Hafsatul Kiram!

Written by Rabiatu Mashi SkPublished on 2018-12-12 15:15:49Category RomanceYarinyace mai tunani da halin manya, ta taso da soyayyar yayanta manemun mata kuma mashayi, duk duniya babu wacce yaa tsana kamar ita, a haka aka ɗa aura aurensu haɗin iyaye tare da saka ran ko zata iya canja mishi halayya. tags: #Hafsatulkiram #Umar #HaquriDuba was labarai »

HAFSATUL KIRAM

 

 

 

 

NA

 

Rabiatu sk msh

(babymsh)

07014628776

 

07014628776

 

COPY RIGHT©

RABI’ATU SK MSH

HAKKIN MALLAKA (M)

RABI’ATU SK MSH

GODIYA

 

 

 

 

 

GINGINA A GAREKU

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Tafi minti shabiyar (15) da kofin glass a hannunta ta cikoshi da hollandia milk mai sanyi, tana tsugune da zumbuleliyar hijabinta tana jiran ya amsa anma kamar baisan da mutum a wurin ba yaci gaba da aikin da yakeyi a computer.

Cikin ƙarfin hali ta ƙara miƙa mishi tare da cewa "gashi" kamar wanda ke jira kafinta ƙarasa ya daka mata wata uwar tsawa da saida ta firgita dan a tsorace take yace,

  "sau nawa zan faɗa miki banson ganin wannan mummunar fuskar taki? Ki ɓacemun da gani".

Da sauri ta miƙe jikinta na kyarma cikin rashin sa'a kofin dake hannunta ya faɗi ya tarwatse duka ya ɓata mishi jiki da wasu takardun gabanshi

  Cikin zafin rai ya miƙe yana huci ya bata wani kyakkyawan mari, nan da nan idonta ya kawo ƙwalla tana kallonshi a tsorace cikin ɓacin rai yake magana,

  "bazan gaji da faɗa miki na tsaneki ba, ko kadan banason kallon fuskarki, ko ƙarar tafiyarki na tsana a gidannan, wannan wane irin ƙaddararren aurene? Anya kuwa ba mayya aka haifa mana a family ba? An rasa me so ni za'a liƙamun, ko kaɗan ke ba ajina bace, na tsaneki"

  Da sauri ta zaro ido tana kallonshi yaja tsoki ya koma ya zauna, danne zuciyarta tayi duk da tsoran dake ƙara cika mata zuciya, a hankali tace,

  "kayi haƙuri don Allah" ya mata banza, jin yayi shiru yasa ta ɗauki takardun da sauri ta fara gogewa a zuciye ya ƙara miƙewa ya ɗaga hannu da niyyar ƙara marinta ta duƙar da kai da sauri bayan taja da baya a razane saboda bata manta da zafin na ɗazu ba, duk ta dafe kumatunta da hannunta tana zaro ido.

 

Dai dai lokacin na shiga gidan, da sauri ya maida hannunshi yana kame-kame, yasa hannu ya dago fuskarta dake duƙe ta rumtse ido tana gunjin kuka, yana murmushi yace,

  "meye na kuka kuma? Ki share hawayenki bari inje in canza kaya"

Ta ɗago tana kallonsh cike da firgici da mamaki duk lokaci ɗaya, kafinta fara raba idanu cikin falon harta hangoni, da sauri itama ta fara ƙoƙarin murmushin yaƙe tace,

 "to shikenan, bari na kwashe"

  Can ƙasa muryarshi cikin karsashi yace,

   "karki kuskura ki taɓamun komai" sannan ya wuce ɗakinshi.

Yana ficewa Hafsat ta miƙe da azamarta ta ƙaraso inda nake tana murmushi tace,

  "sannu da zuwa Aunty Rabi'atu"

Nayi tsaye ina kallonta kawai, kamar tasan meke raina, ta ƙara faɗaɗa murmushinta,

  "kinga fa Aunty, abu na zubar mishi a jiki, na ɗauka zaimin faɗa shiyasa harna fara kuka. Nayi murmushin ƙarfin hali nace,

"kinanan yanda kike Hafsatul kiram tun kina ƙarama abu kadan ke sakaki kuka"  

 Umar ne dake tahowa bayan ya canja kaya yace,

  "Aunty Rabiatu ce a gidanmu? Sannu da zuwa Aunty gaskiya munji daɗin zuwanki"

Ba tare dana kalleshi ba muka gaisa, sannan ya fita hardasu ɗagoma Hafsatul kiram hannu, a raina nace 'maza kenan' 

  Yana fita na maida hankalina gaba ɗaya kanta, na buɗe baki da shirin tambayarta abunda idona suka ganianma tana fahimtar hakan tun kafin iyin magana ta miƙe tsaye tana murmushi tace,

  "Auntyna shine baki taho da takwara ba? gaskiya naji daɗin zuwanki, kamar kinsan ina da labaran dazan baki da yawa, Amma ki fara faɗamin me zakici? Yau girki na musanman zan miki"

   "girki kuma? Daga zuwana dai, ai kya bari ko gaisawa mu ƙarasa yi, yanzu dai zauna ki faɗamun..."

    Da sauri ta katseni, 

 "to bari in kawo miki ko ruwa dai, kayannan da Hajia ta bada a kawomun tunda kinzo bari in ɗauko ki gani, kuma kinga jiya muke maganar zuwa gidanki da Ya umar, munata saka rana har dai kin rigamu zuwa"

Inason yi mata magana anma taƙi ta tsaya da surutun da take duk ƙoƙarinta na son ɓoye damuwarta, ganin bata da alamar tsayawa da maganar, yasa na ɗan kamota na juyo da ita muna fuskantar juna nace, 

  "Ya isa haka, damuwar da kike ciki tayi yawan da bazaki iya ɓoyeta har a kasa ganeta ba Hafsat, ki kwantar da hankalinki, ki faɗamun miye gaskiyar abunda idona ya ganemin? Daman zaman da kukeyi da Umar kenan duk da soyayyar dake tsakaninku? Ko wani laifin kika mishi da ya sanyashi canjawa haka?"

 Girgiza kai tayi, nan da nan Hawayen da taketa ƙoƙarin ɓoyewa suka fara zuba a idonta, nan ta fara shessheƙar kuka da sauri na riƙota ina lallashi, yanayin kukan nata dole ta bani tausayi duk da bansan meke damunta ba, daƙyar na lallasheta ta fara magana,

  "babu soyayya tsakanina da Ya Umar Aunty, bai taɓa sona ba duk tsawon lokacinnan zama muke kawai, zan faɗa miki komai Aunty, anma kiman alƙawarin bazaki faɗa a gida ba, kimun alƙawarin baki faɗama kowa", duk ta rirriƙe hannuwana, Nace,

  "bazan faɗama kowa ba Hafsatul kiram, nayi miki alƙawari"

Share hawaye tayi sannan ta fara mun bayani. 

 

    *****

     

     KAFIN AURENA DA UMAR.

 

Kamar yanda kika sani Aunty, mu huɗu ne a wurin mahaifana Alh. Ahmad shahararren mai kudi, da haj fatima, ni kaɗaice mace a wurinsu, wannan dalilin yasa suke matuƙar ji dani, da duk wani danginmu.

 Mahaifina su biyune a gidansu shida Momie Khadija yayarshi, mahaifiyata ma su biyune ita da ke Aunty Rabi'atu, Rayuwatah na taso cikin farin ciki da gata, kuma duk da son da iyayenah kemin bai hanasu bani tarbiya ba, Alhamdulilah na samu ilmin addini sosai dai-dai gwargwado. 

  Lokacin dana ƙare secondry Momie Khadija ita da kanta tazo har gida tafiya dani, lokacin kuna moscow, ranar na shirya muka wuce Kaduna cike da farin ciki duk da banson rabuwa da Momma anma inajindaɗin zama gidan momie Khadija, ita yaronta ɗaya Ya umar.

 

Shi kaɗai ne matsalata a gidan, ko kaɗan jininmu baizo ɗaya ba, shiyasa ma bani shiga harkarshi kullum ina cikin ɗaki ina ƙara nazari akan littafaina na islamiya.

 Ranar da mukaje na iske Zahra tazo gidan, ɗiyar Aminin Daddyn shi, kinsan Zahra, Kinsan rashin tarbiyarta da rashin kamunkai, da kuma wayewarta duk dasu taje gidan. Don randa naje gidan tana sanye da riga da wando sunyi matuƙar matseta daƙyar rigar ta rufe mata cibi, gashinnan yasha gyara harda canja mishi colour amma batayi ƙari ba, da ganinmu ta taso ko kunyar kayan jikinta bataji ta rungume momie tana mata oyoyo,

 Momie ta faɗaɗa fara'arta,

   "sannu zuwa Zahra, saukar yaushe?"

  "jiya"

 "Ayyah! Kuma sai baki tarar dani ba"

 "eeh na iske Ya Umar ai, shi yacemun kunje katsina"

 Momie dajin haka duk sai naga fuskarta ta nuna alamun rashin jin daɗi, anma bata nuna mata ba, ta tambayeta yanda ta baro ƴan gidansu,

 Nina fara ma Zahra magana amma bata amsa ba sai wani irin kallo data bini dashi tana yatsina.

 Nidai ban kulata ba don nasan babu abinda zata nunamin, gata, ilimi, kyau, da kuɗi duk babu wanda ban fita ba, Wayewah indai irin tatace bani fatan in yita har abada, sannan kuma ba itace ta kawoni gidan ba, na ɗauki kayana na wuce ɗakin da nake sauka idan naje gidan.

 

Da dare ina ɗaki ina karatun Qur'ani, mai aikinsu tazo kirana inji Momie, daman da hijabi na ina kaiƙarshen aya na rufe na ajiye sannan na fito, a dinning na hangesu su duka sun hallara, 

  Momie tace, "kedai zaman daki yai miki Hafsat ko kaɗaici bakiji"

  Murmushi nayi cike da kunya naja kujera na zauna, babu wanda na samu ko arziƙin kallo daga gareshidaga Zahra har Umar, Sai nice na gaishe da Ya Umar, yayi kaman baiji ba.

 Momie ta kalleshi tace,

  "ga Hafsatul kiram fa, tana gaisheka kayi shiru"

  Yace "lafiya"

Sai lokacin na ɗago na kalleshi, Ya Umar kyakkyawan gaskene da bazan iya misalta haɗuwarshi ba, kasa ɗauke idanuwana nayi daga kallonshi, ƙila jikinshi ne ya bashi tsarguwar ana kallonshi, ya ɗago kyawawan idanunshi muka haɗa ido gabana yayi mummunar faɗuwa nayi sauri na duƙar dakai cike dajin kunya.

 Wani uban tsaki yaja da har saida momie ta ɗago ta kalleshi tace,

  "lafiyanka?"

Kamar baison magana Yace,

 "ruwannan yayi sanyi da yawa"

Momie tace, "ok bari in magana a kawo maka wani" 

  Zahra tayi saurin cewa,

  "nawa ma babu sanyi Momie bari na zuba mishi," ta fara tsiyayawa a Cup Lokacin momie ta gama ta miƙe tana cewa,

  "shikenan ma"

 

Momie na tafiya Zahra ta miƙe ta koma kujerar kusa da Ya Umar ta miƘa mishi Cup ɗin ruwan tace,

  "gashi Yayan", Ya girgiza kai, 

  tace, "kasha babu sanyi"

  Yace "na ƙoshi"

Tashi tsaye tayi taje ta dafa kujerar da yake tana kai kofin bakinshi tace,

   "nifa sai kasha ruwannan" Tana ƙara manne mishi jikinta na gogar nashi.

Abun dariya abun takaici, kasa daurewa nayi Abincin dana saka baki ma daƙyar na haɗiyeshi na miƙe nabar musu wurin.

Daga ranar na daina daɗewa a dinning, Momie na gamawa zan bita mubar wurin, ko kaɗan ban shiga harkar Ya Umar da Zahra, saboda yanda sukayi nisa kullum suna maƙale da juna tana ƙara cusa mishi kanta.

 Nikam dai bansan mena musu ba duk suka tsaneni bama kamar Zahra tunda daman Ya Umar bamu shirisaboda wai na fiya ƙauyanci, nidai ƙoƙarina kawai na zauna da kowa lafiya, Momie kam na matuƙar ƙoƙarinta ganin mun shaƙu da Ya Umar Ko fira suke tana yawan sakani, kafin inyi magana Zahra zata amshe suci gaba.

   

Kaman yanda na saba, rannan mun haɗu muna break fast, sai turawa nake kar Momie ta rigani tashi, da yake nike kusa dasu, bansan lokacin da tsautsayi ya kaini na hango hannunshi maƙale cikin na Zahra ba, da sauri na kauda kaina garin sauri har fork ɗin dake hannuna ya suɓece duk suka ɗago suna kallona, na tashi kawai da gudu nabar wurin ba tare dana ƙarasa break ɗin ba, don nasan tabbas Momie ta rigani tashi daga wurin saina ɗanɗana kuɗata.

 

Akwai ranar da ina ɗakin Momie ina sanya mata kayan guga a wardrobe ta shigo tana tambayata,

  "Umar ya dawo kuwa?"

Nace "wallahi ban sani ba momie, anma inya dawo ai zai shigo ne" 

 Tace, "dubomin ki gani in yana dakinshi dai, sai kiran wayanshi nake bai ɗaga ba"

  Cikin ladabi nace, "tohm Momie" na tafi kira matashi,

 A saɗaɗe na ringa tafiya cikin ɗakin nashi, don da naji motsinshi in faɗa mishi kawai in gudu, anma harna karasa shiga ɗakin bayanan, sai dai ko ina a ɗakin duk yayi datti yanda dai kikasan ɗakin maza yake, an baza kaya ko ina ga takardun office duk ya baza da wasu ledojin choculates dana cweets harda kwalayen lemuka, mamaki ne ya kamani yanzu duk tsaftar Ya Umar yake zama da ɗaki a haka? Ko ƴan aiki ai sai ya saka su gyara mishi.

 

Wata zuciyar tace 'ki gyara mishi mana' ganin bainan yasa na yarda da maganar zuciyatah, na aje hijab ɗina gefe naci gaba da aikin gyara mishi ɗakin, ina cikin gyara Momie ta shigo,

  Ta saki murmushin jin dadi tana kallon yanda nake aiki, da sauri na dakata saboda ganinta, duk fuskata tayi alamun rashin jin daɗi, kaman zanyi kuka nace,

  "kiyi haƙuri Momie banzo na faɗa miki bainan ba sai na tsaya wannan aiki"

   tace "haba dai Hafsat, na biyoki ne kawai inji ko lafiya, sannu kinji kinga kullum faɗan dattin ɗakinnan nake mishi anma yaƙi yarda a gyara mishi, yau gashi ƙanwarshi na rabashi da jejin nan".

 Sannan nayi murmushi ina rufe fuska,

  "Allah ya miki Albarka Hafsatul kiram" Kaina a ƙasa na amsa da "Amin"

 Momie bata daɗe da tafiya ba na kammala komi ɗakin ya fito yayi fess yayi kyau kaman bashi ba, na maida hijabi na don dama sauri nake karya dawo ya iskeni,

Ina niyyar barin ɗakin kuwa suka shigo shida Zahra tana maƙale dashi kamar ta koma jikinshi, bakinsu a haɗe sunata abubuwan dai dabai dace ba. 

Da sauri na kauda idona daga kallonsu, gashi sun ruga sun ganni, duk suka tsaya cirko-cirko, Zahra sai harara ta take kaman idonta zai faɗo.

  Raɓasu nayi na nufi hanya ina shirin wuce ya fizgoni na dawo baya, a tsorace nake jikina na kyarma hawaye ne suka fara zubomin, fuska a ɗaure cikin ɓacin rai da kakkausar murya yace,   

  "waya shigo dake ɗakina harda kaudamin kaya? Nace miki ina da buƙatar gyaran dakine? Duk abinda kikaga na ajiye nasan inda yake kin tashi kin haɗemun, ke wace irin jakace? Ko kinga ina shiga harkarki?"

Kasa magana nayi tashin hankali ƙarara a fuskata, daƙyar na iya cewa

  "kayi haƙuri don Allah", wurgar dani yayi cikin huci yace,

  "ɓacemun da gani, duk sanda kika ƙaramun wannan karambanin saina ɓallaki a gidannan".

Da sauri na nufi hanyar fita Zahra namin dariyar mugunta, hawaye ne suka zubomin cikin ƙunar zuciya daga abun arziƙi zai gwashaleni, koda yake ni taimako ne na mishi bada wani manufa ba.

 

Tun a lokacin zaman gidan ya fita raina amma ganin yanda Momie keson zamana gidan yasa kawai nake daurewa, ranar ko falo ban sake leƙawa ba.

  Washe gari saida momie ta sake aikena kiranshi, banison musa mata, saboda ba tarbiyatah bace, don haka cikin faduwar gaba na shiga falon ɗakin, ina ɗan ƙwala mishi kira anma banji motsinshi ba, kaman in koma in faɗa mata, sai kawai na wuce bedroom ɗinshi cikin faduwar gaba na ɗan tura ƙofar da yake a buɗe take, Abunda na gani ne ya ƙaramun faduwar gaba na zaro ido ko motsi na kasayi,

 Yauma Ya Umar ne na hango rungume da Zahra, babu kayan kirki a jikinsu yana shafata ta ko ina, idanunsu a rufe,

  Nayi matuƙar razana tsayuwama ta gagareni da saurina na juya tare da sakin ƙofar da sauri ƙafafuwana suka harɗe da hijabina na fadi a wurin, duk hankalinsu ya dawo ƙofa ina shirin miƙewa in gudu suka fito da sauri Zahra na ƙoƙarin rufe jikinta da bedsheet.

 

Suna ganin nice ya jawo Zahra ya ƙara mannata jikinshi yanamin mugun kallo yace,

  "wai ubanme ke shigo dake ɗakina kinamun leƙe? Kinyi mugun rainani ko?"

 Ban iya cewa komai ba sai hawayen da kawai ke zuba a idona har lokacin na kasa tashi daga faɗuwar da nayi, ya takamun ƙafa sosai harda murzawa don mugunta, na fasa ƙara ya duƙo saitin fuskata da sauri na matsa yana shirin shaƙoni na gudu ɗakina.

  Ina fita Zahra taɗan kalleshi da alama ta ɗan tsorata,

  "nifa kardai ace Momie take faɗamawa"

  "wannan da ko maganar kirki bata iyayi a gaban mutanen ne zata faɗa?" yaja tsoki ya wuceta, sannan itama taɗanji hankalinta ya kwanta.

 

Faɗawa nayi saman gado ina sharar hawaye, nasha kuka sosai ni kaɗai cikin ɗaki, da naga bazaimun ba na ɗauko Qur'ani naci gaba da karatu, sai sannan na samu nutsuwar zuciya, ina mamakin wannan tsana da Ya Umar yamun, da kuma irin zaman da suke yi da Zahra, babu tsoran Allah ko kaɗan a zukatansu, ko gajia basuyi da saɓon Allah koda yaushe.

  Bayan Sallahr magrib Momie ta shigo ɗakin ina saman sallaya, Na ƙirƙiro murmushi tace,

  "sannu da zaman daki Hafsatu"

Bayan murmushi bansan amsar dazan bata ba, 

  "Yanzu ba daɗewa, Daddynki ya kirani, wai na riƙeki da yawa, yaushe kikeso ki koma?"     

 Duƙar da kaina nayi kamar ince mata ko gobe ma, anma ina matuƙarjin kunyar momie, sai dai nace,

  "nan da can duk ɗayane Momie duk sanda kukace" na ƙara sadda kaina ƙasa saboda hawayen da kesonzubomin.

  Mun daɗe muna fira da Momie don indai tana gida bataso ta ganni nayi shiru, ko ɗaki nake ta ringa aike a kirani kenan, saida aka kira isha'i har ta miƙe zata tafi ta juyo ta kalleni tace,

  "ɗazu kin tarar da Umar ɗin kuwa?"

A rikice jikina na kyarma nace,

  "ban iskeshi ba a ɗakin, tace "idan kin gama sallar kije ki ganomin inya dawo, kice ya sameni a daki.

  Gabana ya fadi da sauri na dago kai duk na zaro idanuna lokacin harta juya zata tafi, hawayene suka kwararomin, meyasa Momie keson sakani masifa ne? Bansan tsautsayi da ƙaddarar da suka sakani biyota kaduna ba, ko kaɗan banson shiga harkar Ya Umar, ita kuma Momie ta dage tanason taga mun saba.

 Babu yanda na iya, ina gama sallolina na tafi jikina babu ƙwari, Zahra na falo tana kallo batasan wucewa ta ba a hankali kamar mai koyan tafiya na ƙarasa ɗakin duk a tsorace nake.

 

Har bedroom ɗinshi na duba bainan sannan na sauke ajiyar zuciya na juyo da sauri na nufi hanyar fita,

  A ƙofa mukayi karo dashi, da sauri na ɗago kaina tare da matsawa gefe a tsorace gabana na ƙara faɗuwa.

 Gani nayi ya tafi tangal-tangal zai faɗi da alama a buge yake bansan sanda nayi sauri na riƙoshi ba, na zaunar dashi saman kujera sannan na juya da sauri zanbar ɗakin, ji nayi ya riƙoni da ƙarfi ya jawoni na faɗa jikinshi yana buɗe ido yana lumshewa.

 Cikin muryar maye yace,

  "ina zaki tafi ki barni? Yau sai na cire hijabinnan inga abinda kike ɓoyewa"  

  Hankalina a tashe na fara ƙoƙarin ƙwacewa amma ba ƙaramin riƙo yaimun ba, Ya fara ƙoƙarin haɗa jikina da nashi, sai tureshi nake inaci gaba da ƙoƙarin ƙwacewa, wurin kiciniyar ƙwacewa ya fara ketamun hijabi duk hankalina ya tashi a ruɗe nake gashi ko ihu nayi babu mai jiyoni, duk ya ketamin hijabi, sai roƙonshi nake anma ko saurarena baiyi,

 Da dai naga ba cikin hayyacinshi yake ba na gartsa mishi cizo, ya sakeni da sauri na tureshi na ƙwace, saiga Momie ta shigo a ruɗe na koma bayanta jikina na kyarma sai hawaye nakeyi,

  Cikin takaici Momie ke mishi magana  

 "yanzu Umar bazaka daina wannan halin naka ba haryanzu? Kullum cikin rantsuwa kake da zaka daina anma har yau kaƙi ka canja hali?"

  Faɗa sosai take mishi anma baice komi ba, baimasan tanayi ba sai layi da yake daƙyar yake ɗaga idanu.

 Momie tace "bazanyi magana dakai ba cikin maye, idan kaa dawo dai-dai zaka gamu dani ne". sannan ta ƙaraso wurina tana tambayata,

 "meya faru?"

Tsabar ruɗewa bata bari na bata amsa ba, har lokacin jikina kyarma yake bakina ya kasa cewa komi da sauri na juya nabar dakin ina ƙanƙame da jikina ina kuka.

 

Ranar banyi barcin kirki ba, Allah ya sani bazan iya wannan zaman ba, ban kuma san abunda zaimun a gaba ba, don haka tun cikin dare na tashi na hada kayana tunda safe Momie ta shigo ɗakina kafin ta fita office ta iskeni gaban kayana ina hawaye,

  Gaisheta nayi kaina a ƙasa ina ƙoƙarin share hawayena anma kaman ana tunkuɗosu, taa daɗe a tsaye kafin taja numfashi ta fara magana,

   "bazan hanaki tafiya ba hafsat, daman shawarar da nayi kenan, anma kiyi haƙuri hafsat akan abunda ya faru, kuma kimin alƙawarin bazaki faɗama kowah ba"   

 Ɗaga mata kai nayi ina hawaye ta dafa kaina tace "Allah ya miki albarka Hafsatul kiram"

  Ta daɗe tana bani haquri, kaman itace tamun laifin, nikam godia nake ga Allah da bai bawa Ya umar sa'a a kaina ba, sai da ta tabbatar hankalina yaɗan samu nutsuwa, sannan ta saka driver ya kaini gida.

 

Su Mommana sunyi farin ciki da dawowatah gidanmu don nima naji daɗi sosai na ɗan samu natsuwa, ko kaɗan ban bari su momie sun gano damuwatah ba, na iske Daddyna ya nemamin admission zanci gaba da karatuna, har motah ya siyamin saboda zuwa makaranta, duk da nace bazan iya driving ba sai dai driver ya dinga kaini, don ko motah naƙi in koya.

 

Kwatam ranar dana cika sati biyu da dawowa, ina kwance ɗakinah kiran Mommana ya shigo a wayata, ina dauka tace in sameta falon Daddy, raina bai kawomun komai ba, na tashi na tafi ba ɓata lokaci.

 Zaune na iskesu Momma da Daddy, Momie Khadija da mijinta Alh Ibraheem, sai Ya Umar daya sunne kai ya zauna ƙasan kujera.

  Na shiga tashin hankali, cikin ruɗewa muryata na kyarma na gaishe da kowa gabana sai faɗuwa yake,na samu wuri na zauna nima na sunnar dakai ƙasa.

 Daddy na ne ya kira sunana, a hankali na dago kai yaci gaba da magana

  "kinyi mamakin ganin Momien ki tare da ɗan uwanki ko? Koma ince wannan zaman da mukai, dan uwankine yazo da maganar neman aurenki, munyi farin ciki sosai, daman burinmu kenan mu haɗa aurenku, da fatan kema bazaki ƙi amincewa ba, anma fa sai kina so, karkiji komai ki faɗa mana abunda ke ranki".

 

 Jikinah ya fara kyarma da sauri na dago kai ban iya tsaida hawayen firgicin dake zubomin ba, idan nace banison Yaa Umar naayi ƙarya, Kuma bazan iya ƙin bin umarnin iyayenah ba, anma idanna tuna abubuwan da suka faru kuma sai inji bazan iya zaman aure dashi ba.

 Rasa amsar dazan basu nayi, kuka mai ƙarfi naji na ƙoƙarin ƙwacemun, da sauri na tashi cikin sassarfa ƙafafuna na harɗewa na tafi ɗakina na faɗa gado ina kuka,

  Bansan shigowarta ba, sai dai naji ta dafani da sauri na tashi zaune kaina a ƙasa, Momie Khadija ta fara magana cikin damuwa,

  "bazanso mu takura miki ba muyi miki dole, idan har bakison Umar babu mai takura miki, anma alfarma nake nema a wurinki ki amince da aurennan don nasan ke kadai zaki iya taimakamin wurin canjashi, kinfi kowa sanin halin da yake ciki, yana buƙatar mace ta gari kaman ke Hafsatul kiram, wacce zata nusar dashi ya dawo hanya, wacce zata kula dashi, ina sakaran shiryuwar Umar ta dalilinki, ki taimakei Hafsat,Don Allah ki manta da duk abunda ya miki ki amince da auren, Ko kinaso kicemin baki haƙura da abnda ya muki ba?"

 Damuwa ce sosai a fuskar Momie da bazan iya jure gani ba, share hawaye nayi ina murmushin dole nace,

 "na amince da wannan auren Momie, insha Allah zan kasance mai biyayya a duk wani Umarni naku"

 Farin ciki sosai na gani a fuskar Momie tayita sanyamun albarka harta fice cikin murna, taje ta yima su Momma albishir suma sunyi farin ciki sosai, a ranar aka sanya lokacin aurenah da Ya Umar wata ɗayakacal.

 Tunda aka saka ranar aurenmu ban ƙara ganinshi ba, anma yana kirana a waya wani lokacin, harda bani kulawa ta musanman, duk da inajin kamar Momie ce ke tilastashi kirana, anma inajin daɗi saboda duk da firar tamu ba wani yawa gareta ba, cikin ɗar-ɗar zan gaisheshi ya amsa shikenan bamu da wani abin cewa, sai dai wani lokacin zanji momie na faɗa mishi abinda zaice, nikam ko yayane inaso, indai kulawar Ya Umar ne, saboda yanda soyayyarshi take ƙara shigemin zuciya.

 

Lokacin bikinmu banyi wani hidima ba, walima ne kawai da wa'azi, an ƙara tunatar da mata irin muhimmancin biyayya ga mazajensu, da kuma haƙƙoƙin maza akan matansu. Wa'azi sosai mai ratsa jiki,

 Akwai wani hadisin manzon Allah (S.A.W) da yake cewa;

  “idan da ace miji yana da wani gyambo, koda yana zubarda mugunya ko jini, sai matarta tsotseshi, bata biyashi haƙƙinsa ba”

   Kenan dai komai mace zatama mijinta bazata taɓa biyanshi haƙƙinsa ba, dolena zatayi ta mishi biyayya tunda aljannarta ma a ƙarƙashin ƙafarshi take.

  

Ranar juma'a aka ɗaura aurena da Ya Umar, Alhamdillah ɗaurin auren ya samu shaidar mutane da dama, unguwarmu ba masaka tsinke.

 Kuka kaini gidana dake Abuja da yake a can yake aiki, washe gari akai walima kowa ya watse ya barni, bayan ke Aunty Rabi'atu kin ƙaramun nasiha sosai.

 Da dare ina zaune tsakiyan gado bayan kowa ya tafi, nasha lulluɓi da ƙatuwar hijabi na har lokacin kuka nake ga kewar Momma da tausayin kaina.

  Wallahi Aunty, Ya Umar bai shigo gidannan ba sai ƙarfe dayan dare ya wuce, tun ina duban agogo har na gaji, zaman ya isheni anma na kasa kwancia, inata sakaran dawowarshi.

 

A buge ya shigomin, yana tafiya yana haɗa hanya kaman zai faɗi da sauri na ɗago ina kallonshi, ya fada saman gado kafafuwanshi a ƙasa.

 Wasu zafafan hawayene suka zubomin, bazan iya misalta halin dana shiga ba a ranar, na daɗe a zaune ina kallonshi kafin in miƙe daƙyar na gyara mishi kwanciya sannan na koma na zauna naci gaba da hawaye,

 Ranar daren aurenah, ranar da kowacce Amarya take kwanan farin ciki, ranar tarihi, ranar cikar buri,danar da kowa yake tunata yayi farinciki,

 Ni wannan ranar da baƙin ciki tazomin, ranar da bazan taɓa mantawa da ita ba, ranar banyi barci ba saboda baƙin ciki da takaici, kwana nayi ina sallah ina kai kukana ga ubangiji, tare da Addu'an nema ma mijina shiriya da kuma samun zaman lafiya a tsakaninmu.

 

Washe gari duk da barcin dake idona ga gajiar hidima, haka na daure ina gama sallolina da azkar na shiga kitchen na haɗa mishi break fast ɗin da nasan yafiso a zaman da nake gidansu, sai ƙamshine ke tashi duk ya cika gidan, dai-dai cikinmu na ɗauko da niyyar jerawa a dinning.

 Hangoshi nayi zaune da kwalbar abinsu na maye da banmasan ko meye ba, hannunshi da kofi yana zubawa, gabana ne yayi mummunar faɗuwa, ko breakfast baiyi ba zai kama saka ma cikinshi abinda zai cutar dashi, 

 Gabanshi nakai mishi, na fara jerawa ko kallona baiyi ba harna gama zuzzuba mishi na miƙa mishi gabanshi, Idanunshi jawur ya ɗago kanshi yanamin mugun kallo duk na tsorata ganin kallon da yakemun, miƙewa yayi tsaye a zuciye yasa hannu ya ture kayan break fast ɗin, wasu suka farfashe duk abincin ya zube, wanda ma basu ƙarasa zubewa ba ya turesu da ƙafa.

Da yatsa ya nunani yace, 

  "karki kuskura ki ƙara nunamin wannan baƙar fuskar taki, a idon duniya ne kike matata anma ni bazan taɓa iya kallonki a matsayin mata ba, ke kanki kinsan ke ba sa'ar aurena bace, don haka samun zaman lafiyarki karki shiga harkata",

  Yaja tsaki ya wuce ya barni a tsaye kamar wadda aka dasa hawaye na tsiyaya a idona.

  Da rana ban fasa ba, na shirya mishi girkin rana mai daɗin gaske, wanda na tabbatar ko daga jin ƙamshin zaiyi sha'awar yacishi, na saka hijab ɗina na ɗauka na nufi ɗakinshi da yake bai fita ba, da sallamata na shiga, yana zaune yana waya dagaji macece, har saida nayi nadamar shiga ɗakin saboda irin maganganun da yake furta mata,

  Nesa da inda yake na tsaya zan ajiye mishi, 

  "ke" ya kwatsamun tsawa harna kusa sakin abincin.

  Ina tsaye jikina na kyarma ya ƙaraso inda nake, 

   Ya kama kunnuwana ya murɗe, nan na fara shessheƙar kuka,

  "ke bakijin magana ko?"

  "kayi haƙuri, naga bakaci komai ba"

   "ina ruwanki da abinda zanci? Ko yunwa zata kasheni an faɗa miki zan iya cin wannan jagwalgwalon naki? Eyeh!?"

 Na fara girgiza mishi kai ina hawaye, kunnena namun zafi kaman zai cire.

  Ya buɗe food flask ɗin, soup macoroni ne ko a ido yayi kyau sosai, banyi aune ba naji ya juyemunshi a jiki, zafin girkinnan ya ratsamun jiki kaman ya zubamun wuta, a haka ya juyemun komai a jikina, na kasa motsawa banda kyarma babu abunda jikina keyi.

 

Tun daga ranar da aka kawoni gidan Ya Umar har yau takaicinsa kawai nake sha, kullum ƙoƙarin kyautata mishi nake da mishi biyayya ban taɓa gazawa ba, duk da baicin girkina ban taɓa fashin yi masa ba, sai dai yanzu a dinning nake aje mishi, yanda na aje kuma haka zan ɗaukeshi.

 Baisan cina ba, bai san shana ba, ba ruwanshi damin sutura, bai damu da yanda na kwana ba sai nice ke zuwa gaisheshi kullum babu fashi, a taƙaice dai babu wani haƙƙin auren daya taɓa saukemun.

 Kullum cikin yi mishi addu'a nake ban taɓa gajia ba, kullum dare nake rabawa ina roqa mishi shiriya,

 Na share hawayena bayan na gama jin labarin auren Hafsatul kiram, na nisa sannan nace,

  "ya labarin Zahra? Momie Khadija tasan irin zamannan da kukeyi?"

 Ban taɓa faɗama Momie abinda yakemun ba, kuma ban tunanin ta sani duk da tana yawan kawo mana ziyara, sai dai komai ita kemun tunda suka dawonan Abuja da zama,

 Bansan yanda suka rabu da Zahra ba, anma naaji labarin tayi aure dai, neman matanshine dai babu abinda ya canza.

Kuma bawai waje yake fita yayi ba, cikin gida yake shigowa dasu, wani lokacin ma sai dai yamin wulaƙanci ya fiddoni falo a ɗakina zasu kwana da wadda yazo da ita", ta ƙarasa maganar da hawaye.

 

Cike dajin haushin Umar na kalleta nace,

   "gaskia bazan iya barinki a wannan halin ba, tashi ki shirya kayanki hafsatul kiram, bazan tafi in barki gidannan ba, bazaki zauna yaci gaba da wulaƙantaki ba, kina yarinyarki zaki zauna da baƙin ciki? Bzan taba yrda ba saina nema miki haƙƙinki, idan shi baisan darajarki ba mu mun sani, ai ba haka ake zaman aure ba"

  Riƙe hannuna tayi tana girgiza kai tace "bazan tafi ba Aunty, akwai inda yafi ƙima da daraja a wurin mace fiye da gidan mijinta? Kema kin faɗamun haka, a yanzu kam dani da babu duk ɗayane a wurishi, kinga koda na tafi bazai damu ba, sannan ga fushin mahaifiyarshi dazan sakashi, bazanso hakan ba Aunty, bazanso abinda zai ɓata mana zumunci ba don Allah aunty karki faɗa, ni nasan insha Allah akwai ranar da mijina zai shiryu, akwai ranar da zai juyo gareni, Allah nake roƙo koda yaushe kuma shi yafi kowa sanin halin da nake ciki, kuma duk wani mai haƙuri yana tare da Allah"

 Maganganunta sun kashemun jiki sosai, anma duk da haka sai nace mata,

  "Kinsan kuwa idan akwai laifin Umar akwai naki a ciki?",

Da sauri ta kalleni tace, "laifina kuma?" 

Na ɗaga mata kai nace, "tabbas! Shekara ɗaya tsakaninki dashi ace kin kasa jawo hankalinshi? Tinda kike dashi ya taɓa ganin surar jikinki? Kullum cikin abaya kike koni zan iya cewa baifi sau ɗaya na taɓa ganinki ba hijabi ba, ko a gida cikin ɗaki ke kaɗai sai kin saka hijab, haba Hafsatul kiram aure fa dabanne, namiji kamar yaro yake mai lallashinsa yakeso, Cire kunya zakiyi ki nuna mishi soyayya, su da yake wulaƙantaki kansu basu fiki diri da ƙira mai kyau ba, Allah yayi miki anma kibar mijinki cikin halaka yana kula matan banza a waje, Idan Umar abinda yakeso kenan nizan maidaki kaman ƴan matan nashi, ki cire kunya ki dinga tarairayar mijinki, ki dinga saka mishi irin suturar da yakeso" 

  Girgiza kai tayi tace, "Aunty son gaskiya nake yiwa Yaa Umar, nima son na gaskiya nakeso yamin,saboda duk soyayyar da aka ginata ba don Allah ba akwai lokacin da zata gushe, bazanso ya faɗa sona saboda sha'awa ba ko wani abu na jikina, nasan bazai ɗore ba, inaji a jikina wata rana zai soni, anma bazan canja daga yanda nake ba don in yaudareshi ya faɗama sona, Idan zai soni ya soni a yanda nake, Ki tayani addu'ah kawai Aunty"

 Jikina ya gamayin sanyi, tabbas ta fini gaskiya indai namiji bai sonka, tohm ƙiyayyar tananan duk wani kissa da iyayi bazasu samo soyayyarshi ba, suma mutanen wajen jikinsu kawai yakeso bawai suɗin yakeso ba,

Na share mata hawaye nima ina hawayen nace "shikenan Hafsat Allah ya karkato miki hankalinshi gareki ya sanya soyayyarki a zuciyarshi ke kuma ya ƙara muki haquri da juriya, insha Allah zanci gaba da tayaki addu'a" 

  Tayi murmushi tare da rungumeni tace "nagode Auntynah" nan naci gaba da kwantar mata da hankali, sai bayan isha'i nabar gidan cike da tausayinta har lokacin umar bai dawo ba.

 

***

12pm Hafsatul kiram na zaune falo tayi jugum don duk irin daren da Umar zaiyi bata iyayin barci sai ta jira ya dawo.

Kamar kullum tare suka shigo da wata daga cikin ƴan matanshi ta ɗaura kanta saman kafaɗanshi suna tafe cikin nishaɗi,

 Baiko kalli inda take ba suna tafiya yace "ki kawo mana coffee", sannan suka wuce ɗakinshi, kamar wadda ƙwai ya fashe mawa ta tashi ta nufi kitchen,

  Wurin saukewa tana can tunani ruwan zafi ya zubar mata a ƙafa, da sauri ta ajiye, ta koma baya tana yarfe hannu wani irin azaba takeji har wurin yayi ja,

Muryarshi ta jiyo yana cewa "ke wace irin kidahuma ce? Komi aka sakaki saikin ɓatama mutane lokaci" 

  Da sauri ta juye musu ta nufi ɗakin nashi, Rungume ta iskesu da juna yana shafa mata bayanta, A zafafe ya ɗago fuskarshi yace, "idan jahilci ya hanaki sallama knockn ma bazaki iyayi ba?"

 Rumtse idonta tayi cikin jin zafin kalamanshi, a ranta tace duk sallamar da nayita ƙwalawa?, anma a zahiri sadda kanta tayi tace,

   "yi haƙuri" Yaja tsoki ya juya yanama budurwarshi magana a hankali

Saman bedside ta ɗaura musu ƙafarta mai toyewar tadan bugi gadon ta saki ƴar ƙara ta tsugunne wurin ta dafe ƙafar tana hawaye.

  Kallonta yayi yaga yanda ƙafar tayi ja, muryarshi ba yabo ba fallasa bai mata tsawar daya saba ba yace,

  "jira kike sai naace ki ɓacemun da gani?"

 Da sauri har hijabinta na harɗeta tabar ɗakin, Hawaye na zuba a fuskarta,

 

A ƙofar ɗakin ta jingina a bango idonta a rufe tace, "Ya Allah ka yafe mishi, ka dawo dashi hanya".Sannan ta wuce ta nufi ɗakinta. 

  Da safe ta gama jera mishi break fast a dinning, tana ɗakinta kiran Momie ya shigo mata, da sauri ta ɗauka cikin girmamawa take gaisheta

 Sun gama gaisawa cikin kulawa momie tace, "kuna tare da Umar?" Gaban Hafsat ne ya faɗi tace,

  "eeh Momie gashinanma"

 Momie tace, "tohm bashi wayar"

   Zaro ido tayi kamar gaban momie a tsorace, maganarta na harɗewa tace,

  "kin kirashi ne Momie? yanzu....Yana....", sai kuma tayi shiru duk ta rasa abinda zatace, Murmushi momie tayi don tasan basu tare shiyasa ma tace ta bashi,

  "shikenan kice mishi ya kirani", Hafsatul kiram tace 

   "tohm", ta sauke ajiyar zuciah.

Momie na kashewa Umar ta kira, da sauri ya janye budurwarshi daga jikinshi duk ya nutsu ya ɗauki kiran, cikin tattausan lafazi momie ke mishi magana tace,

   "ina hafsatul kiram?"

    Yace "gatanan Momie"

  "toh bata wayar", Shiru yayi alamar baida gaskia, Momie ta sauke ajiyar zucia sannan tace,

  "anya kuwa Umar baka gudun haƙƙin yarinyarnan ya kamaka? Allah ya baka mata mai haƙuri anma bazaka daina cutar da ita ba?

  Yace "momie ita tace nayi mata wani abin?"

  Tace, "kaji tsoran Allah Umar, mata irin Hafsatul kiram wahalan samu ne dasu a zamaninnan namu"Shiru yayi zuciarshi na mishi ƙuna, Momie tace  

  "kuma ka kawomin ita kafin ka wuce office"

  Yace "momie...", 

  ta kashe wayan

Har wani hucin ɓacin rai yake wai baƙauyiyar yarinyarnan zai ɗauka a motanshi, in wani cikin abokanshi ya ganshi da ita ai sai su mishi dariya.

  Ya banka ƙofar ɗakin da take, ya shiga da sauri ta ɗago kanta a tsorace, ya wurga mata wata uwar harara yace  

  "ni zakije ki haɗa da mahaifiyatah?"

Ta sadda kai saboda ko kaɗan bataso tai mishi musu, Sai da ya gama faɗanshi sannan yace 'ta tashi su tafi'

Ta miƙe daman tayi wankanta tsaf da hijabinta jikinta don hafsatul kiram akwai tsafta, da son gayu kullum cikin ƙamshinta take mai dadi, 

Tare da budurwarshi suka fita suna zaune gaba, ita dai duk jinta take a takure ta rasa inda zata ajiye idanunta, duk taa ƙagara su isa, 

  A ƙofar gidan yayi parking mai gadi na ƙoƙarin buɗewa ya dakatar dashi, tsayawa tayi bata bude motan ba ya juyo ya galla mata harara ba tare da yayi magana ba, Da sauri jikinta na kyarma ta buɗa motan ta fita yaja tsaki a fili yace,

  "duk dai yanda za'ai da jaki sai yaci kara", Hawaye ne suka zubo mata, don tsabar ƙunar zuciah ma kasa matsawa tayi.

  Da gayya yaja motar da ƙarfi har yana bugeta ta faɗi wurin ya tara mata ƙura yayi gaba, Ta share hawayenta tare da kakkaɓe jikinta sannan ta shige gidan tana ƙoƙarin dai daita kanta.

 Da murnarta ta shiga gidan, Momie taji daɗin ganinta, ta rasa inda zata saka ta sai nan-nan takeyi da ita, tace,

  "shi Umar ɗin bazai iya shigowa ya gaisheni bane?"

 Hafsatul kiram tace,

  "A'ah Momie anata mishi wayane office da muna hanya shiyasa yace sai ya dawo ɗaukana"

  Momie tace "ki faɗamin idan akwai abinda yake miki, ni nafi kowa sanin halin Umar"

 tana murmushi tace, "ba komi Momie, Yaa Umar yana kulawa dani sosae" ta kasa ɗago fuskarta saboda hawayen dakeson zubo mata.

 Duk yanda Momie taso ta fahimci damuwarta bata bari ba, ta sake sosai duk da kunyar Momie da takeji, da dare ma baizo ba sai wurin 10 harta farajin barci,

Momie ta haɗesu su duka ta musu nasiha mai ratsa jiki shidai saurarenta kawai yake, kamar karta bar gidan Momie don wani irin farin ciki takeji data daɗe batayi ba, 

 Da taje shiga motar har ta buɗe baya zata shiga ya daka mata tsawa yace,  

 "naayi miki kama da driver ne?", Da sauri ta buɗe gaba ta zaune duk ta takure yaja mota suka tafi.

 A hanya tunani take yaune rana ta farko da suka taɓa kasancewa tare ba tare da yana cikin maye ba ko yana tare da wata, lallai ya kamata tayi amfani da wannan damar wurin tunasar dashi Abinda ya manta.

  A hankali ta rufe ido duk ta tsure a tsorace take da zazzaƙar muryarta ta fara magana,

 "Yaa Umar, kayi haƙuri da abunda zan faɗa, anma wani nauyine Allah ya ɗauramun na faɗa maka gaskia,Basaina fada maka ba kaasan illar shaye-shaye, kaasan illar zina, domin manzon Allah (S.A.W) Ya hanemu da shan giya, kuma Allah (S.W.T) yaa fada a cikin ayoyinsa na alqur'ani akan haramcin zina, kuma duk wani mai aikata zina bazai taɓayin arziƙi ba, Allah yana fushi dashi kuma tafi kowanne aiki laifi a wurin ubangiji, Akwai hukuncin shari'a kuma, Zina bashi ce Yaa umar! Idan ba'ayi da......,"

  Wani wawan burki taji yaja a tsorace ta ƙara maƙure kanta jikin ƙofa, sai da taji shiru sannan ta buɗe ido a tsorace don ita duk tunaninta Abinda take faɗane ya ɓata mishi rai, gani tayi hankalinshi ma ba wurintayake ba duk abnda take faɗa baji yake ba, cikin tashin hankali ta maida kallonta bakin titi da yake kallo,

  Wata budurwace tsaye bakin titin, tana sanye da doguwar riga da bata ida kai mata ƙasa ba, taa matse jikinta sosae kanta ko dankwali babu sai wani guntun mayafi, da manyan kalaba a kanta.

  Ya kalli Hafsatul kiram ta sadda kai, yaja tsoki yace,

  "a samanki zata zauna? Ki fice ki bata wuri",

  Kasa maida hawayen da sukazo mata tayi, ta tashi jiki ba ƙwari ta koma baya ta zauna.

 Fita yayi wurin budurwar, suka ɗanyi magana sannan suka shigo tare,

 Suka zauna sai kallonta yake Yace,

  "kinanan da kyaunki deezy,"

  tayi murmushi tace, "kuma inanan da soyayyarka honiee, Hankalinka kwance kaa wani manta dani"

  Yace "waya isa ya manta dake zuma? Allah ina sonki da yawa haryanzu",

Ya kamo hannunshi ya haɗa da nata kamar mai shirinyi mata kuka yace, 

  "na rasaki a wancan lokacin, yanzu bazan taɓa bari ki gujemun ba"   

  Rungumeshi tayi tace, "bazan taɓa rabuwa dakai ba Umar"

 

Deezy Budurwar Umar ne tun lokacin da yayi karatu ƙasar waje, suna matuƙar son junansu tunda suka gama makaranta basu ƙara haɗuwa ba sai yanzu, Itama abuja take,

 Hafsatul kiram sai ta zama ƴar kallo, duk ƙoƙarin da take na tsaida hawayenta ta kasa hanasu zuba, haka yake tuƙi suna shan soyayyarsu hannunshi daya ke tuƙi daya na riƙe da nata,

 Sun daɗe kafinsu isa gidan saboda yanda yake driving a hankali, yanayin parking hafsatul kiram ta buɗe motan ta fita ta barsu, har jiri ne yake ɗaukarta saboda tsananin tashin hankali.

 

Dakinta ta wuce daman tayi sallolinta tun gidan momie, harta kwanta Momie ta kirata, tace "kunje gida lafiya?" Hafsat tace,

  "lapia lau Momie harzan kira kuma nayi tunanin kunyi brci"

  Tace, "ina fa zanyi barci banji yanda kuka isa ba, ina Umar ɗin?"

 Ta kalli gefenta hawaye suka zubo mata sannan ta tashi ta fita falo inda Umar da Deezy suke tace,

  "gashinan Momiena", 

sannan tasa hannu biyu ta miƙa mishi wayar tace "momie ce" Da sauri ya ansa duk ya ruɗe sukai maganaya gama ya miƙa mata wayar,

Deezy ce ta ƙare mata kallo sannan tace ma Umar, 

  "wannan a gidannan take?"

Da alama yanajin ciwon abinda zai faɗa daƙyar ya cije ya iya cewa,

  "matar da aka auramun ce",

da mamaki tana yamutsa

  tace mishi,

  "yanzu Honie duk kyawawan ƴan matanka wayayyu ka ƙare da auren wannan?"

 Yace "babu yanda na iyane honiee, Anma tunda gaki kin dawo gareni yanzu banda wata damuwa", Tayi murmushin jin dadi sannan ta watsama Hafsatul kiram harara,

Juyawa tayi tabar wurin ta wuce ɗakinta, inda sabo ya kamata ta saba, taa daɗe kafin barci marar daɗi ya dauketa. Kamar kullum ta tashi tsakar dare tayi sallolinta, ta daɗe tana miƙa kukanta wurin ubangiji bata koma barci ba saida tayi sallar asuba, ta shiga kitchen ta hada mishi break fast sannan ta koma ta kwanta, 

 Batasan fitarsu ba, sai dai ta farka basunan Tayi shiru ita kaɗai, duk da ta saba da kaɗaici anma shiru ya isheta ga damuwa data ke mata yawa.

 

Dawowar Deezy rayuwan Umar, ya daina shigoma Hafsatul kiram gida da ƴen matah, itama Deezyn bata ƙara kwana a gidan ba.

 Sai dai ta daina ganinshi Hafsatul kiram, bai shigowa gidan sai dare yayi sosai kuma tunda safe zai fice,

  Nan danan hafsatul kiram ta fara rama, kullum da hotan Umar take kwana a ƙirjinta, don zaifi mata dadi ta dinga ganinshi tanajin muryarshi koda zai mata dukan tsiya akan tai rashinshi. (Allah sarki hafsatul kiram, ita nata son akan wanda bai dace ba ya faɗa).

 

Zaune take Hafsatul kiram ta saka hotan Umar a gaba hawaye na zuba a idonta ita kadai ke magana cikin kalar ban tausayi "Yaa umar mai yasa zakamin wannan hukuncin? Zan iya jurar ko wanne hukunci daga gareka anma banda wanda zai nisanta ni da ganinka, Meyasa ka tsaneni? Meye bakaso wanda nake dashi? Zan iyayin komi dazai sanyaka farin ciki, Rayuwatah ne kawai ban iya ƙararwa saboda inason inyita ne tare dakai, Anya kuwa akwai ranar da zaka so ni?"

  Daga bakin ƙofa taji an bata amsa da 

   "A'ah," da sauri ta ɗago tana kallon Deezy har lokacin hawaye na zuba a fuskarta, Deezy taci gaba da magana 

  "babu ranar da honieenah zai soki, ni kaɗai yakeso, kin gane ba? Igiyoyn aurenki da suke kanshi ba wani Abu bane, don bazaki taɓa mallakar zuciarshi da gangar jikinshi ba, Sunana deezy! Bazan taɓa bariwata ta shiga zuciar Umar ba bayanni.

 Hafsatul kiram bata tanka mata ba suka jiyo muryar Umar na kiranta, tayima Hafsatul kiram kallon sama da ƙasa ta juya ta fit,! Zama tayi saman gadon tana ci gaba da kukanta.

 

A ƙofar fita falon sun jera shida Deezy zasu fita momie ta shigo, sakin hannunta yayi ta matsa daga kusa dashi, wani irin kallo Momie ta watsa mishi duk ya rikice cikin in ina yace,

  "Momie Deezy ce", 

 ya kalli Deezy ganin ko gaishe da Momie batayi ba yace,

  "gaa momiena fa"

Harda duƙawa ta gaishe da Momie cikin jin kunyar kayan dake jikinta, fuskar Momie ba yabo ba fallasa ta amsa sannan tace,

  "Deezy ko zaki bamu wuri muyi magana da d'ana?"

   Tace "Awk Mum"

Ta juya ta nufi hanyar fita, Umar Yace 

  "ki jirani inzo, ta ɗaga mishi kai ta fita,

 Momie ta kalli Umar cikin mamaki tace 

  "wai umar meka ɗauki aurene? Gidanka zaka shigo da wata macen? Har yau kai bazaka nutsu ba? Nayi zaton idan na aura maka Hafsat zaka dawo hankalinka kasan me kake, anma kana cutar da yarinyar da babu ruwanta"

  Yace "Momie ki fahimceni nifa...."

 Ɗaga mishi hannu tayi,

  "naa riga na gama fahimtarka Umar, ƙarama tun wuri ka koyama kanka son Hafsatul kiram, idan har bazaka iya bata haƙƙoƙinta na aure ba nizan nema mata haƙƙinta!"

  Da sauri ya kalli momie cikin mamaki,

  Ta daga mishi ka,

  "tabbas nizan ƙwatoma hafsatul kiram haƙƙinta, don bazai yiwu kaci gaba da cutar da ita ba don kawai tana haƙuri dakai"

  Juyawa tayi ta fasa shiga wurin Hafsatul kiram saboda yanda Umar ya gama ɓata mata rai, tsaki taja tun farko sune suka sangarta shi da soyayyarsu wai danshi kaɗai ne suka haifa, ga hafsatul kiram nan da take ita kaɗai mace a wurin iyayenta hakan baisa sunƙi bata tarbiya ba, yarinya mai nutsuwa, kawaici, haƙuri da biyayya.

 Umar kasa motsawa yayi daga inda yake saboda tsananin ɓacin rai da tashin hankali, zuciar ƴan maza taɓaci kamar ta fasa ƙirjinshi ta fito.

  Juyawa yayi ya nufi ɗakin Hafsatul kiram da batasan meke faruwa ba, fitar Deezy ƴan uwanta suka kirata suna fira cike da kewar gida, sai dai taji ya banko ƙofa cikin bacin rai, da sauri jikinta naa kyarma tace "brodzas zan kiraku"

  Bata jira me zasu ce ba ta kashe wayar.

 Miƙrwa tayi tsaye cikin tsoro jikinta na kyarma ya shaƙota cikin zafin nama ya nannaɗeta cikin hijabin jikinta duk idanunta sun firfito sumane kawai batayi ba don tsananin tsoro,

 Cikin daga murya yake magana,

  "sau nawa zan faɗa miki ki daina shiga tsakaninah da mahaifiyatah? Na faɗa miki sau ba adadi bn sonki, ban ƙaunarki, na tsaneki, Baƙin ciki yake ƙaramun ganinki a cikin gidannan, Ban taba tsanar abu ba duk duniyar nan kaman yanda na tsaneki"

 

Jefar da ita yayi gefe guda ta faɗa saman gado ta saki wani irin kuka mai cike da ban tausayi, Juyawa yayi cikin fushi zai bar ɗakin yaci karo da Momie tsaye bakin kofa,

 Gefe yaja ya tsaya yanaci gaba da huci kamar zaki.

  Momie tace, "miye haka Umar?" Cikin huci idanunshi sunji jajir yake cema Momie,

 "Kinji da kunnanki ba? Deezy kawai nakeso Momie, Na auri Hafsatul kiram ne kawai saboda farin cikinki, anma bazan taɓa iya kallonta a matsayin matah ba, Raina ƙunah yake a duk lokacinda na tuna wai itace matatah hakan na cutar da zuciatah, Na auri Hafsatul kiram saboda umarninki, kinyi farin ciki ba? Anma hakan bazaisa in zauna da ita a matsayin matah ba".

  Ya juya ya fita fuuuu kamar mai shurin tashi sama, Da sauri hafsatul kiram ta tashi ta jawo akwati ta fara haɗa kayayyakinta, Momie ta ƙaraso inda take cikin sauri har tana harɗewa tace,

  "me kike shirinyi Hafsatul kiram? Daina zuba kayan tayi sannan ta ɗauki jikkarta ta rataye kanta a ƙasa tana hawaye tace,

  "gidanmu zan tafi momie, ni kaɗaice matsalar Ya Umar, Bazanso in sakashi a damuwa ba, ƙara in tafi inyi nesa dashi"

 Momie tace, "kina nufin kin haƙura dashi? Hafsatul kiram tace,

  "na haƙura da auren Ya Umar Momie, zaɓ barshi yayi rayuwarshi da wacce yakeso"

  Momie ta dafa kafaɗarta tace "son da kike mishi fa?"

 Shiru Hafsatul kiram tayi, Momie tace,

  "duk son da kike mashi zaki tafi ki barshi?"

Tace "Inason Ya Umar Momie, anma idan har na kasa sakashi farin ciki bai cancanci kullum in dinga ƙuntata mishi ba, ya faɗa da bakinshi ba son ganina yake ba, Momie banison abinda zai ɓatama Ya Umar rai", Ta juya taci gaba da tattara kayanta" 

 Momie tace,

   "nasan kinyi haƙuri Hafsatul kiram, kina da matuƙar biyayyah, Na kasa sama miki farin ciki a rayuwar aurenki, karki tafi kibar Umar yana da buƙatarki, nayi miki alƙawarin zan nema miki 'yancinki anma don Allah karki tafi"

  Rumtse ido tayi yanda momie ke lallashinta, bangare ɗaya kuma ga farin cikin Umar da tsanar daya mata, Bataso ta tsaya wani tunanin dazai karyar mata da gwiwa, ta kasa hada ido da Momie saboda wata irin kunyarta da takeji,

 Kanta a ƙasa daƙyar maganarta ke fita saboda tsananin kuka tace "kiyi haquri Momie na kasa zama suruka ta gari a gareki, na kasa zama matar da ɗanki zaiyi alfahari da ita, Kiyi haƙuri Momie anma bazan iya ci gaba da cutar da zuciar Ya Umar ba, Nice matsalarshi, idan na barshi zaiyi farin ciki, hakanne burinah"

 

Ta ɗauki akwati da jikkarta a rataye ta nufi kofa,

  Kafin takai ƙofa Momie tace,

  "shikenan ki tafi hafsatul kiram" Ta tsaya tana share hawaye ba tare data juyo ba, Momie ta matso kusa da ita tace,

  "ki tafi hafsatul kiram bazan hanaki ba, shi baiji maganatah ba, kema da nake da yarda a kanki zaki tafi ki barni, shikenan duk ku gujemun, Nasan kinyi haƙuri da yawa ko kadan banga laifinki ba", Ta ƙarashe maganar kamar mai kuka,

 Da sauri Hafsatul kiram ta jiyo, hawaye ta gani a fuskar Momie, itama kukan ne ya sake zo mata cikin tashin hankali take cewa,

  "kiyi haƙuri Momie, ki yafemin don Allah, Babu inda zan tafi in barki"

  Rungumeta Momie tayi tace "bakimun komi ba Hafsatul kiram, naji daɗi sosai Allah yayi miki Albarka"

   Cikin shessheƙar kuka tace,

  "anma Momie ya zanyi da ƙiyayyar da Ya Umar yamun?"

  Momie tace "karki damu Hafsatul Kiram, Yanzu idanun Umar a rufe suke, Dole wata rana zaiyi dana sanin Abinda yake miki, kici gaba da haƙuri kinji, Amma don Allah ki daina maganar tafiya gida"

  Tace "na daina Momie", 

Momie ta daɗe tana kwantar mata da hankali da kalamai masu daɗi, sai da ta tabbatar ta samu nutsuwa sannan ta mata Sallama ta tafi,

 

Haka Hafsatul kiram taci gaba da zaman haƙuri da Umar, duk abubuwan da take mishi bata fasa ba, in tayi mishi abinci sanda yaga dama yaci, randa bai dawo gidanba sai dai yanda ta ajiye ta ɗaukeshi haka,

  Yau da fever ta kwana haka ta daure da safe ta tashi ta haɗa mishi break fast ta jera, sannan ta koma daki taci gaba da jinyar kanta, Ita kaɗai cikin gida take ta fama da rashin lafiya,

 Haka ta yini da tsananin rashin lafiya har dare ta kasa fitowa, girki ma kasayi tayi sai dai tea taketa sha gashi ko magani bata dashi.

 

 

Da dare Umar ya dawo, bai ganta falo ba tana zaman jiran dawowarshi kamar yanda ta saba, ya duba dinning bata ajiye mishi abinci ba, ɗakinshi ya wuce yana tunanin kodai ta tafiyanta ne?

  Yace, "data kyautawa kanta kuwa"

 

Umar ne zaune yana kallon ball, ya hango hafsatul kiram na fitowa sanye da riga da wando sun matseta sosai, ta zubo gashinta da yasha gyara ta rataya dan mitsitsin gyale a kafaɗarta, tana tafiya cike da salo da rangwaɗa buɗe baki yayi yana kallonta harta ƙaraso inda yake bai sani ba,

 Ta mika hannu ta ciro mukullan mota a aljihun gaban rigarshi sannan ta juyo ta nufi hanyar fita, cikin tsawa yace,

   "ke! Ina zakije?"

  Tace "inda kake zuwa kullum mana Zan fitane nima inyo abinda kake yowa, ka kasa tsaremun kanka ni miye amfanin na zauna ina tsare maka kaina? Baka damu da zamana a gdannan ba miye amfanin inta zama?"

  Cikin ɗaga murya yace,

   "kina da hankali kuwa? Kefa macece"

  "su wanda kake fita kana tafiya wurinsu ba mata bane?" Miƙewa yayi cikin ɓacin rai da niyyar marinta, 

  da zafin nama ta riƙe hannun tace,   

   "ban gama ba!"

Kallon mamaki ya bita dashi kafin ta maidashi ya zauna kamar wanda akaima satar kuzari, ta duƙo saitin fuskarshi wannan karon cikin tattausan murya mai cike da damuwa take magana,

  Tace "kasan yanda mutum keji a duk lokacin da yayi ƙoƙarin nunar da jama'a babu abinda ke damunshi, anma babu abinda yake tafiya mishi dai-dai? Kasan yanda mutum keji idan yana murmushi a fili, anma yana kuka a zuciarshi? Kasan yanda mutum keji idan mafarkinshi, burinshi, abinda yakeso ya kasa mallaka?

Kasan yanda mutum yakeji idan wanda yafiso ya tsaneshi ya fifitashi fiye da wani? Ni kaɗai nakejin haka a zuciata, nasan wata rana dolene kaima zakaji hakan, Zanci gaba da sonka da zuciyarda kullum take ƙuna a kanka, Zanci gaba da sonka da wannan marainiyar zuciar tawa, Soyayyatah nada ƙarfin da babu wanda zai iya maka kwatankwacinta har Abada!!!"

 Firgigit Umar ya farka daga barcin da yake, dafe kanshi yayi maganganunta na cikin mafarki na dawo mishi, jikinshi yaayi matuƙar sanyi, Abubuwa da yawa ke dawo mishi cikin kai. Tabbas akwai wani abu tattare da wannan mafarkin

  Dai-dai lokacin Hafsatul kiram ta farka dafe da ƙirji, itama irin mafarkin da tayi kenan, innalillahi wa'inna ilaihir raji'un kawai take maimaitawa, istigfari kuwa tayi yafi cikin carbi, Hawaye ne a fuskarta, a fili take furta,

  "Ya Allah ka yafemin, ya Allah karka nunamin ranar da zanyiwa mijina magana irin haka, Ya Allah karka nunamin ranar dazan saɓa mishi", Hannu tasa ta share hawayenta.

 Lokacin gari harya fara haske batasan sanda barci ya ɗauketa saman sallaya ba, Miƙewa tsaye ta farayi da niyyar shiga kitchen ji tayi bazata iya ba, jikinta yayi zafi sosai, ga wani irin jiri da takeji,

  Daƙyar ta miƙe, ta ɗaura niƙab ta fita ta ba ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan kuɗi ya sawo mata magani, komawa gida tayi don bazata iya jiranshi ba saboda wani irin jiri da takeji ga ciwon kai mai zafi.

 Umar ya fito da shirin tafiya office har lokacin jikinshi a sanyaye yake, ya duba dinning bai hango break fast ba, daga nesa ya dinga leƙen kitchen kozai hangota anma batanan, ji da kanshi ya hanashi dubawa ɗakinta ya nufi hanyar fita,

 Sai daya fita daga falon a hanya yaga ɗan aiken hafsatul kiram tsaye da leda yana jiranta da yake basu shiga gidan, Umar ya kalleshi yace,

  "wannan laidar fa?"

Cikin girmamawa Yace,

  "hajia ce ta aikeni in siyo mata magunguna"

  Miƙa hannu yayi jikinshi duk ba ƙwari ya ansa yace,

  "yi tafiyarka kawai"

Komawa yayi cikin gidan, ya shiga ɗakinta can ya hangota ƙarshen gado ta nannaɗe wuri ɗaya sai kyarmar sanyi take, matsawa yayi inda take ya tsaya yana ƙare mata kallo,

 Jikinta ya bata ana kallonta, a hankali ta buɗe ido, ganinshi da tayi tsaye ya sanyata saurin tashi zauneGabanta na faduwa ta kasa hada ido dashi,

  Saman bedside ya ɗaura mata ledar magungunan sannan yace,

  "baki lafiya ne?", ɗaga mishi kai tayi muryarta na rawa saboda yanayin yanda takejin jikin tace,

  "masassara ce kawai, nasan idan nasha magani zanji sauƙi"

  Shiru tayi wani irin farin ciki na ratsata, wai yau Yaa Umar ne da shigowa ɗakinta ba tare da yayi mata tsawa ba ko rashin kirkin daya saba,

 Ɗaga mata kafaɗa yayi na nuna rashin damuwa, ya buɗe baki zaiyi magana kira ya shigo a wayarshi, ɗauka yayi da sauri yasa a kunnenshi sannan ya juya ya fita yana cewa,

  "Honiee, haba kema kinsan bazan iya fita office ba tare da munyi waya ba"

 Wani hawayene suka zubo ma Hafsatul kiram tabi bayanshi da kallo, tabbas tana cikin damuwa.

 

Maganin tasha sannan ta koma ta kwanta tanajin wani irin radaɗi a cikin zuciarta, A haka barci ya dauketa cike da mafarkai kala-kala, Masu daɗi da marassa daɗi.

 Sai kusan 11am ta farka, lokacin kan yaa rage mata ciwo anma jikinta babu ƙwari, Tana dafa bango har takai toilet, ta shiga tayi wanka sannan ta fito,   

  Lokaci ɗaya harta fara ramewa daman ba ƙiba ne da ita ba, Mai ta shafa kawai da hoda, sannan ta ɗauki kayanta ta saka, ta daɗe tsaye a gaban madubi tana kallon kanta babu hijabi, hawayene suka zubo mata, ta ɗauki wayarta tana kallon hotan Umar wani sonshi na ƙara shigarta.

 A fili ta furta "kayi haƙuri Ya Umar da ban zamo kalar matar da kakeso ba, na kasa zama kalar matar da kakeso"

Kira ne ya shgo wayarta daya katse mata kallon Umar din nata, sunan Aunty Rabiatu ta gani rubuce a secreen ɗin, dadine ya ratsa mata zuciah daman tana kewar Auntyn tata, sai da ta zauna bakin gado saboda yanda takejin tsayuwar sannan ta dauka,  

  "Auntyna ina tunaninki sai gashi kin kirani"

  "haba Hafsatul kiram anyama kina tunawa dani? Ya naji muryarki kamar baki lafiya?"

  Tace "laah waini Aunty? Babu komi ƙalau nake"

   "ki faɗamun gaskiya kodai Umar ɗinne har yanzu?"

  "A'ah wallahi Aunty masassara nake anma da sauƙi, anma ynzu komi yaa wuce tsakanina da Ya Umar, Yana sona sosae"

  "wane irin da sauƙi kunje asibiti ne?"

  Hafsatul kiram tace, "A'ah nasha magunguna fa"

  "maganar kawai, anashan magani ne ba bisa ƙa'ida ba? Bari in kirashi yanzunnan ya kaiki asibiti"

  Tace "Aunty naaji sauƙi fa," bata jira ba har wayar ta katse, Ta jingina da gado tana tunanin masifar dazai sauke mata inya dawo,

  Umar ne zaune cikin mota da Deezy, yana wasa da yatsun hannunta yana kallonta idanunshi cike da soyayya,

   "ke kaɗai nakeso zuma, ya kamata ki yarda da hakan, kawai tana zaunene a gidana anma ke kaɗai nakeso" 

  cike da damuwa tace,

  "ko kanason Hafsatul kiram ko bakason ta matarka ce, tana zaunene a gidanka a matsayin matarka, niko fa? bazaka gane irin sonda nake maka bane, Wlhy idan har ban aureka ba zan iya kashe kaina, bazan iya jurar rashinka ba"

 Yace "kima daina tunanin hakan, Umar naki ne ke kaɗai, ni kaina bazan iya rayuwah babu ke ba, ke kadaice farin cikinah, Kuma kin kusan zama mallakina"

  Kiran daya shigo wayarshi ne ya katseshi, ya ɗauka ya kara a kunne, 

  "to", kawai yake cewa har ya gama wayar, ranshi yayi matuƙar 6aci, watau yarinyar nan ta fara had'ashi da dangin mahaifiyarta ba? Kaasa daurewa yayi, sallama sukai da Deezy yaja motarshi da gudu ya nufi gidan saboda yanda yakejin zuciarshi.

 

Hafsatul kiram ta shirya tana kwance bakin gado tana jiran dawowarshi har niƙab taa ɗaura, Auntynta ta kira tace ta shirya anma duk da haka zuciarta fargaba take,

  Da ƙarfi ya buɗe ƙofar ɗakin ya shigo kamar zai ɓallata, ta miƙe tsaye tana kallonshi a tsorace yace,

  "ita batasan ina da abinyi bane da zatace saina kaiki asibiti? Na fada mata ba lokaci ne dani ba anma tawani matsa saina kaiki asibiti"

  Kanta na a ƙasa bata bari hawayen da suka tarar mata sun fito ba tace,

  "kayi haƙuri, batasan kana busy bane, anma idanka bani izini zanje da kaina, Nasan baka da lokaci,bazata san baka kaini bama"

  Shiru yayi yana kallonta a sanyaye yanason yaji tausayinta anma tsanarta ta hana, yace,

  "nina hanaki fitane? Kije duk inda zaki mana"

 

Wuceshi tayi ta fita, tana tafiyarta har bakin titi daƙyar tana haɗa hanya ciwon kanta naa ƙaruwa,Tsayuwar mota taji a bayanta bata waiwaya ba sai dai yasha gabanta da mota baice komi ba ya buɗe mata, sai da ta waiwaya ko ina taga ko ba ita ba, sannan ta buɗe motar ta shiga cikin mamaki da tsoro ta maida kanta gefe yaja motar suka tafi,

 Tsadadden asibiti ya kaita, yananan aka dubata aka basu result da magungunan da zata dingasha, fuskarshi ba yabo ba fallasa ya maidata gida.

  Tace, "nagode," ya kauda kai gefe baice mata komi ba.

 

Da tasha magungunan taa ɗanji sauƙi anma duk da haka jikinta ba ƙwari, ciwon zuciah ne akace yana so ya kamata,

 Ranar ma barci ta wuni yi bata samu tayi komi ba, sai data farka taga takeaway ya ajiye mata, Hawayene suka zubo mata da ita kanta batasan dalilinsu ba.

 

Kwana biyu tayi tana jinya sannan ta ɗan samu sauƙi, bai zaman gidan anma yana ajiye mata abinci shima bazai mata magana ba sai dai inta fito ta gani,

  Taji sauƙi, taci gaba da yi mishi girki kamar yanda ta saba da gyaren ɗaki anma ta daina zaman jiran dawowarshi falo, sun daina haɗuwa kamar matar kulle kullum tana cikin daki.

 

Rannan ya sameta ɗakin zaune kan sallaya tana karatun Qur'ani kamar wanda aka turo yayi mata tsaye saman kai cikin hargowa yace,

  "waike me kike nufi da zaman ɗakinnan? Wani sabon salo ne kija ace ina muzguna miki ba?"

 Da sanyayyar muryarta tace,

  "A'ah kawai na lura ganina ne ka tsana a gidannan, Ina takura maka shiyasa nake ƙoƙarin daina nuna maka fuskata"

  Shuru yayi yana kallonta, kafin ya juya ya tafi duk ta kashe mishi jiki.

 

Washe gari ya dawo daga office mai gadi ya buɗe mishi gate zai shigo da motar, 

  Yace "Ranka shi daɗe ɗazu an aiko Hajia bata lafiya"

  Umar ya kalleshi a firgice yace,

   "Momie bata lafiya? Meya sameta?" Yace,

  "wlhy ban sani ba anma Hajia tanan tafi, tace idan kazo a faɗa maka tayita kiranka bata samu ba"

  Shiru yayi kafin yace,

   "shikenan"

Fasa shiga gidan yayi ya juya ya nufi hanyar gidan nasu zuciarshi cike da tunani kala-kala. 

 Yanayin parking ya buɗe motar ya fita cikin sauri ya ƙarasa falon Momie, kwance ya hangota Hafsatul kiram na gefenta da towel a hannunta ta jiƙashi da ruwan sanyi tana d'ora mata a goshi, sai sannu take mata fuskarta cike da damuwah kamar ciwon a jikinta yake.

 Gani tayi Momie na ƙoƙorin tashi zaune, ta taimaka mata ta zaunar da ita sai sannu take mata, Yana tsaye batasan da zuwanshi bama sai kallonta yake yanda take kula da Momie ya kasa dauke kai,

  Ƙarasawa yayi kusa da Momie da sauri Hafsatul kiram ta miƙe ta bashi wuri ya zauna yace,

  "ya jikin momie?"

  Tace, "da sauƙi daman zafin masassara ne, yanzu kam Alhmdlh jiki yayi sauƙi da taimakon Hafsatul kiram tun ɗazu take nan tana kula dani"

  Baice komi ba, don Hafsatul kiram ma fita tayi ta basu wuri lokaci-lokaci take shiga ta dubo Momie.

 

Basu bar gidan ba sai bayan isha'i, a motar Umar duk yaayi suku-suku dashi

Tare suka shiga gidan bayan ya gama parking, babu mai yima wani magana cikinsu ya nufi ɗakinshi, itama harta juya zata tafi nata kamar ance ta jiyo,

  Maciji ta gani ya tafi sululu inda Umar yake, da sauri ta ƙwala mishi kira.  

   "Ya Umar"

  Ya juyo yana kallonta baima kula da macijin yaa kusa zuwa inda yake ba,

 Lura da hakan da tayi ya sanyata rugawa da hanzarinta ta riƙe kan macijin idanunta rufe ta murɗe kan, yakai mata saara, anma bata sakeshi ba saida kan ya fita taa faɗi ƙasa luuu, da sauri Umar ya riƙeta ta faɗajikinshi.

 

A ruɗe ya ɗauketa ya fita da ita zai saka mota, mai gadi Ya taso yana cewa  

  "lapia ranka shi daɗe?"

  Cikin ruɗewa ya faɗa mishi sannan Yace,

  "buɗemin gate asibiti zamuje"

Mallam mai gadi yace "ranka shi dade ai kamata yayi ayi mata na hausa, anyi sa'a kuwa bani rabuwa da maganinshi bari in ɗauko, da hanzari yaje ɗakinshi ya ɗauko,

  Umar duk ya ruɗe sai jijjigata yake, jiƙa maganin akai ya ɗura mata a baki yanda zai shiga cikinta, yana shafa mata ruwa a fuskarta,

  Tana buɗe ido ta fara kwarara Amai baƙiƙirin a jikin Umar duk ta ɓata mishi jiki, shikam sannu kawai yake mata ta

a kasa magana jikinta ba ƙwari duk yayi laƙwas kallansu kawai take tana lumshe ido daƙyar saboda wahalan da tasha,

  Ɗaukarta yayi ya kaita d'akinshi, ya kwantar da ita saman gado yaa kasa canza mata kaya ko hijabin yaa kasa cire mata, sai dai ya kunna mata A/C, toilet ya shiga yayo wanka ya gyara kanshi,

 Ƙasa ya saukar da filo saitinta ya kwanta, baiyi wani barcin kirki ba hankalinshi na kanta, ita kam barcinta takesha cike da gajia ga wahala kuma,

 

Ana kiran sallar Asuba ta bud'e idonta a hankali, lokacin ya fita masallaci bai tasheta ba, ta shiga toilet tayo alwala ta fito ta tada sallah bata koma ɗakinta ba, hannunta nayi mata zogi sosai, daurewa kawai take,

  Gari har ya fara haske ya shigo tana zaune saman sallaya ta gama azkar, riƙe take da hannunta sai cije baki take saboda azaba ya shigo, ta miƙe da sauri zata bar d'akin, 

  Yace,

   "ina zakije?"

  Tace "break fast zan haɗa, gari harya fara haske"

"da baki lafiyar?" 

  Tace "ai zai bari ne",

ta wuceshi zata fita ya riƙota ya maidata kan gado ta zauna, ya ciro maganin Aljihunshi, ya kamo hannunta, ya fara shafa mata a hannunta,

   "malam mai gadi yace idan aka shafa miki insha Allah zai daina miki zafi"

  Batace mishi komi ba, kallonshi kawai take riƙe da hannunta, cike da shauƙi batasan ma sanda ya gama ba, shima tsayawa yayi yana kallonta da sauri ta sadda kai, 

  Ya ɗan nisa cike da jin kunyar kanshi Yace,

  "Tabbas Hafsatul kiram, Momie tayi gaskiya, Bazan taɓa samun mata kamarki ba, ke mace ta gari ce, kowanne namiji zaiyi alfaharin samunki a matsayin mace, naa dad'e ina cutar dake, don Allah ki yafemun hafsatul kiram, Kin sadaukar da taki rayuwar saboda ki ceci tawa kawai, duk da kinsan zaki cutu, don Allah ki yafemun"

 Ɗago kanta tayi ba tare dasun haɗa ido ba tace,

  "Ai kai mijina ne Ya Umar, tsare haƙƙoƙinka, yi maka biyayya, da bin umarninka ya zamemin dole, ka daina kunyata ni wurin neman yafiya a wurinah"

Tashi tayi ta fita, ta barshi zaune jikinshi duk yaayi sanyi da kalamanta, kaasa motsawa yayi maganganunta naayi mishi yaawo akai, anya akwai sauran mata irin Hafsatul kiram a duniya? 

 

Ɗakinta ta wuce ta kwanta, sai kallon silin take tana juye-juye, jinta take a wata duniyar daban, ta kasa gane farin ciki take kome? Yanayin data kasa ganewa kenan,

  Tana cikin tunanin ya shigo da shirin tafiyarshi office, ya ajiye mata take away Ya duƙa saitin fuskarta ta rufe ido, 

  Yace,

  "akwai abinda kikeso in taho miki dashi?"

   Tace, "A'ah, Allah ya kiyaye hanya, ya dawo dakai lafiya" Bai samu fuskar ƙara yi mata magana ba duk kunyarta yakeji ma yayi sukuku, Yace,

  "idan dai kinji kina buƙatar wani abu kimun waya"

  Batace mishi komi ba harya tafi,

 

Bayan kwana biyu, Da yamma Umar ne da Deezy zaune wurin wani shaƙatawa, yayi shiru ya rasa ta inda zai fara mata, fuskarshi cike da damuwa yaa kasa bud'e baki ya mata magana,

  Tace "Masoyi ka kirani kayi shiru, gashi da alamar damuwah a fuskarka, Hafsatul kiram ce ta ɓata maka rai ko?"

    Ya girgiza kai yace,

   "tabbas inada damuwah, Anma ba daga Hafsatul kiram bane, tabbas na cika son kaina, na damu da farin cikina ne kawai ban damu da nata ba, Deezy na cutar da rayuwar Hafsatul kiram da yawa, Anma ya isa haka, yanzu ne na gane inason matata Hafsatul kiram, kiyi haƙuri da soyayyarmu"

  Miƙewa tayi tsaye kamar wadda aka tsikara, tana nunashi da yatsa tace,

  "meka ɗaukeni ne Umar? Ka maidani kamar wata ƙwallon da zaka buga duk sanda kakeso? Kason irin sonda nake maka anma duk sanda na saki jiki muna soyayya saika barni?"

  Yace, "ki fahimceni Deezy, Hafsatul kiram matatah ce, nasan dole zakiji ciwo a zuciyarki, wannan ciwon shi Hafsatul kiram ta dade tanaji a zuciarta, Bazan iya ci gaba da aikata kuskure guda ɗaya a rayuwatah ba, Inason Hafsatul kiram"

  Bai jira me zatace ba ya raɓa ta gefenta ya wuce, tace,

  "ka saurareni Umar!, u cant just leave me like this"

  Ko waiwayenta baiyi ba ya wuce yabar wurin.

 

Yana isa gida ɗakin Hafsatul kiram ya wuce tana gaban madubi, tsayawa yayi yana kallonta yaa kasa d'auke idonshi a kanta, ba ƙaramin kyau tai mishi ba, wannan ne rana ta farko daya fara ganinta babu hijabi, juyawa tayi suka haɗa ido taga ita kawai yake kallo ko ƙiftawa ba yayi. Sai lokacin ta lura bata saka hijabi ba kunya duk ta lulluɓeta ta jawo hijabinta ta saka.

 

Sannan ya saki ajiyar zuciah ya ƙaraso inda take, tsayawa tayi tana kallonshi ba tare dasun haɗa ido ba, hannu yasa ya cire mata hijabin, ta sadda kanta kunya duk taa lulluɓeta,

  Hannu ya sanya ya ɗago da fuskarta yace,

   "nafison ganinki a haka Hafsatul kiram, ki daina ɓoyemun kyawunki"

  Tayi murmushi har lokacin idanunta a ƙasa, ya zaro takardu a cikin aljihunshi ya miƙa mata, 

  tace, "na menene? Yace "ki gani da kanki.

 Takardun asibiti ne, Awon H.I.V, duk babu ta dago ta kalleshi,

  Yace "Addu'ar da kika daɗe kina yimun ne Allah ya amsa, zan miki alƙawari tsakaninah dake, daga Yau babuni babu wata mace, babu ni babu shan duk wani abin dazai sakani maye, ki yarda dani Hafsatul kiram Inasonki sosai zan sanyaki farin ciki har ƙarshen rayuwatah"

 Rumtse ido tayi daɗi na ratsa mata zuciah, ji take kamar tafi kowa farin ciki da dace, lallai mahaƙurci mawadaci, buɗe baki tayi zatayi magana tama rasa me zata faɗa, murmushi kawai take a fuskarta

 

Wayarshi ce tayi ringing, ya ciro ya duba sunan Deezy ne a screen ɗin, Hafsatul kiram ya kalla yaga bashi take kallo ba ya maida wayar silent ya ajiye, wani kiranne ya ƙara shigowa bai ɗauka ba harta ƙara katsewa, kusan sau biyar da yaga bata da niyyar daina kira ya kalli

Hafsatul kiram Yace,

  "ina zuwa", 

da murmushi a fuskarta ta ɗaga mishi kai ya fita falo ya ɗaga wayar,

  Muryarta da alamar kuka take magana,

  "honiee don Allah karka gujemun, bazan iya rayuwar da babu kai a tare dani ba, inasonka karka cutar dani ta wannan hanyar"

  Yace, "kiyi haquri Deezy Hafsatul kiram ita kaɗaice matata, da ita kaɗai zan kasance har abada"

  "kana nufin ka daina sona?"

Bai bata amsa ba ya kashe wayar, Ya juya ya koma wurin hafsatul kiram.

  Wurgi tayi da wayar ta tarwatse zuciyarta kamarta fashe duk abnda ke kusa da ita saida tayi wurgi dashi, ta faɗa saman kujera ta saki wani irin kuka,

 

Hafsatul kiram ta kasa sakin jiki da Umar, shi kuma sai ji yake da ita yana bata kulawa, idan ya shigo bai bari ta zauna nesa dashi, data tashi zai bita inda zai dinga kallonta, Ko kitchen zata shuga suna tare, wata irin kulawa ta musanman yake nuna mata.

 

Ranar week end tare suka shiga kitchen, sai abnda bata sanyashi ba yakeyi, mai ne ya fallatsar mata a hannu da sauri ta janye tana yarfe hannun, ya ƙaraso inda take da sauri hankalinshi duk ya tashi, bata kulashi ba ta juya taci gaba,

  Baiga fuskar taɓa hannun nata ba, cikin muryar damuwa yace,

  "ƙonewa kikai?"

   "A'ah"

  kawai tace mishi taci gaba da abinda take, daman maganar kenan tsakaninta dashi ko kad'an bata sakar mishi fuska,

  Harta gama duk don son ta mishi magana yace,

   "ki shirya yau gidan Momie zamuje"

  Da murnarta tace,

   "dagaske?"

    "da wasa nake", ɓata rai tayi taci gaba da zuba mishi abinci,

   Yace, "kinga ni dagaske nake, ki shirya dana gama canja kaya kawai zanyi zamu tafi,

  "Tohm"

   kawai tace mishi,

Tare suka shiga gidan sai ƙoƙarin jerawa yake da ita, tana shiga falon da sauri ya kamo hannunta ya riƙe, juyowa tayi tana kallonshi cikin tuhuma ta ɗaure fuska, ya kashe mata ido ya jawo hannunta saitin bakinshi yana shrin mata kiss, ta zaro ido tace,

   "Yaa umar",

  Tana ƙoƙarin janyewa, Momie tayi gyaran murya duk suka waiwaya,

  Har lokacin hannunta na saƙale a cikin nashi sai ƙoƙarin cire nata take anma yaƙi saki duk kunya taa kamata,

  Momie sai murmushin daɗi take tace,

   "Yanzu kam na tabbatar da ka canja", 

  da sauri Yace, "na canja sosai mana Momie"

  Tace, cikin zolaya "anma Hafsatul kiram ce sanadi, Itace ta canjaka da kyawawan halayenta"

 Murmushi kawai yake bakinshi yaƙi rufuwa yace,

  "tabbas Momie Hafsatul kiram ce ta canjani, na canja sosai kuma ina sonta, Nayi miki alƙawarin zan riƙeta amana, zan sanyata farin ciki har ƙarshen rayuwatah, Bazan taɓa bari tayi damuwah ba,"

   Nomie cike dajin daɗi tace,

    "gaskia naji daɗi sosai, Allah yayi muku albarka"

   Yace "Ameen Momie, ga ajiyatah nan, banson in barta ita kaɗai ne akwai wurin da zanje"

  "ka tabbata dai ba irin wurinnan bane?"

  "ba can bane wallahi Momie"

  Ya juya yana kallon Hafsatul kiram ta sadda kai cikin jin kunya, Addu'a ta mishi sannan ya juya ya tafi.

 

Gidanshi ya koma saboda yayi mantuwa, tun daga nesa yake hangen motar Deezy tana ƙoƙarin shiga gidan, yana niyyar komawa da sauri ta juyar da motarta tasha gabanshi, tamke fuska yayi yama ƙi fitowa, sai itaje ta sameshi, ta buɗe motar ta shiga, tun kafin tayi magana ya rigata,

   "Deezy sau nawa zan faɗa miki ki daina nemana? Na faɗa miki yanzu babu wata alaƙa tsakanina dake, soyayyarmu tazo ƙarshe"

  Idanunta jajir take kallonshi cikin ɓacin rai, a hankali kamar mai rowar magana tace,

  "kaa tuna dana faɗa maka mutuwa zanyi idan har ban sameka ba?? Idan har soyayyarmu tazo ƙarshe, Rayuwata ma taazo ƙarshe"

  Ta zaro wuƙa ta saita a maƙoshinta tana kallonshi,

  Cikin ruɗewa yake kallonta maganarshi na sarƙewa yace,

   "me kike shirinyi"

  "naasan kana sona dear, don Allah ka faɗamin kace kana sonah, idan har na ƙirga uku baka faɗa ba zan kashe kaina ne"

  "haba Deezy ki daina mana, wannan ba wasa bane," ya matsa zai nufeta yana ƙoƙarin amshe wuƙar, ta ja da baya tana cewa "ba wasa nake ba, wlhy zan kashe kainane a gabanka, Kawai ka faɗa, kace Ina sonki Deezy", 

  girgiza kai yayi zaiyi magana kafin yace wani abu ta yanka hannunta,

  Jini keta zuba a ruɗe ya rumtse idonshi yace,

   "ina sonki honiee"

  Rungumeshi tayi cikin farin ciki tana share hawaye, 

  "ni daman naa sani, nasan kana sona Umar, Hafsatul kiram ce takeso ta rabamu, bazan taɓa bari ba, bazan taɓa bari ta rabamu ba,"

  Ta kwantar da kanta jikinshi tana ta sambatu.

 

Shikam shiru yayi kamar wanda aka dasa, ya kasayin komi, ya rasa me zaiyi,

   Takarda ta ɗauko da biro cikin takardunshi ta miƙa mishi tace,

  "ka rubuta mata takardarta yanzu, don Allah umar karka bari ta ƙara rabamu"

  Cikin mamaki yake kallonta yace,  

   "kinyi haukane Deezy?"

  "indai a kanka ne ka kirani da koma miye Idan bazaka rubuta ba nizan rubuta kakai mata, harta fara rubutun ya fizge takardar ya kekketa"

  yace, "baki da hankali, taya kike tunanin zan iya sakin Hafsat? Ina sonta bazan taɓa rabuwa da ita ba"

 

Ba tare da tace mishi komi ba, ta buɗe motar ta fita idanunta naa zubar da hawaye,

 Dafe kanshi yayi cikin tashin hnkali ya jingina da kujerar, tunani ne ke mishi yawo a ƙwalwa, Ya rasa samun mafita, ji yake kamar ya rufe ido ya buɗe yaga mafarki ne, bai taɓa shiga tashin hankali irin haka ba,

  

Ya gama abunda zaiyi, yana sauri ya koma gidan Momir wurin matarshi, yaji shigowar kira a wayarshi, ya duba number Deezy ce kamar bazai ɗauka ba kuma saiya ɗaga, shiru yayi daga can aka fara magana Muryar namiji ne,

   "daga asibiti ne an kawo mna patient mai wannan number tayi accident, kuma wannan number ne aka kira ƙarshe"

  da sauri ya taka burki yana tambayar,

   "wane asibitin?" Ana faɗa mishi da sauri ya juya motar ya nufi asibitin,

 

Ɗakin da aka faɗa mishi ya shiga tana kwance idanunta a rufe, a goshinta da hannu ne kawai taji ciwo sai dai har lokacin bata farka ba,

  Tsayawa yayi yana ƙare mata kallo, tunaninshi duk ya tsaya jinshi yake kamar bashi ba, shiya biya duk kuɗaɗen da ake buƙatah, likitan yace zasu iya tafiya data farka indai akaga babu wata matsala,

  Har magriba bata farka ba saida ya fita sallah ta fara buɗe ido a hankali tana ƙare ma ɗakin kallo, 

  Hafsatul kiram ce taji shiru bai dawo ba, kasa daurewa tayi ta ɗauki wayarta ta fara buga mishi taji ko lafiya, wayar na kusa da Deezy ta fara ƙara, dubawa tayi taga wayar Umar ta miƙa hannu ta ɗauka, sunan Hafsatul kiram ta gani a jiki ta d'auka tana murmushin mugunta.

  Hafsatul kiram tace "lafiya Yaa umar? Naji shiru ne baka dawo ba, kuma kace bazaka daɗe ba"

 Muryar Deezyce ta doki kunnuwanta,

   "lafiya lau yake Hafsatul kiram, kuma tare yake dani, karki damu"

  Hankalin Hafsatul kiram ya tashi, jikinta har kyarma yake wayar ma fara gagararta riƙewa tayi,

  Deexy taci gaba da cewa,

   "nina rasa irin wannan naci naki, honieenah Yace bai sonki ya faɗa miki yafi a ƙirga anma kin kasa fita rayuwarshi, don tsabar rashin zuciya daga Ya fara nuna miki kulawa shikenan kin saki jiki babu ko ɗan jan ajinnan, ai nikam Hafsatul kiram rakiyarmu kawai kikazo"

 

Kuka ne yaso ƙwacema Hafsatul kiram, da sauri ta fara kokawar korar hawayen dakeson zubo mata, don bai kamata ta bari Deezy taci gaba da rainata ba, cikin ƙarfin hali da jarumta tace,

  "ai wanda yasan darajar aure shi ke yima mijinshi biyayya, bazaki taɓa ganewa ba tunda bayi kikayi ba, bazan taɓa rabuwa da Ya umar ba matuƙar igiyoyin aurenshi na akaina wanda nasan bazai taɓa rabuwa dashi ba, soyayyar gaskiya daban take Deezy kuma na tabbatar da yanzu Ya Umar na yimun ita to miye amfanin in tsaya ja mishi rai bayan nasan kuma zan haƙura a gaba? Na yarda dason da Yaa Umar kemin,ina da yarda sosai akan mijina, bazan taɓa zarginshi ba Deezy ki canza wani salon,"

  Cikin hargagi Deezy ta fara magana don bata taɓa tunanin Hafsatul kiram nada baki haka ba,

   "ni kike faɗa ma haka? Kin manta da Umar nawa ne? Wulaƙanta rayuwarki, ƙaramin aikine a wurine, da ƙyastawar hannu kawai zan iya ƙuntata rayuwarki idan har ban rabaki da Umar ba, ba sunana Deezy ba"

  "ki canza, don Ya Umar bana mata mararsa kamunkai bane irinki, cika bakinki bazai taɓa tasiri a wurina ba",

Ta kashe wayanta bata jira me zata ce ba,

 

Kifa kai tayi saman gwiwa ta fara kuka tana tunanin to meya kai Umar wurin Deezy? Kar dai ace har yanzu suna tare. Har isha'i bai nemeta ba baizo sun tafi ba,

 Batason ta bama zuciarta dalilin da zataji haushinshi kota zargeshi, shiya sanyata share hawaye taci gaba da ƙuncin rai kawai, koda Momie ta tambyeta sai tace "yana hanya",

  Sai da ya ajiye Deezy gida don daman ba wani ciwo taji ba, sannan ya wuce gidan Momie, koda Momie ta tambayeshi inda ya tsaya cewa yayi wani abu mai mahimmanci ne ya tsaidashi,

 

A hanya suna tafiya da Hafsatul kiram zasu koma gida, duk haƙurinta kasa daurewa tayi don batason ta zauna da zarginshi, a hankali tace,

  "Ya Umar wane irin aikine ya ɗauke ka har cikin darennan?"

  Duk ya rikice zufa na feso mishi daƙyar ya iya cewa,

  "banma gama abunda nace miki zanje yi ba, office aka kirani, kira mai mahimmanci shiyasa na tafi"

  Daga kai kawai tayi Yace,

   "wani abu?"

  "A'ah Momie ce kawai ke cigiyarka",

 

Ajiyar zuciyah kawai ya sauke don ko kaɗan yanzu baiso yayi abinda zai sosa zuciyar Hafsatul kiram, Har sukaje gida bai dawo dai dai ba.

 Ɗakinta ta wuce shima ya wuce nashi don sunci abinci gidan Momie gashi a gajiye take, tana shiga shirin kwanciya tayi ta kwanta sai gashi shima ya shigo,

 Sauri tayi ta rufe ido kamar mai barci saboda kunyar kayan data saka duk sun bayyanar da surar jikinta, tsayawa yayi yana ƙare mata kallo wani irin Abu na fizgarshi daya kasa daurewa sai da ya ƙarasa inda take ya tsugunna dai dai saitin fuskarta, rufe ido tayi a hankali yake matsar da fuskarshi saitin tata ya haɗa bakinshi da nata, Rumtse ido tayi wani abu har cikin tsakiyar kanta, A hankali ya furta,

   "Ina sonki Hafsatul kiram, inason kyawawan halayenki, I've Fallen In Love With You And I'll Never Let You Go. I Love You More Than Anyone, I Don't Know What I'll Say, But I'll Never Stop Loving You, Each And Every Day"

 Hawayene taji suna ƙoƙarin zubo mata da sauri ta juya ta gyara kwanciarta, hawaye naci gaba da zubo mata yaci gaba da cewa,

  "kada ki taɓa juyamin baya Hafsatul kiram, don Allah ki kasance tare dani"

  Hawayen farin ciki ne kawai ke zubar mata, harya gama sambatunshi ya tafi dakinshi

 

Ranar kwanan farin ciki Hafsatul kiram tayi data tashi sallar tsakar dare taa daɗe tana kwarara godia ga ubangiji, bata gaza wurin ƙara nemawa Umar shiriya ba duk da ta tabbatar yanzu ya shiryu,

   Washe gari kasa daina farin ciki tayi, komai cikin annashuwa takeyi, tunda wuri ta gama haɗa mishi break fast, ta shirya cikin riga da siket na material tayi kyau sosae,

  Tana zuba ma Umar abinci kasa daurewa yayi da kallonta ya kamo tattausan hannunta yana murzawa, Ta d'an marairaice fuska,

   "Ya Umar abincin fa?"

  Ya langaɓar da kanshi,

  "kiyi aiki da hannu ɗaya"

Batace komi ba duk ta takura taci gaba da zuba mishi, Tana gamawa ya kamo ɗayan ma ya zaunar da ita yana kallonta,

  Da sauri ta sadda kai Yace,

"don Allah ki daure ki bani damar da zaki kalli cikin idona koda sau ɗayane Hafsatul kiram, Tsananin sonda nake miki banda damar dazan iya bayyana miki, anma wata ƙila zaki iya gani cikin idona, Ina sonki sosai Hafsatul kiram" 

  Murmushi tayi,

  "nagode", Har lokacin ta kasa ɗagowa su haɗa ido,

  "ni bazaki ce kina sona ba? Plz ki faɗamun ko zanji daɗi"

  Tafi minti biyu kafin ta iya buɗe baki daƙyar ta saka hannu ta rufe fuskarta,

  "ina sonka Ya Umar", Da sauri ta gudu ɗakinta, harya tafi basuyi sallama ba saboda wata irin kunyarshi da takeji.

 

Yana zuwa office wurin parking ya iske Deezy tsaye tana jiran zuwanshi, da sauri ta ƙaraso yana buɗe mota yayi kamar bai ganta ba zai tafi tasha gabanshi tace,

  "wai meyasa kakemin haka? Wulaƙancin ya fara yawa, Don Allah ka gane irin sonda nake maka, bazan iya rasaka ba"

 

Taɓe baki yayi yace,

  "kin riga kin rasani, bazaki taɓa samu nah ba, zakisha mamaki na idan har baki rabu dani ba, Jiya kin saka nayi ma Hafsatul kiram ƙarya, Bazan taɓa yafema kaina ba idan harna ƙara cin amanarta, Ki fita hanyata tun wuri", Ya wuce ta zai tafi,

 

Da ƙarfi tace,

  "haka ka faɗa? Ka gama yanke hukuncinka ba?, inaso ka sani idan har ban sameka ba bazan taɓa bari wata ta sameka ba"

 Ɗaga kafaɗa yayi yana Mata kallon matsalarki ce,

  "ban damu ba, kiyi duk abinda zakiyi", 

Ya juya ya barta wurin a tsaye tana huci ta shiga motarta ta kwantar da kanta saman sitiyari zuciarta na

a tafasa, wani tunani ne yazo mata a fili tace,

  "tabbas Ƙara in ɗauka mataki da wuri" Taja motarta tabar wurin.

 

Hafsatul kiram na zaune falo tana duba littafin hadith, suka buɗe ƙofar ɗakin da ƙarfi suka shigo, Su biyu ne maza gardawan ƙatti ko wanne da mugun makami a hannunshi,

  Da sauri ta miƙe tana kallonsu a tsorace duk ta rikice maganarta na harɗewa tace,

  "waya shigo daku gidana har cikin d'akina?"

  Deezy dake shigowa daga baya tace,

  "nice nan na shigo dasu, Kinyi mamaki ba? Meya sanya? Miye dalilina? Nasan tambayar da zakimun kenan duk da kinsan amsoshinsu, na lura ke kaɗaice matsalarmu nida Umar, idan har yana ganinki bazai ƙara kulani ba, bazan taɓa yarda kiyi nasara a kaina ba, bazan bari ki rabani dashi ba, tabbas yau zan kawo ƙarshenki.

 

Ta maida ƙofar dakin ta rufe da makulli,

   "yau zan kawo ƙarshen matsalata da Umar". Tana matsowa inda Hafsatul kiram take.

  Hafsatul kiram duk ta rikice ta ruɗe sai ja da baya take, juyawa tayi da niyyar rugawa Deezy ta sanya mata ƙafa ta faɗi ƙasa ta saki ƙarar azaba,

 

Ta kalli ƙattin da tazo dasu tace "kuyi sauri mubar gidannan, minti biyu karta ƙara shan numfashin duniyarnan"

  Ruɗewa Hafsatul kiram ta ƙarayi jin furucin Deexy ga wani irin buguwa da ƙugunta yayi sanadiyyar faɗuwan da tayi, Addu'ah kawai take a zuciarta duk tunaninta yaa kwance, anma duk da haka bata fidda ran Allah zai fitar da ita daga hannunsu ba.

  

Umar na office hakanan yaji gabanshi naa faɗuwa ya rasa sukuni duk ya kasa wani aiki ga takardu gabanshi, tunanin Hafsatul kiram kawai yake, wayarshi ya ɗauko yace, 

 "bari ya kirata dai yaji ynda take ko hankalinshi zai kwanta"

 

Wani daga cikin ƙattin ne ya matso inda Hafsatul kiram take fuskarnan tashi kallonta ma kara mata tashin hnkali yake, ta kasa furta komi saidai hawayen da take tana girgiza kai kamar tababba, Deezy kam na gefe sai murmushi take cikin nishaɗi,

  Wayar Hafsatul kiram ce tayi ƙara da sauri ta ja jiki wurin kujerar da wayar take ta miƙa hannu ta ɗauka zatasa a kunne, su duka ƙattin suka kece da dariya sannan wani yakai mata sara a hannun da wayar take, da sauri ta saki wayar ta kauce anma duk da hka sai da ya sameta jini ya fara tsiyaya,

   Wata razananniyar ƙara ta saki tana kallon jinin dake zuba tana hawaye cikin kakkausar murya yace,

  "ke har kina da damar ɗaukar waya a gabanmu? Lallai jinkirin da mukai wurin kasheki ne yasa kika fara samun ƙarfin gwiwa! Yanzu zamu gama dake",

  yakai mata wani uban naushi a hanci, ta fasa uwar ƙara cikin azaba, jinta take kamar ba'a duniya ba, kanta na juya mata kamarta cire fuskar ta huta.

 

Akan kunne Umar sun manta basu kashe wayar ba yayi wata irin zabura cikin rudewa bai tsaya wani tunani ba ya nufi hanyar fita, Abokinshi suka hadu ƙofar shigowa yana kallonshi duk ya fita hayyacinshi yace,

  "lafiyaka kuwa Umar?"

  "ƙalau nake Ahmad, don Allah kazomin da ƴan sanda yanzu gidana"

  Ahmad yana zaro ido yace, "lafiya kuwa? Meke faruwa?"

  "kai dai kayi abinda nace plz", ya tafi zai fita idonshi rufe ya kusan kaima bango karo,

Da sauri Ahmad yace mishi,

  "ga ƙofarnan", 

cikin ruɗewa Yace, 

  "na sani juyawa zanyi"

Ya ƙara dosar wani bango cikin mamaki Ahmad yace,

  "anya kuwa kana iya zuwa gidannan? Ni kaƙi faɗamun abinda ya faru"

  Yace "zan iya mana jikinshi ba ƙwari ya fita wajen motarshi,

 

Ikon Allah ne kawai ya kaishi gidan saboda wani irin gudu da yake shararawa gashi duk a ruɗe yake tafiya kawai yake, mai gadi ya taso ya buɗe mishi yana ganin yanda Umar ya shigo da motar yasan lallai babu lafiya donshi baimasan da zuwansu Deezy ba.

  Da gudu ya ƙarasa cikin gidan ya banka ƙofar falon da sauri ya jita a rufe, makullanshi ya jawo cikin hannunshi na kyarma ya buɗe ya banka ya shiga yana maida numfashi.

  Su Deezy duk sukayi cirko-cirko suna kallonshi, duk ta ruɗe tashin hankali bayyane a fuskarta,

  Wata irin zuciyah ce tazo mishi hango Hafsatul kiram na numfashi, dai-dai lokacin ƴan sandan sun ƙaraso, Cikin zafin nama ya ƙarasa inda take ya cakumi wuyanta ya fara kai mata bugu, idanunta duk sun firfito cikin tsoro, ihu kawai take daƙyar ƴan sandan suka ƙaceta duk taji jiki, ƙattinma suna ƙoƙarin guduwa ƴan sanda suka cafkesu.   

  Kamar wani zaki ya koma ana janyeshi Yana shakota Ahmad cikin ɗaga murya yace,

  "dukanta zaka tsayayi kota lafiyar matarka?" Sannan ya saketa hankalinshi ya fara dawo mishi da sauri ya ƙarasa inda Hafsat take jini na zubar mata ta ko ina.

 

Da sauri ya sungumeta hawaye na zuba a idonshi ya nufi hanyar fita, ya sakarma Deezy wani mugun kallo dake numfashi daƙyar idonta ɗaya jini ya kwanta, ya kalli ƴan sandan muryarshi cikin rauni da ban tausayi, kasa fita tayi maganar yana Kallon Hafsatul kiram da batasan inda kanta yake ba.

  Ahmad ne yaja motar zuwa asibiti ganin halinda Umar yake, a motarma ya kafa mata idanu ko ƙiftawa bayayi, ji yake kamar idan ya ɗauke idonshi akanta zata daina numfashi, hawayenma sun tsaya mishi sai dai wani abu da yakeji a zuciyarshi.

  Suna isa asibitin da sauri likitoci suka amsheta aka shiga da ita emergency, Umar kasa zama yayi duk yanda Ahmad ke bashi baki bai masan yanayi ba, kasa motsawa yayi ya kafe idanunshi wuri daya,

  Ahmad yace, "ka daure ko magana kayi zai rage maka damuwa, anma ina ganinka cikin halinnan nima bazan samu nutsuwar zuciyah ba, namiji kake pa, Hafsatul kiram addu'arka kawai take buƙata"

  Kasa cema Ahmad komi yayi tunanin yanayin da yaga Hafsatul kiram yayi yake, ko ina zubda jini take,Ta hanci da baki ga rauni a hannunta, likita ne ya fito da sauri Ahmad ya ƙarasa inda yake, Shikam Umar ko motsawa ma baiyi ba kallon likitan kawai yake.

  Likitan Yace "tana buƙatar jini ne cikin gaggawa, saboda taa zubda jini da yawa"

  Jikin Umar babu ƙwari yaje aka aunashi, jininsu yazo dai-dai cikin sa'a, har lokacin ko yayi magana bata fita duk ya shiga damuwa, Shima gado aka bashi saboda yanda yanayin jikinshi.

  Bayan awa shida Umar ya farka, kuma ya soma samun sauki, zafin da zuciyarsa takeyi ya rage sosai, 

  Bayan ya farfaɗone yaga Momie tazo, ta mishi sannu, sannan take tambayarsa meya faru dasu, 

  Nan ya kwashe komai ya gaya mata, 

 Momie tace,

  "wannan wace irin macece, sai kace bata da imani, Allah yakiyaye gaba" 

  Umar yace "ameen",  

Hafsatul kiram shiru-shiru kakeji bata farkaba, harkusan dare, nan kuma hankalin Momie dana umar yaƙara tashi, gashi gorar jinin da aka ƙara mata harta kare, amma hafsatul kiram shiru, 

 Momy da Umar suna zaune a gefen gadon Hafsatul kiram misalin ƙarfe goma na dare, 

  A firgice Hafsatul kiram ta sandara ihu, 

  "wayyo zasu kasheni, Ya umar kaceceni", ta tashi da ƙarfi, 

  Momie ta riƙo ta tana kauce-kauce,  Momy tace,

  "Hafsat Momy ce fa, ki buɗe idonki ki ganni"

  A hankali Hafsatul kiram ta buɗe idonta, suka haɗa ido da momy nan ta fashe da kuka, ta rungume Momy,

 Momy ta ƙanƙameta tana shafar bayanta, "kiyi shiru ki daina kuka, insha Allah komai yazo ƙarshe, kinji" 

  Hafsatul kiram tana shassheƙar kuka ta share hawayenta, ta fito daga jikin Momy, Momy tace,

  "kikoma kan gado ki kwanta",

  Momy ta riƙe hannunta, kafin su ƙarasa bakin gado, taji kanta na sarawa, kamar zai fita, wani irin zafi takeji, 

 Jiri ya fara ɗibarta, tana hannun Momy ta sulale ta faɗi kasa, 

  Tashin hankali na gano ƙarara a fuskar Umar, Momy tayi saurin riƙota tana jijjigata amma ina ta suma, a gigice Momy ta cewa Umar,

   "jeka kirawo likita" 

 Umar ya fita da gudu yaje ya kira likita, 

  Likita yazo yana duddubata yaga komai da sukayi mata normal, ba wata matsala, 

 Ya juyo ya kalli Umar,

  "ba wata matsala bace kawai shock ne ya ɗibeta amma ba wata matsala a cikin aikin da mukayi mata,"likitan yaɗan dakatar da maganarsa, a lokacin ya ɗaura hannunsa a kanta ya buɗe idonta ɗaya, sannan yasake ɗaura hannunsa a tsakanin wuyanta, sannan yaci gaba da cewa,

  "karku damu ba wata matsala insha Allah zuwa ajima zata farka, ku fita waje ku bata lokaci yanzu tana buƙatar hutu"

 

 Jikinsu ba wani kwari suka tashi suka fita tare da likita,

 

A can kuwa gefen Deezy, a ranar sunsha duka a gurin yan sanda, saida sukayi musu likis, suka galabaita sannan suka daina dukansu, 

  Da Kuma zancen gobe za'a makasu a gaban kotu,

Washe gari, 

 

Hafsatul kiram tafarka, cikin kwanciyar hankali, Umar yaje gida ya kawo musu kayan break.

 Momy ta haɗa mata tea, mai kwauri ta riƙa bata aka samu taɗan sha, daga nan kuma ta koma bacci, 

 

 9:00am Umar ya koma gida yayi wanka, sannan ya dawo asibiti ya sanar da Momy cewa zaije koto, 

 Momy tace, "Allah yabada saa",

 Umar yace "ameen, saina dawo, harya yabi hanya saikuma yadawo yace "inda wani abu da kuke bukata sai akirani asanar dani " 

  Momy tace "toh," 

Tsaye yayi yana kallon hafsatul kiram, wani mugun tausayinta yakeji, 

 Can dai ya juyo ya wuce koto, 

Koto tacika makil, 

 Deezy da sauran ƙattinta duk suna cikin kuliya, 

 Lauyan da Umar ya ɗauka, ya tashi yana bayani sosai daga ƙarshe ya ƙare da cewa "wannan shari'ar bata buƙatar jan dogon lokaci, domin wadanda ake ƙara sun amsa laifinsu na yunƙurin kisan kai, saboda haka ina rokon wannan koton da tayi gaggawar yankewa waɗannan mugayen mutane hukunci" lauyan yaɗan rusuna kafin yace,

  "nagode ya mai girma mai sharia", yana gama faɗan haka ya koma ya zauna, 

 Alƙali yaɗan tsaya yana ƴan rubuce rubuce, kafin yadago kansa yace, "abisa hujjoji da kuma kwararan dalilan da lauya ya bayar, koto ta yankewa waɗan nan mutane hukuncin zaman gidan yari shekara goma, tare da horo mai tsanani, sannan kuma babu beli" 

 Deezy ta ƙwalla ihu a cikin koton, ta dafe kai tana kuka, cike da nadama, tayi matuƙar danasanin abinda ta aikata, 

  Nan alkali ya daki tebur nan kaji koton taɗau sautin "kotttt" kowa yamiƙe tsaye saida alkali yafita sannan kowa yafita,

aka ja su Deezy aka wuce dasu gidan yari, 

  Umar kuwa yayi godiya ga lauyan sannan ya bashi kuɗaɗe masu yawa, sannan ya janyo motarsa yadawo asibiti, 

  Hafsatul kiram na farke ya shigo ɗakin, 

  

Sukayi ido hudu, ya sakar mata murmushi kafin ya ƙarasa wurinta yace,

   "ya jikin, ciwon ya daina miki zafi dai ko?"

   "dasauki" 

  "Allah ya baki lafiya" 

    "ameen" 

Ya gyara zama kusa da ita, yana kallonta cike da tausayi, kaman ya maida ciwon a jikinshi yakeji.

 

Satinsu ɗaya a asibiti, Hafsatul kiram ta samu kulawa sosai a wurin Umar, duk abinda takeso shi yake mata, ita kanta mamaki take yadda taga umar ya nuna damuwarsa sosai akanta,

  Saida Hafsatul kiram taji sauƙi sosai sannan aka sallamesu, suka dawo gida ..

Gidan Momie suka wuce, duk da taji sauƙi sosai anma Momie cewa tayi ta kwanta ta huta tunda jikin nata bai ida ƙwari ba.

 Sai da dare yayi Umar yaji shiru-shiru Momie batace suzo su tafi gida ba, sai kame-kame yake anma ta shareshi sai da yaga wuri ya ƙure ne ya shiga ɗakinta ta tsare Hafsatul kiram tana cin abnci ya shigo.

  Ta dago ta kalleshi tace, "ashe baka tafi ba? Yanzu nake cewa ka tafi ko bankwana babu"

  Da sauri ya ɗago kai duk ya ɓata fuska yace,

   "ban tafi ba Momie ita nake jira",   

    "itawa?" Ya saci kallon Hafsatul Kiram data sadda kai tana wasa da yatsunta,

   "nidai Momie kin gane fa, cikin shagwaɓa har lokacin bai saki fuska ba,

  Kanne dariyarta tayi ba tare data kalleshi ba tace,

   "ba yanzu ba saita samu sauƙi sosai don bazan baka ita a haka ba"

   "ta samu sauƙi fa Momie, kuma nima zan iya kulawa da ita"

    "ba yanzu bafa nace"

Juyawa yayi sumi-sumi yabar ɗakin cike dajin haushi, kaasa tafiya yayi yabar gidan nan ya zauna falo yanata saƙe saƙe yake, Ga wata irin soyayyar Hafsatul kiram da take fizgarshi, wani irin so yake mata da ko kadan baison ta mishi nisa ga tausayinta da yake lulluɓe dashi.

 

Momie ce ta fito lokacin dare ya fara nisa, can ta hangoshi kwance saman doguwar kujera ya ɗaga kanshi sama, da mamaki take kallonshi,

   "har yanzu kananan kenan?"

  Baice komi ba sai dai ya tashi zaune,   

   "idan ma nan zaka kwana ne ai kaasan inda ɗakinka yake, tashi ka tafi" tana nuna mishi hanya.

  Miƙewa yayi saida taga ya tafi sannan ta tafi ɗakinta harta shiga ta dawo tana leƙenshi, gani tayi ya dawo, cikin sanɗa ya nufi ɗakin Hafsatul kiram da sauri ta fito tana daga murya tace,   

  "ina kuma zakaje nan?"

Sosa ƙeya yayi, 

  "Momie ban mata sai da safe ba"

"tayi barci, zoka tafi bazaka kwanarmin anan bama, yarinya bata lafiya bazaka bartatai barci ba?" 

 

Momien ya sake yima saida safe, sannan ya ya fice daga falon duk baijin daɗin zuciyarshi yaso ya tafi da Hafsatul kiram.

  Ranar kwana yayi juyi saman gado daya juya fuskar Hafsatul kiram yake gani, matsuwa yayi gari ya waye yaje ya ganota,

 

Washe gari tunda safe Umar wanka kawai yayi ya shirya cikin sauri ya nufi gidan Momie.

  Hafsatul kiram ma farkawarta kenan ta shiga wanka ta fito ɗaure da towel ganin safiya ce batayi tunanin wani zai shigo ba, sai da tayi tsakiyar bedroom ɗin ta hangoshi kwance saman gado ya tsura mata ido, da sauri ta zaro ido jikinta har ya fara kyarma ta rasa yanda zatayi, kunyar kanta takeji sosai,

  Da gudu ta juya da nufin komawa toilet, ya taso cikin zafin nama yasha gabanta,

   "ina zaki koma ne?" Shiru tayi kanta a ƙasa kamar ƙasa ta tsage ta samu wurin ɓoyewa saboda tsananin kunya, ya ɗago kanta suka haɗa ido da sauri ta rumtse idanunta ya saki murmushi,

   "kinajin kunyar mijinki ko?"

Batace komi ba don ko motsi ta kasa, shi kuma kallonta kawai yake wata irin sha'awarta na fizgarshi, sai kallon bakinta yake dake matuƙar burgeshi, Idonta rufe sai dai taji bakinshi cikin nata ta ɗan zabura anma ta kasa buɗe idonta, cikin ƙwarewa yake kissn dinta duk jikinta yayi sanyi a haka har tsayuwar ta fara gagararta, ya riƙota gam,

  Motsin tahowar Momie sukaji da sauri ta turashi ta ɗauki abayarta dake saman gado ta saka tana maida numfashi, 

  Momie na shigowa ta tsaya kallonshi cikin mamaki ta riƙe baki tace 

   "mezan gani haka? Tunda safe ko farkawa bamuyi ba?"

  Yana sosa ƙeya yace,

   "gaisheku nazoyi kuma naga yanda ta kwana da jikin"

   "nagode da gaisuwar, mai jiki kuma taji sauƙi"

  Shiru yayi ya rasa amsar dazai ba Momie kamar ba itace tace bata ida warkewa ba, ji yake kaman yace to tunda taaji sauƙi a bashi matarshi su tafi.

  Sai kuma baice komi ba har ya gama zamanshi yaga dai Momie bata da niyyar fita ta barshi da matarshi, saiya fito kawai anan yayi break fast sannan ya wuce office cike da tunanin hafsatul kiram.

 

Momie mace ta samo wacce zata gyara mata Hafsatul kiram, kullum cikin gyaran jiki ake mata da kayan ƙarin ni'ima da ake ɗura mata, ita dai tana shane kawai, Kullum cikin gyara mata jiki ake, fatarnan tata tayi haske tayi kyau sai sheƙi take, ga wani irin kyau da take ƙarawa kamar ka sace ka gudu.

  Umar kam ya samu wurin zuwa kullum yana maƙale gidan Momie duk da bata barinshi zama tare da Hafsatul kiram, wani irin sonta ke ƙara shigarshi in yana tuna abinda ya mata a baya har zubda mata hawaye yake yana ƙara jinjina haƙurin Hafsatul kiram.

  Yana matuƙar kewarta da kyawawan halayenta, sanyayyar muryarta da sanyayyan yanayinta, Jinshi yake kamar yaafi kowa maraici da Hafsatul kiram bata tare dashi.

  Yau tunda yazo yake neman hanyar da zaiga Hafsatul kiram, batasan da zamanshi a falo ba ta fito tana sanye da riga da siket na atamfa kanta yasha ƴan ƙananan kalaba ta ɗaure ta tsakiya, ta gabanshi tazo zata wuce sai dai taji ya riƙo hannunta.

  A tsorace ta juyo suka haɗa ido sannan ta saki ajiyar zuciya da taga shine, ta sakar mishi murmushinta mai burgewa da zazzaƙar muryarta cikin nutsuwa da tattausan lafazi tace,

  "Ya umar ka wuni lafiya?", Ya harareta da wasa,

  "kin damu da hakan ne? Duƙar da kanta tayi, ya ɗago fuskarta,

   "banson shirunnan Hafsatul kiram ki ɗago kimin maganan plz, meya hana momie ta bani matata?"

  Riƙe baki tayi tace,

   "ni inazan sani Yaa umar? Nimafa inajin tsoran komawa"

   Da sauri ya zaunar da ita suna fuskantar juna cikin tashin hankali yace,

  "tsoranme? Faɗamin"

   Duk ta marairaice fuska tace,

  "Deezy bazata ƙara dawowah ba?"

Duk tayi matuƙar bashi tausayi tabbas hafsatul kiram ta juri abubuwa da yawa akan soyayyarshi, shikam dame zai iya saka mata, girgiza kai yayi cikin dauria yace,

  "bazata taɓa dawowah ba hafsat, babu macen data isa ta shiga tsakanina dake, nayi miki alƙawarin ni naki ne har abada"

  Sunkuyar dakai tayi ta kasa cewa komi can cikin zuciyarta wani daɗine ke ratsata Yaci gaba magana,

  "kewarki nake Hafsatul kiram cikin kowanne bugun zuciyatah, duk sanda na rufe idona na buɗe, kullum cikin kewarki nake, gidanmu yaimin duhu sosai da babuke a cikinshi, daman haka ne idan mutum nasonka bazakaji ZAFIN SOn ba, sai dai kana shareshi idan yana baka kulawa, sai randa ka fara sonshi ne zakaji ZAFIN SON a cikin zuciarka, ina fatan ban makara ba da roƙonki yafiyarki"

  Girgiza mishi kai take,

  "don Allah Ya Umar ka daina roƙona yafiyarka, wallahy ni komai ya wuce wurina, kaifa mijina ne kuma kana da haƙƙi a kaina, don Allah ka daina"

  Shima share hawayen yake duk dauriyarshi kalaman Hafsatul kiram na matuƙar sanyaya mishi jiki, cikin ƙarfin hali yace,

   "wai hafsatul kiram baki iya fushi bane? Tunda nake ban taɓa ganin ɓacin ranki ba, ta yaya zan gane na cutar dake? Don Allah idan na miki ba dai-dai ba ki dinga nunamun, don in kiyaye"

  Murmushin ƙarfin hali tayi,

   "Mace ta gari mai neman Aljanna a ƙarƙashin tafin ƙafar mijinta bazata taɓa fushi dashi ba, baka taɓa ɓatamun rai ba duk ɗan adam ajizi ne Ya Umar yana buƙatar uzuri, Bn ta'ba bama zuciyatah damar da zata kamaka da laifi ba, komai kaimun nasan kana da dalilinka"

  Shiru yayi ya kasa ce mata komi, kalamanta na dusashe nashi, tabbas Hafsatul kiram nada kaifin tunani da hangen nesa, inama ace duk mata haka suke? Tsabar ya rasa mezai ce mata, ya kamota kawai ya rungume matarsa, ji yake kaman wani ne zai ƙwace mishi ita, ji yake kaman ya maidata jikinshi ko yaji sauƙin soyayyar da yake mata, wani irin zazzafan so yake mata da bai misaltuwa.

 

Momie ce tsaye kansu, duk taji abubuwan da suke faɗa, 

   "shine zaka zo ka sakamun ɗiya kuka ko? In kayi haƙuri ai ta kusa dawowa ne, anma ka yarda ka ƙara matsa mata cikin gidannan zan ƙara lokacin dawowarta ne"

  Tagumi ya zuba kamar maraya yana kallon Momie tana faɗa duk ya wani zama kalar ban tausayi ta cema Hafsatul kiram tashi ki shiga,  ki kwanta ki huta karki biye mishi kinji ko,

 Babu musu ta miƙe ta tafi ɗakinta sai da takai ƙofa ta juyo tana waigen mijinta shima ita yake kallo da sauri ta shige ɗaki cikin jin kunya.

 

Ranar tunda ya fita bai dawo ba sai dare, ya shigo gidan cikin sanɗa ya shige ɗakin Hafsatul kiram, Tana zaune tanacin dahuwar kazar da Momie ta kawo mata ya shigo da sauri ta miƙe,

   "ya Umar baka tafi ba"

Yace "na kasa daure zuciata in tafi ne, Allah Hafsatul kiram ina cutuwa da rashinki don Allah ki tausayamin kizo mu tafi",

  ta zaro ido tace, "mu tafi ina? Momie bata ce bafa"

  "Momie bazataƙi yarda ba idan kikaje da kanki kika faɗa mata kin warke ta barki mu tafi ba", ta zaro ido tana kallonshi tace,

   "ni dai bazan iya ba, ina matuƙar jin kunyar Momie"

  Yace, "shikenan bazaki tausayina ko? Ki taimakeni plz na sanki da tausayi da taimako"

   "ba haka bane Ya Umar kaasan inajin kunyarta fa"

  Yace, "haba Hafsatul kiram taawa babu wahala fa nasan zaki iya, Basaikin kalleta ba, kanki na a ƙasa kina wasa da yatsun hannunki cikin kunyar nan taki kice 'momie naa warke pa yaushe zan koma gidana?"

  Ta zaro ido tana kallonshi yayi murmushi itama murmushin tayi tace,

  "nikam bazan iya hakan ba"

  Yace, "babu wahala pa ki gwada ki gani"

  Tace "nidai a'ah Ya Umar, kayi haƙuri please, banso ina maka gardama"

Ya dafe kai yace,

  "ni na kasa gane dalilin da yasa Momie ta hanani kene, Ke kuma babu ruwanki hankalinki kwance,Kokin daina sona ne?"

  Da sauri ta girgiza kai zatayi magana kuma ta fasa ta sadda kanta, Yace,

  "ki fadamun mana Hafsatul kiram"

Ɗago kanta tayi tana kallonshi sannan ta ware manyan idanunta tace,

  "Momie"

   "kinajin kunyar Momie ba? Muje tare mu fad'a mata mu munso tafiya gida kinga bzata hana please"

  A hankali tace "Momie gatanan bayanka tana jinka", da sauri ya juya wurin momie tayi tsaye ta ɓata rai hannunta a harɗe fuskarnan tata babu wasa take kallonshi,

  Saida ta ƙaraso gabansu sannan tayi murmushi tace,

  "Duk na fahimceku", tana kallon Umar "bazaka koyama ɗiyata rashin kunya ba, yanzu dai dare yayi kazo gobe ka ɗauki matarka ku tafi"

  Wani irin farin ciki ne ya bayyana a fuskar Umar don tsananin jin daɗi kamar ya rungume Hafsatul kiram yakeji, ya matsu sosai Hafsatul kiram ta koma gidanshi ya fara nuna mata soyayyar da yake mata da kulawa.

 

Washe gari yana dawowa daga office gidan Momie ya wuce, Hafsatul kiram na zaune ana zana mata lallea hannu ya shigo da fara'arshi cikin nishaɗi ya zauna, Suka gaisa da Momie sunata fira, Hafsatul kiram kau tunda ya shigo ta gaisheshi ta duƙar dakanta, bata yarda ta ɗago ba duk da jikinta na bata ita yake kallo.

 Kasa daurewa tayi taɗan ɗago da idanunta, tana ɗagowa suka haɗa ido da sauri ya mata alamar yanason magana da ita, ta waro ido sannan ta girgiza kai tana nuna mishi Momie, langaɓar dakai yayi yana mata alamar ta taimaka, ɗaga kafaɗa tayi alamar bazata iya ba sannan ta duƙar da kanta.

  Sai dai kawai ta ganshi ya durƙusa gabanta saman gwiwoyinshi da sauri ta waro ido ta rasa yanda zatayi don kunya, ya langaɓar da kanshi yana kallonta yace,

  "nasan bazaki taɓa mantawa da abubuwan da suka faru a baya ba, nasan na cutar dake, na azabtar dake, A yau zan ɗaukar miki alƙawarin kulawa dake, sanyaki farin ciki bazan taɓa barinki ki kuka ba har abadah! Ina sonki Hafsatul kiram"

  Duƙar da kanta tayi tasa hannu ta rufe fuska, Momie kam don tsananin jin dadi sai murmushi kawai take, ta shima Umar Albarka sosai sannan ta musu fatan zaman lafiya da farin ciki mai ɗorewa,

 

Da dare suka tafi gidansu cike da farin ciki, suna isa gidan yana riƙe da hannunta, ya bud'e mata ƙofar, cikin mamaki take kallon falon

  Ya ƙawatashi da fitilu kala-kala yayi matuƙar haɗuwa, ta juyo ta kalleshi ya kashe mata ido, tana ƙarema ɗakin kallo suka ƙarasa ciki,

  Har gaban cake ya kaita yana murmushi sannan yace "welcome back my lovely wife", Sannan ya watso mata flowers masu kyau da ƙamshi ta rufe ido ta buɗe a cikin jin daɗin yanda Umar yaketa ƙoƙarin sakata farin ciki.

  Ranar ta zame musu ranar farin ciki, bayan sunyi alwala sunyi sallar miƙa godia ga ubangiji wacce basuyi a daren farko ba, sun daɗe suna jero addu'o'i, 

cikin zaƙuwa Umar yaja hannun Hafsatul kiram zuwa gado, Ganin irin kallon da yake mata yasa nasan wannan al'amari bai buƙatar in tsaya daukar rahoto cikin hanzari na rufo musu ƙofar. 

 Soyayya sosai da kulawa Hafsatul kiram ke samu daga wurin mijinta Umar, ko motsi tayi yace,

  me take buƙata?' Wani irin so yake mata fiye da duk tunanin mai karatu, yanzu bata da kewar gida duk sanda take da buƙatah yana kaita don duk abinda zai sakata farin ciki yakeyi, yafiya kam kullum cikin roƙonta ita yakeyi, itakam ƙoƙarida take kullum na ta sakashi mantawa da abubuwan da suka faru ne.

 

Bayan shekara shida 6..

Hafsatul kiram ce kwance saman ƙirjin Umar sai zuba mishi shagwaɓa take yana wasa da gashin kanta yace,

  "kin shigo cikin rayuwata kin canjata da kyawawan halayenki, i'm a changed person, koda yaushe inajin sonki a cikin zuciyatah, kome kike ƙaramun sonki yake, na yarda dake Hafsatul kiram, ina sonki sosai,Ina matuƙar alfahari dake"

  Murmushi tayi ta ɗago tana kallonshi suna shaƙar numfashin juna tace,

  "ba zuciyata kawai na baka ba ya Umar, na mallaka maka kaina, ruhina, da duk wani abu dana mallaka komi naka ne, banida abinda ya ragemin kullum cikin yi maka addu'ah nake mijinah, nagode sosai da soyayyar da kakemun, Zan soka har abada, babu abnda zai rabani dakai" ta kwantar da kanta jikinshi,

  Ya shafi gashin kanta yana murmushi

  "ke mace ta gari ce Hafsatul kiram, duk zamana dake baki taɓa saɓamun ba, ina Alfahari dake"

  Abubakar da ƙanwarshi Zainab suka rugo suka rungume iyayensu nasu, tare suka haɗa baki sukace,

  "Muma muna Alfahari dake sosai Mum, muna alfahri da samun uwa ta gari"

  Hawayen farin ciki na share sannan na musu gyaran murya duk suka juyo suna kallona, Abubakar da zainab suka rugo sunamin oyoyo, Na kalli Umar nace 

  "Don Allah ka ƙara riƙe mana Hafsatul kiram amana, mace d'ayace a cikin miliyoyi"

  Girgiza kai yayi yace, "A'ah Aunty Rabiatu, Hafsatul kiram d'ayace a cikin duniyar nan, tun bayan labarin Rabiatul badawiyya da naji, ban ta'ba jin labarin macen dake matuƙar biyayya ga mijinta ba kamar Hafsatul kiram, ina yima kowanne namiji fatan samun mace kwatamkwacinta, da fatan suma matan zasuyi koyi da irin kyawawan halayen"

 Murmushin jin daɗi nayi Hafsatul kiram ta taso saitin kunne na ta raɗamun,

  "Aunty ya kamata kiyima masu karatu sallama hakanan, Allah yasa zasuyi koyi da Abinda suka karanta

 

Alhamdulillah...

Anan na kawo ƙarshen wannan littafi nawa Hafsatul kiram, ina fatan Abinda nayi kuskure Allah ya yafemun!! 

 

Ta samu soyayyar mijinta babu boka, babu malam ba tare data bi wata hanyar ba ta nuna zaƙewa, sai tsantsar addu'ah, haƙuri, juriya, biyayya, sadaukarwa, kau da kai, tunani da hangen nesa, mutumtawa da girmamawa, Babu wanda zakaima wannan a soyayyar bai ɗaukeka da ƙima da daraja ba ya fifita ka akan komi, duk mai haƙuri duk daɗewa zai samu wadata, duk wanda yayishi ƙarshensa farin ciki ne, biyayya na da matuƙar amfani a zaman aure, Allah ya bamu ikon farantama mazajenmu, yasa mana haƙuri dasu ya bamu ikon yi musu biyayya, Allah ya bamu ikonyin amfani da abinda muka karanta muka ƙaru dashi.

 

Sadaukarwa!!

Wannan littafi sadaukarwa ne ga hafsat Ahmad tijjani, Allah ya rayaminke da kyawawan halaye irinna hafsatul kiram, ya baki miji na gari, wanda zai soki tun farko a kula dake, wanda bazaki taɓashan wahala a zamanku ba, ameen!!


Tags: #Hafsatulkiram #Umar #Haquri
4910
0
10
1
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

maryam2018-12-23 13:02:33