Ismaha Zainab! 2019

Written by Umm NassPublished on 2019-03-27 19:50:53Category Adventure:Abubuwa masu yawa sukan buƙaci tausasawa da killacewa ga makusantan su. Amma idan aka samu tsaiko da rashin su, sai asamu rauni da gajiyawa ga wanda ke ɗauke da jigilar hakan, wata ƙila kuma ya ƙare rayuwar sa cikin yaƙe ba dariyar dake wanzuwa daga ƙasan ruhin sa ba. MUSADDIƘ acikin rayuwar ISMUHA ZAINAB kamar sandar dake yima makaho jagora aduk wani taku da zaiyi aduniyar sa... Ku shiga cikin labarin dan ganin zunzurutun alfanun dake dake cikinsa, ba wai sunan ba tasirantuwa ga kyawawan abubuwan da sukan sa zuciya nishaɗi. tags: Bandariya #jarabta #kyautatawa #soyayyaDuba was labarai »

[2/16, 9:37 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©by *😘Um Nass 🏇🏼*


® *NAGARTA WRI.ASSOCIATION*بسم الله الرحمن الرحيم


*_Alhmdulillah, Godiya ta tabbata ga Allah (S.W.A) mai kowa mai komi wanda ya yarde mana cikin ikon sa da rahmar sa muka sake kasantuwa a tare, ina roƙon Allah ya bani ikon kammala wannan labarin cikin sa'a da nasara mai yawa._*


_Haƙiƙa godiya ta tana da yawa ga dubun masoya na a yayin da na ga kuna farin ciki da murna a lokacin da kuka yi karo da SHINFIƊAR labarin nan, sosai nake farin ciki kuma nake yinku Allah ya bar ƙauna Son So FISABILILLAH_


 TSOKACI:

*DUK abin da za ku gani a cikin wannan labarin mai daɗi ko aƙasin sa tofa ƙirƙira ne ba wai da gaske bane, idan kuma a kayi katari da samun wani abu da yayi kamancecciniya da rayuwar wani to yayi haƙuri ba da sani na hakan ta kasance ba, idan kuma kuka yi karo da wani kuskure a cikinsa, ina roƙonku da ku ankarar dani a kan lokaci cikin Kamala ba da cin Fuska ba 👏🏻*


BABI NA ƊAYA


*Ƙauyen Kwalam*


Ƙaramin gari ne, ɗaya daga cikin ƙauyukan Ringim, wanda idan aka cureshi a wani garin ba zai wuce girman unguwa guda ɗaya ba, mutanen garin sun kasance abu guda, ma'ana kusan ahali guda ne da suka fara rayuwarsu a cikin ƙauyen, ƙalilan ne a cikin su baƙi wanda suka zo dan su zauna, abu guda mai muhimmanci idan ka kalle su zaka ga tsago guda akan kumatunsu, kamar na mahauta amma ko kaɗan basu da alaƙa da su, sai dan hakan ya zama al'ada a gare su ne yin tsago a fuskarsu, wanan kenan.


Ƙofar gidan cike yake taf da mutane, wasu suna tsaye a yayinda wasun su suke zaune. Daga cikin gidan kuma wata mata ce a zaune da lilliɓin mayafi a kanta, tana zaune a kan kujerar tsugunno, gabanta kuma bahuna ne da fanteka na taliya da ɗan wake, tana zubawa wasu, tana karɓan kuɗin wasu, da alama sana'arta ce hakan, duk da aƙallah ba zata wuce shekaru ashirin da ɗaya ba, amma yanayin rayuwa da wahalar aikin da take zai nuna ta kai shekaru talatin a duniya, tana da kazarniya da fara'a wajan bawa ko wani mutum Haƙƙin sa.

Cikin abun da bai wuce awa guda ba abincin ya ƙare sai aka samu sauƙin mutanen, duk da wasu suna zuwa ana ce musu ya ƙare, haka suke komawa gida cike da jimami da takaici, dan duk garin abincin ta ne mai rahma da kuma daɗi, matsala ɗaya idan baka yi sammako ba baka samun sa, kasancewar su mutanen ƙauye ne da yawan su ɗumame ke jiran su a gida dama kuma abincin nata ya kasance na matasa ne masu karkaɗe jiki da nuna su sun wuce cin tuwo (Lolx).


Tashi tayi ta tattara kwanukan da aka ɓata ta fara haɗa su waje ɗaya tana wanke su, kafin ƙarfe goma gidan na ta yayi tsaf kamar ba a ɓata shiba, ɗaki ta shiga ta tadda ƙaramar yarinyar ta wanda ba zata wuce shekara uku ba tana barci hannunta a bakinta tana tsotsa, shafa kanta tayi tana murmushi gami da sauƙe ajiyar zuciya, kamar mai jira ta buɗe idanuwanta tarai a kan Mahaifiyar ta, baki ta wangale sannan ta mirgino jikinta ta ɗora kanta a kan cinyar mahaifiyar tata "Luyyah", ta faɗa tana shafo Fuskar mahaifiyar tata, itama murmushi tayi ta shafa Fuskarta "Kin tashi?", kai ta ɗaga mata tana dariya, miƙewa tayi da ita ta fito waje ta surka ruwan sanyi dana ɗumi ta mata wanka sannan ta goyota suka koma ɗakin ta shirya ta tsaf cikin doguwar rigar atamfa da ɗankwalin ta, masha Allah yarinyar tayi kyau mutuƙa, duk da kasancewar ta baƙa ce amma ba baƙin wuluk ɗin nan b, sai magana dara-dara da gashin saman ido wanda yake da yawaita musamman idan ta rufe idon, sai hancinta wanda bashi da yawaitar tsayi amma ya taimaka wajan dai-daituwa a kan fuskar tata mai ɗan faɗi, bakinta ɗan mutsugul kamar loma ba zata shige ta ba, gefen fuskarta kuma akwai kwantattun gashi wanda yake nuna cewar tana da gashi, kanta a kitse yake da kitson shuku wanda saida aka tufkesu aka duƙunƙune saboda yawan su, akan Fuskarta akwai ɗan siririyin tsage a kumatunta na dama hakan ya ƙara fito da kyanta.

"Masha Allah, Yarinya ta kin yi kyau", ta faɗa tana murmushi itama baki ta wangale tana dariya sai juyawa take, can kuma ta ɗano bakinta ta fara shafa cikinta "Luyyah Abinci", ta ƙarasa faɗa kamar mai shirin yin kuka.

"zo muje kici abincin kar kiyi kuka." da murnarta ta fice wajen da gudu bin ta tayi tana murmushi "Oh Ismaha Zainab sarkin ci", kai tsaye kitchen ta shiga ta taddata tana kalle-kalle kwano ta ɗauko ta ruƙo Hannunta suka fito barandar da ke tsakar gidan, tabarma ta shimfiɗa musu suka zauna kana ta buɗe abincin Taliya ce da tumatur yayyanke a kanta sai gefe kuma yaji ne a ɗan ƙaramin kwano, dariya Ismaha Zainab ta fara yi tana tafa hannunta "Taliya", hakan yasa Luyyah yin dariya sanan ta ce "Oya kice Bismillahi sai ki fara ci."

"Bicmillah", tace tana kaɗe hannunta duk da ba wai ci gareta mai yawa ba amma idan kaga yanda ta dage tana walwala da ɗai sai kace duka zata ci, bata kai ga kammala ciba ta tsinkayi sallama, sai da gabanta ya faɗi gane muryar mai sallamar, ba kowa bace face Tani Matar yayan mijinta.

"Wa alaikumussalam, maraba da Yaya Tani", ta faɗa tana taro ta da dariyar da take ta yaƙe, kallon sama da ƙasa ta mata sannan ta kwaɓe baki "Ahh lallai ba shakka, Hajiya Ruƙayya baki da matsala ke kam kin tada kai da sulalla ga gardawa suna shawagi a kowata safiya ta duniya, bawan Allah Idrisu ana can neman halaliya bai kuma san wainar da a ke toya masa a gida ba."

Ɗago kanta ta yi tana kallon Tani ɗin, wannan ba shine karo na farko da ta saba mata haka ba, bata san mi ta tsone mata a rayuwa ba gashi har ta kai matakin da ko uwar mijin su yanzu ta tsane ta bayan kuma a baya itace take sonta kamar ranta ƙarshe ita ta zama sila na ƙulluwar auren ta da Idris ɗin. Kafin ta farga ta sake wata magana Tani ta janye kwanon Taliyar da yake gaban Ismaha Zainab ta fara kai loma bakinta "Tunda ba'a mana tayi ba mukam ai zamuci ko ran mutum baya so, iyaka dai a mana Allah ya isa ita kuma yanzu ta zama riga a jikin kowa."

"Haba dai yaya Tani ai kin girmi na miki Allah ya isa, inama abin yake?", ta faɗa tana ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi, baki ta ƙara taɓewa "Ke kika sani da kinibibin ki." Tass ta gama cinyewa ta suɗe hannunta sannan ta ɗauko leda ta juyo yajin "Wanan yajin zan tafi dashi gida dama yau wara da Mai zanyi." daga haka ta kakkaɗe jikinta, "Innarsu Kamalu ce ta aiko na kira ki idan kina da lokacin ta, dan gama yanzu baki da lokacin mata sai ƙatti masu cin riba biyu."


"Zanje Yaya, jira ni mu tafi tare." ta faɗa da idanuwanta da suke shirin zubar da hawaye gabanta naci gaba da luguden faɗuwa, tasan ƙila wani faɗan ne yake jiran ta a gaba, kiran surukar ta babu alkhairi ko kaɗan a cikinsa, dan ma ta auna arziƙi da bata tako da kanta tazo ta same taba.

Ɗaki ta shiga ta ɗauko Hijabi sannan ta ruƙo Hannun Ismaha Zainab suka nufi waje bayan ta kulle ɗakin ta da ƙofar gidan, sannan ta cewa Tani da take faman doka mata harara "muje Yaya". Bai wuce gidaje shida bane tsakanin su ko ina ta gifta sai kaji yara da matasa na kiranta suna gaida ta cikin walwala, wasu kuma su kira Ismaha Zainab dan yarinyar akwai shiga rai da dariya, hakan ya ƙara ƙular da Tani sosai gashi dai su biyu suke tafe amma dan wulaƙanci babu mai kiran ta sai dai su kira wata Ruƙayya, ƙwafa tayi ta ƙara jijjiga kai, ƙarshe ta ƙara sauri ta tafi ta bar Ruƙayya da take gaisawa da wani "Innar Ismaha yau na makara ban samu abinci ba."

"Ai kuwa Muntari yau kam kayi barci da yawa, ka ci ɗumame ai." ta faɗa tana dariya dan tasan ba abinda ya tsana kamar tuwo, kai ya girgiza yana ɓata fuska "Allah ya tsare ni da cin ɗumame yana sabon sama ban ci ba balle kuma da ya kwana."

Dariya tayi "To ai ɗumamen yafi daɗi."

Kai ya girgiza yace' "Allah ya tsare ni dai da cin sa, ina zaku je ne haka naga kamar kuna sauri?" Yayi saurin sauya hirar.


"Wallahi nan zamu je gidan su Baban Zainab Innar sa ta aiko kirana."

Kai ya gyaɗa yana tambayarta "Lafiya dai ko?", kai ta girgiza "Ban dai sani ba sai naje, kaga abokiyar tafiyar tawa ma ta wuce ta barni", ta faɗa lokacin da ta ankare da ɓacewar Tani.

Alawa ya ɗauko a cikin Aljihun sa ya miƙawa Ismaha Zainab, "gashi amaryass wannan na toshi ne, duk da baki ajiye min abincin kari na ba, ku isa lafiya", ya faɗa yana yin murmushi gami da juyawa da muryarta da bata fita tace' "na gode kuma na cinye yanzu duka", dariya suka yi dukan su har da Muntari yayi gaba abinsa yana ɗaga musu hannu, matashi ne ɗan shekara sha bakwai, haka yake tsokanar Ismaha Zainab da sunan amaryar sa wai yana sonta.Sai a lokacin hankalinta ya dawo kanta samu tayi gabanta na ci gaba da faɗuwa tuna tsawon lokacin da ta ɓata, hakan ya sata ƙara sauri, cikin sanyin Murya ta yi sallama sai dai ga mamakin ta babu wanda ya kulata a cikin mutane huɗun da suke zaune. Jikinta ne ya yi sanyi kamar kazar da ƙwai ya fashe ma a ciki, haka ta ƙarasa ta samu waje ta tsugunna "Innah ina kwana", kai ta juyar gefe ba tare data amsa mata ba, sake gaida ta ta sake yi, cikin hargowa ta juyo tana kwatsa mata tsawa "an faɗa miki ban jiki bane, ko kuma kin ɗauka ni kurma ce kamar mahaifin ki wanda baya ji sai an ƙwala masa murya?". Da sauri ta ɗago tana kallon ta kai ta gyaɗa mata cikin ƙara murtuke fuska "duk abin da kike yana dawowa yana samu na, kin maida gidan ɗana dabdalar tara ƙartai da zuwan kina siyar da abinci, sam ba zan lamunci wanan abin ba, idan shi Idirisun kun shanye shi to fa ni a tsaye nake, dan haka cikin biyu dole ayi ɗaya ko ki haƙura da sana'ar ki ko kuma ki haƙura da aurenki." ido ta ɗago wanda tuni hawaye ya cika su "amma Innah shi ma Idris ɗin ai yasan ina sai da abincin, asali ma da shawarar sa na fara siyarwa, kuma duk wanda yace maza na cika min gida to maƙaryaci ne dan babu masu shiga gida na sai yara ƙanana."

Hannu Tani ta tafa tana salati "wato mu ne maƙarya tan naki kenan? Idan gardawa basa shiga gidan ki taya suka san kamanninki? Tunda muka doso layin nan ake faman kiran sunan ki kuma duk cikin su babu yaran, ƙarshe ina tahowa nayi na bar ki?", ta ƙarasa maganar tana hararar ta, ƙarfin hali Ruƙayya tayi saboda yanzu kam an kawo ta gejin inda ba zata jure ba "Tunda haifa ta a kayi a garin ba taka haye bace ai dole su san suna na, kuma dole idan an gaida ni na amsa saboda an girmama ni."

Azabure Tani ta miƙe tana nuna ta da hannu "akul ɗin ki Ruƙayya, kada ki faɗa min babu daɗi, kinsan koda nake ba ƴar gari ba ai ina da dangi anan ɗin, balle ki faɗa min magana."

"Ni dai ban ce ke ba, idan ma kinji haushi to ke kika so kiji."

"Da kyau Ruƙayya ashe rashin kunyar da ake faɗa min taki ta wuce yanda nake tunani, a gabana yau kike musayar magana dani, zan ɗauki mataki idan shi Idrisu ɗin ne yace kina min rashin kunya zan kawo ƙarshen abun, kuma dole ki taƙaita tara gardawa a ƙofar gidan ki idan ba haka ba to sai dai ki san inda dare ya miki, wama ya sani ko kina rage dare da su ɗinne?".

Kai ta sunne ƙasa tana riƙe hannun Ismaha Zainab wanda ta lafe a jikinta, ji tayi an finciki yarinyar "zo nan uwar ƙiwa baki san ki gaida mutane ba, to nice dolen ki da ko kallo ban ishe kiba ja'irar yarinya." Innar su Kamalu ta faɗa, kuka Ismaha Zainab ta ƙwala wanda yasa su toshe kunnuwansu, bakinta ta yi saurin bugewa hakan yasa jini zuba saboda haɗuwar da yayi da haƙoranta, wani rikitaccen ihu ta ƙara callarawa saboda zafin da taji, sosai kukan ke taɓa Ruƙayya amma bata da damar yin magana, hakan ya sa ta miƙewa tsaye "Innah ni zan koma gida." 

"Saboda an taɓa ƴar ki tana kuka shine zaki ce zaki tafi? To ki gayas amma yau a nan zata wuni, dan ko taƙi bata da kamar ni." kai ta girgiza bata ƙara magana ba ta musu sallama tana jin Ismaha Zainab na callara kuka tana kiran sunanta "Luyyah", amma bata tsaya ba sai sauri data ƙara ta fuce ta bar gidan..

🥀🥀🥀🥀

#UM NASS

#NWA

#Cmnts nd vote

#DA AMANA

[2/16, 9:37 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©by *😘Um Nass 🏇🏼*


®NAGARTA WRI..ASSOCIATION


BABI NA BIYU (Page 2)


Da saurin ta ta ƙarasa fitowa, tana jin sautin kukan ta har ranta, ta ɗauki tsawon lokaci a ƙofar gidan, sanan taja ƙafafuwanta ta bar gidan, kai tsaye gidan su ta nufa a inda ta tadda mahaifiyar ta a zaune tana tankaɗe gari, gefe ɗaya kuma mahaifin su ne yana duba wasu litattafan sa. Ɗagowa sukayi suna kallon ta cikin mamaki dan bata saba zuwa a irin wannan lokacin ba, tafi zuwa da yamma ko dare wani lokutan ma idan mijinta yana gari bata fiya zuwa ba.

"Lafiya Ruƙayya? Ina kika baro Isim ɗin?". Mahaifiyar ta ta tambaya tana dakatawa daga tankaɗen da take yi, murmushin yaƙe ta yi sannan ta tsugunna ta fara gaida su "Ina kwana Babuji? Innarmu ya kuka tashi?".

"Alhmdulillah lafiya lau muke". Babuji ya amsa yana kallon fuskarta.

"Ina kika baro min matar ta wa?", ya tambaye ta yana ɗan murmushi itama murmushin tayi kafin ta fara magana' "tana wajan Innar su Kamalu".

"Amma na ga bata saba da suba, asali ma ƙiwa take musu, mi yasa kika bar ta salon kisa wani cutar ya kamata?". Innar mu ta faɗa cikin faɗa-faɗa, kai ta girgiza cikin murmushin yaƙe mai kama da kuka "so nake ta saba da su Innar mu, ƙiwar da take musu ta yi yawa gashi suna son ta suma, shi yasa na fara kai ta can ɗin dan ko ina akaje aka dawo sune dolen ta."

Kai ta girgiza cikin takaici "eh duk da su ne dolen ta Amma ai tayi ƙanƙanta a bar ta a wajan su, duka ma nawa yarinyar take da har yanzu bata kai shekaru biyar ba, wannan zalinci ne daga ke har Innar su Kamalun da ta biye miki ta karɓi yarinyar duk da kukan da zata yi mata, ita ai bata da asara da damuwa idan wani abun ya same ta, amma kuma ke ce da asara idan maƙo yayi sanadiyar mutuwar ɗiyar ki." Daga haka ta cigaba da tankaɗen ta ba tare data ƙara tanka mata ba.

Jin maganar Innarmu ba kaɗan ba ya tsorata hakan ya sata ɗaukewar numfashi na wasu lokutan, babu yanda za tayi yanzu kam ta riga tayi sake, tana kuma addu'a a kan Allah ya kare mata ɗiyar ta a duk inda take. Can ta juya kallon ta ga Babuji "Babuji shin akwai aibu a cikin sana'a ta ne da mutane suke ta sauya maganganun su a kaina?", ɗagowa yayi daga duba littafin da yake yana kallon ta. "Ban Fahimci maganar ki ba Ruƙayya, wani abu mutane suke faɗa a kan ki?".

Kai ta sunkuyar ƙasa tuni hawayen da ke idonta ya zubo "Innar su Kamalu ke magana akan sana'ar ta wa wai ina cika gida da maza, dole na zaɓa ko aure na ko kuma sana'a ta."

"Mi yasa zata sanya miki doka? Bayan kuma da sanin mijin ki kike wannan sana'ar, idan ta hana ki neman kuɗi zata ɗauki nauyin ki ne? Ko kuwa shi ɗan na ta ne zai ɗauke miki ko wani nauyi na ki? Bayan shi ba mazauni bane a gari balle ya fuskanci wata matsala taki ya iya magance miki ita." Innar mu ce take magana cikin ɓacin rai da takaicin maganar su Innar Kamalun, hannu Babuji ya ɗaga mata "A'a Ballu suna da gaskiyar su suma, duka nawa Ruƙayyan take da zata na sana'a irin ta tsoffin mata, kina ga yanda kullum gidan ta yake a cike da maza ana layi, nima dai na goyi bayan su a kan ta nemi wata sana'ar tayi amma banda wannan."

Baki buɗe suke kallon Babuji kafin nan Innar mu ta cafe maganar' "Tafɗijam kai ma kasan wannan abu ne ba mai iyuwa ba, Allah ya rufa mata asiri wajan sana'ar ta tana samun alheri sannan kuma kace ta sake wata, faɗa min mi zata siyar a wannan garin wanda zai maye mata gurbin sana'ar ta? In dai ba baƙin ciki irin na mutum ba kowa a garin nan yasan maza a ƙofar gidan ta suke tsayawa, iyaka su tura yara da kuɗi a karɓo musu abincin", miƙewa tayi tsaye tana kallon Ruƙayya "Duk wanda zai ƙara miki suka a kan sana'ar ki to kice ya ɗauki nauyin ko wata buƙata taki, a ciki har da mijin ki Idirisun, idan taƙamar su saki ko wani abu ba a kan ki a ka fara zawarci ba, zaki samu maza dubu suna jiran ki."

"Dakata-dakata Ballu wani irin magana ne haka, kina so ki zama tsani guda na wargajewar zaman lafiya a gidan ƴar ki, yanzu idan kika ɗora ta a kan wannan mummunar aƙidar kina tunanin akwai mai aurar ta ne, shi zawarcin daɗi ne da shi aka faɗa miki? To ki jini da kyau muddum ta kaso auren ta sai dai tasan inda zata zauna amma ba a gidana ba". Yana gama faɗar haka ya tashi ya fice abinsa yana faɗa kamar zai aro baki. Da ido suka bishi a yayin da Ruƙayya ta ɓalle da sabon kuka, lallashin ta Innar mu take tana bata haƙuri a kan kada ta ɗauki maganar Babuji da gaske barazana ce kawai yake yi, taci gaba da sana'ar ta tunda Allah ya dafa mata, daga haka tayi sallama ta tafi a kan kada a kai Ismaha Zainab bata nan.


******


A ɓangaran Ismaha Zainab babu sauƙi tun bayan ganin fitar Luyyah take ajiyar zuciya, kukan ma ya gagara futowa sai hannunta tasa tana tsotsa can kuma barci ya ɗauke ta a nan tsakar gidan, babu wanda ya ƙara bi ta kanta iska da ƙura haka suka yita buɗeta, sai da ta shafe awa biyu tana barcin sannan ta tashi, da ƙyar ta buɗe idonta wanda duk ƙasa ta buɗesu, hannu tasa tana mitssika idon jin yaji ya sata callah ihu, da sauri Innar su Kamalu tazo, bakin ta sake buge mata ta ƙara mata da ranƙwashi a tsakiyar kai "Wanan yarinya an yi jarababbiya, haka kawai ki tasani gaba tun safe ki isheni da ihu, kamar da nake yankan naman jikinki", duka da tsawar da ta mata ya haɗu ya zamar mata abu biyu wanda suka ƙara rikita ta ta saka wani gigitaccan ƙara, wanda saboda ƙaran sai da Innar su Kamalu ta toshe kunnenta, Tani kuma da sauran matan gidan guda biyu suka fito aguje suna tambaya "Lafiya kuwa Innar Kamalu?", takaici da baƙin ciki ne ya hana Innar tanka musu, sai dai kafin suyi wani yunƙuri ta ɗauki kara ta fara kwaɗama Ismaha Zainab "Na lura yarinyar nan so take ta sani a bakin duniya, daga mata magana shine take kwantsama min ihu kamar da nake yankar naman jikinta, to bari na dake ta idan yaso sai tayi kukan mai dalili." Innar su Kamalu take magana tana dukan Ismaha Zainab kamar Allah ne ya aiko ta, duka a cikin su Tani da matan Ɗan lami babban ɗan Innar Kamalu babu wanda ya yi yunƙurin karɓar ta, Kuka take tana jan zuciya dan tuni muryarta ta ɓace ba'a jin sautin kukanta.

Kamar an jefo shi haka ya faɗo gidan ba tare da ya yi sallama ba, abun mamaki da tsoro ne suka tarar masa a lokaci guda ganin Innar su ta gwaggwafe tana dukan yarinya ƙarama kamar mai shirin raba ta da rayuwarta, cikin hanzari da sauri ya ƙarasa ya fige yarinyar daga gaban Innar su Kamalu yana tura innar, rikica ta faɗa kan garin da suka shanya, cikin muryarsa mai kama data ƙauraye ya fara magana yana rangaji kamar zai faɗi "Haba- haba mana Inna yanzu idan ban da ɗaukan alhaki da mugun ta mi zaki ɗauka a jikin wannan ƴar mitsitsiyar yarinyar wanda ko gama sanin kanta bata yi ba? Dan mugun ta kin yakice ta a jikin Uwar ta gashi ko yini guda kin kasa zama da ita". Sannan ya juyo ga kallonsa ga su Tani da Kululu matan ɗan lami "Ku kuma tsoffin munafukai kuna gani a gaban ku za tayi kisan kai amma ba uwar da kuka tsinana, idan tayi kisa har ku za'a haɗa a ɗaure ai, munafukai ku kun gagara haihuwa kun zauna kuna ta faman cinyewa mutane abincin su." kai suka sunkuyar cikin rashin gaskiya suna jin sun muzanta a kan maganar da ya musu.

"Ni dai nafi ƙarfin gorin ka Kamalu, dan sai da na yi haihuwa ɗai-ɗai har guda bakwai a gidan nan, kawai zama ne da yaran ba sayi suke komawa, kuma ko yanzu Alhamdulillah ina da uku a raye gara ka sauya salon zancen ka." Tani ta faɗa tana jujjuya ido da baki. Baki ya taɓe sannan ya ce "Waɗan nan munanan yaran na ki da ko ature aka kasa sai ƙyar a samu mai ɗauka, ai dasu gara babu, shi yasa kuke baƙin ciki a kan wannan yarinyar, har abada kuwa ba zaku haifi koda mai rabin kyanta bane, kuma daga yau duk shegiyar dana ƙara ganin ta ɗauko yarinyar nan daga wajan uwar ta ta kawo ta gidan nan aradu sai na yanke ta." yana gama faɗar haka ya ɗauki Ismaha Zainab suka fuce. Da ido suka rakasu, a ciki an rasa wanda zai tanka yayi masa magana, har zuwa lokacin Innar su Kamalu na cikin gari tun hankaɗatan da Kamalu ya yi bayanta ya amsa da wata ƙara ta gagara miƙewa. Tani kuma baƙin ciki da tsanar Ismaha Zainab ne suka dirar mata a cikin zuciyarta, yau ita Kamalu ya ciwa mutunci da Fuska, saboda ita ya kuma aibanta mata yaran ta, duk da tasan ba wai wani abu bane mai wahala a wajan sa ya aikata musu abin da ya faɗa, amma kuma ta yi alwashin sai ta ƙuntata ma rayuwar Ismaha Zainab, tun yanzu an fara hango tazarar da take tsakanin ta da yaran ta ina ga in ta girma, ai sai dai ta tusa yaran ta a gaba tana kallo, saboda haka taci alwashin ko za ta shiga halin ƙaƙa sai ta salwantar da rayuwar Ismaha Zainab ɗin, ba ma ita ɗaya ba har da Uwar da ta kawo ta duniyar. Kululu dai babu bakin magana sai hawayen daya zuba a cikin idonta, saboda tun da tazo gidan nan ko ɓatan wata bata yiba, gara Tani ita da abin ganin ta, Kamalu ya saba da yi mata gori amma bai taɓa yin wanda taji zafinsa kamar yau ba, jiki a sulluɓai ta koma ɗakin ta tana mai fidda hawaye a cikin idonta.


******


Tun ƙarfinsa ya doka ƙofar gidan wanda ya sata buɗewa babu jinkirtawa, a tsaroce ta miƙe tsaye tana barbaza ido da son ganin wanda ya yi mata wannan aika-aikar, gabanta na cigaba da faɗuwa, fuskarsa babu walwala ya ƙaraso har gaban ta ya sauƙe Ismaha Zainab daga goyatan da ya yi a bayansa, tana ganin inda take ta ruga da gudu ta maƙalƙale ta "Luyyah", ta faɗa tana fara jero ajiyar zuciya akai-akai dan tuni hawaye sun bar zuba a kan fuskarta, shafa kanta take itama tana jin wani mugun tausayin yarinyar, ko bai faɗa mata ba tasan ta wahala, da ƙyar ta aro dauriya da murmushi ta fara masa magana' "Mijin irin wannan doko ƙofa sai da kasa ƴan hanjina suka amsa, ka bani tsoro sosai ina tunanin masu ɗaukar mutum ne har gida ai."

Wata Uwar harara ya aika mata asaitin ta kafin nan ya buɗe baki ya fara mata magana da faɗa-faɗa "Da sanin ki kika baro yarinyar nan a can gidan? Saboda rashin tausayi da hankali kin san tayi ƙanƙanta kuma ba wai kulawa zata samu a wajan suba, yanzu ma ba dan Allah ya kai ni a kan lokaci ba da ƙila sun kashe miki ƴa kinga kece da asara ba suba."

Murmushi ta yi duk da a ƙasan ranta tana jin wani turnuƙun zafi "ta ya zasu kashe ta Kamalu bayan suna sonta? Kai ne dai baka fahimta ba, amma ta iyu laifi ta yi masu suka hora ta, shi kuma hukun ta yaro a kan laifin da yayi gyara ne, ka dai na faɗar zasu kashe ta, haka idan wani yaji zai ɗauka gaske ne bayan kuma Innar ku tana nan na tabbata ko ƙuda ba zata bari ya cije taba in dai a gaban ta ne."

Baki buɗe yake ganin ta tunda ta fara magana cike da takaicin abun data faɗa ɗin, harara ya ke aika mata da ita amma kuma ko a jikinta sai Murmushi take yi, tsuka ya buga da ƙarfi sannan ya yi magana' "Baki da hankali ashe dama Ruƙayya? Na ɗauka su Tani ne marasa hankali ashe ke na ki haukan a sakaye yake, ko makaho ya zauna a gidan nan zai ji izayar da suke mata zai fayyace rashin ƙaunar da suke mata, hmmm babu laifi kici gaba da kallon su a matsayin masoyan ku, amma kuma daga wannan ranar kar ki ƙara kai ta ita kaɗai gidan idan ba haka ba duk abin da a ka mata akan ki zan rama", yana gama faɗar haka ya buga sandar sa da addar da take hannunsa sannan ya juya ba tare daya ƙara saurarar ta ba a yanda yake ji a ransa tsab zai iya bibbige Ruƙayya saboda takaicin abinda take faɗa, kiran sa take tana dariya amma ko juyowa bai yi ya saurare ta ba wanda hakan ke nuna mata ransa a ɓace yake, murmushi ta bishi da shi "Kamalu mai dawa, autan Inna baka bar uban kowa ba koda kuwa innar ka ce." ƙirarin da mutanen gari da abokan sa suke masa kenan, in dai a kan gaskiyar sa ce to tsaff zai wanke mutane ya sassare su. Kallon Ismaha Zainab tayi da jikinta yayi buɗu-buɗu da ƙasa kai ta girgiza cike da tausaya mata sannan ta cire mata kayan jikinta ta surka ruwan ɗumi ta mata wanka, a lokacin taga shacin bulala ɓaro-ɓaro a bayanta koya ta taɓa wajan sai ta saki kuka, tausayin ta ne ya kamata ba ta san lokacin da hawaye ya zuba a cikin idonta ba, tunda ta haifi Ismaha Zainab bata taɓa kai hannunta da sunan dungurin taba balle kuma ta kai ga duka, amma yau sai gashi dukan ma da aka mata ko babba sai haka, Allah ne ya kawo Kamalu akan lokaci ba dan shiba bata san ko wani irin duka kuma zasu mata ba, haka ta ƙarasa mata wankan tana kuka sannan ta ɗauke ta ta zoze mata jikinta da Rabb, ta sa mata shimi dan ta sha iska, abinci ta ɗauko mata a kwano tun kafin ta buɗe ta ƙarasa da saurin ta ta janyo kwanon, jalof ɗin shinkafa da wake ne, nan tasa hannu ta fara ci kafin nan ta cinye na bakinta ta ɗauko wata lomar ta kai, tsayawa tayi tana kallon ta abin da ban mamaki da tausayi wai Ismaha Zainab ke irin wannan cin abincin wanda ko kaɗan abinci ba damun ta ya yi ba, ta iyu tun abincin da suka ci a gida bata ƙara ci ba, "Luwa Luyyah", ta faɗa tana kai wata lomar bakinta, tashi tayi ta ɗebo mata ruwan, karɓa tayi ta sha mai yawa sannan taci gaba da cin abincin ta, sai da ta cinye fiye da rabin abincin sannan ta bar shi ta kora da ruwa a nan ta kwanta kafin Luyyah tayi wani yunƙuri barci ya ɗauke Ismaha Zainab, mugun tausayin ta ne ya kama ta bata san lokacin da hawaye ya zubo a cikin idonta ba, tana kallon ta tana kallon yanda take sauƙe wahalallan numfashi.
🥀🥀🥀🥀🥀

 Afwan kwana biyu kunji ni shuru mun samu matsalar rashin wutar lantarki ne, amma yanzu ta gyaru zakuna jina akai-akai koda ba kullum bane In sha Allah.


#IsmuhaZainab

#NWA

#Cmmnts and Share

#Da amana🤝

[2/16, 9:37 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB💍*


©BY *😘UM NASS🏇🏼*


BABI NA UKU (Page 3)


Washe gari:


Ƙofar gidan a cike take taff da mutane kamar yanda ya zama sabo, wasu suna tsugunne suna cin abincin yayin da wasu suke gefe ɗaya a tsaye da alamun jira suke a zubo musu nasu.

Wani ɗan Almajiri ne wanda bazai wuce shekara 7 ba yake zirga-zirga tsakanin masu gidan da wajen da alama shine mai karɓan kuɗi da kuma kai musu abincin da suke siya.

Buguzun-buguzun take tafiya kamar zata tashi sama fuskarta babu walwala ko kaɗan a cikinta gefe ɗaya kuma Tani ce da kululu ƴan koranta suke take mata baya har cikin gidan, dai-dai lokacin da Ruƙayya take zuba abinci gidan ta tsaf-tsaf babu hayaniya da tarkace a ko ina ɗin nan na kwanika, dan tana siyarwa tana wankewa, duk wanda ya ci a kwanon ta sai ta wanke kana ta zubawa wani a cikin kwanon, batayi aune ba taji an tankwaɓe kwanon da take zuba abincin, zubewa abincin yayi a ƙasa kwanon ya kife, cikin ɓacin rai ta ɗago dan taga waya mata wannan aika-aikar, ganin Fuskokinsu da tayi yasa gabanta faɗuwa ga kuma Innar su Kamalu sai huci take kamar baƙin maciji, "Ni zaki maida ƙaramar yarinya sa'ar ki, na kafa doka a cikin gidan ɗana amma kisa ƙafa ki shure, saboda kin shahara kin gawurta da bin maza da maida ƙofar gidan ɗa na sansanin bariki, wannan ya shiga wannan ya fita." ta faɗa tana huci kana ta janyo fantekar taliyar tayi jifa da ita, nan ta komaɗe sauran taliyar ciki ta zube, ido Ruƙayya ta runtse hawaye na zuba a cikinsa, wannan tozarci wannan cin kashin yayi yawa, kafin ta buɗe idonta tarr akan Innar su Kamalun wanda taci gaba da tijarar ta "Tunda baki da mutunci baki san girma naba, a yanzu na janye ko wani zaɓi dana baki dole ne kibar gidan nan a yanzu-yanzu na baki ƙwararan saki uku Cirr a madadin Idirisu." hannu su tani suka ɗaga suna tafawa ita da kululu "Shikenan magana ta ƙare."


Kallon su take baki a buɗe cikin mamakin maganar su, da ƙyar ta aro dauriya tayi murmushin da bai wuce na saman laɓɓa ba "Inna ai baki da ikon da zaki sake ni kice na saku, domin igiyar saki na tana hannun Idris, sai dai idan ya dawo kina da iko da duk wata dama a matsayin ki na mahaifiyar sa da zaki tirsasashi kice ya sake ni, sannan ina baki haƙuri akan gidan ɗanki da kika ce ina sana'a amma kuma ke kika janyo hannuna kika shigo dani gida na a matsayin matar da zata zauna a gidan, sannan abu na gaba da shawarar ki ne na fara sana'a ta dan haka yanzu babu wanda ya isah yace bazan yi taba, dan baku da abin da zaku bani."

Baki buɗe Innar su Kamalu take kallon ta cikin mamakin maganar ta, a sanin ta ko musayar magana bata taɓa haɗasu da Ruƙayya ba amma kuma yau sai gashi ita ke faɗa mata magana mai zafi haka, mamaki da tsoro ya sandarar da ita ta gaza magana, hakan yasa Tani ta ɗauki salati "Lallai Ruƙayya wuyanki ya isa yanka, yanzu Innar su kamalun kike faɗawa haka? Mahaifiyar data halallaƙo mijin ki kike cewa bata da ikon sakin ki, amma kuwa in baki manta ba duk duniya babu wanda ya kai ta a wajan kamalu, haka idan ta saka masa kara baya tsallakawa, ko a wannan gaɓar nasan iyaka yace to amma ba wai yace hukuncin ta bai iyuba, sai gashi ke kin maida mata magana son ranki, lallai idan da ranka zaka ga abubuwan mamaki." ta ƙarasa maganar tana matsar hawayen munafurci.

"Ni ai ban san abin faɗa ba ko kaɗan, lamarin Ruƙayya yau ya wuce na masu hankali, Innar kamalu yau kam an nuna miki iyakar ki, fatana da roƙona ɗaya Allah yasa basu asirce miki ɗan kiba, inada naga tana magana da ƙarfin gwuiwar ta kamar ta shiryawa hakan." Kululu ta faɗa tana gyara tsayuwar ta da riƙe haɓa wanda yake nuna tsantsar jimami da tausayin Innar kamalu.


Jin maganar su yasa innar kamalu ƙara haukacewa nan ta shaƙe wuyan Ruƙayya ta haɗa ta da bango, cikin tsantsar masifa da hargagi ta fara magana "Aradun Allah jinina yafi ƙarfin ki ɗiyar kurma, ni zaki maidawa magana Ruƙayya? Duk gatan da na miki, sai yanzu na ƙara samun dalilin da yasa yanzu na tsane ki, saboda kin koma bin bokaye da kuma neman maza kamar karya." kakari take idanuwanta sunyi ja sun furfito waje saboda azabar shaƙar da Innar su kamalu ta mata, ba wai ba zata iya ƙwatar kanta a wajen ta bane yasa ta ƙyale ta, a'a so take ta bata damar da za tayi abun da zai sa zuciyarta ta huce a kan jin haushin ta da take, idan akwai wani dalili da zai sa Innar kamalu ta shaƙeta haka ba zai wuce na zugar maƙiyan da suka kewaye ta bane. 

_"Kiyi haƙuri da duk abin da zaki gani ko ji a nan gaba Ruƙayya, Allah ya sani ina son ki sosai, hankalinki nutsuwarki da kuma tarbiyyar da iyayen ki suka baki sune suka yi rinjaye a cikin zuciyata na yarda na janyo ki cikin ahali na, a duk cikin ƴaƴa na nafi yarda da nutsuwar Idrisu shi yasa na je na nema masa auren ki, saboda zai yi iya ƙoƙarin sa wajan kula da ke da sauƙe duk wani nauyi da yake kansa, ina roƙon ki da kiyi haƙuri ki toshe kunnuwanki daga sauraran maƙiyan ku."_ kalaman Innar su kamalu a lokacin da aka bada auren ta ga Idris, akwai kusanci mai yawa tsakanin su da ita da soyayyar da take mata kamar ɗiyar cikinta, tabbas komi yana da iyaka amma a wancan lokacin idan akace mata Innar su Kamalu zata mata ƙiyayya kwatan-kwacin wannan to zata ƙaryata hakan, amma sai gashi yau rayuwarta take nema da ɗaukewar numfashi a tare da ita, idanuwanta ne ya fara yin sama alamar zai ɗauke saboda ƙofar numfashin data toshe babu hanyar futa, hannayenta ta saki suka sauƙa ƙasa, ji tayi an fincike Innar Kamalu daga riƙon da ta mata an wullata can gefe ɗaya, ita kuma ta sulale ta durƙusa a wajen tana faman maida numfashi akai-akai, idanuwanta jajir da su saboda azaba.

Ihu ta fara ji yana kaure gidan hakan ya sata ɗago da rinannun idanuwanta cikin mamaki da tsoro taga su tani suna nufar hanyar waje wanda take a garƙame kamar an rufe, ƙara kallon wajan tayi amma bata ga abin da suke yiwa Ihu ba, can ta murtsuka idanuwanta da suka sauya kala zuwa jajaye nan ta fara gani da kyau, ƙara mirtsike idonta tayi dan gaskata abin da take gani *ISMAHA ZAINAB* ce riƙe da sharɓeɓiyar bulala wanda ta ninkata tsayi da girma sai binsu take tana tsula musu hatta Innar su kamalu da take a zaune ta kasa miƙewa daga jifan da aka mata bata tsira ba saida ta shauɗa mata bulalar sau uku, gantsarewa tayi tana ci gaba da ihu. 

 Tsoro da fargaba ya hana Ruƙayya miƙewa balle tayi magana, dan ji tayi kamar an ɗaure ta a wajan, hatta bakinta yaƙi buɗuwa balle tayi magana, bata ƙara tsorata ba sai da taga ta yi tsalle ta buɗe ƙofar gidan, da hannu ta musu nuni da ƙofa nan suka ruga da gudun tsiya takalman su a hannunsu, dariya ta sa mai ƙarfi tana ɗaga kanta sama, can kuma tayi shuru ta sulale ƙasa ta kwanta.

Da ido Ruƙayya ta bita har yanzu ta kasa tsinana komi sai bugawa da ƙirjinta yake yi da ƙarfi, "Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un!, mi hakan yake nufi ?? Mi ya faru da Ismaha Zainab?? Ya Allah kada ka jarrabe ni da abin da yafi ƙarfi na." ta faɗa hawaye na tsere akan fuskarta..
🥀🥀🥀🥀🥀 

Wayyo da Alama Ismaha Zainab tayi gamo. kuyi haƙuri da ganin yawaitar rubutu na, zan iya baku Read more ɗaya zuwa biyu amma idan yafi haka yawa ana samun gajiyawa wajan gundurar karanta labarin, cmnts naku na ƙaranci, Anty Jidda hop yau ba zaki yi tsallaken pgs ba.#Um Nass

#NWA

#CMNT, LIKE, SHARE

#DA AMANA🤝

[2/16, 9:37 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB💍* ©BY *😘Um Nass 😘*


 _FOLLOW ME ON WATTPAD. @UmNass_® *NAGARTA WRI.ASSOCIATION* BABI NA HUƊU (page 4)


 

 Kamar mai jin tsoron ta haka ta ƙara takurewa a waje ɗaya tana kallon yanda take sauƙe numfashinta a hankali, ta ɗauki tsawon lokaci bata samu ƙwarin gwuiwar rarrafawa dan ta tinkari Ismaha Zainab ba, domin gani take kamar ba ita ba, ido ta lumshe cikin fatan ace mafarki tayi ba a zahiri ba "LUYYAH Abinci anci." Ta tsinkayi muryar Ismaha Zainab adai-dai lokacin da take faɗawa jikinta, firgici gami da tsoro yasa ta buɗe idonta Tarr a kanta, ita ɗince jikinta tsaf babu alamun ƙasa ko ƙura kamar a lokacin ta mata wanka, kanta ta bibbiga sannan ta sake kallon inda ta faɗi ta kwanta amma babu ita babu alamun ta, kafin tayi wani yunƙuri ta tsinkayi muryar ɗan Almajirin da yake kai kawo tsakanin masu siyan Abincin ta "Innar Ismah gashi ki zuba ma Muntari yace har da na jiya zai fanshe, ga jaka guda na duka zaki zuba masa taliya da ɗan-wake."

Kallon ta ta kai ga tarwatsattsiyar fantekar da Innar su kamalu tayi jifa da ita amma cikin mamaki da al'ajabi taga babu ita a wajen, asali ma wajan a share yake fess kamar ba'a taka shiba, waige ta farayi nan taga Fantekar a mazaunin da ta saba ajiye ta idan zata siyar da abincin, zuciyarta ce ta tsinke da tsoro mai tsanani, nan tayi saurin ture Ismaha Zainab daga jikinta amma kuma hannayenta suka kasa yin hakan, da sauri ta sauƙe kallonta a kan fuskarta, itama kallonta take ido cikin ido wani abune a cikin ƙwayar idon nata mai kalar blue da taruwar ruwa mai sirkin maiƙo a cikin idon, nan take jikin Ruƙayyan yayi sanyi laƙwass kwata-kwata tunaninta ya ɗauke tama manta da abin daya faru a tsakanin lokacin, sai sake tsinkayar muryar ɗan Almajirin tayi "Innar Isma jirana yake yace da sauri fa."

 

 Saurin zuwa tayi gabansa ta karɓi kuɗin "Oh Garba kai dai kace baka son Uban gidan ka ya daɗe a waje" ta faɗa tana murmushi, shi ma dariya yayi yana ƙara mata bayani ya ce' "jiya ai yasha wuya da ya makara a tashi, asali ma haka ya yini sai da dare yasha shayi da burodi a wajan Na Inna, duk da haka bai ji yanda yake soba, dole yau ya gimtse barcin sa ya taho da wuri saboda kar a sake mai-mai."

 Dariya take sosai sannan ta miƙa masa abincin cikin kwanon roba da gani ya haura na adadin kuɗin daya buƙata "gashi kace yayi ƙoƙari ya cinye duka idan ma bai ƙoshi ba ya aiko a ƙara masa wani, har sai yaji ya cike ramin da ya haƙa."

 Ido Garba ya ƙwalalo waje cikin mamaki kafin yayi dariya "aradu koshi raƙumi ne yaci wanan Abincin ya ƙosa har dare bai biɗar wani abun ba." Murmushi tayi bata ce masa komi ba har ya fuce, sai a lokacin Ismaha Zainab ta ƙaraso kusa da ita tana faman turo baki "Luyyah nima anci abinshin." juyawa tayi tana kallon ta cikin kulawa da murmushi a kan fuskarta ta janyo ta haɗe da ɗora ta a kan cinyarta kana ta zubo mata taliya dan tafi sonta, da hannunta ta fara bata tana ci tana murmushi, abin yana ɗaure mata kai ganin yanda Ismaha Zainab ta buɗe ciki tana cin abincin sosai, wanda ta zuba mata ta cinye tass kana tace a ƙaro mata ɗan-wake zata ci, shima wanda ta zuba mata sai da ta cinye shi, gashi kuma bata buƙaci ruwa ba, saɓanin a baya duk lokacin data ke cin abinci tana korawa da ruwa asali ma shan ruwan yafi cin abincin ta yawa, amma kuma yau an samu ban-banci da tazara ta yanda bata buƙaci ruwa ba har cin nata yayi nisa, magana take so ta mata ko gardamar zuba mata abincin amma kuma kamar an ɗaure bakin asali ma samun kanta tayi da jin daɗin ganin yanda take cin abincin hankalinta kwance.


Tana gama ci ta sauƙa a kan cinyarta ta nufi ƙofar fita, kasa mata magana tayi har ta fice, sai a lokacin tunaninta ya dawo a kan mi yasa bata tsaida ita ba, sam Ismaha bata ƙaunar fita waje balle yin wasa da yara amma kuma sai gashi yau da kanta ta fice har tana gudu cikin kazarniya da kuzari, tagumi ta rafka a wajan tana son tuno wani abu amma kuma ta gagara tuna ko miye ne, a haka Garba yazo yana kai kawon mata ciniki kafin wani lokaci abincin nata ya ƙare tass, shima ta zuba masa nasa ya ci, har wannan lokacin babu Ismaha Zainab babu alamar ta. Dole ta tashi Garba akan yaje ya nemo mata ita.


******

Da gudu suka gifta mutane wajen suna ihu da kuka kamar sa tada garin amma babu wanda ya kula da su, asali ma babu wanda ya ankare da wanzuwar su a wajen, haka suka ƙarasa gidan nasu nan suka warwatsu yashe a ƙofar ɗakin Innar su kamalu, wanda garin gudu tayi hantsilawa yayi biyar a waje, ko ina a jikinta ciwo yake mata, hawaye shaɓe-shaɓe a kan fuskarta "Kin cuce ni Tani, ina zaman zama na kika angiza ni nazo mu tafi Ruƙayya taƙi jin magana ta, ashe rabon na janyowa kaina wahala da azaba ne." hawaye ne ya ci gaba da tsere a kan fuskarta wanda tayi futu-futu da ƙasa, da ƙyar ta ƙara jan ƙafafuwanta ta kai jikin bango ta jingina tana maida numfashi.

 "Uhmm Innar kamalu nima banyi tsammanin zamu tadda wannan azabar ba wallahi, duka ta ko ina jikina duk shatin bulala, anya wanan yarinyar ba Aljanah bace, dan Aradu idona baya tantance ko kamannin ta sai sauƙar duka da naji."

 Hanci Kululu taja ta face majina cikin tsoro da fargaba ta fara magana "Kinga Tani ki raba mu da batu a kan wannan, mu muka kai kanmu da bamu jeba da ba abin da zai same mu, Allah yasa bakin wahalar mu kenan, nan gaba sai musan shirin da zamu yi."

 Shuru Innar su Kamalu tayi bata tanka musu ba, a ranta tana kissima martanin da zata ɗauka a kan Ruƙayya da ɗiyar ta "Tabbas yarinyar nan tafi kama da ƴan ruwa, ni tun farko bana jinta a jikina, ashe ba jinina bace." Innar su kamalu ta faɗa tana sharce gumi a kan fuskarta. Nan aka shiga kallon-kallo tsakanin Tani da Kululu suna masu jinjina maganar Innar su kamalu a kan gaskiya tsagwaranta.


*******

 Tafiya yake yana ta faman ƙwala mata kira Ismah Abu kina ina ne, sai da ya shiga gidajen da suke maƙotaka da su, amma babu ita babu dalilin ta, gajiya yayi ya dawo gida ya sanar da ita "Innar Ismah bata gidajan dake kusa fa, na duba babu ita." ido ta fiddo waje cikin tashin hankali ta sai ta kallonta gare shi, "Na shiga uku ni Ruƙayya, Ina zatje a wannan garin.?"

 Kafin tayi shuru ta tsinkayi maganar Ismaha Zainab ita kaɗai take tafiya tana magana "Ai munyi faɗa da kai, kalka ƙala min magana." tana gama faɗar haka ta wuce su ta shige ɗaki tana kumbure-kumbure ba tare data kulasu ba, baki buɗe suka bita da kallo daga Ruƙayyan har Garba Almajiri.....
🥀🥀🥀🥀🥀🥀


_To fa gamu dai cikin tafiyar taki kaɗan ya rage labarin Ismaha Zainab ya sauya sallo, ku daure ku ɗauƙo ko wata mutuntaka taku da nagartar da take a tare daku sai ku magantu dan ra'ayin kanku. Ina miƙa tarin gaisuwata ga ɗaukacin masoya na masu bibiyar labari na a duk inda kuke ina muku Ƙaunar Ƙauna Fisabilillah_
#Um Nass

#plx Cmnts, vote, share 

#NWA

#DA AMANA

[2/16, 9:37 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB💍*


©BY *😘Um Nass🏇🏼*


_FOLLOW ME ON WATTPAD @UmNass_


® *NAGARTA WRI. ASSOCIATION*


_*Ba ko wata soyayya bace ake buɗe ta ta yanda duniya da mutanen cikin ta zasu gaskata hakan tun kafin ka magantu, wasu suna ninke nasu muradin a zuciyarsu ta yanda zasu kalle shi daga nesa suyi murmushi saboda jin daɗin su, akwai banbanci tsakanin abin da ka so da wanda duniya zata kira shi a matsayin wanda kake so, kamar haka nake ji a cikin Labarin Mamarsu bazan kira ta da tawa ba dan har yanzu bata cika ma'aunin hakan ba, amma dai ina son BOSS acikin ko wani labari. Lolx 🤪 thank so much Dear Sadiya Jegal ki sanar da Mamansu akwai mai yinta da babbar murya a cikin labarin Talauci ba madogara bane 🤝🏼*_BABI NA BIYAR (Page 5)


Basu yi yunƙurin mata magana ba illa rakiyar da suka mata da ido, domin a jikinsu ko wata laka ta sanyaya daga kuzarin da suke da ita, sabuwar Ismaha Zainab suke ga a gabansu wanda take cike da kuzari da surutu maganar ta ta dawo mai sauti da fidda harrufa da ƙarfin su, saɓanin a baya da sai ka kashe kunne ka matso da ko wata nutsuwa gare ka sannan zaka tantance maganar ta. Ɗaki ta shige ba tare data kallesu ba sai can ta sake fitowa tsakar gidan ta makawa Garba Almajiri harara "Kada ka kala duwa nema na kana ƙwala min cila a maƙota." kai ya iya ɗagawa alamun to dan tsoron ta ne yaji ya shige shi sosai.

Kitchen ta shiga ta fara buɗe-buɗen kwanikan da aka wanke can ta fito da ƙatuwar langa da taliya da ɗan-wake a cikin ta, baki ta wage tana dariya sannan ta shimfiɗa tabarma ta zauna "Kai kul kusa min wawa, ku bali kowa zai samu, ai yana da yawa." ta faɗa tana matso da kwanon gabanta, sai faman zumɓura baki take, waiwaye aka fara tsakanin Garba Almajiri da Ruƙayya, suna neman waɗanda take ma magana amma basu ga kowa ba, nan jikin Garba ya fara rawa ƙarshe ya ruga da gudu waje Ruƙayya na kiran sa amma ina bai tsaya ba, dan shi kam ya haƙiƙance ba ƙalau Isma Abu take ba kamar yanda yaga alamomin hakan a tare da ita.

Cikin sanyin jiki Ruƙayya ta ƙarasa kusa da ita ta zauna kanta ta fara shafawa cike da soyayya da tausayinta "Ke da wa kuke cin abincin kike cewa kar su miki wawa?" ta tambaya cikin tsoron amsar da zata fito daga bakin Ismaha Zainab ɗin.

"kawayena ne Luyya." amsar da ta bata kenan tana ci gaba da cin abincin, duk da ba loma take ƙatuwa ba amma cikin abin da bai wuce mintuna biyar ba ta cinyen abincin duk yawan sa. Kamar gunki haka Ruƙayya ta tsaya tana binta da kallo komi na kanta ya tsaya cak ta kasa yin motsi balle tayi magana sai da ido take binta da kallo, maganarta ta sake tsinkaya tana cewa "Yauwala ku jila na ajiye kwanon sai musha luwa." da gudu ta shiga ta ajiye kwanon ta koma ta ɗauki buta ta wanke hannayenta, sanan ta buɗe randar ƙasar da take tsakar gida ta ciko moɗa kamar abin almara tass ta shanye ruwan sannan ta ajiye moɗar "Ayi lige-ligen shiga ɗaki kuma." nan ma ta shige da gudu ba tare data kula da ita ba, kai ta dafe da ƙarfi "Akwai gundumemiyar matsala, tabbas Ismaha Zainab ba ita kaɗai bace." ta faɗa hawaye na sirnanowa daga cikin idonta, wanda na tausayin yarinyar ne da rayuwar da zata shiga, tayi ƙarama ace ta fara fuskantar ƙalubale haka daga mutanen ɓoye, duk da su basa raina ruwan shuka.


Tashi tayi ta leƙa ɗaki a nan ta taddata tayi ɗai-ɗai a kan gadon ta tana barci, kinkimar ta tayi ta goya ta ta ɗauko gyalen ta ta rufe gidan, kai tsaye gidan su suka nufa kafin taje ta jiggata saboda nauyin da taji Ismaha Zainab ɗin ta ƙara yi mata.

 Da fara'a Innar mu ta tare ta tana kiran "Maraba da baƙi, yau kishiyar aka goyo haka dan abin haushi." ta faɗa tana ƙoƙarin kwanto ta daga bayan, sai dai kamar an jona mata shokin haka taji an jata, da sauri ta janye hannunta "Kai naga ba sanyi a ke ba amma kuma kayan ku ya ɗauki sanyi har yana jonawa mutum wuta." Innar mu ta faɗa tana barbaza idanuwa cikin fargaba da tsoro, kallon ta Ruƙayyan tayi "Wuta kuma innar mu?" ta faɗa cikin mamaki sannan ta sa hannunta da zummar sauƙo da Ismaha Zainab daga bayanta itama ji tayi shokin ya jata da sauri ta ɗauke hannun nata "Ikon Allah" ta faɗa tana yarfe hannayenta, gashi ta gaji sosai da goyon da tayi asali ma ƙirjinta ne yake amsawa da wani irin nauyi.


"Innarmu na shiga uku" kalmar data faɗa kenan hawaye yana zubo mata daga cikin idanuwanta.

Dafe ƙirji Innar mu tayi "Kaddai kice min Innar su kamalu ne suka rabo ki da gidan ki yau ma?." kai ta girgiza tana hawaye, bakinta ta buɗe tana so ta faɗa mata matsalar da ta sami Ismaha Zainab amma kuma abin takaici da mamaki madadin haka sai ta ji harshenta na sarrafa maganar da ba ita tayi niyar faɗa ba "Ko kaɗan Innar mu da wasa Innar su kamalu ta shiga lamurra na to shari'a ce zata rabamu, ni yanzu banƙi aure na ya rabu ba a kan su rabani da sana'ar da na dogara da ita, dan wasu lokutan gara marar aure tana da pancin kai da yin duk abinda taga dama, amma nifa sai nafi wata uku ban ji labarin Idris ba ban kuma san a ina yake ba, a baki ne yake sanar dani yana zuwa Legas neman kuɗi, amma bani da hujja da shedar da zan kira hakan da gaske, idan ya tafi babu ɗan aike na gaisuwa balle nasa rai a kan zan samu saƙo daga gare shi, faɗa min ba dan sana'ar nan da nake ba ƙila da tuni na dawo gida da zama, taya zan yarda da tirjiya daga gare su bayan basu ɗauka sun bani ba." ta ƙarasa faɗar maganar cikin ɗacin zuciya da ƙunci wanda aƙalla ta daɗe tana danne hakan a ƙasan zuciyarta, amma koda wasa bata taɓa sha'awa da gigin sanar da wani ba balle kuma iyayenta, baki buɗe Innar mu take kallon ta cikin al'ajabi da tausayawa, koda wasa bata taɓa hasashe akwai ƙunci a cikin rayuwar Auren ɗiyar tata ba. Dan babu wanda za yace yau gashi sun zauna sun tatattauna matsalar gidan ta da shi, asali ma kullum cikin yaba daɗin zaman gidan take.

 

 Hannunta taja ta zaunar da ita a kan tabarma kana taci gaba da kallon ta "Kina so kice min Idirisu baya baki wadataccan kuɗi idan zai yi tafiya?" Kallon Innar mu take tana son tuna abinda ta faɗa amma ta gaza tunawa "Tambayar ki nake kin min shuru?"

 Kai ta fara girgizawa tana in-ina "A'a ba haka nace ba, wanda zai wadace ni har ya dawo ne baya bani." baki ta buge mata cikin fushi da jin haushi "Ƙarya kike min, kina so ne ki kare mijinki, bayan kin fara karanto matsalar sa, duk tsawon wannan lokacin kina zaman haƙuri amma ana miki kallon kitse har ana yada mana magana, ashe zaman ci da kanki kike yi, to wallahi bazan lamunci hakan ba bari Baban ku ya shigo."

 

Dai-dai lokacin ya shigo yana gimtsa fuska alamun yaji duk abun da suke tattaunawa "Yauwa Alhamdulillah gara da ka shigo a wannan lokacin, ashe Ruƙayya nan shashasha muka ajiye, duk tsawon lokacin nan zaman ci da kai take amma bata taɓa faɗar hakan ba sai yau, da Allah yasa zanji, wata ƙila saƙar zuci take ta fito fili, to yasin Allah bazan yarda ba dole a sake zama tsakanin mu da Idirisu da iyayen sa da suka hana tamu ɗiyar shan ruwa."

 Kallon ta yake a lalace kafin ya ƙara gimtsa fuska ya kai kallonsa ga Ruƙayya "Da gaske ne abin da Innar ku take faɗa?"

 Kai ta girgiza sannan ta gyaɗa kamar ƙadangare, "Baki zaki buɗe ki masa bayani, kin zauna kina cutar kanki a aikin banza." Innar mu ta faɗa kamar ta buge ta.

 Hannu ya ɗaga mataa "Ya isa haka Ballu" ya faɗa cikin tsawa da hargowa, shuru tayi tana muzurai sannan ya sake juyawa ga Ruƙayya "Na ɗauka ke mai hankali ce ai da naga kin kame kanki baki taɓa kawo mana ƙara ko suka akan mijinki ba, ashe ke sakarya ce da kike ƙoƙarin butulcewa ni'imar da Allah ya miki, idan mijin ki baya sauƙe miki nauyin da yake kansa hakan da mi ya rage ki? Asali ma Allah ya baki wata hanya ta samu ne da rufawa kai asiri, tunda ya saka miki nasibi a cikin sana'ar ki, dan haka ki tashi ki koma gidan ki kar na ƙara ganin baƙar ƙafarki da sunan kin kawo ƙarar mijin ki, idan kuma kika kuskura kika kaso auren ki to sai dai ki nemi wani sabon Uban amma fa ba ni ba."

 Yana ƙarasa faɗar haka ya dira mata tsawa wanda ta sata miƙewa da sauri ta nufi waje "Haba Baban su ya zaka yanke irin wannan hukuncin haka ba tare da kayi bincike ba, wata harara ya wurga mata kafin nan ya juyo da kallonsa saitin ta "Nasan ke kike ƙoƙarin hana yarinya ta kwanciyar hankali a gidan ta, to bazan lamunta ba ko kaɗan, tunda bata nema ta rasa ba a gidan ta mi zai sa ta ɗaga hankalinta, wasu ma da mazajan nasu a gari amma basu ɗauki nauyin suba kuma basu da sana'ar da zasu riƙe kansu, su wannan suce ma Allah mi?" kai ta sunkuyar ƙasa maganar sa akwai alamun gaskiya "Haka ne malam"

 "To kinga ita bata kawo mana matsalar ta a kan tana cikin damuwa ba, yau ɗin ma idan ki ka bibiya ba wannan ne ya kawo taba, tunda dana tambaye ta shuru tayi."

 "Tabbas da alama bata shirya faɗa ba." Innar mu ta faɗa tana murmushi a ranta tana jinjina ma yarinyar tata da fatan Allah ya cigaba da kare ta da sana'arta.

 A nan ya cigaba da kwantar mata da hankali da bata baki dan yasan soyayyar dake tsakanin su da Ruƙayya zai yi wuya idan bata saka abun azuciyarta ba..


******

 Tunda ta fita a gidan take tunanin mi ta faɗa haka? abinda ya kaita daban wanda ta faɗa daban, mi hakan yake nufi ne?

 Turuss taja ta tsaya ganin mutum a zaune a tsakar gidan, cikin mamaki ta murza ido tana kallon sa "IDRISS" shi ma kallon ta yake cikin fuskarsa da babu burbuɗin rahma "Daga Ina kike?" tambayar daya watso mata yana ƙara tamke fuska kenan, sororo tayi tana kallon sa cikin mamaki baki buɗe.

🥀🥀🥀🥀🥀#IsmuhaZainab

#cmnts and share

#NWA

#Da amana🤝 ©Um Nass

[2/16, 9:37 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY *😘UM NASS 🏇🏼*


_FOLLOW MEE ON WATTPAD @UmNass_


® *NAGARTA WRI. ASSOCIATION*
BABI NA SHIDA (PAGE 6)


Wata uwar tsawar ya sake kwaɗa mata yana miƙewa a kan ƙafafuwansa "Nace daga ina kike? Kin saki baki da hanci kina kallo na tabbacin baki da gaskiya kenan, ko wace macen arziƙi idan mijin ta yayi tafiya takan kare kanta har yaje ya dawo, amma ke kusan ko wani zuwa nayi sai na tadda saɓanin hakan, ina tunanin wani abu anya kina kare kanki amatsayin ki na matar aure?"


 Mamaki gami da al'ajabi ya kusan sandarar da Ruƙayya daga tsayen da take, wannan ba Idris ɗin da ta sani ba ne? Wani sabon Idris take gani wanda fuskarsa babu rahma balle a samu sassauci a cikin ta "Mi kake son faɗa min ne Idris? Kana so kace min kana zargi na ne wajan mu'amala da wasu mazan saɓanin kai da kake halaliya ta?" zuwa wannan lokacin hawaye ya fara tsere a kan fuskarta.

Baki ya taɓe gami da ɗaga kafaɗarsa kana yace' "Idan ma haka tunanin ki ya baki, to hakan ne." yana gama faɗar haka ya wuce fu abin sa kamar zai hankaɗe ta, da ido ta bishi cikin tashin hankali da al'ajabin abin da ya sauya mata Idris ɗin ta. _"Mi yake son faruwa dani ne? Mi yasa lammura na suka sauya a ɗan tsakankanin nan? Ya Allah ka kawo min ɗauki kar ka jarrabe ni da abin da yafi ƙarfi na."_

 "komi zai faru dake alkhairi ne, ke dai kada ki karaya ɗan taki kaɗan ya rage ƙaddarar ki ta sauya." wata murya ta bigi kunnuwanta, nan ta fara waiwaye ko zata ga mai maganar, amma babu shi babu alamun sa, hakan ya sauƙar da tsoro mai yawa a ƙasan zuciyarta, dai-dai lokacin da Ismaha Zainab take mutsu-mutsu alamar tana son sauƙowa "ki tauke ni" ta tsinkayi muryarta da ɗan amo, hankalinta ne ya dawo jikinta nan ta ankare da Ismaha Zainab da take bayanta, sauƙeta tayi nan ta fara mata dariya kafin ta maƙalo hannunta ta jata zuwa ɗaki, kamar raƙumi da akala haka ta shiga binta ba tare data ce mata komi ba.


******


Tafiya yake buguzun-buguzun kamar zai tashi sama, duk inda ya wuce mutane sukan kira shi su masa barka da zuwa, wasu kuma sukan yi mamakin ganin sa a hargitse kamar zai tashi sama, dariyar yaƙe kawai yake musu shi kan sa bazai ce ga abin da yake damun saba, haka kuma ba zai ce ga inda nutsuwar sa take ba har ya shiga gidan su da sallama.


"Lale da mutanen kudu, maraba da zuwa" Innar su Kamalu da su Tani suka faɗa cikin haɗin baki gami da yawaita murmushin su akan Fuskarsu.

Murmushi shi ma yayi ya samu kujerar tsugunno wanda ya gani a ƙofar ɗakin Innar su Kamalu "Yauwa Innar mu na same ku lafiya?" ya faɗa yana dai-daita kallonsa gare su, nan suka shiga haba-haba da shi kamar zasu mai dashi ciki, wanda hakan yana cikin kissar su da shirin da suka yi "Tani kawowa Idirisu abinci dan da alama bai samu tarba mai kyau ba balle aje batun cin abinci." Innar su Kamalu ta faɗa tana gyaɓe baki da ƙif-ƙifta ido.

Baki buɗe Idris yake kallon su amma ya gaza yin magana har sai da tani ta kawo masa ɗumamen tuwo da miyar kuka koriya fatau da ita da ganinta ta samu rauni na kayan haɗi a tare da ita, zuciyarsa yaji ta fara tashi lokacin da warin miyar ya bugi hancinsa "Yanzu irin wannan miyar kuke ci a gidan nan? Haba wannan ai idan na cita sai a samu matsala." ya faɗa yana toshe hancinsa da hannayensa.


"Amma lallai an yi ja'irin yaro, da ka samu muka baka abincin ma, shine zaka nuna mana cewar ka shiga burni kanka ya waye, to wannan abincin shine ya gina ka har ka kai matakin yanzu, kuma mun gode Allah halak ne wannan, ina matar ka ko a gida baka same taba balle kasa ran zata baka abinci kamar wannan." jin an anbaci matar sa bata gida yasa yayi saurin ɗagowa yana kallon Innar su kamalu cikin mamaki.


"Ya akayi kuka san Ruƙayya bata gida lokacin dana dawo?"

Harara ta buga masa gami da ƙara yamitsa fuska kamar da taga sabon kashi "Uhmm duk garin nan waye bai san halin da Ruƙayya take ciki ba, ka fita waje neman halaliyar ka ita tana nan tana yawon bin gidan maza, idan kuma safiya tayi maza ne suke ta karaskiya a ƙofar gidan ka, wannan ya shiga ya ɗana wannan ya shiga ya ɗana, amma a haka ta rainawa mutane hankali da sunan tana sana'a ne, bayan wanda suka ga abin da take aikatawa suna dawowa su faɗa mana." tana faɗar haka ta ɓarke da kukan munafunci wanda babu hawaye a cikin sa sai gunji da ihu, miƙewa yayi tsaye saboda zufar da ta cigaba da wanke masa jiki, ko ina a jikinsa rawa yake mamaki tsoro da fargaba suka daskarar da shi.

 "Ruƙayyan ce take wannan aika-aikar?" ya sake faɗa yana fifita hannayensa a jikinsa ko ya samu yaji sauqi daga zafin da yake ji.

 "Ƙwarai kuwa Idris, Wannan Ruƙayya ta sauya daga wadda ka sani, halin ta ya samu banbanci daga kyawawan Halayyarta da ka sani a baya, to mu da muke mata nasiha mu faɗa mata gaskiya babu zagi da tsinuwar da bata mana, a taƙaice har Innar su kamalu bata ishe ta kallo ba."

"Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un" kalmar da yake nanatawa kenan, saboda abin yafi ƙarfin zuciyarsa ta ɗauka, nan ya tsugunna yana hawaye na dana sani da takaici a kan abin da ya ji da wanda idonsa ya gani, kafaɗarsa Innar su kamalu ta dafa "Ka godewa Allah da kaji ka kuma gani, lokaci bai ƙure maka ba, kai kake da ikon kawo ƙarshen wannan al'amarin." miƙewa yayi ya fita ba tare da ya waiwaye suba, da ido suka bishi har ya fice a gidan kana suka tuntsure da dariya suka tafa a tare kamar wasu sa'anni.

  

"Gaskiya Innar su Kamalu ke ta musamman ce, gashi cikin sauƙi kin warware matsalar da take taki ce da kan ki." kululu ta faɗa dan sai a lokacin ta samu bakin magana, saboda mamakin jin tunzurawa da zugar dasu tani suka yi.

"Hmm wannan ai soman taɓi ne, muddum Ruƙayya bata bar gidan nan ba hankalina ba zai taɓa kwanciya ba, zata gane kuren ta da abin data faɗa a kaina na iƙirarin bani da ikon sakin ta."

Dariya duka suka yi nan suka fara jujjuyawa suna taka rawa alamun sun ji daɗin nasarar da suka samu."


*****


Can kuma a gidan Ruƙayya Muntari ne ya zo suna gaisawa yana tambayar Ismaha Zainab Matar sa, hararar sa take tana faman murguɗa baki alamun bata so, dariya yayi kana ya zaro ɗari biyu daga aljihunsa ya miƙawa Ruƙayya "Gashi Innar Ismaha gobe bazan samu fitowa da wuri ba, sai ki ajiye min taliya da ɗan-wake na jaka guda, naci na barshi." ya ƙarasa faɗa yana dariya, itama dariyar ta masa.

"Sannu acici kazar gona duk kai ɗaya zaka cinye abincin ɗari biyu?"

"Eh mana, idan ban yi sa'a bama ya zama maleji."

Haɓarta ta riƙe tana jinjina kai kana tace "To fa akwai matsala dan gobe bazan yi abinci ba, Baban Ismaha Zainab ya dawo, kaga yana buƙatar hutawa zuwa kwana biyu sai na ɗora abincin ko?"

Ido ya ƙwalalo waje cikin mamaki da tsoro "Haba mana Innar mu dan kawai mai gidan ki ya dawo sai ki ƙiyin abin da ya zama jiki a wajanki? Gaskiya mu a wajen mu da matsala saboda mun riga da mun saba da cin naki duk garin nan babu inda zamu muji daɗi kamar naki."

"A'a Muntari akwai mata da yawa da suka fini ƙwarewa ta wannan fanni, kayi haƙuri kwana nawa ma zai yi ya koma, idan ya tafi sai na ɗora akan na baya."

Kafin yayi magana yaji an shaƙe masa wuyansa, cikin tashin hankali Ruƙayya ta kai kallonta ga mai wannan aika-aikar Idriss ne, cikin kaɗuwa da tsoro ta fara magana "Sake shi Idris kada kayi kisan kai, mi ya maka da zaka shaƙe shi." tana maganar tana hawaye sai girgiza masa hannu take, amma bai tsaya ya saurare taba, asali ma ci gaba yayi da dukan Muntari sai da ya galabaitar dashi kana ya sake shi dan kan sa, a lokacin yake maida Numfashi sama-sama, bai tsaya samun nutsuwa ba ya ruga waje da gudu, a lokacin ya juyo da kallonsa ga Ruƙayya "Ki kace kar nayi kisa? Bayan abin da idona ya gane min, kunnuwana suka jiyo min sautin da na jisu a bakin da ba zai min ƙarya ba."


Kallon sa taci gaba da yi cikin mamaki da kaɗuwa "Mi kake nufi da maganar ka Idriss?"

Ta faɗa tana Durƙushewa a kan gwuiwoyinta tana faman kuka da gunji, saboda taso fahimtar inda maganar sa ta dosa, a yayin da yake tsaye a kanta yana ta faman balbale ta da masifa kamar zai bigeta, kai take girgizawa tana ƙara sautin kukanta, hakan ko kaɗan bai sa yaji tausayinta ya kuma tsagaita daga faɗan da yake mata ba.

 "In dai har abin da idanuwana suka gane min gaskiya ne, to na tabbata babu wani abu da yayi saura na yarda a tsakani na dake, zan kuma nesan ta kai na daga duk wani abun da zai sake haɗa fuskata da taki."

Hawaye ne ya ci gaba da zuba a cikin idanuwanta, hannayenta biyu tana haɗesu waje guda, magana take son yi amma ta gagare ta fita a kan laɓɓanta, so take ta samu damar kare kanta daga mugun zargin da mijin nata yake son mata, amma kamar ana ƙara kulle mata bakin nata ne, sai dai kallon da yake mata ya ƙara tsoratar da ita, hakan yasa ta aro dauriya da juriya ta fara magana "A'a Idris ko wani abu yakan buƙaci bincike da samun tabbaci a kansa, amma ba tare da ka nazarci komi ba ka yanke hukunci hakan ko kaɗan bai kamace kaba sam-sam."

Hannu ya ɗaga yana jijjiga jiki kamar wata mace "Ke ai ya kamace ki da kika kasa tsare kan ki, na ɗauka ƙarya ne abun da su Tani suke faɗa ashe tsagwaran gaskiye ce tsirarar ta a shimfiɗe a cikin maganarsu, dan haka yau ɗin nan zan kawo ƙarshen matsala ta ba sai an je ko ina ba, na gode Allah da ya nuna min gaskiya."

Saurin ƙarasawa kusa da shi tayi tana ƙara yawaita hawayenta ƙafafuwansa ta riƙe tana fatan ya bata dama ɗaya ya kuma kalle ta da idanuwan basira, uzuri take son yayi mata a kan tantance gaskiya a kan kalamanta, numfashi take fitarwa akai-akai tana magana cikin dashewar murya "Ka dubi girman Allah kada ka yanke min hukunci cikin fushi da ingizawar sheɗan ba tare da ka binciki komi ba, kada idanuwanka su rufe daga ganin abun da baka da tabbaci a kansa Idris, ina iyaka ƙoƙari na wajan kare kaina daga duk wani mugun abun da zai kawo shamaki a tsakanin yardar da take tsakani na da kai, dan Allah kada ka aikata abun da zaka zo kana dana sanin yin sa daga baya."

 Haure ta yayi da ƙafarsa hakan ya sata wuntsulawa baya ta buga kanta da wani dutse nan take kan ya fidda jini, zafi da raɗaɗin da take ji ya sata dafe wajan cikin kaɗuwa da tashin hankali ta sake kai kallonta gare shi, fuskarsa babu ɓurɓushin rahma ya fara nuna ta da ɗan yatsansa manuniya "Na tsaneki Ruƙayya na tsani komi da zai fito daga bakinki, dan haka bana buƙatar wani ƙarin lokacin da zan baki wanda zai jefa zuciyata cikin wata damuwar, wanda nake cikinta ma ta isheni dan haka kafin na fito ki tattara komi da yake mallakin ki kibar min gidana, na sake ki saki uku."

ƙirjinta ta dafe da ƙarfi take jin bugawar zuciya tana barazanar fitowa daga ƙirjin nata, haka kuma ta fara bubbuga kunnuwanta da suka fara mata amsa kuwa da ƙara mai amo, dafe kunne tayi tana kai kallonta gare shi, kai ya gyaɗa mata yana ƙara tamke fuskarsa haɗe da bata tabbaci a kan maganarsa, dai-dai lokacin Ismaha Zainab ta fito daga ɗaki, hannunta a cikin bakinta tana tsotsa, ganin sa ya sata saurin ƙarasawa ta maƙalƙale rigarsa ta fara magana wanda bata fitowa "Babu alawa bitcik" hankaɗe yarinyar yayi ya tura ta kan Ruƙayya cikin rashin sa'a kansu yayi gwara nan yarinyar ta fara tsanyara ihun kuka, cikin mamaki da ƙarfin hali tace "Idris muguntar ka ta wuce kai na harda ƴar ka da ka haifa da cikinka."

Tsawa ya kwatsa mata ya fara nuna ta da hannunsa "akul ɗinki ki ƙara danganta ta da ɗiya ta, dan ni kokonto nake a kan ba ɗiya ta bace, dan ko kaɗan bata kama dani, dan haka ki kwashe ta kije can ki nema mata uban ta ki kuma tabbatar kin bar min gidana kafin na dawo, munafukar Allah Annamimiya kawai." yana ƙarasa faɗar haka ya fice Fuu kamar Iska ya bar gidan, da ido suka bishi wani dunƙulelen abu ne ya tsaya mata a maƙoshinta hawayen da take shirin yi suka ɗauke daga cikin idanuwanta.

Miƙewa tayi ta shiga ɗaki bata jima ba ta fito da lilliɓi a kanta sai kayanta a ƴar ƙaramar jaka gana mazgo ta ɗauko ɗiyar ta da take ta faman binta duk da cewar tana tafiya da girman ta hakan bai sata ƙin ɗaukan taba asali ma goyata tayi da zani ta janyo ɗakin ta rufe, kana ta janyo ƙofar gidan, juyawa tayi ta masa kallo na ƙarshe sannan ta fara tafiya cikin sauri ganin idanuwan mutanen garin a kanta da alama sun fahimci abin da yake faruwa da yawa suna tsaigumi a kanta, ƙara sauri tayi tana hawaye a kan fuskarta, ta shiga gidan su da sallama a bakinta.

Sai dai kafin ta kai ga zama taji an kwatsa mata tsawa "Ke ma dai kin san idanuwanki da kunya ki shigo min gida, dan haka ki fice ki bar min gida, bana buƙatar baragurbi a cikin zuri'a ta." saboda a lokacin Idris ya gama zayyanewa Babuji abin da yaji da wanda ya gani, duk da innar mu tace kada ya yarda amma ina ransa ya kai ƙololuwar ɓaci yana ƙara jin kunya ya fita gari a nuna shi a matsayin uba gare ta.

A hautsune ta juyo ga kallonta ga wanda yake maganar Fuskarsa babu alamun rahma a kanta cak hawayen da yake zuba a kan fuskarta suka tsaya "Babuji" Fuska ya ƙara tamkewa ya mata nuni da ƙofa "Ai na faɗa miki muddum kika kaso auren ki sai dai ki nemi wani uban bani ba. Fuce ki bar min gida na" kallon gidan tayi ta kai kallonta ga Innar mu wanda kanta yake sunkuye ko da bata ɗago kai ba tasan ba zata yi magana ba, tunda har taƙi yarda ta ɗago kanta, akwai alamun yarda da sharaɗin dake tsakanin ta da mahaifinta sai dai yanayinta ya nuna tsantsar damuwa akwai yiyuwar hawaye ne yake zuba a kan idonta.

 "Innar mu kina jin Babuji na kora ta, kema kina zargi na baki yarda dani ba, idan duk duniya zata juya min baya taƙi yarda dani na ɗauka ku zaku rungume ni ku min uzuri ku yarda da gaskiya ta." Muryarta akwai rauni a cikinta hakan yasa Innar mu ɗago kanta itama idanuwanta cike da hawaye, murmushin yaƙe ta mata wanda da gani yafi na kukan ciwo "Allah yana tare da ke Ruƙayya na tabbata idan akwai wanda ya cuci wani a tsakaninku sakayya zata fito, ki tafi ko ina ne amma ki bar masa gidansa, Addu'a ta zata riske ki a duk inda kike." tana gama faɗar haka ta shige ɗakinta, kallonta ta kai ga Mahaifin ta wanda ya ƙara gumtse fuska "Fita!" ya mata nuni da ƙofa, juyawa tayi tana murmushi da hawaye wanda yafi kuka ciwo.


🥀🥀🥀🥀🥀🥀

  

 _Ina ji kamar nayi ma LUYYA HAWAYE Adai-dai wannan lokacin, rana ɗaya komi ya sauya mata, mi hakan yake nufi? Nasan yanzu kun riga da kun fahimci inda labarin ya dosa, ku daure ku aro ko wata Kima da take a tare da ku da mutuntaka ku sanbaɗa comments, ku magantu dan ra'ayin kan ku, hakan zai taimaka min wajan isar da saƙon da nake son isar muku_


#IsmuhaZainab

#NWA

#Vote nd cmnt

#Da amana

[2/16, 9:37 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©by *😘Um Nass🏇🏼*


 _FOLLOW ME ON WATTPAD @UmNass_® NAGARTA WRITERS ASSOCIATIONBABI NA BAKWAI (Page 7)


Kallon gidan ta cigaba da yi, hannunta saƙale a jikin na Ismaha Zainab wanda sai faman dariya take da tsalle-tsalle, bata da damuwa ko kaɗan.

"Ina zan dosa a wannan garin?" tambayar da take ma kanta kenan, duk da cewa tana da ƴan uwa da yayya a garin amma bata jin sha'awar isa gare su, hasashe take a kan suma zasu iya korarta kamar yanda mahaifin ta ya kore ta duk da soyayyar da take tsakanin su na Uba da Ƴa, kallonta ta kai ga mutanen da suke zaune a gindin bishiyar da take tsallake da gidan su, tsarguwa tayi da kallon da suke jifan ta da shi, fuskarsa na nuna alhini da tirr da halinta.

"Ai dama rana dubu Allah ke arama ɓarawo yayi ta sharholiyar sa a duniya, amma idan Allah yaso bayyanar da gaskiya cikin rana ɗaya tak asirin mutum yake tonuwa, ko kaɗan ban taɓa tsammanin kamilalliya kamar Ruƙayya wanda ta samu kyakkyawar tarbiyya da nagarta tsatso kamilallai zata aikata kwatan-kwacin abin da tayi a yau"

 "Banda abinka NA-TA'ALA ai shi mutum mugun ice ne, sanin abin da ke cikin baɗininsa kuwa sai Ubangijin sa, kai dai kawai kaga mutum amma karka tona baƙin halin dake a tare da shi."

 "Haka ne Kallamu, Allah ya shiryar mana da zuri'a"

"Ameen-Ameen sai dai hakan."


 Hirar mutanen ta soki dodon kunnuwanta wanda hakan yasa zuciyarta ƙara samun zafi da rauni "Tabbas Idris ya cuce ta, ya kuma zalince ta, ta hanyar yaɗa ta a duniya a kan abinda bashi da tabbaci a kan gaskiyar sa, amma kuma ta bar shi da Allah shi zai fidda gaskiya a tsakanin su, babu abin da yayi mata saura na ƙima a cikin wannan garin wanda zata yi tunƙaho da alfahari a gare shi, zaman garin ya fice mata a rai tana jin tsanar komi da ya fito a garin, amma tafi tausayawa rayuwar Muntari sanin yana hannun matar uba, ko wani hannu zai kama kuma? Tambayar da bata da amsar ta kenan hakan yasa ya ja hannun Ruƙayya suka nufi tasha. 


Motar Ringim ta nufa dan itace ta cika ana jiran mutum ɗaya hakan ya kawo mata sauƙin tafiya, dan dama ji take kamar tayi fuka-fukai ta tashi tabar garin, zuciyarta ta bushe ta ƙeƙashe daga zubar hawaye.

Kuɗin motar ta biya mutane na kallon ta mafiya yawan ƴan tashan sun san fuskarta dalilin abincin ta musamman matasa, kondostan motan ne ya fara washe baki "Innar Isma kice zaki maraita mu da cin taliya gobe?" kallonsa tayi kana ta ƙirƙiro murmushi ba tare data ce masa komi ba, jikinsa ne yayi sanyi duk da yasan ba haka ya saba ganin taba amma yana da tabbacin akwai damuwa a tattare da ita, hakan yasa yaja bakinsa ya tsuke har suka isa cikin garin Ringim.

A nan fasinjoji suka fara sauƙowa kowa yana kama gabansa, tashar ta kalla tana ganin mutane da suke ta hada-hadar su ba tare da sun damu da kowa ba.

"Ina ya kamata na nufa?" tambayar da ta jefawa kanta kenan, dan ko kaɗan bata jin sha'awar zama a cikin Ringim dan yayi kusa da garin su, hakan yana nuna cewar bata bar matsala ba, dan ko yaushe zasu iya haɗuwa da mutanen garin su musamman da ya zama Ringim gida ce a wajen su, kullum cikin zuwan ta suke, koda ta samu wata ƙima a garin za'a samu wanda zai mata dirar mikiya ya faɗi abin da yaji a kanta na gaskiya da ƙarya, ya goge ƙimar da zata samu a idon mutanen.


"HAƊEJIA JIGAWA" muryar wani kondostan mota ta bugi kunnenta yana faman ɗaga hannu "Haɗejia Jigawa saura mutum ɗaya" maganar da ya sake yi kenan, ji tayi zuciyarta na ingiza ta a kan ta tafi ta shiga motar, hakan yasa ta ƙarasawa kusa da kondostan motar "Ina son zuwa Haɗejia" ta faɗa ba tare data haƙiƙance a kan tana son zuwa garin ba, ba kuma dan ta san garin ba, asali ma sunan sa kawai take ji a bakunan wasu, sai dai a yanda take jin zuciyarta na azalzalar ta babu abin da zai dakatar da ita daga zuwa garin.


Baki kwandostan motar ya washe nan ya ɗauki ɗan ƙullin kayanta yana faɗin "Taho muje Hajiya" bayan sa tabi suka nufi wajan mota babba (Bos) nuni ya mata da kujerar data rage a nan ta hau tana karanto "Bismillahi" a kan laɓɓanta kana ta zaunar da Ismaha Zainab a kan cinyarta, bata ƙara ma kowa magana ba ganin babu wanda ta sani, mafiya yawa maza ne sai matan da ba zasu wuce uku ba a cikin motar, damuwar da take tattare a cikin zuciyarta ba zata bata damar da zata musu magana ba hakan yasa ta kwantar da Ismaha Zainab a kan ƙirjinta ta jingine kanta a kan kujera tana lumshe ido, sosai hayaniyar mutanen wajan ta takura mata ji take har tsakiyar kanta, ƙaran rufe motar da taji an yi shi ya sata buɗe ido, kwandostan motar ne ya shigo shi da Direba nan ya fara karɓan kuɗin motar mutane ɗari biyar babu ragi babu ƙari, kuɗin ta zaro ta miƙa masa kana ta sake rufe idonta, ba dan tana jin barci ba sai dan tana so tabar jin raɗaɗin da take ji a cikin idanuwan nata.


Tafiyar Awa ɗaya da rabi ne ta kawo su cikin garin Haɗejia kamar yanda taji mutane suna faɗa, hakan ya sata buɗe idanuwanta tana warasu dan ganin inda ƙaddarar rayuwarta ta kawo ta, mutane take ga ta ko ina suna kai wa da kawowa ga kuma manyan plaza da yawa a cikin ko wata gaɓa wanda yake bata tabbacin garin akwai yawaitar ƴan kasuwa a cikin sa, mamaki take yanda mutane suke hada-hadarsu a garin, kamar a ranar ake cin kasuwar garin, hakan ya bata tabbaci akan wani ci gaba ne ya same ta, hamdala tayi ga Allah a lokacin da motar su ta tsaya a cikin tashar garin, kasancewar ta ta ƙarshen shiga motar hakan ya bata damar fara fita, tabi tashar da kallo tuni ƴann dako sun nufo ta suna tambayar ina za'a kai mata kaya, murmushi tayi ba tare data ce musu komi ba, dan ita ko kaɗan bata samu nutsuwar da zata ɗauki wasu kaya a gidan ba, banda kala huɗu data ɗaukar musu ita da Ismaha Zainab, tana sa rai a kan washe gari a ɗebo mata kayanta, sai gashi Babuji ya rusa ko wani fatan da take da shi ya kuma tarkata ya koro su ba tare da tayi tsammanin zai iya aikata mata hakan ba.


"Hajiya almuru fa ya fara yi, ga yarinyar ki da alama ta gaji." taji wani dattijo na mata magana da alama fita zai yi a cikin tashar, juyawa tayi ta kalle shi tana ƙoƙarin yin yaƙe amma damuwar dake tare da ita ya daƙushe ko wani karsashin ta, juyawa tayi ta kalli Ismaha Zainab wanda take lumshe ido gami da tsotsar yatsanta a hannu, hakan ya bata tabbacin tana jin yunwa ne amma ba zata iya faɗa ba, kallon ta ta kai ga mutumin cikin yarda da kamalar da taga a tare da shi ta fara magana "Mu baƙi ne yau na fara zuwa garin nan, ban sani ba ko zan samu gidan da zan zauna haya a cikin saba."


 Kallon ta yayi kamar mai nazartar yanayin da take ciki, can yaja ajiyar zuciya kana yace "Ba damuwa akwai wani gida da na sani na haya a maƙotan mu, sai dai gidan yawa ne ko zaki iya zama a cikin sa, suna bada hayar ɗaki ɗaya a kan dubu goma ne, amma zaki iya bada rabi daga baya sai ki cika musu rabin dan kar ki takura."


 Risinawa tayi har ƙasa sanan ta fara masa godiya "Na gode sosai, yawan ba shine abin dubawa ba, tunda har na samu gidan zama Allah ya saka maka da mafificin alkhairi."


 Murmushi yayi kana ya kai hannunsa ya ɗauki Ismaha Zainab wanda zuwa wannan lokacin ta fara gyangyaɗi "Bari na taimaka miki da ɗaukan wannan yarinyar, ke kuma sai kiji da ƙunshin kayan ku." daga haka ya fara tafiya tabi bayan sa tana masa godiya sosai.


 Sai da suka tsallaka titi sannan suka kangara tafiyar da bata wuce ta mintuna 20 ba suka zo unguwar, wani lungu suka kangara a nan taga taron gidaje mafiya yawa na matsakaita ƙarfi ne, sai dai fa akwai yawaitar kwatoci a lungun wanda baya rasa nasaba da zaman su na lungu da nan ce kaɗai hanyar gudanar sa, jikin wani gidan siminti yaja ya tsaya mai wawukekiyar ƙofa "Yauwa kinga nan shine gidan hayar da nake faɗa miki, bari na kira mai gidan" kallon ƙofar gidan tayi a nan taga zaure mai girma shima sai dai ko ina a malale yake da siminti har zuwa ƙofar gidan da yake da ƴar baranda mai tudu, ji tayi zuciyarta ta samu nutsuwa ko ba komai ta huta da cakuɓi idan damina tayi a yanda taga gidan ashinfiɗe da siminti.


 "Yauwa ga mai gidan nan ya ƙaraso" ta tsinkayi muryar mutumin hakan ya sata dawowa daga tunanin data shiga.


 "Malam isubu kai ne ka samo mana baƙuwa haka" mai gidan ya faɗa yana faɗaɗa murmushi a kan fuskarsa, shi ma murmushi yayi kana ya bashi amsa "Ai kuwa dai yanzu muka haɗu a tasha take ce min baƙuwa ce gidan haya take nema, to nasan ba'a rasa ɗaki a nan shi yasa nace tazo muje sai ta duba ko akwai wanda zai mata."


 Kai ya jinjina yana gamsuwa da maganar Malam Isubu "Ai kuwa ka kyauta, bari nayi sallama sai mu shiga ta duba ɗakin." daga haka ya fara rafka sallama a ƙofar gidan, sai da yaji an amsa gami da bashi izinin shiga, kana ya mata shiga tsakar gidan, duka matan suna sanye da lulluɓi a jikinsu yana shiga suka fara gaida shi, ya amsa da fara'arsa.


 "Baƙuwa na kawo zata duba ɗaki." kallon ta suka yi kana suka fara ɗan murmushi "Maraba baƙuwa." cikin haɗuwar harshensu kamar sun tanadi hakan.

 Kai ta gyaɗa tana murmushi itama har suka kai ga wani ɗaki na kusan ƙarshen gidan, a gaban sa akwai ɗan lungu kamar kitchen dan haɗe yake da rumfa "Yauwa Bismillah shigo Hajiya." 


 Shiga tayi tana kallon ko ina na ɗakin da yake malale da siminti ga rufin kwano da wani abu wanda ya katange kwanon bata rarrabe a kan ko miye ba, amma kuma da ganin sa zai taimaka wajen kare zafin rana, ɗakin yana da girma sosai, kallonta ta kai ga Mutumin tana murmushi "Yayi min, nawa ne kuɗin hayar."


 "Dubu goma ne na shekara guda" ya faɗa yana murmushi, itama murmushin tayi ta kai kallonta ga Malam Isubu, wanda yayi murmushi dan ya fahimci abin da ta ke nufi.


 "Alh. Isa amata alfarma ta bada rabi mana, tunda baƙuwa ce ta bada kuɗin raɓi ala basshi daga baya sai ta biya sauran, tunda zata buƙaci kayan amfani na yau da kullum."


 Kallon ta yayi kana ya kallo Malam Isubu ba tare da yayi magana ba ya juya yana ƙoƙarin ficewa a gidan, da ido suka bishi cikin firgici da tsoro, baya ga Malam Isubu da jikinsa ya gama yin sanyi.
🥀🥀🥀🥀🥀🥀
 _Afwan ! Afwan!! Kaina bisa wuya ina baku haƙuri na rashin jina da baku yiba kwana biyu, na shiga rububi da yawa ne, amma in sha Allah zakuna jina akai-akai, nagode sosai da dakon jiranku._


 *Gaisuwa ta ban girma ga jinjina gare ki Dear Sadiya Jegal nagode da kulawar ki*
#Um Nass

#cmnts, like nd share

#NWA

#Da Amana

[2/16, 9:39 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


© by *😘Um Nass 🏇🏼


® NAGARTA WRI. ASSOCIATION


 Wanan shafin Sadaukarwa ne gareki *_Real Mai Dambu ce_*


BABI NA TAKWAS (Page 8)


Tarar gabansa Malam Isubu yayi "Baka ce komiba zaka juya Alhaji Isah, idan babu halin ta baka rabin inaga ai gara kayi magana yafi kayi shuru?"


Kallonsa yayi sanan ya kalli Ruqayya da ɗiyarta wanda tun kallon farko da ya mata yaji tausayinta ya kamashi, duk da bai san mi yake damuntaba amma akallon farko idan ka musu xaka fahimci akwai wani al'amari mai girma atare da su. Murmushi yayi sanan ya fara magana "Banda abinka Malam Isubu aini da kai duk ɗaya ne, ko kyauta kace na sata ina mai tabbatar maka da cewar hakan za'ayi, balle kuma lamani akan bada rabi zuwa wani lokacin, wanan shi yafi komi sauƙi agareni, shi yasa ma banyi maganaba, ta bada abin da ya sauwaƙa kawai ba sai na bita bashiba, idan Allah ya kaimu wata shekarar da kwana sai ta bada kuɗin shekara gudan idan tana da wadatar hakan."


Ajiyar zuciya suka sauƙe akusan tare tsakanin Luyya da Malam Isubu suka kuma fara yi masa godiya cikin haɗuwar baki, musamman Ruqayya dataga abin kamar amafarki ko kaɗan batayi tsammanin zata samu rangwame awajan Alhajinba ayanda ta lura da shi, amma kuma saɓanin tunaninsu sai gashi ya musu fiye da abin da suka buqata, ƙullin kayanta ta kunce ta lalubo kuɗi nan ta qirgi dubu biyar ta miqa masa, acikin kuɗin ya zari dubu ɗaya ya bawa Malam Isubu kana ya zari wata dubu ɗayan ya damƙawa Ismaha Zainab "Gashi ki siyi biskit da alawa." mamakinsa ne ya kama Ruqayya hakan ma aɓangaran malam Isubu godiya suka ƙara masa har sai da yaji ba daɗi "Mutum ai rahma ne malam Isubu aduk inda yake baya rasa amfanin da zai maka da kuma ranar da zai ma, kamar kai gashi ina zaune ka kawo min ƙaruwa har gida, ni ya kamata na maka godiya." yana gama faɗar haka ya juya ya fice, bayansa Malam Isubu yabi shima yana ɗagama Ismaha Zainab hannu har suka fice.


 Ɗakin Ruqayya tabi da kallo tana kuma ganin ɗan qunshin kayanta, ga wata yunwa data mata dirar mikiya alokaci ɗaya, ko tantama batayi Ismaha Zainab najin fiye da wadda takeji "Allah gamu gareka, acikin sabuwar rayuwa da garin da bamu da wani da zamu kirashi da sunan danginmu, ka bamu mafita da sauqi acikin rayuwar da zamu fuskanta karka ɗora mana abin da bazamu iyaba."

Tana gama faɗar haka ta jiyo sautin kukan Ismaha Zainab sai faman cakwaikwayeta takeyi "Luyya Abinci" kukan take babu ƙaƙƙautawa kamar da ake mintsininta, to amma ita kanta taga dauriyar yarinyar, ba zata iya tuna yaushe ne taci abinciba, cikin sanyin murya ta fara mata magana "Kiyi haƙuri bari na bada asiyo miki abincin kinji." kai ta gyaɗa sai dai har xuwa wanan lokacin hawaye bai bar zuba acikin idanuwantaba, sai hannu da ta saka ta fara tsotsar bakinta.


 "Assalama alaikum" sautin muryar Malam Isubu ya doki kunnenta.

"Wa alaikumussalam maraba" ta faɗa tana ɗan ƙaƙalo murmushi.

 Shiga ɗakin yayi hannunsa ɗauke da tabarma sai kuma ɗaya hannun da yake riƙe da kwano babba, kallonsa take har ya ajiye kayan kana ya ɗago da kallonsa gareta yana murmushi "Naga baku da komi ne na shinfiɗa shine na kawo muku tabarma da bargo aciki, akwai kuma gidan sauro saboda muna da yawaitarsa anan, acikinsa akwai ƴar ƙaramar fitila saboda duhu sai kuyi maleji dashi kafin kuma garin ya warware muku, wanan kuma abinci ne Mai ɗakina ta gama shine na karɓo muku sai kuci, ga ruwan leda (pure water) sai kuyi maleji da shi, sanan idan kuna buqatar wani abu ku min magana gidana shine na huɗu kafin nan, idan wani abu na amfani ko aike ya tashi kima mutanen da kuke gida ɗaya magana zakiji daɗin zama da su."


Risinawa tayi har ƙasa tana jin wani hawaye na zuba acikin idonta "Na gode sosai malam, Allah ya saka maka da mafificin alkhairi, tabbas ka gama mana duk wani taimakon da ko wani baqo yake buqata, Allah ya raya maka zuri'a ya rufa maka asiri duniya da lahira kamar yanda ka rufa mana namu asirin."


"Ameen ya Allah" ya faɗa yana faɗaɗa murmushinsa dan sosai yaji daɗin addu'ar tata, daga haka ya fice ya barsu yana musu sai da safe.


Tabarmar ta ware ta shimfiɗa musa afaffaɗan ɗakin tabarmar da girmanta qwarai gefe ta kawar da bargon da gidan sauran da ya kawo wanda ko wata igiyarsa yake maƙale da ƙusa, ɗan murmushi tayi aranta taji sanyi sosai, ashe aduniya akwai mutane na gari har yanzu wanda sukeyi dan Allah? Ta faɗa tana zaunar da Ismaha Zainab akan tabarmar sanan ta janyo da kwanon abincin gabansu, tuwon laushi ne na hatsi wanda yasha tuqi da ganin yanda yake sheqi, ga kuma ya samu qarin armashi na miyar ɗanyan kuɓewa wanda tasha qananun kifi na ƙawara, ga man shanu daya daki hancinta, ganin tuwon da ƙamshin miyar su suka taimaka wajan ƙara hautsina cikinta ya ankarar da ita tarin yunwar data tara, Ismaha Zainab kuwa tuni ta fara dariya tana tafa hannayenta "Luyya Tuwo anci" ta faɗa tana qara washe haqoranta.

"Yanzu kuwa zaki ci Ismaha Zainab indai abinci ne." tana gama faɗar haka tayi Bismillah ta fara bata abaki haɗiya kawai take bata tauna, sai da ta cinye fiye da rabin abincin sanan tace "An ƙoshi, luwa" ruwa ta bata tana kallonta cike da tausayi, sanan itama ta fara cin abincin, sosai taji daɗinsa hakan ya sata cinyeshi tass bata ankareba sai jin kwanon tayi wayam babu komi. Hakan ya sata suɗe hannu ta gyara shimfiɗarta dan tuni Ismaha Zainab ta ɓingire tayi barci, aranta ta ƙara shima malam Isubu albarka saboda taimakon da ya musu, sai da ta kammala yin shimfiɗa ta kwantar da Ismaha Zainab kana ta fito tsakar gida, alokacin har almuru ta gabato ana kiraye-kirayen sallahr magrib, kallonta takai ga tarin matan da suke tsakar gidan sai kai da kawowa suke, wasu kuma suna zaune ana cin uwar hira ba tare da sun miƙe dan su gabatar da sallahr da ake kiraba, ƙarasawa tayi kusa da su ta musu sallama, amsawa sukayi suna ɗan murmushi atare, sai wadda ta hakimce agefe fuskarta babu yabo babu fallasa ta amsa, murmushin yaƙe Ruqayya tayi kana tace "Dan Allah ruwa zaku ɗan sanmin na ɗauro alwala." kallonta sukayi kamar sunga sabuwar mutum, kamar ba zasuyi mata maganaba, hakan yasa jikinta yayi sanyi ta fara qoqarin juyawa tabar wajan, saboda kallon da suke mata yasa ko wani karsashin dake atare da ita ya gudu.🥀🥀🥀🥀🥀

 *GIRMAMAWA*


#Um Nass

#NWA

#cmnt like nd share

#Da amana

[2/16, 9:39 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY *😘UM NASS 🏇*


® NAGARTA WRI. ASSOCIATIONBABI NA TARA (Page 9)


Har ta fara taku ɗaya biyu taji sautin muryar ɗaya daga cikin mazauna wajan "Ga buta can akusa da famfo, akwai ruwa acikin famfon banɗakinma kuma akwai ruwa acikinsa, bamu da matsala da ruwa kowa yana amfani da shi, ba'ayima baqo ko ɗan gida iyaka da shiba."


 Wani sanyi taji ya ziyarci zuciyarta, dan idan akwai abin da taqi jini acikin rayuwarta bai wuce matsalar ruwaba, xata iya jure komi amma banda rashin ruwa domin shine mahaɗin rayuwa, wanda amfaninsa yake da mutqar yawa agareta, murmushi tayi wanda har haƙoranta suka bayyana cikin jin daɗi ta ɗan risina tana kiran "Na gode sosai" kana ta juya ta ɗauki butar ta shiga toilet ɗin abin ya ƙara burgeta ganinsa tsaf-tsaf babu qazanta da zarni kamar yanda ta san da yawan banɗakin haɗaka ana samun irin haka, da kuma tarin ƙazanta.


 Hankali kwance ta gama uzurinta ta fito ta ɗaura alwala kana ta shige ɗakinta, sai da ta rama sallolin da ake binta sanan ta fara jero Azkar da Addu'o'i duk na neman yardar Allah da bata kyakkyawar rayuwa ita da ɗiyarta, tana zaune har aka kira sallahr Issha'i ta miƙe ta gabatar da ita haɗi da yin shafa'i da wutiri, anan taji kamar an sauqe mata wani nauyi dake bisa kanta, iska ta ko ina take shigarta hakan yasa taji barci na fizgarta, ba shiri ta shiga cikin sangenta ta kwanta tana karanto musu Addu'ar kariya ita da Ismaha Zainab duk da ta mata abaya.


****

Washe gari:


Abin ya bata mamaki ƙwarai ganin bata farka da wuriba har sai da taso makara, hakan yasata tashi ta ɗauro alwala ta gabatar da sallahr Asuba, tunani take ta ina zata fara neman abubuwan buƙata, duk da taga mutanen gidan suna da sauƙin kai, amma bata son ta zame musu matsala da nauyi atare da su, sai dai abu ɗaya da yake mata yawo akai shine matambayi baya taɓa ɓata aduk inda yake, haka ba'a haɗa rashin sani da shuru, idan ta dunƙule kanta ta gaza tambaya to zata sha wahla sosai acikin zamantakewar da zatayi da su, wanan tunanin yasata miqewa cikin hanzari ta fita tsakar gida, jin motsin mutane da maganarsu jifa-jifa.


 "Assalama alaikum" ta fara yin sallama ga wanda take maƙotaka da ita, aƙalla ta girmeta amma idan ka ganta sai ka ɗauka bazata wuce sa'artaba wanda hakan baya rasa nasaba da zama acikin marayar da take da ƙarantar wahlar da take ciki yasa shekarunta ɓuya.


Ɗagowa tayi ta kalleta kana ta ɗan faɗaɗa murmushi akan fuskarta mai faɗi "Wa alaikumussalam, har kin tashi kenan?" ta aika tambayar asaitinta tana murmushi.


Itama murmushin tayi kana ta gyaɗa kai "Eh! Na tashi, nama makara ai akan yanda na saba tashi, banji motsin kowaba shi yasa ban fitoba sai yanzu da naji naki."


"Ayya sun tashi sun koma barci ne, nima ina ƙoƙarin sallamar yara ne zasu tafi makaranta."


Kai ta sake gyaɗawa tana murmushi "Allah sarki, ina kwana? Bamu gaisaba"


Dariya tayi mai sauti tana ƙoƙarin hura wuta acikin murhu "Aifa, mun tashi lafiya? Ya baƙunta?" ta qarasa tambayarta tana dariya mai sauti.


"Alhamdulillah, dama tambayarki zanyi ko zan samu shago akusa na siyo sabulun wanka da soso, sai bokiti, da kuma abin wanke baki?"

Kai ta gyaɗa tana ɗora tukunyarta akan wuta "Eh akwai amma sai anfita bakin titi."


"Yauwa nagode sosai, bari naje na siyo kafin Ismaha ta tashi."


"Ga Zakar nan ki bashi ya siyo miki, inaga sai yafi sauƙi, amma yaushe da wanan safiyar zaki fita ki bar yarinya."

Daɗi ne ya kamata ganin yanda ta samu kulawa awajan matar "Aikuwa nagode sosai, dan dama bazan iya gane wajen ba sai da tambaya."

Dariya matar tayi mata "Da kin ɓata kenan, dan lungun nan yasha bada mutane, musamman baƙi."


Kai ta jinjina tana murmushi "Sai da na ayyana hakan araina alokacin da muke shigowa, abin ya bani mamaki danaga gari guda aɗan qaramin lungun da muka biyo." ta qarasa maganar tana dariya itama, itama tayata tayi. Daga haka ta shige ɗaki ta fiddo da kuɗi 2k ta bawa Zakar wanda har ya shirya tsaf dashi cikin shigar makarantarsa, hakan ya bata sha'awa mutuƙa har taji tana fatan wata rana zata saka Ismaha ɗinta acikin makarantar.


Mintunan da basu gaza gomaba sai gashi ya dawo niƙi-niƙi da kaya, anan ya ajiye mata ya bata chanjin kuɗinta 200, 50 ta wara aciki ta bashi, amma firr mamansa tace bazai karɓaba har ina abin yake, shima da yake yaron mai hankali ne sai yaƙi karɓan kuɗin yace baya so, ta masa Addu'a yazo na ɗaya amakaranta, sosai taji yaron ya birgeta nan ta shi masa albarka da fatan nasara acikin rayuwarsa, saboda harda Man shafawa ya haɗo mata da kuma powder mai mudubi duk da bata bashi saƙon da itaba, amma ya fahimci tana da buƙatarsu, ga kuma ƙarin abin burgewa harda abin wanke bakinma biyu ya siyo babba da qarami, sai sabulun wanki da omo mai ƙamshi wanda shima bata kokonto akan na wankin ne, sai ƙaramin turare mai ƙamshi.

"Kai gaskiya naji daɗi, amma kuma duk acikin kuɗin dana bada aka yo wanan siyayyar, gashi harda sanjima?"


Murmushi Mamansu Zakar tayi "Ai danma ba kasuwa kika shigaba da abin sai yafi haka sauƙi."

"Ikon Allah, lallai nan akwai rahamar kaya." ta faɗa tana murmushi da tashi ta nufi ɗakin.

 Kayan wankan ta ɗauko tayi lilliɓi ta sake fitowa wajen "Allah yasa dai babu kowa abanɗakin." ta faɗa tana kai kallonta ga Maman Zakar da take fifita wuta amurhu.

"Aikuwa babu kowa, dan basu tashiba sai anjima kiga suna ta faman yin layin shiga."

Dariya tayi ta shige banɗakin tayi wankanta, lokacin data fito ta tarar har Maman Zakar ɗin ta kammala girkin da take tana juyewa, saurin shigewa ɗaki tayi.


 ƙunshin kayanta ta ware wanda basu wuce kala ukuba nan ta shiga warasu tana ganin sakacinta na barin kayanta acan, gashi dole saita nemesu, ba kuma ta san ta ina zata fara neman kuɗi acikin ɗan lokacin nanba, sana'ar da zatayima lalimece dan bata san ta ina zata faraba, gashi abubuwa da yawa tana da buqatarsu.

"Ya Allah ka zama gata na, ka kawo min ɗauki." ta faɗa tana rintse idonta da ya cika da hawaye, kayan ta ɗauko ta saka dai-dai lokacin da Zakar yayi sallama aqofar ɗakin.

 "Zakar shigo mana" ta faɗa bayana ta amsa masa sallamarsa.

Shigowa yayi ya ajiye mata kwano "Wai gashi inji mamanmu." ido ta fiddo waje cikin mamaki dan ko kaɗan bata saka aranta zata samu abinciba, asalima tunanin abin da zata ci idan Ismaha Zainab ta tashi.

"Kai nagode sosai, harda wahala? Kace mata nagode kaji Zakar?"


"To" yace yana fita acikin ɗakin, da ido ta bishi tana ganin nutsuwar yaron duk da bazai wuce shekara goma ba amma zaka ɗauka shekarunsa sun wuce haka, musamman idan akayi la'akari da tarin nutsuwar da yake da ita.

Bayan fitarsa Ismaha Zainab ta tashi tana mutsittsika ido "Luyyah" ta faɗa ganin bata kusa da ita, kafin ta fara ƙoƙarin wage baki tayi kuka.


 "Ganifa Isma Abu" ta faɗa tana yaye Gidan sauron daya katangeta da ganinta, sai kuma tayi shuru ta fara murmushi, nan ta fiddo da ita ta naɗe kayan shimfiɗar, ɗaukanta tayi ciɗak ta fiddo da ita waje anan ta ɗorata akan sabon fo ɗin da Zakar ya haɗo musu cikin siyayyar da ya musu.

  Kallon gidan take har zuwa wanan lokacin babu motsinsu, abin yana bata mamaki ace barci yayiwa mutum katutu, su ina suke da wanan gatan, tun asuba mace ta tashi agida tana kujuba-kujubarta bata komawa sai wani sabon daren, amma gashi har rana nason buɗewa babu motsinsu, itama maman Zakar ta koma ɗakinta haka ya bata tabbacin ta sallami yara ƴan makaranta ta koma barci abinta.

 Ɗaukan Ismaha Zainab tayi ta shige da ita banɗakin ta mata wanka sanan ta shigo da ita ɗaki, saida ta shiryata tsaf sanan ta janyo musu abincin da Zakar ya kawo musu, jalof ɗin Taliya da wake ne wanda tasha taruhu da qananun kifi ga qamshin kori da ya qara mata armashi, aifa nan Ismaha Zainab ta fara murna da washe baki, sai da suka ci suka rage saboda yawan abincin data zubo musu, ta qara haƙiƙancewa da jinjinama karamci irin na mutanen garin, duk da bata taɓa saninsuba asalima bata taɓa kawowa aranta zatayi rayuwa acikin garinba, sai gashi akaro na farko Allah ya haɗata da mutanen arziƙi, tun sauƙarta agarin ta fara cin karo da karramawa da karamci atare da su. 

Bayan sun kammala ci ne suka sha ruwa nan suka sake kwantawa ganin babu wani abun daya rage musu kuma, dan mutanen gidan suma ƴan hutu ne basu farkaba, amma sama-sama ta fara jiyo hayaniyarsu aɗakunansu, bata kuma tsaya waiwayarsuba ta kwanta dan su sake matsewa.


******* Bayan Wata Ɗaya"


Rayuwa ta miqewa su Ruqayya acikin garin Haɗejia wanda ta samu sauyi da yawa, zamansu da mutanen gidan da suke haya sai sam barka, ko kaɗan faɗa baya haɗasu domin bata shiga sabgar da ba'a kasawa da ita, abu ɗaya ne yake bata matsala shine rashin lafiyar Ismaha Zainab da yawan tsokanarta, wani lokacin kwana take batayi barciba ta ringa surutun da bata ganewa, duk lokacin da tayi yunƙurin sanar da wani kuma sai taji ta gagara tunawa, haka aɓangaran yaran gidan bata ragar musu ko ya aka mata magana saita yima mutane rashin kunya, wanan ya kawo mata tsaikon daƙushe ko wani farin jinin da take da shi, dan tuni aka bar yi mata wasa, sai Zakat da yake ƙulafuncinta, ya kuma matsawa Ruqayya saida ta sata amakarantar da yake zuwa, duk da yana matakin gama makarantar.


Acikin lokacin kuma zumuncinsu ya miƙe da Malam Isubu da matarsa dan ta ɗaukeshi tamkar Yayanta, bata da gidan zuwa da tattauna matsalarta sai anan shida matarsa, ahankali ya fara nazartar matsalar da take jikin Ismaha Zainab, dan wani lokacin Yarinyar takan yi masa gizo acikin idonsa. Sai dai duk sanda yayi yunƙurin bata magani ko mata Addu'a yakanji kansa ya tsaya cak, komi na bakinsa ya fara damalmalewa, idan kuma akace dare yayi to aranar babushi babu barci haka zaiji ana juyawa da shi, idanuwansa kuma yaji kamar wasu kwari suna biki acikinsa, ba shiri ya fita asabgar yarinyar idan ya ganta kuma sai ya fara jin jikinsa yana rawa, ta ko ina hanyar yakicesu yake nema, amma kuma ya kasa dan har ga Allah yake jin soyayyar Ruqayya kamar qanwarsa, qarshe dai ya bata shawara ta ke yin sana'ar da takeyi agarinsu dan ko a iya lungun nasu zatayi ciniki, ya kuma bata shawara itama ta koma Islamiyya ta manya asati sau biyu, wata qila zatayi dace d samun warwaruwar matsalar dake tare da su..


🥀🥀🥀🥀🥀🥀


 _Tofa har yanzu dai ina baku haƙuri na ɗan tsaikon da ake samu wajen rashin ganin post ɗin, ni kaina bazance ga daliliba amma yanayin rayuwar da uzuri kan yiwa mutum dafifi alokacin da bai shiryaba yakan sa asamu jinkiri_


 *Matsalar Ismaha Zainab mai wahla ce ina jin tausayin Luyya taya zata fara warware ƙulin dake jikinta? Ku daure ku nemo wanan Kimar taku ku magantu dan mutuntakar da take taku ce sai ku magantu dan ra'ayinku*


#Um Nass

#NWA

#Cmnts, Like, nd share

#Da Amana

[2/16, 9:39 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB💍*


©BY *😘UM NASS🏇*


®NAGARTA WRI. ASSOCIATION


BABI NA GOMA (PAGE 10)


 Sosai taji daɗin shawarar da malam Isubun ya bata, dan dama tana son fara yin sana'a gudun kada ƴan kuɗin da take da shi ya ƙare akan hidimar yau da gobe, sai dai batun zuwa Islamiyya ne ta jingineshi gefe ɗaya har saita ƙar-ƙare Iddarta kamar yanda Addinin musulunci ya shara'anta.

 Kasuwa taje da kanta ta siyo injin murza taliya ta kuma siyo kayan amfanin da zatayi aiki da su, acikin kwana biyu dayin maganarta da Malam Isubu ta fara yin sana'ar taliya da ɗan-wake duk da kaɗan tayi aranar farko gudun kada tayi jangwaɓo Amma cikin ikon Allah data fita bakin titi tass ta ƙare, haka matan gidan da suke zaune da yawansu sun siya saboda sha'awarta da sukayi, da kuma kashe yunwarsu ta farko kafin su ɗora nasu.

Amma ta zakar daban ta bashi nasa dan ƙin karɓan kuɗin da mamansa ta bashi tayi, idan akwai wanda take jin daɗin zama da ita fiye da kowa agidan to babu shakka Maman Zakar ne da ɗanta, sune wanda suke jure ko wani fitsara ta Ismaha Zainab da rashin kunyarta, haka suke nuna soyayyarsu akanta koda abayan idonta ne.


 Ahankali kasuwar ta fara buɗe mata tuni sunanta ya sauya daga Ruqayya ya koma Luyyah mai saida Taliya da ɗan-wake saboda jin sunan abakin yaran gidan da suke haya tare, wanda ya samo asali ne daga bakin Ismaha Zainab da suke jin tana kiranta da shi, suma kansu matan gidan bakin yaran suke bi tun suna tsokanarta da maida abin wasa sai gashi ya zauna abakinsu raɗau.

  

Masu suna Ruqayya dama su biyu ne agidan sai gashi an samu bam-banci da nata, ita kam bata ko damuwa asali tana jin daɗin sunan kasancewar ƴarta ɗaya tilo da take kiranta da shi.


*****

Bayan Watanni Shida:


Awaɗan nan watanni guda shidan da suka faru an samu sauyi mai yawa acikin Rayuwar Luyya ta yanda ta fara zuwa Islamiyya, kanta ya ƙara waye ta fahimci duk abin da yake faruwa da ita abaya tana da nata sakacin, haka ta duƙufa da karanta Addu'o'i daga Hisnul-muslim (garkuwar ko wani musulmi) haka take fakar Ismaha Zainab ta tofa mata acikin ruwan shanta, tun tana amayarwa ko bakinta ya gimtse yaƙi shiga, har ta yakice ko wani tsoron da yake tare da ita, take mata ɗura, ahankali sai aka samu ɗan sauƙi kaɗan rashin kunyarta ta ragu, amma kuma sai ta samu azababben surutu da tambaya mai gundurarwa ga mutane.


*****

Gudu yake faman shararawa ababban titin dake Matsaro, kasancewar safiya ce hakan ya ƙara masa bawa motar wuta, akai-akai yake buga tsaki yana kallon agogon Azurfar dake saƙale atsintsiyar hannunsa, wanda suke farare tass da su da gargasa ajikinsu, Yarinyar daya hango tana tsalle akan titin ba tare data kula da shiba, yasa yin hon da ƙarfi amma kuma abin haushin ko ajikinta asalima ci gaba tayi da tsallenta tana gwalon wani gefe, wani wawan birki yaja ya tsaya wanda saura ƙiriss motar ta buge yarinyar, tsoro ne ya kamata ta durqushe awajan tana jero ihu "Wayyo ya kashe ni, shikenan la mutu la bar ganin Luyya aa Ya Zakal ɗina" abin da take ta nanatawa kenan tayi kwanciya warwas akan titin, ta runtse ido gam, ita ala dole ta mutu.


Takaici ne ya kama na cikin motar hakan ya tilasta masa fitowa acikin motar, tasbihi na fara jerowa axuciyata ganin tsantsar kyan da yake da shi, fari ne tas da shi yana da wadatar magana afuskarsa, wanda ko kaɗan bata buɗewa akai-akai take lumshewa da ƙawatuwar gashin idon da suka taimaka mata wajan futar da kyanta, hancinsa bashi da tsayi sosai amma bazaka kirasu da daƙusassuba asalima sun dace da kewayayyiyar fuskarsa wanda saje ya fara fitowa ajikinta, bakinsa yana da ɗan faɗi kaɗan acikinsa akwai jerarrun fararen haƙora ƙananu dasu sai ushiryar data ƙara musu kyau duk da gajartarsu, bashi da tsayi na sosai amma bazaka ajiyeshi acikin gajerun mutaneba, ta ko ina ya haɗu duk da shekarunsa bazasu haura 18 ba amma tun yanzu kyansa ya fara fitowa, masha Allah itace kalmar dana nanata kenan.


 Tunkararta yayi cikin takunsa mai nutsuwa duk da yana cike da haushinta amma hakan bai hanashi tafiya cikin nutsuwaba, tsugunnawa yayi yana kallon yanda take ihu idanuwata arufe tana kiran ta mutu, sanye take cikin kayan makaranta ja mai gidan dara-dara hakan ya fahimtar da shi makarantar dake kusa take zuwa, yarinyace da bazata haura shekara biyarba, amma ganin ihu da birgimar da take ya bashi dariya ainun, ya ɗauko wayansa ƙirar kamfanin LG mai madannai ya fara mata vedio record, sai da ya gaji kana ya maida wayar aljihunsa, ɗaukanta yayi ciɗak ya maidata bakin titi kana ya ɗauko dunƙulalliyar ɗari biyar ya haɗa ajikin hannunta, da sauri ta buɗe idonta tana kallonsa, ganinsa sanye cikin fararen kaya da kuma hasken fatarsa ya ƙara ruɗar da ita ta fara wani kukan "Wayyo sarkin mutuwa agabana" nan ta ƙara runtse idonta tana sabon kukan.


Murmushi yayi mai ɗan sauti yana kallon jikinsa ahankali ya fara magana da muryarsa mai sanyi, wanda idan baka kasa kunne da kyauba ba zaka ji mi yake faɗaba "Ke Baby ban kaɗekiba, nima mutum ne kamarki." Ido ɗaya ta buɗe jin muryarsa kamar ta yara, nan ta tuntsure da dariya kuma har tana riƙe ciki, kana ta nunashi da hannu, nan shima ya fara dudduba jikinsa, ai nan ta ƙara masa dariya, abin sai ya ƙumar da shi ya juya zai tafi, da gudu tasha gabansa tana haki tana nuna shi, tana ƙara yin dariya, haushine ya ƙara kamashi aransa yace "Wanan yarinyar ba mutum bace" ya ƙara raɓawa ta gefenta ya wuce.

 "Kai ƙato mai mulyar yara" yaji sautin maganarta nan ya tsaya cak, sai alokacin ya fahimci abin da ya sata dariya, juyawa yayi ya nuna kansa "Ni?" Ya tambaya.

Kai ta gyaɗa masa kana ta matso kusa da shi, ta miƙa masa kuɗin da ya saka mata ahannunta "Luyya tace kal ina kalɓan abu ahannun ƙato, zai yanke min kai" bata jira abin da zaice ba ta buɗe hannunsa ta saka masa, kana ta juya da gudunta "Sai anjima mai mulyar yara" da ido yabita yana murmushi sai da yaga ta shige wani lungu sanan ya faɗa motarsa yajata, shi kaɗai yake tafiya yake murmushi, duk yanda yake sauri saida ya ɓata lokaci gashi har mutane sun fara buɗe shaguna akasuwa.


 Ahaka ya ƙara yawaita gudun motarsa har sai da ya shiga unguwar G.R.A Acikin wani tamfatsetsan gida ya tsaya yana ƙara yima motarsa hon, da gudu mai gadi ya wangale masa ƙofar ya shiga, hannu ya ɗaga masa yana masa barka da zuwa mai gida, shima kai ya ɗaga gami da miqo masa hannu ta jikin window motar, wajan adana motoci yakai motar tasa wanda ko kaɗan bata kama sauran motocin da suke gidan kyau da tsaruwaba, ajiyeta yayi kana ya fito ya nufi ɓangaran da zai sadashi da palon gidan, kamar yanda yayi tsammani mutanen gidan basu tashiba sai masu aiki da suke kai-kawo apalon.


 "Barka da safiya Yallaɓai" sautin mai aikinsu ya daki kunnensa, ɗago da limsassun idanuwansa yayi ya kalleta kana ya gƴaɗa mata kai, anan ya fara daddana wayarsa ba tare da yayi maganaba.

  

 Agogon dake hannunsa ya sake dubawa ganin har 8:30am yasashi miƙewa ya nufi kitchen ɗin dake palon, wata er dattijuwa ce take kai kawo anan tana faman juye kayan karin data shirya.

Gyaran murya yayi wanda ya ankarar da ita da zuwansa kitchen ɗin, baki ta washe tana ɗan risinawa "Uban ɗakina har ka fito ashe?"

Kai ya gyaɗa mata kawai yana dube-dube, da sauri ta ɗako kofi ta haɗa masa tea ta miƙa masa "Nasan wanan kake buqata, ko ahaɗa maka da soyayyan dankali?"


Kai ya girgiza "Nagode Baba" abin daya faɗa kenan ya koma palon ya zauna, da ido tabishi tana murmushi "Uban ɗakina kenan. Shi dai abinci bai dameshiba ko kaɗan" sanan taci gaba da aikinta, ta fito ta jere akan daining table ɗin dake gefen palon, har lokacin yana zaune yana kurɓan shayin.


 "A'a Musaddiq ka dawo dama? Shine baka shiga ka sanar daniba kake zaune apalo" Muryar wani dattijo ta ratso kunnensa, ahankali ya ɗago ya kai kallon ga mahaifin nasa, sanan ya risina ya fara gaida shi "Barka da safiya Abba, Mun tashi lafiya?"


Zama yayi akan kujerar yana fuskantar ɗan nasa cike da soyayya "Alhmdlh lafiya lau Musaddiq, ban san ka dawoba ina ta jiranka ashe kai kana nan palo azaune?"


Kai ya gyaɗa "Eh ban jima da dawowaba ai?"


"To ya batun tafiyar taka?"

Kai ya juyar da gani baya son tafiyar ahankali yayi magana "Mako mai zuwa In sha Allah komi xai kammala."

Dafa kafaɗarsa yayi cikin sigar lallashi "Allah ya kaimu, ka kwantar da hankalinka kaji, in sha Allah lafiya zaka je ka dawo ka samemu, fatanmu dai ka samu ci gaba akan komi."

"Amma Abba ni bana son barin ƙasata, bana son yin nisa daku, ananma zan iya yin karatuna ba sai nabar jahata da ƙasataba."


Murmushi yayi kafin yayi magana ya tsinkayi muryar Mahaifiyarsa "Kabar Rarrashinsa Alhaji koda baya so dole ya rabu damu, ana nuna masa gata da soyayya amma shi yana dojewa, muma ai muna son iyayenmu muka rabu da su."


Atare suka juya suka kai kallonsa gareta fuskarta murtuk babu fara'a.


🥀🥀🥀🥀


#Um Nass

#NWA

#CMNT, LIKE AND SHARE.

#DA AMANA

[2/16, 9:39 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY *😘Um Nass 🏇*


®NAGARTA WRI. ASSOCIATIONBABI NA SHA ƊAYA (Page 11)


 Kallonta suka ci gaba da yi har ta qaraso palon kana ta zauka akan kujerar da take fuskantarsu "Musaddiq karatunka yana da muhimmanci agaremu, bama mu kaɗaiba hatta kai zaka fi samun nutsuwa idan akace acan kakeyinsa, ka dai san ƙasar nan tamu da yanayin da take ciki baka buƙatar wani tuni akan abin da ya kamata kayima kanka." 


 Murmushi yayi mai sauti wanda da ganinsa na takaici ne, duk da kasancewarsa ba mai musu da jayayya ga maganar mahaifan nasaba amma awanan gaɓar yanaga kyautuwar tanka musu ita "Amma kuma duk da raunin ƙasar nan Umma tana da karatu, mutane da yawa sun amfana da moruwar karatun da ke cikinta, ba lallai ne sai agarin nanba ko wani gari zan iya zuwa nayi karatuna, ni dai kawai naji araina cewar ina tare da ku, banyi nisa da gida ba."


 Kai ta girgiza kana ta miƙe tsaye "Bizarka ta riga data fito haka kuma an ɗaukeka amatsayinka na ɗalibi, kaga wata magana kuma yanzu ɓata lokaci ne." tana gama faɗar haka ta ƙarasa daining dan karin kumallo.


 Magana yake sonyi amma kuma yasan ko kaɗan bazai iyaba, dafa kafaɗarsa Abbansa yayi, yana aika masa da murmushi mai nuna kulawa agareshi "Ko ina gidane ga musulmi Musaddiq, musamman da ya kasance ƙasar musulmi zaka je, Addu'ata agareka da fatana ako yaushe shine Allah ya sanya albarka akaratun da zakayi, Annabi s.a.w yace "Mu nemi ilimi koda zuwa birnin Sin ne" dan haka Misra batayi nisaba asalima gida ce, duk lokacin da kayi marmarin jinmu akwai waya zaka dawo ka taddamu lafiya, shekara kwana ce. Tashi muje muci Abinci." ya qarasa maganar yana riƙe da hannunsa, wanda yake jin hankalinsa ya kwanta ya kuma samu nutsuwa da tausasa kalamansa da mahaifin nasa ya masa, Abbansa ya iya bi da mutum, cikin soyayya yake yin magana da yaransa, saɓanin Ummansa da ta fiya tsawa da hancini ga yara, uwa uba bata zama dan taji matsalolin yaranta, jiki asanyaye ya miƙe ya bi bayansa suka nufi daining ɗin wanda har Ummansa ta fara cin nata abincin ba tare data kulasuba, sai da ya zo ne ta miƙe ta zubama Abbansa kana ta zuba masa ta tura gabansa "Ka tabbatar ka cinye." ta faɗa tana aika masa da harara, shi abinma dariya ya bashi kamar wani yaro ƙarami, haka ya fara cin abincin, can kumar daya tuna wani abu ya tsaya "Umma Jidda fa? Banji motsintaba"

Murmushi tayi gami da gyaɗa kai tana haɗiye lomar dake bakinta "Yau da wuri ta tafi makaranta tace suna da text ne, kuma yanzu so take tana ɗaukan kyautar mai zuwa da wuri makaranta, last time ɗin daya wuce ƙawarta aka bawa." ta qarasa maganar tana dariya wanda suma suka tayata da dariyar sai Abba da ya ƙara da cewa "Oh Jiddah rigima, shi yasa yau ba'a tasheniba ashe?"

 "Aikuwa nima agurguje aka min sallama wai na fiya rashin sauri" nan suka ƙara saka dariya gaba ɗaya.


 "Kema kenan Umma yau anga rashin hanzarinki?" Musaddiq ya faɗa yana murmushi, wanda shine yafi yawa akan dariyarsa.

 "Zata zo ta sameni ai" ta faɗa tana jinjina kai, wanda hakan ya ƙara bawa Abba dariya.

  

"Lallai yau naji ku keda ƴar fadarki." sai alokacin ta ankare ta rufe bakinta.


"Na manta ashefa ku ƴan jam'iyyar adawa ne na faɗa muku."


 Tashi sukayi suna dariya Abba ya kalli agogo "Nikam zan Wuce Umman Jiddah sai kuma na dawo?"

"To Allah ya kiyaye ya tsare hanya, ya dawo da kai lafiya Abban Musaddiq" ta faɗa tana murmushi wanda yasashi dariya shima.


Idan har akwai abin da yafi komi yima Musaddiq daɗi bai wuce daddaɗan zaman da iyayensa sukeba, cike da soyayya da kulawa, shi yasa ko kaɗan baya son yayi nisa da su, amma kuma ƙaddararsa tasa ya fara karantar Islamic edication gashi kuma abaya yayima kansa katoɓarar shifa jami'atul Azhar zashi ta misra, wanda yasa mahaifinsa nema masa karatu acan.


Ahaka ta rakosu har harabar Adana motocin musaddiq ya shiga mazaunin Direba Abbansa ya shiga baya, nan take mai gadi ya wangale musu ƙofa suka jaa yana musu fatan sauqa lafiya.


Asalin Musaddiq:


Mahaifinsa Alh. Adam mai katako hafaffan garin Haɗejia ne dake jahar jigawa su huɗu iyayensu suka haifa shine ɗa na uku agidansu akwai yayyansa Ibrahim da Abdullahi sai Qanwarsu Autarsu Khareematu, sun taso da tsantsar kulawa daga mahaifinsu malam Habu da iya Hauwa, dai-dai gwargwado sun samu ilimin Addini dana zamani wanda alokacinsu ana kama yara ne akaisu makaranta da qarfi to aciki akayi dace aka tisa ƙeyar Adam da yayyansa guda biyu, aranar iyayensu sunyi kuka dan abin ya zame musu abin nuni ana dariya duba da kowa yana ɓoye yaransa idan ana kamen, sai dai cikin ikon Allah hakan ya zame musu alkhairi domin karatun ya musu amfani, sai gashi Ibrahim ya samu aiki malamin makaranta shi kuma Abdullahi ya zama lauya acikin koti hakan ya ƙara ɗaukaka darajar gidan nasu, tuni iyayensu suka fara alfahari da shima gobnati albarka, alokacin da aka yaye su Adamu sai aka ɗaukeshi aiki amatsayin malamin jinya, duk da alokacin mutane kansu na duhu sunfi ganewa da maganin gargajiya, ba ƙaramin wahla yashaba wajan wayar musu da kai, yakan kuma yi ƙoƙarin kula da iyayensu, ahankali samunsa sai ya ninka na yayyansa saboda shagon daya buɗe na siyar da magani, tafi-tafi sai gashi Allah ya albarkaceshi ya buɗe shagon saida kayan gine-gine sai dai yafi qarfi afagen saida falanki, nan sunansa ya sauya akafi kiransa da Alh. Adamu mai katako saboda sauƙin da yakewa mutane, acewarsa kowa agarin danginsa ne, aɗan tsakan-kanin nan suka biyama iyayensu zuwa ƙasa mai tsarki suka sauƙe farali, bayan dawowarsu akayi bikinsu duka harda Karimatu wanda ta Auri abokin yayanta Hussaini shima lauya ne mai.

Sai ya zama ana yima gidansu inkiya da gidan masu doka.

 Auren zumunci Alh. Habu yayima Adamu da er ƙanwarsa da take hannun matan uba suna gana mata azaba, tun rasuwarta yaso karɓanta amma ubanta ya hana ganin abin yaƙi ƙarewa ya sameshi daya Aurama ɗansa Adamu ita, dan alokacin yayinsa suna da mata da yara uku, uku sanin matsayinsa yanzu aguje ya bada auren aka ɗaura ba tare daya sanar da mataanba, dan tsaf zasu iya hana auren, Maryama nutsattsiyar yarinya mai haƙuri amma takurawar da ta samu yasa ta dawo shuru-shuru da kuma masifa, abu kaɗan sai ya hassalata, sai dai kyakkyawa ce ƙwarai.


Bayan shekara biyu Allah ya albarkacesu da samun ɗa namiji da kanta tace yasa sunan Mahaifinsa Abubakar suke masa alkunya da musaddiq, saida yafi shekara goma sanan aka haifa masa qanwa Anan suka saka mata Hauwa'u taci sunan Mahaifiyar Maryama da ta Adamu dan suna ɗaya garesu.


Daga nan haihuwar ta tsaya musu cak, sai suka ɗauki son duniya suka ɗora akan yaran baya kakaninsu kamar su cinyesu musamman Musaddiq da yake da nutsuwa uwa uba haquri matsalarsa ɗaya miskilanci.


Zumunci tsakanin Ahalinsu kuma sai sam barka, Musaddiq ya qare makarantar gaba da prmmry inda ya karanta ɓangaran arabiya domin shi atsarinsa yafi son Ilimin Addini fiye dana zamani, duk da ana musu turanci amma bai kai Arabic yawaba, tun alokacin yacema Abbansa shifa Misra zaije yayi karatu dan nan ne maƙurar karanta Arabic yana son Addinisa yana kuma son ya iya yaren da yafi ko wani yare daraja, sai gashi yanzu kuma yana jin babu daɗi da tafiya ta zo Wanan kenan.


*****


Kuka take tana birgima tana jifa da duk abin da yake jikinta "Wallahi ban yaldaba Allah, Allah kuwa ni sai kin ciyo min babana, kulum kulum inaga jiddo babanta ke kaita makalanta, da yayanta amma ni cai dai ya xakal ya kaini, Allah ban yaddaba."

Kukan taci gaba da yi, ganin taƙi kulata yasa ta matsa kusa da ita ta fara jan kanta tana goga mata hawayen fuskanta "Luyya ko kulma ce" sai alokacin ta leƙa fuskanta abin daya bata tsoro bai wuce ganin hawaye na zuba akan Fuskar Luyya ba.

Kuka take na tausayin rayuwar da suke ita da Ismaha ɗin acikin shekara biyun da suke fama da gidan haya, duk da sun samu alƙibla mai kyau da rayuwa mai ƴanci, zama cikin wayayyun mutane masu sanin hakkin ɗan Adam, amma ko kaɗan hakan ya kasa mantar da ita gida da abin daya barota dashi, kukan da Ismaha Zainab take ya tada mata da mikin da ta binne acikin zuciyarta acikin shekara biyu, iyayenta da kuma Idriss acikin wata rayuwa suke? Baqin fantin da aka mata take fatan ace ta warwareshi, amma kuma yayi kusa ayazu ta koma, yayi sauri da yawa tabar garin da akaƙi karɓan uzurinta aka kuma wofintar da ita. 


 Gashi abin da takaici tace tana zaman kanta agidan haya mai tarin mutane, tasan tambaya ɗaya ce zata zo bakin mutane shine ta koma Karuwanci ta samu Lasisin yinsa. Wanan tunanin daya zo kanta shi ya ƙara tada mata hankali nan sautin kukanta ya qaru.


Hawaye taji ana goge mata cikin sanyin murya tace "Yi hakuli Luyya nabal kuka, bana con babal nawa, tunda baya xuwa ganina." daga haka ta ɗora kanta akan cinyarta tana sauqe ajiyar xuciya, hannunta ta ɗora akanta tana shafa hawaye na bin kwarmin idonta.


🥀🥀🥀


#Um Nass

#NWA

#CMNT, LIKE, SHARE

#DA AMANA

[2/16, 9:39 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY *😘Um Nass 🏇*


®NAGARTA WRI. ASSOCIATIONBABI NA SHA BIYU (page 12)


 Kallonta taci gaba da yi har taji sauqar numfashinta ahankali, wanda yake bata tabbacin da cewar barci ya ɗauketa, ajiyar zuciya ta sauƙe mai ƙarfi kana ta gyara mata kwanciyarta akan ƙatuwar katifar da take yashe atsakar ɗakin, acikin shekaru biyun da sukayi ta samu alkhairi da yawa wajan sana'arta, hakan yasa ta gyara muhallin da suke ciki ta siya ƙatuwar katifa da kuma ma'adanar ajiye kayansu.

Acikin waɗan nan shekarun da suka wuce ba zata ce bata da manema masu sontaba, asalima ita ke gudunsu, saboda komi zatayi tana duba makoma da rayuwar da ƴarta tilo zata faɗa agidan da xa'a kirata agola, wanda bata shirya jin wanan kalmarba, amma kuma ako ina tayi aure dole akira ɗiyarta da wanan sunan, sai kuma dalili mai girma na daƙusar da sana'arta da zata iya faruwa, wanda itace silar barinta garinsu, aranta tana jin bata shirya zaman kashe wando ba, amma kuma babu dalilin da zai hana aharamta mata neman halaliyarta.


Miƙewa tsaye tayi ta fara kai kawo atsakar ɗakin, ganin hakan bazai mataba ya sata miƙewa ta zari Hijabinta, awanan lokacin tasan zata samu Malam Isubu agida, tana buqatar abokin shawara, fitowa tayi ta yima Maman Zakar sallama akan zata leƙa gidan Malam Isubu amma ga Ismaha Zainab na barci ta kular mata da ita, to tace mata tana binta da kallon tuhuma ganin yanda idanuwanta suka kumbura, sai dai ganin tana sauri yasa bata dakatar da itaba balle ta tambayeta, har ta fice tana mamakin abin da yasata kuka.


Bata da shamaki da shiga gidansa hakan yasata yin sallama ta kutsa kai "Maraba da Luyya innar Ismaa Abu" Faɗar matar Malam Isubu cikin tsokana da barkwanci, kamar yanda ta saba yimata ako yaushe, murmushi tayi ta samu kujerar tsugunno datayi karo da ita atsakar gidan ta zauna.


"Gidan shuru haka, ina yaran suke? Ai da na turo miki Ismaha Zainab ta tayaki hira"

Haɓa tayi saurin riƙewa "A'a na yafe wanan tayin nata, dan idan tazo sai ta gauraya min gida ta kuma saka min ciwon kai da tsinanniyar tambayarta marar amfani."


Dariya Luyya tayi mai sauti har tana riƙe ciki ganin yanda Iya Kaltum take magana cike da tsoro da sarƙewar murya "Kaii Yaya Kaltum har haka kike tsoron ƙawar taki, ai yanzuma sa'a kikayi tana barci da tare zamu taho, amma nasan tana tashi zata taho."


"Ai gara, na gode Allah da tayi barci ai."

"Wajan Yaya Isubu nazo, Allah yasa yana nan?"


"Eh yana nan, kin taki sa'a dan yanzu ya qare cin abinci ya shiga ɗaki ya ɗan rintsa, amma nasan yaji maganarki."


"A'a barshi ya kwanta anjima sai na dawo."


 "Ina kuma zaki bayan kin zo, barci ai baya samu ga talaka awanan ranar"

Murmushi tayi tana jinjina kai "Duk da haka dai ni na katse maka jin daɗin naka. Ina yini Yaya Isubu?" ta ƙarasa faɗa tana murmushi, shima dariyar yake yana kallon fuskarta wanda har yanzu akumbure take ga kuma shatin hawayen da aka goge ya bushe, Zama yayi akan tabarmar da Iya Kaltum take kai kana ya fuskanceta.


"Lafiya lau Ruqayya, mi yake faruwa naga Fuskarki da damuwa."


Kai ta sunkuyar ƙasa ahankali ta fara magana, wanda hakan yasa Iya Kaltum miqewa zata bar musu wajan "Ki zauna yaya kema ba xaki rasa abin da zaki faɗaba" Luyya ta faɗa wanda hakan yasa Iya Kaltum zama tana kallonta.


"Muna sauraronki Ruqayya, Allah yasa matsalar da take tafe dake ba babba bace?" 


"Awajena babba ce yaya Isubu sai dai awani ɓangaran kallon ƙarama za'a mata, yau Ismaha Zainab tazo min da tashin hankali mai girma, ina kuma jin tsoro kada matsalar nan gaba tafi haka muni."

Kallonta sukayi cikin mamaki kana suka fara magana "Wata kalar matsala ce haka Ruqayya?" Nan ta zauna ta faɗa musu rigimar da Ismaha Zainab ta mata akan nemo mata Babanta.

Numfashi taja ta fuzgar da iska mai ƙarfi "Ba ƙin kaita gida nayiba Yaya kun riga da kun san matsalar data baroni da garinmu, ina jin tsoron na maidata har yanxu ƙurar bata lafa ba, araina nafi son duk lokacin da zan koma gida na koma da kimata, na koma da ɗumbin girmamawa daga wajan mutanen garinmu."


Kai ya jinjina cikin gamsuwa da maganarta "Na fahimci matsalarki Ruqayya, amma akwai abu guda da zai sama miki nutsuwa, Kiyi Aure saboda shi zai cika miki duk wata kamala da kimar da ya kamata ki samu, haka zai ɓoye ko wani miki da ke tare da ke ya kuma ɗaga ɗarajarki." 


Numfashi taja mai qarfi sanan tace "Ina jin tsoron yin Aure Yaya Isubu, halin maza duka ɗaya ne, bana son asamu wata matsalar da zata daƙusar dani daga neman halaliyata, haka ina jin tsoron tozarcin da zai biyo baya ana jifan Ismaha Zainab da kalmar Agola, ka sani duk gidan da zanje itace kalmar da zatayi ta ɗawainiya damu, ga Ismaha Zainab ba haƙuriba cewa xatayi sai ta rama azo ana ta rigima ni wanan ne bana so."


Kai ya jinjina kana yayi murmushi "Ai ba duka bane suka zama ɗayaba Ruqayya, kafin kiyi auren dole asharaɗanta sharaɗi tsakanin wanda zaki aura akan sana'arki, sanan maganar agola da kikeyi dole kiyi haƙuri ki toshe kunnenki, lamarin mata wuyar sha'ani gareshi kodan kishin da zasuyi da ke zasu ƙuntatawa ɗiyarki, amma kiyi haƙuri ki danne in sha Allah alkhairi zai maye gurbin sharri, ki kyautata zato aduk inda zaki ga mutane, Ismaha kuma da wayonta zata ƙwatarma kanta ƴanci koda anfi ƙarfinta, ke dai ki nemi zaɓin Allah, amma kumafa har yau Alh. Isah nata min zarya akan maganar aurenki." ya ƙarasa maganar cikin sigar zolaya wanda yasa ta rufe fuskarta cikin jin kunyarsa.


"Maganar malam gaskiya ce ni kaina hankalina yafi miki kwanciya da auren Alh. Isah saboda shi mutumin kirki ne kowa yabonsa yake akan sauƙin kansa, daɗin daɗawa zai riƙe miki ɗiyarki da daraja saboda yana da rufin asirinsa dai-dai gwargwado mutane na yabonsa akan kula da iyalinsa, abin armashi kuma gidansa abakin titi yake, kinga kasuwarki bazata mutu ta abinciba, inaga hakan alkhairi ne agareki in sha Allah, kinga kin huta da biyan kuɗin haya." ta ƙarasa faɗar maganar tana dariya, hakan yasata yin dariya itama.


"Na gode sosai Allah yabar ƙauna atsakaninmu, Yaya Isubu nabar komi ahannunka."

"Aikuwa yanzu zan kirashi na sanar dashi nasan zaiji daɗi sosai."


Bata tashi awajanba ya kira Alh. Isah yana ɗauka ya fara da dariya "Yau dai ina ɗauke da kyakkyawan Albishir, dan na tayaka yaƙi ga Ruqayya, duk lokacin daka shirya sai kazo muyi maganar ɗaurin Aurenta."


 Daga can ɓangaran ya miqe "Bama wanan wasan da kai Malam Isubu, fiye da shekara guda ina neman Auren Ruqayya bata bani fuskaba amma yau kace ta amince."

Dariya yayi mai sauti dan wayan acikin amsa kuwa yasata suma kuma su Iya Kaltum suna jinsa "Gata kuyi magana idan baka yardaba." aifa jin hakan yasa Ruqayya ficewa da sauri, dan kunyar Malam Isubu take ji sosai musamman yau ɗin, dariya yayi yaci gaba da waya yana sanar da shi ta gudu amma idan ya samu lokaci yazo asa ranar biki.


Bai wani ja da tsayiba yace shi ashirye yake dama dan haka bai jinkirtaba ya kawo kuɗin Aure da sadaki dubu ɗari.


Cikin abin da bai wuce mako biyuba aka gama hidimar bikin Luyya da Alh. Isah gidanta abakin titi ne ita da sauran matansa biyu yana da yara guda bakwai mata huɗu Maxa uku uwar gidan ce mai yara biyar maza uku mata biyu sai ta biyun mai yara biyu mace da namiji.

Gidansa qato ne sosai mai yalwar tsakar gida sai doguwar barandar da akayi mai ɗauke da ɗakuna uku daga gefe kuma akwai ɗaki guda biyu nasa ne mai ɗauke da palo da banɗaki aciki ɗayan kuma na yarane, daga zauren parko akwai ɗakin yara da yayi na maza sai kuma shago aƙofar gidan.


Yana da kyakkyawar mu'amala da mutane sai dai yana da soyayyar ƴaƴansa baya taɓa haɗasu da kowa, sai dai basa ji ko kaɗan musamman yaran uwar gidan mugunta garesu hakan yasa ake samun hatsaniya da Amaryarsa dan ita bata jurar zalincinsu duk da basa bar mata, idan kuma ta faɗama mahaifinsu haƙuri yake bata yace lamarin yara ya gaji haka, wanan lamarin na ɓata mata rai amma kuma bata taɓa hasashen barin gidanba dan komi akwaishi awadace tun daga kan cima zuwa sutura yakanyi komi dan fita hakkinsu, wanan shine babbar matsalar gidan.


Ahaka aka kawo Luyya da Ismaha Zainab maman Zakar najin babu daɗi zata rabu da maƙociya ta gari, haka suma sauran mutanen gidan sai dai sauƙinsu ɗaya suna unguwa ɗaya, lungu ne ya banbantasu. Dai-dai gwargwado Malam Isubu yayi bajinta ya tsayama Luyya acikin hidimar aurenta da matarsa dan amatsayin ƙanwa ya ɗauketa, haka Iya Kaltum taje hidimar gidanta ta tsaya kai da fata ita da maman zakar da sauran mutanen gidan cass suka mata jere na kayan ɗaki wanda acikin kuɗin sana'arta ta ware kuɗin ta bama Malam Isubu yayi mata hidimar siyan kayan ɗakin, Masha Allah ga mai rufin asiri komi yayi kyau dan saida aka cika ɗakin da kaya.


Bayan kai amarya da watsewar mutane ɗakin ya rage daga Luyya sai Ismaha Zainab da tayi barci akan gadon ƙasa-ƙasa take jin hayaniyar mutanen gidan wanda take sauƙa da faɗuwar gabanta, dan bata san kalar zaman da zasuyiba awanan qaton gidan.


 🥀🥀🥀🥀


Ɗit-ɗit ku hasko min rayuwar Luyya da Ismaha ɗinta agidan Alh. Isa.... Ku aro juriya da ko wata Kima taku ku magantu akan ra'ayin da yake naku ne. 😄


#Um Nass

#NWA

#Cmnts, like, nd share

#Da Amana

[2/16, 9:39 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY 😘Um Nass🏇


®NAGARTA WRI. ASSOCIATION


BABI NA SHA UKU (page 13)


 Kallon ɗakin taci gaba dayi tana nazarin rayuwar da zasuyi da Alh. Isah bayan ada ta sakankance akan ta haƙura da sake sabuwar rayuwar Aure, duka maza abu guda ta ɗaukesu masu son kansu, marasa adalci da tausayi ga matansu.


Motsin shigowar Alh. Isah ne ya ankarar da ita daga dogon tunanin data shiga, lokacin da sukayi ido biyu saida gabanta ya faɗi da ƙarfin gaske, ba zata iya misalta abun da taji agame dashiba, sai dai ta hango tsantsar walwalar da take ɗawainiya da shi alokacin daya shigo bakinsa awashe, wanan ya bata nutsuwa kaɗan aƙasan zuciyarta amma bata kawo hakan mai ɗorewaba.


"Amarya kinsha ƙamshi." kalmar daya faɗa yana ƙarema ɗakin kallo kenan har ya diresu akanta, kai ta sunkuyar saboda sabuwar kunyarsa da ta sauƙa aƙasan ranta.

 "Ɗiyata tayi barci har haka" ya faɗa yana shafa kan Ismaha Zainab data bararraje tana sauƙe numfashi.

 Miƙewa yayi tsaye yana karkaɗe babbar rigarsa "Ki mata shimfiɗa sai kixo muje ɗakina, bari na zo." yana gama faɗar haka ya fice daga ɗakin.


Da ido tabishi aranta tana tunanin yadda zasu raba shimfiɗa da ɗiyarta, amma kuma idan ta tuna girman haƙƙin miji akan matarsa sai taga wanan ba komi bane, arayuwar da tayi awanan garin ta koyi abubuwa da yawa dangane da Addininta ko anan ta godewa Allah dayasa alkhairi acikin barinta garinsu.


Miƙewa tayi ta gyarama ismaha Zainab shimfiɗarta kana ta tofeta da Addu'ar kariya.


Cikin nutsuwa ta gyara zamanta aɗakin tana kallon yanda Ismaha Zainab take sauƙe numfashi hakan ya bata tabbacin tana jin daɗin barcin da takeyi.


"Yauwa kin gama komi?" Alh. Isah ya faɗa yana shigowa ɗakin.


"eh na gama"


"To taso muje gasu Salamatu can na tarasu."


Miƙewa tayi tabi bayansa ba tare da tayi maganaba har suka shiga ɗakinsa. Azaune tagansu dukkaninsu ɗibga-ɗibga dasu kamar da aka hura musu iskar taya, ido suka zubo mata wanda yasata faɗuwar gaba dan ba kyakkyawan kallo suke mataba, asalima kallo ne da yake nuna tsantsar tsanar da suka mata, zama tayi anesa dasu take fuskantar Alh. Isah.


Gyaran murya yayi cikin muryarsa mai Amo ya fara magana "Abin dayasa na taraku anan ba dogon abu zan faɗa mukuba, wanan da kuke gani itama matace kamar ku, sanan bana son tashin hankali acikin gidana, dan bazaku takura min ku shiga rayuwataba bayan na wadataku da duk wani abu najin daɗi." sanan ya juya ga Ruqayya ya nunata da hannunsa "Kece baƙuwa Ruqayya waɗan nan duk yayyanki ne, bana son wani abu na tashin hankali yabiyo baya, abu mafi muhimmanci bana haɗa soyayyar ƴaƴana data kowa, dan haka ki kula da kyau kada ki shiga abin da bai shafekiba, wanda ba zakiji daɗin sa ba." daga haka ya janyo leda mai zanen zabira ya miƙa musu "Gashi gasasshiyan nama ne akwai ƙaramin ɗauri da babba, ƙaramin shine naku babban kuma na yarana, bana son ku musauya musu." karɓa sukayi suka hura hanci da harare-harare, wanda bai san sunayiba, da ƙyar sukayi ɗaga luta-lutan jikinsu suka tashi.


Da ido Luyya ta bisu cikin mamaki daya daskarar da ita, yau kuma wata ƙaddarar ce ta wuntsulota wanan gidan, da alamu mijinsu bai san komi akan sha'anin aureba, bayan ci da sha da sutura sauran al'amuran ko oho.


Wata ledar ya janyo ya buɗeta namane shima gasasshe da ɗuminsa sai albasa da aka yayyanka, ɗaya ledar kuma lemon kwalba ne guda biyu, hannu ya fara murzawa yana washe baki "To Amarya matso muci kinji."


Kai ta girgiza ba tare datayi maganaba dan ta cika da mamakinsa sosai da sosai, bai jira taci ko karta ciba ya fara yagar naman yana korawa da ruwan lemo hankalinsa kwance, bai ƙara mata tayiba har saida ya cinye fiye da rabin naman kana ya saki gyatsa "gashi nan idan kina iya ci sai kici, nikam barci nakeji."


Daga haka ya ƙarasa shiga ɗakin, kanta ne ya kulle ta fara tunanin, mi yake faruwa ne da ita,, bata da wanan amsar kafin kuma ta lalimo abin da zatayi tunani akai ta tsinkayi kiransa daga cikin ɗakin, wanda ya sata miƙewa tabi bayansa cike da faɗuwar gaba.


******

Washe gari ta riga kowa dake gidan tashi ta shirya tsaff ta yima Ismaha Zainab shirin zuwa makaranta, sai faman tambayarta take "Luyya yau asabon gida muka kwana? dakinki yayi cau? Kullum agado zan kwana? Amma kuma ina yazakal ɗin?" Kai Luyya ta ɗafe tana kallon Ismaha da bata gajiya da magana.


 "Wacce kike so na Amsa miki aciki?"

"Duu" ta faɗa tana dariya, kai ta girgiza cikin murmushi kafin tayi magana aka hankaɗe labilen ɗakin ba tare da anyi sallamaba matashin saurayi ne ya wurga musu harara "Ki fito malama ki ɗora mana abinci muna jin yunwa kada ta hallakamu, kun cikama mutane gida da surutu sassafe ke da wanan jarababbiyar ƴar taki."

Cikin mamakin rashin tarbiyyarsa Luyya take kallonsa yanda yake magana baya ko jinkirtawa balle yasha numfashi, kafin tayi magana ta tsinkayi muryar Ismaha Zainab "Ai dai bani bace jalababba ba ce kai."


Afusace ya shigo ɗakin ya bige mata bakin nan take jini ya fito wani ihu tasa mai ƙarfi wanda yaja Luyya runtse idonta "Na ƙara ji kinyi magana saina karyaki." ya faɗa yana ficewa aɗakin "Anyi din mugu accaluma."

Tana kuka tana maganar bai juyoba sai waje da yayi abinsa, kallon LUyya tayi datake ƙoƙarin fita aɗakin.


"Luyya Ni bana con nan gidan, mu koma gun yazakal"


Bata sauraretaba ta fice ta barta ai nan ta fito tana ihu da birgima wanda saida ya tada mutanen gidan gaba ɗaya, dama yaransu sai sunga dama suke zuwa makaranta dan ba'a tsawatar musu.

"Kai yau mun haɗu da jaraba sassafe ahanamu barci, uban mi za'a mata ne?" taji Muryar Salamatu uwar gida cikin kaushin murya da alama ko sallah batayiba dan fuskarta alamun barci ne ajikinta, kallonta Ismaha Zainab tayi, sai kuma tabar kukan ta fara tuntsirewa da dariya tana nunata, hakan yasa salamatu kallon jikinta tana son ganin abin da takema dariya, amma bataga komiba, sanye take da ɗaurin ƙirji sai gashinta daya miƙe atsaye kamar an mata shuka ahakan wai kalba aka mata.


"Uban mi kikema dariya ajikina?" ta faɗa cikin faɗa tana harararta..

Aifa nan ta ƙara tuntsirewa da dariya dai-dai fitowar matasan gidan da Alh. Isah "Luyya kallo tuleliya da ita babu liga, gashinta kamal na goluba, kiga ya'un balci abakinta ya buɗe." nan ta sake fashewa da dariya, nan kuma mutanen wajan suka fara kallonta suma suka tuntsire da dariya harda Alh. Isah da yake ƙoƙarin fitowa, yi suke suna duƙawa, hakan ya fusata Salamatu ta iyo kan Ismaha Zainab gadan-gadan zata daketa.....


🥀🥀🥀🥀

😂😂😂caiii..


#Um Nass

#NWA

#CMNTS, LIƘE ND SHARE

#DA AMANA

[2/16, 9:39 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©by *😘Um Nass 🏇*


®NAGARTA WRI. ASSOCIATION


Babi na sha Huɗu (page 14)


Ganin da tayi ta nufota da gudu yasa ta ruga ta ɓuya abayan Luyya, can kuma ta saketa tace "Luyya balni zakiyi ta dukani" sai ta ruga bayan Alh. Isah tana "Sabon Babu kalka bali ta duka ni, kaga dai tuleliya ce mutuwa zanyi idan ta dukani" haba nan suka ƙara tuntsurewa da dariya.


"Ai yau babu Uban daya isah ya hanani dukan wanan shegiyar yarinyar agidan nan, idanma abaya kinama mutane iskanci suka ƙyaleki toni yau baki isah ki minba" wawuro ice tayi atsakar gidan ta nufi inda Alh. Isah yake Nanfa Ismaha Zainab ta callara qara, tana ruƙunqlƙume Alh. Isah "Sabon Babu kalka bali ta dakeni, Allah ƙalfi zatayi kaga mulyalta irin ta ƙatun maxa ne."


 Saurin rufe bakin Ismaha Zainab yayi da ɗaya hannunsa, ɗaya hannun nasa kuma yana riqe da cikinsa, saboda dariyar da yake, cikinsa ya ƙulle, wai muryar maza ga Salamatu.

 Duka yaran gidan da mazan dariya suke idan aka ɗauke Salamatu da take jin ta muzanta, bata taɓa jin ɓacin rai irin na wanan ranar ba, afusace ta finciko Ismaha Zainab zata daketa, hakan yasa Luyya runtse idonta dan ko kaɗan bazata hana Salamatu dukantaba.


Aɓangaran Alh. Isah kuma ƙarfinsa ne ya ƙare wajan dariya, yayi maganama ya kasa dan har yanzu bai bar yin dariyarba, sai kallon Salamatu yake yana jin wata dariyar na zuwar masa, yasan dai ƙatuwace amma bai taɓa lura girmanta yakai akirata tuleliliyaba sai yanzu daya ganta agabansa ɗaure da zani kamar doyar da aka lilliɓama tamfal.

  

Gefe ɗaya kuma Rabi ce kishiyar Salamatu itama dan dariya har zama take gashi ko kari basuyiba suka tashi da wanan abun dariyar, suma yaran sai yi suke.

Itacen ta ɗaga zata daketa nan Ismaha Zainab ta cukuikuye zanin nata ta shige jikinta, kafin tayi yunƙurin cireta ajikinta kuma hannunta ya gaji ƙarshe icen ta ajiye ta fara ƙoƙarin ɓam-ɓareta ajikinta cikin rashin sa'a ta cireta ita da zanin jikinta daya yage saboda riƙon ƙarfin da Ismaha Zainab ta masa, saurin durƙushewa Salamatu tayi saboda babu komi ajikinta sai gajeran wando dabai kai gwuiwartaba, ina rami ta afka haka takeji awajan.


 Ba shiri Alh. Isah ya karɓe zanin daga hannun Ismaha Zainab da take ta dariya tana nuna Salamatu, sauran ƙananan yaran suma suna dariya "Lah kunga Maama da wandon maza" hawaye ne ya shiga zuba acikin idon Salamatu wanan tozarci har ina, bata taɓa jin kunya da takaici kamar na yauba, yarinyar cikinta itace ta mata wanan ɗanyan aikin? Kafin tayi wani yunƙuri taji an lulluɓa mata zani ajikinta Alh. Isah ne yana ƙunshe dariyarsa "Yarinya ce, bai kamata ki biye mataba, yanzu gashi agaban yara kinji kunya." tashi tayi ta xari buta ta shige makewayi.


_"Zan koyawa wanan Aljanar yarinyar hankali."_ kalmar data faɗa kenan tana ɗauro alwala, ko sallah batayiba wanan masifar da mi tayi kama.


 Aɓangaran Luyya kuma kai ta girgiza tana aikama da Ismaha Zainab Harara "Allah ya shirya min ke Zainab." sanan ta matsa kusa da Alh. Isah wanda har wanan lokacin bai bar murmusawa ba "Alhaji mi za'a dafa na karin safe? Ga yara sun tashi."


Kallonta yayi cike da murmushi akan fuskarsa, kana ya juya kallonsa ga yaran "Mi kuke son ci yanzu?"


Cikin haɗuwar baki sukace "Doya da ƙwai da biredi da shayi." kallonta yayi cikin murmushi sanan yace.

"To kinji abin da zaki dafa." yana gama faɗar haka ya shige ɗakinsa, wani takaici da haushi ne ya kamata "Ikon Allah ana tambayarka kana tambayar yaranka."

Komawa tayi tayi ɗakinta ta ɗauko tukunya ta haɗa ice kana ta nufi ɗakin Salamatu "Yaya ina kayan abincin suke?"

Harara ta aika mata saboda har ga Allah haushinta takeji musamman yanzu da sukayi rigima da ɗiyarta "Jeki Rabi ta nuna miki." daga haka ta karkace ta kwanta ranta na mata suya, amma kuma Ruqayya ta cika mata ido ba zata iya mata rashin mutuncin data so yi mataba.


Bata ɓata lokaciba ta fara haɗa musu karin da taimakon Khadija ɗiyar Salamatu yariyar akwai nutsuwa atare da ita duk da baxata wuce shekara gomaba, sai ƙanwarta wadda suke sa'anni da Ismaha Zainab mai suna Hafsat, da ganinta bata ji, Babbansu shine mai shekara sha biyaar Usama wanda bashi da kirki asalima shine ya taso Ruqayya dan ta musu aiki ya kuma bige bakin Ismaha Zainab, wanda yake bin bayansa mai shekara sha biyu Musa yana da rashin ji amma kuma baya shiga sabgar da bata shafeshiba Khadija ke bin bayansa mai shakara goma sai mabiyinta Haruna ɗan shekata bakwai, Hafsat itace auta acikin ɗakin Salamatu.

 Rabi kuma yaranta na farko sunansa Walidi ɗan shekara shida sai qanwarsa Bilkisu mai shekara uku, Walidi baya ji sosai jan faɗa gareshi ga mugunta hakan yasa suke yawan faɗa da Musa yake dukansa, shi kuma sai ya huce akan Autarsu Hafsat, abin da yake kawo hargitsi kullum agidan sai anyi faɗa tsakanin iyayensu.


Bayan kammaluwar karin kummalon ta koma ɗakin salamatu "Yaya na gama, kizo ki raba." Cikin mamaki Salamatu ta jiyo tana kallon Ruqayya, dan azamansu da Rabi koda wasa bata taɓa cewa ta raba girkin data dafa tun farkon zuwanta gidan.

Kai ta girgiza ta tashi zaune tana fuskantarta "A'a kije ki raba abinki, ki warema kowa nasa."


 Murmushi Luyya tayi "Yaya ai kece babba ni kuma baƙuwa ce agidan nan ban san ya kuke rabonkuba, gadai shi can na gama dan Allah kizo ki raba zaifi wadata kowa."


Tashi tayi cikin sanyi jiki ta nufi waje tun aɗaki dama take jin qamshin soya doyar tasan zatayi daɗi, haka ta raba ta zubawa kowa dai-dai lokacin da yaran gidan suka fito tsakar gida, Ismaha Zainab kuma tana faman ƙunshe baki gudun kada tayi dariya duk da taga Salamatu tasa kaya ajikinta.


 "Luyya nifa na kusa makala amakalanta, ki kila yazakal yazo mu tafi." kanta ta shafa kafin tayi magana suka tsinkayi muryar zakar, da gudu taje ta taroshi tana murna zasu tafi makaranta.


Risinawa yayi ya gaida Salamatu ta amsa da ɗan fara'arta dan yaranta basu taɓa gaidataba, cikin sauri ta miqawa Luyya kasonsu "Gashi kiyi ki sallameta su tafi, gana Alhaji Kuma sai ki miƙa masa"

Karɓa tayi tana rusunawa to yaya, kallonta takai ga zakal ta miƙa masa "Maza ka kai muku ɗaki kuci, da sauri, kada ka biya surutunta ta makararku."

Murmushi yayi ya karɓa duk da aƙoshe yake amma yasan bazata bari yace ya ƙoshiba.


Yau agidan Alh. Isah ko wani yaro ya cinye karinsa yana santi dan akwai kulawa da tsafta shi kansa shayin ya samu qarin armashin kayan ƙamshi saɓanin abaya da lipton da sugar ake musu, haka doya da ƙwai itama babu ƙarnin da suka saba ji alokutan baya.


*****

Danne-danne yake acikin na'ura mai ƙwaƙwalwa can kuma ya tsaya cak ya ƙurama wani abu ido yana murmushi shi kaɗai, ido ya lumshe yana buɗesu aransa yana aiyana inama ace yana tare da wanan abun.

 "Musaddiq banga kana shirin tafiyaba? Duk da kasan gobe ne tafiyarka." Muryar Ummansa ta tsinkayi kunnuwansa.

Gabansa ne ya faɗi sam ya manta da batun tafiyar, kai ya dafe "Ya Rabbi" kamar an mitsineshi haka ya miƙe ya zari mukullin mota "Ina kuma zakaje ina maka magana?"


Bai juyoba ya ƙara ƙarfin takunsa "Wani abu na manta yana cikin kayan shirin tafiyana ne." daga haka ya fice apalon, fatan dawowa lafiya ta masa tana ƙara dai-daita zamanta akan kujerar da take zaune.


 Tafiya yake yana baza idanuwansa agefen titin dake Matsaro ko wasu yara yaga da unifoam yana ƙura musu ido, har ya kusan shafe titin, amma baiga abin da yake fatan ganiba, tsaki yayi ya buga sitiyarin motarsa, yana shirin juya motarsa, kamar ance ya kalli gefe ya hangosu su biyu suna tafe ita da yayanta sai surutu take tana tafa hannayenta, shi kuma yayan nata yana kallonta yana murmushi.


Tsayar da motarsa yayi agefe ya fito yana jiran ƙarasowarsu, basu kula da shiba har suka kusa wucewa ta gabansa, ganin da gaske zasu wuceshi yasashi buɗa muryarsa "Baby" bata jishiba tana ta faman dariya da tafa hannu, shima tsintar kansa yayi da murmushi yana jin daɗin ganinta haka "Baby" ya faɗa yana ƙarasawa kusa da su, cakk ta tsaya jin muryar da kamar ta santa da sauri ta juya tana kallonsa, hannunta ta riƙe akan haɓarta alamar tana tunani, can kuma ta sake kallonsa "Baki ganeni bane?" ya sake mata magana, sai alokacin ta ɗauki muryarsa ta faɗaɗa dariyarta "Laah Yazakal kaga ƙato mai mulyar yaran danake faɗa maka." ta ƙarasa maganar tana dariya wanda yasa zakar shima biye mata, hakan yasa Musaddiq kallonsu yana murmushi shima, aransa yana girmama shirmen da suke dashi ita da yayan nata.


🥀🥀🥀🥀🥀


_Ko wani abu yana da kyau dai-dai nasa kyan, amma acikinsa akwai wanda yafi ko wane kyau, bazance zai zama cikinsuba amma idan kuka kimanta girman tausasawar da take cikin aiki da abun ƙwarai da kanku zakuyi alƙalanci akan zamowarku fiye da kowa._


#Um Nass

#NWA

#cmnt share nd like

#Da amana

[2/16, 9:39 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY *😘UM NASS🏇*


  

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION_Lokuta da dama ɗan Adam yakan kasance cikin bulayi da rashin madafa akan anya ba shi kaɗai ke kiɗansa da rawarsa ba ba tare da mataya a tare da shi ba? Sai gashi daga baya idan yayi haƙuri da tsaikon da ake samu, yakan samu cincirindon dafafi na dubban masoya, a raina naji tasirin dake cikin Alƙalami ya zarce na dubban takkuba, na kuma haƙiƙance akan jinginar da nawa muradin dan girmama naku fatan. Gare ku masoya masu bibbiyata a duk inda kuke wannan labarin gaba ɗaya sadaukarwa ne gare ku nagode sosai._


BABI NA SHA BIYAR (page 15)


 Hannayensa ya harɗe akan ƙirjinsa ya cigaba da kallon su suna dariya, can yaga abin nasu bana ƙarewa bane yayi gyaran murya. Take suka shiga taitayinsu suna wurga ido, musamman zakar da yaga fuskar mutumin kamar babu alamun rahma a tare da shi, cikin ƙoƙarin son zamewa ya fara matsawa da baya da baya, amma kafin ya kai ga matsaya ya tsinkayi muryarsa.


 "Kada ka tafi ka barta." cakk ya ja ya tsaya yana kallonsa, murmushi akan fuskarsa ya zare wani ƙaramin akwati a cikin Aljihunsa, hannun Zakar ya kama ya ɗora masa wannan abin "Nasan kana a matsayin yayan ta ne a yanzu, kana kuma da wayo a kanta, ka ajiye mata wannan kada ka nunawa kowa, idan har Allah ya aranta mana tsawon rayuwa nan da shekaru goma ka bata shi, na tabbata a duk inda nake zan neme ta adai-dai wannan lokacin."

Karɓa yayi yana jujjuya ɗan akwatin da aka kewaye shi da leda mai ƙyalƙyali, ya masa kyau sosai amma ganin yanda aka tantankeshi yana nuni da cewar koma miye a cikinsa yana da muhimmanci.


 Hannu ya miƙa ma Ismaha Zainab cikin murmushi da saurinta ta miƙa masa tana dariya, suka gaisa "Musaddiƙ sunana ba ƙato mai mulyal yara ba." ya ƙarasa magana yana kwaikwayon muryarta, hakan ya sata dariya ita da Zakar kafin itama ta ɗaga idonta tana jujjuyawa alamar son magana, kai ya gyaɗa mata cikin nuni da ta faɗi abin da yake ranta. 


"Icmaha Dainab, nima ba baby ba", hakan da ta faɗa yasa su dariya sosai, cikin rashin fahimtar kalmar Icmaha ɗin ya kalli Zakar.


"Mi take nufi da Icmaha?".


"Ismaha Zainab zata ce haka ake faɗa mata."


Murmushi yayi sosai har haƙoransa suka bayyana "ISMUHA ZAINAB ko dai? Sunanki Zainab?" ya faɗa cikin sigar tsokana wanda ya sata yin murmushi kafin ta zame hannunta daga nasa.


 "Ya zakal mu tafi kal amin bulalal makala."


Kai ya gyaɗa cikin dariya sannan ya kalli Musaddiƙ "Makaranta zan rakata kada ta makara."


Hannu ya saka a cikin Aljihunsa ya ɗauko rafar 50 ya danƙama zakar, saurin buɗe ido yayi yana girgiza kai gami da matsawa baya alamun kuɗin sun bashi tsoro "Luyya ta hana mu karɓan kuɗi ko kaɗan ne, balle wannan mai yawa gasu sababbi."


Kallon yaron yayi yana tuna ranar daya fara haɗuwa da Ismuha Zainab idan bai manta ba itama haka ta sanar da shi a lokacin da yayi mata kyautar kuɗi "Wacece Luyyah?" Ya samu kansa da yi musu tambaya, da zai yi wuya ace mamansu ce.


 "Ummanmu ce ni da ya Zakal" yaji sautin Muryar Ismaha Zainab na sanar da shi matsayinta. 


"Ok. Kuzo na ɗauke ku a hoto saboda ina tunawa daku." da sauri Ismaha Zainab sarkin son hoto ta matsa kusa dashi ta fara lanƙwasa da kareraya, tun yana ɗaukan ta har dariya taci ƙarfinsa ya kasa dan abin da take ya wuce bashi mamaki sai dariya. Maƙalo wuyansa tayi tana cunno baki "Oya Mai mulyal yala ka mana tare." kallonta yayi yana murmushi kafin yayi wani yunƙuri ta danna ta ɗauke su, ƙara maƙalƙale shi tayi tana dariya a haka ta ɗauke su sannan ta sake shi ta ja hannun zakar da yake ta musu murmushi.


Hannu ta ɗaga masa cikin sigar tsokana "Cunanka wahala kawai mai mulyal yala yafi min cauƙi, sai anjima." tana gama faɗar haka ta ruga da gudu zakal na bin bayanta.


Samun kansa yayi da yin murmushi yana kallon inda suke har suka ɓace ma ganinsa, ƙafa yaja ya shiga cikin motar kana ya bar unguwar zuciyarsa fess da farin ciki.


Lokacin da yaje gida ya tadda Ummansa da Abbansa har sun fara cin abinci, hakan yasa shi ƙarasawa ya rusuna ya gaida Abbansa, cikin kulawa ya kalle shi "Ya shirye-shiryen tafiya?" 


Kai ya rausayar yana ɗiban farfesun kifi a flat "Alhamdulillah Abba" 

Kai ya jinjina kafin yayi magana Ummansa ta aika masa da harara "Da alamun za'a jimu akan wannan tafiyar, dan har yanzu bai ɗora ɗaya kan ɗaya ba dangane da shirin tafiyar."


Murmushi yayi cikin nuna kulawa da soyayya ga ɗan sa "Har yanzu yana da sauran sa'o'i ashirin da huɗu ai Maryama. Tun yanzu na fara jin kewar ɗa na." ya ƙarasa maganar yana shafa kafaɗar Musaddiq."


Baki ta taɓe tana goge bakinta da tushu "Ku dai kuka jiyo." daga haka ta miƙe tana kallon Musaddiƙ " Ka tabbatar ka kammala da wuri kaje ka haɗa kayan ka, kada kayi mantuwar wani abu kazo kana dama-dama."


"In sha Allah ba zan yi mantuwa ba Umma." yana murmushi yana danna wayar sa.

  

Abbansa ya miƙama wayar yana murmushi, karɓa yayi yana kallon hotunan da suka yi, yana dannawa yana dariya, wanda yaga yana kallon Ismaha Zainab ya ƙurama ido sun yi kyau mutuƙa "Wacece wannan ɗana?" 


"Ismuha Zainab, bai wuce wata guda da haɗuwarmu da ita ba." anan ya sanar da Abba abin da ya haɗa su har zuwa yau, dariya sosai yake yi yana jinjina ƙarfin ƙuruciyar da take ɗawainiya da ita.


"Ina sonta Abba, idan na gama karatu zaka aura min ita?".


Cakk Abba ya tsaya daga murmushin da yake ya ƙurama Musaddiƙ ido, wanda shima ya kafe shi da nasa idon masu ruwan zaiba-zaiba "Yaushe zaka jira wannan yarinyar? Da duka shekarunta ba zasu wuce biyar ba, naka shekarun sun ninka nata sau biyu."


"Ni dai kawai ina sonta Abba, zan kuma jira ta zuwa lokacin data girma."


Murmushi Abba yayi dan yasan wannan yarinta ce shima take damunsa, duk da magana ba damun Musaddiƙ tayi ba sai gashi yanzu yana jan magana akan lamarin yarinyar da ba tafi sa'ar Jidda ba.


 "Allah ya kai mu lokacin, Mutuƙar muna raye zan tsaya maka amma da sharaɗin ka bar damuwa akan tafiyar ka haka zaka tsaya kayi karatunka kazo mana da kyakkyawan sakamako. " 


Kai ya gyaɗa cikin jin daɗi "Na amince Abba, na maka alƙawarin zama fiye da kowane ɗalibin da ka samu labarin ƙwazon sa."


"Fatan alkhairi ɗa na" ya faɗa yana murmushi, shima murmushin yayi yana rungume Abban nasa.


"Maza kaje ka haɗa kayanka kada kayi latti kaji angon Ismaha." tashi yayi da sauri ya shige ɗakin sa yana dariya kamar da aka masa albishiri da gidan Aljannah.


Washegari ya riga kowa tashi cikin walwala yake wanka, dan mafarki yayi mai daɗi wai sun yi aure shida Ismaha Zainab.

Tsaff ya shirya yake jiran fitowar su Abban sa, lokacin da suka fito ba ƙaramin mamaki tayi ba na ganin yanda yake walwala kamar ba shine yake cika da batsewa akan tafiyar saba.


Kallon Abba tayi cikin mamaki "Abun mamaki Abban Musaddiƙ, yaron ka ke walwala a wannan ranar."


Kai ya ɗaga yana kallon Musaddiƙ da keta faman washe baki, har sauri yake suyi su tafi, jidda ce ta marairaice tana kallon sa "Ɗan uwa wai tafiya zaka yi kabar ni?".


Kai ya girgiza mata cikin faɗaɗa murmushinsa "Karatu zanje ƙanwata, duk inda nake ina tare dake bazan taɓa barinki ba."


Hakan da taji ya sata yin murmushi ta rungume shi "Idan zaka dawo ka iyo min tsaraba kaji?"


Kai ya gyaɗa mata yana bata tabbacin kawo mata ko wata tsarabar da take so.


"Lokaci na ƙurewa ya kamata mu tafi?" Umma ta faɗa tana dai-daita mayafin ta a jikinta.

Daga haka suka ɗunguma suka fita dan masa rakiya zuwa filin jirgi.


Lokacin da suka je har an fara kiran masu tafiya, rungume su Musaddiƙ yayi yana jin kuka na shirin zuwar masa "Bani da tabbacin kai wa tsawon shekarun nan ina raye, ban sani ba ko zan dawo na taddaku dukkanin ku, ina son yin tsawon rai da rayuwa tare da ke dan na baku kulawa irin wanda ɗa ke bawa iyayen sa, sai dai hakan yayi wuya a gare ni. Ƙaddarar zamana daku bata tare, amma zanci gaba da yi muku Addu'a akan Allah ya kare min ku da karewar sa ya ƙaddara haɗuwar mu daku. Idan na muku laifi ku yafe min." yana gama faɗar haka ya sake su jin sunansa da a ke ta faman kira. Kan Jidda ya shafa cikin murmushinsa mai ƙayatarwa "Kiyi karatu sosai ƙanwata, ki kular min da Abba na sosai." yana gama faɗar haka ya juya da gudunsa bai ƙara yarda ya juyo ba, dan hawaye ne shimfiɗe akan fuskarsa.


A ɓangaren su Umma maryam itama hawaye ne cike akan fuskarta, tana son yaran ta amma tana nuna kawaici da kyara a tare dasu, ba dan bata son su ba sai dan kawaici irin na hausawa. Yanzu da taga ya mata nisa na sosai ta tsinci kanta da zubar hawaye.

Cikin sanyin jiki suka shiga mota kowa zuciyarsa fall ƙunci da kewar Musaddiƙ ga kuma kalamansa masu raunata musu zuciya Addu'ar kariya suke masa da fatan nasara a cikin rayuwar da zai yi a ƙasar da ba tasa ba.


****


🥀🥀🥀🥀🥀🥀


_Washh na manta daɗin dake cikin rubutu, hakan ya sani jim wuyar dake tare da shi, ku magantu kuyi amo da kowata muryar da take taku, wannan kimar dai ita nake biɗa kawai._


#Um Nass

#Cmnt, like nd share 

#Da Amana

[2/16, 9:39 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY *😘Um NassNAGARTA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA SHA SHIDA (Page 16)


  A zaune suke a tsakar gida jifa-jifa suke hira wadda a cikinta maganar Luyya da Salamatu tafi yawa, Rabi kuma na gefe tana gyatsina baki.


 ƙarshe ta tashi ta ɗora sanwar tuwo ta barsu a zaune "Ni kam mi yasa kuke barin su Usama suke zaune haka kara zube ba tare da suna zuwa makaranta ba? Gashi ƙannansu ma sun bi sahun su suma basa zuwa."


Gwaɓe baki Salamatu tayi cikin nuna halin ko in kula ta fara magana "Wato Ruƙayya ko kaɗan Alhaji baya son a yima yarannan faɗa da tsawa, domin a baya idan na matsa musu ƙarshe sai dai rigima ta kai ni ga barin gidan nan, shi yasa yanzu ba ruwa na kowa ya gyara ya sani."


Ido Luyya ta fiddo waje cikin tsantsar mamaki "Amma kuwa wannan ba gata yake musu ba, a nawa zaman da nayi a garin nan na ƙaru da abubuwa masu yawa na ci gaban rayuwa. Zan iya cewa ilimi shine babban gatan da iyaye suke bawa yaransu, musamman saboda halin rayuwa."


"Hmm kar ki tona zuciyata kiji ƙunan da ke cikinta, Allah ya sani ni kam ina son karatu, duk da cewar ni ban samu damar yinsa ba."


"Hirar mi kuke yi ne naji kun shiga yanayin Alhini?" Rabi ta tambaya tana zama kusa da Luyyah.


"Akan maganar karatun yarannan ne, take cewa muna tilastasu zuwa"


Ido ta ƙwalalo waje cikin tsoro da alhini "Bar batun nan kin ji, waya isah ya takurama yaran Alhaji ya tsinkayi tafiyarsa na jiran sa."


Dariya suka saka gaba ɗaya, sai dai a zuciyar Luyya ta qudurta sauya ma mutanen gidan nan rayuwa, tun daga kan mai gidan har zuwa su kansu mata da yaran gida, tabbas akwai rashin wayewa da ƙarantar ilimi a tare da su, dama ana samun haka har a cikin garin da za'a ƙira shi da maraya? Abin ya mutuƙar bata mamaki da tsoro, ta kuma gode wa Allah da nata zaman yasha bam-bam da nasu.


Kallon gefen da yaran gidan suke wasa tayi, taga Ismaha ZAINAB a tsakiya tana faman yi musu manyance, idonta ne ya kai kan Asshe ƴar gidan Rabi wanda Walidi ya kwatsama duka dan ta ɗora ƙafarta a kansa, kafin tayi kuka Ismaha ta toshe mata baki "Kiyi haƙuli zan lama miki."

Juyawa tayi da kallonta ga Walidi ɗan gidan Salamatu, harara ta buga masa "Mun daina wacan da kai tunda kai mugu ne ka balmana wasan mu."

  

Hararar ta yayi cikin jin haushin ta dan dama ya fisu girma a wajan, aƙalla zai yi shekara bakwai "Babu inda zani. Ke awa za kice nabar wasan?".

 Bata masa magana ba ta tashi taja hannun Asshe da sauran yaran Khadija da Bilki yaran Salamatu suka biyo bayanta, sabon wasan ta kafa ba tare da ta sake kallonsa ba. 


Labari take basu suna dariya wanda yawanci akan makarantar da take zuwa ne, tana ƙara ƙawata musu daɗin da ke cikin makarantar "Kunga ko a makalantar har lilo muke hawa, mu hau kan banci, wata Aunty ɗin mu mai gashi bucucu ta linga kalanto Ingilishi, bafa a magana ilin wanda muke yi."


Tagumi suka buga cikin jin daɗi ina ma suke zuwa makarantar da take zuwa "Ya zakal yace ina da kokali, yana ta siya min alawa da kuɗinsa. Haka ma Aunty ɗin mu tace ni akwai kwalwa." ta ƙarasa tana buga kanta da hannu gami da yin dariya.


Suma dariyar suka sa, Khadija mai wayon cikin su ta ce "Ni kam idan Alhaji yazo zance ya kai ni irin makarantar ku."


Suma sauran yaran suka fara kiran "Muma muna so sai muna tafiya abunmu mu huɗu ko?" kai Ismaha Zainab ta ɗaga cikin jin daɗi "Wallahi kuwa."


Walidi ne ya matso ya zauna kusa da Ismaha Zainab yana dariya "Ai dai nace na bar dukan kowa, kina hirar dani kinji."

Baki ta turo gami da shan kunu bata yi magana ba "Allah na daina dukan ta"


"Kai ka rantse fa?"

Kai ya gyaɗa cikin tabbatar mata "Eh na rantse da Allah ya ƙonani idan na kuma dukan ta."


Sai alokacin ta saki fuskarta tana dariya "To ka bata haquli".


Da saurinsa yace "Yi haƙuri kinji Asshe."


"Na haƙura" daga nan suka ci gaba da labarin da take basu na makaranta ƙarshe shima Walidi yace yana so zai sa a kai shi.


Murmushi Luyya tayi dan tun zuwan su gidan aka samu sauƙin faɗan da ake da yaran, duk da har yayansu Usama na jin haushin Ismaha Zainab ko idan sun haɗu ya ranƙwashe ta ko ya dake ta, amma ko kaɗan bakinta baya mutuwa sai ta masa Allah ya Isah, sai dai a ɓangaran sauran Musa ƙaninsa shi baya shiga shirginsu asali ma wani lokacin zaman gidan bai dame shiba, iyaka yaci abinci ya koma wajan abokanan sa, amma yana zuwa makaranta lokaci zuwa lokaci saɓanin Usama, haka Haruna babban yaron Rabi shi ko kaɗan basa ma zama inuwa ɗaya da Ismaha Zainab shi mugunta ita rashin kunya, koya ya mata abu sai ta rama shi yasa bai fiya zama a gidan ba.


*****


Karo na uku kenan tana yunƙurin yi masa magana amma kuma tana ga yana mata gizo da kwarjini akan idonta, duk da ba wai abu ne mai nauyi akan laɓɓanta ba amma kuma yana da kyau ace ta magantu akansa saboda muhimmancin sa a wajan ta.


Gyaran murya yayi sannan ya kashe radio dake kusa da shi, fuskarsa ƙunshe da murmushi "Faɗi abin da kike son faɗa Ruƙayya"


Ɗagowa tayi da sauri tana kallonsa kafin tayi magana ya tari numfashinta "Tun zuwan ki nasan akwai magana mai muhimmancin dake tafe dake, baki da wani shamaki ki faɗa kawai."


Kai ta sunkuyar ƙasa cikin fargabar abin da zata faɗa "Ina neman Alfarma a gare ka ina son naci gaba da sana'ar da nake a gida."

Ƙuri ya mata da idonsa kamar mai nazarin wani abu "kina da damuwa akan zamanki a haka ne? Asani na dai komi na buƙata na rayuwa dai-dai gwargwado kin wadata da shi, mi yasa kike son wahalar da kan ki bayan ga ƴan uwanki nan suna kwance abin su?"


Ɗago da idonta tayi tana kallonsa fuskarta ƙunshe da murmushi "Ko kaɗan bani da damuwa, asali ma na wadata da ko wani abu da mace take buƙatar mallakar sa a gidan mijinta, na kuma kerewa mataye da yawa daga dukkanin falalar jin daɗin da suke mafarkan samu a wajan mazajen su."

Ɗagowa tayi da idonta tana kallonsa wanda yake yalwatata da murmushi da gani najin daɗin kalamanta ne. Numfashi ta ja sannan ta cigaba dan ta samu ƙwarin gwuiwar cigaba da magantuwa.


"Ina son naci gaba da ɗaukaka darajar miji na ta hanyar taya shi ɗaukar nauyin wasu lammura nawa, ina kuma son sauƙaƙa masa tarin hidimar da zata tunkaro ni a lokacin da uzururruka suka sha kansa. Ina so na dogara ga abin hannu ba tare dana tsaya jiran wanda zaka bani ba."


Kai yake jinjinawa a ransa yana yaba kaifin hikima da basirar da Ruƙayya take da ita, yana kuma ganin sakaci irin na mijin da yayi gigin bari ta kuskure masa "Na lamunce miki yin sana'ar da duk kike son yi, na kuma baki duk wata dama da yarda akan ba zaki aikata abu marar kyau ba."


Murmushi tayi cikin ƙara ƙarfafa gwuiwa ta rusunar da kanta "Na gode sosai, Allah ya ƙara yalwata maka arziƙinka ya ɗora ka akan maƙiyan ka, ya baka nasara akan ko wani buri naka."


"Ameen ya Allah".


Ɗan jimm tayi alamun son yin magana "Akwai wata magana ne?."


"Eh akwai magana akan yaran gidan nan."

Fuska ya ɗan sauya dan baya son jin wani abu game da su marar daɗi "Wani abun suka miki? Idan sun miki ba dai-dai ba kiyi haƙuri amma na sanar da ke bana son abin da zai dagula musu lissafi da rayuwarsu."


Murmushi tayi cikin jan hankali "Ko kaɗan basu min komi ba, asali ina yaba alkhairi da kyakkyawar tarbiyar da suka samu, wanda kai tsaye zan kira hakan a matsayin jigo daga kyawawan ɗabi'un da suke naka ne suka gado shi."


Murmushi yayi har haƙoransa suka bayyana, yana jin fankama da ɗagawa a tare da shi, shi kam Ruƙayya ta gama siye ko wani ɓangare na zuciyarsa da kyawawan kalamanta.

"Abu ɗaya nake so ka ƙara akan wanda ka shimfiɗa na rayuwarsu, shine ka ƙarfafa musu gwuiwa wajan cika muradai da fatan da kowani yaro yakan so ace shine a kai a yayin da kwanakin sa suka ɗaga daga ƙarami zuwa babba, ka basu ilimi da tallafawar aljihu da kulawa a kansu, ka danni zuciyarka wajan jin sauti da kukan takurawar da za'a musu a kan karatu. Wannan shine gatan da zaka musu, suyi alfahari da zamowar ka a matsayin mahaifi gare su a lokacin da suka mallaki hankalin kansu, za kuma su ɗaga murya dan duniya ta jisu a kan girman tasirin mahaifin su, zasu tsaya akan dukkanin wata jigila da lammura naka idan girma ya risƙe ka. Amma idan akwai jahilci mai lulluɓe da dattin babu zasu rayu suna takaicin zaman ka a matsayin uba gare su."


Ko wata kalma da take futa a bakinta tana sauƙa tun daga kan kunnuwansa har zuwa zuciyarsa, bai taɓa jin magana mai ɗaci da daɗin wannan ba, cikin sauƙi take isar da saƙon da ya kamata yaje kunnensa tun a shekarun baya, amma kuma bai taɓa jin tasirin maganar ba kamar a wannan lokacin. Murmushi yayi yana kallonta cikin bata ƙarfin gwuiwa akan kalamanta "Na gode."


kalmar da ya faɗa yana tashi ya nufi ɗakin sa, jikinta ne yayi sanyi, har ta fara jin tsoron ko dai bai yarda da shawarar da ta bashi ba, miƙewa tayi kamar kazar da ƙwai ya fashe ma a ciki ta bishi da fatan shiriya.


  

****


Tun safe ta gwauraye gidan da ihu tana kururuwa "Allah yau sai kowa ya tashi, haka kullum kullum wannan Udaman yana duka na." ihu ta cigaba dayi wanda yasa mutanen gidan fitowa, abin mamaki tako ɗale a bayan Usama wanda ya kasa sauƙe ta ko ya ya juya dan ya sauƙe ta sai ta maƙalƙale masa wuya, numfashi ya fara furzawa, dan ba ƙaramin gumi da wahala ta haɗa masa ba.

 "Yau na taɓo Masifa a gidan nan", kalmar da ya faɗa kenan yana bin sauran mutanen gidan da kallo, gashi daga shi sai gajeran wando da shimi, baya so ta masa abin da ta yima Maman sa Salamatu, daga magana.


🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀

 _Ban san ya kuka ji a kan wannan shafin ba, amma ku aro ko wata martaba taku sai ku magantu akan daɗi da rashin sa da kuka ji, hakan zai faru ne dan ra'ayin kan ku, ni kuma zan samu karsashi da ƙarin ƙarfafa ko wata kalma tawa dan magantuwa._


#Um Nass

#Cmnt, like nd share

#Da amana

[2/16, 9:40 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY *😘Um Nassb🏇*


®NAGARTA WRI. ASSOCIATION


 _Allah sarkin daɗi inji ɓarawon takanɗa. Duk ta yanda naso na bayyana jin daɗina da godiya agareku abin ya girmi laɓɓana. Allah kaɗai ke iya gane karatun baibai alokacin daya faɗa duniyar masu kunne. Yanzu ne na qara miqe qafa na kuma girmama kalmar da kowa yake faɗa akan KIMA! Kuɗi zai iya siya maka komi amma banda ita, dan haka komi zaka rasa arayuwa ka rasa amma karka taɓa bari ka rasa kimarka._


*😃Mai Dambu ke ko! Acikin mutane masu dama da suke kewaye dani zance ke ɗaya ce tilo da kika zama daban acikinsu, ta fuskar magantu da kowata kalma da ta zama mallakin bakinki, ina miki fatan alkhairi ina kuma fatan zumuncinmu ya ɗore har gaba da Abadan, ngd sosai*

  


BABI NA SHA BAKWAI (Page 17)


 Cirko-cirko mutanen gidan sukayi kowa ya kasa ƙarasawa wajansu, Salamatu kam ɗaurin ƙirji ne ajikinta hakan yasata ƙin ƙarasawa dan bata manta abin data mataba. Kuma har ga Allah ita yarinyar tsoro take bata yanzu, ta ɓangaran Rabi ma ko kaɗan batayi gigin karɓar Usama daga ɗamarmareshin da Ismaha Zainab tayi ba, acikin zuciyarta daɗi take ji dan dama yafi kowa mugunta agidan da baƙin hali.


 Numfashi yake fuzgarwa, da ƙarfinsa yake ƙoƙarin rabata da jikinsa, amma kuma hakan ya gagara, ga ɗan banzan ihun kukan da takeyi wanda ya cika masa kunnuwa.

Tsawa Luyya ta kwatsa mata wanda bata taɓa yi mata irinta ba, dan yanzu abun na Ismaha Zainab ya zama rigima kuma, amma madadin ta tsorata ko ta sake shi, sai ta ƙara cuno baki tana maka mata harara, wanda tasa gaban Luyya faɗuwa, wannan ba Ismaha Zainab bace, ta faɗa acikin zuciyarta gaban ta naci gaba da faɗuwa.


hakan yasata yin shuru, sai dai ga Ismaha Zainab ƙara tunzura ta tayi ta ci gaba da maƙalƙaleshi "Allah bana co."


Ganin idon mutane gidan akansu yasata aro dauriya da juriya taci gaba da yi mata magana, amma azuciyarta tsoro ne fall ranta "Ki sake shi nace, ko kuma ranki ya ɓaci yanzu nan."


Kamar tana ƙara cewa ta ruƙun-ƙumeshi haka ta masa, shi kansa ya gaji, ya jikkata dan jin nauyinta yake kamar na ƙartai goma ne suka danneshi, hawaye yake akan fuskarsa da ƙyar ya haɗa kalmomin bakinsa ya fara mata magana "Kiyi haƙuri ƙanwata ki ɗaga ni, Allah daga yanzu bazan ƙara dukan kiba." ya faɗa cikin dashasshiyar muryarsa wanda take futa da ƙyar.


Hakan yasa yaran gidan Ihu da ilo, wanda Ismaha Zainab ta ƙara musu da ƙarfafa gwuiwa ta hanyar cewa "Ƙato Udama na kuka, maza sai ka min doki iya baba ko jan cauka" kafin ma ta ƙarasa maganar ya tsugunna akan ƙafafuwansa ya fara mata, bai kuma damu da cewar gidan akwai cukowar mutane acikinsaba, aransa yana takaici yana kuma jin ɗaci yanda yarinya ƙarama ta zame masa jidali. 


Dukansa yaji tanayi tana halba ƙafafuwanta "to to baka waqal idan kana tafiya."


Cikin sauri ya fara "Doki iya baba, doki iya baba."


"BA haka akeba Allah ni na fasa sauƙa." 


"Kiyi haquri ban iya ba, ki koya min kinji?" dariya tasa da ƙarfi Su Hafsat da khadija na tayata. 

Takaici yasa su Salamatu komawa ɗaki duk da suma suna dariya, Usama ɗan ƙwalisa yaron da ko aikensa ba'ayi agida, yau gashi ya ƙare da rarrafe agidan, akuma gaban ƙannensa da ko inuwa ɗaya baya ƙaunar ace sun haɗa.


"Assha! Ya da haka kuma ƴar baba?" maganar Alh. Isah wanda shigowarsa gida ya tsinkayi sabon aikin da ake, dan yau futar wuri yayi kasuwa kasancewarta lahdi, yana da baƙi masu sari.


Sauƙa Ismaha Zainab tayi daga bayan Usama taka kakkaɗe hannunsa "Doki Iya baba ya min." ta ƙarasa tana washe bakinta.


Kallon Usama yayi, wanda ya gagara tashi zaune fuskar nan kamar an aiko masa da saqon mutuwa "Da girmanka kake wasan rarrafe atsakar gida. Ko kayan arziqi babu ajikinka."


Kai ya gyaɗa ba tare daya yi masa magana ba ya kaɗa kai ya shige ɗakinsu. Da dariya yara suka bishi suna tafawa da Ismaha Zainab wanda take jujjuya idanuwanta.


  "Allah ya kyauta" Kalmar da Alh. Isah ya faɗa kenan sanan ya ƙarasa wajan matansa "Idan kowa ya karya ina son ganinku ku da yaranku." yana gama faɗar haka ya shige ɗakinsa.


 Kowa mamaki yake suna kuma cike da al'ajabin tarasu da Alhaji zaiyi.

Cikin sauri kowa ya gama haɗa cin abincinsa suka nufi ɓangaran Alh. Isah, dai-dai lokacin da shima ya gama nasa ɗurin.


Gaidashi sukayi ya kallesu ɗaya bayan ɗaya kana ya fara magana "Abin da yasa na taraku anan ba komi bane face akan matsalar yaranku."


 Nan aka shiga kallon-kallo tsakanin Salamatu da Rabi, wanan shine karo na farko da Alh. Isah ya kira yara da nasu.


"Wata matsala kuma Alhaji?"


Gyaran murya yayi cikin tsukewar fuska "Daga gobe litinin ko wani yaro agidan nan zai fara zuwa makaranta, ta boko data Islamiyya, babu wani uzuri ko hujjar da za'a kawo min akan ƙin zuwan su, na bada dama ga kowani malami ya hukunta ku idan kunyi ba dai-daiba, sanan duk wanda yayi fashin zuwa acikinku ina mai tabbatar muku zan cireshi acikin yarana."


Azabure suka ɗago suna kallonsu "Akan makarantar Alhaji?"

Kai ya gyaɗa musu yana basu tabbacin hakan "Qwarai da gaske, koda Bilkisu ce, kunga itace qarama acikinku." 


Daɗi ne ya cika iyaye matan sanan ya kalli Usama da musa "Ku kuma zaku koma aji huɗu amatakin makarantar gaba da sikandire. Dan haka na riga dana gama muku komi, harda ƙannanku su Khadija su na haɗasu acikin makarantar da Ismaha Zainab take zasuna tafiya tare."

Sanan ya juyar da kallonsa ga Walidi da Haruna "Kuma makaranta ɗaya na sama muku dan haka duk wanda yayi fashi idan ɗan uwansa bai faɗa minba to zan haɗa horon mutum ɗaya na baku." da sauri suka fara girgiza kansu, yayin da sauran yaran suka cika da farin ciki suma zasuna yin lilo da ingilishi irin wanda Ismaha Zainab takeyi.


Juyowa yayi ga su Salamatu ya ɗanyi murmushi "Akwai Islamiyyar matan Aure anan layin d aka buɗe ta malam Idris daga magriba zuwa issha, kuma zan yanko muku takardar fara zuwa, an samu sauyi da ci gaba na rayuwA, ilimi shine babban jigo da gatan da zan baku fiye da tarin sulalla. Sanan kada kuce lokaci ya ƙure muku kunyi girma da yin karatu, a'a har yanzu akwai sauran damarmaki anan gaba mutuqar bawa na raye yana da lokacin da zai san Addininsa, aƙarshe kuma ga wanan" ya ɗauko kuɗi acikin Aljihunsa ya basu dubu biyar biyar "Kuyi jari dasu ku nemi sana'ar da duk kukega zaku tallafi kanku da ma wani naku da ita."


Sanan ya bawa yaran ɗari biyar biyar akan su yi wata hidimarsu da ita.


Godiya sosai suka shiga yi masa. Ranar kamar sallah awajansu, ko da wasa basu taɓa tsammanin samun koda rabin abin da suka samu ayanzuba.


Allah Al-hakim kalmar da suke nanatawa kenan. Zuciyar Luyya kamar ta fashe dan farin ciki, ko acikin mafarkinta bata taɓa tsammanin zata sauya Alh. Isah ba, aɗan qaramin lokaciba, sai gashi cikin ikonsa da hikimarsa ya sauya akalar lammuransa garesu ya sauƙaƙa fahimta da duk wata doguwar wahaltuwa atare da shi.


  ****

Gidan Alh. Isag ya sauya acikin ƙan-ƙanin lokaci haka kuma ilimi ya fara ratsa zukatansu dama sassan jikinsu. Shi kansa yanzu ya fahimci ashe da haukarsa yake yake kiranta da soyayya. Dan yanzu kullum safiya sai sun gaidashi hatta Bilkisu saita gaidashi, kafin yace amasa abu kuma sun masa.

Ɓangaran Luyya itama ta fara sana'ar taliya da ɗan wakenta tuni mutane sun fara zuwa siya suna mata layi, zumuncinsu da malam Isubu ya ɗore sosai dan wani lokacin har sabulu da omo take aikama matarsa dashi kansa.


Duk lokacin data samu sarari takan kai musu ziyara harda gidan data zauna haya, aduk faɗin garin Haɗejia bata da ƙawa ko aminiya kamar maman Zakar, da ita take tattauna ko wata damuwa da jin daɗinta.


Suma su salamatu yanzu an bar zaman banza da jarin da Alh. Isah yabasu take saida mai fari da jaa ita kuma Rabi take saida omo da sabulu sai kayan magi. Idan kuma suka kammala aikinsu sukan samu Luyya ta koya musu karatun da aka musu amakaranta har ta ƙara musu wani.


*****


ZAKIRAI

KANO STATE


Zaune yake aƙaton shagon da yake cike da kayan siyarwa kama daga kan yadika zuwa atamfofi duka abin daya danganci tufafi na gargajiya zaka sameshi acikin shago.


Mutane ne suke ta dafifin shiga wasu suna fita, fuskarsa ƙunshe da yalwataccan murmushi. Matashi ne wanda shekarunsa bazasu wuce goma sha biyar ba amma kuma acikin fuskarbsa akwai kamala da nutsuwa.

Hakan yasa mutanen da suke ciniki da shi suka haƙiƙance da gaskiyarɓsa. Basa kuma buƙatar ragi akan abin daya faɗa musu farashin sa.


An samu sauƙin mutane ya rage shi kaɗai ashagon, wanan ya bashi damar zurfafa tunaninsa, kafin wani lokaci hawaye ya ɓalle akan kyakkyawar fuskarsa.

 "Ya Allah! Lafiya Mukhtar kake kuka awanan lokacin?"


Furgigi yayi yana goge hawayen da yake zuba akan idonsa, ganin ko waye yasashi sauƙe ajiyar zuciya "Ba komi Azil."


"Kamar ya babu komi? Bayan ga hawaye ya cika fuskarka. Kawai dai kace ban cancanci matsayin da zanji damuwar ka bane."


Da sauri ya girgiza kansa gami da ƙaƙalo murmushi "Ko kaɗan Azil, asalima damuwata ƙarama ce, ina tunanin gida ne da inna ta. Ban san awani hali takeba yanzu."


Kai ya girgiza cikin tausaya masa "Lokaci yayi daya kamata ka koma gida Mukhtar, shekara kusan uku tun daka fito baka waiwayi garin ba. Ka samu dama da mallakar abun hannunka dai-dai gwargwado. Mi zaisa kaci gaba da ɓatama kanka lokaci wajan jinkirta zuwa mahaifar ka?"


Ɗagowa yayi yana kallonsa can yayi murmushin da bashi da maraba dana takaici "Koya naso sanar da kai bazaka ganeba. Akwai duhuwa mai ƙarfi wanda tafi ƙarfin ido ya ganta, sarƙaƙiya ce mai yawa acikin hanyar tare da taimakawar ƙayoyi masu huda tafun sawu. Ni bana buƙatar komi acikin wanan yanki, kawai so nake na gansu ina jin sautin kuka da ihunsu alokacin da aka samu caƙuɗaɗɗiyar fahimta tsakaninmu da su."


Cikin mamaki Azil ya fiddo da idonsa "Mi kake son sanar dani?"

Murmushi yayi kafin yayi magana wasu masu siyan kaya suka zo "Rai dai mai tadda Buri."


🥀🥀🥀🥀🥀🥀


_Nikam kowama gwanina ne, ban san wa yafi cancanta da sadaukarwaba. Sai dai idan har kun magantu dan cikar muradinku ku ɗauka wanan mallakinku ne._


#Um Nass

#Cmnts, like nd share

#Da Amana

[2/16, 9:40 PM] Oum Nass: *🏌ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY *😘UM NASS🏇*


®NAGARTA WRI. ASSOCIATION


BABI NA SHA TAKWAS (page 18)


 Tsawon wata guda kenan yana ɗauko ɗan-akwatin da zummar ya buɗe, amma wata zuciyar na tsoratar da shi, tana tuna masa girman amana da alƙawalin daya ɗauka na cewa ita zata buɗe da hannunta.


Iska ya furzar abakinsa yana jin wani abu na yawo agame da ita da shi. _"Mi yasa yake kallonta? Rana ɗaya kawai ya sata farin ciki kawai dan ya ɗauketa ahoto."_ ya qarasa maganar kamar wani ke kusa dashi, sanan ya buga wani ƙaton tsaki.


"Wai kai lafiyarka ne Zakar? Kwana biyu na lura da kai ka fiya ƙunci da yawa." maganar mahaifiyarsa ta ankarar dashi akan abin da yakeyi.

Ashe kowa ya kula da shi "Ba komi Mama. Na matsu ne na gama karatuna na fara aiki, kinga sai ku aura min Ismaha Zainab?"


Ido ta ƙwalalo waje, cike da al'ajabi ta fara magana "Kai Zakar bana son shirmen banza kaji ko, har nawa kuke kai da Ismaha ɗin da zaka shiga wani batun aurenku da ita? Ko da wasa karna ƙara jin wanan maganar abakinka, dan zan sassaɓa maka."

Baki ya turo gami da kwaɓe fuska bai dai ce komiba dan yana shakkar Mamansa, sai dai aransa yasan bazai bari wani ƙato mai muryar yara ya masa ƙwaceba. Zai kuma dage yaci gaba da bawa Ismaha Zainab kulawa har zuwa girmansu sai ya sanar da ita.


******


MISRAH

JAMI'ATUL AZHAR


Ajin ne ya ɗauki shuru kamar babu wanzuwar bil'adama acikinsa, sai muryar malamin da yake ta faman yi musu karatu cikin harshen Larabci wanda daga ji yanda yake fiddashi kasan ya aikatu wajan fafutukar neman ilimi. Haka kuma ya alaƙanta matsayi biyun daya taka na zamansa mai ilimi da kuma haifaffan ƙasar laraba.


Bayan ya kammala ya buƙaci wani ya ƙara yin sharhin abin daya koyar dasu, shuru ne ya ratsa ajin har tsawon muntuna uku, can Musaddiq ya tashi ya fito gaban Ajin fuskarsa ko kaɗan babu fara'a, cikin muryarsa mai sanyi da amo ya fara jawabi fiye da wanda malamin yayi, nan aka shiga yi masa tafi haka malamin ya masa jinjinar yabo, ya ɗora da cewar kowa yake buƙatar bayani kai tsaye ya nufi Musaddiq zai fahimtar dashi, daga haka yasa kai ya fice acikin Ajin.


 Tattaro litattafan sa yayi ya fice yabar ajin. Gindin bishiya ya samu ya zauna shi kaɗai, dan baya son hayaniya, haka baya son duk wani abun da zai hanashi jin daɗin tunanin da zaiyi.


"Ƙato mai mulyal yala" sautin maganarta yake ji acikin kunnensa, ido ya runtse yana murmushi "Mi yasa sai da lokaci ya ƙure min kika shiga cikin rayuwa ta? Nayi fatan ace kullum muna atare ne nida ke."


 "Lafiya kake magana kai ɗaya musaddiq?" da sauri ya buɗe idonsa ganin Ma'aruf abokinsa ya sashi yin ɗan tsaki "Ka fiya takura Ma'aruf. Kazo ka katse min jin daɗina." ya ƙarasa faɗa yana ƙoƙarin ɗaure fuskarsa wanda tun da yaji maganar Ma'aruf yaji ransa yayi mugun ɓaci.


"Allah ya baka haƙuri Abokina. Banga jin daɗin da kakeba ne, dan nafi tsammanin kayi gamo shi yasa ka ware cikin mutane kake magana kai ɗaya. Na kula da ko wani motsi naka kullum sai ka zauna anan kana magana kana dariya. Anya bakayi gamo ba?"


Wata harara Musaddiq ya buga masa cike da jin haushin ma'aruf ɗin "Abin da yafi gamo nayi dai, ɗan sa ido kawai." Yana gama faɗar haka ya fara ƙoƙarin tattara littafansa zai bar wajan.


Da sauri Ma'aruf ya riƙeshi "Yi haƙuri abokina. Darasin malam khalil zaka min tuni dan Allah, sam ban fahimci komi aciki ba."

Hararsa yayi sanan ya zauna "Dama ina zaka sani hankalinka yana ga matan larabawa."


Dariya sosai Ma'aruf yayi bai dai ce komi ba har ya gama yi masa karatun Sanan yayi masa magana "Kai ai na lura kana da garanti auren gida za'a maka. So ni ka barni na bawa idona haƙƙinsa ƙila na dace."


Kallonsa yayi kawai bai masa maganaba ya miƙe jin ana kiran sallahr Zuhur "Kasan Khairat ta mutu akan ƙaunar ka? Ko ɗazu saida ta tare ni da magana akanka kana mata wulaƙanci. Gaskiya ya kamata ka sauya halinka wallahi har tausayi take bani." 


 Murmushin gefen baki yayi bai kuma tanka masaba yaci gaba da tafiya. Tsaki Ma'aruf yayi "Wasu lokutan zama da Miskilin mutum akwai ban haushi wallahi."

Dariya Mussadiq yayi har haqoransa suka bayyana "Wata riba ce acikin magantuwa marar alfanu? Da xaka kulle haƙoranka ka datse harshenka daga furta sautin yasasshen zance, da ka samu alfanu da sauƙin tambaya irin wanda akanma mai rarar baki ita."


Daga haka bai ƙara ce masa komi ba ya shige masallaci, da ido Ma'aruf yabishi cikin murmushi da takaici "Kaji ɗan sarkin azanci"


******

ƘAUYEN KWALAM

RINGIM L.G


Tagumi ta rafka yayin da ta shiga duniyar tunani, ita kanta tasan bata yima Autarta Adalciba, mi yasa ta biyema Hukuncin da Babuji ya yanke?


"Ke kam ya kamata ki sauƙaƙawa zuciyarki wanan tunanin da kikeyi. Yau kimanin shekara biyar kenan amma kin kasa huttar da ranki, idan bakiyi a hankaliba sai kin haɗu da cutukan zamani."


Ɗagowa tayi da raunannun idanuwanta wanda suka cika da hawaye "Kace mana na Hutar da raina bayan ban san halin da ɗiyata take cikiba, Wallahi nayi dana sanin barinta da nayi ta tafi. Nayi babban kuskure dana ɗaukeka amatsayin Mijin dake ɗaukar ko wata jigila da nauyi na matarsa."


"Ballu kin san mi kike faɗa kuwa?"


"Ni kuwa nasan mi na faɗa, ai gashi nan tun yanzu hakkin Ruqayya na bibiyarku. Kai kanka kasan baka da kwanciyar hankali."


Kujera yaja ya zauna yana kallon Ballu "Wallahi kawai dakewa nake ina ƙoƙarin na manta abin daya faru abaya. Allah ya sani zuciyata cike take da alhini da al'ajabin ko wani hannun Ruqayya take? Haka ko wani dare barci yakan ƙauracewa idanuwana saboda furgicin dana kan riski kaina acikinsa."


Baki ta taɓe cikin jin haushi da takaicinsa "Ai dama can maza halinku ɗaya ne, kullum mace itace bata da gaskiya sai ku, yanzu ai gashi ya auro dai-dai da shi." tana gama faɗar haka ta shige ɗaki tabarshi anan zaune.


Ya daɗe yana saƙa da warwara kafin nan ya miƙe ya tashi ya fita waje, dan yau kam babu fuskar da zai zauna agida.


****


"Har ni zaka yiwa Iskanci da tijara, uban mi kake ajiye min agidan da zakace bazan fita na nema ba? Tun farko na sanar da kai cewar ni ba irin tsohuwar matarka bace daka raina kake kuma danne mata haƙƙinta." Tsaye take akan sa tana zazzaga masa masifa son ranta, ban da hawaye babu abin da yake zuba acikin idonsa, wanan masifar har ina?


Ɗago da runannun idonsa yayi yana kallonta cikin ƙarfin hali ya fara magana, dan har ga Allah shi tsorontama yake ji "Yanzu Haule ni kike zagi kike zazzaga min ruwan masifa agida? Ai ko banci albarkacin shekarun dana bakiba na samu daraja amatsayina na mijinki."


Kallon kai gara ta masa kana ta ƙara cokalo da ɗaurin ɗankwalinta gaban goshi, cikin izgilanci da fankama ta fara masa magana "Ina kamar maza atare da kai idirisu, balle aje matsayin baka kalmar miji? Ai ni wallahi nabar ganin ka amatsayin miji tunda na gama fahimtar kai azzalumin miji ne wanda yake haɗa kai da mata dan ya yaɗa zalunci agidansa."


Duk kalmomin bakinsa nemansu yayi ya rasa, da ido yake binta da kallo kafin ya tashi yana share hawayen fuskarsa "Ba komi rayuwa ce. Kiyi idan zaki samu riba" Yana gama faɗar haka ya ɗauki ɗan ƙullin kayansa ya jefa aɗaki bai ƙara gigin shiga lamarinta ba ya fice.

Rakiyar harara ya samu gaami da dogon tsaki "Aikin banza kenan gayyar Arna a Idi, aini kam na ci dubu wallahi."


Bai ce mata komi ba duk da kunnensa yaji abin da take faɗa, to mima ya kaishi tanka mata bayan bata shakka da shayin su doku su warama hammata Iska. A lokutan baya idan yayi yunƙurin dukanta ƙarshe shi ke jin jiki, kasancewarta ringijejiya ƙirar mutanen farko.

Ƙofar gidan ya tura yana faman ƙwaala kira "Innar Kamalu! Innar kamalu!!"

Cikin sauri ta fito zaninta ahannu tana kallonsa, duk su Tani sun fito suma ganin yanda Idirisu ya shigo musu afurgice "Lafiya Idi kake ta ƙwala kira tun daga waje? Yaushe ka dawo na ganka wujuga-wujuga? Allah yasa ba ɓarayi ne suka tareku ahanya ba?" Duka wanan tambayar tana yinsu ne cikin ruɗewa ganin yanda yayi zuru-zuru.


"Ai gara ace ɓarayi ne suka tareni da de ace wanan masifar da nake ciki."


"Wata masifa kuma?" Suka faɗa atare kamar an tunzurasu. Afusace ya juyo gasu Tani ya fara balbalesu da masifa "Koma wata masifa ce ai kune kuka janyoni cikinta. Kun sa na rabu da matata mutumiyar kiki cikin hassada irin taku da ƙyashin da yayi muku katutu azuciya. Yanzu gashi tun kan aje ko ina hakkinta sai bibiyata yake, to wallahi na gaji Inna kisan yanda zakiyi dani, ki raba auren da kuka ƙulla da waccan mai ƙirara samudawan."


Kallonsa tayi cikin sanyin jiki, ita tama fara tunkarar Haule yarinyar da ta shuka mata rashin mutunci. Ƙarshe sai da mutane suka ƙwaceta ahannunta, ranar tayi kuka wanda tunda aka haaifeta bata taɓa irinsa ba, gumi ta fara gogewa afuskarta cikin rawar murya ta fara magana "Indai wani abun Haule ta maka tofa sai dai kayi haƙuri, dan ba ruwana da shiga sabgar gidanka, amma ga Tani nan tunda ita ta ƙulla komi sai kuje ta warwareshi."


Ido tani ta ƙwalalo waje "Ni kaza. Allah ya ɓoyi kurwata naje ta zauneni." tana gama faɗar haka ta koma ɓangaranta tana faman sababi dan wani murɗawa cikinta yayi wanda ba shiri ta zari buta sai makewayi.


Da ido suka bita, cikin dauriya Innar su Kamalu ta fara magaana "Kayi haƙuri Idi, shi haƙuri da mace ibada ne ladanka yana ga Allah."

Kallonta yake cikin mamaki "Dama ashe kin saan da wanan Inna?"

Bata ce komi ba dan tasan inda maganarsa ta dosa ƙarshe ɗaki ta shiga ta barshi anan.

"Allah ka kawo min ɗauki, ka fiddani daga wanan masifar."


******

NUROOL YAQEEM Islamic prmry


Kallon dafifin yaran yake yana kallon ƙaton yaron da yake dafe da kansa yana ta faman rusa kuka, idan ya kalli hannunsa yaga jini sai ya sake fashewa da ihu "Wayyo jini-jini wayyo kaina." shine kalmar da yaron yake faɗa.


Gefe ɗaya kuma wata yarinya ce da batafi rabin mai kukan ba tana ƙifta ido tana kuma ƙunshe dariyarta, musamman da taji yana rusa ihu yana kiran jini-jini.

Rasa abin faɗa malamin yayi can dai yace "Mi ya haɗaku da shi har kika fasa masa kai?"


Baki ta kwaɓe tana ƙunshe dariyarta "Kawaifa dan mula wasa dashi, shine na luga da gudu to to cai ya bini kacan zololo ne ba ganin ƙasa yakeba shinefa ya faɗi da banci ya kadashi." magana take babu tsayawa balle taja numfashi.

"Allah ƙarya take malam wani abu ta buga min akaina ina zaune."


Nan itama ta haƙiƙance akan ba dukansa tayiba wasa suke, idan ba hakaba atambayi ƴan ajinsu. Tasan bayanta zasubi dan kowa a ajin yasan da Zaman Ismaha Zainab suna kuma jin tsoronta dan yanzu zata maka hauka.


🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀


_ Yau dai na ɗora akan wanda na saba, na kuma aikatu dai-dai iyawata, duk da ƙarancin jin daɗin da ke ɗawainiya dani ayau. Da zaku daure kuma ki himmatu wajan tattara ko wata Kima taku koda badan ra'ayinkuba, da na qara aro ko wata dauriya dan baku wanda yafi ko wanne._


#Um Nass

#Cmnts, like nd share

#Da Amana

[2/16, 9:40 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY *😘UM NASS🏇*


NAGARTA WRITERS ASSOCIATIONBABI NA SHA TARA (page 19)


Shuru ne ya karaɗe wajan can malamin ya juya yana kallon Ismaha Zainab da take ta faman ƙif-ƙifta ido "Amma dai kin san nan ba wajan wasa bane? A taƙaice kuna cikin aji ba a kaɗa muku lokacin wasa ba."


Baki ta cunno ba tare da tayi magana ba "Oya maza bashi haƙuri kafin na zane ki yanzun nan."

Shuru tayi bata ƙara tanka masa ba haka kuma bata da niyar bashi haƙurin. A zabure malamin ya tashi kamar zai dake ta "Yi haƙuli Abdul" ta faɗa tana ɗano baki.

Kai kalamin ya jinjina yana ƙara bawa Abdul haƙuri akan abinda ta masa, gami da cewa karya ƙara yin wasa a cikin aji.

"To", ya faɗa kana ya ɗauke shi aka saka masa magani da bandeji a wajan, a zuciyarsa yana cike da takaicin Ismaha Zainab gashi babu ko mutum guda da yabi bayansa asali ma kowa tsoron ta yake.


Aji suka koma aka ci gaba da yi musu darasi har zuwa lokacin tashi yayi aka tashi bata tankawa kowa ba. Sai a hanya ne suna tafe ta tare Abdul yana ƙif-ƙifa ido, sosai yaji tsoron ta ya kama shi duk da cewa ya girme mata amma kuma ta ƙware wajan mugunta. Cikin rawar murya ya fara magana "Ni ki barni na tafi gida, ai na bar yin wasan da ke."


Harara ta zabga masa ba tare da ta matsa daga kan hanyar ba "wa yace ka kai ƙalana wajan malam Kabil.?"

 "Ni magani naje a bani ba ƙaranki na kai ba."


Kan nasa ta kalla da yake manne da bandeji can kamar zata masa wani abu, sai kuma ya bata tausayi ganin yanda idanuwansa yayi rau-rau "To ka biyani haƙulin da na baka ɗazu."


Ai bai jira ta ƙarasa ba yayi saurin cewa "Allah ya baki haƙuri ƙawata Ismaha Zainab, Allah ya huci zuciyarki."

Kai ta gyaɗa cikin jin daɗin haƙurin da ya bata, sannan ta kalli su Asshe da suke jira tazo su tafi gida "Muje mu, kai kuma kalka ƙala min magana daga yau."

Kai ya gyaɗa yana fatan ta tafi dan zuciyarsa cike take da tsoro da fargaba. Yayi sa'a bata tsaya ƙara bin ta kansa ba.


Koda suka fara tafiya a hanya ta bugama su Khadija kashedi a kan karsu sake su faɗa a gida, dan idan Luyya ta mata faɗa zata huce a kansu. 

Da sauri suka ce ba zasu faɗa ba. Ranta fal farin ciki ta tafi gida.


 ******

An dai samu sauyi da cigaba mai yawa a cikin rayuwar su Luyya da Ismaha Zainab, haka gidan Alh. Isah ilimi ya samu diga-digan zaman sa, ta yanda suke gudanar da kishinsu cikin sanyin hali, da wuya kaji suna sa-in-sa mai ƙarfi a tsakaninsu.

Shi kansa Alh. Isah ba ƙaramin jin daɗin zaman gidan yake a yanzu ba, wasu lokutan yakan Zauna yana bawa Abokanansa labarin yanda gidansa yake.


Sai dai fa har yanzu a ɓangaran Ismaha Zainab abubuwan ta na ruɗar da Luyya, dan duk lokacin da ta mata faɗa ko ta dake ta to a ranar bata samun cikakken barci, asali ma sai dai taji kanta na sarawa ko tana magana marar kai ita ɗaya, ko tayi ma mutum magana baya jinta.

Haka kowa a gidan yana shakkar shiga lamarinta ganin yanda take wajigasu idan sun so bata wahala.

Amma abun mamaki a makaranta bata taɓa ƙetare ta ɗaya ba, haka a Islamiyya tana da ƙoƙari mutuƙa, duk da ƙanƙantar shekarunta hakan baya hanata yin Hadda.

A haka ta kammala primary cikin nasara mai yawa da kyaututtuka daga malaman ta. Da yawa a cikin ɗalibai ƙanƙana suna murna sun rabu da jangwam uwar masifa. Haka suma malaman tasu murnar da alhini take tafiya, dan tana da ƙoƙari ƙwarai da gaske, takan ciyo musu kyaututtuka a sauran makarantu idan an haɗa gasa.

Haka a wajan rigima kullum sai ƴan ajinsu sun kawo musu ƙaranta.


*****

"Tabb wallahi bana son cigaba da wannan makarantar, haka kawai zan yi ta zama a waje ɗaya. Allah ni dai makarantar kwana zanyi, ai ance min can akwai daɗi ga abinci mai ɗanɗanon kaza, a banɗaki kuma harda famfon yima mutum tsarki."


 Tunda ta fara maganar bakinta ko kaɗan bai huta ba, sai dai ta samu tayi daga Khadija wanda take ƙaryata maganar tata "Ƙarya ce fa irin tasu Sa'adatu, har wata makaranta ce za'a samu famfon da zai yiwa mutum tsarki, banda rainin hankali."


Saurin buge mata baki Ismaha Zainab tayi, cikin jin haushin zata ɓata mata tsarinta ta fara kai kallonta ga Luyya wanda bata ma san tana yiba, dan cikin dake jikinta ya mata nauyi sosai, a shekara biyar a gidan Auren ta sai yanzu Allah ya ƙaddara samun ciki a gareta, bayan wahalar laulayin da tasha.

 "Luyya ni dai a kai ni makarantar kwana, ko kaɗan bana son makarantar jeka ka dawo."


Kai ta gyaɗa mata kawai dan bata shirya yin musu da Ismaha Zainab ba sanin ko taƙi ba haƙura zata yiba "Idan Alhaji yazo sai ki sanar dashi, amincewar sa akai shine nawa."


 "Ni dai bana son makarantar kwana wallahi, sai dai taje ita ɗaya." cewar Khadija gami da aikama da Ismaha Zainab da harara.


"Nima bana buƙatar naje da kowa, sai kuyi ta zama a gida ai."


Lokacin da Alh. Isah yaji batun makarantar da Ismaha Zainab take so, yaso ya hana ta amma ganin dagiyarta da kwarzana ihun data fara yasa shi cewar zai kai ta, ƙarin daɗawa shi asallarsa ko banza ya huta da bawa mutane haƙuri akan rafke yaran mutane da take yi.

Usama kuwa da ya samu labari har da rawa ya taka, asali ma shi ya karɓi kuɗin siyayya ya siyo mata kaya ragajab. Da taimakon wani malamin makarantar kwana Kamilu Ibrahim, Alh. Isah ya samawa Ismaha Zainab makarantar kwana ta ƴan mata dake Kaugama.


Ranar sai da Ismaha Zainab ta hana ɗaukacin ƴan gidan barci da murna da ihu, dan kullum tana gidan su Sa'adatu tana bata labarin yanda makarantar take, ƙara ƙawata mata daɗi da kyanta take yi. Hakan ya sata yin fankama akan ta kusa ta huta da cin Taliyar Luyya da ɗan-wake wanda ba ko yaushe ake sabunta musu abincin ba, tun wanzuwar fara ta.


****

"Ismaha Zainab ɗokinki yana yawa a kan wannan makarantar, amma ni Allah ya sani hankalina bai kwanta da tafiyar kiba. Ban sani ba ko wani alkhairin ne yake jiranki a can." numfashi taja ta fuzgar da iska mai ƙarfi a bakinta, cikin sanyin muryarta taci gaba da yi mata magana "Ina so kimin alƙawalin ba zaki yi shiririta a makaranta ba, ki kauda ko wani sabon abin da kika tadda a can mutuƙar bai shafi karatun kiba, ki gujewa afkawa ruɗin momyn makaranta zuwa ƙawa da ɗiya bayan ni da kika bari a gida."

Kai ta gyaɗa "Allah bazan yiba Luyya na miki alƙawari."

 Murmushi tayi, dan tasan tunda ta rantse to babu dalilin da zai sata aikata hakan "Ba ko wani abu bane yake da kyau idan an kalle shi, wani abun sai an zauna dashi a ke gane aibunsa, ki lura da kyau Ismaha Zainab idan a cikin tafiya babu guzuru mai kyau gundurarwa gare ta, ki kulle idanuwanki ki toshe kunnuwanki daga jin sauti da duhun da baya bada amo mai kyau. Ina daga nan zan cigaba da miki Addu'ar kariya ke ma kada kiyi wasa da Addu'a kinji?"

Kai ta gyaɗa ta rungume Luyya sai a lokacin nadamar barin ta gida yayi, kamar tace ta fasa amma kuma taya zata ƙi bayan akwai tarin abubuwan da suke jiranta na jin daɗi a can.

"Zan yi kewar ki Luyya. Amma nasan zan dawo na ganki da sabuwar ƙanwata."


Tana gama faɗar haka ta sake ta tana dariya ta ɗaga mata hannu, har ƙofar gida suka rakota kasancewar Alh. Isah ne da Usama zasu kai ta a motarsa.

Hannu suke ɗaga mata suna mata bye-bye.


🥀🥀🥀🥀🥀


*Rabuwa babu daɗi komi rashin daɗin zaman da a keyi.*


 _hhhh ga fa Ismaha Zainab a hanyar tafiya bodyn skull, ku hasko min rayuwar da zata fara ga sabbin mutane. Amma ai zata iske naman kaza da kuma famfo mai tsarki. Lol_

*GIRMAMAWA*


#Um Nass

#Cmnts. Like and share

#Da Amana

[2/16, 9:40 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY *😘Um Nass 🏇*


NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA ASHIRIN (PAGE 20)


 Tafiyar awa guda ce ta kai su makarantar ƴan mata dake Kaugama, Tun a bakin get jikin Ismaha Zainab yayi sanyi, ganin makarantar kewaye da wayoyi "Anya za'a samu abin arziƙi a nan?" tambayar da ta yima kanta kenan, sai dai kafin ta lalimo amsar da ya kamata ta ƙarfafa zuciyarta an wangale musu get suna shiga, tsitt kake ji babu motsin ɗalibai kasancewar safiyar Litinin ce kowa na aji yana ɗaukan darasi.

"Fito Ɗiyata" Alh. Isah ya faɗa yana ƙoƙarin fitowa, fitowar itama tayi cikin unifoarm ɗinta farin hijab farar riga sai zani mai gida-gida launin kore da fari da ɗan kwalinsa.

Kallon ko ina take a makarantar babu wani na sabunta da zai tabbatar mata da ƙawar da aka bata a cikin labarin.


Wani office suka nufa itama tana bin bayansu, sai a lokacin ta fahimce ashe mai ɗaukan sunan ɗalibai ne. Bayan ƴar taƙaitacciyar gaisuwa suka danƙa musu amanar Ismaha Zainab, lokacin yace su jira a kira musu wanda suka sani dan ta kai ta Ajinsu.

Da murna Sa'adatu tazo tana washe baki ta gaida Alh. Isah da Usama da fara'arsu suka amsa sai a lokacin ta kai dubanta ga Ismaha Zainab cikin nuna jin daɗin ganinta ta rungume ta tana mata Maraba da zuwa, ƙamewa tayi tana binta da kallo sai baza ido take tana ƙiftasu.

Anan dai suka juya suka tafi suka barta kamar tace ta fasa amma ɗoki da murna ya hana tabi ta kansu, Usama kuma sai washe haƙori yake ya ɗauko kuɗi ya ƙara mata a kan wanda Alh. Isah ya bata sannan suka juya suka bar ta.

Hannunta Sa'adatu ta riƙe ta kai ta Ajin da a kace ta kai ta J.s.s 1A, lokacin malami yana cikin ajin. Gabatar da ita tayi a matsayin ta na sabuwar ɗaliba sannan ta juya ta barta da zummar idan an tashi zata zo su ɗauko kayanta su nufi Hostel (Ɗakin ɗalibai).

Malamin ne ya nuna mata bancin gaba wanda yara biyu suke kai, zama tayi suka cike uku, daga nan ya cigaba da koyar dasu darasin Nahau Wadiy.

Bayan an kaɗa ƙararrawa ya fita a lokacin hankalin ƴan bancin ya dawo kanta. Da murna suke mata barka da zuwa, suka fara gabatar mata da sunayensu Maryam Wada sai kuma Hauwa Tanimu, duka ba zasu wuce sa'anninta ba "ISMAHA ZAINAB IDRIS" ta faɗa cikin murmushi. Nan suka fara dariya "Sunanta zainab" itama dariyar tayi suka shiga fira har suna ce mata makonsu ɗaya da zuwa suma basu daɗe ba. A haka wani malamin Adab da Insha'i ya shigo hirar tasu ta katse.

Bayan ya ƙare aka kaɗa musu zuwa karɓan abinci, a lokacin kusan 11:30am mamaki ne ya kamata da taji cewar sai a lokacin za'a karɓi abincin safe.

"To mi kuke ci da safe? Dan yanzu kam ai an kusa zuwa lokacin rana, taɓ wannan ai sai hanjin mutum ya tsittsinke."

Dariya suka mata sosai sannan Maryam Wada tace "Dama ai sai dai kayi kwaɗon ƙanzo ko kwaki idan kuma akayi sa'a ka karɓo tuwon dare sai kayi kwaɗonsa ya mafi daɗi." 

Ido ta ƙwalalo waje cikin tashin hankali ta fara magana "Wani kwaɗon tuwo kuma bayan ance har shinkafar kaza ana rabawa? Allah ya sauwaƙe ma haƙorana tauna kwanannan tuwo"

Dariya sosai suka sa, cikin dariyar Hauwa Tanimu ta fara nuna Ismaha Zainab "Ashe fa shinkafar Kaza, to garama ki ware yarinya, anan sau ɗaya ake raba nama a sati a haka ma tsoka ɗaya kawai za'a baki, yo kika samu tuwo ai kin kere sa'a, dan shi kansa tuwon samunsa sai mai rabo, balle har ya waye miki."


Kai ta girgiza cikin son ƙin ƴarda da hirar tasu "Ko da wasa bazan taɓa yarda da wannan maganar taku ba. Haba sai kace wasu akuyoyin ɗaure."


Shuru sukayi basu ƙara tanka mata ba har suka ƙarasa wajan karɓan Abincin, ido ta ƙwalalo waje ganin dogon layi wanda a lissafinta kusan mutum ɗari uku ne, sai faman ture-ture a ke da kokawa, gefe ɗaya kuma masu mulki ne sai faman gyara layin suke suna dukan mutane.


"Na shiga uku ni Ismaha Zainab wannan uban layin na miye kuma?"


"Na karɓan abinci ne mana" suka amsa mata a tare suna ƙoƙarin bin layin.

'Taɓɗijam! Gaskiya ni bazan iya bin wannan dogon layin ba, haba sai kace da a ke dafa raƙumi kuga inda ake dukan mutane kamar wasu jakkai."

Ta ƙarasa faɗar haka tana ƙetare mutane tana kallonsu, kafin su Hauwa Tanimu su mata magana tuni tayi gaba abinta da ido suka bita suna mata fatan Allah kare jikinta. 


Lokacin da ta fara ƙetare mutane tuni kallo ya koma kanta ana kiran "Za tayi tsallaken layi." wanda kuma suke jan numfashi da qyar saboda takuresun da akayi tuni suka fara ƙoƙarin janyota tayi baya, amma ina tama matsa daga bin layin tana tafiya.


"Kee gidan Uban wa zaki shiga? Ba kyaga ana bin layi?" Wata ƙatuwar mace ta faɗa fuskarta murtuk babu walwala.


Ɗaga kai Ismaha Zainab tayi tana kallonta, ko kaɗan Fuskarta babu daɗin gani saboda muni hanci duk ya cika mata fuska, ga idanuwanta jajir kamar ba mace ba. Share ta tayi ta cigaba da tafiya abinta, sai dai kafin tayi nisa taji an fizgota baya "Dan Hancin takalmin Uwarki ba dake nake magana ba. Oh ke a dole sabuwar zuwa ko?"


Ido ta ƙwalalo waje jin an mata wani bahagon zagi "Tashin hankali wato kaga salo-salo kala-kala ashe cigaba na wajan diskim har da su hancin takalmi ake zaga." Ta ƙarasa faɗa tana nuna matar gami da kwashewa da dariya "Kinji mulyalki kuwa? Wallahi kamal na ɗan dakon kashi"

Bata kai ƙarshen maganar ba gaba ɗaya mutanen wajan suka kwashe da dariya, tun daga kan jiniyas har zuwa sauran prefect ɗin wajan.

"Kan bala'i nice mai muryar mai kwasan kashi?" prefect ɗin ta faɗa tana iyo kan Ismaha Zainab da take ta dariya tana nunata.


"Eh Allah idonki kuma yayi jajir kamar mai shan jini, dama ance akwai masu shan jini a makarantar kwana, ke ma kina cikinsu ai?" ta ƙarasa maganar tana ƙwalo ido gami da gumtse fuska alamun ta shiga yanayin tausayi. 


Wani gungumemen takaici ne ya kama matar a yayin da take jin ta muzanta kwarai, wani abu zata yima wannan yarinyar ta huce takaicinta. Gashi hatta sauran ƙawayenta suma dariya suke mata ga juniors ɗinsu da suke ta faman dariya a na kallonsu.


A fusace ta nufo ta da zummar ɗauke ta da mari sai dai kafin ta kai ga haka Ismaha Zainab ta ruga da gudu, binta ta shiga yi tana ce ma sauran ɗaliban ku kamota ku kamota, amma dake ta shahara a gudu gata ƴar ƙanƙanuwa a kansu sai wahalar dasu take, wasu ma gwara suke zubewa a tare, ƙatuwar kuma mai dakon kashi ta fusata sosai ta ƙara gudu, ciɗak ta taro Ismaha Zainab kasancewarta doguwa ko wani taku ɗayanta biyar ɗin na Ismaha Zainab ne.


Ganin da tayi ta kamo ta hakan ya sata dakatawa ta ɗaga hannunta sama alamun ta kamu, sai da ta bari ta sakankace a kan ta kamata ta shige ta ƙarƙashin ƙafarta ta koma baya, nan ita kuma ta wuntsula ta kifu akan baki da fuskarta "Wayyo Allah nah ta kashe ni" ta faɗa da ƙarfi gami da sauti mai ƙara.

Nan kuma kallo ya koma kanta wasu suna ƙara dariya Musamman Jiniyos wanda dama haushinta ya gama cikasu, ɗan banzan mugunta gare ta ga shegen duka, yau a sauƙaƙe Allah ya rama musu.

Kasa tashi tayi saboda raɗaɗin da azabar da take ji abakinta da goshinta, da kuma hancinta. Cikin abin da bai wuce minti guda ba bakinta ya haura ga ƙasa da yawu da yake zuba, haka goshinta yayi tsini sosai da hancinta.

Kasa ɗaga kai tayi balle ta koma wajan, hukuncin da zata yima yarinyar take nema ta rasa. 

 Gefen Ismaha Zainab kuma ta je bayan wata mai jan Hijab da Alama itama firifet ɗin ce "Dan Allah ki ɓoyeni kar ta dake ni, kinga dai ke kina da kyau kuma bakiyi kama da masu shan jini ba. Allah idan ta kamani nasan shikenan na mutu bazan ƙara ganin Luyya da Ya zakal ba, kuma ni ai ban mata komi ba, kinga ai ban zage taba dai ko?"

Ta ƙarasa maganar tana ƙara maƙalƙaleta. Dariya ta hana wannan yin magana so take ta dai-daita muryarta amma ta kasa, tun bayan fara diramarsu take kallonsu tana dariya, gashi yanzu tazo ta ishe ta da wasu maganar.

Janyo Ismaha Zainab tayi ta ƙura mata ido sai faman ƙiftasu take, "Masha Allah" ta faɗa ganin yanda idanuwan Ismaha Zainab suke farare ƙall gasu da girma da yawaitar gashin ido, duk da ƙanƙantar ta amma a kallon farko zaka fahimci tana da wani abu a tare da ita, wanda zai sa ka sota.

"Ya sunanki?"

"Ismaha Zainab Idris kuma ni yau aka kawoni, ance akwai shinkafar kaza ana badawa anan. Gashi daga zuwa naga ana bin ƙaton layi, ni bana so ya ƙale ban samu ba."


Dariya sosai matar take "Shinkafar kaza a nan kwalejin?" ta faɗa tana nuna Ismaha Zainab da take faman washe baki, dan duk a zaton ta akwai ɗin.

"Eh mana haka Sa'adatu maƙociyar mu ta faɗa min."

Kai ta jinjina gami da riƙe hannunta "Oya zo muje ki bama Anty Jummai haƙuri kada ta buge ki."


Da sauri ta girgiza kai tana riƙe hannunta "A'a ni Allah jinina zata zuƙe, Luyya tace ba ruwana da kowa. Ke ma dan naga kin yi kala mai kyau ne irin ƙato mai mulyar yara ɗina ba zaki bari a dake ni ba."


Dariya take sosai kai yarinyar nan Allah ya yassare mata surutun tsiya "Waye kuma Ƙato mai muryar yara?"


Kai ta gyaɗa tana son bata labarinsa "Muje dai ki karɓa min shinkafar kazar kada ta ƙare, kinga mutane sai ƙaruwa suke."

Kai ta girgiza "Sai kin je kin bata haƙuri ko kuma kibi wannan dogon layin."


Ido ta ƙwalalo waje cikin jimami ga ƙoshi ga kuma kwanan yunwa.....


🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀


_Nasan dai a tsakanin kwana biyu kun gaji da duba hanyar ganin Ismaha Zainab, da yawa kuma sun ƙosa da ganin jinkirin yayi yawa._


*Ku ɗauka amatsayin sarƙafewar lokaci dakan iya samun mutum alokacin da bai shirya hakan ba, zanso nayi ta yawaita alƙalamina har zuwa ƙarshen labarin ba tare dana tsaya ba, amma shi so a duk inda yake baya taɓa zama samu. Ku magantu ku kuma aikatu ta hanyar faɗar ra'ayinku akan ko wani layi da jarumin dake cikinsa, ni kuma zan tayaku ƙarama labarin armashi. GIRMAMAWA*


#Um Nass

#cmnts like nd share

#Da Amana

[2/16, 9:40 PM] Oum Nass: *🏌♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY *😘Um Nass *


®NAGARTA WRI. ASSOCIATION


Babi na Ashirin da ɗaya (Page 21)


 Ganin tana ƙara ɓatawa kanta lokaci yasa ta ɗaga ƙafa, ta nufi wajan siniyo Jummai da kunya ta hanata tashi. Tausayinta ne ya kama Ismaha Zainab, ganin yanda halittun Fuskarta ya ƙara hau-hawa, ƙunshe bakinta tayi tana sunkuyawa dai-dai kanta "Kiyi Haƙuri Anty Jummai"


kafin ta ƙarasa ta kifeta da mari wanda ya sata wuntsulawa tayi baya, sanan ta bita ta ci gaba da dukanta tana boll da ita kamar Allah ne ya aikota, kuka ya gagara fitowa a bakin Ismaha Zainab balle hawaye, asalima duk dukan da take mata dunƙulewa tayi awaje ɗaya ta cusa kanta ajikin cinyoyinta.


Da sauri siniyon data tura Ismaha Zainab ta shiga tsakanin su, ganin yanda Jummai ke dukanta kamar Allah ne ya aikota.


"Haba mana Jummai! Wanan dukan da kike mata ai sai ki kasheta. Bakiga sabuwar zuwa bace. Mima ta sani akan rayuwar makarantar? Idan kin dunƙule shekarun ta duka nawama yarinyar take?"


 Harara Jummai ta aika mata kamar idanuwanta zasu zubo "Ni da za'a barni babu hisabi wallahi kashenta zanyi, ban taɓa jin na tsani mutum ba kamar wanan, kigafa irin abin da ta min?" ta faɗa tana duba jikinta da yayi futu-futu, haka fuskarta duk ta ɗaure da zafi.


Dariya ce ta kama Siniyo Shamsiyya, ganin yanda Fuskar Jummai ta koma "Uhmm koma dai mi ta miki ke kika janyoma kanki. Lokuta da yawa ke kike fara shiga lamarin sabbin zuwa, gashi kin daɗe da sanin cewar yara ne sai da lallami." tana gama faɗar haka ta ɗaga Ismaha Zainab da take dunƙule waje ɗaya, abin mamaki da ruɗarwa furr ta kasa ɗaga ta.


Jijjigata ta farayi amma ko motsawa batayi ba, balle ta iya ɓam-ɓareta daga haɗa kai da gwuiwar da tayi. A tsorace ta kai kallonta ga Jummai "Na shiga Uku! Wanan yarinyar kamar dutsefa taƙi motsawa balle ta jijiga."


"Ƴar rainin hankali ce ai" Jummai tayi saurin tarar ta, sanan cikin fusatuwa ta nufi inda suke tana ƙoƙarin hankaɗa Ismaha Zainab, kamar wutar lantar ki ta jaka da ƙarfi hakan ne ya faru ga Jummai lokacin data kai hannuta jikin Ismaha Zainab, kafin tayi wani yunƙuri tayi baya da ƙarfin gaske aka gwarata ajikin bishiyar Mainar da ke wajan "Wayyo Allah nah!" kalmar data sauƙa akan bakinta saboda azabar data sauƙar mata alokaci ɗaya.


Kallonta Siniyo Shamsiyya tayi cikin kaɗuwa da al'ajabi, kafin tayi magana ta tsinkayi Muryar Ismaha Zainab "Anty mai kyau ki kaini na karɓi shinkafar kazar tunda ta haƙura." Furgigi tayi takai kallon ta ga Ismaha Zainab wanda take murmushi tana tsotsar hannu abinta, babu wani alamu ajikinta da yake nuna an daketa ko kuma shatin rauni. 


Kanta ne ya ƙara ɗaurewa, tayi hanzarin kai kallonta ga Siniyo Jummai wanda take runtse ido, hawaye na zuba cikin jin zugi da azabar da bayan ta yake mata.

  

Bakin magana ta rasa, gashi wani tsoro da shakkar Ismaha Zainab ɗin ya dirar mata alokacin, cikin rashin kuzari ta riƙe hannunta suka tafi wajan karɓan Abincin. Kwano ta miƙa aka bata, duk da akwai layi mai yawa, amma kasancewar ta mai muƙamin Shugabar ɗalibai amakarantar yasa bata ɓata lokaci ba ta karɓa mata. 


Ido Ismaha Zainab ta buɗe waje, lokacin da idonta ya sauƙa akan Faten masar da ke cikin kwanon. Ruwa ne aciki sosai, ita kuma masar ta dawo kamar kwaɓaɓɓan kwaki, sai yakuwa bushasshiya da ganyen Albasa da yake yawo acikinta, hannu ta kai ta lakuta taji hannunta ya nutse ciki.


"Minene wanan ɗin?" ta faɗa cikin furgici da tsoron kaishi cikin bakinta.

Dariya Siniyo Shamsiyya tayi cikin son ƙular da Yarinyar tace "Wanan shine muke kira da Mandula, acikin yarenki kuma Shinkafar kaza" ta ƙarasa maganar tana tuntsurewa da dariya.


"Na shiga uku! Yanzu da gaske wanan cinsa akeyi? Nikam idan naci mutuwa zanyi" ta ƙarasa maganar cikin yanayin tausayi da alhini ashimfiɗe akan Fuskar ta, awani sashi kuma na zuciyar ta yanaga tsagwaran wautar ɗaliban da suke ƙoƙarin kashe kansu da kokawar bin layi.


 "Ba zaki mutuba, tunda muma bamu mutuba. Akwai daɗi sosai idan kika saka abakinki, shi yasa muka saka mata suna Mandula."


Kallon Siniyo Shamsiyya take, tana ƙara kai kallonta ga abin da aka kirashi Mandula, sanan ta girgiza kai "Duk da kince yana da daɗi, amma babu kokonto akan cewar mutum zai iya ɓarkewa da Zawo idan yaci shi."


Dariƴa sosai Siniyo Shamsiyya tayi, wanda zuwa yanzu kuma ta gaji da bata amsar duka tambayar da takeyi, ganin layi ya ragu mutane kaɗan ne suka rage, ga kuma tana son taje ta samu Siniyo Jummai dan taji awani yanayin take "Oya maza jeki samu ƙawayen ki sai ki musu wanan tambayar, ina da abubuwan yi agaba na."


 Kai ta sunkuyar kafin ta juya ta tafi, ba tare data lara ce mata komi ba, itama da ido ta bita har ta ɓacema ganinta sanan ta sauƙe ajiyar zuciya. 


Azuciyar ta taji tana son yarinyar ga shiga rai, amma kuma abin da ya faru tsakaninta da Jummai ya ɗaure mata kai sosai, "Koma dai miye ne atare da ita, na tabbata akwai dai lauje cikin naɗi" ta faɗa tana sauƙe ajiyar zuciya.


*****

"Wallahi tunda nazo duniya, ban taɓa jin tsoro da furguci kwatan-kwacin wanda naji yauba."


"Ni kaina ina cikin ruɗu ganin yanda kikayi baya da ƙarfin gaske, gashi kuma yarinyar ko kaɗan jikinta bai nuna shatin dukan da kika mata ba. Gaskiya kaina ya ɗaure sosai."

  

"Ai duk dukan da na mata ji nake kamar ajikina ne nake duka, ko ina ajikina ciwo yake min sosai wallahi."


"Wai mi ya faru ne? Tun ɗazu kuna magana ku kaɗai mi ya faru ne?"


 "Uhmm miye baima faruba Faty. Wata sabuwar ɗaliba aka kawo yau...... Daga nan ta sanar da ita duk abun daya faru awajan karɓan abinci "Wallahi ni ban taɓa ganin hatsabibiyar yarinya mai kamar iffiritai ba irin wanan yarinyar." Jummai ta ƙarasa maganar tana jinjina ƙarfin wahlar data sha.


Dariya sosai Faty da Shamsiyya sukeyi kasancewar su duk Firifet kuma abokanai ɗaya.

"Ni ba wanan ne yafi bani mamaki ba, illa jifan da akayi da ke, kuma wai babu wanda ya gani duk cikin ɗalibai." faɗar shamsiyya tana jijjina kai.

Cafe maganar Faty tayi "Wani lokacin ai Jummai tana da matsala, ko kaɗan bata san yaro ba, balle kuma sabin zuwa, haka zata ware tana jibgarsu, kamar Allah ne ya aikota, gashi yanzu ai kin janyowa kanki ciwon jiki garin muguntar ki."


Kai ta gyaɗa tana cije baki "Ai wallahi yanzunma ba haƙura nayi ba, zamu sake haɗuwa ne da ita."

"Allah ya kyauta, amma nikam ina son yarinyar kada ki ƙara dukan ta." Shamsiyya ta faɗa tana ƙata faɗaɗa murmushi akan fuskar ta.


Hakan ya ƙara ƙular da Jummai ta buga tsaki ta shige Aji tabarsu.


******

 Tagumi ta rafka tana ƙara kallon Abincin dake gabanta, sai yanzu taga wautar ta akan yarda da maganar da Sa'adatu ta mata. Musamman idan tayi la'akari da tarin ƙanzon da take zuwa karɓa gidan su, wanda yake cin Kazar Shinkafa mi zaiyi da wani ƙanzo "Wayyo Allah."

Ta faɗa tana dafe kanta, dai-dai lokacin da ƙawayen ta suka zo "Wai har yanzu baki gama cin abincin ba? Gashi har an kusa kaɗa komawa aji ." Hauwa Tanimu ta faɗa tana zama akusa da Ismaha Zainab.

"Yanzu tsakani da Allah ace wanan abin shine abincin da zanci?" ta faɗa tana jujjuya kwanon abincin ahannun ta.


"Kinga zaki ɓatama kanki lokaci ne abanza, nan kwaleji ce ba zaki samu fiye da haka ba. Yo ke ai kin samu mai yawa ma, namu baifi rabinsa ba fa." Maryam Wada ta faɗa tana murmushi, dan su yafito musu akayi, saɓanin ita da Siniyo Shamsiyya ta karɓa mata cikin kwano.

"Mtss! Ke yawa ya dama, wallahi ji nake kamar zanyi amai idan na kalleshima. Idan baku ƙoshi ba ku ɗauka ku cinye."


Basu jira ta gama maganaba suka janyo shi, suna ci suna kuma sanar da ita kwana nawa ne zata fara ci itama, adai juri zuwa rafi. Suna gamawa ana kaɗa musu shiga aji, da sauri suka shige gudun kada azo ana dukansu.


Lokacin da aka tashesu ta sanar da su Maryam kayanta na bakin get, hakan ya sasu zuwa dan su taimaka mata, dai-dai zuwan Sa'adatu, basu tsaya ba suka nufi wajan get ɗin dan ita tana aji Biyar ne sauran ta ɗaya. Ta gayyato sauran jiniyas suka ɗaukar mata kayanta sai hostel ɗinsu.


Anan kuma Ismaha Zainab ta fara kallon ɗalibai kowa na nufar ɗakinsu, ita kuma duk sanda ta wuce zataji ana kiran Sa'adatu Musa ƙanwa mukayi? Eh take ce musu kawai har suka dangana da ɗakin nasu.


Wata wawukekiyar santa taga, inda yara marasa galihu suke ajiye akwatinansu da rayuwar su anan, kasancewar basu da yayyan da zasu nemi arziƙin zama akwanar su.


Amma su da ɗan dama, dan tana zuwa siniyo suka fara yan-yameta da murnar sun samu ƙanwa. Dan Sa'adatu akwai mutane duk da cewa akwai dabi tsakanin ƴan Aji biyar da shida amma ita tana shiri daasu.


Wata siniya Marwa ce ta karɓi katifar Ismaha Zainab ta ajiye akwanar ta, sanan ta karɓi akwatinta shima ta ajiye acikin jerin akwati biyun da suke kwanarta.


"Daga yanzu kin zama ƙanwata, anan zakina kwana" ta faɗa tana nuna mata gadon, sama kasancewar sa mai hawa biyu ne sama da ƙasa, kai ta gyaɗa tana murmushi.

Bayan ta huta aka kawo mata shinkafa fara da mai da yaji, tayi mamaki ƙwarai da inda aka sameta, hakan yasata ci babu ƙaƙƙautawa har tayi hani'a.

 Daga nan ta rafka uban tagumi tana tunanin Luyya, da irin rayuwar da suke, nan kuma hawaye ya fara zubar mata, tana hararo wautar da tayi, gashi yanzu ƴan uwanta suna gida abin su.


Janta Marwa tayi yawo suna zuwa ɗaki-ɗaki duk inda sukaje takance ƙanwar ta ce, da yawa suna mamakin ƙanƙantar da take da shi, amma kuma tana da kyau na gaske, ga kuma gashi kwance akanta wanda yara janyo mata masoya. Kun san dai en bodin akwai son mai kyau da gashi. Lolx


DARE:


Dare ya tsala sosai ta yanda kowa ka juya yana faman barci da minshari, ayayin da Ismaha Zainab ke faman juyi akan gadonta, jifa-jifa takanji surutun mutane awaje wanda muryoyin ko kaɗan basuyi kama dana mutane ba, haka kuma takanji ana jan mayafin da take lilliɓe ajikin ta, tsoro sosai ya kamata wanda bata taɓa jin irinsa ba, ga kuma futsari daya cika marar ta amma babu halin motsawa, ido ta ƙara runtsewa dan jin muryar take tana kusantowa inda take, wani ƙara taji asaitin kunnen ta wanda ya sata sakin fitsarin da take ji, tana ƙara jan bargon da runtse ido da ƙarfi. 


 Gangarawa Futsarin nata ya farayi bai tsaya ako inaba sai abakin Marwa datake gadon ƙasa tana sauƙe munshari, baki buɗe take barcin, jin ruwa ya shige bakinta kai tsaye ya sata farkawa da tashi zaune.


"Ikon Allah yau kuma ruwa ake awanan lokacin?" kalmar data faɗa kenan tana bin inda ruwan yake zubowa da ido, tuni ya jiƙa mata matashin kwanciyar ta.


Sauƙa tayi ta miƙe tsaye jin babu alamun sauƙar ruwa akan kwano, hannun ta takai ga kan katifar Ismaha Zainab tajita a jiƙe jagab da Futsari "Kan Bala'i! Futsarin yarinyar nan na shanye kenan" ta faɗa da larfi tana ƙoƙarin kai mata duka.......


🥀🥀🥀🥀🥀🥀


*😂Acikin ko wani abu akwai wanda yake zama kishiya ga jin daɗinsa, ko ya magantu akansa ko kuma ya zuba ido dan ya rinjayi laɓɓansa sauƙe nauyin hakan.*

_Ba saina ce komiba nasan kun riga da kun gane maganar, ku ɗauko faya-fayai na ingizawa dan ku suffantu da suffa mai wahalar samu, sai ku ɗauko juriyar da take mallakin ku, ku sanqama bayani acikin kundin dayafi muku sauqi wajan isar da ra'ayinku, ni kuma zan tanadarma ko wani layi ɗaya na maganarku amsar da zata gamsar da ruhinku wanan shine *GIRMAMAWATA*_


#Um Nass

#cmnts, like, vote and share

#Ana tare🤝

[2/16, 9:40 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY *😘Um Nass 🏇*


®NAGARTA WRI. ASSOCIATION


BABI NA ASHIRIN DA BIYU (PAGE 22)


 Hannu takai da zummar ta daketa sai kuma taga rashin kyautawuwar hakan, nan ta shiga surfa masifa har dai Ismaha Zainab ta tashi take mitsittsika ido, wanda yayi dai-dai da tashin ɗaukacin mutanen ɗakin.

"Sauƙo min akan gado munafuka! Ashe ko gama futsarin kwance bakiyiba aka kawo min ke?" tana magana numfashinta nayin sama saboda ɓacin rai, babban takaicinta fitsarin yarinyar data haɗiya har cikin ta.


 Sauƙowa Ismaha Zainab tayi, jikinta jagaf da futsari abin da bata taɓa yiba kenan tun ƙuruciyar ta, amma yau itace akema tijara haka wata kunya ne taji ta dirar mata wanda bata taɓa jin irin taba, hawaye kuwa kamar an ɓalla famfo haka yake zuba akan fuskar ta. 


Watso mata katifar ta tayi a santar da sauran yara marasa galihu suke kwana, sanan ta ci gaba da wurgo mata sauran komatsanta "Tun farko da nasan haka kike da babu dalilin da zaisa na gayyato ki kwana ta. Ga tsiyar kayan ki nan kije can ki ƙaraci futsarin ki."


 "Yau naji tujara ke Marwanatu mi yasa baki da haƙuri ne? Da wanan tsohon daren kika cikama mutane kunne da masifa, gashi kin hana kowa yin barci." Wata dattijuwar tsohuwa ta faɗa tana fitowa daga wani ɗaki da alama mallakin ta ne, haka kuma itake da alhakin kula da ɗaliban da suke cikin ɗakin.


Baki ta murguɗa duk da duhu ne amma kasan bata da kunya ko kaɗan "Futsarin kwance fa tamin ya shiga har bakina, da taci sa'a ma ban daketa ba iya faɗan ne ai ta ji daɗi."


"Wacece ne ta miki Futsarin?" ta sake faɗa dai-dai lokacin da take dallara fitilar hannu.


Da hannunta ta mata nuni ga Ismaha Zainab wanda take raɓe tsamo-tsamo.cikin futsari. Tausayin ta ne ya kamata "Wanan da ɗaukan alhaki ma kike. Yarinyar nan duka nawa take? Awanan bam-bamin faɗan naki sai na ɗauka da sa'arki kike Mtss" ta ƙarasa maganar tana buga tsuka.


Sanan ta koma ɗakin ta ba tare da tayi magana ba, sauran mutane ɗakin suma suka kwanta da yawa suna jan Allah ya Isa akan hanasu barcin da Marwa tayi.

Hannuta Sa'adatu ta riƙe cikin tausayi, asaninta bata taɓa ganin Ismaha Zainab hakaba. Da wuyama kaga abu ya ɓata mata rai balle tayi kuka harda jan zuciya. Rungumeta tayi tana sauƙe ajiyar zuciya akai-akai tanaga wanan tozarcin ya isa haka.


"Shikenan yi haƙuri, zo muje mu kwanta ashimfiɗa ta." daga haka taja hannun ta bayan ta cire mata kayan jikinta ta sauya mata wani, suka kwanta akatifar ta duk da ƙan-ƙantar ta, amma ta ishesu. Rungume Sa'adatu tayi tana sauƙe ajiyar zuciya mai yawa, har ga Allah nadama ce da kuma tarin dana sani suke sauƙar mata na zuwa wanan makarantar, dama ace zata dawo da jiya yau, to da babu makawa zatayi fatan ace ta soke ko wani zirƙilli da zaƙewar da tayi akan zuwa wanan garin.


*****

 HAƊEJIA


Tun bayan tafiyar su Ismaha Zainab hankalin Luyya ya tashi ƙwarai, fargaba da tsoron abin da zai iya zuwa ya dawo ya cika mata zuciya.

Allah ya sani tana mutuƙar jin tausayin ɗiyarta, kwatan-kwacin yanda take sonta, akwai matsalar da ke ɗawainiya da rayuwar Ismaha Zainab wanda babu wanda ya sani sai ita, amma kuma itama ta gaza nema mata maganin da zai zama kariya agareta. Daɗin daɗawa ƙiriniyar ta da take ƙara ninkuwa acikin ko wata rana, gashi yanzu ta tafi garin da babu uwa babu uba ba kuma gwaɓa, sai dai jiki magayi, Allah dai ya kareta kawai.


Dai-dai dawowar su Usama da Alh. Ali suke sanar da mutanen gidan sun bar Ismaha Zainab acan sai rawar kai take "Gaskiya makarantar jeji ce sosai, gata kuma alungu akwai tazara mai yawa kafin ka isa cikin gari." Usama ya faɗa yana kwaɓe baki, duk da ba shiri suke da Ismaha Zainab ba yaji kewar barin ta agarin nan.


"Dama yawanci haka makarantar kwana take ai, kaɗan ne ake samun su acikin gari." Alh. Isah ya faɗa dan ƙarara ya hango tashin hankali ashimfiɗe akan fuskar Luyya.


"Wallahi yau ɗaya kunga gidan nan tsit, kamar babu yara acikin sa, su kansu jinsu suke sukuku babu wata walwala atare da su." Salamatu ta faɗa cikin yanayin alhini da jimamin tafiyar Ismaha Zainab.


"Aifa ina xasuji kuzari mai sasu magana bata nan, suma sai ahanzarta kaisu makarantar, ko zasu samu abu ɗebe kewa." Rabi ta faɗa tana murmushi. Duka yau babu yaron dayazo kawo musu ƙara ko ya shigo da kuka, kama daaga yaran gidan har zuwa na maƙota. 


Tashi Luyya tayi ta shige ɗaki ba tare data ce musu komi acikin hirar tasuba, wata azaba take ji na sauƙo mata tun daga kan cinyarta har xuwa mararta da bayanta, idan har zata iya kintata to babu shakka naƙuda ce ta zo mata awanan lokacin, ko kuma ita ta zungurota dan tun jin maganar Usama gabanta ya faɗi, wanda yayi faɗuwar ne da tasowar ciwon da takeji yana ɗawainiya da ita.


Da ido suka mata rakiya ba tare da sun fahimci abin dake damuntaba, sai Alh. Isah ne yayi ƙarfin halin binta ɗakin dan yaga mi yake faruwa, ganin da yayi tana ɗawafi aɗaki tana kaiwa da kawowa ga gumin daya jiƙata sharkaf yasashi saurin ƙarasawa "Yaya dai Ruqayya mi yake damunki? Ko abarce?" ya tambaya cikin ruɗewa.


Murmushin yaƙe tayi babu magana sai girgiza masa kai da take muryar ta har ta fara rawa "Ban sani ba. Ina ji dai kamar bayana zai ɓalle, ƙafafuwana sun min nauyi da ciwo."


"Subhanallah. Salamatu! Salamatu!!" ya fara ruga mata kira da sauri ta shigo ɗakin "Lafiya dai Alhaji wanan kiran hakan?"


"Inafa lafiya, inaga Ruqayya ta hau naƙuda ne, ku kintsa na kaiku asibiti muga."


"Wayyo sannu kinji" ta faɗa tana kai kallonta ga Luyya da take durƙushe gumi na ta zuba ajikin ta, cikin ruɗewa ta ɗauko hijabi ta saka mata itama ta sa nata da taimakon Alh. Isah suka kamata suka kaita mota, rabi kuma sai faman sannu take mata da kuma na Allah ya sauƙeta lafiya, jikinta duk ya ɗauki rawa, Allah ya sani ita yanzu tsoron haihuwarma take, wata ƙila shi yasa Allah ya tsaida mata ita tun daaga kan Bilkisu, itaama salamatun hakance tun akan Hafsa haihuwar ta tsaya musu har sun fara tunanin rabo ya ƙare musu ashe yana tare da Luyya.


Da gudun gaske Alh. Isah ya kaisu mataniti dan sune sukafi maida hankali wajan kula da mai haihuwa saɓanin general da ta zama ta kowa da kowa.


 Suna zuwa aka shiga da ita ɗakin haihuwa, sai kaiwa da kawowa suke tsakanin Salamatu da Alh. Isah hankalinsu idan yayi dubu to ya kai ƙololuwar tashi.


 Cikin ikon Allah ya sauƙeta lafiya ta haifo yara biyu duka maza. Murna tsakanin Salamatu da Alh. Isah ba'a magana "Ikon Allah" abun da suke ta faɗa kenan, har zuwa lokacin da aka gyarata aka kaita ɗakin hutu, tun alokacin Salamatu ta fara kiran Rabi sanan ta kira Iya kaltum matar Malam isubu nan suka shiga barka da murna ɗauke abakinsu, kafin a sallamesu saiga Iya kaltum ta qaraso tana washe baki "SannU Luyya sai da kika kore min ɗiyata kuka fito kukuma" ta faɗa tana ɗaukan Ɗaya daga cikin yaran, babu abin daya rabasu da Mahaifinsu sai dai kaɗan acikin kamaninsu da yayi zubi dana Ismaha Zainab wanan kuma baya rasa nasaba da jini ɗayan da suka haɗa.


 Sanan ta juya takema su Salamatu da Alh. Isah barka da arziqi, shikam bakinsa yaƙi rufuwa sai kai da kawowa yake, da ance ya kawo kaza yake zuwa da sauri ya kawo musu. Sai da sukayi awa biyar sanan aka sallamesu ganin lafiya lau Luyya ɗin take.


Anyi hidima sosai inda maƙota da abokan arziƙi suka zo suna yara an bar musu sunayensu Hassan da Hussain wanda kamarsu ta ɓaci ƙwarai dan ba'a iya banbance su. 


Haka su Usama suma sunyi rawar gani sosai shida sauran ƴan uwansa, Zakar ma yasha murna sosai sai dai yaji takaici da Ismaha Zainab bata nan ta haihu, asalima shi baya garin aaka kaita body sai dawowa yayi ya tarar baata nan.


*****

KAUGAMA


Tun bayan faruwar al'amarin Ismaha Zainab ta dawo shuru-shuru, ta kuma haƙiƙance akan daɗin zance da kukutawa yasa Anty Sa'adatu yi mata ƙarya akan makarantar, sai dai abin daɗi shine har zuwa wanan lokacin ko wata hidima tata kama daga ruwan wanka da wanki Sa'adatu ke matasu, wasu lokutan ma ita take mata wankan, hakan yasata take girmamata, amma tsakaninta da Marwa banda harara babu abin dake haɗasu, itama ba wai ƙyaleta tayiba akai-kaice takan yi mata dariya musamman idan ta tuna da tasha futsarin ta.


Yau kimanin mako biyu kenan da zuwanta makarantar amma babu wani sabon abu da ta ga, komi na abincin makarantar ya isheta, kamar yanzu da tasa kwaɗon ƙanzo agaba tana ta rafka kuka "Ni wallahi bana so Allah na gaji da cin wanan abun. Wayyo Allah Luyya ni taliyar Luyya nake son ci."


 Da ƙarfi take kukan tana buga ƙafa, hakan yajanyo hankalin mutane sosai kanta.


 "Ƴar uwa wanan ƙanwar tamu akwai rigima, ki rarrashe ta mana" Hauwa Ahmad ta faɗa kasancewarta ƙawar Sa'adatu haka aminiyarta ta kusa.


"Kema dai kinsan halin Ismaha Zainaba ƴar uwa, kona rarrasheta ba shiru zatayi ba, tunda gida ya faɗo mata arai yanzu."


"Zo muje dai mu bata haƙuri ai ankusa hutu ma, duka bai wuce sati uku ba yanzu."


"to muje" ƙarasawa sukayi kusa da Ismaha Zainab da take faman kuka kamar ana zugara.


"Ya isa haka ƙanwata, yi haƙuri kinji. Ba dai gida kike son zuwaba?"


 kai ta gyaɗa "Eh ina son cin taliyar Luyya, kullum anan ƙanzo da abinci marar daɗi ake bani."


Dariyar ta taso gimtsewa sanan taci gaba "To kiyi shuru zakije gidan, ai ankusa yin wata drama mai kyau, idan kika kalleta saima kin manta da luyya ɗin."


Baki ta washe cikin jin daɗi, wani abu ne Dramar da har zai mantar da ita luyya ɗinta "Da gaske?" 


Kai Hauwa Ahmad ta gyaɗa mata tana bata tabbacin maganar ta "Saima kinga yanda ake ake rawa da kiɗa, abin akwai armashi sosai."

Ayanda taga ƙatuwa Hauwa na ƙawata mata kyan abun, to babu shakka tasan zaiyi kyan kalla, dariya tayi tana tafa hannunta "Allah ya kaimu. Yaushe za'ayi?"


"Umm ranar Asabat ne, kwanaki biyu masu zuwa kinga yau Alkhamis."


Kai ta gyaɗa cikin jin daɗin labarin ta fara cin kwaɗon ƙanzonta duk da shaƙetan da yake, ga kayan daɗinta dangin su madara amma ance ba zatacibba sai an kusa hutu, ko mi hakan zai mata oho musu.


Ahaka Hauwa tayi galabar lallashin Ismaha Zainab tun daaga lokacin tabar kuka sai idan taje ta samu ƙawayenta su Hauwa Tanimu da Maryam Wada ta musu bayani akan an kusa Yin Drama da rawa mai kyau mai daɗi, har gida sai kun manta, su dai iyaka su mata dariya dan sun san ba wani abun azo agani bane, kawai ƙawatawa ne da kurantawa irin nasu.


Ranar Drama:


Tun safe Ismaha Zainab take takurama Sa'adatu akan tayi ta shirya ta kada su makara akare musu, kasancewar shirin na safe ne yasata yin sauri suka shirya suka fita da yawa acikin ɗalibai sun kama wajan zama, wasu kuma suna zuwa, Ismaha Zainab sai faman washe baki take tana dariya adole zataga abin da zaisa ta manta da Luyya ɗinta.


Can bayan hallaruwar kowa malamai sun zo suma, aka fara drama abin daya bawa Ismaha Zainab takaici ganin ɗalibai ne irinsu suke shigar kayan maza da mata, wasu harda furfura ma kamar tsoffi, ƙara baza ido tayi ko zataga abin da yafi wanan kyau amma dai su ɗin take gani, wani abun kamar kayi kuka dan takaici, amma abin haushi sai dariya da tafi ake tun daga kan ɗalibai har zuwa malaman nasu.


Can kuma sai aka kawo ƙwarya guda uku aka ajiye, ɗaya da ruwa acikinta sai ƴar ƙarama tana yawo acikin ruwan sauran kuma aka kifesu, masu kiɗa suka zo suka fara kiɗan rawa, sauran ɗalibai ƴan rawa aka fito suna rawa, hakan da Ismaha Zainab ta gani ya ƙara bata haushi kawai ta fashe da ihu tana kuka "Allah bana so, ni dai akaini gida wajan Luyya." Ihu take tana birgima awajan wanda ya janyo hankalin mutane da yawa kansu, da sauri Sa'adatu ta janyota gefe ita da Hauwa Ahmad.


 "Ya Allah! Ismaha Zainab ya kike so nayi ne?"


"Ni dai ku kaini gida wajan Luyya." ta faɗa tana jan ajiyar zuciya.

Kai ta dafe can dabara ta zo mata "Bakiga babu mota anan ba, kuma idan kina so akaiki sai an zaneki da bulala kuma ki biya dubu goma kuɗin mota."


Kai ta gyaɗa tana share hawaye "Eh na yarda, ai Luyya zata biya kuɗin Motar idan munje. Ni dai bana son makarantar nan."

Kallonta takai ga Hauwa Ahmad da take ta dariya "Da aikifa agabanmu Yar Uwata."


"Babba ma kuwa." Hauwa Ahmad ta faɗa tana dariya...🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀


_😂😂Chaiiii jiya naci dariya naga masu son Ismaha Zainab da masu ƙinta, kowa na magantuwa da abin da ya ke sarqafe acikin nasa ruhin. Nagode sosai da cmnts naku naji daɗin juriyarku acikin shafin hakan yasani aro dauriyata dan qarfafa muku gwuiwa ina fatan zaku ji daɗin wanan shafin zaku kuma tattaro Kimar da ta zama mallakinku ku qara magantuwa akan ra'ayinku._

 *GIRMAMAWA* 


#Um Nass

#Cmnts. Like nd share

#Da Amana 🤝

[2/16, 9:40 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY *😘Um Nass 🏇*


® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
 _Kina ina HAIMA Darling dama ƴan Eliquince Association wannan page kwacankwaf naku ne, ina kuma godiya da fatan alkhairi a gareku._


BABI NA ASHIRIN DA UKU (Page 23)


Kuka taci gaba dayi tana ihu wanda ya janyo hankalin ɗaliban, musamman wanda suke kusa da su.

"Kinga kin janyo hankalin mutane kanki, kowa kallonki yake, haba Ismaha Zainab mai dariya, ke da bakya fushi balle kuka, idan yaran unguwarku suka ji za suna tsokanarki su bar jin tsoron kifa." Maganar da Sa'adatu take cikin sigar lallashi, duk da ranta ya kai ƙoluluwa wajan ɓaci. 


Share hawayen fuskarta tayi ta kalli Sa'adatu cikin jin takaicinta da bushewar zuciya ta fara magana "Ai dai ke kikace idan nazo zanci shinkafar kaza, kuma kikace akwai Famfo mai tsarki."

Shuru tayi tana kallon Sa'adatun wanda take faman mata muzurai ganin mutane sun kewaye su, hakan ya sa taji kunya akan ƙaryar da ta mata, baki Ismaha Zainab ta cije duk da ƙarancin shekarunta a wannan lokacin amma a cikin zuciyarta tana jin zafi da ƙunci, ta sake waiwayar Hauwa Ahmad itama tana murmushin da yafi kuka ciwo "Ai dai kince zanga Dramar da zata sani na manta da Luyya ɗina ko?" kai ta girgiza cikin murmushin da su kansu suka ji tsoro da fargaba ya cika su "Duniya ta cika da ababen ƙawa na shagalar da mutane su faɗa cikin ruɗinta. Amma ni ban yi shekaru da nisan da zan manta da Mahaifiyata a cikin taba, wata ƙila akwai abinda yafi wannan daɗi wanda ke sa ɗiya ta manta da Mahaifiyarta, sai dai ni zan yi ta Addu'a da fatan kada nayi tsawon rayuwar da zan shiga wannan matakin da zan Manta da Luyya a cikin duniyata." Murmushi tayi a karo na biyu tana girgiza kanta "Wannan! Wannan abin da kuka kuranta min ya sani jin tsoro da shakkun mutanen da suke kewaye ni. Indai akwai hisabi akan babba da yaro to na tabbata zamu tsaya dan amana hisabi da ku Mussaman ke Anty Sa'adatu, da na ɗauka kina sona ne ashe kina min ƙiyayyar da babu wanda ya taɓa min ita. Kin ingizani ta yanda naji ɗoki dayin nisa da Ƴan uwana ina musu kuri da fankamar tadda abin da zan gani fiye wanda muke tare, mutane sukan so siyama kansu Kima dan su tsira da alkhairan da zasu samu daga bakin mutane, ashe wasu sukan zubar da ko wata dama tasu dan su siyar da tasu Nagartar. Nagode." tana gama faɗar haka ta tafi ta barsu, da ido suka bita da kallo ina rami na faɗa haka Sa'adatu take ji, wannan abin kunya har ina, ƴar ƙaramar yarinya ta titsiyesu tana faɗa musu maganganu masu kauri da girma.

"Wallahi naji kunyar da ban taɓa jin irinta ba tun da nake a rayuwata." Sa'adatu ta faɗa tana girgiza kai lokacin da mutane suka fara raguwa daga kallonsu.


"Gaskiya dai baki kyauta mata ba da kika mata ƙarya, duk da nima na mata amma bai kai naki da kika zama silar zuwan ta makarantar nan ba. Gashi yanzu yarinya ƙarama ta gasa mana magana duk saboda ke." Hauwa Ahmad ta faɗa tana jinjina kai da alhinin maganar da har yanzu take dawo mata a kunnenta.


"Ya zanyi ƴar uwa? Wallahi har a zuciyata ina son Ismaha Zainab, abu ɗaya ne yake haɗani da ita rashin jinta da tsokanarta, za kiyi mamaki idan nace miki ta fitini kowa a gidansu da unguwarsu, gashi mahaifiyarta Allah ya hore mata haƙuri da kawaici tana cutuwa a rashin jinta, kullum cikin biya da bada haƙuri take, shiyasa na yanke shawarar na ƙawata mata jin daɗin makarantar nan wata ƙila idan tazo zata shiryu ta rage wasu abubuwan koda bata rage duka ba."


Kai Hauwa Ahmad ta jinjina cikin gamsuwa da maganar tata, dan ranar farko da taga dabin da sukayi da siniyo jummai tasan akwai rashin ji a tare da ita "Duk da haka da gaskiya kika faɗa mata sai yafi miki jin kunyar nan, gashi a gaban jiniyas ɗin mu ta faɗa mana magana, duk da gaskiya ta faɗa mana."


"Hmm ba zaki gane ba, ta koya naso faɗa miki Halayyar Ismaha ba zaki fahimta ba." 

"Bazan gane ba kam tunda ba gari ɗaya muke ba, balle kuma ace muna unguwa ɗaya." tana gama faɗar haka ta tafi ta barta a wajan a tsaye tana neman mafita.


****

Duk abin dake faruwa a gaban Idon Siniyo Shamsiyya ya faru da Jummai da fuskarta har yanz bata gama dai-daituwa ba dan bakin yana nan sai a hankali "Kai amma naji daɗin ganin yanda Aljanar yarinya nan take kuka da hawaye, sai yanzu naji zuciyata ta huce jin haushinta da nake ji." Jummai ta faɗa tana faɗaɗa murmushi akan fuskarta.


Kai siniyo Shamsiyya ta girgiza cikin jin takaicin Siniyo Jummai da Sa'adatu "Wallahi da ba dan Sa'adatu Dota ɗin sister bace da babu abun da zai hanani na hukunta ta akan ƙaryar da ta yima yarinyar nan, amma yanzu idan na taɓa ta cewa za tayi dama ina kishinta bana sonta da dai sauran maganganunta na mita, tunda yarinyar nan tazo nake bin motsinta tana da fara'a duk da akwai damuwa kaɗan a zuciyarta na kewar gida, amma tana karatu."

Baki Jummai ta taɓai cikin nuna halin ko in kula "Kidai faɗi gaskiya malama, kina jin haushin Sa'adatu har yanzu dan Lateepha na sonta. Amma idan banda haka mine abun hukunta aini ta min dai-dai wallahi itace maganin aljannun yara irin wannan."

 "Mtsss ana ga ƙura kina ga yaƙi, ni wallahi bata ma gabana, bari naje na lallashi yarinyar nan kada ta je inda firfawa zasu dake ta." Tana gama faɗar haka ta sa kai tabar Jummai da take aika mata da harara ita kam tana jin haushin yarinyar da duk wanda zai kulata, sai dai ta fahimci siniyo Shamsiyya tayi nisa a son yarinyar gashi ƙanwar Sa'adatu ce balle ta kai tsaigumi wajan Lateepha.


 *****

Hanyar da taga Ismaha Zainab tayi tabi tana dubai-dubai cak kamar ance takai idonta ta ganta a ƙofar wani aji ta rafka tagumi, hawaye na zuba tana gogewa, hannunta kuma riƙe da wani kara tana faman zanawa a ƙasa, ajiyar zuciya Siniyo Shamsiyya tayi sannan ta ƙarasa inda Ismaha Zainab take, ta samu wajen zama a kusa da ita tana faman aika mata da murmushi, duk da bata ce mata komi ba asali ma bata juyo ta kalle taba.

"Kina jin Haushin Anty Sa'adatu ne saboda tayi miki ƙarya?" jin hakan yasa Ismaha Zainab juyowa tana kallon Siniyo Shamsiyya wanda itama ta tsare ta da ido tana kallonta.

Kai ta girgiza "A'a bana jin haushinta ni, kawai ina jin kewar gida da Luyya ɗina."


"Amma shine kike mata magana da ƙarfi haka, baki san a nan doka bace ƙarami yayiwa babba wanda ya girme shi da aji magana da ƙarfi?"

Murmushi Ismaha Zainab tayi sannan ta cije bakinta, kamar ba za tayi magana ba sai kuma ta ɗago ta kalli Siniyo Shamsiyya "Luyya ta faɗa min mutane sukan so a basu girma da zuga wanda zata ingizasu zuwa ga halaka, amma idan kana so kaga rauni da ɓacin ransu kayi musu magana akan kuskuren su cikin sanar dasu gaskiyar da take ta zahiri."


Shuru siniyo Shamsiyya tayi tana jinjina ma kaifin basirar yarinyar, gata ƴar ƙarama amma kuma tana zaro kalmomi masu girma wanda ko ita da take ƙatuwa ba zata iya faɗar su ba "Kina yawan kiran sunan Luyya fiye da yanda kike tuna sunanki, wacece ita a wajanki."

Murmushi Ismaha Zainab tayi mai sauti wanda kana gani kasan na jin daɗi ne "Mamana ce. Ita ta haife ni bayan wahalar da tasha wajan ɗawainiya da cikina, sannan ta ɗauki nauyin komi nawa fiye da wanda suka rayu da iyayensu biyu suke samu." Murmushi ta ƙarayi mai sauti sannan ta kalli Siniyo Shamsiyya da take kallonta "Kinsan mi Anty Mai kyau?"

Kai Siniyo Shamsiyya ta girgiza cikin son jin abinda zata faɗa, dariya tayi sannan ta girgiza kanta tana bubbuga ƙirjinta "Anan nake jin bugawar sunan Luyya da tunaninta a cikinta, kullum gari ya waye takan ce min "Idan nayi tsawon rayuwa zan baki ko wata kulawa, na baza kunnena dan jin muryarki, koda bazan yi dariya ba a raina zan samu tabbacin kina lafiya." idan kuma nayo tsokana aka kawo mata ƙarana, kin san bata dukana kamar yanda Babar su Usama ke dukan su Khadija sai dai tace min "Allah ya baki tsawon rayuwa Ismaha Zainab cikin shiriyarsa, amma bana fatan yaranki suyi ƙin ji irin naki." 


Dariya ta tuntsire mai yawa, a gefen Siniyo shamsiyya sai ta tsinci kanta da jin nishaɗin labaran Ismaha Zainab "Wai fa kinji ƴar ƙarama dani ce zan haihu, duk lokacin da Luyya tayi wannan maganar dariya nake mata nace zan bar yin tsokana, amma sai tace min ta sani abubuwa da yawa akan samu sauyawars u wasu sauyi na har abada wasu kuma barci suke ana tsoron farkawar su a cikin mummunan lokaci."


 Shafa kanta Siniyo Shamsiyya tayi "Mamanki tana sonki sosai, nasan tana jin kewar ki fiye da yanda kike jin tata, amma ya akayi ta bar ki kika zo nan?"


Ido ta rintse sannan ta sauya fuska kamar za tayi kuka "Kuka nayi ta mata ina rigima sai an kawo ni, ita kuma bata son kukana gashi dama bata da lafiya sosai, shine fa tace ma faɗa ma Abban su Usama idan ya yarda itama shikenan, to dama shi yasan bana jin lallashi ina faɗamar yace to, ashe rabon naci wuya naci ƙanxo mai maƙure wuya yasa na dage akawo ni, Usama kuwa sai murna yake ashe yasan da wuya." hawaye ne ya zubo ma idonta a lokacin da ta gama maganar.


Dariya abun yaso bawa siniyo Shamsiyya yarinya kamar mai rayuwa su biyu dariya bata mata wuya kamar yanda kuka yake mata sauƙi "Ayya yi haƙuri kin ji ƙanwata mai Kyau, masu kyau basa yawan kuka, komi aka musu dauriya suke, Sa'adatu ta miki gata ta hanyar hutar da Luyyanki a kan jurar hayaniyar ki, watarana zaki gode mata."

Kai ta ɗago tana kallon Shamsiyya sannan tayi murmushi "Ni yanzu ma na gode mata ai, na ƙaru da abubuwa masu yawa a zaman a a cikin makarantar nan, kinsan Luyya tace min ko ina a wajan Musulmi gida ne sai dai idan baka riƙe shi a gidan ba yakan zame maka jeji kuma kufayin da za kayi ihu ba tare da an ankare da kai ba."

 "Masha Allahu. Lallai Allah ya baki Uwa ɗaya wadda ta zama daban a cikin dubban Uwaye. Ina fatan wata rana naga Luyya ɗin nan ko zan samu kaɗan daga cikin hikimar da take da ita."


Ido Ismaha Zainab ta buɗe cikin jin daɗin kalaman Siniyo Shamsiyya "Anty Mai kyau kina da kirki sosai, idan Luyya tazo min zan haɗaki da ita, au ashe fa da nisa, zan bata labarinki har da na ƙatuwa mai shan jini."


Dariya sosai Siniyo shamsiyya tayi sanin da Jummai Ismaha ZAINAB take ta ruƙo hannunta tana kallon ta "Bafa haka sunan taba, ba kuma ashan jini a nan, sunanta Siniyo Jummai. Nima kuma sunana Shamsiyya ba Anty mai kyau ba."

Kafaɗa ta maƙale sannan ta taɓe baki "Allah tayi ƙatuwa da yawa, kuma fa muryarta akwai ban tsoro, shi yasa nake tunanin ko masu shan jinin mutane ne. Ke kuma kina da kyau ga kina da kirki shiyasa aka saka miki sunan rana saboda hasken da take da ita, gashi kuma tana da abubuwan ƙarama mutane lafiya, ni dai zan kiraki da Anty Mai kyau kamar yanda nake ce ma Unmmm Mai Mulyal yala. Allah sarki shima yana da kirki ko yanzu yana ina, haka yayi ta mana hotuna a wayansa yana bamu kuɗi ni da ya Zakal muƙi karɓa saboda Luyya ta hanamu karɓan kuɗi a wajan mutane."


Dariya sosai Shamsiyya take tana kallon Ismaha Zainab ita dai a iya saninta bata taɓa ganin yarinya mai baiwa da hikimarta ba ga iya tsara zance kamar babba "Bakya gajiya da magana, zan so naga ƙato mai muryar yaran nan shima, kina yawan magana akan sa."

Kai ta gyaɗa cikin ƙara bawa kai ƙwarin gwuiwa "Kuma fa sau biyu na taɓa ganinsa, amma kuma har yanzu ina ganin kamanninsa, wata rana har mafarkinsa nake muna ɗaukon hoto, ko yana koya min karatu, shi yasa ma ban manta da shiba har yanzu da nake baki labarin sa."

Ido Shamsiyya ta fiddo waje cikin mamaki "Ba yayanki bane?".

Dariya ta tuntsure sannan ta gyaɗa mata kai, dai-dai lokacin da ɗaliɓai suka fara fitowa dan komawa Hostel ɗinsu, hangowa Sa'adatu tayi ta miƙe tsaye tana kaɗe jikinta "Sai anjima Anty mai kyau, kinga Anty Sa'adatu sun fito."

Kai ta juya tana kallonsu suna tahowa, sam ta manta da sun ɓata lokaci a nan ashe lokacin tashi har yayi babu ita, ganin Lateepha ya sata ƙin miƙewa ta kai kallonta ga Ismaha Zainab "Ba fushi kike da Sa'adatun ba ne."


Kai ta girgiza tana ƙara yalwata murmushinta "Fushi ai suffar sheɗani ne yakan mallake zuciyar mai yinsa yasa ya aikata ba dai-dai ba, Luyya ta hanani yin fushi komin girman laifin da mutum yake min, balle kuma Anty Sa'adatu da nake son ta sosai." tana gama faɗar haka ta ruga da gudu tana kiran Anty Sa'adatu, rakiyar ido Shamsiyya ta mata tana murmushi ta tashi tabi bayanta, dan bata gaji da ganinta ba da kuma jin maganarta.


Kallonta su Sa'adatu suke suna mamaki duk da ita ta riga da ta san Ismaha Zainab bata da ruƙon a zuciyarta.

"Sannu Anty Mai hanci" ta faɗa ma Lateepha ganin yanda ta kafe su da ido tana son ƙarin bayani musamman ganin yanda suka taho tare da cigaba tayi da maganarta "Anty Sa'adatu hira fa muke da Anty mai kyau tana da kirki itama Ina sonta kinji." Kallon-Kallo aka tsaya yi tsakanin Sa'adatu da Siniyo Shamsiyya da take murmushi, hakan ya ƙular da Lateepha ta buga tsaki ta bar wajan, wanda yasa su binta da ido...


*******

Misrah


🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀


 *Nasan dai a wannan shafin dole abu ɗaya ya burge ku acikinsa, bazan iya hasashen saba amma zan kintata shine kalmar Uwa ku magantu akan ta da tasirin da take da ita a cikin duniyar goben mu.*

_Karku manta da wannan Kalmar ta *GIRMAMAWA* da nake baku a cikin ko wani shafi na labarin Ismaha Zainab, hakan dan faranta ranku ne_


#Um Nass

#Cmnts, like nd share

#Da Amana

[2/16, 9:40 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY *😘Um Nass 🏇*


🔥® NAGARTA WRITERS ASSOCIATION
BABI NA ASHIRIN DA HUƊU (PAGE 24)


 MISRAH


 "Ni wallahi har mamakin ka nake Musaddiƙ kana ɓata ma kanka lokaci da yawa a kan wanan ƴar yarinyar. Ga Khairat babbar yarinya ƴar gidan jakadan Nigeria ta mace a kanka kana wulaƙanta ta, ya kamata ka sauya hali da tunani fa."


Kallonsa yayi yana lumshe ido fuskarsa ƙunshe da murmushi, cigaba yayi da daddana na'ura mai ƙwaƙwalwar da ke gabansa ba tare daya tanka masa ba.

  

Tsaki Ma'aruf yayi kana ya miƙe yana bibbiga litattafansa "Kanada ɗaga kai da wulaƙanci Musaddiƙ. Wata ƙila saboda Allah ya fifita matsayinka fiye da namu, ya kuma albarka ce ka da tarin ilimi da kyau gami da farin jini a wajan mutane shiyasa kake nuna halin ko in kula a kan duk wanda ke raɓar ka. Babu komi kayi haƙuri da shiga rayuwarka da nake yi."


Juyawa yayi da zummar barin wajan, wanda Musaddiƙ ya bishi da rakiyar ido kamar ba zai masa magana ba, amma kuma yasan rigimar Ma'aruf wannan ba shine karo na farko da suka saba sa-in-sa akan maganar Khairat ba, bai kuma san dalilin da yasa yake adawa da soyayyar da yake nunawa Ismuha Zainab ba duk da ƙarancin shekarun ta.


 "Ma'arufff!" Ya kira shi cikin sassanyar muryarsa mai fita da nutsuwa da amo mai daɗin ji. Cak ya tsaya amma bai juyo ba dan yana cike da jin haushin share shin da yake yi. Murmushi Musaddiƙ yayi sannan ya miƙe ya nufi kusa da shi, gabansa ya sha yana kallon sa gami da Murmushi wanda ya zama ɗabi'a a gare shi "Na ɗauka kai ne mutum na farko da zaka bada labarin kyawawan ɗabi'u na, ka kuma kare ni a duk inda kaji za'ayi suka a gare ni ko kuma a ɓata min suna ta hanyar jingina ni da Mummunar sifa kwatankwacin yanda kayi." 


Murmushi yayi mai sauti yana naɗe hannayensa a ƙirjinsa, idonsa fess akan na Ma'aruf da shi ma yake kallonsa "Kimanin shekara uku muna tare da kai amma kuma har zuwa yanzu ka gagara yi min uzuri da adalci a kan ɗabi'ar da bani na siya ma kaina ba. Matsalar ka kullum akan maganar Khairat ni kuma ga wanda zuciyata ke so take ta dakon jira akan lokaci ya aranta min kasancewa tare da ita."

Kai ya girgiza yana ƙara yawaita murmushi, a cikin idonsa yake hango kamanninta da komi nata "Ina sonta duk da ƙarantar ta, tabbacin da na samu akan zan iya samun ta shine ya baro ni da ƙasata bayan na cire hakan a raina. Kai abokina ne na kusa ina son ka dunga min adalci akan ko wata kalma da zaka jinginata a gare ni. Bana son hayaniya bana son magana wanda bazan anfana da alkhairi a cikin taba."


Yana gama faɗar haka ya koma mazaunin sa ba tare daya ƙara bi ta kan Ma'aruf ba.

Kunya ce ta kama shi sosai jin kalaman da suke fita a bakin Mussadiƙ, tabbas yau ya kai shi maƙura tunda ya fallasa abin da ke ransa, duk da a tsawan shekaru ukun da suka yi yasan abu da yawa a kan Musaddiƙ ɗin, haka kuma ya daɗe da sanin matsayin da yarinyar ta taka a zuciyarsa, amma kuma ya kasa fahimtar mi yasa shi baya taya shi son ta? Bai kuma san mi yasa yake adawa a duk wani abun da zai zamo na tsaginta.


Juyawa yayi yana kallon Musaddiƙ wanda ya cigaba da daddana wayarsa kamar babu wani abun dake damunsa, yana da zunzurutun wahala kaga damuwa akan fuskarsa koda kuwa kai ka baƙanta masa rai, haka kuma ba zai taɓa nuna maka ransa ya ɓaci ba a cikin ruwan sanyi yake hukunta ka da shurunsa, shi yasa yake mamaki da yanda har ya kamu da soyayyar yarinya ƙarama.

"Kayi haƙuri kaji abokina, ina jin haushi na ma magana ka ƙyale ni. Har yanzu na kasa yin sabo da shurunka."


Murmushi yayi sannan ya rufe laptop ɗin nasa ya miƙe tsaye "Lokacin lacture ya gabato kada mu makara."

"Amma ai bamu gama maganar da muke ba, ba kuma ka bani amsa akan abin dana faɗa ba."

Kai ya girgiza yana ɗaukan litattafansa ya fara fita, da baya ya bisa yana ƙara masa mita akan ƙin bashi amsar da yayi.

"Ma'aruf mana! Ba ko wata tambaya bace take samun amsa, shi kuma shuru a duk inda yake yana zuwa a muhallin amincewa ne, ka koyi zama da kurma koda na rana ɗaya ne zaka amfana da baiwar da Allah ya bashi."

  

Baki ya kwaɓe cikin ƙara jin takaicin sa "To ma miye maraba tsakanin kai da kurame, wani lokacin garama a bar ni da kurma nasan baya ji na."


Shi dai murmushi yayi ya ƙara ɗaga ƙafafuwansa dan ganin idan ya biya Ma'aruf zai kwana yana mita shi har mamaki yake wani lokacin kamar mace haka yake da mita.


*****

KAUGAMA


Yau ranar juma'a hakan yasa duk ɗalibai suke nufar wajan taro a cikin hostel, gaban wata ƙatuwar bushiyar maina, wanda duk itace mafi yawa a cikin makarantar, amma wannan ta fi sauran girma har kwanciya tayi, gata kuma a tsakiyar hostel ɗin, shiyasa ma jiniyas suke ma wajan kirari da dandalin sharri, dan ko wata ƙura aka kwaso a nan a ke dire musu.


 Gashi kuma duk ranar juma'a sai an tarasu an ƙirƙirar musu laifi na gaira babu dalili. To yau ma dai hakan ce dan duk malamai sun tafi hutun mako.

  

Kamar ko wani taron da ba na alkhairi ba siniyo jummai ke buɗe shi da ashariya da ƙirarin da take ma kanta akan na wadda tafi kowa "Yau babu sallama da buƙatar gabatar da kaina a gare ku. Sai dan zan yi muku albishir da cewar wannan satin nacin dunduniyar takalmin uwarku ne da kuma ɗankunnin da ke kunnenta, musamman ƴan aji biyar. Jiya nayi sanarwa akan a kai min ruwa kitchen da ƙyar mutane talatin suka kai, dan haka zan kira suna."

Nan kuma aka shiga kallon-kallo tsakanin ƴan aji biyar da sauran jiniyas ɗin, tsawa ta buga cikin muryarta mai tsoratarwa "ƴan aji biyar ku ware gefe, sauran jiniyas kuma ƴan aji ɗaya zuwa uku su tafi ɗaki."

 Nan aka rage daga ƴwn aji biyar sai na huɗu, gefe ɗaya kuma Ismaha Zainab ce ta tsaya tana muzurai, ko shakkah bata yi wannan mai ƙirar masu shan jinin ba alkhairi zata shuka ba.


Komawa tayi kusa da Sa'adatu wanda dan tsoro da fargaba har ta fara kuka, sanin bata kai ruwa jiya ba "Anty Sa'adatu ai dukan ku za tayi? Kuma ai kun fita yawa kuje ku tarar mata mana. Shine kuke kuka tun yanzu?"

A tsorace ta juya ta kai kallonta ga Ismaha Zainab sam bata yi tsammanin zata tsaya ba balle ta zo har inda suke "Ke Ismaha ki tafi ɗaki kada ta dake ki."

Kafaɗa ta maƙale cikin jin tausayin sa'adatun sannan ta zauna a wajan itama.

Rarrashinta ta fara yi akan ta tafi amma kuma taƙi tafiya, a haka aka kawo bulallai tari guda, tun a nan idonsu ya raina fata idan aka ɗauke Ismaha Zainab da ta fiddo ido waje cikin mamaki "Tabɗijam kamar za'a bugi jakkai."


🥀🥀🥀🥀🥀


_Yau bana jin typing akai na sai da na daure nayi saboda faranta muku rai kawai._


*Ba ra'ayina bane saka zagi cikin labari amma ga duk wanda yayi bodyn skull yasan wannan ƙarami ne daga cikin ɗabi'ar makarant, akan haka nake neman fahimta daga gare ku.*

*GIMAMAWA*


#Um Naass

#cmnts, like nd share

#Da Amana

[2/16, 9:40 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY *😘Um Nass 🏇*


® *NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*


BABI NA ASHIRIN BIYAR (Page 25)


Kallon bulalin taci gaba da yi, sanan ta kai kallon ta ga Sa'adatu wanda take ƙara sautin kukan ta. Allah ne kaɗai yasan irin azabar da za'a musu yau, ayanda ta kalli tuleliya Jummai na ɗaga bulalin fuskar ta babu ɓur-ɓushin rahma, tasan dole ta dakesu sosai.


Kai ta girgiza cikin tausayin Sa'adatu da sauran ƴan aji biyar ɗin, ta fara magana "Allah kalku bali ta dakeku. Kun tsaya kuna ta kuka tun kafin tazo kusa da ku."

Ɗagowa sukayi suna kallonta cikin jin haushin ta Sa'adatu ta buga mata tsawa "Ki wuce ki tafi ɗaki kafin ranki ya ɓaci! Haba yarinya sai azababban surutu, ina ruwank i da kukan mu." ta faɗa cikin ƙarfin hali tana aika mata da harara.

Tashi tayi kamar zata tafi sai ta koma kusa da wasu ta zauna, ta rafka tagumi hannu bibbiyu.


Cikin isa da ƙasaita Jummai ta ƙaraso ta fara kiran sunayen wanda suka kai mata ruwa, su talatin tace su ware gefe, sanan ta juyar da kallon ta ga tarin ɗaliban da basu kai mata ruwan ba, murmushi tayi wanda da ganinsa na muguntar da ta tanadar musu ne "Wato ku tabbatu shahararu ko? Har wuyanku yayi kauri da girman da zanyi nema akai min ruwa amma kuƙi kaimin ko?" 


Saurin girgiza kai sukayi cikin haɗuwar baki suka fara magana "A'a Anty Jummai dan Allah kiyi haƙuri."

"Kumin shuru banzaye, ƙazamai, kucakai, an faɗa muku ina buƙatar haƙurin da zaku bani ne? Ku kalleku wasu gajoji daƙiƙai daku. Maza ku hau layi." ta faɗa tana ɗaukan ɗaya daga cikin bulalin bishiyar da aka zubar mata agaban ta, tuni jikin su ya ƙara ɗaukan rawa, masu raunin xuciya kuma sun fara kuka acikinsu.


"Jiranku nake, kada ku ɓata min lokaci." nan suka shiga ture-ture wasu na baya wasu na gaba, ganin hakan yasa Ismaha Zainab miƙewa ta nufi gaban ta. Kallon ta Siniyo Jimmai tayi cikin mamakin abin da ya kawota wajan awanan lokacin, duk da gabanta ya faɗi, sanin cewar ita ba mutum bace kusan zata kirata da Aljanah ifirituwa, Amma hakan baisa ta nuna ba asalima fuska ta tsuke, cikin shan kunu da dakiya ta fara magana "Ke kuma Uban mi kike anan wajan? Ba nace kowa ya tafi ɗakinsu ba?"


Kallon ta Ismaha Zainab tayi sama da ƙasa kafin ta riƙe haɓarta, kamar mai tunani "Naga ke ɗaya ce zaki dakesu duk da suna da yawa." Kai ta gyaɗa tana aika mata da harara murya ta rage sanan ta ɗan yafito ta da hannu "Bakya tsolon hannun ki yayi miki ciwo?"


Takaici ne ya kama siniyo Jummai, dan da fari ta ɗauka wani abun arziƙin zata faɗa mata, harda rage murya "Abin da yafi gajiya zanyi, shegiyar yarinya mai siffar aljannu, idan baki matsa ba ta kanki zan fara dukan." ta faɗa cikin kurari ba dan zata daketan ba, dan har yanzu bata manta wuyar data shaba wajan dukanta.


Baki Ismaha Zainab ta ɓata cike da jin haushin zagin da Siniyo Jummai ta mata, ta juya ta fara tafiya, kallonta takai ga Sa'adatu wanda ta haɗa kai da gwuiwa tana rafka kuka ita haushintama takeji, tafi kowa ragonta da saurin kuka.


Ji tayi ta ƙara musu tsawa, saida taga akwai tazara mai yawa tsakaninsu sanan ta kirata "Ke Tuleliya mai Mulyal ƴan kashi kinga." da sauri Siniyo Jummai ta kai kallonta gareta, gani tayi ta haɗa hannunta ta ɗora asaman kanta alamun ƙaho sanan taja kunnenta ta buɗe hancin ta, sanan ta ɓaye baki tayi wani ihu "Jaki-Jaki ai dai a Aji ance ke kike zuwa ta lamba ta kashi. Kuma mugu azzaluma ce kika ce ina kama da Aljannu, ai dai bani ba, tunda bana shan jinin mutane." tana gama faɗar haka ta fara tsalle gami da juya ido, dariya sosai ƴan Aji biyar suka kwashe da ita, sauran masu kukanma suke neme shi suka rasa sai dariyar da suke. 


Ina rami na Afka, haka siniyo Jummai taji, kunya da tsananin ɓacin rai suka dirar mata alokaci ɗaya, yarinyar nan ta rainata sosai, shaƙiyancin ta ya wuce na sauran ɗalibai sabin zuwa, sai rashin kunya.


Afusace ta nufeta gadan-gadan da zuman dukan ta, zuciyar ta na ingiza ta.

Dariya Ismaha Zainab take mata da gwalo dan ta ƙara tunzura ta, bata guduba asalima kamar da take jiran ƙarasowar ta tana yin tsalle-tsallenta.


Sai da tazo kusa da ita taji tayi karo da wani abu kamar fasashshiyar kwalba, wata azaba ta fara ji tun daga tsakiyar kanta har zuwa ƙafar ta, tsugunnawa tayi tana dafa ƙafar ta, cikin ƙaraji da Ihu ta ƙwalla ƙara "Wayyo Allah na shiga uku! Wayyo ƙafata" kalmar data faɗa kenan, lokacin da idon ta yayi tozali da babban ɗan yatsan ƙafar ta na faman reto, alamun ya yanku saura ƙiris ya faɗo.


Kuka taci gaba da yi tana riƙe da kan ta da ƙafar ta, hakan yaja hankalin ƴan aji biyar ɗin data ware suka nufe ta, dan ganin abin da ya sami ƙafar ta. 


Ƙarasawa kusa da ita Ismaha Zainab tayi tana yamutsa fuska, cikin nuna tausayinta agareta "Ayya Tuleliya Anty Sannu kinji." bata kulata ba taci gaba da jijjiga ƙafar ta, murya ta rage ahankali sanan ta fara magana "Luyya ta sanar dani cewar "Ita Faɗaɗawa rayuwace, tsukewa kuma mutuwa ce. Rayuwa itace yiwa kowa fatan alkhairi, son wawushe komi wa kanka babu komi acikin sa face halaka." Uhm kingani Tuleliya dake amma tun kan aje ko ina, ɗan aikenki ya dawo gareki." ɗagowa siniyo Jummai tayi tana kallon ta cikin mamakin maganar yarinyar, zuwa lokacin kuma sauran yaran sun kewaye ta, takaici da kunyar kanta ya kama ta, ga dai yarinyar nan tun haɗuwar su bata huta ba, kawai an kawo mata masifa dan kamar ita aka kawowa makarantar. 


Jin sautin muryar ta tayi cikin kunnen ta, kamar tana faɗa mataa abin kirki "Kina jin zafi ko? Duka wanda kika tara da zumma dukan su suna jin haka tun kafin ki dake su, sharri Azzalumi ne idan ka siyar da ruhinka ga shekaɗan inuwar sharri ba zata taɓa barin ka ba."


 Tana gama faɗar haka ta miƙe tana kiran "Akaita asibitin makarantar." 


Nan ɗalibai suka taimaka mata, ƙafar ta sai faman jini take, ta taka ma ya gagare ta, gata ƙatuwa. Suna tunanin yanda zasuyi da ita saiga Sauran Siniyas ɗin musaman firifawan makarta da shugaban ɗalibai Shamsiyya "Ya Allah! Garin yaya hakan ta faru Jummai?" Ta tambaya tana saita kallon ta ga sauran jiniyas ɗin, kai suka sunkuyar dan duk wanda ya buɗe baki da zummar yayi magana dariya zaiyi, ita kuma Jummai baki yaƙi buɗuwa sai hawaye ne yake zuba, idan kuma ta kai kallon ta ga yatsanta da ya kusa cirewa, sai ta ɓarke da ihu kamar saniyar da ke jin yunwa.


 "Biyoni tayi zata dakeni, shine fe kawai tayi karo da fasasshiyar kwalba, ta karceta." taji muryar Ismaha Zainab tsagal agabansu tana magana cikin nuna jimami da alhini.


Kallon ta siniyo Shamsiyya tayi tana son ta tambayi mi ya kawota wajan, amma kuma ganin yanda Siniyo Jummai ta fara Jikkata, yasata tace suyi sauri akaita phamacy.


Nan aka kwasheta kamar kayan wanki tangire-gire aka mata wasu suka riƙe ƙafar ta, wasu kuma hannyen ta, dan tace ƙafarta bata takuwa.


*****

Janta take tun ƙarfin ta akan tazo su bar wajan, gefe ɗaya kuma Hauwa Ahmad keta faman waiwaye idan sun haɗa ido ita da Ismaha Zainab sai su tuntsure da dariya. Fizge hannunta tayi daga janta da take "Ha'ah! Nifa na gaji Anty Sa'adatu." ta faɗa tana cuno baki, nan kuma ta tuntsure da dariya harda riƙe ciki, su dai sai kallon ta suke, Sa'adatu kam jikinta banda rawa babu abin da yake, tsoron ta bata san matakin da Siniyo Jummai zata ɗauka akansu ba kuma "Dan Allah Ismaha Zainab ki rufa min asiri, ki futa alamarin Siniyo Jummai."


Kallonta tayi tana yamutsa fuska kamar ba ita ke dariyar ba "Allah Anty Sa'adatu ke kike tsoronta, wai dama haka kike raguwa da tsoron duka?" murya ta rage ta ɗan sunkuya tana musu alamun suma su sunkuyo, kamar umarni suka haɗa kai atare "Nifa na tara ƙasa da yawa nasa fasasshiyar kwalba aciki dan ta taka. Lokacin da kika ce na tafi sai na koma baya anan naga kwalbar maganin ciwon ciki, shine na fasata na ɗauki ƙatuwar na ɓoye acikin ƙasa, sauran na saka ajakata. Shi yasa naƙi tafiya nake tsalle dan ta biyoni." tana gama faɗar haka ta tuntsure da dariya, suma suka tuntsure da dariya idan aka ɗauke Sa'adatu da cikinta ya bada sautin ƙara "Ismaha yaushe kika zama ƴar ta'ada?" ta faɗa tana ƙwalalo ido


 "Kin san dai mugunta babu kyau. Luyya kuma ta hanaki ai, babu ruwana nikam."


Baki ta cuno ta fara tafiya "To ai itama muguntar zatayi, kuma da na bari da yanzu tana laftar ku kamar jakkai." tana tafiya tana gunguni akan gobe ma ba ruwan ta da su, da ƙyar Hauwa Ahmad ta lallasheta tana mata godiyar taimakon da ta musu. Sai alokacin ta ware har suka ƙarasa ɗakinsu.


Cikin Abin da bai wuce mintuna biyu ba, labari ya warwatsu tsakanin ɗalibai, akan abin daya faru da siniyo Jummai, masu murna nayi masu kiran calama Allah ya kara, suma nayi.


 Wasu kuma suna kiran alhakin su ne, duk inda Ismaha Zainab tayi kuma ƴan Aji Biyar na kiranta suna nuna mata Soyayya dan itace sila, da yawansu ta birgesu.


****

Ido ta runtse hawaƴe na ta silala, haka kuma tana jin sautin Muryar yarinyar acikin kunnenta kamar yanzu take mata.

Kallon sauran firifawan tayi cikin jin takaici ta fara magana "Duk acikin ku babu wanda yake tsayawa yayi min kara idan lokacin duty nah yayi, amma kuma ni idan naku ne ina tsayawa kan jiki kan ƙarfi sai na fiku zaƙal-ƙalewa akai, duk dan ina son taya ku. Amma yau gashi sanadin dokar da aka taka min na kusa rasa ƙafata, ku sheda ne akan faɗa da zagin dana sha awajan malam Abdul saboda anyi rashin ruwa a kitchen."


Kai suke jin-jinawa dan sai da tayi fatik akan hakan, kuma ita ta cika ruwan "Kiyi haƙuri Jummai, Allah ne ya ƙaddara miki hakan, amma kinsan muma mukanyi ƙoƙarin tayaki idan buƙatar hakan ta taso, sanin kuma da mukayi anfi jin tsoron ki amakarantar yasa bamu tsaya ba yau." Firifet Laure ta faɗa tana tsume Fuska dan itace mataimakiyar ta.


Harara ta aika mata sanan ta yamutsa fuska "Ke dama ai bana sakaki alissafi Laure."


"To yanzu ya kike so ayi?" Siniyo Shamsiyya ta faɗa tana kallon ta, duk da tana da sanyi sosai amma yau kam ta ƙulu ganin ƙawar ta, aminiyar ta, acikin wanan halin.

Hawayen munafurci ne ya zubo afuskar ta, dan ta ƙara karya musu gwuiwa "So nake ku tayani ɗaukan fansa, muyi zagaye cikin dare mu daki jiniyas tun daga kan ƴan J.S1 har zuwa S.S2."

  

Tafa hannu Lateepha tayi tana girgiza kai "Baki da damuwa ƙawata, cikin daren nan ma za'ayi." ta faɗa tana kai kallonta ga Siniyo Shamsiyya dan taga ko zatace a'a. Kai ta sunkuyar sanan ta gyaɗa kai, ba zata iya yin musu wa Lateepha ba, haka kuma bata son awanan karon ta ƙara dasawa Jummai wani baƙin cikin. Shi yasa ta basu nata ƙwarin gwuiwar ganin duk sauran firifawa sunyi amana da maganar.


🥀🥀🥀🥀🥀

_Ayayin da duniyarka ta cika da sauqaqawa sai ka samu masu rangwantawa na dakon jiranka, idan kuma akace zuciyarka tayi faɗi sai ka tadda shimfiɗa mai cike da Yalwatuwa na jiranka. Abubuwa da yawa sukan faru ba tare da mun tsammaci zuwansuba kwatsam muke ganinsu acikin duniyarmu._

*Bazance na kaiba dan zai zama ɗagawa amma kuma ga wanda ya fahimci yaren yasan akwai Tsagwaran _GIRMAMAWA_ araina naji mutuntakar ta hauhawa na kuma ga girman da ya kamata ace na yabeshi, ba zan faɗi sunanba dan bana so duniya ta ɗauka ta kambamashi da abin da ya girmi matsayinsa, zuciya sirrin sirrintaka ce ga abu mai girma da cancanta wanan Kalmar ta fara zata kuma ci gaba da tafiya acikin duniyata muddum raina GIRMAMAWA*


#Um Nass

#Cmnts, Like nd share

#Da Amana

[2/16, 9:44 PM] Oum Nass: *🏌🏻‍♀ISMAHA ZAINAB💍*©By *😘Um Nass🏇🏼*


*® NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*
BABI NA ASHIRIN DA SHIDA(Page 26)Farin ciki ne sosai ya kama Siniyo Jummai, lokacin da taga duka firifawan na bin bayanta, hakan ya sa ta fara ɗana tarkon muguntar da zatayi ma jiniyas ɗinta, sai dai azuwa lokacin tana fargabar kada labari ya isa ga Ismaha Zainab.

    

 "Tunda an gama miki ɗinki sai ki tashi mu tafi ai." Siniyo Shamsiyya ta faɗa tana kafe Jummai da ido.

 Tashi tayi ba tare data tankaba, fatanta kada abin data shirya ya wargaje. "Muje to." bayan dai-daituwarta akan ƙafafuwanta, wanda ɗayar bata kaita ƙasa sosai ba. A zuciyarta tana aiyana irin kalar ramuwar gayyan da zatayi.

 Murmushi Lateepha tayi, lokacin da idonta ya sauƙa akan na Siniyo Shamsiyya. "Mun gode Dear."

Ɗan harararta Siniyo Shamsiyya tayi ba tare da tace komiba ta fice ta barsu anan, suna mata rakiyar dariya, dan su da kansu sun-san rinjayarta sukayi, har ta amince da bukatar dukan ɗaliban.

            

****

    Har yanzu a bangaren Sa'adatu hankalinta yaƙi kwanciya, jikinta yayi matuƙar sanyin dan tasan halin Siniyo Jummai, ba zata taɓa hakura ba, sai ta rama abinda aka mata.

 Fargabar rashin sanin abin da zata iya musu, shine yake ƙara faɗar mata da gaba, gashi Hauwa Ahmad itama ko ajikin ta itama. Abar batun Ismaha Zainab agefe, ita akwai ƙura akanta da zun-zurutun yarinta atare da ita, dan farin ciki take hankalinta kwance.


 Zuwan Hauwa Ahmad ya katsewa Sa'adatu tunaninta, zama kusa da ita Hauwa tayi cike da farin ciki, dan har yanzun bata bar dariyan abinda Ismaha tayi ba, idanunta nakan ismaha yanda take ta faman rubutu alittafinta, kamar ba wani abun da ta aikata yake damunta, sannan ta sake kallon Sa'adatu bakinta ɗauke da magana.

"Ya dai Yar uwa? Naga kin rafka uban tagumi hannu bibbiyu, kamar wanda labarin mutuwa ya isketa."


 Harara ta aika mata tana sauƙe ajiyar zuciya "Kinfi kowa sanin dalilin tagumina ai."

Ƴar dariya Hauwa Ahmad tayi, ganin yanda Sa'adatu ke son ɗora mata laifi akanta "Matsala ta ɗaya da ke, shine baƙin tsoron da har yanzu yake ɗawainiya dake. Nifa wallahi naji daɗin abinda Ismaha Zainab tayi ma Siniyo Jummai, badan ita ba da wallahi mun kaɗe har buzunmu. Qila da har yanzu bamu gama kukan tanadin muguntar da take shirin yi mana ba." ta kai ƙarshen maganar fuskar ta ɗauke da fara'a.


"Hmm! nikuwa bana farin ciki, dan nasan sarai Siniyo Jummai ba kyalemu zatayi ba, sai tarama abinda aka mata, tsorona ɗaya karsu hucce akan waɗanda basu-ji-ba-basu-gani-ba, dan nasan ta sarai da tanadin mugunta." Yanda Sa'adatu tayi maganar kaɗai, zaka kafahimci tarin damuwa da tashin hankali a tare da ita.


 Sai alokacin Hauwa Ahmad ta farga da shukar da sukayi a idon makarwa "kin faɗi gaskiya Ƴar Uwata, wallahi sam na manta da wanan ɗabi'ar ta Siniyo Jummai. Allah dai ya jisshe mu alkhairinsa."


 "Ameen" Sa'adatu ta faɗa tana rafka uban tagumi, ga wankin da ta ɗebo tasashi agaba, ta kasa yinsa.


      *****

"Wallahi yau sai munci kan dunduniyar malafar takalmin uwar yaran nan, ga baki ɗaya tundaga kan aji ɗaya har zuwa aji biyar, sai sun san sun taɓo mu, babu tausayi balle sassauci." Laure mataimakiyar Siniyo Jummai ta yanko wannan maganar, tana zuge ganyen bulalin da aka zargo musu. tana cin alwashin akan genaral dukan da zasuyi, dan ta bama Siniyo Jummai ƙwarin gwuiwa akan yaufa tana tare da ita.


     Lateepha ta amshi maganar daga bakinta, cike da zakewa da abinda zasuyi yau "Allah ya kaimu dare dai."

  Maganar da sukayi taja hankalin da yawa daga cikim ɗaliɓai, nan tsoro da dirar musu acikin zuciyarsu, da fargaba akan dare yayi.

Kafin wani lokaci maganar ta gama zagaye tsakanin sauran Jiniyas ɗin. 

 

Lokacin da labari ya isa ga su Sa'adatu sai da cikinta ya ɗuri ruwa. Kasancewar suna tare da Hauwa awanan lokacin "Ni dama nasan hakan sai ta faru, dole ba za suyi shuru su ƙyalemuba. Mun shiga uku!" Sa'adatu ta faɗa tana ɗora hannu akanta.

     Kallonta Hauwa Ahmad tayi, zuciyarta fal tsoro kamar zata faɗo.

 

"Yar uwa meye abinyi yanzu?" kallonta Sa'adatu tayi dan jin yanda ta jefa mata tambaya bayan itama bata san me zatayi ba.

"Hmm! Ai babu wani abin yi kuma, kin san yanda muke ido ganin muna da alaqa da firifet, kowa haushinmu yake ji. Gashi yanzu duka ya zama haɗaka." 

 "Amma dai..." ganin Ismaha Zainab tana zuwa gurinsu yasa suka datsa maganar babu shiri, suka zuba mata ido, ganin yanda take walwalarta, tana zuwa ta tura musu baki tana faɗin.

"Aunty Sa'adatu me kuke cewa? naga kuna kallona."

   "Babu kome Ismaha Zainab, kawai muna hiranmu ne." Hauwa ta bata amsa, murmushi tayi itama ta zauna gurinsu shiru sukayi suna tunanin yanda zasuyi da Ismaha Zainab, basa so ta ƙara haɗa musu wani bala'in.


    Haka sukayi ta juyayin Al'amarin har dare yayi, ranar abinci ƙin ciyuwa yayi awajan jiniyas ɗin makarantar, musamman wanda suka san da labarin dukan.


Hikima ce tazo ma Sa'adatu lokacin da zasuyi shimfiɗa, sai ta gyara ƙarƙashin gadonsu, ta sakama Ismaha Zainab kafitarta anan, sanan ta kare gaban da baggon kayansu. da zata kwanta suka nuna mata

gurin da zata kwanta.


    Taso tayi gardama akan ba anan ai take kwanciya ba, amma da taga fuskar sa'adatu babu wasa yasa ta tashiga ta kwanta har bacci yayi gaba da ita.


     ****

DARE:


Da dare bayan kowa ya kwanta, wasu sun kasa bacci, yayin da wasu zuciyarsu ya kasu gida biyu, suyi bacci in yaso idan akazo dukar sun tashi wasu kuwa karyatawa sukayi.


   Kusan karfe sha biyu na dare FIRIFAWA suka dira ɗakin su Sa'adatu, tuni ɗakin ya gauraye da ihun yara, dan takan wanda suke santa suka fara, ko wata firifet saida ta musu bulala aƙalla takai biyar, marasa imani aciki sune suke musu goma-goma, haka suka bi kwana-kwana suna fito da jiniyas ɗin da suke ciki, ba ruwansu da alaqar dake tsakaninsu da yayyansu. Idan kuma sukaga ƴan aji biyar ne to sai sun ruɓanya musu dukan da ya fi na sauran jiniyas ɗin.


 Daga nan suka bi kowani ɗaki suna zane su kamar Allah ne ya aiko su.


 Ko wani ɗaki sautin kukan jiniyas ne ya karaɗe shi, babu mai lallashin kowa, babu mai bama wani haquri acikinsu.

 Hakan ce ta kasance da ɗakinsu Ismaha Zainab, kukan da suke shi ya tasheta abarci, lokacin har an gama dukansu sun fita.

 

Kallonsu tayi taga sai kuka suke, takaici ya kamata, ta mirgino ta fito shimfiɗarsu "Wai mi aka muku kuke kuka ne?"


   Banza da ita suka yi da ita suka ci gaba da kukan su. Bata haƙura ba, ta sake tambayar su "Ku dai bakwa rabo da kuka wallahi, kun fiya ragonta da langwami kamar ba ƙatu-ƙatu ba." ta ƙarasa maganar tana yatsina fuska, dan yanzu kam haushinsu take ji sosai akan saurin kukansu, musamman ma Sa'adatu.


Qin kulata sukayi, dan har yanzu jikinsu na musu zafi, ganin sun ƙi bata amsa yasa ta jin haushi tace "Toh! Ai shikenan karku faɗa ɗin, kuyi ta kukan kawai."


   Tana rufe bakinta taji sauƙar bulala ajikinta, ihu ta ƙwala, kafin ta dawo daga duniyar zafi da azaba ansake kara mata wani, juyawa tayi cine da tashin hankali taga waye yake mata irin wannan azabar, bata santa ba, dan sauran firifawan sunyi nasu sun gama, sanan Laure ta zo ƙari daga baya, ita kawai bulala uku-uku take musu ta wuce, amma akwai zafi sosai acikin bulalarta, acewarsu har ƙashin mutum take ratsawa saboda zafin hannunta, shi yasa da wuya ta daki mutum sai ya kaita maƙura.

 Karon farko tun zuwanta da aka mata duka har ya ratsa jikinta, tsoro da firgici yasa ta fashe da kuka tana tsalle, saboda azabar dukan Laure.

 Tana gama mata ta yima su Sa'adatu ta ƙara gaba abinta, sai faman kuka suke, wanan bulala ukun tafi guda hamsin ɗin da aka musu zafi adaren yau.

 

 Kallon hannunta Ismaha Zainab take, tana sosa bayanta tana dariya "Wayyo Luyyah! Sun kashe ni da raina." kalmar da take ta faɗa kenan tana tumami akwanar tasu, kukan nata ma sai ya fi basu dariya wai danma uku rak aka mata.


 ****

Washe-gari Litinin:


 Ko wani ɗalibi yayi wankinsa, manyan kuma harda masu guga, sai sauri suke su fita da wuri sananin yau akwai wani tanadin da aka musu. 

 Sai dai ƴan aji biyar acikinsu tun daga ƙofar ɗakinsu aka tilasta musu jan gwuiwoyinsu zuwa bakin get ɗin da zasu shiga school ɗinsu.

  Basu kuma da ikon ƙin yi dan akwai firfet ɗin ɗakinsu wanda suke tsaye akansu, dole suka fara jan gwuiwa suna hawaye.

 Ranar kam ta zame musu baƙar rana ajerin ranakunsu amakarantar, ƙafafuwansu duk suka ɗuri ruwa saboda tazarar da ke tsakaninsu.

 Wasu kuma acikinsu wandunansu saida ya fashe dalilin qaya da take kartarsu.

 Da qyar suke iya tashi gwuiwarsu ta riqe sanadin dukan ruwan da take.

 Kuka kam sunyi shi, ganin yanda ƙafarsu ta ɗuri ruwa yasa Ismaha Zainab fashewa da kuka itama, tana ji kamar ajikinta ciwon yake, musamman ganin Sa'adatu sai shafa ƙafar take tana fifitawa, sanan tana ƙara sautin kukanta.

 Kai take girgizawa tana tauna fatar bakinta, idonta kuma ya sauya kala zuwa shuɗi-shuɗi, jikinta kuma ya fara rawa kamar aka kaɗa mata gangi.


 *****

HAƊEJIA


   Zaune take tana shayar da Hassan bayan Husain ya gama shan nasa yayi bacci, a zahiri idanunta nakan yaron, a baɗili kuwa zuciyarta naga Ismaha Zainab, kewarta da tunaninta sun hanata sakat, dafe zuciyarta tayi da taji tana bugawa da qarfi "Hasbunallahu wa ni'imal wakil." kalmar data faɗa kenan tana ƙoƙarin zare maman daga bakin Hassan.

 Kwantarshi tayi tana ƙara riƙe da saitin zuciyarta wanda har yanzu bata bar bugawa ba "Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un" kalmar da take ta faman nanatawa abakinta.

 

 "Lafiya maman ƴan biyu? Na ganki haka afurgice." Alh. Isah ya faɗa lokacin da yake shigowa ɗakin.

 Kai ta girgiza cike da jin nauyinsa afuskarta "Wallahi gabana ne yake ta faɗuwa. Ina jin tsoron wani abu na shirin faruwa da Ismaha Zainab adai-dai wanan lokacin."


 Murmushi yayi sanan ya zauna akusa da ita, yana shaƙar ƙamshin turaren dake jikinta "Ke dai kin sata aranki ne da yawa, shi yasa kike tunanin wani abun na faruwa da ita."

 Murmushi yayi yana kallonta tana sunkuyar da kai ƙasa "Ba haka bane Abu Usama. Kasan dai dole zan sata araina, idan kayi la'akari da sabon dake tsakanina da ita."

 Murmushi tayi tana jinjina kanta "Ko wani dare inaga tsayinsa saboda rashinta atare dani, nasan da ace tana nan zatayi murnar ganin ƙannenta." 

 

"Amma dai kin san ƴar fari ce ko? Ya kamata ki koyi kara akanta da kawaici."

 Hannu tasa tana rufe fuskarta, dariya sosai Alh. Isah yayi, sanin da yayi Ruqayyarsa ta sauya, tun bayan tafiyar Ismuha Zainab, kallum cikin maganarta da tunaninta, saɓanin abaya da bata taɓa yin maganarta sai dai idan tayi rashin ji ta tsawatar mata. Amma ko dukanta kayi ko afuska ba zakaga damuwa atare da itaba.🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀


_Tofah! Akwai cakwakiya zallah agaba, ku hasko min tarin matsalar da zata iya faruwa ga sauyuwar fuskar Ismuha Zainab. Kalma ɗaya tak ta isah ta qarfafa min gwuiwa akan magantuwa da kuma shimfiɗa kalmar *GIRMAMAWA* agareku._


 *Gayyata! Gayyatah! Ina farin cikin gayyatar en uwa da abokan Arziqi zuwa bikin Uncle ɗina da Za'ayi aranar Asabat mai zuwa. Yakubu Muhammad Ubali da Amaryar Maryam.....*


 Daga yau zaku jini shuru har tsawon wasu kwanakin, kasancewar hidimar bikin da zamu yi. _Saura naji an kirani da sunan Ganɗoki_ 😎
#NWA

#Ismaha Zainab

#Cmnts, like nd share

#Da Amana


   

©Um Nass

[2/16, 9:44 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY *😘Um Nass 🏇🏼*


® *NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION*


_Alhmdlh! Munyi biki lafiya mun kuma gamashi lafiya. Na gode da Addu'ar fatan alkhairin dana samu abakunan ku._


Babi na Ashirin da Bakwai (page 27)


Kwantar da Hussain tayi, ganin yayi barci tuni, sanan ta tofesu da Addu'a dukansu su biyu.

Ko wani motsin da take akan idon Alh. Isah yake, aransa yana girmama nutsuwa irin ta Ruqayya "Komi naki mai kyau ne Ruqayyah." Ya faɗa yana murmushi gami da kafeta da idanuwansa.


Ido ta lumshe ta buɗe su tarr akan nasa idon, sanan ta mayar masa da salon murmushin sa "Duk abin da kaga yayi kyau a duniya ta na tabbatar kai ne silar faruwar sa Abu Usama."

Kai ya girgiza ba wanan ne karo na farko da yayi yabo agare ta ba, ta dawo da yabon kansa, wanan yana cikin hikimar iya sarrafa harshe irin na Ruqayya, take kuma kwashe rabo mai yawa na muntutakar da yake yima sauran mutane.


"Har yanzu babu abin da ya sauya agareki. Lokuta masu yawa nakan ɓata lokaci wajan nazari da ganin wauta irin na mijin da yayi sake kika kuskure masa."

Mikin da yake zuciyar ta ya tada mata, kewar da tayi na gida da iyayen ta duk sun dawo, hawaye ke barazana sauqa akan idon ta tayi saurin riƙeshi, kana ta fuskance shi "Akwai ƙaddara wadda take rubuce acikin littafinmu, wasu lokutan mu ci karo da mai zaƙi, ayayin da kuma wata take tafiya da mugunyar ɗaci mai ɗatata zuciya da maƙoshi. Idan kuma ka saita fuskar ka ga kallon su Hussain zaka fahimci ƙaddarar data fitar da su atsakanin mu ita ce ta zama mafarin barin mahaifa tah!" Ba zaka ɗauka akwai damuwa ashimfiɗe akan fuskar ta ba, ayayin da take fidda ko wata kalma ta maganar ta ba. Amma kuma a baɗini ranta kamar wuta take jinsa, ga faɗuwar da gaban ta yake har yanzu ƙara ƙaruwa take.

Miƙewa tayi ta da sauri "Bari nayi alwala Abu Usama, wani abu na shirin faruwa da ni, wanda da alama ba na alkhairi bane."

Da ido ya bita har ta fice aɗakin, maganar ta akwai maƙurar gaskiya wanda babu son kai da son zuciya acikin ta, idan kuma yayi nazari ya fuskanci idan ta nufa kamar tana masa tuni akan ba dabara ko wauta ke sa mutane samu da rasa abin da yake mallakinsu ba, wani aciki ikon Allah ne. 

Bai ji motsin shigowar ta ba sai gani yayi ya fara sallaha, hakan ya sashi miƙewa ya nufi nasa ɗakin dan ya samu fuskantar wasu abubuwan da ke gaban sa. 


Ta daɗe tana Addu'a hawaye na zuba akan idanuwan ta, mafiya yawan Addu'ar tata akan Ismaha Zainab ne na nema mata kariya daga mugun abin da zai same ta aduk inda ya ke.


********

Ƙafarta ta fara jefa wa cike da gushewar hankali, ko ina ajikinta rawa yake da karkawa, amma abun mamaki babu wanda ya kula da jirkitawar kamanin ta, asalima hankalin su yayi gaba wajan kuka da fifita ƙafafuwansu.

Inda ta hango taron firifawa ta nufa kamar ana hankaɗa ta saboda saurin da take, taku uku ya rage ta ƙasa kusa da su, kamar ƙiftawar ido wani farin haske ya shige jikinta, tsayawa tayi cak kamar an dasata awajan, ahankali kuma numfashinta ya fara sassarƙewa nan ta tsugunna awajan tana dafe da ƙirjinta.


 Tahowa firifawan suka yi sai a lokacin suka ankara da wanzuwar su awajan "Kee!" Siniyo Laure ta faɗa kasancewar ita ce tafi kusa da ita. 

Bata ɗago ba balle suyi tsamanin ta jisu "Kan ubaccan." ta faɗa tana ƙoƙarin sauƙe bulala ajikin ta.

Ɗagowa tayi da idanuwan ta da suke gama hargitsewa saboda azabar da take ji aran ta, gefe ɗaya kuma ta kasa sarrafa kanta, wani abu ke shamaki da barazana da lafiyar ta, tana so ta ƙarasa tana ji an riƙe ko wata jijiyar da take jikinta.

 "Uban mi kika tsaya yi anan? Kinaga sauran ɗalibai ba kowa sai ke tabbacacciya shahararriya ko?" Siniyo Jummai ta faɗa tana fiffito da idanuwan tah, ganin yanda Laure ta tsaya awaje ɗaya.

"Ina-ga-fa bata da lafiya." Siniyo Shamsiyya ta faɗa tana ƙoƙarin ƙarasawa kusa da ita da fuskar tausayi.


Kafin ta ƙarasa kuma Jummai ta tare ta "Wasu lokutan ke kike siyo mana raini awajan jiniyas ɗinmu, taya kinaga yarinya fess da ita amma kice wani bata da lafiya? Tantama nake akan alaƙar da ke tsakaninki da ita. Mi kika ɗauke ta? Mi kuma kika ɗauke mu?"


Tsayawa Siniyo Shamsiyya tayi cak, juyowa tayi tana kallon Jummai da sauran firifet ɗin da suka tsaya suma suna kallon ta da alama jiran amsar da zata fito abakinta "Kamar ya? Wata banzar magana kike Jummai?"


"Uhm! Kinfi kowa sanin abin da nake nufi, ko wata rana kulawar ki akan yarinyar nan tana yawa, idan bata da lafiya mi zai tsayar ta anan? Kina ga idon ta fess akan mu."


 Magana take son yi amma kuma ta rasa abun da zata faɗa mata saboda ta kaici, ji tayi an dafa kafaɗar ta wanda yasa ta juyowa, Lateepha ce tana mata murmushin da bai kai zuci ba "Idan kina son ta ba sai kinyi haka ba, xaki nunawa duniya matsayin da take da shi awajan ki ba. Ki saurari zuciyar ki sai ki tsaya akan ƙafafuwanki. Na tabbata ayanzu bakya buƙatarmu kamar yanda kike buƙatar kasancewa da ita."

Tana gama faɗar haka ta wuce ta barta anan tana yima su Jummai magana akan su tafi lokaci na ƙurewa, da ido ta bisu da kallo tana girgiza kai _"Adai rayuwa irin ta makarantar kwana, ko yaya ka aikata kulawa da tattalin wanda ƴake ƙasanka sai an maka bahaguwar fassara"_ 

Ƙafafuwanta ta ja ta ƙarasa kusa da Ismaha Zainab wanda take tsugunne tana kuma riƙe da ƙirjinta. "Bismillahi" ta faɗa tana riƙo hannun Ismuha Zainab, akan neman tsarin Allah daga sheɗan wanda yake son rinjayar zuciyar ta zuwa mummunan alaƙar da take fatan shimfiɗawa tsakanin ta da yarinyar.

Kamar an jona mata shokin ɗin wuta haka Ismaha Zainab taji, cikin ɗan ƙanƙanin lokaci kuma nutsuwar ta ta dawo jikin ta, nauyin da take ji a ƙirjin ta ya ɗauke cak, baki ta wangale tana dariya ganin wanda ke kusa da Ita "Anty Mai Kyau." ta faɗa cikin muryarta mai cike da karaɗi.


"Mi kike anan ke ɗaƴa?" ta jefa mata tambaya tana ɗaga mata kai.

Juye-juye ta fara yi amma ganin babu kowa ya sata saurin tashi tana kakkaɗai jikin ta "Tare muke da su Maryam fa anan."

Kallon ta tayi, ta lura da yanda ta ruɗe a lokaci ɗaya "Tashi mu tafi kawai, kinga babu kowa anan." 

Tashi tayi ba tare da tace komi ba, suka nufi wajan Assambili kasancewar litinin ce, sauran ɗalibai duk sun hau layi baka jin motsin kowa, saboda tsayuwar firifet atsakan-kanin ko wani layi da yake wajan.

Sata tayi alayinsu tana murmushi ta shafa kanta "Ki daina bari ƴan ajin ku na ɓace miki."

Kai ta gyaɗa mata ba tare da tace komi ba, sai murmushin da take mayar mata da shi itama.


*********

Bayan mako biyu.


Alokacin ne aka gabatar da hutun ɗalibai bayan kammaluwar jarabar zangon karatu na farko.

Ismuha Zainab ta zo amatsayin ɗaliba ta biyar, acikin su 96 ɗin da suke ajin, ihun kuka take wai malamin ya cuceta duk ita take na ƙawayen ta jarabbawa amma kuma sun fita da maki.

Takaici da haushi ya kama sa'adatu ta bige mata baki "Gobe ma sai ki ƙara basu ai, uwar kinibibin tsiya."

Tana gama faɗar haka ta tashi ta barta.


Dole ta ƙunshe vakinta tayi shuru, ahaka suka ci gaba da shirya kayan tafiyarsu hutu gida.


Ranar Juma'a:


Duka ɗaukacin ɗalibai na murna da Ihun tafiya gida, ayayin da Ismuha Zainab take jin kamar ta wuntsula dan murna.

Cikin sa'a sai ga Usama yazo ɗaukanta shi da wani abokinsa, ai da murna taje ta tare shi. 

Ihu take tana maqaleshi wanda sai da ta kusa kadashi ƙasa "Dan Allah kiyi haquri ki sakar ni." kalmar da ya faɗa awahale, yana takaicin zuwan da yayi ɗaukanta, wanda Alh. Isah ya takura masa.

Sakin sa tayi sanan ta tuntsure da dariya "Kaga in-da ka zama tulele acikin wata ukun da nayi ban ganka ba?"

Kallon jikinsa yayi sanan ya girgiza kai "Ai dole, saboda babu ciwon kai agidan mu acikin wanan watannin."


"Ayya kace kun sha ciwon kai ban sani ba, amma dai ban da Luyya kai kaɗai kayi sa?"

"Ina kayan ki ne? Kizo mu tafi lokaci na ƙurewa, kin san yau Juma'a akwai xuwa masallaci agaba na."


Juyawa tayi da gudu tana faman rugawa Anty Sa'a kira, anan suka haɗu da Siniyo shamsiyya da Murna take faɗa mata anzo ɗaukan ta, sai an koma hutu kuma. 

Kai ta shafa mata "Muje na ga tafiyarki to. Mu sai anjima" 

"To" tace tana riƙe hannunta, anan suka haɗu da Sa'adatu har ta kai kayan su. 

Har mota siniyo shamsiyya ta rakata, suka gaisa da Usama da yake ya faman washe mata baki, sai da taga shigarsu mota ta risina ta ce ma Ismaha Zainab "Ki gaida min da Luyya sosai."

"Za taji in sha Allah, nima idan kije ki gaida min da maman ku." tana yalwata Murmushi akan fuskar ta, ta maida mata da martanin Murmushin ta.

Dariya Siniyo Shamsiyya tayi sanan ta girgiza kai, yarinyar nan akwai surutu, har motar su ta fita a makarantar tana tsaye tana ɗaga musu hannu.


 ******

Haɗejia loading........


🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀


#NWA

#ISMUHA ZAINAB

#CMNTS, LIKE, SHARE

#UM NASS

#GIRMAMAWA

[2/16, 9:45 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY *😘Um Nass 🏇🏼*


_FOLLOW ME ON WATTPAD @UmNass_BABI NA ASHIRIN DA TAKWAS (Page 28)Bata jira motar ta gama tsayawa ba ta fara ƙoƙarin buɗewa dan ta fice, hannunta Usama ya riƙe ya aika mata da harara "Ke mahaukaciyar ina ce da bazaki bari na ƙarasa tsayar da motar ba? Salon ki jaza min masifa ko?"

Baki ta turo cikin gunguni ta fara magana "Ni dai ba mahaukaciya bace."

Banza yayi da ita kamar bai jita ba, hannunta ta fizge ta futo amotar da ihu ta faɗa gida, tuni yaran sun cika ƙofar gidan suna ihun murna "Ismaha Zainab ta dawo" Ihun da suke sai ka rantse wani zaman daɗi suke da ita.

Har gida suka shiga da ita, wasu na ɗauke da jakar kayanta da kuma litattafan ta.


Ihu ta ƙwala da qarfi hangowar Luyya na fitowa a ɗakinta, qan-qameta tayi ta fara ihun murna kusan kada ita tayi saboda jin daɗi.

"Ya Rabb! Wanan ai sai ki kada ni." 

Sassauta mata riqon tayi sanan ta tuntsure da dariya "Nayi kewar ki ne Luyyah."


"Iya kewarta kaɗai kikayi banda mu ko?" Salamatu ta faɗa tana ɗago kanta daga jikin Luyya.

Fuska ta rufe sanan ta rungume ta "Ai har da ku duka Maman Usama" tana dariya take maganar, utama dariya take kafin tayi yunƙuri su Khadija suka ruqun-qumeta suna murna.

"Ku sake ni kada ku ƙarasa ni." tana qoqarin zare jikinta daga nasu.


Sakinta sukayi suka ware gefe ƙofar ɗakin Rabi anan suka fara mata albishir ɗin Luyya ta haifi Tagwaye maza, ihu tasa ta hankaɗe su ta shige ɗakin Luyya, suma suka bi bayan ta Yuuu kamar kaza da ƴar ƴanta.

 Kai Rabi ta girgiza tana dariya "Yau kuma sai ta Allah ai."

Sanan ta bi bayansu, lokacin ana rige-rigen ɗaukan su Hassan da sauri ta mutsu tsawa sanin Luyyah ba zata ce komi ba "Maza ku fito ku barta ta huta, kada ku tada mata yara." Nan suka fara qoqarin tashi suna dariya.

"Ku tsaya ku karɓi alawarku." jaka ta zuge ta ɗauka ledar alawa mai tsinke ta raba musu suna murna wasu na kiran sai sun dawo anjima.

Su khadija ma tafiya sukayi suka barta ta hauta, idan ta kalli Luyya sai ta kalli su Hassan "Wai Luyya duka ke kika haifo su"

 Murmushi tayi ta gyaɗa mata kai "Wai Allah sannu kinji." 

Dariya ce ta kama Luyya kafin ta harareta "Ki zo ga abincin ki kici."

Da sauri ta kwantar da su tana washe baki "Luyya kin ajiye min taliya"


Kai ta girgiza "Ke da kika gaji da cin taliya mi xakiyi da ita yanzu? Ni ban ajiye miki ba."


Rai ta ɓata tana ƙoƙarin fara hawaye "Ai dai ba yanzu nace na gajiba tun tafiyata, kuma ni Allah ina son taliyar."

Murmushi tayi ta janyo kwanikan dake jere agabanta ɗaya farfesun kifi ne manya da su, sai ɗaya kwanon da akayi mata jalof ɗin taliya da wake ne sai nama da dangin kayan ganyan da ya ƙara masa armashi. Gefe kuma jog ne mai riqe sanyi da aka dama mata zoɓo acikinsa da qanqara.

"Wow duk ni ɗaya Luyyah?" ta faɗa tana haɗiyar yawu.

Sosai ta bawa Luyya dariya ta gyaɗa mata kai "Ko kina son wani abun ne sai na miki."


Rungume Luyya tayi saboda daɗi sai hawaye "Ni dai bana son makarantar nan Luyya ki sauya min wata, kullum dukan mu ake ana zaginmu kamar jakkai."

Shafa kanta Luyya tayi "Ai kin bar damarki tun abaya, kiyi haquri ki ƙarasa daga inda kika fara."

Sakin ta tayi ta share hawayen ta, sanan ta share hawayen da ke zuba afuskar ta, murmushi tayi mata "Dama nasan yanzu bakya sona tun da kin haifi wasu yaran."

Tana gama faɗar haka ta janyo kwanon jalof ɗin Taliyar ta fara ci "Wow! Luyyah kinji daɗi kuwa. Amma dai ke kika girka ko."

Kallon ta kawai Luyya take ba tare da tace mata komi ba, sai murmushin da take aika mata da shi.

 "Oh ashe da rabon zan sake cin irin wanan abinci, kin sanfa tun da naje kullum sai na ƙirga adadin kwanakin da suka rage min."

Dariya tayi ta girgiza kai "Anty mai kyau tace na gaida ki, tana da kirki ita ce bata dukana amakaranta, har tace wata rana zata so ta ganki." tana ƙarasa maganar tayi murmushi ita ɗaya. 

Kai ta ɗago ta kalli Luyya da ta kafeta da ido sai kallonta take tana murmushi ita ɗaya, tsayar da cin abincin tayi "Luyya bakya magana sai kallo na kike."

Kai ta girgiza "Har yanzu kina nan da surutun ki? Nayi kewar surutun ki mai hawa kai da takurawa. Sai nake miki kallon sabuwar Ismaha saɓanin wanda na sani."

Ido ta ƙwalalo cikin mamaki "Ai na zama sabuwa Luyya?" sanan ta fara dudduba jikinta tana son ganin abin da ya sabunta ajikinta.


Dariya Luyya tayi mai sauti "Kin ɗan ƙara girma ne acikin wata ukun da ban ganki ba, sai dai kuma da naga kina walwala da santin cin taliya abin ya bani mamaki kamar ba ke kike murna da zaki huta da cin taliya ta ba."


 Dariya ta tuntsure da ita har tana ruƙe baki "Wai kin san kuwa tunda naje makarantar banga taliya ba. Sai wasu abinci marasa daɗi, idan nace xan kwatanta miki kamanninsu nasan har hawayen tausayi na zakiyi." tana ƙarasa maganar ta tuntsure da dariya, itama dariya Luyya ɗin tayi gami da girgiza kai.


"Wato har haka hawayen nawa yayi sauƙi ko?"

 Kai ta girgiza dai-dai lokacin da ta janyo kwanon farfesun kifi gabanta "A'a ko kaɗan. Kawai nasan kina sona da yawa, ba zaki juri jin labari marar daɗi awajena ba." 


 

Murmushi tayi ta sauya akalar hirar ta ta "Ya karatun ki? Inji dai baki tsaya kinyi hiririta acikinsa ba."


 Kai ta girgiza "Ba daɗi fa Luyya, babu mai min bitar karatu nah, hakan ya sa naji kewar gida sosai."


 Harara ta aika mata da ita "A taƙaice dai saboda rashin gida kin zama cikin aji ko?"


 Baki ta rufe tana girgiza kai "A'a malaman ma sun cuce, kamata yayi ace nazo ta ɗaya biyu saboda ƙoƙarin da nake, kawai sai suka yi min cuce wai nazo ta biyar fa."


 Murmushi Luyya tayi sanan ta fara buɗe jakar makarantar ta, tana duba littatafan karatu da rubutun ta, ko wanne da ta duba akwai rubutu haka idan an basu aiki tana yi, ɓangaran gwaji da jarabawa ma duk ta samu maki mai yawa.

 Murmushi tayi "Aima kinyi ƙoƙari sosai gashi cikin ku 96, amma dai zangon gaba ki daure ki dawo da makin lamba ta ɗaya."

 Kai ta gyaɗa tana dariya "Na gode Luyya."

 Kai ta gyaɗa mata alamar ƙarin bayanin godiyar da take mata, dariya tayi tana tattare kwanikan "Da daddaɗan abinci mana."

 Dungure ta tayi gami da ƙara faɗaɗa dariyarta, dai-dai lokacin da take fita da kwanikan abincin.


 Karo sukayi da Ya Zakar nan ta qwala ihun murna shima yana biye mata "Qanwata oyoyo, yanzu naji ana cewa kin dawo shine na garzayo na samu ƙanzon da aka rago."


 Dariya ta saki tana kiran "Cab! Aini ko a makarantar bana jurar cin ƙanzo."


 Dariya yayi yana nunota "kinga yanda kika dawo baƙa saboda cin ƙanzo?"

 Kai ta girgiza tana aika masa da murmushi "Ance dai idonka ya samu matsala baka banbance baƙi da fari."

 Ido ya ƙwalalo cikin mamaki "In ji wani maƙaryacin?"

 

 Dariya tayi sanan ta wanke hannunta anan suka baje da hira har sauran yaran gidan suka shigo, kowa dai ya nuna jin daɗin zuwan Ismaha Zainab musamman yanda gidan yayi marecin hira mai tsayi.

 Lokacin da Alh. Isah ya dawo da murnar sa ya fara magana "Yau dai nasan ba abincin dare agidan nan saboda sauran ƙanzon da aka dawo mana da shi."


 Dariya sukayi duka gidan sanan Ismaha Zainab tayi magana "Ai babu ƙanzon da yayi saura Abba. Ƙanzo yayi rana."

 Dariya ya saki sanan ya miƙo mata bakar leda "wanan gashi duka naki ne, ki yi yanda kike so, ki fanshe watannin da kikayi baku gana ba."

 Karɓa tayi da sauri wani ƙamshi ya ziyarci hancinta, tana buɗewa taga gasasshiyar kaza ce da kuma baru guda biyu shima gasasshe, ihu ta ƙwala da qarfi ta rungume Alh. Isah "Na gode Abba. Wai ashe rai kanga rai." ta faɗa tana sakinsa.

 Dariya duka suka sa sanan ya bata amsa "Muddum da rai komi mai sauƙin haɗuwa ne."

 "Abba ina tamu" Musa ya faɗa yana murmushi, miƙo musu leda biyu yayi "gashi taku data iyayen ku, amma kada aɗaukarma Ismaha Zainab ta-ta" 


 Anan fa hirar ta ƙara aramshi shima Alh. Isah ya zauna aka ɗora da shi "Yaufa ciwon kai ya dira agida, tun daga zaure ake jin sautin muryarku na tashi." Usama ya shigo yana magana.

 "Kai kuma kana tafiya kana manta sallamarka ahanya." Ismaha Zainab ta bashi amsa dan ta fahimci da ita yake, nan aka kwashe da dariya.

 Janyo ledar gabanta yake ƙoƙarin yi tayi saurin janyewa "Ko yara Abba ya hanasu ci, balle kai tulele da kai."

 Dariya su Khadija suka saka masa bakin ta ya buge "Ciwon kai kawai."

"Eh dai ban badawa Tulele kawai"

 Miƙa masa Luyya tayi "Rabi da ita Usama, wanan sai maganarka ta qare ita bata gajiba."

 "Aifa dan kamar ƙara mata surutu akeyi.

 Sauran yaran dai banda dariya babu abin da suke musu hadda Alh. Isa "Lallai yau gida yayi albarka, na manta yaushe ne muka zauna har haka akayi hira." Salamatu ta faɗa tana lunƙuma lomar kaza abakinta.

 "Gaskiya dai nima na manta hakan."Rabi ta bata amasa tana jinjina kai.

 "Ai tunda ciwon kai tazo to hira sai kun gaji da ita ma." Usama ya tare su da magana.

 "Allah bana so, Abba kana jinsaa fa."


 "Usama zamu ɓata, daga zuwanta baka kawo mata komiba sai zunzurutun tsokana."

 Baki ya riƙe "Nayi shuru."

 Daga nan suka ci gaba da hirarsu cike da nishaɗi.******


Dawowar Ismaha Zainab ya sauya ɗabi'a da halayya ta dan kullum ita ke share ɗakin Luyya da tsakar gidansu, sanan ta matsama su Khadija suma su sharo ɗakin iyayensu, tsakar gidan kuma saboda girmanta ita tare suke haɗuwa suyi. 

 Haka ɓangaran wanke wanke su uku suke haɗuwa suyi. Wani saɓi na farko wani na biyu har zuwa ɗauraya sukan sabinta tsarin tsakaninsu, khadija da Ismaha zainab sai kuma Hafsat duk da Khadija ta girmesu amma kuma tare suke ko wani aiki.

 

 Haka kuma tsokanar da take tayi sauqi malam Isubu har gida yazo azuwan yazo biko da jaje dan sau ɗaya taje gidan, kullum tana ƙunshe agida, saɓanin abaya da sai tayi sau uku huɗu.

 

Da sun gama aiki kuma tana ɗaki tana faman yiwa su Hassan aiki, kafin wani lokacin har sun fara ganeta,, dan wani lokacin har goyo da wanke musu jiki take kamar wata babbar mace.


 Ahaka hutunsu ya qare cikin lokacin da bai kai ya kawoba, kowa agidan sai da yayi kukan barinta gidan, saboda atsakan-kanin lokacin ta qara dasa shaquwa atsakanin yaran gidan, musamman da suke komi tare, zuwa islamiyya da kuma aikin gida.

 Har mota maqota ke miqo mata kuɗi suna mata fatan sauqa makaranta lafiya.

 Da kuka da komi ta shiga mota bayan doguwar nasihar da Luyya ta ƙara mata akana ci gaba da kula da karatunta.

 

 Kaugama ta ɗauka. Shiga ta biyu.🥀🥀🥀🥀🥀🥀 


 *Har yanzu akwai saqon da ya kamata ya isa, amma ban saniba ko nayi rakiyar hanya awajan isar da shi? Daga gareku nake buƙatar samun tabbaci akan iya adadin ƙwazon da nayi acikin wanan tafiyar.*


 _Zaku iya kankaro ko wata Kima da take mallakinku, sai ku magantu akan ra'ayin da yake naku ne, ni kuma zan baku kalmar da take daban acikin kalmomi dubu, ba yawanba abin da ta ƙunsa na zunzurutun alkhairan da take tafe da shi_


 *GIRMAMAWA*#Ismuha Zainab

#NWA

#UM NASS

#CMNTS LIKE ND SHARE

#DA AMANA

[2/16, 9:46 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©by *😘Um Nass 🏇🏼*


_FOLLOW ME ON WATTPAD @UmNass_


BABI NA ASHIRIN DA TARA (Page 29) Agurguje:


Komawar Ismuha Zainab akaro na biyu, bata kula harkar siniyi duk abin da aka sata da to kawai take binsu, karatun ta kawai take saboda ta cika ma Luyya burin ta na zamowa ɗalibar da tafi ko wacce ɗaliba ƙwazo.


A hankali rayuwa ta ci gaba da gara, kwanaki na ta gudu, ayayin da wanda suke matakin ƙananu su samu ɗaukaka izuwa manya.

Ismuha Zainab ta sauya daga Ismuha Zainab ɗin baya mai tsoka surutu da sa ciwon kai.


 Wata sabuwar Ismuha Zainab ce mai cike da nutsuwa da kamala, girmama manya da bawa yara hakkinsu amatsayinsu na qanana akanta.


*****

Bayan Shekaru Takwass.


Ƴan mata ne su uku suka fito daga BINYAMINU USMAN POLYTECHNIC hannayensu ɗauke da litattafai wanda yake alaqantasu da kasancewar su ƴan jami'a.


Biyu ne acikin su suke magana sai ta tsakiyar da murmushi kawai take yi, ahaka suka fito bakin titi suna neman abin hawan da zai kawo su gida.


"Yau fa zamu sha wahla samun abin hawa." ɗaya daga cikin su ta faɗa cikin alamun gajiyawa.


"Gara muna tafiya dan tsayawar mu anan kamar ɓata lokaci ne." Ɗayar ta bata amsa, wanda dama su ne suke magana tun fitowarsu a college ɗin.


"Aikuwa dai, gara mu ci gaba da tafiyar." nan suka ci gaba da tafiyar, har zuwa wanan lokacin ɗayar bata yi magana ba, sai dai yanayin fuskarta idan ka kalla kasan yanayinta babu daɗi.

 Wayar ta ce ta fara ƙara alamun ana son magana da ita, hakan ya sata dakatawa daga tafiyar da suke, suma tsayawa sukayi dan jiranta, murmushi tayi bayan ta ga sunan dake jinin kawayar ta kara akunnenta ba tare da tayi maganaba.

"Wai bakya jina ne ina magana?"

Murmushi tayi mai sauti sanan ta miƙa ma ɗaya daga cikin ƴan matan wayar karawa tayi akunnen ta dai-dai lokacin da ya sake magana "Kuna ina yanzu ne?"

 "Mun fito daga lacture, yanzu gida zamu taho, abun hawa ne yayi wahla anan Yaya Usama?"


Murmushi akayi daga ɗaya ɓangaran "Hafsat ke ta miqa ma wayar?"

"Eh! Yaya kasan hali ai yanzu magana wuya take mata." 

  

Dariya sukayi atare yace "Gani ahanyar dawowa, naje malam madori ne dama."

"Tam yaya sai ka zo."

Miqa mata wayar tayi tana dariya "Kawai sai ki miqo min waya ba tare da kinyi magana ba."


Dariya tayi mai sauti "So yake mu fara raba hali awaje, ni kuma kaina ciwo yake min."


"Ai kuwa gashi nan zuwa, dan yace daga malam madori zai biya ya ɗauke mu."

Kai ta gyaɗa ba ta sake magana ba, dai-dai lokacin da motar sa ta tsaya agaban su. Ƙarasawa su duka biyun sukayi sai ita da ta tsaya ta harɗe hannayenta aƙirjinta tana kallonsu.

  

Motar ya buɗe ya zuro da qafafuwansa ya fito yana murmushi, dariya ce ta kamata ganin yanda ya fito ɗan lukuti da shi yana faman shafa ciki "Chaii tulele Udama ina zaka kai wanan tumbin naka."


Harara ya aika mata da shi yana dariya shima, sanan ya kai kallonsa ga jikinsa "Wato har yanzu ba zaki daina ce min tulele udama ba ko?" 


Ƙwafa yayi ya jijjiga kai wanda hakan yasata saurin kama kunnenta "Yi haquri Yaya Usama angon Naja Luta baban Suhaima mai kyau."

 Haba nan suka fara dariya dukan su "Kirkinki kaɗan ne Ismaha, Anty naki ma baki barta ba kenan?"

"Ni dai muta fi gida Yunwa nake ji, ga kaina na min ciwo." tana qoqarin buɗe motar ta take magana, dan yanzu idan ta biye ma Usama sai su ɓata lokaci suna magana.


"Acici kazar gidan gona, ci ba qiba asarar gari, ina zaki ci daga ina kike ci, ke wai ko ƴar dauriyar nan ma bakya yi?"


Bata tanka masaba har ya fara tuƙa motar, game kawai take da wayarta ba tare da ta musu magana ba, duk da tana jin hirarsu jifa-jifa "Nifa mamaki ne yake kamani, har yanzu ban daina mamaki yanda ciwon kan gidanmu ya sauya sheqa ba."

"Kai yaya baka manta zance, kusan kullumfa sai kayi magana akan hakan." Khadija ta faɗa tana murmushi akan fuskarta.


Kai ya gyaɗa "Mamakin ne yaƙi barina har yanzu." ta ƙarasa maganar yana yin parkin ɗin motar sa dan har sun kawo ƙofar gida.

 Kafin ta fito taji an buɗe mata ƙofar mota, juyawar da zatayi sai taga Ya Zakar, baki ta buɗe cikin mamaki "Mutanen bauchi sauƙar yaushe?"


 Murmushi yayi yana kallon agogon Azurfar dake hannunsa "Qarfe 10:30am na safiyar yau na shigo"


Kai ta gyaɗa cikin gamsuwa da maganar tasa. Fitowa sukayi suka nufi gida atare sanan yayi saurin tsayar da ita kafin ta shiga gida.

Hannu yasa acikin aljihunsa ya miqe mata wani ɗan akwati wanda aka rufeshi da leda mai santsi da zubin fulawa ajikinsa.

Karɓa tayi cikin rashin fahimtar abin da ya ƙunsa "Minene wanan ya Zakar?"


"Wanan shine ya taso ni yau daga Bauchi, saboda na sauƙe nauyin da yake kaina." 

"Kamar ya kenan?" ta sake jefa masa tambaya cikin mamaki.


Murmushi yayi, yana gyara tsayuwarsa "Shekara tara goma kenan yau ina ajiye da shi, kullum ina tunanin yaushe ya kamata na baki, kin tuna wani mutum da kike kiransa mai Mulyal yala?"

Murmushi tayi saboda kullum tana tuna shi, wasu lokutan har mamaki take da take ganinsa amafarkin ta, wanda hakan na cikin dalilin sa shi aranta da tayi.

"Minene alaqarsa da wanan akwatin kuma?" ta sake aika masa tambayar tana murmushi, sunan sa na asali ya ɓace akanta.

 "Saboda shine mamallakinta, shi ne ya ɗaura min alhakin kula da ita har zuwa lokacin da girma ya riskeki, aqiyasina yanzu kina shekarar qarshe ta kammala H.N.D ɗinki."


Murmushi tayi ta gyaɗa kai "Na gode yaya Zakar."

"Nawa ne ladan godiyar?" 


Baki ta rufe sanan ta girgiza kai "Ka faɗi abin da kake so, zan baka shi mutqar bai fi qarfi na ba."


Ƙureta yayi da ido kamar zai ce wani abu sai kuma ya girgiza kai "Wani lokacin, har yanzu akwai sauran lokaci."

"Akan mi kake magana Ya zakar?"


"Ba komi, ki shiga gida zuwa gobe zamuyi magana da ke."

"Ok! Allah ya kaimu"

Daga haka sukayi sallama, har ta isah gida tana jinjina alqawali irin na yaya Zakar da kuma tarin kulawa da alkhairin da yake agareta, yunwar da take ji ma ta neme ta ta rasa, saboda farin cikin da take ji yana malala axuciyarta.


 "Nifa ina da ayar tambaya akan wanan alaqar da ke tsakaninki da yaya zakar ɗinki, lokuta masu yawa ina tsammanin anya ba rufa-rifa ake mana ba? Dan ni zallar soyayya kawai nake gani a idonsa." Usama ya faɗa yana ƙoƙarin tsokanarta, hakan ya sata tsayawa tana ƙwalalo ido, cike da mamaki.

  "Haba dai yaya usama! Ya zakar amatsayin yaya na ɗaukeshi, bana buƙatar wata alaqa ta shiga tsakanin ni da shi, idan ka ɗauke ta yaya da ƙanwarsa."

  Baki ya taɓe kamar mace "Ni dai ban yarda ba, kema kuma naga sonsa ai kike." nan su Hafsat suka tuntsure da dariya ita da Bilkisu. Dan tuni anyi auren Khadija, wanda aka haɗasu tare da Yaya Usama aka musu tare.

 Qafa ta fara bubugawa ta kai kallonta ga Salamatu "Mama kin ganshi ko?" tana shirin yin kuka, dan wani haushi ne ya cika mata zuciya, wai Ya Zakar take so.


"Kai dai Usama idan baka tsokani Ismaha Zainab ba baka jin daɗi, gashi tun ƙuruciya yanzu ka ajiye iyali amma baka bar tsokanarta ba. Tashi ka bar mana gida ƙaton kawai." Salamatu ta faɗa cikin son bin bayan Isamaha Zainab.

Ai nan aka sa masa dariya, shima miqewa yayi yana bibbige rigar sa "Ni dai ban san mi yasa ake min haka agidan nan ba, shi kenan dan nayi aure bazan sake agidanmu ba sai ance na zama ƙato." yana gama faɗar haka yayi waje, sai ka rantse fushi yayi amma hakan ba zai hanashi dawowa anjima ba.

Kyakkyawan sauyin da aka samu kenan agidan Alh. Isah kansu duka ahaɗe yake, dan Usama yanzu yana sahun matasa masu kuɗi da suke ci ta hanyar saida kifi ɗanye da kuma banda, musa kuma yanzu yana aikin jami'in tsaro a dutse, shima yana da matarsa ɗaya mai suna Sabira da ɗansu Khalil.

Sai Haruna da walidi da suke bautar qasa ayanzu.

 Alhmdlh Musa da Usama sun haɗa kansu wajan tallafa mahaifinsu sun qara qawata gidan nasu, ko wata mace an mata ɓangaran ta daban, ƴan biyun Luyya ma yanzu sun ajin qarshe amakarantar primary.

Luyya ta tashi daga sana'ar abinci ta koma saida kayayyakin atamfofi da shaddodi haɗi da takalma, saboda buɗin da aka samu da arziqin, sai dai lokaci zuwa lokaci takan samu kwangilar yin kayan biki kamar su cake da dibilan zuwa alkaki.


Suma su Salamatu yanzu kayan d suke siyarwa ita da Rabi sun samu ɗaukaka daga kaɗan zuwa katan-katan, ataqaice dai iyalin Alh. Isah suna cikin kwanciyar hankali da wadata mai yawa, dan tuni suma sun sauqe farali.

Acikin ko wata rana sai ya godema Luyya da zamowarta haske acikin iyalinsa har ta musu gatan samun ilimi, kishi kuma babu batinsa dan sun samu gatan ilimin addini ta haka suka kafa kishinsu cike da nutsuwa.


Wanan kenan


*******


Zuciyarta ke azalzalarta akan ta buɗe sakon, wanan dalilin ne ya hanata tsayawa ta ci abinci, duk da tarin yunwar da take azalzalar ƴan hanjinta.


Zama tayi akan gadon da Luyya ta fara warware takardar da tayima ɗan akwatin zagaye, wani qamshi ne mai daɗi ya cika mata hanci, nan taji zuciyarta, ta harba, ido ta lumshe ta buɗe sanan ta buɗe akwatin, ido ta gwalalo waje ganin haɗin sarqa da ɗan kunni da zobe ne na silver aciki, wanda suke ɗa zagayen zuciya acikinsu, da kuma ɗigon dutsin daimond ajikin ko wani, sai ƙyalli suke da haske, da ganinsu zasu ja kaya da ƙuɗi wajan siyansu, ido ta ƙwalalo waje cike da mamaki sanan ta dafe qirjinta da yake barazanar fita saboda tsoro "Na shiga uku ni Ismaha Zainab."

Tana ɗagosu wata ƴar takadda ta faɗo da rubutun da bai gaza layi biyar acikinta ba, saurin ɗauka tayi ta warwareta hannu na rawa _"Tafiya maganin gari mai nisa, shekara kwana, kyawawan mafarkai masu qawata nisa dare, acikin ko wata sa'a ina lissafi da kusantowar muraɗina gareni, ki yi murmushi, zanci gaba da jiyo sauti da amon muryarki aduk inda nake. Kii dakace ni."_


Ta karantar takaddar tafi aƙirga tana faman murmushi, ba kalmomi ne masu tsada acikin ta ba, asalima idan ta haɗa da sauran saqonnin samarinta qila ya zama masu rauni, amma kuma shekaru da dakon jiran da akayi wajan isar da shi gareta, ya sauya salon labarin da take ji take gani.


*"Ina dakon ka"* kalmar da ta faɗa afili kamar yana gabanta.


🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀


_Kalmar tayi sauqi da yawa ko? Ku tattara Kimar da ta zama mallakar kanku, sai ku aro juriyar da ta ke zagaye ko wata gaɓa ta yatsunku, ku magantu ku kuma haqiqance akan iya ra'ayin da yake naku acikin wanan shafin, nasan zaku iya saboda sauqin dake cikin abin da ya zama naka, akan wanda xaka tsammace shi._


*GIRMAMAWA*


#Ismuha Zainab

#NWA

#CMNTS, LIKE ND SHARE

#DA AMANA


  


  😘Um Nass🏇🏼

[2/16, 9:46 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY *😘Um Nass 🏇🏼*


Babi na Talatin (Page 30)


 Naɗe wasiƙar tayi ahannunta sannan ta maida ita inda take, kallon sarqar tayi da kyau, ahankali sai ta ke jin xuciyarta na bugawa da qarfi kafin wani lokaci kuma tsoro ya fara shigarta.

Ido ta rintse tana karanto duk Addu'ar da tazo bakin ta. Sai dai babu wani alamu da ya sauya hakan.

 Miqewa tayi tsaye tana riqe da kanta wanda take ji kamar zai faɗo saboda nauyin da ya mata, can kuma ya fara rinjayarta tilas ta tsugunna a qasa tana qara juye-juye, wani sauti taji mai qara da amo akunnenta, nan take ta rufe kunnuwan nata, amma kuma kamar ta kunna qaran ne sosai acikin kunnenta.


Kafin wani lokaci kuma jikinta ya fara karkarwa nan ta sulale qasa tana maida numfashi da qyar, har kuma alokacin kunnenta na rufe da hannun ta.

  

Shigowa ɗakin Luyya tayi, da sauri ta qarasa kusa da ita ganin yanda take jujjuya kai tana riqe da kunnen ta, girgiza ta take tun qarfinta tana kiran sunan ta"Ismuha Zainab! Lafiya kike."

Bata jita ba dan har yanzu kunnuwan ta na cike da ƙara "Hasbunallahu wa ni'imal wakil." Addu'ar da Luyyah tayi cikin jin tsoron abin da Ismaha Zainab take yi.

 Qaran ne ya ɗauke cak akunnenta, ahankali ta ɗago daga durquson da tayi, kana ta sauqe hannun ta da yake dafe da kunnenta.

"Luyyah!" ta faɗa cikin muryar wahla, wanda yasa Luyya jin faɗuwar gaba, musamman da taga idanuwanta sun koma jajir da su.

 "Lafiya kike?" ta aika mata da tambayar tana kafe ta idanuwanta.

Kai ta girgiza dan ko kaɗan ba zata iya tuna abin da take ji ba, sanan ayanda take jin laɓɓanta sun mata nauyi ba zata juri yin bayani ba.


Miƙewa tsaye tayi kamar zata faɗi, "Ya Allah!" ta faɗa tana jize bakinta.

"Mi yake damun ki ne?" Luyya ta aika mata da tambayar cikin tsoron amsar da zata fito abakinta, dan ayanda taga idanuwan ta da yanayin jikinta ya tuno mata da matsalar da take ta ɗawainiya da ita tsawon shekaru goma sha biyar da suka shuɗe abaya.


 "Nima ban saniba Luyya, amma ina jin haushin komi da zai gifta agare ni."


Cikin tsoro Luyya ta fiddo ido waje, sanan ta miqe tsaye tana ƙara kai kallonta ga Ismaha Zainab "Kamar ya kina jin haushin komi? Mi kika fi jin haushi ayanzu?"

 Kallon Luyya tayi sanan ta girgiza kai, tsugunnawa tayi ta ɗauko saƙon da Zakar ya bata, harda wasiƙar ta miqa ma Luyya "Shekara goma kenan tana jira nah, ɗazu ya Zakar ya bani amatsayin sauƙe nauyin da ke kan sa, sai dai ayanzu babu abin da na tsana kamar saqon da wanda ya aiko da shi."

Da sauri Luyyah ta buɗe ta karanta, kasancewar yanzu ta samu ilimi sosai ciki harda karatu da rubuta wasiƙa, saida ta karanta sanan ta kalli Sarƙar cikin tsoro da tashin hankali take juyata, tana kuma kissima adadin kuɗin da aka kashe wajan siyan ta da kuma girman wanda ya iya bayar da kyautar ta.

"Ya Allah!" Kalmar da Luyya ta faɗa kenan, cikin hanzari ta ɗauki wayarta ta fara lalimen wata lamba, sanan ta danna kira "Ina son ganinka yanzu nan." abin da ta faɗa kenan bayan an ɗaga kiran, sanan ta kashe wayar.


Zama tayi abakin gado tana dafe da kanta, tuna ni birjik marasa amfani ke ta safa da marwa acikin zuciyar ta, idan har akwai wani abu da yake da burgewa da kuma armashi ga rayuwar ɗiya mace budurwa to ba xai wuce wanan ba, amma kuma saɓanin tunanin kowa da jin daɗin su ga Ismuha Zainab hakan gazawa ce ko kuma baƙar duhuwar da take lilliɓe da ita ce take son dakatar da ko wani jin daɗi nata.

 Numfashi taja ta fuzgar da iska abakinta "Ni banga wani abin jin haushi anan ba, idan har na fahimci wanan saƙon kamar tun kina ƙarama yake son ki, haka kuma yana son labarin ya riskeki alokacin da tunaninki ya kai ki auna fahimci zuciyarki." Luyya ta faɗa tana kallon Ismaha Zainab wanda ta zauna kusa da ita tana dafe da kanta.


 Kai ta girgiza cikin nuna halin ko-in-kula ga maganar "Wanan shine babban kuskuren da nake ga yayi, duk da atsawon shekarun nan ina ganin kamanninsa suna xuwa min amafarki na har ma muyi hira, yanzu kuma da naga wanan tsohuwar ajiyar da sunan sa yasa ni jin tsanar sa, da duk wani abun da zai zo daga gareshi."

 Mamaki ne ya kama Luyya sosai wanda ta gaza ɓoye shi "A mafarkin ki kuma?" 

Kai ta gyaɗa tana murmushi "Eh!"

"Amma alokacin kina jin haushin sa ne?"

Kai ta girgiza mata "Ina son ganinsa ne awanan lokacin, har bana so na tashi abarci." sai ta ɗan yamitsa fuska kuma kamar taga wani abin ƙyanƙyami "Nifa na tsani ace ana SONAH Luyyah, amma kinga shima ya janyo na tsaneshi."


 Baki buɗe Luyya take binta da kallo, sai yanzu ta fara tunanin akan rashin zuwan samari zance wajan Ismaha Zainab, duk da ga Bilki da Asshe su maganarsu tayi ƙarfi, amma tafi tunanin ko lokaci ne baiyi ba shi yasa har yanzu babu wani alamu daga gefen Ismaha Zainab.


Kai ta dafe da qarfi kafin tayi magana ta tsinkayi sallamar Zakar ya shigo ɗakin.

Saurin dai-daita nutsuwarta tayi sanan ta nemi da ya shigo, dan wanan maganar Sirri ne babba agareta.

 Shigowa yayi ya gaida ta cikin girmamawa, itama da fara'a take amsawa sanan ya zauna.

 

 "Wani abu ne ya bani mamaki Zakar."

 Kallonta yayi cikin neman ƙarin bayani "Kamar wani abu kenan Luyyah?"

 Miƙa masa saƙon tayi cikin son ƙarin bayani akan sa"Da gaske ya ɗauki shekaru goma atare da kai?" 


 Kai ya gyaɗa mata, sanan ya mata bayani daga farkon haɗuwar su, da duk abin da ya faru har zuwa ranar yau da ya miƙa mata "Daga lokacin da ya bani saƙon nan nake ji kamar an ɗora min kaya akaina, ban taɓa samun nutsuwa acikin zuciyata ba har sai yanzu da na isar da saƙon xuwa gareta."


 Numfashi ta ja ta furzar da iska "Amma mi yasa tun awancan lokacin baka sanar dani ba?"

 "Saboda ina tsoron amanar da aka jingina ta akan kafaɗu na, ina kuma tsammanin idan har na faɗa miki kamar na ci amana ne, saboda zaki buƙaci ganin abin da yake ciki, ban taɓa sanin minene acikin ta ba duk tsawon shekarun da take da shi awajena."


 "An samu matsala sosai Zakar, ina jin tsoron abin da zai je ya zo akanta." ta ƙarasa maganar tana kai kallon ta ga Ismaha Zainab, da take riƙe da kanta, Kamar babu wanzuwarta acikin ɗakin.

 

 "Wata irin matsala kuma Luyyah?" akwai tsoro da firgici acikin maganar sa, musamman da ya kai kallonsa ga Ismaha Zainab wanda take lulluɓe da Hijab idanuwan ta arufe.


 "Ban san ya zan kwatanta maka ba, ummm ko ka sake haɗuwa da shi aduka tsawon wanan shekarun?"

 

 "Gaskiya ban sake ganinsa ba."

 "Ya Allah!"

"Mi yake faruwa ne Luyyah?"


 "Ina son maida masa da saqon sa ne."

 

 "Kamar ya?"

Murmushi tayi ta miqe akan ƙafafuwanta "Baka da hausa ne hala? Idan ka haɗu da shi ka gane shi, dan Allah ka kawoshi gareni."


 Dariya yayi shima dan shi maganar ta Luyya ƙara sashi aduhu take, miƙewa shima yayi tsaye "Allah yasa na ganshi to, bari na tafi naga yau sarautar mutumiyar akusa take."


  Dariya yaƙe Luyya tayi dan ko kaɗan bata jin daɗin yanayin da take ganin Ismaha Zainab acikin sa, haka kuma abin yana tsaye mata sosai aranta.

 


********

Dutse air pot:


 Jirgin da ya ɗauko fasinja daga Misrah ne yake sauƙa, kafin wani lokacin dafifin mutane sun fara ɗaɗɗaga kansu dan ganin ɗaya daga cikin wanda suka zo tarya.


 Bayan ya tsaya ne aka janyo doguwar matattakalar da xata sauƙaƙama masu fitowa hanya, ɗaya bayan ɗaya fasinjojin suka fara sauƙowa.

 Can kuma wani balarabe ya fito cikin shigar farar jallabiya kansa kewaye da hirami fari, hannun sa sanye da agogon baƙi, haka takalminsa ma baƙi ne sai sheƙi yake, da ganinsa kasan ya kashe kuɗi wajan haɗa su.

 Jakar da ke hannunsa ya ƙara tiƙewa ahankali yake rufe ido yana buɗe shi.

 "Ƙasa ta" ya faɗa cikin hausar sa da take tafiya da rauni, da kuma amo mai sanyi.

 Saƙƙowa yake yana baza idanuwansa manya dan ganin mutanen da yake tsamannin sun zo dan ɗaukansa.

 Murmushi ya saki alokacin da yayi tozali da Abban sa da Umman sa.

 Anasu ɓangaran kuma sai dudduba suke basu ga ko mai alamun ɗan su ba "Anya kuwa yai yace zai dawo Abu Musaddiq."

 Fuska ya kwaɓe cikin alhini da rashin ganin ɗan nasu "Tabbas wanan jirgin ya biyo, gashi har fasinja sun gama sauƙowa babu alamun mai kama da shi."

 Baki ta buɗe zatayi magana, sai dai ganin balaraben da ya rungume mijinta ya sata sakin baki cikin al'ajabi take kallon sa "Abba nah!"

 "Saurin ɗagoshi yayi yana ƙare masa kallo "Ikon Allah Musaddiƙ kai ne ka dawo balarabe haka?"

 Murmushi yayi bai ce komi ba ya koma ya rungumi Umman sa "Nayi kewar ku sosai Umma."

 Bayan sa ta shiga shafawa cikin murmushi da haƙoranta suke bayyana take shafa bayansa "Maraba da dawowa gida Yaron Abban sa."

 

 "Kai Umma kina ga ya zama ƙaton balarabe kike kiran sa da yaro har yanzu."

 

Sakinta yayi ya juyar da kallonsa ga mai maganar, ido ya fiddo waje cikin mamaki yake nuna ta "Umma wai Jidda ce haka?" ya ƙarasa tambayar yana riƙe haɓarsa alamar mamaki.

 "Eh mana, kai kuwa shekaru goma ba wasa ba ai."


 "Nikam ku shige muje gida, ayi ko wata hirar daga baya, garinmu da nisa" Abba ya faɗa yana buɗe bayan motar sa.

Nan itama Umma ta shiga motar, su kuma suka shiga ɗaya daga cikin motar dake tsakiyar ta su daɗin, motoci huɗun da suka zo taryarsu, biyu atsakiyarsu, daga nan suka ɗauki hanyar Haɗejia.🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀


 _Tafiyar ta dace da sauƙin da ke cikin ko wani amo na sauti dakan fita alokacin da aka so ko kuma akasin haka, nasan ko bance komi ba xaku fahimci karatun da ke ratsa dodon kunnuwan ku, ku magantu akan ra'ayin ku kawai, sai ku aro ko wata juriya da take mallakin ku, nasan hakan akwai sauƙi acikinsa, xan ci gaba da baku kalma mafi kyau acikin dubban kalmomi._


*GIRMAMAWA*#Ismuha Zainab

#NWA

#CMNTS, LIKE AND SHARE

#UM NASS

[2/16, 9:47 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


 ©by *😘Um Nass 🏇🏼*


® *NWA*


 _Ayayin da duniyar ka ta cika da kyautata wa sai ka samu masu karramawa agefe suna jiranka, wasu mutanen sukan bada lokacin su dan su giramamawa wanda yake tare da su, koda basu da alaƙa da su, ayau ina bada Kalmar Giramamawa ta gareki *FATIMA MOROKI* na gode sosai da tarin kulawa_


PAGE 31 Tafiyar awa biyu ce ta kawo su garin Haɗejia, tun daga ƙofar shiga garin Musaddiq ke wara ido, komi ya sauya an samu sauyi sosai da ci gaba agarin, ga dandazon mutanen da suke ta zirga-zirga kamar aranar kasuwar garin ke ci.

 

 "Masha Allahu." kalmar da yake faɗa kenan akan laɓɓan bakin sa.

 Har suka shiga unguwar su ta G.R.A nan ma wani sabon kallon ne, saboda kyawawan gine-gine na kece raini da suka fara masa mara ba da shigowa, hata gidan su an ƙara faɗaɗa shi da sabbin abubuwa na zamani ataƙaice tsarin gidan gaba ɗaya ya dawo wani kala daban.

 Murmushi yayi yana girgiza kansa ba tare da ya ce komi ba har suka shiga gidan.


 Yayi mamakin ganin ƴan uwa turum agidan suna jiran sa, kwarya-kwaryar liyafar dawowar sa aka fara yi, wanda hakan ba ƙaramin daɗi ya masa ba.

 Tabbas kowa yabar gida gida ya barshi, ya yarda da wanan kalmar ta hausawa, ayau ya jishi daban, ya kuma dawo sabon mutum.


 Bai samu kansa ba sai wajan la'asar liss, shima saboda mafiya yawa sun tafi gida jansu, agurguje ya shiga ɓangaran sa, yayi wanka ya shirya cikin farin yadi wanda aka masa aiki da baƙin zare, ya sa baƙar hula da baƙin takalmi, sai agoga baƙi da ya sa, sanan ya feffesa turare ajikinsa.

 Agurguje ya kalli agogon dake hannun sa, ƙarfe 5:30 na yamma, ɗan tsaki yayi ahankali, yana fatan Allah yasa ya kada dare ya masa.


 Fitowa yayi ya nufi sashin Umman sa, suna zaune a palo ita da Jidda da Abban sa wanda shima yau bai fita ko ina ba, da sallama abakin sa ya shiga palon, wanda turaren sa ya rigashi isah.


 Atare suka juyo suna kallon sa cikin mamaki Umma ta fara magana "Ina zuwa kuma haka da yamma sakaliyya?" 


 Kai ya ɗan sosai yana murmushi cikin muryar sa mai sanyi "Zan ɗan zaga garin ne Umma."


 "Amma ai ka bari ka huta kafin ka tafi ko? Duka awarka nawa da zuwa ko barci ba ka samu kayi ba fa."

 

 Murmushi yayi sanan ya kalli Abban sa da sauri yayi Murmushi "Ki barshi yaje ya dawo, tun da kikaga har yayi kwalliya haka, fitar tasa na da muhimmanci ai."

 Kai Umma ta gyaɗa tana murmushi "Ko dai ya samo maka suruka ne ba'a so naji?" Baki ta ɗan taɓe "Idan tayi wari maji ai."

 

 Kunya ce ta kama Musaddiq ya kalli Abba ba tare da yayi magana ba, mukulli mota ya miƙa masa "Rabu da ita ɗan Abba, su bari idan tayi warin sa ji amma ba yanzu ba."

 

 Fita yayi cikin hanzarin sa, mamakin gano shin da Umma tayi yake.

 Dariya Jidda tasa masa tana kiran "Yaya nah nazo na maka rakiya?" ko juyowa baiyi ba balle tasa ran zai amsa mata, hakan yasa su yi mata dariya, "Maganin ki ai" Ummah ta faɗa tana dariya.

 

 "Nima tsokanar sa nake Umma, yaushe xan bi Yaya nayi zaman kurame ahanya." ta ƙarasa maganar tana dariya, wanda suma suka tayata, daga nan suka kangara wata hirar wanda mafiya yawa akan halayyar Musaddiƙ ɗin ne.


*****


 Karo na uku kenan yana zagaya unguwar yana kara dawowa, komi ya sauya acikin unguwar, babu kuma wata sheda da ko alama da xai iya ganeta atsawon shekarun da suka wace.


 Birki ya take yaja ya tsaya, yana fuzgar da iska abakin sa, wani zafi yake ji acikin ƙirjin sa yana kuma ɗora laifin da wauta irin tasa, mi yasa tun farko bai karɓi Adireshin su ba? Babu wata shedar da ya taɓa karɓa wanda zai gane su awanan lokacin.


 Wayar sa ya zaro ya kunna bidiyon da ya ɗauke ta lokacin haɗuwar su ta farko maganar ta yaji tana kiran "Wayyo Luyyah na rabu da ganin ki na mutu."


 Ido ya fiddo waje cikin jin daɗi da farin ciki, saboda sunan Luyya da yaji yana ganin kamar ya samu gidan ne, haka kuma kamar matsalar sa tazo ƙarshe.

 

 Wajen da ya kaɗeta ya janyo yana ƙura masa ido, neman wata alama yake da zai gane wajan ko Allah zai sa ya tambayi Luyya ɗin, dan ayanda yaji sunan ta wani kala da ban yasan bazai yi wuyar samu ba.

  

 Waiwaye ya shiga yi yana fara duddubawa can ya hango mashigar lungun, sai dai ƙarin shagunan da aka samu da sabon titin da akayi alayin ya taimaka wajan ruɗar da shi. Ajiyar zuciya ya sauƙe mai nauyi "Alhamdulillah" ya faɗa yana tada motar sa, ƙarasawa yayi wajan shagon da samarin da yaga kamar mazaunin samari ne, tun ƙarasowar motar samarin suke binta da kallo, da yawa numfashin su har tsayawa yake, dan ko ba'a faɗa musu ba sun san ta ciyu Naira kuma ta koka, cikin nutsuwa ya fitowa a motar hakan yasa hankalin samarin ya ƙara iyowa kansa, da yawa suna kiran "Masha Allah, ko basu sani ba sun san balarabe ne dama xai shigi motar nan."

 Ƙarasawa yayi kusa da su yayi musu sallama cikin muryar sa mai sanyi, da sauri suka amsa suna rige-rige.

 "Dan Allah tambaya nake?"

Da sauri suka shiga kallon-kallo tsakanin su, jin hausa na fita abakin sa "Allah ya sa mun sani."


 "Gidan Luyyerh nake tambaya."


 Kai suka girgiza "Gaskiya babu mai irin wanan sunan na Luyyerh anan unguwar." wani matashi ya bashi amsa cikin bashi tabbacin tambayar da yayi.

 

 "Ya Rabbi!" Musaddiƙ ya faɗa cikin jimami da alhini.

 "Baka san sunan mijin ta ko wani daga cikin yaran gidan ba?"


 Kai ya riƙe yana shafa goshin sa kamar mai son tuno wani abu, can kuma yayi saurin yin magana "Tana da yarinya inaga sunan ta Ismuha Zainab."


 Da sauri wani ya tashi "ohh ce mana zakayi Luyya ai, yanda ka faɗa ne sai yayi kala da sunan ƴan gayu, gidan Alh. Isah gashi can abakin titi." ya ƙarasa maganar yana nuna masa gidan.


 Da kallo ya bishi yana sauƙe murmushi "Na gode sosai." hannu yasa a aljihun sa ya zaro kuɗi ya miƙa musu, da sauri suka karɓa suna ta rabtaga musu godiya.

 Har ya shige motar sa "Ina son baƙi irin wanan masu ƙamshin nera, ba wai ƙamas na ƙamure mai warin dauɗa ba." wanda yayi masa kwatancan gidan ya faɗa yana dariya, suma sauran matasan suka tayashi da dariya, anan aka shiga raba kuɗi, suna jinjina ƙarfin kirki da kuɗin mutumin, wasu kuma suna son sanin alaƙar da ke tsakanin sa da Luyya duk da sun san tana da jama'a amma wanan na Musamman ne.


 Lokacin da ya isa ƙofar gidan ya daɗe acikin mota gaban sa na ta faman bugawa, tunani yake akan ta ina zai fara, mi kuma ya kamata yayi awanan lokacin.

 Dafe zuciyar sa yayi da yaji bugun ta na ƙaruwa, kamar ance ya kalli ƙofar gidan ya hango wata matashiyar budurwa na fitowa, ido ya ƙwalalo waje cikin mamaki abin da zuciyar sa ke hasaso masa akan ita ce Ismuha Zainab ɗin sa, kai ya girgiza "Bana jin zata kai wanan girma."

 Saurin fitowa yayi acikin motar ya ƙarasa wajan ta, har zuwa lokacin ƙirjin sa na harbawa da qarfi da qarfi.

 "Assalama alaikum wa rahmatullah" ya faɗa yana kallon ta, da sauri ta juyo kallon ta ga mai sallamar, ƙuri ta masa da ido tana tunanin ina ta san mai irin muryar nan? Mai kuma kamar nan?

 Kallon-kallo aka shiga yi ita bata amsa masa ba shi kuma bai ƙara yin wata magana ba.🥀🥀🥀🥀🥀
#Ismuha Zainab

#NWA

#Cmnts, like nd share

#GIRMAMAWA


  ©Um Nass

[2/16, 9:47 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©by *😘Um Nass 🏇🏼*


_Follow me on wattpad @UmNass_


Page 32


 kallon-kallo suka ci gaba da yi tsakanin su ba tare da wani ya ƙara tankawa ɗan uwan sa ba.

 "Bakya amsa Sallama ne ƴan mata?" sautin muryar sa ta sake ankarar da ita, da kuma haƙiƙan cewa akan sanin mamallakin muryar.

Kallon sa ta sake yi sai kuma ta samu kanta da jin shakkar sa "Wa alaikumussalam" ta amsa masa sallamar sa, sanan ta fara ƙoƙarin juyawa dan ta shige gida.

 Duk wani motsin da take yana ƙara tuno wasu abubuwa acan baya, duk da sauyawa da shekarun da aka ɗauka amma kuma dole akwai wani abu da yake kyautata zato akan itace.

"Baby Ismuha Zainab" ya faɗa cikin muryar sa mai sanyi, cak ta ja ta tsaya, sai yanzu ta tuna ko waye, duk duniya mutum guda ne ya fara kiranta da haka, bayan shi kuma babu wanda ya sake kiranta da wanan sunan.

Juyowa tayi gaban ta yana luguden faɗuwa, mamaki gami da tsoro duk sun sauƙar mata alokaci ɗaya, bayan tsawon shekarun da aka ɗiba bata sake ganin sa ba, balle labarin sa sai atsakanin kwana biyu da Ya zakar ya kawo mata saƙo daga gareshi, amma kuma abun mamaki gashi yazo yana kiran ta ya ganeta.

 "Wanene kai? Ya akayi ka san suna nah?"


Hannayen sa ya harɗe akan ƙirjin sa yana murmushi, azuciyar sa yana hamdala da tasbihi ga Allah, wanda ya sauƙaƙa masa tarin wahalar neman ta.

"Ai kya bari mu gaisa kafin ki fara jero min tambayoyin ki."

Haushi ne ya kama ta sosai, ji take kamar ta maka masa mari, duk da ta gane shi daga yanda yake magana zuwa kamanninsa da ta sani abaya, sai dai haske da tsayin daya ƙara, muryar sa ta ƙara ƙanƙancewa fiye da abaya, ita har mamaki take ana samun maza da buɗaɗɗiyar murya amma shi tasa ta fiya sanyi da yawa.

 Hannun ta ta harɗe itama akan ƙirjinta tana aika masa da harara "To gaida ni mai muryar yara."


Ido ya waro waje cikin mamaki, kafin kuma ya samu kansa da murmushi, yana nuna kansa yana nuna ta "Ni zan gaida ki ma? Bayan kirana da kikayi da mai muryar yara."

Kai ta gyaɗa masa cikin gundura da magana da shi "Naga kamar kafi son yin gaisuwar ne fiye da abin da ya kawo ka, muryar ka ma tafi ta yara ƙanƙanta saboda su idan sukayi magana akwai ƙarfafawa acikin ta, kai kuma kamar wanda kullum yake rayuwa cikin barci." ta ƙarasa maganar tana cuno baki.


 Tunda ta fara maganar yake kallon ta yana kallo kansa, gashi ta ko ina yafita tsayi, dan tsaf zai ci abinci akan ta yana tsaye nan, amma kuma ko tsoro babu atare da ita take faaɗar magana.

Kai ya girgiza yana ƙara kallon ta "Baki sauya ba har yanzu? Na ɗauka surutun ki da tsokanar ki ya ragu, ashe dai suna nan" murmushi yayi mai sauti ya ƙara matsowa kusa da ita anan ta ɗan matsa baya cikin mamaki da fargabar abin da zai yi, risinawa yayi kusa da ita ta yanda tsayin su ya dai-daita "Jiran da nayi bai wadata ba har yanzu, daga ɗaƙiƙa na fara lissafi har zuwa shekara ina cike da zumuɗi da ɗokin dawowa ganin ki, gashi ina ganin ki na samu tabbacin ke ce, sai dai banbanci kaɗan da aka samu Waccan Ismuha Zainab ɗin tafi ki murmushi mai kyau, ta fiki iya magana mai daɗi, ki tambaye ta saƙona ya risketa awajan yayan ta? Idan ta ce miki eh, ki mata albishir ɗin dawowa ta gare ta, ki kuma bata tabbacin zunzurutun soyayyar da nake mata tun kafin ta san wacece ita, zan kuma dakace ta akan alƙalanci tsakanin mai kyau da marar kyau."

Yana gama faɗar haka ya juya da zummar barin wajan, da sauri ta sha gaban sa tana kallon sa, cikin jin haushin kalaman sa da maganar sa, tsayawa yayi yana kallon ta shima.

 "Tabbas saƙon ka ya riske ta akwana biyun da suka wuce, amma daga lokacin da tayi tozali da shi ta tsaneka tun kafin ta tuno kamanin ka."

 Da sauri ya dafe ƙirjin sa inda saitin zuciyar sa take buga da ƙarfi jin maganar ta, kallon idon ta yayi yaga tsantsar gaskiyar da take cikin maganar ta.

 Murmushi tayi mai sauti wanda da ganin sa najin haushi ne "Ka na mamaki ne?" ta aika masa da tambayar "Ina zuwa." tana ƙarasa maganar ta shiga gidan da ɗan saurin ta, bin ta yayi da kallo har awanan lokacin yana mamakin abin da kunnuwan sa suka jiye masa, bai gama tsinkewa da mamaki ba ya ganta ta sake dawowa hannun sa ta kama ta saka masa ɗan akwatin da ya bawa Zakar ya bata "Wanan shine saƙonka da ya riske ni akwana biyu, na dawo maka da shi saboda bana Son ka, bana son ko wani abu da zai gifta tsakani na da kai wanda zai alaƙanta ni da So! Bana so a soni! Na tsani ko wani namiji da zai ce yana so nah! Na tsani masu ɓata lokuta sun akan kalmar yaudara ta So! Dan Allah ka fita acikin rayuwa tah! Ina girmama ka karka bari na ma tsana ta sosai."

 Tun da take maganar ya ke bin idonta da bakin ta da kallo, tsoro da mamaki ne yake kama shi, zuciyar sa kuma sai bugawa take da ƙarfi-ƙarfi, _"mi yake shirin faruwa da ni ne?"_

 Tambayar da yake yima kansa kenan ba tare da ya samu amsar ta ba, ɗago da idonsa yayi yana kallon ta wanda itama kallon sa take bai fahimci irin kallon da take masa ba har ta juya zata koma "Ɗan tsaya dan Allah." tsayawa tayi ba tare da ta juya ta sake kallon sa ba, aranta tana jin ƙunci da ganin halin da yake ciki, sai dai kuma wani sashi na zuciyar ta na jin haushin sa da duk wani namiji musamman wanda zai zo mata da saƙon ina sonki.

 "Duk abin da kika faɗa min da gaske ne? Da gaske kike bakya so nah?" muryar sa ta ƙara sanyi sosai.

 Juyowa tayi ta kalle shi sanan ta aika masa da harara "Ya wuce wai tunda ga tabbaci nan ahannunka na dawo ma da abin da ka bani tsawon shekaru goma."


 Murmushi yayi mai ciwo kana ya ƙara sa kusa da ita, hannun ta ya kama ya ɗora mata sarƙar "Ki riƙeta amatsayin kyauta ba amatsayin abin da saurayi yake bawa budurwar sa ba, shekaru goman da tayi ba atare da ni ba ta sa min sa rai akan samun ki, amma kuma ƙaddara bata bani damar hakan ba, amma har yanzu ban fidda rai akan zan same ki ba, har yanzu zuciya bata rage wani abu daga soyayyar da nake miki ba, asalima duk abin da kika faɗa ya ƙara min ƙwarfin gwuiwa akan na ci gaba da son ki. Addu'ar da na daɗe inayi na tabbata ba zata faɗi ƙasa ban za ba, har yanzu baki gama sanin wacece ke ba, amma kuma ni nasan komi akanki ciki harda abin da ya hana ki so ni, xanyi yaƙi da shi har sai na tabbatar da zamana Mai Nasara akan sa."

 Yana ƙarasa maganar ya juyo da sauri-sauri ya shige motar sa, da matsanancin gudu ya fige ta kamar yanda ransa yake masa zafi da zugi.

  

 Da kallo ta bishi har ya ɓace ma ganinta, hannun ta ta kalla tana bin akwatin da ta bar mata, haka kuma ko wata kalma ta maganar ta na dawo mata sabuwa "Har yanzu ban san wacece Ni ba?" mi hakan ke nufi? Kai ta girgiza ta shige gida.


 Ɗaki ta nufa anan ta tadda Luyya tana duba littafin Addu'o'i ahannun ta zama tayi agaban ta kafin wani lokaci hawaye ya zuba ƙasa, wanda ya sauƙa akan ƙafafuwan Luyya, da sauri ta kalli inda hawayen ke xuba Ismaha Zainab taga tana faman zubar hawaye. 

 "Subhanallah! Lafiya kike kuka Ismaha?"

 Kai ta girgiza mata "Da gaske ne har yanzu ban gama sanin kai na ba Luyya? Har yanzu ban san ko ni Wacece ba?"

 Tun da ta fara maganar gaban ta yake faɗuwa, har ta zo ƙarshe sanan jikin ta ya fara karkarwa "Wa ya faɗa miki haka?"


 Ɗan akwatin ta ɗauko ta fara nuna mata "Wanda ya bani wanan kyautar yanzu muka rabu da shi aƙofar gida, na sanar da shi bana son sa da duk wani abun da zai fito daga gareshi, sai dai hakan bai dame shi ba, asalima ya sanar dani yasan komi dake tare dani wanda ya zama silar ƙiyayyar da nake masa."

 Hawayen idon ta ta share ta goge "Da gaske ne akwai wani abun da ban sani ba na rayuwa ta? Wane ne Baba nah da ya haife ni? Ina iyayen ki da ƴan uwanki da duka sauran dangin da zan kira ahali nah?"

 Mutuwar zaune Luyya tayi tun da ta fara maganar take kallon ta, cike da mamaki da tsoro gami da fargabar wata tambayar da zata fito daga bakinta.

 Jijjigata Ismuha Zainab take sautin kukan ta na ƙara ƙaruwa "Kinyi shuru Luyyah, Mi yasa kika gudo kika bar su? Mi yasa tun da kika zo ko bayanki bakya waiwayawa balle ki koma? Ina son sanin wacece ni Luyyah, bakya ga lokaci yayi da ya kamata nasan hakan?"


 Tana gama faɗar maganar ta kwanta tana kuka, hawaye ne ya shiga zuba daga idon Luyyah itama, tabbas ko waye wanan ya ɓallo mata ruwa, lokaci kuma yayi da ya kamata ta waiwayi baya, ta koma gida ta nemi yafiyar iyayenta duk da cewar su suka koreta, amma atsawon shekarun nan komi zai faru ya kamata ta koma ta gan su, ta sauƙe fargaba da nauyin da yake ɗawainiya da ita aƙasan ruhinta. 

 Wanan fargabar, wanan damuwar, wannan ruɗaɗɗan al'amarin da ke ɗawainiya da ƴarta ya kamata ya tsaya haka nan.

 Nauyi taji Ismaha Zainab ta mata, kafin ta farga ta zube agaban ta, idanuwan ta sun kafe sunyi sama, numfashin ta kuma ya ɗauke.


 Ƙara Luyya ta saki da ƙarfin gaske wanda ya janyo hankalin ɗaukacin mutanen gidan suka shigo ɗakin suma, dan ganin mi yake faruwa.🥀🥀🥀🥀🥀🥀


_Kuyi maleji da wanan, kuyi haƙuri akan jina da kukayi shuru, wasu al'amura ne suka sha kaina, yanzun ma bani da tabbacin ci gaba da kawo muku labarin akai-akai, sai yanda hali yayi dai, ngd_


 *GIRMAMAWA*#ISMUHA ZAINAB

#NWA

#UM NASS

#CMNT, LIKE ND SHARE

#DA AMANA

[2/16, 9:47 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©BY *😘Um Nass🏇🏼*


Wattpad @UmNass


Page 33


 Da hanzari Rabi ta ɗebo ruwa mai sanyi a friegh ɗin dake palon Luyya, aka fara yayyafa ma Ismaha Zainab, amma kuma ko kaɗan bata motsa ba, asalima kamar sun ƙara yayyafa mata wani abun da zai ƙara sanƙarar da ita.

 

Kai take girgizawa tana ƙara dunƙulewa awaje ɗaya, hannunta kuma duk adunƙule suke awaje ɗaya.

 Hawaye ne ya fara sartun zubowa a idon Luyya ga wani tsoro da fargabar da ke shigar ta.

 "Hafsat ɗauki waya ki kira min Abbanku yazo mu kaita asibiti." salamatu ta faɗa tana ɗora kan Ismaha Zainab akan cinyar ta, wanda tana ɗorawa take zamewa.

 "Anya wanan rashin lafiyar tata yana da alaƙa da asibiti Yaya? Ki kalli yanda take sanƙarewa tana ƙara dunƙulewa awaje ɗaya, kuma numfashin ta na fita akai-akai." Rabi ta faɗi maganar tana nuni da yanayin da Ismaha Zainab ke ciki.

 "Mi kike tunani akai?"

Kallon Luyyah tayi wanda har zuwa wanan lokacin tana dafe da kanta, bata ɗago ba, hawaye ne kawai yake zuba a idon ta, haka kuma tana jin wani abu na taso mata aƙasan ranta akan komawar su gida.


 "Ina tunanin Jinnu ke damun ta gaskiya."


 Shuru ne ya ƙara cika ɗakin, kowa da abin da yake saƙawa aƙasan ransa. 

 Shigowar Alh. Isah aruɗe shi ya kawo sauyin shurun da ɗakin yayi, domin tuni Hafsat ta kirashi awaya "Subhanallah! Mi ya samu Zainab ɗin haka?" ya faɗa yana ƙarasawa kusa da ita, hannun sa da ya ɗora ajikin ta yaji kamar ya taɓa shokin ɗin wuta, da sauri ya janye hannun nasa.

 Yana kallon ta har awanan lokacin hannunta na ɗunƙule kamar yanda take acure awaje ɗaya, ba ƙoƙarin da Salamatu ba tayi ba akan ta wareta amma abin ya gagara, ƙarshe idan ta kai hannun ta sai taji ana janta da shokin ɗin wuta.

 "Abin nata ne sai kurum Alhaji, munyi tsammanin ma suma tayi amma daga baya sai muka ga kamar shafuwar Aljannu." Rabi ta faɗa cikin ƙarfin gwuiwa dan duk an rasa mai bakin magana acikin su, Luyya kuma sai faman sharar hawaye take afakaice, batare data tofa nata batun ba.


 Da saurin sa ya tashi "Bari to na kira malam Ado mai ruƙiyya, dama yanzu na wuce shi a masallaci."

 Bai jira maganar su ba ya fice da saurin sa kamar xai wuntsula baya. *****

Tunda ya bar ƙofar gidan zuciyar sa ke ƙunci da tafarfasa, ƙarshe dai kasa yin tuƙin yayi ya samu gefe ɗaya ya tsaya, ahankali yake sauƙe ajiyar zuciya, wani abu kuma na ƙara tokare masa aƙasan zuciyar sa.


 _"Minene laifin sa? Wani irin zunubi ya aikata haka atsawon rayuwar sa? Bai taɓa tsammanin fuskantar turjiya da ruɗarwa daga Ismuha Zainab ba, amma kuma gashi komi ya sauya, aɗan ƙanƙanin lokaci. Ta daƙusar masa da ko wani sa rai da yake da shi akan ta da dukkanin wani farin ciki na rayuwar sa."_


 kiran sallahr da ake amasallacin kusa da inda yake shi ya ankarar da shi da gabatowar magrib awanan lokacin, fitowa yayi cikin nutsuwa ya nufi ƙofar masallacin, anan ya ɗauki buta ya ɗaura alwala kana ya shiga masallacin.

 Bayan an idar da sallah ya daɗe yana xaune har aka samu sauƙin mutane awajan, ya rage daga shi sai Limamin da ya ja su sallah, shima yana faman duba wasu litattafai ne.

 Magana ya fara jiyowa sama-sama hakan ya sashi ɗagowa kai ya kalli masu maganar, limamin ne da wani mutum bai ji farkon maganar ba sai ƙarshen amsar da Limamin ya bada "Banƙi ta taka ba Alh. Isah, amma yanzu nabar yin ruƙiyya saboda tsorata iyalina da akeyi, acikin su ma har yanzu idan na uwar gidana ya tashi ƙarshe garin take bari ta yanki jeji."

 "To amma Malam Ado baka san wanda yake ruqiyyar ba ka haɗa ni da shi?"

 Kai ya girgiza cikin son kawar da batun, dan aƙallah yanzu tsoron duk wani abun da ya shafi Jinnu yake, ba akan karan kansa ba sai akan iyalin sa da ake fanshewa "Gaskiya bana ce maka ga takameman mutum ɗaya ba, amma ka sake bincikawa agaba."

 

 Shuru Alh. Isah yayi yana dafe da kansa, tausayin Ismuha Zainab da halin da ya barota kawai yake ji.

 Tashi musaddiƙ yayi ya nufi inda suke, wani tausayi da haushin Limamin duk ya cika shi, ace yana da sani akan wanan yace yabar yi, saboda wata barazana ta banza da wofi, mi yasa bai bawa iyalin nasa Addu'ar kare kansu ba? Anya ma ya iya Ruƙiyyar da ake kukutawa ma.

 "Idan babu damuwa muje gidan sai na duba yarinyar taka" 

 Da mamaki Alh. Isah yake kallon sa, ganin matashin saurayi na maganar yin Ruƙiyya ko dai baiji abin da ya faɗa ba "Yaro jeka sha'aninka kaji, magana nake akan cirema ɗiyata aljannu ba wai zana mata jarrabawar makaranta ba."


 Murmushi Musaddiƙ yayi sanan ya risuna "Eh duka naji maganar da kukayi ai, idan ka shirya nemawa ɗiyarka magani da sa rai da waraka ka wuce muje na ganta."


 Cikin sanyin jiki Alh. Isah ya tashi, dan dai kawai ance ba'a ƙin ta mutum, amma banda haka da yaushe xai yi kasadar tunkarar wanan yaron da batu na iskokai, sai da suka fito waje kuma yaga kayan dake jikinsa da kyakkyawar kamannin sa gabansa ya shiga lugudan faɗuwa _"Shikenan ta faru ta ƙare, wata ƙila aljanin jikin Ismaha Zainab ɗin ne ya zo min asuffar mutum"_ maganar da Alh. Isah yayi yana goge gumin da ke fuskar sa.


 "Magana kake ne Baba?"

"A'a. Ina duba hanyar ne naga bata da kyau, kada ka ɓata kayan jikin ka."


 Kallon wajan Musaddiƙ yayi, yaga babu wani rashin kyan sa, asalima bakin titi ne da kwalta malale awajan, "Ba damuwa, idan ya ɓaci na wanke."


 "Na gode Allah."

 Ya faɗa dai-dai lokacin da suka ƙara so gidan, ido Musaddiƙ ya wara cikin mamaki, domin dai yasan nan ne gidan su Ismaha Zainab, ja yayi ya ɗan tsaya ganin yanda Alh. Isah ke ƙoƙarin shiga gidan.

 "Taho mana samari ai nan ne gidan."


 Shiga yayi yana dafe da zuciyar sa da take bugawa da ƙarfi, fatan sa kada ya haɗu da Ismuha Zainab ta sake sauƙe masa wani kwandon tujarar, ko kuma tayi tsammanin wata manufar ta kawo shi ta daban.

 Da tarin tunane-tunane ya shiga gidan ƙarƙashin jagorancin Alh. Isah dake ta masa kuwar ya shigo.

 Har sai da suka shiga ɓangaran Luyya yana biye da shi, sai wara idanuwa yake, amma baiji motsin kowa ba, asalima gidan kamar anyi mutuwa babu sautin komi dake gudana acikinsa.


 Dakatawa yayi daga bakin ƙofar ɗakin sanan ya sanar da Alh. Isah akan ya fara masa iso da mutanen gidan kada ya shiga kai tsaye.


  Shiga ɗakin palon Alh. Isah yayi cikin gamsuwa da bayanin yaron, ayanayin daya bar Ismaha Zainab ahaka ya same ta babu wani sauyi da aka samu na ci gaba, kowa yayi jugum-jugum a ɗakin.

 "To ku kintsa da mai Ruƙiyyar nake, yana ƙofar palo yana jiranku."


 Tashi su salamatu sukayi suka bashi waje wasu kuma suka yafa ɗankwalinsu suka lillaɓe jikin su da shi, sai Luyya data saka hijabi ajikin ta, ganin haka yasa su salamatu sake gyara nasu lilliɓin.


  "Shigo malam." Alh. Isah ya faɗa yana wara hannunsa da nuni ga ƙofar palon.


 Shiga yayi da sallama ɗauke abakinsa, kansa aƙasa yana jin bugawar zuciyar sa na ƙaruwa, amsawa sukayi cikin haɗin baki, amma kuma da mamaki suke binsa da kallo, musamman ganin sa da sukayi matashin saurayi, gashi kuma da ance za'a kirawo malam Ado mai ruƙiyya.


  "Wanan ce marar lafiyar?" cikin sanyin muryar sa yake maganar, yana nazarin halin da take ciki.

 "Eh itace." suka amsa masa cikin haɗuwar baki.

 Kallon Alh. Isah yayi sanan ya kalli tarin mutanen da suke ɗakin "Ya kamata su fita daga ɗakin, kai da maman ta sai ku tsaya ku riƙeta, abani ruwa akofi."

 Da sauri hafsat ta fita ta ɗebo ruwa akofi ta miƙa masa, sanan ta fita waje ganin kowa ya fice, ya rage Luyya da Alh. Isah, sai kuma malam Musaddiƙ mai ruƙiyya.

 Ruwa ya karɓa yayi Addu'a aciki sanan ya fara yayyafa ma Ismaha Zainab, wanda har awanan lokacin bai fahimci ita ce awajan ba, ƙara ta sa mai ƙarfin gaske tana ƙara miƙewa, sai alokacin yaga Fuskar ta, ido ya waro waje cikin mamaki, kafin ya ankare yaji an bige kofin dake hannun sa ruwan ya zube, cikin hanzari yakai kallon sa ga wanda ya masa wanan aika-aikar Ismaha Zainab yaga idon ta ya rikiɗe ya koma kalar fari da ratsin kore-kore ajikin sa "Ba munce kada ka dawo ba? Ko bakaji tace bata son ka ba? Miyasa komi sai kai? Mi yasa ka takurama rayuwarmu?" wata kakkausar murya ta faɗa cikin ƙaraji da jin haushi.

 Nan aka shiga kallon-kallo tsakanin Luyya da Alh. Isah suna kuma kai kallon su ga Musaddiƙ ɗin.

 "Mi hakan yake Nufi?"🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀 _Taku kaɗan ya rage mu kai ga gaci, koda bance komi ba kun fahimci zunzurutun muhimmanci dake cikin wanan tafiyar, kalma guda mai amo wanda take fita da umarninku ta wadace ni, ku himmatu ku kuma magantu akan dai-dai da rashin sa acikin Kimar da take taku wanda tafi ko wacce, akan hakan zan ɗauko mafi kyau da soyuwar kalma agare ni *GIRMAMAWA*_#ISMUHA ZAINAB

#NWA

#UmNass

#Cmntns, like, and share

#Da amana

[2/16, 9:48 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©by *😘Um Nass 🏇🏼*


_Follow me on Wattpad @UmNass_


Page 34


Murmushi yayi bayan ya gama sauraran abin da Aljanin Ismaha Zainab ya faɗa, ba tare daya yi magana ba ya fara karatun ruƙiyya, nan ta fara ihu da murgine-murgine, sautin kuka kala-kala wanda yasa Luyya tsorata ga wani tausayin Ismaha Zainab daya kamata, ganin yanda ta fara bubbuga kanta aƙasa.

Miƙewa tsaye Musaddiƙ yayi yana buɗe Muryar sa da sauri-sauri yake karatun hakan yasa Ismaha Zainab dunƙulewa awaje ɗaya, kukanma ya gagara sai matse kanta da take da hannun ta.

"Dan Allah kabar karatun nan kana ƙona mu, kayi haƙuri zamu fita yanzu." cikin wata wahalalliyar Murya wanda Amon ta yake fita da ƙarfi-ƙarfi akayi maganar.


Shuru yayi sanan ya zauna yana fuskantar Ismaha Zainab da take duƙunƙune wanda azahiri take nan, amma abaɗini mutanen kanta ke kusa.

Fuska ya tamke sosai cikin dakakkiyar muryar sa da take fita da ɗan ƙarfi, duk da sanyin ta amma jin sautinta kan iya sa buguwar zuciya "Mi yasa kuka shiga jikin ta? Tun yaushe ne kuke wahalar da ita haka? Aiko ku akayi ko kuma ku kuka aiko kanku?" tarin tambayar da ya musu wanda tasa Ismaha Zainab ɗagowa idanuwan ta har yanzu ahargitse suke gwanin tsoro, harara ta aika masa sanan ta mayar da kanta ba tare da tayi magana ba.

Kai ya gyaɗa sanan yaci gaba da karatu, nan tasa ihu da kururuwa "Nace kabar ƙona mu, kasan shekarun da nayi ina jikin ta? Kana ina nake bata kariya aduka tsawon shekarun ta? Haba ka tausaya min mana, ka min adalci akan ta." cikin murya mai wahala da sauti marar daɗi ake maganar.

 "Naga kamar kafi son na ƙona kan ai, wani adalci kake magana bayan wahalar da kake bata da iyayen ta."

"Ni ban taɓa bata wahala ba. Asalima kariya nake bata a iya tsawon rayuwar da mukayi tare, ko iyayen ta basu san da zamana atare da ita ba saboda kawar musu tunanin da nake yi, amma lokaci ɗaya daga zuwan ka komi nawa ya taɓarɓare, kasa abun da na fusata har na zo kowa ya gane."

Kallon-kallo ake tayi tsakanin Alh. Isah da Luyya suna mamakin maganar da Aljanin yake, a ina Malam ɗin ya san ta, asanin Alh. Isah da Luyya baƙo ne awajan su, kusan ma yau ya taɓa ganin sa.

Tunanin su ne ya katse lokacin da sukaji Muryar Musaddiƙ na daka wa Aljanin tsawa "Ni ba wanan na tambaye ka ba, mi yasa ka shiga jikin ta? Abin da kawai na tambaye ka."

  

"Akwai wata rana da suka je gidan Innar kamalu, to alokacin Mamarta ta tafi tabarta agidan, bayan sun mata horon yunwa sun dake ta suka shanya ta arana, to alokacin ni kuma nazo wucewa kasancewar gidan hanya ta ce kuma akwai wani ɗan uwanmu awajan bolar gidan, duk abin da sukayi akan ido na wanan yasa naji tausayin yarinyar, musamman da naji Tani tana ƙoƙarin yi mata asiri saboda tafi yaran ta kyau."

"Hasbunallah wani imal wakil." kalmar da Luyya ta faɗa cikin karkarwar murya da tsoro, ta dafe ƙirjin ta da yake barazanar ɓallewa saboda bugawar da zuciyarta take yi.


"Daga lokacin sai na zama kullum ina tare da ita, nakan zo na jata muyi wasa awajen da ba kowa xai ganta ba, ahaka wata rana Innar Kamalu tazo da Tani suka fara yima Luyya masifa akan ta bar sana'ar ta, har suka fara jifa da kayan siyarwar tata, alokacin Tani tazo da ƙullin maganin da zata yima Ismaha Zainab asirin da babu wanda zai so ta, ƙarshe kuma ta shiga duniya da yawon karuwanci, to shine sai nazo asiffar Ismaha Zainab na zane su da bulala, sanadin da asirin ya karye baiyi tasiri akanta ba, to kuma a ƴan tsakan-kanin lokacin Idiris ya dawo daga tafiyar da yake, haka kuma su Tani da Innar kamalu suka tusashi da ƙaryace-ƙaryacen banza, bayan sun bashi ruwan da yake ɗauke da Asirin da xai tsani Luyya, aranar bana nan gaskiya ina ƙasar habasha na je duba kakana, koda na dawo rigimar sakin da yayi ma Luyya na tadda to shine na yanke kawai ta bar garin, na kuma ci gaba da hura mata wutar ƙiyayyar garin ta hanyar bin hanyar da babu wanda zaiyi tsammanin tana nan."

Tunda ya fara maganar jikin kowa yayi sanyi acikin su, musamman Musaddiƙ da ya cika da mamaki "Wacece Tani ɗin da Innar kamalu?" tambayar daya samu kansa da yima aljanin kenan, saboda girman lamarin da kuma abin da suka aikata ga Luyya.


"Innar kamalu kakar Ismaha zainab ce, wato wadda ta haifi babanta, ita kuma Tani matar babban ɗanta ne, dama kuma tana jin haushin sana'ar da Luyya take da samun da tayi, asalima ita ta shiga ta fita ta raba soyayyar da Innar kamalun take yiwa Luyya ta hanyar yi mata asiri. Tsawon waɗan nan shekarun da akayi nakan bawa Ismaha Zainab kariya ta sosai, duk wanda yazo da niyar cutar da ita nakan samu hanya mafi sauƙi da xan fanshe, hatta ƙiriniyar ta da rashin jinta na taimaka wajan haɓakar su, to nakanyi baya-baya saboda Addu'ar da mamanta take yawan yi mata alokacin, shi yasa ba kowa ya gane ina tare da ita ba."

Kai Musaddiƙ ya jinjina cikin gamsuwa da bayanin Aljanin "Amma kace baka cutar da itaba aduka yawan shekaru goma sha biyar ɗin da kake tare da ita?"


"Eh!"


"Mi yasa kasa mata tsanar ko wani namiji arayuwar ta?"


Kai ta girgiza cikin ƙosawa da tambayar tasa "Bani nasa mata wanan ƙiyayyar ba, asalima tana riƙe da ko wani hoto da cin zarafin da Mahaifinta yayi ma mamarta, da kuma abin da kakanta yayi na korarta agidan sa, wanan dalilin yasa take ga duka maza son kai gare su da rashin sanin haƙƙin mace, um......ummm sai kuma na taya ta da..."


"Ka taya ta da mi? Asanina dai shekarunta sunyi ƙanƙantar daa zata riƙe duk abun da ya faru wanan lokacin, taya kuma yanzu zata adar da shi? Har ta saka shi aranta? " ya aika masa tambayar afusace, wanda ta sa jikinta ya ɗauki rawa "Eh to! Ni na bata hoton abun da ya faru amafarkin ta, na kuma ƙara mata da jin haushin ko wani namiji, saboda ina son ta, ina jin tsoron wani ya shiga tsakanin ta dani, musamman ma kai dana fahimci zaman mu bazai taɓa iyuwa ba kasancewarka malami masani akan addini da kuma abin da ya shafi aljannu."

Hannun sa biyu ya haɗa alamun roƙo "Dan Allah kada ka kore ni, kada ka rabamu da ita, da gaske ina son ta tun kafin ka santa."

Goshinsa Musaddiƙ ya riƙe ya fara murzawa yana aika kallon sa tsakanin Luyya da Alh. Isah wanda suka kasa aikata komi, fargaba da ruɗani duk ya cika su.

"Nasan ka san babu wata soyayya dake tsakanin Mutum da Aljan, kamar yanda kace tausayin ta kake awancan lokacin, inaga yanzu lokaci yayi da zaka barta tunda ta samu ƙarfi da ko wata alfarmar da zata iya kare kanta."


Abun mamaki kai ta shiga girgizawa "Ba xan iyaba Musaddiƙ"


 Karatu ya fara yi ba tare da ya saurare shiba tun yana jijjiga kai yana riƙewa har dai yaci gaba da ihu, yana ya tsaya zai fita, amma bai saurare shiba yaci gaba da karatunsa, ƙara ya saki da ƙarfin gaske sanan ya fara bubbuga kan Ismaha Zainab ajikin bangon ɗakin, tuni wajan ya fara fidda jini tsoro ne ya kama Luyya ta fashe da kuka tana roƙon ya tsaya kada ya kashe mata ɗiya, amma bai tsaya ba, ƙarshe yayima Alh. Isah inkiya akan ya riƙe Luyya ɗin, shi kuma ya riƙe Ismaha Zainab da hannun sa, yaci gaba da karatun, wani hawaye ne ruwan ƙasa-ƙasa mai kauri ya fara fitowa daga idon Ismaha Zainab da hancin ta "Dan Allah ka bari zan fita yanzu." muryar da bata fita sosai akayi maganar, hakan yasa musaddiƙ tsayawa daga karatun da yake.

"Ta ina zaka fita?"

"Ta duk inda kace na fita, tanan zan fita."

 "Fita ta hancin ta to."


Kafin ya rufe bakin sa ma ta fara jero atishawa har sau uku "Alhamdulillah" Musaddiƙ ya fiɗa yana sharce gumin fuskar sa.

Cikin haɗuwar baki Alh. Isah da Luyya suma suka faɗi "Alhamdulillah"

Ganin Ismaha Zainab ta ɓungire ta fara barci.

 "Kin dai ji duk abin da Aljanin nan ya faɗa, silar zaman sa jikinta da kuma abin da yake faruwa."

Kai Luyya ta ɗaga saboda bakin ta yayi mata nauyi wajan magana.

 "Masha Allah, duka adunƙule dai wanan sakaci ne irin naku na iyaye, kukan bar yaranku sakaka ba tare da addu'a ba, wasu lokutan hidimar rayuwarku ta kujuba-kujubar yau da gobe takan hanaku tsayawa ga kyakkyawar ibada, baku da damuwa sai akan gobenku da kuma abin da zata zo muku da shi, gashi koda yau ɗin tana gagararku riƙewaa, neman ilimin Addini acikin rayuwar ƴa mace abu ne mai mutƙar kyau, kasancewarta makaranta ta farko acikin rayuwa da duniyar yaranta. Yanzu ga babbar matsalar da aka samu, amma ki gode Allah da ba azzalumin aljani ne ya shiga rayuwarku ba, da ƙila abin yafi haka muni. Allah ya ƙara kare mu da kariyar sa."

"Ameen ya Allah, mun gode sosai malam Musaddiƙ."


Miƙewa yayi yana kallon agogon sa kusan awa guda da rabi kenan har lokacin sallahr Issha'i ya gabato "Akwai maganin da zan haɗo mata in sha Allahu zuwa gobe, yanzu dare yayi kuma bani da wasu ahannu na, sai dai kafin nan kuna iya mata amfani da zam-zam ku shafe mata duka jikinta da shi, a tabbatar kafin ta kwanta ta ɗauro alwala da Azkar na barci. Sai kuma ka karɓo mata maganin ciwon kai da na ciwon ta a kyamis"

"To in sha Allah za'ayi, mun gode Allah ya biyaka da mafificin alkhairin sa."

 "Ameen ya faɗa yana ƙokarin ficewa aɗakin."

"Malam ka tsaya ka karɓi abin sadaka mana."


Juyowa yayi ya kalli Alh. Isah cikin mamakin jin ya karɓi wai abin sadaka, kai ya girgiza yana murmushi "Masu yi dan Allah sukan tsammaci sakamako ne kawai agare shi, idan kuma ya ratso tsakanin ahalinmu sai mu kirashi da kyautatawa agare su."

Yana gama faɗar hakan ya fice cikin takunsa da sauri, murmushi Luyya tayi kawai ta girgiza kai.

"Mi yaron nan yake nufi ne Ruƙayya? Tun farko cikin kasada da tsoro na masa jagora, gashi ya ɓige da wani maganar da ban gane ba."

Dariya tayi ganin yanda Mijinta ya ruɗe yake faman raba ido "Ban gane ba nima, amma ina tunanin kamar yana nufin kansa yayima, idan kuma na kintata dai-dai ka samu surukin malami."


Ido ya fiddo waje har yanzu kansa ya ƙulle "Kimin hausar da zan gane mana."

Kiraye-kirayen sallahr da ake da shigowar su Salamatu atare yasa su katsewa daga maganar da suke.

 "Alhmdulillah! Jiki yayi sauƙi, tunda gashi naga tana barci haka." Salamatu ta faɗa tana ƙarasawa kusa da Ismaha Zainab da take ta faman sauƙe ajiyar zuciya.


"An dace?" Rabi ta aika tambayar asaitin Luyya.

Kai kawai ta ɗaga cikin murmushi "Na gode sosai maman Walid"

 Kai ta gyaɗa itama cikin faɗaɗa murmushin ta "Alhamdulillah, Allah kai ne abin godiya."


Anan suka zauna suna ƙara jajanta wa junan su Alh. Isah kuma ya fice ya nufi masallaci.🥀🥀🥀🥀🥀🥀

👏Abubuwa da yawa sukan faru acikin wanan duniyar, ayayin da ko wani abu yana da tasa iyakar, idan aka haɗa kalmomi guda na juriya da rauni ga sashi biyun da suke ɗauka, sai muga hakan ba komi bane face sawa aka, kalma guda tayi tsayi idan kuma muka ambaci rabi sai ta samu tawaya wajan isar da saƙon._

 *GIRMAMAWA*#IsmahaZainab

#NWA

#UmNass

#Cmnts, vote and share 

#DaAmana🤝

[2/16, 9:48 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


 😘Um Nass 🏇🏼 Page 36


 Ƙauyan Kwalam


 Tunda motar su ta shiga cikin garin bugun zuciyar Luyya ya ƙaru, bin ko ina na garin take da kallo, babu wani abu da ya sauya agarin, yana nan dai ayanda ta fice ta barshi, idanma akwai sauyi to bai wuce na manyata da dattijan garin suka ƙara yiba, sai kuma yaran da ta tafi tabarsu duk sun dawo samari.

 Komin daɗewar shekarun da aka ɗauka bazata taɓa manta gidansu ba, da kwatance ta nuna musu gidan, har suka kawo ƙofar gidan, yara na biye dasu suna ilo.

 Jin hayaniya aƙofar gidan su yasa Babuji fitowa yana daddogara sanda, tsufa ya ƙara kamashi wanda sai da taimakon Sandar yake iya tafiya.

 Ganin mota sabuwa aƙofar gidansa da kuma baƙin mutanen da suke fitowa acikinta yasashi yin mamaki.

 "Bayin Allah ba nan bane gidan mai garin ai, sai kun ɗanyi gaba. Kai Kallamu mi yasa baka kaisu gidan Mai garinba?"

 Ya ƙarasa maganar yana nuna wani yaro wanda bazai haura shekara goma ba "Su suka zo nan da kansu, basu tambayemu ba."

 Hawaye ne yake zuba akan Idon Luyya, da gaske mahaifinta takega agabanta. Babuji ɗin daya haramta mata shiga gidansa tsawon shekaru goma, sautin muryarsa ce ta dawo mata kunne kamar alokacin yake bata umarni _"Kema kinsan idonki da kunya ki shigo min gida, bana buƙatar balagurbi acikin Zuri'ata. *Fita*."_ maganar da Babuji ya mata awancan lokajin ta sake dawo mata akanta.

 Kai ta fara girgizawa tana ƙoƙarin komawa cikin motar, hannunta taji an riƙe wanda yasata tsayawa gami da juyowa, Alh. Isah tagani yana riƙe da hannun nata yana girgiza mata kai fuskarsa ƙunshe da murmushin ƙarfafa mata gwuiwa "Wanan shine mahaifinki Ruƙayya, ki kalla da kyau, yana buƙatar tallafawa adai-dai wanan lokacin. Shekaru sha biyar rabanki da ganinsa, ina tare dake aduk wani motsin da zakiyi."

 "Abu Usama..!"

 "Muje."

 Abun daya faɗa yana datse ko wata magana da take son fitowa daga bakinta, yajata har gaban Babuji ɗin, da yake ta faman binsu da kallo.

 "Baba wajanku muka zo. Mu baƙine daga Haɗejia."

 "Haɗejia! Ikon Allah ku ƙaraso daga ciki, lallai maraba, kunsha hanya, maraba."

 Ya faɗa yana shiga cikin gidan da musu nuni da hanya alamun su biyo bayansa.

 Binsa sukayi abaya har suka ƙaraso tsakar gidan, anan ya fara ƙwala kira "Ballu! Ballu!! Fito da abin shimfiɗa munyi baƙi ne ashe."

 Fitowa tayi hannunta ɗauke da bujukura (Tabarma mai faɗi) ta shimfiɗa musu tana kiran "Lale maraba da baƙi, ku zauna."

 Zama sukayi akan taburmar ita kuma ta shige ɗaki ta ɗebo ruwa mai sanyi a kafarar da take ɗakin, cikin kwanan sha mai kyau ta kawo musu.

 Ɗauka Alh. Isah yayi ya sha sanan Usama ya sha, Luyya kam sai kallon iyayen nata take amma ta kasa ko motsi, gefe ɗaya kuma Ismaha Zainab ce take riƙe da hannu Hassan da Hussain sai wurga ido take tana aika kallonta tsakanin tsofaffi biyun, wanda ta kasa ban-bance alaƙar da take tsakaninta da su.

 Bayan gaisuwar da sukayi Babuji yayi gyaran murya ya fara magana "Asanina dai bani da ƴan uwa ko guda acikin garin Haɗejia, amma kuma lamari da iko na Allah sai gashi ance nayi baƙi daga garin." ya faɗa yana murmushi wanda yake nuna dattakon sa da kuma Girmama baƙin nasa.

 

 "Haka ne kam." Alh. Isah ya faɗa yana murmushi, sanan ya nuna Luyya da hannun sa "Amma wanan baku shedata ba itama?"

 Sai alokacin suka ƙura mata ido, suka kafeta da shi, can kuma kamar an zaburi Ballu ta miƙe tsaye ta ƙaraso kusa da ita "Ruƙayya!" 


 "Ruƙayya kuma?" babuji ya faɗa yana ƙoƙarin tashi daga inda yake yana matsowa wajansu.

 Kai Ballu ta gyaɗa sai kuma ta shafa fuskarta "Eh Ruƙayya fa! Wanan Ruƙayya ɗina ce Malam, ni dama nasan Ruƙayya tana raye malam, zo kaga wallahi wanan Ruƙayyarmu ce, duk sauyawar da zatayi bazan kasa ganeta ba." sai kuma ta fashe da kuka tana rungumeta.

 Itama kukan tasa tana ƙara maƙale Ballu "Innarmu!" ta faɗa cikin Muryar kuka.

 Sun ɗauki lokaci ahaka kafin su saki juna, kowa awajan cike yake da tausayin su, Babuji ma kasa haƙura yayi saida ya matsa yana shafa kan Luyya yana faman kiran "Ikon Allah, ikon gaske, ashe da rabon ina da sauran kwanan da zan ƙara sakaki acikin idona Ruƙayya." yana maganar yana share hawayen da yake zuba akan idonsa.

 

 "Ayi haƙuri haka nan, kukan bashi da amfani ko kaɗan."

 Tsayawa sukayi suna ƙara kallon Luyya suna neman yafiya agareta, Babuji ya ɗora da bata labari.


 "Tun bayan barinki garin nan da mako uku muka fahimci gaskiya, wanda maƙotanki da kuma abokanan Muntari suka zayyana abin da ya faru. Bahaguwar fahimta Idirisu yayi muku har ya kaishi ga zartar da hukunci, yazo kuma ya sameni ya faɗa min abin da kunnensa yaji da wanda mahaifiyarsa take faɗa akanki. Zuciya bata da ƙashi Ruƙayya naji ƙunci na kuma ga tarin muzanta akan ɗiyar danafi so acikin yarana aka kama da aika saɓo." Baki ya ciza cikin jin takaicin maganar da yake, duka ido suka ƙura masa suna ƙara baza kunnuwansu dan jin abin da zai faɗa.

  

 "Bayan gaskiya tayi halinta muka bazama nemanki, tun daga Ringim har zuwa sauran garurruwan da suke maƙotaka damu amma babu ke babu dalilinki, haka muka zauna muka sha kukanmu nida Innarki da sauran ƴan uwanki, muka ci gaba da yin Addu'a akan Allah ya bayyana ki aduk inda kike. Innarku kullum cikin kuka take, tana ƙara jingina laifi akaina da zama tsani na barin garin da kikayi. Kiyi haƙuri ki yafe min kinji Ruƙayya, son zuciya da tsoron ƙasƙanci awajan mutane yasa na aikata babban kuskure arayuwata."

  

Kowa awajan zuciyarsa ta karye ta kuma tsinke da jin tarin tausayin Babuji da Innarmu.

 Hawayen Fuskar ta Luyya ta goge sanan tayi murmushi "Bakayi laifiba ko kaɗan Babuji, asalima sila ka zama na samun wata ɗaukaka acikin rayuwata, haka kuma Allah ya ƙaddara min shi acikin shafikan rayuwar da zanyi aduniyata. Nagode Allah daya wanke ni, ya kuma bayyana gaskiyar abin daya faru. Addu'ar da Innarmu tayi min Allah ya karɓeta, ya kare ni ya kuma zame min gata fiye da wanda yake rayuwa da danginsa awaje ɗaya, tabbas ban taɓa mafarki da tsammanin cigaban dana samuba alokutan da nake rayuwa awanan garin, sai dai kuma lamari na Allah da buwayansa sai ya sabunta ni. Tun bayan barina gidan nan na nufi tasha.......... Labarinta ta basu tun daga barinta garin har zuwa yanzu da ta dawo.

  

 "Allahu Akbar! Allah mai hikima ne, wanda yake amsa addu'ar bayinsa, yake kuma sakanyawa bayinsa idan an cucesu." Innarmu ta faɗa tana share hawayen kan fuskarta.

 "Tabbas kinga rayuwa Ruƙayya, kin fahimci ɗaci da ƙunci dake cikinta, sai dai Allah ya kareki da ya tsarkake miki zuciya, ya haɗaki da mutane masu jin tsoronsa wanda suke yin alheri saboda shi kawai." Babuji ya faɗa sanan ya ƙarasa kusa da Alh. Isah "Ban san da bakin da zan gode maka ba yaro, ka auri Ruƙayya ba tare da bincike akan sanin ko waye ce ita ba, ba kuma tare daka nemi wani daga cikin danginta ba, ka maida ita ɗaya daga cikin ahalinka, ita da ɗiyarta ba tare da nuna ban-banci da gajiyawa ba. Tabbas samun irinku kaɗan ne, sai dai ina maka Addu'ar Allah ya sanyaka acikin Aljannah Fiddausi, ya kuma kare bayanka."

 "Ameen ya Allah." Suka amsa cikin jeruwar harshe.

 

 "Ai Baba samun Ruƙayya amatsayin mata Rahma ce babba agareni, ta gyara kowata ɓaraka da take tsakanina da ahalina, haka kuma maganar bincike da neman sila duka shurme ne, wani lokacin akan samu ban-banci tsakanin gaskiya da ƙarya, amma kuma nagartar ta da kyakkyawar ɗabi'arta su suka zama tsanin da ya ƙara min buri da fatan zama tare da ita. Shi kuwa ɗa na kowa ne, ba'a masa mugunta, dan baka san wanda zaka mora ba."

 Kai suka gyaɗa cikin jin daɗin maganar tasa. 

 "Wanan Sune tagwayen da kika Haifa Luyya?" kai ta gyaɗa tana murmushi.

 "Ikon Allah! Kuzo nan kunji, ga kuma Abu itama ruwan Haɗejia ya hura ta, har yanzu tana tsotsar hannun ne? Naga miskilancin nata ya ƙaru." Innarmu ta faɗa cikin salon tsokana.

 Aifa nan aka saka dariya, barin Usama da dama ta zama abar zolaya agareshi "Ai har yanzu tana cizon hannunta Innarmu. Bakiga bakin nata ya ƙara tsukewa awaje ɗaya ba."


 "Aifa sai yanzu na lura." ƙin kulasu tayi taci gaba da murmushi da daddana wayarta.

 "Usama tashi kasa yara su shigo da kayan ko?"

 Tashi yayi yafita waje, wanda har yanzu akwai cin-cirindon yara suna kewaye da motar, but ɗin motar ya buɗe ya fara fito da kayayyakin abinci, nan yara suka fara ɗauka suna shigar dashi cikin gidan. Nan Luyya tashi ita da Ismaha Zainab suka girka musu abin da zasu ci mai ɗan sauƙi, jalop ɗin shinkafa wanda tasha kayan lambu da kifi banda, nan suka zauna suka ci ana ta hira da barkwanci, aɗan tsakanin nan aka samu shaƙuwa sosai tsakaninsu.


 Kafin wani lokacin kuma labari ya fara baza gari ga Luyya ta dawo, ta zama hajiya mai kuɗin gaske.

 Nan ƴan ganin kwakwaf da bin sila suka zo suka fara ganema idonsu gaskiya, da yawa kuma suna ma su Innarmu da Babuji barka da arziƙi. Haka yayyan Ruƙayya duk sun zo suna ta maida zance da kuma tunanin bayan rabuwa.


 Yamma sakaliya Alh. Isah da Usama suka tashi suna shirin komawa gida, sai dai zasu bar Luyya da yaranta anan tsawon mako guda, godiya da sanya albarka ya shasu sosai awajan Babuji da Innarmu.

 Har wajan mota suka rakoshi, suna ƙara sallama. Kamar daga sama suka hango wani mutum da kayan ajikinsa yayi duƙun-duƙun yana ta faman sauri ƙarshe kuma ya sako gudu yana ɗaga musu hannu "Ku tsaya karku tafi dan Allah." hakan yasa Alh. Isah tsayawa daga buɗe motar da yake, yana kallon mutumin, ga can bayansa kuma mata ne guda biyu suma cikin shiga marar kyau, ɗayarma riƙeta akayi tana faman tafiya kamar mai koyan ta-ta-ta.

  

 Ajiyar zuciya ya saki lokacin da ya isa gabansu. Sai kuma ya fara maida numfashi akai-akai yana wurga kallonsa tsakanin mutumin da Luyya.

 Ƙasa ya tsugunna kafin su ankare kuma hawaye ya fara zuba akan idanuwan sa "Ruƙayya dan Allah.." sai kuma ya kasa ƙarasawa saboda kukan da ya taho masa da takaicin gibin da yayima rayuwarsa tun farko.

 "Idriss kai ne ka dawo haka? Ya Allah!" Luyya ta faɗa tana rufe fuskarta da tafikan hannunta tana sauƙesu da zubar hawaye akan idonta.

 Kallonsa Alh. Isah yayi sosai mutumin ya bashi tausayi, ko bai tambayaba ya samu tabbaci akan shine tsohon mijin Ruƙayyar sa.

 Matanne suka ƙaraso suma suka zube kamar Yanda Idris yayi anan, mutane tuni sun kewayesu suna kallon su, kasancewar abun kallo bashi da yawa.


"Ruƙayya Ƴarta kina ina?" innar su kamalu ta faɗa tana laliben hannunta, saboda idonta da ya samu matsala bata gani sosai, sai dururu shima kuma ba can ba sai an mata jagoranci. 

 Da sauri Luyya ta zuba agabanta tana riƙe hannunta bakinta na rawa tace "Gani Innar Kamalu, mi ya samu idonki bakya gani ne?"

 Kai ta gyaɗa hawaye na zuba akan idonta "Haƙƙi, haƙƙinki ne yake ta ɗawainiya damu Ruƙayya, tun bayan rabuwarku da Idirisu al'amura suka dagule mana, zalincin da muka miki cikin son zuciyarmu ya dawo kanmu, Idirisu ya Auri Haule ƙawar Tani tazo tayi ta gasa mana aya ahannu mu da shi babu wanda bata taka ba, kullum kukan Idirisu akanki ne da neman inda kike ya nemi yafiyarki wata ƙila Allah ya rangwanta masa, har zuwa yanzu da nake miki zance komi namu na kadara da rufin asiri ya ƙare Idirisu ya rabu da zuwa Legas neman kuɗi saboda haɗuwa da sukayi da ƴan fashi, suka yashesu bayan dukan da suka lakaɗa musu. Itama Tani gata nan dai, dan mijinta ya ƙara aure daya gane baƙin halinta da hassadar ta, ya bita da saki uku ƙwarara, kasancewar ta marainiya da kuma yaran da muke dasu da ita yasa na roƙi alfarmar ya bata ɗaki ɗaya, ta zauna da yaranta, haka ta koma aikin wankau da casa idan lokaci yayi dan ta samu kalen abin da zata ci. Tabbas mun zalince ki, zalinci mafi girma arayuwa, zuwanki ya zame mana kamar wani kankarar ƙunci da sauƙe nauyin da yake kanmu, muka taso dan mu nemi yafiya agareki."

 Kuka tasa mai sauti adai-dai wanan gaɓar "Dan Allah Ruƙayya kiyi haƙuri ki yafe mana, ko zamu samu sassauci daga halin da muke ciki agarin nan, kowa gudunmu yake yana tsoron raɓarmu saboda abun da muka miki, ki kalli dai yanda na koma da Idirisu wanda yake fama da riga ɗaya kullum."

 Hawayen tausayinsu ne ya shiga zuba a idon Luyya "Na yafe muku Innar Kamalu, wallahi na daɗe da yafe muku, ko alokacin banga laifin Idriss ba, na ɗauki hakan amatsayin ƙaddara da kuma rabo ne ya fidda ni agidansa. Kinga mijin dana aura can ga kuma yarana tagwaye guda biyu dana haifa tare da shi, wanan rabon shiya fiddani daga gidan Idris ya kuma ɗaukaka darajata fiye da wadda nake ciki abaya."

 Kai take gyaɗawa duk da bata gani sai bin wajan take da kallo, haka Idriss ya fashe da kukan baƙin ciki da dana-sani da abin da yayima kansa.

 "Barka yaro, kaikam ka gama samun duk wani arziƙi da jin daɗi na duniya, samun Ruƙayya amatsayin mata babban arziƙi ne ga mutum."

 "Tabbas haka maganarki take. Nagode." Alh. Sule ya faɗa yana murmushi, wanda yasa Idirisu ɓarkewa da kuka.

 "Ina Isma Abu take." Innar su kamalu ta faɗa tana jin nauyi da kunyar tambaya 

 Da hannu Luyya ta yafito Ismaha Zainab wanda take share hawaye akan fuskarta, tabbas wanan shine mahaifinta, waɗan nan fuskokin su take gani aduk mafarkanta na baya, take kuma jin tsana da ƙiyayyarsu tana taruwa aranta. Da ƙyar ta haɗiye yawu mai ɗaci ta ƙarasa kusa da su, tanaga girma da Kimar Luyya aƙasan ruhinta, mace mai maida alkhairi da sharrin da ake mata.

 Hannunta Luyya ta riƙe ta damƙashi ana Innar Kamalu "Ga Ismaha Zainab nan Innar kamalu." shafa fuskarta tayi tana hawaye "Allah ya Albarkaci rayuwarki kinji ƴar nan."

 "Ameen" ta iya faɗa tana juyar da kanta ko kaɗan bata ƙaunar ganin su.


 "Ruƙayya kiyi haƙuri da maganar da na miki akan Ismaha Zainab awancan lokacin."

 "Ya wuce Idris, na kuma daɗe da manta hakan."


 Sun ɗauki tsawon lokaci ahaka suna jajjan rayuwa da nadama har lokaci ya fara tafiya.

 Ƙoƙarin tafiya su Alh. Isah suka sakeyi sai kuma sukaga wata mota ta tsaya agaban tasu.

 Da ido suka bi motar cikin mamakin mamallakinta.

 Wani matashin saurayi ne ya fito wanda aƙalla shekarunsa bazasu wuce 30 ba. Cikin kyakkyawar shiga da kamala, tunda ya fito yake faɗaɗa Murmushinsa har ya ƙaraso kusa da su.

 "LUYYA ƊINMU!"


 Ido ta ƙwalalo waje saboda gane ko waye ne, "MUNTARI! Ya Allah." ta faɗa tana rufe bakinta da kuma murmushi, wanda yake nuna najin daɗin ganinsa ne.
  🥀🥀🥀🥀🥀🥀


_Yaufa na magantu da yawa, na kuma aikatu, na san da yawa sun hasaso abubuwa da yawa, maza ku kimanta zunzurutun kimantarwa da muke da ita, sai ku magantu dan ra'ayin kanku, akwai dai *GIRMAMAWAR* nan tana jiranku aduk kalmar da kuka ajiye dan magantuwa._
#IsmuhaZainab

#NWA

#cmnts, like and share

#Da amana.

  

 UmNass

[2/16, 9:48 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


©by *😘Um Nass 🏇🏼*


_√Ote me on Wattpad @UmNass_


Babi na 35


 A gajiye liƙis ya ƙarasa gida, kai tsaye ɓangaran sa ya shiga, ya sake watsama jikin sa ruwa, saboda zafin da yake ji.

 Ga kuma tarin tausayin Ismaha Zainab da ya gama cika ko wani sashi da lungu na zuciyar sa, ashe da akwai babban dalilin da yasa taƙi amincewa da tayin soyayyar sa, ashe duka tsawon lokacin da yake tunanin ta aƙasan ransa tana fama da wata matsala mai yawan gaske.

 Har ya fito abanɗakin zuciyar sa na cunkushe da tarin tunani, wani sashi kuma na zuciyar sa na godema Umman sa wajan jajircewar da tayi har ya tafi wata duniya karatu, wata ƙila da har yanzu ana kame-kamen wanda zaiyi Ruƙiyya wa Ismuha Zainab ɗin sa, da kuma wani ƙato ne zai gane masa ko wata sura ta jikinta.


  Jallabiya ya zura ajikinsa, bayan ya shafa mai ya kuma bi ko ina na jikin sa da turaruka masu ƙamshi. Ɓangaran iyayen sa ya nufa, yasan har sun gaji da baza idon ganin sa, daga zuwan sa yau ya fita, fitar da zai iya kiranta da sa'a ko kuma rashinta.

 Da sallama akan laɓɓansa ya shiga palon gidan, cikin haɗuwar baki suka amsa masa, sanan suka zuba idanuwan su gareshi.

 "Ashe ka jima da dawowa ma? Mu muna nan muna jiran dawowarka da muka ji shuru, gashi baka ɗora layinka akan waya ba balle mu kira da shi." Abban sa ya faɗa yana faɗaɗa murmushi wanda da gani najin daɗin ganin sa ne.

 "Eh! Ban jima da dawoba Abba, wanka kawai nayi."

 "Masha Allah, barka da baka ɓata ahanya ba ai."

 Ido ya waro waje kafin yayi murmushi mai sauti "Ɓata kuma Abba? Ai ko Jidda bana jin zata ɓata agarin nan balle ni."


 Dariya Umma sukayi ita da Jidda kafin ta sako musu baki cikin hirar "Ai Jidda sai taje ta dawo kai baka dawo ba, saboda shekarun da aka ɗauka baka nan, saɓanin ita da ta rayu agarin ta kuma tashi acikin sa."

 Kai ya gyaɗa cikin yarda da maganar "Duk da haka nima sai da nayi shekaru kamar nata agarin kafin na fice acikin sa."

 "Amma ai akwai sauyi da yawa da aka samu wanda babu kai acikin sa."

 "Kaɗan ba." ya faɗa yana ƙoƙarin tashi daga kusa da ita, ya koma kusa da Abban su.

 "Koma yaya ne an samu ai, shine harda tashi."

 "Umma fa! Maganar ki ne akan ɗiyar ki fa, bakya so ace tayi ƙasa."

 Dariya sosai suka saka masa ganin yanda yake maganar yana kwaɓe fuska, hadda jiddan da take zaune awajan itama saida ta dara "Ƙyale su yarona, da baka nan bakaji yanda suka cika ni da kukan rashinka da sukayi ba, amma kaga yanzu suna taɓa ka, dama bakin su yayi tsami suna son su fanshe tsamin da yayi ashekarun da baka nan."

  

 "Aifa naga alamar hakan Abba." ya faɗa yana zama kusa da shi.


"Bani labarin inda kaje, Ka dace dai inji?" Abba ya tambayeshi yana wara hannun sa alamun tambaya.

 Murmushi yayi sosai, sanan ya fara murza goshinsa "Ina jin Yunwa, Jidda kawo min abinci naci."

 Da sauri ta tashi ta shige kitchen, sai alokacin ya kalli Abba da ya kafe shi da ido, murmushi yayi yaci gaba da murza goshin sa "Bazan iya cewa na dace ba Abba, amma dai na taki sa'a da ban wuce yau ba."

 

 "Kamar wata irin sa'a kenan?"

 "Umm! Kamar yanayin gari da kuma wuraren da suka sauya, sosaifa." ya ƙarasa maganar yana murmushi, shima Abba dariya yayi mai sauti, gane yandA maganar ɗan sa ta dosa.

 "To shikenan Allah ya taimaka, idan lokaci yayi dai ya zama nine na farkon zagaya garin."

 "Abba mana!" ya faɗa yana ƙara murza goshin sa. Da alamu hakan ya zama ɗabi'a da halayyar sa.


 "Hirar mi ake aka ware ni? Sai sautin dariyarku kawai ake ji."

 "Hirar ce tsakanin Aboki da abokin sa, babu ke aciki." Abba ya faɗa yana murmushi.

 Dai-dai lokacin da Jidda ta ajiye farantin abinci agaban Musaddiƙ.

 Baki ta taɓe "Ai shikenan, danma dai ina da tawa ƙawar balle nayi takaici."

 Buɗe filas ɗin abincin yayi tuwon shinkafa ne sai miyar bushasshiyar yakuwa, da ta sha kifi sai man shannun da yake ta buɗaɗa ƙamshi, ga kuma farfesun kayan ciki, gefe ɗaya kuma lemon kwakwa ne da abarba acikin jog "Masha Allah, wanan gara haka Ummanmu, yau akwai shagali kenan." yana murmushi yake maganar ya sauƙo aƙasa yana tanƙwashe ƙafafuwan sa.

 Dariya suka masa sanin yanda yake mutuƙar son tuwon shinkafa da miyar kuɓewa bushasshiya, idan ya same su baya barin su.

 "Bari na tayaka Yaya nah." Jidda ta faɗa tana gyara zamanta itama, kai ya gyaɗa mata kawai.

 Haka suka ci gaba da hirarsu cikin soyayya da kulawa, suna cin abincin anayi ana barkwanci cike da nishaɗi.


******

 10:20am


Aƙofar gidan su Ismaha Zainab tayima Musaddiƙ, yaro ya aika yayi masa sallama da Alh. Isah, wanda dama yana zaune bai fita ba, cikin tsammani da sa ran zuwan malamin da yayi ruƙiyya wa Ismaha Zainab.

 Da sauri ya fita jin ana kiransa, Musaddiƙ yaga cikin shigar farar shadda gizna tasha aiki ga kuma saƙaƙƙiyar hular dake kansa wanda ita kaɗai ta ja kaya na kuɗi.

 Aransa yake jinjina ikon Allah da yasa yaron ya taimake shi, ko kaɗan baiyi kama da ƴan gari ba, asalima yafi kama da jinsin larabawa.

 "Assalama alaikum wa rahmatullah." 

 "Wa alaikumussalam wa rahmatullah wabara katuhu" musaddiƙ ya amsa yana miƙa ma Alh. Isa hannu gami da rusunawa yana gaida shi, cikin girmamawa.

 Bayan gaisuwar da sukayi ya tambaye shi ya mai jiki.

 "Jiki Alhamdulillahi da sauƙi sosai malam, jiya da muka mata duk abin da ka faɗa an dace sosai."


 "Masha Allah! Allah ya ƙara mata lafiya"

 "Ameen ya Allah"

 Leda ya miƙa masa "Ba maganunnuwan kamar yanda na alƙwarta maka, ɗaya na turaren hayaƙi ne, ɗaya kuma na shafawa ajiki ne idan zata kwanta, sai kuma Addu'o'in da zata yawaita yi akullum na kariya daga sharrin mutum da Aljan, in sha Allahu ta rabu da su kenan."


 "Nagode sosai malam, Allah ya saka da alkhairi, ya ƙara buɗa maka."

 "Ameen, ba komi."

 "Ka shigo ka duba ta, tana zaune ma yanzu haka."

 Agogon hannunsa ya kalla, sanan ya ƙaƙaro ɗan murmushi "Ina da uzuri sosai Abba, amma ka gassheta da jiki, Allah ya bata lafiya."

 Juyawa yayi ya nufi motar sa da ɗan saurin sa "Malam kuɗin maganin kuma fa? Ban san sunanka ba zaka tafi."

 "Musaddiƙ" ya faɗa yana ƙara sauri dan baya ƙaunar ya ƙara haɗuwa da wani kuma.

 "Ikon Allah." Alh. Isah ya faɗa yana cike da mamakin halayyar Malam Musaddiƙ kamar yanda ya faɗa masa.


 Cikin gidan ya shiga bayan yaga ɓacewar motar Musaddiƙ har yanzu bakinsa ɗauke yake da zunzurutun mamakin yaron.

 Ɗakin Luyya ya shiga ya isketa suna zaune da Ismaha Zainab wanda kamar ba ita ta gama bige-bige ba ajiya, idan aka ɗauke bandejin dake goshinta to babu wani tabo na ciwon da yake alaƙantata da rashin lafiya.

 da sallma abakinsa ya shiga ɗakin, bayan ta amsa masa ya ɗora da magana.

 "Ikon Allah, Malam Musaddiƙ ne ya zo yanzu, ga maganinnuwan da Addu'ar da yace tana yi."

 Ya faɗa yana dai-daita zamansa akan kujerun da suke palon.

 "Shine kuma bai shigo mun gaisa ba."

 

 "Sai da na masa tayi akan ya shigo yaga jikin ta, yace sauri yake."

 "Allah sarki." 

Zaman sa Alh. Isah ya gyara yana faman girgiza kai "Wallahi yaron nan yana mutuƙar bani mamaki Ruƙayya, halayyar sa da nutsuwarsa sun girmi shekarun sa, bashi da alama ta rauni ko wata tawaya atare da shi, asalima kana ganin sa kasan iyayen sa hamshaƙan masu arziƙi ne, ya kuma jiƙu juƙuwa irin ta Naira da kobo."

 Murmushi Luyya tayi tana ƙara kallon Mijin nata, da yake ci gaba da kwarzanta mata Musaddiƙ ɗin "Mamaki nake da zamowar sa malami masanin addini, saɓanin sauran matasan da suka zaɓi ilimin boko da wayewa fiye da komi na rayuwa, sashi guda kuma ina girmama iyayensa da suka ɗorashi akan turba mai kyau, ayanzu da na kalleshi sai nake tuna rayuwar da naso jefa yarana abaya, da Allah bai kawoki cikin duniyar mu ba wataƙila da yanzu kan iyalina ya daɗe da tarwatsewa."


 "Allah yakan buɗewa bayinsa ƙofafi da yawa na ɗaukaka da ci gaba acikin rayuwar su, duk abin dakaga mutum yayi to dama can Allah ya ƙaddara masa shi, haka kuma mutane da yawa sukan zaɓar ma kansu abun da sukega ya dace da rayuwar su, wasu marar kyau wasu mai kyau, kaɗan ne suke dace su sami mafi kyau acikin mai kyau ɗin, wanda kuma ya samu to haƙiƙa ya dace ya kuma rabauta da duk wata dama acikin damarmaki na rayuwar yau da gobe, tabbas ni kaina nayi mamakin ganinsa matashin saurayin da yake da ilimi sosai, ina kuma fatan ace inama ace shi ɗin jinina ne."


 Numfashi taja ta fuzgar da iska abakin ta, har alokacin Alh. Isah na kafeta da idanuwan sa yana ƙara baza kunnuwan sa dan jin tarin magana mafi daɗi daga bakin matar tasa "Kai ai uba ne, da kake amsa sunanka na uba mai kuma tsayuwa acikin duniya da rayuwar yaran su, na tabbata koda ban shigo rayuwarka ba Allah zai dubi bayanka da kyakkyawar manufar da kake da ita akan yaranka ya dafa musu, ya basu kulawa acikin tsawon rayuwar su, ko wani mutum yakan yi Addu'ar Allah ya bashi yara, amma bai damu yayi Addu'a akan samun yara nagari masu albarka ba, kawai dai su idan suka samu sauran duk saura ne zai kuma shiga cikin sahun lissafi. Bayan hakan kuskure ne babba idan muka yi duba da Hadisi cikin sahihul bukhari inda Annabi s.a.w yake cewa "Ku nemi kariya daga sheɗan acikin tarawa da iyalinku da kuma abin da Allah zai iya azurtaku da shi awanan lokacin." acikin wani hadisi makamancin wanan ya ƙara bayani yace "Da ace wani acikinku idan yayi nufin tarawa da iyalinsa zai ce _"Bismillahi, Allahumma janabna sheɗan wa jannabinasheɗan ma razaƙatana."_ idan acikin wanan aka ƙaddara masa samun ɗa to sheɗan bazai taɓa kusantarsa ba har abada." wanan ma yana daga cikin sahihul bukhari. Amma yanzu ya rayuwar mu take, an samu sauye-sauye da yawa, rayuwa kawai muke cikin rashin sanin alfanun inda zamu dosa."


 Hannu Alh. Isah ya tafa yana kuma haɗawa da kabbara "Allahu Akbar! Kaji hikima daga bakin matata Ruƙayya. Allah ya miki albarka Ruƙayya yasa ki gama da duniya lafiya."

 "Ameen" ta faɗa tana ƙoƙarin rufe fuskarta da hannayenta guda biyu.


 Maganin ya ɗauko yana mata bayanin ko wanne acikin sa, kasancewar aliƙe yake da bayanin yanda ake amfani da shi, da kuma maganin da suke yi.

 "Ko kin san yaron nan ko biyar bai karɓa awaje na ba, da na masa maganar kuɗi ma tafiya yayi ya ƙyaleni."

 "Allah sarki, kasan akwai masuyi dan Allah, wanda suke jira daga gareshi, ƙila shima hakan ne."

 Dariya yayi yana jinjina kai, sanan ya kai kallon sa ga Ismaha Zainab wanda idanuwan ta suke lumshe kamar babu ita awajen.

 "Nikam ina mamakin miskilancin Ismaha Zainab yanzu, nasan idonta biyu amma kuma kinga kamar babu ita awajen."


 Kallonta tayi ta girgiza kai kawai, dan tun tashinta abarci batayi maganar data haura biyar ba, har zuwa yanzu da garin Allah ya waye.

 "Gata nan dai."

Abin data faɗa tana ta taɓa goshinta, fuska ta ɗan yamutsa ba tare data buɗe idanuwan ta ba.

 "Allah ya sauwaƙe, ni zan fita kasuwa sai na dawo."

  

"To adawo lafiya Alhaji, Allah ya kikaye ya buɗe ya hore maka da hanyar samu ta hanyar halak."

 

 "Ameen. Ameen."

 Ya faɗa yana ficewa aɗakin.******


 Bayan wata guda:


 Acikin ranakun nan an samu sauyi da ci gaba sosai, lafiya ta ɗore ajikin Ismaha Zainab, sai dai ƙarancin maganar ta da ya ninka na da, asalima idan ba dole ba sai ta yini ba tayima kowa magana ba.

 Akuma ɗan lokacin ne shaƙuwa ta shiga tsakanin Alh. Isah da Musaddiƙ dan kusan duk Juma'a yakanyi sallah a masallacin unguwar ya ƙarasa ya gaida Alh. Isah ya tafi abinsa.

 Wanan halayyar ta ƙara masa girma da kuma kima a idon Alh. Isah, kullum cikin yabon sa yake da sanya masa albarka.

  

 Ganin Lafiya ta samu awajan Ismaha Zainab yasa Luyya ta tambayi Alh. Isah akan tana son zuwa ganin gida Ringim, bai musa mata ba sai amincewar dayayi da kuma bata ƙwarin gwuiwa akan zuwan, ciki kuwa harda rakiyar tafiyar da zai mata da kansa.


 Murna da godiya ta sha yi harda hawayen farin cikinta, wani kima da mutuntakar Alh. Isah ta ƙara hauhawa acikin idonta.

 

 Awashe gari ya tada Usama wanda shi ne zai tuƙa su zuwa gidan, sai tsokanar Isamaha Zainab yake bata kulashi ba. Saboda yanzu magana wuyar gaske take mata. Har ƙofar gida su salamatu suka rakota suna mata Allah ya kiyaye hanya, bayan cikata da sukayi da tsaraba tun daga kan suturar sawa har xuwa ƴan abin daba'a rasaba.

 Ahanya ma kuma saida suka tsaya suka ƙara siyayyar kayan tsaraba tun daga na abinci zuwa na kayan sawa, abin dai masha Allah....


 *****

ƘAUYAN KWALAM

 Ringim L.G
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀

 _Wasu lokutan nakan so bada dama da tsagwaran *GIRMAMAWA* dubbanku, amma nasan idan nace zan faɗi sunayenku tofa zan cinye shafi guda wajan jero sunan, ku ɗauki kalmar ku yafa akaran kanku, ga kuma duk wanda yake biye dani wanan sadaukarwar tasa ce._#IsmahaZainab

#Um Nass

#NWA

#Cmnts,like nd share

#Ana tare

[2/16, 9:48 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


*😘Um Nass 🏇🏼*


Page 37


 Ƙarasowa kusa da ita yayi yana murmushi, duka mutanen wajan kallonsa suke cikin rashin fahimtar waye, idan aka ɗauke Idirisu da yake jin ya ƙasƙanta agabansu, wataƙila da babu haƙƙinsu akansa da shine yake da matsayi da ɗaukaka irin tasu.

 Risinawa yayi har ƙasa ya gaidasu, da murmushi akan fuskarsu duka suka amsa cikin haɗuwar baki.

 "Muntari kaine ka zama haka?" Luyya ta faɗa tana murmushi, kai ya sosa cikin sigar jin kunyarsu.

"Na samu labarin zuwanku ne ai awajan Bura, shine na taho ina ta Allah-Allah na sameku, ashe da banzo akan lokaciba da kun tafi."


 "Allah sarki, ai ni ina nan har kwana biyu, Mai gidana ne zai koma yau." ta ƙarasa maganar tana nuna shi da hannunta, juyawa yayi ya kalli Alh. Isah ya sake gaidashi cikin girmamawa.

 Sosai Alh. Isah ya yaba da hankalin yaron "Mukhtar ya Iyalin?" 


Kai ya sosa yana murmushi "Har yanzu babu Iyali Alhaji, ku tayamu da Addu'a dai."

Kai ya gyaɗa yana murmushi "To Allah ya kawo nagari, amma dai kayi ƙoƙari kada ka mai-maita shekara kana gwauro" dariya suka saka masa ganin yanda yake ƙara sunkuyar da kansa yana sosa ƙeya.

Agogo Alh. Isah ya kalla sanan ya sake yi musu sallama akan zasu tafi, fatan Alkhairi da sauƙa lafiya suka musu, Babuji da Innarmu na ƙara miƙa musu godiya.


Sai da sukaga ɓacewarsu sanan suka koma cikin gida. Anan suka bar su Idirisu suma suka kama hanyar nasu gidan, cikin jin kunya da dana-sani mai yawa.

 

 Shigarsu gida aka zubama Muntari abinci, sai da yaci yasha ruwa, ya rage daga shi sai Luyya aka sake sabuwar gaisawa kana Luyya ta kalli Muntari "Bani labarinka Muntari bayan rabuwarmu, dan naga sauyi sosai ayanayin ka.


 Murmushi yayi sanan ya girgiza kansa "Abun da ya faru aranar nan ya zame min mafari na ƙunci da zubar hawaye agareni, musamman dana zama Sila na wargaza miki dukkanin farin cikin ki, da duk wata alfarmar da kike da ita agarin nan. Lokacin dana samu labarin korarki da Babuji yayi, nayi kuka, kuka na sosai. Ƙarshe nima zaman garin nan gagarata yayi, saboda kallon da mutanen garin nan suke min, lokuta da dama sukan aibatani da tsiniwa agareni, hakan yasa na tattara kayana nabar garin nan, bayan mun siyar da gonarmu ta gado Innata ta haɗa min da kuɗin dake hannunta, muna kuka muka rabu. Ban tsaya ako inaba sai a Zakirai anan na yada Zango, kinsan lamari na Allah da nayi kwana biyu agarin, naga yanda mutanen garin suke tafiyar da mu'amularsu cikin amana da gaskiya kawai sai naji garama na Zauna agarin yafi min kwanciyar hankali, da ɗan kuɗin da yake hannuna na kama hayar shago akasuwar garin, na shiga cikin Kano na fara sarar kayayyakin sawa daga yadika na maza zuwa atamfa mai sauƙin kuɗi. Cikin ƙanƙanin lokaci Allah ya sanya albarka akasuwancin nawa, ƙarshe shagon da nake haya na siyeshi ya zama nawa, ganin damar dana samu sai na koma karatun boko har na samu matsayin digri afannin kasuwanci, Alhamdulillah hakan da nayi sai ya ƙara taimaka min awajan sana'ata yanzu kaf garin Zakirai zance babu mai shaguna kamar ni. Acikin shekarun nakan zo garin nan cikin dare dan ganin Innata da tambayar ko ansamu labari akanki, amsa ɗaya nake samu akan har yanzu babu labarinki. Ko kwana bana ƙarayi nake tattarawa na koma, saboda jin tsoron abin da zai-je-ya-zo idan mutanen garin nan suka ganni, ƙarshe na samu labari gaskiya ta fito, har baban Ismaha Zainab yaje gidanmu neman yafiyata, hakan yasa na fara sakin jiki nake shigowa akai-akai ganin mahaifiyata."


Numfashi Luyya ta sauƙe bayan gama sauraron maganar da Muntari "Masha Allah, amma duk da irin wanan cigaba da nasarar da ka samu ka gagara ajiye iyali?"


 Kai ya gyaɗa cikin yanayin alhini da takaici ya fara magana "Ina naga wanan lokacin da nutsuwar, kullum ina cikin bada cikiya da bin gari-gari wajan nemanki, gani nake kamar ni nake da duk wani alhaki na tarwatsuwar farin cikinki da barin gidan auranki. Hakan yasa bani da lokacin ɓatawa wajan sauraran ƴan mata. Sannan kuma.... Ummm.. Ummm" ya kasa faɗar maganar tasa yana faman sosa ƙeyarsa alamun nauyi da jin kunya da maganar tasa ta masa.


 Murmushi Luyya tayi tana jinjina lamarin Muntari da kuma kawaici irin nasa "Sanan kuma mi? Wanan ba hujja bace da zata hanaka yin aure Muntari, ko ka manta lamari na Allah da yakan sauya al'amuransa ta hanyar aiko da ƙaddara ga bayinsa mai kyau ko marar kyau dan ya gwada imaninsu, ka cire cewar kai ne kake da alhaki akan rabuwar aurenmu da Idris, dama can iya wa'adin zaman da aka ɗibar mana kenan muyi arayuwa, abu na gaba naji daɗin yanda ka samu sauyi da ci gaba acikin rayuwarka, amma kuma banji daɗin jinkirin da kayiba wajan ƙin ajiye iyali ba, ƙila da yanzu ka samar min da takwara." ta ƙarasa maganar cikin salon tsokana wanda ya sashi dariya shima.


 "Ai kin min alƙawalin aura min Ismaha Zainab ne. Wanan dalilin yasani jiran tsammanin ganinku, na kuma ƙudurce araina muddum ban gankuba babuni babu aure."


 Ido Luyya ta fiddo waje cikin mamakin maganar tasa, kafin kuma ta ƙaƙalo murmushi "Wasa kake Muntari, bayan lokacin duka batafi shekara uku aduniya ba."

 Kai ya gyaɗa fuskarsa babu alamun wasa "Ta iyu alokacin ke wasa kika ɗauka, amma ni har azuciyata da gaske na riƙe alƙawarin, ina kuma Addu'a da roƙon Allah ya bayyana min ku idan ina da rabon yin aure aduniya, dan nasan muddum ban sameku ba, babu ni babu aure har abada. Sai gashi Allah ya amsa min Addu'ata jin labarin zuwanku."


 Tunda ya fara maganar gumi yake zuba akan fuskar Luyya, tsoro gami da Al'ajabi suka cikata. Kallon Muntari take tana so taga wata alamar da zata nuna cewar da wasa yake, amma kuma babu alamun hakan, sai gaskiyar da take gani atsakiyar idonsa da kuma fuskarsa.

 Kai ta dafe tana ƙara jin zubar gumi akan ko wata gaɓa ta jikinta "Ya Allah!" ta faɗa cikin rarrauniyar Muryarta.....
🥀🥀🥀🥀🥀🥀


 _Tofa alƙawali dai ance kaya ne, ban saniba ko wanan tsohon alƙawalin zai cika, ammafa da alama mai guri ne yazo zai kore mai tabarmar da ya bararraje akai._ 😁😁😂


Kuyi malejin shafin *GIRAMAMAWA*#IsmahaZainab

#UmNass

#NWA

#Cmnt,Like,share

#DaAmana

[2/16, 9:48 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


*😘UmNass🏇🏼* _Acikin ko wani shafi da suke wanzuwa da gifta tsakanikanin ku, nasan akwai mutane da yawa da sukan aro dauriya agareni dan su bani ƙarfin gwuiwa wajan ci gaba, na ku na musamman ne hakan yasa na baku shafin kyauta cike da *GIRMAMAWA* agareku:

 ANTY MAIJIDDA MUSA

 MRS USMAN

 Ummu Rahma


 Page 38


  Ta ɗauki tsawon lokaci tana riƙe da kanta, ko wata kalma ta maganar da Muntari yayi dawo mata sabuwa take acikin kunnuwanta. _"Toma ta ina zata fara? Ta wata hanya zata gamsar da shi akan matsalar Ismaha Zainab? Taya zai fahimci har yanzu akwai ban-banci tsakaninta da sauran mutanen da suke rayuwa su kaɗai? Duk da cewa an samu sauƙi da sauyi atare da ita amma har yanzu bata da tabbacin ta warke sarai musamman idan tayi la'akari da taurin kai na Aljannin da yake tare da ita. Amsar da ya kamata ta bawa Muntari ta ɓacema kwanyarta, idan ta sanar dashi zaiga kamar son bashi Ismaha Zainab ɗinne bata yi."_ saƙe-saƙen da take aƙasan ranta ne ya sha kanta.

 Ɗagowa tayi taga ita yake kallo da alamun sauraron amsar da zata bashi, murmushi tayi sanan ta gyara zamanta "Har yanzu cike nake da mamakinka Muntari, amma kuma da naga tabbaci atare da kai sai mamakin ya ɗauke daga kaina."

Murmushi tayi tana gyaɗa kanta, tana son ƙarfafawa kanta gwuiwa akan maganar da zata faɗa "Zan turoma Ismaha Zainab ka nemi soyayya daga gareta, muddum ta amince zan tsaya maka har ka aure ta."


Murmushin sa ne ya ƙara yawaita akan kyakkyawar fuskar sa "Nagode Luyya ɗinmu." kai ta gyaɗa tana yalwata nata murmushin ta shige cikin gida zuciyarta cike da fargabar abin da zaije ya zo, da ko wani taku na ƙafarta tana jin-jina girman al'amarin da zai wanzu tsakanin Muntari da Ismaha Zainab.


******

 Lokacin da Alh. Isah suka dawo gida tuni gari ya kaure da kiraye-kirayen sallahr magrib, hakan yasasu wucewa masallacin unguwar kai tsaye, suka bi jam'in sallah.

Bayan fitowarsu ne sukayi karo da Musaddiƙ wanda shima amasallacin yayi sallah.

 Risinawa yayi ya gaida Alh. Isah fuskarsa ƙunshe da fara'a ya amsa.

"Taho mu ƙarasa gida malam musaddiƙ, dan yanzu dawowarmu daga tafiya agajiye nake."


 "Ayya bari to na wuce gida, gobe sai na dawo in sha Allah."


Juyawa yayi da zummar tafiya wanda yasa Alh. Isah ya riƙo hannunsa yanayin fuskarsa ya sauya zuwa damuwa "Nifa amatsayin ɗana na ɗauke malam musaddiƙ, hakan yasa nake ta gayyatarka dan kasancewa ɗaya daga cikin iyalina, ko wata rana na gayyaceka zuwa shiga sai ka kawo min uzurin da zai hana hakan faruwa. Ban san ko aranka akwai wata manufa daban akanmu ba, duk tsawon lokacin da muka ɗauka atare kaƙi bani dama guda ɗaya da zan kyautata maka."


Saurin ɗago kansa yayi ya kalli Alh. Isah wanda duhu ya ɗan farayi, sai dai hasken farin lantarkin daya cika kan titin ya taimaka wajan samarwa wajan da haske mai kyau, shi yasa yaga yanayin fuskarsa da kuma gaskiyar maganarsa.

_Toma taya zai shiga gidan mutanen da yake jin kunyarsu sosai? Bai shirya fuskantar Ismaha Zainab awanan lokacin ba, shi yasa yake gocewa duk wata hanyar da yake da tabbacin zata sadashi da ita. Amma da alamun hakan bashi da amfani, tunda gashi mahaifinta na ƙoƙarin yi masa bahaguwar fahimta._

 "Ba haka bane Abba, kawai inajin nauyi da kunyar shiga gidan ne."

 "Ni na gayyace ka ai malam Musaddiƙ, kaga wancan ƙaton abokin naka shi korarsa muke amma ya maƙale mana duk da yana da nasa iyalin, hakan bai hanashi zuwa ya cinye mana tuwo ba."

Dariya yasa ganin yanda Usama ya fara turo baki kamar ƙaramin yaro "Baba kaima ka biya ta yarinyar nan Ismaha Zainab ko?"


"A'a kawai gaskiyar data faɗa nake nanatawa, kada kazama irinsa kaji ɗana Musaddiƙ. Wuce mu tafi maza na fara jin yunwa." dariya yake yana magana wanda yasa shima musaddiƙ ɗin yin dariyar.


"Allah Baba har na fara jin kewarta, barin ma da babu wanda zan tsokana yanzu." ya faɗa yana yamitsa fuska.


Dariya Alh. Isah yayi dai-dai lokacin da suka ƙaraso gidan "Ai itama ta huta yau, dan zatayi barci babu ciwon kai."


Shi dai Musaddiƙ shuru yayi amma yana jin babu daɗi _"ina kuma Ismaha Zainab ɗinsa ta tafi?"_ tambayar da yayiwa kansa yake jin tsoron amsar da zata same shi.

 Ahaka suka shiga cikin gidan kai tsaye, wanda mutanen gidan suka yi ta masu sannu da zuwa, bayan sun zauna aka kawo musu abinci, nan ma sai da Alh. Isah yayi da gaske sanan Musaddiƙ yasa hannu sukaci, Usama kam dama lomarsa yake hannu baka hannu ƙarya, kasancewar sa ma'abocin hidima wa cikinsa.


 Bayan sun kammala Alh. Isah ya buƙaci son magana da Musaddiƙ ɗin, anan Usama yayi musu sallama zai ƙarasa gidan sa. 

 "Ka gaida Matata Suhaima." Alh. Isah ya faɗa yana murmushi, to yace yana ƙara yima su Salamatu sallama.

 Bayan tafiyarsa shuru ya ratsa tsakanin Alh. Isah da Musaddiƙ na ɗan wani lokaci.


 Gyaran Murya Alh. Isah yayi wanda yasa Musaddiƙ jin faɗuwar gabansa ya ƙaru "Malam Musaddiƙ magana nake son yi tsakanina da kai amatsayin uba da ɗansa."

 Ɗagowa yayi ya kalli Alh. Isah wanda shima kallonsa yake yana faɗaɗa murmushi akan fuskarsa "To Abba, ina sauraronka."

  

 Gyara zamansa Alh. Isah yayi sanan ya dai-daita nutsuwa da maganarsa "Tun farkon ganina da kai naji zuciyata ta nutsu da kai da kuma hankalinka, araina kuma nake girmamaka da iyayen da suka tsaya maka wajan baka ingantaccan ilimin islama. Sai dai abu guda wanda banji daɗinsa agareka ba shine yanda ka ɓoye min soyayyar da kakeyima Ismaha Zainab, asalima sai na lura kamar kana gujema haɗuwa da ita da duk abin da zai kusantaka da ita."

 Cikin sauri Musaddiƙ ya ɗago kansa yana kallon Alh. Isah wanda shima ya kafeshi da nasa idon yana murmushi.

 "Ƙwarai nasan kana sonta malam Musaddiƙ, haka kuma zuciyata ta aminta da kai ya kamata ka sameta, amma nafi son ka ƙwarara zuciyarka amatsayinka na namiji ka fuskanceta, ka sake jarraba sa'arka ni kuma zan tayaka da Addu'a, yau taje garinsu za kuma ta iya ɗaukan sati biyu koma fiye da haka basu dawo ba. Bana so asami wata matsala ko giftawar wani da zai shiga tsakanin soyayyarka."

 Kallonsa kawai Musaddiƙ yake zuciyarsa cike da ƙaunar mutumin, Ashe akwai surukai irin waɗan nan aduniya? Goshinsa ya fara murzawa yana son ajiye matsayi da maganar Alh. Isah aƙasan ransa, godiya ya kamata ya masa ko kuma kunyarsa zaiji.

 Amma amatsayin Uba yake so ya bashi kowata girmamawa, gefe guda yana so ya sanar da shi abin dake wakana tsakaninsa da Ismaha Zainab ɗin, cikin sanyin muryarsa ya fara magana "Na goda Abba. Amma ba gudunta nakeba, ina jin tsoron sake jin kalmar tsanar da take fituwa daga bakin Ismuha Zainab ne, da bakinta ta sanar dani bata sona." ya ƙarasa maganar cikin rawar murya wadda kanaji zuciyarsa acike take da jin haushin maganar.


 Murmushi Alh. Isah yayi sanan ya dafa kafaɗar Musaddiƙ ɗin "Amma ai kai kana sonta ko?" kai ya iya gyaɗa masa kawai "Ka sake gwada sa'arka to, ka kuma cire maganar da tayi nacewar bata sonka aranka, ni nasan aduk inda ɗana yaje dole za'a soshi." ya ƙarasa maganar yana dariya, wanda yasa Musaddiƙ sunkuyar da kansa ƙasa.

 Nan dai Alh. Isah ya masa kwatancan garin da suke da kuma gidan yana ƙara ƙarfafa masa gwuiwa akan yaje ya sameta hakan zai ƙara tabbatar mata da soyayyar da yake mata.

 Godiya ya masa sosai, yana kuma sauƙe fatan alkhairi agareshi, tabbas ya gama yi masa komi daya nuna soyayyarsa da ƙaunarsa akan bashi dama wajan neman ɗiyarsa, to mi kuma yayi saura ya rage agareshi?ai babu shi kam.


 Tafiya yayi gida cike da ɗoki gani yake kamarma an bashi Ismaha Zainab ɗinsa, tunda har Mahaifinta ya bashi dama da dukkanin yardarsa agareshi.


 Da Abbansa yayi karo yana shirin shiga gidan, saboda sallahr issha'i daya dawo.

 "Malam Aboki sai yanzu aka shigo ne?" 

 Dariya Musaddiƙ yayi sanan ya Murza goshinsa fuskarsa ɗauke da murmushi wanda yaƙi ɓacewa, risinawa yayi ya gaida Abban nasa, ya amsa shima fuskarsa da fara'a. Haka suka jera suka shiga gidan atare.

 Daining Abba ya nufa dan dama lokacin cin abincinsu kenan, zama Musaddiƙ yayi kusa da shi yana ƙara yalwata fara'arsa. 


 "Abba gobe Zanje Ringim in sha Allah."

 Ɗagowa yayi daga buɗe filasan abincin dayake gani, ya saita kallonsa ga Musaddiƙ ɗin "Mi zaka iyo a Ringim malam Musaddiƙ?"


 Goshinsa ya murza yana ƙara faɗaɗa murmushinsa sanan ya matso kusa da Abban nasa ya rage magana "Wajan surukarka Ismaha Zainab, ba dama kace zaka nema min aurenta ba tun kafin na tafi karatu."

 Ido Abba ya waro waje sanan ya riƙe haɓarsa, cikin kwaikwayon raɗar da yake masa kamar wani na ganinsu "To ƙato mai muryar yaran taka ta girma ne?"

 Murmushi yayi sanan ya sake murza goshinsa wanda hakan ya zama ɗabi'arsa "Abba shekara 19 fa yanzu take."

 "Ya Allah! Ɗana ya kusa girma." ya faɗa yana dariya sanan ya sake rage maganar sa "Amma tare zamuje dai na rakaka amatsayin babban abokinka ko?"


 Ido ya walo waje sanan ya fara girgiza kai da saurinsa "A'a dai Abba ni kaɗai zanje, idan ta ganka ai sai taƙi fitowa."

 Hannu Abba ya tafa yana salati kamar wata mace, dai-dai nan Umma suka fito ita da Jidda "Lafiya Abu Musaddiƙ kake ta rafka salati?"


 "Inafa lafiya yau ɗana ya fara ƙina, wai bazan rakashi zanje wajan budurwarsa ba."

 Dariya Suka saka masa ita da Jidda sanan taja kujera ta zauna, ita kuma jidda ta fara zuba musu abincin "Allah ni har ka tsorata ni, shi yasa naji kuna ta faman ƙus-ƙus sai da abu yazo gangara da aka ƙi faɗa, gashi ai ka faɗa kowa yaji."

 Nan kuma ya rufe bakinsa da hannunsa yana kallon Musaddiƙ "Bani na faɗa ba dai ko?" dariya sukayi gaba ɗayansu sanan suka fara cin abincin banda Musaddiƙ daya buƙaci kayan Fruit kaɗai yasha ya miƙe, yana musu sai da safe.


 Jidda ma data gama tafiya tayi tabar iyayen nata, anan Abu Usama ya sanar da ita maganar zuwan Musaddiƙ Ringim agobe, fatan alkhairi tayi tana jin daɗi aƙasan ranta ɗanta guda zaiyi aure, ashe akwai wanan ranar aduniyarta? Hawaye ne ya ke ƙoƙarin zuba a idonta tayi saurin gogewa tana jin kewa da rashin iyayenta atare da ita.******

 Ƙamshin turaren daya haɗu da Sassanyar muryarta da take fita da sallama su suka ankarar dashi zuwanta wajan.

 Ɗagowa yayi yana kallonta yana sauƙe ajiyar zuciya dan har ya fidda rai akan zuwanta. Wanda sai da Luyya tayi fama da ita akan saita je ko kuma ta saɓar mata. Zuciyarta babu daɗi ta shiga ita tun farko mutumin bai mataba, ba wai bai haɗu bane, a'a haɗuwar jinin su ne bai zo ɗaya ba.

 "Wa alaikumussalam" ya amsa yana faman washe bakinsa cikin fara'a. Hakan ya ƙara ƙular da Ismaha Zainab aranta tace _"Jibeshi babu aji sai faman washe baki yake?"_ baki ta taɓe sanan ta gaidashi nanma ya amsa da fara'arsa.


Daga haka shuru ya karaɗe wajan sai shi da yake ta faman kallonta, ta hasken fitilar data cika wajan.

 Miƙewa yayi tsaye shima ganin bata da alamar Zama duk daya ce ta zauna ta nuna masa saurin da take da barcin da take ji.

 shi dai kam ya kasa ɓoye mamakin sa, wai Ismaha Abun sa ce ta zama cikekkiyar mace haka.

 "Masha Allah." ya faɗa bayan ya dai-daita tsayuwarsa akan ƙafarsa yana fuskantar ta.

 "Luyya ta faɗa miki komi akaina na san. Sai dai ƙarin da zanyi bai wuce baki tabbacin ƙaunar da nake miki ba tun kina ƴar mitsitsiyarki."

 Ɗagowa tayi cikin takaici da jin haushin maganar wai tun tana ƴar mitsitsiya? Baki ta turo "Umhm" 

 "Yanzu kuma dana ganki sai naji cewar Allah ya halicceki ne saboda ni kaɗai, ataƙaici lokaci yayi da ya kamata ace kin zama mallakina gaba ɗaya. Gaskiyar magana shine bazan ɓata lokaci da yawaba, iyaye zasu shiga maganar kafin ki koma, kinga nima ba mazaunin nan bane, sai mu zauna abinmu a Zakiraini idanma bai mikiba sai na kaiki ko kano na kama miki gida. Allah na tuba ai mu ko ina gida ne awajanmu." ya ƙarasa maganar yana washe baki cikin dariya.


 Haushi gami da takaici suka dunƙulewa Ismaha Zainab awaje ɗaya. Wai wanan adole yayi digree gaskiya an cuci karatu ma, ga magana sak ta marasa kai da gani tuwon ƙauye ya ratsashi.


 "Kinyi shuru, da alamun kin amince da maganata. Ni dama nasan ba zaki ƙi amincewa ba. Sai ki min lissafin abin da zaku buƙata na bakin."

 "Ikon Allah" Dariya ce ta kamata duk da zamanta Miskila dariya na bata wuya, sai gashi yanzu tana yi tana ƙara ƙyaƙyacewa.

 Kallonta yake shima yana dariyar tabbas ta amince da shi, yo mi ya rage kuma ai gobema a ɗaura musu auren.

 Nunashi take tana ƙara dariya, sai kuma ya tsargu ya fara bin jikinsa da kallo, kafin ya sauya fuska.

 "Wai dariyar mi kike min ne?" ya faɗa da ɗan ƙarfi-ƙarfi.

Rufe bakinta tayi da hannunta tayi shuru, sai ta ƙara kallonsa "Yaya Mukhtar ai kai mijin babba ne, ina zaka kai ƴar mitsitsiya irina? Kayi haƙuri zuciyata cike take da girmamaka ako yaushe, ina kuma kallonka amatsayin uban da zai min wakilcin aure. Umm abu guda ɗaya da zan sanar da kai, shine kayi haƙuri ka makara, zuciyata da wanda take Mutƙar So amatsayin mijin aure."

 Tana ƙarasa faɗar haka ta juya ta shige gida. Baki sake ya bita da kallo har ta ɓacema ganinsa.

 Kai ya girgiza ya shuri takalmansa ya fice ko sallama bai tsaya yima Luyya ba yabar gidan.🥀🥀🥀🥀🥀🥀*GIRMAMAWA*


#IsmuhaZainab

#NWA

#Cmnts,like, share

#DaAmana

[2/16, 9:48 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


*😘Um_Nass* 🏇🏼


Page 39


 Har ta shiga gida tana faman dariyar maganar Muntari, wanda hakan yaja hankalin Luyya take tambayarta har ta dawo? Eh kawai tace mata sanan ta shige ɗakin Innarmu. 

 Tunani ne ya shiga kai-kawo acikin kwanyarta tana auna ƙiyasin rayuwarsu ita da Luyya komi ganinsa take kamar acikin barcin da kan ɗauke mutum ya farka, gefe ɗaya kuma na zuciyarta na cike da kewa da kaɗaicin mutum ɗaya "Ko ina ya shiga?" dan tun ranar data ce bata sonsa bata ƙara ganin gilmawar sa ba.

Da tarin tunane-tunane barci yayi awun gaba da ita.


******

Tun da gari ya waye ya shirya tsab cikin farar shadda wanda hakan ya zama ɗabi'arsa sanya fararen kaya. Kusan duka kayansa kalar fari ne, ɗan banbancin da ake samu bai wuce na zaren da ake yima kayan nasa ado dashiba.

Sai dai yau komi da ya sa ajikinsa fari ne tun daga kan takalmi da agogon azurfar dake hannunsa har hularsa da take ɗauke da adon fari da sirkin ruwan zuma kamar yanda aikin da ke jikin shaddar tasa ya zama kalar ruwan zuma da sirkin farin zare.

Jikinsa ya feshe da nau'ikan turaren da suka zama mahaɗin kwalliyarsa.

 Wayoyinsa guda biyu ya ɗauka wanda suma sukayi shige da yanayin shigar jikinsa.

Cikin nutsuwa ya fito daga ɗakinsa ya nufi ɓangaran iyayen nasa, asaman daining ya samesu suna karyawa, hakan ya sashi ƙarasawa yana murmushi.

Sai da ya tsugunna har ƙasa ya gaida su suka amsa cikin jeruwar haɗuwar bakinsu, fuskarsu ƙunshe da fara'a. Sanan jidda ta gaidashi itama tana satar kallonsa.

 "Har ka fito kenan?" Umma ta aika da tambayarsa tana murmushi.

Kai ya shafa kana ya murza goshinsa "Eh Umma."

"Ka karya ga abinci nan"

Kujera yaja ya zauna saitin Jidda yana kallon Abbansa da yake cin abinci bai sake magana ba "Umma amma dai jiya anma Abbana horon yunwa agidan nan? Dan naga yau ko kwalliyar tawa bai yaba ba."

 Dariya suka saka masa sanan suka juyo da kallonsu ga Abba wanda ya ɗan taɓe bakinsa "Ni ina zan gane kayi kyau, bayan kace bazan maka rakiya ba."

 Dariya Musaddiƙ yayi sanan ya murza goshinsa "Jidda nah nayi kyau ai ko?"


Kai ta gyaɗa tana murmushi "Sosai ma, nasan tana ganinka sai ta sume saboda kyan da kayi."

Dariya yayi sanan ya dunƙule hannunsa yana murmushi "Nagode ƙanwata."

  Dariya Umma ta saka "Yau dai naji kan Aboki da abokinsa tun kan aje ko ina."

  

"Waya faɗa miki kinji kanmu? Kawai ban son yin magana mai tsayi ne yau."

Abba ya faɗa dai-dai lokacin da yake goge bakinsa da tishu "Kayi kyau sosai Abokina." ya faɗa yana laliben aljihunsa rafar 1k ya ɗauko guda uku ya dire masa agabansa "Ga wanan kayi mata tsaraba dashi, na biya kuɗin kwalliyar nima."

 Mamaki da jin daɗi suka cika Musaddiƙ ba shiri ya sauƙa akujerarsa yaje ta bayan Abba ya rungume shi "Na gode sosai Abba nah. Allah ya ƙara girma da Arziƙi."

"Ameen ya Allah." ya faɗa yana bibbiga kafaɗarsa.

"Amma wanan kuɗin bakaga yayi masa yawa?" Umma ta faɗa tana kallon kuɗin tana mamaki.

"Ni inaga kamar yayi kaɗan ma, amma kina batun yayi yawa. Na tura takaddunsa wajan mataimakin govnor idan Allah ya shige mana gaba za'a ɗaukeshi aiki amatsayin lakcara idan kuma sunga matsayinsa yafi hakan zai iya samun fiye da wanan, kinga alokacin zai ɗauki wata jigila da hidimar kansa."

Kai ta gyaɗa tana murmushi "Allah ya taimaka to."

"Ameen ya faɗa yana riƙo hannun Musaddiƙ wanda mamaki ya hanashi yin magana "Muje naga tafiyarka lokaci na ƙara tafiya."

Suma su Umma miƙewa sukayi suka takashi har wajan motar suna masa fatan sauƙa lafiya da saƙon gaisuwa ga surukarsu.

 Har ya fice yana ɗaga musu hannu, gefe ɗaya kuma hawaye ke zuba a idonsa, zuciyarsa cike da ƙaunar iyayensa da jin kewarsu atare da shi, kamar da zai bar garin gaba ɗaya.

 Tafiyar awa ɗaya da rabi ce ta kawo shi Ƙauyan Kwalam, wanda sai alokacin yake jin fargaba da tsoron abin da zai faru a haɗuwarsu da Ismaha Zainab.

Da tambayar kwatancan da Alh. Isah ya masa ya samu gidan ba tare da ya sha wuya ba.

Fitowa yayi acikin motar tasa, zuciyarsa cike da fargabar abinyi. Da ƙyar yayi ta ƴan maza ya tura wani yaro akan ya kira masa Ismuha Zainab.

Da gudu yaron ya shiga cikin gidan tun azauren farko ya fara ƙwala mata kira. 

"Ya Allah!" ta faɗa tana dafe da kanta saboda jin kiran yaron take har tsakiyar kanta.

"Ya akayi ne?" ta aika masa da tambayar cikin ɓacin rai da ganin zallar rashin tarbiyyar yaron.

"Wai ana kiran Ismaha Zainab inji wani aƙatuwar mota awaje." yaron ya ƙarasa maganar yana buɗa hannunsa da son kwatancan girman motar.

Harara ta aika masa sanan tace "Kaje kace bata nan."

"Kai tsaya" Luyya tayi saurin dakatar da yaron "Je kace tana zuwa."


Juyawa yaron yayi ya fice kana Luyya ta maida kallonta ga Ismaha Zainab ta zabga mata harara "Kin dai san bazai wuce Muntari ba shine kikace ace bakya nan, wataƙila jiyama korarsa kikayi shiyasa ko sallama bai min ba. Kar na ƙara jin kin wulaƙanta waninsa ma balle kuma ace shi da kansa. Tashi kije ki shirya" ta ƙarasa maganar da yi mata tsawa, wanda hakan yasa Ismaha Zainab tashi jiki na rawa.

Karo na farko kenan da Luyya ta mata tsawa acikin shekarunta, wai kuma saboda ɗan ƙauyen digree ɗin data saka masa suna.

Kai ta jinjina tana hararo zunzurutun wulaƙancin da zata masa, tana goge hawayen da ya zuba akan fuskarta.


Gyalenta ta ɗauko ta yafa kasancewar jikinta tsaff bata jima da yin wankaba, dan gari taso su zagaya ita da su Hassan shine Innarmu ta jasu rakiya wajan ta'aziyyar mutuwar da akayi aƙasan layin. Itama Luyya abinci take ƙarasawa zata je musu gaisuwa idan su Innarmu sun dawo. Wanan ya kawo mata tsaiko acikin tafiyarta.

 Har ta fito waje tana ƙiyasta kalar tijarar da zata yima Muntari.


Turus taja ta tsaya ayayin da idonta yayi tozali da wanda bata taɓa tsammanin ganinsa ba. Ido ta murza tana ƙara warosu waje dan samun tabbacin shi ɗin ne.

Shi dai ta sake gani yana harɗe da hannunsa fuskarsa ɗauke da murmushi. Ganin ta gagara ƙarasowa kusa da shi yasashi taka sawunsa ya matsa kusa da ita.


 Aduk cikin takun da yake yana tafiya da ƙara bugawar zuciyarta ne wanda shima tasa zuciyar ke bugawa da ƙarfi-ƙarfi.

Bai san yayi kewarta ba sai yau da yake ganinta agabansa, bai kuma ƙara hararowa kansa sake yin doguwar rayuwa da tsayin kwanaki ba tare da ita akusa da shi ba.

Numfashi ya ja ya fuzgar da iska mai ƙarfi yana sassauta muryarsa mai sanyi "Bakiyi tsammanin ganina ba ko?" Yana maganar yana kafeta da manyan idanuwansa. 


Jin sautin muryarsa da sauƙar idanuwansa akanta sun ƙara sanyaya duk wata gaɓa da take jikinta. Kai ta iya gyaɗa masa tana murmushi wanda ya fara tun daga ƙasan zuciyarta har zuwa laɓɓanta.


"Sai dai ina fatan ba mafarki nake ba, hakan azahiri ya zo min."


Ido ya waro waje jin maganarta, wanda ita kuma ta ankare da katoɓarar da tayi, hakan yasa ta rufe bakinta da hannunta tana cizawa.

Murmushi yayi sanan ya ƙara sassauta muryarsa "Ni da nake tunanin zansha kora da kara da kuma atule daga yara da duwatsu. Amma saɓanin tsammani na kiran da naji akunnuwana da sautin muryar da yake futa daga taki zuciyar zuwa tawa da gaske ne."

Amamakance take kallonsa kafin ta buɗe baki tana cire hannunta daga bakinta "Ba gaske bane, dan har yanzu banji wanan sautin da amon acikin zuciyata ba." baki ta ɗan taɓe tana ciza yatsanta "Nifa na daɗe da manta ka, yanzuma mamakin ganinka nake agarinmu da kuma dalilin zuwanka da aika kirana da kayi, bayan na daɗe da baka matsaya guda acikin tafiyar."


Tunda ta fara maganar yake murmushi har zuwa lokacin data direta, sanan ya wara hannunsa daga harɗeshin da yayi akan ƙirjinsa "Amma ai baki hana zuciyata ci gaba da sonki ba! Baki kuma hanani abota da taki zuciyar ba! Baki kuma daina zuwarmin acikin barci da ido biyuna ba! Sanan baki hana sautin muryarki isah inda nake ba."

 Ido ta waro waje jin maganar da yake yana tsareta da shanyayyun idanuwansa, yana kuma wurga hannu kamar yaron da yaso rigima. 

Baki ya ƙara taɓewa ya sassauta muryarsa yana daɗa harɗa hannayensa aƙirjinsa "Tunda kin kasa dakatar da waɗan nan abubuwan atare dani inaga bazai kyautu ace na dakata daga kusantar inda kike ba. Iya tazarar da take tsakanina da ke bai wuce na bugawar zuciya da ƙiftawar idoba, aduk inda kike nakan iya ƙiyasta yanayin da kike, zuciyarki kan rinjayi tawa da son jigila da hidima akan ko wani motsi naki."

Goshinsa ya murza da hannunsa yana kallon wani gefen damansa "Ban taɓa hararo kaina acikin wanan garin ba. Asalima ban taɓa jin sunansa ba sai adalilinki. Zan iya jure ko wata wahala da ƙunci adalilinki, amma bazan iya jure nisantarki ba, bazan iya haƙura da Soyayyarki ba."


Kowata kalma ta maganarsa tana dukan zuciya da gaɓoɓin jikinta, tana jin farin ciki na cike gun ƙuncin da yake ranta, tana jin alfahari da girman kai na so ya zarta matsayinta, kanta take ji yana yawo atsakiyar gajimare.

"Ya Allah!" ta faɗa tana sauƙe numfashi da cizan hannun da ya zama abin tsotsarta ashekarun ƙuruciyarta. Sai dai ayau tana son buɗe zuciyarta da bawa Musaddiƙ dama akan amsa tayin soyayyarsa, tana son datse ko wani shamaki da zai zama katanga na rabuwar atsakaninsu.


Idan har amsa masa soyayyar sa zaisa tayi nisa da Muntari nisa irin na har abada to kuwa zata amsa masa koda kalma ɗaya ce acikin jerin gwanon maganar da yake mata. Musamman ayanzu da take jin ta wasai take jin nauyi da ƙuncin da ƙirjinta yayi ya buɗe.

Hannunta ta harɗe akan ƙirjinta sanan ta kai kallonta ga Musaddiƙ wanda shima yana kallonta kamar mai nazartar abin da ke ƙasan ranta "Idan kuma acikin abin da ka jero yanzu akwaishi azuciyar Ismuha Zainab fa?"

  

Kai ya girgiza "Ban gane maganar ki ba?"

Murmushi tayi sanan ta kawar da kanta zuwa kallon gefenta "Ba abune mai sauƙiba samun dama daga cikin damarmakin da muke da su aduniyarmu. Amma idan ina da sauran fata da godiya bai wuce samun managarcin mijin da zai shimfiɗa rayuwarsa wajan ɗaukar nauyina atare da shi ba." juyo da kallonta tayi saitinsa tana kallon idonsa.

 "Tsawon lokaci da shekarun dana ɗauka aduniyata ina yinsu ƙarƙashin ganin kulawa da soyayya daga mahaifiyata, acikin hakan na samu uban riƙon daya haɗani cikin nasa ahalin ya tallafemu cikin soyayya da kulawa irin ta uba da yaransu. Ya bata kulawa irin ta namijin duniyar dakan sadaukar da duk wani jin daɗi nasa saboda matarsa."


Murmushi tayi sanan ta ciza hannunta "Musaddiƙ acikin rayuwar Ismuha Zainab sai ya zama kamar inuwar da take bin mutum aduk lokacin daya cira ƙafafuwansa. Tana jin sauƙa da nauyin dake fita daga zuciyarta da sunanka, idan akwai abu guda da yafi bani wahla acikin rayuwata to na tabbata bazai wuce sabunta ɗaukaka matsayin daka ke dashi acikin duniyata ba."


Ƙwakwalwarsa ce ta toshe ko kuma kunnuwansa ne suke masa gizo? Maganar da Ismuha Zainab ɗinsa take masa yake son ajiye matsayin daya samu aƙasan ranta. Idan akwai rana mafi kyau da jin daɗi acikin duniyarsa to zai iya kiran wanan ce mafi kyau.

"Dan Allah faɗa min abin da kike son sanar dani acikin sassauƙan harshe. Kwanyata ta kasa adana faifan bayanan da kika min."

Ya ƙarasa maganar yana haɗa hannayensa biyu alamun roƙo, wanda yasata rufe fuskarta da tafikan hannunta.

" Nikam mi nayi yau ne? Katoɓarar magana, kuma ga Musaddiƙ." wata zuciyarta ta bata amsar tambayar da take yima kanta.

Ba komi ai tunda na sauƙe nauyin da yake kaina.


"Ya Allah! Kibar bani wahla mana Baby Ismuha" ya faɗa yana murza goshinsa da yin murmushi.

Buɗe idonta tayi dai-dai lokacin da kallonta ya sauƙa akan ƙarasowar Muntari da su Innarmu da su Hassan wajan.

 Murmushi tayi lokacin data ga kallon da Muntari yake aiko musu, wanda babu maraba na harara ne da jin haushi.

Da fara'a Innarmu ta ƙaraso "Wato korata dama kikayi, kinsan balaraben mijina zaizo dan kar ya ganni yace baya sonki ko?"

Dariya suka saka mata banda Ismaha Zainab da ta sauya fuska "Ya akayi kika dawo yanzu bayan ance sai yamma zaki dawo?"

 Mayafinta ta gyara tana murmushi "Rabon ganin sabon mai gidana mana." ta ƙarasa maganar tana dariya.

Risinawa yayi ya gaida ita ta amsa tana dariya sanan ya miƙama Muntari hannu, ba yabo ba fallasa ya amsa yana ɗan ɓata fuska.

Ƙarasawa su Hussain sukayi suna riƙe hannunsa su biyun "Yaya Musaddiƙ waya rakoka?"

"Ni kaɗai nazo.?

"Amma dama kasan garin ne? Jiyafa muka zo."

Murmushi yayi ya shafa kansu "Abba ne yamin kwatancan gidan." sanan ya lalibi aljihunsa ya ɗauko musu alawoyi masu tsada da kuma kuɗi ƴan 200 guda goma "Ku gaida min Luyyah." da gudu suka shige gidan suna godiya da ɗaga masa hannu.


 Mamaki ne ya kama Ismaha Zainab har ta kasa ɓoye mamakin ta "Ya akayi kasan su Hassan?" ta aika tambayar tana kafeshi da ido.

Hannu Innarmu ta tafa "Kunji min yarinya, ya akayi yasanki bai san ƙannenki ba?" fuskarta ta rufe sam ta manta da su Innarmu na wajan.


"Nikam Innarsu ki shige ki barmu mana, kinzo kin hanamu magana." Ismaha Zainab ta faɗa tana turo bakinta.

Hannun Musaddiƙ Innarmu ta riƙe "Kai zo mu shiga gidda na tarbeka yaro, yo wanan ai baka iya zaɓeba ta barka atsaye shirim kamar bishiya ai sai ka gaji." dariya yayi yana son janye hannunsa daga riƙon da Innarmu ta masa, amma kuma abin ya gagara jansa take har suka shige gidan tana faman mitar idan ta matsu ta shigo gidan, an bar baƙo awaje duk da tazarar tafiyar da ya sha.


Hannunta ta ciza tana ƙoƙarin bin bayansu, anan ta tsinkayi Muryar Muntari digree "Wanan shine wanda kike so ɗin?" juyowa tayi ta kalleshi fuskarsa gum kamar an aiko masa da saƙon mutuwa. 

Murmushi tayi "Kai ya kaga zaɓen nawa Baba Mukhtar?"

Harara ya aika mata sanan ya juya ya fasa shiga gidan.


Dariya ta saki mai sauti sanan ta shiga gidan, tuni Innarmu ta kawowa Musaddiƙ abinci da abin sha, ga kuma fura da nono, dan tun zuwan su Luyya gidan baya rabuwa da kayan ƴan gayu.

Har ƙasa ya tsugunna ya gaida Luyya wanda sai abakin Innarmu yaji ainahin sunanta da kuma yanda Ismaha Zainab ta ɓata mata suna lokacin tana koyon magana.

 Dariya yake yana tuna abin data masa lokacin da yazo da mota, wai ta mutu tabar ganin Luyya.

Tashi Innarmu tayi ta bar masu wajan dan suji daɗin zantawa, amma aranta kam ta yaba da hankali da ƙaunar yaron tana kuma jin soyayyar haɗuwarsa da Ismaha Zainab.


 Furar ya iya sha kasancewarsa ma'abocin soyayyarta, sanan ya sha ruwa ya fuskanci Ismuha Zainab "Wata rana zaki min damun fura irin wanan ko?"

Murmushi tayi sanan ta girgiza kai "A'a"


"Mi yasa?" ya faɗa yana wara ido.

"Yaushe zaka tafi?"

Fuska ya sauya "Har kin gaji da ganina ko? Bari na tafi yanzu kafin ki tara min yara masu atule." ya fara ƙokarin tashi.


"Nifa ba korarka nake ba." tayi maganar idonta nayin rau-rau kamar zatayi kuka.

Komawa yayi ya zauna yana ɗan murmushi kaɗan "To mi yasa kike tambaya ta?"


"kawai dai ina son na sani ne."


 "Sai bayan munyi aure zan tafi. Dan na zo kenan."


Ido ta waro waje cikin mamaki "Kaii!"

"Eh mana, ko har yanzu bakya sona ne?"

Hannunta ta ciza ba tare da tayi magana ba "Wanan hannun naki yana shan wahala da jure azabar da ake masa, wajan cizon sa."

 Cire hannun tayi tana kallonsa, sanan tayi murmushi "Ai baya jin komi."

"Mi yasa kike cizon sa?"


Kai ta girgiza "Ban saniba nima, amma kuma ina jin daɗin hakan, musamman alokutan da nake cikin farin ciki, da kuma lokutan da nake cikin kewar wani abu."


Goshinsa ya murza da hannunsa sanan ya kalleta "Yanzu kina farin ciki da ganina kenan?"

"Fiye da yanda ake kiransa."

Hannunsa ya ɗaga sama yana ta godiya ga Allah.

Ranar agarin ya yini sallah kaɗai ke tashinsa yaje masallaci. 


Aranar ya saba da Innarmu da Babuji harma da Luyya ita kam nata farin cikin daban yake, sanin ko waye Musaddiƙ da baiwar da Allah ya masa ba ƙaaramin abu bane agareta samun sa amatsayin suruki.


Lokacin dayazo tafiya ya dirar musu rafar 1k guda biyu wanda suka ƙi karɓa amma ya nuna musu Abbansa ne ya bashi yace ya kawo musu.

Har jikin motarsa Ismaha Zainab ta rakoshi tana murmushi, ja yayi ya tsaya yana kallonta.

"Ina ji kamar naci gaba da tsayuwa ahaka ina kallonki, tun yanzu na fara jin kewarki na ratsani. Anya zan iya tafiya ma."

Murmushi Ismaha Zainab tayi sanan ta harɗe hannayenta akan ƙirjinta kamar yanda shima yayi "Ina jin fiye da abin da kakeji Musaddiƙ. Amma kuma idan na tuna kana maƙale acikin ko wata bugawa da zuciyata sai naji zan samu abokin hira atare dani."

 "Kin san dai ina sonki fiye da yanda mutum yake son kansa ko? Ban shirya tarin tunzurawa da ƙaguwar da zuciyata zata ci gaba da yimin akanki ba."

 Fuskarta ta rufe sanan ta ɗaga masa hannu da zummar komawa gida "Tsaya ki amsa." motarsa ya buɗe ya ɗauko da wata leda mai ƙyal-ƙyali acikinta ya miƙa mata "Ƙaramar kyauta agareni, ina fatan ba zaki dawo min da itaba idan na sake dawowa." yana maganar yana ƙafeta da idanuwansa.

 Numfashi taja ta fuzgar da iska sanan ta karɓi abin daya bata, ta rungumeshi aƙirjinta "Komi naka yana da kyau, duk abin da zai fito daga gareka yana da muhimmanci arayuwa da duniyata."

 Murmushi yayi ya murza goshinsa yau kam ranar nan tafi masa ranaku dubun da suka wuce suka barshi, wata sa'a ce haka yau yataka? Anya ba musauya masa Ismuha Zainab Ɗinsa akayiba? 

 Motar ya shiga badan ya gaji da kallonta ba sai dan zuciyarsa ba zata iya jure sake tsayuwa haka da itaba, dan ji yake kamar ya rungumeta, amma yana jin tsoron take iyakar dake tsakanin halal da haram, zai ƙara haƙuri ta zama mallakinsa.. 


 Hannu ya ɗaga mata yana aika mata da murmushi, itama anata ɓangaran tana jin kewa da zunzurutun ƙaunarsa atare da ita.

 Har ya ɓacema ganinta tana ɗaga masa hannu.

 Ajiyar zuciya ta sauƙe mai ƙarfi sanan ta shiga cikin gida.

  

 Kai tsaye ɗaki ta shige ta buɗe ledar daya bata, wayace ƙirar iphone 7+ sai kuma awarwaron zinare da kuma agogon da ganinsa ya tona tsadar dake cikinsa.

 Wayance tayi ƙara alamar shigowar saƙo, da sauri ta duba.

 

 _"Acikin ko wata rana akwai guda da takan zama zaɓaɓɓiya aduniyar farin ciki, yau ta zama mafi tsada da ƙawatuwa acikin jerin kwanakin dubun da suka wuceni. Ina son ki sosai!"_


  Ta karanta saƙon yafi aƙirga tana jin sauƙa da numfashinta keyi cikin farin cikin.

 "Ya Allah!" anya yau nice?

 Ta ƙarsa maganar tana cizon yatsanta.


 _"Zama na musamman acikin mutane abu ne mai wahala, amma samunka sai ya zama babbar sa'a da riɓanya darajar da take tawa. Nagode da kulawa da kuma tarin alkhairanka agareni. Ina maka fatan sauƙa lafiya."_

 Amsar saƙon data tura masa kenan sanan taci gaba da dudduba wayar.


 Adadin wayar da sukayi taana da yawa har ya isa gida suna waya da jin sauƙar su lafiya. Aranar dai Ismaha Zainab bata aikatu ba kamar yanda suma basu buƙaci ta aikatun ba.


 *****

 Acikin mako biyun da sukayi agarin shaƙuwa ta shiga tsakaninta da Musaddiƙ da duk wani ɗan uwanta, kusan sau biyar yana zirga-zirgar zuwa gidan dan har ya maida garin gida agareshi.

 Hatta Idrisu yasan da zamansa ya bisu da fatan alkhairi, sai dai akan Ismaha Zainab bashi da wani kataɓus asalima duka ragamar auren ya damƙashi ne ga Alh. Isah wanan ya janyo masa kima mai yawa, haka kuma tuni Alh. Isah ya bashi jari har na 200k akan ya nemi wata sana'ar da zai tallafi kansa da ita. Ranar kam yayi kuka yabishi da Addu'a mai yawa, daɗi kam ya masa yau ga ruƙon ɗiyarsa ga bashi tallafi.

 Su Innarsu Kamalu ma saida Musaddiƙ ya jiƙasu da abin arziƙi acikin sati biyun da suka wuce komi nasu ya sauya.

 haka aɓangaran Muntari ya sallama ya bar ma Musaddiƙ musamman daya lura Ismaha Zainab ta maidashi kamar wani kakanta.

 Ƙarshe dayaga hoton Hafsat ƙanwar su Usama ya nemi ta masa hanya. Hakan kuwa akayi. Ita tuni tabada kai ammafa da sharaɗin sak dai ya mata gida amahaifarta Haɗejia, bai wani ja batunba dan yana sonta baya kuma son ta kuskure masa kamar yanda Ismaha Zainab ta masa.


Ranar da iyayen Musaddiƙ suka je neman aurenta aranar ne shima nasa iyayen sukaje. Wani abun daɗi Yaya Zakar sun jone da Bilkisu ɗiyar Rabi. Dan ya hango shaƙuwa da soyayya ga Musaddiƙ kullum hirararta da labarinta na musaddiƙ ne. Hakan yasa baiyi saki reshe ba ya kama Bilkinsun sa.

 Nan aka saka bikin watanni uku masu zuwa.

 Ranar kam ta zamewa MusAddiƙ tamkar ranar sallah yayi sadaka yayi azumi duk akan cikar burinsa daya matso.. Rana bata ƙarya.......
🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀


_👏👏👏👏👏Kalma ɗaya tak, taa isa ta cike min gurbin daya rarike acikin kwanyata. Wanan Kimar, wanan martabar da zaku magantu akanta nake biɗa._
#IsmahaZainab

#UmNass 

#NWA

#Cmnts, like share

#Girmamawa

[2/16, 9:48 PM] Oum Nass: *🏌🏼‍♀ISMAHA ZAINAB 💍*


*😘UmNass* 🏇🏼


Last page 40


Hidimar biki sosai ake aduka ɓangarorin guda uku. Kaya na gani na faɗa Musaddiƙ ya haɗama Ismaha Zainab ɗinsa wanda Abbansa ne ya tada matar ƙaninsa suka je suka haɗo masa, sanin cewar Umma bazata ba.

Ahidimar Auren jidda kawai take sa ran zata baje kolin ta amatsayinta na ɗiya kuma ƙawa agareta.


Tun ana saura mako uku biki Salamatu ta gayyato ƙawarta Asma'u mai gyaran jiki ƴar sokoto tun data zo take faman dirzarsu tun suna mita da maƙalewa har suka saki jiki ganin duk abin da suke abanza.

Tuni fatarsu tayi santsi da sheƙi musamman Ismaha Zainab data bam-bamta da su, kyanta ya ƙara fitowa sosai da sosai. Duk wanda ya kalleta sai ya ƙara juyowa ya kaleta. Atsakanin kuma basa haɗuwa da Musaddiƙ sai waya da suke kusan ƙarar da yini suna yinta, da musayar saƙonni atsakaninsu.


Ahaka har makon bikin ya zo tun daga ranar Juma'a aka fara gudanar da hidimar bikin wanda ta zo amatsayin ranar sakin lallai da kamun hannu ga angwaye, ko wani gefe babanninsu ke hidima awanan ranar.

Ɓangaran Amare ƙawayansu kan ɓoyesu har sai an basu kuɗi sanan su bada asaka musu lallai. Su kuma Angwaye zasu zauna aƙofar gida da abokanansu akan fararen kujeru anan mata zasu samesu afesa ma ango turare wanan shine sakin lallansu.


 Ranar Asabat da misalin ƙarfe 11:30 dubbanin mutane suka sheda ɗaurin Auren Musaddiƙ Adam da amaryarsa Ismaha Zainab Idris sai Zakar Abdullahi da Bilkisu Isah, Mukhtar Bello da Hafsat Isah. Ƙofar gidan Alh. Isah cike yake gam da mutane. 


Ranar Musaddiƙ yayi dariya mai tafe da hawayen farin ciki, ashe da gaske kuka yakanzo asigar farin ciki? Tambayar da yakema kansa kenan lokacin da yaji kunnuwansu sun bashi tabbacin Ismaha Zainab ta zama mallakinsa na har Abada.

Rungumar Ma'aruf yayi yana sauƙe ajiyar zuciya akai-akai "Majnun Ismaha zainab" Ma'aruf ya faɗa yana murmushi da bibbiga bayansa.

"Ina tayaka murna abokina Allah ya baku zaman lafiya."

"Ameen" ya faɗa yana goge hawayen da yake zuba akan fuskarsa, sanan sauran abokanansa suka fara zuwa suna masa murna.


 Duk wata hidima da liyafa ta bidi'a ya soketa ya hana, to dama itama ba ra'ayin abin da zai zame mata hayaniya da ciwon kai takeba, ganin haka da yayi sai yasa duka sauran angwayen haɗe kansu suma suka ce ayi walima da wa'azi.

  

Acikin gida kuwa tun lokacin da sukaji an ɗaura aure gaban amaren ya fara faɗuwa, komi na jikinsu ya zama cikin sanyi wani nauyi suke ji sosai yana sauka akansu. Kallon-kallo aka shigayi tsakaninsu babu mAi iya magana.

Ƙara wayar Ismaha Zainab tayi alamun shigowar saƙo acikinta, saurin buɗewa tayi ganin sunan mamallakin saƙon. Murmushi tayi tun kafin ta buɗe wanda hakan yaja hankalin su Hafsat ya dawo kanta.

  

 _"A Yau duniya ta sheda zamanki mallaki nah! Inajin kaina fiye da sarkin dake kan karagar mulkinsa."_

Wani saƙon ne ya sake shigowa tayi saurin buɗewa _"Mutane sukance abin daka samu yana da banbanci da wanda zaka samu agaba, sai dai ni na miƙe ƙafa da sa ran akan kyawawan ranakun da zasu zo min idan ina tare dake."_

 Hannunta tasa tafara ciza yatsanta tana murmushi, zuciyarta na ƙara buɗewa da so da ƙaunar Musaddiƙ ɗinta.

  Dariyar da taji an saka mata yasata ɗagowa, ganin su Hafsat tayi suna nuna ta "Wallahi kin kusa zarewa Ismaha Zainab, gaba ɗaya Musaddiƙ ya maidaki wata kalar Ismaha Zainab daban." Bilkisu ta faɗa tana ƙara dariya.

 Ido kawai ta wara sanan tayi murmushi ba tare data ce komi ba "Miskilancinki akanmu kaɗai yake zuwa, amma idan kina tare da Musaddiƙ sai ki koma kamar aku dan surutu." Hafsat ta faɗa tana aika mata da hararar wasa


 Kai ta gyaɗa tana shimfiɗa murmushi akan fuskarta "To ya ranku yake? Kuma kuyima mazajanku mana, baba muntari da yaZakal."

Duka suka aiko mata cikin haɗuwar hannu da gudunta ta tashi ta fice tabar musu ɗakin tana gwalonsu.

Gidan cike yake da ƴan uwa da abokan arziƙi su Innarmu da Innar su kamalu duk suna nan, harda Tani da Haule matar Idirisu ta yanzu.

Tani kam tuni ta ƙara sanyi ganin daula da arziƙin da Luyya take ciki "Lallai ta ƙara yarda Hassada ga mai rabo taki ce babba. Yau gashi Ruƙayyar data tsana take cin arziƙinta da kuma alfarmarta, haka kuma aɓangaran Innar kamalu tayi kuka tayi danasani da neman yafiya daga bakin idrisu da Luyya yafi aƙirga, har sun gaji da yafe mata.

 Ko ina Ismaha Zainab ta gifta mutanen Kwalam suna janta da wasa da tsokana, ta zama tamkar wata tauraruwa acikin su. Ko ina ta gifta takan tafi tabarsu da ƙamshin turaren daya zauna mata ajikinta, haka fulawar da aka zizirama hannunta ta ƙara fito mata da sirrin kyan yatsun hanunta.


 Da yamma aka shirya amarai da sauran ƴan biki Malama Hareesa Usman tazo ta gabatar da wa'azi mai ratsa jiki wanda mafiya yawa tana magana akan girman hakkin miji akan matarsa da kuma hakkin matar akan mijinta, har ta gangaro wajan kula da tarbiyyar yara idan Allah ya basu zuri'a. Daga ƙarshe ta rufe da yima Amare Addu'a fatan alkhairi da zama lafiya da mazajansu.

 Kowata mace da ke nan jikita yayi sanyi Haule matar Idirisu harda kukanta nan nadama ta shiga ranta da tsoron azabar da zata risketa idan ta mutu da nauyin idirisu akanta.

Suma haka amarai suka sha kukansu, da fargabar nauyin da aka aza musu akansu.


 Washegari lahdi bayan angama yini da daddare ƴan ɗaukan amarya suka zo, daga ko wani ɓangare motoci ne shaƙe aƙofar gidan, ko wata amarya da motar da zata ɗauketa.


 Riƙo hannayensu akayi aka sadasu da palon Alh. Isah inda suke zaune shida Idirisu da kuma su salamatu dan yima amarai nasiha.

Gyaran murya yayi sanan ya kallesu "Nikam ba sai na ce muku komiba, domin ku da kanku kun san abin daya dace da rayuwarku. Sanan acikinku babu wanda nayima auren dole zaɓin ranku ne na baku, iyaka na ƙara baku haƙuri akan zaman aure, wanda yasha ban-ban da zaman gidan iyaye. Zaku tadda abubuwa mabam-banta acikinsa, wata ƙila kuga abin da kukafi ƙarfi abaya shi zaifi ƙarfinku agidan mazanjanku, wata ƙila kuma kuyi karo da abin dayafi ƙarfinku abaya kunzo kunfi ƙarfinsa anan gaba. Ku ɗauki hakan amatsayin fifiko da ɗaukaka matsayin da Allah ya muku, ku kalli rayuwar aure amatsayin ibada sai tazo muku da tarin alkhairi na lada da samun rabauta arayuwarku ta gaba. Iya abin da zan faɗa muku kenan Allah ya kare fitina ya haɗa kanku da mazajanku." sanan ya juyo ga Idirisu "Malam idrisu ko kana da abin faɗa?"


Kai ya girgiza yana murmushi "Babu komi Alhaji, ai ka riga daka faɗi komi. Sai dai nace Allah ya kaɗai fitina atsakaninsu da mazajansu." toma shi mi ya sani da zai faɗa? Ya faɗa aƙasan zuciyarsa.


Murmushi Alh. Isah yayi "Ameen, ai kayi kyakkyawar Addu'a." sanan ya juyar da kallonsa gun matayensa "Kufa kuna da abin faɗa?" kai suka girgiza suna musu fatan alkhairi sai Luyya da ta ɗanyi gyaran murya bakinta na motsi alamun tana son yin magana. 


 "Faɗi abin da kike son faɗa Maman biyu." Alh. Isah ya faɗa yana murmushi.

Kai ta sunkuyar sanan ta fara magana tana jin nauyinsu agabanta "Ba komi Alhaji. Duk abin da zamu faɗa ai ka haɗa ka faɗa."


Bawai maganar bace babu aranta, amatsayin ɗiyarta ta farko take jin nauyin faɗar magana akanta agaban kowa.

Kai kawai Alh. Isah ya gyaɗa ba wai ya yarda bane, sai dan lokaci na ƙara tafiya gashi ana jiransu awaje.

"To ku rakasu ana jiranku." sai alokacin kuka yazo musu suka rungume junansu gam suna kuka. Wanda hakan ya karyama iyayensu ransu shi kansa Alh. Isah hawaye ne akan fuskarsa yayi saurin gogewaa.

 Da ƙyar aka ɓam-ɓaresu kowacce aka sadata da motar da tazo ɗaukanta.


****

 Tunda ta shiga motar kanta ke sunkuye tana faman rizgar kuka bata taɓa tsammanin zata bar gidansu da Luyya ɗinta atsakanin lokacin ba, amma sai gashi aure ya rabasu rabuwa ta har abada, sai dai tazo da sunan ziyara ta tafi.

Kallonta yake yana jin kukanta yana taɓa zuciyarsa, ido ya rintse ya buɗe da ƙarfi hannunsa ya kai ya riƙo nata hannun, wanda sai alokacin tasan akwai wanzuwar mutum akusa da ita. Wani sanyi da shokin ne sukaji ya sauƙa ahannayensu lokacin da ya haɗu awaje ɗaya.

Cikin hanzari ta janye hannunta amma duk da haka saida ya riƙo hannun ya ɗora akan cinyarsa, kallon zanan fulawar da aka mata da baƙi da jan lallai yake, shafa hannun yake yana jin santsi da laushin fatar, tsintar kansa yayi da kaiwa saitin bakinsa yana sumbata.

Wani abu ne ya ɗarsu daga kanta zuwa ya tsunta wanda yasata saurin kalloshi tana jin faɗuwar gaba.

Ido ya lumshe ya buɗe mata yana murmushi "Bazan iya hanaki kukaba, dan nasan yanda kike cike da kewar luyya. Amma kuma zuciyata bazata iya ɗaukan dukaba, ki barni na lallashi zuciyata dan idona ya gaza zubda nasa hawayen."

Baki ta turo sanan ta fara ƙokarin ƙwace hannunta amma madadin hakan sai ta tsinci kanta rungume ajikinsa.

"Ya Allah!" ta faɗa tana son tashi, amma gam ya ƙanƙameta yana sauƙe ajiyar zuciya ahankali.

"Yanzu kam zaki iyayin kukanki harda ƙari, kinga hawayen sai yana sauƙa akan zuciyata."

  Mamaki da al'ajabi ya hanata yin magana, sai ƙara lafewa da tayi ajikinsa tana sauƙe ajiyar zuciya, nutsuwa ta musamman na sauƙa mata.

 "Umhm! Banji kina kukan ba." ya faɗa yana sumbatar goshinta.

 "Ai dai ka sakeni kafin na samu iskar da zata taimakawa hawayena su zuba." tana maganar tana ƙokarin ƙwatar kanta.

Gyara mata zaman yayi ajikinsa "To ki ɗagani mana." 

Haushin yanda ya riƙeta da yanda yake magana kamar ita ta ɗaneshi yasa ta ciji hannunsa ba shiri ya saketa yana yarfa hannu "Kai! kai!" yana fifita hannunsa da ɗaya hannun, yana kuma hurama hannun iska da bakinsa.

Dariya tayi tana ƙoƙarin rufe bakinta, hakan yasa ya juyo yana kallonta, ganin tana dariya yasashi yin murmushi, yana lumshe ido, wayansa ya ɗauko ya ɗauketa ahoto ba tare data ankareba sai hasken da taga na camerar, saurin juyowa tayi nanma ya ɗauketa.

Baki ta turo kamar tana shirin magana ya ɗauketa, dariya tayi yana "Iyee amaryar Musaddiƙ ta iya selfie."

Wayan ta je da zumar ƙwacewa yayi ɓoye, yana dariya. Dai-dai lokacin da motarsu ta tsaya aƙofar gida. Nan ƴan kawo amarya suka buɗe ta tayi saurin rufe fuskarta da mayafi ta fita. Ajiyar zuciya ya sauƙe ya kwanta abayan motar bayan fitarsu.

Sai da ta tsaya tayi Addu'a kafin ta zura ƙafarta acikin falon har ɗakinta kan gado Baba Yaniro ta kaita ta ajiyeta. Sanan suka bita da Addu'ar samun dauwamamman farin ciki.

Ƴan kai amarya sai masha Allah suke ƙira suna leƙa ko ina na gidan da aka cika mata shi da kayan aladu.


Sai da sukazo tafiya tasa kuka tana ihu amma babu wanda ya saurareta suka gudu suka barta. Sai Jidda ƙanwar Musaddiƙ da zata jira ƴar rakiyar ango su miƙata gida.

Ita ta zauna tana lallashinta kasancewar sa'anni suke da juna.


 Su huɗu suka shigo da abokanansa Ma'aruf da kuma wasu guda biyu wanda suma baƙi ne.

Ƴar tsokana ce ta shiga tsakaninsu kafin su ɗora da yi musu nasiha sanan suka musu sallama da fatan alkhairi.

Rakasu yayi har wajan motocinsu sanan ya dawo bayan ya danƙa amanar Jiddansa ahannun Ma'aruf akan ya kaita gida Ummanta na jiransu.

Dariya yayi yana masa godiya "Ai kuwa nagode dan nima na samu tawa matar akusa" duka ya aika masa ya zame yana masa sallama.

 Ɗakin ya dawo a inda ya barta anan ya tadda ita, da murmushi ya ƙarasa ya zauna akusa da ita "Amaryata bakya laifi." ya faɗa yana ƙoƙarin yaye mayafin dake jikinsa.

"Masha Allah." ya faɗa yana zagaye hannayensa akan fuskarta, hakan yasata wara idanuwanta tana kallonsa, shima nasa idon ya waro yana murmushi "Kin san nima ina da su ko?"

Kai ta iya gyaɗa masa "Amma naki yafi nawa kyau." ya faɗa yana ɗora hannunsa akan saman idonta, yana sauƙeshi har zuwa kan laɓɓanta "Ina son wanan, ina son jin harrufan dakan fita acikinsa." ahankali ya isar da bakinsa ya ɗora shi akan nata ya fara sumbata. Ido ta lumshe bata hanashi ba sai dan kansa ya saketa, kai ta sunkuyar ta rufe fiskarta da tafukan hannunta.

Riƙe hannun nata yayi ya sauƙe shi yana leƙan fuskarta "Kunyata kikaji?" kai ta girgiza masa alamun eh, murmushi yayi sanan ya Sumbaci hannun nata "Ɗazu kin cije ni ahannu na, dan haka yanzu zan rama." da sauri ta fizge hannunta ta ɓoyeshi abayanta "Oh ashe ba daɗi." ya faɗa yana ƙoƙarin riƙo hannun, nan suka fara kokuwa ita tana ƙoƙarin ƙwacewa shi kuma yana son fiddowa "Musaddiƙ mana! Kayi haƙuri kaga kai babba ne idan ka rama hannuna zai cire." 

"Ke kuma ƙarama ce kenan?" kai ta ɗaga masa tana dariya "Naƙi wayon" ya faɗa yana danneta da ƙyar take fidda numfashi "Dan Allah kayi haƙuri. Kaga numfashina ya riƙe." 


Wuyanta ya fara sumbata yana ƙara shinshinar ƙamshin dake jikinta, turarenta ne yake bugarsa yana ƙara rikitashi hakan yasashi tashi ya nufi kitchen ya ɗauko filet da kofuna guda biyu.

Ledar da suka shigo da ita ya ɗauko ya buɗeta kaji ne har guda huɗu manya gasassu sai kuma madarar halandia da ziza ya fiddosu ya zuba acikin kofin ya tuttula ya fiddo kazar ya ajiye acikin filet.


 Tashi yayi ya ɗauko Ismaha Zainab ciɗak ya ajiyeta aƙasa "Nasan duka asatin nan baki samu lokacin da zaki ci abinciba, dan haka ni da kaina zan zauna na baki."

 Itafa yau mamakin Musaddiƙ take gani take kamar ba Musaddiƙ ɗinta ba.

"Nikam na ƙoshi." rai ya ɓata ya yago cinyar kaza ya kai bakinta "Haa bakinki" ƙin buɗewa tayi hakan yasashi ya cusa mata, ba shiri ta karɓa tana dariya, shima dariyar yake "Yarafa akema ɗura ba babba ba."


"Amma ai yanzu kikace min ke yarinya ce ko?"

"Ta wani ɓangaran ni ai babbace."


Kai ya jinjina "Gara hakan ai." yana murmushi yana ƙara jinjina kai.


Saida yayi da gaske taci da ɗan dama sanan ya ƙyaleta shima yaci, anan yace ta tashi su ɗauro alwala suyi sallah. Saida sukayi brush sanan sukayi sallah raka'a biyu.

Ya daɗe yana musu Addu'a sanan ya juyo ya riƙe kanta ya mata Addu'a.


 Tun anan labari ya sha ban-ban.

 Fatan alkhairi amarai.


******

Bayan mako biyu.


Acikin wanan kwanakin shaƙuwa da soyayya mai ƙarfi ta samu wajan zama tsakanin ma'aurata. Wani tattali da ƙauna mai zafi Musaddiƙ yake nunawa Ismaha Zainab, lokuta masu yawa takanji tausayinsa da ƙarin ninkuwar soyayyarsa aranta, musamman yanda yake nuna mata zallar ƙauna.


Awanan ɗan tsakankanin ne oper aikinsa ta fito amatsayin babban lakcara ajami'ar horar da lauyoyi dake Ringim. Hakan yayima Ismaha Zainab daɗi sosai tayi murna da samun kusancin wajan aikin mijinta da mahaifarta.


Sai dai kullum yakanje ya dawo acewarsa bai shirya yin kwanaba haka kuma ringim kamar unguwa take awajansa.


 Wata biyar da bikinsu ta ziyarci gida wanda shine zuwanta na kusan huɗu ne. Sai dai wanan ya zama na na daban dan haɗaka sukayi dasu Hafsat akan suje su haɗu. haɗu dasu Hafsat, Khadija, da kuma Bilkisu. Wanda yanzu take ƙokarin tafiya bauchi tare da yaZakar kasancewar anan yake aikinsa.


Hira suka sha kamar ba zasu rabuba, dan Usama ma zama yayi daram yaƙi fita kasuwa, wai yaushe su zauna haka agida.

Kallon su Bilkisu da Hafsat Ismaha Zainab take tana na musu shaƙiyanci, dan ta lura dukkaninsu suna da ciki, sai hasken da suka ƙara da kuma zaɓen abincin da suka ishesu da shi, na Hafsat har ya ɗan dago riga, ita kuma Bilkisu ta ƙara zama luta da ita.

"Uhmm kemafa kinyi kama da mai cikin, duk da baki ƙara ƙiba ba, ko kuma rama?" Khadija ta kaɗa tana ɗaga mata gira.

Nan kuma ta shiga dudduba jikinta baki ta turo "Nikam banda komi Anty Khadija."

Baki ta taɓe "Kyayima wasu alaye dai amma banda ni."

Anan musu ya kaure tsakaninsu ƙarshe dai tayi shuru tana faman turo baki ita bata da komi. Dariya suka shiga mata tun tana ƙulewa har ta ware suka faɗa wata firar, ranar dai kamar kada su rabu amma ganin dare yayi yasa kowacce mijinta Yazo ɗaukarta.


 ****


Bayan Watanni Takwasss


  Tun daga wajen gidan hayaniyar su da harshensu ke tashi. Daga cikin falon kuma ƴan uwan Ismaha Zainab ne. Khadija, Hafsat, Bilkisu sai Naja matar Usama suna ta hira cikin dariya da barkwanci.

 "Nifa abin mamaki yake bani wai Ismaha Zainab ce da jaririya." Khadija ta faɗa tana kallon Jaririyar da bata da maraba da Mahaifinta sak.

 "Wallahi nima mamaki nake Khadija, musamman idan na tuna labarin shaƙiyancin da tashayi abaya awajan Abban Suhaima." Naja matar Usama ta faɗa tana murmushi.


Dai-dai lokacin da Ismaha Zainab ta fito cikin rantsattsen Less ɗinta kalar sararin samaniya da filawa mai rantsin fari ga sarƙa da awarwaraye ahannunta suma farare, sai takalminta shima marar tudu fari. Ƙamshin da sukaji shi ya ankarar da su fitowarta adai-dai lokacin suka juyo suna kallonta.

 Tafiya take tana rangaji kamar wadda take tsoron taka ƙasa baki sake suke binta da kallo har ta zo ta zauna akujerar da Khadija take kai, sanan ta kanne idonta ɗaya tana ɗaga musu gira da wara hannunta "Wanan kallon fa?"


Ajiyar zuciya Suka sauƙe atare kafin cikin haɗuwar baki suce "Kinyi kyau!"

Gira ta ɗaga musu "Na sani ai"

Duka Khadija ta aika mata "Har yanzu kina da wanan ɗabi'ar taki ta gwaliya ko."

 Zamewa tayi tana dariya "Da zafifa Anty Khadija."

  

Sanan ta juyar da kallonta ga sauran mutanen ɗakin "Matar yaya Udama naji kina gulmata fa, keda Anty Khadija."

 "Kenan laɓe kika mana." Hafsat ta faɗa tana ɗaga mata hannu.


Harara ta aika mata sanan ta taɓe baki "Haba kin san na girmi nan, kawai dai baiwa gareni idan anyi maganata sai naji." Ajiyar zuciya ta sauƙe sanan ta kalli jaririyar da take hannun Khadija.

 "Akwai abubuwa da yawa da nake ganin giftawarsu acikin rayuwata, wanda nake ganinsa kamar mafarkin da yake zuwar mana acikin barcin mu. Cikinsu kuwa harda wanan Amatullah"

 Kallonta sukayi cikin son ƙarin bayani, hannunta tasa ta ciza abakinta "Amatsayin Uwafa nake mamakin kaina."


Dariya suka mata atare sanan Bilkisu ta kalleta tana ƙoƙarin sauyama yaronta kayan jikinsa "Kamar ba kece mai tsokana da takalo faɗa ba. Ni dai ina fatan kada babynmu tayi rigima irin taki."

Ido ta lumshe ta buɗe sanan tayi murmushi "Ni kaina ina fatan hakan. Sai dai kawai nasan ƙaddara na sabunta al'amuranta ta kuma riɓanya mai kyau acikin mararshi. Musamman idan akayi katari da mafarin daya zama ingantacce."

 "Kema ai mai kyau ce Ismaha Zainab, halayyarki abar so ce ko ashekarun ƙuruciyarki."


 Kai ta girgiza tana ƙara yalwata murmushinta "A'a Anty khadija, kibar batu akaina. Mu tafi ga tushen abun."

 "Wa kenan?"

Ido ta ɗaga tana musu fari kafin ta nuna ƙirjinta saitin zuciyarta "Mijina! Bugun zuciyata!"

 Ido suka fiddo waje suna kallonta "Da gaske Anty Khadija ban taɓa tsammanin jin ƙauna mai zafifaba kamar tasa, ban kuma taɓa hararo jin daɗi da zama kamar Kowata maceba sai da na zauna ƙarƙashin kulawar Musaddiƙ."

 Tagumi sukayi suna kallonta kamar da tayi gamo "Muma ai muna jin hakan atare da namu mazajan" Hafsat ta faɗa tana aika mata da harara.


 Dariya tasa tana nuna ta "Chaii Baba mutarin ya koyi love ne babu labari."

 Nan suma suka tayata yin dariyar, ajiye yaronta tayi ta tashi da zummar dukan Ismaha Zainab, tana ganin hakan ta miƙe ta ruga waje.


Karon da sukayi da mutum yasata tsaya Musaddiƙ taga yana murmushi kafin nan ya rungumeta "Kada wadda tazo ta taɓa min matata." tsayawa Hafsat tayi tana kallonsa ya Haɗe girar sama da ƙasa. Kafin ta farga kuma taga ya fara sumbatar Ismaha Zainab da sauri ta juya tana salati da tafa hannu.

 Dariya yayi yana dunƙule hannunsa da ɗaga babban yatsansa ya kaishi ƙasa 👎


   *TAMMAT BIHAMDILILLAHI.*

 _Anan na kawo ƙarshen labarin IsmahaZainab. Ina fatan zaku ɗauki abin da yake mai amfani ku zubar da marasa amfanin cikinsa._

 _Karku manta komi aciki ƙirƙira ne ba wai gaskeba, idan an samu wanda yayi dai-dai da rayuwar wata to ina mai bata haƙuri katari ne da kuma dace._

 

 *Tabbas akwai mutane da yawa da sukan nuna bajintarsu acikin labarina da kuma ƙoƙari wajan dakon jirana, kuna da yawa bazan iya faɗar sunayenku ba. Amma ku sani ako yaushe ina baku kalmar Girmamawa ta agareku da godiya mai ƙunshe da fatan alkhairi. Sai kuma Allah ya sake haɗamu acikin wani labarin.*


 Nagode .


HAJARA AHMAD HUSSAIN (UmNass)


Tags: Bandariya #jarabta #kyautatawa #soyayya
13765
0
1
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!