CIWON IDANUNA

Written by Benaxir OmarPublished on 2018-12-12 16:19:33Category Romance(BASED ON A TRUE LIFE STORY) (wannan labarin gaskiya ne, yafaru, sai dai nacanja gari, suna dakuma wasu abubuwan, I just hope it should be useful) tags: #Romance #Love #MarriageDuba was labarai »

CIWON IDANUNA NA


Benaxir Omar

(NWA)


(BASED ON A TRUE LIFE STORY)


(wannan labarin gaskiya ne, yafaru, sai dai nacanja gari, suna dakuma wasu abubuwan, I just hope it should be useful)


Wawan birki naja, gabana ya tsinke ya fad'i, numfashina na kokarin daukewa, tunanina ya tsaya cak, na sa hannu na murza idanuna don tabbatar da cewa ba bacci nakeyi ba, bakuma mafarki nakeyi ba, na kuma tabbata ba gamo nayi ba, toh ko dai gamon ne?

A tarihin rayuwata nasan India da kyau, nasan larabawa da kyau nakuma san jinsin Fulani da shuwa harma hausawan kasanmu da kyau, sai dai a film ko labari, tadi ko wasa, bantaba ganin halittar 'Da namijin dake gabana ba, nayi ayatul qursiyu natofa ajikina, gashi dai bai matsamin akan hanyan ba balle nasa ran wucewa, da alamu ya bugu iya buguwa, ya sha wani Abu.

"innalilahi wainnailaihi rajiun" na ambata wa kaina a lokacin Dana kara hada ido na danashi, dogo ne , fari ne ,saidai ba fari can ba akwai alamun dishewa a alamarinsa, yana da dogon hanci, gashin kansa ta kwanta luf tamkar na bahaushen balarabe, idanunsa manya ne,, saidai Wanda bature kekira da sexy eyes, a lumshe suke tamkar yanajin bacci gasu farare sol, 

innalilahi wainna ilaihi rajiun shinaci gaba da ambata dasauri najuya akalar motar dan barin gurin, zuciyata takasa amincemin cewa mutum ne ba aljanniba, ina tafiya ina waigawa don tabbatar dacewa baya biyoni


Nashiga uku ni Nadra nayi gamo da katar!!!!!


Dasauri na nufi gida, maigadi yabude min gate nashige, tsantsan rikidewa mantawa nayi ban rufe kofar ba balle nacire key din, dakina na nufa kai tsaye, Allah ya taimakeni mammy( mahaifiyata) batanan narufo kofan nafada kan gadon, na lumshe ido ina tunanin halittan da nayi, nidai banyi gamo ba, mutum ne zahirin gaskiya, ahaka bacci ta kwasheni ban farka ba sai magrib, na dauro alwala nayi sallah,na mike na fito falo inda naga mammy na shirya dinning abinci abamama(mahaifina, yadda natashi naga yayuna nakiranshi), 

"ke kuma wani sabon salo kika samu na bacci dayamma!, ko dai jikinne?"


" a'a mammy, wlh nadawo gun tela ne, daga kwanciya ashe bacci ya kwashen,"


"toh ai saiki zo ki nutsu kisha ruwa, kullum ke zakiyi azumi amma kina mantawa , bayan nace miki manzon Allah SAW ya umurcemu da mu gaggauta shan ruwa, mu jinkirta suhur, amma banda ke, ki kiyayeni fa" 


"oops, mammy naci dabino a daki AI" na nufi hanyar kitchen don maganan gaskiya na manta azumi nakeyi, tsantsan damuwan Dana Shiga yau, kuma kasanchewar yau baayi rana ba, nidai na nufi talatu ta hada mini kayan shan ruwa nazauna zanci, ikon Allah saikuma nagagara CI, tunanin bawan Allah yadamen, yakamata na koma gun ko zansameshi, toh amma ko ma shi giyan wake baza'a barni nafita ba, tuni dabara yafado min, namike na leka falo abamama nacin abinci, na zauna gefensa ina murmushi, shima murmushin yakeyi


"lafiya auta?, ko jikin ne? "


"ae daddy ciwon kai ne shine nakeso ko zanfita na leka chemist"


"subhanallah, ya za'ayi kije ke kadai?, ina kamal ? kirashi yazo yakaiki, shi ko wani dai a samarin gidan nan!" nayi murmushi nace "toh" jikina na bari naleka daki nadauko mayafi na da mukullin mota na, Nazo nawuce, fannin samarin gidanmu na nufa, su rai shida narinka buga musu dakuna, Wanda dama dakuna shida ne a bq din, kowa da nasa, yaya kamal bayanan donhaka na buga na ya amir, yana shirin fita asham ,


"ya amir abamama yace ka rakani asibiti" ya kallen ta gefen ido batare da yayi magana ba yana kokarin rufe dakin nasa , na maraice kaman zanyi kuka, bai amsa ba nabi sawunsa, daman ban sa araina zai kulani ba, miskilancinshi daban ne, nidai inzai fita dani shikenan, motar sa yanufa nabi bayansa kaman agwagwa da yayanta,


"wani asibiti?"


"reemee"


dama a gida nayi analysing cewa daga gidanmu wani asibiti zanbi Wanda dole nabi wannan hanyar naganshi? Nagano remee ne kawai, aikuwa muna yanko kwanar fita daga layin , hasken wutan titin ta haskoshi yana zaune sanye da jallabiya, gabana ta tsinke ta fadi, ba shiri nace "yaa amir ka tsaya" yaja birki tare da juyowa alamun tambaya, ban kulashi ba nabude kofan motan, dasauri na nufeshi, bashiri ya amir yabiyoni kaman na zauce, ina zuwa nasa hannu nataba shi, ya Allahu, mutum ne, ba aljanni ba, dagowa yayi yakallen idonsa tayi jaa hasken wutan ya haskashi sosai, gabana bata bar fadiba, cikin sassanyar murya mai zaki wanda kunnena yajiyomin yace "lafiya?"jinayi an janyoni da karfi aka wurgani mota


"ya amir ka tsaya mudaukeshi, ba mahaukaci bane , wallahi mutum ne, ba aljanni bane"

CIWON IDANUNA 2

[01:19 AM, 10-Jul-16]

by Benaxir Omar

2??CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

(NWA)

(BASED ON A TRUE LIFE STORY)

Ba tare da ya saurari kalamuna ba ya jefani motar, wani bakin ciki naji ya gulleni a rai hawaye ya soma ruwa a idanuwata ina kallonsa har muka wuce, yaa Amir in banda jan tsaki babu abinda yakeyi nasan ranshi ya baci anma nashi kadan ne akan nawa, da zai auna bakin ciki na da nashi da zai san cewa shi wasan yara yakeyi, rai a bace nace kaina ke ciwo akaban magani muka biya kudi muka fito, a hanyan komawa haka nayita lekawa ki zan ganshi, aikuwa yana kwance akan wata kujera kamar wani sarki muna shiga gida mammy tana falo zaune dasu yaa kamal duk sunyi jigum suna jiranmu ganina yasa tamike da hanzarinta "zo auta na, meya faru? sun baki magani? kan yadena ciwo?"

na lumshe ido jim yadda ta kamo kaina " toh mammy kin rike kan" dasauri ta sake tana tofa min addua, mikewa nayi na nufi daki ba tare da na kula yayuna dake cikin falon ba, tabbas sunsan ina cikin damuwa don a yanda nake da gagara da kansu suke korata daga falon amma yau ni ce a nutse hakan ya daga hankalin mammy batasan ciwon so bane ya damen Allah sarki ni, sallahn ishai nayi nayi nafila sannan nabi lafiyan gado sai dai bacci ya kaurace wa idona, tunani da fargaba ya damen , dafarkon ina tunanin waye bawan Allahn nan nabiyu ina tunanin ya akayi yake sheme a wajen? ko dai maraya ne? bai da yan uwa ne? meya sameshi? oh ni Nadra a kunnena aka kira asuba, dakyar na mike nayi nakoma kan gadon nan bacci barawo ya saceni.

Ban farka ba sai karfe sha biyu na rana, mummy na zaune a gefeta ta tsura min ido dasauri na mike nace " mummy nace miki kidena bude ni da extra key, narufe kofan fa"

" ke yar nan, saboda tsautsayi ne kinsa hankalina yatashi daga kwanciya kin kwanta kaman gawa dole na saki a gaba ina gadi" dariya tabani sai dai na daure nace " wanka zanyi natafi lalle da saloon kinga jibi sallah"

" tashi to! ko kefa yanzu nasan auta ta tawarke anma kwanciyan ki bana son shi ko kadan" tana fada ta mike tanufi toilet ta kunna min heater sannan tafara ciro towel nayi murmushi sannan nace " ayya mammy dai, banma gaysheki ba, ina kwana? ina abamama?"

"lafiya lao, ya jikin naki? yaje aiki anma zai dawo dawuri yasan baki da lafiya ai"

"da yayi zamansa na warke nikam" na nufi toilet na rufo kofan, ruwan da ya danyi zafi nashiga na kunna ina wanka a hankali ina tunani har na fito mammy tafice dasauri na shafa mai dama nayi alwala na , nayi sallah nasaka abaya baki da bakar jaka sai snickers baki kasancewar inada haske sosai yasa nayi kyau fuska na farau farau na fice mukullin motata na dauka nayiwa mammy sallama sannan na fice, yau banci saa ba domin kuwa banga bawan Allahn nan ba nadamu matuka sai dai naji dadin rashin ganinsa a wajen, toh ko dai sai dare yake zuwa? anma ranan da yamma na ganshi, tunani dai barkatai araina nawuce saloon sannan naje gidan lalle ban gama lalle ba sai karfe shida na yamma dasauri nafito don tafiya gida, dai dai gun na tsaya banganshi ba , toh ai yana azumi, anma ranan a buge yake kuma ana azumi, Allah ya kyauta, da tunani na nufi gida har ankira sallah domin masallacin gidanmu har an idar nasamu nashige ciki, naci karo da rikakkun samarin gidanmu wai sun shigo shan ruwa, bakinciki kaman ya kasheni ganin dukkansu sunkai aure anma sunbar mammy da musu abun shan ruwa, ganin sun baje a falon abamama na kan dinning yasa na murtuke fuska sannan nace " mu dai mungaji da ciyar da manya, kowa ya fito da mata ayi aure abar min uwa ta huta" yaa usman ne yasamin kafa sai gani Dim akasa,

" wayyo Allah mammy zasu kasheni" dasauri ta nufi kaina

" Usman ka kiyayeni, bana son bakin mugunta, karya tayi? yara kunanan dirka dirka kunki aure, duk mata zan nema muku" bai ce komi ba sai harara dana ke kwasa, yaa amir kam daman ba mai magana bane, su yaa kamal kuma yunwa ta debe shi baya magana sai yayi nak, mikewa nayi na dauki tray dina da aka zuba min nawa kason na nufi kan dinning gun abamama , muna ci muna tadi har muka gama, nan muka dawo falo ana tadin sallah, yaa kamal yace " zanyi hawan daushe fa, tunda abamama bai son hawa zan shiga ayari kawai , tawagan sarki kawai zamu duru mu shiga, da fatan zaki zo kallon hawa? don naga bakya son zuwa?"

" me zanje yi in banda shan rana inyi baki kirin nasamu ruwan gida ya karben nayi haske"

" aikuwa sai kinje" haka dai muka yita tadi da yayuna har goma tayi kowannensu yamike ya nufi fanninsa, ina dokin sallah gashi saura kwana biyu ne!3?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

(NWA)

************

Yau take washegarin sallah, sannan kuma hawan daushe a garin bauchi, tun karfe tara na safe dana mike na fada bandaki wanka nayi nazo gaban madubi nafara kwaliyya, sai dana tabbatar nayi kyau na kalli kaina sosai ajikin madubin sannan na yi murmushi na bude wardrobe dina nadauko kayan da zansa, super wax ce peach nd green colour yasha lafiyayyen dinki dana saka aka yimin a abuja, na saka sannann na kara dauko gyaleta na yafa ta agefe, na jefa wayata da powder cikin jaka da turare kwaya daya sannan na fito ina murmushi, yaa Amir na jirana mutafi kallon hawan daushe dama su yaa kamal sun dade da tafiya kasancewar shi zaiyi hawa, mammy na falon abamama nafito muka wuce, yaa amir ke jan motar har muka isa state low cost inda zanhadu da yan ajinmu domin dadin kallon, duk da cewa ni yaa kamal nafito kalla.

Anfara kallo rimi rimi abu yayi kyau ayi dariya ayi kallo nida kawata amma ty munata dariyan wani daya ke rawan shoki na ga tawagan gaba sunzo wucewa, ban lura da sunan tawagan ba , sai dai na hangoshi gabana ya tsinke ya fadi, na kara zura ido tabbas shine! rabon da na ganshi tun ran jajibar dana ganshi a hanyan komawa gida daga kasuwa , innalilahi wainna ilaihi rajiun gabana sai bugawa takeyi, yasha farin rawani da farin kaya duk da fuskansa arufe take bai hanani ganesa ba, dasauri rike da coke din hannuna na isa gabansa na mika masa, duk da yana kallon sama bai hanashi sauko da fuskarsa muka hada ido ya lumshe idonsa sannan ya karba,

"nagode" cikin sassanyar muryarsa ya fada

agefeta wata sai daga masa hannu takeyi " Yaa Aliyuu! Yaa Aliyuu!! Yaa Aliyu!!!" na kalleta ina murmushi ko ba komi nasan sunansa , drinks din hannunta takoma dasu don ya riga yakarba na hannuna, ko yayi tunanin muna tare ne oho

'ALIYU HAIDAR' nafada acikin raina, sannan naja numfashi

na juya na koma na ci gaba da daga masa hannu, zuciyata tayi wani sanyi, naji sanyi araina, haka na rinka fara'a har su yaa kamal suka wuce, cikin jin dadi nazauna inajiran yaa amir saiga wannan yarinyan dasauri na rike gyalenta tajuyo tana murmushi nace mata " inbazaki damu ba don Allah tambaya nakeyi?"

ta gyra tsayuwarta tana kurban ruwa daga goran hannunta sannan ta gyada kai alamun tana jina

"Yaa Aliyu danaji kince yayanki ne?"

"ohh!! hamma Aliyu? yes, same mum same dad" naja numfashi sannan nace " don Allah numbanshi zaki bani " batare data ce komi ba ta kirgo min numban nikuwa na saka awayata, numban ba wahala sauki gareshi don harna rike, special number ne, sannan tace Aliyu hameed sunan,godiya na mata sannan na wuce, kuma sai data sanar min cewa yayanta ne na lura cewa suna kama asalin kama sukeyi , murna kaman me ahaka muka isa gida da gudu naje na rungumi mammy, ina dariya ita kanta tasha mamaki domin tayi sati bata ga farin cikina irinna lokacin ba , daki na nufa nayi adding numban a whatsapp, dpnshi hotonshi ne dasauri naje nayi saving nasa a wallpaper na, sai juyi na keyi, yau zanyi baccin dadi,Allah na gode maka Allah. na saka hannu na danna layin yayi ringing har ya gama baa dauka ba, dasauri na kara dannawa wannan karon ya dauka cikin sassanyar murya yace

"hello"

jikina yana bari nace "hy ina wuni" sai kuma yayi shiru zan kara magana ya kashe wayan, nakara kira kawai naji switch off, innalilahi wainna ilaihi rajiun4?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

(NWA)

Nakara kira naji akashe, sai kawai hawaye yabi idanuna nayi ragon azanci dana karbi numbern kanwar, oh Allah ni ga samu ga rashi, haka na zauna inata kiran numban bai shiga ba, akalla nakai awa biyar ranan walwala ta kadan ne na tsaya tunanin rayuwata ma tukunna, nasan mai karatu ya matsu yaji wacece ni!, ga tarihina kadan kuji,

Sunana Nadrah Ahmed ni ce ya mace agun iyayena, inada yayu maza kwaya shida, yaa kamal first born, sai yaa Amir, yaa Usman, yaa Anas, Yaa faisal, sai yaa ahmed kafin ni, ni kadai ce mace kuma yar gata, a gidanmu anhada manyan maaikata domin kuwa yaa kamal lawyer ne, yaa Amir banker, yaa usman quantity surveyor, yaa Ahmed da yaa faisal na medical school suna medicine, yaa anas kuma yatafi maritime sai ni danake karanta architecture a atbu, Abamama yana bala'in son yaransa, duk abunda muke bukata yana mana, tunda natashi izuwa yau bantaba rashin wani abu ba ko acikin kawayena nafita zarra, nadawo abun kwatance, shekaruna ashirin cif a duniya sannan kuma ni banda tarukucen kawaye kawata kwaya daya ce Ammaty, itama don iyayenmu abokai ne munsan juna, inada gagara da neman tsokana fara'a dakuma son mutane, sai dai bana shiga mutane, Allah yaban ilmi da wayo sosai, inada farin jini sosai agun samari tun daga yara zuwa magidanta sai dai duk cikinsu babu wanda raina ke biyawa, asalima ni bantaba soyayya ba bansan so ba bankuma san dadin so ba sai yanzu danake shan azabanta, nake son hauka domin kuwa so ne yafita acikin addini, ni kaina nasan yayi yawa anma yazanyi da raina? iyayena basa kaunar fushi ta domin anhaifeni da ciwon zuciya lallabina sukeyi duk abunda nakeso anamin haka zalika yayuna, acikin yayuna nafi shakuwa da yaa kamal nakan manta inada mahaifi domin duk wani nauyi yadaukemin, ba yabon kai ba samarin gidanmu duk flowers ne maana sunada kyau domin gidanmu duk farare ne babu baki a gidanmu gamu da manyan idanuwa da gashi basai nakara bayani ba mai karatu zaigane cewa yan mata ba karamin safa da marwa sukeyi a gidanmu ba anma samarin gidanmu sun rufe ido babu niyyar aure akansu, tunda babu wanda bai kai aure acikinsu ba, ya Ahmed ma da nake binsa ma shekaranshi ashirin da shida. Iyayena asalinsu yan gombe ne Abamama kuma shuwa ne , mammy yar gombe sai su Abamama suka koma zama a gombe sanadin zamansu kenan,

Labarina kenan kadan ne anma nasan nayi bayani dakowa zaigane5?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

******* Wayan haidar na kashe har dare, ban hakura ba domin sai kira nakeyi baya shiga, karfe goma dai dai nakira wayan naji akunne, nan naja numfashi domin kuwa ji nayi kaman zan sauke aikin hajji, bai dauka ba harta tsinke hakan yasa na kara kira, wannan karon yana daukawa yayi sallama

"salamu alaikum"

dasauri na amsa masa "waalaikumsalam" sai kuma nayi shiru, ina tunanin me zance, can dabara ta fadomin nayi gyran murya sannan nace " ina wuni yaa haidar" sai yayi jum kafin yace "lafiya" alamun bai gane waye ba'

" na kira ne na gaysheka dama "

"nagode" yana fadan haka ya katse wayan, na zurawa wayan ido kaman zai bani amsan tambayoyin dake cikin raina, nayi jum can dai na ajiye wayan nasa caji naficr falo, yau ba kowa don hatta mammy tana fannin abamama donhaka na kunna tv nayi kallo duk da ban fahimci kalilan ba , zuciyata tayi tunanin shi wanda ayanzu yazame min alada, na dauko cake ina ci saikuma wani dabara ya fadomin nayi murmushi na kashe tvn na koma daki don yin bacci wanda rabi tunanin haidar ne.

******* karfe sha daya nashirya tsaf na fito bayan sallama da su mammy zanje gidansu ammaty, ahanya na tsaya ko zan ganshi anma ban ganshi ba donhaka nawuce abuna, yau dai nasa araina insha Allah saina ganshi, ko sha biyun dare zankai a gidansu ammaty sai najira yafito naganshi , gate din gidan abude wanda baisa nayi mamaki ba domin gidansu ammaty haka yake cika duk sallah, gidansu babban gida ne sosai kuma gidan sarauta, nayi parking agefe sannan na haura sama fanninta, arufe ne donhaka nawuce na hajiyanta saidai kuma wasu yanmata nagani a zaune suna gaida hajiyan, na tsugunna na gaida ta har na mike naga ta gefen, tabbas idan brain dina yana aiki wannan itace tabani numban Aliyu jiya tace min yayanta ne uwa daya uba daya bansan lokacin dana fara murmushi ba muka gaisa, itama murmushin tamin duk da nasan bata ganeni ba.

Na zauna agefenta sannan na rage muryata nace "kinganeni?" ta kara kallona sosai sannan ta girgiza kai " jiya a filin hawa muna tsaye tare"

"ohh oh ke na bawa numban hamma Aliyu ko?" na daga kai sannan tace " kin kirashi ko? don naga jiya wayanshi tawuni a kashe " na yi murmushi sannan na girgiza kai

" bani bane nake nema, wata kawata ke so daman"

" ayya! Allah yasa ya kulata"

"banganeba"

" arayuwa idan kika cireni ni kanwarsa damuke uwa daya uba daya hamma bai tsayawa da wata mace kuyi maganan da tafi na minti goma"

ji nayi gabana ta tsinke ta fadi

" anya kuwa? wannan kawar tawa tanada kyau fa sosai"

"hmm ko itace aljanna kuwa, muna nam dake duk randa muka kara haduwa zaki bani labari" na girgiza kaina ina tausayin kaina sai dai naji dadi cewa baya kula kowa, ko ba komi kishi na zai kwanta, mikewa nayi nafice don naga dakin sai cika akeyina koma fannin Ammaty saikuma naga kofan abude, da gudu ta rungumeni tana dariya

" bebz na zata baza kizo bane ai"

"who born me!"

na riko ta dasauri muka zauna akan gado sannan nace

" akwai wasu dana gani a dakin hajiya yanmata guda uku kinsan su? "

" su Amrah kenan, yaran gidan tofi , Hameed tofi, kwaya daya kenan sai sauran daga fadan sarki me ya faru?"nayi gyran murya sannan nace

" shi Hameed tofi yaransa akwai maza?"

"bebz yhne kam? ko kinga flower hamma Aliyu ne?"

"ya akayi kika san shi nake nufi?"

" haba mana shi kadai ne dan gidan Hameed tofi daga shi sai Amrah"

" shine baki taba ban labari ba?"

" noo nadrahh karki cemin kinfars sonshi? you better stop! karma kiyi garaje, wallahi wannan flowern daga nesa zaki ganshi ki hakura dashi baya kula mata afterol me zakiyi da me shaye shaye?? shi ya kawo kanwarshin ai, yanzu haka yana kasa" hankali na atashe na ruko ta

" Ammaty don girman Allah don darajan manzon Allah, kitaimaka min, tunda nake dake for the past fifiteen years baki taba ji nace ina son wani ba, kitaimaka min wallahi zan iya rasa raina idan ban mallakeshi ba, kiyi hakuri kimin hanya, na ajiye duk wani girman kai na ya mace ko alfahari na ya mace , kitaimaka kimin hanya" ina fada hawaye na Zubo min a fuska abunda yayi matukar bata mamaki don ganin yadda take kallona bakinta a bude, ta rike hannuna sannan tace

" nasan Hamma Aliyu, yana da kyau wanda ni kaina na yi crushing dinshi harna hakura, kintuna lokacin da muke school nace miki naga yayan wata family friend dinmu inasonshi? nayi ta damunki? ki kayita zagina? shinefa! bani kadai ba duk wata mace da zata so hamma baya sonta wallahi wulakan ta ki zaiyi, kinsan mai shaye shaye bawai ya mallaki hankalin mutunta ki bane, kije kidaure ki hakura, ahankali zaki manta dashi" na kalleta na share hawayen idona " wallahi bazan iyaba, Ammaty zuciyata na ciwo, nakai sati ina muradinsa, ko kallonsa ne nayi ban da damuwa, wallahi zan jure duk wani wulakanci, ko da kullum zaina dukana ne zan jura Ammaty duk abunda yayi wallahi kara sonshi nakeyi, jarabawa ce wallahi daga Allah" kuka nakeyi sosai Ammaty kuwa baki a sake tace " lallai nadrah kinyi nisa bakyajin kira, ko ince son hauka yakamaki6?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Ina kallonta ta mike sannan ta leka ta window, sai kuma ta juyo sannan tace "muje" jiki na bari na bi ta muka sauka kasa, yana cikin mota yasaka kafansa daya ta waje daya ta ciki, yasauke kujeran motan kida na tashi a hankali, Ammaty tayi sallama ya amsa ba yabo ba fallasa hakan ya gwadamin cewa halittanshi ce rashin murmushi amma duk da haka nikam yamin kyau, na gagara dauke idona akansa duk da Ammaty yake kalla kaman baisan akwai halittar mutum a gefensa ba, tace "Amrah nake nema, tazo tanan?" ya girgiza kai alamun a a sannan yaci gaba da danna wayar hannunsa, yatsunsa na bi da kallo, nan na lumshe ido tare da dogon istigifari, hannu na taja muka bar wajen ganin banda niyyan motsawa, har mun shigo ciki ta tsaya tareda cewa " kin dai ga kalam wulakancinsa daga nesa, ki kama kannki kifita alamarinsa, it is not meant to be" nayi murmushi sannan nace " wallahi yakara burgeni, naji na kara sonshi" hannu tasa ta makeni akai tuni na haura sama ina dariya, munci karo da Amrah tana hanyan dakin Ammaty, nan muka tsaya da ita tana gaisawa da Ammaty

"Daga ina kuke?"

"Munje gaida Hamma" sai ta juyo ta kallen sannan tace

" har yanzu bata farfado bane?"

Ammaty tayi murmushi sannan tace "dolenta ai yanzu kam"

ido nasa musu, suka tafa sannan suka cigaba da magana, alamun sunsan juna suna kuma tare.

Amrah taja hannuna muka shiga cikin dakin Ammaty, na zauna ina kallonta domin mugun kama suke da yayan nata,

"ina so ne ki sanarmin kina sonsa kokuma a'a crushing kikeyi bayan kwana biyu zaki gaji dashi?", jiki na bari nace " wallahi ina sonshi, don Allah' damuwa ta muhadu dashi zan jure duk wani wulakanci don in faranta masa" dahaka ta ce " Hamma nada wuyan shaani, akwai yanmata kala kala masu kai mara hari amma Hamma baya kulasu, asalima shi yake wulakantasu, bantaba jin wanda ta jureshi na wata hudu ajere ba, ni kaina da zansami wanda hamma zai kula ko ya sota wlh da na ji dadi, Hajiya kanta ta damu , sai dai nasan kema zaki gaji, amma ni zanyi kokari na hadaku zanna zuwa gidanku da shi kekuma saikiyi sauran, Allah yabaki saa" na ja numfashi ko kadan banyi dar ba balle tsoro nace " na yarda nikuwa zan baki mamaki" murmushi tayi alamun taji anma bata yarda ba, muka mike muka rakota kasa, sauran suntafi shikuwa yana jiranta, har bakin kofan motan mukaje tayi sallama, akaro na farko naga yayi murmushi, tareda fitowa, tace "Hamma ga kawata ku gaysa sunanta Nadrah" ya kallen a fizge idanuwansa kaman yana jin bacci a lumshe farare zubin madara manya dara dara, sannan yayi murmushi " sannunki" sai da ta juyo ta kallen alamun mamaki wanda nima da Ammaty shi mukeyi.


7 CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Bansan lokacin dana mai da murmushin ba, saikuma yakara dacewa "kinzo kina neman Amrah aina kika samota?" wani kunya naji da muka gane gaba daya ba wa ni yake wa murmushin ba, da Ammaty yakeyi, ta ce " a sama, ashe tana can tana jirana itama" ya gyda kai ba tare da ya kallen ba yashiga motarsa, wani murmushin takaici nayi amma a zuciyata nace ' ko dukana zakayi ka bazan daina bibiyanka ba' Amrah ta jawo ni gefe sannan tace " kinga ke kikace zaki iya, kar wannan karamin abun ya bata miki rai, akwai abunda yafishi anan gaba" nayi yake da hakorana sannan na gyada kai anan tashige suka tafi ni da Ammaty kuma muka koma sama, duk jikinta yayi sanyi taga dai baza ta iya shiru ba tace " yanzu dagaske kikeyi zaki iya?"

" zan iya mana, sa kai yafi bauta ciwo"

ta lumshe ido tamike kan gado batare da tace komi ba nima sainaji kawai natafi gida, tafara bani haushi akan meyasa zata hanani sonshi, duk da nasan Ammaty da fadan gaskiya komim dacinta Amma bazan iyaba donhaka na dau jakata na ce " bye bye zan wuce gida" bata ko kulani ba hakan ya tabbatar min ranta ya baci donhaka na fice na wuce gida.

Abamama na falo yana karanta jarida dasauri na nufi kanshi na zauna agefensa, jingina kai na nayi da gefen kujeran na lumshe ido, Aliyu kawai nake hange, murmushin da yayi dakuma maganarsa duk ta tsaya min akai, jinayi Abamama yace " lafiya ko jikinne?"

" a'a kawai dai inajin jiri ne"

" zan hanaki tuki to, kar watarana kije kisami matsala duk inda zakije ki kira yayunki su kaiki, meye sukeyi da bazasu iya kaiki ba?"

" Abamama makaranta fa, kayi hakuri bazaa sani matsala ba insha Allah" bai ce komi ba amma nasan bai gamsu ba, Yadda Allah yabani miskilan yayu ta ina zanfara yawo dasu ayadda nake yawo a atbu kaman gidan baba na? yaa kamal ne kawai yake da surutu da shiga jama'a toh shikuma kullum yana office tunda babban barrister ne, yaa faisal , yaaa anas da yaa ahmed kuma zasu koma makaranta acikin satin nan don haka yaa Amir ne da yaa usman sukayi saura, Yaa Amir in ya tafi bank tun bakwai na safe sai shida na yamma yake dawowa, Yaa usman ne kadai zance nakan ganshi a gida inya gudo office to shikuma son jiki da son baccinsa bazai sa ya yarda yayi yawo dani ba, nikuma na tsani driver yayi yawo dani duk sai inajin wani iri gwara dai Abamama yataimaka kar ya kwace motannan, banda lafiya sosai shiyasa iyayena ke lallaba ta, komi kankanta damuwata suna kokarin kawar da shi.

******

Yau zamu koma makaranta don haka dawuri na shirya zan wuce hanyan Aliyu ko zan ganshi amma ban ganshi ba, kusan sati biyu kenan da nake duba hanyan tunda naganshi sau biyu ban kara ganinshi ba, to ko wucewa yakeyi agun? yakamata ma nayi binciken waye shi da duk abunda ya shafeshi, nasan cewa Ammaty ba zata bani amsa ba donhaka dasauri na dauki wayata ina hanyan atbu nakira suleimanu, suleimanu dan ajinmu ne a makaranta muna dan mutunci dashi kuma cikakken dan bauchi ne donhaka na ce mishi " kasan Hameed tofi?"

" kai Nadrah waye a bauchi bai sanshi ba?"

nayi mamakin kalamunsa tunda ni bansanshiba sai da na fara son dansa donhaka sai nace

" waye shi?"


8 CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

" Babban dan kasuwa mana, Sannan yana siyasa kadan, ga kuma sarauta!"

" yayansa nawa? ko baka saniba?"

" na sani mana, abokin babana ne"

" yauwa gani a gate din school, kana ina nazo na sameka?"

" ina cafteria sai kinzo"

da rawan jiki na kashe wayan na fara sauri, ko ba komi zan samu labarin Aliyu yau, ina isa na ganshi a kofan gun na kashe motan na sauka sannan na isa gunshi , yana murumshi nikuwa ina cikin zulumi

" Nadrah ko dai kin fara son Aliyu ne?"

a tsorace na kallesa " me yasa kamin wannan tambayan?"

" saboda yau kece ta goma sha uku a cikin makarantan nan dakika min tambayan waye hameed tofi, kuma duk akan Aliyu ake bincike"

"hmm, yanzu dai bani amsa ta"

" toh barin fada miki kamar yadda na fada wa sauran, gidansa yana new gra, sannan matarsa daya yaransa biyu, Amrah da Aliyu, Aliyu dan shekara talatin amma inkin ganshi zakice Dan shekara ashirin da biyu ne yana da karamin ruwa, kanwar sa Amrah shekaranta ashirin da daya, sannan Aliyu , likitan aikin zuciya ne , wato Cardiac surgeon, sannan tun yana shekara sha shida babansa yakaisa california, inda yaje Stanford University School , anan yayi medical school dinsu har yazama cikakken likita shekara biyu da suka wuce yadawo nigeria, yafara aiki a nigeria a national hospital abuja, can california ba yadda basuyi dashi yafara aiki dasu ba saboda yana da ilmi sosai, yaje kasashe daban daban inda suka turashi yayi aikin zuciyan amma yaki ya musu aiki, dawowansa nigeria atake national hospital suka daukeshi kuma yaje, daga shekara biyu zuwa yanzu yayi aiki yakai guda sittin da hudu babu failure aciki, yanzu haka yazama hot cake, toh anan shikuma ya samu saran gudowa bauchi ko wani sati zaki ganshi yazo, ko sallah hatta azumi gaba daya anan yakeyi, tunda kika tambaya waye shi nasan cewa kin taba ganinshi, kin ga kyaunshi, toh saidai yana da matsala daya, yana shaye shaye, wasu dunce asiri yan gun aikinsa suka masa, wasu kuma sunce tsabar tension din aiki yafara tunda fara aikinsa yafarayi baiyi a yarinta ba, nutsattsen mutum ne, sai dai arayuwansa babu halittar dake masa saukin wulakantawa kamar mace, zai daraja sauro fiye da ke, kinga dai na gayamiki komi akanshi amma zanrufe magana ta dacewa kiyi hakuri ki taimaka karki fara sonshi wallahi zaki wahala, kina da mutuncinki da kyaunki kar ya wulakantaki"

wani harara na sakar masa sannan nace " nayi maka kama da wacce zata hakura? ko kuma wacce zaa wulakanta?

shiru yayi sannan ya cigaba " kanwarsa da uwarsa kadai ke cin daraja a idonsa, yana da ilmin addini daidai gwargwado sannan ko zaki mutu bazaki ganshi da aboki ba, shi kadai ke rayuwansa"

" yanzu dai kace yana zuwa bauchi ko wani sati?"

" ae, sosai ma, inkinji ana DR. Haidar Tofi toh shine"

nayi ajiyan zuciya na koma mota,

OH NI NADRA YA ZANYI? ku ban shawara9?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Whatsapp dita na hau nafara duba ko yana kai sai dai banga alamun hakan ba, na gama tunanina tukunna na shige lectures, duk da naji wani sonshi yakaru mun, naji kaunarsa da kuma kwanciyan hankali a tattare dani duk saboda shi, wayata na dauko sakamakon ji da nayi ana kirana dubawan da zanyi naga sabuwar lamba da bansaniba, don haka na dauka ba tare da nayi magana ba

"hello! Nadrah!! Amrah ce!!!" "oh oh sis yakike?"

"lafiya lao ya karatun?, kinata inane?"

" ina department dinmu amma yanzu zan fita daga school din, hope lafiya?"

"yes jirani a department din naku, zanzo na baki sako ne"

ina zaune ina jiranta duk da hankalina yatashi don son jin wani irin sako ne haka akeson bani, ina zaune motarta ta karyo kwana ba ita take tuki ba alamun tana tare da driver ne, nafito na tsaya itama tafito rike da wasu takardu, ta mikamin tana murmushi nima na amsa na yi murmushin.

" komi game da rayuwarsa na cikinnan, nayi risking kaina na dauko miki, kisamu kiduba zuwa gobe kidawo min dashi domin yaje jos yau gobe kuma zai dawo, babu abinda zaki bukata a tattare dashi da babu anan"

Na rungumeta tsantsan farin ciki sannan nace "gobe zan kawo miki insha Allah i promise" da sauri tajuya nima na koma motata,Ac na motan na kunna sannan nafara bude takardan hotunansa ne tun yana yaro tun daga first birthday dinsa har na talatin da yayi wata biyu da suka wuce, na duba date din sannan naga dai dai yake da nawa 27th May, hotunanshi da abokai yawanci turawa ko ince dukkansu turawa sai kuma nashi da Amrah sai Hajiyarsu da Babansu, family tree dinsu baida girma ko yawa donhaka tuni nagama gani, saikuma wani littafi kaman slum book da ya cika abubuwan da yakeso da wanda ya tsana, lonely message dakuma yadda dai yake rayuwa ina gamawa na rufe na nufi gida, Ranan banyi bacci ba har washegari inata rubutawa banyi niyyan shiga makaranta ba amma da na tuna Amrah zata shiga ba shiri nafito alokacin karfe sha daya, Mammy ce ta katseni " kije min mobile mart ki sayomin magic coal" na amsa da "toh" sannan nafice takardun suna hannuna don gudun kar rawan kaina ya kwasheni na yar dasu awani waje, ina shiga Amrah ta kirani a waya " kina ina? kiyi sauri ki kawo wallahi yana gari yanzu haka" dasauri na dauki coal din zantafi kenan naji na bugu da karfi, tuni takardun hannuna da hotunan suka watse a kasa, sanye yake da tshirt da jeans, gashin kansa ta kwanta luf luf, gabana ne ya tsinke yafadi ganin Aliyu ne, jiki na bari na fara tattarawa yayinda shikuma yaketa "sorry" da sauri na sunkuya zan tattaro littafannan kafin ya gani, aikuwa nayi kuskure domin kuwa idonsa cak akan hotonsa kwaya daya, a nutse yasa hannu don yadauko, bansan lokacin da na sunkuya kasa ba zan dauko, hannunmu ya gogi juna, sakewa nayi da karfi domin jin zirrrrr tun daga saman kaina har kasa, bazan san yanayin da idonsa take a farko ba amma a sanina dashi Aliyu na da fararen ido sabanin wannan lokacin hada ido da zamuyi idonshi ta kada tayi jaa, ya tattaro files din gaba daya ya rike a hannunsa ya bude daya bayan daya yana gani,alokacin ji nayi kaman wata barauniya kaina a kasa inajira naji saukan mari ko duka, gashi tsabar rawan kaina har da photo copyn wasu, na shiga uku ni,

" what is this?" ya tambayen cikin dagaggiyar murya mai alamun fushi, bance komi ba don haka ya kara tambaya ta

" babe am asking you what is this?" jiki na rawa bakina ma haka nace " Am so sorry" riko ni yayi da karfi yafito dani daga shagon yaciro wayansa wanda bansan wazai kira ba " kina ina? kizo yanzu ki samen a mobile mini mart" na danji sanyi domn jikina yabani cewa Amrah yakira, daya daga cikin maaikatan yafito yana tsaye da tsawa Aliyu ya kalleshi tare da cewa " what?!"

" kudin coal din hannunta ne bata biya ba" yafada jiki na bari, a wulakance yacire gudan dubu daya kwaya biyar ya jefeshi dashi "keep the change" tuni ya dauka ya shige ciki, muna tsaye hankalina a tashe yayinda shikuma ko kallon inda nake baiyiba balle inyi tsammanin tausayi, lallai yau zanga wulakanci, yayima ko zan iya zuciya dashi don ni kaina dawainiya dashi tafara damuna nadena karatu kamar yadda nakeyi da tunda na hadu dashi, muna haka sai ga motan Amrah wannan karon itane tazo, da sauri tafito ganina a tsaye kamar almajira , binta yayi da kallon tuhuma sannan yace " how did my original credentials and diary get to her?" kallona tayi alamun na kwafsa ta juya za tayi magana yasa mata hannu alamun tamasa shiru,

"get lost" sannan ya juyo kaina alokacin ya kare min kallo daga sama har kasa sannan ya wurga min a gabana ya matso kusa dani ya sunkoyo yadda zan iya jinsa sosai, sannan yace " kar kisha wahalan nacin sai kin saya zuciyata, zuciyata is too high for your liking, you cant deal with me, dubunki sunyi sun hakura , me zai hana ki hakura? ki dena wahalar min da kanwa" yana gama fada yajuya ya kalli Amrah sannan yace " sai kinzo".10?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Numfashi ta tsayawa tayi cak na wasu dakikai tsantsan yadda gaba na take fadi, Oh rabbi am ina kallonsa ya shiga motarsa ya fice dasauri Amrah ta karaso kaina ta rike hannuna tana tambaya ta "Meya faru hope bai miki komi ba?" na gyada kai alamun ae sannan tajani muka shiga motata sai dana zauna na dafa kaina kan steryn motan sannan tace " jiki na yabani zai soki, saboda yanzu da wata ne nayi imani da Allah sai ta kwashi wulakanci but kiga yadda yayi miki harda miki magana fa" nayi murmushin takaici sannan nace " kinsan meya fadamin ne?" anan na sanar da ita tayi murmushi sannan tace " kar fa kice zaki hakura wannan ba wani abu bane, kingama da files din na tafi dashi?" na gyada mata kai ta cire wanda nayi photocopy sannan ta waresu tarike.

"Hamma Aliyu likita ne nasan kinga komi but amma yau dasafe yake sanar damu cewa TH na nan bauchi sun daukeshi aiki, i mean finally ya yarda ya musu aiki don tunda yadawo ake safa da marwa, ya yarda akan ran thursdays zaina zuwa duba duk masu problem na zuciya agun har kuma idan bazai yiwu anan ba sai aturasu can abuja, Ammaty ta gayamin cewa kema kina fama, this might me an oppotunity for you kije wannan karon, sannan nasan Ammaty kawarki ce sosai, karkice bata sonki sosai wallahi tana gudun miki wulakanci ne tunda tasan Hamma amma kinga Hamma baya miki ai ko?" ni farin cikin labarin datake sanar dani yasa na ma manta metake nufi bansan lokacin da na rungumota ba , akaro na farko a rayuwata ina farinciki da ciwon zuciyan da nake dashi, zan yi amfani da wannan daman , muna sallama tafice nikuwa na wuce makranta lectures dinma ba ganewa nakeyi ba , na samu nayi submitting assighnment dina nafito na nufi hostel gun Ammaty, tana ganina ta daure fuska nikuwa ko ajikina haka muka wuni taki sake jiki sai mita takemin akan Aliyu nikuwa hotonsa na dauko nasa a wallpaper na wasu kuma sakawa nayi nahada video, sai yamma na tafi gida, aikuwa ina isa gida naga motoccin samarin gidanmu a cikin gida har inacewa meya faru yau basu je aiki bane, ina shiga ciki naga Yaa kamal da Abamama sun riko mammy a gigice na wurgar da jaka na dama Mammy na da ciwon zuciya wanda dukkanmu kowa na kyautata zaton ko gadonta nayi, hawaye na bin idanuna abayan jikina nacire dankawalin na yafa a kafadata ina kuka ina rike da hannunta da sauri yaa kamal ya tukamu yaa amir na biyomu a baya muna isa aka wuce da ita TH muna isa ICU aka kaita , Abamama yafara magana da likitotin wasu sun rufa akanta amma naga Abamama sai waya yakeyi dana matso kusa hawaye na bin idanuna na ce " Abamama zata samu sauki ko?" yajuyo ya kalleni sannan yayi murmushi " insha Allah auta na zata samu karki damu, yanzu akwai kwararreb likitan zuciyan agari ana nemansa ne yazo ko zai dubata bai dauki wayan ba" dasauri nace " meye sunanshi?"

" Dr. Haidar tofi, sun ce so far shine kwararre sosai wanda zai iya dubata ba tare da wasu naurori ba yagane meke damunta" bansan lokacin da na bar cikin asibitin da gudu na nufi mota ba , wayata na dauko sannan na kunna, na kira wayan Amrah bata dauka ba , nakra wayan Aliyu shima bai dauka ba, kara kiransa da zanyi yana dauka a gigice nace " nasan ka tsaneni don girman Allah ka taimakeni, mahaifiyata rai a hannun Allah wallahi na maka alkawari in ka taimaketa yanzu zan dena takura maka wallahi, don girman Allah"

cikin sanyin murya yace " waye ne?, daga ina?" wasu zafafan hawaye suka zubo a idona nace " Hamma don girman Allah ni ce wacce na dauki credentials"

sai kuma yayi shiru sannan ya kashe wayan, in kara kira naji a kashe , jinginuwa nayi agefen motan ina kuka zuciyata kaman zai fadi yayuna ma kowa a rikice a duniya inason iyayena fiye da duk wani abu da nake dashi gashi rayuwar mahaifiyata yana rawa, wayata naji tana kara ina dauka na ga shine dasauri na dauka hannu na bari,

" kin tabbata inna dubata bazaki kara damuna ko kanwata ba?"

jiki a sanyaye nace " ae i promise" ya kashe wayan , yayinda nikuma na zurawa wayan ido, nafi minti sha biyar agun har na mike zan shiga naganshi yashigo yana dan sauri yana nannade hannun riganshi sanye da farin coat dinsu , na bishi da sauri yana shiga suka gaisa da Abamama har zai shiga nace " Hamma!" ya juyo ya kallen daga sama har kasa sai alokacin na lura ashe kaina ba dankwali gashin kaina duk ya zubo kasa, anan yajuya yafice nikuwa nayi ajiyan zuciya adai dai lokacin muka hada ido da Abamama kafin ya tambayen nace " Yayan kawata ne" sai ya juya baice komi ba, muna zaune har mintuna arbain sannan yafito Abamama yabishi suka fice nan ma suka share mintocci sannan yadawo, yace " zamuje abuja saboda akwai aikin da yake son mata nan kuma basu da kayan aiki, yanzu yasata akan magunguna yakuma min bayanin ciwon dalla dalla , sai yanzu nasan na hadu da likita duk yawace yawace da mukeyi banji bayanin da ya kama min hankali irin wannan ba, yanzu yace a barta ta tashi a bacci tukun" ajiyan zuciya nayi don farin ciki su yaa kamal ma sai yanzu suka iya zama tunda muka zo, gashi su yaa ahmed sai waya sukeyi suji ya jikin mammy, ficewa nayi don shan iska naje gefen motan ina zaune, wayata naciro ina duba hotonshi gashi na masa alkawarin rabuwa dashi inya duba Mammy yanzu ya dubata , toh ta ina yasan cewa Mammy ce? ko Abamama yamishi bayani shima kuma yaganmu tare?, gashi bazan iya saba alkawari ba don haka bazan kara takura shi ba zanna kallonsa daga nesa inyaso ciwon sonshi sai ta kasheni kawai , hawaye ne suke bin idanuna ji nayi mutum akaina daga idon dazanyi naga shine

" Ciwonta ba mai tsanani bane sosai ana mata surgery zakuji shiru" yana fada yana mikomin tissue na karba ina goge hawayena sannan yace " da fatan baki manta da alkawarinki ba?" nan ma na gyada masa kai , yayi murmushi sannan yace " na gode" yajuya zai tafi na kamo riganshi ta gefe hawaye na bin idona sannan nace

" Nasan duk wata mace da zata ga ko taji abunda nayi zata ji haushi iya matuka domin na bada mata, amma ban damu ba yau zan fada maka irin son da nake maka, naga kana dangantani da sauran matan da suke binka wallahi ni daban ce kuma wataran zaka shaida so ne dana ke maka donAllah ba don abun duniya ba, ba kuma zandena ba karkaga don zandena takura ka yazama na dena sonka wallah ko kadan , sonka yanzu na fara sai dai na mutu" shiru yayi yana manaki a sanyaye yafice nikuwa na ruguje da kuka alokacin na lura ashe Abamama na tsaye a bayanmu yanajin bayanina.11?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Ya karaso a hankali sannan yace " meya faru? har kike fadan wannnan kalamun wa namiji?" jikina a sanyaye na saka kaina a kasa domin na balain jin kunya a duniya bana boye komi wa Abamama don haka sai naji wani iri jin yaji yakuma gane me nake nufi, ganin ban bashi amsa ba yasa yace " idan munje gida zamuyi magana" na gyada kai biye da ajiyan zuciya, kafin nan zansamo bayani ko amsan da zan bashi, wucewa nayi nabi bayansa muka tsaya dasu yaa kamal dukkansu suna jimami, har lokacin Mammy bata tashi ba, ganin na gaji da zama yasa na cigaba da yawo a asibitin cike da tunanin makomar son da nakewa Aliyu, tsaye na ganshi da wani suna gaisawa hakan yasa na tsaya ina kare masa kallo, ya matukar burgeni wani dadi nakeji idan ina kallonshi har suka gama gaisawa yabiyo ta hanya ta, da sauri na kau da kaina ina neman hanyan buya kar yayi tunanin da gangan nake binshi aikuwa nayi latti domin kafa ya samin nayi tuntube na fadi, screen din wayata ce tafashe na dauko a hankali na karkade gyale ta sannan na dauko wayan ina dubawa, ko kadan zuciyata bata tunkushe ba balle naji haushi duk da tsananin son wayan da nakeyi, wayar yayi da kuma tsadai bala'i amma nayi murmushi kafin na dago har ya fice, girgiza kaina nayi sannan na ci gaba da tafiya.

Ban koma ba sai magrib , ina isa naga suna ta alwala suna shirin Zuwa masallaci , yaa kamal na ganina yace " kiyi sauri ta farka dama ke muke nema ina kika kai wayanki?" sai alokacin na duba ashe wayan da ta fashe ta mutu, nayi murmushi nace " wayar ta fadi a hannuna dazu ta fashe ne wallahi" kallon mamaki suka bini dashi don abinda bantaba yi ba kenan, fasa waya! suna wucewa na shige ciki Mammy na zaune sanye da drip a hannunta murmushi tamin dasauri na isa gefenta na zauna, "mammy ya jikin?" "da sauki lele ta" na rungomota na kwanta ajikinta kadan, duk da dan nauyi da nake dashi, bai hanata rikoni ba, jina ajikinta yasa hawayen da suke makale suka karasa fitowa, tuni nayi rafin hawaye a jikinta, zama tayi da kyau tare da cewa "lafiya? ba fa yau na fara kwanciya ciwo ba, ko akwai abunda ya sameki ne?" ai kaman ta kara min hawaye, wasu zafafan kuka naji tuni nafarayi da karfina, ita kuwa tsayawa tayi tana ganin ikon Allah, har su Abamama suka shigo cikin dakin ban bar kuka ba sannan bantashi nayi salah ba, yana shigowa ta bishi da kallo shima kallon nawa yakeyi duk da babu mamaki a fuskansa, tace masa " ka ganta fa, tun da tashigo take kuka, ko akwai abunda ke samunta ne? tana daga min hankali" hanyoni yayi muka fice waje, ya zaro min ido " baki da tausayi ne? kina ganin halin da mahaifiyar ki take ciki amma kina so ki daga mata hankali meye amfanin haka? karki kuskura ki gayamata komi har sai ta samu sauki kinajina ko?" gyada kai nayi tare da wucewa toilet na dauro alwala, nayi sallah yaa kamal kuma suna gefen Mammy hartayi bacci, likitan da yazo dubata yace dasauki kar a daga mata hankali sannan kar atasheta a bacci, washegari za'a wuce da ita abuja, suu yaa kamal sun tafi gida ni kadai narage da umma lami kanwar mammy da tazo bayan isha har lokacin Mammy bata tashi ba, mu zamu kwana da ita duk da damuwan da ya cunkushe min bai hanani addua wa Aliyu da mahaifiyata fata ta shiryuwan Aliyu ko zai bar shaye shayen da yakeyi musamman da na tuna Amrah tace mun karfe goma na dare zuwa sha biyu toh duk acikin maye yake yinta, a wannan lokacin nake masa addua har bacci ya kwashen.

Can acikin baccin naji Umma lami na salari farkawan da zanyi naga Mammy tana aman jini, a gigice na mike ina kiran sunanta amma shiru babu amsa sai amai, ficewa nayi ko dankwali babu na nufi corridorn tunda aka fito da ita daga ICU ankaita ward nurse nagani na rikota ta biyoni ganin halin da mammy take ciki ta fita da gudu don kiran likita, alokacin na fara kiran wayan Aliyu bai dauka ba can na kara kira bai dauka ba sai data kusan tsinkewa cikin maye ya dauka alokacin na duba naga lokaci karfe sha daya saura, wasu zafafan hawaye suka biyo sahun idanuna da karfi nace " ka taimaka Mammy babu lafiya sai aman jini take don Allah ka bar mayennan kazo ka ceceta" dulum naji ankashe waya, a gigice na wurga wayan lokacin likitoti sun shigo kenan aka fitar damu , tunda nake bantaba shiga tashin hankali irin wannan ba mammy na kwanciya a asibiti amma bata aman jini minti sha biyar cak sai gashi sunfito, kowa a sanyaye don alokacin har su abamama sun iso asibitin dasu yaa kamal, likitan ya tambayi waye guardian dinta abamama yace shine anan yake cewa Allah ya dauki ranta, INNALILAHI WAINNA ILAIHI RAJIUN jiri naji yana diba na sai kawai gani a kasa bansan inda nake ba12??CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Bude idona da zanyi banga kowa ba illa shi da yake tsaye, rike da takarda ahannunsa yana kalla, daga gani anyi echo ne ko scanning wanda dama ba sabon abu bane aguna tsantsan yawaita yi da nakeyi, sai dai bansan dalilin kwanciya ta ba na tsaya tunanin me ya faru dani, cak na tuna da rasuwar mahaifiyata bansan lokacin da na fara kokarin mikewa ba hakan ya jawo da hankalinsa kaina, dasauri ya riko hannuna da nake kokarin cire calula da akasamin na ruwa, ba tare da yace komi ba ya mayar da hannun ni kuma idanuna ya cike da hawaye nace masa " da wasa ne ba ta mutu ba ko?"

ba tare da tsagaitawa ba kawai yace "da gaske ne" wani karfi yazo min tare da tsantsan tsana a fuskata na kalleshi sannan nace " tunda ka kashe min mahaifiya ai dole kazo ka danne ni anan, ka barni naje naganta!" da karfi nake fadan maganan sai dai kuma babu alamun tsoro ko mamaki a fuskanshi da nake furtawa, fizge hannuna na yi da karfi ina kokarin saukowa, da karfi ya rikoni yayinda yakira nurse dasauri ta shigo dakin suka fara kokarin danneni amma ina ihu nakeyi ina kuka abarni naje naga mahaifiyata, ga munanan kalamun da nake jifanshi dashi don gani nakeyi rashin zuwansa da wuri ya kara janyo dadewan rasuwanta, wani irin kuka nakeyi alokacin da ya damkoni da karfi idona yana kallon nashi " meye haka?" "kina nema ki kashe kanki, do you have idea how many days kikayi anan?, keda ya kamata ki zama kina mata addua amma kina kuka kaman bakida tawakkali?" sauran hawayen da suke fuskata su suka kara makalewa alokacin ya sakeni ya jingineni, yace nurse din ta kawo min ruwan tea na sha, karewa asibitin kallo nayi sai dai bangane dakin ba, tsantsan yawan kwanciya a asibitin TH nariga nasan kalan dakunan su, wannan dakin babbane sannan babu kowa aciki sai nurse mai kula dani sai shi dayake tsaye ya zura min ido, damuwata mahaifiyata ban iya danne raina ba donhaka nayi kuka ta mai isa na dukkansu ba wanda ya lallasheni na rasa ta inda zan fara tunanin cewa mammy ta rasu ta barni, wuni nayi ina kuka kuma abun mamaki har lokacin yaki fita a dakin anzo ankirashi yaki fita hatta wani tsoho wanda nake tsammani babbanshi ne yazo yakirashi yace bawanda ya isa ya fiddashi sai dai yabar aiki a asibitin haka suka hakura suka fice, sai magrib yafita yaje sallah, alokacin na tambayi nurse din wani asibiti ne ganin bata da niyyan ko lekawa waje, tace national hospital abun ya matukar bani mamaki me yakaini asibitin? nida nake bauchi? sai dai na hadiye komi na tsaya tunanin toh ina yanuwana kaman tashiga raina aikuwa tace " brothers dinki suna zuwa dare dare su ga yakike, ba'a barin kowa ya zauna ne sai nurses" shiru nayi hawaye na ci gaba da zubo min har bacci ya kwashen.

Bude idona da zanyi naga shine a zaune a gefeta yana kokarin gyra min bargo na, hannu naja zan rufe jikin da kaina don gudun kar ya tabani bai kulani ba sai da ya rufe sannan ba tare da ya kallen ba yacewa nurse din " idan zata iya mikewa kisata tayi sallah, its over a six days tana kwance ba full abinci babu sallah babu wanka" bansan lokacin da na zaro ido sosai ina kallonsa ba, yanzu yana nufin kwanana shida bana hayyacina? lallai na jijjiga Allah sarki ko ya abamama yake ciki yanzu sai Allah, ankai Mammy kenan babu ni , Allah sarki mammy na,da taimakon nurse din ta mikar dani sai da naji jiri tsantsan babu karfi a jikina muka shiga bandakin ta min wanka duk da gardaman da na mata sai da naji Aliyu na cewa in ban tsaya ba zai shigo yamin nasan zai rina donhaka tuni na nutsu na yi wankan na dauro alwala, ina fitowa naga kaya akan gadon ya siyo ita ta taimaka min na sakasu sannan ta shimfida min sallaya na ma rasa hanyan da zanfara biyan sallolin dake kaina, gashi bazan iyayi a zaune ba donhaka da na zauna sai dana biyasu kaf sannan namike na kwanta agun bansan bacci ya kwashen ba.

Hannu naji akaina bude idon da zanyi naga yaa kamal da yaa Amir dukkansu sun rame sunyi baki can gefe Abamama ne dasu yaa usman, wani kuka yafito min ba shiri kawai na fara, dukkansu ba wanda ya iya lallashina hatta Abamama dake gefe yana sharen hawaye, yaa usman ne yazo yake cemin " ki daina kuka addua zaki mata karki manta kema baki da lafiya kuma ciwonki baya son tashin hankali kidena damuwa kinji?".13??CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Gyada kai nayi amma na gagara tsagaita kukan saiga Aliyu yashigo ganin yadda nake kuka harda tari ya karaso kaina da sauri yace " don Allah kuyi hakuri ku barta haka, ganinku daga mata hankali yake and kunsan yanayin jikintan na muku bayanin ciwonta" ba shiri suka fara ficewa aikuwa na mike da zummar na bisu, rikoni yayi da karfinsa amma ina daujewa tare da yin wani irin kuka dukkansu da kuka suka fice sunan Mammy kawai nake kira ina cewa " yaa kamal don kunga mammy bata nan shine zaku tafi ku barni ko? Abamama harda kai ? don Allah kudawo kukaini gun Mammy wayyo Allah na nashiga uku" da karfi Aliyu ya kwantar dani nurse din tamin allura saikuma bacci.

In tagaita muku rayuwata Ni Nadrah rayuwan da na shiga sakamakon rashin mahaifiyata yasa har wani hauka hauka nakeyi na mintuna, ga ciwon dake damuna wanda duk yan gidanmu boye min sukeyi babu mai fadamin, kullum suna guna a asibiti duk da ba ko yaushe ake barinsu su zauna aguna ba don da zaran na gansu Mammy nake tunawa to anan zanfara kuka yakai ga har zuciyata inajin abu a tokare tamkar fata haka ya cunkushe sai wani lokaci jini yabiyo kasan hancina, gashi Hamma Aliyu da na sani ya canja domin kuwa baya bari kowani likita ya kula dani sai shi sannan a fadin yaa kamal tunda aka kawoni asibiti garin yadena zuwa bauchi safe rana dare hidima ta yake, sai dai har lokacin maganan da ta wuce minti goma bamu tabayi ba, gani nakeyi da yana kusa baiyi wannan shaye shayensa da Mammy bata rasu ba, A hankali na fara samun sauki da taimakon adduoi da yanuwana suka sani aciki da saukan qurani tuni na warware nan aka fara batun sallama, Randa zaa sallamen ina kan gaba don ko ba komi zan ga hasken rana da na farin wata rike da hoton Mammy na akirjina wanda na dauka acikin kayan yaa kamal ba yadda baiyi nabashi ba naki yarda, Aliyu ne yashigo dakin yace duk su fita zaimin magana suna ficewa ya kallen sama da kasa sannan yace " sallamanki ba yana nufin kije ki kwakulo wani sabon ciwo bane kidaure ki lallashi zuciyanki da damuwanki karki kuskura zuciyanki ta buga ta biyu saboda ta buga ana farko kuma ke kanki kingani bai miki ta dadi ba, nayi bayanin ciwonki wa mahaifinki ki sameshi zai gaya miki dallah dallah harda na mammynki , last but not the least karki yadda ki fara soyayya a yanzu!" shi kanshi da ya fadi maganan jira yakeyi yaji me zance aikuwa na bashi mamaki tare da cewa "toh" sannan na fito duk da cewa ya kaikaya min inda ke min zafi amma ban nuna masa ba muna fitowa na shiga motan Abamama yana gidan baya sai driver agaba muka nufi hanyan airport sai bauchi kawai , shigowata gidan sai naga tamin girma jira nakeyi naga mammy amma har lokacin shiru, a hankali na nufi dakinta ina dubawa kaman zan ganta zama nayi akan gadonta na bude wani sabon shafin kuka, Umma lami ce tashigo dakin ta rikoni amma ina itama sai kuka sai da mukayi mai isanmu nayi alwala nayi sallah rakaah biyu na mata addua, duk sai naji gidan yamin girma duk da akwai yayuna da sauran mutane Abamama kam kana ganinshi kaga damuwa aranshi duk da cewa mutum ne mai dauriya da hakuri sai dai akan mammy sai addua kawai.

A yammacin ranan Ammaty tazo donma umma tace min da ita akayi sadaqan ukun mammy kullum tana zuwa da kuma yan ajinmu na makaranta duk sunzo su, alokacin ma sai zuwa akeyi taaziya mutane daban daban, aciki harda Amrah donma Sunzo da hajiyansu da nake asibiti a abuja, jikina babu karfi Amma haka na daure nake zama , Abamama yaje TH yadauko min likita da zai na duba ni duk da banso ba amma yace naje falon saboda gudun tashin ciwona, shigana falon yana zaune kansa akasa kare masa kallo nayi kallo daya, saurayine ban jin zai kai talatin, sai dai asain bahaushe ne mai kyau yana rike da wayansa na zauna, yayi murmushi sannan yace " yajikin naki?"

" da sauki"

" me da me yake damunki yanzu?"

" ciwon kai ne kawai bayan nan sai jiri kadanina fada ina wasa da yatsuna dago idon da zanyi naga idonsa a kaina tuni na kawar da idona banason irin kallon da yake min,

" ya karin hakuri?, Allah ya jikanta ya mata rahama" na amsa da "ameen" anan yayi gwaje gwajensa sannan ya koma ya zauna yace " ki rage tunani" shiru nayi alokacin yayi ta min nasiha masu shiga jiki, jikina yayi sanyi na share hawayen da suka zubo min sannan yace akawomin abinci da naki yarda da kanshi yake diba yana bani, yayi ta tadi yana son sani dariya tun bana yi har nazo na sake raina don ya cire min kawaicin dake raina, da na gama ci sannan ya tafi.

Acikin satin na koma makaranta cikin ikon Allah Dr.Hisham ne yake kaini duk aikin da yakeyi zai yanke yazo ya kaini sannan idan na gama sai yazo ya daukeni, a duk lokacin da yaga ina kadaici nan zai debe min kewa abinci kuwa safe rana dare yana kansa da kansa yake bani, daga yayuna har Abamama godiya suke masa sosai domin kuwa yana taimakona yana ragemin kadaici, tuni na saba na fara dawowa yadda nake duk da tunanin Mammy da kuma tsananin son Aliyu da nakeyi wanda rabona dashi tun a asibiti a abuja kusan wata hudu kenan.

Mun gama exams din makaranta alokacin na dawo gida hutu , Umma lami ta tafi garinsu ya zama da ga ni sai talatu mai aiki sai masu gadi sai kuma yayuna da Abamama,inda Abamama yafara takurawa yaa kamal yafito da mata don yayi aure ko dan albarkaci na, Hisham kuwa munsaba duk da kokarinsa na nuna min yana sona, tsananin kulawa da yake nunamin dasauransu bai sa na fara sonsa ba, zuciyata tana nan akan bakanta na Aliyu, wani lokacin na kan kwanta a daki nayi kuka sosai na share hawayena na fito, Amrah kuwa munsaba sosai itakam har kunya na takeji intaji yayan nata baya nemana nima kuma ban nemeshi ba sai dai alkawarin da nayi masa ne ban manta ba nacewa bazan kara damunsa ba,

" nikam yanzu kin dena son Hamma Aliyu ne?" cewar Amrah wata rana da tazo gidanmu

"me kika gani?"

" na ga kin daina sonshi"

" ae mana, mutumin da baya sona ai dole na bar sonshi"

"hmm, ban yarda ba"

" me yasa?"

" sai dai banyi tadinsa ba sai kin min, duk da baki nunawa kin damu amma na lura kina son sanin halin da yake ciki" zahirin gaskiya ta fada sai dai abunda yafi cimin rai shine duk kulawan da yamin a asibiti dama ba sona yakeyi ba? alokacin na dauka so na yake amma tunda na dawo bauchi bai kara waiwaiya ta ba abunda yafi komi cimin rai kenan, zanso na tambayesa akwai tambayoyi da ya kamata na masa,kaman ta shiga raina tace " yau zai zo gari bansan ko kina son ku hadu ba"

" ae inaso , saboda ina da tambayoyin da zan masa"

" ba damuwa inyazo zan sanar dake"

aikuwa yana isowa ta kirani a waya, yana asibiti na dauki mota na fice , dai dai shiga asibitin na hadu da dr.hisham yana ganina ya fara murmushi " yau abun mamaki kin zo ganina"

yake nayi tare da cewa " a a gurin Dr. Haidar na zo" tuni annurin fuskanshi ta bace tunda yasan girman Aliyu araina kusan kullum sai nayi magananshi, ban jira yace komi ba nasa kai naje office dinsu yana shirin fita na shiga donhaka yakoma ya tsaya files din hannunsa yake duba ba tare da ya kalleni ba yace " lafiya?"

" nazo na tambayeka ne" "inajinki"

" kulawa da kayi da ni a asibiti me yake nufi?"

" tausayi"

" ban gane tausayi ba"

" mahaifiya ta wuce wasa, alokacin kuma kin rasata, i was trying to be a good doctor" yana gama fada yazo zai wuce na sa hannu na toshe kofan, hawaye na zuba a idona don alokacin na gagara rike bakin cikina nace masa " kana nufin kace wasa dani kayi kenan?"

" if its how you think YES" " Aliyu ina so ka sani, Soyayya ba karya bace, za ka yita kuma zakaji ko akwai dadi ko babu dadi" zuramin ido yayi na mintuna sannan yace " ko zanyi soyayya bazanyi dake ba, ballema bazanyi ba , me zaisa nasawa kaina ciwo akan wani abu wai shi soyayya, kiyi wa kanki nasiha domin sa soyayya ko damuwa aranki ba naki bane a wannan lokacin" yana gama fada ya fice nikuma me zanyi inbanda kuka kaman raina zai fita, Dr.Hisham ne ya shigo office din ya kalleni daga farko har kasa sannan ya zauna agefe yana kallona sai dana gama kuka na yaja numfashi sannan yace "yaushe zaki daina sawa kanki cutar da babu magani? yaushe zaki daina hangen abunda ba naki ba ki dubi abunda ke gefenki? shin baki lura da gefenki ba sai hangen nesa?""14?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

" Hmm! kayi hakuri dani ka daina sona Allah zai kawo maka sauki da wacce tafini"

"tayaya za'ayi na hakura dake? bayan kuma kinsan irin son da nake miki, kin koya min yadda zan soki"

" Yadda kake jin ba zaka iya rabuwa dani ba haka nima nake jin bazan iya rabuwa dakai ba, Soyayya ba karya bace, don haka bazan iya tursasa raina akan abunda nasan bazai yiwu ba" Shiru yayi kafin ya ce " ki fito mu tafi" " ba tare muka zo ba" girgiza kai yayi jin amsan da na bashi sannan ya fice, da kyar na sulale jiki na koma mota sai da nayi kuka mai isa na kafin na tafi gida.

A lalacewan rayuwa har nayi exams dina na gama, yanzu ko Ammaty na fita hidimanta na ajiyeta agefe, rayuwata ta dawo ni kadai kamar mayya, yayuna daga masu makaranta sai masu aiki babu mai zaman gida haka ma mahaifina.

********** Rayuwa taci gaba da wuce min cikin daci da bakin ciki, domin wulakancin Hamma sai karuwa yakeyi baya kulani duk inda yake nikuwa ina makale awajen, sai dai ya tozartani ya wuce domin akwai ranar da mun shiga jifatu tare dashi bai san ina binsa ba keken hannunsa nake kalla duk abunda ya saka nima sai nasa, har akazo gun biya ban saniba na bugeshi da nawa juyowan da zaiyi yaga nine hannu yasa ya gaure ni da mari, alokacin na lura akwai guntun maye akansa, ya zageni sama da kasa ya kuma ce kar na kuskura na kara hada hanya dashi, hakika babu munin tozarta irin wannan hawaye ne suke bin idona sai dai bai gama maganar ba ya fadi agun da gudu naje na rikoshi hankali atashe mutane suka tayani kaishi mota na nufi asibiti dama kuma tun akan hanya na kira Amrah na sanar da ita, ta rigamu isa asibitin anan suka bashi gado ya sha baccinsa, ina zaune agun ya farka a razane na mike na bar dakin domin tun marin da yamin na tsorata dashi, a mota nan ma naci kuka na wanda ya zamo abinci agareni, A duk lokacin da nake kukan sai na tuna da Mammy domin kuwa da tana raye bazan yi wannan kadaicin ba, Uwa da dadi, koma wa ta gida na sami Abamama a falo yana ganina ya sauke jaridar hannunsa yace nazo, ina zama ya dafa kaina ya tsura min ido sannan yace " Meye matsalarki?" " yake nayi domin kuwa ni kaina nasan banda amsan tambayan anan yaci gaba da cewa " prof. ibrahim na department dinku yakiran, yace wannan semestern bakiyi kokari ba ko kadan, ke da kike da cgpa 4.76 me kuma yadawo dake 1.23? inyee? fisabililah meya sameki donAllah don annabi Nadrah!" a iya rayuwata zan iya kirga sau nawa mahaifina yakira suna na, yau muryarshi ta tabbatar min da cewa yaji ciwon result dina, katsemin tunani yayi yace "I am very disappointed in you! ya gayamin yace min ko kadan a aji in banda tunani ba abunda kikeyi, lectures ma baki zuwa, to ina kike zuwa? why would your cgpa drop massively like that? me yake damunki? worst result" tsaban bakin ciki bansan lokacin da na fara wani irin kuka ba, tsayawa yayi yana kallona bakinshi a bude " me kuma nayi? ba fa dukanki nayi ba!" "wayyo Allah mammy!" kukan da nake masa kenan, kawai sai na bashi tausayi nan fa ya fara lallabina sai hakuri yake ban nikuwa sai da nayi mai isata, duk atunaninsa batun mammy ne nikuwa harda batun Aliyu a alamarina, sai da muka gama sannan yamin waazi sosai yace na hakura da batun sa damuwa araina mammy insha Allah tana can tana aljanna, ban dai ce komi ba nan nashige daki, aikuwa dare nayi Hajiyatu takirani, Hajiyatu kakata ce mahaifiyar mammy, nan tayita lallabina itama sannan tace zata zo itama da kanta don umma lami ta tafi, sai da na nuna mata inajin bacci ta kwanta, anan nayi bacci sai dai rabi da rabi domin rabi mafarkin aliyu nayi. ********** Amrah tana IT a TH don haka na samu daman da zanna zuwa kullum don ganin Aliyu idan yana gari, duk da sai weekends yake zuwa nima sai weekends nake zuwa mata, in yana gari kullum tana office dinsa nima haka nake binta muje mu zauna, idan naje yadda ake ajiye dutse a manta dashi haka yakeyi dani sai dai ya kula kanwarsa amma nikam ko kallo banna isansa, ni kuwa zama nakeyi na zuba masa na muzurai musamman in yasaka kayansu farare na likitoti yasa gilashin idonsa kyau yakemin sosai kaman na hadiyesa, duk da shareni da yakeyi baya damuna damuwata shine in zan ganshi na gama biyan bukata ta, ko kuma inje inbi layin marasa lafiya in anzo kaina sai inshiga yana ganina yake daure fuska ko ya koreni ko kuma in yan mutuncinsa na kusa yaleko yacewa nurse karta barni nashigo takaini gun wani doctor bazai dubani ba kuma babu yarda na iya sai dai na hakura, ganin nafi sati biyu yana min haka da safe naje asibitin na kama layin inajira sai da naga saura mutum daya a gabana na fito da inhalern sannan nayita shaka, uhm ni ba asthma kuma inhalern ma mai karfi sosai, kuma dama nayi overdose din maganin ciwona atake agun na fadi , ji nakeyi kirjina yana nauyi sosai , sai suka yakemin kaman zai fadi, numfashi na yafara tsarewa dauka na sukayi cak suka nufi daki dani aka kirashi, yazo shi kaina idona ya tsaya kallona ya tsaya yi ganin ni ce yajuya ya tafi nurse din tana rikoshi amma bai juyo ba, tun ina gani har idona yarufe na sume bankuma san inda nake ba.15?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Bude idona nayi a hankali sai kuma naga hajiyati, lumshe idon nayi don yaji da kuma iska da naji yana shiga min idon, riko hannuna naji anyi na kara bude idon a hankali sai kuwa naganta ido ya kumbura sosai bayanta kuma su yaa kamal ne da wata budurwa tana zaune itama cikin gyale tayi kyau sosai, hajiyati da sauri ta riko ni sosai sannan ta ce "ya jikin dai lele?" gyada kai nayi a hankali yayin da nake jin wani irin nauyi a kirjina kaman zai fadi kasa, ta daga kaina a hankali ta jingina da jikin pillow yaa kamal da wannan budurwan suka karaso kaina cikin sanyin jiki, cikin sanyin murya ta ce " ya jikinki?" na kalleta ina kokarin murmushi yaa kamal yace " sunanta ummi aisha" anan na gane me yake nufi wato dai budurwarsa kenan, a dai dai lokacin wani tari ya zo min a kirji ba shiri na yi shi wanda sai da nayi nadama domin kuwa ji nayi tamkar kirjina zai fado haka naci gaba da tarinnan kaman zan mutu a gigice yaa kamal yafita don kiran likita hajiyati kuwa duk ta rude haka zalika ummi aisha idonta duk ya ciko da hawaye, anan kawai sai ga tarin jini , na rike a hannuna ina kallo hankalina yayi balain tashi domin mammy na tuna itama haka tayi wannan tarin sannan ta rasu, duk da bansan sauran labarin ba, Abamaama boye min yakeyi ba yaso na sani, Dr.Hisham ne ya shigo a guje idonsa tayi jajur nan nurse ta biyo bayanshi, alokacin tarin ya tsaya, sai bari da jikina yakeyi wani allura yamin sannan ya kwantar dani fuskarshi kaman zaiyi kuka cikin takaici yace " don girman Allah hajiya ku taimaka yarinyannan ta daina tunanin da takeyi , ba karamin illa yake kara mata ba, ciwonta bai kai haka tsanani ba magani tana sha zai sauka don ma gadon shi tayi amma yanzu ta janyo wa kanta wani babban cuta daban fisabililah" a yadda yake maganan cikin tsananin damuwa yasa ita kanta hajiyati tana damuwa daukan wayanta tayi ta fara kiran Abamama yana dauka tace yayi sauri yazo, cikin minti ashirin sai gashi aikuwa tana kuka tace dr.Hisham ya masa bayani shikuwa dama kaman jira yakeyi ya zauna nan yace masa " Baba zan yi magana ne ba a matsayin likitan Nadrah ba zanyi magana ne a matsayin abokinta sannan kuma mai sonta"

Abamama ya zaro ido don yanayin da Hisham yake magana dole jikin mutum yayi sanyi anan ya cigaba da cewa " Baba Nadrah tana da damuwa bansan ko ka sani ba, Amma akwai likitan mu anan likitan zuciya ne, Nadrah tana sonshi sosai amma baba baya sonta, son da take mishi yasa yanzu gaba daya ta dawo haka, wani zai dauka ko rasuwan mammy ne amma acikin dari kashi saba'in saboda shi ne, idan batayi hankali ba zata iya rasa ranta, kaga tsantsan nuna kaunar da take masa gudunta yake yi, nayi iya kokarina in janye hankalinta akanshi amma na kasa" dukka dakin kowa tsit yayi Abamama ya kallen amma na rasa gane kallon meye daya , gyran murya yayi sannan yace " wato Hisham na gode sosai da wannan labarin da ka bani, nayi sake sosai akan y'ata tun rasuwar mahaifiyata, Amma naji dadin wannan bayani insha Allah zan dau mataki da gaggawa" yana gama fada ya fice yabar dakin, ya kamal kuwa kaina ya iso alokacin sakon harara nake turawa Hisham shi kuwa ko ajikinsa ya fice yabarni irin wato na ci kaina kawai, yaa kamal yayi murmushi sannan yace " me ya hanaki fada mun tuntuni?" juya kaina nayi domin shi kanshi ya sani da ace fada masa nayi in bai makeni ba toh zansha mari cikin biyu za'ayi daya, ummi aisha kuwa jugum tayi tana ganin ikon Allah.

Tun ranan Abamama bai dawo cikin asibitin ba, haka zalika ban hada ido da Haidar ba, hajiyati kadai ke jinyata sai yayuna idan sun zo, duk na jime na dawo abun tausayi, Ammati kullum tana cikin yimin test a makaranta, sati na na biyu Abamama ya shigo da Visa a hannunsa ga kuma epassport wanda ina tsammani nawa yayi renewing don tayi expire , jiki a sanyaye na zauna ina kokarin gaisheshi nan ya katseni

" na saka kamal ya hada kayanki dukka zamu hadu a airport, ki wuce dubai kije gun Ammi(kanwar Mammy da take zama acan) , skul nan zanmiki differing ko kuma na nema miki transfer idan zai yiwu"

tun da ya fara kallonsa nakeyi har ya idda yana gamawa nace "Abamama ba zanje ba".

wani kallon mamaki yamin daga shi har hajiyati domin yadda na fada da confidence dina babu tsoro aikuwa ya gyra tsayuwa sannan yace " Nadrah idan zaki mutu anan sai an dauki gawanki ankai can don haka ki tashi ki zo ki wuce na karba miki ticket ki wuce abuja jirginku zai tashi karfe biyun dare.16?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Tashi nayi na mike na riko kafarsa ina kuka "Abamama kayi hakuri bazanje ba " ko kulani baiyiba, ya fice yana goge gefen idonsa alamun share hawaye a fuskarsa,kowa sai da ya tausaya min kukan da nakeyi agun, Yaa kamal ne yasa nurse din ta min wanka na shirya tsaf asibitin suka sallamen mukayi sallama da hajiyati da kuka, airport muka nufa cikin minti arbain da biyar muka isa abuja, muka yi zaman awa biyar, awannan zaman dr.Hisham yakirani mukayi sallama, muryarsa duk ta dishe alamun yana cikin bakin ciki, ni dai ko ajikina tunanina duk shine Aliyu, na kira numbanshi bai dauka ba don haka nakira Amrah nace mata zanyi tafiya amma zandawo don Allah ta gaishemin da yaa Aliyu tayi dariya kafin ta amsamin. Anan ma take sanar dani cewan yana abuja, rokonta nayi ta turo min address dinshi yana zaune a maitama har dadu house number nayi murmushi sannan na kashe wayan. Anan muka shiga ethopian airline nan ma muka tsaya a addis baba wanda ke birnini ethopia, mukayi awa uku kafin muka wuce dubai duk wannan lokacin yaa kamal bai tanka min ba kaman kishiyoyi waya san meyake damunsa, oho nidai ina kissa yadda zan gudu,daga airport dinsu muka zauna jiran Motan gidan Ammi da zai zo yakaimu sharjah inda suke da zama, Yaa kamal yaje nemo mana coffee duk kayanmu na ajiye anan na mike sadaf sadaf na bar kayan agun sannan na koma cikin airport din na tambayi yaushe zansamu jirign zuwa nigeria a daren mutumin ya kallen yace nan da awa biyu, na ce to inaso na biya, yayi dariya sannan yace "ai bazai yiwu ba" duk cikin harshen turanci muke magana, a gigice nace masa " me yasa?" ya kallen yace " wannan fa international airport ne ba state zakije ba" duk da haka ban yarda ba nace " toh duba ko akwai wanda sukayi cancelling flight dinsu" yayi murmushi ganin yadda na rikice kuma nake juyawa in kalli bayana in kalleshi,nan ma yace babu, wayata na ciro na kunna dama mtn dina ne akai, tuni na kunna wifi dina a gigice na hau whatsapp ganin asiri na zai tonu yasa na shiga ladies tsaf tsaf babu kazanta daga masu shiga sai masu gyra makeup dinsu da masu gulma wasu turanci wasu larabci dama ladies ya gaji haka, na hau whatsapp dina sannan na ga iby, iby kuma abokina ne sosai anan natuna yana zama a dubai, a gigice na mishi magana, na ce masa gani a kasarsu amma inason komawa, tambayata yayi da wani layi nake amfani nace masa da wanda nake whatsapp kawai ganin wayansa nayi , na dauka ya tambayeni me ya faru, nan na masa bayanin komi dama asali yasan Aliyu don haka kawai da na masa bayani yace ina ina? na sanar masa da gani a airport , nan ya bani hakuri yace na nemi hotel na kwana yana da mutane a embassy zai roka ko za'asami mai zuwa gobe, nan ma nafara kuka don Alah yagani bazan iya kai gobe ba, haka nan dai nafito ina share hawayena rike da wayata a hannu sai jakata, aikuwa ganin yaa kamal nayi agabana, idonsa tayi jajur alamun yana cikin tashin hankali yace " daga ina kike?" cikin rikicewa dan zufa har ya ketomin nasan kalan ubana da zanci, nace " toilet naje" bai ce komi ba yayi gaba nayi bayansa ina waige kamar barauniya, nikam na shiga uku idan ban koma ba, ya zanyi da hamma Aliyu , mota muka shiga muka wuce sharjah cikin minti arbain muka isa gidan Ammi, buga kofan mukayi aka bude numfashina ne ya tsaya cak ganin wanda idona ke nunamin17??CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Ido na a zazzare nace "Hamma!" ya lumshe idonsa a hankali sannan yayi murmushi yace "Hamma kuma?, ku shigo daga ciki" harshensa a juye, alamun hausan ba ta zauna ba,ya wangale kofan , rike da jakakkunan mu muka shiga bani kadai ba hatta yaa kamal sai daya bisa da ido, Ammi ce ta sauko biye da Fido(yarta ta fari, wacce muke sa'oni da ita) da sauri ta rungumoni nikuwa abun al'ajabi yamin yawa sai kallonshi nake nace mata "Ammi yaushe Hamma Aliyu yazo nan?" ta kalleshi sannan ta juyo ta cemin " Hamma Aliyu kuma? Fahad dai ko?" na saki jakar hannuna bakina a sake, inaaa ai raina mun hankali zasuyi da hankalina, ya za'ayi ina ganin Hamma Aliyu acemin Fahad, nace "Ammi kina gani kuwa da kyau? Hamma ne fa!" ta yi murmushi sannan tace " Fahad taimaka kaje ka haura mata da kayannan sama, inaga stress ke damunta kasan da sauran ciwonnan ajikinta" tafiya yayi yabarni nikuma Fido ta rikoni mukaje dakin da aka sauken, wanda shine dakinta, babban dakine komi pink kana gani kasan dakin yan'mata ne ya sha ado da komi, muka zauna ta kunnamin heater na shiga nayi wanka na samu tafito min da dogon riga na sanya nayi sallah sannan muka sauko kasa, duk da riga da wando ne ajikinta ta tumbuke gashin kanta, Yaa kamal na kan dining yana aika sakon abinci abunka da mai ci, ya kallen sannan yacewa Ammi " Ta zauna anan tunda zamanta acan rikici take janyo mana da kayan kunya, idan tasamu makarantan ma dukka, ni dai gobe zan wuce" ina zama na riko cokali sannan nace " idan na tabbatar da Hamma Aliyu ne na gani dazu bazan bika ba, Amma idan bashi bane zan bika" zura min ido sukayi a lokacin shima ya sauko jallabiya ce a jikinsa tayi matukar yi masa kyau, ya zauna akan dinning din sannan ya fara cin abinci yana danna wayan hannunsa, idona kyam a kansa ina kokarin fitar da cewa shi dinne Hamma Aliyu ba wani ba, Amma ina duk abunda nagani ajikinsa tsak na Hamma, sai dai shi yafi Hamma manyan ido da kuma ginin jiki( wato six packs) daga gani baya wasa da lafiyarsa, namiji ne a zube, hannu fido ta sakamun na juyo sai da naji kunya domin duk idonsu na kaina tace " kinsawa Bappah na ido" na harareta ta gefe sannan naci gaba da jefa shinkafar da ke gabana duk da bawai tamin dadi irinna gida nja bane.

******** Washegarin ranan Yaa kamal ya bar dubai ya koma nja ya barni da jimami da kuma ganin ikon Allah, duk ya ajiye min magunguna na da komi da zan bukata, ko da iby yakirani nace masa a a nafasa tafiya, Fido na zuwa makaranta da sauran yaran Ammi guda hudu dukkansu maza, Mubarak,Alhassan,kabir, da Abbakar sai ita fido dukkansu suna makaranta acan haka zalika Ammi na da shago a cikin kasuwansu don haka takan fita tace , Fahad yana aiki shima duk da bansan gun aikin ba gidan anwatse anbarni ni kadai kamar mayya sai masu aiki, na kimtsa kayana na ajiye sannan na sauko na kunna tv, bana gane yaren nasu don haka na kashe na dauko wayata. Ina kewar gida don haka nakira Abamama, ya dauka cikin sanyin jiki na gaisheshi ya amsa sannan yasamin albarka " Kiyi hakuri ki cire ranki akanshi kinji? ina nan muna miki adduan wanda yafishi alheri, zaki gani kema kiyi addua Allah zai musanya miki shi da wani" "Amma Abamama shi nakeso fa" "kina wasa da ikon Allah ne? ke kam kiyita addua kinji?" da haka na kashe, na kira hajiyati, Ammaty da kuma su yaa Amir da su yaa ahmed, dukkansu yayuna sai dana kira, kowannensu wa'azi daya yake min na nutsu nayi karatu sannan nacire Hamma Araina, wanda idan sun fada dariya nakeyi banjin akwai halittan da nakeso fiye dashi alokacin arayuwata.

kwankwasa kofan akayi da sauri na sauka naje na bude a zatona Fido ce ko Ammi saikuma na ganshi, gabana yayi mummunan fadi sannan nace " Ina wuni" bai amsa ba sai murmushi da yake min yashigo ya rufo kofan sannan yace " baki gaji da zama ke kadai ba?"

" na gaji mana, gobe zanbi ammi kawai" ya yi murmushi sannan yace " zo kiga" na tsaya ina kallon shi dasauri ya janyo abayata sannan yayi dani ta bayan gidan, wani irin teddy bears na gani ajere a ajiye, juyowa nayi na kalleshi sannan nace " na waye haka?"

" wata budurwa ta ce, kullum idan na kai mata sai tasa adawomin dashi, shine nake ajiyewa ko akwai wacce zata dauka wataran" na dauko daya na rike wani irin kamshi teddyn yakeyi na rungume ina lumshe ido tunanina aina nasan turaren, gabana tayi Dam ta fadi dana tuna cewa na Hamma ne, dago idon da zanyi na ga shima kallo na yakeyi nan ma gabana ta kara fadi dasauri na bar wajen, yau nikam nashiga uku bugun zuciya zata kasheni a gidannan idan banfice ba, falon na koma shima sai ya nemi gu yazauna ya hade kafansa daya kan daya yana danna waya, nashiga uku haka Hamma yakeyi idan zai zauna shima, zura masa ido nayi ko kyaftawa banyi

"wannan kallon ba zaisa na shake ba kuwa?" muryarsa ce ta katseni a razane na kawar da fuskata sannan nace " wani kallo fa, tunani nakeyi"

"tunanin Hamma ko?" na gagara amsawa shikuwa ya tashi yabarni a falon, nan ma nabishi da kallo tabbas idan ban tattara kayana na bar wannan gidan ba zan iya karamin hauka.

*****

Sati na daya agidan Ammi na dawo tamkar yar gida, don asai munsaba dasu zuwansu dubai ne last year yasa bama haduwa, shima aiki yazo yi mijin nata na shekara biyu yana gamawa zasu koma acewar Ammi domin ita batason zaman can tafison zaman nan musamman ma da Mammy ta rasu hankalinta yadawo nja, kauna duk sun gwadamin banda abun cewa sai godiya, Abu daya ke cimin kwarya a tuwo, ko cin abinci Fahad yakeyi sai naga kaman Hamma ne, gashi sai shigemin yakeyi mutum ne mai son mutane, fara'a dakuma saukin kai, haka zai jamu nida fido muyi yawo mu dawo gida, sannan duk fita sai yadawo mana da kunshin leda, ina matukar jin dadin zaman gidan Ammi sannu a hankali na fara mantawa da duk wani abu dake faruwa dani haka zalika shakuwa ta shiga tsakanina da Fahad, ko chewing gum naci sai na ajiye masa, haka zalika shima ko me ya samu sai ya ajyemin, hankalin Abamama ya kwanta sosai atunaninsa bazanyi maraicin uwa ba kuma hakanne sai dai kuma a duk lokacin da na ga yadda Ammi take dasu fido sai na tuna da Mammy ko Hamma na kan shiga toilet nayi kuka har sai kuka yafita araina, in rarrashe kaina, babu wanda yasani har wata rana da Fahad yashigo kirana kawai yaji shishikan kuka dasauri yarinka buga toilet din na bude yaga yadda idona ta kumbura tayi jajur, tuni ya lallaboni muka zauna akan kujeran dakin, zuramin ido yayi yana jira na masa bayani amma na kasa nan ma wani sabon kuka na farayi don tuna min da Hamma da yayi zuciyata na ciwo, wani irin kaikayi nakeji aran nawa, ina zansa kaina naji dadi , wayyo Allah na Hamma, wayata naciro da sauri na fara kiran numbanshi duk da nasan ba dauka zaiyi ba tunda naje kusan kullum sai nakira numbanshi amma baya dauka, nakira bugun farko ya dauka a razane na tashi sannan nace "Hamma!" bai ce komi ba sai dana kara kiran sunan nasa "Hamma!!"

" i taught nace ki daina kirana, ke wacce irin mutum ce?" ji nayi an fizge wayan , juyowan da zanyi kawai na ga Fahad yadda yakarba haka yakarba ya tika wayan a kasa, Tasssss ya fasata idonshi tayi jajur tunda nake ban taba ganin shi awannan yanayin ba, nashiga uku.18?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Ba tare da ya kalleni ba yajuya yafice nikuwa na tsugunna na tattara wayan sannan na koma daki, bakin ciki da takaici wayata mai uban tsada ya kama ya fasamin wallahi zai ga madarar rashin mutunci, zuciyata ta cigaba da kuna shi kuwa ban kara ganinsa ba aranan.

*****************

BAYAN SHEKARA DAYA Lafiya akace uwar jiki toh haka ta kasance dani, domin kwanciyar hankali na samu nayi bulbul kwata kwata bana da damuwa, na so shiganakaranta, don har transfer na nema anma bansamu ba domin cgpa na ya sauka sosai, American university dinsu na cika , gashi kuma archictecture and art desighn shima almost shekara biyar, Ammi tace na bari kawai tunda mun kusa dawowa nja,don haka sai dai na raka Ammi shago, muyi yawo mu ga duniya , shakuwar dake tsakanina da Fahad ya zama hatta abinci tare mukeci, bana ci idan baya nan safe idan yafita aiki haka nake zama jugum sai dai mu wuni muna chatting, wani lokacin har skype mukeyi , ni nake gyra masa daki sannan na wanke masa a machine idan sunyi datti mu hada akai guga, yayuna kuma mu kanyi waya dasu, su hajiyati da Abamama duk hankalinsu ya kwanta ganin ina cikin kwanciyan hankali, alokacin har na fara jin haushin kaina , meye na gani ajikin Hamma? idan kammanine gashinan sak ajikin Fahad , hallayar da nake nema ajikin namiji kuwa shima gashinan, saukin kai, kyauta, fara'a ga ilmin addini domin Fahad har karatu yana kara min, duk munayi to ahaka na shaku dashi shakuwan da yasa na kanyi sati biyu zuwa uku ban tuna da Hamma Aliyu ba, ga Adduoi da Hajiyati da Abamama suka dade suna min , Hajiyati kam saukan alqurani ta saka aka rinka min Alhamdulilah na dawo asalin Nadrah ta, kwanciyan hankali saikuma maraicin uwa duk banyi shi ba sai dai na tuna da ita.

****** Mijin Ammi ya gama aikin da yazo, don haka tuni muka tattaro muka dawo gida nja, gidansu na bauchi kerarriya a gra wanda duk wanda zai wuce gidan dole ya juyo yakara ganin wannan gidan, mun tarar da gidan tsaf tsaf ga mamakina na ga Amrah da wata dattijuwa yar gayu daga gani ita ta haifi Amrah, na gaisheta tana da fara'a sosai naga sai barkwanci sukeyi abun yaban mamaki sosai, sun san juna ne? sannan aina suka san juna da su Ammi? na kalli Fido na ce mata "meye alakarsu? " abun ya matukar bata dariya, don haka sai kawai tace " ki bincika da kanki zaki sani" nayi mamakin ganin gidan, domin kuwa kowa da dakinta nida fido sai dai fanninmu daya ne, haka sauran yaran Ammi. kayan mu kawai muka ajiye amma gidan babu abunda babu, sanin garin fiye da Fido yasa muka fito da ita na tambayi Ammi mota ta kuma bamu akan zamu je ko jifatu mu siyo abubuwan da muke bukata su tootthbrush da sauransu, sanye da abaya duk muka fito munyi matukar kyau idan aka cire kyan fatanmu da kuma kyalli da mukeyi , duk inda muka wuce sai an juyo an kalle mu, muka shiga cikin jifatu muka tsinci abubuwan da zai mana amfani , sannan muka fito muka dawo gida, shigowar motata yayi dai dai da lokacin shigowar motarshi , Gabana ne ya tsinke ya fadi haka kawai amma kuma murmushi ne a fuskata, sauke glass din motar yayi ganin fido yana murmushi ita kuwa tace "Cousin!" annurin fiskata gaba daya naji ta dauke don sai alokacin na tabbatar da cewa ba fahad bane Hamma ne, hannuna na rawa na dawo baya kadan duk da glass din dake idona baisa na gagara mishi kallon muzurai ba, suka gaisa da fido sannan ya juyo yace " daga ina?" tace " mun fito jifatu" kallona yayi amma jikina ya na bani baigane ni ba to ko ya ganeni ma kadan daga aikinsa yayi banza dani, ya ja yawuce nima na shige ciki , ina shirin parking motan tace " baki gane shi bane?"

"na ganeshi mana"

" na ga kin shareshi"

" banda case da shi"

mamakine ya ciko fuskanta don dai tasan cewa inba mafarki take ba hotonsa nake damunta ada dashi nace inasonshi, tasan tarihin soyayyata bawai bata sani bane, gashi ina nema na raina mata hankali.

Har dare ban ga Fahad ba nima dama na gaji sosai don haka wanka nayi na sauko kasa gun Ammi tana kan dinning tana gyra plate na ce mata "Ammi meye alakar Fahad da Hamma?" ba taso na mata wannan tambayan ba don haka ajiye cokalin hannunta tayi sannan tace " Nadrah! dawowan mu banso shi ba saboda ke, nayi iya kokarina na hana fido ko duk wani acikinsu su fada miki wani abu dangane da Aliyu, tunda ga halin da kike shiga akansa don haka kawai kiyi hakuri kibar maganan nan kicire ranki kinga kin samu lafiya yanzu hankalin kowa ya kwanta, Abamama ma baya garine da kin ganshi yanzu amma su kamal ma suna tahowa don haka bana so ki tayar musu da hankali" na gane me take nufi don haka kawai nace mata " wallahi Ammi na hakura da Hamma , na daina sonshi ni yanzu ba ruwana na miki alkwarin ba zakiji wani matsala a tattare da ni ba, don Allah ki fadamin kinga yanzu na ganshi a waje, kuma ban kulashi ba"

"Nasan zaki yi mamakin kammaninsa, kammaninsa da Fahad yayi yawa, duk da cewa kanin Babansu fido ne wannan kam kin sani ai amma da Hameed tofi wato mahaifin Aliyu da kuma Babansu fido,Uncle Usman, da Fahad uwarsu daya Ubansu daya, ma'ana dai a takaice Fahad yana matsayin Bappah wa Aliyu" tsananin mamaki ya kamani, haba mana dole mana, kammanin yayi yawa ace kuma munyi zaman sama da shekara amma ba'ataba fada mun ba, lallaima Ammi sannunta da kokari, na girgiza kai cikin mamaki sannan nace "Ammi da gaske kar ki damu ni dai ba zaki kara jin wani abu daga gareni ba" ina gama fadin haka na mike na koma daki ina tsananin tunani duk da cewa ina jin dar-dar araina ayanzu shakuwar da nayi da Fahad yafi karfin tunanin mutum, akashi dari cikin son da nakeyi wa Hamma kashi 60 yanzu wa Fahad nake wa, Allah ya gani yanzu son da nake masa ba kaman da ba, na manta da al'amarinsa duk godiya wa Allah da taimakon adduan yan'uwa yasa yanzu ni kaina na huta. damuwata da addua'na shine tunda ina cikin kwanciyan hankali Allah yasa na dauwama ahaka tunda ni ban iya controlling love life dina ba, Ashe ni kam Nadrah ina nawa Allah na nashi tashin hankali rikici da kuma damuwa na dawo cikinta kenan.

(zan ci gaba insha Alah jibi, kada ku manta its a true life19?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Karfe tara na dare su yaa kamal suka shigo cikin gidan, ina zaune da gyada a hannuna ina barewa da sauri na zubar akan carpet din na rungumoshi, yaa Amir da yaa usman suna bayansa dukka rungumosu nayi ina kukan murna, yaa kamal harda dan kwallanshi shima , muka zauna sai tadi anan na tabbatar da yayuna sunyi kewata, sama na hau na debo akwati na kwaya daya nace zanbisu, Ammi abun mamaki tace " sai ina?"

"Ammi zamuje muyi kwana biyu da fido don Allah Ammi" Fido da rawan jiki ta hau sama ta hado kayanta nikam tsabar rawan jiki fita nayi na shiga mota ina jiransu su gama gaisawa da Ammi na saka kayan a booth sannan na jingina jikin motan ina danna wayan hannuna , horn akayi a bakin gate din lekawan da zanyi naga wata benz ce take shigowa tsayawa nayi don nasan bazai wuce masu zuwa sannu da zuwa bane, suka bubbude kofan suka fito, wasu tsoffi ne guda biyu sai mai tukawan da ban ganeshi ba don yana ciki kafanshi ne kawai ta waje, na je na risina na gaishesu suka amsa suna zolayata duk da ban ganesu ba amma summin farin sani, har na juya zan gaidashi kawai annurin fuskta ta dauke gabana ya tsinke ya fadi, tuni na danne raina na bata rai sannan na koma jikin motan, ina kallonsa ya fito sanye da farar riga da jeans ta masa kyau sosai ya saka hannu a aljihu yanda akayi halittan dutse haka yayi nima kuwa na shareshi amma nasan da ace da ne dasauri zan nufeshi naje ina rokonshi ko ina masa magana, tsoffin suka shige ciki shi kuwa ya jingina da motar, nima tsayawa nayi har da daukan hotuna ina turo baki, yaa kamal ne suka fito suna tadi suna dariya cikin nishadi, ganin sa yasa suka nufeshi suka mimmika masa hannu, suka gaisa cikin mutunci duk da nasan gaisuwan bai kai zuci ba na yaa kamal, don idan akwai halittan da ya tsana toh yabiyo bayan Aliyu, acewarsa shi yayi sanadi Mammy ta rasu da baizo da wuri ba, sannan nima ciwukan da nayi duk shine sanadi sauran su yaa amir ne kawai suke kulasa, ba karamin danne zuciyata nayi ba gurin ganin yadda suke masa murmushi yadda nake jin haushinsa so nake kawai kowa ma kar ya kularsa, na rasa dalilin jin haushin duk da cewa gabana yana fadi idan na ganshi bayan kuma tsoronsa da nakeji da bansan ya akayiba domin da bana tsoronsa ko kadan. Bayan sun karaso ne fido tasa kayanta dake motan sienna ne dukka muka duru ciki sannan muka zauna, tuni aka fara tadin yaushe gamo, fido kuwa ta gagara sakewa na lura kuwa yaa Amir sai kallonta yake har dai muka isa, dakin tsaf tsaf ma'ana sun gyra da sukaji na dawo , Allah sarki dukka masu aikin gidanmu sun hallaru suna jira, harda hawayensu da suka ganni, nima sai da naji kuka musamman dana tuna da Mammy ina share kwalla har muka kimtsa kayanmu tsaf.

Daren ranan dai bamuyi bacci ba sai tadi da fido da su yaa kamal, Anan ya Amir ya kirani falon Abamama na zauna ina kallon tv domin na lura magana mai muhimmanci zai min

"yanzu ya zakiyi maganan skul? kinsan differing kikayi kije tunda ana hutun second semester zaa shiga first semester kije ki duba, and ki tabbata this time around you don't mess up please i beg you!, ki ajiye namiji a rayuwanki kiyi karatu mazan ma inkinyi karatu sunfi mutunta ki, namiji in baki da ilmi he wont respect you kamar yadda idan kina da ilmi, sannan ko aure kikayi kiduba rayuwa kigani komi na tafiya da zamani, azamanin yanzu duk auren da za kiga anyi mace mai ilmi da wacce bata da ilmi akwai banbanci, namiji idan ya san ya sakeki sannan kina da ilmin ki yasan zakije ki nemi aiki you have nothing to loose amma wanda yasan ko ya sakeki zaki wulakanta bazai damuba kuma ki duba dakyau mace mai ilmi tafi zamaan daraja kinemi ilmin addini da boko i know dukka kina kokari amma ki kara kafin ki tafinnan gaba daya kin dawo shiru ne, sannan Abamama yabiya muku hajj ke da fido yayi hakan ne appreciation na rikeki da sukayi da gaskiya zakuje kuyi aikin hajj ku dawo idan time yayi" kafin ya karasa na yi samansa na rungumosa shi kanshi yayi mamakina saboda yanda nake dan tsoronshi fiye da sauran yayun nawa, ina zubar da hawayen farin ciki ban taba kawowa zan koma aikin hajji kusa ba tunda muntaba zuwa da Mammy Allah sarki mammy na, sallama ta yayi sannan na koma daki, yaa kamal na ganina yace " amir ya sanar miki?" ban amsa ba na nufi kan fido ina cewa " taho masoyiya habibaty, an biya mana aikin hajji insha Allah zamu tafi ooo" fido ma murna takeyi sosai tsabar farin ciki ranan sai bayan asuba mukayi bacci.

Washegari sai karfe biyu muka tashi, karyawa mukayi sannan mukayi wanka na dauko mukullim motata nayi kewarta sosai, ba mu nufi ko ina ba sai gidan su Ammaty munyi farin cikin ganin juna, sai anan take cemin aurenta saura sati biyu raina yayi matukar baci domin bata fada mun ba sai take cemin ai ta bari sai na dawo ne, muka samu tama ajiye mana ashobe da yake sun saba sosai da fido tun acan ganin junane basu taba yiba, ta ajiye mana ashobe kyauta, naji farin cikin wannan labarin har raina harda kwalla ta, hajiyanta ma taji dadin ganina Allah yasa damu zaayi da zanyi bakin ciki sosai, fitowar mu take cewa Amrah ta aiko kudinta domma ashoben bata dade da fitar wa ba don haka ko zamu samu mu kai mata, banso ba sai sai kar Ammatyn tayi tunanin ko da akwai wani abu tunda na gwada mata anzama daya, nan na karba ashoben guda uku na tuka muka nufi gidansu Amrah, babu komi araina nidai kawai kunya nakeji kar na hadu da hajiyansu duk abunda nayi abaya, horn nayi muka shiga ciki, A falon kasa muka sami Amrah tsalle tayi tana murnan ganina, na kalleta duk da nayi kewanta amma na boye mata saboda kar tayi tunanin don yayanta ne, ta jani muka hau sama fido na biye da mu agida, bayan gaisuwa take cewa " dama inada magana, nasan ko na miki awaya ba zaki yarda da batu na ba" na kalleta nace " me yene?" ta ciro wani album ta mikomin hade da diary bude page din farko naga sunana, dasauri ta rufe tare da cewa " ba'anan zaki duba ba, tafiya zakiyi kije gida ki nutsu ki karanta" na gyada kai tare da cewa toh muka sauko kasa bayan mun mika mata ashoben , duk na matsu na ga meye ina shiga motan text message ta shigo wayana budewan da zanyi na ga fahad ne yaturo kaman haka

" Nadrah tun randa na fara ganinki kika zamto wani sashe na rayuwata, sai dai abun yadawo love triangle ganin cewa wani kikeso bani ba yasa na baki fili ki fito daga kangin dakike ciki tukunna, Alhamdulilah naga yanzu kinyi sanyi burina ya cika, Nadrah burina a yau na aureki, Nadrah ina sonki " jikina a sanyaye nayi murmushi sannan na bude diaryn don son ganin meye aciki page na biyu na duba hotunana ne suka zubo, wanda nake makaranta, nake lectures, na asibiti da dai sauransu , sai kuma wani printed copy na rubutu sai naga ashe text messages na draft akayi printing alamun anason atura akafasa duk anyi printing dinsu, na farkon

" Nadrah i love you"

" Nadrah am sorry"

" Nadrah ba laifina bane"

"Nadrah kyi hakuri ki karamin lokaci"

" Te amo!"

" i love you in every language " dasauri na cigaba da karantawa domin na rude in bude bayan naga Aliyu Hameed tofi

innalilahi wainna ilaihi rajiun
20?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Sauran pages din na bude aikuwa sai ga wani dan karamin envelope, ina budewa naga zobe ya fado, zoben Mammy ne da ta bani na nemeshi na rasa ashe yana gunsa, kwalla ke biyomin kasan idona duk na rude riko fido nayi da take gefe nace " fi -fi -fido kiga? fido dama yana sona boyemin yakeyi? fido na shiga uku naji dadi innalilahi fido" Daure fuska tayi ta kwace ta wurga ta baya sannan tace " meye hakan? i thought mun wuce maganar nan just because kinga wannan messages din doesnt mean he has confessed, ga mai sonki don Allah don haka ki bar zancen wani can da baisan darajanki ko ciwonki ba " shiru nayi na gagara cewa komi domin tunda nake rabon da naji farin ciki irinna ranan tun mammy na da rai, ganin banda niyya tukamu yasa ta karbi motan sannan ta ja mu, har muka tafi bata kara tanka min ba, nikuwa aduniyan Allahn nan hankalina ya bala'In tashi na rasa ya zanyi har muka shiga gida ina makale da takardun, Fahad kuwa jin shiru banyi replying ba yasa yayi tunanin ko bana so ne nan da nan hankalinsa ya tashi yahau kiran wayata alokacin tsabar gigicewa kasa daukan wayan nayi ina kallo cikin minti sha biyar sai gashi ya shigo gidan. A.C ne a falon amma gumi ne yake fito min sai yake nakeyi, ya kallen ya kura min ido nima da naga haka sai na juya kaina, zama yayi dirsham ya kalli fido sannan yace " Meya faru ne ?" tana harara na ta mayar masa da komi yayi gum kaman bazai ce komi can dai ya daure yace " yanzu should i await reply?" gyada kai nayi da sauri domin bani da amsar basa alokacin bai tashi ba haka zalika nima ban motsa ba, Amma duk na matsu yabar gidan, muna zaune sai ga yaa kamal ya shigo suka gaisa sannan ya shiga ciki, Fido ta mike itama ta bamu wuri, sai harara na takeyi da ido nidai ban kulata ba domin ni kaina bansan wani irin hali nake ciki ba,can dai ganin babu maganan da zanyi yasa ya mike sannan yace " zan tafi, zamuyi waya anjima kinji?"

"Allah ya kaimu"

Yana fita na mike da sauri nayi daki na tattaro komi da hotunan na ajiye agabana ganin ba zan gane komi ba yasa na dauko wayata nakira Amrah,

"Amrah bangane kan abun da kika bani ba"

"Dama nasan za ki neme ni yanzu meye daya kike son ji?"

"Aina kika samu? shi ya baki ki bani?"

" a'a abunda nasani shine bayan tafiyarki kinsan shi da problem din shaye shayen nan, toh alokacin yayi accident and fortunately da ya farka sunanki ya kira, munyi mamaki sosai amma da ya farka yayi denying yace bashi ya fada ba, secondly na shiga dakinshi gyrawa naga wadannan pix din, daga abunda na gano shine yana stalking dinki ne while kema kinayi which means ke ce baki san yanayi ba, duk abunda kikeyi yasani ignoring yakeyi wanda har yau ba wanda yasan dalili, ni kuma ganin haka nayi risking life dina na nemo duk takardu da pics har wayanshi na dauke na dauko wadannan messages din, last news and the bad one shine Hajiya tayi mishi mata last three months,bai taba zuwa ba sai jiya yanzu dai maganan da nake miki yarinyan tana sonshi sunanta zahra, Sonshi takeyi kaman tayi hauka barin ma yanzu da take ganin yafara kulata zaki sha fama don mahaukaciya ce bata da dadi duk stalkers dinsa ta koresu" Kaina naji na sarawa wani bakin ciki naji ya tokareni yawun bakina ya kafe, har wani daci daci nakeji a makoshi daukan takardun nayi na watsa a dustbin din dakin, jiri naji yana kokarin dibata, Arayuwa ganin Aliyu da wata shine the least i've expected a tunanina tunda yakini toh zai ki kowacce mace, to meye amfanin takardun tunda gashi ya fara son wata wannan labari bai min dadi ba ko kadan, kirjina naji na bugawa da karfi kaman zai fita rarrafe nayi na janyo kwayan maganina na hadiya sannan na jinginu da wardrobe din dakin ahaka Fido tazo ta samen, tambayan duniyannan tamin naki amsa mata,

"Aliyu ne?" shiru "Fahad ne?" nanma shiru jan jikinta tayi tafita takira Yaa kamal zuwanshi ganin yadda nake ya daga ni ya daurani kan gado hankalinsa atashe fido tana masa bayanin meya faru, tsaki ya ke taka kaman zai cire bakinsa

"Wacce irin Mahaukaciya ce Amrahn nan? Meya fara kaiku gidan? Waima ya zaayi daga dawowa sukara jawo mana balai wannan ai jahilci ne" mitan da yakeyi yashigo dasu yaa Aamir da suke falo yana matsifa yana cewa Amrah bata da hankali, Fido kuwa ta tsorata domin bata taba ganina haka ba, hawaye na bin idona tsananin kishi na cinyeni su suna faman nemomin lafiya ni ina tunanin hanyan samun wannan zahran, Amma Hamma baida kara duk shekarun danayi ina sonsa rana daya yaje yana son wata , Fahad ne ya fadomin arai to ko nace inason Fahad nasan yaudaran kaina nakeyi saboda son da nake wa Aliyu ya ninka na Fahad babu hadi, nikam na shiga uku da na sani da zamana nayi acan ban dawo ba.

Abamama a daren ya dawo , Tunda nake bantaba ganin bacin ransa ba sai aranan

"Nadrah me kikeyi haka kaman bakida mafadi? kin taba ganin anyi son maso wani? toh wallahi bari kiji in fada miki wannan karon bazan dauki hauka ba, Soyayyan banza soyayyan wofi akanki aka fara? Ina Kamal? wuce ka kira min Fahad tun suna can yake gwadamin yana sonta dawowansu ma yazo ya samen, ka kira min shi idan har zai iya yazo a daura musu aure juma'a na gaji da haukan banza haukan wofi.21?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Ji nayi kaman an zuba min garwashi a raina, idona na kekkeshe nace "Abamama wallahi bazan auri Fahad ba, Abamama wallahi Aliyu nakeso don Allah" ina fada ina kuka ganin Abamama bai kulani ba yasa na riko kafansa, tun da nake arayuwata bai taba saka hannu ya dake ni ba amma ranan sai da Abamama yamin dukan ba bantaba ji ba, yamin dukkan da har duniya ta nade baza'a min irinshi ba tun yaa kamal na kallo har yazo yana rike Abamama amma da igiyan inji Abamama ya faffasamin jiki yana haki yace " Ki mutu! nace ki mutu!! yarinya zaki jamin abun kunya fisabililah ana ganin mutuncina a gari bazan dauki rainin hankali ba" ficewa yayi numfashina na daukewa amma bai ko juyo ya kalleni ba yaa kamal ne yakaini sama don ma fido bata gidan sai yamma tadawo a daren zazzabi mai nauyi ya dauken, Ban damuba na fito da magrib alokacin ba kowa a falo ban nufi ko ina ba sai TH rike da takardun da Amrah ta bani,alokacin nasan yana asibitin motanshi na gani naje na tsaya ina jira yafito kaina na ciwo sosai numfashina ma dakyar yake fitowa, na fi minti talatin kafin yafito daga asibitin yana kokarin cire farar rigar dake jikinsa idonsa sanye da farin glass na likitoti yana isowa yabude motan alokacin na tsaya agabansa dago idonsa yayi ya kallen sannan yace " lafiya?"

" kana sona me yasa baka fada mun ba, gashi za'amin auren dole ka fito amana aure"

tsayawa yayi yana kallona baki a sake sai da ya ajiye rigan ta bayan motan sannan ya juyo yace " wa ya yaudareki da wannan kalamun SO? na ce miki bana sonki! ba zan taba sonki ba ki fita a idona, ganinki kadai na samin ciwon kai" riko shi nayi hannunsa yasa da karfi ya tunkude ni hawaye na bin idona na mika masa takardun "wannan fa? wannan meye ne?" Kallon takardan yayi amma bai ko kula ba ya buge ya fadi sannan yashiga motarshi alokacin ya leko yace " Ki daina wahalar da kanki! bana sonki bantaba sonki ba sannan bana tsammani zan soki, kije kiyi ladabi a gidanku" yana tafiya da gudu na shiga motata nima na bishi a baya, yana tafiya ina binsa har ya isa Wani hotel na kalli hotel din ban taba shiga ba balle nasan ya yake, ni dai binsa nakeyi abaya, ya dauko wani jaka yashiga nima na bisa, a reception ya tsaya ya karbi mukulli sannan yashige, naje na tambayi matan dakin da yake tace nayi hakuri basu raba information akan customers dinsu, zaman jira nayi har dare bai fito ba ganin wayan yaa kamal yasa nafice , ina isa gida na ganshi a kofar gida rike da akwati shida fido na zaro ido sannan nace " ina zamuje?"

" zaku koma gidansu fido ne, anan baki da mai lura da fitanki dukkanmu ba zama mukeyi ba ki koma wajen Ammi" yaa kamal ya fada cikin damuwa domin kuwa fuskarshi harta fada fido ma duk ta bi ta damu bance komi ba, don ni dukan da nasha banason na kara shan irinsa agun Abamama.

Ko da muka koma gidan su Fido Ammi zaunar da ni tayi tana min wa'azi amma yadda maganan ya shiga haka ya fita, ta samu dakyar ta lallaba Abamama akan yabari mu sasanta da Fahad kafin a daure mana auren, dakyar ya yarda, nikuwa Fahad dauke masa wuta nayi gaba daya ya gagara gane kaina na koma ruwa tsundum ba juyin duniyan da baiyi ya lallabani ba amma nayi kunnen shegu sai madaran wulakanci da yake fuskanta nima nake kwasan nawa agun Hamma Aliyu.

********

Rayuwa ta ci gaba da tafiya So dana keyi wa Aliyu sai gaba takeyi, wayata password Aliyu, screen saver na hotonshi laptop dina ma komi Aliyu, magana ta Aliyu, duk da ankoma skul amma ina nan idan yana gari ina makale a asibiti agefenshi har ya saba ma, a bakin fido naji tana cewa yacewa Zahra zasuyi soyayya amma sai tayi hakuri don yanada wata mayyar yarinya incase in mun hadu da ita tayi hakuri ta shareni, ni kuwa innaganta kukan bakin ciki nakeyi, idona har ya zama kumburerre tsabar kullum ina hawaye, gashi bai daina shaye shaye ba, ganin Ammi zata takura min akanshi surutun mutane ya fara samin ciwon kai yasa na tattara naje na kama daki a off campus, Fido kuma cathering skul tashiga kafin ta samu skul anan din, ban tashi sanin obsession din da nake wa Hamma Aliyu da gaske bane sai da naganni a bayan gari naje neman cocaine, tunda cocaine take sha shima, kiri kiri na dawo yar shaye shaye don Hamma yanayi, Amma kasancewar ni kadai ce ba wanda yasani, duk abunda nasan Aliyu na so shi nakeyi hatta Abinci nan nalura bai son cin danwake tuni na washi dan wake, haka ma kifi shima har Amai nakeji idan naji karninsa da kuwa inason kifi kamar me, na lallace na dishe karatun ma kawai yi nakeyi anytime soon atbu zasu iya korana amma ban damu ba, Aliyu kuwa duk inda naganshi sai na bishi duk da nasan zai disga ni amma ban damuba, bawan Allahn nan ko sense of humour bai dashi balle tausayi, duk abunda nake tunani shine maybe ko yana boyemin yana sonanen bayan ga komi a hannuna, sau dubu nakan zubar a dustbin amma haka nake lalumawa na dauko abuna, nayi photocopy yakai fifty copies incase in zan manta shi awani wuri, hotunan da text dinma dukka ina kallonsu, sai da wata rana nafito kenan daga aji nace bari na leka asibiti ina isa kuwa na ganshi nafito da takardun ya kallen sannan zai wuce na mika masa tareda cewa " don girman Allah ka taimaka don Allah kaduba kaga menene aciki" fizga yayi da karfi yabude alamomin mamaki ta bayyana a fuskanshi sannan yace "Aina kika samo wannan forged papers din?" cikin jin dadi nace "Amrah tabani"

"Toh Amrah ta yaudareki , ba ni nayi ba, karya takeyi, if thats the reason why kike bina toh kicire hope wallahy bani nayi ba" ya wurga min sannan ya wuce

ban yarda da magananshi ba amma jin yayi rantsuwa yasa nakirata awaya tace mun tana gida don haka naja mota na nufi gidandu tana tsaye kaman mai jirana akofar gidan, nace " takardun nan"

"wanne fa?"

"wanda kika bani ki kace Hamma ne yayi yace bashi bane"

" am sorry, ba shi yayi ba amma nayi ne so that karki cire hope dinki akanshi i want you guys togeda" bansan lokacin da na rikota ta wuyan riga ba na dunkule ta kaman zan mata duka idona cike da hawaye yana shirin zubowa fuskana kuwa bansan wani matsayi yake dashi ba sannan nace mata

" Amrah! kin ma san me kikayi kuwa? me yasa zakiyi haka? ni fa mutum ce and you dare play with my feelings? har ina zaman zamana na manta dashi kin dawo kin cusamin shi kinsa sai son maso wani nakeyi, Haba mana ashe baki da imani? you are very heartless, i hate you to the co" ina gama fada na saketa na shiga motana na kwantar da kaina nayi kuka kaman raina zai fita, da ina da yadda zansa kaina na daina son hamma wallshi tallahi da nayi, bakin ciki kaman ya kasheni sai da nayi kukata mai isata sannan na ja motan nafice.22??CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Ranan yadda naga rana haka naga dare, damuwan duniya tamin yawa nayi kuka, kukan da na dade banyi shi ba idona ya kumbura, anan na tabbatar Aliyu ya zamo min CIWON IDO, adakin na rufe kaina sati na daya banje lectures ba, sannan banje gida ba, ko Ammi takirani yi nake kaman karatu nakeyi haka fido cikin saa bata leko ba gashi a satin zamu fara bikin Ammaty, na karbo dinkina na shirya sai dai duk wanda yaganni yasan ina cikin damuwa, yayuna ko dun nemeni cemusu nakeyi ina karatu ga shaye shaye da na saka agaba, tun inayi aboye har batu ya zaga atbu kasancewar abu arewa its very awkward mace da shaye shaye, nan zagi yakoma kan Abamama domin cewa akeyi shi ya sakalta ni, yabani mota at young age masu zuwa gurina ma masu kudi ne sai dai duk namijin da zaizo min kallon mace na ke mishi, babu human feelings, wulakanci suke kwasa hakan yasa suke hakuri, dr.Hisham ne kadai nasan yana yawan kirana kuma nake kulashi shima don baya gari ne da kullum zaizo yaganni yatafi yin wani course acan kasan waje, ban damu ma nasan wani kasa bane nikam.

Bikin Ammaty yazo day 1 muka fara da bridal shower a matsayina na babban kawa nayi kokarin boye damuwata na shiga cikin kawaye mukayi shagali sosai, washegari akayi walima sai mothers night, duk wannan events din gidan amarya ne kuma naji dadinsu sosai kuma alhamdulilah yadda nayi kokarin boye damuwata munsha goggoro munyi rawa.

Ran asabar aka daura aure da yamma akazo kai amarya, duk motoccin da sukazo na gani da fada ne, na shirya tsaf akan zansamu motan da zanshiga nida fido saboda Amarya da tsoffi zata tafi, ina tsaye wasu yanmata biyu suma kawayen Ammaty ne, suka zo suka tsaya ta baya na duk da basusan ina gun ba inaji suna zage zage "dan rainin hankali me yake gadara dashi? don yaga yana da kyau, ai laifin wannan jakar ce Nadrah ko wa take, ba tasan haushin da take bani, ina zata kai dan shaye shaye har za'a shiga motansa yana koran mutane wawa kawai, itace asararriya ai" dayan ta karba da "kullum na ganta sai bakin ciki ya zo min kina mace iya mace to wani iskanci ne kuma wannan kina makale wa wani, na jima ance ansa aurensa da Zahra ba? itama sai wani ji da kai take gayyan mahaukata"

Zuciyata tana tafasa na rasa yadda zanyi da rayuwata duk naji karfina yakare idona yayi jajur na juya ina kallonsu alokacin suka ganni dukkansu jikinsu yayi sanyi sun tsorata, sai dai bance komi ba amma na juya don zuwa neman motan da zan shiga fido ma da ta tsaya waya tuntuni barinta nayi agun, ji nayi wani abokin ango yana cewa ga mota ba tare da wani tunani ba na bude gidan baya na shiga, su biyu ne agaban ban dai lura ba da ko su waye shi na gefen ne yake ta surutu yana cewa

" kai kam Aliyu kana bani mamaki, yan mata suna sonka kaima sai ka so su, use her and dump the fool, ji yadda ka wulakanta wadancan abun bai min dadi ba, haka kake tozarta wannan Nadrahn ji yadda take sonka, zata iya komi akanka yarinya ga kyau ga kudi ga ilmi mtsww abokina ba kayiba" Aliyu dake gefe wanda farawan maganan abokin yasa na gane shine hankalina yabi ya tashi yace " if magananta zakamin ka fita min a mota, nace ma zahra nakeso bana son wata bayan ita wallahi na tsaneta, mace ba kamun kai kaga zahra da hijab da liqab take yawo, bata hawa mota so she wont dare challange me"

bazan iya hadiye kukana ba fitowa nayi a motan na fita da gudu, motata na shiga na buya inagani fido na kirana naki dauka, nayi kuka, nayi kuka har numfashina yana neman dauka, in dai abunda yakeso kenan insha Allah na daina yawo haka, gida na wuce ban nufi ko ina ba, haka akayi dinner banjeba asali ma kashe wayata nayi, aka kai amarya hankalin kowa ya tashi amma ban damu ba sai bayan kwana biyu da gama biki na kunna wayata naje gidan Ammi, hankalinsu yatashi sai dai ni ko ajikina Abamama yamin fada sosai yace kar na kara kashe wayata.

Tun daga ranan da naji kalamun abokin Aiyu bayan fitowa ta daga gidan Ammi na tattara naje kasuwa na siyo hijabai guda goma sha biyu, liqab guda biyar da safa guda biyar, duk wasu english wears dina na ajiye su agefe , motata na ajiye agidan haka nake shiga makaranta, duk da wahalan da nake sha amma haka nake zuwa, duk saboda Aliyu ya tausaya wa rayuwata ya taimaka min ya kulani, da farko bai saniba saida na koma asibiti da naji yana gari randa ya fara ganina da liqab yayi matukar mamaki sosai, abun ya daure masa kai, don har dariya yayi abunda ban saba gani yana yi ba, bugun farko yace " karen hauka ne ya cijeki23?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Na kalleshi ina hadiyan bakin ciki "A'a ba karen hauka bane karen sonka ne ya cijeni" yaja tsaki ya girgiza kai sannan yace "matsamin nikam" haka ina kallonsa ya manna min hauka ya tafi.

Tuki nake yi a dai dai titin zaranda,go slow yayi yawa sakamakon gidan mai da aka kawo mai kuma ana wahalan mai,don haka kawai na tsaya jira a dan ragu, Aliyu na gani tsaye a bangaren titi agaban motarsa alamun ta tsaya masa, na fito da sauri na nufi gabansa, ina kokarin masa magana ya wurgo min wani harara da bansan da shi ba na tsaya ni kuwa ina kallonsa

" bace min anan" hararansa nayi ta gefen ido for the first time in my life naji babu tsoro araina nace masa " naki din" na lura batir din ce ke da matsala don haka na koma cikin lumana na bude tawa motan, na ciro ta abunda ban taba yi ba arayuwata duk da nauyin da nake ji baisa na je nakai masa ba na ajiye agaban motan tare da cewa " ciro na ciki kasa wannan" bai kulani ba nikuwa na daga batir din nazo zan cire na ciki wani wawan fizga naji yamun sannan ya wirgani gefen titi, fadi nayi don sai da hannuna yafitar da jini, wata mota ce ta tsaya agefen titin wani mutum dattijo fari sol bafulatani ya nufoni da sauri,

"Subhannalahi baka da hankali ne?"

dago ni yayi yana min sannu da jiki, kafata ta gagara mikewa sai kuka nakeyi don azaba, duk da babu alamun damuwa a fuskarsa amma akwai alamun tsoro a lamarinsa, yana gaida mutumin amma bai kulashi ba da tsawa yace " riketa mu sata mota , ashe baka da hankali ban saniba? mahaukacin inane kai?" suka jawoni suka sa ni a motan, yasa Aliyu ya rufo dukka motan shi kuma ya nufi asibiti dani, ahanya yace nakira wani danuwana nikuwa nakira yaaa kamal, a gigice yace gashinan zuwa dama yana kusa da asibitin.

Cikin minti goma aka wanke min gurjewan da nayi, sai likitan yace akira mai gyra kawai aja kafan don targade ne, anan nayi zuru zuru da ido alokacin yaa kamal ya isoshi duk ya rude, yana tambayan me ya faru?

Dan tsohon cikin takaici yace " kayi hakuri don Allah wani Da na ne ya bugeta, don Allah kuyi hakuri yanzu dai mai gyra zaa samo" yaa kamal yace " bakomi baba" juyawan da zaiyi yaga Aliyu abaya yana mikawa Tsohon key din motata, ya ce masa " me kuma ka zo yi anan? ko ka zo kasheta ne?" yadda yake maganan da tsantsan tsana shikuwa tsohon yana ta bawa yaa kamal hakuri

" Baba ba kasan abunda bawan Allahn nan ya ja mana ba, ya lalata mana dangi, ita kenan tilo kwaya daya mace, amma ta ruguza rayuwanta saboda shi" anan fa yabawa bawan Allah labarin haduwa a da Alliyu rasuwan mamy, wulakanci da yake min, barina kasan da duk wani abu dai, yana kai kuwa sai ga Fahad da fido a gigice sun iso, tarar da labarin wanda yaa kamal ke bayarwa fido ta fada musu abunda ya gigita su gaba daya nacewa ina shaye shaye kuma shima sanadin Aiyu, dogon salati sukayi gaba dayansu cike da mamaki, fido ta basu labarin wulakancin da nake sha wanda yaa kamal bai sani ba harda saka hijabai dana fara ma shima duk bata bar aya daya ba, tsohon nan yayi salati yayi salati cikin jimami yace " aikuwa naji dadin sanar dani da kukayi wannan bayanin, don kuwa daga nan babu inda na nufa sai gidan Hameed tofi wato mahaifinsa, kanina ne uwa daya uba daya kuma ni nan nace muku kuje ku kira min mahaifinta ma'ana wakilanta, na muku alkawari babu mahaluki da ya isa ya hana aurennan, in kunga baayi ba sai wani ikon Allah inma ni ko mahaifinsa mun mutu ko kuma shi Allah ya dauki ransa, ko kuma yarinya da bakinta tace batason auren, in babu ko daya toh wallahi za'a daura gobe, waye mahaifinta?"

yaa kamal cikin mamaki da bata barshi ba, mamakin jin ina shaye shaye yana jira a watse yaci ubana,yace "Ahmed Ahmed"

" tazo gidan sauki tunda na mishi farin sani yamin farin sani, bari ma nakirashi".24?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Ciro wayanshi yayi sannan ya jira , dukkan mu mamaki mukeyi can dai yace " Alh hameed kwana biyu dai yagarin?"

" oh Allah sarki don Allah kana gida ne?, zanzo ne yanzu da wata babban bukata"

"sai nazo"

haka kuwa ya kashe wayan sannan yace " kuje gida, nan da awa biyu mu zaku ganmu " binsa mukayi da kallo, Aliyu ma yabishi duk gumi ya fito masa, alamomin tashin hankali a tattare dashi,fido kuwa sai murna takeyi adole ita zanyi aure, nikuwa bazan san wani yanayi nake ciki ba, farin ciki ne ko meye? Allahu a'alam har muka shiga gida Abamama na zaune da abokinsa ya tarbeni yana min ya jiki alokacin yaa kamal yake mayar masa da abunda ya faru nikuma muka haura sama don na huta.

Muna zaune mukaji karan motocci muka leka aikuwa motocci muka gani, Suka shiga falo da babban riga, hankalina ya gagara kwanciya sai yawo nakeyi a daki na kasa zama guri daya, sunfi awa biyu duk na matsu su tafi musan me ake ciki, Addua ta Allah yasa Abamama ya yarda, gabana sai fadi yake, yanayin da nake ciki bansan ya zan misalta ba, suna tafiya nayi sauri na shiga toilet don gani nakeyi ba zasu yarda ba, hankalina ya tashi sosai sai addua nakeyi ko wanne yafito daga bakina, muryan Abamama naji yana cewa "ina autan take?" Hannu na rawa na bude kofan toilet din na fito sannan nace "ga-gani" murya na rawa nafito ahankali yajuya nikuma na bi bayansa, ganinsa nayi da yayuna duk sun nutsu a falon kowa sai bina yake da kallo, can gefe kuma buhun goro kwaya biyar da katon din chewing gum da buhun gishiri su kuma ban kirga nawa nawa ba, anan naji numfashina ya yi daidai koma meye na san Abamama yakarbi goron gaisuwa, na nemi gu a lungu sannan na zauna kaina akasa

" Da farko inaso ki sani, Duk abunda kikeyi, kikayi, kike kuma kanyi da ban saniba yau nasani, nagode da abunda kikayi min, kin tozarta ni agun jama'a tarbiyan da na baki kenan? kin zubar akan titi? saboda soyayya? akanki aka fara shi? toh insha Allah tazo gidan sauki" ya jefo min bandir din dari biyar guda hudu sannan yace " ga sadakin ki, ran jumaa insha Allah za'a daura aure, sannan ga wannan" ya miko min atm card,nasa hannu na karba ba tare da na duba naga nawani bank bane

" ki kai wa Ammi kuje kano gobe ku suyo kayan daki, akwai taron da Mammy ta dade tana miki, ita Ammin zata nuna miki, Allah ya shiryeki, ya kuma miki albarka, ya kareki, domin wannan aure na amince ne don nasan ko nace a'a ni zaki tozarta, kisani duk wulakanci da zaki fuskanta awannan gidan ke kika siya da kudinki, domin kuwa shi Aliyun ba yaso, iyayensa kadai ke so, a labarin da yazo min ma ance mahaifiyarsa tace danta bazai auri yar shaye shaye ba bansan yaushe kika fara shaye shaye ba amma kinga ance kinayi alhali ba kiyi" wani wawan yawu na hadiye gabana na fadi addua ta kar yaa kamal yayi subutan baki,

" toh kinga irin wannan wulakancin yanzu kika fara shanshi, zai wulakantaki zai koya miki darasi, sai dai duk abunda yamiki karki kuskura, Na maimaita miki karki kuskura ko da gigin hauka ki dawo min gida, bazan lamunci zawarci ba, tunda ke kikaji kuma kika gani"

Ni dai ko oho damuwata ta biya , bansan lokacin da naje na rungumo Abamama ba, idona cike da hawaye,

"nagode Abamama, nagode Abamama, i love you" Dukkansu sunyi mamaki sosai , yaa kamal kam juya kai yakeyi cikin bakin ciki

"Amma Abamama don Allah don annabi fisabilalah kasan gidan wahala zataje, wahala zatasha, anan fa nake gaya maka yace sai dai ta zauna da kanta shi baya sonta"

" kai kam banace ka daina mai da magana baya ba?" Abamama tsawa yayi masa tuni ya sunkuyar da kansa, nikuwa ko ajikina hankalina akwance na shige ciki fido na kan gado na fada kanta ina tsalle, can dai na sauko nayi sujjada, na daga hannu na gode wa Allah hawaye na bin idanuna amma ban damu ba nidai bukatata ta biya, insha Allahu ko Aliyu yana dukana yana marina ne zan yarda na aureshi, zan kuma zauna dashi, wayana na jawo naga messages guda biyu, daya Amrah daya Fahad Tayani murna yayi aciki sannan ya nuna bakin cikinsa na rasa ni yakuma ce, aduk lokacin da na shirya ko na fito na gaji da zama da Aliyu yana shirye da ya aureni, tsaki na ja tare da cewa oho dai duk kowa gani yakeyi kaman ba zan taba zama da Aliyu ba, ni kuwa nayi alkawari abunda zai sa na hakura da Aliyu babu shi a fadin duniya, rabuwa da Aliyu sai dai mutuwa ce ta daukeni. na Amrah kuma hakuri take bani akan abunda tamin sannan tace tana tayani murna na shigowa danginsu.

Washegari da sassafe Fahad ya kawo Ammi, Duk da abun ya bata mamaki atake ta nuna bata yarda ba, acewarta zanje na wulakanta ne na tozarta, Abamama ne ya jata suka shiga cikin falo bansan me yace mata ba suka fito na ga tana Allah sanya alheri, mota muka shiga muka wuce kano alokacin na fito da atm din na ga na first bank ne, Ammi tace in munje sai dai kawai mu basu atm su cire ta p.o.s haka kuwa mukayi, Nida fido agefe Ammi tana biye damu naje na zabi kayan daki duk abunda nakeso shi nake diba, sai mu basu atm su cire sai mutafi, mukayi bill akan za'a turo bauchi , tunda ga kayan kicin har kayan daki duk da ni bansan ya akayi Ammi tasan daki nawa bane cemin tayi sun ce mata daki uku ne falo biyu, haka mukayi siyayyan dukka muka sauka a hotel washgari muka dawo.

Duk tadin da nake muku ban saka Aliyu a idona ba kuma ban damu ba, tunda nasan ya zama nawa yanzu duk rikicinsa zai dawo hannuna,Allah sarki ni, su Ammi da su hajiyati da dai sauran yanuwan mammy duk sun cika gidan, yanuwan Abamama ma duk sun iso akan washegari zaa daura aure nikam nace ko walima ba zanyi ba, Allah Allah nake akaini, anje ammin jere, nikuma ina fama da mai dilka da take zanzarani, yayuna kaf dinsu sun dawo sun gwada min so kowa so yake ya faranta min duk da bawai suna son mijin bane amma ya zasuyi da ransu, aranan aka kawo kayan aure akwati set biyu, akwatuna takwas tabbas sun samin kaya alhamdulilah na godewa Allah,abu dai sai matsowa yakeyi, Ran jumaa da karfe goma na safe aka daura aurena da ALIYU, Ranar farin cikina, ranar cikar burina, Ranar alfaharina, Ranar farkon alherin rayuwata, rana da bazan manta ba, an aura min farin ciki na, hasken rayuwata, ruhina, abun bege na, abun kallo na, zuciyata, sanyin idaniyata sannan sunan na musamman da naga na dace na sanya masa wato CIWON IDANUNA25?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

A ranar na yarda cewa SO shine mahadi na rayuwa, Yayuna suka taso ni agaba kowanne jiki a sanyaye nikuwa ko ajikina,damuwata shine akaini gidan mijina, Yaa kamal ya zaunar dani yamin waazi haka Abamama dadu Hajiyati duk dauriyata sai da naji na karaya, anan nayi kuka sosai musamman dana tuna da Mammy Allah sarki Mammy na, Abamama yasa na masa alkawarin babu ruwana da kayan shaye shaye, yace natuna mammy ya za taji idan tana raye? nayi kuka sosai su Ammi ne suka sakani a mota da akazo diban amarya, ba laifi motocci sunzo iya zuwa, muna isa gidansu aka ware mana fanni daya kamar yadda aka saba da al'adan yan bauchi sai Amarya ta kwana a gidansu ango kafin washegari su wuce hakan ta kasance dani aka kaimu aka bamu sashi daya, Amrah ce ta shigo da wasu maaikata a bayanta suna rike da trays na snack wasu kuma drinks , ta gayshe da mu sannan ta ajiye har tana zolaya ina amaryan? su Fido ne agefena da Ammaty su Ammi kam tunda suka damkani suka tafi,

Wata mata tashigo da akwati a hannunta tace " gashi kayan da amarya zata saka, za'ayi dinner anjima" tana fita Fido ta ajiye agefe, suka gyra min bayan gida nayi wanka nayi sallah sannan na fara shiri haka yan kawayena da basu wuce guda biyar ba, mai kwalliya ma Amrah ce ta shigo da ita tamin kwalliya nasa gown din tasamin head da komi nasaka takalmi sannan muka fito tafiya multipurpose gun dinner, awaje aka bude min mota na shiga gefena Aliyu ne, yasha babban riga yayi kyau sosai Riganshi kalar rigata milk colour, kamshinshi ya cika motan sosai, Fahad ne yake jan motan, na ga kokarinsa da dauriyansa, nasan dannewa yakeyi amma yana cikin damuwa, shi dai yace mun ko shekara nawa ne zai zauna ya jirani,Fido na gefenshi suna yi suna zolayana, Amma tunda na shiga motan Aliyu bai gwada ko ajikinsa yasan akwai halittan mutum agefensa ba, nidai ko ajikina, atunanina shine tunda an daura aure anyi mai wuya, muka fito muka tsaya muna jira a sanar da zamu shiga alokacin ya juyo ya kalleni sama da kasa sannan yaja tsaki yajuya, oho dai oooo tunda ba yanda zakayi dani,gurin yasha ldecoration kam ba laifi ko ni kaina sai danaji dadi araina nishadi nakeji har muka shiga muka zauna a gun da aka tanadar na zaman mu, tuni masu daukan hoto, masu video kowa yayo caaa yana daukanmu don tsananin kyau da mukayi, Ba karamin alafahari bane ace mace irina ta mallaki Aliyu, mata da dama suna jira suka matarshi ikon Allah ganinan kuwa, toh Allah yasa gidanane, nidai nasan zan jura komi.

Dinner yayi dadi alhamdulilah duk da mutumina kam yaki murmushi ba yabo ba fallasa, Hajiyansa ma da tazo mana manni sai da tace "Hamma ina alkawarin da kamin?" tuni yahau murmushin dole, Amrah ma sai shige min take ba yadda na iya dole na sake raina da ita, ko da aka koma gida ta jawoni falo tace zata min magana anan tace " Nasan abubuwan da nayi bai dace ba, amma bazan gaji da baki hakuri akan ki yafeni ba, Aliyu na dai gaya miki bawai yanason wata bane, wacce Hajiya ta hadasu zahra ma yanzu magana ya lalace, ta kuma ja masa kunne akan ya faranta miki rai haka zalika ta haramta masa sakinki, tunda an daura aurenku duk wani abu mai sauki ne, kiyi hakuri da danuwana nasan kina masa SO na hakika, Ubangiji Allah ya barku tare, ya kade fitina, ya kareki daga sharrin yanmatan waje, mugun ji da mugun gani, magana ta biyu shine zan ce miki Aliyu danuwana ne kinga tare muka tashi idan kina so ki mallake shi ki san hannunki, maana girki, tsafta da ladabi wadannan abubuwa dasu zaki sayeshi" godiya na mata sosai, washegari akayi budan kai da yamma akayi hawa daredare aka kaini asalin gidana, mutane sun watse ina jira ango yazo, tun karfe sha biyu da naga bai shigo ba nacire raina, mikewa nayi na yi wanka nasaka rigan baccina ina shirin kwanciya naji ana buga kofa, da sauri na fita ta falon don ganin waye, ina bude kofan ya fado ajikina, warin giya yakeyi da sauri na toshe hancina ina kare masa kallo, na ja jikina a hankali na kwantar dashi zan mike ya jawo hannuna yana cewa "Zahraa, Zahraaa" wani bakin ciki ya gulloni amma haka na mike na jawoshi da kyar ina kokarin gyra mishi kwanciya kawai ji nayi ya kwararo min amai ajiki, ohh Ni nadrah anfara kenan! na cire riganshi na barshi da singlet nikuma na shiga na cire rigan na sanyo towel da katon hijab sannan nazo na goge masa jiki na feshe shi da turare, na tashi zantafi ya janyo hannuna haka na zauna agefenshi ina kallonshi yayita tikan baccinsa, haka nayi bacci azaune kiran sallahn farko ya farka ji kawai nayi an tunkudeni kasa na buge kaina ajikin centre table " Baki da hankali ko? wa ya baki izinin taba jikina? wa ya baki daman cire min kaya? kina da hankali kuwa? ke jahilar inane? kinsa ammin auren dole bai isheki ba zaki min fyade? mtswww doluwa kawai" yana gama fada yaja jikinsa ya tafi, wanka yaje yayi ina kallonsa yacire kayan yazo yaje ya zubar ashara acewarsa na taba shi kuma kyankyamina yakeji, Allah sarki ni Nadrah.26?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Wanka yayi yazo falo ya zauna, alokacin ni kuma na zaga gidan na gani dakyau masha Allah komi ya zauna dai dai, na shiga kitchen na soya chips, na soya kwai sannan na hado da kayan tea na jera akan dinning, na zo na durkusa agabansa nace " na gama breakfast, ko na kawo maka nan kaci?" idan inda Allah yayi halittan dutse toh haka Aliyu ya mayar dani, na mike jiki a sanyaye naje nayi wanka naci kwaliyyata don atamfa ta na saka riga da skirt ruwan goro nayi dauri sannan na feshe jikina da turare, na fito cikin mamaki na ganshi da indomie agabanshi yana ci ya hada tea, zama nazo nayi akasa agefensa nace " kayi hakuri ban san indomie kakeso ba na maka chips, gobe insha Allah zan gyra" nan ma bai kulani ba yana kallon bbc news dinsa, nima sai na zauna kawai a kasa ina wasa da yatsuna, haka kawai naji ya fara tsaki

" ke wacce irin wawiya ce? kin zo kin sakani agaba sai shakewa nakeyi na ci kudinki ne ban biya ki ba ko meye?" mikewa nayi tsum tsum na bar falon saboda kar ma ransa ya baci yace zai bar gurin.

Yan zuwa kallon gidan Amarya sai zuwa sukeyi akai akai, sa'a ta daya bai fita ba yamin kara , ko ince yabi umurnin mahaifinsa, sunzo sun gama ganin gida, Aliyu ba ruwansa dannewa yakeyi wani lokacin yake kulani agabansa nikuwa naji dadi ko ba komi bai tozarta ni ba, sati biyu ana zuwa ana tafiya, sai dai Aliyu bai taba cin abincina ba, ba yamin magana mai dadi in har yamin magana to fada zaimin, bai taba shigowa muhallita ba, balle yakiran nasa, dama ni bansa raina ba, tsanani yasiyo abinci yayi sallah ko ya dauki waya yayita waya wanda jikina yana bani da zahra yakeyi sai dai ban tabbatar ba, inaso rana daya na tabbatar da cewa ita ce dinne, sati biyun cif da safe na dafa indomie da tea na hada masa a dinnig yau kam na fara yin wanka ne saboda rashin mutunci da zan farayi , yayi na marmari yanzu zan fara masa hali na, tunda har ni matarsa ce ya zama dole akansa ya sauke hakkinsa na miji na ko ta wani fanni, balle na saba ganin matsifarsa don haka bana jin tsoronsa.

Da farkon fari daurin ture kiga tsiya nayi, daurin da wasu ke kira da na kilakai, na cikaro daurin gaban kaina na jera komi akan dinning yana zaune na zo na tsaya akanshi

"abincinka ya dahu" bai kulani ba, as usual dama nasani don haka na nemi gu na zauna, ganin banda niyyan tashi yasa ya mike zai shiga kitchen na bishi abaya, ya ce " matsamin" ganin na tare masa hanyan shiga, na rike kunkumina sannan nace " bazan matsa ba!!! nace maka bazan matsa ba! wallahi tallahi sai kaje kaci wancan abincin bazaka sani asara ba" mamaki ta cika a fuskarshi don idona har yayi jajur ya dauko hannu zai matsar dani wani kara nasaka masa da karfi nace " Kar ka kuskura ka tabani, wallahi kar ka fara!" juyawa yayi simi simi yaje ya zauna a dinning din yana kallon idona ina kallon nasa, ya bude ya fara ci , gabans fadi yakeyi domin kwakwaran tsawa yamin zan iya sake fitsari a wando, amma haka na danne na cije don yaga kalan hauka ta daban ne da nashi, yana ci kaman yana cin kashi nace masa " meye kaman kana shan magani?"

" babu, when last kikayi adduoinki?" wani dariya ne yakeson ya kufce min amma na daure, ohh kar dai yana tunanin ina da aljannu ne? ah lallaima to, sannunsa, ban amsashi ba sai da ya gama ci na tattare gun sannan na koma falon na zauna, ganin ban kula sa ba yasa ya ci gaba da kallonsa a nutse, daki naje na kira Amrah,

" yayanki na tsoron aljannu ne?"

dariya tayi sosai sannan tace " da aljannu da mage baya son su ko kadan" na mata godiya na kashe wayata, nakira fido nace inason mage ta kawomin yau don Allah, duk da tayi mamaki don tasan banaso amma tace toh , dawowata falon naji yana waya, baza kunnuwa ta nayi don jin me zai fada,

" haba zahrah ki bari gobe zanzo" wato jin zahra da nayi mikewan da zanyi nayi kansa na kufce wayan na wurgata a kasan tiles ji kakeyi taaaaass akasa, a harzuge ya miko yakai hannunsa kaman zai dakeni ni kuwa na zura masa ido don babu alamun tsoro araina, ya kamo kaina sai da dankwali na yacire gashin kaina ya tamko idonshi kaman zai fadi , ya zaro su

" waya baki izinin taba min waya, ke wawiyar wacce gari ne?"

" Wawiyar ka ce ni, haka kawai ina matar ka ta sunna zaka zo kana waya da wata agabana, akan meye toh? wallahi tallahi sau dubu kayi waya agabana sau dubu zan fasa" wurgani kasa yayi da karfi yaja tsaki ya shiga dakinsa sai gashi ya fito da kwalba , salati nakeyi araina ina kallonsa ya bude ya kwankwada yasha, yana sha yans kallo, ina takure agefen kujeran falon wani hawayen bakin ciki ya fara zubo min, nashiga uku na Aliyu, ai kuwa ban idda tunani na ba naganshi akaina, finciko ni yayi yana shinshina gashin kaina kaman kare, nayi nayi na kwace kaina amma fuzgata yayi yana kokarin yaga min riga, banda mai ceto na awajen, abun bakin ciki abun takaici, mijina na sunna ya keta min haddi a yanayin maye, ya sanni a ya mace acikin maye, baya hayyacinsa, bai ragar min ba ko kadan ,haka yabarni agun ya juya yayi baccinsa, nayi kukan bakin ciki kaman raina zai fita, idona ya kumbura sosai amma ya zanyi da raina, nace naji na gani zan iya, ban isa nace bazan iyaba. Kafin ya farka na lallaba rayuwata naje na kimtsa kaina na rufo kofan dakin don karma na ganshi , ban fito ba sai dare alokacin yana kallo ko ajikinsa bai nuna yasa akwai abunda ya faru ba, duk da dingishi da nakeyi na wahala. Sabuwar waya na gani a hannunsa, wato har yaje yasiyo sabuwa, toh ni kuwa bazan gaji da fasawa ba.

Rayuwa ta ci gaba da tafiya min, duk wata ya mace da tayi aure tana yin haske tayi kyau tayi fari tayi jiki, ni kuwa na rame nayi baki, gashi makaranta ma munkusa komawa hutu duk da strike akeyi, Fido ta kawo min mage alokacin da ta kawo yasa mai gadi ya fita dashi, in inaso yaci abincina rikice masa nakeyi kaman mai aljannu in bahaka ba sai dai nayi asara, shaye shaye kuwa sai dai bai dawo daga aiki ba, dama Babansa ya nema masa transfer zuwa nan, idan yaje yagama ganin patients yadawo sai kuma yahau shaye shaye dama shi hes not a fan of friends, shi kadai yake rayuwansa, in kuma yayi shaye shaye toh ranan inada tabbacin zan kwana cikin kunci domin kuwa fyade yake min, in yana hankalinsa yayita kyankyamina in baya hankalinsa kuma kaman ya cinyeni ya rinka sumbatu kenan, shi kenan na dawo inji , ahaka na gano inada ciki daga laulayin da na fara, na yanke shawaran sanar masa, da sharadin zan zubar wato ranan sai da na gwammaci kida da karatu domin kuwa gwadamin yayi zai iya hallakani idan na zubar da cikinnan

"burin hajiyata ta samu jika, don haka dole ki haifa"

bansan lokacin dana mayar masa da magana ba nake ce masa " Sau dubu kasha giya na gani , sau dubu zan zubar da cikinka sai dai kasa iqwa ka kasheni bayan biyayyen auren da na nuna maka, iskanci kala kala yau da na kwana da kai gwara na kwana da kare" wani wawan mari ya saukemin wallahi sai da naga wuta a fuskata, kafin na karasa dagowa ya kuma sakemim wata marin.26?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Wanka yayi yazo falo ya zauna, alokacin ni kuma na zaga gidan na gani dakyau masha Allah komi ya zauna dai dai, na shiga kitchen na soya chips, na soya kwai sannan na hado da kayan tea na jera akan dinning, na zo na durkusa agabansa nace " na gama breakfast, ko na kawo maka nan kaci?" idan inda Allah yayi halittan dutse toh haka Aliyu ya mayar dani, na mike jiki a sanyaye naje nayi wanka naci kwaliyyata don atamfa ta na saka riga da skirt ruwan goro nayi dauri sannan na feshe jikina da turare, na fito cikin mamaki na ganshi da indomie agabanshi yana ci ya hada tea, zama nazo nayi akasa agefensa nace " kayi hakuri ban san indomie kakeso ba na maka chips, gobe insha Allah zan gyra" nan ma bai kulani ba yana kallon bbc news dinsa, nima sai na zauna kawai a kasa ina wasa da yatsuna, haka kawai naji ya fara tsaki

" ke wacce irin wawiya ce? kin zo kin sakani agaba sai shakewa nakeyi na ci kudinki ne ban biya ki ba ko meye?" mikewa nayi tsum tsum na bar falon saboda kar ma ransa ya baci yace zai bar gurin.

Yan zuwa kallon gidan Amarya sai zuwa sukeyi akai akai, sa'a ta daya bai fita ba yamin kara , ko ince yabi umurnin mahaifinsa, sunzo sun gama ganin gida, Aliyu ba ruwansa dannewa yakeyi wani lokacin yake kulani agabansa nikuwa naji dadi ko ba komi bai tozarta ni ba, sati biyu ana zuwa ana tafiya, sai dai Aliyu bai taba cin abincina ba, ba yamin magana mai dadi in har yamin magana to fada zaimin, bai taba shigowa muhallita ba, balle yakiran nasa, dama ni bansa raina ba, tsanani yasiyo abinci yayi sallah ko ya dauki waya yayita waya wanda jikina yana bani da zahra yakeyi sai dai ban tabbatar ba, inaso rana daya na tabbatar da cewa ita ce dinne, sati biyun cif da safe na dafa indomie da tea na hada masa a dinnig yau kam na fara yin wanka ne saboda rashin mutunci da zan farayi , yayi na marmari yanzu zan fara masa hali na, tunda har ni matarsa ce ya zama dole akansa ya sauke hakkinsa na miji na ko ta wani fanni, balle na saba ganin matsifarsa don haka bana jin tsoronsa.

Da farkon fari daurin ture kiga tsiya nayi, daurin da wasu ke kira da na kilakai, na cikaro daurin gaban kaina na jera komi akan dinning yana zaune na zo na tsaya akanshi

"abincinka ya dahu" bai kulani ba, as usual dama nasani don haka na nemi gu na zauna, ganin banda niyyan tashi yasa ya mike zai shiga kitchen na bishi abaya, ya ce " matsamin" ganin na tare masa hanyan shiga, na rike kunkumina sannan nace " bazan matsa ba!!! nace maka bazan matsa ba! wallahi tallahi sai kaje kaci wancan abincin bazaka sani asara ba" mamaki ta cika a fuskarshi don idona har yayi jajur ya dauko hannu zai matsar dani wani kara nasaka masa da karfi nace " Kar ka kuskura ka tabani, wallahi kar ka fara!" juyawa yayi simi simi yaje ya zauna a dinning din yana kallon idona ina kallon nasa, ya bude ya fara ci , gabans fadi yakeyi domin kwakwaran tsawa yamin zan iya sake fitsari a wando, amma haka na danne na cije don yaga kalan hauka ta daban ne da nashi, yana ci kaman yana cin kashi nace masa " meye kaman kana shan magani?"

" babu, when last kikayi adduoinki?" wani dariya ne yakeson ya kufce min amma na daure, ohh kar dai yana tunanin ina da aljannu ne? ah lallaima to, sannunsa, ban amsashi ba sai da ya gama ci na tattare gun sannan na koma falon na zauna, ganin ban kula sa ba yasa ya ci gaba da kallonsa a nutse, daki naje na kira Amrah,

" yayanki na tsoron aljannu ne?"

dariya tayi sosai sannan tace " da aljannu da mage baya son su ko kadan" na mata godiya na kashe wayata, nakira fido nace inason mage ta kawomin yau don Allah, duk da tayi mamaki don tasan banaso amma tace toh , dawowata falon naji yana waya, baza kunnuwa ta nayi don jin me zai fada,

" haba zahrah ki bari gobe zanzo" wato jin zahra da nayi mikewan da zanyi nayi kansa na kufce wayan na wurgata a kasan tiles ji kakeyi taaaaass akasa, a harzuge ya miko yakai hannunsa kaman zai dakeni ni kuwa na zura masa ido don babu alamun tsoro araina, ya kamo kaina sai da dankwali na yacire gashin kaina ya tamko idonshi kaman zai fadi , ya zaro su

" waya baki izinin taba min waya, ke wawiyar wacce gari ne?"

" Wawiyar ka ce ni, haka kawai ina matar ka ta sunna zaka zo kana waya da wata agabana, akan meye toh? wallahi tallahi sau dubu kayi waya agabana sau dubu zan fasa" wurgani kasa yayi da karfi yaja tsaki ya shiga dakinsa sai gashi ya fito da kwalba , salati nakeyi araina ina kallonsa ya bude ya kwankwada yasha, yana sha yans kallo, ina takure agefen kujeran falon wani hawayen bakin ciki ya fara zubo min, nashiga uku na Aliyu, ai kuwa ban idda tunani na ba naganshi akaina, finciko ni yayi yana shinshina gashin kaina kaman kare, nayi nayi na kwace kaina amma fuzgata yayi yana kokarin yaga min riga, banda mai ceto na awajen, abun bakin ciki abun takaici, mijina na sunna ya keta min haddi a yanayin maye, ya sanni a ya mace acikin maye, baya hayyacinsa, bai ragar min ba ko kadan ,haka yabarni agun ya juya yayi baccinsa, nayi kukan bakin ciki kaman raina zai fita, idona ya kumbura sosai amma ya zanyi da raina, nace naji na gani zan iya, ban isa nace bazan iyaba. Kafin ya farka na lallaba rayuwata naje na kimtsa kaina na rufo kofan dakin don karma na ganshi , ban fito ba sai dare alokacin yana kallo ko ajikinsa bai nuna yasa akwai abunda ya faru ba, duk da dingishi da nakeyi na wahala. Sabuwar waya na gani a hannunsa, wato har yaje yasiyo sabuwa, toh ni kuwa bazan gaji da fasawa ba.

Rayuwa ta ci gaba da tafiya min, duk wata ya mace da tayi aure tana yin haske tayi kyau tayi fari tayi jiki, ni kuwa na rame nayi baki, gashi makaranta ma munkusa komawa hutu duk da strike akeyi, Fido ta kawo min mage alokacin da ta kawo yasa mai gadi ya fita dashi, in inaso yaci abincina rikice masa nakeyi kaman mai aljannu in bahaka ba sai dai nayi asara, shaye shaye kuwa sai dai bai dawo daga aiki ba, dama Babansa ya nema masa transfer zuwa nan, idan yaje yagama ganin patients yadawo sai kuma yahau shaye shaye dama shi hes not a fan of friends, shi kadai yake rayuwansa, in kuma yayi shaye shaye toh ranan inada tabbacin zan kwana cikin kunci domin kuwa fyade yake min, in yana hankalinsa yayita kyankyamina in baya hankalinsa kuma kaman ya cinyeni ya rinka sumbatu kenan, shi kenan na dawo inji , ahaka na gano inada ciki daga laulayin da na fara, na yanke shawaran sanar masa, da sharadin zan zubar wato ranan sai da na gwammaci kida da karatu domin kuwa gwadamin yayi zai iya hallakani idan na zubar da cikinnan

"burin hajiyata ta samu jika, don haka dole ki haifa"

bansan lokacin dana mayar masa da magana ba nake ce masa " Sau dubu kasha giya na gani , sau dubu zan zubar da cikinka sai dai kasa iqwa ka kasheni bayan biyayyen auren da na nuna maka, iskanci kala kala yau da na kwana da kai gwara na kwana da kare" wani wawan mari ya saukemin wallahi sai da naga wuta a fuskata, kafin na karasa dagowa ya kuma sakemim wata marin.


27

Na riko gefen kumatu na sannan nayi murmushi nace " ai kayi babban kuskure, da ka kuskura ka taba min jiki" shigewa ta daki na dauki waya na kira hajiyansa ina kuka, hankalinta ya tashi sosai take tambaya ta meya faru nikuwa dama abunda nake jira kenan " Hajiya Hamma ya tsaneni, marina yayi don yace na zubar da cikina naki yarda, yakawo min magani wai sai na sha" salati ta doka, ta sanarwa ubagiji sannan tace ga ta nan zuwa, nayi hakuri, dama haka nake jira don haka na ci gaba da ukan zafin marina saboda kar idona ya washe, gogan kuwa yana dakinsa can bai san me nake kulla masa ba, kararrawa naji don haka da sauri na langwabe akan gado, shi yaje ya bude mata kofan inaji tana tsigaleshi har suka iso dakin, yana kokarin mata bayani tace ya rufa mata baki kafin ta gwabjeshi, tazo kan gadon aikuwa ga idona ya kumbura, juyawan da zata yi ta fara masa fada kaman zata masa duka, nikam shiru kawai nayi daga gefe ina dariyan mugunta, tana gamawa ta lallabani taban hakuri sannan ta fice ta tafi, wato da ya rufo kofan gidan ya zo dakin kunnena ya jawo,

" baki da hankali ko ke mahaukaciyan inane? ni zaki yiwa sharri? yaushe muka fara wannan wasan dake?" nikuwa sai cewa nake " wayyo kunnena, don Allah ka sakeni" sai da ya mikoni falo sannan ya wurgani, ina kallonsa yayi matsifarsa ya gama ni kuwa ko ajikina damuwata ya sake min kunne, amma yadda yake murdawa ji nake kaman kunnen zai fita, munfi minti ashirin ahaka nikam har bacci ya fara kwasata ma ahaka, ficewa yayi ya dauko giyansa yana sha, duk da cewa na saba dan guntun nawa shaye shayen kafin na aureshi ba karamin dannewa nakeyi ba idan naga yanayi, su yaa kamal ma basu zauna ba gun sawa amin saukan qurani da adduoi, ina gani ya na sha bakin ciki kaman ya kasheni amma na mike na bar masa falon, asalin babban falon gidan na wuce na zauna ina tunanin duniya da rayuwata, duk da nasan auren so aka min amma shi kam Aliyu sai dai yace auren dole, kiyayyar da yake min da ya ragu sosai ba kadan ba, ada baya shayin yimin mugunta amma yanzu naga ya daina, akwai abubuwa da dama da yakan gani kuma ya kawar da kuuwa sai nasha zagi da matsifa, bankade kofan na ga yayi gabana yana fadi na tashi na fara laluman hanyan barin falon, domin nasan sauran idan har ban matsa ba aikuwa rikoni yayi ina kokarin kubcewa ya dankoni yana fisgana yayi dakinshi da ni, aikuwa nasan tawa ta kare, ranan muguntan ranan daban ne, nayi kuka daman in da sabo na saba da wannan wulakancin.

A boye na fara shan magunguna don zubar da cikin dake jikina, zan zubar ba don bana son haihuwa dashi ba sai don inason ya daina shaye shayensa tunda naga yana son abunda na haifa, randa ya fara kamani da magani a daki ne, na kurba kenan ya shigo dakin cikin maye, rikoni ya farayi ina kaucewa, wani mari ya sakarmin ya wurgani kan gado,

" maganin me kike sha?" kallonsa na tsaya yi, yayi balain yin kyau, tshirt da jeans ne ajikinsa gashin kansa ta kwanta luf luf, ji nayi kaman na rungumosa, wani mari da ya sakarmin yasani na dawo daga tunanin da nakeyi, na rike fuskata ina kallonsa cikin rashin damuwa,

" meye kike kallona kaman mayya?, cikin nawa zaki zubar, ba nace kar ki zubar ba? akan me yasa zaki ce sai kin zubar?"

" ta yaya zaka ce na raini cikin da ubansa ba yaso? kana wulakanta ni kullum akan me zan haifa maka, na gaya maka fa wallahi bazan haifi da ina faman wulakanta agidannan ba"

tsaki yaja ya fice, ranar har dare bai dawo gida ba kuma nasan baya asibiti don ranar ba dutynsa bane, na fara gigin bacci naji motsinsa a falo ina lekowa na ga abun mamaki, zahra ce ta shigo dashi yana cikin maye, wani kullin bakin ciki ya tokareni ina kallon su yana shashimanta, ita kuwa tana kokarin shigowa dashi, wasu hawayen bakin ciki suka fito min na fito falon don ganin ikon Allah, tana ganina mun hada ido amma naga ta cigaba da janshi da ya zauna tana kokarin cire masa rigan shi don ajike yake, dasauri nace " malama lafiya?"

wani harara ta sakarmin ta cigaba da abunda takeyi , fizge shi nayi a hannunta ina kokarin mayar masa da rigan domin banga dalilin da zaisa wata tazo ta cirewa mijina na sunna kayan jikinsa ba, ganin haka yasa ta koma kan kafansa tana kokarin cire mai takalmi na juyo rike da kunkumi sannan nace " ki tattara ki tafi, nagode zan karasa sauran" wani harara ta doka min sannan tacigaba nikuwa na cire hannunta da karfi kafin nace mai ta kai min mari a fuska, idan da sabon mari na saba dana mijina amma karyan wata mace ko wani halitta a duniya mijina ya maren kema ki maren agun wannan raini ne babba, ba tare da tunani ba na dau hannuna na saita a fuskanta na zuba mata kwaya biyu dama bakin cikinta na shirin kasheni a gidannan, taki rabuwa min da miji, ko kawa muka farayi , wato da ta saita cikina ta ringa gulli ina ihu shi kuwa yana kokarin tashi ya rabamu amma ina jini ne yabiyo ta kafafuna ihun da na karayi da karfi sai da ya shigo da maigadin gidan

" innalilahi wainnailaihirajiun"


28

Salatin da yakeyi yasa Aliyu ya mike ya rabamu, dakyar zahra ta bar gidan nikuwa aka nufa asibiti dani, aikuwa suka bani labarin ciki ya zube, ko ajikina Allah ne ya kawo min sauki sai dai radadin zuci bai barni ba, hajiya kuwa da ta saka Aliyu agaba kaman ta kasheshi dan bakin ciki, anmin wankin ciki sannan aka sallameni bayan kwana biyar lokacin na warke sosai, Ammi da fido sai zirga zirga sukeyi akaina, ga yaa kamal ma da yaa usman sukam tausayi nake basu, acewarsu nayi baki na rame na lalace kaman bani ba, dama nikam nasan rayuwata ta dade da lalacewa.

Na fito daga daki zan shiga falo naji Hajiya tana yiwa Aliyu fada

" ina kara jadadda maka, wallahi zaka yi nadama a rayuwanka, a zamanin yanzu ka samu mace mai sonka don Allah wannan yanayi da wuya, kai baka tausayinta ne, dama bazaka taba sanin amfanin abu ba sai babu shi, wata rana zakayi kuka da idanunka, zakayi nadama sannan zaka zo ka fadamun cewa lallai Nadrah matar zama ce" hawayen dake makale agefen idona suka karaso nikuwa me zanyi inba kukan ba,

" ka fada mun me take maka da baka so? ayau inna kirata na fada mata zata daina!?"

" Babu, kawai bana sonta ne"

"shikenan sai ka kasheta tunda baka sonta, mahaukacin banza mahaukacin wofi" ina ji tafice ta bar masa falon, ni kuma na koma daki da sauri domin kar yazo ya samen.

Rayuwa ta ci gaba da tafiya yayinda ciwon jikina yaci gaba da girma ni bansaniba, sai dai daukewan numfashi lokaci lokaci musamman idan raina ya baci wanda dama bacin rai na aura kullum ina cikinsa, wani lokacin hakarkarina ko cikina zai kumbura duk da magungunan da nake sha, ga high blood pressure, gashi ko shara nayi zanyi saurin gajiya, amma duk wannan damuwan da nake ciki ba ruwan Aliyu aduk lokacin da bukatunsa ta tashi kaina yake yi, ranan da na fara ki kam ma igiya ya janyo ya daureni yayi abunda zaiyi yafice ya barni, ranan na yi kukan da bantaba yi ba washegari idona a kumbure har bana iya gani, tsantsan tsana yake gwada min tunda nayi fada da zahra, ga shaye shaye sai abunda ya karu, kar kuji haushi na amma duk wannan abun da yakeyi ban taba nadama daidai da rana daya in daina sonshi ba ko na rabu dashi, na lalace har bana son fita makaranta kam ma ajiyewa nayi agefe bansan stand dina ba, yayuna insun kiran awaya haka nake cewa bana gari sai ince muntafi abuja da Aliyu saboda kar suzo suga halin da nake ciki, ahaka na dauki ciki wannan karon banda karfi balle na ce zan zubar duk da cikin yana wahalar dani amma haka ma danne don Aliyu ya gwadamin cewa Hajiyarsa na son jika , imagine bashi yakeso ba fa, Hajiyarsa ke so ,na raini ciki har haihuwa na haifi Ya mace, aduk wannan lokacin Aliyu bai ragarmin cin mutunci ba, nikuma ban daina masa duk biyayyan auren da duk wata ya mace takeyi wa mijinta, abinci , gyra kai duk wani abunda macen so takeyi inayi , bai taba yabawa ba, sai dai ya kushe bai taba nuna jin dadi ba amma haka nake fama dashi , Ran suna Akasa wa yarinya suna Fatima amma muna kiranta Junainah, naga mutane kam sai dai nasha mita kowa cewa yakeyi na rame nayi baki na lalace, nayi tunanin albarkacin haihuwar da nayi Aliyu zai dubeni ya mutunta ni amma ina Aliyu yayi gaba kuma.

HAMMA ALIYU.

Haihuwar da tayi yasa aka kawo ugonzoma wacce zata tayata zama, ya zama dole nasan inda dare yamin don bazan so na yi agabanta ba balle ta fadawa hajiyata, ban iya zina ba ban kuma taba yiba, duk da Nadrah tana tunanin inayi da zahra, zahra duk kokarinta na in biye mata banyi ba, akan Nadrah na fara sanin wacece mace shima alokacin maye, maganan gaskiya bana son Nadrah ban taba sonta ba, kuma bana jin akwai ranan da zan sota, kullum idan nafita asibiti bana dawowa da wuri wani lokacin ma sai sunyi bacci, ko zanyi shaye shaye na ma ba nayi agida balle akai report wa hajiya,

RANAR NADAMA****

Ranar da nayi nadama shine ranan da Nadrah suka cika kwana ashirin da hudu da Junainah, ta kawomin ruwan wanka alokacin na dan yi shaye shaye na, bai gama sakeni ina kallonta ta juye ruwan, dogon riga ne ajikinta ta tumbuke gashin kanta ya kwanta luf luf, ta juyo zata fita navrufe kofan, idonta narai narai tace " kayi hakuri nasan abunda zakayi ina jego, kayi hakuri na gama duk abunda zakayi sai kayi" janyo ta nayi da karfi ita kuwa tana kokarin faucewa tana bani hakuri. wurgata nayi kan gado nabi sahunta tana kokarin guduwa gashi banga igiyan da na saba daureta dashi ba, wani wawan mari na sakar mata bataji ba saboda in da sabo ta saba da marin da nake mata kullum na janyota na tura mata yadin riga na abakinta don kar tayi ihu ajita duk da kokarin guduwa da takeyi wannan karon wani duka da naushi nakai mata sai da na mata lukwis tun tana kokarin faucewa harta nutsu, hawaye kawai ke bin idanunta, na mike bayan na gama abunda zanyi har na shiga wanka na fito bata motsa agun ba

" ki tashi ki bar min daki" shiru naji bata motsa ba nayi kanta na tokareta da kafa nan ma bata motsa ba, na sa kaina akirjinta naji bata motsi,

" innalilahi wainna ilaihi rajiun" jan ta nayi da karfi na bude kofan na kira inna wacce ta fito a gigice don jin yadda nake kiranta

" inna ta mutu, inna nemo ruwa" arude ta debo ruwa tazo ta yayyafa tana salati a gigice amma Nadrah bata motsa ba,

" kai ba likita bane? ka duba mana meke damunta?"

alokacin ina zan san me nakeyi, awh ashe ni likita ne, na sa kaina a kirjinta na shiru, hannuna awuyanta nanma shiru, idonta da na bude ya kafe, i just dont want to believe it amma nasan Nadrah babu ita, da karfi nake danna kirjinta

" Nadrah ki tashi! wallahi na dauna kuntata miki"


29

A gigice na dauke ta na fito na saka ta a mota ban nufi ko ina ba sai reemee clinic domin shine asibiti mafi kusa atare damu, suka shigar da ita sai dai ko minti biyar basuyi ba suka fita, likitan yafito yana bani hakuri, don nasanshi yakan duba Nadrahn idan taje check up,damko shi nayi da karfi idona jajur na ce masa " me ya sameta? hope ta samu sauki?" ya girgiza kai yace " kasan asali tana da congenital heart defect its fortunate yanzu ta rasu of heart failure, kai kasan irin wannan conditions din and what she has gone true" a hankali na sulale jikina nayi kasa , tunda hajiya ta haifeni ban taba ganin tashin hankali tsantsa irin na wannan lokacin, Fahad ne yashigo da gudu fido na biye abayansa, ganin yadda nake suka gigice suma, idona yayi jajur ya kafe, kaina ya daina aiki balle yayi tunani, haka na shiga na na zura mata ido alokacin suka rufeta, kasa motsi nayi daga gun sai ga kamal yazo, hada ido muka yi dashi ya sa hannu ya maujeni da karfinsa kaman wanda muke filin boxing, jini ne yafito daga bakina kafin nayi wani tunani ya hadani da bango sai duka yakeyi hawaye na bin idonshi, Fahad ne yazo ya raba da kyar yana ce masa " baka da hankali ne? in kaji masa ciwo fa?"

" ni daya kashemin kanwa? wallahi kotu ce zata raba mu da kai" kiri kiri ina gani kamal yakira yan sanda yace su rabani dasu kar naje kusa da gawan, ni da matata hmm, munkoma gidansu duk da ni abaya nake binsu gida yacika makil harda su hajiya na dasu Amrah, Ammi, Amir, usman , yusuf da dai sauran mutane kowa ya hallaru an taru wanda yaban mamaki, gashi inna ta taho da junainah a hannunta wacce sai kukan yunwa takeyi sai ruwa suke dan bata amma ina yadda take tsala kukan har kasan kirjina nake jin kukan, ina makale agefe Abamama ya shigo da motarsa ya taho ahankali falon aka babbashi waje, ya tsuguna agaban gawan shi baiyi magana ba shi bai tashiba anan na tabbatar da kuka yakeyi ta kasa, mamaki yacika su gaba daya hatta Hajiyati sai da ta sa baki "Alhaji ina dauriyanka? ko da Mammy ta rasu bakayi kuka ba don Allah kayi hakuri" yana sheshekan kuka akasa yace " bakin cikina daya shine Nadrah ta tafi tabbas ni na kashe yata tunda ni nakaita gidan ajalinta" kowa dai jikinsa yayi sanyi barin ma ni dana dawo abun kallo, a tsakure a gefe idona kaman zai fadi don yaji, Abamama yace zaa mata wanka an daga ta ankaita daki guda aka ajiye akan washegari zaa kai ta masaukinta, hajiya ce takirani awaya " kana ina? kazo gida ka samen" tana fada ta kashe wayan, ni kuwa jiki a mace na karasa gidan tun daga gun masu gadi naga gidan aciki haka na haura har gun hajiya dama Alhaji baya nan amma adaren zai dawo zai bi jirgi, tana kan sallaya hawaye ke bin idonta na tsuguna agefe sannan na jirata, ta tofa adduanta tayi sheshekan kukanta sannan tace

" Aliyu, ban taba nadaman haihuwarka ba sai yau, ashe baka da imani? kasan kuwa kai ka kasheta? ko ka zata bazamu sani bane? likitan ya fadi komi! kar kayi tunanin zaka buya abayan ciwon dake damunta, haka kawai zuciyar mutum zai buga ne? dole akwai dalili, kuma likita ya fada mana daga binciken da yayi ,Aliyu yakakeso muyi dakai don Allah don annabi, Aliyu nikam na yafeka a yayana wallahi, bazan iyaba, ka dake ta bai isheka ba, ka mata fyade bai isheka ba, yanzu tana jegon ma bata tsira ba habawa kai wani irin dabba ne? nayi nadaman haihuwanka Aliyu, zaka ga sakayya in dai Nadrah ce, ga yarinyannan ta soka, ban jin na taba ganin mutum da akaso kaman haka, ga duk abunda kake mata shanyewa takeyi bata fada, ta juri wulkancinka,Allah zai sakamata kajira wannan, sannan yarta daka cuta ka mayar marainiya itama kashirya karban hakkinta agun Allah, haba Aliyu, Haba Aliyu" tana fada tana kuka kaman ranta zai fita, jikina a sanyaye kaina akasa na kasa magana na nufi dakina na gidan, rufo kofan nayi na zauna, idona dai gashi akafe, yayi jajur amma na kasa saita tunani na, wani nauyi nakeji a kirjina kaman zai fadi, duk wani addua dana sani yinshi nakeyi, Innalilahi Nadrah, nadrah ki yafemun yadda naga rana haka naga dare, da asuba na kwara ruwa na nufi masallaci sannan naje gidansu, ina zaune sai adduoi nakeyi, kamal in ya ganni ji yakeyi kaman ya kasheni Abamama ne ya hanashi , an mata wanka aka kirani na mata addua, ahankali na zauna agabanta ina kallonta tayi fari tayi kyau sosai, fuskanta har alamun murmushi yakeyi, jikina na bari kirjina yana bugawa, nayi adduan har da na shiga bayan gida inaga sai danayi don gigicewa, ina kuka nace Nadrah ki yafeni, ki yafeni, kiyi hakuri Nadrah, na miki alkawarin zan so Junainah fiyeda yadda kika so ni, Na-Na-Nadrah kiyi hakuri, inayi ina sheshekan kuka, sai alokacin hawaye suka zubo kaman ruwan famfo, innalilahi wainna ilaihi rajiun, ina gani aka dauketa mukaje kaita masaukinta, ni na rufe ta muka fito amota hawaye sai zuba sukeyi.30?? CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Kamal ya so ya kaini kotu, Abamama ne ya hana shi acewarshi ko albarkacin junainah kar ya tozarta ni, ni kuwa duk a tsarge nake gani nakeyi duniya na kallona a matsayin mai kisan kai, Wanda tun daga ranan nayi Nadaman shaye shaye, lallai tur da wannan halin zai kai ka ga aikata babban kuskuren da tunaninsa kadai zai iya saka ka hallaka, kullum ina zaune inbanda wanka bana iya komi sai addua wa Nadrah, amma bashi zaisa yanuwanta suji tausayina ba, kowa ya tsaneni na tabbata da za'a basu wuka ace su kasheni da sun aikata mummunan kisa, domin kuwa kaca kaca zasuyi dani.

Zahrah kuwa gani takeyi dama ta sameta tuni ta cigaba da shigemin zai zarya takeyi agidan Hajiya, Hajiya kuwa tausayinta takeji bata kuma taka mata birki acewarta kar na kuskura na wulakanta ta yadda nayiwa Nadrah, ban tsaneta ba sannan kuma bawai ina sonta can can bane, sai dai abunda na lura da ita shine ita sha'awata takeji ba sona takeyi ba, babu soyayya sai zallan shaawa nayi tunanin hakanne ganin yadda take makalemin ko yaushe, da wasu abubuwa da take min wanda ni nake kawar da kai, Ammi ce ta karbi junainah tuni ta aka bawa Ammaty ta fara shayar da ita da izinina wacce alokacin itama tana da Da haka mijinta ya Amince , tabbas tayi jarumta acikin kawayen Nadrah ita zara, ni kuwa tsananin soyayya da tausayin Nadrah nakeji yasa ko yaushe ina hanyan gidan sai nasa akawota, na rinka saye saye kenan.

BAYAN SHEKARA BIYU.

Tun rasuwan Nadrah hankalina ya tattaru yakoma kan aiki na, asalima U.S naje na karo wani course wanda aka turani, dawowa ta kenan Junainah ta koma yan'mata na samu har tafiya takeyi, don ta koma gun Ammi, tasan Ammi kuma itace mahaifiyarta don haka take gani, randa ta ganni ta kalleni kaman bakon ta, sai da naji gabana ya fadi domin kuwa tsantsan kammanin Nadrah na gani a fuskanta, hakan yasa ta tuno da ita, an barni da ita adaki tuni tasa kuka kaman taga dodo har tana shidewa, na mike a gigice na rikota nan ma ta fara kuka wallahi kaman zan kasheta da sauri fido ta shigo ta karbeta, abun duniya ya dameni ga wani jarababben sonta da radadin sonta da nakeji, haka suka dauketa inaji ina gani, tun daga ranan idan naje bana iya ganinta, in ta ganni kaman zan kasheta haka take kuka tun abun baya damun su har su ka fara damuwa sosai, nima abun ya fara damuna duk yadda na so shige mata bana iyawa domin gudu na takeyi, gashi zan siyo mata tarkace na yara in wani ya bata zata karba nikuma inna bata bata so, ban tashi nadama da tashin hankali ba sai da hajiya ta kirani na nutsu agabanta sosai sannan tafara " aurenka da Nadrah ka ki ta, ka tsaneta ka kuntata wa baiwar Allah har kayi sanadinta, toh yau gani gaka Allah ne shaida ta, a matsayina na wacce na tsuguna na haifeka zan aura maka zahrah, idan ka aureta ka kuntata mata ban yafe maka ba, idan ka bata mata rai ban yafe ba, idan ta zubar da hawaye domin ka ban yafe maka ba, idan ka saketa ko da abayan raina ne ban yafe ba" gabana yana fadi idona yayi jajur ba halin mata musu domin banga fuska ba, haka na mike cikin rashin kwarin gwiwa na nufi gidana wanda ya zamti shi zaa saka Zahrah aciki, tunda zahra tasan zaa mana aure bata damuwa da lamarina tunda dama nima na dade da fita sabgarta hakan yasa nima ban damu ba.

RANAR AURE Duk da shirye shiryen da akeyi na biki ni bai damen ba, suka gama event aka daura aure wanda nikam ranan agidan Ammi na wuni ina kallon Junainah wacce ta daura min karan tsana da ban saniba tuni na tsargu da kaina na fara tunanin ko sakayyan Allah ce akaina ban san wani sakayyan mafi muni na tattare agabana ba sai da nazo gida, kasancewar Hajiya tamin magana bana kuma kaunar na fada fushinta yasa na lallaba rayuwata na shiga dakin amarya gudun kar na batawa amarya rai, don raya sunna, munyi sallah muka ci nama duk da kamewan da amare sukeyi wannan baiwar Allah idonta kyam ba kunya ba tsoron Allah haka dai har muka kwanta.

Babban bakin cikina shine Ban samu zahra a budurwa ba akasin Nadrah wacce duk da a maye na kwana da ita nasani, na biyu Zahra bata iya wankan sallah ba innalilahi wainna ilaihi rajiun wannan balai da me yayi kama, Fita nayi don neman abinci yayinda take bacci har na dawo bata tashi ba, haka muka wuni ranar don ko da ta tashi babu sallah da rigan baccinta tazo tana makale dani.

Ayanzu kullum sai na tuna da Nadrah na zubar da hawaye idan Zahra ta kunsa min bakin ciki da farko ga kazanta, ga rashin kunya da rashin kamun kai kirikiri take dura min ashar duk da zafin zuciyata ban isa na rama ba don mahaifiyata tace bata yafe ba, bata iya girki ba don randa ta girka min taliya sai da nayi amai tsantsan kuiya bata wanka sai yamma gata da body odour tsantsan kazanta ba shiri na nemo mai aiki amma zahra ta koreta acewarta zance inason mai aiki in banda tsantsan kishi babu abunda ta iya, ni kyankyaminta nakeji duk wannan adon da takeyi yanzu babu shi, idan nafita gun aiki haka nake zama nayi uban tafumi ina tunani ga bakin cikin zahrah ga damuwan junainah.


31

Akwai randa nayi operation a TH na shigo a gajiye, ga yunwa ga bacci da gajiya duk ya taru mun Allah -Allah nake yi naga na mike na kwanta amma da na shigo wani wari da naji gidan yakeyi, ba'ayi shara ba tana sanye da rigan bacci sai chatting take yi, nayi tsaki na wuce daki na na rufo kofan, amma hankalina bai kwanta ba kar wani bakon kunya yazo ni zanji kunya don nasan zarah ba kunya zata jiba, kuma yanzu da zan mata fada kiran hajiya zata yi ta fara kuka hajiya yanzu zata fara kwashe min albarka,cire rigan nayi na iso cikin gidan na dauki tsintsiya na share gidan tsaf, nayi mopping dukka zahrah na zaune tana kallona kaman kishiyanta, ina gamawa na dauko turaren wuta na kunna sannan na kunna A.C bana son kazanta ko kadan, idona na jajur naje nayi wanka sannan nayi sallah nabi lafiyan gado, ji nayi kawai ana shafani agefe bude idona naga Zahrah, lallaima yarinyannan bata da hankali don tsabar rashin kunya tana gani nagama aiki amma tsabar iskanci tazo min don ta biya bukatarta bansan lokacin da na tunkude ta ta fadi akasa ba,

" in ke jahila ce toh naje makaranta, ki fita min daga daki kafin na miki rashin mutunci wallahi" janta nayi na fidda ta da karfi na koma na kwanta sai bacci mai dadi, acikin baccin ana buga min kofa da karfi kaman zai fadi na mike da sauri don wallahi hannu nakai ina budewa na kwasheta da mari " don ubanki ba nace ki rabu dani ba? ke mahaukaciyar wacce gari ce?, banza kazama ba zaki kasheni ba" gani nayi ba ta dago fuska ba sannan halittanta kaman ba itaba, kafin nace me naji ankai min wani wawan mari

"ashe baka da hankali ban sani ba Aliyu? dama saka ta kakeyi kayita duka? shine yau ni zaka dau hannu ka mareni? ni na tsuguna na haifeka? lallaima kana so in tsine maka ne? innalilahi wainna ilaihi rajiun na haifi yaro dan cikina yazo ya mareni" yadda ta maren tsugunawa kasa nayi don jikina na bari, yau nine na mari mahaifiyata oh God i deserve to die, kuka ta farayi tana cewa dama nayi niyyan kasheta, tunda nake bantaba ganin mahaifiyata haka ba, haka ta saka zahrah agaba suka fita suka barmin gidan, daga office aka fara kirana akwai aikin da zamuyi bansan lokacin da na kashe wayan gaba daya ba, Bazan iya misalta tashin hankalin dana shiga ba domin ji nayi dama na mutu akan wannan bakin cikin, gida naje har lokacin Zahra tana makale agefenta yadda nake ji kamar na tashi na kasheta amma ya zanyi mahaifiyata tana tsaye akan magananta , ji nayi kaman na ce na saketa domin na tsaneta, na tsani ganinta ba tsani zama da ita amma nasan akan maganan zahrah hajiya zata iya tsinemin albarka don dama tana barazanan, nayi zaman roko da ban hakuri amma hajiya ko kallona batayi ba zahra na makale agefenta harda kukana amma hajiya bata kulani ba ,Amrah ma tazo ta sa baki duk a banza amma zahra na bada hakuri ta bugamun sharudda tace ta hakura na dau matana mutafi gida, a hanya kaman in wurgata a rami in wuce sai dai na tuna bayanin hajiya da sharuddanta na farko ma shine karna batawa zahra rai, duk abunda take so zan mata ko inaso ko bana so , babu tsawa balle harara balle tsangwama duk bakin ciki nake hadiya wallahi zuciyata kaman nayi hauka, ban kulata ba haka itama bata kulani ba, washegari da sassafe nabar mata gidan, a asibiti aka kawo emergency wata za'a mata aiki nine zanyi aikin, a tarihi nayi aiki atleast guda sha uku successfully ko fiye da haka amma ban taba jin aikin danayi babu karfin gwiwa ba sai wannan, damuwa sai cina yakeyi, ina fitowa daga aikin na yanki jiki na fadi, tuni suka bani gado.


32

Abokan aikina ne ya dubani nan yaji mamaki sosai

" meya sameka ne? yau kai ne mai son daurawa kanka pressure, ka daina fa its so risky" nayi murmushi domin ni kadai nasan me yake damuna, Amrah ce ta shigo da sauri dakin tana haki kaman wacce kare ya koro

" Hamma ya jikinka?" tana fada tana kare min kallo,

" Kalli yadda kayi baki ka rame, meya sameka?" likitan ya fita ya bamu guri nikuma na tashi na dan zauna na jinginu da pillow sannan nace " ya hajiya?"

"lafiyanta lao ta damu wallahi taso tazo amma ankai mata Junainah shi yasa ma ta turo ni, kayi hakuri don Allah yaya" shiru nayi natuno da Nadrah da ace tana raye na tabbata babu abu makammancin haka da zai faru,

" Amrah sakayya nake gani na ubangiji, duk abunda nayiwa Nadrah shine Allah yake mata sakayya, wallahi nayi nadaman abunda nayi, arayuwata yanzu Nadrah nakeso Amrah, duk zama idan na zauna, duk motsi duk dakika dare da da rana sai nayi tunanin irin wulakancin da na yi mata, na jahilce kaina dana wulakantata, samun mace kaman Nadrah awannan zamanin ba abune mai sauki ba, kiga abunda zahra take mun, babu tausayi asalima ni jikina na bani bata sona, don da tana sona ba zata taba min wannan wulakancin da takeyi ba, ta hadani da mahaifana" jikina a sanyaye nake fada mata abunda ke damuna, tayi shiru tayi tagumi sannan ta shiga bani hakuri, ni dai haka na danne domin kuka naji yana son fito min kuma abun kunya ne nayi agaban kanwata, har ta gaji da zama sannan ta tafi nima mikewa nayi na koma office ina hada wasu takardu, amma kirjina ciwo yakeyi, damuwan Nadrah shine araina, da na gama hada komi na tattara na koma gida, junainah na wasa da ball a hannunta, naga wata sanye da abaya sai da gabana ta fadi domin idan sama da kasa zata hade na zata Nadrah ce, jikina na rawa na matso kusa da ita kawai naga fido ne ta katse min tunani da " ina wuni Hamma" ban samu daman ansa ta ba na juya zan dau junaina amma kukan da ta sakamin kaman na caketa da wuka da sauri fido ta zo ta dauketa sannan ta matso da ita kusa da ni, tana ta cusa kanta cikin gyalenta yayinda fido ta fito da hannayenta ta mika min, nasa hannu na rike duk da tana kukan tuni take jijjigata, hakan yasa tayi shiru, tana dan rera mata waka, har raina naji dadi sosai na zura mata ido kaman bazan daga idona akanta ba, har ta tsargu taja Junainah suka koma cikin gidan na bi bayansu, falo suka shiga nima haka naje na zauna agefe, tana mata wasa nikuma ina kallonta, ban taba nutsuwa na kallo Fido ba sai ranan, suna asalin kama da Nadrah don gizo take min, Hajiya data sauko tamin ya jiki ma ban bi takanta ba, damuwa na Junainah ta kulani duk da banajin kwarin jikina. Abinci naci da kyar na mike nabar gidan.

Zahrah na kwance akan kujera yau anyi shara an dan kimtsa gidan duk da haka ban kulata ba nayi daki, domin idan akwai halittan dana tsani gani to yabiyo bayan zarah, ina kwance ta shigo, rike da kwankwaso

" Hamma ka dubani banda lafiya" keyn mota na wurga mata,

" kije asibiti" tayi shiru sannan ta dauka ta fice, tunda ta fita zahra bata dawo gida ba sai goma sha dayan dare, alokacin na kulu iya kuluwa jira nakeyi kawai ta dawo naji, tunda gashi nakira asibitin ance bata je ba, tana shigowa ina zaune a falo

" daga ina kika fito?"

"asibiti"

"wani asibiti?" bata kulani ba tayi hanyar daki, a harzuke na mike na janyo ta ina sauke numfashi, fizgewa tayi tamin kallon sama da kasa sannan ta shige dakin tana jan tsaki ta rufo kofar, wani wawiyar yawun bakin ciki na hadiye sannan na dawo na zauna, kaina har ya fara jiri, if not saboda hajiya zan iya marinta na mata duka sannan na turata gidansu, wannan ai karamin karuwanci take min agida, daki naje na kunna A.c amma bashi zaisa ban hada zufa ba, ranan banyi baccin arziki ba ina tunanin hanyan bullowa Zahra, laifin da tayi bai isheta ba washegari da sassafe ta kunna waka ta hau rawa, daga ita sai rigan bacci, tun ina jan tsaki har na mike na shiga toilet nayi wankan dole na fito, har lokacin bata daina ba, na ja tsaki na fito anan na tuna ashe keyn motan na hannunta,da akan na koma nace ta bani na gwammace na hau machine na tafi gun aikin haka, ina zuwa asibiti akace directorn mu na kirana, na nufi office dinshi bayan mun gaisa yake cemin

" na lura kwana biyu kana cikin damuwa, me zai hana kaje ka huta na kwana biyu ko? in ka dawo sai ka cigaba" shiru nayi sannan nayi godiya na fice, sai dana shiga office din anan ake sanar min wacce nayiwa aiki jiya ta rasu, surgeryn wasnt a success, shiru nayi naje office na kwanta kaina , na tuna lokacin nadrah tana raye duk lokacin da nake cikin damuwa a office idan ta ganni bata zama, snacks zata nemo min bayan kwaliyya da kamshin da takeyi, tana mun tattausan lafazi duk da bana kulata sai dai na mata tsawa.


33

Irin abunda Nadrah take min nake tunawa kaman in dawo da baya, Allah sarki, dama baka sanin amfanin abu sai bayanan, zuciyata na radadi ina lumshewa ina ganin Nadrah da murmushinta, ko meye na mata bata jin haushi , bata zuciya sannan bata min rashin kunya.

Atakaice nadawo banda aiki kenan tunda ance naje na huta na kwana biyu, nikam gwara na tattara natafi abuja, toh nan ma hajiya tace ban isa ba sai dai na tafi da zahra, ni kuwa da inje da zahra ta kutsa min bakin ciki gwara na zauna anan dukkanmun mu zauna haka, zan jira har su kara kirana na koma tunda ma anci sa'a ba'a karbi license dina ba, zirga zirgan Junainah nasa agaba alokacin ana son sata a makaranta, zuwa nayi na bada dubu dari uku nace gashi duk makarantan da akeso a bauchi a sata,Ammi tace yayi yawa amma nace ta barshi sauran ayi mata shopping, Fido bata nan alokacin don haka sai na zauna akan zan ga junaina while ita nakeson gani, ni kaina bansan dalilin da yasa na keson ganin fidon ba, bata fito ba sai can yamma, tayi kyau sosai , sanye da dogon riga kore yasha aiki ta tumbuke gashinta ta gefe , daurin dankwalin ya zauna dam dam,sai kawai naga kamar Nadrah, zuciyata tana bugawa sosai na tsorata, Ammi har ta gane tayi gyran murya da sauri na sunkuya kaina akasa ina sosawa nayi murmushi itama murmushin tayi alokacin fido ta gaishen na amsa cikin ladabi sannan ta nemi guri ta zauna, ni kuwa nabi ta da kallo gabana yana fadi wanda ni kaina narasa meyasa ne, Ammi ce ta lura da hakan tace " yau kanwarka gizo take maka?" na sosa keya sannan nace "wallahi ,Nadrah nake gani fa suna kama sosai" tayi murmushi sannan tace " haka mutane ke cewa, wai kaman yan biyu, bayan kaine kake kama da fahad ko tambayansa baka yi" na girgiza kai ina murmushi nace "" tun rasuwan Nadrah ya daina min magana, dashi da kamal kaman su kasheni haka suke ji, bayan abunda ya faru da Nadrah wallahi kaddara ce, ni kaina ina Nadama sosai, Allah yayi hanyan ajalinta kenan amma nayi Nadama Ammi har yau ina ganin sakamako, bana ganin farin ciki arayuwata tunda ta rasu sai sakkaya" Dukkansu shiru sukayi inbanda Junainah da take ta wasa da Ammin, hakuri dai tayita bani, yayinda Fido ke kara gayamun yadda Nadrah ke sona , tace lokacin da Nadrah ta fara shaye shaye ba wanda yasani, ita dai ta taba ganin wiwi ne shima batayi tunanin sha takeyi ba tayi zaton zata saka a gashi kaman yadda mata ke hada man gashi daga baya tazo taga ba haka ba, tace lokacin da Nadrah ta ganni da zahra a mota tana bin mu abaya, tsabar sauri sai data buge motanta ita kanta taji ciwo sosai amma bata damu ba, abubuwa da dama wanda ya narkan min da zuciya ina kallon fidon gaba daya yanayin jikina ya canja.

Ban bar gidan ba sai tara na dare cikin ikon Allah na nufi gida, kofan gidan arufe don haka na ciro mukullai na bude na shiga, shiru naji alamun babu kowa sai dai tunda naga mota awaje nasan tana ciki, har na je zan bude dakina naji nishi kaman mutum kaman ba mutum ba, na juya ahankali sannan na nufi inda na ke jin karan, murda hannun kofan nayi na bude ba tare da nayi wani tunani ba, Zahrah ce akwance da wata haihuwar iyaye, salatin da nayi yasa suka juyo suna kallon na, na koma dakyar ina jan kafana babu mafi munin gani irin abunda na gani yau, numfashi na daukewa ya farayi na fara rike kujera na zauna duk ina numfashin sama sama, ta fito dasauri tabar gidan bansan lokacin da na mike naji karfi ajikina ba na ha wayan cable na shiga dakin na rufo kofar, da na fizgota da karfi na fara dukanta wallahi sai da cable dinnan ya tsinke, na cire belt shima ya tsinke, sai da na tabbatar numfashi ma dakyar takeyi sannan na rubuta mata saki uku na damka mata nace tabar min gida adaren kuma idan ta kuskura ta waiwaye hajiyata ta tabbata sai na kasheta34??CIWON IDANUNA

NA

BENAXIR OMAR

Yadda naga dare haka naga safiya, sai juyi nake akan gado can dai na dauro alwala nayi masallaci, a wajen gidan nake ganin maigadin sai gyangyadi shima yake kofar a wangale hakan ya tabbatar min da Zahra ta bar gidan, da na idar da sallah na dawo anan bacci yadam dibeni.

Wayata ce tayi kara hakan ya tasar dani daga baccin da nake na dauka na saka a kunnena ba tare da duba sunan naga waye ba,

"kazo gida yanzu ka sameni" tana gama fada ta kashe wayan, yayinda ba shiri na fado daga kan gado na shiga toilet, gabana sai fadi yake ina tunanin me zanje na tarar a gidanmu, minti sha biyar yakaini gida tun daga bakin gate naci karo da motan drrivern hajiyan Zahra, dama nasan zaa rina, na shiga nayi sallama dukkansu suna zaune tamkar wanda suke jirana, na tsuguna na gaishesu hajiyan zahrah ta amsa ba yabo ba fallasa yayinda Hajiya ta kam ko kallona batayi ba,

"Me ya hada ka da Zahrah?" idona na kai kanta na zura mata ido, tana sanye da hijabi , munafukar yarinya su suke batawa masu hijab suna, Allah sarki saboda wannan kucakar na wulakanta Nadrah wayyo Nadrah,

"Tambayanka na keyi meya hadaku?" hajiya ta katseni daga dogon tunanin da nakeyi kafin na bada amsa zahra ta cabe baki tace "Hajiya da gaske ni nace ya sake ni, naga kaman ina takurashi har yanzu yana kewar tsohuwar matarsa"

"maganan banza maganan wofi, yaushe ka fara son Nadrah? yarinyar da ka wulakanta, ai ba kaga komi ba, kadan kenan daga rayuwarka har kukan jini sai kayi akanta, ina kai wasa da soyayyan wata? tsabar ka raina min hankali shine bazaka zauna da matar taka ba? toh ka mayar da ita" Harara na sakewa Zahra jin karyar da tayi babu alwala balle sallah sannan nace " hajiya saki uku ne ba daya ba" wani naushi ta sakemin sai da hajiyan zahra ta riko ta

" ka tashi ka bani wuri, kanaso ka kasheni ne? Haba Aliyu!" jiki tsum tsum na mike na bar musu falon, waje nazo amma na gagara nutsuwa, abu daya nake tunani yadda zan lallabata tayi hakuri hanya daya ne, ta ganni da mata babu abunda ta tsana kaman ganina haka, to yazanyi yanzu kam bazan taba yin aure ba sai auren so.

Gidan Ammi na nufa don ganin Ya ta ko zanji sanyin rayuwa, a tsakar gida na tsince su,Fido na turata a keke sai da gabana ya fadi da ta juyo tana min murmushi,Nadrah na gani sak a fuskanta, Junainah na ganina ta tafara buya abayan fido tamkar taga dodo, jiki a sanyaye na karasa muka gaisa na mika mata hannu amma sai "a'a" take cewa

"unma fido kay ki kaini gun dodo! unma fido kay ki kaini gun dodo!!" tana fada tana buya, fido ta janyo ta tana murmushi

" ba dodo bane abbanki ne!" amma ganin zata miko ta guna ta saka wani irin kuka mai tsanani dole ta janyeta suka shiga ciki ni kuma na bisu abaya na gaida Ammi kaina akasa tana ta murmushi ni kuwa na zurawa Fido ido ina sosa keya, Ammi lura da hakan yasa ta mike tabar falon, duk kokarina na janta da hira taki sakewa alamun na takurata da kallo har aka kira sallah kafin na bar gida, Abbanmu ne yakiran yanemi yaji dalilin sakin zahra nace masa ita tace na saketa, tunda ita ta fadi hakan zan rufa mata asiri, acikin kwana biyu akazo aka tattara kayanta Allah yasa babu rabo a tsakaninmu, ni haushi da kyama take bani, nanma tunanin Nadrah ne araina da Nadrah nada rai da duk wannan bai faru ba duk da hajiyata gani takeyi tamkar wani mugunta nayiwa zahran nace karta fada.

Na mayar da gidan Ammi gidan zuwana, sai na fake da zuwa ganin junaina amma zahiri fido nake gani, bata da surutu akwai ta kamun kai ga kunya duk abubuwan da takeyi yasa na kamu da sonta fiyeda yadda nake zato, gun aikina ma dana koma duk da an dakatar dani dayin surgery akan zasu turani wani course naje nayi nafara processing, ina fitowa daga gun aiki gidan Ammi nake zuwa anan nake cin abincin dare nayi sallah ina zuwa gida sai dai nayi bacci, wata ran mukan hadu dasu Amir ko usman ko Kamal, akwai randa na hadu da Abamama shi kanshi yayi mamakin ganina anan Ammi tace masa ai kullum ina zuwa ganin junainah, itama junyn yau da gobe sai Allah ta rage tsorona sai dai har lokacin bata kaunar tsayawa kusa dani kullum ta gefen Ammi ko Fido, Nayi iya kokarina in gwadawa fido tsananin son da nake mata amma baiwar Allahn nan ta matar dani baho, gwadamin takeyi ba ta masan meye nakeyi ba balle ita kanta soyayyar, gata da ado da kwaliyya, ranar nayi kokari zan sanar mata nasha wanka na bayan na dawo daga aiki naje gidan, junainah na bacci don haka kawai na zauna muna gaisawa ta kawomin abinci tana murmushi har ta tashi zata wuce nace "Firdausi ji mana" ta tsorata sosai daga yadda ta kallen domin kuwa na gani a fuskanta tace "toh" sannan ta sallami su abakkar da muhd kabeer suje suyi wasa don suma kullum suna gefenta in ba wai in sun koma makarantan boardn ban,

"Akwai abunda nakeson ssnar miki kuma ya damen hakan yasa nace gwara na sanar miki ko zanji sanyi araina" kanta akasa ta gyada kai sannan naci gaba

" Kinga tsakanin mu babu boye boye sai gaskiya, kinga junainah ta saba da ke sosai tamkar mahaifiyarta kuma anci sa'a ni mahaifinta na ganki na fara sonki, So da bana tsamannin na taba yiwa wata mace ina miko kokon barata ki taimaka ki amince ki soni" murmushi tayi wanda ya fara bani hope sannan tace "Da gaggawa zanyi hanzarin kin amince maka, kamanta bahaushe na cewa in kaga gemun danuwanka na ci da wuta ka shafa wa na ka ruwa? kayi hakuri banjin zan iya zaman aure da kai, Junainah ta girma tace meye?"

"hmn, Firdausi Karki min illah, ban taba wasa da so ba, bakuma zanfara akanki ba, nasan inada mummunan kaddara a tattare dani don Allah ki manta da wannan, kinga gani gaki ga Juny, kuma ba haramun bane "

" uhm, Hamma kenan! bar ganin Allura kankanuwa karfe ce, wannan junainah da kake wa kallon ba tasan komi ba inta girma taji labarin yadda kukayi da mahaifiyarta me zata ce akaina?"

" ni ki daina min magana da karin magana bana ganewa, yanzu dai kije kiyi tunani, koma meye don Allah"

"babu tunanin da zanyi, na yanke shawara ta kuma shine bazan iya zama da kai ba" tana gama fada tabar min falon, shinkafar dake gabana naji duk ta fitamin akai, mikewa nayi nabar gidan.

Tun daga ranan naga sauyi agun fido, ta daina zama a inda nake da zaran nazo zata hada Junainah dasu muhd kabeer ta shige daki ko basa nanma sai dai ta hadota da mai aiki, duk jikina yayi sanyi yayinda alokacin nakejin wani irin tsantsan son Fido araina , kyakywar numfashi nayi sai na tuna da ita, gaba daya nayi loosing control, ciwon zuciya zai iya kama ni ahalin da nake ciki gashi dama jinina yahau, akwai randa adaki ina zaune kawai naji na fara hawaye, abun ya matukar bani mamaki na danna wayan fido tana jin nine ta kashe wayan, ni ko ganinta na samu nayi naji dadin rayuwata amma babu hali.

Randa naje nasa araina sai na ganta na aika mai aiki taje tace tazo taki fitowa, nasan abu daya zaisa tazo shine junainah tafara kuka sikuwa na danne raina duk da abunda na tsana kenan naji kukan ta na dauketa, kukan data farayi kaman taga malaikan mutuwa ba shiri saiga fido ta fado a falon ko dankwali babu da sauri na rufo kofan ta karbi junainah tana lallashi nikuma na tsaya abakin kofan, kallonta kawai da nakeyi wani sanyi nakeji araina, ashe haka so yake da dadi? haka so yake da daci? haka so yake da radadi?

" ka matsamin"

"don Allah kiyi hakuri wallahi ina sonki, bantaba furtawa wata mace wannan kalamun ba sai ke" ficewa naga zatayi na riko hannunta da karfi ta fizge sannan tace cikin bacin rai "Don't!! karka kuskura ka fara ina ganin mutuncinka, ko giyan hauka kasha don't you dare touch me" ta bankade kofan ta fita, bantaba jin zafin nadaman shan giya ba sai ranan, ashe skwai ranan nadama , duk wanda yamin gori bana damuwa amma akan na fido sai dana zubar da hawaye.Nafi minti talatin a zaune can dai na yanke shawaran samin Ammi ko zata tsawata mata, ina zuwa na tarar da ita a falonta na gaisheta cikin ladabi sannan nace

"Ammi nazo neman alfarma duk da nasan ban cancanci wannan alfarma ba"

"ina sauraronka, Allah yasa alheri ne"

"sosai ma, Ammi ki aura min Fido wallahi na yi alkawarin yi mata duk abunda takeso, bazan cuceta ba, wallahi tallahi Ammi ina sonta" murmushin da tayi sai daya fadar mun da gaba sannan tace

" kai kuwa Aliyu ka taba ganin An ciji mumini a ramo sau biyu? ai da zaran an cijeshi na farko in har shi mumini ne bazai kuskura yace zai koma ba".


35

Gabana ne ya tsinke ya fadi jin magananta duk da cewa ban gane me take nufi ba sai taci gaba da cewa " kayi hakuri, kar ma ka fara dauko wannan magana domin ba mai yiwuwa bane" tana gama fada ta mike tabarni shimfide agurin, wai ya ma za'ayi ahanani auren yar'uwata? tunda fido cousin dita ce, Babanta kanin babana ne, na mike nabar gidan da zummar yana dawowa gari nazo na sameshi na sanar mishi abunda ke raina, shikam ayadda yake sona sosai nasan zai aura min ita.

Fido ta samu aiki na state library na bauchi hakan ba karamin dadi naji ba domin zan iya haduwa da ita ko batayi niyya ba, domin naga salon data samu kenan gudu na kaman zan cinyeta. Randa na fito daga asibiti na isa state library har wani murmushin jin dadi nakeyi yau zanga fido nakai sati uku ban ganta ba , tana gudu na duk maita na haka nake hakuri, motarta na gani don haka naje na ajiye tawa agefe sannan na shige ciki, tana zaune tana filing wasu takardu na shiga office din nayi sallama,tunda ta dago kanta taga nine ta mayar ta sunkuyar, sai na dawo kaman munafiki, wanda ke zaune agefenta ya kallen ganin yadda na tsaya ya fara tattarawa zai fita, wani irin harara ta sake tare da cewa "Ina kuma zakaje?", ya koma ya mayar yazauna sannan ya sunkuyar dakai, kafafuna ne suka fara rawa domin yadda ta hada fuskanta ko dila albarka, haka na tsaya tagama abunda takeyi yafita sannan cikin izza da ji da kai tace "lafiya? akwai taimakon da zan maka?" na zura mata ido sosai, abaya ce baka ta saka gyalen tayi matukar kyau, sai kamanninta da Nadrah ya sake fitowa. "Ya juny?" "kar ka cemin tun daga wata duniya kazo nan don ka tambayeni junainah, na tabbata akwai dalili don haka bar rabewa ka fada mun menene" yadda take maganan ba wanda ya isa ya kawo mata wani raini, bansan ta iya hada rai haka ba, na ja kujeran na zauna sannan nayi murmushi nace "tunda haka ne barinje straight to the point, Fido kiyi hakuri,ki tausayawa raina bazan iya rayuwa babu keba" wani dariya tayi wanda sai dana tsorata don ganin wasu yadda takeyi, bata amsa ni ba taci gaba da rubutunta can kawai naga ta tattari komi ta hada jakanta ta fita nakuwa bi bayanta kaman mahaukaci har dai dai main kofan shiga motarta, gashi dama an sauko daga masallaci gurin ya cika sosai kowa na neman hanyan wucewa, ganin ta shareni zata shige motanta yasa na rike gefen gyalenta aikuwa sai da na gwammaci ban rike ba, sai da nayi nadama don ta tozartani iya yanda baa taba tozartani ba, a fusace ta juyo cikin bacin rai tace "Kai wani irin mutum ne, ko kasha giyan hauka ne? nace ka rabu dani! ka rabu dani!! bana sonka dole ne?! idan ka kara biyoni yan sanda ne zasu raba ni dakai" ta figi motanta tawuce,babu wanda ya fado min arai sai Nadrah, lokacin data biyoni asibiti gun aiki randa ta fara sanya hijabi tazo gwadamin, haka na disga ta agaban mutane nace mata ko tasha giyan hauka ne, ashe da zafi, ashe da radadi, ashe da ciwo, na shiga uku, kaina na rike naja gefe na bata waje domin naga bawani tausayi zata iya dagani ta kasheni na ziyarci lahira babu shiri, gashi mutane nata kallona kowa ya nemi guri ya tsaya, tunda uwata ta haifen ban taba jin kunya irin na ranan ba, hakika fido ta tozartani ji nayi kaman nayi hauka don bakin ciki amma bakomi muje zuwa bazan daina sonta ba, duk yadda nayi nayi zuciya da ita na kasa, da zaran inason saka tsananta araina sai dai inji wani sabon shaukin sonta ya kamani ya karu har nakejin zan iya hauka idan ba'a hadani da ita ba.

Randa na yanke shawarar ziyartar oga kwata kwata mahaifinta ranan da zulumi na kwana, yana falo na shiga muka gaisa yana fara'a yana dariya sannan muka gaisa na zauna ina sosa kai " Me ya faru babana?" Ammi tana gefe itama sai murmushi take don tasan me zan fada amma naga alamun babu damuwa atattare da ita,

" na zo ne neman alfarma"

"wanne fa?"

shiru nayi ina fargaban fada masa domin ina tsoron jin amsa ta, Ammi tayi dariya sannan tace " yazo tambayanka auren fido" .


36

Yayi Murmushi sannan yace "Na baka, duk abinda na mallaka ai na Danuwa nane" Yadda Ammi ta bata rai ta mike sannan tace " bangane abun danuwanka ba, jiya na gama maka bayanin dalilin da yasa ba naso ahada aurennan" hannu ya saka mata alamun ta masa shiru hakan yasa ta juya kanta tana jan numfashi shi kuwa yace " zanyi magana da alhaji gobe , Fido ta zama naka insha Allah, ni na isa in hanaka wani abu da kakeso aguna? bayan mahaifinka shine silan duk abunda na mallaka a duniya in ita ta manta ni ban manta ba" farin ciki ya zo min na mike cikin gaggawa ina godiya gidanmu na nufa domin babban daron yana gun hajiyata yanzu nasan sai ta hanani auren Fido tace zan wulakantata kamar sauran matan, dakinta na nufa tana kan sallaya na gaisheta ta amsa sama sama dama tunda na saki zahra dama ta daina min murmushi ko sake fuska kam tunda Nadrah ta rasu ta fara tamke fuska sakewan kadan ne shima acikin mutane,

"Hajiya nazo neman alfarma ne"

"inaji"

"Na roki mahaifin Fido ya bani aurenta ya amince inaso don Allah ko Alhaji yakiraki akan maganan kisa albarka shine nace barin fada miki"

Kallona ba tayi ba sai data idar da adduanta sannan ta juyo tace " so kake yi itama ka aurota sai ka wulakantata ka raba mutuncin dake tsakani? ko ka manta mahaifinta danuwan Alhaji ne? ba zaka cuci yarinya ba ingaya maka in har kaga ka aureta toh na mutu ne" Yadda tayi maganan babu alamun wasa a tattare da ita don haka nasan ba wasa take yi ba jiki a sanyaye nabar mata dakin kafin ta kara harzuka, gidanana na nufa sai gani ina sallah tsakar dare ina rokon Allah ya bani fido har da kuka na, anan na tabbatar da ina sonta tunda abunda ban taba yi ba kenan, nasan ko da duniya da yayanta zasu taru suce zan auri fido idan hajiya ta tace a'a babu wanda zai aura min ita, abu daya nasan anyi shima bata so daga baya da aka lallabeta ta yarda wato aurena da Nadrah, yadda aka bata labarin yadda take sona aka lallabeta yasa ta amince amma bayan haka sai dai batace abu ba toh ya zauna, mutum daya ne zai iya juya min ita shine Allahn da ya halliceta na yarda komi baya gagaransa.

Rikici sosai akayi akan maganan auren domin kowa ya amince amma Hajiyata da Fido sunce basusan batu ba haka Ammi ma, wannan mutane uku kadai sun isa su hanani kwanciyan hankali ko da ace andaura, Ammi ta dage bazaa yi auren cin amanar yaruwar ta ba, Hajiya tace bazan raba zumunci ba haka zalika fido tace bazata ci amanan nadrah ba, Ni abun da ya damen shine na kasa ganewa tana sona ne ko ba ta sona? dukka hayaninyansu baisa na hakura ko na daina addua ba tuni na dukufa agaban ubangijina na rokeshi na kuma kai kuka na agareshi, Alhaji yayi iya kokarinsa ganin ya shawo kan hajiya amma batu yaki ci yaki cinyewa, tun ina azumin har nazo na fara ramewa , kana ganina kaga tsantsan damuwa ga idona yafito guli guli inbanda kasusuwa babu abunda mutum zai tsinta ajikina, na dawo kaman dan maula kullum ina kofan dakin hajiya ko zata amince mini amma kaman bawa haka hajiya ke yi dani, ta koreni na dawo na zagen dukka naki zuciya, wataran haka nake zama akofan dakinta inta kuka amma ko ajikinta rufe ma kofanta take, Amrah tun bata kulani ko jin tausayina tadawo itama tana tayani zama toh haka hajiya ke hadamu ta koremu, tace bazamu mayar da ita tsohouwar banza ba,

" yaushe yaushe zahra tagama Idda? zaka kawo min batun mace, kai kenan sai kace bunsuru? kabi wannan kabi wancan? daga karshe ka wulakantasu toh ban isa karaba zumunci yadda kayi afarko ba inaji ina gani nida hajiyan zahra mun daina mutunci kaman da saboda kai dan iskan yaro maras ta ido!" kullum mitan kullum daban ban taba zuciya ba, akwai randa tun safe dana dawo daga asibiti nake zaune akofar dakinta ba ci ba sha, sallah ma agun nakeyi kuma dama kwanana uku banci abinci ba, asali abinci rabona dashi tunda ta hanani fido,haka ma zauna ina jingine da bango ga wani sanyi da akeyi jikina na bari amma naki tashi karshe suma nayi awajen. ko da farkawata ganin hajiya nayi tana kuka cikin damuwa, duk da bansan meye ba nariga nasan nadama takeyi akan abunda tamun, lallabani ta rinka yi nikuwa na kara langwabewa domin samun biyan bukata nace "Hajiya ki taimaka ki aura min fido, wallahi nayi alkawarin Riketa amana" shiru tayi ba taban amsa ba sai dai nasan da sauki ba kaman da ba bata rai zatayi ta zagen, a gidan na kwana aranan washegari Amrah da gudu tazo daki take sanar mun hajiya ta amince da batun aurena da Fido acewarta tace kar ma rabone yake so yazo duniya ta hana Allah ya kasheta kuma ayi auren, sujjada nayi ina godiya wa Allah da ya nuna min wannan rana don wani dadi naji araina karshen wahala ta tazo ko ince karshen sakayyar Nadrah kaman yadda mutane suke fada, wanda ni ayanzu gani nakeyi duk da nine ajalinta, rabo ne ya kasheta domin da tana raye bazan taba auren Fido ba, Allah shine masani akan al'amuransa, duk da haka ban nuna na watsake a damuwata ba danaje gaishesu a falo alhaji ya kallen cikin tausayi yace "sannu ko! kaman ba Aliyun da na sani ba dan gaye dan kwalisa, yanzu duk kayi baki ka fita hayyacinka" sosa kaina nayi ina murmushin karfin hali hajiya kuwa sai tura min sakon harara takeyi kaman ba itace take ta shekan kuka ba,

" Ka ce kai sai yar'uwarka dama mahaifiyar ka ce taki amincewa amma yanzu ta amince yanzu zamu garzaya zuwa neman aure, sai dai inaso Aliyu kayi hankali kaji? ka nutsu, mata da kake gani ba'a biyewa yarintarsu, har yau bamusan rabuwarka da zahra akan meye bane amma ni ina kyautata zaton gajen hakurinka ne kawai, ka koyi hakuri da fahimtar mace kaji? kowa daka gani da haka yake rayuwa in baka fahimcesu ba toh an rinka rabuwa dasu kenan" Shiru nayi har ya gama waazinsa wanda na dauki kowanne nasaka araina, don ni yanzu jina nakeyi kaman ban taba aure ba yanzu zan fara.

Acikin satin aka kai gaisuwa aka bada sadaki akasa rana har lokacin bana ganin sassauci agun Fido, asalima ita kam tattarawa tayi tabar gidan wai taje gidan Hajiyati kakarsu, yadda bazan iya zuwa ba tunda tasan yas kamal na gun haka sauran yanuwan Nadrah, Ni da kaina nasiyo kayan gyran gida ina tsaye suna gyra, dakaina naje na hado kayan aurenta wanda daga Nadrah har zahra babu wacce ta samu irinshi, na tura mata kudi a account dinta duk da bata tambaya ba, ba ta kuma nemeni ba illa sako da ta bayar abani na nude takardan cikin zumudi duk da ga waya amma ta tsallake tayi a takarda jiki na bari na bude na fara karantawa kamar haka

Daina farin cikin ganin wasikata don nasan yanzu haka jikinka bari yakeyi, na yine na sanar maka cewa bana son rawan kai ban kuma ce ka samin dukiyarka a account ba, idan dashi kake sayan zuciyan yanmata to kasani nawa yafi karfin dukiyarka , magana ta biyu bar farin cikin burin ka yacika zaka aureni kaiconka! ashe har zaka manta laifin da ka aikata wa yaruwata? kana tsammani zan manta ne? kayi shirin taron bakin ciki a rayuwarka! acikin gidanka! a mafarkinka! a duk yanayin da kake ciki, .


37

Yaga wasikar nayi ko ajikina domin babban burina na aureta, kuma tunda an amince komi zaizo cikin sauki, Haka dai aka fara shirye shiryen biki, ba yabo ba fallasa tayi biyayya duk da bansan yanda iyayenta suka saka ta amince ta kuma daina damuwa ba har na fara tunanin ko tana sona boyewa takeyi? walima akayi sannan aka daura aure, mummy wannan karon taki yin dinner acewarta kunyan jama'a kadai ma ya isheta , Randa aka daura aure tazo ta zaunar dani kaman karamin yaro

"Aliyu wannan karon ba doka nake baka ba rokonka nakeyi, don girman Allah ko bayan raina ko firdausi yanka fatarta takeyi tana ci ban yarda ka saketa ba saboda zaka raba zumunci, in kasancutar baiwar Allah zakayi ka fada tunda wuri musan makomar mu, in har ka saketa ban yafe maka ba, Allah ya isa tsakanina dakai kuma" wannan ne karo na farko da hajiya tamin kashedi mafi ban tsoro kaina akasa nace "Hajiya wallahi ina sonta kiyi hakuri don Allah insha Allah ba abunda zai faru ma" jiki a sanyaye na koma falon alhaji shima haka ya ajiyeni kaman karamin yaro yamin waazi sosai, ya gwada min rayuwar mata da yadda ake tafiya dasu yace " Su mata da kake gani rauni garesu, kuma kai zaka tarbiyartar da mace yadda kakeso arayuwa, hakuri da mace dole ne, kar kace zaka yiwa mace dole baayi musu, raayi da dai sauransu, kuma kayi HAKURI, kayi HAKURI, sannan kayi HAKURI! ka kai zuciya nesa ka jini ko babana?" na gyada kai sannan yasamin albarka na tashi na fito jiki a sanyaye.

Aranan aka kai amarya dare-dare wannan karon ba'ayi wani bidi'an kaita gidanmu ba tukunna, kai tsaye gidanta aka kaita har lokacin gabana fadi yakeyi haka kawai nake bala'in fido, kajina naje na siyo da fresh milk, dakina na nufa nayi wanka na canja kaya sannan na nufi hanyan dakinta, ina murdawa naji ansaka key , na buga amma shiru akeji, nakira sunan fido kaman muryata zata tafiya amma baiwar Allahn nan ko motsinta ban jiba, na ajiye kajin na jingina da bakin kofan na rasa me zanyi, anan bacci ya kwashen ban tashi ba sai asuba, ina farkawa kawai na ganni a yashe kaman kayan wanki , na janye jikina nayi daki na dauro alwala na nufi masallaci, dawowa ta naga dakin abude na leka naganta akan sallaya na isa gun na zauna na jira naga ko zata idar, baiwar Allahn nan data fara sallah sai dana kai sawun wani baccin kafin ta idar, na farka na samu tayi wanka tana zaune tana danna wayanta, gaisheta nayi sama sama ta amsa tare da cewa "zan gyra dakina ka fita don Allah" jiki a sanyaye na fice na yi wanka sannan na fito.

Wunin ranan tayi shi a daki da zaran na shiga zata ce min na takura ta haka nake fita tsumtsum, duk yadda naso ta kulani ta nuna bata san batu ba dama daga gidanmu ake kawo abinci, sai ta dibi nata tabar min nawa.


THE END 38

Sati daya muka jera da fido muna wasan kura, da zaran na zauna agu sai ta tashi asalima sai inaga kaman kyankyami na takeyi, Da zaran na fita sallahn magrib toh kafin na dawo zata danna sakata wa kofanta sai kuma da safe, ranan da na gaji tun daga asuba agida na fara sallah naki matsawa balle ta samu hanyan kulle kofa, magrib nayi na tattara sallayan na shiga dakin ta dashi da kayan tea na da kajin da nasa akawo min duk na ajiye, ta shigo tana kallona rike da kunkumi " ka fita min adaki" ina zaune agefen gado ban kalleta ba balle nasan tana wani abu, ta kara matsowa " magana nake maka" na kalleta idona yayi jajur wanda ni kaina bansan halin da nake ciki ba, tsorata tayi ta juya ta dauki pillow daya zata fita hakan ya tabbatar min da lallai tana da niyyan barmin dakin, hannunta na riko da karfi ta juya zata fizge tamin yadda ta saba yi da sauri na rike dayan hannun na zura mata ido, duk matsifan idonta sai da ya tafi babu shiri, juya kanta tayi na sa hannuna na juyo da kan nata sannan nace "ki kalleni kimin rashin kunyan, kinsan hukuncin macen da ta gujewa mijinta ko baki saniba" duk jikinta yayi sanyi hakan ya tabbatar min da lallai tana sona ko da kuwa son kadan ne, domin da bata sona zata fizge jikinta ne tabarni agun, " kin wahalar dani fido, nasan nayi kuskure amma ko Allah muna yi masa laifi ya yafe mai yasa ke bazaki yafe ba? ki na amfani da Nadrah ne ki bata min rai amma na tabbata kinada hujjanki daban, kiyi hakuri wlh na azabtu da yawa, kece mace ta farko dana fara so kuma kece ta karshe da yardan Allah kiyi hakuri Fido", sauran hawayen dake makale a idona ne ya zubo,janta nayi ahankali nace muyi sallah a sanyaye ta saka hijab , na jamu sallahn isha sannan mukayi nafila, na juyo zan mata addua naga hawaye fam a idonta, atake na rikice " me ya sameki don Allah? kiyi hakuri idan na bata miki rai" na janyota ina rarrashinta a hankali , kuka tayi sosai, harda shesheka abun har ya fara bani tsoro na rasa dalili gashi taki magana, dakyar na lallabata na tofa mata addua sannan na shimfida ta akan gado.

Washegari da sassafe da rawar jiki na tashi na daura mata ruwan wanka, na tasheta a hankali amma kunya yasa gaba daya ta gagara fitowa ganin haka yasa nabar mata dakin don ta samu ta kimtsa, jiki na rawa na hada mana abun karyawa na jera a dining ina jira tazo muci, ashe haka aure yake da dadi idan kana so kuma ana sonka, masha Allah yanzu nasan nayi dace, Bayan samun fido a cikakkiyar mace, na samu fido mace mai hakuri, kunya da ilmi, hangen nesa da zurfin tunani, ta dawo abun alfahari ga dangina, Ashe ta dade tana sona tun Nadrah na raye sai dai kasancewwar yaruwarts na sona yasa ta hakura, tabbas nayi dace, da wuri naje na dauko junainah, Fido taci gaba da riketa tamkar yar cikinta wannan karon Juny ta daina tsorona ba kamar da ba kasancewar kullum tana ganina kuma ina hadawa da adduoi Allah ya jikan mahaifiyarta.

BAYAN SHEKARA BIYU

Shigowa gida nayi don na gaji mun fito daga wani surgery na tarar da Junainah a tsakar gida , tana ganina tazo da gudunta "Abamama oyoyo" nayi dariya sosai ina janta har muka shiga jiki aikuwa Fido ce ta fado ajikina itama da salon nata oyoyon, "wayyo zaki kasheni "

" kana mutuwa zan bika"

" ina kika bar Rahama da Amira?"

" suna daki"

"muje, nikam bana hanaki barin min yan biyu su kadai ba, don kin samu Allah ya baki su? wannan baiwa haka?" tana murmushi ta riko junainah mukaje har dakin na zurawa yan biyun da Allah ya bani kyauta ido, suna mugun kama dani , hawaye naji sun fito min nasa hannu na goge, fido ta kallen sannan tace " zaka fara ko?"

" uhm! ba abunda zan fara,Allah ya jikan Nadrah Allah yasan dalilin daukan ranta, rabon wannan yan biyun domin kuwa da ina aurenta bazan taba aurenki ba, Allah yabar wa kansa sani,Allah ya barmin ke matata" na rungumo ta ina goge hawayen da suka makale.

BISSALAM***

Na gode da kukayi hakuri da nayi har na gama wannan littafin, i just hope fadakarwan dake ciki mutane zasu gani GAREKU SAMARI DA YANMATAN YANZU MASU WULAKANTA MASU SONKU , MAI KUDI, TALAKA, MAI KYAU KO MARAR KYAU DUK DAGA ALLAH NE , MUBAR WULAKANTA MASU SONMU DOMIN BA MUSAN INA GOBE ZATAJE DAMU BA.

I dedicate this book to all FCK ladies nd ZAUREN KARATU i love you all. sai kun jini a BABU RUWAN KWAI DA ASKI


Tags: #Romance #Love #Marriage
4698
2
4
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

mimi2019-08-23 12:43:41thanks alot.dis is nice

Allah ya kara basira2019-01-03 16:44:18