Hakkin Kisa!

Written by Rabiatu Mashi SkPublished on 2018-12-12 17:33:14Category HorrorKoda yaga jini a jikinta bai ɗauka wani abu bane, kowacce cikakkiyar mace ance hakanne a daren farkonta, wani k'arfima yakeji yana k'arazo mishi, a tak'aice dai bai k'yale Hajna ba sai ana kiran Sallahr Asuba, ya kwanta samanta yana maida numfashi. Ko kaɗan bai kula da numfashinda ta dainayi ba saida ya dawo hankalinshi, ya mik'e yana dubata jinine kaca-kaca a jikinta, gadon ya ɓaci sosai, a ruɗe yake kallon jini, sannan ya fara taɓata ko motsi batayi. Cikin k'arfin hali ya ruga fridge ya ɗauko robar ruwan faro mai sanyi sosai, ya juye mata anma ko motsi batayi, duk kallon abun yake kamar a mafarki, ya ɗan kwantar da kanshi a k'irjinta anma babu alamun numfashi? Hannuwanshi ya ɗaura saman kai ya fasa ihu, jikinshi har kyarma yake yana hawaye, TA MUTU NE KO SUMA TAYI?? ya tambaya kanshi. Shin idan ta mutu meye sanadin mutuwar ta? Wa yake da alhakin kisan hajna? Ku biyoni don jin wannan labari mai cike da sarkakiya tags: #Hajna #FatalwaDuba was labarai »

☠HAK'K'IN KISA☠

   👽👽👽👽

       1-5

©Rabiatu sk msh

   ®NWA


Ku matso kuji masoyanah, ina fatan kowah yayi Sallah lafiya, Zakuna samu HAKK'IN KISA kullum insha Allah anma banda ranakun juma'ah, a ranakun juma'ah kuma ku kasance dani a littafin ZAMAN AURE, abunda zan iyayi kenan, fatana dai hakan bazai rikitaku ba, ina yima kowa fatan Alkhairi


www.babymsh.blogspot.com


    Wani babban gidane na hango ɗan madaidaici, cike da mutane har waje, masu kuɗi harda masu k'aramin k'arfi shiga kawai suke suna fita, ga motocinan birjik har basu gajiya da tsayawa, lallai da alama gidannan bikine ake, biki na er gatah ma kuwa, bazan iya wucewa ban bawa idona abinci ba har in samu labarin kawowah Masoya.

   Kai tsaye na kutsa cikin gidan, lallai na zaune baiga gari ba, manyan mata ne a wurin masu ji da kansu, ga Uwar Amarya da keta tarban bak'i, ni kaina na samu karramawa, dana zauna kwasar girki ma saina manta da abunda ya kaini, sai dai naji ana hayaniyar kai amarya, da hanzari na na mik'e, don dolene ma inje gidan amaryarnan.


*****

Ankai Amarya tsantsareren gidanta, sai da kowa ya gama tafiya ya rage ita da k'awayenta, Ango da abokanshi sukazo, saida suka gama tsokana, da suka tashi tafiya suka musu nasiha sosai mai ratsa jiki, basu daɗe ba suka tafi, don Ango kamar ya korasu saboda zumuɗi.

  Saida ya rakasu ya dawo yana gyara babban riga, sai washe baki yake irinna angwaye, 

  "Amaryata, bayan kuɗin siyan bakinma baza'a buɗen fuska ba?"

  Hannu tasa zata yaye mayafin, ya ɗaura hannunta saman nashi suka buɗe a tare, "wao! Masha Allah, Godia ga Ubangiji daya mallakamun wannan kyakkyawar mace a matsayin Matatah"

  Murmushi tayi har kyawawan hak'oranta suka fito, "Gaskia nayi dace Hajna, taya zan bayyana miki farin cikin da nakeji yau gani tare dake a matsayin Matah da miji?"

  "bakai kaɗai ba Masoyi, burinmu ne mu duka ya cika, yanzu sai mu fara mik'a godiyarmu wurin Allah (S.W.T) daya bamu ikon ganin wannan rana"

  "Yanda kikace Amaryatah" ya rigata mik'ewa, tabi bayanshi da kallo, harya shige toilet, wani soyayyarshi na k'ara shigarta, zuciyarta tanason Abdul da yawa, kyakkyawan saurayine da kowacce mace zatayi mafarkin samu, tananan tana sak'ar zuci harya fito, sannan ta mik'e tayo Alwalan itama.


  Gado ta haye kawai ta juya baya ta kwanta bayan sun gama, "Nifa ban yarda da k'oshinnan ba, nasan hidima bazaki samu lokacin da zakici komi ba, plz indai baso kike in ɗura miki ba"

   "Allah da gaske na k'oshi," ita tsakaninta da Allah ta k'oshi, shima bai wani ci kazar da yawa ba ya ajje, kayan jikinshi ya rage sannan ya haye gadon shima.

   "bazaki rage kayannan ba?"

   "um-um sanyi ake"

Jawota yayi ta faɗa jikinshi, "sai in rufeki anan" ɗan tureshi tayi zata juya, ya matseta gam, a hankali yake mata magana a kunne cikin raɗa, "karki barni plz, ki tsaya a haka" cikin sexy voice, gaba ɗaya ya kashe mata jiki, tunnan numfashinta ya canja, ta k'ara shigewa jikinshi.

   "kayannan ya miki nauyi" ya k'ara raɗa mata a kunne, jin ko motsi batayi ba ya fara rabata dasu, sannan ya jawo bargo ya rufesu, tana manne a jikinshi sai shafa bayanta yake ita kuma tana k'ara manne mishi. A hankali duk ya rabata da kayan jikinta.

  Rikicewa yayi ya fara wasa da jikinta, tun tana mak'alewa har itama ta saki jikinta, wani salo mai k'ara rikitarwa yake zo mata dashi, duk da hakan dak'yar ya shigeta, batasan sanda ta fasa wani uwar k'ara ba, sannan ma ya jishi a wani sabuwar duniyar, ya k'ara k'aimi ihu kawai take, tun tana toshe baki harta farayi da k'arfi tana jin wani azababben ciwo, inaa Abdul baimasan tana yi ba.


  K'arshema kasa ihun tayi, koda yaga jini a jikinta bai ɗauka wani abu bane, kowacce cikakkiyar mace ance hakanne a daren farkonta, wani k'arfima yakeji yana k'arazo mishi, a tak'aice dai bai k'yale Hajna ba sai ana kiran Sallahr Asuba, ya kwanta samanta yana maida numfashi.

  Ko kaɗan bai kula da numfashinda ta dainayi ba saida ya dawo hankalinshi, ya mik'e yana dubata jinine kaca-kaca a jikinta, gadon ya ɓaci sosai, a ruɗe yake kallon jini, sannan ya fara taɓata ko motsi batayi.

  Cikin k'arfin hali ya ruga fridge ya ɗauko robar ruwan faro mai sanyi sosai, ya juye mata anma ko motsi batayi, duk kallon abun yake kamar a mafarki, ya ɗan kwantar da kanshi a k'irjinta anma babu alamun numfashi?

  Hannuwanshi ya ɗaura saman kai ya fasa ihu, jikinshi har kyarma yake yana hawaye, TA MUTU NE KO SUMA TAYI?? ya tambaya kanshi.

   Bai hak'ura ba ya sauka ya fara jijjigata da hannu, kaman yana jijjiga filo ne ba wani motsin kirki, kaman zautacce ya fara zagayen gidan, duk wani taimakon gaggawa da yake tunanin zai saka Hajnarshi ta tashi yaa bata anma shiru, duk inda tashin hankali yakai yaa wucenan.

   Tunani ya fara yi, ya kira likita ne ko kuma ya kira sauran dangi? Da yake baima da lokacin tunanin bai tsaya shawara ba gaba ɗayansu ya kirasu, yana ganin kiran mahaifinshi da sauran dangin amarya, bai iya ɗaga na kowa ba tunda ya samu ya faɗa musu suzo ba lafiya.

   Kusan tare suka iso, mahaifanshi da nata, da kuma likitan daya ma waya, ya sakata a gaba hannuwanshi saman kai, zufa kawai yake gaba ɗaya babu k'walla a idanunsa.

   

   Turus sukai suna kallonshi zaune ya tasa Hajna a gaba, "lafiya meya faru?" mahaifinshi ne ya watso mishi tambayar.

  Shi kanshi baisan meya faru ba, ballantana yasan amsar dazai basu, da hannu kawai ya nuna musu Hajnar dake gabanshi.

  Ummanshi tace "Hajna ba? Munga Hajna ce, dalilin kiran daka mana duk ka tada mana hankali mukeson ji"

  Maman Hajna ce ta saki jikkarta tana ihu bayan hango jini malala jikin Hajna, sannan ta lura da shima jinin yanda duk ya ɓata shi, "Na shiga Uku, wannan jinin ko ai ya wuce lafiya? Meka ma 'yata?"

  Sannan duk suka k'arasa saman kanta yanda ta kakkahe babu alamun numfashi a jikinta.


  Yanda Mamanta ta cika gidan da ihu tana maganganu, duk ya k'ara ɓata ma Abbanshi rai, ya kalla likitan, "Me kake jira? Ka dubata musan meke faruwa da ita"

  "tohm Alhaji" da sauri ya k'arasa inda take, en gwaje-gwaje kawai ya mata sannan ya ɗago duk yana kallonsu, duk ya haɗa zufa.

  "kai muke saurare, ka faɗa mana meya sameta?"

  "bazan iya ganewa ba Alhaji, abunda dai na sani, AMARYA HAJNA TA RIGAMU GIDAN GASKIA"

  take ɗakin suka ɗauka salati gaba ɗaya, banda Abdul~azeezu da k'afafuwanshi suka kasa ɗaukansa, ya tafi luuu zai faɗi, Maman Hajna ta cakumoshi.

   "k'arya kake wallahi, kai baka isa ka kashe mun y'ata ba, wallahi baka isa ba, y'atah bzata mutu ba"

  Duk da Abbanshi shima cikin tashin hankalin yake, saida yace "Hajia kudai iya kalaminku"

  "kalamim banza da wofi, naqi in iya kalamin, a gabanka fa, jiya da dare aka kawo mishi y'ata, daga shi sai ita, yau sai gawarta zai nunamin? Wallahi baka isa ba saika faɗamun abunda ka yima y'atah"

   "Magana ake maka, ka barmu cikin duhu me kayiwa matarka? Meyasa ka kasheta?"

  Da sauri ya ɗaga kai yana kallon Abban nashi cikin mamaki ne ko firgici, 

   Mamanta tace "mefa zata mishi, kawai jininta ya bayar, ni daman nasan kuɗinnan da yayi da wuri ba banza ba, wallahi jinin ɗiyata bazai tafi a banza ba"

   A hankali yake furta, "Hajna ta mutu? Shikenan kin tafi kin barni? Daman kin shigo rayuwatah ne dan ki barni cikin k'unci da kaɗaicin rashinki?"


  Don tsabar haushi Abbanshi ya ɗauka kwalban humranta ya mishi jifa samankai duk ta tarwatse, take shima fuskarshi ta fara zubar da jini.

  "Mu zaka maida sakarkarun banza? Tambayarka ake a ina ka bayarda jininta?"

  "Jininta kuma? Wallahi tallahi ni badan yankan kai bane, na rantse da Allah Abba nima bansan komai game da mutuwar Hajna ba"

  Wayanshi ya ɗauka yana kiran police, "idan kaje zaka musu bayani ne"

  Yama rasa mezai faɗa ya kare kanshi, kallonsu kawai, Ummanshi kam duk zuwanta batace komai ba, suna gani aka tafi dashi police station, ita kuma aka wuce da gawarta asibiti donyin binciken musabbabin mutuwanta.


©Rabiatu sk msh


: ☠HAK'K'IN KISA☠

   👽👽👽👽

       6-10

©Rabiatu sk msh

   ®NWA


www.babymsh.blogspot.com


 Zuwansu police station Abbanshi ya gama harzuk'a, ganin yanda yaketa hayaniyar faɗa anma Abdul ko magana ma bai musu, shiru kawai yayi yana kallon k'asa, donshi ganinshi yake ma kamar a mafarki, jiran lokacin farkawarshi kawai yake.

  Jijjigashi da mahaifiyarta keyi tana kuka ne ya dawo da hankalinshi kanta yana kallonta, faɗa take da dukkan muryarta.

  "wallahi ka saurareni dakyau kaji, bazan taɓa yafe HAKK'IN KISAn y'ata ba, kai gara ma ka buɗe baki kayi magana, don wallahi koda dukkan dukiyatah zata k'are saina wulak'antaka Abdul, tana da gata, bazatayi mutuwan rashin galihu ba"

  Ta jefar dashi wuri ɗaya kaman tsumma, abunnan da yake ba k'aramin k'arama Abbanshi haushi yake ba, bama kaman da dukkan tambayoyin da akai mishi yak'i ya buɗa baki ya bada amsa.


  Abba ya dafe kanshi, "ka cuceni Abdul, anma kanka ka cuta, ka jefar da duk wani tarbiyyar dana maka, a ganina samun duniya bai isa ya sakaka ka kashe Hajna ba, yarinyar data nuna maka soyayyar da bazaka taɓa samun matar da zata maka shi ba, meyasa Abdul? Wacce irin dukiyah ce ban sakar maka ba? Wanne gata ne ban nuna maka ba? Meyasa zaka kashetah? Wannan abun kunyar har ina? Wallahi yau nayi dana sanin kasancewarka ɗana"

  A raunane yake kallon mahaifinshi yana hawaye, "Abba ta yaya? Akan wanne dalili zan kashe Hajna? Wallahi bansan komai akan mutuwarta ba, na faɗa muku muna cikin auratayya ne kawai sai dai naga ta daina motsi, kuma na rantse da Allah ba fyaɗe na mata ba"


  "K'arya kake, k'arya kake wallahi kashemun y'a kayi,"

   "Miye ribana idanna kashe Hajna? A tunani na koda idanuwanku Abun Allah ya kiyaye, Abun Allah ya kiyaye" saida ya gama jinjina maganar sannan yaci gaba.

  "ace koda da idanuwanku kuka ganni da wuk'a ina sokawa Hajna zakuce ne idanunku ne suka muku k'arya, ta yaya zan iya kashe macen dana fiso fiye da rayuwatah? Wallahi ku yarda dani ni ban kashe Hajna ba"

   "Saboda kana tunanin mun maka wannan yardar ne shiyasa ka kasheta? Idan bakai ka kashe Hajna ba waye ya kasheta? Ka faɗa mana maganar da hankali zai ɗauka mana"


  Shiru yayi yana hawaye, shi kaɗai kaman zautacce yake furta "Hajna ya zaki tafi ki barni? Ya zaki bar masoyinki cikin masifa da kuma rashinki? Ta yaya zan iya rayuwar da babu ke a cikinta? Kin mutu kin huta, Ya Allah ya ɗauka rayuwatah nima in tafi in iske Hajna tah, Hajna nine Abdul ɗinki, da kikasha yimun alqawarin zamu kasance tare duk wuya duk daɗi, don Allah ki kasance dani har yanzunma"

   Mamanta ta kwaɗa mishi wani irin marin da bai taɓajin irinsa ba, "Mak'aryacin banza kawai, soyayyar banza ce wannan kake nuna mata bayan ka kasheta"

  Kafin ya dawo dai-dai Abbanshi ya fara haɗashi da bango, k'anwarshi khadija ce ta ruga wurin Ummansu da tunda sukaje ko k'ala batace ba.

   "Umma don Allah ki hana Abba, yanzu ko tausayin Yayanmu bakiji? Wlhy nina yarda dashi gaskia yake faɗa" girgiza kai kawai Umma tayi ta k'ara gyara tagumin da tayi da hannuwa biyu.

  

Dak'yar suka k'waceshi a hannun Abba, aka kaishi aka gark'ame daga k'arshe ma hana kowa ganinshi akai. Kafin azahar k'ofan station ɗin ya gama cika da en uwanshi dana Hajna, da sauran en gulma, garuruwa kam babu inda labari baije ba, kowa da abunda yake faɗi, "guba ya saka mata a abinci, asiri ya mata, jininta ya bayar ga dodon tsafinshi" harma da masu cewa "wani abu ya yanka a k'asanta, ai jininta ya shanye" maganganu dai sunyi yawa, ko wanne gidajen radion Kano ka gano labarin dai ake watsawa.

  "Ango ya kashe amaryarshi a daren amarcinsu, anma yana ik'irarin shima gawarta kawai ya gani, koya gaskiyar lamarin yake? Sai dai munji ta bakin Angon"


  Ɗan k'aramin yak'i k'annen Hajna su 3 maza suka so tarawa a k'ofar station ɗin, faɗi suke sai an fiddo musu da Abdul sun k'watar mata hakk'in kisanta, khadija kuka kawai take tana rok'on Ummansu tasa a fito da Yayansu, saboda duk hayaniyar da ake bai hanata jiyo ihunshi ba.

   "Umma karki bari a hukuntashi akan laifin da bai aikata ba, wallahi Yayanmu bazai taɓa iya kashe Aunty Hajna ba"

  Umma ta dafa kafaɗarta "wacce Hujja gareki akan hakan? Ke yarinyahce khadija har yanzu bakisan komi ba"

   Baki buɗe take kallon Umma, "Umma kina nufin kema kin yrda akan yayanmu ya kasheta?"

   "bazance miki eeh ba, anma yaran yanzu ne ba'a shaidansu"

  Rasa me zata k'ara cewa tayi, ta sulale kawai ta zauna wurin tana kukan tausayawa yayanta.


©Rabiatu Sk Mashi


☠HAK'K'IN KISA☠

   👽👽👽👽

       11-15

©Rabiatu sk msh

   ®NWA


 Wahala sosae Abdul ya shata a hannun hukuma, cikin kwana biyu ba aikin da sukeyi saina dukanshi akan dole saiya amsa laifinshi na kisan Hajna, yayi bak'i sosae ya rame, ga tunanin Hajna dhunshi akansa. Allah sarki Abdul, kullum cikin kuka yana tunanin yanda rayuwa ta canja mishi lokaci ɗaya.

  

 KOTU

Ranar talata 6june, kotu ta cika mak'il domin sauraren k'arar Abdul da mahaifiyar Hajna ke tuhuma da laifin kashe mata ɗiyarta a daren Amarcinsu.

  A lokacin da aka shigo da Abdul mutane da yawa sun tausaya mishi, wasu kuma suna mishi Allah ya qara maganinshi kenan, HAKKIN KISAN dayama matarshi ne ke wahalar dashi, anma fa ko babu zuciyah a k'irjinka dole ka tausayawa yanayin da Abdul ya shiga.

  Saida alk'ali ya tsawatar sannan aka tsagaita da surutu, mai gabatar da k'ara ya tashi ya gabatar da k'arar da aka ma Abdul sannan ya koma ya zauna.


 Alk'ali yayi gyaran murya "ina lawyern mai k'ara?"

  Ya mik'e tare "Sunana Barrister Alqaseem muhd, nine lauyan wanda ke k'ara"

  Sannan ya koma ya zauna, Alk'ali ya kalla Abdul "ko kana da lauya?"

  Ya girgiza kai bayan ya share hawaye "bani dashi Ya mai shari'ah"

   Ya gyaɗa kai sannan yace "lawyern mai k'ara ko kana da tambayoyin da zaka ma wanda ake tuhuma?"

  "Ina dasu Yamai shari'a"

 Ya mik'e zuwa inda Abdul yake.


  "da farko zanso ka faɗamun wanne irin aure kukayi da marigayiyar matarka daka kashe?"

  Saida wani abu ya soki zuciyarsa, 'shikenan har Hajna ta zama margayiya' ya tsani ynda ake dangantashi da kisanta, shirun da yayi ya saka Br. Alqaseem ya k'ara cewa.

  "ina nufin auren zumunci aka muku, ko kyautarta aka maka ko kuma auren soyayya kukai?"

  "Auren soyayya mukai da ita"

  "zaku kai tsawon wanne lokaci a tare kafin kuyi aure?"

  "zai kai shekara 3"

 "tun sanda kuka fara soyayya kake da k'udurin kasheta ko sai daga baya ka canja ra'ayin kasheta?"

  Tuni k'afafuwanshi suka fara gardamar ɗaukarshi, k'irjinshi na bugawa da sauri daman can k'arfin hali yake, "Ban kasheta ba, wallahi bani na kashe Hajna ba, soyayyar tsakani da Allah nake mata, ban taɓa tunanin cutar da ita ba" yana magana yana gunjin kuka.

    "anma dai ka tabbatar a raye aka kaita gidanka ko?"

  "eeh"


  Ya juya wurin Alk'ali, "iyakar tambayoyin dazan mishi kenan yamai shari'ah, idan kotu ta bani dama akwai tambayoyin dazan ma mahaifiyar marigayiya Hajna"

  "kotu ta baka dama,"

 "idan mahaifiyar Hajna na kusa kotu tana son ganinta"

  Da sauri ta taso cikin zumbuleliyar hijab ɗinta da cazbaha a hannu tana ja, bayan tayi rantsuwa akan zata faɗi gaskia, Br. Alqaseem ya gyara tsayuwa.

   "Hajia maimunatu, ko zaki faɗa mana dangantakar dake tsakaninki da marigayiya Hajna"

  "y'atah ce ta cikina, nice na haifeta"

   "kina nufin a hannunki ta girma?"

  "a hannunah take tun tashinta"

   "shin Hajna tana da wata ɓoyayyan ciwone dake damunta? Ina nufin irin ciwukannan dake cin jiki a hankali"

  "Gaskia bata dashi, idanma tana dashi zata faɗamunne, don ko tuntuɓe tayi saita nunamun, haka ta taso tun yarintarta"

  "akwai wasu wanda take faɗa dasu ko kuma wanda kike zargi akan mutuwar y'arki bayan Abdul?"

  "yarinya ce nutsattsiya, mararson hayaniya, bata da wani abokin faɗa, wama zai kasheta bayanshi? Shine nan ya kashemun 'yata, azzalumi kawai, insha Allahu sai yaga k'arshenshi" ta k'arasa maganarta tana kuka.

  Ya koma ga Alk'ali, "wannan shari'ar mai sauk'i ce yamai shari'ah, duka shaidu sun gama tabbatarwa babu wani wanda ya kashe baiwar Allahn nan Hajna, sai mijinta Abdul, da wannan nake rok'on kotu mai adalci data yankewa Abdul hukunci mai tsanani yanda sauran mutanen dake burin kashe matayensu su ɗauka darasi daga gareshi, ta kuma k'watarwa mahaifan Hajna HAKK'IN KISAN 'Yarsu, ngde yamai shari'ah"

  Ya koma ya zauna, alk'ali na en rubuce-rubuce sannan ya ɗago da kanshi.


  "zamu ɗaga sauraren wannan shari'ah zuwa 15 ga wannan watan da muke ciki, don haka kowanne ɓangare suyi k'ok'arin kammala tattara shaidunsu, za'a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma har zuwa lokacin"

 "kotuuuuu!!!"

 

Waiwaye Adon tafiya.....


©Rabiatu sk mashi


 ☠HAK'K'IN KISA☠

   👽👽👽👽

      16-20

©Rabiatu sk msh

   ®NWA


www.babymsh.blogspot.com


ASALIN LABARIN.

 Bayero University Kano

Tafe take a hankali cikin takunta na nutsuwa, bak'ace anma ba can ba, fatarta mai kyau da shek'i, tana da dogon hanci da dara-daran idanu masu k'ara ma fuskarta kyau, ɗan k'aramin bakinta da ko kaɗan ta motsashi sai dimple nata ya fito, bata da k'iba jikinta dai dai, sai dai bata da rama ko ina a cike take.

   Wuri ta samu ta zauna ta fito da wayanta tana shirin kiran k'awarta, kawai sai dai taga mutum a gabanta. Ba k'aramin faɗuwa gabanta yayi ba, bama kaman da ta ɗaga kai sukai ido huɗu dashi, kodai Aljanine? Don kyan nashi har yayi yawa, batasan sanda ta tsurama kyawawan idanunshi kallo ba, a yayinda shima yake kallon nata.

  Yaɗan kalla wayan hannunta, sannan ya koma kallanta "Plz wayan hannunki zaki aramun?" wani daddaɗan sauti ya sauka a kunnanta da tunda take bata taɓa sauraren kamansa ba.

  Ta ɗauke idanunta "amfani nake da ita" ta faɗa da sanyayyan muryanta

  "nima bzan gudar miki da ita bane, anan zanyi waya kawai na baki"

  "ina taka?"

    "na barta a gidane ina sauri zan fita lecture, plz karki tsaya tambya wayan da zanyi tana buqatan sauri ne"

   

  Mik'a mishi wayan tayi, kafin ya amsa tace "ka tabbatar ba layinka zaka kira donka samu numbana ba?"

  Ya girgiza kai "o'oh"

  Saida ya tabbatar ya rik'e wayan a hannunsa, sannan yace "Idan kuma numbana kikeso ki faɗa na miki saving"

   Harara ta aika mishi sannan ta mik'e zata anshe wayanta, ya cillata ɗayan hannun tare da kashe mata ido "soriyo"

  Bayan ya kanga wayan a kunne ya sake cewa "naga en mata da yawa suna tambayana numbane, wasu suna aikomun da nasu, kekam a kyauta zan miki saving"

   "niba kaman wasu en matan bane ai, kamasan waye saurayina? Ko kaɗan bzaka haɗa kanka dashi ba....."

   "Shhhht" ya ɗaura hannunsa saman leɓe yana nuna wayan alaman ta shiga, ta harareshi cikin k'ulewa.


  "wa'alaikis salam Ummana" ya faɗa, anma bata jiyo me ake cewa ɗayan ɓangaren.

   "Abdul ɗinkine, kira nayi na miki albishir"

  "abunda kika daɗe kinaso, ynzu haka gani tare da surukarki"

  "Da gaske Ummana, na samu Matan aure wacce hankalina ya kwanta da ita, da layinta ne ma na kira ki"

   "Ameen Umma, Ameen, Ameen Ummana" tunda ya fara magana ta buɗe baki tana kallonshi, mamakinshi sosae take, wannan wanne irin mutum ne? 

  Ji tayi ya ajje mata waya a gabanta, "ngde sosae Hajna"

   Ina yasan sunana kuma? Qila a wayan zai gani, ta kalleshi ya sakar mata murmushi, "sai mun sake haɗuwa"

  Kasa ɗauke kai tayi tabi bayanshi da kallo, yanda yake tafiya cikin aji, ya haɗu ta ko ina, kyakkyawane na ƙarshe anma da alama bai ɗauka rayuwarshi da zafi ba, ta taɓe baki.

   Ji tayi an taɓota ta baya "wow Hajna, wannan guy ɗin fa?"

   "ohon mishi, aron waya yazo, yayi shiriritanshi ya k'ara gaba"

  "watau ke duk namijin da yake sonki mashiririci ne ko? Jifa yanda ya haɗu, ga kyau ga gayu"

  Ta girgiza kai "meerah! Idan ya miki ki aureshi mana"

   "da ni yake so kam dana more, muje ko?"

  Ta mik'e ba tare data k'ara cewa komai ba.


   Kafin ta isa gida ta manta da batunshi, ɗakin mamanta ta wuce.

   "Sannu da gida mama"

   "yauwah sannu da hanya"

  Taɗan kwanta jikinta "wallahi na gaji da yawa Mama"

  "kici abinci saiki huta mana, wannan son jiki naki har yayi yawa"

   "Maryam bata dawo ba?"

  "an tafi ɗaukota, su muhseen ma yanzu suka tafi exam"

   "shysa naji gidan shiru, nima na tafi inɗan runtsa kafin lokacin sallah"

  

   Ruwa ta watsa, sannan ta canja kaya mararsa nauyi, ta haye gado ta jawo wayanta, whatsapp ta shiga bayan ta buɗa Data.

  Tana cikin reply taci karo da bak'uwan numba, batasan numbanba, anma da yake sallama aka mata saita amsa kawai.

   "yauwa daman ke kaɗai nake online ina jira"

  Mamaki ya cikata da taga sak'on, "ban gane ba, waye yake magana?"

   "wanda kike tunani a ranki mana"


©Rabiatu sk msh


 ☠HAK'K'IN KISA☠

   👽👽👽👽

      21-25

©Rabiatu sk msh

   ®NWA


Wannan shafin Sadaukarwa ne gareki Momiena, DIDI ANEESA( HALEEMA G KHALEEL), babu kalmomin da zan iya amfani wurin gode miki akan soyayyan da kikemun da kuma addu'o'inki gareni ko yaushe, tabbas ke Uwahce ta gari, ina miki fatan samu zuriya ɗayyiba, ya kuma k'ara zaman lafiya da mai gidanki. Ameen ya rabbi.


www.babymsh.blogspot.com


   "ni babu wanda nake jira, qila dai ba numban bane"

  "Taya numbanki zata kuskuremun? Ba Hajna bace?"

  "Yh nice" ta maida ansa cikin mamaki.

    "idan kin bani dama zanzo gida yanzu muyi magana"

   Ta zaro ido "A'ah gsky"

  "Meyasa, ko kina tsorone?"

   "Yh saboda ba'a cirar kai ta waya shiysa zakazo gidan?"

  Daria ya tura mata "kozan cire na kowa ae bnda naki, saboda ba'a satan zuciyah a chat dai shiysa zanzo gidan"

    Dariya tayi sosae, hakanan takejin nishaɗi fira dashi, ta maida mishi da dariya kawai.

    "yaushe kenan zanzo?"

  Cikin zolaya tace "Yanzu"

   "Yanzu mota ta tsaya k'ofan gidanku lek'o ki gani"

  "nasan wasa kake ai"

  "ki fito dai"


 Sai kuma ta fara tsorata, ta ɗauka mayafi ta ɗaura a doguwar rigar dake jikinta sannan ta fita a falo ta wuce mama da er Autarsu Maryam, tana "Aunty ina zakije?"

   "yauwah zo muje" ta kama hannunta suka fita tare, mai gadinsu na mata magana ko kulashi batayi ba, ta tsaya jikin k'ofa ta kamo Maryam.

  "Sistanah dubamun kiga in akwai mota a k'ofan gidannan" don ita duk a tsorace take, gani take data lek'a zata dawo babu kai.

  "eeh Aunty ga wata haɗaɗɗiyan mota nan"

  "akwai mutum a ciki?"

    "A'ah, gashinan dai ana sauke glass ɗin, laaah! Aunty nan yake kalla, wani farin saurayine mai dogon hanci, kinga kanshi kuwa? Gashinshi irinna indiyawa ne, ga...."

  "ke sarkin surutu gyaramunnan" ta matsa, sannan ta ɗan duk'o iyakar tsawan maryam itama zata lek'a, sai dai taga mutum shima ya lek'o, ta zaro ido ya ɗaga mata gira da sauri ta mik'e bayan taja baya.


   "Abdul ko?"

     "Yauwah ashe kin rik'e sunana"

  Har Maryam ta ajjesu musu fararen kujeru, "Ya Abdul ka shigo daga ciki"

  "ka gani ba, sunan naka b wani wahalan rik'ewane dashi ba"

   "ngde sosai Maryam ashe haka kika iya tarban bak'i?" ta ɗaga mishi kai tana dariya, sannan ta ruga ta shige gida.

  Saida suka Zauna, sannan ta gaisheshi a kunyace, "kinga saurina ko Hajna? Tunda na koma gida nake bama Ummana lbrnki, na kasa shiru da zancenki kaman yanda na kasa daina ganin fuskanki, shiyasa nace bara dai inje inyi saurin amayar da abunda ke zuciyatah kona huta da zogin da take mun"

  Er dariyarta tayi, "lallai kam ka cika sauri da yawa"

  "towh anma kinga laifina? Ynzu dai faɗamun me kikeji game dani?"

    "Da wuri haka?" tana lulluɓe fuska

  "eeh mana, idan har zuciyoyi biyu sun haɗu kuma me ake jira? Ni mutum ne da ban iya son Abu ba Hajna, tun lokacin dana haɗu dake zuciyatah ta kamu da soyayyanki lokaci ɗaya, ban tunanin zan taɓa samun kamanki a raina, shiyasa na sanar da Ummana, awa biyu ya ɗaukeni na bayyana miki abunda ke raina, Idan baki farajin So na ba a yanzu sai yaushene zaki faraji?" 

    "Anma kasan akwai soyayyar dake shiga lokaci ɗaya da kuma wacce sai anyi sabo ba?"

   "hakane, bama saikin faɗa ba Hajna, yanzu hankali na ya kwanta, saboda kinsan akwai soyayyan da ake ganewa ba tare da an furta ba ba?"

  Dariya tayi ta k'ara rufe idanunta.

   "Sai meya ragemun ma? Meya rage? Miye ya rage? Yauwah na tuna.... A tak'aice dai cikakken Sunana Abdul-Azeez, ni haifaffen garinnan ne, anma ina karatu a k'asar Spain, ina shekaran k'arshene, nine na farko a wurin Ummana da Abbana, sai k'anwata Khadija, mu kenan a ɗan k'aramin Family namu, saura me ya rage da kikeson sani?"

   "Ba komai, nima nice ta farko a wurin Iyayena, sai k'anne 4 maza Uku, Muhseen ke bimun, sai Alhassan da Alhusein, da Autarmu Maryam, ina shekara ta biyune a bayero University, Mamana ita kaɗai ta rage mana, shekara biyu kenan da rasuwan mahaifina"

   "Ayyah, Allah yaji k'anshi, ya kyautata makwancinshi"

   "Ameeen" duk yayi shiru ta bala'in bashi tausayi. A haka suka gama firan duk jikinshi a sanyaye. Yana k'arajin tausayin Hajna da soyayyarta


©Rabiatu sk msh

[

 ☠HAK'K'IN KISA☠

   👽👽👽👽

       26-30

©Rabiatu sk msh

   ®NWA


 Tana shiga Falo ta iske duk k'annenta suna jiran shigowan ta, sai wannan ya kalla wannan suyi dariya, ta ɓata rai "ku kuma miye kuke ma daria"

   Alhassan yace "kawai muna taya Ya Abdul murna ne, yau ya cira tuta har auntie ta tsaya fira dashi"

   Muhseen Yace "kinga kuwa yanda fira ke miki kyau auntie? Hakanan baki kula kowa duk farin jinin nan naki"

   Alhassan ne ya sake bashi amsa, "ba firan ne ya mata kyau ba, kawai dacewa ne da sukayi"

  Tsagal Maryam tace "Hakane fa Yaya"

   Alhusein da son girma ya harareta, "ke rufe ma mutane baki manyanki na magana" taja baki ta lafe ta kwanta. Haka suka gama firansu cikin nishaɗi, kowa dai ya yaba da Abdul.

   Koda ta shiga ɗakin Mama, tambayanta kawai tayi "waye mahaifinshi?" 

   Sanannan mutum ne indai ka kwana ka tashi zakasanshi a garin kano, yana da kuɗi sosae da kyauta, ga mutunci da halin taimako duk inda yaji ana buk'ata.


  Cikin ɗan lokacin da Abdul yayi kafin ya koma makaranta sukayi sabo sosai da k'annen Hajna, ko da ya koma ma kullum suna gaisawa harma da mamanta, Ummanshi har gida ta turo da Khadija ta tafi mata da Hajna, tayi matuk'ar yabawa da halinta, yarinya mai kunya da nutsuwa dai dai matan da take ma Abdul ɗinta fatan samu. Zumunci sosae ya shiga tsakanin dangin biyu.

 

*** ***

Hayaniyar da yaji ne ta dawo dashi daga dogon tunanin daya tafi, muryar mace yakeji da mai tsaronshi, kaman yasan muryan anma ya kasa tuna ko na waye

  "kiyi hak'uri hajia, doka ce babu wanda zai shiga ganinshi"

  "ni kuma dolene na ganshi kota yaya, ko kwana ya kama inanan har saina ganshi"

   "ki taimakeni Hajia karkimun silar aikina"

  "nawane Albashin naka?" cikin gatse ya faɗa mata kuɗin da sunmafi albashin nashi, ta ajje mishi wanda suka ninka abinda ya faɗa.

  "anma dai bazaki daɗe ba ko hajia?"

  Ta ɗaga mishi kai, yana washe baki ya rakata har inda Abdul yake, daman idanunshi a hanya, da mamakinshi yake kallonta.

   "Meerah?"  

     "Abdul kaine ka koma haka?"

  Tuni hawaye ya gama wanke mishi Fuska, "Meerah k'awarki ta tafi, Hajna ta tafi ta barni"

  Duk yanda taso danne zuciyarta saida ya sakata kuka, 

   "kayi hak'uri Abdul, kwatsam daga komawata sai naji wannan mummunan abu daya faru dkai, abinda ya maidoni garinnan kenan, ni kaina na yarda bazaka taɓa kashe Hajna ba, shiyasa ko nawa zan kashe saina nema maka lawyer, dole ne ma a gano waye yake da HAKKIN KISAN Hajna"

  "wannan wata tatsuniyah ce da ni kaina na fito daga cikinta, bani buk'atan wani lawyer ko wnda zai kareni, a halin yanzu nafi son na mutu na tararda Hajna can mu sake wani zaman, bzan iya rayuwar da babu Hajna a ciki ba"

   "kasan kuwa me mutane suke faɗa a kanka Abdul? Ka daure ka bani haɗin kai Abdul, karda abunda ya faru da Hajna ya sake faruwa da wasu matan, ka bari mu gano waye silan mutuwanta?"

   "NINE!!" ya faɗa cikin k'araji, sannan ya sassauta murya, "babu wanda yayi silan mutuwan Hajna bayanni Meerah, ko baki fahimci labarin bane? Na daina jin haushin duk wanda zai dangantani da mutuwanta, Inajin ihun Hajna meerah, tana kuka anma na kasa k'yaleta, wlhy da nasan Hajna zata mutu bzan taɓa kusantarta ba, Allah kaɗai yasan dalilin mutuwan Hajna"

   "kuma shine zai fitar dakai, nasan bazaka taɓa kashe Hajna ba, na yarda dakai Abdul koda kuwa kaine ka faɗamun da bakinka, kada ka saduda, karka taɓa amsa laifin da ba naka ba,"

   "na gode da yardar da kikamun Meerah, kece mutum ta biyu data yarda da ban kashe Hajna ba, hatta iyayena sun juyamun baya, har sun saka na fara shakku akan kodai nine na kasheta"

   "insha Allah ko waye yake da HAKK'IN KISAN Hajna sai ya bayyana kanshi"

  "ta yaya?"Ta saukar da numfashi, tana kallon Abdul duk ya koma kalan tausayi, tabbas abun a tausaya mishi ne, ita kanta shaidane akan son da yake ma Hajna, rashinta kaɗai ya isa ya saka rayuwanshi cikin ruɗu, ga kuma HAKKIN KISANTA da akeson ɗaurawa kanshi.

   "Hajia lokacinki ya cika," ta jiyo muryanshi daga bayanta.

  A raunane da k'ara kallon Abdul bayan ta mik'e, "na tafi Abdul, saina sake dawowa tare da lawyer" bai iya ce mata komai ba, saboda kukan da yaci k'arfinshi, itama tana kuka ta tafi.


©Rabiatu sk msh


☠HAK'K'IN KISA☠

   👽👽👽👽

      31-40

©Rabiatu sk msh

   ®NWA


www.babymsh.blogspot.com


   Sanda Meerah ta k'ara dawowa tare da lawyer, Abdul ya k'ara ramewa duk yayi bak'i, kamanninshi sun canja kaman ba wannan hadaɗɗen Abdul ɗin data sani ba. Lawyern kanshi ya tausayawa Abdul da yanda ya ganshi.

   Ya kalla Abdul cikin k'arfafa gwiwa "ka kwantar da hankalinka Abdul, insha Allah komai zaizo mana cikin sauk'i"

    Meerah tace "k'warai kuwa, domin Allah yana tare da mai gaskia, gani tare da lawyer, ka daure ka bashi haɗin kai duk tambayoyin daya maka"

  "nifa na riga dana faɗi duk abunda na sani"

  Murmushi lawyern yayi, "tohm aeni banji ba, ka daure ka sake bani labari"

   "idan na baka Hajna zata dawo gareni? Na faɗa ma Meerah bana buk'atan lawyer, abu ɗaya nafi buk'ata yanzu shine na tarar da Hajna inda take"

   "kenan baka da buk'atar sanin ko waye ya kashe Hajna? Kafison ka mutu kowa yana maka kallon wanda ya kashe matanshi a daren farko? Haba Abdul, Hajna bata cancanci hakan daga gareka ba, kai kafi cancanta daka jajirce wurin gano wanda yake da hakk'i a kisanta"

   

  Maganganun Meerah sunyi matuk'ar tasiri a zuciyarshi, su suka k'ara k'arfafa mishi gwiwa, "A daren Aurenmu ne kaman kowanne Amarya da ango, nayi k'ok'arin raya sunna tare da Hajna, kuma wallahi ba fyaɗe na mata ba da amincewarta, sai dai na ɗago naga bata motsi jini ko ina a jikinta, na ɗauka ma suma tayi, sai da likita yazone ya tabbatar mana da Hajna ta tafi, Har yanzu ina jiyo kukan Hajna a kunnuwana, ina jin kukanta anma na kasa sauka a jikinta, shikenan Hajna...."

  Ya kasa k'arasawa saboda kuka, sai lawyern ne ke dafa kafaɗanshi yana bashi baki, shi kanshi idanuwanshi sun cika da hawaye,

  "Wannan wani rikitaccen Al'amari ne, yanzu abunda mukafi buk'ata shine takardar likita akan binciken dalilin mutuwanta" 

  Meerah ta nisa sannan tace "nifa nafi kallon wannan abun a matsayin asiri, idan ba asiri ba haka kawai daga Auratayya sai mutuwa?"

   "hakane kam, yanzu kai Abdul babu wanda kake tunani dazai iya mata hakan? Don zai iya yiwuwa abinda Meerah ta faɗa gaskia ne"

  "Laifin me Hajna tayi ma wani dazaiyi mata hakan? Bata da abokin faɗa, ko kaine ka mata laifi itace mai baka hak'uri, tun zamana da Hajna ban taɓa ganin tayi ko musayar yawu da wani ba, don haka babu wani da nake zargi akan mutuwanta.


   "Akwai, tabbas ni akwai wacce nake zargi" duk suka maida kallonsu a kanta.

  "budurwanka Haneefah"

    "wacece Haneefa?" 

Abdul yace "wata yarinyah ce dana taɓa taimakawa, a hanya na ganta tana tafiya tana haɗa hanya, duk taa fita hayyacinta, na ɗauketa na kaita asibiti, sai daga baya take faɗamun en fashine suka tsaresu ita da direbanta suka anshe komai nasu, shine duk suka tsorata kowa yayi hanyarshi, na kaita gida kwana biyu ta huta sannan Ummana ta saka aka maida ita gida, tunda tamun zancen soyayya na bata hak'uri, shikenan rabona da ita, babu abunda ya haɗata da mutuwan Hajna"


   "Akwai kuwa, Hajna bata taɓa faɗa maka bane saboda batasan damuwanka, anma akwai ranar da Haneefa ta taɓa iskemu gidansu Hajna lokacin ta fito rakoni, da waya hannunta tana chat dakai, wani wawan burki taja sannan ta fito daga motan tana mana kallon sama da k'asa, sannan ta kalla Hajna.

   "nan ne gidansu wannan wawuyar Hajnar?"

  Bata nuna taji haushi ba, saima tace mata, "da wawayun Hajnar kike magana"

  Tunnan tasha jinin jikinta, ko bata faɗa ba nasan ganin ajinta dana Hajna ba ɗaya bane shiyasa tasha jinin jikinta.

  Ta nunata da yatsa, "zuwane na miki gargaɗi akan kula Abdul da kikeyi, idanma asiri kika mishi kiyi saurin karyawa, don nawane ni kaɗai"

   "tohh fa, baiwar Allah ai..." da sauri ta saka hannu ta dakatar da Hajna.

  "kinga nayi kama da wacce zata saurare maganarki? Zuwa nayi in faɗa bawai a faɗamun ba, idan kinji kanki kika taimaka," itadai Hajna murmushinta kawai take, tana ganin yanda na taso da faɗa ta rik'e. Harta juya sai kuma ta dawo.


   "nasan fa Abdul kuɗinshi akeso, idan nace zan rabaki dashi harta da gidan da kuke ciki zai anshe kayansa ne, ki faɗamun ko nawa zaki iya siyarmun da soyayyanshi, kar kiji komai ki faɗa koma nawa ne"

  "uban waye yace miki shiya siya gidannan? Ko an faɗa miki kowa matsiyaci ne kaman ke?" Hajna ta rik'oni, 

   "ke ba dake nake ba, idan kika k'ara sakamun baki a cikin maganata sai kinyi nadamar sanin Hajnar ma da kikai"

  Cikin murmushi tace, "nawa zaki iya siyen Soyayyan Abdul ɗin? Million 2?"

    Haneefa harda saurin ɗaga kai, "idan su suka miki" Hajna ta girgiza "million biyar?" 

   "million 10??"

  "ke talauci hauka ne?"

     "million 20??"

  "lallai kinma koma sata"

  "ae har yanzu ban faɗi farashin soyayyar Abdul ba, kinsan me yasa?" cizgar kai tayi cikin jin haushi.

   "saboda babu shi, idan har kina tunanin akwai kuɗin da zasu iya siyar miki soyayya, tohm kinyi babban kuskure"

  "kece kikayi kuskure Hajna, da kike tunanin zaki iya ja dani, mu zuba ni dake, indai Abdul ne gaki gashinan, zaki gane wacece Haneefa"

  Tana gama faɗar hakan ta juya ta barmu, a lokacin na tsorata k'warai da zantukan Haneefa, naso Hajna ta barni na faɗa a musu tsakani, anma ta hana, tace babu wanda ya isa ya mata Abunda Allah bai nufa ba, da haka tasa muka bar maganar.


   "Maganarki gaskiya ne, zamu buk'aci Haneefa a wannan binciken namu"

  Abdul ya nisa sannan yace "babu hannun Haneefa a kisan Hajna"

   "meyasa zakace haka?"

  "saboda Haneefa ta rigani aure, tun kafin aurenah da Hajna akayi aurenta, tunda ta samu wani ta hak'ura tunda daman tasan ba sonta nake ba"

  "toh fa, wannan case ɗin naka yana da matuk'ar ɗaure kai, tunda nake ban taɓa haɗuwa da case mai rikitarwa irin wannan ba"

    "abun da bai taɓa faruwa bane ko a tatsuniya, me yasa saini kaɗai zai faru dani? Duk cikin mutanen dake duniyar nan, Meyasa saini kaɗai?"

   "A'ah Abdul, Allah na sonka shiyasa yake maka wannan jarabawar domin ya auna imaninka, kayi k'ok'arin cin wannan jarabawar, komai ya faru dakai karka ɗauka don kai kaɗaine Allah bai so, ka gode mishi zaka ga Alkhairin abun"

   "Allah yajiqan Hajna"

  "Ameen ya rabbi"


 Duk wani bayani da gakeson ɗauka ya gama, yayi rubutunshi, duk da shi kanshi case dinnan ya gama ɗaure mishi, baisan ma ta inda zai fara bincike ba, gashi lokaci ya k'ure an kusa yin zama na biyu.

   Tun bayan fitarsu ya jingina kanshi yana hawaye, ya rasa tunanin me zaiyi, shi duk wannan abun ana k'ara fama mishi ciwon mutuwan Hajna ne.

   "me yasa kika shigo rayuwatah Hajna? Meyasa kika shigo rayuwata kinsan zaki tafi ki barni?"

   "kin mutu kin huta da rikicin dake duniyarnan tamu, ya Allah kaji k'an wannan baiwa taka"


©Rabiatu sk msh


☠HAK'K'IN KISA☠

   👽👽👽👽

       41-50

©Rabiatu sk msh

   ®NWA


www.babymsh.blogspot.com


KOTU...

Yau kam kotun har tafi ta rannan cika, babban kotun ta cika mak'il har babu wurin zama, mutane daga wasu garuruwan sunzo sauraren k'aransu Abdul.

  Shari'arsu itace ta biyu bayan Alk'ali ya gama sauraren wata, sannan aka gabatar da k'ararsu Abdul.

  "lauyoyinsu suna kusa?"

 Br Alqaseem ya mik'e "Sunana Br Alqaseem Muhammad, lauyan wanda yake k'ara"

  Lauyan Abdul ma ya mik'e "Sunana Br Ahmad Saeed, lauyan dake kare wanda ake tuhuma" shima ya zauna.

   "lauyan wanda ake tuhuma, ko kana da tambayoyin da zaka ma wanda kake karewa?"

  "ina dasu ya mai shari'ah" ya tashi ya k'arasa inda Abdul yake.

    "Malam Abdul, ko zaka sake faɗama kotu abun daya faru a daren 4 ga watan 6" ya gyaɗa kai, sannan ya k'ara tariyo duk abunda ya faru a daren amarcinshi.

  Sannan br Ahmad yaci gaba da magana, "Ya mai shari'ah, idan munyi la'akari da bayanan da Abdul ya bamu na sanadiyyar mutuwar matarshi, baida wani alak'a da kisan nata, domin kuwa ya taka sawun ɓarawo ne, domin kuwa babu wani ango dazai kashe matarshi a daren aurensu na farko,"

  "idan kotu ta bani dama, zan gabatar da hujjata ta farko da zata k'ara tabbatar ma da kotu cewa Abdul bashi da Hannu akan kisan matarshi Hajna"

   "kotu ta baka dama"

     "Meerah Sayyid, wacce ta kasance Aminiya a wurin marigayiyah"

   "idan Meerah Sayyid tana kusa kotu tana son ganinta" ta taso ta tafo, da alama itama tana cikin damuwa, don babu wani kuzarin kirki a tare da ita.

    

  "Malama Meerah, a matsayinki na k'awa, ko kuma Aminiya a wurin Hajna, me kika sani a alak'ar Hajna da Abdul"

   "Duk da Hajna na matuk'ar son Abdul, bazai kai koda kwatan son da Abdul yake mata ba, ban tunanin koda na second Abdul zaiyi tunanin cutar da Hajna, Aminiyatah ce Hajna, duk duniya babu wanda yasan sirrinta kamar ni, kuma haka nafi kowa sanin soyayyar dake tsakaninta da Abdul, tabbas Abinda ya faru dasu wata jarabta ce ta Ubangiji, anma Abdul mutumin kirki ne, bazai taɓa iya aikata abunda ake tuhumarshi dashi ba"

   Sun taɓa samun saɓani a tsakaninsu?

   "a tsakanin Harshe da hak'ori ma ana saɓawa, duk inda aka zauna dole ne za'a saɓa, a iyakar sanina dasu sau ɗayane suka taɓa samun saɓani, a dalilin tayi rashin lafiya bata sanar mishi ba, shima anan take ta bashi hak'uri suka shirya"

     

  Ya juya wurin Alk'ali, "iyakar tambayoyin da nake dasu kenan ya mai shari'ah"

   "lauyan mai k'ara, ko kana da tambayoyin da zaka ma Meerah?"

   "ina dasu yamai shari'ah"

   Ya k'arasa inda meerah take "Malama Meerah, zanso jin tsawon wanne lokaci ne kikasan Hajna?"

  "k'awatah ce tun daga nursery school"

   "kina nufin nursery school kawai kukai tare ko kuwa dukkan makarantu tare kukayi?"

  "tare muke har high institution"

  "unguwarku ɗaya?"

    "a'ah Anma ko yaushe muna tare"

   "kenan ko zatayi fira da Abdul ma kuna tare?"

   "A'ah anma dai bata ɓoyemun abunda take neman shawara daga gareni, da ace Abdul yana da wani halin da take zarginshi dashi, nice mutum ta farko da zata faɗa mawa"

    "ta yarda da Abdul matuk'a ba?"

  "k'warai ma kuwa"

     "baki tunanin shi Abdul ɗin yana da wani ɓoyayyen hali da ita kanta Hajnar bata san dashi ba?"

  "gaskia ban tunanin hakan...."

  "biron dake hannunshi ya jefeta dashi,"da sauri ta duk'e tayi matuk'ar tsorata.

   Yayi murmushi, "a tsayuwar da nayi nan kinyi tunanin zan iya jifanki?"

 Ta girgiza kai, "toh me yasa na jefeki? Kenan kowanne mutum zai iya canjawa ko yaushe?"

  Ta ɗaga kanta, kuma ta girgiza, duk taa rikice.

   "magana zakiyi ba kaɗa kai ba"

  Br Ahmad ya mik'e, "objection Ya mai shari'ah, barrister baida hurumin dazaina rikitata"

  "Barrister Alqaseem ka kiyaye"

  "Nagode ya mai shari'ah, iyakar tambayoyina kenan" ya yafi ya zauna


Barrister Ahmad Saeed ya tashi tsaye "idan kotu ta bani dama zan gabatar da shaidata ta ta biyu, kuma shaidar da zata tabbatarma da kotu babu hannun Abdul a kisan matarshi Hajna"

  "Kotu ta baka dama,"

     "Dr Hameed, likitan da yayi bincike akan dalilin mutuwan Hajna"

   "Idan Dr. Hameed yana kusa kotu tana son ganinshi"

  Bayan ya fito, yayi rantsuwa akan zai fad'a gaskiya, sannan ya ciro takadda, "wannan itace takardar binciken da mukayi akan dalilin rasuwar Hajna," sannan ya bada aka mik'a ma Alk'ali yaci gaba da kora bayani,

  "a binciken da mukayi, kamar yarda yan fannin lafiya da kimiyya suka sani koda (kidney) itace take tace duk wani abu daya shiga cikin mutum, ta tura na jini wurinshi, na ruwa haka, fitsari, zufa da sauransu. Idan ta gaji da aikinta tana bari suna dank'arewa a wajen saboda sunyi yawa fiye da yanda zata iya d'auka. Wannan taruwan da zaiyi ya dank'are a wuri d'aya saiya zame ma mutum kamar wani dutse ko nau'i na ciwo daganan sai a fara samun matsalar fitsari, and other kidney diseases irinsu kidney stones, phylo nephritis da sauransu, kuma tana iya k'ara tarama mutum by product ɗinta a jiki, kamarsu uric acid wanda yake kaman dusar k'ank'ara, idan ya taru ya daskare sai ya gangaro kan kafafu musanman guiwa yana haifar da gout."

   Ya nisa sannan yaci gaba "Abinda k'odar Hajna ta nuna mana yayi matuk'ar firgitamu, haka kuma munyi mamakin yadda take rayuwa a haka duk da baa mamaki da ikon Allah,duk da k'anwarta tace tana yawan ciwo amma tana da dauriya da k'arfin hali, shiyasa ma bata bari mamanta ta sani, duk da k'odar tata ta hagu tafi illata da hakan shiyasa ta daman ke taimaka mata wajen rayuwa, a iya bincikenmu abunda muka gano kenan, k'odarta a cunkushe take da wasu irin tarkace tana fama da cuta shekara da shekaru"

   Sakamakon binciken da muka samu a hanta (liver) ta Hajna yayi matuk'ar tsorata mu, domin har wani ɓangare na hantar tata ya fara zama kore-kore, lokacin da mukayi LFT (liver function test) mun gano wasu parameters din basu aiki yarda ya kamata anma a haka take rayuwa cikin ikon Allah"

   "iya binciken da mukayi kenan, amma duk da haka bazamu iya cewa dalilin daya kasheta kenan ba, duk da shima zai iya kasheta har lahira, abun da mukafi tunani shine, akwai wani ɓangare daga k'asan Hajna, wanda yayi weak, dalilin ɓallewae jinin da tayi kenan lokacin da mijinta ya kwanta da ita,"


  Tunda likita ya fara bayani, tuni jikin Maman Hajna ya jik'e sharaf da zufa, sai k'ifta idanu take, ta ɗan fiddo da kunnanta yanda zataji dakyau, jikinta har kyarma yake, Addu'a kawai take Allah yasa binciken ya tsaya iyakarnan.

  Maman Abdul kam kasa zama tayi kaman mai cutar basur, da wasu maza biyu daga bayanta da suke ta matse'matsen fitsari, nikam abun saiya ɗauremun kai, Maman Hajna da Umman Abdul kuma miye nasu a ciki??


   Br Ahmad yace "da waɗannan shaidu nawa nake rok'on wannan kotu mai adalci data wanke Abdul daga zargin da ake masa na kisan matarshi, domin kuwa babu hannunshi a cikin mutuwarta, daman can Hajna tana fama da rashin lafiya, Abdul sawun ɓarawo ne kawai ya taka"

   "Ina da ja Ya mai shari'a" inji br Alqaseem

  "idan Abdul sawun ɓarawo ya taka, kenan waye ya kashe Hajna? Bance ban yarda da bayanin likita ba anma ai Hajna a hannun Abdul ta rasu, don Haka babu wani mai HAKKIN KISAN Hajna sai Abdul"


  Alk'alin kanshi shari'arnan tana chaja mishi k'walwa, tana daga cikin shari'o'in da yake masu rikitarwa, ya gama ributunshi sannan yace "zamu ɗaga wannan shari'a zuwa sati mai zuwa, a ranar ne kotu zata yanke hukunci, kowanne ɓangarori suyi k'ok'arin tattara hujjojinsu zuwa wannan lokaci"

  Kooootuuuu...!!!


©Rabiatu sk msh

☠HAK'K'IN KISA☠

   👽👽👽👽

      56-60

©Rabiatu sk msh

   ®NWA


www.babymsh.blogspot.com


 Umman Abdul, tare suke da Abbanshi a mota wurin komawa gida, sai dai yayi tagumi duk ya shiga damuwa.

    "wai kinsan wani abu Hajia?"

  "A'ah saika faɗa Abban yara"

    "wallahi ni gaba ɗaya kunyar kaina nakeji, yaronnan yana kuka yana faɗa mana ba shine ya kasheta ba, anma muka kasa yarda"

   "tohh yanzu an tabbatar da bashine ya kasheta ba? Ni naga kaman ka fara saukowa Alhaji"

  "Haba Hajia, bakiji bayanan da likita yayi ba? Nifa daman can don kar ace na goya mishi bayane shiyasa kika ga ina haka"

   "Hmm" kawai tace, shima da yaga kaman batason maganar sai yayi shiru kawai.


  Wata mahaukaciyar dariya taji ta cika mata kunne, da sauri ta zabura ta juya inda yake "kaine kayi dariya?"

   "na miki kama da yanayin dazan dariya ne?" juyawa kawai ta k'arayi, can kuma ta k'arajin an ɓarke da wata dariyar, da sauri da saka hannuwa ta toshe kunnuwanta.

   Cikin dariyar kuma da wata razananniyar murya akace "HAKK'IN KISA, ninan zan ɗauka Hakkin kisan da kaina, tunda kuka kasa magana a gaban kotu"

  Wata irin k'ara ta fasa ta rirrik'eshi, "wai lafiyanki Hajia? Tuk'i fa nake"

  "nidai muyi sauri mubar wurinnan Aljanune hanyar"

   "ai kece Aljanar"


  Da shigarsu gidan ɗakinshi ya wuce, 

   "ki kawomun abincina tun safe banci komai ba"

  "tohh Alhaji, kaima dai ne duk ka...." hannu ya saka ya dakatar da ita, "ki kawomun ɗaki" kaɗa kai tayi ta shige kitchen.

   Saida ta buɗa ta tabbatar abincin akwai zafinshi sannan ta rufe daman khadija ce mai girka mishi, tana cikin harhaɗawa a tire taji abu ya faɗo mata akai, da sauri ta duk'a tana duba ko miye, gabanta ne ya faɗi taja ajiyar zuciya tayi baya.

  K'ullin magani ne ta gani, sarai ta gane ko maganin miye anma ta ina yazo nan? ta duk'a hannunta na kyarma zata ɗauka, maganin taga kaman yana ja da baya, mamaki ya cikata haka ta dinga bin maganin zata ɗauka yana matsawa, kawai ta mik'a hannu da sauri zata cafkoshi, hannunta na dira k'asan ya bugu, take ta farajin kaman girgizan k'asa, komai na kitchen ɗin kaman zai faɗo mata idan ta ɗaga kanta sai taga kaman ana jujjuyawa da ita.

   Tana dawo da kanta ta duba babu maganin, hankalinta ya tashi ta ringa ihu a kitchen ɗin, gashi ba daman ta gudu data mik'e za'a mayar da ita daɓas ta zauna, idan taja gwiwa kuma kaman ba tafiya take ba sai maidota ake, ta bala'in tsorata ga wata irin mahaukaciyar dariya data cika mata kunnuwa.

   Saboda ihun da take da kuma tsabar tsorata bata kula da komai ya lafa ba, sai dai ta buɗa ido taga Abbansu Abdul tsaye jikin k'ofa.

   "nikam Hajia don Allah yau menene yake damunki? Kinbi kin cika gida da ihu kaman wata yarinya"

   Da sauri ta rarrafa inda yake, "Aljanune, wallahi Aljannune kitchen ɗinnan, na rantse akwai Aljanu"

   "badai a gidana ba, Idanma Aljanun ne da ihu zaki koresu? Don Allah ki saba da addu'a a bakinki mana"

  "Naji nidai, mubar wurinnan" duk ta rirrik'eshi ko kanta tak'i dagowa idanunta a runtse.

    "muje kinma manta da yunwar da kika bar mijinki da ita?"

   "ga abincin can"

 Ya tafi zai ɗauka da kanshi, ta bishi tana rik'e dashi, tsoki yaja bayan ya buɗa abincin.

   "yanzu wannan shine abincin?" 

  "eeh shine"

     "wannan ne abincin da zanci? Haba hajia, nidai bansan meke damunki ba yau, anma don Allah kiyi k'ok'arin canjawa"

  Da sauri ta ɗago tana duban abincin taga meye dalilin da yasa mijinta keta faɗa haka, abinda ta ganine yayi matuk'ar razanata, yanzunnan fa take kitchen ɗin anma har ya canja haka.

  Ruɓaɓɓun Vegetables ne ta gani, cabbage, carrot, dasu tattasai, ga lakar kifi da aka yaɓa daga sama duk sun cakuɗe da ɗanyen cous-cous. 

  Sakinshi tayi ta ruga da gudu ɗakinta a tsorace, girgiza kai kawai yayi baima bi ta kanta ba yabar gidan kawai.


  Har dare bai dawo gidan ba, ita kaɗai ga tsoron da takeji, daman Khadija tun bayan abunda ya faru da Abdul ta daina fira da kowa, ta daina zaman falo, data gama abunda take zata shige ɗaki kawai tayi kwanciyarta tana tunanin ɗan uwanta, inta gaji ta ɗora Alwala tana mishi Addu'an Allah ya fitar dashi.

   Umman Abdul tunda ta shige ɗaki, ta rurrufe ko ina, sannan ta kunna wutace, ta kwanta daga baki-bakin gado tana raba idanu, gabanta sai faɗuwa yake, a haka har barci ya fara ɗaukarta.

  Can cikin barcin barcin ta fara jiyo kukan jarirai a hankali, tama ɗauka duk mafarki ne saida taji kukan ya fara yawa ta farka a firgice, jariri kuma? Ina zasu samu jariri gidannan?

  Muryoyin jariran sai k'ara yawa suke, kuma kaman yana matsowa inda take, sai dube dube take a ɗakin gabanta na faɗuwa tuni ta fara kuka.

   Kukan na k'ara yawa gabanta na tsawaita faɗuwa, sai wurwurga ido take ko ina, idonta na kaiwa kan mirrow ta kusan haɗiyar zuciya, jarirai ne kwance ta ko ina, cikin ɗakin, har inda take tsakiyar jariraine sun baibayeta, ai data k'walla k'ara anan ta faɗi sume.


A gidansu Hajna kuwa.

Dukan k'ofar da ake ne ya tashe ta daga wahalallen barcin da baifi minti biyu da ɗaukanta ba, a ruɗe ta tashi ta ida yaye zanin gadon tana kakkaɓe fuskanta, Maryam ta tsaya tana kallonta da mamaki.

   "Mama" ta ɗan saurara daga kakkaɓe kakkaɓen da take idanu a rufe take kallon k'ofa.

   "buɗe idonki Mama kin farka, nice Maryam"

   Sannan ta buɗe idonta tana kallonta cikin jin kunya tama rasa me zatace "lafiya yau baki fito ba? Har 11 tayi baki break fast ba, Gwaggo Hauwa tace ko a kawo miki nan?"

   "A'ah ganinan fitowa, kar kuma a k'ara dawowa a dameni"

   "tohh Mama" harta juya zata tafi.

   "ke jirani mu tafi tare"

 Ta dawo zata shigo ɗakin "ki jira nace ba kizo ki zauna ba"

  Ta kwashi zanen gadon zata wuce toilet tana rufe bayanta, Maryam da bata gani ta k'yale tace "Mama duk kin jik'e a bayanki, kalla katifarki ma"

   "ke baki ganine? Bakiga zufar da nake ba? Mummunan mafarki nayi"

   Ta zaro ido "Mafarkin ban tsoro?"

   "kin isheni da surutu"

  "nayi shiru Mama, da nice ko a mafarki addu'a zantayi, sai dai abun tsoran yayi zufa bani ba"

  "shirun kenan? Don bake kikaga abunda na gani bane"


   Ta shige kewaye tana magana ko addu'an shiga bayi batayi ba, zanen gadon ta fara wankewa, tana shirin cire kayanta ta hango shower na girgiza, ita kaɗai take girgizawanta, sai zare ido take tana jiran taji ta inda zata jiyo dariyan, anma bataji ba sai dai showern dake girgiza kaman zata ɓalle, gabanta na faɗuwa kamn ta fasa ihu take kallonta.

  Can saiga ɓera ya fito daga ciki, yana fitowa ta daina motsi a hankali ta sauke ajiyar zuciyah, da taga kaman fita zaiyi ta tafi buɗe mishi k'ofa, yana kaima bango karo sai ya zama dunk'ulen magani bak'ik'irin, sannan aka kwashe da wata daria, ae batasan sanda ta buɗe k'ofan tayi waje da gudu ba, anan ta wuce Maryam ko kanta bata bi ba.


©Rabiatu sk msh

☠HAK'K'IN KISA☠

   👽👽👽👽

      61-66


©Rabiatu sk msh

   ®NWA


www.babymsh.blogspot.com


 A falonta sukaci karo dasu Muhseen, suma suna shirin shigowa suga idanta tashi shiru bata fito ba, bayansu ta koma ta lafe.

  "Hajna! Hajna ce, wlhy fatalwan Hajna ce bata mutu ba"

  "kamarya bata mutu ba?"

  "nidai bata mutu ba tananan" 

  Da dai suka lura a tsorace take, suka zaunar da ita suna mata addu'a harta ɗan samu barci sannan suka fita suka barta.


Maman Abdul

Saukan ruwan da taji jikinta ne ya farkar da ita ta tashi tana ihu sosae, sai da taga Khadija a kusa da ita ne sannan tayi shiru tana zazzare ido.

   "Umma kinyi mafarkin ban tsoro bazaki farka da addu'a ba?"

  "ina take addu'an? Ke kinga abunda na gani kuwa?"

   "A'ah Umma, me kika gani?"

  Shiru tayi tana tunana abunda ya faru a ɗakin, sannan ta fasa ihu, 

  "jarirai ne, da kukansu cike da ɗakinnan, Allah na gansu a mirrow"

  Khadija shiru tayi tana tausayin maman tata, anya ba halin da Abdul ya shiga bane keson ruɗata? Don ita gani take maman ta damu da Abdul kawai dai don ba yacce zatayi ne.

   "Umma ki kwantar da hankalinki, mafarkine kawai, ki dinga addu'a zaki samu natsuwa"

  "tohh naji, naji" ta juya a hankali tana kallon mudubi, wata fuskace taci karo da ita marar kyaun gani, an yak'e hak'ora cako-cako ana mata dariya, da sauri ta k'ank'ame fuskanta.

   "kin gani ko, ga mutun can ta mirrow"

  Khadija ta kalla, "Umma babu komai fa, daman keda ke a tsorace kin kalla madubi?"

  "tashi ki rufeshi"

Ta tashi ta ɗauka towel ta rufe.

  "shikenan ko Umma?"

Bata nutsu ba tadai ci gaba da kalle-kalle.


A can wani gida, wata mata ce ta saka roban kaya a gabanta. Wata dake kusa da ita ta karkaɗa kai.

   "lallai Hajia saratu, ina magana anma banda amsa ko?"

  "kikace me?" ta faɗa cikin nuna rashin kulawa.

  "sai yaushene zaki daina wannan harkar ta cutar da mutane?"

  Ta gyatsina fuska ba tare da ta kalleta ba, "shikenan mu haɗu mu daina, in daina harkar da nake ke kuma ki daina samun ido da bak'in ciki"

   "bak'in ciki ne ma nake miki?"

  "tohm da miye? Shikenan tunda kikaga na fara samu kika bi kika sakamun ido, don kinga babu harkar da takai wannan samun kuɗi a yanzu"

  "kuma babu wanda ta kaita halakar da mutane ba, ke kanki kinsan yana cutarwa anma kike siyarwa"

  "oho akwai wanda nakema dole sai ya siya ne? Abunda sukeso kenan, ko an faɗa musu da illanshi ba daina siya zasui ba"

   "shikenan ke kuma...."

Ta dakatar da ita, "kinga Hajia barira, idan ba cinikayya zata kawoki gidannan ba, don Allah na yafe zuwan naki"

   "nikam Allah ya tsareni da siyen kayannan, nasan ciwon kaina"

  "eeh sai kibar wanda basusan ciwon kansu ba suzo"

  "Hajia saratu yau nice kike ma iyaka da gidanki?"

  "eeh anyi miki, tunda ba son zaman lafiya kike ba"

  "masha Allahu, kinga tafiyatah" ko magana bata k'ara mata ba har tabar gidan.


  Tana fita wata matar na sako k'afa gidan, 

   "gafaranki dai Hajia saratu"

  "A'aaah Hajjaju makkatun, sai yau nake ganinki?"

  "Haba duka nayi sati da barin gidannan? Kinsan yanzu in nace zan fita anyita zuwa nemane, yanzu ma don naga na wurina sun kusa k'arewa ne na dawo sari"

    "kinsan kuwa akwai wani na musanman nanan aka kawomun shekaranjia, na hana kowa ke nake ajje mawa"

  "yauwah hajiata, ɗaukomun shi na gani"

  Wata er k'aramar k'walbace ta ciro a kwali ta mik'a mata, ta ansa tana buɗewa kuma tayi baya.

  "yadai hajjaju?"

    "wannan ae tsutsotsi ne"

   "tsutsa kuma? Yanzu fa na ajeshi da hannuna"

  "gashi dai ki gani da kanki"

  Ta mik'a mata, Hajjaju saratu ta kware ido ɗaya ta mak'ale ɗaya tana lek'en cikin kwalba, sai dai taji wani lafiyayyen naushi.


©Rabiatu sk msh

☠HAK'K'IN KISA☠

   👽👽👽👽

      66-70

©Rabiatu sk msh

   ®NWA


  A gigice ta dawo baya, nan danan kurmin idonta ya canja launi, Karime ta tashi tana rik'ota,

  "lafiya dai Hajia saratu?"

  Ai batasan sanda ta saketa ba sabida wani lafiyayyen mari da taji yaa sauka a fuskanta.

   "A'ahh hajia daga tambaya kuma sai mari?"

 Sannan hajia Saratu ta fara dawowa, "Uban waye ya mareki? Ki barni in tashi in rama naushi na dai"

  "wurin wa? Ni wlhy ban nausheki ba"

 Nan fa rigima ta kaure, kowa yana cewa ɗan uwanshi ne ya dakeshi, suna can hayaniyarsu sai dai sukaji gidan ya cika da wata mahaukaciyar dariya. Cikin wata irin murya aka fara daria.

   Duk suka k'ank'ame juna, suna sauraren ta inda ginin gidan zai fara faɗo musu, gashi sun rasa daga inda dariyan ke fitowa.

  "waye nan? Wake tsorata mu?"

  Aka gaggaɓe da wata irin daria, cikin muryar da tayi matuk'ar razana su akace "daga cikin waɗanda kukayi sanadin mutuwansu ne, na dawo ɗaukan HAKKIN KISANA"


  "mu bamu kashe kowa ba, na rantse da kwarankwatsa ta faɗomun babu wanda na kashe" babu amsa, sai dai dariyar da aka ci gaba dayi, a hankali kuma sai sukaji ashe dariyan daga cikin kwalban ne, duk suka zuba ido suna kallo.

   Sai da wurin yayi tsit, saiga wasu munanan k'wari sun fara fitowa, gasunan ba kyaun gani, bak'ik'irin da jajayen idanun da sunfi jikinsu girma.

  Duk sunyi matuk'ar firgita da ganinsu, gashi suna son su rufe ido kaman an kafesu, kowannensu kyarma yake, sun dunk'ule wuri ɗaya.

  A hankali k'warin suka fara haɗewa wuri ɗaya, suna zama kaman yanayin kai, sai da ya zama k'aton kai, marar kyaun gani ga idanuwa ta ko ina da k'aton baki, ihu kawai suke don ba k'aramin firgitasu yayi ba.


  Nan take ya fara aman k'warin suna zuwa suna baibayesu, ae basusanma sun saki juna ba kowanne ya kama gabanshi yana ta kanshi. Wani irin cizo suke mai gigitawa, gashi in suka kama fata basusan su saki ba, kowannensu ihun azaba kawai yake saida suka fara shinshino mutuwa sannan k'warin suka bar jikinsu kowanne ya jigata.

   Awa Uku suna jinyar wurin da k'warin suka cijesu, ko ina yayi fari tas ba jini, sai dai ko yaya iska ya shiga wurin kaman ana hura wuta suke ji, ko magana ba mai iyayi. Sai da sukasha wahala sosae, sannan wurin ya koma yana haɗewa, tsaf ciwon ya koma kaman ba'a taɓayi ba.

  Cikin mamaki suka tashi suna dudduba jikinsu, kaman babu abunda ya faru.

   "Na shiga Uku ni Saratu, yau mike shirin faruwa dani?"

  "nice nan na shiga tamanin Hajia, ko uwarme ya kawoni gidannan? Wallahi tashi zaki ki fiddani in tafi"

  "inaaa, ae nima bazaki barni ba"

  Ko mayafi bata tsaya ɗauka ba su duka sukayi k'ofan gida da gudu, Hajia Saratu itace me saurin zuwa buɗe gida, tana taɓa k'ofan sai dai taji anyi jifa da ita baya har saida ta dangana da bango, idonta da yasha naushi ta fara lalube, don ji take kaman an k'arasa cireshi.


   Aka k'ara kwashewa da wata gigitacciyar dariya, 

   "ae kuda barin gidannan, sai kun shirya zuwa kotu kuyi bayani, ku amsa HAKKIN KISAN dake kanku"

   

   Hajiya karime ta rarrafa inda Hajia saratu take, kaman abun kirki ta sak'ala hannunta cikin nata ta fara ihu.

   "Wayyo Allah mun shiga Uku ni da Hajia saratu! Mun shiga Uku nida Hajia saratu!! Wayyo Allah mun shiga Uku"

  Da wata kakkausar murya akace "Ae babu wanda zai jiyoku balantana a kawo muku agaji"

  Ita dai Hajia Saratu harta fara fita hayyacinta, sama-sama ma take jiyo Karime, ita kuma sai kuka take muryarta ma ta daina fita.

  Suna cikin haka sai dai suka ji an fara janye karime, tana kuka ta mik'a hannu zata rik'o Hajia saratu, anma bata da k'arfin daga ido ta kalleta ma.


©Rabiatu sk msh

☠HAK'K'IN KISA☠

   👽👽👽👽

      71-75

©Rabiatu sk msh

   ®NWA


www.babymsh.blogspot.com


Wattpad

@Rerbeeart_sk


  Abubuwan Maman Hajna sun fara munana, ko ita kaɗai take zaune kaman mai shirin zaucewa, ta ringa ihu tana faɗin Hajna ta dawo a fatalwa zata kasheta. Sai su Muhseen sun ringa rufe mata baki, buge hannun take.

   "ku barni in faɗa, Hajna ce ta dawo ba kowa ba"

  Sai dai suyi shiru kawai suna kaɗa kai.


  A daren Ranar da za'a koma kotu, tana zaune Umman Hajna da k'aton carbi tana ja, batasan ma me take faɗa ba tunda hankalinta ba wurin yake ba.

   Giftawan mutun take gani, ta k'ara zare ido tana ci gaba da jan cazbahanta da sauri, nan da nan zufa ta fara karyo mata, ta buɗe baki da k'arfi tana karatun da batasan ma me take faɗa ba, sai dai taga tsayuwan mutum a gabanta, ta kasa ɗago kanta, sai dai taji kaman an ɗago da kanta.

  Kallon mummunan fuskan take jikinta na kyarma ko ina, har ya suɓuce a hannunta.

   "Kin shirya zuwa kotun kiyi bayani kuwa"

  "don Allah kimun rai, wallahi na tuba na daina"

  "karma ki tuba ɗin, Gobene zaman k'arshe a kotu, babu wanda yasan gaskia saike, don haka idanma baki je kinyi bayani ba..."

    "Hmm nice nan zan ɗauka hukunci da kaina"

  "zanje, zanje wallahi...."

Kafin ta gama rufe baki fatalwan ta ɓace.


  Umman Abdul na kwance gefen Abbanshi, tuni yayi barci ya shareta, yanzu kwata-kwata barcinta bai wuce na minti biyar, sama-sama tanayi tana tashi dube-dube.

  Can idonta yakai kan madubi, rubutu ne da jan pen an rubuta.

   "Idan har kinason ci gaba da rayuwa, ki faɗi gaskia a gaban kotu gobe"

   Jikinta na kyarma ta fara tattaɓa Abban Abdul, yana jinta ya mata banza, don ya riga da yasan halinta haka zasu kwana fana firgita sai ya tashi babu komai, tun tana tadashi a hankali harta fara dukanshi tana kuka.

  Tashi yayi a harzuk'e, "miye kuma? Meya faru?"

  Hannunta na kyarma take nuna mishi mirrow, kaman yanda ya zata, babu komai.

   "miye a jikin mirrown?"

  "Gashinan, rubutu ne, wlhy kasheni zatayi?"

  "wacece? Ni banga rubutun komai ba"

  Ta juya tana nuna mishi, itama bata ga komai ba, ta rirrik'eshi tana kuka kawai. Shareta yayi ya tashi ya shiga toilet ɗauro Alwala.


   Daren ranar dukkansu kwana sukayi saman sallaya, Meerah, Khadija, Abban Abdul, da kuma Abdul ɗin, kowannensu Addu'an neman nasara yake mishi akan shari'ar da zasuyi gobe.

  Banda Abdul daya gama fidda rai daga fita zargi, kullum addu'anshi Allah yakai haske a kabarin Hajna, mantawa yake da kanshi a addu'anma, addu'anshi kawai Hajna yake mawa, saiya tuna halin daya shigane hankalinshi yake tashi.


   Tuna maganarshi yake da Meerah marecen ranar, tana son kwantar mishi da hankali anma ta kasa ɓoye kukanta.

  "ka kwantar da hankalinka Abdul, koda mun rasa Hujja, Addu'an da muke bazata taɓa faɗuwa a banza ba, insha Allah, Allah zai kawo mana mafita"

   "yanzu shikenan duniya zata ci gaba da kallona a matsayin wanda ya kashe matarshi?"

  "koda duk duniya zata yarda da hakan, ni bazan taɓa yarda ba Abdul...."

  Kukane ya hanata k'arasawa, ta juya zata bar inda yake a rufe.

  "meeerah!!" ya k'wala mata kira, tsayawa tayi ba tare data waigo ba.

    "Nagode Meerah, ngde da taimakon da kikamun, ko bayan raina bazan manta da abunda kikamun ba, inama ace Hajna tana raye? Na tabbata zatayi Alfahri fiye da wanda take na samunki a matsayin k'awarta"

  Bata iya cewa komai ba saboda kukan da take, sai dai ta juya kawai tabar wurin.

   Share hawayenshi yayi ya jingina da bango, inda hawaye na k'arewa shikam da tuni ya daɗe da manta yana dasu, shikenan gobe za'a yake mar hukuncin kisa?

  

Baradai muje mezai faru goben, matsoratan masoyana😜😄😄


©Rabiatu sk msh

☠HAK'K'IN KISA☠

   👽👽👽👽

      76-80

©Rabiatu sk msh

   ®NWA


www.babymsh.blogspot.com


Rerbeeart_sk @wattpad


Kotu....!

Ta cika ta tumbatsa, ko ina mutanene ba masaka tsinke, a can na iske en RAZ novella sun riga kowa zuwa, su Maryam tapeeda, dr meenert, murjar baba, umman sayyida, da marymaama kam suna gaba baba, en KHADIJA CANDY novels gayya guda sukayo, ASHNUR ma naa hangota da tawagarta, PHERTY zahra exam take anma ta ajje sai da tazo kotu jin yanda zata kaya, en MU FARKA MATA daman a can gari ya waye musu, en ILILEE novels kowa yazo sai hange nake ina zan hangoshi? Ga UMMU ABRAR ma tazo da Abrar ɗinta a gaba (if u knw wat i mean😆).

   Wasu en mata dake kusa dani naji suna maganan wata mata da miji, ae ba k'aramin burgesu suke ba, mijin sai ririta matan yake kaman ita kaɗaice er gata a dunia, jin yanda suke zuzuta couples din ya sakani waiwayawa ba shiri, "wazan gani haka?" abunda nace kenan.

  Dariya yayi yana nunata "MATATAH CE"

   "kaikam Najib har yanzu baka daina faɗin matarka bace?"

   "ina ae har a Aljannah na ringa faɗa kenan Saudat Matatah ce"

  Sama-sama muka k'arasa gaisawa da Sauden Najib, saboda hango best couple ɗina da nayi, Majeeda da Majeeda rik'e da kyawawan yaransu, sai mita yake mata shifa baison zuwa irin wurin hayaniyarnan ta kawoshi, kusa dasu HAFSATUL KIRAM ne da Ya Umar ɗinta.


  Shigowan Alk'ali ne yasa kotun tayi tsit, kowa ya nutsu, shari'arsu ce ta farko, aka gabatar da ita, barrister Ahmad ya fara mik'ewa, shima da ganinshi yana cikin yanayi. Idan ya kalla Abdul da yanayin da yake duk sai yaji ya k'ara sarewa, don yaune ranarsu ta k'arshe.

   "Shaidar da nake da ita a yau, itace cikakken bayanin likita akan cutan data kashe Hajna, wanda suka k'ara zurfafa bincike suka gano"


Likitan ya fara bayani, da takardar report a hannunshi.

    "wannan report ɗin mun nemo bayani ne a wurin likitan dake duba Hajna lokacin da take raye kan Matsalar infection da take fama da ita. Report din ya nuna cewa tana yawan fama da infection wanda hakan kesa tana zuwa asibiti don duba lfyrta. Likitan yace duk zuwa ana mata HVS/MSC( High viginal swab/microscopic, culture and sensitivity) don ganin kalar microorganisms din dake cikin gabanta da neman maganin da zai kashe kwayar cutar Dan da nan.

Wani lokacin ma idan abun yayi kamari sai anyi mata ECS/MCS(endo cervical swab/microscopic, culture and sensitivity) Wanda idan ta dace magani tana dadewa abun bai tasar mata ba. Amma kuma mun dauki hakan ne a makaranta take kwaso infection din sbd kwamacala ta bayin makaranta da kuma fitsari inda bai kamata ba.

   A binciken da mukayi kan vigina din Hajna mun gano wani tsuro wanda haduwar wasu abubuwa da bamu san ko miye ba suka dunkule waje daya duka tsuro sai ya zama kamar tumour. Sai ya tsiro mata daidai idan an wuce labia majora, labia minora wajen vulva dinta kafin a kai cervix. Shine abinda ya fashe a gaban Hajna har ya kawo wannan jinin mai yawa da muka gani faca faca a jikinta da gadonta.

  Tambayarmu a kan Abdul itace shin yana shan wani abu ne da ke kara karfin maza kafin yayi aure ko kuma kasha kwaya ne ranar da aka kawo maka Hajnah

   Sbd yadda yaje ma Hajna abun tambayane,babu yadda zaayi namiji ya sadu da mace na tsawon wannan lokacin tun wajen 11 na dare har asuba) alhalin lfyrshi lau bai sha komai ba.

  Dadewar da yayi yana saduwa da ita ne ya kawo fashewar wannan abun 

Amma da ya sadu da ita na kankanin lokaci ta kuma hanyar hankali da ko tsautsayin zai faru zai zo ne da sauki sosai."

  Barrister Ahmad yayi gyaran Murya bayan an mik'a ma alƙali takardan, 

   "wannan shine bayanin ɓoyayyar cutan da Hajna ta daɗe tana fama da ita, Ya mai girma mai shari'ah, ina fatan wannan hujjar zata zama gamsarshiya wurin wanke Abdul daga laifin da ake zarginshi dashi"

   "ina da ja Ya mai shari'ah" inji barrister Alqaseem.

   "bai kamata shari'arnan ta k'are a haka ba, idan mukai nazari akan bayanin likita na k'arshe, mun yarda da batunshi na cewar Hajna nada cutan Infection wanda har iyayenta basusan da tana zuwa wurin likita yana dubata ba, anma shida kanshi likitan yayi bayani kan cewan inda Abdul baisha wani abu dazai k'ara mishi k'arfi ba abun zaizo da sauk'i, kenan har yanzu HAKK'IN KISAN hajna yana kan Abdul"

  Ya maida kallonshi akan Abdul, "Malam Abdul, tunda har anzonan, bai kamata kaci gaba da wahalan da shari'ah ba, wanne irin magani ne kasha ka jema Hajna a daren data rasu?"

  Girgiza kai kawai yake, "babu abunda nasha, wallahi tunda nake da idona ba ban taɓa ganin maganin k'arama maza k'arfi ba, ban taɓa sha ba, mezai sakani shan abunda zai cutar da Hajna ma?"

   

  Barrister Alqaseem ya juya kan Alk'ali, "ina ganin duk hujjojin da kotu take buk'ata kan dalilin mutuwan Hajna sun kammala, Abdul yayi amfani da matarshi Hajna tun daga k'arfe 11 na dare har zuwa Asuba, wanda wannan ba k'aramin cutarwa bane a gareta, bayannan kuma bai tashi je mata ba saida yayi amfani da maganin daya k'ara mishi k'arfi, bisa duba da wannan hujjojin nake rok'on kotu da tayi gaggawan yankewa Abdul hukunci, domin babu wanda yake da HAKK'IN KISAN hajna bayanshi"

  Barrister Ahmad dafe kai yayi kawai ya koma ya zauna domin kuwa yama rasa da wanne kalamin zai k'ara kare Abdul, Alƙali ya duk'a yana en rubuce-rubucenshi, gaba ɗaya kotun tayi tsit kowa da abunda yake sak'awa a ranshi, k'aran kukan Meerah kawai ake jiyowa, Abban Abdul ma duk da k'arfin halinshi saida ya zubda hawaye, Umman Abdul daman baizo da ita ba saboda Halin da take ciki na tsorata.

   Anan wurin Abdul ya duk'ar da kanshi yana hawaye, kanshi na matuƙar sara mishi, tunanin Hajna na dawo mishi sabo, ɗaga kanshi yayi yana kallon Meerah, yanda take kuka da alama tama fishi shiga tashin hankali, Allah sarki khadija, yasan tana can gida tana ta mishi Addu'a.


  Maman Hajna ce Zaune, idonta rufe tamak'i buɗewa saboda wani abubuwa dake mata yawo saman kai, tana jin hayaniya anma tayaya zata iya buɗa baki ta faɗi gsky gaban wannan jama'ar? Buɗe ido tayi da niyyar ta k'ara k'are musu kallo, wani k'aton kai ne mai ban tsoro, babu tsoka ko kaɗan sai k'ashi ya taho baki buɗe ya kusan kaima fuskarta karo, ta fasa wani uban ihu ta rufe ido.

   Cikin kunnanta ake mata wani irin tsawa, "Bazaki faɗa ba? Ki buɗe baki kiyi bayani, ki faɗi gaskia nace"

  A ruɗe ta mik'e, "zan faɗa! Wallahi zan fafa" kowa ya juya kallo ya koma kanta, harta alƙali tsawa yayi da rubuce-rubucenshi.

  Saiga Umman Abdul tare da wani mutum irin en k'auyennan, kaman an jefosu sun dira gaban kotu,

  Umman Abdul tace "a dakata, ba shine ya kasheta ba"

   Maman Hajna tace "eeh bashi bane, nice nan nayi silar mutuwar y'ata"

  Umman Abdul tace "A'ah nice dai, nice nayi silar mutuwarta" ta kalla mutumin da sukazo tare,

   "gaskia mukazo mu faɗa ko?"

  Shikam Abdul kallonsu kawai yake da mamaki, Ummanshi kuma? Meya haɗasu da mutuwan Hajna?

  Mutumin yace "k'warai ma kuwa, babu mai HAKKIN KISAn baiwar Allahn nan Ya mai shari'a sai mu, domin kuwa ni naga abunda na gani, sati guda kenan HAKKIn ta ya hanani runtsawa, idan na kwanta na ringa ganin kawuna kenan, kai ido buɗe ma cikin tsorata nake"

  Daga can baya suka jiyo murya na cewa "muma haka, Mune nan Mukai silar mutuwan Hajna, gaba ɗaya mutuwanta ta hana mana sukuni" su Hajia karime ne, hango Maman Hajna da sukai a tsaye ne ya saka har suna rige-rigen K'arasawa inda take.

   Hajia saratu tace "kiyi hak'uri Hajia, anma dole mu faɗi komai a gaban kotu yanzunnan, domin kuwa rayuwanmu na cikin hatsari indai bamu faɗi gaskia ba"

  "k'warai ma kuwa, duk kwanakinnan cikin tashin hankali muke, hak'uri zakiyi kawai Hajia mu muka ga abunda muka gani"


  Gaba ɗaya kotun ta hargitse, kowa da abunda yake faɗa, mamaki faal a zuciyoyin mutane, sai da Alk'ali ya tsawata sannan kowa yayi tsit.

  "ya isa haka, kotu ba wurin sauraren hayaniya bane, idan da maganar da zakuyi a gaban kotu zaku fito ku faɗeta" su duka kamar walk'iya sai gasu sun wuntsilo gaban kotu.

  Alk'ali yama Maman Hajna Umarni akan ita za'a fara saurara.


Kumin Uzuri, wallahi hannuna ya gaji naso kuji komai a yau, anma ku k'ara hak'uri zuwa next page plz


©Rabiatu sk msh

☠HAK'K'IN KISA☠

   👽👽👽👽

       81-100


©Rabiatu sk msh

   ®NWA

Wattpad @Rerbeeart_sk


www.babymsh.blogspot.com


🔚🔚🔚


 Maman Hajna tayi gyaran murya cikin damuwa ta fara magana.

  "Nice nan na haifa Hajna, kuma babu wanda yake da Hakkin Kisanta saini, nasan kowa zaiyi mamaki dajin hakan, anma ba abun mamaki bane idan kunji bayanin dazai fito bakina, fatana kawai sauran mutane zasu ɗauka darasi karsu aikata irin aikin wautar da nayi"

   "tun lokacin da likita yayi bayani kan mutuwan Hajna, na shiga k'ok'onto, domin bansan wanne irin hukunci za'a yankemun ba, shiya hanani magana"

  "na kasance tun kafin haihuwar Hajna, nakejin mutane na magana kan indai kana da yarinya ɗiya mace, kamata yayi tun kafin ta girma ka fara gyarata da magungunan mata ba saita girma an mata aure ba, da wannan burin nayi aure harna samu cikin Hajna, kuma cikin sa'a Allah ya bani rabo da ɗiya mace, tana da shekara 7 muka haɗu da Hajia karime mai bada magani, tun daganan take kawomun magungunan da bansan asalinsu ba, nake ɗurama Hajna, kullum cikin bata magungunan tsumi nake, hardana tsarki dana matsi, da kaina nasan Hajna badon tanaso ba take amsar magungunan nan, anma ko a fuska bata taɓa nunamun ba, da yake yarinya ce mai biyayya"

   Alk'ali ya nisa sannan yace "kenan magungunan da kike batane silar cutar data sameta?"

  Hajia Saratu tayi karaf tace "k'waraima kuwa, domin nima mutane da yawa na kokamun akan wannan matsalar"

   "kenan kunsan yana cutarwa kuma kuke saidawa?"

  "Itama ae mun faɗa mata yana cutarwa"

  Kallonsu kawai yake da mamaki, gaba ɗaya kotun jikinsu yayi sanyi, ya kalli maman Abdul, 

  "menene abunda zaki faɗama kotu kan mutuwar Hajna?"


  "tabbas ni nake da abun faɗa, duk da bayanin da tayi yayi kama da nawa, ta faɗi silar cutan Hajna, anma nice nan nayi Silar mutuwarta, domin kuwa tunda aka saka ranar auren Abdul da Hajna, na fara amsar magunguna a hannun wannan mutumin da yake tare dani, shine yake kawomun magungunan k'ara ma maza k'arfi, ni kuma nake ba Abdul ba tare da saninshi ba, duk da baisan ko miye ba, anma a dole nake matsa mishi yasha, bayanin da zanyi kenan yamai shari'ah"


  Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, shine abunda wasu daga cikin mutane kotun ke ambata, gaba ɗaya Meerah a firgice take dajin wannan bayanin, ballantana Abdul da yake jin maganar kaman saukar aradu.

  Alk'ali ya ringa girgiza kai cikin mamakin wannan iyaye, gaba ɗaya abun ya ɗaure mishi kai.

   "wannan wanne irin iyayene nake gani a gabana? Iyayen da zasu bama yaransu abu bayan kuma sunsan zai cutar dasu kawai da sunan gyara? Gyaran da ɓacinshi yafi amfaninshi yawa, yau wa gari ya waya? Abunda kika daɗe kina mata gyaran kanshi ya k'are a daren farko? Wallahi wannan kuskurene babba, gareku iyaye da kuma ku masu saida magungunan da bakusan asalinsu ba da sunan gyara, abun kunya ma wasu matan ne da kansu keshan abunsu"

  Ya kalla Hajia salame, "kina da aure? Yaranki nawa?"

   girgiza kai tayi cikin jin kunya, "bani da aure a yanzu, ban taɓa haihuwa ba sanadiyyan shan magungunan matan da nake"

   "kefa?" ya tambaya Hajia karime "aurena huɗu anma babu ko ɗaya"

   "kun gani ba? Wallahi magungunan nan ba k'aramin illa sukewa mutane ba, gaba ɗayama kun sanya ɓacin rai na manta abunda ke gabana"


   Duk'awa yayi yana en rubuce-rubuce, sannan ya ɗago kai kowa yayi shiru yana jiran yaji mezai faɗa,      

  "Bayan nazari da dogon bincike akan wannan shari'a, mun gane cewa Abdul bashi da laifi ko kaɗan akan mutuwan Hajna, domin kuwa gasha magungunannan ne a bisa rashin sani, sannan kuma abunda ya faru dashi a ranar aurensu da Hajna ba laifinshi bane, ya faru ne akan Maganin da yasha cikin rashin sani, don haka kotu ta wankeshi daga zargin da ake mishi"

  "Sannan kuma gaba ɗaya mutanen nan, babu wanda HAKKIN KISAN Hajna bai rataya a kansu ba, don haka kotu ta yanke musu hukuncin shekaru goma a gidan yari, Maman Hajna, Umman Abdul, da kuma sauran masu maganin nan guda Uku"

  Kotu.....!!!  


Umman Abdul anan wurin ta duk'e tana kuka, Umman Hajna kam Ɗaura hannu tayi akai tana ta ihu kaman wacce ake zarema rai, Hajia karime ta rungume Hajia saratu,

  "kaicon mu, kaicon duk wata macen dake bama er uwarta mace maganin dake cutarwa akan gyara, kaicon wannan hali namu yanzu gashi abunda ya jawo mana"


  Tsananin farin ciki Meerah batasan sanda ta taso ta rungume Abdul ba tana dariya, anan inda yake tsaye yana ma mahaifiyarshi wani irin kallo na tausayawa, ganin Abbanshi na zuwa inda yakene, cikin dubara ya cire Meerah daga jikinshi.

  Yana ɗaga ido ya hango Hajna tsaye cikin farare kaya, tana murmushinta mai kyau, kallon Meerah tayi tana mishi alama cikin murmushi, a haka harta ɓace gaba ɗaya.


Alhamdulillah

Anan na kawo k'arshen wannan gajeran labari nawa, kuskuren dake cikin Allah ya yafemun, Allah kuma ya bamu ikon amfani da darasin dake ciki.


SADAUKARWAR Takice Auntie Sis, Allah ya k'ara girma, tabbas babu wanda yasan halin karamcinta sai wanda ya zauna da ita.


Godia Mai yawa ABDULAZEEZ ILILEE, Allah ya k'ara basira da ɗaukaka, muna tare dakai a littafin BARE


Jinjina ta musanman ga k'ungiya mai Albarka, NAGARTA WRITERS ASSOCIATION, Allah ya k'arama mana haɗin kai, Ameen.


RAZ nawa, banda kamanku Amrah A msh, ZahraBB, Alah yabar k'auna.


Gaisuwa ga dukkan makaranta littafinnan, dama masoyana gaba ɗaya, Allah yabar k'auna, kuci gaba da kasancewa dani a littafin ZAMAN AURE, wani zaman ma yanzu za'a fara.


Domin gyara da shawarwarinku +2348032133670


©Rabiatu sk msh


Tags: #Hajna #Fatalwa
3234
0
4
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!