JARABTARMU KENAN!

Written by Maryamerh AbdulPublished on 2018-12-12 10:17:22Category Mystery/Thriller"I missed you sister, wallahi duk kewarku nakeyi, mutumin nan kad'ai zai hanani zuwa, amma naji zai tafi umrah, dan Allah yana tafiya ki sanar dani ko ki sanar da Usama" hawayen da take k'ok'arin hanashi fitowa ne ya sauk'o, ta share da gefen mayafinta sannan tace "Jabir Baban kake cewa mutumin nan? Bazaka zo ka nemi afuwar mahaifinka ku rabu lafiya ba Jabir?". Dogon tsaki yaja sannan yace "wallahi wallahi kinga irin maganar nan naki kadai yake hanani d'auka wayanki, Usama da yake biye miki ma wallahi dan na rasa yanda zanyi dashi ne, but nikam hak'ok'ina nawa ya tauye bai nemi afuwata ba? Shine ni dan na tafi na barsa zan nemi afuwarsa? Tsaya ma in tambayeki, wani hak'k'i ne na mutumin nan a rayuwana na tauye ban bashi ba da har zan nemi afuwarsa?". Kai tsaye Maryam tace "kak'i bin umarninsa a lokacin da yace lallai ku dawo gida." dariya yayi yace "wannan kawai? Ni kuma fad'a min, hak'k'ok'i nawa Baba ya tauye min a matsayinsa na mahaifina? Bayan bak'in halin da yake nuna mana? A rayuwana ban taba ganin mai bak'in hali irin nashi ba wallahi, kuma bana fatan in sake had'uwa dashi har abada". Kuka mai k'arfi ne ya kubce wa Maryam na tsananin bak'in ciki da takaici, wannan wani irin rayuwa ne d'a ya siffanta mahaifinsa da kalma mafi muni?. tags: #Mahaifi #Jarraba #soyayya #kauna #jinkai #mutuwarzuciyaDuba was labarai »

๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARRABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 1


   Gudu take acikin motar ta k'irar corollar x fara k'al sai k'ura ke tashi, mutanen unguwar da suka gano wacece tambayan junansu suke "yau lafiyar Maryam kuwa?" Wad'anda basu gane ta ba kuwa zagi suke binta dashi, dan tabbas gudun nata ya wuce misali kuma acikin anguwar da babu titi, ta bad'e kowa da k'ura bata ma san tayi ba. 

   Sai da ta hau babban titi sannan ta karya kwana ta samu tayi parking inda babu wanda zai takura mata, fuskarta manne take da bak'in gilashi, kana kallonta zaka gano b'oyayyen b'acin rai da ke lullub'e a fuskarta, kanta ta d'aura akan sitiyarin motar bayan ta cire gilashin. Sai da ta d'au minti biyar masu kyau sannan kuka mai ratsa zuciya ya kubce mata, fad'i take 

  "why Baba? Meh yasa bazaka canja ba?" Sai da ta d'au minti goma tana mai zubda hawaye sannan ta d'ago ta share ta mayar da gilashin nata ta kunna motar ta d'auki hanya duk da bata san tak'amaiman inda zata ba. Wata zuciyar tace kije cikin G.S.U ki zauna ki sha iska kamar yanda kika saba. Bata yi wani tunani ba ta d'auki hanyar Gombe State University.

  Tazo dab da yankar kwanan da zai sada ta da makarantar taga K'anwarta Muneerat cikin wata mota da wani saurayi mai suna Kamal. Karya kan motarta tayi ta bisu a baya hankalinta a tashe, rusar gudu suke akan kwaltan nan, dak'yar Allah ya bata ikon shiga gabansa a lokacin da ya shige wani layi a guje ganin Maryam na binsu a baya, ji kake kusssss! Ta taka birki shima ya taka.

  Buga sitiyarin yayi yana cewa "shet!" Muneerat kuwa tsaki ta ja can ciki ta kawar da kai. Fitowa tayi ta gyara mayafinta milk color da yake barazanar fad'i, sanye take da doguwar riga material (fitted gown) kalar blue da ratsin milk, takalmin k'afarta milk da adon blue a jiki. Cib-cib kayan ya mata kuma ya bala'in karbarta, kasancewar skin nata ba bak'i bane haka zalika ba fara k'al ba. Doguwa ce daidai misali sannan tana da kyau na k'in k'arawa, dan kuwa duk gidansu a cikin mata babu wanda zai nuna mata kyau, diri, ilimi da nutsuwa.

   Side d'in da k'anwarta take ta nufa ta bud'e k'ofar, ba tare da tayi musu magana ba ta janyo hannunta ta fito da ita, k'ofar ta mayar ta rufe da k'arfi sannan ta kama hanyar motar ta, sai da ta wurgata cikin motar ta rufe sannan ta zagaya dan komawa kujerarta. Fitowa yayi a hasale yana cewa "meh haka ne Maryam? Ya kike son b'atawa mutum jin dad'insa ne?" Bata yi niyyar tanka masa ba sai da ya zo dab da ita yana cewa "yarinyar nan sonta nake, kuma in bamu fahimci juna ba tayaya zamu fara maganar aure?".

  Cike da masifa ta juyo take maida masa martani had'e da nuna sa da yatsa "Kamal in na sake ganinka tare da k'anwata wallahi kotu ce zata raba mu, in kai ne namiji mutum d'aya da ya rage wanda Muneerat zata aura ina mai tabbatar maka saidai ta k'arata a gida babu aure, dan ko na mutu ina mai tabbatar maka babu mai baka aurenta, in kuma sonta kake da gaske ka canja hali kaga ko za a hanaka mu'amala da ita." Ta ja tsaki ta shige motar ta barshi a inda yake. Muneerat kuwa sai kumbure-kumbure take ita ala dole an b'ata mata sha'ani. 

  Babu wanda yayi magana a cikin motar har suka isa gida, Maryam duk da gilashi na idonta hakan bai hana Muneerat gano hawaye takeyi ba, zuciyarta nan take ya karye taji hawayen ita ma na barazanar sauk'o mata amma ta dake. Bayan sun shiga gida Maryam ta janyo ta har suka shiga k'uryar d'akinsu, zaunar da Muneerat tayi tana cewa "me zan miki ki daina zubar da mutuncinki da mutuncinmu a idon duniya? Meh kika nema kika rasa daga wurina ko daga wurin yayunki? Maraici yasa kika canja hali Muneerat? Meh Mama ta rage ki dashi wanda mahaifiyarki take miki?" Jijjiga Muneerat takeyi tana mai zubar da hawayen takaici, ji take kamar ta hau ta da duka ko zata ji sassaucin zafin da zuciyarta keyi.

  Dak'yar ta daidaita kanta bayan tayi kuka mai isarta, Muneerat ma hawaye ne cab a fuskarta, sai da ta daidaita sannan ta fara yi mata nasiha mai shiga jiki, kuka Muneerat ta shiga yi sosai tana mai cewa "duk laifin Baba ne, wallahi in ina da zunubi 100 Baba na da 80, dan shi ya sani wannan halin, kuma Anty Maryam wallahi babu wani iskancin da na taba yi, duk iskancina ban taba zina ba kuma bani da niyya, buk'ata na in samu kud'in da zan biyawa kaina da k'anwata buk'ata, kuma da na samu nake barin komai har sai wata buqatar ta taso" 

Maryam tace "baki da yayyun da zasu biya miki buk'ata ta kud'i har sai kin zubar da mutuncinki kin sab'i Allah? Kamar bakisan halin Kamal na b'ata 'ya'yan mutane a garin nan ba? Ni daga yau na d'auki nauyin d'auke muku wannan, daga zarar an biyani albashi ki rubuta min abubuwan da kuke buk'ata zanyi muku, but dan Allah" ta had'e hannyenta biyu tana cewa "kada in sake ganinki da Kamal da sauran 'yan iskan nan".


        ๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARRABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 2


Sai da ta tabbatar ta janyo ra'ayin Muneerat akan bak'in halin da ta d'auko sannan ta bar d'akin cike da murmushin jin dad'i a fuskarta, a ranta tana cewa *na gama d'aya insha Allah, saura biyu masu wuyar gaske, Allah ka bani ikon dawo da familynah yanda yake a da* .

  Kwana biyu da faruwar haka, Maryam na zaune a d'akin Mama idonta a lumshe kasancewar yau Asabar babu aiki, da gudu Nasreen ta shigo tana cewa "Anty Maryam Jabir ya k'ira Mama, wai kije kuyi magana" kamar an tsikareta ta mik'e tana cewa "tana ina?" Tun kafin a bata amsar har ta fice, daga nesa taji Nasreen tana cewa "tana garden". Gudu ta sa tana mai matuk'ar jin dadin zatayi magana da Jabir bayan kwanaki masu yawa da yak'i d'auka wayarta. 

Ai kuwa tana isa Mama ta mik'a mata cike da farincikin da ya kasa b'uya daga fuskarta, karb'ar wayar tayi tana cewa "wallahi Jabir duk ranar da muka had'u sai ka sha rankwashi biyu masu kyau, ina yayar taka ina k'iranka kak'i d'auka ko?" Daga can b'angaren kuwa dariya sosai yayi kana yace "dan ma yanzu nace a baki mu gaisa, sai in kashe wayar inga ta tsiya".

Tun kafin ya gama fad'a take cewa "yi hak'uri dan Allah, nasan zaka iya" sukayi dariya gaba d'aya sannan yace "I missed you sister, wallahi duk kewarku nakeyi, mutumin nan kad'ai zai hanani zuwa, amma naji zai tafi umrah, dan Allah yana tafiya ki sanar dani ko ki sanar da Usama" hawayen da ke k'ok'arin hanashi fitowa ne ya sauk'o, ta share da gefen mayafinta sannan tace "Jabir Baban kake cewa mutumin nan? Bazaka zo ka nemi afuwar mahaifinka ku rabu lafiya ba Jabir?".

Dogon tsaki yaja sannan yace "wallahi wallahi kinga irin maganar nan naki kadai yake hanani d'auka wayanki, Usama da yake biye miki ma wallahi dan na rasa yanda zanyi dashi ne, but nikam hak'ok'ina nawa ya tauye bai nemi afuwata ba? Shine ni dan na tafi na barsa zan nemi afuwarsa? Tsaya ma in tambayeki, wani hak'k'i ne na mutumin nan a rayuwana na tauye ban bashi ba da har zan nemi afuwarsa?".

Kai tsaye Maryam tace "kak'i bin umarninsa a lokacin da yace lallai ku dawo gida." dariya yayi yace "wannan kawai? Ni kuma fad'a min, hak'k'ok'i nawa Baba ya tauye min a matsayinsa na mahaifina? Bayan bak'in halin da yake nuna mana? A rayuwana ban taba ganin mai bak'in hali irin nashi ba wallahi, kuma bana fatan in sake had'uwa dashi har abada". Kuka mai k'arfi ne ya kubce wa Maryam na tsananin bak'in ciki da takaici, wannan wani irin rayuwa ne d'a ya siffanta mahaifinsa da kalma mafi muni?.

Tsaki yaja yace "ai indai akan mutumin nan ne kuka dubu zakiyi har ki mutu bazaki daina ba. Sai anjima nikam ki gaida mutanen gida" bai jira ta amsa ba ya kashe wayar d'ib. Cikin kuka ta kalli Mama da hawaye ya cika idonta tana mai yi mata murmushin da bai kai zuciya ba, hannu ta mik'a mata alamar tazo inda take, da gudu ta iso ta rungumeta ta cigaba da kukan da ya zame mata jiki, dan duk ranar da tayi waya da Jabir da kuka take 'karewa, haka in tayi waya da Usama. 

Kamar daga sama taji muryar Baba yana waya yana isowa inda suke, bata san lokacin da ta mik'e ta share hawayenta tana neman hanyar da zata gudu ba, kafin ta tsayar da tunaninta har ya shigo wurin ya kashe wayar yana kallonta, murmushi ta k'ak'alo tana cewa "ina wuni Baba" d'auke kansa yayi kamar bazai amsa ba, can ciki taji yace "lafiya". Zama yayi a kujerar da ke gefen Mama ya d'aura k'afa d'aya kan d'aya ya bud'e jaridarsa yana karantawa.

A sulale ta tashi zata bar wurin yace "wai Hadiza yarinyarkin nan ba zata yi aure bane? In ta rasa miji ne ku fad'a min in nemo mata, dan na gaji da ganinta a gida sai tsufa takeyi, kuma kinsan zagi zata jawo miki, tun wancan talakan da ta kawo ban sake ganin wani yazo ba. Kuma dubi kayan da take sawa" ya fad'i hakan yana nuna kayan jikinta da yatsa, daga sama har k'asa ta kalli kayan jikinta, mama ma kallon kayan tayi sannan ta kai dubanta gareshi.

   Doguwar riga ce 'yar kanti mai tsagu daga k'asa, sai skintyt da tasa pink ta ciki harda d'an kwali "Tana gidan ubanta me laifin kayan jikinta, da fita tayi shine za a zageta ko ince a zage mu, kuma maganar miji Allah ne bai kawo mijin ba har yanzu, ai da ya kawo ita kanta bazata so zama babu sutura ba, dan aure sutura ce" cewar Mama.

A harzuk'e baba yace "kayan jikinta ne zaki ce babu laifi, irin kayan karuwai? 'Yata kam bazatayi irin wannan shigen ba" mama sai da tayi dariyar takaici sannan tace "meh kake nufi?" Maryam fita tayi daga garden d'in dan bazata iya sauraron kalaman baba marasa dad'i ba, ta rasa gane me zata yi wa mutumin nan. D'akinta ta shige ta kulle k'ofar sannan ta fad'a gado. Nan ta fara tunanin ko waye mahaifinsu da iyalinsa kamar haka:-

Alhaji Muktar Dala wani hamshak'in mai kud'i ne, shahararren d'an kasuwa kuma sananne, ya kasance mutum mai son a sani kuma mai fariya, baza a ce bayi da kud'i ba amma kudin da yake dashi bai kai ace yayi suna irin yanda yake dashi yanzu a garin Gombe ba, mutum ne mai mutunci da kyawawan halaye a idon jama'an gari dan yana taimakon talaka da taimakon musulunci. Tabbas mahaifina bazan zageshi da rashin ibada ba, saidai kash! wadan nan halayen nasa mutanen waje kawai ke ganinsa dashi, dan kuwa matansa da yaransa sai dai ace wayyo Allah!!!


        ๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARRABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 3


  Alhaji Muktar na da mata uku, matarsa ta farko sunanta Jidda muna k'iranta Maman Usama, tana da yaro 'daya aka auro mahaifiyata Hadiza muna k'iranta Mama, Allah ya bata yara uku sannan ya auro matarsa ta uku Laila wacce muke k'iranta Mommy kamar yanda tace mu k'irata.

Maman Usama na da yara hud'u, Abbakar shine d'an ta na farko wanda ya rasu da jimawa, sai Muneerat, sai Usama, sai kuma autarsu Aisha. Mamana kuwa yaranta biyar, mace ce 'yarta ta farko Fatima tana aure a Kano, sai ni Maryam, Jabir, Mus'ab, sai auta Nasreen. Amaryar Babanmu yaranta biyu duk mata ne, Shamsiyya da Zahra.

Rayuwar gidanmu baza a k'irasa rayuwa mai dad'i ba haka zalika kai tsaye bazaka ce babu dad'i ba, dan kuwa rayuwa ne da yake da dukka fanni biyu, wato dad'i da kuma rashin dad'in duk muna d'anawa. Tun da na tashi a gidan Alhaji Muktar ban tab'a ganin ranar da Baba ya wayi gari har yamma ya koma makwancinsa baiyi masifa ba, imma yayi wa iyayenmu imma yayi mana. 

Abun fad'a da wanda ba na fa'da ba duk sai yayi mita, mutum d'aya ne bai d'aukan masifan sa a gidanmu ita ce Mummy, bai isa yayi wa yaranta ba indai tana nan, yana fara mata zata mayar masa ba kaman sauran matan nasa da basu da abin cewa sai dai su basa hak'uri ko da kuwa sune da gaskiya. Ana hayayyafa ana k'ara girma akan masifa da hayaniya ya ragu sai k'aruwa yake yi.

    Bazan manta ba akwai ranar da baba ya biyoni har d'akin mama yana masifa "Mara hankali, wawuya, kwab'ab'b'iya" zagi mafi sauk'i da zai iya fitowa daga bakin Baba kenan. Harzuk'a yayi kamar zai makeni na kauce, ya cigaba da cewa "la'ilaha illallah" yana tafe hannu alamar mamaki wai dan na kaucewa bugunsa, juyawa yayi yana mai kai dubansa wurin Mama sannan yace "Hadiza kinga 'yarki? Anya yarinyar nan 'yata ce?" 


Ya fad'i hakan yana kallon mama had'e da nuna ni.

   Cike da k'osawa da maganarsa tace "haba Alhaji, ya zaka yi ta fad'an mugayen kalamai akan 'ya'yanka? Harshe fa yana gyara abu kuma yana b'atawa" bud'an bakinsa yace "ai dama nasan ke kike goyon bayan duk iskancin da sukeyi" ya nuna ta da yatsar sa yana cewa "ki kiyayeni fah".

In raina dubu yake baba ya b'ata min a ranar wallahi, a gabana yake nuna mahaifiyata da d'an yatsa a laifin da ba laifi ba... Tsakin da yayi shi ya jawo hankalina zuwa garesa shi ko ya juya ya fice.

Kukan da nakeyi ya 'kara tsananta, na sa fuskana a tsakanin cinyoyina ina mai zubar da hawaye tare da sautin kuka a hankali. Mama ta rik'o ni tana cewa "haba Maryam" ta d'ago fuskata tana mai share min hawayena, tayi murmushin da bai kai zuciyarta ba har hak'oranta suka bayyana. 

   "Ke da ya dace k'annenki suyi ki hanasu ke ce zaki sani gaba kina kuka? Ai yakamata yanzu kinsan halinsa, ki daina damun kanki, halinsa ne wannan bazai iya dainawa ba sai kun hada da addu'a". Dariyar da akeyi daga bakin k'ofa shi ya ja hankalina na kai dubana dan ganin wanda ke dariyar k'eta irin haka.

  Muryar da naji shi ya tabbatar min Jabir ne k'anina tun kafin ya d'aga labulen yake cewa "dama kamar nasan abin da zan tarar kenan, ai tun daga garejin ya hau ta da masifa suka shigo tare, ashe har ke yazo ya balbale ya fice". 

Babu wanda ya tanka masa ya samu wuri ya zauna akan kujera yana cewa "da kin saki ranki ma, yana can ya kame akan wannan kujerar tasa yana danna waya hankalinsa kwance, ya ma manta da yayi miki masifa, sai in ya ganki kuma zai tuno, kema ai hakan zakiyi. Ni kuna bani mamaki ma wallahi" ya dauke kai bayan yaja k'aramar tsaki had'e da mike k'afa. 

    Cikin muryar kuka nace masa "laifin me nayi da har zai ce anya ni 'yarsa ce? Bayan haka ya nuna mahaifiyata yana gaya mata maganganu a gabana, me hakan ke nufi? Dan kawai nayi masa shara ina kwashewa na taka skirt dina saura kad'an fa in fad'i, ai sannu ya dace ya bini dashi, amma dan kawai dattin ya zube shikenan ya fara masifa, har na kwashe na shigo gida bai ishesa ba sai da ya biyoni yana masifa..." 

Kuka yaci k'arfina na kasa k'arasa abinda nake cewa, Jabir yaja tsaki yana cewa "aikin banza, ni ke kike bani haushi ma ba shi ba wallahi, sai kace bakisan baba ba" ya tashi ya fice ranshi b'ace yana gunguni.

    Share hawayena nayi ina mai jin tsanar mahaifina yana tsananta a cikin raina, dan zan iya cewa ban tab'a jin tsanarsa irin ranar ba. nace wa mama "Jarrabtarmu kenan samun mahaifi irin wannan?" tace "kuyi masa addu'a, komai zaiyi daidai da izinin Allah" na ja numfashi ina mai takaicin fitowa daga gidan Alhaji Muktar Dala. Wannan kenan!

Kad'an kenan daga halin Baba. Bayan hakan banbanci tsakanin yaransa baya masa wahala, yana matuk'ar son yaran Maman Usama fiye da sauran. Duk abinda suka nema na kudi ko na makaranta yana basu ba tare da anji kansu ba. 


        ๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARRABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 4


Yaran Mummy za a hana musu amma zata kwatar musu indai tasan yana dashi, masifarta da kwatowa yaranta 'yanci shi yasa Baba yake musu daidai gwargwado duk da ba da son ranshi yake yi ba, dan naga alamar baba yana da mak'o sosai indai iyalansa ke nema ba 'yan waje ba.

Yaran Mama kuwa abun ba'a cewa komai, dan Mama mace ce mai alkunya da kawar da kai, duk masifan da baba zai yiwa yaranta bata tanka masa, hasalima yi zatayi kamar bata d'akin, haka zasu je neman kudi ko da na makaranta ne sai an kai ruwa rana sannan za a samu, in ko ba na makaranta ba na buqatan kai ne, sai dai suyi hak'uri uwarsu tayi musu in tana da shi, in ko bata dashi su hak'ura. 

Irin wannan rayuwar tasa na matuk'ar bani mamaki, har ina tunanin shin tun asali haka yake ko yanzu ya fara? Bazan manta ba ranar da naje hutu gidan anty Fatima ta bani amsar tambayata a lokacin da take bani labarin zaman ta da baba har aurenta, tace

"Maryam hak'uri zakuyi da baba, k'annenmu ne zasuji dadinsa dan lokacin tsufa yazo masa, abinda yayi mana ina da tabbacin bazai yi musu ba dan bazai iya ba lokacin bayi da k'arfin haka." Da mamaki na kalleta naga tayi murmushi ta kawar da kanta gefe.

Ban fasa fad'an abinda ke bakina ba nace "ke har tunanin haka kikeyi? Lallai kinyi aure kin manta Baba, Jabir fa last term takalmin da kika tura masa tun kwanaki na makaranta wannan brown sandal din kin tuna shi?" Ta kad'a kai alamar eh, na cigaba da cewa "in ba dan Jabir yana kula da takalmi ba ma babu wanda zai jima da takalmin kamar shi, sai last term yaje gun Baba dan ya saya masa wani........" 

Anty Fatima cike da mamaki ta tsayar dani da cewa "wai takalmin yake anfani dashi har last term?" Dariya ta bani dan sai da na dara sannan nace "ai bakiji abun mamakin ba kin wani ware ido, wai da yaje gun Baba kinsan meh yace masa? Wai bayi da kud'i, kuma a ranar fa aka kawo masa kud'in hayan gidan sa kusan miliyan d'aya, amma wai babu kud'i, toh ko ba a kawo masa kud'in ba Baba zai ce bayi da kud'i ne? Sai da Jabir ya nace akan bayi da takalmin zuwa skul monday sannan yace masa ya d'auko takalmin ya gani".

Anty Fatima tace "ya gani yayi meh dashi?" Cikin dariya nace " wai ko ya b'aci ko bai b'aci ba, daga k'arshe ma d'ari biyu ya basa wai ya gyara takalmin sai ya sake b'aci sannan a basa kud'in sabo". K'aramar tsaki taja tana cewa "mutumin nan bazai tab'a canja hali ba kenan. Tun da fa haka yake da wannan halin... Ya sukayi toh?" Dak'yar na tsagaita dariyar da nakeyi nace 

"kinsan Jabir da zuciya, kud'in ya bar masa ya tafi yace baya so, kud'in break hamsin d'in da ake bamu shi ya tara Mama ta cika masa ya saya wani, shi Baba ko a jikinsa, bai ma sake tada maganar ba bare yaji kunya yace masa gashi. Wallahi da Usama ke neman takalmin nan da an saya masa babu musu, duk da ba mai tsada za a saya masa ba".

  "Hmm!" Tace ta gyara zama ta fara bani labarin yanda Baba ya had'ata aure da d'an abokinsa, cewa tayi "bana son auren nan baba ya sa dole, kuma in naqi gidansa ba dad'i zanji ba, Allah da ikonsa yasa Mama tayi binciken halin Umar aka tabbatar yana da hankali, sannan fa nayi auren nan, amma ansha gwagwarmaya sosai har banason tunawa. Yanzu gashi harda rabon yara uku, kuma Umar ko auren soyayya mukayi iyaka abinda zai min kenan, Allah ya rufa min asiri, amma Babanmu kam sai Godiya". Bayan nan:-

Sunana Maryam, tun ina da shekaru 6 nasan waye baba daga sama har k'asa bare yanzu shekaru na 17 ina aji 6 a sakandare amma ban taba jin b'acin rai da bak'in ciki akan banbancin da yake nuna mana ba sai rannan, ana saura sati d'aya mu koma boko, islamiya kam mun koma tun satin da ta gabata. Zaune muke a tsakiyar gida muna shawarar yanda zamu tunkari Baba da maganar uniform na makarantar boko da islamiya. 

Muneerat da Aisha suka ce "mun saya na islamiya last term, in muka ce zamu k'ara kar'ba zai hana, sai dai ku kar'bi naku na islamiya ku kad'ai, na boko kuma mu hada dukkanmu mu kar'ba" Nace "eh hakane, Allah yasa ya bamu. Saura in mukaje kuyi shiru ku barni inyi ta magana har ya kora mu" na fad'i hakan ina nuna su Jabir. 


         ๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARRABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 5


Baba na shigowa bayan yaci abinci muka sameshi a d'akinsa dukkanmu mu 'yan sakandare tunda mu ne manya, mun kai mu biyar, sallama mukayi suka amsa shi da Maman Usama, zama mukayi a nutse muka mik'a gaisuwa, babu laifi ya amsa gaisuwar mu amma yana jin mun fara maganar kudi ya had'e girar sama da ta k'asa.

Tun kafin in gama bayani Muneerat ta kar'ba tayi nata bayanin kamar yanda muka tsara. Ya dakatar damu da cewa "bani da kud'i nikam, daga an fara maganar an kusa komawa makaranta kun dinga k'wak'ulo abubuwan da zaku amshi kud'i aguna kenan, toh bani dashi yanzu kam".


  


  Muneerat tace "Baba tun muna js3 fa aka mana uniform, dan da zamu shiga ss1 ma a makaranta aka bamu uniform kai baka saya mana ba, gashi yanzu muna k'arshen term a ss1, muna shiga makaranta ana ganin kayanmu a kod'e, wallahi baba kai ma kasan yaranka sunfi k'arfin zagi a garin nan" 

Washe baki yayi alamar yaji dad'in maganarta, wallahi babu kaffara da ni na fad'i maganar nan fatattakeni zaiyi daga d'akinsa yana zagi, amma da mamakina murmushi yayi yana cewa "ai ko dan kada a zageni ina samun kudina zan saya muku duk abinda kukeso, yanzu ku nawa ne kuma ku lissafa min kudin anjima Muneerat tazo ta kar'ba". 

  Maman Daddy kwarai taji dad'in yanda aka fifita Munnerat akaina duk da cewa nice Babba kuma ni ya dace ace inyi komai, har murmushin jin dad'i take, bai dameni ba nace masa "mu had'a harda na islamiyar kenan?" Murmushin da ke fuskarsa ya d'auke yana kallona sai huci yake, in ka kalli fuskarsa zaka d'auka ashar na d'ura masa. 

Fuskarsa yana da kyau da haske, hancin nan suwat kamar biro, daidai gwargwado Baba yana da kyaun sura abinda yayi masa cikas shine kyaun hali da bayi dashi. "Bani da kud'i nace, sai wani lokacin in na samu" ya d'auke kai kamar ba shi yayi maganar ba, zanyi magana kenan ya dakatar dani da cewa "bani dashi satowa zanyi in baku? Ku tashi ku bani wuri".


  


   Salap-salap muka mik'e babu wanda ya sake magana, Muneerat da Aisha muka bari a d'akin muka fice ni da Jabir, Mus'ab da Usama kowa da abunda yake sak'awa a ransa. Direct d'akin Mama muka je muka fad'a mata yanda mukayi, hak'uri ta bamu sannan ta tabbatar mana komai zai wuce. 

Washegari mukaje muka saya yadin uniform. A hanyarmu ta dawowa Muneerat tace zata saya musu jakar makaranta ita da Aisha Baba ne ya basu kud'in jiya bayan mun fita. Da mamaki na kalleta, yanayin kallon da na mata yasa jikinta ya mutu taji da ma bata fa'da min ba. 

Raina ya mugun b'aci yau kam, ina neman uniform na islamiya an hanamin aka d'auki kud'i aka bata na sayan jakar makaranta, bayan jakunkunan da suke dashi? Meh Baba yake nufi damu ne? A raina na k'uduri niyyar k'in zuwa islamiyar gaba d'aya sai ya saya min, dan bazanje makaranta da uniform d'in da ya gama tsufa har ya canja kala ba. 

Mun kai d'inki, maza telansu daban, mu mata namu daban, kud'in d'inkin dukka-dukka ya kama dubu biyar da d'ari uku. Dan takaici ko kallon k'ofar Baba banyi ba, ban ma san wanda yaje ya kar'bi kud'in ba, amma ina kyautata zaton Muneerat ce.


        ๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARRABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 6


K'arfe biyu da rabi daidai ina Kwance kan kujerar Mama na lumshe ido zuciyata sai k'una take ina tunanin abinda yake faruwa damu a gidan nan, kamar ba ubanmu ba, mama ce ta shigo ta ganni kwance babu alamar zanje islamiya, taba kaina tayi tana cewa "baki da lafiya ne?" Ban bud'e idona ba na amsa ta da "a'a" a tak'aice. 

"Meh yasa bazaki je islamiyar ba toh yau ma?" Kai tsaye nace "bani da uniform" had'e rai tayi tana kallona, na bud'e ido d'aya ina kallon fuskarta na sake rufewa, dan na d'au alwashin ko meh zai faru bazanje islamiya ba. 

Juya mata baya nayi kamar ban ganta ba. Ji nayi tana cewa "karatu zakije koya ko kuma nuna sabon uniform? Iyaka gatan da zaki samu daga gun mahaifinki shine ilimi, tunda bazaki samu wani gatan ba ki samu ki kwashe wannan gatan da yayi muku na saku a boko da islamiya, ina mai tabbatar miki bazakiyi da na sani ba".

Tashi nayi na zauna hawaye na bin kuncina ina kallon Mama, a raina nake cewa *bakisan abunda yake faruwa in naje makarantar bane, in mu mun rik'e sirrin gidanmu wasu k'awayensu suke fad'awa, sai mu zama abun nunawa da baki dan baza a iya tunkaro mu ba* rungume mama nayi ina mai zubar da hawaye, bata tanka ni ba bare ta hanani.

Shafa bayana takeyi har taji nayi shiru sannan ta samu damar yi min nasiha, bayan ta gama ne na sanar da ita abinda k'anne na sukeyi, nace "su basu gane cewa in har suka b'ata mu sun b'ata kansu, suna ganin kamar soyayya baba yake nuna musu in ya basu abu mu ya hana mana, kuma mama tunda mun haqura munyi shiru a bar abun a gida mana, har makaranta fa zata je ta fad'awa qawayenta, kuma bata san duk abinda ta fad'a yana dawo min ba, in tazo guna kuma sai ta nuna tana tausaya mana, na ma rasa gane matsayin Muneera wallahi mama" na cigaba da kukana.

Mama ta ja numfashi tana cewa "in ita tayi haka ai ke kin fita hankali, sharesu zakuyi ku cigaba da rayuwarku, watarana sai labari" cikin shesshek'ar kuka nace "anya ba asiri akayi wa baba ba? Ya mahaifinka zai na maka hali irin wannan?" Daga bakin k'ofa Jabir yace "in ma asiri ne wallahi ya had'u da halinsa, dama asali yana dashi, da akayi asirin sai yayi yawa".

Nan shima ya zauna muka cigaba da tattauna matsalolin baba da yanda yake raba kanmu, dan kuwa muddin yana zab'e ya fifita wasu kan wasu lallai kanmu zai rabu kamar yanda ya fara rabuwa a yanzu. kuma ba zama zaiyi ba, ko ba tsufa akwai mutuwa, dole watarana ko mu tafi ko shi ya tafi ya barmu, kuma k'annenmu da yayunmu su ne namu, in ya raba yanzu had'uwar kanmu anjima abu ne mai matuk'ar wahala.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARRABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 7


Yau ta kama Juma'a, tun safe muke dafe-dafe da soye-soye dan bak'in da baba yace zaiyi, komai sai da baba ya cire mak'udan kud'i ya bada aka sayo dan fita daga kunyar bak'insa, mama ce da girki, hakan yasa komai a hannunta yake, an kammala komai na girki saura juice da aka je sayowa, kafin a dawo har bak'in sun iso.

Baba da kansa ya shigo kitchen yana duba abubuwan da aka dafa, bakin nan har kunne sai washewa yake dan anyi masa abinda yakeso, da murmushi a fuskarsa yace akai falonsa a ajiye akan dining table, ina daga kitchen na kwalawa Usama da Jabir k'ira akan suzo su kai abinci.

Bud'an bakin Baba yace "ku dai matan zaku kai, ku sa kaya mai kyau ku kai musu, tashi kije ki k'ira Muneerat mana" Mama tace "ya kuma 'yan matan zasu kai bayan akwai maza a gidan? Haba dai, mutuncin mu ai yafi komai, da babu mazan ne sai su su kai, amma ga maza god'ai-god'ai suna zaune ace mata zasu kai wa maza abinci suna giftawa sai kace tallansu akeyi?" Baba bai tanka ta ba ya bawa Usama da ke tsaye a bayansa hanya ya shigo shi kuma yasa kai zai fice daga kitchen d'in daidai lokacin da na qara kwalawa Jabir k'ira.

Mama tace "kin manta Jabir yaje sayo juice bai dawo bane?" carap a kunnen baba, dawowa yayi yana cewa "matar nan baki da hankali ashe? Tun d'azu bak'i sunzo kin bawa d'anki yaje yawonsa koh? Jiransa kikeso suyi ko meh?" Mama tace "ayya, yaran ne sun gaji, kuma ka manta kud'in juice din ai sai daga baya ka bayar, tun lokacin da ka bayar ya fita, ko minti talatin baiyi ba fah".

Bud'an bakin baba sai cewa yayi "mak'aryaciya, ni in bada kud'i tun safe amma kina ce min ban jima ba......" Ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, mama dai sunkuyar da kanta tayi tana jin duk kalmar da yake yab'a mata har Jabir ya shigo da ledar juice d'in bai bari ba, nan ya koma kansa. 

Dama da haushin ta hana 'yan mata su kai abinci sai ya had'a dukka ya balbalesu, ni ko barin wurin nayi dan baxan iya jin zagin da mahaifina ke yiwa mahaifiyata da ko tanka sa tak'i yi ba. Jabir da Usama ne suka k'i tafiya, sai da ya gama ya fice sannan suka ja tsaki a tare suka kalli juna, idanunsu yayi jajir tsaban b'acin rai. Hak'uri suka bawa Mama da ta kasa d'ago fuskarta sannan suka fara kai abincin kamar yanda ya umarce su kafin ya tafi.

Ina tsaye k'ofar d'akin Maman Usama ina jiran fitar Baba daga kitchen naji Muneerat da Mamanta na dariyar abinda ya faru tsakanin Mama da Baba, ashe tun farawar abun suke lek'enmu ta window, har fitan baba basu bar dariya suna zagin mama ba, ko sun manta cewa su ma yana kansu? Dan baba bai ragawa kowa indai masifa ne. Cike da b'acin rai na wuce d'akin mama na fad'a kan gadonta ina sharb'ar kuka na. 

Har mama ta shigo d'akin ta zauna a kujerar da ke bakin k'ofar ban daina hawaye ba. Ina kallonta ta ajiye kanta bisa k'afafunta ta fara kuka mai sauti, na tabbata bata san ina nan ba da bazata yi Kukan nan ba, dan na sha ganin Mama tana kuka a k'uryar d'aki, in ta fito kuma kamar ba ita ba, in muna yi ma hana mu takeyi, yau gashi ganin idona mutumin nan yasa mahaifiyata kuka? Ban gama maganar zuci ba Nasreen ta shigo d'akin, wanda shekarunta bazai wuce sha uku ba.


        ๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARRABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 9


Ranar kam anyi rigima iya rigima wanda har ya kai ga Maman Usama ta sauk'e wa Usaman mari, shi kuma yace muddin Muneerat bata daina ba sai yaje ya fad'awa Uncle Usman, da yaga masifar tak'i k'arewa fita yayi yaje ya k'ira Uncle Usman dan anguwar mu d'aya, lokacin k'arfe tara da rabi na dare.

Uncle Usman halinsa yasha banban da na Baba, dan duk matsala in ya taso a gidanmu shi yake solving mana, kuma yana zama yayi mana nasiha game da halin mahaifinmu, yana yawan ce mana muyi hak'uri, zai daina nan gaba, yau ma kamar kullum sai da ya tsaya kowa ya fad'i nasa sannan ya bi mu d'ai-d'ai yana fad'a mana kuranmu, ni ya bawa gaskiya, ya d'aurawa Muneerat laifi, sannan yayi wa Usama fad'a akan marin yayarsa da yayi duk da tana da laifi, sannan ya had'a mu yaran gaba d'aya yayi mana fad'a, ya kausasa murya akan in ya sake jin abu makamancin haka zai b'ab'b'alla Muneerat. Sai da ya sallame mu sannan ya koma kan iyayenmu.

Yayi wa Maman Usama nasiha da kuma nuna mata illar abunda takeyi, haka ya gama musu nasiha gaba d'aya tana ta zumb'ure-zumb'urenta sannan kowa yaje ya kwanta.

Daga wannan lokacin bakin Muneerat yayi tsit, duk da ta daina yi min magana, amma naji dadin daina gulmana da take kaiwa makaranta. Rayuwa ta cigaba a yanda take dan babu sauyi...

A kwana a tashi yau na gama rubuta jarrabawata ta k'arshe, na rubuta jamb kuma score dina yayi daidai da course din da nakeson karanta wato Political science. G.S.U na nemi admission kuma ban wani sha wahala ba na samu na fara zuwa.

Tun safe yau na tashi ina shirin zuwa makaranta dan ina da class 8, sai da na gama shiri na wuce kitchen dan samun abinda zan ci. Maman Usama na gani a kitchen na gaida ta sannan nace "ba a gama breakfast ba?" Tace min "eh, da kikasan zaki je makaranta me ya hanaki fitowa ki d'aura abinda zakici? Ni ban gama ba" ta juya ta fice, na kalli gas cooker na ganshi yanda yake, rabonda ayi refilling yayi sati biyu, dan baba yak'i bada kud'in. 

Kallon stove nayi na isa wurin na duba ko akwai kalanzir naga babu ya k'are, ina da tabbacin Maman Usama ce ta juye sai zatayi girki ta sake d'urawa, a raina nace "kowa da bak'in halinsa". Tab'e baki nayi sannan na fito na wuce d'akin mama.

Bacci naga tana yi, na duba jakan da ke rataye a kafad'ata naga naira d'ari biyu ne aciki, ko kudin mota bazai isheni ba bare abinci, ban tashe ta ba na duba inda take ajiye kud'i na samu naira d'ari biyar na d'auka na fice daga d'akin. Tun da na doshi k'ofar da zai sada ni da garejin gidanmu na fara addu'ar Allah yasa baba ya gama exercise d'insa yana d'aki dan har ga Allah yau banson hawan jini da b'acin rai. Ban gama tunanina ba naji alamar gudu a bayana ana iso ni, sai da na had'iye miyau sannan na juyo dan in gaishe shi, da yake baba yafison gudu da safe akan zuwa gym, ranar da baison fita da safe zaki ji shi yana ta zagaye cikin gida wai exercise yake ranar da yake jin fita kuwa waje yake zuwa yayi ta gudu sai ya gaji ya dawo.


       ๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARRABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 10


Da murmushin dole nace "ina kwana baba" bai amsani ba ya tsaya yace "ina zaki je?" Kaina a k'asa na amsa shi da cewa "makaranta, ina da lectures 8 gashi yanzu har 7:25 yayi" ban kalli fuskar sa ba bare inga yanayinsa, ji nayi yace "makarantar da kike fakewa dashi ya fara isata, dama maza ki turo miji ayi maganar aure, kud'i makarantar da nake biya ya huta" bai jira amsa ba ya wuceni ya cigaba da gudunsa.

Yau dai raina a dagule na fito daga gida, sai addu'ar Allah yasa a waje in samu farin ciki. A bakin titi na tsaya ina neman napep, da alamar nayi sammako dan ko iya hangena ban hango napep ba, wayata na d'auko baby nokia da mama ta saya min ina danne-danne, ko ni bansan meh nake dannawa ba, in shiga nan in fita in koma can, kawai dai in samu abun yi. Kamar daga sama naji muryar Mubarak saurayina yana cewa "sweery" juyowa nayi da murmushi a fuskata.

Sanye yake da polo shirt blue mai ratsin fari, sai wando fari mai kyau, fuskar nan nashi kamar kullum cike da annuri da murmushi. zaune yake a cikin motarsa Honda mai kyau bak'a, nuni yayi min da in shigo ya sauk'eni, banyi musu ba na shiga na rufe k'ofar sannan na kai idona bisa fuskar sa ina murmushi. 

Fari ne mai karan hanci amma sai dai yana da d'an fad'in hanci, yana da pink lips da idanu kyawawa tubarkallah. Maganarsa ne ya katseni tunanin da na lula "tunda bazaki gaishe ni ba ina kwana?" Kawar da kaina nayi gefe ina duban hanya ban daina murmushin da nakeyi ba nace "yi hak'uri, ina gaisuwa ranka ya dad'e".

Sai da yayi min iyayi irin nasa akan bazai amsa ba sannan ya amsa, mu ka cigaba da hira har muka isa farfajiyar makaranta, yayi parking sannan yace "saura 10minutes, muyi hiran 5minutes sai ki tafi ko?" Kallonsa nayi ina cewa "ya zan katseka kuma, bayan ka kawo ni har k'ara minti biyar zakayi? fitowa kayi zaka je gun aiki fah ka manta ne?" 

Tab'e baki yayi yana kallo na ta gefen ido, dariya nayi nace "zamu had'u ai" "a'a wallahi, ni na fara gajiya da binki gidan k'awaye, wataran ma sai kince zaki zo mu had'u kice baba na gida bazaki iya fita ba, gida nakeson ki bani izini inje in yaso duk lokacin da nake ra'ayin ganinki sai inje" ya marairaice yana cewa "please sweery".

Kallonsa nayi sannan nace "bayan baka son zuwa aiki, taya zan ce kaje gida? Da wani kud'in zaka biya sadaki na? In kanason kaje gida kana zuwa aiki akai-akai, kaga sai ka tara mana na sadaki da sauran abubuwa" na fad'i hakan da alamar wasa.

Dariya yayi sannan yace "kice dai kina korata, zamuyi magana anjima, dan Allah kada ki koma gida, flash me kina fita daga lectures zan zo muyi maganar nan da ke, dan wallahi na gaji" ban amsa shi ba sai dariyar da nakeyi har na fita daga motar nayi gaba na barshi bayan nace "bye".

Yanda yace hakan nayi, bayan na fito daga lectures na danna masa flashing, bai iso cikin makaranta ba har 12, lokacin da ya iso ina shan kunun aya mai dad'in gaske wanda k'awata Muslima ta kawo min, ni d'aya nake zaune ina jiran k'arfe biyu dan shiga wani ajin, Muslima ta tafi hostel tare da wata 'yar ajinmu, ni d'aya suka barni anan ina jiran Mubarak Habibinah. Da ya iso kam mun sha hirarmu ta soyayya, sannan daga bisani ya nemi izinin tura magabatansa gida, ce masa nayi sai nayi magana da mamana in yaso sai muyi teking 1st step, yaji dad'i sosai dan ban tab'a nuna masa na yadda zan aureshi kamar yau ba.

Mubarak dai na had'u dashi ne akan titi, ranar na fito daga gida zanje kasuwa na ganshi, anan yayi ta min magana nak'i kulasa har na shiga kasuwa bai daina bina ba, a jere muke tafiya kamar tare muka shigo kasuwar, hakan yasa na kar'bi wayarsa na sa lambana kamar yanda ya buk'ata sannan na samu ya tafi, tun daga ranar dai ni bansan ya akayi har naji na fara sonshi ba, so marar misaltuwa, he is my 1st love, kuma a tunani na my last dan shi nake burin gani matsayin mijina.

Asalin sunansa Mubarak Dawaki, mahaifinsa ya rasu tun da jimawa, yana da yaya da kuma k'anne biyu, Alhamdulillah suna da wadata dan babu abinda suka nema suka rasa, Mubarak na aikin gwamnati albashinsa a kowani wata dubu arba'in da uku kunga kuwa Alhamdulillah ana samun na kashewa shi da k'annensa da mahaifiyarsa. Yayi makarantar boko ya tsaya a matakin degree, ya nemi aiki wurare da dama da zai iya samun salary fiye da hakan amma Allah bai sa ya samu ba, dan haka ya hak'ura yake fama da wannan kafin Allah yasa ya samu wani.


        ๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARRABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 8


Zama tayi gefen mama ta rik'o hannunta. Murmushi mama tayi bayan tayi dabarar goge hawayen da ke fuskarta, Nasreen tace "Mama Baba ne koh ya tab'aki? Ai naji maman Usama tana fad'awa Anty Muneerat abinda ya miki, mama mu bar gidan nan mana tunda baya sonmu, ni bana sonsa tunda yana sa ki kuka" bansan lokacin da nace "nima wallahi na tsanesa na tsani gidansa" 

Mama da mamaki ta juyo tana kallona dan bata san ina d'akin ba, tashi nayi nazo inda take sannan nace "mama meh yasa kika auri mutumin nan bayan kinsan halinsa? Haka zakiyi ta zama cikin bak'in cikinsa?" Murmushi mama tayi kafin tayi magana Usama da Jabir suka shigo, duk sun had'e rai. 

Mama tace "kun gama kaiwa?" Usama yace "mama wallahi kuna ragawa mutumin nan, tun ina d'an masa addu'ar shirya har na daina, tsantsan k'iyayya nake masa mai wuyar fassarawa, shi bai san abinda yakeyi yana b'ata future dinmu bane?" Ya ja tsaki ya kawar da kai. Jabir yace "next year zamu gama tsinannen makarantar nan ai ko? Hmm" ya kalli Usama shima Usama ya kallesa sukayi murmushin tak'aici.

Mama dai kamar kullum hak'uri ta bamu had'e da nasiha, ta nuna mana lallai lallai mahaifin mu ne, kamar yanda zamu so ta haka zamu soshi, zan iya cewa dai maganganunta sun shiga kunne d'aya suka fita ta d'ayar, dan babu wacce ta shiga zuciyarmu ta zauna. Hasalima kowa da abunda ya k'udura a ransa.

Haka muka cigaba da rayuwa a gidanmu, kullum cikin b'acin rai, halayensa ko kad'an baya sauyawa, wani lokacin sai kayi mamakin abinda Baba zai maka. Tsakaninmu 'ya'yansa kuwa zan iya cewa da farko kafin Maman Usama ta tsirfo sabon halinta muna zaman lafiya sosai, dan duk tsiwar Momy da masifarta bai hanata had'a mu da yaranta ba, bata son raini hakan yasa bata sake fuska, amma yaranta ta nuna mana k'annenmu ne sannan su ma ta nuna musu mu ne nasu, lallai tana da hali mai kyau dan ban taba jin wani yayi k'orafi akanta ba.

Tun da na shiga aji 6 maman Usama ta fito da halinta, k'arfi da yaji takeson raba mu da k'annenmu wai ita a ganinta tunda mahaifinmu na nuna mana banbanci meh na had'in kai kuma? Muneerat ita ce babba, kuma tafi kusa da mamanta sosai, hakan yasa duk abunda mamanta tace tayi a take zata aikata. Usama ne ke nuna mata illar haka shiyasa basu shiri ko da wasa da mamansa, Muneerat kuma da ke ta girmesa haka zaiyi ta mata magana akan ta daina biyewa Mamansu amma fir tak'i, har ya fita sha'aninsu ya rik'i Aisha dakyau dan tana jin maganarsa fiye da maganar mahaifiyarsu.

Tun Muneerat na k'ananan munafurcin ta agida har ya koma makaranta, zama zatayi ta zage ni ta zagi 'yan d'akinmu son ranta tana fad'an irin abinda baba ke mana wai duk dan ta samu a daina ganinmu da daraja a k'i mu, tun tanayi ana b'oye min har k'awayenta suka fara zamewa suna fad'a min, ni kuwa sai dai ince musu ku k'yaleta yaranta ke damunta, in na dawo gida in fad'a wa Mama.

Kamar kullum yau wani k'aryar ta shirga wa k'awayenta kuma aka fad'a min, zan iya cewa shine kafurar k'aryar da tayi min na k'arshe, nayi kuka har na canja kamanni da naji wannan k'aryar, ban iya zama har aka tashi ba na tattara takadduna na bada excuse aka barni na koma gida. Da dare har d'akinta naje na sameta wai muyi maganar nutsuwa da ita dan ta daina abinda ta koya sabo.

"Muneerat yaushe jiya naje gun Baba nace ya bani kud'i ya hana har mama taje gunsa tana rok'onsa ya mareta?" Tabbas naga alamar razana a fuskarta amma ta dake ta d'auke kai, na cigaba "yaushe kika tab'a ganin baba ya mari matarsa duk da cewa nasan halin baba babu kyau" A gadarce tace min "ko da baba bai mari matarsa ba ai ya nuna banbanci a tsakaninmu kuma ke ma kinsan akwai banbanci, shiyasa nake nunawa duniya cewa tsakaninmu fah akwai katangar k'arfe duk kuwa da cewa ke d'in yayata ce, tunda har ubanmu.............." 

Sauk'ar marin da taji a fuskarta shi ya dakatar da ita, waigowa tayi dan ta ga wanda ya sharara mata mari taga Usama na huci, da Usama ya k'ara minti d'aya bai kai marin nan ba toh ina da tabbacin yatsuna biyar ne zasu shafi kumatun Muneerat, ina da 'yancin da zan hukuntata tunda nice babba, kuma babu wanda ya isa yace min meh yasa? Abunda yafi bani mamaki bai wuce yanda Muneerat ta fitsare a lokaci k'ank'ani ba, har zata kalleni tayi min rashin kunya? Ni Maryam? Lallai Muneerat ta manta ni wacece wurin jibgan yaran da suka raina ni, ina kama girmana dan na girma ta d'auka bazan iya jibgarta kamar yanda nakeyi da ba koh?


    ๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARRABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 11


Nayi wa mama maganar mubarak kamar yanda nace, kuma ta bani goyon baya 100% sannan tace zata fad'awa Baba dan yayi shirin tarbar bak'i. Lokacin da na sanar da Mubarak har ihun murna sai da yayi yace min next week zai turo. Baba ma da aka fad'a masa baiyi musu ba, yace sai sunzo.

Yau da misalin k'arfe biyu magabatan mubarak suka samu isowa gidanmu dan neman aurena, cikin mutunci suka tsaida magana, amma sai dai kash, abinda Baba ya nema gunsu yafi k'arfinsu dan zunzurutun kud'i yace zasu bayar, na sadaki kad'ai ya ninka albashin Mubarak biyu, banda k'ananan abubuwa da za'a iya nema daga baya. Sun nemi ya rage amma fir yak'i, da suka takura sai cewa yayi ya rage dubu ashirin a cikin 150thousand da ya buk'ata. Haka suka fice jiki a sanyaye suna magana k'asa-k'asa dan basu zaci Baba zai musu haka ba yanda suke jin ana yabonsa a gari, kawai sun yanke maganar akan baya son bada auren ne, dan kud'in yayi musu yawa, banda kayan da zasu saya da kud'in sdakin yarinya harda zunzurutun kud'i haka? 

Lokacin da naji labarin nan nayi kukan tak'aici, tambaya nakeyi "shin baba me zaiyi da kud'i haka? Dan ina da tabbacin in an bashi kud'in a aljihunsa zai sa" Mubarak dai yace yaji ya gani zai biya, amma mahaifiyarsa tayi fafir tayi jan ido tace bata yadda ba, duk wani rarrashi da ban baki da yasan zai yi dan ta yadda ya aureni tak'i. Dole yabi umarninta, dan yayansa ma da yake ganin team nasu d'aya yau yabi ra'ayin mahaifiyarsu yace bai yadda a auro Maryam 'yar Alh. Muktar Dala ba.

Ina cikin makaranta ina zaune, tunani ne fal raina, yau kwana biyu kenan da fasa maganar aurenmu da Mubarak, ya ma kasa yi min magana ta waya sai text yayi ya fad'a min abinda mahaifiyarsu tace. Ban masa reply ba haka nak'i d'aga wayarsa. 

Ba wai dan yayi min laifi ba sai dan kunyar shi da nakeji. Ji nayi an zauna a gefena, waigowar da zanyi naga Mubarak zaune cikin k'ananan kayansa, fuskarsa cike da damuwa. Bansan lokacin da na fashe da kuka ba, fuskata nasa tsakanin cinyoyina ina mai zubar da hawayen rashinsa, duk da ba kuka mai sauti sosai nake ba ya gano zubar da hawayena.

Tambayar da yayi min ne ya sake dulmiyar dani kogin kunya, naji kamar in nutse dan wallahi bani da amsa, ko ni bansan amsar ba, tambayar da yayi min shine "meh yasa babanki yayi min haka Maryam bayan yana da kud'in da zai iya aurar da yaransa ba sai an taimakesa ba?" Kuka mai sautin da yafi na d'azu ya kufce min, sai da ya juyo ya fuskance ni sannan ya d'ago fuskata, na runtse idanuna dan kunyar shi da nakeji. A raina ina cewa "shikenan an daina ganin mutuncin baba kenan"

Muryarsa cikin rawa yake min magana "Maryam duk da kinsan ina sonki babanki ya gama b'ata ki wurin mahaifiyata, dan ita gani take baya son na aureki shiyasa yayi hakan, maryam ki daina kukan nan, insha Allah ni ne mijinki, kiyi iya k'ok'arinki dan gano dalilin da yasa yayi hakan, ni kuma ina mai tabbatar miki zan shawo kan mama insha Allah". 

Ni Maryam nasan ko ana ha maza ha mata bazan iya canjawa baba ra'ayinsa ba, hakan yasa na share hawayena ina mai murmushin dole, na fuskancesa sosai ta yanda zai gane babu wasa cikin magana ta "Mubarak munyi kyakkyawar rayuwa wanda muke burin zama tare har abada matsayin mata da miji, ka bi mahaifiyarka nima in bi mahaifi na, mu d'auki abun nan da ya faru matsayin k'addararmu kawai, nagode kuma ka yafe min in na tab'a yi maka wani abu".

Da mamaki Mubarak yake kallona, dan ya d'auka zuwansa zai kawo maslaha ya kuma kawo mana mafita, ban bari ya tsaida tunaninsa ba na tashi na bar wurin, hanyar waje na bi dan bazan iya d'aukan komai ba in na shiga aji. Adaidaita na tsayar ya wuce dani gida ina mai zubar hawaye.


  ๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARRABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 12


Rabuwar da mukayi da Mubarak kenan na har abada, wanda shine silar k'in karb'ar tayin soyayya na kowani d'a namiji har yanzu, bazan tab'a manta shekarar ba, dan shekarar ta zama min bak'ar shekara wanda bana fatan Allah ya sake maimaita min, a shekarar ne na rabu da Mubarak abun sona, abun alfahari na abun begena kuma farincikina. 

A shekarar ne Jabir da Usama k'anne na maza wad'an da nake jin son su a raina, wad'an da nake matuk'ar ji dasu kuma suke ji dani, bani da tamkar su kab cikin 'yan uwana suka guje mu suka guji mahaifarsu a dalilin Baba, bazan tab'a manta yanda abun ya kasance ba:-

Ranar alhamis da dare munyi hirar da bamu tab'a yi ba dan washegari zasu wuce Bauchi zana jarrabawar UTME kasancewar sunyi tsallake sun zana jarrabawar fita daga sakandare tare da Mufeedat, a ranar Usama da Jabir sukayi sallama da kowa ba tare da mun gane manufarsu ba, sai da suka rok'i yafiyar kowa sannan suka saya wa kowa abun da in ya gani zai tuna dasu, sunje gun Maman Usama suka d'an yi hira duk da ba wani sake musu tayi ba sannan suka juyo d'akin Mama wanda dama tun asali nan ne wurin hirar mu da dare, ba mu kad'ai yara ba har Mommy ranar ta zage tayi hira ashe shine rana ta k'arshe da zamu samu damar zama irin haka. Bazan manta abinda ya dakatar damu daga hirar da muke sha cikin farinciki da annashuwa ba, dan kuwa muna cikin k'yalk'yalewa da dariya Baba yazo da masifarsa, sai da yayi mana tas sannan yace kowa yaje ya kwanta, ran kowa a b'ace aka bar masa falon ko ince ya biyo mu a baya yaja mata k'ofarta shima ya wuce nasa d'akin.

Washe gari da safe na tashi nayi shirin zuwa makaranta dan yau ajin k'arfe goma nake da, sai da na ci abinci na fito dan zuwa makaranta, nayi sallama da Mama tayi min addu'ar da ta saba na Allah ya tsare ya bada sa'a, har na iso bakin k'ofar fita na tuna bamuyi sallama da k'anne na ba na juyo a guje har jakar da ke kafad'a ta na sauk'owa ina sake janyowa dan kada ta hard'e min k'afa ko ta fad'i. Ko sallama banyi ba na bud'e k'ofar d'akinsu. 

Ganin tik'a-tik'an jakkuna yasa nayi turus ina kallo, parking sukayi na duk abinda zasuyi anfani dashi, hatta takalma da takaddunsu ban gani inda suka saba ajiyewa ba, duk juyowa sukayi suna kallona.

Sun tsorata da gani na hakan yasa na zargi akwai abunda suke aikatawa, sai da na kulle k'ofar d'akin sannan nace "meh yaran nan sukeyi?" Ina mai kallonsu, Jabir ya d'auke kai yana cewa "me kuwa? Muna shirin tafiya mana" ban tanka shi ba na samu gefen gado na zauna sannan nace "sai da nayi ta baku shawarar ku tafi ranar sunday, monday kuyi exams d'in ku dawo kunk'i, kuga kayan da kuka kwashe sai kace zaku je kuyi shekara" Jabir yace "makaranta zakije ki tafi kada kiyi letti, nasan sallama zaki ce kika zo mana, mun karb'a kuma mun gode".

Haushi maganar tasa ta bani shiyasa na mik'e ina cewa Usama "Allah ya kiyaye hanya, kuna isa ka k'irani, wannan yaron....." Na zungure kan Jabir ina cewa "ya bala'in raina ni, zaka dawo ka same ni ai" dariya dukka sukayi sannan na fice nima ina dariyar, daga nesa naji Jabir na cewa "in kuma ban dawo ba ai shikenan kya yi ta yi da Mus'ab". Ban d'auki maganar tasa da muhimmanci ba shiyasa ban amsa ba na tafi. Ashe shine gani na na k'arshe dashi.


  ๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARRABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 13


Daga ranar bamu sake jin labarin Jabir da Usama ba tsawon sati biyu, an neme su duk inda aka san zasu iya zuwa babu su babu labarin su, Tashin hankali babu wacce bamu shiga ba, munyi kuka har mun gode Allah. Tun Baba baya maganar har ya zama kullum sai ya tambaya "kunji labarin yaran nan?" Ya nuna kulawarsa akan b'atan su kuma ya nemesu daidai gwargwado amma babu su babu alamar za'a ji abu akansh, wayoyinsu duk a kashe. Fad'in irin tashin hankalin da muka shiga b'ata lokaci ne.

Bayan sati biyu da kwana uku da barin su gida, ina zaune wurin mama nayi shiru ita ma haka, kowa da abunda yake sak'awa a ransa, na tabbata kamar yanda nake tunanin k'annena haka ita ma su take tunawa. Wayar Mama ne tayi ringing na tashi na d'auko mata dan yana d'an nesa da mu, new number na gani tun kafin na iso ta na d'auka ina ce mata "sabon lamba ne" sannan na mak'ala mata a kunne ita kuma ta furta "Assalamu alaikum".

Hamdalar da naji tanayi babu tsayawa yasa na iso dab da ita ina mai kallon fuskarta da naga alamar hawaye ya ciko mata idanu, sai da ta maimaita Alhamdulillah sau biyar sannan tace "Jabir" ware ido nayi ina mai sake matsowa had'e da sa kunnena jikin wayar dan in tabbatar da gaske Jabir ne ya k'ira, Mama bata barshi yayi magana ba ta jero masa tambayoyin da ko ni aka tambaya zan rasa wanne zan amsa, a tak'aice yace "kada ki damu Mama, lafiyan mu k'alau".

"Lafiyarku k'alau shine wayoyinku duk a kashe? Ina kuka shiga kuka d'aga mana hankali?" Cikin rashin damuwa yace "mun tafi inda zamu samu rayuwa mai inganci, Mama kinsan bazan iya zaman gidan Baba ba, nafison in nemi na kaina amma ya hana, ya hanani k'ananan sana'a duk da ba shi zai bani kud'in jari ba, shi bai biya min buk'atu ba, bai biyawa mahaifiyata bare k'annena ba, tayaya zan samu kwanciyar hankalin da zan iya zama? Bayan haka ga zagi, masifa da rashin furta kalamai masu kyau, kullum in kaga mahaifinka sai zuciyarka ta tsinke, ni gaskiya Mama na k'iraki ne ma in fad'a miki bazan dawo ba sai na zama mutumin kaina, fatana in samu kyakkyawar addu'a daga gareki". 

Zata yi magana ya katse ta da cewa "dan Allah, dan Allah Mama kada ki ce in dawo dan bazan iya dawowa ba, bazan iya ganin mahaifina na cin zarafinki a idanuna babu abinda zan iya yi ba, kiyi hak'uri kiyi min addu'a da fatan alkhairi, nan ba da jimawa ba zan cireki daga wannan Jarrabar da Allah ya sauk'o miki" Yana gama fad'an haka ya katse wayar ba tare da ya jira amsarta ba, a tare muka saki kuka mai sauti, muna kan kukanmu mukaji Maman Usama a takiyar gida tare da Baba tana fad'a masa Usama ya k'irata ga yanda sukayi. 

A take Baba ya k'ira wayarsu suka k'i d'agawa dukka, daga baya ma kashe wayar sukayi mukayi ta k'ira a kashe. Wasa-wasa munyi wata cur babu Usama bare Jabir, Baba yayi musu text kuma ina da tabbacin sun gani dan ya nuna delivery report, umarni ya basu da kakkausar lafazi akan lallai lallai su dawo amma sukayi biris suka share shi, sai ma canja number da sukayi gaba d'aya. Har yau da nake baku labari babu wanda yasan inda Jabir da Usama suke, sai dai su k'iramu lokacin da suke ra'ayin mu gaisa.

Al'amarin Baba kuwa babu ragi sai ma k'aruwa da yayi, mantawa yayi da rayuwar su Usama, sai wani sabon salon da ya tsirfo na zagin Maman Usama da Mama akan tafiyar da yaransu sukayi, har ya kai ga ko gaishe shi sukayi sai ya ga damar amsawa, shi a cewarsa da had'in bakinsu yaran suka tafi.


  ๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARRABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 14


Maryam da ke kwance akan gado ta mirgina ruf da ciki ta janyo filo ta d'aura kanta akai sannan ta lumshe idanunta, zafafan hawaye suka zubo ta gefen idanunta sakamakon tuno da abu na uku wanda ya faru a cikin shekarar da take k'ira bak'ar shekara. Ahankali ta furta "Allah yaji k'anku Maman Usama da Mus'ab" bata bud'e idanunta ba ta cigaba daga inda ta tsaya:-

Bayan tafiyarsu Jabir da wata uku wata mummunar lamari ta wakana a gidan Alh. Mukhtar, mun shiga tashin hankali kuma munyi rashi matuk'a, Maman Usama asalin 'yar jahar Gombe ce tana zama a k'auyen Kumo, k'aramar gari ne kuma babu nisa da Gombe, ta shirya tsaf domin ziyarar iyayenta sakamakon jimawa da tayi bata je ba. Sun sami matsala sosai da Baba a wannan lokacin wanda har ya kai ga daina cin abincinta, alal hak'ik'a har yau da nake aiki bayan na gama skul bansan meh ya had'asu ba. ana washe gari zata tafi suka shirya, cikin farinciki suka rabu a ganina tunda naga da murmushi ta fito daga d'akinsa.

Ikon Allah yasa aka yi rabuwar mutunci dan dukkanmu mun rakota har bakin mota, ni na rufe mata k'ofar motar ma tana dariya tana cewa "bazaki zo mu tafi ba ko Maryam, ai ga Mus'ab zai wakilce ki" dariya kawai nayi dan ban saba wasa da ita ba bare muyi yau. Shafa kan Aisha nayi ina cewa "ki gaida min Kaka in kinje, kice mata ta baki abun dad'i ki kawo min tunda banje ba bare in d'auka da kaina".

Sosai muka saba da Kakar Kumo, duk lokacin da Maman Usama zata je tare muke zuwa, matar akwai barkwanci da son kyauta, ina bala'in son zuwa gunta, wannan karon ma cikina ke d'an ciwo kuma ina da tabbacin wata na ke min sallama, banson inje inyi ta ciwon ciki in rasa walwala shiyasa nak'i zuwa. Maman Usama ke driving sai Momy da ke gefenta, zata kwana sai washe gari ta dawo da motar ta barsu a can. Aisha, Mus'ab da Zahra kuma na baya sai washe baki suke har suka fice daga gida muna d'aga musu Hannu.

Da misalin k'arfe hud'u na rana muna zaune a tsakar gida, ni da Mama, sai Muneerat da Shamsiyya Nasreen na d'aki tana bacci, Muryar Baba muka ji yana cewa "Innalillahi, ku dawo dasu kawai, barin iso in sameku" yana fad'an haka yana k'arasowa cikin gida. Bai bi ta kanmu ba ya shiga d'akinsa, Mama hankali a tashe ta bi sa dan yanayin fuskarsa ya nuna ba lafiya ba duk da dama asali ba fara'ar yake yi mana ba.

Muna zaune inda muke amma babu wanda ke magana cikinmu kowa da abunda ke ransa. Sai da suka d'au tsawon minti goma sannan suka fito, fuskar mama na fara kai dubana wanda ya bala'in tsorata ni, a tare muka tashi da sauran yaran muka iso Mama, hawaye ke fita daga idanunta, a tunani na Baba ne yayi mata wani abun da har ya hanata daurewa ta fara kuka tun daga cikin d'akin. Dukkanmu tambaya d'aya muke maimaita mata "Mama meh ya faru?" had'e da girgiza ta.

Kalamanta da suka doki kunnuwanmu ne yasa mu yin shiru, rik'e Muneerat tayi dan a yanda ta koma inaga iska kad'ai marar k'arfi na iya zubar da ita a wurin. Cewa tayi "Maman Usama sunyi accident, ana hanyar dawo dasu gida". Innalillahi nake furtawa a raina, bayan wannan na kasa yin komai, tsugunawa Muneerat tayi a wurin tana mai zubar da hawaye tana cewa "mutuwa sukayi da kike kuka haka Mama? Ku fad'a mana gaskiya ko Mamana mutuwa tayi" a tare muka kama ta ni da Mama, Kalmar Innalillahi nake furta mata a fili dan ta karb'a, sai da na maimaita sau biyar sannan ta bi ni muka cigaba da yi.

Bamu d'auki minti talatin ba mukaji motoci har uku a cikin gidanmu, dukkanmu muka tashi tsaye muna jiran a shigo mana dasu. Uncle Usman ne ya shigo tare da matansa biyu, sai da muka zauna sannan yayi mana nasiha tare da tunatar damu mutuwa, tun da ya fara maganar muka gane rasuwa sukayi, kuka muka fara sosai harda shesshek'a. K'arar wata motar muka ji shi kuma ya mik'e, sai da ya isa bakin k'ofa sannan yace za'a shigo da gawar yanzu, Momy da Aisha da zahra suna asibiti.


  ๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARRABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 15


Ban tab'a kukan mutuwa irin lokacin da aka shigo da gawar Maman Usama da Mus'ab k'anina ba, duk da munsan bai kamata muyi kukan ba amma zuciyarmu ta kasa barin zafi da k'una, kukan da mukeyi kad'ai ke sassauta mana abinda muke ji, na tausayawa Muneerat matuk'a, dan tun da Aisha ta shigo ta rungumeta ta cigaba da kuka mai tsuma zuciya.

Aisha ce kad'ai bata ji ciwo sosai ba a cikin motar, gurjewa tayi kuma an wanke an sa mata bandage aka dawo da ita. Momy na asibiti a kwance taji ciwo a k'afarta ta dama, sai bugewa da tayi a goshinta, Zahra kuwa bleading takeyi sosai ta cikinta, hakan yasa aka shiga da ita dan duba lafiyarta. 

Bayan anyi musu wanka aka kai su gidansu na gaskiya, Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, tabbas duk mai rai mamaci ne, Allah ya kyautata k'arshenmu. Bayan kwana bakwai da rasuwarsu aka dawo da Momy gida harda Zahra, wannan hatsarin da sukayi shi yasa har yau Momy ke d'ingisawa in tana tafiya, haka zalika yana yi mata ciwo wani lokacin. 

Zahra kuma an tabbatar mana da cewa ta samu rauni sosai a mahaifarta, likita ya tabbatar mana da cewa in aka fita da ita kasar India wata k'ila a samu nasara da izinin Allah, a yanzu haka bayi da tabbacin mahaifarta na iya d'aukan ciki duk da k'arama take, baya tsammanin in ta girma zai dawo daidai.

Maganar Usama kuwa yana jin labarin mutuwar mahaifiyarsa suka kamo hanya, tun a hanya suka k'irani a waya, rana ta uku na zaman karb'ar gaisuwa da misalin k'arfe biyu na rana suka iso, kuma a wannan lokacin suka sake k'irana suka sanar dani, saidai suna fargabar yanda Baba zai karb'esu, ce musu nayi su shigo kawai, akwai mutane bazaiyi masifa ba. 

Daga nan ban sake magana dasu ba, haka zalika bamu yi waya dasu ba. Sai dare nakeji daga wurin Mama Baba fata-fata ya musu kuma ya jaddada musu kada su k'ara tako k'afarsu gidanshi tunda sun masa uwar shegu lokacin da yace su dawo. Bud'an bakin Jabir cewa yayi "ai dama ba zaman gidanka muka dawo yi ba, Mamanmu ta rasu muka zo gaisuwa da karb'ar gaisuwa sannan muyi mata addu'a, bayan wannan meh zai sa mu dawo bak'in gidanka mai tarin kayan takaici da bak'in ciki".

In tak'aice muku zance Baba har bin su da takalmi yayi yana wurgi, a guje suka bar gidan, Allah ya so babu bare, 'yan gida ne kawai shiyasa maganar bata fita waje ba, alal hak'ik'a babu wanda yasan guduwa sukayi, sai dai tsegumin mutane wanda ba'a rasa ba.


  ๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARRABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 16


Momy ce ta fito ranta b'ace daga d'akin Baba, tana tafiya tana d'ingisawa dan k'afar bai daina ciwo ba, ina zaune a bakin k'ofar Mama na hangota, zuwa tayi ko kallona bata yi ba ta shige d'akin babu ko sallama. Sai da na waiga na sake kallonta sannan na cigaba da yankan farcena ina tunanin meh ya b'ata mata rai haka?

Can naji shesshek'ar kukanta tana magana k'asa-k'asa Mama na cewa "ki kwantar da hankalinki zamu san yanda zamuyi". Daga nan ban sake jin abinda suke cewa ba, tashi nayi na bar wurin ba dan na gama yankan farcena ba sai don in Mama ta ganni a wurin zata min fad'a, dan ta hane mu da lab'e kuma muddin na cigaba da zama a wurin zanji maganar ko da ba dukka ba. 

Ban je na duba Mama ba har sai da nayi sallahr la'asar, bayan na cire hijabina na fito dan taya ta abincin dare. A hanya muka had'u muka d'unguma zuwa kitchen ba tare da ta min magana ba. Haka dai ranar muka gama girkin babu hirar kirki. Da dare naga Uncle Usman yazo gida, suka had'u a falon Baba dukkansu, ko meh sukayi? oho!

Dukkansu sun fito daga d'akin babu mai fara'a kowa ya wuce d'akinsa, sai da aka kwashi sati d'aya ana abu d'aya a gidan nan babu sauyi, kullum Momy sai tayi kuka, idanunta sun koma jazur, ta daina kwalliya ta daina kula mu kamar da.


Ranar da aka cika sati d'aya ina zaune a gefen Mama ina tayata tsefe kanta Momy tayi sallama, sai da muka amsa ta shigo, fuskarta na fitar da wani annurin da na kasa gane na meh ne, rabona da ganinta tana farinciki tun rasuwar Maman Usama. 

Sai da ta samu wuri ta zauna sannan tace "Uncle Usman ya cika min kud'in Yaya" (da yake yaya take k'iran Mama) ta cigaba da cewa "Allah yayi masa albarka, bazan tab'a manta karamcin da yayi min ba" sai ga hawaye ya sauk'o mata. Mama ne tace "ki daina kuka, Allah ya kawo mana sauk'i godiya yakamata muyi masa, Allah ya rufa mana asiri". Nidai kallonsu kawai nake dan bansan akan meh suke magana ba. 

Sai da suka gama jaje da farin cikinsu sannan Momy ta fuskance ni tace "ki kawo miji kiyi aure Maryam, indai kika biyewa Babanku d'in nan wallahi bazaki yi abun kirki ba. Mahaifinku ne dole kuna sonshi amma abunda yayi min ya nuna min baisan karamci da abinda yakamata ba.........." Nan ta zayyane min duk abinda ya faru, ashe dan ance ya bada kud'in da za'a kai Zahra asibiti shine yace bazai bayar ba, sai da uncle Usman yazo da kansa sannan yace shi bayi da kud'i sai ya samu, daga baya kam cewa yayi a duba ta FMC na Gombe mana, sai an kashe kud'i an fitar da ita waje. Akan wannan ne aka yi ta tashin hankali. 

Mama ta had'a gwal nata ta sayar, haka Momy ta sayar da nata amma kud'in basu cika ba, ta sake tambayar sa ya cika mata amma yak'i, a lokacin dai Uncle Usman ne ya tattaro kud'i ya bata ta cika dan ta kaita asibiti, bayan haka uncle Usman ne ya rakata har India suka gama komai sannan suka dawo. Wannan abun da yayi har yasa Momy tattara kayanta dan barin gidan.

Mama ce ta hanata kuma ta nuna mata rashin dacewar tafiyar. A k'arshe dai bayan ta kai Zahra ta dawo tace ita bata ga ta zama ba tunda ta samu lafiyar 'yar ta, dakyar uncle Usman da Mama suka hanata. Ba dan taso ba ta zauna aka cigaba da zama a k'ark'ashin Baba cikin rashin jin dad'i da walwala.

Cigaban labari:- 


Maryam ta furzar da iska daga bakinta sannan ta furta a fili "Allah ka taimakeni in dawo da Jabir gida, Allah ina rok'onka ka sauya min halin Mahaifina" ta share hawayenta da hannunta sannan ta lumshe idonta bacci mai nauyi ya d'auketa kasancewar fashin sallar da takeyi bata farka ba sai da Mama ta tashe ta dan ta koma d'akinta.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARRABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 17


Zaune take a cikin ofishinta, kunnenta sak'ale da earpiece tana danne-danne da laptop, bakinta na motsi alamar bin abinda takeji takeyi. Knocking akayi mata daga bakin k'ofa amma shaf bata ji ba, ta cigaba da abinda takeyi tana mai kai duk hankalinta ga computer. Sai da aka sake knocking na uku sannan aka bud'e k'ofar aka shigo, d'ago kanta da zata yi taga Boss nata, mik'ewa tayi da hanzari tana mai cire abun kunnenta had'e da furta "sorry sir." dan alamu ya nuna ya fusata in tayi la'akari da yanda ya had'e fuskarsa.

Masifa ya fara mata yana mai cewa "aiki kika zo yi ko jin wak'a, problem na mutane kenan, an basu aiki instead su sa hankalinsu kan aikinsu sai suyi ta shiririta" babu abinda take furtawa sai "sorry sir." Had'e da russunawa alamar girmamawa. 

A fusace ya matso wurin computer ya cire earpiece, da mamakinsa yaji karatun Qur'ani ke fita na Sheikh Ahmad Sulaiman. Kunya ta rufe shi, daga bakin k'ofar yaji ana cewa "kazo ka zauna, sai masifa kake yiwa mutane ka ajiyeni" yana kan magana yana k'arasowa cikin office d'in, baki bud'e ya tsaya kallonta, ita kuwa tana kallonsa ta had'e rai ta d'auke kanta.

Muryar Boss nata ne ya katse su yana cewa "sorry Musty, na zo amsar files d'in ne ina ta k'wank'wasa qofa bata ji ni ba, ashe ta sa abun nan a kunnenta sai jin wak'a take" ya fad'i hakan yana d'ago earpiece d'in da ya cire. Maryam dan takaici ko d'ago kai batayi ba bare ta kare kanta, indai kare kanta shi zai kawo mutuncinta a wurin wannan d'an siririn mutumin(in ji ta, dan ba siriri bane) toh ta gwammace kada ya ganta da mutunci.

Babu laifi kyakkyawar mutum ne son kowa k'in wanda ya rasa, fatar jikinsa sai shek'i yake tsabar hutu da jin dad'i, tabbas akan wannan mutumin na yadda da fad'in "hutu da kwanciyar hankali na k'ara wa mutum kyau" dan kuwa naga alamar kyawunsa bayyanan ne, farat d'aya zaka ajiye sa ajin farko wurin kyau, in ka k'are masa kallo kuwa zaka gano hutu da jin dad'i ne kawai ya k'ara masa kyau. Suit ne bak'a a jikinsa da takalmi bak'i mai yalk'i alamar ta sha wanki. 

Kana ganinsa kaga gaye d'an hutu mai ji da naira. Yatsa d'aya ya d'aga masa alamar yayi shiru sannan ya mik'awa Maryam hannu alamar ta mik'o masa takaddun. Mik'a masa kawai tayi ba tare da ta kai dubanta gare shi ba, shi ma gogan d'auke kai yayi ya juya ga Boss na Maryam yana mai cewa " Umar ba dan na samu abu mai muhimmanci ba yau kasan baza mu kwashe da kyau ba, babu mai ajiyeni ya shanya kamar kayan wanki ka sani" dariya Abokin nasa yayi yana cewa "na sanka Abokina" suka fice suna magana k'asa-k'asa.

    Idanunta ta juya sannan ta ja tsaki, a ranta tana cewa da ban sanka ba shine zaka min burga, ta sake jan tsaki ta cigaba da aikinta. Fitar su ke da wuya wayarta ta d'au ruri alamar tana neman agaji, kamar bazata d'aga ba ta kai hannunta ta d'auko wayar idanunta na ga aikin da takeyi, amsa wayar tayi ta d'aura a kunnenta tana mai cewa "Assalamu alaikum" muryar da taji ne ya sata had'e girarta tare da turo baki. Sai da ya amsa sallamar ta sannan ya cigaba da cewa "wai dama a Wannan makarantar kike aiki? Haba Maryam me laifina da kika kasa karb'ar soyayyata? Tun da na d'aura idona akanki na nemi labarin ki, rashin kula maza da kikeyi duk naji amma duk bincike na ba'a ce min kina wulak'anci ba, shin menene dalilinki na wulak'anta ni? Dan kawai ina sonki?" 

Ita dai tun da wannan nataccen ya fara k'iranta bata taba jin bata kyautawa ba sai yau, ita sunansa ma bata rik'e ba, ya cika naci da kafiya, sai da ta furzar da iska sannan tace "dan Allah kayi hak'uri, kasan na fad'a maka ba aure bane a gabana yanzu...." Dakatar da ita yayi da cewa "me kike nema a duniya bayan wanda kika samu? Aure kawai kike buk'ata, duk wani abunda zaki nema a ganina in kikayi aure zai fi miki sauk'i, alal ak'alla ki bani dama ki ga yanda nake sonki da burin baki duk wani jin dad'i da kowace mace take buk'ata a gidan aurenta, kuma na miki alk'awarin barinki ki cika burinki in har bai sab'a wa shari'a ba, in tak'aice miki ko da yafi k'arfinki zamu had'u mu biyu muyi yak'i dan cimma burinki, fatana ki fahimceni ki bani dama".


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 18


Da alamu maganarsa ya shigeta, dan kuwa yanayin fuskarta ya nuna ta gamsu da maganarsa, saidai kuma hakan bazai sa ta fasa cimma burinta na gyara gidansu da mahaifinta ba, dama alal hak'ik'a ba wai sonshi ne bata yi ba wannan ra'ayi nata yasa take kawo duk wani abunda zai sa taji bata sonshi, ta kushe shi ta ayyano komai da zai sa taji baya burgeta wanda can k'asan zuciyarta soyayyarsa ce ya malale tana faman yakicewa. 

Mustapha Lukman shine sunansa, d'a ne a gidan Alh. Lukman, babban gida ne masu nagarta da mutunci, Allah ya bawa Alh. Lukman kud'i fiye da sauran 'yan uwansa, kuma ya kasance shine babba a cikin yara biyar da Allah ya bawa iyayensu. Gida ne mai girman gaske, dan duk wad'an nan yara biyar d'in a gidan suke tare da iyalansu, kowa da sashensa, soyayyar da suke wa junansu da had'in kai da suke dashi ya kawo hakan.

Alh. Lukman yaso ginawa kowa nasa gidan amma sai k'aninsa ya bada shawarar yayi musu a wuri d'aya kowa da b'angarensa dan yaransu su tashi tare kamar yanda su suka tashi tare. Zaman lafiya sukeyi da mutunta juna sai abunda baza'a rasa ba na zaman mata da zaman tare. 

Mustapha shine d'an gaban goshi a wannan gidan, dan kuwa kowa ji dashi yake kasancewar yana mai musu biyayya ga duk buk'atunsu, duk da ba shi ne babba ba ana basa girma sosai, mutum ne mai fara'a da sakin fuska ba kaman sauran yayun nasa ba, shine d'a na uku a cikin gidan. Yayi makarantar sakandare had'e da degree cikin sa'a, yanzu haka shekarunsa bazasu wuce talatin da d'aya ba. 

Entrepreneurship ya karanta duk da ba abinda yaso karanta kenan ba, amma mahaifinsa ya sa masa wannan ra'ayin dan ya tafiyar masa da kasuwancinsa ko da tsufa yazo masa. Makarantar da Maryam ke aiki L.P (k'irk'irarre) university na mahaifinsa ne, kuma shi ke tafiyar da makarantar sai dai bai cika shigowa makarantar ba sai da dalili. 

Ranar da Mustapha ya fara ganin Maryam a ranar ya tsayar da ita a titi a bakin hanya, hakan yasa taji bai burgeta ba, dan a yanzu a ganinta duk namijin da zai tsayar da mace a titi bai san mutuncin mace ba. Ko sauraronsa bata yi ba bare su fahimci juna, haka ta shige motarta ta koma gida ba tare da tasan yana binta a baya ba, daga wannan ranar ya fara k'iranta yana aika mata sak'on zuciyarsa, k'in aminta tayi kamar yanda ta saba korar duk wani saurayi mai neman aurenta yazo da kalmar "Ba yanzu zanyi aure ba, ba aure a gabana yanzu ka min afuwa" duk da ta fad'a masa hakan bai hana shi k'iranta da neman yardarta ba, dan kuwa duk cikin matan da ya nema a baya bai tab'a jin son mace irin yanda yake sonta ba, a ransa dai yace ita ce "sarauniya".

Jabir da Usama fa? Wani irin rayuwa suke gudanarwa tun korarsu da Baba yayi? Ina suke? Makaranta suke ko sana'a? In makaranta ne wa ke biya musu kud'in makarantar? Ku biyoni a sannu dan jin amsar wannan tambayoyi.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 19


Taku yake na k'asaita yana fitowa daga hall d'in da ke cike mak'il da mutane, fuskarsa alamar damuwa yana waige-waige, wayarsa da ke hannunsa ya kunna ya fara k'ira, rashin d'aukan da baiyi ba yasa shi runtse ido had'e da damk'e wayar kamar zai fasa ta. Kamar daga sama yaji muryar sa yana isowa da gudu yana cewa "holdup ne ya rik'e ni, am very sorry" bai tanka sa ba ya k'araso ya rungumesa cike da tsantsar farinciki, murmushi ya sake shima ya rungume k'anin nasa. 

Sai da suka d'au minti biyu mai kyau rungume da juna sannan ya d'ago ya mik'a masa hannu yana cewa "congratulations my brother Jabir" murmushi yayi shima ya mik'a masa hannu yace "thank you, but you're late, sai da aka gama komai d'an tilon d'an uwan da nake dashi anan zai zo graduation ceremony d'ina".

Usama ya kama kunnensa ya rusuna yace "ayi min afuwa, ba laifina bane, kasan Lagos ba sai na fad'a maka ba. Mu shiga ciki kada sauran ma ya wuce ni" ya kamo hannunsa suka shige ciki. Jabir Da Usama kenan a cikin jami'ar Lagos, yau ya kama rana ta k'arshe da Usama yake kammala karatunsa na chemical engineering wanda ya shafe shekaru biyar zuwa shida yake karanta. Jabir ya dad'e da kammala karatunsa dan course na shekara hud'u ya karanta b'angaren kasuwanci. Tuni ya samu aiki a wani matsakaicin company da albashi mai d'an kauri.

Tun daga ranar da suka fice daga garin Gombe basu sake waiwayan garin da sunan komawa gida ba, waya dai suna yi da Maryam da Mama sai Muneerat da Momy, wannan ma sai a b'oye dan kada Baba yaji gudun fitinarsa. 

Alal hak'ik'a zan iya cewa Baba manta dasu dan duk ranar da ya tuna su baya fad'an alkhairi akansu, tun yana b'ata wa Mama rai har ta daina d'aukansa bare ya dameta, maganarta da Jabir da Usama kuwa bai wuce nasiha da fatan alkhairi ba, sai kuma gargad'in da take yawaita yi musu akan bin mahaifinsu.

Shirye-shiryen dawowa suke amma babu murna a tare dasu, Jabir na had'a kayansa a cikin matsakaicin jaka da bazai d'auki kaya fiye da goma ba, sai cusa kaya yake yana tsaki ta ciki. Usama kallonsa yake yana k'ok'arin rufe tasa jakar da ya cika nak da kaya, sai da ya zauna akai sannan zip d'in ya rufu. 

Babu wanda yayi magana har suka kammala kowa da abin da ke ransa, gado suka koma suka kwanta dan su runtsa saboda gobe da safe zasu d'au hanyar Gombe. Kana kallonsu kasan suna cike da fargaba da tsoro.

Usama yace "ka qira Mama? Me tace da kace zamu zo gobe?" Jabir sai da ya juya masa baya sannan yace "me zata ce kuwa, wallahi in ba dole ba bazan koma Gombe ba, na tsani mutumin nan iya tsana, banson inje in sake samun wani tashin hankalin" ya ja tsaki had'e da cewa "ai zamu tsaya Kano sai jibi mu isa dan bazan iya zaman mota tun daga Lagos har Gombe babu hutu ba". Usama yace "duk yanda kace, nidai fatana Allah yasa mu isa lafiya kuma Allah ya d'aura mu akan Baba" Jabir bai tanka sa ba sai ma tsakin da ya ja.

Washe gari tun asuba suka d'au hanya cikin Motar Jabir 406, Usama ke tuk'i Jabir na zaune gefensa, tun suna tafiya basu hira har suka sake suna kwasar dariya, sun cire wannan fargabar da suka kwana dashi. Dama suna da d'an guntun snacks da juice cikin mota hakan yasa basu tsaya ko ina ba sai birnin Kano. 

Kai tsaye gidan abokin Jabir suka isa dan kuwa yace lallai-lallai gunsa zasu kwana dan tun da ya gama gininsa bai zo ganin gida ba. An karb'esu cike da mutunci da k'aunar juna, abinci da abin sha kam sun ci sun sha sunyi mak'il suka ture saura gefe, sun sha hira kamar ba gobe dan sai da k'arfe ukun dare suka samu suka runtsa.

Washe gari da asuba suka yi sallama da mutanen gidan suka kama hanyar Gombe, yau kam babu sauran hira dan tun da suka bar garin Kano Usama ke kallon titi dan ba shi ke tuk'i ba, zuciyarsu dukan uku-uku take dan fargaban abunda zasu tarar a wannan gidan. Sun sha k'ira daga mutanen gida tun ba Maryam da hak'oranta suka kasa rufuwa ba, minti-minti zata k'ira tana tambayar "kuna ina yanzu?" Tun suna d'auka su amsa ta har suka shareta.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 20


Da misalin k'arfe uku na rana suka isa, kai tsaye hanyar gida suka bi sai dai suna isa kwanar da zai sa da su da gidan ya ja ya tsaya, buga sitiyarin motar yayi hawaye mai zafi ya zubo masa, bai san lokacin da kuka ya kufce masa mai sauti ba yana mai jin k'unar rai, Usama kallonsa yakeyi cike da mamaki, dan in akwai wanda ya dace yayi kuka bai wuce shi ba amma ya daure ya cije, ya fita ya bar gidan mamanshi na nan, yau ya dawo bata gidan kuma bata duniyar gaba d'aya, ya rasa soyayyar mahaifi tun da jimawa gashi ya rasa na uwa, bayi da gatan da ya wuce Mama, ta zame musu uwa da uba, lokacin da suke zama Lagos suna buga-bugansu babu mai tura musu kud'i sai ita, sai kuma Maryam da ta fara aiki ta taimake su........ 

Muryar Jabir ne ya katse shi "wallahi da ba dan kai da Maryam kun matsa min in zo ba bazan zo gidan nan ba, yanzu ma zuciyata na kwab'a na kada in je, ina tsoron wani abun da Baba zai yi, Usama bazan iya zuwa ba" yana gama fad'an haka ya kunna motar yana k'ok'arin komawa baya, hannunsa Usama ya rik'e yana cewa "lafiyanka kuwa? Calm down Jabir, ya zaka na yin abu kamar ba namiji ba, mun bar k'annenmu mata cikin halin uk'uba na mahaifinmu su kad'ai, kasan irin rayuwar da suke ciki? Mu ne maza, mu yakamata mu kwato musu 'yancin su, mu kad'ai zamu iya daidaita cikin gidan nan wallahi, Baba tsufa ya ke bai dace mu guje su ba, in mukayi haka munyi son kai kuma babu k'auna irin ta d'a da mahaifi tsakaninmu da Baba".

Wani kallo Jabir ya watsa ma Usama da jajayen idanunsa, Usama ya cigaba da cewa " yes nasan zaka ce baka sonshi baka k'aunarsa, amma duk abinda zaiyi maka mahaifinka ne, babu ta yanda za ayi ka cire wannan jinin nasa da ke yawo a jikinka, kasan me ke d'awainiya dakai yanzu? Zuciya da shaid'anin da baya son d'an Adam ya shiga rahamar ubangiji, ka kore sa Jabir, duk lokacin da kaji b'acin rai irin wannan akan mahaifinka ka kore shaid'anin da ke juya zuciyarka, kayi wa Baba addu'a sannan ka fad'a masa gaskiya kamar yanda kake da zuciyar fad'a masa a da, sai dai ba irin yanda kake masa ba, kayi masa cikin lumana da girmama shi, ka masa biyayya dan ka samu rabo, ina mai tabbatar maka bazaka tab'a da na sani ba, lokaci kad'an zaka ga ya wuce, duniyar gaba d'aya nawa take? Hak'uri zakayi ka cinye wannan jarrabawar. Yanzu ka dawo nan ni zan isar damu gida, kana addu'a insha Allah zaka rage wannan zuciyar naka" bai amsa shi ba ya fito ya koma mazaunin Usama, shi kuma ya koma mazaunin driver ya kunna motar yayi gida.

Horn yake dannawa a bakin gate d'in ya kai minti biyar ba'a bud'e ba, Usama da kanshi ya sauk'a ya bud'e ya koma motar dan ya shigo ciki. Yasa hancin motar kenan mai gadin ya fito daga bayan gida da buta a hannunsa yana cewa "ya zaka shigowa mutane gida haka kawai malam" bai tanka sa ba ya shiga yayi parking sannan suka bud'e motar suka fito. Masifa yake musu akan su bar gidan dan ba a basu izinin shigowa ba da mamakinsa sai ganin su yayi sunyi hanyar shiga cikin gida. Ai kuwa a tare suka shiga dan ya tsorata dasu, kuma abinda yafi bashi mamaki bai wuce ganin manyan kayan da ke jikinsu ba, hakan ya nuna masa ba mutane ne masu cutarwa ba. 

Da gudu Maryam ta fito da ta ji sallamar su, zuwa tayi ta rungume su dukka a tare tana murna da d'an guntun hawayenta. Haka Muneerat, Momy da sauran yaran gidan suka zo suma suna mai yi musu sannu da dawowa, babu wanda bai rungume su ba cikin iyayen nasu da k'annensu, sai a sannan mai gadi ya basu hak'uri ya gaida su sannan ya fice yana mamakin dama Alh. Na da manyan yara haka bai tab'a ganinsu ba? 

Falon Mama suka shiga dukkansu suna mai cike da farin ciki, an kawo musu abinci sun ci sun sha suna labarin makarantar da suka gama, Momy baki har kunne tana sa albarka, sai da suka nutsu bayan sunyi sallah sannan suka zauna suka fara bada labarin zamansu a Lagos, hankalinsu a kwance suke labarin dan Maryam ta tabbatar musu Baba ya fita sai shida na yamma zai dawo.

Usama ne ke da bakin hira dan Jabir har yanzu zuciyarsa a cushe take, baya tsammanin zai iya jure rashin mutuncin Baba, Allah yayi sa da zuciya da k'watar hak'k'i, haka kawai bazai bi mutum da lallami bayan shi ne da gaskiya ba, anya bazai sake tattara kayansa yayi gaba ba in yaga abun bazai yu ba?shi bazai iya ganin b'acin ran mahaifiyarsu ba, ya gwammace ayi ta azabtar dashi akan a tab'a Mama.

 Tunanin da ke ransa bai barsa yaji zancen Usama ba, cewa yake "ai dama tun farko da shirinmu muka tafi, mun tara kud'i da yawa sannan muka bar nan, muna zuwa can muka fara sana'ar saye da sayarwa, kuma abun da ikon Allah ba jari ne mai yawa ba amma a wata uku muka tara kud'in registration namu, shikenan muka fara zuwa makaranta, har na gama makaranta shago d'aya ne damu, da na samu aiki kuma sai muka sa haya muka watsar da wannan, da salary nah muke biyan kud'in makarantar Usama har ya gama cikin sa'a. Wallahi mama albarkar ku ke ta bin mu shiyasa tun da mukaje bamu samu wani k'alubale ba. Abun dai sai godiyan Allah". 

Sunyi ta hira har maghrib basu sani ba, da yake k'ofa da window a rufe basu ji k'irar sallah ba, suna cikin hira suka ga mutum ya bud'e k'ofar d'akin yana kallonsu d'ai-d'ai fuskarsa kamar yanda suka bari haka suka dawo suka samu wato a murtuk'e babu fara'a. Tsawa ya daka musu sai da suka tsorata, Muneerat da sauran yara suka tashi sum-sum suka bi ta bayansa suka bar d'akin, Maryam, Jabir, Usama, Momy da Mama kawai ke zaune kansu a k'asa kamar marasa gaskiya, k'arasowa yayi d'akin yana cewa "kun mayar min gida kamar gidan mahauta sai shewa akeyi" ya nuna Jabir da Usama kaana yace "wad'an nan kuma wa ya basu izinin shigo min gida? Bance kada wanin ku ya sake tako k'afarsa yazo min gida ba? Ko bakuji gargad'in da nayi ba kwanaki? Ohh! Kun raina ni kenan? Ko uwarku ke d'aure muku kuke abunda kuka ga dama". 

Ya juyo kan Mama ya nuna ta da yatsa yana cewa "Hadiza ki kiyayeni fa, gida na ne wannan ba gidanki ba da zakiyi abunda kikeso, dama nasan ke kike sa su wani abun" Jabir cikin b'acin rai yace "kada ka sa uwata a ciki dan bata san komai akai ba, kayi damu mana tunda mu kana da iko akanmu kuma mu mukayi maka laifi, mun tafi bata tsira ba mun dawo maka ma bata tsira ba...." Usama ya matse k'afarsa ta k'asa dan yayi shiru an kuwa yi sa'a yayi shirun sai dai ba dan ya so ba.

Sauk'ar mari yaji a fuskarsa ko bai d'aga kai dan ya dubi wanda ya maresa ba yasan Baba ne, yawu mai d'aci ya had'iye ba tare da yayi magana ba, zagi Baba yake yana masifa, ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, duk da hak'urin da suke bashi kamar k'ara ingiza shi suke, daga k'arshe cewa yayi su fice masa daga gida tun kafin yayi musu illa. Anan ne Mama ta samu damar magana.

Cewa tayi "ni ban tab'a ganin inda mahaifi ke yiwa d'ansa haka ba, kai da kanka ke korar 'ya'yanka bayan shekaru masu yawa da tafiyarsu daga gidanka? Kai da yakamata ka rungumesu ka rik'esu da kyau dan kada su sake tafiya su barka, su kad'ai kake da a yanzu, babu wanda zaka samu da ya wuce su, tun da sun gane kuren su suka dawo kuma suka ce kayi hak'uri ai yakamata ka d'aga musu k'afa ko dan tarbiyyarsu da Allah ya d'aura maka....." Bata kai ga k'arasawa ba Baba ya dawo kanta yana cewa "ki bi su ke ma, ni dama nasan ke d'in nan kike zuga su, ku fice dukka ku bar min gida" babu tsoro a tare da Mama tace "ka bani shaidar da zai bani damar barin gidanka kaga in ban tafi ba, ina mai tabbatar maka minti biyar bazan k'ara ba"


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 21


Cike da mamaki ya juyo yana kallonta, ba shi kad'ai ba, hatta Momy da sauran yaran da ke d'akin kallon mama suke cike da mamakin furucinta, tabbas Baba ya kai ta mak'ura tunda har ta iya furta masa hakan, Maryam ce ta kasa hak'urin yin shiru tace "Mama" tare da rik'e hannunta tana juyo da ita dan ta k'arewa fuskar Mama kallo, shin da gaske take? Tabbas fuskar Mama yanuna hakan.

Hawaye na zuba daga fuskar Maryam take cewa "saki kike nema mama? Kinsan abun da kike fad'a? Kinsan dai babu kyau ko? Ya zaki bar mu ki tafi Mama? Kiyi tunanin Nasreen in kina ganin ni babba ce zan iya kula da kaina, Aisha ma na buk'atarki mama, kiyi hak'uri ki bar maganar nan" kuka mai sauti Maryam take zubarwa cike da k'unar zuciya da tausayin kansu.

 Mama ce ta sake firgitata da fad'in "k'warai nasan bai dace in nemi saki agun mijina ba, amma a yau ina mai farincikin nema, muddin ya bani takardata wallahi bazan k'ara minti 5 acikin gidan nan ba, na gaji da irin rayuwar da nake gani, dan mutum yayi shiru yana sa ran watarana komai zai canja, akan ya canja sai b'aci yake gaba d'aya, a bashi hak'uri kamar ingiza shi ake ya aikata abunda yafi wanda ya aikata a baya, ina matarka banji dad'i ba, ina uwa banji dad'i ba, yaushe zanji dad'i kenan? Ka manta tsufa yake zuwa maka ba k'uruciya ba? Nidai gaskiya ban tashi naga mahaifina yana haka ba, duk ranar da uban wasu ya d'auki jaka zaiyi tafiya bak'in ciki ake amma banda gidanka, kai yanzu kafi son yanda kake rayuwa kai kad'ai ba tare da 'ya'yanka kusa da kai ba? Baka yadda da kowa ba sai kanka, baka bawa matanka da 'ya'yanka farinciki ba waye zaka bawa? Kai kana ganin hakan gata kake musu? Wallahi da ba dan Allah ya shiryar maka da 'ya'yanka ba zakayi mamakin lalacewar da zasuyi".

Kallon Baba tayi cikin ido sannan ta cigaba da cewa "kaga kud'i, yana sa mutum halaka, ka biya wa d'anka buk'ata ma ya ake k'arewa da tarbiyyarsu bare baka biya ba? wallahi addu'ar mu shi kad'ai ya shiryar da yaran nan ba wai yin ka ba, baka d'auke su matsayin 'ya'yanka ba, kullum bak'in cikin yau daban na gobe daban, shekara talatin da abu nake zaune a gidan nan amma ban tab'a samun farinciki daga gunka ba, in baka tab'a ni ba ka tab'a 'yan uwana ko 'ya'yana".

Hawayen da take hanashi zubowa ya zubo mata ba tare da ta shirya ba, sharewa tayi da bakin d'an kwalin da ke d'aure a kanta sannan ta samu wuri ta zauna, dan kuka ne ke k'ok'arin kubce mata tana hana shi fitowa, zuciyarta na mata zafi, sai ajiyar zuciyar da take sauk'ewa tana sharar kwalla a sannu-sannu. Kowa jikinshi yayi sanyi cikin d'akin, Jabir da Usama ne kawai basuyi k'walla ba sai kuma gwarzon da yake ta huci kamar zaki, da ganin idanunsa kaga ranshi ya mugun b'aci, bai tanka ta ba sai nuna k'ofa da yayi yana kallon Usama da Jabir, a tak'aice dai yana nufin su fice. (Hmm lallai ko wannan shine JARABTARMU, bai saduda ba kenan).

Momy da tun da aka fara maganar bata sa baki ba ta isa wurin Mama tana bata hak'uri, sun d'au minti biyar a tsaye basu bar gidan ba haka zalika basu tanka shi ba, sai muryar mama da take kuka kawai ke tashi a cikin d'akin. Tsawa Baba ya daka musu yana cewa "bance ku bar min gida ba, ku fice min daga gida tun kafin in muku abinda zakuyi da na sani" k'ok'arin neman abu yake a cikin d'akin, hakan ya tabbatar wa Mama bugunsu yake da niyyar yi.

Cike da takaici take cewa "Allah wadai da irin wannan zuciyar, nayi da na sanin zama dakai har muka hayayyafa, muka haifi yara masu hankali da basu san komai ba kake azabtar dasu, ina mai tabbatar maka Allah zai tambayeka, wallahi 'ya'ya amana ne a wurinmu, suna da hak'k'i akanmu haka zalika muna da hak'k'i akansu, ka daina neman fushin ubangiji da hannunka" jan majina tayi sannan ta kai dubanta garesa tace "na rok'e ka da Allah ka dubi yaran nan kada kayi abun da zaka yi da na sani nan gaba, baka san.........." Muryar shi cike da b'acin rai ya tsayar da ita da cewa "Hadiza ki tashi ki bi su, ku fice min daga gida yanzun nan, na sake ki, wallahi na sake ki saki d'aya tunda har ni kika raina kika fara gaya wa magana, abunda baki tab'a yi ba iya shekarun da muka yi da ke, in ma zuga ki akeyi ki je ki k'arata a gidan da na d'auko ki, jahila kawai wacce batasan darajar mijinta ba, ku fice min daga gida".

Tun kafin ya gama maganar sa mama ta mik'e, hijabinta kawai ta d'auka sai purse nata, hanyar waje tayi ba tare da ta sake yiwa kowa magana ba, Jabir da Usama da Maryam suka bi ta a baya, Momy kuwa hak'uri take basa tana cewa bai dace yayi haka ba, nuna ta yayi da yatsa yana cewa "ki bita mana kema in bazaki iya zama dani ba" ai kuwa dama Momy ba daga nan ba wurin masifa, haka sukayi ta ce ce ku ce tsakaninsu, tana cewa nima ka sake ni mana kaga in ban tafi ba, da yaga ta fishi masifa ficewa yayi daga d'akin yayi waje.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 22


Mama ce ke tsaye a bakin k'ofa ko alamar hawaye babu a fuskarta sai ja da idanunta yayi alamar tasha kuka, Maryam da Usama ke bata hak'uri akan kada ta tafi, Jabir dai ya kasa mata magana, hawaye ke sauk'a daga idanunsa yana kallon mahaifiyarsa tare da tuhumar kansa, ya tabbata shine dalilin rabuwar su, da ba dan shi ba har yanzu tana gidan aurenta da dad'i ba dad'i, duk yanda suke tsammanin zasu shawo kan Mama kada ta tafi tak'i yarda, sai ma cewa take "dare yana yi bazan samu mota ba in tara yayi, ku barni in tafi kawai, zan muku addu'a tunda Allah ya had'aku da Jarrabar mahaifi, sai dai duk runtsi Usama da Jabir kada ku bar gidan nan, ko da gutsure naman ku zai na yi kada ku yadda ku fita, babu inda ya fi muku gidansa, shine mutuncinki ba wai gallafiri a titi ba bayan kuna da uba, ku rik'e k'annenku tunda ku ne manya, in sunyi laifi ku gyara musu banda duka, tun ba Jabir da zafin zuciyar nan naka ba, ka daina d'aukan abu da zafi, ku rik'e junanku da amana ku so junanku ku so mahaifinku". 

Babu wanda ya tanka mata akan wannan batu sai magiyar da Maryam take mata tana mata kuka akan kada ta tafi, Jabir ma ya sa baki amma hakan bai gyara komai ba, tarar napep tayi da taga yazo wucewa ta inda suke, haramar shiga take Maryam ta rik'e ta, Jabir kuwa yace da mai napep ya tafi, mama na cewa ya tsaya suna cewa ya tafi, mai napep yaga abun nasu na neman mayar dashi wawa kawai ya tafi ya barsu.

Jabir ne ya yanke shawarar zuwa gidan Uncle Usman dan ya fad'a masa abinda ke faruwa ko zai yi wa mama magana tunda yaga alamar bata da niyyar komawa gidan Baba, yana zuwa kuwa ya samesa yana zaune a falonsa, yayi mamakin ganin Jabir amma bai samu damar tambayarsa yaushe suka dawo kuma ya labari ba dan fad'a masa da yayi akwai matsala. 

Ficewa sukayi tare suka isa gun Mama da ta had'e rai dan sun korar mata mai adaidaita, da taimakon Allah da sa bakin Uncle Usman Mama ta yadda zata kwana gidansa washe gari ta wuce gida, nan ma dak'yar ta kora su Maryam su koma gida dan cewa sukayi su ma gidan uncle Usman zasu kwana.

Ranar babu wanda yayi baccin kirki a gidan, kowa da abun da ke damunsa, Maryam bak'in cikin Baba da sakin da yayi wa mahaifiyarta ke damunta, Jabir da Usama kuma da na sanin dawowarsu gida suke, a ganinsu da ba su dawo ba hakan duk bazata faru ba, Momy kuwa bata ji dad'in wannan sakin ba, muddin Mama ta bar gidan ita ma ta tabbata zamanta yazo k'arshe a cikin gidan. Baba kuwa mamakin Mama yake yana sake juya maganganunta, duk da haka ya kasa barin zuciyar sa ya yarje masa tana da gaskiya, sai ma bak'in ciki da haushinta da yake ji a k'asar zuciyarsa.

Washe gari tun da asuba Mama ta bar gidan Uncle Usman, babu yanda baiyi da ita ba amma tak'i zama, ko wanka batayi ba bare cin abinci ta fito bakin titi neman adaidaita sahu, Uncle Usman ne ya biyota da motarsa, nan ma dak'yar ta yadda ta shiga ya kai ta gida, sauk'e ta kawai yayi ya koma gida dan har lokacin gari bai gama wayewa ba.

Tun tana shiga tayi karo da mahaifiyarta a bakin k'ofa tana ajiye butar da ke hannunta, da alama daga bayi take, cike da mamaki ta tsaya kallon 'yar tata da alamar tambaya a fuskar ta, murmushi ta sakar mata ba tare da tace komai ba ta rik'e hannunta suka shige d'aki. Gaisawa kawai sukayi ta nemi gado dan ta huta, idanunta har zafi suke tsabar baccin da takeji da kukan da ta gama yi jiya da dare, Inna bata hanata ba sai ma zama da tayi akan sallayarta ta janyo casbaha ta cigaba da ja, a ranta kuwa tunanin me ya kawo d'iyarta gida warhaka takeyi.

Can gidan Alh. Muktar kuwa tun k'arfe bakwai kowa ya farka sai yaran da suke bacci kuma ba a tashe su ba, taruwa sukayi a d'akin Mama suna mayar da abunda ya faru jiya, Mufeedat da bata san abunda ya faru ba sai a wannan lokacin, kuka ta saki tana mai Allah wadai da zuciya irin na mahaifinsu, Maryam ma kuka ta fara sabo har Momy sai da tayi kwalla saboda maganganun da yaran ke furtawa yana tab'a zuciyarta. 

Can bayan wasu mintuna Jabir yayi gyarar murya ya fara da cewa "yanzu ba kuka zakuyi ba, mafita kawai muke nema, me shawararku akan wannan? Ni dai a ganina mu bar maganar Mama ta dawo gidan nan, matsalata bai wuce ya zamu shawo kan baba mu saita masa kwakwalwa ya fara tunani kamar kowani uba ba, ya bar wannan halin nasa muji dad'in mahaifi ko da na k'aramin lokaci ne a rayuwar mu, muddin bamu had'e kai muka yanke shawara d'aya ba baza mu tab'a samun biyan buk'ata ba, tabbas Baba mahaifinmu ne kuma bazamu so hak'k'inmu ya kai sa wuta ba, haka zalika zuciyarmu bazata yarda ta yafe masa ba, amma mu taimakesa mu nuna masa gaskiya dan mu tsirar da kanmu da shi kanshi daga wuta, ku fahimce ni mu tafi tare, in har kun aminta zamu had'e kai mu nuna wa Baba gaskiya, ina mai tabbatar muku zan sauk'ar da kai inyi komai dan cimma burinmu".

Usama yace "gaskiya ina tare da kai a wannan batu, kuma na tabbata Maryam ma na tare damu haka zalika Mufeedat, Momy kuma addu'a zata taya mu dashi sai kuma shawara in zata iya bamu wannan gudumawar kenan, dan wannan yak'inmu ne mu kad'ai" gaba d'ayansu sunyi na'am da wannan batu, kowa ya share hawayensa suna mai farincikin wannan shawara da Jabir ya yanke musu.

Mufeedat tace "to kowa ya aminta da wannan ai ba nan matsalar take ba, ya zamu shawo kan lamarin? Meh zamuyi? Kunsan Baba duk inda kuke tunani ya wuce nan, sai mun fara zaku ga ya dakatar da mu da wani abun al'ajabin kuma" Maryam tayi murmushi tace "ai dai duk abinda Baba zaiyi bai fi k'arfin ayar Allah da hadisi ba ko? Kawai abunda zamuyi mai wahalar anan shine "Hak'uri" indai mukayi wannan toh da sannu zamu cimma burinmu, ina mai tabbatar muku ideas ne zasuyi ta zuwa mana da yardar Allah, dan Allah yaga zuciyar mu da niyyar mu".


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 23


A b'angaren Mama kuwa bata b'oyewa mahaifiyarta komai ba, tun daga tafiyarsu Jabir, dalilin tafiyar su har zuwa dawowarsu yau da abunda ya faru har ya kai ga sakin da Baba ya mata, hannu ta d'aura akan kafad'ar Mama tana murmushi had'e da cewa "tabbas ke 'yata ce kuma nasan tarbiyyar da na miki mai kyau ce, Alhamdulillah... Tun da nake da ke baki tab'a kawo min k'arar mijinki ba duk da kuwa nasan kina cikin matsala, na sha jin k'orafi a wurin Maryam amma ban tab'a tunkararki dashi ba dan sirrin ki ne tunda har kika b'oye kika ajiye shi a gidanki kuma kike iya k'ok'arinki dan gyara matsalar amma Allah bai yi ba" hannunta da ke kan kafad'ar 'yarta ta juyo da fuskarta dan Mama ta fuskance ta da kyau, murmushin da ke fuskarta bai d'auke ba sai ma k'ara washe bakin da takeyi, sai da ta share hawayen da ke zuba daga fuskar Mama sannan tace "dariya ya kamata kiyi, kiyi farinciki Kubra(sunan da take k'iran Mama dashi kenan) tunda har kika samu yara nagartattu masu bin umarninki masu sonki, dan ya sake ki sai meh? Iyaka kiyi masa addu'a kuma ki d'aura yaranki hanya mai kyau dan su tsirar da mahaifinsu, in har Allah yayi mai rabo ne zaki ga ya canja in kuma ba mai rabo bane hak'uri zakuyi dukka sai kuma yafiya da zaku yi masa, in suka yafe masa Allah ma zai yafe masa, ki daina kuka kina wahalar da kanki akansa. Ki zauna ki gama idda, Allah ya kawo miki alkhairinsa". 

Sai da tayi mata nasiha had'e da shawarwari sannan Mama ta dawo da walwalarta, matsalarta d'aya yanzu ya zatayi ta bawa 'ya'yanta gudumawa akan mahaifinsu bayan basu tare? Addu'a kad'ai zata iya yi tare da fatan alkhairi.

Da misalin k'arfe goma na safe Baba ya fito cikin shirinsa na manyan kaya da hularsa a hannu yana lank'wasawa, a bakin k'ofarsa ya tsaya ya k'walawa Momy dake d'akinta k'ira, sai da ya k'irata sau biyu sannan ta jiyo sa ta amsa, bata wani b'ata lokaci ba ta fito ta iskesa tsugune yana duba takalminsa, tsaki yaja yana cewa "wannan takalmin kin goge kenan? Duk k'ura a hakan zan fita mutane su raina ni? Ke d'in nan zakiyi abu mai kyau kuwa?"

 Momy da ta daidaita tsayuwarta tana kallonsa sai da ya gama ya dasa aya sannan ta d'auko wani bak'in takalmi da ya ture gefe ta fara cewa "wannan na nuna maka kace min eh shi zaka sa na goge maka, kuma ai kasan ko wani sati muke goge maka takalma, gobe ne zai cika sati dan satin da ya wuce Mama ce tayi, kuma fisabilillahi ina k'ura a wannan takalmin?" Ta fad'i hakan tana goga yatsarta akan takalmin da yake cewa akwai k'ura had'e da nuna masa yatsar nata. 

Kallonta yayi yana cewa "k'arya zan miki kenan? Abu duk datti kina gani kina sake ce min babu datti. Ina da idanu kamar na kowa, ko dan kinga ina da glass zaki d'auka bana gani sosai?" Ya karb'i takalmin da ta goge d'in ya mayar dashi jerin takalmarsa da ke bakin k'ofarsa sannan ya janyo tsumman da suke goge takalmin ya mik'a mata yace "goge min, wannan nakeso na fasa sa wancan, in bazaki goge ba ina da hannu kuma ina da yara" murmushin takaici tayi ta karb'a ta goge masa sannan ya sa kai ya fice, addu'ar da take masa ma ko amsawa baiyi ba ya fice daga gidan. 

Ajiyar zuciya tayi tana mai nema masa shiriya, dan abun nasa ko tsoho albarka, kullum sai ya samu abun masifa hankalinsa ke kwanciya. Sai da ta goge sauran takalman ta kad'e k'urar sannan ta bar wurin zuciyarta na mata ba dad'i, dan ma yau ya sameta a sanyinta dan maganar da sukayi da yaran ya kashe mata jiki, da ko yau zasuyi masifa dan ita bata d'aukan irin abun da yakeyi.

A garage suka had'u da Jabir da Usama sanye da k'ananan kaya, suna ganinsa kuwa suka tashi daga kujerar robar da ke wurin suna mai sake wa mahaifinsu murmushi kafin ya iso inda suke, Baba kuwa yana ganinsu ya d'auke kai kamar bai ga mutane ba, gaishe shi suka yi suna mai russunawa alamar girmamawa, ta gefe Baba ya kallesu sannan ya juya yana neman driver kamar bai ji gaisuwar ba, yayi mamakin rashin ganinsa a wurin kamar yanda ya saba. Kuma gashi inda zaije wuri ne mai muhimmanci dangane da business nasa. 

Muryar Jabir yaji yana cewa "Baba mu je ni in kai ka ko Usama, ni na cewa driver ya tafi tunda mun dawo zamu na kai ka ko ma ina ne kafin mu fara aiki. In yaso ko hutun sati biyu ne in yayi sai ya dawo" kallon da Baba ya watsa masa yasa shi shan jinin jikinsa, amma duk da haka baiyi da na sanin yin hakan ba dan yana ganin zaman su wuri d'aya zai basu damar janyo ra'ayinsa har ya yafe musu sannan ya fahimci abinda yakeyi baya kyautawa. 

"Ni nace ka bawa driver hutu? Dan ka dawo wa ya baka izinin shiga sabgar gidana? Ka nace sai ka zauna a gidana na barka wallahi kada ka shiga abinda bai shafeka ba" yana isowa nan a maganarsa ya matso daf dashi ya mik'a hannunsa yana cewa "bani makulli na" Jabir yace "kayi hak'uri Baba, babu wani farinciki da zamu samu a duniya balle a lahira in kana fushi damu, ka bamu dama mu wanke laifin mu, ka bari mu kyautata maka ko zamu samu sassaucin rayuwa" agogon hannunsa Baba ya duba sannan ya bud'e k'ofar gefen driver ya shige, da murmushi fuskar Jabir ya tab'o Usama yana masa nuni da yaje ya kaisa, Usama duk da zuciyarsa na tsinkewa bai hana fuskarsa nuna jin dad'i ba, ya shige motar yana mai tada wa dan barin harabar gidan. 

Baba kuwa har cikin ranshi bai so ba, dan kawai yayi latti kuma baya son maganar da zai karya mishi zuciya yasa ya shiga motar. Ba tare da ya kallesa ba ya fada masa inda zai kai sa yana mai d'auke kai kamar ba shi yayi maganar ba. Usama kuwa kunna radio yayi tare da sa wani cassette na wa'azi da Jabir ya sayo yau da safe na Sheikh Ja'afar Mahmud Adam mai taken "Hak'k'in 'ya'ya akan iyayensu da Hak'k'in iyaye akan 'ya'yansu".


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 24


Har suka isa babu wanda yayi magana cikin motar sai wannan wa'azin, dan ma inda suka je akwai nisa hakan yasa wa'azin ya d'an yi nisa ya hau zafi. Parking kawai yayi Baba ya sauk'a tun kafin Usama ya kashe motar, a gurguje ya kashe ya kulle motar ya bi shi a baya, dan ya d'au alwashin a cikin sati biyun nan zai sa kansa tsundum cikin harkokin Baba ya gane dan ya hutar dashi tunda girma ya fara zuwa masa kuma fannin da ya karanta kenan wato "kasuwanci" tare suka shiga inda aka tanadar musu dan tattaunawa, sai da d'aya daga cikinsu ya tambayi Baba "dama kana da d'a babba haka baka tab'a nuna masa hanyar kasuwancin mu ba? Ni da ina da yaro kamar wannan ai da yanzu ina gida ina kwance." 

Dariya dukka sukayi harda Baba da ya kai dubansa kan Usama dan tambayan da yazo ransa "taya akayi suka gane d'ana ne?" kamannin da sukeyi ya hasko sannan ya d'auke kai suka cigaba da tattaunawa game da kayan su da aka rik'e a border.

Sun gama tattaunawar cikin sa'a tare da yanke abunda zasuyi guda d'aya wanda shi Baba ne zai je har Abuja kan maganar. Tafiyar zai kama sati mai zuwa ranar asabar, daga shi sai d'aya daga cikin abokanan sana'ar tasu wanda yake da k'aramin shekaru, sai kuma Usama da suka yanke shawarar zaiyi rakiya dan shawarar da ya bayar game da tattaunawar, farko Baba yace a'a amma da yake mutanen wurin sun kula da yanayin kamun kan Usama suka nace dole dashi za ayi tafiyar sabida shi ma ya samu experience ( dan ma basu san abinda ya karanta ba) Murmushi kawai Usama yayi had'e da godiya sannan suka fice daga wurin dan komawa gida. 

A dawowa ma wa'azin nan dai aka cigaba da ji daga inda aka tsaya, hak'ok'in iyaye dama aka fara sannan aka gangaro kan hak'k'ok'in 'ya'ya, tun da aka fara bayanin wannan Usama ya daina gudu, dan yana son ko bai gama ji a yau ba ayi rabi, gobe a k'arasa sannan a sa wani. Haka yayi ta yawo dashi cikin garin nan da sunan hanya babu kyau har suka isa gida, duk da hakan dai wa'azin bai k'are ba.

Shigowa gidan kawai yayi ya wuce d'akinsa fuskar nan a had'e tamau kamar an masa wani abun, ta window Maryam da Muneerat suka hango shigowarsa, sai da ta sauk'e ajiyar zuciya sannan tace "saura namu aikin Muneerat, lets go" ware idanu Muneerat tayi tana kallon Maryam, da mamaki Maryam take kallonta da alamar tambaya, irin menene? Muneerat tace "a hakan zamu je? Kin ga yanda ya had'e rai? Muna zuwa ai kashin mu ya bushe, in bai wawwanke mu da mari ba ma in zama k'arago, ki bari mu d'an k'ara lokaci kafin nan ya huce".

Maryam tayi tsaki ba tare da ta amsa ba, janyo tray na abincin tayi sannan tayi hanyar waje, bata kalli Muneerat ba bare tace ta d'auko tray na ruwan, babu yanda ta iya ta sungumi tray din ta bi Maryam a baya. Bugun zuciyarsu ya tsananta a lokacin da suka doso k'ofar, addu'ar da Maryam ta kama yi a fili Muneerat ta kama, sai da suka iso daf k'ofar sannan suka kalli juna cike da tsoro da fargaba.

Numfashi Maryam ta sauk'e sannan ta k'ak'alo murmushi a fuskarta tayi Sallama had'e da murd'a mabud'in k'ofar bayan ta rik'e tray da hannunta d'aya ta manneshi da tumbinta dan kada ya fad'i, ta d'an tura k'ofar kad'an ta yanda in ya amsa sallamar zata ji, rashin amsa sallamar ya sata doka wani sallaman da muryar da yafi na d'azu. Can k'asa taji ya amsa, sai da ta kalli Muneerat da tayi tsuru-tsuru tana cewa Allah yasa kada ya amsa a ranta, sannan ta tura k'ofar ta sa kai bayan ta daidaita tray a hannunta murmushi fal fuskarta kamar da gaske.

Baba da yake zaune kan gadon sa ya d'ago kansa yana kallon abun mamaki, wani sabon salo wai ba matar sa ne suka kawo masa abinci ba, abun ya masa wani iri, har suka ajiye abincin suka samu wuri suka zauna kusa dashi a k'asa bai d'auke idonsa daga kansu ba, sai da Maryam ta gaida shi sannan Muneerat ma ta bi da nata gaisuwar. 

Can ciki ya amsa yana d'auke kai tare da kawar da tunanin da ke ransa, Maryam ta d'auko plate da ke kan tray d'in dan ta zuba masa yace "ina Momy?" Zuciyar su ya buga a tare, sai da ta tattara nutsuwarta sannan ta iya bada amsa "eh mu muka ce da Momy zamu kawo maka abinci...." Bai bari ta gama ba ya dakatar da ita da cewa "ce miki nayi ina Momy? Kina bani amsa daban" Muneerat tayi caraf ta amsa da "tana d'aki". Bai sake magana ba har ta zuba abincin a plate ta mik'a masa, karb'a yayi yana mai kallonsu cikin ido, jira yake yaji da meh suka zo.

Kallon da yake jefa musu ya sa suka daburce suka kasa aiwatar da abinda suka yi niyya, so suke ko ta yaya su saba da mahaifinsu shima ya saba dasu, wata'kila hakan zai sa ya daina sauran abun nasa. So suke ahankali ko da zai na yab'a musu magana suna d'an hira, ta hirar nasu zasu nuna masa abinda yakeyi ba kyau, babu fahimtar juna babu sakin fuska bare sabo ta yaya zasu nuna masa kuskuren abinda yakeyi? Hakan da wuya inji Maryamerh.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 25


Har ya gama cin abinci basu yi k'wak'k'waran motsi ba bare suyi magana, haka suka tattara kayan abincin sukayi gaba cike da jin haushin kansu. "Duk ke kika sa muka kasa yin komai" maganar Maryam ya sa Muneerat tsayawa had'e da juyowa dan kallon yayarta, ta cigaba da cewa "next time ni d'aya zanzo, da baki nuna min bazaki iya ba da zan iya magana" bata tsaya taji meh Muneera zata ce ba tabi gefenta ta wuce da tray nata a hannunta, Muneera kasa magana tayi ta tsaya kallon Maryam, daga bisani ta tab'e baki tasan duk haushin Baba ne takeson hucewa kanta, hakan yasa tayi shiru bata tanka ba ta bi ta a baya.

"Muneera" tun daga bakin k'ofa Usama ke k'wala mata k'ira, har ya iso cikin gida bata amsa ba, hakan ya sake tunzura shi ya had'e rai, cikin sauri yayi hanyar d'akinta, babu abinda yafi tsana irin a ajiye shi zaman jira, tun d'azu yake jiransu zasu fita gun Mama har k'arfe 4 ya wuce basu fito ba, cak suka ci karo da Maryam, "haba dan Allah" yace cikin sanyin murya "kinsan ba abinda na tsana irin a ajiyeni ina jira" murmushi tayi sannan tace "kamar nasan fad'an da zakayi kenan shiyasa na hanata amsawa, ba laifinta bane ni ce ban gama abinda nakeyi ba na sa ta jirani, da ita ta fito nasan fad'a zakuyi kamar ba yayarka ba, ita ba za ta yi hak'uri ba kai kuma ba za ka bata girmanta ba". 

Ba yabo ba fallasa ya amsa da "yanzu ina take? Dan Allah ku fito mu tafi dan mu dawo da wuri, yanzu zaki fara kawo min k'abli da ba'adi salon yara su ji ta girmeni su raina ni, dama tun asali ba shiri muke ba kin sani" bai ji ta cewan ta ba ya fice da hanzari. Basu k'ara minti biyu ba suka fito cikin atamfarsu iri d'aya sai banbancin kala, Maryam nata red mai zanen flower green ta yafa mayafi green, Muneera kuma blue da zanen flower yellow ta yafa mayafi yellow. 

Basuyi minti sha-biyar ba suka iso gidan kakar tasu, Jabir suka samu a tsakiyar gidan zaune akan tabarma ya shantake yana hira da kakar tasa sai dariya yake, yana hango Usama yace "yauwa kaka gashi nan ma, munyi laifi tare amma ana min fad'an ni kad'ai wai in kai maka sak'o, kaga gwanda da kuka zo yanzu dan sauran fad'an nata kwakwalwata bazata d'auka ba" bugu ta kai masa tana dariya sannan ta kai dubanta gare su. Muneera da ta zauna a gefenta ta kamo bayan ta had'e rai tana cewa "sai yau kika san gidana dan mamanku ta dawo?" Muneera tace "makaranta ne wallahi Kaka, muna project har yanzu bamu gama ba, kuma kinga last month muka gama final exams amma har yau bamu gama project ba. Yi hak'uri ina gamawa nan zanzo in miki sati". Kallonta tayi da kyau dan tasan fad'a kawai Muneera take, gaisuwar Maryam kaka ta amsa tana mai kai dubanta gare ta tare da mik'a mata hannu suka yi musafaha sannan ta amsa na Jabir ta cigaba daga inda ta tsaya. Sosai ta musu fad'a akan tafiyarsu dan baiyi anfani ba, sanadin su Mama ta bar gidan aurenta, amma tunda ya faru a d'auke sa matsayin k'addara a fuskanci gaba kamar yanda Kaka tace.

Wayar Maryam da ke ta ruri cikin purse nata ta d'auko ta duba mai k'iranta sannan ta shige d'aki dan magana dashi, tun jiya Mustapha ke k'iranta bata samu damar d'auka ba dan tashin hankalin da take ciki kuma yau ma bata samu ta k'ira sa ba, sai da ta d'auka ta kai wayar kunnenta sannan tace "Assalamu alaikum ranka ya dad'e, ayi min afuwa nasan nayi laifi" har d'an rusunawa tayi kamar yana kallonta sannan ta fad'i hakan. 

Sauk'ar da ajiyar zuciya yayi har k'arar taji sannan yace "indai ba laifi nayi ba aka min wannan horor gaskiya ban hak'ura ba sai an bani hujja mai k'arfi ma kuwa". Ta bud'e baki zatayi magana kenan Mama ta fito daga bedroom, hakan yasa ta sauk'ar da wayar daga kunnenta tana mai murmusawa had'e da fad'in "ina wuni Mama" mama cike da murnar ganinta ta amsa gaisuwar sannan tace "ki gama wayar, ina waje wurin su Usama in kin gama" Maryam ta amsa da "toh". Sai da Mama ta wuce sannan ta mayar da wayar kunnenta tana cewa "sorry" ya amsa da "ba komai, ina kika je haka? Mama bata gida ne? Naji kince ina wuni mama? Ba ma wannan ba, haka mata ke fita ba tare da neman izini wurin mijinta ba?".

Dariya tayi sannan tace "zamuyi magana anjima idan na koma gida, ayi min uzuri, insha Allah mijina bazaiyi fushi dani ba in na fada masa uzurina" Mustapha yace "anyi miki uzuri uwargidata, take your time. I love you and take care of yourself for your king". Ta amsa da "i will sir, you too" sannan ta katse wayar.

Ta same su suna hira cike da nishad'i, samun wuri tayi gefen mama ta zauna ta rik'e hannunta sannan aka cigaba da hira, Kaka dai yau tayi musu nasiha sosai game da rayuwa sannan mama ta d'aura da nata, Maryam da Mufeeda sarakan kuka sai da sukayi hawaye sannan suka bar gidan da misalin k'arfe biyar da minti hamsin.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 26


Parking d'in da Usama yayi a parking space yayi daidai da kwala k'iran sallar da Ladani yayi a cikin loudspeaker, da yake masallacin na kusa da gidansu sai ya zama kamar a cikin gidan ake k'iran sallah, da gudu-gudu Jabir ya fito daga motar dan ya biyosu kasancewar dama adaidaita ya bi yaje gidan kakar tasu. Wurin famfon da ke harabar gidan ya isa ya kunna ya fara alwala ba tare da ya d'auko buta dan tarar ruwan ba. Usama bayan ya kulle motar Maryam da Muneera sukayi hanyar gida shi kuma ya isa wurin famfon dan yayi alwala su je masallaci.

Fitowar Baba yayi daidai da gama alwalar Jabir kuma yayi daidai da isowar Maryam da Muneera bakin k'ofar da zai sada su cikin gida, a tsorace suka koma baya suka bashi hanya kansu a k'asa, kallonsu yakeyi d'ai-d'ai cike da b'acin rai sannan ya kai dubansa ga Jabir da yake sauri sakamakon jin kabbarar harama da akayi a masallaci. Tsawa ya daka masa "dawo nan" ya k'ara da cewa "duk kuzo nan marasa hankali" bayan ya kalli Usama.

Jabir bai k'ara ko da taku d'aya ba ya dawo haka Usama ya iso, fad'an dawowarsu warhaka yakeyi tare da tuhumar su inda suka je, nuna Jabir da Usama yayi yana cewa "kun dawo zaku koya wa yarana yawo ko? Kafin ku zo basu tab'a kai war haka a waje ba, in kun saba yawo a can inda kukaje toh ni baza ku min a gidana ba, ku tafi can inda kuka saba ku cigaba da yi" ya dawo da dubansa wurin Maryam da Mufeeda "ko halin uwar taku da ta tafi ta barku kuke son d'aukowa? Toh bazan d'auka ba" ta inda yake shiga ba ta nan yake fita ba, sai da yaji anyi kabbarar tashi daga sujjada wato anyi raka'a d'aya an shiga ta biyu sannan ya fice sai huci yake suna binshi a baya dan zuwa masallaci, Muneera da Maryam kuma suka shige gida.

Dawowarsu ya cigaba daga inda ya tsaya, a cikin tsakiyar gida ya ajiyesu sai masifa yakeyi suna bashi hak'uri, matsalar shi kuma kada a bari ya fara masifa, yana fara fad'a ranshi ke k'ara b'aci kuma masifar tayi gaba kenan, sai yayi har ya wuce daidai laifin da akayi sannan ya hak'ura, laifin da tun kana k'arami kayi toh ranar da ya fara maka fad'a tas zai kwafo ya zuba maka ya k'ara b'ata komai. Babu wanda ya tanka sa kamar yanda yayi tsammanin Jabir mai tankawa ne ya samu damar korarsu daga gidan, banda hak'uri ba abinda suke bashi, Jabir sarkin zuciya ya danne zuciyarsa ya bada hak'uri, sai da Baba ya gaji dan kansa sannan ya shige d'aki ganin babu mai mayar masa bare ya samu biyan buk'ata.

Kowa d'akinsa ya wuce ransu ba dai-dai ba, kwanciya Maryam tayi tana kallon ceiling ranta a dagule, fad'an sa dan sun dad'e a waje dai-dai ne, amma abun bai kai ga zagi ba, bai kai ga zagin tarbiyyar su ba bare kawo maganar halin uwar su da shi kansa yasan ta basu tarbiyya daidai gwargwado, tunda suke da Mama bata tab'a ganin ta fita ba tare da izinin Baba ba, amma yau gashi yana zaginta dan kawai ta fad'a masa gaskiya, hawayen idanunta ya sauk'o ta gefen fuskarta, bata hana ruwar hawayen zubowa ba sai ma tunano abinda zai k'ara sata kukan takeyi ko zata ji sauk'in rad'ad'in da zuciyarta yakeyi in ta samu kuka mai tsawo.

Har sai da aka k'ira sallar isha'i ta tashi, bayan ta idar ta sake kwanciya tana mai janyo bargo dan sanyin da ke ratsa ta, wayarta da ta ajiye bisa kujerar d'akin taji ya fara ringing, tunowa da tayi sunyi zata k'ira Mustapha ya sa ta hanzarin tashi tana dafe kanta da yake barazanar fad'ar da ita dan jirin da taji na kwasarta. D'aukan wayar tayi tana mai duba wanda ke k'iranta, sai da ta murmusa sannan ta kai wayar kunnenta tana cewa "laifi kan laifi, a dai yi min afuwa ka riga ni k'ira" cewa yayi "ya na iya da matar tawa da take wahalar min da zuciya, zan dai ga ranar da zaki zama tawa gaba d'aya inga ko zaki cigaba da gasa min gyad'a a hannu".

Sai da ta koma kan gadonta sannan ta amsa da cewa "yanzun ma ba da son raina nake shareka ba, in mukayi aure kam sweetness d'in da zaka samu sai ya maka yawa, sai ka fara tunanin anya Maryam bata fi sona ba kuwa?" Bai san lokacin da dariya ta sub'uce masa ba, dariya ita ma ta tayashi sannan ya katse ta da cewa "kema dai kinsan tunanin da bazanyi ba kenan, dan ke kanki shaida ce nafi sonki" tace "a'a nafi sonka" musu suka fara yi kamar yanda suka saba sannan ya dakatar da muhawarar da cewa "naji, ban yadda ba amma a bar maganar a haka, ina jinki sweery, is like my baby has something in mind da ke damunta, don't ask me ta yaya na gane, kawai ki fad'a min, am all ears".

Dariya tayi tana cewa "ni ko meh ke damuna? Fad'a min tunda kasan akwai abu? Naga alamar kai mai gani ne har hanji" ta k'arasa da sigar zolaya "hmmm! Maryam kenan. Naga alamar baki d'auke ni yanda na d'auke ki ba, mace ce ke, kina buk'atar wanda zai na kula da damuwarki, wanda zaki fad'awa matsalarki ya baki shawara ta gari, ko da yake nasan Mama ta zame miki sister kuma friend, duk ta maye miki wannan gurbin" ya fad'i hakan da sigar tsokana shima.

Shirun da tayi ya tabbatar masa da hasashen da yakeyi akan akwai abinda ke damunta gaskiya ne, sai da ya sauk'e ajiyar zuciya sannan yace "Maryam speak up, ki fad'i damuwarki a inda za a kwantar miki da hankali, bazakiyi da na sanin sanar dani ba" b'angaren Maryam kuma hawaye ke malala daga idanunta tunowa da tayi yanzu ita kad'ai ce, Mama bata tare da ita bare ta kai mata kukanta a lokacin da take buk'atar hakan, a zuciyar ta take sak'a da warwara akan sanar dashi damuwarta amma inaaa wani sashe na zuciyarta na tunasar da ita fallasar da zatayi wa mahaifinta da ake gani da mutunci a cikin garin Gombe, duk runtsi duk wahala bazata tona asirin gidan su ga saurayi ba, tunowa tayi da Maganar k'awarta Muslima "ba ko wani namiji zaki fad'a wa damuwarki akan gidanku ba, infact zan iya cewa bai dace ba, dan fallasa ne, kuma zai iya janyo raini tsakaninsa da 'yan gidanku, ko mijinki akwai abinda bazaki so ya sani ba akan iyayenki saboda ki guje musu raini bare saurayin da wata'kila ma ba auren za'ayi ba". 

Muryarshi ya katseta da cewa "kinyi shiru? Shirunki na tabbatar min ba lafiya ba" sai da tayi gyarar murya sannan tace "no, kaina ke ciwo, muyi magana gobe, yanzun kaina sosai yake ciwo" shiru dukka sukayi na d'an lokaci sannan ta k'ara da cewa "and about akwai abinda ke damuna ko wani abu related to haka da kake tunani hasashenka ne kawai, lafiyana k'alau, bani da wata damuwa yanzu sai godiyar Allah kuma nagode da kulawarka" basu k'ara wata magana mai tsawo ba bayan wannan sukayi sallama.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 27


Washegari da safe ya kama ranar Monday da misalin k'arfe 9, Maryam ce ta had'a breakfast na Baba akan tray ta kai masa d'akinsa, ta samesa tsaye yana kallon kansa a jikin mirror da ke mak'ale da murfin wardrobe nasa yana sa bottles na rigarsa, ta madubin ya kalleta ya d'auke kai, murmushi tayi sannan ta ajiye tray d'in ta zauna tana cewa "Baba ina kwana" "lafiya" yace a tak'aice bai sake kallonta ba sai ma bud'e wardrobe d'in da yayi, agogonsa ya d'auko yana k'ok'arin sakawa tayi k'arfin halin tashi ta matso gunsa "Baba barin sa maka" kamar tasan kallon da zai mata yasa ta duk'ar da kai ko kallon fuskarsa batayi ba bare ya tsorata ta.

Hannunta ta kai zata karb'i agogon taji yace "yaushe kika fara sa min agogo?" Hakan da ya fad'a bai hanata karb'ar agogon daga hannunsa ba tare da k'ok'arin saka masa, wani tsawa ya daka mata wanda ya razana ta sai da ta girgiza tana komawa baya, kallonsa tayi tana mai cewa a ranta "wannan wani irin mutum ne?" Muryarsa taji yana cewa "ki bar nan nace".

Bata saurareshi ba, yi ta yi kamar bata ji shi ba, matsowa ta sakeyi daf dashi tana sak'ala masa agogon, bayan ta saka masa ta d'auko turare ta fesa masa sannan ta sauk'e murmushi tana cewa "Baba kayi kyau, wannan kwalliyar ko anty zaka kawo......" Shiru tayi tana tauna maganar da tayi niyyar fad'a, ta tabbata in ta fad'a mari zata sha, kallonsa tayi shi kuwa kallon mamaki yake binta dashi.

Murmushi ta sake yi tace "Baba kayi hak'uri kada ka d'auka raini nayi maka, gani nayi rayuwar duniyar gaba d'aya kad'an ne, busa kawai muke jira mu mace, Mala'ikar da aka tanadar dan yin busa umarni kawai yake jira, in ma ba ayi busar ba lokaci ba a hannunmu yake ba, ko yau ko gobe ko jibi Allahu a'alam, so nake in samo aljannata, atleast ko ba komai in samu wani lokacin da na tab'a spending da mahaifina mai dad'i" hannu ya d'aga mata alamar tayi shiru sannan ya bi gefenta ya wuce, fuskar sa dai bai nuna dad'i ko akasin haka ba.

Juyowa tayi tana mai isa wurin tray na abincin dan zuba masa, shi ma Baba zama yayi a bakin gadonsa yana duba takaddunsa da ke ajiye akan bedside drawer, tana kan zuba abincin taji yace "da mijinki kike yiwa wannan bautar da kin samu lada, ni bana buk'ata" kallonsa tayi da serving spoon a hannunta wanda dashi take zuba masa farfesun kazar da Momy tayi, mamaki ne fal a fuskarta tana kallonsa kamar ba shi yayi wannan maganar ba, ajiyar zuciya ta sauk'e tana mai dawo da murmushin da ya b'ace daga fuskarta, sai da ta gama zuba masa komai ta mik'a sannan ta zauna tana mai fuskantar sa had'e da tsara maganar da zata masa akan auren da ya ambata.

"Aure ai lokaci ne, kuma bana fatan inyi aure ban samu lokacin mahaifi na ba, ma'ana ban samu beautiful moments da nake dreaming ba, nafi son ina kwance wataran in tuna dariyar da mahaifina yayi min dan na masa abu da ya sashi farinciki ko kuma shi d'in ma da kanshi ya sani dariya, alal ak'alla ko hira mai tsawo ko ya bani labarin kasuwancinsa ni kuma in bashi labarin makaranta na ko kuma wurin aikina" ta k'arasa maganar tana mai kallon fuskarsa. Bai yi alamar zai amsa ta ba sai cin abincinsa yakeyi.

Bayan ya gama ta kwashe kayan abincin zata fita yace mata "banson kina kawo min abinci daga yau, ki bari Momy tana kawo min, na hutar da ke, sannan wannan wandunan da kike sawa sai ki sa hijabi akai in kin fita ki cire d'in wallahi kada in sake ganinki dashi, dan kin girma baki fi k'arfin duka ba a wurina" batayi mamaki ba dan yace tana sa wando ta sa hijabi in ta fita ta cire dan ya saba zagin kayan ta da kayan karuwai, dawowa tayi ta zauna tana fuskantarsa "insha Allah bazan sake sa wando da hijabi in fita ba, nagode sosai da ka nuna min baka so, amma maganar kawo maka abinci kayi hak'uri in cigaba da kawo maka" hannu ya d'aga mata yana cewa "na yafe, bana buk'ata".

Sauk'ar hawaye kawai taji a fuskarta, ji tayi zuciyarta na mata k'una, idanunta suka kasa sauk'a daga kallon baban nata da hankalinsa ma bai gunta, bata goge hawayen ba tace "Meh yasa baka so? Saboda baka sona, ko saboda bana maka biyayya matsayin 'yar ka shiyasa baka son in kyautata maka" ta fad'i hakan ne cikin muryar kuka hakan ya jawo hankalin Baba wurinta yana kallonta. Hawayen da ya gani a fuskarta ya sa zuciyarsa karyewa, d'auke kai yayi dan baya son karaya, baya son a nuna masa baya yi daidai, baya son raini haka zalika bai son sabawa da yaransa saboda kud'in da zasu na nema agunsa, wani lokacin yana kallonsu zuciyarsa zata rad'a masa kud'i suka zo nema shiyasa yake had'a rai tamau da zarar ya gansu. 

Tsaki ya ja ya tashi ya sa babban rigarsa ya d'auki abubuwan da zai d'auka ya fice daga d'akin, sai da yaje bakin k'ofa yace "ki fito in rufe k'ofana" tray d'in kawai ta d'auka ta wuce kitchen ba tare da ta sake kallonsa bare yi masa magana ba. Sai da tayi kukanta a k'uryar d'aki sosai sannan ta canja kayanta tayi shirin tafiya office.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 28


Ta isa office goma ya d'an gota, da hanzari ta isa cikin office nata sanye da shade bak'i a idanunta dan bata son a gane ta sha kuka saboda idanunta sunyi ja sun d'an kumbura. Bud'e k'ofar kawai tayi ta sa kai ba tare da sa ran ganin kowa a ofishin nata ba, da mamakinta sai ganin Mustapha tayi zaune sanye da k'ananan kaya, long sleeve shirt da blue jeans trouser. Idanunsa kawai ya d'ago ya d'aura kanta hannunsa rik'e da wayarsa, murmushi ya sakar mata had'e da cewa "highly welcome".

Numfashi ta sauk'e sannan ta k'araso ciki bayan ta kawar da bak'in cikin da ta kwaso daga gida. Murmushi ita ma ta sakar masa bayan ta amsa da "Thank you". Sai da ta ajiye jakar laptop nata da purse nata sannan tace "tun yaushe kazo nan? Sorry am late" ta fad'i hakan tana kallonsa bayan ta zauna a mazauninta, wayarsa da ke hannunsa ya ajiye kan table ya gyara kujerar da yake zaune dan ya fuskance ta sannan yace "don't worry, dama nafison in riga ki zuwa saboda inga yanayin ki" numfashi ya ja ya sauk'e sannan ya cigaba "look Maryam tunda bakison fad'a min matsalar ki inason muyi aure as soon as possible saboda in zama kusa dake ina k'arfafa miki gwiwa, tun da na had'u da ke nasan akwai abinda ke ranki wanda yake damunki, na kwana biyun nan kuma har yayi yawa".

Kallonta yakeyi haka ita ma ke kallonsa ta cikin kwalbar da ta mak'ala a idanunta, murmushin fuskarta bai d'auke ba kuma batayi niyyar amsa shi ba, hannunsa ya kai daidai fuskarta zai cire glashin nata tayi baya tana cewa "No please" annurin fuskarta ya d'auke dan ta nuna masa bata son hakan.

Numfashi ya sauk'e ya d'auke dubansa daga gareta yana kallon gefe, daga bisani yace "kinsan dai ba tab'a ki zanyi ba ko? Ki cire tunda bakiso in cire miki, so nake muyi magana, wallahi am serious maganar da ya kawo ni kenan dan mu fahimci juna muyi maganar aurenmu nan kusa, cause na gaji Maryam" ya fad'i hakan yana jingina bayansa jikin kujerar da yake zaune yana kallonta cikin ido. "Amma munyi dakai sai lokacin da nayi niyya zamuyi aure tun kafin mu fara dating? Meh yasa kake kawo maganar yanzu? I don't want to talk about it".

"Maryam why are you punishing me this way? K'arara baki fito kin nuna bakya sona ba amma sai kwana kike min, bakya son aurena, bakya son sharing matsalarki dani, komai baki so kuma baki fad'a min dalili d'aya mai k'arfi ba, ki daina wahalar dani da maganar da zamuyi sa rana d'aya mu gama, just say it MALAM MUSTAPHA BAZAN IYA AURENKA BA DAN BANA SONKA, hankalinki ya kwanta in daina takura miki nima in daina b'ata wa kaina lokaci, duk ba yara bane mu".

Kallonsa kawai takeyi dan bata san meh zata ce ba, hawayen da ke yawo cikin idanunta take mayarwa dan bata son ya gane halin da take ciki, so matuk'ar so take yi wa Mustapha wanda ita tasan bata tab'a yi wa wani mahaluk'i a duniya irin ta ba, tun yana magana ranshi a b'ace ya fara yi mata da lallami, hawayen da ya cika idanunta ya sauk'o mata amma dalilin gilashin da take dashi sai bai bari ya fito ta yanda Mustapha zai gani ba, ma'ana gilashin ya tare hawayen.

Kalmar da yake cewa ta furta na BATA SONSHI shi yafi komai d'aga mata hankali dan tana yi sosai fiye da zatonsa, amma bazata iya aurensa yanzu ba, shirun da tayi ya harzuk'a yaji kamar raina masa hankali take yi, da girmansa da komai in ba so ba meh zai kawo sa gun yarinya yana mata magiya, a k'ufule ya mik'e ya d'auki wayarsa ya kama hanyar fita daga ofishinta. 

Kuka ne ya ci k'arfinta ta cire gilashin ta d'aura kanta a table da ke gabanta ta fara kuka mai sauti, ji take in batayi kukan ba zuciyarta zai buga, kuka take sosai ta rasa mafita, bazata iya barin mahaifinta cikin rayuwar da yake ba, tasan Allah ke fahimtar da mutum in yayi niyya but a ranta tana jin akwai silar shiryuwar mahaifinta kuma ita ce da k'annenta.

Kukan Maryam ya dakatar dashi bakin k'ofa ya kasa fita, ji yayi kamar ya koma shima ya zauna ya taya ta kukan ko hankalinsu dukka zai kwanta, dak'yar ya iya dawo da tunaninsa ya fice daga ofishin dan yasan babu abinda zai sa Maryam ta fad'a masa damuwarta, zai taya ta da addu'a har Allah ya biya mata buk'atar ta kuma ta amince da maganar aurensu.

Kwana biyu da faruwar haka, tashin hankali da bak'in ciki babu wanda Maryam bata shiga ba, Baba da gaskiyarsa ya nuna bai son ta sake kawo masa abinci, rannan da ta kai masa korarta yayi ta bar d'akin tana mai zubar da hawaye. Mustapha kuwa tun daga wannan ranar bai sake neman Maryam ba, shi a nashi ya barta in ta huce ta k'irasa, ita kuwa ta rasa meh zata ce masa in ta k'ira hakan ya hanata nemansa, kana kallonta zaka gano akwai abinda ke damunta.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 29


Dawowarta daga office nata kenan a gajiye ta shiga d'akinta bayan ta gaida Momy ta sanar da ita dawowanta, bayan ta ajiye jakanta da tarkacen da ta shigo dasu kai tsaye ta fad'a ban d'aki dan tayi wanka, bayan ta gama wanka ta fito da towel kad'ai a jikinta ta samu gefen gado ta zauna, bata iya yin komai ba dan garin akwai zafi sosai, janyo pillow tayi ta kwanta ta gefe tana kallon k'asar d'akin nata, duniyar tunani ta fad'a taji knocking a bakin k'ofarta.

Da hanzari ta diro k'asa tunawa da tayi towel ne kad'ai jikinta, dan ma tasan Jabir da Usama indai suka zo d'akin mata basu shiga sai an basu izini, ba kamar wasu gidajen ba da zaki ga yaya ko k'ani ya shiga d'akin 'yan uwansa mata kai tsaye ba tare da tunanin irin halin da zai same su ciki ba, duk da sun san mata da son zama da half-vest, under-wear da sauran kayaki na shan iska musamman lokacin zafi hakan baya hana su shiga d'akin, a ganinsu ai muharramansu ne, sam hakan baya daga cikin abinda aka ce zaka iya yi da muharramarka, ganinsu a cikin wannan yanayi shad'ani na iya shiga ya b'ata komai ba tare da kasan kayi hakan ba. Haka agun mace bai kamata ta shiga d'akin yayunta manya kai tsaye ba tare da neman izini ba, Allah yasa mu gane.

Sai da ta sa doguwar riga ta d'aura d'ankwalinta sannan ta bud'e k'ofar, Usama ta gani tsaye sanye da k'ananan kaya, hanya ta bashi tana mai sake masa murmushi, yatsa ya d'aga mata alamar yana zuwa sannan ya kwalawa Jabir k'ira, tun daga nesa ya amsa yana cewa "sai yanzu taga damar bud'e k'ofar, ni dai ban isa da wannan jan ajin ba, ko ya saurayin naki yake yi dake oho, ko da yake k'urnu ne dole ya biye wa shirmenki" yana isowa kuwa ta kai masa bugu, sai da yayi k'ara sannan yace "wai dan an fad'a miki gaskiya kika buge ni haka?".

K'ara masa tayi tana cewa "Allah ka raina ni, ni yayarka ce fa, Usama fad'a masa ni yayarsa ce" Usama da yake zaune kan gadonta sai dariya yake cewa yayi "Toh dai Jabir kaji anty babba tayi magana, ka nutsu dama tun kafin tayi punishing naka" dariya dukka sukayi suka shiga ta rufe k'ofar, jabir gefen Usama ya zauna akan gado ita kuma ta samu wuri ta zauna a k'asa tana fuskantarsu.

Jabir ne ya fara magana da cewa "Kayi shiru Usama, muyi abinda ya kawomu mu bar nan, in bazaka yi magana ba ni in fad'i nawa, ka bani izini?" bai jira amsa ba ya cigaba da cewa "kinga when am serious kinsan da gaske nake, toh let's be serious about this, i mean about abinda zan fad'a yanzu, yanzu shekarunki nasan ashirin da hud'u, kinyi makaranta boko da Islamiya, kina aiki sannan kin mallaki hankalin kanki, kada ki duba halin da muke ciki a gidan nan kice zaki cuci kanki dan abunda ya tab'a faruwa dake a baya, ki fuskanci rayuwarki ki gyara naki rayuwar ki bar Baba da halinsa, mu muna tare dashi da yaddar Allah zai daina abinda yakeyi, ki kawo miji kiyi aure shi ne kad'ai mutuncinki da martabarki, kada ki kawo komai a matsayin hujja ko dan kare kanki, girma kike ba yarinya kike k'ara zama ba, abinda zai faru ko kina nan ko kina gidan aurenki ba makawa zai faru, ki sa hakan a ranki ki yadda da hukuncin Allah".

Girgiza kai Maryam takeyi da murmushi a fuskarta "amma Jabir ka manta abinda Baba yayi min da na kawo masa wanda nakeso ko? In kai ka manta ni bazan manta ba, haka kawai bazan kawo wani baba ya sake maimaita abinda yayi min ba a daina ganinsa da mutunci, mutuncin mahaifina yafi min komai, ku bar maganar tun wuri dan ba abu ne mai yiwuwa ba".

Tsaki Jabir ya ja mai kyau yana kallonta cike da b'acin rai "wai ke wace iriya ce? Shi bai duba nashi mutuncin ba ke zaki duba masa? Ke naki mutuncin bai dameki ba sai nasa? Mutumin da bai san darajarki ba bare k'imarki? Wallahi wallahi kada ki d'auka wasa, muddin kika d'auki wannan matsayin excuse toh ki tabbata shine zai k'ara haddasa mana k'iyayyan mahaifinmu a ranmu, dan babu adalci a lamarinsa in ya sake yin hakan". Usama yace "Maryam ki dai yi tunani, nasan ke mai sauk'i ne in abu yazo kanki, Muneera nake tunani da shegen taurin kanta wallahi".

Jabir yace "kai dai zata yi wa taurin kai dan k'aninta kake, ni kuwa ai yayanta ne, bata isa ta kawo min wargi ba dan tattake ta zanyi, ana duba muku abu ku kuna d'auka sonku ne ba'a yi, in mutumin nan ya nuna bai buk'atar mu ni da Usama zamu gane dan mun masa laifi, amma meh laifinki da yake k'inki yake k'yamar ki zauna kusa dashi, kuyi aure hankalinku ya kwanta ku bar komai gun mu, insha Allah komai zai daidaita". Maryam bata sake magana ba sai kai kawo da maganar tasu ke yi a kanta har suka gama suka bar d'akin bayan sunce tayi tunani mai kyau akan maganarsu.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


            


Page 30


Yau ya kama Sunday yayi dai-dai da ranar da akayi Baba zasu tafi Abuja, tun da asuba suka gama shirinsu, motar Baba aka d'auka Usama ne zaiyi driving, har bakin mota Usama ya raka su yana mai yi musu addu'ar samun nasara tare da Allah ya kiyaye hanya. Momy da sauran yara a bakin k'ofa suka tsaya suna d'aga musu hannu, Baba ba yabo ba fallasa ya d'aga musu hannu tun kafin ya shiga mota, yana shiga kuwa ya had'e rai har suka bar gidan. Sai da suka d'auki d'ayan mutumin (Malam Yunusa) a gidansa sannan suka bar garin Gombe da misalin k'arfe 7:30.

Basu isa Abuja ba sai k'arfe tak'was na dare sakamakon tsayawan da suka yi a hanya, hotel suka samu suka kama d'aki biyu, Baba shi kad'ai Usama kuma su biyu, bayan sun ci abinci sunyi sallah bacci kawai sukayi sakamakon gajiyan da sukayi, musamman Usama da yayi driving.

Washe-gari ya kama monday tun safe suka fita aikin da ya kawo su, basuyi sa'an samun abinda suka fito nema ba amma an tabbatar musu zuwa gobe zasu samu ganin chief comptroller. wasa-wasa har kwana biyu babu abinda yayi gaba, ran Baba yayi matuk'ar b'aci dan ba a tab'a raina masa hankali irin haka ba, har yau sun kasa ganin mutumin wanda a girme yasan ya girmesa. Baki dai Usama sukayi ta basa sannan ya hak'ura, duk da dama ba abinda ya isa ya yi, dole dai yayi hak'urin tunda shi yake nema. 

Yau kwana hud'u kenan da zuwan su Abuja amma ganin chief comptroller yayi musu wuya, abu da Nigeria, dole suka hak'ura suka bar office d'in cike da b'acin rai. Hotel suka koma kowa ya shige d'akinsa cike da rashin sanin abun yi. Bayan minti talatin da dawowarsu Usama wayarsa tayi k'ara, ganin sunan abokinsa Ibrahim k'arara jikin wayar ya sa shi murmusawa sannan ya d'auka ya kara a kunnensa yana mai cewa "yane mutumina" ta d'ayan b'angaren aka ce "ai baka da kirki Usama, yanzu na k'ira Abduljabbar(wani abokinsu) yake ce min kana Abuja, ko ka neme ni kasan kuma ina nan" da hannunsa d'ayar ya rufe idanunsa yana girgiza kai, shi da yake aikin Baba ina ya tuna da yana da aboki a Abuja, sai da Ibrahim ya sake magana sannan ya samu damar cewa "Wallahi bazaka gane bane mutumina, tare da Oga nake munzo ganin chief comptroller akan rik'e kayansu da akayi, kuma kasan Naija, yau kwana biyu ko ganinsa bamu samu munyi ba, dawowarmu daga office nasu kenan Wallahi".

"Eyyah don't worry, yanzun kana ina? Kazo mana ka sameni in yaso sai musan yanda zamuyi, akwai yaron wani custom comptroller da na sani, he is a very good friend of mine, maybe he can help you ku samu ganinsa, ka dai zo kawai sai musan yanda zamuyi"... Sai da ya bashi address na inda yake sannan suka ajiye wayar, rigarsa da ya cire ya d'auko ya saka, Malam Yunusa kam tuni yayi bacci hakan yasa ya fice ba tare da ya sanar dashi zai fita ba.

Awanni uku da faruwar hakan Baba ya fito daga d'akinsa ya nufi d'akinsu Usama, knocking yayi ak'alla sau uku sannan Malam Yunusa ya bud'e masa k'ofar idanunsa cike da bacci "lokacin Sallah yayi har ya wuce, kada kace min duk bacci kuke bakuyi sallah ba?" Ya fad'i hakan yana lek'a kan gadon ko zai ga Usama, malam Yunusa yace "nidai nayi baccin, amma Usama ina kyautata zaton ya fita, dan babu alamar mutum a toilet". Annurin fuskarsa ya d'auke jin cewa Usama ya fita, cikin kakkausar murya yace "ina zai je a garin Abuja? Wa ya sani? Kuma ya zai fita bai sanar dani ba?" Tsaki ya ja ya koma d'akinsa dan d'aukar wayarsa ya k'ira Usama, sai da ya zauna akan gadonsa sannan ya fara bincikar lambar dan k'in saving yayi jiya da ya k'irasa.

Sai da ya d'au fiye da minti goma yana neman lambar bai samu ba, sakamakon numbobin da yayi ta k'ira kuma aka k'irasa jiya akan maganar had'uwa da comptroller, daga k'arshe ya yanke shawarar karb'an lambar agun Malam Yunusa. Ya same sa a toilet lokacin da ya shigo d'akin, hakan ya sa ya zauna a bakin gado yana jirar fitowarsa. Baiyi minti uku ba ya fito. 

Lambar kawai ya tambayesa ba tare da wani tunani ba, Malam Yunusa cike da mamaki yace "wai Usaman ne baka da lambarsa?" Baba cikin rashin amsar bayarwa yace "bansan inda layin yayi ba, in ba haka ba ina dashi mana" Malam Yunusa bai kawo komai ransa ba ya d'auko wayarsa ya karanto masa lambar. Sai da yayi dialing ya sake kashewa ya fice daga d'akin dan baison Malam Yunusa yaji abinda zai ce wa Usama. A harabar hotel d'in ya tsaya sannan ya dannawa Usama k'ira cikin b'acin rai, fuskar nan a kwab'e kamar bai tab'a dariya ba.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 31


Usama na zaune bisa motarsa wayarsa ya fara ringing, a lokacin yana jiran Ibrahim ya fito daga gida suje wurin abokin nan nasa, dan sunyi waya ya fad'a musu inda yake kuma ya shaida musu zai jirasu tunda Ibrahim yace masa magana ce mai muhimmanci. Lokacin da ya ga k'irar har zuciyarsa sai da ya tsinke, kafin ya d'auka wayar Ibrahim ya fito yana cewa "muje ko, sorry na ajiyeka" hannu ya d'aga masa alamar ya tsaya sannan yayi receiving.

 Sallamar da yayi shi ya bawa Baba damar sauk'e masifarsa, ko sallamar bai amsa ba ya fara masifar fitar da yayi "wato ka kasa hak'uri da neman matan naka dan muna tare shine ka saci jiki ka fita babu wanda ya sani..." Hakan da Baba ya fad'a yasa Usama kallon Ibrahim wanda babu haufi yaji duk abinda Baba yace, wayar tasa irin baby nokia d'in nan kuma volume na wayar kamar china, aciki yake sa layin da yake waya dashi babbar wayarsa kuma layin subscription ne a ciki.

Idanunsa a lokaci d'aya yayi ja dan bak'in ciki da b'acin rai, babu abinda yafi b'ata masa rai irin kalaman da Baba ke jifansa dashi wato neman mata, kuma kalamansa duk a kunnen abokin sa, Allah yasa Ibrahim yasan halinsa kuma aboki ne na kusa, amma duk da haka ai sayar da hali ne, kunyar da yaji yasa ya kasa rage muryar wayar.

Yaso ya fahimtar da Baba inda yaje amma ko saurararsa baiyi ba, daga k'arshe ma cewa yayi "ka dawo yanzun nan ina jiranka" duk wannan maganganun a kunnen Ibrahim dake gefe kamar bai jin abinda ake fad'a. Bayan ya kashe wayar babu wanda ya samu k'arfin gwiwar yin magana, sai da suka d'auki minti biyu sannan Usama yaja numfashi ya tab'a abokinsa yana cewa "muje mana".

Ibrahim ya juyo ya kallesa yace "muje ina? Wurinsa kawai zaka koma, babu anfanin tashin hankali, am very sorry na saka cikin matsala, ban d'auka abun zai zama haka ba" Usama da murmushi a fuskarsa yace "indai Baba ne wallahi ka share sa, haka muke ta fama dashi, yanzu in na koma masa haka bani da abunda zai sa ya hak'ura, amma in naje da bayani mai kyau akan ganin wannan comptroller din am very sure zai sauk'o, tsufa ne ya fara zuwa shiyasa abu kad'an zaka ga ya hau fad'a" dak'yar yayi convincing d'insa suka tafi.

Sai da suka yi hira sosai su uku sannan suka kawo maganar ganin comptroller, yaron mai suna Mu'azzam ya bawa Usama numban babansa sannan sukayi sharing lamba tsakaninsu suka cigaba da hira, a cikin zamansu na awa d'aya da rabin nan Baba ya k'ira yafi sau talatin, daga k'arshe ma kashe wayar yayi gaba d'aya dan bai son b'acin rai. Sai da Ibrahim ya nace su tafi sannan sukayi sallama, dan Usama da Mu'azzam akwai son hira.

Bayan ya kai Ibrahim gida sai da yaje yawonsa sannan ya wuce hotel dan amsa k'iran Baba ba dan ya so ba. A yau dai ya fidda ran zasu iya gyara Baba, sunyi addu'ar har azumi sai da Jabir ya sa su sukayi, sallahr dare sunyi iya k'ok'arinsu, gashi suna k'ok'arin shiga jikinsa amma yana yakice su, meh zasu yi masa da wuce wannan? Shi dai yana komawa gida shawarar da zai basu shine kowa yayi ta kansa, duk mai rabon shiga aljannah zai shiga, amma su basu isa su sa mahaifinsu kan hanya ba. 

Da tunanin nan ya isa cikin hotel d'in, yana fitowa ya hango Baba yana isowa wurin motar kamar zaki, baiyi gigin isowa wurinsa ba dan yasan hakan zai jawo musu idanun mutane, gwanda ya zauna parking space su gama komai asiri a rufe, sauk'e masa mari Baba yayi ba tare da ya tanka sa ba, Usama ya rik'e kuncinsa da hannunsa hakan ya hana Baba k'ara masa wani marin, duk da hakan bai tsiraba, juyosa yayi ya kai masa dundu a baya sannan yayi hak'urin fara fad'a, tun mutane suna wucewa har suka fara juyowa suna kallonsu, shi dai Usama uffan bai ce ba sai ma sauk'ar da kansa da yayi k'asa yana wasa da makullin motar da ke hannunsa, sai da ya gama dan kansa ya juya ya shige ciki ya bar Usama a wurin.

Bud'e k'ofar yayi ya koma cikin motar ya zauna sannan yasa kuka kamar mace, maganar baba ya sashi tunawa da mahaifiyarsa, cewa yayi "mamanka bata koya maka wannan tarbiyyar ba na raini, iskanci da yawon banza ba, ko ka fara shaye-shaye ne Usama?". Kukan da yakeyi mai sauti kad'ai ya sanyaya masa zuciyarsa, amma a ransa ya k'udurce bazai k'ara sa kansa a harkar Baba ba, kowa ya nemi tasa lahirar.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 32


Washe-gari da k'arfe tara na safe Mu'azzam ya k'ira Usama akan yayi masa magana, kuma yace ya k'irasa sai su san yanda za'a yi su had'u, yayi masa godiya sannan ya kashe wayar. Ya k'irasa har sau biyu bai d'auka ba na uku sannan ya d'aga, bayan sun gaisa ya fad'a masa ko shi waye da dalilin k'iransa, cike da fara'a yace ya gane sa. 

Ce masa yayi yazo office yanzu dan zaiyi tafiya zuwa anjima, baiyi wata-wata ba ya fad'awa Malam Yunusa yanda sukayi, da hanzari suka gama abunda zasuyi suka fito dan sanar da Baba, Usama dai yayi hanyar waje yana cewa "ina jiranku a waje nikam", kwata-kwata bai son ganin Baba yau, jin haushinsa yake kamar ya gudu ya bar Abujan ko hankalinsa zai kwanta.

Sun isa k'arfe goma ya wuce, k'iran mutumin yayi ya sanar dashi isowarsu, ce masa yayi zai turo wani dan yayi musu iso, hakan kuwa akayi, basu yi minti biyar ba wani d'an saurayi ya iso inda suke yana tambayarsu ko Usama na cikinsu suka amsa da "eh", tare suka shiga yayi musu jagora, yau dai ya tabbata sun samu ganin chief costom comptroller sun zauna sun tattauna game da abunda ya kawo su ya kuma tabbatar musu yana dawowa daga tafiyarsa zai san abunyi.

A cikin mota kowa farinciki yake harda Baba wanda hak'oransa suka kasa rufuwa, Usama yana kallon murmushinsa yaji haushin kyautata masa da yayi, ji yayi da ma ya barsa cikin b'acin rai kamar yanda shi ya kasa bawa iyalansa farinciki, wata zuciyar tace mahaifinka ne, in baka taimakesa ba waye zai taimakesa? Annurin fuskarsa dai ya kau, Allah-Allah yake washegari yayi su kama hanyar gida ko zai samu sa'ida in ya ga Mama ya fad'a mata abin ransa.

A b'angaren Maryam da Mustapha kuma abun dai ba'a cewa komai, tun yana iya share ta har ya kasa daurewa ya k'irata, bai kawo mata maganar ba balle a dawo gidan jiya, hakan yasa suka cigaba da soyayyarsu kamar da duk da Maryam bata koma daidai ba saboda zargin kanta da take na rashin yi masa adalci/kyautata masa.

"Ni sa'anki ne? Ina gaya miki magana kina kawo min wani banzar excuse naki? Ko Maryam da na fad'a mata bata fad'a min abinda kike fad'a min yanzu ba, harda cewa Allah ya kiyayeki da aure yanzu, lafiyanki? Dan ma nak'i zuwa tunkararki tun farko nace Maryam ta fad'a miki kenan, da ni nazo na fara miki maganar meh zaki ce?" Muneerat gefe take kallo ta turo baki tana had'e rai, ita a dole an shiga rayuwarta, sai da Jabir ya sake cewa "na fad'a miki ki kawo miji ayi muku aure, kin gama degree aiki kawai zaki nema".

Turo bakin ta k'ara yi "Amma fisabilillahi kunsan Baba, waye zan samu mai kud'i a yanzu wanda Baba bazai kora ba? A dai yi wa Maryam tunda ita tana dashi, nidai har yanzu ban samo sa'an Baba ba, ban samo wanda Baba bazai zaga ya kora ba, in kuma ku zaku aura min duk wanda na kawo ai ga Abdallahnah, aiki ne kawai bai samu ba, kuma kasan Baba sarai ba bari zaiyi ba, shiyasa nake rok'anka dan Allah kayi hak'uri in jira yayi kud'i sannan in turo sa" Jabir dan haushi ji yayi kamar ya kai mata bugu "dan uwarki ke zaki basa kud'in? Ko kina da tabbacin zaiyi kud'i nan kusa ke kuma ki zauna zaman jira? Arziki in Allah yayi zakayi ko yau sai kiga Allah ya bud'ewa mutum hanya, Muneera ki fita idona in rufe da son duniyan nan naki" ya fad'i hakan yana nunata da yatsa.

Can ciki tace "Baba dai zaka ce a raba shi da son duniya, ba duk shi yasa muke haran masu kud'in ba" matsowa yayi kusa da ita yana kawo kunnensa wurin bakinta yana cewa "fad'i dakyau inji, cewa nayi ki fad'a dakyau inji insan baki da kunya" babu alamun zata amsa shi, hakan yasa ya daidaita tsayuwarsa sannan yace "wallahi da ke da Maryam d'in nan kun isheni, tun ana muku da lallami sai an fara fad'a, ana nuna muku dama ku kuna kallon hagu" ya tashi yayi hanyar waje yana cewa "na gaji daku, in Usama ya dawo yasan yanda zaiyi daku, in kunso ku dawwama a gida kada kuyi aure, marasa tunani kawai".


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 33


K'arfe hud'u yayi musu acikin garin Gombe, Malam Yunusa suka fara ajiyewa sannan suka wuce gida. Sun isa gida kowa ya wuce dakinsa,, ko godiya Baba bai yiwa Usama ba, duk da mahaifinsa ne amma kalma mai kyau in yayi masa akan taimakonsa da yayi ai zaiji dad'i saboda gobe ya sake yi masa, amma kamar bai san Usama ne ya nemo musu hanyar ba. Momy ce ta kai wa Baba abinci d'akinsa, Usama kuwa sallah yayi ya kwanta yana jiran Jabir, aikin gama ya gama a ganinsa, ya fita daga hanyar Baba tunda Allah yasa sun dawo gida lafiya.

Minti sha-biyar yana kwance yaji sallamar Nasreen a bakin k'ofarsa, sai da ya amsa tace "ka bud'e min k'ofar bazan iya ba" dariya yayi ya taso yana cewa "duk jikin nan naki baki da k'arfi kenan" bata amsa shi ba sai da ya bud'e k'ofar tace "abincinka na kawo, kuma banson in ajiye a k'asa dan bazan iya d'auka ba shiyasa nace ka bud'e min" ta ajiye abincin tace "Anty Maryam tace bakason ku gaisa ne kak'i shigowa tun da ka dawo? Ita tace in kawo abincin ma" ta fad'i hakan tana murmushi, shima murmushi yayi yace "kice mata gani nan zuwa. Ina Jabir yaje?" Tab'e bakinta tayi ta d'aga kafad'arta tace "oho fah, naga sunyi fad'a da Anty Muneera ma" gyara zama tayi a gefensa ta cigaba da cewa "kullum sai yace tayi aure tak'i, wai ita ba yanzu ba, d'azu kafin ya fita a d'akin Momy dukkansu sukayi maganar, da suka k'i shine yayi ta fad'a, kowa ya kasa masa magana dan ransa ya b'aci da gaske, tun da ya fita shine har yanzu bai dawo ba" ta k'arasa maganar da fuskar tausayi.

D'auke kai yayi ya d'iba abincinsa akan plate ya fara ci dan bai dawo dan ya sake b'acin rai ba, ganin ba tanka ta zaiyi ba yasa ta cigaba da cewa "ya Usama kayi musu magana mana, kowa a gidansu ana aure mu ba'ayi a gidanmu, k'awayena a school duk yayunsu sunyi aure banda namu" ta fad'i hakan kamar zata yi kuka, dariya ta basa har sai da ya murmusa yace "kije ki basu shawara mana, in muka taru akansu dukkanmu zasu yi zuciya" ware ido tayi tana kallonsa, a ranta tana cewa Jabir ma basu ji nasa ba sai nawa? 

A fili kuwa tace "gwanda Anty Maryam zan iya fad'a mata, amma Muneerat?..." Ta kad'a kai tana cewa "a'a ina tsoronta wallahi".


Sauk'ar da numfashi yayi ya ajiye plate na hannunsa ya kalleta "kinga Nasreen addu'a zamuyi musu Allah ya zab'a musu mafi alkhairi, in kuma zaki iya fad'a musu abinda kika fad'a min ki takura musu da hakan zasu ji suna son faranta muku, in kuma bazaki iya ba kiyi shiru har sai lokacin da suka ji gidan nan ya ishesu". Haka suka gama magana yana nuna mata aure lokaci ne, ta sa su a addu'a har ra'ayin auren ya shiga ransu. A ganinsa rashin mafad'i ne, da Baba yana da tunani shi zai sa su kawo miji su daina wannan rawar idon, ga Mama da yake tunanin ita zata jawo ra'ayin yaran nata tayi shiru ko maganar bata yi.

Tare suka shiga cikin gida da Nasreen, sai da ya shiga d'akin Momy suka gaisa sannan ya wuce wurin 'yan uwansa, bai yi musu maganar komai ba dangane da tafiyarsu bare maganar aure, hirar 'yan uwa sukayi har da Muneerat, basu tashi ba sai maghrib kowa ya tashi dan yin sallah. A masallaci suka had'u da Jabir, bayan sun fito daga masallaci yace "ina ta nemanka har hak'uri na ya k'are" hannunsa ya rik'e ya janyosa bakin titi ba tare da wani k'arin bayani ba, Jabir sai tambayansa yake, amsa d'aya ya basa "muje inda bazaka iya janyoni mu dawo gida ba sai mu samu wuri in fad'a maka". Hakan kuwa akayi, wani benchi ya samu a gefen titi suka zauna sannan ya labarta masa duk abinda Baba ya masa na cin fuska a Abuja.

Ya k'ara da cewa "ni abun nan ya fita raina, tun da muka dawo daga Lagos muke k'ok'arin kyautata masa, in zaiyi abu baya duba inda ya dace yayi, sai kaga yanda ake kallonmu a hotel d'in, kuma wallahi Ibrahim nasan har yau abun nan yana ransa kuma zai na kallona dashi" Jabir ya numfasa yace "yanzu ya kakeso ayi? What's on your mind da ka kawo ni nan? Ina ce ko a gida zamu iya gama maganar?" "Baka gane ba yanzu? Toh so nake muje wurin mama ayi ta ta k'are, zanje in fad'a mata komai game da shawarar da na yanke, sannan in nemi shawararta bayan haka in bata shawarar sa Maryam da Muneerat aure".

Kallonsa yake da mamaki, daga bisani ya ja guntun tsaki ya kai dubansa gefe yana kad'a kai, Usama yace "meh?" Kallonsa yayi sannan yace "kai ne ka karaya tun yanzu bayan kai ke k'arfafa min gwiwa? Meh hakan da zakayi yake nufi? Ka bar maganar kai k'aransa gun Mama, Kai abun nan da yayi maka shine ya b'ata maka rai?" Ya kad'a kai yace "jiya wai kasan meh Maryam ke fad'a min? Wai kud'in makarantar Muneerat Baba yak'i biya, dak'yar yazo ya biya kud'in registration kawai, komai na gama makaranta project and everything Maryam ce tayi mata, dan ma Muneerat da Maryam na home business kuma dama Maryam ta bar mata komai a hannunta ita da Mama, da kud'ad'en nan sukayi komai dan rufin asiri, yanzu jarin ya karye ba business, da aikin Maryam kowa ya dogara, gwanda mu muna da shagonmu na Lagos every month muna da cash".

Usama ya dakatar dashi da cewa "ai shawara d'aya ce mu share mutumin nan mu duba k'annenmu, mu ba dad'i k'annenmu ba dad'i, ni sai yanzu na fara jin haushin hanani neman aiki da kayi wai in taimakawa Baba, gashi yanzu wa gari ta waya?" Jabir dai baiyi magana ba "yanzu ya maganar aikin naka na Lagos da kake nema?" Jabir yace "sun ce zasu nemeni, ina dai jira har yanzu". Sun tsayar da magana akan zasu sami Mama da zancen Maryam da Muneerat, maganar kai k'ara kuma a barsa zuwa nan gaba.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 34


Bayan sati d'aya da faruwar haka Mama ta nemi ganin yaranta dukka a gida, daga Maryam har Zahra auta 'yar Momy suka d'unguma zuwa gidan bayan sun tabbatar Baba ya fita da drivansa kuma bazai dawo da wuri ba, yara suka shiga motar da Usama suka dawo dashi daga lagos, Jabir ne ya ja su mufeeda na gaba, saura yara hud'un na baya. Maryam da Usama kuma adaidaita suka bi bayan sunga tafiyar su Jabir.

Gyarar murya Mama tayi bayan sun gama gaisuwa da d'an wasar da suka saba yi tsakaninta da 'ya'yanta, nasiha ta fara yi musu daga su har yaran mai shiga jiki, ta nuna musu muhimmancin hak'uri da yafiya, sai da ta gama ta dasa aya sannan ta nemi keb'ancewa da manyan 'ya'yanta. Nasreen da sauran yara suka shige wurin 'yar tsohuwarsu da tun da suka gama gaisawa ta basu wuri tana cewa "wannan zaman Mama da 'ya'yanta ne, ni nayi ciki".

Mufeeda da Maryam suka matso kusa da Mama suka zauna a k'asa saboda Jabir na zaune a kujerar gefenta, Usama bai tashi daga kujerar da yake ba dan dama yana kusa da Mama, sai da Mama ta tabbatar hankalinsu duk ya zo gunta sannan ta fara maganar da ya sa ta nemi ganinsu.

 "Nasan ban tab'a muku magana irin wannan ba, amma kamar yanda kuka sani komai kamawa take, abunda ya faru a baya a kanki Maryam ya wuce, ku d'auke shi matsayin jarrabar da kowani bawa zai samu ta kowani fanni da Allah yaso jarrabar sa, wasu ta fannin iyaye, wasu matan ta fannin mazajensu, maza kuma matayensu, wasu ta fannin aiki, wasu da rashin lafiya, wasu da arziki, kowa dai da irin nasa, duk abinda ya samu bawa jarrabawa ce, kuma dan Allah ya jarrabi mutum bai zama bazai cigaba da rayuwarsa ba kenan, wasu hanyar samun aljannarsu kenan, wasu kuma jarrabar sai ya zama musu alkhairi a rayuwarsu, bayan wuya sai dad'i".

Ta numfasa sannan ta cigaba da cewa "nasan Jabir da Usama sun muku maganar aure, wanda ko ni na dad'e da tunanin hakan, amma Allah bai bani ikon fad'a muku ba saboda wasu dalilai wanda a yanzu nake ganin babu anfanin kawo wannan a rai" ta kalli Maryam sannan ta sauk'e k'wayar idanunta akan Mufeedah ta sake musu murmushi tace "bazan tab'a bawa 'ya'yan da Allah ya bani amana gurguwar shawara ba, haka zalika bazan so ku shiga rayuwa maras dad'i ba ko kuma ku tauyewa kanku hak'k'i, lokaci yayi da ya dace ku fidda miji kuyi aure, ba wai dan wani dalili ba sai dan mutuncinku da kuma cika sunnar annabinmu, kamar yanda nake sa ran zaku yi iya k'ok'arinku a duniya dan kuyi ibadarku haka nake sa ran zaku rik'i aure ibada kuma ku yi shi saboda Allah, ba a yin aure dan dukiya, ba'a aure dan wani dalili na daban na son zuciya, aure ibada ne kuma abunda yafi dacewa a duba shine son da yarinya ke wa wanda zata aura ko kuma shi wanda yake mata, idan har akwai so tsakaninsu na hak'ik'a irin wanda addini yace ayi to alal hak'ik'a za samu zaman lafiya da yaddan Allah".

Haka tayi musu nasiha mai ratsa jiki, sai da ta tabbatar ta kashe musu jiki da kalamanta sannan tace "zan jira labari mai dad'i nan da sati, ke kuma Mufeedah wannan Abdallahn naki in da gaske yake ya turo, in ya turo sai a d'aga auren zuwa lokacin da ya shirya, duk da naji Jabir yana cewa yaron yana da sana'a, ba cewa kayi yana zama a shago ba Jabir?" Ta fad'i hakan tana kallonshi ya amsa da "eh, kuma yayi makaranta yana kan neman aiki" mama tace "toh ai kinji, tunda zai iya biyan sadaki ya baki abinci da sutura da sauran Hak'k'ok'inki ai shikenan, ba a san yanda Allah zaiyi ba nan gaba, kina sonshi yana sonki nasan zakuyi hak'uri da juna".

Mufeeda dai bata da ta cewa, kuma ta yanke shawarar tura shi gida duk abinda Baba yayi ita babu ruwanta, ba dan tafi son Abdallah ba meh zai hanata tura Harun, yana da kud'i haka babansa yake da a ranta ta k'ara da sai dai d'an iska ne, bazamu shirya ba in mukayi aure... Haka dai suka gama magana tsakaninsu, kowa ya fad'i ra'ayinsa kuma an warware musu shakku da tsoronsu, abunda ya rage kawai shine suyi magana da samarin nasu dan turowa gida.

A waya Mama ta k'ira Momy bayan tafiyarsu ta sanar da ita yanda sukayi, ta k'ara da cewa in yaran sun shirya tsakaninsu zasu sanar da ita dan ta sanar da Baba, sosai Momy tayi murna tana cewa "Allah ya kaimu mu sha biki, naji dad'in wannan al'amari". Maryam da Mufeedah dai haka suka dawo gida sukuku suna tunanin yanda zasu tunkari wad'an da suke so da maganar, sai kuma fargabar amsar su, Maryam dai matsalarta d'aya in Mustapha ya tambayeta meh yasa ta canja ra'ayi lokaci d'aya meh zata ce?


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 35


A GURGUJE PLEASE!!!


Usama ne ya shigo guje cikin gida yana k'iran Momy da Maryam, muryar sa kad'ai ya nuna farincikin da yake ciki, a tsakar gida suka had'e dukka har da Momy, Mufeedah ma ta iso dan taga alamar labari mai dad'i za'a bayar kada ayi babu ita, tun kafin ya fara magana Jabir ya shigo murmushi fal fuskarsa.

"Yanzu aka turo ana neman Jabir a Abuja kamfanin NNPC, ana son ganinsa ranar Monday, yayi sending komai nasa Lagos sai gashi Abuja ne suka nemesa" cike da murna suka fara ambatar "Alhamdulillahi" Maryam ta mik'a masa hannu sukayi shaking tana ce masa "congrats bro, Allah ya bada sa'a yasa alkhairi" haka Mufeedah tayi masa, Momy kam shafa kansa tayi tana mai kwararo masa addu'a. Huging juna sukayi da Usama yana ce masa "sai Abuja bros, can't wait inga ka fara aiki"... Murna sosai sukayi daga bisani ya wuce gidan Mama dan ya sanar da ita, ita ma tayi murna suka had'u da kaka suna ta masa addu'a had'e da nasiha.

Bayan ya dawo yace wa Usama yana son suje gun kakarsa, tun da suka dawo basu je gun iyayen maman Usama ba, kuma ga tafiyar Jabir wanda tare zasuyi da Usama kuma basu san ranar dawowarsu ba, washe gari suka tsayar da zancen zasu je su wuni, basu fad'awa kowa ba sai Mama da Momy, sun musu addu'a kuma sun basu kayan k'walamar da zasu kai musu. Sunje sun sami kowa k'alau, kakarsu na jin ance Usama ne ta fara kuka dan bata ganesa ba da ya shigo d'akinta, duk hak'uri suka tsaya bata har tayi shiru bata d'auki tsawon lokaci ba ta fara hira kamar ba ita ba. 

Sai da zasu tafi sannan k'anin Maman Usama ya kawo takardun shagunan da ya saya a Gombe ya baiwa Usama, kud'in gadonsu da Baba ya bayar ya juya har ya samu ya sayo musu shaguna shida yasa haya a ciki, shi yake kula da harkokin shagunan har yau da Allah ya dawo da Usama ya damk'a masa, sauran kud'ad'en kuma yace zai tura masa ta banki. 

Sosai suka yi murnar zuwansu sukayi godiya sosai suna mai tuna Maman Usama, anyi mata addu'a haka zalika masu saurin hawaye suka zubda, K'annen Mamansa sunyi musu fad'a k'in zuwan da sukayi wanda suka b'oye da makaranta ne, kuma yanzu sun gama zasu na zuwa duk hutun da suka samu daga wurin aiki. Basu bar garin ba sai k'arfe biyar, an cika su da kayan tsaraba sannan suka baro 'yan uwansu cike da farincikin ganinsu cikin k'oshin lafiya.

"Maryaaam" Mustapha ya ja sunan nata wanda sai da yasa ta runtse idanunta, jin muryar tayi daga kanta zuwa tafin k'afafunta, yanayin da ta shiga ya hanata amsa shi sai da ya sake cewa "kyaleni ma zakiyi ina k'iranki ko?" Sai da ta sauk'e ajiyar zuciya sannan tace "ina sonka Mustynah, I can't wait any longer kazo kawai a mana aure" dariya ta basa sosai dan sai da ya dara, yasan wasa take tunda ba yau ta fara fad'a masa haka ba in ta shiga irin wannan yanayin, had'e rai tayi kamar yana ganinta tace "bye" bata jira amsar shi ba ta katse wayar, da gaskiyarta wai fushi tayi, tana masa maganar aure yana mata dariya, meh ma yake nufi? Ta ja tsaki ta wurga wayar gefe ta juya ma wayar baya duk ta had'e rai. Sai da ya gama tsara maganar da zai fad'a mata sannan ya kirata, k'in d'auka tayi har ya yanke, sai da ya k'ira na biyu sannan ta mirgina ta lalubo wayar ta d'auka ta sa a kunne.

"Haba Baby, meh na fushi bayan kinsan duk yanda kikace haka akeyi, yi hak'uri dan nayi dariya, kawai banson maganar da kikayi ya kwad'aita min samunki yanzu ne shiyasa na kawar da dariya, but am sorry bazan k'ara ba kinji babynah?" Turo baki tayi tana cewa "wa yace maka yau wasa nake? Ni da gaske nake kazo ko gobe ne" abun dai shi ya d'aure masa kai "Maryam da gaske kike in turo? Kada ki ja raina dan Allah" ya fad'i hakan da nuna alamar ta tausaya masa, sai da tayi murmushi sannan ta nuna masa da gaske take, cike da murna ya tabbatar mata zai sanar da iyayensa, kuma shi so yake ayi da wuri tun kafin ta sake wani shawarar, dariya ya bata tana cewa "ai bazan fasa ba, kai dai kawai ka turo, duk ranar da kukayi magana da su Baba sai ka sanar dani shawarar da kuka yanke saboda nima in sanar a gida". Mufeedah ma haka ta sanar da Abdallahnta, baiyi musu ba shima dan yana expecting za'a nemesa a inda ya nemi aiki a satin nan.

Abu kamar wasa a cikin sati biyu Mustapha da Abdallah sun gama komai, jira kawai suke a sanar da Baba ya tarbesu, duk b'angaren iyayen mazan sun bada goyon baya d'ari bisa d'ari, ba a b'ata lokaci ba aka sanar da Baba yace yana jiran isowarsu sati mai zuwa, iyayen Mustapha ne suka fara zuwa sannan na Abdallah. Kamar yanda akayi zargi haka Baba yayi, dan kud'i mai tsoka ya nema, mutunci dai ya zube, amma da yake yara na son junansu haka aka daure ta b'angaren Mustapha, amma Abdallah abun baiyi musu dad'i ba saboda da rufin asirin Allah suka dogara.

Mufeedah tayi kuka kamar ranta zai fita, Maryam ce kad'ai take bata baki dan Jabir da Usama suna can Abuja sai a waya suka ji labarin komai, abu d'aya Jabir yace mata "ki cewa Abdallah yayi abinda zai iya, sauran abun ku bar mana zamu san yanda zamuyi da mutumin nan" haka ko akayi, dubu d'ari da ashirin ya bayar, na sadaki dubu hamsin sauran kuma ayi sauran hidima dasu, Baba bai yi musu ba sai da ya shigo gida ya watsa mata kud'in wai ta aurar da kanta, bata iya cewa komai ba sai kuka. Momy ta tattara kud'in ta ajiye a wurinta tace a cigaba da sha'ani.

Ansa ranar auren Mustapha da Maryam wata uku, Mufeedah da Abdallah kuma bai yarda an sake zaman sa rana ba, cikin mutanen gidan babu wanda ya tanka shi dan Jabir yace su shareshi sai ya dawo. Mufeedah har gun Mama taje tana kuka, ita a ganinta da basu ce ta tura ba hankalin kowa a kwance, duk laifinsu take gani, Mama dai rarrashinta tayi tana mai k'arfafa mata gwiwa.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 36


Wata d'aya Jabir sukayi a Abuja sannan suka dawo gida, a lokacin ya kama saura watanni biyu da sati d'aya auren Maryam, Baba suka samu a d'akinsa dan su tattauna maganar Mufeedah, shi dai ce musu yayi babu ruwansa, Jabir ya numfasa yace "Baba a ganina tunda ka karb'i kud'in ba anfanin jan lokaci, ayi tare da na Maryam in yaso nata kud'in in bai isa ba sai ace musu su k'ara...." Tsawa Baba ya daka masa "na tab'a neman shawara agunka? Ku tashi ku bani wuri kafin in sab'a muku".

K'in tashi sukayi hakan yasa Baba ya harzuk'a ya kama zage-zage, daga k'arshe dai yace "kuje ku ce musu azo a d'aura, ana dubawa yarinya inda zata ta huta ku kuna cewa rufin asiri" yayi ta masifa dai iya son ransa basu tanka sa ba, sai da ya gama sun tashi zasu bar d'akin sannan Usama yace "kud'in nan dai ba mutuwa mutum zaiyi dashi ba, kai baka bawa iyalinka ba amma kana nema wani ya baka" ya tab'e baki ya k'ara da cewa "Allah dai ya bamu wadatar zuci". Fita sukayi daga d'akin a guje dan sun san maganar dole ta tab'a shi, ai kuwa ranar ansha zagi a gidan, cewa yayi baison ganinsu a gidanshi sun raina shi, Usama da Jabir kuwa suka ce fir babu inda zasu, gidan Ubansu ne babu inda yafi musu nan.

Daga k'arshe dai fita sukayi daga gidan suka kyaleshi ya k'araci masifar sa ba mai tanka sa, sai can dare suka dawo, hakan kuma bai hana auren Mufeedah ba, abunda yafi bak'anta mata rai bai wuce yana kallonta zai had'e rai ya gaya mata magana ba, wani abun nasa ko mata sai hakan, tun abun na sa ta kuka har ta fara gudun had'uwa dashi dan taga alamar abun nasa ba na raguwa bane. 

Wasa-wasa lokacin aure sai gabatowa yake, lokacin da aka kawo kayan aurensu ansha daru, dan kayan Maryam yafi na Mufeedah yawa, hakan ya jawo hayaniya dan Baba cewa yayi ta bada shi ta bashi kunya, ranta ya b'aci tace wa Momy ta sanar da magabatan Abdallah ta fasa auren su kwashe kayansu bata so, abu kamar wasa dai ta rufe ido tayi masifarta a tsakiyar gida, hauka tuburan tayi ranar, kayan ta zube musu a cikin gida ta kwaso sauran kud'ad'en ta jefa akan akwatunan tana cewa su zo su kwashe, su da suka ce ta turo Abdallah su zasu sake sanar dasu ta fasa.

Maryam ta bata hak'uri har da kukanta amma baiyi anfani ba, sai da Jabir da Usama suka zo sannan suka samu damar shawo kanta, nuna mata sukayi hakan da tayi da Baba ta yi wa hakan zai sarara mata ya daina yi mata abinda yakeyi akan Abdallah, amma yanzu ta bashi damar cigaba da yin yanda yaso tunda yaga alamar tana jin haushi. Tayi kuka kamar zata shid'e haka Maryam na tayata, Baba dai zaginsa da habaicinsa baiyi anfani ba tunda ba a fasa shirin auren ba sai ma k'arfin gwiwa da ya k'ara mata, a ganinta in ita batayi fighting ba k'annenta ne zasuyi wahalar nan gaba, hakan ya sa ta jajirce tayi mirsisi da ido tace sai inda k'arfinta ya k'are indai auren Abdallah ne kamar ta yi ta gama da yardar Allah.

Daga ranar Mufeedah bata barin Baba ya gaya mata magana akan Abdallah, yana gaya mata magana zata mayar masa daidai da wanda ya fad'a mata, kuma sai ta mayar da abun wasa, akwai lokacin da yace mata "Mutum ya rasa wanda zai kawo sai mai zama a shago, nawa ya samu wa kansa bare matarsa" dariya tayi tace "Allah sarki Baba, ai mazan k'warai ba kansu suka sani ba, sai sun wadatar da matansu sannan suke tuna kansu, kaga indai ni ne zama a shagonsa zai wadatar dani kuma har in tsammasa, wadatar zuci yafi komai" shi ma dariyar yayi ya bar wurin.

28th June 2015 yayi daidai da ranar da aka d'aura auren Mustapha da Maryam, Abdallah da Mufeedah, ranar asabar da misalin k'arfe sha d'aya a harabar gidansu dake jeka da fari. Uncle Usman ne ya zama waliyinsu dukka, bakinsu har kunne sun kasa b'oye farincikinsu, babu laifi Baba bai nuna halin nasa ba, amma ana gama d'aura aure ya shige d'akinsa ya kwanta. Usama da Jabir ne suka gudanar da komai da ya dace, anci ansha anyi mak'il sannan aka sha walimar maza, ba'a tashi ba sai da akayi sallahr azahar.

A cikin gida kuma babu wanda bai zo ba cikin 'yan uwa da abokan arziki, yayyu da k'awaye duk an taru a d'akin Maryam sai tsokanar amare ake, kina shigowa kyallin amare zaki gani, wanka kawai sukayi amma jikinsu sai k'yalli yake, murmushi dai bai b'acewa daga fuskarsu. Dariyar shak'iyancin k'awaye kawai zakaji suna shewa, fitowar Mufeedah daga wanka yayi dai-dai da shigowar Mama d'akin, tayi wanka tasha d'ankunne da sark'a haka d'aurin kanta yayi d'as kamar budurwa.

Cikin k'awayen amare wad'an da suka saba da Mama suka kama tsokanar ta, dariya kawai tayi tana kai dubanta gun Maryam da take neman man shafawanta "ku sa hijabi ku zo d'akina yanzun nan, ba sai kun shafa komai ba" ta kalli 'yarta Fatima sannan tace "daga zuwa tsokanar amare kin samu wuri kin rakub'e kin manta da maganar da aka fad'a miki" baki ta rufe da hannunta tana ware ido alamar ta manta. Bata k'ara minti d'aya ba ta kamo su suka fito sai d'akin Mama har cikin bedroom.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 37


Mama ce ta ciro wani abu daga cikin wardrobe nata a cikin ghanamostgo, da yake tun ana satin biki ta dawo gidan ta zauna dan ayi hidimar bikin 'ya'yanta da ita(ta gama iddarta kada ku manta) ajiye musu tayi akan gado ta fita daga d'akin dan k'iran k'anwarta tazo ta taya Fatima cika sauran aikin gyarar amaren da suka fara. Wasu mayuka suka ciro daga ciki masu k'amshi acikin robobi sun kai biyar, kowanne da kalar k'amshinsa, wani roba suka samu d'an k'ank'ani suka d'ibi kowani mai suka had'e su wuri d'aya.

Mik'a musu sukayi tare da basu umarnin shafawa a jikinsu, babu musu kowacce ta sa hannu ta fara shafawa, k'amshin turaren da aka musu ya had'e da na mai d'in da suka shafa sai ya bada wani daddad'an k'amshi. Sai da suka tabbatar sun gama aikinsu sannan suka basu kayan sawa, na shafawa sun shafa musu, na sha sun basu sun sha sannan suka k'ira mai kwalliya ta cancad'a musu, ba su suka gama ba sai biyu da rabi, bridal gown suka sanya komai iri d'aya sai banbancin launi, Maryam ta sanya dark Blue da style na net golden, Mufeedah kuma ta sa Maroon. 

Turare suka basu na humrah suka shafe ilahirin jikinsu sannan aka feshe su da arabian perfume, masha Allah amare sunsha kyau har sun k'oshi. Tun daga d'akin aka fara hotuna da amare har suka fito cikin gida, nan hayaniya ya kaure kowa na fad'an albarkacin bakinsa akan amare, wannan yace Maryam tafi kyau wannan yace Mufeedah. Partyn da ba'a je ba kenan sai k'arfe uku da rabi bayan kowa yayi sallahr la'asar, dama amare sai da sukayi alwalar su sannan aka yi musu kwalliya hakan yasa sukayi sallah sannan suka kama hanyar Laila visitors suite dan gudanar da partyn da angwaye biyu suka shirya.

Mota d'aya amaren suka shiga sai da aka kai su harabar hall d'in suka had'u da angwayensu da sauran k'awayensu, kyallin da sukeyi ke kya ce ba Maryam da Mufeedah da kuka sani bane, Mustapha rud'ewa yayi da ya bud'e k'ofar motar, dama Mufeedah fita tayi ta koma d'aya motar kamar yanda suka tsara ita ma ta samu mijinta a d'ayar motar kafin a nemi shigowar su, kashe masa ido tayi tana mai sake masa murmushin da ya zautar dashi, sai da ya sauk'e nauyayyar ajiyar zuciya sannan ya shiga motar had'e da rufewa. 

Can k'arshe Maryam ta koma ta zauna ta b'oye fuskarta tana mai dariya k'asa-k'asa, ji tayi yace "Maryam kin ganki? Ko dan na jima ban ganki ba shiyasa kika sauya min? Amma kin kyauta da kika b'oye min kanki har tsawon wannan lokaci, in ba haka ba zan iya ta'asa irin wannan kyallin kyau da kikayi" bata tanka sa ba kuma bata d'ago ta dubesa ba hakan yasa ya janyo ta kusa dashi yana mai lalubo fuskarta, bata hanasa ba dan tasan yayi kewar ganin fuskarta, sati uku kenan bata bar shi ya ganta ba dan tana son yayi d'aukin ganinta.

D'agowa tayi tana mai kallonsa da wani sigar da ya kasa tantance kalarsa, baiyi wata-wata ba ya kai bakinsa kan nata yana mai lumshe ido tare da shauk'i da kwad'ayin d'and'ana zak'in leb'b'anta, ji yake kamar bazai kai ga abinda yake muradi ba.

Baiyi nasarar samun abinda yake ransa ba sakamakon d'aura yatsunta biyu da tayi akan nasa lips d'in tana mai langwab'ar da kai sigar shagwab'a, idanunsa ya bud'e wanda ya canja launi yana dubanta alamar "why?" Bakin ta turo sannan tace "kaga lipstick d'ina zai b'ata ka kuma fita zamuyi taron jama'a, banson ka b'ata lips naka haka banson ka b'ata min kwalliya na, dan kaga aurena shine kad'ai zan na tunawa yana sani nishad'i" ta d'age gira tana cewa "ka gane ai" bai samu damar amsawa ba aka k'wank'wasa mirror na motar ana cewa "ku fito toh, kun ajiye mu muna zaman jira bayan anjima zaku kasance da juna, wannan wani irin azarb'ab'i ne da rashin hak'uri" cewar Muslima k'awar Maryam.

Bata jira cewar shi ba ta b'alle murfin k'ofar ta sa k'afarta waje, hannunta da ke cikin nasa tayi k'ok'arin janyewa amma yak'i bari, kallonta yakeyi haka zalika fuskarsa ya nuna bai so hakan ba, dawowa tayi ta d'ago fuskarsa tana cewa "hey mr. Handsome, Maryam is now yours, officially wed." Ta fad'i hakan tana mai d'aga masa gira.

Bai daina kallonta ba kuma bai tanka ta ba, hakan yasa ta dawo cikin motar ta rufe k'ofar ta had'e rai kamar zatayi kuka tana cewa "ai sai kayi yanda kakeso, gani nazo" yanda ta turo bakin ya bashi dariya, bai san lokacin da ya k'ank'ameta a jikinsa ba yana cewa "I Love You Maryam, atleast ki barni insan an d'aura mana auren mana" ya cirota daga jikinsa ya manna mata peck a kumatu yace "ashe kin damu dani ban sani ba, come-on mine, let's go" murmushi tayi ta fice daga motar.

Hannunta yake k'ok'arin rik'ewa dan shiga katafaren hall d'in da aka k'awata da abubuwan k'yalk'yali da wutar da ya haske wurin ke kya ce dare ne, nok'e hannunta takeyi tana hana shi, sai da yayi mata magana a kunne sannan tace "Baba dai nake tsoron ya ga video d'in, zai ce rashin kunya ne" kallonta yake da mamaki "Matata ce fa ke? Meh laifi dan na rik'e hannunki?" Bata kawo komai ranta ba tace "nidai kayi hak'uri a gama bikin nan lafiya kada Baba ya samu abun fad'a" baki bud'e yake kallonta dan bai gane abinda take nufi ba, kallon da yake mata yasa ta tuno da maganar da tayi, cikin i'ina ta fara cewa "Allah tsoronsa nake yagani".

Bai tanka ta ba ya kamo hannunta ya fara tafiya, batayi k'ok'arin k'wacewa ba dan idanun mutane na kansu haka zalika yanayin d'amk'ar da yayi bazata iya k'wacewa a sauk'i ba, su biyu ke gaba sai Mufeedah da Abdallahnta a baya sai k'awayensu da ke biye dasu. Kid'an da aka sake musu ya basu damar takawa ahankali, tuni Maryam ta mance da batun Baba ta shiga rawa ahankali cikin nutsuwa, bakin nan har kunne ta kasa daina murmusawa. Sai da suka tik'i rawa dukkansu a tsakiyar fili kamar bazasu daina ba MC ya dakatar yana mai cewa amare su isa kujerunsu da aka tanadar domin su.

Party yayi party anci ansha an danse, anyi hotuna kamar ba gobe, anyi lik'i dai-dai gwargwado, k'aton cake d'in da akayi mai parts biyu yafi d'aukan hankalina, sai da na d'auki hoton a wayana dan burgeni da yayi. D'aya an rubuta "M&M" d'aya an rubuta "A&M", couples d'in kowa b'angaren sunansa ya tsaya, sai da su Maryam suka yanka nasu cake d'in sukayi feeding juna sannan Mufeedah sukayi nasu. An gama komai k'alau an fara watsewa sannan Maryam ta tuno Baba da fad'an da zaiyi in yaga shagalin da akayi, duk da ba wani abun rashin kunya akayi ba amma ita tsoronsa take, abun fad'a baya masa kad'an.

"Mustapha magana nake" kallonta ma baiyi bare ya amsata, ya gaji da yi mata explaining akan Baba bazaiyi fad'a ba, sai da ta sake magana sannan yace "Maryam kinsan banson abinda kikeyi? Ranar auren ma bazaki barni inyi yanda nakeso ba? Wai Baba meh zaiyi dan yaga yaransa suna cikin farinciki sun auri wad'an da suke so?" Shiru Maryam tayi dan taga alamar ba gane mata zai yi ba. Sai da suka sallami kowa sannan suka fara shirin tafiya gida da sauran k'awaye da abokansu da suka saura. Shi da Maryam motarsu d'aya Mufeedah da Abdallahnta motarsu d'aya.

Basu bar harabar wurin ba sai da kowa ya shiga motarsa, zaune suke a baya hannunsu sak'ale da juna, Maryam dai fara'arta ba kaman da ba duk yanda taso ta d'auke tunaninta akan abun nan ta kasa. Numfashin Mustapha da taji a fuskarta yasa ta dawo da dubanta garesa, matsawa baya tayi dan dauriyarta ya k'are, abunda yake k'ok'arin yi mata yafi k'arfinta. 


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 38


"Please stop" tace tana mai sauk'e kanta k'asa, kasa kallon fuskarsa tayi dan bazata iya ba tana jin nauyinsa, ita duk karance-karance da hirar ta da k'awaye tasan ana iya ganewa in sun shiga irin wannan yanayin, ita kuma gani take bazata iya had'a ido da kowa ba in aka gano ya tab'a ta ko wani abu ya shiga tsakaninsu.

Murya can k'asa yace "what's your problem?" "Ni kunya nake ji, kuma ai kai ne kak'i min abunda nakeso" sauk'e numfashi yayi yace "meh nak'i miki? Wai dan nak'i sake hannunki d'azu? Ji yanda za'ayi tunda Baba ne bakison ya gani" ya gyara zamansa sannan yace "kinga wannan event d'in da akayi da wanda za'ayi gobe na bud'an kai ko meh ne kuke k'iransa, su cassette d'aya za'a sa, wanda Baba zai iya gani kuma ai na d'aurin aure da walima ne?" Ta gyad'a kai alamar eh sannan ya cigaba "su kuma sai a sa su wuri d'aya, wancan na events namu, na walima da aure kuma na manya" sai da ya kalleta da kyau sannan yace "hakan ya miki?" Murmushi ta sake tana tafe hannu had'e da girgiza kafad'arta, ko batayi magana ba hakan na nufin ta amince da hakan.

Musa da yake jan motar ya juyo dan jin k'arar tafin da Maryam ke yi yana cewa "toh dai, kamar ba ita na gani tana had'e rai ba d'azu. Wai kai Musty ba jan aji ne, ka manta yanda ta gwara kanka kafin ta yadda ta aureka?" Ya fad'i hakan da alamar wasa, Mustapha yace "meh na juyowa bayan kasan ma'aurata ne anan? In kaga abinda yafi k'arfinka sai kace meh?" Musa yace "ka bini ahankali ko inyi parking anan ka isar da matar taka gida" dariya sukayi dukka sannan Maryam tace "ayi mana afuwa nikam a mayar dani gida" nan dai hira ya kaure tsakaninsu, suna yi suna tsokanar juna har suka iso harabar gidan. 

Nesa da mutane ya kai su da zai fita yace "kuyi sallama tun yanzu, kunsan dai bazaku had'u ba sai gobe" ya nuna Mustapha yace "yanzu zan mayar dakai gida kaga lokacin d'aukan amare yayi, minti biyar na baka dan ta samu ta shiga ta d'an shirya ta fito mu kaita". Mustapha bai yi musu ba dan yasan halin Musa yana fad'ar maganar da baiyi masa ba zai fasa fita daga motar ya fasa bada minti biyar d'in. Fitar sa ke da wuya ya janyota jikinsa "kin wani biye masa sai hira kike kin manta dani" kanta ta sauk'ar tana dariya k'asa-k'asa, juyo da fuskarta yayi yana kallonta, ita kuwa ta runtse idanunta, tuni k'irjinta ke bugu wanda ta rasa gane dalilin bugunsa. 

Jin leb'b'ansa tayi bisa nata hakan ya sa ta ware ido, mamaki ne ko tsoro na rasa gane mata, ahankali yake k'ok'arin janyota kusa dashi, hannunshi da ya kai bayanta yasa ta jin wani shock, bata san lokacin da ta runtse idanunta ba tana jan numfashi. Kamar an tsikareta taji wani k'arfi ya zo mata ta cire hannunsa tana mai janye bakinta. Bai ji haushinta ba dan yasan in bata hana ba abun zaifi haka, shiru sukayi dukkansu na d'an wani lokaci.

"Look at me my pretty girl" juyowa tayi kamar zatayi kuka ta rik'o hannunsa, ta dai kasa kallon fuskarsa dan nauyinsa da take ji, d'aura hannunsa tayi dai-dai zuciyarta tana cewa "duk kasa zuciyana ya tsinke, kaji yanda yake bugawa? nikam bazan sake yadda a bamu ko 2minutes bane tunda tsorata ni za ka na yi" dariya abun nata ya basa, bai iya cewa komai ba sai "sorry" juya masa baya tayi wai ita tayi fushi tayi ido hud'u da Baba da yake kallon cikin motar k'uri da idanunsa, bata san iya mintunan da yayi ba, da alamu dai daga d'akinsu Jabir ya fito.

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, na shiga uku" tace, Inda take kallo Mustapha ya kai dubansa, Baban dai shima ya gani, ji yayi zuciyarsa ya tsinke, kansa ya sauk'ar k'asa yana mai jin nauyin kallon da Baba ke jifansa dashi. Bata sake masa magana ba ta bud'e k'ofar ta fita, ko ta kan Muneerat batayi ba bare jiran sauran k'awayen nata tayi cikin gida. Wanka ta fad'a tayi kamar yanda aka umarceta da ta shigo ta sauya kaya zuwa atampa riga da skirt, powder kawai ta shafa sai man baki, mayafin ma Anty Fatima ce ta yafa mata. 

A d'akin Mama suka had'u da Mufeedah cikin shige irin nata, had'e su akayi dan musu nasiha kamar yanda al'adar bahaushe yace. Bayan iyaye mata sun gama nasu aka kai su d'akin Baba dan shi ma yayi musu nasa, Momy ce tayi musu jagora sai Anty Fatima da ke binsu a baya, wuri suka samu a k'asa suka zauna duk kawunan amare a k'asa, Momy ce tayi magana "toh Alhaji ga 'ya'yanka nan za'a kai su gidan mazajensu, kayi musu fad'a had'e da nasiha kamar yanda kowani uba ke wa 'yar sa in za'a kaita gidan aurenta".

murmushi Baba yayi wanda har sai da ya fitar da sauti, babu wani kalmar da ya fito daga bakin baba sai "yaran da suka san komai tun a waje meh zan sake fad'a musu? Allah ya raba ni da fitsararrun 'ya'ya, Allah kuma yasa mazajenku su iya zama daku a yanda kuke, nidai nasan ban bawa yarana tarbiyyar iskanci ba" bai k'ara komai ba akan hakan, haka zalika ko da wasa bai nuna yaji haushin furucin da yayi ba.

Nidai banyi mamakin maganarsa ba dan nasan za'ayi hakan ko ma fiye, amma Momy bakinta bud'e take kallonsa, haka Anty Fatima. Muneerat da ke lullub'e cikin gyale har d'agawa tayi tana kallonsa, da yaga kallon yayi masa yawa ya tashi ya fice ya bar musu d'akin, nidai banda kuka babu abinda nakeyi, dan maganarsa ta dakeni, tsorona d'aya kada maganarsa ya bi mu ya hanamu zaman gidan miji.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 39


Haka aka d'auki 'yan matan nan zuwa gidajen iyayen mijinsu kamar yanda al'adar gombawa yake, ranar aure ana kai yarinya gidan iyayen miji, a can za'ayi wunin biki sai yamma a kai su gidajen mazajensu, haka wannan ma akayi, an kai Maryam gidan iyayen Mustapha, Muneerat kuma gidan iyayen Abdallanta, a can suka kwana washe gari akayi bud'an kai na Maryam a Laila visitors suite, na Muneerat kuma a wani k'aton fili aka k'awata da kayan ado sai manyan speakers da aka ajiye a center da kuma wasu kusurwar filin dan cashewa.

Anci an sha an cashe, anyi b'arnar kud'i, dan Mustapha da yazo bud'e kan amaryar tasa makullin mota ya ajiye mata sannan yayi mata lik'i da dollars, 'yan uwansa mata fidda raini sukayi dan a cewarsu basu son raini, lik'i sukayi mata na dubbai, yara kuma d'ari biyar-biyar suka lik'a ma amaryar yayansu, Anty Fatima da ke gefen amarya duk kud'in da aka lik'a wa amarya take kwasa ta zuba a cikin jaka, a cewarta kada wasu su kwashe bayan na amarya ne.

Da wuri aka gama dan mutane su samu halartar na Muneerat, da misalin k'arfe hud'u aka fara gabatar da nata wanda har amarya Maryam sai da ta halarci bud'an kanta, nan ma sunyi bidiri dai-dai k'arfinsu, kuma amarya Muneerat ta samu kyautuka fiye da yanda mutane sukayi tsammani. Yamma lik'is aka kai kowacce gidanta, masu ganin gidan amare suka gani, sai da kowa yayi sallar maghrib sannan aka watse, kafin isha'i ba'a bar kowa gidan amare ba.

K'arfe tara Maryam taji dirin motar Mustapha lokacin tana toilet tana alwala, da hanzari ta fito ta d'aura d'an kwalinta sannan ta hau kan gadon ta janyo mayafinta ta yafa, ruwan fuskarta ta goge da hannunta ta tuna ta wanke kwalliyarta, jin alamar ya shigo pallon yasa ta hanzarin tashi ta janyo jakarta da aka ajiye mata a cikin wardrobe ta koma da gudu kan gadon, daidai ta yaryad'a powdern a hannunta ta goga akan kumatunta na dama taji muryarsa a bakin k'ofarta yana cewa "yanzu zan kawo maka, kafin ka cinye ni".

Hakan da taji yasa ta gane ba shi d'aya bane, ajiye powdern tayi ta janyo mayafin dan ta rufa akanta, tun kafin ta aikata hakan ya shigo, hakan yasa ta rufe fuskarta da mayafin ta danne da hannayenta, zaman 'yan borin da tayi akan gadon take k'ok'arin gyarawa, tak'i bud'e fuskarta dan farar powder ne bata son ya gani, k'aramin aikinsa ne ya samu abin tsokana.

Jinsa da tayi a gefenta yasa ta cewa "ai sallama akeyi" cewa yayi "au na manta, akwai abinda nakeson ganewa ne, naga sai b'oye fuskar ake bayan ba haka amare suke yi ba" hannunsa ya sa kan mayafin yana k'ok'arin janyewa daga fuskarta yana cewa "tsaya in koya miki yanda akeyi, ina ce akai ake d'aurawa" kawar da fuskarta tayi gefe tana cewa "um-um please, ka fita kayi sallama sannan ka sake shigowa", cigaba da janye mayafin yake yana cewa "sai naga abinda kike b'oyewa zanyi yanda akeso" kokawa suka fara yi, tana cewa dan Allah ka bari, basuyi aune ba suka ji an k'wank'wasa k'ofar ana cewa "mun tafi mukam, da baka ce mu shigo ba ai tunda kasan ajiye mu zakayi".

Murya ya d'aga yana cewa "sorry friend, gani nan zuwa barin kawo maka" tashi yayi ya koma wurin dressing mirror ya d'auki key, jinsa da tayi a nesa da ita yasa ta sake hannunta, batayi tsammani ba taji ya fizge mayafin sai idanunta k'uru-k'uru da farar hoda a kumatunta. Fashewa da dariya yayi ya fice daga d'akin bai daina dariyar ba, bawa abokinsa makullin yayi ya basa hak'urin rashin fitowa da wuri sannan ya koma d'akin.

Kafin ya shigo ta gyara fuskarta ta koma mazauninta ta gyara mayafinta, zama yayi gefenta yana murmushin farincikin samunta, kanta a k'asa tana wasa da yatsunta, sai da ta gaji da kallon da yake mata tace "Ehmm! Kasan banson kallo da yawa ko, kana sani inji ba daidai ba fa" kawar da fuskarsa yayi yana mai sauk'ar da ajiyar zuciya "Maryam farinciki nake, you are now mine, har kwalliya ake min shine nake jin dad'i" ya fad'i hakan da sigar tsokana, ai kuwa ta tura baki. Sai da suka gama wasa da dariya sannan ya bata izinin tashi tayi alwala dan suyi sallah, kai tsaye tace "nayi ai, sallar isha'i zanyi ka shigo". Dafe goshi yayi yace "Oh Maryam, bakiyi sallah ba kika bari mukayi ta hira, tashi kiyi sallah sai muyi namu sallahr".

Sai da ya jirata tayi sallahr isha'i sannan sukayi nafila raka'a biyu, yayi mata tambayoyi akan addini ta basa amsa daidai gwargwado kuma ya yaba da k'ok'arinta. Sai a sannan ya rik'e hannunta suka fito palor. Fresh yoghurt, fruits da naman da ya shigo dashi ya d'auko plate ya zuba musu, kamar yanda kowace amarya ke nok'e-nok'e daren farko haka Maryam tayi. Daga nan suka koma d'aki suka raya wannan dare mai albarka cikin jin dad'i. 

Daren Muneerat da Abdallahnta haka ya kasance, cike yake da albarka da nutsuwar da kowannensu ya samu. Amaren biyu sunsha yabo da albarka daga wurin mazajensu kasancewa sun same su kamar yanda kowace budurwa kamila ake samunta, tun daga ranar har zuwa satin auren sosai suke nunawa junansu k'auna da kulawa kamar su had'iye junansu. An kawo cassette na biki an raba, kowa an bashi nashi, manya nasu daban haka k'awaye da abokai daban.

Ranar da aka cika sati ya kama asabar, da misalin k'arfe takwas da rabi Maryam na zaune akan kujerarta a palor tana kallo taji wayarta na ringing a d'aki, da hanzari ta tashi har da sassarfa dan kada ya katse, a tunaninta habibinta ne dan ya fita gidan iyayensa kuma ta bashi sak'on sayo mata ice cream, tana kyautata zaton k'iranta yayi ya tambayeta wani flavor takeso. Sis Muneerat ta gani akan screen na wayar, sai da tayi murmushi ta d'auka a ranta tana cewa (sistar nan tawa tana ji dani, d'azu da safe dai mukayi waya).

Muryar Muneerat taji tana cewa "kinji abinda Baba yakeyi a gida?". Cike da fargaba tace "a'a meh ya faru" ta k'arashe maganar da alamar zak'uwa. Nan ta labarta mata Baba ya ga cassete na events "yanzu haka fad'a yake a gida wai zamu b'ata masa suna, tun d'azu nakeson k'iranki Abdallahnah yana nan banson yaji, sai yanzu na samu sarari, na d'auka Nasreen ta k'iraki".


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 40


Cikin muryar ta da ke nuna bata ji dad'in abinda baba yayi ba tace "ya Baba zai mana haka? An d'aura aure sannan akayi events, shiyasa da kuke ta cewa ayi events kafin aure nak'i, abinda nake gudu kenan kuma gashi a hakan ma ya faru" Muneerat tace "hmm abun nan ya dameni, kinsan wai da Jabir yake fad'a masa hakan ba laifi bane tunda an d'aura aure kawai ya hau kansa da masifa yana ce masa d'an iska, kinsan ranar auren nan bamu dawo da wuri daga gun events ba" Maryam tace "eh" Muneerat ta cigaba da cewa "Jabir da Usama sun dawo da wuri su da abokansu, is like wai wak'a suka sa suna cin abinci ana hira tsakanin friends kawai Baba ya shigo ya dinga bala'i yana zage-zage wai sun cika masa gida da wak'a, basu gama cin abincin ba ma abokansu suka ce sun tafi" Maryam tace "eh ai na gansa lokacin ina tare da Mustynah, ashe lokacin ya gama masifar kenan?".

"Hmm ai ki bar mutumin nan, yanzu maganar da nake miki Jabir ya tattara kayansa zai tafi Abuja wurin aikinsa, Usama ma yace zai bi sa. Abun takaicin ma wai da Jabir yace ba laifi Baba ya hayayyak'o har da marinsa, abun da yafi bashi haushi kenan yasa yace zai tafi shi bazai iya ba ya gaji". Maryam tace "yanzun tafiya zasuyi gobe? Tsaya in k'irashi yanzu, in munyi magana zan k'iraki" ta katse wayar.

Jabir na kan gadonsa kwance ruf da ciki idanunsa a lumshe wayarsa ta fara ruri, kamar bazai d'aga ba dan jin jikinsa yake a mace, laluba wayar yakeyi akan gado ba tare da ya bud'e idanunsa ba, sai da wayar ta katse sannan ya samo ta, bai duba wanda ya k'irasa ba ya rik'e wayar a hannunsa, zuciyarsa a cunkushe ya rasa meh zaiyi a rayuwarsa yaji dad'i. Wayar da ke hannunsa aka k'ara k'ira, bud'e idanunsa yayi ahankali yaga sunan Sister a rubuce, sai da ya ja d'an guntun tsaki sannan ya d'auka yace "hello" ahankali kamar marar lafiya, ko gaisuwa bata tsaya sunyi ba ta fara:

"Jabir please kada ka tafi irin na da, in ma ka tafi aikinka kana zuwa time to time, Usama kuma ba anfanin tafiyansa tunda ga shops na Mamansa yana dubawa, kai dai da zaka je aiki ka tafi dan ya zama dole, amma Usama ba anfanin tafiyarsa" tsakin ya sake ja sannan yace "dan Allah Maryam ki kyalemu, kowa yayi rayuwarsa yanzu kam" Maryam tace "kasan Allah in kuka tafi baku ji maganar mama ba, yanzu ma zan k'irata in fad'a mata" kai tsaye yace mata "ki fad'a mata, nidai babu wanda zai hanani tafiya, sai ki k'ira Usaman ki hana sa, amma ni aikina zanje so am out of this" yana gama fad'ar haka ya kashe wayar gaba d'aya. 

Haka ta k'ira Usama yace mata tafiya kamar yayi, babu irin hak'urin da bata basa ba yace tayi hak'uri zasu na duba k'annensu amma bazai zauna a gidan ba shi kam. Ta gama waya dashi kenan tana shirin k'iran mama Mustapha ya shigo, murmushi ta sakar masa ta isa wurinsa tana masa sannu da dawowa, bata isa inda yake ba kamar yanda ta saba, in ya fita ya dawo tana masa welcome hug+peck a kumatunsa. Yana kallonta ya gane akwai abinda yake damunta, isowa yayi inda take ya janyo ta jikinsa ba tare da yayi mata magana ba.

Shiru sukayi na d'an wani lokaci sannan yace "what's wrong wify?" Ya fad'i hakan yana mai cire d'an kwalin kanta tare da mayar da gashin kanta baya wanda a ranar ta tsefe shi ta wanke ya taya ta sukayi stretching gashin, gashinta ba bak'i bane sannan bayi da tsawo sosai ya dai sauk'o mata wuya, gashinta irin gashin nan ne da ake k'ira rubber hair, stretching d'in da akayi shi bashi damar sauk'owa kafad'arta. Mayar da gashin yake baya yana mai cewa "bazaki fad'a min ba ko? Naji kada ki fad'a min" ya cirota daga rungumar da yayi mata ya rik'e kafad'unta yana mai kallonta cikin ido, tun tana kallonsa ita ma kamar yanda yake kallonta har taji kunya ta sauk'e kai, kamar bazaiyi magana ba yace "something is wrong with you am sure, in baki wuri kiyi abinda kike da niyyan yi? Naga kamar waya kikeson yi da nazo kika ajiye wayar kamar mara gaskiya".

Kallonsa tayi tana mai langwab'ar da kai "babu komai fa, trust me ina da gaskiya, Mama nakeson k'ira zamuyi magana" murmushi yayi sannan yace "ok, ina palor in kin gama" ya juya zai fice daga d'akin ta dakatar dashi da cewa "fushi kayi?" taku uku tayi ta iso inda yake, rungumarsa tayi ta baya tana mai d'aura kanta a bayansa had'e da kamo hannayensa ta gaba ta furta "I'm sorry please kada kayi fushi" juyowa yayi yana mai kallonta da mamaki yace "meh zai sa inyi fushi? Banyi ba Allah ina jiranki, ki gaida Mama kinji? All I want you to know is that I love you and I will be with you in good and bad times".

Sai da sukayi exchanging sweet words tsakaninsu sannan ya bata damar k'iran mahaifiyarta, yana fita ta danna mata k'ira ba tare da ta lura da lokaci ba, Cikin bacci taji k'arar wayarta, a hankali ta tashi ta isa wurin wayar tana mai duba wanda yake k'iranta a wannan lokacin. Ganin 'yar ta yasa baccin da take ji ya wartsake da hanzari ta d'aga wayar, bata amsa gaisuwar Maryam ba ta tambayeta lafiya? Maryam bata b'oye komai ba ta sanar da ita abunda ya faru da abinda yake shirin faruwa. Basu ajiye wayar ba sai da Mama ta tabbatar mata zata yi magana da yaran nata kuma komai zai koma dai-dai suyi ta addu'a. 

A cikin daren mama ta k'ira Usama, hak'uri nan ma ya bata yana cewa shi tafiya zai yi, babu yanda bata yi ba daga k'arshe ma k'arya yayi mata akan wayarsa zai d'auke ba caji, gobe kafin su tafi zai je dan suyi sallama, ba ta so hakan ba amma babu yanda ta iya kuma bazata iya sa shi dole ba, in tayi haka kamar ta tauye masa hak'k'i ne a ganinta, shiyasa ta yi masa maganar a matsayin shawara da kuma abinda ya dace. Bata nemi Maryam ba dan bata son ta d'aga mata hankali kuma tasan tana tare da mijinta bazata so ta zama watsatstsiyar uwa mai k'iran 'yan'yanta da tsakar dare ba bayan tasan suna da mazajensu kusa dasu.

A ranar dai Mustapha ya kasa gane wa Maryam, kwance take bisa k'irjinsa amma bacci ya kasa zuwa mata sai motsi takeyi, daga k'arshe ma da taga ya jima baiyi magana ba ta d'auka bacci yayi ta koma gefe ta kwanta tana mai hasashen meh Mama suka yi da Usama. Bacci b'arawo shi ya sace ta bata san lokacin ba, ita dai Mustapha ya tashe ta dan tayi sallahr asuba.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 41


Da safe ma haka tayi iya k'ok'arin ta dan kada Mustapha ya gane wani abu, amma abinda bata gane ba shine tuni Mustapha ya gane akwai matsala kuma tabbas daga gidansu ne, sai da sukayi breakfast sannan Mustapha yayi wanka yayi shirin fita. 

Sun fito bakin k'ofar bedroom nasa suna tsaye tana gyara masa bottles na rigarsa shi kuma yana gyara hularsa tace "saurin meh kakeyi haka? Yau fah Sunday ai kamata yayi ka fita lokacin da kayi niyya" murmushi yayi ba tare da ya kalleta ba yace "kinsan kwana biyu ban fita aiki ba, ranar Friday da naje naga alamar sun min kwab'a, kuma kinsan baba laifina zai gani ba nasu ba tunda ni aka bawa wannan aikin" murmushi ita ma ta sakar masa tana mai karb'ar hular hannunsa dan ta gama gyara bottles d'in, sai da ta gyara masa hular dab'as a kansa sannan tayi baya tana kallonsa daga sama har k'asa, yatsunta ta d'aga tana mai kad'a kai alamar yayi kyau ya fito very fine. 

Wayarta da ta bari a d'akin ya fara ruri, hannunsa ya mik'a daga bakin k'ofar ya d'auko mata wayar ya mik'a mata yana mai cewa "Mama ce" da hanzari ta iso kusa dashi ta karb'i wayar ta kara a kunnenta, da gangan ya janyo ta kusa dashi yana mai kallonta cikin ido, gaisawa sukayi sannan mama ta sanar da ita yanda sukayi da Usama "yanzu suka bar nan, babu yanda banyi dashi ba yak'i, yace in ya huta zai dawo da kansa, kada mu dam wai dan ba irin tafiyar da muke tunani zasuyi ba". 

Idanunta taji sun cika tam da hawaye ta kasa yi wa mama maganar arziki, sallama sukayi ta kashe wayar tana mai k'ok'arin hana hawayen da ke idanunta sauk'owa, kanta ya d'aura bisa k'irjinsa yana mai shafa bayanta, zuciyarta da ke mata zafi yasa ta kasa daure kukan, dama kuka bai mata wahala, kuka mai sauti ne ya kufce mata, abu d'aya ya furta mata "cry as much as you can, I will wipe away your tears bazan tab'a gajiya ba, i don't want to see you depressed, kiyi kuka in shine zai iya kwantar miki da hankali" sai da ta gaji dan kanta sannan tayi shiru.

Hannunta ya rik'e suka koma d'aki ya kwantar da ita, bai nemi jin damuwarta ba saboda yasan ba fad'a masa zatayi ba, AC ya kunna mata ya lullub'e ta da bargo sannan ya bar gidan yana mai tausaya mata, a lokaci d'aya kuma yana mai jin haushin k'in yarda dashi da bata yi ba har yanzu. Dak'yar ya iya kawar da wannan tunanin daga ransa dan ya samu yayi abunda ya fito dashi, bai koma gida ba sai bayan sallahr azahar. Ta tarbesa kamar yanda ta saba ta gabatar masa da abinci sannan yayi wanka.

ใ€ฐใ€ฐใ€ฐใ€ฐใ€ฐใ€ฐใ€ฐใ€ฐใ€ฐใ€ฐใ€ฐใ€ฐใ€ฐใ€ฐใ€ฐใ€ฐ

A kwana a tashi ba wuya yau wata uku da faruwar hakan, rayuwa tana tafiya cikin kwanciyar hankali, Usama da Jabir suna can Abuja sunk'i dawowa, anyi musu magana har an gaji amma babu abinda ya sauya, tun Maryam bata nuna damuwarta har ta fara nunawa, ita a rayuwarta bata da wani burin da ya wuce had'in kan familynta, amma kullum sai k'ara tab'arb'arewa yake, a da ta d'auka dawowarsu Jabir zai canja komai amma ashe ba haka abun yake ba, addu'arta d'aya Allah ya kawo musu canji a cikin rayuwarsu.

Yau Maryam tun safe ta tashi ba lafiya take jin ta ba, ji take ranta na b'aci zuciyarta na k'una sakamakon mafarkin da tayi akan Jabir, Usama da Baba. Tun da safe Mustapha ya gane hakan dan murmushin kirki bai samu ba sai dai ta k'ak'alo kamar dole, yau dai yayi alk'awarin sai Maryam ta fad'a masa damuwarta, in tak'i kuwa hakan zai tabbatar masa da zarginsa gaskiya ne.

Sai dare ya sameta a d'aki tana kankare farshenta da ta shafa nail lacquer(cortex) (wankan tsarki zatayi shiyasa take kankarewa, takan shafawa a lokacin da take al'ada dan kwalliya, amma da zarar ta gama zata kankareshi tsab sannan tayi wankan tsarki) kumbure-kumbure take tana zancen zuci bata san ya shigo ba, zama yayi gefenta ya d'an ture kafad'arta da nasa kafad'ar. Waigowa tayi ta kallesa tana mai sake masa murmushi sannan ta cigaba da abinda takeyi.

"Ina so muyi magana" ya fad'a a tak'aice yana mai d'aure fuska alamar ba maganar wasa yazo mata dashi ba, ajiye abun hannunta tayi tana fuskanto shi tare da tattaro hankalinta gaba d'aya ta damk'a masa, tace "ina jinka ranka ya dad'e" hannunta ya rik'e ya sauk'e ajiyar zuciya "ni mijinki ne ko? Kuma kinsan ina sonki?" Kad'a kai tayi tana mai yi masa murmushi "meh yasa ka tambaya bayan abinda ka tambaya a bayyane yake?" Kai tsaye yace "saboda ina son in tabbatar kin d'auki hakan a kanki ba wai a baki kawai ba" ya numfasa sannan ya cigaba "Maryam tun kafin muyi aure na fuskanci kina da damuwa, bazan iya cewa ga dalili ba amma ina kyautata zaton family issue ne, akwai abinda nakeso ki gane da ni, mijinki ne ni kuma ina sonki, bana son ganinki cikin tashin hankali, a ko da yaushe ina son muyi farinciki tare muyi bak'in ciki tare amma kink'i bani dama, yau dai ina son ki fad'a min damuwarki ko shawara ne in baki, na gaji da ganin yau kin tashi cikin farinciki gobe akasin haka".

Shiru tayi kamar bazata amsa ba kanta a k'asa, ya bud'e baki zai fara wata maganar yaga ta d'ago tana kallonsa da hawaye ya malale fuskarta, share hawayen tayi tana mai yi masa murmushi sannan tace "na san kayi k'ok'arin hak'uri da yanayi na a duk ranar da na tashi cikin b'acin rai kamar yau, amma ba laifina bane da nake kasa b'oye damuwata akan family nah...." Nan ta fayyace masa komai, tafiyar su Jabir ta farko da tafiyarsu a yanzu, tayi k'ok'arin b'oye wasu halaye na baba kamar mak'o da rashin sakin fuska da kuma rashin yarda da wani sai kansa, amma ta fada masa yawan fad'ansa da baya kan kowa, duk wanda yayi abu in bai masa ba sai yayi masa fad'a babu ruwansa da ina ya dace, wa ya dace ko kuma abinda ya dace ayi fad'a akai. 


Ta fad'i hakan dan ya zamo hujja game da barin su Jabir gida, ta fad'a masa hanyoyin da suka bi dan nunawa baba illar hakan amma ya faskara. Kallonta yayi cike da mamakin maganarta "hakan kad'ai yasa suka bar gida ko akwai abinda kike b'oye min?" Sauk'e kai tayi k'asa dan bata tsammanin akwai ranar da zata fad'a masa halin Baba daga farko har k'arshenta, in dai yana da shawara ya bata kawai shine matsalarta, numfasawa yayi yace "alright, naga alamar akwai wasu dalilan wanda baki son fad'a, but am happy anyway tunda kin sa ni a cikin matsalarki" ya d'ago fuskarta yana kallonta yace "kamar ina da shawara Maryam, let's try this ko Allah zai sa Baba ya gane manufarku".


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 42


"Shawarata anan shine, tunda kince kunyi duk abinda kuke tunani bai yi anfani ba meh zai hana ku fito b'aro-b'aro ku fad'a masa abinda yake ranku? Kinsan wani lokaci mutane basu gane kwana-kwana sai an fito fili an fad'a musu ko ma meh ne, wata'kila Baba ma hakan ne, kuyi masa magana mai shiga jiki, kuyi masa magana daga zuciyarku, ku k'ask'antar dakai ku nuna masa shi babba ne sannan ku fad'a masa abubuwan da yakeyi, daga bisani ku nuna masa illar hakan da abunda ya haifar kamar tafiyar yaransa, ku nuna masa yanzu ne lokacin da yake buk'atar yaransa kusa dashi, in yana haka bazasu so zama dashi ba bare su dafa masa akan sana'o'insa" sai da yayi mata bayani dalla-dallar abinda ya dace suyi sannan yayi musu addu'ar samun nasara tare da k'arfafa mata gwiwa.

Sun tsayar da magana akan gobe zata k'ira 'yan uwanta dukka dan su had'u suyi masa maganar tare kamar yanda Mustapha ya bata shawara tayi hakan, taya ta yayi suka kankare farshen tayi wanka ta fito tayi sallahr isha'i had'e da nafila sannan suka kwanta bacci mak'ale da juna.

Ta k'ira 'yan uwanta dukkansu kuma sun bada goyon baya, sun tabbatar mata zasu halarci taron, Usama ne kawai ya kashe mata jiki dan cewa yayi "Baba bazai canja ba sai duniya ta waina sa, ku daina wahalar da kanku" dak'yar dai ya yarda zasu dawo tare da Jabir in ya kar'bi hutu daga gun aikinsa. Anty Fateema tayi farincikin wannan gayyatar da aka mata kuma tayi na'am da wannan shawarar, sun ajiye ranar lahadi mai zuwa zasu hallara a palon Alh. Muktar da misalin k'arfe goma na safe. 

Sai da suka gama had'a komai tsakaninsu sannan ta fad'awa Mama da Momy, addu'a suka bi su dashi suna mai sa musu albarka, lokacin da Momy ta fad'awa Baba 'ya'yansa zasu zo magana dashi ranar lahadi cewa yayi "meh zasu zo su fad'a min" "ban sani ba nikam, ka k'irasu ka tambayesu dan ni sak'o aka bani in isar kuma na isar". Bai sake magana ba ya bar d'akin, ko zai jira su ko bazai jira su ba oho, ita dai addu'arta Allah yasa hakan ya kawo sauyi a rayuwar gidan.

Ranar lahadi da misalin k'arfe tara Mustapha yayi parking a bakin k'ofar gidansu Maryam, hannunta ya rik'e yana mai yi mata murmushi "Allah ya bada sa'a, kina addu'a har ki shiga cikin gidan dan ki shiga da k'afar dama" ita ma murmushin ta mayar masa tana cewa "insha Allah mine" cikin zolaya yace "ko mu shiga tare ne in Baba ya koraku kika tsorata in kamo ki, dan naga alamar a rud'e kike kada ki fad'o ki sa ni jinya" bugunsa tayi a kafad'a tana mai turo baki sannan ta ajiye kanta a kafad'ar tasa tana, sai da ta d'auki lokaci sannan tace "tsoro nake, zuciyata na tsinkewa kamar baba bazai sauraremu ba" yatsarsa ya d'aura akan leb'b'anta yana cewa "shhshh! Ki daina fad'an haka Maryam, jiya kin kasa sukuni kin kasa bacci kina kai kukanki gun mahaliccinki, ko kin manta Allah baya bacci yana sane da komai kuma yana amsa addu'ar bayinsa? Be strong and trust me watarana sai labari". 

Kalaman k'arfafa gwiwa yake mata har sai da ya tabbatar ta samu nutsuwa sannan ya bata izinin shiga gida, fitowa tayi daga motar ta rufe tana mai d'aga masa hannu Muneerat ta iso cikin keke napep, bakin ta har kunne ganin yayarta da tayi, sai da ta biya mai adaidaita ta iso wurinsu tana mai sake musu fuska, rungume Maryam tayi sannan ta gaida Mustapha da ke cikin motarsa, bye yace wa Maryam sannan ya wuce su kuma suka shige gida hannunsu mak'ale da juna.

Dai-dai misalin k'arfe goma suka hallara a palorn Baba, Anty Fatima tun ranar asabar ta iso garin Gombe, Jabir da Usama flight suka bi ranar asabar, k'arfe sha-d'aya na safe suna garin Gombe. Kowa ya hallara a parlon banda k'ananan yara, Momy na zaune gefen Baba yaran kuma dukka suna zaune a k'asa.

Kamar yanda suka tsara haka abun ya kasance, Anty Fatima ta fara yi musu addu'a dan bud'e taro, Maryam ta fara bayani kamar haka "Alhamdulillah, kamar yanda muka buk'aci ayi wannan taro haka ya kasance an amsa mana buk'atarmu, mun gode da wannan dama da ka bamu Baba, Allah yaja tsawon rai ya k'ara girma" suka amsa dukka da "ameen" ta cigaba da cewa "taron nan dai zan iya cewa na k'aruwar mu ne gaba d'aya, kuma da muka taru anan ina da tabbacin kowannenmu cikin yara muna da abun fad'a bansan ga ku manyanmu ba" ta d'aga idanunta ta kalli Baba da fuskarsa babu yabo babu fallasa, idanunsa akanta yana son yaji mak'asudin taron da akayi, sauk'e idanun tayi a k'asa tana mai cewa "Baba maganar da muke tafe dashi mai nauyi ne, amma muna rok'onka da ka fahimce mu kuma ka bamu damar sauraran mu, sauraranmu da fahimtar manufarmu kad'ai muke buk'ata a wurinka a yau" shiru tayi dan jin amsar sa.

Tab'e baki yayi sannan yace "ina jinku, kada ku b'ata min lokaci dan ina da abunyi" ya fad'i hakan yana mai duba agogon hannunsa, Usama da yake gefen Jabir da yaga abinda Baba yayi "hmm" yace yana mai girgiza kai alamar abun nan dai bazai yi aiki ba ya kawar da kai gefe yana kallon window. Abinda yayi bai kashe mata gwiwa ba, murmushi ta sake sakar masa tana mai cewa "insha Allah, mun gode".

"Kamar yanda ka sani dukkanmu nan yaranka ne sai kuma matar ka d'aya wacce dukkanmu anan muka d'auke ta mahaifiya, mun tashi a gidan nan cikin had'in kan juna Alhamdulillah tsakaninmu yaranka haka zalika matanka kafin k'addara ya gifta tsakani Allah ya d'auki ran d'aya, rabuwa kuma ya shiga tsakaninku da d'aya, bazamu ce baka bamu tarbiyya ba dan in mun fad'i haka munyi k'arya, ka sa mu islamiya inda muka koyo addininmu haka zalika ka samu boko wanda a yanzu dashi muke samun gashin kanmu, bayan haka in munyi laifi kana gyara mu dan kada mu sake aikata wannan laifin, mun gode kuma mun jinjina maka" ta d'ago kanta ta kalli fuskarsa taga alamar yaji dad'in zancenta.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 43


Murmushi tayi sannan ta cigaba da cewa "d'an Adam tara yake bai cika goma ba kamar yanda hausawa suke cewa, amma abinda aka fi so shine musulmi yayi abinda ya wajaba a kanshi, ya biya mutane hak'k'ok'insu dan ya samu rabauta Allah ya jib'anci lamuransa haka zalika ya samu rahamarsa ranar k'arshe, na farko Baba abinda yasa muka kawo maganar nan shine hak'k'in yaranka da ke kanka, hak'k'in matanka, samun lokacin 'ya'yanka, fad'a akan abinda bai dace ayi fad'an ba sannan uwa uba inda ya dace ayi fad'an".

"Baba in ka kula da rayuwar gidan ka da yanayin yanda kake tafiyar da naka rayuwan zaka ga akwai gyara wanda sai ka kai zuciya nesa sannan za'a samu gyaran, da farko zan fara da tafiyarsu Jabir na farko, kamar yanda kowa yasan dalilin tafiyarsu nasan kai ma ka sani, amma barin fad'a saboda kafi gane abunda muke gudu, rashin basu hak'k'insu na kud'i, lokacinka, murmushin ka basu samu bare lokaci, fad'a da zagin iyayenmu yafi komai d'aga mana hankali, sai kuma kamar yanda nayi magana da Jabir na kula da akansu kawai fad'an nan da zagi da hantara yake zasu iya daurewa amma abun har akan iyayensu, kuma gabanmu kake yin duk wani abunda yazo ranka baka tunanin zamu ji zafin hakan, kuma akan abinda bai taka kara ya karya ba kake yi musu hakan, shiyasa suka gujeka suka guje mu baki d'aya dan bazasu iya ganin iyayenmu cikin bak'in ciki ba"

Fuskarsa da ya had'e kamar bai tab'a dariya ba ta kalla, da sauri ta kawar da kanta ta cigaba da cewa "illar hakan muke gujewa kuma da alama ta samu gurbi, na farko dai tsufa kakeyi kuma yaranka k'anana suna tasowa, in baka ja yaranka a jiki ka sa su a hanyar kasuwancinka ba wa zaka samu yayi maka jagoranci in k'arfinka ya k'are? In baka yarda da yaranka ba wa zaka yadda har ka bashi ragamar dukiyarka? In baka sake mana fuska ba tayaya zamu gane kana k'aunarmu har mu ma mu nuna maka ta hanyar kyautata maka? Illolin hakan suna da yawa Baba, shine muka zo da k'ok'on barar mu, ka duba abubuwan da muka fad'a maka muna fatar hakan yasa a samu gyara, yana da kyau magidanci yana zama yana duba yanayin rayuwar gidansa, yana adalci tsakanin iyalinsa ko baya yi? Yana kyautata musu ko baya yi? Yana basu hak'k'ok'insu ko akwai inda ya gaza ya gyara? Allah yana yafewa bawa abinda yake tsakaninsa da bawa ne kawai amma baya yafe abinda ke tsakanin bayi biyu har sai wanda aka cuta ya yafe, shiyasa ake son ka yawaita tunano irin abubuwan nan dan ka nemi yafiya daga wad'an da ka b'ata wa".

Maryam tayi masa nasiha kuma ta fad'i duk abinda ya dace ta fad'a Baba bai tanka ba, bayan ta gama ta dubi kowa a d'akin duk jikinsu ya mace dan nasiharta ta k'arshe ya ratsa kowa, tayi ne akan ranar k'arshe da zabar da mutum zai samu in ya shuka tsiya a duniya, bayan ta gama tace ko da akwai mai k'arin bayani, Jabir da Usama suka ce "a'a kin fad'i komai" haka Anty Fatima tace, Momy dake gefe ta d'an k'ara nata bayanin daga k'arshe kowa yayi shiru yana mai sauraran abinda Baba zai ce.

Kamar bazaiyi magana ba yayi gyarar murya ya fara da cewa "in na fahimci zancenku dukka kuna nufin in tsuguna in baku hak'uri na muku laifi koh?" A firgice suka d'ago suna kallonsa, babu wanda ya iya cewa komai sai Momy da take tafi tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, kai kam yaushe za a fad'a maka magana baka juya ta ta zama abun fad'a ba? Daga nema maka hanyar sauk'i yanzu ka kawo maganar bada hak'uri, cikin maganar Maryam da magana na waye yace ka bamu hak'uri? In har bamu hak'ura ba kuma bamu son rahamar Allah ya shafeka ai bazamu kawo maka maganar ba shiru zamuyi, in munje lahira ka bamu hak'k'inmu, maganar da yaran nan suka kawo maka shine suna so ka canja, tunda su sun d'auka suna so k'annensu suji dad'i kuma su hutar dakai ka zauna a gida su cigaba maka da sana'arka tunda tsufa yazo maka".

Tsaki kawai ya ja ya tashi ya bar musu palon ya shiga d'akinsa ya kulle da makulli, Muneerat, Maryam da anty Fatima suka sa kuka, Usama da Jabir suka tashi suka bar palon cike da takaici da tausayin kansu. Kuka sukayi mai isar su Momy na basu hak'uri, dan kansu suka hak'ura suka bar palon. Gidan dai a ranar kamar gidan makoki ya koma, sai yamma Mustapha yazo ya d'auketa ita da Muneerat dan su ajiye ta gida.

A cikin motar ne Mustapha ya sa su hira har da dariya, anan ne Muneerat take fad'a musu Abdallah ya samu aiki, ita ma tanaso ta fara aiki yak'i barinta wai sai dai tayi sana'ar gida, Maryam ta turo baki tana kallon Mustapha da yake kallonta da gefen ido, tace "d'aya suke mazan nan wallahi, ni ma ba gashi an hanani aikin ba, gwanda ke baki fara ba bazaki ji haushi ba, ni na saba da zuwa aiki amma wai aka hanani" ta k'arashe maganar tana mai nuna fuskar tausayi, dariya Mustapha yayi sannan yace "gaskiyansa, tunda ya samu aiki sai ya bada jari ai meh a ciki?" Ya kai dubansa ga Maryam yace "ke tun yaushe nake binki kiyi deciding meh kikeso kiyi banda aikin kink'i, ina jira ne ki gama shawara".

Nan suka fara sabon hira, shi yana fad'a musu dalilinsa na k'in aikin mace su kuma suna rusawa dan a ganinsu ba hujja bane, a ganinsu indai mace zatayi boko toh a barta taci guminta kawai, in kuma basu son aikin toh a hanasu bokon gaba d'aya, nan shi kuma yayi opposing wannan shawarar na hana mata boko, a ganinsa boko(degree) na da anfani wurin mace shiyasa ake bari ayi amma ba dan aiki ba. Su dai sunk'i yarda da dalilansa dan kawai yace yana goyon bayan hana su aiki da akayi, har suka isa gidan Muneerat maganar da suke yi kenan, dak'yar suka tsayar da maganar ta samu ta shiga gida su kuma suka wuce nasu gidan.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’”               ยฎNWA 


             


Page 44


A gurguje:-


Sati biyu da faruwar hakan, Jabir sun koma Abuja, Anty Fatima ta koma gidan mijinta, al'amura suka cigaba da tafiya kamar yanda aka saba banda Baba da ya sauya, kullum cikin zullumi yake, Momy ta tambayeshi matsalarsa bai ce uffan ba, bayi da lokacin kansa bare na lura da abinda akeyi a gida ya samu na fad'a, kana ganinsa kasan cikin damuwa yake, Momy tayi iya k'ok'arinta ta kwantar masa da hankali amma abun yaci tura, bai son zama a wurinta kullum yana d'aki yana faman waya da abokan sana'arsa, tana shigowa kuwa zai kashe wayar dan kada taji, in ta takura masa ya fad'a mata kuma su gama da fad'a ta bar masa d'akin.

Zaune yake a garden na gidan hankalinsa kwata-kwata baya jikinsa, tunani yake mai zurfi akan abubuwan da yake samunsa kwanakin nan, gani yake hak'k'in yaransa ke bibiyarsa ko kuma wani daga cikinsu ya k'ullacesa shiyasa Allah yake jarrabarsa da dukiyar da yafi so fiye da komai, zai iya cewa komai ya tab'arb'are masa tunda aka damfaresa mak'udan kud'i irin wannan, bai tab'a tsammanin mutum kamar sa zai fad'a cikin yaudarar mutane irin wannan ba. Tsaki ya ja yana mai kawar dakai gefe yaga Momy na zaune gefensa, nauyayyar numfashi ya sauk'e yana mai kawar da kansa daga gefenta.

"Yanzu haka kakeson ka zauna bazaka fad'a min damuwarka ba? Ai ko shawara ce zan baka ko kuma addu'a" dakatar da ita yayi da cewa "wasu suka damfareni kud'i masu yawa, munyi dasu zan tura musu kud'i sannan su turo min kaya, ashe 'yan 419 ne ban sani ba, ni wai nafi kowa wayo ina ganin kayansu da araha nace inaso, ban fad'awa kowa ba na tura musu kud'i bayan bamu tab'a business dasu ba, infact zan iya cewa gusar da tunanina sukayi dan duk wani hanyar da za'a iya kama su ban bi ba, direct na basu kud'i ba a sansu ba, ba a san inda suke ba bare a kamo su, ana cikin haka shagunan da nake dasu anan cikin kasuwa wai yayi tsada masu hayar wurin almost dukkansu suka fita, shaguna biyu ne suke aiki yanzu sai wad'an da kayana suke ciki" ya k'arashe maganar cikin damuwa, 

Dafa kafad'arsa tayi tana mai cewa "ka yadda da k'addara kayi tawakkali insha Allah komai zai wuce, da ai bakayi tsammanin zaka samu d'aukaka hakan ba Allah ya baka...." K'arar wayar Baba ne ya dakatar da ita, duba wanda ya k'irasa yayi sannan ya murmusa yace "kaya sun iso kenan? Drivern babbar motana ne da na aika su kwaso min kaya daga Kano" d'auka yayi ya kai kunnansa yana mai doka sallama, maganar da ake fad'a masa yasa shi tashi tsaye, Momy ma ta tashi dan taji komai a kunnenta "yallab'ai akwai matsala, muna hanya mun kusa shiga garin Bauchi mota ta kama da wuta ta k'asa, sai da wutar taci sosai sannan muka ankara, yanzu haka maganar da nake maka motar da kayan da ke ciki k'urmus sun k'one, mu ma dak'yar muka fito dan motar shiga daji tayi". Wayar da ke kunnensa tuni ya fad'i a k'asa bakinsa bud'e ya kasa tab'uka komai, Momy da ke gefensa ta fara nanata masa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" amma ya kasa maimaitawa, dishi-dishi ya fara gani daga k'arshe idanunsa suka rufe ya fad'i k'asa.

Momy duk ta rud'e ta rasa abunda zatayi, sai tayi kamar zata fita daga garden d'in sai ta dawo ta girgiza shi tana mai cewa "ka tashi dan Allah" duk dauriyarta sai da hawaye ya zubo mata, daga k'arshe ta samu k'arfin fita daga garden d'in a guje dan neman taimako. 

Hanyar waje ta nufa ko mayafi babu drivern Baba ya tare ta, ce masa tayi "ya fad'i ka taimakeni" bata k'ara komai akan hakan ba ta shige gidan ya bita a baya, kasa d'aukan Baba yayi shi d'aya hakan yasa ya fito neman wanda zai taya sa, mutane ya samu a waje ya fad'a musu suka shigo tare dan sa Baba a mota a kaishi asibiti. Sai da suka shiga mota sannan ta tuna Uncle Usman, Nasreen da ke gefe tana zubar da hawaye ta sa ta je ta fad'a masa ya same su a FMC (federal medical center).

An karb'eshi da gaggawa aka shiga duba lafiyarsa, kafin awa d'aya Uncle Usman ya iso, Maryam da Mustapha sun iso dan Nasreen ta fad'a musu a lokacin da taje gidan Uncle Usman aka ce mata baya nan, matansa ne suka k'irasa a waya suka fad'a masa Nasreen kuma ta k'ira Maryam ta fad'a mata.

Awa biyu likitoci suna kan Baba, nurses har sun gaji da yawace-yawace amma bai farfad'o ba, daga k'arshe dai sun gano kan lamarin, bayan ya farfad'o suka masa allurar bacci suka sa masa drip sannan suka fito dashi dan kai sa d'akin da za a ajiyesa. Muneerat da ta iso yanzu taga ana fito da Baba, duk ya rame yayi bak'i, kuka ne ya kufce mata ta kasa isa wurin Maryam da kuka yaci k'arfinta, dak'yar ta samu k'arfin gwiwar isa wurin su, had'uwa sukayi dukkansu suna mai gabzar kuka, tun Mustapha na rarrashi har ya gaji yace su tashi ya mayar dasu gida tunda kuka ne ya kawo su, nuna b'acin ransa da yayi yasa suka danne kukan suka had'u da Mama suna jimamin abinda ya sami Baba.

Kwanaki uku Baba baisan inda yake ba, ranar da ya fara bud'e ido yaga Jabir, Usama, Maryam da Muneerat zagaye da gadonsa, ji yayi kamar mutuwa zai yi hakan yasa hawaye ya taru a idanunsa ya fara bin gefen fuskarsa ahankali yana mai kallonsu d'ai-d'ai, Momy da ke rik'e da hannunsa ita ma hawayen ke fuskarta tana mai murmushin farfad'owar da yayi, Jabir ne ya fita ya k'ira masa likita dan ya duba sa. 

D'awainiyar da yaransa suke yi dashi ya sake kashe wa Baba zuciya, har yau ya kasa magana da yaransa dan baisan meh zai ce musu ba, ya riga yasa a ransa duk abinda ya samesa hak'k'in yaransa da ya kasa sauk'ewa Allah yake bi musu... A hankali yake samun sauk'i har abinci yake ci sosai, kwanansa goma a asibiti likita ya basu tabbacin washegari zai sallamesu dan ya samu sauk'i, a ranar Mama da Kaka suka ziyarci Baba a asibiti, tun bayan farfad'owarsa basu sake dawowa ba sai yau, Jabir da sauran yaran duk suna d'akin, "Jabir" baba ya k'ira sunansa, da hanzari ya iso gunsa dan jin abinda yake nema, ce masa yayi "ku matso kusa inason magana daku" dukkansu suka iso inda yake suna mai sauraronsa.

Daga kan Mama da Momy ya fara ya nemi afuwarsu da yafiyansu a inda ya kuskure, sun tabbatar masa basu rik'e sa ba, dama matsalarsu bai wuce 'ya'yansu su samu soyayyar mahaifi ba. Bayan ya gama dasu ya koma kan yaransa, nan ma duk sun tabbatar masa sun yafe haka zalika sun tabbatar masa komai zai daidaita da yardar Allah, daga k'arshe yayi musu nasihar kulawa da k'annensu da kuma godiya gare su da suka tsaya tsayin daka dan nuna masa gaskiya, ranar dai an rabu cikin farinciki da k'aunar juna, mafarkin Maryam ya tabbata dan basu bar asibitin ba ranar sai da sukayi hira da baba kamar ba shi ba, Mustapha yana zuwa kuwa ta bashi pleasant news dan ya tayata murna.


๐Ÿ’”๐Ÿ’” *JARABTARMU KENAN!!!* ๐Ÿ’”๐Ÿ’” ยฎNWA 


Page 45


Da asubar fari wayar Maryam ya fara ringing, Mustapha ne ya tasheta yana mik'a mata wayar tare da cewa Momy ce ki amsa, kafin ta samu damar d'auka wayar har ya yanke, a take aka sake k'ira ta d'auka, muryar Momy taji alamar ta sha kuka tana cewa "Allah ya kar'bi ran mahaifinku, yanzu ma haka muna gida da safe za'ayi jana'izarsa" mutuwar zaune Maryam tayi ta kasa furta komai.

Mustapha da yake kwance ya taso yana dubanta, an katse wayar amma bata ajiye ba, wutar da ke gefensa ya kunna yana kallonta da idon bacci, tambayarta yake meh ya faru? Ya mata wannan tambayar sau uku bata amsa ba, girgizata yake yana mai cigaba da tambayarta, rungumesa tayi ta sake kuka sosai, bata iya furta komai ba sai "Baba ya rasu". Dak'yar ya samu tayi shiru, sallahr asuba kawai sukayi ko hijabin sallahr bata cire ba suka wuce gida.

Da misalin k'arfe tara na safe aka kai Baba makwancinsa bayan anyi masa wanka, mutuwar Baba ya gigita mutane musamman wad'an da suka je wurinsa jiya, cikin yaransa babu wanda bai ji mutuwar ba, dan jiya ya sa su baccin farinciki, wasunsu sun kwana suna mai ayyana zaman da zasuyi da Baba idan ya dawo gida, Muneerat kam har da mafarkinta wai suna hira da Baba a tsakiyar gida kowa yana cikin farinciki, ashe duk mafarki ne bazai tab'a zama gaskiya ba.

Mutuwar Baba darasi ne ga kowa, bai san mutuwa zai zo masa nan kusa ba, kamar yanda 'ya'yansa suka kwana suna mai hasashen yanda rayuwarsu zai koma hakan shima ya kwanta yana mai wannan hasashen, da misalin k'arfe biyun dare ya farka da matsanancin ciwo, bai kai k'arfe uku ba rai yayi halinsa. (Kayi anfani da damarka dan ribatar lokacin da Allah ya tak'aita maka na rayuwar duniya, in ya wuceka bazai sake dawowa ba, lokaci ba a hannunka yake ba, yau ko gobe ne lokacinka baka sani ba, shiyasa ake son mutum ya yawaita aikin alkhairi da istigfari)

An gama zaman makoki an watse sai yaransa da ke zaune a gida sun kasa tafiya, Anty Fatima da tazo tun Baba yana asibiti ta fara shirin komawa gida dan makarantar yaranta da ta bari a can wurin dangin mahaifinsu, Maryam da Muneerat sai da Mama ta tsawata sannan suka fara shiri, rana d'aya suka tafi suna mai zubar da hawaye tare da fatan Allah yaji k'an Baba ya gafarta masa kurakuransa. Bayan kwana goma Jabir ya koma Abuja ya bar Usama a nan Gombe yana kula da al'amuran gidan da kuma wanda mahaifinsu ya bari kafin a raba gado.

Bayan shekaru uku:-


Momy na zaune a palonta suna hira da Mama da ta kawo mata ziyara, hira suke suna dariya kamar basu tab'a zama kishiyoyi ba, sallamar Maryam da Muneerat suka ji daga bakin k'ofa suka amsa, Maryam ta shigo rungume da 'yarta mai shekara d'aya da watanni biyu, Muneerat kuma na biye da yaronta da ya shigo a guje mai shekaru biyu da watanni biyar sai dariya yake a ganinsa ya tsere wa Mamar tasa, Cike da murna suka shigo d'akin ganin Mama ya k'ara fad'ad'a murmushin su.

Hira suke tsakaninsu cikin jin dad'i Jabir da Usama suka shigo d'akin, Jabir na ganin Maryam yace "wai ke dole sai kin biyo ni, mutum ana gudunsa yana bin mutane" Maryam tace "haba d'an k'anina, gobe kace zaka tafi shiyasa nazo, banason ka tafi ban ganka ba saboda banson inyi missing naka" nan ko ya had'e rai dan k'iransa da tayi da "d'an k'anina" dariya dukka sukayi banda shi da ya had'e rai, Mama ne ta tare masa da cewa "kina gani d'ana ya girma aurensa kawai muke jira ki k'ira sa da d'an k'aninki, so kike matar tasa ta raina sa tace shi k'arami ne ko?" Dariya dukka sukayi har dashi yana mai sauk'e kai alamar jin kunya, daga nan kuwa aka shiga hirar auren Usama da Jabir da za'ayi nan da watanni biyu masu zuwa.

Familyn Alhaji Muktar haka ya koma, rayuwa cikin jin dad'i suke kamar ba su ba, wani lokaci Maryam in ta zauna tana tunano rayuwarsu a da sai dai taji hawaye na zuba a idanunta, a da in aka ce mata rayuwa zata sauya ta zama haka zata rantse tace k'arya ne, amma gashi abu kamar a mafarki, nothing is impossible a wurin Allah, yau gata da mijinta abun k'aunarta harda baby Allah ya azurta su, Muneerat ma da nata d'an saurayin da cikin wata uku k'unshe a mararta, Abdallahnta da Baba yake zagi dan bayi da aikin yi sai zaman shago yau Allah ya d'aukaka sa suna cikin rufin asirin Allah kuma suna rayuwa mai dad'i cike da k'auna, meh yafi hakan a rayuwar duniya? Ka samu masoyinka mai k'aunarka sannan ka samu wadata. Nidai nace babu abinda yafi wannan!

Alhamdulillah 


Thanks to all my dear ones, na tak'aita labarin saboda wasu dalilai, naso yafi haka amma Allah bai bani iko ba, ina rok'on Allah ya bamu damar anfani da darussan da ke ciki, kuskuren da nayi a cikin wannan rubutu ina rok'on Allah ya gafarta min.


Gaisuwa gareku masoya litattafaina, k'arfin gwiwar da kuke bani shi ya kai ni ga kammala wannan littafin, Nagode sosai Allah ya bar k'auna.


Jinjina gareku k'ungiyata NWA, nagode da taku gudunmawar ta nagarta, Maryaaamah na godiya tare da fatan alkhairi. 


Thank you so much Aichaa for your support, kinfi kowa k'aunar littafin nan.


Thank you All... With love MARYAMERHABDUL

Tags: #Mahaifi #Jarraba #soyayya #kauna #jinkai #mutuwarzuciya
2789
0
6
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!