Fayrooz 1 (edited 2019)

Written by Ashnur PyarPublished on 2019-02-14 21:50:47Category SpiritualFAIROOOZ labari ne mai cike da tarin sark'ak'iya da abubuwan na ban Al'ajabi! Maryam yarinya ce da taso cikin rayuwar kad'aici, domin ba ta san kowa ba sai Datijjon Mahaifinta Malam Hafeez, wanda suke rayuwa cikin wani keb'antaccen daji, wanda gaba da bayanshi, ita da Mahaifin nata ne kad'ai bil'adam da ta san suna zama a cikinsa. Malam Hafeez shahararren Malami ne da ya k'ware a fannin ilmin da ya danganci bincike na Tarihi! Yana da tarin litattafai, wad'an da yake gudanar da ayyukan bincikensa, Maryam tilon 'yar tashi, ba ta da wani shamaki da dukkan litattafan Mahaifin nata, sab'anin wani littafi guda d'aya tak, wanda a ka yi masa rubutu da launin ja, shud'i da kuma kore, rubutu ne da manyan bak'ak'e a jiki, wanda aka rubuta suna *FAIROOZ* a jiki!. Wata rana, Maryam ta yi nasarar d'auko littafin Mahaifinta mai suna *FAIROOZ* ta bud'e, abin mamaki! Da bud'ewarta wani irin haske ya soma fitowa daga cikin littafin, lokaci guda kafin ta farga, wannan hasken ya zuk'e ta zuwa cikin littafin, wanda hakan ya yi sanadiyyar tsintar kanta cikin wata sabuwar duniya ta daban da wacce muke ciki!. Ku biyo Alk'alamin Ayshnur pyaar domin jin cikakken labarin. tags: Al'ajabi Nishad'i Tarbiyya Soyayya Addu'aDuba was labarai »

FAIROOZ

 

NAGARTA WRITERS ASSOCIATION

 

FAIROOZ!

 

Daga Alk'alamin Ayshnur pyaar✍️

 

  Babi na farko. 

 

BISMILLAHIRRAHMANIR-RAHEEM

 

Daddad’ar iska ce take kad’awa cikin sanyin safiyar ranar Laraba wanda masu iya magana kewa kirari da Laraba tabawa ranar samu.

Kishinged’e take kan kujera mai kama da gado, yayin da iska ke kad’awa da siraran gashin da suka zubo a gefen goshinta. 

Cike take da farin ciki tare da nishad’in, ganin cewa yau ta yi nasarar d’auko LITTAFIN da kullum Babanta ke mata shamaki a kansa. Tana sa ran yau lallai zata ga abin da ya dad’e yana b’oyemata a cikinsa!.

MARYAM kenan ‘ya a gurin Malam Hafiz, shahararren Malami mai bincike a kan a bin da ya shafi TARIHI na duniya.

Maryam ita ce ‘ya d’aya tilo a gunsa bata san kowa ba sai Mahaifinta. Kasancewar a daji suke da zama. Tun bayan kammala karatunta suka tattara komai nasu suka koma cikin daji, ita kanta ta rasa dalilin aikata hakan daga wajen Mahaifinta!.

Mahaifiyarta tun bayan haihuwarta ta rasu. Wannan shi ne dalilin da yasa bata san kowa ba sai tarin littattafan Babanta wanda a kullum yake cikin aikin nazarce-nazarce dasu. Maryam tana da ikon tab’a duk littafin data ga dama a cikin d’akin karatun Babanta, sai dai akwai littafi d’aya daya hanata tab’awa wanda iya abin da take iya hange a jikinsa shi ne wasu zane da a kayi da wasu launika guda uku. Red, blue and green(wato launin ja da shud’i da kuma kore).

Amma ba ta iya fahimtar abin da aka rubuta da sauran kalolin sai na k’arshen da aka yi rubutu da manyan bak’i FAIROOOZ......shine abin da take iya ganewa a jikin littafin.

 

Yadda aka yi har Maryam ta sami nasarar d'auko wannan littafin sirrin baban nata a yau shine.

Ya kasance a duk ranar laraba ta duniya Maryam takan gyarawa Babanta cikin d'akinsa ko'ina da ina, kasantuwar Malam Hafiz yakan bar gida ya shiga daji, in ya tafi tun safe sai yamma yake dawowa, duk da tilon 'yar tasa tayi-tayi akan ita ma ya rink'a zuwa da ita ko ba kullum ba, amma Sam!yaki amincewa, ta kuma rasa dalilinsa a kan hakan. 

Tun tana jin tsoro idan ya tafi ya barta har tazo ta sabar ma kanta, shine dalilin kuma da yasa takan yi gyare-gyaren kowane sak'o da sak'o na ciki gidan idan baya nan.

 

Yau ma ta kasance ranar Laraba ce, kamar kowane mako yadda ta saba yi, ta kammala gyara ko ina sai d'akin littattafan Baban nata kad'ai ya rage.

 

Inda ta shiga ta fara goggoge littattafansa wad'an da suka yi k'ura, tana cikin haka kwatsam! Saita hango wani K’aton akwati akan tebur wanda yaja hankalinta ga barin goge gogen data keyi.

K’arasawa tayi daidai kan tebur d’in. Akwatine gashi nan duk k’ura ya b’ata shi.

Sai ta sanya hannuta ta d'an share saman sa, Nan take taga wani haske ya bayyana akan saman akwatin wanda tsananin fitar hasken yasa dole sai da taja baya.

Bayan b’acewar hasken da 'yan wasu dak'ika, wasu manya manyan zanen rubutu ne suka fito b’aro b’aro kala d'aya sak! Da launikan rubutun nan da ta ke gani a jikin (littafin SIRRI na Babanta) kamar yadda take kiran littafin a wajenta!.

Ba wasu launika bane, face kalar nan na red, blue da green (launin ja, shudi, da Kore) Har’ ila yau ma, rubutun na k’asan wancan littafin shi ta k’ara gani, rubutu ne da manyan baki ya fito kamar na littafin nan data ke son bud’awa FAIROOOZ…………taga an rubuta ajikin akwatin.

Daga k’asan sunan kuma wani d’an kogon ramine kamar nan ne wajen mabud'in akwatin.

Maryam da karambani, tasa d’an yatsarta a daidai saitin ramin dake jikin madanni ta danna nan take akwatin ya dare gida biyu!.

Wani kyakkyawan takobi ta fara yin tozali dashi, yana shek’i da haske daga tsakiyar cikin akwatin, daga gefe guda kuma kwari ne da baka, sai sulke sannan da wani d’an k’aramin akwati mai yanayi kamar daidai da girman littafi. 

Hannu tasa kan k'aramin akwatin ta d’auko shi, ba tare da yin wani dogon tunani ba ta bud'e....jikinta sai rawa yake yi domin ta san lallai yau ba k’aramin karambani tayi ba, na tab'awa Mahaifinta akwatin sirrinshi.

Bude k’aramin akwatin da tayi, idanuwanta suka gane mata wani sabon littafi fes-fes dashi! Wanda bashi da maraba da irin wanda Mahaifinta ke hanata d’auka cikin tarin littattafansa, domin gani tayi komai na jikin littafin iri d’aya ne, shi ma wannan har da rubutun nan masu launin ja, shudi da kuma Kore.

Cike da farin ciki ta sanya hannunta gami da ciro littafin daga cikin akwatinsa, har zata rufe akwatin sai idon ta yakai kan wani kyakkyawan k’yalle mai launin fari da ja, wanda ya burgeta sosai, shi ma a cikin d'an k'aramin akwatin yake.

Hannunta ta sanya ta d'auko kyallen, ta kara shi a hancinta wani lallausan k’amshi mai sanyi ne ya shiga ratsa illahirin duka k'ofofin shak'ar iskarta, uhhhmm……… ta shak’i k’amshin tare da lumshe idanuwanta.

A hankali ta bud'e idanuwanta, tana jin wani sabon yanayi a tare da ita, maida d'an karamin akwatin littafin ta yi ta ajje.

Sai kuma ta fara tunanin 'Yanzu idan Baba ya dawo kuma fa! Ya zanyi in yazo ya fahimci cewa gane na bud’e wannan akwatin!?

Akwatin da kwata-kwata be barinsa a fili, domin idan ya fita duk iya duban da za ta yi cikin d'akin bata tab'a ganinsa ba. Yau gashi yayi kuskuren barinshi a fili, har ita kuma ta shiga ta bud'e masa akwatinsa na sirri!.

Tsaye ta yi jim, na wani d'an lokaci. Kafin ta ci gaba da zancen zucin da take yi

'Na san lallai dai duk yadda aka yi mantawa ya yi yabar wannan babban abu mai mahimmancin gaske a wurinsa, inba mantuwa ba, babu abin da zaisa Baba ya bar akwatin nan waje, balle har ni kuma na kai ga samun damar d'aukar abin da nake matuk'ar muradin son ganin ko me ke cikinsa. Wato littafin nan mai suna FAIROOZ!'

Sai ta rungume littafin a k'irjinta, tana lumshe Idanuwanta.

"Dole nasan abin yi, kafin Baba ya dawo ya fahimci abin da nayi!'' Ta fad'a a fili.

 

         Babi na biyu.

 

Maryam na nan tsaye tana sak'e-sak'e cikin zuciyarta, sai dabara ta fad'o mata!

D'ayan d'akin Babanta Malam Hafeez ta nufa da d'an k'aramin akwatin a hannunta.

Littattafansa ta d'auka, ta rink'a gwada wa, ko za ta sami wanda girmansa zai zo d'aya da akwatin hannunta.

Cikin ikon Allah ko ta sami wani littafi da ya shiga ciki daidai, sai ta sanya marfi ta rufe. Ta koma da gudu d'akin da ainihin babban akwatin yake, ta sanya k'aramin aciki, sannan ta jawo b'ari da b'arin marfin akwatin daya bud'e dazu bayan ta danna madannin nan, ta had'a akawatin ya kulle.

Ta kalli littafin dake hannunta ta rungumesa a k'irjinta cike da jin dad'i.

Har ta juya da nufin barin d'akin sai wani tunani ya sake zuwar mata kuma, wasu k'ullin kaya taje ta d'auko masu datti da k'ura a jiki ta kakkab'a su akan akwatin, ya dawo kamar yadda yake a farko, "yauwa! Yanzu ko Baba ya dawo bazai gane na shigo wurin zo nan ba, bare aje ga tunanin na bud'e akwatinsa!"

Fitowa waje tayi gami da jawo k'ofar ta rufe.

Lambun gidan nasu ta nufa cikin jin dad'i da walwala.

Kujerarta da ta saba hutawa a kai ko da yaushe nan ta zauna.

 

CI GABAN LABARIN

K'urawa littafin idanu ta yi sosai.

 

'SHIN WANENE FAIROOOZ?'

Tambayar da tama kanta kenan cikin zuciyarta. Wanda daman ta dad'e tana yiwa kanta wannan tambayar ba tare da tab'a tunani ko mafarkin samun amsarta ba!

Wani lallausan murmushi ta saki, kafin ta furta, "YAU ZAN SAN KO WANENE FAIROOOZ!"

Hannunta ta sanya ta bud'e littafin dake kan cinyoyinta....shafin farko1..... fuskar kyakkyawan saurayi fari mai k'warjini da cikar zati ta fara yin tozali dashi, yana zaune akan doki fuskarsa tana fidda murmushi mai cike da annuri!

Maryam ta k'ara b'ude shafin dake gaba........sai ta sake ganin hoton saurayin a bakin wata k'orama ya d'aga hannu sama da alama wasa yake yi da wasu zanen tsuntsayen da ta gani saman hoton nasa.

Murmushi ta yi abin ya burgeta, sai ta k'ara bud'e shafin gaba shafi na uku......nan kuma kwance ta gansa cikin filawowi yana wasa da wata 'yar tsuntsuwa a hannunsa! Adaidai nan Maryam ta rufe littafin ta murmusa.

Tace "Daman fuskar wannan kyakkyawan saurayinne Baba ke b'oye min kullum! To me ya sanya?

Me yasa Baba yake b'oyemin littafin nan? Ashe ma ba komai bane ciki."

Sai dai da ace Maryam ta san abin da take k'ok'arin tonowa kanta a dalilin wannan littafi da ta rik'e a hannunta, da ba ta yi marmarin d'aukosa daga inda Mahaifinta ya b'oye shi ba, bare har ta kai ga bud'ewa!

 

Hannu tasa ta sake bud'e littafin zuwa daidai shafin da ta tsaya, sannan ta bud'e na gabansa, nan ma tozali ta sake yi da kyakkyawan saurayin nan yana dariya kanshi d'aure da kyalle mai launin fari da ja, k'yallen ya matukar yin kyau a kan lallausan bakin gashin dake kansa.

''A'a! Wannan ai kamar irin k'yallen dana d'auko ne cikin akwatin Baba!"

Fito da k'yallen ta yi ta duba da kyau taga komai iri d'aya da wanda ke d'aure a goshin hoton saurayin dake cikin littafin hannunta.

K'amshin dake jikin k'yallen ya sake bugun hancinta sai taji wani sanyi ya ratsa ta har cikin zuciyarta. Kyawawan 'yan yatsunta ta sanya ta shafa hoton doguwar fuskar saurayin tana lumshe idanuwanta.

"FAIROOZ!"

Ta ambata a fili, ga mamakinta sai taji an sumbaci 'yan yatsunta.

Firgigit! Maryam ta yi, had'e da bud'e idanunta dan ganin wanene ya tab'a ta.

Amma bata ga kowa ba.

"A'a! Subhanallahi, anya ba ji nayi an tab'ani ba? Ko kuwa mafarki nake yi ne?

Ko da yake wani irin mafarki kuma idanuwana biyu. Amma dai tabbas ni na ji an tab'a ni."

Ajiyar zuciya ta sauke, sai kuma ta basar kawai, had'e da b'ude shafin gaba.

 

Ba ta ga komai ba nan, ta k'ara b'ude wani shafin, nan ma babu komai.

Ta sake b'udewa sai ga hoton wata K'ORAMA, gaba kad'an kuma hotunan wasu kyawawan tsuntsayene guda uku.

"Hmm ni dai ban ga abin da yake na b'oyo ba cikin wannan littafin! Ni hotunan ma kawai burgeni suke."

Maryam ce ke ta maganarta ita kad'ai.

Tana k'ara bud'e shafin gaba, taci karo da hoton kyakkyawan saurayinnan wanda ta yiwa lak'abi da suna FAIROOZ, duk'e jini na zuba daga goshinsa.

"Subhanallahi! to ya a ka yi haka ya faru kuma? Meya same sa ne?" Maryam ta tambayi kanta.

Gaba d'aya sai ta ji zuciyarta tayi bak'i, ba ta so haka ba.

Ta k'ara bud'e shafin gaba, zanen wani k'aton jeji da manya manyan itatuwa masu duhu ta gani.

Ta kai idanunta can k'asan shafin, saboda wani abu da take hangowa gaba kad'an da zanen bishiyoyin.

Ruf!..................Taji an rufe mata idanuwa ta bayanta.

Cike da tsoro da tsananin firgici Maryam tace, "WANE NE!?" Ta yi maganar ne da k'arfi cike da razana.

 

Dariya ta ji anyi tare da fad'in. "Eh lallai wato har kin ma manta da cewa yau zamu zo ko!?". Maganar da ta ji kenan ta bayanta.

Mai maganar Macece, inda ta ci gaba da fad'in "Ba yau Laraba ba, ko kin manta ne? 

Ajiyar zuciya Maryam ta sauke bayan ta gane muryar wacce ke maganar. "K'awata Amma gaskiya kin razana ni sosai ko!" Maryam ta fad'a had'e da murgud'a bakinta.

Esha cool ta yi dariya "Haba k'awalli sau nawa ina rufe maki ido baki tab'a jin tsoro ba sai na yau?

Cikin sauri Maryam ta d'aga k'arkashin kujerar hutawan da take kai, dan tunawa da ta yi da LITTAFIN FAIROOZ dake hannunta, cikin dabara ta b'oye littafin a k'arkashin kujerar ta gefen da take zaune. wani b'angare na zuciyarta kuma, na cike da jin haushin k'awar tata Easha cool wacce ta katse mata abin da take yi.

Esha cool kamar yadda Maryam ta kira ta da haka, d'aya ce daga cikin k'awayen Maryam, su HUD'U ne. Bisa al'adar k'awayen, duk ranar laraba sukan zab'i gidan d'aya daga cikinsu sukai ziyara.

Kuma duk lokacin da suka ziyarci juna, suna kasancewa cikin farin ciki sosai.

Amma yau sam, Sai Maryam taji ba ta ji dad'in ziyarar ba kwata-kwata, duk dama sauran basu k'ara so ba tukun.

'Kome ya kawomin hakan?' Ta tambayi kanta.

"Ke! Ina ta magana kinyi shiru ina hankalinki yayi ne wai?" Easha cool ce tayi magana, wanda hakan yayi sanadiyyar dawo da Maryam daga kogin tunani da ta shiga.

 

Kafin ta kai ga ce wani komai, sai ga HALIMA ita ma ta k'araso rai a b'ace.

"HALIMA kenan, hali dubu babu na banza, har kin k'araso kenan kema". Cewar esha cool.

"Eh na k'araso mana tun da ba haka kika so ba!"

Inji wacce Esha ta kira da HALIMA, sai faman cika take tana batsewa.

Fad'a ta fara yiwa wa Esha "Wato kin san zamu taho nan mu dukanmu amma shine ki ka yi wucewarki ko jira babu ko!?

"I'm so sory k'awas nayi laifi tuba nake, ayi min hak'uri." Cewar Esha cool tana me d'aga hannuwanta alamun rok'o. 

''Shi ke nan ya wuce, amma next time( nan gaba) ki ka sake wuceni bazan hak'ura ba last warning na fad'a maki."

"Eh naji dai."

''Ni kike cewa kinji dai? Lallai Esha cool wuyanki yayi kauri har ya isa yanka!"

"Eh d'in." Cewar Esha.

Aiko hali dubu tabi ta da gudu, Esha kuma ta ruga amma kan taje ko ina Hali dubu ta damk'eta nan suka zube a k'asa cikin flawowin lambun suna dariya, dama abin da yasa suka fi son ziyartar gidan k'awarsu Maryam kenan, saboda suna samin shak'atawa da wasanni na jin dad'i da annashuwa a cikin lambun gidan.

 

Maryam ce ta kama hanya domin k'arasawa inda suke, a dai-dai nan Amina wacce suke kira da ( Mrs Hydar, ta gadanga k'usar yak'i) ita ma ta iso wurin.

"Yau wato shine kuka yi tahowarku ni kuka barni ni kad'ai ko!?" Abin da Mrs Hydar ta fara fad'a kenan da isowarta wurin. Caraf! Hali dubu ta amshe da cewa 

"inji wa!? Ai Esha ce ta kamo hanyarta ita kad'ai ko jira babu, ni ma yanzun nan na iso cike nake da jin haushinta dan ina biya wa gida aka cemin ai tace wai a fad'a min ta yi gidan mu zamu had'e a can, nan ko k'arya take wutowa tayi."

"To duk ya isa haka a kashe wutar haka nan" Cewar Maryam wacce suke yiwa inkiya da (rai da so).

 

        Babi Na Uku.

 

K’awaye HUD’U kenan, wad’an da suka rik’e k’awancensu da gaskiya ba su bari ta watse ba, tun bayan kammala karatunsu.

MARYAM ita ce wacce suke wa nickname da (RAI DA SO) sai

HALIMA wacce suke kira da hali dubu babu na banza, amma in wata cikinsu najin 'yar tsoka na sai suce mata babu na zab’a. Sai Aisha wato (Esha cool).

Sannan sai Amina ( Mrs Hydar) wacce tun ba ta yi Aure ba suke kiranta da hakan saboda tsabagen son da take ma sunan Hydar, a ka yi dace kuma Allah ya had'ata Aure dame sunan.

Cikin ziyarar da suke kaiwa junansu, sun fi ziyartar Maryam sosai a bisa dalilin, d’auke ta da Mahaifinta Malam Hafeez ya yi, tun bayan kammala karatunsu, suka koma rayuwar daji shi da ita, wanda babu wanda ya san dalilinsa akan hakan ba.

Dukansu basu so rabuwa da ita ba, amma shi Malam hafeez yace zaman shi cikin jejin yafi mai kwanciyar hankali a halin yanzu, saboda cikin gari na tuna mai da wani abu da ya faru a can baya!.

Wannan ne dalilin da yasa suka d’aukar wa Maryam alk’awarin ziyartarta fiye da sauran gidajen juna da suke ziyarta, domin su rink'a deb’e mata kewa tare da k’ara gina dank’on zumuncinsu.

Yau wannan ziyara nasu bai wa Maryam dad’i ba, domin dai ta kasance cikin zuciyarta tana Allah-Allah su tafi ko za ta sake duban fuskar kyakkyawan saurayin nan, wanda haka kawai ta tsinci zuciyarta da bengen sake kallon fuskarsa, gashi hankalinta ya matuk’ar tashi na ganin fuskar mai yalwataccen murmushi a cikin jini.

Amma duk da jinin dake fuskar tasa, idan ka kalleshi za ka d’auka murmushin ya ke yi. 'Allah sarki FAIROOOZ nawa!' Ta raya cikin zuciyarta.

Sunyi ‘yan hirarrakinsu tamkar yadda suka saba yi a ko da yaushe, duk da dai yau sun fahimci k’awar tasu Maryam ba ta cikin yanayi mai dad'i, domin yau ko binsu bata yi ba, inda sukan je su tsinko kayan marmarin da suke sha yayin da suke hira.

Su kad’ai suka je, bayan sun dawo sun wanke wad’an da zasu sha, wanda zasu tafi da shi gida kuma sun ajje gefe guda, suna sha ana hira, Maryam ko tun da ta d’auki wani nunan-nen d'an k’aramin Apple ja guda d’aya a hannunta, tana rik’e da shi bata sha ba sai jujjuyashi kawai take a hannunta, ta k’ura mai idanu sai kace madubi take kallo.

Gaba d’aya hankalinta ba ya tare da ita, ta mance shaf da Mutane ma a gabanta.

“K'awa anya babu abin da ke damunki kuwa? ko dai akwai wani abu da kike b’oye mana ne?” Cewar Esha cool.

Firgigit tayi had'e da dawowa daga kogin tunanin da ta shiga, ta amsa da cewa ''Haba babu wani abu cool baby kawai dai yau na tashi banjin dad’in jikina ne shi yasa……'' 

 

Caraf Hali dubu ta cafke tun ba ta kai k'arshe ba.

 

“Kinsan shi kansa yawan zama wuri d’aya yana kawo haka ko? Ba yadda ba muyi dake ba ki fidda Miji a maki Aure kink'i...." 

''Dakata Don Allah!.'' Maryam ta dakatar da k’awarta daga k’orafin da ta fara mata, tana me d'aga mata hannunta.

''Kin san ba na son irin wannan zancen ko! To ya isa haka?''

“Is OK girls, kar a fara tone-tone, ya kamata mu koma fa domin time d'in ma duk ya tafi " Cewar Mrs Hydar.

''Gaskiya ne kam rai da so! To zamu zo mu koma'' Esha ta fad'a.

Nan take kuma sai taji kewar k’awayen nata ya kamata, tare da tunanin anya yau ta kyauta masu kuwa? Domin gaskiya ba haka suka sa bayi da ita ba.'

Godiya ta yi masu, inda ta k’ara da cewa “kuyi hak'uri don Allah, yau ba na jin dad’in jiki nane.”

“Ah! Kar ki damu fa, Allah yasa rabon soyayya ne a ka samo mana! Allah yasa wani gwarzonne ya siye mana zuciyarki." Esha da Hali dubu suka tafa suna dariya don sun lura kamar ciwon soyayya ke damunta.

Nan dai suka yi sallama tare da basu sak’on su gaisar mata su Nafisa, Nabila yarinyar Maman Andad, Bintu Junaid." Nan dai Maryam ta fara lissafe-lissafen sunan k'awayensu.

Hali dubu tace ''Ke ya isa haka duk za su ji."

Har sun juya za su tafi Maryam tayi sauri ta ruk’o Mrs Hydar, nan da nan taji idanuwanta sun kawo k'walla, gani take tamkar ba ta kyauta masu ba. 'Wanda ya taso yazo wurinka tun daga cikin gari har cikin JEJI, ai ya gama maka komai, to amma ya na iya, tunanin SAURAYIN DAKE CIKIN LITTAFINN NAN NE ya dagula min lissafina.' Duk cikin ranta take wannan zancen.

Su ko sun tsaya suna kallon ikon Rabbi! Maryam ta rik’o hannun ‘yar uwarsu sannan tana tsaye kuma tana ta faman sake-saken zuciya ba tare da tace komai ba.

Mrs Haydar ta rik’e baki tare da fad’in. ''Ke lafiyar ki Kuwa? kin rik’e ni ke baki sake ni ba kuma ke baki ce komai ba?”

K'wallar dake mak’ale a idanuwanta ne suka sub’uce mata. Tace ''Friends ina fatan ban b’ata maku rai ba? Don Allah kuyi hak’uri.”

 

Gaba d’aya suka had'a baki lokaci d’aya “Baki mana komai ba ‘yar uwa.''

Esha ta k’ara da fad’in “Ai daman yau da gobe sai Allah! Allah dai ya baki lafiya.”

''Ameen Ameen.'' Sauran suka amsa.

''Ba kice a gaida maki da Maman Ahmad ba kin san tana can 'yar uwa laulayi ya b’oye ta.'' 

“Allah sarki wayyo ku gaida min ita please, af! Na ma tuna kuce ina gaida namecy Maryam lbrahim litee, dasu Aisha ibraheem el ladan.'' Haka Maryam tayi ta lissafo sunayen k’awayen nasu kamar ba za ta k’are ba. 

Hali dubu ce tace "kai ku zo mu tafi kunji! Wannan in har muka biye mata ba za ta gama wannan lissafe- lissafen nata ba, idan ta rai da so ne to tabbas an rink'a yi kenan har mu kwana anan". Dariya suka yi ga baki d'ayansu.

Sannan suka k’ara yin ban kwana, cike da nishad’i da farin cikin ganin junansu. 

Rakiya Maryam ta masu har zuwa k’ofar gida.

Suna barin gidan Maryam ta ruga da gudu cikin lambu inda ta b’oye littafinta, don daman tana Allah-Allah su tafi.

LITTAFIN dake d'auke da sunan FAIROOZ ta sake d’aukowa, sannan ta bud’e.

Shafin nan da ta ga fuskar kyakkyawan Fairoooz d’inta cikin jini, kamar yadda ta rad'a amai suna, shi ta sake bud’ewa. 

K’urawa shafin ido tayi sosai, tare da mayar da dukkan hankalinta ga kallon duhuwan bishiyoyin nan wad’an da ta gani d’azu, a tunaninta wai ko zata iya fahimtar wani abu a ciki, sai dai harta gaji da kallon hoton ba ta iya gano komai ba.

Shafin gaba ta sake bud’ewa, a nan kuma sai ta ga hoton shafin ya sha babban dana sauran shafukan. Wani irin zane ta gani mai kama da rafi-rafi kamar kuma rijiya mai d’an zurfi.

Zanen nan da take wasi-wasin rafi ne ko rijiya ta kasa banban cewa, shi ta gani d’auke da wata alama a tsakiyarsa, kamar an juya ruwan ciki juyi sosai! To a dai dai tsakiyar inda ruwan yayi alamar zurfi, saboda juyasan da a ka yi, nan taga shaidar wani haske mai k'yalli sosai a tsakiyar ruwan ya soma tasowa.

Kallon hasken ta rink'a yi tana mamaki, saboda taga yana motsi tamkar ba cikin littafi yake ba.

Sannan wani abin da ya k’ara rud’a tunaninta shine, ganin da ta yi tun da ta bud’e shafin, rijiyar da take kallo, ko rafi ne ma ita dai ta kasa banbancewa, hasken dake fitowa daga tsakiyar hoton, gani ta yiyana kad'awa kamar cikin iska!.

 

Haka wannan hasken ya ci gaba da kad'awa yana motsi kad’an kad’an, Maryam dai tana nan zaune tana kallon ikon Allah! hasken na ta k’aruwa a gabanta.

Maryam da karambani sai kawai ta yanke shawarar sa hannunta domin tab’a hasken dake tasowa daga cikin littafin, tana tab’awa kuwa sai taji ta zuuuuuuuuuuu…..........Gaba ɗayanta hasken ya zuk'e ta zuwa cikin littafin, ma'ana ta shige cikin littafin da take kallon hotuna cikinsa!.

 

         Baba Na Hud'u

 

 

Ga mamakin Maryam sai ganin kanta tayi ta ɓullo cikin wata sabuwar duniya daban, da irin wacce muke ciki!.

Domin duniyar da ta tsinci kanta, ko da ta duba sararin samaniyan-sa saita gansa launin green da blue ( kore da shuɗi) sharrrr.... 

Maryam ta duba inda take gaba da baya, gabas da yamma, ba ta ga kowa ba.

Daga can gefe guda kuma ta hango littafin da take kallon hotuna cikinsa yana nan kamar yadda yake bai canza daga shafin da ta buɗe ba.

"Ikon Allah! ta ya aka yi nazo nan kuma? Wannan wace irin duniya ce!?""

A lokaci ɗaya kuma tsoro ya ziyarci zuciyarta, nan take ta fara karanto Addu'oi a bakinta, bakin nata har rawa yake yi saboda tsoro da firgicin da ta ji sun hana ta sak'at. 

Bata jima tana tasbihi ga rabbussamawati ba! taji wata 'yar nutsuwa ta shigeta, nan take ta ji ta sami k'warin gwiwa sosai!.

Tafiya ta fara yi zuwa inda ta hango littafinta, tana zuwa daidai wurin ta kai hannu domin ta d'auka, sai littafin ya matsa daga inda yake, ta sake kai hannu karo na biyu nan ma littafin ya sake matsawa, ba tare da kuma ta ga wanda yake taɓa littafin ba. Zuwa yanzu Maryam taji tsoro yayi k'aura daga zuciyarta, dan haka sai ta ci gaba da bin littafin.

Babban burinta kawai shine ta samu damar rik'e littafin a hannunta, ko da Allah zai sanya taga hanyar da littafin zai maida ita duniyar da ta baro.

 

Bin LITTAFIN Maryam ta ci gaba da yi, amma har ila yau bai tsaya ba, tana cikin haka ne taga littafin ya bi wata hanya, ya shige cikin duhuwan wasu bishiyoyi. Dai-dai da irin wad'an da ta gani a hotun dake cikin littafin me sunan FAIROOZ!.

Ba ta tsaya yin wani dogon tunani ba, ita ma ta shige cikin duhuwar da ta ga littafin ya shige, wanda har yanzu ba ta san wanene ke janye littafin yake tafiya da kanshi ba.

 

Addu'a ta ci gaba da yi har ta shige gaba d'aya cikin duhuwar, anan ne kuma ta nemi littafin ta rasa babu shi babu alamarsa.

 

Ita kanta ba ta iya ganin ko da tafin hannunta, bare kuma littafin da ta biyo cikin wurin.

 

"A'a! Lallai yau ni dai na san na d'ibo ruwan dafa kaina". Maryam ta fad'a a fili.

 

Kamar walk'iya kuma, sai taga haske faal! ya mamaye gun a lokaci d'aya, ba tare da ganin wanda ya kunna hasken ba.

 

Faruwar hakan ke da wuya, ta hango wani d'an k'aramin zomo, amma kalar jikinsa a madadin fari, sai ta ganshi blue da green (shud'i da kore). Kama baki ta yi.

"Wannan shi kuma wani irin zomo ne haka?.'' Kafin Maryam ta gama mamakin kalar dake jikin zomon da ta gani, sai ta hango zomon ya doshi wata hanya da 'yan tsalle-tsalle irin nasu, ba tare da b'ata lokaci ba ita ma tabi bayansa, a zuciyarta tana tunanin k'ila ko zata samu hanyar fita daga wannan sabuwar duniyar da ta tsinci kanta ciki.

D'an zomon nan na zuwa wata k'ofa sai ya jingina da jikin k'ofar, hakan na faruwa sai gani tayi ya b'ace, babu shi babu alamarsa.

Ita ma ba ta yi wata- wata ko jiran yin shawarar komai ba, taje ta jingina da k'ofar. Kamar dai yadda zomon yayi ita ma tayi tare da fad'in ''Komai ta fanjama....fanjam.''

 

B'at! Ita ma, sai ta b'ace!.

 

         Babi Na Biyar.

 

Wani yalwattaccen sabon fili ne kuma ta tsinci kanta cikinsa.

Wuri ne mai matuk'ar kyawun gaske! Wanda duk wata halittar da ta tsinci kanta a gun, sai ya burgeta. Haka kawai Maryam taji kamar ta yi ta zama a wurin. 

Daga gefe guda kuma na cikin filin, wani kyakkyawan lambu ta hango mai cike da kayan marmari da nau'in itatuwa daban-daban.

Daga k'asa kuma wasu launukan filawowi ne, suma kala daban-daban, masu kyawun kallo da ban sha awa.

Daga gefe guda can kuma ta hango wata k'orama, wacce ruwanta ke da matuk'ar haske sai gudana ya keyi abinsa.

Duka wad'an nan abubuwan Maryam tayi nazarinsu ne cikin dak'ik'un da basu wuce biyar ba. Daga nan inda take tsaye tana iya hango hasken ruwan k'oramar nan da yadda ruwan cikinsa ke tafiya a hankali a hankali. Dama kuma k'ishi ya ishi Maryam, musamman saboda gudun da ta sha wajen bin zomon da ta gani bayan shigowarta cikin wannan sabuwar duniya.

Bakin k'oramar ta k'arasa, sa'annan tasa hannuwanta ta d'ibo ruwan da bismillah ta fara sha.

Hajiya Maryam barka da zuwa BIRNIN SOYAYYA!''

Daga bayanta taji wani irin tattausan murya mai narkar da zuciyar wanda duk ya kasance ma abocin saurarenta.

Amma duk da dad'in muryar nan da Maryam taji, hakan bai hanata razana ba, dalili kuwa tun da ta tsinci kanta cikin sabuwar duniyar bata ga kowa ba, bare motsin wani, sai ko wannan d'an zomon da ta gani d'azu, wanda a sanadiyyar shi ne ta ganta ta b'ullo gun lambun data ke shan ruwa a k'oramar dake cikinsa yanzu!.

Cikin firgici had'e da razana ta waigo lokaci d'aya tare da mik'ewa tsaye daga tsugunnan da ta yi a bakin k'oramar da take shan ruwa.

Ba kowa idanuwanta suka gane mata ba face fuskar wannan kyakkyawan saurayin da take kallon hotunansa cikin littafin daya zuk'eta zuwa cikin wannan duniyar, wato saurayin da ta yiwa lak'anin suna da FAIROOOZ!.

Murmushi ya sakar mata tare da k'ara maimata abin da ya fad'a da farko,

Hajiya Maryam barka da zuwa BIRNIN SOYAYYA!''.

"Bawan Allah wane ne kai! Ya a ka yi kasan sunana, kuma ina nake a nan yanzu?'' Lokaci guda ta jero masa wad'an nan tambayoyin.

Murmushi ya sake yi, ba tare da yace mata komai ba, juya muryarsa yayi tare da yin wani abu kamar fito, fiuuuuuuuuu...sauti mai dad'i ya fita kai kace usur ya hura, nan take sai ta ga sun b'ace daga wancan lambun da suke ciki, sun b'ullo kuma a wani sabon lambu, wanda ya k'ere wancan na farkon kyau da tsaruwa!.

Domin a wannan lambun har da wani babban rumfa ta gani mai ado da k'awa na kayan k'yalk'yalin haske, ko ina cikinsa hasken k'wayaye ne ya cikasa tamkar wutan lantarki, ga wata darduma ta alfarma an shinfid'e a k'asa gaba d'aya! Daga gefe guda kuma wani tebur ne, cike yake da kayan Abinci da kuma kayan marmari na nau'in itatuwa daban-daban.

"Bismillah!." Ya nuna mata hannunsa alamar ta shiga cikin rumfar.

 

Ta bud'e baki da niyar yin magana sai ya dakatar da ita da hannunsa. Yace, ''Dakata! Kar kimin gardama, don ba a yin musu a nan.''

Cikin sanyin jiki Maryam ta taka zuwa cikin rumfar, kamar yadda ya umurce ta.

Tana sanya k'afafuwanta akan shinfid'addiyar darduman dake cikin rumfar, wani irin tattausan laushi taji sun ratsa k'afafuwanta.

Laushin da Maryam taji a k'afafunwanta tun da take bata tab'a jin abu mai tushi irin wannan ba, wannan ya faru ne duka a sanadiyyar taka kafet d'in da ta yi, a lokaci guda kuma taji wani abu mai sanyi daga jikin kafet d'in yana fesowa a k'afarta tamkar yayyafin ruwa. Nan da nan kima k'amshi ya gauraye wurin.

Duk inda ta sanya k'afarta sai taji wannan ruwan mai sanyi yayi feshi a tafin k'afarta, sanyin yana ratsata har cikin jikinta. Kayan dake jikinta ma nan take suka canza zuwa wata shiga irin ta alfarma tamkar sarauniya sai shek'i takeyi.

Abin ya baiwa Maryam mamaki ganin kayan dake jikinta suma sun sauya, ba tare da sanin wanda ya sauya mata su ba. 'To ko dai duniyar Aljanu na kawo kaina ne? Idan ba haka ba taya za'a canzawa Mutum kayan dake jikinsa kuma ba tare da shi ya canza su ba!'.

Tana cikin takawa kuma, daga saman kanta wasu k'ananan furanni ne taji sun fara zubo mata a jiki, suma kansu furannin k'amshi suke yi, da haka suka k'arasa zuwa dai dai inda babban teburin yake.

Wurin da Kujeru biyu masu fuskantar juna suke, nan saurayin ya nuna mata, tsayawa ta yi cak! Yayin da suke kallon juna ido cikin ido.

Har zuwa wannan lokacin, tsoro ba wai yayi k'aura daga cikin zuciyarta bane, dakewa kawai take yi, domin ta san ba ta da wani zab'in ko mafita da ya wuce tabi umurninsa, sai ko Addu'a da take ta kwararawa cikin zuciyarta. Domin Allah ya yi Maryam da rik'on Addu'a, dalilin marik'inta wanda ya tarbiyantar da ita a kan rik'o da Addu'a tun tana 'yar k'aramarta.

Saurayin ya yi murmushi, kamar ya san abin da take yi cikin zuciyarta.

'Tabbas ya san Maryam nan gaba kad'an za ta dad'a tabbatar da anfani da mahimmancin rik'o da ADDU'A!.

A tunaninta, ko da ma tace za ta gudu, to taya za ta gudamma Mutumin da b'acewa yake yi? Sannan kuma idan ma har ta gudun to ina za ta je?

Ba ta fa ma san a ina take yanzu ba, littafin kansa daya kawota wannan duniyar ma shi kanshi ya b'ace mata!.

         

        Babi Na Shida.

 

Hannu ya sanya ya jawo d’aya daga cikin kujerun da suke fuskantar juna, yace, ''Zauna gimbiyar Fairoooz, wannan ita ce kujerarki.''

Wannan karon kam Maryam ba ta yi k’ok’arin gardama ba, ganin lokacin da ta yi gardamar da zasu shigo cikin rumfar ba ta sami riba ba, sai ma gajeran kashedi da ta samu daga wurin wannan kyakkyawan sarayin.

Cikin nutsuwa ta zauna kan kujerar da ya janyo mata, zamanta ke da wuya, ga mamakinta, sai ga baki d’aya kayan dake jikinta suka sake sauyawa zuwa wasu kayan alfarma mai ado da duwarwatsu tamkar na zinari sai k’yelli suke da walwali, domin sun ma fi na d’azu kyau nesa ba kusa ba, nan da nan ita kanta Maryam kyawunta ya k’ara fitowa, fuskarta sai sheki take tamkar wata cikin taurari.

Gyaran murya kyakkyawan saurayin ma abocin murmushi ya yi, sannan ya fara magana da cewa ''Cikin tambayoyi guda uku wad’an da kika min d'azu, zan baki amsar k’waya d’aya tak! Kawai. Sai ki fad’amin wanne daga cikinsu kika fi buk’atar na amsa maki?

'Wannan shi dai akwai murmushi, duk sadda na had'a idanuwa dashi, murmushi nake gani a fuskarsa. Haka ko a bakin k’oramar da suka baro nan ma murmushi yake yi.'

''Kin yi shiru baki ban amsa ba?'' Muryar kyakkyawan saurayin ya katse mata zancen zucin da take yi.

K'ura masa kyakkyawan Idanuwanta ta yi, shi kuma ya sake murmusa mata.

'Wannan shi wai bai gajiya da yin murmushi ne!? Ni kyawunsa ma na ga yafi na hotunansa dana kalla cikin littafi, yafi kyau a fili nesa ba kusa ba'.

Ba tare da da yin wani dogon nazari ko tunani ba, dangane da tambayar da yayi mata, kawai sai ta mayar mishi da amsa cikin zak’uwa.

''So nake na san ina ne nan! A ina muke yanzu?'' Cike da d’oki ta k'arasa maganar.

Murmushi ya sake yi tare da cewa, ''Kin yi tambaya mai sauk’in amsawa, wanda a tunani na ban d’auka ita zaki yi ba.''

Ya d’an ja dogon numfashi tukunna, sannan ya ci gaba da cewa, ''Da ace kin sake tambayata taya aka yi kika zo wannan duniyar? Da kuma yadda aka yi nasan sunanki, to da ko kinsan wasu abubuwa masu matuk’ar mahimmancin gaske, dangane da rayuwarki, wad’an da nasan kina da buk’ata da son saninsu ko ba yanzu ba, domin suna da matuk’ar mahimmanci wajen amsa miki tambayar neman sanin hak'ik'anin ko ke wacece!''.

Cikin sauri ta d’ago kanta tana kallonshi, idanuwanta d’auke da mamakin jin yace ba ta san ko ita wacece ba.

Tambayar da takewa kanta "Taya a ka yi Mutumin da ban san ko wanene ba, ban tab’a ganinsa ba, yake ik'rarin cewa ni bansan kaina ba?"

Ganin ta kafesa da Idanuwanta ne yasa shi cewa “k’warai abin da na fad’a haka yake, ke kanki ba ki san ko ke wacece ba, sai dai kash! Kamar yadda na fad’a maki a farko yanzu amsa d’aya zan baki.

Tambayar da kika min yanzu, kin buk’aci sanin ina kike ne a nan, to amsar dai bata canza ba daga batuna na farko, wato nan da kike gani DUNIYAR SOYAYYA CE! Kina cikin BIRNIN MASOYA! Masoyi kad’ai da masoyi ke iya shigowa cikinta, walau masoyan da suke tare ko wad’an da basa tare, jinsin Mace ko Namiji, Mutum kuma ko Aljani. 

Duniyar nan da kike gani ana zuwanta ne kawai a bisa dalilin soyayya, kamar yadda kema na san dalilin soyayya kika zo nan!.”

Cikin mamaki ta d’ago kyawawan idanuwanta ta sauke su a fuskarsa, idanun nata har ila yau cike suke da ayar tambaya.

Murmushi ya sake yi, kafin yace, “wannan gaskiya ne Maryam, abin da nake fad’a haka yake, tabbas! Mak’asudin zuwanki duniyar nan SOYAYYA CE.

Sai dai akwai abubuwa masu wuyar gaske a cikin duniyar nan, akwai manya-manyan HADA’RURRUKA, RUD’ANI, K'ALUBALI tare da abubuwan ban AL'AJAB! Lallai akwai gagarumin aiki a tare dake, nan gaba kad'an ba da jimawa ba.

Ga Abinci nan kici kisha duk abin da kike da buk’ata, na cika ki da surutu, zan barki yanzu, sai anjima za ki ganni, ki sani Maryam baki da muradin zuciyar da ya wuce FAIROOZ!''.

Kafin Maryam ta sami halin yin magana.

B’at! ya sake b’acewa, ta nemeshi ta rasa.

'Shin wanene FAIROOZ!?' Maryam ta tambayi kanta.

 

       

      Babi Na Bakwai.

 

''Yeih Fairoooz koun hei! Yeih sab kya hei? (Wai shin wanene wannan FAIROOZ d'in? Me wad'an nan abubuwan duka suke nufi!?'' Maryam ce duk ta fad’i haka cikin harshen indianci, muryarta kamar za ta yi kuka, kana kallon fuskarta za ka ga tsantsar rud’ani gami da tashin hankali!.

A hankali Maryam ta tashi daga inda take zaune. Dalilin wata hanya da ta hango.

Hanyar ta doshi wani makeken gida, wanda ke can gaba da inda rumfar da taso yake.

Wanda kwata-kwata da Idanuwanta basu hango mata wannan gidan ba.

 

Kafin Maryam ta k’arasa ga k’ofar gidan, sai kuma ta tsaya cak! Tana shawara. 

'Ta k’arasa ne ko kuma ta tsaya, shin idan taje yanzu ta shiga gidan ta san gidan wanene? Kuma ba ta san menene a cikin gidan ba!'

Tana nan tsaye dab da k’ofar gidan, daga inda take tsaye tana iya hangen d’an mak’ulli da aka sagale a jikin k'ofar, da alama shine mabud’in shiga cikin gidan.

Maryam na nan tsaye tana ci gaba da tsake-tsakenta, ba ta kai ga yanke shawarar abin yi ba, kamar daga sama sai taji ance,

"INA ZAKI KUMA?''

Da saurinta, ta juyo dan ganin mai maganar.

Kyakkyawan saurayin nan ne ma’abocin murmushi ta sake gani yana yi mata murmushinsa. 

''Ina zuwa haka da sauranki ta fairoooz!?”

Ya sake fad’i cikin murya mai taushi.

Dubawan da Maryam za ta sake yi sai ta ga wayaaam! Babu wannan gidan da take harin zuwa. 

'Yanzu-yanzu nan kenan shima ya bace, babu shi babu alamarsa?' Ta tambayi kanta.

Cikin tsoro da firgici ta sake dawo da dubanta ga kyawawan saurayin, kafin tace wani abu ya rigata yin magana.

''Ya aka yi ke dana bari cin Abinci kuma shine kika taso zuwa nan! Shin kinsan ina ne nan kika zo kuwa?''

Cikin muryar kuka Maryam tace, ''Don Allah bawan Allah kai wa Allah ka daina razanar dani, ka taimakeni ka fad’amin ko kai wanene? Kuma waya kawo ni wannan duniyar!?” 

Sunkuyo da kansa ya yi dai dai fuskarta, ta yadda har suna iya jin saukar numfashin juna. 

"D’ago idanunki ki kalleni, tun da kince Allah!''.

Ba ta musawa umurninsa ba, cikin sauri ta d’ago da kyawawan fararen idanuwanta, ta saukesu a cikin nasa. Wani irin abu yarrrrr taji a jikinta. 

Yace, "Sunana FAIROOOZ ibn ABBAS! Idan kina muradin son jin cikakken labarin koni wanene, sai kin saki jikinki dani, bazan cutar da ke ba, kin ji?”

“To...h.” Ta amsa mishi cikin raunatacciyar murya me d'auke da sautin kuka.

''Taho muje kici Abinci kin ji, na san yunwa kike ji sosai, ga shi karambani bai bari kinci Abincin dana bar miki ba, kuma na san baki yi sallah ba, ko da yake kina cikin fashin sallah kwanakin da suka wuce, amma yau ai kin fara kafin ki shigo nan."

Cikin mamaki Maryam ta d’ago kanta!.

Aiko tana d’agowa suka had'a idanu, Fairoooz ya kanne mata ido d’aya, a lokaci guda kuma ya haskata da wani kyakkyawan murmushi. Cikin sauri Maryam ta sa hannu ta rufe idanuwanta.

Haka kawai sai taji ta tsinci kanta cikin jin matsanancin kunyarsa, wani nauyinsa ya saukar mata, sannan ga wani sabon yanayi da ta soma tsintar kanta ciki game da wannan kyakkyawan saurayi mai k’warjini da haiba, wanda har yanzu ba ta san cikakken wanene shi ba!.

''Tunanin me kike yi? Na ce ki taho muje ko!?''

Firgigit Maryam ta sake yi, dalilin farkawar da ta yi, daga kogin begen da ta shiga.

Cikin nutsuwa suka fara tafiya, har suka k’arasa ga rumfar alfarman dake d’auke da kayan Abincin da ta bari a d'azu.

Yanzu ma sake zama sukayi suna masu fuskantar juna. 

Ganin bata ce komai ba sannan kuma tak’i tab’a wani abu daga cikin jerin tarin Abincin dake gabansu, shi ya sanya Fairoooz yin Bismillah, ya fara cin Abincin, wanda ko da Mutum Ashirin ne suka taru wurin kowa zaici ya k'oshi, ba tare da sun iya cinyewa duka ba.

“Kici Abinci nace, ba na son maimaita magana fa fiye da sau d’aya! Gashi ke nayi maki magana yanzu ya kai sau uku.'' 

Sai da ya lumshe Idanuwansa, sannan yace,

''Kawai idan na yi magana ayi abin da nace.!” 

Maganarsa ta sake dawo da Maryam daga duniyar wasi-wasin da zuciyarta ke ciki.

Tunani ta keta sak’awa tana warwarewa, tambayar kanta take 'Shin ta ci Abincin nan ne ko kar taci?

Gashi dai ina jin yunwa sosai, sai dai ban san ainihin daga inda aka samo wad'an nan Abincin ba, shin yanzu idan naci, Abincin Mutane ne naci ko na ALJANU? Sannan FAIROOOZ Mutum ne shi ko kuma AlJANI?"

''Kibar tunanin da kike yi tukunna, ki daure ki ci Abincin, idan kin gama ci zan miki bayani, na san akwai tambayoyi masu yawa k’unshe cikin zuciyarki.

Sannan ina buk’atarki da ki daure ki saki jikinki dani, ki d’auka cewa tamkar mun dad’e da sanin juna ni da ke, idan kin yi k'ok'ari kin gama ne, sa’annan sai na fad’a maki ko Abincin na su waye? Da kuma wanene Fairoooz d’in naki!.”

Kallonsa ta kuma yi da sauri, tana mai mamakin yadda a ka yi yasan abin da take tunani cikin zuciyarta.

Suna sake had’a idanu sai ya kanne mata ido d’aya, ''Kinsan ni mallakinki ne ke kuma tawa ce!”.

Sai da ya d’an dakata, tare da sauke numfashi a hankali, sannan ya d’ora da cewa, “Na san tambayar da za ki yi min shine, ya aka yi nasan abin da kike sak’awa cikin zuciyarki? To ka da ki yi mamaki a kan hakan, domin ni ke da mulkin zuciyarki! Ni muradin zuciyarki ce! Nine masoyinki na hak’ika, kinsan da ni dake soyayyace ta gaskiya a tsakaninmu, Allah ne ya had’a soyayyarmu tun muna K'ANANA. Saboda haka komai naki nawa ne, nawa kuma naki ne, har da tunaninki ma duka mallakina ne, musamman kuma ma yadda ya kasance a kaina kike tunanin naki!''.

 

Maryam da dai taga babu sarki sai Allah. Ga kuma kalamai masu rikirkita tunani da Fairoooz ke ta jero mata, tamkar yana son ta tuno wani abu, ita kuma Allah ya sani bata tuno komai!.

 

Sai ta yi Bismilla kawai ta fara cin Abincin.

 

'Tun da na ga alamar kamar yana sona, nasan ba zai cutar dani ba. Kuma kowa ya dogara ga Allah to ya isar masa a kan komai!'.

 

Cikin zuciyarta take wannan zancen.

 

        Babi Na Tara.

 

Tace, "Menene wad'an nan kuma!?”

Fizgo hannunta kawai yayi cikin tsananin sauri suka kama gudu, domin ba shi da cikakken lokacin da zai ba ta amsar da take buk'ata a daidai wannan lokacin.

Gudu suke ba k’akk’autawa.

Ya yin da bak'ak'en Jemagun nan ke bin bayansu suma, suna kawo farmaki a kan Maryam. Amma sai dai Fairoooz ya tsare ko ina yana kareta, ta hanyar sukarsu da takobin da ya bayyana a hannunsa.

Suna cikin wannan halin ya soki guda d’aya daga cikinsu akan kahon zuci, nan take ta tarwatse ta zama bak’in gari had'e da zubowa k’asa.

Ganin haka yasa Fairoooz ya k’ara k’aimi wajen ci gaba da kai musu farmaki daidai saitin k'ahon zuciya, don neman cin galabansu.

Duk wacce ya soka daidai saitin k’irjinta sai ta tarwatse ta zubo gari-gari bak'i a k'asa.

Haka ya ci gaba da kar kashe bak’ak’en halittun Jemagun nan ba k'akk'autawa, ana cikin haka ne Fairooz bai yi aune ba, wata daga cikin Jemagun ta mamayesa ta d'ayan gefen da Maryam take, ta zagaya, ba tare da ya ganta ba. Bai san abin da ya faru ba kawai sai dai yaji Maryam ta k’walla wani irin k’ara mai k’arfi!.

''Aaaah…!''

Cikin zafin nama ya juyo, waigowar shi yayi daidai da sadda Jemagiyar ta k’ara kaiwa Maryam suka, lokaci d’aya kuma ta k’ara kartarta a hannunta. Nan take jini ya fara fita a hannun nata.

Cikin b’acin rai Fairooz ya kai ma Jemagiyar nan wani wawan suka a k’irji, nan take ta tarwatse ita ma ta fad’o k’asa matatta.!

Sai dai Maryam ta sami wawan mummunan rauni.

Fairoooz yaja Maryam gefe guda, zuwa cikin wani d’an kusurwan rami mai kama da kogo, bayan ya samu yaci nasarar k’arasa kashe wad’an nan bak’ak’en Jemagun da suka kawo masu farmaki gaba d'ayansu.

Ya sanya hannu a jikin rigarsa ya fito da wani d’an k’yalle, iri d’aya ne sak! da wannan k’yallen da Maryam ta d’auko a akwatin da ke cikin d’akin Babanta, mai launin ja da fari.

Raba k’yallen gida biyu ya yi, sannan ya kamo hannunta yace da ita, “Rintse idanuwanki!” Ba musu Maryam ta rintse idanunta gam!.

 

Fairooz ya sanya b’ari d’aya na k’yallen da ya raba, ya soma goge jinin da, zuwa ainihin cikin raunin ciwon da aka jimata, ya yi hakan ne don ya gane irin munin da raunin yayi.

Kuka ta saka cikin murya mai ban tausayi.

''Ki yi hak’uri Maryam ki gafarce ni, na ga iya ciwon, zan kuma samo maganin da za a sanya mishi yanzun nan don ya ciko.''

D’ayan b’arin k’yallen ya d’auko, sannan ya sanya ya d’aure ciwon daga saman hannunta domin tsaida jinin dake zubowa, ba a d’au wani dogon lokaci ba jinin ya tsaya.

Idonta Fairooz ya fakaita, ya hura mata wani iska daga bakinsa a fuskarta, ba tare da ta fahimci ya yi hakan ba.

Yace, “Ina zuwa, kid’an jirani kad’an.” Ko kafin ya kammala rufe bakinsa, Idanuwanta suka fara lumshewa alamun barci. 

Bayan ya fito daga wannan d’an kusurwan gun da suka b’uya, ba jimawa barci ya yi awon gaba da Maryam. Hakan na faruwa Fairoooz ya sake b’ullowa cikin ramin da suka sami mafaka, ganin har ta yi barcin ne ya sanya shi murmushi domin ya san abin da ya yi mata.

Tsugunnawa ya yi, hannunshi yasa ya shafa inda taji ciwon, bayan wasu ‘yan dak’ik’u kad’an, ya sanya hannu ya warware d’an k’yallen da ya d’aure mata raunin dashi tun a farko.

Yana kwance k’yallan ya k’ara shafa wurin, nan take ciwon dake hannunta ya b’ace ko k’warjene babu alamarsa!.

Murmushi yayi, tare da mik’ewa tsaye, ya tsaya ya d’an k’are mata kallo tun daga sama har k’asa na tsawon wani lokaci, kayan da ke jikinta suma sai ya nuna su da hannunsa, nan take suka sauya. Murmushi ya sake yi sannan ya fice daga kogon ramin.

Bai jima da barin gun ba Maryam ta farka, amma ba ta bud’e idanunta ba.

Sai da ta jima kwance a wurin ba tare da ta motsa ba, kafin a hankali ta soma bud’e idanuwanta.

Bayan ta bud’e su gaba d'aya, sai taji hannunta fayau kamar babu wani alamar rad'ad'in raunin da aka ji mata. Tana ta da kanta kuma sai ta ga wasu sabbin sutura na daban da wanda take sanye dasu da, a jikinta.

D'ago hannunta ta yi, ta kai dubanta zuwa inda taji rauni d'azu a dalilin farmakin da wata daga cikin Jemagun nan ta kai mata. Ga mamakin Maryam sai taga ba ciwon, babu alamarshi! Gaba d’aya ya b’ace kamar da d’ai duniya bata tab’a samin wani rauni a wurin ba. Alhali d'azu-d'azu jini ke ta zuba a hannun nata, da wani irin ciwo mai tsananin rad’ad’i da ta rink’a ji a lokacin, wanda ba don d’an barcin da ta samu ya d’auketa ba, gaba d’aya da azaba ya isheta. 

Ta d’aga hannu ta juya ta sake juyawa, ba ta dai ji rad’ad’in komai ba. Murmushi ta yi, "Na san wannan bai wuce aikin Aljani Fairooz!''. Ta fadi a fili.

Domin yanzu a iya hasashenta, ta gama tabbatarwa kanta kawai da Aljani take huld’a, kuma babban damuwarta shine yadda take k'ara jin wani bak'on abu dangane dashi, yana ratsa cikin zuciyarta! A kowace dak'ik'a bak'on al'amarin sai k'aruwa yake yi a gareta.

"Allah ka sanya ba son shi dai nake yi ba!". Maryam ta furta cikin wani irin wahalallen yanayi.

Sannan ta yi hamdala ga sarki Allah, na samun waraka daga ciwon da take ji a hannunta.

Mik'ewa tsaye ta yi, ta fito daga wannan d'an mab’oyar ramin da Fairooz ya barta cikinsa.

Bayan Maryam ta fito sai ta d’an d’aga kanta sama dan ganin wai ko har yanzu wad’an nan bak’ak’en Jemagun suna nan. Amma ba ta ga komai ba sai dai hasken sararin samaniyar nan mai kalar kore da shud'i sharrrrr...Wanda har zuwa yanzu ta kasa gane wani irin duniya ce wannan.

Ta sake kai dubanta k’asa, inda jemagun suke ta fad’owa a d’azu lokacin da Fairooz ke fafatawa dasu, nan ma ko b’irb’ishen alamunsu bata gani ba.

Hakanne ya baiwa Maryam tabbacin komai ya dawo dai-dai.

Tafiya ta fara yi a hankali, ba tare da ta nemi sanin ina FAIROOZ yake ba.

A haka har ta soma nisa daga inda suka yi mab’oya, sannu a hankali take tafiyar, can sai ta hango wani abu kamar ruwa na kwararowa daga saman wani tsauni.

Sauri ta k’ara yi, cike da zak’uwar ko za ta isa wurin da take tsammanin ruwa ne take hangowa.

Abin mamaki tana k’ara kusantar wurin, ruwan kuma na k’ara yi mata nisa, madadin ya zama ta zo kusa, sai taga ta k’ara baya, sai da taci tafiya iya tafiya, gashi kuma har yanzu bata kai wurin da take hango ruwan ba, gashi ta gaji lik’is sai ta zauna a k’asa tana mayar da numfashi!.

 

Tunanin Fairooz ta fara yi, "Allah sarki bawan Allah, yanzu idan ya dawo zai ga bai ganni a inda ya barni ba, tabbas kuma na san zai tafi nemana.

Ko wani hali yake ciki a yanzu?" Sai ta yi murmushi.

A tunaninta ganin irin nisar tafiyar da tayi, to tabbas yanzu ta b'ace ma FAIROOZ.

 

Bata farga ba, tana cikin wannan tunanin kawai sai ta hango k'asar dake gaba kad'an gareta yana ruftawa tamkar girgizan k'asa, gadan-gadan kuma k'asar dake rugujewar ta fara nufo kanta.

Cikin tsananin tsoro da firgici Maryam ta juya da baya, hanyar da ta fito nan ta nufa, gudu ta fara yi, tana yi tana waigen bayanta, sai dai kafin tayi wani nisan azo a gani k’asar dake rugujewar nan har ta zo kanta!.

Ba tare da tayi aune ba, kawai sai ji tayi k’asar ta rufta da ita cikin karkashin k’asa.

''Innalillahi wa inna ilaihi raji un….Inna lillahi wa inna ilaihi raji un.'' Abin da bakin Maryam ke furtawa kenan.

Daidai fad'awarta cikin ramin ta k'walla kiran sunan Fairooz da murya mai k'arfi, tunaninta ko zai ji ta. 

Fad'i take, ''Fairooz don Allah ka zo ka taimakeni…''/Amma ina’ ruftawa kawai k’asar ke yi da ita tana k’ara yin k’asa.

Can taji ta daki wani abu gaaam! wani duhu mai tsanani ya taso ya rufe cikin k'wak’walwar kanta, daga nan ba ta k’ara sanin inda take ba kuma.

*** 

A hanakali a hankali take bud’e idanuwanta, yayin da suka soma bud’ewa kad’an kad’an suna, da haka har ta samu daman bud’e su gaba d’aya.

Wani k’aton rami ne ta tsinci kanta a ciki.

A hankali ta rink’a kewaya idanunta cikin ramin harta samu halin k’are ma ramin kallon tsaf. Ba ta ga komai ba a cikin ramin, face wasu manya manyan akwatina wand’an da bata tab’a ganin irinsu ba.!

Domin ga mamakin Maryam gani tayi kowanne akwati guda, k’asansa yana manne ne tun daga cikin karkashin k'asa, samansu kuma da kad'an ya rage su tabo saman ramin da take ciki, tamkar dasa akwatunan aka yi a wajen. 

Maryam ta kai hannu gefen kanta ta d’an shafa, wani d’an tauri-tauri taji wurin ya yi, alamar kumburi, da alama buguwar da ta yi d’azu ne bayan fad'owarta cikin ramin, wanda ba ta ma san dame ta buge ba.

Sake tab'a goshin nata ta yi tare da fad'in “Asshh!” Cikin alamun jin zafi, ta yi saurin d'auke hannun nata ta daga kan goshinta. 

Cikin dabara ta samu ta mik’e tsaye. Kafin ta fara tafiya cikin sand’a tana lamb’o, kamar wata wacce take tunanin akwai wani mai rai a wurin, wanda idan ta yi motsi mai k'arfi zai iya jiyota.

Akwatu nan da ta hango d’azu, wurinsu taje, tana tsayawa gabansu sai gani ta yi sun fara motsawa, a hankali suka dawo k'asa daidai da tsayinta.

D’aya bayan d’aya ta rink'a binsu tana kallo, duk k’ura ya bad'e jikinsu, gashi sunyi yanar gizo-gizo alamun dai sun dad’e a wajen.

Da Bismillah Maryam ta kai hannu ta share saman akwatin farko, wanda ke daf da gabanta. Nan take sai taga fuskar wasu k’ananan yara guda biyu!.

Gaba kad’an ta k’ara matsawa, sannan ta sake share saman wani akwatin dake jere a wurin, dam! Taji gabanta ya yi wani mummunar fad’uwa, saboda fuskar wanda ya bayyana jikin kan akwatin, bashi da maraba da fuskar Mahaifinta Malam Hafeez!.

        

       BABI NA GOMA

 

''Abbana!." Maryam ta fad'i cikin tsananin razana da kad'uwa, lokaci guda tana mai dafa kirjinta da hannuwanta.

 

"Me kuma ya kawo siffar fuskar Babana a nan wajen? Wayyo ni Maryam wai me ke faruwa dani ne?” ta k'arasa maganar wasu zafafan hawaye masu d’umi suna gangarowa daga idanuwanta.

 

''Ya Allah ka kawo min agaji akan wannan al’amarin.''

 

'Ko da yake duk abin da ya faru, ni na janyowa kaina, ba irin kashedi da irin jan kunnen da Baba bai min ba akan karna kuskura na bud’e wannan littafin, amma nak’i ji, gashi yanzu halin da na jefa kaina ciki, ban san ma taya zan yi in koma gida ba!'. Ta raya cikin zuciyarta.

 

A hankali kuma tace, ''To ko da akwai wani b’oyayyen lamari dake tattare da littafin nan ne da ya kawo ni wannan duniyar!? Ko shi ya sanya Baba ya yi ta b'oyeminshi bai bari sam na kai garesa?''

 

Ajiyar zuciya mai nauyi ta sauke. Sannan ta sanya hannunta ta share hawayen dake zubowa a kan k’uncinta. Gaba d’aya zuciyarta cike take da tsoro da kuma firgici, amma fa duk da hakan ba ta daddara ba.

 

Da karambanin Maryam, sake sanya hannunta ta yi, ta share saman k’aton akwatin da ta ga zanen fuska sak! Da irin fuskar Mahaifinta a jiki.

 

K’urawa zanen Idanuwanta tayi sosai na tsawon wani lokaci, tana nazarin shi da kyau! Sai a sannan ne ta lura ashe akwai d’an banbancin fuskar wannan zanen dana Abbanta. 

 

Domin shi wannan a yanzu da take dad'a kallonsa, ta iya gano alamar zanen gemu mai tsayi a fuskar dake jikin akwatin, d’azu tsananin razana da firgici ne ya sanya bata lura da wannan ba.

 

Bin tsayin zanen gemun tayi da kallo tana mamaki, gashi nan dogo a jikin akwatin, daga k’arshen gemun ne kuma sai ta lura da wani d’an k’aramin abu na shek'i, yana fitar da haske kad’an-kad’an. Idan hasken ya kawo sai ya kuma ya d'auke.

 

Maryam ta sunkuyar da kanta daf da akwatin, tana k’ara duba abin dake shek'in da kyau! Aiko abin da ta gani ya bata mamaki ashe wani d’an k’aramin key ne (wato mabud’i) shi ke fidda wannan hasken yana d’aukewa.

 

Nan take ta fara ja da baya tana fad’in “Ina! Wannan karon bazan k’ara karambanin bud’owa kaina wani abun ba kuma, ai na yi hankali, in ma samu naga na fita daga cikin halin da na jefa kaina yanzu."

 

''Matso kusa...d'iyata kar...ki koma.'' Wata shak’akk’iyar murya ce taji ta fad’i haka daga jikin akwatin.

 

Lokaci guda kuma fuskar Babanta da take gani ya rikid'e ya koma kan k’warangwal.

 

''Kar ki gaza daga jarumtar daki ka fara…na shirin ceton rayuwar d'anuwanki 'yata...''

 

Maryam ta waiga ta k’ara waigawa ba ta ga kowa ba, ta dai tabbata maganar daga jikin zanen fuskar akwatin nan ne take fitowa!.

 

"Ki d’auki mabud'in nan...ki bud'e hanya....k'ofa ce! Allah zai taimake ki...ke kad'ai ke da ikon cimmasa...domin mu munyi iya yinmu..." D’if kuma sai taji maganar ta d’auke lokaci guda kamar d'aukewar wuta.

 

Kafin tayi yink'urin yin wani abu kuma, ta jiwo wani irin k’ara mara dad’in ji ya karad'e illahirin cikin ramin, wanda ta kai har sai da ta sanya hannu ta toshe kunnuwanta wad'an da take jin suna barazanar toshewa saboda tsananin k'arar dake tashi cikin ramin.

 

Ta d'auki lokaci mai tsawo a hakan, kafin ta iya bud’e kunnuwan nata, amma kuma tana bud’ewa taji maganar da aka yi mata kafin zuwan sautin k'arar, na sake yi mata kuwwa cikin kunne tamkar a lokacin ne ake yinsa. 

 

Sai dai a wannnnan karon muryoyi bibbiyu ne ke fitar da kalaman, sai faman maimata kansu suke yi tamkar an yi tariyarsu ne daman an ajje. ''Ki d’auki mak’ullin nan ki….d’auki mak’ullin nan…..ki bud’e hanya…ki bud’e hanya….K’ofa ce…k’ofa ce….Allah zai taimake ki…..!Allah zai taimake ki…..ke kad’ai ke da ikon cimmasa...ke kad’ai ke da ikon cimmasa….domin mu munyi iya yinmu…..domin mu munyi iya yin….!!!''

 

Haka wad’an nan kalmomi su kai ta maimaita kuwwa cikin wannan ramin da Maryam ke ciki da k'arfi tamkar an sanya sifika.

 

Hajijiya taji ya fara d'ibarta, kanta na wani irin sarawa, ganin ramin tayi yana juyawa da ita, abinda ke k’asa na komawa sama...Runtse idanuwanta da k’arfi ta yi, ta rink’a nanata kalmar, Lahaula wala k'uwwata illah billah!

 

A nan take ta yanke jiki ta fad’i k’asa, wani duhu mai tsanani ya mamaye ko’ina cikin k’wak’wakalwarta, daga nan kuma ba ta k’ara fahimtar wani abu ba. Ta fad'i k'asa sumammiya.

 

***

 

Sai da Maryam ta d'auki wani lokaci mai tsawo, ba tare da ta san inda take ba, can dai Allah ya sanya ta farka.

 

A hankali ta tashi zaune, tana rik’e kanta, k’ok’arin tuno ainihin inda ma take yi, domin ta so ta manta komai dangane da kanta.

 

Nan take k’wak’walwarta ta shiga caji, ma aikantar isar da sak’onni suka fara aiki, nan da nan ko tariyar abin da ya faru tun farko suka soma dawo mata fresh. Tun daga sadda littafin nan ya zuk’eta ta shige cikinsa, da tsintar kanta a wata sabuwar duniya da tayi, littafin da ta sake gani, da yadda ta kasa d’aukarsa, d'an zomon da ta bi, zuwa had’uwarta da kyakkyawan saurayin nan wanda ta kira da sunan Fairooz, da irin abubuwan da suka faru a tsakaninsu har da fafatawar daya yi da halittun jemagun da suka biyosu, zuwa inda ya fita ya barta. Tsaf! Sai da Maryam ta tuno komai, har fitar da tayi daga inda saurayin nan ya b’oyeta.

 

Wanda hakan shine ya yi sanadiyyar rabuwarta dashi, ba ta sake sa shi cikin idanuwanta ba.

 

Ta tuno da zuwa wurin ruwa da tayi, da ruftawar da k’asa yayi da ita cikin rami…..zuwa abinda ya faru cikin ramin duk sai da ta tuno komai!. “Alhamdulillahi.” Ta fad'a tana d’aga hannunta sama.

 

Godiya ta ci gaba da yiwa Allah, da yasa har yanzu take cikin hankalinta, ashe ba hauka ta yi ba.

 

A hankali k'wak'walwarta ta soma nazarin kalaman nan da ta ji ana fad'a mata kafin ta suma. 'To wai mai hakan duka yake nufi ne? Na ji ance d'iyata, hakan na nufin akwatin gawar Abbana ne a ciki ko me? To da yaushe ma Baba ya rasu, in rasuwa yayi to wa zai sashi cikin akwati bayan binnewa ake yi. Sannan kuma ance CETON D’AN UWANA! Shin wanene d’an uwan nawa, wani d’an uwa gareni wanda ni ban sani ba? Me kuma ya sameshi wanda har ni ce kad’ai zan iya taimakonsa?' Gaba d'aya wad’an nan tambayoyi zuciyarta ce take yi mata su, kuma ta san ba ta da amsarsu!.

 

Mik’ewa tsaye tayi a sanyaye, jikin akwatin da aka ce ta d’auki d’an mabud’in nan ta nufa, ta riga ta gama yanke shawararta ta k’arshe, domin ba ta da wani zab’in da ya wuce d’aukar wannan d'an mak’ullin, tana ganin hakan shi ne abin da yafi dacewa ta yi, mai yuwa a nan zata sami amsar dukkanin tambayoyinta!.

 

Bismillah tayi had’e da kai hannu domin zare d'an mak’ullin daga jikin akwatin.

       

 Babi Na Sha D'aya.

 

Tana zare mabud'in daga jikin akwatin, wani irin haske ya biyo bayan wurin da ta d'auke key d'in.

Inda za ta sanya key d'in ya fito sosai tana gani. Hakan ya sanya ta saita mabud'in daidai jikin ramin, sannan ta murd'a. 

Ga mamakin Maryam wannan tangamemen ramin da take cikinsa, taga ya rikid'e ya koma wani babban fili wanda babu komai, sai face wani dank'areren gida guda d'aya tak! A tsakiyar cikin filin.

Daga inda take tsaye wani lallausar darduma ne mai d'auke da launin ja, shinfid'e tun daga inda take har zuwa bakin k'ofar wannan babban gidan dake tsakiyar filin da ta b'ullo.

Ba tare da tsoro ko jin wani shakku ba, Maryam ta yi Bismillah tare da d'ora k'afafuwanta a kan wannan jan darduman, domin ta san abin da ake nufin ta da ta aikata kenan.

A hankali ta rink'a takawa har zuwa k'ofar gidan, hannu ta kai ta murd'a k'ofar tana me karanto Addu'o'i a bakinta.

Tana sanya k'afafuwanta cikin gidan, lokaci guda ta ga ya rikid'e zuwa wani yalwataccen, k'ayataccen lambu mai matuk'ar kyau da girman gaske!.

Wani irin nishad'i ne ta ji ya ziyarci zuciyarta lokaci guda, domin Allah ya yi Maryam da tsananin k'aunar lambu a rayuwarta, shi ya sanya ma Mahaifinta ya samar mata da lambun shak'atawa cikin gidansu wanda ke tsakiyar Jeji, a wancan duniyar da ta baro.

 

Tsoron dake zuciyarta duka ta mata dashi, yayin da wasu kyawawan filawowi masu matuk'ar kyau da haske, suka d'aukai hankalinta.

Cikin sauri ta gangara daidai inda take hango flowers masu kyau! Tana zuwa kawai ta sanya hannunta ta cizgo guda d'aya ta kara a hancinta, lumshe Idanuwanta ta yi domin wani k'amshin dad'i da ya shiga ratsa ta. 

Sai da ta jima, kafin ta kau da d'an k'aramin filawar daga hancinta.

K'urawa flower idanu ta yi tana kallonsa, saboda tsananin sha'awar da ya ba ta.

Kwatsam! Wani irin abu ne mai matuk'ar haske da sauri ta ji ya gifta cikin k'wak'walwar kanta, dalilin kallon flower'n da tayi.

Hoton fuskar wata kyakkyawar yarinya k'arama wacce ba za ta wuce shekaru takwas ba ta hango, tana kama jikin wani matsakaicin dogon matashin saurayi ta bayansa, alamar so take ya ba ta wani abinta da ya karb'ar mata.

''PREM!''. Daddad'an sautin muryar yarinya ta kira sunanshi.

Wani irin firgigit Maryam ta yi, had'e da bud'e Idanuwanta, dalilin wannan abu da ya gitto cikin k'wak'walwarta, duka wannan abin ya faru ne cikin abinda bai wuce 'yan sakanni ba.

Maryam ta rik'e kanta saboda wani kalar juyawa da ta ji ya fara yi mata. Sautin muryar kyakkyawar yarinyar ya ci gaba da amsa kuwa cikin k'wak'walwarta.

''Prem!...Prem...!!...Prem...!!!''. 

Runtse idanuwa Maryam ta yi, tana k'ara rik'e kanta gam! K'wak'walwar kanta ya shiga caji, tana k'ok'arin sake tuno wani abun game da yarinyar nan da ta gani, tare da sunan PREM da taji ta ambata.

"PREM!'' Tak'ara nanatawa, 

'A ina na tab'a jin sunan nan!?' 

Sai dai duk wani yunk'urin da Maryam ta yi don ta sake tuno wani abu, ta gagara, don da ta yi k'ok'arin tsananta tunanin da take yi, sai ta ji juwa na d'ibarta.

Kallon flower'n dake hannunta ta sake yi, nan take wani sabon jiri ya k'ara d'ibarta kanta na wani irin juyawa, cikin sauri ta yi wurgi da d'an flowern dake hannunta, zaman dirshan tayi a cikin lambun, had'e da dafe kanta.

Sosai take k'ara jinjin na abinda ya faru da ita cikin d'an k'ank'anin lokaci.

Sai data dan jima a haka sannan ta samu 'yar nutsuwa.

A lokacinne ta fara k'arewa lambun kallo, tana nazarinsa.

Gaba kad'an da inda take zaune ta gefen damanta, wasu korayen bishiyoyi ne kewaye da gun. Gefe kad'an kuma wata 'yar madaidai ciyar rumfa ce, ta hango.

Cak! Kuma sai ta mik'e tsaye, ba tare da ta gama nazarin cikin lambun da take yi ba.

Takawa ta fara yi a hankali ta fara kewaye lambun, ba za to ta hangi wani babban kwamin wanka irin na zamani (Swimming pool).

Maryam ba ta yi wata-wata ba, ta doshi wurin da saurinta.

Tana zuwa ta sami waje daga bakin swimming pool d'in ta tsugunna, hannayenta ta sanya ta rink'a d'ebo ruwan tana sha, bata damu da kyau ko rashin kyawunsa ba, saboda tsananin k'ishin ruwan da take fama dashi tun lokacin da ta je shan ruwa wajen wani dogon tsauni, har k'asa ya rufta da ita.

 

Sai da ta sha sosai, sannan ta yi hamdala.

A kallon idanu ruwan yana da haske k'alk'al, haka ma a bakinta, ba ta ji wani sauyi ba.

'Tun da na d'an ji dama-dama, bari na d'an zagaya cikin lambun nan, in gani ko zan sami wani ruwa mai tsarki wanda bana wanka ba, domin in yi sallah!.

Idan kuma ban samu ba, sai na dawo nayi da wannan d'in, tun dai kamawa tayi'. Ita kad'ai, take wannan zancen a cikin zuciyarta.

Zazzagawa ta fara yi cikin lambun, zuciyarta na tattare da nishad'i.

Aiko ba ta sha wani dogon wahala ba, ta cimma wani kyakkyawan wuri mai matuk'ar kyau da k'awan gaske! Ga tarin furannin da kusan ma sunfi wad'an da ta baro a baya kyau! Had'e da wata 'yar k'aramar k'orama daga can gaba.

Kama baki ta yi, tace, "Wai ita wannan duniyar duk inda Mutum ya tsinci kansa sai yaga gaban yafi baya kyau!?''

 

'Duniyar Aljanu ce fa!' Wani sashe na cikin zuciyarta, ta tunatar da ita.

 

Cikin hanzari tace, ''Uhmm, bari dai na duba abin da ya kawoni.'' 

 

Takawa ta yi zuwa bakin k'oramar, ruwa ne mai haske k'al-k'al, sai k'yalli yake yana ta gudu abinsa gwanin ban sha awa, cikin farin ciki ta ka'rasa, inda ta sunkuya ta d'ebi ruwan ta sake sha.

 

Sannnan tayi alwala dashi.

 

Bayan ta mik'e ta fara sak'e-sak'e a zuciyarta. 'To wai shin yanzu wace sallama ce ma zanyi? D'azu dai na san nayi Sallar Zuhur! Tun daga wannan lokacin kuma ban sake yin wata ba, gashi ban san iya lokacin dana d'auka ba, dalilin doguwar suman da nayi. 

 

Da ina tare ne da Fairooz, tabbas da ya fad'a min'.

 

arin gun bawan Allah nan wanda na sama suna Fairooz, ta girgiza kai tareda yin

 

Murmushi tayi tana girgiza kanta, dalilin sunan Fairooz da ta ambata. 

 

Ta ci gaba da tuno lokacin rabuwarsu, tun bayan da ya bar ta cikin kogon ramin nan. "Ko yanzu a ina yake? Ko wani irin hali zai shiga, idan ya dawo bai ganni ba?"

 

'Gashi dai inda nake nan yanzu nan, hasken rana nake gani sosai, kenan anyi sallar la'asar mai yuwa ma dare yayi anyi magriba da isha'i harma da Asuba, tun da dai ga sabuwar rana ta sake fitowa, bari in had'a nayi duka ya Allah ka yafe mun.'

 

Wuri mai tsafta Maryam ta samu, inda ta shinfid'a mayafinta, tare da fuskantar inda take tsammanin nan ne gabas! Ta fahimci hakan ne, ta hanyar yin la'akari da inda taga rana ta fito.

 

Haramar salla ta yi, bayan ta tayar da ik'ama, sannan tayi kabbara.

 

A d'abi'ar Maryam sam! Ba ta wasa da ibadarta ko kad'an, hakan ne ya sanya duk da irin halin da ta tsinci kanta, bai sa ta manta da Ubangijinta ba.

 

 

   BABI NA SHA BIYU

 

 

Bayan Maryam ta rama sallolin dake kanta duka ta idar, ta d’aga hannuwanta sama tana rok’on Ubangiji, muryarta a bayyane take fad’in.

 

“Ya Ubangijina Allah! Kaine Mahaliccin sammai da k’assai kai kad’ai ke da iko akan komai daka halitta.

 

*MUTUM DA ALJAN* mu duka *halittarka ne*! Ina rok’onka ya Allah, da ka bayyanamin wannan b’oyayyen al'amari dake faruwa dani, ya Allah ka ganar dani duniyar da nake ciki! da kuma inda nake a yanzu, da dalilin zuwana, ka kuma taimake ni ka bani ikon komawa gida gun Abbana......'' 

 

Kuka sosai take yi, lokacin da ta ambaci sunan Mahaifinta.

 

Ta ci gaba da cewa,

 

“Ya Allah a duk halin da Abbana yake ciki dalilin rashina, ka sanya masa nutsuwa da sassauci cikin zuciyarsa, ka kuma fitar dani daga wannan sark’ak’iyar dana jefa kaina ciki!."

 

Haka Maryam ta d’au dogon lokaci mai tsawo tana ta Addu'a! Sannan ta shafa.

 

Ta d’an jima zaune a wurin da ta yi sallar, kafin ta m’ike tana mai yin hamdala ga Allah mad'aukakin sarki, domin ko ba komai taji ta sami nutsuwa cikin zuciyarta. 

 

Tafiya take sannu a hankali, ya yin da iskar lambun ke kad’awa da lallausan bak'in gashin kanta, wanda ya fito ta jikin mayafinta.

 

Duk wannan badak’alar da tasha gashinta yana nan da shek'insa, sai dai d’an k'ura kawai da ba za a rasa ba.

 

Cikin lambun ta shiga sosai tana zazzagawa, inda a k'arshe ta tsinko wasu ‘ya’yan itatuwa.

 

K’oramar nan ta d’azu ta koma, ta wanke su fes!.

 

Daga nan ta koma zuwa cikin wannan rumfar da ta hango d'azu lokacin da tunanin k'aramar yarinyar nan ya gifta cikin k'wak'walwarta.

 

Daidai saitin wasu kujeru biyu masu fuskantar juna ta tsaya, nan take ta tuno da Fairooz d’inta! Kamar yadda ta sanya masa suna.

 

Janyo kujera guda d’aya tayi ta zauna, sannan ta fara cin 'yan'yan itatuwan da ta tsinko, ko za ta samu su yi mata maganin yunwar da take ji.

 

Tana kammala shan fruits d’in, ta koma bakin k’oramar nan, inda ta sake d’ibar ruwan cikinsa ta wanke hannayenta a gefe guda. 

 

Sannan ta sha ruwan tayi hamdala ga sarki Allah.

 

Ta koma bakin runfar tana wasu ‘yan tunane-tunane cikin zuciyarta, can sai ta ji sha’awar komawa bakin swimming pool d’in nan na d'azu, ko za ta samu ta d’an d'auraye jikinta.

 

Hakan kuwa tayi, bayan ta koma wurin kwamin wankan, ta d’auraye wuraren da take so a jikinta, sannan ta zauna daga bakin pool d’in.

 

Kallon ruwan take cike da sha'awa, inda a hankali ta d’an zirara k’afafuwanta tana k’arkad'a su cikin ruwan.

 

Wal! Wannan abin mai haske ya sake gittawa ta cikin k’wak’walwarta, da sauri Maryam ta kama kanta, ya yin da wani sabon hoto ya sake bayyana k’arara a cikin k'wak'walwarta.

 

Kamar d’azu k’aramar yarinyar nan ce wacce ba za ta wuce shekara sha biyu ba, tare da wannan saurayin wanda a k’alla zai iya kai kimanin shekaru ashirin da bakwai, su ta sake gani a bakin swimming pool d’in, wanda take zaune ita ma a gefensa daidai wannan lokacin!.

 

Saurayin na zaune daga d’ayan kusurwan, ya yinda ita ma yarinyar tana daga can d’ayan b'angaren.

 

'' *SAPNA*. Your turn please… Come on..come on.!.”

 

Kyakkyawan saurayin ne ke cewa k'aramar yarinyar, wacce ya kira da sunan *Sapna* yana tafi da hannayensa, yana ci gaba da fad’in 

 

“Common my one, common! Ko kin yarda kinyi failing, in zama winner!?''

 

Cikin sauri yarinyar ta shiga girgiza kanta alamar ba ta yarda ba.  

 

Yace, “Then go on my dear, common!...”

 

Sai ko yarinyar ta d’auki k’wallo guda d’aya daga cikin tarin k’wallayen da suke gefenta, ta wurga ta masa, ta hanyar cilla k'wallon da k’arfi! Wanda k’arfin wurgin da tayi dashi yasa k’wallon tafiya da gudun gaske, ya yin da shi kuma kyakkyawan saurayin yabi k’wallan da niyar kamawa amma sai k'wallon ya wucesa.

 

Tsalle yarinyar ta kama yi tana fad’in 

"Yeeeeh PREM! I win now, for the first time!." 

 

Tana cikin tsalle tana murna, ba tare da ta lura ba, sai dai ta ji k’afarta ta zame daga bakin pool d’in.

 

"PRE….M"!… wannan k’aramar yarinyar ta k’walla k'ara da kiran sunan saurayin, da iya ka cin k’arfinta! Sanadiyyar zamewar da k’afarta ta yi daga bakin swimming pool d’in.

 

Cikin sauri ya waigo dalilin kiran da yaji ta k'walla masa, alhali da har ya yi nisa daga wajen swimming pool d’in, dalilin tafiyar da yayi don d’auko k’wallan da tayi masa jifa mai k’arfi dashi.

 

Yana waigowa yana cin karo da ganin daidai lokacin da k’afar yarinyar ya zame…..jikake tsunduuuum…..! Ta fad’a cikin ruwan.

 

Cikin wani irin rud’ewa ya kira sunanta da

 

"SAPNA...!."

 

Amma ina ta riga ta fad’a cikin ruwan, har ta soma wuntsil-wuntsil domin ba ta iya wanka a ruwa ba.

 

Cikin izza ya fara gudu domin komawa bakin pool d’in ta can b'arayinsa, yana k’arasawa kuwa bai yi wata-wata ba ya afka cikin ruwan tunjum! Ya fara nink’a ya, sauri yake yana k’arawa, yana yi yana kiran sunan yarinyar, domin akwai tazara sosai a tsakaninsu.

 

Da yake ba ta iya ruwa ba, kanta sai nutsewa yake tana d’ago hannuwa tana amsa kiran sa tare da fad’in sunansa.

 

Ko da ya k’arasa gareta tasha ruwa sosai, ya kamata ya ciccib’ota daga ruwan zuwa waje, a wannan lokacin ko motsi ba ta yi.

 

“Sapna!..Sapna...!!.'' Ya rink'a kiran sunanta da k'arfi.

 

Domin gaba d’aya duk ya rud’e.

 

Cike da k'arfin hali, ya soma matso ruwan da ta sha a cikinta, ruwa na ta fitowa ta bakinta da hancinta.

 

Sai da ya gama matse mata ruwan ya kama jijjiga jikinta yana kiran sunanta, amma ina ko motsi ba ta yi.

 

Kumatunta yake d'an bubbugawa, yana fad'in,

 

''Ki tashi dear Sapna ki tashi, kar ki tafi please kar kice za ki barni....'' Sai sambatu yake amma shiru kake ji yarinyar ba ta ko alamar motsi.

 

Ya sanya bakinsa cikin nata domin yi mata (mouth to mouth respiration) ya jawo numfashinta ya sake jawowa, amma ba ta ko alamar motsi.

 

D’ago fuskarsa ya yi, wacce take jik’e da hawaye sharaf-sharaf da k’arfi ya furta,

 

"Spnaaa....!''

 

Nan take shi ma ya fad’i akan jikinta sumamme.

 

Can bayan wani dogon lokaci yariyar ce ta sauke wani dogon numfashi, tare da fara motsa hannuwanta alamar ta soma farfad’owa kenan, daga bisani idanuwanta ma ta bud’e su duka.

 

Kyawawan idanuwanta suka sauka a kan fuskar kyakkyawan saurayin dake sume jikinta.

 

Hannunta tasa ta shafo fuskarsa tare da kiran sunanshi a hankali,

 

'' *Bhayya Prem!*” Shiru.

 

Sai ta ci gaba da shafa fuskarshi, tana kiran sunansa, can ya yi firgigit ya farka! Yana me k’ara k’walla kiran sunan yarinyar tamkar wani zautacce.

 

Da k'yar ta samu ta kamo hannuwansa ta rik'e cikin nata, tace.

 

“Gani a nan Ya Prem, ni ce fa, ina nan tare da kai!”

 

A hankula ya sauke wata sassanyar ajiyar zuciya, yana dubanta, ganin cewa tabbas ita d'in ce ta farfad'o ba ta Mutu ba, hakan ya sanya shi k’ank’ameta cikin jikinsa yana fad’in,

 

''I love you...! I love you...!!.

 

I really love you mera Sapna!.''

 

Sun jima a haka rugume da juna yana mai k’ara jin shauk’in ta a cikin zuciyarsa, ita kuma sai sauke ajiyar zuciya take ba adadi saboda wuyar data sha cikin ruwa.

 

Bayan komai ya lafa, suka rabu daga rungumar da suka yi, bai yi wata-wata ba ya d’auke ta cak! ya doshi k'ayataccen rumfar dake cikin lambun da ita, zuciyarsa na wata irin azalzala.

 

'Yanzu inda ya rasa ta fa!? I can't imaging life without Sapna!.' Duka cikin zuciyarsa yake wannan zancen.

 

Shinfid’a ta ya yi akan lallausan darduman dake malale cikin rumfar, domin lambun gurin k’ayataccen lambu ne, kuma da alama wannan lambu dan musamman aka ta na de sa!.

 

Ita dai bin shi kawai take da kallo, fita waje ya yi, sashen gidan dake manne da lambun ya nufa.

 

Bayan wani d’an lokaci ya dawo d’auke da suturar mata masu kyau a hannunsa, ya tsugunnar da gwiwowinsa har k’asa, sannan ya tallabota.

 

Jik’akk’un kayan da ke jikinta ya fara k’ok’arin cire wa, sauri tayi ta kama hannunsa, tana girgiza mishi kanta, bai ko saurareta ba, sa hannunshi yayi ya cire hannun nata daga rik’on data masa.

 

Za ta yi magana yasa d’an yatsar sa akan bakinta, had'e da fad'in

 

''Shhhh….'' Alamar ta yi shiru.

 

Ba tayi masa musu ba, haka nan ta k’yalesa, don ta riga ta san halinsa, ba abinda zai hanasa abin da yayi niyya.

 

Jik’akk’un kayan dake jikinta ya cire, sannan ya canja mata da wad’an da ya d’auko cikin gida.

 

“Shukriya meri Prem!.” Cewar k'aramar yarinyar.

 

Murmushi ya sakar mata, tare da nuna ta da d’an yatsarshi, yace.

 

“Daga yau babu wasa a bakin ruwa na soke, kar ki k’ara tsayawa bakin ruwa kin ji ko!.” 

 

''Yes! Prem.'' K'aramar yarinyar ta amsa.

 

Sai da ya dafa gashin kanta, kafin yace 

 

“Da kyau! Yeih yahi mera Sapna!.” (wannan ita ce Sapna ta!).

 

Kwantar da kansa yayi a kan jikinta tare da lumshe idanuwansa……..A dai-dai nan, hankalin Maryam ya dawo jikinta daga wannan dogon tunani da ya sake ziyartar cikin kwakwalwarta.

 

Cikin mutuwar jiki Maryam ta tashi daga bakin swimming pool d’in.

 

Jikinta ya matuk'ar yin sanyi lak'au, da wannan tunanin da ya sake zuwan mata.

 

Komawa ta yi cikin rumfar nan, inda ta sha fruits, rumfar sak! Da wanda ta gani cikin tunanin da ya zo k'wak'walwarta, tabbas a cikinsa ne, wannan saurayin ya canzawa k'aramar yarinyar kayan jikinta.

 

Zama ta yi a kan kujera, had'e da yin tagumi, lallai kamar akwai abin da take son sake tunawa, amma kuma bata k’ara tuno komai ba.

 

Sake tashi tayi, tare da nufar wannan dank'areren gidan da ta biyo ta cikinsa d’azu, har ya fito da ita zuwa cikin lambun.

 

Bayan ta isa, ta kai hannu tare da bud'e k'ofar gidan.

 

Wani babban falo ne ya bayyana a gareta, ba tare da tsoron komai ba, ta kutsa kanta cikin falon.

 

Inda ta fara 'yan dube-dube a cikinsa, wai ko Allah zai sa ta ga wani abu wanda zai k’ara taimakonta wajen tunano abinda, ke zuwa mata cikin k'wak'walwarta, dangane da 'yar k'aramar yarinyar nan, da wannan Namijin saurayin.

 

Sai dai duk iya dubawarta, ba ta sake ganin wani abu ba, wanda zai taimaketa wajen kawo mata sabon tunanin da k'wak'walwarta ke yi.

 

Sai dai akwai wani d’aki k’wara d’aya da ta hango, k’ofarsa na ta fidda haske mai k'yalli sak! Da irin na mak'ull'in d'azu.

 

Cikin hanzari Maryam ta doshi k’ofar, domin hanyar da za ta mayar da ita gida kawai take nema, don ta gaji da wannan duniyar da ababen dake faruwa a cikinta.

 

Tana zuwa ta sanya hannunta ta b’ude k'ofar, tana mai furta sunan Allah a bakinta.

 

D’aki ne mai kyau amma duk yayi k'ura, alamar dai ya dad’e babu kowa cikinsa.

 

Daga can tsakiyar d’akin kuma ta hango wani tebur, d’auke da k’aton littafi a jikinsa!.

 

''Ya Allah ka sanya littafin nan ne daya kawoni wannan duniyar da nake ciki...” Ta raya cikin zuciyarta, lokaci guda tana me k’arasawa cikin tsakiyar d’akin, daidai gaban teburin.

 

Abin mamaki, kamar yadda tayi zato, hakan ce ta kasance, domin tana dubawa sai taga littafin sak! Da littafinta, anyi rubutun suna b’aro-b’aro a jikinsa, rubutun sunan FAIROOOZ!. 

 

''Alhamdulillahi!” Maryam ta ambata tana me lumshe idanuwanta.

 

'Lalle kuwa wannan littafina ne.'

 

Ba tayi wata-wata ba hannunta ta kai, tare da yin bismillah ta d’auki littafin.

 

Fita waje tayi cike da farin ciki, tana me yin hamdala ga Allah mad'aukakin sarki, gani take cewa hanyar komawar ta gida yazo insha Allah!.

 

Bayan ta nemi wuri ta zauna, ta kai hannunta da Bismillah, domin fara bud’e shafukan dake jikin littafin.

 

BABI NA SHA UKU

 

Ko da Maryam ta bud'e littafin, kamar dai wancan lokacin da ta fara bud'e sa ne......Yau ma shafin farko...fuskar kyakkyawan saurayi nan fari mai k'warjini da cikar zati ta gani, zaune akan doki.

 

Rik'e yake da takobi, fuskarsa tana fidda murmushi mai cike da annuri.

 

Maryam ta k'ara bud'e wani shafin na gaba........ sai ta sake gani hoton saurayin a bakin wata k'orama ya d'aga hannunsa, yana wasa da wasu zanen tsuntsaye da ta gani a saman hotonsa.

 

Haka Maryam ta ci gaba da bud'e shafukan littafin nan, tana ganin wad'an nan hotunan da ta riga ta gansu tun a kwanankin baya, tun daga kan k'oramar nan...zuwa wasu kyawawan tsuntsaye guda uku...har zuwa shafin da hoton jarumin nan yake a duk'e jini na zuba daga goshinsa....ras! gaban Maryam ya sake fad'uwa kamar wancan lokacin.

 

A hankali ta kai hannunta wajen bud'e shafin dake gaba, wanda shine daidai shafin da ya zuk'eta a wancan lokacin.

 

Maryam na tsammani kamar wancan lokacin zata ji littafin ya sake zuk'eta, amma sai ta ji shiru hakan bai faru ba, shiru-shiru ta dakata wai kowani abu zai faru, amma bata ga komai ya faru ba.

 

Cikin fargaba da sanyin jiki ta yanke shawarar bud'e shafin dake gaba da wannan.

 

Runtse idanuwanta ta yi, ba tare da ta bud'esu ba, hannunta na kakkarwa, saboda tsoron abin da zai iya faruwa, ta bud'o shafin dake gaban wanda ya zuk'eta.

 

Ta dad'e a haka tana Addu'a'oi, kafin daga bisa ni ta bud'e idanuwannata!.

 

Tozali tayi da hoton wata babbar tsuntsuwa mai kama da jemage.....ya yinda d'aya daga cikin fukafukan tsuntsuwar ya soki gefen cikin wannan kyakkyawan jarumin saurayin. Hoton kanshi da alama da d'igon jini aka zanashi!.

 

Dam! Maryam taji wani abu ya soki k'ahon zuciyarta! Domin ko ba zata taba mantawa da kamannin wannan tsuntsuwar ba.

 

Nan take ta rik'e kanta gam-gam! Wannan abin mai hasken ya sake giftawa cikin kwakwalwarta.

 

Wannan lokacin kam tabbas ta tuno komai, ta tuno abinda take k'ok'arin tunowa tuntuni, komai ya dawo mata sabo fil!, tamkar a lokacinne abin ke faruwa, bata tab'a tunanin zata manta da abinda ya faru a wannan ranar ba, bata tab'a tsammanin zata manta wannan ranar a cikin kwanakin rayuwarta ba!.

 

Hawaye masu tsanani zafi suka soma zuba daga idanuwanta, 

 

''Tabbas shine!...Shine...'' Ta kama fad'a tamkar wata zararriya.

 

Malam Hafeez

 

A b'angaren malam Hafeez kuwa, ko da ya fita gida bai zarce ko ina ba sai inda ya saba zuwa a duk ranar LARABA ta duniya. 

 

'Ya d'aukarwa kansa zuwa wannan wuri ne a duk ranar laraba, tun bayan faruwar wani mummunan al'amari daya shafi zuri'arsu baki d'aya! Dalilin da ya janyo tarwatsewar illahirin gidansu, yau kimanin shekaru uku baya kenan.'

 

Bayan ya isa dai-dai wurin ya sauko daga kan dokinsa, ya sami jikin bishiya ya d'aure dokin nasa, kamar yadda ya saba. Ya d'auko jakar tafiyarsa wacce yakan fito da ita in dai zai shiga cikin dajin.

 

Gun wasu K'ABURBURA guda hud'u ya dosa, biyu daga ciki k'ananu ne, ya yinda ragowar guda biyun kuma na manyane.

 

Gefe kad'an akwai wata bishiya mai yalwar ganyayyaki da suka samar da inuwa, cikin inuwar dake k'ark'shin bishiyar Malam Hafeez ya shinfid'a tabarma mai kyau ya zauna, sannan ya bud'e jakarsa ya fiddo da Al'qur ani mai girma ya soma karantawa.

 

Sai da yayi karatu sosai kamar yadda ya saba yi duk ranar laraba, yau ma ya d'aga hannunsa sama yana rok'on Allah cikin murya mai d'auke da sautin kuka.

 

''Ya Allah ina rok'on ka akan wad'an nan bayi naka, idan har suna raye ne, ya kasance ba Mutuwa suka yi ba! Ya Allah ka bayyana mini su na gansu!.

 

Idan kuma ba su da rai! Ya Allah ka kai rahamarka da jink'anka garesu Albarkacin Alqur'aninka mai girma!.

 

Kafin ya kammala wad'an nan abubuwan da yayi, har yamma tayi, dai-dai lokacin da yakan koma gida.

 

Saboda haka yana gama Addu'a'oinsa ya kama dokinsa, inda ya sakar mishi linzami, inda ya nufi hanyar gida, yana me hanzarin komawa wajen 'yarsa MARYAM daya bari a gida. Don yana tunanin yau kamar har ma yaso ya makara kan ainihin lokacin komawarsa.

 

Gudu yake sosai akan dokinsa, tun da ya kusa daf da gida, yaji gabansa ya soma fad'uwa, yana k'ara kusanto gida bugun zuciyarsa na k'ara k'aruwa, duk sai yaji jikinsa yayi sanyi.

 

Haka nan dai ya k'arasa yana mai karanto Addu'o'i a bakinsa, don bai san menene dalilin fad'uwar gabansa ba, shaf! yama mance da wai ya bar wani akwati a bud'e.

 

Tun da ya iso harabar gidansa jikinsa ya fara sanyi ganin cewa Maryam ba tazo tarbarsa kamar yadda ta saba yi kullum ba idan ya dawo gida.

 

A sanyaye ya sauko daga kan dokinsa, bai ko tsaya d'auresa ba, nan yabarsa a tsakar gidan, da yake dokin ya saba da gidan kawai inda ake d'auresa ya nufa, ya yinda shi kuma Malam Hafeez cikin sauri ya nufi b'angaren d'akin 'yarsa yana mai kiran sunanta.

 

Tunaninsa, 'Mai yuwa ba ta da lafiya ne.'

 

Sallama yayi a bak'in k'ofar, shiru ba'a amsa ba.

 

Ya sake yin sallama har sai da yayi sau uku! Babu amsa, sannan ya d'an yaye labulen d'akin kad'an, tsammaninsa zai hangota kwance ba ta da lafiya, amma sai wayam! bai ga kowa ba.

 

'To ina Maryam ta fita ne bayan kuma ba ta zuwa ko ina, matuk'ar ba da izinina ba?'

 

Mamaki ne fal! Cike da zuciyarsa, nan ya fara zagaya gidan yana nemanta.

 

Can hankalinsa yaje kan d'akin ma adanar littafansa, nan ne kad'ai bai duba ba.

 

Ba tare da tunanin komai ba ya k'arasa, inda ya bud'e labulen d'akin, anan ne fa labari yasha banban, domin ganin k'aton akwatin sirrinsa ya yi a waje kan teburin dake tsakiyar d'akin, tabbas sai yanzu ya tuna da shi ya fito da akwatin d'azu da safe, ya kuma manta bai mayar ba.

 

"Kar dai yau ace marainiyar yarinyar nan ta bud'e akwatin nan, ta d'auko wannan littafin daya zaman mana annoba a cikin zuri'armu baki d'aya......!''

 

Ya fad'a da karfi.

 

Cikin d'akin ya k'arasa shiga, amma kuma dai bai ga alamar an tab'a wani abu ba, duk da haka dai sai ya k'arasa kan tebur din, bud'e akwatin yayi don samun tabbaci ko ta bud'e ko kuma bata bud'e ba.

 

"Kai anya! Bana tunanin Maryam za ta bud'e akwatin nan."

 

Hannu ya kai wajen bud'e akwatin.

 

Sai dai ko da ya bud'e akasin tunaninsa ya gani, don yana yin ido biyu da cikin akwatin ya gane littafin dake ciki bana ainihin bane, domin wautar da Maryam tayi ta manta ko da ta canja littafin da mai dai-dai size d'inshi, to wanda tasa ba shida suna, shi wannan babu sunan FAIROOZ a jiki.

 

Nan take Malam Hafeez yayi zaman dirshan a gun ya dafe kansa hawaye na zubar masa kamar ba babban Mutum ba, gwanin ban tausayi,

 

Ya dad'e yana zubar da hawaye tare da ambaton INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI UN!.

 

Sai da ya jima yana fad'in haka sannan ya d'ago kansa yana cewa.

 

''Yake 'yata, mai yasa kika aikata haka!? 

 

Yanzu kema sai da kika bisu? Mai yasa zaku barni ni kad'ai? 

 

Yanzu na rasa kowana kenan?" 

 

Haka yayi ta fad'in kalamai cikin sambatu, can daga k'arshe ya tashi ya mik'e tsaye yace,

 

"Kai! Dole nima yau na bi bayanku, dole nasan halin da kuke ciki!."

 

Kai tsaye d'akin adana littattafansa ya koma wani cupboard ya nufa wanda ke daidai wata 'yar kusurwa kamar lungu a cikin d'akin.

 

Bud'e cupboard d'in ya yi, ya soma fiiddo wasu litattatafai, daga bayan takardun dake gaban cupboard din, bayan ya gama fitar dasu, nan take wani littafin ya bayyana sak! tamkar dai irin wan can na farkon da Maryam ta d'auke, an rubuta sunan FAIROOZ a jiki.

 

A hankali ya sanya hannunsa wajen zaro littafin daga ma adaninsa.

 

     BABI NA SHA HUD'U

 

 

        FLASH BACK!

 

Alhaji Yusuf Saleh! Shuwa ‘arab ne na asali. Tare da Matarsa Binta Musa.

Ita da shi Auren zumunci ne aka yi masu.

Mahaifin Yusuf, wato Abdulhakeem, wanda jama'a ke kiransa da Saleh, Mutum ne mai kud’in gaske!. 

Binta ta kasance ‘ya a wurin k’anin Abdulhakeem, tun da Allah ya yiwa iyayenta rasuwa sanadiyyar wani hatsarin Mota da suka yi, a wancan lokacin Allah ya amshi ransu gaba d’ayansu.

Tun daga nan rik’on Nana Binta ya dawo wurin shi Mahaifin Yusuf Mijinta, ya d’auke nauyinta gaba d’aya a hannunshi, domin dama ita kad’ai ce iyayen nata suka bari, kamar yadda shima yake da d'a guda d'aya tak!.

Babu irin gatan da Mahaifin Yusuf bai nunawa Binta ba, hakan ne ya hana ta yin kukan maraicin rashin iyayenta.

 

Sai dai saboda tarin arzikin da Abdulhakeem ya tara, hakan sai ya janyo masa tsana cikin 'yan uwansa, wanda a k'arshe aka samu wasu daga cikinsu, suka yi masa asirin da ya zamo sanadiyyar barinsa k'asarsu gaba d'aya.

 

Ana cikin haka ne kuma d’ansa Yusuf ya dawo daga karatu, suka had’u da Binta a gidan Mahaifinsa, nan fa sai soyayya ta k’ullu tsakaninsu ba tare da d’aukar wani dogon lokaci mai tsawo ba, aka d’aura masu Aure.

 

Tun da suka yi aure kuma sai Allah bai nufe su da samun haihuwa ba, kullum Addu'ar wad’an nan ma’aurata bai wuci na Allah ya azurtasu da samun zuri’a ta gari ba.

 

Wasa-wasa har suka shekara biyu amma shiru kake ji babu wani labari, tun Binta na b’oye damuwarta ga Mijinta har ya kasance damuwarta ta fara fitowa fili.

 

Ko da Yusuf ya fahimci halin da Matarsa take ciki, sai ya shiga kwantar mata da hankali.

 

Amma babu wata nasara da ya samu, domin Binta kullum cikin tunani take, sanadiyyar hakan, Yusuf shima sai ya fara damuwa, dama dannewa yake yi.

 

Damuwar Yusuf ta sake k’aruwa ne bayan daya ga damuwar Matarsa Binta yayi tsanani.

 

Abinci ma ba ta wani cinsa wadatacce yadda ya kamata, saboda yadda ta d'auki lamarin ta sanya a ranta, har wata 'yar rama ta soma, ganin hakan yasa Mijin nata ya samo mata wani d’an abokinsa Khaleed, ana kiransa Imam, domin ta rik’e shi a wurinta.

 

Abin ikon Allah! Yaron bai cika watanni biyu ba a wurinta, Allah ya karb’i rayuwarsa.

 

Tun daga nan suka sawa zuciyoyinsu dangana, tare da ci gaba da kaiwa Allah kukansu.

 

Bayan shekaru hud’u da Aurensu, Allah da ikonsa ya albarkaci Binta da samun juna biyu. Wohoho! Murna a wurin wad'an nan bayin Allah ba a magana.

 

Tarairaya, da kulawa babu irin wacce Binta bata gani ba daga wurin Mijinta, haka ta b’angaren surikinta, marik'inta, Alhaji Abdulhakeem. Kayan haihuwa kuwa tun cikin na d'an wata d’aya aka fara tanadinsu, sune sayi wannan sayi wancan, duk saboda zumud'i.

 

     BAYAN WATA TARA!

 

A wata safiyar Jumma’a, Binta ta tashi da nak’uda, tasha matuk’ar wahala sosai inda daga k’arshe Allah ya sauketa, ta sami haihuwar kyawawan yara guda BIYU duka maza.

 

Murna kuwa gun wad'an nan ma auratan ba a cewa komai, nan take kakansu yasa aka had'o kayan jarirai, komai aka siyo saiti bibbiyu.

 

Ranar suna raguna hud'u aka yanka k’osassu, banda sauran naman kaji da aka yanka, a tak’aice dai ansha shagali sosai! Abinka da masu akwai.

 

Inda 'yan biyun suka ci sunan HAFEEZ da ABBAS.

 

Sai dai babban abin bak’in cikin da ya faru kuma, tun bayan haihuwar yaran sai Mahaifiyarsu ta kwanta ciwo bata jima ba tace ga garinku nan.

 

Allahu Akbar! Ranar da a ka yi sadakar bakwai na rasuwar Mahaifiyarsu, ranar kakansu Abdaulhakeem shima ya koma ga mahaliccinsa.

 

Allah mai iko, sai ya kasance Yusuf ga ‘ya’ya da yake ta buri ya samu, amma kuma ba farin cikin rayuwarsa, Matarsa da Mahaifinsa gaba d’aya sun rasu.

 

Wata dattijuwar Mata ya d'auko mai kula masa da 'yan jariransa, gashi daman shi bai san kowa k’asar Nigeria ba, domin Mahaifinsa ma zuwa yayi ba mahaifarsa bace. D'an Asalin k'asar Chadi ne.

 

Yusuf bai tab'a samun halin ziyartar k'asar Mahaifinsa ba, tun da ya yi wayau. Saboda boarding school ya yi karatu, lokacin kuma da ya kammala karatun secondary 'yan uwan Mahaifinsa sun riga sun mishi asirin barin k'asarsu.

 

Tun da ya kammala boarding waje Abbanshi ya tura shi, yana k’are k’aratunsa na degree a England kuma sai Mahaifinsa ya tura sa INDIA can yayi master’s yana dawowa ne Allah ya had’a shi da Binta anan gidansu.

 

A duk cikin k'asashen da ya zauna, ya fi jin dad'in k'asar India.

 

Yusuf da dai ya ga bashi da wata mafita dangane da zaman kad'aicinsa, ya sanya shi yanke shawarar barin gida kawai na wani d’an lokaci tukunna ko da zai sami sauk’i a zuciyarsa, don gaba d’aya kewa ta masa yawa, ko ina ya kalla a gidan Mahaifinsa da Matarsa yake gani, ya had’a kayansa da ‘yan marayun ‘ya’yansa suka chale India.

 

Ashe Yusuf tun kafin ya taho India ya riga ya sanar da d’aya daga cikin abokansa na can k’asar India, Harukhan don ya samar masa gida mai kyau inda zai zauna, amma ko da suka iso sai abokin nasa ya nuna masa sam shi bai yarda da hakan ba, ya buk'aci da ya zauna a cikin gidansa, tunda babban gida ne gidan nashi, hakan ko aka yi. 

 

Yace Matarsa kuma ta ci gaba da kula masa da ‘ya’yansa, dama suma Allah bai tab'a basu haihuwa ba, duk da hakan bai wa Harukhan ba, sai da yasa aka k’aro wata mai kula da tagwayen 'ya'yan Yusuf, domin ta rink'a taimakawa Matarsa, don samun cikakken kulawa.

 

Haka wad’an nan yara suka ci gaba da samun kulawa mai inganci, kwanci tashi ba wuya a gurin Allah, Hafeez da Abbas har sun kai munzalin shiga Makaranta a ka sanya su Makarantar Addini dana boko, idan sunje Makaranta sun dawo a nan gidan kuma sukan k’ara d’aukan karatu wajen abokin baban nasu domin HARUKHAN. Babban malamin Addini ne sosai! Saboda haka sai ya zama b’angaren Addini ma basu sami wata matsala ba.

  

 

     BABI NA SHA BIYAR

 

BAYAN SHEKARA TALATIN.

 

Hafeez ya zama cikakken _*historiology*_ mai ilimi a fannin da ya shafi tarihi ya yinda shi kuma Abbas ya zama *Medical Doctor* Cikakken likita.

 

Bayan kammala karatun nasu ne kuma aka d’aura masu aure da kyawawan ‘yan Matan da suka zab’o, wanda dama tuni suka dad'e da k’ulla alk'awarin Aure a tsakaninsu.

 

Hafeez ya sami Matarsa wacce ake kira da Zeenat Aman 'yar k'anwar Matar Harukhan, Abbas Kuma Darweesha Shehu, ita kuma 'ya ce a wajen abokin Harukhan, dukansu Indiawa.

 

Ranar bikin kam an sha shagali, bayan d’aurin aure aka kai kowacce cikin d’akinta, aka barsu daga su sai angwayensu.

 

Ko da Yusuf yaga ‘ya’yansa sun sami ilmi mai inganci gashi kuma har sun kai ga munzulin yin Aure! Shi kuma ga tsufa ta fara cimmasa sai yayi niyar sadasu da ainihin Mahaifarshi Nigeria, domin su san asalin gida ko da ta Allah ta kasance.

 

Ya sanar da amintaccen abokinsa Harukhan, nan take ya karb’i wannan shawara tashi domin ganin dacewarta, sai dai a gefe guda ya nuna jimaminsa k’warai na wannan rabuwa da za suyi.

 

An sanya ranar da zasu koma gida Nigeria daga India bayan bikinsu da wata d’aya, ranar kuwa nayi suka biyo jirgi sai k’asar gado Nigeria.

 

Bayan komawarsu, babban fili Mahaifinsu ya siya aka yi ginin gida gini na musamman, don filin da aka ware wajen yin ginin gidan, za’a iya sake yin wasu gidaje a cikinsa, ba tare da an takura ba.

 

Ya sayi wannan dank’areran filin ne saboda gaba, yana son zuri’arsa su zauna waje d’aya, su taso gida d'aya, dangi d'aya, ba tare da wani rabewar kai ba, tun da shi gano 'yan uwan Mahaifinshi ya zame masa abu mai wuya.

 

Anyi ginin gidan kowa da b’angarensa ma’ana sashensa, amma idan suka fito duka zasu iya had’uwa a falo d’aya.

 

Bayan kowa ya samu ya kintsa an natsa a sabon gidan, gaba d'aya Alhaji Yusuf ya tara ‘ya’yan nasa tare da Matayensu ya k’ara yi musu nasiha kan zaman aure, ya kuma shawarcesu da yin hak’uri a da duk halin da suka sami kansu domin rayuwa cike take da jarabawa! Sannan kuma babu wanda yasan gawan fari a cikinsu.

 

**

 

Lafiyayyen Asibiti Alhaji Yusuf ya ginawa Abbas tare da komai na buk’ata daganne da kayan aiki. B’angaren Hafeez kuwa sashe na musamman a ka ware masa cikin gidan, inda yake zama ciki kullum tare da tarin manya-manyan littattafansa, yana aikin bincike, kullum cikin nazari yake. Ya binciki tarihi ya kuma rubuta, wasu kuma ya yad'a.

 

A wannan lokacin ne ya sami damar rubuta cikakken tarihin Mahaifinsu!.

 

Kwanci tashi ba wuya a wurin Allah, yau shekara guda kenan da auren wad'an nan ‘yan tagwaye inda Darweesha tayi miscarriage (b’ari) sau Biyu, ta b’angaren Hafeez kuwa ko b’atan wata ba ata bayi ba.

 

Dr Abbas kuma ya binciki Matayensu duka lafiyarsu lau babu wata mai matsala ko lalura ta rashin haihuwa, saboda haka ne suka zubawa sarautar Allah idanu.

 

       BAYAN WATA SHIDA

 

Cikin ikon Allah kuma sai darweeesha ta sake samun ciki. Samun cikin Darweesha ya dad’a tayar da hakalin Zeenatu ganin cewa ita ko b’atan wata bata tab’a yi ba.

 

Kusan shekara biyu kenan da aurensu, Hafeez kullum cikin ban baki yake da bata hak’uri yakan ce da ita, karta cire rai, domin ba'a cire rai da rahamar Allah, za ta iya samun ciki a kowane lokaci idan har Allah ya nufa.

 

Saboda ire-iren ban bakin da Mijinta ke mata ta rink'a samun sassauci cikin zuciyarta.

 

Kwanci tashi har cikin Darweesha ya isa haihuwa, yana cika wata tara da sati biyu, ciwon nak’uda ya kama Darweesha, a lokacin suna tare da Zeenat, taji mararta ta fara ciwo kad’an-kad'an.

 

Tun tana daurewa har takai ga fara cizon leb’e, ta kama k’ugunta nan da nan Zeenat ta k’araso gunta tambayarta take,

 

“Sister lafiya kuwa?”

 

Ina Daweesha babu bakin magana sai faman juye-juye take yi, cikin sauri-sauri har da sassarfa Zeenat ta nufi sashen Mijinta Hafeez, inda yake gudanar da ayyukansa na nazarce-nazarce in dai yana gida, nan take ta fad'a mai abin da ke faruwa ga yar uwarta.

 

Cikin hanzari ya nemi layin Abbas ringing d'aya ya d'auka, nan ya fad'a masa abinda ke faruwa ya kuma umurceshi da dawowa gida. Ba tare da bata lokaci ba Dr. Abbas ya baro Asibitinsa.

 

Ita kuma Zeenat ta koma wurin Darweesha ta ci gaba da taimaka mata, wacce gaba d'aya zuwa wannan lokacin duk ta fice daga cikin hayyacinta.

 

Addu’o’i Malam Hafeez ya yi ya tofa a ruwa ya kaiwa Matarsa ta tallafeta ta bata tasha, a daidai nan Abbas ya shigo ganin halin da Matarsa ke ciki ya firgitashi, ya sani cewa self medication ba kyau, to amma Matarsa tana bukatar taimako na gaggawa, k'ok'ari ya yi ya saita hankalinsa da tunaninsa wuri d'aya, sannan ya firfito da kayan aikinsa waje, ya fara duba ta, nan take ya fahimci babyn ba a daidai ya taho ba. 

 

Sannan a yanayin halin da take ciki idan aka d'auki lokaci mai tsawo ba tare da an juya babyn ba, za a iya rasa d'aya daga cikinsu. Abin mamaki kuma ko a scanning d'in Daweesha ta yi na karshe kan yaron a (cephalic position) yake, wato kai a k'asa.

 

Waje ya fito ya kira d’an’uwansa Hafeez ya sanar dashi abin dake faruwa, yace zai yi k'okarin juya babyn in shaa Allah, saboda idan ance su wuce Asibiti komai zai iya kasancewa kafin su isa.

 

In da ya nemi Yayan nashi da ya sanar da Mahaifinsu, amma kar ya fad'a mishi halin had'arin da Daweeshat da babynta ke ciki.

 

Nan take Hafeez ya wuce, tun ya sanar da Alhaji Yusuf cewa Daweeshat tana nak'uda, ya shiga yi mata Addu'ar’ar Allah ya kawo abin da sauk'i, duk da bai ma da masaniyar kan badak'alar da ake ciki.

 

Abbas kuma ya koma kan Matarsa, shimfid'eta yayi a gadonta na musamman, sannan ya yi Bismillah da Addu'ar samun nasara, nan ya shiga k'ok'arin juya kan yaron, bai d'auki wani dogon lokaci ba cikiin ikon Allah ya samu nasarar juya kan babyn ya dawo daidai.

 

Cikin abin da be wuce mintuna goma ba Daweeshat ta ta haifo wani santalelen yaro Namiji kyakkyawan gaske! Mahaifinsa ya d'aukeshi cikin tsantsar farin ciki da murna sannan ya yanke masa cibi. 

 

Kiran sallah ya yi masa a kunnensa na dama tare da ik'ama a kunnensa na haggu kamar yadda Addini ya koyar. 

 

Habawa murnar da wannan iyalin suka shiga, abu ne dai bai zayyanuwa, duk wanda ka kalla cikinsu cikin annuri za ka ganshi da annashuwa. 

 

An gyara uwar jariri da jaririnta.

 

Jama’a kowa yazo ganin jinjiri sai yayi santi, tare da yabon tsananin kyauwunsa, to ruwa biyu fa gana shuwa arab, gana India abin sai wanda ya gani.

 

B'angaren Zeenat kuwa tunda aka haifi yaron yana hannunta, don kowa yazo ganinsa a hannunta yake karb'ar shi.

 

      BABI NA SHA SHIDA

 

Haihuwar wannan jinjiri yakawo wa Alhaji Yusuf samin sauki sosai cikin zuciyarsa, domin da ya kasance cikin tsananin damuwa a kan rashin haihuwan ‘ya’yan nashi, don har ya fara zargin ko de shi yaranshi suka biyo? musamman ma b’angaren Hafeez da ko b’atan wata ba a tab’a yi a gidansa ba.

 

Sai dai ko zuciyarsa ta kawo masa wannan tunanin, yakan tuna cewa kowanne d’an Adam da irin nasa jarabawar rayuwar! Sai ya yi saurin kawar da zarginsa.

 

Lokacin da yaji ance surukar shi tana nak’uda cikin matsanancin hali zuciyarsa ta ingiza matuk'a ga tunanin baya, lokacin haihuwar Matarsa marigayiya Binta.

 

Hakan yasa ya shiga Addu'ar Allah tsare faruwar hakan ga Matar d'ansa, bai tsagaita da Addu'o'i ba, har sai da a ka haifo mashi kyakkyawan jika son kowa, ya yi hamdala sosai tare da k'ara godewa Allah.

 

Ranar suna ansha shagali sosai da sosai a inda jariri yaci sunan FAIROOOZ!. Ma’ana the king (sarki), ko kuma ace the winner( Mai Nasara) ko victorious (wanda yayi Nasara) duka dai kalamace ta d’aukaka da harshen Indian ci!.

 

Bayan sunan Fairooz da sati d'aya, Mahaifiyarsa Daweeshat ta fara ciwo mai tsoratarwa da firgitarwa, babu wanda yasan mafarin ciwon, sai dai kawai aka ga ta yanke jiki ta fad’i k'asa, bayan farfadowarta kuma ta sake wani suman!.

 

A dole suka d'auketa sai Asibiti can inda Dr. Abbas yake aikinsa, da isarsu, ma’aikatan jinya (Nurses) suka tarbesu’ da gaggawa, ganin yanayin halin da Daweeshat ke ciki.

 

Rarrabuwa suka yi inda wad'an su daga cikinsu suka tallabeta irin yadda ake d'aukar mara lafiya, biyu daga ciki kuma suka d'auko gadon tura mara lafiya, sannan suka tura gadon zuwa Emergency Room ( d'akin bayar da taimakon gaggawa).

 

Daman sun riga sun sanar da Likita, yana zuwa kuwa yaga iyalansa ne ai, bai yi wata-wata ba ya fara aikin daya kamata akan Matarshi, tare da bayar da umurnin a kira d'ayan abokinsa Dr. Sa’eed saboda shi yafi dacewa da dubata, tun da shi Matarsa ce, tausayi da sanayya kansa ya iya aikata abin da ba daidai ba, ba kuma don rashin iyawa ba.

 

Bayan dogon lokaci, aka fito da Daweeshat daga emergency room, sannan a ka yi Admiting a wani keb'antaccen ward na musamman.

 

Ba da jimawa ba kuma aka sake zuwa aka d’auki Darweeshat zuwa wani d’akin bincike, domin har yanzu jini sai zuba yake a jikinta.

 

Nan fa hankalin 'yan uwanta ya k’ara tashi, Dr. Abbas ko ya koma gefe kamar ba likita ba, don ya kasa tab'uka komai, k’arfin hali kawai yake yi, amma ji yake kamar zai fad’i.

 

Zeenat wacce ke rik’e da jinjirin Darweeshat wato FAIROOOZ a hannunta, sai faman rar-rashinsa take yi saboda kukan da yake ta tsalawa, Hafeez cikin damuwa ya dubi ‘yan uwansa yace, 

 

''Gashi ita Zeenat ba haihu ta yi ba, to ko za a yi wata dabarar da ruwan mamanta zai zo ta bashi yasha ne, tun da ba musan lokacin da za su fito da ita ba ko akwai wata dabarar da kuke ganin za mu yi?

 

"Nima tunanin da nake yi kenan." Dr. Abbas ya fad'a a kasalance.

 

“A’a Sam! Ba za a yi haka ba!.” Muryar Mahaifinsu, kakan yaro, dattijo Yusuf ne suka ji daga bayansu, a lokaci guda duka suka waiga suna mai mamakin ganinsa, domin ba da shi aka taho ba.

 

“Ba za a yi haka ba!.” ya sake maimata abin da ya fad'a.

 

Dubansu yake da Idanuwansa, sannan ya ci gaba da cewa,

 

''Sai dai a nemo madara a bashi yasha, domin ba musan abin da Allah zai yi nan gaba ba...''

 

Kafin ya k'arasa bayanin abin da yake shirin fad'a masu, Dr. Sa’eed ya fito yana goge zufa da handkerchief d'in hannunsa, sannan yaja Hafeez gefe guda.

 

Bayani ya yi masa, na abinda ke faruwa da Daweeshat. Ana buk'atar jini, domin za a k'arawa me jegon, ya k'ara da fad'a mishi cewa jininta ya hau sosai!.

 

Ashe tun bayan haihuwar Daweeshat take zubar jini mai yawa, ba tare da kowa ya sani ba, din bata fad’a ba.

 

Nan take Hafeez yace a d’ibi jininsa, Dr. Abbas naji ya ce a’a nasa za a d'iba.

 

Babansu yace, ''Yanzu ba lokacin gardama bane, ku bari Hafeez ya bayar, kai Abbas kana buk'atar nutsuwa da kwanciyar hankali, bai kamata a d'ibi jininka ba.''

 

Dr. Abbas yace ina shifa zai iya.

 

Alhaji Yusuf ya san halin 'yan biyunsa, yace, ''To shikenan, in dai babu matsala Abbas ya bayar d'in.''

 

Anci sa a kuwa jininsa irin wanda zai iya ba kowa ne, ba b’ata lokaci aka gudanar da komai yadda ya dace, bayan an mishi gwaje-gwaje, aka d'ibi jinin nashi, sannan aka sanyawa mai jego.

 

Dr. Sa'eed Abokinsa ne yazo yana masu bayani akwai buk'atar yin X-Ray amma na k’irji, don ganin yanayin halin da zuciyarta ke ciki, dalilin yadda jininta ke dad'a hawa sosai ga bleeding (zubar jini), sannan kuma idan abin ya motsa, numfashinta yana yi kamar zai d'auke.

 

Dr. Abbas ya sanya hannu ya dafe kansa, yana mamakin abin da yasa Matarsa ba ta fad’a mai wani abu na damunta ba, har sai da yanzu lamari ya zama ya b’aci sannan yake sani!.

 

Haka nan dai yake ta wannan tunani a ransa, gani yake kamar shima har da laifinsa, nan dai Abokinsa ya ci gaba da kwantar mishi da hankali, har sai da yaga ya sami nutsuwa, yace su ci gaba da Addu'a’a kawai shine abin yi, sai da ya tabbatar hankalinsa ya komo jikinsa sannan daga k’arshe ya koma kan aikinsa.

 

Bayan Dr sa’eed ya kammalla dukkan gwaje-gwajen da zai yi akan Matar Abokinsa, sannan ya rubuta abin da ya dace, ya bawa Nurse’s d’in, don yi mata amfani da prescription d'in da ya rubuta, yace ayi maza-maza ba da b'ata lokaci ba.

 

K’ofar office d’insu ya bud’e ya shiga, yana shiga sai ya tadda abokinsa Dr. Abbas zaune, yayi tagumi da hannuwa biyu.

 

Dr Sa’eed ya k'arasa gareshi tare da dafa kafad’arsa yana fad’in,

 

''Ka kwantar da hankalinka Abokina, wannan jarabawace, ka kuma san irin wannan larurar ba bak’on abu bane a wajenmu, na san da cewa akwai damuwa amma don Allah kayi hak’uri.”

 

sai a dai dai nan ne Dr. Abbas ya d’ago da idanuwansa da suka yi jawur dasu yace,

 

“Aboki! Ba wai ciwon ne ya tayarmin da hankali lokaci d’aya ba, ‘A’a, yadda ya zama tana ta zubar jini mai yawa har na tsawon mako guda ga mai jego, kai ka san ko menene, kasan abin da nake gudu.

 

Result d'in da hakan zai iya haifarwa shi nake tsoro.”

 

“Karka damu muyita Addu'a’a in shaa Allahu za a sami sakamako mai kyau."

cewar Dr. Sa’eed.

 

"Toh! Allah yasa." 

 

"Ameen."

 

Da haka suka rufe zancen, bayan jinin da aka sanya wa Darweeshat ya k’are, aka cire mata.

 

Da ta d’an sami hutu aka d’auketa zuwa sashen da za’a yi mata hoton k’irji (X-Ray) Wanda za a hasko komai gaba d’aya harda zuciyarta, don ganin ko da akwai matsalar da suke zargi.

 

 Anyi hoton da komai an gama daga nan aka mai da ta, d’akin da aka kwantar da ita da farko.

 

'Toh Jama'a! Ga dai Fairooz an haifeshi! Shin daman Mutum ne shi ba Aljani ba ko ya ya? In har Mutum ne ta yaya aka yi Maryam ta had'u dashi a wata Duniya can ta daban? Sannan Abubuwan da suka faru duka a tsakaninsu Menene sirrin? Ku dai ci gaba da bin Alk'alamin Ayshnur pyaar don gano bakin zaren.'

 

BABI NA SHA BAKWAI 

 

Bayan an fiddo da result (sakamako) na hoton da aka yiwa Daweeshat, Dr. Sa'eed yace akai mishi office d'insa.

 

Kafin ya tashi ya shiga ciki, ya d'auka tare da bud'ewa.

 

Ya d'auki lokaci mai d'an tsawo yana nazarin result d'in, daga k'arshe ya mayar da hoton cikin envelope, sannan ya d'auki wata 'yar paper mai d'auke da k'arin Information game da sakamakon ita ma ya duba.

 

Bayan ya gama karantawa, ya ninke sannan ya mayar da ita cikin envelope d'in.

 

Shiru ya yi na wani d'an lokaci, ajiyar zuciya ya sauke, sannan ya tashi zuwa Office d'in da Dr. Abbas ke zaune da d'an uwansa.

 

K'arar bud'e k'ofar office d'in da aka yi ne, ya maido da hankalinsu Hafeez duka gareshi.

 

Hafeez da Dr. Abbas ya fara kira, suka koma ciki office d'insa tare, ya dad'e yana masu nasiha da kalamai masu taushi inda daga bisani ya fad'a masu result d'in Daweeshat, wanda HEART FAILURE (ciwon zuciya) ne aka gano, a sakamakon zubar jinin da ta rink'a yi, da kuma yadda jininta keta hawa sosai, ashe ta dad'e tana jin ciwon k'irji kad'an-kad'an babu wanda ya sani, tun kafin haihuwarta.

 

Dama abinda Dr. Abbas ya guda kenan, saboda hakan na faruwa ne yawanci idan mai jego tayi ta fama da uncontrol bleeding mai yawa wanda ba a san dashi ba. 

 

Dr. Sa'eed yayi iya k'ok'arinsa wajen tausar zuciyar Abokinsa, tare da sauran 'yan uwansa. Inda ya k'ara da basu shawarar cewa matuk'ar za a bi tsare-tsare da dokokin kula da mai ciwon to abin zai zo da sauk'i.

 

Bayan sun gama magana aka kira sauran 'yan uwan suma aka sanar dasu komai, tare da kafa masu sharad'in cewa yanzu dole sai sun kula da ita sosai, tare da kiyayewa da gujewa duk wani abinda zai b'ata mata rai!. Domin lallai b'acin rai ko damuwa shine zai dinga bayar da gudummawa wajen tashin ciwon, amma inde an kiyaye dokoki in shaa Allahu ba za a sami wata matsala ba.

 

Bayan wasu kwanaki aka sallamosu daga Asibitin tare da tabbacin cewa jikin Darweeshat ta warware gaba d'aya.

 

Haka suka dawo gida mai jego ta warke a zahiri, tamkar ba ita bace ke ta suma a kwanakin baya. D'anta ko Fairooz yanzu da kanta take basa mama yasha, akasin kwanakin da ba ta da lafiya, sai dai a goge jikin maman nata a sanya masa a baki ya sha, ba tare da ma ta sani ba domin bata cikin hayyacinta.

 

Haka suka ci gaba da gudanar da rayuwa lafiya lau.

 

FAIROOOZ

 

Kyakkyawan yaro kenan mai k'warjini da farin jini, tsananin kyawunsa yasa jama'a wasu na zund'en cewa "Anya ko MUTUM ne shi ko ALJANI!."

 

Tun bai wuce watanni shida ba, mak'otansu daga gida daban-daban suke shigowa d'aukarsa, sai dai in lokacin bashi Abinci yayi aje a karb'osa, Zeenat kawai don ba ta da yadda za ta yi ne take bari a fita dashi, gudun bakin jama'a, kar a hana su wani ya fad'i mugun abu akansa.

 

Da zarar an karb'o shi kuwa 

kafin a gama basa mama, za ka tadda Zeenat ta kasa ta tsare, tana jiran a kammala ta karb'eshi, kar wani ya riga ta amsar shi.

 

Ba k'aramar kulawa Zeenat ke baiwa Fairooz ba, da zarar ta karbe'shi za ta gudu sashenta da shi tace in anzo nemanshi ace sun yi barci.

 

Lokacin da Fairooz ya fara tafiya, shi da kanshi yake neman Mami Zeenatu, saboda tsananin tsabon da ya yi da ita, don Mahaifyarshi Daweeshat tuntuni ta koma 'yar kallo, tun yana jaririnsa ta huta da wahalar raino.

 

Tun da ya fara cin abinci ko d'akin Maminsa Zeenat yake kwana, idan safiya tayi nan za ta mai wanka ta shirya shi tsaf, sannan su fito zuwa sashen Mom Daweeshat, a can duka suke had'uwa suyi breakfast, iyayensa Maza na fita aiki mak'ota ko 'ya'yansu, za su fara sallama domin d'aukarshi zuwa gidajensu.

 

Musamman wata mak'ociyarsu Maman Kubra kullum sai ta d'auke shi zuwa gidanta can yakan had'u da yaranta suna wasa, saboda haka ya taso da wayo da kuma son Mutane sosai.

 

BAYAN SHEKARA UKU!.

 

Shekarun Fairooz uku kenan, amma wayonsa da tunaninsa, yafi k'arfin na shekarunshi. Idan yayi wani abin kai Babba nan zai barka tsaye cike da mamaki.

 

Gashi ya taso cikin tsantsar so, k'auna da kulawa ta wurin iyaye 'yan uwa da abokan wasansa, kowa sonshi yake gashi da ban sha'awa, ko da yaushe baka rabuwa da ganin lallausan murmushi mak'ale a gefen fuskarshi,

saboda yawan murmushinsa wasu har suna mai lak'ani da *smiley boy*.

 

Makaranta kuwa dama yana cike shekaru uku aka sanya shi, komai aka nuna masa nan da nan ya rik'e shi, da wuya kuma ya manta.

 

Maminsa Zeenat a kullum tana koyar dashi d'abi'u masu kyau, wajibine dashi ake tashi *sallar asubahi* a kowace rana, bata damu da k'arancin shekarunsa ba. Da sun tashi za ta sa shi yayi alwala, sannan ayi sallah tare da shi cikin *jam'i* da 'Yar dardumarsa a gefe, a masallacin dake cikin gidansu.

 

Da sun dawo masallaci zasu fara karatu da *Maminsa Zeenat* takan koya mai karatu dai-dai da k'wak'wal- warsa, ba ta cika masa, gashi yana da saurin d'aukar abu. Tana koya masa karatun *Alqur'ani mai girma* tun daga fatiha suka fara, har sun kai har *suratul kausar* sannan takan zab'o Addu'o'i marasa tsayi daga cikin *sahihul Muslim* tana koya masa, kai duk wanda yaga Fairoooz awannan 'yan shekarun nashi dole ya birgeka.

 

Da sun gama wannan kuma za ta bud'o takardun Makarantarsa nan ma su d'an tab'a, domin tunatar dashi homework d'insa, wanda suke yi da dare, kafin su gama wannan duka sai kaga har rana ta fito.

 

Dazarar rana ta fara fitowa, za suyi su Addu'a su tashi.

 

Daga nan *Zeenat* da kanta za ta yiwa Fairooz wanka, dama tun kansu kammala karatun *Asubah* ake d'aura ruwan, da sun gama kuma ruwan wankan shi yana cikin ready, domin akwai masu aiki a kowane b'angare na gidan, amma Zeenat bata yarda wani yayi wa FAIROOZ wanka, da kanta take shiryashi cikin uniform d'insa, sannan su fita zuwa sashen Mahaifiyarsa, inda anan ake had'uwa ayi breakfast gaba d'aya iyalan gidan.

 

Da zarar sun isa sashen Daweeshat, Fairooz gaisar da iyayensa yake fara yi kamar yarda Zeenat ta koya masa, sannan su zauna su karya sai driver ya d'auke shi zuwa Makaranta. idan ya tafi Makaranta kuma sai yamma, da yake makarantar tasu had'e yake boko da Islamiyya.

 

Idan lokacin tashinsu ya yi, da Zeenat Maminsa ake zuwa d'aukoshi a cewarta, yini guda bata ga d'anta ba, to dole taje tarbarsa kuwa. 

 

Haka rayuwar ta ci gaba da kasancewa a tsakanin wannan iyalin.

 

**** ***

 

Kwanci tashi har Fairooz ya kai shekaru shida, a wannan lokacin ya kammala *Nursery school* d'insa harma ya shiga *primary* anan ko wayonshi ya k'ara dad'uwa.

 

Fairooz ya taso da sha'awa na son yin drawings (zane-zane) ko mai ya gani sai ka ga ya zanashi, zane kuma yake yi mai kyawun gaske! In dai baya Makaranta, ko kuma ba home work suke yi tare da zeenat ba, to za ka same shi yana 'yan zane-zanensa cikin drawing boom, domin komai ya gani sai yayi k'okarin ya ga ya zana shi.

 

Ana haka wata rana Fairoooz ya dawo daga Makarantarsu, ko jimawa bai yi da kammala cin abincinsa ba, sai ga wani d'an mak'ocin su jabeer ya shigo kiran shi zuwa gidansu, da yake can akwai yara da yawa, bayan fitarsu Zeenat ta kalli Daweeshart tace,

 

"Didi (sister), ta ci gaba da magana cikin harshen india "Nifa yanzu ina ganin lokaci yayi da ya kamata Fairoooz ya daina fita zuwan gidajen mak'otar nan, saboda gudun d'auko tarbiyar da ba tamu ba, kinga yadda yake da saurin d'aukar abu da zarar yaga anyi."

 

Daweeshat tayi murmushi tare da kallon zeenat tace,

 

"Ai d'anki ne, kina iya yin duk abin da kiga yafi dacewa akanshi, nima nayi wannan tunanin, zancenki gaskiya ne, ya kamata mu dakatar dashi, daman ana barinsa k'ari da abokanen wasa da bai dasu a gida,to amma yanzu kinga yana zuwa school." 

 

Jin amsar da Daweeshat ta bayar yasa Zeenat gyara zama tare da fad'in "To Didi Allah nima daman abin da ke raina kenan, gaskiya ya kamata kawai ya daina fitar, tun da yayi wayau sosai kuma ya na saurin d'aukar abu, Allah yasa idan an hanashi kar su sake ganin ko rowarshi ake masu, kinga haka ranar ma......''

 

Ba ta kai k'arshe sai ga sako daga surukinsu ya aiko cewa su je.

 

*

Zaune suke a k'asan kafet domin girmamawa ga surukinsu, ya yinda shi kuma yake zaune a d'aya daga daga cikin lumtsatssun kujerun dake falon.

 

Alhaji Yusuf yayi gyaran murya irin tasu ta manya, tare da yin murmushi, bayan sun gaisa, ya fara da cewa,

 

''Abhi takh Fairooz nahi ghar aya?'' ( har yanzu Fairooz bai dawo gida bane?)

 

Sunkuyar da kai k'asa suka yi.

 

Zeenat ce ta amsa da cewa "Ya dawo."

 

Alhaji Yusuf ya ci gaba da maganarsa cikin harshen Indianci, ''To yana ina!?''

 

Zeenat ta amsa da cewa Jabeer ne yazo shine suka tafi gidansu tare.

 

''*Ve kya karte hai*? (Me suke yi ne)?''

 

Bai jira amsar da zasu bashi ba ya ci gaba da maganarsa,

 

''Ina son a daina barin Fairoooz bin yaran mak'ota gidajensu, domin yanzu ya fara girma kuma yana da wayau na d'aukar abubuwa cikin sauri, to kar a b'ata mana kalar tarbiyar da muke bashi, lokacin da yake k'arami sosai ban hana bayar dashi ko zuwansa ba, saboda kar aga cewa muna rowarsa don munga Allah ya bamu d'a mai baiwar kyau! Farin jini da k'warjini, duk wanda yagansa sai yaso d'aukar shi, idan ba'a bada shiba za ayi ta mana kallon masu wulak'anci.

 

To amma yanzu an wuce wannan matakin, bana so a k'ara barinshi zuwa gidansu jabeer domin ranar yazo yana bani labari cewa in sunje kallo ake sanya masu kuma na lura ba wai kallo mai amfani suke yi ba, kun kuma san dokar dana sanya a gidan nan, baya kallo idan ba films da ya shafi *cartoons* ba, suma irin na tarihi wanda suka shafi Addini da kuma wanda zai k'arawa yaro kaifin tunani!.''

 

Sai da ya d'an nisa, sannan ya ci gaba,

 

''Wannan shine dalilin kiran naku na san kuma kuna k'okarin bashi tarbiya mai kyau, domin baku fito daga gidan banza ba, iyayenku masu Addini ne. Ku tashi ku tafi Allah yayi maku *Albarka gaba d'ayanku*." 

 

''Ameen.'' Suka amsa.

 

Daga nan suka tashi, tare da komawa zuwa sashensu.

 

Bayan sun koma d'akin da suke hira kafin a kirasu, junansu suka kalla tare da yin murmushi a lokaci d'aya.

 

Zeenat tace, "Kinji Abba da maganar da muke yi ko!? Lallai dole mu d'auki mataki da wuri.''

 

A Tsarin Alhaji Yusuf, shi sam bai yarda da kalle-kallen fina finai ga k'ananan yara ba, baya ra'ayi.

 

Ko da Fairooz yake shi kad'ai Allah ya bashi a matsayin jika, soyayyar da yake yi masa, bai hanashi sanya dokar hanasa yin kalle-kalle ba, duk da ya sani a wajen wasu Mutane suna kallon hakan a matsayin takura ne.

 

Amma shi bai yarda da wannan ba, yana ganin yadda gurb'acewar tarbiya na yara yake sosai a cikin kallon fina-finai.

 

Ko da kasancewar surukansa, Indiawa ne, amma har fina finan k'asarsu bai ce su bar Fairoooz yana kalla ba, kasantuwar su kansu Indiawa da ada aka sani suna da tsantsar *kunya* cikin fina-finansu, amma yanzu sun fetsare ga barin al'adunsu masu yawa, sai k'okarin koyi da *nasara* Yahudawa, wad'an da daman burinsu bai wuci su b'ata tarbiya da koyarwa irin ta Addinin musulunci ba. Shi yasa mafi yawa daga cikin wasu fina-finansu, za ka ga suna k'ok'arin cusa rashin imani, da k'ek'ashewar zuciya ga Al'umma.

 

Idan ba ayi taka tsantsan ba, yaro k'arami sai kaga yana koyon rik'e bindiga, sata, ko shaye-shaye da sauran ire-iren muna nan d'abi'u marasa amfani.

 

Wani K'arin abin haushi shine yadda ya zama suma b'angaren fina-finan Hausa suka watsar da, da yawan koyarwa na Addini da al'adar Malam Bahaushe, sun koma ga k'ok'arin kwaikwayon wad'an can yahudawan, wa inda basu yarda da Allah ba, anan ina amfanin kallo ga yaro! Tun da ba tarbiya zai samu ba sai dai b'acinta.

 

Bayan Alhaji Yusuf ya sanya an dakatar da Fairooz fita, gudun kar jikan nasa ya shiga takura ta kewa ko kad'aici, tunda bashi da abokanan wasa sai Maminsa, shi kuma yaro ba a rabashi da wasa kwata-kwata, sai ya sanya aka had'a mashi wani k'ayataccen lambu mai kyawun gaske, tare da filin wasanni a cikin gidan nasu.

 

Fili na musamman aka warewa lambun, aka zuba k'ayatattun fulawowi masu kyau. 

 

Sai dai ga mamakinsu, Fairooz yafi sha'awar lambun fiye da wajajen wasannin da aka tanadar masa, domin cikin wannan lambun, nan rayuwar Fairoooz ta dawo, in dai bai cikin gida to zaka same shi a garden, saboda sha'awar wurin da yake matuk'ar yi.

 

Haka zasu zauna da Zeenat suyi ta wasanni cikinsa, har ta da homework dinsa anan cikin lambun suke yi, komai yake so haka nan Zeenart ke biye masa.

 

B'angaren zane-zanensa ko sai abinda ya k'aru, duk wata flower da ke cikin lambun nan, bi yake yana zanawa, sannan yayi colouring.

 

Da kakanshi yaga lallai hankalinsa ya karkata da wurin yana kuma sha'awarsa sosai, sai yasa aka sake yin wani sabon lambu na musanman wanda yafi na farkon kyau, aka shuka 'ya'yan itatuwa masu dad'i da zak'i aciki, sannan aka samar da k'orama mai kyau tare da hasken ruwa!.

        FAIROOZ

 

      BABI NA SHA TAKWAS!.

 

Sabon lambun da aka sake yanzu yafi na farkon k’awatuwa da birgewa, cikin sabon da aka yi akwai wurin hutawa na musamman da aka ware a gefe guda, an cikasa kuma da fitilu masu fidda hasken launi iri daban-daban, akwai wata rumfa kuma da aka yi tana d’auke da babban teburi na cin abinci da kayan marmari nau'i daban-daban, sai kuma kujeru wad’an da suka zagaye babban teburin cin abincin da ke tsakiyar rumfar.

 

Daga can gefe guda kuma cikin lambun wani babban swimming pool (tafkin wanka).

 

Amma sai dai Alhaji Yusuf bai nunawa Fairoooz wannan sabon lambun ba.

 

Yanzu shekarun Fairoooz goma sha d’aya, amma har ya kai class 5 (aji biyar ) a *primary school* saboda early study da aka sanya shi, idan ka ganshi yana zubo karatu gwanin ban sha’awa.

                      

Wata rana Zeenat tana shirya Fairoooz domin tafiyarsa Makaranta, ya lura da ita ta nayi tana d’an daddafe kanta gefe guda, alamar tana jin ciwo a kai.

 

“Mami ba ki da lafiya ne?'' Ya tambayeta cikin raunatacciyar murya, damuwa kwance a fuskarshi.

 

“Haan mera beta'' (eh d’ana)

 

''Me ke damunki ne?''

 

"Kawai dai ina jin d’an ba dad’i ne, amma ba wani abu, kar ka damu kaji."

 

Ya fidda d’an yatsarsa guda, kamar yadda suka saba yi fa ita, ya nunata, tare da fad'in,

 

''Sure Mami!?'' (kin tabbata Mammi)

 

Tace, ''Haan mera beta! (K'warai d'ana)

 

Dariya suka yi gaba d'ayansu,

da haka suka rabu bayan ta kai shi har d’akin Darweeshat da kakansa ya masu sai ya dawo kamar yadda suke yi kullum. Yana shiga Mota, ta tofa mishi Addu'a, driver ya ja su suka nufi hanyar fita bayan an bud'e masu gate.

 

Fairooz ya d'ago hannu yana wa Mamminsa bye alamar sai ya dawo, ita ma hannun take d’aga mai har Motarsu ta b'ace gaba d’aya.

 

*

 

Lokacin da Fairoooz ya dawo daga Makaranta da sallamarsa ya shigo gida kamar yadda ya saba, d’akin Daweeshat ya nufa domin gaishe da ita kamar yadda Zeenat ta koya masa.

 

Ya yi sallama shiru ba’a amsa ba, sai da ya jera sallama har sau uku bai ji an amsa mai ba, kai tsaye d’akin Mamminsa ya nufa.

 

Nan ma yayi sallama har sau uku bai ji an amsa mai ba, nan take ya bud’e labulen d’akin, a zatonsa zai ga zeenat kwance tun da ya san ya barta ba ta d’an jin dad’i.

 

Amma akasin haka ya gani, d’akin ba kowa ciki daga ita har Darweeshat, sashen kakansa ya k’arasa nan ma bai tadda kowa ba, yaje b’angare da Babanshi *Hafeez* ke ayyukansa na rubuce-rubuce da bincikensa, nan ma bai ga kowa ba, hankalinsa ya k’ara tashi sosai!.

 

Kai tsaye Babban falon gidan ya nufa inda aka ajiye Telephone (wayar tarho) na gidan, da niyar kiran lambar iyayensa.

 

Yana isa gun wayar, ringing na shigowa.

 

Cikin sauri Fairooz ya d’auka tare da yin sallama.

 

“Assalamu alaikum.” 

 

''wa alaikumussalam.” Aka amsa ta d’ayan b’angaren.

 

Ko da Fairooz ba ganin mai maganar yayi ba, amma ya gane muryar Daddy'nsa (Hafeez) ne.

 

Sai da ya gaishe shi tukunna, sannan ya fara magana cikin raunin murya,

 

''Daddy kuna ina ne!? Na dawo gida ban ga kowa ba....kuma....''

 

'Ka kwantar da hankalinka Fairoooz!. Daddynsa ya katse sa.

 

''Tare kuke da driver ko!? 

 

“Eh.''

 

“To kira shi, sai muyi magana ta wayar, mun fita ne zai kawo ka inda muke.''

 

Ba musu Fairoooz ya fita waje, ya fad’awa driver'n sak'on Daddynshi na cewa yaje.

 

Tare suka koma zuwa cikin Babban falon gidan inda ya bar wayar,

har yanzu a kan layi take, sai da Fairoooz ya fad’awa Daddy'nshi cewa,

 

“Ga direban na kira shi.” Sannan ya mik'a masa wayar.

 

Ya fad’a masa inda za su zo su samesu, sannan ya kashe wayar.

 

Fairoooz bai ko tsaya canja uniform d'insa ba, ya shiga Mota suka d’auki hanya ba tare da ya san ina ne suka nufa ba.

 

Yana ji kamar ya tambayi direban ina su Dad d'insa? A ina yace suje su same su. Amma duka ya kasa yin tambayar ko guda d’aya.

 

Cikin zuciyarsa, yana ta mamakin abinda yasa iyayenshi fita gida su duka!.

 

Nan take gabanshi ya fad’i ras! Da yaga sun karya kwanar da za ta kaisu Asibitin Daddy'nsa. 

 

'Kar dai jikin Mammina ne ya kawo su Asibiti? Domin tun da safe na san mun rabu da ita ba ta jin dad’i sosai!.'

 

Cikin zuciyarsa duka yake wannan maganganun.

 

Yanzu kam ya tabbatar Asibitin suka nufa, ganin har sun iso k’ofar gate d'in da za ta sadasu da cikin Asibitin.

 

Direba yayi horn mai gadi ya bud’e masu gate.

 

Direban ya waigo ya kalli Fairoooz yace,

 

“Zo muje in kaika d’akin dasu Dad suke, sun zo ganin mara lafiya ne.”

 

Ba musu Fairoooz ya kama k’ofar Motar ya bud’e, sannan ya fito waje, direban shi ma ya fito tare da rufe Motar.

 

Direban ya kamo hannun Fairoooz ya rik’e, sannan suka shiga ciki, inda Dr. Abbas ya yi masa kwatance ya nufa, ya kuma gane.

 

K'ofar wani d’aki suka dosa, wanda aka rubuta Room Number Thirty daga saman k'ofar.

 

Dakatawa direban ya yi, kafin su k'arasa isa, sannan yace da Fairooz, 

 

“Ka shiga ka same su suna ciki.”

 

Fairooz ya d’aga kai ya sake kallon nomban d’akin, ya kuma gane sarai! Shine d’akin da ake kwantar da 'yan gidansu. 

 

Lallai babu wani wanda su Dad suka zo gaisarwa, Maminsa ce kawai ba ta lafiya ake b’oye mishi.

 

Cikin kuka had’e da gudu Fairoooz ya doshi d’akin yana zuwa.

 

Kai tsaye ya kai hannu ya na shirin bud’e k’ofar, abin da kunnuwansa suka soma jiyo masa ne, ya dakatar dashi daga k'ok'arin bud’e k'ofar da yake yi.

FAIROOOZ

 

Daga Alk'alamin Ayshnur pyaar

 

       BABI NA SHA TARA

 

Muryar Aunty Mami wato (Darweeshat) ya ji a daidai inda take fad’in,

 

“Kuma ko da ban rayu ba wajen wannan aikin da za’a mun, *BAN YARDA A FAD’AWA FAIROOOZ CEWA NI CE NA HAIFE SHI BA*.” 

 

Ta d’an sauke ajiyar zuciya irin na wanda ke jin ciwo, sannan ta ci gaba da cewa, 

 

“Meri baheen (My sister) ki ci gaba da rik’onsa kamar yadda kika saba, Fairoooz d’anki ne, babu kuma buk’atar nace ki rik’e amanarsa, domin duk wani abin da ya kamata Uwa ta gari ta yiwa d’anta, kin yiwa Fairooz shi.”

 

Kowa a cikin d’akin k’wallah yake zubarwa saboda yadda maganganun Daweeshat ke dad'a karyar masu gwuiwa.

 

Bud’o k’ofar da aka yine yasa ko wannen su waigowa ban da Daweeshart wacce dama already fuskarta, tana kallon k’ofar.

 

FAIROOOZ suka gani tsaye hawaye sharkaf sun jik’a mishi fuskarsa.

 

Hafeez da Babansu Yusuf, suna tsaye daga gefen hagu na gadon da Darweeshat ke kwance da rigar Asibiti, irin wacce ake sawa Mutum in za’a shiga dashi d’akin tiyata.

 

Abbas kuma da Zeenat suna daga gefen dama, kallo d'aya za kaiwa fuskar Dr. Abbas ka gane d’umbin damuwar dake tattare dashi. Zeenat ko kuka take yi mara sauti sai hawaye da yake ta zubowa a fuskarta tana sharewa. 

 

Da gudu Fairoooz ya nufe ta, durk’usawa tayi tare da bud’a masa hannuwanta, yana zuwa ya fad’a k’irjinta ta rungumeshi, kuka ya keyi sosai.

 

Zeenat rarrashinsa take tana shashshafa sumar kansa, can ya d’ago da kanshi yana kallon ta.

 

“Mami, da gaske wai bake bace kika haifeni ba?”

 

“Fairoooz kai d’ana ne! D'ana ne kai har abada!.” Ta bashi amsa cikin kuka.

 

D’ago kansa yayi ya d’an zamo daga jikinta kad’an, sannan ya kalleta ido cikin ido yace,

 

"Mamina, daman ba ki tab’a haihuwa ba? kece daman ya kamata in rink’a yiwa Addu'ar ki sami haihuwa ba Aunty Mami ba! Kuma shine baki tab'a fad'amin ba...'' Yasa hannu ya share kwallan daya zubo mai, wad’anda har yanzu sun gagara daina zubowa daga idanunsa.

 

Magana yake tamkar ba k'aramin yaro ba, sai kace Babban Mutum me cikakken hankali.

 

Gaba d’aya jikin kowa a d’akin yayi sanyi da kalaman da Fairoooz ke furtawa.

 

Sakin Zeenat yayi daga rungumar da ta yi masa, gadon da Mahaifiyarshi ke kwance ya nufa idanunsa sunyi jawur, sai da ya kai har inda take kwance, kawai sai ya tsaya yana kallonta, kallon- kallo suke yi da ita.

 

Shi Fairoooz idanunshi cike suke da alamun tambayoyi, ita ko Daweeshat kallo take mai wanda ke fassara abubuwa da yawa.

 

Alama tayi mishi da hannunta cewa ya matso inda take.

 

Sunkuyawa yayi daf da ita, hannunta tasa tana mai shafar k'uncinsa, k'walla na zubo mata, bai san lokacin da ya rungumeta ba yana ci gaba da kuka mai tsuma zuciyar wanda ke saurarensa.

 

Daidai nan Dr. Sa’eed ya bud’o k'ofar d’akin tare da wasu ma’aikata maza su biyar, suna biye dashi a bayansa.

 

Cikin sigar tausayawa yace “Kuyi hak’uri fa Babban likitan dana kira ya k’araso, shi zai yi aikin kuma lokaci yayi, za’a shiga da ita yanzu.''

 

Fairoooz na jin haka yako k’ara k’ank’amenta yana kuka, anyi-anyi ya saketa yak’i.

 

Zeenat ce ta k’arasa gun, magana tayi mai cikin kunnesa ya waigo ya kalleta, gyad’a masa kai tayi alamar tabbacin abin da ta fad’a mai da gaske take, cikin lallab’awa ta janyesa daga jikin ‘Yar uwarta, rarrashinsa ta ci gaba da yi, amman ita ma hawayen ne ke zuba daga idanunta.

 

Sauran wa’inda suka shigo tare da Dr. sa’eed ne suka tura gadon da Daweeshat ke kwance zuwa wani d’aki.

 

Dr. Sa'eed ya zauna, ya dafa kafad’ar abokin tare da cewa “Ka kwantar da hankalinka abokina, da yardar Allah za’ayi nasara, nasan ka da hak’uri da tawakkali, dama kuma haka ake son bawan Allah na kwarai ya kasance mai tawakkali a kowane irin hali ya tsinci kansa.”

 

Nan ya zauna bai tafi tare da sauran likitocin ba, ya ci gaba da tausar zuciyar Abokinsa domin ya riga ya tsara yadda za’ayi komai.

 

'Me ya tado ciwon Daweeshat?'

 

     8 HOURS EARLIER

 

Bayan tafiyar Fairoooz Makaranta, sai Zeenat ta lek’a d’akin Daweeshat tace,

 

“Sister yau ban jin dad’i sosai, zan d’an kwanta ciki karki jini shiru ban fito ba.” 

 

Daweeshat ta amsa da “Eyya sorry Sis Allah ya kawo sauk’i, karki damu nima nan kaina yau ina jin ciwon k’irjina namin kad’an-kad’an.”

 

“Subhanallahi! Ke ma?''

 

''Wallahi kuwa.''

 

''Eyya sannu to, Allah ya yaye mana baki d’aya.''

 

“Ameen Ameen. Ki je ki kwanta ki huta kawai, nima yanzu zan kwanta.''

 

Zeenat tace ''Toh Sister.''

 

Sun rabu akan haka Zeenat ta wuce d’akinta.

 

Ashe Lokacin da aka fita da Fairoooz a Mota, mak’ociyarsu Mahaifiyar Jabeer tana tsaye a bakin k’ofar gidanta, kama baki tayi tare da bin Motar da kallo tace,

 

''Toh ashe yaron nan daman yana nan, amma k’iri-k’iri suka hana shi shigowa wasa da su Jabeer, sannan suma ba’a bari suna shiga wajensa!?

 

Tab lallai ma, aiko bari yau sai na ga k’arshen k'wak'wazon d'a, idan Fairoooz d’in finsu Jabeer yayi sai naji, don kawai anga yana da kyau!.”

 

Haka nan ta ci gaba da masifarta, su Jabeer yaranta ne, amma kuma sam! Basu da wadataccen tarbiya, makarantar ma kanshi bai damunsu ya yi ba, sai su iya k’in zuwa makaranta a dalilin kallo, Mahaifiyarsu kuma ba hanasu take yi ba.

 

K’ofar gidansu Fairoooz ta dosa tana zuwa tayi knocking, mai gadi ya taso daga inda yake, ya tambaya, 

 

"Wanene?"

 

Ta bashi amsa da, “Maman Jabeer ce daga nan mak’otarku.” 

 

Sai da ya d’an lek’a tukunna ya tabbatar da ita d’in ce, sannan ya bud’e k’ofar, ya gane ta sarai tana yawan son zuwa gidan, don dai kawai fuskane da ba ta cika samu ba a gun Matan gidan, ba ta da halin kirki sosai, ta fiye munafinci, a zahiri ta nuna tana yinka bayan idonka kuma ta b'atanceka.

 

Tana da surutun tsiya, har cewa Mutane take yi wai su zeenat suna wulak'anta Mutane ne don sunga su indiawa ne.

 

Tun bayan haihuwar Fairoooz ta soma shiga gidan, taje barka har da suna, daga nan kuma ta soma shiga gidan akai-akai, amman da suka fahimci halayyarta na son gulma, tsegumi da rashin tarbiya ga ‘ya’yanta sai suka yi baya-baya da ita, daman don dai kar tace sun wulak’antata ne suke kulata, ita kuma sha’awarsu take ta ga India-wa kyawawa.

 

Duk da cewa su Zeenat basa wulak’anta ta, amma Mahaifiyarsu Jabeer gani take mu’amalarta dasu, ba ta samun yadda ita take so.

 

Tsegumin da ta fara yi a tsakaninsu kuwa taso Daweeshat ta dai na barwa Zeenat d’anta FAIROOOZ, don tana jin haushin yadda kowani lokaci sai dai a sameshi a hannun Zeenat, sai dai ko da ta kawo tsegumin zancen Daweeshat sai ta kusheta, daga wannan lokacin ta k'ullaci Daweeshat cikin ranta, domin ta nuna mata hanyar da ta dace amma tak'i bi.

 

Kai tsaye d’akin Daweshat ta nufa, da yake ta riga ta san gidan.

 

Daweeshart na kwance tana d’an jin jiki, don k’irjinta gaba d’aya a tokare take jinsa, ya matsa mata, kuma ko Mijinta ba ta fad’a mawaba. Wannan yana daga cikin halayyar Darweeshat nauyin baki, ba ta cika son magana ba, ko abu ke damunta sai ya kai ya kawo take magana.

 

Sallama taji a k’ofar d’akin ta kamar daga sama tare da bubbuga k’ofar.

 

Ta amsa sallamar lokaci d’aya kuma ta mik'e da k'yar tare da nufar k’ofar d’akin don ganin ko wanene.

 

Tana ko bud’ewa suka yi kicib’is da Maman Jabeer, Daweeshat na gaisheta amma Matar ko tsayawa ta amsa ba ta yi ba, ita a dole ranta ya b’aci, nan ta fara sirfa masifa da bala’i dama halintane ta saba.

 

Ta inda take shiga bata nan take fita ba, akan me za a hana ‘ya’yanta zuwa wurin Fairoooz, kuma shima an hana shi zuwa wurinsa, Ko dan sun ga ana sonshi ne, shima fa Mutum ne kamar kowa.

 

Daweeshat na k’ok’arin yin magana amma tak’i saurarenta, maganganu marasa dad’i ta rink’a fad’i.

 

Daweeshat ta yi tsaye kurum, tana mamakin hali irin na Maman Jabeer. 'Duk sauk'in kan da suke yi mata ba ta gani, a tunaninta idan da wasu ne ta samu, ko inda suke ba za su barta ta shigo ba.'

 

Ba abin da ya fi yiwa Darweeshat zafi a zuciya cikin kalaman Maman Jabeer, irin cewar da tayi,

 

“Har ke mai d’a kwaya d’aya za ki yiwa Mutane rowarsa? Ku da ba haihuwa kuke yi ba, zuri’arku da baku gaji iri ba, Fairoooz d’in ma waya sani ko d’an halak ne, wa ya san inda aka samo shi."

 

Cike da dauriya Daweeshat tace, ''Idan Fairooz d'an halas ne ina tunanin kin fi kowa sani, tun da akan idanunki aka haifesa, batun haihuwa kuma wannan na Allah ne ba wani iri da ake gado, wanda Allah yayi nufi da cewa zai haihu, to zai haihu ko mun daren dad’ewa.”

 

A fusace tace, ''Oho dai, mu munsan sirrin da ake b'oye wa, idan d'an halas ne a haifo masa wani k'anin.''

 

Tana gama yab’a mata wad’an nan bak’ak’en kalaman ta juya ta barta a nan tsaye, sauri-sauri take dan ta san ba k’aramin ta’asa tayi ba.

 

Tana zuwa gun mai gadi tace, ''Na fito.” 

 

Ya bud’e mata k’ofa ba tare da kowa na cikin gidan ya ganta ba, daga Daweeshat da ta yiwa tijara, sai mai gadin kad'ai suka san shigowarta.

 

Nan take jikin Darweeshat ya fara rawa a nan inda Maman Jabeer ta barta tsaye, zuciyarta na har bawa da sauri da sauri wani irin zafi mai tsanani da rad’ad’i take Ji. Da k'yar ta iya komawa cikin d'akinta, sai kyarma take yi tamkar na mai jin sanyi.

 

Tayi sa’a kuwa wayarta na kan kujera, nomban Zeenat ta kira.

 

Kamar a mafarki Zeenat taji k’arar ringing d’in wayarta sama-sama don har barci ya d’an fara d’aukarta, tana dubawa sai taga sunan ‘yar uwarta, cikin sauri ta d’auka tana tambayarta,

 

''Lafiya kuwa sis ba yanzun nan muka rabu ba?”

 

Cikin rarrauniyar muryarta dake fita can k’asa-k’asa taji Daweeshat na fad’in,

 

''Sister ki....zo don.....Allah.”

 

Da sauri Zeenat ta tashi, ita kanta ba dad'in jikinta take ji ba, tana ganin jiri haka nan ta nufin d’akin Daweeshat.

 

Kwance ta tadda ta cikin wani irin mawuyacin hali, mamaki k’arara ya bayyana a fuskar Zeenat don ba tayi tunani ciwon da Darweeshat tace tana ji har ya kai haka ba.

 

Ta tallabo ta tana kiran sunanta,gani tayi idanuwanta na rufewa a hankali a hankali, sakinta tayi da gudu ta nufi wurin Mijinta don sanar dashi abinda ke faruwa, daya ke ba nisa yayi ba yana cikin library d'insa na gida. 

 

Ko da suka k'araso Darweeshat ta riga ta suma.

 

Da taimakonsa suka sanyata a Mota, kai tsaye Asibiti suka dosa.

 

Suna zuwa aka amshe zuwa d’akin bada taimakon gaggawa (Emergency Room).

 

Duk abin nan da ake yi Zeenat dauriya kawai take. 

 

An yiwa Darweeshat duk abin da ya dace, don sai da k'yar, aka shawo kanta. Sai da Malam Hafeez ya tabbatar an sami kanta tukunnna sannan ya kira k’aninsa ya sanar da shi suna cikin Asibiti.

 

Kan kace wani abu sai ga Dr. Abbas ya taho da kayan aiki ajikinsa da alama daga aiki yake cikin yi, bai ma san da zuwansu ba, domin Asibitin mai girma ne, in kana wani b'angare ba lallai kasan meke faruwa a wani sashen ba, kuma akwai wadatattun ma'aikatan likitoci masu yawa na fannin cututtuka daban-daban, wannan dalilin ne ke k'ara d'aga sunan Asibitin a kullum.

 

Lokacin da ya shigo d’akin da suke Darweeshat ma harta farfad’o, cikin sanyin jiki ya cire rigar aikin dake jikinsa ya rataya a gun da akayi domin hakan.

 

Bakin gadon da take kwance ya k’arasa sannan ya zauna kusa da ita, sunkuyo da kanshi jikin gadon yayi bayan ya zuba mata idanunsa.

 

Kallon juna suke ido cikin ido, sai kawai ya fara zubadda hawaye. “Why Darweeshat! Why?'' Cikin raunatacciyar murya Dr. Abbas yace da ita.

 

Sai da ya share k'wallar dake zuba daga Idanuwansa yace, "Me ya faru dake ne, akwai wani abu da nake miki ne, wanda ke b’ata maki rai? Kin san had’arin da ke tattare da sanya damuwa ga me larura irin taki kuwa, ko kina mantawa da matsalar ciwon dake damunki ne?"

 

ya sake share hawayensa tare da fad'in, ''Ko so kike na rasa ki?'' Wannan karan ya k'arasa maganar tasa ne cikin kuka, tamkar k'aramin yaro.

 

Ita ma k’wallar take yi, ji take kamar ta bud'e baki ta fad’a masa abin da ya faru tsakaninta da mak’ociyarsu, kamar ta fad’a masa bama wai yau ne rana na farko da ta fara gaya mata magana mai zafi ba, ta san lallai da sai Naman Jabeer ta gane kuskurenta! Amma ina, Daweeshat ta kasa magana, da tayi yink'urin yin magana sai ta kasa cewa komai, takan ji bakinta yayi mata nauyi, kuma da zarar ta tuna maganganun da Maman jabeer ta fad'a mata sai numfashinta ya fara fita sama-sama.

 

Ganin halin da take ciki yasa Dr. Abbas rik’o hannunta ya matse cikin nashi, ace gashi likita cikakke, amma Matarsa tana fama da irin wannan babbar matsalar, kuka yake yi kamar karamin yaro.

 

Hafeez dan'uwansa yaja shi waje yana bashi hak’uri, da ban baki.

 

Dr. Abbas yana jinsa ne kawai, domin shi kad'ai yasan abinda yake tunani.

 

Nan Hafeez ya sanar dashi zai je gida domin sanar da Mahaifinsu halin da ake ciki, saboda bashi ma da labarin abinda ke faruwa, Hafeez yak’i fad'a mishi ne tun kafin tahowarsu, saboda gudun tashin hankalinsa idan da ya ga Daweeshat a lokacin, ya riga ya fara tsufa, yanzu abu kad'an ke tayar da hawan jininsa.

 

Tare suka koma Asibitin da Alhaji Yusuf, don Hafeez na zuwa gida ya fad’a mishi sun kai Daweeshat Asibiti yace,

 

“Subhanallahi! Garin yaya, me ya faru?”

 

Daga nan kuma yace su tafi tare to.

 

Suna zuwa suka taradda Dr. Sa'eed ya bayar da bayani cewa zuciyar Darweeshat ce ta kumbura wato (Cardiomegaly), a sanadiyyar jinin da ke d’iga ta bayan zuciyarta (valve regurgitation) saboda yawan tunanin da take yi a wasu lokutan.

 

Dalilin kumburin kuma yanzu sai an mata aiki a zuciyarta, wato ( heart valve surgery).

 

“INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN!.” Abinda bakin kowannensu ke fad’a kenan.

 

Wannan shine abinda ya faru bayan FAIROOZ ya tafi Makaranta, cikin wannan halin ya riske su a Asibiti.

 

BABI NA ASHIRIN

Lokacin da Fairooz ya taradda ba kowa a gidan, ta b'angaren iyayenshi suma sai a daidai nan suka tuna da lokacin dawowarsa gida yayi, Hafeez ne ya kira wayar gida har suka yi magana da Fairooz.

Fairooz yayi shiru, hawaye na ci gaba da fita daga Idanuwansa.

Yanzu ya fahimci sirrin da aka b'oye masa, yanzu ya san hak'ik'anin Mahaifiyarsa ta ainihi, ya gane Darweeshat ce ta haifeshi ba Zeenat ba, duk irin son da yake yiwa Maminsa, da ita ma irin son da take yi masa, ashe ba itace Maminshi ba, al'amarin ya rikita tunaninsa.

Cikin zuciyarsa gani yake Maminsa ba ta kyauta mishi ba, ganin cewa ita ta koya masa yin Addu'a a bayan kowace sallar farillah idan suka idar, tace masa Allah yana saurin amsar Addu'ar yara k'anana kamarshi, sai gashi be tab'a yi mata Addu'ar samun haihuwa kamar yadda yake yiwa Aunty Mami ba.

 

Yana nan rungume a jikin Zeenat sai shashshek'ar kuka yake yi.

Daweeshat kuma an shiga d'akin tiyata da ita.

Idanunsa cike da k'walla ya d'ago yana duban Zeenat yace,

"Mami ki daina kuka, idan Allah ya yarda ba abinda zai sami Aunty Mami kinji? Kuma Aunty Mami za ta gani sai kin haifamin *baby girl sister*. Kema kuma a d'akin Aunty Mami za ta zauna.'' A dole Fairooz ya sanya Zeenat yin murmushi ga hawaye na zuba a fuskarta.

Hannunsa yasa yana share mata hawayen da ke zuba daga idanuwanta, suma sauran 'yan d'akin duka hawaye suke zubarwa, suna kallonsu cike da tausayawa abin da k'aramin yaro Fairoooz yake fad'a, yaron wayonsa ya wuce tunaninsa.

Cikin ikon Allah aka kammala aikin Daweeshat cikin nasarar, kamar yadda likita ya sanar dasu, kuma ya bada bayanin cewa ba za ta farfado da wuri ba, dalilin alluran da aka yi mata, yace za ta iya kaiwa kwana biyu ma ba ta farka ba, saboda haka kar hankulansu ya tashi. 

D'aki na musamman aka basu inda za su yi jinyarta, kafin zuwa lokacin da zata warware gaba d'aya a sallamesu.

Ganin Dr. Abbas ya yi jigum, Hafeez ya dafa kafad'arsa, Dr. Abbas ya d'ago kai yana dubansa cikin raunin murya yake fad'in, 

''D'anuwana ina mamakin yadda Daweeshat ta k'are da kasancewa cikin irin wannan larurar, a matsayina na wanda ke duba marasa lafiya, amma abin har ya zama ya girmama a gareta ba tare da masaniyata ba! D'azu ina jin wasu patient na fad'in Matar da a ka yiwa aiki Mijinta likita ne.''

Sai da ya share hawayensa ya ci gaba da fad'in,

''Ni ina can ina kula da lafiyar al'umma, amma gashi na Matata.....''

''Ba laifinka bane d'an uwa.'' Hafeez ya katse shi.

Hannunsa ya rik'o kafin ya ci gaba da cewa "A mafi yawan lokaci wasu Mutane sukan d'auka cewa idan Mace na auran likita shikenan ciwo iri kaza ba zai kamata ba, har fad'i za ka ji suna yi yaza ayi ace wance na fama da ciwo kaza alhalin Mijinta Dr ne.

Wanda idan an sanya maganar a ma'auni na hankali, sam! abin ba anan yake ba, gaskiya ne likita na bayar da magani asha, amma Allah ne ke warkarwa, kuma sanin cututtuka da likita yayi bashi zai hana Matarsa ko shi kansa d'inma kamuwa da wata cuta ba, illa iya ka dai, su ma'aikatan lafiya sukan bi duk wasu matakan tsaro da kulawa wajen kare kansu gwargwadon saninsu, amma cikakkiyar kariya Allah ne ke bayar da ita, ita rashin lafiya jarabawace ta Ubangiji idan Allah ya jarabci Mutum da rashin lafiya ko a d'akin magani yake kwana sai yayi ciwo."

Da wad'an nan tausasan kalaman d'an uwansa, Dr. Abbas yaji ya sami sauk'in rad'ad'in da zuciyarsa take yi masa. Domin da gani yake kamar ko shine be bawa Daweeshat kulawar da ta dace ba.

Tunda aka yiwa Daweeshart aiki, Zeenat ta kasance kullum cikin Busy, ga kula da Fairoooz sannan ga zaryar zuwa Asibiti, don ma Dr. Abbas ya hutar da ita da dare, shi ke kwana a wajen Matarsa a inda ita kuma Zeenat take tafiya da Fairoooz can gida su kwanta. 

Da sassafe idan ta tashi za ta shirya Fairooz a wuce dashi Makaranta, kafin ya dawo za tai Abinci ta kai Asibiti da lokacin dawowar Fairooz yayi za ta koma gida tayi masa wanka sannan yaci Abinci, da sun kammala kuma za ta d'aukoshi su dawo Asibitin tare, sai dare su koma gida su bar ta tare da Dr. Abbas.

Duk abinnan ko da ake yi Daweeshat ba ta ma san inda kanta yake ba domin har wannan lokacin ba ta farfad'o ba.

 

BAYAN SATI D'AYA.

 

Lokacin Daweeshat ta fara samun sauk'i, a wani dare Fairoooz sun koma gida da Zeenat kamar yadda suka saba, ta gaji sosai, kwanciya kawai take son yi, amma saboda d'an gaban goshinta yana da homework sai ta tsaya tayashi yi kafin ta kwanta. 

 

Can suna cikin yin homework d'in, sai ji tayi cikinta ya k'ulle gefe d'aya, da sauri ta rik'e wurin da hannu, kafin wasu 'yan dak'ik'u kuma mararta ma ta ce dawa aka had'ata in ba da ita ba.

Nan take marar ta d'auki ciwo me tsananin zafi, sai juye-juye take yi.

Fairoooz yaga Maminsa tana cije baki tana juyi, tambayarta ya soma yi,

"Kya howa Mami?'' (Mami me ya faru).

Amma ina ta kasa magana.

Abin da ya hango a jikinta ne ya k'ara bashi tsoro, da gudunsa ya rugad'akin Daddy Hafeez, yana zuwa kawai sai ya fashe masa da kuka.

Hafeez ya dubesa cike da mamaki yana fad'in, "Fairoooz lafiya! Me ya faru?" 

Fairooz kam ba amsa kuka kawai yake yi yana cewa "Mami ita ma....."

"Maminka!? Ba karatu kuke yi ba?" Fairooz ya gyad'a mishi kansa.

Ganin sai kuka yake yasa Hafeez ya kamo hannunsa zuwa d'akin da suke karatu.

Cikin jini ya sami Zeenat inda take kwance gaba d'aya duk ya b'aci da jini.

 

"Subhanallahi! Zeenat me ya sameki haka, daman ba ki da lafiyane?" Ganin sai murd'e-murd'e take yi kuma ta kasa amasa mishi, yasa shi k'arasawa gareta cikin sauri.

 

Hannunsa yasa ya tallabo da ita zaune, dubawa yayi yaga lallai jinin dake fita jikinta ya wuce na k'a'ida, yace, "Ya zama dole mu koma Asibiti cikin daren nan."

 

B'angaren Mahaifinsu *Yusuf kakan Fairoooz* ya shiga da sallamarsa, zaune ya tadda shi akan dardumar da suka idar da sallar nafila ba jimawa.

 

Sallar nafila ce wacce sukan yi kullum, tun bayan da aka yiwa Mahaifiyar Fairooz aiki, suna rok'on Allah ya tashi kafad'unta. 

 

Addu'a Alhaji Yusuf yake yi afili, "Ya Allah don isarka da ikonka, rahamarka da jink'anka, ka bamu ikon cin wannan jarabawa da ka jarabci wannan zuri'a tamu dashi, tun daga kan rayuwata, na rasa iyayena, na zo kuma na rasa Matata uwar 'ya'yana, suka tashi cikin maraicin rashin uwa, ya Allah ka dubi wanna k'aramin yaron da tausayinka! ka tashi kafad'un Mahaifiyarsa. Ita ma 'Yar uwarta da ba ita ta haifeshi ba, ta kuma rungumeshi tare da rik'e amanarsa ya Allah ka ba ta ikon haihuwa, ka ba ta haihuwa me albarka Albarkanci Annabi masoyinka."

 

Yana kai wa daidai nan ya shafa, tare da amsa sallamar da d'anshi Hafeez yayi. 

 

"Baba Zeenat ce ita ma ba ta jin.dad'i sosai" Abinda Hafeez ya fad'a kenan cikin rawar murya.

 

''Hasbunallahu wa ni'imal wa kil. Me ya sameta ita kuma?"

 

''Bleeding (zubar jini) take yi." Hafeez ya amsa masa.

 

"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un."

 

"To mu tafi Asibiti da ita kawai."

 

Hafeez yace,"Baba da ka zauna sai ni in kaita, daman don na sanar da kai abin da ke faruwa ne."

 

"A'a ba za ayi haka ba muje Asibitin tare kawai, me zan zauna yi a gida 'ya'ya na ba lafiya, yi hanzari kasa ta a Mota gani nan fitowa."

 

Sai da ya b'ude Motar, sannan ya dawo ya sami wani zani mai kyau ya k'ara rufe mata jikinta dashi, d'aukarta yayi cak! sai cikin Mota.

 

Kujerun da ya kwantar na gidan baya ya shinfid'ar da ita, yayi mata sannu ta amsa da k'yar, har a wannan lokacin hannuwanta na rik'e da mararta.

 

Ya zagaya zai shiga gidan driver, Mahaifinsa ya dakatar dashi.

 

"Ba zai yu kayi tuk'i a wannan yanayin da kake ciki ba, gashi dare ya yi, na riga na kira driver ya....Bai gama k'arasa fad'in abinda yake cewa ba, sai ga direban ya iso.

 

Alhamdilillahi gama shi nan ya k'araso."

 

Da yake dama ma'aikatan gidan duk a cikin gidan suke, sashensu daban aka ware masu.

 

Alhaji Yusuf ya rik'o hannun Fairooz suka shiga gidan gaba tare da direba, ya umurci Hafeez daya zauna tare da Zeenat.

 

A haka suka nufi Asibiti, suna zuwa kuma ba tare da b'ata wani lokaci ba aka karb'esu.

 

Bayan wasu awanni Nurses biyu Mata suka fito tare da Dr. Sa'eed, daga d'akin da aka shigar da Zeenat ciki, offishinsa suka shiga suka ajje Files d'in dake hannunsu, shi kuma ya kira Dr. Abbas.

 

BABI NA ASHIRIN DA D'AYA

 

Dr. Sa'eed sun d'auki lokaci me tsawo kafin suka fito daga office d'insa, jikin Dr. Abbas ya yi sanyi sosai, kallo d'aya za ka yiwa fuskarsa ka fahimci tsantsar damuwar dake bayyane a jikinta.

 

Dr. Sa'eed ne ya nufi inda suke zaune, shiko Dr. Abbas tunda ya kalli fuskar d'an uwasa sau d'aya suka had'a idanu sai ya sunkuyar da kanshi, bai k'ara kallonshi ba kuma be k'arasa inda suke ba, yana tunanin ta yadda yayanshi zai ji, ko ya karb'i abinda ya faru.

 

Tun kafin Dr. Sa'eed ya isa wurin da suke, Hafeez ya mik'e tsaye yana tambayarsa. 

 

"Ya ake ciki Dr, me ya sameta ne, tana dai lafiya ko?"

 

Domin daga alamar da ya gani a fuskar d'anuwansa ya san wani abu ya faru.

 

"Kwantar da hankalinka Hafeez Matarka tana nan lafiya." cewar Dr sa'eed.

 

"To amma Dr. Me ya sanyata zuban jini ne? Shin Jinin ya tsaya yanzu?"

 

"Karka damu ya tsaya, zan ba ka amsar tambayarka na abinda ya sameta, amma so nake sai ka kwantar da hankalinka tukun don Allah, kasa nutsuwa da tawakkali wajen fahimtar abinda zan fad'ama kaji."

 

Hafeez yace "In shaa Allah, amma duk menene ya kawo wannan maganar?"

 

"Na san ka yarda da cewa Allah shine me yin duk yadda yaso, a kuma kowane irin lokaci, shi ke bayar da kyauta ga duk wanda yaso, lokaci guda kuma idan yaso sai ya karb'i abinsa..."

 

"Dakata Malam." Hafeez ya fad'a lokaci guda tare da cakumar rigar Dr. Sa'eed.

 

"Idan Matata ta Mutu ne kawai ka fito fili ka fad'amin Dr. Bana son wani b'oye-b'oye" 

 

Ya fad'a idanunsa har sun soma cika da k'walla.

 

"Ka saurareni Hafeez Matarka ba mutuwa tayi ba, sai dai kyautar da Allah yayi maku ne ba tare da kun sani ba, Allah ya canza lamarinsa."

 

"Ban gane me kake nufi ba Dr."

 

"Shiyasa nake so ka kwantar da hankalinka, idan har ka nutsu da kyau za ka fahimceni."

 

"To na kwantar" ya fad'a a tak'aice, zuwa yanzu jikinsa ya fara sanyi, ya gano kamar akwai wani sabon abu na daban wanda likitan keson fad'a masa, amma Zeenat ba mutuwa tayi ba.

 

Shi ko Alhaji Yusuf tun a nasihar da Dr. Sa'eed ya fara yiwa Hafeez, ya riga ya fahimci inda kalamansa suka dosa, Addu'a kawai ya fara yi kan Allah yasa d'ansa ya fahimci abinda za'a sanar mishi, ya zamo me tawakkali akan hakan."

 

Dr. Sa'eed ya dafa kafad'ar Hafeez ya jashi suka zauna a kujera mai kyau, sannan ya ci gaba da yi masa bayani,

 

"Hafeez wato abinda ya faru Matarka Zeenat ta samu stress me yawa a 'yan tsakanin nan, wanda har yaso ya zamar mata over-work, mu kuma duk bamu sani ba.

 

Hafeez ya karb'a da cewar "Ba wai bamu sani bane Dr. Mun san da irin aikin da Zeenat keyi, k'anina Abbas yayi-yayi ta rage, amman tace ba komai bane, ita lada take nema, Dr. Sa'eed ina son ka sani Zeenat baiwar Allah ce ta sosai shiyasa kaga na damu dana san halin da take ciki, ka fad'amin don Allah." Ya k'arasa maganar tasa kamar zai yi kuka.

 

"To ai dukkanmu mun kasance cikin rashin sani wanda masu iya magana ke cewa *yafi dare duhu* idan da mun san cewa Zeenat ba ita kad'ai bace, to da dole mun hana mata wad'an nan ayyukan da ta rink'a yi.''

 

Cikin wani irin yanayi Hafeez ke dubansa, lokaci d'aya k'irjinsa ya fara bugun sauri-sauri.

 

Dr. Sa'eed ya ci gaba da cewa, ''Rabo ne Allah ya baku kai da Zeenat na samun ciki babu wanda ya sani, a k'arshe kuma stress da yayi mata yawa saboda rashin k'warin da cikin beyi ba shine ya janyo mata zubar jini, mun kuma yi iya ko'karinmu don ganin cikin be fita ba, amma hakan be samu ba, yanzu haka Zeenat ta sami miscarriage (b'ari) ciki d'an wata uku.

 

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un!." Iyakacin abinda ya iya fitowa daga bakin Hafeez kenan, ya yanke jiki zai fad'i, Dr. Sa'eed ya tarosa da hannayenshi.

 

Dr. Abbas dake gefe guda ya rugo da gudunsa, rungumar d'an uwanshi yayi cikin wani irin yanayi.

 

Yace, "Daman abin da nake gudu ke nan gashi ya faru, d'an uwa ka tashi please!.'' Ya fad'i da k'arfi yana jijjigasa, amma Hafeez ko alamar motsi ba ya yi.

 

Nan take Dr. Abbas ya ja wani dogon numfashi tare fad'i a jikin d'an uwannasa.

 

Fairoooz ya hangi iyayenshi gaba d'aya sun daina motsi, kansu yayi yana kuka, yana fadin su tashi.

 

A haka nan ma'aikatan da Dr. Sa'eed ya kira suka zo suka janye Fairoooz daga jikinsu.

 

Kakanshi Yusuf ne ya rik'esa, zuciyarshi cike da damuwar halin da iyalinsa gaba d'aya suka shiga, Matan da Mazan duka a kwance.

 

Be yi mamakin sumar Abbas ba, domin ya san shak'uwar dake tsakaninsu, kusan tun suna yara shi da Hafeez, in dai abu ya sami d'ayansu zai yi wuya d'ayan be yi ba shima.

 

Yana kallo aka d'auki kowannensu a gadon da ake tura marasa lafiya.

 

BABI NA ASHIRIN DA BIYU

 

  Hafeez sai da ya yi kwana hud'u a gadon Asibiti, saboda tsananin jimamin jarabawar da ta gitto masa, bai tab'a tunanin Zeenat na da ciki ba, bai tab'a mafarkin za su sami ciki a wannan lokacin ba, sai gashi kuma Allah'n da ya basu ya karb'i abinsa. 

 

Illahirin gidan gaba d'aya sun yi bak'in ciki da faruwar wannan al'amarin, ba kamar Hafeez wanda kullum cikin kukan zuci yake, da farko kamar ba zai bar damuwa ba, ganin cewa abinda yake nema kenan ku san shekaru goma sha hud’u, sannan Allah ya bashi wannan arzikin ba tare da ya sani ba kuma ya karb’i abinsa.

 

Allah kenan bayan da baya hukunta al’amarinsa.

 

Daga k’arshe dai haka nan ya hak’ura ya fawwala ma Allah dukkan lamarinsa, da taimakon nasihar da Mahaifinsu ke yi masa tare da d’an uwansa Abbas.

 

Sai ya duk’ufa rok’on Allah, akan yadda ya bashi wannan kyauta kuma ya karb’a, da ya sake bashi arzikin wani d’an ko ‘ya masu albarka.

 

Bayan sati uku lokacin an sallamo Daweeshat tare da Zeenat daga Asibiti, Daweeshat ta warke garau inka ganta ma ba za ka d’auka itace kwanakin baya take kwance ba ta san inda kanta yake ba.

 

B'angaren Zeenat ita ma ta warware kamar ba ita ce ta yi b'ari ba, domin har ta ci gaba da sauran harkokinta, amma an hanata yin ayyukan da ta ke yi masu yawa kamar da, don gudun kar ta sake samun wani cikin ba’a sani ba a k’ara asararshi.

 

Ko Zeenat ta so tsawaita damuwa dalilin wannan b'arin cikin da tayi, Fairoooz kan d’ebe mata kewa matuk'ar suna tare.

 

Da ya ga alamar ta yi tagumi zai nufeta da surutansa, har sai ya tabbatar ta yi dariya.

 

A irin hakan ne wata rana Fairooz ya hango Zeenat da tagumi, k'arasawa ya yi gareta da cewa, 

 

''Mamina tunanin me kike yi? Ko babynki da aka ce babu shi kike tunani? Ohh! Na ma gane wato yanzu baki sona ne ko, wancan babyn kike so? shiyasa kike damuwa? Ba komai.”

 

Sai ya juya mata bayansa alamar yayi fishi.

 

Ko da zeenat ta ga haka, sai ta matsa wurinsa tana rarrashinshi.

 

''Mami idan kin haihu kenan za ki barni ko? Na san za ki daina sona?”

 

Murmushi tayi, cikin zuciyarta tace, 'Fairooz akwai iya salon magana.'

 

A fili kuma tace, “Ba haka bane d’ana, kai kad’ai nake so! Babu wanda zan nunawa soyayyar da nake yi maka, ko da kuwa d’an da na haifa ne a cikina, sai dai ka san wani abu beta?''

 

Ya girgiza kansa alamar A’a, “Idan Allah ya bani haihuwa, ina son duk soyayyar da nake gwada ma kai kuma ka nunawa abinda zan haifa, ku taso tare cikin zumunci ka ji? Promise me mera beta."

 

"Haan (yes) I promise." Sai suka k’ulla hannayensu.

 

Nan Fairoooz ya tashi yana tsallen jin dad’i, daga nan ya jata suka yi cikin lambun gidan. 

 

A can ckin lambun ma haka Fairooz ya rink'a sanyata dariya, a dole Zeenat ta bar duk wata damuwa dake damunta cikin zuciyarta.

 

    BAYAN WASU WATANNI

 

Gaba d’ayansu zaune suke zagaye da dining table, sun kammala cin Abincin dare, basu tashi daga wurin ba Fairoooz ne ke ta zuba surutu da sunan yana basu labari.

 

''Mamina yau ma idan na kwanta barci na san zan sake yin mafarkin babyn nan taki fa, kullum sai na ganta, tana mik’omin hannu ke kuma kina bani ita."

 

Gaba d’aya suka sa dariya, Daweeshat tace “Shikenan dai Fairoooz ka zama *dream boy* kullum sai kayi mafarkin wannan yarinya, to Allah dai ya kawo mana ita a gaske.

 

Cikin sakewar fuska Kakansa yace, "Ku k'yaleshi da gaskiyarsa fa, shi ya san wacece yake gani, ato kuka sani ma ko Matarsa ce.''

 

FAIROOOZ najin ance Matarsa ya amshi maganar da cewa, ''Toh ai Matata ce daman."

 

Dariya suka yi gaba d'aya.

 

Hafeez yace, "Fairoooz in dai har mafarkinka ya tabbata gaskiya ko, Maminka ta samu ciki har ta haifi yarinya Mace to Matar kace ita halak, na baka ita."

 

Abbas wanda bai ce komai ba tun da ake zancen sai murmushi yake, sai a sannan ya a amsa da fad’in, ''Ubangiji Allah ya tabbatar da hakan, zan fi kowa jin dad’i.

 

Gaba d’ayansu suka amsa da, ''Ameen.”

 

Zeenat ko da ba ta ce ko mai ba sai hannu tasa ta rufe idanunta, ganin zancen wasan Fairooz ya dawo maganar manya.

 

Maganar mafarkin nan shine zancen Fairooz gaba d’aya a ‘yan kwanakin nan, tun bayan da aka sallamosu Maminsa daga Asibiti.

 

Kullum Fairoooz ya tashi barci zai ce yayi mafarki ya ga Zeenat tana bashi kyautar wata yarinya kyakkyawa, idan yau bai yi mafarkin nasa ba to ko gobe sai ka ga ya yi, tun ana d’auka wasa yake yi ko kuma shirme ne na yara yanzu sun gane da gaske ne mafarkin nashi ba shirme bane.

 

            ****

 

A kwana a tashi, shekarun Fairoooz har sun kai goma sha biyu, amma idan ka kalleshi za ka d’auka shekarunsa sunfi haka, ya k’ara kyau da haske ga k’warjini kana kallonsa kaga *jinin indiawa*.

 

A wannan lokacin ya kammala karatunsa na *primary school* kakansa ya sanya aka samar masa Makaranta a can *India*, don can yace yake son yayi secondary school wurin kakanninsa b'angaren iyayenshi Mata.

 

A cewar Alhaji Yusuf, yana da kyau suma ya saba dasu ya san dukkanin Asalinsa.

 

Fairoooz na tsananin son karatu amma tun da aka ce zai yi nisa da Mamminsa, gaba d’aya sai ya koma mara sukuni, yaji sam ba ya ma son karatun in dai har sai ya rabu da Mammi Zeenat.

 

Damuwarsa da tunaninsa kawai shine yadda za ace ya daina ganin Maminsa na tsawon wani lokaci, ba wai Makarantar jeka kadawo bane.

 

Tunda Fairoooz ya fara fishi aka rasa mai shawo kansa, kakanshi yace ya baiwa Zeenat aiki tasan yadda za ta yi ta rarrasheshi tunda d’an gidanta ne.

 

Daga nan aka ci gaba da shirye-shiryen tafiyar Fairoooz Makaranta *India* an kammala had’a masa duk wani abin buk’ata, amma har zuwa wannan lokacin Zeenat ta kasa rarrashinsa, ita kanta jimami take yi na yadda za tai nisa da Fairoooz lokaci d’aya.

 

Tsawon shekaru goma sha biyu suna tare abinda ke rabata da shi kawai inya tafi Makaranta, sai kuma barci lokacin daya kara wayau sosai.

 

Komai ya kammala na tafiyar Fairoooz, amincewarsa kawai ake jira shida Mamminsa, don kowa a gidan ya san cewa idan har Zeenat ta amince da tafiyar nashi, to ta san ta yadda za ta shawo kan Fairooz shima ya amince.

 

Kakanshi yasa aka kira mai Zeenat har d’akinsa ta sameshi, tambayarta yayi kan yadda suka yi da Fairoooz, cikin jin kunya ta fad’a masa cewa ba ta yi magana dashi ba, amma za su yi magana a wannan ranar in Allah ya yarda.

 

Sanya mata albarka ya yi, ta tashi ta fice daga d’akin tana mai zubar da k'wallah daga idanunta. Tana jin kunyar surukinta, ba yadda za tayi, ya zama dole ta rarrashi Fairoooz ya amince.

 

   BABI NA ASHIRIN DA UKU.

 

Zeenat ta duba Fairooz cikin d'akinsa baya ciki, ko ina ta duba bashi nan, murmushi tayi don tasan inda za ta sameshi.

 

Kai tsaye lambun gidan ta nufa.

Kamar yadda tayi hasashe ko, zaune yake ya k'urawa flawowin dake a gabansa idanu, k'walla nata gangarowa daga idanunsa, da alama yayi nisa cikin duniyar tunani da yake ciki.

Nan take tausayinshi ya k'ara kamata, tasa hannu ta share k'wallar da suka zubo mata ita ma, cikin nutsuwa da k'arfin hali ta k'arasa inda yake zaune ta zauna.

Bai motsa daga inda yake zaune ba, hannu tasa ta juyo da fuskarshi yana kallon fuskarta, ta shiga share masa hawayen dake sauka a fuskarshi.

"Kya huwa mera beta?''

Be ce da ita komai ba, sai Idanuwansa da ya zuba mata.

''Don ance za ka ci gaban karatunka a k'asarmu shine kake fishi? Yanzu karatun ne kuma baka so ko yaya? Kai da na sanka da son karatu Fayrooz, ace kuma kana fishi akan tafiya Makaranta." 

Juya mata baya yayi ba tare da ya amsa ba, duk yadda tayi ta rarrashi Fairoooz yak'i amsa mata, ta rasa ya za tayi, can sai wata dabara ta fad'o mata.

Tace, "To shikenan tun da ba za ka kulani ba nima nayi fishi, kuma na fasa haifo ma tera sapna didi( k'anwarka ta mafarki)." 

Ai nan da nan Fairooz ya juyo jin an ambaci sunan Sapnar shi,(mafarkinsa).

Murmushi tayi a zuciyarta tace 'Yaro dai yaro ne.'

"Ni ba fushi nake yi da karatu ba Mammi.''

''To menene mera beta?'' Zeenat ta tambayeshi cike da kulawa.

Yace, ''Bayan gani nayi tare dake ake so ayi hanyar da za a rabani dake, inje can inda ban san kowa ba, kuma bani da abokin hira, wa zai dinga koya min Addu'oi, wa zai dinga yimin Assignment da home..........."

"Waya fad'a ma za ka rabu dani beta?" Zeenat ta katse mishi zancensa.

A hankali ta ci gaba da cewa, ''Ko ina kaje muna nan tare ni da kai, ba wai ina son kabarni bane Fairooz, nima ina jin tafiyarka har cikin raina!.''

Ta d'an ja dogon numfashi sannan ta ci gaba,

''Kayi hak'uri, kayi biyayya ga abin da grandfa yace kayi kaji?"

Hawaye na ci gaba da sauka daga idanuwanshi yace, ''Toh...''

"Har yanzu baka hak'ura bako? Ba ta jira amsar shi ba ta ci gaba da cewa,

 

India fa gidane a wurinka ba bak'on waje za ka ba Fairooz, tare za ka zauna dasu *Nani (grandmothers)* d'inka fa.

"Mami nifa babban abinda ke damuna ji nake idan na tafi ba zan sake ganinki ba, kamar ba zamu sake had'u.......'' Saurin toshe masa baki tayi hakan ya hanasa k'arasa abinda yake niyyar fad'a.

Ni da zan Haifa maka baby sis Matarka kamanta ne? Ina nan har kaje ka dawo in shaa Allah, kafin ka dawo za ka tadda na Haifa ma *tera Sapna*."

wani irin farinciki yaji har cikin zuciyarshi.

Murmushi ya rink'a yi domin yana son yaji an masa maganar *k'anwarsa ta mafarki*. 

Zeenat tace, "Another suprise mera beta! Na sanya an gyara ma wani kyakkyawan lambu a gidanmu, don har ya ma fi na gidan nan kyau." 

Dad'i ne ya k'ara kama Fayrooz, fad'awa ya yi jikin Zeenat tare da rungumeta.

Da haka ta samu ta shawo kanshi, Fairoooz ya amince da tafiya Karatunshi can k'asar *India* Mahaifar iyayensa Mata.

*

Ranar tafiyar Fairooz shi da Zeenat sun sha kuka sosai, rabuwarsu rabuwa ce ta masoya, wad'an da suka kasance cikin tsantsar so da shak'uwa, don sai da k'yar aka iya b'anb'are Fairooz daga jikin Zeenat.

Iyayensa Maza ne suka kaishi filin jirgi, inda bayan komai ya kammalu Jirginsu ya d'aga daga Nigeria.

 

Bayan tafiyar Fayrooz Zeenat ta koma d'akinta ta k'udundune kanta cikin bargo, wani irin zazzab'i-zazzab'i ne ke neman rufeta, dalilin rabuwa da d'an gidanta Fayrooz.

 

Duk yadda taso ta b'oye damuwarta ta gagara, kuka ta rink'a yi, ba ta san sabon da ta yi da Fayrooz ya kai har haka ba, sai bayan da bashi.

 

Hafeez shi ya rink'a bata baki, har ya samu hankalinta ya d'an dawo jikinta.

 

Shi kanshi ya san Matarsa sai tafi kowa kewar Fayrooz.

*

Fayrooz a cikin jirgi shima haka ya yi ta zubar da hawayen kewan Maminsa.

A airport na new Delhi jirginsu ya yi landing can k'asar india. Suna sauka, kakanninsa suka zo tarbarshi da yake sun riga sun san da zuwansa.

Daga nan suka wuce da Fairoooz zuwa masauk'i.

Lokacin da Fairoooz ya taka cikin gidan Iyayen Mamminsa ya ga yadda aka soma haba-haba dashi, ashe masu son shi ba iya gidansu kad'ai ya tsaya ba, don sai da kakarshi ta yi da gaske, sannan 'yan uwa da abokan arziki suka barshi ya k'arasa isa cikin d'akinsa.

Yana zama cikin d'akin Mamminsa ya fara kira kafin daga bisani ya gaisa da sauran iyayenshi.

Rayuwa sai ta dawowa Fairooz sabuwa a k'asar India, tun yana bak'unta a hankali a hankali har ya fara sabawa, musamman saboda yadda Mutanen gidan ke nuna masa tsantsar kulawa.

Bayan sati d'aya Fairoooz ya fara zuwa Makarantar gaba da primary, daya dawo kuma zai wuce islamiyyarshi.

Kullum safiya kafin yaje Makaranta sai ya gaisa da iyayensa, haka ma idan ya dawo, duk abinda yayi saiya bawa Zeenat labari, lambun da ta masa alk'awari kuma ya taraddashi, kusan ma yafi wanda yake hutawa a gida k'ayatuwa, ba k'aramin farinciki yayi ba, wannan lambun sai ya taimaka sosai wajen d'ebe masa kewa, yana ganin Maminsa ciki.

 

     BAYAN SHEKARU BIYU.

Lokacin Fairoooz har sun fara shirye-shiryen shiga aji uku na Junior secondary school, a wannan lokacin ya riga har ya saba da k'asar India, sai anyi hutu yake zuwa wajen iyayensa.

Shekarunsa sun kai goma sha hud'u, amma inka ganshi zaka d'auka yakai shatakwas, ya k'ara girma kyawunsa da haibarsa sun fito sosai, ga baiwar k'warjini inka kalle shi dole sai ya baka sha'awa, Fairooz akwai hankali da natsuwa komai dai nashi sambarka.

Akwai wani gida na aminin kakanshi dake kallon gidansu Fairoooz.

Me gidan wato *Anand bakshi* gwani ne k'warai *agun hawan doki, fad'a da makami, harbi, da sauran dabaru na kara kai a fagen yak'i*, ya kasance yana koyar da yara Matasa salo iri daban-daban na yak'i.

Fairoooz yayi sha'awar shiga wannan Makaranta ta training, aka sanyashi, cikin k'ank'anin lokaci ya zama *zakaran gwanjin dafi* acikin matasan dake koyon dabarun yak'in, ko da wa aka had'ashi sai ya doke abokin karawarsa, inya koma gida ya kira Maminsa a waya, labari kuwa Zeenat na shansa.

 

BABI NA ASHIRIN DA HUD'U.

 

Da sun fara wasan training za kaji gaba d’aya filin an d’auka da kirari Fayroooz! Fayroooz!! Fayroooz!!!. Kuma ko da wa aka had’ashi gwaji to shi ke cinye gasar, nan da nan sunan Fayrooz ya karad’e ko ina.

Dressing d’in da suke yi, shigen na 'yan Chinees masu koyar da kareti, Fayrooz ya kasance yana yawan yin dressing d'insa da farin kaya, akwai wani *band* na jan k'yalle da yake d’aurawa a goshinsa da k'ugunsa wannan shine kalar shigar da yafi yi sosai a duk lokacin training d’insu.

Bacin haka yana dressing kala-kala masu matuk'ar kyau, ba ranar da ba ya hawan doki, Abokansa suyi ta yi masa hotuna.

Dangane da *mafarkinsa* kuwa har a wannan lokacin yana yinsa babu abinda ya sauya, yana yawan ganin Zeenat ta haifi yarinya Mace kyakkawa tana mik’a mashi ita, kullum suka yi waya sai ya ba ta labarin mafarkinsa na kyakkyawar yarinyarta, wacce ya yiwa lak'ani da sunan Mera SAPNA wato Mafarkina!.

Wata rana Malamin Fayroooz yaron marigayi *MALAM HARUKHAN (Malamin daya koyar da iyayenshi maza lokacin da suka zauna india) suna karanta tarihi, ya bashi tarihin Sayyada Maryam Mahaifiyar Annabi Isah (A.S), irin halayyarta da tsantsar tsoron Ubangijinta, hak’urinta, irin yabon da ta samu acikin Al-k’ur’ani mai girma da sauran d’abi’unta kyawawa nan take Fayroooz yaji sunan ya kwanta mishi a zuciya.

 

Ranar da suka yi waya da Zeenat ya rok’eta da cewa in har ya kasance da gaske ta haifi ‘ya Mace, to yana son ta sanya mata suna *MARYAM* da indianci kuma yace zai rinka kiranta da Mera Sapna wato (mafarkina!) saboda yawan mafarkin yarinyar da yake yi.

 

Zeenat ta yi dariya tare da cewar, ''Wannan Sapnar taka dai Allah ya kawota a gaske Fayrooz!.''

''Ameen Ameen Mamina.''

Batun sunan da ya zab'a kuma tace dashi be da matsala, tun da ‘yar tata da yake fatan a Haifo ai Matarsa ce.

*

Wata rana Fairoooz ya kwanta barci bayan Yayi Addu’oinsa kamar kullum, sai yayi mafarkin Zeenat kamar yadda ya saba tana mik’a masa kyakkyawar yarinya.

Sai dai abinda ya bashi tsoro yau da wannan mafarkin nasa, shine Zeenat na mik’a masa yarinyar sai yaga wani irin k’ura bak’i ya taso ya lullub’e Zeenat din a inda take tsaye, kiran sunanta ya dinga yi itama tana kiran nashi, bayan wani lokaci k’uran ta d’auke, wayam! Fairoooz ya ga ba Zeenat babu alamarta.

''INNA LILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN!.'' Abinda bakinsa ya rink'a furtawa kenan lokacin da ya farka.

Ya dad’e a zaune yana nazarin wannan sabon mafarkin da yayi, wanda ya sha baban dana sauran kwanakin da yake yi.

Sai da yayi Addu'a sosai kafin ya sauko daga kan gadon da yake kwance.

Fairoooz ya d’auko wayarshi da niyyar kiran Zeenat, sai yaji wayar tashi ta d’au ringing, sunan Mamminsa ya gani, incoming call cikin sauri ya amsa wayar.

''Assalamu alaikum Maa." 

“Wa’alaikumussalam beta.

Kafin yace komai ta d'ora da cewar, 

Mubarakun, Mubarakun meri beta, tum Maa banne walo (Congratulation,Congratulation my son! Your Mom is going to be a mother) very soon in shaa Allah.

Kya!? Tum kya bolo meri Maa?” What!? Me kike fad'a me Mamie?/Fairoooz ya fad’a cikin k’araji, 

Zeenat tace “Haan meri beta (Eh haka ne d’ana) da gaske ne abinda nake fad'a mafarkinka ya kusa zama gaskiya in shaa Allah, Mamienka ta sake samun baby."

Wani irin tsalle Fairoooz ya daka, wanda shi kanshi bai san sadda yayi shi ba, ya kuma ji k’ara da bai san ko na menene ba, nan suka shantake da hira, farin ciki da tsantsar shi da Maminsa.

Bayyana farin cikin da Fairoooz ke ciki abu ne me wahala, gaba d’aya ma ya manta da zancen mafarkinsa da yayi niyar fad’a Mata.

Sai bayan da suka gama wayar tukunna Fairooz hankalinsa ya dawo jikinshi, nan yaga b’arnar da yayi.

Ashe kufunan tangaran ne da aka kawo masa Tea safe a ciki ya fasa su.

Murmushi yayi tare da girgiza kansa.

“Wallahi ban ma san abinda nayi kenan ba, ya Ubangiji Allah ka tsawaita rayuwar abin dake cikin Mamina, ya Allah ka sanya ta haihu lafiya, Allah ka albarkaci abinda ke cikin cikinta ka kuma sanya Mace ce.” 

Ya lumshe idanu tare da fad'in *Mera Sapna!.*”

       

       BAYAN WATA D'AYA.

 

Fairoooz ya dawo gida hutun jarabawarsu da suka yi ta kusa da k’arshen kammala Junior secondary school.

Ba don komai yazo hutu gida ba a wannan lokacin sai don cikin Zeenat, tun da ya dawo kuwa kowa a gidan yasha mamakin yadda fairooz ke

tarairayan Mamiensa.

Riritawa ba irin wacce bai nuna mata, ko cokali ba ya bari ta da’auka da kanta, komai take so to shi zai yi mata, haba-haba yake yi da ita sai kace k'wai. 

Shi ke ba ta Abinci da kansa tun da yazo gida hutu, k’afafunta sun kasance suna mata ciwo wani sa’in ma har da d’an kumburi, kullum saiya matsa mata k’afafun kafin ta samu yin barci, ko da ta nemi hanasa yakan ce,

"Karki manta Mami ke ce fa uwar goyona, komai zan maki ba zai kama k’afar wanda ke ki ka min ba saboda haka ki barni kawai.''

Baya barin d’akinta sai ya tabbatar da tayi barci tukunna, yakan ja bargo ya rufeta da yake lokacin sanyine, sannan ya kulle mata k’ofa.

Da rana ma kamar wani mai gadi yini yake yana gadinta, motsi d’aya idan tayi zai tambaya tana buk’atar wani abu ne? kai in dai ka ga Fayrooz ya guda daga wurin Maminsa to sallah zai yi, ko kuma ita tace ya tafi abinsa.

Shi Fairoooz a yadda yaso ma ba zai koma Makaranta ba, shi dai a nemo masa wata Makarantar ya zana jarabawarsa a gida kawai, Maminsa tace ba ta amince ba ganin baifi saura wata biyar ba ya kammala gaba d'aya ya dawo gida, dan Final Exam za suyi. Tace gara ya yi jarabawarsa acan inda ya yi karatun.

Ko da hutun su ya k’are haka nan Fairooz ya koma Makaranta ba don yaso ba, amma fa kullum sai sunyi waya Maminsa domin jin lafiyarta dana baby, lokacin cikin Zeenat yakai wata uku yana neman na hud'u.

 

     BAYAN WATA BIYAR

 

Lokacin cikin Zeenat ya kai watanni takwas, hakan kuma yayi daidai da cikar Fairoooz shekara uku akasar India.

A lokacin baifi sauran wata guda ba, su kammala karatunsu ba, shi kam gaba d’aya ya k’osa ya koma gida, ba kalar magiyar da bai ma Mami Zeenat ba kan ta amince ta rok’a masa ‘yan gida ya dawo, amma sam! Zeenat tak’i amincewa tace shida zuwa gida lallai sai sun gama zana jarabawarsu ta J.S.S.

An tsayar da magana kan cewa da zarar sun kammala jarabawa zai dawo gida Nigeria gaba d'aya, domin kowa ya san idan ma an hana Fayrooz dawowa tunanin *sapna ba zai barshi ya ci gaba da karatun a can ba.*

     INDIA

Ana gobe su Fairoooz zasu kammala jarabawarsu Maminsa Zeenat ta kirashi a waya vedio call, da babban albishiri na cewa ta haihu.

Allah yayi Zeenat ta haihu sannan kuma an sami *baby girl*.

Murna wurin Fairoooz abin sai wanda ya gani, ga kyakkyawar yarinyar nan an gwada masa ita amma ba halin ya amsheta, ji yake kamar ya mik’a hannu yaji Babyn a jikinshi.

Jarabawar kanta ji yake kamar ya barshi kawai ya dawo gida, sai dai ya san ba za su shirya da kakanshi akan hakan ba, dole sai ya zana paper ta k’arshe tukun na sannan ya dawo gida.

 

FAIROOOZ

 

Daga Alk'alamin Ayshnur pyaar

 

BABI NA ASHIRIN DA BIYAR

 

            

      *NIGERIA*

 

Tun daga nesa ya hango Mutane a k'ofar gidan, murmushi ya soma yi ya raya cikin zuciyarsa. 'lallai yarinyar nan Allah ya ba ta farin Jini, tarin Jama'a haka tun ma ranar sunan bai zoba kenan!.'

Da k'yar ya samu ya shiga cikin gidan saboda Mutane.

Cikin gidan ma Mutane ne a cikinsa amman Mata.

Duk inda Fayrooz ya wuce sai ya ga an bishi da kallo, 'Kai to ko dai yau ake sunan ne?' Ya tambayi kansa game da yin, k'wafa 'Wato ni aka ma wayau."

Sallama ya yi a k'ofar d'akin Maminsa had'i da kutsa kai ciki don bai ko jira a gama amsa sallamar da yayi ba ya cusa kai, domin yayi niyar ya yiwa Maminsa surprise ne.

 

Saboda tun wayar da suka yi daren jiya ranar da suka kammala exam, ce mata yayi an ce ana son ganinsu a school washegari saboda haka sai jibi zai iso gida, hakanne yasa bai fad'awa kowa tahowarshi ba.

Iyayensa ya gani a zazzaune cikin falonta amma ban da Maminsa Zeenat, sosa k'eyarshi yayi cikin jin kunyar yadda ya shigo d'akin, daga bisani cikin ladabi ya tsugana ya fara gaishesu.

Jaririyar ya hango a hannun Daweeeshart cikin sauri ya k'arasa gabanta yasa hannu ya d'auki yarinyar.

Wani irin sanyi mai dad'i yaji tare da sabon farin ciki yana mamaye zuciyarshi, fiye da yadda yaji ranar da aka mishi albishir da haihuwarta.

Yayi godiya ga Allah subhanahu wata'ala, da ya karb'i Addu'ar da yake yi a kullum kan Maminsa ta haihu lafiya, gashi ta haihun kuma abinda yake tsanin so da muradi *'Ya Mace*!.

 

Lallai Allah abin godiya ne, *MAFARKINSA* kuma ya zama gaskiya!.

"*Mera sapna*" Fayrooz ya ambata a fili.

"Kai dubi yarinyar wallahi kamar Mamiena take sak! Komai nata dana Mamie take kama, wai ina Mamien take ne ma? Ko tana ciki ne?"

Shi kad'ai yake ta magana babu wanda ya amsa mishi.

Jin ba wanda ya k'ara cewa wani abu cikinsu tun bayan gaisuwar shi da suka amsa me, yasa shi d'ago da kansa.

Kallon fuskokinsu yake yi d'aya bayan d'aya sai a lokacin ya lura babu walwala a tare da kowannensu, zumud'in daya shigo dashi ne ya hanashi fuskantar hakan tun a farko.

Ras! Fayrooz yaji gabansa ya fad'i,

"Ina Mamiena?" Ya sake maimata tambayar da ya yi a farko.

Tsam kakanshi ya mik'e tsaye yasa hannu ya karb'i yarinyar daga hanunshi, Daweeshat ya mik'awa, kamo hannun Fayrooz ya yi ba tare da yace dashi komai ba ya nufi k'uryar d'akin Zeenat dashi, tare suka shiga.

Abinda idanun Fayroooz suka hango ne ya sanya numfashinsa d'aukewa na wasu 'yan dak'ik'u, cikin tsoro da firgici ya juyo da kallonsa ga kakansa.

''Daadaji b...an....gane ba, mene...ne wancan nake gani ba?" Ya fad'a cikin rawar murya had'e da nuna inda yake kallo.

 

''Fayrooz Maminka ce daren jiya Allah ya yi mata rasuwa....''

 

Iyakar abinda kunnuwansa suka iya jiye masa kenan, daga kalaman da kakansa ke fad'a, wani irin duhu mai tsanani ya lullub'e idanuwansa, nan take ya fad'i k'asa sumamme.

Ruwa aka yayyafa masa tare da shafa masa a fuska, nannauyar ajiyar zuciya ya saukar gami da bud'e idanuwansa lokaci guda, ya sake kallon makarar gawar dake cikin d'akin d'auke da gawar da kakanshi ke ik'rarin cewa Maminsa Zeenatu ce.

"Ina sam! Hakan ba zai yu ba, Mamina ba ta rasu ba na sani.''

Kallonsu ya yi da hawaye sharkaf a fuskarsa ya ci gaba da cewa, ''Ku fad'amin ina take! Nace ku fad'amin inda Mamina take, ina take ne!?''

Zabura yayi zai tashi, rirrik'esa suka yi ana tofa masa Addu'o'i. 

''Jiya-jiyan nan fa muka gama waya da ita...tace dani ta haihu, ta ya za ayi ace dani ba ta nan....'' Haka Fairoooz ya rink'a fidda kalamai na sambatu gwanin ban tausayi, idan ka kalleshi tamkar wani zautacce duk wanda ya kalli halinda yake ciki a wannan lokacin sai ya tausaya masa.

"Baba kana ganin zamu tsaya kuwa har Fayroooz ya dawo cikin hayacinsa? Gawarta tana ajiye fa tun safe ina ganin kawai ya kamata a kaita makwancinta ni daman na san haka za ta faru." Cewar Dr. Abbas Mahaifin Fairoooz.

"Hakan ba zai yuba Abbas wasiyyar tace fa, tace kar abinne gawarta sai tare da Fayroooz, wajibine cika wasiyyar mamaci matsawar ba sab'an Allah bane, idan muka tafi da ita yanzu gaba d'aya mun karya alk'awarin da muka daukar mata,

zai dawo hankalinsa yanzu in shaa Allah."

Kakanshi ne ya furta wad'an nan maganganun, lokaci guda yana tuno da Zeenat ta tab'a fad'a mishi cewa Fayrooz komin abin da ya b'ata masa rai da anyi masa nasiha mai shiga jiki had'i da rarrashi yake saukowa, kuma ko kafin ya bar gida shi ma ya shaida hakan, don da abinda Zeenat ke samun nasara a kanshi kenan ko yaushe, kuma yake jin maganarta fiye da ta kowa, saboda tana yi masa nasiha da rarrashi.

Nasiha kakanshi ya shiga yi masa cikin kalamai masu taushi da ratsa zuciya.

"Fayrooz ina son ka kasance d'aya daga cikin bayin Allah masu dauriya da tawakkali akan kowani irin hali ko yanayin da suka tsinci kansu ciki, ka yarda da cewa Allah shine ke rayawa kuma shi ke kashewa aduk lokacin da yaso, rayuwarmu duka a hannunsa take! shine me fitar da Matacce daga rayayye, idan yaso kuma ya fitar da rayayye daga Matacce! Wannan duka na daga cikin ayoyin Ubangiji.

Idan yaso d'a sai ya rayu da iyayensa, haka kuma idan yaso d'a sai ya rayu ba iyaye, wani tun yana jinjiri, wani ma kuma sai ya girma ya fara sanin dad'insu, mutuwa za ta shiga tsakani.

Rayuwar kowane mumini na k'warai cike take da jarabawar Ubangiji! Ka yi k'okari ka kasance mumini na k'warai, me yarda da k'addararsa me kyau ko mara kyau.''

Sai da ya d'an nisa, kafin ya ci gaba da cewa,

''K'addarar da ta zo mana me kyau shine Allah ya baiwa Maminka cikin yarinyar da kake ta rok'onsa a kullum ya kuma sanya ta haifeta lafiya a raye, k'addara mara dad'i kuma ya karb'i Maminka daga garemu lokaci d'aya.''

Sai da ya share hawayen dake zubar masa, ya ci gaba da maganarsa.

''Bamu san abin da Allah ya b'oye tsakaninka da wannan jinjira da ya baka ba, domin wannan jinjirar takace Fsyrooz! Ina k'ara rok'onka da kayi k'ok'arib zama me tawwakali fayrooz, rasuwar Zeenat ba kai kad'ai ta shafa ba, Mutuwa ce da ta shafemu dukkanmu.

Na san ya zama dole za ka yi mamakin rasuwar Zeenat. Amma ba'a mamaki da ikon Allah abin da ya faru daren jiya misalin k'arfe uku na dare Maminka ta fara rashin lafiya Zazzab'i mai tsanani ne ya rufeta, bata d'auki wani lokaci mai tsayi sosai ba ta d'an sami sauk'i, don har munyi sallar Asubahi tana raye, sai kuma jikinta ya sake dawowa karo na biyu.

A madadin zazzab'i sai jikin ya fara sanyi zamu tafi Asibiti tace A'a, kar mu wahalar da kanmu domin ita lokacin ta ya riga yayi jikin kowannen mu yayi sanyi a lokacin, mun tambayeta dalili tace ita tasan abinda take gani, kuma tana rok'onmu da Allah kar a d'auketa zuwa Asibiti domin ka da a wahalar da gawarta, abinda take so shine mu ba ta takarda da abin rubutu za ta bar maka sak'o.

Duka muna tsaitsaye akanta sai hawaye kowa keyi mun kasa gane abinda ke faruwa, tun kan ka iso gida Zeenat tace mana yau zaka dawo, don ta san lallai yau sai ka zo gida, duk da a waya kace mata sai gobe, ta rubuta takarda tace a baka idan ka iso, sannan ta bar wasiyya kar a rufeta sai tare da kai daga nan ta rufe idanuwanta bayan wani lokaci muka ji tayi kalmar shahada shikenan."

Kuka sosai Fairoooz ya keyi, zuwa wannan lokacin kuma hankalinsa ya dawo jikinsa, saboda dogon nasihar da kakanshi ya yi mishi, sai dai tsananin tashin hankalin da yake ciki ya gagara barin jikinsa.

"Abinda yasa na sanar da kai mutuwar Mamminka a haka, saboda tun kafin ka iso gida muke shawarar ta hanyar data dace a fad'a ma, yadda ba za ka tashi hankalinka ba, amma mun rasa, ganin haka yasa ina ganinka na yanke shawara ta k'arshe, ina tunanin hakan da nayi shine kawai mafita don kowani irin b'oyo za'ama k'arshe dai dole ka sani kuma gashi kai kad'ai ake jira mu kaita gidanta na gaskiya." 

Sai da ya kai daidai nan ya sauke ajiyar zuciya.

"Ka daure yanzu ka tashi, kayi k'ok'arin cika wasiyyar Maminka, ka tashi muje a kai ta gidanta na gaskiya, shine cikar halaccin soyayyarka a gareta."

A haka nan Fayrooz ya daure cikin k'arfin hali, har aka yi jana'izar Maminsa Zeenat suka dawo gida.

'Kulli Nafsin za'ik'atil Maut!.'

 

      *BAYAN SATI D'AYA*

 

Aka sanyawa jaririya suna Maryam kamar yadda Zeenat ta bar wasiyyarta, domin ba ta manta da alk'awarin da ta yiwa Fairoooz ba, akan sunan da yake so ta sama 'yarta in har ta haifi 'ya Mace.

B'angaren Fayrooz kallo guda za ka masa ka karanci yadda gaba d'aya kamaninsa suka sauya, cikin k'ank'anin lokaci har ya fad'a, amma duk da haka ya d'auki nasihar kakanshi sosai, bai bari tunani yayi galaba akanshi ba, ya daina kuka, sai Addu'o'i kawai yake ta kwararawa zuwa ga Maminshi.

Da yammaci yana zaune a d'akinsa, Wasik'ar da marigayiya Zeenat ta bar masa ya d'auko, idanunsa ya kawo k'walla, yana tunanin sak'on da zai tarar a ciki.

Yarinyar da Zeenat ta bari ya jiyo tana kuka.

"Mera sapna!.'' Ya fad'i a fili gami da mik'ewa tamkar an tsikaresa.

Ko da yaje d'akin madarar jarirai mai kyau ya tadda ana had'a mata, saboda yunwar da take ji.

Ana gama had'awa ya karb'i madarar da yarinyar ya rungumeta a k'irjinsa, zuciyarsa tana jin tsananin so da kuma tausayin yarinyar.

Wasik'ar da Maminsa ta bar mishi na a hannunsa kai tsaye lambun dake cikin gidan ya nufa.

Yana shiga ciki ya fara ganin hotonsu shida Mami Zeenat suna wasa, sai dariya take yi masa.

Hawaye masu d'umi suka gangaro daga idanuwansa, inda suka yiwa kansu masauk'i akan k'uncinsa.

A hankaki yasa handkerchief d'insa ya gogesu yana fad'in,

"ALLAHUMMA AJJIRNI FI MUSIBATI WA AKLIFNI KAIRAN MINHA!."

Wuri mai kyau Yasamu ya zauna, sai da ya ba yarinyar madararta tasha ta k'oshi tukunna, sannan ya d'auko wasik'ar da Zeenat ta bar masa domin karantawa.

 

Tammat bi hamdulillah.

 

Masu karatu anan ne na kawo k'arshen FAIROOOZ littafi na farko, kurakuren da nayi cikinsa Allah ya yafemun, darassun dake ciki kuma Allah yasa a amfana dasu, sai mun had'u a Fayrooz, kashi na BIYU.

 

Shin wani irin sak'o ne FAIROOOZ zai gani cikin wasiyyar da ZEENAT ta bar masa?

shin yaya RAYUWAR JINJIRA MARYAM ZA TA KASANCE?

 

SHIN INA LABARIN MALAM HAFEEZ? Wanda ya dawo gida bai ga 'yarsa Maryam ba, har yayi kuka ya gama, a k'arshe ya d'auko littafin da yace ya zamar masu annoba, ya bud'eshi da niyar bin Maryam duniyar da take ciki...

 

Menene dalilin komawar Malam Hafeez DAJI da zama?

 

Menene abinda Maryam tace ta tuna, yanzu ta tuno komai a wancan duniyar da ta ke ciki?

Wad'an nan tambayoyi, dama sauran wanda ban kawo ba suna nan k'unshe cikin littafin FAIROOOZ kashi na biyu in Allah yaso.

Note: Fairoooz part 2 zai zo da bakandamiyar labarin maganar da hausawa kecewa *RAMAWA KURA ANIYARTA! Don haka karkuyi confused.

Masu Iya magana na cewa alheri dank'one, baya fad'uwa k'asa banza, kamar yadda alherin da zeenat ta yiwa fairooz zamu ga amfaninsa nan gaba kad'an a cikin littafi na biyu.

 

Taku ce har kullum, Ayshnur pyaar❤ naam hei mera.

 

 

 

 

Ashnur pyar❤ 

naam hei mera.

 

 

 

 

 

 

 

Tags: Al'ajabi Nishad'i Tarbiyya Soyayya Addu'a
11380
7
1
2
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

2019-10-02 05:56:47

khady AL2019-09-22 21:37:37Pls anyi na biyun

2019-08-22 20:18:53

Ashnur pyaar2019-07-16 04:11:55In shaa Allah

Ashnur pyaar2019-07-16 04:11:55In shaa Allah