Hadin Gwarmai!

Written by Umm NassPublished on 2019-01-05 13:03:33Category RandomBa abin mamaki bane wata rana ƙaddararmu ta iya sauyawa ba Abdallah. Kamar yanda ƙaddara ta fidda kai atsakankanin mu, duk da kasancewar mu ba ƙabila ɗaya ba, shi yasa na kira Haɗin da suna Haɗi irin na Gwarmai.... Wanan labarin ƙirƙirarran labari ne, akwai Ilimintarwa gami da nishaɗantarwa acikin wanan labarin, mafi ƙololuwar birgewa acikinsa shine juriya da kuma haƙuri acikin duniyar da ta cika ka da maƙiyanka. tags: Kaddara #juriya #hakuriDuba was labarai »

[10/17, 9:03 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI* 🎊


©by *😘Um Nass🏇🏼*


® *MADUBI🔎WRI.ASSOCIATION*


"Da sunan Allah mai rahma mai jin qai.,

 Ina roqon Allah ya shiryar damu ya tabbatar damu akan tafarkin musulunci har xuwa qarshen rayuwarmu."

 

 "Wanan labarin qirqirar lbr ne sai dai xai iya xama wani 6angarai Na rayuwar da take faruwa agaske awanan xamanin.,idan aka samu wani/wata yayi daidai da irin rayuwars to suyi hqr ba da su nakeba."


  

 Sanan wanan shafin Na sadaukar d shi dungurugum dinsa ga *"ANTY MAIJIDDA MUSA*" da dukkanin masoya labarin Um Nass 🏇🏼kada kuyi missing din lbr nan domin akwai sarqaqiya mai yawa acikins.Nishadi,Rikici!danganta!!!da kuma SoyayyA."Page 1

 

 *YOBE STATE*


GUMSA karamin qauyen dake qarqashin YADIN BUNNI duka acikin jahar YOBE state.,Rayuwar garin dauke take da sanayya Wanda awani sashi guda xamu iya kiransu da En uwa guda, sai dai duk da haka suna da wani rauni daban da xai iya rarraba kai tsakaninsu. musamman idan xa'ayi la'akari da yanda rayuwa ta zama ayau kalma daya CE ke mgn afahimta cikin sauqi akuma girmamaka a idanuwanka itace *NAIRA* xai iya kasancewa suma awajansu haka ko kuma asamu akasin hakan."Tafiya yake yana gyada kai wani lkc kuma ya girgixa kamar mai bada amsa da kuma mai tmby.,qafafuwansa dauke suke d silifas Wanda bashi da maraba da babu sbd tsananin wahlar da sukasha da gajiya da rayuwa ko ina a6ule yake ajikinsa.,haka kuma adaure yake da Leda ko kadan baya raba mai sashi daga jin zafin rana da kuma takawar qaya aqafarsa.

 Rigar da take jikinsa ta kode mutqa ta yanda ba xaka iya banbance ainihin kalarta ta asaliba,haka kuma wandan jikinsa duk gwuiwarsa afarfashe take.


 abin mmk duk da yanayin da yake ciki fiskarsa qunshe take da murmushi haka kuma duk inda yaga taron mutane yakan daga musu hnnu gami da musu sallama.,sai dai ko kadan basa iya maida masa koda da sallamar da yake musu balle yasa ran xasu masa murmushi kwatankwacin yanda yake musu.


 "Sakaran yaro kawai ko kunyar tafiya bayaji acikin wanan yanayin nasa.,haba mi xa'ayi da dangin tsiya gayyar talauci.,sai shegen yage baki yake yana jijjiga kai kamar kadangaran da yaso mutuwa.,"

 Wani daga cikin mutanen da suke xaune agindin bishiya yayi mgn bayan wucewarsa.

Gaba daya mutanen suka kwashe da dariya wasu acikinsu har adungura suke SBD dariya"kai sule sharrinka d yawa yake Aradu, shi kadangaren da ya so mutuwa haka yakeyi dama" daya daga cikin mutanen ya fada yana qara 'kya'kyacewa da dariya. 

 "Sosai kuwa haka yakeyi sai dai Na yaron nan har yafi kama da Wanda yaxo GAF da mutuwa."

 "Kaii sule ka barmu haka kada ka kashe mu da Daria"suka fada suna masu dariya.can wani acikinsu yayi gyaran murya kafin yayi mgn "ni kuma yaron yana mutqar burgeni ko yaushe fiskarsa dauke da fara'a kamar gonar auduga,kana sau dubu xaku hadu dashi yama mgn kaqi kulashi amma bazai ta6a damuwaba hakan bazai hana idan ya sake ganinka ya maka mgn ba."

 

 Kwa6e baki sule yayi kafin yayi tsaki "ina abin birgewa anan.ai sai dai kace masa shashasha dan yafi mahaukaci ban takaici,kullum baki ayage kamar 'kofar da takema ba'ki maraba d shigowa."

 Dariya suka qara sawa sadai Wanda ya yabaishi jijjiga kai kawai yayi "Akwai baiwa atare da wannan yaron ba kowa xai iya fahimtarsa ba.amma Na tabbata wata rana xata bayyana kanta."

 "Kai halilu yaushe ka zama malmin taurari mu bamu saniba.da alama baiwar tasa ta mahaukata masu dariya ce,Sbd ayanda yake yafi kama da mai dauke da ifiritai akai."

 Dariya sukayi suna ihu harda buga qafa kamar da suka samu wata daukaka.,haka sukaci Gaba da aibata shi ta hanyar ganin naqasar dake atare da shi..


*****

 Cikin sanyin murya ya shiga yin sallama awani zagayayyen Gida duk kewaye yake da karare sai "yar buka 'kwaya biyu agidan gefe daya kuma bandaki ne Wanda aka xagayeshi da buhu sai kuma bishiya t maina data cika gidan da inuwa zan iya cewa wannan itace jin dadinsu agidan sbd nanne kadai wajan hutawarsu.


 "Wa alaikumussalam"

 Wata dattijuwa ta amsa daga can tsakiyar gidan inda take ta fama da hura wutar kara idanuwanta duk sun CIKA da haya'ki da kuma hawaye.

 

 Da saurrinsa ya 'karasa kusa da ita yana 'ko'karin dagata daga gaban wutar"Ummi bari Na hura miki wutar kinji .,je ki zauna a inuwa,.mi yasa baki bari Nazo Na d'ora miki girkinba.?"

 Magana yake cikin sanyin murya da damuwa afiskarsa hannunsa ri'ke da ita ya kaita ya zaunar da ita.sanan ya koma ya harhada wutar da 'kyar yayi nasarar hurata idnuwansa sunyi jajir,.

 "Ummi mi zaki dafa .?"yana duba 'karamar tukunyar da take gaban murhun ba wani abin kirki bane aciki busasshiyar yakuwace sai dakekkiyar gyada da daddawa da kuma ruwa aciki.

,juyowa yayi cikin jimami yake sake tambayarta "Ummi mi zakiyi da wanan abun."

 

 Murmushi tayi sanan tace "Dahuwar 'kanzo zanyi ko har ka manta yanda akeyinta ne."

 Dariya yayi yana shafa kai sanan ya Dora tukunyar akan wutar.,daga bisani y zo ya zauna kusa da ita"Sam Na manta da hakan Ummi sbd lkc da aka dauka bamu Dora tukunya agidan nan ba.," fiskarsa CE ta nuna damuwa qarara "ko yaushe ne zamu samu sauyi acikin rayuwarmu Ummi?zcyta ta fara rauni sosai inaga kamar nayi wani laifi ne arayuwata.kowa guduna yake yana 'kyamata kawai SBD ina talaka Ummi.yanzu babu mai iya min mgn awanan garin koda Na musu sai dai su kauda kai daga ganina.,haka ko aiki naje nema basa bani cewa suke zan goga musu 'kashin tsiya na shafa musu daud'ar talaucin dake jikina.,"


 Kai ya kawar cike da jin zafi a ma'koshinsa kafin yayi murmushi yana kallon mahaifiyar tasa "ke kadaice kike haba-haba da ganina Ummie,kike zama dani kiyi hira dani hatta abokaina duk sun gujeni.,ina tunanin wata rana xata zo Na fiddaki daga cikin whlr rayuwar nan ba.amma ban San yaushe ne ba.?ban saniba ko zan iya zama wani abu arayuwa Na jiyar da ke wanan dadinba,musamman idan naga ko wata rana wahalarmu 'karuwa takeyi.,"


 Murmushi sosai tayi tana 'ko'karin hana hawayen dake idanuwanta zuba,wani abu mai daci ke ma'kale acikin ma'koshinta Wanda hadiyar yawu ke mata wahla adai dai wanan lokacin."Allah yana sane da kai *ABDALLAH* haka kuma bai manta da kaiba,ka daina damuwa da mutanen d basa kulaka,kabar 'ko'karin 'kir'kirarma kanka laifi awajan mahaliccanka.,ka zama mai yawan godiya agareshi da ya barka da ranka da kuma lafiyarka.ka ta'kaita burinka Na hango rayuwar jin dad'i agaba hakan zai sa ka zama mai wadatar zuciya.,Abdallah lomar da take 'kunshe abakinka itace loma ba wanda take ri'ke ahannunkaba domin tsautsayi zai iya bi ta kanta har ta kai da zubaiwa."

 Jijjiga kai yayi yana murmushi sosai "nagode Ummi kullum ina godewa Allah da ya bani ke amatsayin mahaifiyata,.,Allah ya barmu tare Ummi har gaba da Abadan."

 Murmushi tayi tana girgiza kai"Allah bazai barni ba Abdallah shekaru sun ja ga mutuwa Wanda ko yaushe 'kara kusantowa gareni take,kai dai ka ro'ka min Allah yamin rahma yaji 'kaina ako yaushe.,"

 Miqewa yayi yana girgiza kai kusan ko yaushe wanan itace 'karshen hirarsa da mahaifiyarsa burinta kadanne awanan rayuwar.


"Ina 'kanzon yake naga kayan hadin sun dahu sosai.,"ya tmbyt yana duba tukunyar da hannu ta nuna masa tana murmushi aranta tana jin kaunar tilon dan NATA.,

 Haka ya zauna tsaf ya gama girkin ya zubo musu suna ci suna lbr mai ban dariya kamar da dai duniya basu da wata damuwa..******

*KANO NIGERIA* 


 'Karan jiniya ne ya gauraye babban titin grain haka kuma ko ina matakan tsaro ne suke kai kawo gashi mutane atsattsaye an hanasu wucewa.zafin rana da 'kagauta Na mutane yasa zuciyarsu 6aci suna tsaki suna Allah wadai da mulki irin Na wanan 'kasar musamman da ake musu halin takukkunkumi akan mutumin da su suka za6a da Kansu.

 "Mulki ko zalinci tabbas yaci ace yanzu munje inda muke bu'kata amma SBD zalinci an tsaida mu arana fiye da awa guda muna jiran mutum daya ya wuce"mgn da wani dattijo yayi yana goge gumi afiskarsa mashin dinsa duk yadauki zafi.

 "Sai haquri Baba idan akace kai talaka ne a 'kasar nan kana da whl ai.,"

Na kusa da shi ya bashi amsa shima ransa ya kai mutqa wajan 6aci.

"To Allah ya mana maganin wanan matsalar."

 "AMEEN wanan itace Addu'ar da zamuyi tayi kenan."

 

 Adaidai wanan Lokacin gwanon motocin governor suka fara wuce gaba da baya sojoji ne dauke da manyan bindigogi haka agefen motar governor din police ne akan manyan mashinansu fiskarsu babu alamun fara'a kamar da dai duniya saqon mutuwa nee ya riskesu.

 Haka suka wuce shiff kamar zasu tashi sama suka wuce bataliyar mutanen da aka dakatarma aiyukansu.

 Sai alokacin aka basu hannu suka wuce da yawa suna ta mita wasu kuma suna fargabar abin da zasu tadda awajan aikinsu.


****

Ahankali ta fara sauqowa daga kan matattakalar benin fiskarta fayau babu hargitsattsiyar kwalliyar zamanin nan. Sai dai da ganinta kasan jin dadi ya ratsata sosai idan akayi la'akari da doguwar rigar rigar dake jikinta qirar Dubai mai duwatsu agaba haka tayi Rollin din dan kwalinta hannunta zage da agogon diamond Wanda Yake mahadin sarqar jikinta.kallo daya zaka mata ka fahimci ko ita wacece.

 Matashiyar budurwa mai matsaikacin shekaru 19 Aduniya.,bata da yawaitar kyau Wanda za'a 'kirata da kyakkyawa.,sai dai idan ka zauna da ita zaka fahimci nagartar da take da ita.

 "Barks da sfy maa"

T gaida mahaifiyarta tana 'ko'karin kwantar da kanta acinyarta "yauwa my dota har kin tashi."

 Kai ta daga mata alamar eh,murmushi tayi sbd sanin miskilancin "yar tata "oya maza ga Abinci can tashi kici,"bana jin yunwa yanxu maa"

Rai mahaifiyar tata ta 'kara 6atawa "Yazu kuwa za'a jimu da kee khaleesat har zuwa yaushe ne zaki koyi cin abinci kullum sai ana fama dake."

 Rai ta 6ata sosai kmr zatayi kuka. Ko kadan bata kaunar cin abinci.

 "Ki tashi nace kafin raina ya gama 6aci"maa t fada cikin tsawa Wanda hakan yasa khaleesat miqewa idAnuwanta har ya kawo ruwa.

 Kafin ta 'karasa kan dinning taji jiniya ta karade gidan d sauri ta fice duk da Koran da Maa din take mata bata waiwayoba balle ma ta tsaya.

©by *😘Um Nass🏇🏼*

[10/17, 9:03 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI🎊*


 *©😘Um Nass🏇🏼*


® *MUDUBI 🔎 WRI.ASSOCIATION*PAGE 2


"Murmushi Maa tayi gami da girgiza kai "Bazaki sauya ba khaleesat,har yanzu babu abin da ya rage a tare da ke na 'kuruciya dangane da 'kiyayyar da kike ma abinci."

 Mi'kewa itama tayi domin zuwa tarar mai gidan nata,adai dai lokaci kuma aka turo 'kofar falon gami da yin sallama.

 Wani Hamsha'kin dattijo ya shigo fiskarsa dauke da murmushi kallo daya zaka masa kasan ko shi waye saboda yanda jikinsa da kayan da ke sanye atare da shi ya nuna asalin ko shi waye,kana ya fiddo da tsagwaran kwarjinin dake a tare da shi.

Kasan cewarsa shugaba agidan da kuma zamansa a matsayin governor Na jahar kano Alh.Muhammad Dan yaro kenan.hannunsa riqe Dana khaleesat tana faman zuba masa surutu Wanda mafiya yawanta tambaya ce akan labarin inda yaje da kuma tsarabar da ya kawo mata.


Sosai yake biyeta yana mata dariya duk da tarin gajiyar da ya kwaso ajikinsa.

 Da sauri Maa ta tareshi tana 'kara fad'ad'a murmushinta ayayin da gefe daya take aikama da khaleesat harara,dauke kai tayi daga kallonta taci gaba da surutunta

 "Barka da zuwa your excellence"

 Murmushinsa ya fadada gami da samawa Kansa mazauni acikin manyan kujerun da suka 'kawata palon

"Barka kadai Ru'kuyya, ya na sameku?"

Ya amsa mata lokacin da ya daidaita zamansa har yanzu hannunsa ri'ke suke dana khaleesat ta 'kara cukuikuye sa kamar zai gudu ya barta.

 "Alhamdullah lafiya lau.

"Da alamar ka debo gajiya,.ita kuma wanan magen zata 'kara maka wata gajiyar da shegen surutunta,da son jiki".

 Murmushi yayi kana ya kai kansa ga diyar tasa Wanda maganar Maa ta sata turo baki alamar jin haushin kiranta da magen da tayi


"Dady kana jin Maa tana kirana da mage ko?"

 Shafa kanta yayi yana dariya saboda yanda tayi maganar 'kiris hawaye ya zuba a idanuwanta

"Ki 'kyale maa ni Na tabbata kee ba mage bace." 

Juyo da kallonsa yai ga ita ya sauya fiska

"Inaga kina takurama uwata idan bana nan Rukayya hakan yasa Sam bata Sakewa da ke,ki duba fa kamar ta shekara bata ganniba nasan kina barinta cikin kadaici kina sabgar gabanki da sauran yaranki."


 Baki Maa ta saki tana ganinsa ayayin da khaleesat ta qara shigewa jikinsa tayi luff kai langare kamar marayan da ya rasa danginsa alokaci guda.

"ikuwa ba'a zageniba idan ba'a gode minba kullum ina fama da ita kamar yaron goye ko abinci kafin taci sai mun gama kewaye gidan nan da ita.,yanzu hakama mgnr muke taji shigowarka ta ruga da gudu."

 

Kallonsa ya Kai gareta yana girgiza kai "Assha har yanzu bakya cin abinci uwata ko asibiti zan sake fitar da kee adubaki."

 Da sauri ta girgiza kai "a'a dady yau ne kawai ban ci abincinba fa shima dan ban dade da tashi abarci bane."


 Ajiyar zcy y sauqe "to kinji dalilinta ai sai ki bar matsa mata."

 "Kai har ka yarda kenan?"da mamaki tayi tambayar.

 "Sosai kuwa uwata ai bata 'karya"

 Jijjiga kai tayi "Allah ya kyauta to.Abinci zaka fara ci ko zakayi wanka ne?"

 Idonsa ya kai sama kamar mai nazari can yace "wanka dai daga baya naci abincin.,"kai ta gyada sanan ta nufi hanyar da xata sadata da dakinsa hannunta riqe da "yar 'karamar jakarsa "bari Na hada maka ruwan wankan."

 Tashi yake 'ko'karin yi "yauwa uwata daga ni nayi wanka ko? sai nazo muci abincin tare."

 Gira ta daga masa kana ta sakeshi ba tare da tayi mgn ba.

 Murmushi yayi yana girgiza kai babu wani sauyi atare da rayuwarta sai dai duk da muskilanci irin nata wani lkc tana zama suyi hira sosai."


 Lokacin da ya shiga daki tuni Maa t hada masa ruwan wankan.,taimaka masa tayi wajan cire kayan jikin nasa.

 Kollonta yake "Nagode Ru'kayya har yanzu babu abin da ya sauya a halayyarki,lokuta masu yawa sai nake tuna rayuwarmu a baya,inaga babu Wanda ya kaini dace da samun mace ta gari,duk da ayanzu bana Samunn lokacin zama tare da ku hakan bai hanaki gajiyawa da hidimta minba."


Murmushi tayi mai kyau"wa yake gajiya da Neman aljannarsa? har abada zan ci gaba da shimfide rayuwata wajan hidima agareka, mut'kar hakan zai saka farin ciki"

 Kai ya girgiza "Na yarda da wanan.,"

 Hanyar toilet din ya nufa "saura kizo ki min wankan kuma."ido ta fidda waje kafin tayi dariya sbd tuna rayuwar da ta shude abaya kafin ta fiddo masa kayan da zai saka.********

Gumsa

 YOBE STATE


"Tun da ya tashe yake faman jidar ruwa yana CIKA randunan gidan nasu har rana ta fara haske alokacin ya gama ya shiga share tsakar gidan nasu duk da cewa babu datti mai yawa.yana gamawa ya koma wanke-wanke da sauri yake yin aikin burunsa ya gama kafin Umminsa ta tashi.ko kadan baya son yaga tana aikin whl.

 Bayan ya gama kuma ya shiga tunanin abin da zasu ci har lokacin bata tashi abrc ba.

 Waje ya FIta yana fatan Allah yasa ya samu dan aikin da zaiyi awanan safiyar duk da yasan babu Wanda yake kulashi acikin garin. 


 Cikin sa'a yna fita ya tadda mai gida yana diban masu aiki zuwa gonarsa amasa gyara sbd Noman ranin da zaiyi.,. Mai Gida shine babban mai arziqin garin nasu dan ko mai gari wani lokacin yakan zo ya kar6i Aron kudi awajansa,ko kadan bashi da kirki akan kudi zai iya 6atawa da kowa sanan idan ya baka bashi tofa sai ka hada masa da Na ruwa,sanan idan ka hanashi akan lokaci yasa arufeka.,amma duk da haka 'kofar gidansa baya rabuwa da masu kar6an bashi da kuma masu masa fadanci.

 Hadiyar yawu Abdallah yayi ya rintse ido dan ko kadan jininsa bai jitu da shiba asalima yafi kowa tsanarsa acikin garin.


 Rintse ido yake yana tafiya ahankali har ya 'karaso India yake kansa a 'kasa bugun zcyrsa Na 'karuwa da fargabar yanda zasu kwashe da mai Gida mutumin da bai 'ki jinin abashi wu'ka ya caka masa ya mutuba acewarsa mugun 'kashin tsiyarsa bashi da ranar da zai musu gara mutuwars.....


©by *😘Um Nass🏇🏼*

[10/17, 9:04 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI* 🎊


 ©by *😘Um Nass 🏇🏼*


® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION*  _💃🏻💃🏻gang gang it's for u FEE,._ ```HAPPY BIRTHDAY 🎂🍡🍼🍧 FEENAT JA'AFAR.``` *Wish U many-many 100 years 😃lolx.* ```Allah ya albarkaci rayuwarka ya sanya alkairi.,Nasarori da kuma ingantacciyar rayuwa acikin shekarun da zaki qara agaba 😃👏🏼```Page 4


Kafad'arsa ta shiga bibbigawa alamar rarrashi,zcyrta cike da 'kunci.Abin da zai sa Abdallah kuka to ya kai ma'kura na sosai.


 Janye shi tayi daga jikinta,ta goge masa hawayen daya ke ambali afiskarsa,kai ta girgiza masa alamar ya bari tana murmushin 'karfin hali,kana ta ja hannunsa zuwa gindin bishiya Wanda taburmar kaba ke shimfide a inuwar wajan.

 Zaunarshi tayi awajan sanan ta koma ta debo masa ruwan randar 'kasa Wanda yafi ko wanne sanyi.

 Mi'ka masa ruwan tayi baiyi musu ba ya kafa kai ya shanye Tass., shi ya manta yaushe m rabonsa da ya sha ruwa tun lokacin da yake jidar ruwan gidan.

 Saida ya kusan shanyewa sanan ya dire kofin yana sau'ke ajiyar zuciya.


 Kollonsa Ummie take cikin tausayawa rayuwar da suke agarin,. Bashi da wani aibu atare da shi,haka ba 'karamin abu ke sashi yin fushi ba balle hawaye.


 "Ka 'kara yin ha'kuri Abdallah,har yanzu akwai sauran lokaci kafin mu bar garin nan."

 Kai ya girgiza yana kallonta cikin raunanniyar muryarsa "Kullum haka kike fad'a Ummie,da sauran lokaci-da saura.,har sai zuwa yaushe ne lokacin zaiyi? Ko sai sanda ba'kin ciki da 'kiyayyar mutanen garin nan ta halaka mu.?"


 Murmushi tayi tana kallon fiskarsa " ko kad'an 'kiyayyar mutane ba zata hallakamu ba.,asalima sai dai ta 'kara mana wani ci gaba,duk mutanen da kaga sun samu d'aukaka arayuwa idan ka duba tarihin rayuwarsu sun fiskanci 'kalu bale daga mutanensu. Haka kuma idan ka duba tarihin Annabawan Allah da salahan bayi suma hakanne garesu. Ka 'kara ha'kura zamu bar garin nan ba alokacin da mutane suka tsanemu ba,sai dai idan 'kaddarar mu CE tazo da hakan."

 

Kai ya daga yana murmushi badan y gamsu da maganar ba sai dan sabawa da jinta da yake a lokuta makamancin wanan. Amma da zata bashi za6i to da sun bar garin nan sun 'kara gaba.


 Mi'kewa tayi ta shiga bukarta,bata dauki lokaciba ta dawo hannunta dauke da kwano ta ajiye agabansa.

 "Minene wanan Ummie?"

 "Abinci ne na ajiye maka tun da safe baka dawoba har yayi sanyi."


 Da mamaki ya bude kwanon dan wake ya gani har ya sauya kala zuwa Jaa alamar an dauki lokaci da yinsa.

 "A ina muka samu dan wake har haka Ummie? Dan nasan duk garin nan babu mai bamu kyautar abinci koda zamu shekara da yunwa ta halakar da mu."

 Dariya tayi ganin yanda ya rikice da tmby lkc daya "Ikon Allah mana Abdallah,kasan rahmarsa yawa gareta.,baya hanama bayinsa samunta sai idan sune suka 'ki."


 Murmushi yayi sosai "Haka ne Ummie,amma nasan akwai hanyoyi da yawa na samunta."

 

 "Abdallah mana.,ho aiki nayi aka biyani na samu kudin,bayan fitarka na shiga ma'kota ko zan samu aiki,nayi sa'a suka bani surfe da wanki har na 150 shine na mana abincin da su,. Nasan kana son 'Dan wake sosai,shi yasa naso da zafinsa ka sameshi."


 Kallonta yake,bai San mi zaiyiba adede wanan lokacinba,. Kaunarta ce take ninkuwa acikin zcyrsa _"Anya akwai wanda ya kaishi dace da samun uwa ta gari? Mai tsantsar sonsa?Tabbas idan babu ita arayuwarsa to da shima tuni labarinsa y shude."_


 "Hawayen na miye kuma yanzu?"

 

Maganar Ummie ta dawo dashi daga duniyar tunanin da ya tafi. 

 Fiskars ya ta6a da mamakinsa hawaye ne,kai ya girgiza yana murmushi "kawai dadine yamin yaawa Ummie,yau na zagaye kaf garin nan dan na samu aiki komin 'kan'kantarsa na samu na kawo miki abinci,amma hakan ta gagara."

 Murmushi yayi mai sauti "Tun Dana zo duniya kike ta dawainiya dani,gashi har yanzu baki gajiyaba.,ko wata rana burina bai wuce na hidimta mikiba,da da hali ko numfashi zakija ni zan miki. Amma rashin sa'ata ya hana hakn faruwa."maganarsa ta sartse adai-dai wannan ga6ar.

 

 Kansa ta shafa tana murmushi "Ba ko wasu buruka Namu bane suke tabbata ba Abdallah,sai dai mu yi hasashen yuyuwarsu Ababa.,sanan kabar maganar ina ta dawainiya da kai.Uwa bata ta6a gajiya da hidima da d'anta koda zata 'karar da rayuwarta wajan kula da shi."


 "Na gode Ummie"

Kai ta girgiza had'i da yin murmushi "Oya bud'e bakin na baka abinci,surutun ya isa haka."

 Zama ya gyara ya bud'e bakin ta fara bashi kamar 'karamin yaro.

 Daga nan ta shiga bashi labarin da zai sashi manta damuwar da yake ciki..******KANO Nigeria Sauri-sauri takeyi saboda makarar da ta kusayi.,agurguje ta 'karasa shiryawa,jikinta kamar anyi 6arin turare saboda mahaukacin 'kamshin da take bud'dawa.

 Cikin takunta na 'kasaita ta fara tafiya kamar mai tausayin 'kasa, amma anata ganin sauri take.


 'Kamshin turaren da sukaji yasasu jiyowa.,baki bude Maa take kallonta da mamaki ...


©by *😘Um Nass 🏇🏼*

[10/17, 9:04 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI* 🎊


© *😘Um Nass 🏇🏼*


 ® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION*


 

 😀Gareku "yan *FEENAR JA'AFAR NOVELS* wanan shafin duka naku ne. Ban ware kowaba, kuyi yanda kuke so dashi sadaukarwarku CE 😘
PAGE 3 "Ahankali yaci gaba da 'karasawa har ya zo kusa da jerin mutanen da sukayi cirko-cirko da alamun suma suna jiran tsammani ne.

 

 Ganinsa yasa hankalin mutane yakai wajansa, mafiya yawa kuma suna masa kallon mamakin zuwansa, saboda sanin yanda ko kad'an jininsu bai jitu da Mai Gida ba.

 "Hala kayi rafkanuwa kazo nan ko?Dan idan ka duba duk nan masu bid'ar aiki ne,kuma wadanda suka saba da maida sule ya koma fam."Wani daga cikin jerin mutanen ya jefoma Abdallah tambaya gami da mugun hararsa.,

 Kai ya gyad'a yana dariya kamar yanda ya zama d'abi'arsa."Ba 6atan kai nayiba. Maida Sule ya koma FAM ya danganta da yanda ka d'auki amfanin kudin awajanka,dan ka tara ka amfana da su wajan sarrafasu sarrafasu?Ko kuma dan duniya ta sheda hankan?"


 Kallonsa yake da mamaki dan bai zaci zai iya maida masa magana haka ba."kace mi?" Ya 'kara jifansa da tambaya.

 Kai ya girgiza yana murmushi ba tare da ya 'kara bi ta kansaba, ya kai kallonsa ga Mai Gida wanda shima alokacin ya fahimci da zuwan Abdallah wajan.


 Kicin-kicin yayi da rai kamar yaga mutuwarsa "Ya akayi kai? Mi kazo yi nan wajan?" 

 Dariya Abdallah yayi duk da faduwa da gabansa yayi, ya 'karaso kusa da Mai Gidan yana shafa kai"Ina kwana Mai Gida.?"

 Hannu ya d'aga masa cikin 6acin rai "Ri'ke gaisuwarka bana bid'arta. Dalilin zuwanka nan nake son ji."

 Murmushi yayi kafin ya fara magana yana gyad'a kai"Umm dama aiki na fito nema,sai kuma akayi sa'a naga kana daukan ma'aikata,.shine nima nazo ka daukeni koda rabin kud'in da zaka basu ne sai ka bani. Na baro mahaifiyata babu ko Abincin da zata ci yanzu."


 Tsaki Mai Gida yayi gami da 6antarar goro abakinsa"Kuma sai akace maka cikin ma'aikatan da nake d'auka harda shashashu aciki ko?" Dariya mutanen wajan suka 'kyal'kyale dan sun san za'ayi haka, wasu kuma harda ihunsu Na jin dad'i.


 Kai ya sunkuyar yana girgiza shi duk da ransa ya sosu hakan bai hanashi yin murmushi ba "Zan iya duk abin da kace ayi Mai Gida. Ka daure ka daukeni."


 "Yo da nace bazaka iya bane? Kunji min sakaran yaro.,aikin ne nace bazan baka."

 

 "Mi yasa? Ko na maka wani laifin ne?" Muryarsa da sanyi sosai yake maganar,amma duk da haka babu alamun 6acin rai atare da shi, 'kasan zuciyarsa kuwa damuwace sosai."


 "Mtssss..."yaja dogon tsaki,kafin ya 'kara hade fiska tamau "Wai kai wani irin yaro ne? Kanka babu kwanya hala? Nace bazan baka aikiba,dalili kuma saboda halinka,kana tafe kana wage baki kamar garin da babu 'kofa.Sanan abu mafi muhimmanci shine nafi kowa tsanarka awanan garin,dan haka ka tafi ka bani waje kana 6ata min lokaci."

 Kai ya girgiza yana murmushi yace "Allah ya baka ha'kuri"sannan ya juya ya tafi, ko jiran amsar da zai bashi bai tsaya yajiba, zuciyarsa kamar ta fito saboda takaici.

 _"Ko sai yaushe ne zai samu sassauci daga wanan 'kyama da kyarar da mutanen garinsu suke masa?"_

 _"Babu rana. Wata 'kila 'kaddararsa bata tare dasu. Aance rashin zuciya gareshi,amma duk lokacin da zai nemi aiki daga garesu sai su shiga kyararsa tun kafin su jarrabawa iyawarsa akan aikin."_

 

 Wanan shine tarin tambayoyin da Abdallah yake ma kansa,yake kuma amsasu da kansa.

 

 Bayan tafiyarsa mutanen wajan suka shiga tafi da jinjinawa Mai Gida.,Wanda hakan ya 'karama Kansa girma,dan idan akwai abin da ya tsana bai wuce Abdallah ba,shi kansa ba zaice ga daliliba.,amma wani sashi Na zuciyarsa yana girmama 'karfin halin yaron,ko kadan bazakaga fiskarsa da damuwaba.******

 Haka Abdallah ya gama zage garin Gumsa ba tare da ya samu aiki ko Na kwasar kashi ba.

 Ba kuma dan babu aikin bane ya rasa,a-a sun dai hanashi sbd jin haushinsa da suke da kuma tsoron zai iya goga musu 'kashin tsiya da talaucin dake tare da shi.


 Gajiya yayi da zage gari ga yunwa da zafin ranar da ya gama ratsashi,ya nufi gida yana tausayin rayuwarsu shi da mahaifiyarsa.,


Fargabarsa daya rashin sanin halin da zai taddata,jiki asanyaye ya shiga gidan bakinsa da sallama. 


 Da murna Ummi ta tareshi "Abdallah Na sannu da zuwa,tun dazu nake dubaka shuru hankalina ya tashi sosai,saboda baka saba irin wanan dogon zangon ba awaje"

 

 Tausayin mahaifiyarsa yaji ya cika zuciyarsa da kuma tarin 'kaunarta _"Allah sarki uwa mai dadi."_ Kalmar da ya fada azuciyarsa sanan ya 'karasa kusa da ita ya rungumeta.,

 Tuni dauriyarsa ta 'kare sai hawaye ne yake masa tsere a idonsa,Wanda harda sautin kukan.

 

 "Ya Allah! Abdallah lafiyarka kuwa? Mi ya faru kake kuka haka?"


 'Kara 'kan'kameta yayi kamar da za'a 'kwace masa ita "Na gaji Ummie. Na gaji da rayuwa acikin ma'kiyana,Garin nan ya isheni haka Ummie. Ya kamata mu barshi haka."


 Rintse Ido Ummie tayi tana jin rad'ad'i sosai Azuciyarta......© *😘Um Nass 🏇🏼*

[10/17, 9:05 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI 🎊*


 © *😘Um Nass 🏇🏼*


® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION*Page 5


  

 Ahankali ta tako zuwa kusa da su,kamar mai koyon magana "Maa na tafi skull,yanzu Jidda ta kirani take fada min text din da zamuyi."


 "Abincin fa?kinsan duka yau baki ci komiba..

 

 "Bana jin yunwa ne Maa.,idan na tsaya kuma zan 6ata lokaci"


 "Amma khakeesat wannan uban turaren da kika saka ai yayi yawa.,kin dai San babu kyau, kina mace amma kullum kina saka turare mai 'karfi."


 Fiska ta sauya cikin damuwa "Maa na manta kiyi hqr gaba na gyara."

 Kai ta girgiza "ba mantawa kikayiba,da saninki kika sa,dan haka maza kije ki sauya kayan jikinki kisa na hankali."

 

 'Kafa ta fara bubbuga tana 'ko'karin kuka "Maa na makara fa.text xamu baifi 10_mint's ashigaba."


 "Ko da'ki'ka guda CE ta rage sai kin sauyo kaya kuma kici abinci."

 

 Ihu tasa da 'karfin gaske kamar da aka daketa,tana shirin zama tayi birgima, dady yayi saurin d'agota.

 "Assha ya haka Uwata,?Ru'kayya ki barta ta tafi mana. Kina ji tace text gareta"

  "Dama kai kee sangarta ta,ba damar na mata fada sai ka kareta."

 

"Ba haka bane,kinga zaki sa ta 6ata kwalliyarta. "Yan matan yanzu saida 'kamshi musamman "yar Jami'a,ni ban ga abin fada ananba Sam. Ko kin mata matsayinta ne?"


 Ido ta Bud'e da mamaki take kallonsa ta mai-maita tambayar tasa "Matsayi,? Wani matsayi gareta wanda yafi na ko wace mace aduniya.?."


 Murmushi yayi mai sauti sanan ya maida kallonsa ga khaleesat.hannunsa ya shigar cikin Aljihun jamfarsa ya fiddo da bandir din 1000 guda uku ya sanya acikin Jakarta ."Kici Abinci a skull kinji,sannan kima security dinki magana su tabbatar ba'a samu matsala ahanyaba."


 Kai ta gyada tana murmushi kana ta rungumeshi "Nagode dady."sannan ta sakeshi ta dagama Maa hannu "bye-bye"

 Harara ta zabga mata Wanda hakan ko ajikinta,. Saima dariya da takeyi ta tafi.

 Juyowa kan Dady tayi "Bana jin dadin abin da kake ma yarinyar nan.tayi 'kan'kanta da ri'ke kudi har 300k. Wani abu zata siya a makaranta har haka.?"


 Tashi yayi ya dauki 'karamar jakarsa "Ni na tafi office"

 Tashi itama tayi cikin sanyin jiki "Baka son laifin khaleesat ko kadan,ina jiye mana tsoron rayuwa da rudun zamani."

 

 Murmushi yayi Wanda bai kai zcy ba"Ban San yaushe ne bakinki zai fadi alkhairi akan dukkanin lammuran khaleesat ba? Ki fara banbance matsayinta da sauran mutane kafin muyi magana."


 Yana gama fadar haka ya fice ya barta. Da6ass ta zauna akan kujera wani hawaye mai zafi ya zubo mata.,

 _"wanan wata irin rayuwace? Mi yasa ko yaushe matsalarta da mijinta akan khaleesat me?"_

Ido ta runtse da 'karfi kamar taga abin tsoro _"ya Allah ka kare min khaleesat a duk inda take,kada ka bari rud'in duniya ya rud'eta kamar yanda ya rud'i mahaifinta."_


 Wanan itace mafi yawan Addu'ar da takema d'iyar tata,haka nan hankalinta yana tashi duk lokacin da dadynta ke gari,. Domin shike 'kara ruguza ko wani tsarin da tayi mata.


*******

 Lokacin da khaleesa ta fita tuni security dinta sun bude mata 'kofar mota,da ido ta musu alama akan ita zatayi tu'kinta.

 Gaban motar suka bude mata ta shiga sanan suka koma tasu motar suke binta. Wasu agabanta wasu abaya sai jiniya ke tashi.da d'ai duniya sai ka d'auka governor ne zai wuce.


 Tsaki take aranta domin ta tsani wanan rayuwar.da zasu barta ita kadai da hakan sai ya fi mata dad'i. Amma wanan umarnin dadynta ne ko bata so sai sun bita.


 'Karan jiniyar tasu yasa basu samu jinkiri daga mutaneba ko ina suka zo wucewa hanya ake basu.


 Lokacin da suka shigo makaranta kallo ya koma kansu,mafiy yawa sun san wadda ke ciki.,da yawa suna buri inama sune da wanan ikon,da babu abin da zai sasu yin karatu awanan 'kasar.

 

 Abin da basu saniba shine rayuwar khaleesat da akwai banbanci mai yawa.adole take samun ban-banci da rayuwar mutane.ko yaushe tana sha'awar gwada rayuwar marasa 'karfi taji abin da suke ji.


 Sai da suka kawota har side dinsu sanan suka tsaya aguje wani ya bude mata 'kofa ta fito.

 Harara ta maka masa saboda haushin da taji. "Yi haquri madam" ya fad'a yana sunkuyar d kai 'kasa.

 

Kafin tayi magana ya rigata shiga holl d'in hannunsa ri'ke da Na'ura k wata kujera saida ya duba tsaronta da kuma ingancinta,hatta Wanda mutane suke kai saida ya le'ka matsinta da su kansu mutanen.

 Wanan b sabon abu bane awajansu dan sun saba da hakan mut'kar khaleesat zata shigo lecture.***

GUMSA


Sauri yake sosai kamar ya kife fuskarsa 'kunshe da fara'a, babu ranar da ta kai masa yau., idan yayi la'akari da zuwan da lauwali yayi masa..,

 Mai Gari ke 'kiransa da kansa.,zai bashi aikin da bai ta6a irinsa ba,kamar yanda yaji lauwalin ya fada.


 To amma gsky ya fada shi bazai iya tuna ranar da wani a 'kauyen ya bashi aikiba koda na kwasar kashi ne,.


 Sai dai dariyarsa CE ta tsaya. ganin mutane sha'ke afadar wasu A zaune wasu kuma a tsattsaye.

 Idanuwansu duka akansa babu wata alamar fara'a ko kadan.

 Gabansa ne ya Shiva faduwa yana ta kiran sunan Allah.

©Um Nass🏇🏼

[10/17, 9:05 PM] Oum Nass: *HADIN KWARMAI* 🎊


 *©😘Um Nass* 🏇🏼


® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION*PAGE 6


 Gabansa ne yaci gaba da luguden faduwa.,ga fargaba da ta 'kara cikashi,Musamman da yaga fiskokin mutanen babu rahmar farin ciki atare da su. Da qyar ya samu ya d'aga 'kafarsa ya 'karasa wajansu,bakinsa d'auke da sallama.,

 Mai gari ne kadai ya iya amsa masa,ayayin da sauran mutanen suka kawar da kai gami da tsaki,sai kuma kus-kus dim maganar da ta cika wajan..


 Sunkuyawa Abdallah yayi cike da girmama ya fara gaida mai garin. "Barka da wanan lokacin yalla6e" 

 "Barka kadai Abdallah.ka samu sa'kon 'kirana kenan?"


 Kai ya sunkuyar yana gyad'awa fiskarsa dauke da fara'a "shine dalilin zuwana ma rankai dad'e."


 Gyaran murya yayi hankalin mutanen ya dawo garesu,kowa y nutsu "Amma naso ace da mahaifiyarka kazo nan."

 

 Kai ya d'ago da mamakin jin batun mai garin. "Jakadan kiran ni kadai yace na zo ba tare da mahaifiyata ba.,kana ya sanar dani aikin da zaka bani na mamaki."

 Kuri mai gari yayi yana kallonsa,yana nazarin yaron ko kadan bashi da wata damuwa,ko kuma wata tawaya atare da shi Wanda mutanen garin suke 'korafi akansa.


 "Haka ne,kasan ya matsayinka yake awajan mutanen garin nan?"

 Tambayar da Mai Gari ya masa Wanda ta sashin murmushi mai sauti,kana ya kai kallonsa garesu duk Wanda suka had'a ido dashi sai dai ya bishi da harara.


 Baki ya wangale cike da dariya dan ko kad'an baya jin haushinsu yanzu "Kamar 'kudan Zuma da mutumin da yasa turare yalla6e"


 Murmushi sosai Mai Gai yayi,sanan yakai kansa ga sauran mutanen garin yanayinsu ya 'kara sashi murmushi kamar sa hadiye Abdallah dan harara.

 "minene 'korafin ku akan Abdallah? Gashi agabanku sai Ku maimaita mana damuwarku."


 Zuruf Sule yayi kasancewarsa sarkin kaud'i awajan da za'kal'kalewa "Zamansa ne bama so atare da mu yalla6e,naci gareshi da rashin zuciya. Abin takaicinma shine yanda ya maida dukkanin mutanen garin nan mahaukata kamarsa."

 " 'Kwarai kuwa yalla6e, wanan yaron fitina CE garemu, duk lokacin da ya ra6i mutum sai ya tafka asara. Inma ta dukiya ko kuma ta kadorin mutum."

 Wani ya cafke maganar da sule ya fara. Haka wajan y kaure gaba d'aya da hayaniya,kowa fadar laifin Abdallah yake da son akorasu agarin ya barshi.

 

 Baki bude yake kallonsu har ya rasa abin da zaiyi,mamaki ko alhini?


 Hannu Mai garin ya daga musu "ya isah haka Ku saurara"

 Nan sukayi shuru suna huci kamar Wanda suka shiga dandalin dambe.


 "Abdallah kaji abin da mutanen garin suka hadu akansa.?"

 Kai ya gyad'a yana murmushi,ayayin da zuciyarsa ke tafarfasa kamar an d'orata akan garwashi.

 _Dama ya San za'ayi hakan. Mut'kar basu daina 'kiyayyar da suke masaba,to wata rana zasu da6a masa wu'ka.,baima ta6a kawowa akan sazu sa akoreshi agarinba._


 "Kana da wata magana akan haka? Ko 'korafin da zakayi kaima?"maganar Mai Gari ta dawo dashi daga tunani da zuciyarsa ta wullashi.


 Dariya yayi kamar yanda ya zama d'abi'ar sa"A'a rankash dad's,bani da ja akan hakan."


 Zama Mai gari ya gyara yana kallonsa,Sosai yaron kee burgeshi awani gefen kuma yana jinjina halayyarsa,ko kad'an bashi d damuwa,haka kuma yana tausayinsa da rayuwar da zai fada,ahakama yana rasa aikinyi balle akace yabar garin ko anini baya da shi. Sam ba'a masa adalciba idan hakan ta faru.


  "Shikenan Abdallah zai bar muku wanan garin, kodan shima yasamu sa'ida da rangwame daga 'kaluben da yake fiskanta awajanku."

 Uhu wajan ya kaure da shi harda sowa,wasu na rawa suna jijjinawa Mai garin.

 Toshe kunnuwa Abdallah yayi gami da runtse idanuwansa,

 _Tabbas wanan 'kiyayyar ta kai 'karshe.,Saboda zai bar garin mutane suke ta wanan murna.,Ya Allah kasa alkhairi ne zai fidda ni daga garina._"


 "Ya isa haka Ku saurara" Mai gari ya fada cike da takaicin mutanen garin nasa,Wanda ya kirasu da marasa Adalci.


 Tsit kakeji wajan yayi shuru sai "yan 'kus-'kus na mutane Wanda ba'a jiba."Abdallah zai bar muku garin nan, amma da sharadin zaku masa kud'in mota Dana guzurin tafiya.,dan kun San bashi da shi bai kuma bada ajiyarsa ba."

 Nan aka shiga kallo-kallo tsakanin mutanen,. Murnarsu ta koma ciki, A6angarn Abdallah kam murna 'kal ransa yana kuma girmama Adalcin na Mai garin nasu.


 Murmushi yayi sosai yana 'kara kallon mutanen nasa "Baku shiryaba kenan?"ya jefa musu tambaya jin wajn yayi shuru.


 Da sauri Mai Gida ya mi'ke "Mun shirya sosai,kudin mota ba matsala bace ni zan bada."

 Kallone ya koma kansa,mafiya yawa suna mamakinsa musamman idan akayi la'akari da yanda yayima kudi kyakkyawan sani.

 

Cikin takaici Mai garin yake kallonsa "Shi kuma kud'in guzurinfa?"

 Kafin yayi shuru daukacin mutanen wajan suka fara jefa kudi agaban Mai garin ,daga masu d'ari biyu sai masu d'ari biyar kadan ne suka jefa Naira 100.


 Baki sake Abdallah yake kallonsu,haka mai gari yana jinjina qarfin qiyayyar da suke ma wanan yaron.

 Dubu biyar Mai gida ya ajiye "ga kudin motar nan,harma Dana jari nasan ya samu."


 Bakin magana Abdallah ya rasa farin ciki zaiyi ko kuwa ba'kin ciki.

 Idan zaima zuciyarsa Adalci to frn ck ya kamata ace yayi adai-dai lokacin da ya gaji da rayuwa cikin ma'kiyansa.Ashe su har sun fishi gajiyawa d ganinsa.


 "Shikenan Abdallah kayi ha'kuri kabar garin nan,'kila alkhairi ke jiranka agaba, kayi ha'kuri kaji,ina tsoron rayuwa da mutanen dake xagaye da kai,shi yasa bazan so kaci gaba da zama ananba."

 Lalubar aljihunsa yayi ya dauko dubu biyu "ga wanan ka 'kara da shi,"


 Murmushi Abdallah yayi ya fara tattara kud'ad'en da aka harhad'a masa "Ba komi rankai dad'e ina godiya da Adalcinka gareni. Yau din nan zamu bar garin nan."


 "Ai dama ko SAA guda ba zamu bari ka 'karaba,abanza zamu Tara maka kud'ad'anmu"daukacin mutanen suka hayo kansa.

 Dariya yayi yana girgiza musu kai..,daga nan ya tashi yayi hanyar Gida.


 Duuuuuu mutanen sukayi dafifi suna binsa abaya kamar da ya kashe mutum yake shirin guduwa.


 Hayaniyar da Ummie taji ya sata fitowa,cike da tashin hankali da fargaba take ganin mutanen......

*NOTE*


 _KUyi haquri da rashin ganin post dina kwana biyu,yarona ne babu lafiya amma yanzu yaji sauqi. In sha Allah zakuna jina ko yaushe.ina mutqar godiya da jinjinawa gareku da kulawarku gareni nagode sosai 😘_ 

 *Ana tarefa irin sosai da sosai dinnan 😃🤝🏼*©Um Nass🏇🏼

[10/17, 9:05 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI* 🎊


 *©😘Um Nass 🏇🏼*


*®MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION*PAGE 7


 

 Gabanta ne yaci gaba da faduwa,tana kallon fuskokinsu babu rahma ko kad'an.,abin mamakin yanda suka tuso 'keyar Abdallah agaba.

 _"Allah yasa ba wani laifi wanan yaron ya musuba."_Addu'ar da takeyi azuciyarta kenan.


 Kasa ha'kurin jiransu tayi ta rugo da gudu har gaban Abdallah din "Lafiya Abdallah? Mi ya faru da kai, haka mutane suka biyoka?"


 Dariya yayi yana kallon mutanen,Wanda kowa suka had'a ido hararce take biyo baya.

 Kai ya shafa yana ri'ke hannun Ummien nasa "Ba abin da nayi Ummie. Wadan nan "yan rakiyata ne, daga wajan mai gari muke"


 Kallonta takai ga mutanen Wanda maganar Abdallah ta 'kara fuskata su."Kayi sauri ka had'o kayanka,kar ka maida mu wasu sakarkaru anan" wani ya fada yana 'kara sau'ke fushunsa akan Abdallah.


 "Kamar ya ya had'o kayansa? Ina zai je.?"Ummie take tambaya cikin tashin hankali babu waanda ya kulata,ri'ke hannun Abdallah tayi Wanda yake 'ko'karin shiga gidansu "Abdallah wai mi yake faruwa ne.? Ina xakaje da kayan naka?"

 Murmushi yayi yajata suka shiga gidan. Su kuma mutanen suka tsaya a'kofar Gida suna masu 'kara hantararsa akan yayi Sauri ya fito basu da lokaci.


 'Daki ya wuce ya fara had'a kayansa cikin sauri,. Ri'keshi Ummie tayi tana girgiza kai "Abdallah mana ka min..."muryarta ta fara sarqewa Sam ta kasa masa tambayar da ya kamata ace ta masa,fargaba CE da tsoro ya cikata sosai.

 Juyowa yayi yana fiskartarta,girgiza mata kai yayi yana murmushi "Ummie bana fad'a miki wata rana 'kiyayyar mutanen garin nan zata kaini wata duniya da banba?"

 Kai ta gyada hawaye na zuba daga idanuwanta tana girgiza kai,murmushi ya sakeyi Wanda da ganinsa na takaici ne "Hasashena akan ma'kiyana ya zama gaskiya,yau duka mutanen garin nan sun kai 'karana ga mai gari......."nan ya zayyana mata dukkanin abin da ya faru.

 Sanan ya 'kara yawaita murmushinsa "Sam 'kaddarata bata atare da su Ummie, kamar yanda kika fad'a abaya. Zan bar garin nan idan hakan yana cikin 'kaddarata"


 Hawaye sosai ya shiga zuba a idanuwan Ummie,kai ta ke girgixa masa,ta hango tashin hankali mai yawa atare da shi.

 "Sam bazaan bari ka tafi ka barni b Abdallah,kai ne rayuwata,kai kad'ai nake gani naji frn ck atare da ni. Kayi ha'kuri Abdallah, ni na janyo maka wanan rayuwar, da tuni mun fara sabawa da sabuwar rayuwa awani wajan. Ban ta6a tunannin 'kiyayyar da mutanen garin nan suke maka har ta kai hakaba. Bazan jure rayuwa anan babu kaiba."


 Kai ya girgiza mata yana share mata hawaye "Ummie yanzu ba lokacin kuka bane,lokaci ne na farin ciki da samun sabuwar rayuwa."

 

 'Kofa sukaji ana bugawa kamar za'a 6allata, ga kuma hayaniyar mutanen garin ta 'kara yawa "kai jiranka muke fa. Uwar mi kake had'awa agidan da ba kayan kirki gareka ba."maganar su ta cika kunnuwansu.

 

 Da sauri Ummie ta shiga d'akinta ta dauro kayanta a d'an kwalli wanda basu wuce kala ukuba dama.

 "Fito mu tafi Abdallah kafin mahaukatan nan su shigo."

 Ledar 'kullin kayansa ya d'auko shima ya fito.


 Basu musu maganaba suka sa kai suka wuce,binsu suka farayi abaya har sai da suka kawosu rafin garin,. Sanan suka ja tunga suka tsaya.


"To sai Ku wuce da sauri,dan kunsan kuka kai yamma munari na iya futowa ta hallaka Ku."

 Sule ya fad'a cike da izgili. Yasan Munari Aljana ce wadda take fitowa daf da almuru idan kuma ba'kone yayi gigin fad'awa rafin tasa ta 'kare.


 Dariya yayi yana girgiza kai "Mun gode sosai. Mun tafi sai kuma Allah ya sake 'kaddara saduwarmu."

 Kamar had'in baki sukace "Har Abadan abadina ba zamu had'uba."


 Girgiza kai yayi yana dariya _"wad'an nan mutanen ba zasu sauyaba Sam."_

 Bai 'kara musu maganaba ya ri'ke hannun Ummie suuka yi gaba.

 

 Cikin ikon Allah suka tsallake rafin. Nan sukayi sa'ar samun akori kura tayo lodin ice.


 Tsayarta sukayi jin cewar Yadin Bunni ta nufa, kana suka shiga duk da matsi da takura haka suka hau saman icen.

 Tafiya CE ta wahla sukayita Wanda tudu da kwari ga kuma wahalar da ice ke 'kara musu.


 Hamdala sukayi ga Allah lokacin da motar ta shiga Garin.

 Atasha aka tsayar da su suka sau'ka.

 Nan suka fara kallon-kallo da rarraba idanuwa saboda rashin sanin taka maimai din inda zasuje.

 

 "Abdallah ko zamu zauna an an garin ne?"Ummie ta tambayata fiskarta kunshe da damuwa.


 Ido ya fiddo waje kafin ya Shiga girgiza kai "Ummie ni ko a Damaturu bazan zaunaba balle nan garin.Ummie YOBE gaba d'ayanta ma bana bu'katarta ayanzu, kamar yanda itama bata bu'katata."


 Kano!Kano!!Kano state !!! maganar wani kwamdasta ta ratsa kunnuwan Abdallah.


 KANO ya sake mai-maita sunan garin fiskarsa 'kunshe da fara'a.


 "Kano Ummie.Nan zamu tafi,zamuyi nisa da yankinmu, nisan da had'uwa zaiyi wahla da mutanen GUMSA."


 Kai ta jijjina tana alhiniN Barin mahaifarta "Muje....…"


*©Um Nass🏇🏼*

[10/17, 9:05 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI* 🎊


 ©by *😘UM NASS 🏇🏻*


*Follow mee on Whatppad @UmNass*


® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION.  _"Alhmdlh Alhmdlh in sha Allah na dawo xan ci gaba.,ina mana barka da sallah da ftn Allah ya kar6i ibadinmu da mukayi acikin watan da ya gabata Ameeen."_
 Page 8 Kai tsaye suka nufi kwandostan motar dake faman ambatar Kano.

 "Zamuje kano malam INA motar da xamu shiga?"

 Maganar da Abdallah yayima kwandostan Wanda yasashi washe bakinsa "a a Bismillanku to ga motar can." 

 Nuni ya musu da hannunsa kana yayi gaba zuwa ga motar cikin hanzari suma suka bishi.

 Cikin sa'a suka tadda saura mutum uku motar ta CIKA Wanda suna shiga wani yazo shima ya shiga.

 Kudin motar Kwandosta ya shiga kar6a har sai da ya kar6i na kowa sanan ya miqama Direban ya wari abin da xai basu.

 Tuni Direban yazo ya shiga ya kunnata bakinsa dauke da bismillah,.

 Abin da ya qarama su Abdallah nutsuwar xuciya jin Addu'a abakin wanan Direban wanda abune mai wahla jinta abakin Direban tasha.


 Tafiya suke cikin kwanciyar hankali, baka jin komi sai surutun mutunen motar Wanda har baxaka iya tantance nawa xaka jiba.

 Domin kowa buqatarsa nasa ya xama mafi rinjaye ga mutane.


 Tafiya tayi tafiya Wanda mafiya yawan mutanen sunyi barci saboda Nisan dake tsakanin yobe da kano ba kada bane.

 Idan ka dauke Direba da yake tuqi sai kuma Abdallah Wanda ya shiga kogin tunanin yanda rayuwarsu xata kasance akano ko da dadi ko kuma akasin hkan.


 Yini guda suka cinye ahanya kafin su fara hango gine ginen garin kanon Wanda mafiya yawansu dauke suke da tambarin kwankwasiya akansu.


 Tuni mutanen da sukayi barci sun tashi zaune suna bama idanuwansu abincin.


 Baki Abdallah ya saka yana qara bude idanuwansa ganin mutane birjik ta ko INA da dai duniya sai kace ba'@ mutuwa.


 Ahaka suka rinqa kutsawa duk da yawan go slow din da yake tsayar dasu har suka shiga tasha.

 Ananfa kowa ya fara qoqarin sauqa domin xuwa inda xashi.,sai fa Abdallah da Umminsa da Sukayi curko curko na rashi sanin madafar inda xasu.


 "Abdallah gamu a Kano gari mai cike da mutane Wanda kowa rayuwarsa yake, yanxu INA xxamu nufa?"

 Idonsa ya rufe ya bude ahankali kafin ya saita muryarsa Wanda take dauke da fargaba,domin azahiri shi tsoron yawan mutanen da yakega agarin yake balle kuma tashar ma da take cike da mutane,."kafin wanan tunanin mu nemi abinci muyi sallah Ummie domin yunwa nake ji sosai ga sallah kuma da muka Tara akanmu."

 Kai ta jijjiga alamar gamsuwa kafin sun hango wata dattijuwa mai diyar da abinci Wanda mutane sukayima qawayana alamar jira.

 Qarasawa kusa da ita sukayi bakinsu dauke da sallama.

 Amsawa mutanen wajan sukayi kafin nan suka maida hankalinsu ga mai sai da abin cin.


 "Mi kuke so abaku?"

 Ta Jefa tambayar tsakanin Ummi da Abdallah Dan ganinsu da tayi ya tabbatar mata su din baqi ne.

 500 Abdallah ya miqa mata gami Da Dan rusunawa "Abinci xaki bamu,ko wani iri ne bamu da xa6i."

Kallonsa take ganin fiskarsa dauke da murmushi da kuma girmamawa acikin mgnrsa.


 Shinkafa da miya ta zuba musu hadda kafi Wanda da alama ta zarce yawan Adadin kudin nasu.

 Sanan ta bude wata kula akusa da ita ta miqo musu robar zo6o mai sanyi guda biyu.,

 "Gashi kuje can kuci akwai ruwa da makewayi idan kuna buqatar yin sallah." Ta fada musu fiskarta dauke da fara'a Dan sosai mutanen suka shiga ranta duk da ba wani mgn sukayi da ita na tsawan lokaciba.


 Godiya suka shiga yi mata Dan wanan karamcin yasa sun samu wani qarfin gwuiwa akan lallai sun shigo kano da qafar dama.

 Karo na farko an girmamasu an kuma yi musu maganar cikin fara'a da sananin kimarsu....
 _Tofa rider's gamu acikin Kano ga kuma sauqaR da aka fara yima Abdallah.,da alama qarshen wahlarsa ta xo....._


  _Ku dai ci gaba da bibbiyata amma kuyi hqr ganin page gajere sbd muna fama da rashin NEPA_

 *Marsalar Dan 9ja kenan 🤥*
©by *😘Um Nass🏇🏻*

[10/17, 9:05 PM] Oum Nass: [6/21, 2:59 PM] 😘Um Nass🏇🏻: *HADIN GWARMAI 🎊*


 ©by *😘UM NASS 🏇🏻*


*WHATPPAD @UmNass*


® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION*
PAGE 9"Kaga wani lamari na Allah ko Abdallah?ban ta6a tsammanin ganin farin ciki da girmama atare da mutaneba,idan nayi la'akari da yanda rayuwarmu ta xama acikin garimu...


 Maganar Ummie kenan lokacin da suka dai-daita zamansu akan tabarmar dake shimfide ashagon da suka shiga.

 Kai ya gyada yana yalwata fara'ar fiskarsa wanda ta Dade da xama jiki atare da shi." Ni kaina mamakin da nake kenan Ummie. Amma hakan yana daga cikin ikon Allah, sai dai muyi fatan samun fiye da haka agaba."

 

 "Haka ne kam,muci abinci muyi sallah sai mu nemi muhalli tunda naga akwai rarar kudi atare da mu...  Bismillah sukayi sanan suka fara cin Abin cin fiskarsu dauke da farin ciki ga kuma wata nutsuwa ta musamman da take sauqa atare da su.


  Bayan sun kammala suka yi hamdala ga Allah sanan sukayi alwala..

 Abdallah ya ja musu jam'i.,sun dauki lokaci suna Addu'a akan Allah ya kawo musu dauki da fatan hakan shine samun warwarar matsalarsu.

 Daga nan suka miqe domin magrib ta fara kawo basu samu madafar da xasu jingina ajikintaba.


 Sallama Ummie tayima mai saida Abincin mutane sun ragu sosai da Alama abincin NATA ya qare Dan sai harhade kayanta takeyi.

 " Wa alaikumussalam, har kun fito kenan?"ta amsa mata fiskarta dauke da fara'a.

 "Eh mun kammala.ga kwanonki da robobinki,mun gode sosai Allah yaji qan mahaifa."

 

 "Ameen,Ameen"


Ta kar6a tana jin dadin Addu'ar da ta mata,da mamakinta taga kwanon awanke fess hata robar zo6on itama awanke take.

 Dagowa tayi tana fadad'a fara'arta "Umm nace amma dai Ku baqi ne awanan garin ko?,Dan naga kwanikana fess awanke,..


 Kai Ummie ta gyada "Eh! yau muka fara shigowa wanan garin.,mu mutanen Yobe ne.,yanxuma Sauri muke muje mu nemi wajan da xamu samu haya koda d'aki daya ne.,Dan gama naji ance haya agarin nan tana kudi....


 Murmushi Mai Abinci tayi kafin ta gyara zamanta." Gaskiya ne wanan.,amma idan ba zaku damuba Ku bini gidana mana kafin zuwa gobe idan Allah ya kai mu,sai asa anema muku.,kano da fadi sosai,Dan ni dai zuciyata ta nutsu da Ku,gashi nima gidana daga ni sai Dana Wanda baxai fi Sa'an yaronki ba."


 "Ikon Allah to ai mun gode sosai hajiya, har ban San baki gode mikiba ma...


 " karki damu wanan ai duk yiwa kaine,Allah yana son bayinsa masu taimako."


 Kallonta takai ga Abdallah Wanda Sam hankalinsa baya kansu,Asalima ya raja'a a kallon mutanen da suke harkarsu ba ruwan wani da wani."


 

 Zabura yayi ya juyo jin sunansa

[6/21, 3:38 PM] 😘Um Nass🏇🏻: Da Ummie ta qira "Na'am. Ummie mu tafi ko,.?


 "Ai Allah ya hutarmu wahla, wanan matar tace xamu xauna agidanta saboda dare yayi, kafin xuwa gobe afara cikita mana gidan haya dai-dai kudinmu."


 Ido ya fiddo waje "ke kuma kika ce mi Ummie?"


 "Yo Amincewa mana nayi,kasan dai yanxu bamu San wa xamu fara yima cikiyaba,kasan yanda wanan qasar tamu ba wuya an cuceka balle kuma gari kamar Kano,na kazo na zo."


 Kai ya jinjina "To amma ita kina da tabbacin ta gari ce?danfa mugu baya kama Ummie,kar muyi gudun gara mu tarda zago agaba."


 "In sha Allah INA mata kyakkyawan tsammanin,dan xuciyata ta Aminta da ita."


 "Allah yasa to hakan ne agaske ma.."

 Ameeen ta Amsa,


 "Yauwa kuxo mu tafi ga mota har na gama loda kayana."

 Maganar Mai Abinci kenan ta doki kunnuwansu yayin da take qarasowa kusa da su.


 "To" suka fada suna fadada fara'arsu atare da ita,kafin su shiga cikin motar direba yaja.
 *******

 Government House Cikin nutsuwa take sarrafa na'urar computer dake gabanta.,fiskarta na nuna tsantsar gajiyawar dake atare da ita.

 Dan tsaki tayi akaro na farko kafin ta dago ta dauki kofin dake gabanta Wanda yake dauke da lemo acikinsa.

 

 Kar6a tayi ahankali tana dada yamutsa fiskarta kamar da ta sha magani.

 Sanan ta sake maida hankalinta ga computer taci gaba da dannata,.ahankali ta sauqe numfashi Sanan tayi murmushi afiskarta..."Na gode Allah da na magance wanan matsalar kuma."


 Sai a lokacin mahaifiyarta ta dago ta kai kallonta gareta "Matsalar mi kuma?bakya rabo da shiririta khaleesat."


 Fuska ta marairaice alamar mgnr Maa ta 6ata mata rai "bafa shiririta nakeba,wani Abu mai muhimmanci nakeyifa."


 "Uhmm ya wuci ace game kike,.nasan dai baki da aikin daya fishi acikin computer ki. Shi yasa Sam banga amfanin siya miki itaba,.ace abun karatu ya koma na wasa."


 "Maaa fa,"

 

 Ta fada idanuwanta da alamar hawaye acikinsa "ba wani Maa,ba game din kikeba.?"


 Kai ta girgiza dan awanan ga6ae kam tana bude baki hawaye ne zai zubo.idan akwai abin da ta tsana to bai wuce fada ba,gashi ko kadan Maa bata gajiya da yi mata shi."


 Miqewa tayi ta tattara kayanta, ta haye saman dakinta ba tare da ta sake cewa komiba.


 Kai Maa ta girgiza "Allah ya shirya ki khaleesat. Magana kadai ke baki wahla da saki kuka, ban San kuma mi gaba xakiyi ba idan kikayi Aure.,,?"


 Miqewa tayi ta shige dakinta itama jin ana qiraye-qirayen sallahr magrib..."   ©by *😘Um Nass* 🏇🏻

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: [6/23, 3:14 PM] 😘Um Nass🏇🏻: *HADIN GWARMAI* 🎊


 ©by *😘Um Nass🏇🏻*

.

*Whattpad @UmNass*


® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION*
PAGE 10  "Tafiya suke akan titi yayin da su Abdallah suka baza idanuwansu suna ganin gari.,

 "Lallai Kano da girma take,ga bil Adama kamar ba'a mutuwa."


 Fadar Ummie Wanda tasa Mai saida abinci dariya ita da direba.

 "Ai kadanma kikaga dan da yawa yau ana hutun xuwa'aiki da kinga mutane fiye da haka."

 Kai ta jinjina alamar gamsuwa "Ai ko iya haka aka bar mutum ya isa ya sheda cewa garin Babba ne."


 Haka dai suka ci gaba da tafiya har suka shiga unguwar WALAWAI Wanda da ganinta kasan unguwar ta marasa qarfi CE.

 Haka duk tudu da kwari ne acikinta Wanda dole yasasu tafia ahankali.


 Adaidai qofar wani gida suka tsaya Wanda shine mai dan alamar qarfi acikinsa.

 "Yauwa Alhmdlh.Allah ya kawo mu gida, sai mu sauqa ko?"

 Ahankali suka sauqa acikin motar, suka tsaya har direba ya gama sauqe musu kayansu.


 Daga nan Mai Abinci ta sallameshi.

 Mukulli tasa ta bude gidan sanan ta juyo tace "Bismillanku Ku shigo ga gidan."

 Kayanta suka fara tayata dauka sanan suka shiga gidan bakinsu dauke da sallama.


 Zaure ne xaka fara karo da shi sai daki guda daya ajikinsa,tsakar gidanta er madaidaiciya da rumfa data ke kallon zauren ga dakuna biyu ajere,. Saifa simintin da yake malele atsakar gidan Wanda ya fito da tasirin kyansa azahiri.


  "Wa alaikumussalam,sannunku Ku shigo mana."

 

Tayi saurin tarar su tana shimfida tabarma atsakar gidan kasancewar yanayin zafi da muke acikinsa.


 Murmushi ta qara yalwata fiskarta da shi"Kunga Dan akurkin da nake rayuwa acikinsa,INA fatan ba xaku takura da zama acikinsa ba.?"

  

 Saurin girgiza kai sukayi atare kafin Ummie tayi magna"Masha Allah.,hajiya wanan ai yafi qarfin aqirashi akurki sai dai ace masa fada guda.,domin samun gurin xama abune mai mutqar wahla, musamman awanan garin da yake cike da Dan Adam,.Alhmdlh gida yayi Allah ya Sanya alkhairi acikin xamanmu ya nisanta mu daga fitinar shedan".


 "Ameeen,Ameeen" suka fada cikin hadin baki.

 "Hajiya mukam ai kin gama mana komi sai fatan Allah ya saka miki da mafificin alkhairi, samun mutum na gari Wanda yake taimakon mutanen da bai saniba abune mai wahlar.,musamman idan mukayi la'akari da yadda rayuwa ta koma ayanxu,babu yarda tsakanin baqo da Dan gari saboda balagurbin da suke fakewa da baqunta suna cutar mutane."maganar da Abdallah yayi muryarsa cike da nutsuwa acikinta,Wanda hakan ya qara Samar da nutsuwa axuciyar mai Abinci.


 '"Haka ne yaro amma ni kam tun ganina da Ku xuciyata ta samu nutsuwa da ku,Sam vakuyi Kama da mugwayen mutane ba...

 Ku tashi muyi alwala muyi sallah kada lokaci ya wuce."


 Miqewa sukayi gaba daya suka daura alwala,anan tayima Abdallah kwatance masallacin da yake kusa da su jin ana tada iqamar shiga sallah,.yayin da ta shimfida musu sallaya biyu suka tada tasu sallahr ita da Ummie....  

*******


 Abin cin dare ta gabatar musu bayan hallarsu awaje guda,.

 Adai-dai lokacin da ne wani matashin saurayi ya shigo gidan cikin sallama.


  Amsa masa sukayi atare suna duba qofar shigowa.,

 Saifa Mai Abinci da ta Dora da cewa "Arfat ka dawo Ashe?"


 Kai ya gyada yana miqama Abdallah hannu,alamar musabaha,saurin miqa masa yayi yana qara masa da murmushi "Allah ya yarda,yau da wuri na dawo, Dan a lokacinma baki dawoba,shine na shiga wajan Naseer."


 "Eh yau ban samu dawowa da wuriba"


 "Ayya baqi mukayi kenan,.Umma sannu da hanya,?mun yini lfy?"

 Cikin girmamawa yake gaida Ummie Wanda hakan ya sata jin dadi sosai azuciyarta., tana qara jinjinama Mai Abinci ta samu yaro nitsattse ko ta wajan maganarsa xaka tabbatar da nagartarsa."

[6/23, 3:53 PM] 😘Um Nass🏇🏻: "Alhmdlh lafiya lau.,ya aiki?"

 "Sai godiyar Allah..


" Allah ya taimaka, ya sanya maka albarka...


 "Ameeen ya Allah.

 Suka fada atare,sanan ya gyara zamansa yana kallon mahaifiyar tasa.,

 Murmushi tayi Dan ta San manufarsa nayin hakan " Baqi mukayi yau suka zo garin suna Neman inda xasu xauna,shine nace su zo gidana kafin asamu gidan haya,kasan yanxu samun haya yana wahlar.,gashi sunyi tafiya mai Nisa mutanen yobe ne."

 

 Kai ya jinjina alamar gamsuwa da maganar Mahaifiyar tasa,yana son halayyarta ta taimako,."inaga su zauna mana kawai tunda akwai yalwar wajan xaman,idan yaso sai muna kwana da namijin,ke ma kina buqatar Wanda xatana debe miki kewa, saboda dare abin tsoro ne kafin nasan halin da kike ciki ita ta sani,.ma'ana dai ba fataba xama mutum daya sai dole....


 

 "Kai masha Allah nima da haka nake ta tunani amma sai nakega kamar ba xaka yardaba."

 Kai ya girgiza yana murmushi "Mama ai kin koyar dani taimakon mutane,sanan kin sanar dani mutum rahma ne aduk inda yake..." Kana ya juya ga kallonsa wajan su Ummie da Abdallah Wanda suka qame cikin al'ajabin karamcin mutanen nan "Idan babu damuwa Ku zauna damu iya tsawon lokacin Da kuka so Ku zauna awanan garin namu." 


  Kai suka iya gyadawa kafin Hawayen da zan qirashi na farin ciki ya zuba a idanuwan Ummie."Alhmdlh mun godema Allah wanan yana daga cikin rahmarsa da ya Sanya mu haduwa da mutanen kirki,har ban San da bakin da zan gode mukuba.,Amma INA fatan Allah ya ri6anya muku da ninkin Abin da kuka mana na alkhairi."


 Riqe hannunta mai abinci tayi kafin tana share mata hawaye "Ba komi na fada miki wanan yima Kaine."


 "Allah ya saka da alkhairi Hajiya,mun gode Abokina" shima Abdallah ya fada yana hade hannayensa waje guda alamar godiyar mai yawa CE,Wanda baxai iya fadar komiba...


  

  Murmushi sukayi kafin suce "Ameeen" atare ahankali Mai Abinci ta shiga gabatar musu da sunanta...


  "Sunana Fatima amma ana qirana da Anta ni er Asalin Dan batta ce, Aure ne ya kawo.ni nan garin,.zama mukayi na Amana da Auwalu mahaifin Arfat har na tsawon shekaru shida kafin Allah ya axurta mu da samun haihuwar kabir shine muke kiransa da Arfat.,ban ta6a rasa wani abuba duk da qaramin qarfin mijina amma Muna cikin wadatar xuciya,.

 Shekarar Arfat goma Allah yayima mahifinsa rasuwa sakamakon hatsarin mota,alokacin nayi kuka sosai sbd iyayena basu Dade da rasuwaba.


 Kun San zumuncin yanxu bashi da qarko,hakan yasa na fara sana'ar Abinci atasha Dan na inganta rayuwar Dana da ilimi ,Alhmdlh yanxu ya gama jami'a sai dai aiki da yayi masa wuya shine yake aiki a garejin gyaran mota.."


 Wanan shine tarihinmu INA fatan xamu zama en uwa.mu kuma zama abokan shawarar junanmu..


 "In sha Allahu, Allah yaji qansu da rahma yasa mutuwarsu Hutu ce.haqiqa kema Kinga rayuwa hajiya."


 Kai ta girgiza kawai kafin tace "muci Abinci ya fara yin sanyi gashi dare yayi,kuma kuna buqatar Ku huta." Jikinsu ne kowa ya Mutu musamman da rayuwarsu tayi kaamancecceniya data juna.,.banbanci bai wuce yanda mutanen garinsu suka qyamacesuba....


 Haka suka Dan caccakali abincin suka tashi.,

 Sallhar issha'i sukayi suka kwanta kowa yana tuna quncin rayuwarsa....


 Sai dai wani 6angare na xuciyarsu na hankaltar dasu girman qaddara.....
     _😀👏🏼kuyi Haquri da wanan akwai wahla sosai acikin typing...sai dai ban muku Alqawalin ganin post dina kullum ba amma xanyi qoqarin yi duk lokacin da na samu dama...Ina mutqar godiya sosai a yanda kuka kar6eni da kuma soyayyarku ga labarin *HADIN GWARMAI* Sosai nake yinku 😘_"
©by *😘Um Nass* 🏇🏻

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI* 🎊


 ©by *😘Um Nass🏇🏻*


 *Whattpad @UmNass*


® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION*
 PAGE 11
Washe gari...


 Tun da sukayi sallahr Asuba basu samu sake xamaba, Dan kiciniyar girki suka shiga,sosai Ummie ta ke taimakawa Mama Anta Wanda hakan ya kawo sauqin aikin nasu,suka gama shi cikin kazar niya da tallafi atsakaninsu. Haka suka share gidan suka wanke tukwane da kwanikan da suka gama amfani da su..,


 Wanka sukayi suka shirya kana Mama Anta ta xubo musu Abinci.

 Fiskarta shimfide take da farin ciki na kasuntuwarsu atare,da d'ai duniya sai ka rantse sun dade da sanin junansu.,harma ka daukesu amatsayin dangi Guda.


 "Assalamun Alaikum" muryoyin Abdallah da Arfat ta fito atare kamar an CE suyi HADIN baki.


 "Wa alaikumussalam wa rahmatullah" suma suka amsa musu suna murmushi..


 "Lallai kun iya kiwo," Mama Anta ta fada tana kai kallonta garesu.


 Qarasawa sukayi sanan suka xauna suna kai kallonsu ga Abinci da suka ci,farfesun kayan ciki ne sai kuma jalof din taliya gefe guda kuma ruwan zo6o ne mai sanyin gaske.

 Cikin nutsuwa suka fara gaidasu da girmamawa.,

  

 "Barkanmu da safiya Ummie da Mama"

 'Yauwa barka dai Abdallah ya kwanan baqunta kuma"Mama Anta ta amsa masa tana fadada murmushinta gareshi.


 Sunkuyar da kai yayi yana murmushi "Alhmdlh muna godema Allah,sanan muna qara muku godiya sosai Allah ya..."

 Saurin dakatar da shi tayi "Abdallah mana,ai mun gama wanan maganar tun jiya ko,ya kamata kaima ka barta haka nan.,"


 Girgiza kai kawai.yayi kafin ya kai ganinsa ga Ummie Wanda yau ta zame masa sabuwa,bai ta6a ganin walwala da farin ciki atare da itaba kamar na yau. Duk da ko yaushe tana qoqarin nuna masa hakan amma kallo daya xaka mata ka fahimci xuciyarta cike take da quna da gajiyawa awancan lokacin. Amma na yau babu surki farin ciki ne shimfide axcyrta.na gasken gaske. Hankinta kwacankaf yanaga Arfat Wanda yake gaidata cike da barkwancinsa.


 Wata qanqarar farin ciki yaji tana sauqa acikin xuciyarsa.,. Azuwa yanxu yanaga matsalarsu ta Riga da ta zo qarshe..


 Maganar Arfat ta katse shi daga dogon tunanin daya Lula,"Muci Abinci mana kafin ka sake komawa wani kogin tunanin.,da alama akwai wata acikin rayuwarka Wanda ka barta acan ko?"


 Ido ya qwalalo waje kamar daya ga abin tsoro,kafin ya girgiza kansa,.. _"to shi INA ya samu wani qwarin gwuiwar tunkarar mace,bayan suka daukacin mutanen garin na nuna qyama agareshi."_


 Dariya suka fara masa lokacin daya sunkuyar da kansa qasa.,abadini xuciyarsa ta shiga bugawa yayin da kwanyar kansa ta fara hasko masa rayuwar da suka baro abaya.,

 

 Kansa ya dago ya kallesu,.Idanuwansa sun kada sunyi jajir Wanda hakan ya basu tsoro musamman Ummie sa Wanda zata iya cewa murmushi yafi yawa acikin rayuwar yatonta.,duk da anxo dai-dai ga6ar da rauninsa yake,.haka anata 6angaran itama an taso mata da tsohon mikin da ke Addabar rayuwarta atsawon rayuwarta, yake mata qaiqayi kamar ra6uwar qurji axuciya...


 "Arfat kune mutane na farko da na ta6a ganin soyayya da kauna a idanuwanku,idan na dauke mahaifiyata da take ji kamar ta mun numfashi.," numfashi yaja ya furxar da iska mai xafi cikin sassanyar muryarsa yaci gaba "Ni banyi tsammanin acikin wanan duniyar xan xauna da mutanen da xasu soniba bayan mahaifiyata. Musamman idan na hararo farkon rayuwata har izuwa girmana,rayuwa CE mai cike da garari da qyama gami da tsantsar tsana,ban ta6a jin wani yayi min magana da tausasawaba,bayan mahaifiyata.. Balle har nasa ran za'a kaunaceniba."


 Kallonsa suke baki asake sunma kasa auna Inda xasu saka maganarsa.... Da qyar Arfat yayi magana Dan mama Anta kanta ya Riga daya gama kullewa "kamar ya Abdallah,?shin acikin jeji kuke rayiwarku kai da Ummienka,?babu mutane atare DA Ku.?" Murmushi yayi Wanda da ganinsa kasan mai ciwo ne.."Akwai mutane sosaima agarin, kuma mafiya yawan cikinsu akwai alaqa ta jini atare damu,sai dai sa6anin tsammaninka,yafi min sauqi ace dama can ban sansuba.domin atare dani sun xama tamkar buhun da aka daure da qaya,koya suka samu dama 6ulashi suke son ransu.,"


  

 "Kanmu ya kulle sosai Abdallah,xai fi mana sauqi ka mana magana da yaran da xamu gane,sbd koya kayi magana kana qara shigar damu cikin duhu kake." Murmushi yayi kafin yayi magana Ummie NSA tayi "Yazu kuwa xaku fito aduhun da kika shiga.."


 Zama ta gyara yayin da ta kai kallonsu garesu Wanda suka maida hankalinsu gareta.


 Ido ta rufe ta bude ahankali kamar alokacin ne take ganin abin daya faru....._"plss kuyi malejin wanan 😛🤪I hop Baku gyara xama ba Dan labari na gaba_"
©by *😘Um Nass* 🏇🏻

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI* 🎊


 © by *😘Um Nass 🏇🏻*


*WHATTPAD @UmNass*® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION* PAGE 12  

 *ASALIN LABARI* "Mu mutanen YOBE STATE NE kamar yanda na fada miki..

 Mahaifana sun kasance Fulani ne mazauna garin YADIN BUNNI mahaifina ya kasance Malami ne sosai, Wanda yake koyar da dalibai karatun Addini,hakan yasa muke kiransa da Malam duk da sunansa na gaskiya Muhammad,amma anfi qiransa da inkiyar Hammadu.,mahaifiyata ita kadaice matarsa,Sunanta Salaamatu,muna qiranta da Innah,...


 Allah ya azurtatasu da yara guda uku dukaninsu mata ne babbar itace Sa'adatu,ana qiranta da sa'ada sai kuma Deejah sai ni da na kasance auta Haajarah.,


 Akwai kyakkyawar mutunta juna tsakaninmu,haka kuma rayuwar gidanmu da babanci sosai da sauran mutanen Garinmu kasancewar Babanmu malami ne.

 Haka ko kiwo bai yarda mujeba,ataqace koda talla xamuje sai mun yane kanmu da hijabi sa6anin sauran Fulani da suke rayuwarsu cikin shiga ta asalin fulani..


  Mutanen Garinmu sukanyi ta qorafi akanmu, musamman kasancewarmu mata,haka kuma malam yana tsaye akanmu,acewarsu wanan mutuwar xuciyace irin tasa,ya tsaya yana hidimtawa er er mata.,


 Da yawa acikin en uwan mahaifina da suke uba daya har tunkararsa suke akan ya saki Innarmu ya auri matar da xata Haifa masa yara maza,ko kuma ya qaro Aure,.haka zaisa auduga ya rufe kunnensa iyaka ya CE musu,"Haqiqa godiya ta tabbata ga Allah, da ya azurtashi da yara mata,a haka ma wani ya Nema ya rasa,haka kuma baxai kasance mai yiwa Allah butulciba akan ni'imar da ya masa."

 Wanan maganar ta kawo Rarrabuwar kai tsakaninsu,suka kuma hanashi da shiga dukkanim lammuransu,ataqaice dai suka barshi amatsayar sun tsameshi daga cikinsu...

 Wanan shine qalubale na farko da muka fara cin karo da shi..


 Tun daga lokacin malam ya dage da koyar damu karatun alqur'ani da kuma sauran litattafan Addini,fiqhu,tauhid hadis da sauransu,yana kuma nanata mana wanan shine kadai gatan da xai mana arayuwarmu.."  *****Hamza shine mutum na farko da muka shaqu da shi awajan sayar da nono na,haka kuma kullum yakan zo Dan yasha damuna,...

 Mutum ne mai barkwanci da ban dariya duk da miskilanci irin NAwa da kunya sai da na sakar masa,muna hira,Wanda Mafiya yawan hirar tasa akan sana'ar da yakeyi ne Na dako akasuwa da kuma yima mota lodin,.

 Sanan yakan bani labarin garinsu.,.

 Mun shafe wataanni uku atare da shi cikin sabo.,kwatsam sai rayuwar ta sauya mana atare sabonmu ya zarta tsammanin ya koma soyayya mai zafi.,,

 Yayyana suna mun fada da gargadi akan Hamza amma idanuwanmu sun Riga da sun rufe,.


 Tabbas nasan kuskure ne zan tafka,.idan nayi la'akari da bambamcin harshe da al'adar da muke da ita mu da en garin su Hamza Wato GUMSA.,

 Sun kasance Baburawa ne masu kambama Al'adarsu akan Addininsu,.,

 Haka kuma mafiya yawansu basa yarda a Auro musu wata qabilar daba tasuba,acikin al'adarsu ma Sam babu auren waje saifa tsakaninsu..  Idonmu ya rufe daga ni har Hamza Wanda magana har ta kai ga Malam,.


 Mamaki da tsoro ne ya dirarma malam,.Wanda na tabbata bai wuce akan sanin inda nake qoqarin jefa kainaba..


 Kirana yayi cikin Tausasawa kamar yanda ya saba mana magana"Haajarah da gaske ne kina soyayya ba tare da sanina ba?"


 Tambayar da ta jefa zuciyata saurin harbawa,.naji kaamar nayi sa6o arayuwata,duba da qaran cin shekaruna alokacin ban wuce 15 ba,sanan kuma ga yayyana Wanda dama an Riga da an sa musu lokacin auransu.,ni CE dai basuyi tsammanin har xan kai ga soyayyaba,.duk da ba Sabon abu bane awajan Fulani aurar da yaransu da wuri...


 "Ina tambatarki kinyi shuru."


 Bani da za6,i Dan INA jin ko wata kalma guda da Mala yakeyi,tana bugawa da zuciyata., kai na gyada masa,Dan ban iya qaryaba a rayuwa ta ba,.


 Kallona yake yana girgixa kai cikin damuwa "wanene sh?"


 "Hamza., suna zaune a Gumsa,nanne mahaifarsa.,Neman kudi ke kawoshi garin nan ko wata rana."


 "Amma kin San ko ya mutanen garinsu suke.?" Bai jira amsataba yaci gaba "ban hango miki sauqi rayuwa acikin mutanen da suke fifita al'adarsu fiye da Addinisuba Haajarah."


 "Na sani Baffa Malam,. Shidin zai iya zama sa6aninsu,kasancewar zamansa agarin qidayayye ne."


 Yanxu kam ya yarda da zurfin da Autarsa tayi akan soyayya,yana ji ba zai iya hanata abin da take soba,kasancewarsa malami masani.,


 "Mine ne tabbacinki akan sa,?kin manta cewar KO WANI TSUNTSU...(first novel nawa) yana yin kukan gidansu ne,kana tarbiyar farko ana giniwa da ita ne har abada."


 Kai ta qara sunkuyarwa, sbd awanan ga6ar ta saddaqar da ta rasa amsar badawa,.,amma bazata bari arasa da hamza ba...  "Yau a gobe tana iya sa wasu halayyar ta sauya,musamman idan ilimi ya yawaita atsakankani." Murmushi yayi mai Sauti Wanda ya qarama Hajjo faduwar gaba sosai..


  "Ki turo min shi yazo xanyi magana da shi..,Amma ki San abu guda ba'a fafe goga ranar tafiya,duk lokacin da kika tsinci kanki aatare da su,kada ki koka da kowa sai kanki.,bana buqatar jin qorafi atare da su..... Nannauyar ajiyar xuciya ta sauqe sanan tayi hamdala ga Allah ." Na gode sosai Baffa Malam"


 Kai ya girgixa yana qoqarin Neman dauriyarsa "ki kira min innarku idan kinje...."


_Kuyi maleji da wanan.,..Akwai gwarama sosai Acikin wanan labarin....._ 


©by *😘Um Nass🏇🏻*

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: [7/2, 6:17 PM] 😘Um Nass🏇🏻: *HADIN GWARMAI* 🎊


  ©by *😘Um Nass🏇🏻**Whtppd @UmNass*


® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION*PAGE 14


"Wanan ai maganar banxa ce. Sam abin da baxai ta6a iyuwa bane..,dama ba Neman kudi ne yake kaika Yadin Bunni ba.,?Munafurtarmu kake kana fakewa da Neman kudi kana Neman aure a can?" Maganar mahaifinsa Wanda ya miqe tsaye, bakinsa da kumfa jikinsa sai 6ari yake saboda tashin hankali..


 Gumi ne ya fara tsattsafoma Hamza,.Dan Sam baiyi tsammanin ganin tashin hankali kamar haka awajan mahaifinsaba..


 Durqusawa qasa yayi akan gwuiwoyinsa kafin ya hada hannayensa waje guda "Dan Allah Baba karka haramta min auren Haajara akan wani dalili naku ba qabila da al'ada,.Alhali hakan ba Addini bane. Ko kadan ba soyayya bace take kaini Yadin Bunni ba,Asalima mun hadu Da ita akasuwa ne kafin mu fara soyayya kan..."


 "Dallah dakata min haka" mahaifinsa ya fada da kakkausar murya., Wanda yasa kowa dake wajan ya tsorata.,baya Innar Hamza da goggonsa da suka qanqame junansu saboda tsorata..

 A 6angaran hamza tashin hankali ya hango na sosai a wajan mahaifin NASA.. Zuciyarsa taci gaba da bugawa kamar ya Faso qirjinsa Dan tsoro..

  

 Cikin kakkausar muryarsa yaci gaba da magana"Bana son maganar banxa anan Hamza,kafi kowa Sanin Cewar ko kadan bana daga qafa akan al'adata,kuma bana rangwantama mutanen daba qabilata bane..ya kaike Neman qaqaba min balagurbi acikin zuri'ata...kayi kadan ka kuma yi tsararo wajan isa da tsallake umarni na.. Maza ka farka daga rud'ad'd'an mafarkin daya daukeka. Dan bana jin zan baka dama koda dai-dai da bakin allura ne.."


  Yana gama fadar haka ya tashi yana kakkabe rigarsa,. Qoqarin tafiya yake amma Hamza ya riqe qafafuwansa,tuni ya fara gunjin kuka,.wanda ya basu mamaki,.kowa yasan hamza da dauriya Dan sun manta yaushe rabon suga hawaye yana Zuba acikin idonsa..

 Baki Baba ya saki yana kallon Hamza Wanda sai ajiyar xuciya yake,haka kuma ya qanqame qafarsa gam.., cikin sarqeqqiyar murya ta Wanda yayi kika ya gode ya fara magana.

 "Zan iya jure komi Baba,zan iya haqura da ko wata kalar al'adarku.,Amma INA roqonka da girman Allah Da ka barni na Auri Haajara..Zuciyata ba zata iya jure rashintaba.,na roqeka Baba,ka CIKA min wanan burin nawa guda daya tak."


 Hankade shi yayi daga ruqon da ya masa.,kana ya nuna shi da hannunsa "To kuwa sai dai ka Mutu.. Dan gara min ganin gawarka akan na aura maka bare."


 "Tabdijam wanan maganar ma ai almara ce.kai da ganin yanda yaron nan ya dage ba banxa mutanen nan suka barshiba,.kagafa Yaya yanda yake kuka kamar qaramin yaro,ni har na manta rabona da ganin hawayensa."

 Maganar gwaggonsa kenan qanwar babansa,wanda take riqe da al'ajabin abin..


 "Barni da sakarai Harira,. Na dauka Hamza yana da hankali na sosai,shi yasa har na lamince masa xuwa neman kudi wani garin,Ashe xai janyo mana masifa."

 Risinawa yayi dai dai yanda Hamza yake tsugunne hannunsa dafe da kansa"Kaji da wai ko Asiri suka maka,sai dai ya kasheka amma babuni babu hada zuri'a da dangin Fulani masu yawo da sandina."


  Yana gama fadar haka yayi waje abinsa,har kuma lokacin yana ta fada.,

 Qirjinsa Hamza ya dafe saboda azabar zafin da yake masa,.kunnuwansa sai amsa masa kuwa yake akan batun mahaifinsa..


  _Aduk lokacin da masifa ta tunkaroka ana son ka yawaita fadar"Inna lillahi wa inna ilaijirraji'un"amma ba ka tsaya kana qunci da damuwana_"

 Maganar da Haajara ta fada masa lokacin da aka dora masa sharri akasuwarsu..

 Take ya sake maimaita Kalmar "Inna lillahi wa innah ilaihirraji'un"


 Da qarfin ya shiga fadarta,.Wanda yasa gwaggonsa da iya suka qaraso kusa da shi...


 Jin yana maganar da yaren da basu fahimtaba anan suka qara rafka salati "Salati ga Annabi yake.,Shikenan ta faru ta qare.,Ashe ba iya asiriba harda tsubbu suka koya masa." Fadar gwaggo tana sharce gumi agoshinta.


 Iya Indo kuma tuni ta fara matsar hawaye tana face majina.

 "Tabbas mutanen nan sun cucemi,Allah ya saka mana,kiga yana suka maida Hamza sauna,yanq riqe da qirji yana dalasimai irin nasu..."


 Qarasowa tayi kuwa da shi ta shiga tofeshi da yawu,bayan ta debo toka amurhu tana zagayeshi... "Indai Asiri suka maka yanxu xasu sakeka,.har ni za'ayima qaniyanci,d'ana daya xa'a salwantar min" ci gaba tayi da xagayeshi kafin ta hura masa sauran tokar ajikinsa.


 Wani qululun baqin ciki ne ya kama Hamza. Tashin yayi tsaye yana goge fiskarsa,kunyar kansa yake jima,,na kato6arar fa iyayensa sukeyi,ko salati basu iyaba amma ahaka suke qyamatar wani,suke kuma qiran Kansu musulmi.Tur da wanan rayuwar..


 Ficewa yayi daga gidan ba tare da ya sake ce masu komiba.


 Da ido suka bishi kafin gwaggonsa ta matso kusa da Iya Indo..

[7/2, 7:28 PM] 😘Um Nass🏇🏻: "Yaya Indo nifa na fara jin tsoron wanan lamarin,.kiga yanda ya kusa bangaje mu.,anya ba harda manta Uwa suka bashiba.."


 Ido Iya Indo ta fiddo waje "Kaii Harira bana jin haka,Dan yanda na masa magani da tokar nan yasashi tashi da sauri,kin San maganinta nan take ne,yanxu haka ya tafi ya kewaya ne,Dan sai ya kasayar da duk sihirin da suka masa..Shi yasa ya tashi a sukwane.."


 Dariya Harira ta saki sanan ta kashe da shewa,take iya Indo ta tayata suka kashe.."lallai Yaya Indo kin San kan gari,magani nan take,ni na dauka kema cikin rudewar kike kamar ni"


 Ido ta faralla sanan ta kakkabe hannunta "Haba Harira ai jinina yafi qarfin sihiru,muna nan da ke Hamza yabar batun mutanen nan har abada."

 Dariya tayi ta qara jinjinama iya Indo "Yaya baki da sauqi gaskiya,bari nazo na tafi Almuru ya fara kawo wa kai,gobe xanzo naji yanda labari ya tsaya, Dan Sam baxan bari ayi wanan abunba,ga diyata nan Lantana ta Dade tana haukan son Hamza,Ni ce nake taka mata birki ganin kamar bata kai lokacin Aureba."


 Ido iya Indo ta fito waje,kafin ta kaka6e baki cikin takaicin Hariran ta fara magana"Amma lallai Harira ke sakarya ce,ai gashi nan kinaga ya kusan debo mana alaqaqai,ba gara lantanaba sau dubu da wanan gayyar qarnin man shanun."


Dariya tayi sanan ta qara jinjinawa Indo "gaskiya Yaya ke maqura ce,bari na tafi dai xuwa gobe na zo mu tattauna akan batun."


 "To madallah sauqa lafiya,ki gaida yaran."


 "Za suji d kyau,"

 Daga nan ta tafi tana yage baki,lallai gara da akayi haka,cikin sauqi ta samu banz,indai Lantana ta auri Hamza to sukam kakarsu ta yanke saqa,Dan xata bugi qirji kaf garin babu matashin da ya kai shi kyau da abin hannunsa,,.. _"Wani dadi ne yafi wanan?oh Allah karka kasheni sai dadi yazo min."_
********wanene Hamza,?

 Shi kadai ne awajan iyayansa garba da ladingo Wanda aka musu auren zumunci,.sun shafe shekaru Biyar kafin su samu haihuwar Hamza Wanda tun Daga kansa kuma ko 6ari uwarsa bata qaraba,acikin al'adarsu basu fiya yin mata biyuba.hakan yasa suke son hamza kamar ransu,sai akayi sa'a Sam bai fiya maida hankali akan tsarabe-tsarabe na al'adarsuba,tun yana yaro ya fara xuwa cikin Yadin Bunni Neman kudi har kawo girmansa.

 Gwaaggo Harira itace qanwar mahaifinsa sai yayansa Lawan Wanda shi babu ruwansa da shiga shirginsu,.duk da yana da zafi,amma yana sakarma yaransa sosai suyi abin da suke so..Wanan kenan


*****

 A 6angaran hamza yana fita ya rafka tagumi aqofar gidansu,xuciyarsa na ci gaba da azalzalarsa,

 Sai dai ya Dan samu sauqi sakamakon addu'ar da yayi..


 Takaici yake da yanda rayuwa tazo da shi da wanan surquqin qauyen mai cike da gidadawan mutane.


 Qirjinsa ne ke masa nauyi sosai yayin da yake ganin duhuwa na giftawa atsakanin idanuwansa.


 Miqewa yayi ya fara takawa yana lalimen hanyar da zata sadashi ga gidansu..

 

 Amma hannunsa ya gagara isa ga Inda yake buqata.

 Duhu ne ya lilli6e ganinsa,ahankali yaji komi ya tsaya cak akansa kwanyarsa tabar hango masa komi.


 A hankali idonsa ya rufe ya Fadi qasa.,cak numfashinsa ya dauke.....

®by *😘Um Nass🏇🏻*

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: [6/29, 8:17 PM] 😘Um Nass🏇🏻: *HADIN GWARMAI* 🎊


 ©by *😘UM NASS 🏇🏻*


*WHTTPAD @UmNass*


® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION* PAGE 13  _"Har bansan iya Adadin godiyar daya kamata nayima dunbun masoyana ba,musamman masu son labarin littafin *HADIN GWARMAI*.Amma Ku dauki wanan page amatsayin sadaukarwa gareku. Sanan cikin ko wani lokaci INA Tsammanin gyara daga gareku.,ba kawai dad'in labarin nake so kujiba,.Ku duba kuskuren dake cikin sa sai Ku magantu akansa,.ta yanda xan samu qwarin gwuiwar yinsa.., comments naku yana da Mutqar amfani agareni,..Sosai Um Nass🏇🏻take yinku 🤝🏼_"

  Hamdala tayi gami da sauqe nannauyar ajiyar xuciya,bayan fitowarta daga dakin Baffa malam...


 Kallonta Innah takeyi cikin jimami,Dan ayanda ta ganta cikin walwala bata raba dayan biyu Baffa malam ya amince da Auranta da hamza..

 "Innah kije inji Baffa malam."


 Maganar Haajarah ta doki kunneta,Wanda batayi tsammanin har ta qaraso kusa da itaba haka.. Tashi tayi jiki asanyaye kamar kazar da qwai ya fashema acikinsa..


 Da sallama ta shiga d'akin da yake mamallakin Baffa malam,Wanda babu komi acikinsa sai gadon qarfe qarami da kuma tabarmar kaba,Wanda aka shimfida buxu akanta,gefe daya kuma tarin litattafan Addini ne ajere cikin kulawa da tsafta.


 "Wa alaikumussalam wa rahmatullah" ya amsa mata yana mata murmurshin da iyakarsa la66ansa..


  Qarasowa tayi ta xauna akusa da shi, tana tanqwasa qafuwanta,kwatankwacin yanda yayi NASA xaman....


 "Allah ya taimaki Baffa malam,.na samu isowa lokacin da saqonka ya riskeni."


 Kallonta yayi,sanan ya girgiza kai,Sam bata da damuwa,haka kuma sauqin kanta ya xama abu guda da yake qara yin alfahari da samun ta amatsayin matarsa.


"Na sani Salamatu,ko kadan bakya jinkiri wajan CIKA Umarni na..

 Magana CE akan Autarki,INA fatan kin dai san Wanda take so,?Dan abakinku naso na fara jin ko shi waye."


 Kai ta jinjina masa tana kallonsa,ba tare data yi maganaba "Na fahimci Nisan da Haajarah tayi acikin soyayyar yaron nan.,kin sani baxan ta6a yima diyata auren doleba,ko.kuma na tirsasa mata,ta yanda xan samata qunci da jin haushi na tsawon rayuwarta.,na Amince mata akan za6inta. Musamman Dana binciki halayyar yaron bashi da Matsala ko kadan,sai dai en uwansa da mutane garinsu.INA tausayama hajarko rayuwa acikinsu.. Amma komi baxai gagari Allah ba,.Idan har yayi nasarar samun Amincewar ahalinsa." 


 Kallonsa Inna tayi Wanda tuni idanuwanta sun kawo ruwa,tun da ya fara magana xuciyarta ke bugawa.,fargabar da take cikinta na tsoron abin da Baffa malam xai fada,ya Riga daya fadeta...


 "Amma malam kanaga acikin hakan babu kuskure.,hajarko yarinya ce, har yanzu bata San mine ne so ba,ataqaice ma bata gama fahimtar kantaba balle wani abu so.,tayi qarama da rayuwa acikin wadan nan mutane,musamman idan ka duba banbancin dake tsakanin qabilarmu da tasu,haka wajan al'adarmu ma, gsky ban hango mata sauqi rayuwa atare da suba."


 Kai ya girgiza mata yana goge mata hawayen da ke zuba a idanuwanta,shi kansa bashi da wani za6in Wanda ya wuce wanan,amma Allah ya sani yana mutqar tausayama rayuwar da er tasu ke qoqarin jefa kanta..

[6/29, 9:06 PM] 😘Um Nass🏇🏻: "Ki dauki wanan amatsayin kaddararta,sannan ki kalli So amatsayin abin da ke girmewa shekaru da kuma quruciya,inaga tunda ita ta xa6arma kanta shi,to ta shiryawa kanta yanda xatayi rayuwa tare dasu.. Xanyi magana da yaron da take so,..inaga zan hadasu aure tare da yayyanta.,akan haka bana so ki nuna damuwarki,ki daure kina mata Addu'a wata qila ta samu sauqin rayuwa acikinsu,ba mu San ko akwai Wani abu da Allah ya 6oyeba acikin wanan lamarin... Qila alkhairi ne xai biyo bayan wanan.."


 Ajiyar xcy ta sauqe,Wanda take jin zafi da nauyin da qirjinta ya mata kamar xai fito ya fasata..


 "Allah ya tabbatar mana da alkhairan sa,ya mana kariya daga riskar duk wani sharrin dake acikin wanan al'amarin.."


 "Ameen salamatuna.,hakan ya kamata kinayi, Allah ya miki albarka,ya kare bayanki.."


 Murmushi tayi daga nan suka shiga hirar duniya,Wanda mafiya yawa tunatarwa ne malam yake mata akan rayuwa da kuma yanda ta kaya...musamman dai matsalar da auren dole yake sawa,.. Hakan yasa ta samu nutsuwa acikin xcyrta 80%na daga fargabarta ya kau,..
  *******


 Zaune yake agaban Baffa malam ya sunkuyar dakai qasa,bayan Hajarko ta Isar masa da saqon da Baffa malam ya bata,akan ta turo masa shi..


 Kallonsa yake cikin tsinaki,yana nazartarsa,Wanda shurun daya ratsa dakin ba qaramin fargaba da tsoro ne atare da Hamxa ba...


 Aransa yana jin ya rasa hajarko rasawa na har abada,Dan ga Alamu mahaifinta bazai iya daukan kasadar bashi itaba,.musamman idan ya duba cewa su din wasu mutane ne gidadawa masu rikitacciyar rayuwa.., sa6anin su da suke rayuwa da ilimi na Addini da kuma wayewar da tayi qaranci aduniyarsu...  "Da gaske kana son Haajarah?"tambayar da taxo masa cikin baxata da kuma faduwar gaba...

 Dagowa yayi yana kallon Baffa malam Wanda shima kallonsa yake yi..." INA sonta da gasken gaske..."


 Ya amsa masa yana sunkuyar da kansa qasa".

  Kallonsa yayi na tsawon daqiqa goma, kafin ya sake jefa masa wata tambayar "Wani irin so kake mata ?"


 Awanan ga6ar kam ya rasa amsar bayarwa,amma wani sashi na xuciyarsa na tunatar masa akan duk kuskure guda da zaiyi yana nuna na rasa hajarko ne,.,haka kuma dama daya tak Baffa malam xai samu ya soke tsakaninsa da ita..


 "Ina mata so Fiye da yanda Manomi yakema gonarsa,. Fiye kuma da yanda fulani ke qaunar shanunsu.,duk lokacin da xata shiga damuwa xanyi qoqarin rabata da ita,har na shimfida farin ciki acikin zuciyarta."


 Kallonsa yake yana shimfida murmushi.,idan har zai samar da adalci to tabbas wanan bashi da wata makusa,ko alamun yana da dabi'un da en garinsu suke da shi,xai iya xama zakka ne acikinsu kamar yanda Hajarko ta fada...


 "Ka shirya yin auranta,.?sanan ka tanadi Kalmar kariyar kai daga mutanenka...,"


  Gumi ne ya shiga xubo masa, Dan sam ya manta cewa akwai qaya agabansa...


  "Tabbas na shirya Auren Haajarah,.sai dai ban saniba ko akan hakan zai iya zama damuwa da ahalina.,amma ko yaya ne dai INA da qwarin guiwa axuciyata,xan tabbatar da na samu hakan daga dangina..."


 

 Murmushi sosai Baffa malam yayi,duk da shima xuciyarsa akwai damuwa na jefa diyarsa cikin bataliyar maqiyansu,amma kuma sonta daya gani shimfide a idon hamzan ya isah ya bashi tabbacin xai iya kareta aduka rayuwar da xasuyi...' "Ban San mi xakayi ba,haka ban San ya xaka faskanci en uwankaba,.amma duk lokacin da kayi galabar samun Kansu,kuzo tare dasu zan aura maka Haajarah.,amma atsakan kanin nan bana buqatar yawaitar hirarku atare da ita,face ka warware matsalarka da danginka."


  Bazata yaji maganar Baffa malam,,Wanda farin cikin sa ya gagara buya,.

 Risinawa yayi yana ta godiya kamar dai da aka damqa masa hannunta ayanzu "in sha Allah zan kare sharadinka.,Allah ya qara girma na gode sosai.."


 Shafa kansa yayi yana murmushi "Allah ya maka albarka,ya kuma bada sa'a.,kana iya tafiya.."
  Miqewa yayi gami da yiwa Baffa malam sallama.,da qara yi masa godiya..


 Da kallo Baffa malam ya bishi yana fadada fara'arsa.,baiyi tsammanin ganin nutsuwa atare da shiba,idan ya danganta shi da inda ya fito..  ********

Bai qarama xaman ko daqiqa guda agarinba ya tattara ya koma gida...yau duk Wanda ya Ganshi yasan yana cikin farin ciki..


 Ko kadan bai yarda ya tsaya awani wajanba face gaban mahaifinsa,Dan ayanda yakeji baiqi yau suje su dauro masa auren Haajarah ba...


 Cikin zaquwa da gaggawa yayi sallama, adaidai ya tadda mahaifinsa da qanwarsa suna hira..


 Da kallo suka bishi suna amsa sallamarsa"ya dai Hamza wanan farin cikin na miye."


 Qanwar babansa ta tambayeshi,har xuwa yanxu bakinsa abude yake.


 Kai ya fara sosawa yana murmushi "daga can Yadin Bunni nake,mahaifin yarinyar da nake so ne, yace ya bani ita na turo iyayena."


  Ido suka qwalalo waje yayin da mahaifiyarsa da qanwar babansa suka dafe qirji kamar an sasu jeranta magana...


 "Mun shiga uku"


 "Tabdi jam" mahaifinsa ya qara da NASA batun....

 *_Cakwakiya ta soma_* 🎊
 ©by *😘Um Nass🏇🏻*[6/29, 8:17 PM] 😘Um Nass🏇🏻: *HADIN GWARMAI* 🎊


 ©by *😘UM NASS 🏇🏻*


*WHTTPAD @UmNass*


® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION* PAGE 13  _"Har bansan iya Adadin godiyar daya kamata nayima dunbun masoyana ba,musamman masu son labarin littafin *HADIN GWARMAI*.Amma Ku dauki wanan page amatsayin sadaukarwa gareku. Sanan cikin ko wani lokaci INA Tsammanin gyara daga gareku.,ba kawai dad'in labarin nake so kujiba,.Ku duba kuskuren dake cikin sa sai Ku magantu akansa,.ta yanda xan samu qwarin gwuiwar yinsa.., comments naku yana da Mutqar amfani agareni,..Sosai Um Nass🏇🏻take yinku 🤝🏼_"

  Hamdala tayi gami da sauqe nannauyar ajiyar xuciya,bayan fitowarta daga dakin Baffa malam...


 Kallonta Innah takeyi cikin jimami,Dan ayanda ta ganta cikin walwala bata raba dayan biyu Baffa malam ya amince da Auranta da hamza..

 "Innah kije inji Baffa malam."


 Maganar Haajarah ta doki kunneta,Wanda batayi tsammanin har ta qaraso kusa da itaba haka.. Tashi tayi jiki asanyaye kamar kazar da qwai ya fashema acikinsa..


 Da sallama ta shiga d'akin da yake mamallakin Baffa malam,Wanda babu komi acikinsa sai gadon qarfe qarami da kuma tabarmar kaba,Wanda aka shimfida buxu akanta,gefe daya kuma tarin litattafan Addini ne ajere cikin kulawa da tsafta.


 "Wa alaikumussalam wa rahmatullah" ya amsa mata yana mata murmurshin da iyakarsa la66ansa..


  Qarasowa tayi ta xauna akusa da shi, tana tanqwasa qafuwanta,kwatankwacin yanda yayi NASA xaman....


 "Allah ya taimaki Baffa malam,.na samu isowa lokacin da saqonka ya riskeni."


 Kallonta yayi,sanan ya girgiza kai,Sam bata da damuwa,haka kuma sauqin kanta ya xama abu guda da yake qara yin alfahari da samun ta amatsayin matarsa.


"Na sani Salamatu,ko kadan bakya jinkiri wajan CIKA Umarni na..

 Magana CE akan Autarki,INA fatan kin dai san Wanda take so,?Dan abakinku naso na fara jin ko shi waye."


 Kai ta jinjina masa tana kallonsa,ba tare data yi maganaba "Na fahimci Nisan da Haajarah tayi acikin soyayyar yaron nan.,kin sani baxan ta6a yima diyata auren doleba,ko.kuma na tirsasa mata,ta yanda xan samata qunci da jin haushi na tsawon rayuwarta.,na Amince mata akan za6inta. Musamman Dana binciki halayyar yaron bashi da Matsala ko kadan,sai dai en uwansa da mutane garinsu.INA tausayama hajarko rayuwa acikinsu.. Amma komi baxai gagari Allah ba,.Idan har yayi nasarar samun Amincewar ahalinsa." 


 Kallonsa Inna tayi Wanda tuni idanuwanta sun kawo ruwa,tun da ya fara magana xuciyarta ke bugawa.,fargabar da take cikinta na tsoron abin da Baffa malam xai fada,ya Riga daya fadeta...


 "Amma malam kanaga acikin hakan babu kuskure.,hajarko yarinya ce, har yanzu bata San mine ne so ba,ataqaice ma bata gama fahimtar kantaba balle wani abu so.,tayi qarama da rayuwa acikin wadan nan mutane,musamman idan ka duba banbancin dake tsakanin qabilarmu da tasu,haka wajan al'adarmu ma, gsky ban hango mata sauqi rayuwa atare da suba."


 Kai ya girgiza mata yana goge mata hawayen da ke zuba a idanuwanta,shi kansa bashi da wani za6in Wanda ya wuce wanan,amma Allah ya sani yana mutqar tausayama rayuwar da er tasu ke qoqarin jefa kanta..

[6/29, 9:06 PM] 😘Um Nass🏇🏻: "Ki dauki wanan amatsayin kaddararta,sannan ki kalli So amatsayin abin da ke girmewa shekaru da kuma quruciya,inaga tunda ita ta xa6arma kanta shi,to ta shiryawa kanta yanda xatayi rayuwa tare dasu.. Xanyi magana da yaron da take so,..inaga zan hadasu aure tare da yayyanta.,akan haka bana so ki nuna damuwarki,ki daure kina mata Addu'a wata qila ta samu sauqin rayuwa acikinsu,ba mu San ko akwai Wani abu da Allah ya 6oyeba acikin wanan lamarin... Qila alkhairi ne xai biyo bayan wanan.."


 Ajiyar xcy ta sauqe,Wanda take jin zafi da nauyin da qirjinta ya mata kamar xai fito ya fasata..


 "Allah ya tabbatar mana da alkhairan sa,ya mana kariya daga riskar duk wani sharrin dake acikin wanan al'amarin.."


 "Ameen salamatuna.,hakan ya kamata kinayi, Allah ya miki albarka,ya kare bayanki.."


 Murmushi tayi daga nan suka shiga hirar duniya,Wanda mafiya yawa tunatarwa ne malam yake mata akan rayuwa da kuma yanda ta kaya...musamman dai matsalar da auren dole yake sawa,.. Hakan yasa ta samu nutsuwa acikin xcyrta 80%na daga fargabarta ya kau,..
  *******


 Zaune yake agaban Baffa malam ya sunkuyar dakai qasa,bayan Hajarko ta Isar masa da saqon da Baffa malam ya bata,akan ta turo masa shi..


 Kallonsa yake cikin tsinaki,yana nazartarsa,Wanda shurun daya ratsa dakin ba qaramin fargaba da tsoro ne atare da Hamxa ba...


 Aransa yana jin ya rasa hajarko rasawa na har abada,Dan ga Alamu mahaifinta bazai iya daukan kasadar bashi itaba,.musamman idan ya duba cewa su din wasu mutane ne gidadawa masu rikitacciyar rayuwa.., sa6anin su da suke rayuwa da ilimi na Addini da kuma wayewar da tayi qaranci aduniyarsu...  "Da gaske kana son Haajarah?"tambayar da taxo masa cikin baxata da kuma faduwar gaba...

 Dagowa yayi yana kallon Baffa malam Wanda shima kallonsa yake yi..." INA sonta da gasken gaske..."


 Ya amsa masa yana sunkuyar da kansa qasa".

  Kallonsa yayi na tsawon daqiqa goma, kafin ya sake jefa masa wata tambayar "Wani irin so kake mata ?"


 Awanan ga6ar kam ya rasa amsar bayarwa,amma wani sashi na xuciyarsa na tunatar masa akan duk kuskure guda da zaiyi yana nuna na rasa hajarko ne,.,haka kuma dama daya tak Baffa malam xai samu ya soke tsakaninsa da ita..


 "Ina mata so Fiye da yanda Manomi yakema gonarsa,. Fiye kuma da yanda fulani ke qaunar shanunsu.,duk lokacin da xata shiga damuwa xanyi qoqarin rabata da ita,har na shimfida farin ciki acikin zuciyarta."


 Kallonsa yake yana shimfida murmushi.,idan har zai samar da adalci to tabbas wanan bashi da wata makusa,ko alamun yana da dabi'un da en garinsu suke da shi,xai iya xama zakka ne acikinsu kamar yanda Hajarko ta fada...


 "Ka shirya yin auranta,.?sanan ka tanadi Kalmar kariyar kai daga mutanenka...,"


  Gumi ne ya shiga xubo masa, Dan sam ya manta cewa akwai qaya agabansa...


  "Tabbas na shirya Auren Haajarah,.sai dai ban saniba ko akan hakan zai iya zama damuwa da ahalina.,amma ko yaya ne dai INA da qwarin guiwa axuciyata,xan tabbatar da na samu hakan daga dangina..."


 

 Murmushi sosai Baffa malam yayi,duk da shima xuciyarsa akwai damuwa na jefa diyarsa cikin bataliyar maqiyansu,amma kuma sonta daya gani shimfide a idon hamzan ya isah ya bashi tabbacin xai iya kareta aduka rayuwar da xasuyi...' "Ban San mi xakayi ba,haka ban San ya xaka faskanci en uwankaba,.amma duk lokacin da kayi galabar samun Kansu,kuzo tare dasu zan aura maka Haajarah.,amma atsakan kanin nan bana buqatar yawaitar hirarku atare da ita,face ka warware matsalarka da danginka."


  Bazata yaji maganar Baffa malam,,Wanda farin cikin sa ya gagara buya,.

 Risinawa yayi yana ta godiya kamar dai da aka damqa masa hannunta ayanzu "in sha Allah zan kare sharadinka.,Allah ya qara girma na gode sosai.."


 Shafa kansa yayi yana murmushi "Allah ya maka albarka,ya kuma bada sa'a.,kana iya tafiya.."
  Miqewa yayi gami da yiwa Baffa malam sallama.,da qara yi masa godiya..


 Da kallo Baffa malam ya bishi yana fadada fara'arsa.,baiyi tsammanin ganin nutsuwa atare da shiba,idan ya danganta shi da inda ya fito..  ********

Bai qarama xaman ko daqiqa guda agarinba ya tattara ya koma gida...yau duk Wanda ya Ganshi yasan yana cikin farin ciki..


 Ko kadan bai yarda ya tsaya awani wajanba face gaban mahaifinsa,Dan ayanda yakeji baiqi yau suje su dauro masa auren Haajarah ba...


 Cikin zaquwa da gaggawa yayi sallama, adaidai ya tadda mahaifinsa da qanwarsa suna hira..


 Da kallo suka bishi suna amsa sallamarsa"ya dai Hamza wanan farin cikin na miye."


 Qanwar babansa ta tambayeshi,har xuwa yanxu bakinsa abude yake.


 Kai ya fara sosawa yana murmushi "daga can Yadin Bunni nake,mahaifin yarinyar da nake so ne, yace ya bani ita na turo iyayena."


  Ido suka qwalalo waje yayin da mahaifiyarsa da qanwar babansa suka dafe qirji kamar an sasu jeranta magana...


 "Mun shiga uku"


 "Tabdi jam" mahaifinsa ya qara da NASA batun....

 *_Cakwakiya ta soma_* 🎊
 ©by *😘Um Nass🏇🏻*

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI* 🎊


 ©by *😘Um Nass* 🏇🏻


*WHATPPAD @UmNass*..® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION* _"Inna lillahi wa inna ilahirraji'un,.Haqiqa ko wani rai sai ya d'and'ani dacin mutuwa,haka kuma ita mutuwa ba'a shirya mata xuwa take ba zata,wani lokacin ta dauke mana Wanda muke so muke jin dadin rayuwar xama dasu,. "Haqiqa INA miqa dumbum ta'axiyyata ga Er Uwata Qawata *Mummy Rukky* na rashin babban yayansu da sukayi ajiya,Allah yaji qansa da rahma da dukkanin en uwanmu da suka rigamu gidan gaski.👏🏼"_ PAGE 15  Tun fitarsa ransa yake 6ace, kowa ya hadu dashi sai ya masa tad'in sabon salon da dansa Hamza yazo da shi,awani 6angaran kuma yace sa6o..

 

 Da yawa abokanansa sun qara xugashi akan "ko mi hamza xaiyi kada ya sauqo akan dokin naqin daya hau."

 Wasu kuma suna tunzurashi akan yana gab da rafka asara,Dan kaf qauyen an camfa duk Wanda ya auro mata awaje to suna yin sallama ne da talauci,harma su zama aminaine,.

 Tabbas baba garba ya tsorata da wanan batun.,Dan idan akwai abin daya tsana awanan duniyar bai wuce talauci ba..


 "Allah ya min tsari da talauci,da nayi abokata da talauci na gammaci mutuwata,itace ta har abada idan an tafi ba'a dawowa"baba garba ya fada bakinsa da kumfa..,

 "Kana da gaskiya,gara kasan mutuwa da faduwa qasa war was,"


 Tashi yayi ya shuri takalminsa, "Bari naje na qara ja masa kunne"


 "Ya kamata kam,Dan da zafi-zafi akan bigi qarfe"

 Suka qara tunzurashi da qara azalzalarsa..

 Ji yake kamar yayi fiffike yaji shi agaban Hamza, Sauri yake burum-burum ba tare da ya tsaya ba,duk da qiran sallahr daya karade kunnuwansa..


 Tuntu6e yayi da wani abu azauren gidan NASA..


 "Kai jama'a wai ladingo wata irin macece ke,.kullum burunki ki ganni da rauni ajiki,na tabbata wata rana gawata xaki so gani.." Ya fada yana kumfar baki muryarsa da karadi,Sam bai lura akan mutum bane yayi karo da Shi ba kasancewar zauren akwai duhu.,


 "Ladingo! ladingo.,"ya shiga zura mata qira yana ci gaba da sukuntunsa.." Daga nan babu Inda xan d'ara Dan qila agaba kuma kin jera qarafuna.'


Da gudu gudu ladingon ta fito,.jin qiran da Baba Garba ke xura mata "lafiya malam qira tun azauren gida kuma.,." Kafin ta idda qarasawa taci karo da mutum itama yif ta afka kansa...


 "Wayyo Allah,." Kalmar data qira abakinta..,

 "Ahaf kema kinji abin da naji,.kadan Daga cikin muguntar da kike shinfida min ahanya kullum kenan.'


 "Ikon Allah Garba dama ba kai nayi karo da Shiva yanxu,?"


 "Ni gani agefe INA jira ki zo ki dauka tarkacen da kika ajiye."


  "Mun shiga uku,Aradun Allah da mutum nayi karo garba.,kuma da alama baya numfashi sak gawa."


 Ido ya qwalalo waje kamar tana ganinsa,tuni gumi ya jiqashi,. "Kibar maganar wasa ladingo wani gawa kuma ana xaman lafiya."


 "Takwarankwatsa mutum ne baya motsi garba,.Mun banu"


 Ta fara magana tana face majina,., da sharce hawaye..


 Quuuuuluuuluulu kake ji cikin Baba garba ya fara sauti.."karki taara mana jama'a Ladingo,. Je ki kawo mana fitila mu haska sai muga ko miye."


 Da gudu ta ruga gida,cikin abin da bai wuce daqiqa gomaba ta dawo. Hannunta har karkarwa yake dauke da fitilar kwai....


  Ido suka fiddo waje cikin kaduwa da tashin hankali..,na ganin Hamza kwance war was baya numfashi...kamar HADIN baki suka qwala Ihu "Wayyo Allah Hamza"suka shiga girgizashi...  " Shikenan ya Mutu ya barmu, hamza kayi Haquri ka miqe.."Baba Garba ya fada cike da tashin hankali,.


 "Ai duk kai kaja mana,ka cucine Garba,muddum hamza ya mutu baxan yafe makaba,,Dana daya tak aduniya..Wayyo Hamza na.."Ladingo ta fada tana qara callara ihu.


 

 Gumi ne ya shiga zubowa Baba garba,ga kuma hawaye shima daya wanke masa fiska,can kuma Kamar an xabure shi ya miqe afaske yayi wajee.


 "Jama'a Kuzo Ku taimakeni,..Kada Hamza ya Mutu"yana fada da ihu kamar sabon kamu.,

 Nanfa mutanen garin suka fara nufoshi da gudu,.


 Kafin wani lokacin qofar gidan da zauren ta CIKA taff.


  Sai dai abin takaicin duk cirko-cirko sukayi babu mai hikimar sa masa ruwa..


 Wasuma hannu suka d'ora aka suna qiran ai Hamza ya Riga daya Mutu,Dan ko motsi bayayi..,


 Tuni wajan ya kaure da ihun mutune,na kuka wasu suna tuntsurawa qasa suna buga qafafuwansu......

_"Afwan kuyi malejin wanan,.Naso yin fiye da haka,Allah bai nufaba banda chag yau " I'm so sorry 👏🏼In sha Allahu gobe zaku jini har sai kunce bakwa so.lolx"_
©by *😘Um Nass*🏇🏻

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI* 🎊


  ©by *😘UM NASS 🏇🏼*


*Whtppd @UmNass*


® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION* PAGE 16 Kururuwar kukan mutane CE ta cika unguwar gaba daya,kafin wani lokaci maganar mutuwar Hamza ta xagaye garin Gumsa gaba dayansa...

 

 Cikin abin abin da bai wuce mintuna biyarba qofar gidan ta cika danqam da mutane,mata kuma sai kururuwa suke suna matsar hawaye,Iya Indo sai jijjiga kai take tana ihu harda birgima,.

 Abin takaicin sun kasa koda dauke gawar Hamza agabansu,haka suka ci gaba da kuka.


 "Ku matsa min na wuce." Muryar wani Dan dattijo ta ratso wajan hannunsa riqe da cocilan.(touch light)yana haska bataliyar mutanen da suka cika wajan,da kuma Neman hanyar da xai wuce.


 Take mutane suka bashi hanya sanin ko shi waye agidan. 

 Fiskarsa dauke da damuwa da takaici ganin abin dake faruwa awajan,.ga Hamza akwance war was baya numfashi,ga kuma bataliyar mutane akansa marasa amfani.

 Dan sun gagara yi masa kata6us,.bai yima kowa magana ba har ya qarasa kusa da hamza,risunawa yayi dai-dai saitin Kansa,ya kai hannunsa kan hancinsa yaji shuru babu alamar numfashi, sai ya sake kara kunnensa akan qirjinsa nanma yaji shuru babu alama,.

 Ido ya rintse sosai ya bude yana sarewa da Hamza ya kuma yarda akan lallai mutuwa ta daukeshi awanan ga6ar.

 

 Can ya miqe ya kama tsintsiyar hannunsa Dan ya dagashi,da sauri ya juyo ya kalleshi yana qara riqe hannunsa,harbawar jijiyarsa yaji Wanda take taimakawa wajan bugawar xuciyarsa..


 Da sauri ya shige cikin gida ya debo ruwa akofi,har tuntu6e yake saboda sauri,

 Bai tsaya jinkiriba ya kwararama Hamza ruwan ajikinsa,wata doguwar ajiyar zuciya yaja sanan ya bude idanuwansa ahankali saboda nauyin da suka masa.

 Kallonsa ya kai ga wanan dattijon take ya miqe ya rungumeshi yana hawaye sai Jan xuciya yake.

  

 Hayaniya CE ta cika wajan Wanda yawanci Na mamaki suke akan ba mutuwa Hamza yayiba,Ashe doguwar suma yayi,wasu kuma aciki suna ma iyayensa barks.,tuni Iya Indo ta wartsake daga birgimar da take ta fara taka rawa," Allah Na gode ma,da baka dauke min rayuwar Hamza ba,nasan da tawa rayiwar nima tazo qarshe."

 Maganar da take fada kenan yayin da mutane suke sake yi mata barka da Arxiqi,.


 Anan kowa ya kama gabansa suna cike da al'ajabin wanan abin..

  Gida ya rage daga Baba Garba sai ladingo da harira Wanda tasha kuka ta more,Dan abin ya daketa jin hamza ya Mutu,.bayan kuma yanxu suka rabu da shi.. _(Basu da masiniyar Allah Na iko akan bayinsa Wanda yake yin abin da ya so akuma lokacin da ya so._ 

 _Kamar haka mutuwa take daukan En uwanmu,.masoyanmu,da kuma iyayenmu,ba tare da mun shirya rabuwa dasuba,ko kuma munyi tunanin tafiya xasuyi su barmu,.wata rana sai dai labarin tamu mutuwar ya riske wasunmu._

 _*Ya Allah kasa muyi kyakkyawan qarshe.Ameen*_)


  Bibbiga bayansa ya Shiga yi cikin sigar lallashi "ya isah haka kukan Hamza, wata damuwa CE haka taso tarwatsa xuciyar maxa,.matsalar soyayya ko?" Dattijon ya fada yana murmushi,da sauri Hamza ya dago Kansa ya kalli shi,.

 Kai ya jijjiga masa yana qara fadada murmushinsa "Acikin wanan Rayuwar tamu,babu abin da ke saurin kassara matashin saurayi kamar matsalar soyayya,INA fatan ba rabuwa tayi da kaiba."

 

 Rungumeshi yayi gamgam kamar wani xai kwace masa ji.,

 "A'a Baba lawan ba guduna tayiba,asalima iyayenta sun bani auranta duk lokacin da nawa iyayen suka Amince,su Baba ne suka hanani aurenta."


 Idonsa ya dago ya kai kallonsa ga baba garba da iya Indo ya wurga musu harara,take suka sunkuyar da kawunansu qasa,sai dai gabansu na faduwa akan hukuncin da Yaya lawan xai yanke.,Dan sun San ba ruwansa da matsalar al'ada,Indai akan batun yaransa ne,to komi suke so xai barsu suyi,mutqar ba sata bane da kuma zinace-zinace,acewarsa wadan nan qasqantattun abubuwa ne da kuma qazanta Wanda bata goguwa ajikin mutum koda yana kwana acikin kogin maliya.

 Wanan yasa yaransa suke da ra'ayi na daban agarin basa kuma damuwa da shirgin kowa,sai dai idan ka shiga nasu xakaji babu dadi."


 "Mi yasa suka hanaka aurenta?bama wanan ba mi yasa baka sameni kai tsaye ka fada minba,ka fada musu."


 "Yaya lawan bafa er garin na bace,fulanin Yadin Bunni nefa,kuma babanta malami ne sosai,tun yanxu sun fara koya masa dalamusain sihirinsu INA ga in ya aureta an mun shiga tara ma?"fadar harira tana qyafta idanuwa.

 Wata uwar tsawa ya kwatsa mata "Dallah rufe min baki sakaryq kawai,ke mi kika sani da zaki bada labari,kullum kanki aduqe agida,sai agidan wasu kike iya miqashi,Akul dinki da shiga wanan maganar idan ba hakaba saina sassa6a miki sakarya kawai,mai baqin halin jaraba."


 Tsumu tayi tana hura hanci,Dan tana tsoransa na gaske,tun asali baya ragar mata.,balle kuma akan batun yaransa,duk da Hamza ba dansa bane yana sonsa fiye da yaransa,asalima shi ya Sanya masa sunansa. Ya kuma yayeshi da kansa,akwai shaquwa sosai atsakaninsu da soyayya.


 "Gobe da yardar Allah xamuje Yadin Bunni din,xan nema maka aurenta,idan akwai yiyuwama zan bada sadakinta.,"

 Wani farin ciki ne ya lilli6e Hamza, tuni ya qara qanqame kawun NASA، yana kwararama kawun NASA godiya.

 Shafa Kansa yayi ya miqar dashi tsaye "Tashi mu tafi gida mu kwanta," ba musu hamza ya miqe yana fadada fara'arsa,.. 

 Kallon iyayan NASA yayi sunyi tsumu-tsumu kamar ruwa ya cisu,Ga kuma damuwa afiskarsu ashimfide amma babu damar magana,.

 "Garba ka shirya xaka mana rakiya,saura ka tsaya ka 6ata mana lokaci,Dan sai na sa6a maka. " to Yaya zan kiyaye da wuri zan shirya"


 "Ba laifi,na tabbatar da hakan agobe."

 Daganan yaja hannunsa suka barsu anan baki sake.


 "Lallai da aiki agabanmu sosai Yaya,muddum aka auro mana fulanin Yadin Bunni,dama ya lafiyar kura balle taga nama."


 "Uhmm Harira yanxu ai mun xama En kallo tunda maganar ta koma hannun Yaya lawan, bamu da dabara kuma,sai dai mu jira lokaci,sai muga abin da xamu gani,amma ba lallai mu iya kar6ansa ba." Yana fadar haka ya kakkabe jikinsa ya shige cikin gida.


 Da kallo suka bishi kafin iya Indo ta miqe itama "Tsugunno bata kamamuba harira,baxan ta6a son wanan yarinyar ba,koda sun samu rabo atsakani,baxan kar6eshi amatsayin Jinina ba."

 

 "Da kyau Yaya Indo nima zan tayaki da wanan yaqin,ta yanda zata gudu da qafafuwanta.,bari na tafi gida kuma,sai kuma gobe idan Allah ya kaimu zanxo naji yanda ta kasance."


 "Ba laifi,Allah ya fassheki dare."""***""**""..

 WASHE GARI.


 Kamar yanda Baba Lawan ya alqawarta ma Hamza, tun gari da hantsi suka shiga mortar dake jigila xuwa Yadin Bunni,Wanda hira CE take ratsawa tsakanin Baba lawan da hamza,sai kuma baba garba da ya zama kamar kurma binsu kawai yake ba mgn.

 Babu kuma Wanda ya kula dashi,saima yi da sukayi kamar basu San da zamansaba,.hakan ya qara masa takaici na sosai axuciyarsa,yake saqa da mugun zare.


  Hamza ne ya musu jagoranci har gidan su Haajara,..

 Zuwansu qofar gidan cike da masu daukan karatu abun gwanin kyau.,. 

 Take Baba lawan yaji nutsuwa axuciyarsa yasan ko ba komi dansu ya fidda zakka agarin,ya kuma samo musu kyakkyawan reshen da xasu jingina atare dasu,na samun yawaitar ilimi acikin zuri'arsu.".


 Baffa malam na ganinsu ya fadada fara'arsa ya taresu,.


 Gida ya shiga ya dauko tabarma ya shimfida musu azaure,.kana ya Umarci Inna data hadoma baqinsa damun fura da kuma zabbi gasassu,"


 "Bismillanku Ku zauna"ya fada yana fadad'a fara'arsa garesu,.

 Zama sukayi an an suka fara gasshe-gasshe kana Baba lawan ya Dora da " Mu iyayen Hamxa ne,mun zo akan batun nema masa auren diyarka,kamar yanda Addini ya tanadar,da kuma izini da ka bashi akan ya turo mahaifansa,. Muna fatan Yardar Allah acikin wanan hadin da kuma dorewarsa na har Abada."


 Kai Baffa malam ya gyada yana qara shimfida murmushi akan fiskarsa "Haqiqa na bama Hamza diyata Haajara akan duk lokacin da iyayensa suka amince da Aurensu,. Tabbas nayi farin ciki sosai da xuwanku,.Dan Allah ya wani har azuciyata INA son Hamza,domin yardar da na masa da ganin yanda yake son diyata da gaskiya,.sai dai Banyi tsammanin iyayansa zasu aminceba,idan nayi duba da qarancin fahimtar dake tsakaninmu da Ku."


 Murmushi baba lawan yayi,yana girgiza kai "Haka ne,amma anamu gidan akwai Dan ban-banci da sauran gidajan,musamman akan abin daya shafi maganar aure,Ina bama yarana za6in Matar da suke so,domin shi aure ana ynsa ne da fatan ya dore har abada."


 "Wanan gaskiya ne,.na bama Hamza auren Haajara nan da mako biyu yaxo adaura musu aure,Dan tare xan hada Dana yayyanta biyu."


 "Alhamdulillah,abu yayi kyau mun gode d

Sosai."

 Zungurar baba Garba yayi Wanda ya sunkuyar da kai kamar baya wajan.


 Nan yayi saurin yin murmushin yaqe yana qara godiya.، 


 Anan aka gabatar musu da fura wanda aka da mata da Zuma,da kuma gasassun zabbi,.


 Anan suka ci suna yabawa da karramcin da aka musu,Dan basuyi tsammanin samun koda rabinsa bane.


 Miqewa sukayi suna godiya sanan baba lawan ya bada 5k kudin na gani INA so,sai kuma 10k kudin sadaki,..


Anan sukayi sallama akan sai nan da mako biyu xasu dawo adaura auren da kuma kayan lefenta.."""***"""**..


 Abin yazo musu abazata Dan basuyi tsammanin lamarin xai xama da sauqi hakaba,.amma awani 6angaran idan aka duba yanda baba lawan yayi tsaye akan lamarin xaisa aqara jinja nama abun.


 Tuni labarin Auren Hamza da er fulanin malamin Yadin Buunni ta karade kauyan gumsa,da yawa acikinsu suna Allah wadai da rayuwar Wanda baisan kishin garinsuba da kuma riqo da al'adarsaba.


 Haka a6angaran Iya Indo taji takaici ta kumayi alqawarirrika masu yawa na hana ma yarinyar kwanciyar hankali tare da assasawar xugar gwaggo Harira da sauran danginta,..Yayin da agefe guda Hamza da Haajara suke far in ciki da shiryama rayuwar aurensu,,kudi sosai yake bata akan tayi hidimar biki da shi,da qyar take kar6a wani lokacin mq sai dai ya ajiye mata yayi tafiyarsa..

 

 Auduga suka da suka toshe kunnuwansu daga jin xugar mutane da kuma harari musu aibun auren da ba'a kai ga qullashiba.


 

 ****"


  _*"👏🏻Hannyena biyu nake Baku haquri,wajan jina shuru wasu kuma xasu CE jan hankali yayi yawa,.amma dai Ku qara haquri dani mutum ba'a tsarama kansa yanda xai tafiyar da al'amuransa,wani lokacin xaka so xaquwa da kammala labarin da ka farashi,amma idan wani tsaikon ya taso dole ka jinge naka ka kar6i abin da Allah ya tsara maka.,Tabbass nasan akwai masoyan labarin Hadin gwarmai da yawa amma banyi tsammanin soyayyar takai hakaba,wasu saqonninsu na tadda jingim a inbox dina,yayin da kiran wasu baya yankewa,.na gode sosai naku tukaicin Da kyautar,INA fatan ganin comments masu yawa da like,kuna iya yin qorafinku kai tsaye,. Idan ya kama xan Baku haquri ko kuma na gyara.,gwargwadom iyawata... 😀😘😍"*_ ©by *😘Um Nass🏇🏼*

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI 🎊*


 ©by *😘Um Nass 🏇🏼*


*Whattpad @UmNass*


® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION*
 PAGE 17 Ance duka abin da aka sa masa lokaci bashi da wuyar xuwa.,kamar hakance ta kasance ga Hamza dama sauran mutanen da suke tsakanin garirruwan guda biyu.


 Yau ta kama ranar daurin Auren Hamxa Wanda mafiya yawan En garin suka noqe,asalima da yawa cewa sukayi babu inda xasu je,gayyar tsiya gayyar Na ayye,auren da babu abun da xai amfanar dasu sai tsiya da talauci..


 Haka a6angaran iya Indo tace ko kare bata gayyataba balle mutum,Dan wanan toxarci ne agareta,ace duka yawan mutanen garin Wanda suke amatsayin dangi guda danta tilo ya fidda zakar auren bare,.barenma Wanda ta hada jinsi da fulani,.

 Da ana dawo da abin daya faru baya tabbas da xata so dawo da lokacin da Hamza yaso fara kasuwanci a Yadin Bunni ta kuma soke masa wanan burin NASA,.qila Da tun farko tayi tijara akan hanashi xuwa da har abada baxaiyi gigin ganin wasu dangin da ba nasuba har ya auro musu jangwam. _*(Ta manta girman qaddara Wanda take xuwa ta tasheka,duk qoqarinka baka isa ka sanja abin da Allah ya qaddara makaba acikin rayuwarka.)*_


 Wanan bata zama damuwa awajan Hamza ba Dan ya tsammanin ganin fiye da haka atare da mutanen dake kewaye da su.


 Duk yanda Baba Garba yaso ya noqe, ya kawo uxuri, akan qin xuwa daurin Auren, abin yaci tira,Dan ko kadan Baba lawan bai bashi wanan damar ba,bai kuma bar qofa guda da xai kawo masa wargiba.

 Asalima ko wata jigila ta hidimar bikin da shi ake yinta,haka ya tirsasashi bada gudun mawarsa aka hado mata kaayan lefe,kala bakwai suka mata duk dan nuna bajintarsu,hadi da takalmi da jaka da mayafi.


 Qaton gida Baba lawan ya bama Hamza Wanda dama yayi shi da sunansa,.Wanda yake da dakuna biyu da rumfa sai tafkekiyar tsakar gida,da bishiyar darbejiya,gefe kuma bandaki ne (toilet) da madafar Abinci(kitchen).

 Haka ya miqa masa mukullin gidan da takardun da suke dauke da shedar sunansa.

 Bakin godiya ya rasa,sai hawaye da yake Wanda da ganinsa Na frn ck ne,ya qara tabbatar da cewa duk duniya babu mai kaunarsa kamar Babansa lawan. Musamman har Sabin dinkuna yayi masa Na fitar biki kala biyar,. D


 Kai ya girgiza masa ya ja hannunsa shida sauran yaransa maxa. da kuma Baba garba suka dauki shatar motar da zata kaisu Yadin Bunni da kuma waddD xa'a dauko Amarya da danginta guda daya itama. ""***""***""


 Qofar gidan Baffa malam cike yake da mutanen danqam da d'ai sai kace ranar Idin sallah ne. Hakan ya qara tabbatar da nagarkarsa da kuma kimarsa da mutanen garin suke gani.da kuma muhimmancinsa acikin rayuwarsu,idan akayi la'akari da kasancewasa babban malami.


 Suna xuwa aka fara musu murna.

 Anan suka qarasa shiga inda Baffa malam yake da shaqiqan abokansa,.

 Anan aka fara gabatar da daurin Auren kamar yanda Addinin musulunci ya tanadar,dubun nan mutane ne suka sheda daurin Auren Hamza Abubakar da kuma Haajara Muhammad akan sadaki dubu goma..


 Kabbara aka dauka awajan kana amsa kuwa ta dauki qara ga kuma madaukinta Na sheda daurin auren da akayi.


 Hamdala da sujjada Hamza yayi yana godiya ga Allah.,farin cikinsa abayyane yake awanan lokacin,ta yanda bakinsa ya gagara rufuwa.

 Mutane sai Sam barka suke masa suna miqa hannu yayin da maroqa suka fara sana'arsu ta kirari da sanya albarka arayuwar Auren nasu.


 ***

Lokacin da mai shela ya sheda Auren Haajara da Hamza samun kanta tayi da faduwar gaba, tuni jikinta ya dauki rawa Wanda tilas ta durqushe awajan.,jin kanta take kamar an axa mata nauyi akanta..


 "Hasbunallahu wani imal wakil.,Alhamdulillah ala ni'imatihi tatimussalihat" addu'ar da Haajara ta shiga jerantawa kenan,duk da tana jin kanta kamar an axa mata qatoton dutse..

Anan mutane. Suka shiga tsokanarta da murna.,amma INA xuciyarta take ji tana mata nauyi,.ga fargabar da ta CIKA ta.tsayuwa ta gagareta atsakanin qafafuwanta.


 ****"""***

 Bayan SA'A Biyu:-


 Durqushe suke su uku agaban mahaifansu Baffa malam da Inna,Kansu asunkuye aqasa suna sanye cikin manyan hijabai.


Gyaran murya yayi kana ya kirayi suayansu daya bayan daya,ya miqa musu kudi ahannunsa ya kuma Dora da jawabinsa "Wanan shine sadakin Aurenku.,Yanxu kun shiga wata sabuwar duniya da kuma sabuwar rayuwa,sanan xakuyi rayuwa da Sabin mutane sa6anin Wanda kuka xauna dasu abaya,.ta iyu Ku tadda ban-banci mai yawa ko ta fiskar dabi'a da al'adar mutane.,idan kunga haka kuyi haquri kuyi koyi da abin da kuka tadda mutqar bai sa6awa Addinin islama ba. INA muku nasiha da kuji tsoron Allah adukanin lammuranku,Ku zauna da maxajanku da gaskiya da Amana,sanan Ku tuna cewa ibada kuke,haka kuma Aljannah kuke nema,itakuwa ba'a samunta da sauqi sai an sha wahla.,kashedinku da bayyana sirrin miji domin hakan hanya CE ta bude qofofin axaba.Ina roqa muku rahmar Allah da yardarsa Addukanin lammuranku ya Sanya muku Albarka acikin zamantakewar Aurenku,ya kare fitina acikinsa..Allah ya sanya muku Albarka Ku da abin da xaku Haifa agaba.kuyi haquri da Abin da xa Ku gani,musamman ke Haajara INA mutqar baki haquri.,ki tattara dukkanin nutsuwar da haqurinki waje daya ki fiskanci rayuwa acikin mutanen da basa buqatarki acikinsu."


 Hawaye ne ya shiga tsere tsakanin fiskokinsu.yayin da suka rungume mahaifin NASA suna roqansa gafara.,shafa Kansu yayi yana jin kaunarsu Na CIKA xuciyarsa ga kuma raunin da ya CIKA xuciyarsa Na rabuwa da su.


 Inna ya kai kallonsa gareta "Baki CE komi ba salamatu."

 Kai ta girgixa tana goge hawayen fiskarta "ka gama fada musu komi malam,INA musu fatan alkhairi dai acikin xaman takewarsu,Allah ya sanya musu Albarka." Kai ya jinjina yana "Ameen"

 Anan masu daukan Haajara suka aiko ana jiranta.nan hankalinsu ya tashi suka maqalqale inna suna kuka.,da qyar qannen Inna da yayyanta suka 6an6are Haajara suka kaita mota awanan lokacin qara ta sa sosai tana "Na FASA Auren Ku barni da innata,. Dan Allah karku rabani da da En uwana."

 Tuni xuciyar Inna da yayyan Haajara ta karye ta shiga daki,sam baxata juri ganin tafiyar yarantaba.

 Amma ya xa'ayi Aure ya gaji haka.

 Sata akayi amota sanan yayar Inna da qannenta biyu suka shiga motar sai maqociyarsu Wanda ta kasance Aminiyar Inna CE.,

 Suka kama hangar Gumsa xuciyarsu cike da tararrabin Abunnda xasu tadda..."""***"""*


 Tafiya suke babu mai magana acikinsu sai lallashin Haajara da suke yi,Wanda tayi kukan ta gaji sai Jan xuciya take.

 Sai ji sukayi har sun iso garin,Wanda hakan ya Hassada faduwar Gaba mai qarfi axuciyar Haajara ..yayin da mutanen garin suke bin motar da kallo,Wanda da ganinsa Na takaici ne.


 Aqofar gidanta motocin suka tsaya Wanda xuwa lokacin mutane sun CIKA taf kamar ana rabon kudi,ba xuwa sukayi Dan murnaba sai Dan ganin jangwamar da aka kawo musu.

 Jikin Haajara ne ya dauki karkarwa da kuma wata fargaba data sauqar mata axuciya kamar an buga guduma akanta.
©by *😘Um Nass🏇🏼*

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI* 🎊


©by *😘Um Nass 🏇🏼*


*Whatpad @UmNass*


® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION*
 PAGE 18
 Jikinta ne yaci gaba da karkarwa kamar da taga wani abin tsoro,Sam ta gagara sauqe qafafuwanta qasa, "ki sauqa da Bismillah tare da yaqini acikin xuciyarki" maganar gwaggonta ta Samar da nutsuwa atsakanin xuciyarta,..

 

 Hannayenta ta riqo da zummar yi mata jagora,ixuwa gidan da yake amatsayin Na Aurenta.,

 "Bismillahi" ta ambata atsakanin la66anta Wanda sautin iya kunnuwanta kadai ya isah... 

 Faduwar gaba CE ta durar ma xuciyarta alokacin da ihun mutanen garin dake xagaye da motar da suke...


 "Tabdijam lallai Hamxa ya debo mana alaqaqai,.yo anan INA abin so? kugafa jiki qerere kamar da ta roqa asan mata.,wai danma acikin kaya take.,ga wani zulmemen Hijabi kamar da take muhallin Takaba.."

 Sautin muryar wata dattijuwar tsohuwa,bakinta cike da gore,da ganinta irin fitinannun tsoffin nan ne.


 "Bari kawai Altum ai Hamxa ya dauko masifa da kudinsa,..Ki zuba ido mako biyu yayi Kadan labarinsa xai sauya."


  "Tabbas banda ja akan batunki Uwani."


 Duk wanan maganar da suke akunnen Haajara take.Wanda hakan ya qara tsoratarta.,haka kuma jikinta yaci gaba da karkarwa.

 Har aka wuce da ita cikin gida mutane basu bar fadar maganar da take nuna 6atanci akan xaman takewar Auren nasu.

 Da yawa acikinsu suna nuna tsantsar qyamarta acikinsu.

 Yayin da wasunsu suke son mata kallon qurulla duk da fuskarta arufe take.

 Zaunar da ita gwaggonta tayi abakin gadon yayin da sauran mutane Ukun suka biyo bayansu,. Jikinsu amutqar sanyaye.,Dan sunji duk abin da mutanen garin suke fada.


 Numfashi yayar Inna taja, takai kallonta ga Haajara, Wanda ta damqe hijabinta sosai kamar da xa'a rabata da shi..

 "Ban hango miki sauqi da jin dadi acikin wanan garinba Haajara,xuciyata tun yanxu fargaba take akan tafiyar da xamuyi mu barki atare da su.,labarin halayyar mutanen garin kawai Muke ji,amma ban ta6a tsammanin sun gawurta hakaba."


 Numfashi ta ja ta furzar kafin ta kai kallonta ga sauran En uwanta,kana ta juya idanuwanta ga Haajara "Amma qaddara ta rigayi fata,mai afkuwa ta afku,yanxu bamu da sauran iko akanki,sai dai mu tayaki da Addu'a,kiyi haquri kema ki miqa lammuranki ga Allah xai Isar miki adukkanin lammuranki,sanan xai kareki daga sharrin mutanen nan,babu Abin da ya gagari Allah, ki kuma kula da mijinki,ki dauka shi kadai ne ya rage miki awanan duniyar,sanan ki fidda ranki daga tunanin mutanen nan,amma kiyi iya qoqarinki wajan sauya musu koda kadan ne acikin halayyarsu,kada ki bari su rinjayeki da munanan dabi'unsu,."


 Baki Haajara ta toshe, amma duk da haka sai da wani kuka mai qarfi ya qwace mata.,durqushe wa tayi aqasan qafafuwanta cikin muryarta da bata FIta sosai "Ku min rai Ku koma dani gida Inna,ban shirya wanan tashin hankalinba,baxan jure rayuwa acikin tulun maqiyaba.,Na haqura da son Hamza, karku tafi Ku barni anan.." Kuka ne yaci qarfinta ta qara durqushewa aqasa tana buga hannunta..

 Sosai xuciyoyinsu suka karye suka shiga matse hawaye "Bakin Alqalami ya Riga daya bushe Haajara,kin bar wanan damar tun abaya,yanxu kuma xaki fahimci gaskiyar abin da kika siyama kanki, zaki rungumi Qaddarar da aka Riga aka rataya miki,.sai dai ko da wasa kada kiyi gigin kai qara wajan Baffa malam,Dan wanan yana cikin sharadin Aurenki da Hamxa,Wanda ke da bakinki kika amsa kika kuma amince da shi."


 Wani Ihu tasa Mai qarfi Wanda ya tilasta musu toshe kunnuwansu,buga hannunta take aqasa ba tare da taji zafiba..


 Ihun da take yasa basu fahimci mi ke faruwa awajeba. "Ki rufa mana asiri Haajara kiyi shiru kada ki Tara mana mutane aka." Aminiyar innarta ta fada tana dagata,.

  

 "Jar Ubaccan Ai kun makaro,. Tsubbun naku har haka ya gawurta da kawo Amarya za ta fara mana Bori agidan Dana.,.To ko matsafutu yaci uwatar balle Dan bori., Ni za'a yima lalata Agidan Dana,. Ihuhu jama'a Ku kawo min dauki."

 Iya Indo CE take wanan karadin Wanda tun zuwansu akaje aka tsegunta mata,sanan aka sanar da ita suna ta dalasimai Na tsafi suna ihu. Sai kuma akayi rashin sa'a shugowarta yayi dai-dai da ihun da Haajara ta sa.


 Kafin wani lokaci gidan ya cika da mutanen garin,yayin da hayaniya ta CIKA gidan,.

 "Ai Na fada miki Yaya Indo wanan Auren babu komi acikinsa sai fitina.,in banda lamarin Asiri mi hamza zaiyi da wanan mai qirar sandar, gashin tun kan aje ko INA sun fara yada halinsu."


 "Ai kuwa sunyi kadan,.sunyi tsararo,komin sammankonsu ni atafe Na kwana Dan jininmu yafi qarfin Asirinsu."


 "Haba bayin Allah,ya daga xuwanmu babu taryar arxiqi,saima qoqarin jifanmu da mugwayen magana da kukeyi,.wanan wata irin rayuwace haka,daga kawo amarya shikenan kuma sai yada hali,.ya kamata kuna aiki da hankalinku dai."yayar Innah ta fada xuciyarta kamar t fashe Dan takaicin mutanen garin,.jikinta har rawa yake saboda 6acin rai,.ga kuma Haajara data qanqameta cike da tsoro atare da ita. "Lahaula,." Suka fada atare suna tafa hannayensu,.,kafin Iya Indo ta Dora da magana kamar xata ari baki "kuji min maganar banza da wofi., Uban waye xai muku tarbar arxiqi,duk garin nan kunga masu yawo da sanduna ne?ko kunga masu curin qwarya aka.,?ba dai kun kawota ba,to sai kuzo Ku fice kubar mana gida,gayyar tsiya gayyar Na aye,.masu kama da mayu." Ihu mutanen garin suka fara suna tafawa Iya Indo saboda jarumtar data nuna.


 "Tabdijam.,Amma anyi gingima-gingiman jahilai anan.,kallemu da kyau, ko kadan bamu da kamar mayu atare damu,.wanan Kalmar tafi kyau da dacewa da Ku,.idan banda tsautsayi da qaddara banga abin tsinta awanan garin nakuba,.Wanda yake cike da duhun jahilai,.da kuma munanan mutane Wanda basu da maraba da dabbobi."Aminiyar Inna ta fada Dan ko kadan bata da haquri.


 Nan fa mutanen garin suka iyo kanta kamar xasu cita nama danye.


 " Ku dakata"aka fada da wata murya mai tsawar gaske.,take suka tsaya kamar an qamar da su..


 "Kada Wanda yayi gigin ta6asu,ai baqinmu ne.,ba Na uban kowaba agarin nan,Na miye xa'a zo acika mana gida,Dan salon munafircinku da baya qarewa..maxa kuzo Ku fice kafin raina ya kai qololuwar 6aci." Baba lawan ne yake maganar nan ransa in ya kai dubu to ya 6aci..take su ka fara wucewa daya bayan daya,Dan suna mutqar tsoronsa,bashi da wargi Sam.


 Juyawa yayi ga En uwan Haajara "Dan Allah kuyi haquri akan abin da mutanen garin nan suka muku.,Ku bar maganar a iya nan kada Ku kaita ga can garin naku.,hakan xai xama toxarci ne agaremu."


 "Ba komi in sha Allah anan zata tsaya,.amma yanxu xamu tafi Dan daqiqa guda baxamu qarayi agarin nan ba." Gaggo ta fada

 Tana kallonsu "Ku tashi mu tafi kafin acillo mana wuta ta qona mu."


 A taake suka miqe jikinsu na 6ari Dan sun tsorata da mutanen garin.


 "Ku tsaya Ku ci abinci mana ko ruwafa Baku shafa.." Baba Lawan ya fada.


 "Tab mun yafe Baba,.numfashin da muka sha agarin nan ma ya wadatarmu abinci da ruwa..Haajara sai wata rana Allah ya kadai fitina." Riqesu tayi tana kuka tana cewa ta tuba,amma basu sauraretaba Dan rige rigen FIta suke.,

 Jagora baba Lawan ya musu har wajan motar da ta kawosu akan ta maidasu har gida.


 Godiya suka masa suna qara bashi amanar Haajara fiskarsu dauke da hawayen tausayinta..


 Yayin da suka barta durqushe tana gunjin kuka atsakar gida .........


  *_Tofa 😢wata rayuwace xata fara atare da kewayawar maqiyanta?idan aka cire mutum guda Wanda yayi sanadin xuwanta garin.._*

 *_Wani wuna zaku kira wanan chapter ,.cmnts naku Na da Amfani sosai 😘👍🏼kuyi haquri kuma da rashin editing page din nan_*
©by *😘Um Nass 🏇🏼*

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI*🎊


©by *😘Um Nass 🏇🏼*


 *_Follow me on whatppad_*


® *MADUBI 🔎WRI,ASSOCIATION*

 PAGE 19
 Kuka take mai cin rai.,yayin da wani maqoqo ya tokare mata a wuyanta.,daci take ji gefe guda kuma numfashinta ya sarqe saboda tashin hankalin.


 Hawayen nata ya tsaya cak,kamar ruwan da akayi ya dauke,sai ajiyar xuciya takeyi akai-akai,ga tarin kewar gida data addabi xuciyarta,.da kuma tulun tsoron yanda RayuwA xata kaya da ita,aduniyar data CIKA taf da maqiyanta.,.


Hannayanta biyu ta daga sama tana Addu'a *_"Ya Allah kai ne kake da iko akan dukkanin bayinka,kai kafi kowa sanin dalilin kasan cewata anan,ya Allah ka kareni da karewarka,ka katangeni daga dukkanin wata fitina,ka kuma bani ikon cinye duk wata jarraba da xata xo min,ta dadi data wuya._*"


Tashi tayi ya karkade jikinta Wanda yayi budu-budu da qasa,dalilin birgimar da ta shayi.,

 Ruwa ta diba ta shiga makewayi tayi wanka kana ta dauro alwala,.

 Daki ta shiga ta shimfida abin sallahrta, cikin nutsuwa ta fara yin sallah ta rama sallolin da ake binta.

 Ta dade tana kai kukanta ga Allah idanuwanta cike da hawaye..,bata so tana danganta laifin da NATA ne,idan har xatayi imani to kamata yayi ta rungumi qaddararta hannu biyu.


 Tashi tayi ta gyara fiskarta tasa kwalli a idanuwanta,aqoqarinta Na kauda rinewar da idonta yayi,sanan ta saka kayanta ta sa turare mai sanyin qamshi.,


 Cikinta ne ya fara ihun yunwa da murdawa,yana tunatar da ita train yunwar data tara akwanakin biyu kafin bikinta.,

 Tabbas idan ba qarya tayiba, ta manta wani abu shi abinci arayuwarta, dan tashin hankalin da take ciki bai bata damar tunawa da shiba.


 Cikin nata ta danqe jin yana mata murda ta sosai.,gashi babu kowa agidan kamar ba sabuwar amaryaba,.inama taga mutune balle tasa ran samun abincin da xata ci..


 Kwanciya tayi akan abin sallahr tana riqe da cikinta,. _"Qila ajalina ne ya Matso kusa.,Ya Allah kaji qaina da rahmarka,ka yafe min laifukan da Na aikata maka.,"_ Addu'ar da take maimaitawa kenan tana jiran mutuwa ta qaraso ta dauketa. Sallamar da akayi CE tasata yunqurin tashi amma ta kasa,saboda wani jiri da yake Neman kwasarta ya kaita baya.


 Tilas ta koma ta kwanta tana maida numfashi sama-sama.


 Shurun da yaji ne yayi yawa yasashi tunanin ko sallah take,hakan yasa ya nufi dakin Nasu,amma da mamakinsa sai ya ganta akwance tana fidda numfashi sama-sama ga hawayen dake xuba ba tare da Qa'ida ba.


 "Subhanallah Haajara lafiya." Ya fada yana qarasawa kusa da ita. 

 Dagata yayi xaunar da ita,ya jinginata ajikin gadon, kallonta yake cike da tausayi,awani sashi kuma Na xuciyarsa tana tuhumarsa akan rashin adalcin daya mata,ya daukota daga mutane masu nagarta ya jefo da ita ga mutanen da basu da maraba da Namin jeje.


 Hannayensa yasa ya share mata hawayen dake tsere afiskarta,amma kamar qara xubansu yake yi."Kiyi haquri Haajara, Na sani ban kyauta mikiba,.Na rabaki da mutane masu nagarta,wadanda suke sonki,Na dawo dake nan duniyar mai cike da tartsatsayin wuta,lallai Na CIKA mai son kaina,.ban san mi xanyiba adai-dai wanan lokacin,.amma abu guda daya da nasani shine Na Ina sonki so Na gaske,zan kuma xame miki kariya.,zan maye miki gurbin dangink da kika rasa,.zanyi dariya atare da kee,idan kuka yazo Min xan 6oye daga ganinki,farin ciki kadai xamu raba atare,. Mutqar numfashi da iska Na kai kawo ajikina.."  Murmushi tayi jin kalaman Hamxa,.Wanda Na suka zame mata kamar ruwan qanqara ne atsakiyar sahara,wata nutsuwa take ji tana sauqar mata axuciyarta, kafin ta sauqe numfashi ta firzar da iska abakin..


 Kallonta takai ga saitinsa, Wanda ya qura mata ido kamar xai maidata cikinsa. 

 "Akwai abubuwa masu yawa da sukan ratso atsakanin dukkanin al'amuranmu,wasu kuma sukan xama masu gwara tanadinmu,.ahankali sai mu samu tawaya ta fiskar kasawa da gajiyawa Na rayuwar Dan Adam,.Wanda hakan ya xama halittace da kuma dabi'a Na ko wani mutum..,"

 Numfashi ta sake ja tana furzar da xaxxafar iska abakinta,.yayin da Hamxa ya qura mata ido,Sam bai fahimci INA maganarta ta dosaba, asalima bai San mi take son fada masaba,. 


 Fahimtar da tayi cewar bai gane manufar kalamanta ba, ya sa ta murmushi mai sauti,. "Ka janye maganar Alqawalin da ka min,saboda bana so Allah ya kamaka da laifin kasa CIKA min alqawali.,ka bani qwarin gwuiwa akan yanda xan fiskanci gaskiyar rayiwar da take matsowa kusa dani koda ace baka tare dani,.wasu wahalhalun rayuwar riba ne ga Wanda ya juresu,ya kuma yarda da cewa Allah yana tare da shi.,Abu guda nafi buqata atare da kai,.shine kamin uzuri Aduk lokacin da Na aikata maka ba dai-daiba,.kayi haquri da halayyata alokacin da xuciyata ta kai qololuwar 6aci,.Na sani jure fushin xuciya abu ne mai wahla.,ka daina neman yafiyata akan kawo ni nan garin,dama can Allah ya qaddara kasantuwata atare da Ku." Kallonta yake yana jin wata sabuwar soyayyarta Na sauqa atsakanin xuciyarsa.

 Wani dadi ne yafi wanan,.gaskiya babu Allah ya masa kyauta da abin da yafi lu'u lu'u daraja mace ta gari..


 Rungumeta yayi yana shafa kanta yana gyada kai "Na gode Haajara,.Allah y miki albarka,ya bani ikon sauqe duk wani haqqinki da ke kaina...


 " Ameen ta fada itama cikin muryarta data gama daskarewa.. "Yunwa nake ji sosai Hamza." Ta fada afiskarta qunshe da rauni. "Ya Rabbi" ya fada yana shafa kansa,cikin hanzari ya miqe ya janyo ledar da ya shigo da ita,


 Kana ya maxa ya dauko kwano da kofuna.


 Gasasshen nama ne yasha albasa da quli-quli sai kuma biredi,.gefe kuma madarar shanu CE ya juye musu akofina..

 "Bismilla zo ga abinci,Sam Na manta wallahi,. Kiyi haquri da barink da nayi da yunwa."


 Kai ta girgiza ta Na murmushi,. Wanan halayyar ta Hamza ita kadai ke qara sata fadawa sonsa,sai dai tana fata hakan ya dore iya qarshen rayuwarsu.


  Da Bismillah qunshe abakunansu suka fara ci,Wanda kunya da nauyin hamza ya hana haajara sakewa taci abincin sosai.


 Lura da hakan da yayi ya shiga dura mata tun tana sunkuyar dakai,.har ta ware tana dariya yana bata..


 Hakan ya mantar da ita acikin duniyar da suke, dariya take mai sauti yana tayata..


 Qarshe dai bai sake fitaba, xama yayi suka ci gaba da hirarsu Wanda mafiya yawa barkwanci ne.


 Sallahr issha ya jasu kana ya wakilcesu yin nafila da taimakon Haajara akan koyi da sunnar ma'aiki ga dukkanin wasu sabbin ma'aurta.....
****** Bugun qofar da ake ya sasu tashi afirgice,.yayin da jikin Haajara ya hau 6ari,.

 "Kaddai 6arayi ne suka kawo mana farmaki awanan tsohon Daren." Haajara ya fada jikinta yana qara karkarwa..


 "Kai bana jin hakan,.dan garin nan ban ta6a ji anyima wani sataba,kingama sallah ake amasallaci,.ba 6arawo bane."


 Bugun qofar aaka sakeyi Na wanan karon yafi qarfi Dan kamar Marmara aka doka.

 Kafin kuma magana ta biyo baya "Hamxa ko kazo ka bude min qofar nan ko yanxu na Tara maka mutane,."


 Ido ya fiddo waje yana kallon Haajara itama firgita tayi dan ta gane ko wayece.


 "Iyata Indo,mi tazo yi awanan lokacin????" Ya tambaye yana xura rigarsa jikinsa sai 6ari yake SBD tashin hankali....

  _What do you expects next chapter 🤔?? Mine ya kawo iya Indo awanan lokacin,.Ku qoqarta kuyi comments Ku fadi naku ra'ayoyin, hakan Nada amfani sosai._


  
*😘Um Nass 🏇🏼*

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI* 🎊


 ©by *😘Um Nass 🏇🏼*


 *_FOLLOW ME ON WHTPPD_*


® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION* PAGE 20 Jiki Na rawa ya nufi qofar,., xuciyarsa Na ta bugawa da qarfi,Dan har ga Allah ya xata Baba garba ne wani abu ya sameshi ko kuma ya Mutu..


 Bude qofar yayi yana magana "Mi ya samu Baba Garba,.Allah ya sa dai ba mutuwa yayiba.," ya fada bakinsa Na rawa Dan ko kula baiyi da yanayin Iya Indo ba balle ya hararo lafiyarta lumi.


 Hannu ta Dora Aka cikin yanayin tashin hankali ta fara ihu "Na shiga Uku ni Indo.,qiyayyar da kake mana har ta kai ta fatan mutuwa Hamza,.to ba Garba bane ya Mutu ni CE Na Mutu,.ja'irin yaro mai sunkuyayyan kai.,"


 "Yi haquri Iya Indo yanda Na ganki da wanan Asubar yasa Na xaci ba lafiya va."


 "Ba xan haqura ba nace,aikin banxa kawai,." Ta hankadeshi ta shige gidan tana ci gaba da sababi.,"Ai ni yau tsawon dare ma Na gani,.fatana kada Allah yasa abun da nake tunani ace ya faru,."

 "Mi kike tunani Iya Indo.?


 Dakin da take tunanin nan aka kai Haajara ta tasamma shiga.," Idonka xai gane maka idan Na shiga"


 Da gudu Hamza ya tare Iya Indo,wani qululun baqin ciki ne yake turnuqeshi,ga tarin takaicin mahaifiyar tasa,.wata rayuwa CE wanan ne."Kiyi haquri Iya Indo kinga ko tashi Haajara batayiba,.xuwa Safiya sai kixo kiga koma miye.,amma yanxu ba lokacin xuwa gidan mutane bane,atsarin musulunci ma akwai haramcifa."


 Tsayawa tayi cak,.kafin ta juyo fiskarta,Wanda hakan yasa Hamxa sauqe ajiyar xuciya kenan Dan atunaninsa Iya Indo ta haqura da shiga dakin,..

 

 "Ai ko mai gari yanxu ya kai mawar tashi.,balle ita karan kada miya.,kai tsaye kace min kada Na shiga dakin saboda kayi girman da zaka kwana da mace Hamxa,amma ba ka kawo min wani sharhinka Na banxa da wofiba,idan akayi gaba kuma nasan kafirtani xaka iyayi."


 "Ya Allah" Hamxa ya fada yana sunkuyar da Kansa qasa kalaman Iya Indo sun girmi kunnuwansa.


 Kai kawai yake girgixawa ba tare daya fadi wata magana abayan hakanba..,toma mi xai ce?


 Wucewa tayi tana ci gaba da yin sabon sababinta,.

 Jikin Haajara in banda karkarwa babu abin d yake,tsoro ne da fargaba Na Iya Indo ya tarar mata,Dan tabbass tana shakkar gatsau dinta,ba ruwanta Da sakayawa balle alkunya,toma INA kunyar anan, take.?


 Tunaninta ne ya tsaya cak alokacin da taji an yaye mayafin data duqunquna da shi.,Sam batayi tsammanin xata iya yaye mata ba.

 Ido ta runtse hawaye Na xuba atsakanin rufaffun idanuwan NATA.


 "Oh ni Indo yaran yanxu Sam babu haquri,duk saurina Hamza sai da ka haiqema yarinyar nan daren farko.,wata jarabace wanan,.?Wanda xamani ya xo da ita,ada sai mace ta shekara tana gudun miji amma banda yanxu,ana kawo mace kamar mai jira sai ta miqe qafa itama,.,awani 6angaran kuma sai kaji shuru babu ihun Neman agaji,.komi qanqantar mace ana kaita gidan mijinta sai kaji luqus babu motsinsu,." Harara ta wurgama Haajara Wanda take jin kamar ta maqureta "tashi daga duqunqunen da kike munafukar Yarinya." Ta daka mata tsawar da tasata miqewa xaune,.


 Azabar xafin da take ji atsakanin qafafuwanta ya tunatar da ita raunin dake jinta,ido ta runtse wasu hawaye masu xafi suka sauqo mata.,

 Kai ta sunkuya qasa,Dan baxata juri hada idanuwa da Iya Indo ba,.wanan toxarcin da mi yayi kama. Wai kuma adole surukarta CE.


 Tsaki iya Indo ta Sakeyi "ki tashi kije ki kwalfi ruwa arandar sanyi muje Na miki tsome,."

 Kai ta girgixa tana son magana amma bakinta yayi nauyi.


 Zaninta ta raruma tasa ta miqe atsaye,.sosai jikinta kee amsawa aduk wani motsin da tayi,.

 Tafiya take kamar mai koyan yinta Wanda hakan ya qara qular da Iya Indo,ason ranta tayi fatan kada wani Abu ya shiga tsakaninta da Hamza, amma sa6anin son ranta ta tadda mai afkuwa ta afku,.


 Hankadata tayi Wanda yasata yin gudu kamar ta kifa " Dallah kibar min tafiya Da sal6i wa ya aikeki,"


 Fitowa sukayi,a Inda suka bar Hamxa anan suka Tarar da shi,Kansa asunkuye,.xuciyarsa Na masa quna da tafasa amma babu damar yayi mgn.,gani yayi abin xai yi yawa idan yayi shuru.,"Iya Indo ki bari Na dafa mata ruwan xafi mana,.gama ice canfa Na hada INA shirin hura wutar kika zo,.ruwan sanyin xai mata Illa ajikinta,kiyi haquri kinji."


 Hannu ta shiga tafawa cike da takaicin Hamza "Tabdijam lallai Hamza wuyanka ya kai,.Ashe badan Na xoba kai xakayi komi,.to baxan bari ka dafa mata ruwan xafinba,da Na sanyi xatayi,,kasan da illar ka kasa haquri har sai da ka haiqe mata.,"


 Kai ya girgiza yana sunkuyarwa qasa,.can ya xari bokiti.,"Bari to Na diba muku ruwan wankan."


 Hankadeshi Iya Indo tayi "kafa kiyayeni Hamza,ka fita idona Na rufe,idan ka matsa da yawa xan haramta maka xaman garin nan balle ka qara ganin wanan abar.,ka fice ka bamu waje ana sallah Amasallaci amma kana tarewa awajan mace."


 (Uhmm kunji Matar da bata ko yi alwala ba taxo mita gidan mutane itake ma wani kashedin tafiya masallaci.) Fita yayi daga gidan Dan yana shakkar Iya Indo akan abun da tace,ba qaramin aikinta bane ta masa baki.


 "To maza ke kuma ki dibi ruwan INA ganinki,." Cikin karayar xuciya ta kwalfi ruwan ta dauka da qyar,.duk da axabar da takeji ajikinta da kuma ciwo,haka ta tattara dauriyarta ta fara tafiya.,


 Ga mamakinta tana shiga Iya Indo tabiyo bayanta,.bata tsaya bin komiba ta shiga kwara mata ruwan tun daga tsakiyar kanta har xuwa qafarta,.wani axababben sanyi ne ya ratsa Haajara qofofin jikinta takeji kamar ana watsa musu qanqara.,.

 Bata qara jin axabar da tafi wananba sai da taji iya Indo ta tsomata asauran ruwan sanyin,ta kuma banqwara mata qafafuwanta.,


 Ihun da bata shirya yinsaba tayi.,

 Wanda hakan yasa Iya Indo kaima bakinta duka, tuni gun ya fashe sai jini "kinibabbiyar banxa.,da Uban wa ya kaiki,gobema sai ki qara yarda ya kusanceki,.kullum sai Na muku sammako kamar haka."


 Tana gama fada ta fice daga bandakin.,

 "Bari Na tafi naji liman Na sallamewa kada wani yaje ya fadama baba lawan an ganni anan."


Ta fita ba tare da sanin a wani hali tabar Haajara ba..**""""***"""


 Fitarta yasa Hamxa fitowa daga inda ya 6uya,.yana sauqe ajiyar xuciya.,

 Sauri yake ya samu Haajara ya bata haquri, ya kuma dafa mata ruwan xafi.


 Yana shiga yasama qofar sakata, da gudunsq ya shiga daki amma bai gantaba.


 Hakan yasashi nufar bandaki jin babu motsinta,.

 Sai dai abin mamaki ganinta yayi azaune cikin bahon ruwan sanyi.


 Ido ya fiddo waje cikin kaduwa da tsoron muguntar da Iya Indo ta mata,.


 Qarasawa yayi cikin sagewar qafa,."Haajara"ya kirata yana ta6ata shuru yaji babu alamun numfashi ajikinta.


 Hannunta ya daga sama yana ajiyewa ya dawo..


 Ihu ya saki mai qarfi yana dagata daga cikin bahon.....


*😘Um Nass 🏇🏼*

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI* 🎊


 ©by *😘Um Nass* 🏇🏼


 _*Follow me on whatppad @UmNass*_


® *MADUBI 🔎 WRI.ASSOCIATION* PAGE 21 Daki ya wuce da ita,sai faman sumbatu yakeyi,hawaye ya CIKA fiskarsa,kan gado ya doreta,sanan ya sake rugawa ya debo ruwa mai sanyi a randa,da gudunsa ya dawo ya kwara mata ruwan ajikinta,.


 Wata duguwar ajiyar xuciya ta sauqe,.tana qanqame jikinsa daga sanyin da ya kai mata farmaki.,kafin nan ta fara jero atishawa wata Na korar wata,.

 Ajiyar xuciya shima Hamxa ya sauqe yana share hawayen da ya taru atsakanin idanuwansa"Alhmdulillah., Allah Na gode ma."ya fada yana daga hannayensa sama,da rarrafe ya qarasa kusa da Haajara ya riqe hannayenta,.,yana kallon fiskarta Wanda take qoqarin bude idanuwanta,.


 "Sannu Haajara,sannu kinji,." Maganarsa da taji yasa ta bude idonta,Dan jin kanta take kamar zai fado saboda zafi,.

 Murmushin qarfin hali ta masa sanan ta gyada kai alamar amsawa,."Bari na dafa miki ruwan zafi kinji."bai jira amsartaba ya ruga tsakar Gida.


 Itatuwa ya garqama amurhu masu yawa,sanan ya hura wutar,ya dauko tukunya ya CIKA ta da ruwa ya Dora,.


 Cikin lokaci kadan ruwan ya tafasa,ya surka da Na sanyi ya kai mata bandaki,.


 Daukota yayi kamar jaririya ya maidata bandakin,ya dauko tsumma kana ya fara mata dundume,saboda sanyin daya ratsata ko kadan bataji zafin ruwanba,asalima dadinsa take ji, tana jin raguwar sanyi ajikin NATA,.akai akai take sauqe ajiyar xuciya.,


 Ganin ta ware yasashi fitowa daga bandakin,ya hada mata wani ruwan dumin da kuma wani a buta,.

 Ya miqa mata,.


 "Ga wanan ki shiga cikinsa idan kin gama gasa jikin naki,.wanan Na butar kuma kiyi wankan tsarki da shi."

 Kai ta sunkuyar qasa Dan wata kunyar Hamzan CE ta dirar maata,wani sashi Na xuciyarta najin tausayinsa,da kuma sabuwar soyayyarsa.,.


 Ruwan shayi ya dafa mata sanan ya tafasa musu taliya,kasancewar akwai komi Na abinci agidan nasu,haka kuma dangin Haajara sun hado musu da kayan gara., firr iya Indo taqi kar6an komi acewarta basu San da wani tsubbin aka kawo kayan abincinba.,

 Haka kuma sauran En uwansa ma suka Qi kar6a,. Baba Lawan yace ya qyalesu su suka rasa ai.,


 Dan haka bai sha wahla ba ya gama komi,dai-dai fitowar Haajara Abandaki,. Ya riqota yana qoqarin dagata ya kaita daki.,"Ka bari xan iya tafiya,naji sauqin jikina,."ta fada muryarta a sanyaye 


 Kai ya dago ya kalleta,amma bata yarda sun hada ido ba.

 Bai CE komiba ya dauke ya kaita dakin,kayan Da xata sa ya dauko mata kana ya shimfida mata darduma,. "kisa kayanki kiyi sallah gari yayi haske."


 Kai ta gyada masa,.tana son yin magana amma ya fice Adakin,

 Murmushi ta bishi da shi ita kadai,sanan ta saka kayanta,ta kabbara sallahr,.

 

 A hankali taji nutsuwa ta sauqar mata,.yayin da wata ni'imtacciyar iska ke ratsa dukkanin jikinta.


 Tana idarwa Hamza ya shiga da abinci a fleet, da kuma shayi Wanda ya sha kayan qamshi,

 Miqa mata yayi "ki fara shan wanan kafin kici abinci,xakiji dadin cikinki."

 

 Kar6a tayi tana mamakin yanda ya iya aiki kamar mace,.kur6a tashi ahankali Dan tsoronta kada ya qonata,amma ga mamakinta sai taji dai-dai abakinta, ga kuma qamshin kayan HADIN da suka wargaya abakinta,. Ido ta lumshe ta bude su akansa,.,

 Kai ya daga mata,alamar jiran sakamakon girkin nasa,ido ta bude masa tana murmushi "Da dad'i sosai,da alama Na huta yin girki,"


 "Tsawon lokacin da kike so,xan miki girki har sai kince bakya so."


 "Kasan baxan ta6a cewa bana so ba ai,.amma ya akayi ka iya aikin mata,bayan girki Na mata ne."


 "Saboda irin wanan ranar,kinga bana buqatar taimakon wasu."


 Kai ta sunkuyar saboda kunyarsa da ta dirar masa "kiyi haquri akan abin da Iya Indo ta miki,da ace INA da ikon hanawa to tabbas da xan hanata shigowa gidan nan,.amma mahaifiyata CE,ko yaushe burina mu rabu lafiya,.Haajara INA tsoron abin da xai iya faruwa anan gaba,idan nayi la'akari da abun da ya faru ayau,inaga har yanxu ban miki adalciba,Na so kaina da yawa."


 Bakinsa ta rufe tana murmushi "mun gama wanan maganar tun jiya Hamza, koya zamu so jin dadin rayuwa ba xamu iya sauya qaddararmu ba.,Iya Indo ba asurukata Na daukeba,INA mata kallon mahaifiyar data haifeni ne,zan jure duk wani abun da xata min."


 Hannunta ya riqe yana murmushi Wanda Na qarfin hali ne "Allah ya miki Albarka Haajara ya kareki da dukkanin kariyarsa,ya albarkace da samun yaran da xasu tallafi rayuwarki."


 "Ameen,.mu ci Abinci hamxa yunwa nake ji sosai."


 Haka suka fara cin abincin suna musayar magana,wajan taya junansu rarrashin xukatansu da kuma bada haqur akan abin da xai iya faruwa da su...*********Yinin ranar Hamza ne yayi duk aikin gidan Dan fir hanata yin aiki yayi,ko shara hanata yi yayi,iyaka yace ta xauna yana kallonta suna fira.

 Duk yanda yara En gulma suka so shiga gidan hanasu yayi,musamman da ya San En leqen Asirin Iya Indo ne..,

 Ko ya bude musu qofa cewa yake barci take bata da lafiya,.

  


 Saida yayi girkin rana shinkafa da miyar kifi banda,.Wanda qamshin daddawa ke tashi,abin yabar bama Haajara mamaki sai al'ajabi,Wai Namiji da iya miya.,


 Sai alokacin ya bude qofar gidan,..

 "Ban San Mi yasa ba,amma xuciya ta bata amince min, da FIta Na barki ke daya agidan nan ba,. Bana son wani ya xo ya rugaza miki farin cikin dana Dan Adana miki."


 Kallonsa take ido cikin ido tana ganin gaskiyar maganar da yake fada,daga qasan xuciyarsa take.


 "Kar ka damu,guda ka tafi ka barni In sha Allah guda xaka zo ka taddani,kai dai ka rufe idanuwanka daga kallon ko wace mace awaje,ka tuna kabar wata agida tana jiran dawowarka.,"


 Tsayuwarsa ya gyara yana fadada murmushinsa Wanda haqoransa suka fito ana kuma jin sautin sa "kin San wani abu,?duka garin nan babu mata sai maxa,kinga kenan babu Wanda xan kalla."


 Baki ta rufe tana dariya sosai "Kaii Hamza,duka yawan matan garin nan,.?"


 Kai ya daga mata "A idanuwana maza suke kallonsu.,"

 Dariya sosai ta shiga yi tana qoqarin yin magana sukaji an bugi qofar gidan da qarfi,.

 Afirgice suka juyo gaba dayansu Dan kallon gwanin da yake musu wanan bugun,.


 Yayin da xuciyar Haajara kamar ta fado saboda tsorata da tayi,..,musamman ganin Wanda ya shigo fiskarsa babu alamun rahma ko kadan..

 

 "Sannu tabbatacce ai ni xuwa nayi naga er gwal din da ke gidan nan.,Wanda har aka hana yaranmu shigowa su ganta,."


 "Gwaggo Harira sannu da xuwa." Ya fada yana qoqarin danne damuwar da ke fiskarsa.

 "A'a riqe Sannunka Hamza,ai yanxu ban kai wanan matsayin atare da kaiba,.zuwa da kai yafi saqo,INA Lu'u Lu'un naka take,diyar masu buxu da sanduna..."


_"😢plxx kuyi Maleji da wanan, kaina yana Min ciwo sosai,Ku tayani da Addu'a_"

®by *😘Um Nass 🏇🏼*

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI* 🎊


©by *😘Um Nass 🏇🏼*


 *_FOLLOW ME ON WHATPPAD @UmNass_*


® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION*Page 22


 Kai ya sunkuyar xuciyarsa na masa zafi, da maganar gwaggo Harira tayi akan Haajara,.

 Tsinkayar muryar Haajara yaji tana gaidata cikin sarqaqqiyar muryarta,Wanda ko ba'a fada masaba yasan cike take da tsoronta.,


 "Sannu da xuwa Inna Harira,Shigo daga cikin Gida mana."


 Juyowa tayi ta mata wani mugun kallo kafin ta bita da harara da tofin yawu,.

 "Yanxu hamza akan wanan abar Ka tada hankalinka,.Ka janyo mana abin Gori agari,Aradu ko ni da nake mace aqafa aka daura min ita ban janta."


  Kai Haajara ta sunkuyar qasa hawaye na xuba a idanuwanta"Gida kam dole na shiga na ga tsiyar da aka kawoki da shi,ni tsorona Allah tsorona baqin talaucin da na hango yana qwanqwasa muku qofa agidanku."


 "Haba gwaggo Harira, wanan wani irin fatan tsiya ne kike mana,.bayan xagi da kika qare mana kuma,minene laifin Haajara?xuwan da ta'ayi amatsayin suruka,?bafa ita ta kawo kanta ba,Aurota nayi na kawota saboda INA sonta." Hamza ya fada da ihu yana huci saboda 6acin rai,Wanda har ya manta wace 

Gwaggo Harira agabansa.,


 Hannu ta Dora aka ta fara sallati "Hamza ni kake ma fada da ihu haka?Ni Harira Hamza? Da kyau yanxu na qara tabbatar da girman asirin da ya rasa,."


 Juyawa tayi ga Haajara Wanda ta takure awaje daya "Da kyau Yarinya kin biya malaminki da tsada,sai dai akan mutum guda ya miki aikin,ki jira namu martanin."


 Sanan ta juya ga Hamxa Wanda jikinsa yayi sanyi "Yaya Indo CE ta turo na qiraka,idan Ka so kaje kiran nata,."


Daga haka tasa kai ta fice agidan ta banko musu qofar gidan.


 Tsugunnawa Haajara tayi aqasa ta dafe kai tana hawaye "Mi yasa?Mi yasa Ka maida mata da maganarta akaina Hamxa,?wanan ba gata Ka min ba,Ka qara jefani ne ga tarin Qayar dake dauke da garwashin wuta,"


  "Zuciyata ba xata iya jure ganin ana miki cin fiska irin wanan ba Haajara,na kuma nade Hannayena nayi shuru,Sam baxan iyaba."


 Miqewa tayi tsaye ta nufi qofar shiga cikin gidan,ba tare da ta CE masa komiba,.saurin tarar gabanta yayi "Baki CE komiba xaki wuce ki barni.."


 Kallonsa tayi ranta duka a6ace yake sosai "So kake nace maka wani abu?bayan tun jiya muke ta nanata magana guda daya da kai,.Daga yanxu bana buqatar tallafinka da kuma Sanya baki aduk abin da aka min agarin nan,Ka barni da baqin fantin da Ka Riga ka goga min,dan Allah karka sake tsafeni da wani ta hanyar nuna kariyarka akai na.."


 "Amma Haajara...."


 "Har yanxu kana da damar gyara min kuskuren da nayi,kada ka taimaka wajan sanyawa na qara tsanar kaina.,"tayi saurin katseshi daga maganar da yake shirin yi,.

 Bata sake bari ta saurari wata maganar da xai yiba,ta ra6e ta gefensa ta wuce..


 

 Dafe kansa yayi Wanda yake ji yana Sara NASA,awani 6angaran Na xuciyarsa kuma tana jin haushin abun da ya aikata,Wanda duk aqoqarin kare Haajaran da yakeyi ne,sai dai kuma ayanxu ya fahimci ya qarama wuta fetir ne, ba tare da ya ankareba,.

 Haka kuma wata soyayya da Tausayin Haajaran Na ratsa ko INA Na jikinsa,wai a kwana daya da tarewarta amma matsaloli suna ta cin Karo da junansu wata Na Kore wata,.


 Tunawa yayi da Kiran da akace Iya Indo Na masa,Wanda kuma bai San mi xai tararba a can.,


 Tafiya yayi ganin yana qara 6atawa kansa lokaci,haka kuma yana qarama kansa laifi ne,.


 Tafiya yake xuciyarsa nata lugudai.


 Duk Inda ya wuce mutanen garin Na binsa da kallo suna qus-qus,idan kuma ya musu sallama babu mai amsa masa,saima juyar da kai da sukeyi.,


 Mamaki ne ya cikashi Na sosai,akan abin da ba Addini ba amma sun riqeshi gam,har ya qarasa gidansu babu Wanda ya tanka masa,balle yasa ran xai samu dan qirarin da angwaye suke samu idan sunyi aure, abin bai tsaya kan manyaba ko yara da sun hangoshi sai su xura da gudu kamar sunga dodo,sosai abin ya daure masa kai,.

 Cikin sanyin jiki ya qarasa gidan muryarsa araunane yayi sallama,Amma ko tari babu Wanda ya masa tsakanin Iya Indo da Gwaggo harira,da suka baje kolinsu suna qus-qus dinsu.,


 Qarasawa yayi yaja kujerar tsugunno ya xauna,.

 "Iya Indo barka da yamma,naji ance kina qirana."


 Sai lokacin ta juyo ta kai kallonta gareshi "Kenan da ban tura kiranka ba baxaka xo ka gaidani ba kenan,.?"


 "Amma ai naga mun gaisa tun asubar fari."


 Harara ta watsa masa Wanda ta sashi sunkuyar da kai qasa "Da naje taimakon matarka ba,yanxu Hamza qaurin idonka har ya kai ka cima gwaggonka Harira mutunci daga yin aure,sanan ka garqame qofa Dan baqin hali ka hana yara shiga gidanka,. Kuma duk da sanin yaran qanenka ne,Abin da nake jiye maka tsoro shine ya sameka tun kan aje ko INA,"

 Xama ta gyara ya sake kai kallonta saitinsa "Bari kaji wani abu daga ranar yau Na haramta maka sake kusantar wanan Matar taka,Dan Sam ba xan had'a jini da su ba,ataqaice bana son Dan da xata haifa atare da kai."


 Ido ya dago cikin razana da tsoro tuni gumi ya wanke masa fiskarsa,.


 "Kika CE mi Iya Indo?" Ya fada muryarsa tana rawa Dan ya kasa samun nutsuwa,.


 "Nace ban yafe maka ba idan ka sake kusantar yarinyar da ka kawo mana,."Miqewa yayi tsaye gumi yana tsattsafowa akan fuskarsa.


 Kallonta yake yana Jin maganar tana maimaituwa akansa.


 "Inna lillahi wa Inna ilaihirraji'un." Kalmar da yake maimaitawa kenan gumi Na xuba ta ko INA ajikinsa.....


_maleji plxx har yanxu bana jin dadi,_*😘Um Nass 🏇🏼*

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI* 🎊


 ©by *😘Um Nass 🏇🏼*


 *_Follow me on whatppad @UmNass_*®by *MADUBI 🔎WRI. ASSOCIATION*

PAGE 24Matsananciyar rashin lafiya Haajara ta fara yi,Na zazza6i mai xafi da kuma ciwon go6o6in jiki,ko hannunta bata iya dagawa saboda ciwo.,

 Da fari tayi tunani akan axabtuwar aikin da takeyi ne babu qaqqauta acikin ko wata rana take tambayarta.,

 Amma daga baya kuma taji ciwon ya zarce tunaninta,bayarwa tayi akan Ajalinta ne ya risketa alokacin,,musamman yanda ko yatsunta bata iya dagawa,.


 Hankalin Hamza ya tashi sosai da ganin wanan ciwon Na Haajara,Wanda ko kadan bai ta6a ganin irinsaba,.


 Hakan yasa ya ruga da gudu xuwa gidansu,.yana hakki ya fado gidan yana qwalama Iya Indo kira,.


 Arude ta fito daga daki tana riqe da xaninta a ahannu "Mi ya faru Hamza wanan kira haka.,?"


 Rurqusawa yayi yana haki yana nuna qofar waje "Nace wani abun ne ya faru,?mi ya sameka awajen,?ko wani ne ya biyoka.?"


 Kai ya girgiza da Sauri muryarsa tana rawa ya fara magana "Haaa....Haaaja...Haajara ce."

 "Mi ya samu Haajaran Mutuwa tayi ne.?"

 Kai ya girgiza da sauri "A'a bata da lafiya ne,tana Gida ko hannunta bata iya dagawa."


 Baki ta ta6e kafin ta yi "Mtssss.,aikin Banza dama akan wanan duk kabi ka rude,?yo ni INA ruwana da wani rashin lafiyarta,Allah ma yasa mutuwa xatayi kowama ya huta da wanan Annobar,.tunda ka Aurota ka kawota babu abin da ta tsinana mana yau wata shida kenan,amma dubeka komi naka qara ta6ar6arewa yake,Neman kudin da kake xuwa birni kamar an daureka,baka iya jimirin tafiya,baifi ka FIta sau biyu asati ba,. Ni wanan jaraba ta isheni,Allah ma ya sa ta musu ko Na samu hankalina ya kwanta,."


 Kai ya dago afirgice jin mugun aljafa'in Da IYa Indo take masa,hakan yasa shi miqewa jikinsa Na 6ari,Dan ko kadan kunnuwansa ba xasu juri jin mugwayen kalamanta ba. Tafiya yayi da gudu yana tsorin kada mugun fatan Iya Indo ya fada kan Haajara,lallai kuwa da shima ya mutuwar xaiyi.,


 Da gudunsa kamar mai shirin barin gari ya nufi wani gidan da yake aqarshen garin.,

  

 Sallama ya fara yi babu qaqqautawa,daga can aka amsa akace ya shigo.,


 Wata dattijuwar macece ta barbaza kayan itatuwa ko INA agidan maganin gargajiya ne,.

 Fiskarta tasha dige-digen fanti da kwalli,sai zazzare ido takeyi,kamar sarkin da kashi ya kama a fada.


 Ita CE mai maganin garin,takan fadi jinyar da ke jikin mutum,En garin sun yarda da ita sosai,ta yanda ko naquda mace take sai dai akinkimota akawo ta gidan,amma ko kadan bata xuwa gidan mutane,ahaka take NATA kasuwancin da kuma kafa musu sharuddai Wanda wasu basu da alaqa da jinyarsu,sai dai yanda jahilci ya musu katutuwa ko mi ta fada sukan yarda da shi da gasken gaske.


 Gassheta ya fara yi ta amsa tana kallonsa dama da qasa.

 Kaii ta gyada masa sanan taci gava da muxuranta "kaje kai tsaye ixuwa batun da ya kawoka."ta fada da muryarta marar dadin ji,cikin yaren baburanci,Wanda ya xauna abakinsu,.


  

 " Mata ta CE bata da lafiya zaxxa6i mai xafi ya kamata,ko hannunta yau bata iya dagawa,ko INA ajikinta yana mata ciwo ne."ya fada ba tare da tsaya Jan numfashiba,.


 Kallonsa tayi kafin ta kauda kai ga tulun maganunnuwan da ke gabanta.


 "Mi yasa Baka daukota ka kawota ba." Ta fada da muryarta marar mai amo.

 Tuni fargaba da tsoronta ya dirarma Hamza Dan jin muryarta yake yana ratsa dukkanin jikinsa,duk da cewa ahankali take yin maganar.,


 Kansa ya sunkuyar qasa,yana naxarin maganar da xai fada mata,haka kuma yana tsoron fahimtar da zata masa.


 "Idan baka shirya kar6ar mata maganinba ka tashi ka bani waje." 

 

 Da6ass ya xauna aqasa ya dago Kansaa yana kallonta,cikin sarewa da karaya ya fara magana "Bani da abin hawan da xan kawota nan,saboda yazarar dake tsakanin gidanmu da nan,haka kuma babu Wanda xan tunkara da sunan dauki ko agaji akan ya daukota ya kawota,ataqaice ko da kudina ne baxan samu wanan alfarmar ba,."


 Kallonsa take da mamaki afiskarta "Kamar yaya kenan,.ba Dan garin bane kai,ko kana da wani ciwo ne?da xai sa arasa mai daukan matarka.?"


 Qunci ne ya lilli6e xuciyarsa wani ciwo ne ya taso daga maqoshinsa mai daci.,"Nasan ba xaki kasa samun labarin Hamza ba Wanda ya Auro er Yadin Bunni acikin garin nan ba,.daga lokacin da nayi wanan Auren xuwa yanxu babu wata magana ta kirki ko ta sa6ani da ta qara shiga tsakanina da mutanen garin nan,. Kowa gudunmu yake yana qyamarmu kamar Wanda Annoba ta afka masa,da yawa acikinsu fatan Mutuwa suke ga Matar Dana auro,taya xasu kawo min dauki wajan kawota wajan magani,. Ban San ya xan kwatanta miki rayuwar da mukeba,amma ayanxu idanuwan kowa da kunnensa yana garemu ne da fatan jin mummunan labari akan mu,. Nazo wajanki da sa ran xaki taimaka mana,ki bama matata magani koda baki gantaba,haka kuma kina da yawaitar Ilimin sanin magani da tausasawa akan marasa lafiya,.ban San ko kema xaki iya mana wanan taimakon ba...."


 Ya fada yana hada hannayensa biyu,ga hawaye da ya kwanta acikin idanuwansa.,

 Kallonsa "Yar mai ganye takeyi,sosai ta CIKA da mamakin abun da yake faruwa agarin,duk da cewa ta sha jin masu kar6an magani suna bada labari akan auren da yayi,da kuma irin baqar izayar da Matar tasa take sha awajan surukarta,bata dauka tsananin ya kai har haka ba.,

  Abu kamar acikin tatsuniyar Gizo,saboda kawai ya auro yarinyar daba yarensu dayaba,.

 Tsuka tayi mai sauti Wanda har hamza yajita akunnensa,tsoro ne ya kamashi ganin ko kadan fiskarta babu rahma balle rangwame,.. 

 Asalima maganinta take harhadawa ba tare da ta tofa masa ko da kalma guda bace.


  " Ya Allah"ya fada yana lumshe idanuwansa dan ya San baxai samu sassauci daga wajan ko wani mutumin garin Gumsa ba,shikenan yana gani Haajara sai dai ta Mutu bai nema mata maganiba,,,........  _kuyi Haquri da wanan.,naso yi muku fiye da shi,amma INA gama rubutawa ya goge ban San ya akayi Na rasashiba 😢._"© *😘Um Nass 🏇🏼*

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI 🎊*


 ©by *😘Um Nass 🏇🏼*


_*follow me on whatppad*_® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION*

PAGE 23
  Sosai ya tsorata da maganar Iya Indo,wanan wani irin bahagon hukunci ne take qoqarin yi.,

 Durqusawa yayi akan gwuiwoyinsa, ya hada hannayensa biyu "Iya Indo wanan bai kamata ba Sam amatsayinki Na mahaifiyata,ko a musulunce akwai cutarwa aciki,kuma hakan zunubi ne sosai,. Xai iya kasancewa ya zama tozarci ne akan sunnar da Annabinmu ya koyar damu ita,kada kija hannu Na da kanki ki hankadani fadawa wuta,aranar da bani da bakin da xan kare kaina,bani da uxurin Da xan fadama Ubangijina,. Ke mahaifiyata CE wadda tayi sanadin xuwana duniya,kina da haqqi da iko akaina,haka kuma ta sanadinki ne xan samu rahmar Ubangijina,amma itama Haajara tana da haqqi a amatsayinta ta mata awajena,akwai sharuddai da haqoqi masu yawa Wanda Allah ya wajabta ma ko wani magidanci,kuma qin aikata su kamar taruwar xunuvi ne,.. Dan Allah ki sassauta hukuncinki akaina Iya Indo kada haqqinta yayi mana yawa."


 Baki ta saki tana kallonsa daga ita har gwaggo harira kafin kuma ta rufe bakin,.kamar ba xata CE komi ba,can kuma ta miqe tsaye ta Dora hannunta akansa "Ban San ka fara wa'axi irin haka ba Hamza,da tuni Na Sanar da limami samun wakili aduk lokutan da bai samu Jan sallah ba,."murmushi tayi mai sauti Wanda da ganinsa Na tsantsar mugunta ne. " Shikenan kayi yanda kake son yi Hamza,amma kada ka sake shiga rigimar matarka,ko kuma ka kuskure wajen kareta awajanmu,daga wanan lokacin xata Na iyo ice sanan xata Na mana surfe da niqan hannu Na dutse,har sai ta sarrafa garin,zata Na xuwa rafi diban ruwa sai ta CIKA komi Na gidan nan,koda tsinke nabar kawar da shi agidan nan,.

 Haka kuma idan lokacin Noma yayi itace mai alhakin yin noma amadadinka,."


 Tashin Hankali,qarara a idanuwan hamza,ta ko INA xuffa CE take keto masa,idanuwansa sun kada sunyi jajir,ga kuma bugun xuciyarsa da take qara yawa kamar xata 6allo qirjinsa ta fito, bakinsa ne ya shiga rawa yana son jeranta harrufan da xai fada,amma muryarsa ta dauke gaba daya.,

 Da qyar ya iya bude bakinsa yace "Kiyi Haquri Iya Indo xan haqura da kusantar ta,ki janye mata wanan aikin,yayi yawa agareta,xan haqura da komi ma Inna amma kada Na cutar da ita,ta fiskar daukan laifin da ba NATA bane Dan Allah ki janye wanan sunyi nauyi da yawa."


 "Lokaci ya qure maka Hamza,baka da wani xa6i atsakanin hakan,sanan duk Wanda kaje ka fadama da sunan ya kawo muku dauki,to ban yafe maka ba,.amma kana da wani za6i guda akan hakan,"

 Da sauri ya dago kai alamar son jin ko miye,. "Ka saketa ta koma inda ta fito.,"


  Miqewa tsaye yayi,.daga durqutson da yayi,ya nufi hanyar qofar fita yana dafe da xuciyarsa,Wanda yake jin kamar ana rura garwashi acikinta,.


  "Ya xaka tafi muna magana da kai,.ko ka xa6i Na farkon ne,ta tabbata tana mana bauta.,"


 Bai iya tsayawa ba,balle kuma ya juyo,. _"Wata magana kuma ta rage musu?Ai babu tunda ta riga ta daqusar da rayuwarsa?Toma ta Yaya ne xai taimaki Haajara?aduk cikin abubuwan da aka lissafo masa baya jin akwai masu sauqi acikinsu,haka kuma xuciyarsa ba xata jure rabuwa da itava,xaiyi shuru ne ya xuba musu ido kamar yanda Haajaran ta 6uqata."_


 Haka dai yayi ta saqa da warwara ba tare da ya samu matsaya guda da ya cimma ba,.  ****"""""*****

"Yaya Indo bakyaga wanan aikin yayi mata yawa,kinga fa akwai yarinta akanta,ga rashi sabo,duk da Na tsani yarinyar INA ga hakan kamar akwai cutarwa da yawa,kada ma ace yaya lawan ya samu labari,kin san mun kade."

 Murmushi tayi mai ciwo "Wanan kadai itace hanyar da xanyi Na wanke kaina awajan mutanen garin nan Harira,xasu fahimci baiwa aka kawo min ba suruka ba,. Ke ma kin sani,yanxu babu Wanda ake maganarsu agarin nan kamarmu,haka kuma xamu xama warararru agarin nan ta yanda fitama sai ta gagareni kin sani ai,ba sai na maimaita mikiba.."

 Kai ta gyada "haka ne kuma yaya Indo,lallai kiyi da bara kin fidda mu daga zamantowa mujiyoyi.,Allah ya shige mana gaba,."


 "Ameen Harira,ai yaron nan ya janyo mana abun kunya,har mu mutu baxai barmu ba..


 "Haka ne kam,banda yaya lawan ya tsaya masa da ai hakan baxata ta6a faruwaba,."


 Kwafa tayi ta jijjiga kai,"Zanyi maganinsu ai,.

 Daga nan suka ci gaba da saqa da mugun xare,suna shuka tsiya son ransu,.

 

 Haka a 6angaran Hamza ya kasa sanar da Haajara yanda sukayi da Iya Indo, kawai dai yace mata yaje kiran,amma bai fada mata abin da sukayiba,.ranar dai barci sai 6arawo amma ya dade yana juyi yana nema musu mafita,sai dai har barci ya daukeshi bai samu wata qwaqqwarar huja ba.


   ******"

Washe gari haka Iya Indo ta Sake doko Asubanci ta nufi gidan Hamza,tijarar da tayi ranar daya gabata haka ta sake yinta,ta ma Haajara wanka da ruwan sanyi ta kuma tsomata cikinsa,

 Sanan ta fada mata sharrudan aiyukan da xata farayi Na gidan,kamar yanda ta fadama Hamza,. "To kawai ta iya CE mata,Dan rawar sanyin da take ya isheta.,

 Ba yanda ta iya tana saka kaya tayi sallah,sanan ta nufi gidan Iya Indo,Hamza Na kallonta amma babu damar yin magana,saima hawaye da yaji ya jiqa idonsa,.

 Daga nan ya xauna ya gyara musu nasu gidan,bai ma yi sha'awar fitaba saboda babu Wanda yake marmarin yi masa magana,dan haka babu amfanin ya fitan.,


 A6angaran Haajara tun da taje gidan Iya Indo bata xauna ba aiki ta yi sosai,ta hado mata da kayan wankinsu ita da Baba garba, duk da sanyin da yama jikinta karo haka ta fara wankin tana hawaye tunawa da qarin aiyukan da akace xatayi su,.


 Ranar dai ta bautu Wanda bata ta6a yin irin ta ba ko INA ajikinta qaran ciwo yake,

 Har ta gama musu tuwon dare ta tafi,ko sannu babu balle gdy ataqaicce ko abincin data girka ba'a bata damar cinsaba,.


 Kamar kaxar da qwai ya fashema aciki ta nufi Gida ana kiraye kirayen sallahr magrib,ga yunwar da taci ta cinye jikinta,kamanninta sun nuna tsantsar gajiyar data lullu6eta,.

 Ta ko Ina ta gifta yara da manya ke binta da kallo,kafin yaran su fara mata Ihun mai shanu da sanduna.,

 Tuni suka fara binta suna ilo sai da ta juyo ta kallosu suka ruga da gudu,

 Hawaye ne ya xuba a Idonta yayin da xuciyarta ta CIKA da qunci ,..

 Da qyar ta gane gidan nata,.

 Da sallama ta shiga gidan,.

 "Wa alaikumussalam" Hamza ya amsa ya taho da saurinsa ya riqota,.


 "Sannu Haajara sai yanxu kika gama,.?" Murmushi ta masa ta daga kanta sama,.

 Riqota yayi ya xaunar da ita, da saurinsa ya shiga kitchen ya shaqo mata abinci cikin farantin Silva mai girma,ya hada mata ruwan shayi mai dumi ya kawo mata,..

 Da kansa ya fara bata ruwan shayin ta sha, kana ya miqa mata abincin,Hannu baka hannu qwarya ta fara cin abincin,kallonta kawai yake yanaga yanda take turashi kamar xa'a qwace mata,kallonsa yake yana jin tausayinta Na sosai,.

 Ruwa ya debo ya miqa mata ta sha,abin da ya bashi mamaki ganin ta cinye abincin nan tass,duk da yawansa,.

 "Alhamdulillah" ta fada yayin da take ajiye kofin ruwan,.


 Saa alokacin wata gajiya ta sauqar mata,.

 "Hamza Na gaji sosai,gashi ko INA ajikina ciwo yake min"


 "Sannu kinji Haajara,Na dafa miki ruwan zafi,.bari Na hada miki ruwan wanka." Tashi yayi da saurinsa ya hada mata ruwan wankan,cidak ya dauketa ya kaita bandaki ,"ki gasa jikinki sosai,." Kai ta gyada masa sanan ya fice ya barta,.


 Wankan tayi sosai taji dadin jikin ta,.

 Ta fito ta daura alwala,sanan ta gabatar da sallahar da ake binta,tayi sanan ta gabatar da Issha'i,.

 Ta Dade Rana Addu'a tana hawaye,Dan indai akaci gaba da mata wanan baqar Izayar,xata samu Matsala agaba...

 Kallonta hamza ya xauna yanayi,kafin ya qaraso ya fara bata labari Na ban dariya,mafiya yawa akan kasuwanci da garinsu ne,.ahankali kewar Gida ta fara cikata.,takega kamar alokacin ne abun ke faruwa.***""""""****


Kwanaki Na tafiya lokuta Na ta tsere tsakanin bugawar ko wata daqiqa tafe take da qunci da bara xana arayuwar Haajara,ko yaushe dare yayi fargaba CE cike axuciyarta Na yanda gari xai waye da ita,.


 Acikin kwanakin da suka wuce ta saba da tulun axabar aikin da takeyi,haka kuma ta haqura da ko wata dariya akan fiskarta,kusan duk inda ta wuce binta ake da kallo Wanda yake dauke da tsantsar qyama atare da ita,.


 Babu mai mata magana,kowa gudunta yake,,acikin wanan lokacin kuma taci karo da laulayi mai tsananin xafi......

 *😘Um Nass🏇🏼*

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI 🎊*


 ©by *😘Um Nass 🏇🏼*


 *Follow mee on whatppad @UmNass*


 Page 25


 

 Maganin nuwan NATA ta ci gaba da harhadawa,tana diban wasu tana xubawa acikin jakar fatar dake gabanta,

 Kafin ta miqe tsaye tana dogara sanda, ta nufi hanyar waje,.


 "Tashi muje naga Matar taka.,"

 Ba zata yaji maganar tata hakan yasashi tunanin ko kunnensa ne bai jiye masa dai-dai ba. "Kikace mi ne.?"


  Dan tsaki taja mai sauti kafin ta tur6une fiskarta "Nace ka tashi muje ka rakani Na duba Matar taka,tun farko kai ne ka janyo mata wanan uqubar ai,kasan mutanen Garinku masu riqo da Al'adarsu,amma ka dage ka rakico er mutane,ni nama fi ganin laifin iyayenta da suka dauko ersu suka kawota wanan garin,kamar basu damu da itaba ma,ka tashi ka min jagora Na ganota,kafin su kai ga hallaka musu er."ta qarasa maganar tana dira masa tsayawa,ba shiri ya miqe jiki Na 6ari dan sosai ya tsorata da hargowar Matar,a hakama yana jin maganarta Na ratsashi balle kuma ya kai ga ta dira masa tsawa.   Gaba yayi ya fice agidan, ta biyo bayansa tana janyo qofar gidan,Sanan ta dori bayansa,duk inda ta wuce mutane ne suke duqawa har qasa suna gaidata,yayin da suke mamakin abin da ya fiddota daga gidanta,.

 Sanan suka fara tunanin hadinta da Hamza,.

 Wasu da yawa kuma suka dori abayanta suna take mata lafiya,bata CE komi ba,dan yanxu tana jin takaicin mutanen garin da basu iya rungunar qaddara ba.


  Haka suke tafiya suna ratsa mutanen garin kowa Na kai gasuwa da mamakin fitowar "Yar mai ganye awanan lokacin,.


 Mamakinsu bai qaruba sai da sukaga ta tasamma shiga gidan Hamza,nan jikinsu yayi sanyi wasu kuma suka yo CAA akanta akan kada ta shiga gidan saboda gidan Annoba ne,duk Wanda ya shiga ya hadu da tawayar SA'A.murmushin takaici tayi daga haka bata tanka musu ba,ta kutsa kai cikin gidan.,Hamza Na namata jagoranci har suka shiga dakin da Haajaran take,yanda ya barta akwance haka ya taddata,ko alamun tayi motsi babu.


 Dagata yayi yana faman jeranta mata " Sannu ,sannu Haajara ga mai magani xata dubaki.,"


 Murmushi ta iyayi kafin ta iya magana "Kayya Hamza,nikam nasan ba tashi ma xanyiba,amma INA roqonka da ka daure ka nema min yafiya awajan iyaye Na,nasan hadda hakkinsu ne yake bibiyata ayanxu." Hawaye ne ya xubo mata,shima idon sa cike fall da hawaye "In sha Allah ba xaki Mutu ba Haajara,cuta ba mutuwa bace,xaki tashi da yardar Allah."


 Tausayinsu ne ya qara kama "Yar mai Ganye ta qarasa kusa da Haajara ta tsugunna.,


 " Sannu kinji Yarinya., bari Na duba naga mi yake damunki..."daga nan ta daga hannun nata ta fara juya fiskarta,.


 Sanan ta juyo ta kallo Hamza "ka kawo min ruwa akwano mai tsafta,." Da Sauri ya miqe ya nufi waje bai jimaba ya dawo hannunsa da ruwa acikin kwanon sha,


 Jaakar fatarta ta bude ta debo magani ta xuba acikin kwanan,ya samu mintuna Biyar sanan ta dago maganin,"tasarta xaune sai ta sha maganin"

 Dagata yayi xaune ya karata ajikinsa,ta bata maganin ta sha,.

 Sosai t sha maganin saboda dama qishi ta takeji,gashi bashi da dacin da xai hanata shansa,.


 Ahankali taji jikinta yana saki, kasalar da take ji tana raguwa ajikinta,.

 Wani maganin ta dauko mai dan maiqo,ta miqa ma Hamza "gashi wanan ka shafe mata jikinta da shi.,sanan daga yanxu kada ta qara yin aiki mai wahla,ko kuma abarta ta xauna da yunwa,akwai jaririn ciki ajikinta Wanda xai iya yin wata uku,wahlar da cikin yakesha yasa yake baraxanar fita ajikinta,." Miqewa tayi tsaye tana kallon Hamza fiskarta babu walwala "ko da wasa kada labarin cikin nan ya fita agarin nan,xai fi kyau Ku riqe bakinku,sanan xan gargadi mahaifiyarka da sassauta mata dan idan wani Abu ya samu cikin nan lallai xa'a samu matsala anan gaba."

 Sanan ta kai kallonta ga Haajaran ta shafa mata kanta "Ban san mi ya rudeki ba kika yarda kika shigo garin nan da zaman aure,amma komi zai faru ya Riga ya faru,ki dauka rabon cikin nan ne ya qaddara miki shigowa cikin nan,INA fatan nan gaba ki samu sauqin matsalolinki.,duk lokacin da kike buqatar wani taimako kije gareni kai tsaye,xan taimaka miki gwargwadon iyawata."


  Hannu biyu hamza ya hada yana "Mun gode sosai,har ban san da bakin da zan miki godiya ba,karo Na farko mun samu Wanda ya nuna tausaya warsa akanmu,ya nuna damuwarsa acikin matsalarmu,Allah ya saka da alkhairi."


 Kai Haajara ta gyada tana fadada murmushinsa,cikin raunanniyar muryarta itama tayi godiya "Na gode sosai,Daga yanxu xan daukeki a matsayin Uwa agareni,Na gode."


 Kayanta ta fara tattarawa,tana murmushi itama "Na gode da matsayin Uwa da kika bani,daga yanxu xan kula da lamarinki acikin garin nan tamkar er da Na haifa aciikina."


 "Nawa ne Adadin kudin da xamu biya.?"Hamza ya tambayeta yana sunkuyar da kai,Harara ta wurga masa kafin ta fara magana.,


 "Kana tunanin kudinka xai biya soyayyar uwa akan erta,ni kawai naxo ne dan Na taimaketa,yanxu kuma da ta daukeni amatsayin Uwa,xan tsaya mata Aduk kanin lammuranta,ciki harda yaqar mutanen garin nan."


 Tana fadar haka ta sa kai ta fice ba tare da ta jira cewarsu ba.,


 Da ido suka bita suna girmama ikon Allah,dan shi kadai ne xai kawo musu wanan sassaucin da Samar musu da sanadi ta hanyar shigowar "Yar mai Ganye cikin rayuwarsu.,


 Ayanda mutanen garin suke girmamata ko mai Gari baya samun wanan Girmamawar.


 Da sauri Hamza ya fito waje dan mata rakiya,sai dai yana FIta yaga mutane dan kam aqofar gidan,.,sun kewaye " Yar mai Ganye suna ta tambayarta mi ya kawota gidan Hamza,bayan ko kayan bata ta6a shiga gidan ko wani mutum Agarin ba.,


 Dai-dai lokacin da Iya Indo ta qaraso Ita da Harira cikin rikicewa kin labarin "Yar mai ganye agidan Hamza.,

 Ganin mutane jingim ya qara tabbatar musu da gaskiyar maganar,ga kuma " Yar Mai Ganye mutane kewaye da ita.,


 Numfashi ta jaa mai qarfi sanan ta fara magana "Ya Ku mutanen wanan Garin Na Gumsa,haqiqa tashin hankali Na baraxanar tun karo mu,ta yanda kuke takurawa wanan Matar Hauren,hakan ya sa daya daga cikin Rauhanain da ke hidimta min yace,Idan har banzo Na ga yarinyar Na rarrasheta ba,amadadin En gari komi xai Iya faruwa,qarshe Annoba CE xata sauqa awanan garin namu,Wanda shi kansa bai san wata Annoba bace,.dan haka Kashedina agareku,lallai Ku fita alamarin wanan yarinyar,Ku sakar mata Mara tayi fitsari,dan ko kallon banza mutum ya mata LA shakka zai samu tawaya acikin rayuwarsa." Tana gama Fadar haka ta buga sandarta sau uku.,


Anan kuma mutanen garin suka kaure da ihu,wasu jikinsu ya dauki rawa,saboda tashin hankali da tsoro.,


 A 6angaran Iya Indo kuma tuni fitsari ya 6alle mata,.jikinta ya shiga karkarwa hawaye sha6e-sha6e akan fiskarta.,


 "Na shiga Uku ni Indo,wanan masifa da mi xan kwatanta ta,Allah ka 6oyi kurwata,daga wanan ranar Na fita a shirgin gidan Hamza,." Gaba daya kowa ka gani awajan arude yake,Murmushin Nasara "Yar mai Ganye tayi sanan ta kutsa tsakanin mutanen tayi tafiyarta abinta,.


 Nan kuma tsoro ya sake kamasu,kowa ya koma yana shafo Hamza yana dariyar yaqe,.

 Shi abin mamaki ya bashi da dariya Lallai gaskiyar Hausawa da suke cewa maganin biri karan maguzawa......

 _"Lolx tofa ga mutanen Gumsa da yanda al'amura suka xo musu,da alama xasu Qi cin Biri ne su ci Dila,,.Sai dai babu tabbacin xasu iya dorewa, aqidar mutum bata iya barinsa,mu dai je xuwa dan taqi Kadan ya rage ta tsallake rijiya da baya."_
© *😘Um Nass 🏇🏼*

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI 🎊*


 ©by *😘Um Nass 🏇🏼*


 *follow me on whatppad @UmNass*® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION*
  _*this page for u MUWASKATU KHAN 😝😛Happy birthday 🍼Wish U many many 1 million years 😀loz Allah ya albarkaci rayuwa,ya rabaki da kwalliyar iffiritai.,duk da naga kin Dan qara wayo yanxu,.wink🤪"*_
 PAGE 26 Gaba daya garin ya kaure da maganar da "Yar mai ganye ta fada,Wanda yawanci mutanen tsoro ne da tashin hankali ya ke baraxana arayuwarsu,.wasu kuma da yawa suna Allah wadai da wanan Matar da ma Hamza Wanda yayi sanadiyar kawo musu Ita,.


 Take ko INA ka bi labarin da ake kenan ba ababba ba ba a yaroba.,


 Jiki babu qwari Iya Indo taja Harira suka bar wajan,. Basu zame ko inaba sai gidan Iya Indo.


 Tagumi suka rafka babu mai magana acikinsu,idan aka dauke Iya Indo da ta xagaya bandaki sau uku tana zawo.

 Fitowa tayi akaro na hudu daga bandakin,xaninta ahannunta,yana qoqarin faduwa.,


 Da qyar ta kawo kan tabarma ta kwanta,tana maida numfashi.,"Sannu Yaya Indo." Gwaggo Harira ta fada tana nuna tausayawarta akan fiskarta,.yayin da dariya ke cinta ganin yanda Iya Indo tayi la'asar kamar wanda ta tashi daga jinyar shekara.

 Kai Iya Indo ta daga mata tana numfarfashi,kafin ta fara magana "Ban San ta INA xan fara gyara kura-kurena ba Harira,.Aradun Allah tsoro ya gama ratsa Duk kanin wata ga6a ta jikina,cikin bugawar da xuciyata take tafe take da faduwar gaba,tun jawabin da " Yar mai ganye ta fada,kin San duk abin da ta fada gaskiya ne,.saboda kusancin ta da Aljannu da iffiritai,sanan qarin tsoro Na kada tsautsayi yabi ta kaina,saboda ni ce kan gaba atakurama yarinyar nan,."

 Numfashi ta jaa ta tashi xaune jin cikinta Na qoqarin hautsinewa,."Inaga tun yanxu nawa ajalin ya sauqa ya kamata mu je akan lokaci mu bata haquri,wata qila Na samu sassauci daga zawayin da ya tasam mini.,"


 Miqewa tayi da sauri ta xari buta ta sake shiga bandakin.,


 Sosai dariya ya kama Harira duk da itama maganar iya Indo ya qara rudar mata da ciki,musamman da ya kasance tana daya daga cikin masu bada gudun mawar cin zarafin Haajara,.


  Fitowar Iyaa Indo yasa ta miqewa jikinta Na rawa "Yaya Indo maza saka mayafinki mu tafi gidan Hamxa,Dan mu bama matarsa haquri Aradu nima na fara jin tsoro da kaduwa,.Na rashin sanin Annobar da zata sauqo mana."


  Mayafinta ta janyo ta nufi hanyar waje,anan sukayi kici6us da Baba Garba yana Sauri shima jin labarin abun da "Yar mai ganye ta fada akan Matar Hamza.,.


   " Oh oh INA kuma xaku je haka kamar korarru,furu-furu da Ku." Yanaa maganar yana duba yanayinsu sai zare ido suke da hura hanci,kamar masu shirin tseren gudu.


  "Zamu je gidan Hamxa ne,mu duba matarsa dazu yazo ya sanar damu bata da lafiya."harira ta rattabo bayani tana ci gaba da sauri wajan maganar,.Kallonsu yayi Na wucin gadi sanan ya dai-daita tsayuwarsa " Baku ji mi ake fada agariba?abin da "Yar Mai Ganye ta CE akanta,karku sake Ku qara mata wata mugunta ko xutarwa,Dan naji rade-rade agari cewar mutum xai iya xama Biri ko 6era,,Dan qin fada " Yar mai Ganyen tayi,tasan Annobar xa ta samu mutum."


 Quuuuuu..luuuuu..luuuu cikin Iya Indo da Harira ya bada sauti,.kafin su fara tseren shiga bandaki atare,sai dai tuni Harira ta Riga Iya Indo kaiwa bandakin,hakan yasa iya Indo kasa riqewa ta saki NATA atsayen da take,.

 Tuni wajan ya gume da doyi Na tashin Hankali,qudaje suka iyo kanta,.


  "Assha Assha Indo da girmanki kika saki kashi atsaye." Baba Garba ya fada yana toshe hancinsa.,


 Idonta fall hawaye ta fara magana,bakinta Na rawa "Kai ma kasan zawayi baya ruquwa Garba,musamman a irin wanan lokacin Na qarawa mai tsoro fargaba."


 Kai ya kada ya fita "To ai shikenan idan ta fito sai kuyi hanzari ki gyara jikinki,INA jiranku a waje muje tare dubiyar."


 Sunkuyar da kai tayi tana duba jikinta wanan tozarci da mi yayi kama.,.


 Ahaka Gwaggo haarira ta fito ta sameta,qudaje Na faman binta,.


 "Wayyo Yaya Indo kece da kashi haka ajiki." Sosai dariya ta kamata duk yanda taso gimtseta ta gagareta,.

 Dole sai da ta fito,Harara Iya Indo ta banka mata sanan ta shiga bandakin ta wanke jikinta da omo kana ta wanke kayan,duk da yanda ko INA ajikinta yake mata ciwo.,


 "Harira dauko min kayana adaki dolena nayi wanka Na wanke kayan nan.,ki kuma wanke wajen da Na tsaya kafin Na fito"

 "To"ta fada tana gimtse dariyarta,kaya ta dauko ta miqa mata ta sama,kasancewar Bandakin marar rufi ne.,


 " Yauwa sai muyi sauri mu tafi,Dan Garba yana jiranmu da shi xamuyi wanan tafiya dubiyar." 

 Bata jira maganar Harira ba ta qarasa shanya kayan nata,tayi gaba.


 Aqofar gida suka iske Baba Garba yana kaiwa da kawowa.,

 "Muje garba mun fito,sai famar dawurwuri make,." iya Indo tana kallonsa tana muxurai.,..


  "Mrss ba doleba,kun takurama yarinyar mutane,haka kawai kuna son masifa ta sauqo mana agari."


  "Amma ai ba ka hanaba,hasalima kana da naka tagomashin akan quntata Matan da mukayi,wanan abun kai da kai,.ai kowa mai laifi ne acikinmu.." 


 "Ya Isah haka,muje gidan dai."


 Daga nan ta janyo qofar suka tafi,babu mai yiwa wani magana acikinsu,kowa da qunshin damuwarsa.,


 Mamaki ne ya kamasu ganin mutanen garin wasu Na shiga wasu Na FIta,sai dai idan sukayi la'akari da yanda "Yar mai Ganye tayi magana hakan ya isa ya tabbatar musu Abu guda ne ya kawosu,shine Neman sulhu da kwanciyar hankali.,.


  Sallama Iya Indo ta shiga kwad'awa tun qarfinta,kafin mabiyanta suyi tasu suna.,

 Faduwar gaba CE ta dirarma Haajara jin sallamar Iya Indo,bata San da wacce ta xoba,.


 Dan abin Na daure mata Kai Ganin mutanen garin NATA sintiri xuwa dubata,gashi Hamza bai dawo ya qara mata haske akan hakanba,.

 Dan maqotanta biyu su har shara da wanke-wanke suka mata,suka kuma kai mataa ruwan wanka,da taimakonsu ta kintsa jikinta,har ta xauna a qarqashin bishiyar dake tsakar gidan,.


 " Wa alaikumussalam "Ta amsa musu muryarta asanyaye,.

 Da sauri Iya Indo ta qarasa kusa da ita " Sannu, sannu kinji Haajara,tun dazu da yaron nan Hamza ya fada min rashin lafiyarki,hankalina ya Gaza kwanciya,fatana Nazo Na dubaki,sai kuma babansa yace mu jira mu taho tare,.mi ke damunki haka kika xabge jinyar rana daya,ai daga yanxu babu mai qara takura miki agarin nan,dama can ba da San raina kike wahala ba,amma lamari idan ya hadu da En xuga babu yanda xanyi,waifa ahaka duk cikin qoqarin gwadaki muke,muga kamin ludayinki,.kai banxar shawara ma ba tayiba."


 Ta fada tana qyafta ido,.yayin da Baba Garba da Harira sukayi sunqum suna jin Iya Indo,bama da Haajara da ta xama kamar sassaqen gunki tana jin surutun Na surukar ta da take yi babu tsayawa....


   _🤣🤣 tofa wanan gaskiya ne ko rudewa ?Har yanxu Iya Indo bata wanke kantabafa,.ban San mi xakuce awanan chapter ba,Amma dai INA fatan kunyi nishadi kunyi dariya,Ku sanqama comments naku,Dan Na tabbatar da hakan..._

© *😘Um Nass 🏇🏼*

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI*


*😘Um Nass 🏇*


_*Follow mee on whatppad @UmNass*_


® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION*


 PAGE 27


Nan kuma tasha jinin jikinta jin babu Wanda ya qara tanka mata,.can ta lura da sakin Layin da ta so yi ."Ya dai kikayi shuru,ko har magana ma bakya iyayi,bayan ga6an jikinki naji ance bakya iya dagawa,"

Kai ta girgixa ahankali ta fara magana "A'a Iya Indo da sauqi sosai,"

 Baki ta Dan ta6e kafin ta wurga mata harar gefen ido,takaici ne ya qara kamata akan wanan abar yau ta yini tana xawo,harda yi a tsaye,.

 "Mtsssss" ta buga uban tsakin da ba tasan ya fitoba,saurin buge bakin nata tayi Wanda har ta fidda jini,"Washhh Allah Nah"ta fada jin bakinta ya kaure da radadi.,

Kallonta Haajara tayi cikin tausayawa,da kuma tsoron yanayin da taga surukar tata kamar Wanda hauka ya fara kamawa,da fari ta fara da 6arin surutu,bayan nan tayi shuru,ita kadai tayi tsaki ta kuma hukunta bakin nata ta hanayar kai masa duka.


 Kallon Baba Garba tayi cikin fargaba ta gaidashi,da saurinsa ya Amsa "lafiya qalau,lafiya lau Yarinya,ya sauqin jikin naki kuma,."


  "ALHMDLH da sauqi sosai Baba."

 "Sannu Haajara Allah ya baki lafiya,naga ai jikin naki yayi sauqi,ayanda Hamxa ya ke fada bamuyi tsammanin xamu ganki hakaba." Gwaggo Harira ta fada tana qoqarin danne dariyar Iya Indo Wanda ta riqe bakinta GAM.,


 Kallonsu take daya bayan daya,Wanda ta kasa fahimtar mi suke son mata,amma ta tabbata aduka garin nan bata da maqiyan da ya wuce su,.


 "Eh naji sauqi bayan Na sha magani.,"

 Sosai take qoqarin danne duk wani haushinsu da yake taso mata,awani sashin kuma fargabar abin da xasu mata takeyi,sanin basu da daukan lammuranta da sauqi ta fiskar tausayawa atare da ita...


 "Muna baki haquri akan duk abin da muka miki atsakanin xuwanki,har xuwa yau,kin sani mun sani babu wani farin ciki da xamu kira muce mun baki shi,amma dai kiyi haquri sharrin shedan ne da kuma rudun xuciya,daga wanan ranar akasin hakan baxai qara faruwaba." Baba garba ne yaDAke magana muryarsa da dattako kamar ba tsohon da sa qafa ya haure ko wata girmamawarsa ba,. Ya kuma bada tagomashin quntata ma rayuwarta,atsakan kanin watannin da suka shude,Wanda tabonsu ya gagara goguwa akan xcyrta akuma idanuwanta,asalima cikin ko wata daqiqa fefen rayuwarta kan dawo mata,.musamman rashin sanin yanda iyayenta suke da En uwanta,.

Tsawon watanni shiddan da tayi su,babu wani daga cikin danginta da ya kawo mata xiyara,haka babu Aiken gaisuwa daya gifta atsakaninsu,.duk saboda tsoron abin da xai je ya dawo.,


  Farin ciki ya kamata tayi adai-dai wanan lokacin ko kuma kuka,.Amma idan ba butulciba ya kamata tayi godiya ga Allah da ya tsamota daga tulun wahalhalun rayuwa,ya daukaka darajarta akan mutanen da suke daqusar da rayuwarta,yau gasu agabanta suna Neman yafiyarta.


 Hawayen daya jiqa fiskarta ta share tana fadada murmushinta "Ni baku yi min komiba Baba,a iya tsawon xamana da Ku,Na dauki hakan amatsayin koyarwa Na Darrusan rayuwa,Wanda ban ta6a yinsuba,.ahakan Ku qara min ilimi Na rayuwa,wanda ko wasu iyaye suke bama yaransu,dai-dai fahimtar yanda suke ga yaron xai dauka,.Dan haka babu komi Na gode da kulawarku..."


Jijjiga kai yayi,shi bai San mi ya rudeshi ya biyema shawarar mata ba,ya kuma bi xuciyarsa wajan assasa tsanar Yarinyar nan,xai iya cewa hakan sakarci ne,musamman idan yaga nutsuwar da ke shimfide atare da yarinyar.


  "Mun gode Yarinya,Allah ya miki albarka."

Ya miqe tsaye yana kallon Iya Indo data riqe bakinta GAM,saboda jinin da ya fidda,haka kuma ya kumbura suntun kaamar da tayi karo da dutse., "to ni xan koma gida,idan kun gama mu tafi,ko kuma nayi gaba abina.?" Ya fada yana raba kallonsa tsakanin Harira da Iya Indo..,


 "Mun gama muma,." Sanan ta shafa kan Haajara "ki qara haquri damu,Na San xuciyarki har yanxu bata samu nutsuwa da ganinmuba,amma da gasken gaske muke neman yafiyarki,awanan ga6ar komi xai iya faruwa da mu,mudum baki yafe manaba."


 Kanta taji ya qara kullewa,ya kuma mata gimm, dagowa tayi tana kallon Iya Indo Wanda har yanxu bakinta yana rufe da hannunta,sai faman wurwurga ido take,can ta saki hannun nata daga rifewar da tayima bakinta da shi,sosai ta tsorata ganin yanda bakinta ya hau kai kace Na sheda ne,.lolz "Har yanxu ban fahimci akan mi kike magana ba,."


 Hannunta ta riqe GAM hawaye Na xuba a idonta,Dan gani take wanan tsautsayin da take takawa ayau,duk yana daga cikin sharar fagen afkawar Annoba kanta.,"Bazan iya kwatanta miki yanda nake jiba,amma INA roqonki,da kice kin yafe mana."


  Duk da ba shaquwa da soyayya atsakaninsu da ita,amma tana mata kallon kima da matsayi,amatsayinta Na uwar da ta kawo mijinta duniya,Wanda yake kasa farin cikinsa ya bata,."Na yafe muku duniya da lahira Allah ya yafemu tare."


 "Ameen mun gode Allah ya baki lafiya., Harira mu shiri ko.?"

 Harira da dariyar yanda Iya Indo ta rude da kuma yanda bakinta ya qara tsini ta cikata,har sai da ta duqa,hakan ya qara baqanta ran iya Indo, ita kadai tasan Axabar da takeji ayau,.fatanta daya kada tayi mutuwar wani.


Kai ta kada tayi gaba,bata qara bi ta kan Harira ba tayi gaba abinta,.


 Da sauri itama ta bi bayanta tana dariya "Ku jirani mana Yaya Indo,." Ko kulata batayiba ta ci gaba da tafiya,garin gudu da dariyar bata luraba taci karo da qaton dutse farcen qafarta ya fice,ta kuma wuntsula taci ta kaa,ta fadi rijib,Wata azaba ta dirar mata tun daga tsakiyar kanta har xuwa Dan yatsan qafarta,wani razanannan Qara ta saki ba tare data shiryaba "Wayyo Na Mutu Na lalace,.wayyo qafata da kaina,da kwankwasona.,"ihu take tun qarfinta Wanda hakan yaja hankalin mutanen wajan,,da sauri iya Indo da baba garba suka dawo,,.


Dagata yayi yana duba farcenta da ke faman reto, " Assha,garin Yaya haka Harira,wanan ciwon ya girmama gaskiya,."

 Kai take kadawa tana hawaye Dan ta ko INA axabace ke ratsata.,"karo nayi da wani Abu,aradu kamar giftawar ajali haka ya kwatsani aqasa."


 Kai Baba Garba ya girgixa cike da takaicin Hariran "Ajalin ne xai giftaki ki iya magana haka,nifa ban son shashancin banxa kin sani ai,tashi mu tafi Gida lokaci nata tafiya,nabar abubuwan yi masu muhimmanci,shegen yawonki da shiga Sharo va shanu duk shi ya janyo miki haka,gobe ma sai kiyi gigin qarawa ai.,kin bar gidanki kina yawon Neman magana." Fada yake kamar xai ari baki haushinsa yake son hucewa akanta,.


Iya Indo mi xatayi in ba dariyaba,duk da bakinta Na ciwo hakan bai hanata fanshe dariyar muguntar da Harira ta mataba,.


"Dadina da gobe saurin xuwa, kamar ba yanxu kika gama min dariyaba,ashe nawa mai sauqi ne."

Kai Harira ta sunkuyar tana faman cije baki,ga ciwo ga takaicin fadan da Yaya Garba ya kwarxanta mata acikin mutane,harda su gori,tashi tayi da qyar qasusuwan jikinta Na faman qara,haka ta fara digisa qafa,bata qara CE musu ci kanku ba, har ta shige su.,


Kai tsaye gidan "Yar mai Ganye taje ta kar6i magani,sanan ta wuce gidanta,bakinta qunshe da buruka da alwashi Na tabar xuwa gidan Iya Indo har gaba da Abadan,,Amma kuma idan tayo tsumm sai taga wanan duk mai sauqi ne akan ace sun xama birrai ko 6eraye,tana kallon farcenta da ya xama fata ga ciwon kai mai xafi,tuni hawaye ya shiga xuba a idonta,Dan ba qara haihuwa da rani.....


 **""""""******""


 Lokacin da Hamxa ya dawo Gida yaji dadin ganin jikin Haajara ya warke,anan take sheda masa sauyin da aka samu,Na xuwan En garin dubata,harma da xuwan su Iya Indo da abin da ya wakana,.murmushi yayi mai sauti har haqoransa Na fitowa waje...


  "Haqiqa babu abin da ya gagari Allah,haka shike sauya xuka tan bayinsa,ki dauki hakan amatsayin wata rahma da iko Na Ubangiji Wanda yake kawoma bayinsa sauqi da sauqi acikin rayuwarsu,.ni kaina banyi tsammanin hakan xata faru cikin sauqiba,....Anan ya kwashe dukkanin abun da ya faru tun xuwansa gidan " Yar mai Ganye har barinta gidan,da kuma abin da ta shedawa mutanen garin...."


Dariya take har tana riqe cike jin labarin shirin da "Yar mai ganye tayi cikin sauqi ta samu na sara " Lallai babu abin da ya Gagari Allah,sanan ya kawo "Yar mai ganye cikin rayuta Dan ya kawo min sauqi daga axabar bayinsa.,hakan ya qara tabbatar min da qarfin da Addu'a da tasirinta take da ita., na godema Allah,Na kuma gode maka Hamxa,haqiqa ban San ya xan kwatanta farin cikin da naji ayauba,inaga tun kafin haduwarmu da kai,tun lokacin da hankalina ya gama CIKA.,Ina fatan hakan ya dore min har qarshen rayuwata..."


Murmushi yayi yana jijjiga kai yana jin Annashuwa da farin ciki atare da shi,ganin Haajara cikin irin yanayin da yake fatan ganinta.,


 "Ban San mi gobe xata bamuba Haajara,Amma INA fatan hakan ya dore har gaba da Abadan,sai dai idan igiyar rayuwa ta juya miki wani gefen kiyi qoqari ki tuna da Allah,ki kuma roqeshi sassauci,tabbas xai jiki xai kuma amsa miki,kada jarrabawar rayuwa nan gaba tasa ki butulcema ni'imomin da Allah ya baki."


 Hawaye ne ya fara xuba akan kuncinta,Dan kalaman Hamzan suna tunatar da ita mahaifinta Baffa malam,Wanda yawanci nasiharsa akanta kamar wanan ne,ko yaushe xata qara ganin iyayenta,da En uwanta,,...


  "Duk lokacin da kika so kika samu sauqi,da kaina xaj kaiki gaban su Baffa malam." Yana murmushi yana tabbatar masa da maganarsa,bakinta ta rufe Dan batayi tsammanin maganar xuciya CE ta fito filli ba....


 Daga nan ya ci gaba da qarfafa mata xuciya da gwuiwa akan rayuwa da kuma abubuwan da take zuwa da su..


  "********"**


  Ahankali rayuwa ta sauyama Haajara ta samu sauyi na farin ciki,kowa yana haba-haba da gaidata,girmamata suke kamar xasu goyata.,

 Haka kowa kaffa kaffa yake da 6ata mata,sosai shaquwarta da 'Yar mai ganye tayi qarfi ta yanda komi nata bata 6oye mata,haka nan ta mayar da ita kamar mahaifiyartq.,


Itama kuma ta dauketa amatsayi diyar data haifa da cikinta,hakan ya qara mata kima da daraja a idanuwan mutanen Gumsa,..

 Sanan adan tsakakanin ta warke sarai sai dai kyau da tayi ta murje,na jin dadi da kuma xaunar ciki ajikinta,awanan lokacin Hamza ya dauketa ya kaita ganin Gida,..

 Iyayenta sunji dadin ganinta ahaka,hankalinsu ya samu nutsuwa sosai,ganin bata da damuwa,haka ta xagaya gidan En uwanta suma sun qara samun Imani axukatansu,Dan basuyi tsammanin zasuga Haajara cikin wanan kyakkyawar kamarba,musamman sanin ko suwaye take rayuwa dasu,.haka itama bata bude cikinta ta fada musu tarin wahalhalun da ta riskaba har xuwa yau,tabar hakan a matsayin sirrinta, tsakaninta da mijinta da kuka Allahnta,Wanda shi ya kareta da abin Dake tare da ita..


  Haka ta dawo Gida da kewar iyayenta da En uwanta,hawaye fall fuskarta musamman tunawa da tayi babu ranar sake haduwarsu,Dan su sheda mata ba xasu samu damar xiyartarta duba da tsananin da ke tare da garirruwan nasu,.


 Ahaka suka dawo da sha tara ta Arxiqi,nan ta rarraba ta kai gidan iya Indo da gidan baba lawan,,haka ta jidarma "Yar.mai ganye nata kason,maqotanta ma ta aika musu da gwaggo Harira,.


   


 **"""""**


 Watan Haihuwar Haajara ya kama Wanda mafiya yawan En garin suna buri akan cikin Wanda kowa idonsa akansa,fatansu suga abin da xa'a Haifa Dan su sheda tsautsayin da aka kawo musu garin,..


Naquda CE ta kama Haajara tuburan Wanda da gudu Hamza yaje Gidan Iya mai ganye ya kirata,.

Itama cikin rudewa ta taho,cikin ikon Allah ba'a dauki lokaciba Haajara ta sankato danta kyakkyawa mai kama da ita,sai dai yanayin kalar fatarsa da tayi shige data babansa,hakan yasa ya samu kala mai sirki mai wuyar samu shi ba fariba ba kuma baqiba.,,


  Guda iya mai ganye tayi sau uku ta kintsa Haajara,da kanta tama jaririn da Haajaran wankq,Dan dama tasa Hamxa ya Dora ruwan wanka.,


Da murnarsa ya kar6i yaron da iya Mai ganye ta miqa masa,bakinsa kamar gonar Auduga,ya shiga wageshi,.

Kafin wani lokaci Gida ya CIKA jangam da mutane saboda kowa burinsa ya ga abin da aka Haifa,Wanda ya janyo aka kawo musu jamgwama.,,


 Su Iya Indo anyi kane-kane da da ahannu Wanda ta hana mutane daukansa,Dan yanxu tace mutane munafukai ne,sai kuma Goggo Harira da suka shiryota,Wanda sai da Iya Indo taje biko sanan suka shirya...,,...


Washegari Hamxa ya je ya sanar da iyayen Hajara haihuwar da tayi,nanfa suma suka shiga murna,En uwanta suka fara shirin xuwa suna,Dan wanan karon Baffa malam yace shima xaije Dan haka Inna tq shirya suje tare,yana son yima jikansa Addu'a.....


  Akuma lokacin ne igiyar qaddara ta sake juyawa daga dariya ta koma alhini,sai dai kowani mutum baya sanin mi xai faru dashi da wasu da yawa sun sauya qaddararsu tun kafin aukuwarta......   _washhhhh ban San ko wanan chapter ta muku dadiba,amma dai nayi qoqarin cikata gaba daya sai dai gajiya da qawa xuci ya hanani iddasa labarin da ya kamata ya CIKA ayanxu...©Um Nass

 

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI 🎊* ©by *😘Um Nass 🏇🏼*


 *_FOLLOW ME ON WHATPPAD @UmNass_*® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION*
 PAGE 27  Shiri sosai ake ta ko wani 6an gare,Iya Mai Ganye tayi ruwa tayi tsaki akan wankan jegon Haajara da jaririnta,.haka duk wata cima da xata kawo mata kuzari ga lafiyarta itake dafawa,tana qara tsumasu da maganinnuwan da xai basu lafiya,.


Har zuwa lokacin mutanen Gumsa na mamakin yanda alaqar Haajara da "Yar mai ganye ta dore,amma da yawa suna danganta hakan da cewa Umarnin da iffiritan Aljannu suka bata ne,na kyautatana Haajaran saboda gudun afkuwar Annoba acikin garin.


 Ranar da suka CIKA kwana Uku da Haihuwa suna zaune Ita da Hamxa da Dan jaririnsu,alokacin Iya mai ganye ta tafi gida,kallon jaririn take tana kallon Hamxa da yayi musu quri da Ido,Murmushi tayi ta miqa masa jaririn,ya kar6a hannunsa yana rawa har yanxu bai qwarai da daukan Jaririnba " Har yanxu banji ka masa kuduba ba,banji sunan da ka rada masaba."

 Kallonta yake yana murmushi "Ai naga Sai ranar suna ake radin sunan,kuma duka yau kwana uku kenan da haihuwarsa."


  Kai ta girgiza tana murmushi "wanan al'adace kawai Hamxa amma a qa'idar musulunci ranar da aka Haifi yaro ake fara masa kiran sallah da kuma kudubar sunansa,Ana son kunnen yaro ya fara jin Girman Ubangijinsa da kuma Addininsa,wanan shine Abu mafi muhimmanci sauran duk Bidi'a CE."


 Kai ya girgixa yana gaskata maganarta,sanan ya miqo mata yaron "ki masa kudiba da sunan da kike son ya amsa,Wanda ya miki dadi axuciyarki." Mamaki ne ya kamata,tana kallonsa baki bude "Ban ganeba Hamxa."


 "Wanan alqawali ne Dana dauka,duk lokacin da muka haihu ke xaki za6arma yaranmu suna,.Idan ban manta ba kin sha sanar dani suna linzami ne yakanbi mai shi,Wanan maganr hausawa CE amma idan na koma baya da Hadisin da kikq sanar dani,Wanda Annabi s.a.w ya hanemu da sanyama yaranmu sunaye marasa amfani,domin shi suna yana xama ajikin mutum yabi halayyarsa,kamar yanda ya sauyama wani sahabinsa suna daga zafi ya koma sauqi..,"Dan haka na baki dama ki za6a ma yaranmu suna,ki masa kud'uba da kanki."


  Kai ta girgixa tana murmushi,sanan ta kar6i yaron,ta masa kiran sallah akunne sanan ta masa kudubar sunansa..

 Miqa masa shi tayi tana murmushi "ABDALLAH"

 Ido ya lumshe yana budeshi cikin sigar farin ciki.,"Sunan da kika sanya masa kenan.?"


Kai ta daga tana yalwata murmushinta "Bawan Allah kenan,ina fatan ya kasance Bawan Allah ya amsa sunansa na Abdallah.,ya xama mai juriya da haquri." Tana maganar cikin tsoro Wanda ya ziyarci xuciyarta,bata San dalilin da ya sanya hakanba.


 "Ameen ya Allah" sanan ya kar6i yaron yana masa wasa duk da baya fahimtar mi yake CE masa,asalima idonsa arufe yake.,


  "INA SON ABDALLAH,har cikin xuciyata,kyautar da Allah ya bani,ina fatan xaki kula da tarbiyarsa da karatunsa,bana son yayi rayuwar jahilci kwatankwacin ta mutanen garin nan,.kimin alqawalin xaki jure ko wani matsatsi da quncin rayuwa,atare da shi,har xuwa lokacin da hankalinsa ya kai daukan jigilar kansa,koda bana a Raye ki barshi ya rayu da mutanen garinsa,ko wani juyi na qaddara ya rikida ki barshi ya koyi dauriya da jure ko wani qalubale daga mutanensa,ko bayan Raina ki min wannan alfarmar."

 

 Kalamansa sun sanya rauni da faduwar gaban da ke tare da Haajara hakan ya sata fara hawaye,awanan rayuwar da duniyar da suke ciki mi xaisa Hamza yin wanan maganar,kasa jurewa tayi ta fara hawaye "Ban San ya xan koyi rayuwaba muddum akace babu kai acikinta,.ka daina Dan ganta yiyuwa rayuwata muddum akace babu kai acikinta,baxan iya maka wanan alqawalinba Hamxa Dan nasan taku Kadan xan biyo bayanka."awanan ga6ar sosai take kuka harda Jan xuciya,shima xuciyarsa ta karye amma haka nan ya tsinci kansa da faduwar gaba,yana ji kamar wani Abun xai yi ya faruwa da she.


 Shafa kanta yayi yana qoqarin maida hawayen da ke baraxanar xubowa daga idonsa." Ba ko wani Abu bane muke so muke buri akansa ya CIKA ba.,haka acikin ko wani rai da motsinsa tafiya yake da ajali,bamu da masaniyar wa xai Riga wani tsakaninmu,ki daina cewa ba xaki iya rayuwa babu niba,kin sani Allah shi ke tsarawa ko wani bawa rayuwarsa,haka kuma yarda da qaddara mai kyau ko marar kyau yana daga cikin shika-shikan musulunci,haka kuma Imani ne.,Hamza ne kadai xai tafi amma mahaliccin kowa da komai yana nan,dama bani nake baki ko wata kariyaba,shine ya qaddara hakan..,karki xama mai butulcewa rahmar Allah...."


 Ko wani saqo da qofa na jikinta yana kar6an saqon da Hamxa yake qoqarin isarwa ajikinta,haka ta gamsu da gaskiyar daya shimfida asaitin maganarsa "Astagfurillaha wa Atubu ilaihi" Kalmar da ta Shiga maimaitawa kenan,.


  Kafin ta Dora da "In sha Allah,zan jure koma miye,amma kabar wanan maganar awanan ga6ar baxan iya jurewaba ko Kadan.."


 Kai ya girgixa yaci gaba da yima Abdallah wasa "Su Baffa malam fa suna hanyar xuwa,nan da kwanaki hudu."


 "Da gaske?" Cikin zaquwa da farin cikin da ya CIKA xuciyarta,Dan Sam batayi tsammanin Baffa malam xai iya xuwaba,.

 "Ya sheda min hakan da bakinsa,muddum Allah ya bashi rai da lafiya xuwa lokacin,xai xo yayima jikansa Addu'a." "Ya Allah ka tabbatar da wanan lokacin.,xanga Innah ta da su Adda Sa'adah.,Ya Allah dadin xai kai da yawa." tana murmushi take fadar haka, shima murmushi yake yana jin dadin yanayin daya ganta aciki na farin ciki.**"""""***

RANAR SUNA.,


  

  ABIN mamaki kusan Rabin mutanen garin ke Shiga da fice tsakanin gidan Hamza da gidajensu,wasu da yawa kuma suna mamaki jin sunan da aka sanyama yaron Abdallah,Wanda ko Kadan babu mai irin sunan acikin danginsu,haka Sunyi mamaki rashin karar da hamza yayi na qin sanyama yaronsa sunan Baba Lawan duba da ruwa da tsakin da yayi wajen gudanar da Aurensa,harma da qarin bada gudunmawar Gidan xama agareshi...,


 Shima kansa abin ya bashi mamaki,,musamman da En xuga Sukayi Caaa akansa "Yanxu wanan dami tayi kama ace Hamxa ya kasa maka kara da sunanka,ko adangi babu mai irin wanan sunan.,balle ace sunan wani ne."


 Kai ya girgixa yana son gaskata maganar mutanen garin nasu,sai dai wani sashi na xuciyarsa ko Kadan bayaga laifin Hamzan,asalima ko wani mutum yaana yin abin da ya kwanta masa arai ne,to shi miye NASA aciki.,

 "ALLAH ya raya abin da aka Haifa,suna ai ba wani abun bane,ko wani yaro yana amsa sunansa ne tun kafin yaxo duniya."


 Amsar da ya basu kenan Dan ko Kadan baya so ya basu qofar da xasu samu damar raba xumuncin dake tsakaninsu.


 "Amma dai kasan duk da haka ba'a maka karaba,sanan bisa al'ada sunanka ya dace asa." Wani daga cikin mutanen da yafi karadi awajan ya fada.,

 Murmushi Baba lawan yayi yana yalwata fiskarsa da fara'a "Banda abinka mutari ai yanxu aka fara haihuwar ko,kuma ba qareta akayiba,mutuqar Hamxa yana da rai,sanan har yanxu bai sanja ni amatsayina na Uba ba,Asalima ni ya samu da shawarar sunan jaririn,na kuma amince akan ASA masa Abdallah,."


 Yana gama fadar haka ya karkade jikinsa ya tashi Dan dama aqofar gidansa suke ana radin sunan,yana raba musu goro da alawa suka fara masa wanan cagwadar.,da famfo na xuga.,tashi sukayi jikinsu babu laka kowa ya kama ganansa suna cixan yatsa.


 Anan kuma Akaci gaba da gabatar da gudanar da hidimar suna,

 A6angaran Iya Indo ma gidanta cike yake da En tsegumi,suna ta magana akan haihuwar Haajaran da sunan da Hamxa yace "Ni dai babu ruwana,Ku rufa min asiri da maganar lamarin gidan Hamza da iyalinsa,Dan ban shirya xama 6eriya ba."


  Nan kuma jikin Matan yayi sanyi,Dan sun manta da batun da er mai ganye tayi akan lamarin Haajaran.,.


 Nan kuma aka fada yabonta da kodanta Kyan jaririn,.Wanda iya Indo take jinsa har ranta,wani lokacin tana mamakin yanda take kaunar yaron idan ta tuna alwashin data dauka akan babu ita babu Jinin Haajara,.  Raguna guda biyu Hamza ya yankama Haajara manya na suna,.


 Cikin Ikon Allah su Baffa malam suka samu zuwa garin shida Inna da Adda sa'adah da kuma Adda Deejah,.Dan qiri qiri mutanen Yadin Bunni sukaqi zuwa,duba da cin fuskar da aka musu alokacin kawo Haajara,hatta Aminiyar Innah cewa tayi mijinta ya hanata xuwa idan kuma ta kuskure xuwa abakin Aurenta..


 Duk da sunji babu dadi amma haka Baffa malam yace su wuce suje su kadai ma sun wadatar ai.,


 Murna kamar Haajara xata kife harda hawayen farin cikin ta,En garin kuma suka kewayesu suna kallon tsantsar kyau da kamar da sukayi dukaninsu. Sai Baffa malam da ya musu kwarjini ta yanda basu kawo musu wargiba,.


  Adakin zaure aka sauqesu nan hira ra ringa wakana,Innah sai kallon Haajara suke,tayi sanyi da shuru-shuru sai yawaitar dariyar da takeyi.


 Kar6an yaron Baffa malam yayi ya masa Addu'a sosai,saanan ya bude gabansa ya masa Addu'a ta kariya daga afkawar zina,ya bude qirjinsa ya masa Addu'a ta sanyin xuciya da hali.,..

 Yaron bashi da maraba da shi,sai duhun fatar da ya sirka da ita,.

 Murmushi yake yana "Na samu aboki daya da daya,Amma fatana kar ya kar6e min Mata."

 Dariya duka suka sa sai Innah da ta qara "Nikam ai na samu miji sabon jini Malam,kawai dai baxai iya maye naka wajanba,tsufanka yafi yarintarsa kyau."


  Nan aka qara saka dariya awajan,sanan Adda sa'adah ta kar6i yaron "Masha Allah Baffa malam ai wanan kamar ka ya sato,Dan ya kwace maka mata."


  "Aifa sa'adah abin da nake son fada na manta.," Nan Dariya ta qara yawaita,.


 "A a wanan kalarsa mai tsada ce Adda sa'adah,kinga masu tsada zai samu.,amma Innah ai ta masa tsufa.," fadar Deejah tana dariya.,

 Baki Innah ta riqe tana murmushi "Hodi jam su deejah anyi Da agabana kike koda yaron ki,kai yaran nan babu kunya ko Kadan malam.,nima ba auren nakeba ina xan kai gayyar kashi da fitsari..," Dariya suka saka nan suka ci gaba da hirarsu,.Haajara dai baki yaqi rufuwa iyaka tayi murmushi ga kuma kunyar iyayen nata da take ji.,sosai.,


 Anan Hamza yazo suka gaisa yana musu godiyar samun damar xuwan da sukayi,sanan ya kira "Yar mai ganye ya fada musu muhimmancinta da Amfanin ta awajansu,haka bai 6oye musu dukkanin rayuwar da Haajara tayi ba,.

 Sosai suke hawaye suna kuka anan Baffa malam yayi ta yima " Yar mai Ganye godiya,yana hawaye,gashi itama "Yar Garin CE amma ta babanta da su,.Dariya tayi tana girgixa kai "Babu komi daa ai na kowa ne,duk da ban ta6a haihuba ina jin tausayin yara ina kuma sonsu,sai gashi Allah ya bani Haajara,Dan haka amatsayin diya take awajena."


 "Duk da haka mun gode Dan Allah ki qara kula mana da Haajara ko bayan ranmu,ki zame mata uwa.,da uba,bata da kowa anan garin sai mijinta sai kee." inna ta fada tana face majina,abun da take gujema diyar tata kenan,amma yanxu ya xasuyi da wanan rabon,Wanda duk cikin En uwanta itace kadai ta fara haihuwa,su ko cikinma basu dashi..


 "In sha Allah xan kula da amanar da kuka bani,na gode."


 Gyaran murya yayi Baffa malam yayi "wanan ma wani sabon ilimi ne da darrusan rayuwa Haajara,ki godema Allah acikin jarrabawar da ya miki,sanan ki yafema mutanen da suka aikata miki laifin nan,haqiqa Allah yana son bayinsa masu yafiya,sanan ki rungumi danki,ki tarbiyyantar da danki ta hanya madai daiciya ki,koyar dashi ilimin Addinin musulunci,kada ki bari abarshi abaya wajan ilimin zamani dai-dai gwargwadon iyawarki.,Allah ya kareku gaba daya."


 "In sha Allah Baffa,." Anan ya ci gaba da musu nasiha mai ratsa jiki,Wanda yasa jikin er mai ganye yin sanyi Dan ta qara samun ilimi na rayuwa Wanda bata da shi,DUk da acikin tarayyar da tayi da Haajara ta qara sabon ilimi....


 Daga nan aka kawo musu abinci suka ci suka sha,sanan ta basu naman sunan.,. Sha Tara ta arxiqi suka kawo mata na sunan da kayan yara,harda kuma yajin daddawa na mai jego da jarka biyu ta man shannu.." Kamar ba xasu rabu ba suka tafi xuciyar kowa cike da damuwa da alhini ba Haajara da take ji kamar sun rabu kenan,.

 Sau biyu suna fita Inna tana dawowa tana shafa kanta "Allah ya miki albarka Haajara ke da xuri'arki ya baki juriya da haquri akan komi,kiyi Haquri idan rayuwa ta sake sauya miki,ki rungumi danki shi xai xame miki abun alfahari da farin ciki anan gaba."


 Haka itama Adda Deejah ta dawo tana rungumarta tana hawaye.,"Ina ji kamar kar na tafi na barki anan er uwa,amma ki qara haquri kowa da yanda Allah ya tsara masa rayuwarsa,kina cikin Addu'armu,ko yaushe xamu saki,xamu tunaki.,"


 Kai take gyadawa tana share hawaye,sanan ta sake rungume Baffa malam "ka yafe min Baffa na,."

 Shafa kanta yayi yana jijjigata "Na yafe miki Haajara Allah ya miki albarka."


 Sannan ta rungumi Adda Sa'adah "Adda sai wata rana kema ki yafe min kinji."


 Kai ta gyada tana hawaye,Allah ya sani tana mutqar son Haajara,haka jininsu yazo daya ko Kadan baata son ganin damuwarta,yanzuma ji take kamar ta dauketa su tafi,amma Aure ya shata layi mai kauri atsakaninsu."


 Kanta ta shafa ta janyeta ajikinta ta fice suma su Inna suka bi bayanta.,

 Tana kuka har hamza ya rakosu ga shatar motar daya dauko musu.,.sai Hannu suke daga mata suna goge hawayen fiskarsu,.

 Shima Baffa malam duk da yana namiji sai da hawaye ya xuba a idonsa tunawa da rayuwar da "yarsa take aduniyar da bata da kowa sai Mahaliccinta,Amma Allah yana sane da kowa,shi xai kareta aduk Inda take.


  Iya mai ganye CE ta jata suka Shiga gidan tana bata haquri,sanan shima Hamza ya wuce kasuwa ganin 6acewar motar su Baffa malam.. Tafiya suke babu Wanda yake magana acikinsu sai can Baffa malam yayi magana " ko babu ranmu Dan Allah Sa'adah ki kula da zumunci da er uwarki Haajara.,Ina jin tausayinta da yanda qaddara ta sauya akalar rayuwarta,xuwa duniyar da take cike da maqiyanta.

 Share hawaye take itama "In sha Allah Baffa malam xamu riqe xumunci muddum rayuwa taci gaba da bamu damar yin hakan."


 Sa'ada ta fada,sai dai kafin Deejay tayi magana sukaji Motarsu ta fara Hantsilawa tana juyawa, "Inna lillahi wa Inna ilaihirraji'Un" Kalmar da suke mai maitawa kenan sai dai kuma kafin wani lokaci motar ta kife da su cikin kwankwatsewa da hayaqi da take fiddawa,.Sai jini da ya wanke ko wani gilashin motar........

   _Kullu Nafsin za'ikatul Maut............_


  ©By *😘Um Nass. 🏇🏼*

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI* 🎊 ©by 😘 *Um Nass* 🏇🏼Page 28 Hatsarin ya faru ne kafin qarasawarsu Yadin bunni,Dan GAF suke da shiga garin,Tuni mutane sun kawowa motar tasu dauki,sai dai cikin kaduwa da tashin hankali ake zare mutanen da ko numfashi basa fitarwa.,


 Ambulance CE ta zo da jiniya ta kwashesu zuwa General hospital Na garin Yadin Bunni,.

 Sai dai cikin rashin sa'a dukkanin su Hudu rai yayi halinsa sai mace guda daya da ta samu karaya guda bakwai a qafafuwanta,.


  Ayanda motar ta kwantsame ko kadan basuyi tsammanin xa'a samu mutum mai rai acikintaba,amma wani Ikon Allah sai gashi an samu Wanda take da rai,duk da ta samu raunuka da karaya amma dai ta tsallake rijiya da baya.,


  Lokacin da likitocin suka ga Baffa Malam sosai suka kadu suka shiga tashin Hankali,Dan kowa agarin yasanshi ya kuma San matsayinsa Na Baban malami agarin.,.


 Kafin wani lokaci Mutuwar Baffa malam da iyalansa ta zagaye garin Yadin Bunni,.

 Anan Hakimin Garin yazo ya bada Umarni adaukeshi akai shi gidansa da sauran wadanda suka rasu amusu sutura.

 Sai dai yaji labarin mutum daya data rage Wanda itama tana cikin rayuwar qala waqila ne,rai ko kai Mutu ko kai.,

 Fatan samun lafiya ya mata yana fidda hawaye a idonsa,Allah ya sani yana son Baffa Malam mutum ne mai gudun duniya,haka ko kadan bashi da fushi,masanin Alqur'ani Wanda yake aiki da shi,koya ka muzguna masa da murmushi yake binka.,

 Kowa acikin Garin ya sheda karamci da martabawar Baffa Malam,.

 Hatta En Uwansa da suka samu labari sai da suka zo suna kuka suna hawaye,tsawon rayuwar da sukayi suna quntatama Baffa Malam bai ta6a nuna damuwarsa akansu ba,asalima binsu yake da murmushi,yana girmamasu aduk inda ya gansu.,


 Sai dai lokaci baya jira,balle ya jirasu su gyara kuskuren da sukayi abaya,.Haka mazajan su Adda Deejah da Adda sa'adah suka shiga tashin Hankali sunyi kuka sosai,bama ya mijin Deejah Wanda tabi sawun Iyayenta,ga kuma Adda sa'adah da take asibiti cikin rashin sanin a inda take...,


 Nan akayi suturarsu su ukun aka tura gawar direban Garin Gumsa Dan shedar da aka samu a motar daga gumsa ya daukosu,.

 Duk da qarancin wayewa alokacin amma suna da tattalin dokar tuqi tun alokacin.,

 Bayan an kaisu makoncinsu kowa ya kama gabansa sai fatan Allah yaji qansu kuma,Dan babu wani shaqiqin da ya rage musu da xa'ayi xaman makoki,suma En uwansa tuni sun koma al'amuransu,musamman da sukaji labarin a kan hanyarsu ta baro Gumsa hatsarin ya faru,. Dan suna da tabbacin En garin ne suka musu ture ko wani surkulle suka mutu،,dama ba wani kyakkywar alaqa CE atsakaninsu ba. *""""********


 Tun bayan tafiyar su Baffa Malam ta tsinci kanta da faduwar gaaba mai tsaanani,Wanda take ta mai maita kalmar"Inna lillahi Wa Inna Ilaihirraji'un."amma kamar tana qara tunxura xuciyarta ne tana ci gaba da harbawa.,


 Can kuma taji wata qara akunnenta wanda ta sata rawar jiki,ga bugun xuciyarta kamar xata 6alle tsakanin qirjinta ta bugu,.,Hawayen da ba tasan ko Na miyeba ya shiga xuba daga Idanuwanta.,ga Abdallah da yake ta faman callara kuka yana kiqewa,ta bashi mama yaqi qar6a sai kuka yake ba ji ba gani,samun kanta tayi da fashewa da kuka itama,Dan ta kasa sanin mi yake faruwa da ita,duba da Yanda ko INA ajikinta yake rawa,.


 Ahaka Hamza ya shigo gidan yana ta sharce gumi idanuwansa sunyi jajur,sai dai ganin halin da Haajaran take ciki da jaririnta ya qara sashi Jin Tausayinta,haka kuma ya Na qoqarin nemo dauriyarsa., daukan jaririn yayi yana jijjigashi "Yi haquri Abdallah bawan Allah,yi Haquri masu yi Dan Allah.,Yi haquri kama Ummi dariya itama ko tayi dariyar." Luff yaron yayi kamar yana jin mi yake fada,sanan ya shiga ajiyar xuciya akai akai.,..


 Zama yayi yana kallon Haajaran Wanda har yanzu bata bar kukan ba.,"Oh ni ban ta6a ganin mai jegon da take kuka abikin sunan jaririnta ba, sai kee.,kinga shima yayi shuru sai ki share hawayenki."


 Cikin sarqewar murya ta fara Jan zuciya "Ba saboda shi nake kukaba Hamxa,ji nake kamar Na rasa komi nawa aduniya,xuciyata sai bugawa take da qarfi,INA jin wani tsoro Wanda ban ta6a jinsaba tsawon rayuwata.,ban San ya zan kwatanta maka ba Hamxa,amma kaji labarin su Baffa Malam sun Isa gida?"


 Kalmanta sun qara sanwa xuciyarsa jin tausayinsa,ya sunkuyar da kansa qasa,ko kadan baya so taji labarin da taji,duk da bai samu tabbacin gaskiya bane,amma bai San ya Haajaran zata ji ba idan maganar ta kasance gaskiya ne.


 Kafin yayi magana kururuwa ta CIKA gidan da salatin matan dake gidan "Shikenan Gaje yau bango ya fadi,Talle ya tafi ya barta da gwagwarmaya.,"

  Kallon Hamxa tayi tana qoqarin fahimtar inda maganarsu ta dosa.

 Kai ya girgixa mata cikin nuna rashin sanin ihun da suke yi.


 Miqewa tayi da Sauri ta fita tsakar gidan,ganin mata tayi a tsattsaye wasu Na Tafa hannu suna riqe ha6a "Mi yake faruwa ne ?" Tana tambaya kamar mai tsoron amsar da xa'a bata.

 

 "Talle ne mijin Gaje yanzu aka kawo gawarsa sunyi hatsarin mota,kinsan direba ne,Dan shi ne ma ya dauki baqinki da suka tafi daxu,basu kai ga qarasawaba motar ta hantsila sai gawarsu aka fitar.,"wata mata mai Dan banxan karadi da surutu ta ke rattabo bayani,ba tare data kula da yanayin da Haajara ta fadaba,Kodan awajansu hakan ba Wani abu bane mai wahla. Dan su shedama mutum mutuwar wani daga cikin danginsu.


 "Inna lillahi Wa inna ilaihirraji'un,.Allahumma ajirni fi musibati haza wakallafni khairan min ha."wanan itace Kalmar da Haajaran take ta nanatawa afili kafin wani duhu ya lilli6e ganinta ta fadi qasa.********


 Ido ta runtse ta bude hawaye suka biyo baya,sanan ta kai kallonta ga saitin mutanen dake gabanta.,

 Kamar hadin baki suka ja Numfashi alokaci guda,yayin da hawaye ya CIKA idonsu sai faman shareshi shi suke yana sake xubowa..,


Musamman Abdallah Dan sai yau ya ta6a jin rayuwar gwagwarmayar da mahaifiyarsa ta sha,ashe shi bai ga komiba.,sai ma dadin da yaji, idan ya danganta rayuwar da mahaifiyarsa tayi.,


  " Lallai kinga Rayuwa Um Abdallah,.Ban ta6a jin kwatankwacin Wanda yayi rayuwa kamar takiba."

.

 Murmushi Ummie tayi tana share Hawayen da ya xuba akan idonta,ganin rayuwar take tana giftawa ta idanuwanta,kamar yau ne abun yake faruwa.


 "Naga rayuwa sosai Hajiya,amma acikin labarin da Na baki bai wuce kaso goma acikin darin Wanda muka sha agaba ba.,lokaci ya tafi da yawa,kinga har ana qiran sallah Zuhur baki fitaba,nasan da yawa suna jiran abincinki."


 "Ban ta6a jin wanan labarin ba Ummi,. Mi yasa ko da wasa baki fada minba.?" Hawaye ya wanke fiskarsa sosai,sai Jan ajiyar xuciya yake.....


  "Ai gashi yanzu kaji ko,kada ka bari hakan ya dameka,.maxa Ku tashi kuyi haramar tafiya masallaci kai da Arfat.,kun tasani gaba kuna kallo kamar allon magiji."

  Kai suka girgiza suna murmushi,Wanda yake tafe da hawaye,daga nan suka miqe jiki asanyaye suka daura alwala suka tafi masallaci...


 Miqewa itama Mama Anta tayi ta daura alwalar ganin yau ta makara bata tafi tasha ba.,Allah ne yasan mutanen da suke jiranta,Dan shaf ta manta bata bude wayarta ba.,da kiran mutanen tashar ya ankarar da ita ,,sai dai har zuwa wanan lokacin tana al'ajabin rayuwa irin Wanda Haajaran tayi,kamar ashirin film,ashe hakan yana faruwa da gaske,.oh Allah daya gari bam-bam.


  Ganin Ummin Abdallah tayi har ta dauro tata alwalar ta xo,hakan ya sata tada iqama ta fara,Dan yanzu wani nauyin Haajaran takeji da kaunarta kamar er uwar da suka fito ciki daya...


  Bayan sun idar da sallahr ta qurama Ummi ido tana ganin yanda ta Dade acikin sujjadarta,sai shassheqar kukanta takeji,Dan da alama hakan ya xama jiki agareta,shi yasa ta manta akwai mutum akusa da ita...


  Har ta sallame kanta Na qasa tana ci gaba da yin Addu'a,..


   Daki Mama Anta ta shiga ba jimawa ta fito da hijab ajikinta da jaka,tana magana da waya ahannunta "kabiru ya baka zoba,gashi har axahar tayi INA jiranka,..

 Shuru ta danyi alamar sauraran mai maganar,"manta wayan nayi arufe,amma tunda kasan aikinka ne kaini sai ka xo ko ban kirakaba,."


  "INA jiranka to."ta kashe wayar tana kallon Ummie da taka qura mata ido tana murmushi " Ummie Ni zan tafi,ga abinci nan idan kinji yunwa kici,idan kuma wani abun kike buqata akwai komi a kitchen sai ki daafa,idan su Abdallah sun dawo ki zuba musu suma.,sai Na dawo."


 "To Hajiya Allah ya kiyaye hanya,Allah ya vada sa'a"


 "Ameen ameen,karfa ki yarda kiyi tunani da yawa,yau kinyi kuka kin magantu ki kwanta ki huta."


 Kai ta gyada tana qaqalo murmushi,kaso 50 cikin 100 Na damuwarta ya ragu,ahankali take jin nauyin da xuciyarta tayi tana raguwa,sai dai abu ne mai kamar da wuya.,ace ta xauna ba tare Da tuna Hamza ba,iyayenta da kuma er mai ganye,.ga kuma Addah Sa'adah Wanda rayuwa tayi juyin kaxar kuku da zumuncinsu,.. Qaddarar rayuwa da gajiyayyun mutane ya shata layi mai girma a tsakaninsu...  "Ummie., Ummie." Sunan ta da Abdallah ya fada ya sata saurin dawowa daga duniyar da ta tafi.,

 Murmushi ta qirqiro "Har kun dawo Abdallah,?INA Arfat din kuma.?"

 "Ya shiga daki sauya kayansa xai tafi gareji,shine xan tambayeki INA son rakashi,amma naga kina aciki damuwa,Na fasa fitar."

 Shafa Kansa tayi tana murmushi "A a Abdallah kuje abinku.,nima barci xanyi banji xuwankuba,Na fara gyangyadi."


 Baya son musu da ita ne amma bai yarda ba, kai ya gyada yana murmushi "To Ummie sai mun dawo."


 "Allah ya kiyaye INA arfat din axuba muku abinci Ku ci,kafin Ku tafi."


 Kai ya girgiza yana yamutsa fiska "Bana jin yunwa Ummie,ban San ko Arfat dinba."

 "Nima aqoshe nake jin cikina,zo mu tafi kaga Na makara nima.,Ummie mun tafi sai mun dawo."


 Da murmushi ta bisu da kallo "Allah ya kiyaye ya bada sa'a."


  tabi bayansu har taga tafitarsa,kana ta sama qofar sakata,ta koma acikin gida...

    *😘Um Nass🏇🏼*

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI 🎊*


 ©by *😘Um Nass 🏇🏼*


_*FOLLOW ME ON WHATTPAD @UmNass*_


® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION*  PAGE 29


 Tafiya suke kowa da tunanin da yake,musamman Abdallah Wanda yake jin tausayin mahaifiyarsa da rayuwar wahlar da tasha,ashe shi bai ga komiba.،


 Hannunsa Arfat ya riqe ganin sun fito bakin titi,amma hankalinsa baya jikinsa,ajiyar xuciya ya sauqe ya fara kallon ababen Hawan da suke ta kaiwa da kawowa,ga manyan gine-gine da kuma symbol Wanda yake dauke da hotunan mutane na tallar company da kuma na En siyasa.,


 "Lallai inda aka ci gaba nan ne gari,kaga ba ruwan wani da wani,babu mai kallonka ya maka magana,ko aibunka ko yabonka,kowa sabgar gabansa yake."


 "Sai ma ka zauna agarin xaka fahimci hakan,Kano akwai dadin xama,gashi kowa yana fafutukar Neman na kansa,cibiyar kasuwanci CE sosai,haka kuma babu sana'ar da xakayi baka samu nasibi acikinta ba,Allah ya sanya ma garin Albarka sosai,shi yasa ake ma garin take da Kano ta dabo tumbin giwa koda mi kazo an fika."


  "Harda rigima ko?"

Dariya sukayi gaba dayansu kafin Arfat yayi magana,sukaji qaran jiniya,da kuma dandazon police sai bude Hanya suke suna dakatar da mutane.,. Haka kuma suka kashe hanyar babu Wanda xai wuce.


 Dan qaramin tsuka Arfat ya ja yana duba Agogon hannunsa "Kaga wanan shine damuwa,duk lokacin da akace Governor xai wuce ko wani babban Dan siyasa sai an katsema mutane uzurinsu,ana hanasu wucewa."


 Murmushi Abdallah yayi "Wanan shine girman ai Arfat,amma ace shugaba xai wuce babu alamunsa."


"Mtssss Giraman kai dai,amma mine babancinsa da mu,tunda duka mutane ne."


 Kai ya girgiza yana dariya mai sauti,Dan mitar Arfat bai San awani matsayin xai sataba,.


 Kafin yayi magana dandaxon motocin suka fara wucewa acikin hanzari kamar masu shirin tashi sama.,Hannu Abdallah ya daga sama yana dariya "Asauqa lafiya." Ya fada da qarfinsa duk da babu Wanda xai jishi,musamman idan yayi la'akari da motocin da suke lilli6e da glass dinsu.


 Mutanen wajen ne suka juyo suna kallonsa,cike da mamaki,su Kansu police din wajen saida suka kalleshi da kyau,amma ko alamun damuwa basu ga afiskarsa ba,jijjiga kai sukayi suka bi bayan motocin governor din,sanan aka saki hanya mutane suka fara wucewa,amma da yawa saida suka tankama Abdallah "Amma dai kai baqo ne agarin nan ko,?da alamar baki da aikin da xakayi mai muhimmanci shi yasa kake masa fatan sauqa lafiya,yayin da kowa ke tsaki yana kawar da kansa."


 "Ko daya,INA da abunyi sosai,gani nayi ko babu komi shi shugabanmu ne,xaifi kyautuwa mu bishi da fatan alkhairi,."


 Kallonsa mutumin yayi,yaga sai fara'a take,tsaki yayi ya buga Mashin dinsa "Ina tunanin wanan yana da ta6un Hankali,babu amfanin yin magana da shi."cike da mita yake maganar ya tafi.


Anan suka rakashi da dariya shi da Arfat,."kaga irinta ai Abdallah ya kamata ka sauya rayuwarka,akwai banbanci tsakanin nan da inda ka baro."


 Shima dariyar yake "Wanan Halayya CE fa Arfat,da zan sauya da na sauya lokacin da maqiya suka kewaye ni,amma har yanzu ban samu sauyi ba."

 "Duk da haka dai ka sauya taku kada aci gaba da maka kallon marar Kai."


 Dariya yayi yana son gaskata maganar Arfat din amma dai da kamar wuya.,


 Ahaka suka qarasa wajan gyaran motar su Arfat din,da mamakinsa ogansu bai masa fadaba,saima tambayarsa da yayi dalilin da yasa ya maka duk da hakan ba halinsa bane.


 Haquri ya bashi yace Dan uwansa ne suka zo jiya,yana kuma nema masa aiki anan,.kallon Abdallah yayi hankalinsa ya kwanta da yaron,hakan yasa ya kar6eshi babu tangarda.

 "Zo tare dani sai ka fara ganin yanda aikin yake,ka maida hankalinka sosai kaji.,"


 Risunawa sukayi atare suka fara godiya,.Musamman Arfat da yasan halin Ogan nasu baya kar6an baqo cikin sauqi,.


  


  ****""""****


 Gaba dayansu sun Hallara awaje daya bayan kammaluwar cin Abincin dare,.

Anan Arfat ke basu labarin a abin da Abdallah yayi da kuma samun aikinsa,.

Dariya Sukayi cikin farin ciki Umminsa ta kema Arfat godiya,.


  "Ai mun zama daya Ummie."


 "Nikam na qagu naji ci gaba n Labarinku Ummie Abdallah,ko da nake wajan kasuwancina hankalina akan jin ci gabaan labarin rayuwarku yake.,na Dade banji abin da ya sani qawar xuci kamar wanan ba."


 "Nima haka Mama Allah-Allah nake mu dawo mu ji ci gaban labarin,." Arfat ya kar6i maganar cikin xaquwa da son jin abin da ya biyo baya.


 "Yanzu kuwa xakuji ci gaban labarin.....   *****"""""**"


Arude mutanen wajan suka iyo kan Haajara,haka Hamxa da yake daki bai San lokacin da ya fito cikin rudewa ya nufi Haajaran ba,jin ihun mutane da kuma salatin da suka rafka abaibai.


 "Ku bani ruwa" ya fada yana miqawa maqociyarsu Abdallah,Wanda xuwa lokacin barci ya daukeshi.


 Ruwan aka bashi ya kwarama Haajara,sai jin Jan xuciyarta akayi da qarfin gaske.


  "Dan Allah ku CE min mafarki nake,karku CE da gaske ne iyayena sunyi Hatsarin mota sun Mutu,.Dan Allah karku CE maraici ya kewayeni gaba da baya." Maganar da take cikin yanayi na gushewar hankali da tsoro,.


  Dagata Hamxa yayi ya karata ajikinsa,bai damu da tarin mutanen da suke gidanba,Wanda babu makawa sai tsegumin ya fita waje.

  

  "Acikin duka abin da kika fada babu Wanda yake ba gaskiya bane Haajara,Allah da ya baki su yafiki sonsu,shi yasa ya kar6i rayuwarsu alokacin da yake son komawarsu gareshi.,kada zafin quna na rashi yasaki manta cewa Allah yafiki son su,haka kuma mutuwa tana kan kowa,kada kiyi butulci ta hanyar godema Allah da rahmar da ya miki,ayanxu addu'arki kawai suke buqata."


 Miqewa tayi tsaye "ya kamata naje Yadin Bunni yanzu Hamza,INA da tambayoyin da ya kamata na samu amsarsu.INA son naga kabarin iyayena na musu Addu'a.harda En uwana ma."


Jikinsa ne yayi Sanyi ya ci gaba da jijjiga kanta "YANZU dare ya Riga da yayi Haajara kafin muje duhu ya shiga,ki bari gobe sai muje.,"


 "Bazan iyaba Hamxa,ko kadan baxan iya jure kwana guda agarin nanba,ka barni na samu damar yima iyayena Addu'a."


 Kai ya dafe na rashin Sanin Abin da zaiyi "bakya ga yanzu da qaramin goye atare da kee,duka mako guda kenan da haihuwarki.,kiyi haquri duk inda kike addu'arki xata riskesu."


Miqewa tsaye tayi ta shiga daki sai ganinta yayi da hijab ajikinta,kar6an Abdallah tayi daga hannun Yawuro ta goya shi,"ko da yau na haihu xan tafi Hamxa, ba kasan zafi da qunan da nakeji axuciyata ba,wani sashi na xuciyata yaqi yarda akan iyayena sun rasu,xan je na samu gaskiyar kokonton da nakeji wata qila ba gaskiya bane."


Ganin da yayi ba acikin hankalinta takeba yasashi saurin miqewa., Dan yasan ko mi xaiyi ba xata dakataba,mukulli ya dauki ya rufe dakinta yana kai kallonsa ga mutanen da basu da alamun tafiya,asalima suna baxa idanuwa suna wullashi tsakanin Hamza da Haajaran,Dan tsab suke samun tsaigumin fada."Inaga wanan taron sunan ya watse,.kun riga da kunga halin da ake ciki,xamuje Garin su Haajaran Dan ganin ko gaskiya ne."


 Tashi sukayi suna zura takalmansu tsumu-tsumu suka tafi "ko banza mun samu abin fada."


 Madadin su nufi gidajensu sai suka nufi hanyar gidan Iya. Indo,wasu kuma suka nufi gidan Gaje Dan tayata alhinin mutuwar Talle direba.


 Gidan ya garqame da mukulli ya riqe hannun Haajara Wanda har zuwa yanzu bata San a inda take jefa qafafuwanta ba.,

 Duk inda suka gifta mutane ke binsu da kallo suna tsegumi "Aikin banza ko baka riqe Hannun ta ba ai duniya ta sheda ita matarka CE,musamman da t xama Annoba agaremu,." Wani mutum ya fada yana gatsina fiska,baima yi la'akari da yanayin da suke cikiba.


 "Hmm INA yau ne ake bikin sunan yaron da suka Haifa,,mi ya kaisu fitowa kuma Mudi?"

"Yo ni Ina na sani?qila wani sabon salon nuna asan sun haihu ne suka fito da goyo hannu asarqafe,nuna son A sani cin tsire a maqabarta."


 Dariya mutanen wajan suka yi "Kai mudi amma naga kamar suna cikin damuwafa,ya kamata ka tambayesu."


  Baki ya rufe yana tafa hannu "Allah ya 6oyi kurwata Dan ba'u,ammafa naji ana Talle direba yayi hatsari dazu aka kawo gawarsa,ahanyar kai iyayen matarsa Garin su.,gaba daya motar akace ta kama da wuta bayan an cire Talle iyayenta ko tokarsu ba'a samuba,ba mamaki can zasu tafi."


 Ido suka fidda waje Dan dama su uku ne awajan "Kai Mudi shine baka je wajan binne gawar ba,muma ka fada mana,ai da munje."


 "Tabdijam ni inaga ba mutuwar Allah sukayiba fa,wata qila shima yaron nan yazo da sabuwa tasa Annobar,kanaga dai gawar Talle ne ta tsira,sauran duk tokarsu ma babu,inaga hakan wata masifa CE ta tunkaro mu."


Nan suka qara yin tsamo-tsamo suna son gaskata maganar Mudi din.


 Haka a6angaran matan da suka dauki hanyar gidan Iya Indo bakin su car magana.,ko sallama basu tsaya yiba suka afka gidan "Kai ya haka babu Ahu ba gafara kamar an hankado ku?" Iya Indo ta fada tana muzurai.


  Yawuro CE ta cafke maganar "Ai dole ki ganmu ahautsine taron suna ya watse ya koma na mutuwa."


 Qirji ta dafe da qarfi "Na shiga uku ni Indo mi ya faru,kardai jaririn ne ya koma."

 "A a bashi bane,.iyayen Haajara ne sukayi hatsari ko tokarsu ba'a fitarba,ga Talle direba dai an kawo gawarsu,yanzu haka su Hamxa sun tafi Yadin Bunni Dan ganin tabbaci,karkiga yanda ya rude ke kyace iyayensa ne suka rasu,sai ihu yake da qyar muka lallasheshi ya iya shuru suka tafi."


" Na shiga uku ni Indo,da yaron nan ya xama kenan,ya tafi baya tsoron shima suyi hatsarin."


  "Yaya Indo nifa Ina kokonton wani abu,ace daga zuwa suna sai hatsari,anya babu sirkin Annoba ajikin yaron nan,kinaga fa ance su iyayenta ko tokarsu bata tsira ba." Harira ta fada tana xaxxare ido.


 "Kai bana jin wanan Allah dai ya kawo,amma har yaushe aka haifi yaron da xa'a CE ya samu sirkin Annoba." Iya Indo ta fada cikin tsoro Dan ko kadan bata so ace ta yarda da maganar ganin mutane awajan,haka kada ta magantu abun ya dawo kanta.


 Jin bata yardaba yasa jikin En gulma yayi sanyi,hakan ya sasu tashi jiki asulu6e suka nufi gidan Gaje dan mata ta'axiyya.


 "Ku jira muje tare," iya Indo ta fada tana miqewa tsaye,.


  Acan dinma dai babu wani alamu Da xai nuna anyi rashi dan gaje sabgar gabanta takeyi,ko da akaje mata gaisuwa sai tace "Ai kun San ba yanzu zan shiga ta kababa,sai bayan kwana bakwai,gashi ba wani jikoki gareshiba balle su fara masa,sai jikokin yayansa ne gasu can adaki sun shiga takaba,ku qarasa ku musu gaisuwa."


 Tana idda maganar taci gaba da dakanta tana wulla ta6arya sama tana rera waqa.,. 


 Sanin gaskiyar maganar da Gajen tayi yasa basuji mamakiba suka nufi dakin kowa na qirqiro kuka da ihu ana shafa hannu jikokin yayansa da suka fansheshi,gabansu shaqe da suyar nama da nono kindirmo azuwan abincin da zasu ci na takabar da sukeyi..."


*********


  Lokacin da su Haajara suka nufi tasha duk Wanda suka cema xasu Yadin bunni qin zuwa yake dann sunce su da hanyar Garin sai bayan mako guda,idan komi ya lafa.,


 Kuka sosai Haajara tasa wani sashi na xuciyarta na tuna mata da wawtar da tayi har ya kaita ga auran En Garin nan,sai dai lokaci ya qure mata.,


 Da qyar suka samu wani dan Yadin Bunni da ya kawo kaya xai koma ya daukesu,.tafiya suke babu mai yiwa wani magana acikinsu kowa da abin da yake,sai Ajiyar xuciyar da Haajara take sauqewa akai akai.


 Ahaka har suka zo Garin sai dai da mamakinsu qofar gidan su Haajaran a garqame take da mukulli babu alamun akwai mutane balle masu zaman makoki.,


 Kallonsa tayi cikin tashin Hankali "Hamza ko dai ba gaskiya bane,?iyayena suna da rai,kaga qofar gidan arufe."


 "Nima abun da ya bani mamaki kenan,mutuwar da akayita yau amma ace babu mai xaman makoki.,"


 Kafin yayi wani yinquri sai ga wani yazo wucewa yana ganin Haajara ya fara mata ta'axiyya "Sannu Haajara sannu kinji,kinyi rashin iyayenki da er uwaki,Allah yaji qansu da rahma,ita kuma sa'adah Allah ya bata lafiya,naso zuwa asibitin ma to ban samu Sarari ba amma xanje na dubata." Magana yake ba tsayawa baima lura da yanayin da take ciki na kaduwaba,.


 "Kana nufin Adda sa'adah tana Raye ita."

 Kwarai ma kuwa tana Asibiti gobnati adakin agaji da hatsari."


 Bata jira qara maganarsa ba ta nufi hanyar kamar sabon kamun hauka.,shima binta Hamxan yayi yana gudu-gudu,cikin tafiyar rashin nutsuwa sai gasu sunzo asibitin.


 Kowa sai kallon Haajaran yake tana faman sumbatu "Da gaske Adda sa'adah ta rage min,Allah na gode maka,da ka bar min Addah Nah ta xama majingina agareni,Allah ka tashi kafadunta."


 Kai tsaye ta nufi dakin da aka fada mata,Hamxa na take mata baya,da saurinta ta qarasa inda ta hango Addah sa'adah cikin bandeji a nannade "Kada ki qarasa kusa da ita." Aka fada mata cikin kakkausar murya,


 Juyowa tayi ahautsine sanin muryar a wani shudedden lokaci.,"Bana so ki sake ra6ar matata,tun lokacin da kika rufe idonki kika tura kanki ga halaka daga lokacin matsaloli suka fara baraxana ga rayuwar danginki,kinyi nasarar kashe iyayenki da yayarki kada kiyi kuskuren da wani tsautsayin xai sake afkama Sa'adah ki fita arayuwarta kije matsalarki da kika janyo da kanki ta qare atare da ke...Wanan shine kallo na qarshe da xan sake miki xan dauke Sa'adah ixuwa wata duniyar daban,sai kije ki rayu da gidadawan mutanen da babu Allah Arayuwarsu....." Kamar gudumar Ajali haka take jin sauqar maganar tasa,bata sake qaunar marmarin bude Idonta ta ga gaske ne abun da ake fada mata,so take ace wanan duk mafarki ne,.amma data bude idonta taga hakan gaskiya ne,dole idonta ya qeqashe kukan yaqi sauqa sai sauqe numfashin da ta farayi akai-akai,ta dafe qirjinta Wanda kukan da Abdallah yakeyi ko kadan bai shiga kunnentaba,maganar ke mata amsa kuwa akunnenta...............  _*Ina Neman barar Addu'arku mamana bata da lafiya 😭👏ciwon ciki na matsa mata lokaci zuwa lokaci.*_

   ©by *😘Um Nass🏇🏼*

[10/17, 9:08 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI 🎊*


©by *😘Um Nass 🏇🏼*


  _*Follow me on whatppad @UmNass*_


® *MADUBI 🔎WRI.ASSOCIATION.*

   


  _"Haqiqa godiyata agareku mai yawa ce.,Na gode Mutqa,Alhmdlh da sauqi sosai atare da lafiyar Mamanah.,"_


 _*Ku dauki wanan shafin Amatsayin naku ne duk Wanda suke karanta Labarin HADIN GWARMAI ngd da kulawarku,dan haka ga tukuici agareku 😘❤*_Page 30 Kallonsa take tana dafe da qirjinta da yake mata xafi "Kada kamin haka AADA kada ka rabani da er uwata,ita kadai ta rage min kamar yanda ni kadai gareta,duk abin da yake faruwa bani na tsarawa kai naba,dama can Qaddara tace,haka mutuwar iyayena da hatsarin da suka shima cikin qaddarar Ajalinsu ne,amma daga cikin ikonsa sai ya bar Adda Sa'adah da rayuwar ta,Wanan wata hikimarsa ce da aya mai girma,idan ka juya labarin amatsayin ni ce tushen Ajalinsu,haqiqa ka jahilci lamarin kaima,Na sani ko wani rai Yana da Silar Ajalinsa,amma wani baya kashe wani face sai lokacin Mutuwarsa Yayi,sai ya xama sila na Ajalinsa." Ajiyar xuciya taja mai qarfi ta Hada Hanyenta duka biyun "ka yi haquri ka duba maraicin da ya kewayeni alokaci daya,kada ka yanke igiyar xumuncin da take riqe damu,ni da Adda Sa'adah,.


 Kallonta yayi sheqeqe duk da xuciyarsa na nuna masa gaskiyar maganar Haajaran Amma yaqi ya bada tabbacin hakan,har yanzu akwai sashin da yake Nuna masa Wanan ba sila bane qirqirarran abu ne da mutane Gumsan suka shirya,.dan Babu wani abun da suka sani na imani da xaisa suji tsoron Allah,su Qi aikata 6arna.," Uhm sai yanzu kika San da hakan Hajarko,ki ma bar maganar Sa'adah ta rage miki aduniya,ki dauka duka danginki sun qare,dan har Abada babu Wanda xai sake saurararki,balle ya kawo miki dauki,ki tafi abinki,idan Sa'adah ta warke xa'a kasafta Gado a aika miki da naki,amma ke da ita har Abada.,kina 6ata ma kanki lokaci ki wuce ki tafi."


Dafe kai tayi,Wanda take jinsa kamar xai fado saboda azabar ciwo,kallon gadon da Adda Sa'adah take tayi,Wanda ko kadan bata cikin hayyacinta,bata San aduniyar da take ba,sakamakon Allurar barcin da aka mata,.


 Qoqarin magana take Hamxa ya tari numfashinta "Ya isa haka Haajara,xo mu tafi.," cikin sanyayyiyar muryarsa da ta cika da rauni yake mata magana,.,

 Kallonsa tayi tana son ta ga abin da ta gani ya sata nacewa da sonsa,har ta hadu da wanan hargitsin rayuwar da qunci,amma bataga komiba sai tsantsar tausayawa da raunin da taga atare da shi uwa Uba son da take masa."


  Kallon Adda Sa'adah ta sake yi akaro na ba Adadi kafin ta juyo ta kai kallonta ga AADA "Na gode AADA zan fita arayuwarku in sha Allah,amma ka kular min da Adda Sa'adah, daga yau ba xaku sake jin labarinah ba,sanan bana buqatar Gadon Idan an raba ka bama Adda Sa'adah wata qila xata amfana da shi agaba."

 Bata sake saurararsa ba tayi waje, kuka na cinta amma bata so tayi shi,qoqarin danne kukan da ya taho mata take yi amma hakan yaqi yiyuwa."


 Da taimakon Hamxa ta iya ganin gabanta,sai a lokacin ta farga da kukan da Abdallah yake yana ajiyar xuciya..


 "Sauqarshi Haajara ya gaji da goyo nan,ki bashi mama ya sha."

 Ba tare da tayi maganaba ta samu wani waje acikin Asibitin ta sauqeshi,ta fara bashi mama,tuni yayi tsit sai Jan xuciyar da yake da tsosa kamar xa'a qwace masa.,.

 Kallonta Hamxa yayi yana tausayawa rayuwarta,wanda duk shine silla,tabbas ya so kansa da yawa,bai kuma San ta INA xai fara lallashinta ba,.

 Miqewa tayi ta sake Goya Abdallah abayanta "Mu koma gida kawai."


 Kallon Garin yayi da yanda duhu yayi dan alokacin ake qiran sallahr issha'i, "Bana jin xamu samu motar da xata shiga Gumsa awanan lokacin,dan dare yayi,duk mai xuwa kasuwa ya koma gida awanan lokaci."


 

 "Sai mu tafi da qafarmu ai,bana son na ci gaba da zama agarin nan,dan na San ba xan qara samun tallafi daga kowa ba,na Riga na rasa komi da yake nawa acikin Garin nan,saura na koyi rayuwa da kasa tunashi,amma ban saniba ko hakan zai xama mai sauqi agareni." Ta qarasa maganar tana murmushi wanda yake tafe da hawaye,da ganinsa na takaici ne,da bawa xuciyarta qwarin gwuiwa.


  "Kiyi haquri Haajara da xan iya dawo da jiya ta koma yau wallahi da na dawo da dagiyata akan aurenki na janye,har kunyar hada Ido nake da kee,ban San kuma da Kalmar da xan fara rarrashinki na nemi yafiyarki ba." Hawaye ne ya xubo a idonsa har yanzu ganin baikinsa yake da alhakin komi a dalilinsa ya faru,to amma ya xaiyi da hakkinta da yake kansa mutqar bata budi baki ta yafe masaba.,


  Murmushi tayi ko ba komi tasan Hamza na sonta,haka itama Wanan baya cikin abin da xata qirashi da sanadi acikin labarin "Mi yasa sai jiya,?dawo da abin da ya Riga ya faru baya qarama mutum komi sai 6acin rai,ga Gobe na daga mana Hannu mu Sanya tunaninmu akanta,kabar dawo da shudadden labarin da ya Riga ya wuce,mu rungumi qaddarar data hadamu ta fidda Abdallah atsakaninmu,hakan zaisa mu godema Allah abisa rahmar da yayi mana."


 Kai ya jinjina yana gaskata kalamanta,"Na gode,Allah ya miki albarka ya kare ki aduk inda kike.,ya rabaki da sharrin maqiya."


 "Ameeen tare da kee."

 Daga nan suka nufi hanyar barin Asibitin.,

 Tafiya suke suna tunanin ina xasu samu abin hawa,sai dai ko kadan babu wani alamar xasu samu motar da xata shiga Gumsa awanan lokacin,.

 Dan wasu ko kallonsu ma basayi,

 Hanyar garin suka tasamma duk da duhun da yake wajan amma babu tsoro atare da su,xuciyarta Haajaran ta Riga da ta dake,ita bataqi ba ma tayi karo da Ajalintaba,ta gaji da rayuwa,fafutuka take da numfashinta tana jefa qafarta,amma gani take kamar ba tafiyar takeba... Ahaka suka shiga maqetarar hanyar cikin sa'a wata mota tazo wucewa ta gabansu tana tafe tana bada qaran inji da haqin da yake fita ajikinta,da ganinta ta gaji da rayuwa dan komi ajikinta babu alamun nagarta atare da shi,tsayawa yayi yana kallonsu,Dattijo ne matuqin motar,yanayinsa ya nuna tausayawa atare da su"Ku kuma INA xaku je awanan duhun ? Kuna tafiya babu haske,bakwa jin tsoron ku hadu da mugun abu."


  "Gumsa xamu je,abin hawa ne bamu samuba,dare ya mana,"

 Kallonsu yayi can yace "ku shigo mu tafi nima nan nayi,"

 Shiga sukayi suka gaidashi ya amsa da fara'arsa.,

 Daga haka suka ci gaba da tafiya babu wanda yayima wani magana acikinsu.,

 Har suka shiga garin Gumsa "Alhamdulillahi" suka fada atare "Ina kuka nufa,?"dattijon ya tambayesu,

 Kwatancen unguwar Hamxa ya masa anan ya qarasa da su har qofar gidan nasu "Nawa ne kudinka Baaba?"

  "Ku barshi kawai,nayi saboda Allah.,amma nan gaba idan dare ya riskeku atafiya kuna haqurin kwana,dan kaga akwai iyali atare da kai ga yaron goye,.dare abin tsoro ne ko da hasken wata agari."


 Godiya suka masa sosai sanan suka shiga gidan,yaja motarsa yayi gaba.


 

  ******"""***

 Bayan watanni shida :-


 Acikin wadan nan watanni Haajara ta rungumi qaddarar rashin danginta da tayi,haka bata qara waiwayar Yadin Bunni ba,balle taji labarin Halin da er uwarta take ciki,kamar yanda AADA ya buqata,ta sani abu ne mai wahla ace ya barta sunci gaba da zumunci,saboda tsananinsa agareta hakan ya xama shudadden labari,ta rungumi Abdallah da Hamxa amatsayin danginta,shima ko Yaya yana fadi tashi akanta,kyautata mata yake sosai,duk da yanxu samunsa bashi da yawa,dan tuni ya bar xuwa Yadin Bunni Neman kudi,saboda Alfarmar da Haajara ta nema atare da shi,tana tsoron kada shima tsautsayi ya rabata da shi,haka bata son tuna koda sunan garin,amma kuma ako wata rana sai ta tuna er Uwarta Adda Sa'adah ko awata duniyar take,itama bata waiwaiceta ba., Rayuwa taci gaba da garama Haajara kamar babu wata damuwa atare da ita,acikin wadan nan kwanakin an samu sauyi sosai agarin,musamman naci gaba da dorewar xumuncinta d mutanen garin,


 Haka Abdallah yayi 6ul-6ul dashi ya ware Iya Indo na aikowa akai mata shi ya yini agidan.

 Son yaron take har ranta,fiye da mahaifinsa,haka ta fita alamarin tsangwamawa Haajaran,. Yanayi ne ya xama na damuna mutanen garin sai fadi tashin gyara gonarsu suke,amma shuru ruwa bai sauqo musuba, gari na yin duhun hadari ga qaran cida kamar xa'a kece da ruwa,amma sai hadarin ya wuce babu alamun sauqar ruwa.,

 Nan hankalinsu ya tashi saboda anci wata uku ana sa ran sauqar ruwa agarin amma shuru sai dai hadari ya hadu ya baje.,


 Sauran garurruwann da suke maqotaka dasu tuni amfanin gonarsu ya fara kyau,shukokinsu sun fito,.Nan suka tasamma gidan "Yar Mai Ganye,dan lamarin yasha Kansu basuyi tsammanin akwai Fari kamar nasu ba.


 Tsumm tayi tana kallonsu,dan bata da amsar da xata iya basu,xaman da tayi da Haajara ta fahimci Addini da musulunci,haka ta fita alamarin camfe-camfen mutanen garin,haka ta bar Hulda da mutanen 6oye iyaka ta vada magani amma shirka ta gujeta,.kallonsu tayi kowa fiskarsa babu Kyau,ba alamar rangome.,can taja numfashi ta furzar da iska" Kuyi haquri inaga lokaci ne bai yiba na damunar,dan da yawan lokuta ana samun juyawar shekara ne,qila sai agaba damunarmu xata sauqa."


 Ihu suka sa da qarfi kamar HADIN baki suka ce "Karya ne wanan labarin," kafin wani dattijo ya cafe maganar "yau har an fice wata uku da sauyawar lokacin,muma muna riqe lissafi ai tazarar bata wuce ta wata daya,amma sai gashi yanzu har watanni uku kenan,mun sha wahla mun gyara gonakinmu amma babu ruwa babu alamunsa.,sai dai idan akwai wata qulalliyar,ko kuma wanan ce Annobar da kikaqi fada mana tun farko akan wannan tsinaniyar yarinyar,da wanan tashin Hankalin ai gara ace mutuwa mukayi ma,babu noma ai babu rayuwa."


  "Kwarai kuwa Mudi wanan maganarka gaskiya ne.." Mutanen garin suka fada,

 Fargaba ne ya kama "Yar mai ganye Sam ta manta da wanan maganar,ko kadan batayi tsammanin sauyawar labarin alokaci kadan ba.


 "Gaskiya ba wanan bace Annobar,dan yanzu komi ya wuce tsakanin Haajaran da ku En garin nan,sai dai mu jira xuwa wani lokacin idan ruwa bai sauqoba sai mu fara Addu'a akan Allah ya yafe mana qila mun aikata wani sa6o ne,amma idan muka tuba Allah mai rahma ne mai jin qan bayinsa sai kuga ya bamu ruwa."


 "Kan Ubaccan,yanzu kenan mu duka masu laifi ne,amma kin raina mana hankali ma,yaushe kika San Allah ma wai,ke da kike tare da iffiritai ai magana xaki musu kawai su sauqar mana da ruwa,dan baxamu jira wani lomacinba,kafin lokacin kuma ai mun Mutu kenan."


 "Qwarai kuwa mudi,kawai ki kira iffiritai basu suka hanamu quntatawa yarinyar nanba,dan haka sai suxo su share mana kukanmu,idan ba hakaba Aradun Allah xa'ayi bala'i agarin nan."wani ya cafke maganar da Mudi ya dauko,


 Daga haka suma En garin suka qara ihu suna fadar " gaskiya ne,gaskiya ne."


 Dafe kai "Yar mai Ganye tayi,ga fargaba da tsoro da ya CIKA xuciyarta, "Subhanallah,!Allah ya mana tsari da bala'i,kun ta6a ganin yanda Aljannu suka sauqar da ruwan sama,wananfa kuna qoqarin yin sa6o ne,Allah shike sauqar da Ruwan sama,haka shike yin komi da komi,su Kansu Iffiritain da kuke magana maqaryata ne,yarda dasu shirka ce Babba,kuji tsoron Allah ku kyautata niyarku,sai kuga rayuwarku ta dai-daita,ni yanzu na fita aharka da Aljannu."  "Kan bala'i ashe Wanda ya Mutu xai rayo kuwa,kenan dama can qarya kika shirga mana akan batun yarinyar nan,har muka yarda,amma gashi babu abin da ya sauya xani saima masifa data afko mana na fari.."Ahargitse wani dattijo yayi magana, 


 Kafin tayi wani yunquri ya dauki qoton dutsi ya jefa mata akanta,tuni Jini ya 6alle agoshinta wajan ya cure.,


 Nan suka shiga jifanta ta ko INA ba shiri ta ruga da gudu tana ihu suna binta,qarshe ta shiga karanto " Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un,Allahumma ajirni fi musibati haza..."da qyar ta tuno wanan Addu'ar wanda Haajara ta koya mata ita,.

 Aikuwa kamar an tsaayar da mutanen garin suka tsaya cak suka bar binta sai jifanta da suka ci gaba da yi.,

 Ta jikkata sosai ta kuma wahla duk jikinta tabon jifa ne,sai da tabar hango mutanen garin da garin sanan ta samu bishiya ta xauna tana maida numfashi,.


 Komawa sukayi suka cinnama gidanta wuta suna zage-zage saura mu je mu samu Annamimiyar yarinyar nan itama.,


 Gidan Haajara suka tasamma wanda tuni labari ya isa kunnenta akan abin da suka yima "Yar mai Ganye,Hannu ta Dora akai ta fara kuka tana ihu,shikenan ta rasa dukkanin gatanta,.

 Yanzu wa xai maye mata wajan Iya Mai Ganye Matar da ta maidata diyar cikinta.,


 Bata kai ga Alhiniba ta fara jin jifan qofarta da dutsuna,ga kuma hargowar mutanen garin da Ihunsu,.


 " Maza fito munafuka mai qashin tsiya,.ashe rayuwarmu kika xo dauka bayan kin gama kashe iyayenki,matsalar bata tsaya akan mijinkiba har saida ta shafemu,.

 Minene namu aciki mukuma..""


 Jifan qyauren gidan suka ci gaba dayi kamar xasu cireshi, tuni jikin Haajara ya dauki karkarwa ta saddaqar da mutuwa xatayi,shikenan tata ta qare ayanxu babu kuma abin da xai tsayar da mutanen garin daga hallakata,

 Ga Abdallah da ya fara rusar kuka saboda tsorata da yayi da hargagin mutanen garin.......

   _"Tofa duk inda akayi da jaki dole dai sai ya ci kara,ban San ya kukaji akan wanan chapter ba amma kuyi qoqari kuyi comments hakan xaisa na fahimci yanda kukaji,karku manta ku danna tauraro ba xai rageku da komiba,.._"

 ©by *😘Um NAss🏇🏼       *[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMAI* 🎊


 ©by *😘Um Nass 🏇🏼*


_*Follow me on whatppad @UmNass*_


® *NAGARTA WRI.ASSOCIATION*


  


  _😍Gaskiya nagode sosai Sis Sanah and Anty Ybk da dedicated dina da kukayi a novel naku,gaskiya ne sosai nake jin dadin labarinku ta yanda alqalaminku yake sarrafa labari,abun birgewa akwai tsari sosai acikinsa,.Albishir ga makaranta novel Koda Baku ta6a karatuba Ku daure Ku karanta *KAIDINSU* KUji yanda igiyar rayuwa ke jujjuya akalar tauraruwar littafin,haka kuma yanda mata su ke baja koli wajan hada tugu da KAIDINSU ataqaice ta ko ya Na fada muku ba xaku ganeba sai kun karanta xaku bada labarinsa agaba._

 _*Nasan a labarin Ga IRINTA NAN tuni an wuce wasu da yawa amma idan kukaje Whatppd xaku sameshi a sauqaqe.,baxan fada muku dadin labarinba idan kunje xaku jiyema kanku 😀*_
Page 31


 Jikinta ne yaci gaba da rawa ga kukan Abdallah da ya qara rikita ta ya hautsina tunaninta,wani rugugi taji da qara mai amsa amo,ba shiri ta xari hijabinta cikin shada da saddaqarwa ta nufi waje.,.


 Ganin mutanen garin tayi afusace kamar masu shirin tada gari guda,kowa fiskarsa gum babu alamun rahma,. Tuni ta saddaqar da rayuwa ta bada amanna akan mutuwa CE xata dauketa,.


  "Munafuka algunguma wadda tayi gadon tsafe tsafe da sirdabaru,yau dubunki ta cika,ko ki karya asirin da kika shigo mana gari da shi,ko kuma yanxu mu dauki rayuwarki,Dan baxamuyi mutuwar wani ba,balle ki karmu da yinwa,wanan kisan mummuqe kenan to munfi qarfin ki mana kisan yunwa." MUDI ya fada yana huci Dan shi baiqi ya shaqeta awajan ta mutuba,domin ya San ko kasheta yayi bashi da zunubi asalima ya rage mugun iri ne.


  "Kalleta kamar mutum afiska Ashe kurace da fatar akuya,ai mun Dade muna baikin auren nan Na Hamza,Wanda bai tsinana mana komiba sai masifa agari,gashi yau wata uku cirr babu ruwan sama babu dalilinsa,mi ake da auren Fulani dangin surkulle." Dan Ba'U ya cafke maganar,nan mutanen garin suka hayayaqo ma Haajaran kamar zasu cinye ta nama danya,.

Jikinta in banda rawa babu abin da yakeyi,ga tsoron ta inda xata fara musu magana "Kinyi shuru algunguma,kiyi maza ki karya asirin da kika zo da shi,ko kuma yanxu ki mutu, Na tabbata idan muka kasheki bamu da hakkin kisan kai,asalima mun fidda mugun Iri aduniya,."


 Neman amsar da xata basu take amma ya gagara jerata,hawaye take tana furzar da xaxxafar iska acikin bakinta,qirjinya Na tsere tsakanin harbawar xuciyarta da gudun da jinin jikinta., "Ban San abin da kuke magana akansaba bayin Allah,Ku min bayanin yanda zan fahimta."


 Azabure Mudi ya kwatsa mata mari tuni taurari suka fara gilmawa a idonta wani duhu ya xiyarci mahangarta "Kun ji min er rainin hankali,mu zaki cuta ki raina mana wayo,tunda muke agarin nan Bamu ta6a fiskantar yanayin Fari ba adamina sai yau Adalilin xuwanki,komi ya ke sukurkucewa yake barin muhallinsa,waccen munafukar " Yar Mai ganye data daure miki gindi tuni mun qona gidanta mun korata,saboda tun farko ita ce tasa muka miqe qafa muka sakar miki,amma duk da haka sai da kika cucemu,kika mana asirin da xamu rayu da yunwa.."ya qarasa maganar yana Huce hargowar da yake ba qaramin sa mata ciwon kai tayiba,.

Durqusawa tayi aqasa tana fidda numfashi.,"Ya Allah kai ne Allah,kai ne mai badawa kai ne mai hanawa,idan rayuwata CE tazo qarshe ya Allah kai qaina ka min rahma,kasa Na huta da wanan hargitsattsiyar rayuwar,.idan kuma INA da sauran rayuwa ya Allah ka kawo min mafita."ta fada tana hawaye muryarta bata fita,ga kuma jini da ya ke xuba abakinta,dalilin Marin da Mudi ya mata.,


Miqewa tayi tsaye ta fiskanci mutanen garin,Dan tuni xuciyarta ta bushe ayanxu bata jin fargaba ko tsoron fada musu ko wata magana "Tabbas ban San dalilin da yasa ruwa yaqi xuwaba,amma idan aka samu fari agari Na jinkirtawar ruwa to mutanen garin ne suka manta da Allah,suka fara aikata sa6o shi yasa shima Allah ya manta da su,ya qyalesu da iyawarsu akan ko xasu yima Kansu komi,ban San ya kuke ji arankuba amma Na tabbata kun shagala da Neman duniya da kujiba-kujiba akan yanda wasu suke rayuwa,.aduk cikinku xaku tuna yaushe kuka zauna kukayi Istigfari akan laifin da kukayi Wanda kuka sani da Wanda Baku saniba,.xaku iya tuna yaushe kuka hadu kukayi sallah a jam'i guda atare da junanku,.?aduk lokacin da kuka hadu kuna hira tsakaninku kuna Ambaton Allah awajan zamanku ko da sau daya ne.?" Wanan tambayar da qaraji take yinta,tuni jikinsu yayi sanyi suka sunkuyar da Kansu,wasu kuma suka fara magana qasa-qasa,.

 Numfashi taja ta furzar sanan taci gaba da magana "Ku kanku kunsan mutum baya ta6a sauqar da ruwan sama ko ya daukeshi muddum kuka cire son zuciya alamarinku,. Allah s.w.a da Kansa yana cewa acikin alqur'ani mai girma "Mu ne muka halicci sammai da qassai,muka CIKA sama da Ado Na taurari da wata,haka muke sauqar da ruwan sama Wanda yake sauqa a qasa da izinin Allah,muke fidda tsirrai daga cikin qasa,ayayin da kuka shukata,Baku da masaniyar tayaya ne muke fidda wannan shukar,wanan wani iko ne Na Allah.,"sanan awata ayar acikin alqur'ani yana bamu labari akan yanda manyan kafirai suke qin bude ido da ganin gaskiya,duk da za'a tambayesu "waye ya hallici sammai da qasa,zasu CE Allah ne,idan aka tambayesu wa yake sauqar da ruwan sama?anan ma zasu ce Allah ne,."

Har yanxu lokaci bai qure mana ba,Ku waiwayi xukatanku Ku cire son zuciya alammuranku Ku nemi kusancinku da Ubangijinku,xai jiku Dan ya fada ma Annabi s.a.w "Idan bawana ya tambayeka akaina,Ni INA ko INA,idan ya roqeni zan amsa masa.."

 Haka kuma hadisi ya inganta daga Annabi s.a.w yace "Allah s.w.a yace "Haqiqa Ni INA tare da bawana mutqar wannan vawan ya ambace Ni,idan ya roqe Ni xan bashi,idan ya sake roqona zan qara masa,,sai dai INA fushi da bawan da baya roqo Na."


 Wata qila kun manta kuma bakwa roqon Allah shi yasa ya manta daku,amma ko da sau daya ne Ku xauna kuyi Istigfari zakuga sanji arayuwarku,daga wanan lokacin kada Wanda ya qara xuwa qofar gidana yana qoqarin qaqaba min abin da bani da ikon yinsa bani da qarfin yinsa,zan jure ko wani cin fiska naku,amma banda Wanda zaku sani cikin sa6on Allah."tana gama maganar ta hada hannayenta biyu ta juya da zummar barin wajen nasu,.

Tafi taji da qarfi anayi,ahautsine ta juyo Dan ganin mai yinsa,Hamza ne fiskarsa dauke da fara'a,Dan tun lokacin da gungu mutanen suka xo qofar gidansa yaji labari,hakan yasashi rugowa da gudu cike da fargaba,sai dai sa6anin tunaninsa yau Haajara ce ta fuskanci mutanen garin ta fada musu gaskiya babu tsoro babu shakka duk da yawan da suka mata.,


  Ganinsa da tayi ya karya mata zuciya tuni hawaye ya shiga xuba acikin Idonta, saurin qarasawa yayi kusa da ita,ya kunce Abdallah abayanta da yake t faman ajiyar zuciya,alamun yaci kuka ya gaji,.

"Ban San ya zanyiba hamza ta ko INA ji nake akwai ciwuka da quna akusa dani,duk inda Na waiga duhu nake gani,anya xan iya ci gaba da jurewa,."


 Kai ya shiga girgiza mata yana kallon mutanen da sukayi tsumu tsumu kamar Wanda ruwa ya cisu,su basu tafiba su basu ci gaba da maganaba,.

 "Astagfirillaha wa Atubu ilaih." Kalmar da ya fada da qarfi kenan yana sake maimaita wa,kamar hadin baki suka sake fada da mutanen wajan, hakan ya Samar da frn ck axuciyar Haajara itama ta maimaita kalmar,Nan sukaji CIDa kafin su ankare ruwa ya kece da qarfin gaske,.


 Anan suka fara ihu suna sowa kafin wani lokacin mutanen garin sun firfito waje suna nufar qofar gidan Haajaran ba tare da sun damu da yanda ruwa yake jiqasu ba,da yawa acikinsu labari ya riskesu wash agaban idonsu abin ya faru da maganar da Haajaran ta fada musu,sai dai abin takaici yawanci cewa suke ga Matar Hamza ta sihirce su Mudi sun kasa mata duka,sai maimaita dalasiman sihiri suke suma,anan fa aka shiga tseren xuwa qofar gidan Dan jin ta vakin Mudi da mutanen da suke dafaa masa baya,.


 Abin takaici a dai-dai wanan lokacin ne mutanen suka tasamma qofar gidan,Wanda ihu da sowar mutane yayi yawa babu Babba babu yaro...........

   _Naso yi muku fiye da haka amma ganin yawan cikiyar labarin da ake yasa Na Gaza yin sa yanda naso,kuyi malejin wanan_ ©by *Um Nass*

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HADIN GWARMA* 🎊


©by *😘Um Nass🏇🏼*


Page 32


  Kafin wani lokaci qofar gidan su Haajara ta cika taf da mutane, wasu acikinsu suna ihu yayin da wasu suke rawa, basu da damuwa da ruwan da yake jiqasu, takaici ne ya cika Haajara ta shige Gida ta barsu, amma duk da haka bata tsiraba dan sai da wasu matan suka so suke tambayarta sahirin da ta karantawa su Mudi, domin dai sunzo ne da zummar illata ta amma suka tadda su suna rawa da ihun murna, haka ko qwarxane babu Wanda kuka daketa.

 Kallon tsaf ta masu ba tare da tayi magana ba, ta shige daki ya kwantar da Abdallah, sannan ta sake fitowa wajan Matan da sukayi dandazo xuwa gidanta, har yanzu suna tsaye kamar yanda ta barsu, haka kuma ihun da su Mudi da muqarrabansa suke bai raguba.

Kallon tsaf ta musu sanan tayi murmushi Wanda bashi da maraba da Na takaici, ko sai yaushe ne za'a samu sauyi agarin nan? Tambayar da bata da amsarta kenan, idan tayi la'akari da kasancewar matan atsattsaye kamar masu shirin takwana, kawai saboda son jin abin da bai shafesu ba.

 "Haajara kin yi shuru muna tsaye kamar wasu sakarkaru, har yanzu muna mamaki, kada dai kin ma mazajenmu suddabaru ne? Idan kuwa haka ne babu Wanda zai rabamu da kee, sun zo da zummar muzguna miki amma kinji sai ihu suke kamar saunaye." Wata fusatacciyar mata ta ke magana tana watsa idanuwanta tsakanin Haajara da mabiyanta.

 "Maganarki gaskiya ce Ladi, muna saurararki, gaki er qaramar Yarinya amma duk kina qoqarin maida mutane mahaukata ta hanyar sihircesu, wanan masifa ta isheni Ni Uwatale."


 "Ni ban yima mazajenku komi ba, asalima Na tunatar da su ne akan abin da ya wajaba ace suna tunawa ako yaushe, na kuma kwadaitar da su romon lada da nasarar da mutum yake samu muddim ya miqa lammarunsa ga Ubangijinsa, wanan ihun da suke yi kuma ni kaina ya isheni amma hakan nasan dabi'ar suce idan abin farin ciki ya samesu suke yi, to wanan ma haka ne, kuna iya xuwa Ku samu mazajan naku Ku tambayesu, amma na roqeku Ku daina jingina ni da Kalmar sihiri ko tsafi, wanan shirka ce babba kuma abin qyamata ne ga Wanda ya san hukuncin aikata su."

 Kallon ta suke baki a sake da kuma tsantsar mamaki,duk wanan maganar da take ba xasu ce ga abu guda da suka fahimta ba "mi kenan hakan yake nufi?" Ladi ta Jefa tambayar asaitin Uwatale "To nima ina na fahimci maganar d tayi, kawai dai tana wani surkullenta ne, mukam ai mun hadu da masifa da jidali, kuzo muje mu samesu sai mu tambayesu." 

  

 "Amma ina da wani kokonto fa" ta juyo da kallonta saitin Haajara "mazajenmu sun zo nan dan su miki bore akan Annobar farin da muka fiskanta, sai dai abin mamaki suna xuwa nan kuma sai ga ruwa, hakan baya cikin surkullenki ne? Wanan zai zama rainin hankali ne fa."

 "Kwarai kuwa Uwatale, maganarki gaskiya ce, muma abin da ya daure mana kai kenan, amma saboda ta raina mana wayo shine tace bata surkulle, to masallaci kike yawo da shi akanki kenan?" Ladi ta jefa mata maganar ta qarshe da izgilanci, wanda yasa sauran matan suka kaure da ihu "Baki da dama Ladi" suka fada suna jinjina mata.


Tsayuwarta ta gyara tana goge ruwan da ya jiqa mata jikinta, sanyi take ji ta ko ina yana ratsata, ko kadan bata kaunar ruwan sama ya daketa, hakan yana sata mura sosai Wanda zata dauki tsawon lokaci tana fama da ita.

 "Wanan Ikon Allah ne, mutum baya yin sihiri dan yin wani abu wanda Allah kadai yake da iko akan yinsa, sai dai idan ya roqeshi xai kawo masa dauki, haqiqa Addu'a makami ce ga duk wani mummuni mutqar ya yarda da ita."kanta ta dafe da yake Sara mata sakamakon dukan da ruwa yake mata " Ku samu mazajanku Ku tambayesu, zasu muku bayani dai-dai fahimtarsu, ina jin rashin wadatacciyar lafiya atare dani." Tana gama fadar haka ta shige daki ta barsu atsaye sunyi tsamo tsamo cikin ruwa, kasa cewa komi sukayi suka fice xuwa lokacin ihun da su Mudi suke ya sarara sai maida zance suke akan abin da ya wakana, sai dai fa Mudi harda qarin dan gishirinsa akan cewar ido ta rufe ta bude shi jajiri sai ga ruwa ya sauqo, anan fa mutane suka dinga fadar nasu qarin gishirin da qaryar, madadin a samu sauyi na rayuwarsu sai qara afkawa da sukayi ga 6ata..


 Ahaka aka dai sukayi ta tsaigumi da yamudidi agari, har xuwa lokacin Da suka gaji dan Kansu suka bari.

Sai dai atsakanin lokacin babu wani sanji da aka samu dan tun da sukaga an samu yawaitar amfanin gona suka ci gaba da tafiyar da rayuwarsu kamar da, haka basu fasa zagin Haajara da muzguna mataba, asalima yanzu kowa ya dauke wuta akan lamarinta, babu masu mata magana cikin dadin rai ko ita tayi musu a daddage suke mata,dan har yanzu suna adawa da zamanta agarin da kasancewarta silar komi na wargajewar kwanciyar Hankalinsu.


********Bayan shekaru Biyar.


Rayuwa ta ci gaba d tafiya da dadi babu dadi, acikinta an samu sauye-sauye na raguwar hali da mungwayen dabi'un mutanen garin an kuma samu sauqin camfin da sukeyi, duk hakan ya faru ne ta sanadin tsayiwar da Haajara tayi da haquri da jajircewa akan mutanen garin, dan bata fasa sanar da su gaskiyaba da kuma yi musu magana duk da sharetan da suke yi. Har xuwa kuma wanan lokacin bata sake samun labarin Adda Sa'adah ba, haka kuma babu wani saqo da aka nemeta da shi agarin nasu.

Abdallah yayi wayo ya qara baki, ya taso da kazar-kazar da fara'a ko kadan baka ganinsa da fushi ko yaushe fiskarsa da dariya sai dai hakan bai hana yara sa'anninsa cin zalinsa ba, idan ya zo wasa da su babu wanda yake kulashi dan iyayensu sun hanasu wasa da shi acewarsu zai maida su mahaukata, hakan yasa da ya fita suke cin zalinsa su bishi da duka, sai dai ya koma Gida yana kuka.


 Ganin yanayin da yake ciki yasa Haajara Neman alfarma akan Hamxa ya kai shi makaranta boko da aka bude a qauyen dake baya da su. Shima tinanin da yake azuciyarsa kenan amma yana Shakkar mutanen garin da abin da zai biyo baya, amma idan yayi la'akari da ci gaba ne na yaronsu sai yakega gara ma ya kaishi Indai magana ce ta mutanen garin dama halayyarsu ce.

 Hakan kuwa akayi bai tsaya shawara da kowaba ya nufi gidan Baba Lawan wanda ayanxu ya qara manyanta kai tsaye ya sanar da shi abin da yake shirin aiwatarwa, da kuma neman shawararsa akan amincewarsa ko a'a.

 Wanan maganar ta farantawa Baba Lawan fiye da tsammanin Hamzan "Haqiqa tun lokacin da naga Haajara da tarbiyyar gidansu naji araina ita alkhairi ce acikin zuri'ar mu, sai dai ban San alkhairin zai fara a kan fafutukar Neman ilimi ba, aduka cikin kauyen nan babu wanda ya ta6a kai yaransa makaranta duk da sai da aka zo aka sanar damu kafuwarta, ni kaina yanzu takaici nake na ganin sauran yaran en uwanka suna yawo agari amma sun Qi kaisu makarantar, duk da qoqarin da nake akan hakan yaqi yiyuwa." Numfashi yaja yana fadada fara'arsa "Ka zama zakka acikin zuri'armu Hamxa, Allah yayi maka albarka, na bada goyon baya kaje ka kai Abdallah makaranta, ka toshe kunnenka akan duk abin da mutanen garin nan zasu fada ciki kuwa harda Iyayenka."

Wani farin ciki ne ya cika Hamxa bai ta6a hasashen zai samu goyon baya daga wajan Baba Lawan ba, duk da cewar yasan bashi da matsala da damuwa, gaza 6oye farin cikinsa yayi ya shiga yima Baba Lawan godiya, Kansa ya shafa yana murmushi, komi na Hamza da ban yake da na mutanen garin, wani lokacin yana mamaki da kasancewarsa haka, amma idan yayi duba da yanda ya fara rayuwa acikin wayayyun mutane hakan ba komi bane face dace da yayi.

Bai qara 6ata lokacina ya sanar da Haajara yanda sukayi, itama tayi mamaki tayi murna, su dai komi na su idan ya zo giftawa Baba Lawan ne kadai bazai nuna adawa da qyamatarsa ba.

Daukan Abdallah yayi ya kaishi makaranta kyakkyawar tarba ya samu daga malaman makarantar harda kuma Uniform da litattafan yaron kyauta suka bashi, suka qara da sanar da shi gobnati na daukan nauyin karatun yaran har xuwa kammalawarsa, godiya yayi ta yi musu yana jin farin ciki aransa. Haka ya dawo gida cike da murna ya shedama Haajara itama Hamdalah tayi tana godewa Allah da komi yake xuwa musu cikin nasara.

Ahaka Hamxa ya fara kai Abdallah makaranta idan ya dawo gida kuma Haajara ta masa bitar karatun da aka musu ta kuma koya masa littafan Addini da Alqur'ani mai girma, kafin wani lokacin karatu ya fara zama abakin Abdallah kasancewarsa yaro mai kwanya gashi ba wasa yake fitaba balle ya samu abin da xai shiririntar da shi.

Lokacin da mutanen Gumsa suka farga da karatun da Hamza yake kai Abdallah ji sukayi ina wuta su afka su ranar haka suke ji, ganin Abdallah da shigar makaranta ya qara musu jin qiyayyar su Hamxa da Haajara ga Hassada wadda ta cika zukatansu, musamman wasu daga cikinsu suka tareshi da maganar "Yanzu Hamza dan rashin sanin ciwon kai da nuna rashin kishi sai da ka dauki danka ka kaishi makarantar boko, kaf garin nan wa kaga ya kai yaron sa? Sai kai da baka rabo da abin da xa'a na cewa kaine."

 Murmushi yayi ya gyara tsayuwarsa "Wanan ai ba abin damuwa bane, idan kuka duba ci gaba ne sosai arayuwar yaranmu, kuma ya kamata Ku saka naku yaran dan yanxu wanan karatun da kuke gani abin alfahari ne arayuwarsu ta gaba, bamu San mi Allah zaiyi agaba ba, ta iya yiyuwa su xama wani abun arayuwarsa ta gaba."

"Allah ya tsare mu, kai dai da ka sa kanka sai kaje ka qarata, mine sabo acikin karatu wanda bamu ganiba, aikin banza aikin wofi, ai ni Iyayenka su suka barka kake tayin abin da ka ga dama agarin nan aka rasa wanda xai taka maka birki, mi za'ayi da haihuwa irin taka Aradu gara ace 6ari akayi da bamu fiskanci wanan tijarar da muke gani agari ba."

 Zuciyar Hamza ta motsa da maganar Mudi wanda ko kadan baya wajan amma sai tsintar maganarsa yayi, shi baiga abin da ya tarewa mutanen nan ba, dai-dai gwargwado yana girmamasu yana sauqe nauyin da yake kansa amatsayinsu na manya, amma ko yaushe suna jifansa da munanan kalamai, ko tari bai masaba ya sa kai ya wuce ji yake da bai girmeshi ba da babu abin da zai hana shi dukansa, amma ina ya girme masa da shekaru "Aikin banza kai, mu za'a yima feleqe da nuna barikancin an auri diyar fulani." Mudi ya ci gaba da magana da kumfar baki su dai mutane sai tayashi suke da nasu mitar.

Haka a 6angaran iya Indo itama da labari ya risketa tuni ta tasamma gidan Hamza ta fara tijata da fada, akan Hamza ya rainata da baiyi shawara da itaba ya zartar da hukuncin da zuciyarsa take so. Haquri ya bata yana kwadaita mata dadin da ke cikin karatun harma da sheda mata Baba Lawan ne yace ya kaishi.

Jin batun daga Baba Lawan ya fito yasata yin shuru amma tana shakkar maganar ace duk garin nan babu inda ake samun matsala da kawowa sauyin lamari sai agidanta, wanan maganar ta tsaya mata har ta kasa yin haquri sai da ta tasama Baba Garba batun "mi yasa shi Yaya Lawan kullum gadararsa akan yaronmu ne? Bayan ga nasa yaran bai sa sun kai jikokinsa makaranta ba sai da abin yazo ta kan Hamxa, gaskiya haquri na kusa gazawa awanan 6angaran, ya kamata ya barmu mu sauqe namu nauyin na iyaye da yake kanmu, ya barmu muyi iko da yaron mu a taqaitaccan lokacin da ya rage mana."

 "Gaskiyar maganarki Yaya Indo, ni ai naso da wuri nazo muka je gidan Hamxan da babu abin da zai sa ki barshi, dole sai ya fidda Abdallah daga makaranta, wanan ai yafi auro uwarsa da yayi zunibi, duk garin nanfa babu wanda ya ta6a kai dansa makarantar ko ta hanyar makarantar hana bi akayi, amma da yake shi tabbatacce ne ya kuma gawurta sai da ya dauki dansa ya kaishi."


 Tagumi Baba Garba ya rafka sanan yayi mulmul da baki wanda yake nuni da abin na bashi takaici, kafin ya dai-daita zamansa ya fara magana cikin karaya "Sanin kanku ne bamu da qarfi da zamuja da Yaya Lawan idan kuka duba girmansa da matsayinsa akanmu, haka kuma shaquwar da take tsakanin sa da Hamza, ta ko ina muka ce xamu shiga lamarin to zamu zama abin nuni agarin nan, yanzu ma ya aka qare balle kuma aga mun fara fada atsakaninmu Wanan ai abin kunya ne." 

Shuru duka sukayi suna jinjina maganat Baba Garba haka kuma sun haqiqance da gaskiya ya fada, sai dai ko kadan zuciyar Iya Indo ta bushe akan wanan karar ta gaji da ganin qunci da yake faruwa ta sanadin yaronta.

Miqewa tayi azafafe "Inaa bazan Juri hakan ba, awanan ga6ar dole na tankawa Yaya Lawan koda mutanen garin nan zasu taru atsakiyar kaina ne."

  "Ina goyon bayanki nima Yaya Indo, babu dalilin da zai sa ki Haifa anuna miki Iko akan sa." Harira ta fada tana qara tayata zafafa lamarin, kallonsu Baba Garba yayi cikin rashin sanin abin da suke shirin yi, Ba dai Tawaye xasu yima Yayansa Lawan ba??


  


   "Washhhhh Na gaji fa yini guda ina abu daya"


 Amma mi kukega Iya Indo da Gwaggo Harira zasuyi ??? Kuci gaba da bibiyata acikin labarin Hadin Gwarmai ina mutqar godiya ga daukacin masoyana, sosai nake yinku Allah ya bar kauna..

  


 © by Um Nass 

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: HAƊIN GWARMA 🎊


©by 😘Um Nass🏇


  BARKANMU DA SALLAH ƳAN UWA. ALLAH YA MAI-MAITA MANA. 👏


  

Page 33


  Kallonsu yake yana wir-wirga idanuwansa a saitinsu, ganin da gaske suke ga kuma k'arin baɗama miya gishiri da Harira takeyi yasa shi mik'ewa tsaye ba tare da ya shirya ba "Ni dai kam babu ruwana, kun San halin Yaya Lawan sarai ba kanwar lasa bane, barin ke Harira kin San ba shiri kuke da shiba amma yanzu zaki k'ara rura wata wutar bayan ga wata can baki kai ga gama kasheta ba."

 "Uhmm Yaya Garba kenan, ai gaskiya na fad'a duk abin da yake yima Hamza ya ta6a k'ok'arin yima "Ya"yansa ne? Ina duk cikin jikokinsa babu Wanda yaje makaranta Boko sai Abdallah da yake ba jikan d'an cikin sa bane, Wallahi ina bayan Yaya Indo sai dai komi za'ayi ayishi."

 Goge fiskarta Iya Indo tayi wanda maganar Harira ta Sosa mata wani ciwo aranta, har yasa zuciyarta ta karya "Yau na k'ara tabbatar da k'aunar da kike min Harira, tunda har kika fahimci k'unci na akan batun nan, Nagode miki sosai da sosai." Ta k'arasa maganar tana face majina ahancinta, sanan ta kai kallonta ga Baba Garba "Kai dai kam kaji haushin kanka Garba, ko kadan baka san ciwon kanka ba, ga dai ƴar uwarka Harira yau ta fahimci ƙuncin da nake cikinsa, amma kai ka kasa jiyema kanka haushin, kada Allah yasa kayi ruwan mu harda koginmu ma."

Tana gana faɗar haka ta warci zaninta akan igiya "Zo mu tafi Harira, yau komi ta banjama banjam." 

Binta Harira tayi tana karkaɗa ƙafafuwa, da kallo Baba Garba ya bisu, amma ko kaɗan baiyi yunkurin tsaidasu ba, sai dai fatan sa'a da ya bisu da shi.


 Tafiya suke babu mai yiwa wani magana acikinsu, sai dai Harira da take ƙara azal-zala Iya Indo akan kada ta yarda da mulkin kama karyar da Yaya Lawan ke musu tsowon shekaru, har take ƙiran hakan da mugunta fitsarin fako, ya killace yaransa yana janyo musu abin kunya da gori agarin Gumsa. Wanan zugar ta ƙara tunzura Iya Indo har suka kai ga ƙofar gidan Baba Lawan bata ita tankama Hariranba, dan jin zuciyarta take kamar ta faso saboda fushi.

Cikin sa'a suka samu BaBa Lawan azaune aƙofar gida, babu wanda yayi masa sallama sai tsayawa da sukayi akansa, kallonsu yayi ya kauda kansa ba tare da ya tanka musuba.

"Wajanka muka zofa Yaya Lawan." Kallonsu yayi tuni ya gimtse fiskarsa wanda hakan ya sa musu jin shakkarsa. "Oho ai nayi zatan kun samu taɓuwar hankaline, kun zo buguzum-buguzum kamar sabin kamun hauka, uwar mi zan muku da kuka tsaya akaina haka? Ko kuwa ni ɗin sa'anku ne?" Ya ƙarasa maganar yana kwatsa musu tsawa, tuni sun zube awajan suna karkarwa, saboda tsorata da sukayi, ko da can Yaya Lawan bashi da wargi ko ba'a masa laifiba yaɓa neman dalilin yin faɗan, balle kuma aka taɓashi.

Bakinsu ne ya ɗauki karkarwa sunma rasa hanyar da zasu bi su faɗa masa abin da ya kawosu, sai mangarar junansu suke "Tun da baku da abin faɗa ku tashi ku bani waje marasa hankali kawai, kuna girma kuna ƙara tambaɗewa, ke kuma harira ki wuce gidanki zan haɗu da mijin naki shima idan shi yake barin haka sakaka kullum kina tafe, to ya sakoki dan bazai iyu ace baki da maraba da marar aureba." Jin hakan da Harira taƴi ba shiri ta arce da gudu dan duk abinta tana shakkar mijinta, haka tana tsoron abin da zai-kai-ya-kawo muddum akace Yaya Lawan ya sameshi da wanan batun.

 Basu tsaya sallama ba kowa ya kama gabansa, dan itama Iya Indo ta tsorata da maganar ta Yaya Lawan, kusan jurwaye yayi musu mai kama da wanka, kada garin neman gira su rasa ido, itama ya kashe mata nata Auren.


Da numfarfashi ta isa gida tana haki, a inda tabar Baba Garba anan ta tarda shi "Har kun dawo? Ina Hariran kuma? Ko dai baku samu Yaya Lawan ɗinba?" 

"Dan Allah ka barni da wanan tsinanniƴar tambayar taka. Haba ko zama banyiba ka cika ni da tambaya, mi ake da hali irin na Yaya Lawan mutum sai ɗan banzan kwarjini kamar zaki." Ta ƙarasa maganar tana tsaki, jin kalmarta ta ƙarshe yasa Baba Garba ya fahimci inda maganar ta Iya Indo ta dosa, dama kuma abin da yake jiye musu kenan tun farko, murmushi yayi ya gyaɗa kai "Allah ya kyauta."

"Na gaba dan wanan kam ya riga daya faru." Ta cafe maganar cikin takaicin abin da Yaya Lawan ya musu, ai gara da Garba bai bisuba da ƙila yasa ya saketa awajan, da na shiga uku ni Indo. '

"Magana kike ne?" Baba Garba ya sake tambayarta, rufe bakinta tayi da hannunta dan batayi tsammanin zai jiyota ba "A'a ni kadai nake maganata."

Kai ya gyaɗa kamar ƙadangare dan ya kasa fahimtar inda ta dosa, amma idan ya tuna Baba Lawan da sanin da ya masa sai yaga hakan ba komi bane. Daga haka basu kara magana ba kowa da abin da yake saƙawa.


******

BAYAN SHEKARA BAKWAI.


 Awanan shekarun abubuwa da yawa sun faru anyi rashi da yawa ciki harda Baba Lawan da Baba Garba mutuwar da ta daki Haajara da Hamza wanda sunyi kuka sun gode daga ƙarshe suka samu dagana, sai dai har zuwa yanzu babu wani sauyi da ya samu na daga halayyar mutanen garin, haka karatun Abdallah yaci gaba da tafiya dai-dai gwargwado, kuma Hamza ko kaɗan bai gajiya wajan dawainiyar kaishiba, awanan lokacin Haihuwa ta ɗaukema Haajara cak tun tana damuwa akan rashin haihuwarta har ta samu dangana, Hamza ke bata baki akan Abdallah ma ya ishesu wani ya nemi ɗayanma bai samu ba, ammafa ba'a nan damuwar takeba musamman Iya Indo take rufo kai ta samu Haajara ta zageta tass akan ta zama juya ta kuma zame musu Annoba da masifa, wani faɗan ma bashi da amfani haka Haajara zata sha kukanta ta lallashi kanta dan bata fatan Hamza ya ganta awanan ranar.

Haka aɓangaran Abdallah ya gama primmary ya ɗora da makaranta gaba da ita, har awanan lokacin Hamza ke kaishi a kekensa ya ɗaukoshi, mutanen gari kuma basu fasa magana akan dakon wahlar da Hamxa yakeyi ba, wasu ƙirama suke ya haukace da surkullen mutane, amma hakan bai damu Hamza ba dan farin ciki yakeyi sosai idan yayi la'akari da yanda Abdallah yake da ƙoƙari amakaranta, haka kuma malamansa suna ji da shi kasancewarsa ɗalibi mai hazaƙa, ga fara'a dan da wuya ayi faɗa dashi, hakan yasa ya rike miƙamin shugaban ɗalibai tun a prmry ɗinsa, yanzu ma da yake jss1 yana amatsayin shugaban ajinsu ne, dan makaranta ahaɗe take da ci gabanta, ga nauyin karatun da gobnati take ɗauka, dan har wanan lokacin mutanen garin basuyi amana da karatun zamaniba, ƴan ɗai-ɗaikun mutane ne suke ƙokarin tura yaransu, suma ba kullum suke zuwaba, sai sun bushi iska, amma Abdallah baya wanan fashin ko kaɗan asali yana karɓan ƙyautukan ɗalibin da yafi ko wanni ɗalibi zuwa makaranta, ta ko wani fanni yana zama na ɗaya ne. Wannan kesa iyayensa alfahari da kuma rufe kunnuwansu daga jin maganganun mutanen garin.

BAƘAR RANA:

Baƙar ranar da ta wargaje komi na farin cikin da yayi saura arayuwar Haajara, ranar da ta kira da rashin sa'arta acikin duniyarta.

Wayewar garin da suka tashi da matsanancin tashin Hankali, gawar Hamza aka kawo mata jikinsa duk jini ko gane kamannisa ba'ayi, gefe ɗaya kuma Abdallah ne yake ta ihu shima kayansa sun rine da jini, Hatsarin mota sukayi ahanyar su ta dawowa daga kai Abdallah makaranta, wata mota akori-kura tabi ta kan su kasancewar akan keke suke, abin yazo ma da Hamza da ƙarar kwana ko shurawa baiyiba ya mutu, mai motar bai tsayaba ya ranta aguje sai Abdallah da ko ƙwarzanan ciwo babu ajikinsa.

Zuciyarta ce ta buga da ƙarfi ganin gawar Hamza agabanta, ɗuf taji acikin kanta komi ya ɗauke, kamar bata atare da ruhinta kafin ayi wani yunƙuri tuni ta zube awajan bata numfashi. 

Sallati mutanen wajan suka ɗauka "Shikenan itama ta bi sahun Hamza, tabi bayansa ta mutu" ɗaukacin mutanen da ke wajan suka faɗa. Sai dai babu wanda yayi yunƙurin ya tabbatar da gaske ne Haajaran ta mutu ko kuwa dai tsorata ce ta sata doguwar suma, ahaukace Iya Indo ta shigo gidan tana runtuma ihu ita da Gwaggo Harira.

"Ku kauce ku bani waje, shikenan Haajara kinyi nasarar ganin bayan ɗana, ni nasan wanan tsinanniyar makarantar da babu alkhairi acikinta itace zata zama ajalinsa, ashe hasashena ya zama gaskiya, yau Hamza kabi sahun Garba ka barni ni kaɗai da tarin Annobar iyalinka." tana maganar tana runtuma ihun kuka wanda acikin mutanen masu ɗan imani suka fara matsar hawaye.

 "Ai ga matar tasa can ma ta mutu itama ganin an kawo gawarsa." wani mutum ya cafki maganar yana matsar ido.

Sai alokacin suka kula da Haajaran wanda ta fadi babu ko alamar numfashi, Abdallah na rungume da Ita yana kuka, afusace Iya Indo ta tashi ta nufi kansu kafin mutane su farga ta shiga dukan Abdallah da Haajara wanda ba ko numfashi batayi "Ni zaku ha'inta, laifin mi ɗana ya muku? Mi yasa kuka saka masa da mutuwa? Shegen Yaro kai ko ƙwarzanan ciwo babu ajikinka, amma ga gawar Ubanka nan ashimfiɗe, ni kokwanto nake akan wanan ba hatsari bane wata ƙullalliyar kuka haɗa, mi yasa kai baka ji ciwoba sai shi ɗaya ne?" maganar da Iya Ido take cikin ruɗewa da gushewar hankali tana dukan su Haajara da Abdallah, amma acikin mutanen babu wanda yayi yunƙurin hanata wasu ma da yawa cewa suke "Aifa wanan abin dubawa ne ga dai Abdallah babu ko ƙwarzanan ciwo ajikinsa, kamar badashi akayiba, cuta kam an riga da an cuceki Indo."

Anan kowa ke tofa albarkacin bakinsa, abin takaici babu wanda yayi yunƙurin masa wanka akillaceshi dan kaishi makwancinsa na gaskiya.

Wani dogon numfashi Haajara ta jaa wanda ya tsorata iya Indo ba shiri taja da baya daga dukanta da takeyi, motsi ta farayi da hannayenta da ƙafafuwanta anan mutane suka fara ja da baya dan tsammaninsu mutuwa tayi ta dawo, ko kaɗan sun manta da batun suma tayi ta dawo, ahankali ta fara buɗe idaninta ta fara kallon mutanen wajan ɗai-ɗai wanda dukansu atsorace suke, baya Iya Indo da take jin zuciyarta na bugawa kamar zata faso ƙirjinta dan tsoro, idonta takai ga gawar Hamza wanda yake shimfiɗe agabanta cikin jini fiskarsa kamar mai murmushi, _"Bana son al'adar garin nan mai cike da bidi'a Haajara, ko mutuwa mutum yayi basa iya masa wankan da musulunci ya shara'anta, abin takaicima kawai ruwa ake kwara maka atashi akaika da ƙyar ake iya samu agabatar maka da sallah, Nikam idan na mutu ke zaki min wanka ki shiryani cikin likafani na, bana buƙatar ace jahilan mutanen nan sun min."_ 

_"Haba Abu Abdallah mi ya kawo batun mutuwa da wankan gawa awanan lokacin, nikam bana fatan Allah ya ɗauki ranka ya barni dan duniyata zata min faɗi zan rayu cikin tsoro, ban san ya zan kwatanta makaba, amma na roƙeka kabar wanan maganar, tun yanzu jin zuciyata nake kamar zata faɗo saboda tsoro."_ Hawaye yabiyo bayan maganar ta Haajaran, kai Hamza ya girgiza yana murmushi "Banda abinki Haajara mutuwa ai dolece, tana kuma kan kowa, bamu san yaushe ne zata ɗauke mu ba, yanzu ne gobe ne ko anjima ne, dole wata rana dai za'a wayi gari babu mu, ina faɗa miki haka ne dan ki sauƙe nauyin da yake kanki aduk lokacin da akace na rigaki mutuwa, haka kuma idan kece kika rigani mutuwa nima ni zan miki wanka, karki min kukan mutuwa, kiyi haƙuri da abin da na taɓa yi miki ki yafeni ki kuma yawaita yimin Addu'a da Sadaka idan na mutu, ki kula da Abdallah kici gaba da bashi ƙarfin gwuiwa akan neman ilimi da juriya, Nasan zaki shiga maraici zakisha wahla aduk lokacin da kika wai-waiya baki ganniba, ban san mi zai faruba amma nasan zaki fiskanci ƙalubalen rayuwa akewaye da maƙiyanki." Numfashi yaja yana ƙoƙarin danne hawayen da yake son zubo masa, dan tuni Haajara ta ɓarke da kuka ta duƙunkune ajikin Hamxan shafa kanta yake alamar lallashi, yana so ace bakinsa ya kulle yayi shuru, amma yanaji kamar ana ƙara angizashi akan yin maganar, jikinsa yake ji kamar ba nasa ba, ga yawan faɗuwa da gabansa yakeyi _"Inama ina da iko da dama da zan roƙi mutuwa ta jinkirta min zuwa wani lokaci, sai dai mutuwa bata sallama balle ta ƙwanƙwasa ƙofa, kiyi haƙuri kinji ki rungumi Abdallah kiyi Addu'a alokacin da kika shiga ƙunci Allah yana tare da ke."_ Hirar da sukayi da sukayi da Hamza adaren jiya ta shiga dawo mata kamar alokacin yake faɗa. "Ashe dama da gaske Hamza yake da yake cewa zai tafi ya barta? INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN" kalmar da ta shiga mai-maitawa acikin zuciyarta kenan, idanuwanta sun bushe sun ƙeƙashe daga zubar hawaye, tashi tayi ta nufi gawar Hamza ta ɗaga kansa tana kallo, bata so tayi masa hawaye kamar yanda ta buƙata, so take ta samu karfin zuciyar da zata cika wasiyyar da ya bashi ta hanyar cika masa muradinsa. Kallon Abdallah tayi da yake rakiɓe a inda ta tashi yana sauƙe ajiyar zuciya, tabbacin yasha kuka ya more, sai mutanen da suka matsa can nesa suna aika mata da kallon tsoro, ga Iya Indo da suka haɗe kai ita da Harira suna faman karkarwa, bata fahimci yanayi da suke cikiba, ta juya kallonta ga Abdallah ya fito shi tayi da hannu ya taso ɗa saurinsa, "Zaka iya kama min Abbanka mu kaishi banɗaki mu masa wanka?"

Kai ya gyaɗa alamar zai iya, sai dai ba abu ne mai sauƙi ace sun iya ɗaukan gawa su biyuba, kallon mutanen wajan tayi da suma suka zuba mata ido suna kallon sabon fi'ili.

 "Dan Allah ku taimaka min ku kaishi banɗaki zan masa wanka na suturceshi." kallon-kallo aka shiga yi amma ganin idonta arine jajir dashi yasasu saurin kinkimarsa, dan har yanzu gani suke kamar itama gawarce ta miƙe.

 Bin bayansu sukayi ita da Abdallah ta haɗa ruwan ɗumi wanda ta ɗora dan yin Abincin rana wanan tashin hankali ya samesu.

 Kallon su mutanen wajan suka tsaya, ganin yanda suke masa wanka ita da Abdallah cike da nutsuwa mataki-mataki.

Abin sai ya zame musu sabo suke ganin kamar sun muzanta ashe su kwamacala suke, ahaka suka gama ta sanya masa likkafani da taimakon mutanen wajan, sanan aka fito dashi tsakar gida anan ta daɗe tana masa Addu'a ta neman yafiya da rahma, kana mutane suka ɗaukeshi aka fita dashi, har awanan lokacin lokacin idanuwan Haajaran aƙeƙashe suke babu alamar hawaye, Iya Indo kam anci kuka an gode ana ta makawa Haajara harara dan lokacin da akazo fita da gawar Hamza ihu tasa tana birgima tana Adawo mata da shi.


  

  "Ban san ya zakuji aranku akan wanan shafinba, amma nima nA rubutashi badan yamin daɗiba, sai dan zuwan labarin ahaka."


©Um Nass


HAƊIN GWARMA 🎊


©by 😘Um Nass🏇


  BARKANMU DA SALLAH ƳAN UWA. ALLAH YA MAI-MAITA MANA. 👏


  

Page 33


  Kallonsu yake yana wir-wirga idanuwansa a saitinsu, ganin da gaske suke ga kuma k'arin baɗama miya gishiri da Harira takeyi yasa shi mik'ewa tsaye ba tare da ya shirya ba "Ni dai kam babu ruwana, kun San halin Yaya Lawan sarai ba kanwar lasa bane, barin ke Harira kin San ba shiri kuke da shiba amma yanzu zaki k'ara rura wata wutar bayan ga wata can baki kai ga gama kasheta ba."

 "Uhmm Yaya Garba kenan, ai gaskiya na fad'a duk abin da yake yima Hamza ya ta6a k'ok'arin yima "Ya"yansa ne? Ina duk cikin jikokinsa babu Wanda yaje makaranta Boko sai Abdallah da yake ba jikan d'an cikin sa bane, Wallahi ina bayan Yaya Indo sai dai komi za'ayi ayishi."

 Goge fiskarta Iya Indo tayi wanda maganar Harira ta Sosa mata wani ciwo aranta, har yasa zuciyarta ta karya "Yau na k'ara tabbatar da k'aunar da kike min Harira, tunda har kika fahimci k'unci na akan batun nan, Nagode miki sosai da sosai." Ta k'arasa maganar tana face majina ahancinta, sanan ta kai kallonta ga Baba Garba "Kai dai kam kaji haushin kanka Garba, ko kadan baka san ciwon kanka ba, ga dai ƴar uwarka Harira yau ta fahimci ƙuncin da nake cikinsa, amma kai ka kasa jiyema kanka haushin, kada Allah yasa kayi ruwan mu harda koginmu ma."

Tana gana faɗar haka ta warci zaninta akan igiya "Zo mu tafi Harira, yau komi ta banjama banjam." 

Binta Harira tayi tana karkaɗa ƙafafuwa, da kallo Baba Garba ya bisu, amma ko kaɗan baiyi yunkurin tsaidasu ba, sai dai fatan sa'a da ya bisu da shi.


 Tafiya suke babu mai yiwa wani magana acikinsu, sai dai Harira da take ƙara azal-zala Iya Indo akan kada ta yarda da mulkin kama karyar da Yaya Lawan ke musu tsowon shekaru, har take ƙiran hakan da mugunta fitsarin fako, ya killace yaransa yana janyo musu abin kunya da gori agarin Gumsa. Wanan zugar ta ƙara tunzura Iya Indo har suka kai ga ƙofar gidan Baba Lawan bata ita tankama Hariranba, dan jin zuciyarta take kamar ta faso saboda fushi.

Cikin sa'a suka samu BaBa Lawan azaune aƙofar gida, babu wanda yayi masa sallama sai tsayawa da sukayi akansa, kallonsu yayi ya kauda kansa ba tare da ya tanka musuba.

"Wajanka muka zofa Yaya Lawan." Kallonsu yayi tuni ya gimtse fiskarsa wanda hakan ya sa musu jin shakkarsa. "Oho ai nayi zatan kun samu taɓuwar hankaline, kun zo buguzum-buguzum kamar sabin kamun hauka, uwar mi zan muku da kuka tsaya akaina haka? Ko kuwa ni ɗin sa'anku ne?" Ya ƙarasa maganar yana kwatsa musu tsawa, tuni sun zube awajan suna karkarwa, saboda tsorata da sukayi, ko da can Yaya Lawan bashi da wargi ko ba'a masa laifiba yaɓa neman dalilin yin faɗan, balle kuma aka taɓashi.

Bakinsu ne ya ɗauki karkarwa sunma rasa hanyar da zasu bi su faɗa masa abin da ya kawosu, sai mangarar junansu suke "Tun da baku da abin faɗa ku tashi ku bani waje marasa hankali kawai, kuna girma kuna ƙara tambaɗewa, ke kuma harira ki wuce gidanki zan haɗu da mijin naki shima idan shi yake barin haka sakaka kullum kina tafe, to ya sakoki dan bazai iyu ace baki da maraba da marar aureba." Jin hakan da Harira taƴi ba shiri ta arce da gudu dan duk abinta tana shakkar mijinta, haka tana tsoron abin da zai-kai-ya-kawo muddum akace Yaya Lawan ya sameshi da wanan batun.

 Basu tsaya sallama ba kowa ya kama gabansa, dan itama Iya Indo ta tsorata da maganar ta Yaya Lawan, kusan jurwaye yayi musu mai kama da wanka, kada garin neman gira su rasa ido, itama ya kashe mata nata Auren.


Da numfarfashi ta isa gida tana haki, a inda tabar Baba Garba anan ta tarda shi "Har kun dawo? Ina Hariran kuma? Ko dai baku samu Yaya Lawan ɗinba?" 

"Dan Allah ka barni da wanan tsinanniƴar tambayar taka. Haba ko zama banyiba ka cika ni da tambaya, mi ake da hali irin na Yaya Lawan mutum sai ɗan banzan kwarjini kamar zaki." Ta ƙarasa maganar tana tsaki, jin kalmarta ta ƙarshe yasa Baba Garba ya fahimci inda maganar ta Iya Indo ta dosa, dama kuma abin da yake jiye musu kenan tun farko, murmushi yayi ya gyaɗa kai "Allah ya kyauta."

"Na gaba dan wanan kam ya riga daya faru." Ta cafe maganar cikin takaicin abin da Yaya Lawan ya musu, ai gara da Garba bai bisuba da ƙila yasa ya saketa awajan, da na shiga uku ni Indo. '

"Magana kike ne?" Baba Garba ya sake tambayarta, rufe bakinta tayi da hannunta dan batayi tsammanin zai jiyota ba "A'a ni kadai nake maganata."

Kai ya gyaɗa kamar ƙadangare dan ya kasa fahimtar inda ta dosa, amma idan ya tuna Baba Lawan da sanin da ya masa sai yaga hakan ba komi bane. Daga haka basu kara magana ba kowa da abin da yake saƙawa.


******

BAYAN SHEKARA BAKWAI.


 Awanan shekarun abubuwa da yawa sun faru anyi rashi da yawa ciki harda Baba Lawan da Baba Garba mutuwar da ta daki Haajara da Hamza wanda sunyi kuka sun gode daga ƙarshe suka samu dagana, sai dai har zuwa yanzu babu wani sauyi da ya samu na daga halayyar mutanen garin, haka karatun Abdallah yaci gaba da tafiya dai-dai gwargwado, kuma Hamza ko kaɗan bai gajiya wajan dawainiyar kaishiba, awanan lokacin Haihuwa ta ɗaukema Haajara cak tun tana damuwa akan rashin haihuwarta har ta samu dangana, Hamza ke bata baki akan Abdallah ma ya ishesu wani ya nemi ɗayanma bai samu ba, ammafa ba'a nan damuwar takeba musamman Iya Indo take rufo kai ta samu Haajara ta zageta tass akan ta zama juya ta kuma zame musu Annoba da masifa, wani faɗan ma bashi da amfani haka Haajara zata sha kukanta ta lallashi kanta dan bata fatan Hamza ya ganta awanan ranar.

Haka aɓangaran Abdallah ya gama primmary ya ɗora da makaranta gaba da ita, har awanan lokacin Hamza ke kaishi a kekensa ya ɗaukoshi, mutanen gari kuma basu fasa magana akan dakon wahlar da Hamxa yakeyi ba, wasu ƙirama suke ya haukace da surkullen mutane, amma hakan bai damu Hamza ba dan farin ciki yakeyi sosai idan yayi la'akari da yanda Abdallah yake da ƙoƙari amakaranta, haka kuma malamansa suna ji da shi kasancewarsa ɗalibi mai hazaƙa, ga fara'a dan da wuya ayi faɗa dashi, hakan yasa ya rike miƙamin shugaban ɗalibai tun a prmry ɗinsa, yanzu ma da yake jss1 yana amatsayin shugaban ajinsu ne, dan makaranta ahaɗe take da ci gabanta, ga nauyin karatun da gobnati take ɗauka, dan har wanan lokacin mutanen garin basuyi amana da karatun zamaniba, ƴan ɗai-ɗaikun mutane ne suke ƙokarin tura yaransu, suma ba kullum suke zuwaba, sai sun bushi iska, amma Abdallah baya wanan fashin ko kaɗan asali yana karɓan ƙyautukan ɗalibin da yafi ko wanni ɗalibi zuwa makaranta, ta ko wani fanni yana zama na ɗaya ne. Wannan kesa iyayensa alfahari da kuma rufe kunnuwansu daga jin maganganun mutanen garin.

BAƘAR RANA:

Baƙar ranar da ta wargaje komi na farin cikin da yayi saura arayuwar Haajara, ranar da ta kira da rashin sa'arta acikin duniyarta.

Wayewar garin da suka tashi da matsanancin tashin Hankali, gawar Hamza aka kawo mata jikinsa duk jini ko gane kamannisa ba'ayi, gefe ɗaya kuma Abdallah ne yake ta ihu shima kayansa sun rine da jini, Hatsarin mota sukayi ahanyar su ta dawowa daga kai Abdallah makaranta, wata mota akori-kura tabi ta kan su kasancewar akan keke suke, abin yazo ma da Hamza da ƙarar kwana ko shurawa baiyiba ya mutu, mai motar bai tsayaba ya ranta aguje sai Abdallah da ko ƙwarzanan ciwo babu ajikinsa.

Zuciyarta ce ta buga da ƙarfi ganin gawar Hamza agabanta, ɗuf taji acikin kanta komi ya ɗauke, kamar bata atare da ruhinta kafin ayi wani yunƙuri tuni ta zube awajan bata numfashi. 

Sallati mutanen wajan suka ɗauka "Shikenan itama ta bi sahun Hamza, tabi bayansa ta mutu" ɗaukacin mutanen da ke wajan suka faɗa. Sai dai babu wanda yayi yunƙurin ya tabbatar da gaske ne Haajaran ta mutu ko kuwa dai tsorata ce ta sata doguwar suma, ahaukace Iya Indo ta shigo gidan tana runtuma ihu ita da Gwaggo Harira.

"Ku kauce ku bani waje, shikenan Haajara kinyi nasarar ganin bayan ɗana, ni nasan wanan tsinanniyar makarantar da babu alkhairi acikinta itace zata zama ajalinsa, ashe hasashena ya zama gaskiya, yau Hamza kabi sahun Garba ka barni ni kaɗai da tarin Annobar iyalinka." tana maganar tana runtuma ihun kuka wanda acikin mutanen masu ɗan imani suka fara matsar hawaye.

 "Ai ga matar tasa can ma ta mutu itama ganin an kawo gawarsa." wani mutum ya cafki maganar yana matsar ido.

Sai alokacin suka kula da Haajaran wanda ta fadi babu ko alamar numfashi, Abdallah na rungume da Ita yana kuka, afusace Iya Indo ta tashi ta nufi kansu kafin mutane su farga ta shiga dukan Abdallah da Haajara wanda ba ko numfashi batayi "Ni zaku ha'inta, laifin mi ɗana ya muku? Mi yasa kuka saka masa da mutuwa? Shegen Yaro kai ko ƙwarzanan ciwo babu ajikinka, amma ga gawar Ubanka nan ashimfiɗe, ni kokwanto nake akan wanan ba hatsari bane wata ƙullalliyar kuka haɗa, mi yasa kai baka ji ciwoba sai shi ɗaya ne?" maganar da Iya Ido take cikin ruɗewa da gushewar hankali tana dukan su Haajara da Abdallah, amma acikin mutanen babu wanda yayi yunƙurin hanata wasu ma da yawa cewa suke "Aifa wanan abin dubawa ne ga dai Abdallah babu ko ƙwarzanan ciwo ajikinsa, kamar badashi akayiba, cuta kam an riga da an cuceki Indo."

Anan kowa ke tofa albarkacin bakinsa, abin takaici babu wanda yayi yunƙurin masa wanka akillaceshi dan kaishi makwancinsa na gaskiya.

Wani dogon numfashi Haajara ta jaa wanda ya tsorata iya Indo ba shiri taja da baya daga dukanta da takeyi, motsi ta farayi da hannayenta da ƙafafuwanta anan mutane suka fara ja da baya dan tsammaninsu mutuwa tayi ta dawo, ko kaɗan sun manta da batun suma tayi ta dawo, ahankali ta fara buɗe idaninta ta fara kallon mutanen wajan ɗai-ɗai wanda dukansu atsorace suke, baya Iya Indo da take jin zuciyarta na bugawa kamar zata faso ƙirjinta dan tsoro, idonta takai ga gawar Hamza wanda yake shimfiɗe agabanta cikin jini fiskarsa kamar mai murmushi, _"Bana son al'adar garin nan mai cike da bidi'a Haajara, ko mutuwa mutum yayi basa iya masa wankan da musulunci ya shara'anta, abin takaicima kawai ruwa ake kwara maka atashi akaika da ƙyar ake iya samu agabatar maka da sallah, Nikam idan na mutu ke zaki min wanka ki shiryani cikin likafani na, bana buƙatar ace jahilan mutanen nan sun min."_ 

_"Haba Abu Abdallah mi ya kawo batun mutuwa da wankan gawa awanan lokacin, nikam bana fatan Allah ya ɗauki ranka ya barni dan duniyata zata min faɗi zan rayu cikin tsoro, ban san ya zan kwatanta makaba, amma na roƙeka kabar wanan maganar, tun yanzu jin zuciyata nake kamar zata faɗo saboda tsoro."_ Hawaye yabiyo bayan maganar ta Haajaran, kai Hamza ya girgiza yana murmushi "Banda abinki Haajara mutuwa ai dolece, tana kuma kan kowa, bamu san yaushe ne zata ɗauke mu ba, yanzu ne gobe ne ko anjima ne, dole wata rana dai za'a wayi gari babu mu, ina faɗa miki haka ne dan ki sauƙe nauyin da yake kanki aduk lokacin da akace na rigaki mutuwa, haka kuma idan kece kika rigani mutuwa nima ni zan miki wanka, karki min kukan mutuwa, kiyi haƙuri da abin da na taɓa yi miki ki yafeni ki kuma yawaita yimin Addu'a da Sadaka idan na mutu, ki kula da Abdallah kici gaba da bashi ƙarfin gwuiwa akan neman ilimi da juriya, Nasan zaki shiga maraici zakisha wahla aduk lokacin da kika wai-waiya baki ganniba, ban san mi zai faruba amma nasan zaki fiskanci ƙalubalen rayuwa akewaye da maƙiyanki." Numfashi yaja yana ƙoƙarin danne hawayen da yake son zubo masa, dan tuni Haajara ta ɓarke da kuka ta duƙunkune ajikin Hamxan shafa kanta yake alamar lallashi, yana so ace bakinsa ya kulle yayi shuru, amma yanaji kamar ana ƙara angizashi akan yin maganar, jikinsa yake ji kamar ba nasa ba, ga yawan faɗuwa da gabansa yakeyi _"Inama ina da iko da dama da zan roƙi mutuwa ta jinkirta min zuwa wani lokaci, sai dai mutuwa bata sallama balle ta ƙwanƙwasa ƙofa, kiyi haƙuri kinji ki rungumi Abdallah kiyi Addu'a alokacin da kika shiga ƙunci Allah yana tare da ke."_ Hirar da sukayi da sukayi da Hamza adaren jiya ta shiga dawo mata kamar alokacin yake faɗa. "Ashe dama da gaske Hamza yake da yake cewa zai tafi ya barta? INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIRRAJI'UN" kalmar da ta shiga mai-maitawa acikin zuciyarta kenan, idanuwanta sun bushe sun ƙeƙashe daga zubar hawaye, tashi tayi ta nufi gawar Hamza ta ɗaga kansa tana kallo, bata so tayi masa hawaye kamar yanda ta buƙata, so take ta samu karfin zuciyar da zata cika wasiyyar da ya bashi ta hanyar cika masa muradinsa. Kallon Abdallah tayi da yake rakiɓe a inda ta tashi yana sauƙe ajiyar zuciya, tabbacin yasha kuka ya more, sai mutanen da suka matsa can nesa suna aika mata da kallon tsoro, ga Iya Indo da suka haɗe kai ita da Harira suna faman karkarwa, bata fahimci yanayi da suke cikiba, ta juya kallonta ga Abdallah ya fito shi tayi da hannu ya taso ɗa saurinsa, "Zaka iya kama min Abbanka mu kaishi banɗaki mu masa wanka?"

Kai ya gyaɗa alamar zai iya, sai dai ba abu ne mai sauƙi ace sun iya ɗaukan gawa su biyuba, kallon mutanen wajan tayi da suma suka zuba mata ido suna kallon sabon fi'ili.

 "Dan Allah ku taimaka min ku kaishi banɗaki zan masa wanka na suturceshi." kallon-kallo aka shiga yi amma ganin idonta arine jajir dashi yasasu saurin kinkimarsa, dan har yanzu gani suke kamar itama gawarce ta miƙe.

 Bin bayansu sukayi ita da Abdallah ta haɗa ruwan ɗumi wanda ta ɗora dan yin Abincin rana wanan tashin hankali ya samesu.

 Kallon su mutanen wajan suka tsaya, ganin yanda suke masa wanka ita da Abdallah cike da nutsuwa mataki-mataki.

Abin sai ya zame musu sabo suke ganin kamar sun muzanta ashe su kwamacala suke, ahaka suka gama ta sanya masa likkafani da taimakon mutanen wajan, sanan aka fito dashi tsakar gida anan ta daɗe tana masa Addu'a ta neman yafiya da rahma, kana mutane suka ɗaukeshi aka fita dashi, har awanan lokacin lokacin idanuwan Haajaran aƙeƙashe suke babu alamar hawaye, Iya Indo kam anci kuka an gode ana ta makawa Haajara harara dan lokacin da akazo fita da gawar Hamza ihu tasa tana birgima tana Adawo mata da shi.


  

  "Ban san ya zakuji aranku akan wanan shafinba, amma nima nA rubutashi badan yamin daɗiba, sai dan zuwan labarin ahaka."


©Um Nass

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARAMAI 🎊*


©by *😘Um Nass 🏇🏼*


® *NWA*


*_INA TAYAKI MURNA ƴar Uwa Batul Mamman da ƙarƙare labarin KASHE FITILA da kikayi, haƙiƙa labarin ya faɗakar fiye da yanda mutum zai kwatantashi, ya kuma nishaɗantar na sosai da sosai acikin abin da yake faruwa awanan rayuwar akuma duniyar nan tamu baki ɗaya, duk wanda take karanta novel bata karanta shiba zan iya cewa ba novel ɗin take karantawaba kawai tana bulayi ne wajan lalimar abu marar amfani, mun gode kwarai Allah ya ƙara miki Fikra da hazaƙa har Abada bazamu mantaki ba, muna kuma biye da ke aduk kanin labarin da kika fara._*


 *AKANCE YABON GWANI YA ZAMA DOLE*

_WANI Lokacin baka sanin kimar da take tare da mutum da nagartarsa sai har zama ya haɗaku, A Yau ina shedawa Duniya muhimmancin da ke tare da zama da mutumin kirki wanda yake sadaukar da lokacinsa saboda ya dafawa wanda suka haɗu dashi koda bai sanshiba, kamar haka ne Atare da ƴar uwata *SANAH S MATAZU* Nagode adukkanin komi, *Anty Maijidda Musa* kece silar kasancewata da mutane na gari, wanan shafin Sadaukarwa ce agareki._


 Page 34


Gidan ne yaci gaba da hargitsewa da ihun mutane na koke-kokensu, wanda da yawa sunayi ne dan su nunama iya indo suna tare da ita, suna kuma tayata kukan rashin ɗanta guda ɗaya data mallaka.

Sai dai hakan ya gaza a ɓangaran Haajara dan idanuwanta ya ƙeƙashe daga zubar ƙwalla, wani ɗaci ne yake kewaye maƙoshinta, gani take kamar ba gaske bane, taya ma za'ace Hamza ya tafi ya barta awanan lokacin da take buƙatarsa, amma kuma gaskiya ne, da hannayenta tayima Hamza wankan gawa, ta kuma killaceshi da tufafin da ya zama gadon kowa, shikenan dai rayuwar, yanzu wani jin daɗi ne ya rage mata? Babu shi adai wannan duniyar tata.

Kallon mutanen wajan take ɗai-ɗai tana ji inama itace take kuka da hawaye, amma ba irin nasu kukan na kururuwa da tanadar ma kai azaba ba, kuka take sonyi na samun sassauci daga zafin raɗaɗin da take ji acikin zuciyarta. Gefe guda kuma Abdallah ne atakure yana ta jan zuciya, tabbacin yayi kuka ƴa gode, yafito shi tayi da hannunta dan ko kaɗan bata jin bakinta zai iya buɗewa da sunan yin magana.

Tahowa yayi da saurinsa ya faɗa jikinta yana jan zuciya, kai ta shiga shafa masa tana bubbuga bayansa, da ƙyar ta iya buɗe bakinta ta fara masa magana da sarƙeƙƙiyar muryarta mai cike da rauni "Ya kamata ka ƙarfafa zuciyarka Abdallah, kaje ka sauƙe nauyin dake kanka amatsayinka na ɗa guda da ya mallaka, ka tafi da wanda suka ɗaukeshi, ka masa sallah ka kuma rakashi makwancinsa, ka nema masa rahma da sassauci daga Mahaliccin kowa da komi, wanan kaɗai yake buƙata atare da mu, shine gatan da zamu masa amatsayinmu na masoyansa."

Kamar an zabureshi ya miƙe tsaye, yana ƙarfafa ƙafafuwansa da son ɗaukar nauyinsa ya nufi wajan da akema Hamza sallah, tare da shi aka gabatar da sallahr Gawar Hamza aka rakashi makwancinsa, duk da ƙarancin shekarunsa amma shine ya dage ya riƙe kan mahaifinsa tare da taimakawar mutane uku suka dai-daita kwanciyarsa amakwancinsa, kowa kallonsa yake yana mamakin dauriyarsa da kuma jarumtarsa, kasancewarsa yaro ɗan shekara goma sha biyu aduniya yayi abin da manyan ma ke gagararsu aikatashi, dan da yawa acikinsu akwai wanda baya zuwa maƙarbata dan raka gawa, acewarsa yana tsoro ne, amma kuma abin mamaki sai ga Abdallah yazo ya kuma saka mahaifinsa cikin makwancinsa, ya tsaya yana rufeshi cike da dauriya da ƙoƙarin ɗauke hawaye acikin idanuwansa.

Bayan kammaluwar rufeshi ya tsugunna yana ta jero masa Addu'a, suma sauran mutanen sai suka tsugunna suna mulum-mulumtu da bakinsa, dan basu san mi zasu ceba ga kuma kunyar ƙaramin yaron da ya nuna ilimi da keresu afannin komi, har yanzu wanda suka tsaya akan wankan gawar Hamza suna ganin muzanci atare da su, duba da yadda mace ta tsaya tayi komi cike da kulawa da ilimi wanda abin sai da ya basu sha'awa da birgewa, ga kuma yaro ƙarami shima na ƙara dulmiyar da su acikin duniyar kunya da gajiyawa, shi yasa suka nemawa kansu madafa wajan tsugunnawa suna mulumtu da baki.

 Ya daɗe yana nemawa Mahaifinsa Rahma da gafara sanan ya miƙe haɗe da hawaye afiskarsa, murmushi yayi tunawa da san ran da yake mahaifinsa ya dace da samun Shahada da yardar Allah.

Wanan ya ƙara shagaltar da mabiyansa suka fara jin tsoron ko ya samu taɓin hankali ne, amma idan ba hakaba taya yane ana kuka shi yana hawaye da dariya, tsaki sukayi ahankali suka fara tafiya bakam-bakam dan yaɗuwar wanan guntun haukan na Abdallah acikin gari.


*******

A gefen Haajara kuma bayan tafiyar Abdallah ta miƙe tayi wanka kamar yanda musulunci ya bada Umarni akan duk wanda ya wanki gawa to shima wanka ya wajaba atare da shi, ta ɗauro Alwala kana ta sanya kayanta da suke marasa kyau da ƙaton Hijabinta, ta fara jero nafila tana nemawa Hamza Rahma da sassauci, sai alokacin hawaye ya zubo mata mai ɗaci musamman data samu tabbacin ta rasa Hamza rasawa na har Abada, ya kuma yi mata nisa nisan da bazata iya kamoshiba.

Jin ihun mutane da birgimar da su Iya Indo sukeyi yasata miƙewa tsaye ta fito waje duk da jirin da takeji da duhuwar data lilliɓe idanuwanta.

"Ku kuwa bayin Allah ku sauƙaƙama kanku da rayuwarku akan wanan koke-koken naku mana, wanda bashi da wani amfani face ƙarawa kanku dashi mamacin baƙar Azaba.

Dan Hadisi ya gabata daga Annabi s.a.w yana cewa "Anna'iha (mace mai kukan nutuwa, da kuma mai kira irin na jahilai (Itace wanda take ihu tana tumami tana kiran bango ya faɗi, ko gata ya faɗi, ko kuma dai ihu na kuka marar dalili), idan bata tubaba ta mutu to za'a tasheta ranar lahira tana sanye da tufafi na sarir (wani tufafi ne mai kama da sasari wanda yake ɗauke da wuta ajikinsa, wanan kayan shine wanda za'a sanyawa duk wata wadda take ihu da kururuwa mutƙar bata tubaba ta mutu.)"

Sanan cikin wani Hadisi shima Annabi S.A.W yace "KASHEDINKU da kukan mutuwa, dayiwa mamatanku ihu da kururuwa domin hakan yana ƙara musu narkon azaba ne." Kunga kenan ba so kuke nuna masaba haka kuma ba gata kuke nuna masaba wajan yi masa kuka da kururuwa, zaifi muku kyau kuyi Addu'a agareshi."

Ta ƙarasa maganar tana ƙoƙarin share hawayen dake zubo mata acikin idonta. Sai dai kafin ta farga tuni Iya Indo ta shaƙeta tana huci "Kunji min munafukar yarinya, ɗannawa ya mutu kice bazanyi kukaba, har yaushe aka haifeki da zakiyi ƙoƙarin hanani kuka, yanzu nake ƙara tabbatar da zargina akan cewar ke kikayi wani ƙulle-ƙullen da Hamza ya mutu dan ki gaje komi nasa, to na ganoki Aradun Allah ko tsinke babu wanda zai baki, Munafuka Algungumar yarinya, kin kashe iyayenki yanzu kin kashe min ɗana." Duka tana hakan ne tana hawaye ko ina ajikinta rawa yake, yayin da Haajara ta shiga kakarin azaba "Kaicon rayuwata, kaicon ruɗin dake cikin wanan duniyar nan idan har akace masoya suke ƙoƙarin kashe masoyinsu saboda wani ɗan abin duniya, mi zan samu aduniyar da babu Abu Abdallah? Kasancewarsa mutum guda ɗaya daya zama rumfa agareni, ya kuma yi saura acikin Duniyata." 

"Ƙarya kike, kina abu kamar wata mutuniyar kirki, ai mun san komi yanzu da babu Hamza sai ki zauna kici uwar da zakici acikin garin nan." Gwaggwo Harira ta cafe maganar, wanda dama tana da haushin Haajaran, gashi kuma ta zame musu Annoba da Alaƙaƙai acikin rayuwarsu.

Matan dake tsattsaye suna wajan sai baza idanuwa suke, suma dai maganar da Haajaran tayi ba wai gamsuwa sukayi da itaba, tun Iyaye da Kakani suke kukan mutuwa basu taɓa yin karo da wanan maganarba, tabbas biri yayi kama da mutum idan akace Haajara ce ta zama Silar Ajalin Hamza ba zasuyi mamakiba, musamman kasancewarta kaska mai raɓar jini, ga kuma ko alamun damuwa batayiba balle tayi hawaye, shi yasa ko kaɗan basuyi yunƙurin ƙwatarta ahannu Iya Indo ba dan kowata Uwa zata iyayin haka koma fiye da hakan.

"Kekam kina da takaicin Rayuwa Indo, ga ɗan banzan ƙwarin rai atare da ita kamar ɗiyar mayu, duk shaƙar da kika mata ta gaza ɗauke numfashinta." wata mata ta cafke maganar da ko kaɗan ba'a kasa da itaba, hakan ya ƙara hautsina zuciyar Iya Indo ta fara kilar Haajarar nan take numfashinta ya fara yin sama-sama, kafin wani lokaci tuni ta bar motsi awajan.

Nan hankalin mutanen wajan ya ƙara tashi kafin wani lokaci sun kwasa aguje suna ihu suna kiran Iya Indo ta kashe matar Hamza, ta ɗauki fansar yaronta.

Jin haka yasa jikin Iya Indo karkarwa dan bata shirya kashe matar Hamza ba, bata san tsautsayin da yasata aikata mata dukan da takeyi mataba, dan har ga Allah ta sani ita mutuniyar kirkice, acikin ko wata mu'amala tata tana ƙoƙarin kyautata mata, sai dai kuma ita ce ta zama silar mutuwar ɗanta tilo, taya zata iya yafe mata? Durƙushewa tayi awajan ta fara rizkar kuka, ko ina ajikinta rawa yake, sai dai kafin tayi wani yunƙuri tuni gidan ya ƙara cika da mutane, dan mazan da suka kai Hamza sun dawo suka iske mata na gudu suna kururuwar Indo ta kashe Haajara, nan suka rintimo aguje suma.

Sai dai kafin su farga Abdallah yayi kan Iya Indo yana jijjigata yana kuka, wanda hakan ya ƙara tsorata Iya Indo dan ko kaɗan yaron ya hargitsata ƙwayar idonsa ta isa ta tsoratata nan itama ta faɗi ƙasa asume....


  _Kuyi malejin wanan, duk da ƙarancin lafiyar dake tare dani ina son na ƙarfafawa kaina gwuiwa wajan bawa masoyana cigaban labarin, nasan awanan shafin ban faranta mukuba amma kuyi haƙuri da yanda labarin yake take, hakan Ƙaddara ce wanda take rubuce acikin rayuwar kowa, mutuwa kan bimu ta ƙwanƙwasa mana ƙofa koda ace bamu shirya zuwantaba, ita kuma Jarrabawar rayuwa anayima mummuni wanda yake da tsarkakkiyar zuciya ita ne. Nagode da dukkanin kulawarku akaina._


  


©bƴ Um Nass

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI 🎊*


© *😘Um Nass 🏇🏼*


® *NWA* 


_Ina Alfahari daku masoyana Aduk inda kuke, masu bibiyar labarin HAƊIN GWARMAI aduk inda kuke ina kaunarku wanan shafin duka mallakinku ne kuyi yanda kuke so da shi, Nagode._


Page 35


  Da sauri mutanen wajan suka ɗauka ruwan Randa mai sanyi suka shiga kwararawa Iya Indo da Haajara wanda hakan ya sasu jan doguwar ajiyar zuciya kamar haɗin baki, kamar an zabure su suka miƙe gaba ɗayansu sai alokacin Abdallah ya saki Iya Indo daga cakumar da-ya mata ya nufi Haajara ya rungumeta yana ajiyar numfashi akai-akai, kallonsa take kafin ta ƙara rungumeshi ajikinta, yanzu take jin cewar ta rasa komi da kowa aduniya, Abdallah kaɗai ya rage mata, ya kamata ta ƙarfafa zuciyarta kodan ta samu farin ciki, wanda tasan abune mai mutƙar wahla ace ya sameshi.

Kallonta takai ga mutanen wajan wanda har ta cika da mamakin ganinsu, dan maza ne jingim awajan idan ba ƙarya idanuwanta yake mataba zata iya cewa duka mutanen garin ne akanta maza da mata.

"Sannu Indo Allah ya baki dangana da haƙuri haƙika kinyi rashin yaro jarumi, sai dai kuma da alama Allah ya albarkaceshi da nagartaccen yaro mai nutsuwa." Liman ya faɗa yana kai kallonsa ga Abdallah wanda yake rungume da Haajara.

"Yau yaron nan yayi abin da ba'a taɓa yinsaba atarihin garin nan, dashi akayi sallahr gawar mahaifinsa aka binneshi ya tsaya yana ta jero masa Addu'a wanda dalilin haka muma muka tsugunna muna ta nemawa Hamza Rahma, karo na farko atarihin wanan garin namu da hakan ta faru, kuma duk adalilin jikankine, gaskiya Hamza yayi FARAR HAIHUWA wanda ta kafa tarihi mai kyau awanan garin namu, duk da muna masa kallon mahaukaci ne marar amfani acikinmu." ya ƙarasa zancan yana faɗaɗa murmushinsa domin dai har ga Allah yaron ya birgeshi yau, kuma yaji ya kwaɗaitu da rayuwar da yakeyi har yake hango shima za'a samu wanan sauyin agidansa.

Wani sanyine ya kwaranya azuciyar Haajara wanda babu tantama na farin ciki ne, jin labarin abin da yaronta ya aikata ya tabbatarwa da duniya cewa shiɗin mai ilimi ne, haka kuma ba mahaukaci bane kamar yanda suke hasashe akansa, sai dai bata kai ga matsaya da samun wanda zata raba wanan farin cikinba ta tsinkayi muryar Mudi ya cafe magana "Amma lallai Liman yau ka tabbata marar hangen nesa, duk nisan Iliminka ka kasa fahimtar inda alƙiblar da yaron nan yayi, abin kunya da tirr ne agaremu." tuni jikin Liman yayi sanyi dan shi baiga abin aibu a abin da Abdallah yayiba, yaron da yake komi da nutsuwa da ilimi, mine aibu da abin kushe anan? Idan banda rashin jin tsoron Allah da kuma son zuciya irin ta Mudi, sai dai kafin yayi yunkurin magana Mudi yaci gaba "To bari ni nayi magana ta gaskiya, Yau yaron nan ya nuna rashin Imanin da ke tare dashi, tun ina ƙarami ya iya jure zuwa kai gawa makwancinta, wanda sanin kanku ne ko mu manya sai mai ƙarfi da dauriya ke iya zuwa, sanan shi yayi bake-bake aka kwantar da babansa acikin kabari, kafin kuma kowa yayi yunƙurin fara rufeshi shine dai mutum na farko da ya fara tila masa ƙasa yana rufeshi, wanan ya nuna mana dama can ya ƙagu da mahaifin nasa yayi ya mutu yabar ganinsa, kuma ni har yanzu ban yarda mota ce ta bige Hamza ta ƙyale Audullah ba sai dai shirinsa ne wanda yabarwa kansa shida mahaliccinsa."

Tuni wajan ya kaure da hayaniya da ihun mutane, barin Iya Indo da ta ƙara ɓarkewa da kuka tana jijiga kai "Ɗana guda daya tak dana mallaka aduniyar nan, ya mutu mutuwar wulaƙanci da cin amana ta wanda yake so, wai ɗan cikinsa da matarsa da-ya-auro duk da ƙalubalen daya fiskanta akan auren amma sakamakon soyayyar daya nuna musu kenan." Share hawayen fiskarta tayi ta miƙe tana face hancinta "daga ranar yau ina so ku sheda babu ni babu iyalan Hamza har abada babu kuma abin da zai ƙara shiga tsakaninmu dasu, yanda suka kashe min ɗana na barsu da Allah zai saka min dai-dai da abin da suka min, kuma duk wanda yake ƙaunata ya dafa min wajan fita alamarin gidan Hamza da tausaya musu."

Tana gama faɗar haka ta fice waje fuuuu ƴan koronta suka bi bayanta suma suna ta aibanta Abdallah da tirr da rayuwar da suka ɗorawa kansu na cin Amana.

Miƙewa Liman yayi yana kallon Mudi "Kai dai mudi ka cika ibilishi mai tada zaune tsaye, amma babu komi da sannu haƙƙin yaron nan da izayar da-ka-masa zata juyo kanka, kuyi haƙuri Haajara, Allah yana tare da ku zai kuma kawo mumu ɗauki aduk inda kuke, ni dai bani da ƙarfin zuciya da wadatar da zan dafa muku." Yana gama maganar ya miƙe yana bibbiga rigarsa yana share hawayen tausayinsu da ya cika idanuwansa. Rayuwa da kalar jarrabawar da ƙaddara ke zuwarwa yarinyar nan yana tausaya mata, yana kuma jin tsoron abun da gobe zata haifar mata dashi, ayanda ya fiskanta mutanen garin najin haushinsu da burin ɗaukan fansa agaresu wanda bashi da dalili.

"Mtsss aikin banza mu za'ayima feleƙe da nuna an san Allah, ai kaima ba wani ilimi garekaba kake baza uban rawani da gemu kai gaka na Allah, to mudai mun faɗi gaskiya kuma muna kan bakanmu za'a dama damu iya damawa har muga ƙarshen maci amana." maganar mudi yana bin su Haajara da harara sanan suka fice duuuu shida tawagarsa da sukayi saura.

"Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, Allahumma ajirni fi musibati haza, wakallafni khairin minha." kalmar da Haajara take nanatawa tana jan zuciya kenan, shima Abdallah ya shiga mai-maitawa dan ya fahimci sun shiga wata rayuwa mai wahla da tsoratarwa kenan acikin kewayawar maƙiyansu.


*****

Mutuwar Hamza ta tuna musu da sanin matsayinsu, ta kuma ƙara fargar dasu akan ko su waye suke rayuwa da su, domin tun ranar da Hamza ya rasu babu wani mutum daya ƙara zuwa gidan da sunan yi musu ta'aziyya, ko kuma aduba lafiyarsu, rayuwa ta fara musu wahla ta yanda babu mai shiga lamarinsu, har ta kai Abdallah yana yini agida aduk lokacin da ya dawo amakaranta, domin yana fita ne za'a shiga gulma da tseguminsa yara kuma suna jifansa suna buɗeshi da kasa suna masa ilo ga wanda ya kashe ubansa, tuni rayuwar ta fice masa akai kullum yana cikin kuka, wanda tun Haajara na lallashinsa har itama ta farayi, tana tuna wasiyyar da Hamza yabar mata akan kula da Abdallah da kuma barinsa ya rayu amahaifarsa, wanan alqawalin ke daƙusa duk wani karsashinsa nason barin garin, to idan ta tafima ina zataje? Bayan bata da kowa aduniyar nan.

Ahaka har ta fita atakaba, anan kuma suka fara cin karo da matsala dan Abincin da suke riritawa ya ƙare, basu da ko ƙwayar hatsi agidan, nan hankalinta ya ƙara tashi babu wanda zata tunkara da batun taimako abata abinci, shawara tayi ta shiga bin gidajen maƙota ko zata samu aikin da zatayi abata abinci, amma babu wanda ya saurareta wani gidanma ko kallonta ba'ayi, tsoronta kada Abdallah ya dawo ya tadda basu da abincin da zasuci, amma kuma duk ƙoƙarinta da dabararta hakan ya gaza samuwa, dan saida t gama zagaye gidajan garin babu inda aka kalleta, tunaninta taje gidan Iya Indo ko zata tausaya mata, amma kuma kota haɗiya malam saboda maraicewa bata jin zata samu tausayawa da jin ƙai daga gareta, hakan ya sata rafka tagumi ga cikinta dake kururuwar yunwa, hawaye ya fara zuba a idonta na tausayin kansu, sai yanzu taga rashin da sukayi acikin rayuwarsu.

Sallama Abdallah ya rafka wanda ta sata faɗuwar gaba da jin tsoron abin da zaice.

"Washhh Allah Ummie nah nagaji da yawa, yau ban samu wanda ya rago min hanyaba sai aƙafa na taho, ga wata wahalalliyar yunwa dake cina tun amakaranta, kai gaskiya yau na wahlafa danma ina da sauri ina ta Allah-Allah nazo gida naci abinci."

Ya ƙarasa maganar yana washe haƙoransa farare tass dashi wanda ko kaɗan baya gajiya da gogeshi da gawayi da alum, ga yawaita asuwaki da carbi, shiɗin yaro ne mai kyau da tsafta komi nasa yanayi ne cikin tsafka.

Kallonsa tayi tana ƙoƙarin son yin magana sai dai kafin takai ga yin magana ya miƙe ya nufi kitchen ya fara lalimen abinci, sai dai ganin kwanika ayanda suke tun wanke-wanken da yayi da safe kafin ya tafi makaranta babu alamun an taɓasu ma balle ace asamu abinci acikinsu, ya fahimci komi ba sai an faɗa masaba, jiki asanyaye ya fito tsakar gida yana ƙoƙarin ƙaƙalo murmushi afiskarsa.

"Kayi haƙuri Abdallah yau mun wayi gari bamu da ko ƙwayar hatsi agidan nan, nayi ƙoƙarin na sama maka koda wanda zakaci ne amma na gaza samun aikin da zanyi na samu abinci." hawaye ne ya zubo daga idonta, share mata hawayen yayi yana murmushi "kibar kuka Ummie Allah yana tare damu, bari kiga na fita zan kawo miki abinci da yardar Allah."

"A'a Abdallah ka..."bata kai ƙarshen maganarba ya ruga da gudu yana dariya "Sai na dawo Ummie nah"

Da kallo ta bishi tana murmushi tana kuma yi masa fatan alkhairi, bashi da damuwa shikam ko kaɗan da sanya abu arai.

💋💗Wanan saƙon gaisuwace daga zuciyata, keɗin ta musammance ƙawata MUBARAKATU SHEHU, Ngd da dukkanin komi.😘

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI* 🎊


©by *😘UM Nass 🏇*


® *NWA* 🔎


 _Alhmdlh Allah mun gode maka da ni'imarka agaremu na samun ƙaruwa yara har biyu acikin mako guda da kuma karɓan baƙuncin ɗaya daga cikinsu, ina tayaku murnar sauƙa lafiya Babyn Nass nd Myyy Rouƙayyth Ubangiji ya raya mana su akan tafarkin musulunci yasa masu jin ƙanmu ne._

*_Ina kuma taya Anty YBK da murna akan ƙarƘare novel ɗinta na GA IRINTA NAN, haƙiƙa daɗin labarin da kuma faɗakarwar da yayi yana da yawa dan ya gaza yanda zan kwatanta muku shi, mun gode mutƙa Allag ya ƙara fasaha da basira sai mun jiki asabon rubutu 😅 lolz*_ Page 36


 Sai da ya shafe tsawon yini guda kafin ya dawo, duk inda hankalin Haajara yakai to yakai ƙololuwar tashi, dan ko ƙaɗan zuciyarta bata barta ta hutaba, tsoro da fargaba ne suka cikata jin shuru Abdallah bai dawo gidaba, tabbas tasan babu wanda zai kulashi aduka cikin garin nan balle ya bashi abinci amma kuma idan ta tuna babu abin daya gagari Allah sai taji nutsuwa aranta, duk da haka saida ta fito waje tana tambayar mutane ko sunga Abdallah? Amsa daya suke bata A'a basu ganshiba wasu kuma su shareta kamar basu san da halitta atare da suba.

Gajiya tayi da nemansa ta dawo gida ta rafka uban tagumi "Ya Allah ka karemin Abdallah aduk inda yake, kada ka jarrabeshi da faɗawa hannun mungwayen mutane." Ta ƙare Addu'ar tana share hawaye akan fiskarta, dan zuciyarta akarye take tana jin tsoron abin da zai-kai-ya-kawo.

"Assalama alaikum Ummiena" sallamar Abdallah ta kareɗe dodon kunnuwanta, miƙewa tayi azabire cike da ɗoki ta nufeshi, rungumeshi tayi tana sauƙe ajiyar zuciya, shima ƙanƙameta yayi yana maida numfashin wahla da kewar mahaifiyar tasa.

"Ina ka tafi Abdallah nah? Hankalina yakai mutƙa wajan tashi da rashin sanin inda ka nufa."

"Kiyi haƙuri Ummienah! Naje BULARAFA ne (Bularafa wani ƙauye ne dake kusa da Gumsa bashi da nisa sosai haka atazarar tafiya amota ₦100 ne kuɗin motar zuwa garin, dan da yawa wasu aƙafa suke jure tafiya garin saboda kusancinsa da kuma samawa kuɗinsu sauƙi."

'BULARAFA KUMA? MI YA KAIKA GARIN NAN?" ta tambayeshi cike da mamaki tana ɗagoshi daga rungumar data masa, sai yanzu ta ƙare masa kallo ta kula da yanda kayansa sukayi duƙun-duƙun, ga kuma bakar leda Ahannunsa. Jan hannunta yayi ya kaita kan tabirmar data ke shimfiɗe atsakar gidan, sanan ya samu shima ya zauna, har yanzu binsa take da kallon mamaki.

Murmushi yayi yana goge gumin dake shartu afiskarsa "Lokacin dana dawo naga Falalu na loda ice amotarsa zai kai garin, yana kuma sa yara suna tayashi, koda na dawo nan naga babu abinci kuma nasan bamu da hanyar samunsa, shine na fita naje na sameshi na roƙeshi nima zanyi ɗiban icen, da ƙyar ya yarda yarda ya ɗaukeni, muka masa lodin icen ya tambaya ko da wanda zai rakashi acikin yaran suje asauƙe icen zai biyasu, kowa yaƙi sai ni na bishi mukaje muka kai tare. Kiyi haƙuri Ummie nasan idan na faɗa miki ba zaki amince na bishiba, gashi bami da hanyar da zamu samu abinci duk garin nan babu mai tausayinmu, babu wanda zamu jewa da kukanmu ya share mana, shi yasa na yanke shawarar tafiya, amma kiyi haƙuri ki yafeni, acikin kuɗin daya bani na siyo mana garin kwaki dana ƙuli-ƙuli ko kwaɗanta kwakin mayi, ga kuma sanjin Naira Ɗari gobe saimu karya da ita."

 Kallonsa take fiskarta ƙunshe da mamaki da farin ciki, sai dai ko kaɗan taƙi yarda ta nuna farin cikinta, asalima tausayinsa ta fara ji yana kewaya zuciyarta, rungumeshi tayi yana shafa kansa "Allah ya maka Albarka Abdallah, haƙiƙa kai rahma ce agareni, sai dai ko kaɗan bana so kana yanke hukunci da kanka kafin kayi shawara dani, babu laifi acikin neman halak amma inaga kamar kayi ƙanƙanta da fiskantar wanan rayuwar, dama ina da dama da iko to da kuwa ni zan tallafama rayuwarka har zuwa girmanka, amma nayi rauni amatsayina na mace wadda bata samun sassauci daga mutanen da suke kewaye da ita."

Tashi yayi yana share mata hawayen fiskarta "Karki damu Ummie Allah yana sane damu, kuma shi zai tallafi rayuwarmu, wata rana zakiji komi kamar acikin mafarki yake faruwa, ban san ganin kukanki, daga wanan ranar da yardar Allah zanci gaba da bin Falalu mutƙar ya amince idan kuma an samu matsala zanna zuwa Bularafan ina yin ko dako ne, dan garin yana da yawaitar mutane, gashi babu wanda ya sanmu balle ya datse mana hanyar samunmu acan."

 "A'a Abdallah ko kaɗan bazan juri ganinka cikin wahla ba, ka bar maganar nan zanyi ƙoƙarin ganin na samu wata sana'ar da zata riƙemu"

Murmushi yayi mai ciwo "koda ma ace kinyi babu mai siya agarin nan, mutanen da suke baƙin ciki da ƙyashiɓ baki aikin da zaki tallafa musu ina ga suzo su siyi abu awajanki, kiyi haƙuri kibarni ina bin Falalun kafin masu zuga su farga." Kallonsa take yanda yake magana cikin nutsuwa kamar ɗan shekara 30 aduniya.

Shafa kansa tayi tana murmushi "Shikenan Abdallah na yarde maka, Allah ya kare min kai, ya sa ka shiga da ƙafar dama ya kareka daga muyagun mutane."

"Ameen Ummienah." daga haka ya miƙe ya shiga kitchen ya ɗauko kwano shi ne ya kwaɗanta musu kwakin sukaci yana bata labarin makarantarsu na dariya tayi wani kuma tayi murmushi, shikam bashi da damuwa ko kaɗan baya barin zuciyarsa ta zurfafa wajan tunani, duk wanda ya gansu yasan sun mutƙar shaƙu da junansu da kuma soyayya.


 *******

Rayuwa taci gaba da gara kwawunan Haajara da Abdallah yau fari gobe tsumma, tuni sun saba da rayuwar kaɗaicin da suke ciki, haka kuma Abdallah ya dake da bin hanyar Bularafa tun suna zuwa tare d Falalu har mutane suka masa tsegumi ya kori Abdallah, amma wanan bai dameshiba dan tuni ya dake da bin hanyar garin ƙafafuwansa sun dake, hakan yasa asirinsu ya rufu dan ko yaya ne basa yini da yunwa aƙalla zasu samu cin abinci sau biyu arana.

Haka aɓangaran karatun Abdallah dagewa Yake sosai dan idan an tashesu kai tsaye baya dawowa gida yake wucewa Bularafa.

Tuni ya manta da damuwar mutanen garin da kuma ƙiyayyar da suke masa, bashi da aboki bashi da ƙawa sai Haajara itace uwa uba abokinsa.

Haka kuma ko wata rana yakan je gidan Iya Indo ya gaidata koda zata koroshi da sanda da zagi amma dariya yake mata, haka kuma yana bata ɗan kuɗi idan ya samu awajan aiki, wanan duk shawarar Haajara ce akan kada ya sake ya yadata dan tana sonsa kuma bashi da wadda ta fita aduka duniyar nan, tun yana damuwa har ya marmartar da abin, ko zaginsa tayi sai ya mata dariya yace Aure dai ba saki ko batayi shi yanayi, zai ajiye mata ɗari ko hamshin amma ta wullo masa abinsa, ko ta kanta baya bi yabar wajan ya tafi. Idan taga tafiyarsa kuma sai ta fara sharar hawaye tana sa masa albarka ta ɗauki kuɗin, ita dai ta gaza fahimtar abin da take ji agame da Abdallah amma tana jin tausayinsa da soyayyarsa axuciyarta, kuma ko kaɗan bata jin tsanarsa kamar yanda ta ke nuna masa.


 Ahaka tafiya ta miƙe Abdallah ya kammala karatunsa na gaba da primmary wanan yasashi ƙara duƙufa da neman kuɗi tun ƴan garin najin haushinsa har suka haƙura suka sakar masa, dan bai nema ya rasaba fatansa mahaifiyarsa ta rayu ba tare da yunwaba, da kuma Kakarsa ɗaya data rage masa Iya Indo wanda bata da mai tallafa mata, duk da tana da yawaitar ƴan uwa agarin suna bata komi na buƙata amma shi aganinsa kula da ita wani nauyi ne babba akansa.


*****

Abin mamaki hukumar makaranta ta ɗauke nauyin karatunsa zuwa matakin digree acikin babban birnin garin Damaturu. Kasancewarsa ɗalibi mai ɗinbin Hazaƙa da ilimi acikin ƙauyen wanda duk cikin sa'aninsa shine ya dage yaci jarabawarsa, haka kuma shine wanda malamai suka sheda yawaitar zuwansa duk zafi da sanyi da kuma damuna.

Wanan labarin sai ya zame musu kamar ruwan sanyi ne atsakiyar sahara, Haajara tayi dariya tayi kuka tayi sujjada na farin ciki, sai dai saɓanin hakan awajan Abdallah ko kaɗan shi baiyi wani maraba da wanan sakamakonba, "Mi yasaka cikin damuwa kuma Abdallah? Bayan burinka na gab da cika, inama mahaifinka na raye yaga wanan ɗaukakar da nasarar data dumfaroka." sai kuma zuciyarta ta karaya, tuna burin da Hamza yasha akan Abdallah har ana gobe mutuwarsa magana ɗaya yake akan Abdallah ya zama zakaran gwajin dafi, ya samu bam-bancin rayuwa mutanen garin, ya kafa tarihin da kowa ya gaza kafashi acikin garin, yau gashi wanan fatan da burin na gaf da isah amma babu Hamza ƙasa ta rufe idanuwansa "Allah yaji ƙanka Hamza, ya tabbatar da rahma acikin makwancinka, yau ga ɗanka na ƙokarin zama abin da kake burin ya zama sai dai idanuwanka na lulluɓe."

"Ni bana son wannan karatun Ummie."

Ahargitse Haajara ta juyo tana kallon Abdallah cikin kaɗuwa da son ƙarin bayani akan abin da kunnuwanta suka jiye mata " kace mi ne? Mi yasa baka son karatun da ka daɗe kana burin yinsa?"

Hawaye ne ya zubo acikin idanuwansa "bana son nayi nisa da kee ne Ummie, bana ƙaunar duk wani abun da zai nisanta ni da ke, idan na tafi Damaturu babu wanda zai kular min da kee. Gaskiya ni bazan iya tafiya na barki acikin garin nan ba."

Kai ta girgiza tana murmushi "Allah yana tare da Ni Abdallah, shi ne zai kula dani, ka je kayi karatunka ka rungumi Nasarar da take tare da kai, wanan rahma ce babba Allah ya maka, dan yana duba rauninmu shi yasa ya fiddoka daga duhun jahilci, ya kuma buɗe maka ƙofa mai sauƙi ta samun wayewar rayuwa, karatun da zakayi shine zai wanke min zuciya, da sama min nutsuwa, sai dai ina umartarka da kada ruɗun zamani da wayewa yasa ka shagala da rayuwa ka ɗauki munanan ɗabi'ar da bata da kyau, kamin alƙawarin kare kanka da tarbiyarka, ka min alƙawarin zaka kiyaye dokokin Allah kada ka tsallake iyakokin da Allah ya gindaya maka amatsayinka na mutum musulmi, ka san komi ba sai na tuna makaba, ka guji abin hannun mutane dan babu abin da yake ƙarawa face tozarci, ka guji zalunci ka guji zinna domin ita abin ƙyamace haka bashi ce dake tafiya tana dawowa idan kayi sai anyima wani naka, kaji tsoron Allah aduk lokacin da kayi yunƙurin aikata wani mummunan aiki, kaji tausayin na ƙasa da kai ka zama mai yafiya da rangwame akan ko wani abu, ka guji Addu'ar wanda aka zalunta dan bata da shamaki ga Allah."

Ta ƙarasa maganar tana kallon idanuwan Abdallah wanda suke jiƙe da hawaye, maganar da Ummiesa take masa jinsa yake har ransa kamar tana masa nasiha ne irin ta wasiyya ne.

Kai yake gyaɗawa kamar ƙadangare dan bakinsa yayi masa nauyi, da ƙyar ya iya buɗe bakin nasa "In sha Allah Ummie na miki alƙawalin kiyaye duk sharuɗanki. Amma kuma Iya Indo fa, bana son ta shiga damuwar rashina duk da ba magana mai daɗi ke haɗamu da itaba."

"zanyi ƙoƙarin kyautata mata dai-dai iyawata, ka fara shirin tafiya makaranta."

Daga haka ta miƙe ta shiga madafa ta ɗora musu tuwo.

Washe gari bayan tafiyar Abdallah Bularafa ta nufi kasuwa da ƙyar ta shawo kan dilallai ya siyi duka kayan ɗakinta sai katifa da tabarma ta bari, hatta kwanikan jeranta saida ta siyarsu, iya na amfanin gida ta rage. Duk da bai mata cinikin ƙwaraiba hakanma taji daɗi dan kowa ƙin kulata yayi sai shine ya yarda ya siya.

Komawa tayi kasuwa tayima Abdallah siyayyar duk abin da tasan zai buƙata sanan ta dawo da kuɗi kaɗan ahannunta bata damu da yiwa kanta siyayya ba, amma tana jin farin ciki Abdallahnta zaiyi karatu mai zirfi har matakin digree.

Sai bayan magrib ya dawo gida yana kiran washhh cike da gajiya atare da shi, sannu ta masa ta nufi madafa ta ɗauko masa abinci, dambun tsaki tayi wanda ya sha albasa da mai sai tashin ƙamshi yake.

Tun kafin yaci yawun bakinsa ya tsinke hakan ya sashi fara ci ba tare da jiran jin ba'asin samuwarsa ba.

Sai da ya cinye yayi nak ya kora da ruwa sanan ya kalli Ummie yana murmushi "Ya ɗaukeni tsawon lokaci naci abinci mai daɗin wanan Ummie, a ina kika samu kuɗi haka ina ta Allah-Allah akan na dawo gida na barki babu abinci."

Murmushi tayi itama cike da farin ciki "Hanyar Allah yawa gareta ai Abdallah, yau cikin rahmarsa ya sama min hanyar samu ko baka nan."

Kallonta yayi ya jinjina kai yana murmushi "Alhamdulillahi" abin daya faɗa kenan ya nufi ɗakinta, da sauri ya fito kamar yaga abin tsoro "Ummie ya naga ɗakin naki wayam babu kaya acikinsa." kai ta gyaɗa tana ɗan yamitsa baki "Na gaji da ganin tarkacen ne Abdallah shine na siyar na maka siyayyar tafiya makaranta, shekaru kusan Ashirin ina fama da abu ɗaya, kawai sun isheni ina son zama haka saboda sauƙin aiki." kallonta yayi amma sam bai gamsu da maganarta ba, kawai yasan ta siyar dan hidimar tafiyarsa ne, hawayen tausayinta da soyayyarsa suka shiga zuba a idonsa "Allah ka bani ikon kyautatawa mahaifiyata fiye da yanda ta kyautata min." kalmar daya faɗa kenan yana share hawayensa.

"Magana kake ne?"

"A'a Ummie kawai ina jin kewar kwanciya ne yau akan gadonki gashi ya min nisa."

Murmushi tayi itama dan sarai taji abin da yace "shima dai yau ya huta ai, ga dai katifa nan ita na bar maka."

Kai ya gyaɗa yana murmushi ya shige ɗakin.


******

Tafiyar Abdallah ta sa Haajara cikin damuwa sosai dan abincin cinta wahla yake mata, dole ta shiga neman aikatau wata rana ta samu wani lokacin kuma ahanata, amma duk da haka bata fasa zuwa nema gobe, Iya Indo har gida take zuwa ta mata tass akan ta mata mugunta da manaƙisa jikanta yayi nisa da ita, suma kuma ƴan garin sai gulmace-gulmace suke akan ta tura ɗanta koyan nasara saboda kafirci.

Haka dai rayuwarta ta koma wata bahaguwa iyaka tayi dariya ta wuce.

Shima aɓangaran Abdallah ya dage da karatu kasancewar yana karantar ɓangaran injiniyarin, haka yana fita wajen makaranta duk lokacin da bashi k cikin ƙunci na rashi, duk da tana ƙokarin ɓoye masa amma kamarta ta hana agane.

Bashi da ƙawa bashi da aboki karatunsa kaɗai yasa agaba yakeyi dan yasan shine gatan da zai yiwa kansa da mahaifiyarsa.

Ahaka ya kammala karatunsa cikin nasara da dacewa ko kaɗan bashi da matsala da malamansa da ƴan uwansa ɗalibai kowa haba-haba yake da shi, ahaka ya dawo gida cike da nasara.

Sai kuma salon ya sauya dan sosau ƴan garin suke nuna ƙyashinsa da hassadarsa ƙiri-ƙiri suke nuna masa ƙiyayya da tsana har ta kai ga sunyi silar da sai da aka koresu acikin garin, daga lokacin da Abdallah ya fito da matakin karatu da ƙoƙarin kawo sauyi da gyara agarin sai ƙiyayyarsa da hassadar mutanen garin ta zama abu guda, suka haɗe kawunansu har sai da suka sa aka korosu daga mahaifarsu..


****

Numfashi Haajara ta ja tana murmushi "Wanan shine labarinmu ni da Abdallah, wanan shine abin da ya sa muka baro mahaifarmu."


 Kallonta suke dukkaninsu jiki asanyayye haka idanuwansu jiƙe da hawaye tsakanin Mama Anta da Arfat an rasa mai yiwa wani magana acikinsu..


  

 _💗😘Tofa gamu dai cikin tafiya, sai yanzu muka kai ga inda ya kamata ace mun daɗe da barinsa, sai dai abin da Allah ya tsarama bawansa shine mai kyau wanda ke warware tsarin da kai kayima kanka, ku daure kuyi comment na gaji da ganin like da Vote ina son ganin comment dan na samu qarfin gwuiwar rubuta muku labarin cike da karsashi._


 ©by *😘Um Nass*

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI 🎊*


©by *😘UM Nass 🏇🏼*


® *NWA 🔎*


 _Wanan shafin naku ne ƴan Feenat ja'afar novel ina jin daɗin comments naku da haƙurin bibiyar labarin Haɗin gwarmai, sosai nake yinku. 😘_
Page 37


 CI GABAN LABARIN:


Shuru ne ya ratsa na ɗan wani lokaci, kafin Mama Anta ta sauƙe numfashi "Haƙiƙa kunga rayuwa Haajara, ban san ta ya zan faɗi yanda wanan labarin ya daki zuciyataba, amma da yardar Allah komi yazo ƙarshe yanzu, ku rungumi hakan amatsayin ƙaddarar rayuwarku, wanda bawa baya taɓa tsallaketa, amma kuma labarinku ya taɓa zuciyata sosai da sosai, Allah ya rabamu da zama da jahilai."

"Ameeen" suka amsa cikin haɗin baki.

"Ya kuma labarin Iya mai ganye, bayan korar da mutanen Gumsa suka mata baki sake samun labarinta ba?" Tambayar da Mama Anta ta watsoma Haajara kenan. Numfashi taja mai kyau ta furzar da iskar bakinta "Tun lokacin da ta samu ta tsere ban sake jin labarintaba, ko mai kama da ita ban sake ganiba, amma har zuwa wanan lokacin ina mata Addu'a da fatan duk inda take tana tare da mutane na gari, dan ko kaɗan bana yiwa koda maƙiyina yin rayuwa kwatan-kwacin wadda nayi." Ta ƙarasa maganar tana share hawayen da ya zubo mata, tuno mata da mama Anta ya tada mata wani miki acikin zuciyarta, tana jin kewar rabuwa da macen data zame mata uwa alokacin da take buƙatar jin ƙai da tallafawa makusanta ta, amma kuma akalar alƙalamin ƙaddararta yasa tayi nesa da ita alokacin da take buƙatar kasancewa da ita, take kuma fatan rayuwa da ita.

"Kiyi Haƙuri Ummu Abdallah, in sha Allah tana cikin ƙoshin lafiya, nasan abin da kikeji acikin zuciyarki, akwai zafi da ƙuna, amma yanzu ba lokacin kuka bane dan jiya ta riga da ta wuce, duba can Abdallah na kallonki shima idanuwansa jiƙe da hawaye, duk da kina bashi ƙwarin gwuiwa abaya, yau kuma kina so ki saka rauni acikin zuciyarsa." ta ƙarasa maganar cikin raɗa gudun kada su Abdallah suji, dan har zuwa wanan lokacin Arfat ya gagara yin magana, kawai kallon Abdallah yake da Umminsa yana jajjaɓin rayuwar da sukayi.

Murmushi Haajara tayi ta share hawayen fiskarta "Abdallah nah kukan mi kakeyi?"

Kai ya girgiza yana faɗaɗa fiskarsa da dariya "Kawai dai ina jin kewar wani abu atare dani, inaga kamar yanzu ne abubuwan suke faruwa, ashe ni banga komiba Ummie? Idan nayi la'akari da tarin wahalhalun da kika fiskanta abaya kafin samuwata"

Murmushi tayi kafin tayi magana Mama Anta tayi "Gaskiya kam naka mai sauƙi ne, amma kuma duk idan muka cure labarin awaje ɗaya zamu kirashi da ƘADDARAR RAYUWARKU, wadda ko baku shirya zuwantaba sai ta riskeku, nasan hakan yana ɗaya daga cikin ɓujerewa maganar Iyaye da Haajara tayi tun farko, wata ƙila da kinbi shawarar Baffa malam Da Inna da bazaki wahla hakaba, amma samuwar Abdallah atsakiyar labarin ya nuna mana cewar ƙaddarar Haihuwarsa ce ta kaiki Gumsa. Shi yasa ko yaushe ake so mutum yana Addu'a akan Allah ya tsareshi daga faɗawa aikin Dana-sani wanda hausawa suke cewa ƙeyace, da kuma faɗawa cikin mummunar ƙaddara."

"Gaskiya ne maganarki Mama Anta, Allah ya karemu da karewarsa yasa bakin wahalarmu kenan aduniya." faɗar Ummie tana share hawayenta, saboda maganar da Mama Anta tayi ya tuna mata iyayenta "Ya Allah ka tabbatar da Rahma acikin Kabarin iyayena."

"Ameen ya Allah." suka amsa atare.

"Dare yayifa sosai ya kamata muje mu kwanta haka nan, akwai abubuwan yi agabanmu masu yawa gobe idan kwananmu ya kai." Mama Anta tace tana kallon su Arfat da sai faman ƙif-ƙifta ido yake.

Murmushi yayi ya miƙe yana riƙe da hannun Abdallah "Haka ne kuma, ɗan uwana tashi mu tafi mu kwanta kada mu kasa tashi oga ya fara faɗa."

Miƙewa yayi yana murmushi shima "Aifa, sai da safenmu Ummie da Mama."

"Allah ya tashemu lafiya" suka faɗa suna miƙewa tsaye suna nufar ɗakin barcinsu.


******

Taƙi take cikin farin ciki da jin daɗin yanayin da take cikinsa, bata san mi yasa take jin wanan nishaɗinba, amma tana danganta hakan da samun saiƙin mabiyanta atare da ita.

Ko ina ta wuce babu mai kallonta balle yayi tsammanin matsayinta, asalima kallonta ake da matsayi irin na masu matsaikatan ƙarfi.

Fitowarta daga makarantar su kenan, lacture ɗin yau ya mata daɗi sosai ƙila hakan shi yasa take jin nishaɗi acikin zuciyarta.

Ƙuuuuuu - ƙittttt motarta ta bada wani ƙara mai sauti, kafin ta ankare ta kashe kanta da kanta.

"Ya Rabbi" ta faɗa tana mai ƙoƙarin fitowa, fahimtar injin motar ya samu taɓuwa. Fitowa tayi ta buɗe gaban motar tuni hayaƙi ya bigi hancinta, ba shiri ta toshe hancinta amma duk da haka sai da ta fara yin tari. "Aikuma shikenan motar nan ta tashi a aiki, duk yanda nake ƙawarta da sonta, yanzu gashi ta tsayar dani atsakiyar titi." ta faɗa tana ɓata fiska kamar zatayi kuka, gashi babu kowa akusa da ita.

Motar ta koma ta ɗauko wayarta ƙirar iphone 7+ sai faman tsaki take ita ɗaya, cikin sanyin muryarta ta fara magana "Isya direba ka taho min da mota da kuma mai gyaran mota, motana ta tsaya ina hanyar dawowa daga makaranta, ina dai-dai wajan baban titin nan daya raba da unguwa uku." sai da ta dakata taji maganar da yayi sanan ta datse kiran.

Motar ta rufe ta jingina ajikinta tana kallon mutanen da suke wucewa jifa-jifa, wasu kuma cikin abin hawa, da yawansu harkokin gabansu suke, ko basu faɗa mataba akwai rauni atare da su.

 Wasu matasa ta hango suna tafe suna magana tun daga nesa ta kula ɗayan baya magana sai yawan murmushi da gyaɗa kai, haka kuma duk ta inda suka wuce yakan ɗagawa mutane hannu ba tare da la'akari da sun amsa ko basu amsaba.

Sake gyara tsayuwarta tayi ganin na kusa da shi ya ɓata rai yana magana kamar yana faɗa, sai dai da mamakinta ɗayan bai damuba asalima yawaita murmushinsa yayi har haƙoransa suka fito.

 Mamaki take anya wanan Bakano ne? Ga dai yanayin shigarsa kamar ta mutane amma kuma da alama kansa akwai motsi, kafin tayi yinƙuri sun hau Adai-daita sun wuce ta gabanta, samun kanta tayi da jin haushi dan atunaninta zasu ƙaraso kusa da itane.

 Wata baƙar motace ta tsaya agabanta da ganinta ta ninka kuɗin motarta da ta tsaya mata. Kallon motar tayi ta biga tsaki tana duba agogon dake saƙale ahannunta, da sauri direban motar ya fito yana risinawa "Ayi haƙuri Madam na biya ta wajan masu gyaran motar amma yace masu gyaran basu ƙarasoba, ga mukullin motar ki tafi zan jirasu ni anan idan sun zo sai mu tafi da wanan ɗin."

Kallonsa tayi batayi magana ba ta karɓi mukullin motar, "Ka daure ka tsaya aduba min lafiyar motata, nafi jin daɗin tafiya acikinta fiye da kowacce mota." ta faɗa cikin sanyin muryarta.

Sanan ta koma ta tattara kayanta ta maida cikin motar daya kawo mata.

"In sha Allah madam" ya faɗa yana risinawa, har ta shige motar sai ta yafito shi da hannu, da sauri ya ƙarasa kusa da ita ta window motar ta miƙa masa kuɗi ƴan 500 guda shida "wata ƙila za'a ɗauki lokaci kafin suzo, ka siyi abinci idan kaji yunwa, duk yanda kukayi kana iya kirana ka sanar dani."

Faɗaɗa fiskarsa yayi yana sanƙama mata godiya, ba tare da ta jirashiba tayi gaba abinta.

Da kallo yabita yana murmushi "Rayuwarki mai kyau ce Khaleesat duk da matsayinki na ɗiyar govnor mai ci amma kina ƙoƙarin ɓoye matsayin da kika taka, ga sauƙin kai." ya faɗa yana jujjuya kuɗin data bashi, cikinsa aƙoshe yake bashi da yunwa, ya kalli motar data bar masa yana mamakin ƙaunar da takema motar, gashi itace mafi sauƙin kuɗi acikin motocin gidan......  

©by 😘Um Nass

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI 🎊*


©by *😘Um Nass 🏇🏼*


 _Dedicated to Um Almustpha and Ummu Hanan_


Page 38


A mutƙar gajiye ta ƙarasa gida, ita kaɗai tana tafiya tana tsaki, abin na bata mamaki yanda tashi ɗaya ranta ya ɓaci haka, sai dai ta danganta hakan yana da nasaba da lalacewar da motarta tayi ahanya.

Hon takeyi babu ƙaƙƙautawa wanda yaja hankalin mai gadin saurin buɗe wagegen get ɗin gidan, da gudu ta shigo gidan kamar zata bankeshi, cikin sauri ya matsa yana mamakin abin da yasa Khaleesat wanan saurin, asaninsa dai hon ɗaya take ta jira zuwansa amma kuma yau kamar an sauyata, da fari yayi tsammanin baƙo ne amma ganin motar gidan ya tabbatar masa da itace.

Ƙarasawa wajanta yayi bayan ya rufe ƙofar "Ranki daɗe nace ko lafiya?"

Kallonsa tayi tana ƙoƙarin ƙirkirar murmushi, amma sam babu daɗi acikin zuciyarta da ƙyar ta iya gyaɗa masa kai, daga haka tayi gaba abinta, a babban falo ta tadda Maa azaune tana daddana waya alamar tana son kiran wani awaya "Sannu Maa" ta faɗa ba tare da ta tsayaba, ta nufi ɗakinta, tsayawa Maa tayi daga danna wayar da take, tana kallon ɗiyar tata sai dai kafin ta yi magana har ta shige ɗakinta, mamaki ne ya kamata dan ta san ko kaɗan Khaleesat ba zata ganta azaune taƙi zuwa ta faɗa mata jikiba saninta da son jiki kamar mage, haka kuma bata saba yi mata sannu ta wuceba koda zata mata to tana jikinta ne zata mata, miƙewa tayi ta nufi ɗakin Khaleesat ɗin dan jin abin da ke faruwa da ita sai dai tana shiga taji ƙaran zubar ruwa alamar ta shiga wanka, zama tayi akan gadon tana jiran fitowarta.

 "Maaa" Khaleesat ta faɗa tana kwantar da kanta akan kafaɗar Maa ɗin, hakan ya sata saurin ɗagowa, dan wata duniyar tunani ta lula har bata ji motsin fitowarta ba, ajiyar zuciya ta saki tana shafa kan Khaleesat wanda take ta faman ajiyar zuciya akai-akai "Mi ya faru da ke?" Maa ta faɗa cikin muryar lallashi.

Kai ta girgiza kafin ta buɗe baki tayi magana "Ba komi Maa, kawai bana jin daɗi ne, motana ta lallace ina tsaka da tafiya, wata ƙila hakanne yasani damuwa." Murmushi Maa tayi ta miƙe tsaye tana zaunar da khaleesat akan gadon, sanan ta nufi ma'adanar ajiye kayanta, doguwar riga ta ɗauko mata mai ratsin Ja da fararen duwatsu wanda suka taimaka wajan ƙawatuwarta, "Wata ƙila akwai wani abun daban da yake damunki wanda baki saniba, amma karki yawaita ɗorawa kanki damuwa wadda bata da amfani, ki roƙi Allah alkhairi akan komi, amma kada ki bari damuwa tasa ki sauya daga kyakkyawar ɗabi'arki, mota mai sauƙi ce tunda akwai masu gyara idan wata kike buƙata akwaisu da yawa agidan nan, ko sabuwa kika bukata bazata gagara ba zaki sameta." Ta ƙarasa maganar tana murmushi, kana ta miƙawa khaleesat kayan da ta zaɓo mata, karɓa tayi tana murmushi dan tuna ɗabi'ar mahaifiyar tata, aduk lokacin da take cikin damuwa takan zauna ta kawar da duk wani uzuri dake gabanta har sai ta fiskanci matsalarta ta ragu.

Zama tayi akusa da ita ta fara shafa mata mai kamar wata baby, sai dai da alama hakan ya zama sabo awajanta "Nifa bana son ko wace mota Maa, ina jin daɗin tawan ne kawai, saboda nuna matsayina da take cikin masu matsakaitan matsayi, wani abu kuma yau na tsaya acikin gari naga yanda mutane suke rayuwarsu cikin sauƙi, kamar basu da matsala duk da yanayin shigarsu ta nuna rauninsu, nikam ko sau ɗaya ina son yin rayuwa kamar ta kowa musamman masu ƙaramin ƙarfi, na lura hidimarsu akwai sauƙi cikin rayuwarsu." ta ƙarasa maganar tana murmushi, wanda hakan yasa Maa yin murmushi ita, idan har akwai karatun data riƙe ɗa waƙa bai wuce wanda khaleesat take mai-maitawa akullum ba, shine kasantuwarta tare da mutane masu ƙaramin ƙarfi "Muma awasu shekaru haka muke, gaskiya rayuwar talaka akwai daɗi musamman wanda yake da wadatar zuciya, dan yafi mai arziƙi kwanciyar hankali ma, sai daifa wasu lokutan babu wanda ya kai talaka faɗin-rai da ƙunci musamman idan akayi dace bashi da wadatar zuciya, kullum acikin ƙunci yake, ki samu lokaci ki gwada yini acikinsu zaki fahimci sauƙi da wahlar da take cikin rayuwa shi kansa arziƙin wahla ce ga mai shi, amma ko yaushe kina godewa Allah abisa ni'imar da ya miki, karki zama marar godiyar Allah, dan da yawa wasu na fatan samun koda rabin matsayin da kika taka ne."

Kai ta gyaɗa tana ambatar "Alhamdulillah ala kullu hallin."

 Akuma wanan lokacin Maa ta gama yi mata kwalliyar ta miƙe "Ki saka kayanki ki fito muci abinci, saura kiyi barci ƙarya da ruwan ƙanƙara zan tasheki." dariya Khaleesat tayi dan tasan tsaf Maa zata aikata mata hakan, kullum faɗansu akan cin abinci ne, amma yau kam bata shirya jin faɗan Maa ɗin nataba dan babu mai kareta Dadynta baya garin balle ya tare mata.


*****

Zaune suke agaban Ogansu kai a sunkuye kamar masu gaisawa da surukansu "Ai kun san baku kyautaba sam, yanzu ƙarfe nawa?" ya faɗa yana duba agogon da yake hannunsa, kai suka kara sunkuyarwa "Ayi haƙuri oga matsala aka samu yau muka makara, amma in sha Allah daga yau ba zamu kara makaraba."

Kai ya gyaɗa yana sassauta fiskarsa "Kai baƙon zuwa ne saboda kai zan muku wanan alfarmar, amma shi Arfat ya sanni sarai koya mutum ya makara babu shi a aikin ranar, amma yau ta wuce."

Kai suka risina dukkaninsu suna faɗaɗa fara'arsu "Godiya muke oga." suka miƙe suna nufar cikin garejin "Amm nace ba" gaba ɗaya suka juyo suna fiskantarsa "Akwai gyaran motar da take jiranka Arfat, tun ɗazu direban yake kai-kawo anan dan motar ta uban gidansa ce, sai kuje gashi can yana zaman jiranku, kuje da Abdallah kana gwada masa kan aikin."

Ya faɗa yana faɗaɗa fiskarsa da murmushi, suma murmushin sukayi gaba ɗaya kafin Arfat yayi magana "Ƙila sai dai shi ya koya min dan matakin Digree gareshi afannin nan." Arfat ya faɗa yana murmushi, ido oga ya fiddo waje "Da gaske kake Arfat?" Saurin tararsa Abdallah yayi yana murmushi "A'a oga faɗa yayi dan ya tsokane ni." daga haka yaja hannun Arfat ɗin suka nufi inda mai direban yake jiransu.

"Mi yasa baka so na faɗi Baiwar dake tare da kai?"

Kai ya girgiza yana murmushi "Ita Baiwa ai ba bayyanata akeba Arfat, idan har akwaita to da kanta take bayyana kanta, ka barni nayi rayuwa cikin sauƙi ba tare da na fayyacewa duniya ko ni wayeba, har sai su da kansu sun fahimce ni da kansu."

Kai Arfat ya girgiza yana murmushi "Kasan mi? Zaiyi wuya awanan Duniyar da muke ciki asamu mai hali irin naka, domin yanzu muna cikin wata rayuwa ne ta nuna fifiko da son a sani acikin zamantakewa, wanima sai kaga ba kowan kowaba amma ya ɗorawa kansa ƙarya da banzar rayuwa akan sai duniya sun san shi, Madallah da rayuwarka mai cike da sauƙi."

"Suma dan basu fahimci illar dake cikin hakanba da ko sha'awar nuna kansu ba zasuyiba, amma dai kowa na kai duka ne da sandar da take hannunsa ta iyu suna da nasu dalilin nayin hakan."

"Ba wani dalili face na ƙaryar da ta cika zukatan mutane, da kuma nuna ɗagawa atsakaninsu."

Murmushi Abdallah yayi mai sauti sanan ya yima Direban magana dan zuwa lokacin sun ƙarasa kusa da shi "Barka da zuwa, kayi haƙuri mun ɓata maka lokaci da yawa."

Fiskarsa ya ɗan yalwata da fara'a "Yauwa ba komi sannunku da fitowa, muje motar ce ta tsaya ahanya."

 "To" suka amsa suka nufi Adai-daita ta kaisu wajan motar. Duba motar suka fara yi wanda Arfat ya gagara fahimtar inda matsalar take, dole ya koma baya yana yiwa Abdallah alama "Nifa na gaza tashinta, kazo ka ƙoƙarta"

Kai ya gyaɗa ya fara dubata cikin abin da bai gaza mintuna gomaba motar ta tashi, "Ba wani abu mai wahla bane ruwa ne ya ƙare mata har injin ya ɗauki zafi da yawa, gashi dama yana buƙatar hutawa."

Kai Arfat ya ɗaga yana murmushi "Ai nayi tsammanin ya tashi a aiki ma, danaga ko gizau yaƙi yi."

Dariya sukayi atare sanan ya dubi Isya direba "Ina mai motar take?"

"Ta wuce gida ai, bari na kirata."

"A'a kawai kace mata tabar takurawa motar ne, dan da alama motar ta gaji da ita."

Ido Isya ya fiddo waje yana dariya "Ai madam ba zata iya barin motar nan ba, baka san yanda take jin daɗinta bane."

Baki ya taɓe yana kallon Arfat da ya zuba musu ido yana kallonsu "Mu je ko?"

"Kai! Muje Ina? Kuɗin aikinfa?"

Kai ya dafa yana dariya "oh na manta sam" sanan ya juyo kallonsa ga Isya direba "kuɗin aikinmu malam direba."

Dariya yayi sanan ya shiga tambayarsa nawa za'a bashi

"Ɗari biyar ma ai yayi ko?" ya faɗa yana kallon Arfat da takaici ya kamashi "A'A Kyauta ma muka musu ma" sanan ya ture Abdallah "Ka kawo dubu biyar, kaga mun bar aiki agabanmu da yawa."

Kai Isya direba ya gyaɗa kafin ya ɗauko kuɗi a Aljihunsa ya miƙa musu "Ga dubu Goma" sanan ya kai kallonsa ga Abdallah yana murmushi "Na gode abokina kana da kirki da sauƙin kai, zan so yin abota da kai."

Shima dariya yayi ya karɓi kuɗin daya miƙa musu, sanan ya wari dubu biyar ɗin ya miƙa masa sauran "Dubu biyar ne kuɗin aikinmu, idan ka ƙara mana kamar ya zama da ƙuntatawa, akwai masu buƙata ahanya wanda basu da ƙarfin da zasu nema da guminsu, sai ka basu."

Daga haka yaja hannu Arfat yana ɗagawa Isya direba hannu wanda shi kuma yayi mutuwar tsaye yana kallonsa.

Ta gefe ɗaya kuma Arfat ke aika masa da Harara yana ji kamar ya nausheshi, yau ga ƙoshi ga kwanan yunwa.

Ayayin da shi kuma yake ta faɗaɗa fara'arsa baima san mi yake masaba, yau gashi yayi aiki an biya shi, abin da abaya ya nema ya rasa.....©by Um Nass

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI 🎊*


©by *😘Um Nass 🏇*


 _Dedicated to Ummu Faɗimatu and Tsohuwa Aisha Adamu_


Page 39


 Tafiya suke babu wanda ya ƙara yima ɗan uwansa magana acikinsu, kowa na ƙulla tunanin da yakega yafi masa sauƙi, har sunyi nisa suka fara jiyowa hon ɗin mota abayansu, tsayawa sukayi sai dai da mamakinsu Direban da suka yima gyara ne yake bin bayansu, dakatawa sukayi suna fiskantarsa, kai ya leƙo ta jikin motar yana washe bakinsa "Abokaina kuzo na rage muku hanya na maidaku wajan aikinku, naga akwai yiyuwar ɓata lokaci wajan jiran abin hawa anan."

"Aikuwa mun gode sosai" Arfat ya faɗa yana buɗe bayan motar, dan kada ya bawa Abdallah damar da zaiyi musu, jijjiga kai yayi yana murmushi sanan ya buɗe gaban motar ya shiga, "Mun gode" ya faɗa cikin sanyayyiyar muryarsa.

"Ba godiya ai mun zama abokai daga yanzu, ina son zama da mutanen kirki masu sauƙin kai, Sunana Isyaku ku miye sunanku?" ya faɗa yana juyowa kusa da su, kai Abdallah ta gyaɗa dan surutun Isya ya dameshi, baya son mutane masu rawar kai haka, duk da ya taso cikin ƙiyayyar mutane hakan bai sashi zaƙuwa da son ƙulla abota cikin sauƙiba, idan aka cire girmamawa da gaisuwa tofa baya buƙatar wata sabuwar alaƙa atsakaninsa da wani.

"Abdallah baka magana ne kayi shuru muna ta magana" Muryar Isya Direba ta bigi kunnesa, da sauri ya ɗago yana mamakin jin sunansa da ya ƙira "Ya akayi kaji sunana?"

Dariya sukayi "Ai na faɗi maka hankalinsa baya tare damu" Arfat ya faɗa yana ƙara sakin wata dariyar.

Shima murmushi yayi yana kallonsu "Kace har gulmata kukayi ina zaune? Kun kyauta ai"

"Laa! Ba gulmarka mukeba, kawai dana tambaya shine Arfat ya faɗa min sunayenku, gashi dana sake magana sai naji shuru baka bani amsaba, anan yake cewa ka tafi tunanin ƴar budurwarka." Isya ya ƙarasa maganar da jan baki wanda yasa Abdallah dariya, daga haka ya makawa Arfat Harar sanin maganar da yake babu komi cikinta face tsokana, aifa suka samu abin yi suna tsokanarsa yana kawar da kai, tun bai ware da Isya ba har ya sake masa musamman da yaga Arfat ya sake da shi kuma yanayin shegarsu tazo ɗaya, ahaka har suka ƙaraso garejin da suke gyaran motar, nanma kamar kada su rabu har sai da Ogansu ya ankare da dawowarsu ya taho yana musu magana akan jiran da yake musu ga aiki na ƙaruwa, sanan sukayi sallama da Isya ya tafi yana ɗaga musu hannu.

 Suma hannun suka ɗaga masa sanan suka nufi wajan aikin, Abdallah ne ya miƙawa Ogan nasu kuɗin aikin da sukayima Isya direba, kallonsa yayi cikin mamaki dan yasan bai tambayesu ba, haka ba kasaifa yaransa suke bashi kuɗiba dan sunje wani wajan sunyi aiki.

"A'a yaro wanan kuɗin ai naku ne ko anini bazan ɗaukaba dan halak ɗinku ne, ku kukayi aikin da guminku." Ogan ya faɗa yana murmushi wanda da ganinsa na yaji daɗin abin da Abdallah yayi.

Kai ya ƙara sunkuyarwa "Nasan da haka Oga, amma ai ta dalilinka ne muka samu aikin, da ace ka-so waninmu zaka tura yayi ka ɗauki ko wani abunne aciki zamu ji daɗi."

"Baka fahimta bane har yanzu Abdallah wanan kuɗin ku ne aduk inda kukayi aiki a waje to bani da kaso acikinsa."

"Na fahimta, na gane amma dan Allah ka ɗauki wani abu aciki."

"Shikenan tunda ta haɗani da Allah." ya zari 1k acikin kuɗin "Wanan ya isheni, na gode, Allah ya sanya alkhairi da albarka acikinsa." ya ƙarasa maganar yana shafa kan Abdallah wanda yake binsa da murmushi, gefe ɗaya kuma Arfat ne ya saƙale hannayensa yana binsu da kallo, bai san awani mataki zai ɗora Abdallah ba, amma kai tsaye zai ƙirashi da mutum wanda yake farantawa wasu koda zai ƙuntata, wanda yake zaune da mutane da zuciya ɗaya babu ƙyashi balle asamu hassada acikinsa, sai yanzu yakega baikin mutanen Gumsa da sukayi sake da barin mutumin da ya tara komi na rayuwa, shi yasa akace aduk inda mutum yake baya rabuwa da wani baiki atare da shi, amma sukam sun saki reshe sun kuma riƙe huda bama ganyeba.

Ahaka suka yi aikinsu cikin nitsuwa da kwanciyar hankali, sosai Oga Haruna ke kulla da duk wani motsi na Abdallah awajan aikin, sai dai kuma saɓanin yanda yayi tunani madadin Arfat yana koyawa Abdallah wani abu to Arfat ɗin ke koya awajan Abdallah, dan yana lura da su ko wani aiki ne yazo Abdallah ke maida hankali akansa, abin ya bashi mamaki ya kuma zuba musu ido bazai musu maganaba, dan ya fahimci Abdallah baya son asan ƙwarewarsa, amma kuma duk da haka zai musu ta manya ya tura ragamar aiyukan atare da su, dan sosai yake jin yaron azuciyarsa gaskiyarsa da nutsuwarsa ya sanar da shi matsayinsa.


*****

Agajiye suka dawo gida dan yau kam sun aikatu iya aikatuwa, kamar kuma haɗin baki motoci sukan samu matsala, amma sun ɗauki hakan amatsayin kasuwarsu ce ta buɗe da kuma hanyar samun abincinsu ta bunƙasa.

"Sannunku Ummie da Mama yau da wuri kika dawo haka?" Arfat ya faɗa yana warware tabarmar ya kuma miƙe ƙafafuwansa dan jin sauƙin gajiyar dake ɗawainiya da shi.

"Yauwa Arfat sannunku, ai kunne da sannu" faɗar Ummie tana dire musu Abinci da zoɓo agabansa ga kuma fure water mai sanyin gaske.

"Ai yanzu gajiyar zata barsu ganin wanan garar agabansu." Mama Anta ta faɗa cikin sigar tsokana, kafin takai kallonta ga Abdallah wanda yake faman murmushi yana kallon Ummiensa babu ƙiftawar ido "Abdallah ɗana duk gajiyar ce ta hanaka yin magana? Ko kuma harda yunwa? Dan naga idonka yaƙi rabuwa da kallon abincin"

Kai ya girgixa yana dariya "A'a Mama, aini yau ko yunwar ma bana ji, saboda farin ciki da ya cika min zuciya, wai yau ni nayi aiki aka biyani cikin so da girmamawa, ba tare dana roƙa asaniba, abin da abaya ko kyauta ƙin barina yi akeyi, sai nake ganin hakan kamar amafarkina."

Tausayinsa ne ya kamata ganin yanda yake maganar cikin sanyin murya, duk da ta lura hakan yanayinsa ne ajinisa kuma yake, amma harda rashin samun abokanan wasa tun yana yaro, Kallonta takai ga Ummiensa wanda ta sunkuyar da kai tana goga hannunta acikin idonta, da alama hawaye ne ya zubo mata tana kuma gudun kada wani ya gani, sai dai ta makara dan tuni idanuwanta sun gani, kawar da kallonta tayi ta maida kan Abdallah wanda yake yalwata idanuwansa akanta yana ƙara faɗaɗa murmushinsa.

"Wanan ai kaɗan ne daga cikin ikon Allah Abdallah, aduk lokacin da ka samu wasu suna ƙinka to agaba dasu zaka samu dubbanin wanda suke sonka, sanan acikin ko wata rayuwa ta mutum abubuwa biyu ke zama kishiyar juna farin ciki da baƙin ciki, sanan bawa baya taɓa dauwama akan abu guda ɗaya dole wata rana ya samu sauyi acikinsu, dan haka wanan kaɗan ne daga ciki rahmar da Allah yayi mana, na gaba sai yafi na yauma, dan haka ake son bawa mai haƙuri da juriya aduk inda yake, kai dai ka roƙe gaskiya da amana zakaga nasara na ɗago maka hannu."

Kai ya gyaɗa yana jin ƙaunar matar har ransa, sune mutane na biyu bayan Ƴar mai ganye da suka nuna musu soyayya "Na gode Mama in sha Allah zan ke tuna shawararki."

Anan kuma Arfat yayi magana "Malam nifa yunwa nake ji, ko kazo muci ko na cinye na bar maka sauran, dama yau kasa munga-samu-munga-rashi."

Aifa jin haka Abdallah ya tintsire da dariya Ummie ta jefeshi da muhuci yayi saurin kaucewa "Wani abun ya muku acan na ƙauyanci ko?"

Aifa nan Arfat ya tintsire da dariya kafin yayi ƙwafa "Inaa ai gara ƙauyanci akan abin da yayi mana, wani muka yima gyaran mota ya biya mu harda alherin dubu biyar amma fir Abdallah yaƙi karɓa ya mayar masa, wai ya bawa masu buƙata mabarata ahanya, shi yana da ƙarfin nema."

Tafa hannu Ummie tayi tana sallati wanda yasa mama Anta da Abdallah yin dariya itama har ta ƙarasa da dariyar dan tasan za'ayi hakan indai Abdallah ne, dama ya aka ƙare balle yanzu da ya samu sana'ar yi.

"Da kyau ɗana lallai ka cika Abdallah bawan Allah, kaci gaba da haka ka burgeni." Mama Anta ta faɗa tana jinjina masa, yayin da Arfat ya bishi da harar wasa "Ai kuwa ya haɗu da wahla, ina ne ba'a ihisani, ai nabar yarda yana bina cinikin aiki gara yana tsayawa daga baya-baya gudun samun asara irin wanan."

"Gaskiya kam nima ina bayanka Arfat, yau kunga ta-leko-ta-koma"

"Bari kawai harda kukan zucifa nayi Ummie"

Haba nan suka saka masa dariya "za kayi na filima indai Abdallah ne" Ummiensa ta faɗa tana ƙara sakin dariya..

"maza kuci abincinku kada yayi sanyi." Mama Anta ta faɗa tana dariya dan idan Arfat ƴa fara surutu ko kaɗan baya gajiya.

Ahaka suka ci gaba da hira da tsokana wanda idan ka kallesu zakayi tsammanin ƴan uwane da suka shaƙu mutƙa..


******

Tsaye take tana duba motar bayan ta shiga ta kunnata ta zagaye gidan da ita, sanan ta sake kai kallonta ga Isya wanda yake faɗaɗa fara'arsa ganin uwargijiyarsa cikin walwala fiye da tsammaninsa.

"Amma ai na faɗa maka ka kirani ka sanar dani duk yanda kukayi awajan gyaran, mi yasa baka kiraniba?" ta faɗa tana shafa motar wata soyayya ta musamman takeyi motar fiye da tsammanin mai zato.

"gani nayi akwai yawaitar kuɗi awajena kuma basu da tsadar aiki shi yasa na biya, idan nazo na miki bayani, dan da fari wanda yayi gyaran motar 500 ya buƙata sai abokin aikinsa ne yace 5k dan da alama shi baƙo ne agarin."

Kallonsa tayi ta yalwata murmushinta har fararen haƙoranta suka bayyana, wanda atsakan-kaninsu akwai ushirya data ƙara musu kyau, ga kuma lotsawar kumatunta na gefen dama "500 awanan rayuwar mi zata musu? Ko 5k ɗin da suka buƙata ai ta musu kaɗan isya, ƙaunar da nakema motar nan zan iya basu ko 100k ne ko fiye da haka ma."

"Na sani madam, shi yasa na ƙara musu da wata 5k ɗin saboda kyautatawa, amma saboda kuɗi bai damu yaronba firr yaƙi karɓa yace halak ɗinsa ta isheshi akwai masu buƙata wanda basu da ƙarfin da zasu nema na basu.

Juyowa tayi ahautsine cikin mamaki take kallonsa "Awanan rayuwar awanan duniyar da zamanin da muke ciki akwai wanda za'ayima kyautar kuɗi yace ya yafe baya buƙata?" ta faɗa cikin muryarta mai sanyi da Amo wanda xaka tabbatar da tana cikin mamaki da ruɗani.

"Kwarai kuwa an samu madam, ni kaina nayi mamaki kafin yau ban taɓa ganin anyima bakano kyauta yaƙi karɓa ba, shi yasa nake kokonto akansa anya BAKANON gaskeni?"

Kai ta girgiza tana ƙara mamakinta "LALLAI YA KAMATA NA HAƊU DA SHI."

Ta kalli Isya wanda shima kallonta yake da mamaki wanan bai san mi hakan ke nufiba.


_to nima dai ban saniba amma kanawa kunyi haƙurifa kada kuce na ci muku Hanci, amma agarinmu ana cewa idan kana son kaga yanda kuɗi ke gudu ana kamoshi ka je KANO. Lolx. Ina son KANAWA sosai saboda suna sona nima.😘


©by😘Um Nass🏇

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI 🎊*


©by *😘Um Nass 🏇🏼*


Page 40


Kai ta jinjina masa "Tabbas ina son haɗuwa da shi, wataƙila akwai wata baiwa atare da shi wanda zan ƙaru da ita." 

Kallonta Isya yaci gaba da yi sai yakega kamar ba Madam Khaleesat ɗin da ya saniba, wani tunani ne ya ɗarsu aransa akan maganarta, kafin ya sauƙe ajiyar zuciya ya gyara tsayuwarsa "Tabbas akwai baiwa atare da Abdallah, sai dai kai tsaye bazan iya musalta miki yanayinsa ba madam, ta iyu nayi ragi acikin halinsa, sai dai azaman awannin da nayi da shi ayau na fahimci shi mutumin kirki ne, wanda samunsa zaiyi wuya awanan lokacin."

Murmushi tayi akaro na ba adadi ta sake kallon motarta, sanan ta dubi Isya da yake cike da mamakin Khaleesat da abin da ke sata nishaɗi kawai saboda gyaran mota "Ba Baiwarsa nake son ganiba Isya, ina son ganin Nagartar da ke tare da shi, ka shirya gobe in sha Allah zamu fita ka rakani ta wajansu, da safe kafin na wuce skull." tana ƙarasa faɗar haka ta shige cikin gida ba tare da ta jira abin da zai ce ba, da kallo ya bita yana ƙara saƙa maganganun da tayi masa, sai dai ya gagara ajiye su acikin matsaya guda, idan akace ya banbace Baiwa da Nagarta to acikin muhalli ɗaya zai ajiyesu, amma kuma sai gashi an samu bam-banci akan maganar.

Ajiyar zuciya ya sauƙe gami da shafa fiskarsa "Zan so ganin abin da zai faru agobe, zuciyata ta cika da kwaɗaituwa da son riskar gobe, ban kuma san ya za'ayi magana tsakanin kurma da bebe ba." ya faɗa afili yana murza goshinsa, juyawa yayi da zummar tafiya sai dai kafin ya kai ga tafiya Lantana mai aikin goge-goge ta fito, ta zura masa kira, tsayawa yayi yana fiskantarta, sai faman washe baki take tana fara'a ta miƙa masa bandir ɗin 500 "Gashi inji Madam khaleesat" ido ya ƙwalalo waje cike da farin ciki, wanan shine bazata, dan baiyi tsammanin wanan kyautar ba, duk da yasan khaleesat akwai kyauta da tausayin na ƙasa da ita, nanfa ya yalwata fiskarsa da fara'a ya kuma zari guda shida ya bama lantana amatsayin tukuicinta, itama godiya tayi dan shi yasa ko kaɗan bata ƙyashin a aikota wajan Isya koya aka masa kyauta sai ya yagarma na kusa da shi, ta tabbata aciki sai ya ƙara bawa wani agaba, dan shi mutum ne me badawa ko kaɗan baya jiran sai ya wadatu, wanan ne dalilin da yasa tasu tazo ɗaya da khaleesat dama mutanen gidan baki ɗaya.


*****

  Da sauri-sauri suke shirin fita dan ganin yanda rana ta fito har kusan 10 kafin su fita su samu abin hawa aiki ne, jiya sun makara wanda har Oga Haruna yayi musu magana, darajar Abdallah da matsayinsa na baƙo ya sasu yi musu uzuri, to amma yau kam basu da wani uzurin da zasu bada.

"Ku tsaya kuci abinci mana, sai faman sauri kuke kamar kwa kifa." Ummie ta faɗa tana ƙoƙarin kawo musu abin karin-kumallo, da sauri suka girgiza kai kamar abin haɗin baki "A'a Ummie mun makara mukam, zamu siya ahanya."

"Oh ni Hajjo! Yanzu ga abincin agida ba zaku ciba har sai kun fita zaku nemi na siya."

"Kema dai Ummin Abdallah bakya gajiya, ki ƙyalesu mana, ba da saninsu suka koma barcinba sun san zasu je aiki, aini calama Allah yasa oganma ya korosu."

"A'a ba aminba wlh Maman Arfat, a inane ba'a makara? Jiya hirar da mukayi ta janyo musu makara, kema ina da ƙyar kika tashi abarci kina murtsika ido."

Ido Mama Anta ta fiddo waje "Au saboda na yima yaranki faɗa shine nima za'a min tawa tsarabar."

Nan kuma suka sanya mata dariya su dukansu "Shi yasa nake yinki Ummienmu, kuma idan bama siyan abincin waje ai itama Mama babu mai siyan nata, kamar kiran kasuwa muke mata daga tamu mazaɓar." Arfat ya faɗa cikin sigar tsokana, wanda yasasu yin dariya gaba ɗayansu.

 Jifansa da muhuci Mama Anta tayi wanda ya sashi miƙewa ya fice "Abdallah taho mu tafi, kada Mama tasa mu ƙara makara."

"Kunji min ja'irin yaro, ni zan sashi ya makara ma, Allah ya shiryeka Arfat" Mama Anta ta faɗa tana murmushi, wanda Ummie ta tayata "ai ke kike riƙesu da wata maganar daban."

Tashi yayi yana murmushi "Sai mun dawo Mama da Ummie."

Cikin haɗin baki suka amsa masa "Allah ya bada sa'a ku dawo mana lafiya."

"Ameen ya Allah."

Sanan ya fice ya samu Arfat dake tsaye aƙofar gida yana jiransa. Anan suka fara tafiya da sauri-sauri cikin Sa'a suka samu Adai-daita tana fitowa alayin basu tsaya jinkiriba suka hau.


****

"Ya kamatafa nima na samu wata sana'ar da zanyi, dan zama hakan bazai iyuba, ko ba komi mana tallafawa juna." Ummie ta faɗa tana kai kallonta ga Mama Anta dake shirin tafiya Tasha saida abinci.

Kallonta tayi da mamaki kafin tayi murmushi "Wata sana'a zakiyi kuma Ummin Abdallah? Bayan tun da kuka zo ke kike min hidimar abincin da nake saidawa, acikin kaso 80 cikin 100% ke kike komi, gashi Yaronki na samu dai-dai gwargwado balle nace zakiyi hidimarsa, haka ayanzu nake jinki kamar ƴar uwar da muka fito ciki ɗaya, komi zan iƴa miki babu gajiyawa, sai dai ban saniba ko hakan bai mikiba akwai wani tunanin da kike yi? Ni kaina adole nake sana'ar Tasha, ga wanda bai fahimcekaba kallon bariki yake maka, wasu kuma suna maka kallon ɗan iska, tun ina damuwa gashi har ya zama jiki agareni, na kuma yi sabo da sana'ar fiye da yanda nayi tsammaninta, na samu rufin Asiri wanda banyi tsammanin zan sameshiba, sai dai har gobe ina Addu'ar Allah ya kawo min wani canji acikin rayuwata da zan bar sai da Abinci a Tasha, duk da samun da ke cikinsa. " ta ƙarasa maganar cikin sanyin murya da murmushin da bashi da maraba da yaƙe, wasu ciwukan azuciya ake binne zafinsu, idan kayi ƙoƙarin ɓuɗeshi to zai zafafa ko wani sashi na jikinka.

Kai ta sunkuyar ƙasa cikin sanyin murya da jin nauyin Mama Anta ɗin, ita ba haka take nufiba amma gashi tayi mata bahaguwar fassara. Sai take jin tausayin Mama Anta ɗin, ashe duk abin da mutum yake koda na Alheri ne da dogaro da kai akwai ƙunci acikinsa? Lallai gaskiyar mutane da suke cewa kada kaga mutum ko yaushe yana dariya kayi tsammanin kullum cikin farin ciki yake, da zaka bibiyi zuciyarsa akwai ƙunci da baƙi yana ƙoƙarin binneta dan ƙarfafawa wanda suke tare da su gwuiwa.

"Kinyi shuru? Ko kuma na tafi idan na dawo mayi maganar?" ta tsinkayi murƴar Mama Anta wanda ta kafeta da ido.

"A'a ba haka nake nufiba Ƴar Uwa, gidan ke min faɗi da girma idan kuka tafi, wanda hakan yake nuna harda rashin sabon da nayi, amma idan babu damuwa zanso ko yara nakema karatun Alqur'ani dan ɗebe kewar kaɗaicin da ke damuna, amma ba wai dan na samu wani abun duniyaba."

Kallonta tayi tana jinjina ƙarfin basirarta, haƙiƙa su alkhairi ne atare da su, kai ta jinjina tana faɗaɗa murmushi akan fiskarta "Madallah da kasancewarki atare da mu, bari na dawo sai muyi maganar anutse kinga yanzu ana jirana, ya kamata ki samu ki huta kema."

"Allah ya dawo da kee lafiya ya kaiki lafiya, zan gwada kwanciyar ko barci zai ɗaukeni."

Har ƙofar gida ta rakata, ta shiga cikin taxi ɗin da ke jiranta, sanan ta ɗaga musu hannu har suka ɓacema ganinta.


*****

Lokacin da suka isa garejin basu samu matsala da oganba asalima da fara'a ya taryesu, suka gaisa amutunce sanan suka fara aiki, wanda dama akwai wanda basu ƙarƙareba.

Kallon Abdallah yake wanda yake cikin farin ciki sai aikinsa yake cike da ƙwarewa da walwala, gyaran murya yayi wanda yasa Abdallah kallonsa ya masa inkiya da ido alamar ko da magana? Kai ya ɗaga masa sanan ya fara magantuwa "Na ganka cikin Annashuwa da karsashi wanda ban san dalilinsa ba, na jin daɗin aikin ne? Ko kuma na samuwar wani abun ne daban?" ya ƙarasa maganar yana ɗan taɓe baki da ƙura masa ido.

Murmushi yayi yaci gaba da aikinsa ba tare da ya tanka masaba, matsawa yayi kusa da shi "Wani lokacin shurunka na nuna min abubuwa da yawa, wata ƙila ko ina takura maka ne, baka buƙatar abokin da zaku raba farin cikinku tare, shikenan kayi haƙuri daga yau zan yi ƙoƙarin daina matsanta maka akan matsalarka."

Da sauri ya ɗago yana riƙe hannunsa "A'a Arfat ba haka maganarka takeba, wani lokacin bani da amsar tambayarka ne, shi yasa nake zaɓar yin shuru amadadin magana, ya kamata kana min uzuri har zuwa yanzu ban ƙwarai da yin maganaba saboda abaya ni da Ummie nah kawai nake magana, bayan ita ban san ya zanyi magana da sauran mutaneba, ka fahimci hakan Arfat ina mutƙar ƙoƙari wajan koyar hakan. Ban san mi yake sani farin cikiba, amma wata ƙila bazai rasa nasaba da yanda nake son yin aikiba tun abaya."

Rungumeshi Arfat yayi yana murmushi "Shi kenan na fahimta yanzu, kayi haƙuri da raguwar zuciyata mai cike da ƙawa zuci akan abu."

"Kai ai ɗan Uwana ne koya kayi abu kyau yake da kai, da ni ke da zuciya irin taka da tuni mun ƙula abota da Allura da magani."

Gaba ɗaya suka saka dariya kafin Arfat yayi magana sukaji tafi abayansu, atare suka juyo suna kallon mai tafin, "Isya" suka faɗa cikin haɗin baki suna dariya suma ganin yanda yake dariya.

"Na gaida ƴan uwan juna Abakanan juna kuma" ya faɗa yana sake yalwata fara'arsa.

"Tun yaushe kazo nan ba bamuji zuwanka ba?" Arfat ya tambayeshi yana dai-daita tsayuwarsa

"Lokacin da kuke rungume juna kamar wanda suka shekara basu haɗuba." 

"Kai ko?" Abdallah ya faɗa yana jijjiga kai.

"Ni, ko kuma gaskiya ba?"

"To munji mi ya kawoka yau ko baka da aiki ne? Ko kuma motarku ta sake samun matsala?"

Baki ya rufe yana dafe kai "Oh! Oh, tare muke da Madam tazo ganin Abdallah ne, amma kunga na manta shaf, kuzo muje."

Ido suka fiddo waje kafin kuma Arfat ya saki dariya "A'a nikam ina da aikinyi kuje kada oga ya ankare da rashinmu duka."

"Haba mana Arfat kazo muje, Allah yasa ba wani abu ne ya samu motarba." Abdallah ya faɗa yana dafe zuciyarsa, wanda yasa su Arfat sakin dariya shi da Isya

"Babu abin da ya samu motar, kasan na faɗa muku Madam na son motar sosai to ƙila gyaran da ka mata ne taji daɗinsa, ka daure muje tun ɗazu muke jiranka." ya ƙarasa faɗa yana marerece muryarsa.

Baiyi maganaba ya juya ya nufi hanyar da yake tunanin anan suke, da sauri Isya yabi bayansa yana nuna masa inda suke har suka kawo gaban motar, wanda ya shedata, tsayawa yayi yana gyara tsayuwarsa kafin yayima Isya inkiya akan ya mata magana, kafin ya kai ga mata magana ta buɗe motar ta zuro ƙafafuwanta, wanda suka sha jan lallai mai kyau sanan ta fito gaba ɗayanta cikin shigar da tafi ƙauna doguwar riga sinfurin Dubai mai sheƙin duwatsu tayi rolling ɗin kanta da ɗankwalin, idanuwanta sanye cikin farin galass wanda ya ƙarama ƙwayar idanwanta kyau, shagala Abdallah yayi da kallonta dan atsammaninsa ya ɗauka Babar mace zai gani, amma kuma ya akayi yaga matashiyar budurwa wanda ba shakka bazata haura shekara 20 ba, da sauri ya dai-daita nutsuwarsa yana kallon Isya "Banga madam ɗin nakaba, gashi lokaci nata tafiya nabar aiyuka da yawa."

Kai ya risina yana masa inkiya da hannu "Wanan ai itace Madam ɗin nawa da nake faɗa maka." 

Ido ya fiddo waje yana kallonsa dan wanan ko aƙanwa ta masa kaɗan, sanan yayi murmushi yana kallonta kamar yanda ya zama ɗabi'arsa "Sannu da zuwa Madam" ya faɗa cikin muryarsa mai sanyi, wanda ta sa zuciyar Khaleesat bugawa da ƙarfin gaske, sanan ta zare glass ɗin da ke cikin idonta, ta ɗora da nata Murmushin wanda ya ƙara ƙawata fiskarta "Ba Madam ba Khaleesat" ta faɗa tana saita kallonta ga Isya wanda ya fahimci Ma'anar hakan, ya matsa ya basu waje.

"WAYE KAI?" Ta tambayeshi wanda ya sashi ɗagowa da rinannun idanuwansa, tuni bugun zuciyarta ya ƙaru sau 360 tana tsoron Amsar d zai fito abakinsa........©by 😘Um Nass 🏇

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI* 🎊


©by *😘Um Nass* 🏇🏼


Page 41


Kallonta yaci gaba dayi da hargitsattsun idanuwansa kamar mai son tuno wani abu, amma sai ya kauda kai bashi da niyar yin magana, wani sashi na zuciyarsa na tambayarsa akan mi yasa zata masa wanan tambayar? Bashi da amsar da zai bata, kodama ace yana da akwai baya buƙatar ya amsa matan, juyawa yayi da zummar barin wajan, ya fara taku ɗaya zuwa biyu fahimtar abin da yake son yi yasata saurin tarar gabansa, ta ƙura masa ido cikin yanayinta mai sanyi ta langaɓar da kai kamar wata marainiya, "Baka amsa min tambayataba zaka tafi." kallonta yayi ido cikin ido sai kuma yaji bazai iya mata abin da yayi niyaba, amma kuma acikin tambayarta akwai rainin wayo tayama Yarinya ƙarama zata sashi gaba ta titsiyeshi da tambayar rainin wayo, matsawa yayi ya raɓe ta gefenta yana shirin tafiya, hanya ta bashi ya wuce har yayi taku kusan uku sai ya tsinkayi muryarta.

"Na ɗauka kai ɗin mutum ne mai sauƙin kai kamar yanda na samu labari, na ɗauka zan sameka da Nagarta atare da kai kamar yanda naji labarinka, ashe ko jurar faɗar sunanka ba zaka iyayi ga wanda baka saniba, to tayaya ne zaka taimaki wanda suke buƙatar taimakonka? Uhmm kama bar nunawa mutane akwai mabuƙata kai kanka kana buƙatar hakan, nazo da karsashi atare dani nason sanin ko waye kai, amma ganinka da nayi ya sanar dani ko kai waye, dan haka bana ma buƙatar na ƙara maka wani sani daban." kamar ana caka masa mashi haka yake jin sauƙar ko wata kalma ta maganarta, juyowa yayi da zummar yi mata magana sai dai kafin hakan ta shiga cikin motar, ta bata wuta ba tare da-ta-bi ta kan Isya ba.

Bin motar yayi da kallo har ta ɓace ma ganinsa, jikinsa ne yayi sanyi yana son tuna abin da ya akaita, shi kansa bai san mi yasa yayi mata hakaba, musamman idan ya tuna tazo ne saboda shi, ido ya rufe ya buɗe yana jin wani ƙunci da zafi acikin ransa, ji yayi an dafa kafaɗarsa ta baya, juyowa yayi da sauri yaga Isya direba ne "Ba tare kuka tafiba?" ya tambayeshi cikin muryar mamaki dan bai gama tantancewar ita kaɗai ceba ko su biyu.

"Shine abin daya bani mamaki nazo jin ko ta manta tare muke tafe, amma ban taɓaga ɓacin ran madam kamar hakaba, ka mata wani abu ne?" Isya ya tambayeshi yana kafeshi da idanuwansa, shuru yayi kafin yayi ɗaga kai "Tambayata tayi WAYE NI? Shine ban mata maganaba ta tafi."

Kallonsa yayi kafin ya girgiza kai "Ban san mi yasa Madam ta damu da kai har hakaba? Abune mai mutƙar wahla Madam ta shiga lamarin wani koda an sata bata fiya kasawaba, akaro na farko yau ta zo dan kawai ta ganka ta kuma sanka, sai gashi saɓanin tunaninta ka buɗa mata ƙasa a ido, kasa na fara jin kunyar kaina tun yanzu, ina kuma tuhumar kaina akan yabonka da nayi akallon farko da na maka, ashe kai ɗin kamar kura ce sanye da fatan akuya, bana buƙatarka atare da ni." yana gama faɗar haka shima ya juya yayi tafiyarsa, jikin Abdallah ne yayi sanyi ya dafe kai yana son sanin mi ya aikata haka arayuwarsa, koda alokacin da ya samu tsangwama da ƙiyayyar mutanen garinsu bai taɓa aikata kusan wananba, amma kuma sai gashi yau wanda suke sonsa ya saka musu da mafi munin sakamako.

_"Har yanzu kana da sauran lokacin da zaka gyara kuskuren da kayi tun kafin lokaci ya ƙure maka"_ wata zuciyar ta tunatar da shi, kamar wanda ya farka amafarki yayi saurin ɗago kansa ya shiga lalime da jijjuyawa, can ya hango Isya yana ƙoƙarin hawa mashin da gudu ya ƙarasa wajan sai dai kafin ya ƙarasa har sun ja mashin ɗin sun tafi.

Kai ya dafe yana tuna abin daya aikata, gashi kuma bashi da hanyar da zai sake samunsu.

"Ya Allah" ya faɗa yana rintse idanuwansa, karo na farko acikin rayuwarsa ya aikatama wani mutum abin ƙunci bama ɗayaba har mutane biyu "Mi yasa?" yake tambayar kansa yana dafe da kansa, ya ɓata lokaci mai tsayi awajan yana duba ko wata mota da take giftawa, yana fatan ace yaga Khaleesat ko Isya direba ne acikinsu.

"Abdallah" ARFAT ya kira sunansa yana dafa kafaɗarsa, dagowa yayi da idanuwansa wanda suka sauya kala daga farare zuwa sirkin Jaa.

"Ya salam mi yake faruwa ne na ganka ahargitse?"

Kai ya girgiza yana fidda zazzafan huci "Ban kyautaba ko kaɗan Arfat, ban san mi ya shiga kainaba har na aikata abin dana yiwa Isya da Madam ɗinsa, yau an buƙaci sanina amma na gagara magana, madadin hakan sai na sare duk wani karsashi da tabbacin da suke tunanin samu akaina" murmushi yayi wanda da ganinsa na takaici ne "Karo na farko yau an ƙirani da nakasasshe wanda yake buƙatar tallafin mutane " yana gama faɗar hakan ya raɓe ta jikin Arfat ya koma garejin.

Kallonsa Arfat yake ya gaza fahintar inda maganarsa ta dosa amma yasan koda ya tambayeshi abune mai mutƙar wahla ya sanar dashi gundarin maganar ta yanda zai fahimta, "Allah ya kyauta" abin daya iƴa faɗa kenan sanan shima ya nufi garejin dan kammala aikin daya fara.

Lokacin da ABDALLAH ya isa sai ya samu kansa da tsayawa a inda Khaleesat ta tsaya, maganganunta ne suke ta Amsa-kuwa acikin kunnensa, murmushi yayi ya fara dube-dube kamar mai neman wani abu, cikin dace ya hango wata ƴar ƙaramar jaka adai-dai inda motar su ta tsaya, ƙarasawa yayi ya ɗauka, yana buɗewa yaga waya ƙarama sai ATM da wasu takaddu yana buɗewa yaga docments ne na Makaranta mai ɗauke da sunan KHALEESAT MUHAMMAD AADA sai ƙaramin hotonta tana dariya, ƙurama hoton ido yayi yana murmushi sai kuma ƙirjinsa da yaji yana bugawa da ƙarfi, tsoro ne ko kuma fargaba bai saniba.

"Ya dai Bawan Allah kake tsaye kana murmushi kai ɗaya?" Arfat ya faɗa yana dariyar shaƙiyanci dan tun tahowar Abdallah yake biye dashi yana kuma ganin duk wani motsinsa, murmushi ya sakeyi ya miƙa masa jakar "Garin fushi ta mantasu." karɓa yayi yana kallon hoton ba tare daya duba sunantaba, ya gyaɗa kai yana murmushi "Kai ammafa yarinyar nan ta haɗu, ya kamata ka jefa ƙuri'arka ko zaka dace, idan kuma baka ciki kamin hanya mana Abokina."

Kallonsa yayi ya maka masa harar ya wurce hoton "Kawai da ganin mutum baka sanshiba sai kace kana so, dan kaine ɗan sarkin soyayya?"

Kai ya gyaɗa yana faɗaɗa dariyarsa wanda da ganinta ta shaƙiyanci ne "Kwarai kuwa, ai hakan shine yake faruwa, ko ku bakwa haka agarinku?"

Hararsa yayi ya fara tafiya ba tare daya amsa masaba "Ni kawai naji daɗin mantuwar da tayi, hakan ya bani tabbacin akwai haɗuwarmu da ita anan gaba, zan samu damar da zan gyara kuskuren da nayi."

"Wani kuskure kayi Abokina ?"

Kai ya girgiza yana yalwata fiskarsa da Murmushi "Oga na baza ido da alamu kai yake nema" nan kuma ya juya idonsa ga kallon oga Haruna wanda yake duba ma'aikatansa da aikin da suke nan yayi wuf ya ruga da gudu ya ƙarasa wajan motar dayake gyarawa, da dariya Abdallah ya bishi kafin ya rufa masa baya.


*****

Tafiya take tana bawa mptar wuta, kawai giftawarta akega wanda da yawa mutane suna tsorace da irin tuƙin da take, ɗai-ɗaiku acikin mutane ke mata fatan alkhairin sauƙa lafiya, yayin da wasu suke jifanta da zagi, amma ita kam ko ajikinta dan tafi buƙatar ta kai ga inda zataje, ranta amutƙar ɓace yake _"Mi yasa na damu da shi? Mi yasa nake jin haushinsa haka? Har yanzu zuciyata na ƙara son sanin waye shi? Ya Allah!"_ ta faɗa tana runtse idonta dan jin zuciyarta take na mata zafi, ikon Allah ne ya kaita makaranta lafiya da ƙyar ta samu wajen adana mota ta ajiye tata, ɗora kanta tayi ajikin sitiyarin motar tana jin ƙunci na ziyartar zuciyarta, amma bata son ta bawa kanta damuwar da zai sa kowa ya fahimci rauninta, ƙwanƙwasa glass ɗin motar motar da akeyi ne ya ankarar da ita, da sauri ta ɗago ta zuge glass ɗin motar ɗan murmushi tayi ganin wanda ke ƙwanƙwasa mata motar "SIDDIƘATY" ta faɗa tana ƙoƙarin sai-saita muryarta.

"Tun ɗazu naga shigowarki amma kuma sai naga baki da alamun son fitowa, ina fatan dai ba dole aka tursasaki zuwaba? duk da nasan kina son skull da karatu, sai dai ko wani abunne ya saki damuwa haka." ta kafeta da ido.

Kai ta girgiza tana murmushi "Ko kaɗan yau duka barci ne bai isheniba, da kamar bazan zoba amma bana son yin fashin ko wata lacture da za'a mana."

"Aifa ga idanuwanki nan da muryarki har yanzu basu dawo kalarsu na ainihiba."

Buɗe motar tayi tana ƙokarin fitowa, anan ta shiga lalimen jakarta da mamakinta babu ita, babu alamunta, kai ta dafe tana son tuna a ina ta barta, dan tana da yaƙinin ta sakata acikin mota, "Ya Allah, tabbas na wullarta agarejin nan."

"Ya dai? Mi kika wullar? Mi ya kaiki gareji."

Numfashi taja ta furzar da iska tana duba agogon dake saƙale ahannunta "Muje lacture lokaci yayi."

Ta ɗauki sauran tarkacenta tayi gaba Siddiƙa na biye da ita, tasan miskilancin Khaleesat ba sanar d ita zatayiba, shi yasa bata ƙara bi ta kantaba, ta bi bayanta, mutane da yawa suna mata magana iyaka ta ɗaga musu hannu ko murmushi dan bata jin son magana ayau kam, wanda kuma suke kallonta amatsayin ɗiyar govnor mai ci sukan yi ƙoƙarin ƙarasawa dan su samu hanyar shiga jikinta, amma hakan baya burgeta, dan har takaici take da saninta da akayi, ita bata burin wani girmamawar ƙarya atare da mutanen da suke kewaye da ita.

Haka aka gama lacture bata wani fahimta sosaiba dan hankalinta baya jikinta, tana gamawa ta fito ba tare data nemi tsaya Siddiƙa ba ta nufi motarta tayi gaba abinta.

Da kallo Siddiƙa ta bita tana mata fatan sauƙa lafiya "Wani lokacin miskilancinki da zurfin cikinka na bani takaici Khaleesat, kina da damuwa amma bakya son kowa ya sani." ita kaɗai take maganar tana ƙwafa.


***

Agajiye ta isah ya gida ta shige ɗakinta ba tare data duba Maa ta sanar da ita dawowarta, Toilet ta shiga ta watsa ruwa ajikinta kana ta ɗauro alwala dan alokacin ana sallah Zuhur bata tsaya wata kwalliyaba dan bata bukatar yinta, doguwar riga ta zira ajikinta mai taushi marar nauyi kalar sararin samaniya, sai hijab ɗan madai-daici ta shinfiɗa abin sallah, sai da ta iddar da sallah da yin azkar sanan ta miƙe ta ninke abin sallahr ta zauna akan ɗaya daga cikin kujerun da suke ɗakin, anan ta ɗauki babar wayanta ta fara lalimen wata numba cikin sa'a taji shigarta bata daɗe tana ƙaraba aka ɗauka da sallama, ƙirjinta ne ya buga da ƙarfi jin muryar kamar ta san mamallakinta.

"WAYE KAI" ta faɗa cikin sanyin muryarta.. 

Murmushi Abdallah yayi mai sauti dan ya fahimci ko wayece, gyara zamansa yayi, da alama wanan ɗabi'arta ce son sanin mutane, ita da take buƙatar kayanta ya zata fara da tambayar Waye mai ɗauke da wayar, "BAWAN ALLAH" ya faɗa ataƙaice yana murmushi da son jin mi zata kuma faɗa.

Anata ɓangaran kuma ta kalli wayar kamar mai kallon fiskar mutumin "BAWAN ALLAH" ta sake mai-maita sunan daya ƙira kansa da shi.........©by *😘Um Nass🏇*

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: HAƊIN GWARMAI 


© UM NASS


PAGE 43


  Sai da ta ɓacema ganinsa sanan ya sauƙe ajiyar zuciya, wani nishaɗi take ji atare da shi wanda bai san ko na miyeba.

Juyawa yayi da niyar barin wajan anan sukayi karo da Arfat tana fama washe baki sai sauri yake, tararsa yayi yana tambayarsa ina zashi? Hannunsa ya riƙe yaci gaba da tafiya har suka zo kusa da mashin ɗin da Madam Khaleesat ta nuna masa, mamaki ne ya kamashi na sosai dan yasan Arfat bai san ko daga ina mashin ɗin ya fitoba, bai sake tsinkewa da mamakiba sai da yaga ya sa mukullin mashin ɗin ya kunna.

"Wato lamarin Ubangiji da girma yake, duk lokacin da ya so yakan buɗe ƙofofin rahma ga bayinsa, abin da ban taɓa hasashensa akurkusaba sai gashi yau cikin Rahmar Allah garemu ya kawo mana shi." Arfat ne ke magana yana hawa kan mashin ɗin "Wani lokacin baka san daga ina ne mabuɗin arziƙinka yakeba, har sai ya matso gareka, lallai hanyar samu da yawa take idan kuma kace zaka daƙusheta kamar kayima Allah butulci ne."

Shi dai Abdallah ganinsa ya tsaya yanayi ba tare da ya ce masa ci kankaba, sai dai har zuwa wanan lokacin mamaki yake ta inda maganar Arfat ke Isa, kafin yayi magana yaja mashin ɗin yayi gaba abinsa kamar ma bai san da tsayuwarsa awajanba, kansa ne ya ɗaure "To ko dai dama ba Madam khaleesat bace ta zo da mashin ɗinba tsokanarsa take? Dan yayi mamaki dama ina ita ina masa kyautar mashin mai mutƙar tsada, tunda gashi fama ta ke da tsohuwar mota" baki ya taɓe ya ɗaga kafaɗa "Ita ta sani, ni dama ba damuna kyautar tayiba." ya faɗa kamar yana magana da wani, sanan ya nufi cikin garejin da ci gaba da aikin da yakeyi.

Sai dai kafin ya kai ga shiga yaji ƙarar mashin ɗin da Arfat ya fita da shi, gabansa ya jaa ya tsaya kana ya cire hular kwanon da ke kansa fiskarsa ɗauke da mashin "Yau ɗaya jina nake kamar dan shugaban ƙasa, gani nake kamar nafi kowa ayayin da nake jan mashin ɗin nan, tamkar ana ƙarama rayuwata farin ciki ne."

Dariya maganar tasa ta bawa Abdallah wanda yayita harda ƙyaƙyatawa abin da yasa Arfat tsayawa kenan yana kallonsa, dan bai taɓa ganin dariyarsa hakaba, sai da yayi mai Isar sa sanan yayi shuru "Tabbas alamu sun nuna hakan koda ace baka faɗaba."

Shima dariya yayi ya sauƙa akan mashin ɗin, sanan y miƙa masa mukullin mashin ɗin da wasu takaddu, karɓa yayi yana son ƙarin bayani "wanan mukullin mashin ɗinne da takaddun da suke sheda mallakinka ne, ladan tsuntuwar jakar da kayi ne daga madam ɗinka, cike yake taf da mai ga daɗin tafiya, ban tsaya jiran rakiyarkiba sai da nasha romon daɗinsa, kasancewata mutum na farko a hawansa" baki ya sake washewa "Banyi tsammanin samun koda 10k bane saboda tsintar guntuwar wayar da kayi, da takaddun da xa'a iya sabunta wasunsu, amma abin mamaki kyautar Mashin sabo wanda sai wane da ɗan wane ke mallakarsa, kuɗinsa kaɗai ya isa wani mallakar gida da sana'ar da zai rufawa kansa asiri. Abin tambayar anan saboda tsuntuwar akayi kyautarsa ko kuma dama ana son yin kyautar tasa? Sanan wacece Madam Khaleesat? Na tabbata ba ƴar ƙananan mutane bace."

Shuruu Abdallah yayi yana kallon Arfat kansa shima ya kulle da wani bahagon tunani, girgiza kai yayi yana wassafo kamaninsa.

Anya wankin hula ba zai kaishi dareba? Mi yasa zuciyarsa ke son kaishi muhallin da ya daɗe da masa nisa, nisanma na sosai ɗin nan? Kamar ace mutum ya ɗago sama da hannunsa wanan abune mai mutƙar wahla. Tafiya yayi yana jujjuya takaddun mashin ɗin a hannunsa ba tare da ya cema Arfat komiba, haka shima dan yasan yana buƙatar yayi tunanin, cak ya tsaya, ya juyo ga kallonsa ga Arfat "A ina zamu samu Isya direba? Shi kaɗai ne yake da damar da zai amsa mana tambayar mu?"

Kai ya girgixa "Gaskiya ban san ina zamu sameshiba, dan ko lambar wayarsa bani da ita kuka samu saɓani."

Bai sake cewa komiba ya jinjina kai yayi gaba.


****

Da gudu-gudu ta ƙarasa ta faɗa kanta tana maƙalƙaleta cikin dariyar dake nuna cewar tana cikin farin ciki.

"Ya Rabi! Wanan ai zaki ƙarasani, ki rugurguzani, irin wanan afkawar da kika min"

Sauƙar da kanta tayi ta kwantar akan kafaɗarta tana sauƙe ajiyar zuciya, "Kaii Maa ina naga nauyin da zan rugurguza ki, nifa gaskiya na gaji ina son Abu na ya dawo."

Murmushi Maa tayi ta na shafa fiskarta "Sai ki faɗa masa ai, dan ke ta gaban goshinsa ce."

Fiska ta kwaɓe kamar mai shirin yin kuka "Bayan kullum kullum mukayi waya da shi cewa yake na saka ido yana tafe, Allah kwa na gaji da jin magana ɗaya."

Dariya Maa tayi kafin nan tace "Kunɗu kusa ai."

Ƙaran wayar Khaleesat ne ya katsar musu maganar tana duba taga baƙuwar lamba, ido ta ƙura mata kafin ta taɓe baki har ƙiran ya katse.

"Mi yasa baki ɗaukaba?"

"Ban san mai ƙiranba ne"

"Wanan ba kyakkyawar ɗabi'a bace, dan baki san mai ƙiraba sai ki-ƙi ɗauka, kinsan uzurin da mai kiran zai bada? Wani lokacin sai kiga matsuwa ce ko kuma buƙata da zai sa akiraki, wani lokacin kuma wanda ya sanki ne bashi da kuɗin da zai kira awayarsa dole sai ƴa ari waya, kinga idan akace baza'a ɗauki baƙuwar lamba ba sai asamu damuwa wanda da ka ɗauka da hakan bata faruba, zai iya kasancewa taimakonka za'ayi akan abin da baka saniba, kinga ke kikayi asara ba mai kiranba. Kada hakan ta sake faruwa kina jina ko?" ta faɗa cikin tsawa wanda yasa khaleesat hawayen da bata shirya ba dan ta tsani tsawa arayuwarta.

Kafin tayi magana kiran ya sake shigowa da saurinta ta ɗaga tana jan zuciya, ido ta fiddo waje jin muryar mai maganar "KAI NE DAMAN?"

Kallonta Maa tayi ganin yanayinta ya sauya daga damuwa zuwa farin ciki kai ta girgiza tana murmushi tabar mata wajan ta nufi kitchen dan ganin lokaci ya tafi.


Note:

Kamar bakwa buƙatar wanan labarin ganin yanda bakwa iya yin koda godiya balle dogon comments, vote kuke yi shima ba kowa ke iya yinsaba, ina ɓata tsawon awanni biyu koma fiye da haka saboda na faranta muku, amma kun gagara ɓata mintuna biyu kuyi comment, dan haka zan haƙura da yin publish ɗinsa anan na koma yima ƴan whtspp dan su suna buƙatar sa da bani ƙwarin gwuiwa akan yinsa cike da so da karsashi.


 © UM NASS

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: HAƊIN GWARMAI🎊


©by 😘Um Nas🏇🏼


Page 42


 Kallon wayar tayi kafin nan ta taɓe baki "Kowa ma bawan Allah ne."

Saurin tarar numfashinta yayi "Ba kamar ni dana amsa matsayi biyu ba, kasancewata Bawan Allah haka mutane suke kirana da sunan, saɓanin sauran mutane da suke da sunan da ake kiransu da shi."

Baki ta sake taɓewa saboda maganar na ƙara ƙular da ita, abin da ta lura kuma shi ɗan rainin hankali ne "Uhmm wayar da kake magana da ita tawa ce, a ina zan sameka? Akwai wasu takaddu masu mihimmaci atare da wayar, Allah yasa ka gansu atare da wayar.?"

Ido ya rufe ya buɗe yana jin sauƙar ko wata kalmar maganarta acikin jikinsa.

"Eh na samesu atare da ita, amma kuma nawa ne ladan tsintuwar da nayi?"

"Kana buƙatar lada ne bayan kasancewarka Bawan Allah?"

Faɗaɗa murmushinsa yayi, wanda ya bada sautin da ya isa kunnenta "Sosaima dan ko wani abu yana buƙatar kyautatawa ko?"

Itama murmushi awanan gaɓar, dan ta fahimci akwai barkwanci atare da wanan mutumin "Shikenan zan turo maka da ladanka, idan zan aiko akarɓa min wayar, ka faɗi a inda zan aika a sameka."

Kai ya girgiza kamar tana ganinsa "A'a kizo da kanki, dan zakifi bani ladan tsuntuwar da nayi mai tsoka, kizo garejin gyaran mota na baban titin dake hanyar Jami'a, sai ki kira ko zaki sameni."

Shuru tayi tana nazari, dan ko kaɗan bata fatan sake fita awanan lokacin, haka bata buƙatar komawa wanan wajan, amma kuma wayar da takaddun nada muhimmanci atare da ita, numfashi taja ta furzar da iska abakinta, dan wata gajiya ke mata sallama da maraba, ga kuma baƙin cikin daya ɗarsu aranta, sai dai bata son sanar da koma waye ko ita wace, badan hakaba da ta bashi kwatancan gidansu, amma kuma idan tayi la'akari da cewar ita ke nema dan haka zaifi kyau taje da kanta.

"Shikenan zanzo yanzu na karba In sha Allah" ta faɗa cikin muryar ta mai sanyi da alamun gajiya atare da ita, sai dai aɓangaran Abdallah ta saka masa bugun zuciya da tsoron da bai san ko na miye ba.

Bin wayar yayi da kallo bayan ta datse kiran kafin ya ƙara magana, shi kaɗai yake murmushi kamar da yayi tsuntuwa mai tsoka.

Ji yayi an shaƙe da dariya wanda ta sashi juyawa, ganin Arfat akansa ya sashi ƙoƙarin dai-daita nutsuwarsa.

"Anya Abdallah baka zurma acikin tafkin So ba? Ni dai ban taɓa ganinka ka haƙiƙance kana surutu kamar hakaba."

Ido ya fiddo waje kamar yaga abin tsoro "Ko ɗaya, rabani da Soyayya awanan lokacin, ina ni ina ita, ai da gani ta wuce matsayina, uhmm kawai dai Yarinyar tana bani dariya ne."

Kai ya gyaɗa yana murmushi "Daga dariya kuma sai ta koma baka tsoro."

Kallonsa yayi bai ce komiba dan ya fahimci inda maganarsa take, akai-akai yake duba lokaci da wayar yana fatan ta sake kiransa, sai dai kuma shuru babu alamun kiran, yana son kiran Numbar data kirashi yana ganin rashin dacewar hakan.

Har lokacin tashinsu yayi babu ita babu alamunta hakan ya dameshi sosai tun yana dannewa har ya gagara ya faɗama Arfat "Kaga har zamu tashi bata zo ta karɓi jakartaba."

"Ƙila wani uzurin ne ya hanata zuwa." daga haka ya ci gaba da tattare musu kaya, cikin rashin kuzari Abdallah ya fara tayashi haɗa kayan, sanan sukayi sallama da oga Haruna.

Tafiya suke babu magana sai dai ko wata mota tazo giftawa Abdallah na binta da ido, yana fatan sake ganin Madam kamar yanda yaji Isya na kiranta, amma ko alamun motarta babu, Arfat na ankare da shi sai faman dariya yake har suke tare mai Adai-daita suka tafi, ahanya ne Arfat y fara magana "Ya kamata mu siyi mashin dan inaga ɗawainiyar zatafi mana sauƙi idan akace muna da abin hawa namu na kanmu." Arfat ya faɗa cike da mita da nuns gajiyawa da neman abin hawan da suke ako wata rana.

"Aifa" kalmar da Abdallah ya faɗa yana bin wata mota da kallo kamar ya wuntsula, janyoshi Arfat yayi cikin ƙunan rai "Wai kai lafiyarka? Tun da muka fito na lura da kai kamar wani taɓaɓɓe, kowata mota tazo giftawa ka dinga binta da kallo, yanzu kuma kabi wata kamar zaka wuntsula waje kanaga yanda garin nan yake cike da ababan hawa kaje wani marar hankalin yabi ta kanka."

Numfashi yaja yana ƙoƙarin dai-daita nutsuwarsa "Hankalina ya gaza kwanciya, gani nake kamar zata zo ta tadda bama nan, dama ace na karɓi kwatancan gidansu to da zai fimin sauƙi na kai mata."

Kallonsa Arfat yayi jin yana magana cikin sanyin muryar data ninka tashi dariya ce taso kamashi amma ya gimtse "Ka kira Layin data kiraka da shi mana, kaji ko lafiya?"

Wayar ya fara dannawa yana kiran no da aka kirashi da shi, amma kuma arufe baya shiga "A kashe yake."

"To kayi haƙuri zuwa anjima sai mu sake gwadawa."

Kai ya gyaɗa ba tare da ya sake maganaba, ya lumshe idanuwansa, ahaka suka isa gida.

Bayan sun sallami mai Adai-daita suka cusa kansu gidan, sai dai abin mamaki yau gidan nasu acike yake da yaara da ƴan matasa suna ta karatun Alqur'ani lamarin da yasu mamaki kenan, dan basuyi tsammanin za'a samu yawaitar mutane hakaba.


Mb:

Kwanaki biyu da yin maganar makarantar da Haajara tace zata buɗe dan ɗorama yara karatun Alqur'ani, badan ta samu wani abu na daga kuɗiba sai dan ta samu romon ladan da ke cikin koyarwa, hakan yasa mama Anta sanar da su Arfat shima yaji daɗin hakan, dan da kansa ya sanar da limamin unguwarsu shima yaji daɗin hakan baiyu ƙasa agwuiwa ba ya shelantawa mutanen unguwar, da fari ba'afi mutum biyar bane suke fara zuwa, wanda hakan yasa jikinsu Arfat ɗin yin sanyi, sai dai kuma basuga damuwa atare da Ummien Abdallah ba asalima murna tayi da hakan, ahankali kuma sai ake samun daɗuwar ɗalibai, dan Mama Anta har da ita ake ɗorin takance Madallah da kasncewarta atare da Ummien Abdallah, dan da yawa ƴan unguwar suna musu kallon ƴan uwane.

Sai dai saɓanin tunaninsu yau gidan cike yake taf da ɗalibai, wasu ma ba'a fara musu ɗoriba.

Ƙarasawa Abdallah yayi yana murmushi, ya ɗauki Alqur'ani ya fara yima wasu ɗorin cikin daddaɗar muryarsa da kuma fiddawa ko wani baƙi haƙƙinsa.

Kujera Arfat yaja yana kallonsa cike da Sha'awa, haka itama Ummien nasa tana jin wata soyayya da alfahari atare da yaron nata.

Hakan ya kawo sauƙi sosai wajan kammaluwar ɗorin karatun, daga nan ya jeranto musu Addu'a suka shafa aka tashi.

 Ƴan matan ke binsa da kallo wasu na ƙawata kyansa yayin da wasu suke fatan ya zama mallakinsu, dan wasu har tuntuɓe suke garin waiwayensa, dan wanan shine karo na farko da suka fara ganinsa.

Kallonsu Ummie tayi bayan gidan ya rage sai su kaɗai, "Sannunku da dawowa, Arfat ɗana ƙaraso mana ga shinfiɗa zatafi maka sauƙin ware gajiyarka." ta faɗa tana shimfiɗa murmushi afuskarta, da sauri Abdallah ya dawo kan shimfiɗar yana turo baki kamar yaro ƙarami "Nima da ba'a ƙiraniba ai zanzo na zauna ɗin."

Nan suka yi dariya "Oho dai haka ma ba kai aka yima tayiba." 

Sai lokacin Mama Anta ta ɗago da kanta daga tilawar karatun da take, dan ɗori aka mata shi yasa take ƙoƙarin son riƙewa, harara ta bugawa Arfat ta maida kanta taci gaba da karatunta.

Dariya Arfat ya saki "Su Mama yau an koma makaranta ko magana ba'ayi." jifansa tayi da takalmin dake kusa da ita, yayi saurin matsawa "Allah ya shiryaka Arfat." ta faɗa tana murmush.

"Ameeen Mamanmu" adai-dai lokacin Ummie ta gabatar musu da abinci da abin sha, "Maza kuyi sauri ku chi abinci kada akira sallahr magrib."

Zama suka gyara suka fara ci, sai dai ko kaɗan Abdallah bashi da kuzarin ci, sai faman caccakar cokali yake, adai-dai lokacin Mama Anta ta shafa Addu'a ta ɗago da kanta taga yanda Abdallah ke juya cokali. 

"Abdallah ya baka cin abincin? Ko baima daɗiba ne na girka maka wani?"

Saurin girgiza kai yayi "A'a mama yunwa ce dai bana ji sosai."

Dariya Arfat yayi yana kai loma bakinsa "Ai suraka kikayi Mama sai dai ta ɓacema ganinsa, wanan shi ya hanashi cin abinci."

 "Wai haka ne Abdallah?" ta sake tambaya tana faɗaɗa murmushinsa, tashi yayi daga cin abincin ya nufi ɗakinsu "Karya yake min Mama" Dariya suka saka gaba ɗayansu ganin yanda ya tafi yana sassarfa.

Da kallo Ummie ta bishi tana sauƙe ajiyar zuciya, aranta tana fatan abin da Arfat ya faɗa ya zama gaskiya, sai dai tana jin tsoron yiyuwar hakan, idan tayi la'akari da matsin da suke ciki, ga kuma rashin dangin da zasu tsaya masa akan lamarin. Numfashi taja tana ƙara faɗaɗa fuskarta da murmushi dan da kamar wuya Abdallah yayi wanan kasadar.

 Anan Mama ta tambayi Arfat gaskiyar magana, yace "Tsokanarsa nake Mama" sai ya sanar dasu abin da ya faru, numfashi Ummie taja tana sauƙe ajiyar zuciya, "Na gode Allah" ta furta ba tare da ta san ta faɗi hakanba.

Kallonta sukayi cikin tuhumarta, sai kuma ta faɗaɗa fara'arta "Naji mamakin hakan." ta faɗa tana kallonsu sai kuma suka saka dariya dukkaninsu.


*****

Ko wata rana tazo Abdallah cikin duba hanya yake, yana dakon jiran ganin Khaleesat Amma shuru babu alamunta, ya kuma kirayi layin data kirashi sau ba adadi amsar ɗaya ce arufe layin yake, wani lokacin kuma tayi ta ringim amma ba'a ɗaga.

Sosai ya damu da son ganinta, sai dai zuciyarsa na jin tsoron ko dai ta ganeshi? Shi yasa taƙi zuwa. Tun yana lissafin kwanakin har ya koma lissafi da sati, Arfat na hankalce da shi, da kuma ko wani motsinsa, ya sauya sosai, murmushinsa ya ragu akan na da, dan sai su ɗauki lokaci baiga yayi murmushiba, kullum hankalinsa na kan ƙofar garejin da shigar ko wata mota idonsa na kanta, amma babu alamunta babu kuma shedar zata zo, tuni ya sare sai kallon hotonta da yake shi kaɗai zakaga yana murmushi yana tuna hirarsu da ita.

Sai dai karatun da yake taya Ummie idan sun tashi yakan rage masa tunani, sai damuwar da take damunsa akan shisshige masa da ƴan matan sukeyi, wasu kuma har wasiƙa suke aiko masa, ko takansu baya bi, ganin abin na neman yi masa yawa yasashi daina yin ɗorin koda sun dawo to amasallaci yake tsayawa har sai anyi sallahr magrib yake shiga gidan, tun su Mama Anta na tambaya har suka haƙura suka zuba masa ido, ya dawo miskilin gaske fiye da tsammani, magana na masa wuya balle akai ga matakin dariya.

Arfat yayi faɗan yayi magiyar har ya haƙura ya fita acikin lamarinsa. Iyaka aiki ya haɗasu sai kuma idan yaso tsokana yace ga motar Madam nan, nan zai miƙe azabure yana dube-dube, nanfa zaiyi ta masa dariya.


 ****Bayan Wata Biyu.

Ahankali take tuƙa motar kamar bata son isa inda take nufa, kai tsaye ta samu wajan da yake na adana motocin, sanan ta zuro da ƙafafuwanta wanda suka ƙawatu da jan ƙunshi tare da kewayawar baƙin takalmi ƙirar Dubai, Fitowa tayi cikin shigarta ta rai-da-rai doguwar riga mai launin ruwan zuma da adon baƙin duwatsu, sai baƙar jakar da ke rataye ahannunta, sai agogon da yake ɗaure atsintsiyar hannunta mai launin ruwan zuma sheƙin da yake ya nuna asalinsa na zinare, Fuskarta fayau babu yawaitar kwalliyar daga kwalli sai powder fara da kuma lips abakinta, hakan ya fito da ainihin kyanta.

Dai-daita tsayuwarta tayi tana jingine da motarta, ta fara lallatsa wayarta kafin ta kai wayar kunnenta, cikin sanyin muryarta data ninka ta kwanakin da suka wuce "Ina garejin dai-dai wajan adana motoci." Kalmar data faɗa kenan ta datse kiran, tana duba agogon dake hannunta.

"Assalama alaikum" taji muryar da take mata amsa amo acikin kunneta ko wata rana, da sauri ta ɗago kanta sukayi kallon-kallo fiskarsa ɗauke da murmushi.

Amsa masa sallamar tayi ta kawar da kanta ba tare da ta sake masa maganaba, akaro na biyu ta sake kallon agogon da ke saƙale ahannunta, sanan ta sake daddana wayar tata, da mamakinta taji ƙaran wayar akusa da ita, dagowa tayi suka sake haɗa ido miƙa mata wayar yayi yana murmushi wanda bai san ko na miyeba, amma tun lokacin da yaga kiranta yake jin kamar an sauƙe masa wani nauyi aƙirjinsa, ganinta da yayi kuma ya sashi jin farin ciki mai yawa.

"Mi yasa wayanki kullum arufe? Idan kuma an kiraki bakya ɗagawa? Tsawon watanni biyu kullum cikin jiranki nake kizo ki karɓi wayarki da kayanki, ko wata rana sai na duba hanya ko zanga zuwanki, har na fidda rai akan zaki zo ki karɓa."

Baki ta taɓe tana kallonsa ido cikin ido "Daga lokacin da naji wayar na wanan garejin naji bana buƙatarta, ban san mi yasaba amma araina inajin bana son sake ganinka, dalilin da ya hanani zuwa kenan, yanxu ma wata damuwa ce ta tashi nazo karɓan takadduna, amma ko kaɗan banyi tunanin kai ne ka tsinci jakataba."

Mamaki ne ya kama Abdallah, amma kuma daya tuna abin da ya faru abaya, sai yakega ta masa da sauƙima, murmushi yayi yana gyara tsayuwarsa.

"Koda ace na sanar dake WAYE NI?"

Kai ta gyaɗa tana kallon idanuwansa "Hakan bazai ƙareni da komiba, na gode da adana min kayana da kayi." ta faɗa tana karɓan jakar dake hannunsa.

Saurin janyeta yayi yana kallonta "Ina ladan tsuntuwar da nayi."

jakarta ta buɗe ta miƙa ɗauko mukulli ta miƙa masa, kallonta yayi cikin mamaki "Ban san waye yayi tsuntuwarba, amma ga ladan tsuntuwarsa nan." ta faɗa tana nuna masa wani mashin ƙirar Bike, kai ya fara girgizawa yana murmushi ya miƙa mata takardun "Bana buƙatar wanan, abu ɗaya nake buƙata shine kiyi haƙuri akan abin da na miki abaya, sai daga baya naga rashin dacewar hakan."

Karɓa tayi tana murmushi bata masa maganaba ta shiga mota, da sauri ya ƙarasa kusa da motar kafin ta rufe "Bana son na zama silar ɓatawa wani rai, hakan da nayi yasa ni yin dakon jiranki tsawon watanni biyu dan kawai na baki haƙuri, na hukunta kaina da rashin walwala inaga kamar kowa yana jin haushina ne, ashe ni nake jin haushin kaina da kaina." ya ƙarasa maganar cikin sanyin muryarsa.

Murmushi ta sake yi "ka daina hukunta kanka, saboda Rayuwarka taka ce, idan ka so ka gayyato masu tayaka jin daɗinta ko ka koresu, babu mai ganin aibunka."

Murfin motar ta ja ta rufe ta bawa motar wuta, da kallo ya bita yana murmushi wanda zan iya cewa kamar yafi kuka ciwo, har tayi nisa ta tsaya ta leƙo da kanta ta ɗaga hannunta ta dunƙule tabuɗe babban yatsan sanan ra juya shi ƙasa, alamar faɗuwa kenan, sanan ta ja motar, dariya ce ta suɓuce masa wanda babu makawa ta farin ciki ce.. .

   {washhh yaufa nayi ƙoƙarin faranta muku, ku daure kuma ku faranta min ta hanyar yin cmmnt.} ©UM NASS

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI 🎊*


©by *😘Um Nass 🏇🏼*


_KINA INA KHADEEJA JA'AFAR dama ƴan *Sophie nd VC novel da ZAUREN BIYUN AUNTY* duk ku matso wanan shafin naku ne, kuyi yanda kuke so da shi, ngd sosai da cmnts naku 🤝🏼_


Page 45


ABDALLAH


Tsawon kwanaki biyu kenan yana baza ido da kunne dan jin kiran Madam Khaleesat amma shuru babu labarin kiran, tun yana sa rai har ya haƙura gashi baya son ya kirata gudun kada tace ya takura mata da kira.

Aɓangaran Ummiensa makarantar da ta buɗe ta samu ɗaukaka sosai ta yanda matan aure suma suka roƙi alfarmar aware musu ranakun da zasu na zuwa ɗaukan karatun, dan da yawa mazajansu ne suka zo suka roƙi wanan alfarmar, haƙuri ta basu akan zasuyi shawara da ƴar uwarta. Ko da ta samu Mama Anta da maganar murna tayi tana hamdala ga Allah take ta amince ta bata shawara akan ta ware ranaku uku ga matan aure sauran ranaku huɗun kuma sai tayima ƴan mata da yara. Shawarar tayi mata daɗi sosai hakan ya sa bata jinkirtaba ta sanar da su, sunyi farin ciki da kansu iyayen yaran suka yanke shawarar bata kuɗin wata ko wani ɗaliba ɗaya 200 firr ƙi tayi sai da suka roƙeta suka kafa hujja akan ko lokacin da khalifa Umar yake mulki ya bama malamansa albashi dan rage hidima haɗe da hujjar da ya kafa akan basu da inda suke zuwa dan neman kuɗi face koyarwar da suke, to itama ba wata sana'ar ta riƙa ba face koyarwar. Hakan da ta ji yasata amincewa cikin ikon Allah wata nayi kafin tayi magana ko wata ɗaliba ta kawo kuɗin watanta, wanan ya rage musu hidima dan raba kuɗin biyu take ta ɗauki kaso ɗaya ta bawa Mama Anta ɗayan, sai sun kai ruwa rana take ɗauka shima ba dan amfanin kantaba idan ta fita takan biya ta siyomata kayan sawa kama daga kan riguna dogwaye masu sauƙin kuɗi zuwa atamfa da shimi siket na ciki har da hijabi, sai sun fafata sanan take karɓa kullum cikin godiya take mata akan hidimar da take mata wani lokacin har kuka takeyi idan ta tuna wahalar da suka sha abaya, kullum cikin godiya ga Allah take, amma kuma tana hango girman ƙaddarar data sa ta baro gumsa bayan jurar wahlar da tasha abaya, takan danganta hakan akan sauƙin rayuwa da jin daɗi ne yasa Allah ya yanke musu wahlarsu.

Zama suke cike da Amana da ƙaunar juna haka ko kaɗan babu hancini da tsangwamar da zata nuna cewar sakaye suke agidan, da yawa mutanen unguwar yanzu girmama Mama Anta suke saɓanin abaya da suke mata kallon ƴar tasha mai sayar da abinci, zuwan Haajara ya kawo mata haske da buɗi acikin lammuranta, ahankali sai taji bata sha'awar sayar da Abincin da take saboda ilimin da ya fara shiga kanta, tanaga kamar tana ƙasƙantar da darajartar duk kuwa da cewa halak ɗinta take nema.

Nan Ummien Abdallah ta bata shawara tanayin kaɗan agida sai afitar da shi ƙofar gidan, abin mamaki ranar farko da sukayi abincin nata tass ya ƙare har ana nema, tun daga wanan lokaci ta hutar da ranta da zuwa tasha ta ke saidawa agida cikin ikon Allah cinikin har ya ninka na da hakan ba ƙaramin daɗi yayima Arfat ba ya dinga godema Ummie lalai ya yarda su haske ne acikin rayuwarsa, ya ƙi jinin zuwa tashar da take amma babu yanda ya iya idan ya tuna cewar lokacin basu da mai dafa musu.


***

Tafe suke akan mashin ɗinsu wanda suna tafiyar ne kamar basa so, tsaki Arfat yayi yana duba agogon dake hannunsa "Abdallah kayi sauri mana sai tuƙi kake kamar mai tsoron hanya, kana faman tafiyar hawainiya, Allah na tafe aƙasa ya fimu saurin tafiya ma ga rana nata kwallarmu." ya ƙarasa maganar yana faman tsaki, murmushi Abdallah yayi yana duba hanya "A'a Arfat ban yarda da kasada da rayuwaba, nasan komin daren daɗewa zamu je, ina laifin wanan tuƙin da nakeyi awanan garin da ya cika da ababen hawa, koya nayi kuskure sai an samu matsala."

Tsaki yayi sanan ya kauda kansa "Ɗan dakata." tsayar da mashin ɗin yayi agefen titi sauƙa Arfat yayi sanan ya kalli Abdallah "Sauƙa kaima" sauƙa yayi ba musu Arfat ɗin ya fara hawa sanan yace "Hau muje Hawainiya, dan idan na biyaka sai mu kai yamma bamu kai inda zamu jeba, da wanan tafiyar taka marar karsashi, ba tattalin rayuwarka kakeba, dan nasan bata tare da kai, kabar tunanin yarinyar da har yanzu baka gama sanin wacece itaba? Ta iyu ɗiyar wani hamshaƙin mai kuɗin ce koma shugaba, dan haka ka rufawa kanka asiri dan sawun giwa ya take na raƙumi, haka kuma kowata ƙwarya da abokin burminta, gara ka tsaida ranka da abin da zai fissheka."

Murmushi Abdallah yayi kana ya hau mashin ɗin "Ni ban damu da matsayin da ta takaba Arfat, abin da nakeji atare da ni indai shi ake kira so to lallai ya shammaceni, ya kuma kaini matsayin da ban taɓa hasashen zan hauraba, ban damu da ko ita waceceba abu ɗaya na sani zanyi ƙoƙarin jure ko wata wahla ne akan abin da nakeji, ina ji araina ita ɗin rabona ce, haka kuma babu wani abu da zai rabani da ita, sai yanzu nake tunanin Ƙaddarar haɗuwarmu ce tasa na baro mahaifata."

Kai Arfat ya jinjina yana murmushi adai-dai lokacin suka zo madakata wanda aka datse ko wani mutum, ga tarin ƴan sanda da suke ta faman muzurai da bindiga gefe ɗaya manyan sojoji ne suma masu baƙar fiska da ban tsoro, tsaki Arfat yayi ahankali "Ko sai yaushe ne zamu samu ci gaba? Ko wata rana ta duniya idan govnor zai wuce sai an dakatar da mutane ba tare da sanin uzurin da ya baro su da gidaba, amma saboda mutum ɗaya kawai an kashe uzurin kowa, koda marar lafiyar da yake gaɓar mutuwa ne, barinsa ake atsaye ƙila har ajalin da yake gudu ya riskeshi awajan."

Kai Abdallah ya jinjina wanan shine karo na biyu da ya taɓa ɗatsar hanya alokacin wucewar govnor bai san mi yasaba amma yau ko kaɗan baya jin farin ciki azuciyarsa, kamar yanda kwanakin baya yaji, maganar Arfat ta ankarar da shi akwai rashin Adalci acikin wanan tafiyar, amma kuma suka iya idan suka tuna suna aƙasar da talaka bashi da ƴancin kai sai abin da ya gani, ƙasar da kuɗi da mulki ne kaɗai suke magana aji koda ba gaskiya bane.

Juyawa yayi gefe anan yaga abin daya ɗaga masa hankali wata yarinya ƙarasa kayanta duƙun-duƙun kanta na zubar da jini ahannun wata dattijuwa, sai hawaye take tana kuka, tana roƙon mai mashin ɗin daya ɗaukosu akan su sauya hanya, amma fir yaƙi sai hura hanci yake akan ta nan yafi kusa kuma adalci ya mata daya ɗaukosu dan kuɗinsa ko kaɗan bai kaiba.

Tausayinsu Abdallah yaji ya kamashi yana tuna wasiyyar da Ummiesa ke masa akullum na jin tausayin wanda bashi da ƙarfi da taimakonsu dai-dai iyawarsa. Nufar wajan su yayi yana tambayarta ko lafiya tabar yarinyar jini na zuba ajikinta? Kuka ta fara yana face hanci ga yarinyar numfashinta na barazanar ɗaukewa.

"Wani mai mota ne ya kaɗeta ya gudu ya barta anan, shine yara suka faɗa min nazo na ɗauketa, yaro mu talakawa ne bani da ko sisin magani marainiya ce, gashi yanzu hanyar an kasheta babu damar tafiya zuwa asibiti."

"Babu wata hanyar dole sai wanan?" ya saita tambayarsa ga matuƙin mashin ɗin.

'Babu" ya faɗa ataƙaice yana muzurai.

Da sauri matar ta tareshi tana runtuma kuka "Bawan Allah ta mutu numfashinta ya ɗauke, wayyo ni Marka na rasa Mero" ta faɗa tana gunjun kuka tana girgiza ɗiyar tata, tuni kallon ya dawo kansu, karɓarta Abdallah yayi ta ɗora hannunsa akan ƙirjinta alamun akwai numfashi yasa sanar da ita tayi suma ne, amma tana raye.

Cikin takunsa mai ƙarfi ya fara tunkarar titin matar na biye da shi, amma kafin ya gifta sojojin suka masa Caa akansa, kallonsu yayi da idanuwansa da suka sauya kalla daga fari zuwa jajaye idanuwan da ko yaushe cikin lumshewa da jin barci suke yau sun buɗe tarr cike da takaicinsu da ɓacin rai yace "Ku matsa ku bani waje marasa Amfani, ina tunanin ko wani mai ɗamara ya tashi yin alƙawari akan zaiyiwa ƙasarsa aiki da hidima yake ba tare da cin amana ko gazawaba, amma awajanku kun karya wanan alƙawarin madadin haka uzurin mutane kuke datsewa kawak saboda mutum ɗaya, hatta marar lafiyar da yake jiggatuwa ba zaku iya masa alfarma aceto rayuwarsaba ta hanyar sadashi da asibiti."

Kallonsa suke kamar basu fahimci abin da yake faɗaba, ko kaɗan basu bashi alamun sassauciba saima bindiga da suka kara akansa, ransa ne yaji ya ƙara ɓaci sosai ido ya rintse yana jin wani zafi acikin ransa wanda bai taɓa jinsaba.

Mutanen wajan duka sun zuba musu ido sai Arfat da yayi mutuwat zaune dan sai lokacin da aka sakama Abdallah bindiga akai sanan ya fahimci ko waye, mamakin abin da Abdallah yayi ne ya sashi daskarewa awajan kafin yayi wani yunƙuri jiniya ta fara karaɗe wajan da suke alamun bayyanar govnor awajan.

Tuni matakan tsaron sun ƙara kasawa da tsarewa dai-dai lokacin da motar govnor ta kawo kai Abdallah ya buɗe idanuwansa da suka rine yayima ƴan sandan da suka kewayeshi wata uwar ingiza tuni sun watse sun hau kan titi, dole motocin da suka taho suka tsaya cikin mahaukacin birki.

"MAZAA" Ya faɗa cikin muryar da ta firgita mutanen wajan harda sojojin da suka nufeshi da zumar dukansa, anan sukaga ya zame musu kamar wani Zaki duba da ƙwayar idonsa data sauya kallo ga ɓacin rai da ya haddasa masa karkarwar jiki, buɗa masa sukayi kai tsaye ya nufi motar da yake da tabbacin ta govnor ce ya buɗe gidan baya ya shiga "Muje Asibiti" Ya faɗa cikin muryarsa da ta cika da Amo da kaushi.

Juyawa direban yayi yana kallon govnor cikin karkarwar jiki ga kuma P.A agefen direban wanda shima hannunsa ya ɗauki rawa, kai govnor ya gyaɗa masa yana murmushi, yana kallon Abdallah yana jinjina ƙarfin zuciya da Yarda da kansa wanda har ya sashi yin abin da yayi yanzu, buɗe jaridar dake hannunsa yayi sanan yaci gaba da karantawa, ba tare da ya tankama Abdallahn ba, anan shima direban ya juyar da kansa yayi Umarni da sauran motocin da suke gabansa da bayansa ta hanyar bluetooth ɗin da kee kunnensa suka miƙi hanya suka nufi pravite hospital ɗin da ake duba yaran masu kuɗi dama ƴan siyasa.


Gaba ɗaya mutanen wajan suna ɗauki ihu da tafi sai dai babu wanda ya iya yin magana ganin mugun kallon da sojojin wajan suke musu, sai dattijuwar mahaifiyar yarinyar da ta fara ihu tana kwarzantun ina zasu kai mata ɗiyarta, kallonta Arfat yayi yace ta hau sai subi bayansu, dan shima hankalinsa atashe yake mutƙa ga fargaba da tsoro, yau Abdallah yayi abin da bai taɓa tsammanin zai iya aikata koda makamancinsa bane......


_😂Tofa ga dai Abdallah yayi ƙundunbala ya afka cakwalkwalin gidan govnor, Anya sojoji da ƴan sandar da ya ture zasu ƙyaleshi? Uhmm oh! Oh faɗa da Aljani babu kyaufa, Abdallah ya taro martch bashi da ƴan wasa😂😂_

©😘UM NASS🏇

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI 🎊*


 ©by *😘Um Nass 🏇*


Page 44


Zamanta ta gyara tana kishin giɗa akan kujerar "Ya akayi ka samu lambata? Asanina dai ban baka ita da kainaba?"

Aɓangaran Abdallah shima dariya yayi mai sauti sanan ya gyara zamansa "Nima ban san ya akayiba tsintarta nayi akaina, wata ƙila da kika manta jakarki sai kika bar lambar akaina."

Dariya tayi sosai wanda yasa shima ya dara, gyaran murya yayi wanda ya sata barin dariyar da take "Mi yasa ka kirani?" ta tambayeshi tana taƙaita dariyarta.

Ajiyar zuciya ya sauƙe "Kiranki nayi na miki godiya, bayan tafiyarki ɗan uwana ya bani mukullin mashin da sunan mallakina, amma inaga kamar na ɗora miki nauyi ne akanki, har ga Allah kawai na faɗi ladan tsuntuwa amatsayin barkwanci, bawai da gaske ba, ban kuma kawo akan kyautar zata girmi tsuntuwar ba." ya ƙarasa maganar yana murmushi, akwai sanyi da rauni acikin muryarsa wanda hakan kusan ɗabi'arsa ce.

Ido ta lumshe ta buɗe sanan ta fara magana "Umm kawai saboda godiya ka kirani? Kabar wahlar da bakinka saboda har yanzu ban biya ladan tsuntuwar da kayiba saboda muhimmancinta, zan kiraka wani lokacin." tana gama faɗar haka ta datse kiran, da kallo yabi wayar yana murmushi wani sashi na zuciyarsa na girmamata da kowata kalma da zata sauƙar akwai nutsuwa da girmamawa acikinta, amma kuma mi yasa bata fiya tsawaita magana da shiba? Gashi dai shi ya kirata da kuɗinsa amma kuma gashi ta katse kiran kafin ya ci gaba da magana.

Tashi tayi ta nufi kitchen anan ta tadda Maa na bada umarnin abin da za'a dafa musu, wani kuma tana gwada musu, kasancewarta mace mai tsantsani da tsafta ki kaɗan bata yarda amata kwamacalar girki agidanta, wasu lokutan ma da kanta take yin girki idan mai gidanta yana nan.

"Sannu Maa" ta faɗa tana kai kallonta ga sauran ma'aikatan da ke madafar "Barkanku da aiki"

"Yauwa Madam" suka faɗa cikin haɗin baki.

"Kin gama wayar kenan?" Maa ta faɗa tana shimfiɗa murmushi akan fiskarta, kai ta gyaɗa sanan ta bar kitchen ɗin, da kallo Maa ta bita tana murmushi sanan tabi bayanta itama aɗaki ta taddata tana ƙoƙarin cire kayan jikinta, shigowar Maa ya sata dakatawa zama tayi tana murmushi "Ya sunan surukin nawa?" ta tambaya tana ƙoƙarin zama abakin gado, ido ta fiddo waje kamar mai jin tsoron wani abu "Suruki kuma Maa?"

Kaa ta ɗaga tana kafeta ido "Wanda ya kiraki awaya."

"Oh Bawan Allah" ta faɗa tana murmushi "Bawan Allah kuma?" 

"Eh haka ya faɗa min sunansa, ba wani saninsa nayi sosai da sosai ba." anan ta faɗa mata haɗuwarsu har zuwa dalilin kiranta da yayi, "Ban taɓa ganin mutashin sarauniya mai hankali da yakana atare da shi ba Maa, sai nake masa kallon mutum na da ban, wanda bai damu da duniyaba, ko amaganarsa da yanayinsa zaki fahimci yana da nutsuwa Maa, ina ji ina ace Yayana ne shi ko wani daga cikin ahalina." ta ƙarasa faɗa tana murmushi wanda ya fiddo da wani sirri aƙasan ranta, daga haka ta shige toilet tabar Maa azaune kamar gunkin da aka sassaƙa, acikin ko maganar da Khaleesat tayi akwai wanda ta taso mata da tabo wanda ya zama shuɗaɗɗen abu acikin tarihin rayuwarta, amma har xuwa yau kullum yana bujuro mata acikin idanuwanta, da gilmawar ko wata daƙiƙa tana jin kewa da kaɗaici acikin ranta. Hawaye ne ya zubo ma idonta tayi saurin sharewa ta miƙe kamar kazar da ƙwai ya fashema aciki ta nufi waje.

Kai tsaye ta nufi ɗakinta ta shiga bincike can ta ɗauko wasu awarwaro da zobuna na duwatsu masu ratsin fari da jaa da ganinsa na fulani ne, kallonsu take tana tuna abun da ya haɗata da su, da kuma wanda ya mallaka mata su, "In dai har akwai wani dalili da zaisa ni tsawon rayuwa, to bai wuce na roƙi dama guda ɗaya da zan gyara kuskuren da nayiba, ya Allah ka yafe min ka bani dama guda ɗaya tak da zan gyara kuskuren da nayi." ta ƙarasa faɗa tana kife kanta akan gwuiwarta, wani kuka mai ƙarfi ne ya bujuro mata wanda yinsa take tana ta shessheƙar kuka, ji tayi an dafata wanda ya sata saurin ɗagowa, dan atunaninta Khaleesat ce ta shigo, dan bata ji motsin shigowarta ba, sai dai saɓanin tunaninta Abu Khaleesat ne, hawayen fiskarta tayi saurin sharewa ta fara yaƙe baki tana dariya "Sannu da dawowa Yallaɓai, ko motsin shigowarku ban jiba."

Kafeta yayi da ido "Ina za kiji dama bayan kin lula duniyar tunani harma da kuka."

Zama yayi ya janyota jikinsa "Na dawo cike da ɗoki na son kasancewa tare da ku, amma saɓanin abin da nake fata na tadda ki cikin yanayin damuwa, na ɗauka babu wani abu da zai sake saki damuwa ayanzu, kasancewar Allah ya ɗaukaka mu, ya kuma ɗaga ɗarajarmu akan wasu, minene Matsalar Um Khaleesat?"

Hawayen da take ƙoƙarin dannewa sune suka zubo mata acikin idonta "HAƘƘI! Shine yake ɗawainiya dani Abu khaleesat, har yanxu zuciyata ta kasa jurewa da jin sauti da kukan da muka barota tanayi, ko wata rana wasiyyar da Malam ya bar min tana kai-kawo acikin kunnuwana, tsawon shekaru ashirin kenan ina ƙoƙarin danne hakan azuciyata amma na kasa, dan Allah kamin wanan alfarmar yau kaɗai na roƙeka ka barni naje naji labarinta da halin da suke ciki." ta faɗa tana haɗa hannayenta guda biyu hawaye na tsere akan fiskarta.

Shima hawaye ne yaji ya tararma idonsa ya san koma mi ya faru shine sila, shine dalilin faruwar komi, hakan ya sashi jin kunya da nauyin matar tasa akan faɗa mata gaskiyar labarin da ya ɓoye mata, amma kuma yau ya zama dole ya sanar da ita.

Bayanta ya fara bibbigawa da sigar lallashi, "Kiyi haƙuri Um Khaleesat, mun riga da munyi babban kuskure acikin rayuwarmu, ki mani wata ɗaya kenan da aiki ya kaimu garin nasa yarana suyi min bincike amma amsar ɗaya ce babu mai irin sunan, kasa yarda nayi naje dan yi musu alheri ko zan samu gaskiyar maganar amma nima bata sauya zaniba, ƙarshema harda rantse-rantse akan basu da ko mai sunan da ya dangaceta."

Tashi tsaye tayi tsaye anan ta fara bibbiga kanta da bango tana kuka "Kaico nah! Kaicon wanan rayuwar data shagalar dani da yin sake da haƙƙin da ya rayata akaita, Allah na tuba ka yafe min kada ka kamani da laifin da na aikata saboda son zuciya, Allah ka ƙaddara sake haɗuwarmu kafin na zo gareka." da sauri ya tashi yana riƙeta, faɗuwa tayi tana tureshi ta zauna tana kuka kamar yarinya ƙarama.

Shima hawayen yake yana tunanin mi ya kawo wanan maganar da an daɗe da barinta, amma wata ƙila ƙaddararsu ce tazo ahakan, lokacin da zasu tone abin da ya binne atare da su ne ya fito, dana sani wanda bata da amfani ita ce ta samesu.


****

Tsawon kwanaki biyu al'amura sun taɓar-ɓare agidan govnor mai ci babu nishaɗi babu walwala kamar da, kullum Maa ta zauna cikin kuka da hawaye take, abin na damun khaleesat sosai wani lokacin itama zama take tana kukan ganin hatta Dadynta shima ya sauya daga danin da ta masa, walwala tayi ƙaranci agidan nasu, kafin wani lokaci ta rame saboda rashin sabo da halin rayuwar da taga iyayen nata suke ciki. Alokacin Maa ta ankara da katoɓarar da sukayi na barin damuwarsu ta shafi ɗiyar da bata san komiba, asalima kafin bayyanatar abubuwan suka faru.

Samunta tayi tayi tagumi tana zubar da hawaye "Assha ya kuka kuma ɗiyar Dady, wa ya taɓa min ke?" ta faɗa tana ƙoƙarin janyota jikinta, kamar ƙaramar yarinya ta kwanta ajikin Maa "Ni bana jin daɗin gidan nan yanzu Maa, gani nake kamar ba gidanmu da na sani abaya ba, farin ciki yayi ƙaranci, ko awajan Dady bana ganin kulawar da nake samu abaya, Maa anya zan jure zama ahaka? Taya bazan yi kuka ba, koda ace ruwan hawayena zai ƙare?"

Murmushi Maa tayi tana shafa kan Khaleesat "Yi haƙuri ɗiyar Dady, munyi laifi amma daga yanzu ba zamu ƙaraba, ki tayamu da Addu'a Allah ya kawo mana sauƙi da ƙarfin jure ƙaddarar da son zuciyarmu ta janyo mana."

Tashi tayi daga kwancen ta ke ta kai kallonta ga Ummie cikin yanayin tsoro da fargaba "Son Zuciya kuma Maa? Akwai abun da ya faru wanda ban saniba?"

Murmushi Maa tayi ta shafa kan Khaleesat ta miƙe tsaye "Ke dai ki tayamu da Addu'a, idan lokaci yayi zaki sani, amma kada ki yawaita tambaya kinji." kai ta gyaɗa ba dan ta gamsuba sai dan musu baya cikin ɗabi'a da tarbiyar da mahaifanta suka mata.

 "In sha Allah zan tayaku da Addu'a Maa.

"Yauwa Leesat Allah ya miki albarka.

Daga haka ta fita tana baata umarni lallai-lallai ta fito suci abinci atare.

Awajan cin abinci sai janta da hira da tsokana Dady yake wanda hakan yasa ta ta saki jikinta kamar babu abin da ya faru, ƙoƙarin danne damuwarsu suke ganin yanda damuwarsu ta haɗa harda ita kanta, aɓangaran Dady ma abun biyu yaso zame masa ga sagayan ƙauyuka da suke dole yayi tafiya bayan dai-daituwar al'amuran gidan sa.


 ****

Abdallah Fa?


©by UM NASS

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI 🎊*


©by *😘UM NASS 🏇🏼*


Page 46


   Cikin abin da bai haura mintuna gomaba sai gasu acikin asibitin, wanda ƙatuwarta ta wuce musali da ɗai sai ka rantse akan ba asibiti bace, dan tafi kama da wajan buɗe ido ko kuma na nishaɗi musamman shukokin fulawar da suka ƙara ƙawatuwarta.

Cikin hanzari motocin suka tsaya adai-dai lokacin Abdallah ya buɗe motar ba tare daya kalli gefen da govnor yakeba, hannunsa rungume da yarinyar wanda bata ko alamun numfashi, da sauri likitoci suka nufeshi cikin gadon da ake tura marasa lafiya suka saka yarinyar sanan Abdallah yabi bayansu shima cike da fargaba da alhini.

Dafashi yaji anyi wanda ya sashi saurin juyowa wani dattijo ya gani wanda jin daɗi da kwanciyar hankali suka boye shekarun da yake ciki, idan bakayi saniba zaka ɗauka ɗan shekaru 40 ne amma kuma ya haura hakan. Fari ne ba na sosaiba sai doguwar fiskarsa da farin glss akan idanuwansa, cikin arniyar shigar da ta nuna asalin wadata atare da shi, kallonsa Abdallah yaci gaba da yi yana son sanin inda yasan mai kama da fiskar amma ya gaza tunawa.

"Ka kwantar da hankalinka in sha Allah ƙanwarka zata samu lafiya, an shiga da ita wajan aiki, akwai yawaitar ƙwararrun likita atare da ita."

Numfashi Abdallah yaja kafin yayi magana saiga mahaifiyar yarinyar da Arfat sun ƙaraso cikin kuka take kiran Abdallah "Bawan Allah ina yarinyar tawa? Allah yasa bata mutuba." ta faɗa tana face majina da hawayen da yaƙi barin idanuwanta.

"An shiga da ita ɗakin taimakon gaggawa in sha Allah yarinyarki zata samu lafiya." sanan ya juya ga wanan mutumin "Wanan ce mahaifiyarta, ni kawai taimakonsu nayi ganin tana cikin mawuyacin hali da fafutukar neman rayuwarta, ban san tsawon lokacin da irin hakan take faruwa ga marasa ƙarfiba wajan nuna rashin adalci ƙarara, mota ta bigeta mai motar ya gudu ba tare da ya tsayaba, ahaka kuma ma'aikata suka datse hanyar wucewa saboda mutum ɗaya kawai, wanda badan dafawar talakawa da soyayyar da suka masa bana jin zai samu matsayin da suke kai."

Numfashi yasa yana furzar da iska mai zafi Arfat na zungurarsa yana masa alama da ido amma ko kaɗan baiyi shuruba saboda ransa da ya kai ƙololuwa wajan ɓaci "Arfat ka barni na magantu dai-dai iyawata, nasan koda zan ƙare rayuwa aƙarƙashin kurku zan faɗi abin da ke min ciwo arai, mutane suna kaɗa ƙuri'a cikin yarda da sa rai akan wanda suka zaɓa ɗin zai kare rayukansu da dukiyarsu harma da lafiyarsu, amma daga lokacin da ya ɗane akan mulkinsa sai dai sunaga gilmawar ƙurarsa da kuma ƙeyarsa wanda ko sun ƙwala kira ba zai jiba, karo na biyu kenan da ganina ana datse hanya wanda aciki harda motar agaji ta asibiti ɗauke da marar lafiya, ga kuma ma'aikatan da suke gaggawa cike da fargaba akan suna ƙoƙarin rasa aikinsu, wanan anya adalci ne Arfat? Gaskiya duk da bani da ƙarfin da zanyi yaƙi dashi zanyi kuka da idona alokacin da naga abin da bazan iya magance shiba, ya Allah ka kawo mana sauyi acikin wanan rayuwar kada ka barmu da iyawarmu." yana ƙarasa faɗar haka hawaye ya fara tseren gudu akan fiskarsa, jikin mutanen wajan ne yayi sanyi shi kansa wanan dattijon sai da yayi hawaye sanan ya jinjinama zuciyar imani da matashin saurayin yake dashi, Arfat ne ya ƙarasa wajansa yana bashi baki adai-dai lokacin kuma wani likita ya fito yana sharce gumi "Ya ake ciki likita?" suka tareshi suna cike da fargabar amsar da zai basu "Alhmadulillah munyi nasarar dai-daituwar numfashinta, haka wajan da taji rauni duk mun wanke mun saka magani da bandeji, yanxu haka an kaita ɗakin hutu zata samu lafiya in sha Allah" ya faɗa yana murmushi.

"Zamu iya ganinta likita?"

"eh zaku iya ganinta." alokacin hankalin likitan ya kai ga wanan dattijon dake tsaye da saurinsa ya risina "Yallaɓe yanzu kake tafe? Sam ban gankaba wallahi"

Murmushi yayi ya nuna masa mutane "ba komi Dr. Naseer ai tare muke tafe dasu, abata kulawa ta musamman da komi da ake buƙata suma abasu abinci wadatacce" 

"In sha Allah xa'a basu yallaɓe" hannunsa yasa a aljihun ya ɗauko rafar 500 ya miƙawa likitan yana ta faman godiya sanan ya ƙarasa ɗakin da aka kai yarinyar anan ya dubata ya musu fatan samun sauƙi, ya ɗauko rafar 1k ya miƙawa Dattijuwar, anan ta rinƙa godiya tana matse hawaye, ikon Allah kenan ganin abin take kamar mafarki hannunta har karkarwa yake saboda tsoron kada ace mata ba da gaske bane.

Juyawa yayi ga Abdallah wanda yake ta masa godiya yana murmushi har yanzu bai san ko waye wanan dattijonba "Mun gode da taimakonka, Allah ya ƙara arziƙi mai amfani da albarka, yaji ƙan mahaifa"

 "Ameeen" duka wajan suka faɗa sai Dattijon da yayi ƙurr da ido yana kallon Abdallah yana kallonsa amatsayin mutum na daban ahankali yake jin nutsuwa da soyayyarsa na shigarsa yana kuma kallon fiskarsa aransa yana ji kamar yasan yaron, amma kuma a Ina? Bai saniba, ƙarasawa yayi kusa da Abdallah yana murmushi "Yaro minene sunanka?"

"Abdallah" ya faɗa ataƙaice yana murmushi wanda ya ƙara masa kyau da fito da nagartarsa.

"A wata unguwa kake agarin nan? Minene aikina.?

Kallonsa yayi kamar xaiyi musu dan tambayar mutum ta gundureshi "Unguwa Uku layin, bakaniken mota ne" ya faɗa yana haɗe rai dan baya buƙatar sake masa wata tambayar, fahimtar da dattijon yayi ya sashi murmushi ya ɗauko rafar 1k guda biyu ya miƙama Abdallah, kallonsa yayi kafin ya kawar da kai cikin muryarsa mai sanyi ya fara magana "Ka bar kuɗinka bani buƙatarsu, iya taimakon da kayi mana ma ya ishemu yallaɓe, ina da ƙarfin da zan nemi halaliyata, idan ka bani wanan kuɗin zaka sa min rauni acikin zuciya, ta yanda kullum naga masu wadata zanyi tsammanin xasu bani kuɗin kamar yanda ka bani."

Kallonsa ya tsaya yanayi cikin mamaki da kaɗuwa ya fara juya kuɗin dake hannunsa, awanan zamanin awanan lokacin akwai masu irin wanan zuciyar dama? Kafin ya kai ga magana ya tsinkayi muryar Abdallah nayima Mahaifiyar yarinyar sallama da fatan samun sauƙi, idan kuma sun samu wadatar lokaci zasu sake zuwa dubata, godiya tayi ta masa tana sanya masa albarka.

"Sai anjima yallaɓe" ya faɗa ƴana murmushi, kai kawai ya iya ɗaga masa kafin su fita aka turo ƙofa Isya ne ya shigo yana magana "Yallaɓe ana ta jiranka a wajan taro sai kiran wayanka suke"

"Ya Allah muje to." ya faɗa yana yima matar sallama, kafin ya ji su Abdallah sun kira shi cikin haɗuwar murya "Isya manyan ƙasa" cak ya tsaya yana jin sanda Isya yayi murmushi yana dariya "Abdallah bawan Allah, Arfat kune anan?"

Hararsa Abdallah yayi kafin ya ɗora da "A'a mutum-mutumin mu ne.

Dariya sukayi gaba ɗaya anan Abdallah yayi masa mita "Su Isya masu madam, ka tsaya ka saurareni ma kaƙi, ai da na ɗauka da gaske kai abokine, ashe tsumman roba ne da bayajin wuta sai hayaƙi." dariya sukayi gaba ɗayansu, kana Isya ya haɗa hannunsa yana basu haƙuri "Zanzo na sameku har gareji kunyi haƙuri akwai magana." daga haka ya fice cikin gudu-gudu da sauri ganin Ogansa ya wuce.

Cak su Abdallah suka tsaya suna kallon-kallo cikin kaɗuwa da mamaki ganin Isya ya shiga ɗaya daga cikin motocin govnor ɗin, abin da ya ƙara bawa Abdallah mamaki bai wuce ganin taruwar ƴan jaridaba, sun kewaye wanan Dattijon da ya biya kuɗin jinyar Mero ɗiyar Marka suna son sanin alaƙar dake tsakaninsu da ita.

Abin da basu saniba tun faruwar al'amarin ƴan jarida ke bayansu suna ɗaukan rahoto har zuwa shigarsu ɗakin marar lafiyar da kuma fitowarsu.

"Yallaɓe sunana Fatima Alhassan daga K.A.S TV munga abin da ya wakana atsakaninka da wanan mutane ko zaka iya faɗa mana alaƙar da kee tsakaninka da su."

Kallonsa ya kai ga Abdallah wanda yayi tsai yana cike da al'ajabin kasancewar wanan Datijjon shine govnor dama, lallai yayi shuka a idon makarwa, murmushi govnor yayi kana ya fara magana "Su ɗin sun kasance tamkar Ahlina ne, bama su kaɗaiba duka mutanen da suke cikin wanan jahar da kewayenta ina musu kallon Ahalina ne d kuma dangi agareni."

"Kenan ba alaƙar jini ce ta haɗakuba, itama kamar sauran mutanen gari take?"

"Haka ne amma kinyi mantuwa alaƙar data wuce ta jini ta haɗamu, shine kasancewarmu duka musulmi, sanan kuma kasancewata shugaba agareta wanda zai kare haƙƙi da nauyinta da ya rayata akaina, kinga kenan itama ta zama sashi acikin dangina."

Tsayuwarsa ya gyara yana duba agogon da ke saƙale ahannunsa kana ya ɗago yaci gaba da magana "Zanyi amfani da wanan damar waja isarwa da al'ummata da saƙon ban haƙuri akan dakatawar wucewarsu aduk lokacin da nazo wucewa, wani lokacin bani da masaniyar saboda ni ake datse zirga-zirgarsu amma daga wanan ranar zai zama na ƙarshe, sanan ina roƙonsu dasu bamu haɗin kai wajan dai-daituwa ababan hawa akan titi, musamman wanda suke ƙetare iyaka dayin tuƙin ganganci, zamu sanya matakan tsaro ako wani titi da saƙo duk wanda aka kama da karya ɗaya daga cikin wanan akwai tara akansa, ina fana zaku bamu haɗin kai, na gode sosai."

Yana ƙarasa maganar yayi saurin shiga mota mutane nan suka fara ficewa daga harabar asibitin.

Ƴan jarida kuma aka samu abin faɗa nan sukayi ta ƙara nasu abin.

Kallon Arfat Abdallah yayi "Kaina ya kulle Arfat, wanan Dattijon shine govnor? minene alaƙar Isya direban madam Khaleesat da shi?"

Kai Isya ya jinjina "Tabbas shine govnor, ina ganinsa ajikin fosta da jarida shi yasa nake maka alama da kayi shuru, ban san mike tsakanin alƙar Isya da suba, sai dai ina hasashen ita ɗiyarsa ce, gashi kuma yau ka masa wankin babban bargo tass" murmushi yaayi kana ya ɗora da "Abdallah bawan Allah, wanda yakeyi dan Allah, yauma ka sake min baƙin cikin mallakar dubu ɗari" ya faɗa yana harararsa wanda tasa Abdallah faɗaɗa murmushinsa duk da zuciyarsa na cike da Alhini da fargaba abin da zaije ya zo, amma maganar da govnor yayi ta sashi jin farin ciki da ƙwarin gwuiwa ga kuma ƙarin gishiri da ƴan jarida sukama labarin kan nagartar govnor ɗin nasa amatsayin wanda babu kamarsa......


   

🥀🥀🥀🥀


 _Tofa! Gamu dai cikin tafiyar, taƙi kaɗan ya rage azo dai-dai wajan, ƙiriss ya rage labarin ya sauya salo, ku daure kuci gaba da bibbiyata ta hanyar ƙarfafa min gwuiwa wajan yin cmnts naku._


 ©by *😘Um Nass 🏇*

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI 🎊*


©by *😘Um Nass 🏇🏼*


Page 47


  GUMSA


Tun ranar da suka kori su Abdallah suka cika da farin ciki dan har ƙwarya-ƙwaryar raƙeshewa suka haɗa, Mai Gida shi ya ɗauki nauyin duk abin da aka ɓatar, ranar kam ta zarce sallah awajansu sun rabu da manyan maƙiyansu Annoba agaresu.

Kwanaki sun shuɗe sun haura satittika ahankali Iya Indo ta shiga damuwa mai tsanani musamman idan ta tuna dai-dai lokacin zuwan Abdallah, ranar da ta samu labarin an koresu agari tayi kuka har sai da idanuwanta suka fara dururu da ƙyar ta lallashi kanta tayi shuru "Shikenan yanzu na rasa wanda zan kalla amatsayin ahalina" dan duk kusancin dake tsakaninta da sauran mutanen garin bai kai ga Abdallah ba.

Ahaka Harira tazo ta sameta cike murna da shewa "Yau mun hura da masifa da jaraba sama da shekara Ashirin muna fiskantar garari da ƙalubale na waɗan nan Annobar yau gashi kamar anyi ruwa an ɗauke babu Haajara babu Abdallah sarkin iyayi, kai barkanki Yaya Indo kowa agarin nan yana miki murna da kara."

Kai Iya Indo ta gyaɗa sanan tace "Uhmm" ta miƙe tsaye tana tattare-tattaren kaya marasa dalili, amma jin zuciyarta take baƙiƙƙirin.

Tashi Harira tayi ta nufi Iya Indo "Ba haka ya kamata ace na gankiba, na ɗauka zan ganki cikin walwala ɗa farin cike kasancewar damuwarki ta riga ta ƙare, matsalarki ta tsawon shekaru ashirin yau ta tafi kamar samuwar ruwa da ɗaukewarsa."

Ɗagowa Iya Indo tayi da mamakin Harira hawaye ne sharɓan acikin idon Iya Indo "Assha! Lamari ya ɓaci, Yaya Indo mi aka miki na kuka?" juyawa tayi tana dudduƙa dan jin ƙafafuwanta take kamar bazasu ɗauketaba, kujerar tsugunne ta janyo ta zauna ta rafka uban tagumi, da rinannun idonta take kai kallonta ga Harira cikin murya mai rawa wanda ta ƙoshi da zubar hawaye ta fara magana"Na ɗauka Haajara itace matsalata arayuwa, abin da na kasa fahimta shine ita haskece acikin duniyata, Hamza ya mutu ya barni sai dai ba tafiya yayi yabarni da kewarsaba ya barni da mutane biyu masu jiɓantar lammurana, da kuma sanyani farin ciki aduk lokacin da nake cikin ƙunci, uhmm kinsan ko wata rana sai Abdallah yazo gidan nan? Sai kuma ya cika min randunana da ruwa ya wanke min kayan sawata sanan ya ɗauki kuɗi ya bani duk da magana mai daɗi bata shiga tsakanina da shi sai zagi da hantara, amma hakan bazai hanashi min murmushiba ba kuma zai sa washe gari ya zo ya ganniba." durƙushewa tayi awajan ta fara gunjin kuka "Kaico nah! Kaicon rayuwata da ta cika da son zuciya dan ba wai ƘIYAYYA nakema Iyalan Hamzaba face SON KAI na da ya cikani, yau ina ranar hakan, gashi sunyi nisa dani ta iyu har na mutu bazan ƙara ganinsuba." Kuka take mai cike da gunji da ban tausayi wanda yasa Harira itama yinsa "Tabbas Hamza ya iya haihuwa, da ya tashi haihuwa ba mutum ya haifoba zinariya ya haifo mana, amma SON ZUCIYArmu ya hanamu ganinsa, nima duk sati sai Abdallah ya kai min ziyara, yana kula dani fiye da yaran da na haifa da cikina, amma bana son koda kallonsa, tabbas HAƘƘIN waɗan nan mutanen ba zai taɓa barinmu ba, Ya Allah kasa su faɗa ahannu na gari aduk inda suke" ta ƙarasa faɗa tana rungume Iya Indo anan suka sha kukansu babu mai rarrashinsu, sai da sukayi suka gode.

 Ahankali rayuwa ta ci gaba da garama mutanen GUMSA cike da walwala ƙarƙashin kawar da idon maƙiyansu. Ahaka damina tazo kowa yana ta hada-hadar gyara gonarsa. Ruwane yazo musu da ƙarfin gaske wanda ba'a fashin rana ɗaya ba'ayishiba, ayini akwana anayi, tun suna murna da samuwarsa har ya taɓa walwalarsu dan ya hanasu gudanar da kasuwancinsu balle kuma aje batun noma, abu kamar wasa ruwa ƴa fara musu Ambaliya gonakinsu da suke murna da sunyi kyau ruwa ya haɗiyesu ya cisu, duk abin da suka noma ƙarshe sai dai yabi ruwa.

Abincin da suka ajiye kuma agida shima sunbi ta kansu, dan babu wani shiga-da-fitar da suke balle susa ran zasu samu fataucin abinci. Ahaka suka shafe watanni shidda ana zuƙa ruwa gidaje na ta yin rusau ga rashin abinci, ahaka suka fara harhaɗuwa asauran gidajan da ruwan bai daƙusarba, sai dai sun shiga matsi da takura na zafin talauci da yunwa, ga marasa juriya sai kamuwa suke da rashin lafiya haka ma yara ƙanana da yawansu sun rasu kaɗan ne sukayi sauran rayuwa.

Sunyi kuka sunyi Addu'a da ƙyar mudi ya tuno Istigfarin sa Haajara tasa su faɗa alokacin da suka shiga halin fari, baiyi ƙasa agwuiwa ba ya sanar da sauran mutanen garin, nan suka duƙufa da yi, amma kuma har yanzu bata zauna zaniba, gashi kuma babu wanda zasu ce ya zama silar faruwar wanan masifar to kowa zasu jinginawa hakan.??

 Lokacin da damina ta wuce sun tashi basu da ko ƙwaya ta gero da aka fidda agarin dole sai maƙwaftan ƙauyukansu ke kawo musu ɗauki shima ba isarsu zaiyiba, ƙarshe MAI GARI ya shiga garin Yadin Bunni ya kai kukansu ga hakimin garin.


******

Shuru ne ya ratsa palon duk da akwai mutane acikinsa amma baka jin bakinsu, sai ƙaran Allon magijin kallon dake sarƙafe apalon. Abin yazo musu abazata lokacin da suka tsinkayi muryar mai bada labarai tana magana "Wani abu mai mutƙar wahla wanda awasu lokutan ana iya samun makamantasu ayayin da aka biga gangar siyasa, sai dai awanan gaɓar yazo da salo mai ban mamaki domin wani matuƙin mota ne ya kaɗe wata yarinya ya gudu yabarta yashe atiti, ayayin da tawagar Govnor Muhammad Aada ta bayyana, kai tsaye ya dakatar da gilmawarsu ya ɗauki yarinyar cikin tashin hankali ya kaita asibitin da masu manyan ƙuɗi ƙusoshin ƙasarnan suke zuwa, ya tabbatar da tsaro da kulawar likitoci atare da ita har sai da yaga fitowarsu da alamun nasarar aikin da suka yima yarinyar. Wani abun da yafi bada mamaki shine maganar da govnor yayi na cewar "Ko wani mutum ajaharsa ɗaya ne daga cikin ahalinsa, da kuma ƙara ban haƙuri ga matane akan datse zirga-zirgarsu da ake ayayin wucewarsa. Yau mutane da yawa suna jin farin ciki aransu da yawa suna fatan dauwamar Govnor Muhammad Aada acikin matsayinsa har gaba da Abdan da fatan nasara adukanin lammuransa. Nice taku Fatima Alhassan daga K.A.S TV"

 Numfashi Maa ta jaa ta kai kallonta ga Abu Khaleesat wanda ya ƙurama Ƴar jaridar ido yana murmushi "Da gaske ne abin da naji Abu khaleesat?"

Ido ya lumshe ya buɗe yana girgiza kai "Shine sila, amma banyi ko ɗaya daga cikin abin da aka lissafaba."

"Waye shi?" Maa ta faɗa tana gyara zamanta da miƙa hankalinta ga kallon mijin nata. Adai-dai lokacin khaleesat ta kai hankalinta ga mahaifin nata tana baza kunne da son saurarar abin da zai faɗa.

"Abdallah! Sunan da ya ambata amatsayin nasa, tabbas na yarda suna yakanyi tasiri ajikin mai shi, ban taɓa ganin mutum marar tsaro da yarda da kai kamarsa ba... Anan ya sanar da ita duk abin da ya wakana tsakaninsa da Abdallah.

Tashi Khaleesat tayi kamar an zabureta "Tabbas shine, na tabbatar shi kaɗai ne mutumin da za'ama kyautar kuɗi ya ƙi karɓa acikin wanan garin, ba kuma najin za'a samu mutum na biyunsa, ban san ya akayi al'amurA suke son haɗamu da shiba, amma awanan gaɓar ya kamata na matso dashi gareni na tabbata yana da muhimmanci Aduniyata."

Gaba ɗaya kallonta suke cikin mamakin jin kalamanta tashi guda ta rikice tana kai kallonta ga mahaifin nata.

"Kin sanshi kikace Khaleesat"

Kai ta jinjina tana tabbatar da hakan "Na sanshi DADY, shine ya gyara min motata kwanaki da tasamu matsala, na biyashi da bashi kyautar kuɗi amma yaƙi karɓa" ta faɗa tana murmushi.

"Tunda kikace yana gyaran mota to shine, dan haka ya faɗa min da bakinsa."

"Har yanzu kaina ya kulle Abu Khaleesat, banga yaronba amma ina hasashen ya taka wani matsayi arayuwarsa, ko bai zama cikin masu Arziƙiba to yana da zuciya mai girma." wani abu ne ya taso acikin zuciyarta da kanta wanda yasata saurin dafe ƙirjinta ahankali ta shiga nanata "Inna lillahi wa inna ilaijirraji'un" da gudu suka iyo kanta suna lafiya ɗagowa tayi idanuwanta tuni sun sauya kala zuwa Jaa murmushin yaƙe tayi sanan ta girgiza kanta "Ba komi ƙirjina ne yake min suka har tsakiyar kaina, amma zanji sauƙi in sha Allah" ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa saurin riƙeta Abu Khaleesat yayi yana riƙe da ita har suka isa ga ɗakinta "Nasan har yanzu zuciyarki bata samu nutsuwaba akan ɓacewar ƴar uwarki, amma ki sani shi mutum baya taɓa gujema ƙaddararsa"

Kallonsa tayi da rinannun idanuwanta wanda tuni hawaye sun shiga ambaliya acikinsa, kai take girgizawa tana kuka "Wanan ba Ƙaddara bace Abu Khaleesat, wanan ƙirƙiraran abune da ka haifar dashi cikin son zuciyarka, da son kai atare da kai, nasan da alokacin lafiya ta wadaceni da idanuwana biyu da komin rintsi bazan bari ta kuskure minba, kai ne silar komi madadin ka barni na ƙarasa warkewa cikin gushewar tunani ka kawoni garin nan, har Abada bazan gushe ina ganin baiƙinka ba Aada."

Hawaye ne ya zubo daga idanuwansa, yana jiye ma kansa mutuwa da ɗaukeshi acikin wanan yanayin, kukan da take da roƙonsa da take shine yake masa Amo akunansa amma duhun zuciya da jahilci awancan lokacin ya hanashi ya saurareta, tabass ya zaluncesu yasha mafarki da ganinta cikin matsananci hali tana kuka tana ƙiransa amma ya dake ya toshe kunnuwansa awanan lokacin.

 "Ina ji araina akwai dalilin da zai sake haɗamu da ita Um Khaleesat, nasan Allah zai amsa Addu'armu wata rana ya ƙara haɗa fiskokinmu da ita, kiyi haƙuri nasan ni ɗin mai laifi ne agareki sosai."

Miƙewa tayi tana murmushi hawaye na zuba acikin idanuwanta tana girgiza kai "Ta ya hakan zai faru? Bayan hargitsewar lammuran da suke sarƙafe awani bigire mai tsayi, bana jin akwai wanan hasashen sai dai ina fatan idan akwai alfanu acikin rayuwata ya kasance an Ƙaddari haɗuwarmu da ita alokatu na gaba, zan so hakan Aada." ta faɗa tana raɓe jikinta ta kewayeshi da ido ya bita yana dafe kansa.

 "Dady Mi yake faruwa ne?" ya tsinkayi maganar Khaleesat saurin dai-daita nutsuwarsa yayi yana ƙirƙira murmushi "HAƘƘI Khaleesat, ki tayani Addu'a akan Allah ya kawo min sauƙi na samun warwaruwar matsalarmu." yana gama faɗar haka ya raɓe ta kusa da iya ya wuce.

Kallonsa take kamar wanda aka dasa wanan shine karo na biyu da taga Iyayenta acikin wanan yanayin, "WAI MI YAKE FARUWA GA AHALINA?" ta tambayi kanta bata da wanan amsar sai dai zata tayasu Addu'a da fatan Allah ya kawo sanadin kautuwar damuwarsu.

Ta Inaa wanan maganin yake?

Wayanta ce ta ɗauki ƙara wanda ko kaɗan bata maraba da jin ƙaranta hannu ta kai da zimmar katse kiran amma sunan da ta gani ɓaro-ɓaro akan allon wayar ya hanata datse kiran "BAWAN ALLAH" ta faɗa tana murmushin da bai wuce laɓɓanta ba.....  🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀


©by *😘Um Nass🏇*

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI 🎊*


©by *😘UM NASS 🏇🏼*


Page 48


Wayar taci gaba da kallo tana murmushi sanan ta danna maɗaukin kiran ta kara akunnenta, "Assalama alaikum wa rahmatullah" muryarsa ta karaɗa dodon kunnenta ba shiri ta nemi wajen zama saboda bugun da zuciyata tayi.

"Wa alaikumussalam wa rahmatullah" ta faɗa tana daidaita muryarta wanda take fita da sauri gami da sarƙewar harshe.

"Tsawon kwanaki ina ta daki jiran kiranki amma shuru, gashi zuciyata ta gaza jure hakan, shi yasa na kiraki dan na tunatar da ake mutumin da kika manta."

Kai ta girgiza tana murmushi "Ta ya zan manta bawan Allah acikin duniyata? Kawai dai na gaza yin sabo da yawan magantuwa ajikin waya ne, gashi ina kan jarabawar ƙarshe amakaranta, wanan dalilin ya ƙara shagalar dani da samun lokacin da zanyi magana."

Kai ya gyaɗa kamar tana kallonsa sanan ya gyara muryarsa "Kin san wani abu?"

"A'a sai ka faɗa"

"Ko danma shikenan, ba sai na faɗa ba."

"Haba mana Abdallah, ka sa min rai ka faɗa kawai"

"Ya akayi kika san sunana?" ya tambaya cikin mamaki, dariya tayi wanda ta sashi yin murmushi "Au dama sunanka kenan?" ta sake jifansa da tambayar tana dariya, shima dariyar yake, wanan yarinyar akwai shega atare da ita, amma yana mamakin sauƙin kan da take da shi.

 "INA SONKI"

Cakk ta tsaya daga dariyar da takeyi "Kace mine?"

"Ina sonki..

"Kasan abin da kake faɗa? Ko kuma dai kanka ya fara samun matsala? Baka san ko wacece ni ba amma kake cewa kana sona" ta jero masa waɗan nan tambayoyin cikin mamaki da faɗa-faɗa.

"Tabbas nasan abin da nake faɗa, haka kuma babu ruwana da sanin ko ke wacece, abu ɗaya na sani shine ina sonki tsakani da Allah, ba tare da na shiryama faɗawa cikin soyayyarkiba, na tabbata kema zaki soni." ya faɗa yana murmushi, sai dai abin da ya sashi ruɗewa jin maganar Khaleesat.

"Har Abada bazan soka ba Abdallah, ka farka daga mafarkin da yake ruɗarka, kai da kanka zaka yima kanka adalci akan kyautuwar soyayyata ko kuma ƙuntatawar da zaka samu, ina maka kallon mutum mai hankali wanan yasa na fara ƙoƙarin ƙulla abota da kai, amma kafin tafiyar tayi nisa na fahimci kana da damuwa da yawa, kada ka sake ƙoƙarin yin wanan kuskuren." tana ƙarasa maganar ta datse ƙiran wayar, sanan ta dafe ƙirjinta da yake bugawa wani farin ciki take ji na sosai da sosai, sujjada shukhri tayi tana godema Allah, tabbas batayi hasashen hakanba ko acikin mafarkinta, amma kuma ta san ta daɗe da riftawa acikin Son Abdallah, kawai tana ƙoƙarin danne hakan a ƙasan ranta, amma kuma dole ta jarraba Abdallah har sai taga tsawan Wahla da ƙuntatawar da zai iya jurewa akan soyayyarta.


******

Bin wayar yayi da kallo yana jin sautin muryarta cike da Amo da gargaɗi yana sake amsa-kuuwa acikin kunnuwansa, idanuwansa ya rufe yana dafe da ƙirjinsa wanda yake masa zafi "Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un" yake ta maimaitawa akan laɓɓansa wanda suka masa nauyi, dafashi akayi da sauri ya juyo ganin Ummie yayi tana kallonsa cikin tausasawa da fargaba "Mi ya faru Abdallah? Mi yake damunka?"

Kai ya shiga girgizawa yana ƙara riƙe kansa da yake jin kamar zai ɓalle "Mi yasa rayuwa ta fiye ƙuntatawa ne Ummie? Ko kuwa dai ni kaɗai ne mutumin da yazo duniya cikin rashin sa'a? Duk abin da zan so kuskure min yake ya tafi ya barni, na tabbata awanan gaɓar bazan iya jure hakanba Ummie, ni ban damu da matsayin da take dashiba ina sonta tun kafin na san wacece ita, bazan iya haƙurin barintaba."

Kallonsa Ummie tayi sanan ta zauna fuskarta ƙunshe da murmushi "Duk abin da kaga ya samu bawa dama can yana rubuce ajikin allon ƙaddararsa, sai dai ka miƙa hannu ka karɓeta, shi yasa ako yaushe ake son bawa ya kasance mai Addu'a akan ƙarfin jure rayuwa mai cike da wahla, Abdallah ko wani mutum aduniya yakan samu sauƙi da ƙunci acikin rayuwa sai dai rayuwa bata cika zama amuhalli gudaba." gyaran murya tayi tana faɗaɗa murmushi ta "Wace Yarinya ce ta maida min yaro rago daga jarumin dana sanshi."

Kai ya sunkuyar yana murmushi "Sunanta kawai na sani amma ban san komi akantaba Ummie, abu ɗaya na riƙe shine tana da sauƙin hali da gudun duniya duk da kasancewarta ƴar manyan mutane."

Ido ta fidda waje "Bana son rigima Abdallah, kada ka ɗauko abin da yafi ƙarfinka, ka nemi dai-dai matsayinmu ko a unguwar nan ne, dan ina ankare wasu saboda kai suke zuwa karatu."

Miƙewa tsaye yayi yana ɓata fuska kamar zaiyi kuka "Ina sonta Ummie, ina ji araina batafi ƙarfina ba, ki dai tayani da Addu'a Allah yasa alkhairi ne haɗuwarmu da ita."

Kai ta jinjina sanan tace "In sha Allah, amma ina jin tsoron ƙulli da takarda dan da taji ruwa zata narke"

"Ba zai gagaraba Ummie wanan ƙullin da sasari akayishi." ya faɗa yana ficewa dan yaga kallon da Ummie take jifansa da shi na mamaki ne.

 Saida ya kai bakin ƙofa sanan ya juyo "Ummie wanan Abdallahnfa ya sauya akan na da, ina son zama kamar ko wani mutum, ban saniba ko zan aro jarumtar da Abuna yayi alokacin neman ƴar fulani." wawurar muhuci tayi zata jefeshi da gudu ya fice yana dariya, itama dariyar take tana girgiza kai, sai take hasko shuɗaɗɗen al'amarin daya wuce abaya.

"Allah ya tabbatar da rahma acikin makwancinka Hamza" ta faɗa tana share hawayen da ya zuba a idonta.


******

Duk yanda Abdallah yake tunanin sauƙin lamarin abin ya zarce saninsa, domin ko kiran Khaleesat yayi bata ɗaukan wayar idan kuma ya matsa da kira sai ta rufe waƴar gaba ɗaya, yasha tura mata saƙonni ta ma'ajiyar wayarta amma babu amsa babu kuma wata alamar taga saƙon, yanzu ne yake dana sanin sanar da ita abin da yake cikin zuciyarsa, da fari yanaga faɗar itace tafi sauƙi amma kuma sai gashi madadin sauƙi azabtuwa yake da rashinta.

Ta ko'ina so yake ya samu kusanci da ita, amma bashi da cikeken adireshin gidansu. Zaune yake ya rafka uban tagumi kamar yanda ya zama ɗabi'arsa tun bayan kaucewar komi daga gareshi, aikinma ba sosai yakeyi ba sai ƙarfin hali, tun Arfat na shareshi har yazo yana bashi haƙuri akan ya haƙuri ta ko ina Khaleesat tafi ƙarfinsa, idan yayi la'akari da matsayin iyayenta tofa sai dai yazo amatsayin hadiminta.

Sosai ransa yake ɓaci aduk lokacin da yaji maganar da Arfat ɗin yake faɗa "Nasha faɗa maka Arfat ka faɗi alkhairi akan wanan al'amarin ko kuma kayi shuru idan ba zaka iya faɗarsa ba, baka san mi Allah ya ɓoye atsakaninmu ba, amma koda ban samu Madam Khaleesat ba ina mata son da ban taɓa jin irinsa arainaba."

Dariya Arfat yake yana riƙe cikinsa "Oh waifa kaima Madam kake ƙiranta kamar yanda ma'aikatanta suke kiranta, na kasa yarda cewa wanan Abdallah da na sanine lokutan baya."

Shuru yakeyi ya ƙyaleshe ko kuma ya tashi ya bar masa wajan. To yauma diramar da suka sha kenan ya koma gefe yana riƙe da haɓa cikin jinyar abin da ya sameshi, hannayensa yaji an cire daga tagumin da yayi wanda ya ankarar da shi wanzuwar wani akusa da shi, abin da baiyi tsammaniba Isya ya gani yana murmushi "Ya da tagumi haka Bawan Allah kamar wanda y samu labarin rashin Ahalinsa alokaci guda?" ya faɗa yana kanne masa ido ɗaya, wata ƙanƙarar farin ciki ce ta sauƙa azuciyar Abdallah ganin Isya da yayi ji yake kamar ya samu maganin matsalarsa.

"Ai kusan hakan ne, ƙilama gara hakan akan abin da nakeji aƙasan zuciyata, waima tsawon wanan watannin ina ka maƙale? Duk da sanar damu da kayi akan zaka zo."

Kai ya sunkuyar yana faɗaɗa murmushinsa "Afwan abokina, xama ne bana samu saboda ziyarar ƙauyukan da muke kaiwa."

"Yauwa ni ranar naganka acikin tawagar govnor bayan asanina kai direban Madam Khaleesat ne." dariya Isya ya sa harda tintsirawa sanan ya dai-daita nutsuwarsa "Wai kana nufin har yanzu baka gama sanin wacece Madam Khaleesat ba?"

Kai ya gyaɗa yana murmushi "Ban san komi akantaba bayan sunanta"

Dariya Isya yayi sanan ya miƙe yana kallon agogon dake hannunsa "Kaga fa aikena Madam tayi hanya ta biyo dani tanan."

Zuraff Abdallah ya miƙe tsaye "Muje na rakaka na gaji da zaman waje ɗaya."

Bai fahimci komiba ya gyaɗa kai suka shiga mota atare suka tafi sai faman jansa da fira Isya yake shidai Allah-Allah yake su isa wajan Khaleesat.

Tun shigarsu unguwar jikin Abdallah yayi sanyi musamman da yaga sun shiga govment house anan ya ƙara raina kansa ta ko ina matakan tsaro ne daga sojoji sai ƴan sanda, gidan da yafi ko wanne suka dirfafa anan yaga tsaro da tashin hankali ga manyan ƙofifi ko wanne sai an bincekusu duk da Isya sananne awajan hakan bai hana an binciki motarsa ba da shi kansa, anan Abdallah ya fara tsorata anya bai janyowa kansa ruwa ba.

Tabbass babu ta inda burinsa zai cika tun yanzu ya gane akwai tazara mai yawa tsakaninsu, har abada na gaba yayi gaba bai kuman san tsawon shekarun da zai shafeba kafin ya kai koda rabin matsayin da suka takaba.

Allah mai kyauta mai ƙari mai yanda yaso alokacin da ya so, wanda yake zaune baiga gariba, ni ko anan aka barni labarina ya cika...........


   

 🥀🥀🥀🥀🥀🥀


®by *😘Um Nass🏇*

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI 🎊*


 ©by *😘UM NASS 🏇🏼*


_*💃 Gang💃 gang💃This page for u Khadijat candy Happy birthday to u wish u more of Allah's blessings n love, khairan fidduniya wal akira amin.*_


Page 49


 Ido sosai Abdallah ya buɗe yanaga sabuwar duniya har suka shiga harabar gidan anan ya fara tasbihi acikin zuciyarsa yana tsarkake Allah wanda yake ɗaukaka wasu ya kuma ƙasƙantar da wasu cikin ikonsa da buwayarsa. Ahaka yaci gaba da bin gidan da kallo har suka kawo inda aka tanada saboda ajiye motoci, motoci ne tsala-tsala babu mai sauƙin kuɗi acikinsu, saifa ta Madam Khaleesat wanda yana ganinta ya shedata mamaki ne ya kamashi ganin wanan tarin motocin amma kuma ta nacewa mota ɗaya mai sauƙin farashi "Yauwa to fito muje ko" Muryar Isya ta ankarar da shi, fitowa yayi daga cikin motar yake bin gidan da kallo ta ko ina ma'aikata ne suke kaiwa suna kawowa a harabar gidan, hannu yake miƙa musu yana gaidasu da murmushi akan fiskarsa, saɓanin su da fiskokinse dake kamar an aiko musu da saƙon mutuwa, ganin yanda yake miƙa musu hannu da murmushi yasasu sassauta fushin da fuskarsu take, nan suka ware suna tambayar Isya "waye shi dan sunga mutane da yawa tsoronsu suke amma shi gashi yana gaidasu da girmamawa yana murmushi akan fiskarsa?"

"Abdallah kenan, haka sunansa yake, haka kuma halayyarsa take da wuya kuga fuskarsa na ƙunshe da fushi"

"Aikuwa ga alamun hakan nan mun gani."

Fitowa tayi cikin shigar fakistan mai kalar sararin samaniya da ratsin fari ajikinsu sai gyalansu da ta yane kanta da shi, fiskarta babu kwalliya wanda hakan ya zama kamar ɗabi'a atare da ita, bata da damuwa da tarkacen kwalliyar zamani, cikin nutsuwa take aje takun tafiyarta tana kare da waya akunnenta alamun dai tana amsa kirane, alokacin Isya ya farga da fitowa da sauri ya bar wajen ma'aikatan ya nufeta har ta kai ga motarta.

"Barka da fitowa madam" ya faɗa yana ɗan risinawa, adai-dai lokacin ta sauƙe wayan akunnenta ta ɗanyi murmushi "Yauwa barka dai Isya, ka dawo kenan?"

"Eh yanzu dawowata ina shirin kiranki naga fitowarki."

"Madallah, ya saƙon ina fatan ka isar da shi inda ya dace"

"Eh! Na kaimusu suna ta godiya da miki Addu'a gaskiya ba ƙaramin daɗi waɗan nan tsofin sukaji dan da yawa acikinsu har tambaya suke akan abin da ya hanaki zuwa dan sun damu da rashin ganinki kwana biyu, haka suma yaran duk dai abu ɗaya ne suna son ganinki, da ƙyar na lallaɓa su na taho na bar su."

 Murmushi tayi mai ƙayatarwa alamun taji daɗin labarin nasa "Na gode Isya, in sha Allah zanje na dubasu."

"Barka da Yamma Madam" muryar ta daki dodon kunneta cikin salo da bazata wanda batayi tsammanin jintaba, da sauri ta juyo da kanta asaitin inda ta tsinkayi muryar, kasa gaskata abin da ta gani agabanta tayi hakan ya sata lumshe ido da buɗesu, dan tayi tsammanin ko ba dai-dai idanuwanta suke ganiba, Murmushi Abdallah yayi ya kafeta da manyan idanuwansa wanda suke lumshe kamar mai shirin barci ga kalarsu data bambanta da ta sauran mutane saboda madadin baƙar ƙwayar shi tasa ruwan ƙasa ce, saurin dai-daita nutsuwarta tayi sanan ta ɗanyi murmushi wanda iyakarsa laɓɓanta "Yauwa barka dai Bawan Allah" sanan ta juya wajan Isya tace "Tare kuke tafe ne?"

"Eh madam hanya ce ta kaini ta wajansu sai na tsaya mu gaisa koda zan taho yace na jirashi zai min rakiya."

Kai ta jinjina tana murmushi "Yayi kyau" sanan ta juya ga Abdallah wanda ya ƙura mata idanu, shigowarsu gidan ya raina kansa ta yanda ya fara tunanin janyewa daga batun yana sonta, amma kuma yanzu da yake ganinta agabansa baya jin koda yaƙi ne ya taso zai sauya daga sonta.

"Dama ina nemansa, ummm ka bamu waje Isya zan nemaka daga baya."

"To Madam nagode" ya faɗa yana risinawa kana yabar wajen nasu yana ma Abdallah magana "Idan ka gama ina jiranka acan"

"To" yace masa har ya ɓace daga ganinsu anan kuma ya sake tsinkayar maganar Khaleesat "Ina fatan ka farka daga ruɗun mafarkin daya jaka akwanaki da suka wuce, ka fahimci bambancin dake tsakanin mage da ɓera kullum cikin gudun neman rayuwa yake yayin da ita kuma take binsa dan farautar rayuwarsa."

Murmushi yayi fahimtar inda maganarta ta dosa "Har yanzu ban farkaba, bana kuma fatan na farka ɗin saboda mafarkin yana bani tabbaci akan samuwar abin da nake so, abune mai mutƙar sauƙi samun dai-daituwar mage da ɓera musamman alokacin da suka shiga komar ƴan farauta, ba lalai su so wani yayi nasara akansu ba."

"Idanuwanka basu ganema abin da nake son ga ganiba, Abdallah kai mutum ne mai sauƙi da kyakkyawar mu'amula ga mutane, rayuwarka cike take da nagarta da abin birgewa bana so na zama silar rabuwarka da abin da yake mallakinka ne, ina so kaci gaba da rayuwa a muhalli mai kyau, amma naga kamar kai baka yiwa kanka sha'awar wanan rayuwar."

 Acikin maganarta akwai gaskiyar da ya kamata ace ya yarda da ita, amma kuma zuciyarsa taƙi yarda ta bashi wanan haɗin kan, ko wata kalmar da take fita aharshenta sauƙa take da ruruwar soyayyarta, taya yane zaiyiwa kansa sakiyar da babu ruwa? Zaiyi ta jarraba sa'arsa har sai yaga abin da ya turema buzu naɗi "Ina son nayi rayuwa mai daɗi fiye da wanda nakeyi ayanzu, amma kuma ke kika fara bani wanan damar, shi yasa naso gwada sa'ar da nake da ita."

 Ido ta fiddo waje cikin mamakin jin maganarsa "Ni kuma?"

Ido ya rufe ya buɗe sanan ya dai-daita tsayuwarsa akan ƙafafuwansa "Tabbass ke kika bani wanan damar, domin kin zo min amatsayin mutum kamar kowa, sanan sauƙin da ke tattare da ke yaƙi bayyana asalin yawaitar wadatar da kike da ita, sai na sakaki acikin rukunin tsaka-tsakin mutane amma ba wadda zata girmi nawa matsayin na sosaiba, ni ban san komi akankiba bayan sunanki, har zuwa lokacin da na sanar da ke abin da yake cikin zuciyata, bai wuce sa'a gudaba da na fahimci ke ko wacece, kaina ya kulle da yawa ƴar gidan govnor guda tana yawo amotar data gajiya da rayuwa kana tana yawo babu masu kula da ita babu mai kareta ta yanda za'a gane matsayin data taka koda bata magantu akansa ba" murmushi yayi ya girgiza kansa "Ban taɓa hasashen hakan arainaba, amma akaro na farko da na ganki zuciyata ta ƙula alaƙa da taki zuciyar, Ina sonki" ƙarasa maganar cikin muryarsa mai rauni wanda take tafiya da sanyi ajikinta, dole sai da ta ɗago da kanta saboda jin sauƙar muryarsa acikin ko wata gaɓa ta jikinta, Agogon hannunta ta kalla sanan ta ɗago da kanta tana kallon Abdallah "Har yanzu baka fahimci hausar da nake makaba, amma bazan tirsasaka akan ka yardanba, sai dai zan so ka gwada jarumtarka agaban Dady, kaje masa da batu akan neman Aure nah, da yardarsa, a yanzu ba wai sai an ɗauki lokaciba."

Idanuwansa ya buɗe tarwai yana kallonta cikin mamaki da jin maganarta, haka kuma yajita kamar cakuwar ƙaya akunnuwansa "Ban fahimci maganarki ba."

Murmushi tayi mai kyau wanda yake ɗauke da ma'anoni da yawa, sanan ta yi magana "Ina nufin ka gana da mahaifina amatsayin wanda kazo neman aurena ayanzu idan kuma ya amince da hakan sai ka fara neman yardata."

Kai ya dafe kafin yayi magana Khaleesat ta fara daddana wayanta "Kana da sauran lokaci da kuma zaɓi ko ka tsaya ko kuma ka fece, amma ka daure ka gwada sa'arka..

_"Ta yayane zai tinkari mutumin da ya gama ciwa fiska akwanakin da suka wuce? Da wani ido zai kalleshi ya kuma buɗe bakinsa akan yazo neman auren ɗiyarsa? Ina matsayin da ya taka balle har yakai shi ga yin magana da govnor mai ci awanan lokacin? Wanan shiryayyen al'amari ne nason masa kora da hali wanda yafi kora da kara?"_ Maganganun da Abdallah yake acikin zuciyarsa cike da ruɗani atare da shi, murmushi khaleesat tayi sanan ta fara ƙoƙarin buɗe motarta "Da alama ka karaya tun yanzu Abdallah, ina da abubuwa masu yawa waɗanda suke sa muhimmanci agabana idan ka shirya sai ka kirani."

 Da sauri ya datseta yana kafeta da idanuwansa "Na shirya kisa akaini wajansa."

Chakk ta tsaya daga shiga motar da take ƙoƙarin yi, batayi tsammanin jin wanan maganar atare da shiba, kallonsa tayi tsaf babu wani alamun tsori a tare da shi, kai ta jinjina kana ta ɗora da "Kace ka shirya?"

Murmushi yayi ya harɗe hannayensa akan ƙirjinsa "Tabbas na shirya fiskantar ko waye akanki, ko nayi nasara ko na faɗi ni bai dameni muddim na isar da saƙon da yake raina."

 Wayanta ta fara daddanawa tana murmushi "Kaje kama Abdallah Iso awajan Dady sai kazo ku shiga tare." iya abin da ta iya faɗa kenan sanan ta datse kiran ta shiga motarta, yatsu biyu ta ɗaga masA tana murmushi ta ja motar ta barshi anan, da ido yake binta ba tare da ya fahimci ina ne za tajeba.

Adai-dai lokacin Isya ya ƙaraso yana murmushi "Gaskiya da sa'a kake Abokina, ranar farko da zuwanka gidan nan gashi zaku gana da Yallaɓai da kansa, abune mai wahla a irin wanan ranakun kaga yana saurarar baƙi amma kuma kai ina sanar da shi yace ka ƙarasa."

Kallonsa Abdallah yayi kana yayi murmushi wanda bashi da maraba da na yaƙe, amma azahirance zuciyarsa na harbawa kamar ta faso ƙirjinsa.

Da sallama ya shiga cikin palon wanda ƙamshinsa da sanyinsa ya fara masa maraba tun kafin ya shigeshi, ido ya lumshe yana Tasbihi acikin zuciyarsa "Allah Al'hakim" ya faɗa yana zura ƙafafunsa na dama, ƙawatuwar palon ya zarce tunanin mai tunani balle afaɗeshi amma kuyi hasashen kyautuwara anaku hangen ɗima-ɗiman kujerun da suka yima palon ƙawayan ya isah shagalar da wanda yake kansu tunanin aduniyar da yake bai rabe da ƙarasa bawa idanuwansa haƙƙinsaba ya tsinkayi muryar Isya Adai-dai lokacin da idanuwansa suka sauƙa akan tafkeken hoton Khaleesat sanye cikin riga da wandon fakistan ta yane kanta da gyale tana dariya da alamu bata shirƴa ɗaukan hotonba aka ɗauka amma tayi kyau fiye da tsammani "Yallaɓe fa baƙon naka"

"Yauwa isya" sautin Muryar da ya ji ya sashi dai-daita nutsuwarsa ya zauna akan kafet ɗin da laushinsa ya wadaci mai kwanciya barci cike da walwala.

"Abdallah ko?" ya faɗa yana faɗaɗa murmushinsa, ɗagowa yayi yana kallon mutumin _"kenan wanan shine mahaifin Khaleesat? Kuma govnor jahar kano? Tambayar mi kuma kake bayan kaga zahiri agaban idonka ga kuma ɗiban kamar da suke da ita."_ sashi na zuciyarsa na tambaya da bashi amsa, risinawa yayi cikin girmamawa ya fara gaidashi "Barka da Yammaci yallaɓe, na sameku lafiya?"

"Alhmadulillah, Ina fatan lafiya ce ta kawo gidan nan? Duk da kai ba mutum bane mai buƙatar nuna gajiyawarsa wajan roƙo da karɓin kuɗi daga hannun mutane ba."

Zuciyarsa ce ta harba yana tunanin ta ina ne zai fara magana, ga dai damar ganin mahaifin nata ya samu amma kuma ya cika gabansa da kwarjini, anya bai wuce gona da iriba?

"Ina jinka Abdallah" ya sake tsinkayar muryarsa ɗauke da murmushi da ƙarfafa masa gwuiwa.

Da ƙyar ya samu ƙarfin Iya magana "Ban san ta ina zan faraba, amma bana so ka ɗauki hakan amatsayin raini ko nuna isa a inda babu Isar, wani lokutan muna iko da rayuwarmu akan tamu ce amma kuma ko kaɗan bamu ke sarrafa zukatanmu ba, idan har bamuyi da gaskeba takan iya ɗaukarmu ta jefa acikin muhalli mai cike da sarƙaƙiya da cikar ƙayoyi acikinsa, idan kuma mukayi sa'a sai ta kaimu ga inda yafi ko ina taushi da sanyi, ina jin tsoron abin da zan faɗa anan , tsoro irin na wanda ya cika da Sa rai ya zo ya rasa." ya ƙarasa maganar yana kallon fuskar Dady Khaleesat, shi ɗinma kallonsa yake yana son yaji inda maganarsa ta ƙunsa dan ko kaɗan bai fahimci abin da yake faɗarba.

"Kaje kai tsaye ga maganarka dan ban fahimci abin da kake son sanar da niba."

"Ina neman izinin awajenka na neman soyayyar Ƴarka KHALEESAT"

Tuni murmushin da yake shimfiɗe akan fiskar Abu Khaleesat ta ɗauke cak ta koma kamar haɗuwar hadarin da yake barazana da sauƙar ruwan sama "Kace Mine?" ya faɗa cikin muryarsa mai Amo wanda tasa Maah saurin fitowa daga ɗakinta abunne ya bata mamaki ganin matashin saurayi durƙushe agabansa da ganinsa ba wadata gareshiba aƙalla yadi ne ajikinsa wanda ƙuɗinsa ba zai haura 2k ba kansa babu hula hakan ya fito da yalwatacan gashinsa wanda yake a murmuɗe a kwance kamar na indiyawa baƙi siɗik da shi, wanda ya ƙara haska chaculat ɗin kalar fatar jikinsa bata ga fiskarsaba amma kuma taga gefen fiskarsa da yake zagaye da saje wanda aka gyarashi ya ƙawata fiskar tasa, gabanta ne yaci gaba da faɗuwa haka nan sai kuma ta tsinkayi muryarsa mai sanyi da rauni acikinta abun da ya fito abakinsa ya sata tsayawa cikin mamaki da ganin ƙarfin halinsa.


 "Ina neman izinin awajanka akan fara soyayya da ɗiyarka Khaleesat." 

 "Tashi tsaye" ya faɗa cikin kakkausar muryarsa, miƙewa Abdallah yayi yana kallon Abu Khaleesat da ya fara nuna shi sama da ƙasa "Ka tsaya ka kalli kanka ajikin mudubi kuwa? Aduka rayuwarka ka taɓa sanya tufafin da yakai na dubu 10? Zaka iya tuna yaushe ne kaje gidan cin Abinci kaci Abincin 5k kacal?" murmushi Abu Khaleesat yayi kana ya ɗora da magana "Ban san wani suna ya kamata na bakaba, amma idan na kiraka da sakarai maloho inaga shine yafi dacewa da kai, abaya na ɗauka kai mutum ne mai cikekken hankali sai yanzu na fahimci kai bagidaje ne wanda yake kai kansa inda Allah bai kaishiba, Nawa aka biyaka kazo kace kana son Khaleesat? Dan na tabbata gasa aka sa dan ɗan caca babu abin da bazai iyayi ba, kasan matsayin Khaleesat acikin gidan nan? Itace haske arayuwar gidan nan sanan kuma jugon walwalar kowa da kowa, Taya kake tsammanin talaka liƙis da kai zaizo neman Auren ɗiyata na bashi? Kaima ka yauɗari kanka, ka kuma cuci lokacina dana ɓata akan jiranka, dan haka maza ka ɓace daga ganina tun kafin nasa arufeka."

 Tun da Abu khaleesat ya fara magana zuciyar Abdallah ta fara tafasa kamar an ɗora garwashin wuta acikinta amma kuma ya hana idanuwansa bashi damar nuna rauninsa da ɓacin ransa ƙarshe sai murmushi yayi wanda yafi na ko yaushe fiddo da kyansa "Acikin maganganun da kayi duka ka faɗi gaskiya, sai dai abu ɗaya ne kayi kuskure acikinsa shine kirana da kayi ɗan caca, babu abun dana ƙyamata acikin rayuwata face aikata abun da Allah ya haramta, sanan ita caca babu wani abin amfanuwa da moruwa acikinta face ƙasƙantar da mawadaci da tozartashi alokacin da ya ƙishi, gaskiya ne ni ɗin talaka ne marar wadatar abun hannu kamar yanda ka faɗa amma kuma ina da wadatar zuciya, ina godewa Allah akan matsayin da ya ajiyeni na talaka saboda ina samun lokacin da yake nawa da na bauta masa, kasan wanene talaka afahimtata da kuma yanda Annabi s.a.w ya sanar da sahabbansa? Hadisi ya tabbata daga Annabi s.a.w yace da sahabbansa "Kun san waye talaka acikinku? Sai sahabbansa sukace 'Shine wanda bai tara komi na azurfa da zinarai ba' sai Annabi s.a.w yace "A'a wanda yafi kowa talauci acikinku shine wanda zaizo ranar lahira yana ɗauke da aikin ladansa har yana rinjayarsa saboda yawansa, amma da anzo masa hisabi sai aji ya cuci wanan ya zalunci wanan ya kuma ha'inci wanan ahaka za'a fara janye ladansa har sai ya dawo bashi da komi daga nan sai afara ɗaukan zunnuban mutane ana azawa akansa har ya rinjayeshi daga nan sai a jefashi cikin wutar jahannama, wanan shine mafi talauci acikinku." sanan awani hadisi Annabi s.a.w ya sanar da sahabbansa "Shin bana sanar daku wanda yafi kowanne acikinku wadata ba? Shine wanda yake mallakar zuciyarsa yake da iko akanta, yake godiya da abin da ya samu komi ƙanƙantarsa." to kaga kenan Alhmdlh bana da arziƙin da zan kirashi nawa wanda zai zama mabuɗin fitina agareni kamar yanda Allah s.w.a ya faɗa acikin alqur'ani mai girma "Lallai haƙiƙa Dukiyoyinku ɗa ƴa ƴanku fitinane agareku." haka Annabi s.a.w yace "An sanyawo ko wata al'umma fitinarta kamar Annabi luɗ A.s aka jarrabeshi da yin luɗaki ga mutanensa wanan ya zama fitina agareshi, haka Annabi nuhu yayi wa'azi tsawon shekaru mutanensa suka juya baya, haka annabi salihi mutanensa na kama kifi alokacin da aka haramta musu, da sauran Annabawa kowa da tasa fitinar, ni kuma sai aka jarrabu Al'ummata da fitinar Kuɗi sai ta shafe duk waɗan nan fitintunun na baya." ma'ana dai sanadin kuɗi mutane suke afkawa aikata alfasha zinace-zinace neman jinsi atsakaninsu, sata, ƙarya da kuma shaye-shaye, ga kuma zubar da jini atsakaninsu, duk da zaka duba da kyau ka tambayi silar wanan fitinar kuɗi shine mabuɗin ko wata fitina."

Numfashi yaja ya ƙara faɗaɗa murmushinsa "Kace Khaleesat tamkar Fitila ce agidan nan, aganina ka ƙasƙantar da matsayinta domin ba'a iya gidan nanba aduka wanan rayuwar zaiyi wahla asamu kamarta, domin bata da girman kai da nuna matsayin ita ɗin wacece? Wlh da ban zo naganka amatsayin mahaifintaba ban taɓa hasashen ɗiyarka bace domin ko kaɗan alamunta nutsuwarta da hankalinta da sanin ya kamanta da take da shi ya ɓoye naƙasun tarbiyyar da yaran masu kuɗi suke da shi, hakan yasa har zuciyata ta kamu da soyayyarta ba tare dana san wacece itaba, ban kuma buƙaci sanin ita ɗin waceceba, Allah ya baka kyautar Lu'u Lu'u mai daraja da tsada shine baiwar Haifar Khaleesat nasan mutane da yawa da zasu san ita ɗin ɗiyarka ce zasu zaɓeka saboda ita, ka zauna sau ɗaya ka godema Mamanta nasan itace silar ginata akan wanan tafarkin, na gode da lokacinka da ka bani, zanci gaba da jarraba sa'ar da nake da ita na dawo gareka akaro na biyu akan neman Auran Khaleesat."

Yana gama faɗar haka ya juya yana murmushi ido suka haɗa da Maa na take zuciyarta ta harba da ƙarfi tana ganin wani abu acikin ƙwayar idonsa kamar wanda ta taɓa agani acikin wani ido daban, amma a ina ne?"

Risinawa yayi ya gaidata ya tafi abinsa ba tare da ya tsaya jin ta amsa ko bata amsaba, gaba ɗaya da ido suka bishi cikin sanyin jiki da mamakin kowata kalma da take fita acikin laɓɓansa har kuma zuwa lokacin bashi da alamun nuna ya raunata ko yaji haushin maganar da Abu Khaleesat ya masa asalima hankali kwance ya faɗi ko wata kalmar da yake Fiddawa.

 "WAYE SHI?" Maa ta tambaya tana kallon Abu Khaleesat wanda shima ya juyo da kallonsa gareta nan suna shiga musayar kallo ba tare da an samu mai tankawa atsakaninsu ba........


_👏👏👏raff! Rafff raff yaufa nayi ƙoƙarin faranta muku duk da kasancewata cikin alhinin rashin ɗan uwana, ya kamata kuma ku faranta min ta hanyar tattaro ko wata kamala taku da mutuntakar da kuke da ita ku sanƙama cmnts ku magantu akan dai-dai ki akasinsa._


 🥀🥀🥀🥀🥀🥀


©by Um Nass

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI 🎊*


©by *😘Um Nass🏇🏼*


Page 51


 Hira suke cikin walwala da farin ciki ko kaɗan basu da damuwa atare da su, domin kallo ɗaya zaka musu ka fahimci su ɗin ahali guda ne da suke cike da jin daɗin rayuwar da suke acikinta yanzu walwala ba irin ta wanda ya tada kai da Nera ba irin ta talakan da yake da tufin asiri yake kuma da wadatar zuciyarsa. Labaran da ya cika ko wata tasha agidan radio yanzu ma shine ya cika kunnuwansu _"Assalama alaikum Jama'a masu sauraran Tashar Al'umma, kamar yanda bakwa raba mu da kawo muku labarai masu faranta rai da birgewa, wani ma ya zama tsani ga rayuwarku wajan dafa muku cikin qara walwalarku da nauyin aljihunku. To yauma gamu da wata sabuwar talla shahararran kamfanin nan mai suna MADUBIN AL'UMMA na neman ma'aikata haziqai fasihai afannin Injiniyarin wanda suka taka matakin digiri, qofar aiki abuɗe take ga duk mai buqata ya garzaya ya miqa takaddunsa, kada ku karaya en uwa ku jarraba sa'arku wanda baku san a ina take ba."_

"Yau kusan kwana biyu kenan ko wata tasha ka kamo tallar abu guda take, hatta ajikin jarida basu barmu mun hutaba, ko bamu da ra'ayin siya sai sun ajiye mana, Anya wanan neman na lafiya ne?"

"Suna neman ma'aikata ne, mi zai hana ka gwada Abdallah tunda kana da takaddunka ahannunka kuma sunyi kyau."

"A'a Arfat bana sha'awar aikin kamfani, wanda nake yi ma ya isheni."

"Banda abinka ɗana a inane ba'a neman sauyi? Balle sauyi na alkhairi, akwai banbanci tsakanin aikin kamfani dana gareji, kuje tare da Arfat ya raka kamfanin da takaddunka wata qila anan arziqinka yake." Mama Anta ta faɗa tana murmushi, kallonsa ya kai ga Ummie wanda ta gyaɗa masa kai alamun yarde masa "Kaje ka gwada Abdallah, tunda mamanka tace kaje, qila sauyin alkhairi ne yake nufoka."

"In sha Allah gobe zamu je." ya faɗa cikin sanyin muryarsa, dan da zasu lura shi baya maraba da aikin kamfani, domin yana ji akwai kasada acikinsa, haka kamfani baya ɗaukan asara komi qanqantarsa kayi kuskure to zaka biya ko arufeka, ataqaice dai shi yana tsoron aiki da mutanen da idanuwansu ya buɗe akan soyayyar kuɗi.

"Karka damu Abokina In sha Allah zamu dace." Murmushin yaqe yayi sanan ya jinjina kansa ba tare da ya sake tanka musu acikin hirarsu ba. Idanuwansa ya lumshe kamar mai gyangyaɗi ahankali sautin maganar Abu Khaleesat take dawo masa akunne _"Shi a iya rayuwarka ka taɓa saka tufafin da ya kai 10k? Ka taɓa cin Abincin da kuɗinsa ya kai 5k kacal? Nawa aka biyaka kazo kace kana son ɗiyata? Dan ɗan caca komi awajansa caca ake da shi."_ Idanuwansa ya qara rentsewa sosai yana kuma qoqarin toshe kunnuwansa wanda yake ji kamar ana zazzaga masa maganar acikinsa ne.

"Lafiya kake Abdallah" Arfat ya faɗa yana dafa kafaɗarsa, saboda tun lokashin daya rintse idonsa yake ankare da shi, sassauta numfashinsa yayi da yake fita da qarfi ya buɗe idanuwansa da suka sauya kala zuwa jajaye, "Kaina ke min ciwo." 

"Ayya sannu kaji, bari na ɗauko maka magani kasha sai kaje ka kwanta ka huta." Mama Anta ta faɗa tana tashi daga zaunen da take.

"Sannu kaji Allah ya baka lafiya" Arfat ya faɗa cike da tausayawa akan idanuwansa.

"Ameen ngd" ya faɗa cikin yana lumshe idanuwansa, mamaki yake akan al'amuran wanan duniyar da mutane suka cika da son kansu, fiye da nauyin da yake kansu, amma shi baiga baikin Abu Khaleesat ba dan ko wani uban da yake da matsayi irin nasa zaiyi farin ciki ne da samun suruki dai-dai matsayinsa ko kuma wanda ya ɗara nasa matsayin, amma talakan garin kamarsa yaje neman auren ɗiyar govnor ai yayi rashin kunya, ya kuma so kansa da yawa.

"Gashi maza sha ka samu ka huta kaji ɗana." sautin muryar Mama Anta ta farkar da shi daga saqa da qullin da yake, karɓa yayi yasha sanan ya miqe "Na gode, sai da safenku."

"Allah ya tashemu lafiya ya ba sauwaqe maka." suka faɗa cikin haɗin baki.

"Ameen" ya faɗa kana ya shiga ɗakinsu da yake xauren gidan, kwanciya yayi ya lumshe idanuwansa kamar mai barchi, can kuma kamar an mintsineshi ya ɗauko wayarsa Tecno wanda kuɗinta bazasu haura 5k ba ya fara daddanawa can kuma ya rufeta ɗif haɗe da idanuwansa.


*******

Litattafai ne birjik agabanta tana dudduba wa, ta janyo wanan ta kauda wanan, kanta ya ɗauki xafi sosai saboda jarrabawa ɗaya data rage musu, ko kaɗan bata fatan ta samu carry over duk da cewar ba abu ne mai sauqi abata shiba, amma bata so an bata maki kamar sadaka gara ace da kwanyarta ta sameshi, da kuma guminta, anata ganin wanan shine gatan da zatayiwa kanta ta kuma samu martabar da zatayi tunqaho da ita agaba ɗaya duniyarta, wayarta tayi haske alamun saqo ya shigo, tsaki tayi kamar ba xata buɗeba, amma zuciyarta na bata dama da ɗokantuwa akan ta buɗe ɗin, datse karatun da take tayi kana ta ɗauko wayar ta shiga cikin saqon :

_"Ba ko wani abu bane yake da kyau a idoba, wani abun sai ka ɗauki lokaci kafin ka gane kyan da yake da shi, lokaci zai zo da zai iya sauya komi da yake akwai zai kuma bamu damar zama acikin inuwa guda, ba tabbaci nake da shi akan gobena ba fata nake akan hakan ya kasance, zanyi qoqarin cika mafarkaina da kyawawan furanni domin su tayani qawata fatana."_


Bawan Allah


Ta karanta saqon yafi aqirga ba dan bata fahimci abin da saqon ya qunsaba sai dan kalmomin da akayi amfani da su masu cike da hikima acikinsa, murmushi tayi sanan ta rufe takaddun da ta barbaza ta kwanta akan gadonta wanda ya wadaci mutane goma su kwanta ba tare da wani ya takurama waniba.

_"Fatan alkhairi_" Iya abin data rubuta kenan ta tura, sanan ta ɗauro alwalar kwanciya barci bayan ta karanta Addu'o'i ta kwanta zuciyarta cike da farin ciki wanda bazai rasa na saba da saqon da taci karo da shiba."


*******

Duk yanda yaso ya kawo tsaiko akan tafiyarsa abin yaci tura domin agaba Mama Anta da Arfat suka sashi har sai da ya shirya tsaff cikin shiga irin ta ma'aikata da manyan masu tsafta farar riga ce ajikinsa sai liktayin baqi daya ɗaura awuyansa yayi amfani da baqin wando hannunsa saqale da agogon Fata fari qafafuwansa sanye cikin fararen takalma sau ciki. "Masha Allah yarona kamar rainon turawa, da alamu yau zaka haɗa go slow na 'yan mata ahanya." kalmar da Mama Anta ta faɗa cikin murmushi kenan saboda kyan da yayi mutqa, kai ya sunkuyar yana murmushi cikin alamun kunya dai-dai lokacin Ummie ta miqo masa takaddun karatunsa"Gashi nan, Allah ya taimaka ya bada sa'a"

"Ameen ya Allah Ummie" ya faɗa yana karɓan takaddun daga hannunta.

"Arfat ka kula min da ɗana, ka tabbatar ya samu yin komi kafin ku dawo."

"Kaii Mama sai kace wani yaro, wanan qaton saurayin kike bada sallahun akular miki da shi." Arfat ya faɗa yana dariya ganin yanda Abdallah yake jifansa da hararar wasa "Koma dai yaya ne nace ka kular min da shi banda tuqin ganganci."

"Oh Mama, na biyaki har tafiya cewa zakiyi na masa ma, oya taho mu tafi yaron Mama." da tsokana yake jefa ko wata kalma ta bakinsa hakan yasa Mama Anta ta kai masa bugu yayi wuf ya fice sai dariya su Ummie suke musu, su dai kullum kamar kaka da jika haka suke tafiyar da rayuwarsu.

Bayansa Abdallah yabi yana ɗagama su Ummie hannu har saida suka ɓacewarsu akan idonsu sanan suka dawo gida. Ajiyar zuciya Ummie Abdallah ta sauqe wani abu ke taso mata aqasan ranta wanda bata san ko miye shiba, haka nan tana jin kamar tayi kewar wani abu atare da ita, ko wani abu ne wanan? Mama Anta ce ta ci gaba da janta da hira da labarai wanda yasa ta wartsake daga duniyar tunanin data lula, ahaka suka fara hidimar girkin abincin da Mama Anta take siyarwa dan yanzu abun ya qara yawaita dan mutanen tasha kanzo har gida su siya banda mutanen unguwa kullum Hamdala Mama Anta take tana qara godewa Allah da ya kawo Su Ummie cikin rayuwarsu."


*****

Tafiyar rabin awa ce ta kawo su kamfanin saboda tazarar tafiyar da ke akwai tsakanin gidansu da kamfanin danma amashin suke ba motaba, hakan ne ya basu damar kutsawa ta tsakanin motocin dake wajan hakan ya taimaka musu wajan isa akan lokaci, wajan cike yake taf da masu neman aiki wanda ya basu mamaki sosai "Anya ba zamu komaba Arfat? Dan zamu ɓata lokaci da yawa kafin azo kanmu?"

"Matsalata da kai saurin karaya kenan, ba inda zamu koma har sai ka shiga an maka gwaji." 

"Ai shikenan, muje."

Qarasawa sukayi suka samu ɗaya daga cikin kujerun d mutane suke zaune suka zauna.

Ahaka mutane suka fara raguwa har layi yazo kansu, fargaba ta cika Abdallah akan abin da zai zo yaje, dan wanan shine karo na farko da ya samu kansa cikin irin wanan wajan, sai da Arfat yayi da gaske sanan ya rakashi har wajan da ake jarabbawar.

Cikin fargaba ya shiga mutane yaga su uku zaune akan kujeru ga qaton tebir dake gabansu da takaddu, kusa da ko wani mutum akwai na'urar isar da magana ajiki.

Da sallama ya shiga suka Amsa ɗaya daga cikinsu ya masa nuni da kujera ya zauna, kana ya miqa takardunsa, dubawa suka farayi suna jinjina kai daga hanun wanan zuwa wanan har ya gama zagaya su ukun."

"Takaddunka sunyi kyau mutqa, sai dai abin tambayar anan iliminka ne ya vaka ko kuma kyauta aka baka? Dan abune mai wahla awanan zamanin asamu matashi kamarka da kyawawan takaddu haka."

Murmushi Abdallah yayi kafin yayi magana "Wanan ma yana cikin jarabawar da kuke yiwa ma'aikatanku?"

"A'a yi haquri, mi nene tsammaninka da zuwa nan wajan neman aiki?"

"Sa rai, Sa rai akan cewar kamfanin yana da nagarta da kuma tausayawa wanda yake na qasa da shi."

"Mi za kayi da albashinka idan aka fara baka shi akaro na farko?"

Murmushi yayi sanan ya kawar da kansa gefe ɗaya "Ban saniba gaskiya."

Kallonsa sukayi gaba ɗayansu cikin mamaki suke kallonsa "Baka saniba kace?"

"Eh ban saniba, domin komi dalili yake nema, ta iyu nace ga abin da xanyi da shi sai kuma asamu akasi yazo wanda zai wargaje abin da na shirya yinsa, ataqaice dai bani da ilimin sani akan gobe ne, sai abin da ta bani shi xan sa hannu na karɓa."

Kallon-kallo aka farayi tsakanin masu tambayar mamaki ne ya kamasu domin da yawa da suke musu tambaya kowa na bada amsar abin da zaiyi da kuɗin albashinsa idan an tambayeshi, amma kuma wanan saɓanin tunaninsu bashi da tsari akan kuɗinsa.

Miqa masa takaddunsa sukayi suna murmushi kafin su ɗora da cewar "Ba zamu ɗauki wanda bashi da tsari arayuwarsa ba."

Karɓa yayi yana murmushi shima "Na gode sosai, amma ba tsari ne bani da shiba, buri nane kaɗan akan al'amuran duniya da abin da suka zama qawa acikinta ba." daga nan ya miƙe yana qoqarin barin ɗakin fuskarsa qunshe da murmushi wanda suka gaza gane ko na miye.

"Nawa ne farashin kuɗin" ya tsinkayi muryar ɗaya daga cikin ma'aikatan wajan, cak ya juyo yana kallonsu da mamaki "Kamar ya kenan yallaɓai?"

"Nawa kamfani zata biyaka amatsayin albashinka na farko."

Murmushi yayi yana lumshe ido dan fahimtar inda maganarsu ta dosa "Muna tayaka murna ka samu aiki awanan kamfanin, zaka iya fara zuwa aiki ranar monday." suka faɗa cikin haɗin baki .

Wani farin ciki ne ya cika zuciyar Abdallah wanda bai taɓa tsammanin jin irinsaba, godiya ya fara musu suka shiga jinjina masa tare da miqa masa tambarin kamfanin da lambarsa, sauran bayani kuma sai ya zo zai ji ɗaga shugaban kamfanin.


 Da murnarsa ya fito ya rungume Arfat yana dariyar farin ciki "Arfat na samu aiki awanan kamfanin." 

"Alhmdlh" Kalmar da Arfat ya faɗa yana qara qanqame Abdallah....


🥀🥀🥀🥀🥀🥀


©by Um Nass

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI 🎊*


©by *😘Um Nass🏇🏼*


Page 50


Janye idonsa yayi daga kallon da ta kafe shi da shi, kana ya ɗora da murmushi "Abdallah Bawan Allah" abin da ya sanar da ita kenan sanan ya fara lallatsa romote ɗin dake hannunsa, qarasowa tayi kusa da shi ta zauna akujerar da take saitin wajan zamansa.

"Ba sunansa nake son saniba Abu Khaleesat, bayani nake son ji akan ko waye shi? Acikin idanuwansa akwai jarumta ko kaɗan bashi da tsoro, gashi kuma yana da nutsuwa atare da shi."

Kallonta yayi yana murmushi kafin ya tsuke fuska "Wani lokacin kina da damuwa Um Khaleesat, ni kaina bayan sunansa ban san wani abu akansaba, amma zaki iya tuna ranar da akayi hira dani a asibiti na kai wata yarinya?" kai ta gyaɗa ba tare da tayi magana ba "To shine matashin saurayin da ya tareni ya kuma ɗaukaka darajata acikin mutane, ina son wanan qumajin nasa, da yarda da kai da yake da shi, waifa duk da matsayinsa da yake na talakan gari amma ahaka yazo neman izinin kiran Khaleesat" dariya yayi mai kyau sanan ya girgiza kansa "Ban san mi ya bashi wanan jiji da kai ɗinba, amma ina son salon yaron, ni kuma zan tabbatar da baiyi nasara akan wanan wasanba."

Kallonsa Maa tayi cikin mamakin maganar da yayi, kamar ba shine yake yabon yaronba akwanaki biyun da suka gabata, amma kuma sai gashi yanzu yana qoqarin ya aibanta yaron "Ni kuma sai nakega babu wanda ya dace da rayuwar Khaleesat kamar shi, akallon farko da nayi masa naji ya taɓa zuciyata, tabbas ba kowani mutum bane yake zama na kirki, amma wanan irinsa kaɗan ne awanan duniyar tamu."

Kallonta yayi kafin yayi magana cikin murya mai zafi "Kullum kina yin abu kamar ba ke kika haifi Khaleesat ba, wallahi da ace ba'a gabana kika haifetaba da cewa zanyi tsintota kikayi, taya kike tunanin zan ɗauki erta guda ɗaya tilo na bawa talakan gari, ta yanda zata sha wahla."

Miqewa tayi tsaye tana kakkaɗe hannayenta "Kana yin abu kamar ka manta mafarin ko wani mutum aduniya yana farawa da sufuli bane, amma wata ƙila kai ka shagala da rayuwar jin daɗin daka faɗa yanzu, uhmm Aada masu Arziqin qasar. Ina fatan baka manta asalin ko na waye arziqinba? Kada wata rana suzo karɓa kace baka san da shiba, HAQQI ba zai barka ba Aada, gara tun yanzu kayi gaggawar neman yafiyar ubangijinka, mutuwa zuwa take bata jira bata kuma qwanqwasa qofa balle kace ta jiraka. Ita kuma kaza garin tone-tonenta take tono wuƙar mutuwarta." tana gama faɗar haka ta shige ta barshi anan baki sake, kafin wani lokacin gumi ya fara sartu akan goshinsa sai tsantsameshi yake duk da masuburbuɗar sanyi na ratsa ɗakin amma kamar ba ta aiki.


 ********

Tun futar Abdallah daga gidan ya rasa mi yake masa daɗi lokacin da Isya ya nufeshi yana washe baki akan ya fito kai kawai ƴa gyaɗa masa yana murmushin da har yanzu iyakarsa kan laɓɓansa, mota ya ɗauko ya ɗauke shi yana qoqarin maidashi gareji "Kai ni gida kawai Isya dan yanzu lokacin tashi ya riga da yayi." 

"To ba matsala." sanan ya fara daddana wayarsa ya kara akunnensa "Ka wuce gida kawai kada ka jirani." kalmar da ya faɗa ya datse kiran wayar, sanan ya qurama titin da suke ratsawa ido.

"Tsawon shekara nawa kana aiki a gidan govnor?" ya saita tambayarsa yana faɗaɗa murmushinsa.

"Wai yau tsawon shekara biyar inaga dan tun kafin yana matsayin ɗan majalisar jaha muke tare."

Kai ya gyaɗa yana murmushi "Yana da kirki sosai Isya, awanan lokacin ba'a samun shugabanni masu sauqin kai irinsa."

Dariya Isya ya saka yana buga sitiyari "Gaskiya ne yana da sauqin kai, amma wani lokacin shi ɗin murɗaɗɗan mutum ne, sai ka masa kallon mutumin kirki amma kuma wani lokacin bashi da kirki, amma kaga matarsa ta daban ce, awanan rayuwar ana samun matan shuwagabanni da juya akalar mulki, amma ita ko kaɗan bai dametaba, dan awasu lokutan sai dai kaga mata suna zuwa gidanta, amma da wuya ace ta fita sau ɗaya amako sai idan fitar ta dole ce, balle ace ta shiga zauren matan govnoni, rayuwarta cike take da sauqi da sauqaqawa acikin lammuran duniya." 

"Amma erta Khaleesat fa?"

Baki Isya ya rufe yana jinjina kai "Kasan abin da ake kira da ruwan dare zaga duniya. To ita tamkar ruwan sama ce da yake sauqa yake fidda mutane daga fari ya kuma shayar da dabbobi daga qishi da yunwa, ya saka mutane cikin walwala da gamsarwa, ataqaice ita ɗin mutum ce ɗaya da ɗaya samun irinta awanan duniyar abune mai wahla, dan ta zarta mahaifiyarta sauqin kai da buɗa hannayenta wajan bada alkhairi. Haka bata damu da kasancewarta er govnor ba wasu kai da kanka zaka shedi hakan."

Numfashi Abdallah yaja ya furzar da iska acikin bakinsa "Ina son Khaleesat Isya" wani wanan burki Isya yaja ya tsaya kana ya kai kallonsa ga Abdallah wanda shima ya shiga zare ido dan ganin abin da yasa Isya jan burki haka amma bai ga komiba, ya juya yana kallon Isya wanda da mamakinsa shi Isya ya qurawa ido kamar mai son ganin wani abu ajikinsa "Ya da kallo haka malam? Kana tafiya ka ja birki ni duk tunanina wani ka kusa bugewa."

Kai Isya ya girgiza yana kallon Abdallah "Wani abu naji akunnena yana min gizo kamar kai kace kana son Madam Khaleesat."

Murmushi Abdallah yayi masa sanan yace "Ba gizo kunnuwanka suke makaba, gaskiya suka jiye maka, Ina son Khaleesat tun ranar dana fara ganinta, ko kaɗan bana jin ta girmewa matsayina, kai dai ka zuba ido zakaga abin mamaki."

"Kai kanka abin mamakinka yawa gareshi Abdallah, ban taɓa ganin mutum irinka ba, da fari na ɗauka siyasa ce amma sai na fahimci aqida ce, hmm zan so yin tsawon rai ko dan naga gasar mutuwa da sai mai rabo ke tsira."

"Ja mota mu tafi Rai dai.."

Motar ya kunna ba tare da ya sake tankawa ba, amma azuciyarsa ya cika da tsantsar mamaki da tu'ajubin Abdallah, aqofar gidansu ya sauqeshi "Na gode, ba zaka shigo ku gaisa da Ummie ba?"

Kai ya girgiza masa "Wani lokacin zanzo mu gaisa yanzu ina sauri ne."

"To ngd sosai, fatan alkhairi Abokina."

"Kaima haka Angon Khaleesat" ya faɗa cikin tsokana wanda yasa Abdallah yin murmushi, dan yaga abin kamar gatse ne yake masa, "Wata rana zan shayar da kai ruwan mamaki, wanan fata kayi amma lokaci kuma zai cika warware mana." bai tsaya jiran amsar da zai faɗaba ya shige cikin gida.

Kai Isya ya girgiza "Allah ya kai damo ga harawa na tabbata koda bai ciba zaiyi ɓarna son ransa" sanan ya kunna motarsa yayi gaba abinsa.


 ****

Shuru sukayi kamar babu ɗaukacin mutane awajan, abin zai baka mamaki idan kaga yanda sukayi zugum-zugum kamar wanda saqon mutuwa ya riskesu.

Can ya nisa ya gyara zamansa akan kujerar da take lilawa kafin ya ɗago ya fara jeranta kallonsa akan mutanen suma kallonsa suke "Bamu da wani zaɓin da ya rage ayanzu, inaga kawai mu rufe company nan shine abu mafi sauqi agaremu, shima ba wai zamu tsira da wani abunbane idan kukayi la'akari da ya da aka biyomu maqudan kuɗaɗe, zai iya zama asara agaremu dan zamu radhi bamu da ko anini acikinsa."

 Ya qarasa maganar yana sharce gumin da yake zuba akan goshinsa da tushu ɗin da ke gabansa.

"Gaskiya Yallaɓai kar arufe kamfanin nan, saboda tsoron faɗuwar da zamuyi, mi zai hana mu nemi ma'aika wanda suka qwarai akan fannin injiniyarin ta yanda zasu ɗago da fasaharsu, idan muka jarraba mukaga anyi dace falillahil hamdu, idan kuma an samu akasin haka sai mu sake jarrabawa, amma saboda tsoron faɗuwar hannun jarinmu da aka samu idan muka qi ai mun yi babban Asara."

Kai ya girgiza yana murmushi "Har yanzu baka fahimtaba Saleem? Ina muke da kuɗin da zamu biya tsoffin ma'aikatanmu ma balle aje mawar biyawa sabin da zamu ɗauka, kaima kasan akwai ganganci da kasada acikin wanan al'amarin."

"Ba wai zamu biyasu da fariba kamar yanda aka saba biyan ma'aikata, dole sai munga qwarewarsu akan aikin ne, duk da ayanzu ba'a fiya samun masu Fikra akan wanan fanninba amma ya kamata mu jarraba."

"Haka ne yallaɓe ya kamata mu bi shawarar Saleem wata qila anan mafitar tamu ta kee."

"Shikenan tunda kunyi haɗaka wajan magantuwa akan abu guda, amm Saleem sai a tallata Hajar tamu akan neman ma'aikatan da suka qwarai wajan injiniyarin, da kuma takaddunsu lalai a isar da saqon akafafan yaɗa labai na radio da da kuma na TV bana son awuce wanan makon."

"An gama Yallaɓai" daga haka suka fara tashi ɗaya bayan ɗaya suna fita aɗakin taron.

 Kansa ya riqe yana murza goshinsa wanda ya cika da tarin damuwa ya samu halattar ciwon kai, wata guda kenan da afkuwar daqushewar ma'aikatar tasa duk wanda suka saka hannun jari suna janyewa kamar haɗuwar baki, saboda samun matsala ɗaya takk na maci amanar ma'aikatar tasu.

Alh. Ahmad Naseer kenan shugaban kamfanin qere-qere na *MADUBIN AL'UMMA* kamfani ne dake zaune da diga-digansa cikin aiki tuquru da nagarta, hakan yasa ya samu dafawar manyan mutane wajan saka hannun jarinsu dan tafiyar tayi nisa, Alh. Ahmad Nasir mutum ne mai kamala da sanin ya kamata uwa uba gaskiyar da yake da ita, babu zalinci acikin al'amuransa, mutumin jigawa ne kasuwanci ne ya kawoshi kano wanda ya kafa kamfaninsa yana da mace guda ɗaya da yara uku Muhmad (Ameen) shine babba ɗan shekara biyar sai Jidda da take binsa 3yrs sai qaramin Isma'il mutum ne mai kula da haqqin daya rataya awuyansa, yana da iyaye da en uwa da yake kula da su cikin dukiyarsa haka matarsa mai suna Zainab mace ce mai hankali da girmama na gaba da su.

Alhmdlh kamfaninsa ya tasa ta yanda ya zama xakaran gwajin dafi acikin garin Kano yana ɗaya daga cikim manyan kamfanonin da ake ji da su agarin, wani kamfani dake qasar China ya basu kwangila akan qera sabuwar wayar da zata zama sunfuri na sabuwar shekara, kuɗaɗe masu yawa suka basu sai da aikin yayi nisa ana gaf da cima manufa ɗaya daga cikin ma'aikatan ya saidawa wani kamfani aikin da sukayi kana ya gudu yabar qasar da maqudan kuɗaɗe, wanan ya kawo barazana acikin kamfaninsu da kuma son warwarar Nagartar da suke da ita.

Shi yasa suka faɗa cikin zauren tattaunawa akan neman mafita yanzu dai sun tsaya amatsaya guda ɗaya ta neman sabin ma'aikata dan yin aikin da yafi kowanne..


  


_"Yau kam babu yawa kasancewar ranar da muke ciki itama gajera ce mai cike da lada da yawa. Mi kuke tunani da fitowar Alh. Ahmad Nasir cikin labarin haɗin gwarmai? Duk da bai kai hamshaqi ba zamu kira shi da......."_


🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀
©by Um Nass

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI 🎊*


©by *😘Um Nass🏇🏼*


Page 52


Murna sosai sukeyi awajan yayin da ɗaukacin mutanen wajan suka cika da mamaki domin kowa ya fito babu wani alamun nasara ko na ɗaukeshi aiki duk da dafifin da mutane sukayi na zuwa neman aiki, kai suka jinjina wasu sunaga qarfin sa'ar da yake da shi wasu kuma suna ga rabonsa ne ya tsaga hakan.

Haka suka nufi gida fuskokinsu ɗauke da farin ciki wanda ganinsu ya isa ya tona sirrin dake cikin zukatansu.

"Mama! Ummie ku fito maza da sauri-sauri" Arafat ya fara kiransu tun daga zaure cikin ƙaraji da sautin da yake nuna tsantsar farin cikin da yake ciki, da sauri suka fito kamar haɗin baki "Lafiya Arfat wanan kira tun daga qofar gida?"

"Lafiya qalau Abdallah dai ya samu aiki ai dole na kira ku da ihu."

"Alhmdulillah" suka faɗa cikin haɗuwar harshe kana Ummie tayi sujjada anan ta godiya ga Allah, nan suka cika da murna da farin cikin samuwar aikin Abdallah wanda ko kaɗan basuyi tsammanin hakan ba.

Nasiha sosai Mama da Ummie suka masa wanda mafiya yawanta akan ruqon Amana da gaskiya ne wanda yana cikin ɗabi'unsa da kuma abin da ya riga ya sani, sai dai tuni da suka masa na bam-bamcin mutane da zaiyi mu'amala da su kasancewar idanuwansu ya buɗe da zamani da soyayyar kuɗi wanda ke makafintar da su har su faɗa halaka, godiya ya musu dan Nasiharsu ta samu matsugunni sosai acikin zuciyarsa yana kuma girmamasu da jin soyayyarsu aqasan ruhinsa.

"Zo muje wata ƴar unguwa" ya faɗawa Arfat yana fita waje "Sai mun dawo Mama, Ummie" ya faɗa yana ɗaga musu hannu, suma hannun suka ɗaga masa tare da fatan dawowa lafiya "Wani lokacin idan Abdallah yayi abu kamar da quruciya atare da shi, amma ina son yanayinsa sosai, har raina nake jin qaunarsa kamar ni na haifeshi." Mama Anta ta faɗa fuskarta qunshe da fara'a, murmushi Ummie tayi sanan ta ɗora nata "Nasha sanar da ke cewar Abdallah naki ne, dan yanzu bashi da wata uwar da ta wuce ki, ba sai ɗan da ya fito daga tsaginka ne yake zama ɗaba wani lokacin Kima da Martaba takan baka soyayyar er erye fiye da wanda ka tsugunna ka haifa."

"Ina mamakin gidadancin da mutanen Gumsa sukayi na rabuwa da ku Um Abdallah, sun rabu da kyautar da tafi ko wacce sun kama gadar waru."

Murmushi Ummie tayi "Ƙaddarar haɗuwarmu da ku ce tasa muka rabu da su, kin san duk abun da Allah ya tsarama bawansa shi bashi da tsumi bashi da dabara dole sai yaje ya sameshi."

Kai Mama Anta ta jinjina "Haka ne kam, Allah yasa mu dace"

"Ameeen" daga nan suka faɗa cikin wata hirar wanda ta shafi al'amuran rayuwa wanda yake kai kawo awanan duniyar tamu.


******

"Wai ina zamu je ne haka kamar masu shirin barin gari?"

"Kai dai ka kara haquri mana Arfat mun kusa."

Shuru yayi ba tare da ya qara maganaba sai hanyar da yaci gaba da bi, ya lura da Abdallah da yake cikin tsantsara farin ciki, tsammaninsa baya rasa nasaba da samuwar aikin da yayi "Arfat nifa ina tunanin yanda zan rabu da Oga Haruna gashi munyi sabo da shi sosai, yana ganin girmana amma tashi ɗaya yaji ɓa bar aiki da shi na faɗa wani wajan." ya tsinkayi muryar Abdallah da sauyawar yanayin da yake ciki daga walwala zuwa damuwa.

Ɗan tsaki yayi kafin yayi magana "Ko wani mutum yana son ci gaba arayuwarsa Abdallah, shi kansa oga Haruna idan soyayyar gaskiya yake maka to zai tayaka murnan samun wanan aikin ne, amma kada ma ka damu kanka har ka samu ƙunci acikin zuciyarka."

Kai ya gyaɗa dai-dai lokacin da yake gangarawa Babar jamiya'ar garin, mamaki ne ya kama Arfat ganin inda suka zo "Mi kuma ya kawo mu nan wajan?"

"Kai dai ka zuba ido mana"

Shuru yayi bai sake tankawaba har suka shiga makarantar da take cike da ɗalibai sai kaiwa-da-kawowa suke ba ruwan wani da wani, amma shigowar su Abdallah Kallo ya koma kansu duk inda suka wuce idanuwan mutane na kansu, kallon da basu san sunayiba basu kuma fahimci dalilin yinsaba, burki yaja ya tsaya atsakiyar makarantar sanan ya fara barbaza idanuwansa, wani ne yazo kusa da shi cikin girmamawa ya risina yana gaidashi "Yallaɓai ga Khaleesat ɗin can yanzu ta fito daga jarabawa."

Da mamaki yake kallon mutumin domin yasan wanan shine karo na farko da ya zo cikin makarantar "Ya akayi kasan wajanta yazo?" Arfat ya tambaya wanda ya kasa ɓoye mamakin dake kan fiskarsa.

Kai ya shafa yana murmushi "Ko makaho ya ganshi ai yasan yayanta ne shi, duba da kamannin da sukeyi da ita." Mamaki ne ya ƙara cikasu amma kafin su farga yayi gaba yana cewa "kama ganta can ta nufi wajan motarta."

"Wanan inaga ya samu matsalar gani ne." Abdallah ya faɗa yana taɓe baki, yayin da kan Arfat ya kulle ya gaza yin magana "Kai dama wajan Madam Khaleesat ka kawo mu? Abdallah mi yasa baka jin shawara ne? Sanin kanka ne yarinyar nan tafi ƙarfinka, ni dai babu ruwana acikin wanan batun."

"To da wa yace kayi ruwa dama, kaga na qara samun dalilin haɗuwa da ita tunda an fara cewa muna kama, nasha jin cewar idan jininku ya haɗu da mutum har kamanni kukeyi, Musamman idan haɗuwar jinin ta soyayya ce."

"Hm lallaifa masoya, waima ya akayi kasan makarantar tasu?"

Murmushi yayi wanda haqoransa suka bayyana "Akan abin da kake so zaka iyayin komi dan ka isa gareshi, Isya ya nuna min makarantar kwanakin baya." yana qarasa faɗar haka yaja mashin ɗinsa ya nufi wajan da ƴa hango Khaleesat su biyu ita da wata da alama qawarta ce dan jingine suke ajikin motar tana magana tana murmushi wanda ya qara mata kyau afiskarta.

 Qaran mashin ɗin da taji asaitinsu ya sasu dakatawa daga hirar da suke suka ɗago da kallon ga saitin inda qaran ya fito, mamakin ganinsa take anan ga kuma shigar da bata taɓa ganinta ajikinsaba, gaskiya ne Abdallah kyakkyawane wanda bata taɓa tsammanin kyan nasa ya kai hakaba, yayin da wani sashi na zuciyarta ke tunatar da ita wanan ba shi bane. Duk wanan tunanin tayi shine cikin daqiqar da bata wuce biyarba, sanan tayi qoqarin saita nutsuwarta.

 Da murmushi ya qaraso wajansu yana kafeta da idanuwansa wanda suke a lumshe kawar da kanta tayi daga kallonsa da takeyi "Ina tayaki murnar kammaluwar jarrabawarki ƙanwata."

Da mamaki ta ɗago tana kallonsa, da son sanin inda ya samu labarin kammaluwar jarrabawar tata ayau, ganin mutane awajan yasata aro dauriya da jarumta ta faɗaɗa murmushinta "Na gode ɗan Uwa, amma ka makara sosai dan nayi tsammanin kai ne mutum na farko da zaka fara min Murna."

Hannayensa ya haɗa waje ɗaya alamun roqo ya langaɓar da kansa "Ban makaraba dan na daɗe da tsammanin wanan lokacin, duk da mutane da yawa sun miki na tabbata nawa zai zama na musamman ne wanda ake dakonsa." sanan ya matsa kusa da ita ya risina ta yanda ita kaɗai zataji abin da ya faɗa "har yanzu zuciyata na nan akan abun da take so, cike da qawatuwar mafarkai, kici gaba da duba ko wata daqiqa da zata gifta cikin sa rai da tsammani, lokaci kuma zai bani damar kasancewa atare da ke, koda ace babu wanda zai qarfafa min gwuiwa akan hakan zan zama mutum na musamman adukkanin rayuwarki." yana gama faɗar hakan ya ɗago yana qara yalwata murmushi wanda ya fito da kyansa sosai, murmushi itama tayi sanan ta ɗauko kati ajakarta, hannunsa ta ruqo ta ɗora katin ta dunqule hannayen nasa kana ta sassauta sautin muryarta "Wani lokacin kamar jarumi kake naka salon, amma zanso ka cimma mafarkinka ya zama gaskiya, duk da hakan abune mai mutqar wahla, ka sake gwada wata damar nan da wata guda ka tabbatarwa da duniya manufarka akaina ciki harda Mahaifina, a lokacin ya baka amincewar Aurena daga lokacin da kayi nasara akan haka to zan dauwama cikin soyayyarka Muddum raina, karka manta wata ɗaya ne ya rage maka ka fara buga wasan." daga haka ta kai kallonta ga Arfat wanda shima yayi kasaqe yana kallonsu Abun nasu gwanin birgewa sosai, sanan yayan da tayi amfani da shi ya qara taimaka wajan ɗaurewar kansa, _Yaushe Abdallah sukayi sabo har haka shida Khaleesat da zata qirashi da yayanta?_ Tambayar da bashi da amsarta dole sai Abdallah ne zai warware mata. Itama qawarta da suke tare kallonsu take cikin mamaki da son sanin abin da suke faɗa, amma tasan Khaleesat bazata faɗa mataba sabod tsantsar miskilancinta.

"Ka wanke kanka yanzu, amma ka riga kowa hallatar bikin tayani murnar qare karatuna ranar Asabat."

Kai ya jinjina yana murmushi kana ya juyar da kallonsa ga qawar tata "Qanwata babu gaisuwa ne?"

Kai ta sinne qasa cike da kunya kafin tayi magana "Ai naga kamar baka son gaisuwar idonka ya rufe akan qanwarka kaɗai ka sani."

Kai ya dafe yana rufe bakinsa "Yi haquri mu gaisa yanzu, ya kike? ya karatu? Ina fatan kun gama jarrabawa lafiya?"

Dariya tayi sanan ta girgiza kai "Waɗan nan tambayoyi masu yawa haka, wacce kake so na Amsa maka?"

"Duka, kuma alokaci ɗaya."

"Gaskiya sunyi yawa, amma dai tunda kace duka gaba ɗaya Alhmadulillah."

Dariya kawai yayi ya jinjina kai ba tare da ya sake ce mata komiba, shi dai Arfat mamakin Abdallah ya cikashi ganin ya sake sai magana yake kamar ba shine wanan miskilin da magana take masa wahla ba, balle aje matakin dariya, duk da yasan murmushi ɗabi'arsa ce amma yin dariya mai sauti abune mai wahla awajansa, amma sai gashi yau yana dariya mai sauti.

"Abokinka baya magana shi?" ya tsinkayi maganar Qawar tata sai alokacin ya tuna suna tare da Arfat wanda ya kafeshi da kallo, kallonsa ya kai ga Arfat ɗin yana masa inkiya da kai kafin ya kawar da kansa ya dubi Khaleesat wanda take daddana wayarta tun bayan maganarsu da qawarta ta shafe babin magana kamar babu wanzuwarta awajan.

"Ya hanani yin magana ne, shi yasa nayi shuru na zama ɗan kallo." ya tsinkayi muryar Arfat ɗin cike da zolaya, bai tanka masaba sai murmushi da yake kana ya kai idonsa ga agogon da yake saqale ahannunsa.

"Arfat mu tafi ko? Lokaci yaja da yawa."

"To mu tafi, am banji sunan qawar tawa bafa." ya faɗa yana kallonta da sigar zolaya.

"Siddiƙa" ta faɗa tana murmushi, shima murmushin yayi sanan ya qara da ɗaga mata hannunsa alamun bye-bye.

"To qanwata sai mun haɗu." Abdallah ya faɗa yana kallon Khaleesat da ta kafesu da nata idanuwan, kai ta gyaɗa masa ba tare da tayi maganaba har yaja mashin ɗin suka tafi. Dai-dai lokacin Siddiqa ta sauqe Ajiyar zuciya wanda taja hankalin Khaleesat wajanta ta juyo tana kallonta "Baki taɓa sanar dani kina da Yaya Mai kyauba Leesat, da tun akan lokaci na roqi Alfarmar ki min iso ga zuciyarsa." kallon mamaki Khaleesat tabi Siddiqa da shi ba tare data tanka mutaba, duk da haka taci gaba da yin maganarta "Ban taɓa ganin en uwan da suke kamaba kamar ke da shi, gashi halayyarku kusan iri ɗaya shima bashi da jiji da kai da kuma ɗagawa irin ta yaran manya."

Zuwa yanzu mamakin khaleesat ya gaza ɓoyuwa har sai da ta tanka mata "Wai ke wa ya faɗa miki shi ɗin yaya nane?"

Kallonta tayi sanan ta girgiza kai cike da murmushi "Bana buqatar kimin wata borin kunya malama, kammanin da kuke da shi ya Isa ya sanar da kowa shi yayanki ne, hatta kalar fatarku iri ɗaya ne, sai buɗewar idon da kika fishi da shi, da hasken fata, amma idan kika ɗauke wanan komi naku iri ɗaya ne."

Kallon Siddiqa take cike da mamakin jin maganarta wai suna kama da Abdallah, anya ba matsalar gani ta samuba? Sai dai kafin tayi magana ta sake tsinkayar muryar wani ɗan Ajinsu "Madam kun haɗu da yayanki kuwa? Dan naga shigowarsa har na nuna masa inda kuke, gaskiya kuna kama sosai, sai dai nayi mamaki da ban taɓa ganinsaba haka kuma ban taɓa ji ko acikin labariba kina da ɗan uwa haka." ido ta fiddo waje tana kai kallonta ga saitin mai maganar haka tana juyar da idonta ga Siddiqa wanda itama kallonta take da son neman qarin bayani awajanta, ido ta runtse tana hasko kamannin Abdallah wanda bata taɓa kawo ɗiban kamannin da sukeba, sai ayanzu da suka faɗa ta kula da wasu abubuwa, da sauri ta buɗe idanuwanta ba tare da tace musu komiba ta shiga motarta da gudu take tuqata xuciyarta na mata zafi da zugin so take ta kai ga inda ya kamata ace ta kai amma ta ina zata fara??


🥀🥀🥀🥀🥀🥀 

Taqi kaɗan ya rage kada ku manta kimar da ke tare da ku ayayin da kuka magantu dan ra'ayinku, bazan san saqon yana isa garekuba har sai kun magantu kun kuma martaba hakan, mintuna biyar sun wadace yin cmnts.©by Um Nass

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI 🎊*


©by *😘Um Nass 🏇*


Page 53Kai tsaye garejin Oga Haruna ta nufa sai dai abin takaici babu Abdallah babu Arfat, mafi munin labarin da taji shine Abdallah ya samu aiki a wata ma'aikata dan haka yabar aiki a garejin nan, sanan sun manta sunan Ma'aikatar da yake aiki balle su sanar da ita, hankalinta bai bata cewar ai Isya ya sanshiba, cikin sanyin jiki ta shiga motar tana lallashin zuciyarta akan lallai zaizo bikin kammaluwar karatunta dan haka ta wartsake ta nufi gida.

 Ahaka ta shiga gida duk ma'aikacin da ya gaidata kai take ɗagawa wani kuma tayi kamar ba tajiba, abun ya basu mamaki sosai sanin halayyata ba haka takeba, wata qila gajiya ke ɗawainiya da ita, kalmar da suka faɗa atsakanin zuciyoyinsu.

 Da sallama aqasan maqoshinta ta qarasa wajan Maa da take hakimce akan kujera mai zaman mutum biyu, hannunta ɗauke da littafin Addu'o'i ba taji ko sallamartaba sai jin mutum tayi akan cinyarta "Khaleesat yaushe zakiyi hankali ne? Ki shigo kanki tsaye babu sallama salon ki tsoratar da mutane."

"Nayi sallama Maa." ta faɗa muryarta da sanyi sosai tana lumshe idanuwanta, hakan yasa Maa saurin kallon fuskarta.

"Mi yake damunki Khaleesat?"

Kai ta girgiza "Ba komi Maa"

Ido ta qura mata kafin nan ta shafa kanta cikin muryar lallashi ta fara magana "Duk da baki faɗa min abun da yake damunkiba ina hasashen wani abu agame da ke, kwanaki wani saurayi yazo wajan Abbanki yake cewa yana sanki ya bashi dama, ban saniba ko kin sanshi, dan yaron ba mai arziqi bane asalima talaka ne."

Idanuwanta ta buɗe tarwai tana nazartar maganar Maa ɗin kafin ta buɗe baki tace "Kin ganshi da idonki Maa?"

Kai ta jinjina alamun bata tabbacin ta ganshin "Ya kikaga kamanninsa idan kin dangantashi da nawa?"

Ido ta qurawa Khaleesat kamar aranar ta fara ganinta, anan ta fara qiyasto kamannin saurayin, ji tayi gabanta ya faɗi sosai da sosai Musamman data tuna qwayar idonsa da fiskarsa, ta kuma kalli Khaleesat ɗin akaro na biyu, miqewa tsaye tayi tana kaiwa da kawowa kafin ta dafe qirjinta da yake bugawa kamar zai faso qirjinta "Ya akayi awanan lokacin banga ɗiban kamar da yake dani ba?" ta faɗa tana dafe kanta "Ya Rabbi kasa hasashen da nake akansa gaskiya ne."

Tashi itama Khaleeaat tayi tana nufar Maa ɗin "Kin sanshi ne Maa? Yau mutane biyu ke kiransa da yayana a makaranta, har suna zuzuta kamannin da muke da shi."

Kallonta Maa tayi kafin ta girgiza kanta cikin dauriyar data Ara ta yafawa kanta "Ban saniba, kamace da ɗiban kama kawai, kasancewar ko wani mutum ance yana da mai kama aduniya har bakwai, amma kuma idan kika dangata cewa Ubangijin daya haliccemu ɗaya ne to sai kiga hakan ba komi bane cikin Ikonsa da buwayarsa."

Kai ta fara girgizawa tana danne damuwar data taso masa "Badda wanan Maa, dole zai kasance akwai wani abu tsakaninmu da shi, idan babu a ina ya samu qwarin gwuiwar da zai ce yana sona? Kai bama wananba akwai wani abu da kuke ɓoye min keda Dady dole akwai ranar da gaskiya zata fito."

Ruqo hannayenta Maa tayi ganin tana qoqarin sauqe mata rigima "Ki yarda dani Khaleesat ban san komi akansaba, ko sunansa ban saniba dan babanki bai bani wanan damarba, amma araina naji ina sonsa ina kuma fatan ya zama mijinki, kada kiyi la'akari da talaucinsa kiyi la'akari da halayyarsa na tabbata shi kaɗai ne mutumin da zai soki ya riqeki tsakaninsa da Allah, ki roqi zaɓin Allah sai ki jira Ikonsa akan ki, na tabbata lokaci zai zo da zaki fahimci ni da abin da yake qasan raina, kada ki min bahaguwar Fassara." ta qarasa maganar tana zubar qwalla tuno abubuwa da yawa acikin rayuwarta data ahalinta wanda lokaci ɗaya suka shuɗe kamar sauqar ruwa da ɗaukewarsa, shekaru 25 kenan tana cikin alhini da kaɗaici aduniyar da babu wanda zata kalla tace nata ne sai Ƙhaleesat ɗin da ta zama kyauta agareta wanda har ta fidda rai da samunta. Rungumeta Khaleesat tayi tana zubar qwalla azuciyarta take tunanin rayuwar Maa da ta sha bam-bam data Dadynta alokuta masu yawa tanaga girman qaddarar data zaunar dasu a inuwa ɗaya har xuwa wanan lokacin.


******

Shuru ne ya cika ɗakin taron baka jin qaran komi sai na fanka da na'urar sanyaya waje (AC) duk da yawaitar mutane awajan amma kuma hakan bai basu damar yin maganaba, jefi-jefi sukan duba agogon da yake saqale ajikin hannayensu, dai-dai lokacin aka turo qofa aka shigo cikin takunsa wanda yake nuna jarumta da nutsuwa atare dashi, sanye yake cikin riga kalar sararin samaniya sai baqin wando da takalmi baqi sau ciki, hannayensa saqale da agogon fata baqi, ɗan risinawa yayi cikin muryarsa mai sanyi "Kuyi haquri akan rashin zuwana akan lokaci." kai suka jinjina cikin gamsuwa da maganar tasa duk da ba wani bayani yayiba, amma nutsuwarsa ta burgesu sosai, da hannu ɗaya daga cikin ma'aikatan ya masa nuni akan kujerar da zauna, zama yayi yana fuskantar kujerar da take fuskantar kowa wanda da alama mammalakin kamfanin ke zaune acikinta.

"Jama'a Assalama alaikum" ya faɗa yana gyara agogon dake saqale akan fiskarsa, cikin haɗuwar baki suka amsa "Wa alaikumussalam wa rahmatullah"

"Agurguje duba da lokacin da muka ɓata ina yima baqinmu maraba da shigowa wanan kamfani namu mai albarka, da fatan zamu haɗa kai mu gudanar da aikinmu cikin amana d jajurcewa da gaskiya, sanan wani Ishu mai girma dan gane da aikin da zamu faɗa shine sarrafuwar sabuwar qira ta wayar zamani wanda babu irinta, ina fatan acikin baqin da muke dasu akwai mai wanan fasahar atare da shi?"

Shuru ne ya cika waje ayayin da aka fara kallon-kallo tsakanin tsofin ma'aikata da sabin da basu wuce su biyuba, ganin shurun yayi yawa yasa shi miqewa tsaye ya fara jawabi cikin tausasawar murya "Duk da kasancewa wanan shine abu na farko da xan farayi, to kafin mu shiga gundarin aikin ya kamata mu cire tsoro da shakkar da take zukatanmu dan na lura sune abun da suka cika zukatanmu, daga yanzu zamu faɗa aiki ne ta amfani da na'ura mai qwaqwalwa (system) akwai wani tsare-tsaren da zamu saka musu matakan tsaro saboda waɗanda suke da son zuciya, ku yarda dani akan wanan aikin in sha Allah zanyi qoqarin ganin ya kammala acikin mako guda."

Kallonsa sukayi da mamaki duba da wahlar da take cikin aikin ta ya zai iya gamashi acikin mako guda ko dai baiji abin da aka faɗaba, gaza shuru Alh. Naseer yayi "Kaji abun dana faɗa kuwa Abdallah? Ina magana akan sabon qira na wayar tafi da gidanka da zamuyi, duk da bamu da ishasshen lokaci saboda mutanen da suka bamu kwangilar amma akwai sa rai nan da wata ɗaya zasu iya ɗaga mana qafa."

Kai ya jinjina yana murmushi wanda ya zama ɗabi'arsa ga su kuma da ya zama baqo awajansu hakan sai ya qayatar da su "Naji Yallaɓai kawai ina buqatar kayan aiki da mutanen daka yarda dasu guda uku dan haɗaka acikin wanan aikin."

Kai ya jinjina yana son ganin qwazonsa akan wanan aikin "Zan baka mutane biyar saboda sauqaqa aikin ya tafi akan lokaci."

"Na gode" ya faɗa yana risinawa, daga haka aka rufe taron da kuma bada umarnin Abdallah ya tsaya.

Bayan ficewar kowa ga rage Abdallah da Alh. Naseer ne awajan anan ne ta fara masa bayani akan yanda aikin zai tafi da mutanen daya wara masa amatsayin mataimakansa, sosai yaji daɗin bayanin na Abdallah haka yaji soyayyarsa acikin zuciyarsa duk da kasancewar wanan ce rana ta farko da zuwansa, amma nutsuwar yaron ta kwanta masa, hakan yasa ya bashi yadda akan aikin, tashi yayi tsaye "Zo muje na kaika ɗakin da zakuyi aikin." daga haka ya fita Abdallah na take masa baya, wani qaton office ya kaishi mai na'ura kala-kala acikinsa ga kujeru da tarin littatafai awajan, nuni ya masa da wani wata kujera "Ina fatan nan yayi maka?"

Kai Abdallah ya gyaɗa yana qarewa wajan kallo tsaruwar ɗakin kansa abin burgewace ga wani ni'imataccan sanyi da yake ratsa ko ina na jikinsa.

Juyawa yayi yana bashi tabbacin zai turo masa da ma'aikatan da zasuyi haɗaka awajan aikin sai ya zauna ya fara da abin da yakega zai iya."

  Zagaya ɗakin yake yana kallon komi da yake akillace aɗakin abun ya qayatar dashi ya kuma burgeshi sosai da sosai. Hamdala yayi yana godiya ga Allah haɗe da neman Allah ya bashi ikon yin aikin da aka sashi.

Wayarsa ce ta ɗauki qara alamun ana kiransa, ɗago wayar yayi yana duba wanda yake kiran nasa, sunan Khaleesat da ya gani ya sashi murmushi yana girgiza kai, amma bashi da alamun ɗaukan kiran har ya yanke, wata zuciyar na gwaɓarsa akan rashin kƴautuwar qin ɗaukan kiran, sai dai yana fatan ace ta sake kiransa amma shuru babu alamun wani kiran zai shigo har tsawon muntuna biyar, dole ya danna kiranta sai dai har tayi qara ta yanke bata ɗaukaba, ya kuma sake kira har sau 5 amma sai dai ta gama qara ba aɗukaba, kai ya girgiza yana murmushi "Gidan rigima kenan, qila tayi fushi." kafin ya rufe baki saqo ya shigo da sunanta cikin sauri ya buɗe saqon dan ganin abin da aka rubuta _"Kalmomin magana yawa garesu, idan an fara bata yankewa badan an qayyadai yawaitar yanda za'ayiba, sai dan zuwanta alokuta mabambanta. Ina tayaka murnar samun dama da matsayi zama mutum na musamman, kayi qoqarin ganin mudubi ayau ka kalli abun da ya kamata ka samu amsarsa da kanka."_ karanta saqon yake yana mai-maitawa amma kuma ya gaza fahimtar abin da saqon ya qunsa, da kuma manufar saqon, mi ya haɗashi da kallon mudubi kuma? Wata tambaya yake da ita daya rasa amsarta? Kai ya dafe yana son hasko kalmomin duk da ba abu ne mai wahla awajansa ba amma yau gashi ta bada shi.

Dai-dai lokacin kuma mutane biyar suka shigo da bashi shedar su ɗin mataimakansa ne, dole ya wartsake ya durafafi aikin da yake gabansa ba dan ya samu matsaya akan saqon Khaleesat ba sai dan yin abin da ya ɗauki alhakin yinsa ba tare da an sashiba, sai dan yanaga baiwar da yake da ita da taimakon mutumin da yakega kamar Ahalinsa ne, musamman karaya da raunin daya fara cin karo da shi akan fuskarsa.

🥀🥀🥀🥀🥀🥀©by UM NASS

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI 🎊*


©by *😘Um Nass 🏇🏼*


_Ina mutqar godiya da Addu'o'inku, Alhmdlh munji sauqi sosai nida yarona, Ngd sosai da kulawarku Rabbi yabar Kauna saboda shi._


*Wanan shafin sadaukarwa ne gareku Sadiya Jegal (Talauci ba madogara bane) da maman saddiqa (Er uwata jinin jikina) ngd sosai da kulawarku da qaunar labarin Haɗin Gwarmai, sosai nake yinku.*

   

Page 55


 Wajan ne yaci gaba da kaurewa da hayaniyar mutane wanda mafiya yawa sun cika ne da mamakin Abdallah dan da fari sunyi tsamannin yayan Khaleesat ɗin ne, to amma kamar da take tare da su babu shakka ɗan uwanta ne na jini, ɓangaran masu hotuna kuma suna ta aikinsu sai faman ɗaukansa suke shida Khaleesat, ayayin data kafeshi da ido ta kuma cika da mamaki, kai ta girgiza tana murmushi sanan taja hannunsa zuwa gun yanka cake ɗin, daga nan hankalin mutane ya iyo kansu suka rufar musu baya suna bama idanuwansu abinci. Cake ɗin ta yanka ta fara baza idanuwanta tsakanin Dadynta da Maa, sai dai ganin yanayin Dady ya so tsoratar da ita kawai dariyar yaqe yake yana faman goge gumi agoshinsa, murmushi tayi ta ɗauko cake ɗin da ta yanka ta sama Abdallah Abakinsa, anan wajan ya ɗauki sowa da tafi, saɓanin Dady daya qame ya kuma cika da mamaki da takaici, _Mi hakan yake nufi?_ tambayar da yake son yima Khaleesat amma kuma maganarta ta dawo dashi daga duniyar tunanin daya faɗa "Amatsayin Yayana ɗaya tilo aduniya na ciyar da shi wanan cake ɗin, bakwa buqatar wata amsa daga garemu idan kukayi la'akari da kamar dake tsakanina da shi." Murmushi tayi ta juya tana kallon Maa wanda tayi mutuwar tsaye jin maganar ɗiyar tata, shima Abdallah awanan lokacin qirjinsa na harbawa da sauri da sauri, ci gaba tayi da magana cikin nutsuwa da murya mai sanyi "Shi jinina ne nan da wani lokaci kaɗan xaku sake halattar taron bikinmu." mamaki ne ya kusan kashe Dady da yake wajan, ta ko ina ji yake gumi na zuba ajikinsa, musamman da yake kallon Abdallah da Khaleesat ajere babu abin daya babanta kamanninsu idan aka ɗauke hasken fatar da zata nuna masa, sai tsayin daya fita da shi kasancewarsa namiji, kai ya dafe yana kiran "Hasbunallahu wani imal wakil" ya akayi awancan lokacin bai gano kamanninsa da itaba, kallonsa ya kai ga Maa wanda hawaye yake zuba acikin idanuwanta tana goge ganin mutane awajan, ahankali ta sirare tabar wajan, dai-dai lokacin da yake qoqarin binta yaji an dafa kafaɗarsa cikin hautsinannan yanayi ya juyo, ganin wanda ya dafashin yasashi sauqe ajiyar zuciya da murmushi wanda bai kai zuciyaba "Ashe Abdallah shima yaron wajanka ne, na daɗe ina neman inda nasan yaron ashe kama yake min da ɗiyata Khaleesat, gaskiya ka more da ɗa mai hikima da basira ga hankali."

"Uhmm ba laifi." ya faɗa yana son wucewa.

"Baka tambayeni a ina nasanshi hakaba?" mutumin ya sake magana yana washe bakinsa yana dai-daita zaman glass ɗin dake idonsa.

"Ina jinka ai Alh. Naseer" ya faɗa yana aro dauriya da murmushi kasancewarsa mutum mai muhimmanci da kima a idonsa, kai ya jinjina yana murmushi "Shine sabon ma'aikacin da muka ɗauka akamfaninmu awanan shekarar, da taimakonsa ne muka farfaɗo daga barazanar da take nufo kamfaninmu, gaskiya ya samu ilimi mai kyau, yana da baiwa mai yawa atare da shi." kallonsa yake kamar yaga sabon mutum tun fara maganarsa, sanan ya kai kallonsa ga Abdallah wanda suke ta fira shida Khaleesat da sauran mutane suna dariya, murmushi shima yake yana kai kallonsa ga Alh. Naseer sai yanzu ya samu amsar tambayarsa, "Dama akamfaninku yake aiki ya samu kuɗi haka?"

Faɗaɗa murmushinsa Alh. Naseer yayi "Tabbas dan da ace nasan shi jininka ne sai na ninka masa yafi haka, amma kuma akwai abin da yake bani mamaki, taya yana matsayin ɗanka ya kasa samun aiki atare da kai sai ya fita ya nema awaje?"

Gabansa ne ya faɗi ya ɗauko dauriya ya fama jikinsa "Yana son yin amfani da baiwar da yake da ita ne." 

Kalmar daya faɗama Alh. Naseer kenan bai sake tsayawa yayi maganaba yayi gaba, yana tsoron wata tambayar da zata sake fitowa daga bakin Alh. Naseer ɗin.

 Cikin takunsa ya isah wajan MC ya karɓi abin magana ya yima mutane godiya akan halattar taron da sukayi ya kuma musu fatan alkhairi da sauqa guda lafiya, maganar qarshe data bawa mutane mamaki shine sheda musu Auren yaransa nan da lokaci qanqani da fatan sake haɗuwarsu alokaci guda.

 Anan ya bawa M.C bututun maganar yayi gaba yana yima Abdallah mgn akan idan ya gama suzo shida khaleesat su sameshi.

Abin da ya sasu bugawar zuciya da qirjinsu alokaci ɗaya. Sai dai ganin mutanen da suke zagaye da su ya sasu aro dauriya suka ci gaba da walwalarsu. Har aka gama kowa ya watse ya rage Abdallah da Khaleesat da suke tunanin samun Dady.

"Ka samo mana kalmar faɗa agaban Dady dan nikam ko wata magana tawa ta gudu." ta faɗa cikin sanyin muryarta kamar zatayi kuka.

 "Wanan abu mai sauqi ne ai muje kawai." ya faɗa yana murmushi sanan suka shiga palon da sallama abakinsu, babu wanda ya iya Amsa musu tsakanin Abu Khaleesat da Maa ɗin dan dukkaninsu sunyi zugum-zugum, waje suka samu suka zauna kamar marasa gaskiya, suka sunkuyar da kansu qasa. 

Shuru ne ya ratsa palon kamar babu wanzuwar mutane awajan "Ya mukayi da kai Abdallah awancan karon?" ya tsinkayi muryar Abu Khaleesat wanda ta faɗar masa da gaba.

"Kace ba zaka bawa talaka Auran erka ba."

"Umhmm." ya sake faɗa yana kafeshi da ido.

Murmushi yayi yana ɗago kansa yana kallon Abu Khaleesat ɗin "Ni kuma ba talaka bane Dady na sanar da kai tun awancan lokaci, haka kuma ayanzu ina tabbatar maka da samuwar aiki da rufin asiri wanda ya ishi ko wani bawa zama cikin kwanciyar hankali."

"Nawa ne Albashinka?" ya tambayeshi yana kallonsa shima.

Kai ya girgiza masa "Ban saniba." ya faɗa yana murmushi, kallonsa Abu Khaleesat yake cikin mamaki yana ganin tsagoran raina masa hankalin da amsar da yake bashi "Baka saniba kace."

Kai ya ɗaga yana murmushi "Zan iya faɗa maka qasa da abin da aka bani ko kuma wanda ya haura wanda aka bani, amma kuma idan nace soyayyarka zan nema zan faɗa maka abin da ya min azuciyata, ni kuma bana son faɗar dai-dai ko akasinsa, ataqaice komi yana buqatar sirri ne, kamar kai ne na tambayeka nawa ne kake samu aduk watan duniya kaga aciki akwai bin qwaqqwafi da son wuce iyakar da ba takaba."

Kai Abu Khaleesat ya jinjina yana murmushi alokacin Maa da ta qura masa ido take ganin ko wata kalma da magana da zaiyi kamar er uwarta, hatta maganarsa irinta Malam mahaifinsu ce.

"Abdallah ɗana" ta faɗa cikin sanyin murya da hawayen da ta gaza boyewa acikin idonsa, jin muryar kamar ta Umminsa yasa shi saurin juyawa yana kallonta "Ummie" ya faɗa yana son ganin abin da idanuwansa ya gane masa, ɗan Murtsuka idonsa yayi dan yasan ko giyar wake yasha bazaiga Ummie anan ba, itama kallonsa take da yanayin dataga ya shiga, tashi tayi taka shafa fuskarsa kamar makahon da yake laliben wani abu, shima kallonta yake yana son tuna wasu abubuwa amma ya gaza tunasu, da sauri ya miqe tsaye yana ja da baya da baya, so yake ya qaryata abun da idonsa yake gani, fuskar Ummiensa yake gani ata wanan matar, sam bai shirya ruɗar da kansaba.

"Dady nima ina sonsa." suka tsinkayi muryar Khaleesat wanda ta sauya ruɗanin da yake ciki, cak ya tsaya daga shirin barin palon da yake, juyowa yayi yana kallonta cikin mamaki, ta jinjina kai "Tun ranar dana fara ganinsa nake sonsa Dady, bazan iya rayuwa babu shiba." jin sauqar maganarta yake cikin ko wata gaɓa ta jikinsa ido ya runtse yayi ya buɗe yana kallonsu, _wanan Ahalin wanan gidan wanan matar akwai abun da yake tsakaninsu da shi, to amma minene, Umminsa ce amsar tambayarsa amma yasan bazata yarda da abin da ya faɗaba, mi yasa ta kirashi da Abdallah ɗanta? Mi yasa yake kama da ita da ɗiyarta? Wanan ba kamace kamar yanda yake tsammaniba dole akwai alaqa atsakaninsu. Akwai abin da Ummiensa ta manta bata faɗa musu ba ko ta ɓoye musu acikin labarinta._ Waɗan nan sune maganganun da yake yi acikin zuciyarsa, bai ce komiba ya juya da zummar barin palon sai dai akaro na biyu maganar Abu Khaleesat ta sake datse ko wani hanzari nasa "Abdallah ina son ganinka da Ahalinka gaba ɗaya agobe, ban kuma ware kowa acikinsu ba, ka kawo minsu agobe da safe, ban san mi zakayi ba amma ko baka kawosuba zansa aɗauko minsu." Juyawa yayi yana kallonsa yaga babu gizau ko rangwame akan fuskarsa, juyawa yayi tana kallon Khaleesat da mamanta wanda suma kallonsa suke, murmushi yayi ya gyaɗa kai "In sha Allah mutqar muna numfashi zamu zo, kai dai ka nemi ko wata mutuntaka taka da zaka basu, dan zan iya jure ko wani abu amma banda abun da zai sosa ran Ummienah." yana gama faɗar haka ya buɗe qofar ya juya fice, da ido suka bishi har ya turo musu qofar, sai alokacin Khaleesat ta miqe ta kalli mahaifan nata "Ba ko wani mai kuɗi bane ake kiransa mai Arziqi acikin talakawa akan samu da yawa masu Arziqi da bada rayuwarsu dan kare danginsu, bana son rayuwar da zanyita ba tare dana waiwayi bayanaba, bazan jure tafiya babu waiwaye acikintaba, ina son Abdallah amma bazan bari sonsa yasa acutar da shi da danginsaba, zan haqura dan naga ya rayu yana farin ciki, kada ka cutar da su Dady in dai baka sonsa atare dani, to zan haqura na barshi yayi rayuwarsa kamar ta baya."

Murmushi Dady yayi ya miqa mata hannu da gudu ta faɗa kanta yana bibbiga bayanta "Ba zan cutar da suba, zan bashi Aurenki ne, zan kuma samu amsar tambayar da nake nema atare da shi." 

"Da gaske Dady" ta faɗa tana murmushi da share hawayen daya zuba a idonta, hanci ta lakuce mata yana murmushi shima "Da gasken gaske ma."

Rungumeshi ta qara yi tana murmushi, shima murmushin yayi yana kai kallonsa ga Maa wanda tun tafiyar Abdallah take jin kamar an kafeta awajan, zuciyarta har yanzu lugude take, gani take gobe ta mata nisa kamar yanda Abu Khaleesat ta ce, amma kuma taga yaron yana ja da baya lokacin daya haɗa ido da ita, mi kenan? Kaddai yaka jin tsoronta ne? Dan taga ko ganin fuskarta baya sonyi, dalilin qoqarin fitarsa kenan.

Juyawa tayi tana kallon Khaleesat da Babanta wanda suke cike da nishaɗi basu da wata damuwa sukam, sai yanzu taga tayi ganganci ta kumayi wauta na barin damarta tun abaya, gashi ta kasa sauqe nauyin da yake kanta atsawon shekaru.

 Ɗaki ta shige tabarsu ba tare data musu maganaba, suma basu tanka mataba.


*******

Tun bayan barinsa gidan yake saqa da warwara yana ta tunanin ta inane zai fara, har yanzu fuskar mahaifiyar Khaleesat ke masa gizo, ahaka ya qarasa gida cikin sanyin jiki da fargaban abin da zai-zo-ya-je dan tabbas yasan idan har bai kai Iyayensa ba to Abu Khaleesat zai sa aɗauko masa su.

 Cikin sanyin jiki da murya yayi sallama ya shiga gidan lokacin duk suna zaune suna kallo apalo sai fira suke cike da nishaɗi da walwala, acikin kwana biyun da sukayi kowa ya gansu yasan hankalinsu akwance yake basu da wata damuwar da zata damesu balle hankalinsu ya tashi, ba aikin wahla sukeba iyaka su dafa abincin cikinsu suda yaransu, dan har mai musu shara da moping Abdallah ya kawo musu.

Kallonsa sukayi suka amsa atare, xama yayi dai-dai lokacin Arfat ya shigo yana kiran "Washh" ya miqe akan kujera yana kallon Abdallah "Yanzu dawowarka amma?"

Kai ya gyaɗa masa yana murmushi "Ya kasuwar?" 

"Alhamdulillah, ammafa babu hutu akwai hayaniya. Ya faɗa yana dariya suma su Ummi suka sa masa dariya "Yo ba gara kasuwar kana zaune ɗam ba, da fa da sai qaran injina da motoci, ga baqar fuska da mutum yake." Mama Anta ta faɗa tana dariya itama, aifa nan suka saka musu dariyar gaba ɗaya "Aikuwa gashi yanzu har tumbi ya fara haɗawa saɓanin da da yake ɗauke ciki saboda shiga qarqashin mota." Abdallah ya faɗa cikin sigar zolaya nan Arfat ya miqe yana shafa cikinsa "Haba dai idonka bai gani malam, Umminah wai cikina ya qaru."

Kai ta girgiza tana gimtse dariyar data ke shirin fitowa "A'a cikinka a shafe yake sam babu tudu."

"yauwa dama ke ce mai ido mai kyau agidan nan." nan suka sa dariya suka ci gaba da hirarsu yayin da Abdallah yayi shuru ya faɗa duniyar tunani.

"Ɗana mi yake damunka?" Mama Anta ta faɗa tana dafa kafaɗarsa, kai yayi saurin ɗagowa yana kallonsu kafin ya sunkuyar da kai qasa ganin sun kafeshi da ido.

"Ba komi Mama"

"Ban yarda ba, karka sa su mana dariya kaga suna kallonmu."

Kai ya fara sosawa yana murmushi "kawai dai, kawaifa..." sai kuma yayi shuru, itama murmushin tayi tana kiran "Wace yarinya ce?"

Saurin ɗagowa yayi yana kallonta, kai ta gyaɗa masa tana murmushi "Nasan maganar ba zata wuce akan mace bane, shine nake tambaya a ina iyayenta suke."

"Gidan gobnati, mahaifinta ne yace yana son ganin kowa nawa agobe." kai ta jinjina tana kallon Umminsa da tayi shuru tana kallonsu. Kamar ba zatayi maganaba can ta nisa tace "Ka tabbata acan ne? Kuma mahaifanta sun yarda ka tura iyayenka?"

Kai ya gyaɗa yana sunkuyar da kai qasa "Tabbas Babanta ne yace muje da duka ƴan gidanmu."

Numfashi taja sanan ta furta"To Allah ya kaimu goben, ai sai mu je." ajiyar zuciya ya sauqe yana murmushi yana yima Mama Anta godiya sanan ya ruga ɗaki da gudu, sai Arfat da ya bi bayansa cikin mamakin maganar tasa.

"Taya yane zamu nema masa Aure awanan lokacin? Kin san dai mace bata neman Aure ko?" Ummi ta faɗa cikin sanyin murya tana share hawayen kan fuskarta, kai ta jinjina sanan tace "Na sani, amma baki ji en gidansu ake son ganiba, muje muji abun da yake wakana, idan akwai yiyuwar auren sai muje mu roqi kawun Arfat yaje masa neman auren."

Kai ta jinjina sai yanzu hankalinta ya kwanta "To Allah ya kaimu goben."

"Ki kwantar da Hankalinki In sha Allah komi zaizo da sauqi Um Abdallah." murmushi tayi ta girgixa kai, ita kaɗai tasan mi take ji azuciyarta.


*****

"Mi kunnuwana suka jiye min Abdallah? Ba dai gidan govnor kaje neman Aureba?" Arfat yayi maganar cikin kaɗuwa da tashin hankali.

Kai Abdallah ya gyaɗa yana murmushi "Kuma har ta amince tana sonaba, dalilin da yasa Mahaifinta yace muzo gobe kenan."

"Kaiii" Arfat ya faɗa cikin qaraji da kaɗuwa, ruqo hannunsa Abdallah yayi "Ka yarda dani Arfat ba zan kaiku inda za'a cutar da kuba, akwai ruɗani da abun mamaki wanda nake son samun Amsarsa agoben." 

"Kamar yaya kenan?" Arfat ya tambayeshi cikin mamaki, juya masa baya yayi yana qoqarin shiga toilet "Idan munje zaka ganema idonka abin da na gani." daga haka ya shige yabar shi anan baki buɗe cike da mamakin qarfin halin Abdallah.


*****

Tafiya suke babu wanda yake magana sai dai wani wajen idan sunzo Mama Anta takan sanar da Ummi sunayensu, ahaka har suka qaraso gidan gobnati, wanda tun dosar wajan gaban Ummie ya fara bugawa da qarfi-qarfi har saida ta dafe qirjin nata tana nanata "Hasbunallahu wa ni'imal wakil." da kuma "Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un" sune kalmar da take ta nanatawa amma har wanan lokacin babu abin da ta sauya, gidan da yafi ko wanne sukaga sun shige haka duk inda ma'aikatan suka fara dubawa da sunga Abdallah ke tuqa motar sai su fara gaidashi, lamarin daya bawa Arfat da Mama Anta mamaki kenan, musamman Arfat da yasan ko yaushe suna tare d Abdallah ɗin, gidan da yafi ko wanne girma da matakan tsaro nan suka nufa "Abdallah ina kake son muje ne? Da kace gidan gobnati na ɗauka na qananan masu matsayi ne, ammafa nan kamar gidan govnor kake kaimu?" kai ya gyaɗa yana murmushi "Nan ne Mama."

Salati ta fara rafkawa ita ba abin tace su juyaba dan gashi sun zo har gidan, Ummie da take jinsu bata ce komiba sai murmushi da tayi tace "Allah yasa ba duka zakusha ke da ɗan nakiba, dan ko ana tambaya cewa zanyi ban sanshiba."

Dariya Arfat ya saka sanan yace "Balle kuma ni Ummie sai mu tashi a en rakiya ne mu."

"qwarai ɗana" ta faɗa tana murmushi wanda har xuwa yanzu qirjinta bai bar bugawa da qarfiba.

"In sha Allahu Alkhairi ne ya kawomu." dai-dai lokacin da yayi farkin ɗin motarsa awajan Adana motocin yana murmushi "ku fito muje"

Fitowa sukayi suna kallon ko ina na gidan, kai suke jijinawa suna ganin duniya a inda take, lallai wasu basu da matsala adai wanan duniyar.

Har cikin palon suka shiga kai tsaye saboda ansan da zuwansu bakinsu qunshe da sallama, babu kowa apalon sai masu aiki suna kaiwa da kawowa, da kallo Ummie da Mama Anta suka bi ko ina na palon "Masha Allah" Ummie ta faɗa tana yima kanta masauqi akan manyan kujerun dake palon kallonta ta kai ga hoton Khaleesat wanda yake maqale ajikin bangon ɗakin, gabanta ne ya qara bugawa da qarfi tana sake kallon hoton, "Abdallah wanan fa?" ta faɗa tana nuna hoton, alokacin idanuwan Mama Anta da Arfat yakai kan hoton, suma suna kallon Ummie "Kamar ke amma wanan ta fiki quruciya." Mama Anta ta faɗa tana mamaki, kai Arfat ya girgixa yana murnushi "Itace surukar takufa, kama ce kawai da ake cewa kowa nada mai kamarsa."

Kai Ummie ta girgixa tana murmushi gefe ɗaya qirjinta na bugawa ta sunkuyar da kanta dai-dai lokacin da suke jin takun tafiya yana tunkarosu, bata ɗagoba har saida takun ya taqaita.

"Kuyi haquri mun barku azaune shuru ku kaɗai." taji wata muryar da ko amafarkinta ba xata taɓa manta wanan sautinba, kafin tayi wani yunquri ta sake jin magana "Abdallah ya naganku ku kaɗai? Kai da nace har mahaifanka, banga namiji babba ba ko ɗaya?"

Dai-dai lokacin Ummie ta ɗago da fuskarta tana jiyowa inda sautin muryar yake fitowa, sai akayi dace shima awanan lokacin yakai kallonsa ga ita "AADA" Mamaki da Al'ajabi suka dirar musu alokaci ɗaya "HAAJARA" Ya faɗa yana murza idanuwansa yana kai kallonsa ga Ummie da Abdallah.

Adai-dai lokacin ne Khaleesat da Maa suka qaraso palon amma ganinsu atsaye cirko-cirko yasata kai kallonta ga mutanen palon, Mutuwar tsaye tayi kafin wani lokacin ta yanke jiki ta faɗi qasa." da sauri sukayi kanta banda Haajara data juya bayanta, komi yana dawo mata kamar yanzu ne rayuwarta ta fara.

Bata san mi suka yiba sai tsintar maganarta tayi akusa da ita "Dan Allah Karku ce min mafarki nake, kada na farka daga kyakkyawan yanayin nan, kamar er uwata Hajarko nakega agabana, kuce dani gaske ne Hajarko ke nake gani ko idona ne yake min gizo."

Murmushi Ummie tayi tana kallon Yayar tata da babu abin da ya sauya arayuwarta sai hutu da jin daɗi ga wata haiba da nagarta data qara samu, kallon ko ina na jikinta take da gwala-gwalai da tufafu na keta raini ko ina ta wuce ansan mace ta wuce mai ji da kanta. "Ni kike gani agabanki Adda Sa'adah, nice ban mutuba." sanan takai kallonta ga Abdallah "Ina fatan ba nan ne gidan yarinyar da kake neman Aurentaba? Ina fatan waɗan nan basu ne iyayen yarinyar da ka kawo mu neman Aurentaba?"

Kai yake girgizawa cikin sarqewar murya yace "Nan ne gidan, sune kuma iyayenta."

Miqewa tayi tsaye tayi "Ka gaggauta cireta aranka, ka goge komi nata daga cikin rayuwarka, koda ace ku kaɗai ne kuka rage awanan duniyar na haramta maka aurenta har abada bazaka taɓa aurenta ba, koda ace xaka mutu ne akanta, to xan ɗauki qaddarar binneka acikin kabari akan ka aureta." kowa awajan kallonta yake cikin mamaki sanan ta qarasa kusa da Khaleesat wanda tuni hawaye ya wanke fuskarta "Kiyi haquri erta ba qinki nakeba har azuciyata naji ina kaunarki tun dana kalleki nasan ke jinina ce, akwai duhuwa wanda tafi qarfin ido ya ganta balle ya kamata atsakanina da mahaifanki, wanan dalilin yasa bazan taɓa yarda wata alaqa ta haɗamu da iyayenkiba koda ta zama a inuwa guda ne, balle kuma aje kan batun Aure." tana qarasa faɗar haka ta juya kallonta ga Mama Anta wanda ta riga data fahimci komi bata kuma buqatar qari, miqewa tsaye sukayi suka fita apalon ba tare da sun ce komiba "HAAJARA KARKI TAFI KI BARNI DAN ALLAH KI TSAYA KI SAURARENI." Maa ta faɗa tana hawaye sosai banda Aada da ya kasa kataɓus dan ko ina ajikinsa gumi yake "Lokaci ya qure Addah sa'adatu, ayanzu bani da wani wanda zan kalla aduniyata nace nawa ne idan kika ɗauke waɗan nan mutane biyun, bani kuma da kunnuwan da zan jiyoki balle sautin da zai fito abakinki."

Cikin sarqewar murya ta fara magana "Ni ni nicefa Addarki sa'adatu."

Juyowa tayi tana kallonta sanan ta ɗora da murmushi "Waccan Addar tawa ta mutu alokacin da iyayena suka rasu, wanan sabuwa ce wanda Aada ya sabunta ta acikin duniyarsa, ya kareta daga faɗawa mugunyar mutane da raɓuwar Annoba atare da ita, na ɗauka ya mantar da kee sauran abubuwan da suka danganci ahalinki." tana qarasa faɗar haka ta ja qofar ta rufe da qarfi da gudu-gudu ta qarasa wajan motar "Arfat karɓi ka jamu da sauri, bana qaunar kallin wanan gidan." cikin sauri ya karɓi mukullin ya bawa motar wuta Da gudu Maa ta fito tana kiransu amma basu tsayaba umarni take bawa mai gadi amma bai san mi taceba sai qofar daya buɗe yana ɗaga musu hannu da fatan sauqa lafiya, ɗurqushewa tayi awajan tana gunjin kuka da buga hannayenta aqasa......


  


🥀🥀🥀🥀🥀🥀


_ 😥Ya Rabbi! Yaufa Maa ta sani zubar da hawaye, amma kunga laifin Haajara? Ban san ya kukaji akan wanan chapterba amma dai nikam ......._


©by Um Nass

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI 🎊*


©by *😘Um Nass🏇*


 *_Ba ko wata kyauta bace take da qayatarwa, sai dai idan akayi la'akari da girman zuciyar mutum hakan ya wadaceka, Na baki wanan shafin mai cike da Armashi ina kuma tayaki murnar qara shekarar haihuwarki qawata! er uwata! REAL MAI DAMBU CE, Sosai nake yinki ina kuma fatan zamuncinmu ya ɗore har gaba da Abadan_*


Page 54


  

 Bayani yayi musu akan yanda aikin nasu zai fara, daga nan suka duqufa kowa da abin da yakeyi basa hutu ko kaɗan sai Sallah da cin Abinci ne yake tsaidasu, haka idan lokacin tashi yayi sauran sukan tafi subar Abdallah yana ta abu ɗaƴa, lamarin da yake bawa sauran ma'aikatan mamaki kenan idan sukayi la'akari da kasancewarsa baqo, amma kuma sai gashi yana sadaukar da lokacinsa akan abun da ba shi da wata riba akansu, amsa ɗaya yake basu "Da naka da na wani duka abu guda ne, nasarar da za'a kira takace bata da wani armashi amma idan akace ta zama taku zakuyi dariya kuyi murna atare wanda hakan zai qayatar ya kuma bada Armashi." duk lokacin da yayi wanan maganar sukan ɗauke shi wani mutum daban awanan duniyar.


Bayan kwana Huɗu:


Kowa ka gani awajan yayi tsumu-tsumu kamar tsimman da ya kwana cikin randa, haka sun kewayeshi suna fatan ace nasarar da suke ta dakonta yau ta bayyana, gefe guda kuma Alh. Naseer ne ya rufe idonuwansa gumi ta ko ina na sartu ajikinsa kamar wanda sukayi tseren gudu.

Hankalinsa ne ya qara tashi ganin Abdallah ya dakata daga danna na'urar mai qwaqwalwar da yake, cikin rashin kuzari ya juyo da fuskarsa ga kallon ɗaukacin ma'aikatan kamfanin, kai ya girgiza wanda yasasu saurin sandarewa tuni cikin Alh. Naseer ya fara barazanar juyawa _"Shikenan duk wani sa rai da nake da shi ayanzu ya dawo sufuli, babu kuma wani abun da zai gifta da xai sauya min qaddarata."_ acikin zuciyarsa yake maganar yana qoqarin barin wajan, sai dai kafin ya kai ga hakan Abdallah ya juyo musu da fuskar Na'urar "Alhmdulillah munyi nasara aiki ya kammalu." kamar sauqar qanqara haka yaji maganar Abdallah acikin ransa nan take fuskarsa ta washe daga qunci zuwa dariya, tsugunnawa yayi ya fara jero sujjadar shukhriyy har sai da aka riqeshi ayayin da wajan ya kaure da ihun murnar ma'aikatan, cikin bazata suka ɗaga Abdallah sama suna murna wanda shima sai dariyar yake yana jin daɗin ganin farin ciki azukatan mutane, kuma wai shine Sila wani daɗi ne yafi wanan? Gaskiya babu shi.

Can bayan hayaniya ta nutsa Alh. Naseer ya qira masu aikin ya sanar dasu kammaluwar aikin nasu, cikin abin da baifi mintuna talatinba sai gasu sunzo, fuskokinsu a tsuke dan sunyi tsammanin ko qarya ya musu, sanin babu wani mai qwazo da har zaiyi wanan aikin cikin mako guda da yin yarjejeniya atsakaninsu, dan haka suka zo da shirin ta kwana ko kuɗinsu ko aikinsu.

 Murmushi Alh. Naseer yayi ganin yanda suka zo fuskokinsu gam kamar an aiko musu da labarin mutuwar danginsu, waje ya nuna musu akan su zauna, "Ba zama muka zoba Alh. Naseer, kawai ka nuna mana aikin da kayi, dan bamu da lokacin ɓatawa, wanda muka ɓata abayama ya isa."

Kai ya jinjina yana murmushi da hannu yayima Abdallah nuni, nan take ya fara nuna musu aikin da sukayi, ai tuni mutanen suka samu wajen zama fuskokinsu qunshe da fara'a suna jinjimama qwazon kamfanin nasu, har ya kai qarshen bayanin nasa, saboda daɗi ɗaya daga cikinsu ya rungume Abdallah yana shafa kansa gami da murmushi "Tabbas ban taɓa hasashen yiyuwar wanan aikinba, idan nayi la'akari da wahlarsa awajanmu, amma kuma abin mamaki sai gashi ya iyu fiye da tsammaninmu."

Nan take ya janyo na'urarsa ya fara daddanawa abin da bai gaza muntuna biyarba wayar Alh. Naseer ta ɗauki qaran shugowar saqo, dubawa yayi sai dai cikin kaɗuwa ya sake ɗago kansa yana duba mutanen da suke wajan, yana kuma kai kallonsa ga wayar dake hannunsa, murmushi yayi yana miqewa da dafa kafaɗar Alh. Naseer "Wanan shine tukuicin aikin da ka mana, gaskiyar mutum takan sa ya taka matsayi mai yawa acikin rayuwarsa, muna son hulɗa da mutane masu Amana Alh. Naseer"

Yana qarasa faɗa yayi ma ƴan uwansa inkiya akan su tafi, kasa motsi Alh. Naseer yayi har saida suka tafi bai sake yin maganaba, sai Abdallah da ya matso kusa da shi ganin kamar ya shiga ruɗani "Lafiya yallaɓe." firgigi yayi ya miqawa Abdallah wayar da ke hannunsa, ido shimq ya qalalo waje ganin Alert har na Biliyoyin kuɗi akan ɗan wanan aikin, ya faɗa yana sake nazaratar kuɗin yana kuma tsammanin ko idonsa ne yake masa gizo "Waɗan nan mutanen anya lafiyarsu kuwa yallaɓai? Kaga wanan maqudan kuɗin akan wanan ɗan aikin."

Miqewa tsaye Alh. Naseer yayi ya rungume Abdallah tsam yana sauqe ajiyar zuciya tsawon muntuna biyar suka shuɗe sanan ya sakeshi yana kallonsa sanan yayi murmushi "Kai ne kake ganinsa qaramin abu, saboda kana da baiwar da ta zarta aiki irin wanan, amma awajanmu da su gagarumin aiki ne wanda har mun fidda tsamani akan yiyuwarsa, haqiqa kai kyauta ne daga Allah wanda ya bamu kai alokacin da muka yanke qauna da sake damawa acikin duniyar ɗaukaka, gashi da aiki ɗaya ka dawo mana da martabar mu da kimar da ke tare da kamfanin nan, nagode sosai Abdallah."

Sanan ya danna na'ura alamun kira akan taro na gaggawa, nan manyan ma'aikata dama qananan ma'aikatan suka fara dafifin zuwa ɗakin taro,. Fuskarsu qunshe da fara'a dan sunsan yau ranar farin cikinsu ce. Bayan hayaniya ta lafa kowa ya samu wajan xama Alh. Naseer ya miqe yana farawa da godiya da kuma jinjunawa ma'aikatan nasa waɗanda basu juya masa bayaba lokacin da kamfaninsu ke barazanar daqushewa, haka kuma ya yabawa Saleem amatsayinsa na ja gaba wajan bada shawarar ɗiban ma'aikata, sanan ya ganganar kan matakin nasara da yabawa Abdallah wanda yake amatsayin baqo acikinsu, gashi ya basu qwarin gwuiwa, ataqaice yace Abdallah yayi jawabi, miqewa yayi yana kallon ma'aikatan da fuskokinsu ke ɗauke da murmushi akan fuskokinsu farin cikinsu ya gaza ɓoyiwa awanan lokacin, shima nasa abayyane yake duk da ba abune sabo akan fuskarsaba yawaitar murmushi, da sallama ya fara suka amsa amsa sanan ya ɗora da jawabi ataqaice "Ba wani abu zance mai yawaba, face abun da ya zama jiki acikin rayuwarmu, duk lokacin da mutum ya janyo hannunka akan ka shigo inuwarsa to kamar ya ɗauki rayuwarsa ya damqa amanarka ne acikin rayuwarsa, kayi farin ciki kai ɗaya hakan ba wani sabon abu bane awajan kowa, amma idan ka kira mutane ka jiyar dasu wanan daɗin koda kai ba zakayiba, to zaka samu nutsuwar zuciya, idan muka cire son kai acikin zukatanmu zamuyi rayuwa ne kwatankwacin yanda tsuntsu ke rayuwarsa, yana wayar gari bashi da komi agidansa amma idan ya tashi zai samu abincin da zai wadaceshi shi da iyalansa, na gode sosai." ya samu waje ya zauna, anan aka shiga tafa masa kalamansa sun taɓa zuciyar mutanen da suke wajan haka da yawa sunji soyayyarsa na shiga zuciyarsa, ba kowa keda zuciya irin tasaba.

 Daga haka taro ya tashi da alqawartawa ko wani ma'aikaci karɓan Alabashinsa agobe da kuma qarin ihsani na abun da suka samu awanan lokacin. Nan farin cikin mutanen ya qaru da dan da yawansu dama abincinsu ya fara qarewa, kowa fuskarsa qunshe da farin ciki mai yawa yana godewa Abdallah akan canjin Alkhairin da yazo musu da shi.

 Bayan watsewar mutanen ya rage daga Alh. Naseer sai manyan ma'aikatan kamfanin, sai ya shiga tambayarsu Adadin kuɗin da zasu bawa ma'aikatan nasu, da yawa cewa suke abasu kashi ashirin acikin abin da ake basu abaya, kai ya jinjina sanan ya juyar da tambayar ga Abdallah akan nawa ya kamata abawa ma'aikatan, cikin jin qwarin gwuiwa ya ce "Yallaɓai inaga ko wani ma'aikaci aninka masa akan abin da yake ɗauka abaya, na tabbata hakan zai sasu farin ciki, idan kayi la'akari da yanda suka jajurce tsawon lokaci ba tare da sun nuna qosawa ko gajiyawaba."

"Tabbas hakan shine yafi dacewa, gobe in sha Allah ina buqatar ganin halartar mutane da wuri saboda afara musu albashi, akan lokaci."

Daga haka taron ya watse da yawa acikin manyan ma'aikatan suma suna murna lallai gobe akwai wasshagare walle.

 Cikin abin da bai gaza kwanaki ukuba aka gama biyan ma'aikatan kamfanin kowa ya cika da farin ciki da mamakin abin daya samu na Albashi wanda basuyi tsammaninsa ba, wasu daga cikin masinjojin kamfanin harda hawayensu wanda da alama na farin ciki ne.

Sanan aɓangaran Abdallah ma hakan take musamman lokacin da Alh. Naseer ya miqa masa takaddu da mukullaye ɗauke da sunansa, takardar farko ta gidace danqarare dake Ɗorayi sai Mota BMW ga kuma zunzurutun ƙuɗi Naira Million 5 mallakinsa, kai ya fara girgizawa yana bazai karɓaba shi sun masa yawa, sai dai kalmar da Alh. Naseer ya faɗa yasashi tilas ya karɓa "Amatsayin ɗan uwana na ɗaukeka Abdallah, ayau idan zanyi alfahari da dukiyar dana samu to na tabbata zaka zama mutum na farko da zan kira da Silar samuwarta, dariya ya kamata muyi atare ba wai mu raba damuwaba, komi nada iyakarsa." Wanan furucin ya karyar da xuciyar Abdallah _"Ashe akwai mutane irin su Alh. Naseer awanan duniyar? Tabbas ko wani abu yaka da iyakar zagayawarsa, wani abu yakega yana gilmawa acikin rayuwarsa wanda ya faru acan baya, amma kuma yana ganin abun kamar mafarki ne ga mai yin barci, gashi dai abin da baiyi tsammaniba yau shine ya mallakeshi, rungume Alh. Naseer yayi yana murmushi da hawaye karo na farko yayi hawayen farin ciki acikin rayuwarsa.


********

Duk inda ya gifta acikin unguwar binsa ake da kallo domin ganin sabuwar mota dall tama giftawa, abun ya zame musu sabo kuma baqo duk da an samu sanji naci gaba a unguwar, amma saboda yawaitar kwatoci da rashin kyan layin ba kowata mota ke shigowaba saifa taxi ko adai-daita sune sukafi qaurin suna ashigowa.

Kai tsaye yaja ya tsaya aqofar gidan Mama Anta wanda hakan yaja hankalin ƴan matan da suke fitowa daga ɗaukan karatu tsayawa, dan kallon mammalakin motar nan, koda bai kaiba amma sunaji ya taka matsayi babba, sai dai abun da yasasu sandarewa bayyanar Abdallah acikinta, ya fito fiskarsa qunshe da murmushi yana taku akan qafafuwansa cike da ƙasaitar da qarfafa takunsa akan sawayensa, sandarewa ƴan matan sukayi har saida ya shige gidan, kamar haɗin baki sukayi ajiyar zuciya alokaci guda "Ya rabbi inama ace wanan mutumin ya zama mallakin zuciyata, wallahi tun kafin yau nake jin ina sonsa, da ko wani furuci na maganarsa inajin kamar yana aza min qaunarsa ne." wata ƴar siririya ta faɗa tana warwarɓa dogayen hannunta.

"Uhmm lallai Zubaida ai da ganinsa kinsan ya wuce ajinki, ni kaina duk da ina sonsa bazanyi wanan gangancinba, gashi dai ta ko ina nafiki fasali da diri amatsayin ɗiya mace." wata uwar haarara ta watsa mata kafun ta ɗora da "Kan Uba amma Shema'u kin gama ci min fuska, ina kyan anan mace adunqule kamar curin tubali, gajartarki zai yaba ko bajajjan hancinki da ya gama cika fuskarki har idanuwanki suka nutse?"

Aifa nan sauran ƴan matan suka tuntsure da dariya ayayin da faɗa ya kaure tsakanin Shema'u da zubaida. Da qyar aka ɓanɓaresu.


******

Rawa take tana tattaki tana qara juyawa cikin farin ciki da jin daɗi ayayin da suka kafeta da ido suna murmushi da dariya. Abun akwai qayatarwa acikinsa duk da suna farin ciki amma nata na musamman ne, "Kai Allah Al'Hakimu mai rahma mai jin daɗi, haqiqa godiya ta tabbata ga Allah, oh ni faɗimatu ban taɓa jin daɗin daya wuce wananba."

Dariya suka qara saki sanan Abdallah ya matso kusa da ita "Tabbas godiya ta tabbata ga Allah Mama sanan daga gobe in sha Allah zamu tattara kayan buqatarmu mu koma sabon gida, babu saida abinci balle hayaniya."

"kai ta ɗago tana kallon Abdallah cikin rashin fahimtar maganarsa."

Kai ƴa gyaɗa yana jinjina mata "Zamu koma gidan da Alh. Naseer ya bani a ɗorayi nan sai musa haya, acikin kuɗin da aka bani na ware muku million ɗaya rabi keda Ummie sai kuna jujjuyawa, Arfat kuma na kama masa shago acikin kasuwar kwari ga Million Uku sai ya Zuba jari acikinsa, bana son zaman garejin nan nasa."

Gaba ɗaya tsayawa sukayi daga dariyar da suke suka qurawa Abdallah ido, kamar masu son jin abin da maganarsa ta qunsa, matsawa baya Mama Anta tayi "A'a Abdallah kar muyi haka da kai, wanan abune da bazai iya yiyuwaba, bazamu so kanmu mu rabaka da abun da ka mallakaba awanan lokacin." tana magana tana girgiza kai.

"Tabbas Abdallah ka sauya tunani har yaushe akayi daren da gari zai waye, gaskiya baxamu rabaka da Arziqinkaba, kai kuma ka zauna babu."

Kallonsu Ummie take tana mamakin maganganinsu kafin ta kalli Mama Anta fuskarta ɗauke da hawaye "Na ɗauka kin ɗaukeni tamkar Ƴar uwar da kuka fito ciki ɗaya atare? Na ɗauka kina kallon Abdallah amatsayin ɗan d kika haifa da cikinkI, ashe duka hasashe nake ba gaskiya bane, ban taɓa tsammanin son da kike nuna mana a iyaka fatar baki bane sai ayanzu, yau nayi hawaye na takaicin rashin ɗan uwan da zamu zauna mu raba farin ciki tare da shi, ashe kawai da damu ake zama ayi tarayya idan daɗi yazo sai ka zama ɗan tsako?"

Kallonta Mama Anta take tana girgiza kai "A'a Um Abdallah wlh har azuciyata ke ɗin ƴar uwata ce, kuma inama Abdallah soyayya kwatankwacin Arfat koma fiye da shi."

Hannu Ummie ta ɗaga cikin qarajin da bata taɓa yin irinsaba "Ba gaskiya bane Mman Arfat, kibar faɗar maganar da idanuwanki zasu qaryataki. Uhmm lokacin da kika ruqo hannayenmu kika zaunar damu qarqashin kulawarki ba tare da mun mallaki koda aniniba alokacin na girmamaki nake fatan Allah ya ara min dama koda guda ɗaya ce wanda xanga yawaitar murmushi acikin idanuwanki, nakanji inama ina da iko na sauqe miki duk wata wahla da faɗi tashin da kike akanmu dan kawai kiga munyi farin ciki, mun kuma mallaki komi kafin azo ana kiranmu da maqasqanta, yau gashi na samu wannan damar ina son saka miki duk da baxamu iya miki koda rabin abun da kika manaba, kin sa hannayenki kin ture wanan damar, tabbas baka da masaniya akan qaddararka wallahi da ba zamu zauna da ku acikin inuwa ɗaya ba." hannun Abdallah ta ruqo "Zo mu bar musu gidansu Abdallah, kafin yau ban taɓa ganin qiyayyar mu acikin idanuwansu ba amma furucinsu ya sanar damu kosu waye muke tare da su."

 Saurin shan gabansu Mama Anta da Arfat sukayi, ba tare da sunyi maganaba suka rungumesu "Wasu irin mutane ku da abun duniya bai rufe muku idoba? Ban taɓa jin qunci da zafi azuciyataba sai yau danaga kin gaza fahimtata, kiyi haquri karku tafi ku barmu xamu zauna har gaba da abadan, zamuyi dariya atare muddum rai." ta qarasa faɗa tana sauqe hawaye akan fuskarta agefen Arfat ma sai ɗaga kai yake, dan magana gaza futa abakinsa.

Kafin wani lokaci sun koma dai-dai farin suke suna jinjinawa Abdallah "Haqiqa duk inda arziqin bawa yake sai yaje ya takoshi, haka kuma komi daran daɗewa wahla mai iyaka ce."

Acikin wanan daren suka tattara kayansu na buqata Abdallah da Arfat suka fara kaiwa shi kansa Arfat yayi mamakin girman gidan da aka kira wai mallakinsu ne yanzu, ga get da tangamemiyar tsakar gida, gefe wajan ajiye motoci ne, ko ina agidan shukokin fulawa ne mai qayatarwa, ɓangare uku ne acikin gidan ko wane da ɗakuna uku ne da toilet acikinsu sai palo da yake tsakiyar ɗakunan da kitchen agefe guda kuma wajan cin Abincin ne.

"Allah mai kyauta da qari mai azurta mutum lokaci ɗaya." Kalmar da Arfat yake faɗa yana bin ko ina na gidan da kallo, murmushi Abdallah yakeyi azuciyarsa yana Tasbihi da tsarkake Ubangiji.

Cikin lokaci kaɗan suka gama kawo kayan tun adaren Mama Anta da Ummie suka yima maqota sallama da masu zuwa ɗaukan karatu wajansu, sosai sukaji babu daɗi amma kuma da sukaga ci gaba ne suka samu sun tayasu murna da fatan Allah ya sanya alkhairi, amma kuma sun rabu da mutanen kirki, haka Amasallaci su Arfat suka sanar da batun tashinsu, da yawa suma sun jajanta akan tashin nasu, domin azaman da sukayi da su sun samu qaruwa da wayewa ta ilimi ga Iyalansu an kuma samu ci gaba ta fanni tsafta da ladabi ga matansu, to amma dama haka rayuwa ta gada duk daɗinka da mutum dole wata rana ku rabu ko babu rabuwa ta ido akwai mutuwa wanda ita ta har abada ce.


*******

Govment House (GIDAN GWABNATI)


Tun daga qofar farko ta shigowa gidan cike take da matakan tsaro wanda ya ninka na baya ƴan sanda ne da sojoji harma da masu binduga daɗi, ko wata mota da zata wuce sai a cajeta an kuma duba katin da yake alaqantaka da samuwarka awajan awanan ranar.

Daga gidan Govnor kuma abun ya sha bam-bam domin ta ko ina manyan mutane ne ƴan boko masu ji da kansu wanda suka kwanta cikin Nera suka kuma tada kai da dollers ta ko wani rukuni kowa so yake yafi kowa awajan, hakan yasa kwalliya ta sha bam-bam ba ga en matanba ba kuma ga samarinba, abun qarin armashi awajan harda manyan iyaye wanda dukkaninsu masu manyan matsayi ne aqasar.

Harabar gidan an qawatata da Adon furanni ta masu kalar fari da ja sai tsakiyar wajan da aka qawatashi fiye da ko inna domin ɗan tudu ne sai kujeru guda uku ta tsakiyar tafi sauran girma da qawatuwar Ado, ga qaton cake wanda aka kunna kyandira ajikinsa an kuma qawatashi da Ado ajikinsa, gefe ɗaya kuma sautin kiɗa ne yake tashi ba mai hargitsa kwanyar mutaneba sai wanda yake sauqar da nutsuqa axuciyar mai sauraransa. 

Sautin kiɗan ne ya sauya kala lokacin da aka sanar da fitowar jagoran taron nan mutanen wajan suka miqe daga xaunen da suke.

Ahankali ta fara zuro qafafunta wanda suke sanye cikin farin takalmi na silver mai tudu qafafunta zagaye cikin qunshi na jan lallai wanda suka qara fito da kyan qafafuwan haɗe da dacewa da takalmin dake qafar tata, doguwar riga ce ajikinta itama fara mai santsi ta samanta an qawatata da manyan fulawoyi masu kalar Silver da kuma ɗigon duwatsu ajikin ko wata fulawa, hanunta saqale da agogo fari da ganinsa ya fallasa tsadar kuɗaɗen da ya sha sa zoben daimond dake cikin ɗan yatsanta na tsakiya, fuskarta fayau babu kwalliya ta tashin hankali daga kwalli sai lipstick da tasa akan laɓɓanta tayi rolling ɗin kanta da ɗankwalin doguwar rigar jikinta, sai farin glass ɗin da ya zauna akan fuskarta. "Masha Allah" kalmar da ɗaukacin mutanen wajan suke faɗa kenan yayin da yawa samarin wajan suka shagala da ɗokantuwa da son nuna bajintarsu awanan ranar, wasu kuma suka ci buri akan mallakarta amatsayin matarsu, musamman da sukaga gefenta Iyayenta ne azagaye da ita suna nuna tsantsar kulawa agareta da soyayyar da suke mata.

Anan aka fara buɗe taron wajan da Addu'a sanan Abu Khaleesat yayi godiya ga ɗaukacin mutanen da suka halacci taron kammala karatun ƴarsa ɗaya tilo aduniya, ya kuma musu fatan komawa gida lafiya.

Daga nan mutane suka fara zuwa suna kawo gifts ɗin da suka kawo mata amatsayin na murnar kammaluwar karatunta, kai kawai take gƴaɗawa amma hankalinta na kan get ɗin shugowa gidan har kuma yanzu bataga koda alamunsa ba balle tasa ran zuwansa, agogon hannunta ta sake kallo akaro na ba Adadi sanam ta ɗanyi siririyin tsaki akan laɓɓanta. Adai-dai lokacin M.C ya buqaci data zo ta yanka cake nan kuma taji ranta ya qara ɓaci, tashi tayi cikin sanyin jiki ganin mutanen da suke wajan suma sun qosa hankulansu ya kai wajan.

Dai-dai lokacin wata farar Mota ta soko hancinta harabar wajan, anan duka mutanen wajan hankalinsu yakai kanta, da shagala da ganin haɗuwarta, duk da ba abune sabo awajansuba amma ganin yanda aka tsarata da zamanta er madai-daiciya sai abun ya qayatar da su, tsayawa tayi cak tana saita kallonta ga motar da son ganin mamallakin cikinta, ahankali aka buɗe motar ya fara zuro da qafafuwansa wanda suke sanye cikin fararen takalmi sau ciki, ya ajiyeta awaje sanan ya fito shima cikin fararen rigar kot da wandon fari qal da shi, sai liktayin ɗin da yake sirki da kalar silver hannayensa saqale cikin agogo wanan karon ba na fata bane silver yasa, fuskarsa fayau tasha gyara sai sajensa ya samu matsugunni akan fuskar tasa, gashinsa bashi da maraba dana indiyawa saboda naɗewar da yayi awanan lokacin, sosai mutane suka shagala da kallonsa wasu kuma suka fara murza idanuwansu suna son ganin haqiqanin abun da idanuwansu yake gani gaskiya ne ko kuma gizo ne, glass ɗin daya sa akan idanuwansa ya qara taimakawa wajan fiddo da kamanninsa da Khaleesat, hakan ya qara ruɗar da mutane mutqa shi kansa govnor Muhammad Aada saida gabansa ya faɗi awanan lokacin, ya kai kallonsa ga Maa wanda ta dafe qirjinta tana ganininsa, sai dai kafin su ankara ya qaraso wajan yana shumfuɗe da murmushi akan fuskarsa, ya kai kallonsa ga Khaleesat wanda ta shagala da kallonsa da mamakin shigarsa irin tata ido ɗaya ya kanne mata yana murmushi, ga ya qarasa wajan M.C ya karɓi abun isar da sauti ya fara magana cikin sassanyar muryarsa mai taushi "Da fari ina bawa ɗaukacin mutanen wajan nan haquri akan rashin zuwana akan lokaci, sanan ina kuma miqa godiya mutqa da kasancewarku anan wajan dan taya er Uwata, qanwata, Kuma Masoyiyata halattar taron tayata murnar qare karatunta, Abun burgewa da qara Armashi kuma shine ina sheda muku cewar INA SONTA, INA KUMA FATAN TA ZAMA MATATA UWAR ER ER NA, duk ba sabon abu bane saurayi yaso budurwa amma awanan labarin zai zama daban idan kukayi la'akari da matsayina na talakan gari da son er masu garin, amma abun qwararar gwuiwa anan shine kasancewarmu qarqashin kulawar mutum guda da kuma alqawarantawa duniya cewa duka ahali guda muke babu ban-banci tsakanin mai Arziqi da talaka, wanan hujjar ta wadace akan isar da roqona da soyayyar KHALEESAT." sanan ya qarasa kusa da khaleesat ya ranqwafar da kansa "INA SONKI." nan wajan ya ɗauki tafi da sowa da ihun samarin wajen, sai dai wasu da yawa sun qame sun cika da mamaki sosai, ciki harda Khaleesat da Mahaifanta.🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀


Rapppp👏👏👏rappp anfa zo dai-dai wajan, ku hasko min idon Abu Khaleesat, ku kuma kira Abdallah da sunan da ya dace da bajinyarsa awanan chapter, yau na magantu na kuma aikatu ya kamat kuma ku tattaro ko wata nagartarku dan ku qwarara min gwuiwa.
©UM NASS

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI 🎊*


©by *😘Um Nass 🏇🏼*


_Afwan jiya na samu ruɗanin saka lambar shafi madadin 55 sai na saka 45 yanzu ga 56_


Page 56


Kuka taci gaba da yi tana buga hannayenta aqasa lamarin daya ja hankalin ma'aikatan wajan, da yawa suna mamakin ganin uwar gijiyar tasu cikin wanan yanayin, sai dai ko da wasa ba suyi gigin tunkararta ba balle suyi mata magana.

Tsugunnawa akayi akusa da ita cikin sigar lallashi ya fara magana "Kiyi haquri sa'adatu in sha Allah zanyi qoqarin ganin na shawo miki kan Haajaran, tunda Allah yasa mun ganta kuma tana cikin garin nan komi yazo da sauqi, ki tashi daga nan wajan hankulan ma'aikata gaba ɗaya akanki yake, hakan babu daraja ko kaɗan."

Ɗagowa tayi da rinannun idanuwanta "Daraja, Darajafa kace Aada! Ina darajar take ayanzu da qanwata ta guje ni take min kallon gawa? Ina sauran darajar da zanyi tutiya da ita a idon duniya bayan na gaza riqe alqawari da Amanar da mahaifinmu ya bamu? Hmm Aada ka cuceni ka zalinceni haqqina dana er uwata bazai taɓa barinka ba, na tsaneka na tsani komi daya zama naka ne. Ka shayar dani mugunyar guba mai ɗaci qarqashin jahilci da son zuciyarka." tana gama faɗar haka ta hankaɗeshi ta wuce tabar wajan karo sukayi da Khaleesat wanda take ta zubar hawaye ganin halin da iyayenta suke cike, ga kuma tarin damuwar data mata katutu aqasan zuciyarta, duhu ta fara gani yana lilliɓeta ahankali sai takega uku-huɗu kafin ta rarrabe abin da yake damunta ta yanke jiki ta faɗi, da gudu Maa tayi kanta tana kiran sunanta tana kuka, hakan yaja hankalin ma'aikatan da suke gidan suka taho da gudu dan kawo mata ɗauki, da sauri Aada yazo da zummar ɗaukanta "Kada ka kuskura ka raɓi erta, kada munannan hannunka ya ce zai ɗauketa, koma mi ya faru kai ne silar shigarta cikin wanan halin." Cak ya tsaya yana kallonta ga wata uwar kunya da ta gama lulluɓeshi musamman ganin ma'aikatansa da suke masa kallon-kallo "Isya kama min ita mu kaita Asibiti." cikin sauri ya kamata suka sata amota suka nufi asibiti, babu alamun numfashi atare da ita, akai-akai Maa take share hawayen fuskarta, gefe guda kuma tana jin zafi da quna acikin ranta.

Cikin tafiyar da bata wuce ta mintuna 30 ba suka zo asibiti saboda jiniyar da ake tayi yasa suka samu sauqin wucewa, agaggauce likitoci suka iyo kansu da keke aka ɗauki Khaleesat akayi ɗakin taimakon gaggawa da ita, kafin wani lokaci en jarida sukayi caa akansu suna ɗaukan rohoto da son sanin abin da yake damun ɗiyar govnor Muhammad Aada, amma basu samu amsarba dan likitoci na kanta haka mahaifiyarta ta kasa magana sai kuka take.


*****

Tuqi yake cikin hanzari da qagauta amma duk cikinsu babu wanda yake magana kamar babu wanzuwar mutane acikin motar, hakan ya taimaka masa wajan kawosu gida akan lokaci, duk cikinsu babu wanda yayi magana sai sauqa da sukayi suka shiga palon shuru babu mai magana acikinsu.

Ruwa Arfat ya ɗauko mai sanyi a friegh ya tsiyayo akofi kai tsaye ya nufo kujerar da Ummie take ya miqa mata "Karɓi ruwa kisha Ummie" karɓa tayi tana kallon fuskarsa kana ta ɗora da murmushi "Na gode Arfat." sanan ta kafa kanta bayan tayi Bismillah ta fara sha, ahankali sanyi ya jiqa maqoshinta, zafin da take ji acikin maqogwaranta ya fara raguwa, tass ta shanye ruwan ta miqa masa kofin, sanan ta lumshe idanuwanta. Babu wanda yayi mata magana acikinsu kowa ya fara harkar gabansa sai Abdallah ne da yayi shuru ya riqe kansa da yake jin kamar zai faɗo saboda zafin da yake masa, shikam baiga laifin Ummien nasaba ko kaɗan amma kuma idan ya tuna ai Khaleesat bata da laifi asalima bata san miye alqarsu da iyayentaba. Ba yadda xaiyi dole ya jure komi qunci da zuciyarsa xatayi, bazai taɓa tunkarar Ummie da maganartaba koda kuwa xai rasa ransa ne, idan ya tuna wahalhalun da ta jure abaya, to nasa mai sauqi ne. Ji yayi an dafashi da sauri ya buɗe idanuwansa wanda suka sauya kala daga fari zuwa jajaye Mama Anta ya gani akusa da shi tana miqa masa ruwa mai sanyi, ba tare da yayi maganaba ya karɓa ya sha ahankali yaji zuciyarsa na sanyi "Kayi haquri ɗana, nasan kana cin zafi da quncin rabuwa da masoyiyarka amma kuma komi zai wuce na tabbata Ummienka xata huce na ɗan lokaci."

Murmushi yayi yana girgiza kai "Ni ban damuba Mama na tabbata Ummie nada gaskiya, kuma ni na haqura da batun soyayyar Khaleesat Allah zai bani wanda ta fita komi da komi, sai dai bazan iya kankareta azuciyataba saboda ita ɗin jinina ce." yana gama faɗar haka ya miqe ya shige ɗakinsu da ido Mama Anta tabi shi tausayinsa yaka ratsa ko ina na jikinta, ku kuma taku qaddarar kenan farin cikinku bashi da yawa, ta faɗa tana mai cike da tausayinsu.

Yinin ranar haka suka wuni sukuku babu wani mai walwala da kuzari acikinsu, domin ita kanta Ummie ta kasa yin walwala kamar ko yaushe komi za tayi tana yinsa ne cikin sanyin jiki da kuzari, haka har zuwa wanan lokacin ta kasa jurewa, yanzunma dai azaune suke sun saka abinci agaba babu wani mai cin na kirki sai caccakalar cokala da suke, gajiya tayi da juya cokalin da yake hannunta ta ɗauki ruwan lemon kwakwa da madara ta sha, ta koma gefe tana kallon yanda Abdallah yake juya nasa cokalin qarfin hali yake kawai yana qirqirar murmushi har yake magana da Arfat.

 Tashi tayi ta koma kan kujerar dake palon ta kunna TV cikin sa'a tayi karo da labaran da akeyi ayanzu, zama tayi taci gaba da kallon masu gabatar da labaran adai-dai lokacin aka hasko asibiti da maɗauka labarai suna nuno Khaleesat wanda ake turata acikin gadon marasa lafiya, babu numfashi atare da ita, gefenta kuma Adda Sa'adatu ce tana ta matse hawaye tana ture mutane, kafin ta rarrabe kuma ta tsinkayi maganar mai rahoton "Ayau ne aka kawo er gidan Govnor Muhammad Aada ranga-ranga babu numfashi atare da ita, lamarin daya ɗauki hankalin mutane ya kuma basu mamaki, kasancewar jiya aka gama shagalin murnar gama karatunta, abun tambayar anan minene ya haddasa mata bugawar zuciya alokaci ɗaya? Har yanzu bamu samu wanan amsarba domin mahaifiyarta tana ta kuka ta gaza bayani, likitoci kuma suna kanta basu bamu tabbaci akan zata rayu ko kuma akasin hakanba, awanan lokacin kuma muke ta laliben ina Mahaifinta yake da bai samu halattar zuwa asibitinba?"

Hankalinsu ne gaba ɗaya ya tashi musamman Abdallah daya qwarai daga cin Abincin da yake ruwa suka fara dafifin miqa masa amma tarin yaqi tsayawa, tuni idanuwansa ya sauya kala zuwa jajaye, da qyar aka samu ya risina sai dai har zuwa lokacin yana dafe da qirjinsa da yake masa zafi da zugi.

Kashe TV ɗin Ummie tayi ta shige ɗaki ba tare da tayi musu maganaba, zama tayi akan gadon dake ɗakin ta haɗe kanta da gwuiwarta, ta fara kuka mai sauti, wanda rabonta da yinsa ta daɗe, zata iya cewa tun mutuwar Hamza bata sake yin kuka hakaba, sai yanzu da taga er uwarta cikin yanayin damuwa, alamun motsi taji akanta hakan ya sata ɗagowa da sauri tana goge hawayen da yake zuba afuskarta ido biyu sukayi da Mama Anta wanda tun shigowarta ɗakin ta biyota, ganinta cikin yanayin damuwa tasan za'ayi hakan "Ba kuka ya kamata kiyiba Ummu Abdallah, kina da damar da ya kamata ace kin ceci rayuwar Khaleesat, ba wai so nake nace ki alaqanta Aurenta da Abdallahba, bani da masaniya akan gaibu amma ina da yaqinin kashi tamanin cikin ɗari na damuwar Khaleesat ke ce silarta, acikin labarinki naga kina da yafiya da haquri da kuma yima mutane uzuri, amma kuma sai gashi yanzu ataqi kaɗan kina so ki rasa duk ladan haqurin da kikayi." ɗago idonta tayi suka haɗa ido da Mama Anta, kai ta gyaɗa mata kana ta zauna akusa da ita, ta riqo hannayenta "Duk da cewa ban kaiki ilimi ba amma kuma zan faɗa miki wasu abubuwa da kika manta, Sa'adah er uwarki ce, duk duniya baki da wani amadadinta ayanzu naga qauna da soyayya acikin idanuwanta alokacin da take ganin fuskarki, haka lokacin da taga kina qoqarin barinta naga karaya da rauni ashimfiɗe a idonta, naga tsoro mai sunan tsoro da ruɗewa tana binki, duk matsaƴin data ke kai hakan baisa ta gagara biyoki tana ihu tana kukaba duk da akwai hadimanta aharabar gidan."

Murmushi tayi na nuna takaici "Idan har haqurin da kikayi da mutanen Gumsa abaya har zuwa laifin da suka miki bai hanaki jin haushinsu kin gujesuba har sai da suka koreki dan sun gaji da ke, mi yasa yanzu kika tafi kika barta?"baki ta buɗe da zummar yin magana tayi saurin datsarta "Aada shine wanda ya hanaki ganin Adda Sa'adah alokacin da bata san inda kanta yakeba, shine ya miki laifi ba itaba, idanma tana da laifi aciki bai wuce na dawowar hankalinta ba tare data sake nemankiba, amma kema kina da naki laifin tun alokacin kika datse ko wata hanyar da zata sadaki da ita, kika haramtawa makusantanki shiga garin balle asamu labarinki ko naki, aduk cikin labarin nan idan kika dunqulesu waje ɗaya cutar kai da kai ne, Aada shine tsanin komi acikin tafiyar, amma Khaleesat bata da laifi ita ɗin ɗiyarki ce idan har da kara, Annabi s.a.w yace "Mafi alkhairi acikin mutane shine wanda yake haquri yake mallakar zuciyarsa daga fushi, yake yafewa en uwansa idan sun cutar da shi, ya kuma musanya alkhairi da cuta."

Kiyi sassautawa zuciyarki ki kuma yafewa Adda Sa'adah ki saurareta koda sau ɗaya ne kiji uzurinta."

Ɗagowa tayi tana kallon Mama Anta ɗin wanda tunda ta fara maganar take zubar hawaye, rungumeta tayi tana sauqe ajiyar zuciya ba tare data ce komiba can ta miqe ta ɗauki mayafinta ta kalli Mama Anta ɗin "Muje Asibitin Mmn Arfat, ina son ganin Adda Sa'adah yanzu."

Murmushi tayi itama ta ɗauki mayafinta sanan ta ruqo hannunta, a inda suka bar su Abdallah anan suka tararsu sunyi zugum-zugum, "Ku tashi muje Asibitin da aka kwantar da Khaleesat." ba zata sukaji maganar wanda sukayi saurin ɗagowa suna kallonsu, musamman Abdallah daya miqe yana faɗaɗa fuskarsa da murmushi "Da gaske Ummie?" ya tambaya yana washe bakinsa, murmushi tayi mai sauti tana jin tausayin ɗan nata ɗaya da suka sha gwagwarmayar rayuwa tare, ashe da ta cuceshi ta haramta masa ɗorewar walwalarsa, kai ta gyaɗa masa tana share hawayen daya zubo acikin idonta, rungumeta yayi yana sauqe ajiyar zuciya "Nagode Ummie," sanan ya kai kallonsa ga Mama Anta yana mata murmushi kai ta girgiza masa itama wanda yasashi ficewa da sauri ya kunna motar.

Shiga sukayi kowanne fuskarsa ɗauke da walwala musamman ganin Abdallah da yake tuqi cike da hanzari da jin daɗinsa "Wai kasan Asibitin ne naga sai tafiya kake kanka tsaye?" Mama Anta ta faɗa tana faɗaɗa murmushinta.

"Na sani Mama, mun taɓa kai wata yarinya da aka buge abakin titi."

"Oh amma kasan ba qaramar asibiti za'a kaitaba."

"Mama ai ya zama ɗan gari da daɗewa ko ina take zuwa ya sani, ni wani wajanma ban saniba dan kamar jela haka ya zame mata" Arfat ya datsi maganar yana murmushi wanda tasa Mama Anta darawa dai-dai lokacin suka shigo Asibitin sukaga motoci bila Adadin, ga tarin ma'aikatan jarida da suka kewaye Asibitin, kamar ana filin rantsar da shugaban qasa ne. Lolz

 "Tofa!" Abdallah ya faɗa yana dai-daita tsayuwar motar tasa, ta ko ina ma'aikata ne suke kaiwa da kawowa "Yaufa babu kanta wanan matakan tsaro har ina" Mama Anta ta faɗa tana qoqarin buɗe motar.

"Ai dole ɗiyar govnor mai ci ajaha, dole asa ido akanta gudun matsala." Arfat ya bata amsa ahaka suka fito suka nufi ɓangaran da suke tsammanin nan aka kwantar da Khaleesat, abun mamaki duk inda suka wuce ma'aikatan sai dai su sara musu ba tare da sun bincikesuba lamarin daya bawa Mama Anta mamaki har ta tambayi Arfat dariya yayi sanan ya mata alama da fuskarsa data Abdallah anan kuma ta jinjina kai tana son bada gaskiyar kwatancanasa.

Anan suka samu wani likitan suka tambayeshi ko an samu dai-daituwar numfashin nata? Ajiyar zuciya ya sauqe yana musu nuni dasu biyo bayanshi dan ayanda yaga kamaninsu da marar lafiyar ko ba'a sanar da shiba yasan su makusantanta ne, ɗakin da take ciki ya nuna musu "Mun samu dai-daituwar numfashinta sai dai har yanzu bata farkaba, mamanta tana ciki ko magana bata iyayi sai faman kuka take, naga ku en uwanta ne ku kwantar mata da hankali ku kuma bata shawarar ta bata abin da take so, dan zuciyarta na iya bugawa, ayanzuma da qyar mukayi nasarar dai-daita mata numfashinta, sai abu na qarshe ku taqaita magana kada ku tasheta." yana gama faɗar haka ya juya yabarsu anan, murɗa qofar Abdallah yayi ya shiga sanan suma suka rufa masa baya, da ita suka fara yin tozali akwance akan gado idanuwanta arufe fuskarta tayi suwal kamar data shekara bata da lafiya, daga gefenta kuma Maa ce ta kara kanta ajikin gadona sai faman ajiyar zuciya take, a yanda suka lura bataama san da zuwansu ba.

Qarasawa Ummie tayi kusa da ita cikin sanyin jiki ta tsugunna akan gwuiwoyinta "Adda nah" azabure ta ɗago tana kallon inda taji sautin ganin Haajara akan gwuiwoyinta sai take tunanin kunnuwanta ne da idanuwanta suke mata gizo, hakan yasata bubbuga kunnuwan nata, ta kuma murza idonta amma dai ita ɗin ta sake gani agabanta "Nice Addah ba gizo na mikiba" jin hakan ya sata sauqa da sauri ta tsugunna ta rungumeta nan sautin kukanta yaci gaba da qaruwa itama Ummie kukan take tana sauqe ajiyar zuciya, jinta ajikinta ya tuna mata wacece ita aduniyarta, yayarta er uwarta mafi soyuwa agareta, wanda take bata kulawa fiye da wadda iyayenta suke bata, take dariya da dariyarta take kuka idan taaga damuwarta, mi ya shige kanta da har ta faɗa mata magana abaya "Mi yasa? Mi yasa kika tafi kika barni Addah?" ta jefa mata tambayar tana janye jikinta daga rungumar da ta mata, riqo hannunta Maa tayi tana hawaye acikin idanuwanta wanda sunqi tsayawa "Ba tafiya nayiba Hajarko, ko kaɗan ban gujekiba Asalima bani da ishasshen hankalin da zan tuna ko wacece ni" kallonta Ummie take "Kamar ya bakya cikin hankalinki?"

"Tabbas bana cikin hankalina lokacin da muka samu hatsari amota ni kaɗai na rage nima kaina ya bugu sosai ta yanda na manta duk abun daya faru dani abaya, hakan yasa aka turo mu asibitin kano, daga nan Aada ya siyar ko wata kadara tamu ta gado da aka bar mana ya taho dani, anan yaci gaaba da kulawa dani yake bani kulawa tsawon shekara ɗaya ana abu guda babu ci gaba dole muka samu gida ya zauna ya kuma kafa kasuwanci ahaka ya haɗu da aboki na qwarai yasashi faɗawa harkar siyasa daga matakin Kansila zuwa ɗan majilissa alokacin ne na na haifi Khaleesat ya fitar dani qasar Germany cikin ikon Allah na samu lafiya, alokacin ya sanar dani duk abin daya faru bai ɓoye min komiba har yanda kukayi da ke a asibiti, nayi kuka sosai nayi kaico da hali irin nasa saida muka shafe wata biyar bana masa magana na kuma ɗaga hankalina akan sai mun dawo gida saboda naje na ganki, amma qaddarar Allah alokacin muka ankare da rashin lafiyar Khaleesat zuciyarta ce aɗan kumbure dole muka zauna muke ganin likita da kulawar da ake bata, sanan aɓangaran Aada na matsa akan yaje ya binciko min ke saboda hankalina yana kanki, sai dai gangar siyasa da afkawarsa ciki yasashi shagala bai bi takan nemankiba, haka muka shafe shekara goma sha biyar acan anan Khaleesat tayi karatunta har ta kammala scndry nima ganin zaman da nake bashi da wata amfani yasani fara karatu acan, tare muka gama da ita sanan ne muka samu dawowa qasar nan, alokacine ne hankalina ya qara tashi akan zuwa nemanki babu Aada saboda baya samun zama ya faɗa cikin rububin neman takarar govnor kano awanan lokacin, kullum nakan ɓoye kaina aɗaki nayi ta kuka ina kallon sarqarki da hotunanki amma bazan iya kai kaina inda kikeba, sai acikin wanan shekarar naje har can sai dai na tadda labari marar daɗi wai mutanen garin sun koreku saboda sun gaji da ganinku, nayi kuka nakuma yi Addu'a akan Allah ya haɗani da ke kada ya ɗauki raina ba tare dana haɗu dakeba, wanan shine abun daya kawo tsaikon rashin nemanki, amma kiyi haquri ki yafe min dan Allah." ta qarasa maganar tana haɗe Hannayenta biyu tana roqon Haajaran, riqe hannayenta tayi itama tana hawayen "Na sani ba qaramin abune zaisa ki juya min bayaba Addah, koda ace duniya zata juya min baya na tabbata zaki ruqo hannuna mu zauna atare, na riga dana yafe miki, na kuma ɗauki hakan amatsayin qaddarata wanda bazan taɓa guje mataba ko kuma asauya min ita, naga rayuwa Addah Sa'adah naga yanda igiyar rayuwa take ta wujujjuga rayuwata son ranta, amma daga baya sai na ɗauki laifin amatsayin nawa tun farko da ban dage akan Auren Hamzaba qila da ban fuskanci rayuwa wadda tayi dai-dai da HAƊIN GWARMAI da mutane suke faɗaba, sai dai kuma haɗin ya haɗu ta yanda ya fidda Abdallah atsakaninmu, qila da ban san ya zanyi da wanan rabon mai wahla ba." Murmushi tayi tana share hawayen fuskarta sanan ta girgiza kanta "Bani labari bayan barinmu daga sunan Abdallah." xamanta ta gyara sanan ta janyo Ummie ta kwanta akan cinyarta kamar yarinya qarama ta haka ta fara bibbiga bayanta "Addah labarina bashi da daɗin ji, amma ko maqiyina bana masa fatan yin koda kwatankwacin rayuwata ne.....daga nan bata labarin rayuwar da tayi tun bayan aurensu da hamza har zuwa yanzu da take agabanta, kuka Adda Sa'adatu take tana qara rungume Ummie kamar da xa'a qwace mata "Ban taɓa Hasashen akwai irin wanan rayuwarba koda acikin mafarkina bane, ban taɓa kawo araina auren jinsin daba nakaba zai iya kawo qiyayya haka, amma nasu ba qiyayya bane son zuciya ne da jahilcin da yayi musu katutu, na godewa Allah da barinku garin ya zama mabuɗin alkhairi acikin rayuwarku, yanzu sai dai labarinsa." ta faɗa tana share hawayen sai alokacin idanuwanta yakai kan su Mama Anta da suke tsaye suna kallonsu kowa na share hawaye yana tausayama rayuwar da sukayi "Ashe ba ke ɗaya kika zoba Hajarko?"

Tashi tayi zaune daga kwanciyar da tayi akan cinyar Maa ta dafe kanta "Allah na manta ne sam Addah" sanan ta tashi ta janyo hannun Mama Anta wanda take kallonta kamar taga sabuwar halitta wanan tana da bambanci da Ummie Abdallah data sani abaya "Addah kinga wanan ita ta maye min gurbinki, ita ta janyoni cikin inuwarsu muka zauna atare." kallonta Maa tayi tana murmushi ta miqa mata hannu "Na gode sosai Allah ya saka miki da gidan Aljannah Firdausi, awanan duniyar samun mutane irinku abune mai mutqar wahla."

"Ba komi Addah ai yiwa kaine." Mama Anta ta faɗa tana murmushi sai alokacin ne Khaleesat ta sauqe ajiyar zuciyar da takeyi, dan tun shigowar su Ummie ta farka, sai yau taji tarihin Mamanta da danginta, lallai mahaifinta ya kasance Azzalumi mai son kansa ya raba zuminci saboda son zuciya da neman duniyarsa ido ta runtse ta buɗesu akan Abdallah wanda yake kallonta shima fuskarsa qunshe da murmushi _Ashe ba iya soyayya take masaba haɗuwar jini ce irinta en uwan juna, lallai Allah ba yanda baya ikonsa, gashi ya sanya sun zama tsanin haɗuwar iyayensu bayan tsawon shekaru, ido ta lumshe ta buɗe tana jin wani qarfi na ratsa ko ina na jikinta hakan ya bata damar miqewa zaune wanda ya ankarar da su sukayi saurin riqeta suka zaunar da ita, anan ta qurama Ummie ido tana kai kallonta ga Maa basu da wani banbanci na kamanni sai girman da zai nuna ɗaya ta girmi ɗaya, murmushi tayi taka sunkuyar da kanta, cikin haɗuwar baki suka fara mata sannu da jiki kai ta gyaɗa tana murmushi dai-dai lokacin aka turo qofar ɗakin aka shigo, Abu Khaleesat ne idanuwansa sharkaf da hawaye ko ina ajikinsa ajiqe yake da gumi, qofar ɗakin ya tura ya rufe ya qaraso kusa da su ya shimfiɗa gwuiwoyinsa aqasa kana ya haɗa hannayensa biyu "Ban san da wata kalmar zanyi amfaniba wajen roqonku gafara da yafiyaba, amma koda bazaku yafe minba ina roqon da kuyi haquri abaya nasani harda qarancin ilimi da jahilcin da yake ɗawainiya dani yasa na koreki Hajarko, bayan haka idanuwana sun rufe akan tsoron kada na rasa Sa'adatu saboda ina sonta sosai, ke sheda ce akan hakan, yau naga sakayya da tashin hankali abun da nake qawarsa yana barazanat barina ayau naji tsoron rasa erta ɗaya dana mallaka da matar danake so kamat raina, naji na tsani mulki da komi wanda ya shagalar dani adalci acikin ahalina, nayi kuka alokacin dana sauri tarihinki Hajarko nayi turr da kaico da rayuwata nasan ni ɗin ne silar wargaza ko wani sa rai da kike dashi, sai dai Allah ya nuna min sakaya tun aduniya naga qiyayya daga idanuwan erta da mata, na ga zargi acikin idanuwan mutane da kuma tuhuma ayau, tabbas ban cancanci ko wata yafiya da gafara daga garekuba, amma duk da haka zan roqeku Alfarmar kuyi haquri ku yafe min dan Allah ba dan halinaba." ya faɗa hawaye yana zuba acikin idanuwansa. Riqe hannayensa Ummie tayi tana kallonsa da murmushi akan fuskarta "Kabar kuka Aada mun yafe maka, kula da Aada da kayi kaɗai ya fansheka awajena, na ɗauka cikin saninta ta gudu ta barni, daya baya n fahimci ashe soyayyar gaskiya kake mata hakan yasa baka gujeta alokacin data manta wacece itaba, na gode d sadaukarwarka agareta, mun yafe maka Allah ya yafe mu gaba ɗaya, dama can haka qaddarata tazo ba kai ne silarta ba sai dai sanadi kawai." ta qarasa faɗa tana murmushi wanda yasa suma yin murmushi, tashi yayi yana mata godiya ya rungume Abdallah "Na daɗe ina tunani akan kalamanka Abdallah daga baya sai na fahimci nine talaka ashe ba kaiba, sai yanzu naji na sauqe wani qaton nauyi da yake qirjina na gode sosai, duk duniya ayanzu babu mai hanaka Auren Khaleesat sai idan mutuwa ce ta gifta atsakani."

Ya faɗa yana murmushi yana girgiza kai daga nan wajan ya ɗauki dariyarsu da Hamdallah gaba ɗayansu.

 "Amma ina son a ɗaura Auren a GUMSA." gaba ɗaya suka juyo suna kallonsa, Kai ya jinjina yana kuma tsare fuskarsa daga tuhumar da suke masa........🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀


Oh oh Anya hakan zai iyu kuwa😢©by Um Nass

[1/4, 3:03 PM] Oum Nass: *HAƊIN GWARMAI 🎊*


©by *😘Um Nass 🏇*


Last page 57


 "Da gaske kake?" Abu Khaleesat ya tambayeshi yana murmushi akan fuskarsa.

Kai ya gyaɗa yana kai kallonsa ga Ummie "Duk yanda zasu mana ko su gujemu ba zamu taɓa rabuwa da suba, ba zamu iya sauya su daga jikinmu ba su ɗin namu ne koda bazasu gode manaba."

Ajiyar zuciya Ummie ta sauqe sanan ta faɗaɗa murmushin fuskarta, takai kallonta ga Aada "Ya kamata muje ganin gida, tsawon shekaru mun fito saboda wasu dalilai, ayanzu kuma da muke atare ya kamata mu koma kodan sauran danginmu da suke can."

Kai ya jinjina shima cikin gamsuwa da maganar tata "Gaskiya ne maganarku, idan Khaleesat ta warke sai mu tafi ko acikin wanan makon ne." ya faɗa yana kai kallonsa ga Maa da khaleesat ɗin wanda fuskarta taqi ɗaukewa daga murmushin da take, ko wani motsin da zatayi idonta na kan Ummie ne "Ni kam na warke Dady ko yau zamu iya tafiya" suka tsinkayi maganar Khaleesat wanda ta sasu waro ido suna kallonta, sai alokacik ta hankalta da katoɓarar da tayi hakan ya sata saurin rufe fuskarta, abun da ya sasu dariya kenan suka ci gaba da hirarsu cike da so sa kauna, anan Arfat ya sanar da Khaleesat shimafa ba za'a barshi gwauroba ta masa hanyar qawarta Siddiqa dan dama tun da ya ganta yaji yana sonta, sosai taji daɗin maganar da yayi hakan yasata kiran Siddiqa awayar akan tazo ta gida yanzu-yanzu, to tace mata sanan t kai kallonta ga Arfat wanda yake ta washe baki, hannu ta miqo masa tana tsare fuskarta "Ka kawo kuɗin kamfen" ta faɗa tana matse fuska hakan ya sashi yin dariya yana jan hancinsa "Ke ai Hajiya ce bakya buqatar wani kuɗi awajena."

Ido ta qwalolo waje tana tsumewa "Shikenan baka sonta da gaske ashe? Amma banda haka komi yawan kuɗina ai zaka kawo ihsani."

Hannusa yayi saurin zurawa cikin aljihunsa ya fiddo da damqin kuɗi ya saka ahannunta hakan ya bawa kowa dariya, Mama Anta taja ta ruqe haɓa "Yaran yanzu sam baku da kunya." 

"Ki bar min ɗana ta wataya lokacinsa ne." Ummie ta tare tana murmushi.

Anan aka sallamesu a asibitin suka koma gidan govnor nan anan suka tadda Siddiqa har ta rigasu zuwa, ta fara tambayar abin daya faru, da hannu ta nuna mata Arfat wanda ya kafeta da idanuwansa har saida ta tsargu, shigewa su Maa sukayi suka barsu awajen ya rage daga Abdallah, sai Arfat da kuma su ɗin.

Da sauri ta washe bakinta tana miqawa Abdallah hannu "Yayanmu kwana biyu" 

Kai ya gyaɗa yana murmushi "Bakwa neman mu shi yasa."

Baki ta rufe tana kiran "Laa nema kai, kawai dai ban san ta ina ne zan faraba."

Alokacin Arfat yayi gyaran murya "Na dai lura ni kaɗai akema wariyar launin fata, kowa ya tashi sai dai yace Abdallah amma ni ko nuna an gannima ba'ayi."

Dariya sukayi ganin ya tsume ya juyar da bayansa, da sauri ta qarasa tana bashi haquri ahaka suka ware suna fira har ya gangara kan abin da yake ransa, bai sha wahlar samun kantaba musamman da ya sanar da ita Abdallah da Khaleesat za'a haɗasu kasancewarsu en uwa ne, hakan yasata sanyi jiki ta kuma karɓi Arfat da hannu bibiyu amatsayin abokin rayuwarta, wanan haɗin yayi mutqar yima su Aada daɗi atake ya kira mahaifin Khaleesat ya sheda masa qudurinsu da kuma inda ya kamata ayi bikin, to bai jaa da tsayiba asalima murna yayi ya shedama Abu Khaleesat komi yana hannunsu za kuma su zo adaura auren duka atare dana su Abdallah.

Abin mamaki cikin kwanaki uku aka gama sanar da ɗaurin Auren Khaleesat da Abdallah wanda duka asanarwar da akayi za'a ɗaura ne a yobe state da yawa sun cika da mamaki amma da suka tuna mafari da tsushen Aada ɗin sai suka ci buri akan hallartar bikin da kuma tanadin kuɗin motarsu.

Awanan lokacin ne suka kama hanyar zuwa Yobe tun kafin suje matakan tsaro suka fara basu kariya da buɗe musu hanya saboda sanin zuwansu da sukayi, govnor yobe da kansa yaje ya tarosu ya musu jagora sai da suka zauna adamaturu suka huta na kwana ɗaya, sun samu karramawa mai yawa da tarba awajan govnor da mutanensa daga nan ya musu rakiya har xuwa Yadin bunni abun ya qayatar da su mutqa musamman Haajara da ta baza ido tanaga sauye-sauyen da aka samu agarin an kuma samu ci gaba sosai, har qofar gidansu sukaje anan ta cika da mamakin ganin gyaran da aka yima gidan ya dawo ginin zamani, kallonta ta kai ga Adda Sa'adah wanda take murmushi da hawayen da ke zuba acikin idonta "Tun lokacin dana zo nemanki ban samekiba, nasa aka gyara gidan ina fatan da burin wata rana mu sake xama acikinsa atare da ke." Rungumeta Ummie tayi tana sauqe ajiyar xuciya tana godiya da Allah wanda ya qaddari haɗuwarta da er uwarta.

 Sauqa sukayi suka shiga gidan ga jiniya da tsaro daya cika garin hakan yaja hankalin mutane suka fara dafifin zuwa wajansu ganinsu, abin da ban mamaki ganin er ern Ɓaffa malam anan labari ya riski en uwan Baffa malam suka zo da yawansu suna fuskantar rayuwa ganin talauci da wahla yayi musu katutu, kuka suke suna roqon su akan su yafe musu abin da suka musu haqiqa Mamman yayi sa'a yayi gaskiya da yace Allah ya bashi kyautar da tafi ko wacce ya kuma kirayi er er mata Rahma ne agareshi, yau gashi yaransa sun taka mataki mai yawa su kuma babu abin da yara mazan suka tsinana musu face wahla da janyo zagi agari, Allah yaji qan Baffa malam, kalaman da suke ta faɗa kenan suna kuka "Ameen" shine abin da suke faɗa anan suka cika kasu da kuɗi mai yawa suka kuma sheda musu Auren yaransu Khaleesat da Abdallah abin ya musu daɗi sun kuma yi farin ciki da haɗuwar kansu, haka suka qara godewa Aada kasancewarsa maraya ya kuma sakawa Baffa malam da Alkhairi har ya riqe ersa da dukiyarsu tsakani da Allah.

Bayan sun qara kwana ɗaya anan suka kama hanyar Gumsa tun daga hanya abun ya fara bawa su Abdallah mamaki domin titi aka musu mai kyau babu gargada haka suka shiga cikin garin nanma sukaga an ɗan samu sauyi ako ina akwai famfon ruwa saɓanin abaya da sai mace taje rafi ɗiban ruwa, kai suka jijina suna faɗin Ikon Allah an ɗan samu ci gaba kenan agarin nan?

Murmushi Aada yayi ba tare da yace musu komiba ahaka suka shiga garin da tarin motocinsu da jiniyarsu wanda yasa mutane shiga taitayinsu suka nufi gidan Mai gari, su ɗinma nan suka nufa xuwansu yasa mutane qara tsayawa cirko-cirko har saida suka fito, tabbas sun raina kansu domin ganinsu sukayi kamar wasu sabbin halittu, taburmar da take shimfiɗe mai gari yasa aka sake kaɗeta aka ɗauko wasu agida aka sake shimfiɗawa suka zauna, gaisawa suka fara yi suna duqawa har qasa dan sun sheda Aada ɗin zuwansa na biyu cikin garin kenan shine kuma ya bada kwangila aka musu titi da magudanar ruwa, godiya suka qara masa akan hidimar da ya musu amma ko kaɗan basu gane waɗanda suke tare da suba, da hannu yayi ma mai gari nuni "Nace ko ka gane waɗan nan mutane biyun." 

Ido Mai gari ya wala waje yana qare musu kallo sanan ya girgiza kai "Ina waɗan nan en hutun ai ba tantama iyalinka ne su." murmushi yayi ya girgiza kai sanan yace "Sune mutanen dana zo nema kwanaki kace min an koresu agarin, wanan Abdallah ne da mahaifiyarsa Haajara matar Hamza ɗan gidan Baba Garba da Iya Indo." ido duka mutanen wajen suka buɗe waje anan suka fashe da kuka suna neman gafararsu, da yawa suna sanar da su yanda rayuwa tayi walagigi dasu bayan barinsu agarin, da kuma yanda ruwa yayi musu Ambali har suka rasa matsugunni.

Mudi da sule kam fuskarsu suka fara mari saboda takaicin rayuwar da sukayi abaya, ko ina ajikinsu kirci ne da quraje kayansu ayayyage suke ko kyan gani babu, tabbas wanan Alhakin su Abdallah ne ya ke cinsu, gefe ɗaya kuma Mai gida ne yake ta faman lalime da hannunsa yana son taɓa Abdallah yana kukan da babu hawaye acikin Idonsa, ya haɗu da cutar makanta sanadin man suya daya fallatsu a idonsa garin tsayewa matarsa akan kada ta cinye masa nama, hakan ya zama silar makantarsa har kuɗinsa ya qare amma babu alamun waraka, duka matansa suka tafi suka barshi dama ba haihuwa yakeba suka en korensa suka juya masa baya haka yaci gaba da shan wahla qarshe dai bara ya koma, kai Abdallah ya jinjina da Ummie suna ganin girman qaddara da iko na Allah yau mutumin daya fi kowa Arziqi aqauyensu ya koma talaka mafi qasqanci da sai yayi bara zai samu abin da zai ci.

"Iya Kakata tana nan?" Abdallah ya jefo tambayar ga mai gari. Kai ya jinjina yace kuzo muje gidan nata tana nan.

Nan suka ɗunguma gaba ɗaya har mutanen garin anan suka sameta azaune ita da gwaggwo Harira suna faman taɗi sun saka qanzo agaba suna ci babu yaji balle mai, da sallama mai gari ya shiga su Abdallah suka rufa masa baya "Yau mai gari da kanka kazo, Allah yasa dai ba wani laifi yaron nan ya sake yiba." gwaggo harira ta faɗa tana qoqarin matse hawayen kan fuskarta, domin dai itama rayuwace ta juya mata baya tun bayan mutuwar mijinta matan er enta suka bar mata ɗore domin ba daɗinta suke jiba, haka ɗan Autanta ya ɓaci da shaye-shaye kullum cikin hanyar zuwa wajen mai gari take yana ja mata kunne akan ɓatashin da tayi, suka kangare ɗayan ya zama ɓarawo yayin da ɗayan ya zama ɗan shaye-shaye kusan kullum tana hanyar zuwa gidan mai gari saifa awajan yaranta mata take jin daɗi suma mazajansu ba wata wadata garesuba sai rufin asiri, gorin yau da ban na gobe daban awajan kishiyoyinta hakan yasata tattaro nata kayan tazo gidan Iya Indo suke zaune tare.

Murmushi mai gari yayi yace "A'a ba laifi yayiba yau Alkhairi ne ya kawoni jikanku ne yazo yaron wajan Hamza" azabure iya Indo ta miqe tana riqe da zanin hannunta wanda ya gaji da duniya ya gama koɗewa ya quje ko ina ajikinsa ɗinkin zare da Allura ne "Mai gari bama wanan wasan da kai, dan Allah karka zolayeni kace Audullahi ne ya dawo gareni."

Murmushi yayi ya riqo hannunta wanda har kakkarwa yake ko ina ajikinsa jijiyoyin wahla ne "Da gaske nake miki Iya Indo ga Audullahin nan agabanki da Haajara" ya kai hannunsa yana nuna mata su, kallonsu suke alamun hutu da jin daɗi ya zauna ajikinsu, nan fa Iya Indo da gwaggo harira suka saka kuka atare suna neman yafiyarsu akan Abin da suka musu abaya.

 Rungumesu Ummie tayi ita da Abdallah saboda tausayama rayuwar da taga sunayi ta yafe musu "Har Abada bazata taɓa barin Mahaifan Hamza su shiga wahlaba domin ya qare rayiwarsa yana wanzar da farin ciki acikin duniyarta. Haka suma aɓangaran su Iya Indo suna ta kallon Abdallah da Haajara wai waɗan nan sune iyalan Hamzanta sune ababan da Hamxa ya bar mata take wulaqantawa tabbas duk abin da ya baka dariya wata rana zai baka tsoro, misali akan Abdallah da Ummiensa yau sun zama sanyi da haske acikin duniyarsu. Qarin daɗawa yau jikanta zai Auri ɗiyar govnor wanda ko acikin mafarkinta ba xatayi hasashen samun damar auren er mai gariba, tabbas ta yarda rabon bawa da Arziqinsa duk inda yake sai yaje ya tako, ashe ba qyashi mutanen garin suka musuba mabuɗin alkhairi suka shimfiɗa suka buɗe musu.

Anan aka suka zauna akayi ta fira da sanar dasu abubuwan da suka faru, agidan mai gari aka sauqe su akan musu abinci da soye-soyen kaji da zabbi ga nono kindirmo da aka kawo musu ko ina nan nan ake da su.

Cikin mako ɗayan da sukayi aka qara gyara garin an gima musu makarantar Islamiyya da masallaci sanan aka kawo malamai daga cikin damaturu da Albashi mai tsoka dan koyar dasu karatu aranar da aka buɗe makarantar aranar dubbanan mutane suka sheda Ɗaurin Auren ABDULLAHI HAMZA GARBA DA KHALEESAT MUHAMMAD AADA sai kuma SIDDIQA ADAM ELHUSSAIK DA ARFAT ISMA'IL ɗaurin Auran daya haɗa mutanen manyan qasa aranar mutanen gumsa suka qara sheda cewa ita hassada tana cin mai ita ne tana kuma qarawa wanda ake yiwa qofofin arziqi sun qara haqiqancewa Allah ne ya zaɓi Abdallah yake sonsa shi yasa ya kere ko wani abu da suke tsammani qarshe sai gashi aqarqashinsa suka samu ci gaba ya san musu daya abin da ya tara arziqinsa bai sa ya gujesuba asalima zuwa yayi ya janyo hannayensu dan su lasa. Sai gashi mutane suna fadanci awajansa da son nuna sanayya atsakaninsu, Iya Indo tayi kuka ta godewa Allah tabbas Hamxa yayi gaskiya inama Baba Lawan da Hamza suna raye yau dan sunga abin da suka hango wanda idanuwansu ya rufe awancan lokacin. 

Daga nan duka mutane suka watse suma su Ummie suka fara shirin tafiya suka shedawa mutanen garin tafiya xasuyi da Iya Indo dan Abdallah shine dolenta ai nan gwaggwo Harira ta fashe da kuka tana roqon su tafi da ita itama, dan Yaya Indo ce kaɗai take jin daɗinta acikin garin, kai Abdallah ya jinjina dan ya san soyayyar da take tsakaninsu tun yana yaro atare da yake ganinsu kullum har mamaki yake da yanda take barin gidan Aurenta take zama agidan Iya Indo, qarshe dai ya tusa qeyarta data Autan ɗanta wanda baifi sa'ansaba suka ɗaga sai Kano, mutanen garin suna ta ɗaga musu hannu suna matse hawayen su, rayuwa kenan babu yanda bata kayawa bawa.

Sai da suka koma ta Yadin Bunni suka yima yayyan Baffa Malam sallama sanann suka taho sun shiga garin Damaturu anan suka kusan kaɗe wata tsohuwa tana tafe da qarfi Isya yaja burki hakan yasa sauran motocin dakatawa, nan tsohuwar ta ruɗe ta fara waiwayawa, ganin tarin motocin dake bayanta yasata dakatawa, da sauri suka fito suna duba ko lafiyarta, qalau ba abin da ya sameta.

Shurun da sukaji yasa su Ummie fitowa su duba cikin kaɗuwa da Al'ajabi takai kallonta kan fuskar matar, har Abada bazata manta wanan Fuskar ba "Mama" ta faɗa cikin rawar murya hakan yasa su kallon matar itama ta kai kallonta ga matar amma bata ganetaba, da gudu Ummie ta qarasa kusa da ita "Mama baki ganeniba, Haajara ce erki matar Hamza agarin Gumsa."

Hannunta Maman ta riqe tana kallonta cikin faɗaɗa fuska da murmushi "Ikon Allah Haajara ke ce kika dawo haka, Allah buwayi mai yanda ya so, ina ta Addu'a acikin ko wata raka akan Allah ya kare min ke, nakanyi kuka idan na tuna halin dana barki agarin, amma nasan ko da wasa bazan iya komawa cikinsaba." ta faɗa tana rungume Ummie tana shafa fuskarta "Ummie wacecec wanan ɗin?' Abdallah ya tambaya yana kallonta. Janyewa tayi tana riqe da hannunta "Mama mai ganye ce Abdallah" Anan suka saka kabbara itama tana cike da mamakin ganin Abdallah dama su Iya Indo, "Ina zaki je Mama?" kai ta jinjina "Gani nan dai bani da masauqi tun bayan barina gumsa rayuwa take min whl yau ina nan gidan masu kuɗin ina musu aiki gobe ina can."

Anna Ummie taja hannunta suka shiga mota "Daga yanzu kinbar wahla Mama xaki zauna damu har qarshen rayuwa."

Motar suka shiga sai kano, anan su Iya Indo suka fara wara ido suka kallo har zuwa gidan da suka shiga kansu ya cika da mamaki ashe basuga komiba kallo yana gaba. 

 Bayan sun sauqa suka ci abinci da abin sha aka bawa kowacce ɗakin da zata zauna su Ummie ma furr hanasu komawa gidansu Maa tayi acewarta bazata qara bari Ummie ta mata nisaba zasu zauna atare har gaba da Abadan

 Ɓangare biyu aka warewa su Abdallah shida Arfat agidan suka zauna sanan Aada ya ɗauko ko wata kadara da take mallakin Ummie da Maa ya danqa musu amma suka qi karɓa sukace ya riqe awajansa shi yafi dacewa ya ci gaba da riqewa, koda ya samu Abdallah akan maganar shima cewa yayi hakan shi ya dace domin shi dai aikin da yake ya isheshi yana jin daɗin zama akamfaniN Alh. Naseer ya kuma bashi dukkanin wata yardarsa.

Qarshe dai dole haqura yayi sai dai ya buɗe ma Abdallah wani kamfanin na qera mota ya damqa masa takaddun sa sanan aɓangaran Khaleesat itama ya buɗe mata super merket na saida komi da komi, ana kula mata da su kuɗi yana shigo mata, ya kuma qara bama Arfat jari mai tsoka ta yanda ya haɗe shagon ya zama plaza guda daga kayan atamfofi xuwa na kwalliya da takalma komi da ruwanka, sanan ya ɗauki maqudan kuɗi ya bawa Siddiqa kasancewarta ersa itama, shagon kayan ɗaki ta buɗe na mata itama ake kular mata da su. Autan Gwaggo harira shima yanzu ya nutsu sosai Abdallah ya jashi ajikinsa ya bashi aiki akamfaninsa, sanan ya nemo mata ya Aura. Shima Isya tuni yayi Aurensa Abdallah ya janyeshi daga matsayin sa na direba ya sashi acikin kamfaninsa dan idan har xai tambaya waye sila to ya tabbata Isya zai shigo cikin labarinsa, shine mutumin da ya zana sila ta haɗuwarsa Da madam khaleesat ya xama tsani na haskaka rayuwarsa cikin walwala da jin daɗi.


Bayan shekaru biyar:


Zaune suke aqaton palon daya ke gidan suna fira cike da nishaɗi acikin waɗan nan shekarun sukan kai ziyara Gumsa da Yadin Bunni haka da yawa sun taimakin mutane sun basu aiki, siyasar Aada ta qara samun muhalli agarin kano hakan yasa mutane suka dage saida ya zarce domin ko ina aka je maganarsa ake da Adalcin da yake shimfiɗawa.

 Da gudu yaran kusan biyar suka shigo gidan biyu kai ɗaya biyu kai ɗaya sai babbansu wanda shine baya gudun Asalima tafiya da gudu sai murmushin da yake yi kan Ummie suka faɗa yayin da wasu sukayi kan Maa da Mama Anta "wayyo Allah xaku qarasa mu" suka faɗa cikin haɗuwar baki haakan ya sasu yin dariya sosai "Kai ku tashi kada ku karya mana iyaye ku baku da asara." khaleesat ta faɗa tana korarsu hakan yasa su Ummie qara qanqamesu "To ina ruwanki jikinki ko namu?" suka faɗa wanda hakan yasasu yima Khaleesat gwallo, qafa ta fara bugawa alamun zatayi kuka, da sauri taji an ruqo hannunta juyawar d xatayi taga Abdallah ne hakan yasata faɗawa jikinsa tana qoqarin kuka "qyale su Ummie kema kin san halinsu gwaleki zasuyi akan jikokinsu."

Hannu su Maa suka fara tafawa "Kun jimin yara da rashin kunya, ɗauke matarka ku tafi aqyale mana jikokinmu" Maa ya faɗa tana gimtse fuska hannunta Abdallah ya ja ya ce "Zo mu tafi zasu nememu ai" Siddiqa da take ta faman lissafi acompureter ta sai alokacin ta ɗago tana murmushi da hannun ta tayima ɗaya yaron magana, wanɗa da ganinsa kamar an tsaga kara da Abdallah "Mujahid mi ya faru suke gudu haka zasu qarasa mana Iyaye"

Kai ya sinne yana tauna hannunsa kamar bazaiyi magana "Wai cewa sukayi ayi tseran gudufa."

Kai ta girgiza tana murmushi tana kaunar yaron sosai kasancewarsa mai nutsuwa ga miskilanci, acikin wanan shekarun haihuwar ta ɗaya mace suka haifa aka sanya mata sunan Ummei suke qiranta da Khairat sai kuma Su Abdallah daya fara haifan namiji shine muhammad sunan Abu Khaleesat suke kiransa da Mujahid, bayan shi ta haifi tagwaye mace da namiji aka saka sunan hamza da Maaa sai ake kiransu da Abeed da Abidallah. Sai Autan gwaggo harira shima matarsa ta haihu aka sanya sunan Iya Inso ake kiranta da Aisha.

Kai ta girgixa ba tare data musu maganaba ta nufi shashinsu jin alamun dawowar Arfat ta barsu anan suna hirarsu da shirme soyayyar jikokinsu abayyane take acikin idonsu ta yanda ko kaɗan basa ɓoyeta.


 ****

Suna fita ɗaga palon ya ɗauketa ciɗak bai sauqetaba sai anasu palon hakan ya sata murmushi tana kallonsa sai miqar da hannu yake yana kiran "Washh na gaji da yawa, nauyinki ya qaru akan na da."

Baki ta fara turowa tana bibbiga qafa "Dama dan kace ina da nauyi ka ɗaukoni, bana koma wajan su Ummie." ta juya kamar zata koma, da saurinsa ya riqo ta ya ɗagata yana jujjuyata apalo hakan ya sata yin dariya mai sauti, har saida yaga tayi dariya sanan ya sauqeta ya xanarta akan cinyarta "Ke ɗin kin zama wata mahaɗin rayuwata, jini da tsoka na rayuwata, hakan yasa ko kaɗan bana gajiyawa da kallonki duk lokacin da nake tare da ke sai nake jina kamar sarkin da yake mulkar duniya, bana taɓa gajiyawa da ɗaukanki ji nake kamar dama can ina tafiyane da taimakawar ganganar jikiki, sosai nake sonki nake kuma fatan qare rayuwata aqarqashin baki kulawa da dukkanin farin ciki."

Murmushi take mai sauti taka kallon bakinsa da yake fidda sautin ko wata kalma hakan yasata kwanciya akan qirjinsa ta sauqe ajiyar xuciya akai akai "Ban san.ya rayuwa zatayi dani aduniyar da babu kai ba, ka cika duniyata da farin ciki, ka qawata zuciyata da qarfafa guiwa daga mai rauni zuwa mai jarumta, na ɗauka kai mutum ne kamar kowa sai daga baya na fahimci kai ɗan baiwa ne ka sanar dani abubuwa masu muhimmanci ta yanda na Fahimci kalar kukan KO WANI TSUNTSU... Ada na ɗauka idan nayi TAURIN KAI zai kawo min kowani cikar burina sai daga baya na fahimci shi kansa TAURIN KAI MAFARI NE NA WAHLA Ina sonka fiye da yanda Khairata ta Sadaukar da soyayyarta ga MA'ARUF alokacin da tayi SARTSE da samunsa dolo kuma marar wayo Afannin rayuwa da xamantakewa."

  Kanta ya shafa yana qayatar da murmushi mai yawa asaman laɓɓansa "Kin mayar da wanan Abdallah jarumi ta yanda yake tunkarar ko wata matsalarsa ba tare da ya duba matsayin da ya takaba, daga baya na fahimci gaskiyar Amatullah da tayi GUDUN NASARA atare da Saleem aboki, sai dai labarin yasha bam-bam dana BINTU ZAHRA ita kuka take saboda gararin rayuwa sai dai duk da haka bai kai wanda NABEELA tayiba acikin RAYUWARTA. Zan tsaya miki na qawata ko wani jin daɗi na rayuwarki fiye da wanda Abunah yayi lokacin daya farga da HAƊIN GWARMAI ne ke tsakaninsa da Ummienah."

Daga haka ta qara qanqameshi tana murmushi shima yanayi.


🥀🥀🥀🥀


 ALHAMDULILLAH anan na kawo qarshen wanan labarin na HAƊIN GWARMAI wanda ya ɗaukeni tsawon watanni shidda ina rubutawa, tabbas godiyata agareku tana da yawa wajan jajurcewarku da haquri wajan bibbiyar labarina kuna da yawa ta yanda bazan iya lissafo sunayenkuba amma adunqule ina alfahari da waɗan nan grps ɗin da kuma godiyata agareku:


FEENAT JA'AFAR NOVEL

MUSHA KARATU NA YBK

ZAUREN SANAH

AISHATU NOVEL (MMN ANSAR)

SOPHIE AN VC NOVEL

KHADEEJA CANDY NOVEL

Dama sauran grps ɗin da ban san sunansuba saqonninku yana riskata ina kuma godiya sosai agareku.

Sanan daga qarshe ina miqa jinjina ta musamman agareku ANTY JIDDA MUSA da SANAH S MATAZU qwarin gwuiwarku acikin tafiyar labarina tana da yawa har ABada baxan manta da kuba, ngd sosai da dukkanin komi.


Idan da rai wata qila ku sake jina acikin sabon Labari.


©by Um Nass


Tags: Kaddara #juriya #hakuri
9627
0
1
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!