Izinah ce!

Written by Queen MeemiPublished on 2018-12-13 14:50:18Category Non-fictionDariya ya kwashe da ita sai da ya hura huci yanda har ta jiyo ta wayar ya ce: "lalle Shukura harkin manta waye ni? ai to ki sani duk inda kike na sani,ke duk wani takun ki akan idona yake, akwai wani target da nake akanki kuma hak'a na yakusa cimma ruwa,ina baki shawara daki samawa kanki Lafiya ki sallama na rasa inda kika koyo taurin kai yanda nasanki simple baby ceke" tags: #iznah #rayuwaDuba was labarai »

 *⚜IZINAH CE⚜*


    *❣NA❣*

      

*♠QUEEN MEEMI♠*Nagarta writer's Association(NWA)...✍🏽*HAPPY SALLAH TO YOU OLL MY FANS ALLAH YA MAIMAITA MANA MUGA BAD'IN BAD'A D'A AMEEN**PAGE 1*
Hawayen dake kwance A saman fuskar ta ta share ta mik'e cike da kasala tana maijin Jiri na neman kwasarta.


kiran wayarta ne ya karad'e d'aukacin ilahirin d'akin da take ciki, da sauri cike da Razana akan fuskarta ta juya da alamar tsoro akan fuskarta. Jayuwa tayi kusa da wayar takurawa screen din wayar ido. Jikinta na rawa ganin me kiran wayarta ta, tafi minti biyar atsaye har kiran ya katse bata d'auka ba. Adaide lokacin ya kuma shigowa cike da fargaba ta d'auka had'e da cewa "hello" daga can akai magana yayin da ta saka Speaker domin taji da kyau.

   

   

Dariya me maganar ya kwashe da ita.... "Uwargidan Musty" 


dafe k'irji tayi donjin muryar wanda take tsammani,take ranta yayi matukar b'aci da kakkausar murya ta maida mai magana.

 "Haris na gaya maka ka rabu dani! meya sa kake san sani amatsala ne ehe?? Akanka na canja layi taya akai ka sami wan nan?? ka takurawa Rayuwa ta kaji tsoron Allah!"

  

 Dariya ya kwashe da ita "lalle Shukura harkin manta waye ni? ai to kisani duk inda kike nasani duk wani takun ki kisani akwai wani target danake akanki kuma hak'a na yakusa cimma ruwa,ina baki shawara daki samawa kanki Lafiya ki sallama na rasa inda kika koyo taurin kai yanda nasanki simple baby ceke"

  


 "Enugh! Haris" ta fada cike da fusha "baka da tunani ne? nifa matar Aurece! don haka ka fita harkata domin na maka nisa kasani ina d'auke da igiyoyi uku akaina sunnar ma'aiki nake yi don haka ka rabu dani haba sekace baka san kima da darajar sa ba! to this is the first nd last da zaka kara kirana if not zan baka Mamaki".

  


K'it ta kashe wayar ta zauna ta dafe kai dake sara mata, wasu Hawaye ne ke kwaranyo wa akan beauty face nata idanuwan ta sunyi luhu-luhu alamar ta dad'e tana kukan.

  

 **********

  

 Ya Dad'e tsaye akanta yana kallota Wanda ita ta Lula Duniyar tunani D'an gyaran murya yayi ta d'ago firgigit cike da tsoro kar Allah yasa beji wayar da tayi ba. Dan murmushi ta saki ta mik'e "Mustyna welcome" cike da D'an tsoro.

  

  

 D'an kallonta yayi yace "Shukra na yade? na ganki duk kin birkice" kafad'arsa ta dafa "Mustyna yaushe ka shigo?" kamota yayi suka zauna gefen gado yace "yanzu na shigo na ganki kin Lula duniyar tunani kode tunani na kike ne??"

  

  

Murmushi tayi tace "eh mana tun d'azu nake missn d'inka."

  

  

Dariya yayi ba wani nan kede na rasa kwana 2 me kika sa aranki, duk kin fad'a haba babyna kome ke da munki ai seki gayamin ni zan share miki Hawaye."

  

 Gabanta Ne ya fad'i nan ta tuno da kahon zukar da Haris ya kafa mata tun sati uku da suka wuce kullum sayya kirata yana Mata barazana.

  

 Hure Mata ido yayi firgigit ta dawo daga k'aramin tunanin data lula "yace inaga senaje anmin checking naki" dariyar yak'e tayi tace I know my dear nasan ka damu dani, Murmushi yayi ya lakuce Mata hanci "Ashe kinsan zan iya Amma kike sakaci." Dariya tayi med'an sauti ta mik'e tsaye "Oya muje kayi wanka ka canja kaya kaci abinci."

  

 "Yawwa babyna" nan suka mike atare suka fita daga d'akin.

  

 


*********Can kuwa b'angaren Haris bayan ta katse wayar ya k'urawa wayar ido cike da zogin Zuciya ya cillar da phone d'in kan gadonsa yana cije leb'e tare da shafa sumar sa, murmushi yayi "ni shukra zataiwa haka! lalle dole na nuna mata kuren ta domin ta lalatan tsari na hannunsa ya d'unkule ya D'an daki gefen gadon ya mik'e yana kai-kawo a d'akin azuciye ya fita harabar gidan su ya d'auki motar sa ya fice.Drect gidan abokinsa uzaifa ya tafi yana k'ok'arin shiga Shi yana fita ya gano Shi "Aa frnd daga ina?" yace "kai raina abace yake" uzaifa yace "meyafaru?"


jingina yayi jikin motarsa yace "wai shukra ni tayiwa haka?" uzaifa yace "to wai mesa bazaka k'yaleta ba komi taima ai yanzu tayi Aure."


Da k"arfi ya daki motar sa "No uzaifa babu yarinyar da zatai min haka na k'yaleta" uzaifa yayi tsaki "sekai tayi to dama an gayama don kunyi rayuwa baya dole sai ta Aureka tab! ja jiki" haushi ne ya ishi Haris yabar wajen tare da kokarin kiran wata new budurwa da yayi suka hau hira wan nan kenan.ku biyo ni donjin wainar da za a toya aciki karde ku bari abaku labari domin ba a sanin dad'in abinci se an d'and'ana taku QueenMeemi ce.👑

[15:50, 12/27/2017] ‪+227 90 29 04 44‬: . *⚜IZINAH CE⚜*


     *❣NA❣*


 *♠QUEEN MEEMI♠*

  

 Nagarta Writer's Association(NWA)

  


 *PAGE 2*

  


 *Vote me on wattpad @Queen-Meemiluv*


********


 Zaune take a falonta tana karanta wani littafi taji Ana knocking door D'an tsaki tayi ta tashi ta bud'e razana tayi da gudu tayi baya can kuma ta tsaya tana mai zare ido cike da in ina tace "Haris wai Mena tsare maka ne? ka rabu dani da da yanzu aiba d'aya bane Me yakawo ka gidana ehe?"

  

 Murmushi yayi yana k'ok'arin shigowa nan ta danna k'ofar da k'arfi yayi baya taga-taga zai fad'i nan ta tsaya tana huci "wlh ka fita konaima ihun kwarto."

  

 Shuky yanzu har kin mantani ni haris kin manta rayuwar da mukai abaya karki hukuntani da rashinki mana kece life d'ina" 

  

Wani kuka ta saka kaicona ni shukra nayi dana saninka arayuwa gashi yanzu ka hanani sakewa agidana nan ta d'aga murya "na gayamaka ka rabu dani nayi aure yanzu don haka ka k'yale ni wlh zanma ihun kwarto."

  

"Ke shukra dakata Haris ya ambata wane dare ne jemage be gani ba .....? to kisani ni Haris na biyo miki ta laluma kinkasa fahimta wlh zan biyo miki ta bayan gida komi ta fanjama- fanjam."

  

Numfashi taja na kuka "ta Allah ba taka ba Allah bazai baka damar keta haddin sunnah ba insha Allahu."

 

 Murmushi yayi ya juya ya fita daga ainihin gate d'in azuciye ta d'au Hijab ta fita gun Maigadi tace "yanzu Lawan mesa zakabar wan nan ya shigon gida Hajiya kiyi hkr wlh bansan baki sanshi ba cemin yayi Shi Dan uwan me gidanne."

 

 "To Amma kasan ance Sai ka bugo waya ka tambaya ko?"

 

 "Ayi hkr hajiya mantuwa nayi"

 

 "To daga yau karka Kara barin wani namiji ya shigo koda tace Shi Dan uwane Sai ka bugo an tabbatar."

 

 yace "insha Allahu" 

 

 Nan tajuya ta shige gidan direct d'akinta ta shige ta fad'a gado ta rushe da kuka wayyo na shiga uku ni shukra meke shirin faruwa da ni? na cucu kaina nayi danasanin sanin haris gashi yana neman dagulamin lissafi agidan aurena sai maganganu take hade da kuka ta. kusa rabin awa ganin karfe 2 dede har tayi yasa ta mik'e tayi toilet tayo alwala tayi sallah san nan tashiga kitchen Dan d'orawa musty sanwa.

 

 

 **********

 

 Dukan bencin dake gabansa yayi ya zuki taba ya furzar ya kalli sani yace "wlh k'aryar Shuky ta sani kwandon shara ta manta irin Rayuwar da mukai ba irin son dabata nunan ba Amma kaga tashi d'aya tayi aure wai harni zanje gidan ta tace zataimin ihun gardi."

 

 

 Sani ya mik'e "to kai har ma ta ina kasan gidan ta" haris ya harareshi "kai kasan idan inason Abu dole na samu ko? to sannu ahankali na gano gidan ta" Sani ya bashi hannu suka tafa "shegen kaya nasanka ba kada dama."

  "Kuji tsoron Allah domin duk abinda kuke wlh yana kallonku" atare Haris da sani suka Juya ganin uzaifa yasa haris yayi tsaki "wai uzaifa na gaya ma in baza kaban shawarar yanda zanyi na kwato shukra ba to ka k'yaleni Uzaifa yayi Dariya kadai juri zuwa Rafi .......... ku rasa inda zakuyi tambad'ar ku sai gun matar aure Haris yace malam ba ruwanka."

 

 Shiru uzaifa yayi bai K'ara cewa komi ba ya zauna jim kad'an awajen san nan ya mik'e yayi tafiyar sa.

 


 ******


 Zuwa tayi ta sunkuya tana d'aura mai zaren takalimin sa shikam inbanda kallonta ba abinda yake "iluv u my wifey" ya furta d'agowa tayi ta kalleshi "me too darling" d'auko turare tayi ta farfesa masa suna murmushi hannunta ya rik'e yace "my wife agaskiy nayi dacen macen kirki datasan salon kulawa da miji akullum na kalleki sainaji shauk'in sonki."

 

 

 k'uramata idon da yayi ne yasa taji kunya tad'an hure mai Ido murmushi yayi "the most beautiful woman" dariya tayi me sauti "hmm mustyna kana kod'ani fa da yawa"

Nan takalli agogo "Oya muje kayi breakfast bansan ka makara gurun aiki."

 

 "Okey madam" yayi mata wani cool smiling nan da nan taji zujiyarta ta narke haka sukai breakfast ta rakashi har mota ta bashi peck a kumatu tajuyo sunawa juna bye.

wani dad'i Mara musaltuwa takeji agaskiy ita shukra tayi sa ar miji domin tunda sukai aure yake gwada Mata san yayyar soyayya suna kaunar junan su murmushi take ta bugawa har ta shiga falon ta k'irrr wayarta tayi k'ara take k'irjinta ya buga daramm!

 

 Domin harga Allah ta manta da wani bacin rai Amma kiran nan ya tuno mata da barazanar haris akanta. Jikinta na b'ari ta wullar da wayar kan kushin dede lokacin wayar ta katsae can kiran ya kuma shigowa duba wayar tayi taga sunan mamanta b'aro-b'aro akai nan ta dafe k'irjinta cike da jin dad'i domin har ga Allah ta d'auka haris ne.


 Da sauri ta d'auka "hello mama dagacan maman tace ya ina ta kira bakya kusane??"

 

 "Eh mama ina kitchen" "ok dama ina son gaya miki ne Zahida ta haihu an samu namji yakamata ki daure kije" "kai Amma nayi murna mama Allah dai ya raya gobe ko jibi zan shigo sai zainab ta rakani tunda bansan gidan ba" mama tace "Okey Allah y kaimu sai kima duba abbanku don bai jin dadi"

Dan muskutuwa tayi daga zaman "to mama ki gaidashi sai nazo" nan ta katse.

 

 

 

 Daga taskar Queen Meemi

[15:50, 12/27/2017] ‪+227 90 29 04 44‬: . *⚜IZINAH CE*⚜

 

    *❣NA❣*


*♠QUEEN MEEMI♠*

 


Nagarta Writer's Association(NWA)

 


 PAGE-3


*Vote Me on wattpad@Queen-Meemiluv*


*******


Goslow ake yi na fitar hankali sai tsaki take tare da dana sanin bin hanyar ita aganinta hanyar tafi mata sauk'i da gidan nasu.Ganin ko motsi motoci basi yasa ta kashe motar ta D'an sunkuya.Can kamar 10 mint motoci suka fara ja ahakan ta samu damar wucewa feeeeee motar ke gudu can ta D'an duba mirrow taga Ana binta ta baya duk kwanar da tayi sai taga motar na binta k'irr wayarta tayi k'ara ganin zainab ke kiranta yasa ta dauka tasa speaker "Hello Zee kin ganni shiru ko?"

 Zee tace "eh wlh" 

"Hold off ne ya tsareni" zee tace "nidai inajira don har na sare" dariya tayi "sorry sis."

 Gani tayi ansha gaban motar ta gabanta ne ya fadi ganin Haris Shan kunu tayi yasa Dariya "duk guje- gujenki wollahi sai kin bi abinda nakeso" zaro Ambulance yayi ya wulla gaban motar ta yace idan kin gani ki yankewa kanki shawara domin su sun isheni na mik'asu ga Mijinki kinga kuma taki ta k'are zab'i ya rage naki" wani Munafikin Smiling yayi ya tafi ya shiga motar sa yaja .

 


 Jikinta na rawa ta d'auka ambulance din ta bud'e wani wawan razana tayi sakamakon cin karo datayi da abinda ya d'aga mata hankali .take ruwan hawaye suka wanke Mata fuska kifa kai tayi kan sitiyari tana kuka na fitar rai tunanin tane ya tafi can cike da tarin Dana sani hausawa sukace ashe keya ce tabbas wan nan shine babban kuskuren Dana tafka d.agowa tayi Allah kashiga lamarina ka yafemin kura-kuraina Dana aikata nan ta d'auki hotunan ta cusa a jaka ta ja motar tayi gaba.

 


 Minti ashirin ya kaita gidan su taje ta gaida Babansu tamai ya jiki tafito.

Sai kwala kiran mama mama take "gani nan wannan kiran fa? kamar zaki tashi sama."

 

 "Mama wlh nasan zee na jira na mama tace aikuwa ta dad'e da shiri kuma mama kinga banganta ba bata d'akinta fita tayi da sauri ta ganta gaban mota tace "lalle ke har kin likimo aciki" tace "eh ai Naga ke d'ince sai aslow kin fiya nawa" haka ta jasu suka tafi.

 

 


 Safa da marwa kawai take ad'akin yayinda fuskarta ke d'aukeda matuk'ar damuwa d'age kai tayi "mesa zakana takuramin Haris kak'yaleni nai zaman aurena mana haba! ita kad'ai take magana kamar wacce ta zare tabbas duk Wanda bai gina rayuwa mai kyau ba a samartakar sa lalle ya tafka babban kuskure bantab'a sanin abinda nai zai dawo ba sai yanzu ya Allah ka rufan asiri cikinta taji ya bada kuuuu alamar yunwa ya tsine fuska tayi tare da shafo cikinta Sam bata sha 'awar cin abinci ma domin tarasa madafa.

 

 

Muskutawa tayi ta matsar da hotunan daga gabanta don kallonsu na sawa zuciyarta na tsalle. sanin yau sai shida musty zai dawo shiisa batai k'ok'arin girki ba haka ta zauna ta lula duniyar tunani tiryan- tiryan rayuwar ta tabaya ta fara dawo Mata tamkar ashirin fim.

 

 

   TUNA BAYA

    

Ku biyo Meemi donjin abinda ya wa kana arayuwar Shukra nasan kuna da tarin tambayoyi kan meye alakar haris da shukra da kuma dalilin da yasa ya takura Mata idan kuna biye tiryan tiryan da sannu 'yar mutan kano zata gamsar daku.

    

    

Daga Taskar Queen Meemi.

[15:51, 12/27/2017] ‪+227 90 29 04 44‬: ⚜IZINAH CE⚜


      ❣NA❣


♠QUEEN MEEMI♠
Nagarta writer's Association(NWA
*Vote on wattpad@ Queen-Meemiluv*part- 4
********TUNA BAYA


Gidan Alhaji ibrhim matsakaicin gidane mai d'auke da Matar Aure guda d'aya da yara biyar Nazir shine babba sai Shukra san nan Zainab sai halima da Auta Muhd yana zaune agarin kano a Unguwar tudun wada.Allah ya rufawa Alhaji ibrhim asiri inda daide gwargwado yake da rufin

 Asiri ma'aikaci ne a makarantar Secondry inda da yake shugaba wato principal yana da tsantseni da zafi kan yaransa sun taso cikin tarbiya me kyau da girmama na gaba. Matar sa Hajiya Maryam ta kasance me sauk'in kai da sanin yakamata tana kulawa da yaranta musammm shukra da Allah y bawa kyau data kula kuma tana da rawar kai.
 Suna zaune dukkansu afalon gidan kowa na cin abinci Ana hira in ka dauke Naxir da baya nan yanzu hakan yana can ABU zaria yana karatu. dama Al adar gidan kenan Babansu ne yayi sallahma suka amsa sukai mai sannu da zuwa ya zauna ya basu tsarabar su d'agowa yayi ya kalli maaman nasu yace "ina shukra ne?" 


D'an tab'e baki tayi tace "kasanta da saka abu arai wai don ta fad'i jamb shiisa take ta kuka tun bayan da taje ta dubo" kallon halima yayi "jeki kiramun yayarku" da gudu ta tashi taje d'akin su tana kwance tana kukan.


Halima ta tsaya kanta tace "Dady yace kizo" ahankali ta mik'e ta fita k'ura Mata ido yayi harta zauna yace "yanzu uwata Har yanzu baki daina kukan ba? yara nawa ne suka fad'i Jamb kiyi hkr next yr sai ki zana wata kinji ko" ta d'ago "to Baba" haka ta koma salo -salo.Shukra yarinyace mai shekara 18 alokacin ta gama secobdry Allah yabata k'ok'ari a sch sai akaci rashin sa'a bataci ba, Allah ya zubawa Shukra farincjinin Samari ko yaushe ta fita sai anbiyo ta ance anaso. hakan k'awayenta basa san jerawa da ita saboda tana kashe musu Market ita kuma shukra irin 'yan matan nan ne masu so ace Ana son su duk namijin da yace yana sonta to zata ji dad'i kuma zata bashi number dinta.Yauma kamar kullum sun taso daga islamiya suna tafiya itada k'awarta Mardiyya sun shawo kwana kenan wani Saurayi dake kan mashin ya tsaya agaban su D'an basarwa sukayi saurayin ya sauka yana kallon shukra yace "sannu 'yan mata" Mardiyya tace "kayi hkr sauri muke" shukra ta Dan mintsineta ta maida kallonta kansa ya yi murmushi 'yan mata kozan samu number naki Dan farr tayi da ido "ba matsala" nan ta bashi suka wuce Maridyya tace "nikam shukra kina ban.mamki ke kowa yace yana sonki sai kin kula shi haba sekace bakida class Ai farinjini ba hauka bane duk sanda muka fita inde aka tsaida Ke sekin bada number ke ko tsoro ma bakyaji yanda duniyar nan ta lalace" shukra tace ni mardiyya kinga bansan fa irin haka bakyau wulakanci ne shiisa ki kaga haka" 

Mardiyya ta tab'e baki "adai juri zuwa rafi" kwanar gidansu tazo yasa suka rabu.Tunda ta shiga gida take murmushi Tare da jin alfahri akanta nafa Ita tana da farinjini wajen karfe 7 yaro yayi sallama mama dake bakin famfo tana d'auraye kwano tace "wa'alaikumussslm"


 "wai Ana sallama da shukra" dai -de lokacin ta fito mama tace "Jekace tana zuwa" ya fita ta kalli shukra "sai kije Har tafara tafiya maman tace "zo nan!" Shukra tad'an juyo abinda Zan gaya miki ki kula Naga koyaushe sai anzo sallama dake Haba kinsan dai babanki bai san kina fita hira bako?" sunne kai tayi "tom mama" haka tafita.Arba tayi da saurayinta salihu nan suka tsaya inda suka Saba tsayuwa wajen kamar 20 mint sai ga mota ta faka k'irrr wayarta tayi k'ara ta d'aga na daga cikin motar ne yake magana tace "ok" ganewa da yayi yasa salihu ya yi Mata sallama ya tafi haka ta juya gurin na motar ta tsaya shima ya fito nan suka hau hira kowanne da kalar abinda zai ce mata ganin 8:30 tayi yasa sukai sallama ta koma gida.Nan ta tarar maama nata kallon 'kofa tana ganin ta tayi hamdala yauwwa gwanda ki dawo don nasan yanzu babanku na hanya "ina dai dad'a Jadda da miki ki kula ni fa bansan tara Samari wan nan shegiyar wayar ma bata da amfani don naga sekiyi ta waya sai kace mai bussiness" shukra ta tura baki mama "Wlh niba komi bane kawai de bana san nai masu wulaknci ne" mama tace "tode ki kula ki tsaida guda d'aya" tace "to mama."
Haka ta shiga d'aki ta zauna tana tunani ita Sam duk cikin samarin nata guda biyar da suke zuwa babu Wanda yayi mata kawai de tana Kula su ne saboda zama wuri daya tsutsayi inji sarki..lalleKubiyoni

Daga taskar Queenn Meemi👑.
[15:50, 12/27/2017] ‪+227 90 29 04 44‬: . ⚜IZINAH CE⚜


    ❣NA❣


♠QUEEN MEEMI♠Nagarta Writer's Association (NWA)Part-5**********


Kullum haka k'ofar gidan su sai kaga wani yazo gunta tamkar gidan maza don har jira wasu keyi hatta 'yan unguwa sun gane ta domin duk yan matan layin ba wacce ke tara samari kamar shukra kodan Allah yayi mata k'ira me kyau ne wacce ke d'aukan hankalin samari duk wan nan budurin da ake Alhji ibrhm bai sani ba domin sai 8 yake dawo wa lokacin ta gama sallamar su abun yanawa mama ciwo yauma kamar kullum suna zaune suna cin tuwo atsakar gida sabili da yau da D'an zafi yasa suka shimfida tabarma don susha iska idar da sallar mama keda wiya takalli zainab dake kai lomar tuwo "ina ita shukrar naga kinaci ke kad'ai?"

"Mama Wlh gatacan tana waya ni kuma yunwa nakeji" ran mama ya b'aci ta shiga falon ta ganta tayi d'ai -d'ai ta d'ora k'afa d'aya kan d'aya sai dariya take da alama da saurayi take cikin fushi mama ta k'wace wayar "wai mesa shukra kika canja d'abia ne? Haba! kullum bakida aiki sai waya to wai da suwa ma kike ne? bansan shiririta kode k'awaye ke zugaki ne? turo baki tayi "mama Wlh bakowa da frnds nake waya wanda mukai candy tare" mama tace "bawani nan kide kula na gaya miki atoh! kuma ki tashi ki je kuci abinci inaga ko sallah ma baki ba ko?"

 "Mama nayi fa!" nan ta fita ta zauna Sam jitai abincin ya fita aranta.

Gama cin tuwon su keda wiya yaro ya shigo wai Ana sallama da shukra da sauri mama ta fito "kaje kace bata nan" haka yaro ya fita shukra kuwa in banda turo baki ba abinda take kira mama ta k'wala Mata ta shiga shukra kina jina ko?" Tace "eh daga yau na haramta dodon da ake mana akofar gida haba yarinyr ki dake kin maida gida kullum dare kamar dandalin samari kodan to Wlh karnaji kar na gani don bakiga fad'an da Babanku yayi mani jiya ba kan wani makocin saa ya sameshi amsallaci yayi mai magana wai an sakeki sakaka kina tara samari abin yayi mai ciwo dak'yr na bashi hkr don ransa ab'ace yake" tsoro ne ya shigi shukra don tasan fad'an Baban in aka tab'oshi cike da in ina tace "Mama ki bashi hkr nadena!"

 "Atoh kima cigaba keda kike sanyin karatu kyasa Babanku ya Aurar dake bakiyi karatun ba" jikin shukra yayi sanyi
Sallamar Baba ce ta katse musu maganar nan ta runtuma d'aki aguje mama ta tashi taje tsakar gidan domin harya zauna su halima sun kewayeshi Mama tayi mai sannu da zuwa ta kawo mai try na abincin sa. Har ya fara ci ya d'ago ina uwata take ne?? Wai mesa kullum ita tana d'aki ne?" k'wala kiran ta yayi hantar cikinta ce ta kad'a ta aje wayar ta fita tamkar munafuka don tsoro. Kar yayi mata fad'a nuna Mata jakarsa yayi "bud'e ki d'auko file ahankali ta bud'e ta zaro yace scratch card na jamb na sayo miki domin an dad'e Ana Rigistration don ma naga d'alibaina zasuyi shiisa na sayo miki" mama tace "ikon Allah yanzu har shekara ta zagayo?" baba yace "Wlh Ai kamar yaune game yawan rai" itakam Shukra in banda murna ba abinda take cike da d'oki Baba yace "to abinda Zan gaya miki ki dage ki karatu bana ki shiga makaranta don bansan zaman haka gobe sai kije ki Rigister jiki na rawa ta d'auka "Baba ngd ta shige d'akiHaka dai lokaci yayi ta tafiya har suka zana jamb cikin ikon taci sai zaman jiran admition yau tana kwance sai sharar bacci take hankali kwance Hassana k'awarta tazo sai jitai an d'aka Mata duka ta tashi Hassana tasa dariya "sarkin tsoro yaushe kikazo? tace "ke yanzu dama d'inki nazo ki rakani kuma na gayawa Mama kawai d'auko Hijab naki" tashi tayi "ni kawai kin katsen Sweat dreams d'ina"

 "Kyaji dashi nide yi sauri" sauri- sauri ta shirya suka fita ahankali suke tafiya har sukaje gun me d'inkin da yake ba nisa bayan layin su ne suna zaune Hassana na kwatancen d'inkin da takeso wata dalleliyar motace ta tsaya a wajen. Saurayi da budurwa ne suka fito suka shigo tinda suka shiga idanunwan sa na kan shukra duk da ba wani kwalliya tayi ba amma ta tafi da ruhinsa zama yayi agefen ta "'yan mata" juyowa tayi ta kalleshi ta juya nan Yace "pls In bazaki damu ba ina son number naki" tab'e baki tayi D'an karkatar da kai yayi "Gaskiy kina da kyau Wlh" murmushi tayi ta jin an yabeta jin ya samo lagonta yasa yace to bani number din mana me kyau" nan ta karanto mishi fuskarsa ya shafo "well zaki iya kirana da Haris I wll call u later" Nan k'anwar tasa ta fita suka tafi. Murmushi shukra tayi Hassana ta tab'ata ke taso mu tafi ko da yake naga kinyi Market dama ke duk fita sekin Market dama nice keda farin jinin ki Wlh danayi sha'ani" shukra tace "kinsan Mama ta hanani fita hira sede fa mi waya shima wan nan bansan me zance masa ba" duk randa kukai zaizo kice masa zaki gidanmu kawai seki mai kwatancen gidan namu sai kuna had'uwa a can ammafa inkin wankeshi sai kina yafo min." tafawa sukayi "kin kawo shawara"Daga taskar Queen meemi👑

[15:50, 12/27/2017] ‪+227 90 29 04 44‬: . ⚜IZINAH CE ⚜

      

    ❣NA❣


♠QUEEN MEEMI♠Nagarta Writer's Association(NWA)....✍🏽*Wattpad as ...Queen-Meemiluv*Part- 6*********Cikin D'an k'an-k'anin lokaci Soyayya ta k'unsu tsakanin Shukra da Haris kullum suna kan waya tun safe inya fara bugowa har dare mintuna kad'an -kad'an aikin gida ma shukra ta rage taya mama sai de taita aiki ita tana d'kai tana waya. cikin sati biyu Haris ya siyo zuciyarta don Haris akwai iya kalamai da Lafazi na Jan hankali yau da yace zaizo tun da rana ta cewa mama zata gidan su Hassana zasu taya Mamansu aiki, daya ke yanzu duk randa wani wanda zaizo zance gunta Gidan su Hassanar take kaisu da yake gidansu Hassanar irin gidan nan ne da kowa sai abinda yayi niyar yi wato Uwa ba kwab'a Baban su kuma irin mai zuwa fataucin nan ne sai yayi wata uku bai dawo ba wan nan dalilin yasa suke sake saka ka ,itade mama na Mamakin zuwan shukra Gidan su Hassanar duk da tasan Mardiyya Itace best frnd d'in shukran amma bata zuwa gidan su kamar yanda ta tsira zuwa gidan su Hassanar yanzu saide data tambayeta cemata take karatu ake k'ara masu.

Wata uwar kwalliya Shukra taci tayi balain kyau kamar ka sura ka arce Mama ta d'ago "yanzu shukra keda zaku tayata aiki shine harda fesa uwar kwalliya haka?"

 "Mama Wlh kawai sha awaryi nake innaje Ai ba baci zan ba"

 "Kide kula shukr na gaya miki" wayarta ce tayi k'ara d sauri ta fita haris ne keta kira minti ashirin ya kaita gidan su Hassana da yake bayan Layinsu gidan yake.

Tun daga naisa ya hango ta nan ya zuba Mata eyes har wani lashe lips yake k'araso war ta yasa yace "ashe kallan tsoro nai miki ran nan" Murmushi tayi "mu shiga ciki nan zuka shiga suka je inda aka tanadi kujera don zamansu.Dab da ita ya zauna har yana Gogar jikinta nan tad'an matsa wani kallo yayi Mata "sorry ko! ke d'ince akwai rikita mutum" hira suke sai kod'a ta yake yana yanko mata lafazai na k'auna ba abinda yake inbanda kallon lips nata da yasha red jambaki. kamo hannunta yayi ya rike nan ta fisge ta had'e rai "gaskiya kadaina tab'ani mana haris"

 "Sorry beb bana iya controlling kaina ne kwalliyarki ta tafi dani"

"To nidai ka daina! komi zakai de mi hira Banda tab'a jiki"

 Okay baby afuwan" tare da wani Smilling wana shi kad'ai yasan ma' anarsa yace "babyna ya kamata fa kiyi new phone cuz inaso kema kina Hawa social media D'inan! jifa wayarki Ai kinfi k'arfinta ki bani chance na kawo miki new one" nan tayi murmushi ta kad'a mai idanuwa take yaji jikinshi yarrr! Murmushi yayi ya kalleta "me kikace?" tace "Babana yace bazan rik'e Big phone ba yace sai zanyi Aure wan nan ma saboda frnds nawa ne shiisa ya bani,Samarina da dama sai da sukace zasu bani waya Nace masu Aa"

 "Kai! kai! kai!" Ya fad'a da sauri ta d'ago tace "meye Darling" yace "Dankari yanzu dama kina da wasu samarin?" sunkwi dakai tayi "Ai mun dad'e dasu to nikam inde kina sona sai de ki dai na kulasu" dariya tayi san nan tace "ok dea zanyi yanda kace"

" Dat my baby shiisa nake sonki Wlh sonki har b'argo na nakeji tamkar na Maidaki cikina iluv u so much" Murmushi tayi "luv u too Wlh haris duk cikin Samarina nafi sonka Murmushin samun nasara yayi ganin duhu ya k'arato y mik'e dea ba na wuce nan ya zato bandir 'yan d'ari biyr ya mik'a mata nok'ewa tayi "No darling kabarshi" yanda tayi sai ya Birgeshi "wow babyna iluv u" Murmushi tayi mai kashe rai ta juya dai de lokacin Hassna ta shigo gidan "Aa yau haris ne? yace "eh mana kinga babyna taki karb'ar abin hannuna" hassna da yake Mayyyar Money ce take hannunta ya fara rawa "kasan k'awartawa kwai kawaici" nan ya mik'awa Hassna ta karb'a "gashi ki bata" y zaro yan 100 ya bawa hassana "wan nan kuma naki ne" godia ta hauyi tamakr tsohuwa nan ya fita yana wulla key d'auke da Murmushi kan face nasa.
Shukra dake zaune a falon su Hassna sai Murmushi take Sam ta rasa inda zata tsoma ranta domin haris duk ya kashe Mata zuciya. Hassana ta shiga 'shegiyar kwaba kinga kyan da kikai!"

 "Ya san ranki" nan ta wulla Mata kud'in "to ke wa yake gudun masu gidan rana to bud'e kunne kiji ki saki jiki ki wanki gayu fitar da kike Ai ba'a banza ba kinga Kya dinga kashe abubuwan dake gabanki ba tareda kin takurawa su maman ba" shukra tace "hmm nida mama ta hanani karb'ar kud'in samari"

 Zauna nan yarinya lokacin kine kici arziki a mazaunin sa ki barsa da nice da kyanki da farin jininki da kinga sanabe idan ma kina tsoro to kina kawo ina aje miki bakya ganin yanda 'yan mata ke kashe ado to Ai duk yawaicin kud'in samari suke ci" nan ta zauna ta tsara shukar da yake hassna akwai baki da wayo nan da nan ra ayin hakan ya shigi shukra "hassna ke kam samarinkii sazu sha wan ka kinsan Shi kansa Haris wai duk saina dena kula samarina" 

Hassna tace tab! Ai kowane da mazaunin da zaki ajeshi" dede lokacin Muhd ya bugo wayar shukra da bazata d'auka ba sai kuma t dauka da sauri Hassna ta karb'e waayar ta kashe tace "bari na gaya miki salon yanda zakiyi kan ya kuma bugowa kinga inya bugo sai kice ki wankeshi nan take" nan tai Mata rad'a akunne suka saka dariya "kinga ma cajin wayr ya kare kan y bugo" hassna tace "badamuwa Ai" nan ta mik'e "keni na tafi kar mama Taga na dad'e" nan ta fito ta rakata ,tana zuwa gida bata jima ba Baba ya dawo sukai mai sannu da zuwa nan ya kirawo shukra ad'akinsa taje yace "akwai wani da yake yawan damuna kan maganarki duk da Baban sa ne ke zuwa guna nuna sha'awar hakan sabili da d'ansa ya ganki yana so shiisa na bashi dama yazo Ku sasanta" dam! gabanta ya fad'i "Baba karatunfa? dariya saka "Ai uwata na fiki san kiyi karatu Ai karatu zakiyi shi kawai zuwa zai in kina sonsa to shikenan in kuma akasin hakan se abashi hkr" Dad'i ya kashe Shukra ta tashi ta koma d'aki ........WAYE HARIS.......Kubiyoni dadin book din na gabaDaga taskr Queen Meemi👑

[15:50, 12/27/2017] ‪+227 90 29 04 44‬: . ⚜IZINAH CE ⚜


  ❣NA❣


♠QUEEN MEEMI♠
Nagarta writer's Association(NWA).....✍🏽
page- 7
Wan nan page din nakine My Zahra Abdullahi ❤
*******


WAYE HARISHaris d'ane ga Alhaji Mamman maidala shahararren D'an kasuwa ne dake zaune abirnin kano tsohon D'an kasuwa ne wanda ya dad'e yana taro yana da yara biyar Sawwam shine babba sai Haris Mai bi masa sai Rabia dake Aure a kaduna San nan Khalid da Rufaida. Hajiya sa'adatu Itace Mahaifiyar Haris ita kad'aice Mata agun Alhji Mamman tana da Addini hakan yasa "ya'yanta suka taso cikin d'abia me kyau inka dauke Haris daya fita izakka domin Dan gatan Alhaji Mamman ne duk yafi sansa duk cikin yaransa hakan ya saka ya tashi a sangarce tun yana yaro hajiyaa sadat tayi iya bakin k'ok'arin ta amma abin yaci tura.Shekarar Haris 25 yana da girman gab'b'ai domin inka ganshi sai ka d'auka yayi 30 Allah yayishi da son Mata inde ya had'u dake to sayya siye zuciyarki harki aminta dashi.

Tun dawowar sa daga Turkey inda yayo dgree nasa yanzu hakan yana zaune agida sai de ya shiga wancen motar yafita waccen yace bazai aiki ba balle kasuwanci don yaga Babansa ya sakar mai nera tun Babarsa na fad'a har ta gaji


Dabiar da ya koyo acan inda yayi karatun wato Shan taba ga balain son mata inde ya hadu dake to saiya yanda yayi kuka dinke yan mata ne dashi tuli kuma yana sakar musu bakin aljihu shiisa,suke rubibinsa duk da nawani kyau gareshi Ba saide gayu kawai tabar da yake sha kam Wanda kullum sai sawwm yayi mai fada Amma baiji.uzaifa abokinsa ne da suka taso tun suna yara komai tare suke sede dabiar su tasha bam-bam tun bayan dawowarsa daga turkey ya hadu da sani ya zamanto irin halinsu daya wannan yasa suka zama abokai.

************


Kanta asunkuye yake domin data kalleshi gabanta ke fad'uwa yana dukan Tara -tara ga wani tsoro dake shigar ta tabbas gayen ya had'u wane Haris sai de kwalisa da haris zai nuna mai ,amma ko ta ina yafi Haris Had'uwa dagowa tayi zata kara tantacewa caraf suka had'a ido tayi saurin yin k'asa dakai.


"Uhum me kikace? na dad'e ina sonki se yanzu baban Ku yaban dama inason jin ta bakinki."

Bakinta ne taji yayi nauyi takasa furta ko kalma d'aya take Haris ya fad'o Mata arai ta runtse ido tabbas tana son Haris amma wan nan ma duk wani qualities da take so game da namji ya had'a Murmushi tayi Mustapha dake kallonta yace "dama ance dariyar Mace Amintar ta" nan ya mike ni zan wuce nan ya aje Mata wata leda ya fita.


Tafi minti goma a tsugune "meke nan nayi? Hmm wa kaina tab! banfa amsa ba! Amma har yayi Riga malam lallema wan nan Amma ba damuwa nan ta d'au shegiyar ledar da k'yar ta iya d'aukan ledar ta shige gida.


Lokaci yana ta tafiya hakade musty da shukra ke tasu soyayy kullum Shi zai kira koyaushe ya kira busy Sam bata damu dashi ba ta samarinta take.

Watan musty d'aya tare da shukra ya kuma zuwa nan yake sanar Mata zashi America kan wani course dazaiyi na 1yr kanta asunkuye tace "Allah ya kiyaye" musty yace "shukra nikam bana son tafiyar nan duk da nasan Baba ya bani ke amma samarin zamanin nan ba dama suga me kyau sai suyi ta binta well ki rik'en amana wlh I really luv u...

Ya danyi shiru tare da kallonta "kinsan da su dad nawa ma cewa sukai akawo kud'in angani anaso sai momyna tace abari na dawo wai saurin me ake nikam nasan ina tsoro plss shukr duk ki sallami wani Saurayi dake zuwa nasan bazaki rasa ba domin ke tawa ce ko ba haka ba"

 Sunkuya wa yayi yai mata Murmushi sunne kai tayi na gulma Wani. kwali ya fito dashi ga wan nan waya ce don inason muna gaisawa nayi ma baba magana ya amince na baki" jiki na rawa ta amsa ya zaro wata leda ya bata ya mik'e sai minyi waya gobe jirginmu zai tashi" "Allah ya kiyaye ta fad'a kallonta yayi da murmushi saman face nasa "plss shukrana ki rik'en amana" nan ya fita ta bishi da kallo tabbs Musty ya had'u Amma tasan tafison Haris da gudu ta shig gida "Mama zo kiga wayata."

Mama dake kitchen ta fito nikam Sam da yabi ta tawa dabe baki waya ba duk da de yanzu ammiki katangar k'arfe ma da Samarin an Riga anba dake aishi kenan bake ba kula Samari" shukra azuciyar ta kam yanzu ma ta fara kulasu ta turo baki gaba haka kawai don an badani sai ace bawanda zan kula tab! Maama tace "tunanin me kike?" 

"Aa bakomi mama" ta shige d'aki 
***********


"Kai Amma shukra ki godewa Allah Amma wayar nan tayi kyau yau kece ke rik'e da galaxy S6. Amma musty y birgemu nayi murna."

Shukra tace "Mardiyya kinsan me? bafa wani sonsa nake ba, kawaide ya had'u ne" Mardiyya tace "aini tunda kika ban labari nasan duk ya kere samarinki har wan nan Haris d'in nide sam bemun ba" shukra ta d'aga Mata hannu "Haba agabana kina wani kusheshi" Mardiya ta rik'e Hab'a "kai sis! to meye? Naga yanzu an miki miji to meye kuma naki da Haris" shukra tace "kuma don anmun miji sai nak'i soyayya da wasu tab! ai yanzu na fara ni ai allurar cikin ruwa ce"

Mardiyya tace Wlh nasan Hassana ke zugaki saboda sam itama irin ra'ayinta kenan! ki kula da samarin zamanin nan kinga yanzu duniya ta b'aci tunfa kina had'uwa da na arxiki Wlh sai kinzo duk na tsiya zakina had'uwa kizo kuma ki had'u da wanda zai Zameki jalala dama wasu su ba wani abu ke kaisu gun 'yan mata ba sai iya shege da rage zafi na tabbata kad'an ne acikin samarin naki ke miki zancen zasu aureki don Allah na tambayeki? haris ya tab'ai miki zancen ze aureki??" Shukra ta kalleta ta harareta "bai tab'a ba sai me! yace sai yanemi aiki zaimin maganar turowa" Dariya Mardiyya ta saka "lalle shukr sai kace baki shiga class ba Haba! Wlh duk wanda zai zo ma da zancen aure shine na kulawa ba tatarikuciri ba" Shukra tace "ke ni kin damen wai angaya miki ba aure zamu ba tab!" Maridyy tace Allah ya sawwke nikam da musty nakeyi kuma agidama su mama Shi suka sani bawani Haris ba, akashe waya lafiya sai anjima a islmiyya.Cikin k'ank'anin lokaci shukra ta gane wayar nan domin zuwan da Haris yayi ya ganta da waya ya karb'a duk ya d'ora ta a network yanzu ta rage waya da Samarin sun koma kullum tana chatin sabin shiga seta kai k'arfe 2 na dare tana online tana hira da samari musamman Haris baiyin chat sosai amma saboda shukr saiya dad'e akai.Da in musty y kira tana d'auka suyi hira amma yanzu Sam bata damu ba koya kirama basarwa take taci gaba da abinda take.

Domin acewarta bai iya soyayya ba.


Adaide wan nan lokacin ne kuma Addmition ya fito ta samu kuma murna gunta ba bakin fad'a inda ta samu Northwest university ranar litinin sukaje sukai Rigitration sati biyu tai tana harkar Makarantar har tana gama.


@7:00

 suna tsaye da safe Baba zai fita Mama na tsaye ya kira shukra ta tsugunna "gani baba."

Yawwa "Ranar monday zaku fara Lucture saiki Kula banda shirmen k'awaye da shashanci kiyi abinda ya kaiki wan nan shine buri na" 


Mama tace ni Wlh da zama abi ta tawa dama Aure kaiwa yarinyarr nan se taje can tayi kaga rawarkai gareta Wlh Sam da aurenta zaifi" baba yace "ki Mata addua kawai Aure ai lokaci ne kuma kinga Mustaph baya nan" Mama tace hakane kuma" baaba yace "ni na tafi" sukai mai adawo lafiya.


Mama ta kalleta "Wlh shukra muddin baki maida hankali ba saina sab'ar miki kodan yanda mahaifinki ya jajirce kan karatunki to kema ki dage , kuma banda kule kulen samari da kawayen banza don na sanki shukra" turo baki tayi "kai mama ni Meye ruwana dasu abinda ya kaini shi zanyi"

 "Atoh kima daiyi."


Ranar Litinin da safe k'arfe 8 shukra ta fece kamar zata gidan biki nan ma mama saida kumai Mata kashedi ta kula kamar ta tabud'e Ido ta ganta acan haka ta keji .shigarta school taga 'yan mata da samari kowa na harkar gabansa wasu na zaune suna hira wasu kuma lokacin suke zuwa dayawa wasu basu San fuculty nasu ba wanda itama shukran na d'aya daga ciki haka taita yawo tsayuwa tayi dai de kusa da wani book Shop wasu 'yan Mata sukazo wucewa tace don Allah intambayeku? d'aya ta waigo "Allah yasa munsani" shukra tace fuculty of mass communication nake nema" d'ayar tace "oh da alama ke sabuwa ce ko?" tace "eh."


Murmushi tayi "ai duk new comer sai sun samu hakan, biyomu akwai sis namu course naku daya itama sabuwa ce" Dad'i shukr taji "ngd sosai" nan suka fito shukr tabisu abaya......

[15:51, 12/27/2017] ‪+227 90 29 04 44‬: ⚜IZINAH CE ⚜ 

                                               BY  

                                                           QUEEN MEEMI

                                                       page 8 


  

✍🏻...Nagarta writers Association

           


                                                                                           ''sakale -sak'ale haka take binsu abaya harsukaje fucultyn suka nuna mata k'anwar tasu. "Meena ga k'awa munyi miki itama sabuwa ce" nan Meena ta ce "welcm suna na Ameena abdussalam kefa?" tace "shukra ibrahim" sun dan tab'a hira sukaga anata shiga hall nan suma suka mik'e suka shiga.A kwana atashi yau watan shukra d'aya tana daukan lucture ido ya bud'e sungane kan komi itama Meenar 'yar rawar kai ce duk class nasu ansansu da shegen iyayi da rawar kai gason nuna iyawa.Bayan wata uku Haris ne zaune cikin mota yana kad'a kai sakamakon dad'in kid'an daya keji can ya hangota ta tawo nan ya murmusa tana zuwa tabud'e gaban mota ta shige "My luv harka iso?" yace "waya gaya miiki ina wasa akanki tab!" nan ta murmusa "yawwa kinga sak'on dana turo miki ta whatsup?" tace aa daling wayar ba caji ne" yace "ok" nan ya figi motar sukaja suka bar farfajiyar school d'in tun sati biyu baya kenan ya fara zuwa school d'in yana d'aukanta amatsayin zaina kaita gida sai ya biya da ita wani gun daya san ba mutane ya zauna suyi ta hira, yanzu ma da suke wani waje mekamar gardn a zaune tace "nawan wlh so nake kawai lokacin Auren mu yayai ina sonka sosai" Shafa sumar sa yayi tare da sakin wani murmushi naki wasasa ne domin ni ji nake kamar na had'iye ki nan ya kamo hannunta "baby tab'a hat nawa kiji dariya tayi ta nok'e"


 "Ainasan kana sona" nan ya shafo fuskarta "kina da kyau baby pls ki bani dama na nuna miki son danake miki tace kadena tab'ani bakyau ai soyayyr da muke wlh bame irinta basai katabani ba" nan ya harareta "baby da sauranki ai yanzu soyayya itace ku nunawa juna afili d'an kiss d'in nan da hug duk da ni banayi amma nasan masuyi don bakiga yanda suke burgeni ba" shukra tayi tsai "nikam na tsani soyayyr shan minti gwanda in anyi aure ayi" d'an matsowa yayi kusa da ita baby idan mukai Aure xan baki asalin k'auna jitai jikinta ya canja batai auneba taji bakinsa anata da saurri taja baya ya matse ta kici- kici suka hauyi dak'yar ta k'wace "Haris na gaya ma banason wan nan abun kabari mi Aure mana!" nan ta juya ta d'au Jakarta tayi waje shikam jiyayi jikinsa ya mutu murmushi yayi "baby i luv u" ya mik'e ya bita har takai bakin titi sai zuba sauri take ganin K'arfe hud'u tayi nann hankalinta ya tashi kuma k'a ida duk ran talata k'arfe biyu tana gida Hon taji abaynta babyna "yi hkr tawo muje bazan k'araba wlh sonki da kyanki ke d'imautani wani murmushi yayi nan danan taji wani sonsa taji ta huce ta bud'e gaba ta shiga yaja har unguwarsu ya kaita ya ajeta abayan layinsu.


      
IZINAH CEPage 9                                                                                    k'arfe goma na dare shukra suna kallo wayarta tayi kara ganin layin musty yasa tayi tsaki a yatsine ta d'auka "ina jinka" beyi mamakin yanda yaji voice nata ba domin yasan za a rina sam shukra bata damu dashi ba aganinta be iya soyayya ba, "kina lafiya?"


 Tace "lau" yace "madalla to meye labari? tsaki tayi ciki- ciki babu nan yace ok dama na bugo mugaisa duk ina kewarki" tab'e baki tayi "bacci nakeji" yace "ok saidaaaaaaaa safe" Kit ta kashe Kanma ya kashe mama na kula da ita "ke kuma zumburar me kike? na kula duk sanda yaron nan zai bugo waya sai kina jin haushi ina lefin wanda ya damu dakai dande ba shasha shun samarinki bane shisha" 

"Mama fa bashi bane" tashi tai ta shige daki k'arar kirarn harins ne ya shigo nan taji wasai a zuciyatta.


 "Tawan" naam "nawan wlh my dear wlh kaine araina"

"Nima hakan tawan hau whtsup ki gani" da saurita kimtsa ta kwanta ta hau online Olready yana online gani nawan yace "wlh kamar na had'iyeki nakeji. uhum "haris kenan kanka ka sani wlh babu wanda nake k'auna face kai wlh akanka xan iya komi"


wani dad'ine ya ishe shi jin kalamanta yace "beauty bari kiga wasu pictures amma fa sekin daure don kawai na nuna miki ne wata banzar yarinyace ta turon wai fa ala dole sona take amma sam batada kamun kai." shukr ta hade rai "dama kana da budurwa bayan ni?" ta tura mai sad face.
"Tawan kema kinsan keta dabance banda kowacce budurwa bayan ke wan nan itake kid'anta domin bata gaba na nan ya kalallamet harta hak'ura tace ya turo mata ta gani take ya watso mata wasu bad pictures da sauri ta rufe ido tana sallallmi "amma wann ba tada kamun kai" yace inafa nan tai shiru tana kalla yace "yade?" ta maida mai "wlh wani iri nakeji" nan ya samu dama "ko nazo ne? tace "ina? yace gunki ta watsup nan ta sa dariya ,ganin ya samu dama yace bara na na kiraki haka ya kirata yana ta kod'a surorin jikinta ita kam tanajjn dadi tun tana jin kunya tazo tana sonji jin yanda muryarta ta canja yasa ya hau yi mata maganganun da basu dace ba haka ya tayar mata da hankali yayi mata bye ya kashe.


 Zaune ya tashI "yes hak'ana yakusa cimma ruwa angaya mata ni nawasa ne nan ya nemi layin wata Budurwar tasa ya kira .ita kuwa saida taje tayi wanka lokacin kowa yayi bacci ta dawo ta kwanta ta samu kanta da son dad'a ganin bad pictures din nan wan nan kenan.

IZINAH CE 

 


Page-10 
 Tuni Haris yakoya wa skhr chatin na batsa haka xaita turo mata vedio tana bud'ewa idan sun gama chat ya bugo mata waya su cigaba yana mata xancen batsa tun tana kaucewa har ta saba in basi bama bata jin dadi nan shukr duk t futsare.


 A SCHOOL inta je batasan zaman lucture fita take ga samari kowa a class nasu yace yanaso ta saurareshi ganin canjawar datayi Meena ke mata faad'a amma bataji ,ita Meena barta da raawarkai da iyayi amma tana da kamum kai. dakwa antashi haka haris xaizo y d'auketa su je wani gun hakan y samu damar yimata su kiss da sauran abubuwa da yake dama ya gama koya mata a chat nan abun ya shigeta ba ranar banza ba da bazai yi romance da itaba .


Mama na kula da canjn shukra Intai mata magana tace karatu take tsayawa`a shcl ahakan suka fara exams na second semister nan yad'an d'aga mata k'afa har suka gama akai hutu alokacn hafix y gama ABU zaria yadawo kuwa gida ita kuwa shukr tun dawowar hafiz ta dad'a shiga matsi ga ba damar fita saboda schl ana hutu nan duk ta takura saide tai k'aryar zuwa gidansu hassana .

                                                              IZINAH CE  


  page - 11 


                                                                              yauma da Haris yazo suna zaune a inda ya saba zama gidan su hassana da yake wajen akwai d'an duhu sabili da rumfar dake gun suna hira hannunsa na hijab dinta sai lumshe mai ido take kamar daga sama sukaga wan hassana tsaye sai hararan shukra yake wani kallo ya bugawa haris da borin kunya ya janye hannun itakam shukra kunya ce taji ta kamata.


 "Malam daga yau karka k'ara zuwa nan gidan da sunan xance wato mune banzaye ko ka maida nan gurin lalubarta ko? Dama kune masu b'ata yaran mutane Allah y shiryaka"


 Haris ya mik'e "baby sai munyi waya" ya fita Be kalli wan hassna ba nan kabir ya juyo "kin ban mamaki amma Albasa batai halin ruwa ba kin b'ata wayonki wlh ashe ke ke koyawa hassana futsara ko? to daga yau karna k'ara ganinki "


 Sumi sumi ta mike tayi waje yayi tsaki ya shege gida duk gidan SU HASSANAR shi kad'ai ke taka musu burki kuma suke tsoro.


 Shigar shukra gida Mama dake tankad'e tace "shukra zonan" taje ta zauna ta kalleta tajin jina kai "wato ke yanzu k'afarki bata san zama ko? to ki kiyayeni dln kinga babanku bayanan ko? to aiga yayanku yana nan duk wani abu da kike karki fasa" tura baki tayi gaba tana k'unk'uni zata shige d'aki taji an doke bakin da k'arfi tasa k'ara da kuka "menayi maka?"


 Hafix yace "Mama aiba sa'arki bace tana magana kina tura baki gaba dan kin koyo fitsara ni na rasa meke damunki" harara ta Daka mai ta shige daki cike da haushi biyu.
Daga taaskar Queen MEEMI

[15:51, 12/27/2017] ‪+227 90 29 04 44‬: ,⚜IZINAH CE⚜BYQUEEN MEEMI

Nagarta Writers Association


Page 12-13


Haka rayuwa tayi ta tafiya har hutunsu ya k'are suka koma ba wanda yaji dad'in komawar nan kamar shukra da Haris domin zasu dad'a gamewa soyayyarsu suke hankali kwance.SHUKRA ce tsugunne gefen baba tana matsar k'walla da k'arfi Baba ya daka mata tsawa "Shukra me kike ne? wasa kike ne a makarantar? ace ki rasa me zaki fito result dashi sai pass ina k'ok'arin ki yake? first semister ai kinyi k'ok'ari ace 1.0 haba" Mama dake jan carbita sallame ta d'ago tace "kaima de ka fad'a domin tasa wasa aranta kuma kullum se yamma take dawo wa idan nai magana tace karatu takeyi " kukaa take kanta akasa "Baba kayi hkr wlh nayi yanda ya dace mugwayene Malaman su suke ragewa" "Yimun shiru ke kad'aice a Makarantar ne ?ko ni ba malami bane angaya miki bansan kan Makaranta ba? to wlh karki bari musa k'afar wando d'aya dake inde baki dage ba domin sena sab'a miki kinsan yanda nake fafutukar karatunku kuwa? to ki gyara de tashi ki bani guri."Mik'ewa tayi takoma d'aki.


 Salon da haris ya canja shine hafiz na ajeta a schl shi kuma zai d'aukeeta su tafi wurin hutawa sam yaanzu karatun baya kanta sam bataji fadan baba ba yanzuma daya kaita wani d'an k'aramin restourent don suci abinci d'agowa yayi ya kalleta sam yanzu shukra kunya tabarta ko tsoro bataai kar wani idon sanin yazo ya gantaa ALLAHN daya sota ma ba mutane da yawa. 
Bayan sun gama suka fita yana driving ya kalleta "dear bari na kaiki gidan yayata ku gaisa tana yawan son ganinki" murmushi tayi "kai amma naji dad'in jiin hakan amma schl zan koma" wani shu'umin murmushi yayi "habade kina ban dariya idan muna tare kina maganar schl karki damu dis semister zaki samu score me tsoka ni zan miki shige da fice, anan ne fa muke samun damar had'uwa."
kallonsa tayi ta kashe mai ido d'aya "da d'ina dakai akwai iya tsara kalamai" wani kallo yabita dashi nan suka karya kwanar unguwar suka doshi gidan me gadi ya bud'e gaban tane ya fad'i yayin da ta fito gaba yayi ta bishi abaya suka shiga falon. Wata mata tagani tsaye alamar unguwa zata "Aa wanake gani kamar haris" murmushi yayi "gaade surukarki na kawo" zuwa tai ta rik'e hannu shukra "kai masha Allah ka iya zab'e kaga gidan bakowa maa nima fita zanyi bansan zaku zoba" k'walawa me aiki kira tayi "kawo musu lemo" nan taa kawo Anty ta zauna suka dan tab'a hira "haris yace ki tafi kawai ba damuwa naga anata kiranki" tashi tayi ta ajewa shKr ledar data d'auko "ki gaida gida surukata" ta fita da sauri haris hakn ya bashi damar da wowa kusa daa shukr "babyna yadai" tace "mutafi kawai" murmushi yayi "haba de ki zauna mu huta man Pls dan dauko mun wani cup mana a kitchn naga 'yar aikin tafita wanki" ok tashi tayi yabi bayanta da kallo yaja wani gwauron numfashi da sauri ya zaro wani magani ya jefa a lemon dake gabanta ko mint ba ai ba yaa narke tana dawowa ta zauna nan ya tsiyayi lemon "baby karashe lemon naki mu tafi" ahankali ta d'aauka ta kurb'a gabanta na fad'uwa tas ta shanye kamar magic taji jikinta ya mutu kamar mejin bacci mik'ewa tayi taaji kamar zata fadi takoma ta zauna ganin hakan ya taso yaazo kusa da ita a zuciyarsa yana lalle yau zan cika burinaa 'haka ya hau yi mata su kiss nan da nan ta fita hayyacinta shimaa hakan ganin yana neman wuce gona da iri nan tafara k'ok'arin hanashi amma ba karfi domin ta kasa tab'uka komi acikin wan nan haalain 'yar aiki tazo zata shigo falon ta gansu da gudu ta koma da baya nan hankalinsa ya dawo jikinsa ita kam shukr k'arfin hali tayi ta mik'e tana layi tad'au jakarta tafita zuciyarya ba dad'i ganin hakan shima ya tashi ya fita.
 Shukr har azuciyarta haushinsa takeji sa'arta dayaa be keta mata haddi ba amma duk wani romance ba wanda be da itaba kuka tasaka jikinta na rawa tana tafiya ahankali domin duk abunda suke bata tab'a tunanin zece zai je nan ba tari adedeta sahu tayi tahau haris dake gefe acikin mota sai hon yake ammmaa taki waiwaye gidan su hassana direct tace dan adedeta ya a jeta ta bashi kudi atsorace ta shiga don bata so kabir ya gantaa ya koreta dan d'akin hassna tayi tana zaune sai wulla loma shukr ta shiga kamar yar maye kwanciya tayi akan gadon hassana tace "ke shukr yana ganki kamar mara lfiy" d'agowa tayi hassna bacci nakeji bari inna tashi zan gaya miki" kamar mushe ta hau bacci.⚜IZINAH CE⚜ Page-14-15


 Bayaan awa uku lokacin k'arfe hudu dede shukr ta tashi tad'aan ji dama-dama abinda takeji ya saketaa nan ta tashi tayi wanka tad'auro alwala ta d'akawa hassna dake bacci duka da sauri ta tashi meye tace "sallah haka itama taa mike tayo sukai sallah bayan sun idar hassna ta zauna bakin gado "wai ni k'awas d'azu meya faaru ne naganki a hargitse? ga wayarki sai ring take" Shukra ta tab'e baki "kinsan haris yau ya kusa yimun fyad'e" zaro ido hassna tayi "ke danna ALLAH!" shukr tace "kawai ALLAH ne ya kiyaye nikam daga yau nadena biyewa haris Yana tab'a jikina d'inma na dena yarda" hassana tace "tab aini kin ganni nan duk wani tab'e -tab'e ba wanda bamai da saurayina kawai de banyarda da awuce wani gun ba' kinsan mazan nan da wayo sunfimu kawai ki basar ki mai kaashedi ku cigaba da inda aka tsaya kodan kudin da yake cikaki dasu ai kya hakura" shukr data rik'e baki "au! kema dama kinayi?" Hassna ta fasa dariya "ke yanzu fa da wuya kiga saurayi da budurwa ba ayi" nan shukra taji duk d'an haushi ya fara tafiya (Mata a kiyaye a kula da irin Samarin sa za ana kulawa karkiga wai kinada farin jini ace kowane namji ya kulaki ki tsaya to ahakanne tun ana had'uwa dana kirki har zakizo ki had'u dana banza wanda dama surarki ke rud'arrshi duk yanda zai sai yayi don ya samu biyan bukatar sa seyayi san nan akula da k'awayen banza domin suke hure wa su kunneALLAH ka shirya dukkan matasan dake wan nan d'abia)

 Sun gama hirar shukr ta tashi ta tafi gida. Sati d'aya kenan da faruwan hakan amma haryanzu shurkr fushi take da haris yauma data ke zaune bakin bishiya a sch haris yazo da yake suna zama agun yazo ya zauna" babyna ta juyo nan yace "pls forgive me nashiga wani hali"

" Haris inde kasan ketan haddi zakayi wlh bazan sake kula kaba inama lefin tattab'enin ma da kake ( mu kula ALLAH subhanahu wata ala ya hane mumunai da kusantar zina karkiga wai kuna tab'a jikin juna kuna su kisss da romace kice wai ba komi bane ba wani abu bane tunda ba ai me gaba d'aya ba to wallahi kinyi kuskure domin kin halartar da abinda ALLAH ya haramta Allah ya shirya 'ya'yan musulmi) 


"Haba shukra na wlh bana bacci da cin abinci pls ki yafemun na dena nan ya taro k'walla sai gasu nan shar shar suna sakkowa ganin hakan yasa jikinta yayi sanyi tace "na hak'ura" azuciyarta tana lalle ba k'aramin so haris kemun ba tunda yake kuka Akaina. Ganin hakan yasa ya kalallameta da hira har suka sake wan nan kenan."Kinga Mardiyya idan kinSaan abinda zaki gayan ne To kiyi shiru" mardiya dake zaune kan stool a d'akin shukra shigowarta kenan tana mata fad'a kan abinda take "kinga shukra wallahi watace take min zan cenki itama a schl naku take tace bakya karatu kullum akwai wanda ke zuwa ya d'aukeki haba ina wayonki yake? ki ji tausayin su baba mana duk fafutukar ganin kinyi karatu amma kina yaudararn su haba ki gane mana ayanzu muna wani bahagon zamani wallahi inbakai taka tsantsan ba sai yabi dakai ki rabu da haris sam ba mutumin kirki bane" Shukr ta d'aga mata hannu "wacece wadda ma ta gaya miki ina tasan ke k'awatace? mardiya tace "k'awataace zuwa tayi Gidanmu tana ganin album d'ina taga hotonki shine fa take gayan wlh shukra ki rabu da shi haba! kefa ammiki mijima amma kin sashi kwandon shara wai sunan be iya soyayyaba wlh ba anan take ba, domin irinsu sae an aure suke nunawa ki kula! wlh duk abinda mutum yake Alllah mahaliccinsa nagani Kuma ana rubutawa akwai ranar da gab'ob'inka su zasuyi maka sheda wanda bakinka bazai yiba idan kayi aikin assha dasu su fad'a haaka na alkairi kiji taoron ALLLAH wlh kuma abin kunya ne ace wataran iyayenki suji ba baki naakee miki ba kuma na fita hakk'in kawancen mu"

Shukr jikinta yayi sanyi tace "naji zan dena nan suka canja wata hirar .,
Akwana atashi har Mustaph ya dawo daga tafiya ya gama course inyazo gun shukr saide yayi ta magana amma bata cemai uffan sede tayi ta chat da haris duk da inta dago yana mata kwarjini sam abinda,take mai yana bashi haushi yana damunsa inyayi magana ta tab'e mai baki hakan badon an riga manya sun shigaba da tunanin hak'ura yake da ita sede yabawa zuciyarsa hkr haka zai gaji ya tafi kullum kuma da abinda zai kawo mata ta amshe ba kunya wan nan kenan.Yau Monday hafiz ne ya d'auki shukr ya kaita Makaranta akan babur dinsa yaje ya fakata ta sauka ya juya ko minti batai ba saiga haris yazo yay mata waya tazo motar sa ta shige ya figa dama sunyi dashi zasu munjibir park Hafiz ya dawo sai waige -waige yake domin shkr taa manta handout nata yana tsaye sai mata waya yake akashe ganin meena yasa ya tafi wajenta gaidashi tayi yace "ina k'awarki ne? yanzu na kawota ga handout ta manta nata wai inama take?" dama meena nasan samun damar fadar abinda shkr keyi nan ta gyara mayafi "ai yayanmu wlh sede adage da addua domin tun second semistr saurayi ke fita da ita yanzu nima mun ja baya da kawancen namu don ta canja k'awaye duk adalilin ina gaya mata gaskiy bataji yanzu hakan ya d'auke ta sun fita kullum kuma hakane kana ajeta yake d'aukanta"Idan sane sukayi jajawur jikinsa har rawa yake ya d'ago "meena nagode Allah ya saka insha ALLAH za a d'au mataki"

 "Meena tace to yayanmu sai anjima "ta tafi shima ya hau babur ya tuka afusace.
Daga taskar Queen MEEMI

[15:51, 12/27/2017] ‪+227 90 29 04 44‬: ,,⚜IZINAH CE!⚜ BY


QUEEN MEEMI

✍🏻.Nagarta Writers Assocition
Page-16-17
Afusace ya tuk'a babur d'in zuciyar sa na tafar-fasa nan ya fafara babur dinsa don yaje gida ya fesa, dede yaje Round about ya tsaya don abasu hannu kamar ance ya juya ya nan ya gano shukr gaban mota sai kurb'ar lemo take suna dariya kan ya motsa nan bada hannu nan ya bisu abaya tiryan- tiryan haka yake binsu har suka b'ace mai da gani cikin takaici daya cikashi ya juya yayi hanyar gida mama na kitchn tana had'awa baba abinci don be fita ba yau zainab ma duk sun tafi schl hafiz ya shigo idanu wansaa jajur ya tsaya gefen kitchn kamar yayi kuka,mama ta dago ta kalleshi "hafiz yaa naganka a haka? kallonta yayi "mama ba anyiwa shkr miji ba?"

 "Eh k'warai meya faru?" numfashi yaja mama shkr ta canja wai ashe kuulm na kaita schl ina sauketa saurayi ke zuwa ya d'auketa su fita daga makaranta su tafi wani gun kawarta ta shaida mun kuma bayan na fito wallahi mama da idona naganta gaban mota na bisu abayaa aammaa suka bacen."


 Mama kuwaa suman tsaye tayi zama tayi kan kujera yar tsugunne ta dafe kai na shiga uku yanzu duk tarbiyar da naiwa shkr kuka ta saka "yanzu hafiz bakasan inda ya tafi kaita ba na shiga uku" hafiz yace mama ki hkr kawai muga dawo warta" dede lokacin baba ya fito yana tambayarta inna gama ganin tana kuka ga hafiz atsaaye yasa yace "meya faru ne?" 

malam,yanzu shkr dama dab'iar data koya kenan" taa fashe da kuka "wai meye ne? Baba ya ambata hafiz ya gaya mai "innalillahi wa inna,ilaihi rajuun ya ambata" koma wa daki yayi yana kai-kawo yakasa tsugun nan ya kuma fitowa ya d'auko waya ya dannaa kiran shukr dede lokacin suna zaune itada haris ya manna ta ajikinsa tamkar matar sa sai kashe musu selfie yake wani ai dariya wanii ai murmushi wayarta keta ring amma bata ji sabosa shed'an yana k'awata mata halin da suke ciki wanda dad'i suke ji Apple haris ya d'auko ya bata abaki ta gutsira suna aikawa juna murmushi. 

Acan gida kuwa Baba wajen 20mis call bata d'auka ba hakan ya fusatashi ya aje ya juya ya cewa mama "lalle na yarda zamani ya baci ban tab'a zatan shukr zata biyewa rud'in sa ba duba da tarbiyar da muka bata ko zainab ba zatayi haka ba amma makarantar nan bata karbi shukr ba"

 Mama tace "d'ane ka haifeShi baka haifi halinsa ba", haka baba yak'i fita mama ma hankaalint atashe domin gaabanta har fad'uwa yake.
 Acan kuwa shkr da haris guje guje suke na ma,abota shauk'in soyayya da k'yar ya kamota suka zube agun haka suka gama shanawar su tamakar mata da miji sun manta da hakan haramci ne babba. "Nawan wai yaushe zami aure? kallonta yayi "sekin gama schl" tace "to Allah y kaimu" jakarta ta d'auko ta zaro wayarta ganin kira rututu yasa ta k'walalo ido kiran hafiz dana Baba kamar aci babu, nan gabanta ya fad'i "Allah yasa de ba wani abun ya faru ba" haris dake kallonta "yade babyta?" tace "kiran baba na gani da yawa"

" kema dea meyasa baki kashe wayarba?

 nan ta mik'e "Nawan mutafi kaga k'aarfe 5 dede fa" mik'ewa yayi suka tattare abubuwansu suka sa amota "muje to amma bangajj dake ba" fari tayimai da ido "gobe ma rana ce ai nayi maaka tana dinta" dad'i ne ya kamashi "komai naki swt ne babynaa iluv u so much" nan suka shiga motar ya tuk'a suka d'au hanya .

Mama dake kai kawo sai hawaye take zainab dake gefe "Mama kiyi hkr insha ALLAH yanzu zaki ganta baba ne ya leko "wai har yanzu bata shigo ba?" K'wala kiran hafiz yayi ya fito "jeka dad'a duba hanya" hafiz ya tashi ya fita kicib'us sukayi a soro shukr na shigowa wani banzan kallo ya watsa mata ya duba agogonsa k'arfe shida da rabi besan sanda yaa d'auketa da mari ba kwala ihu tayi "menayi maka?" nuna mata hanya taayi suka shige ciki Mama da Baba ne atsaitsaye fuskar su duk a had'e tsayawa tayi "mama meya faru?" Baba ya daka mata tsawa "kinci gidanku" daga ina kike da wane d'an iskan saurayi ake ganinki dashi?" gabanta ne ya fadi na shiga uku Mama kuwa harara ta bita dashi ta shige d'aki duka taji ko ta inax Mama ta rufeta dashi da caribi wullar da kajarta tayi ta fada d'aki Mama ma ta bita hafiz kam yana kallo Mama tai mata duka baba ma ya shigo da bulala ya mik'awa hafiz "zane min yar iskar yarinyar nan" dama haushinta yakeji nan ya hau jibga tana ihu zainab Dasu auta kuwa sai kuka suke saboda ta basu tausayi seda ta jibgu san nan ya kyaleta inbanda ihu ba abinda take kowa,ya barta a wajenn haka taci kukanta ko abinci batayi ba nan domin zazzabi ya rufeta.

IZINAH CE Page 18-19


Da safe k'arfe goma zainab ta kira shkr da yake yau lahadi ba makaranta cikin tsamin jiki ta tashi ta shiga Baba da maama da hafiz ne zaune tana shiga ciki mama ta harareta ta zauna rakub'e baba yace "yanzu ki gayax mana dawa kike yawo kusan shekara ke tun yaushe ma kuke tare? kallon hafiz tayi ya doka mata harara tsawa baba ya daka mata ba magana nake miki ba!" bakinta ya hau rawa "Baba karatu muke" mari taji an bata bBaba yace "mu zaki raina baki zauna kina karatu a makaranta ba sai wani gardi ne zai koya miki?" Mama tace "ai sun dad'e domin dasu take waya ai nagaya maka ta canja hali" Baba yace "lefin kine ai dabaki k'wace ba" mik'a mata hannu yayi "bani nan wayarki" jikinta na rawa ta bashi "to daga yau ni na sakaki a makaranta ko? to na cireki k'afarki karna k'ara gani awaje kuma mustaph zan gayawa ya turo shashashar banza da wofi wlh kin bani mamaki shukr amma kanki ki kaiwa tashi ki bamu waje" kuka wiwi take ta fad'a kan gadonta "wayyo an rabani da haris wallahi shi nake so" haka tayita kuka har ta koshi ba wanda ya kula da ita cikin kwana 2 duk taa fige ta fita hayya cinta ga ba fita wa nan kenan .
 Yau satin ta biyu kenan ta rasa madafa ga ba School so take kawai ta saamu damar yiwa haris waya cikin saa saiga mardiya nan wajen 3 taji dadin zuwanta Maridya tace "yanaga kin rame?" shkr tace ke Ina cikin wani hali yanzu an rabani da haris an hanani Makaranta an k'wacen waya"


 Mardiya tace "duk me yasa?nan tace kawai don anganni amotar sa" Maridya tace "kinga abinda Nake fad'amiki ko? hmm wallah da ace son gaskiy Yake miki da tuni yazo gidan nan kan Maganarki tunda yaga shiru baya jinkI" Shkr tace Bani aron wayarki pls nan Mardiya ta bata dama ta hardace number din haris ta buga kirr sai ring take wajen three times saai ana hud'u ya d'auka jin muryarsa yasa ta fashe da kuka "haris" nan yace "shkrta meya faru ne? wayarki akashe naje sch naku ance bakya zuwa" nan ta gaya mai dalili yaace "oh no an kwafsa mana" shkr tace "yanzu dai kawai ka turo manya haris" yace "kai inada tafiya wata hud'u kinga kuma sai nayi fafutukar amincewar su Dady don ba lalle a Amincen Aure yanzu ba amma zan san abinyi" nan taace "duk abindaa kaa yanke kabugo number nan" yace to nan ya kashe dama handsfree tasa mardiyya tace "kinga ko wallahi ba Aurenki zai ba jikin shkr yayi sanyi shikam haris sam be d'auki maganar da muhimmci ba haka ya basar domin ba aure agabansa yanzu dan so yana santa amma ba aure agabansa yanzu haka y manta da maganar, sati daya da maganar su ya d'aga egyt bai sake bugo wayarba itakam shkr ganin hakan yasavtasha jinin jikinta duk tayi sanyi ta rasa mafuta.
 Ana hakkan iyayen mustaaph suka kawo kud'in zance dana saka rana inda aka sanya wata buyi domin baba yace baisan asaka da yawa. kuka sosai shkr takeyi kullum idan suka buga wayar haris akashe ga lokacin biki yana k'aratowa mama kuwa shirye -shirye kawai suke ba wanda kebi takan skr tun tana jiran haris har ta ta hkr.
 Yau da take zaune adaki tana jin Rai dangin goro da ake aradio ana gamawa aka sako programm na malama Tasalla nabilsi tana magana akan tab'arb'areaw zamani da rud'ar daya kewa yaran zamani inda take jan hankali kan matan dake biyewa maza suna soyayyar shan minti haka taita kawo ayoyi da tsoratarwa akan masuyi ak'arshe tace da yawa yawan wanda suke hakan sammarin basa Aurensu idan ma,anci sa' a sun aure sun,to zaman zargi zasuyi da rashin girmama juna.kashe radio d'in tayi sabili da jikinta da yayi sanyi ta hau kuka tsoron ALLAH ya shige ta da nadamar biyewa haris da tayi tunani ta hauyi yanzu ya zatayi nan ta d'au d'amarar neman yafiya ga ALLAH da istigfari tun daga lokacin take ta istigfari kullum dare bata bacci sai sallar dare tare da neman yafiya yanzu ko yaushe karatun kur'ani take haka taje tanemi yafiyar mama da Baba suka yafe mata nan taji dad'i yanzu tana saurarar mustaph su mama sunji dadin ganin sauyawarta.
 Haka lokaci yayi taja har lokacin bikin ya k'arato ansha shagalin biki sun shirya da meena kawayenta sun yawaita haka akasha shagali aka mika ta gidanta amarya ta tare Tunda taje gidan mustaph ke Mata wata zafafaffiyar soyayya da kulawa nan danan ya mantar da ita komai ya dasa k'aunarsa aranta ayayinda takeji ba ishi lalle shedan yaso rudarta da tuni ya rabata da jarumin namji a yanzu ne ta gane haris bema iya soyayya ba kan musty nan ta goge haris aranta hakan suke fa rayuwa cike da so da k'auna har bata so ta tuno da abinda sukai tare da haris setaji ranta yaa b'aci  har tukwicin mota musty yayi mata saboda aman lafiya.
 Shekarar ta d'aya yanzu da aure wata rana da yamma tafara ganin kiran haris inda yace ta yaudareshi bata bari ya dawo sunyi Aure ba, bayan tasan yana sonta ita kuma tace yayi hkr tayi aure ALLAH baiyi ita matar sa bace shi kuma yaci alwashun bazai rabu sa ita ba domin tasa ce. 


 kullum sayya kirata ta canja layi wajen uku amma bata sanin inda yake samu t ta shiga tashin hankali duk ta rame domin barazanar da yake kan,sai ta yarda sun cigaba da shanawar su ganin taki hakura yasa ya kawo mata hoton hakan ya dimautata ganin ita dashi a hoton manne da juna suna ta kiss ga hannunsa kan kirjinta bata tab'a zaton ya d'aukesu hoto ahakan ba.
 AN DAWO LABARI

Daga taskar QUEEN MEEMI

[15:51, 12/27/2017] ‪+227 90 29 04 44‬: ,,,⚜IZINAH CE⚜BY


QUEEN MEEMI♠
✍🏻...Nagarta Writers Association
  Wattpad@ Queen-Meemiluv

  

  


Page -20-21_kun cancanci yabo da girmamawa tabbas kun kasance masu matukar mutunci ina ji daku Antis dina Anty maijidda and Antysis ALLAH ya raya zuriarku AMEEN_


ANDAWO LABARI 

juyi tayi tare da muskutawa saboda jin kanta da taji yayi nauyi tashi tayi ta zauna ta rafka tagumi wayarta ta fara laluba amma bata jitaba sai hotunan data jiyo nan ta d'auko ta kallah ta fashe da kukaa a ssalub'e tag tashi ta bud'e wardrobe nata ta cusa a ciki ta mayar falo ta fita ta samu gurri ta zauna ta kalli agogo hud'u saura tunani tafara kode ta gayawa musty ne wata zuciyar ta kwab'eta kan zata taso da balli wayarta ta auka ta latsa numbobi ta kamo sunan mardiya ta rangad'a mata kira ring 2 ta auka shkr tace "aminya kina gida?" Mardiya tace kizo ina buk'atar taimakonki plsss" mardiya tace "meya faru?" "kede sekinzo"

" ok ki jirani zuwa gobe da safe" tace "ALLAH ykaimu" ayanzu mardiyy ce kadai kawar shkr domin itace ke mata kawance na amana tuni ta rabu da hassana domin ba kawar kirki bace nan ta tashi tayi sallah ta shiga kitchn: Bangaren haris kuwa zaune a d'akinsa tsumayi yake yaji kiran shkr kan amincewarta yaji shiru gashi sai buga wayar ta yake akashe nan yaja tsaki "lallema yarinyar nan" kallon kudu da arewa yayi ya mik'e zai fita saiga bala abokinsa nan suka cafke bala yace "yadai mutumina nazo ka bani 4k ne wlh nashiga kwata" haris ya tabe baki yace "kaci sa a dama ina nemanka kasan na sakawa shkr tarko da wuya in bata fad'a ba" tafawa sukai Allah mutumina jerawa sukai suka fita sharholiyarsu.

 

 

 Washegari da safe shukra tun wuri ta tashi tayi breakfast musty Ya shirya ya tafi office karfe goman safee kiran haris ya shigo tak'i d'auka haka yayi ta Kira karshe y turo msg da sauri ta bude inaso ki sani yauda k'rafe hud'u inason ganinki kizo nan city park idan ba hakaba su nan aurenki matacce kuka ta saka na shigaa uku haka ta cire d'ankwali ta hau kuka wiwi har mardiyya ta shigo bata sani ba "lafiya mezangani shkr ko wani abunne ne y hadaku da musty" shkr ta share hawaye "da ace shine ma da sauk'i zamu shirya kanmu mariyya se yanzu nake dana sanin sanin haris domin ya zamemun jaraba yanzu ya hanani zama lafiya agidana" mardiyya ta zauna "wai meke faruwa ne? Kinsani a duhu" nan shkr ta kwashe komai ta gaya mata amma ta rufe hotunan daya kawo mata bata fad'a ba "tabbs shkr haris yacika shed'ani ya rasa me zai kokawa da ita sai sunanar ma aiki" shkr tace "yanzzu hakan nan yayi mani text wai mu had'u anjima inba hakaba , zai mutu" mardiyya tace "tab! wlh karkije haka kawai zzanbaki shawarar karki fad'awa, musty" shkr tace "sis zan gayamai saaboda kardaaga baya yaji kuma abin yafi haka"

  

  Eh daa wan nan ma shkr kede karki soma zuwa" shawarwaari ta bata ta sukai sallama kan zasuyi waya tunda ta tafin ta shiga tunani kiran sane y shigo nan ta shiga rud'ani haka ta dauka azafafe tace "malm kadena kirana"x dariya yasa "shkr kenan har kinmanta shanawar da mukayi ai bakida wata fangima awajena"

  

  jinjina kaitayi cike da takaici me dauke,da tarin nadama "ya isa haka da da yanzu ba daya ba koda na biyemaka kai ka rud'eni yanzu ni kam ALLAH ya shiryeni yanzu kaima ina fatan zaka shiryu"

  

  

 Haris yace "Daga baya kenan yanzu hakan nan gani zaune da waya a hanuuna gefe ga systerm kinji na rantsae inhar yau baki zoba wlh saina watsa hotuna nan duk wata kafar yad'a sakon ni irinau insrgrm, tweeter ,watsup fecebook da suransu kuma sunanki zan saka ke hatta email na mijinki na sani ta nan zan tura mai bazan iya rabuwa dake sabida na dandani zumarki ke macen gaban goshi ce don haka duk abinda zanyi sai nayi dana tura kinga kuwa fitowama saiya gagareki"

  

  

  Jikinta ne ya hau rawa ta wullar da wayar dayake handsfree ne tasa tanajin dariyar sa da k'arfi ta fad'a "haris dan grman ALLAH kayi hkr ka rabu dani"

   "shkr ai sekin dawo gareni zan kyaleki wlh kinji na rantsae in bakizo city park ba karfe hudu saina watsa" jikinta na rawa "zanzo" yawwa "ko kefa banda african time kit,ya kashe" zubewa tayi akan kujera ta dora hannu aka wayyo na shiga uku kaicona dana biyewa san zuciya gashi ta kaini ashe haka rayuwa take tabbas naga izinah ya ALLAH kakawon dauki kwanciya tayi jin kanta na bugawa take,baci yq dauketa.

   

   

   

   

   

   

   

   IZINAH CE 

   

   

   

  Page 22-23

   

   

   

   

  Ba ita ta farka ba sai 3 tun safe ko abinci bata ci ba shayi kawai ta had'a don bata sha awar cin komi msg ne ya shigo ta bud'a "karfa ki manta hudu ta kusa" rafka Tagumi tayi haka ta zari hijab ta dau waya Ta turawa musty cewar ta tafi gidan kanwar babarta motar ta ta shiga tana tafiya tana kuka wajen 4:30 ta k'arasav shigar ta keda wuya ta gano shi gabansa ga drinks yana zuka had'e rai tayi ta doshi wajen atsaye ta tsaya "malam gani" murmushi yayi "kin karya doka amma saboda sonda nake miki na hakura gaskiy nayi rashi" harara take zuba mai ya tako yazo gabanta "dama abinda nakeso kisani shine doka ce duk randa nake bukatarki to zamu hadu a otal tunda kink'i kaso aurenki ki aureni gobe kizo idan ba hakaba kiga aiki da cikawa" mari yaji ta bashi idonta yayi ja "haris bana tsoron ta mutu balle tayi rai duk abinda zakai mu zuba dan halak ka fasa aga wanda zaici kasani duk wanda Allah ya shirya ya shiryu kenan ALLAH shi zai rufan asiri bazai sa na tozarta sunnarsa ba koda zaka kasheni wlh bazan biye makaba wlh nayi dana sanin had'uwa dakai mayaudari"

 

  

  Nan ta juya tana kuka ta tafi cikin fushi ya mike yayi bal da teburrin "saina nunawa shkr bakin rijiy ba wuriin wasan makaho bane wlh saina kashe auren kuma na aureta" afussace ya shige motar sa ya fita.

   

   Tunda ta koma gida take kuka ko girki ta kasa Nan da nan zazzabi ya rufeta ta rasa madafa bata son aurenta ya mutu nan ta kudiri aniyar gayawa musty komai ta fanjama fanjam karfe 6 ya shigo gidan ganin halin data ke ciki yasa ya sunkuceta ya fita da sauri ganin bata motsi asibitin dake gavansu yaje nan suka karb'eta emergency doctor ya dubaata yace damuwa da eashin cin abinci ne sukai mata yawa nan yayi treatment nata 7 ta farfad'o likita ya rubuta magani suka koma gida haka musty yaje ya dafa indomie ya kawo dakyar taci.

   

   

   Bayan Ta gamaa yazo ya zuna ya kalleta dear meya sameki? rungumeshi tayi tana kuka "banason na rabu dakai yazama dole na gayama matsalata tsohon saurayina don ban aureshi ba shine yakemin barazana nanta gaya mai komai amma ta boye zancen hoto idan musty yay ja yace "lalle wan nan zai sanr yazzo gona ta" karbar numbee,din haris yayi a wayarsa ya tashi ya fita.

    

  da kyar ta tashi taje taaa yo alwala tazo ta hau sallah haka ta zauna taita adduaa kan ALLAH ya rufa mata asiri musty kuwa yana fita yaa kira haris ya dauka musty cikin fuahi yace "wlh idan baka rabu da matata ba saina nuna maka baka da wayo"

  

  Haris yace au ta sanar maka " to muzuba ai ba wata fangima sa zakai mun don haka koni ko kai akan shkr"

   

  littfai yazo karshe,ku biyoni donji yanda zata kaya wake nasara? amsar naga QUEEN

   

   

   

   

  Daga taskar QUEEN MEEMI,

[15:51, 12/27/2017] ‪+227 90 29 04 44‬: ⚜IZINAH CE⚜BYQUEEN MEEMI✍🏻...Nagarta Writers Association

   

   

   Page 24-25

   

   


_wan nan shafin naku ne 'yan,Queen Meemi fans godia ba Adadi ALLAH yabar kauna_Musty cikin takaici ya kashe wayar kamar yayi kuka wani zazzafan kishi ya cikashi dan yanda yakeji da ace zaiga Haris ba makawa inda bindiga saiyya harbe shi. tsaki yayi ya koma gidan ya zauna inda shkr ke zaune tana kuka musty ya rungumota yana shafa bayanta nan bacci ya d'auketa k'arfe goma ya tasheta suka tafii daki.
k'arfe goma sha biyu na safiyar lahadi Haris na zaune sai buga k'afa yake sai zuk'ar taba yake yana zaune cikin mota ya zuro k'aafar sa bala ne ya bud'e gaban motar ya shiga Haris yace "big boy yade ko garin ne? haris yace "na rasa yadda zanyii na yakice shkr ina sonta yarinyar ta hadu don nasan shegen mijinta da wuya ya sakota shida ita sun batan rai wallahi sati bazaiyi ba saina raba su na aureta wai harni mijinta zai gayawa magana dole na bashi alamar dazai shiga rud'ani"
 Bala yace kaima kaika zauna Kana batawa kanka lokaci kawai ayita ta kare tunda taki baka had'in kaai ka bata shawarar k'arshe in batai ba kawai seka d'au mataki" yawwa ka kawo shawara nan ya jasu suka tafi bayan kwana biyu shkr hankaalinta ya dawo jikinta tama manta da wani Haris yanzuma da take zaune tana karanta littafin meemi murmushi take don jin yanda jaruman littafin ke zuba soyayya kamar ba gobe. dede lokacin taji k'arar waya bata duba ba ta d'auka "shkr kizo city park anjima da misalin karfe hudu ina son ganinki if not wlh zaki sha mamaki sainaje na tayarwa da iyayenki hankali sai nayi abunda zasu tsine miki" gabanta ne ya fadi haari ashe tsohuwar soyayya na komawa gaba da zalinci don ALLAH kabarni na zauna agidana lafy don ALLAH ka kyakeni"

 

 

 

 "Zancen kikeso shkr wlh in baki zoba ki tanadi abinda zaki shaidawa iyayenki" kit ya kashe zama taayi tana tunani k'arshe ta yanke shawarar zuwa tayi don tayi mai kashedin karshe.haris kuwa sai washe baki yake domin yasan target d'in da yayi dole komai ya cab'e murmushi yayi ya d'au waya "bala kaje ka kai fa ka tabbatar komai ya yiwu bana son asamu matsala ,san nan nan da rabin awa zan bugo maka sai kayi aiki na biyu" nan ya kashe.

  

  

  

  

  karfe hudu daide ta faka motar taa gaban wajen ta bude ta shiga ciki yana tsaye yana ganinta ya tawo "welcm beauty" fuskart a tamke kamar an aiko mata da mutuwa yace "ga guri zauna musha drinka" nan tace "ba zama zanba ka gayan mene ne?"

  

  " pls ki dawo gareni ko kizo mu cigaba da inda muka tsayaa" kallon banza ta watsa mai Allah ya tsare ni wlh da in koma irin rayuwar nan gwanda na rasa raina"

  

  dariya yayi yadau wayarsa yaa kira bala yana dauka yace "lokaci yayi" nan ya kashe yayi murmushi "babya meye?" baya tayi ya bita taji wajen arufe juyowa tayi "malam meka ke nufi ne? 

  

  

  

  AAcan kuwa b'angaren musty lokacin karfe biyar yana kokarin fita daga office don komawa gida yaji kira ya shigo wayarsa sallama yayi daga can akace yanzu hakan nan matarka na tare da tsohon saurayinta suna soyewa kaje city park don idonka ya gane maka" kan yayi magana kit aka kashe take fuskar musty ta canja ya shiga rud'ani da firgita kokwanto yaashiga yayi mezai kai shkr wajen wani juyawa yayi afusace ya doshi motarsa har ya bud'e yaji ana kiransa ganin masinja yazo "yallabai gashi daazu wani yace a baka" mika mai yayi yace "ok"

  

  

  Nan ya shiga gaban motar kanya tashi motar ya bude Haka yaci karo da picture wanda suka d'aga mai hankali yaji duniyar na juya mai afusace ya tuka ya juya baya yaayi hanyar da akai mai kwatance.

   

   

   

   

   Shkr kuwa tsugunnawa tayi tana kuka ta dago "ALLAH zaimin sakayya bazan taba yafemaka ba" ahankali ya tako yazo ya bud"e mata da sauri ta suri jakarta tafita tsayuwa tayi a kusada get don ta dauko muk'ullin mota sai jin hannu tayi ajikinta tana juyowa ta kwashe Haris da mari zatai magana ya kamo hanunnta dede lokacin musty ya danno motarsa tun kan ya budw motar hawaye suka fara ziraro mai afusace ya fito kan Haris yayi Bai aune ba ya janyo shi ya kaimai naushi abaki nan ya dafe gun ita kam shkr na gefe tana kuka musty ya kuma kai masa naushi haris ya tare shima yayi kokarin ramawa musty ya tare ganin hakan yasa shkr ta shiga tsakani ganin mutane sunfara taruwa awajen afusace ya janyo shkr ya wullata mota ya figa. 

 Haris kuwa duk dukan dayaci seda ya Murmusa ganin samun nasara hakan shima ya shiga mota ya tafi. 

 

 

 

 

 Kuka kawai take tirka inda musty ke a tsaye ya dago ya kafa mata jajayen idauwansa da sula rine saboda takaici "Ashe cin amanata kike shkr? ashe maganar da kikai mun k'arya ce kin cucueni kinci amanata, kina da aurena kina bin wani"

 

 " wlh musty tunda na aureka bantaba kula wani ba na gayama tsohon saurayina ne wlh sharri yaso had'an zuwa yayi ya kamota ya matse ta "me kika daukeni? yanzu a ina naganki ?ko zaki cemin bake kika kai kanki ba?" wulla mataa hotuna yayi "wan nan kuma yaushe kuka yi?"

 

 

 Dena gani tayi nadan lokaci san nan ta dawo jiki na rawa ta dauka "wlh bansan anyi ba" dauka tayi ganinta ta dashi sun kafa kai suna selfie kowanne na dariya daya kuma ya kwanto a kafadarta dan sanyi taji daba wancenn hotunan baane da tasan se muatu yakusa makureta

 Shkr kije gida shkr na sakeki saki daya "innalillahi wa inna ilaihi rajuun" kuka ta fasa "haris ka cucen" shikam musty fita yayi kama wani mahaukaci sai kishi dake cin sa.

 

 

 

 

 

 Daga taskar Queen Meemi

[15:51, 12/27/2017] ‪+227 90 29 04 44‬: ⚜IZINAH CE⚜ 
BYQUEEN MEEMI✍🏻...Nagarta Writers Association
Page 26-27

_Wan nan Shafin naki ne kawar Arziki @ nafeesa S Umar thnk 4 your lv and care_


Hijab kawai ta d'auka ganin k'arfe bakwai na dare ta dau jakarta tana kuka musty na zaune a kusa da fulawowi ta fito ta tsaya suka k'urawa juna ido da gudu ta fita ko motarta batayi k'ok'arin d'auka ba ta fita tana tafe tana kuka har bakin titi ta shigata samu adedeta sahu ta shiga suna tafiya tana mai kwatance har k'ofar gidansu bayan ta bashi kud'i ta tsaya domin gabanta ke dukan uku- uku me zata cewa iyayenta! kan abinda ya kashe mata aure ya ALLAH ka bani mafita sadakarwa tayi ta shiga tana mai yak'inin zata fuskanci kowane k'alubale tabbas tasan ta tafka babban kuskure Abaya.
 Sallama tayi mama da baba da hafiz su zainab dasu Auta kowa nacin abinci suna hira gaban mamane ya fadi tace "wa alaikumussalam" nan kowa ya d"ago ido zubewa shkr tayi awajen tana gursheken kuka maicin rai hafiz yace "ke meye ne? baba yace "uwata maiyya faru? mama tace "kode wani abun ya samu musty" d'agowa tayi ta kallesu "mama ya sakeni" gaban mama da baba ne ya bada dam! runtsie ido maama tayi ta zare hannunta daga cin abincin hafiz yace "meya faru?

 

 

 Tashi tayi ta shiga d'aki baba ya kalli mama "Ana wata ga wata" mama ta tashi ta bita d'akin tace "shkr meya had'aku? shkr dake kuka hardasu majina ta kalli mama "tabbas wanda baijiba bari ba yaji hoho mama duk da na da nayi abinda bai daceba amma abinda nayi yana nan mama na cuci kaina" mama tace "dallah malama ki fad'a mana tabbas naaan kece bakida gaskiya" shkr tace "zan fadi komi mama domin ni yanzu tsoron ALLAH ya dada shigana mama nayi samari kala kala kullum kina bani shawara kina hanani acikinsu na biyewa d'aya munyi soyayya ta rashin hankali abun bai tashi mun illah ba sai yanzu ya dawo ya hanani zaman aure kan sai na dawo mai kullum kirana yana mun barazana mama shine silar kashe min aure nayi dana sani" 

  

  

  

 Mama kuwa salati ta hau yi "oh ni 'yasu duniya ina zaki damu baka taba sanin cikin yaran zamani duk wayonka sunfika ban Taba sanin zaki biyewa wani shedani ba!" 

  

  

 "Mama kaddarace yanzu tabbas labarina zai zamanto IZINAH gamasu irin halina domin su san,irin samarin da zasu na kulawa" baba dake tsaye bakin kofa ya kada kai ALLAH yakyauta yanzu aikinga abinda muke gaya miki ko?

  

  

  Shkr ta d'ago baba nagani kuma nayi nadama Kuma tazama IZINAH agaren" baba yace "bazan dau wani hukunci akanki ba sai de na cigaba Da nema muku shiriya naji dadin da kika gane gaskiy" mama cikin jimami ta zaunata dafe kai mutuwar aure ba dadi nan duk sukafita akabar shukr na kuka wan nan kenan.

  

  

  

  

 Haris ne zaune da bala suna kalllon k'wallo yace "mutumina fa auren shkr ya mutu" haris yace "ai ranar naji dadi tabbas ni maI sa'a ne" uzaifa ne ya shigo ya zauna ya kaalli Haris yanzu kai Haris seda kai sanadin Auren yariyar nan ? 

  

 Haris yace "look man bana son shishshigi" nan uzaifa ya wulla mai hotuna "gashi nan kai bala sai ka gaya mai dalili" bala yace ai bangaya makaba ranr da zan aika da picture dinnan uzaifa ya hanani kai masu zafin ,kai wanda nakai ma dak'yar na k'wata agunsa" Haris ya hade rai "amma kai ajawo ne uzaifa bakayi ba wallahi ka b'atan show amma duk da hakan de naci nasara"

  

  

  

 Uzaifa yace adai juri zuwa rafi wallhi kajirayi sakamako mugu kawai kaso ka batawa yarinyar mutane life ALLAH yactaimaketa tayi aure shine kake son kashewa" cikin jin haushi ya tashi ya fita.

  

  Bala yace "uzaifa halinsa sai shi" haris yaa girgiza kai "halinsa sai shi"

  

  

  

  

  Bangaren shkr kuwa yau satin ta biyu a gida duk ta rame ta fad'a duk ta saka damuwa aranta domin gani take kowa ganin ta yake a yar iska duk ta dawo silent mama na Alwala mardiyya ta shigo gidan ta gaidata dakin shkr ta shiga taganta tana kuka ga hoton musty tana kalla zama tayi gefenta shkr ashe haka abi ya faru banji d'ad'in abinda ya faru ba amma hakan ma alkairi ne agareki domin ALLAH ya gwada imaninki ki daure ki cinye jarabawar nan" shkr tace "nagode" nan ta d'an zauna sukayi hira sosai ta tafi.

 Shkr ta shiga kunci ga soyayyar Haris dake cinta .

  

  

  

 Abangaren Haris ma duk ya fad'a gashi har yanzu bai huce ba bak'in ciki yayi mai yawa ko sanvcin abinci baya so hakanaan gidan duk yayi k'ura sai De yayi wanka ya fita kawai domin aransa ji yake shkr ta ci amanarsa.

  

  

  

  

  

 BAYAN WATA BIYU

  

 wata biyu kenan, da rabuwar haris da shkr sai asan nan mahaifiyar musty suka samu labari kiran musty tayi taji dalili nan yace kawai shi ya gaji da zama da itane . umma dake zaume kan kujera me daya afalonta tace zancen banza kenan! To na baka izinin ka maido da matarka" amsa mata kawai yayi ya tashi ya tafi .

  

  

  

 Shkr kuwa yanzu ta dan yi kiba ta rage damuwar saima yawan azumi datake addua take ALLAH tausasa zuciyar musty ita kanta mama shirUn yayi yawa yau da dare ta samu baba da maganar yace nima wlh abun na damu duk da abinda ya faru dole ya dake shi,gashi har ta kusa gama idda, amma gobe zan neme shi"

  

  

  Washe gari da safe kuwa baba ya nemi mustaph dakyar yazo domin yanajin kunya baba yace "tabbas ammaka lefi amma kayi hkr kamaida matarkaVkuma kayi bincike" musty yace "to baba nagode"

  

  

  ALLAH MAJI ROKON BAWA

  

  Uzaifa dake zaune yana tunani tausayin shkr yakeji tabbas yanzu kome tayi abaya haris ne dole ya nemi mijinta cikin sa a ya je har office din musy ya same shi bayan sun zauna yace "tabbas duk abinda ya faru sa makircin haris ne,kan son daya kewa matarka domin tsohuwar budurwarsa ce amma nasan komi agabana suke hakan duk makirci ne don arabaku"

   "musty yace to hotunan fa!" uzaifa yace "duk shima hakan" duk da cewar uzaifa yasan irin soyayyar data gudana tsakanin haris da shkr amma hakan bai sa yace tare sukai ba sai yace duk makircin haris ne nan ya rufawa shkr asiri domin ALLAH yayi gaskiya duk wanda ya rokeshi daya rufamai asiri kome ya aikata zai rufa mai lalle ALLAH ya karbi adduar shkr nan musty yayi mai godiya

   

   

   Byan kamar sati d'aya musty yaje gidan su shkr ya samu baba kan maganar shkr kan yanaso ta koma ya maidata nan baba yaji dadi yayI godia shiga gida yayi yace shkr taje mustu nason ganinta.

   

   

   jiki asanyaye ta fita tunda ta fita ya k'ura mata ido ganin tayi haske ta rame sunkuyar dakai tayi musty yace "yau na maidake kiyi hkr ki koma ALLAH ya yafemu gaba d'aya" hawaye taji ya zubo mata tasan duk abinda ya faru da ita tabbas gaskiy ce itace sila kuma hotunan duk gaskiy ne amma da yake ALLAH gafurur raheem ne idan kayi lefi ka rok'eshi zai yafemaka in har kayi tuba kuma taubatan nasuhan wanda bazaka koma ga aikatashi ba to har idan kabarwa ALLAH lamarinka zai jib'inceshi ya kawo maka mafita.

    

    Tsoron ALLAH ne ya k'ara shigarta ta d'ago ta kalli musty tace "nice da godia" Murmushi yayi mata "yada kuka kuma sorry nayi laifi ko? ashe duk shirin haris ne shiya hada komi seda gaskiy ta fito"

    

  Shkr ta share hawaye na tausayin musty nan don tason ba kowane namiji bane za ai hakan ya maida ita amma,kuma duk wansa yasa ALLAH a lamarinsa,ya isar masa yace "gobe zaki koma ko?" harara takai mai "nak'i" nan ta juya ciki yabita da kallo yana murmushi tare da jan motar yayi gaba ta koma ciki aguje tana dariya mama dake kitchen tayi murmushi tana godewa ALLAH domin kullum dare bata bacci tana ta kaiwa ALLAH kukan ta shkr kuwa wani shaukin soyayyar musty ke ratsata ALLAH ALLAH take gobe tayi domin tayi kewar abinta .

   

  Ring taji kiran nusty ya shigo yace "gobe kishirya zan kaiki saloon" tace to "ogana" musty yace "ki cire layin nan gobe zan kawo miki sabo" tace "tam" nan ta cire ta karya bayan ta kwashe nambobin data keso

Daga taskar Queen Meemi

[15:52, 12/27/2017] ‪+227 90 29 04 44‬: .⚜IZINAH CE⚜ 
BYQUEEN MEEMI
✍🏻...Nagarta Writers Association
WATTPAD@ Queen -meemiluv
Page-28-30
       🔚END🔚


Washegari da safe k'arfe goma musty yazo shkr anshake uwar kwalliya tunda ta fito ya k'ura mata ido dole yana rufe matarsa don tana da kyau shiga tayi yaji wani sanyin kamshi ya bugi hancin sa yace "baby wollahi nik'af zan sai maki kina sawa haba bansan maza na kallonki" murmushi tayi tace yanda kaso haka za'ai mik'a mata sabon layi yayi ta karb'a ta saka a wayarta nan ya kaita gidan saloon yace zaije ya dawo shigar ta keda wuya bata dade ba aka farai mata awa daya da rabi aka gama nan ta kirawo musty yace gashi nan.
 D'an fitowa tayi saboda yace gashi nan dede kwanr haka ta tsaya kawai ji tayi an mata magana haris ne tsaye yana murmushi tsaki tayi ta juya tana jan hirji dawowa yayi gabanta yana kokarin tab'atata nan ta juya ya janyo mayafinta be aune ba yaji sautin hannun shkr takai mai mari dede lokacin musty ya karaso afusace ya fito yazo ya kama wuyan haris ya kaishi bango yakai mai naushi "karabu da matata wallahi sena d'au mataki akanka" naushi haris yakai mai musty ya goce sai da wasu mutane suka rabasu haris ya shiga mota musty yaja shkur yace "kiyi hkr dole na d'au mataki wallahi" be zarce ko ina ba sai police station yakai report akan abinda Haris ke mai nan ya bada sunan sa ya fadi unguwarsa nan duk ya gama san nan ya maida shkr gida bayan ya kaita ya koma gida ya kwanta ya huta k'arfe uku daidai k'anwar mamarta tamaida ita gidanta.

 

 

 

 

 B'angaren haris kuwa karfe 5 na yamma suna k'ofar gida shida wani abokinsa sai tafawa suke motar 'yan sanda ta tsaya suna fitowa suka nunawa haris katin sammaci kan yazo ana nemansa da yayi gardama k'arshe abokin ya bashi baki suka tafi yana zuwa ya tarar da musty a zaune kan kujera suna zaune suna hira da wani dan sanda, suna shiga musty ya aikawa da haris wani banzan kallo nan de aka maida magna musty yace ayi mai iyaka da Haris ya kyale mai mata domin duk abunda ya sameta shine kuma ya sama mata lafy nan aka rubuta arubuce mustY yasa hannu shima Haris ya saka hannu zuciyar sa na tafarfasa hala 'yan sanda sukai mai kashedin duk randa ya kuma se ya kwana gidan maza nan kowa ya kama gabansa

  

  

  

 Tunda akai wan nan abin Haris ya sama mata lafiya ba yanda yaso haka ya hakura da ita nan kuma ya shiga farautar wasu matan da zai yaudara tunda dama halinsa ne.

 yauma da suka dawo daga club suna tafe kida na tashi amotar bala abaya yana dariya wani wawan burki haris yaja ganin waataa zuk'ek'iyar budurwa agaban gefen titi ba wani gardama ya tsaida mota domin tayi mai nan yaa yace "aa yanmata yade? ina zuwa? kallonsaa tayi samada k'asa tayi dariya yace "ko banyi bane? tace "aa kayi mana kamar a landon" lashe leb'e yayi "shigo 'yan mata na kaiki kinga dare yayi" ba musu ta shiga ya figa "ina kikayi? tace "gaba kad'an zan sauka" fuuu haka yake gudu jin hannu yayi a gefen cinyar sa ana tab,a shi ya dago ganin budurwar nan yayi ta kashe mai ido

  

 wani murmumahi yayi abin nema ya samu wayarsa ya d'auka ya bata sakan number d'inki ba tantama ta saka mai bala kuwa duk abinda ke faruwa yana daga baya yana ji sunxo dede wurin ya sauketa se munyi waya tace ok 

  

  

 nan tayi wata kwana bala ya dawo gaba haris yace "kaga wata d'anyar bebi na samu dami akala yanzu zan fanshe tada shkr wan nan ma tafi had'uwa" bala yace "gaskiy ba k'arya"

  

  

 Bangaren shkr kuwa hankalinta ya kwaana ta kame mijinta suna zaman su lafiyaa ko fita shkr bata San yi inde ba ya zama sole ba, idanma zata fitan to musty ke kaita wataan ta daya da komawa sai ga ciki murna gun musty ba kama hannun yaro haka suka hau tarairayar cikin da suka dade suna muradi

  

  

  

Haris kuwa soyayya tayi nisa shida lubna awaya kullum suna manne yau sukayi zasu had'u nan haris ya mata kwatancen gest house Din babansa domin ba a amfani Dashi k'arfe 5 dede lubna taje ta had'u iya had'uwa tana shiga suka fara watse warsu tun a falo idanuwan harin duk sun k'ank'ance tunk'arfe 5 sai wajen har wuraren asuba na dare san nan suka hakr da juna Haris ya rena kansa gurin lubna yayi mamakin ta tunda suka gama ya kasa tashi itakam k'em ta mik'e da k'yar ya tashi tana dawowa idanuwansa suka sauka akan k'afafu wanta

  

  

 Da sauri ya ja da baya ko ko ko fato wani ihu yasa lubna ta tintsire da dariya ta nuna shi da d'an yatssa take kamar and'aga shi samata sake shi dam ya fad'o ya bugu da k'ugunsa

 kuma saka dariya tayi "Haris na dad'e ina neman irinku domin ni ba mutum bace aljana ce ina bin duk namijin dake lalata yaran mutane ina lalata dashi to kaima haka ka fad'o komata karka manta "yan mata wajen goma kayi lalata dasu wasu kuma baka kaida cimma burinka akansu ba" nan ta tashi tayi girgiza ta dawo ainihin suffanta ai yana ganinta ya suma ita kuma ta b'ace.

  

 bashi ya farka ba sai wajen asuba yana tashi yaga gabansa ya kumbura nan ya kirma ihu da k'yar ya kirawo number d'in bala yace yazo ya same shi hakan kuwa k'arfe bakwai na safe yaje ganin halin da yake ciki yasa ya cicci b'esshi yakai mota direct gidansu ya kaishi.

  

  

  

 BAYAN WATA UKU

  

 bayan wata 3 haris ya jigata don ko fitsari baya iyawa ga wani abu dake fito mai yana gadon asibiti sai kuka yake ciwo yaki warkewa ganin hakan yasa aka koma gida ana mai na gargajiya babansa ne ta samo wani malami ganin irin firgitar da yake nan malamin yayi addua yayi mai karatu take birkice yafara wani irin abu malamin ya cewa baban haris "tabbaas ya hadu da aljana kuma sun sadu da aljanar ta saka mai ciwo amma da izinin ALLAH zai warke nan ya bashi rubutu da wasu magunguna cikin ikon ALAH sati d'aya ya fara warwarewa gaban nasa ya rage kumburin saida ya k'ara wata d'aya san nan ya warke tunda ya samu lafiy yazama silent duk ya dena iskanci yadena kula mata balle yayi lalata dasu

  

  

  

 se yanzu yayi nadama shima bala ya shiryi domin ya tsorata da yanda haris yayi ganin hakan yasa dadynsa ya samo mai mata akai mai aure tare da aiki a hade ya fara zuwa aiki nutsuwa sosai ta saukar mai ya shiga makaranta ta koyan addini ta manya da daddare domin yaga IZINAH

  

  

  

 Shkr kuwa summa bar k'asar itada musty domin ya koma yin wani course din a germany wanda zayyo shekara uku acan shiisa ya tafi da shkr

  

 Anan na kawo k'arshen wan nan gajeran littafin nawa inda nayi dede ALLAH ya bamu ladan inda nayi kuskure kuma ALLAH ya yafe mana wasallahu ALA nabiyur kareem 

wa ahlhi wa sahbihi ajma'en 

  

  

  

 Godiya ba adadi ga daukkacin group din da suke bibiyar llittfina sann nan da fans dina masoyana ALLAH ya bar kauna

  

  

 Fans dina na wattpad ALLAH ya bar kauna

  

  

 ALLAH Ya sadamu da Alkairinsa AMeen 

 sai wataran kuma in kun sake jina taku har kullum QUEEN MEEMI

  

  

 FOLLOW ME ON WATTPAD @ QUEEN-MEEMILUV..

[15:52, 12/27/2017] ‪+227 90 29 04 44‬: ⚜ *IZINAH CE*⚜*NA.... QUEEN MEEMI*


Dukkan abinda yayi farko zaiyi karshe yau Allah ya nuna mana karshe *Izinah* 


Masha Allah izinah ya fadakar ya ilmantar ya nishadantar Allah ya kara basira daukaka ya kara karfin ido da zakin hanu 


Allah ya baki ladan fadakarwa ya yafe miki kurakuraniki 👏🏻


Gsky novel yayi kuma gsky wannan novel din yace sunansa kuma izinah ne ga yan matanmu da zawarawanmu masu soyayyar shan minti gsky muna kuskure sosai, da sosai wlh wasu mazan ba kaunar matan suke ba su matan akwai karamar brain suyi ta biyewa mazan kuma kuskure ne babba daga karshe su hanaka zaman aure, kuma ko basu hana kaba ki dubi babban laifin da kuke aikatawa Al'hali Allah ya hanemu da aekatawa kuma Allah bazai barmu haka ba wlh sai ya jarabcemu gwargwadon abinda muka aekata kamar shkr, Haris ya hanata jin dadin aurenta 


One thing da mata masu gane ba tsakaninsu da mazansu su ringa musu rufa2 kuma kuskurene babba tsakaninki da mijinki kuyi zaman amana kuyi sharing damuwarku kuma karki ringa buye masa komai sbd sharrin shaddan kar wata ran kina buye buyenki wani abu ya faru wlh baki da mafuta said Allah kuma in bakya boye masa duk wani tuggu zaki tsallake bi'izinin Allah 


Kawaye gsky kawaye gubace a rayuwa but ba dukka ba bata garin sunfi yawa, sai kiga kawa bazata baki shawara mai kyau ba sai wadda zata bata miki rayuwa kuma ta zame a hada baki da ita a cuce ki, sunan wadda kika aminta da ita wata kawar kuma tagari ce but kuma bama santa Allah ka ganar damu Allah ka bamu ikon Amfani da abinda muka krnta 

Masu irin halin Allah ka ganar dasu su gyara 👏🏻


Mun gode queen meemi Allah ya saka da alkhairi ya raya *Huda baby* ya barki da oga lpy 


Up up meemi more grease ur shaning elbow 


*ILVYSM*❤❤❤❤❤


*ANTI JIDDA*


Tags: #iznah #rayuwa
1468
0
0
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!