Hankaka Mai Da Dan Wani Naka!

Written by Maryamerh AbdulPublished on 2018-12-12 18:53:28Category Non-fictionTrue life story! Labari a kan child abuse da kuma fyade. tags: #fyade #childabuse #HIV #sakamakoDuba was labarai »

HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA


      NA MaryamerhAbdul


        01. Rayuwarta


Assalamu alaikum, Maryam is saying hy to you nd your love ones. Yes am back, but this time with a true life story, ni da kaina labarin ya jijjigani da naji that's why I decide to share it with you all and ofcourse da yaddan meshi, I just pray nd hope abunda zan rubuta ya anfane mu kuma masu hali irin wannan su daina ko ince Allah ya shiryesu ya kuma kare mana zuri'a.


***


Na canja abubuwa da yawa cikin labarin saboda wasu dalilai, kamar sunan mutane da garuruwa. Labarin nan ba ni na k'irk'ireshi ba, in yazo iri d'aya da rayuwar wani/wata yanayin rayuwa ne yazo d'aya kuma ban rubuta shi dan cin zarafi ba sai don gyara, kuma ku sani da yaddar mai labarin na d'aura alk'alamina.


 ***


Yakamata d'an Adam ya sani (mace/namiji) cewa 'ya'ya amana ne a garemu kuma tabbas zai tambayemu game dasu, in ma ya kasance ke/kai ka haifa ko kuma rik'o kakeyi, muddin ka karb'a kaci amana ko ka biyewa son zuciya tabbas zaka ga sakamako. 


***


Labarin nan ya k'unshi cin amana, son zuciya, soyayya, ha'inci, rayuwar aure da tab'arb'arewar tarbiyya. Ku biyo ni dan jin abinda labarin ya k'unsa.....


************************************


   "A ganinka ba soyayya nake nuna maka ba da har na baka abunda mutane da yawa suka gagara samu daga wurina Fu'ad? Ka daina fushi dani akan laifi k'ank'ani irin wannan, mun wuce wannan stage d'in na fad'awa juna tsantsar soyayya da lab'b'a. Action speaks louder than voice"


Kallonta ya tsaya yi yana mai tantance maganan da ta fad'a. Tab'e baki yayi ya d'auke kai kamar bazai amsata ba


"A ganinki zan yadda da cewa sona yasa kika bani abunda ni nasan ba nawa bane kuma ba mallakina bane..." 


Dafe kansa yayi yana kad'awa a hankali, bata iya furta komai ba dan tasan bazai shiga kansa ba a wannan lokacin, musamman in tayi la'akari da cewa ta sha maimaita masa iya gaskiyarta amma yak'i amince mata.


"Babu ma anfanin fad'a miki hakan Surayya, ke kinsan yanda na sameki kuma bazan yadda kina sona ba tunda bakya iya kawo min abunda nake buk'ata a lokacin da na nema"


Hannunshi ta damk'e cikin nata, idanunta na kansa tana lumshesu a hankali cikin salonta. Bata barshi ya k'ara ko da kalma d'aya ba dan a nata ganin furuci bazai iya daidaita mata shi yanda take buk'ata ba. 


"Am here for you now, am sorry"


Wannan kad'ai ta iya furtawa ta cigaba da yi masa abinda tafi k'warewa. Bai iya hanata ba dan dama shine burinsa. 


Ba dan komai yake nuna mata b'acin ransa a duk lokacin da ya nemeta bai sameta ba sai don susuce masa da takeyi da kuma biyewa duk wani tarko nasa, shi shaida ne tana matuk'ar sonsa amma hakan ba shi zai sa ya bata yadda d'ari-bisa-d'ari ba. 


*****


A hankali yake bugun k'afanta tare da k'iran sunanta.

"Surayya! Tashi mana"


Bargon da ke jikinta ta gyara tana mai juyi ahankali, can ciki ta iya furta "umm"


"Kinsan k'arfe nawa? Ko bazaki je gida bane yau? Maghrib fa ya gabato, ana ta k'iranki a wayarki na tabbata daga gida ne"


Mik'ewa tayi tana mai janyo rigarta da ke gefenta tana k'ok'arin sawa.


"Wankan ma bazaki yi ba yau?"

"Nayi latti, meh yasa baka tasheni tun wuri ba Fu'ad? Yanzu wani k'aryar zanyi?"


Tab'e baki yayi ya d'auko mataji ya fara taje sumar kansa yana k'are mata kallo ta jikin madubin da ke gabansa. 


Cikin mintuna biyar ta gama sa kayanta, ta gyara fuskarta had'e da sa hijabinta mai hannu. Jakarta ta d'auko ta isa inda yake tana mai sake masa murmushi, hannunsa ya mik'a mata alamar ta bashi nata hannun. Janyota jikinsa yayi yana mai sanya hannunsa cikin hijabin nata


"Ohh Fu'ad i have to go now, duk abunda na maka bai isheka ba?" 


Tayi maganar ne da alamar tsokana, hakan yasa yak'i kulata ya cigaba da abunda ya fara. Cikin kunnenta ya furta 

"i will surely miss you" 


Murmushi tayi mai d'an k'aramin sauti, ta rik'e hannunsa tana mai yi masa fari da idanunta. 


"Zan zo zance anjima"


Ya riga ta furtawa. Sallama sukayi irin tasu tana mai tabbatar masa cewa zata jirasa sannan ta fice fuskarta cike da annashuwa.


*****


"Salamu alaikum" ta furta cikin sanyin muryarta tana mai shigowa cikin falon. Daga kitchen taji an amsa ta, hakan yasa ta ajiye jakarta da hijabinta da ta cire a d'aya daga kujerun falon ta isa wurinta.


"Sai yanzu Surayya? Ina kika tsaya haka? Baki ga missed calls na Zayyan ba? Ai yazo yana nemanki baki dawo ba, yanzu ya fice inaga masallaci yaje"


Sosa kanta ta d'an yi tana mai murmushin da bai kai ga zuciyarta ba.


"Ai Aunty nasa wayan a silent ne, kuma da naje makarantan sai na biya gidan k'awata, a can ne na d'an b'ata lokaci bansan yamma yayi haka ba"


Anty Hajara bata waigo ta kalleta ba bare ta amsa ta cigaba da yankan kayan miyanta, tasan za'ayi haka, shiyasa bata d'aga hankalinta ba ma dan rashin dawowanta da wuri.


"Barin shiga ciki in d'an watsa ruwa, na gaji sosai wallahi"


"Toh, in kin gama ki d'an zo nan ki taya ni miyar nan, Alhaji na hanya kuma kinga har yanzu ban gama yi masa abincinsa ba, ko sallah banyi ba, ki d'an hanzarta kizo ki karb'eni kinji. Yauwa 'yar albarka" 


Murmushi suka sakarwa juna sannan ta fice daga kitchen ta wuce d'akinta bayan ta d'auki jakarta da mayafinta.


*****


Cikin bacci taji ana lalumarta, bud'e ido tayi ahankali tana mai son gano wanda ke k'ok'arin sanya hannunsa cikin wani gurbi a jikinta, rashin wadataccen hasken d'akin ya hanata tantance ko waye. Cikin muryarta mai nuni da ta kamu da abinda yake mata ta furta 


"Ka daina"

Tana k'ok'arin rik'e hannunsa yana turewa.


"Ya zan daina bayan kema kina son abunda nake miki?"

Ahankali yake maganar, hakan bai hanata gane ko shi waye ba. Jin wanda bazata iya hana shi bane yasa ta hak'ura ta zubawa sarautar Allah ido ya gama wasa da ita ya fice daga d'akin. 


Ahankali ta k'ira sunanshi, waigowa yayi daga bakin k'ofan yana sauraronta

"Yaya Zayyan ka fara kai ni mak'ura, ka guji ranan da zan maka abunda bazaka so ba, mugu azzalumi". 


Kwafa yayi ya fice daga d'akin ya barta tana mai zubar da hawaye.


"Wannan wani irin gida ne Allah ya kawo ni? Na gaji" 


Kuka mai sauti takeyi cike da rashin sanin abun yi. Kafin ta kwanta sai da ta had'u da uban gayyar ya dawo, bai ji kunyarta ba ya furta mata "na dawo fa" ita kad'ai tasan meh hakan yake nufi, ga matansa har uku amma babu wacce ta gano manufarsa sai tsirarrun 'yan matan da suke wurin wanda sunsan halinsa kuma sun san ma'anar hakan a garesu da kuma ita.


Wayarta ta janyo ta tsarawa Fu'ad text, wanda tsantsar kewarsa da kuma kod'a zuwansa na d'azu da abunda yayi mata ne a ciki. Bata fi mintuna biyar da turawa ba ya k'irata, nan ta mance da Zayyan da sauran matsalolinta ta cigaba da soyewa da masoyinta.Wattpad:- @MaryamerhAbdul

HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA


      NA MaryamerhAbdul


        NAGARTA WRITERS ASSOCIATION 


02. Mafarin komai


Idanunta da ke kan Zaituna ta d'auke had'e da tab'e baki. Meh zata ji a wurinta matsayin shawara bayan ita kanta na neman shawarar madafar rayuwa? Tana mamakin k'arfin hali da nuna isan 'yan matan gidan nan, tare suke rayuwa sunsan duk abunda ke rayuwar d'aya daga cikinsu amma har wani yana da k'arfin gwiwar tunkarar wani yayi masa magana.


"Dallah malama ki k'yaleni, kin isheni da shawararki. Ki gyara naki rayuwar mana? Ni meh nakeyi?" 


Ta fad'i hakan cike da b'acin rai, idanunta tsantsar haushi ke yawo a cikinsu. 


"Dan ina fad'a miki gaskiya shine zaki gaya min magana Surayya? Ni fa nasan irin rayuwar da mukayi a gidan nan, shiyasa nake baki shawarar da ta fisheki tun kafin wani yaci galaba akanki rayuwarki ta tsiyace yanda na sauranmu ya zama".


Kanta ta girgiza tana mai mamakin irin taurin kan Surayya, meh zatayi mata da zai sa ta gane manufarta?


"Ina fad'a miki saboda naga duk cikinmu babu mai nutsuwarki da k'in kula samari, ina gudun miki lokacin da zaki kasa saita kanki ki fad'a rayuwar halaka wanda na tabbata tsantsar nadama ne zai biyo baya".


Idanunta ta juya alamar maganan ya fara isarta, bata furta komai ba Zaituna ta cigaba da cewa 


"Kinga rayuwar gidan nan babu mai fad'a maka gaskiya, mu shida tunda na taso ban ga an kwab'i wani ba ke shaida ce, kuma cikinmu ke ce k'arama. Daga kan Suwaiba har ke babu wanda Allah ya kawowa miji kuma duk kinsan dalili, kamar dai yanda nace miki ke d'in dai ke ce d'aya wacce muke sa ran aurar dake hannu meh kyau nan kusa tun kafin lokaci ya k'ure ki zama cikin sahunmu, a shekaru yanzu nasan zaki kai ashirin da biyu..."


Bayani ta cigaba da yi mata tana nusar da ita amma Surayya tunaninta ya tafi maganar da sukayi da mahaifiyarta kwanaki uku da suka wuce.


"Kinga ni bana tare dake Surayya, Antynki ita ce uwa da Uba a gareki, lokaci yayi da zaki fidda miji kiyi aure"


Maganar da mahaifiyarta ta fad'a mata kenan, bata iya mata musu ba a lokacin a ganinta zata manta da maganar, toh gashi yau d'aya daga cikin yayyun nata ke bata shawarar aure saboda kamewarta.


*****


"Surayya!" "Surayya!!" "Tashi ki gani Surayyata 'yar kyakkyawata" 


Hannunta yake shafawa ahankali yake maganar, cikin baccinta mai dad'i take jin maganar tasa. A hankali yake shafa sassan jikin yarinyar da bazata wuce shekaru goma-sha-d'aya ba a duniya.


Kuka ta sake masa kamar yanda ta saba a duk lokacin da ya shigo d'akinta. Hakan bai hanasa ida manufarsa ba, sai da ya biyawa kansa buk'ata ya fice daga d'akin ba tare da wani ya gansa ba.


Kuka takeyi mai shiga rai, har yau ta kasa sabawa da halin mai gidan na wasa da ita. K'aramin kwakwalwarta ya kasa tantance mata abinda yake yi, bata isa ta furtawa kowa abunda yake faruwa a kusan kowani dare ba saboda tsoro dan kakkausar shaidar da yayi mata zai illatata muddin yaji maganar a bakin wani. 


Abun takaicin ba ita d'aya yake yiwa hakan ba, sauran yaran ruk'on da suke tare takan ji suna zancen tsakaninsu, mamakinta d'aya, shin su basu tsoron ya illata su dan sunyi maganar ko dai bai musu kashedi kamar yanda yayi mata ba?


A shekaru sun girme mata, yawancin maganarsu akan halin mai gidan baya wuce 


"D'an iska ni ai da yazo min jiya bugesa nayi nace kada ya kuskura ya tab'a ni, sai yayi ta wasa da mutum bai iya komai ba bayan wannan"


Wasu daga cikinsu kuwa k'yamar abun sukeyi dan basu san meh manufarsa da anfaninsa ba, gani suke nuna isa da girma ne dan an kawosu gidanshi su zauna kasancewarsa mai rufin asiri.


Tun bayan rasuwar mahaifin Surayya mahaifiyarta ta k'ara aure, Anty Hajara ta d'aukota ta kawo ta gidan mijinta kasancewar Allah bai tab'a bata haihuwa ba. 


Ta had'ata da sauran yaran rik'on gidan ana kula dasu, cinsu shan su da duk wani abu da yaro zai buk'ata ana yi musu dai-dai gwargwado, matsalarsu bai wuce Alhajin gidan ba. Ya kasance mai bin yaran da dare bayan kowa ya runtsa, wasu daga cikinsu tun suna tirjewa har suka fara biye masa duk da bai tab'a wuce wasa ba.


Surayya kad'ai ke mugun tsoronsa, duk lokacin da yazo mata bata iya hana shi ko cewa uffan sai dai zubar da hawaye, ko dan k'arancin shekaru irin nata shiyasa bata iya hana shi kaman sauran 'yan matan, ko jan kunnenta da yayi mata yasa take tsoronsa.


*****


Surayya bafulatana ce ta usul, fara kyakkyawa mai tarin nutsuwa da girmama na gaba. A shekarunta sha-uku sassak'en budurci ya fara bayyana a jikinta, kyawunta ya k'ara fitowa.


"Alhaji jiya fa kazo nan, yau ma ka sake zuwa"


"Shhhh!" 


"Gaskiya ba wani inyi shiru, ni na gaji in baka barni ba Allah zan maka ihu, kaje wurin wasu mana sai ni ne?"


Ta k'arashe maganar cikin muryar kuka tana turesa daga jikinta, hasken da ya gauraye ilahirin d'akin yasa ta gwale ido dan bugun zuciyarta da ya tsananta.


"Alhaji ma na lafewa anan kenan?"


Zayyan ya fad'a cike da b'acin rai yana huci


"Ke kuma da ke jaka ce mara hankali kike barinsa ya tab'a ki? Ke kinsan irin hak'urin da nayi a kanki ina jiran ki k'ara girma ashe shima mutumin nan idonshi na kanki? Ni na rasa baban nan wani irin jaraba ne dashi, d'anshi yaga abu meh kyau ashe nashi idon da maitarsa har yafi nawa".


Janyota yayi yana mai kallon yanda take a tsorace da mamakin ganinsa a d'akinta, hannunsa ya d'aura akan lab'b'anta yana yi mata wani shu'umin murmushi.


"Surayya ina sonki, dan Allah ki fad'a min gaskiya, baba ya tab'a shiganki?"


A tsorace ta kad'a kai alamar a'a duk da bata san ma'anar maganan nasa ba, tunaninta d'aya in Alhaji yaji zai yi gunduwa-gunduwa da ita.


Murmushin murna yayi ya janyo ta jikinsa 


"kada ki bashi kanki Surayya, ke tawa ce, na dad'e ina rainon soyayyarki a zuciyata, ki min alk'awarin kare min kanki daga kowa, ni kad'ai ne naki kinji, in kina son wani abu ki nemeni ni kad'ai ne zan iya baki"

HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA


      NA MaryamerhAbdul


     NAGARTA WRITERS ASSOCIATION 


        03. Zayyan


   "Surayya yanzu ke in nace miki zanyi aure ma zaki yadda? Duk shekarun nawa in kin had'e nawa ne? Makarantar ma ban gama ba taya zaki kawo min maganar aure?"


"Haba Fu'ad, ya zaka ce min haka? Abunda ake yi a auren wanne ne baka yi? Abunda ake yin auren dominsa ko kuma ciyar dani da bani kud'in kashewa? Duk kana yi min, gani nayi ya dace mu suturta abunda muke yi mu tsaftace shi, amma sai tirjewa kakeyi kana nuna min ba sona kakeyi ba"


Hawaye ke rige-rigen sauk'a daga idanunta, bata yi tsammanin jin haka daga wurinsa ba, a tunaninta zai yi farincikin shawarar da ta yanke tsakaninsu amma sai ya watsa mata k'asa a ido.


"Surayya please understand"


Dakatar dashi tayi ta hanyar matsawa gefe dan hannunshi da ya kawo zai rik'eta.


"Babu abunda zaka ce min Fu'ad, ba sona kakeyi ba shiyasa baka son muyi aure"


Kuka ta fashe dashi iya k'arfinta. Miyau ya had'iye mai d'acin gaske yana mai runtse idanunsa had'e da damk'e hannunsa, bai d'auka wannan lokacin zai zo da wuri haka ba. 


Jin kukan nata ba mai tsayawa bane yasa shi matsowa daf ita, bai yi k'ok'arin rik'e ta ba sai da ya tattaro duk wani zancen da yasan zai nusar da zuciyarta.


"Babyn Fu'ad na sha sanar dake bana son ganin hawayenki, k'ona min rai yake matuk'a, ki tausaya min ki daina kukan sai muyi magana a tsanake mu san abun yi, ke kinsan ina sonki kuma zan miki duk abinda kikeso"


Bayanta yake shafawa ahankali had'e da janyota zuwa jikinsa, kalamai masu dad'i yake yi mata sai da ya tabbatar sun shigeta sannan ya d'ago da ita.


"Kalleni kiji abunda zance miki"


Bakinta a zumb'ure ta d'ago rinannun idanunta tana k'are masa kallo wasu hawayen na dad'a taruwa a kurmin idanunta.


"Zanyi maganan da iyayena in naje gida next week, duk yanda mukayi zan sanar dake. Ya miki?"


Murmushi ne ya sub'uce mata, k'ank'ameshi tayi iya k'arfinta tana mai nuna masa tsantsar murnarta. Bata iya tantance yanayin fuskarsa ba amma murnar da take ciki ya wadatar da ita a wannan lokaci.


*****


"Malam, kaga ka fita min daga d'akin nan, Allah a yau sai in yi maka ihu ko in had'aka da Anty Hajara, kai ko kunya baka ji kana zuwa wurin 'yar matarka, ni ko ka manta ni wacece a wurin Anty Hajara? 'Yar yayanta fa? Haba, na gaji wallahi"


Janyota yayi da iya k'arfinsa ya toshe bakinta


"Kaji banzan yarinya, yaushe kika girma da zaki hana min abunda na raineki dashi? Ni ke da iko dake ko ke kike da iko dani? A gidana fa kike zaune kike cin arziki, kuma yau rana tsaka zaki taso min da shegantaka"


Duk iya k'ok'arinta na k'watar kanta ta kasa, da hannu d'aya ya danneta yana k'ok'arin cire tufafin jikinta.


Lokaci d'aya ta gallara masa cizo had'e da bugesa da gwiwarta, k'ofa ta bi zata gudu ya kamo k'afarta, bakinsa ya kasa mutuwa


"Ai baki isa ba wallahi, sai da kika girma zaki hana ni lasar zumarki, sai lokacin da zan kwashi gara zaki raina min hankali?"


Cikin kuka take basa hak'uri dan ya k'yaleta amma janyota yayi jikinsa


"Yi min shiru, yau sai kin rainawa aya zak'inta, ni kikeson tonawa asiri tun ban miki komai ba?


"Baba wallahi in baka saketa ba ni da kaina zan sanar da kowa abunda kakeyi"


Daga sama yaji muryar ya doke sa, tsayawa yayi kallonsa yana mamakin ta yanda ya shigo d'akin har yasan abunda yake faruwa.


"Zayyan, meh ka shigo yi nan cikin talatainil laili haka? Lafiyanka?


"Nazo wurin masoyiyata mana Baba, haba dan Allah, yarinyar nan ni take so ka hak'ura da ita mana baba, tun tana maka shiru har ta fara rainaka, ka bar min ita kawai da ni tafi dacewa"


"Kai Zayyanu ni kake fad'awa haka? Ka fice min daga nan"


Ya nuna masa k'ofa da hannunsa. Surayya da ke durk'ushe gefe sai ajiyar zuciya take tana kallon ikon Allah, tun shekaru biyu da suka wuce uba da d'a ke rige-rigen zuwa wurinta, yau dai sun had'u kicib'is kaman yanda take addu'ar hakan ya faru.


Tun ranar da Zayyan ya fara yi mata kalamu da biyewa duk k'orafi nata tafi sakewa dashi akan mahaifinsa, baya tab'a yi mata wani abu in tak'i aminta sab'anin Alhaji da duk kukan duniyan da zatayi sai ya gama abunda ya kawo sa zai tsallake ta ya wuce. 


"Da gaske fa nake Baba, in baka daina takurawa Surayya ba ni da kaina zan kawo matanka su ga abunda kakeyi, nagode Allah mama bata raye bata ga abun takaicin nan ba"


Zufa ke keto masa duk da iska mai sanyin da ke shigowa ta tagar d'akin.


Jiki ba laka yaja k'afansa yabi gefen d'an nasa zai fice


"Kuma baba ba wai yau ne kawai nake nufin ka barta ba, in ka sake zuwa wurinta Allah komai na iya faruwa, kuma kai kasan abunda ya dace kayi dan rufin asirinka"


Bai tanka sa ba ya fice ya bar musu d'akin.


Da gudu ta isa wurinsa ta shige jikinsa tana mai sake wahalallen kuka.


"Shhh! Yi shiru, komai ya wuce daga yau"


Gashin kanta yake mayarwa baya had'e da shafa bayanta. Ahankali ya had'e bakinsu wuri guda, dan kanshi ya k'yaleta ya tsurawa fuskarta da yayi ja ya d'an kumbura dan kukan da ta sha.


Ita ma shi d'in take kallo tana mai sake masa murmushi.


"Happy birthday, abunda nazo fad'a miki kenan na tarar da mutumin nan. Yau kin cika shekara goma sha shida, nazo tuna miki alk'awarin da kika min ne"


Murmushin bai gushe daga fuskarta ba ta sauk'e k'wayar idonta. Murmushi mai sauti yayi ya gyara mata gashin da ya kwanto mata bisa fuskarta.


"Ko za'a bani alk'awarina yau?"


Narai-narai tayi da idanunta, a hankali ta gyad'a kanta alamar a'a cike da shagwab'a tace 


"Ni fa dama ban maka alk'awari ba ya Zayyan, na fad'a maka ina tsoro"


Alamun tafiya suka ji daga bakin k'ofar, tuni ya kashe wutar d'akin ya lafe bayan k'ofa.


Kwankwasa k'ofar akayi Surayya ta isa duk ta daburce ta tsorata. Can ciki ta furta "waye?"


"Nice"


Muryar da taji ya k'ara tsurar da ita. Da hannu yayi mata nuni da ta bud'e k'ofar sannan ta murd'a ta bud'e tana mitsike ido da bayan hannunta.


"Anty Hajara lafiya?"

Ta furta tana mai yin hamma tare da toshe bakinta da d'aya hannunta d'ayar kuma na idonta tana murzawa.


•.•.•.•.•.•.•.•.•.•.•.•


Follow me on Wattpad dan samun complete littafin da ma sauran littafaina 

Kwaiseh Maryamah

BADAK'ALA 

Soyayya ce

Jarabtarmu kenan 

Hankaka mai da d'an wani naka 

Wattpad:- @MaryamerhAbdul 

Thank you

HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA


      NA MaryamerhAbdul


      NAGARTA WRITERS ASSOCIATION 


        04. Hak'urina ya k'are


   "Lafiya... meh ya same ki?"

Ta tambaya tana kallon fuskarta daga bakin k'ofar.


Murmushin yak'e Surayya tayi 

"Babu komai, meh kika gani? Meh ya fito dake da dare haka?"


"Alhaji ne..."


"Alhaji kuma? Meh ya same sa? Meh ya faru? 

Ta tare ta tun kafin ta ida maganarta, cike da mamakin rud'ewarta Anty Hajara ke kallonta, can tace 


"Lafiyanki Surayya? Ko zazzab'i kike?"


Fuskarta ta shafa tana mai sauk'e ajiyar zuciya

"Lafiyana k'alau Anty, baki gama maganarki ba"


"Ohh, dama Alhaji ne ya tashe ni wai inzo in duba ki, toh na d'auka baki da lafiya ne ko wani abu"


Murmushi ta sakar mata tace "lafiyana lau Anty, nagode. Barin koma bacci nakeji sosai"


Ta k'are maganar tana mai yin doguwar hamma.


"Sai da safe"

Ta juya tayi hanyar waje, ware ido tayi ganin zata fita daga cikin falon. 


"Ina zaki je kuma Anty?" 

Cikin d'aga murya ta tambaya.


"Shhh! So kike kowa ya tashi, zanje in duba Zayyan ne, shima ance in duba sa, bansan meh ya same ku ba dukka kuna neman b'ata min baccin yau"


Cikin muryar da ba kowa zai ji ba take maganar. Bata jira amsawarta ba ta fice tayi hanyar d'akin Zayyan da sauran yara mazan.


K'ofar ta rufe da hanzari ta iso inda yake

"Kaji ko? Ka fita ka tafi tun kafin ta ga baka d'akinka ta shiga nemanka. Na shiga uku"


Janyo shi take da iya k'arfinta tana tura shi waje. 


"Dallah ki barni inyi tunanin abunda zai fisheni. Mutumin nan ya kwabsa min Allah"


Hannunta ta had'e wuri d'aya hawaye na sauk'a bisa kuncinta

"Please nidai ka fita kafin Anty Hajara ta dawo".


Bai amsata ba ya kama handle na k'ofar ya bud'e yasa kai yana lek'e, ganin babu kowa yasa shi fita cikin hanzari yayi hanyar kitchen.


A dai-dai wannan lokaci Anty Hajara ta dawo tana mamakin inda Zayyan yaje a wannan lokaci, ganinshi bakin kitchen yasa ta isa inda yake 


"Zayyan kai ne anan? Meh kakeyi anan baka kwanta ba" 


Juyowa yayi ya narke ido kaman mai jin bacci 


"yunwa nakeji nazo duba abin da zan ci, meh ya faru? Lafiya na ganki war haka?"


Ajiyar zuciya ta sauk'e

"Ai kun tsorata ni, naje d'akinka baka nan, duk na tsorata nace ko dai baka dawo gida bane. Barin had'a maka tea tunda na fito kawai"


"A'a"

Ya dakatar da ita

"Na samu bread ma na d'an ci zai iya kai ni gobe da safe. Nagode"


Bai jira amsarta ba ya juya ya fice ita ma ta wuce nata d'akin hankali kwance.


*****


Kwanaki goma bayan faruwar hakan, ta samu sa'ida da ziyarar Alhaji. Zayyan ya tabbatar mata bazai sake zuwa ba dan sunyi magana tsakaninsu kuma sun fahimci juna game da ita.


Sai dai ba nan gizo ke sak'ar ba, Zayyan ya canja nasa salon. A kullum in yazo wurinta sai ya nemi ta bashi damar shiga gonarta, abu ne mai wahalar gaske a ganinta ta iya aminta da buk'atarsa.


A duk lokacin da zatayi hira irin wannan da k'awayenta suna bata tabbacin indai mace ta kasance da namiji toh kowa sai ya d'ago dan wahala ake sha. Bazata manta kalmar d'aya daga cikin k'awayenta


"Kiyi duk abunda zakiyi da namiji amma kada ki yadda ya iso area. A tsaya a wasa aji dad'in rayuwa"


Maganarsu take anfani dashi kuma ta tabbata hakan yafi dacewa da ita dan i zuwa yanzu duk wani dad'i da son abunda ake mata tana ji har cikin k'ahon zuciyarta. Zayyan kad'ai take mu'amala dashi dan bai tab'a neman abunda ya wuce wanda take muradi ba sai dai tun da ta shiga shekara 16 komai ya canja.


"Surayya hak'urina ya k'are, bana son in miki abunda bakya so kuma kin k'i bani dama. Ki gane kin girma mana Surayya. Ke tausayina ma bakya ji ko dan kinga ina sonki shine kike ja min rai kike wulak'anta ni?"


"Ya Zayyan ka gane, ni fa tsoron abun nan nakeyi, ka bari ba yanzu ba please"


Tashi yayi fuuu ya bar mata d'akin, tab'e baki tayi ta cigaba da danna wayarta. Kaman an tsikareta ta mik'e ta fice, so take taje wurinsa ta kwantar masa da hankali ko da bazata bashi abunda yake so ba.


Dai-dai k'ofar d'akin Ummi (d'aya daga cikin 'yan matan rik'on gida) taji muryarsa.


Mamaki bai barta ba ta isa ta sa kunnenta dan tabbatar da abunda kunnuwanta ke saurara.


"I missed you Ummina please kada ki min haka" 


Tangarau take jin muryarsa, hannunta ta d'aura a bakinta tana ware ido. Bata tab'a d'auka Zayyan na bin sauran 'yan matan gidan kaman yanda yake binta ba, ta d'auka ita kad'ai yake yiwa haka kamar yanda yake ikirarin yana mutuwar sonta.


Cikin k'unar rai ta bud'e k'ofar, abunda ta hana masa Ummi ke basa. Ta matuk'ar razana da mugun ganin da tayi, tashi yayi ya iso inda take babu kunya ya wanke kyakkyawar fuskarta da mari.


"Baki da hankali ne zaki shigo ma mutane haka"


Bakinta ta rufe da dukkan hanayenta tana mai hana kukan da ke son fitowa samun hanya. Hawaye tuni sun wanke mata fuska bata iya ganin komai dai-dai.


Kaman wacce kaza ya fashewa a ciki ta fice had'e da ja musu k'ofa ta koma d'akinta. 


Kuka ta shiga yi mai ratsa zuciya tana yiwa kanta fad'a da Allah wadai, lallai Zayyan ya cuceta yaci amanarta. Bata iya runtsawa ba dan zuciyarta a cunkushe take jinsa.


Washe-gari da safe ta fice gidan k'awarta dan ji take gidan yayi mata zafi bata son ganin komai da ya danganci gidan Alhaji.


*****


Yau ya kama asabar, a yau take sa ran jin duk wani shawarar da Fu'ad suka yanke shi da ahalinsa.


Tun safe tayi masa text amma bai mata reply ba, tayi ta k'iran wayarsa nan ma bai d'auka ba. Tashin hankali ta shiga ko abinci ta kasa ci, tunanin abunda ya same sa kawai take yi.


Text tayi masa yafi hamsin bai iya mata reply ko guda d'aya ba. 


Misalin k'arfe sha-d'aya na dare bacci ta nema ta rasa, idanunta a bushe kuka ma ta kasa bare ta samu sa'ida taga wayarta alamar text. Kamar bazata duba ba taga ya k'ara wani hasken. Da alamu msg d'in ba d'aya bane.


"Baby" ta gani rubuce saman wayar. Da hanzari ta bud'e sak'on dan daga wurin Fu'ad ne, doguwar rubutu ta gani hakan yasa tun kafin ta karanta ta sha jinin jikinta dan bai saba yi mata hakan ba.


"Am very sorry Surayya, na kasa d'auka wayanki dan bansan meh zance miki ba, am lost bansan ko zaki fahimce ni ba. Na fad'awa mamana komai amma da ta samu Baba tayi masa maganar am sorry to say yace bazai yu ba, inyi tunanin makarantana. Kiyi hak'uri bazai yu muyi aure yanzu ba. Goodbye"

HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA


      NA MaryamerhAbdul


    NAGARTA WRITERS ASSOCIATION 


       05. Had'uwarta da Zaid


   Kwantacciyar sumar kansa yake gyarawa yana k'arewa kyakkyawar fuskarsa kallo ta jikin madubin d'akinsa.


Matajin da ke hannunsa ya ajiye ya daidaita tsayuwarsa, kallon jikinsa yakeyi daga sama har k'asa daga k'arshe ya d'auko agogon hannu ya mak'ala a tsintsiyar hannunsa.


Farar jamfa ya sanya mai ratsin ruwan toka, hular kansa bugun borno sai shek'i yakeyi wanda yayi shige da kayan jikinsa, annurin fuskarsa bai d'auke ba sai shan k'amshi yake yayi hanyar d'akin Surayya.


A dai-dai k'arfe goma da rabi na safe ta gama shirinta tana yafa mayafin kayanta. Yau sati biyu kenan suna wasan b'uya da Zayyan. 


Da safe take fita ta bar gidan sai yamma lik'is take dawowa. Anty Hajara da ta tambayeta inda take zuwa tace mata lesson suke zuwa tunda suka samu hutu. Kasancewar yanzu tana Ss2 bai sa Anty Hajara tayi mamaki ko binciken gaskiyarta ba.


A bakin k'ofarta suka ci karo jikinta ya gogi nasa, da hanzari tayi baya zuciyarta na dukan uku-uku. Kallonshi ta tsaya yi daga sama har k'asa, kasa d'auke idonta tayi tana mai k'issima irin kyawun zatinsa. 


Dole mata su fad'a tarkonsa dan yana da kyawu da iya sa kaya, ga murmushinsa mai kashe zuciyar mai kallonsa. Daf ita ya iso ta lumshe ido tana mai shak'ar k'amshinsa.


Hannunta taji cikin nasa yana murzawa a hankali, a k'asan mak'oshi ya furta


"Surayya fushin ya isa haka, ina kewarki da yawa"


Yawu ta had'iye sannan ta iya samun damar bud'e idanunta. Hannunta da ke cikin nasa ta cire tana mai kallonsa cike da tsana da b'acin rai.


"Allah ya tsareni da zak'in baki irin naka, Allah ya raba ni da biyewa son zuciya in fad'a halaka. Tir da rayuwa irin naka Zayyan, ka cuceni ka cuci rayuwata. Wallahi bazan tab'a yafe muku halin da kuka sani ciki ba kai da mahaifinka, azzalumai mugaye"


Kuka sosai yaci k'arfinta, hannunta tayi anfani dashi wurin share hawayen da ke malala bisa kuncinta. Hannunta yayi k'ok'arin rik'ewa ta ja baya had'e da jifansa da mugun harara.


Bai saduda ba ya isa inda take ya had'e jikinsa da nata, cizo mai zafin gaske ta gantsara masa bisa k'irjinsa, baiyi wata-wata ba ya saketa had'e da bata marin da sai da taga walk'iya cikin idanunta.


Kalamansa ta tsinkayo yana ja mata kunne

"Ni zaki rainawa hankali, dan kinga ina sonki ina biyewa duk shiririta da yarintarki? An gaya miki ke kad'ai ce mace a duniya? Ke ce zakiyi rashina kiyi rashin abubuwa da yawa game da ni, amma ni..."


Ya nuna kansa cike da izza da isa


"Ina da 'yan matan da suka fi ki class, suka fi ki komai suke kawo min kansu ba ni ke binsu ba. Mu zuba mu gani Surayya, ina nan dake zaki kawo min kanki kamar sauran 'yan mata"


Tsaki ya buga ya fice ya barta a d'akin. Jikinta yayi mugun sanyi ta ma kasa fita daga d'akin, kwanciya tayi ta rizgi kuka iya son ranta tana mai tunanin zantukansa.


Ta d'auka zatayi murna tayi farincikin faruwar haka, amma wani sashe na zuciyarta yana mai raya mata tayi kuskure, bak'in ciki mak'il da zuciyarta.


*****


Watanni uku da faruwar haka


Rayuwa ta sauya, Surayya na rayuwa kamar yanda kowace mace ke rayuwa, sai dai nata rayuwar a yanzu ya kasance cike da bak'in ciki, b'acin rai da ganin laifin wautarta na rabuwa da Zayyan. 


Cikin wannan watannin ta kasance a matse, rashin wadataccen kud'i da kwanciyar hankali.


B'angaren Zayyan da Alhaji kuwa ko kallo bata ishe su ba, hakan ba k'aramin tashin hankali yake sa ta ba.


Kud'in da a da take samu daga wurinsu akai-akai tana ciye-ciye da sayan duk abunda takeso dasu yanzu ta daina. In ta samu kud'i daga wurin Anty Hajara baya wuce na sa kati a waya.


Rayuwar ta mata zafi tunanin yanda zatayi kawai takeyi. 


A wannan lokacin ne ta had'u da Zaid ta hanyar social media. Hotonta tayi posting a instagram ta rubuta a caption nata "feeling lonely".


Hoton yayi masifar kyau, idanunta lumshe gashin idanunta sun fito rad'au saman idanunta, bata yi kwalliya ba sai powder da man bakin da ta shafa. Pink labb'anta ta juya ta wani salo wanda ya k'arawa hoton kyau.


Ta DM ya mata magana, lokaci d'aya ya tura mata katin waya na dubu da d'ari biyar. Lokacin da ta loda katin bud'e baki tayi tana mamakinsa, a k'asa ya rubuta mata "I need your digits(ina buk'atar lambarki"


Numban nata kawai ta tura masa ba tare da tace thank you da katin da ya tura mata ba, a nata ganin bada kai ne, dole ta d'an ja ajinta.


*****


Sati kenan had'uwarta da Zaid, sunyi sabo kamar sun dad'e da had'uwa. Ta sake dashi tana zuba masa shagwab'a iya son ranta yana biye mata.


Tsantsar soyayya yake nuna mata duk da basu tab'a had'uwa ba kasancewar tana Yola shi kuma yana Kano.


Ta yadda da dukkan kalamansa, ta fad'a tarkon sonsa wanda take da yak'inin shi ya dace ya kasance miji a gareta har k'arshen rayuwarta.


Kamar kullum tana lafe cikin bargo tana waya dashi, ta shak'e murya baka iya jin abunda take furta masa.


Idanunta na lumshe tana mai sauraron zancensa. Muryarta kad'ai ya tabbatar masa ta kamu da irin maganar da yake mata.


Cikin kwarewa da sanin abunda yakeyi ya furta mata 

"I need you Surayya, come to me now"


Yanayin muryar da yayi mata ya k'ara jefe ta halin sha'awarsa. Can ciki ta iya furta masa kalaman da in ba shi ba babu wanda zai gane abunda ta fad'a dan yanayinta kamar zata fashe masa da kuka.


"I need you too"


Sosai yayi farincikin jinta haka, hakan ya basa damar ida nufinsa akanta ta waya, bata iya hana kanta ba bare ta hana shi ta biye masa yana zuba mata kalamai da sunan phonesex.


Sosai ta zage tana magana dashi tare da hasashen abubuwan da yake fad'a mata yana faruwa a daidai wannan lokaci.


Bai kashe wayar ba sai da ya tabbatar sak'onninsa sun shigeta, bai jira amsarta ba da yace bye saboda yasan bazata iya amsawa ba ya kashe wayar.


~~~~~~~


Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, I wrote this page with a heavy heart, wallahi zamanin yanzu babu abunda zai gyarasa sai addu'a da sa ido akan 'ya'ya. Samarin yanzu sunsan ko wani hanyar da zasu bi dan su kawar da mace daga kan hanya musamman in sunyi la'akari ta fad'a tarkon sonsu ko kuma aka samu mai rauni.


Ya Allah ga bayinka sun zo wani zamani mai wuyar fassarawa, Ya Allah ka kare mu da 'ya'yanmu daga fad'awa halaka, Ya Allah ka raba mu da son zuciya da biyewa shaid'an. 

Ameen ya Rabb.


@MaryamerhAbdul Wattpad

HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA


      NA MaryamerhAbdul


    NAGARTA WRITERS ASSOCIATION 


       06. Kunyana? Toh ni na dawo a bani alk'awarina....


Riga wanda ilahirin k'irjinta a bud'e da k'aramin wando tasa, yau tasha alwashin samun Zayyan dan ya rage mata zafin da Zaid ya tara mata a daren jiya.


Tun safe ta kasa sukuni ta rasa abunda ya dace tayi, daga k'arshe tayi shawarar jan hankalinsa da suffar da Allah yayi mata.


Doguwar hijabi ta sa ta fito falon gidan inda kowa ke zaune ciki harda Zayyan da ya had'e rai ko kallonta bai yi ba bare ya nuna yasan da zuwanta. 


Hannun kujerar da yake kai taje ta zauna ba tare da shakkan kowa a parlon ba. Babu wanda ya kulata bare a hanata zama sai ma hirar da suka cigaba da yi suna shewa.


Zayyan da ya gama gane tarko take son had'a masa sakewa yayi ya cigaba da danna wayarsa bai nuna ya gane manufarta ko ya kula da abunda takeyi ba.


A hankali ta d'aga hijabin nata ta gefensa ta yanda zai iya ganin kwalliyar da tayi dan jansa. D'auke kai tayi kamar ba da gayya tayi ba sai biyewa 'yan parlon take tana taya su darawa.


Tashi yayi ya kalleta sannan yayi hanyar kitchen, bayan mintuna kad'an ta taso ta biyosa a baya. Cikin matan Alhaji babu wanda ya gano duk abunda ya faru cikin parlon shiyasa ta isa wurinsa ba tare da shakkan komai ba.


Basuyi doguwar magana ba bare wani abu yayi musu cikas ga burinsu. Dak'yar ta iya hana shi wasu abubuwan da yake shirin yi mata ta hanyar rad'a masa a kunne 


"Muna kitchen"


Ajiyar zuciya ya sauk'e sannan ya k'yaleta ya fice ta k'ofar baya ba tare da yace komai ba. Ta sha jinin jikinta matuk'a ganin bai mata magana ba, ko tarkon nata bai shigesa bane? Kada yace bazai zo gareta ba bayan tana son kasancewa tare dashi?


Dak'yar ta iya jan k'afarta tayi hanyar d'akinta, Anty Hajara ne ta dakatar da ita da cewa ta shiga d'akinta ta d'auko mata wayarta. A hanyar d'akin taci karo da Alhaji, murmushi ta sakar masa wanda rabon da yaga tayi masa wannan murmushi har ya manta.


Kallonta ya tsaya yi, ganin haka yasa ta fara kwarkwasa ita duk a tunaninta ta samu wanda zai je wurinta dan sun saba mata da rayuwa tare dasu. D'akin ta shiga ta barshi inda yake bata san lokacin da ya bar wurin ba dan lokacin da ta fito baya nan.


*****


Tun daga ranar Surayya ta dawo ruwa tsundum, ba Alhajin ba bare Zayyan. Zaid tana lik'e dashi a waya, duk lokacin da taji tana buk'atar wani daga cikinsu ita da kanta ke gayyatarsu.


*****


A yau tana sa ran zuwan Zaid daga Kano, tun safe bakinta ya kasa rufuwa kowa ya fuskanci murnar da takeyi.


A lokacin da ya iso gidansu Anty Hajara ta samu ta sanar da ita tayi bak'o


"Haba, ai dama duk wannan fara'ar nayi tunanin wani ne zai zo wurinki. Toh a gaishe shi kuma Allah yasa ayi dashi"


Rufe fuskarta tayi da mayafin jikinta tana dariyar Anty Hajara ta fice ta same sa cikin motarsa.


Tsabtatacciyar hira sukayi dan Surayya ta kasa ta tsare ta hanashi rik'e ko da hannunta bare akai ga wani wuri. Da alamu bai ji dad'in hana shi kanta da tayi ba amma ta cigaba dan tana tsoron afkuwar wani abu wanda zai kawo rugujewar soyayyarsu wanda take fatan ya zarce har aure.


Bai jima ba ya tafi bayan yayi mata k'aryar zai je wani wuri amma zai dawo da dare. Shi kad'ai yasan dalilin yin hakan, dare sirrin bawa a cewarsa.


*****


Da misalin k'arfe takwas ya dawo k'ofar gidan ya danna mata k'ira ya sanar da ita isowarsa 


"Ki d'an hanzarta akwai inda zanje daga nan"


Bata sanar da kowa ba ta fice bayan ta feshe jikinta da turare masu dad'i wanda Zayyan ya sayo mata.


Can ta hango motarsa a d'an nesa da gidansu, babu komai ranta ta isa tana mai yi masa murmushi yana kallonta ta mirror d'inshi. Ta ciki ya bud'e mata k'ofar ta shiga sai zuba murmushi take tana kallon halittar Zaid wanda take fatan kasancewa tare dashi har abada.


"Wow! Ya had'u" ta fad'a a ranta tana mai cigaba da dubansa.


"Meh yasa d'azu ko hannunki kika hanani rik'ewa bayan a waya kince kin yadda in miki komai, dan nazo ko?" Ya tambaya yana mai tsareta da ido


"Ai waya kace Zaid dina, ni kunya nakeji bazan iya maka komai ba, na d'auka zan iya amma da na ganka na kasa"


"Kunyana? Toh ni na dawo a bani alk'awarina ne, in bazaki bani ba shikenan. Ko welcome hug ban samu ba daga wurin Surayyata, ai wannan in na fad'awa abokaina ma sai su min dariya yanda kullum nake maganarki"


Yana maganar ne a dai-dai lokacin da yake sanya hannunshi cikin nata da wani salo irin nasa ta daban. Lumshe ido tayi bata iya tankasa ba bare ta hanasa.


Idanunsa na kanta ko kyaftawa baya yi, so yake yaga reaction nata dan ya samu dai-dai lokacin da ya dace yasa kansa ba tare da tayi masa rigima ba.


Mintuna goma ya samu yanda yakeso, tuni ya samu damar sauk'e mayafinta har ma da kallabinta bayan ya had'e bakinsu wuri guda.


***** 


Ba ita ta shigo gida ba sai wurin k'arfe goma bayan sun gama holewarsu cikin mota. Bata had'u da kowa ba bare wani ya tambayeta daga ina.


K'ofarta tasa makulli dan bata buk'atar kowa yau, dama yawanci in bata son wani ya shigo mata kullewa takeyi da makulli, in aka tab'a aka ji a rufe sai a k'ara gaba.


Kwanciya tayi tana tunanin abunda ya wakana tsakaninta da Zaid.


"I love you Zaid"


Ta furta a fili murmushi yak'i barin fuskarta. Wayanta ta janyo ta tura masa text

"I really enjoyed it, I love you so much. Goodnight"


Yana driving yaga sak'onta, murmushi yayi yana jinjinawa kansa tare da k'issima yanda zai yi da ita kafin ya bar garin Yola, lallai yaga alama zai kwashi gara wurin Surayya, she is damn hot.


"Yarinyar ta kamu"

Ya fad'a yana mai buga sitiyarin motar tare da k'yalk'yalewa da dariya


~~~~~~~~~


MaryamerhAbdul @wattpad

HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA


      NA MaryamerhAbdul


    NAGARTA WRITERS ASSOCIATION 


        07. Na cuci kaina


Iskar safiya mai dad'i ke busota tana kwance akan gadonta. Juyi tayi tana bud'e idonta a hankali, bargo ta ja tana mai lumewa a ciki tare da lumshe ido dan tunano daren jiya da tayi. 


Mintuna biyar da tashinta ta mik'e dan d'auro alwala, ko sallahr asuba bata yi ba sai lokacin k'arfe 7 da rabi ya gota.


Bayan ta idar ta d'auko wayarta dan yiwa gogan nata barka da safiya. Bak'uwar lamba ta gani an turo mata sak'on barka da safiya a k'arshe an rubuta its Umar.


Fuskarta ta kwab'e tana tunanin inda tasan meh sunan da har zai mata text.


"Ohh Umar Ustaz"

Ta furta tana kad'a kai had'e da tab'e baki ta fita ba tare da tayi reply ba.


*****


Yau ya kama asabar Surayya tana gida tana kwance kan kujerar da ke parlonsu tana chating da Zaid d'inta, suna hira jefi-jefi da yayyunta mata('yan rik'on gidan) ciki harda Ummi, takan yi mamakin Ummi a duk lokacin da ta tuna ganinsu da tayi da Zayyan, ko da wasa bata tab'a yi mata maganan ba bare taji kunyanta.


 Hankalinta ta mayar kan wayarta ganin sak'on da Zaid ya turo mata


Zaid:- Kizo yanzu please, kada kice a'a kinsan gobe zan koma

Surayya:- Taya zan zo inda kake Zaid? Kasan bazan iya zuwa ba

Zaid:- Meh kike tsoro? Ba ni kad'ai bane fa Surayya, in ma kina tsoron wani abu zai faru ne, ina tare da abokina


Idonta ta juya tana sa'insa da zuciyarta, ta amsa zataje ko a'a. Daga k'arshe ta tura masa

Surayya:- Send me your address. Zan zo nan da awa d'aya.


Wayarsa ya zubawa ido lokacin da sak'onta ya shigo.


 Tsalle yayi ya dire k'asa sannan ya tura mata address na inda yake. D'akin da yake kwance ya shiga gyarawa yana rera wak'a yana takawa had'e da tafa hannunsa.


A b'angarenta ita ma tashi tayi ta shiga d'akinta dan shiryawa. Atamfa ta saka da hijabinta mai hannu, cikin matan gidan babu mai sa hijabi sai ita duk da ita ma ba kullum ba, shiyasa ake ganin duk tafi su hankali da nutsuwa dan iskancinta a b'oye yake, ko yayyunta basu san abunda take aikatawa ba.


Sai da ta sanar da Anty Hajara sannan ta fice hankali kwance. A hanyarta na zuwa bakin titi ta had'u da Umar Ustaz kamar yanda ta yi masa lak'abi. Kamar kullum sai da ya bita ko zai dace ta saurareshi ta bashi damar shiga jerin manemanta.


Shi ya tara mata adai-daita yayi mata sallama ya koma ita kuma ta wuce wurin Zaid duk da zuciyarta na d'an tsinkewa lokaci zuwa lokaci.


*****

Bayan awanni uku:-


Kuka takeyi mai shiga rai ta kasa motsa ko da yatsunta. Daga samanta har k'asanta babu inda baya yi mata zogi, banda ma zuciyarta da takeji kamar ya tarwatse.


Meh take nema a rayuwarta da har ta kai kanta yayi mata wannan aika-aikar? Meh yake nufi da ita? Meh laifinta na kasancewa 'yar rik'o da har suka b'ata mata rayuwa? Gashi yanzu wa gari ya waya? 


Cikin ranta take furta "innalillahi wa inna ilaihi raji'un" 


Ahankali taji hannunsa cikin nata yana murzawa, runtse idanunta tayi dan jin kaman k'aya mai tsinin gaske ne ya soketa, hawaye masu zafi suka silalo ta gefen fuskanta. 


Awanni kad'an da suka wuce ta kasance cike da farin ciki, amma yanzu ji take duk matsalolin duniya kamar an d'aura mata akanta. 


Can k'asan mak'oshi muryarta ke fitowa

"Meh yasa ka min haka? Ina ta rok'onka amma sai da ka ida nufinka akaina?"


"Shhh! My baby" 

Ya furta a daidai kunnenta, tsikar jikinta suka tashi ta runtse idanunta tana mai jin sauk'ar nunfashinsa a saman kunnenta.


"Nine fa Zaid naki. Dan na karb'i abunda ya dace dani har ya zama laifi kenan? Ai ina sonki shiyasa nayi hakan, na kasa sarrafa kaina ne. Ki daina kuka please"


Kalamai masu dad'i yake jero mata cikin k'warewa tare da shafa wasu sassa na jikinta.


Tuni zuciyarta yayi rauni ta mance da aika-aikar da Zaid yayi mata.

Da kanshi ya taimaketa ya kaita bayi dan ta tsarkake jikinta. Bayan ta gama shirinta ya d'auki kud'i masu yawa ya mik'a mata tare da karb'an account number nata.


Da murmushi ta bar gidan duk da wani fanni na zuciyarta na tunasar da ita ta zubar da mutuncinta. Tayi asarar wannan darajar guda d'aya da kowace mace ke tutiya dashi. Wani irin rayuwa ta jefa kanta? Meh ke shirin faruwa da ita? Shin tayi wa kanta adalci?


*****


"Kiyi hak'uri Surayya, ni dama tun farko nasan ba aurenki Zaid zaiyi ba, ki fita daga rayuwarsa tunda har ya daina kulaki da kansa, ki tsira da mutuncinki tun kafin ki rasa, wallahi Zaid bayi da niyyan aurenki. Shawara dai na baki"


Kukan da take rik'ewa tuni ya kubce mata

"Na nawa kuma? Meh yasa abokinka zai min haka? Sati biyu yanzu ya daina d'aukan wayana kuma babu laifin da nayi masa. Tunda yazo nan ya koma bai sake nemana ba, ko na k'irasa baya dauka, wani lokacin ya katse k'iran"


"Kiyi hak'uri, bai kyauta ba amma ya saba hakan, kiyi hak'uri ki daina kuka ki daina damun kanki"


Bata fasa kukan ba har ya gaji da bata hak'uri ya katse wayar. Wayar ta sake ya silale daga hannunta hawaye ya wanke dukkan fuskarta.


"Na shiga uku, meh nayi wa kaina? Kun cuceni Allah ya isa. Duk a dalilin rik'o na shiga wannan rayuwar. Na shiga uku na lalace"


Kuka takeyi tana mai maganganu kamar zautacciya, cikin k'ahon zuciyarta takeji kamar ya fashe k'ullutun da yake wurin wanda ya kasa kwanciya ya fice ko zata samu sauk'i, kukan da takeyi bai rage mata komai daga tuk'uk'in da takeji a ranta ba. Toshe bakinta tayi dan ihun da takeson sakewa


Cikin Bayi ta shiga rik'e da hijabinta ta duk'unk'une ta toshe bakinta dashi sannan ta saki ihun da a ganinta shi kad'ai ya rage mata dan ta kusa fashewa.

Kuka takeyi jikinta na rawa fuskarta da idanunta sun canja launi har zafi suke mata. Hakan bai hanata dainawa ba dan ta sani wannan shine mafarin kukanta a nata duniyan.

HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA


      NA MaryamerhAbdul


    NAGARTA WRITERS ASSOCIATION 


        08. Na tuba


Tsaye take a tsakiyar makaranta tana kallon yanda 'yan ajinsu ke kai-kawo a farfajiyar makarantar. Fuskarta cike da annuri bayyane da murna da farincikin da take ciki.


Mintuna 40 kenan da fitowarsu daga d'akin jarrabawa, tayi hotuna har ta gaji tayi niyyan tafiya gida. Yau dai ta gama zana jarrabawar Neco saura degree tunda ta samu jamb nata.


A hankali ta fito bakin titi ta tsayar da adaidaita sahu ta mik'e hanyar gida tana jinta kamar tana firewa sama dan dad'i.


A bakin k'ofa ta had'u da Umar, ko kallonsa batayi ba ta shige gida tana mai mamakin nacinsa. Yaci ace ya yi zuciya ya barta ko dan k'in kulashi da takeyi. 


"Da guntun wandonsa a wurin, ala dole shi Ustaz"

Ta fad'a a k'asan mak'oshi had'e da jan tsaki tana mai shiga falon gidan ba tare da sallama ba.


Zayyan kad'ai ta gani a falon, hakan yasa ta d'auke kai tayi hanyar d'akinta. Bata san lokacin da ya isota har ya janyo hannunta tare da damk'ewa ba.


"Ke wai meh ke damunki ne? Duk kin wani canja kin zama salihar k'arfi da yaji. Wallahi da babban murya nake ja miki kunne ki daina guduna dan zakiyi mamakin abunda zan miki"


Bai jira amsarta ba ya saketa ya fice ya barta tsaye. Hawaye masu zafi taji saman kuncinta


"Meh laifinta dan ta kame kanta? Meh laifinta dan ta zab'i hanyar tsira? A da tayi wautar komawa rayuwar da suka koya mata amma a yanzu Zaid ya koya mata darasin da har ta mutu bazata manta ba. Tun ranar da ta tabbatar da Zaid ya yaudareta ta fita daga hanyar namiji, ta duk'ufa kan karatun da dashi kad'ai ta dogara, karatun da Alhaji ya sa ta shi kad'ai zai sa tayi masa fata na gari, amma bayan nan babu abunda zai sa tayi masa addu'a a rayuwarta"


"Lafiyanki kike kuka?"

Muryar Anty Hajara ya katse mata tunaninta. Juyowa tayi ta rungumeta tana mai sake fashewa da kuka a kafad'unta.


Cikin rawar murya Anty Hajara ke tambayarta abunda ya sameta. Bata iya amsawa ba sai da ta d'au lokaci

"Na tuna da Baba ne, Anty Hajara inaso inje wurin mamana tunda na gama exam yau, ko sati biyu ne in dawo"


Murmushi Anty Hajara tayi tana mai d'agota daga jikinta.

"Shine zaki tsaya kiyi ta kuka? Har kin tsorata ni na d'auka wani abu ne ya faru"

Shafa gefen fuskarta tayi tana mai cigaba da cewa 

"Ki shirya jibi sai ki tafi, zan sanar da ita a waya da kaina"


"Nagode sosai, Allah ya biya ya k'ara girma"

Murmushi suka sakarwa juna kowa ya wuce nasa d'akin.


*****


Wasa-wasa yau watanni biyar da gama makarantar Surayya. Rayuwarta cike da kwanciyar hankali take tafiyarwa ba tare da damuwar komai ba, matsalarta d'aya ta saba da kashe kud'i, ta ina zata samu kud'ad'en da take kashewa a da dan ya fara damunta matuk'a.


Dalilin nan kad'ai yasa ta amince da soyayyar Umar, ba dan komai ba sai don tunanin samun na kashewa daga garesa, sai dai abun ba kamar yanda tayi tunani ba, dan Umar baya bata isassun kud'in da take buk'ata, kuma bazata iya tambaya ba gudun raini.


A hakan dai take tare dashi har lokacin da ta samu gurbin shiga FUTY, inda ta fara karantar English and linguistics.


A nan ta had'u da Fu'ad nata har ta karb'i soyayyarsa, bai sha wahalar samun kanta har ta fara bashi kanta a duk lokacin da ya nemi hakan ba, dan yayi mata alk'awarin aurenta.


Had'uwarta dashi bai sa ta daina sauraran Umar ba, dan bayi da wani anfani a wurinta, a nata ganin kuma bazai rageta ko k'areta da komai ba. Fu'ad ya cike mata dukkan gurbin da take neman mai cike mata, ya wadatar da ita da dukkan abunda 'ya mace zata buk'ata, yana zubar mata kud'i kamar bai san darajarsu ba.


Sai dai duk sharholiyar da takeyi babu wanda ya sani a gidansu bare a sab'a mata. 


~~~~~~~


Cigaban Labari


Sati biyu da samun sak'on Fu'ad, Surayya ta canja kamanni kamar mara lafiya, tayi kuka kamar ranta zai fita. Tun tana k'iransa baya d'auka har ya kai ga ya fara rejecting, daga k'arshe kuwa ya kashe wayarsa gaba d'aya dan damunsa da take yi.


Kwance take a gadonta idanunta luhu-luhu a lumshe. Wayarta da yake gefenta ta janyo ta bud'e ta shiga wurin k'ira.


Umar Ustaz ta dannawa k'ira. Ringing biyu ya d'auka sallamarsa ya cike dodon kunnenta. Runtse idanunta tayi hawaye suka biyo gefen kuncinta


"Hello kina jina?"


Ya furta jin shirun da tayi. Yawu ta had'iye sannan ta iya amsa sallamarsa ta gaishesa.


Bata yi dogon zance ba ta fad'a masa shawarar da ta yanke

"Inaso ka turo ayi maganar aurenmu"


Sakanni masu yawa sun gota ba tare da ya amsa ta ba, hakan yasa ta ciro wayar daga kunnenta ta duba, ganin har yanzu yana layi ta sake mayarwa 

"Kayi shiru, baka shirya aurena bane?"


"A'a Surayya, na kasa yadda da abunda kika sanar min ne, da gaske kina nufin in turo magabatana ayi maganar aurenmu?"


Idanunta ta juyasu sannan tace 

"Eh, da gaske nake"


Sai sannan taji ya furta alhamdulillah can k'asa sannan yace mata

"Nagode sosai Surayya, ki sanar da naki magabatan sati mai zuwa insha Allah, nagode sosai"


Hawayen da take k'ok'arin hanasu sauk'a ne suka zubo dan jin yanda yake murna, ji tayi kamar ta mayar da hannun agogo baya ta amshi soyayyarsa tun lokacin da ya nuna ra'ayinsa ba sai yanzu da ta gama fand'arewa ba. Kasa rik'e kukan nata tayi ta katse wayar ta shiga kuka kamar anyi mata mutuwa.


~~~~~~~~~


Wa zai iya cankar abunda zai faru? 

Labari yanzu ya fara tafiya, ku biyoni...


MaryamerhAbdul

HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA


      NA MaryamerhAbdul


    NAGARTA WRITERS ASSOCIATION 


       09. Aurena


Kamar yanda addini ya gindaya, Surayya cikin wattannin da aka sa na aurenta tayi istibra'i, ta karb'i k'addarar rayuwarta ta karb'i shawararta na auren Umar hannu biyu. 


Wattani shida da aka sa ya shud'e, yau Jumma'a ake d'aura auren Umar Faruq Samaila da Surayya Abdussamad, bisa sadaki naira dubu saba'in.


Alhaji mijin Anty Hajara shi ya bada aurenta(liwalinta), Mahaifiyar Surayya tun ana sati d'aya saura biki ta dawo gidan da zama. Zayyan bai damu da aurenta da za'ayi ba, hasalima tunda ta turo Umar gida ya fita sha'aninta, yana wuya su had'u sai in ya zama dole.


Biki yayi biki, anci an sha kowa yayi murna an taya ta murnar aurenta, ciki harda sauran yayyunta da har yanzu Allah bai kawo musu mazaje ba. Cikinsu babu wanda ya nuna kyashi ko bak'in ciki, sun jinjinawa kamewarta da kuma shawarar da ta yanke farat d'aya.


*****


Watanni biyar da auren Surayya, duk wani jin dad'i da mace ke nema a gidan aurenta babu wanda bata samu wurin Umar. Takan yi mamakin yanda yake kula da ita duk da bai sameta matsayin cikakkiyar mace ba. 


A nata tunanin ta d'auka daga ranar da ya kusanceta zata ga sauyi a tare dashi game da kulawa da zallar soyayyar da yake nuna mata, sai ya bata mamaki dan babu sauyi ko kad'an. Hakan yasa ta sakankance tana d'iban soyayyarta son ranta. A ganinta bai gane yanda ya sameta bane kasancewarsa sabon shiga.


*****


Tsananin ciwon kai ke addabarta tun daren jiya, ta sha magani amma sai k'aruwa yake yi, ga zazzab'i da amai da take ta zabgawa tun safiya.


"Tashi muje asibiti"

Yana mai mik'a mata hijabinta ya fad'i hakan

"Ka bari sai anjima in munyi la'asar, bazan iya tashi ba yanzu"


Bai mata magana ba ya sanya mata hijabin tare da d'aukarta a hannunsa ya isa da ita cikin motarsa. Sai da ya gyara mata zama yanda bazata takura ba sannan ya koma mazaunin direba ya kama hanyar asibiti.


Kai tsaye likita ya nemi ayi mata gwajin shigan ciki tare da d'iba jininta dan gwadawa.


"Emm Surayya, kinga ana nemana wurin aiki, in sakamakon ya fito ga kud'i ki hau adai-daita ki koma gida"


Idanunta da ke rine ta d'ago tana kallonsa, 

"Yau Saturday fa, wani aiki kuma?"

Kallonsa takeyi dan ta kasa gane yanayin da yake ciki, tsoro ne ko rashin gaskiya? 

"Lafiyanka?"

Ta sake tambaya tana mai k'are masa kallo, cikin muryar rashin lafiya take maganar.


"Ogana ke nemana, karb'i dan Allah. Muyi magana ko a waya ne in ban dawo da wuri ba"

Karb'an kud'in tayi bata sake masa magana ba har ya fice cikin sauri.


Mintuna talatin da tafiyarsa likita ya nemi ganinta a ofishinsa. Murmushi ya sakar mata ya nuna mata kujerar da zata zauna.

"Ina mijinki?"

"Ya d'an fita, lafiya?"


Kallon takaddun teburinsa yayi sannan ya sake dawo da dubansa gareta.

"Ba sai yana nan ba zan iya baki sakamakon bincikenmu kenan?"


Kai ta gyad'a alamar eh idanunta bai d'auke daga kallonsa ba. 


"Mrs. Umar, inaso ki kwantar da hankalinki, ki sani cuta ba mutuwa bane, ki sa a ranki cewa bazaki mutu ba sai lokacinki yayi. Farko dai sakamakonmu bai nuna kina d'auke da juna biyu ba, amma gwajin jini da mukayi ya nuna mana cewa you're HIV positive, zamu d'aura ki kan magunguna mu baki katin da zaki na zuwa every month dan karb'an magani"


Firgici da tsoro ya hana Surayya magana, jikinta rawa yakeyi tana mai kallon likitan dan gaskata abunda kunnuwanta ke saurara.


Zufa tuni ya jik'a saman hijabinta, sauran maganganun likitan bai shiga kanta ba bare ta fahimcesu. 


"HIV? K'anjamau kenan fa? Ta ina na samo aids? Fu'ad? Yes sai dai Fu'ad, amma kenan in ina dashi na sawa Umar mijina?"


Tuna hakan yasa ta toshe bakinta da hannunta hawaye masu zafi na sauk'o mata, duk maganganun da takeyi a zuciyarta takeyi.


Karb'an sakamakon tayi ta kama hanyar waje, tuni ta nemi cutan da take ji ta rasa, tashin hankalin da take ciki ya wuce ciwon kan da take ji. 


Wuri ta samu a harabar asibitin ta zauna, tunaninta tuni ya toshe ta rasa meh ya dace tayi. Kuka ta shiga yi tana mai da na sani da kaicon rayuwa irin nata.


Bata san iya lokacin da ta d'iba a wurin tana aikin kuka ba sai da taji dirin mota ya tsaya gefenta tare da tsinkayo muryar mijinta.

"Lafiyanki Surayya? Meh kikeyi anan? Kinsan k'arfe nawa? Ana k'iran maghrib fa"


Sai sannan ta duba yanayin garin taga duhu ya mamaye inda take. Kallonsa tayi tana mai tausaya masa, rik'eta yayi ya sa ta a mota tare da karb'an takardar sakamakon nata ya koma mazaunin direba sukayi hanyar gida ba tare da wani ya sake magana daga cikinsu ba.


~~~~~~


Thank you all

MaryamerhAbdul na sonku kwarai

HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA


      NA MaryamerhAbdul


    NAGARTA WRITERS ASSOCIATION 


       10. GWAJI 


"Fu'ad ka tabbata da abunda kake fad'a min?"

Tana maganar ne a hankali idanunta na manne da k'ofar kitchen d'in da take ciki. Hannunta dukka biyu take rik'e da wayar a kunnenta fuskarta sai yoyon zufa yake.


"Wai meh yasa kike ma tambayana ne? Na fad'a miki ni am negative, just last week ma nayi donating jini, k'arshen bani dashi kenan. In kina da aids ma ki binciki wad'an da kikayi mu'amala dasu bayan ni, dan ni kam Alhamdulillah na tsira daga wannan tarkon"


Yana jin yanda take kuka amma ya katse wayar, toh meh zai mata? Can mata da wanda ya sa mata cutar ta. Kusan shekara d'aya da rabuwarsu amma zata k'irasa tana masa wannan banzan tambayar?


*****


Ahankali take girgizashi tana ambaton sunansa. "Alhaji k'arfe sha-d'ayan har ya gota"

Ganin bayi da niyyan motsawa yasa ta fara girgizashi da k'arfi tare da k'iran sunansa cikin d'aga murya.


Ahankali ya iya bud'e bakinsa ya fara magana, bata iya jin komai cikin maganarsa ba dan rikicewa tayi da ganin irin karkarwar da yake yi. Da gudu ta mik'e tayi hanyar d'akin Anty Hajara.

"Yaya, ki zo ki ga abunda ya samu Alhaji, karkarwa yakeyi ko magana ya kasa, na tsorata nikam ban gane masa ba"


Da hanzari ta fito daga bayan gida tana k'ok'arin d'aura zaninta.

"Amarya lafiya? Inace lafiya mukayi sallama jiya kuka kwanta? Ko kun kwana bayi da lafiya ne?"


A hanyarsu ta iya amsata 

"Asuban nan fa da muka idar da sallah yace in tashe sa k'arfe sha-d'aya, lafiyansa lau wallahi bansan meh ya same shi ba farat d'aya"


Hawayen da ke gangaro mata ta goge da bayan hannunta. Biye take da Anty Hajara a baya tana mamakin abunda ya samu mijinta a iya awannin da ta fita daga d'akin dan had'a masa abin kari. 


"Ki nemo wani daga cikin yaran nan mu kai sa asibiti, jikin nasa yayi tsanani Amarya nima ya tsoratani" 

Hannunshi ta rik'e cikin nata tare da ambaton Sannu tana k'ara gyara masa jibgegen bargon da yake jikinsa. Sosai yake karkarwa kamar yana cikin fridge.


Mintuna biyar K'annen Zayyan da sauran yaran gidan wad'an da basu aiki suka shigo d'akin. Dak'yar suka iya d'agosa yana takawa ahankali har suka isa mota.


Anty Hajara da maza biyu cikin yaransa ne suka bi motar, Amarya da sauran suka koma ciki suna mai yi masa fatan samun lafiya.


*****


"Surayya"

"Na'am"

"Wai lafiyanki? Meh haka duk kin d'aga hankalinki kina ta ramewa a banza? Toh ai in cutan bai kashe ki ba ke kya kashe kanki, ki nutsu ki san meh kikeyi dama"


Kallonshi ta tsaya yi cike da mamaki, sati d'aya yanzu da jin sakamakon gwajinta, tayi ta jiran lokacin da mijinta zai tambayeta inda ta samo cutar amma yayi biris kaman bai san da sakamakon ba.


Toh yau dai gashi yazo mata da wani salon wanda ta kasa ganewa.

"meh maganansa yake nufi? Bai ji haushin sa masa cutan da nayi ba kenan, wait, sa masa kuma? In ni na sa masa kenan Fu'ad ne ya sa min kuma ya tabbatar min bayi dashi"


Runtse idonta tayi har ya fice daga d'akin bata iya ce masa komai ba, ta kasa gane abunda ke faruwa da rayuwarta, ta ina ta samo k'anjamau? Bayan Fu'ad da Zaid babu wanda ya tab'a kusantarta a rayuwarta gaba d'aya, toh ko dai cikin su Alhaji da Zayyan ne wani ya goga mata? Dan tabbas taji ana iya d'aukan cutar ta yawu, doguwar sumba na iya janyo canjen white blood cell tsakanin juna, toh ko dai ta hakan ne?


Da sauri ta kad'a kanta alamar a'a tunowa da tayi jiya tayi waya da Anty Hajara kuma ta tabbatar mata har lokacin ba'a tabbatar da cutar da ke damun alhaji ba, da k'anjamau ne da zata sanar mata.


"Zayyan kenan? Toh ni yaushe rabona dashi da har zan samu a wurinsa?"

Ta furta hakan a fili hawaye masu zafi na kwaranya daga idanunta. Lab'b'an bakinta na k'asa ta ciza tana mai kad'a kanta ahankali dan cushewar da tunaninta yayi.


"Umar? Kenan a wurin Umar na samu? No, bazai yu ba, Umar baya neman mata kuma Ustaz ne taya zai samo wannan cutar? Na tabbata Zayyan ne, duk da jikinsa bai nuna mai k'anjamau ba amma shine, yes, ya zama dole in nemesa inji ko yana da wannan cutar".

Duk zancen nan a zuciyarta take yi.


*****


"What? Are you insane? You most be stupid Surayya, ni kike kallon tsabar idona kizo har cikin d'akina kina tambayana ko ina da k'anjamau? Baki da hankali ne? Naga alaman tunda kika auri wannan gidahumin kika rasa tunaninki"


"Zayyan ya isheka, nazo nan ne dan in tabbatar da zargina, ka sanar dani yaushe rabonka da gwajin HIV? In kasan ka kai shekara toh ka gaggauta zuwa asibiti dan ka tari cutar tun kafin tayi maka illa"


Bata jira zancensa ba ta juya zata fice daga d'akin.

"Surayya kinsan meh kike cewa? Kin fa rud'ani? Meh kike nufi?"


"Na dai baka shawara, in ka samu sakamakonka sai ka nemeni in maka k'arin bayani"

Bata juyo ba tayi masa maganar, hakan yasa tana gamawa ta cigaba da tafiyarta cike da nutsuwa zuciyarta na harbawa kamar zai b'allo ya fito daga k'irjinta.


Can d'akin Anty Hajara ta koma dan sanar da ita ta gama su wuce asibitin duba jikin Alhaji.

A hanyarsu ne Anty Hajara ke sanar da ita 'yan mata uku na gidan sun fito da mazajensu har an fara maganar aure. Sosai ta taya su murna amma sai ta tsinci kanta da bada shawarar ayi gwajin jini kafin ayi auren.


"Meh yasa? Baki ma san mazan ba bare kice suna da halin banza"

"Ai Anty ba sai kana da halin banza za'a duba lafiyarka ba, yana da muhimmanci sosai a wannan zamanin ayi gwaji kafin aure, duk da ahalin maza wani lokacin har da na matan kan fusata a duk lokacin da aka nemi yin gwajin, yakamata a gane cewa yin gwajin ba shi zai nuna ba'a yadda dakai ba, ana cutan mata da yawa da wannan cutar a rashin sani Anty"


"Hakane, kinyi gaskiya Surayya, insha Allah zan bada shawarar haka in Alhaji ya d'an samu sauk'i, kin kawo shawara mai kyau, Allah ya dad'a kare mu daga hannun azzalumai marasa tausayi"

Ameen kawai ta iya furtawa dan zuciyarta ya karye, rayuwarta yazo k'arshe tayi asara har abada. Dak'yar ta iya mayar da hawayen idanunta.


~~~~~~~~~

Dan! dan!! dan!!!

Labarin ba mai tsawo bane dama na sanar daku, kada kuyi mamaki in gobe nace muku k'arshe😂 Wasa nake, har yanzu da sauran tafiya.

Ku fad'a min ra'ayinku game da wannan shafin, meh ra'ayinku game da yin gwaji kafin aure?

Ya mazauna wurinku suke d'aukan wannan shawarar na gwaji kafin aure? Nidai sarkin garinmu ya hana d'aura aure sai da gwaji, duk malamin da ya d'aura aure ba tare da gwajin HIV ba yana fuskantar hukunci mai zafi tare da tara.

Zan so jin ra'ayoyinku.

Thank you so much 


MaryamerhAbdul

HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA


      NA MaryamerhAbdul


    NAGARTA WRITERS ASSOCIATION 


       11. ZALIHA


"Ya za'a ce ba'a san meh yake damunsa ba? Meh anfanin kawosa asibitin in har su likitocin da kansu bazasu iya sanin meh matsalarsa ba bare su basa magani. Sun dinga k'ara masa ruwa kenan suna masa allurar bacci, haka akeyi? Ni ban yadda da asibitin nan ba ma, canja asibiti kawai zamuyi wad'an nan basu san meh sukeyi ba"


Zayyan ne ke wannan batu yana tsaye a bakin k'ofar d'akin mahaifinsa tare da Anty Hajara, Amarya da k'anin Alhaji mai suna Salihu.


"Nima dai abun nan yana d'aure min kai Zayyan, sati fa da kwanaki babu wani sauyi bare a fad'a mana tak'amaimai cutarsa"

Kad'a kai Anty Hajara tayi tana mai cigaba da cewa "abun nan akwai d'aurin kai".


"Yanzu dai duk ba wannan ba, zayyan ka tafi da matan gida ni zan ga likitan da kaina mu san abun yi, gaskiya yana cikin ciwo in akayi la'akari da maganganunsa, haka kawai ya dinga bada wasiyya kenan yana cewa mutuwa zai yi"


Hawayen da ya taru a idanunsa ya goge ya cigaba da cewa

"Ban tab'a ganin yaya cikin irin halin nan ba, d'azu ce min yayi ya gwammaci mutuwa da abunda yake ji cikin jikinsa, wannan wani irin cuta ne?"


Duk jikinsu a mace suka bar wurin, kowa da abunda yake ransa game da ciwon Alhaji, wasu na tunanin sammu akayi masa dan wani abun nasa kamar hakan. Komai na jikinsa ciwo yake a nasa fad'an, ji yake kamar ana soka masa allura a dukkan jikinsa, wani lokaci kuwa kamar ruwan zafi ake kwara masa.


*****


Sosa kai Zayyan yayi yana tunanin k'aryar da zaiyi musu dan ya wuce karb'an sakamakonsa, dalilin zamansa a asibitin kenan na tsawon awanni.

"Dan Allah barin d'an duba abu anan kafin mu wuce"

Amsawa kawai sukayi da toh suka shiga motar nasa suna zaman jiransa.


Wurin gwajin jinin ya shiga zuciyarsa na harbawa, ba k'aramin tashin hankali ya shiga ba tun ranar da Surayya ta tunkareshi da maganar k'anjamau, shi lafiyan jikinsa k'alau ta ina zai samu? Shakkun da yake dashi kad'ai yasa shi zuwa gwajin nan, amma ba dan haka ba hankalinsa a kwance yana sharholiyarsa da mata yana jin dad'in rayuwarsa.


Bai wani zama ba aka bashi sakamakonsa likitan na cewa "its negative"

Murmushi ne ya kufce masa tare da cafke hannun likitan yana girgizawa yana hamdala a ransa. Kaman anyi masa albishir da gidan aljannah yake ji. 


Da hanzari ya fito murna fal ransa, bakinsa ya kasa rufuwa ya isa wurin motarsa, sai da ya danna kid'a sannan ya fizgi motar ya bar harabar asibitin. Duk wannan a salon murnarsa kenan.


*****


"Umar magana fa nake, bani da kud'i a hannuna kuma kasan makaranta zanje, tun d'azu fa kai nake jira kaga har zanyi latti"

Ta k'arashe maganar tana duba agogon hannunta.


Ko kallonta bai yi ba ya ciro d'ari biyu ya mik'a mata sannan ya cigaba da aikinsa a komfutarsa(computer)


Karb'a tayi tana kallonsa, ganin ba magana zai mata ba yasa ta fara magana

"D'ari biyu ne zai kai ni makaranta ya dawo dani? Kuma kada inci ko in sha abu? Ka manta kud'in da kake bani na sati ne? In ma ka daina bani na satin ne ai sai ka k'ara min ko d'ari biyar ne in sha abu in naji ishi"


"Dan Allah ki b'ace min akaina, haba! Sai mitan tsiya kika koya. In bakya so bani kud'ina"

Ya mik'a hannunsa dan ta bashi d'ari biyun.


Baki bud'e take kallonsa, mamakinsa bai barta ba. Ganin da gaske kud'in yake so ta mik'o masa yasa ta sa a jaka ta bi gefensa ta wuce.

"Na tafi"

Ta furta can k'asa, bai ce mata komai ba ta bar gidan tana mai takaicin sauyawarsa.


"Ba laifinsa bane, dole yaji haushina tunda na k'ak'aba masa cuta, na ma yi sa'a bai hau ni da duka ya hana ni makarantar ba"

Ta furta a fili tana mai share hawayen da ke sauk'owa daga idanunta.


*****


"Kinsan Allah sa'arki d'aya kina da aure, da sai na mugun ci miki mutunci akan tashin hankalin da kika sani....."


Sheshshek'ar kukanta ne ya dakatar dashi, ya ciro wayar daga kunnensa ya kalli sunan nata da yayi saving sannan ya mayar kunnensa.

"Dan uwaki kukan meh kike min? Dan kinji haushi bani da cutar shine kike kuka? Wai tsaya, ko kece kike dashi shine kike son k'ak'aba min"


Cikin sheshshek'a ta iya cewa 

"Dan Allah ka k'yaleni Zayyan, na baka shawara meh laifina da zaka dinga zagina? Tunda baka dashi kayi hamdala ka tuba ka bar halin da kakeyi tun kafin lokaci ya k'ure maka, wallahi ina fad'a maka hakan saboda ni nasan illar bin son zuciya. Kuma ka sani, mazinaci baya auren salihi sai mazinaci d'an uwansa, a ganinka zaka tsira ko ka b'uya wa fad'ar Allah? Ni dai nawa shawara kuma na baka, wad'an da suka rasa wannan daman shikenan ta wuce musu har abada, kada ka bari ka zama cikinsu"


Bata jira maganansa ba ta katse wayar, yanayin maganarta yasa zuciyarsa da dukkan jikinsa sanyi, tunani d'aya yazo ransa

"Meh yasa take irin wannan maganar? Anya bamu cuci Surayya ba?"


*****


"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un"

Hannunsa dukka biyu ya dafe kansa dashi yana maimaita wannan kalmar.


K'arar bud'e k'ofar d'akin yasa zuciyarsa ta k'ara hautsinewa. Kasa d'ago kansa yayi har ta iso inda yake ta tsaya a gefensa tana masa kallo daga sama har k'asa cike da tsantsar raini. K'arar chewing gum(cingam) da ke bakinta ke fita cas-cas-cas, hannunta rik'e da k'ugunta.


"Toh da ka shigo nan ka zauna ka d'auka bazan iya binka bane? Wallahi ka fa raina ni, naga alamar baka nemi zaman lafiya cikin gidanka ba, kuma tabbas tunda ka auri mace kamar ni toh ka saya da kud'inka. Da Zaliha kake zancen"


K'afansa ta take ta wuce ko a jikinta, huci take kamar namijin zaki har ta fice banko masa k'ofar ta rufe kamar yanda ta shigo.

 Har lokacin bai iya d'ago kansa ba dan ciwo mai rad'ad'i da yake masa.


~~~~~~~~


Waye kuma Zaliha?

Waye mijin nata?

Ya tabbata ba Zayyan ne ya sawa Surayya HIV ba, waye kenan? Umar? Ta ina ya samo in shi ne? In ma ba shi bane to waye?


MaryamerhAbdul

HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA


      NA MaryamerhAbdul


    NAGARTA WRITERS ASSOCIATION 


       12. Yes, ni ke d'auke da cutar nan...


   "Umar, magana fa nakeson mu yi na fahimtan juna, kana d'aure min kai gaskiya"


Bai d'ago ya kalleta ba haka zalika bai daina danne-danne da yakeyi cikin kwamfutarsa ba.

A hasale ta warce na'urar tana mai kai dubanta ciki dan ganin muhimmin aikin da yafi nata maganar.


Gefe ta ajiye ba tare da ta kashe ba ta fuskancesa, kallonta yakeyi ba tare da ya furta komai ba kuma fuskarsa bai nuna halin b'acin ran da zuciyarsa ke ciki ba.


"Kayi hak'uri, muyi magana dan Allah ko hankalina zai kwanta in na samu amsoshin tambayoyina daga wurinka"


Kwayar idanunsa na kan fuskarta ko kyaftawa baya yi

"Kaga sakamakon gwajina Umar banji bayani gamsassa daga wurinka ba...."


"Yi min shiru dan Allah"

Ya dakatar da ita had'e da d'aga mata hannu alamar ta dakata. Cike da b'acin rai ya mik'e


"Sai da kika gama bibiyan samarin naki d'aya bayan d'aya sannan zaki dawo kan mijinki ya zama shine mutum na k'arshe da zaki tambaya game da cutar da yake jikinki? A hakan kike son muyi magana mu fahimci juna bayan kinsan ni ne mutum na farko da yakamata kiyi magana dashi akan matsalarki? Toh kin tambayesu dukka basu dashi, yanzu ba gashi kin dawo min ba?"


Runtse idonta tayi hawaye mai zafi ya sauk'o mata, ta bud'e baki zatayi magana kenan ya sake dakatar da ita


"Nasan tambayoyin naki Surayya, ba HIV ba? Yes, ni ke d'auke da cutar nan mai karya garkuwa jiki, ina da wannan cutar tun kafin in aureki, kuma nak'i sanar dake ne saboda ta hanyar da kike samun biyan buk'atun sha'awarki nima na samo, kinga kenan ayar Allah ya tabbata akanmu mazinaci baya auren wata sai mazinaciya, kin d'auka kin tsira ne da kikayi aure? Kin d'auka duk halayenki ban sani ba? Ina sane da komai naki ki d'auka kamar duk sharholiyar da kikeyi a tafin hannuna nan kikeyi"


Ya fad'i maganar yana mai d'aura yatsarsa na dama a tsakiyar tafin hannunsa na hagu.


"Ki ji ni da kyau, kaman yanda kike biyewa son zuciyarki kike yawo kike samun nutsuwa wurin wanda ba halalinki ba nima haka nayi, kowa na da sha'awa, ko kin d'auka ke kad'ai kike dashi?"


Bakinta na rawa hawaye na malala idanunta na kallon k'asa ta iya furta 

"Ba laifina bane, kuma ai kasan haramun ne Umar" ta k'arashe maganar tana mai d'ago rinannun idanunta.


Dariyar da bai wuce lebb'a ba yayi ya dawo daf ita ya zauna

"Saurareni da kyau Surayya, ke da ni munsan abun nan haramun ne amma muka bari shaid'an ya k'awata mana muka biye masa dan kawai mun kasa hak'urin awanni kad'an ko ma ince mintuna. Sha'awa wani abu ne da Allah ya halicci bawansa dashi, kowa da irin nasa, wasu mai yawa wasu kad'an, wad'an da kike ganin basu afkawa zina kada ki d'auka nasu kad'an ne, su kad'ai suka san irin nasu kuma sun san yanda suke iya dak'ilewa. Meh yasa ni da ke bamu iya hana kanmu ba Surayya? Son zuciya ko?"


Kuka mai sauti ne ya kufce mata, bata tab'a tunanin rayuwarta na baya zai dawo yana fataucinta ba sai yau da Allah ya nuna mata ikonsa akanta, ina ta tab'a tunanin ciwo irin wannan zai shafeta? Da ta kame kanta ta jira halalinta da Allah bazai had'ata da miji irin Umar mugu ba, mazinaci, ko da yake kowa da tasa k'addarar amma nata ya banbanta da na kowani d'an Adam.


"Allah ya had'a mu dai Surayya, ki rungumi hak'uri yanda na runguma, nima k'addara da soyayya ta kai ni ta baro, gashi yanzu duk da na sanin da zanyi bazai min anfani ba. Da na sani k'eya ce"


Tashi yayi ya barta inda take ya fice daga d'akin bayan ya d'auki kwamfutarsa. Ko a jikinsa bai nuna damuwar halin da ya jefa matarsa ba a wannan lokacin, sheshshek'a takeyi ta kasa iya tab'uka komai.


"Allah na rok'ek'a, kai kad'ai ne zaka iya bani abunda raina da ruhina ke buk'ata, afuwarka da yafiyarka nake nema akan laifukan da nayi maka, Ya Allah ba dan halayena ba ka bani farin ciki a rayuwata"


Kwanciya tayi a inda take tana mai rizgar kuka, fuskarta yayi jawur jijiyoyinta duk sun bayyana rud'u-rud'u.


*****


"Ki bani Zaliha, bana so nace miki"

Yana maganar ne a lokacin da yake k'ok'arin k'wace wayarsa a wurinta. Ko kamo wayar ya kasa saboda yanda take tureshi da bayanta da d'ayar hannunta.


"Ni zaka rainawa wayau? Ka aureni kana hira da 'yan mata? Wallahi baka isa ba"


Ganin ya kasa kwace wayar ne ya hutar da kansa ya zauna ya barta dan ta gama binciken wayar, asirin nasa ya tonu sai meh? Meh zata iya yi? Can ciki ya ja tsaki yana kallonta k'asa-k'asa.


"Lahhh! Zaid? Hureran kake soyayya da? K'awata ce fa?"


Kallonshi takeyi dan yayi mata k'arin bayani amma yayi shiru.


"Lallai yau za'ayi bala'i a gidan nan"

Wayar ta wurga kan gado tana mai kunce d'ankwalinta had'e da d'aurashi a kwankwaso ta tunkarosa.


Hannunta d'aya rik'e da k'ugunta ta isa tana mai girgiza tana nunasa da yatsa d'aya


"Meh na rageka dashi a gidan nan? Meh 'yan matan naka suke dashi wanda ba ni dashi? Hurerah? Amma ka cuceni wallahi da ka had'a ni da ita, wannan ma ai raini ne"


Daga sama har k'asa yake kallonta, tabbas tayi gaskiya da tace 'yan matan nasa basu fita da komai ba, dan ta had'u iya had'uwa kawai dai ido irin na Zaid ya kasa ajiye hankalinsa kan matarsa halalinsa.


Masifa ta shiga yi masa tana zagi sai da taji ta gama cire kayan bak'in cikinta tas sannan ta d'auki wayar nasa ta fice dashi sai huci take.


"Toh ina zaki kai min wayar?"

Ya fad'a cikin d'aga murya, a hasale ta amsa masa


"Wurin jatumar da ta haifo d'an iska zan kai ta ganewa idonta abunda d'anta yakeyi, k'arfi da yaji ta sani zama 'yar daba akan mijina, wallahi Zaid da nasan haka halinka yake da banyi gigin karb'an tayin aurenka ba, haka kawai ka mayar dani wata aba daban wanda ni kaina bansan daga ina na tsirosu ba"


"Dan Allah kiyi hak'uri" 

Ya iso daf ita yana mai k'ok'arin rik'e hannunta.


~~~~~~


MaryamerhAbdul

HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA


      NA MaryamerhAbdul


    NAGARTA WRITERS ASSOCIATION 


       13. Ajalina


Harara ta zuba masa tana mai yi masa gargad'in kada ya rik'e hannunta ta ido, hannun nasa ya sauk'e 

"Bazan rik'e ba, amma na rantse na daina Zaliha, kiyi hak'uri mana"


"Inyi hak'uri? In zauna da mazinaci?"

Kuka ta fashe dashi tana mai takaicin Zaid, a lokacin da ya nemi a aura masa ita binta yayi kamar kurar k'arfe tana gudu yana binta, sai da ya had'a da mahaifiyarsa wacce takasance yaya ga mahaifinta ta sa baki, anan ne ta amince dan kunyar da ke tsakaninsu.


Ta sha jin labarin 'yan mata irin nasa amma bata tab'a d'auka ya kai ga zina ba.

"Kiyi hak'uri dan Allah Zaliha ki daina kukan nan, please"


Muryarsa kad'ai yasa ta gane ya damu da kukanta, hakan yasa ta koma kan gadonsa ta cigaba da rizgar kuka saboda yaji ba dad'i ko zai gyara halayensa.


Kusa da ita shima yaje ya zauna, fuskarsa kamar zai yi kukan dan d'aga masa hankali da tayi. Zai rik'e hannun nata ne ya pasa ya sauk'o k'asa ya zauna wurin k'afafunta dab'as yana mai kallon fuskarta da ta rufe da tafin hannunta tana kuka.


Can ciki ya furta "na shiga uku" daga bisani ya iya furta mata

"Zaliha fad'a min meh kikeso? Zan miki Allah indai zaki daina damun kanki, ki daina kukan nan, ke bakya sanin yanda nakeji in kina kuka, ki yi hak'uri ki taimakeni ki rufa min asiri, ni fa mijinki ne, kinfi son ki tona min asiri akan ki gyara abunki da kanki?"


"In gyara abuna da kaina? Tun yaushe nake k'ok'arin yin hakan amma kak'i? Ai ance in yafi k'arfin mace zata iya kaiwa gaba dan a samu sulhu" tayi maganar ne cikin muryar kuka.


Lumshe idanunsa yayi yana mai jin d'aci a ransa, a yanzu ji yake kamar ya bar kowace mace ya kula da matarsa abar sonsa, sosai yake matuk'ar sonta baya son komai da zai rab'eta na ashsha.


"Ni in bazaka daina ba ka rufa min asiri ka rufawa kanka asiri ka sakeni ba tare da kowa yasan halin da kake ciki ba, na gaji"


Maganganunta yaji kamar guduma ya saresa a k'ahon zuciyarsa. Bai iya furta komai ba sai kallonta da yake yi. Shin halin nasa da take k'i har ya kai ta nemi saki? Ashe zata iya rabuwa dashi bayan duk soyayyar da take zuba masa?


Zufa ke keto masa yana furta innalillahi can cikin zuciyarsa.


"Kai kasan ba abunda bana maka a gidan nan, duk lokacin da ka nemeni ina nan tare dakai, ni ko baka nemeni ba ma ina nan, inyi maka kwalliya, in maka abinci, komai ina maka. Amma sai kayi ta neman wasu matan a waje? Ka fad'a min abunda suke maka wanda ni bana yi, kullum sai na tambayeka amma kake k'in kulani. Kai yanzu a watanni ukun nan da aurenmu har yaci a fara jin kanmu muna fad'a Ya Zaid? Ai abun kunya ne wallahi"


Ta k'arashe maganar tana mai sake wani sabon kuka. Mantawa yayi da ta hana shi rik'eta ya rik'e hannayenta yana mai kallon fuskarta, hawayen da ke zubo mata saman fuskarta yafi komai d'aga masa hankali. Bai iya furta komai ba sai had'eta da yayi da jikinsa ya rungume abarsa yana shafa bayanta a hankali dan tsagaita kukan.


Mintuna kad'an ta daina sai ajiyar zuciya da take sauk'ewa. 

"Na daina kinji? Na daina bazan sake ba"


"Promise me"

Tace dashi tana k'ok'arin d'agowa ya hanata. Komawa tayi ta lafe tana mai jin bugun zuciyarsa.

"Umm?"

Tace dan jin shirun da yayi, kenan bazai iya alk'awari ba?


"InshaAllah Zaliha"

"Promise fa nace, in bazakayi alk'awarin ba ka barni inje wurin mama in fad'a mata kawai sai ta......."


"I promise, please ki daina fad'an haka, na daina nace"


*****


Alhaji na kwance gadon asibiti idanunsa lumshe sai nishi da yake fitarwa lokaci zuwa lokaci, da alamu yana masa wahala. A hankali ya bud'e idanunsa ya kalli Amaryarsa

"K'ira min Hajara"


Wayarta ta d'auka ta k'irata sannan ta sak'ala masa a kunne.


"Hajara, ku yafeni Hajara"

"Alhaji kai ne? Lafiya? Jikin ne ya tashi?"

Sauk'ar da nauyayyar nishi yayi sannan ya iya amsa ta da cewa 


"Um-um Hajara, nayi muku laifi nayi wa mahaliccina laifi, nasan bai wuce laifukan da nayi bane ya kwantar dani, Hajara lokacina yazo, ki nema min afuwar yaranki ('yan rik'on da ke zaune a gidan, lokacin da matarsa ta farko mahaifiyar Zayyan ta rasu komai nasu ya koma wurin Anty Hajara) na cucesu ni shaida ne, ki taimaka ki rok'a min su su gafarta min ko zan samu kwanciyar kabari mai sauk'i, kinsan ance tsakanin bawa da bawa babu mai iya yafewa sai sun yafe maka, ki taimakeni ko da bayan raina su yafe min"


Muryarsa ahankali yake fita wani lokacin maganar kan d'auke masa amma ya kasa yin shiru, gani yake da zarar ya rufe bakinsa ajalinsa zai zo kuma bai sauk'ar da wannan nauyin ba.


"Haba alhaji, ka daina irin maganar nan, cuta ba mutuwa bane"

Kuka ne ya kufce mata, meh yasa alhaji yake irin wannan furucin? Tabbas yana wahala amma hakan ba shi zai sa yayi tunanin laifukansa ne sanadi ba. 


"Ni kad'ai nasan yanda nake ji Hajara, ga ki nan ga Amarya tana ji na, yau na karb'i laifukana, na b'atawa 'ya'yanki da yawa rayuwa ciki har da Surayya, ku gafarceni, son zuciya ne kawai da kuma shaitan da yake k'awata min k'ananan yara, nayi da na sani, na tabbata wannan azabar da nakeji a jikina shine silar ajalina, ku gafarceni ku rok'i Allah ya raba 'ya'yanku da irin halina, ku kwab'i Zayyan, ku nuna masa gawana in na cika dan ya zama aya agaresa ko zai shiryu kafin lokaci ya k'ure masa kamar yanda nawa ya k'ure ya yanke ya barni. Nasan zaku zageni bayan mutuwana in kukaji abubuwan da nayi a cikin gidan aurenku, na rok'e ku da ku yafe min ku rok'a min sassauci wurin Allah, dan azabana mai rad'ad'i ne na sani, wanda nake ji a jikina a yanzu kad'ai ba mai iya d'aukuwa bane bare na jahannama".


Amarya da ke gefe tana zubar kwalla ne ta karb'i wayar ta kashe

"Haba Alhaji, rad'ad'in ciwo ba na mutuwa bane. Sau nawa ake ciwo ake tashi? Ka daina irin maganganun nan kana tada mana hankali"


Tari ya d'anyi yana rik'e k'irjinsa dan zafin da yake masa

"Ni nasan ya nakeji Amarya, ki duba fa har yanzu likitocin kame-kame sukeyi, basu san meh larurar tawa ba, har canja asibiti akayi amma duk a banza"


Sharce majina tayi ta goge hawayen idanunta 

"Toh hakan kad'ai zai sa kayi tunanin mutuwa zakayi? Sati mai zuwa zasu fita dakai, insha Allahu zaka samu sauk'i"

"Nidai ku rik'e wasiyya na ku basu hak'uri, babu wani gatan da zan samu daga wurinku irin addu'arku"MaryamerhAbdul

HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA


      NA MaryamerhAbdul


    NAGARTA WRITERS ASSOCIATION 


       14. Zaid da Zaliha


"Ka sakeni Umar, bana buk'atar aure irin wannan na k'addara"


Cikin dasasshiyar muryarta da ke nuni da kukan da ta dad'e tanayi. Sosai kamanninta ya sauya ta rame tayi farin da ba na lafiya ba.


"In sake ki? In sake ki fa kike cewa? Ai Surayya aurena dake shi ake k'ira auren zobe, ba saki ba yaji, ina nan dake har lokacina ko naki yayi"


Bata iya tsagaita kukan ba tace

"In ka min haka baka kyauta min ba a rayuwata Umar, meh na maka da kake saka min da b'ata min rayuwa a shekarun nan da nake dashi? Akwai hakk'ina akanka ka kasa sauk'e min, tunda kaji larurar da ka d'aura min ka canja min, kud'in makaranta kawai kake iya bani, magani, sutura da duk sauran hakk'ok'in ina ka ajiye su? Ko karatun naka iya nan ya tsaya?"


Kallonta yayi cike da b'acin rai yana huci

"Ba dan nasan b'arnar da ke cikin dukan mace ba da yau sai na wanke wannan fuskar naki da tafi, ki b'ace min daga gani kafin inyi abunda ni da ke zamuyi da na sani"


Yanayin maganar nasa bai bata damar tirjiya ko iya mayar masa martani ba, tuni ta koma d'akinta ta bar masa falon duniya na mata bugun da duk rayuwarta bata tab'a d'auka zai mata ba. Son zuciya babu abinda yake kai mutum sai da na sani, shin ta manta da cewa mazinaci sai mazinaci suke aure? Wani toshewar basira ne yazo mata lokacin da take aikata masha'a a rayuwarta da son ranta? Duk wannan ya sameta ne ta dalilin Alhaji da ke neman gafararta a yanzu. Shin zata iya yafe masa bayan uk'ubar da Umar ke yi mata a cikin wannan gida? Abu yak'i ci yak'i cinyewa sai ma k'aruwa da yakeyi duk shud'ewar dare safiya ya bayyana?


Cikin watannin nan uku da take fama da ciwon nan babu abunda yafi bak'anta mata irin sabuwar halin Umar da ya tsiro, ya daina kula da ita sai buk'atarsa ta tashi, ya daina biya mata buk'atar kud'i ko wani iri ne, kud'in rajistar makaranta kawai yake bata babu damuwarsa da littafai na karatunta ko da kuwa biro ne. Shin ya zatayi da rayuwarta? Tunani d'aya ta yanke ta nemi taimakon mahaifiyarta da 'yan kud'i dan kama sana'a, ta nemi sakin yak'i bata, meh zatayi bayan tunawa da inganta nata rayuwar tunda ta salwanta sassan jikinta?


A b'angaren Alhaji kuwa ciwon nasa sai k'aruwa yakeyi, anyi maganin anyi hasashen duk a banza, daga k'arshe d'aukansa sukayi suka wuce dashi India dan neman magani da kuma gamsashshen bayani kan larurarsa. 


Sati biyu suka kwashe a can sannan aka gano inda matsalar tasa yake. Brain tumor da matsanancin blood cancer ke d'awainiya dashi, nan take aka bada shawarar yi masa aiki akan brain tumor bayan an d'aura shi akan magunguna.


Wahala iya wahala Alhaji yasha kafin aka samu damar yi masa aikin. Ba'a tabbatar masa da ya rabu da wannan cutar ba sai dai yaji sauk'i kuma an d'aurashi akan magungunan cancer suka tattaro suka dawo gida.


*****


"Zaid!"

Yaji muryar mahaifiyarsa na k'iransa. Ahankali ya iya bud'e idanun sakamakon hasken da ya yi masa yawa.


Sakanni goma kacal komai ya dawo masa kwanyarsa kamar lokacin abinda ya gani yake faruwa.


Idanunsa ya d'aura akanta hawaye na bin gefen idanunsa. Lumshe idonsa yayi ganin hawayen mahaifiyarsa bisa kuncinta, zafi yaji a zuciyarsa yana mai da na sanin rayuwar da ya d'aurawa kansa. Shine silar komai, shine silar sa mahaifiyarsa zubar da hawaye.


"Meh ya sameka Zaid? Wani irin abu ka gani haka da zai kwantar dakai farat d'aya hawan jini da ciwon zuciya na barazanar kai ka makushi? Meh damuwarka d'an nan ka sanar dani?"


D'aci yaji a ransa jin yanda mahaifiyarsa ta damu da lafiyarsa, muryarta kad'ai ya nuna tsantsar damuwarta. Shi meh ya rage masa a duniya yanzu bayan abunda ya ganewa idonsa a yau? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un yake furtawa a ransa.


"Mama ki daina damuwa kina d'aga hankalinki haka, ke kinsan ba cikakken lafiya ne dake ba, kiyi hak'uri zuwa anjima in ya warware sai aji komai"


Muryar da yaji a cikin d'akin nasa ya k'ara dagula lissafinsa, ji yayi kamar ya tashi ya hau ta duka har lahira ko zai ji sauk'in rad'ad'in da yake ji. Har tana da bakin magana? Har zata iya bawa Mama hak'uri bayan abunda ta aikata? Meh Zaliha ke nufi da take magana kamar ba ita ya gani ba lokuta kad'an da suka wuce wanda shine dalilin fad'uwarsa har ma likita ya tabbatar da zuciyarsa ya samu rauni had'e da hawan jini.


Yana jin duk zancen da sukeyi amma yak'i bud'e idanunsa yana mai jin duk zancen Zaliha na sukar k'ahon zuciyarsa. Bai san lokacin da mahaifiyarsa ta fice daga d'akin ba tana mai addu'ar samun lafiyarsa.


Kusa dashi Zaliha ta dawo ba tare da ta iya yi masa magana ba. Can ciki ya furta

"Ki fice min bana son ganinki"


Mintuna biyu bayan umarnin da ya bata ya bud'e idanunsa, bai ji alamar fitanta daga d'akin ba hakan yasa ya bud'e idanunsa dan bata umarni a karo na biyu.


Hawaye shab'e-shabe ya gani bisa fuskarta hakan ya hana shi furta komai sai ma zurfin tunanin da ya lula. Can ya tsinkayo muryarta 

"Wallahi this is the first time, wannan shine karo na farko da na tab'a samun kaina cikin irin wannan yanayin, kuma nayi da na sani ina mai kunyarka da kunyar mahaliccina"


Yawu mai d'aci ya had'iye ya lumshe idanunsa

"Zaliha kinsan meh kikayi yau?"

Katse shi tayi da cewa

"Na sani, wallahi duk laifinsa ne, ya dad'e yana mai kawo min hari amma ina kaucewa, yau d'in ma bansan meh ya hau kaina ba, haushi naji da bak'in ciki bayan nuna min hotunanka da yayi kana aikata abunda nima na aikata, yayi anfani da b'acin rai da kuma shaid'anin da ya k'awata min ramakon laifin da ke tsakaninka da mahaliccinka, ka gafarceni nayi kuskure"


Sosai ta fashe masa da kuka tana mai jin bak'in ciki a ranta. Shi kuwa ya kasa tab'uka komai, bai tab'a jin d'aci da bak'in ciki irin na wannan lokacin ba. Shin haka yayi ta bak'anta ran matan da yayi mu'amala dasu? Shin haka mazan su suka ji lokacin da suka san ba su ne wad'an da suka fara kasancewa dasu ba? Haka ake ji dama shi bai tab'a sani ba? Kunya yaji ya rufeshi kamar ya gudu inda Allah bazai iya ganinsa ba, sai dai ina zai je? Babu, duk inda ka shiga ko da kuwa cikin k'asa ne Allahu Rabbi na kallon duk wani motsi naka. Ko kuma mutuwar da yake ganin shine hutu a garesa a wannan lokaci zai masa anfani bayan bai tab'uka/aikata aikin alhairin da zai iya cetonsa cikin kabari ba.


Hawaye masu zafi ne suka zubo masa, a karo na farko yana mai jin kunyar halayensa. Meh ya anfane shi cikin d'abi'unsa? Meh ya samu banda tarin zunubbai da tsantsar da na sani had'e da bak'in ciki? Shin akwai bak'in cikin da yafi wanda ya gani a yau? Abokinsa, amininsa wanda suke masha'arsu da 'yan mata tare da matarsa ta sunna cikin gidansa? Subhanallah!


~~~~~~~~~~~


MaryamerhAbdul

HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA


      NA MaryamerhAbdul


    NAGARTA WRITERS ASSOCIATION 


       15. Fu'ad ka guji ranar da rayuwa zata juya maka


"Fu'ad, wannan karon zai zama karo na k'arshe da zan ja maka kunne akan 'yan matan nan naka, ka guji ranar da rayuwa zata juya maka...."


"Haba yaya, bayan Surayya waye kika ga na mata wani abun, Surayyan ma ai na fad'a miki rayuwa ce ta juya mana haka, kuma ai farko nace miki aurenta zanyi, kuma dan yanzu tayi aure ta barni sai kada inji dad'in rayuwana? Abunda na fara zai yi wuya in daina ki gane mana"


Bakin nasa ta buge da bayan hannunta. 

"Baka da kunya fa, zanje in sanar da Mommy komai tunda ka raina ni"


Shiru yayi ya d'auke kai ya turo baki yana mai jin zantukanta da nasiharta dan kawai ta ga wata budurwarsa cikin motarsa. Bayan ta gama ya bar mata abunta inda yake zaune ya fice daga gidan da motarsa.


A bakin hanya motarsa ta tsaya ya fito dan duba abunda ya sami motar. Mintuna biyar yana duba gaban motar yana tab'e-tab'e.


Zaninta da ta d'aura a k'ugunta gefe d'aya na jan k'asa take k'ok'arin gyarawa, hijabinta ruwar madara wanda ya duk'unk'une dan rashin guga ya manne jikinta fuskarta fayau babu alamun lafiya tattare da ita.


Waigowa yayi yana kallonta tana iso inda yake, hankalinta baya wurinsa sai faman waige-waige takeyi alamar neman abun hawa.


"Surayya"

Ya furta yana mai k'are mata kallo, shin kama ne ko kuwa Surayyarsa da ya sani? Surayyar Umar ko zai ce tunda yanzu ta zama ta wani?


Kallonsa tayi ta sauk'e idanunta dan kunyar shi da taji ganin bai ma ganeta ba.


"Lafiyanki Surayya? Meh ya sameki kika zama haka? Kin haihu ne?"


Bata iya d'ago fuskarta ba ta amsa shi

"Lafiyana k'alau Fu'ad, kwana biyu?"


Mamaki ya shiga jin muryarta, tabbas Surayya ce ta koma haka kamar wacce ta haifi yara goma sun birkita mata tunani.


Tambayoyi ya fara jero mata dan son jin irin rayuwar da ta fad'a bayan aurenta, sosai ya kwad'aitu da son jin komai sanin cewa Surayya 'yar gayu ce mai son tsabta, tabbas ba k'aramin abu ne zai hargitsata haka ba, ko nutsuwa bata dashi a jikinta.


"Abu d'aya zan iya fad'a maka Fu'ad, ka bar rayuwar da mukayi a baya ka nemi lahirarka, dan bazaka tab'a samun kwanciyar hankali ba muddin ka cigaba da aikata abun da mukayi, kada ka so jin labarina, nayi da na sani matuk'a kuma ina neman yafiyar mahaliccina ko zan samu d'igon farin ciki a ragowar rayuwata"


Bata jira ya amsa ba ta share hawayen da suka zubo mata tayi tafiyarta duk da kallon neman k'arin bayani da Fu'ad ke jifanta dashi.


Atm card na mamanta ta k'ara damk'ewa dan tabbatar da cewa yana nan inda ta cusa bai fad'o ba. Adai-daita ta tara ta shige bayan ta sanar dashi inda zai ajiyeta.


*****


Juyi yayi akan gado numfashinsa na fita a hankali, tun dawowarsa daga India yaji sauk'i sosai sai dai yakan ji ciwo a dukkan jikinsa lokaci-lokaci. 


"Zayyan"

Ya furta ahankali yana lumshe ido

"Na'am Baba, jikin ne?"


"Zayyan ka tabbata kana abunda nace kayi? Zayyan ni kad'ai nasan irin rayuwar da na jefa kaina, ko ba'a fad'a maka ba kasan ina wahala sai dai bazaka ji uk'ubar da nake ji ba. Ka tuba ka rik'e Allah ka bi dokarsa ka tsira da azabar duniya da na lahira, wallahi duk mai sab'on Allah zai gani, ko bai gani anan ba zai gani a can, wanda ya samu ganin nashi azabar tun a duniya yayi farinciki yayi murna dan rahama Allah ke yi masa, mai hankali kad'ai zai gane isharar tuba ne".


Kad'a kai Zayyan yayi yana mai kallon mahaifinsa cike da tausayawa, yayi masa maganar nan har ya haddace sa amma har yanzu bai daina ba. 


Tunda yaje yayi gwajin k'anjamau ya nemi matattarar iskancinsa ya rasa, sosai Surayya ta d'ura masa ruwa game da wannan batu na HIV, ina shi ina komawa ruwa tsundum? Allah ya tsaresa ya karesa da dukkan 'yan uwa musulmi daga fad'awa tarkon zina.


"baba na daina, ni kaina nayi tunanin canja rayuwata tun kafin ka ja kunnena, kuma nagode sosai da tuna min da kakeyi, yanzu mu kula da taka lafiyar insha Allah komai zai dawo dai-dai tunda wad'an da ka shiga hakk'insu sun yafe maka kafin aurensu, ka sawa zuciyarka salama tun kafin ciwon suganka ko hawan jininka su k'aru akan wanda kake ciki yanzu"


Hawayen fuskarsa ya goge yana mai kad'a kai

"Sun yafe min Zayyan amma Surayya har yau bata ce komai ba, ga Hajara da amarya da suka fita harkana duk da na nuna nadamar abunda nayi wa 'ya'yansu, meh nake jira a duniyar nan bayan mutuwa? Rahamar Allah nake rok'a Zayyan, Allah ya gafarta mana"


Hawaye yaji shima sun taru masa a kurmin idanunsa, cikin taushin murya ya shiga kwantar masa da hankali yana mai k'ara masa k'arfin gwiwa game da neman yafiyar Allah da aikata aikin alhairi.


*****


"Zaid hakan ka yanke tsakaninmu? Ka kasa bani dama in gyara kuskurena? Kenan in kai bazaka iya yafe min abu d'aya da nayi ba taya kake tunanin Allah zai yafe maka naka d'aruruwan? Kayi min uzuri ka tayani neman yafiyar ubangijina, sati kenan baka min magana"


Kuka sosai take yi, bai iya kallonta ba ya d'auke kai yana mai tuno abunda ya ganewa idonsa, tunawa yayi da lokacin da yayi mata alk'awarin daina huld'a da mata, zuwa ranar da ya karya mata alk'awari har zuwa satin da ya gabata da ta aikata kwatankwacin laifinsa.

Shin taya zai iya sawa zuciyarsa ruwan sanyi ya karb'eta su gyara rayuwarsu?


Shin gaskiya take fad'a masa akan shine karo na farko? D'auke wannan zargin yayi tunawa da yayi shine namiji da ya fara saninta, kuma kyawawan halayenta yayi tasiri matuk'a wurin rura wutar k'aunarta, tabbas sharrin shaitan ne, kuma shine yanzu yake son ruguza zaman aurensu ta hanyar nuna masa rabuwarsu yafi masa sauk'i.


Taya zai fara gyara rayuwarsa? Taya zai gyara b'arakar da ya yi? Taya zai samu yafiyar mutanen da ya zalunta? Ta ina zai fara neman su bare ya nemi afuwarsu? Shin wasun su na raye ko a mace? Anya zai samu jin dad'in rayuwa bayan ya gano tab'agazar da ya yi? 


Abu d'aya ya dace yayi, ya inganta rayuwarsa ta hanyar Allah sannan ya nemi gafarar mahaliccinsa akan kura-kurensa, wad'an da ya shiga hakk'insu kuwa zai rok'i yafiyarsu duk ranar da Allah ya had'a su, wadan da suka riga shi komawa ga mahaliccinsa zai rok'i Allah ya sassauci zuciyarsu su yafe masa, zai rungumi matarsa ya rik'eta amana kuma ya kare mutuncinsa da nata. Fatanshi yanzu Allah ya bashi sauk'in ciwon zuciyarsa da kuma hawan jini.


~~~~~~~~~


MaryamerhAbdul

HANKAKA MAI DA D'AN WANI NAKA


      NA MaryamerhAbdul


    NAGARTA WRITERS ASSOCIATION 


       16. K'arshe


Fu'ad tun ranar da ya had'u da Surayya yake jujjuya maganganunta, iya bincikensa ya kasa samo asalin labarinta bayan aurenta, hakan ya k'ara bashi tsoro tare da tunano yanda ya ganta da kuma maganarsu ta k'arshe akan HIV.


Bai k'ara tsorata ba sai da ya danganta Surayya da wannan cutar, shin ko dai cutar take dashi? Tuni zufa ya wanke fuskarsa yana mai jin dukkan gabb'an jikinsa ya sake. 


Bai yi k'asa a gwiwa ba yayi tattaki zuwa gidan yayarsa ya sanar da ita komai game da Surayya da ma abunda ta fad'a masa, bai b'oye mata ba har maganar k'anjamau da tayi masa kwanakin baya.


"What? K'anjamau kuma Fu'ad?"

Idanunta aware hannunta d'aya ta rufe bakinta da ta hangame. 


Shiru yayi bai iya amsata ba dan kwanyarsa ya toshe.

"Fu'ad kada kace min kuna yin abunda yafi k'arfinka? Fu'ad kenan kai ma k'anjamau kake dashi?"


Hawaye sar-sar suka fara sauk'o mata tana kallonsa. Kallonta yakeyi yana mai mamakin furucinta.

"Haba Yaya, wannan wani irin magana ne haka? Tabbas nayi mu'amala da ita amma bani dashi, ki yadda bani dashi dan nayi gwaji bayan aurenta"


"Kayi shiru, kullum sai nayi maka fad'a akan halin nan, ashe abun naka har ya kai hakan? Yaushe maka Fu'ad? In auren kakeso ka sanar mana ayi maka, hakan bazai gagara ba ka sani"


Yawu ya had'iye mai d'aci ya lumshe idanunsa yana mai jin zafi a zuciyarsa.

"Yaya..."

"Ka min shiru, ya zama dole muje kayi gwaji yanzun nan, daga nan ni nasan abunda ya dace dakai, magiyarka da dad'in bakinka bazai yi anfani ba wannan karon Fu'ad. Tashi mu je"


Mayafinta da jakar hannunta kawai ta d'auka ta fice yana biye da ita a baya.


*****


"Mommy gaskiya fa d'aya ce, daga k'inta sai b'ata, nasan meh yasa nace a nemo masa mata yayi aure, in ba so kuke ya jawo muku abun kunya kuna tafiya ana nuna ku ko ku samu yarinya/yaron da zaki na kwana dashi matsayin jikanki ba bisa sunna ba, yanzu daga asibiti muka dawo dan yi masa gwajin k'anjamau"


K'ara ta sake tana toshe bakinta

"K'anjamau?"

Kad'a kai tayi tana maimaita mata kalmar

"K'anjamau fa, ni shawara na kawo, kuma in har baku d'auki mataki akai ba zaku ji kunya"


Bata jira amsa ba ta mik'e ta fice daga d'akin, ko kallon Fu'ad da ke tsaye bakin k'ofar bata tsaya ta saurareshi ba ta bar gidan.


*****


Watanni hud'u da faruwar hakan


Rayuwa ta sauya a wurin Surayya, gadan-gadan ta fad'a sana'a dan dogaro da kai, tuni ta cire babin Umar ta ajiye gefe, bata bar komai cikin hak'kok'insa ba, duk lokacin da ya buk'aci abu daga wurinta bata d'aukan wani lokaci dan sauk'e masa, ta sa a ranta wannan shine k'addararta, dole ta karb'esa ko dan ta samu farinciki a sauran rayuwarta.


A yanzu bata da damuwar komai sai na hada-hadar kasuwancinta, tana zuwa makaranta hankalinta kwance ta dawo da walwalarta. A hakan ta wayi gari d'auke da juna biyu, zuciyarta ya matuk'ar dunk'ulewa da ta tabbatar da wannan zancen, batayi k'asa a gwiwa ba ta sanar da mijinta hatsarin da ke d'auke da haihuwarta. 


Asibiti ya d'auketa ya kai ta dan samun cikakken bayani game da cutarsu akan babyn da ke cikinta, likita ya tabbatar musu babu wani abunda zai samu babyn muddin suka bi dokokin asibiti, bazai yu ta haihu da kanta ba dole ayi mata aiki don ciro jaririn. 


A sannan ne hankalinta ya kwanta, ta samu nutsuwa tare da tunanin tarbiyyar yaranta, ko ba komai ganin gudan jininta a duniya zai matuk'ar rage mata rad'ad'in zuciyarta, tayi wa kanta alk'awarin bawa 'ya'yanta tarbiyyar da ya dace dasu ba irin nata da ya kasance silar gurb'acewar rayuwarta ba. 


Alhaji ya samu sassaucin rad'ad'in ciwonsa bayan samun damar tattaunawa da Surayya, a halin yanzu hankalinsa ya kwanta yana samun cikakken kulawa daga wurin yaransa, b'angaren matansa kuwa sosai aka samu banbanci daga yanda suka saba rayuwa, dan a yanzu banda hakk'ok'insa da ya zame musu dole su sauk'e babu abunda yake had'a su, yayi ban bakin yayi rarrashin babu wacce ta sauk'o daga matan nasa, Anty Hajara ce kad'ai ta iya sawa zuciyarta ruwan sanyi, dalili kuwa bai wuce babu wani abunda ya dace tayi bayan hak'uri ba, girma ya kamata babu halin rabuwa, shin meh ya rage musu bayan bautar Allah dan samun rabo mai kyau?


Zayyan na shirin angoncewa cikin sati biyu masu zuwa, dan dole ya d'angale wando ya zama Ustazin gaskiya, sosai ya canja rayuwarsa, bayi da wannan mugun hali na neman mata sai abunda baza'a rasa ba. Sosai yake samun lokacin mahaifinsa dan kwantar masa da hankali a duk lokacin da jikinsa ya tashi.


A b'angaren Fu'ad kuwa, tun lokacin da yayarsa ta kai k'aransa aka nemi ya gabatar da wacce yake son ya aura, ganin bayi da madafa iyayensa suka samo d'aya daga cikin 'yan uwa aka had'asu dan kare sa daga fad'awa hanya mafi muni wato zina.


Zaid sosai ya nutsu bayan afkuwar mummunan al'amarin nan na matarsa da abokinsa, sosai wannan lamari ya girgiza sa kuma ya zama silar shiryuwarsa ya nutsu wurin matarsa d'aya tilo mai sonsa da zuciya d'aya.


~~~~~~~~~~~~~

Alhamdulillah


K'arshen labarin kenan, na sanar daku cewa wannan labarin wata baiwar Allah ce, nayi canje-canje kamar yanda na sanar daku a farko, sai dai babu abunda ya sauya a jigon labarin da kuma halin da baiwar Allahr ta shiga, Allah ya shiga lamuranta ya bata hak'uri da juriyar d'aukan wannan jarrabawar na rayuwa. Allah ya shiryi masu hali irin su Alhaji, Zaid da kuma Zayyan, su suka bada gudunmuwa mafi yawa cikin lalacewa da tab'arb'arewar rayuwar Surayya. Allah ya ganar da masu hali irin wannan su gane kuskuren da suke tafkawa a bayan k'asa.


Iyaye na da matuk'ar muhimmanci cikin rayuwar 'ya'yansu, domin tarbiyyarsu na k'ark'ashinsu, mafi kyawun tarbiyya shine kula da d'abi'un yaro, lokacin kwanciyarsa, mu'amalarsa da mutane(maza/mata) hatta wayar salularsu abun dubawa ne, sai dai banda takurasu da nuna musu rashin yadda, hakan na k'ara rura wutar bijirewa ko b'oye duk wani abu da sukeyi daga idanunku, wanda ba hakan ake buk'ata ba. Ilimin addinin da yawancin iyaye suke wasa dashi yanzu yana da matuk'ar anfani a rayuwarmu, shine haskenmu, ilimin addini, anfani da ita da kuma tunawa da inda kowannenmu zai je kad'ai zai iya dai-daita rayuwarmu na yanzu. Zina Abar k'yama ce, Allah ya raba mu da dukkan 'yan uwa daga fad'awa wannan tarko. 


Allah ya had'e mu cikin ladan kowani gab'a da aka iya anfana dashi daga wannan labari, Allah ya gafarta min kurakuran da nayi.

Nagode da kulawarku, nagode da hak'urin da kukayi dani duk da k'ailulana inji Anty Maijidda😂. Ina sonku sosai da sosai

Kada ku manta, ku biyoni a Wattpad, kuyi comment da vote.

Ku duba sauran littafaina kafin in sauqe su nan gaba kadan daga Wattpad. Sai mun had'u a littafina na gaba, ina godiya sosai. 😘😘😘😘😘😘

Ina k'aunarku dukka.


MaryamerhAbdul ce👌

Tags: #fyade #childabuse #HIV #sakamako
1509
0
1
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!