Haka Za Ki Min? (True life story 2015)

Written by Aisha Adamu SadiqPublished on 2019-01-03 23:46:06Category RandomA duniyar da ka mika dukkan yardarka ga waninka, ka damka amana, kana ganin kowa nada kyakkyawar zuciya irin ta ka. Hakan ne tsakanin Aysha da Farha, kawaye da suka yarda da juna. Sai dai mi! Hakan bai hana Farha cin amanar kawarta ba ta hanyar neman mahaifin Aysha. Ku biyo labarin sannu a hankali dan jin yanda za ta kaya. tags: Cin-amana #abota #yardaDuba was labarai »

HAKA ZAKI MIN???

 

Na

©Mss_Sanam 

&

ChuchunGaye 

 

GARGADI:Bamu yarda wata ko wani ya canza mana wani bangare na daga wannan rubutu, duk wanda yai hakan bamu YAFE ba. 

 

ARASHI: Muna neman alfarma ga duk wanda yaga wannan labarin yayi kamamceciya da rayuwar ta/shi a gafarce mu, yanayin labarin ne ya zo da hakan. 

 

 

LABARIN.. 

 

 

 

Tafiya suke sannu a hankali cikin natsuwa da kamala, hakan zai tabbatar da kamun kan su da kuma ajin su.. Kallo daya mu kayi ma su muka tantance kyawun su.. 

 

'Yar doguwar wadda fuskar ta ke cike da heavy makeup kamar mai shirin zuwa dinner, ta bude baki tace "Bestie da ma kin koma abinki nan ma ya isa, k'ila in samu lift da na isa bakin titi".. 

 

Wadda aka kira da bestie tace" Haba Farha dear wai yaushe zaki daina hawa lift ne? Am scared of the society nowadays farha, cultism yayi yawa please ki daina shiyasa na so na mai da ki gida da kai na har na dauko mota kika ce na barshi kuma dai kece da rigima gidanku da ba wani nisa ko a kafa zaki iya zuwa".. 

 

Farha tayi murmushin da beauty point din ta ya lotsa tace "never mind Aysha, nasan irin wadan da ni ke tsaidawa kuma ma miye amfanin mutum yana tuk'a flashy car babu mace a ciki, matan ma iri na".. Aysha ta kai mata duka a baya tace" ina guje maki Farha amma ba kya ji, yanzu dai mu k'arasa bakin titi k'ila ki samu keke napep".. Farha tace "bestie ki koma gida kawai zan k'arasa da kai na kinga it's getting late".. 

 

She have no option than ta tafi, dan tasan halin bestyn ta.. Tana tunanin da kyar ne ta jira keke napep lift din da ta saba hawa shi zata hau.. Suka yi sallama suna ma su daga na juna hannu.. 

 

Farha ta k'arasa bakin titi, hannun ta sak'ale da handbag din ta, ta fiddo shade din ta tasa, tana chewing gum.. Sai karkada jiki take, kamar ba ita muka gani dazu tana tafiya gently ba.. 

 

Can wata motor kirar Mazda 3, tun da motar ta danno Farha tabi motar da kallo, numfashi sai da ya dauke na wucin gadi.. 

 

Yatsan ta dake kusa da thumb din ta na hagu ta daga tana dan karkada shi tare da girgirza jikin ta.. 

 

Daidai saitin ta, mai motar ya tsaya, kofar motor din ce ta bude.. Yaudararren murmushi ta saki, tare da yin farrr da idanun ta, ta shiga motar ba tare da wani tsoro ko fargaba ba.. 

 

Sai da ta daidaita akan seat din motar sannan ta kai duban ta ga mutumin tace "thanks 'yallabai".. Cikin siririyar muryar ta da take yaudarar maza da ita.. 

 

Kasa magana yayi dan ta d'ana ma shi tarko.. Yace" ina zuwa' yan mata?" tace "dutsen amare lowcost".. Sai a sannan ta kare ma shi kallo, babban mutum ne da a haife ya haifi wadanda suka fita.. Ba wani kyan azo a gani gare shi ba, sai uban tumbin da ya fito cikin shaddar dake jikin shi dinkin tazarce.. 

 

Sai suka zo unguwar su tace "Nan ma yayi yallabai Thanks".. Yayi dan murmushi yace" idan ba zaki damu ba ina son phone number din ki".. Tace "okay ba damuwa".. Ta amshi wayar shi ta zuba ma shi number din ta ya amsa, tare da cewa" sunan ki fa?" tace "Farha" yace "nice name, am Engr. Yakubu".. Kadan ya hana dariya bata su6uce ma ta ba saboda yanda ya ambaci sunan na shi cikin cika baki".. 

 

Kallon k'urilla ya bita da shi ganin yanda take karkada jiki, dole duk wani lafiyayyen namiji yaji wasu feelings.. 

 

Ya motar shi yayi gaba, ita ma ta wuce gidan su.. Gidan ginin flat house ne, dai dai rufin asirin bawa.. Da sallamar ta ta shiga gidan, mahaifiyar ta dake alwala bakin famfo ta amsa tare da fadin "idon ki kenan Farha ke duk sanda kika fita sai kin kai maraice".. Tace" kiyi hakuri Mami bazan kara ba".. 

 

Mami tace "ai halin ki ne ya zanyi da ke sai addu'a, kin raina kowa gidan nan, Abban ku kadai kike gani da gashi wuce ki ban waje".. 

 

Simi-simi ta wuce dakin su tare da jefar da gyalen ta da jakar ta kan cushion two seater dake dakin.. 

 

Sameera ce ta shigo dakin dauke da food flask hannun ta, ta ajiye tare da zama kan daddumar sallah da ta shimfida tace "wai sai yanzu kike shigowa gida Farha, sai na gyara maki zama tukunna zaki bar wannan halin naki ki fita gida baki san ki dawo kan lokaci ba, uban wa kika maida bawan ki a gidan nan?" Farha tace "Eh na fita kiyi abinda zaki yi shikenan mutum ba zayyi rawar gaban hantsi ba duk a dame shi da surutu".. Sameera tace" Allah ya shirye ki".. Food flask din da Sameera ta bude Farha ta lek'a, tsaki tayi tace "hohohooooo gidan nan kullum dare tuwo gaskiya bazan iya ci ba".. Sameera bata tanka mata ba ta zuba tuwon ta da miyar kubewa busassa ta cigaba da ci.. Farha tayo alwala tayi sallah.. 

 

Tana gama sallar sai mita take yi na tuwon da akayi.. Karshe fita tayi da yake unguwar su akwai mai balango ta siyo tare da wapa Yoghurt din ta..

 

 

Koda ta dawo Abban ta yana zaune a harabar gidan tare da mamin su suna fira tana shigowa ta ganshi sai tayi sauri ta boye hannun ta baya, yana ganin ta yace "Farha zo nan" taje ta durkusa ta gaida shi yace "ina kika fito da daren nan?" 

Sai ta fara "in um am Abba dama", sai mamin su ta ce "kina wani in in kamar barauniya kedai kam kinji haushi Farha wallahi ki gyara rayuwar ki" sai tace "wai fa Alhaji da magriban nan ta dawo tayi sallah sameera ta kawo masu abinci suci shine fa ta hau bakin ta wai ita bazata ci tuwo ba ta tashi ta fita yanzu ma dai gidan ubanwa kika tafi fito da hannun ki mugani", sai Farha ta ciro hannun ta Mami tai salati tace "Alhaji kaga irin abinda nake gaya maka akan yarinyar nan ko?"

 

"Oh ni Fatima ina zan sa yarinyar nan ne wai?" 

"Yanzu indai bada hali irin na farha ba mace da zuwa siyan nama Jama'a wannan wane irin rashin kamun kai ne? toh ai yanzu sai ka tambaye ta ubanwa ya bata kudin da ta siyo naman?"

 

 

"

Sai Abban yace "Farha na raba ku da fitar dare amma ki ka ji ko? Kiji tsoron Allah duk abinda kike ki sani fa Allah yana kallon ki ni ba abinda zance miki illa kiji tsoron Allah tsakanin ki da shi ne ba damu ba ki tashi ki tafi Allah ya shirya ki". 

 

Ta tashi sumui sumui ta wuce dakin su. 

 

Ita kuma Mami sai fada take tana fadin "Alhj duk wannan aikin ka ne kai ne kawai kake bata damar yin yanda taso a gidan nan amma ai Farha na wuce bugu ta yi ba yarinya kamar diyar makafi".. 

Alhaji yace "ai duka ko zagi ba shi zai gyara yaro ba, addu'a da nasiha ita ce mafita".. Tace" toh Allah shi shige mana gaba".. 

 

***************************

Aysha kuwa tana dawowa Ammi ta tare ta da fada,tace "Wai yanzu Aisha badai na hana ki fita da magriba ba" tace "Ammi Farha kawai nayiwa rakiya ba fita nayi ba" Ammi tace "wannan Farhan kowanne yaron arziki yana gidan su ake magrib sai ita wai ita iyayen ta basa mata fada ne?" Aysha tasan halin Ammi dama ba wani son Farha take ba sai kawai tace "kiyi hakuri Ammi Farha fa ba gidan kowa take zuwa ba sai gidan mu".. 

 

Ammi tace "wuce ki bani guri ba Farha ba gidan ku" Ta wuce dakinta tayi Sallah Maghreb. 

 

FARHA DA AYSHA 

 

Wasu aminan juna ne da suka zama tamkar 'yan biyu we don't really have words to describe the kind of friendship they share. 

 

Infact har sun zama tamkar yan uwa koda yaushe zaka gansu a tare idan aka aiki Aysha bata zuwa sai ta biya ta dauki Farha da mota kafin taje har ya zamana Aysha bata iya zuwa ko ina sai tare da Farha. 

 

Koda yaushe zaka gan Farha kan hanyar gidan su Aysha indai ba school Ta je ba.. Shima da ta dawo zata biyo gidan su Aysha.. 

 

Tun Ammin Aysha na d'ari-d'ari da zumuncin Aysha da Farha har dai ta saduda dan amincin su ya k'arfafa bata jin akwai mai iya bata wannan amincin.. Dan Aysha ta mik'a ma Farha duk yardar ta da dukkan zuciyar ta.. 

 

75% na kayan Farha wajen Aysha take samun su dan duk abinda za'a yi ma Aysha a gida sai anyi ma Farha, ko kudi aka bata na shopping to tare suke zuwa suyi.. Har ta kai Abban Aysha idan zai ba Aysha kudi sai ya hada dana Farha.. Kowa na gidan su yasan da zaman Farha.. 

 

ASALIN SU 

Farha kamar yanda kuka ji sunan 'yan asalin garin Dutsinma ne a Jihar Katsina, aiki ya kawo mahaifin ta cikin Katsina a ma'aikatar SUBEB... 

 

Sunan mahaifin ta Alhaji Surajo da

matarshi HHajiya Zainab.. Suna da Arzikin su daidai rufin asirin bawa, dan basu tauye yaran su da komi ba daidai gwargwado. Su biyu kacal mahaifan su suka Haifa daga Sameera yar kimanin shekaru ashirin da biyu (22) dake shekarar karshe a Jami’ar Ummaru Musa Yaradua University Katsina, tana karantar Computer science, sam bata da hayaniya da son karya kamar kanwar ta Farha. 

 

Shekara hudu ne tsakanin Sameera da Farha, inda Farha ke da shekaru 18.. Itama tana karatu a cikin jami'ar ta UMYU tana shekarar farko wato 100 level tana karantar BSc. Biology. 

 

Amincin Farha da Aysha ya samo asali ne a lokacin da aka maido Farha makaranta su Aysha wato Ulul Albab dake nan cikin Katsina, inda zata kammala ss3 din ta anan dan ta samu taci SSCE din ta.. 

 

Ajin su daya da Aysha, da yake Farha akwai cusu daga zarar ta lura da zata ci ribar abota da mutum.. Tun da ta kyalla ido taga Aysha shikenan ta manne mata, har Aysha ta saki jiki da Farha.. 

 

Lokaci daya suka yi Shak'uwa sosai duk wanda yaga Aysha to yaga Farha.. 

Aysha Mahaifin ta Alhaji Kabir shararren mai kudi ne a Katsina.. 

 

Su 4 ne a wajen mahaifin su mata biyu maza biyu ita da kanin ta Adnan ne mafi soyuwa a wurin mahaifin su wanda suke kira da Dady.. Gwargwadon hali yaran gidan suna samun samun kulawa sosai,.. Duk da hakan be sa tarbiyyar su ta gurbata ba.. 

 

Saboda naci irin na Farha har ta kai tayi suna a gidan su Aysha duk wanda yasan Aysha yasan san da zaman Farha.... 

 

Har suka gama secondary school, sai suka sha bambam dan Aysha AlQalam University da yake private University ce.. 

 

Farha ta so ace can ta cike.. Haka ta hakura, kowa da makarantar da yake zuwa.. 

 

Farha da kwashe-kwashen kawaye dan ita akwai nuna san a sani, babu mai raina ta saboda yanayin shigar ta sai a dauka diyar wani don ce komi nata high taste ne.. Wanda da bazar Aysha take taka wannan rawa..

 

Haka kawancen su ya cigaba da tafiya cikin aminci da yardar juna.. 

 

Farhah na da wani abu, sam bata k'aunar ta ga wata ta rabi Aysha duk yanda zata yi sai ta san yanda tayi ta raba Aysha da kawayen ta.. Ta hanyar kawo kushen su wajen Aysha har sai taga ta raba tsakanin su, ta fi son ace ita kadai ce k'awar Aysha.. 

 

*******************************

Farha ce ta fito lectures ita da wasu course mates din ta,riga da skirt ne na lace jikin ta, kayan sun matuk'ar matse ta kamar tayi nishi mai k'arfi su yage, ta yafa AISHA BUHARI veil a kafadar ta irin dai yafa gyalen 'yan bariki.. 

 

Duk cikin su ta fita zakka, sun zo daidai wajen administrative block, sauran suka samu keke napep.. Wayar ta ta fiddo ta latsa wasu numbers ta kira. Aka yi picking a dayan bangaren, ta dan lankwasa muryar ta tace "Cweerie nah na fito lectures ka zo ka maida ni gida".. 

 

Ba mu ji reply din da aka bata ba,waje ta samu ta zauna, kamar 15mins wata mota kirar SABARU LEGACY baka ta tsaya gaban Farha, wani dan matashi ne ya fito daga motar, dan gayu da shi mai ji da kudi da kwalisa.. 

 

Ya kalli Farha yace "my queen ta so mu tafi".. Da kyar ta tashi saboda matsewar kayanta.. Ya bude mata motar su ka shiga, ya harba motar.. 

 

Tace" ni fa yunwa nike ji Habib" yace "okay mu biya meal restaurant".. Ta yatsina fuska tace" toh daga nan mu biya KALAMU WAHEED ko JIFATU zanyi shopping cosmetics dina sun k'are ".. Murmushi yayi tare da riko yatsun ta yakai masu sumba (kiss)...

 

Sai da suka biya meal restaurant suka yi Kat, harda guzirin take away na roasted chicken da fresh milk Farha tayo.. 

 

JIFATU suka nufa, inda Farha ta hau jidar kayan cosmetics, da kayan ciye-ciye irin su sweet, chocolates, biscuits, wafer, drinks, milk, milo, oats, da dai sauran tarkacen kayan kwalama da mak'ulashe.. 

 

Sam bata tausayin bawan Allah nan, haka suka je ya biya kudin ta ATM over 70k.. 

 

Har gida ya kai ta, ko tsoron maganar 'yan unguwar su bata yi, ta dan kalle shi tace "Thanks Habeeb".. Ya dan lashe lips din shi yace" anjima wajen 9pm ina nan zuwa".. Tace "ba damuwa".. 

 

Ya dan rufe idanun shi yace" give me a good bye kiss nd hug".. FARHA ba kunya ba tsoron Allah ta yi hugging da kissing din shi.. Sannan suka fito ya fiddo mata da shopping bags din ta har guda hudu (4)..

 

Baki muka saki muna kallon su tare da mamakin halayyar Farha.. Muna tirrr da halin ta..

 

Tana shiga da kayan cikin gida, Sameera da ke kitchen ba ta je lectures ba ta hango Farha na 'yan lek'e-lek'e dan ta ga idan ba kowa.. 

 

Ta shigar da kayan dakin su, ta na zazzagewa a k'asa Sameera ta shigo, ta rik'e k'ugu ta na kallon Farha ranta a 6ace, tace "Farha gidan uban wa ki ka samo wadannan kayan?".. 

 

Farhah tace" wai ke Yaya Sameera mi ya ruwan ki da kayan da na shigo da su kawai dai sa ido dan kin san ba ki samun kamar su".. 

 

Lafiyayyen mari Sameera ta falla ma Farha dan sai da ta ga wasu taurari na giftawa, ta dafe kuncin ta, tace "ki ka mare ni Yaya Sameera to wallahi sai na rama uban kuturu yai kadan ballatana na makaho".. Sameera bata ankara ba ta ji saukar mari ita ma.. Karaf a idon mamin su. 

 

Mami tace" yanzu Farha saboda rashin kunya ki ka daga hannu ki ka mari Sameera tsarar ki ce ita"... 

Gungunai take yi, Sameera tace "Mami ki duba kiga abinda Farha ta shigo da su daga nayi ma ta magana shine ta fara man rashin kunya"..

 

Sai a sannan Mami ta kalli kayan tace "ina ki ka samo wadannan kayan?", Farha ta ce "Aysha fa ta ba ni d'azu".. Mami ta kad'a kai ta wuce ba tare da tayi la'akari da iyayen kayan ba dan sun fi karfin siyayyar k'awa... 

 

Wani abu ya tokare wuyan Sameera ganin yanda Mami ta kasa daukar mataki akan Farha, tana jiye ma su abin kunya dan suna sakaci da tarbiyyar Farha.. 

 

Farha kuwa hararar Sameera ta rik'a yi a fake, ta jera cosmetics d'in ta kan dressing mirror, kayan tea kuma ta dora saman fridge da ke dakin.. Drinks kuma ta zuba ciki, sannan ta je kitchen ta dawo da plate da wuk'a ta ciro roasted chicken din ta ta d'iba, ta kai ma Mami.. 

 

Ta kalli Sameera ta ce "Yaya Sameera ga na ki".. Sameera ta kad'a kai ta ce" na k'oshi".. Murmushi tayi dan ta san halin Yaya Sameera komi za'a yi ma ta ba za ta ci wannan naman kazar ba, ta na son yayar ta akwai gudun wulakanci ba ta da kwadayi kuma... 

 

Fitowar su lectures kenan, wayar ta tayi ringing, ta yi picking.. Mun dai ji ta ce "toh sai ka zo".. 

 

Engr. Yakubu ne yazo daukar ta yau, mutumin mayen mata ne na bugawa a jarida, tun da ya kyalla ido yaga yanayin Farha yasan 'yar gari ce ita ma.. 

 

Sun fito daga school, sun dan bar wajejen school entrance dayake titin babu yawaitar ababen abin hawa, Engr. Yakubu yayi parking gefen titi ya fito, Farha ma ta fito dawo side din da yake, yana rike da hannun ta yana murza' yan yatsun ta tare da bin ta da wani shu'umin kallo.. Rungume ta yayi tsam.. 

 

Sameera ce cikin keke napep sun gama lectures zata tafi gida around 2:16pm, kamar ance ta leqa wajen gefen titi, kawunan mutane ta hango mace da namiji, gaban ta ya fadi da ta tuno irin kayan da Farha tasa dankwalin ta hango, tsaida mai keke napep tayi tace "malam tsaya dan Allah nayi mantuwa".. Yace" amma baki Kyauta mun ba yanzu mutum biyu kike son in kai har cikin gari?" hak'uri ta ba shi tare da mik'a ma shi naira dari kudin da zata biya shi.. Murmushi yayi ya ja 'yar k'urk'urar shi.. 

 

Tsallaka titin tayi, taje daidai wajen motar da sai da numfashin ta ya dauke na wucin gadi, ganin' yar uwar ta, jinin ta, kanwar ta jikin wani gardi suna romancing juna.. Zafafan hawaye ne suka zubo mata, wani karfi yazo mata da azamar ta ta doshe su, lafiyayyen mari ta sakar ma Engr. Yakubu kwarara guda biyu, ta kalle shi da rinannun idanun ta tace "tir da bak'in halin ka uwa bak'ar fuskar ka, ka ji tsoron Allah ka guji ranar da Allah zai kama ka, kuna manya kuna bin yaran jama'a kuna lalata da su na ku yaran na can gida a killace, toh wallahi ka jira ranar nadama ranar da zaka iske anyi ma wani naka ko diyar ka cikin shege dan duk abinda kayi ma dan wani sai anma naka".. 

 

Jikin shi yayi sanyi, tabbas maganar da ta fada ma shi gaskiya ne, Allah kadai yasan innocent girls da ya yaudara.. 

 

Hannun Farha taja idanun ta na cigaba da fitar da hawaye, bak'in ciki ya tokare mata wuya, ji take kamar k'asa ta bude ta shige ciki, yau kanwar ta ce da aikata irin abinda kullum suke magana akai matuk'ar suka hadu wajen taron MSS(Muslim Students Society). 

 

Ta kalli Farha tace "kin ji kunya Farha yanzu dama irin abinda kike aikatawa kenan daga gani ba wannan ne na farko ba, kin ZALUNCI iyayen mu dake kokarin tarbiyyantar da mu kullum burin su suga sun aurar da mu ga mazaje na gari you really disappointed 😞 me Farha".. 

 

Engr. Yakubu ne ya bude dashboard dake jikin motar shi ya fiddo da bundle din kudi 'yan N500, wajen su Sameera ya nufo ya mik'a ma Sameera yace "nagode kwarai da wannan tunatarwa da kika man hak'ik'a kin tunatar da ni wani abu dana manta nike ganin ba wani abu bane, Allah ya baki miji nagari, kanwar ki kuma ki cigaba da yi mata nasiha"... Ya mik'a ma Sameera kudin tak'i karba, kasa ya ajiye su ya juya ya tafi yana mai nadamar abubuwan da ya aikata a baya yau gashi diyar cikin shi na gaya ma shi magana.. 

 

Hannu tasa ta dauki kudin tare da ambaton sunan Allah ta saka a cikin side bag din ta.. Farhah kunya ta ishe ta, ta kasa had'a idanu da Sameera.. 

 

Haka suka isa gida duk babu walwala a tattare da su.. Abin duniya duk yabi ya ishi Sameera da ta tuno yanda taga Farha.. 

 

Mami ta lura da yanayin su tayi tambayar duniyar nan suka nuna mata ba komi.. Da dare har Farha ta kwanta Sameera ta tada ta tace "ki tashi magana nike son yi da ke".. 

 

Haka ta tashi, Sameera ta yi ma Farha nasiha mai ratsa jiki dangane da rike mutunci a matsayin ta na 'ya mace.. Farhah tayi alkawalin ba zata sake ba.. 

 

 

 

Safiya ta waye Farha ta dauki waya ta kira bestien ta tace "wallahi Aysha ba ki da kirki, Aysha yaushe rabon da kizo gidan mu ai yanzu ya kai shekara ke shikenan ba za ki zo gidan mu ba, kwana biyu ba ki ganni bama ko kirana ba za ki yi ba?"

 

Aysha tace "ki yi hakuri Farha wallahi kin san ba inda ake bari na naje daga school sai gida kuma kwanan nan karatu ya sha gabana dayawa shiyasa ki ka ga ban kira ki ba amma kiyi hakuri". 

Farhan tace "to na ji,wai ke har yanzu baki fitar da wasu kayan ba? Ni fa I need change".. 

Aysha tayi dariya tace "to shikenan sai kin shigo ki duba wanda ki ke so k'awa tah".. 

Ita ma ta yi dariya suka cigaba da firar su gwanin ban sha'awa. 

************************************

 

12pm dai dai Farha ta shiga school dinsu da yake yau bata da morning lecture sai 2pm za su shiga koda taje ta samu wasu kawayen ta,ta zauna cikin su sai firar samari ake,suna nan sai suka ga wucewar wata tsaleliyar mota ta gani ta fad'a ta shiga tsara,kai zan ma iya ce mu ku babu irin ta guda uku a garin,ko wacen su sai da ta saki baki tana kallon wanda zai fito daga motar,Ya Salam ko mu nan da mu ke kallon su sai da nace "Chuchuna rufe bakin". 

Wa ni had'adden gaye ne ya fito wanda na tabbata ya tafi da zuciyar duk wanda yake wurin hatta ChuchunGaye. 😜

 

Kan kace wani abu Farha ta mik'e tsaye ta na tafiya ta na shaking jikin ta, ta rausayawa kamar ganyen bashiya,ga ni kawai mu ka yi ta nufi wurin da yayi parking,tana zuwa tai wa ni far da ido ta kalle shi tayi smiling shima kuwa yai mata murmushi tace "mallam Assalamu Alaikum", yace " wa alaikis salam how may I help you?" Sai ta kara wani murmushin tace "mu na zaune can ne ni da k'awaye na mu ka ga wucewar ka and sincerely speaking ka burge ni so I don't know whether you will mind telling me your name? Sai yace "Woow that's nice thank you, my name is Haneef and you?" Tace "Farha" yace "woow nice name" tace "kaima haka" sai ta kuma cewa "amma ba a school din nan ka ke ba? yace " yes na shigo ne wurin wani friend dina".. 

 

Murmushi ta yi wanda ya bayyana fararen hak'oranta da wushiryarta.. Ta sa ke yin fari da idanun ta, da alama dai ta riga ta saba da hakan.. Tace "Cool wa ne faculty ya ke?" Ya ce "faculty of Education, ya na karantar Educational Psychology".. Ta ce" Wow nice".. Idan ba za ka damu ba in raka ka mana. 

 

Ya gyada kai tare da bude motar ta shiga.. K'awayenta su ka bita da kallo.. Farha kenan "Shu'umar mace".. 

 

Ni da Nafee nah mu ka bisu a baya, mu na ta mamakin rashin kamun kai na Farha. Ya na driving su na firar su kamar sun saba da juna.. 

Har suka isa, ya bar ta cikin motar ya fita tare da kara wayar shi a kunne alamar yana kiran wanda ya zo nema.. 

 

Bincike Farha ta fara ma shi da yake motar tinted glass gare ta, sai ware ido ta ke, Nafee nah ta ce "Chuchuna na san abinda Farha ke nema".. Ni ma nace" ai na sa ni".. Ji mu ka yi ta na magana ita ka dai, tsaki ta fara yi "mtseeww" tace "shi ko wannan banza ba komi ma cikin motar ta tashi da mutum zai laluba, sai shaggun takardu kamar Al_huda-huda"... Dashboard din motar ta bude designers din turaruka ne guda uku à ciki, sai ATM cards guda biyu da credit card da licenses din motar.. 

 

Tsaki ta kuma yi, tare da duba agogon da ke daure a tsintsiyar hannun ta samfurin CITIZEN.. Farha na ji da wrist watch din nan dan ita kadai ce agogon ta mai tsada da take bada fafa da ita, Aysha ta kawo ma ta da Abban su ya dawo daga Paris... Motar su ka doso su biyu dukkan su ba dama wajen iya gayu,Haneef ya bude side din driver yace "Farha meet my friend Sameer".. Hannu ta daga ma shi tace" Hey friend".. Shi ma ya daga ma ta suka gaisa, ta ji dadi yanda ta ji Haneef ya cewa Sameer "ita friend din shi ce".. 

 

Har bakin department din su ya kai ta, bayan sun yi exchanging contact, dan tana da lectures 2pm.. An kusa shiga. 

 

Ya ja motar shi ya tafi, ita kuma ta nufi lecture theatre, ba batun zuwa yin sallah.. 

Tana shiga ta hango friends din ta na dago mata hannu, tare da daga babban yatsan su alamar "thumb up".. Ita kuma sai murmushi take, suna kara fasa mata kai..

 

Farha ce tsaye jikin dressing mirror, sai shafe-shafen ta take yi, ta zamo tamkar wata aljana dan tsabar kyan da tayi.. 

 

Wasu fitinannun kaya ta saka crazy style na atamfa riga da skirt,ta hau fesa turarukan ta da suka tasar ma kala bakwai.. Gabadaya dakin ya gauraye da kamshin turaren.. 

 

Mami ce ta lek'o dakin tace "Haba shiyasa na ji kamshi har falo na ashe Farha ce,wannan turare be yi yawa ba?" Farha cikin muryar shagwaba ta ce "Mami kin san fa mace sai da kamshi".. Mami ta gyada kai tace" haka ne kuma fa".. 

 

Sameera da ke kwance kan gado, da yake weekend ne takaici ya kama ta.. Idanun ta rufe ta na jin maganganun su, Idanun fes akan Farha tayi saurin rintse idanun ta, ta na mai Allah wadai da irin halin Farha, sam ba ta jin nasiha.. 

 

Farha ta dan jujjuya tace "Mami ya ki ka gan ni?" Mami tayi murmushi tace "kinyi kyau autar Mami".. Tsalle ta dan yi, sannan tace" gidan su Aysha zan je".. Mami tace "toh a dawo lafiya auta ki kula dan Allah, ki gaishe man da mamar su Aysha" tace "toh Mami".. 

 

Sameera dai ido ta bi su da shi, addu'a kawai za ta cigaba da yi ma Farha.. Farha an sha kyau, haka ta fito unguwar su ta na taku d'aidaya kamar tana jin tausayin k'asa... 

 

Ta kai kamar 20mins tana tsaye bakin titi bata samu lift ba, keke napep ta tara ya kai ta GRA gidan su Aysha.. 

 

Da sallamar ta ta shiga gidan, tayi hanyar part din Aysha.. Zaune ta iske ta tana kallon wani Philippines movie MELESSA, Aysha ta mik'e tare da tarbo Farha suka zube cikin luntsuma-luntsuman cushions da ke zageye da falon, komi black and red ne.. 

 

Bayan sun gaisa Aysha tace "ooh besty ke dai kin saba ba ki jin komi idan kin sa kayan da suka matse ki?" Farha tace "uhmm ni ba ni son saka over size in koma kamar wata gwaggo ke ma dai naga ba sawa ki ke ba".. Aysha tace" amma dai kin san idan nasa kayan da naga sun matse ni ina saka hijab".. Tace "toh ra'ayin ki ne ai ni dai bani hijabi in je in gaido Ammi".. Aysha tace" munafukar banza ki je gun Ammin haka mana".. Dariya tayi ta ja hannun Aysha suka je ta gaido Ammi, suka dawo suka dasa sabuwar fira..

 

Nan Farha tayi lunch, sai da zata tafi tace "besty ina kayan ne?" Murmushi Aysha tayi tace "mu je ki za6i wadanda ki ke so".. Haka Farha ta daddage ta za6o kayan sawa set biyar cikin kayan Aysha da mayafan su hade da takalma sai turaruka biyu da ta dauka... Mu dai kallo mu ka bita da shi.... 

 

Aysha ta kai ta har gida, sannan ta juya gida dan tasan halin Farha tana iya tsayuwa bakin titi jiran lift... 

 

************************************

Haka rayuwa ta cigaba da tafiya su Farha an shiga 200level, halayen ta babu wanda ta canza sai ma k'aruwa da suka yi, dan idanun ta sun bude sosai, ta yanda koma minene zata iya yi in dai zai kawo ma ta kudi.. 

 

Sameera an tura ta service (NYSC) Kebbi state, sai ya zamo Farha karen ta take ci ba bu babbaka, abinda taga dama take yi, daddyn su ba zama yake ba, ita kuma Mami bata tsawatar ma Farha.. 

 

Inda Allah ya taimake su bata yawon dare, sai dai in ta fita fa yawo kamar ta ci kafar kare.. 

 

Tana school ta fito, tana scrolling contacts da ke cikin phone din ta tana neman drivern da zata kira ya kai ta gida.. Kiran Aysha ne ya shigo, ta ce "Hello besty", "toh ga ni nan na kusa fita bakin gate mu hadu can".. Tayi hang up. 

 

Ta na fita gate din school din Aysha na isowa ta bude ta shiga.. Aysha ta cigaba da driving, ta ce "shopping za mu".. Farhah tayi ihuuu, tace" ki ce Abban mu ya turo kudin".. Aysha tayi murmushi tace "besty ba ki da dama", 

 

GT bank suka nufa, Aysha ta kira Abban ta bayan ta gaida shi tace "Abba kudin shopping din account dina ba kudi" yace "ki shiga wajen Ibrahim ki karbi 20k" tace "Nagode Abba Allah shi karo girma da daukaka" yace "Amin" tace "Abba Farha na gaida ka" yace "toh ki amsar mata 5k ita ma".. Da yake hands-free ne, Farha tayi ma Aysha nuni ta bata wayar, nan ta bata wayar, ta gaida Abban tare da zubo ma shi godiya, tare da lauya harshen ta.. 

 

Suka shiga ciki Aysha ta amso masu kudin.. Kalamu Waheed suka nufa, suka yo siyayyar su... Farhah da zasu dawo tayi lamo cikin seat din motar, kunnuwan ta muryar shi kawai suke karanto ma ta kamar a sannan take gaida shi a waya.. Haka dai har suka isa gidan su Farha..

 

 

K'arar wayar ta ya tada ta daga bacci.. Cikin muryar ma su bacci tayi picking call din,daga can bangaren aka ce "Farha manyan gari", ta dan yi jim sannan tace "ban gane wa ke magana ba?" yace "Haneef ne", tace "Oh Haneef ya gari?" yace "Normal just missing you".. Ta danyi murmushi tace" Missed you too".. Yace "ba wa ni nan bayan kin guje ni".. Tace" karatu ne dai ya sako ni gaba",yace "okay anjima ina nan zuwa", fuska ta ya mutsa tace "ai ko bana gari nayi tafiya sai dai in na dawo", yace "alright I'll be waiting", tace "toh dan turo man airtime please", yace "toh".. Tayi hang up, tare da buga tsaki" mtseww", dan ita ta ma manta da wani Haneef tun da lura daddy's pet ne, ta tura shi a dustbin.. 

 

Shiyasa bata cika son kula 'yan yara ba, gara sugar daddy tafi tatsar su san ran ta.. Bata gama wannan tunanin ba, beep sound ta ji daga wayar ta, ta duba ta ga VTU ne aka yi mata na 5k.. 

Murmushi tayi tare da ambatar "wahalalle da kar ka turo".. Subscription tayi na 2GB da ma subscription din ta ya k'are... 

 

Ko godiya babu, sai shi ya kira yana tambayar ta, sun shigo.. 

 

Tashi tayi, daga ita sai leggings da wata vest ta fito tsakar gidan su dan taji cikin ta na kiran ciroma (yunwa).. Noodles ta fiddo guda biyu medium size, Mami ta fito tace "mi za ki dafa ne Farha?" tace "indomie zan dafa Mami", Mami tace "toh dafa da ni tunda Alhaji bayanan ba sai mun dafa wani abincin ba".. 

 

Ta k'aro guda daya, ta dafa ma su tare da soya kwai.. Ta had'a da ruwan shayi (tea).. Su ka ci su kayi k'at!.. 

 

**********************************

Aysha ce ke safkowa daga saman matattakalar jirgin sama (Aeroplane),ta dawo hutu daga Abuja, ta shak'i sassanyar weather din Katsina dake cike da ni'imar Ubangiji... 

 

Karaf! Kyawawan idanun ta su ka sauka akan wani handsome guy da yayi bala'in tafiya da ruhinta.. Ta rufe idanun ta sannan ta bude su dan a tunanin ta cikin mafarki ta ke.. Wayar ta tayi saurin lalubowa cikin handbag din ta, cikin azama ta yi dialing number din Farha, tana daukar call din ta ce "besty help me out! Wani handsome guy na gani yanzu cikin airport am deeply in love with him, ya had'u fa".. Farha tace" Go for him baby kar ki bari ya ku6uce ma ki", Aysha tace "I can't do that Farha", Farha tace "toh miye a ciki dan rai yaga abinda ya kwanta ma shi dadi na dake kenan k'auyan ci, village girl kawai", Aysha tace "na ji dai".. 

 

Kallo tayi ta bin guy din da shi, har driver din gidan su ya ja trolley bag din ta, ya saka a cikin boot.. Ta shiga ya ja motar, tana ganin guy din ya shiga wata mota ta duk'ar da kan ta.. 

 

 

Washegari wajen k'arfe 11am Farha ta shirya zuwa gidan su Aysha dan tayi ma ta sannu da zuwa ta kuma kar6o tsarabar ta. 

 

Yau shigar mutunci tayi tasha royal blue abaya da design din hot pink color a jiki, tayi rolling kan ta da pink scarf.. Ta nufi gidan su Aysha, part din Ammi ta fara shiga ta gaida ta sannan ta k'arasa gun bestyn ta.. 

 

Ta sauke ta da tray an zuba fruit salad a ciki da kunun aya, sai dambun nama.. Suna fira Farha na kai ma cikin ta.. 

 

Aysha tace "besty ina baki labarin wannan had'adden guy din, har mafarkin shi nayi na kamu da love at first sight".. Farha tayi dariya tace" ai sai da nace ki je ki same shi ke kin tsaya jan aji ga irin ta nan kyan nan dai Allah ya baki, ga kudi ga shiga ta alfarma bare a d'aga ma ki hanci salon mu na mata ya kamata kiyi ki tunkare shi".. 

 

Aysha tace "ke besty raba ni da maza nan gaba yayi man gori gara in danne zuciya ta tunda ba shi kadai bane namiji a doron kasa".. Farhah tace" tab ai ni wallahi in dai naga abinda ya kwanta man a rai banga uban da zai hanani cimma buri na ba, barin ma mutum na da ya'yan banki".. 

 

Kallo Aysha tabi Farha da shi dan Farha ta wuce da tunanin ta,Aysha tace "besty manya Allah ki bi a hankali kinga mazan nan wasun su mugaye ne ki bi duniya a sannu, sam ba halin ku daya da Yaya Sameera ba, ita ba ruwanta bata da rawar kai kamar ki".. Farha ta kyalkyale da dariya tace" Ita ma Yaya Sameera kidahumanci ke damun ta sam bata waye ba".. Aysha ta rike baki tace "ooh ni Farha so ki ke ki fi karfina".. Ta fad'a tare da dan kai mata dukan wasa.. 

 

Nan Farha ta wuni sai gab da Maghreb tabar gidan, shima tana kaiwa titi tayi ma wani sugar daddyn ta text ya zo ya kai ta shan ice cream.. 

 

Bata yi 10mins ba ya iso, ta shiga motar ya ja su.. Mutumin ak'alla ya tasar ma 60 years irin tsofafin nan ne ma su budurwar zuciya, su ci zamanin su su ci na ya'yan su.. Idan auran wuri yayi ya isa yayi jika da Farha.. 

 

Ya kalle ta tare da kanne mata ido yace "sweethert kinyi kyau sai wani fresh kike sake yi".. Ta dan murmusa tare da yin fari da idanun ta tace " baby nah har na fi ka kyau, ba ka ga yanda kike rikid'a bane kamar irin dan 40 years din nan".. Murmushi yayi da wani dausheshen bakin shi ya shafi gefen fuskar yace" sweetheart shiyasa ni ke k'ara son ki ba kamar idan na ji kin ce baby nah sai in ji ni kamar ba a duniyar nan ba, gashi har yanzu kin k'i ba ni dama in warware ma ki irin soyayyar da ni ke maki".. 

 

Jinjina tayi jikin shi cikin yaudararriyar muryar ta take ma shi rad'a a kunne.. Kadan ya hana steering wheel din motar be kwace ma su ba, yayi saurin taka birkin motar.. Yace "kin ga irin ta ko idan kina tare da ni rasa control din kai na nike".. Murmushi ta sake yi ya jawo ta jikin shi ya rungume ta tsam! Na 'yan wasu dak'ik'u sannan ya cigaba da driving suka je yayi mata shopping junks food da sauran tarkace ya kai ta har gida sannan ma anyi isha'i, basu yi Maghreb ba bare isha'i..

 

Rayuwa irin ta Farha kam ba'a magana sai dai addu'ar Allah Ya shirya mu ya shirya k'annen mu ya shirya mana zuri'ar mu da kulluhin musulmi baki daya.. 

 

Koda ta shigo gidan babanta ya dawo daga wurin aiki,dama sai an wuce dakinsu ake kaiwa palour da dakin iyayen nata,tana shigowa ta lallaba ta shige dakinsu ta zube kayan ta sannan taje ta gaida babanta ta dawo daki, koda ta shigo sameera kam ta shirya ta wuce islamiyan dare,Farha kam wuri ta nema ta zauna ta gama buda kayan ta kwasa ta zuba cikin wardrobe dinta sannan ta koma kan gado ta buda whatsApp dinta tana chatting sai ga call din Aysha ya shigo.. Tace 

"Hello Aysha how far?" Aysha tace 

"Fine Farha kin San Allah na kasa manta mutumin nan ke har pic dinshi fa na dauka".. 

Farha tace "to shine baki nuna mun ba ki ka sani ko na san shi".. 

Aysha tace "bari yanzu zan tura mi ki a whats app idan kika gancshi sai ki kira ni"

Tace "to shikenan",koda Farha ta buda har Aysha ta turo,tana ganin guy din sai da zuciyar ta buga kuwa akan haduwar shi,tayi sauri ta kira Aysha,Aysha na dagawa kafin tace k'ala Farha tayi cikin ta da surutu tace "Amma Aysha kin cuci kanki yanzu wannan had'add'en ne ki ka bari ya kubuce mana kaiiiiiiiiiiii! Amma wallahi Aysha ke banza ce kai ni kin ma bata min rai mehn he's so good damn cute".. 

 

Aysha kam dariya kawai take "tace to ni Farha me zanyi kin san dai there is no freaking way zan tunkari namiji ince ina son shi ko?"

 

Farha tace "aikuwa gashi kin ma kanki ni wallahi in nice sai naje don nasan ko d'an uban waye na ce ina so be isa yace baya so na ba,dan ba abinda na rasa a jiki na,ke wai baki san mazan yanzu suna son mata masu confidence ba baby shine your eyes".. 

 

Al'amarin Farha ya wuce hankalin ta, jin ta kawai take dan tasan ko giyar wake ta sha ba ta da gut din tunkarar namiji ta furta ma shi kalmar SO! She believes that in dai rabon ta ko a ina yake he'll definitely come to her.. 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

An sa bikin Sameera da wanda zata aura Jameel wata biyu kacal, ba wani arzik'i gare shi ba na azo a gani, amma saboda suna son junan su tsakanin da Allah, sam babu son kyalekyalen duniya a zuciyar Sameera. 

 

Burin ta ta auri mai son ta da k'aunar ta da zuciya daya, gashi kuwa ta samu dan duk wani abu da Jameel yasan zai faranta ma Sameera rai shi yake yi, sun fahimci junan su sosai.. 

 

Farha kuwa ji take da tana da yanda zata yi da sai ta shak'e Jameel dan haushin sa ta ji, ita kunya ma take ji ace shi zai auri yayar ta.. 

 

Daga kasuwa suka dawo sun yo siyayyar 'yan k'ananan tarkacen kayan kitchen, da k'ananan kitchen appliances.. Tsakiyar dakin suka baje su, Farha tayi tsaki tace "wai Yaya Sameera duk wannan d'okin da ki ke saboda wannan Jameel din ne?" Murmushi Sameera tayi tace "Eh mana Farha abinda rai ke so kenan".. 

 

Farha tace" amma wannan ran be ma ki adalci ba ya rasa wanda zai so sai wannan fuk'ara'un".. Sameera ta d'aure fuska tace "Look Farha ba ni son cin fuska fa, idan ba zaki tayani son abinda nike so ba, bai kamata ki na kushe shi a gaba na ba.. Na ji na gani na ce zan iya ina son Jameel a haka".. 

 

Farha tace" miye na tada jijiyoyin wuya Yaya Sameera? Naga dai ke za ki zauna da shi miye nawa a ciki daga fadar ra'ayi na, zaki yi mamakin mijin da zan aura na nunawa tsara wanda zamu rik'a keta hazo".. Murmushi Sameera tayi tace "yaro yaro ne, ki rok'i mafi alkhairi shi yafi akan wannan dogon burin da kika aza ma kan ki ina jiye ma ki gaba Farha".. Yamutsa fuska tayi, ta cigaba da dudduba kayan da suka siyo.. 

 

************************************

 

Bikin Sameera ya taso gadan-gadan su Farha k'irjin biki ta cima wannan bikin buri, dan sai da Aysha tayi ma su dinkuna na kece raini kala bakwai da ashoben biki da aka fitar na 'yan mata atamfa da material.. 

 

Farha ta tatsi samarin ta san ran ta, ta tara kudi more than 100k, duk wasu kayan interior decoration na gida Farha ta siya ma Sameera su,ganin kudin da Farha ke kashewa sunyi yawa yasa Sameera tambayar Farha inda take samun kudin, nan fa ta zazzage kwadon masifa da bala'i.. Mami kuwa bata ta6a bud'e baki ba ta tambayi Farha ba'asi ba.. Abin ku da jini nan da nan kuma suka dinke.. 

 

Ana sauran sati daya biki aka je jere Dutsinma, ba laifi anyi mata kaya daidai gwargwado, haka kitchen din ta Farha duk wani tattalin arzikin ta wajen siya ma Sameera kitchen appliances ya k'are.. Trolley box guda Aysha ta ciko da English wears sune gudunmuwar ta, Farha ji tayi kamar ta goya Aysha dan dadi.. 

 

Sun fara programs na biki, daga sisters evening, walima sai dinner da Farha ta azalzalama Jameel da Sameera sai anyi.. 

 

An daura auran Sameera da Jameel akan sadaki mafi daraja.. 

Karfe 4pm aka kai amarya gidan ta dake a garin Dutsinma... 

 

Da dare aka shirya zuwa dinner, su Farha k'irjin biki an sha uban gayu kamar ba gobe.. Aysha bata samu damar zuwa kai amarya ba, an dayyi shagalin biki da ita.. 

 

Bikin wan shagali! Anyi biki an k'are lafiya an bar amarya da angon ta.. 

 

*************************************

 

Yanzu ya rage Farha ita kadai a gidan su, taci karenta babu babbaka ita kadai a d'akin su, dama saboda Sameera take rage wasu abubuwan dan ta san halin Sameera sai tayi mata magana.. Duk iskancin ta 10pm tayi bacci, amma yanzu ba Sameera sai ta kai k'arfe 2pm tana chatting da k'artin banza, firar ma ta wuce ka'ida.. 

 

Weekend ne ya kama, ranar Sunday Misalin k'arfe 2pm na rana, Farha ta shirya zuwa gidan su Aysha taci kwalliyar ta kece raini kamar wata d'iyar wani k'usa a gwamnatin.. Tayi ma Mamin ta sai ta dawo ta ja tsigalallun k'afafun ta fita.. Ba ta zarce ko'ina ba sai gidan su Aysha.. 

 

Ta na shiga idanun karaf! Akan jerin motoci gudu uku ma su numfashi, guda d'aya ta tsakiyar tafi sauran k'eruwa, na gaba da na bayan duk mazaje ne guda shida duk cikin shigar suit bak'ak'e fuskar su d'od'e da tabarau. 

 

Motar da ke tsakiya k'irar CHEVROLET IMPALA blue black color sai kyalli take, sauran biyun SUBARU FORESTER ne bak'ak'e sid'ik!.. 

 

Numfashin ta ne ya dauke na wucin gadi, a zuciyar ta take ayyana tun da uwar ta haife ta bata ta6a ganin flashy cars irin su ba... Idanun ta suka sauka akan Abba da yasha farin material na maza, ya aza bak'ar mu had'u a banki, takalman kafar shi ma sandals na maza bak'ak'e, haka agogon hannun shi samfurin ROLEX shima baki.. Fuskar shi sanye da farin gilashi mai kara ma idanu k'arfin gani.. 

 

Kallo daya zaku tantance manyantar shi sai dai jin dadi da wadataccen ilimi yasa ya zama kamar wanda ke tsakanin 45-50... 

 

Gabadaya hankalin ta ya gushe da kyar ta dawo cikin hayyacin ta, ta k'arasa tare da dan russunawa tace "Abba ina wuni? ".. Cikin sakin fuska yace" Lafiya Lau Farha an zo wajen Aysha koh?" Tayi yak'e tace "Eh Abba".. Nuni yayi, har ta wuce yace" Zo".. Ta dawo baya, hannu yasa cikin briefcase din shi ya fiddo kudi ya bata, tayi godiya ta wuce.. 

 

Ta dade gidan ko da wasa bata nuna ma Aysha kudin ba, gabadaya zuciyar naga flashy cars da ta gani, Idanun ta sun rufe sun fara kitsa mata wani abu can.. 

 

Zata tafi Aysha tace "jira ni besty in watsa ruwa sai mu fita tare zan gaido mara lafiya asibiti".. Kamar jira take Aysha ta shiga wanka ta dau wayar Aysha ta shiga bincike cikin contacts din ta.. 

 

 

 

 

 

 

Magana take ita kadai tana cewa "ko wanne suna ma ta saka mata".. Tayi tsaki, Aysha dake tsaye bakin kofar bathroom tace" sunan wa ki ke magana?". Tace "wannan Sadiyar mai dinki da tayi mana dinkunan bikin Yaya Sameera".. Tace "ooh ki duba za ki ga Sadie couture".. 

Ta zuba phone numbers din Sadie, Aysha ta shirya suka fita tare... 

 

**********************************

 

Rayuwa mai dadi suke Farha da Aysha har ya kai kowa yasan su a tare Infact Aysha har bugun gaba take da bata da kawar da ta kai mata Farha "Pari" ma take kiran ta (Angel)

Wata rana Aysha na waya da Wanda zata aura Hanafi sunan shi yake ce mata Aysha akwai maganar da zanyi dake sai tace "Ina jinka Allah yasa alkhairi ce "yace Aysha kisan irin kawayen da kike zama dasu, ki sani fa ance show me your Friend and I will tell you who you are rayuwar duniya kada ki bari a miki shaidar abu 2 1sata 2 lesbian 3 biyar maza abokin ka determine who you are, aiko koda ya gama Aysha ta hasala kawai sai ta kashe wayar....... .

 

 

Allah sarki Masoyan book dinmu "muna masu rokon ku da ku mana afuwa daga ni har chuchun mun koma school bamu da chance shi sa kuka jinmu shiru amma mu kanmu ba son ranmu bane amma in sha Allah zamu kokarta

 

 

 

Shirun da yaji ne ya ankarar dashi cewa ta tsinka wayar sai ya kara kiranta bata daga ba, chan sai kuma ga text ta aika mishi kamar haka ""Hanafi ban gane me kake nufi ba kana nufin ni yar iska ce kenan? Toh idan ni yar iska ce me zakayi da yar iska me zakayi da auren yar iska kuma kake cewa Qawaye na yan iska ka fada min wace Qawa kasan ni da ita idan ba Farha ba? Ko kana nufin Maganar da mutane ke fada cewa Farha Lesbian ce kaima shi kake so ka fada min to wallahi I can tolerate everything amma banda zargin Qawata Infact ko aure mukayi zagi na zaka rika yi so it's better kowa ya kama gaban shi kawai.

Yana gama karantawa mamaki yai mishi yawa , ya za'ayi Aysha ta fifita Qawar ta akaina lallai ma waton ko aure mukayi haka zata fifita wannan banzar yarinyar akan mijinta yarinyar da duniya tayi ma mugun shaida hmmmm Aysha kenan bata san halin dan Adam ba bata san yanda duniyar nan ta lalace ba a yanda halin Farha yake idan Aysha batayi hankali ba ko ubanta zata iya zama da shi, amma duniya ce, sai kawai ya share ra tun ranar bai kara kiranta ba itama bata kira shi ba a haka suka rabu

Fri, 5 Feb, 2016, 16:50 - Amatullah Ayeesha ðŸ'-: HAKA ZA KI YI MIN? ðŸ'" ðŸ'" 

 

{27-29}

Al'amuran Farha sai gaba suke yi sam ta shagala ga duniya, bata tunawa da lahirar ta abinda tasa kan ta shi take yi ba abin da ya dame ta... 

 

Mami ta zuba mata ido bata tsawatar mata, dama Sameera ce mai kwa6a ma ta, to ta na gidan auran ta, hakan yaba ma Farha lasisin baje kolin iskanci ta yanda take so.. 

 

Fitowar ta kenan daga meal restaurant ta hango wata flashy car tayi parking bakin titi, Farha ta canza tafiya dama wasu tsinannun kaya ne a jikin ta, wanda tsakiyar bayan ta da k'irjinta a waje suke, mayafin ta ta nannade shi tsakanin wuyan ta jelar ta sakko zuwa k'ugunta.. Kamar dai ba tayi lullu6i ba.. Matsiyacin kamshin turare ne ke tashi a jikin ta kamar anyi mata barin turare. 

 

Tana isowa saitin motar ta kara lankwasa jikinta yanda zai ja hankalin mai kallon ta.. Bata ankara ba taji muryar mace tace "Hey 'yan mata" , ta daga idanun ta ta kalli matar magidanciya ce da ak'alla ta tasar ma shekaru 40, daga gani ba sai an fada ba cikin hutu take, hannayen ta da wuyanta shak'e suke da dubai gold, har da hujin hancin ta mak'ala chain din da ake mannawa a hanci.. 

 

Farha ta gaida ta, ta amsa fuska sake.. Matar ta kalli Farha tace "kinyi kyau 'yan mata".. Farha ta dan murmusa tace" Thanks".. Tace "Sunana Hajiya Karima", Farha dai murmushi tayi ba tace komi ba.. Ta sake cewa "ya sunan ki?" tace "Farha Suraj".. Haj. Karima tace" nice name".. 

 

Tace "yanzu ina ki ka nufa?" Farha tace "gida za ni" tace "shigo in rage maki hanya".. Ba gardama Farha ta kutsa cikin motar, kamshin air freshener ya doki hancin ta ta lumshe idanunta, cikin motar duk ga teddy bears nan anyi decoration da su a gaban motar da baya.. 

 

Sun fara tafiya ta tambayi Farha unguwar su ta fad'a mata, har kofar gidan su Farha ta ajiye ta, tace "sorry please phone number din ki za ki bani".. Farha ta karanto mata phone numbers din sannan ta kira ta, ita ma tayi saving number din.. Har ta tafi ta sake kiranta, ta fiddo kudi 'yan dari biyar-biyar ta mik'a ma Farha tace" ga shi kya sa recharge card" Murmushi Farha tayi ta amsa tare da godiya.. 

 

Part din Mami ta lek'a ta ga bacci take, ita ma dakin ta ta fada ta cire kayan jikin ta ta kwanta bacci.. 

 

Da dare tana bayan ta gama chatting din ta around 12am, zata kwanta taji wayar ta na ringing tana dauka taga sunan Haj. Karima, tayi picking tare da gaida ta, tayi shiru nan hajiyar tayi ta ma Farha surutu ita dai daga "um sai a. Ah".. Haka har suka yi sallama... 

 

************************ *************

A bangaren Aysha kuwa duk wanda zai kawo mata sukar Farha toh kuwa bata da mak'iyi kamar shi, duk son da take ma Hannafi haka ta rabu da shi duk a dalilin Farha.. 

 

K'awayenta da dama ta rabu da su ma su kawo mata sukar Farha.. 

 

Aysha ce cikin sabuwar motar ta bak'a wuluk k'irar MAZDA 3, ta fito gate din school din su kenan, ta hango friend d'inta Hafsat, ta tsaya tare da yi mata horn, Hafsat ta k'araso cikin motar sannan Aysha ta ja su,wayar Aysha ce ke ringing ta dan rage gudu tayi picking tace "Pari yanzu ni ke niyyar kiran ki idan na isa gida ki kashe driving nike we'll talk later".. Tayi hang up, Hafsat dake gefe tace" hala Farha ce?".. Aysha tace "Eh ita ce".. 

 

Murmushi Hafsat tayi tace" wai ke Aysha ba ki gudun zargin mutane ne akan ku, ya kamata ki bude idanun ki ki farka daga nauyayyen barcin da kike kisan wacece Farha babu wanda be san Farha, da kin ce Farha Duniya an san da ita kike,sam dabi'un ki da halayyar ki basu yi kamamceceniya dana Farha ba in dai ba so kike ki shafa ma kan ki kashin kaji ba".. 

 

Tsawa Aysha ta daka ma Hafsat tace "stopppppp itttttt ke mahaukaciyar ina ce?" Murmushi Hafsa tayi tace "Am just telling you the truth, so duk abinda kika ga damar ce man ki ce na fita hakkin ki ina guje maki abinda zai je ya dawo ne".. Aysha tace" na ji so what! Babu uban da ya isa ya raba ni da Farha dan ni banga aibun ta daga anga muna tare shikenan mutane suyi ta kawo sukar ta I know what Farha can do and what she can't do nafi ku sanin halin ta dan haka bani buk'atar karin bayani".. 

 

Hafsat tace "ai shikenan dai a juri zuwa rafi wata ran tulu zai fashe".. Basu k'ara ma junan su magana ba, har Hafsat ta sauka.. Haka abin yake a wajen Aysha duk wanda zai fadi wani aibu na Farha ta daina ganin mutuncin ko waye, tana k'aunar Farha sosai ta dauke ta tamkar 'yar uwar ta da suke uwa daya uba daya.. Abinda ma take ma Farha ko ' yan uwanta bata ma haka, ta dauki amanarta ta damk'a ma Farha, duk wani sirrin gidan su Aysha na wajen Farha dan ba abinda take 6oye ma Farha.. Amintar su tafi gaban kwatance. 

 

Ecobank ta biya tayi ma kan ta da Farha VTU na 5k, dama duk abinda tayi ma kanta sai tayi ma Farha.. 

 

Haka suke tafiyar da rayuwar su,Aysha bata da magana da ta wuce ta Farha.. Idan har kana son shiryawa da Aysha to kada ka fad'i wani aibun Farha face alkhairi, to za ku dasa da ita.. 

 

***********************************

Aysha ce ke ta kai kawo acikin wani hall da yasha decoration, abin ba'a cewa komi, ba kowa cikin hall din daga ita sai ma su decoration din, daga can gefe muka hango stage da aka ajiye chair & table da cake a sama sai candles.. Sai da ta tabbatar komi yayi yanda take so,sannan ta nufi gida.. Ba kowa gidan duk suna gidan biki sai ma su aiki dake ta kai komo.. Wanka ta shiga ta fito bata tsaya wani makeup, mayukan ta kawai ya shafa da perfumes. Ta saka Abaya ta yana gyalen Abaya.. 

 

Gidan su Farha ta nufa, bacci ma Farha keyi ta d'aka mata duka tace "Pari tashi-tashi bacci ma ki keyi, toh ki tashi ki shirya muje La'asar ta gabato".. Mik'a Farha tayi ta tashi, wanka ta je tayi sannan ta shirya cikin kayan da Aysha ta zo mata da shi, doguwar riga ce armless pusha pink da design na stones a jiki pink da royal blue.. Sai top mai long sleeve royal blue, ta yane kanta da pusha pink scarf.. Ita ma Aysha irin kayan tasa nata pale purple and ash. Sunyi matuk'ar yin kyau, suka fito suka nufi gidan Sanam Makeover ta gwangwaje su da makeup.. Sunyi kyau sosai.. 

 

Hall din da zasu yi Birthday party din suka nufa friends din Farha duk sun iso kun san dai Farha da kwashe-kwashe, ba friends din Aysha ko daya.. Farha tabi hall din kallo yanda ya tsaru,sai da ta hau stage inda zata zauna taga cake din ta,bata san da wane baki zata gode ma Aysha ba.. Sun fara programs din su, dj ya sakar masu cool and soft music... Kallo daya zaka ma friends din Farha kayi masu kudin goro duk 'yan uwan ta ne, an cigaba da shagali har Farha tayi cutting cake din ta.. Wajen 6pm Aysha ta fita dan ka'ida komi ake bata wuce 6pm a waje, Farha ta san da wannan dokar ta gidan su Aysha, tayi mata sallama ta ja motar ta tayi gida.. 

 

Hakan yaba sauran friends din Farha damar cigaba da watsewar su dan dama suna shakkar Aysha. 

Duk iskanci Farha tana boye ma Aysha.. Ba zato ba tsammani Farha ta hango shigowar Haj. Karima, ta jefe ta da murmushi ta zo har kan stage ta mik'a ma Farha wani abu cikin wrapping sheet.. 

 

Sai wajen 9pm suka tashi.. Haj. Karima ta kai Farha har gida.. 

Farha ba maganar sallah haka ta baje gifts din da aka bata na birthday, wrapping sheet din Haj. Karima ta bude ta ware idanun ta sosai, bundles na 1k ta gani wanda jimillar su ya kama 100k.. 

 

Mamaki karara a fuskar ta, haka ta tattura masu SMS na godiya daya bayan daya..

 

 

Akwati na ne set, pusher pink ma su masifar kyau da tsada ajiye bakin motar Aysha ana saka mata su a boot, ta zaro 1k ta mik'a ma drivern gidan tace "Nagode Mal. Mudi", yayi murmushi yace "ni ne da godiya uwar dakina".. 

 

Motar ta ta shiga tare da bata wuta,mai gadi ya bude mata gate ta fita... Bata zarce ko'ina ba sai gidan su Farha. Haka ta samu yaro ya shigo mata da Akwati nan.. 

 

Farha na daki ta ji sallamar yaro ya shigo ya kinkimo akwati ta fito tana kallon shi da alamar tambaya, muryar Aysha ta tsinkayi kunnuwanta.. Murmushi ta saki tare da rungume Aysha tana "oyoyo my angel".. Aysha tayi murmushi tace" Mami na ciki ne?",Farha tace "Eh muje tana nan".. 

 

Aysha ta juyo ta sallami yaron, sannan suka shiga falon Mami ta gaida ta tare da tambayar mutan gida. Nan suka dawo dakin Farha, ta cika gaban Aysha da kayan ciye-ciye.. Suka cigaba da firar birthday din Farha.. 

 

Can dai Farha ta gaza hak'uri tace "besty wadancan boxes din fa?".. Aysha tace" ooh pari ba dai gajen hak'uri ba, it's a surprise for my angel".. Farha ta ware idanun ta tare da zare su ta dafe kirji tace "ban san wasa besty".. Aysha tace" da gaske nike birthday gift din ki ne".. Farha ta buga tsalle tare da rungume Aysha tana ta murna.. Boxes din ta jawo ta bude su sun matuk'ar tafiya da ita, (komu dai sun tafi damu dan can na hango My Nafee kamar ta dauke su).. 

 

Nan Aysha ta wuni sai bayan La'asar ta koma gida. 

 

Kwanaki na ta tafiya Farha idanun ta sun bude sosai yanzu suna 300 level, duk wanda ya kwana ya tashi cikin UMYU babu wanda be san Farha ba.. Cikin salo na gogaggun 'yan bariki Haj. Karima ta jawo Farha a jiki kudi take kashe ma ta kamar ba ta san ciwon su ba... 

 

Mami kuwa kamar Farha ta rufe ma ta baki sam bata ta6a yi ma Farha fad'a ba, Mahaifin ta ba mazauni bane koda yana zaman Farha yar gaban goshi ce.. 

 

Sameera ta haihu ta samu baby girl an sa sunan sirikar ta Zainab suna kiran ta da Aydah.. Rayuwar auran ta cikin kwanciyar hankali bata rasa komi ba wajen mijin ta, har jari ya bata ta fara business tana zuwa Kano tana saro atampopi, laces da materials tana saidawa a gida... 

 

*************************************

Duk wanda yasan Farha toh yanzu ya san ta da Haj. Karima sanin halin Haj. Karima da jama'a da dama suka yi yasa suka yi ma Farha kudin goro, dan matuk'ar Farha bata da lectures to suna tare da Haj. Karima har gida take zuwa daukar ta su je yawo. 

 

Hakan ya shafi martabar Aysha, samari da dama wadanda suka amsa sunan su sun sha kawo k'ok'on barar su wajen Aysha amma daga zarar sun ji labarin kusancin Aysha da Farha sai su janye jikin su sai dai ta neme su ta rasa.. 

 

Kwance take kan makeken royal bed da ke dakin ta taji wayar ta na ruri ta dauka ganin sunan da ke jiki "Muhsin".. Ta dauka tare da gyara kwanciyar ta, suka gaisa.. Yace" dearie jiya kin jini shiru ban zo ba " tace" Eh har na yi fushi ma", yace "Am so sorry anjima bayan La'asar ki duba hanya ina nan tafe", tace "ok toh yau zaka ga Pari", yayi murmushi yace "na lura dai kina ji da wannan kawar ta ki magana daya biyu Pari".. Tace" she's more than a best friend how I wish mu auri miji daya ma", yace "tun ban ganta na fara kishi da ita yanda kike k'aunar Farha ni baki ma nuna man haka", murmushi tayi tace "miye na kishi da Farha da kowa yasan matsayin ta a waje na".. Da haka dai suka gama firar su.

 

Farha ta kira tace" tazo gida ta taya ta tarar bakonta".. Kafin La'asar Farha ta zo suka shirya komi a falon bak'i na gidan.. Farha tace "besty naga dai wannan Muhsin din da ake ta rawar kafa kan shi", Aysha ta dan kai mata dukan wasa tace "He's handsome!".. 

 

Muhsin ne a harabar gidan su Aysha yayi parking motar shi ya fito sannan ya kira Aysha, guy din ya hadu iya had'uwa.. Farha ta tura ta shigo da shi, Farha ta fito ta iso bakin motar da murmushi dauke a fuskar ta.. Tace" mijinmu u'r welcome", kallo ya bita da shi yana tuna inda yasan face din ta, tafi tayi saitin fuskar shi tace "wuce muje mana", murmushin k'arfin hali yayi ya bita a baya.. 

 

Suna isa falon Aysha ta shigo suka sakar ma junan su murmushi.. Nan ya zauna suna fira harda Farha, har tafi Aysha zak'alk'alewa... Hankalin Muhsin na can wajen tunanin inda yasan Farha can ya tuno, ya runtse idanun shi tare da furzar da iska mai zafi..

 

Tunanin shi daya kar dai ace halin su daya, tunda abokin barawo barawo ne, bad company corrupt good manners.. Sama-sama akayi firar nan da shi ya tafi.. 

 

Tun ya bar gidan su Aysha bincike ya sake yi akan alaqar Farha da Aysha.. Tun daga wannan ranar ya daina kiran Aysha ko ta kira be dauka.. Hankalin ta ya tashi dan Muhsin ya kwanta mata a rai.. 

 

Rannan dai ta kira shi akayi sa'a ya dauka, tace "wai Muhsin lafiya ban gane ba kabar ni cikin dahu",wani malalacin murmushi ya saki tare da cewa" Aysha Allah na gani a da na so ki har a yanzu ma dan idan nace ban san ki nayi karya amma saboda tarayyar ki da Farha tasa na tilasta ma kaina rabuwa da ke", tace "Mi Farha tayi da za ka ce saboda ita zaka rabu da ni?" yace "saboda duk wanda yasan Farha yasan halayyar ta, kinga duk wanda yake tare da ita za'a iya cewa halayyar su daya kinga bazan so ace wadda nike so keda irin wannan halayyar ba", cikin tsawa ta dakatar da shi tace "cin mutunci ya isa haka Muhsin, miye na kwana-kwana ka fito fili kace baka sona ba wai sai ka kawo Farha ciki ba kana cikin wadanda ke ma Farha kazafi akan halin da bata da shi".. 

 

Yace" zan zo ki farka daga nauyayyen baccin da kike ki gane wacece Farha".. Haushi yasa ta kashe wayar tare da jifa da ita ta fada gado hawaye na zuba daga idanun ta, zuciyar ta tayi mata nauyi.. Ta kasa gane dalilin da mutane kema Farha wannan kallo sun kasa gane gayu ne kawai yayi ma Farha yawa... Farha ba YAR ISKA bace..

 

Wayar Farha ce ke ringing, fitowar ta wanka kenan d'aure da towel a jiki, sai face towel ta na goge fuskarta da shi sai da ta goge ruwan jikinta, ta jawo stool gaban dressing mirror ta zauna ta na shafe-shafen ta. Sai da ta gama duk abinda za tayi sannan ta duba wayar ta, tsaki tayi ta ce "mtseeww ni fa ban son takura".

 

A karo na biyu wayar ta sake ringing, ta dauka tare da furta" hello aunty", daga can bangaren aka ce "kin gama jan ajin na ki baby kin ga damar dauka?",ta ce" No ba haka bane ina wanka time din". Ta ce "okay kin shirya ko in zo mu fita yawo?", ta kad'a kai kamar ta na ganin ta, ta ce "Eh".

 

Ba'a fi minti goma sha biyar ba ta iso, Farha ta lek'a d'akin Mami ta ce" Mami zan je gidan su Aysha", Mami ta ce "toh ki gaishe su kar dai ki d'ad'e Farha", ta ce "ba zan d'ad'e ba". Bakin k'ofar gidan ta yi parking, Farha ta shiga motar ta zauna. Haj. Karima ce, ta dan shafi gefen fuskar Farha ta ce "baby na kin yi kyau", murmushi Farha ta yi ta ce "Thanks dear". Su na cikin tafiya Aysha ta kira Farha ta yi picking call din, sun dade su na fira har su ka isa gidan Haj. Karima. 

 

Sannan su ka yi ma juna sallama. Su na shiga falon Haj. Karima da ya ji kayan alatu komi na falon pale purple da ash ne. Haj. Karima ta dubi Farha ta ce "wai baby da wa ki ke waya d'ari?", Farha ta ce "Aysha ce", ta ce "duk cikin friends d'in ki na fi tsanar wannan yarinyar", Farha ta ce "Aysha she's a nice girl, ba ta da matsala sam she's my best friend". 

 

Haj. Karima ta ce "saboda hakan na tsane ta ni fa duk wata mace da za ta ra6e ki ban k'aunar ta". Farhah ta ware idanun ta ta ce "why aunty?", Haj. Karima ta gyara zama kafad'arta na gogar ta Farha ta rik'o hannayen Farha ta na murzawa ta ce "saboda ina son ki I love you Farha ki daure ki ba ni farincikin da na d'ad'e ina kwadayi fiye da shekara ina rainon ki Farha kar ki ce man NO". 

 

Mamaki ne k'arara a fuskar Farha, ta zabura ta mik'e ta ce "wace irin magana ce wannan aunty?", ba ta ankara ba ta ji ta rungume ta kamar wata mijin ta. Farha ta yi ta yi ta kwaci kanta ina, ta shiga hannun manya wasu sabbin al'amura Haj. Karima ke ma ta tun Farha na daurewa har ta bada kai ita ma abin ku da jarababba. 

 

Sai bayan la'asar su ka dawo hayyacin su (kaicona Farha ta fad'a halaka). Tun daga wannan lokacin Farha da Haj. Karima su ka dinke kamar tube da tyre. Kudi Haj. Karima ke kashe ma Farha kamar bata san zafin su, kun dai san Farha da son kudi in dai kan kudi ne za ta iya yin komi. 

 

 

**************************

Fuskar ta daure da yanayin damuwa a tattare da ita, ta kalli Asma'u ta ce "Asma'u ban yi tunanin harda ke cikin ma su yi ma Farha sharri ba, abin ma har ya dawo kai na, wannan wace irin mummunar kalma ce LESBIAN", Asma'u ta ce "ai sai ki yi Aysha ban san uwar da Farha ke tsinana ma ki ba amma sam kin kasa gano illar da ke tattare da kawance da irin su Farha da duk wani ko wata 'yan bariki sun san da zaman Farha ke ma kuma kallon da ake ma ki kenan dan ma fa Abban ku da ake ganin mutuncin sa".

 

Aysha ta ce "ni fa komi za ki ce akan Farha ba yarda zanyi ba dan ba ke kadai ke fad'in haka ba, ban san mi Farha ta tsare ma ku ba?", Asma'u ta ce "shikenan Aysha ki cigaba da kawance da Farha za ki sha mamaki duk ranar da ta yi ma ki abinda ko a mafarki ba ki zato".

 

Bayan tafiyar Asma'u ta na kwance d'akin ta abin duniya ya dame ta, kowa ya tashi magana ba mai fadin alkhairi akan Farha kullum cikin kawo ma ta sukar Farha ake, bayan ta san ba haka halin Farha ya ke ba.

 

Kiran Ammin ta ne ya tada ta ta fito ta same ta a main palour din su, ta zauna k'asa kusa da kafafuwan Ammin ta ce "Ammi ga ni", Ammi ta ce "Aysha ki bude kunne da kyau ki ji ni", Aysha ta gyada kai. Ammi ta ce "yanzu kin kyauta ma...". 

 

Muna rokon afuwa ga ma su bin labarin nan bisa ga dan tsaikon da aka samu hakan ya faru ne saboda wasu al'amura da suka sha kan mu.

 

Ammi ta ce "yanzu kin kyauta kenan Aysha ace duk cikin ma su neman auran ki har yanzu kin kasa tsaida guda daya rak!", Aysha ta ce "Ammi In Shaa Allah zan fitar har yanzu babu wanda ya kwanta mun a rai ne". Ammi ta ce kin dai tsaya ruwan ido Aysha". 

 

Daga bakin kofa su ka ji muryar yaya Ibrahim ya ce "ta dai tsaya biye ma Farha Ammi", ya k'araso cikin falon ya zauna tare da wurga ma Aysha harara ta yi saurin sadda kan ta k'asa. Ya ce "Aysha kin kuwa san yanda jama'a ke fad'in munanan dabi'un Farha?", Aysha ta yi karaf ta ce "Allah yaya IB sharri ne ake ma Farha duk wanda zai fad'i wasu munanan halayen ta, ta na da good manners kawai dai...", sauran maganar ta mak'ale ma ta sakamakon wani wawan mari da yaya IB ya sakar ma ta. 

 

Ammi ta ce "ya haka Ibrahim?", ya ce "har ni zan fad'i magana akan wata banza can Aysha ta k'aryata ni", Ammi ta ce "hak'uri ake irin wannan Ibrahim har yanzu da yarinta a tattare da Aysha". Ya ce "Ammi gida ki ke zaune wallahi yawancin mutane idan za su bude baki ba dai su fad'i alkhairi akan Farha ba, infact ta sanadiyyar ta duk ma su neman Aysha ke guduwa saboda sun san Farha da Aysha aminai ne". 

 

Ammi ta ce "ai daga ganin yanayin yarinyar za'a yi ma ta kudin goro dan sam ba ni son tarayyar ta da Aysha dan dai na ga Aysha ta yarda da yarinyar kwarai". Ya ce "ina office aka zo aka same ni akan a tsawatar ma Aysha ta rabu da Farha dan kowa zai dauka halin su d'aya, ba ki ji maganganun da aka fad'i man ba akan yarinyar nan".

 

Aysha da ke ta shashsheka ta na kukan marin da yaya IB ya ma ta, still bakinta be mutu ba ta ce "yaya IB wallahi duk wanda zai fad'i ma haka sharri ya yi ma Farha kawai matsalar ta saka matsatstsun kaya da hawa lift amma sam bata da wasu halayen da mutane ke ganin ta da su kawai dai tsabar gayu ne". 

 

Ammi da yaya IB sakin baki su ka yi ganin irin yanda Aysha ta kasa yarda da maganar d'an uwanta, ta ke ta fama kakkare Farha. Yaya IB ya taso a zuciye zai kai ma Aysha mazga, Ammi ta dakatar da shi ta ce "ka kyale ta Ibrahim tunda ta kasa gane gaskiya addu'a zamu cigaba da yi Allah ya kare Aysha, ita kuma yarinyar can Allah ya shirye ta". Ya ce "Amin Ammi". 

 

*********************

Kwanaki sun ja har sun zama shekara a lokacin Farha da Aysha na shekarar su ta karshe a jami'a. Al'amarin Farha kuwa sai addu'a da cigaba ta samu a mugayen dabi'un ta. Dan har motar kan ta gare ta wadda ta ke hawa 'yar k'aramar TOYOTA PRIUS ash bak'a wulik,wani saurayin ta da ke sana'ar saida motoci ya siya ma ta. 

 

Fitowar ta kenan daga gidan su wanda shi ma an gyara shi tsaf yaji kayan alatu. Za ta shiga mota ta ji an fizgo ta, tare da kwasa ma ta mari ta daga kai ta ga wa ke ma ta wannan aika-aikar. Idanun ta suka sauka akan fuskar Haj. Karima da ta d'aure fuska kamar sa, Farha ita ma ta d'aga shantalelen hannun ta ta zabga ma Haj. Karima mari kwarara biyu wanda har sawun tafin hannun Farha ya fito baro-baro. 

 

Haj. Karima ta ce "ni ki ka mara Farha?" Farha ta ce "an mare ki din", Haj. Karima ta ce "ba laifin ki ba ne laifi na ne da na dauki dukkan soyayya ta na baki har za ki ci amana ta Farha dan kin samu wadda ta fini". Farhah ta girgirza jiki ta ce "kwarai kuwa anci moriyar ganga dole a yada koren ta" ta ce "kin kyauta kuma kin yi da 'yar halas dan haka duk abinda ki ka san mallaki na ne a wajen ki ki maido ma ni". Dariya Farha ta hau kyakyatawa kamar ta6a66a ta ce "to matsiyaciya ki jira yanzu nan ki ga aiki da cikawa kin dai san yanzu ni FARHA na fi k'arfin arzik'n ki". 

 

Cikin gidan su ta shiga, cikin d'ak'ik'u ta fito dauke da shopping bag k'arama ta mik'a ma Haj. Karima ta ce "ga gayyar ki nan", Haj. Karima ta bude "dubai gold ne cikin akwatin su set biyu, d'aya sark'a, 'yan kunne, awarwaro, zabba guda hudu, sai sark'ar k'afa da zoben k'afa guda biyu. Gudan set din sark'a da' yan kunne ne, sai cheque na dubu dari biyar(N500,000)". Murmushi Haj. Karima ta yi ta fita da yake a waje tayi parking. Ita ma Farha ta ja motar ta ta bar gidan. 

 

***********************

Damuwa ce fal a ran shi, ran shi a 6ace sa'adda idanun shi suka sauka akan hoton da ta turo ma shi, k'unshi ne aka yi na black henna (bak'in lalle) a cinyar. Furucin ta yake tunowa san da ta kira shi ta ce "...........

 

Ran shi ne ya k'ara 6aci a lokacin da ya tuno da yanda Farha ta fara takunta. 

 

******4 MONTHS AGO******

Zaune ya ke a office, an kawo ma shi files d'in wadanda zai gani a ranar. K'arar wayar shi ce ta dakatar da shi daga aikin da ya ke. 

 

Ya dauki wayar tare da furta "Assalamu Alykum". 

Daga d'ayan bangaren aka ce "Wa alykumus Salam ina wuni Abba".Jin muryar mace ya amsa da "Alhamdulillah, Rukayya ce?". 

Ta ce "a'ah abba Farha ce k'awar Aysha". 

Ya ce "ok Farha ya mutanen gidan na ku?". 

Ta ce "duk lafiya lau su ke abba".

Ya ce" to madallah ki gaishe su". 

Ta ce "za su ji In Shaa Allah". 

 

Ya yi hang up ya na tunanin dalilin wannan kira na ta. 

 

Bayan kwana biyu ya fito daga meeting shi da wa su client's d'in shi. Beep sound ya ji, sai da ya isa gidan shi dake nan cikin garin Abuja a life camp, bayan ya shirya cook d'in shi ya kawo ma shi lunch sai da ya gama cin abinci shi sannan ya jawo wayar shi, ya danna icon na messages. 

 

Message dinta ya ci karo da shi ta ce "Abba please kud'i ni ke so ko nawa ne ta wannan account number d'in". Ya d'ad'e yana mamakin Farha sai kuma yaga ai k'awar d'iyarshi ce, amintar da ke tsakanin Farha da Aysha ya jawo ta dauke shi tamkar ubanta. 

 

Nan take yayi ma ta transfer kudi ta mobile money. 

 

Daga bangaren Farha kuwa time d'in da kud'in su ka shigo ta bude taga 50k, wani mayaudarin murmushi ta saki tare da furta "tarkona ya kama 'bera". 

 

Tun daga wannan rana duk wata hanya da Farha ta san za ta cusa kan ta ta na yi. Babu wanda ya san k'udirinta. 

 

Uban su gayu Farha ta ci cikin wata arniyar gown ta material kalar pink da pale blue a jiki. Rigar tayi masifar yi ma ta kyau, kafarta sanye cikin high heels ga chain din k'afa ta mak'ala ga na hanci. Ta yafa d'an yololon veil da shi da babu duk d'aya, clutch dinta na mak'ale a hannunta. Fuskarta ta sha uban fenti wanda ya boye gunduma-gunduman k'urajen da suka 6ata ma ta fuska ga ta fara. 

 

'Dakin Mami ta lek'a ta ga bacci take, ta kama hanya keys d'inta a hannunta tana kad'a su. Motarta ta bude ta shiga ta kama gabanta, ba ta zarce ko'ina ba sai gidansu Aysha. 

 

Ta na isa tayi horn mai gadi yaga ita ce ya bude ma ta, tare da yi ma ta barka da zuwa. Ta d'aga ma shi hannu ta isa parking shade. Ta fito ta na tafiyarta ta isassun mata ta na karya jiki. Wani cool k'amshi ta shak'a ta lumshe idanunta tare da sauke su akan mutumin da take muradin ga ni. 

 

Ta ware idanunta tana kallon shi kamar ranar ta saba ganin shi, yana sanye da chocolate color material na maza dinkin tazarce. Saboda gayun shi da kuma boko da ta ratsa shi babu mai cewa shi ya ajiye manyan ya'ya kamar su yaya Ibrahim yafi kama da matasa masu shekara arbain (40years).

 

Ta kai ak'alla mintuna biyar (5 mins) ta na kallon shi, sannan ta samu dawowa hayyacin ta. Ta k'ara canza tafiya har ta iso gaban shi cikin k'issa da kisisina ta mak'e murya kai ka rantse da Allah ba Hausa ta ke furtawa ta ce "barka da dawowa abba, dafatan an dawo lafiya?" ta na magana ta na kashe ma shi idanu kallon mamaki ya bi ta da shi. Kamar kada ya amsa ma ta yayi k'arfin halin amsawa fuska a d'aure. 

 

Sam ba ta damu da yanayin da ya amsa ma ta ba, ta kad'a jiki ta wuce wajen Aysha. Kamar ba ita ba. 

 

Mamaki Abban Aysha yake yanda Farha ke wadannan dabi'un, ya zama dole ya taka ma ta burki ya raba ta da d'iyar shi.

 

Zaune ta ke ta na tunanin hanyar da ya kamata ta bi dan ganin ta isar da manufarta gare shi. 

 

Kalamai ne ta shirya na nuna k'auna da soyyaya sai tayi kamar ta tura sai wata zuciyar ta kwa6e akan aibun hakan. Can dai tayi k'arfin hali irin na ta ta turo sai da ta ga "message delivered" ta tabbatar da cewa sak'onta ya isa in da ta ke son ya isa. 

 

Ta kwanta a ringigine ta na magana ita kadai ta ce "besty ki yafe ni, ban so hakan ta kasance ba, ba yin kaina ba ne am in love with your dad ina son komi na shi, amintakarmu ba za ta iya zama shamaki a tsakanin mu ba, I must fulfilled my dreams at any cost".

 

Ganin sak'onta ya bala'in girgirza shi, yana Allah wadai da irin halin Farha. Ak'alla ta duba alak'arta da d'iyarshi Aysha mana. Lallai ta cika butulu ta rasa wanda za ta ce ta na so sai UBAN AMINIYARTA. Wane irin cin amana ne wannan? Lallai zai taka ma ta burki. 

 

Wayar shi ya d'aga ya ce "Ibrahim ko mi ka ke ka zo gida ka same ni yanzu". Ba'a dauki mintuna talatin ba sai ga yaya IB ya iso gidan, part din Abban su dake farko ya shiga da sallama Abban ya amsa.

 

Ya samu waje ya zauna k'asa kusa da k'afafun Abban, ya ce "Abba ga ni ka kira ni urgently", Abba ya ce "Eh ka duba duk messages d'in da ke cikin wannan wayar kasan da babban d'a ake shawara", Abban da murmushi a fuskarshi. 

 

Wayar yaya IB ya karba ya yi kamar yanda Abba ya ce, yabi messages d'in one after the other. Yanayin fuskarshi za'a kalla a tantance fargicin da ke fuskar shi, zufa ta karyo ma shi duk da A.C da ta sanyaya falon hakan be hana yaya IB zufa ba. Ya d'ago idanunshi da su ka rine jajir! 

 

Ya ce "Abba wace shaid'aniya ce wa...", be ida rufe bakinshi ba wayar ta hau ringing ya mik'a ma Abba, yayi picking tare da maida ta hands-free tare da danna record. 

 

Muryarta ta doki kunnuwansu cikin muryar shagwaba ta ce "Abba na yi ma text you didn't reply back, please help am deeply in love with you a shirye ni ke in 6ata da koma waye in dai akan ka ne, zan iya yin watsi da alak'a ta da Aysha" ka taimaka ka ka ce da ni wani abu". Hang up yayi ba tare da ya bari ta gama maganar da take yi ba.

 

Yaya IB ya ce "Abba ko baka fad'a ba wannan yarinyar Farha ce", Abba ya gyada kai ya ce "ita ce Ibrahim ban san ya zanyi da ita idan ba rashin tarbiyya ba ta yaya yarinyar nan za ta tunkare ni da wannan maganar". Yaya IB ya ce "ka bar komi a hannuna Abba zan yi maganin ta. Dole a raba ta da Aysha dan kwanaki ma har magana na yi ma Aysha". 

 

Abba ya ce "toh shikenan ka bi komi a hankali dai", ya ce "In Shaa Allah Abba". Ya tashi ya fita zuwa cikin gidan ya na kwala ma Aysha kira.

 

 

Da gudu Aysha ta fito d'akinta ta d'are jikin yaya IB fuskarta dauke da murmushi ta ce "sannu da zuwa yaya IB", ya ce "yauwa 'yar k'anwata". Ta shiga kitchen ta ce "ka iske anyi favorite dish d'in ka", ya ce "kawo man dama yunwa ni ke ji". Ta had'o duk abinda ya kamata ta jera a tray ta kawo ma shi tare da shimfid'a darduma ta ce "have a sit and enjoy this tasty food", ya tankwashe k'afafun shi ya fara ci, ya ce "Ina Ammi ne da auta?" ta ce "sun fita zuwa barka can Sabuwar unguwa", ya ce "ok, kwana biyu na bar ganin k'awar ki", tayi murmushi ta ce "Farha ko yaya IB", ya ce "Eh ita ni ke nufi". 

 

Ta ce "cikin week d'in nan ma ai ta zo nan ta wuni", ya ce "hmmm har yanzu dai kin k'i ki fita harkar yarinyar nan ko Aysha?" ta ce "yaya IB ba ka gane ma Farha bane ba ta da matsala ta dauke ni kamar 'yar uwarta", ya ce "na ga alama ai shiyasa na ga ta na neman shiga hurumin da ba na ta ba". 

 

Ta ce "Allah yaya IB har yanzu ba ka gama fahimtar halinta ba ne", ya ce "ya kuwa zan fahimce ta bayan tayi abinda ke kan ki idan ki ka ji shi za ki yi Allah wadai da ita", ta ce "ba ni fata dan banda k'awar da ta wuce ta". 

 

Mamakin irin yardar da Aysha ta ma Farha yake, sam ba ta k'aunar a fad"i aibun Farha. Ya ce "good and fine! Yanzu alal misali idan na zo na ce ma ki ai Farha na son abba ta na so ta aure shi ya za ki yi?". Murmushi tayi ta ce "bare ma na san ba za ta ta6a aikata hakan ba", ya ce "ai misali na ce ya za ki yi?", ta ce "ba zan damu ba Yaya IB dan Farha ta wuce komi a wajena dan zan iya yarda mu auri miji daya". 

 

Wani wawan mari ya zuba ma ta à fuskarta, ya ce "anya wannan yarinya ba shanye ki ta yi ba kuwa? Yanda ba ki ganin laifin ta ko kadan toh wallahi ki kuka da kan ki ke daga yau ban son in k'ara ganin k'afarta cikin gidan nan banza wadda ba ta san ciwon kan ta ba sannan ba ke ba ita na raba ki da ki da ita". 

 

Cikin muryar kuka ta ce "komi za ka mun yaya IB ba zan rabu da Farha ba tunda har yau ba'a ta6a kama ta da wani abun ashsha ba", ya ce "haka ki ka ce koh?", ta ce "Eh ya ce yayi". Ya tashi ya fita. 

 

****************************

BAYAN KWANA BIYU 

Duk wata hanya da Farha za ta bi dan ganin ta janyo hankalin Abban su Aysha tayi amma abin shiru kamar an shuka dussa. Wata idea ta zo ma ta. 

 

Bayan sallar La'asar ta shirya ta fita zuwa gidan mai k'unshi. Black and red henna akai mata har a cinyoyinta ta sa akayi mata bayan sun bushe lallen ya fito das! Ta sa aka dauki pictures na lallen dukka. 

 

Bayan ta koma gida da dare tana kwance ta turo wadannan pictures din. 

 

Zaune ya ke da bowl na fruits salad a gaban shi yana ci yana tura wasu information ta PC. Har ya gama misalin k'arfe tara da rabi na dare (09:30pm). Wayar shi ya janyo da ke chargy ya lek'a WhatsApp. Messages d'inta ya gani wajen guda goma (10),yana shiga yaga pictures d'in har sun bude, tare da message d'in ta ta ce "Abba ga lalle nan nayi ma ka ka gani yayi kyau".

 

Runtse idanunshi yayi sakamakon pictures din da ya gani na ta na lalle da kuma wadanda ta dauka da irin su spaghetti top rabin k'irjinta a waje. 

 

Marking d'in su yayi gabadaya ya tura ma Yaya IB. 

 

Zaune yaya IB yake da matarshi suna zaune suna kallo, anty Amina na massaging legs d'in shi. Yaji k'arar shigowar message na WhatsApp a wayar shi ya jawo tare da budewa.

 

 

Cikin firgici ya tashi wayar ta fad'i a hannunshi. Anty Amina ta mik'e tsaye ta na tambayar shi. 

"daddyn Najeeb lafiya?" 

Komawa ya yi ya zauna. Ya ce 

"kan maganar yarinyar nan ne kin ga kuma abinda tayi yanzu".

Ya nuna ma ta hotunan Farha ta zaro idanun ta na mamakin halin Farha. 

 

Ya ce" yanzu ya ki ke ganin ya kamata ayi?"

Ta ce "yanzu dai a fad'i ma Aysha". 

Ya ce "ki bar maganar Aysha ba ji zata yi ba ai Farha ba ta laifi a wajenta". 

 

Washegari da safe anty Amina ta nufi gidan sirikanta wato gidan su Aysha. Da yake ranar Sunday ce ta shiga ta gaida Ammi sun d'ad'e suna fira kamar ba sirikai ba. Bayan Ammi ta ta shi ta shiga part d'in Aysha tashin ta daga bacci kenan wajen 12pm sannan take kalaci. 

 

Sun d'an ta6a fira da Aysha, anty Amina ta ce "jaje na zo yi ma ki". 

Aysha ta ce "jajen mi?". 

Anty Amina ta ce "jajen abinda Farha tayi ma ki mana". 

Ta ce "ni ba abinda Farha ta mun". 

Anty Amina ta hau sallallami ta ce "yanzu duk yanda maganar nan ta bazu cewa Farha na neman abba ba ki ji ba Aysha?". 

Aysha ta ce "ni fa ban gane ba kiyi mun gwari-gwari yanda zan fahimta". 

 

Anty Amina ta ce "toh bari ki ji Farha dai Abba ta ke so ta aura ita kuma ta nuna ta na son shi". 

 

Da azamarta ta mik'e tsaye ta ce "ba dai Farha ba sai dai in sharri za'a yi mata amma Farha ba za ta ta6a aikata hakan ba I trust her". 

 

Anty Amina ta ce "au haka ki ka ce? Toh shikenan ai za ki ga ni idan sharri akayi ma ta". Ta ta shi ta fita. 

 

Yaya IB ya gama plan d'in shi ya tura duk wani abu daya san Farha tayi da records na kiran da take ma Abba da pictures da copy&paste na chats din ta duk ya tura ma Aysha. 

 

Dawowar ta daga lectures kenan gab da La'asar, wanka ta fad'a tayi tare da alwala tana fitowa ta zura cotton din riga da wando three quarter saboda zafin da ake kwararawa a garin Katsina. 

 

Dinning ta je ta debo jollof d'in couscous yaji veggies da nama ga jug na kunun aya ta zauna cikin daya daga cikin kujerun falon ta tankwashe k'afafunta tana cin abinci a saman cushion din. 

 

Wayarta ta janyo ta kishingid'a tare da kunna data d'in ta tana duba notifications d'in da ta samu a social networking sites. 

 

Number of chats na yaya IB da ta gani ya sata saurin clicking kan sunan shi ta bude message din, duk audios ne ta gani da pictures da wasu chats da aka yi copying. 

 

Karshen messages ta ga ya rubuta "ki karanta a tsanake". Ta bi audios da images ta na downloading dan tayi offing auto-download d'in ta. 

 

Idanunta ne suka kad'a suka yi jajir! Hawaye suka fara zubo ma ta tayi wurgi da wayar ta fad'i k'asa ta cigaba da kuka tana ambaton "HAKA ZA KI YI MIN FARHA?" kuka take ba sassauci. 

 

Gurnanin kukan ta Ammi ta ji ta shigo falon tana tambayar ta, fadawa jikin Ammi tayi ta cigaba da kukanta har sai da tayi mai isarta. 

 

Da kyar ta iya labarta ma Ammi abinda ta ji. Ammi ta ce "ai tun farko ban so tarayyar ki da wannan yarinyar ba saboda yanayin ta kadai zai tabbatar ma da mutum rashin kamun kan ta ga shi nan dai yanzu halinta ya bayyana". 

 

Da kyar Aysha tayi bacci ranar k'osawa tayi gari ya waye. Bata da lectures ranar sai 2pm. Wajen 10am ta shirya ba ta zame ko'ina ba sai gidan su Farha. 

 

Da sallama ta shiga gidan ta lek'a part d'in Mami ta gaida ta sannan ta wuce d'akin Farha ta na zaune tana breakfast. Farha ta ce "lallai yau za'ayi ruwan sama harda k'ank'ara ma yaushe rabon ki zo gidan nan", Aysha tayi murmushi mai ciwo ta ce "uhmmm yau ai gani na zo". 

 

Farha ta ce "kin kyauta besty ta so muyi breakfast", Aysha ta ce "daga gida nike wata gulma na kawo ma ki duba ki gani". Aysha ta mik'a ma Farha wayar ta tare da kunna audio din, Farha na ji ta zaro idanu. Bata firgita ba sai da taga pictures d'in da ta tura. 

 

Sai da Aysha ta tabbatar ta gama gani ta mik'e tsaye ta ce "Nagode Farha sakayyar da zaki mun kenan". Farha ta ce "tsaya ki ji besty ki duba ki gani bani bace ni fa ban san anyi haka ba kawai dai wadanda basu so sugan mu tare suka had'a wannan plan d'in ta ya za'a yi in aikata hakan".

 

Wani wawan mari Aysha ta falla ma Farha. Still Farha denying ta ke ita bata aikata hakan ba, saboda ta raina ma Aysha wayau. 

 

Bayan tafiyar Aysha abin sam be dami Farha ba, ta cigaba da harkokin gabanta. 

 

Hakan yaima Aysha ciwo ganin ga abu k'iri'-k'iri amma sam Farha tak'i ta karbi laifin ta. 

 

Tun daga wannan ranar kowacce ta kama gabanta. Sai a sannan Aysha ta san cewa ba k'aramar illa Farha tayi ma ta à rayuwa ba ta raba ta da duk wasu masu son ta. 

 

***************************

BAYAN SHEKARA BIYU

 

Aysha ce zaune akan high table a wani k'ayataccen hall, wani matashin saurayi ne kusa da ita yana rad'a ma ta magana a kunne tana murmushi. Da gani babu tambaya amarya ce. 

 

Nan muka lallaba wajen jama'ar dake cikin hall d'in, muka ji wa ta na cewa "Gaskiya Suhail ya dace da mata dan suna matuk'ar kama ma".. Nan muka gano suna mijin Aysha Suhail. 

 

Anyi shagulgulan biki na kece raini, dan naira sai da ta koka. An kai ta gidan mijinta da ke cikin Maitama a Abuja. Gida ne na gani na fad'a dan an narkar da naira a gidan. 

 

FARHA

 

Farha ce zaune duk ta yamutse ta rame ga wasu manya kuraje da suka fito ma ta baja-baja a fuskarta da jikinta kamar ba Farha ba 'yar kwalisa. 

 

Tari ta hau yi ba k'ak'k'autawa ta dan jingina jikin gadonta. Muryar Sameera ta tsinkayi kunnuwanta. Kallo d'aya za'a ma Sameera a tantance irin hutun da take ciki fatar ta ta murje tayi fresh and soft, ga wani arnen material jikinta da golds dake walwali a wuyanta, kunnenta, yatsun hannunta da hannunta. Ta zama hajiya. 

 

Yaranta hudu duk tare suke, ta shiga d'akin mahaifiyar ta ta shiga, Mami ta ce "lale marhabin da bak'in London", Sameera da murmushi dauke a fuskarta ta gaida mahaifiyarta, yaranta ma suka gaida ta, suka zauna Mami ta cika gaban su da kayan ciye-ciye. 

 

Sameera ta ce "wai ina Farha ban ji d'uriyar ta ba ko ta fita yawon ta na sabo", Mami ta ce "wane yawo tana can kwance tafi karfin wata biyar ba ta fita". 

 

Sameera ta ce "Lafiya dai ko Mami?" ta ce "ina fa lafiya, Allah kadai yasan abinda ke damun Farha dan bata lafiya". Ta shi Sameera tayi ta shiga d'akin Farha, tsoron Allah ya kamata ganin 'yar uwarta a haka, hawaye suka gangaro kan fuskarta. 

 

Ta kalli Farha ta ce "Miya same ki Farha ki ka koma haka?", ta fashe da kuka ta ce "Yaya Sameera ki yafe mani sai yanzu naga muhimmancin maganganun da kike fad'i mani da ban kai ga wannan yanayi da nike ciki ba na zalinci kai na, harda laifin su Mami da suka gaza tsawatar mani gashi nan yanzu na fada ga halaka".. Dukkan su kuka suke, nan Farha ta kwashe labarin rabuwar su da Aysha ta fad'i ma Sameera. 

 

Sameera ta ce "yanzu wa gari ya waya? Yanda yarinyar nan ke k'aunar ki Farha amma ki mata butulci ai kin zalince ta". 

 

Asibiti aka tafi da Farha in da aka bata gado, likitoci sun yi bincike in da suka tabbatar da cewa Farha na dauke da cuta mai karya garkuwar jiki wato HIV. Ranar Mami, Daddyn su, Sameera da Farha ita kan ta kuka suke ganin yanda rayuwar Farha ta k'are a wulakance. 

 

Sameera sai da tayi sati biyu sannan suka koma Lagos da yake can suke zaune da mijin ta bayan sun tashi daga Dutsinma.. 

 

Rayuwa kenan! Sai ga shi Farha sai dai à dauke ta a juya komi sai dai ayi mata saboda cutar ta riga ta ci jikinta kuma bata shan magungunan da ake bata. 

 

Wannan labari izina ce ga ma su irin halin Farha. Dan duk wanda ya kaucewa fadin Allah da Manzon sa hak'ik'a rayuwar shi/ta na cikin walagagi. 

 

Ire-iren Farha na nan da yawa a cikin al'ummar mu dan haka mu kula da wadanda muke tare da su kunga dai abinda Farha tayi ma Aysha wanda labarin ya faru a gaske sai dan sauye-sauye da aka samu da kuma dan k'arin gishiri. 

 

Anan muka kawo karshen wannan labari na HAKA ZA KI YI MIN? ðŸ'" 

 

SADAUKARWA 

Gareku daukacin masoyan mu, mun gode kwarai, Allahumma shi bar so da qaunar juna. 

 

Na ku har kullum 

Mss_Sanam 

+2348067707799

ChuchunGaye 

+2348068069242 

 

K'ofa a bude take dan kawo gyara ko tsokaci. 

 

Love y'all 

 

 

Tags: Cin-amana #abota #yarda
2093
0
1
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!