rok'e ki Basmah kar kiyi wasa da magani, kinga abunda ya cuce ki kenan ko a baya ma",


   Basmah ta kar'ba ta k'ara godiya ta ajiye a gefen ta.


         *WASHE GARI*

Tunda safe suka hau shiri dan malan yace tare zasu tafi dan ya jajjadawa iyayen ta akan su kula da maganin ta. K'arfe takwas na safe suka gama shirin su tsaf. Basmah ta d'auki ledan maganin ta suka nufi d'akin malan. Sun samu kuwa ya shirya jiran su kawai yake.


    Cike da zumud'I Basmah ke gwadawa me napep d'in gidan su har suka isa, a bakin gate ya tsaya malan ya bashi kud'in suka shiga ciki.


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œ and Zarah~B~B๐Ÿ’•_


ยฉ ~Princess Amrah~

ยฎ ~NWA~

[2:04pm, 17/07/2016] ๐Ÿ’“Amrahโœ๐Ÿผ: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    *JINNUL-ASHIQ*

                 ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                  ๐Ÿ’€

Page 146-150

 Na *Amrah*

  ยฎ *NWA*


 Sallamah sukayi tare da shiga cikin gidan. Dady, mummy, ya Anwar da Zarah ke zaune kowa d a abunda yake sak'awa a ransa, cikin farin ciki Basmah ta fad'a jikin Dady da baima san suna sallamah ba, k'are mata kallo yayi yace "Basmah!",


   Kiran sunanta yasa duk kansu suka dawo da hankalin su. Zo kuga murna wurin kowa musamman ma ya Anwar daya gama ramewa yayi bak'I kamar ba shi ba.


  Basmah tace "tare nake da bak'I", masauki aka basu kafin Mummy ta shiga ta kawo masu ruwan roba da lemo.


   Sai da suka daidaita sannan Basmah ta basu labarin duk abunda ta sani tun fitar su daga asibitin mahaukata da kuma cikin da yake jikin ta. Bayan ta gama ne malan Mu'awuya ya k'ara da nashi.


   Dady yayi mashi godiya sosai har da kud'I ya bashi da koshi bai san adadin su ba amma sam malan yak'I karb'a yace ai shi dan Allah yayi da kuma jikar shi Naja'atu. Ya jaddadda masu maganin ta yanda zatayi amfani dasu. Sai wurin yamma sukayi bankwana suka tafi. Harda kuka Basmah tayi na rabuwa da Naja, nan ta shaida mata ai zasu ringa zumunci.


   Dady ya ro'ki gafarar ta akan sharetan da sukayi basu waiwaye ta ba. Suka rungumi Juna ita da Zarah dan kusan wata hud'u kenan basu had'u ba.


_Dedicated to Basmah mai sanyin ta๐Ÿ˜œ and Zarah~B~B๐Ÿ’•_


ยฉ ~Princess Amrah~

ยฎ ~NWA~

[3:14pm, 17/07/2016] Amrah๐Ÿ’“Pinky๐Ÿ’“durling๐Ÿ˜˜: ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

  ๐Ÿ’€

    *JINNUL-ASHIQ*

                 ๐Ÿ’€ ๐Ÿ’€

                   ๐Ÿ’€

Page 151-155

 Na *Amrah*

  ยฎ *NWA*


     *_LAST EPISODE_*


Tuni Naja ta koma gidan mijin ta, Safna kuwa ta haukace hauka sosai tana tonawa kanta asirin abubuwan da tayi a baya. Maman Mansur kuwa ta nadama akan k'iyayyar data gwadawa Naja. Zumunci sosai suke yi ita da Basmah sun koma kamar 'yan uwa har da Zarah.


    Basmah na hango kwance cikin ta ya fito sosai dan ta shiga watan haihuwa. Kerry mai aikin ta tana mata matsan k'afa. A hankali take jin marar ta tana d'an murd'awa har ta tsananta. Kerry tace mawa ta mi'ko mata wayar ta. Cikin azama kuwa ta mi'ka mata ta kira ya Anwar. Cikin minti kad'an ya dawo a rikice. Asibiti ya kaita sannan ya kira mummy da umman shi ya sanar dasu. Dandanan sai gasu sun iso a tare har da dady.


   Wata nurse ce ta fito take shaida masu Basmah ta haifi yaro namiji lafiyayye amma kuma akwai wani yaron a cikin ta, sunyi bakin k'o'karin su su fitar dashi sun kasa sai dai a yanka ta a fiddo shi.

   Anwar yasa hannu a wata takarda cike da zullumi.


  Minti talatin suka fito cike da jin dad'in nasarar da suka samu sai dai kuma yaron baizo da rai ba gashi da wata kalar halitta. Sukam hamdalaa sukayi saboda ance Basmah lafiyar ta lau.


   Ranar suna jariri yaci sunan malan mu'awuya suna kiran shi da Amir. Ranar kuma Zarah ta kawowa Basmah ivitation card d'in bikin ta. 

   Amir nada wata biyar Naja ma ta haihu. 


   Daga nan kuma sai na isa gidan Basmah da nufin yi mata bankwana, na kuma shaida mata na kammala d'aukar wannan rahoton, tambaya ta tayi "'kawata wannan shine novel d'in ki na nawa?"

   Sai da nayi tunani kafin in fara mata lissafi kamar haka:-

  " *Mahak'urci* " shine novel d'ina na farko. Sai *Babu maraya, yarima saifullah, yaudara, Fadeelah da Nabeelah, Ramuwar gayya, Daukaka daga Allah, Radiya, So da shakuwa, Tsantsar zalunchi, Dr. Rafiq, Ina zanga kdeey, Mai bakin jini, Khaulat, Zafin so, and JINNUL-ASHIQ*. Yanzu kuma gidan su *UMMU HAYDAR* zan ziyarta domin gano halin da suke ciki.


*UMMU HAYDAR* Na nan zuwa very soon insha Allah. Labarin dayake k'unshe da abubuwa da dama, ku kasance tare dani a cikin *UMMU HAYDAR*, labari mai tausayi cike da ilimantarwa. Kar na cika ku da surutu. Kuci gaba da kasancewa dani akoda yaushe.


*ALHAMDULILLAH* anan na kawo 'karshen wannan 'kagaggen labarin nawa. Fatan an fad'akartu kuma an nishad'antu a cikin sa. Allah ya sa haka.


*SADAUKARWA*:- na sadaukar da wannan littafin ga 'kawaye na guda biyu. *Basmah and Zarah~B~B,* Allah ya barmu tare ameen.


Allah ya 'kara maku tsawon kwana *iyaye na abun alfahari na, ina ji daku ina kuma alfahari daku*.


Jinjina ga 'kungiya mai albarka *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*, Allah ya 'kara had'a kawunan mu ya kauda fitina a tsakanin mu.


Banda kamarku shugabanni na *Adda Bena, ummul-fadeelah, Chuchungaye, Feenat Jaafar, maman haneef, babeelo and Nafee Ankerh*.


Godiya ta musamman gare ku *EXCELLENT WRITERS, EXTREME HAUSA WRITERS, GALAXIES HAUSA WRITERS, ROLEX HAUSA WRITERS, MARUBUTA ZALLAH WISDOM HAUSA WRITERS and BEST WRITERS GROUP*.


   Kinfi kowa son wannan novel d'in " *teemah luff*"

Jinjina gareku 'yan uwana *Rabiatu sk msh, Kdeey, Sahaf, Basmah err lele, Qurratul-ayn, Sadeeya Afka, Maman usman, khadeejah candy, rash kardam, Lubee Maitafseer, Queen mimi, haneefa usman, baby Zahra, mrs. Umar, meesha luv, Ummu Abrar, Ummerterh, Nuceyluv, hajar, baby amrah, autar hajia, jidda aleeyu, munaysha, sanah matazu, fido sodangi, jidda jao, miss hafcy, and kausarlove.*

  Bazan manta daku ba *Abdul Mr. Smile, Raheem Jega, Abba ghana, and Ambassador*

  Group d'in *Amrah and Rabiatu sk novels, Nafee And Amrah novella, mu farka mata, Amrah's kitchen* jinjina ta musamman gareku. Nagode da kulawarku da nuna kauna agare ni.

   Da duk wanda ban fad'I ba suna raina.


Princess Amrah kema kowa fatan alkhairi. Allah ya hada fuskokin mu a aljannah.Tags: #Jinnu #Basma #Adduโ€™a
3266
0
0
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!