Badakala

Written by Maryamerh AbdulPublished on 2018-12-12 18:57:44Category Mystery/ThrillerLabarin 'yan mata bakwai mabanbanta kowacce da nata BADAK'ALAR, yaya zasu samu bakin zaren kowanne matsala su warware har su samu rayuwa mai inganci? tags: #Benaxir #Lubiee #Batul #pherty #Rufaida #miemiebeeDuba was labarai »

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


SHARHI:- wannan labari k'irk'irarre ne 


            1


Harabar Cubana (babban wurin shak'atawa) da ke garin Abuja cike yake da motoci kala-kala manya da k'anana kaloli daban-daban, motoci masu yalk'i su suka fi yawa, wasu kamar k'wai, wasu kuwa a manne da k'asa, sai kayi mamakin ta yanda suke iya tafiya ba tare da sun goga k'asa ba, dan tsakanin motar da k'asa bai wuce tsawon babbar yatsa ba, wurin shak'atawa ne na manyan yara, fararen fata sunfi zuwa wannan wurin saboda kalar abincinsu da yanayin rayuwar da sukeyi a k'asashensu shi akeyi a wannan wuri.

K'arfe hud'u da minti goma sha-biyar na yamma Mercedes benz c350 4matic 2015 model kalar ash da tint glass ta shigo harabar, wurin parking ta samu can nesa ta ajiye motar sannan ta bud'e k'ofar ta sauk'o da k'afarta d'aya, k'ok'arin cire makullin motar take ta waigo ta kalli waje. Phertymah Zahra ce, matashiyar yarinyar da bazata wuce shekaru ashirin da uku ba, bak'a ce amma jin dad'i da hutu yasa ta koma chocolate, hancinta a mik'e samb'al sai dara-daran idanunta da take lumshe su ahankali lokaci zuwa lokaci, sanye take da riga dai-dai gwiwa fari da dots na pink da blue, sai wando legenz pink d'ankwali pink, cover shoe ne sanye a k'afarta mai d'an tsini, bak'i mai adon pink da blue.

Muryar Lubiee da taji ya dakatar da ita daga cire makullin nata, ta waigo tana mai kai dubanta bayan motar inda Lubiee ke zaune, sanye take da atamfarta da k'aton mayafin da ya rufe tun daga kanta har zuwa hannunta, wanda ko da ta tsaya ta mik'ar da hannunta har yatsunta wannan mayafin zai rufe ruf ba tare da ta ja shi ba, fara ce mai dogon fuska, wushiryar da take dashi yafi d'aukan hankalin mai kallonta, dan kyawun da yake k'ara mata. Baki bud'e Pherty take kallonta, mamaki zata yi ko dariya? Saboda tambayar da tayi mata wanda ya samo asali daga zancen da suke yi a cikin motar tana da tabbacin ba'a tab'a mata irinshi ba, tambayar ta sake maimaitawa a zuciyarta:-


"wai ke Pherty yaushe zakiyi aure?".

Bata yi niyyar amsawa ba sai ma gyara zamanta da tayi tana mai dawo da kallonta gefenta inda Ummu Abdoul ke zaune, ita ma sanye take da atamfarta da mayafi k'ato irin na Lubiee, kallon da Ummu Abdoul ke yi wa Pherty shi ya tabbatar mata ita ma jira take taji amsar da zata bayar, abun dariya ya bata hakan ya sa ta sake dariyar da duk suka tsaya kallonta cike da mamaki.

Bata kai ga basu amsa ba suka ji dirin jeep grand cherokee fara k'al da ya doso su, kyakkyawar matashiya ce ke tuk'a motar hankali kwance sanye da shade ray-ban, d'an kwali kad'ai ta d'aura a kanta da doguwar rigar kantin da yake jikinta, murmushi ne fal fuskarta da alamu cike take da farinciki, ba kowa ba ce illa Miemiebee 'yar k'walisa, kyakkyawa ce dan ko ta had'e rai bazaka iya hango muninta ba duk nacinka, shekarunta bazai yi sama da ashirin da d'aya ba dan jikinta ya nuna yanzu take cikin k'uruciyarta. 

Batool ce zaune gefenta tana taya Miemiebee darawa, hannunta ta d'aura daidai bakinta tana rufewa dan dariyar kada ya fito sosai, sanye take da doguwar after dress tayi rolling da bak'in d'an kwalin abayar, dimples d'inta shi yafi komai kyau a jikinta, ba fara ba ce kuma kyawunta bai taka kara ya karya ba, zafin jininta da kud'in da Allah ya bawa mahaifinta shi yasa take haskawa cikin 'yan mata. Rufaida da ke zaune baya tace:-


"banson tsokana, yau dai zanji taku BADAK'ALAR tunda Ummu Abdoul ta nemi zama damu nima in samu na tsokana" 

Sai da ta juya idanunta da tafi ji dasu dan manya ne sannan ta gyara mayafinta da ya fad'o wuyanta ta cigaba:-


"ni dai nawa sai naji na kowa" 


basu tanka ta ba suka fito zuwa wurin motar Pherty da take tsaye tana jiran isowarsu. Tun kafin su iso Pherty take cewa:-


"wai wannan 'yar yarabawan bata iso ba har yanzu?".

Basu amsata ba sai ma rungumar da suka yiwa Ummu Abdoul da Lubiee cike da jin dad'in ganinsu, sai da suka gama gaisawa sannan Miemiebee ta iso wurin Pherty tana mai zare gilashinta, rungumarta tayi sannan tace:-


"wacece 'yar yarabawa kuma?" 


Tsaki Pherty ta ja ta mayar da k'ofar motarta tasa key ba tare da ta amsa ba, Batool da ke can wurin Lubiee tace:-


"ke ma da banzar tambaya, waye in ba Benazir ba? Kin sani sarai basu shiri". 

Ummu Abdoul ce ta dakatar dasu da cewa:-


"Rufaida shige gaba ki kaimu, ke kikasan kan wurin, ni da kun bi shawarata ba nan zamu zo ba, ga motoci da yawa da alamu za'ayi hayaniya". 


Rufaida ta kad'a kai tana mai d'aga kafad'arta da wuyarta sama tana cewa:-


"ni nasan inda na kawo mu, babu wanda zai d'aga mana hankali, matured mutane ke zuwa nan, tsabar yanda nake zuwa nan k'ira kawai nake ince ayi arranging min table zanzo by so so time, just like yanda nayi yau, in nuna muku nasan wurin nan ciki da bai, kun sanni sarai banson hayaniya" 

Ta rik'o hannun Ummu Abdoul tana cewa ku shigo ku gani. Direct wurin da aka tanadar musu aka kaisu, sai da suka wuce tafkeken swimming pool da yake tsakiyar wurin sannan suka isa mazauninsu, kujeru ne a jere guda bakwai sai doguwar table da ke tsakiya, jan kujerun sukayi dukka suka zauna, basu d'auki sakanni goma ba aka kawo musu soft drinks masu sanyi kamar yanda Rufaida ta buk'ata. Babu mutane da yawa, hakan yasa suka saki jikinsu suna mai hira tsakaninsu.

BENAZIR


Shigowarta Cubana kenan tayi parking ta fito rik'e da jakarta a hannun dama, makullinta kuma a hannunta na hagu, shigen yarabawa tayi leshi yellow riga da zani, ta d'aura zanin bisa k'atuwar rigarta da babu shape bare style, d'an guntu ne zanin hakan yasa ana iya kallon saman idon sahunta, kad'an ya rage ba a kai ga hango gwiwarta ba, direct ciki ta shige tana mai waige-waige dan neman 'yan uwan nata, ma'aikaciyar da ta tunkarota tun kafin ta kai ga magana Benazir ta d'aga mata hannu alamar ta k'yaleta, waige-waigenta bai zauna a banza ba, dan kuwa ta hango Lubiee da abokiyar fad'arta Pherty.

Da hanzari ta iso su ta ja kujerar da taga babu kowa akai ta zauna sannan tace:-


"sorry am late, event na k'awata naje, ko gida banje na cire kayan ba kun gani" 


Ummu Abdoul da ta gyara zama tana shirin magana Benazir ta dakatar da ita da cewa:-


"ohh Madam, mantawa nayi, Assalam alaikum" sai sannan Miemiebee da Batool suka kwashe da dariya, Pherty kuwa tab'e baki tayi tana mai kawar da kai gefe dan ta tsani d'agun kan Benazir, Rufaida gimtse nata dariyar tayi dan suna shiri da Benazir bazata so bata haushi ba.

Ai kuwa Benazir ta hayayyak'o zata fara masifa Lubiee ta rik'e hannunta ta mayar da ita mazauninta tana cewa:-


"you are late, k'arfe hud'u da rabi yanzu, just sit muyi abinda ya kawo mu". 


Nutsuwa sukayi suna mai mik'awa Uwar gayyar hankulansu, ita kuwa ta murmusa tace:-


"tunda ni na tara mu anan, ni ya dace in fara baku LABARINA sannan inji naku, kun dai san abinda yasa na bada shawarar had'uwarmu anan, so ku bani had'in kai"


Sun bada goyon bayansu d'ari bisa d'ari hakan yasa Ummu Abdoul farawa da cewa:-

"Sunana Safiyya Ummu Abdoul kamar yanda kuka sani, asalina 'yar jihar Taraba ce, a can aka haifeni, a can nayi makarantar primary har da secondary, na gama secondary ina shekara goma-sha-takwas. Alal hak'ik'a mahaifina ba mai tarin dukiya bane saboda baiyi boko ba sai d'an buga-buga da yakeyi, a hakan muke samun na cin yau da gobe, a hakan na samu nayi makarantar boko, Baba yayi k'ok'arin sa k'annena uku da Allah ya bani a boko har ma da islamiya. 


Ni ce babba, kuma bayan haka akwai tazara tsakanina da k'annena, k'anwata da ke bina shekararta goma-sha-uku na gama secondary school, sai mabiyinta da ke shekara goma, sai kuma autarmu da take shekara tak'was. Tun da na fara wayo aka sa ni makarantar islamiya, a lokacin bazan wuce shekara uku zuwa hud'u ba, Allah yayi ni da baki da saurin d'aukar abu, hakan yasa iyayena suka kwad'aitu da sani islamiya ko Allah zai sa in iya karatun addinina tun ina k'arama.


Allah kuwa ya dubi zuciyarsu yasa min son wannan karatun, tun karatuna baya fita sosai saboda ban k'ware a magana ba har ya fara fita tangararau, karatun Qur'an kawai ake yi min a lokacin, daga baya aka fara koya min huruful hija'iyya sannan na gangaro d'aukan litattafai, wasa-wasa nake d'aukan karatu har na kai shekara tak'was, a wannan lokacin ne aka kawo mana harshen turanci wato ENGLISH a islamiyarmu, na wahala matuk'a sannan na iya kamo 'yan ajinmu a wannan fannin, duk da haka ina daga cikin balidayen wannan subject d'in, dan yawancin 'yan ajin suna boko ni kuwa a fannin karatun boko zero nake.

Tun abun baya damuna har na fara damuwa, kullum bani da wata magana a gida sai a sani boko, wani lokaci har da kukana amma duk hakan baiyi anfani ba, Mama kullum cikin rarrashi da ban baki, babu dama in fita islamiya in dawo sai na dawo da maganar nan a bakina, kuma bazan manta ba sai safiya in na fita na samu k'awayena, nan zamu shiga wasa har in manta da batun boko.


 A kwana a tashi tun Baba na tunanin zan daina maganar boko amma abu sai gaba yake, akwai ranar da bazan tab'a mantawa ba a rayuwata, mafarki nayi ina islamiya k'awayena suna min dariyar turancina, a firgice na tashi zuciyata kamar ta fashe dan bak'in ciki, bansan k'arfe nawa bane nidai kawai nasan ina kwance har aka k'ira asuba, banyi motsi ba ina kwance kan katifana ina mai zubar da hawaye har mama tazo dan ta tashe ni inyi sallah.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


              2


       Shesshek'ar kukana taji tun daga bakin k'ofa, da hanzari ta shigo dan abun ya bata mamaki, tunanin meh ya tasheni takeyi har ta shigo, a ranta kuwa sai fad'i take "Safiya da bata son tashi asuba sai an had'a da kwara mata ruwar sanyi yau ita ce ta farka har taji tsoro tana kuka, ko dai mafarki tayi?". 


Zama tayi a gefena ta janye bargon da na rufe jikina har zuwa kaina, jajayen idanuna na bud'e a hankali ina kallonta hawaye na sake kwararo min, janyo ni Mama tayi zuwa jikinta cike da mamakin ganin idanuna a kumbure da alamu na dad'e ina wannan kukan. Ajiye kaina tayi a cinyarta tana shafa bayana fuskana na saitin cikinta, ban daina kukan ba hakan yasa tace:


"gani, ki daina tsoro, babu abunda zai kama ki, mafarki kikayi? Bakya addu'a dama taya ba za kiyi mugun mafarki ba, gobe kiyi addu'a babu abunda zai zo miki a mafarki kinji?".

Rik'e hannunta nayi nace:


"K'awayena kullum sai sun min dariyar turancina, a islamiya basu barni ba yanzu har mafarkina suke zuwa, Ku sani a boko kunk'i" kuka na sake mai sauti dan har cikin raina inason boko, dak'yar ta rarrasheni nayi sallah ita ma tayi nata sallahr ta dawo d'akina. Kwanciya tayi gefena a d'an katifana tana shafa kaina ina sauk'ar da ajiyar zuciya had'e da matsar k'walla a hankali.

Har gari ya fara haske banyi bacci ba kuma ban daina kukan ba, muryar k'anwata Firdausi(Feedoh) 'yar shekara d'aya da rabi naji tana kuka daga d'akin Mama, hakan yasa Mama ta tashi dan ta d'aukota, a hanya suka had'u da Baba rik'e da ita, bansan maganar da sukayi ba sai ganin Baba nayi ya shigo d'akin.


Tashi nayi na sauk'o daga katifana na gaishe da Baba da yake tsaye yana kallona, janyo jakar kayana da yake gefensa yayi ya zauna a kai sannan ya amsa, kaina a k'asa ina kallon simintin da aka filaste cikin d'akin, jira nake inji meh zai ce min, a d'aya b'angaren ina addu'ar Allah yasa ya yadda ya kai ni boko. 


"Boko kikeso? Meh yasa baki da hak'uri ne? Tun ranar da aka haifeki na d'au alwashin baki duk abinda kikeso daidai gwargwado a matsayina na uba, so kike ki nuna min na gaza? Kinsan irin fafutukar da nake yi na neman halal dan in sa ki a wannan bokon da kika k'wallafa rai? Tun ranar da kika fara maganar kinason boko nake iya k'ok'arina dan in samo kud'in da zan saki, kasuwa ba tafiya yakeyi ba, yarinya ce ke bazaki gane abunda nake fad'a miki ba, amma ina rok'on ki da ki daina tada mana hankali, bokon nan da yardar Allah zan sa ki har ki gama amma sai kin nuna min kina da hak'uri kamar uwata, takwararki akwai hak'uri".

Sai da ya gama nasihar sa da fad'arsa sannan nace:


"Baba bazan sake maganar ba, zanyi hak'uri har Allah ya bud'a mana"


"Yauwa Mamana, kiyi mana addu'a kinji, insha Allah zaki samu abinda kikeso, kuma kiyi k'ok'arin sa kai a wanda ake yi miki a islamiya dan ki samu ki kamo sa'anninki in na samu na sa ki a bokon, kinji?". A haka muka gama maganar ya bar d'akin ni kuwa na mik'e a kan gadona sai bacci, ban tashi ba sai da Mama ta tasheni don cin abinci.

Tun daga ranar ban sake maganar boko ba, ko a fuskata bana nuna damuwata, kuma a islamiya sosai nake mayar da hankalina ina koyar English, har ya kai ga malamin da yake koyar damu ya gano ina masifar son boko hakan yasa ya nemi yana koyar dani ni d'aya da safe a lokacin da ake koyar da matan aure, gidanshi da islamiyar namu babu nisa, a kullum idan na iso ni nake zuwa har gida in sanar dashi isowata. 


A lokacin ya gama degree d'insa kenan yana neman aiki, yana da yara biyu da matarsa kuma 'yar uwarsa Sadiya(anty jegal), auren dangi akayi musu tun yana aji uku a makarantar gaba da secondary (university), sosai matarsa take sona, wani lokaci bata barinsa ya koyar dani a cikin islamiya sai dai in shigo har cikin gida ya koyar dani, tabarma zata shimfid'a mana a k'ark'ashin bishiyar dake cikin gidan mu zauna yana koyar dani ita kuma tana aikin gida, wasu lokutan ta zauna kusa damu tana sak'ar kurashi a cewarta da zaman banza gwanda ta samu abun yi.


A kwana a tashi har ya kai ga ya daina koyar dani a Islamiya sai a gidansa, ya kan had'ani da yaransa yana koyar damu a tare, duk wasu subjects da ake koyar da 'yan primary babu wanda Malam Usman baya koyar dani, aikin alkhairin da yake min yasa Baba ya nemesa har sukayi sabo, mutunci sosai sukeyi har Mama na zuwa wurin matarsa duk da Mama ta girme mata.


A lokacin da na cika shekara goma-sha-biyu Malam Usman ya nemi Baba da maganar sa ni a secondary school, Baba baiyi jayayya ba ya d'auko kud'in da yake tarawa ya damk'a masa akan ya sani a bokon, k'anwata Feedoh kuma ta cigaba da zuwa Islamiya sannan kamar yanda ya koyar dani haka zai koyar da ita. Cuku-cuku yayi min ya biya min kud'in zana jarabawar fita daga primary, shi ya koyar dani har na samu na rubuta kuma da yardar Allah na haye. 


Ina shekara goma-sha-hud'u na zana JSSCE sakamakon tsallaken jss 2 da nayi. Cikin sa'a na fara ss1, sosai Malam Usman ya taimakeni har na kammala secondary school a shekara goma-sha-bakwai. Ban samu Mathematics ba a lokacin da naga sakamakon jarabawata, sosai nayi bak'in ciki har da k'walla na zubda, Baba da malam Usman su suka rarrasheni har zuwa shekara na gaba Baba ya biya rabi Malam Usman ya biya rabi dan a lokacin yana aikinsa kuma yana samun albashi mai tsoka.


Na rubuta jamb haka zalika na sake rubuta waec, a lokacin da sakamako ya fito naga na ci ba k'aramin murna nayi ba, Baba sosai yayi murna yana mai yi min addu'an samun nasara a rayuwata. Ban sha wahalar samun kud'in hada-hadar neman makaranta ba don Allah ya bud'awa Baba a lokacin, ya bud'e shagon sayar da kayan masarufi madaidaici a bakin kasuwa. Malam Usman shi ya nemo min addmission a B.U.K na samu karantar accounting, a shekara biyar na kammala komai duk da course d'ina na shekara hud'u ne.


Results d'ina yayi kyau matuk'a hakan yasa gwamnati ta d'auki nauyin masters dina a Turkey, bayyana muku irin farincikin da mukayi b'ata baki ne, dan kuka na zauna na fara yiwa Mama, tun tana bani hak'uri har ita ma ta fara zubar da hawaye dan maganganun da nakeyi akan rahamar da ubangiji yayi min, Feedoh da take rik'e da littafin makarantarta tana karatu lokacin da na shigo kallonmu ta tsaya yi, ganin abun namu ba na k'arewa ba yasa ta cewa:- 


"Haba dan Allah! Wai meh hakan? Ni da kika k'irani a waya kika fad'a min rawa nayi mai isata na tara sauran in kinzo mu danse tare, kuma haka kawai sai kiyi ta rusa kuka kamar anyi mana mutuwa?" 

Ban saurareta ba haka zalika Mama bata tanka ta ba, karatunta ta cigaba da yi dan ta kusa fara NECO, ni kuwa na cigaba da kukana daga k'arshe godiya na fara yi wa mahaliccina ina "Alhamdulillah" sau ba adadi sannan na dire da yin addu'ar Allah ya bani ikon binsa dan ina tsoron wata rana in butulce masa in zama tab'ab'b'iya in manta yawan rahamarsa gareni, irin addu'ar da nakeyi shi ya k'ara sa Mama hawaye, a haka Baba ya shigo ya same mu Malam Usman na binsa a baya.


Nasiha Baba yayi min mai shiga jiki akan rahamar da Allah yayi min, ya k'ara tunatar dani karatun Qur'ani da Sallah, ya jaddada min rik'e addini a duk inda zan samu kaina, sosai nayi kuka ranar, dan cikin nasihar da Baba yayi min babu inda bai tuno min ba, mutuwa, kabari, sirad'i da duk wani azabar da aka tanadarwa wanda yak'i bin mahaliccinsa. Daga k'arshe kowa ya watse na shiga d'akina nayi sallah raka'a biyu dan nuna godiyata ga Allah, ban tashi daga abun sallahr ba sai da k'anina Mus'ab da Autar hajiya suka shigo don tayani murna, hira sosai mukayi har Feedoh ta shigo ta same mu tana mai lissafa min irin murnar da zatayi in hakan ya same ta, a ganinta kuka ba nawa bane.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


           3


Duniya juyi-juyi, yau gani ga fararen fatar da nake gani a talabijin, yaren da ko a tv akeyi ina mamakinsa sai gani yau anayi a gabana ina ji da kunnena, gidajen da ban tab'a ganin irinsu ba sai a TV yau gani ga su har tab'awa zan iya yi, k'auyancina kaf sai da na gama a hanya kafin mu isa masauk'inmu, da yake ba ni d'aya aka bawa wannan scholarship d'in ba, a k'alla mun kai talatin. Sauran 'yan uwan nawa duk k'ok'arin b'oye k'auyancinsu suke don kada ayi musu dariya, ni kuwa ban damu ba sai kalle-kalle nakeyi, k'atuwar mota dama muka shiga kuma ina dab da driver, duk abinda na gani wanda ban sani ba sai na tambaya, ko ince wow! Nima ala dole zanyi na turawa daga k'arshe na kasa na turawan na koma lahh kalli abun nan, sosai na sa su dariya har su ma suka zage muka fara maganar kyawun garin da yarenmu ta Hausa.

Tunda na fara shiga makarantar ban tab'a samun matsala ba, turancin da ban saba yinsa da mutane ba shi ke d'an bani wahala duk da a da ina matuk'ar son magana da turanci dan inaso ya zauna a bakina rad'au. Sannu a hankali na fara sabawa har nayi wata d'aya cikin watanni tara da zanyi a makarantar. Kamar kullum ina zaune akan wani benci da ke tsakiyar makaranta, anan nake zama duk lokacin da na gama lectures d'ina sai yamma in isa gidan da aka kama mana a gefen makaranta. 

Jakana da ke gefena na d'auko na cire wayana na sake mayar da jakar na dai-daitasa akan bencin, sosai nake ji da jakar dan Anty Jegal(Sadiya matar Malam Usman) ce ta bani, wayata na d'auko techno sunanta, 'yar k'arama ce sosai, keypad d'inta ja bayanta kuma silver, da zan baro Nigeria ne Baba ya saya min sabuwa dal, nawa kuma na bawa Feedoh, bai barni a haka ba dan sai da ya bawa Malam Usman kud'i ya canjo min dan in rik'e a hannuna.

Layin Feedoh na dannawa k'ira na d'aura a kunnena, dai-dai ya fara ringing naji sauk'ar ruwa a fuskata zuwa jikina, Allah ya taimakeni bai tab'a wayata ba hakan yasa na matsar da wayar gefe ina mai goge ruwan fuskata da hannuna dan in samu bud'e idanuwana da na runtse. Tun kafin in kai ga hakan naji muryarsa yana cewa "am very sorry", da hanzari na bud'e idon dan ganin wanda yayi min irin wannan wulak'ancin, fitowarsa daga motar kenan yana tunkaro ni fuskarsa cike da damuwa.

Cikin motar tasa na kai dubana jin ana dariya, so nake in gane ni yake yiwa wannan dariyar ko kuwa? Saurayi ne dan bazai wuce shekaru ashirin da bakwai ba, kalar fatarsa shi ya bani tabbacin d'an Africa ne, dariya yake tsakaninsa da Allah kamar ya samu comedy movie yana kallo. Muryar wannan da ya fito daga motar naji hakan ya sa na dawo da dubana gareshi, shima da ganinsa d'an Africa ne dan bak'i ne, sai dai samun hutu yasa ya d'an k'ara haske, hak'uri ya fara bani da harshen turanci, rashin amsa shi da banyi ba yasa ya nuna wannan saurayin da ke cikin motar yana cewa "duk laifinsa ne, shi ya canja mana drinks, ina sawa a bakina naji wanda banaso ne shine na sauk'e glass na zubar".

Sai a sannan nazo wuya, abun bakinsa ya kwara min a jikina? Bansan lokacin da na fashe da kuka ba dan takaici, dama ni abu kad'an ke sani kuka, duk a ganina dan sunga ni talaka ce maras gata shiyasa suka min wannan wulak'ancin. Duk tsayawa sukayi suna kallona dan basu zaci hakan zanyi ba, wanda ke gefena kam kasa magana yayi, na cikin motar ne ya fito ya iso inda nake ya zauna a gefena sannan yace "Malama Safiyya, kiyi hak'uri kiyi mana uzuri, tsokana ne kawai irin na abokina dan yanason kiyi masa magana".

A take naji kukan da nakeyi ya tsaya dan ban d'auka sun iya Hausa ba, kallon mamakin da nake yi masa shi yasa ya d'an murmusa sannan yace "sunana Mubarak Hassan, daga Nigeria nake kuma munzo duba sistarmu ce anan school d'in" ya nuna abokinsa da har yanzu yake tsaye yana kallonmu yace "sunansa Muhammad Yunus ana k'iransa Abba, kuma shi ya kawo mu hanyar nan ma dan kawai ya ganki".

Kallon Muhammad d'in nayi dan ni ban fahimcesu ba, Mubarak ne ya sake cewa "kink'i mana magana tunda muka zo, ko har yanzu fushi kike dan mun watsa miki ruwa? Kinsan kowa da nashi salon had'uwa da mutane, sati d'aya yanzu muna ganinki anan kina waya, da farko munyi zaton matar aure ce ke ganin kullum sai kinyi waya kina smiling, amma da muka zo kusa sai muka fuskanci da 'yan gidanku kikeyi, hakan ya bamu k'arfin gwiwar tunkarar ki, sai dai da muka tambayi wani course mate naki sai yake fad'a mana bakya sauraran samari, dalilin hakan yasa Abba ya k'irk'iro idean neman tsokana, a tak'aice dai anan wurin course mate naki muka san sunanki kuma anan muka san daga Nigeria kike". 

D'ago fuskarsa yayi ya kalli abokinsa sannan yace "kai fa ya dace kayi mata duk wannan zantukan tunda kai ka gani kace kana so". Murmushi kawai yayi yana mai kallon fuskata, tsugunawa yayi a saitina ya langwab'ar da kai "am sorry, na d'auka in nayi miki haka zakiyi min masifa, ta hakan kuma nake sa ran zan samu in shawo kanki muyi shiri har in samu damar karantarki sannan in kawo miki k'ok'on barana, ashe nayi kuskure, bazan sake watsa miki ruwa da gangan ba, nidai kukan da kikayi duk shi ya kashe min jiki, kiyi min afuwa ki fuskanci yanayin da nake ciki, sonki ne yasa".

Kallonsa nayi fuskana babu yabo ba fallasa dan na gaji da jin zancensu da ba gane kansa nakeyi ba. "ba damuwa" nace masa, ban k'ara komai akan hakan ba na d'auki jakana na fara tafiya, sai a sannan na tuna na k'ira Feedoh, da hanzari na duba wayar naga munyi mintuna biyar da 'yan kai sannan ta kashe, ciki-ciki nayi tsaki ina mai cigaba da tafiyana.

Sai da na isa d'akinmu sannan na samu na sake k'iran Feedoh, ko sallamar da na mata bata amsani ba ta fara mitar abunda taji d'azu, "matsalata dake kenan saurin kuka, ya za'ayi a watsa miki ruwa bazaki kare kanki ba kin wani zauna kina musu kuka salon su k'ara raina ki, ai na tsaya inji kin zama mutum ne ko a yanda kike baki sauya ba, ai wallahi da ni ce yau sai sunga abun da yafi hauka". Tsaki na ja na d'auke maganar da tambayan ina Baba, sai da na gaisa da Hajiya da sauran k'annena sannan mukayi sallama.

Farkon had'uwa na da Abba mahaifin Abdoul d'ina kenan, nacin da yayi min shi yasa na kasa d'auke hankalina akansa, sati ya jera yana zuwa inda nake, inda bana tsammanin yasan ina zuwa a can watarana nake ganinsa yaje nemana, tun ina sharesa har ya samu hanyar da ni kaina na rasa gane ta inda ya samota, sai gani tsundum cikin soyayyar Muhammad wato Abba. 

Lokacin komawarsa gida Nigeria yayi dai-dai da watanni bakwai da nayi a makaranta, saura min wata uku in gama in koma gida kenan. Tsaftatacciyar soyayya mukeyi cike da son mallakar juna, ban tab'a tsammanin zan fad'a kogin so irin yanda na fad'a yanzu ba, ko da yake Abba ya kai shiyasa na mace akansa. Komawarsa Nigeria bai hana mu soyewa ba, kusan kullum sai munyi waya muna k'ara jaddadawa juna son kasancewa da juna tare da d'umbin alk'awuran da dukkan masoya suka saba yi a yayin da suke shauk'in so.

Abba asalin d'an Funtua ne jihar Katsina, yana aiki a cikin federal university na Katsina, shekarunsa ashirin da tara, bafulatani ne amma bak'i har wani lokacin ina tsokanarsa "bak'in bafulatani", a tak'aice dai Abba ya cika namijin da baza a kushe ba, namiji ne da kowace mace zata so kasancewa dashi a matsayin mijin aurenta, shiyasa na amince dashi kuma na bashi ragamar soyayyata. 

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


          4


Wata uku kamar wasa yau na gama komai na makaranta sai shirin dawowa, sosai nayi d'okin dawowa dan ban tab'a nesa da gida haka ba, tun saura sati na fara yawo cikin gari dan na tabbata bazan sake dawowa ba, in ban lek'a ba za'a lek'a babu ni. 'Yan canjina da nake k'in kashewa su na samu nayi 'yan tsarabana iya wanda zan iya, a hakan nayi tattare na sai Nigeria my mother land.

A Abuja muka sauk'a da misalin k'arfe hud'u, ina sauk'owa daga jirgi ni'imtaccen iskarmu ta Nigeria na fara shak'a, har cikin raina naji sanyi ina mai godiya ga Allah, direct inda zamu kwana aka kaimu sai washe-gari muka isa Taraba. Malam Usman ne yazo d'aukana a motarsa dan na sanar dashi inda zamu sauk'a a wayar coursemate dina. Feedoh na fara hangowa da d'an sassarfa na isa wurinta na rungume, ji nake kamar in fashe da kuka dan farinciki, bayan mun gama murnar ganin juna da d'an gaishe-gaishenmu muka wuce gida bayan na sa jakana a mota.

Da gudu na shigo gida cike da murna da d'okin ganin Baba da hajiyata, a take na ja birki farincikina da d'okin duk ya gushe, ganin Baba nayi kwance a bakin k'ofar mama akan katifa an d'aura masa ruwa, bugun zuciyata ya tsananta na kasa k'arasawa inda yake, Feedoh da ke bayana ita tayi min jagora har inda yake tana rik'e da hannunah. Tsugunawa nayi a gefensa na d'aura gwiwowina a k'asa, jikina duk ba laka dan banyi tunanin zanga Baba cikin wannan halin ba, duk wayana da Feedoh a kwanakin nan bata tab'a ce min Baba bayi da lafiya ba, haka zalika duk lokacin da na tambayeta dan ta bani shi mu gaisa k'aryar baya nan take min ko kuma tace yana bacci, "meh yasa zata min haka?".

Hawaye naji ya sauk'o min ina mai kallon fuskar Baba da yake bacci, hannunsa na kamo na damk'e na kai shi fuskata ina mai zubar da hawaye, Hajiya naji tace "tashi ki barsa yayi bacci" had'e da shafa bayana, tashi nayi na rungumeta kuka mai sauti ya kufce min, sai da muka shigo d'akinta ta ajiyeni gefen gado sannan na samu damar tambayarta, can ciki nace "meh yasa kuka b'oye min Baba ba lafiya?". Bata amsani ba sai janyo ni da tayi zuwa jikinta ta d'aura kaina bisa cinyarta tana shafa bayana alamar rarrashi, sai da na gama kukana sannan tace "rashin lafiyan nasa ne farat d'aya, munje asibiti wai basu gane meh ke damunsa ba, kuma maganar rashin gaya miki shi ya hana dan kada ki tada hankalinki".

Muryar Baba naji cikin ciwo yana k'iran sunana, ban samu na amsa mata ba bare in k'ara mata wasu tambayoyin da ya dace insan amsar su na fice, ganina da yayi yasa ya fad'ad'a murmushinsa had'e da mik'o min hannunsa, a guje na isa inda yake ina mai sake sabon kuka, hannuna ya rik'e murmushin fuskarsa bai b'ace ba. Dan kaina nayi shiru na samu damar gaishe sa had'e da tambayarsa yaya jiki, sosai yake k'ok'arin bud'e baki yayi min magana yana tambayana yaya makaranta tare da min fatan alkhairi. 

Washe-gari tun safe na fice dan fara fafutukar neman aiki saboda in samu kud'in da zan kai Baba asibiti mai kyau, sosai nake son mahaifina yaji dad'in bokon da nayi dan tabbas ya wahala, rashin sanin inda zan fara neman aikin yasa nayi lik'is a gari ban tsinana komai ba. A hanyata na dawowa na bi gidan Malam Usman dan in gaida Anty Jegal da 'ya'yanta, da farincikina na iso gidan cike da d'oki, sabo da soyayyar da yake tsakaninmu yana da yawa, shiyasa tun da na tunkaro gidan bakina ya kasa rufuwa, haka zalika k'afafuna naji kamar bazasu kai ni gidan ba, ko sallamar da na doka ban jira an amsa ba na sa kai cikin gidan.

Zaune take a k'ark'ashin bishiyar da ke tsakiyar gidan, duk da an zuba interlock an gyara cikin gidan bai sa an cire bishiyar ba, da gudu na isa na rungumeta ina mai dariyar farincikin ganinta, yankan Alayyahu takeyi ko kallona bata yi ba bare in samu tarbar da nake tunani zan samu a wurinta.

Saketa na fara yi a hankali dan damk'eta nayi kamar na samu 'yata da ta b'ata, kallon fuskarta nayi sannan na matsa gefe ina mai gyaran gyalena da ya fad'o k'asa. Can ciki ta amsa gaisuwar da nake mata ta tashi ta shige kitchen ta barni a inda nake cike da zullumin abinda nayi mata, iya tunani na ban mata laifin komai ba kuma da akwai abinda ya had'ata da su Feedoh na tabbata zanji labari. Gajiya nayi da zama na tashi na isa kitchen nayi mata sallama sannan na wuce gida.

Har na isa gida abinda yake yawo a kaina kenan, tambayoyi ne masu yawa a bakina amma na rasa wa zan samu ya amsa min. Har dare yayi muka kwanta ban samu amsar tambayoyina ba hakan yasa na tab'o Feedoh ina cewa "kinyi bacci ne?" "Um-um, meh ya faru?" Tashi nayi na zauna ina mai fuskantar ta dan in samu fahimtar abubuwa daga fuskarta, kai tsaye na tambayeta "meh ya had'aku da Anty Jegal? Ina nufin meh ya faru da bana nan tsakaninku?".

Tashi tayi ta zauna fuskarta bai nuna min abinda nakeson gani ba, murmushi tayi sannan tace "meh ya had'aku dai zance, yanda kika ga ta canja miki haka nima rana d'aya ta canja min, sai daga baya nakeji a wurin 'yarta Futha ashe Malam Usman kishiya yakeson yi mata da ke, wai shi sonki yake yana son ya aureki, a ganinta kin munafurce ta. Yanzu maganar da nake miki ke ake jira dama ki dawo aji daga bakinki, rashin lafiyan Baba ne ma yasa Malam Usman yace kada a miki magana sai Baba ya samu lafiya".

Tsanantan bugun zuciyata da fad'uwar gaba shi ya haddasa min ciwon kai farat d'aya, tsoro, firgici babu wanda ban shiga ba a wannan lokacin, sauran zancen nata duk ban samu daman fahimtarsu ba, naji dai tace min "mu gama maganar gobe" bansan lokacin da na samu kaina akan filona ba, bacci b'arawo shi ya sace ni a ranar, sai ganin hasken safiya da nayi a fuskata, da yake ina fashin sallah kuma Feedoh tasan da haka shiyasa bata tasheni ba.

Hijabi na zura na d'auki pad na sa shi cikin hijabina na fito na d'auki buta na shiga ban-d'aki, sai da na gama kimtsawa na fito na ajiye butar na shiga d'akin Hajiya dan duba lafiyar Baba. Bayan mun gama gaisawa na fito na samu Feedoh na sharar tsakar gida ni kuma na wuce kitchen dan d'aura kumallon safe. A yau dai nayi da na sanin zuwa Turkey karatu, da zama nayi a gida na fara aiki a wannan shekara d'ayar da mun fita daga wannan talaucin da muke ciki, da Baba yanzu baya kwance a gida yana jinya Hajiya kuma na d'aura kayan miya tana sayarwa dan rik'e gida, da ba dan malam Usman ba ina mai tabbatar muku k'annena da sun dad'e da tsufa a gida babu makaranta, shagon Baba da yake bakin kasuwa yanzu a rufe yake an kasa zuba komai, shi kad'ai ne mallakarmu sai kuma gidan da Allah ya rufa mana asiri ya bamu.

Sai da na bawa kowa abinci sannan na d'auki mayafina na fita da purse na Feedoh bayan na duba akwai 'yan canji a ciki. Wurin sayar da sim na nufa, mai arahar ciki na samu d'ari biyu aka bani sim had'e da yi min register, ban b'ata lokaci ba na dawo gida na shige k'uryar d'aki nasa sim d'ina na kunna, katin da na sayo na loda sannan na d'auko jakata na d'auko takaddan da na rubuta lambar Abba, bayan na kofe na danna k'ira ko saving banyi ba, turancin network naji suna ce min sim dina baiyi register ba, tsaki na ja na mayar da takaddan na gyara zamana nayi saving lambar sannan na k'ara k'ira, abunda suka fada min suka sake maimaitawa hakan yasa na wurgar da wayar akan gado na rik'e kaina da dukkan hannayena ina tunanin mafita.

Wayar bai shiga ba sai bayan azahar, na gama cin abincin rana kenan na sake gwadawa, ban d'auka zai shiga ba naji anyi min tallar callertune nasa sannan naji addu'ar larabci na tashi matsayin callertune nasa, bansan lokacin da na hangame baki ina murmushi ba, sai dai kayan takaici bai d'aga ba har ya tsinke, sau biyu na k'irasa bai d'aga ba na ajiye wayar na kwanta zuciyata a cunkushe.

Minti biyar da ajiye wayar naji ya fara ringing, da hanzari na duba naga Abba ne na kara a kunne na bayan na d'auka k'iran. "Assalamu alaikum" na furta a hankali, a gajarce yace "wa alaikis salam", yanda ya amsa min nayi tunanin bai gane ni bane hakan yasa nace "Safiyyah ce", kai tsaye yace "na gane muryar, lafiya?" Wayar na ciro daga kunnena na duba lambar sannan na sake mayarwa nace "meh ya faru kake min magana haka?".

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


        5


"Safiyya ni kika share haka? In k'iraki ma kik'i d'auka, kik'i k'irana in kin ga missed calls d'ina, yau sati d'aya kenan rabon da muyi magana" ajiyar zuciya na sauk'e dan ban d'auka duk had'e ran da yayi min akan hakan bane, hak'uri na basa had'e da fad'a masa uzurina kuma ya fahimceni. Sai da muka gama gaisawa sannan na sanar dashi Baba bayi da lafiya, addu'ar k'arin lafiya yayi had'e da yi min alk'awarin zuwa washe gari tunda zai kasance jumma'a. Sosai nayi murna dan inason ya iso gida a san dashi saboda maganar Malam Usman ya mutu ba tare da sun tunkareni in kasa ce musu a'a ba.

Washe gari,


Da yamma lik'is ya iso Taraba, a gidan k'anin Babansa ya sauk'a yaci abinci yayi wanka sannan yayi sallah. Bai b'ata lokaci ba ya shigo anguwarmu da taimakon kwatancena, a bakin layi ya tsaya dan a can nace ya tsaya zan fito ya ganni sai ya k'araso, k'irana yayi ya sanar dani isowarsa, hijabi na d'auka na fito nace wa Hajiya zan shigo da bak'o, Baba da yake kwance gefenta ya kalleni yana neman k'arin bayani, ficewa nayi ina kallon Feedoh alamar in na fita ta fad'a masa kamar yanda mukayi.

Haka kuwa akayi, kafin in shigo da Abba ta sanar da Baba shine wanda nakeson in aura, tak'aitaccen labarinsa ta bashi kamar yanda na fad'a mata jiya da muke had'a yanda zamuyi akan Malam Usman, a gaskiya ni bazan iya auransa ba ko dan Anty Jegal. Suna kan maganar suka ji sallamar mu, tabarma Hajiya ta d'auko ta shimfid'a tana mai yi masa sannu da zuwa.


Autar Hajiya ce ta shigo a guje ta bayanmu kamar an biyota, saura kad'an ta buge Abba da yake shirin zama akan tabarmar da Hajiya ta shimfid'a masa, birki ta ja ta tsaya tana kallonsa sai hak'i takeyi, dukkanmu kallonta muka tsaya yi dan dama Hajiya na nemanta ta fita ba tare da an sani ba. "Lahh! Kai ne kazo da wata mota mai kyau a k'ofar gidanmu?" Ta tambayesa tana mai rik'e k'ugunta, bata jira an amsata ba ta iso wurin Feedoh ta zauna tana cewa "anty Feedoh shine wanda rannan ya biyoki a mota kika basa lambar wayanki ko?" Mari Feedoh ta kai mata sannan Hajiya ta taso ta rik'o kunnenta ta dawo da ita inda take ta zauna, ajiyeta tayi daram a gabanta tana cewa "yau zaki fad'a min meh yasa in na hanaki abu bakya ji, ban hanaki fita waje ba shine zaki faki idonmu ki tsere?" k'ara take sakewa alamar tana jin zafin rik'on da Hajiya tayi wa kunnenta.


Abba kasa zama yayi ya tsaya kallon Auta da mamaki yana dariyar shirmenta, sai da na sake ce masa "ka zauna mana" sannan ya samu ya zauna yana dariyar dramar da Hajiya takeyi da autarta. Sai da suka gaisa da Baba sannan Hajiya ta ajiye ta a gefenta had'e da janyota kusa da ita sosai suka fara gaisawa da Abba, basu gama gaisawa ba Auta tace "ina wuni? Kazo gaishe da Baba ne?" Ta fad'i hakan tana kallon Babanmu fuskarta na nuna alamar tausayi.


"Eh" yace mata ya k'ara da cewa "yaya jikin nasa? Ya rigima kuma?" B'oye fuskarta tayi a bayan Mama ita wai taji kunya, a nan aka shiga hirar rigimar Auta ana dariya. Feedoh ce ta tashi ta kawo masa ruwa da juice d'in da suka sayo dan tarbarsa. Sai da suka d'an tab'a hira sannan ya koma gefen Baba ya zauna, ya rik'e hannunsa ya fara yi masa addu'a ahankali, bayan ya gama Baba yayi masa godiya, sannan sukayi sallama da Hajiya ya fito Auta na gefensa tana masa hira ni kuma ina biye dasu a baya.

A bakin k'ofa suka had'u da Mus'ab k'anina, hannu Abba ya basa suka gaisa sannan ya juyo ya kalleni yana cewa "Mus'ab ko?" D'aga masa kai nayi alamar eh ina mai yi masa murmushi, "ya akayi kuka fi kama dashi? Har dariyarki fa ya d'auko, dariyarsa da kamannin da na gani shiyasa nace Mus'ab ne, ashe nayi gaskiya" ya sake mik'a masa hannu yana tambayarsa ya yake "ai da yanzu tafiya zanyi baza mu had'u ba, ina kaje haka?" Yana murmushi ya amsa masa cewa "munyi sallar isha'i ne sai na tsaya a majalis d'aukan karatu, sai yanzu muka gama" "ahh yana da kyau, mu isa wurin mota mana" tare dukka muka fito ina biye dasu ina jin hirar da sukeyi.


Boot na motarsa ya bud'e ya fara ciro kayan da yake ciki, drinks ya kawo had'e da maltina da peak na mara lafiya, sai k'aton ledar da ban gane meh yake ciki ba, tare suka shigar da kayan amma shi iyakarsa zaure. Mus'ab da Auta ne suka isar har wurin Hajiya sannan suka fito wurinsa kamar yanda ya umarcesu da dawowa in sun kai. Kud'i ya basu suka k'i karb'a dan duk talaucin da muke ciki baisa mun zama masu kwad'ayi ba, kallona yayi yace "kin koya musu halin naki ko? Kice musu su karb'a dan Allah" dariya kawai nayi na kawar da kai, ganin ba karb'a zasuyi ba yasa ya janyo Mus'ab yasa masa a aljihunsa ya juya ya shige motarsa. Da ido nayi musu nuni da su shiga gida, sai da suka yi masa godiya sannan suka shige, ni kuma na tsaya a daidai k'ofar motarsa nayi masa godiya sannan mukayi sallama ya tafi.

Bayan na shiga gida naga text nasa a wayata kamar haka "ki kula da Baba, ledar nan da Mus'ab ya shiga dashi naki ne... Sai nazo gobe, bye take care!" Murmushi nayi da na karanta text d'in na tura masa sak'on godiya. Atamfofi guda biyu da turare ne a cikin ledar, sai k'aramar envelope cike da kud'i, baki na bud'e lokacin da kud'i 'yar dubu d'ai-d'ai suka zubo a cinyata, Feedoh ce kad'ai tayi murna har da cewa "nikam na bashi ke". Ni b'ata min rai yayi, dan sai da na k'irashi na nuna masa b'acin raina, hak'uri ya bani kawai tare da yi min alk'awarin bazai sake ba. Kafin ya tafi sai da ya had'ani da abokinsa dan ya taimaka min wurin neman aiki.


Ranar Lahadi ya koma Katsina tun safe bayan yazo munyi sallama, a ranar na kai Baba asibiti da kud'in da Abba ya bani, bamu samu ganin likita ba saboda yayi tafiya amma sun tabbatar mana zuwa Alhamis zamu samu ganinsa. Dubu hamsin ne cib-cib kud'in da Abba ya bani, ina da yak'inin zai taimakeni har in fara karb'an salary tunda Safwan abokin Abba ya tabbatar min ranar Monday za'a neme ni a wani private company na mahaifinsa. 


Da dare ina zaune a d'aki ina waya da Abba Hajiya ta shigo, kashe wayar nayi ba tare da nace ina zuwa ba, zama tayi gefena tana cewa "magana nazo muyi, tunda kika dawo bamu samu mun tattauna ba" murmushi nayi nace mata "gaskiya kam, rashin lafiyan Baba duk shi yasa" "eh da hakan ma, nikam wannan Abban a ina kika had'u dashi Safiyyah? Nasan kud'in da kika kai Babanki asibiti dashi d'azu shi ya baki, ya akayi kika karb'i kud'i a wurinsa mai yawa haka?" "Hajiya ni fah ban rok'esa ba, da ya bani ma ni bansan nawa bane dan Mus'ab ya bawa ya shigo dashi sanin kansa da ni ya bawa ba karb'a zanyi ba, sai da na shigo kuma naga da kud'i a ciki" Hajiya ta numfasa tace "amma Safiyya ya zakiyi mana haka? Kinsan da maganar Malam Usman kuma sai ki kawo wani kice shi zaki aura? Kin masa adalci kuwa?".


Kallon Mama nayi da alamar razana, hakan yasa tace "meh hakan ke nufi? So kike kice min baki san da zancen ba ko meh? Kada ma ki fara kare kanki dan mu bamu san wani ba sai malam Usman, abinda nazo in fad'a miki kenan". Tashi tayi ta bar d'akin bayan ta gama fad'an haka, ban iya dakatar da ita ba dan zuciyata ta cushe cike da bak'in ciki, k'arar da wayata yayi shi ya k'ara dagula min lissafi ganin Abba ne ke k'ira, kasa d'auka nayi har ya yanke na kashe wayar gaba d'aya ina mai zubar da hawaye.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


       6


Washe gari tun k'arfe takwas na fito daga gida d'auke da credentials d'ina dan zuwa office kamar yanda Safwan abokin Abba ya umarce ni da isa k'arfe tara, ahankali nake tafiya zuwa bakin titi dan in samu abun hawa, horn naji a bayana kuma da alamar ni ake nufi da in tsaya, d'auke kai nayi kamar ban ji ba na cigaba da tafiyata a hankali, muryar Malam Usman naji yana cewa "ni ne dai, ina zaki je warhaka?" Tsayawa nayi ina mai jin takaici da haushin had'uwa dashi yau, tabbas ya taimakeni a rayuwata amma hakan bai sa ya samu damar tilasta min aurenshi ba, tsanarshi naji ya dirar min nan take, sai da ya sake k'iran sunana sannan na juyo ba yabo babu fallasa na gaishe sa, ban jira ya amsa ba na cigaba da tafiyata.

Fitowa yayi daga motar bayan ya kashe ya biyoni yana cewa "ina zakije?" A tak'aice na amsa da "office" "muje in kai ki mana" "a'a, nagode" "Safiyya kada mu fara haka dake yanzu, ki saki ranki mu tafi in yaso muyi maganar a hanya, naga alamar fushi kike duk da nasan banyi laifi ba, a dai yi min afuwa". Kad'an ya rage in yi masa tsaki, Allah ya taimakeni na kame na k'ak'alo murmushin dole "kada ka damu, zan hau adaidaita" duk nacin da na nuna masa akan zan tafi ni kad'ai a banza nayi, nacinsa ya cinye nawa ya had'iye, dole na koma na hau motarsa ina kumbure-kumbure.

Tunda muka fara tafiya banda inda zanje da na fad'a masa ban ce komai ba, shi yayi hirarsa ya gama k'ala bance masa ba, abunda yafi bani mamaki bai wuce yanda salon maganarsa dani ya canja ba, shi a dole zai zama saurayina, in ya fad'i wani abun instead inji dad'i a wuya nakeji kamar in mak'ureshi dan haushi. Yana isa ko gama parking baiyi ba na fito ba tare da nace nagode ba, k'irana yayi na dawo dan banason in nuna masa halin d'an-Adam, "gashi ki hau adaidaita in kin gama" kud'in da ke hannunsa na kalla, 'yar dubu d'ayansa da ya gama tsofewa yakeson ya saye ni da ita, lallai baisan meh yakeyi ba. Ban karb'a ba nace "nagode, kada ka damu, ina da kud'in dawowa" ban jira magiyan da zai min ba na bar inda yake a hanzarce. Har na shige cikin harabar office d'in banji alamar ya tada motarsa ba, tsaki na ja nayi ciki wurin Safwan, bansan lokacin da ya bar wurin ba kuma ban damu da sani ba.

Ban sha wahala ba, dan ina zuwa na samu Safwan ya gama min komai, credentials d'ina ya karb'a ya kaiwa mahaifinsa ya duba sannan ya nemi ganina, tambayoyin da yayi min da yanayin nutsuwata yasa ya gamsu ya d'auke ni aiki a companynsa, nan take ya k'ira Manager Umar Mahmud ya iso, cike da girmamawa ya gaida shi ya amsa ya gabatar masa dani da kuma fannin da yakeson in zauna wato Staff department ta b'angaren budget, aikina shine duba abubuwan da ya dace da company, in bada shawarar abinda ya dace ayi a budget tare da fad'a musu iya gaskiya ta akan duk abinda ya dace ayi dan samun cigaban company, sosai nayi murna nayi godiya. Sati na sama aka nemi da in fara zuwa aiki bayan Manager ya nuna min inda zan na zama kuma ya gabatar dani a wurin sauran 'yan uwana masu aiki irin nawa.

Tun daga ranar bani da abun yi sai shirin fara zuwa aiki, a wani b'angare ina k'ok'arin yakice wannan addababben malamin da ya isheni da kalaman soyayyarsa, ban nunawa kowa bani son Malam Usman ba amma shi k'arara ya sani bana ra'ayinsa saboda abubuwan da nake masa amma dan naci irin nasa yayi biris kamar bai san ina yi ba. 

Ranar Alhamis na koma asibiti da Baba kuma munyi sa'an ganin likita, da taimakon likitan na samu Baba ya zauna a kujerar da ke gaban teburin likitan, sai da ya koma mazauninsa yana kallon Baba sannan ya waigo inda nake "meh ke faruwa? Meh yake damunsa?" "Actually bamu san exact matsalar ba, yana dai yawan amai, kuma yana hajijiya dan yace yana ganin abu biyu-biyu, munje Yak'ub hospital amma basu gano inda matsalar yake ba shine muka zo nan ko Allah zai sa a dace". Girgiza kai Dr. Yayi ya kai dubansa wurin Baba, "Baba zaka iya amsa min tambayoyina?" "Na'am" Baba yace yana kallon Dr. Da alamu bai gane meh dr. Yake nufi ba, sai da ya sake maimaita tambayar sannan ya amsa da eh.

"Akwai inda yake maka ciwo a jikinka" hannunsa ya d'aura a k'afarsa yace "wani abu na tafiya a k'afana" "bayan nan fa?" Ya girgiza kai alamar babu. Rubuce-rubuce Dr. Ya d'an yi ya d'ago kansa yana kallon Baba "kana magana yanda ka saba yi da ko kuma yana d'an yi maka wahala yanzu" "eh wani lokaci dai, kasan abu da mai rashin lafiya dole magana tayi masa wahala". Tambayoyi yayi mana sosai wani in amsa wani Baba ya amsa, daga k'arshe Dr. Yace dole ayi masa neurological exam, "Babanki ya iya karatu?" Kad'a kai nayi alamar a'a "ya dai iya na larabci" ya jinjina kai "ke kin iya ai ko? Sai ki taimaka mana wurin gwadashi da zamuyi" eh na amsa masa dan sunan da na karanta akan tag d'insa ya tabbatar min shi Christian ne. 

Sunan Hajiya na rubuta masa Hafsat, tsab ya karanta hakan yasa Dr. Yace in koma baya in sake rubuta masa wani abun, da mamaki na tsaya kallon Baba lokacin da yace baya ganin abunda na rubuta bare ya karanta "ki matso mamana bana gani" kuka ne ya kufce min tunawa da nayi cewa Baba har tsokanar ganina yake yi, in ina karatu sai yayi ta cewa "kin matso dashi kusa sosai, idanunkin nan ko nawa da na fara tsufa ya fi shi gani meh kyau" kuma na yadda da hakan dan sai da muka gwada karatu ranar a nesa, shi ya iya karantawa daga farko har k'arshe, ni kuwa ina yi ina matsowa gaba.

Barin d'akin nayi na barsu dan su gama iya gwaje-gwajensu, sosai jikina ya mutu ina matsar k'walla. Sai da suka gama Dr. Ya neme ni dan mu tattauna, wata nurse ce ta fito da Baba zuwa wani d'akin dan yin wani gwajin. Kallona likita yayi yaja numfashi yace "ya ma sunanki?" "Safiyya" nace a tak'aice dan na k'agu inji inda matsalar take, "emm! Nafi suspecting mahaifinki na da brain tumor, shiyasa ganinsa ya ragu, yake yawaita amai, sannan wani abu na tafiya a k'afarsa, bayan nan yana sa shi confusion kamar yanda naga alama sannan magana na yi masa wahala, duk abubuwan nan signs ne na mutum na da brain tumor".

"Menene brain tumor dr.?" Na tambaya dan ban gane cutar ba, Murmushi dr. Yayi ya gyara zamansa yace "Cancer ke kawo brain tumor, in mutum na da cancer ko wani iri ne yana iya spreading zuwa brain, 


Shiyasa da na tambayeki yana da cancer kika ce a'a nayi mamaki, dan a cikin gwaje-gwaje na na gano yana da lung cancer wanda har it spread to his brain, kin gane nufina? Yanzu dai final test ake masa, anan ne zamu tabbatar da hasashenmu, idan har ya tabbata brain tumor ne ya zama dole ayi masa surgery a cire sannan a fara treating lung cancer, idan kuma ba brain tumor bane zai zama lung cancer d'in ne kawai ke d'awainiya dashi, sannan za'a kwantar dashi daga yanzu zuwa lokacin da komai zai dai-daita". 

Kafin ya gama bayanansa sai da idanuna yayi ja dan 'kwallar da nayi ta zubarwa, Sai da ya fad'a min kud'ad'en da zan biya dan a kwantar dashi sannan na bar office d'in zuwa inda ake biyan kud'i, dubu talatin da biyu aka buk'ata kuma na biya. A waya na k'ira Feedoh na sanar da ita an kwantar da Baba. Kafin su iso har result na Baba ya fito kuma ya tabbata brain tumor ne, surgery za'ayi masa wanda a k'alla ana buk'atar dubu d'ari uku.

A lokacin da Hajiya suka iso ina zaune akan kujera nayi tagumi hawaye na sauk'owa a jere, zama sukayi suna tambayana abunda ke damunsa, ganin ban amsa su ba yasa suka fara zubar da hawaye su ma, Hajiya da Mus'ab ne kawai suka iya dauriya, Auta da Feedoh tare muka d'inga zabga kuka kamar ance mana Baba ya mutu. Da k'yar na samu na sanar dasu abinda likita ya fad'a min da kuma kud'in da ake nema dan yi masa aiki, duk dauriyar Hajiya sai da tayi k'walla a ranar.

Da yamma lik'is Feedoh, Auta da Mus'ab suka koma gida dan kawo mana abinda zamu ci, Mus'ab ne kad'ai ya kawo abincin da wasu abubuwan da zamu buk'ata, anan ne muka yi shawarar yanda za'ayi mu samu kud'in aikin Baba, sati biyu masu zuwa sannan za'a biya ni salary kamar yanda mukayi da Baban Safwan, yace "za'a biyaki tare da sauran ma'aikata tunda ke ta gida ce". A yanzu da wannan maganar tasa na dogara sai kuma kud'in da yake wurina dubu ashirin zuwa talatin, sai na Mama da tace zata sayar da gadonta wanda bazai wuce dubu talatin ba shima, Mus'ab ma ya bamu tabbacin baza'a rasa dubu goma sha biyar zuwa ashirin ba a wurinsa dan yana zuwa wurin gyaran takalma kuma ana biyansa. Gaba d'aya kud'in in muka had'a bazai wuce dubu casa'in ba, hakan yasa muka yanke shawarar jiran a biyani salary sai mu had'a da kud'in da yake wurin mu, kafin nan zamu nema ta wani wurin ko Allah zai sa mu cika.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


         7


Monday 8:16


    Da gudu na shigo gida nayi hanyar kitchen na d'auko bucket dan d'iba ruwan wanka, randar da ke wurin na bud'e na fara d'ibowa cikin hanzari har ina zubar da ruwan, motsina da Feedoh ta ji yasa ta fito tana lek'en wanda ya shigo gidan ba tare da sallama ba, ganin nice yasa ta tsaya tana kallon wasar ruwan da nakeyi, "ai gwanda ki nutsu kiyi a hankali dan kina zubarwa..." Yanayin yanda na waigo yasa ta yin shiru tana kallona, "haba Feedoh, ai sai ki tsorata ni" ina gama fad'an haka na cigaba da d'ibo ruwana, "ai ke kika tsoratani kin shigo mana ba sallama, kin ma yi sa'a babu tab'arya ko ice da shi zakiji a kanki ral sai dai ki ganki a k'asa ko a sume". Ban tankata ba na d'auki bokatin na shige ban d'aki.

A cikin minti uku nayi wanka na fito d'aure da zani, da hanzari na shirya cikin material d'ina milk color doguwar riga na shafa powder da lipstick red sai kwalli da nasa a idona, gyallena na d'auko daga cikin akwatina na yafa na fice bayan na d'auki handbag d'ina, ban tsaya duba lokaci ba nayi hanyar waje ina kallon cikin kitchen tare da cewa "Feedoh na tafi" ban jira ta amsa ba nayi waje. Tafiyar sauri nakeyi har k'afana yana hard'ewa, ni da ya dace 8 ina office yau farkon zuwana na sab'a doka, ganin adaidaita yasa naji sanyi a raina, ban tsaya wani ciniki dashi ba na shige muka fara tafiya a cikin raina ina addu'ar Allah yaji k'aina kada a koreni daga aiki.

Ina isowa ya fad'a min kud'insa ba jayayya na ciro na mik'a masa, a hanzarce na shiga ina mai raba ido inga ta inda za'a dakatar dani, banga kowa ba hakan yasa na cigaba da tafiya ina duba agogon wayata, bugewa naji nayi da mutum ta wuntsila saura kad'an ta fad'i na rik'o hannunta, files na wurinta tuni suka zube papers na ciki sunyi d'ai-d'ai, ware ido tayi tana kallon files d'in da yanzu ta gama compiling ya sake had'ewa, juyowa tayi tana mai kallona cike da b'acin rai, ban lura da kallon da take min ba na fara tattaro mata papers d'in da suke zube a k'asa kamar anyi ruwansu bakina kuma bai gaji da furta kalmar "am very sorry" ba.

Har na gama bata daina kallona ba, mik'o mata nayi ina cewa "ban lura bane na buge ki, am late shiyasa duk na kasa tsayar da kaina inyi abunda ya dace" kallona ta sake yi bayan ta kai dubanta ga files d'in da na mik'o mata tace "Safiyya kike ko?" "Eh" Nace mata ina mai sakar mata murmushimurmushi dan jin ta k'ira sunana, na mik'a mata hannu ina cewa "am new here, nice meeting you" kallon da tayi min yasa naji duk na muzanta, kamar bazata bani hannu ba ta mik'o min mukayi shaking can k'asa tace "KDEEY", ban gane sunan nata ba hakan yasa nace "sorry kikace?" Murmushin dole tayi min tace "am Khadija, friends na k'irana Kdeey" tana fad'an hakan ta juya nima na wuce office d'ina.

Tables biyar ne a office d'in, nawa shine ke facing k'ofar shigowa, ana bud'e k'ofar ni za'a fara gani, shiyasa duk fice da shigen mutane ina kallo, babu laifi nayi aiki a ranar duk da ban samu aikin da yawa ba, sai dai kafin lokacin tashi yayi Ogana ya kawo mana files ya raba mana kowa ya duba ya kawo report nasa sannan ayi compilling a kaiwa manager final report. A lokacin na fara karantawa kuma na gano sabon sysytem Khadija Abdulkarim ta kawo musu suke so su fara yi a company d'in shine suka turo mana details na komai game dashi dan neman shawara da k'arin haske.

Alal hak'ik'a bansan Kdeey ce da wannan sunan ba, kuma ko da na sani bazai hanani fad'an abunda na hango game da abunda aka bani aiki akai ba. Sati suka bamu hakan yasa nayi dogon bincike iya iyawata dan zak'ulo anfaninsa da kuma illarsa, sosai nayi nazari akai kuma na fuskanci matsaloli da yawa akan wannan sabon system d'in, ban b'oye komai ba na rubuta duk abubuwan da na hango a cikin paper nayi submitting ranar Friday. Sati d'ayan da nayi ina zuwa office ban tab'a samun matsala da kowa ba sai Kdeey, duk da bamu tab'a fad'a ba amma na lura jininmu bai had'u ba. Kdeey ta fini kyau, ga exposure da iya dressing, d'agun kai da nuna isar da take dashi ne kad'ai banaso amma ta ko ina ta had'u, ban tab'a shiga sabgarta ba tunda na lura jininmu bai had'u ba.

Batun asibiti kuwa kullum idan na dawo daga aiki can nake kwana sai asuba in koma gida dan zuwa aiki. Sosai yake samun kulawa kuma yana samun taimakon da ya dace a bawa mai lalura irin tasa kafin ayi masa aiki, Feedoh da Auta a can suke wuni sai dare su koma tare da Hajiya, da ni da Mus'ab muke kwana tare da Baba wani lokacin in bar Hajiya ta kwana ni in koma gida. Malam Usman, Anty Jegal da Futha sun zo ranar lahadi muka wuni, sai dai banji dad'in yanda Anty Jegal take shareni ba, ko kallon inda nake bata yi ba har ta bar asibitin, gaisuwa kad'ai ya had'amu. Malam Usman sarkin naci kamar yanda nake k'iransa yanzu yafi kowa bani haushi, a gaban matarsa da 'yarsa yake wani kallona yana murmushi ko kunya baya ji, har suka tafi ban sake ba ina zaune gefe na kasa sa bakina a hirar da sukeyi.

Ranar Tuesday aka yanke hukuncin k'in anfani da sabon salon da Kdeey ta kawo, hakan ya k'ara tsaurara k'iyayyar da take min, kuma abinda na lura dashi sauran colleagues d'ina na shakkunta, hakan yasa indai ita ta kawo sabon abu ko kuma ita tayi submitting budget ana tsoron fad'an gaskiya ko da kuwa hakan na nufin fad'uwar company, haka muka cigaba da tafiya a cikin wannan company ina aikina da gaskiya babu shakkan kowa har aka biya mu salary.

Kamar yanda muka tsara haka mukayi, mun tattara kud'in aikin Baba mun biya saura ayi aiki ranar alhamis. A ranar da za'ayi wa Baba surgery ban samu zuwa office ba dalilin hutun da na nema a bani akan rashin lafiyan mahaifina, tun safe babu abinda nakeyi sai addu'an Allah ya sa ayi aiki cikin sa'a, har aka shiga dashi hankalina bai kwanta ba, haka kawai nakejin zuciyata na tsinkewa.

Cikin sa'a aka gama aiki suka fito dashi bayan awowi hud'u da rabi, duk da haka bai sa hankalina ya kwanta ba sai da naga ya farka ya bud'e idanunshi da misalin k'arfe uku na dare, sosai mukayi murna ni da k'annena anyi aiki lafiya sai fatan samun lafiyarsa kafin mu shiga treating cancer. Har na fara zuwa aiki baba bai dawo daidai ba, kwanaki uku aka bani babu yanda na iya dole na fara zuwa hankalina na wurin Baba. 

A ranar da na koma aiki Abba ya diro Taraba dan duba jikin Baba. Bansan da zuwansa ba sai ganinsa nayi da Safwan a cikin office d'ina yana min murmushi, banso zuwansa ba dan banason Hajiya ta d'auka banji maganarta ba, nafison malam Usman da kansa ya janye maganar neman aurena sannan in gabatar dashi kuma ya turo magabatansa. Rashin fad'a min da baiyi ba yana da alak'a da hanashi zuwa da nakeyi tunda aka kwantar da Baba.

A lokacin da muka zo fita daga office muka had'u da Kdeey, tun daga yanayin kallon da tayi wa Abba naji zuciyana bai aminta dashi ba, shiyasa ban bari mun tsaya a inda take ba muka fice muka barta da Safwan. A gaskiya bazan b'oye muku ba naga alamar Kdeey ta yaba da Abbanah ma'ana tana sonshi, dan tun daga ranar ban sake ganin ta had'e min rai ba sai ma shishshige min da takeyi ala dole tanason mu zama k'awaye ni kuma ina shareta dan ban yadda da ita ba kuma bana fatan wani ya shigo ya raba ni da mai sona.

Kwana goma sha d'aya da aikin da akayi wa Baba ciwo ya dawo sabuwa, ina zaune a gefensa naji jikinsa na rawa fiye da yanda nake ganin masu zazzab'i na yi, rawar da yake yi har gadon da yake na girgiza. A guje na fita k'iran likita dan ni d'aya ne a d'akin lokacin, kafin mu dawo Allah ya d'auki ran Babana, duk da ganin jikinsa a sake kuma idanunsa a rufe bai sa na kawo masa mutuwa ba, sai da likita ya duba shi ya tabbatar min da Baba ya mutu".

Kuka ne ya kufce mata a lokacin da ta iso daidai wannan gab'a a labarinta, kuka take sosai Pherty da ke tsaye gefenta na shafa bayanta alamar rarrashi, kukan da takeyi yasa miemiebee mik'a mata tissue dan share hawayenta, kad'an daga cikinsu ne basu zubda hawayen tausaya mata ba. Sai da ta ja dogon numfashi sannan ta cigaba:-

"A lokacin da Baba ya rasu suma ne kawai banyi ba, a daidai lokacin da nake mafarkin bashi duk wata jin dad'i ta rayuwa Allah ya d'auki ransa, na so a ce Baba yana raye a yanzu yaga matakin da na taka a rayuwa, na so Baba yaji dad'in dukiyata ta hanyar bokon da ya sani duk da wahalar rayuwa da Allah ya jarrabemu, abu d'aya na sa a raina Allah baya barin wani dan wani kuma kowa lokacinsa yake jira".


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


        8


   Mun d'auki mutuwan mahaifinmu a k'addara, munyi kukan munga babu anfaninsa, dole muka hak'ura muka rungumi k'addara. Sosai mutane sun mana mutunci mussamman Malam Usman, Anty Jegal da 'ya'yanta, 'yan uwa da abokan arzik'i babu wanda bai zo mana gaisuwa ba, ciki har da Kdeey da sauran abokan aikina.

Sai da akayi kwana bakwai sannan 'yan uwa suka fara komawa gidajensu suka bar mu da kewan mahaifinmu da tunanin yanda za'ayi mu cigaba da rayuwa babu shi. A duk lokacin da na tuna Babu mahaifina na kan ji babu anfanin rayuwata, amma samun Abba kusa da ni ya kan taushi zuciyata da kalamai masu dad'i kuma yakan nuna min Allah shi yake tsara wa bawansa yanda rayuwarsa zai kasance, yadda da k'addara tare da yiwa Baba addu'a shi yafi dacewa inyi a wannan lokacin, sannan inyi tunanin k'annena da yanzu suke k'ark'ashina, a gaskiya na kan karaya in na tuna nauyin da yake kaina amma samun mahaifiya irin Hajiya yasa duk lokacin da naji bazan iya ba ta kan nuna min TANA TARE DA NI.

Rayuwa ta cigaba komai ya sauya da ikon Allah, wata biyu da rasuwar Baba Malam Usman ya tunkareni da maganar aure, a ranar munyi maganar nutsuwa dashi na nuna masa ba wai sonshi ne bana yi ba, banson b'ata zumuncina da Anty Jegal A DALILIN GATAn da yake nuna min tun ina k'arama, na tabbata yana sona kuma yana son ya tallafi rayuwata, ban b'oye mishi ina son Abba ba dan na gaji da kwana, nafison ayi komai a gama, sosai ya fahimceni kuma ya bani goyon baya akan ra'ayina kuma ya rok'eni da rike'e zumuncinmu, maganar aure da ya shigo ciki kada yasa zumuncinmu yayi rauni.

Ba'a d'auki lokaci ba Abba ya turo magabatansa, k'anin Baba suka samu suka dai-daita sadaki da kuma ranar d'aurin aure. Kamar kowani biki k'awaye, dangin amarya da dangin ango sukan samu kansu cikin ayyuka iri-iri na hidiman biki haka ya kasance a nawa, babu wani occasion d'in da akayi dan nace banaso kuma ya amince, walima kawai za'ayi na mata daban na maza daban bayan nan babu wani abu da za ayi na murnar aurena.

RANAR AURE


Malam Usman ne ya zama liwali na ya bada aurena ya karb'i sadaki, Anty Jegal kuma ta zame min uwar d'aki, k'awaye da abokan arziki sun min murna had'e da yi min addu'a. Sai dare aka kai ni gidan da Abba yayi hayansa a nan cikin Taraba, gida ne madaidaici d'aki biyu kowanne da toilet d'insa a ciki sai palor. Cikin gidan ba mai fad'i bane sai dai motoci biyu ko uku ma in an samu k'wararren driver zasu iya parking.

Aurena rayuwa ne mai dad'i wanda bazan tab'a manta irinsa ba, Abba ya nuna min soyayya k'arshe dan ban tab'a d'auka Abbana lover boy bane, komai tare mukeyi kuma bai tab'a b'oye min komai ba haka nima ban b'oye masa komai, farkon abinda ya fara had'a mu shine rashin zamanmu wuri d'aya, shi yana aiki a Katsina ni kuma ina aiki a Taraba, da farko ya nace sai na bar aikin in koma Katsina in nemi wani amma da na nuna masa hakan bazai yu ba ya hak'ura, sai dai mun tsaya akan zai nema min aiki a can idan ya samo min sai in bar nan in koma can.

A cikin watanni biyar da aurena na gyara mana gidanmu, na wadata mahaifiyata da k'annena da abinci, sutura iya gwargwado ina yi ga kuma kud'in makarantar k'annena da nake biya, ban zauna haka ba, shagon Baba da ya bari shi na bud'e wa Mus'ab na zuba masa kaya na sake buga masa katako inda zai jera takalman sayarwarsa tunda naga yafison sana'ar.

A b'angaren aikina kuma na samu nasarori masu yawa sakamakon jajircewata da taimakon company da nakeyi, a yanzu ina aiki matsayin personal manager a company nah (personnel department) kuma tsakanina da Kdeey babu abunda ya canja, naga alamar tunda nayi aure hankalinta ya tashi kuma tsanar tayi tsanani, ban kulata ko kad'an, infact bana d'aukan abunda takeyi a bakin komai dan ni bata gabana, mahaifiyata, k'annena da mijina su ne a gabana kuma ina yin komai dan in faranta musu.

Na samu ciki a wata takwas na aurena, lokacin da na tabbatar da ina da ciki har na wata biyu ban b'ata lokaci ba na k'ira Abba na fad'a masa, sosai yayi murna ya kuma nuna jin haushin baya tare dani a wannan lokaci na farinciki. Sabuwar tarairaya da soyayya Abba ya nuna min da yazo min weekend, wanda hakan yasa ni kuka a lokacin da muke sallama zai koma Katsina, kuka nayi wanda ban tab'a yi masa irinsa ba a lokacin da zai tafi, sai da ya gama rarrashina nayi shiru na hak'ura sannan ya tafi". 

Kallonsu Ummu Abdoul tayi d'aya bayan d'aya sannan tace "ohh sorry, na manta ashe akwai marasa aure cikin taronmu, kada ku ga laifina akwai dalilin fad'a muku irin soyayyar da Abba ya nuna min wanda a yau bana tsammanin ko burbud'insa akwai" ta k'arashe maganarta da muryar kuka, dak'yar ta cigaba mana da labari.

"Bayan na haihu na samu d'a namiji aka rad'a masa Abdoullahi, a gidanmu nayi arba'in sannan na koma gidan mijina cike da kewarsa da zumud'in samun kulawarsa, sai dai kash! Abunda nake tunani ba shi na samu daga garesa ba. Bansan wa ya had'a ni dashi ba, bansan wani gulma akayi masa akaina ba nidai kawai naga ya canja min kuma da alamu zargina yakeyi. A duk lokacin da na kawo sabon kalar soyayya na nuna masa ko da a shimfid'a ne ina gamawa tambayana zai fara "wa ya koya miki abun nan?" Daga nan kuma bazamu samu zaman lafiya ba zai dinga had'e rai yana kumbure-kumbure babu dalili, dad'ina d'aya sai weekend yake dawo min kuma bazai tafi ba sai munyi fad'an wani abu da nayi masa mai dad'i, a kullum tunanina d'aya "shin mutum baya iya zama yayi tunanin meh zan yi wa mijina yaji dad'i sai dai a koya masa? Nidai ban tab'a koyar wani fannin soyayya a wurin wani ba musamman ta fannin da yafi zargina wato soyayyar d'aka, waye ma zai koya min da har zaiyi tunanin koya min akeyi?".

Abu kamar wasa ya zama gaske, ko fita zanyi office sai ya k'irani a waya yana min wa'azin inji tsoron Allah akwai aure akaina. A kullum in zan tafi sai na biya gida dan ajiye Abdoul wurin Hajiya amma ban tab'a fad'a mata abunda yake min ba, kullum ina k'ok'arin hana kaina yi masa wani abunda zai sa yana zargin koya min akeyi, hakan da nayi sai k'ara abun yayi instead ya ragu, na so mu zauna mu tattauna mu fahimci juna akan hakan, amma daga mun fara maganar zai tashi ya fice yana surutai ba tare da na gane masa komai ba. 

Watan Abdoul bakwai Abba ya sawwak'e min bayan dogon maganar da mukayi, a wannan zaman ne na gane yana zargin ina huld'a da managernah, shiyasa nak'i binsa katsina kuma kullum ba office muke zama ba muna fita yawo kamar yanda yace. Ni gaskiya bazan b'oye ba muna shiri da manager ba dan komai ba sai don k'ok'ari na, kuma shirin namu ba shiri bane wanda har za'a ce ya haramta, gaisuwa ce bayan nan kuma shi mai son wasa da dariya ne, bamu tab'a keb'ewa ni dashi ba, bani da haukan kaucewa addinina kuma ban tab'a tunanin cin amanar mijina ba.

Duk wannan badak'alar ina da yak'inin Kdeey ce sila dan sai da ya gama fad'a min komai na gano inda maganar ta nufa, duk wannan shiri ne na Kdeey dan ta k'untata min kamar yanda take ganin na tare mata komai, da farko na k'wace matsayinta na fad'a a ji a company, na biyu na k'wace mata jama'arta abokan aikinmu, na uku kuma Abba wanda duk shi yafi b'ata mata rai.

Ina son mijina uban Abdoul d'ina amma ya raba mu ba tare da ji daga bakina ko bincike ba, nayi takaici nayi kuka fiye da tunaninku a lokacin da ya hanani d'aukan Abdoul d'ina farincikina, babu yanda na iya na tattara kayana na koma gidanmu dan ZAMAN ZAWARCI. A yanzu haka shekara d'aya kenan rabuwarmu, kuma a wannan shekarar ne companynmu suka bud'e branch a nan Abuja suka dawo dani nan, dalilin dawowata nan da zama kenan ina zama tare da Hajiyata da k'annena a nan Mararraba.

K'arshen LABARINA kenan ina sauraran naku".

"Ahh wait, ya zaki ce k'arshen labari? Baki bamu labarin yanda kikayi da Kdeey ba, baki je kin bubbuge bakinta ba bayan kinsan ita ce sila?" Cewar Benazir, Miemiebiee ta karb'e da cewa "wallahi da nice sai ta rainawa kanta wayo, dan bakinta sai ya kumbura bayan na cire mata hak'ora". Anty Lubiee ta numfasa tace "tabbas naji tausayinki Ummu Abdoul, kuma na jinjinawa dauriyarki, Allah yasa hakan shine alkhairi a gareki kuma Allah ya baki ikon cin jarrabawarsa". 

Ameen suka ce dukka sannan Pherty tace "wai Ummu Abdoul da gaske kin hak'ura kin bar mata mijinki? Chabd'i, nifah da kuke ganina in na so abu babu uban da ya isa ya kwace min, shawarata anan tunda bai sake ki saki uku ba ki dawo dashi, ki nemesa kuyi magana ku fahimci juna, kada ki yadda ki nuna masa kina son komawa d'akinki, da zai yu ma ki buga IV ki kai masa na aurenki dan kada yayi tunanin mun zubar da aji ko kin kasa daina sonshi", Benaxir ta karb'e da cewa "exactly, inaga abunda kawai za'ayi kenan". 

Basu gama concluding abun yi ba Anty Lubiee tace "muje muyi sallah ko? Yakamata muyi sallah in da lokaci mu cigaba daga inda muka tsaya in babu kuma mu bari sai gobe". Wuri suka samu a ciki suka shimfid'a darduman da Rufaida ta kawo musu sukayi sallah, rashin isasshen lokaci yasa sukayi sallama kowa ya watse akan gobe zasu sake taruwa a wannan wuri da misalin k'arfe uku da rabi zuwa hud'u.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


NOTE:- a page 2 nayi kuskuren rubuta Yusuf a matsayin k'anin Ummu Abdul bayan Mus'ab ne sunan, sai page 5 nayi kuskuren rubuta Jamilu matsayin abokin Abba bayan Safwan ne asalin sunan, ayi min uzuri please... Thank you


        9


GIDAN PHERTY @ 6am


    Bugun k'afarta yakeyi a hankali yana k'iran sunanta, juyi tayi akan gadon sannan ta bud'e idonta ahankali ta d'aura su akan dattijon da ya dawo gefenta ganin ta farka fuskarshi yalwace da murmushi yana kallonta. "Goodmorning baby" ya fad'i hakan yana shafa fuskarta.

Can ciki ta ja tsaki ba tare da ya ji ba ta mike zaune tana ture bargon da ta lullub'e jikinta dashi gefe. Kallonta ya tsaya yi daga sama har k'asa yana mai yiwa Allah godiya da ya bashi mata irin Pherty. Ganin ta wuce shi ba tare da tayi masa magana ba yasa yace "Haba baby kamar baki ganni ba, laifin meh nayi miki?" Juyowa tayi tana kallon fuskarsa da yake nuna shi d'in babban mutum ne, sanye yake cikin blue shadda sai yalk'i yakeyi alamar yasha guga, tumbinsa ta d'aura idanunta akai tana mai takaicin kasancewa tare dashi. Bata tanka sa ba ta shiga ban d'aki ta barshi tsaye yana nazarin laifin da yayi wa 'yar babynsa.

Har ta fito yana zaune zaman jiranta, ganin ta fito yasa shi isowa wurinta yana langwab'ar da kai, kawar da kai tayi gefe tana goge gashinta da k'aramar towel, kunya yake bata a duk lokacin da yake yi mata abu kamar yaro k'arami. Daf da ita ya tsaya ya kamo hannunta yana mai kallon fuskarta, "Baby fad'a min laifina in baki hak'uri" turo baki tayi tana mai d'aura kwayar idonta a fuskarsa "ina baccina kazo ka tasheni bayan kasan banyi bacci ba jiya" ta fad'i hakan k'walla na taruwa a idanunta. Rikicewa yayi ganin yasa babynsa kuka "no please baby dont cry, gani nayi kinyi fushi dani jiya shiyasa banson in tafi ba tare da na baki hak'uri ba, ni ya dace inyi fushi dake dan jiya sai after 12 na dare kika dawo gida, dan na miki magana kika hau b'ata rai bayan ni ne da gaskiya".

Kuka tasa masa hawayen da ya cika idonta ya sauk'o bisa k'uncinta, zama tayi a k'asa tana shure-shure da k'afarta tana cewa "mutum kenan bayi da freedom na fita lokacin da yaso ya dawo lokacin da yaso, kai kullum ba cikin yawo kakeyi ba kana cewa business trip, yau kana China gobe Malaysia jibi Cairo, na tab'a tambayanka meh yasa? Ni da a cikin gari kawai na zagaya ka tsaya kana ta min masifa" ta cigaba da shure-shure da kukanta na iyayi.

"Ya Rabb!" Yace sannan ya zauna kusa da ita yana janyota jikinsa ya k'ank'ame yana shafa bayanta had'e da cewa "am sorry baby, na yadda ki fita duk inda zaki je amma ki bari driver ya kai ki..." Bai k'arashe maganar ba ta fashe da wani kukan "da girmana da komai na sai driver ya fita dani? K'awayena so kake su yi min dariya" ta k'arashe tana mai ture sa daga rungumar da yayi mata, k'in saketa yayi ya fara rarrashinta, dole ya hak'ura tana fita ita d'aya amma ta daina yin dare, bata musa ba dan tasan babu yanda ya iya da ita ko da zata na dawowa d'ayan dare ne, bare shi da ba zama yakeyi a gari ba ina zai san lokacin dawowanta? 

Sai da ya tayata ta shirya cikin doguwar riga na material ya d'auketa hoto a wayarsa sannan yace "zan tafi, flight na 12 zan bi. Baby ko zamu tafi tare? Its been long bamu fita ba kuma ina missing naki kin sani, dawowar nan ma bata min dad'i ba dan ban samu abinda nakeso ba, mu tafi tare please" ya k'arashe maganar yana sa fuskarsa a wuyanta dan yayi kissing, bai kai ga hakan ba ta d'aga kafad'arta ta hana shi.

Kallonta ya tsaya yi dan ya gane dalilin yi masa hakan, turo bakinta tayi tace "next time in kanason tarba meh kyau tell me before kazo, kuma make sure bazaka b'ata min rai ba kamar yanda ka min jiya" murmushi ya sakar mata yana cewa "ai kin gara ni, ur wish is my command my baby" ya had'e bakinsu wuri guda har sai da ta gaji ta turesa sannan sukayi sallama ya tafi. "Tsohon nan sai nacin tsiya, shi bai girma kuma bai gajiya? Mtsw" ta ja tsaki a lokacin da take hawa stairs.

Ruffaida @ 9:30


Bacci takeyi hankalinta kwance ta lume cikin k'aton bargonta mai laushi, d'aki ne mai girman gaske anyi fenti pink da fari, labulen d'akin pink da fari haka zalika carpet na d'akin, Gadonta k'aton gaske ne italian had'e da wardrobe nasa. K'arar wayarta yasa ta bud'e ido a hankali bacci cike da idanunta, hannunta kawai tayi anfani dashi wurin lalubo wayar. One missed call ta gani manne a screen na wayarta a k'asa kuma an rubuta "MINE" da manyan harrufa, ajiyewa tayi dan ta koma bacci taji ya sake k'ira, manna wayar tayi a kunnenta tace "hello" bayan ta amsa.

"Ki fito ina jiranki waje" "um-um ni ko tashi daga bacci banyi ba bare inyi wanka" daga can b'angaren yace "haba Ruf, kinsan k'arfe nawa? Zanje office fa na tsaya jiranki tun d'azu" rolling idonta tayi tana mai sauk'e numfashi had'e da tunanin amsar da zata bashi, kamar bazata yi magana ba tace "yanzu ka tafi office in na shirya sai in tab'oka kawai" "okay" yace ya kashe wayar. Sai da ta k'ara minti biyar a kwance sannan ta tashi ta shiga wanka, mintunan da ta d'auka a bayin kamar zata canja kanta sannan ta fito d'aure da towel, a wurin kwalliya ma sai da ta d'auki lokaci kafin ta gama tasa kaya, atamfa riga da skirt ta d'aura d'ankwalin yayi kyau sosai, ta feshe jikinta da turare ta d'auko mayafin da zai shiga da kayanta ta yafa. 

Dining table ta nufa, kai tsaye tayi serving kanta ta fara ci tana kurb'an tea,sai da ta kusa kammalawa wata mata sanye da doguwar riga shadda yasha aiki daga sama har k'asa ta nufo ta fuskarta cike da annuri, sai da ta iso dining area sannan tace Ruffaida "kin tashi ashe, na d'auka yau ba tutorial d'in shiyasa baki tashi da wuri ba, ashe kina tafe", juyowa tayi tana mayar mata da martanin murmushinta tace "yanzu na tashi, da yake yau ba da safe bane malamin yace. Ina kwana Mommy" ta gaishe ta tana mai sunkuyar dakai alamar girmamawa, sai da ta shafa kan Ruffaida sannan ta amsa "lafiya k'alau, kada kiyi latti kiyi sauri ki kammala sai driver ya kai ki ko?" Cike da girmamawa ta amsa "toh Mommy, na ma gama breakfast d'in, jakana kawai zan d'auko in wuce" "okay, sai kin dawo toh, Allah yayi albarka". Ta juya zata tafi sannan ta juyo alamar ta manta abu "kinga in kin d'auko jakar kiyi wa Amrah magana ku fita tare, ita ma zata je ina ne ita da k'awarta Meesha, tun d'azu tazo tana jiranta bata gama shirinta ba, in kince zaku fita tare mayb tayi sauri".

"Toh" kawai tace dan Mommy ta b'ata mata plan, babu yanda ta iya dole suka fita tare suka ajiyeta a Baze university kamar yanda ta saba k'aryar tana zuwa tutorial every weekend. Sai da ta tabbatar da tafiyansu sannan ta k'irasa a waya ta sanar dashi tana cikin makaranta yazo ya d'auketa. Ba'a d'auki lokaci mai tsayi ba ya iso inda take cikin wata dank'areriyar Jeep bak'a, kai tsaye ta isa inda yake ta bud'e seat na gaba ta zauna sannan ta fuskantoshi tana mai yi masa murmushin nan nata da yake tafiyar da imaninsa, murmushin yayi mata yace "gimbiya, Gimbiyar Nuraddeen" dariya tayi can k'asa tana mai jin dad'in kalamansa, "gimbiyarka ai tana gidanka, ni ai sai ka fito nake maye gurbinta" ta fad'i hakan tana mai kallon fuskarsa, dariya da annurin da ke fuskarsa duk ya b'ace a nan na gano mutumin ya manyanta, a k'alla zai kai shekaru arba'in da d'aya ko ma fiye.

Numfashi ya sauk'e yana mai kai dubansa waje yana kallon farfajiyar makarantar, minti biyar babu wanda ya sake magana a motar yasa key suka bar wurin. Suna cikin tafiya ya juyo ya kalleta ya sake mayar da hankalinsa kan tuk'in da yakeyi, hannunsa d'aya ya d'aura akan hannunta da ta ajiye akan cinyarta tana kallon titi, d'ayar kuma yana rik'e da sitiyarin motar. Kamar baza ta yi magana ba tace "na d'auka fushi kayi dan na fad'i gaskiya", "na isa inyi fushi? Kiyi hak'uri mu bar maganar da ya fiye mana" bata sake tanka sa ba har suka isa newton park hotel da ke Wuse.

Bai dawo da ita ba sai k'arfe 2:30 cike nak da kaya ya zube mata ya tafi bayan ta k'ira driver yazo ya d'auketa. Ta k'ofan kitchen ta baya ta shigo da kayan a sand'a dan tasan irin gidan nasu da wuya a samu mutum a wannan lokacin a k'asa, d'akinta ta nufa da sauri ta kulle k'ofa dan jin alamar tafiyar mutum, a jikin k'ofar ta lafe tasa kunnenta dan tabbatar da mutum ne ko kuwa? Jin shiru yasa ta sauk'e ajiyar zuciya ta nufi wardrobe nata ta zuba kayan ta ciro ledar ice cream da kayan ciye-ciye da ya sayo mata ta ajiye a gefen gadonta ta shiga wanka.

Da dare suna zaune a pallor suna kallo, Mommy, Amrah, Ruffaida da Shamsu da ke kwance kansa na bisa cinyar Mamansa akayi knocking, mai aikinsu ce ta isa ta bud'e k'ofar ta russuna tace "sannu da dawowa" sannan ta basu hanya. Saurayi d'an kimanin shekara ashirin da hud'u ne ya fara shigowa sannan wani dattijo ya biyo shi a baya, Nuraddeen ne saurayin Ruffaida da ya d'auketa d'azu, amma abun mamaki bayan sun gaisa da Amrah ya d'auki Shamsu sama ya ajiye yayi hanyar stairs yana amsa gaisuwar Ruffaida Mommy kuma na biye dashi a baya.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


       10


Gidan Lubiee


   Zaune take akan gadonta da misalin k'arfe 8:30 Kausar 'yarta ta shigo cikin kuka, yarinya ce bazata wuce shekara takwas ba, fad'owa tayi kan Mamanta tana mai kukan an hana mata sweet d'in da Baba ya kawo, dak'yar ta samu ta rarrasheta ta bata sweet d'in da ta saya dan irin hakan da yake faruwa tsakaninta da kishiyarta, ganin idonta miji zai kawo abu a hana mata a hana wa 'yar ta kuma babu yanda ta iya dan miji ba sauraranta zai yi ba. Hawaye ne ya cika mata ido tunowa da tayi bata da wani gata wurin mijinta, kwana d'akinta sai dai yayi satan hanya, kayan dad'in da yake sayowa amarya da yaranta sam baya bata, abinci sai dai a tsammata ita da gidan mijinta, kayan sawa kam ba'a magana, shiyasa take k'ok'arin neman na kanta, da diploman da take dashi ta samu aiki dai-dai gwargwado ana biyanta, cigaban ne sai a hankali, dan tana buk'atar shiga university ko dan saboda halin rayuwa. 

K'arar wayarta ne ya dawo da ita daga tunanin da ta lula, Ummu Abdoul ce rubuce gaban screen na wayarta k'irar techno android, sallama tayi bayan ta amsa k'irar. "Sai yanzu na kunna data nake ganin sak'on Batool wai tayi tafiya, har fa na shirya ina ta jiranku baku zo ba, nayi ta trying layin Miemiebee da Pherty duk bai shiga ba" dariya tayi sannan tace "kema da wauta, ni zaki k'ira ko wad'ancan, baki san Kamal(mijin miemiebee) ya dawo ba, ai ni dama nasan yau dak'yar mu samu zama, kowa da abunda zaiyi shiyasa ko shiri banyi ba" Ummu Abdoul dariyar ita ma tayi daga bisani tace "yarinyar nan na son mijinta, anyway zamuyi magana ta watsapp sai mu sa rana, kada ku shashantar da wannan zaman dan wallahi zaiyi mana anfani" sallama sukayi sannan ta kashe wayar ta shiga duniyar watsapp dan duba sak'onni.

A daidai wannan lokaci @ gidan Miemiebee:-


"Ni fah sai ka k'ara abincin nan, kaga lokacin da nayi wasting ina maka favorite d'inka, kuma yanzu sai kaci kad'an kace ka k'oshi, ya zanyi da abincin toh? Ba Yola muke ba bare kace a bawa almajiri" ta fad'i hakan tana mai kai masa spoon na shinkafa bakinsa, sai da ya had'iye ya samu damar magana "dan Allah miemie bar ni haka nan, so kike inyi tumbi in zama k'ato, besides nace miki na ci abinci da na fita" ya k'arashe maganar yana karb'an spoon na hannunta had'e da d'auke plate na abincin. Kitchen ya kai ya ajiye yana cewa "so take inyi k'ato, na ci abinci waje kuma na sake cin rabin plate dan kada ta b'ata rai but still banyi k'ok'ari ba" fridge ya bud'e ya d'auki gorar swan water mai sanyi ya fice ya sameta inda ya bar ta.

Kallon ruwan hannunsa tayi ta langwab'ar da kai "kuma ruwan ma bazaka sha nawa ba dan nace ka ci abincina" goshinshi ya d'aura kan tafin hannunsa yana girgizawa a hankali yace "am sorry wife, duk ke ce kika birkita ni" ya karb'i nata da ta zuba masa a cup ya ajiye na hannunsa, sai da ya sha sannan ta sake masa murmushi "ko kai fa sweet, ni ka daina cin abinci a waje saboda kazo ka ci nawa" "toh ranki ya dad'e, gidan ogana naje aka bani abinci, sai ince bazan ci ba? Shiyasa na ci kad'an na dawo na ci naki ya cike min gurbin da na bari" fad'ad'a murmushinta tayi jin ya fad'i haka, tashi tayi ta rik'o hannunsa zuwa d'akinsa dan taya shi shirya kayan da zai tafi dasu gobe.

Kamal shahararren pilot ne wanda ake ji dashi matuk'a saboda k'warewarsa da bin na gaba, shiyasa da wuya ya samu hutun kwana uku idan ya dawo gida, duk da abun nasu timetable ne bai hana shi yawo da tafiye-tafiye ba, yau ma kamar kullum hutun kwana biyu ya samu gobe zai wuce California, shiyasa duk ta langwab'e masa tana zuba masa shagwab'a iya sonta shi kuwa yana biye mata. Da dare bayan sun gama gyaran komai tana kwance kanta bisa cinyarsa hannunta na wasa da gashin hannunsa da yake masifar yi mata kyau "Kamal d'ina" yace "na'am" hankalinsa na kan takaddar da yake dubawa, tashi tayi ta zauna tana mai karb'ar littafin hannunsa dan ya fuskanceta kuma ya bata hankalinsa.

Kallonta ya tsaya yi yana jiran abinda zata fad'a masa, "Sweet aikin nan naka baka gani yana shiga hak'k'ina? Jiya ka dawo garin nan da dare yanzu gobe zaka sake komawa" ta rik'o hannunsa gam fuskarta na nuna tsantsar damuwarta "I need you, can't you see that in my eyes? I need my man close to me, Sweet baka tunanin missing d'in da nake maka zai iya sa ni wani hali wanda dukkanmu zamuyi regreting nan gaba?" Bai barta ta k'ara ko kalma d'aya ba yace "i trust you, kina sona nasan zaki iya hak'urin jirana har inzo miki" kallonsa ta tsaya yi zuciyarta na mata tuni da bazai gane nufinta ba, ita kad'ai tasan halin da take ciki kuma tasan babu wanda zai iya cireta sai mijinta. Bata sake yi masa magana ba hakan yasa ya samu damar kad'aicewa da matarsa halaliyarsa, dad'inta d'aya, duk lokacin da suka keb'e yana k'ok'arin cire mata duk wani kewa da kwad'ayinta, haka zalika in zai tafi yakan bata har da wanda zai ajiyeta batayi buk'atar sa nan kusa ba, mijinta gwani ne ta fannin soyayya shiyasa take mutuwar sonsa.

Washe gari da misalin k'arfe biyu ta fito rakashi suna manne da juna, fuskarta alamar tausayi duk a kwab'e tana jimamin tafiyar mijinta kamar yau ne zai fara tafiya ya barta, ita ta bud'e masa motar bayan ta sa jakar hannunta a baya, matsa masa tayi dan ta bashi hanyar shiga motar ba tare da ta kallesa ba. Ganin baiyi motsi ba bare ya shiga motar yasa ta d'aga rinannun idanunta wanda yake cike da hawaye, bud'e mata hannunsa yayi alamar ta taho gareshi, fashewa tayi da kuka mai tsuma zuciya ta shige jikinsa ya rungumeta, sosai take k'walla zuciyarta na mugun yi mata zafi, she don't want to miss her dear husband, he mean so much to her.

K'ank'ame juna sukayi kowannensu na begen d'an uwansa. Dak'yar ya rarrasheta ya share mata hawaye sannan ya shiga mazaunin driver ta rufe masa k'ofa, sauk'e glass yayi yana mai tunanin irin son da miemiensa take masa, kallonta ya tsaya yi had'e da rik'o hannunta da ta d'aura akan sauran glass d'in da bai lume ba, murzawa yakeyi a hankali yana kallon reaction d'inta a fuskarta, "i will miss you" yace can ciki sannan ya d'aura lips nasa akan hannunta yayi kissing, kuka ne ya kufce mata a guje ta bar wurin ta koma ciki tana mai zubar da hawaye tare da takaicin zama matar pilot, kullum yana sama kamar tsuntsu bayi da lokacin ta sai dai a waya. Sosai tayi kuka har bacci b'arawo ya saceta.

A cikin baccin nata taji d'uriyar wayarta, kamar bazata d'auka ba ta janyo ta amsa ba tare da ta duba sunan wanda yake k'ira ba, muryar da taji yasa ta gane wanda ke magana "ya tafi yau kuma banji kin nemeni ba, ko bakya buk'atana wannan tafiyar nasa?" Tsaki ta ja wanda har na cikin wayar sai da ya ji ta "in ina nemanka ai ni zan k'iraka, bance kada kana k'irana sai na nemeka ba?" Bata jira amsarsa ba ta kashe wayan tana mai sake jin haushin rayuwa irin nata, mutum da aurensa amma yana haramtacciyar alak'a da wasu mazan, ya zatayi ta daina sab'awa ubangijinta da cin amanar mijinta? Ta tabbata idan ta samu lokacinsa ta bar kula wannan banzan, sa'arshi d'aya, komai nasa irin na Kamal abun begenta. Baccin da ta fasashi kenan ta cigaba da kukan zuciya tare da tir da rayuwa irin nata.

BATOOL @ Nasarawa


  Zaune take a gefen Mamanta tayi shiru tana kallon k'asa hawaye na malala bisa kuncinta, tsawar da mama ta daka mata yasa ta firgita "tashi ki bani wuri, kin tsaya kina ta yiwa mutane kuka, kinsan zakiyi da na sani kika aikata abunda kika aikata? Ni bance kada ki k'ara zuwa min gida ba? Zan had'u da Antyn naki da ta tattaru tazo da ke" masifa takeyi tana kumfar baki, daga k'arshe tace ta bar mata wuri tun kafin ta tattake ta tayi kukan da tushe, d'aki Batool ta shiga ta zube a kan gadonta tana mai DA NA SANI, addu'ar ta d'aya, Allah ya kawo mata miji tayi aure ko zai sa iyayenta su saurareta su gafarta mata KUSKUREN DA TA TAFKA a rayuwarta, babu ranar da zata zo Nasarawa ta koma bata yi kukan da zai sa ta zazzab'i ba.

Idan da iyayenta zasu gafarta mata da sunyi tun tuni, amma gashi har yau jelar zuwa take suna k'ara mata bak'in ciki da takaici. "Kai co na, nayi da na sanin aikata laifi irin wannan, ga iyayena na fushi dani a dalilin KUSKUREN DA NA TAFKA" ta d'aga hannayenta sama tace "ya Allah Ka gafarta min kaji k'aina kasa iyayena su yafe min ko dan samun rahamarka ranar gobe, nayi nadama nayi kuskure ina rok'onka Ka bani damar gyara kuskurena, ya Allah ka gafarta min" ta k'arashe maganar da gunjin kukanta har da majina.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


       11


   Sati d'aya cib da faruwar hakan, yau ya kama Asabar kuma yau ne 'yan matan suka sake hallara a farfajiyar Cubana, babu wanda yayi lattin zuwa a yau, hakan yasa suka fara tattaunawa game da wanda zai bada labarinsa. Ummu Abdoul tace Batool ta fara, ita kuwa tace fir bazata bayar ba sai taji na wasu, abun har ya fara b'atawa wasun su rai, daga k'arshe aka dire akan Benaxir ce yau da nata BADAK'ALAR, bata musa ba sai ma murmushin da tayi tana gyara zamanta akan kujerar da take zaune. 

"Bismillahi" tace sannan ta fara "am very glad yau zan bud'e cikina in baku labarina da tun da nake babu wanda ya nuna damuwar ya sani" ta sauk'e ajiyar zuciya ta dubesu d'ai-d'ai sannan ta cigaba da cewa "Sunana Benaxir... Ohpss" ta fad'i hakan tana toshe bakinta alamar tayi sub'utan baki, tace "sorry, my name is ATINUKE, asalina 'yar kwara state ce Irepodun L.G.A, Yoruba ce ni kamar yanda kuka sani kuma na taso cikin babban gida ma'ana babban family, dan familynah na d'aya daga cikin masarautar Yoruba. Ina da yayye da k'anne amma Allah bai tab'a bawa iyayena d'iya mace ba, hakan yasa na samu soyayyarsu tun daga ranar da aka haifeni har zuwa ranar da na bar gabansu.

Kamar yanda labari ya riskeni an haifeni A watar December shekara 1993, a yanzu kenan in kuka duba zaku ga ina da shekaru 23 zuwa 24, kamar yanda kuka san al'adarmu ta Yoruba mai fad'a a ji a family shi yake bada sunan da za'a rad'a wa yaro ko yarinyar da aka haifa, head of the family kenan muna k'iransa Baálé, a rana ta bakwai aka yi bidirin suna irin namu, Honey akayi anfani dashi wurin sa min suna, hakan kuma na nufin zak'i da kuma fatan rayuwata tayi zak'i(dad'i) kamar na zuma, bayan zuma ana iya anfani da abubuwa da yawa kamar Goro, Atare(Barkono), Mai, Siga, Rake, da sauransu, kowanne daga cikinsu na da nashi ma'anar a duniyar yoruba. Baálé ne ya nemi ayi anfani da Zuma saboda rayuwata ta zama mai inganci.

Atinuke aka rad'a min ma'anarsa wanda ya fito duniya dan a tarairayesa, duk wannan gatan na samu ne a dalilin kasancewata mace a cikin yara goma cib da Allah ya bawa iyayena, sosai anyi shagali a wannan ranar haka zalika an watse an barni da sunaye kala-kala, normally yoruba basu da suna kala d'aya, duk wani babba in yazo ya kan rad'a nasa sunan had'e da bada kyautar kud'i ko kaya, nima haka akayi min dan iyayena sun samu kyauta mai yawa ranar sunana.

Tun da na bud'e ido na fara wayo bansan wani abu Musulunci ba, na tashi a cikin addinin Christian bansan wani addini ba bayan wannan, haka zalika iyayena a wannan addinin suka d'aura ni, nayi shekara goma sha biyar ina rayuwata mai dad'i yanda nakeso babu takura, dan sosai aka sangarta ni aka bani freedom, babu wanda ya isa ya taka ni a family a k'yalesa, shiyasa na tashi da taurin kai da kafiya kan abinda nakeso, ban tab'a neman abu na rasa ba, komai da nake buk'ata ina samu sai dai in bance ina so ba, wani lokacin da gangan nake iskancina in take duk wanda na so saboda nasan babu abinda za'a min sai ma a rarrasheni in na tubure nace banyi ba, ko kad'an iyayena basu son kukana haka kakannina da sauran yayyuna, bansan menene b'acin rai ba shiyasa nake jin babu abinda yafi duniya dad'i.

Ina shekara sha-biyar na fara soyayya da wani Taiwo(taster of the world) 'yan biyu ne amma d'ayan nasa ya koma, shima kamar yanda ake sona haka ake sonsa a gidansu, sai dai soyayyar da ake min ya zarce nasa ba wasa ba, da farko iyayena sun so hanani fara soyayya a lokacin saboda k'ank'antata, amma da na nuna bazan daina ba suka hak'ura suka k'yaleni. Sosai nake sonsa fiye da yanda kuke zato, ban tab'a tsammanin akwai rana d'aya da zamu rabu da Taiwo ba dan irin soyayyar da mukayi abun kallo ne, duk inda zanje tare muke zuwa, haka zalika ko makaranta zanje yana biye dani, a dalilin soyayyar da mukeyi yak'i zuwa university ya zauna a gida aka bud'e masa shago dan kawai bai son a k'wace masa ni.

A lokacin da na shiga ss3 akayi baikona da Taiwo aka tsayar da maganar aurenmu, ina gama exams za'a d'aura mana aure ko mutane sa huta da yawon da muke yi a cikin gari sak'ale da hannun juna. Munyi murna iya murna kuma munyi alk'awarin babu rabuwa da juna har abada komai dad'i ko wuya. Duk rashin kunyana da irin soyayyar da mukayi da Taiwo bai sa na bashi damar kad'aicewa dani ba, soyayya dai irin wanda zan iya babu wanda ban yi dashi ba daga kan hugs da danginsa, sosai yaso na bashi kaina nak'i wanda ni kaina bansan dalili ba, zan iya cewa tsoro nakeji kuma zan iya cewa ikon Allah ne, nidai nasan mahaifiyata ko yayyuna babu wanda ya tab'a kwab'ana da hana kaina wa saurayi ko wanene shi, hakan kuma na nuni da rashin kula da rashin sa ido akan 'ya'ya.

A wani hutun da mukayi ranar Alhamis ya kama dai-dai da ranar da na fara shiga wata rayuwar da ban tab'a mafarkin shiga ba, ranar ce mafarin haske da duhu a rayuwata, ranar ya zame min ranar samun ingantacciyar rayuwa wanda nake fata ya zame min mafarin aikin ladana da zai ceceni ranar k'iyama dan rahamar mahaliccina. Tun safe 'yan gidanmu suka fara shirin fita dan zuwa Esie Museum dan halartar festival d'in da ake zuwa yi ko wani April, kwance nake a tsakiyar gida ina kallon giftawar kowa hankalina kwance dan bani da niyyan zuwa, Taiwo ma yayi dani inje nak'i shiyasa shi ma ya fasa zai zauna ya taya ni hira.

Sai da suka gama shiri tsab kowa ya fito dan shiga motar da zai kai su Daddy yazo ya sameni, ban kula da yazo inda nake ba dan hankalina na kan motar da ake gogesa, cak ya d'aukeni yana dariyar firgitar da nayi, bai direni ko ina ba sai cikin d'akina yana cewa sai na shirya mun tafi tare, k'i nayi ina basa uzurina na k'arya dan banason zuwa, har ya hak'ura muka fito ina cigaba da fad'a masa dalilaina naji cousin d'ina Banjoko na cewa "ta bada shi yau ma, sonta yakeyi yana mata duk abinda takeso amma ita for once bata tab'a yi masa abunda yakeso ba" sosai abunda ya fad'a ya b'ata min rai amma banyi magana ba, har sai da suka shiga motocinsu zasu tafi na tsayar da Daddyna nace su jirani in shirya zan bi su, nayi hakan ne dan b'ata ran Banjoko dan nasan babu yanda za'ayi su tafi ba tare da Daddy ba dan convoy mukeyi a duk lokacin da za'a tafi taro dukka gida.

Sai da na shiga na sake wani wanka dan kawai in b'ata musu lokaci sannan na fito na shirya, ahankali nake komai na dan in ja lokaci in b'atawa wanda yake ganin banson Daddy, kwalliya nayi iya wanda zan iya na sa 'yar kantina riga da skirt, na sako takalmina na zubo da gashin attachment d'ina baya na fito ina taku d'ai-d'ai dan in k'ara musu takaici, sai da na bi motar d'ai-d'ai ina kallon fuskokinsu, ganin na samu biyan buk'ata na sake murmushi har hak'orana suka fito sannan na shige motar Daddy na zauna a gefensa muka kama hanyar Esie.

Mun iso da misalin k'arfe sha d'aya har an fara wasanni, kai tsaye inda aka tanadarwa Daddy muka isa ina biye dashi a baya, Mummy da Daddy suka sani a tsakiyar kujerarsu muna kallon wasanni kala-kala wanda kowani shekara ana yinsa, alal hak'ik'a ni ba mace ce mai son irin wannan abubuwan na al'ada ba, hakan yasa na fice daga wurin taro na shiga tafkeken building d'in da aka rubuta Esie Museum, kasancewar a farfajiyar wurin ake wasanni.

Inason shiga ciki a duk lokacin da nazo saboda kallon abubuwan da aka ajiye su na tarihi, kamar hotuna, gumaka, hulunar sarauta da dai sauran abubuwa na tarihi, sosai na sha'afa da kalle-kalle naji sallamar mutum a gefena, bazan ce ban gane meh yace ba saboda ina jin wannan kalma ta "Assalamu alaikum" a makaranta wurin musulman ajinmu, ban amsa ba dan bansan meh zance masa ba, na dai juyo ina kallon kyakkyawar fuskarsa da mamaki. "Sunana Hussain, am very happy to meet you here" ya fad'i hakan yana mai sake min murmushi, sosai kyawunsa ya tafi dani dan kasa magana nayi na tsaya kallonsa.

Yatsunsa ya had'a biyu ya kawo su dai-dai fuskata ya murza sukayi k'ara dan ya dawo dani hayyacina, kawar da kai nayi ina mai jin haushin kaina dan na zak'e da yawa, shirun da nayi yasa yace "tun d'azu naga gilmawarki shiyasa na biyoki dan samun lokacinki, can we be friends?" Mik'a masa hannu nayi dan muyi shaking ina mai yi masa murmushi tare da cewa "yes" da mamaki naga ya mayar da hannunsa cikin aljihun jeans wandonsa ya nok'e kafad'a, kallon fuskarsa nayi fuskata da alamar tambaya, "sorry, am a Muslim, sauk'ar da hannun kada ace na maki wulak'anci" sai da na juya hagu da dama naga babu wanda ya ganni bare ya min dariya sannan na sauk'ar, sosai raina ya b'aci dan ba'a tab'a min wulak'anci irin wannan ba. 

Juyawa nayi na bar wurinsa ya bini a baya yana bani hak'uri tare da fahimtar dani ba wulak'anci bane addininsa ne yayi hani da hakan. Iya kalamansa da sarrafa harshen turanci irin nasa shi ya jawo hankalina wurinsa mukayi sabo a rana d'aya tak, bamu rabu ba sai da ya tabbatar ya wanke kansa a wurina tare da karb'an laambar wayata, bamu bar Esie Museum ba har k'arfe biyar na yamma. Abin da yafi burgeni dashi wayarsa na fara k'arar k'iran sallah zai tashi ya tafi yayi sallah sannan ya dawo, ya iya mu'amala da mutane kuma yana sauk'in hali da shiga rai, sai naji ya burgeni ya shiga raina. A iya zaman da nayi dashi ne yake sanar dani shi copper ne a nan Esie aka turosa, asalinsa d'an jihar Niger ne wato Minna.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


12


Sosai mukayi fad'a da Taiwo bayan na dawo cewar na hana shi zuwa ni kuma na tafi, tun ina bashi hak'uri yana tuburewa har na gaji na shigo gida na share sa, "yaya za'ayi in yi ta bawa mutum hak'uri yana neman raina min hankali?" can ciki na ja tsaki ina kwanciya akan gado tare da kawar da b'acin ran da na kwaso daga wurin Taiwo. Bacci ya fara zuwa min naji k'arar wayata, firgigit na tashi zaune a tsorace ina son gane k'arar meh ya tasheni, jin wayata ne ya sa na k'ara jan tsaki dan bazai wuce Taiwo ba, jikina a mace na d'auko wayar ba tare da na duba meh k'iran ba na sa a kunne na. 

"Hello" yace cikin zazzak'ar muryarsa da ya sani bud'e lumsassun idona ina duba screen na wayar, Hussain ne rubuce kamar yanda nayi saving, bansan lokacin da murmushi ya kubce min ba naji wani dad'i ya ziyarceni, a second goma kacal ya yaye min b'acin ran da Taiwo ya jefani ciki, tuni na mance da batunsa muka yi hira kamar mun dad'e da sanin juna har katin wayarsa ya k'are na k'ira sa muka k'arar da nawa, still bamu hak'ura ba muka koma WhatsApp muka cigaba da hira, ba wai fa hirar soyayya ba, hira kawai ta sanin juna, na fad'a masa ko ni wacece, addinina har ma da engagement d'ina da Taiwo duk babu wanda na b'oye masa.

Wasa-wasa Hussain yayi k'ok'ari sosai wurin k'wace zuciyata daga wurin Taiwo, dan ya kai ga Taiwo zai k'irani a waya yaji call waiting ink'i d'aukan nasa, kuma ko da na gama wayar wani lokacin ina jin haushin k'iransa, a lokaci k'ank'ani naji ya fita raina bana sonshi, tun muna b'oye wa juna soyayyarmu har ya kai ga a kowani k'arshen wayarmu da Hussain sai mun furta kalmar "I love you" wa junanmu, kuma fa ba wai mun sake had'uwa bane bayan farkon had'uwarmu, a'a, soyayya ce da iya jawo hankalin mace irin na Hussain, ina gaya muku bamuyi wata d'aya da sanin juna ba Hussain ya samu damar cusa min son musulunci.

Ba wai dan ina sonshi ba zan fad'a muku wannan maganar, iya gaskiya ta shine Hussain ya kasance mai son addininsa, yana da fara'a kuma bai zagin addinin wasu, bai tab'a kushe addini na ba sai dai ya fad'a min banbancin nawa da nasa, ko kuma yace min mu ma nan bamu bin addininmu yanda yazo, kuma da na duba naga hakan ne, dalilin had'uwata dashi yasa na fad'a neman ilimin addininmu gadan-gadan, sa kaya na sai da ya canja, d'abi'ata da duk wani rashin hankali nawa sai da na daina dan kawai inason in zama mai rik'o da addinina kamar yanda Hussain ke son musuluncinsa.

Hussain ya kasance yana ziyartana a makarantarmu a duk lokacin da na nemi ganinsa, ko da wasa bai tab'a min wani abu na k'i ba, ana cewa mutum tara yake bai cika goma ba nidai kam a wurina Hussain ya cika goma cif, kyawun hali, kyawun fuska, rik'o da addini da sanin yakamata. Taiwo tun yana k'ok'arin danne wulak'ancin da nake yi masa har ya kasa ya fara bibiyar lamurana tare da neman wanda yake hure min kunne, yayi sa'an samun labarin Hussain kuma har ya gano yana zuwa wurina a makaranta, hakan yasa a kullum idan an tashi yake zuwa ya jira zuwansa, sati ya jera yana haka bai samu ganin Hussain ba har ranar wata Litinin da na nace sai yazo wurina kuma ya amsa gayyata ta.

A dai-dai lokacin da aka tashi 'yan makaranta na fito kafin lokacin lesson namu yayi mu 'yan ss3, tun daga nesa na hangosa sanye da Jamfa da hula yana zabga min murmushi, uniform na jikina long sleeve shirt ne fari da guntun skirt blue sai barret blue, murmushin nima nayi masa ina mai farin cikin ganinsa a yau, burina d'aya ne a wannan lokacin in auri Hussain, kuma a yau nayi alwashin sanar dashi muradina dan mu san yanda zamuyi. 

A gefensa na tsaya dai-dai inuwar bishiyar da yake k'ofar makarantarmu, gaishe sa nayi ina mai jin nauyinsa da kunyarsa a yau, minti biyar da bai yi ba da fitowata naji k'arar bugun katako, d'aga kan da zanyi sai ganin Taiwo nayi da abokinsa da katako suna k'ok'arin kai wa Hussain bugu bayan ya durk'ushe k'asa sakamakon bugun da sukayi masa na farko.

A gigice na isa inda yake kwance suna kai masa bugu ta ko ina shi kuwa yana fitar da k'arar jin zafin ko wani bugun da suke kai wa lallausar fatar jikinsa, rumfa nayi masa ina kare sa daga Taiwo da azzalumin abokinsa ina mai kwararar hawaye, k'ok'arin janye shi sukeyi daga k'ark'ashina dan su samu su cigaba da dukansa na fad'a jikinsa ta yanda babu yanda za'ayi su janyesa, sosai nake kuka ina bawa Taiwo hak'uri, ganin basu da yanda zasu yi yasa Taiwo rik'o hannuna cikin zafin nama ya janye ni daga jikin Hussain, tun kafin ya kai ga komawa ya cigaba da bugun Hussain da yake faman kare bugun da abokin Taiwo yake kai masa na cafke k'afafunsa na rik'e ina kuka ina bashi hak'uri, tuni na karya masa zuciya ya dakatar da abokin nasa, ban daina kukan ba kuma ban daina basa hak'urin ba har sai da naga ya umarci abokinsa da barin wurin, kallon mutanen wurin yayi yana musu nuni da kowa ya watse sannan na rarrafa na isa inda Hussain yake a kwance jina-jina, kansa na d'aga na d'aura a cinyana bayan na zauna dab'as a k'asa ina mai jan majina.

Fuskarsa nake shafawa ina tambayarsa is he okay? Ganin bai amsani ba kuma bai bud'e idanunsa ba sai numfashin da yake fitarwa da k'arfi yasa na k'ara rikicewa, Taiwo da yake kallona da mamaki ya iso wurina ya tsuguna yana mai cigaba da kallona. "Meh hakan? Kinsan ke fiancée ta ce kike rik'e namiji kike nuna damuwarki akansa dan yayi min laifi na hukunta sa" bansan lokacin da na kallesa cikin ido da tsana mai k'arfi nace masa "I love him not you Taiwo, he is my other half, i love him more than words can say, shi nakeson aura ba kai ba, abunda kayi masa yanzu shi ya k'ara dasa min k'iyayyarka a raina kuma ya k'ara min soyayyarsa, is left for you ka taimakeni mu kai sa asibiti ko kada ka taimakeni" na k'arashe maganar ina mai tashi tare da k'ok'arin d'aga Hussain, cikin zafin nama ya janyo hannuna na waigo ba tare da na shirya ba, idanunsa cike yake da b'acin rai yana huci, fuskar da a kullum in na gansa sai naji wani farinciki yau shi nake gani yana ruruta wutar k'iyayyarsa, fuskar da a kullum nake cewa yana min kyau yau babu wani kyawun da nake gani face muni da bak'in zuciya, na tsanesa!

"You must be crazy Atinuke, muslim?" Ya fad'i kalmar yana nuna Hussain, "Muslim d'in kikeso?" Cikin zafin nama na k'wace hannuna ina kallonsa, hawayen idanuna suka kafe ina mai aika masa sak'on zuciyata ta tsana ta cikin idanuna, cikin dakewar zuciya nace "yes, i love him, ba sonshi kad'ai ba ma auransa zanyi, banda auren ka rubuta ka ajiye addininsa zan koma, do your worst Taiwo" ina gama fad'an haka na rik'e Hussain, dak'yar ya iya mik'ewa da taimkona duk da nima ina tangal-tangal kamar zan fad'i dan ba k'arfi ne dani ba. Mashin na samu na d'aurasa nace ya jirani in d'auko jakana dan kud'ina yana ciki, a guje na shiga cikin makarantar na fito d'auke da jakana, sai da na daidatasa kuma mai mashin ya tabbatar min bazai fad'i ba sannan na tari wani na hau mukayi hanyar clinic da ke nan kusa.

Dr. Na samu ya dudduba min shi yayi masa allura sannan ya bani takaddar magunguna, Allah yasa ina fitowa da kud'i masu yawa hakan yasa na samu na sallami dr. Sannan na fita dan komawa gida in d'auko wani kud'in dan sayan magani. Kafin in isa gida Taiwo ya rigani ya sanar da iyayena komai abunda ya faru, ciki harda k'irarin auren Musulmi da nace zanyi. A tsakar gida na same su cirko-cirko suna jiran isowata, ko kallon inda suke banyi ba nayi hanyar d'akina, ban damu da k'iran da Mommy take min ba bare kallon da suke min na shiga ciki, inda nake ajiyar kud'i kawai na nufa na ciro kud'aden dukka na sa a purse na fito, a bakin k'ofa muka ci karo da Mommy, Daddy da sauran yayyuna da suke gida.

Ban tsaya ba na kutsa kai cikinsu na samu hanyar fita, janyo hannuna Daddy yayi cike da b'acin rai yana kallona, ganin yanayinsa yasa nayi shiru banyi gardama ba tsoron kada ya hanani fita wurin Hussain. Cikin kakkausar murya ya tambayeni "abunda naji gaskiya ne?" Sai da na sauk'e ajiyar zuciya na kallesa nace "No Daddy, Taiwo ne ya b'ata min rai shiyasa na fad'i hakan, daga ganin mutum yazo wurina sai ya hau dukansa..." dakatar dani yayi dan ganin alamun bayani zan cigaba da masa, "are you sure?" Nace "am very sure" "yanzu ina zakije" ban b'oye masa ba na sanar dashi bayan nayi masa k'aryar Hussain is just a friend, sannan ya barni na fita bayan ya k'ira driver dan ya kai ni.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


       13


    Washe gari tun safe na shirya nayi girki na sa a food flask dan in kai masa, three quarter gown na sa na d'aura d'ankwali na d'auki basket d'in abincin na fita. Driver na samu ya kai ni har ciki muka shiga tare, sosai ya ji sauk'i sai tsamin da jikinsa yayi da kumburin da fuskarsa yayi, normal mukayi magana har hira mukayi muna dariya, ban koma gida ba sai k'arfe sha-biyu dan yi masa abincin dare.

A bakin k'ofa na had'u da Taiwo yana zaman jirana, ciki na umarci driver da ya shiga kada ya tsaya wurinsa, gate aka bud'e mana muka sa kai ko kallon inda yake banyi ba sai danna wayata nakeyi, sai da yayi parking na fito na ciro basket d'in nayi side namu duk da naga shigowar Taiwo. Da hanzari ya iso ni cikin sassarfa ya finciko hannuna cikin zafin nama yana cewa "baki ganni bane?" Ya matso daf dani yana huci idanunsa duk ya k'ank'ance tsabar b'acin rai, ya damk'e kafad'una da hannayensa yace "believe me i can do anything to have you, ciki har da kisa, in kika kuskura kikace zaki guje ni akan wancan gidahumin toh ki kwana da sanin cewa ya bar numfashi kenan" buge hannunsa nayi ina kallonsa cikin ido, ko kusa banji tsoron furucinsa ba duk da nasan zai iya aikata abinda ya fad'a, matsowa nayi nima daf dashi na tabbata yana iya jin sauk'ar numfashina a fuskarsa nace "kayi abinda yafi kisa, ni kuma am telling you dis for the last time, bana sonka kuma bazan aureka ba, Hussain is my one and only love kuma shi zan aura". Ban jira ya sake magana ba na juya nayi tafiyata, daf zan shiga k'ofar da zai sada ni da cikin gidanmu naji muryarsa yana cewa "R.I.P Hussain" juyowa nayi ina kallonsa yana dariyar da na tabbata na mugunta ne, komawa nayi wurinsa na nuna sa da yatsa bayan na had'e yatsuna biyu na murzasu sunyi k'ara "ina gargad'inka da tab'a masoyina, muddin ka tab'a shi you will regret Taiwo" murmushin takaici yayi yana girgiza kai "meh zakiyi? Ke bakya jin kunya ma wai Muslim kikeso? Kina son ki sa familynki da duk wad'an da suka sanki kunya" ya k'ara girgiza kai sannan ya had'e rai kamar bai tab'a dariya ba yace "i will kill that bitch..."

Ban barshi ya k'arasa maganarsa ba na sauk'esa da mari, yatsuna biyar cif ya sauk'a bisa kuncinsa, ban kai ga yi masa magana ba naji sauk'ar mari a fuskata wanda sai da duhu ya ziyarci idona na gigice tsabar zafi, waigowa nayi bayan na shafa inda aka mareni dan ganin wanda yakeson sumar dani a d'an k'ank'anin lokaci, abunda ba'a tab'a yi min ba a rayuwata kenan wato mari, ko a makaranta iya punishment d'ina a samu knee down ko kuma ayi min duka a hannu wanda ina da yak'inin bai tab'a kai wannan marin da yau na sha zafi ba. 

Daddy na gani tsaye yana huci idanunsa yayi ja, b'acin rai tsan-tsa nake hangowa wanda ban tab'a ganin Daddy ciki ba, wani marin ya kai min wanda yafi na farko zafi da gigitarwa, tuni na nemi wurin b'uya dan naga alamar zai iya k'arawa, damk'oni yayi ya janyo ni ganin ina neman wurin guduwa, girgiza ni yayi sai da hanjin cikina suka sake kad'awa naji kamar zan sume tsabar tsoro, "Muslim kikeso? Abunda Taiwo ya fad'a min gaskiya ne kenan? U are in love with him and willing to convert to his religion? Atinuke ina soyayyar da na miki tun kina k'aramarki? Abunda zakiyi mana kenan dan ki biyamu?".

Wani damk'a ya sake min har numfashina yana d'aukewa "Daddy please stop it, zaka kashe ni ne?" "Yes, in har zaki auri muslim gwanda in kashe ki in kashe Hussain" da k'arfin tsiya na k'waci kaina nayi gefe, can nesa dashi na tsaya idanuna sai hawaye yayi ja dan damk'ar da yayi min ba kad'an bane, sai da na ja numfashi na sauk'e na sake ja sannan naji ni d'an dai-dai, a nan ne na samu courage na mayar masa martani "yes Dad ina sonshi, ku kasheni ko ku kashe shi wunt change anything, shi nakeso kuma shi nakeso in aura" da gudu nayi hanyar cikin gidan ganin Daddy ya yi kaina zai sake kama ni, kashe ni zaiyi na sani dan yanda ya biyoni ba k'aramin abu zai sa ya biyo ni haka ba.

Ni na sani duk cikin yaransa babu wanda yake so irina, ya bani duk abinda nake nema na jin dad'i, ya kareni daga duk wad'an da basu sona suke k'iyayya da nasarata, na watsa mishi k'asa a ido na bashi kunya, babu abunda Daddy ya tsana irin Musulunci, yau ga 'yar sa abar sonsa tana son bijire masa dan muslmi, har tana ik'irarin barin addininsu na gado. A guje na shiga d'aki na kulle dan bai bar bina ba, bugun k'ofar yake kamar ya haukace yana son b'allwa dan kawai ya samo ni ya taka wuyana in bar numfashi, irin bugun da yakeyi ya jawo hankalin mutanen gidan, duk sun tsaya kallonsa yana buga k'ofar sai k'ara yakeyi dan k'ofar k'arfe ne, dak'yar Mommy ta samu damar hana shi, janyo shi tayi tana tambayarsa "lafiya? Meh ya sameka haka" ta fad'i hakan tana zaunar dashi a k'asa, kuka ya fashe dashi kamar yaro k'arami ya d'aura kansa a cinyarsa, ganin kukan da yake yi ya tada wa kowa hankali, abunda ba'a tab'a ganin ya yi ba kenan gaban 'ya'yansa.

Cikin kuka Mommy ta iso k'ofar d'akina tana tambayana meh ya faru? Sautin kukana kawai takeji har na tsawo mintuna uku sannan ta bar wurin tana tambayar mutanen gidan meh ya faru? Babu wanda ya bata amsa sai ma kallonta da sukeyi su ma suna neman k'arin bayani, waje ta fita inda Taiwo yake, ganinsa a tsaye yasa ta k'arasa inda yake cikin k'walla, ganinta da yayi haka yasa shi tambayanta meh ya faru, bata iya bashi amsa ba sai nuna cikin gida da take yi da hannunta, rik'eta yayi suka shigo tare inda Baba yake zaune yana cigaba da kuka.

"Meh yake faruwa, please tell me am confused" ta k'arashe maganar cikin muryar kuka, Taiwo bai b'oye musu komai ba, daga farkon labarin har k'arshe babu inda ya bari, sai da ya dasa aya sannan Mommy ta taso cikin k'unar rai ta d'auko tab'arya, da iya k'arfinta take buga k'ofar tana yi min Allah Ya isa" Benaxir ta dakata a nan tana sharar k'walla, kallonsu tayi jikinsu duk a mace saura na shirin zubar da k'walla, Pherty tuni ta fara sharar k'walla ganin yanda Benaxir ke kuka mai tsuma zuciya, tuni ta nemi tsanar Benaxir ta rasa, tsantsar tausayinta da son jin k'arashen bada'kalarta ne ya mamayeta. 

Babu wanda ya tanka ta bayan rik'e hannunta da Ummu Abdoul tayi tana girgizawa dan ta tsagaita kukan, sai da ta sauk'e ajiyar zuciya sannan ta cigaba "a rayuwata ban tab'a kuka da tsorata irin yanda nayi ranar ba, naga mutuwa da idanuna dan kad'an ya rage su b'alle k'ofar su cimmani, Taiwo ne yayi k'ok'arin hana su tare da shawarar su kyaleni har in fito sannan su san abun yi". Basu bar bakin k'ofana ba har k'arfe goma sha d'aya na dare, wando na sa mai aljihu k'ato had'e da zip na zuba kud'ad'e na ciki na lek'a window naga babu kowa sannan na bud'e k'ofar a hankali na fito.

Cikin sand'a na fito har bakin gate babu wanda ya ganni, k'ok'arin bud'e k'ofar nake in fita naga an kulle sa da kwad'o, hawaye naji ya sauk'o min dan babu yanda zanyi in fita daga gidan nan, kamar ance in juya na hango makullin mak'ale jikin window na mai gadi, cikin sand'a na isa na zare na koma dan bud'e k'ofar jin mai gadin yana wasa da ruwa a bayan gida alamar ya gama buk'atarsa yana tsarki. 

A hankali na bud'e k'ofar na cire makullin na fita dashi na kullesu ta baya, ban tsaya ko ina da ba sai asibitin da Hussain yake, da k'yar aka barni na shiga bayan na nuna musu katin da na yanka kafin a kwantar da Hussain. Direct d'akin da yake na nufa cikin zullumin yanda zai fuskanci buk'atar da nazo masa dashi, a hankali na tura k'ofar d'akin na shiga, sai da na rufe k'ofar na juyo na fuskanci gadon nasa. Tsoro, firgici da tunanin yanda zanyi in abunda na gani ya kasance gaskiya nakeyi, tsaye nayi ina kallon gadon nasa kamar babu wanda ya tab'a zama ko kwanciya akai, toilet na duba naga baya nan, babu kusurwan da ban lek'a ba babu Hussain babu alamarsa.

Fita nayi na duba room no. Naga lallai wannan shine d'akin sannan na sake dawowa nayi zaman dirshan a cikin d'akin, kuka ne mai sauti ya kufce min ina tunanin inda Hussain ya shiga, guduwa yayi? Ko Taiwo ne ya sace shi? Ko dai Daddy ne ya d'aukeshi yaje ya kashe shi? Tunanin nan ne ya k'ara dagula min lissafi tare da sani kuka.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


       14


   Sai da safe iyayena suka ankara da bana gida, babu inda ba'a duba ba cikin gidan nan basu ganni ba, mai gadi ne ya shigo ciki yake sanar dasu an kullesu ta waje, sai da aka k'ira mutanen waje suka bud'e su dan na bar makullin a jiki, mai gadi yasha zagi da fad'an Daddy, kad'an ya rage ya sha mari, dak'yar aka shawo kansa ya k'yalesa ya fara fafutukar nemana. 

Taiwo suka fara k'ira ko yasan inda Hussain yake zama yace bai sani ba, drivern da ya kai ni asibiti suka samu ya kai su, mota biyu suka yi, ciki harda Mommy da k'anwarta. K'arfe tara suka isa, d'akin da muka je drivern ya kaisu kai tsaye, babu inda basu duba ba nan ma basu ganni ba sai d'ankwalin kaina, wanda hakan ya tabbatar musu nazo wurin. Cikin rashin abun yi Mommy ta zauna dab'as a k'asa tana kuka da majina kamar k'aramar yarinya.

Ni kuwa a dai-dai wannan lokacin ina bakin titi ina neman mashin d'in da zai kai ni gida, nayi neman iya nema ban samu Hussain ba, na k'ira sa a waya yafi sau hamsin bai d'auka ba, tun yana shiga ya gama ringing ba'a d'auka ba har wayar ta daina shiga, duk da ana fad'a min wayar da nake k'ira a kashe bai hanani cigaba da k'iran layin ba. In tak'aice muku zance duk inda Hussain ya tab'a bani labari indai a cikin garin Irepodun zuwa Esie ne babu inda ban taka ba daga daren jiya zuwa yau, tilis na gaji ga yunwar da yake addabana, banda ruwa babu abunda na sa a bakina tun jiya da na bar gida na kai wa Hussain abinci.

Dak'yar na samu mashin d'in da zai kai ni anguwarmu, banyi jayayya da kud'in da ya zuga min ba na hau muka fara tafiya, nayi giving up akan Hussain, naji ya yaudareni ya fice min a rai, ya zanyi da Daddy da Mommy? Shin zasu gafarceni? Kuka nakeyi akan mashin d'in idanuna jawur sun kumbura, ina yi ina gogewa dan hawayen zubowa suke kamar ruwa, zuciyata a cunkushe na rasa ya zanyi da rayuwata. A bakin k'ofa ya ajiye ni na shigo gida sad'af-sad'af kamar wacce k'wai ya fashewa a ciki.

Tsawa naji daga bayana wanda a lokaci d'aya naji cikina ya murd'e, tun kafin in kai ga juyawa naji idanuna sun rufe, ban sake jin komai ba sai ganin da nayi wa kaina a d'akin Mommy akan gadonta, fanka na juyawa a saman kaina ina kallo naji ni da kaina ina juyawa, lumshe idanuna nayi a hankali hawaye suka bi ta gefen idanuna, Allah ya isa nake ja wa Hussain tare da k'ara tsanar Musulunci, gani nakeyi babu gaskiya a tare dashi sai yaudara da mugunta, kuma na d'auki hakan matsayin hali irin na ko wani musulmi.

Da k'yar na samu iyayena suka yafe min bayan sun ja min kunne tare da gargad'in in na sake irin haka murd'e min wuya zasuyi, basu bar ni haka ba sai da suka k'ara rura wutar tsanar musulunci da musulmai a raina. Cikin sati d'aya tak na dawo da komai nawa face farin ciki wanda na kasa samo sa, Taiwo tsundum ya dawo min baiyi fushi ba, bai k'ara tada maganar ba ma dan bai son b'acin rai, soyayya yake nuna min fiye da wanda yayi min da, ni dai bazan ce bai burgeni ba, bana sanin yana yi ma dan baya gaba na, haka zalika Hussain baya gabana, ni dai na rasa farinciki da walwala a wannan lokacin, ina matuk'ar k'ok'arin ganin na kawar da duk abinda ya faru amma da zarar na kasance ni d'aya bana iya hana kaina hawaye tare da da na sanin yadda da Hussain da nayi.

Kamar kullum ina kwance akan gadona da dare ina matsar k'walla ina tunanin Hussain da yaudarata da yayi naji k'arar wayata, k'in d'auka nayi har ya yanke, sau uku aka jera ana k'ira ban d'auka ba kuma ban duba mai k'iran ba, a na hud'u sannan na mik'e na isa wurin wayar. Numban Hussain na gani a saman screen d'ina babu suna dan nayi deleting layinsa da duk wani abu da ya dangancesa, na haddace layinsa akaina shiyasa ina gani na gane, har ya yanke ban d'auka ba ina tunanin rashin kunya irin nasa, meh yake nufi da zai k'irani? Meh dalilinsa na k'irana bayan abinda yayi min? Ya tsorata ni a lokacin da na nemesa na rasa, da farko nayi tunanin 'yan uwana ne suka hallaka shi ashe guduwa yayi ya barni, sai da ya gano idanuna sun rufe a soyayyarsa sannan ya guje ni.

Hawayena na goge ina mai jan nufashi tare da yiwa kaina fad'a, k'arar wayar da naji ne ya sa ni kallon wayar, Taiwo na gani rubuce hakan yasa nayi d'an guntun tsaki na ajiye wayar gefe na kwanta, bacci b'arawo shi ya sace ni a wannan daren. Tun daga ranar kullum sai Hussain ya k'irani ina k'in d'agawa, da ya gane k'in d'agawa nakeyi sai ya fara yi min text a ko wani k'irar da yayi min, ban hak'uri ne da kalamai masu dad'i had'e da neman alfarmar bashi damar yi min bayani. Ban tab'a yi masa reply ba bare in d'auka wayarsa har kwana hud'u, sai dai na samu kaina cikin farinciki tare da walwala, ban d'auki wayarsa ba amma naji a raina bai yaudareni ba kuma inason jin explanations nasa, jan aji da yanga tare da son nuna masa yayi laifi shi ya hanani d'auka wayarsa.

A rana ta biyar ne nayi niyyar d'auka wayarsa, bayan ya k'irani nak'i d'auka kamar kullum yayi min text kamar haka "My love for you is unconditional. The love for you is so strong and the most powerful feeling that I have had in a long time, I am just at a lost for words when it comes to you. I just wish that their was another way that we could be together without living so far apart right at the time being. I want you to know that I love you and always will and there is nothing that will ever change that about how I feel...I love you sweetheart", "Thank you" na tura masa a tak'aice ban k'ara komai akan hakan ba.

Ganin reply d'ina yasa ya k'ara k'irana, a jere ya k'irani sau hud'u a na biyar sannan na d'aga, jin nace "hello" ya sashi sauk'e ajiyar zuciyar har sai da na jiyosa, "Alhamdulillah" ya furta a hankali sannan yace "Thank you so much da kika d'aga wayana, i can explain, please understand me" bai barni na amsa ba ya cigaba da fad'in an k'irasa ne daga gida urgent shiyasa ya tafi, yayi ta k'iran wayata a kashe kuma yayi niyyan jirana amma a gida aka yi ta k'iransa, dole ya tattara kayansa ya tafi dan mahaifinsa ne bayi da lafiya, kuma ya had'u da gama service nasa da zaiyi aka d'aga, next week zai yi passing out yanzj kenan, shiyasa kawai ya tafi in yaso yazo passing out d'in kawai wata k'ila a lokacin Babansa ya d'an samu sauk'i. 

Ban sake masa ba saboda ban gamsu da hujjojinsa ba kuma a ganina bazan gamsu ba saboda bai k'irani ba tun da ya tafi sai bayan kwanaki, meh ya hana shi k'iran nawa? Na dai yi masa shiru ne ya gama bayanansa sannan nace "ka gama?" Shiru yayi da alama yayi mamakin furucina, kamar bazai amsa ba yace "meh hakan ke nufi? Baki yadda dani ba ko duk maganar da nayi baki ji ba?" "Ko d'aya, ina da abun yi ne, bye" ban jira ya sake magana ba na katse wayar.

Wasa-wasa na dawo masa tsundum na ma manta abinda yayi min, lokacin da yazo passing out yazo har makaranta tare da kyautar doguwar riga mai kyawun gaske, sosai nayi murna nayi masa godiya sannan ya tafi. Bayan tafiyarsa Minna da wata d'aya muka fara WAEC, cikin sa'a muka gama har muka fara NECO, bai dawo ganina ba haka zalika bamu daina waya tare da dreaming na kasancewa a inuwa d'aya ba." 

"Hmm!" Benaxir tace tana mai kad'a kai "abubuwan da suka faru daga baya shine har yau nake fama dashi" ta kalli Pherty tace "in kika kula bana shiri dake, ba wai dan bana sonki ba, kawai tun ranar da kika ce min ke 'yar Minna ce naji kin fita raina, saboda 'yan Minna sunyi min abinda bazan tab'a mantawa dasu ba, da ace ban zauna da musulmai masu halin kirki ba zan iya cewa musulman ne haka kamar yanda wasu Christians d'in ke yi mana kud'in goro a yanzu".

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


       15


"Tabbas ana mana kud'in goro a yanzu, kuma ba komai ke sa ayi mana hakan ba sai kuskuren da wasu daga cikin mu ke yi, sun kasa gane hali namu ne ba wai wanda addini ya koya mana ba, ko da yake sun riga da sun sani, toshewar basira ne kawai ke d'awainiya dasu" cewar Miemiebiee, Batool ta karb'e maganar da cewa "ai duk laifinmu ne, da muna bin addininmu yanda yazo mana da babu wani da zai kawo mana tashin-tashina, amma da yake anga wasu na yi shiyasa suke exaggerating abun". Maganar ya kawo hira mai tsawo tsakaninsu akan yanda ake yi mana kud'in goro, daga k'arshe Benaxir ta cigaba da labarinta kafin lokacin sallar maghrib ya yi, dan a lokacin saura minti talatin.

"A kwana a tashi ba wuya na gama makaranta cike da d'umbun burukar da nakeson cimmawa, nayi farinciki iya farin ciki dan gama makarantana yana d'aya daga cikin steps d'in da nakeson takawa na samun Hussain, kamar yanda nayi dashi ina gama makaranta zamuyi aure ba tare da kowa ya sani ba, daga cikin shirinmu shine idan na gama exams zan tattara muhimman abubuwana mu gudu tare mu je Minna, a can iyayensa zasu gama mana komai, na d'auki yadda, so da komai ma na d'aura masa dan halinsa na gari, ban tab'a d'auka shine BABBAN KUSKUREN DA NA TAFKA wanda zai dinga bina ba, abu d'aya ne banyi da na sanin shigarta ba duk da wani lokaci sashi na zuciyata na nuna min ban kyautawa kaina da iyayena ba.

Ina gama makaranta aka fara hidimar aurena da Taiwo, ban nuna na k'i ba sai ma murnar da nakeyi dan kada su gane akwai abu k'asan zuciyata, ranar da mukayi shirin guduwa tsaf na shirya cikin english wears riga da skirt har da d'an kwali na d'aura, ta cikin skirt d'in wando na sa na zuba k'ananan papers d'ina dan duba result, na d'auki ATM card d'ina da babu wanda yasan ina dashi na sa na zuge zip d'in, na d'auki sauran kud'ad'ena na zuba a purse d'ina na fito kamar zanje wani wuri. Suna zaune tsakiyan gida na fito na wucesu ko kallonsu banyi ba bare inji tsoro kada su gano ni, sai da na wuce su Mommy tace "ina zaki je da sassafen nan, k'arfe tara kin d'au wanka sai kutsa kai kike kina neman fita?".

Ji nayi kamar in shige k'asa duk na daburce, gani nake ina juyowa in ta kalli fuskata ta ga idanuna zata gane guduwa nakeson yi, sai da na had'iye yawu k'ut sannan na juyo ina mai yi mata murmushi had'e da kawar da kai dan kada mu had'a ido "wurin k'awata zanje, akwai abunda zamuyi ne da k'arfe 10:30, shine nakeson zuwa dan kada inyi latti" "look at me Atinuke, you're lying, meh kike b'oye min?" Ba shiri na d'aga kai ina kallonta, rantse-rantse na fara mata ina gaya mata ba k'arya na mata ba, bata kai ga yin magana ba wayata ta fara ringing, Friend na gani rubuce hakan yasa na nuna mata screen d'in sannan na d'auka, Hussain ne nayi saving sunansa haka dan banason a zargi ina waya dashi a kawo min cikas, magana nayi dashi kamar k'awata da take jirana, jin nayi haka ya gane plan ne kawai, dan kaina na kashe wayar bayan na gama conversation d'ina na k'arya, ina kashewa na juya da hanzari ina ce mata "bye Mum, kada inyi latti" ban jira ta amsa ni ba na fice. 

Mashin na hau kai tsaye ya kaini inda zan had'u da Hussain kamar yanda muka tsara, kud'in mashin d'in ma shi ya biya na shige motarsa(Babansa ya saya masa mota bayan kammala NYSC) sai da ya tsaya a wani boutique na saya kayan sawa da wani k'aramin akwati sannan muka bar garin. Hankalina kwance muke tafiya muna hirarmu kamar ba guduwa nayi na bar iyayena ba, wauta da yaranta duk su suka rufeni a wannan lokaci, ban tab'a tunanin wani abu mara kyau zai iya faruwa dani ba, ban tab'a tunanin Hussain zai iya cutar dani ba, infact zan iya cewa nafi yadda dashi akan iyayena, kuma na nemi dalilin wannan yaddan na rasa.

Sai dare muka isa Minna da misalin k'arfe tara, wurin antynsa ya ajiyeni mai suna Benaxir shi kuma ya wuce gida, sosai ta tarbeni cikin girmamawa da k'auna, wanka ta sani nayi bayan ta kai min ruwan zafi, ina fitowa naga abinci ajiye yana jirana, akwatin nawa na bud'e na d'auki k'aramar riga na sa dan bani da rigar bacci, skirt na jikina na sake mayarwa jikina dan bansan abinda zan d'aura yayi min dad'in bacci ba, shigowanta yayi daidai da gama sa skirt d'in, sai da ta ciro min zani mai kyau a goge daga cikin drwarta ta mik'a min tana cewa 


"ki d'aura wannan zai fi miki dad'in bacci"


Ban musa ba na karb'a ina mai yi mata godiya. Bayan na gama shirina na zauna na ci shinkafa da miya had'e da coleslaw dan tasan da zuwanmu. Ina gama wa tace in zan kwanta in hau gadonta inyi bacci, kada in damu, godiya kawai nayi bayan ta fita na d'ale gado na kwanta babu tunanin komai a raina, kamar an shafe babin iyayena daga kwanyana haka naji.

Ban farka ba sai safiya bayan rana ya haske min fuska, da alamu nayi bacci sosai kuma na huta gajiya, ban dad'e da tashi ba ta shigo da murmushi fal fuskarta "kin tashi ne? Ai naga kin gaji shiyasa ban tashe ki ba" sunkuyar da kai nayi nace "eyyah, na tashi yanzu, ina kwana?" "Lafiya k'alau" ta amsa tana mai lek'a toilet nata, "akwai ruwa a heater in zakiyi wanka, in kin gama shiri ki fito kiyi breakfast, ko in kawo miki nan?" Ta tambayeni tana kallona, Murmushi nima nayi nace "a'a, bari in shirya sai in fito inyi a can, nagode sosai da d'awainiya" tace ba komai.

Wuni d'aya kacal nayi a gidanta amma naga gata da soyayya kala-kala, ita ta aika aka sayo min sim na mtn had'e da kati na d'ari biyar dan na cire sim d'ina na karya tun muna kan hanya bayan nayi saving numbers na mutane akan phone. Sosai na sake da ita muna hira har kitchen na shiga tare da ita dan gabatar da girkin yamma, a shekaru bazata wuce talatin da biyar ba, tana da yara biyar, d'aya yana university a Katsina, wanda ta dalilinshi muka had'u da Batool lokacin da na kai masa ziyara, shekara biyu da suka wuce, sai 'yan mata biyu da suke secondary school dukka(boarding), sai 'yan maza biyu, d'aya na primary d'aya na jss1 boarding school.

Washe-gari tun safe na tashi dan in tayata had'a breakfast, sai da na fito naga mijinta na sa wa junior bottles na uniform d'insa, har k'asa na tsuguna na gaishesa sannan na shiga kitchen, ni na fito masa da lunchbox d'insa na mik'a masa suka fice. A k'ofar kitchen naci karo da Benaxir tana fitowa, "har kin bashi? Kar dai sun fice?" Ta tambaya tana mai lek'a palon, ganin basu nan yasa tayi saurin fita wurinsu, cikin kitchen d'in na shiga dan gyara abubuwan da tayi anfani dasu na abincin da tayi wa mijinta da kuma d'anta. 

Ban kai ga fara aikin ba wayanta ya fara ringing, d'auka nayi na bi bayanta dashi kai tsaye ba tare da tunanin wani abu a raina ba, abunda najiyewa kunnena ne yasa na dakata a bakin k'ofar "arniyar zaki ajiye min a gida? Shi yaron bayi da hankali ne da zai kawo ta yace zai aura? Meh yasa bai kai ta wurin mamansa ba" banda hak'uri babu abinda Benaxir take yi da faman yi masa tuni da jihadin da Hussain yake son yi, a iya abunda naji na gane k'yamatar addinina yakeyi ba wai ni d'in ba, nan take na ji ina son in musulunta tun kafin iyayen Hussain su ji su hanani aurensa, komawa nayi na ajiye wayar kamar ban d'auka ba na kama yin abinda nayi niyya. Sai da na gama komai na d'auki waya na sanar da Hussain ina son in musulunta, yana ganin text d'ina ya k'irani cike da murna dan muryarsa bai b'oye min hakan ba.

Ina mai tabbatar muku a ranar na musulunta na nemi a sa min suna Benaxir(unique) dan halaccin da tayi min, ban ma san ma'anarsa ba a lokacin amma da yake babu wani musulmi da na sani mai halin kirki sai ita hakan yas na zabi sunan. A k'alla nayi sati biyu a gidanta, na samu kulawa daga wurinta har ma da mijinta, dan tunda na musulunta yake sake min fuska, ya sayo min hijabi kala biyu tare da Qur'ani da k'ananan litattafai na addin, Benaxir ita ta zama malamata, duk wani abunda ya dace in sani tana k'ok'arin koya min, alwala, Sallah, yanayin sa kaya, sallama, amsa sallama kai hatta shiga toilet sai da ta koya min, na zama 'yar gida ta zame min mahaifiya mijinta ya zame min mahaifi. 

Tunda na bar gida hana rantsuwa sau d'aya na b'oye layi na k'ira Mommy, ranar dai nayi kuka har naji ina ma ban tafi ba, inason sanin halin da na bar su a ciki, muryarta kadai ya tabbatar min bata da lafiya ko wani abu na damunta, damuwar da na shiga a wannan lokacin ne yasa Hussain ya goge layukansu daga wayana ya kofe a nasa wayar yana mai jaddada min zamu kai musu ziyara bayan munyi aure in daina damuwa.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


       16


Watanni biyu da zuwana babu maganar iyaye su san dani bare maganar aure, tun ina d'aukan abun matsayin yayi masa nauyi har na fara fuskantar cewa iyayensa basu karb'i maganar tasa bane, tun ana zuwa har gida a kalleni a yada min maganganu ana zagin kasuwa har ya kai ga yayyensa da k'annensa su zo har gida su min tas banida ta cewa, Anty Benaxir ce bangona mai kare ni, tun ina tausan kaina akan iyayensa bazasu min haka ba har ya kai ga mahaifiyarsa da kanta tazo har gida ta ci min fuska ta zagi anty Benaxir ta tafi babu yanda muka iya. Ko na fad'awa Hussain babu abinda yake iya yi sai ma yace inyi hak'uri zai wuce, soyayya dai babu wanda baya nuna min, ya sani islamiyya ya kawo min meh adaidaita kullum shi zai kai ni ya dawo dani yana biyansa ko wani wata.

B'angaren mijin Anty Benaxir da matarsa ban rasa komai ba na jin dad'i a gidansu, duk da lokacin hutu na sha wahala wurin 'yan matansu guda biyu, Fatima wacce ake k'ira Faty azland da Haneefa, babu kunya ba tsoron Allah zasu min tas, Azland kam harda zungure min kai da yi min gori, kuma aiki suke sani kamar sun sami mai aiki, hatta inner wears d'insu tara min sukeyi in wanke dan a yanzu na koma d'akinsu da zama, ban tab'a k'orafin abinda suke min ba dan mahaifiyarsu ta gama min komai, kuma tana tare min tana tsawatar musu indai sunyi min abu a gabanta, a shekaru na girme musu haka a jiki, amma hakan bai hana su yi min rashin kunya dan ganin babu abunda na isa inyi musu a gidan ubansu.

Yau ya kasance asabar da misalin k'arfe biyu na rana, zaune nake a farfajiyar gidan akan rubber chair da ke k'ark'ashin rumfa ina rik'e da jakan islamiyata idanuna akan wayata ina game, Hussain ne ya shigo hankalinsa tashe yayi hanyar shiga cikin gida, jin muryana na k'ira sunanshi yasa ya juyo inda nake da hanzari yana cewa "babu abinda ya sameki ko, basu miki komai ba ko? We have to go Benaxir, suna so su raba mu..." Bai rufe bakinsa ba naga hajiyarsa ta banko k'ofar gidan ta shigo da wasu 'yan mata a bayanta wanda na tabbatar k'annensa ne, babu inda suka nufa sai inda nake cikin zafin nama suna k'ok'arin cironi daga bayan Hussain, hannuna ya rik'e gam ya mayar dani bayansa yana kallon k'annen nasa, ganin ya had'e rai yasa suka kasa aiwatar da abunda suka yi niyya.

"Hussain ka fita idona in rufe akan wannan yarinyar, na fad'a maka bazaka aureta ba, ba da yawuna ba, ubanka yace baya so nima nace banaso, ka fad'a min yardan da kake nema bayan nawa da na mahaifinka, ka kiyayeni fa" ta k'arashe maganar tana nuna shi da yatsa.


"Hajiya na fad'a miki yardar Allah kad'ai ya isheni, idan baku barni na aureta ba zakuyi asarana ku nemeni ku rasa, tun ina muku a hankali kada ku sa ina d'aga murya akanku ina kwasan zunubi, yarinyar nan ta musulunta ba tare da nace sai ta musulunta zan aureta ba bare ku ce ba dan Allah tayi ba..." "Yi min shiru" ta dakatar dashi, janyo hannuna tayi ta jefani bakin k'ofa nayi tangal-tangal na zube a k'asa, hannunah da ya gogi k'asa sai da ya gurje yana fito da jini kad'an-kad'an, kuka mai sauti ya kubce min.

Bata saduda ba sai sirfa masifa takeyi tana ik'irarin sai na bar gidan yau, Hussain bai tankata ba yayi inda nake ya d'agani sannan ya duba hannuna yace "sorry" yana mai kallon fuskata, ban daina kukan ba sai ma bugun zuciyata da ya k'aru, rik'e da hannuna yayi cikin gida ko kallon Hajiyarsa baiyi ba bare yabi umarninta na ya kyaleni in bar gidan tunda ba na ubana bane, yana shiga ya kulle k'ofar da sakata ya janyo ni ya ajiye ni akan kujera.

1st aid box ya d'auko ya dawo parlon ya fara goge min ciwona ina kuka k'asa-k'asa ina mai janye hannun nawa a hankali dan zafin da nakeji, bai barni ba sai da ya gama ya mayar da box d'in ya shiga d'akina ya d'auko akwatina ya ajiye min a gabana yace "ki shiga ki d'auko sauran kayanki mu bar gidan nan" bai k'ara komai akan hakan ba yayi hanyar fita ya bud'e musu k'ofar ganin zasu iya b'allawa dan ba k'aramin bugu suke yi ba.

Tun kafin su k'arasa shigowa na shiga d'aki na kwaso sauran kayana da handbag d'ina na fito, a parlon na samesu hajiya na ta surfa masa ruwan bala'i, a daidai nan anty Banexir ta dawo daga kasuwan da ta tafi, ganinmu cirko-cirko ta gane ba lafiya ba, ajiye kayan tayi a bakin k'ofa ta k'araso ciki tana kallona ina k'ok'arin cusa sauran kayana cikin jaka. "Meh hakan? Ina zaki je? Gidan uban waye nan cikinsu da zasu yi iko dashi? Babu inda zaki je, wanda yaga yana da iko da gidan nan ya fad'a min in kwashi kayana in tafi nima" Hajiya dariyar k'eta tayi tace "na fi ki hauka, ke kina ganin kinyi baki ko? Toh ina mai tabbatar miki idan baki bari ta fita ba ke da kanki zaki tattara naki ya naki ki bar min gida, a yau idan nace Alhaji ya fitar dake ko awa d'aya bazai k'ara ba zai fitar da ke da 'ya'yanki" tana rufe bakinta ta ciro wayarta ta dannawa Alhaji k'ira, a handsfree ta sa ta fad'a masa buk'atarta ya maimaita "idan wannan yarinyar bata fita daga gidan nan ba Bena na baki awa uku ku fice min daga gida" bai k'ara komai kan hakan ba ya kashe. 

Sosai sukayi rikici ganin abun zai wuce iya wanda na gani yasa na ja jakana nayi waje ina mai sharar kwalla, Hussain ne ya bini a baya yana cewa Anty Benaxir tayi hak'uri ta zauna a gidan shi ya tafi dani zai nemo min inda zan zauna. Bansan ya suka gama ba, Anty Bena dai ta k'irani kuma ta tabbatar min komai lafiya in kula da kaina. Gidan abokinsa ya kai ni kafin washe gari yasan abun yi, nayi masa kuka iya kuka ina ce masa ya barni in koma gida shi ma ya bi umarnin iyayensa, dak'yar ya rarrasheni nayi shiru amma ba wai dan na fasa tafiya ba, na bar gidanmu bare wani gidan?

Washe gari tun safe na fita ban bari matar abokinsa ta ganni ba, Atm machine na biya na cire kud'i sannan na tare mai adaidaita ya kaini tashan da zan samu motar Abuja, Allah da ikonsa ban dad'e da zuwa ba muka tashi. Tunda muka fara tafiya ina kuka har bacci b'arawo ya saceni, wayana a silent na sa dan banason in kashe in tada wa Hussain hankali, mun isa Azahar aka ajiyeni a Jabi park, Hussain na fara k'ira dan bansan ina zanje ba, nasan akwai wata k'awata da take zama anan Abuja ita kad'ai nake sa ran zan samu mafaka a wurinta kafin Allah yasan yanda zaiyi dani. Sosai ya shiga tashin hankali, ganin k'irana yasa ya d'auka da hanzari yana tambayan inda na shiga, ban b'oye mishi ba na fad'a masa, sai da ya gama min masifa sannan yace in k'ira k'awar tawa washe gari zai zo Abuja ya sameni.

A tak'aice dai dalilin shigowana Abuja kenan, kuma har yanzu a gidansu wannan k'awar tawa nake, babu mai takura min sai ma freedom d'in da nake dashi, Hussain ya sani a nan Gwagwalada university wanda har yanzu ban gama ba, bayan haka ina business, kuma dashi na dogara nake biyawa kaina buk'ata, a b'angaren iyayen Hussain kuma na ma cire su daga lissafina dan babu alamar zasu yadda in aureshi, zan iya cewa shi ya ma manta da ni da rayuwata, yayi aurensa yana da yarinya d'aya, A fannin iyayena kuma naje sau d'aya ni da Hussain bayan tarewana a Abuja.

Ina zuwa Daddy na fara cin karo dashi ko ciki bai barni na shiga ba, rufe ido yayi yace bai sanni ba in fice masa daga gida, ganin nak'i fita ya fatattakeni da gudu, a waje na tsaya ina ta zabga kuka Hussain na bani hak'ura, sai da naga 'yan gidanmu d'aya bayan d'aya sannan na tafi bayan Daddy yace in bamu bar masa k'ofar gidanshi ba zai k'ira mana policemen." 

'Tak'aitaccen labarina kenan" ta fad'i hakan tana mai sake musu murmushi, "yanzu bakiyi aure ba kenan har yanzu? Dan wani ya b'ata miki rai ya nuna miki halinsa shine zaki kasa cigaba da rayuwarki?" Cewar Ummu Abdoul, "ni zanyi aure? Hmm lallai, ina makaranta ina aiki ina samun kud'i meh yafi raina? Ai ni bazan fara sa kaina auren 'yan arewa ba bare a maimaita abunda ya faru, banason ciwon zuciya". Pherty tayi dariya tace "an koya miki hankali kenan, ki bari cikinmu mu baki yayanmu, wata k'ila ya iya hak'uri da masifarki" bugu Benaxir ta kai mata a kafad'a tana dariya, kowa sai da ya tofa albarkacin bakinsa sannan suka mik'e don gabatar da sallar maghrib.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


       17


    Wayar Pherty ne ya fara ringing a dai-dai lokacin da ta tada kabbarar harama, babu wanda ya d'auka har ya katse bare su duba wanda ya k'ira, kafin ta idar an k'ira sau uku, a na hud'u ne Miemiebee ta d'aga wayar ta duba sunan, "his highness" yake rubuce a screen na wayar, receiving tayi ta sa a kunnenta tace "tana sallah" "hello" yace kafin yaji sak'on nata, jin tace tana sallah ya cigaba da cewa "ok, in ta idar ta k'irani" cikin muryarsa mai sanyi, bata kai ga amsa shi ba taji d'ib ya kashe. 

Bata ajiye wayar ba sai da tayi iya dabarunta wurin d'aukar numban a nata wayar, haka kawai taji muryar yaron yayi mata, amma his hyness? What if mijin da zata aura ne? Baki ta tab'e irin ina ruwana sannan ta shiga pictures, a dai-dai nan Pherty ta iso tana tambayar waye ya k'irata, "his hyness" tace tana mai kallon fuskarta, ganin b'oyayyen murmushinta yasa taji kishi tare da son sanin waye ne His hyness na Pherty? Ita kuwa d'aukan wayarta tayi ta danna masa k'ira tayi mata nuni da hannu alamar 1minute sannan ta bar wurin tana mai d'aura wayar a kunnenta tana sake murmushin da yake nuna tsantsar farincikinta.

Sai da ta d'auki ak'alla minti uku sannan ta katse wayar ta dawo mazauninta, har lokacin bata daina murmushin ba haka kuma bata daina danna waya ba, mik'a wayar tayi wa miemiebee tace "d'aukeni hoto, his hyness na son ganina" karb'ar wayar tayi ta saita ta d'auketa, "karcak" kakeji flash ya haskata ya d'auketa hoto, a cikin WhatsApp camera ta d'auki hoton, hakan yasa ta mik'a mata dan ta gani, sai da ta tura ta sake mik'a mata tana cewa "k'ara min d'aya" ba musu ta danna ta d'auka, a hanzarce ta danna send hoton ya shiga chats na Pherty da His hyness, hotonsa ta gani shima ya turo mata cikin k'ananan kaya, kyakyawa ne ainun fari tas, yana da k'asumba kwance luf sai shek'i yake, lips nasa da flash ya haska sai yalk'i yake shi yafi komai jan hankalinta a surarsa, ganin zata zak'e da yawa yasa ta fita daga hoton tana cewa "sorry, na tura hoton by mistake" Pherty bata kula da abunda Miemiebee ke yi ba dan tana magana da Batool duk ta k'are wa Hyness nata kallo, karb'ar wayan tayi kawai ta cigaba da chating nata.

Sai da duk suka idar da Sallah suka ci abinci sannan suka samu damar cigaba da tattaunawansu, "alhamdulillah munji labarin mutane biyu, saura biyar kenan, zamu cigaba daga inda muka tsaya ne a yanzu ko kuma sai gobe? Sai mu zo da safe dan inason a cikin weekend d'in nan mu gama komai muyi taking next step" cewar Ummu Abdoul, Rufaida "gaskiya ni gobe akwai inda zanje, sai dai muzo kamar yanda muka saba zuwa". Pherty tace "nidai ina gida, ko k'arfe nawa zan zo i will b free gobe" Miemiebee cewa tayi "zan iya cewa am free, dan yau Swt Kamal yayi tafiya, kunga kenan bani da abun yi sai dai ban sani ba ko zai iya kamawa inje wani wurin, amma da dai a bari sai bayan la'asar d'in zai fi mana" ganin yawancinsu sunfi yadda da a bari sai lokacin da ake zuwa yasa suka tsayar da maganar a hakan. 

Shirin tafiya sukayi dukka, Benaxir ta shiga nata motar ta wuce, Ummu Abdoul da Lubiee suka shiga na Pherty kamar yanda suka zo, Batool ta shiga na miemiebee aka bar Ruffaida anan tsaye tana jiran mai d'aukanta. Sun bar wurin ko minti goma baiyi ba ya shigo harabar, kai tsaye ta isa inda yake suka bar wurin sukayi hanyar gida. Bai tsaya ko ina ba sai cikin gidansa kuma gidan da Ruffaida ke zama wato gidan Mamu wacce yaranta ke k'iranta Mommy.

Cikin gidan suka shiga hankalinsu kwance hannunsa cikin nata sai hira suke a hankali suna dariya, d'akinta ta shiga shi kuma ya hau sama d'akinsa. Babu kowa cikin gidan a yau suka tafi hutu gida can Zaria, Mamu tayi-tayi dashi su tafi tare yak'i a nashi cewar aiki yayi masa yawa wanda maganar gaskiya ba aiki ne ya masa yawa ba, baya son zuwa ne saboda Ruffaida tana makaranta baza'a tafi da ita ba, tafiyarsu zai basu freedom suyi duk yanda suke so a cikin gidan ba tare da an musu cikas kamar yanda akeyi ba a yanzu.

Wanka tayi sannan ta sa kayan baccinta bayan ta feshe jikinta da turare, kamar wacce zata isa wurin mijinta a turaka haka ta shirya tsaf sai k'yalk'yali take. Babu kunya ta isa gareshi a d'akinsa, yana ganinta ya sake mata murmushi ya tashi ya tarbeta, juyata yayi dan ya k'are mata kallo cikin b'ingilar rigar baccin da ta sa, babu abinda takeyi sai dariya k'asa-k'asa dan tasan ta burgesa a yau, rungumeta yayi ya rad'a mata a kunnenta "ina ma zan iya aurenki, da na huta, Ina sonki Ruffy". Bai k'ara komai ba suka lula rayuwar da suka saba, basu la'akari da alak'ar da yake tsakaninsu haka zalika basu jin kunyar mahaliccinsu da yake kallon duk wani aika-aika da b'uruntun da suke aikatawa, wa iyazubillah( Allah ya tsare mu).

Pherty:-


Sai da ta ajiye su a gida sannan ta wuce nata sharholiyar, har gida taje ta d'aukesa suka wuce wurin shak'atawa, sai da ta kai shi ya ci abinci sannan suka wuce hotel d'in da suka saba shek'e ayarsu. (Yaro ne matashi mai jini a jika, Sunanshi Ibrahim Pherty na k'iransa His hyness), Ibrahim ne ya kwab'e fuska kamar zai mata kuka a dai-dai lokacin da ya janye leb'b'ansa daga nata, bud'e ido tayi ahankali tana kallonsa jin ya daina yi mata abinda yake yi nan take, hannunta da yake rik'e dashi ma ya sake ya matsa gefe, kallonsa tayi tana mai rik'e hannunsa tare da kusantoshi tana tambayarsa meh ya faru? Cikin muryarsa kamar zaiyi kuka ya fara da cewa "Pherty a kullum ina da na sanin kasancewata talaka, da ban zama talaka ba babu wanda ya isa ya raba mu bare ya aurar dake ga wani ba ni ba".

"Shh!" Tace tana mai d'aura hannunta akan lips nasa "please stop saying that his hyness, ko da nayi aure ai ina tare da kai, mu manta komai muyi rayuwarmu tunda su suka zab'a mana hakan, besides ta hakan muke samun biyan buk'atunmu, da ban aureshi ba duk kud'ad'en da nake baka ina zan samu? Ka manta babu wanda yasan ina da aure a nan Abuja? Am yours nd u're mine, shikenan" yace "no, you're not mine alone, ai ke kin..." Bata barshi ya k'arasa ba ta toshe bakinsa had'e da yi masa abubuwan da tasan bazai iya jurewa ba. 

Miemibee:-


Bayan ta ajiye Batool a gida direct gida ta wuce ita ma, babu abunda yake mind nata sai hyness na Pherty, waye shi? Ina zan same sa? Shin zai amsa ta gayyata ta idan na nemeshi? Ki dai mijinta ne? Tsaki ta buga tana mai kad'a kai, ta gaji da iskancin da Balarabe yake mata idan ta nemeshi in Kamal nata baya nan, gwanda ta nemo sa ko zai maye gurbinsa, ta tabbata wannan gayen zai fi kashe mata k'ishin ruwanta akan Balarabe, da tunaninsa bacci yayi awon gaba da ita, ko wayanta da yake silent yana ta vibration bata ji ba bare ta d'auka.

Kamal ne ya k'irata sau biyar bata d'auka ba, dan kansa ya hak'ura ya daina k'iranta a nashi tunanin tayi bacci da wuri dan kada kewarsa ya hanata bacci anjima kamar yanda ta saba fad'a masa, tausayinta yaji a ransa yana mai kewar rigimarta, a fili ya furta "I Love You miemienah".


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


       18


Ummu Abdoul @ 9:30am


     Mai take shafawa a k'afarta Feedoh ta shigo rik'e da plate a hannunta. Ajiyewa tayi a gaban Ummu Abdoul ta samu wuri ta zauna ita ma tana fuskantar ta, tana gama shafa man ta janyo plate d'in ta bud'e, indomie da kwai ne a ciki sai fork d'in da ta soka mata dan ci. Sai da ta fara ci sannan Feedoh tace "wai yanzu ni nake ta binki da magana d'aya? D'anki ne fa ba d'an kowa ba, kin bar shi tun yaushe? Shi kenan dan iyaye sun samu sab'ani shi bazai samu jin dad'in uwa da d'uminta ba? Ke kinsan yakamata kije ki duba sa, in so samu ne ki d'aukosa ki kawo sa nan ko hutu ne yayi, shi Abban wani irin mutum ne da baya tausayi?" Ummu Abdoul ajiye plate d'in tayi ta mik'e tana cewa "tunda indomien naki ne bakya son inci sai in bar miki", mayafi ta d'auko ta yafa sannan tayi hanyar fita. "ni dai na gaji da rok'o da neman alfarman a kawo min boy, Hajiya zan rok'a ta barni inje ko ni da Auta ne, in batason Auta taje sai Mus'ab ya raka ni, kuma Allah in na kawo sa ko hannunsa bazaki rik'e ba, zance masa ni kad'ai ke sonsa", maganar Feedoh bai sa ta dawo ba, hawaye ta ji ya cika idanunta dan tausayin kanta da yaronta, ga wani sabon al'amarin da Malam Usman yazo mata dashi da yakeson dagula mata lissafi, ta window ta fad'awa Hajiya ta fita sannan ta fice ta shiga motarta, sai da tayi kuka iya wanda zata iya ta bawa kanta hak'uri ta tada motar ta bar gidan dan zuwa duba Colleague nata da aka kwantar asibiti.

Miemieebee @ 10 am


   Kitchen take tana had'awa kanta breakfast a dai-dai wannan lokaci, wayanta da ke sak'ale cikin aljihun wandon baccinta taji k'arar text ya shigo, sugar cube da yake hannunta ta cilla shi ya fad'a cikin tea da take had'awa tsabar sauri ta ciro wayar ta shiga cikin text d'in. "Who are you?" Kawai yake a rubuce, sai da ta murmusa sannan ta yi reply kamar haka "Hae mr. handsome, zaka sanni kada kayi sauri. Zan iya ganinka yau?" Sai da ta tabbatar sak'on ya tafi sannan ta murmusa ta cigaba da abunda takeyi tana mai tuna farkon sak'on da tayi masa na yabo da zuzuta kyawunsa, daga k'arshe tace masa yana burgeta. Dak'yar ta samu courage na turawa dan tana tsoro da kokonton abinda zai je ya dawo, yaron dai ya mata, zata iya yin komai dan samun lokacinsa. Bai yi mata reply ba sai da ta kammala cin abincinta ta shiga wanka, da wayar ta shiga dan kada yayi reply tana wanka, bata fito ba kuwa yayi mata reply da "No" a tak'aice. 

Ji tayi kamar ta rusa ihu da ta karanta, jiki ba laka ta fito ta wurga wayar akan gado, mai kawai ta shafa sai powder da wet lips. Kwanciya ta sake yi tana tunanin yanda za'ayi ta shawo kan wannan bawan Allahn, wayarta ne yayi k'ara ta janyo ta d'auka ganin Kamal nata ne ke k'ira, a kunnenta ta sa tana turo baki kamar yana kallonta, jin tayi shiru ya gane meh take nufi "haba love, kwana biyu ya saura fa, tun yanzu kin fara k'osawa kina had'e rai? Meh kikeso yanzu tell me?" Cikin shagwab'ab'b'iyar muryanta tace "my husband" da dabarunsa da ya saba yi mata yasa ta sake tayi hira dashi har da dariya sannan suka yi sallama.

Ruffaida @ 11am


    Nuraddeen ne ya fito daga d'akinsa ya sauk'o k'asa cikin dakakkiyar shaddarsa ya nufi d'akin Ruffaida, fitowanta daga wanka kenan tana d'aure da tawul iya gwiwa, ta bayanta ya zo ya rungumeta yana mai cusa kansa cikin gashin da Allah ya hore mata, magana yake mata k'asa-k'asa tana murmushi har ya fara yi mata cakulkuli ta fad'a kan gado tana darawa tana ce masa ya daina, basu yi aune ba suka ji an buga window ana cewa "Ruffaida ke da waye?" Ware ido tayi ganin ya bud'e glass na d'akin yana k'ok'arin d'aga labulen, da gudu ta isa ta danne tana cewa "Haba yaya babba bani da kaya fa kake k'ok'arin bud'ewa" jin ta fad'i haka yasa ya bar kiciniyar bud'ewa.

"Baka fita bane yau?" Ta fad'i haka tana mai yi wa Nuraddeen nuni da ya fita daga d'akin, bai amsa ta ba yace "ke da waye a d'akin nan?" "Babu" "babu kuma kike dariya haka? Ke d'aya zaki yi ta dariya kamar mahaukaciya?" Cikin i'ina tace "waya nakeyi fa da k'awata" tsaki ya ja yace "ni zan fita, tun d'azu nake jira ki bud'e k'ofa in samu inyi breakfast baki bud'e ba, kuma kamar Daddy bai fita ba ma shiyasa na hak'ura nasan ba'ayi ba sai ya tashi daga bacci" washe baki tayi tace "eh nima jiransa nake ya tashi inyi mana abincin, ganin bai tashi ba yasa na sha tea kawai na hak'ura banson girki sau biyu" "na tafi nikam sai yamma zan dawo ko dare ma, kinyi waya da su Mommy? Wai yaushe zasu dawo?" Daga nesa yaji amsar nata da cewa bata sani ba, dan yana tambayar ya k'ara gaba wurin motarsa.

Ajiyar zuciya ta sauk'e sannan ta fara nemo kayan da zata sa, riga da wando ta ciro har da after dress dan anjima in ta tashi fita ta sa. A bakin k'ofa yanzu ya tsaya yayi knocking yana cewa "zan fita, yunwa nakeji zan nemo abinda zan ci" bata amsa shi ba ta zura after dress d'in ta fito tace "mu je tare nima ai yunwar nakeji" bai yi musu ba ya rik'o hannunta suka fito ko kunyar masu aikin gidan basu ji.

Pherty @ 1pm


   Zaune take a gefensa tana kallonsa kamar zatayi kuka, sosai yake tsorata ta in ya d'auke mata wuta, tun jiya bayan rabuwansu bai sake mata ba har yanzu, tayi ta tambayarsa meh yasa ya canja mata yak'i amsata sai ma kallon tv da yake yi a yanzu da tazo har gida dan jin laifinta, zata iya cewa bata yi baccin kirki ba dan yak'i d'aga wayarta jiya bayan ta ajiyesa ta tafi. Sunanshi ta k'ira "Ibrahim" yak'i amsa ta, bata san lokacin da ta sake masa kuka mai sauti tana kare fuskarta da hannunta, lumshe idanunsa yayi dan bai son kukanta, shi matsalarshi d'aya ta rabu da wancan mutumin ta dawo masa shi kad'ai, ya rasa ya akayi ta kasa gane yana kishinta. Jin kukan nata ba na k'arewa ba yasa ya juyo yana fuskantar ta, "am sorry" yace yana mai kallonta fuskarsa na nuna tsantsar soyayyarsa da begenta, "in ka daina sona ne ka fad'a min mana, ko wata ka samu wacce ta fi ni yanzu shiyasa kake min haka?".

Janyota yayi zuwa jikinsa yana mai rarrashinta tare da jaddada mata ita kad'ai ce a k'albinsa, soyayyarta ya mamaye dukkansa bazai iya had'a ta da wata ba kamar yanda ita ta iya had'ashi da wani. Bai kai ga k'arashe zancensa ba wayarta ya fara ringing, shi ya d'auki wayar ya duba wanda yake k'ira, nuna mata yayi taga "Alhaji" sannan ya danna receive ya d'aura mata a kunne, duk da ture wayar da takeyi dan kada tayi magana dashi bai hanasa d'aura mata wayar a kunne ba. "Baby bakya ji na?" Taji muryarsa, har cikin ranta ya b'ata mata rai da ya k'irata a dai-dai wannan lokaci, gaishe shi tayi ya sanar da ita yana hanyar gida yanzu ya sauk'o, sai ka iso kawai tace ta katse wayar.

Cikin b'acin rai Ibrahim ya mik'e yayi hanyar toilet rik'e da wayarsa, bai saurari zancen da take jero masa ba na ban hak'uri ya shiga ya kulle k'ofar, jin bazata tafi ba yasa yace mata "ki tafi wurin mijinki, in kin gama dashi ki dawo min Pherty" bai k'ara komai akan wannan ba ya je can k'uryar toilet ya rakub'e zuciyarshi kamar ta buga, dan kanta ta d'auki jakarta da makullin motarta ta fice dan zuwa tarbar mijinta duk da zuciyarta baya mata dad'i.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


        19


    Zaman da yayi a toilet shi ya bashi daman karanta sak'onnin Miemiebee har ma da hotunanta da ta turo mishi ta watsapp cikin sutura mai kyau, kallo goma zaka mata bazaka gane tana da aure ba, hotunanta da kalamanta su sukayi tasiri akansa dalilin halin da Pherty ta barshi a ciki, tunawa da ya sake yi yanzu tana can tana faranta ran mijinta ta barshi a nan yasa yace yana son ganinta, kamar ta yi ihu dan murna da ta ga sak'onshi. Wanka tayi ta canja kaya ta feshe jikinta da turare, waya tayi masa tace ta shirya yana ina tazo ta same shi? Bai yi mamakin furucinta ba dan kalamunta ya nuna masa 'yar duniya ce, kai tsaye ya bata address nasa ba tare da yayi shakkun wani abu ba.

K'iranshi tayi a waya ta sanar dashi isowanta, ya nemi alfarmar ta shigo ciki shi kad'ai ne ta nuna masa a'a bai dace ba, k'in shigowan da tayi yasa yaji a ransa wayewa ne kawai yayi mata yawa ba wai 'yar iska ba ce kamar yanda yayi zato a farko, cikin motarta ya shiga suka d'an tab'a hira duk da ba wani sabo sukayi ba, da farko ya nemi sanin inda ta sanshi har ta samu layinshi amma tak'i sanar dashi ta share zancen da sanar dashi irin tsantsar burgeta da yake yi, yanayin maganarta yasa ya tabbatar da cewa ta dad'e da saninsa, miemiebee shu'uma ce wurin tsara zance, bata bar wurin ba sai da ta tabbatar ta bar mishi abubuwa da yawa game da ita, fatan ta d'aya ta samu gurbi a zuciyarsa kafin ta kawo masa buk'atarta ta inda baya zato.

Cubana @ 3:50


  Kamar kullum suna zaune a mazauninsu dan jin labarin d'aya daga cikinsu, rashin isowar Pherty shi ya hanasu fara abunda ya tara su, dama tayi text wa abokan tafiyanta akan bazata samu zuwa d'aukansu ba hakan yasa Ummu Abdoul ta biyawa Lubiee ta d'auko ta suka iso, sai k'arfe 4 ta iso Alhajinta ya ajiyeta ya wuce inda zai je. Babu b'ata lokaci Lubiee ta shiga labarinta kamar yanda aka umarceta.

"Sunana Lubabatu amma anfi sanina da Lubiee, asalina 'yar jihar Gombe ce, a can aka haifeni a can nayi makaranta, ban tashi cikin k'uncin rayuwa ba, iyayena suna sona kuma muna da wadata daidai gwargwado, iyayena 'yan boko ne, hakan yasa 'yan gidanmu suka taso cikin boko, babu laifi munyi karatun addini, kuma mahaifiyata na da k'ok'arin kwab'ar mu in munyi ba daidai ba. Ina da k'anne biyu da yayyu uku, matan mahaifina biyu ne kuma mahaifiyata ita ce amaryar Baba.

Tunda na tashi a gidanmu na ga yanda ake kishi meh tsafta, babu boka ko malami, babu dambe bare cacar baki, bansan ko wata daga cikinsu tana aikata hakan ba ta baya amma ni da sauran 'kannena da yayyu na mun musu kyakkyawar shaida akan tsaftatacciyar kishi. Kishi irin na jahilai sai dai mu ji labarinsa, wanda a wani lokacin ina k'aryatawa dan ni ba haka nake gani a gidanmu ba, kamar yanda kuka sani duk abinda ka gani shi zakiyi shaida akai kuma yayi saurin shiga kanka har ka yadda kayi labarinsa.

A wata ranar alhamis na fita FCE Gombe inda nake makaranta yanzu dan ban samu damar shiga university ba sakamakon jamb d'in da nake ta yi ban samu scores d'in da ake buk'ata ba, ina shekarata ta k'arshe hakan yasa lectures d'ina yakan fara da k'arfe d'aya wani lokacin k'arfe biyu ma. A cikin makaranta nake tafiya ni d'aya naji sallamarsa, tun kafin in juyo na fara murmushi, "wai dama zaki shigo makaranta yau ko ki fad'a min? Tafiya dama zanyi yanzu fa" "sorry yayana, nazo submitting assignment d'ina ne yanzu zan koma" kallon tuhuma yake sakar min, hakan yasa na gane nufinsa, hannuna na had'a biyu nace masa "am sorry brada, next tym ko gate na skul zan zo i will let u knw 1st" "good girl, kiyi submitting in mayar dake gida kinji".

Tare muka isa nayi submitting yayi min jagora zuwa inda yayi parking motarsa, muna tafiya muna hira da dariya cikin nishad'i. Ba kowa bane wannan matashin saurayin sai Abubakar, yaya ga k'awata kuma aminiyata Hafsat wacce muke ce mata Sahaf, ba komai ne tsakaninmu ba sai had'uwar jini da girmama juna, muna bala'in shiri kuma malamina ne dan yana koyarwa a FCE inda nake karatu kenan. K'awayena da 'yan gidanmu sun sha fad'a min Abubakar na sona ciki har da Sahaf k'anwarsa, ban tab'a yadda ba gaskiya dan ko sun fad'a min ina denying duk da ni nasan i have a crush on him, gaskiya yana burgeni k'arshe kuma yana sake min sosai muna hira, na sanshi na san halayensa.

Akwai wata rana naje gidansu Sahaf dan ta tayani solving wani maths da na kasa fahimtarsa, ita Kad'ai ce wacce zata iya yi min yanda zan fahimta dan guruwar maths ce, na isa bata gida amma Mama ce ta aiketa kuma ta tabbatar min bata yi nisa ba, d'akinta na shiga na baje litattafaina ina k'ok'arin yin maths d'in da kaina, na b'ata papers ya kai biyar ina gogewa da biro ko in yaga papern. Abubakar ya jima tsaye ta window yana kallon duk shirmen da nakeyi, sai da na kai k'ololuwar b'acin rai na wurgar da birona ina jan tsaki sannan ya shigo bayan ya doka min sallama. Sallamar kawai na amsa fuskata bai d'auke b'acin ran da maths ya k'unsa min ba, akan katifar ta nake shi kuma ya d'auko sallaya ya shimfid'a ya zauna a saitina yana tambayana abun da ya b'ata min rai, question d'in na mik'a masa ba tare da nayi magana ba ina mai tura baki ala dole raina ya b'aci. Sai da ya duba sannan yace "matso ki gani, wannan abun ne har zaki b'ata rai akai bayan kina da ni?".

Sannu a hankali ya fara yi min har muka kai k'arshen na d'aya, bazan ce ban gane ba amma akwai inda har ila lokacin ban gane yanda ake yin sa ba, mik'a min yayi yace ki gwada in gani yana mai b'oye papern da yayi min answern na farkon, gefe na matsa na dage dan in basa kunya, yanayin kallon da yake min na mugunta ne dan yasan ba iyawa zanyi ba, sosai na k'ok'arta sai gani na carke, nayi nayi amma na kasa, tambayarsa ne dai bazanyi ba dan dariya zai min, kamar yasan abunda yake raina yace " zo ki gwada min wannan nima na carke, na kasa k'arasawa" da hanzari na iso kusa dashi dan satar amsan inda na tsaya. 

Mik'a min yayi bayan ya lank'wasa ya mik'e yana cewa ina zuwa, banyi wata-wata ba na bud'e dan ganin solution d'in, can cikin raina kuwa addu'a nake Allah yasa questions d'in irin wanda ya bani inyi ne. "I LOVE YOU" na gani rubuce da manyan harrufa manya anyi masa zanen flower, sai k'asa ta gefe aka rubuta "I so much do!!!" Anyi darkening an bisa sau biyu ko uku dan yayi bluen biro sosai, k'ananan heart yayi guda uku ya jera su mai k'yau ya rubuta "my heart belongs to you alone", rubutun ya tafi dani, da farko baki na sake ina kallon mamaki, bansan lokacin da na sake murmushi ba ganin ya rubuta sunansa a k'arshe harda style nasa, sosai yayi min kyau kuma har cikin raina naji dad'in abun da yayi min a yau. 

Murmushi nakeyi ina mai ciro kad'an daga cikin farin cikin da ya sa ni, d'aga kaina nayi dan duba inda ya shige, a bakin k'ofa na gansa yana tsaye yana kallona, ganin nayi murmushi yasa shima ya murmusa ya kashe min ido ya bar bakin k'ofar ya wuce ya barni cikin duniyar da ya kai ni na farinciki.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


       20


   Naji dad'in jin wannan kalmar daga Abubakar, kuma har cikin raina nayi na'am da buk'atarsa sai dai banyi niyyar karb'a ba nan take, kuma ai dan na sanshi ina sonshi bai zama in yace yana sona in amince nan take ba, dole in ja aji kamar yanda kowace mace ke yi. Ban bar gidan ba a ranan sai da na bawa Sahaf labarin irin farincikin da yayanta ya sani, tsalle tayi tana murnar jin labari mai dad'i irin wannan, sai da ta gama tsallenta ta rungumeni tana cewa "kin zama antynah daga yau" ganin zak'ewan nata yayi yawa yasa nace "wa yace miki zan auri yayanki, kinga tashi ki rakani in tafi gida", tayi rok'o iya rok'o akan in amince masa na nuna a'a bana ra'ayi, ba dan komai ba sai dan ajin da nake ganin ya dace in ja.

Ba'a d'auki lokaci mai tsayi ba na amince masa, babu wanda bai san alak'ar da ke tsakaninmu ba cikin k'ank'anin lokaci, 'yan uwa da abokan arziki sunyi murna kuma sun ga dacewar hakan, wasu cewa suke dama asali akwai abu a k'asa, yanzun ne dai ya fito fili dan munso hakan. Sai da na gama FCE Abubakar ya nemi damar zuwa gida dan neman aurena, ban musa ba dan nima auren nake ra'ayi ba boko ba kamar sauran yayyuna mata da suke gama degree sannan suyi aure. Da na fad'a a gida da farko sunk'i amincewa da hakan, sai dai sunga na nuna ra'ayin auren yasa suka amince da isowarsa gida.

Ba'a d'auki lokaci ba aka aura min Abubakar d'ina, fad'a muku irin murnar da mukayi b'ata baki ne, dan munyi soyayya fiye da yanda kuke tsammani, duk wacce tayi aure kuma ta auri muradin ranta zata gane nufina. Rayuwar aurenmu rayuwa ce wacce d'ai-d'aikun mata ke samunsa, soyayya, tattali, komai ma babu wanda bai min ba Abubakar, he is the best man i've ever seen, yana sona yana gudun b'acin raina, duk abinda nace inaso shi yake min babu ja-in-ja, zan iya ce muku ya shagwab'ani k'arshe wanda babu haufi babu namijin da zan iya zama dashi in ba Abubakar d'ina ba. Aurena dashi bayan shekara d'aya muka tattara muka dawo Abuja da zama, a lokacin ya samu aikin gomnati kuma albashinsa Alhamdulillah, bai dogara da wannan aikin nasa kad'ai ba yana business dan yana da shago a Kano na atamfofi da lesuna, indai kud'i ne bamu da matsalarshi gaskiya, tsakanina dashi sai abunda baza'a rasa ba na zaman tare.

Na fara shiga k'uncin rayuwa ne bayan rashin lafiyar da nayi wanda babu wanda ya d'auka zanyi rai sakamakon zubewar da cikina yayi a karo na uku, mahaifata bata iya d'aukan ciki kamar yanda likita yace, idan nayi ciki sai naje an k'ulle min dan gudun zubewar cikin. Sau uku kenan yanzu ana min hakan amma ban samu nasarar samun d'ana ko 'yata ta kaina ba. Bai nuna min halin namiji ba ko kad'an bai gujeni ba sai ma nusar dani da yakeyi akan yadda da k'addara da kuma tuna min wasu matan da har su koma ga mahaliccinsu basu samun ganin gudan jininsu, in gode wa Allah ni ana sa rai zan iya samu.

Nayi iya k'ok'arina dan kawar da duk wata damuwa a raina, ba dan komai ba sai don ganin farincikin mijina. Kwatsam rana tsaka bayan watanni biyar Abubakar yazo min da wani zancen da yasa na firgita naga yanason guje min ne dan ban haifo masa yara ba, aure yake son yi wanda ni ina da tabbacin zai k'ara aure ne dan ban samo masa yara ba, kenan ya daina sona ya daina tausayina? Nayi kuka iya kuka babu mai rarrashina, kulle kaina nayi a d'akina nayi ta kuka yana bani hak'uri daga waje, yaudara ce da zak'in baki kawai irin na namiji, da yana sona kamar da kuma yana tausayina bazai min haka ba, a nawa tunanin kenan.

Ganin zan kashe kaina da kuka a d'aki babu mai agaji yasa na k'ira mamana cikin kuka na sanar mata abinda Abubakar yake son min, bata nuna min rashin adalci yayi ba kamar yanda nake son in samu wanda zai biye min, nasiha tayi min tana kwab'ana akan furucin da nake yi akan mijina, ashe abunda ban sani ba tuni anyi maganar auren saura sa date sannan ya fad'a min, Mama da sauran 'yan Gombe babu wanda bai ji ba sai Sahaf da ita ma aka k'i fad'a mata dan gudun kada ta sanar dani.

Ita na k'ira a waya na fad'a mata halin da nake ciki, ashar ta sake a lokacin da na fad'a mata Nafee zai aura wacce ake k'iranta da inkiyanta wato Anka, "wallahi kada ki yadda, yarinyar can in aka kawo ta gidanki ai kin shiga uku kin boni, hauka zaki masa a gidan nan ki nuna baki amince ba nasan yana sonki dole ya hak'ura" shawara ta bani dai-dai da wanda zuciyata ta raya min, shiyasa nayi marhaban dashi nayi mata godiya. Taimakon Allah ne yasa tun kafin in bud'e k'ofar in fito naji sallamar Mrs. Umar(Fatima, k'anwa ga mahaifiyar Abubakar), sai da na goge hawayen fuskata na bud'e k'ofar, ganinta yasa na fad'a jikinta na sake sabon kuka, bata hanani ba, sai ma janyo ni da tayi zuwa cikin d'akin ta ajiye ni kan gado, sam bata hanani kukan ba sai da naji kaina na sarawa nayi shiru dan kaina.

"Kin gama?" Tace tana mai kallona, hawaye ne ya sake zubo min tace "gama toh sai muyi magana" "na gama" nace cikin muryar kuka dan naga alamar ko zazzab'i zanyi a daidai wannan lokaci bazata ce min in yi shiru ba, sai da ta fuskanceni sannan ta fara min magana. "Lubabatu, saurareni da kyau muyi magana irin uwa da 'ya, kin d'aukeni uwa ko?" Na kad'a kai alamar "eh".

"Ki d'auke batun Abubakar d'ana ne, magna zamuyi ta gaskiya tsakanin mace da mace, kishiya ko ni nan bana sonta duk da shekaruna amma kinga mijina mata uku ne dashi kuma kinsan ni ce uwar gida, hak'uri shi ya kai ni wannan lokacin, idan da na biyewa zuciya da shawarar k'awaye b'ata gari da tuni ina gidanmu ko kuma na mace ko kuma na bi wata hanyar da zai kai ni ya baro inyi hasara a duniya da lahira. Abu biyu nakeso ki sa a ranki game da auren da mijinki zai k'ara, na farko ki d'auka auren da zaiyi zai cika umarni ne na Allah da yace su auri biyu, uku ko hud'u, idan bazasuyi adalci ba su auri d'aya, na biyu ki d'auke shi a k'addara.

Aurenki da Abubakar ki d'aukeshi matsayin ibada, kamar yanda kike sallah dan bauta wa Allah haka zaki d'auki aure a matsayin bautawa ubangijinki. Kishiya ba ita bace zamanki gidan miji haka zalika ba ita bace korarki daga gidan miji, ki toshe kunnuwanki kuma ki rufe idanuwanki, ki sa Allah a ranki kuma ki karb'eta da zuciya d'aya, a rayuwar nan duk wanda ya cuceka yayi wa kansa, in miji ne shi da Allahnsa. Idan da matan duniya zasu na tuna akwai hisabi da ranar biyan kowa hak'k'insa babu wacce zata d'aga hankalinta akan wani hak'k'i nata da aka tauye, in kinga abu na rashin adalci kiyi magana, idan aka karb'i naki masha-Allah, in kuma ba'a karb'a ba kada ki tada hankalinki ki kai kukanki wurin wani ba Allah ba, dan wanda zaki kai masa is eida ya baki shawarar arziki ko ta tsiya." 

Nasihar da tayi min shi ya hanani aikata abinda nayi niyya, duk ta inda na b'ullo mata akan bai kyauta min ba sai da ta toshe, duk wani abun da ke raina sai da tayi k'ok'arin kawar dashi ta cusa min kyakkyawar ak'ida sannan ta bar gidan. Tun daga ranar ban k'ara nuna masa kishina ba akan aurensa, marhaban nake yi da ita har cikin raina ina mana fatan alkhairi, da ni akayi komai na bikin Nafee da Mijina Abubakar, cikin aminci da zuciya d'aya na tarbeta hannu biyu. 

Cikin sati d'aya kacal na fara cin karo da abun mamaki abun takaici, Abubakar ya fara shareni yana sha min k'amshi, ko na masa magana sai yaga daman amsani, sai inyi kwana biyu ban sa shi a idona ba sai na nemesa da kaina. Bayan ta gama kwana bakwai nata ya dawo min kamar yanda addini ya tsara, a ranar na sha kayan haushi, ko gadona Abubakar k'in hawa yayi bare in samu soyayyar nan tasa mai shiga rai, a duk lokacin da na kusantoshi k'ok'arin guduwana yake, na nemi dalili na rasa, nayi kukana yana ji na ko uhum bai ce min ba bare in samu girman da zai bani hak'uri.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


       21


  Washe gari ko kallona baiyi ba ya tashi ya fice masallaci, bai damu ya tasheni inyi sallah ba kamar yanda ya saba yi. Dan kaina na tashi bayan haske ya gauraye ilahirin duniya, ina shiga ban d'aki fuskana na fara wankewa dan idanuna zogi suke min, kallon madubin da zanyi naga idanuna sun kumbura kamar an hura balloon, sai da na tsorata nan take naji gabana ya fad'i tunawa da nayi Nafee Anka na cikin gidan nan kuma dole in had'u da ita mu gaisa, banson ta gane na sha kuka bare tayi tunanin wani abu. Na wanke fuskana da ruwan sanyi yafi sau ashirin sannan nayi alwala na fito nayi sallah.

Bayan na idar k'in kwanciya nayi a ganina in nayi bacci idanuna bazai samu damar washewa ba, hakan yasa na jingina jikin gadona cike da rashin abun yi. Alal hak'ik'a ni ban saba yin azkar na safe ba, ban saba karatu bayan nayi sallah ba, tun a gida in na k'ok'arta nayi sallahr asuba da wuri toh ina idarwa bacci zanyi sai kuma haske in ya dalle idona ko kuma in an tasheni, yanzu ne Abubakar ke k'ok'ari tashina sallahn asuba, zan iya cewa tunda nayi aure ban tab'a lettin sallar asuba ba sai ranaku k'irgaggu. Ba laifi yana sani inyi azkar wani lokaci ganin ban sa hakan a raina ba yasa shi ya kyaleni nakeyin yanda na so. Ba wai kuma bansan ana yin azkar bane, ganda ne da son jiki irin na d'an Adam da kuma kid'in da shaid'ani ke yi mana a duk lokacin da muka so aikata aikin alkhairi. 

A dai-dai wannan lokaci bai zo kaina da in duk'ufa in nemi buk'atuna wurin Allah ba sai ma banzan tunanin da yake zuwa min dan sanin meh yasa Abubakar ya canja min. Bansan lokacin da bacci ya kwasheni a yanda nake ba, kawai tashi nayi naji wuyana na min ciwo dan rashin daidaituwar da banyi ba, da hanzari na tashi na duba lokaci naga k'arfe goma ya wuce, tsinkar zuciyar da nayi yasa nace "innalillahi wa inna ilaihi raji'un, yau na shiga uku, zai je office ban masa breakfast ba kuma bai tasheni ba, zai yi latti" na k'arashe maganar ina mai fita daga d'akin a hanzarce.

Da Nafee Anka naci karo a dai-dai lokacin da nake haramar bud'e k'ofan d'akin Abubakar, murmushi ne fal fuskarta ganina a bakin k'ofar, cike da mamaki nake kallonta dan banyi tsammanin ganinta a d'akin mijina ba a wannan lokacin, kalamar bakinta ne suka k'ara dulmiyar dani "aww ashe kina tafe?" Ta fad'i hakan tana yauk'i tare da lumshe idanunta, sai da na k'are mata kallo daga sama har k'asa, nace a raina ba laifi tana da kyau, kuma tana da diri dai-dai gwargwado sai dai meh take ji dashi a yau? Sabon salo nace a raina ina mai jinjina canjin rayuwa da na samu a lokaci k'ank'ani.

Ta gefe nabi zan wuce in shiga d'akin ta tare ni tana cewa "ina zuwa malama?" Ta had'e fuska sannan ta fad'i hakan, cike da mamaki na tsaya kallonta. "Meh hakan? Wai yau meh kike ji dashi ne?" "Ohh, gani nayi kin bar min mijin, jiya da dare kin kasa bashi abinda yake buk'ata yau kuma kika kasa fitowa kiyi masa breakfast, dad'in abun yana da ni, bazai rasa komai ba" ta fad'i hakan da murmushi a fuskarta, dariyan takaici nayi ina mai mamakin abun al'ajabi irin wannan, wai yarinyar da ta shigo gidana kwanaki takwas da suka wuce ita ce ke gaya min magana haka? Namiji butulu namiji buhun k'aya.

Damk'a d'aya nayi mata na wulla ta gefe na shige d'akin kai tsaye, dama ba wani jiki ne da ita ba, kyakkyawa ce kuma fara ce, ina kyautata zaton abunda ya ja shi kenan ya auro ta. Bata biyoni ba sanin cewa Abubakar ya dad'e da barin gida, sai da na duba sa sama k'asa baya nan sannan na bar d'akin. K'arfe hud'u ya dawo gidan rik'e da briefcase nasa a hannu, ina jin dirin motarsa na fito cikin kwalliyar da na saba yi masa a duk lokacin da zanje tarbarsa in ya dawo daga office, kwalliyar da yake matuk'ar yabawa idan nayi shi na tsantsara ina mai fatan in ga sauyi a wurinsa.

A bakin k'ofa muka had'u na rungume abuna ina mai yi masa sannu da zuwa, k'ank'ameni yayi yana mai shak'ar k'amshina, har cikin raina naji dad'in yanda yayi min sai dai ban kai ga sakankancewa ba naji ya tureni ahankali, wucewa yayi ya iso wurin Nafee da take tsaye cike da b'acin rai, kafin ya isa wurinta ta shige d'akinta ya bi ta a baya. Abun ya d'aure min kai matuk'a hakan yasa na d'au mintuna masu yawa a wurin ina hango k'ofar d'akin tare da k'issima abinda ke faruwa yanzu tsakaninsu.

Dak'yar na bawa kaina hak'uri na shige d'aki, ita ta kai masa abincin da na girka masa ta karb'i dutynah duk da ba ranar ta bane, ban mata magana ba kuma ban nuna b'acin raina ba, jira nake dare yayi in samu damar kad'aicewa da mijina dan mu tattauna mu gano inda matsalar take dan in gyara, sai dai meh? Har k'arfe 1 1 bai shigo ba, tun ina tsammanin shigowarsa har hak'urina ya k'are na je na buga musu k'ofa. Ina daga bakin k'ofar nake jin duk kalmar da suke furtawa tsakaninsu, shi yake son bud'e k'ofar ita kuma ta hana sai wani kashe masa murya take tana cewa bata gaji dashi ba, iya wuya na zo hakan yasa na bud'e k'ofar na shigo b'acin rai fal fuskata. Abunda na gani ne yasa nayi da na sanin shigowa dan kishin da naji yazo min iya wuya, ji nake kamar in fasa ihu ko naji dad'i a raina.

A hakan na daure na kawar dakai nace "inason magana dakai" "bani da lokaci" yace kai tsaye yana mai shafa gashin matarsa, kallon mamaki na bisa dashi sannan nace "yau a wurina kake, ko ka manta? In mantawa kayi toh na tuna maka" bai kalleni ba bare ya amsani, abubuwan da naga yake yi wa matarsa a gabana shi yasa naji kuka ya kubce min na bar d'akin a guje na koma d'akina. Na sha kuka ranar kamar in shid'e, nayi da na sanin fitowa daga d'akina har naje d'akin Nafee, komai ya fice min a rai banda k'unci da bak'in ciki babu abinda yake raina. 

Cikin daren na k'ira mamana na sanar mata duk abinda ya faru, hak'uri ta bani bayan ta nuna min in share duk wani abun b'acin rai in duk'ufa da addu'a kuma in samu abunda zai na d'ebe min kewa, rashin samun gamsashiyar shawara yasa na k'ira yayata na sanar da ita komai, ita ce ta bani shawarar da naji zan iya d'auka, sai da ta k'unduma masa ashar sannan tace "ki ci ubanta, kinji banza 'yar matsiyata, shi Abubakar d'in ya samu tab'in hankali ne?" Tas ta zage su duk da naji haushin zagin mijina da tayi amma ta faranta min rai dan shawarar da ta bani.

A tak'aice dai mun sha fad'a a gidan nan ni da Nafee, kuma k'iri-k'iri yake take gaskiya ya bi bayanta, tun ina ganin abun kamar a mafarki har ya zame min gaskiya, Abubakar ya daina sona ya daina kula dani, ya daina bani kud'i ya daina min komai, hatta kwana a d'akina ya daina yi, Sahaf ce ta bani shawarar komawa makaranta dan in daina zama ni kad'ai a gida, bai bani daman zama dashi ba bare har inyi masa maganar, ta text na tura masa inason in cigaba da makaranta, reply yayi min da cewa "da kud'in wa?" Da na ga text d'in sai da naji ina ma in mutu da ganin b'acin rai.

A kwana a tashi ba wuya na gaji da duk wata matsalar da zata had'a ni da Abubakar da matarsa, hanya ma banson ya had'a mu, banda abinci da nake dafawa kaina babu abinda yake fito dani, kuskurena d'aya duk abinda ya faru a gidan nan sai na kwashe na fad'awa Mamana da sisterta maman Fatee, hakan ya jawo raini mai yawa da rashin ganin girman sa, duk abinda na fad'a musu basu mantawa bare su hak'ura, wani lokacin na kan manta da abunda yayi min amma su basu tab'a mantawa. A hakan na nemi aiki a wani private school kuma na samu, a text kawai na fad'a masa na samu aiki yace min "Ok" ma'ana ya bani izini.

Tsakanina dashi sai gaisuwa da kuma satar hanyan da yakeyi yazo wurina, wani lokaci har yakan samu nasarar kad'aicewa dani duk da bak'in wahalar da nake sha a gidansa, a hakan har na samu ciki babu wanda ya sani, cikin ikon Allah naje aka d'aure min ban samu wani matsala ba, a lokacin Nafee na d'auke da cikin wata bak'wai. Ta haihu da watanni shida nima na haihu na samu 'ya mace, fad'in rigimar da akayi a gidan nan lokacin da ta gano ina da ciki ba mai fad'uwa bane, har rama Abubakar yayi dan tashin hankalin da ta sa shi ciki".

Numfashi ta sauk'e kana tace "a haka nake rayuwar aurena har yanzu, da kud'in aikina nake zuwa makaranta a nan open university, dashi nake kula da 'yata d'aya tilo, dashi nake komai na sai taimakon mahaifiyata, banson kowa yaji irin rayuwar da nakeyi, dan inason in gyara rayuwar aurena da kaina sai dai rashin abunyi yasa na kasa aiwatar da komai, tabbas nasan Abubakar baya hayyacinsa, da yasan abunda yakeyi bazai tab'a juya min baya ba ko da wasa" ta k'arashe labarin nata tana mai matsar k'walla.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


       22


   Kallonta Ummu-Abdoul ta tsaya yi cike da mamaki da jinjina wannan labari irin nata, a hakan take rayuwa har yau bata nemo bakin zaren ba dan ta san yanda zatayi? Ko Nafee Anka malamai take bi ne? Indai har asiri ke bibiyansu tabbas Lubiee na da babban laifi. Batool da ke gefenta hannun Lubiee ta rik'e tana cewa "insha Allah bazakiyi da na sanin sanar damu labarinki ba, zamu zame miki k'awaye na gaskiya kuma zamu taimaki juna dan fitar da kowacce daga cikinmu cikin rayuwar da muka tsinci kanmu".

Duk sun k'arfafa mata gwiwa kuma sun nuna mata suna tare da ita, sun tabbatar wa junansu cewa zasu zama katanga a tsakaninsu wurin kare junansu daga cikin kowace matsala. Ganin lokaci bai yi nisa ba ko k'iran Sallah ba'a yi ba yasa Batool ta fara nata BADAK'ALAR kamar haka "Sunana Batool Mamman, Nasarawa shine asalin garina, mahaifina hamshak'in mai kud'i ne babu inda ba'a sanshi ba cikin garin Nasarawa da kewaye, Alhaji Mamman Zaure ake ce masa..." Miemiebee ta katseta da cewa "Ai na tab'a jin sunansa kuwa gun Kamal d'ina, rannan sunje wani meeting a Cyprus shi da abokan business d'insa right?" Ta k'arashe maganar tana mai kallonta dan jin amsa.

Cike da rashin abunda zata ce ta sunkuyar da kanta, bata san meh zata ce ba dan bata sani ba. K'arar wayar Ummu-Abdoul ce ya katse su dukkansu, sai da tayi excusing nasu sannan tayi receiving tana cewa "Feedoh kinsan ina yin abu ko?" Daga can b'angaren aka ce "ki dawo gida inji Hajiya" "lafiya?" Tace cikin damuwa, "ki dawo dai tace, yanzu kuma" bata jira tayi magana ba ta katse wayar. Bin wayar tayi da kallo zuciyarta na tsinkewa, "meh ya faru?" Shine tambayar da yake yawo k'wak'walwarta, binta sukayi da kallo dukka suna neman k'arin bayani, sai da ta kallesu d'aya bayan d'aya fuskarta cike da damuwa sannan tace "am sorry i have to leave..." "Ina?" Ruffaida ta dakatar da ita "Hajiya ke nemana, duk Feedoh ta tsorata ni" "eyyah ba matsala, sai mu wuce dukka mu had'u next weekend ko?" Cewar Batool, mik'ewa sukayi dukkansu sukayi Sallama kowa yayi hanyarsa.

Sai da Ummu-Abdoul ta ajiye Lubiee a gida sannan ta wuce gida cike da fargaba. Parking tayi ta fito daga motar rik'e da jakarta, wayarta ne yayi k'arar shigowar text, sabuwar Number ta gani ance mata "Barka da dawowa ranki ya dad'e" cak inda take ta tsaya tana faman waige-waige neman inda me shi yake, ta tabbata meshi na kallonta. Iya hangenta ta kasa gano inda wannan mutumin yake hakan yasa ta shige cikin gidan tana mai kawar da tunanin wanda yayi mata text a daidai wannan lokaci.

Muryar da taji yasa gabanta ya fad'i, "Malam Usman" ta fad'i sunan a fili tana sa wa a ranta nata ya k'are a yau, wannan wani irin abu yake son sata ciki, mayar da hannun agogo baya, history is trying to repeat itself ta fad'i hakan tana mai tuna last sak'on da yayi mata jiya "I still Love you kin sani, ki bani dama". " Toh meh ya kawo sa kuma yau?" Ganin bata da wanda zai bata amsa yasa ta shiga cikin palorn muryarta a sanyaye tayi sallama. D'auke kai tayi ganin irin kallon da ya bita dashi, mayun idanunsa yasa ta sunkuyar dakai ta isa wurin Mama da take zaune akan kujerar palorn murmushi fal fuskarta, sai da ta zauna tace "ina wuni Hajiyata, na sameki k'alau?" "Lafiya k'alau, kin dawo?" Dubanta ta kai wurin Malam Usman, wannan kallon dai yake mata har ila lokacin, murmushi ta k'ak'alo tace "sannu da zuwa, ina wuni?" Ta k'arashe maganar tana sauk'e k'wayar idanunta, daburcewa tayi dan kallon nasa na k'unshe da abubuwan da ta kasa zayyane menene.

Sai da suka gaisa ta tambayi Anty Jegal da Futha da sauran k'annenta sannan ta mik'e ta shiga d'akinta dan watsa ruwa. Auta ta gani zaune kan gadonta tana duba littafin makarantarta, ganin ta shigo yasa tace "yauwa Ummu-abdoul, ki gwada min wannan abun duk na kasa yi" "wani subject ne" tace da ita "physics mana, na gaji da wannan science d'in wallahi" ta fad'i hakan tana ajiye takardar fuskarta na nuna gaskiyar abinda take fad'a, dariya Ummu Abdoul tayi harda tafi dan abun ya bata dariya, sai da tayi mai isarta tace "A hakan zakiyi MBBS? Kin manta lokacin da nake ce miki kiyi abunda zaki iya kada ki sa mu asarar kud'in break" ta k'arashe maganar tana k'yalk'yalewa da dariya harda rik'e ciki, iya wuya Auta tazo, tace "asarar kud'in break kawai kike tunawa? Kud'in makarantar fa?" Tana gama fad'an haka ta bar d'akin dan zuwa wurin Feedoh, ita kad'ai ce zata gwada mata kuma zata gane, sai yanzu take ganin wautanta na tarar Ummu-Abdoul bayan ita Arts &humanity tayi ba science class ba.

Da misalin k'arfe takwas ta fito daga d'akinta bayan tayi sallah tasa doguwar riga da d'an mayafinta, tana da d'an k'iba amma in tayi shigen 'yan mata bazaka d'auka ta tab'a aure ba, zaka d'auka jiki ne kawai na hutu da jin dad'i. A gefen Hajiya ta zauna tana jin hirarsu da Malam Usman, batayi minti goma da zuwa ba Hajiya ta mik'e tace "ki kai shi d'ayan parlon kizo ki karb'i abinci ki kai masa" ta shige ciki ba tare da ta ji amsarta ba. Kallonsa tayi ta k'asa taga idanunsa na kanta, murmushin dole tayi masa sannan ta mike can ciki tace "mu je can" ta fad'i hakan tana nuna hanyar da zasu bi, tana gaba yana binta a baya har suka isa ya zauna sannan ta fito dan kai masa abinci.

Bayan ta kai masa abinci zama tayi a k'asa kamar yanda ya umarce ta, hannunta take wasa dashi tana mai kallon k'asar d'akin, sai da yayi gyarar murya yace "na jira amsarki ban gani ba yasa na biyo sahu, ina jinki yanzu" hankalinsa gaba d'aya ya damk'a mata, ganin bata da niyyar magana yasa yace "bakya sona?" D'ago kanta tayi tana mai dubansa dan ba abunda take nufi kenan ba, aure ne baya gabanta yanzu. Ganin zai sake wata maganar yasa ta riga shi da cewa "a'a ba haka bane, ka dai bani lokaci" girgiza kai yayi yana mai nazarin maganarta, yayi gyarar murya yace "ba matsala, buk'atata yanzu bai wuce ki bani damar nuna miki kalar tawa soyayyar ba, in sona ne bakya yi ki bani dama in nuna miki nawa bajinta sannan ki yanke hukunci" murmushi kawai tayi tana mai kad'a kai alamar ta bashi dama yayi duk yanda yakeso, matsalarta d'aya "ya zatayi da matarsa Anty Jegal?" Bai bar gidan ba sai da sukayi hira mai yawa, tun tana nok'ewa har ta sake tana mayar masa harda dariya.

•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°


Kwana uku yayi a Abuja sannan ya koma bakin aikinsa bayan ya bar mata abubuwa masu yawa da zai sa tana tunawa dashi, soyayya ya nuna mata iya yanda zai iya, ji yakeyi daga ranar da ya mallaki Safiyya bazai sake tunanin wata mace ba bare yayi niyyar k'aro wata, Sadiyya da Safiyya sun ishe shi rayuwa har ya koma ga mahaliccinsa, soyayyarta yana zuciyarsa tun tana k'ank'anuwarta, tun kafin tasan meh duniya yake ciki ya fara sonta, sonta yayi d'awainiya dashi, ya hak'ura ya k'yaleta ta auri wanda takeso, ya tabbata rabo ne ya sake maidota hanyarsa, Allah ya bashi Safiyya shine kad'ai burinsa a yanzu, auren da tayi bai rage masa ko d'igon soyayyarta ba.

A b'angarenta ita ma so take ta samu courage d'in da zai sa ta sanar dashi rashin yiwuwar hakan, sai dai a wani b'angare tana ganin rashin dacewar haka, ga Hajiya ta sa ta a tsaka mai wuya na amincewa dashi, a kullum maganarta baya wuce irin halarcin da Malam Usman yayi mata. Ta rasa abun yi k'wak'walwarta ya toshe, ga wani sabon numban da ya addabeta da texts masu dad'i safe da yamma, kuma abun takaici sai ya k'irata yayi shiru yana jinta tana "salamu alaikum" wani lokaci k'in d'aga wayar take dan tasan muryanta kawai yakeson ji, da zarar ya k'irata ta d'auka tayi sallama ajiyar zuciyarshi takeji, hakan yasa ta gane muryarta yake son saurara kawai.

Ruffaida @ 4pm ranar Laraba


  Zaune take ita d'aya a parlor tana kallo bacci ya d'auketa, bata yi nisa a baccin ba Nuraddeen ya shigo gidan da sallamarsa, makullinsa yayi anfani dashi wurin bud'e k'ofar, tura k'ofar kawai yayi ya juyo yana kallon Ruffaida cikin doguwar riga kwance tana bacci cikin kwanciyan hankali, murmushi ya sake yana kallon irin baiwar halittan da Allah yayi mata. Ajiye jakar hannunsa yayi ya isa inda take ya tsuguna ya fara shafata a hankali, cikin bacci taji ana mata hakan, ahankali ta bud'e idonta tana kallonshi.

Murmushi ta sakar masa ta tashi ta zauna ba tare da ta masa magana ba, biye masa tayi suka cigaba da abinda ya fara. Cikin lokaci k'ank'ani suka fita hayyacinsu, jin fad'uwar abu ta bakin k'ofar shigowa yasa su firgita, gaba d'ayansu suka kalli k'ofar dan ganin ko meh ne, Ruffaida sumewa ne kawai bata yi ba dan tsoratan da tayi. Sadiq(wanda take k'ira Babban yaya, d'a ga Mamu matar Nuraddeen) ta gani jakar hannunsa a k'asa, sai Mamu(Mommy) da ke bayansa idanunta sun cika da hawaye ta rufe idanun d'anta k'arami(Shamsu) sai Amrah da ke gefenta tana kallon ikon Allah.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


        23


    Isa wurinta Sadiq yayi ta mik'e tana shirin b'uya bayan Nuraddeen ya fizgota ya sauk'e mata mari sai da ta koma mazauninta tana rik'e da kuncinta, bugu yayi niyyan kai mata Mamu ta dakatar dashi da cewa "ubanka ya dace kayi wa wannan marin ba ita ba", hawayen da ke fuskarta ta goge ta iso tsakiyar parlon tana kallon Nuraddeen cikin ido, "dama kana da alak'a da Ruffaida shiyasa ka hana aurenta da Sadiq d'anka? Dama abinda ya hanaka bin mu Zaria kenan dan ka samu kad'aicewa da ita?" Kuka ne ya kufce mata ta yi d'aki da gudu tana fidda kuka mai sauti.

Amrah ma kukan takeyi ta bi mamanta d'aki dan bata san abun yi ba, Sadiq ne kawai tsaye yana huci tsabar b'acin rai, Nuraddeen sunne kai yayi dan bai san meh zai yi ba, dubu dai ya cika yau, shi baisan ya akayi ya manta da yau zasu dawo ba, kalaman Sadiq ne ya dawo dashi duniyar tunanin da ya lula. "Daddy wannan 'yarka ce ka manta ne? Ka manta maganar aure ya tab'a shiga tsakanina da ita? Ko da yake bazanyi mamaki ba in nayi la'akari da yanda ka rufe ido ka hana auren, ashe abunda kuke aikatawa a bayan idonmu kenan?" Bai k'ara komai akan hakan ba ya fice jin hawaye na zubo masa.

Mamu zaune take akan gadonta abunda ta gani na k'ara dawo mata kwanyanta, abubuwa da yawa take kawowa a ranta tana sake tabbatar wa kanta cewa sun jima cikin wannan hali bata sani ba, laifinta ne? Ko laifin mijin nata zata gani? Ko kuwa laifin Ruffaida da ke matsayin 'yarta?harshenta taji yana mata gishiri-gishiri hakan ya tabbatar mata hawayen da ta goge ya sake mamaye fuskarta. Ajiye kanta tayi bisa cinyoyinta ta fashe da kuka mai tsuma rai Amrah na tayata. Sallamar Nuraddeen suka ji daga bakin k'ofa, hakan yasa Amrah ta mik'e ta bi ta gefensa ta fice daga d'akin dan zuwa nata d'akin.

Sai da ya d'auki mintuna uku yana tsaye a bakin k'ofar yana jin kukan da take rerawa wanda ya manta rabon da yaji tayi kuka irin haka, dak'yar ya nemo courage d'in isa inda take ya zauna a gefenta, bata hana shi ba dan a dai-dai wannan lokacin bata san meh zata ce masa ba, ya yaudareta ya cuceta, amanar da ta d'auka duk ya rushe mata shi ta ci amanar yayarta wacce ta zame mata uwa da uba a lokacin da bata da kowa, tunawa da hakan ya k'ara tunzurata ta mik'e zata bar inda yake dan jin shi kusa da ita zai iya sata tayi abunda zasuyi da na sani nan gaba, zuciyarta zai sa ta aikata abunda zai iya hallaka shi ko ita d'in ma gaba d'aya su huta.

Hannunta ya rik'e ya dawo da ita mazauninta, kuka ya fashe mata dashi yana mai sauk'a daga kan gadon rik'e da hannayenta, cikin kukan yake cewa "kiyi min duk abinda kikeso dan ki huce Mamu, amma dan Allah ki saurareni" ya cigaba da kuka harda hawaye, bai damu ya goge ba sai rik'e hannayenta da yayi yana girgizawa a hankali dan tayi masa magana, ita ma cikin kukan tace "ka zubar da girmanka, baka da abunda zaka ce min, ka k'yaleni inji da abunda ka k'unsa min na bak'in ciki, ka barni inyi tunanin abinda ya dace inyi" ta k'arashe maganar tana janye hannunta daga nasa, damk'ar da yayi mata yasa ta kasa janyewa, ganin bazata hak'ura ta daina janyewa ba yace "wallahi duk laifinta ne, kayan da take sawa a gidan nan shi ya ja ni zuwa gareta, kuma ta fad'a min da bakinta da gangan takeyi dan ta samu biyan buk'atarta, zakiyi mamaki in nace miki dama asali tana shek'e ayarta hakan yasa kissarta ya hau kaina yayi tasiri". 

Hawayen fuskarta ya tsaya cak tana kallonshi da mamaki, kad'a kai yayi alamar tabbatar mata da abinda yake fad'a gaskiya ne, shi yasan kan matarsa ganin abinda ya fad'a yayi tasiri yasa ya janyota jikinshi yana cigaba da cewa "sanin halinta yasa na hana aurenta da Sadiq, banason d'ana ya auri karuwa" hannunta ta d'aura akan bakinsa jin ya ambaci wannan kalma ta karuwa, mik'ewa tayi ta shiga surfa masifa, ta inda take shiga bata nan take fita ba, tana yi tana zubar da hawaye tare da ik'irarin yau Ruffaida sai ta bar mata gida bazata zauna da karuwa ba, kissarta yayi tasiri kan mijinta bare 'ya'yanta?

Tana yi yana k'ara ingizata yana fad'a mata hakan ya dace. Ruffaida da ke tsaye bakin k'ofar d'akin Mamu a dai-dai wannan lokaci ta juya tana mai zubar da hawaye masu zafi, daga farkon zancensu har k'arshe babu wanda bata ji ba, saboda a lokacin da Amrah ta fito daga d'akin sai da ta bita da harara sannan ta shiga d'akinta, ita kuwa ta mik'e dan zuwa d'akin Mommy ta bata hak'uri, anan ta tarar da wannan batu. 

A guje ta shiga d'akinta zuciyarta na mata zafi, ina ma ta mutu ko zata samu sa'ida, kuka ta shiga rerawa a lokacin da ta durk'eshe k'asa maganganun Nuraddeen na sake yawo a kunnenta, kamar an mintsineta ta mik'e ta d'auko akwatinta ta shiga loda kaya, minti biyar mai kyau batayi ba gama dan kayan nata a wanke a goge suke kawai d'auka takeyi tana jerawa, jakan hannu ta d'auko ta duba abubuwan da suke ciki sannan ta bud'e bedside drawer ta ciro purse nata ta duba atmcard nata yana ciki sannan ta sa a jakar ta janyo akwatin tayi hanyar waje. 

Sai da ta lek'a ba kowa sannan ta fito, a dai-dai isowarta staircase d'in da zai sadata da d'akin Mamu da Nuraddeen taji muryoyinsu suna fitowa daga d'akin, maganar Mamu ne ya k'ara tsoratar da ita jin tace "sai na mata d'an karen duka sannan zan korata, ai wannan ba mutuniyar da za'a zauna da ita bane". Bata jira ta k'arasa maganar ba tayi wuf ta bi ta baya ta fice dan kada mommy ta isota ta mata jina-jina, ga ta k'atuwa zauneta kawai zatayi ta kakkaryata.

•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°

Miemiebee a dai-dai wannan lokaci.

Kwance take a kan gadonta tana chating da masoyinta tallin tal wanda a yanzu ta samu karb'uwa a wurinsa fiye da zato, soyayya suke zubawa juna cikin kwanciyar hankali ba tare da tunanin wani abu ba, daga b'angaren Ibrahim kuma bata tab'a fad'a mishi tana da aure ba, sosai yake kashe ta da kalamansa yana sake dulmiyar da ita cikin kogin sonsa, a dai-dai wannan lokaci ma hirar soyaya suke yi tana kod'a sa dan labarin da ta basa na k'awarta da saurayinta akan he is not romantic, shi yace mata "Nima maybe haka kike cewa k'awayenki, Ibrahim d'in nan is not romantic".

Doguwar message tayi masa kamar haka "ni ban tab'a fad'awa k'awata mummunan abu akan ka ba, meh zan zaga ma? Dressing? I always tell you kana wanka da yawa har banaso dan kada a kwace min kai, ka tuna?


Sweet words? Huh! i have nothing to say about this, kai kasan magananka a kullum its making me feel loved nd special, Ibrahim d'ina, aka ce no one is perfect, but ni har yanzu banga inda ka kuskure ba... Sai dai abu d'aya da ka kasa min" "Tell me, menene na kasa miki?" K'in fad'a tayi sai da yayi ta binta yana rarrashi sannan tace "kana ina inzo inda kake yanzu" gida yace a tak'aice ita kuwa ta tabbatar masa nan da minti ashirin zai ganta.

Hakan kuwa akayi, sai da tayi wanka ta shirya kanta bayan tayi wanka da turare, b'ingilar riga tasa da wando skintyt ta sa bak'ar abaya akai. zuciyarta fari k'al ta hau hanyar gidan Ibrahim wanda ya kasance estate ne tank'ameme wanda Pherty ta kama masa. Tana isa ciki ta shiga ta k'wankwasa masa k'ofa, tun kafin ya bud'e k'ofar k'amshin turarenta ya bugesa, bud'ewa kawai yayi ba tare da ya tambayi waye ba, turarenta ya sanar dashi. Kallonta ya tsaya yi daga sama har k'asa yana mai sakar mata mayen murmushin nan nasa, da sassarfa ta shigo ta shige jikinsa ta k'ank'amesa tana mai sauk'ar da ajiyar zuciya.

Ji tayi ta shiga wata duniyar dan rabon ta da had'a jiki da namiji kwana uku kenan, tun tafiyar Kamal wanda take sa ran dawowarsa a yau. Ibrahim cike da mamaki yayi huging nata back, abunda bata tab'a yi masa ba kenan shiyasa yayi mamaki, sauk'e ajiyar zuciya yayi yana mai shak'ar ni'imtaccen k'amshinta, da k'afarsa ya tura k'ofar ya d'auke ta cak zuwa d'akinsa ya ajiyeta yana shirin fita dan kawo mata abinda zata sha. Hannunsa ta rik'e tana mai fashewa da kukan kissa, tuni ya daburce ya dawo inda take yana tambayarta matsalarta, bata amsa shi ba amma salonta ya sashi gane manufarta, biye mata yayi dan bazai iya jure sak'on da take isar masa ba.

Ba su suka dawo hayyacinsu ba sai da suka kawar wa junansu k'ishi. Sosai tayi mamakinsa, tana cewa Kamal nata k'arshe ne a wannan fanni ashe akwai wanda yafi sa? Nan take taji kishin Pherty ya d'arsu mata, a take ta kawar da wannan tunani tana mai tunano abunda ya faru tsakaninta da Ibrahim, Murmushi tayi tana mai lashe leb'b'anta tare da k'ank'amesa. A ranta farincikin samunsa take, kuma tana mai sake tabbatar wa kanta cewa bazata yi kuskuren b'ata masa rai ba bare har rabuwa ya shiga tsakaninsu, a yanda take jinsa a yanzu babu wanda ya kai mata shi ciki har da Kamal mijinta. (Wa iyazubillah).


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


        24


Ruffaida @6:30pm


    Tafe take tana zubar da hawayen bak'in ciki hannunta rik'e da jakar hannu d'ayar kuma tana jan trolleynta da ta cika da kaya, rashin sanin inda zata je yasa ta kasa shiga taxi dan ko ta shiga bata san inda zata je ba. Tayi tafiyar ak'alla awa biyu kenan bata ma san tayi ba, wayarta da yake ta k'ara ta tsaya ta ciro daga jakar, "MINE" ta gani rubuce ya k'irata yafi sau biyar, jakar ta ajiye ta zauna dab'as akai wani kuka mai cin rai ya sake kubce mata, ihu take d'anyi mara k'ara sosai wanda ita a ganinta shi yake sa zuciyarta lafawa ahankali, kamar an mitsineta ta d'auko wayar da ta ajiyesa a k'asar Allah ta shiga contact, hawaye cike da idonta yasa ta fara matse idanunta dan su zubo ta aiwatar da abunda tayi niyya, ganin hawayen na zubowa wasu na zuwa yasa ta mayar da wayar ta ajiye tana mai cewa "Allah ya isa Nuraddeen ka cuceni, munafuki kawai, Allah ya isa na" ta cigaba da kukan.

Sai da tayi mai isarta ta samu damar goge lambar nasa, a dai-dai wannan lokaci sak'onsa ya shigo wayarta. "Baby! Ina kika shiga? Kiyi min text na inda kike zan zo in same ki in nemo miki inda zaki zauna. Am worried" tana gama karantawa ta k'unduma masa wani ashar ta sa wayar a silent ta mayar cikin jaka. A wurin take zaune har isha'i ta gabato bata tsayar da abun yi ba, tunanin inda zata samu matsuguni take i kafin ta koma Zaria ko kuma ta nemi wurin zama anan tunda tana da 'yan kud'i a account nata. Ummu Abdoul ce ta fad'o mata a rai nan take ta k'irata, sosai tayi k'ok'arin hana kanta kuka tayi mata magana ta sanar da ita inda take ko zata iya zuwa ta d'auketa, Ummu Abdoul dama na cikin gari a daidai lokacin da ta k'irata, direct wurinta tazo dan gida zata wuce a lokacin da Ruffaida ta k'irata.

Miemiebee @6pm


   A dai-dai wannan lokaci tayi horn a bakin gate mai gadi ya bud'e mata k'ofa, hancin motarta na dosa wurin parking tayi tozali da Motar Kamal, zuciyarta ne ya buga kamar zai fito tsabar tsoro, sosai ta tsorata da isowarsa a wannan lokaci, kuma ko k'iranta baiyi ba bare yace mata ya iso kamar yanda ya saba, tunawa da tayi wayarta na silent yasa ta janyo jakarta da ta ajiyesa a cikin mota tun isanta gidan Ibrahim, yawan missed calls nasa da ta gani ya sake kad'a 'yan hanjinta, yawu ta had'iye "k'ut" kakeji ta bud'e murfin motar ta fito. A dai-dai bakin k'ofa taji k'arar text a wayarta, da hanzari ta duba taga daga Ibrahim ne "missing you already" instead taji sanyi a ranta tsoro ne ya k'ara shigarta ta danna wayar ta kashe.

Bud'e k'ofar tayi da makullinta ta gyara zaman d'ankwalin abayar nata sannan ta shigo, sosai tayi k'ok'arin kawar da tsoron da yake fuskarta dan kada ya d'ago ta, ganinshi tayi a zaune yana cin indomie hakan ya tabbatar mata ya dad'e da isowa, isa tayi wurinsa tana mai k'ak'alo murmushi tare da cewa "sannu da dawowa, sorry ban samu damar d'aga wayarka ba..." Bai barta ta k'arasa maganar ba haka zalika bai barta ta zauna a gefensa ba kamar yanda tayi niyya, dakatar da ita yayi da hannunsa ba tare da ya kalleta ba ya cigaba da abunda yakeyi, har ya gama bata samu damar yi masa magana ba.

Tunanin yanda zata shawo kansa takeyi har ya kom d'akinsa, minti uku da shigarsa d'aki ta bishi bayan ta tattaro k'aryar da zatayi masa, zama tayi a gefen gado tana kallonsa yana cire kayan da zai sa daga wardrobe nasa, sai da ya gama yayi hanyar bathroom ta shige gabansa ta tsaya tana mai langwab'ar da kai had'e da rik'e kunnuwanta, "am sorry" ta furta idanunta na zubo da hawaye, "Miemie" ya k'ira sunanta cikin sanyin murya dan ta kashe masa jiki da wannan hawayen nata.

Kasa amsashi tayi ta fashe da kuka tana k'ara ce masa yayi hak'uri, rungumeta yayi yana shafa bayanta dan ta tsagaita kukan nata, sai da tayi shiru sannan yace "kinsan zan dawo yau shine kika fita kuma ina ta k'iranki kink'i d'auka, tayaya bazan yi fushi ba?" cikin muryar kuka ta amsa da cewa "am sorry, na manta wayar a silent ne na raka k'awata shopping, am sorry bazan sake ba" ta k'arashe maganar cikin kuka, "shhhh! Stop crying na hak'ura, kada ki sake min haka kinji Baby?" Ya zaunar da ita akan gado shima ya zauna yace "kinga yanzu kinsa na ci busashshiyar indomie saura kumburin ciki" ya fad'i hakan yana shafa cikinsa yana kwab'e fuska, marairaicewa ta sake yi cikin shagwab'a tace "am sorry", dariya ta bashi hakan yasa yayi dariya ya rungumeta yace "I Love you miemienah" "I Love you too Habiby" ta fad'i hakan tana mai lumshe ido tare da k'ara k'ank'amesa.

Daga nan ya d'auke maganar suka shiga hira, ita tana fad'a mishi irin missing d'insa da tayi shima yana fad'a mata irin nasa missing d'in had'e da bata labarin abinda ya faru a wannan tafiyar, shaff ta manta da sallah sai da ta ga ya fito daga wanka ya tada sallahr isha'i, tare suka idar dan tayi nata a gefe, sai da ta idar da dukka sallolin sannan ya tambaye ta meh ya hanata sallahr mahrib da wuri, nan ma k'aryar tayi masa aka wuce wurin bayan ya jaddada mata azabar da aka tanadarwa mai barin sallah da gan-gan. 

Kamal ya sha mamaki kwarai a yau da Miemie bata nemesa ba kamar yanda a saba a duk dawowansa, baccinta ma tayi hankalinta kwance ta barshi zaune yana danne-danne a laptop nasa, wanda a da sam bayi da lokacin d'aukar laptop d'insa bare har yayi mintuna akai ba tare da tace masa yazo suyi bacci ba, mamaki yayi a ransa yana tunanin meh ya kawo sauyi haka? Bai takurata ba a ganinsa gajiyar shopping ne, wuri ya samu ya ajiye hak'ark'arinsa ya janyota kusa dashi ya lumshe ido yana mai shak'ar k'amshin Miemiensa da yake ji daga nesa dan yau da tayi wanka kwanciya kawai tayi ba tare da sake feshe jikinta da turare ba.

TARABA:- Kdeey @ 7pm


  "Wai da gaske kike kin hak'ura da Abba? Duk k'ok'arin da kikayi ya tashi a banza kenan?" Zuhura da ke kwance akan gadon Kdeey ta fad'i haka a dai-dai lokacin da Kdeey ta sallame sallar Maghrib. Tashi tayi ta cire hijabin ta fara fifita jikinta da hijabin da ta cire tana jan rigarta dan iskan ya shigeta da kyau. "Ai ko da shine k'arshen namiji a duniya na yafe, mutum sai fad'in rai da rainin tsiya? Wulak'anci kamar makarantarsa yaje yayi ya dawo? Ni tun ina jin ina sonshi har na daina ji, tunda ya min haka shima sai ya wahala wallahi, ai ya saki matar tashi amma da yake shi ma mayenta ne gashi ya kasa aure ko meh yake jira oho".

Zuhura tayi dariya tace "ai kin bani mammaki a lokacin da naga kin mace masa, ba laifi yana da kyau, amma fah bai taka kud'i ya kwanta a kud'i ba, ga wani d'agun kan da yake dashi bayi da fara'a sai yaga wannan matar tasa da na rasa meh ya gani a wurinta, ai Abba baiyi ba" Hannu Kdeey ta d'aga mata fuskarta a yamutse tace "kuma bance ki zagan min shi ba, dan nace ban sonshi bai zama na daina sonshi d'in da gaske ba" ta k'arashe maganar tana mai mik'ewa dan barin d'akin, sai da ta iso bakin k'ofa tace "tashi in mayar dake gida, duk kin b'ata min mood" ta ja d'an k'aramin tsuka ta fice.

•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°


   Yau ya kasance Alhamis, tun isowarsu gida daren jiya Ummu-Abdoul ke aikin rarrashin Ruffaida amma tak'i shiru, haka zalika tak'i fad'a mata dalilin wannan kuka nata bare ta fad'a mata dalilin barinta gida da tulelen akwati haka, Hajiya ma da ta tambaya ce mata tayi daga wani gari tazo zata wuce bayan kwanaki. Ruffaida ta nemi alfarmar yau a bata damar fed'e nata badak'alar dan tana neman shawara cikin gaggawa. Ummu Abdoul a watsapp ta sanar da kowannensu buk'atar Ruffaida kuma sun amince da hakan.

Miemiebee @ 3pm, tun safe Kamal yake nane da ita ta rasa yanda zatayi ta gudu dan samun Ibrahim nata, tun lokacin da ta kad'aice da Kamal take jin ina ma Ibrahim ne a wannan lokaci, ikon Allah ne kad'ai ya toshe bakinta bata k'ira sunan Ibrahim ba, duk yanda Miemie ta canja wa Kamal bai kawo komai ransa ba, shi ganinsa tana da sabon ciki shiyasa take guduwansa, amma da ya tambayeta yaushe rabonta da period kai tsaye tace masa "shekaran jiya na gama ka manta ne? Ka tafi ai bana sallah" anan ya shiga mamakin sauyawarta tare da neman dalili, "meh yasa kike guduna? Bakiyi kewata bane? Ko akwai abinda ke damunki?"

Tambayar da ya jera mata kenan yau da misalin k'arfe sha biyu bayan ya nemeta tana nok'ewa, tambayoyin ya jefata cikin rud'ani cikin i'ina tace "meh ka gani?" Kallon tuhuma yayi mata sannan yace "tunda na dawo nakeson kad'aicewa da ke kika k'i bani dama, fushi kikeyi dani kike hana min kanki dan ina tafiya in barki?" Jin ya ambaci fushi yasa ita ma ta lauye da fushin takeyi, ba dan taso ba ta biye masa ta faranta masa duk dan kada ya kawo komai a ransa, Ibrahim dai babu wanda ya isa ya rabata dashi a daidai lokacin da ta fara samun kansa.

Dak'yar Kamal ya barta ta fita tun k'arfe uku da zummar zuwa wurin k'awayenta, da yake yasan maganar zaman nasu baiyi musu ba yace ta dawo da wuri. Sai da ta biya wurin Ibrahim ta rage zafi sannan ya korata dan yana expecting zuwan Pherty shiyasa bai sake mata sosai ba dan kada ta zak'e da yawa, bata nemi sanin dalili ba tattara ta bi gidansu Batool ta d'aukota suka wuce Cubana dan sauraran Badak'alar Ruffaida.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


        25


Gidan Mamu:-


    Sadiq ne tsaye yana kallon Mamu da babu alamar damuwa a fuskarta, tambayar da ya mata yake jiran ta amsa amma ko kallonsa bata yi ba bare tayi niyyar amsawa, sai ma fruits nata da take sha hankali kwance tana kallon "The doctors". Matsowa yayi kusa da ita ya zauna damuwa k'arara ya bayyana a fuskarsa, "Mommy dan Allah ki fad'a min inda kika kai Ruf, na tabbata kinsan inda take shiyasa hankalinki yake kwance, duk da abunda Ruffaida ta aikata she is still my sister, your daughter, nasan k'uruciya da rashin kwab'a yasa ta aikata hakan, besides times without number na sha fad'a miki mijin nan naki tara 'yan mata yake a office amma kink'i yadda bare ki d'au mataki, ni ban ga laifinta ba dan na tabbata Daddy shi ya ja ta har ta aikata abunda ta aikata".

Bakinsa Mamu ta buge jin ya fad'i mummunar magana akan mijinta kuma Ubansa, cike da masifa tace "guduwa tayi" ji yayi zuciyarsa ya buga jin furucinta, ya d'aga kai ya kalleta cikin firgici, tuni ya mance da zafin da bakinsa yakeyi. Cikin masifa ta cigaba da fad'in "eh, nikam fad'a min wanda yafi kusa da kai cikin Ruffaida da Daddynka?" Ta tambayesa tana mai lankwasa hannayenta tare da d'aura fuskarta akai dan yin tagumi idanunta akansa dan jin amsar sa duk da tasan ba amsata zaiyi ba, "Sau nawa nake kwab'anka game da fad'a min magana irin wannan? Karuwar kake fifitawa akan mahaifinka? Ai sai da ya fad'a min na yadda lallai Ruffaida da gayya take sa matsattsun kaya" bata rufe bakinta ba Amrah ta fito daga d'akinta cikin riga mai hannun vest da wando ya d'ameta, bata kallesu ba ta isa wurin Tv ta ciro Charger ta koma d'akinta.

Hakan bai kashe bakin Mamu ba sai ma cigaba da tayi da zagin Ruffaida tare da hamdalan barinta gidan tun kafin ta cafke ta, dan rantsuwa tayi sai ta kakkaryata sannan ta korata, sai Allah ya taimaketa ta tafi tun kafin ta kai ga yin hakan. Sadiq girgiza kai yayi yana mai tunanin soyayyar da Mamu take yiwa mijinta wanda yake hanata ganin gaskiya ko kuma yace tana take gaskiya, cikin 'yan matan biyu Ruffaida da Amrah babu wacce bata sa kaya irin wanda take so a cikin gida kuma babu mai kwab'arsu ko fita zasuyi, shine kad'ai meh musu magana kuma shi yasan Ruffaida tafi Amrah kamun kai da sa sutura meh kyau, meh Daddy ya fad'a mata akan Ruffaida har ta manta amanar da aka bata na rik'e Ruffaida? Ba ma wannan ba, ina zai samu ganin Ruffaida, yana tsoron fad'awarta wani hali.

CUBANA


    Zaune suke da misalin k'arfe 4:30 dukkansu sun hallara, Pherty ce ta d'an b'ata musu lokaci dan yanzu isowarta, kukan Ruffaida kawai yake tashi a dai-dai wannan lokaci, saura sun tsaya kallonta cike da tausayawa sauran kuma na bata hak'uri ta hanyar shafa bayanta da mik'a mata tissue dan goge hawaye, idanunta ya kumbura yayi ja amma duk da hakan bata daina zubar da hawaye ba. Benaxir tayi gyarar murya tace "am sorry to say, but in bazata iya bada labarin ba wata tayi nata kawai in taji zata iya bamu labarin sai mu saurareta, gaskiya tun ina daurewa naga alamar hawayen ke zuwa min" ta k'arashe maganar tana matse kwallar da ya taru mata a idanu, Ruffaida da kuka yaci k'arfinta ta kad'a kai alamar kada wani yayi zata basu labarin, sai da ta d'auki mintoci uku sannan ta fara da cewa:-

"Ina tsoron baku labarina dan kada ku gujeni kamar yanda 'yan uwana suka gujeni, bani da kowa yanzu a rayuwata" hawaye ya sake zubo mata bisa kuncinta tayi murmushin takaici ta cigaba "labarin rayuwata zai zama darasi ga duk 'ya mace budurwa wacce rud'in duniya ke yawo da ita, budurwar da takeson rayuwar duniya bata tuna lahirarta, budurwar da k'yalk'yalin duniya ya zame mata k'awa, a sannu zaku gane nufina in kuka bi ni cikin labarin rayuwata".

Majina ta fiyace sannan ta cigaba da cewa "Sunana Ruffaida Omar, 'ya d'aya tilo da Allah ya bawa iyayena, momynah da daddynah 'yan boko ne, idan nace 'yan boko ina nufin mutanen da suka sa rayuwarsu, lokacinsu da dukiyarsu cikin boko, mutanen da suka yarda da boko kuma suka bashi muhimmanci fiye da yanda ya dace a bayar. Momynah ta tashi cikin maraici kuma ta zame ma Momy wato Mamu mahaifiya dan su biyu iyayenta ma'ana kakannina suka bari, Momynah yayar Mamu ce, ta girme mata da shekaru takwas kuma ita ce ta zame musu uwa da uba, da taimakon Allah sukayi makaranta dan Momy na da k'ok'arin neman na kai duk da kawunnansu sun tallafa musu.

Tayi aure bayan kammala makarantar ta, ta samu miji managarci wanda ya amince da zaman k'anwarta tare dasu wato Mamu, babu abinda ta nema ta rasa a wurinsu na jin dad'in rayuwa. Momy bayan aurenta ta fara aiki a banki dan fannin da ta karanta kenan, shi kuma Daddy Architect ne, da farko kamar yanda aka bani labari iyayena family planning sukayi dan aikinsu a ganinsu bazai barsu su samu damar rainon ciki ba, sai da sukayi shekaru bakwai sannan sukayi niyyar tarbar yara, sai dai kuma da yake haihuwa ba a hannunsu yake ba Allah bai basu ba sai da suka wahala tsawon shekaru biyar suna bin asibitoci sannan ta samu cikina. 

Tunda aka haifeni aka bani duk wani soyayya na duniya, ana min komai kuma an nuna min kud'i, ina shekara uku Mamu ta kawo yaronta Sadiq gida hutu (lokacin tayi aure) a lokacin yana da shekaru biyar, ina sonshi sosai dan ina samu muyi wasa, na saba dashi iya sabo dan lokacin da Mamu tazo d'aukanshi su koma gida zai koma school na tubure nace sai dai in bi su ko kuma a bar min shi, da farko Mamu tafi yadda da in bi ta amma da yake iyayena bazasu iya rayuwa bana kusa dasu ba yasa suka nemi alfarmar barinshi a gidanmu a sashi a makarantar da za'a kaini, a lokacin Mamu na da tsohon ciki sai bata damu ba dan tasan yaronta is in good hands.

Tunda na tashi na bud'e ido naga Sadiq a gidanmu, na saba dashi kuma na mayar dashi abokin wasana, abokin komai nawa, sosai shima yake sona ko da wasa bai son yaga kukana. Dalili d'aya yasa na fara k'iranshi Babban yaya" tayi murmushin da har hak'oranta sai da suka fito sannan ta cigaba "Sadiq na son girma, duk abunda zai had'a mu sai ya nuna min shi yayana ne, ko da wasar duka mukeyi irin na yara in na bugesa zaki ga ya had'e rai yace "ni fa yayanki ne" hakan yasa na canja mishi suna gaba d'aya ya koma Babban yaya kuma da alamu sunan na burgeshi.

Ina shekaru goma sha uku iyayena suka d'aukemu suka kai mu gidan Mamu dan wani tafiya da zasuyi, kamar sun san bazasu dawo ba suka damk'a mata amanata, tafiyar da basu dawo ba kenan aka sanar damu mutuwarsu, ko gawar iyayena ban gani ba dan plane crash sukayi, daga nan ne na koma rayuwa a k'ark'ashin Mamu da Mijinta Nuraddeen" kuka ta tsaya yi sosai har jijiyoyin fuskarta sun bayyana, ajiye kanta tayi bisa table d'in tana mai cigaba da kuka, Pherty da duk hankalinta yake wurin Ruffaida ita ma fashewa tayi da kuka ta mik'e ta bar wurin dan bazata iya ganin irin kukan da Ruffaida take yi ba, tunaninta d'aya wani irin rayuwa ta shiga bayan rasuwar iyayenta?

Ummu-Abdoul ce tayi k'ok'arin saita kanta dan dukkansu kuka suke suna mai tausayawa 'yar uwarsu, hawaye bai daina zuba daga idanunta ba ta dafa kafad'ar Ruffaida da har yanzu kanta na bisa table d'in tace "every soul shall taste the bitterness of death, Allah yaji k'ansu yasa suna cikin hutu, Allah ya ji k'an 'yan uwa musulmi baki d'aya" kad'an daga cikinsu suka samu damar amsawa da "ameen". Da k'yar suka samu damar rarrashinta suna bata baki sannan ta samu damar d'aga kanta hawaye na zarya a fuskarta, sai a sannan Pherty ta dawo mazauninta dan jin k'arashen labarin.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


26


"Zamana gidan Mamu ban rasa komai ba, duk abinda iyayena suke yi min Mamu da mijinta na k'ok'arin yi min, matsalata d'aya inason fiye da haka, nafison duk abinda na gani nace inaso a bani, nafison rayuwar girma, nafison in yi fintinkau cikin k'awayena, Mamu tayi iya k'ok'arinta dan nuna min hakan bazai yu ba, tana da nata yaran, duk abinda take musu nima tana min sai dai a yanda nakeji ina k'aranta, deep down me ina jin k'awayena na gulmana dan na samu canjin rayuwa hakan yasa walwalata ya ragu, na daina shiga k'awaye da sauran abubuwa da zai sa a nuna ni".

Majina ta fyace ta share hawayenta sannan ta cigaba "akwai wata rana Nuraddeen ya fito daga gida ya zagaya ta wurin garden dan d'aukan wani abu nasa da ya ajiye ta window, bayan ya d'auka yasa a aljihunsa har zai wuce ya hango ni zaune ina zubar da hawaye, nayi nisa cikin tunanin rayuwar da nayi a da da wanda nakeyi a yanzu, babu haufi shaid'ani ke min fitsari aka dan kaya masu tsada nake sawa, komai nawa na 'yan gata ne kuma na 'ya'yan masu kud'i matsalar d'aya k'awayena suna da irin abubuwan da nake dashi, ba kaman da ba da duk abinda ya fito sabo in Dady ya fita waje sai ya sayo ya kawo min, duk wani sabon abu na yara da ake tallarsu a TV ni ke fara zuwa dashi makaranta, hakan ba k'aramin d'agani yake cikin k'awaye ba, kuma ni da kaina ina jin wani girma da nishad'i cikin raina.

Zama yayi gefena jikinshi na gogan nawa, anan ne na dawo daga duniyar da na lula, a tsorace na ja gefe ina kallonsa, murmushin da naga yayi min yasa nima na murmusa had'e da goge hawayen fuskata, "meh ke damunki?" Ya tambayeni cikin sanyin murya, "babu" na amsa a nok'e dan nasan ba yadda zaiyi ba tunda ya kamani ina kuka, bai sha wahalar shawo kaina na fad'a mishi matsalata ba, nayi mamakin murmushin da ya sake min yana kamo hannuna, a lokacin abun yayi min wani iri amma ganin shi babba ne kuma mahaifi a gareni nasan bazai cuceni ba, shiyasa na sake ina kallonsa dan jin shawarar da zai bani.

"Ki kwantar da hankalinki, zan miki duk abinda kikeso kinji? Duk abinda kikeso ki sameni ki fad'a min but makesure Mamu kada ta ganki ko taji kina neman abu a wurina, hanawa zatayi dan yanzun ma ita ke hanani yi miki abu, ko kinaso ta hana" da sauri na kad'a kai alamar a'a sannan ya cigaba da k'unsa min abubuwa, sai da ya tabbatar da maganganunsa sun rud'a k'aramar kwakwalwata kuma sun shigeni da kyau sannan ya bar gidan.

Daga ranar komai ya canja, duk abinda nakeso yana kawo min amma a b'oye, abubuwan da zanyi anfani dasu wanda dole a gani yana sayo min ni da Amrah, sai dai nawa yakan fi nata kyau da tsada (Mamu babu abinda ta kawo a ranta a tunaninta yana yin haka ne kasancewarta marainiya) daga nan rayuwata ta dawo kamar da, na dawo da walwalata da ji dakai d'ina har ma ya wuce na da, dan abubuwan da yake min ya zarce misali.

A lokacin da na cika shekaru goma sha biyar na fara fuskantar sabon rayuwa daga wurin Nuraddeen, ni mace ce mai k'ira mai kyau kamar yanda kuka gani, kowani namiji zai mar-marin mace irina bare na k'ara da sa k'ananan kaya d'amammu, wani lokacin da vest nake fitowa daga d'aki inje kitchen duk a idanunsa, da farko bai nuna min maitarsa a fili ba sai da ya fara shiga jikina yana wasa dani, a duk lokacin da na nuna banso yakan nuna min cewa in ban barshi yayi yanda yakeso dani ba zai daina bani kud'i da abubuwan da yake bani a yanzu, har raina banason abinda yake min amma gudun ya daina bani kud'i da kayaki na alfarma yasa nake biye masa.

Tun ina tsoro har ya kai ga ya sabar min, zan iya cewa har missing d'insa nake wani lokaci in mun dad'e bamu samu keb'ewa ba" kuka ne yaci k'arfinta da tazo dai-dai wannan gab'a, dannewa takeyi tun-tuni amma ta kasa saboda wauta da kauce hanyar da tayi duk dan son abun duniya, sai da ta d'auki tsawon minti biyar tana kuka sannan ta samu damar tsagaitawa, a wannan lokaci cikin k'awayen nata babu wanda yayi niyyar bata hak'uri, sun barta tayi kuka dan ta samu sauk'in abunda takeji a ranta.

Sai da tayi gyarar murya tace "Ranar da Nuraddeen ya nuna min nufinsa kuma ya nemi sanina matsayin 'ya mace shine ranar da nayi da na sanin sake masa har yake wasa dani, ranar sai da ya tabbata babu kowa a gida sannan ya dawo ya sameni cikin d'akina, banji tsoron ganinsa ba dan dama mun saba, amma sai dai wannan karon yazo min da wani salo na daban, bai tausaya min ba kuma bai nuna min halin dattako ba sai da ya rabani da mutuncina ya bani bak'ar wahala, duk kukan da nakeyi bai sa ya kyaleni ba, a ranar ina mai tabbatar muku har asibiti sai da naje dan yaji min ciwo, wai ahakan Nuraddeen zai min butulci ya nuna wa duniya cewa ni karuwa ce? Ya manta wannan ranar kenan?" Ta k'arashe maganar cikin kuka tana mai fitar da sauti dasashshiya dan kukan da tayi muryarta sai da ta disashe. 

Maganganunta na k'arshe yasa Miemiebee cewa "bamu gane yace miki karuwa ba? Kin sa mu a duhu" cikin muryar kuka ta amsa da cewa "zan kai ku, a sannu zaku ji komai kuma zaku fahimceni" ta ja majina ta cigaba "bayan ya dawo dani daga asibiti sannan yaje ya d'auki matarsa daga gidan k'awarta, bani da lafiya kawai yace mata kuma bata damu da sanin musabbabin rashin lafiyar ba, ta dai bani kulawa har na warke kuma abun mamaki bata gane abunda ya sameni ba, ni kuma ina tsoron sanar da ita dan na tabbata bazata saurareni ba in nayi la'akari da jan kunne da kuma gargad'in da yayi min akan in na fad'a zai sa a koreni daga gidan in koma rayuwar Zaria cikin k'ask'anci da tozarci.

A haka na gama jinyata ina cikin tsoro da shakku, tun daga wannan rana na k'aurace masa, amma sai dai meh? Nuraddeen shu'umi ne, sai da ya samu damar shawo kaina na sake dashi, hakan ya bashi damar yin duk wani abunda yaga dama, zan iya cewa ya mayar dani matarsa, duk lokacin da yake buk'atana k'irana kawai zaiyi ya sameni a yanda yakeso, kud'i dai babu wanda bana samu daga wurinsa, mota ne kad'ai ya kasa damk'a min nan ma dan matarsa ce, kuma ga shegen zak'in baki da yabo, a kullum yana nuna min yafi jin dad'in kasancewa dani fiye da matarsa Mamu kuma ni da yake ni wawuya ce na zauna akan hakan.

A cikin irin rayuwar da na tashi kenan har na gama secondary school, a lokacin ne Mamu ta kwad'aitar dani auren d'anta Sadiq wanda a lokacin saura shekara biyu ya gama makarantarsa, nayi murna da wannan shawarar nata dan nasan bazan samu mijin da ya wuce Sadiq ba, zai soni kuma zai rik'eni da amana. Abu na farko da ya dace in gane Nuraddeen ba sona yakeyi ba shine k'in amincewa da wannan batu, sai yanzu na tabbatar da cewa k'yamata yakeyi baison d'ansa ya aureni dan ban kasance tsarkakakkiya mai bin dokokin Allah ba.

A lokacin ya yaudareni da cewar baison ya rasa ni shiyasa yak'i yadda in auri Sadiq, yafison in cigaba da karatu sannan inzo inyi aure, a lokacin ma yana kyautata zaton zai samu hanyar da zai aureni, wallahi na rasa gane ina na kai tunaninah da har na yadda dashi, na rasa gane magani yayi min ko kuma hauka ce da yaranta ko kuma kwakwalwa ce kawai irin na 'ya mace.

A hakan na hak'ura na biye masa nak'i yadda da auren duk da shi da kansa ya nemi a bar maganar. A haka na cigaba da rayuwa na mayar da kaina mara gata a wurin Nuraddeen, kwad'ayina da son duniya yasa na banzatar da kaina na cigaba da sharholiyata har jiya da asirina ya tonu..." Anan ta fayyace musu abinda ya faru jiya da dalilin barinta gida har ma kwana da tayi a gidan Ummu Abdoul. "Ku bani shawara? Ya zanyi in dawo da martabata da mutuncina da na zubar? Waye zai aureni a yanda nake a yanzu? Ni ba bazawara ba a idon duniya amma a wurina na zama bazawara, ku taimakeni" ta k'arashe magana tana ajiye kanta akan table tana mai zubar da hawaye.

Pherty ji tayi zuciyarta na bugawa da tsanani, ji takeyi ina ma ita ce yau ta bada nata labarin ko zata samu mafita daga nata badak'alar, abu d'aya yafi d'aga mata hankali, kenan duk namijin da ya sameka ya daina ganinka da mutunci kenan? Kuma ya daina darajaka bazai so had'a jini dakai ba? Does that mean Ibrahim nata ko ta fito daga gidan Alhaji bazai aureta ba? Tirk'ashi!

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


     27


   Kowaccensu shiru tayi tana nazarin labari irin na Ruffaida, banda sautin kukanta babu abinda akeji. Sai da suka d'auki tsawon mintuna biyar sannan Lubiee ta katse shirun da cewa "lallai kina cikin matsala kuma kin tafka babban kuskure na biyewa son zuciya, toh amma meh yasa tun farko baki bamu labarinki ba tun kafin abu ya kwab'e haka?" Ta k'arashe maganar tana mai kallon Ruffaida da har yanzu take kuka, Ummu Abdoul tayi gyarar murya tace "hmm! Kuskure dai an tafka, yanzu meh abun yi? Meh mafita? Kunji dai yanzu bata gida ma, ya zamuyi da wannan badak'alar? Nidai kwakwalwata ta cushe gaskiya" ta fad'i hakan tana mai rik'e kanta da hannayenta.

  Benaxir tayi murmushin takaici idanunta na bisa kan table na gabansu amma ta kasa furta komai sai da Batool tace "gaskiya da kin fad'a mana komai tun farkon had'uwarmu a wannan table d'in da tuni an yiwa tufkar hanci..." Bata k'arasa maganarta ba Benaxir tace "Abunda nake tunani kenan wallahi, lokacin da Ummu-Abdoul ta gama labarinta har rok'onmu akeyi wani ya bada nashi labarin amma tak'i, har pointing d'inta akayi tace no ita ba yanzu ba, toh gashi dole ya kawo ki kin fad'a ba tare da an tirsasa ki ba, sai abu ya kwab'e wai za'a zo neman shawara..." "Ya isa haka" cewar Ummu-Abdoul jin Ruffaida ta tsananta kuka dan jin furucin kowacce cikinsu, ta cigaba da cewa "ya wuce wannan, kowacce daga cikinmu tayi alk'awarin bada gudunmawarta wurin shawo kan kowace matsala idan ta taso, she need us beside her ba wai mu k'ara mata tsinkan zuciya da kalmomin mu ba".

Sai a sannan Pherty ta samu damar yin magana "gaskiya kika fad'a, wannan labarinta kukaji, kuna tuna cewa har yanzu akwai mutane uku da bakusan kalar tasu badak'alar ba, kuka sani ko na wata daga cikinmu yafi nata muni? In kuka gujeta zai hana sauranmu k'arasawa gaskiya, yakamata yanda muka fara mu k'arashe sa lafiya mu ci moriyar wannan zama". Maganarta yasa dukkansu kallonta dan duk cikin zuciyarsu ya basu cewa nata yafi hakan, ganin irin kallon da suka zuba mata yasa tace "meh? Ku cire abunda yake ranku, na ari bakinsu na ci mana albasa, ko kunsan labaran namu mu uku?" Miemiebee tace "toh dai tambayesu, yanzu kunga dama asali munyi akan kowacce in ta bada nata sannan mu san abun yi, in her case in kuka kula is urgent, ya zamuyi?".

Tambayar da tayi yasa suka fara shawarar abinda ya dace suyi wanda sosai ya caja musu kwakwalwa daga k'arshe suka tsayar da maganar zata zauna a gidan Ummu-Abdoul har ranar friday da zasu kai wa Mamu da mijinta ziyara dan warware matsalar da ta kunno. Daga hakan suka diro maganar sauran labaran, sun tsaya akan ranar asabar da lahadi zasu gama jin labarinsu dukka dan jinkirin nasu ya taimaka wurin tab'arb'arewar lamuran Ruffaida, da sun yi shi a lokaci d'aya zasu shawo kan matsalarta da Nuraddeen ba tare da an kai ga kora ko sharri ba.

Da haka suka watse kowacce tayi hanyarta da abunda ya tsaya a ranta, Pherty ta koma gida da tunanin rayuwarta da kuma burinta da take ganin ta kusa cimmawa, tambayar da yake ta yawo akanta dai d'aya ne "Ibrahim zai aureta bayan fitowarta daga gidan aurenta?" A d'aya b'angaren kuma tunani take ya zata fara basu labarin aurenta bayan duk cikinsu babu wanda bai san irin samarin da takeyi ba? Ya zatayi da wannan abun kunyan? 

A ranar dai cikin wannan tunani ta kwana ta ma manta da had'uwar da zasuyi da Ibrahim, shima bai samu damar k'iranta ba dan yayi tunanin mijinta ya dawo ne sanin cewa Pherty bata fashin zuwa wurinsa sai da kwakkwaran dalili. A b'angaren Batool kuwa tunda ta koma gida bata samu sukuni ba, sai da ta shiga d'aki tayi kuka mai isanta sannan ta samu sauk'in k'uttun da takeji a ranta, a kullum in taji labari irin wannan yana tuna mata da rayuwarta, tayi wauta tayi rashin hankali a rayuwarta, a ganinta gwanda Ruffaida iyayenta basu raye balle su furta mummunar kalma gareta, babu abinda yafi d'aga mata hankali irin kalmomin da iyayenta suke jifanta dashi, a kullum in ta samu kanta cikin irin wannan hali ta kan furta "kaicona! Meh nake nema a duniya?". A ranar tayi kuka kamar ranta zai fita, dak'yar aunty Jidderh ta samu damar shawo kanta.

Washe-gari @gidan Miemiebee


  Har motarsa ta rakasa murmushi fal fuskarta, bai k'ara shiga duhu ba sai lokacin da ya rungumeta dan yi mata sallama kamar yanda ya saba, bai kai ga yi mata abunda yayi niyya ba ta janye jikinta daga nasa tana mai sake masa murmushi, k'ofar mota ta bud'e masa tana ce masa bismillah fuskarta cike da annuri, bai d'aga idonsa daga kanta ba dan yana son gano abu daga d'abi'an nan nata sabo, iska ta hura masa a idanu sannan ya sauk'e idon yana mai sauk'e ajiyar zuciya "Miemie are you okay? Kin tabbata lafiyanki k'alau?".

Kallon jikinta tayi har da juyawa dan samun daman kallon bayanta tace "meh ya sameni? Meh ka gani kake tambayana question d'in nan tun jiya?" Matsowa yayi daf da ita yace "ban yadda lafiyanki ba, ko in fasa tafiyar ne in zauna dan naga..." "A'a ka tafi dan Allah" cikin sub'utan baki ta fad'i hakan, kallonsa ta tsaya yi dan tasan ta kofsa, kallon da yake binta dashi yasa ta sha jinin jikinta cikin i'ina ta fara cewa "em ina nufin... Umm ka tafi aikinka kada ka damu dani, am okay na fara sabawa ne da irin aikinka".

Murmushi ya sauk'e dan har cikin ransa ya yadda da kalamanta, rungumeta yayi tsam a jikinsa yana cewa "yauwa babynah, amma sai dai kin canja min, bakison ina zama kusa dake" jin furucinsa yasa ta lalubo bakinsa ta manna masa kiss d'in da ta tabbata ta kwana biyu bata yi masa irinsa ba, dak'yar ta b'anb'are jikinta daga nasa ta gudu cikin gida ta barshi jingine da motarsa yana mayar da numfashi.

Ummu-Abdoul @12:30pm


   "Haba Ruffaida, kinsan baza mu je gidan naku ba meh yasa kika bari na dawo daga office tun 12, ki tashi ki shirya mu je kawai dan idan bamu je ba baza mu samu maslaha ba" Ruffaida da ke matsar k'walla akan gadon da kayan baccinta ko wanka bata yi ba tace "wallahi Ummu-Abdoul shawarar tawa zaku bi kawai, idan Mamu bata huce ba duk bazamu fita daga gidan nan lafiya ba, mijinta munafuki ne kuma tana sonshi fiye da yanda kike zato, duk maganar da zai fad'a mata daram yake zama babu mai isa ya canja shi".

Zaman dirshan Ummu Abdoul tayi tana mai rik'e kanta da yake sara mata, rashin maganar ta ya bawa Ruffaida damar tsara mata maganganu dan kawai kada suje gidan Mamu a yau, tsoro take ji dan ta tabbata Nuraddeen ba k'aramin sharri zai lak'a mata ba in taje ta sanar dasu abinda ya faru, zak'in bakinsa da irin text d'in da yake mata yasa ta karya sim nata ta sa a WC tayi flushing, da zata samu daman flushing na Nuraddeen da matsalolinsa da tuni tayi ta huta. A watsapp Ruffaida ta sanar da abokan tafiyan nata an fasa zuwa gidan Mamu, duk tambayoyin da suke mata na son sanin dalilin fasawar bata samu damar amsawa ba dan rashin sanin tak'amaimai abun fad'a.

Lubiee @ 1:30pm


  Ta idar da Sallahr azahar kenan ta janyo wayarta ta kunna data, anan ne take ganin sak'on Ruffaida na fasa zuwa gidan Mamu, tab'e baki tayi ta kashe datan ta danna wa Mrs. Umar k'ira, bayan sun gaisa take sanar da ita a dawo da Kausar dan ta fasa fita (Gidan Mrs. Umar take kai ta duk lokacin da zata fita office ko wani wuri na daban). Bayan ta bata sak'on ne ta katse wayar ta cire hijabinta ta fito dan zuwa kitchen d'aura abincin da zata ci.

A bakin k'ofar kitchen suka yi karo da Nafee, cikin rashin sani Lubiee ta bangaje ta, bata kai ga ce mata tayi hak'uri ba Nafee ta kwara mata abincin hannunta da yake cikin k'aramin tray, da gangan ta zuba mata dan kwana biyun nan bata samu damar k'unsa wa Lubiee bak'in ciki ba, zafin da taji a jikinta yasa ta k'walla ihu tana k'ok'arin zubar da sauran shinkafar da ya manne mata a jiki. 

Sai da ta gama tsalle-tsallenta ta gama ihunta sannan ta dawo da hankalinta wurin Nafee da ta jingina da k'ofar kitchen d'in tana kwasar dariya har da rik'e ciki. Tun da Lubiee take rayuwar ta a gidan nan bata tab'a jin b'acin rai irin haka ba, zuciya ne ya d'ibeta ta wanke ta da mari, bata jira wani abun ba ta kai mata duka, har k'asa ta kai ta sannan ta tureta ta koma d'akinta ba tare da ta kula da ihun da Nafee ke yi ba. 

Sai da ta shiga ciki taji hawaye masu zafi suna sauk'o mata, lumshe idonta tayi tana mai jin rad'ad'i tare da tunano irin tab'argazar da Nafee ke mata a cikin gidanta son ranta. Bata yi mintuna goma da shiga d'aki ba taji ana bugun k'ofarta cike da hauka, tasan za'ayi haka shiyasa ta kulle k'ofar dan bata da lokacin kare kanta a wurin Abubakar wanda ita tasan ba anfani zai yi ba, ko da gaskiyarta ne takewa zaiyi ya bi bayan matarsa bare yau da ta tab'a lafiyar gimbiyar.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


        28


   Duk bugun da yake yiwa k'ofar bai sa ta motsa ba sai ma janyo wayarta da tayi, danne-danne tayi ta d'aura wayar a kunnenta, can tace "Anty Kausar d'in ta kwana kawai kada a dawo da ita" daga can b'angaren Mrs. Umar tace "lafiya dai ko? Ai yanzu suka fita zasu kai miki ita" lafiya k'alau kawai tace sannan ta kashe wayar bayan Mrs Umar tayi mata fatan Allah yasa lafiya. Ajiye wayar tayi akan bedside drawer ta mik'e hankali kwance ta isa wurin k'ofar, sai da ta tsaya ta saurari abinda yake fad'a "wallahi Lubba idan baki bud'e k'ofar nan ba ranki zai b'aci" tab'e baki tayi sannan ta bud'e hankali kwance tana kallonsu d'ai-d'ai, shi tsaye yake bakin k'ofar Nafee kuma na bayansa, sai da ta sa kai ta lek'a taga yaran Nafee biyu na bayanta sannan ta dawo da dubanta garesa fuskarta a d'aure kamar bata tab'a dariya ba.

Kasa mata magana yayi dan bata tab'a yi masa haka ba in ta b'ata masa rai ko in yana masifa, hasalima kuka kullum take masa duk lokacin da yazo da balbalin masifarsa akan Nafee, muryarta ya dawo dashi daga duniyar da ya lula, "emm! Nace in kanason magana dani ka fad'awa 'ya'yanka su bar nan sannan in saurareka" bata jira amsarsa ba ta koma d'aki, ta tura k'ofar kenan zata rufe ya sa hannu ya tare k'ofar, rufe ido yayi ya kama balbaleta da masifa yana tambayarta meh yasa ta tab'a matarsa, fuskar Lubie fes take kallonsa, sai da ta tabbatar ya k'arashe duk tambayoyin da zai iya mata sannan tace "ka tabbata kanason muyi magana gaban 'ya'yanka?" Bata jira ya amsa ba ta cigaba da magana dan dama bata tambayesa dan ya amsata ba. 

"Ashe dabba ka auro ban sani ba Abubakar, bata da hankali tana son tayi kisan kai? Kai kuma da yake ta wanke ta baka har kana da bakin da zaka zo kana tambayana meh yasa na d'aura hannuna akanta? Kana da hak'k'in tambayana haka? Meh yasa baka tambayeta abunda tayi min ba?" "Dakata Lubabatu..." Hannu ta d'aga masa tana mai kawar da kanta gefe tace "ban gama ba Malam Abubakar, ka kai ni bango a yau, lafiyata yafi min komai ciki har da aurenka, idan bazaka iya adalci tsakaninmu ba ba'a mak'ala maka ni ba, ba auren zobe mukayi ba kana iya sawwak'e min, Abubakar idan kana ganin hak'urin da nakeyi shi yake baka daman take gaskiya toh daga yau na daina sa, ka jawa matarka kunne ta fita harkana kamar yanda ni ban shiga nata, ta fita daga rayuwata tunda ni da nake matarka igiyar aure tsakaninmu na iya kawar da kai na daina shiga taka harkar ita bata da lasisin shiga nawa harkar, idan bazaka iya yi mata wannan jan kunnen ba bismillah bani takardata in bar maka gidanka babu dole".

Ta k'arashe maganar tana mai huci idanunta cikin nasa babu alamar tsoro ko fargaba, tsantsar b'acin rai da tsana yake hangowa kwance cikin idanun uwargidansa Lubbatu, can cikin k'asan zuciyarsa ji yake yana masa k'una, wani abu na k'ara tunzurashi ya furta mata kalmar da take nema na saki amma wani abu da ya tabbatar zuciyarsa ce yana kob'ansa da yin hakan, shirun da yayi yasa Nafee k'arasowa inda suke tana cewa "ka sake ta mana tunda ta nemi haka, tana son kashe maka ni amma zaka barta, baka rama min ba kuma ta nemi ka saketa kak'i..." 

Hannu Lubiee ta d'aga mata tana cewa "malama da mijina nake magana, da kika gama tsara masa naki labarin na fito na katse ki" ta dawo da dubanta gareshi tace "Abbakar, ni barin mata kashedi da babbar murya tunda ka zab'i zama dani" fitowa tayi ta isa inda Nafee take ta d'aga hannu ta had'a yatsu biyu ta murza su ta sake murzasu sukayi k'ara har sau uku sannan ta nuna ta da manuniyarta tace "last warning nake miki, ki fita daga harkata in ba haka ba jikinki zai gaya miki" damk'ar hannunta da akayi ya dakatar da ita, janyota yayi cikin zafin nama ya sa ta cikin d'akinta ya banko k'ofar ya koma wurin matarsa yana rarrashi.

Tuburewa tayi ta sa kuka tana cewa ya daina sonta matarsa tana mata yanda taso ya kasa d'aukan mataki, ganin baza ta hak'ura ba ya koma d'akin Lubiee da zummar ci mata mutunci, ya rasa yanda akayi baya iya mata rashin mutuncin da yake k'issimawa a ransa kafin ya iso inda take, duk da yanda yake jin zuciyarsa na nuna masa bai kyautawa bai hana sa sauk'e ruwan bala'insa ba, a shigowarsa d'akin yaso ya tattaketa ya mata jina jina amma ya k'are a kunfar baki, kaca-kaca sukayi yau shi da Lubiee dan bata raga masa ba ko kad'an, daga k'arshe tuburewa tayi akan sai ya saketa shi kuma ya rantse bazai sake ta ba sai dai tayi yanda zata yi, kuma ya ja mata kunne ta fita harkar matarshi, bai bar d'akinta ba sai da ya k'unsa mata bak'in ciki ta sa kuka ya fice ranshi b'ace yayi d'akinsa dan wani zuciyar na fad'a masa baya kyautawa.

Pherty @ 2:30


   Zaune take a d'akinta ta buga tagumi tana tunanin abubuwa da yawa game da labarin Ruffaida, gani takeyi kamar abunda ya samu Ruffaida ita ma zai sameta tunda ita ma kusan abunda take aikatawa kenan, shin ta fita harkarsa tun kafin Alhaji ya gano ya koreta ko kuma ta zauna dashi har burinta ya cika ta tattara nata ya nata ta tafi suyi aure da Ibrahim? Anya zai aureta ba yaudararta yake yi ba? Wani zuciyar na sake tunatar mata irin son da Ibrahim ke mata, rashin sanin abun yi yasa ta lumshe ido tana tunanin mafita.

Ta bayanta yazo ya d'auketa cak yana juyi da ita yana dariya, da farko ta tsorata dan bata ji shigowarsa ba, ganin shine yasa ta saki ranta har da murmusawa, ganin farincikin nasa ya wuce misali yasa ta doka masa tambaya cike da son jin abinda ya sa shi murna haka, sai da ya gama zagaye d'akin da ita ya direta kan gado yana sauk'e numfashi yace "sonki naji yana sukana a k'albina" ya kashe mata ido bai daina sauk'e numfashin ba, dariya ta shiga yi ba k'akk'autawa tana cewa "ka fara tsufa kai kam, d'an yawon da kayi da ni ka ga yanda kake sauk'e numfashi" ta cigaba da dariyar. 

Tashi yayi yaje gaban mirror yana duba gashin kansa da gemunsa, ganin farin gashi da bazasu wuce goma ba yasa ya dawo kusa da ita yace "a hakan ne na tsufa baby? Ke baki ga yanda kike zama k'atuwa ba ai dole ki min nauyi in wahala in na d'aga ki, nauyin nan naki anya ke d'aya ce ma, matso in gani" ya fad'i hakan yana janyota tare da d'aga rigarta sama wai zai duba ko tana da ciki, ganin babu alama yasa ya marairaice "wai baby yaushe zaki haifo min cute babies kaman ki ne, abu kike sha ko na hana d'aukan ciki?" Ya fad'i hakan yana mai kallon fuskarta, hanjinta sai da suka hard'e jin ya fad'i haka, cikin i'ina tace "haba dai, ina zan samu maganin hana d'aukan ciki? Murmushi yayi yana kusantota, cikin kunnenta ya rad'a mata "yara nakeso 'yan k'anana, kinga Antynki yaranta duk manya, ki barni in samo mana baby" bai sake cewa komai ba haka ita ma suka lula wata duniyar. A gida Alhaji Haruna ya wuni ranar manne da jikin Pherty ko sallah a gida sukayi tare ya hanata sakat, samunshi kusa da ita shi ya d'auke mata tunaninta akan Ibrahim.

Washe gari @ 12pm


    K'iran Ibrahim takeyi a karo na goma sha uku kenan yak'i d'auka, duk ta rud'e ta rasa abunda yake mata dad'i, tunda Alhaji ya fita take kan k'iransa amma bai d'auka ba, tafi tunanin fushi yayi da ita yasa yak'i d'auka ko kuma text d'in da tayi masa jiya yasa yak'i d'auka dan bai amsata ba, ce masa tayi "idan na fito daga gidan Alhaji zaka aureni?" Shirunsa ya d'aga mata hankali, ji takeyi idan bata je ga Ibrahim ba zuciyarta na iya bugawa, ji takeyi bazata iya rayuwa babu shi ba, indai tambayar da tayi masa ne ta janye kada ya amsata ta yafe, kasancewarsa tare da ita yafi mata komai. 

Tashi tayi ta shiga bathroom dan sake yin wanka, bata d'auki dogon lokaci ba ta shirya cikin doguwar rigarta na atamfa, powder kawai ta iya shafawa ta d'auki mayafi da jakarta, a palo ta d'auki makullin motarta ta fita. Sai da tayi wa Alhajinta text ta sanar dashi fitan ta sannan ta tada motar ta bar gidan. Tun da ta doshi gidan zuciyarta ke bugu, ta rasa dalilin tsinkar zuciyarta, sai da ta kai zuciyarta nesa sannan ta iya sa hancin motarta cikin gidan. 

Bugun zuciyarta ya tsananta ganin dalleliyar mota irin nata, kallon motar takeyi har tayi parking ta fito rik'e da makullin motarta, har wurin motar taje ta tsaya kallo dan gane meh motar, dak'yar ta d'auke tunanin da yake neman sata hauka tayi hanyar cikin gidan. Kai tsaye ta shiga ciki ta bud'e k'ofar ba tare da sallama ba, a tsakiyar parlon ta tsaya tana k'are ma palon kallo ko zata ga wani abu da zai sanar da ita motar da ta gani na waye ne.

Ganin ba komai yasa tayi hanyar bedroom, sai da ta kai k'ofar ta waigo ta kai idanunta k'asa gefen kujera taga handbag a bud'e tana iya hango kayan kwalliyar da ke ciki, tsayawa tayi a wurin ba tare da ta samu k'arfin yin komai ba, bata tsayar da tunaninta ba kunnuwanta suka jiyo mata maganar Ibrahim wanda ya girgiza mata zuciya, ji tayi kamar zuciyarta zai fashe, lumshe ido tayi hawaye suka sauk'o bisa kuncinta "Jinki nake a raina yanzu babu wanda yafi ye min ke, ina sonki sosai" maganar yarinyar ya tabbatar mata rungume suke, "awwhh! Zaka karyani kamar za'a kwace maka ni", komawa tayi ta jingina da bango dan jin kanta na juyawa, muryar da taji ya rud'ar da ita tana son gano inda tasan meh muryar amma zuciyarta a cushe bare kwakwalwarta ya samu damar lalubo mata wacece.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


        29


    Bugun zuciyarta ya tsananta hakan yasa ta lumshe idanunta dan samun nutsuwa, sai da ta d'auki mintuna uku a wannan hali kalmomin Ibrahim da budurwarsa na ratsa zuciyarta, ganin zata iya samun tarwatsewar zuciya in bata yi da gaske ba yasa tayi maza ta bud'e k'ofar d'akin, turus ta tsaya dan abun al'ajabin da ta gani, Ibrahim ne kwance da wata hannunsa akan cikinta, idanunta ta d'aura kan fuskar yarinyar dan ganin wacece, zubowar hawayenta yayi dai-dai da ambatar sunanta da tayi "Miemiebee".

A kid'ime Ibrahim ya mik'e ganin Pherty a wannan lokacin, "PHERTY!" Ya ambaci sunanta yana kallonta, muryarsa na rawa yace "meh ya kawo ki?" Ya k'arashe maganar yana kai dubansa wurin Miemie da har yanzu take kwance ko d'ar bata ji ba sai ma kawar da kai da tayi gefe fuskarta ba annuri. Kuka ne ya kufce mata mai cin rai, juyawa tayi da gudu ta fice dan in ta cigaba da zama a d'akin k'afarta bazai iya d'aukanta ba, duk da k'iranta da Ibrahim yake yi bai sa ta juyo ko fasa tafiyar da tayi niyya ba.

Rikicewa shi kuwa yayi, sai yayi kamar zai bi Pherty sai ya dawo wurin Miemie da take kallonsa rai b'ace, daga k'arshe dai ficewa yayi daga d'akin yabi bayanta yana mai k'wala mata k'ira. Tab'e baki Miemiebee tayi ganin hakan ta mayar da kanta kan pillow tana mai gyara kwanciyarta tare da jan rigarta k'asa dan ya rufe mata cikinta.

K'urar motarta kawai ya tarar a harabar gidan, yanda ta ja motar ta figesa yasa yaji kamar ya bita a baya, ihunsa da k'iransa bai sa ta dakata ba sai tunzurata da ya k'ara yi, kuka takeyi sosai zuciyarta na mata zafi, a guje ta fisgi motar ta falala gudu ba tare da tasan inda ta nufa ba, express way ta hau ta saita motar sai gudu take, dan ma Abuja an saba irin wannan gudun shiyasa jama'a basu lura da ita ba bare su gano lafiyarta ko akasin haka.

Daga b'angarensa kuwa ganin fitar ta daga gidan yasa ya dawo d'akinsa dan d'aukar makullin motarsa ya bi bayanta. Ko kallon inda Miemie ke kwance baiyi ba ya d'auki makullin ya fice, bud'e ido d'aya Miemie tayi ta kallesa a daidai lokacin da yake fita daga d'akin, tsaki ta ja ta mayar da idanun nata ta rufe, can kuma ta mik'e ta d'auki gyalenta da sauran tarkancenta ta fice ta bar gidan zuciyarta fes, taji dad'in ganinsu da Pherty tayi yau wala'alla zai sa ta bar mata Ibrahim ita kad'ai sai dai in Pherty ta sanar dashi tana da aure fa? Shin zai yadda ya zauna da ita? Kawar da zancen tayi dan tasan ta dasa masa abunda bazai iya jure rashinsa ba, murmushin mugunta tayi ta tada motarta ta fice.

Direct gidanta ya nufa dan a ganinsa babu inda zata je sai can, ya isa dai-dai lokacin da Alhaji ya dawo gida, an bud'e masa gate kenan shi kuwa yazo ya wuce idanunsa na cikin gidan yana kalle-kalle dan ganin ko motarta na ciki, rashin ganin motarta ya k'ara dagula mishi lissafi, gaba yayi kad'an yayi parking fuskarshi na nuna damuwar da yake ciki k'arara. ACn motarsa ya kunna ya mayar da kansa ya ajiye akan kujerarsa ya lumshe ido, yasan duk inda Pherty take zata dawo gidanta, shiyasa yayi parking a wannan wuri dan in ta shigo layin ya ganta ya samu damar yi mata magana kafin ta shiga gidan wannan mutumin, can ciki ya ja k'aramar tsaki.

Pherty zaune take a motarta ta d'aura kanta bisa sitiyarin motarta tana zubar da hawaye mai cin rai, bayan ta gaji da tafiyar ne ta rasa ina zata je ta samu wurin da babu kowa tayi parking ta shiga aikin kuka, har izuwa wannan lokaci bata san abun yi ba, tunanin yanda akayi Miemiebee tasan Ibrahim takeyi, ya akayi suka san juna? Meh yasa Ibrahim zai yaudareta ya cuceta bayan duk abubuwan da take masa, kud'i, lokaci har kanta ta damk'a masa amma ya mata haka? Cin amanar ma da k'awarta da take ganin sun zama d'aya? What on earth zatayi taji sauk'i a ranta, meh zata yi da zai sa Miemie tayi da na sanin kusantar abunta?

Tayi zurfi cikin tunanin abun yi wani zuciyar ya tunatar mata rayuwar Ruffaida, anan ne ta fara nazarin abunda ya faru a yau, tambayar kanta take yi ko dai Allah ne yayi mata ishara ya jarrabeta da abunda da take matuk'ar so, hakan ya tabbatar mata Ibrahim ko fitowa tayi daga gidan miji ba aurenta zai yi ba, hakan da ta tabbatar wa kanta ya sake sata wani kukan na ganin wautanta, "kaicona" ta furta a fili cikin muryar kuka. "Shin ni na yaudari kaina na cuci kaina ko kuwa iyayena? An cuceni an shiga hakkina ya Allah ka gafarta min ka bi min hakk'ina" wani sabon kukan ya kufce mata.

Cubana @ 5pm


   Dukkansu zaune suke idanunsu na bisa k'ofar shigowa dan ganin shigowarta amma shiru, sun k'ira lambar wayarta yafi a k'irga amma bata d'auka, babu wanda bai hallara ba Pherty kad'ai ake jira, Miemiebee ce kad'ai idonta akan wayarta hankalinta kwance, bata damu da rashin isowar Pherty har zuwa wannan lokacin ba.

A daidai lokacin da agogo ya buga k'arfe biyar da rabi ta shigo harabar Cubana idanunta luhu-luhu alamar ta sha kuka, sai a lokacin ta samu damar yin sallolin da ake binta sannan ta kamo hanya ba tare da ta koma gida ba.

Idanunta a k'asa ta shigo hawaye na d'illa daga idanuwanta, wurin zamanta ta nufa ta ja kujerarta ta zauna bayan tayi musu sallama muryarta na rawa, ido suka zuba mata dukkansu wasun su na tambayarta lafiya bata iso da wuri ba yau, ganin fuskarta ya tabbatar musu ba lafiya ba, murmushi Miemiebee ta sake ganin yanda Pherty ta koma cikin awanni biyar kacal duk dan ta ganta tare da Ibrahim, in ta gansu suna wani mu'amalar ya zatayi kenan? Kawar da kai tayi tana mai k'ok'arin b'oye farincikinta.

Bata yi musu dogon bayani ba Ummu Abdoul ta bawa Batool hak'uri akan ta dakatar da labarinta dan jin na Pherty la'akari da yanda suka ganta da kuma halin da take ciki, ba'a samu matsala daga wurin Batool ba ta amince dan tausayin da kowace d'iya mace take bata a duk lokacin da ta ganta cikin halin irin wannan, ita ma wace irin rayuwa ta tsinci kanta? Gyarar murya tayi ta fara da fad'in sunanta wato Phertyma Zahra Yakubu. "An haifeni a Minna kuma a can na girma...


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


        30


    "An haifeni a Minna kuma a can na girma, na kasance na fito daga gidan yawa dan mahaifina matansa uku yara goma sha shida kuma dukkaninsu babu wanda ya samu cikakkiyar tarbiyya da ilimi na boko bare Arabic. Ni ce 'ya ta hud'u wurin mahaifiyata sauran yayyina dukka mata ne kowacce tayi aurenta tana zaman gidan miji da dad'i ba dad'i, ni takwarar maman mahaifiyata ce wacce ta rasu da jimawa, hakan yasa mamana take sona kuma take min duk abinda nakeso.

Mahaifina ya kasance mutumin da bayi da sa ido akan iyalinsa, baya damuwa da buk'atunsu bare ya biya musu, ba laifi yana k'ok'arin kawo abinci dan ciyar damu amma bayan wannan sutura da komai iyayenmu mata ke yi mana, tarbiyyar 'ya'yansa mata da maza duk ya barwa iyayenmu mata wanda ta dalilin hakan saura suka lalace suka kangare. Duk wata budurwa a gidanmu in ta taso aure ake mata a cikin shekaru 15, baya wuce hakan ko da wasa, yawancin wad'an da sukayi aure su suke kawo mazajensu dan suna sonsu babu wacce aka tab'a kawo mata wani aka ce za'a aura mata dole.

Ni kad'ai ce nake k'ok'arin zuwa islamiyya dan yawancin k'awayena na zuwa, kuma na kan kai abun sayarwana da Mama take k'ulla min, abubuwan ciye-ciye dai na yara duk ina sayarwa a islamiyya, da hakan nake samun damar zuwa Islamiyya kuma ba laifi ina d'aukan karatuna daidai gwargwado. Ina shekara sha uku na had'u da Ibrahim, kaman yanda nake a gidanmu haka shima yake babu arabi bare boko, had'uwan jini da burgeni da yakeyi ya samu matsayi mai girma a zuciyata, babu wanda bai sanni dashi ba a anguwanmu, k'awayena da abokansa har ma da iyayena.

Bai zama abun magana ba saurayi da nayi a wannan shekaru nawa dan an saba yi mana aure da wuri, mun tsara rayuwarmu cikin so da yaranta irin namu, ni ina 'yar shekara goma sha uku shi kuma Ibrahim a lokacin bazai wuce shekara goma sha takwas ba, kuma a hakan kowa ya amince da aurenmu idan na cika shekaru goma sha biyar. Shagon Babansa yake zama kuma mahaifinsa yayi alk'awarin bud'e masa nasa shagon da zaran aurenmu ya gabato.

Tafiya tayi tafiya rayuwata tana tafiya cikin talauci, kasancewata wurin mahaifiyata da samun lokacinta kad'ai yake sani farinciki sai kuma Ibrahim d'ina da yake sona kamar ransa kuma yake min alk'awarin bani ingantaciyyar rayuwa da jin dad'in da ban tab'a samu ba idan munyi aure. A cikin rayuwar da na tashi kenan kunga kenan bansan wata rayuwa ba sai wancan bazan iya sanin akwai wata rayuwar da zata fiye min wancan dad'i ba. Nidai nasan kullum fatana bai wuce in samu cikakkiyar kulawa wurin Baba da samun kud'i ba, a kullum burina shine inyi aure Ibrahim yana biya mun buk'atuna na kud'i, ban fa san auren ba bansan ya ake yinta ba, matsalata in fita daga rayuwa irin wanda na tsinci kaina a ciki tun tasowata na talauci da rashin kula.

Wata rana na d'auki tallan gyad'ana na fito bakin hanya ina sayarwa ina yiwa gyad'ata wak'e hankalina kwance ina tafiya da silifas d'ina da d'an atamfata da ta gaji da tsufa, ko gyalle ban yafa ba d'an kwali kad'ai ke kaina. Taron jama'a na gani d'an nesa dani da alamu rigima akeyi dan hayaniya da ihun da mutane ke yi, da gudu na isa dan bawa idona abinci, duk kutse-kutsena na kasa ganewa idona abunda ke faruwa, fitowa nayi dan in ajiye trayn gyad'ana in koma in kutsa da kyau, kalle-kalle na tsaya yi dan neman inda zan ajiye trayn.

Wani lungu na gani babu kowa nayi hanzarin isa wurin, ban kai ga ajiyewa ba naji an danna horn ta inda nake, juyowa nayi na kalli wata dalleliyar mota fara, sauk'e glass na motar akayi ya fito da kansa waje yayi min nuni da hannunsa alamar in iso inda yake, baki na wage na isa ba tare da tunanin komai ba, trayn na nuna masa ina cewa "akwai na biyar akwai na goma, Alhaji wanne kakeso? Ga dad'i ga gard'i kuma suya mai kyau" na k'arashe maganar ina kallonsa, murmushi ya sakar min ba tare da yace komai ba, kallon drivernsa yayi yace "d'an je can ka karb'o mana ruwan sanyi na roba", ya mik'a masa kud'in tare da nuna masa shagon da ke kusa da wurin.

Bayan tafiyarsa ne ya dawo da dubansa gareni fuskarsa a sake yana murmusa min, mayar masa nima nayi na sauk'ar da idona ina kallon tray na ina gyara ajiyarsu ina jiran ya fad'a min na nawa yakeso, na biyar d'in ne ko na goma. Can na tsinko muryarsa yana cewa ya sunanki? Ban kawo komai raina ba na fad'a masa "Pherty" daga nan muka shiga cinikin gyad'a, dukka ya saye ya biyani kud'ina, da gudu naje shago dan sayo masa bak'ar leda, a kyauta nayi sa'a mai shagon ya bani na dawo wurinsa a guje na mik'a masa bakina har kunne ina murna.

Bayan na mik'a masa ledar ya juye su sannan yace "toh maza aje gida, ki gaida mamanki" ko sai anjima bance ba na arce cike da murna. Ashe abinda ban sani ba wayo yayi min ya siye dukka dan in koma gida ya samu damar bina yaga gidanmu, kamar yanda ya sanar dani ya kai minti talatin yana biye dani sai daga baya wannan dabarar ta fad'o masa. 

Ni kuwa babu inda na zarce sai gida dan ban tab'a yin ciniki irin ta yau ba, a kullum baya wuce in sayar da rabi in nayi ciniki sosai kenan dan wani lokacin baya kai hakan. Ban kula da bina da sukeyi ba har na isa lungunmu, motarsu bazai iya shiga ba hakan yasa drivern ya tsaya ya fito da hanzarinsa dan kada in b'ace masa, sai da yaga na shige wani gida sannan ya dawo ya sanar da Alhaji yaga gidan" kallon k'awayen nata tayi murmushi fal fuskarta amma idanunta cike da hawaye suna rige-rigen sauk'owa, ta cigaba "duk wannan labarin sai daga baya nake jinsa a bakin Alhaji bayan ya samu biyan buk'atarsa akaina. A tak'aice ranar basu bar anguwan ba sai da sukayi bincike game da mahafina sannan suka tafi.

Sati da faruwar hakan ya dawo cike da abun arziki ya samu babana a zaure da yamma inda ya saba zama. Drivernsa ne ya shigo da kayan abinci masu yawa ya jibge a gefe ya fice ya basu wuri, bakin Baba har kunne ya tsaya kallon kayan da Alhaji ya kawo wanda za'a iya bud'e k'aramar shago da kayan, shinkafa, taliya, maggi har da gishiri da jarkar mai, duk dai wani abu na abinci Alhaji ya kawo mana, anan ne ya samu damar gabatar da kansa a wurin mahaifina, sunanshi Alhaji Haruna kuma asalin d'an Minna ne aiki ya kaisa Abuja.

Bansan wani abu bayan wannan da ya fad'awa Baba ba, nidai naga canjin rayuwa cikin lokaci k'ank'ani, aka sani makarantar boko, aka wadatani da mahaifiyata, kai har ma da k'annena da muke uwa d'aya sai da muka samu canjin rayuwa, sake mana kud'i Alhaji yakeyi kamar baya jin zafinsa, shawararshi Baba ya bi ya sani makarantar kud'i na fara zuwa, bai barni haka ba sai da ya k'ara nemo min malamin da zai na koyar dani a gida jin da yayi ban tab'a shiga aji da sunan karatun boko ba.

Nidai ban tab'a kawo wani abu a raina ba sai ma farinciki da k'aunar Alhaji da nayi dan taimakon rayuwata da yayi, kullum idan ya kawo mana ziyara sai mamana ta turani wurinsa mun gaisa kafin ya tafi. A haka na cigaba da rayuwa ina zuwa makaranta har na cika shekaru goma sha biyar, anan ne Ibrahim ya nemi a sa ranar aurenmu dan ya samu abun yi kuma zai iya rik'eni, babban abun dubawa kuwa shine soyayyar da muke yiwa juna, fir Baba yace bai san zancen ba tunda na fara makaranta dole in gama Alhaji bazai yi asarar kud'i ba inje in zubar da karatun cikin murhu, Mama da nake ganin zata biye min ita ma haka tace, babu yanda zamuyi dole na rarrashi masoyina akan ya hak'ura nan da shekara hud'u, kafin nan na gama makaranta sai aure.

Rana bata k'arya sai dai uwar d'iya taji kunya, a shekara goma sha tara na gama sakandare da taimakon mai koyar dani a gida na kammala na zana jarrabawar waec kad'ai. Tun kafin result ya fito Ibrahim ya sake dawowa kan maganar aurenmu" murmushin takaici tayi da ta iso wannan gab'a tana share k'wallar idanunta daga bisani ta cigaba da magana cikin muryar kuka. "Baba ce masa yayi ya bada ni kuma aurena nan da sati uku, da yaga suna neman tada masa magana da nuna masa basu san zancen ya min miji ba ya mik'e ya cire kunya da mutunci ya tsigalesu har da bud'e musu k'ofar langa-langarsa na zaure yana cewa "ku fice min daga gida"

Ibrahim da girmansa ya tsaya yiwa Baba kuka yana rik'o k'afarsa yana rok'onsa kada yayi mana haka amma fir Baba yace bai san da zancen wani ba sai wanda yayi d'awainiya dani da k'annena, ganin bazai sake k'afarsa ba ya ture Ibrahim ya shige gida ya bar sa anan 'yan uwansa suka d'aga sa suka fice dashi yana ta sharar k'walla" ta k'arashe maganar kukan da take tarewa yana cin k'arfinta tana k'ok'arin dannewa, jin bazata iya dannewa ba yasa ta saki kukan da k'arfi tana mai kare bakinta da hannunta dan kada sautin ya fito sosai. Batool da ke gefenta ta cire hannun nata tana cewa "kiyi kukan".


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


        31


    Sai da tayi kuka mai isanta babu mai rarrashi sannan ta cigaba da cewa "k'aramin hauka nayi da naji wannan batu daga Ibrahim, nayi kuka kamar raina zai fita, tun Mama na rarrashina har ta gaji ta daina, alwashi nayi babu wanda zan aura sai Ibrahim d'ina, i promised him i will fight for our love kuma ya k'arfafa min gwiwa ya tabbatar min YANA TARE DANI duk abinda zai faru.

A lokacin da Baba yayi min maganar Alhaji Haruna banji kunyan ce masa bazan auresa ba kuma babu wanda ya isa yasa na auresa, nayi masa rashin kunya iya wanda zan iya ba tare da wani ya kwab'eni ko nuna min banyi dai-dai ba, banji nauyinsa matsayin Mahaifina ba na rufe ido nayi masa yanda nakeso na fice na bar masa d'akin. Tabbas na b'ata ran mahaifina, a ganinsa ko da ya banzatar da rayuwarmu bai bamu tarbiyya ba bai kamata inyi masa rashin kunya irin wannan ba, hakan da nayi masa ya k'ara tunzurashi kuma yayi alwashin ko ta yaya sai na auri Alhaji.

Sati d'aya da faruwar hakan na nemi Ibrahim na rasa, duk wani lungu da sak'on da yake zuwa naje ban samu ganinshi ba, babu wanda yasan inda yake bare hankalina ya kwanta, ganin bani da na yi yasa na wanke k'afana naje gidansu nemansa. Har cikin gidan na shiga kai tsaye ina mai doka musu sallama, mamansa na gani zaune akan tabarmanta tana tsince shinkafa, amsa sallamar tayi tana mai d'ago kanta dan ganin wacce tayi sallama, ganina da tayi a tsaye yasa ta tamk'e fuska ta ajiye trayn shinkafar ta mik'e ta iso inda nake, tsoro sosai ya shige ni na d'auka jibgana zatayi.

Cikin kausasshen muryarta tace "uban meh ya kawo ki gidan nan? Fice min daga gani tun kafin in tattake shegiya mai banzan mahaifi maras sanin kunya bare mutunci" kalamanta yasa na lumshe ido ina mai jin bak'in cikin furucinta akan mahaifina, duk da mun b'ata dashi baya kyauta min amma naji zagin nan da tayi masa har raina, daurewa nayi nace mata "dama Ibrahim ne nake nema kwana biyu ko wayarsa bata shiga nazo dubawa ko lafiya?" 

Ashar ta lailayo ta maka tace "uban meh zaiyi da 'yar matsiyata marasa tarbiyya? Ai da Ibrahim ya aureki gwanda ya mutu baiyi aure ba" ban sake tanka ta ba ta k'arashi zaginta da ci min mutunci na karkad'e bujena na k'ara gaba cikin mutuwar jiki ban samu abunda nakeso ba sai ma zagi da cin fuska. Wasa-wasa kwana biyar rabona da Ibrahim, tun ina damuwa ina kuka har maganganun mutane ya fara shiga kaina akan guduwa yayi ya barni dan bai sona, dan dole na karb'i tayin auren Alhaji.

Kamar yanda Babana yace sati uku na cika aka d'aura min aure, duk wani shagalin biki da kayan amarya da abincin da za'a ci a gidanmu da komai ma Alhaji ne yayi, yayi facaka da kud'i kamar baisan zafinsu ba, na rasa gane dalilin da yasa yake min soyayya ta gaskiya kuma zai iya yi min komai dan faranta raina. Bai ajiyeni a Minna garin da matarsa da yaransa suke ba, ana gama biki aka d'auke ni sai Abuja, wani tank'amemen gidansa da ke Asokoro ya ajiyeni, fad'ar irin daular da na shiga b'ata lokaci ne.

Alhaji ya bani duk abinda nake buk'ata, kud'i, soyayya, lokacinsa da komai ya bani, uwa uba respect, sosai yake respecting d'ina kuma yake gudun b'acin raina. Ina gama amarcewa ya nema min makaranta anan, private uni. na fara zuwa dan samun takardar degree d'ina. Duk da na kasance 'karama dan za'a iya alak'anta ni da sa'ar 'yar alhaji ta uku wacce take da aure har da yarinya d'aya bai hana Alhaji nuna ma 'ya'yansa, matarsa da duniya cewa ni matarsa ba ce, baya kunyan yi min wani abu da shekarun nan nasa, har farin gemu yana dashi amma wallahi babu kaffara Alhaji ya iya soyayya kamar saurayi d'anye sharaf.

Jin dad'i da sa sutura mai kyau ya k'ara fiddo min da cikakken kyauna da 'yan matantaka na, a cikin makarantarmu babu wanda yasan ina da aure, dressing d'ina da yanayin kwalliyata da shiga mota mai tsada sai mutane suna d'aukana matsayin 'yar mai kud'i. Daga nan na fara samun masoya samari kyawawa masu jini a jika, masu kud'i wad'an da idan na fito na nuna matsayin mijina darajata da mutuncina zai d'agu ba kaman alhaji tsoho ba. Anan ne na gane cewar an cuceni da aka aura min shi, kuma mahaifina ya cuceni da ya barni cikin talauci da zaman k'auyanci da tuni na wuce inda ake zato.

Sabuwar rayuwa na fara ina soyayya da duk wanda naso kuma ba soyayya kad'ai ba har kaina nake bawa namijin da naji kwad'ayi, na samu daman yin hakan ne dalilin yawace-yawace da yakeyi da kuma biye min da yake yi in nace ina son abu. Shekara ta uku ina shek'a tsiyata babu wanda ya sani, daga ni sai Allah dan babu wanda yasan ina keta haddin Allah.

Aurena da Alhaji ya bani 'yancin kaina da duk wani abunda mace mai zaman kanta take samu. Wata rana na fita shopping a nan Amigo na gama komai na fito ina toshe da shade d'ina nayi hanyar motana, a nan naci karo da abun mamaki, Ibrahim na gani cikin kod'add'iyar shaddarsa jingine jikin motana, yana ganina ya sake murmushi da alamu ni yake jira, gabana sai da ya fad'i da na gansa cikin wannan yanayi, duk ya b'aci ya lalace sai ramar da yayi da bak'i.

Tunowa da nayi ya gudu ya barni yasa na tamk'e fuska na bud'e seat na baya na sa kayan hannuna na rufe. A hankali ya k'ira sunana "Pherty" ban ma nuna naji ba bare in amsa, bud'e mazaunin driver nayi na shiga ban sake kallon inda yake ba. Ban kai ga rufe k'ofar ba ya rik'e k'ofar da hannunsa hawaye fal idonsa yana cewa "dan Allah ki saurareni". Ganin hawaye na sauk'o masa ya kashe min zuciya naji sabuwar soyayyarsa ta d'arsu min, ganin nayi laushi yasa ya fara da cewa.

"Nasan na yi miki laifi, amma idan kika tsaya kika saurareni zaki san bani da laifi cikin abubuwan da suka faru, ke shaida ce na so ki kuma naso aurenki Allah ne bai k'addaro min nine mijinki ba..." Anan yayi min bayanin abinda ya faru, ashe abunda ban sani ba shine Babana lokacin da na nuna bazan auri Alhaji Haruna ba shine ya sa aka sace shi aka kai sa wani wuri ba tare da kowa ya sani ba, babu duka babu zagi kawai b'oyesa sukayi suna bashi cima mai kyau sai dai ko cikin gidan da suka ajiyesa bai tab'a lek'awa ba, ko a gidansu ba'a sani ba dan aikawa akayi aka ce yace ace yayi tafiya bazai iya ganin aurena ba, duk wannan yana daga cikin plan na Baba. Basu sako shi ba sai da akayi aurena da sati, da ya fito yayi k'ok'arin nuna musu halin 'yan iska amma Baba ya toshe masa baki da maganganu masu tsoratarwa da zaiyi wa iyayensa. 

Bai saduda ba ya shiga binciken inda nake a b'oye har Allah yasa ya gano ina nan Abuja, daga nan ya shiga fafutukar neman kud'in zuwa Abuja, dak'yar ya tattara 'yan kud'insa ya shigo Abuja garin bariki. A wurin abokinsa ya sauk'a a wani baca da yake zama, yau ak'alla sati uku kenan yana neman yanda za'ayi ya ganni sai yau Allah ya bashi dama ya fito ya ga wucewata cikin motata sai ya biyo ni a baya.

Nayi kuka da jin hakan kamar anyi min mutuwa, nayi wa iyayena Allah ya isa ba iyaka dan sun cuceni da suka rabani da mai sona suka aura min k'aton mutumi tsoho ma dai zance wanda ya isa ya haifeni, na rasa gane meh yasa suka zab'i kud'i akan farincikina kuma na tabbata basu tab'a tunanin hakan zai iya sa ni in aikata wani ashsha da duk zai sa mu wahala Allah ya azabtar damu ba. Tare muka bar wurin da Ibrahim, sai da naje boutique na sayo masa kaya irin na zamani sannan muka wuce hotel na kama masa d'aki inda zai zauna kafin mu san abun yi. A ranar ban koma gida ba sai da naji kud'in account d'ina yayi k'asa, siyayya nayi masa sosai na kai masa sannan na koma gida.

Daga nan rayuwarmu ya sauya ni da Ibrahim, duk da yasan ina da miji bai hana shi zama dani tamkar matarsa ba, ni na nuna masa wannan harkar dan shi da farko nuna min yayi bazai yu ba, amma da na zauna nayi masa bayanin plan d'ina da kuma zaman da zamuyi kafin in tattaro kud'in da zan iya samu daga wurin Alhaji sai insa ya sake ni in fito muyi aure sai ya sake jiki ya biye min, duk ranar da Alhaji ya sa k'afa ya bar garin Abuja toh fa ina tare da Ibrahim, Ibrahim shi ya rabani da dukkan sauran samarina da nake kulawa dan yana da bala'in kishi, da Alhajin ma kishi yake dashi bare wasu can, na kama masa gida evry year ina biyan kud'in haya, bayan haka duk wani buk'atunsa na kud'i ni nake masa, na saya masa mota na basa duk wani so da k'auna har muka kai shekara biyu muna abu d'aya.

Lokacin da na gama makaranta Alhaji ya hanani aiki, business nakeyi ina zaune cikin gida kuma duk da business d'in da nake yi bai hana Alhaji bani kud'ad'e masu yawa ba a duk lokacin da na buk'ata, a hakan kuma na cigaba da masters d'ina. Ban tab'a jin bana yin daidai ba sai ranar da Ruffaida ta bamu labarinta..." Lubiee ta dakatar da ita da cewa "wai tsaya Pherty, dama kina da aure baku rabu ba da Alhajin?" Cike da mamaki take tambayarta, lumshe idonta tayi hawaye ya sauk'o kan fuskarta, bata amsa ta ba ta cigaba da cewa "tun daga ranar naji bana kyautawa kuma Ibrahim bazai aureni ba ko na fito daga gidan Alhaji amma wani zuciyar yana nuna min d'unbun k'aunar da yake min, sai yau da naje wurinsa na gano wani abun al'ajabi"

Miemiebee tuni ido ya raina fata tana ganin Pherty zata tona mata asiri amma lafazinta da taji yasa hankalinta ya kwanta har sai da ta sauk'e ajiyar zuciya tana hamdala. "Zuwa nayi na samu Ibrahim kwance da wata a gidan da na kama masa, a gadon da ni na saya masa, ya cuce ni kuma ya yaudareni, nayi da na sanin abunda na aikata kuma nayi wa iyayena Allah ya isa dan duk su suka ja min abinda ya sameni, tunda nayi aure suka samu wadata shikenan suka manta da wani hali da nake ciki, sun samu tank'amemen gida da kayan alatu tuni suka mance da ni da halin da suka jefani" kuka ne ya ci k'arfinta tana cewa "ya zanyi? Allah zai gafarta min in na nemi tubansa? Alhaji zai yafe min? Ni da zan samu ya sake ni ya kwace duk wani kadararsa da ya bani da yafi burgeni dan iyayena su wahala su san sun cuceni sun gama da rayuwata" ta k'arashe maganar tana d'aura kanta akan table na gabanta tana mai zubar da hawaye.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


        32


"Tirk'ashi!" Cewar Lubiee, cike da b'acin rai Benaxir tace "wai meh yasa 'ya'yan musulmai suka d'auki zina wani abu mai sauk'i ne a yanzu? Anya 'yan zamanin nan namu suna ko tsoron Allah suna tsoron wuta? Gar kana ganin haramun amma kai sai ka sa k'afarka saboda tsabar son zuciya, cikin labarin Ruffaida da Pherty ku fad'a min wanda yake da laifi in ba su ba" kukan da Batool ta fashe dashi yasa duk suka dawo da dubansu gareta har Pherty da tun tuni take ta aikin kuka.

Ruffaida ce ta dafa ta tana cewa "lafiyanki?" Cikin muryar kuka take cewa "labarin Pherty mai sauk'i ne in kuka ji nawa labarin, nawa ya sha banban da nasu dan nasu dalili yasa suka yi ni kuwa da k'afana na kai kaina ga halaka ina sane, a rayuwa meh mutum yake nema irin soyayyar iyayensa da yardarsu? Ni duk na rasa a dalilin kuskuren da na tafka, bazan ma k'irasa da kuskure ba saboda ba kuskure ba ce son zuciya ne ya kai ni ya baro, Benaxir maganganunki su suka kashe min jiki tunawa da nayi gwanda kunyar duniya in har ka tuba Allah mai rahama ne kuma zai gafarta maka" ta cigaba da kukan zuciyarta na mata k'una.

Yawu Lubiee ta had'iye zuciyarta na mai dukan uku-uku, ummu Abdoul ta gyara zama tana mai fargabar labarai biyu da takeson ji, anya bazai sa zuciyarta bugawa ba? Haka 'ya'yan musulmai suke da take hakk'in aure? Zina? Kina matar aure kiyi zina? Wa iyazubillah, meh iyaye suke nema a duniya da zai sa su hana 'ya'yansu abinda suke so saboda su samu dukiya, shin iyaye da suke haka sun tab'a tunanin dukiya daga Allah ne haka talauci? Shin sun tab'a tunanin ranar da zasu je gaban Allah hak'kin yaransu na kansu? Shin ya akayi suke mantawa da abunda addininmu ya koyar damu? 

Dak'yar ta saita tunaninta ta fuskanci Batool da take zubar da hawaye "please bamu labarinki tunda is related to nata, sai dai ki d'an hanzarta mu gama kafin mu tafi, kinsan 8 yakamata mu bar nan" ta fad'i hakan tana mai duba agogon hannunta. D'ago da kanta tayi tana cewa "ohppss muyi sallah 1st sai muji naki". Babu wanda ya sake magana wad'an da zasuyi sallah daga cikinsu suka mik'e dan gabatar da sallahr maghrib.

Bayan sun idar ta fara basu labarinta kamar haka:- "na fad'a muku sunana kuma na fad'a muku daga ina nake, kai tsaye zan baku labarin da ya dace kuji, zan fara muku daga daidai inda rayuwata ta canja duk da tun ina secondary school nake fand'ararriya mai yin duk yanda taso a cikin makaranta, duk dai da hakan bai sa na samu tangard'a cikin karatuna ba sai bayan na gama na shiga sabuwar rayuwa wato rayuwar jami'a. Ina shekara goma sha takwas na fara university, kuma a wannan shekarar mahaifina ya damk'a min makullin dank'areriyar mota mai kyau da tsada, ya tura min kud'ad'e masu yawa a account d'ina duk da ina dasu dama dan pucket money da yake bani sunyi yawa har ina tarawa.

Mahaifina na kashe mana kud'i fiye da tunaninku, muna spending yanda mukeso muna rocking life namu, ko wani wata Abba yana fita damu shopping kuma duk abinda muka nuna muna sha'awa zai ce ku d'auka, waya, kaya, da duk wani nau'i na kayan zamani babu wanda bamu sawa, Amma(sunan da suke k'iran mamansu) ce kad'ai ke kawo mana cikas, komai akayi mana sai ta nuna yayi yawa zai b'ata tarbiyyarmu, ko waya ya sayo mana zata kwace ta b'oye ta sayo mana baby nokia, a ganinta munyi k'anana. Hakan da takeyi ba k'aramin b'ata min rai yakeyi ba dan ina da bala'in rawar kai. 

Da na gama skul dama waje zan fita inyi karatu amma ta hana, wai in ma fitan ne sai dai Sudan, ni kuma a lokacin friends d'ina daga masu zuwa Dubai sai Cairo hakan yasa nace indai Sudan ne bani zuwa ko ina gwanda inyi a Nigeria insan ban fita ko ina ba. A nan aka nema min a Katsina Alk'alam sunan makarantar, sosai naji dad'in samun makaranta a Katsina dan babu wanda na sani zanyi rayuwata yanda nakeso babu takura. 

Tunda na sa k'afana na bar gida na d'auki sabuwar rayuwa, tun daga kan kayana zuwa motar da nake hawa ya nuna wa 'yan makarantar ni d'in ba ta wasa ba ce kuma na fito daga babban gida. Ni d'aya nake rayuwata har na kai wata d'aya cur a makarantar, babu wanda na tab'a magana dashi bare mu zama k'awaye, kullum daga lectures sai yawo cikin makaranta ko kuma in shiga cikin gari, daga nan kuma sai k'aramar gidan da aka kama min ni d'aya tal babu mai sa min ido, kusa da makaranta aka samo min duk da Amma taso in zauna cikin makaranta amma bai yu ba.

Wata rana ina zaune a cikin motata na bud'e k'ofar k'afafuna a waje ina danna wayata da hannu d'aya d'ayar kuma ina zuk'an coca-cola ta gwangwani, hankalina kaf yana kan chating d'in da nake yi da k'awayena, banda murmushi babu abunda ke fuskata. Wayar hannuna aka warce ba tare da nasan an iso inda nake ba bare inyi tunanin hakan zai iya faruwa, tsinkar zuciyana yayi daidai da subhanallahi da na furta na wullar da gwangwanin ina neman k'ulewa cikin mota. Hannuna ya rik'e ya kwashe da dan tsoratar da nayi ya basa dariya, wani kallo na watsa masa cike da tsana.

Tsaki na sake masa na warce wayata na sa k'afafuna cikin motar nace "malam am going" dan ya matsa in samu damar kulle k'ofar. Idanuna na bisa k'afafunsa ina kallon takalmarsa k'irar Bruno Magli bak'a sai yalk'i yake, tab'e baki nayi dan nasan wankan nan da gangan yayi sa dan ya sace zuciyata. Ganin bayi da niyyar matsawa yasa na dube shi cikin ido, sanye yake da suit bak'a yasha necktie, k'warjininsa yasa na kau da kai gefe ban iya k'ara wani kwakkwaran motsi ba. "Mutumin nan ya fita rayuwata" nace cikin raina, kamar yaji ni yace "sorry Batool, na takuraki ko? Tun d'azu nemanki nake a cikin school d'in nan ko lecture kin hanani shiga".

Hannunah ya rik'o ya d'agani ya fito dani ya ciro key d'in sannan ya rufe motar, duk wannan abun hannuna cikin nasa yayi, dubana yayi yace "muje" yana nuna min hanyar motarsa, ganin ba tafiya zanyi ba ya gyara hannun rigarsa ya fara k'ok'arin d'aukana, sanin bayi da kunya yasa na sa gudu na isa wurin motarsa na tsaya, dariya yayi ya iso inda nake yana cewa "ashe kina kunya". Motarsa ya bud'e min na shiga ya koma mazaunin driver. 

Hannuna ya rik'e yana murzawa a hankali, banyi k'ok'arin janyewa ba saboda na saba runs, rayuwa da soyayyar nan duk na saba yinsu, ko dan kada ace min 'yar k'auye bazan yadda in disga kaina ba. Lumshe idona nayi na ja numfashi jin ya cigaba da yin hakan, can na tsinkayi muryarsa yana cewa "Batool why can you understand that i love you, kaf makarantar nan babu wacce zan bita kamar yanda na biki, tun yaushe muke abu d'aya, yakamata a samu sauyi mana" ya k'arashe maganar yana matsowa kusa dani, tun kafin in kai ga hana shi naji sauk'ar lebb'ansa akan nawa.

Ware ido nayi da mamaki dan iskancina bai kai haka ba, kwace kaina na fara yi amma yak'i sakina sai da yayi niyya dan kansa. Kuka na fashe masa dashi ina k'ok'arin bud'e k'ofar amma sai dai a rufe, ban kallesa ba nace "ka bud'e min in fita" "bazaki bar motar nan ba sai kin karb'i tayin soyayyata, ina ganinki kamar kin waye ashe da sauranki, kiss d'in ne zai saki kuka? U'r funny".

Duk hawayen da na zubar da magiyana bai sa ya barni ba sai da na amince da soyayyarsa, ya karb'i numbana sannan ya bud'e min na fito, har mota ya rakani ya bani key yace sai munyi waya. Daga ranar dai komai ya sauya, nayi k'ok'arin b'uya amma hakan ya faskara duk inda na shiga Mujahid sai ya samo ni, tun ina share shi ina shan k'amshi har ya kai ga na sake dashi. Soyayya mukeyi k'azamtacciya dan duk lokacin da na shiga motarsa ban fitowa haka sai ya yamutsani, ina jin dad'in hakan sosai kuma hakan da yake min yasa naji soyayyarsa mai yawa kuma bazan iya rabuwa dashi ba. Wasa-wasa har gida Mujahid yake zuwa mu shek'e ayarmu babu ruwan kowa da rayuwarmu.

Mujahid tantirin mai kud'i ne d'an gatan iyayensa, neman mata da zuwa clubs shine halinsa, bai tab'a neman mace bai samu biyan buk'atarsa daga gareta ba, yaro ne mai jini a jika yana final year d'insa a Law, duk sharholiyarsa bai hanashi zaman karatu ba, yana bawa karatunsa muhimmanci fiye da tunanin mai karatu. Wata rana ina kwance a d'aki na k'ira sa nace yazo inason ganinsa ina gida, cikin mintuna 15 ya iso.

Abunda muka saba shi mukeyi wanda a ranar ne na nemi ya yi min abinda bai tab'a yi min ba, duk shaid'ancinmu iya soyayyar shan minti muka tsaya wanda 'yan matan yanzu suka d'auke shi tamkar ado, duk maitarsa da na tara a ranar na sauk'e masa, shi kuwa dama a shirye yake dan dama ya jima da neman yin hakan ina hanasa.

Bai kai ga yi min abinda nake muradi ba ya mik'e yace min yana zuwa ya fice bayan yasa rigarsa, bai yi minti biyu ba ya dawo, duk na k'agu babu abinda nake muradi irin kasancewa dashi, bansan meh yayi ba dan bani da masaniya da abu irin haka, shine rana ta farko kuma ta k'arshe da zanyi mararin karya dokar Allah, shine rana ta k'arshe da na kwana cikin farinciki, tun daga ranar ban sake samun wani farin ciki ba a rayuwata har yau. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ta furta hawaye na malala bisa kuncinta.

"Na yadda lallai duk wanda ya kauce hanya yana tare da da na sani, duk wanda ya d'auki sab'on Allah ado yana da rauni a imaninsa, kuma duk wanda ya take umarnin Allah toh tabbas ko bai gani anan duniya ba zai gani inda ba'a karb'ar tuba, duk wanda ya samu kad'an daga cikin abunda ya aikata na sab'on Allah tun anan duniya ya Gode wa Allah, dan hakan na nuni da Allah yana sonka da rahamarsa, idan kana da wayo sai ka gyara rayuwarka ka daina sab'a masa amma in baka dashi..." Ta kalle su tayi murmushin takaici tace "hohoho! Allah kad'ai yasan yanda zai yi da kai"


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


        33


   "A ranar dai na samu duk wani k'azamar soyayyar da nake muradi, sai k'arfe sha biyun dare na k'yaleshi ya tafi bayan munyi wanka tare, sai da ya jaddada min soyayyarshi gareni ya bar ni fuskata na d'auke da murmushi. A ranar zuciyana wasai na kwanta, babu tsoro, fargaba ko da na sani bare in nemi yafiyar ubangijina, mantawa nayi da duk wannan saboda raunin imani irin nawa, kaico nah! Rayuwar d'iya mace duk kamun kanta in dai bata da mafad'i sai dai ikon Allah amma ni na tabbata babu alkhairi cikin zaman mace inda babu mai kwab'anta, ko da bata aikata babban laifi irin nawa ba toh na shan minti dai ya zama ruwan dare (yanzu rayuwar 'yan boko kenan, wayewa ne a ganinsu suyi soyayya da mace suyi wasa da ita dan rage zafi, suna mantawa da cewa yin hakan na kai mutum ga zina kuma Allah yayi hani da hakan, annabi yayi hani ga kowani d'a namiji tab'a hannun mace bare har ya kai ga soyayyar shan minti, wanda ya k'unshi kiss, hug da abunda ya wuce haka, ina fatan su kwab'i kansu in babu mai kwab'arsu dan duniya ba matabbata ba ce).

Can k'arfe hud'un dare naji fitsari na tashi, lafiya k'alau na shiga ban d'aki na zauna a WC, abun mamaki ga fitsarin ina ji amma ya kasa fitowa, nayi iya k'ok'arina inyi amma na kasa, nayi nishin da duk wani dabara amma yak'i zuwa, na sa hannuna na duba ba komai sai zafin da nake ji kad'an-kad'an, anan ne zuciyata ta kasa nutsuwa, meh yake shirin faruwa dani na tambayi kaina amma ba amsa. Jikina ba laka na fito zuciyata sai bugu yake, zan iya cewa har k'ararsa za'a iya ji in akwai mutum kusa dani. 

Na kwanta zuciyata cike da fargaba da tunanin inda matsalar yake, ahankali nake jin ciwon ciki amma tashin hankali yasa na share ban kula ba. A gigice na farka daga baccin da ya fara sace ni dan murd'awar da cikina yakeyi ya wuce misali, ni kad'ai ne a gidan nan babu mai taimakona, sai a sannan na fara tunanin ko mutuwa zanyi, duk wani addu'a da na sani sai da nayi ta, nayi istigfari ina mai zubar da hawaye, duk da na cire rai dan naji ana cewa in mutum yazo mutuwa yayi istigfari a daidai lokacin da ake zare ransa baya karb'uwa.

Wallahi na d'auka mutuwa zanyi a wannan daren, dak'yar na samu k'arfin d'auko wayana na k'ira Mujahid ina murk'ususu, sau uku ina k'ira bai d'auka ba, ji nayi kamar a maimaita min zuwana makarantar nan dan in samu damar bijirewa buk'atarsa, "shikenan yayi kud'i dani matsafi". Nayi kuka kamar in shid'e, zuciyata kamar ta fashe ga matsananciyar ciwon ciki. Sai can na tuno Hauwa Jabo bayan na gama galabaita. Course mate d'ina ce da mukayi sharing number kwanaki tana zama cikin hostel, a daddafe na iya k'iranta, sai da wayar tayi kamar zata yanke sannan ta d'auka cikin magagin bacci.

Cikin whalalliyar muryana nace "ki taimakeni zan mutu, cikina ciwo sosai ina gida kizo dan Allah" katse wayar nayi dan jin ciwon cikin ya k'aru, minti talatin da k'iranta naji ana buga k'ofana, ban iya tashi ba sai ma rarrafawa da nayi, in nayi kad'an in kwanta in na kasa rarrafawan a kwance nake jawuwa har na isa k'ofar a daidai lokacin da suke shirin b'allawa. Bud'e musu nayi jikina duk ya saki na lumshe idanuna hawaye na malala numfashina na fita sama-sama.

Dak'yar nake iya bud'e idona na kallesu d'aya bayan d'aya, Hauwa ce da Guards biyu na makaranta suka rakota, sai da nace ku taimakeni sannan suka daina kallona da mamakin zabgewar da nayi, d'aukana sukayi cak a hannunsu suka fita dani, basu direni ko ina ba sai cikin clinic na makaranta. Na suma yafi sau biyar ina farfad'owa, wallahi ban tab'a jin ana ciwon ciki irin nawa ba, sunyi duk yanda zasu yi dan gano abinda yake damuna amma abun yaci tura, daga k'arshe dai suka tabbatar musu da cewa abun yafi k'arfinsu sai dai akai ni asibiti a cikin gari.

K'arfe 5 na safe yayi mana a cikin General hospital na Katsina, emergency aka shiga dani dan duba lafiyana, a lokacin ko motsin kirki ban iya yi, Hauwa ce tayi anfani da wayana ta k'ira Amma da Abbanah ta sanar dasu abunda yake faruwa. Flight suka bi na safe suka iso asibiti a daidai lokacin da Dr. yake neman wani makusancina. Ba tare da sun shiga office ba Dr. ya keb'e dasu yana fad'a musu abinda ya sameni, condom ne ya shiga vagina d'ina wanda bazai yu su iya cirewa ba sai sun min aiki.

Fad'in tashin hankalin da suka shiga b'ata baki ne, Abba aka nemi yasa hannu dan shigar dani d'akin theatre amma fir yak'i yana ik'irarin shi bai haifi karuwa ba, gwanda in mutu da kan yasa hannu a ciro abinda ni na nema na hallaka kaina, da bai ga yanda nake ba zance bai ganni ba shiyasa bai tausaya min ba amma ya ganni yaga irin galabaitan da nayi sannan ya fad'i hakan. Duk magiya da maganganun Dr. Game da lallai sai yayi sign dan ana gab da rasani bai sa ya saduda ba, ana maganan death or life amma Abba bai sauraresu ba sai ma cewa yayi su barni in mutu tunda abinda nakeso kenan.

Amma da nake ganin ita ce zata kyamaceni ita tayi sign aka shiga yi min aiki. Ikon Allah kad'ai yasa na rayu dan har an cire rai da samun nasarar wannan aiki, sati biyu nayi ina jinya ina mai da na sanin rayuwar da na jefa kaina, Mujahid text yayi min yana bani hak'uri kan cewa ya san da hakan amma tsoro ya hanashi sanar dani bai d'auka abun zai kawo matsala haka ba, ko zuwa wurina bai yi ba sai ma canja layi da yayi dan cewa yayi bazai iya cigaba da zama dani ba dan yana tausaya min, a fad'arsa kenan dan ni nasan ya gama dani shiyasa ya gudu ya k'yaleni. 

Daga ranar na rasa soyayyar iyayena, na rasa komai nawa ciki har da karatun boko da iyayena suka rantse bazan yi ba, tsanar da iyayena suka min yasa suka koreni Antynah Munay ta d'aukeni ta kawo ni wurinta anan Abuja. Cikin garin Nasarawa babu wanda bai ji labarin abinda ya sameni ba, haka cikin makaranta. Na janyowa kaina da iyayena zagi, na rasa komai a rayuwata, bana tunanin akwai wanda zai iya hak'uri ya danne zuciyarsa ya aureni". Kuka sosai take yi idanunta yayi jawur kanta na sara mata, majina ta ja ta goge hawayen ta cigaba.

"A nan nake zama yanzu, a can Alk'alam muka shak'u da Benaxir har ta had'ani da Ummu Abdoul dan Benaxir a lokacin tana zuwa matsayin yaya ga abokin Mujahid Jabir tana zuwa duba shi a makaranta, sai a labarinta na gano cewa ba yayarshi ba ce mutuncin da sukayi da Benaxir ne ya shafe shi har take zuwa wurinsa, ban tab'a bata labarina ba bare ta kwab'eni har na aikata abunda na aikata na bar alkalam".

Kallonsu tayi d'aya bayan d'aya sannan tace "ina mamakin wasun ku idan suka ce min sun d'auki zina ado, sau d'aya nayi amma nayi da na sani kuma na tabbata ko mijina bazai yi anfani da wani abu makamancin condom in kyalesa ba, ni fa na yadda cewa duk abunda addininmu ya hana toh yana da illa sai dai in masu bincike basu gano ba, wannan abunda ya sameni yana d'aya daga cikin illar zina, in wasu sunyi sun wanye lafiya lahirarsu bazata yi kyau ba, wasu kuwa bazasu tashi k'alau ba tun daga nan duniya, ba'a cire rai daga rahamar ubangiji shiyasa ake son musulmi ya yawaita tuba".

Benaxir ji take kamar ta tashi ta hau su da duka su uku, doguwar tsaki ta ja ta kawar da kai, duk suka kalleta ba tare da sun tanka ta ba Ummu Abdoul tace "i have to talk yau kam, naga abun yana yawa, kunyi alk'awarin bin dokarmu da shawarar da zamu bawa juna, da babbar murya a yau ina baku shawarar dakatar da aikin sab'on da kukeyi kafin mu kai ga k'arshen komai har mu san abun yi. Daga k'arshe ina shawartarku da kuji tsoron Allah, mu guji fushin ubangiji kuma mu tuna abinda ya kawo mu duniya...".

Sosai tayi nasiha mai shiga jiki, duk jikinsu ya mace wasu daga cikinsu har da k'walla, Miemiebee dai ta sha jinin jikinta, ta tsorata matuk'a da zantukan da taji a yau, sai dai bata jin zata iya hak'uri da Ibrahim, ya zama jinin jikinta, kuma at the same time tana son Kamal d'inta, matsalarta bazata iya hak'uri ta jure rashinsa kusa da ita ba, anya zata iya bin dokar nan da aka kafa? Sai da tayi da gaske ta saita kanta har suka gama jin nasihar sannan suka watse kowa yayi hanyar gidansa kafin gobe aji labarin Miemiebee.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


        34


Ibrahim:-


  Tun da aka idar da sallahr maghrib bacci ya fara d'aukansa bayan ya idar a gaban motarsa. Duk wucewar mota idonsa akai duk da hasken fitilar motar na dalle idanunsa daga yanko kwanar, mota ta biyar kenan yanzu da suka wuce babu Pherty ba dalilinta, har ya cire rai da isowarta yaga wata motar ta haske fuskarsa, hannunsa yasa ya kare dan kamar da gayya aka haskoshi, sa ido yayi sosai dan ganin motar da kyau, ai tuni ya b'alle murfin motar ya fito da hanzari dan kada ta wuce ta shige gida ba tare da ya samu damar magana da ita ba.

A tsakiyar hanya ya tsaya ta yanda babu yanda zata yi ta wuce sai in ya matsa, horn tayi masa tun daga nesa da ta gano shi d'in ne ba kamanni bane kamar yanda yazo ranta da farko, ganin ko motsi bai yi ba yasa ta k'ara gudun motar, yanda ta fisgi motar ka rantse sama zata tashi, ko tsoro bai ji ba bare ya bar mata kan hanyar sai ma langab'e kai da yayi yana mai nuna mata cewa yayi nadama tayi hak'uri, bata bari soyayyar da take masa yayi tasiri a zuciyarta ba ta yi kansa da motar, tun yana tunanin zata dakata har ya cire tsammani ya kau da kai gefe yana jiran jin rad'ad'in bugun motar a dukkan ilahirin jikinsa.

Ita ma hakan ya sameta, ta d'auka zai tsorata ya bata hanya sai taga akasin haka. Daf dashi ta iso sannan ta danna birki ji kake "k'iiiiss!!!" K'ura duk ya bad'e wurin, lumshe idanunta tayi tana mai jin rad'ad'i a zuciyarta. Ibrahim da ya kusa suman tsaye dawo da dubansa yayi gareta sannan ya kalli tsinin bakin motarta da ya kusa tab'a shi, ya tabbata ya kai k'ololuwar b'ata mata rai, kashe shi takeson yi ko meh? Addu'a yake a zuciyarsa Allah ya bashi ikon shawo kanta dan ita ce kad'ai gatanshi a yanzu.

Isa wurinta yayi ya tsaya dai-dai k'ofar motar inda take zaune (mazaunin driver) ya k'wank'wasa glass d'in, kumburarrun idanunta ta bud'e da sukayi jawur tana kallonsa wasu zazzafan hawaye na sake sauk'o mata, kamar bazata sauk'ar ba ta danna wani botton sai glass ya fara sauk'a a hankali. Bata yi masa magana ba sai ma d'auke kai da tayi daga dubansa, shiru shima yayi na d'an lokaci sannan ya tara courage na yi mata magana.

"Pherty" ya k'ira sunanta, bata amsa shi ba bare ta kallesa. Numfashi ya sauk'e ya kalli k'asa sannan ya sake dawo da dubansa gareta yana cewa "am very sorry, nasan hakan bai kai ya dawo min da Phertynah ba amma dan Allah kada ki gujeni, ke kad'ai nake dashi a yanzu mai tausayina..." Jan motarta tayi ba tare da ta jira k'arashen zancen nasa ba, da k'arfi ta ja motar duk iya k'ok'arinsa na iso ta kafin ta kai k'ofar gidanta abun ya faskara, tana kallonshi ta mirror na motarta ya durk'ushe a k'asa yana kuka. Hawaye taji ya zubo mata a daidai lokacin da tayi parking motarta. "duk son da nake maka ya zama dole in nisanceka ko dan hak'k'in auren da yake kaina, na cuci kaina da na biyewa son zuciya na sab'awa mahaliccina, ya Allah Ka bani ikon cin jarrabawarka duk da na butulce maka, ni mai tarun laifuka ne ya Allah Ka gafarta min" ta fad'i hakan a fili.

Sai da tayi kuka mai isanta sannan ta shiga ciki ta samu mijinta jikinta duk a mace, yana ganinta cikin halin da take ciki hankalinsa ya tashi ya isa inda take yana tambayanta abunda ya sameta. K'arya tayi masa akan labarin da yau aka bayar ne ya bata tausayi, "labari kuma? Wani labari Baby?" Murmushi ta k'ak'alo tace "ai nace maka muna zama da k'awayena every weekend, ka manta?" "Ohh na tuna, baby shine kikayi kuka haka? Kinga idanunki?" Ya janyota kusa dashi ya rungumeta yace "stop crying kina min asarar hawayenki, kanki ma har ciwo yakeyi kiji yanda yakeyi" ya k'arashe maganar yana tab'a kanta fuskarsa na nuna tsantsar damuwa da tausayinta. Abinci ya bata sannan ta sha magani tayi sallahr isha'i suka kwanta. Ta fannin Ibrahim kuwa sai da ya gama kukansa ya tashi ya kakkab'e bujensa ya k'ara gaba cike da tunanin abun yi.

WASHE-GARI 


  Miemiebee @ 7Am 


    Juyi takeyi akan gadonta ita d'aya komai ya cushe mata, tun da ta tashi asuba kasa komawa bacci tayi tunanin rayuwarta da abun yi duk ya addabeta, a dai-dai lokacin da ta samu mai maye gurbin Kamal yanda takeso kuma ace dole sai ta rabu dashi ta zauna sha'awa ya kasheta? Bazata iya irin rayuwar nan ba, ya zatayi kenan in ta buk'aci mijinta baya kusa da ita? Anya zai yu? "Inaa!" Ta furta a fili tana mai tashi daga kan gadon, tsaki ta ja sannan ta d'auko wayarta ta danna wa Ibrahim k'ira.

K'in d'auka yayi har ya yanke sannan yayi mata text kamar haka "Am sorry, bazan iya cigaba da zama da ke ba, Pherty is my happiness kuma kinsa na b'ata mata rai na yaudareta naci amana, don't try calling me again. Goodbye" a dai-dai lokacin da take k'ara k'ira sak'on ya shigo. Hannunta tasa daidai zuciyarta jin bugun ya tsananta, minti uku tayi ba tare da tayi kwakkwarar motsi ba, daga bisani tace "innalillahi wa inna ilaihi raji'un, wallahi bazai yu ba, zanyi komai dan samunka" tana gama fad'an haka ta mik'e ta shiga wanka. Tana fitowa ta shirya a hanzarce bata zarce ko ina ba sai gidan Ibrahim, sai dai knocking na duniyar nan tayi yak'i bud'ewa, kuma ta tabbata ya ganta dan sai da yazo wurin k'ofar da niyar bud'ewa ya koma, duk magiyanta a banza haka ta koma gida idanunta luhu-luhu dan kukan da ta sha.

Gidan Mamu @ 10am


  "Amrah ki fad'a min duk abinda kika sani game da tafiyar Ruffaida tun kafin ki kaini bango in tattake ki" "wallahi Allah ban san komai akai ba, nidai Mommy naji tana maganar da Daddy shekaran jiya akan su ma basu san inda take ba, bayan wannan ba abunda naji Allah Ya Sadiq" numfashi ya sauk'e jin kalamanta da rantsuwar da tayi, kamar zai sake magana kuma ya fasa ya fice ya bar gidan baki d'aya.

Duk abunda ya dace yayi akan b'atan Ruffaida yayi, gidan k'awayenta da ya sani duk yaje har ma wad'an da bai sani ba ya samu k'awarta Aneeluv ta kai sa amma babu wanda yace ya ganta ko sunyi waya bare ya samu hint na inda zata iya zuwa, ya k'ira mutanen Zaria cikin dubara ya tambaya amma bata je can ba, shi ya zaiyi yanzu? Mommy anya na cikin hayyacinta? Taya zata kori 'yar yayarta da ta zame mata uwa ta bata duk wani jin dad'i na rayuwa? Idan da Maman Ruffaida zata dawo da wani ido zata kalleta? Shi dai ya tabbatarwa kansa duk inda Ruffaida taje sai ya nemota kuma ya kawo wa Mommynsa hujja akan neman matan da mijinta kuma ubansa yakeyi, akan meh zai na cutar da mutane yana sane kuma yayi shiru, ya k'are b'oye-b'oyen da yakeyi tunda abun ya dawo kan sistarshi da yake matuk'ar tausayawa.

Lubiee @ 11am


   Kitchen ta shigo dan had'awa 'yarta quaker oats, tun k'arfe tara da ta tashi ta had'a mata tea ta bata da bread tak'i sha, ita sai quaker oats takeso, sai da taga ta sa mata kuka sannan ta fito dan had'a mata dan bata dashi a d'akinta, duk inda tasan ana ajiye kayan tea ta duba babu komai bare ta sa ran ganin quaker oats, ta tabbata Nafee ne da aikin nan, wato bata son tayi anfani dashi shine taje ta b'oye kada ta gani bare ya jawo fad'a. Ranta in yayi dubu yakai k'ololuwar b'acin rai. Kukan 'yarta da taji tana tunkaro ta ne ya k'ara dagula mata lissafi, ya zatayi da ita yanzu bayan babu abunda takeso, dole sai ta fita kenan? Jin yarinyar ta iso inda take yasa ta d'auke ta tace "kinga babu quaker oats ya k'are" ta bud'e mata inda ake ajiyewa ta tabbatar babu, da yake yarinyar mai hak'uri ce sai bata yi gardama ba, fuskarta dai ya nuna bata ji dad'in abun nan ba.

Ganin haka yasa Lubiee hankalinta ya kwanta a ranta kuma tana cewa zata sayo mata anjima in ta fita dan taga alamar tayi kewar abun sosai, hanyar fita daga kitchen d'in tayi suka had'u da Nafee rik'e da gwangwanin quaker oats, da gangan tayi hakan dan fuskarta d'auke yake da murmushi, ai Kausar na gani ta kalli mamanta tana nuna mata tare da fad'in "momma" tana mai tura baki. Bata saurareta ba suka fice daga kitchen d'in ai kuwa ta saki kuka tana cewa sai an bata, babu yanda ta iya dole ta d'auki mayafi ta sa mata takalmanta suka fita shago sannan ta samu sa'ida.

Tsakaninta da mijinta kuma komai ya canja, ko ganinsa ta daina yi bare yayi satan kwanan da ya saba, abun ya dameta matuk'a amma ta bari a ranta har ranar da k'awayenta zasu bata shawarar abun yi, samun 'yarta kusa da ita shine kad'ai farin cikinta a wannan gidan, yanzu da komai ya gama kwab'ewa hatta abunda zata ci a cikinta ita da 'yar ta Nafee ta toshe duk hanyar da zata samu ko ina ma take b'oyewa oho. A d'akinta take dafa abunda zata ci ita da 'yarta wanda komai da kud'inta take saya babu ko kobon Abubakar a ciki, dad'inta d'aya Nafee bata shiga harkarta yanzu kamar da, shiyasa take ganin matsalar nata mai sauk'i ne zata iya gyarawa da izinin Allah.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


        35


Ummu Abdoul/Ruffaida @11am


    Abincin da Feedoh ta kawo musu suke ci ahankali suna d'an tab'a hira, yawancin maganar Ummu Abdoul ke yi Ruffaida daga umm, sai um-um ko murmushi. Kallonta Ummu Abdoul tayi tace "wai ke bazaki saki ranki kiyi abunda ya dace ba? A hakan kike tunanin zamu iya fighting duk wani matsalar da ta tunkaro mu? Istigfari nace kina yi bance ki d'auke walwalarki ba, komai zai dawo yanda yake insha Allah, dan wani abu ya samu bawa bai zama k'arshen duniyar kenan ba, ki hana kanki sak'at ki takura kanki da tunani, duk kinyi bak'i kin rame".

   Murmushi Ruffaida tayi ba tare da ta kalleta ba tace "meh zan sake yi a duniyar nan inji dad'i? Ai na b'ata rayuwata har abada" hawayen da ya taru idanunta ne suka sauk'o ta goge, ta kalli Ummu Abdoul da ta sake baki tana kallonta, "kiyi hak'uri bazan iya daina zubar da hawaye ba muddin ina cikin rayuwa irin wannan, hakan kuma na nufin har in mutu bazan daina ba dan babu ranar da zan fita daga k'uncin rayuwa" sosai a wannan lokacin ta fara kuka harda shesshek'a, hak'uri take bata amma kamar k'ara zigata take yi ta cigaba da kukan.

   K'arar wayan Ummu Abdoul ne yasa ta tsagaita dan kada ta hanata d'auka wayar, sai da ya kusa yankewa ta d'auka ta kara a kunnenta tayi shiru ba tare da tace uffan ba, sakanni goma da d'aukan wayar taji ance "salamu alaikum" cikin sanyin murya, baki ta saki tana mai mamakin jin sallama daga wannan numban, layin da ake ta k'iranta ana mata shiru yau harda sallama, bata amsa ba ya sake cewa "bak'ya jina ne?" "Ohh, wa alaikas salam, ina wuni?" Ta fad'i muryarta na rawa.

  Murmushi yayi sannan yace "da alamu kina mamakin k'iran da nayi miki, ohh ba k'iran ba dan na saba, sallamar da na miki ko?" Bata amsa ba tace "please waye ne?" Ajiyar zuciya ya sauk'e sannan yace "Abduljalil Umar, baki sanni ba but ni na sanki kuma inason zama frnd naki if u don't mind".

"Am sorry but..." "No banda you're sorry, i want to be your friend kuma kin amince das final, ai ya kamata shiruna ya baki hints na irin tsoron tunkararki da nayi, sati nawa ina k'iranki in kasa magana kuma yau sai kice min no? Kinsan amsar da zaki bani nake tsoro dama shiyasa nake kasa miki magana idan na k'iraki?". Murmushi tayi sannan tace " yi hak'uri malam Abdulja..."

  katseta ya sake yi da cewa "please kada ki fad'a Allah bazan iya ji ba zuciyata zata buga" dariya sosai ya bata dan yanda yayi maganar kamar ya tsoratan da gaske, jin tayi dariya shima ya dara yace "yauwa ko ke fa, we are now friends, zan iya k'iranki ko da yaushe kuma zaki d'auka ko? You will know more about me in kina d'aukan wayana, fatana in samu damar magana da da Malama Safiyya". 

  Sai da sukayi mintuna biyar suna magana sannan ya katse wayar bayan ta tabbatar mishi zata d'auki wayarsa duk lokacin da ya k'ira. Kallon Ruffaida tayi taga tana kwance gefe idanunta a lumshe da alama ta gama kukan nata, sai da ta tashi ta d'auki plate d'in zata fita sannan tace " kina karatun Qur'ani kuwa? Yakamata ki fara dan ki samu nutsuwa" "toh, nagode" kawai tace ta mik'e dan d'auko Qur'anin da ta gani a d'akin.

Cubana @6pm:- 


    "Wannan ai wulak'anci ne, ya za'a yi ta san yau ita kad'ai zata bamu nata labarin kuma tak'i zuwa, ta kashe wayanta ma dan rainin wayo, k'arfe shida yanzu kam kunsan ba zuwa zata yi ba" cewar Pherty cike da masifa, Ummu Abdoul tace "haba Pherty, kiyi mata uzuri, kinsan meh ya tsareta bata fito ba?" "Babu komai" ta amsa kai tsaye sannan ta cigaba "baku san yarinyar nan bane, ni ai na santa shiyasa nayi magana" Batool tace "ina kika santa? Tunda kinsan labarinta ki bamu kawai abun da sauk'i ma kenan" Benaxir tace "no, yanzu abu d'aya za'ayi in an tashi daga nan zanje gidan ta in dubata ko lafiya".

"Mtsw! Da nasan abunda zai faru kenan da ban wahalar da Alhaji ya kawo ni ba" Lubiee ta kalli Pherty tace "wai yau meh matsalarki ne? Sai masifa kikeyi a banza ko addu'a da fatan Allah yasa lafiya bakiyi ba sai kumfar baki" Pherty tayi murmushin takaici sannan tace "ku nemo ta tukunna, in ta fad'a muku reason d'inta na k'in zuwa yau wallahi bazanyi kaffara ba duk abunda tace inyi mata zanyi, idan kuma tak'i fad'a ku yadda ina da gaskiya, bata son bada labarinta ne kawai".  

  Yau dai haka suka gama zamansu babu Miemiebee, ko wacce da abunda yake ranta game da k'in zuwanta suka watse. Benaxir har gidan Miemiebee taje kafin ta wuce gida, sai da aka tabbatar mata bata nan babu kowa a gidan sun fita sannan ta tafi nata gidan tana tunanin inda matsalar take, shin da gaske bata son bada nata labarin ne ko kuwa akwai wani abu a k'asa tsakanin Pherty da Miemiebee?

Miemiebee:-


    Kwance take akan gadonta yau kwana uku kenan tana gudun k'awayenta da kullum sai d'aya daga cikinsu yayi trying layinta a kashe, bacci takeyi amma kana ganinta zaka gane ta fad'a saboda damuwar da ta d'aurawa kanta ga kuma rashin mijinta kusa da ita, ita a yanzu ta fara saduda da bibiyan Ibrahim dan gwaleta da yake yi yayi yawa, har yau bai bata damar ganinsa ba bare tasan yanda zata dawo dashi gareta, sabon layin da ta saya ma ya gane nata ne ya daina d'auka, text sunfi hamsin ta aika masa amma ko reply baiyi ba bare ya nuna ya tausaya mata.

  Cikin baccin taji k'amshin turarensa ya ziyarci hancinta, bud'e idonta tayi a hankali dan tabbatar da hasashenta, tashi tayi ta isa inda yake da gudu ta rungumesa ta saki kuka mai tab'a zuciya. A kid'ime yayi hugging d'inta sosai yana tambayanta meh ke damunta, jin bata tsayar da kukan ba ya d'auketa ya isa da ita bakin gadon, zama yayi ya ajiyeta bisa cinyarsa yana k'are mata kallo, bata daina kukan ba kuma bata sake shi ba sai ma k'ara k'ank'ameshi da tayi hawayenta na zuba a jikinsa.

"Please Mieminah ki daina kina tsoratani in kina kukan nan, duk kin rud'ani tun ina can ina ta k'iranki bana samunki, baki da lafiya ne?" Ya tambaya, kad'a kai tayi alamar a'a, ya sake cewa "meh ya faru toh? Wani ne ya rasu?" D'ago kanta tayi ta kallesa ta share hawayenta ta turo baki, bata kai ga yi masa magana ba ya sake tambayarta "abunki ne ya b'ata? Ko wani abu kikeso?" Duk a rud'e yake mata tambayoyin, kallonsa tayi tace "duk kai ne Kamal, ni gaskiya bazaka sake tafiya ka barni ba" ta k'arashe maganar tana mai k'ara rik'eshi gam hawaye na sulalo mata.

  Sai a sannan ya sauk'e ajiyar zuciya "yanzu missing d'ina ne ya sa kika zabge haka? Kika kashe min waya bayan kinsan zan k'iraki? Haba swthrt duk kin bi kin rud'a ni" "nidai bazaka sake tafiya ba gaskiya" tace tana mai ajiye kanta saman kafad'arsa. Shi da ya dace ayi tattalinsa dan ya dawo daga tafiya shi aka bari da wannan aikin, shagwab'e masa tayi kamar bata da lafiya shi kuwa yana biye mata.

Washe gari manne suka tashi kamar kada ya tashi, har cikin ransa yasan Miemie tayi missing d'insa fiye da yanda yake zato, ba kaman last dawowansa da bata wani tarairayesa ta bashi kulawa ba, soyayya ya zuba mata iya wanda zai iya ita ma ta baje masa nata kalar soyayyar, farinciki da k'aunar da yake tsakaninsu ya dawo fil kamar sabbin ma'aurata.

  Kwance take a jikinsa taji k'arar text a wayanta, kamar kada ta tashi sai dai wani zuciyar yace ta duba dan sabon layi ne babu wanda ya sani, tana dubawa kuwa taga sak'o daga Ibrahim, da hanzari ta bud'e ba tare da ta tuna Kamal d'inta na kusa da ita ba, murmushi ne ya sub'uce mata har sai da Kamal ya tsaya kallonta da mamaki, "Miemie" ya k'ira sunanta, bata daina murmushin ba ta kallesa, girarsa ya d'aga mata alamar menene? Tace "friend d'ina zanje in samu yanzu dole dan karb'an kayanta, mantawa nayi gaba d'aya da na ganka kusa dani" mik'ewa tayi ta ajiye wayar a wardrobe nata sannan ta fad'a ban d'aki, girgiza kai yayi ya gyara kwanciyarsa tare da janyo wayarsa.

   A gurguje tayi shirinta cikin doguwar rigarta na atamfa, bata tsaya kwalliya ba dan lattin da tayi kamar yanda tace masa. Har motarta ya rakata yayi mata peck a goshi sannan ta shiga motarta ta fice daga gidan yana d'aga mata hannu murmushi fal fuskarsa. Ajiyar zuciya tayi tana hawa kan titin da zai kaita gidan Ibrahim nata da ya gayyaceta, tayi matuk'ar mamakin ganin sak'onsa a daidai wannan lokaci, murna ta shiga yi har ta isa gidan tana ji kamar bazata kai ga Ibrahim nata da tayi matuk'ar missing d'insa ba.

Bai sha wahalar shawo kanta ba dan missing d'insa da tayi, kuma a wani b'angaren tayi mamakin zak'ewarsa a yau, daga k'arshe dai ta d'auki abun matsayin missing d'inta da yayi kwana biyu, sai dai meh? Bai kai ga cimma burinsa ba suka ji tafi ta samansu, a firgice ya janye daga jikinta daga shi sai boxers, janyo mayafin gadon tayi ta rufe jikinta tana mai kai dubanta inda take jin tafi.

Pherty ta gani tsaye murmushi fal fuskarta, bata kai ga yin magana ba taga Ibrahim ya tashi ya isa wurinta yana cewa "na miki abunda kikeso, na wanke kaina?" Cike da mamaki Miemiebee ke kallonsu, Pherty bata amsa ba ta isa jikin windown d'akin ta ciro camerar da ta mak'ala dan d'aukansu. Miemiebee bata gane manufar Pherty ba sai da tace "Mr. Kamal zai sha kallo" ta fad'i hakan tana juya k'aramar cameran dan Miemie ta gani da kyau.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


Page 36


Kallonta Pherty tayi tana mai k'ura mata ido, duk da mamaki ya cika ta ganin fuskarta bai nuna alamar tsoro ko firgici ba sai ma murmushin da ke d'auke bisa fuskarta bai sa zuciyar Pherty rauni ba. Ibrahim tsayawa yayi yana kallonta cike da mamaki, "wato hakan bai ma dameta ba" tambayar da yake yiwa kansa kenan. Bai samu amsarshi ba yaga ta janyo rigarta ta saka sannan ta mik'e ta iso wurin Pherty, daf da ita ta tsaya fuskarta har a lokacin d'auke da murmushi zuciyarta wasai bata fargaban komai. Zuciyar Pherty bai gama tsinkewa ba sai da taji muryar Miemiebee tana cewa "zina min zip d'ina" ta juya mata baya.

Sai da ta d'auki sakanni tana mamakin k'arfin hali irin nata daga bisani ta zina mata zip d'in ya rufu. Juyowa tayi tana mai kallonta cikin ido sannan tace "Haba Pherty, dan na k'wace miki Ibrahim kuma sai ya mayar dake yarinya k'arama maras anfani da kwakwalwa?" Dariya ta saki wanda yake nuni da tsantsar ganin wautan Pherty, kallon camerar tayi sannan ta d'aga kai ta kalleta "toh da kika d'auka kina cewa Kamal zai sha kallo kin ko san waye Kamal? Let me tell you little about Kamal Zailani".

Juyawa tayi ta isa kan gadon ta fara tattare abubuwan ta da yake kai tana sawa a jaka tana cewa "Kamal bayi da lokacin nonsense irin wannan, yafi k'arfin kula irinki bare har ya saurareki yaji k'azamtacciyar zance irin wannan" jakan hannunta ta zuge ta rufe sannan ta iso inda Pherty take "kiyi iya yawonki Pherty, kiyi iya shagalinki, tsohon nan dai shine sa'anki ba Kamal d'ina ba, my only hero, duk iya yawon duniyanki ko ganinsa baza ki iya yi ba bare har ki bashi banzar abunda kika d'auka. Na baki daga yanzu har shekaru biyu ki nemo Kamal d'ina, ina mai tabbatar miki sun miki kad'an, kuma by then" tayi rolling eyes d'inta sannan tace "na gama da ke da banzan Ibrahim naki" tana isowa nan a zancenta tayi hanyar waje zuciyarta fes.

Fashewar da Pherty tayi da dariya yasa ta cikin rud'ani, cak ta tsaya a bakin k'ofar tana tunanin abunda yasa Pherty dariya, takun tafiyar Pherty da taji kusa da ita yasa ta gane ta iso bayanta, bata samu courage na juyawa ba sai ma runtse idonta da tayi zuciyarta na tsananin bugawa, cikin kunnuwanta taji muryar Kamal yana cewa "Hello" a tsorace ta waigo idanunta ya dira kan wayar Pherty da yake hannunta ta sashi a handsfree, sunan Kamal ta gani rubuce an k'irasa kuma ga numbansa an nuna a rubuce ta k'asa, bugun zuciyarta bai gama tsananta ba sai da taji Pherty na cewa "ina gaisuwa, k'awar matarka ce ke magana, akwai muhimmin maganar da nakeso mu..." Warce wayar Miemiebee tayi had'e da katse k'iran, k'ok'arin shiga contact takeyi dan goge layin taji Pherty na cewa ko contacts na wayana zaki goge dukka ina da layin Kamal, kada ki d'aukeni mara hankali maras wayo mana Miemie, ki nutsu ki saurareni tun kafin abu ya kwab'e miki".

Cak ta tsaya kallonta fuskarta na nuna tsantsar tsoro da firgicin da ta shiga, tambayan kanta takeyi ya akayi ta samu layin Kamal? Pherty kamar taji tace "kina mamakin yanda na samu numban ko?" Murmushi tayi ta cigaba da cewa "yanda kika samu layin Ibrahim ta nan na samu numban mijinki, abunda asali yake ranki game da Ibrahim d'ina haka yake raina akan Kamal naki, nayi matuk'ar mamakin ganinki da Ibrahim bayan mijinki ta kowani fanni ya had'u, ki godewa Allah mana Miemie".

K'arfin zuciya tayi tace " ke meh yasa baki godewa Allah kin rik'e mijinki ba kike huld'a da wasu a waje?" Pherty fuskarta fes tace "mijina ba irin naki bane, mijina tsoho ne, kuma mijina ba d'an gayu bane ko yayi bazai karb'esa ba saboda girman da yake tare dashi, bayan haka jahilci da son zuciya ya sake tasiri cikin zuciyata, da ni nake muhallinki wallahi ba abunda zai sa in kalli wani namiji bare har in nemi tarayya dashi, mijinki yaro maji k'arfi, kyakkyawa ga kud'i, meh ya wuce hakan a rayuwar 'ya mace, neman 'ya'ya kad'ai ya rage miki" zama tayi a gefen gadon tana cewa "ba wannan yasa na nemi ki nutsu ba, kinga wannan?" Ta d'aga mata camerar tana nuna mata "kina yi min abunda na saki zan baki kiyi yanda kikeso dashi, na baki daga yau zuwa gobe kiyi tunani" tana k'arasa maganar da ke d'auke a bakinta ta tashi ta isa wardrobe na Ibrahim ta ciro jakarta ta fice daga d'akin, sai da ta iso palon ta k'ira sunansa ta k'ara da cewa "ka sameni yanzu a waje" sannan ta fice.

Ficewa Ibrahim yayi ya barta a d'akin jiki ba laka, ina ma ta mutu hankalinta yafi kwanciya da wannan rana irin ta yau, meh Pherty ke so daga wurinta? Shin zata iya mata ko kuwa yafi k'arfinta? Amma Ibrahim ya cuceta ya gama da ita, dama plan ne da ya nemi zuwanta inda yake har da cewa yayi missing d'inta? "Allah ya isa" ta furta a fili kuka mai sauti na kufce mata, tsugunawa tayi a inda take tana kuka mai cin rai, jin zuciyarta take kamar an d'aura mata dutsi haka takeji, sai da tayi kuka mai isanta sannan ta fice daga gidan ko a harabar bata had'u dasu ba kuma bata damu da inda suka je ba.

Katsina:- Abba @ 12pm


Zaune yake a office nasa hankalinsa na can duniyar tunani, tun jiya da Ayshartone k'awar Kdeey ta k'irasa tana fad'a masa abubuwan da Kdeey ta had'a kuma ta fad'a masa game da Safiyya k'arya ne ya rasa sukuni, babu abunda yafi d'aga masa hankali irin cewar da tayi "duk yanda Abba yayi wallahi bazan tab'a gaya masa gaskiya bare ya dawo da matarsa ba, bak'in cikin da naji akansa shima ya d'and'ana rad'ad'in soyayya" wai dama Kdeey sonshi takeyi shine ta raba shi da matarsa uwar d'ansa? Wani irin zuciya ne da ita kuma wannan wani irin so ne? Hawaye yaji yana sauk'a masa bisa kuncinsa, da hanzari ya goge ya mik'e ya d'auki abunda zai iya d'auka ya wuce gida.

Da gudu d'ansa mai suna Irfaan yazo wurinsa yana yi masa oyoyo, sama ya d'aga sa yana yi masa dariya tare da juyasa, Irfaan d'in ma dariya yake sosai yana mai jin dad'in ganin babansa. Sai da suka shiga sannan ya ajiyesa ya isa wurin mamansa ya zauna a gefenta ya gaisheta, hira suka d'an yi sama-sama sannan ya kawo mata zancen Safiyya mahaifiyar Irfaan, bai b'oye mata komai daga zancen da k'awar Kdeey ta fad'a masa ba dan neman shawarar mahaifiyarsa.

Sosai ta fahimcesa kuma ta nusar dashi kuskuren da yayi a baya na yanke hukunci ba tare da bincike ko neman ba'asi ba, daga bisani tace "Safiyya yarinya ce da kowa zai so had'a zuri'a da ita, kuma ko da yaushe kace zaka dawo da ita d'akinta ba abu ne da za'a k'i ba, fatana Allah ya zab'ar muku mafi alkhairi, kuma a son ra'ayina ka dawo da ita ko dan d'an da yake tsakaninku bare nasan akwai k'auna, ka dai yi shawara sannan kasan abun yi".

Bai bar wurinta ba sai da ta yi masa nasiha mai shiga jiki sannan ya mik'e ya isa d'akinsa, tun kafin ya bar inda mahaifiyarsa take ya riga ya gama deciding game da abunda ya dace yayi, fargabansa d'aya, shin Safiyya zata yadda ta dawo garesa? Wani tunani ne yazo masa na tsantsar k'aunar da yasan take masa, nan kuwa murmushi ya maye fuskarsa ya janyo wayarsa dan tsarawa gimbiyar tasa text ko Allah zai sa ya samu karb'uwa.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


Page 37


Tana zaune tare da Hajiya taji k'arar text a wayanta, tun kafin ta d'auka idonta ya gane numban da ke manne jikin screen na wayar, ko a mafarki taga wannan numban bazata tab'a mance shi ba, cikin tsinkar zuciya ta d'auka dan ganin abunda text d'in ya k'unsa "Safiyya, we need to talk, kuma maganar da nakeson muyi ba maganar waya bane, zan iya zuwa gobe Abuja dan mu tattauna?" Tsinkar zuciyarta ya tsananta jin abunda text d'in ya k'unsa, meh zata ce masa? Bata tsayar da tunaninta ba wani text ya k'ara shigo mata, kasancewar bata fita daga text na Abba ba yasa tace 'yan ntwrk ne, sai dai tana yin back taga Abduljalil rubuce, murmushi tayi sannan ta duba ta karanta tayi masa reply da "sai kazo, ina jiranka".

Cikin nutsuwa ta kalli Hajiya tace "emm hajiya yanzu Baban Irfaan yayi min text wai yana son magana dani, kuma bata waya ba yana son zuwa nan Abuja, in bashi dama ko kuwa? Ni fah banison matsala" ta k'arashe maganar fuskarta na nuna alamar gajiya da matsalar rayuwa. Hajiya cikin nutsuwa tace mata in bata son zuwanshi ba sai yazo ba, amma mafi kyau ta saurari da meh yazo, wata k'ila magana ce mai anfani yazo mata dashi, bata bar wurinta ba sai da suka tsayar da maganar cewa suyi ko wani irin magana ne a waya ba sai yazo inda suke ba, tunda shi tun farko bai nemi mutunci da zumunci bayan an rabu ba sai ma kyama da hantara, su ma yanzu basu buk'atar duk wani zance da zai fito daga garesa.

A ranar Abduljalil ya zo wurinta dan gabatar mata da kansa kamar yanda yayi mata alk'awari, shekarunsa bazasu wuce talatin da uku ba, ta kowani fanni ya had'u kuma da alamu yana neman zama fiye da aboki wurin Ummu Abdoul dan zancensa da kuma irin kallon da yake binta dashi ya nuna hakan. Bai tafi ba sai da ya gaisa da Hajiya da sauran mutanen gidan cikin mutunci sai dai bai samu ganin Feedoh ba duk da yaso ganinta dan yakan ji muryarta kullum in ya k'ira Ummu Abdoul. Surutacce ne shiyasa ya samu kanta sukayi hira sosai har da dariya.

Miemie washe-gari @ 10am


Kwance take tana karkarwar sanyi dan zazzab'in da takeji, Kamal na zaune a gefenta yana kallonta cike da tausayawa, can yace "Swthrt kink'i muje asibiti, tun jiya daga zanje karb'an kayan frnd d'ina shikenan na rasa gane kanki har yau, ga zazzab'i da ciwon kai, kuma idanunkin nan kuka kikayi am very sure. Tell me meh yake damunki?" "Babu" kad'ai ta iya cewa bakinta na rawar sanyi, wani k'aton bargon ya sake d'aukowa daga cikin wardrobe ya shimfid'a mata a jikinta, kanta kad'ai ya bari a bud'e ya sake zama gefenta, "ni fa mijinki ne Kamal, kin manta alk'awuran da muka d'aukarwa juna tun kafin muyi aure? We wil b together forever, we will fight for each oda, nd duk wani abunda zai sami d'aya daga cikinmu we wel b dia to calm each oda, meh yasa kike canja abun yanzu bayan yanzu ne ya dace shak'uwarmu da soyayyarmu ta k'aru" bai k'arashe maganar da ke bakinsa ba ya sake murmushi da d'an k'ara yace "Oh my God, baby ar u pregnant? Shine kike zazzab'i ko? Bakya son in sani?" Ya kwab'e fuska yana kallonta.

Hannunta ta ciro daga bargon ta rik'e nasa hannun tana kad'a masa kai, cikin sanyin murya tace "promise me bazaka tab'a barina ba duk abunda zai faru" da mamaki yake kallonta ya kasa amsa mata, sai da ta sake magana yace "dama kina tunanin zan iya barinki? Kina tunanin zan iya barin wacce take sona fiye da yanda nakeson kaina? Zan iya barin wacce take kula dani take kare min hak'k'ina? Meh yasa zaki ce in miki alk'awari bayan kinsa auren zobe mukayi" numfashi ya sauk'e ya k'ara damk'e hannunta ya matso da fuskarsa dai-dai nata yace "I love you Miemie, i promise to love you and be with you for ever, duk laifin da kika min da wanda zaki min bazai sa in rabu dake ba, Miemienah na da ilimi both addini da na boko, muddin baki kauce hanya ba duk laifin da zaki min mai sauk'i ne Miemie..." "What if na kauce hanyan? Zaka barni kenan?" Ta katse shi.

Kallonta ya tsaya yi da mamaki, kad'a kanta tayi akamar ya amsa ta sannan yace "Miemie zanyi k'ok'arin sa ki a hanya, bare meh zai sa ki kauce bayan kina da sani? Kin sani cikin rud'ani, meh ke faruwa? Akwai abunda kikayi ne? Tell me, please kada kiji tsoron gaya min" cike da damuwa yake maganat idanunsa na bisa fuskarta dan ganin yanda zatayi, murmushin da tayi ya kwantar masa da hankali kuma kalamanta suka sake cire masa zargi da fargaban da ya shiga "Babyn Miemie ina sonka sosai, shiyasa nake maka irin tambayoyin nan dan in tabbatar da soyayyar da kake min na nan ko ya ragu" murmushi yayi, kafin ya kai ga magana wayarta ta d'au k'ara, hannunsa ya mik'a ya d'auko wayar ya duba sunan, "Pherty" yace sannan ya mik'a mata bayan ya danna ya d'auka mata.

Ajiye wayar tayi a kunnenta dak'yar ta iya furta "hello" saboda tsinkar da zuciyarta ya shiga yi, daga can b'angaren cikin kwanciyar hankali Pherty tace "Matar Kamal barka da warhaka" bata jira ta amsa ba ta cigaba "make sure kinzo Cubana ranar Saturday dan muji kalar taki badak'alar sannan insan wani abu ya dace in baki kiyi min dan ki samu abunda nayi miki alk'awari" "toh zanzo" kawai ta iya cewa Pherty ta katse wayar. Kamal bai damu da tambayarta game da wayan da tayi ba sai ma wani hirar daban da ya shiga yi mata.

Cubana ranar Asabar


Kowa ya samu Miemiebee zaune tana zaman jira, hakan yasa suka yi mata uzurin rashin zuwa satin da ya gabata, babu wanda ya tada maganar bare su tambayi ba'asin rashin zuwanta. Sai da duk suka hallara sannan ta gyara zamanta ta kurb'i ruwan swan d'in da ke gabanta da jik'a mak'oshi sannan ta fara da cewa "ina neman afuwarku ban samu damar zuwa ba last week saboda wasu dalilai, yau dai tawa badak'alar zaku ji sai dai ina neman ku min afuwa kuma ku fahimceni, duk da ba lallai ne ku fahimci abunda nakeson sanar daku ba".

Numfashi ta sauk'e sannan ta cigaba da cewa "Sunana Maryam amma anfi sani na da Miemiebee, ni 'yar Yola ce kuma cikakkiyar bafulatana. Labarina daban yake da irin naku labaran, dan nawa zan iya cewa labarin son zuciya ne da kuma tsantsar rashin hankali. Na taso cikin jin dad'in rayuwa, kuma na kasance 'ya ta farko a wurin iyayena, muna da rufin asiri tare da wadatar zuci, haka zalika mahaifina malami ne shiyasa ni da k'annena muka taso cikin tsantsar karatun addini da wadatacciyar tarbiyya.

Tun ina aji uku wato Jss 3 na fad'a kogin soyayya duk da kasancewar wanda nakeso bai san ina yi ba, sai dai kuma abu d'aya da na sani shine wannan masoyin nawa da na lak'aba mishi my mr. right ya kasance abokina kuma yayana, dan mahaifinsa da mahafiyata mamansu d'aya babansu d'aya, ma'ana shi cousin d'ina ne. Na shak'u dashi sosai kuma ya nuna min k'auna da soyayya yana kulawa dani, hakan yasa naji ina sonsa kuma inason in kasance matarsa dan kulawar da yake bani yana matuk'ar min dad'i.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


      Page 38


   A lokacin da yazo hutun makarantarsa ina ss2, tun ana saura sati d'aya zai dawo na fara nunawa kowa irin zumud'in da nakeyi, ko meh na samu sai nace zan ajiye Yayana zai dawo, hatta kayan kwalliya ajiyesu nakeyi sai ranar da zai dawo in cab'a ado, nayi lalle ja da bak'i kuma naje saloon, ko mijina ne zai dawo iya shirin da zanyi masa kenan, mamana har tsokanana takeyi amma in nok'e ince ai nayi kewarsa ne. Ranar da aka ce yau zai iso ba k'aramin murna nayi ba, nayi kwalliya nasa sabon kayana tare da yin d'auri, ni kaina nasan nayi kyau kuma zan burge shi.

  Ba a gidanmu zai sauk'a ba amma da yake anguwanmu d'aya ne tun da naji anje d'aukansu na kwaso basket d'in da na shirya masa abincin da nayi na wuce gidansu. Basu iso ba har awa d'aya da 'yan mintuna, har na fara jin haushi dan lokacin zafi ne zufa ya fara b'ata min powderna kuma turaren da na fesa ya fara tafiya. K'anwarsa da muke ce mata Biebie ce ta taimakeni da powder da turare na feshe jikina na gyara fuskata a daidai lokacin da aka wangale musu k'ofa. 

A guje na fita bayan na wullar da powdern ya fad'i ya tarwatse, ban tsaya ko ina ba sai da na jini jikinsa, oyoyo nayi masa, farincikin ganinsa ya kasa b'oyuwa a fuskata. Sauran k'annen nasa suka mara min baya muka rungumesa dukkanmu, dak'yar ya iya b'anb'aremu shima yana sake mana murmushi. Mamanshi da muke cewa Maman Haneep ta janyo ni tana dariyar wautata, sai da mukayi gefe sannan tace "haba Miemie, baki san kin girma bane da zaki je ki ruk'unk'umesa haka" b'ata fuska nayi sannan nace "ai yayana ne, kuma nayi missing d'insa shekaru biyu fa Maman haneep".

Murmushi tayi ta rik'e hannuna muka shiga ciki tana sanar dani aure zai iya shiga tsakaninmu, dan haka in daina shiga jikinsa dan shi ba muharramina bane, sosai maganganunta suka shigeni duk da ni nayi ne dan in burgesa kuma in nuna masa tsantsar farin cikin ganinsa da nayi, nayi na'am da zancenta kuma na karb'i laifina sai dai ban bar wurinta ba sai da na fad'a mata ni sonshi nakeyi kuma ai zata barni in aureshi, bata yi magana ba sai ma dariyar da tayi tana mai kad'a kai a ganinta yarinta ke damuna nan gaba zanji bana ra'ayin hakan.

Ta b'angarenshi kuma sosai ya sake min bai canja min ba, sai ma wani kallo da naga yana yi min wanda na tabbata shima ya kamu da sona, lokacin da na kawo masa abincina zama nayi a gefensa ina cewa "yaya Kamal nikam abincina zaka fara ci dan tun safe na shiga kitchen ina had'a maka". "Aww! Naji dad'ina, ashe Mieminah tayi hankali ta girma, har kwalliya kika koya" fuska na kwab'e jin duk 'yan palon suna min dariya, can k'asa yace min "kinyi kyau" ta yanda babu wanda zai ji yayi maganar dan sak'on nawa ne ni kad'ai.

Kallon sa nayi nace masa "thank you" sannan na zuba masa abincin da nayi masa. Sai da yaci abincin damm yayi gyatsa sannan ya ture plate d'in yana cewa "Alhamdulillah, ashe dai kin iya girki, ko ince harda girki kika koya" Haneep ya cafe da cewa "ai ta iya abinci, idan tayi abinci a gidan Mama Fiddausi ba'a ragewa, shiyasa kullum da rana nake zuwa a weekend dan in ci abincinta". Hirar girkin 'ya'yan nasu suka fara, a yabi wannan ya iya girkin fanni kaza a kushe wanda bai iya ba sannan shima a fad'i b'angaren da ya iya.

Tun daga ranar kullum a gidan nake wuni dan muna hutu. Sosai nake sakewa dashi muyi hira da dariya, har d'akinsa nake shiga in tayasa hira ko gyaran kayansa sai in ko MamanHaneep ce ta korani. Irin kallon da yake bina dashi da irin maganganun da yake min yasa na sake fad'awa kogin sonsa da son kasancewa dashi, yana son yin wanka ma'ana yasa kaya masu kyau gogaggu masu tsafta, duk kalan kayan da yasa yana masa kyau haka zalika yana fitowa kamar d'an sarki in yayi wanka yasa kaya ko da kuwa k'ananan kaya ne.

   Ranar wata jumma'a bazan manta ba da yamma naje gidan, babu kowa sai shi kad'ai Maman Haneep kuma na bacci dan bata jin dad'i. D'akinsa ya nemi muje in tayasa gyaran kayansa da aka goge masa d'azu, mun fara gyaran kenan wayata ta fara ringing, shi ya d'auka ya duba meh k'iran sannan ya mik'a min na d'auka. Murya na nok'e can k'asa ina cewa "i will call you later sannan na katse" ina d'aga idona muka had'a ido na kawar da nawa cikin i'ina nace zanje in sha ruwa in dawo, ni ce ban dawo ba na tsaya d'akin MamanHaneep har muka yi sallahr maghrib sannan nayi mata sallama na fito.

  A harabar gidan muka had'u yana zaman jirana, d'auke kai nayi na bi gefe kamar ban gansa ba. Ji nayi ya kamo hannuna ba tare da ya min magana ba. Bai tsaya ko ina ba sai k'ofar gidanmu yana huci kamar wani abun kirki akayi masa. Cikin kakkausar murya yace "Miemie wa kike dating?" Kallonsa nayi dan banyi tsammanin tambayan nan daga wurinsa ba, jin nayi shiru ya sake damk'an hannuna ya ja ni zuwa wani lungun da ke gefen gidanmu.

 Tsoronshi naji ya sauk'o min lokaci d'aya ganin ya kaini wannan wuri kuma wuri mai duhu, tsinkar zuciya na ya sake tsananta dan bansan meh Kamal ke nufi ba bare insan meh yake shirin yi? Daf dani ya tsaya dan ina jin sauk'ar numfashinsa a fuskata. Sauk'ar da kaina nayi dan kallon da yake min yana sa tsigar jikina tashi, hannunsa yayi anfani da wurin d'ago fuskata yace "don't tell me kin fara soyayya da wani? Kada ki sa inyi da na sanin barinki na tafi skul bayan ban fad'a miki abunda ke raina game da ke ba" idanuna na d'aura a nasa dan gano manufarsa, sauyin idanunsa zuwa ja da na gani ne ya k'ara tsinkar min da zuciya na sauk'e kaina. 

Kamar daga sama naji yace "I Love you Miemie, in ma akwai wanda kike tare dashi gwanda kin rabu dashi tun wuri dan ke tawa ce, kuma tawa ni kad'ai" kallonshi na tsaya yi baki bud'e na kasa tabbatar da maganar da yake fad'a min, idanuna ko kiftawa na kasa yi, shima kallona ya tsaya yi ganin irin kallon da nake binsa dashi.

Iska ya hura min nayi firgigit na dawo daga duniyar tunanin da na fad'a hannayensa ya d'aura a jikin ginin yana mai sani a tsakiya game da k'ara matsowa kusa dani, zan iya cewa kayansa da nawa na gogar juna, zuciyata kamar zai fito na runtse idanuna ina cewa "am sorry Ya Kamal". Bai kai ga yin magana ba aka hasko mu da fitilar mota, kare hasken mukayi da tafin hannunmu dan hasken yayi mana yawa, rage hasken akayi sannan naji muryar Baba yana cewa "meh kukeyi anan? Kamal kai ne? Rashin hankali ka koyo a can kenan kuma ka rasa da wa zakayi sai k'anwarka" ya ja tsaki ya karya kan motarsa ya shige gida bayan ya umarce mu da mu same shi a parlor.

Fad'in rud'anin da kowannenmu ya shiga b'ata baki ne, haka zalika fad'in irin fad'an da Baba yayi ba'a cewa komai, sai da ya gama yi mana fad'a sannan ya koma nasiha, daga k'arshe ya tambaye mu abunda ke tsakaninmu, Kamal bai ji kunyar cewa soyayya mukeyi ba kuma aure mukeso muyi, shi bai ma yi tunanin ina sonshi ko banyi ba, matsalarshi kawai ya sameni kada wani ya kwace masa ni kamar yanda yake yawan fad'a min duk ranar da muka tashi hirar da. Baba bai ce komai ba yace mu tashi mu tafi zai neme mu.

Bai neme mu ba har kwanaki biyar bayan faruwar hakan, ranar da ya nemi magana damu dukkan iyayenmu mata da maza sun hallara, kowannensu fuskarsu babu yabo ba fallasa, sai dai ni da Kamal zuciyarmu banda fargaba da tsoro babu abunda yake ciki. Cikin nutsuwa Baba Zailani (mahaifin Kamal) ya fara da cewa "Kamal da Maryam yau zaman naku ne, munji duk abunda ya faru kuma ku kunsan baza mu d'auki wannan d'anyar aiki daga wurinku ba shiyasa muka yanke shawarar had'a aurenku kafin ya koma bakin karatunsa, idan ya gama karatunsa ya dawo sai ayi biki a mik'a ki gidan ki, bamu lamunta da duk wani abunda zai jawo mana magana a gari ba, haka zalika duk wani abunda zakuyi a idanunmu. Ranar juma'a za'a d'aura auren, ku tashi ku bamu wuri".

Zare ido nayi ina kallonsu daga bisani naji hawaye na silalo min, b'angaren Kamal na kai dubana naga sai murmushi yakeyi alamar yaji dad'in wannan hukuncin da aka yanke mana. Ina had'a ido dashi ya kashe min ido tare da d'aura hannunsa bisa k'irjinsa, ji nayi kamar in kwala ihu duk da wani b'agare na zuciyata na murna da farin cikin samun Mr. Right d'ina, sai dai an b'ata min plan kuma an bada ni ba tare da munyi soyayyar da nake mafarkin samu daga gareshi irin ta budurwa da saurayi ba. A nawa wautan gani nake soyayyar saurayi da budurwa yafi dad'i akan rayuwar aure dan ina gani ana yi haka zalika nima ban rasa saurayi ba duk da son Kamal d'ina na mak'ale a k'albina". 

Numfashi ta sauk'e idanunta na bisa flowers d'in da ke gabanta cikin vessels masu kyau wanda aka d'aura akan table dan k'awata shi. Ta cigaba da fad'in "Kamal ya kore min wannan tunanin kuma ya nuna min babu abunda ya kai rayuwar aure dad'i da kwanciyar hankali had'e da samun nutsuwa sai dai nashi salon ya banbanta da na kowa dan kuwa tunda aka d'aura mana aure bayi da wurin zuwa sai gidanmu safe rana dare, ya shigo inda nake a lokacin da yakeso babu mai ce masa a'a bare a hane shi da hakan. Duk wani nau'i na wasa da mace yana min har wanda ban tab'a ji ba bare insan dashi. Tuni soyayyarsa da begensa ya k'aru cikin raina kuma a kullum babu abunda nake muradi irin kasancewa dashi duk da wasanni ne kawai tsakaninmu baya wuce hakan, na rasa gane dalilin da yasa nake son abun ko dan sabon shiga nake ko kuwa haka dama akeji I dont really knw.

Kamar kiftawan ido hutunsa ya k'are sai shirin komawa makaranta, na shiga damuwa kamar yanda shi ma ya shiga, a kullum in na zauna dashi bani da wani zance sai missing d'insa da zanyi da tsantsar damuwan da nake nuna masa har da k'wallana, babu yanda muka iya dole muka rabu bayan dogon bankwanan da mukayi tsakaninmu mai tsayawa a rai. Sai dai tun ba'a yi sati ba na fara jin bazan iya hak'uri babu mijina kusa dani ba, tun ina daurewa har na fara tunanin hanyar da zan bi dan magance kwad'ayin da nakeji, a kullum in nayi waya da Kamal bamu rabuwa sai nayi masa kukan rashin sa kusa dani, babu abunda zai iya min sai hak'uri da ban baki amma gangar jikina ya kasa hak'uri da juriyarsa. Hakan ne yasa na fara...

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


    Page 39


  Hakan ne yasa na fara neman inda zan rage zafi, sai dai ko da wasa ban tab'a samun wanda zai gusar min da ishina kamar Kamal d'ina ba, da farko naso rik'e mutum d'aya amma da zarar na fara alak'a dashi sai inga ko kwatan Kamal d'ina bai kai ba, shiyasa bana iya zama da namiji mu jima tare. A haka na gama secondary na zana Jamb, ban ci jamb ba sai na jona computer skul na 6months ina cigaba da shek'e ayana ba tare da kowa ya sani a gida ba. 

Sai da na gama computer school d'in ya dawo min dan ya gama makarantar nasa. Cikakken Pilot ya zama kuma yayi iya k'ok'arinsa dan fitowa da sakamako mai kyau, tun yana k'arami yakeson zama matuk'in jirgi, shiyasa iyayensa da ya gama secondary suka tura sa dan cikar burinsa. Ya dawo lafiya kuma ya samu tarba daga wurina mai kyau fiye da yanda yayi zato.

Baba Zailani ne ya samo masa aiki a nan Abuja sai da yayi wata d'aya yana aikin sannan ya dawo aka fara shirin biki. Cikin sati biyu aka gama komai aka mik'a ni gidan mijina da ke Yola shi kuma yana zuwa aikinsa a Abuja. Tun daga wannan lokacin na d'auki wannan rayuwar, indai Kamal baya nan toh ina da wanda zai d'ebe min kewarsa kuma ban kula maza da yawa, d'aya ya isheni sai dai daga zarar naga wani wanda tunanina ya bani zai iya kamo Kamal fagen soyayya zan lik'e masa. Haka har rayuwa ta sauya na dawo nan Abuja wurin mijina ina rayuwata yanda nakeso duk lokacin da baya nan. Ba wai bana sonshi bane, ina matuk'ar sonshi fiye da tunaninku kuma ni da kaina nasan bana kyautawa amma da zarar naji sha'awar kasancewa da wani toh fa babu abunda zai hanani nemo namijin da zai gamsar dani, nayi k'ok'arin nuna masa ya rage tafiye-tafiyen da yakeyi amma ya kasa ganewa...".

Benaxir cikin fushi tace "dallah tsaya, shine labarin da zaki bamu? Ni fah ya isheni jin wannan rashin hankalin. Kina sonshi kike rayuwa da wasu a waje?" Miemiebee cike da b'acin rai ta tsaya kallonta, bata kai ga amsawa ba taji Pherty na cewa "taya ni tambaya dai". " kada wata daga cikinku ta sake raina min hankali, ina ruwanku da rayuwana? Shine labarin rayuwata kuma bance wata ta zageni ba dan bazamu kwashe da kyau ba, da kuke zancenku na banza kunsan ya nakeji? Kunsan ni wace irin mace ce? Idan kunga baza ku iya fad'an alkhairi ba kuyi shiru".

Benaxir tace "idan ank'i fa" "Dan Allah ku bari" Lubie ta fad'a tana buga table d'in "sai kace k'ananan yara? Miemie is dat all? Menene tak'amaiman matsalarki da Kamal? Please tell me?" "Yana zama wurina yana biya min buk'ata duk lokacin da na nemi haka" Lubiee zatayi magana Ummu Abdoul ta dakatar da ita da hannunta.

Numfashi ta sauk'e sannan tace "Alhamdulillah munzo k'arshen labaranmu, yanzu abunda ya dace muyi bai wuce samun maslaha ba. Ta b'angarena yanzu matsalana d'aya ne zuwa biyu, samun d'ana Abdoul da miji na gari mafi alkhairi. Ta b'angaren Lubiee kishiyarta da ta addabeta kuma ina kyautata zaton asiri ne, sai Ruffaida wanda yanzu haka bata gidansu, da farko sai mun samu kan zaren mun warware sannan mu mik'ata ga ahalinta sai kuma fatan samun miji na gari, mu aurar da ita ga mutumin da ya dace".

Ta kalli Ruffaida cikin nutsuwa tace " babu wanda kikeso ki aura ko zai zo mana da sauk'i mu rik'e maganar auren sannan mu kai ga Mamu?" Ruffaida kad'a kai tayi alamar babu, Ummu Abdoul ta numfasa tace "toh Allah ya zab'a mafi alkhairi. Sai ke Benazir, da farko iyayenki sai kuma miji.." "A'a nikam ba wani miji da ke gabana, let me be please. In na samu iyayena shikenan bani da matsala da mazan arewa again" "haba Bena, ke fa muka fara maganar nan dake kuma yanzu ke ce zaki kawo mana cikas tun kafin aje ko ina?".

Rolling idonta tayi tana tab'e baki tace "alright, ina ji" "good. Sai Pherty, a ganina dukkanmu a yanzu sai mun cire abunda yake ranmu sannan mu samu solution, dan maganganunki Pherty sun nuna min ke baki da buri yanzu sai ma Alhaji ya sawwak'e miki ya k'wace duk wani abu nasa da ya baku kije kuyi ta wahala da iyayenki which ba haka ne ya dace yazo mind naki ba, hak'k'in aurenki ya kamata ki gyara farko, idan kin gyara wannan duk wani abunda zai biyo baya mai sauk'i ne idan har tuba na gaskiya kikayi".

Cikin nutsuwa ta kai dubanta ga Batool tace "naki matsalar yana da wahalan gaske, na farko iyayenki suna fushi dake na biyu sunanki da ya b'aci wurin jama'ar gari hakan kad'ai zai kawo mana cikas wurin magance taki matsalar, amma kada ki damu komai zai dai-daita da yardar Allah. Sai Miemie koh, ke kam da alamu babu nadaman laifukan da kika aikata, anya zamu tafi tare kuwa?" Ta k'arashe maganar tana kallon Miemiebee, Pherty ce ta bada amsar da cewa "why not, ai gyara muke nema" ta buge k'afar Miemiebee ta k'asa alamar tace eh, babu yanda ta iya kuwa tace "eh" fuskarta kamar zata fashe da kuka.

  Numfashi ta sauk'e had'e da murmushi dan samun biyan buk'ata, ta cigaba da cewa "yanzu a matsayina na wacce na girme maku dukka zan bada shawarata ga kowanne daga cikinku idan nayi kuskure ku tunasar dani ku gyara min dan kada muyi kwab'a wurin neman gyara". Suka amsa da "hakane" duk da kowaccensu da abunda ke ranta dan kada a kawo shawarar da baza ta iya yi ba.

"Zan fara da wad'an da zasu fara aikinsu daga yau d'in nan, ina nufin daga yanzu, na farko Lubiee, sai ke Pherty da kuma Miemie dan naku matsalar ku da kanku zaku gyara namu addu'a da kuma shawarar da ya dace. Lubiee bazan b'oye miki ba sakacinki da addini yasa duk abunda ke faruwa dake yanzu yake afkuwa, da kin rik'e addininki kika yawaita addu'a da ikhlasi toh babu wani sihiri ko siddabarun boka da zai sameki sai wanda Allah ya k'addara zai sameki, dan annabin rahama ma anyi masa kuma ya kama sa, hakan kuma ba wai yana nufin ka daina dogaro da Allah da addu'o'i ingantattu ba. Yanzun ma bai b'aci ba, ki yawaita karatun Qur'an a cikin gidanki, ki yawaita yin azkar na safe da maraici, in zakiyi bacci kiyi addu'an bacci kuma kiyi alwala kafin ki kwanta..." "A'a, Ummu-abdoul ni akayi wa sihirin ne ba mijina ba?" Da mamaki a fuskarta take tambaya.

Murmushi tayi tana mamakin wannan tambaya nata "toh ke a ganinki zaki iya yak'i da siddabarun bokaye ba tare da kin kare kanki ba? Toh da me zaki kare kanki banda ayoyin Allah? Ki nutsu ki fahimceni, ki rik'e wad'annan abubuwan da na fad'a miki da kyau sannan in fad'a miki abunda ya dace kiyi wa mijinki domin kare shi daga sharrin abokiyar zamanki. Shi a nashi b'angaren zanso da farko ki sa ido sosai akan matar nan tasa saboda gano abubuwa daga wurinta, daga nan ne zamu gano lagonta, sannan..." Ta kalleta da alamar tambaya a fuskarta tace "yana cin abincinki?".

Baki Lubiee ta bud'e ta tsaya kallonta, daga bisani tace "mutumin da ko kitchen nasu ban anfani dashi shine zan masa abinci har ya ci? Lallai ma kina neman magana". Numfashi Ummu-abdoul ta ja tace " toh fah! Abun ba sauk'i, amma ke yakamata ki samo d'an dabarunki da zaki na yi ya samu yana shan ko ruwanki ne, kinga da sai kina karanta Ayatul kursiy, suratul ikhlas da suratul fatiha a cikin ruwan zam-zan kina bashi yana sha, yanzu dai abunda za'a yi akwai wani imam a Annur mosque zamu je mu kai masa kukanmu insha Allah zai bamu shawarwari da addu'o'in da zai taimake mu. Bayan addu'a gaskiya bazan b'oye ba muna da sakaci da k'azanta, k'azantarmu kuma shi yake tasiri har ayi mana sammu ko sihiri a gidanmu a d'akinmu a binne abu bamu sani ba, kamata yayi tunda kika fara ganin sauyi wurin mijinki ki binciki d'akinsa, kiyi masa gyarar da baki tab'a yi ba kina bincike kina karkad'e k'ura da daud'a, ba sai ma hakan ba, meh laifin mace ta gyara d'akin mijinta ta share k'ark'ashin gado, kinga duk wani abunda aka binne ko aka b'oye tsaftarki zai gano miki shi, yanzu dai ki samu daman yi masa wannan gyarar dan ciro duk wani asirin da aka binne masa a d'aki in akwai, kafin nan mun yi magana da malamin sai mu san abun yi nan gaba. Kin gane Lubiee? Ki tattara Kausar ki kai ta wurin Mrs Umar taje hutun sati biyu dan mu kammala aikinmu ba tare da fargaba ko samun cikas ba". 

  Tace "insha Allah zan k'ok'arta inyi duk abinda kika ce" "Yauwa, yanzu na fara samun nutsuwa tunda ana karb'ar shawarata." Ta dawo da dubanta ga Pherty sannan ta koma kan Miemie tace "matsalarku kusan d'aya ne, kuma shawara iri d'aya zan baku amma kafin nan zan so in yi magana da Miemiebee. Ki saurareni da kunnen basira dan maganar da zanyi dake mai anfani ne idan har kika fahimceni, ko ba yanzu ba zai anfaneki nan gaba duk da yanzun ma bata b'aci ba, bamu dai san yanda abun zai kasance ba amma muna fatan komai yazo mana yanda mukeso. Kina jina?"

(Cikin 'yan matan nan bak'wai, wacece labarinta yafi ba ki\ka tausayi?)

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


    Page 40


   "Eh" ta amsa cikin rashin nutsuwa, sai da ta sauk'e numfashi sannan ta fara da cewa "kinsan kuwa addini ya baki daman barin aure muddin mijinki baya biya miki buk'ata? Auren nan ana yinsa ne dan biyawa juna buk'ata, idan har babu wannan satisfaction d'in aure bazai tab'a k'ark'o ya zauna yanda ake so ba, kuma tunda kika fuskanci mijinki baya biya miki buk'atarki na aure kin tab'a tunkararsa da maganar kun tattauna akai dan samun mafita?" Miemiebee tace "ku gane min mana please" ta fad'a fuskarta na nuni da karaya da kuma tausayin kanta da ta samu kanta a ciki, "ni fa bance muku Kamal baya biya min buk'atuna ba, infact ni duk mazan da nayi tarayya dasu babu wanda yake satisfying d'ina irin Kamal da Ibrah..." Tayi saurin toshe bakinta dan kada ta k'arasar da zancen nata.

 "Lah'ilaha illal Allah" Benaxir ta fad'a tana tafe hannu, duk suka tsaya kallonta ta cigaba da cewa "yarinyar nan ta cika 'yar iska, kuna ji ba kunya take k'iran wani Ibrahim wai yafi gamsar da ita? Am telling you yarinyar nan ba k'alau take ba, dole a kaita wurin malamin da zaki kai Lubiee saboda ayi mata ruk'ya, wannan aljanu sun shafeta shiyasa ta fand'are haka". A fusace Miemie ta mik'e ta yo kan Benaxir Lubiee ta tare ta ta janyota ta mayar da ita kan kujerarta, "baku da hankali fa" cewar Ruffaida tana kallonsu ido da baki bud'e.

"Kada wacce ta sake magana in har ba shawara zata bayar ba, tun ba ke ba Benaxir, kiyi shiru ban nemi shawararki ba" cewar ummuAbdoul. Ta dawo da dubanta ga Miemiebee da har yanzu take huci zuciyarta na tafarfasa, hannunta ta d'aura akan nata tace "yi hak'uri ki saurareni, kada kiji zancen kowa bare har ki fasa yin abunda kikayi niyya, wato gyara kura-kuranki, yanzu na gane cewa ba wai biyan buk'ata bane ke kai ki wurin wasu, yawan tafiye-tafiyensa yasa kike hakan, meh yasa bakya azumi dan kare kanki in baya nan? Anyway, kafin mu kai ga magance wannan matsalar yanzu shawara d'aya zan baku ke da Pherty, nasan zai yi muku wahala amma shine kad'ai mafita, kuma ya zama dole ku karb'i duk wani abunda zai biyo baya na sakamakon abunda kuka aikata".

"Ku sanar da mazajenku gaskiyar abunda kuke aikatawa a bayan idonsu dan idan suka ji a wani wuri zai fi muni" a razane suka ce "what?" Miemiebee ta k'ara da cewa "impossible", tsantsar firgici da tsoro ya bayyana a fuskarsu, ba ma su kad'ai ba hatta Lubiee, Ruffaida da Batool sun firgita da jin wannan magana. Benaxir ce kad'ai ta sake murmushi dan wannan magana ya faranta mata rai, ta tabbata kowaccensu zata d'and'ani kud'arta in dai suka bi wannan shawarar. Pherty ce tace "gaskiya bazan iya tunkarar alhaji da wannan batu ba, ina ma kuce in daina bin maza in rungumi mijina? Inaaa! Bazan tab'a fad'a wa Alhaji ina mu'amala da maza a waje ba" ta k'arashe maganar tana kad'a kai hawaye na malala a fuskarta.

"Ummu-abdoul gaskiya yayi tsauri, babu macen da zata iya tunkarar mijinta da irin wannan maganar, barazana ce ga rayuwar aurensu kin sani? Kuma mu zamanmu anan ba raba aure muka zo yi ba sai ma gyarashi da muke shirin yi" cewar Lubiee. Ummu Abdoul ta murmusa sannan tace "kwarai gyara aure muke son yi anan haka zalika bayan gyara aure muna son mu fahimtar da kowacce daga cikinmu yanda zata kyautatawa mahaliccinta, kuma indai a maganar Pherty da Miemie ne wannan dai shine kad'ai hanya. Dalilina na farko shine, duk wannan aika-aikan da sukayi hakk'in mijinsu na kansu, dole su nemi tubansa in ba haka ba ko a lahira Allah zai tuhumesu da wannan, kuma shari'a za'a musu tsakaninsu, da shari'ar lahira ai gwanda su nemi yafiyarsa tun anan sauran zunuban ya zama tsakaninsu da mahaliccinsu? Innal Allah gafurun raheem, zai iya yafe musu indai sukayi tuba na gaskiya. Ko akwai wacce takeson ta mutu da hakk'in wani akanta? A ganina babu abunda zai fi d'agawa bawa hankali irin sab'awa mahaliccinsa da kuma shiga hak'kin wani/tauye masa hakk'i. Tun wuri nake shawartarku, ku gaggauta neman yafiyar mazajenku kuma duk wani hukunci da zasu d'auka akanku ku d'aukeshi matsayin k'addara kuma nau'i na sakamakon ayyukanku, zai iya yiwuwa ta wannan hanyar ko kuma ince wannan horarwan ya zama hanyar da Allah zai yafe miki. Ku ji tsoron Allah kuma kusan duk wani aiki naku a rubuce yake kuma zaku gani ranar da ba'a iya yin k'arya ko neman gafara. Da muna bin hukuncin musuluncin kunsan hukuncin da ya hau kanku?" "Kisa" Ta furta tana mai jin d'acin kalmar a bakinta. Nasiha tayi musu mai ratsa jiki kowaccensu sai da ta zubar da k'walla.

Basu bar wurin ba sai k'arfe takwas bayan kowaccensu ta rungumi k'addararta kuma ta barwa kanta abunda zuciyarta ke k'issima mata. A tare suka fito, Pherty na biye da Miemie har wajen motarta, anan ne ta samu damar cewa "na san abun da ke ranki Miemie, kiyi abunda aka umarcemu ko kuma ni in sanar da Kamal da kaina tare da nuna masa wannan videon, kinsan bazai yi miki da kyau ba". Hawaye sharr yake bin kuncin Miemie tace " Pherty meh kikeso a wurina? Kud'i? Fad'a min ko nawa kikeso zan baki wallahi amma ki daina shiga rayuwata, ki bani wannan videon ni kuma zan miki duk abunda kikeso" murmushin mugunta Pherty tayi tace "kuskuren da kikayi kenan tun daga farko na bin Ibrahim, da baki bi sa ba bazaki tab'a zuwa hanyana bare har in samu abunda zan na threatening d'inki dashi ba, yanzu dai kowa da nashi matsalar, ki bi abunda aka fad'a mana zan sallama miki videon". Bata jira amsar ta ba ta wuce ta bata wuri. 

Kuka tayi mai isarta cikin motar daga bisani taga ba shi zai taimaketa ba ta wuce gida zuciyarta na mata k'una. Kowaccensu yau jiki a mace ta isa gida dan fargaban abunda zai biyo baya, shin zasu samu yanda sukeso na kowaccensu ta fad'a kuma saki ko duka ko cin zarafi bai biyo baya ba? Da wuyar ganewa dan kuwa babu abunda namiji yafi tsana irin a ci amanarsa. Fatansu da addu'arsu dai kada abun ya kai ga saki, dan in har ya kai ga hakan sun samu gagarumar matsala.


Washegari @ gidan Pherty


    Ta zuba tagumi sai zufa da ke keto mata, bata da nutsuwa tun jiya da ta dawo dan firgicin da take ciki. Ta ina zata fara? Meh zata ce masa? Shin zai fahimceta? Ko zai koreta bayan ya mata d'an karen duka? Hannunshi taji a daidai cikinta cikin muryar bacci yana cewa "baby kin tashi? Baki tasheni ba kuma kinsan yau zanje wurin Antynki", sosai ta firgita jinsa kusa da ita, sai da ta nemo nutsuwarta sannan tace "am sorry, na manta ne ban tashe ka ba, ka bari gobe ka tafi mana" ta k'arashe maganar tana marairaicewa fuskarta kamar zatayi kuka, tuni yace "na fasa, amma meh zaki bani in na zauna a gida" ya gyara zamansa yana mai kallon fuskarta.

Murmushin da bai wuce leb'b'anta ba ta sakar masa tace "yanzu muje kayi wanka sai muyi breakfast, akwai maganar da nakeso muyi" murmushi ya sakar mata ya janyota kusa dashi ya d'aura lebb'ansa bisa goshinta yayi kissing sannan yace "ina sonki sosai" lumshe idanunta tayi zuciyarta na k'ara tsananta bugu, bata amsa shi ba ya tashi ya shige ban d'aki ita kuma ta shige kitchen.

Yau dai had'ad'iyar breakfast ta had'a masa, ba dan komai ba sai don son faranta masa da kuma kwantar masa da hankali ko zai yi mata sassauci cikin hukuncin da zai iya mata. Sai da yayi wanka ya gama shirinsa har yazo kitchen bata gama girkin ba, tsayawa yayi ya taimaketa yana mata hira kamar ba babban mutum ba, sai yanzu take sake ganin wautanta na biyewa zuciya, son da Alhaji yake nuna mata yaci ace tayi masa biyayya kuma ta k'aunace sa, amma zuciya da shaid'an sai ya k'awata mata haram akan halas d'inta. Sosai tayi k'ok'arin biye masa tana mayar masa da dukkan zancen da yake yi mata. Cikin kwanciyan hankali da raha suka gama cin abincin suka koma d'aki, zama yayi gefenta jikinsu na gogar juna yace mata "ina jinki baby, fad'i abunda kikeson fad'a min".

Hannunshi ta kamo cikin nutsuwa tace "inason ka bani hankalinka kuma ka fahimceni ka saurari duk wani maganar da zan fad'a maka dan mai muhimmanci ne" hawayen da ya sauk'o bisa kuncinta ta goge zuciyarta na tsananta bugu kamar zai fad'o k'asa, shi kuwa kallonta ya tsaya yi yana mamakin girman maganar da zata fad'a masa da har yake sa ta kuka, "meh ya faru?" Ya furta cikin macewar jiki.

Da sannu ta fara basa labarinta da Ibrahim tun kafin had'uwarsu har izuwa rana irin ta jiya da ta samu shawara daga k'awayenta, kuka takeyi kamar zata shid'e ganin yanda Alhaji yake kallonta, tasan ta tafka babban kuskure wanda bazai tab'a gyaruwa ba. A hankali ya zare jikinsa daga nata ya mik'e zai bar d'akin, rasa abun yi yayi dan maganganunta ya kad'a shi, meh ya rageta dashi? 

Meh ta rasa daga wurinsa? Dan ya aureta shine laifinsa? Dan shi babba shiyasa take tunanin bazai bata soyayyar da k'aramin yaro zai iya bata ba? K'afafunshi da ta rik'e ya dakatar dashi, sosai take kuka a wannan lokaci tana mai neman yafiyarsa, a hankali ya b'anb'are hannunta daga k'afarsa ya bar mata d'akin zuciyarsa na k'una ita kuwa tana mai kukan da tun da take bata tab'a yin irinsa ba, kaico! Wannan wace irin rayuwa ce ta jefa kanta? Ina makomarta? Zubewa tayi a k'asa tana kuka kamar ranta zai fita.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


Page 41


   Awanni biyu da faruwar hakan. kwance take a inda ya barta ya shigo idanunta a lumshe a wannan lokaci ta daina kukan sai ajiyar zuciya da take sauk'ewa da kuma kukan zuciya wanda yafi na waje ciwo, rashin makomarta yafi komai d'aga mata hankali. Muryarshi taji a dake yace "ki shirya kayanki yanzu zamu wuce Minna" bai jira ta amsa ba ya fice wanda ko kallon fuskarsa bata samu nasaran yi ba, bata san meh yasa maganar nan ta "ki shirya zamu je Minna" ya d'aga mata hankali ba ya haddasa mata tsinkar zuciyar da bata san ana yin irinta ba, kamar zuciyarta zata tsage haka ta daure ta shiga d'iban kaya cikin k'aton akwati.

Tasan bazata sake zuwa wannan gidan ba k'arshen zamanta yazo tunda ya nemi ya mayar da ita gida, hawaye take matsa ahankali har ta gama kwasan iya kayan da zata iya d'auka, duk wani abunda zata iya nema sai da ta d'auka dan a ganinta saki ne zai biyo bayan wannan tafiyar, ta fawwalawa Allah kuma ta karb'i wannan sakamako, a ganinta in ta samu yardar Allah bata da wani matsalar rayuwa, sai dai ya zatayi dan samun gafarar mahaliccinta? Gaskiya nasihar da taji jiya da kuma azabar da aka tanadarwa mazinaci ya isheta saduda, wanda tayi ma yawa ne dasu bare ta k'ara wani, ita a ganinta ko shekaru ashirin aka k'ara mata tana istigfari da neman yardar Allah bazai isheta goge zunubban da ta aikata ba.

Hannu ta d'aga sama hawaye na cigaba da malala a kuncinta tana cewa "Ya Allah na rok'eka ka gafarta min kurakuraina, ka bani ikon binka dan samun rahamarka, Allah Ka sa hanyar da nake bi yanzu shine hanyar samun aljannata, ya Allah ni mai d'umbin laifuka ce ka gafarta min" kuka ne yaci k'arfinta dan tuno irin rayuwar da tayi da Ibrahim wanda a tunaninta bata gwada nunawa mijinta halalinta ko kwatan irinsa ba, har bata da kunyar d'aga hannu rok'on Allah? Ya haneta zina ya halalta mata aure amma ita da auren nata ta aikata zina? Wannan abun kunyar har ina? Zuciyarta ne ya mace da tuban da takeson nema, a ganinta Allah bazai yafe mata ba. Kwanciya tayi a bakin gado tana mai rufe fuskarta da mayafinta ta furta "innallaha gafarun raheem", lumshe idanunta tayi bakinta kuma na furta "astagfirullah wa atubu ilaih".

Minti goma da kwanciyarta taji yayi mata knocking, "fito mu tafi" bata amsa shi ba taji alamun tafiyarsa ma'ana ya bar k'ofar d'akin. Janyo akwatin tayi tana tafiya kamar zata fad'i dan nauyin da jakar yayi mata. Dak'yar ta sauk'o da jakar daga sama dan stairs d'in da d'an tsawo, yana palorn yana kallonta har ta sauk'o sannan ya d'auke kai ya wuce waje ta biyoshi a baya janye da akwatinta. Awanni uku ya kai su Minna, tunda suka shiga motar babu wanda yayi magana, dukkansu biyu zaune a baya driver na jansu ko kallon inda take bai yi ba bare ya d'aura idanunsa akanta, ita ce dai lokaci zuwa lokaci take kallonsa dan zuciyarta ya samu nutsuwa amma hakan ya faskara, dan bata tab'a ganinsa ya had'e mata rai suna tare irin haka ba. 

Kai tsaye ya umurci drivern ya wuce dasu main gidansa, horn d'aya aka bud'e musu suka shiga, katafaren gida ne mai sassa biyu, nata da kuma na uwargida sai BQ na yara maza. Ba tare da ya kalleta ba yace ki wuce b'angarenki shi kuma ya wuce b'angaren uwar gidarsa zuciyarsa a jagule. Da farko tayi mamakin furucinsa dan a nata tunanin gida yakamata ya kaita ba gidansa ba, amma daga baya sai tayi tunanin ko bai son driver ko mutane suyi zargin wani abu ne, shiga ciki kawai tayi ta bar akwatinta a motar dan tasan anjima zai kad'a ta gidan ubanta.

Miemiebee @ 12pm


   Safa-da-marwa take a cikin kitchen ita d'aya zuciyarta a cunkushe babu abunda ke mata dad'i, neman mafita take ido rufe ta kasa samu, kukan ma kasa zuwa yayi dan b'acin rai da tsinkar zuciya had'e da rashin mafita da ya dameta. Tunawa da tayi Kamal yau yana dawowa ya k'ara tsinka mata zuciya, zaman dirshan tayi a cikin kitchen d'in ta fashe da kuka mai k'arfi, ita kad'ai tasan yanda take ji, wannan wani irin rayuwa ne? Meh zatayi wa Pherty dan ta saduda ta barta tayi leaving life nata yanda takeso? Kuka takeyi kamar ranta zai fita ahankali taji zuciyarta ya d'an lafa.

Zaune take a tsakiyar kitchen d'in har mintuna 30 ba tare da tasan tayi ba, mik'ewa tayi ahankali dan jin sarar da kanta yakeyi, a daddafe ta isa d'aki ta zube akan gadonta, nan take zazzab'i mai zafi ya lullub'eta, bata san lokacin da bacci ya d'auketa ba sai k'arar wayarta da ya tasheta.

Wayar na yankewa taji alamun an bud'e k'ofa, bata yi gigin tashi ba dan kwata-kwata bata da k'arfin yin hakan, ji take kamar an d'aura mata gingimemen dutse dan nauyin da jikinta yayi mata. Tana kwance ya shigo d'akin ya k'araso inda take, idanunta a lumshe ta kasa ko da bud'ewa dan wahalar hakan da takeji. Zama yayi a gefenta ya d'aura hannunsa a goshinta, jin zafin jikinta ya tsorata shi, "subhanallahi" ya furta yana d'ago kanta ya d'aura akan cinyarsa, a rud'e yace "haba Miemie, baki da lafiya kika k'i sanar dani kina zaune a gida? Kinga yanda duk kika zafge kija rame? Subhanallahi" shafa fuskarta yayi sannan ya mayar da ita ya kwantar ya shiga bathroom ya d'ibo ruwa a d'an matsakaicin roba ya fito rik'e da k'aramin towel da yake ajiye a bathroom d'in. 

Ahankali ya zame mata kayan jikinta sannan ya fara sa towel d'in cikin ruwa yana matsewa ya d'aura mata a jiki. Haka ya cigaba da yi mata har sai da zafin jikin ya sauk'a sosai, ahankali ta bud'e idanunta tana kallonsa, hawaye taji ya bi gefen idonta na d'ayan kuma yabi kan karan hancinta yabi saman idonta yana sauk'a bisa gadon da take kwance. "Sorry" yake ta maimaita mata yana gyara mata kwanciyarta. Kuka ta fashe masa dashi tunawa da tayi da sharad'in Pherty, a rud'e yake tambayarta inda yake mata ciwo, k'in amsa shi tayi hakan yasa ya mik'e ya d'auko doguwar riga bak'i yana k'ok'arin sa mata, sunanshi ta k'ira cikin sanyin murya "Kamal, ina zaka kai ni? Lafiyana k'alau fa ka barni a gida please" bai tanka ta ba sai da ya gama sa mata kayan ya d'aura mata d'ankwalin ya d'auketa cak kamar baby yayi hanyan fita. Magiya ta shiga yi masa da shure-shure tana wuntsila k'afa tana cewa ya ajiyeta, direta yayi fuskarsa kamar ya fashe mata da kuka ya tsaya kallonta, d'akin ta koma ba tare da tace masa k'ala ba ya bi ta a baya. Dolensa ya hak'ura ya fasa kaita asibitin ya cigaba da kulawa da ita a gida har dare.

A ranar dai babu wanda ya samu halartar cubana, dama asali basu sa ran taruwarsu ba a ranar dan aikin/shawarar da suka bayar sun fi son a fara sai next week aji feedback sai a d'aura daga inda aka tsaya.

A b'angaren Ummu Abdoul maza uku kenan yanzu ke binta, Malam Usman, Abba sai kuma Abduljalil da ya nace sonta yake kuma aurenta yake son yi. Abba har Abuja yazo tak'i barinsa ya ganta dan bata son ya famo mata sonshi da tayi k'ok'arin yakicewa daga zuciyarta, ga mijin Anty Jegal da ya rufe ido yake nuna mata soyayyar da bata tab'a zaton yana dashi ba, zuciyarta da tunaninta ya rabu bata san wanne zata zab'a ba, Abba da ya nuna mata halin namiji ko kuwa Malam Usman da yayi mata halacci? Abduljalil da bai san komai game da rayuwarta ba anya zai iya auranta bayan ta sanar dashi bazawara ce ita kuma har da yaro tsakani? Abun dai da cajin kwalwa.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


    Page 42


Gidan Mamu @ 3:50


    Dawowansa daga masallaci kenan ya shiga d'akinsa dan yayi shirin fita, duk da yau sunday sai yasan k'aryar da zai yi wa Mamu dan ya samu yaje office wurin 'yan matan da yaji an kawo masa sweet16, a hanzarce yayi wanka yasa kaya ya d'auki makullinsa ya fice. A bakin k'ofa suka ci karo da Mamu "a'a, ina zaka je kuma haka? Ni da nazo wurinka in tayaka hira" tayi maganar tana kallon jikinsa tana mai shak'ar k'amshin turarensa mai dad'in gaske. 

Murmushi ya sakar mata sannan yace "office zanje, yanzu aka k'irani akwai urgent abu da ya tashi wanda dole sai na isa before 4:30" ya fad'i lokacin tare da kallon agogonsa, ya dawo da dubansa gareta ya janyo ta jikinshi yace "meh na had'e rai, yanzu zan dawo fa". Babu yanda ta iya dole ta kyaleshi tayi masa addu'a sannan ya fita ita kuma ta wuce nata d'akin.

Bata samu daman zama ba Sadiq ya shigo d'akin ba tare da ya mata magana ba ya janyo hannunta suka fice tana kallonsa da mamaki, ko gyalle bai bari ta d'auka ba a dai-dai d'akin Amrah ya k'wala mata k'ira yana cewa ta fito masa da mayafi k'ato. Bai tsaya ko ina ba sai cikin motarsa ya bud'e mata ya zaunar da ita ya shiga nasa mazaunin, sai a sannan Amrah ta fito da mayafin cikin sassarfa ta iso ta mik'a mata. "ina zaka kai ni?" Tace masa tana yafa mayafin a kanta, bai kai ga amsawa ba tace "ai da ka barni na shirya, kaga kayana da wannan mayafin basuyi matching ba".

Sadiq da ya gaji da jin zantukanta yace "wani abu nakeson nuna miki wanda kullum bakya yadda dan soyayya ya rufe miki ido, yau dai zaki gani da idonki insha Allah" ware ido tayi tace "Sadiq kada kace min Daddynka wani wuri zai je ba office ba?" Hanya ta shiga dubawa tana neman motarsa, ikon Allah yasa ta gani bayan sun hau babban titi, hannunshi ta mara tace "gashi can d'an iska munafuki, bi shi muga inda zai je, amma mutumin nan ya cika shu'umi" idonta k'yar akan motar dan kada ya b'ata mata cikin motoci, shi kuwa Sadiq a bayansa yake binsa ahankali, daga shi sai wasu motoci biyu sannan Nuraddeen.

Hanyar office nashi taga yana bi, ta dawo da dubanta wurin Sadiq ta had'e fuska ta murtuk'e "kai kada ka raina min hankali, ba hanyar office nashi kenan ba nan?" "Ki tsaya mana ki gani, ba office zai je ba. Tunda ni nace miki zan kaiki ki jira mana kiga ikon Allah" zuciyarta ne ya tsinke jin furucinsa, indai gaskiya yake fad'a mata Nuraddeen ya cika munafuki, hawaye ne suka taru a idanunta dan fargabar abunda zata je ta tarar.

Har k'ofar office nasu suka isa Nuraddeen bai rab'e ko ina ba, a idonsu ya shige cikin harabar office d'in, mugun kallo ta watsa masa sannan ta ja tsaki ta b'alle murfin motar ta fice, sai da tace "zaka zo ka sameni a gida" sannan ta rufe k'ofar tayi hanyar da zai sadata da inda zata samu Taxi drop. Fitowa yayi yace "haba Mommy, meh yasa bakya yadda dani ne? Kizo mu jirasa yanzu zai fito" a nesan tace masa "banason iskanci, kullum sai dai kasa uwarka ta yi zargin mijinta shine kad'ai buk'atarka dan kawai ka nemi Ruffaida ka rasa, wannan yarinya da zan ganta sai na b'ata mata fuska da acid, hasken nan da dogon hancin ke rud'anka" bata sake ce masa komai ba ta wuce cikin sauri.

Komawa yayi cikin motarsa ya zauna yana zaman jiran fitowar Daddyn nasa, zuciyarsa ya mugun b'aci da tafiyar Mommy, babu yanda ya iya ne da ya janyota ya d'aureta dan ta jirashi, "mtsw" ya ja tsaki a hankali. Minti goma da tafiyar Mamu ya hango fitowarsa, k'aramar yarinyar da take zaune gefensa tana dariya yafi d'aga masa hankali, kamar yayi ihu haka ya ji, ina ma Mamu bata tafi ba ta ganewa idonta ko da wannan ne, wata k'ila bazata yi hawan jini ba dan ya tabbata ranar da ta ganewa idonta mijinta na tare da wata akan gado d'aya sai ta sume ko ma stroke ya wullar da ita. Sai da ya tabbatar sunyi nisa sannan ya biyo su a baya. 

Wani sabon anguwa suka je Gishiri wanda babu mutane da yawa sai sabbin gidajen da suke wurin wasu ko gamawa ba'a yi ba. Daga nesa ya tsaya yaga gidan da suka shiga, da alamu ko mai gadi babu hakan yasa ya dakata sai da ya tabbatar sun shiga duk inda zasu iya shiga har sun d'an huta sannan ya b'alle murfin motar ya fito. Wani zuciyar na kwab'ansa kada ya je amma ya dake sai tafiya yake duk da nauyin da k'afafunsa sukayi masa.

Kai tsaye ya shige gidan kamar yasan cikin gidan. Sabon fenti ya gani mai matuk'ar kyau sai interlock da Ya mamaye cikin gidan dukka. "Wannan gidan waye kuma?" Tambayar da yake yiwa kansa kenan, matsakaici ne kuma da alamu an kashe kud'i mai yawa dan tsara shi. Hanyar k'ofar yayi zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri, daidai wani window yazo giftawa yaji muryar Babansa tangarau yana yabon kyawun surar wata, maganar da yaji ya tabbatar masa yaga wani sassa na jikin yarinyar da ya shigo da ita.

Ido ya runtse ya had'iye yawu mai d'acin gaske sannan ya shige parlon cikin sand'a dan kada aji sa, k'ofar da ya gani ta gefen windown da yaji muryarsu yabi, a bakin k'ofar ya tsaya yana tunanin abunda ya dace yayi, ya shiga ya nuna musu ya gansu ko kuma ya wuce gida kawai tunda ko ya fad'awa Mamansa ba yadda zata yi ba? Numfashi ya sauk'e sannan ya d'aga hannu yayi musu knocking "knock! Knock!! Knock!!!".

°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°


Mamu gida ta wuce kai tsaye bayan ta samu mai taxi, sai da ta shiga ciki ta d'auko masa kud'insa sannan ta samu damar zuwa d'aki ta kwanta, halin Sadiq ba k'aramin isanta yayi ba, mutum da mahaifinsa yake yi masa sharri? Ko dai da gaskiyarsa? Wani b'angare na zuciyarta ya sanar da ita Haka kawai bazai k'irk'iro abu irin haka ya k'ak'aba wa mijinta kuma ubansa ba. Da wuri ta kawar da tunanin da fad'in Ruffaida ce duk take sa shi haka, wai ko yasan inda Ruffaidan nan take? "Nasan maganinka" ta furta a fili sannan ta mik'e ta isa d'akin Amrah.

"Ina wannan k'awar taki, Meesha take ko wa?" Ta fad'i hakan tana zama a gefen gadon Amrah. Ita da take gyara kayanta a wardrobe nata tace "Meh ya tuno miki Meesha yau Mommy?" Murmushi tayi tace "nikam tana da miji? Ina nufin anyi maganar aurenta da wani?" Da mamaki ta juyo tana kallonta, daga bisani tace "lafiya dai ko Mommy?" "Lafiya mana, inaso in sani ne". Cigaba da gyarar kayanta tayi sannan tace "eh, aurenta ma ai ya kusa dan har ansa date, watanni biyu suka saura".

"Kash!!!" Cewar Mommy tana mai rik'e goshinta idanunta a lumshe. "Menene wai? Lafiya dai ko?" "Wai kinga dama mata nake nemawa Sadiq, aure nakeson yi masa" baki bud'e take kallon Mamu, ta maimaita kalmar "aure" sannan tace "yaushe za'a yi masa auren bayan kwata-kwata bai wuce shekaru ashirin da biyar ba, in ya kai kenan ma".


"Ina ruwanki? Ke dai ki nemo min cikin k'awayenki, kyakkyawa wacce tafi Ruffaida kyau da komai" dariya ta so bawa Amrah jin ta fad'i hakan, ta daure dai tace "ba dai wacce tafi Ruffaida kyau ba, mai hankali dai wacce zata girmamaki ta girmama 'yan gidan nan" bata bari Mommy tayi magana ba tace "Khadeejah candy, kin santa ko? Ita tafi dacewa da ya Sadiq, hankali, nutsuwa, ni burgeni takeyi sosai Mommy, ita na zab'a masa".

Tuni Mommy ta washe baki tace "haba dai? Baki ce min tana da kyau ba, nuna min hotonta in gani. Kinsan Sadiq son Ruffaida yake, shiyasa nakeson samo masa matar da zata d'auke hankalinsa da wuri ya manta da wannan karuwar, na tsaneta yanzu sosai, ko ina take oho mata. Gwanda da Allah yasa banyi saurin had'a aurensu ba da yanzu ina da na sani" ta d'an ja k'aramar tsaki ta karb'i wayar da Amrah ke mik'a mata dan ta kalli hoton Khadeejah candy. Sosai ta yaba da kyawunta kuma ta tabbata Sadiq zai sota dan kyakkyawa ce son kowa k'in wanda ya rasa. Bata bar d'akin ba ta shiga yiwa 'yarta hira hankalinta kwance babu abunda ke damunta.

Lubiee @ 4pm


  A tsakiyar parlor take zaune rik'e da Qur'ani tana rera suratul Bak'ara cikin zazzak'ar muryarta, hankali kwance take karatun dan cika umarnin Ummu-Abdoul na cewa "ki yawaita karanta suratul bak'ara a gidanki, ko da baki samu dama ba, ki kunna a wayarki ki k'ure volume ya karad'e gidan dan karanta Suratul bak'ara yana korar aljanu daga gida" tayi nisa cikin karatun taji muryar Nafee na cewa "in zakiyi karatun ki shiga d'akinki mana kiyi. Sabon salo" had'e da yin tsaki ta bar wurin ta koma nata d'akin, bata dakatar da karatun ba bare ta tanka ta sai ma k'ara d'aga murya da tayi tana gyara muryar nata dan yayi dad'in sauraro.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


    Page 43


  Nuraddeen na kwance da yarinyar da aka kawo masa wacce a shekaru bazata wuce goma sha bakwai ba yaji anyi masa knocking, mamaki ne ya bayyana a fuskarsa dan babu wanda yasan wannan sabon gidan nasa da ya gina dan sharholiyarsa da 'yan matansa. Sai da aka sake knocking sannan ya mik'e ya d'auko rigarsa yasa ya isa wurin k'ofar yana cewa "wanene?". Sau biyu ya maimaita tambayan ba'a amsa shi ba hakan yasa ya murd'a handle na k'ofar, a hankali ya bud'e yasa kanshi yana lek'e, wayam ba kowa a bakin k'ofar. Fitowa yayi ya kalli parlorn ta ko ina bai ga alamun mutum ba, babu inda bai duba ba a cikin gidan bai ga kowa ba, a k'arshe dai yasa a ransa iska ne ke blowing k'ofar ya koma ya cigaba daga inda ya tsaya. (Wa iyazubillah).

Sadiq da ya samu damar fitowa daga gidan ba tare da an gansa ba, numfashi ya sauk'e tare da hamdala. A hanzarce ya shiga motarsa yasa key ya bar anguwan yana mai hamdala tare da k'issima abunda zaiyi wanda zai sa Mommy tazo gidan ta kama mijinta red handed. Addu'a yake har ya isa gida bayi da cikakken nutsuwa. Da ya koma ma zancen da Mommy ta tare sa dashi ya k'ara rud'ar dashi, bata yi masa maganan kaita office na Dady da yayi ba sai maganar Khadija candy da bai santa ba bai tab'a ganinta ba wai ita takeson ya aura ko yak'i ko yaso. Meh zai yi wa matar nan ne shikam? Bata k'yalesa ba sai da ta bashi numbanta had'e da tura masa hotonta ta kuma ja masa kunne akan lallai ya k'irata su sasanta kansu, duk wani dabara da iya tsara mace wanda ya sani ya tabbata yayi mata dan ta amince masa, a nata b'angaren kuma ta umarci Amrah ta fad'awa Candy komai dan tana son abun ya kankama cikin lokaci k'ank'ani.

•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°

Kwanaki biyu da faruwar hakan:- Ruffaida @ 11am


   Yau watsapp d'inta taji takeson kunnawa, ba dan komai ba sai don duba sak'onnin k'awayenta kuma taji lafiyar gida. Datan ta kunna kai tsaye ta shiga WhatsApp, messages ta gani rututu daga friends, har ma da 'yan uwanta na Zaria wanda ta tabbata basu san da maganar b'atanta ba. Tayi mamaki da bata ga sak'on Nuraddeen ba (ba abun mamaki bane a ganina) hakan ya sake tabbatar mata yaudararta yayi yake anfani da yarintarta da kuma son zuciyarta, hawaye taji ya sauk'o mata masu zafi, bata kai ga gogewa ba wani sak'o ya shigo mata ta watsapp.

Dubawan da zatayi taga Sadiq ne, messages 21 yayi mata, wasu ta gani, wasu waiting for this message, duk tsantsar damuwansa da ban hak'uri ne sai kuma inda ta shiga da yake tambaya. Ganinsa online yasa ta sake murmushin jin dad'i da bata san lokacin da ya kufce mata ba, tasan Sadiq bazai tab'a k'yamatar ta ba, duk abunda zai mata horo ne da kuma nuna bata yi dai-dai ba. Sai da ta goge hawayenta sannan ta rubuta "ina gaisuwa babban yaya" ta tura masa.

Sadiq a dai-dai wannan lokaci:-


   Zaune yake cikin motarsa a harabar gidansu Khadeeja candy, tun jiya Mommy ta gama isar sa da zagi dan bai je ganinta ba, shiyasa yazo ganinta bai iya jiran yamma yayi ba. Tun daga nesa ya hango ta cikin koriyar atamfarta, murmushin da ke bayyane a fuskarta ya k'ara mata kyau da wani annurin da bai tab'a ganin wata 'ya mace dashi ba, bai san lokacin da ya bud'e baki ya tsaya kallonta ba, sai wani mayen murmushi da ya biyo baya. Kallon k'urilla yake mata har ta iso inda yake, dai-dai glass na inda yake zama ta tsaya sannan tayi knocking dan tinted glass ne bata san yana kallonta ba.

Sai da ya tattaro dukkan nutsuwarsa sannan ya sauk'e glass d'in yana kallonta ba tare da ya yi mata murmushi ba, ganin ta sake masa murmushin nan nata da yake son zautar dashi ya kawar da kai shima ya mayar mata da martani yace "ki zagayo mana ki shigo, rana ai" had'e girarta tayi tace "kana nufin ba shiga zamuyi ba? Tun da ka k'irani kace zaka zo fa na sanar a gida" kallonta yayi dan yanayin maganarta ya burgeshi amma bazai samu ya shiga ba dan ba dad'ewa zai yi ba yana da wurin zuwa.

Dolenta ta shigo suka gaisa sama-sama sannan yace zai tafi, basu wani saba sosai ba shiyasa bai zage ba, a ganinsa sai sun saba sosai zai samu damar yi mata kowani zancen da yakeso ba wai ya b'oye cikin k'albinsa ba. Da mamakinsa ya tsaya kallonta lokacin da ta karb'i wayarsa da yake d'an chating da wani abokinsa tana cewa "bazaka tafi yanzu ba fah, ya daga zuwa zaka ce min zaka tafi" cikin wani salo tayi masa maganar wanda yake nuni da rashin jin dad'in maganarsa. Lock key ta danna a wayar sannan ta ajiye a cinyarta ta dawo da dubanta garesa, ganin kallonta yake yi yasa taji kunya ya lullub'eta, mik'a masa wayarsa tayi tare da rufe fuskarta da mayafinta tana dariyar k'arfin hali irin nata k'asa-k'asa.

Bata san ya akayi soyayyar Sadiq yayi mata cafka d'aya ba, tunda Amrah tayi mata maganarsa taji soyayyarsa ya d'arsu a zuciyarta, ganinshi da tayi yau cikin shigen k'ananan kaya ya sake fiddo da kamalarsa da kuma kyawunsa na d'a namiji, sai taji ina ma an tsayar da maganar aure tsakaninsu. A shirye take ta amsa muradinsa muddin ya nemi turo magabatansa ko da yau ne, a cikin kwanaki biyun da tayi magana dashi ta karanci abubuwa da yawa game dashi duk da ta lura baya wani sakewa da ita. 

Wayar ya karb'a ya ajiye a dai-dai lokacin da sak'on Ruffaida ya shigo masa, hasken da wayar ya kawo yasa yaga Notifications na messages d'in da suka shigo masa, kamar wasa yaga Sis Ruf ta masa Text, jikinsa har rawa yake ya bud'e wayar had'e da shiga kan sunanta, online ya gani a k'asar sunan, da hanzari ya shiga typing kamar haka "where have you been? Kada ki kashe wayanki yanzu zan k'iraki dan Allah. Am worried" sai da ya tura yaji muryar Candy tana cewa "lafiya?" Murmushi ya sakar mata yace "zuwa wurinki yayi min anfani, i have to go now, wani abu ya taso urgent, zamuyi magana a waya cus i hav a lot to tell you" murmushi ta sakar masa tace "olryt" ta bud'e motar ta fito. 

Dai-dai k'ofarsa tazo wucewa ya k'ira sunanta cikin sanyin murya murmushi fal fuskarsa. Murmushi ita ma tayi masa da ta juyo ganin kallon da yake mata, yace "kin min kyau, sosai Khadeeja". Farincikinta bai b'oye a fuskarta ba dan murmushi mai k'ayatarwa ta sake sannan ta sunkuyar dakai tana mai wasa da yatsunta, can ciki tace " thank you" sannan ta juya ta shige gida cikin sauri shi kuma ya ja motarsa ya bar gidan. 

A wurin wani bishiya yayi parking dan yayi magana da Ruffaida, bai bar wurin ba sai da ta bashi sabon layinta kuma ta rok'i kada ya fad'awa kowa sunyi magana sannan ya bar wurin. Sai dare ya samu damar k'iranta dan suyi magana saboda zirga-zirgan da yayi, sosai ya gaya mata kuskurenta kuma ya ja mata kunne akan barin gida tayi, dan dolenta ta fad'a masa zancen da taji Mommy da Daddy sunayi wanda yayi sanadiyyar guduwanta. 

A ranar dai bai k'yale Ruffaida ba sai da ta bashi labarin duk abunda ya had'ata da mahaifinsa, yayi Allah wadai da zuciya irin na Nuraddeen kuma yayi masa fatan shiriya, daga k'arshe ta bashi address na gidan Ummu-Abdoul, bayan yayi mata alk'awarin bazai bawa kowa ba sannan ya samu runtsawa ba tare da ya nemo Candy ba, mantawa da ita yayi a wannan lokaci dan Ruffaida da matsalolin gidansu da ya cika masa kwanya.

Washe-gari:-


  K'arfe goma yayi masa a k'ofar gidan Ummu-Abdoul, a waya ya k'irata ya sanar da ita isowanshi, bata fito ba sai da ta fad'awa Ummu-Abdoul dan dama da suke breakfast ta sanar da ita sunyi magana. Sosai tayi murna da taji isowarsa, har Parlor ta umarceta ta shigo dashi sannan ta kai masa ruwa da kanta suka gaisa sannan ta basu wuri bayan tayi sallama dasu dukka dan zata fita ta d'auki Lubiee su wuce Annur mosque, abunda yasa bata je office ba kenan yau.

Hira sukayi sosai na yaushe gamo, Ruffaida har da k'wallanta na tsantsan da na sani da kuma kewar gida. Sai da tayi mai isarta sannan suka fad'a neman yanda za'a yi su fahimtar da Mommy, ya sanar da ita sabon gidan da ya gani wanda ita ta tabbatar masa nasa ne dan yana kaita gidan kafin ta gudu. Shiru sukayi na 'yan mintuna sannan Sadiq yace "baki da wata da kike ganin in ta sanar da Mommy zata yadda? Dan ni tunanina ya tsaya cak" shiru tayi ta k'ank'ance idanunta alamar nazari sannan tace "ina da plan, and am very sure zai anfane mu. Matso kaji".

Bakinta ta kai dai-dai kunnensa ta sanar dashi abunda take ganin ya dace ayi, murmushi yayi tun kafin ta gama zancen nata, tana komawa mazauninta yace "Good idea. Amma kina ganin Anty YBK bazata gane ba?" Kai ta kad'a alamar a'a sannan tace "ka manta bata yi makaranta ba, muyi anfani da hakan wurin cimma burinmu" yayi na'am da batunta kuma sosai ya jinjina wa k'aramin kwanyarta daga nan suka shiga tsara yanda plan d'in zai kasance ba tare da an samu wani matsala ba.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


    Page 44


Pherty 


   Abun duniya duk ya taru ya mata yawa, har d'an rama tayi a cikin 'yan kwanakin nan. Bata san meh hakan ke nufi ba, tunda ya kawo ta ya ajiyeta bai sake waiwayanta ba, tun tana tsammanin zai bata takaddanta ta tafi har ta cire a ranta ta sa aka shigo mata da jakan kayanta, bata sake ganin ko da motarsa ba bare shi da kansa, hakan ya tabbatar mata baya gari. In taji gidan yayi mata zafi wani lokaci ta je wurin uwargidansa ta taya ta hira da sauran yaran. Ko waya bai mata ba ita ma bata k'irashi ba dan a ganinta ko tayi babu anfani, gwanda ta kyalesa yayi shawarar abunda ya dace da rayuwarsa.

Shirunsa ba k'aramin kasheta yakeyi ba, amma ya ta iya tunda ita ta jawa kanta, a kullum sai ta kulle kanta a d'aki tayi kuka mai isanta, ko abincin kirki bata iya ci duk da yasa driver ya kawo mata cefane masu yawa kamar babu komai tsakaninsu. Bata sanar da kowa daga gidansu tana gari ba dan tafi son idan sakin ya biyo baya su ganta kawai ta dawo musu, su d'and'ani wahalar da ita ma take sha a dalilin son zuciya irin nasu, a kullum sai ta yi musu Allah ya isa dan su suka jefata cikin wannan rayuwar, da basu so duniya fiye da yanda suke son lahira ba ta tabbata hakan bazai faru ba, wani zuciyar dai na nusar da ita cewa iyayenta sunga shi yafi dacewa da ita ne ko da kuwa son kud'in ma ya samu wurin a zuk'atansu, shiyasa take d'an tsagaita addu'o'in da take musu maras kyau.

Kamar kullum tana zaune a tsakiyar parlornta ta saka Tv a gaba idanunta k'yar akai amma hankalinta da zuciyarta basu kan abinda take kallo, hawaye taji ya silalo mata sirr! Ta lumshe idon nata ta bud'e ta janyo wayarta. Lamban Miemiebee ta shiga ta danna mata k'ira zuciyarta a cunkushe. Har ya gama ringing bata d'auka ba ta sake k'ira, sau uku tana k'ira bata d'auka ba hakan yasa tayi mata text "You don't know what am capable of. Kiyi wasa dani kiyi da na sani".

  Ajiye wayar tayi a gefenta ta jingina da kujera ta lumshe ido, ita ba wai tana son b'ata rayuwar Miemiebee bane, tana son ta samu ingantacciyar rayuwa ta daina sab'on Allah dan son zuciyarta, tunda suka had'u kuma ta gano kuskuren da take tafkawa ta k'udira a ranta sai ta kub'utar da Miemiebee ita kuma tayi k'ok'arin yak'i da zuciyarta dan samun rahamar mahaliccinta, yanzu matsalarta d'aya ta samu yafiyar mijinta, in har ta samu wannan toh zatayi komai da zai nuna tsantsar nadamanta da sauk'ar da kai wurin Allah, kuma tayi imanin cewa Allah mai rahama ne kuma zai gafarta mata.

K'arar wayarta ne ya dawo da ita hayyacinta, Miemiebee ce ke k'ira hakan yasa bata yi wata-wata ba ta d'auka ta kara a kunnenta, "Hello" tace cikin dakewar murya, yanayin muryar Miemiebee yasa ta fasa masifar da tayi niyya, kaman bata da lafiya ko kuma tayi kuka, ko dai ta fad'a wa Kamal ne? Kawar da tunanin tayi tace "kinyi abunda aka samu ko kuwa?" Sai da hawaye ya sulalowa Miemiebee sannan tace "na kasa, tunanin inda zan fara ne ya sani rashin lafiya, munje asibiti ma ance lafiyata k'alau damuwa ce kawai yayi min yawa, dan Allah ina rok'onki ki yi hak'uri, bazan k'ara aikata wannan kuskuren ba ko a haka kika barni na horu, amma please ku janye maganar in fad'awa Kamal, bazan tab'a iya fad'a masa ba wallahi" ta k'arashe maganar cikin kuka.

Murmushin tausayawa Pherty tayi sannan tace "kinsan bani da niyyar cutar dake sai nuna miki gaskiya da abunda ya dace? Dukkanmu munyi kuskure babba a rayuwa kuma dole mu girbi abunda muka shuka, nima yanzu haka Alhaji ya dawo dani gida dan bazai iya zama dani ba, na zama k'azanta kuma babu mai son zama da k'azanta, ki taimaki kanki ki tsarkake kanki, ki taimaki kanki ki nemi yafiyar mijinki, muddin ya yafe miki duk wani abunda zai biyo baya kada ki sa a ranki bare ya kawo miki nakasu ya hanaki neman gafarar Allah, ki sa a ranki abunda zai sameki ba komai bane illa sakamakon abunda kika dad'e kina aikatawa, kiyi tuba tsarkakakke, zakiyi mamakin abunda zaki samu nan gaba, shawarata d'aya ki gaggauta sanar dashi ko kuma ni in sanar dashi da kaina, kuma kinsan bazai tab'a yi miki dad'i ba, ki ji tsoron Allah, za'a mutu kuma za'a shiga kabari, za'ayi miki hisabi da duk wanda kika cuta kika shiga hakk'insa, ina guje miki ranar da zakiyi da na sanin k'in bin umarninmu...".

Maganganun Pherty sun shigeta, tun kafin ta kashe wayar take nanata "astaghfirullah wa atubu ilaih" a zuciyarta. Tayi kuka iya kuka tare da neman gafarar mahaliccinta, ta yadda ta kuma karb'i laifinta kuma insha Allah zatayi duk abunda suka buk'aceta, fatanta Allah ya gafarta mata kuma Kamal ya fahimceta yayi mata uzuri kuma yayi hak'uri su cigaba da rayuwar aurensu. Sallah tayi raka'a biyu tana mai tawassuli dashi dan neman biyan buk'ata, addu'a tayi sosai tana zubar da k'wallan tsantsar nadama da da na sani. 

Wayarta ta janyo ta tura masa text "U hav touched my hrt in a special way. No one has ever made me feel the way you do. I pray to God to make u mine in d next world... I can't imagine lyf without u, please be with me forever! Ina sonka, cum back soon ur baby is missing you". A ranar dai yini tayi tana istigfari da salloli. 

Kwana biyu da faruwar haka ya kama ranar Friday:-

Cikin Miemiebee da Pherty zaki rasa gane wacce tafi sauk'ar dakai da mik'a dukkan lamuranta ga Allah.A kowani lokaci bakinsu cikin ambaton Allah yake, istigfari da karatun Qur'ani suka mayar dashi abinci, ma'ana safe, rana da dare suna cikin yi. Suna k'ok'arin yin sadaka da kare kansu shiga duk wani abunda zai kawo shakku ko rauni cikin abunda suka yi niyya. Sun fawallawa Allah komai kuma suna neman yafiyarsa da rahamarsa, hatta sallahr dare yi suke haik'an su zubar da hawaye suna kwararo addu'o'i da neman yafiyar mahaliccinsu, fatansu da buk'atarsu Allah ya gafarta musu kurakuransu.

Miemiebee:-


  Yau Miemiebee ke sa ran dawowar mijinta, kamar yanda yayi mata text ya sanar da ita k'arfe 5 zai iso hakan ya faru. Damuwar ranta duk tayi k'ok'arin yakicewa kuma ta bawa kanta k'arfin gwiwan fuskantar mijinta da wannan batu, a lokacin da ta sanar da Pherty yau Kamal zai dawo sai da Pherty ta kwantar mata da hankali ta nuna mata anfanin yin hakan sannan ta k'arfafa mata gwiwa ta nuna mata ita da sauran k'awayensu suna tare da ita ko da kuwa kowa zai gujeta. Kyawawan kalmomin Pherty ya sata k'walla, tayi mata godiya sannan ta kashe.

Gidan ta gyara shi tsaf, ta sauya mazaunin komai dan ta k'ayatar dashi ta burgesa, komai a goge sai k'yalli da yakeyi. K'aton hotonsu da ta bayar akayi mata ta d'auko ta ajiyesa a saitin k'ofar shigowa a jikin bango, sai wani dogon abu ta k'asa wanda yake manne da glass an rubuta "you're welcome his Highness" da ratsin blue nd golden sai wutan da yake ciki yana canja launi.

Gyaran jikinta tayi har da jan lalle da bak'in filawa akayi mata, d'as a jikinta sai kyalli take kamar sabuwar amarya, duk da ramar da tayi ya bayyana sosai bai hanata yin kyau ba. Light makeup tayi tasa 3 quarter gown d'in ta blue da pink net da akayi masa ado dashi, bata d'aura komai kanta ba dan gyarar da akayi wa gashin nata ba na rufewa bane. Ta fito d'as da ita kamar wata 'yar Nigerian film sai zuba k'amshi takeyi.

Dining table ta nufa rik'e da wani dogon abu anyi design a jiki tare da rubutu 'yan k'anana wanda sai ka d'an matso kusa zaka gane abun da yake jiki. Daidai mazauninsa ta ajiye ta gyara food warmers d'in da ke kan table d'in sannan ta koma d'aki ta d'auko room freshner da kaskon turaren wuta, sai da ta turare dukkan gidan sannan ta sake bi da roomfreshner kala biyu, ita kanta tasan yau ni'iman da ke cikin gidan nan ya isa sauk'ar da nutsuwa da kwantar da zuciya. Tsayawa tayi ta bi d'akin da kallo sai taji wasu hawaye masu zafi na bin kuncinta, da hanzari ta goge dan kada ya b'ata mata kwalliyarta da takeson sace Kamal d'inta dashi.

K'arfe 5:50 dai-dai taji horn na motarsa, maimakon tayi farincikin zuwansa kamar kullum yau tsinkar zuciyarta ne ya tsananta, a take hawaye suka fara sintiri a kuncinta sai da tayi da gaske sannan ta iya tsayar dashi. Wutan palorn ta isa ta kashe, babu abunda ake gani sai wannan wutan da kuma rubutun da yake k'asar hoton nasu sai kuma wutan da ke jikin ACn da ke mak'ale a d'akin yana faman aiki. A gajiye ya sa key ya bud'e k'ofar, kai tsaye ya shiga bai kula da komai ba duk da yaji wani sanyin ni'ima da kuma k'amshin da ya bugi hancinsa. 

K'ofar ya mayar ya rufe sannan ya juyo cikin nutsuwa, idonsa ne yayi tozali da wannan welcome d'in sai kuma kad'an daga hoton da ta mak'ala a saman dan hasken ya d'an hasko masa, wani farinciki yaji ya ziyarcesa mara misaltuwa wanda har murmushi ya kubce masa bai san lokacin ba, a hanzarce ya kunna wutan dan ya kwad'aitu da ganin wannan hoto, yana son ganewa idonsa dukkansa ko zuciyarsa zai samu sa'ida.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


    Page 45


  "Wow" ya furta a fili sannan ya isa inda hoton yake yana shafawa. Kimannin sakanni goma sha biyar yana hakan daga bisani ya juya ya shiga kallon parlon. Komai ya sauya kuma yayi mugun yi masa kyau, "Oh My God" yake nanatawa yana juyawa a tsakiyar parlon tare da admiring komai na parlon, sunanta ya k'ira cikin sanyin murya yayi hanyar d'akinta, bai kai ga barin parlon ba ta fito daga bayan labule tana cewa "am here swtrhrt" ta langwab'e kai tana mai sake masa murmushi, ba k'aramin daurewa takeyi ba dan tun shigowansa ta shiga bayan labule take aikin sharar k'walla. 

Isowa wurinta yayi ko kifta idanunsa baya iya yi dan kyaun da tayi masa, d'aga ta yayi sama yana dariya tare da fad'in "nayi kewar komai naki Miemienah, dama kin iya irin wad'annan abubuwan shine bakya min. OMG! Bansan meh zan miki in nuna miki tsantsar farincikina ba" ya direta ya shiga juyata a hankali yana kallon irin kwalliyar da tayi masa, daga sama har k'asa ya k'are mata kallo, ita kuwa bata da bakin cewa komai sai murmushin da take sake masa, wanda har zuciyarta tayi farincikin faranta masa rai da tayi. 

Had'eta yayi da jikinsa ya bata hug d'in da shi kansa yasan na daban ne kuma yana daga cikin appreciation d'in da zai nuna mata a yau na faranta masa da tayi, cikin kunnenta ya rad'a mata "I love you Miemie" bata samu daman amsa shi ba ya had'e bakinsu wuri guda. Kasa daurewa tayi a wannan karon ta b'arke da kuka tare da k'ank'amesa kamar za'a gudu dashi, cak ya tsaya jin kukan nata da gaskiya take yinsa, a hankali ya k'yaleta yana mai kallon fuskarta.

  "Kada ki karaya" cewar zuciyarta, hakan yasa ta bud'e idanunta ta d'aura k'wayar idonta akansa, murmushi ta sakar masa ta rik'e hannunsa cikin nata idanunta bai sauk'a daga kan fuskarsa ba tace "am happy, am very happy da na saka farinciki irin haka" wani hawayen ya sake gangaro mata, share mata yayi da hannunsa idanunsa k'yar cikin nata yana son gano wani abu amma ya kasa ganewa, hakan yasa yace "lallai sai yau na yadda da cewa komai na sa mace kuka, ciki kuwa harda farinciki" hannunsa yasa dai-dai k'ugunta ya janyota daf dashi, fuskarsa kuma ya kusanto nata fuskar yana mai sake mata lallausan murmushi idanunsa na tura mata sak'onnin da ita kad'ai take iya ganewa.

"Kada ki sake zubar min da k'wallarki, idan kinji dad'i kizo tsakiyar parlon nan kiyi ta tsalle har sai kinji murnar ya isheki, in ma hakan bai miki ba come to me in d'aga ki sama kaman baby ina cafewa ina k'ara wullaki" dariya ya sata hakan yasa duk suka dara sannan ta jashi zuwa d'aki, sai da ta bashi ruwa mai sanyi ya sha sannan ta turashi bayi dan ya shirya kafin a k'ira Sallah. Wanka kawai yayi yasa k'ananan kaya mara nauyi sannan ya tafi sallah ita ma ta gabatar da nata. 

Bayan ya dawo ita tayi serving d'insa abinci yaci yayi nak sannan suka koma kallo, anan ma wani salon soyayyar ta zage takeyi masa shi kuma bakin nan a bud'e sai hak'oransa zaka hanga kamar gonar auduga. Sosai ta tafi dashi kuma ta burgeshi matuk'a, bai d'auka zai dawo ya sameta haka ba, dan lokacin da ya tafi ya barta a hali na rashin wal-wala da kuma rashin lafiya, ta yi masa ba zata kuma ta faranta masa, ji yayi soyayyarta ya mamaye dukkannin sassa na jikinsa, zuciyarshi da gangar jikinsa ya mallaka wa Miemie d'insa ita d'aya.

Bata sanar dashi komai ba har sai da ta shayar dashi zuma wanda shi kansa yasan yau shi d'an gata ne wurin Miemie, bazai ce bata tab'a yi masa abubuwan dad'i irin na yau ba amma zai iya cewa na yau d'in na musamman ne, sai dai meh dalilin yin hakan a yau? Ko akwai wani abu da take b'oye masa na farinciki da ya same su? Da hanzari ya kawar da wannan tunanin yasha romon da Miemie ta tanadar masa. Sai da komai ya wakana sannan tayi niyyar sanar dashi komai. Agogo ta duba taga k'arfe d'aya harda minti goma, sai da ta tattaro duk courage nata sannan ta k'ira sunanshi "Kamal" cikin sark'ewar murya da sanyi.

Bai fasa abunda yake mata da hannunsa ba ya amsa da "Na'am" "bacci ka fara?" Murmushin jin dad'i yayi sannan yace "ai yau bazan iya bacci ba Miemie, kin shayar dani komai a yau bazan tab'a manta wannan ranar ba". Ya dubeta cikin murmushi ya cigaba "tell me, menene my sugar? Yau sunaye kala-kala zan k'iraki dashi" kukan da take tarewa tun fara maganarsa ne ya kufce mata mai k'arfi, da hanzari ta toshe bakin ta mik'e zata bar kan gadon don kwafsawar da kukan ya mata.

Cak ya rik'e hannunta ya dawo da ita ya ajiye kanta bisa sabon mazauninsa wato k'irjinsa, a hankali yake shafa gashin kanta idanunsa a lumshe, dan kanta ta tsagaita kukan tana ce masa "am very sorry" bai amsata ba saboda abubuwa da yawa da yaji zuciyarsa na sanar dashi. Sai da yaji kukan nata ya lafa sannan yace "Tell me, meh ke damunki?" "Ba komai" ta furta a hankali dan a cikin wad'annan mintunan taji bazata iya sanar dashi komai ba.

Tashi yayi ya zauna ya kunna wutan d'akin sannan yace "tashi ki fad'a min duk abunda ke damunki tun kafin ranmu dukka ya b'aci" a kausashe yayi maganar dan nuna mata ta kai shi mak'ura, kafin ya tafi haka yayi ta binta ta fad'a masa damuwarta tak'i, yau dai bazai iya d'aga mata k'afa ba, ko ta fad'a masa ko ya nuna mata b'acin ransa kalan da bata tab'a gani ba kuwa. "Ba magana nake miki ba" ya sake fad'a yana kallonta, cikin mutuwar jiki ta zauna ganin ya had'e fuska kamar bai tab'a yin dariya ba, sosai ya tsoratata cikin i'ina tace "zan fad'a maka wallahi, amma 1st, u have to promise me bazaka yi min mummunan hukunci ba kuma zaka fahimceni".

Kallon da yayi mata ya sake kad'a 'yan hanjinta, tuni wani kukan yazo zuciyarta na tafasa, can ta tsinkayo muryarsa yana cewa "Miemie, ciki kika zubar ko? Babynah kika cire?" Ya k'arashe maganar hannunsa bisa cikinta haka idanunsa na kai, kad'a kai tayi alamar a'a sannan ta k'ara da cewa "No Kamal, ba haka bane. The thing is entirely different..." Numfashin da taji ya sauk'e ne ya dakatar da ita. "Da sauk'i" ya furta idanunsa na kallon k'asa, kallonshi ta tsaya yi idanunta bai daina zubar da hawayen ba tace "what if abunda nayi yafi hakan muni?" Kallonshi takeyi ganin reactions d'insa.

Rinannun idanunshi ya d'aura akan fuskarta, damuwa da firgici ya bayyana cikin kwayar idanunsa, muryarsa da ya gama disashewa yace "dont tell me kin b'ata womb d'inki? Ko ma cirewa kikayi gaba d'aya?" Jin kalamansa yasa taji zuciyarta ya mace, hannunsa ta rik'e tana mai kusanto shi, sai da ta shafa fuskarsa da hannunta na dama idanunta akansa tace "No Kamal, I've been..." Ta kasa k'arasawa ta lumshe idanunta k'yam, "tell me please" yace a hankali yana kallonta dan zuciyarsa ya karaya. A hankali ta furta "I have been cheating on you".

Kamar an tsikare shi haka ya mik'e ya tureta daga jikinsa, "what?" Yace cikin karaji da nuna tsantsar firgicin da ya shiga, kukan da takeyi ta cigaba da rerawa idanunta a k'asa jikinta ya gama mutuwa, cikin zafin nama ya fincikota ta zube a k'asa, kukan cak ya tsaya tana mai mamakin abunda Kamal ke shirin yi, bata kai ga dai-daita tunaninta ba taji shi kusa da ita ya rik'e kafad'unta ya d'agata, jijjigata yayi iya k'arfinsa cikin kausasassiyar murya yace "tell me Miemie, meh hakan ke nufi? gaskiya kike fad'a min ko sona kika daina kinaso mu rabu? Meh na gaza yi miki a rayuwa? So? Duk soyayyar da na baki, na k'ara da yarda da amanar zuciyata kika nemi yi min haka? Why?" Ya k'arashe maganar muryarsa na rawa alamar rauni, zuciyarsa tayi melting, meh Miemie ke son yi masa a yau? Meh take nufi? Shin ta manta dukkan abubuwan da yayi mata a rayuwa ne?

Bata daina kukan ba haka zalika bata iya amsa tambayoyinsa ba. A hankali ya saketa ya koma gefe yana mai juya mata baya, sai da suka kai minti uku kowa da abunda yake ransa sannan tace "Kamal ka min komai a rayuwa, ka bani so, k'auna, dukiya da komai ka bani, abu d'aya ka kasa gane min, ka kasa biya min buk'atana d'aya da kullum nake binka dashi..." Cikin zafin nama ya finciketa yana cewa "menene? Fad'a min abunda na kasa miki da zai sa ki neman wani a waje?" Sai da ta lumshe idanunta sannan tace "Ba wani ba Kamal, wasu zaka ce, dan yau bazan b'oye maka komai ba" a hankali ya saketa yana kallonta, idanunsa yayi ja sai hawayen da ke sauk'a daga idanunsa.

Bata b'oye masa komai ba cikin abubuwan da tayi, kuma bata b'oye masa cewa tun kafin tarewarsu ta fara hakan ba, ta nuna masa tsantsar nadamanta akan ya yafe mata kuma ta nuna masa cewa yanzu shirye take ta zauna dashi zama na amana, zaman da ko kallon wani namiji bazata k'ara ba bare sha'awarta yaci galaba akanta, zata yi k'ok'arin bin duk wani hanyar da addini ya tanadar dan kare kanta daga mummunan sha'awa irin wanda takeyi a kwanakin baya.

Har k'asa ta duk'a tana mai neman yafiyarsa, daga shi har ita kuka sukeyi mai cin rai, ashe haka Miemie ke yi a bayan idonsa? Miemie k'anwarsa da ya yadda da ita fiye da komai? Ita da ya bawa ragamar soyayyarsa da komai nasa ita ce zata yi masa haka? Zuciya ne ya d'ibesa ya hau kanta da duka, idanunsa ya rufe sai hangota yake tare da wasu mazan, ji yakeyi ina ma ya mutu da ganin wannan rana, dukanta yake yana yi mata Allah ya isa ita kuwa banda kuka da magiya babu abunda ta iya tab'ukawa, bai k'yaleta ba sai da yaga tayi lak'was tana fidda numfashin wahala mai k'arfi.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


          Page 46


Washe-gari(Asabar):- Sadiq da Ruffaida


  Dariyar k'eta yakeyi mata duk da sitiyarin mota na hannunsa yana driving, baki ta turo ta d'auke kai dan har cikin ranta ya b'ata mata rai, ya za'ayi yayi waya da wata a gabanta har da k'iranta my one? Bata san ya akayi ta kasa b'oye b'acin ranta ba, dogon tsakin da ta ja ne yasa ya kashe wayar ya fuskance ta har ya gano ranta ne ya b'aci shine yake wannan dariyar.

"K'anwata wai sona kikeyi ne yanzu? Kishi kike baki son inyi aure?" Amsa shi da bata yi ba yasa ya cigaba da magana "naga alamar baki tarbi wannan Antyn naki ba, Candy ce fa wacce na fad'a miki Mommy ta bani ita, actually yarinyan ta had'u ne tuni ta sace zuciyana nace na yadda zan aureta, kin ganta kuwa? Kyakkyawa, silent nd most of all romantic, ke sai kinji muryanta ma..." Dakatar dashi tayi da cewa "wai abunda yasa ka d'auko ni kenan? Banson hirar nan" ta k'arashe maganar tana mai nuna tsantsar b'acin ranta.

Tuni ya sha jinin jikinsa yayi shiru dan yaga alamar bata d'auki maganar nasa a wasa ba. Har suka isa gidan Anty YBK bata sake yi masa magana ba, tana ganin dai yana d'auka waya yayi danne-danne ya ajiye, da alamu sharing text message sukeyi da wannan yarinyar. Hawaye ne ta ji yana sauk'o mata bisa k'uncinta, da wuri ta b'oye fuskarta ta goge har suka isa basu daina musayar text ba.

Kai tsaye suka shiga gidan, bayan yayi parking tare suka fito suka nufi cikin gidan sai murmushi yake zabgawa ka rantse wurin budurwar tasa yazo, can ciki ta ja tsaki sannan ta danna bell d'in, basu jima da dannawa ba d'aya daga cikin masu aikinta ta bud'e musu. Russunawa tayi tace "you're welcome", shi kad'ai ya amsata ita kuwa tuni ta wuce d'akin Anty YBK tana faman kumbure-kumbure. 

A kujeran parlon ya zauna ya cigaba da chatting d'insa ko damuwa da yanayin Ruffaida bai yi ba. Tare suka fito da Anty YBK hannunsu sak'ale da juna, ganin waya a hannunsa kuma murmushin fuskarsa bai d'auke ba yasa tace "wai basu gajiya da juna ne?" ta ja k'aramar tsaki. "Meh kika ce?" Cewar YBK tana kallonta dan taji kamar tayi magana can k'asa, ba komai tace sannan suka isa tsakiyar parlon suka samu mazauni.

Hira suka shiga yi tsakaninsu suna dariya, (YBK uwa ce ga Mamu, baban Mamu yaya ne gareta, d'anta Allah ya azurtashi da dukiya ya d'aukota daga Zaria ya kawo ta wannan makeken gidan ya ajiyeta da masu aikinta, babu abunda ta nema ta rasa). "Ni fa nazo miki hutu ne, kuma kamar bak'ya buk'atana tunda yanzu kin daina nemana ko a waya ne" cewar Ruffaida tana turo baki. "Kaji min ja'irar yarinya, dama Esther nake samu ta duba min lambobinku tana k'ira min ku muna gaisawa, toh yanzu bata nan taje hutu, sauran kuma duk ba can muke d'asawa ba dan basu jin hausa, maganar kuramen nawa kuma ba ganewa suke yi ba" dariya sukayi mata dukka suka cigaba da hirarsu.

Lokacin da Sadiq zai tafi har waje suka rako shi ta d'auko jakar kayanta sannan sukayi sallama ya wuce su kuma suka koma ciki. Hira sukayi ranar da Anty YBK kamar ba gobe, a lokacin da ta mik'a mata wayarta dan ta k'ira mata Mamu k'arya tayi mata wai wayar a kashe. Can dare sannan ta samu damar aiwatar da abunda tayi niyya, simcard na Anty YBK ta cire ta sa a nata wayar dan kada ta b'ata musu plan in an k'ira dan da wayarta zasu yi anfani.

Washe-gari


  Kamar yanda sukayi da Sadiq yau da ya kama ranar sunday zasu yi anfani da wayar Anty YBK su k'ira Mamu a matsayin Anty YBK ta basu sak'o su fad'a mata. Haka kuwa akayi, sai da Sadiq ya tabbatar da Daddy yazo wannan gidan da wata budurwa mai k'arancin shekaru ya k'ira Ruffaida ya sanar da ita. K'uryar d'aki ta shiga ta bar YBK a parlor dan aiwatar da buk'atarsu.

Sai da ta mak'e murya ta gwada yanda zatayi mata magana ba tare da Mamu ta gane ba sannan ta danna mata k'ira. "Salamu alaikum" cewar Mamu bayan ta d'aga wayar, "wa alai..." k'iris ya rage Ruffaida ta amsa, hakan ya sa ta toshe bakinta dan kada qarashen amsawar ya shiga kunnuwan Mamu, tuni ta kawar da batun tace "good afternoon ma, Madam ce tace kije Gishiri ki karbo mata abu yanzu, kamar atamfa tace ko meh? Tace dai in turo miki address na gidan".

Yanayin yanda tayi mata maganar kamar wacce hausa bai zauna a bakinta ba, hakan yasa Mamu bata kawo komai a ranta ba tace "Toh! Ita kuma wa ta sani a nan Gishiri" "i don't know ma, and tace kije da kanki kada ki tura driver ko Ruffaida, in kuma baza ki je ba ki fad'a mata tun wuri taje da kanta" sai da ta dara sannan tace "ohh Mama! yanzu zanje dan dama fita zanyi. ki gaida min ita" ta kashe wayar ba tare da ta amsa ba sannan ta tura mata address d'in.

Mintuna 30 da faruwar hakan:-


  Agogon hannunsa yake dubawa damuwa fal ransa, k'aramin tsaki yake ja lokaci zuwa lokaci. Can ya hango motar Mamu, ajiyar zuciya ya sauk'e tare da furta Alhamdulillah a fili. Ganin a waje driver yayi parking Mamu ta fito ta d'auki wayarta ta duba ta sake d'aga kai ta kalli numban gidan ya tabbatar masa cewa tanason ta tabbatar da shine gidan ko kuwa. Sai da ya tabbatar ta shiga sannan ya b'alle nasa murfin motar ya fito ya isa inda motar Mamu ya tsaya.

Bai amsa gaisuwar drivern nasu ba ya lek'a cikin gidan, Mamu ya gani tsaye dai-dai motar Daddy tana dubawa, da alamu tayi mamakin ganin motar, sa ido tayi a kan glass na motar tana duba abu, gani yayi ta hanzarta ta koma d'ayan b'angaren ta sa kai, sai da ta tabbatar da abunda ta gani sannan ta wuce cikin gidan fuu kamar iska. Ciki ta shige ba tare da tayi shakku ko jin tsoro ba, shima a hanzarce ya shigo gidan ya isa gefen motar da yaga Mamu ta lek'a, shima kansa yasa ya k'ura idanunsa dan ganin abunda yasa Mamu ta shige gidan cike da zak'uwa. "Ahh! D'an kwali ne fa" ya fad'a a fili had'e da yin dariya.

A gaggauce shima ya nufi cikin gidan, muryoyinsu da yaji ne yasa shi shiga kai tsaye dan ayi komai dashi. Tsaye Nuraddeen yake sanye da boxers yarinyar kuma duk'unk'une cikin bargo da alamu ba komai jikinta, Mamu da ke tsaye hawaye na kwaranya daga idanunta kallonsu take dan har ila lokacin zuciyarta bai yadda da abunda ta gani ba. Sadiq ne yayi gyarar murya duk suka juyo suna dubansa, sunyi matuk'ar mamakin ganinsa a wannan wuri hakan bai b'oyu a fuskokinsu ba.

"Babu abunda nake buri a rayuwa irin inga ranar da zaki ganewa idonki abunda wannan..." Ya nuna shi da yatsa cike da k'yama sannan ya cigaba "yake yi a bayan idonki ba, wala alla ko zaki gane kurakuran da kika tafka a dalilin makauniyar son da kike masa, daga ciki kuwa harda banzatar da amanar da Maman Ruffaida ta baki" kukan ta ya tsananta a wannan lokaci neman durk'ushewa take Sadiq ya rik'eta fuskarsa na nuna halin da zuciyarsa ya shiga na tausayi da kuma tsanar hali irin na mahafinsa.

Cike da tsana yake kallonsa, da alamu Nuraddeen bai damu da abunda ke faruwa ba a yau dan babu alamar firgici ko tsoro a tattare dashi. "Kai mahaifina ne, amma bazan b'oye maka ba tun ranan da abokaina suka fara nusar dani halayenka, suna min gori kuma na bincika na tabbatar da gaskiyar zancensu naji na tsaneka, ban tsananta tsanar da na maka ba sai ranar da ka b'ata rayuwar Ruffaida kuma kake anfani da soyayyar da mahaifiyata ke maka kana cutar da ita kana hanata ganin gaskiya, tun ranar da kayi sanadiyyar barin Ruffaida gida nayi alwashin sanar da ita gaskiya, ban samu damar yin hakan ba sai yau kuma banyi da na sani ba sai ma farincikin da na shiga, atleast Mommy zata koyi wani darasi na rayuwa".

Cike da zafin nama Nuraddeen ya iso inda yake ya cakumosa ya janyosa kusa dashi "ashe baka da hankali ban sani ba? Ubanwa ya fad'a maka ina da gida anan da har zaka kawota?" Hannunsa ya buge ya koma baya yana kallonsa cikin raini, yaja tsaki yace "baka fa da sauran girma a wurina bare d'aga muryarka ko fad'anka ya yi tasiri akaina, shawarata d'aya ka canja hali tun kafin lokaci ya k'ure maka" mari Nuraddeen ya sakewa Sadiq yana huci, jin fad'uwar abu "rigijib" da suka ji daga bakin k'ofa ne ya dakatar dasu dukka, ganin Mamu sukayi kwance a k'asa babu numfashi ko kad'an a tare da ita. 

Miemiebee @ 1:50pm


  Kwance take a d'akinta jikinta duk ya mata tsami, idanunta sunyi luhu-luhu dan kukan da tasha tun daren jiya. Jin motsin mutum a kanta yasa ta d'ago a firgice, rabonta dashi tun jiya da ya gama jifgarta ya fice, ko motsinsa bata sake ji ba sai yanzu da yazo yayi mata tsaye aka. Kallonsa tayi tun kafin ta kai ga saita idanunta akansa dan zugin da idanunta ke mata taji ya watso mata kud'i bisa fuskarta, ba shiri ta rufe idanun.

Cikin kakkausar murya yace "ki bar min gida yanzu-yanzun nan, wallahi idan na dawo na sameki sai na lahira yafi ki jin dad'i" fuu ya fice ko sauraron magiyarta da k'aryar kukanta bai tsaya yi ba. Tana jin k'arar motarsa ya fice daga gidan zuciyarta na yi mata k'una, ji take ina ma bata sanar dashi ba, ina ma bata fara aikata wannan mugun abu ba, shin nata illar zinar yafi na Pherty ne? Duk cikin labaran da Pherty ta bata game da abunda ya faru da ita bayan ta fad'awa Alhaji babu duka a ciki, shin soyayyar da Kamal yake mata bai kai na wanda Alhaji yake yiwa Pherty ba ne? (Ni kuwa nace ko kad'an, kowa da irin nashi sakayyar, kuma anfani da tunani da hankali na d'aya daga cikin banbancin yaro da babba kamar yanda kuka gani akan Kamal da Alhajin Pherty). 

A fili ta furta "na shiga uku ni Maryam" tana mai d'aura hannayenta aka. Sai da tayi kuka mai isanta sannan ta d'auki 'yan kayanta cikin k'aramin akwati ta fice daga gidan tana mai fargaban abunda zai faru a can gida Yola, ta tabbata idan mahaifinta yaji abubuwan da ta aikata kamota zaiyi ya take wuyanta da k'afarsa har lahira zai kaita. Jabi park ta isa direct, motar Yola ta shiga zuciyarta a cunkushe idanunta sun bushe ko kukan ta kasa yi banda kukan zuci da da na sani babu abunda takeyi.


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


          Page 47


Lubiee @ 2:30


  Tun safe take aiki d'aya a gidan nan na ganin yanda za'ayi ta shiga d'akinsa, duk iya k'ok'arinta na ganin ta shiga d'akin Abubakar abun ya faskara, Nafee ta bararraje ta b'oye makullin, da alamu ta gano abunda Lubiee ke son yi a 'yan kwanakin nan, dan duk wani abunda takeyi sai ta nemi ta yanda tayi Abbakar ya hana, sun dinga fad'a kenan akan hakan dan ita cewa tayi bazata daina addininta akan wata banza ba.

A kullum sai ta faki idon Nafee ta d'auke robar swan d'in da Abubakar ke sha, ta juye ta d'ura masa ruwan Zamzam d'in da akayi tofi a ciki sai ta ajiye a cikin fridge dan kawai Abubakar ya samu ya sha. Kuma Alhamdulillahi ba'a tab'a kamata tanayin hakan ba bare a samu matsala, yanzu dai binciken d'akin nasa ne ta kasa, kuma tayi alwashin a week d'in nan babu abunda zai hanata shiga ko da kuwa ana ruwan wuta.

Ganin babu yanda zatayi ta shiga ne yasa ta cire rai, amma ta sa a ranta sai ta samo yanda zatayi dan haka kawai wata bazata zo cikin gidanta ta rabata da mijinta ba. Qur'an ta d'auka ta bud'e daga inda ta tsaya ta cigaba cikin muryar nan nata mai zak'i, karatun nata ya karad'e cikin gidan, duk nacinka da k'in jin sauraron Qur'an toh dai Lubiee sai ta sa kaji ko da kuwa shaid'anu na yawo akanka. 

A iya kwanakin nan da ta duk'ufa ta rik'e addininta wani nutsuwa ke shigarta, duk damuwarta ya yaye haka zalika karatun da takeyi yana kwantar mata da hankali, anya akwai wani maganin da ya wuce Alqur'ani mai girma? Tabbas babu, take amsawa kanta, dan da akwai da tuni ta samu daga wurin 'yan uwanta da take kai musu k'arar Abubakar, su d'in ma addu'a suke cewa tayi a kullum amma bata tab'a d'aukan addu'an da suke nufi shine wanda Ummu-Abdoul da malamin Annur mosque suka bata ba.

Miemiebee @8pm a garin Yola


   Rik'e da jakarta ta fito daga cikin park d'in fuskarta duk a kumbure, sai da ta d'auki mintuna goma sannan ta samu d'an acab'a, hawa kawai tayi bayan ta fad'a mishi inda zai ajiyeta ko kud'in da zata bayar bata tambayeshi ba, ta gaji matuk'a jikinta yayi tsami, babu abunda takeso yanzu irin ta kwanta hak'ark'arinta ya huta. Tana sauk'a daga kan mashin ta mik'a masa dubu ta shige gida bata jira ya bata canjinta ba.

"Assalamu alaikum" ta furta muryarta na rawa, sai da ta sake maimaita sallamar sannan taji mamanta ta amsa ta k'ara da cewa "bismillah, waye?" jikinta na rawa sosai tasa k'afarta cikin parlon idanunta a k'asa, jin muryar mamanta tayi cike da mamaki tana cewa "Miemie? Yau kuma zuwa gida ba sanarwa?" Kuka ta fashe dashi ta isa wurinta ta fad'a jikinta suka zauna a kujerar da Mama ta mik'e dan mamakin ganinta cikin dare haka, kukan da taji tana yi ya sake sata wani tunani.

Mamaki k'arara ya bayyana a fuskarta, yawu ta had'iye mai taurin gaske sannan ta samu damar yi mata magana. Cikin sanyin murya tace "meh ya faru? Ba tare dashi kuke ba?" Girgiza mata kai tayi alamar a'a, "sa ki yayi a jirgi yace kizo gida zaiyi tafiya ko?" Ta sake jefata da wani tambayan. Sosai ta shiga rera mata kuka tare da k'ank'ameta, bata iya furta komai ba dan bata san meh zata ce ba, ta ina zata fara? Tayi zina kamal ya korota ko ya saketa? Inaaa! Kaico tayi da wadaran rayuwar da ta d'aurawa kanta.

Rarrashinta Mama ta shiga yi tana bata baki. Har babanta ya shigo bata iya yin shiru dan amsa masa tambayoyinsa ba, tunaninta d'aya ta ina zata fara? Meh zata ce? Ire-iren tambayoyin nan ke k'ara sa ta kuka kamar ranta zai fita. Babanta ne yayi umarni da bincika cikin jakanta ko za'a samu wani abu na shaidar saki, dan izuwa lokacin sun fara zargin ko sakinta Kamal yayi. Zazzage kayan akwatin dukka sukayi amma babu komai sai kaya kala biyar da kud'ad'e, ko d'an turare da d'an kunnaye babu.

"Meh yake shirin faruwa? Wannan wani irin tafiya ne babu kayaki irin na mata?" Tambayar da yake yawo a kansu kenan. Ido Mama ta sa mata tace da mijinta "kaga kuma jikinta kamar wacce ta sha duka, wani wuri a kumbure wani wurin kuwa kamar jini ya taru. Nikam ko b'arayi ne suka shiga gidan naku?" "A'a" ta amsa a take kukan da take yi na k'ara tsananta, tun yana mata da rarrashi har ya fara masifa yana daka mata tsawa akan tayi shiru amma fir tak'i dan tasan muddin tayi shiru toh sai ta nemi abun fad'a.

Wasa-wasa kwana biyu babu abunda Miemie ta fad'a musu, banda kuka babu abunda takeyi. Sun k'ira Kamal sun tambayeshi yace su tambayeta ita tasan komai. "Ya saketa ne?" Tambayarsu amma yak'i amsa tambayar, yin duniyar nan yak'i amsa su daga k'arshe ma daina d'aga wayar yayi dan bazai iya d'aukan abunda suke masa ba, ita da tayi ya dace ta fad'a musu, tunda tayi shiru toh shima bazai fad'a ba sai dai suyi ta zama a haka.

Ruffaida, Sadiq da Mamu a Asibiti:-


  Kwanan Sadiq da Ruffaida biyu a asibiti akan Mamu jiki yak'i sauk'i, banda kuka babu abunda takeyi tak'i kwantar da hankalinta, a kullum in Nuraddeen yazo dubata juya masa baya take bata son ganinsa, shi kuwa laifin duk ya d'aurawa Sadiq kuma gar yake fad'a masa "kana son kashe mahaifiyarka a banza" babu wanda ya tab'a tanka shi sai rana na uku da yazo, juya masa baya tayi kamar yanda ta saba.

Ajiye mata abunda yazo dashi yayi ya isa inda Sadiq da Ruffaida ke zaune yace "kaji dad'i? Ka had'a mamanka da ubanka fad'a duk lokacin da na shigo ta juya min baya? Ga halin da ta shiga na rashin lafiya? Kasheta kakeson..." Muryar Mamu ne ya katsesa "ka fice min daga d'akin nan, we've endured enough. Bamu buk'atarka kuma banason ziyararka, d'ana kuma soyayya ce tsakaninmu da har ya nemi gyara min rayuwa. Allah ya isa tsakanina dakai Nura, bazan tab'a yafe maka ba" ta k'arashe maganar tana kuka.

Sadiq da Ruffaida suka isa inda take suna rarrashi, shi kuwa bayi da bakin magana sai da yayi minti uku a tsaye daga bisani ya fice daga d'akin a zuciye.

Tun daga ranar bai sake zuwa ba, kuma bata k'ara kwana uku ba aka sallameta dan sosai tayi k'ok'arin yakice duk wani damuwa nata dan tanason bawa Nuraddeen kunya. Ranar da ta koma gida a ranar Ruffaida ta koma gidan Ummu Abdoul dan alk'awari tayi bazata sake zama inuwa d'aya da Nuraddeen ba. A ranar Mamu ta tattare kayanta kuma ta umarci 'ya'yanta da kuma masu aikinta duk su wuce gida washe-gari ta sallamesu, kowacce ta bata kud'in aikinta sannan ta shiga d'aki dan kwanciya.

Ahankali ya shigo d'akin cikin sand'a kamar b'arawo. Cikin baccin da ya d'auketa taji yana shafa fuskarta ahankali tare da k'iran sunanta cikin wani sigar da yake anfani dashi a duk lokacin da yayi mata laifi yana son shawo kanta. Bud'e idanunta tayi ahankali ta sauk'e su akan fuskarsa da kullum take ganin annurinsa, a yau kuwa bak'i da muguwar tsanarsa ne ya dirar mata. Cikin zafin nama ta turesa tare da mik'ewa tsaye tana k'are masa kallo "lallai wannan mutumin ya cika d'an bariki, meh yake nufi da zuwa kusa da ita har yake gigin tab'a ta? Lallai mutumin nan d'an rainin hankali ne" maganar da yayi ne ya katse mata zancen zucin da takeyi. 

"Haba matata, yi hak'uri ki daina fushi dani, ki kwantar da hankalinki muyi maganar nutsuwa ki fahimceni, kinsan ina sonki kuma nasan kina sona, sharrin shaid'an ne da kuma Ruffaida da take ziga Sadiq, ba dan hakan ba duk abun nan bazai faru ba kinsan waye ni kuma kinsan halina" murmushin takaici tayi tana mai girgiza kanta had'e da jinjina k'arfin hali irin na Nuraddeen. "Hmm! K'warai kuwa nasan halin ka, kuma daga ciki har da son zuciya da dad'in baki, kai yanzu baka ji kunya ba ka lallab'o har d'akina wai kazo mu fahimci juna? Fahimtan meh bayan abunda na gani?" Yatsunta biyu ta murza sukayi k'ara sannan ta nuna sa da yatsa tace "ka fita idona ka shiga taitayinka? A yau nake neman takardata daga wurinka dan bazan iya zama da fasik'i mazinaci ba, na tsaneka na tsaneka Nuraddeen" ta k'arashe maganar tana mai fashewa da wani irin kuka.

Wurinta ya iso da hanzari yana neman rik'eta ta ja baya tana mai tsayar da kukan da takeyi, nuna shi tayi da yatsa tace "kada ka kuskura ka tab'a ni. Kuma barin fad'a maka, marainiyar da ka cuta kayi anfani da yarintarta ka cuceta ka cuci rayuwarta wallahi sai ka gani a kwanon cin tuwonka, duniya ne duk abunda kayi wa wani Allah sai ya saka wa me shi, ko ba a nan duniya ba akwai ranar hisabi..." 

Hannunta ta had'e biyu ganin yana isota had'e da bud'e baki alamar zaiyi magana tace "am begging you kada ka sake furta uffan muddin ba saki zaka furta min ba, nayi da na sanin son mutum irinka, nayi da na sanin yi maka makauniyar so na baka yadda da dukkan abunda ya dace mace ta gari ta bawa mijinta, zan iya cewa har wanda bai dace ba. Please ka fice min daga d'aki banson magana dakai, banson ganinka kuma bana buk'atar jin ko wani irin kalma daga wurinka muddin ba saki ba" bai saduda ba ya matso kusa da ita tare fad'in "Haba Mamu..." Hannayenta biyu ta toshe kunnuwanta dasu ta kwalla ihu hawaye na malala daga idanunta tana cewa "wayyo Allah".


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


          Page 48


  Isowa yayi inda take ya toshe bakinta da hannunsa, sosai ya kid'ime dan baya son yaransa suji abunda ke faruwa musamman Sadiq, baya son ya gansa d'akin Mamu. Bud'e k'ofar ya k'ara rud'ar dashi, ya ma rasa meh zaiyi har a lokacin ya kasa sake bakinta da ya toshe ita kuwa bata daina kururuwa tana k'ok'arin k'watar kanta had'e da yin ihu ba duk da ba fita yakeyi sosai ba dan hannunsa da ya danne bakin dashi. 

Sadiq, Amrah da Shamsu ne suka shigo d'akin hankali tashe jin ihun da mahaifiyarsu ke zabgawa kamar taga mutuwa. Cak suka tsaya ganin Daddy ne mak'ure da ita, Sadiq ne yayi azama ya iso inda suke yayi k'ok'arin cire hannunsa daga bakin mamansa, turesa yayi ya janyo mahaifiyarsa kusa dashi yana mai duba lafiyar jikinta. "Lafiyanki k'alau ko Mommy, babu abunda yayi miki? Tell me please ki daina kuka" duk zancen nan yana yi ne yana duba jikinta dan ganin illar da mahaifinsa yayi mata, sai da ta tabbatar masa ba abunda yayi mata sannan ya samu nutsuwar kallon mahaifinsa.

Idanunsa tuni sun rine sunyi ja dan a duniya in akwai abunda ya tsana bai wuce a tab'a mahaifiyarsa ba, bare shi baban da ya tsana a yanzu shine zai tab'a ta? ya b'ata musu suna kuma yayi biris kamar bai aikata laifi ba tsabar shi d'an bariki ne rik'akk'e? Da iya k'arfinsa ya isa inda yake ya turesa zuwa bakin k'ofar, banda huci babu abunda yake yi dan b'acin ran da ya shiga ba kad'an ba. 

Har bakin k'ofar ya fidda shi sannan yace "baka da tausayi baka tsoron Allah Daddy, ka tarwatsa mata zuciya kuma kazo neman nakasa mana ita? Dan kai ka nakasa kanka ka nakasa rayuwarka shikenan sai ka nakasa mana wacce zamu gani a rayuwarmu muji dad'i, kasheta kake son yi ko meh? Meh kake nufi da rayuwar mu Daddy? Meh Mommy ta maka da kake saka mata da hakan? Meh zan fad'a maka da zai sa kayi zuciya kuma kayi anfani da karatun da aka yi maka na islamiyya, ni ina shakku ma, anya ka tab'a zama an koyar dakai tauhidi? An tab'a fad'a maka azabar Allah ga duk wanda ya sab'a masa ya bi son zuciyarsa? Kaico da girma irin naka maras anfani".

Cikin jajayen idanu ya juyo yana kallon Mamu. "Shin bakuyi bincike akan wannan mutumin kafin ki auresa ba? Laifin waye zan gani a cikinku? Ke da kika auri mara ilimi irinsa ko kuwa shi da yake take dokokin Allah yana sane? Na tabbata daga sama bazai d'auko hali irin wannan ba sai dai tun asali yana da wannan halin a jikinsa na yanzu yafi k'amari. Shin tun kafin kuyi aure kike masa wannan makauniyar son kika kasa ganin halinsa? Ko kuwa maganar baturen yayi gaskiya na cewa "Love is not blind, it see's all but doesn't mind" indai kinsan haka halin wannan mutumin kika auresa toh kin cuci kanki kin cuci 'ya'yanki".

Sauk'ar mari yaji bisa kuncinsa cikin rashin tsammani, runtse idanu yayi zuciyarsa na tafasa kamar ansa masa garwashi mai zafin gaske. Ba kowa ne ya maresa ba sai Nuraddeen, wani abu yaji a makoshinsa kamar dutse, zazzafar hawaye ne ya fara fita daga idanunsa, a duniya zai iya cewa bai tab'a jin b'acin rai irin wannan ba, wani zuciyar ne ke ingiza shi rama marin nan dan mahaifinsa bayi da wani girma ko mutunci yanzu a idanunsa, amma wani b'angare na zuciyarsa na haninsa da hakan yana mai sake tunasar masa da cewa "duk abunda mahaifinka yayi a rayuwa dole ka bashi girmansa da darajarsa muddin kana son rabauta" kukan da Mamu takeyi da k'arfinta ya sake karya masa zuciya.

Silalewa tayi a k'asa kuka na cin k'arfinta, Amrah da Shamsu suma kukan sukeyi dan abunda ke faruwa a yau ba k'aramin girgizasu yayi ba. Wurin Mommy suka isa suka had'e kai suna mai cigaba da yin kuka wiwiwi. Waigowa yayi zufa ya wanke masa fuska, kallon mahaifinsa yayi cikin ido yace "bazan gaji da fad'a maka gaskiya ba, in har baka ji nasihana ka daina bin yaran mutane kana b'ata musu rayuwa ba duniya zata nutsar dakai, mark my word". Yana gama fad'an haka ya fice ya bar musu d'akin, duk da k'iran da Mamu ke masa bai sa ya tsaya ba, yana jin irin kukan da sukeyi ita da k'annensa ya toshe kunne ya bar side nasu ya wuce d'akinsa.

Washe gari da sassafe ya tattara kayakinsa da duk wani abunda zai buk'ata ya bar gidan. Mutanen gidan basu tashi tafiya ba sai 10am. Sai da Mamu ta tabbatar kowace mai aiki ta kama gabanta sannan ta had'o kan yaranta suka fito. Anan ne akayi daru dan rufe ido Nuraddeen yayi yace ba inda zasu je, da yaga bazata saurareshi ba yace toh ta ajiye masa yaransa ta tafi duk inda zata je ita d'aya.

Bud'an bakinta sai ce mishi tayi "saboda ka samu damar wargaza tarbiyyar da na basu?" Babu yanda ya iya dole ya barta suka tafi bayan ta duba ko ina babu Sadiq babu dalilinsa, ta k'ira wayarsa ma a kashe, da alamu fushi yake da iyayen nasa dukka, hak'uri ta bawa kanta kuma tana da yak'inin duk inda yaje zai dawo ya sameta a nan gidanta da ta saya na Zaria. Bankwana sukayi da garin Abuja suka wuce garinsu na gado.

Miemiebee:-


  Kwance take a d'akinta na gidansu ta jeme ta rame duk ta yi wani iri, idanunta luhu-luhu yayi jawur kamar barkono. Shigowan mahaifinta d'akin ne ya tsoratata ta zauna zuciyarta na dukan uku-uku, zaman da yayi gefenta ya bata damar kallon fuskarsa a had'e yake tam kamar yanda tayi tsammani, muryarsa taji tace "har yau bazaki sanar damu laifinki ba ko? Toh yau kashinki ya bushe a gidan nan, tunda Kamal ya turo miki takardar saki gidan nan sai kin sanar dani wani abun kika yi masa, ko ki fad'a min abunda kika masa ko wallahi Maryam yau in kakkaryaki a gidan nan kowa ya huta".

Kukan da yaji tana yi ya k'ara tunzurashi, "dan uwarki bazakiyi min shiru kiyi bayani ba? Tunda kika nok'e kika k'i fad'an komai nasan laifinki ne, da laifinsa ne da tuni kin bud'e baki kinyi magana, toh gashi shi da muka sa gaba dole sai ya fad'a mana ya turo mana da takardar sakinki..." A tsorace ta kallesa da rinannun idanunta jin Kamal ya saketa. Hannu ta d'aura aka tace "na shiga uku na lalace, wallahi na tuba Kamal, ka tausaya min kada ka sake ni..." Bakinta ya buge da bayan hannunsa, tuni tayi shiru, da kakkausar murya yace "zaki fad'a min abunda kika masa ko sai nace mishi ya k'ara sakin ya cikate uku dukka, ai d'aya ya miki kad'an munafuka"

Duk nacinsa da bugun da yake kai mata bata iya furta komai ba, abu d'aya ta iya ce masa "in na fad'a maka zaka tsaneni, shiyasa nake tsoron sanar dakai" salati yayi da yaji ta fad'i hakan, "wurin boka kikaje Maryamah? Maryamah ina kika bar karatun da nake miki a tsakiyar gidan nan?" ya k'arashe maganar yana rufe bakinsa da d'ayan hannunsa d'ayar kuma yana nuna hanyar k'ofar da alamu cikin gidan yake nunawa. Bakinta na rawa dak'yar ta iya cewa "a'a wallahi, ni ban tab'a zuwa wurin boka ba ban ma san inda suke ba wallahi Allah baba".

Yin duniya tak'i fad'a masa, haka Mamanta tazo ta k'araci ban baki da rarrashi amma duk baiyi anfani ba. Sun rasa ya zasuyi da yaran, shi Kamal yace a tambayeta, sun nace sai ya fad'a ya turo musu takardan saki d'aya, yanzu kam basu da bakin yi masa magana dan sun san laifin daga 'yar su ce.

Lubiee @ 11am:-


   Wayarta ne yayi k'ara alamar ana k'ira had'e da vibration, "vuuuu!!!" Yake yi akan dressing mirror d'inta, da hanzari ta bud'e k'ofar toilet ta fito zaninta a hannu bata tsaya d'aurashi da kyau ba. Kafin ya yanke ta d'auka had'e da cewa "hello" "ok gani fitowa, thank you so much, gani nan zuwa" ta ajiye wayar tana gama fad'an haka. Sai da ta koma toilet d'in ta wanke hannunta sannan ta fito ta d'auki mayafinta had'e da gyara d'aurin d'an kwalinta sannan ta fice zuciyarta wasai.

A bakin gate na gidan ta samesa cikin motarsa, yana ganinta ya fito yana cewa "tun d'azu naso zuwa amma Baba Munnir ya aikeni, sai yanzu ya barni". "A'a kada ka damu wallahi, ban d'auka kai Mrs. Umar zata aiko ba ma, sannu da gajiya na wahalar dakai" murmushi kawai yayi ya ciro bak'in ledar da aka cunkushe shi kamar ba komai ciki yace "ga sak'on, ni zan wuce" ya mik'a mata ta sa hannu ta karb'a tana mai yi masa godiya. "Ka gaida gida ka shafa min kan Kausar d'ita, nayi missing d'inta sosai" "zata ji kuwa, ita ma tayi da alama dan da zan fito take ce min in zanje wurin Maminta zata bini" "Allah sarki, next week zanje in d'auko ta ai, ka gaida su Mrs Umar kace mata na gode kuma zan k'irata" sallama yayi mata ya shiga motarsa ya tafi.

Kamar bazata shiga gidan ba haka take ji, cikin sauri take tafiya zaninta na hard'eta har ta shiga cikin gidan, d'akinta kai tsaye ta nufa hannunta rik'e da wannan ledan, sai da ta kulle k'ofar d'akin nata ta shiga can k'uryar d'aki sannan ta bud'e ledar ta ciro abunda yake ciki murmushi fal fuskarta tace "zan ga k'aryar b'oye makulli da gadi makira".

Ta saki murmushin jin dad'i tana mai d'ago makullin da ta sa akayi mata na d'akin Abubakar, fakan idon Nafee tayi ta samu makullin d'akin ta manneshi jikin sabulu ta kai aka yi mata irinsa da taimakon Mrs. Umar, hakan kad'ai zai bata damar shiga d'akin Abubakar da ta dad'e tana hari. Murmushin da takeyi kad'ai ya isa ya nuna tsantsar murna da farincikin samun makullin nan, sauran abubuwan da zai biyo baya ta bari a ranta dan tabbas asirin wasu yana gaf da tonuwa.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


          Page 49


  Zaune Nafee take a parlon idanunta saitin k'ofar Abubakar, tunda ya fita office ta samu wuri ta zauna duk ihun yaranta da kokuwarsu bai sa ta tashi daga wurin ba sai dai tayi musu ihu daga inda take zaune. Fitowar Lubiee uku yanzu dan dubata, a bakin k'ofarta ta zauna dan kada Nafee ta tashi bata sani ba. Wasa-wasa minti goma da d'auri bata tashi ba bare ta samu damar shiga d'akin. Lokaci ta duba a wayarta k'arfe 10:23 na safiya, bata d'auke idonta daga kan wayar ba taji wayar Nafee na ringing, tashi tayi da d'an gudunta ta shige d'aki har da rufowa dan kada Lubiee taji wayar da zatayi.

Wuf ta tashi ta bud'e d'akin nasa da makullin da aka kawo mata ta shige bayan ta zaro makullin nata ta shiga dashi. Sawa tayi ta ciki ta kulle k'ofar ahankali dan kada a d'agota, sai da ta sa kunnenta taji babu motsi sannan ta sauk'e ajiyar zuciya ta fara duban d'akin, rabonta da d'akin har ta manta, duk ya canja mata duk da ba wani tarkace ne a d'akin ba. Bismillah tayi ta kamo addu'o'i kala-kala, cikin drawer ta fara bud'ewa, tunowa da tayi bata yi alwala ba yasa ta shiga toilet nasa tayi ingantacciyar alwalarta, ta karanta ayatul kursiyyu sannan ta cigaba daga inda ta tsaya.

Takaddun cikin drawer ta ciro dukka sannan ta fidda drawers d'in d'aya bayan d'aya, dama ta wurgo tsintsiyarta ta window kafin ta shigo, dashi tayi anfani wurin share k'ura da dattin da ta gani a wurin. Duk abubuwan da takeyi a hankali take yin su saboda kada a jita. Cikin d'akin nan daga gado, wardrobe, bayan gado, bayan drawer da komai ta duba ta karkad'e babu abunda ta gani, kuka ne kawai bata yi ba dan ta tabbata Nafee ta gama da ita tunda babu wani tsibbu a cikin d'akin, kenan in ma ta binne ba a nan d'akin ta binne ba?

Bata karaya ba ta shiga toilet, nan ma duk inda tasan za a iya b'oye abu ta duba babu, har zata fito daga toilet d'in kamar ance d'aga kanki taga wani b'uli a samar ceiling rufe da leda. Haka kawai taji zuciyarta ya aminta da nan aka b'oye asirin, duk iya k'ok'arinta na isowa ta kasa, ta hau kan kujera ma ta kasa isowa bare ta duba. Moppern da ke wurin tayi anfani dashi wurin ture ledar da aka toshe b'ulin sannan ta samu daman d'aukan dustbin d'in da ta cika da datti ta iso wurin windown da ta sa tsintsiya ta fara juye dattin ta nan, tas ta juye ta wurga tsintsiyar sannan ta mayar da dustbin d'in inda ta samu. 

•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•


     Kunnenta ta sa dai-dai k'ofar ta mayar da dukkan hankalinta can dan jin ko akwai motsi ko murya a kusa, bata ji motsin kowa ba yasa ta bud'e k'ofar ta fito cikin sand'a ta kulle sannan ta koma d'akinta ba tare da kowa ya ganta ba. Ruwa ta samu a cikin fridge na d'akinta tasha tana mai lumshe ido jin nutsuwa ya sauk'o mata. 

Kwanciya tayi ta d'auko wayarta dan duba lokaci, k'arfe 2 har ya gota ta gani "subhanallahi" tace ganin lokacin sallah ya k'ure mata. Da hanzari ta mik'e ta d'auro alwala tazo ta gabatar da sallahr azahar. Bata tashi daga kan sallayar ba sai da ta d'auki Qur'ani ta karanta abunda ya sawwak'a na tsawon mintuna talatin sannan ta rufe ta koma kan gadonta ta kwanta tana tunanin mafita, sai a sannan ta tuno da dattin da ta zubar ta baya, da hanzari ta fice dan kwashewa, jin shirun Nafee yayi yawa a cikin gidan yasa ta gane ta fita ne. Cikin k'ank'anin lokaci ta gama ta koma d'akinta ta kwanta dan ta huta.

Bata tashi ba sai da taji k'iran sallahr la'asar, sai da ta idar sannan ta samu damar had'a tea dan yunwar da ke addabarta. Da misalin k'arfe biyar taji k'arar motar Abubakar, hakan yasa ta fito tana mai jingina kafad'arta da k'ofar tana jiran isowarsa cikin gida, sai da ya shigo ya wuce ta bakin k'ofarta yana kallonta ta gefen ido sannan tace "sannu da dawowa, nace ni fah b'era nake ji a saman d'akina kullum da dare, a duba min a cire min dan yana tsoratani yana hanani bacci".

Juyowa yayi da mamakin maganarta, "b'era kuma Lubba a saman d'aki? a ceiling kenan? Ta ina ya shiga toh?" Ba tare da fargaba ko tsoro ba tace "ta ina kuwa banda d'akinka, ai ga d'akinka ga nawa, kuma indai ya shiga d'akinka toh yana da hanyar da zai shiga ceiling yayi yawo a saman d'akina" Ta k'arashe maganar tana kawar da kai fuskarta a tamk'e babu alamar wasa. 

K'aramar tsaki yaja yana gyara jakarsa da ke hannunsa "toh yanzu ya za'ayi? Ni dai iya sanina babu b'uli a d'akina bare b'era ya shigo har ya shiga ceiling, sai dai ko ta waje ya hau ceiling d'in..." Bai k'arashe maganar ba tace "haa'a! Ya zaka ce haka? D'akin naka ne ban sani ba ko meh? Window babu net kullum ana cikin bud'ewa taya b'era bazai samu hanya ba?" "Toh in ya shiga d'akin na yadda tayaya zai hau ceiling d'in naki?" "Toilet. Kaga in bazaka cire ba ka bani dama in nemo wasu a waje su cire min kawai".

Tana gama fad'an haka tayi hanyar waje dan nemo wanda zai cire mata. "Dakata mana, dawo ki nuna min ta inda ya shiga" turo baki tayi ba tare da ta masa magana ba ta shige gaba ya biyota a baya, dai-dai bakin k'ofar yasa makullinsa ya bud'e tasa kai ciki shi kuwa ya biyota a baya. Kai tsaye ta nuna masa wannsn b'ulin tana mai cewa "ba gashi ba". Kad'a kai kawai yayi dan shi bai tab'a sanin wannan wuri ba, wayarsa yayi anfani dashi ya k'ira d'an gidansa Iro dan yana kusa dasu.

K'aton drum suka samu Iro ya hau dan lek'awa kuma ya samu daman toshewa kamar yanda aka umarcesa, duk lek'e-lek'ensa bai ga komai ba, "mik'o min ledar" yace da Abubakar yana mik'a masa hannu. Lubiee tace "haa'a, kuma banga ka cire komai ba fa? Ka sa hannunka ta gaban nan ka duba ko akwai wani abu da yake janyosa, watak'ila anan yake tara abincinsa ma" kallonta sukayi da mamaki, ita kuwa ta had'e rai ala dole sai ansa hannu an duba, babu yanda ya iya ya cusa hannunsa ya fara lalube. Wani abu ya tab'o ya kasa gane menene, rik'owa yayi da yatsu biyu ya janyo, lokaci d'aya abun ya fad'o sai kuma k'urar da ya zubo a fuskarsa yasa shi k'ara.

Fad'owar abun yasa Lubiee daka tsalle ta koma gefe had'e da d'aga k'afarta d'aya tana cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un". Idanunsa a runtse Abubakar ya rik'esa ya sauk'o ya taimaka masa wurin wanke fuskarsa dan k'urar ya shiga idanunsa. Lubiee da ke gefe matsowa tayi kusa da abunda ya fad'o dan duba menene, bismillah tayi tare da a'uziyya sannan tasa hannu ta d'auka, ledar da ta tura d'azu ne ba k'ullin magani ba kamar yanda tayi tsammani. Tsaki ta ja wanda ya janyo hankalinsu dukkansu gareta, Abubakar ne ya iso inda take ya tsuguna yana cewa "menene?" Had'e da karb'o ledar hannunta yana warwarewa.

Muryar Nafee suka ji daga bakin k'ofar tana cewa "waye a d'akin nan?" Baki ta sake ganin Abubakar da Lubiee cikin bayan gida sai drum d'in da ke gefensu. "Kai!" Tace tana mai rik'e k'ugunta da waro ido dan ganin abun da ke faruwa. A tsorace Abubakar ya mik'e jikinsa har rawa yake ganin yanda Nafee tayi, cikin i'ina ya fara magana dan fahimtar da ita, bai kai ga saita maganar ba Iro ya lek'o da idonsa kwaya d'aya a bud'e d'ayar kuma har a lokacin bai daina yi masa zafi ba sai faman wankewa yake yi. "Hajiya ashe ke ce, ina wuni?" Ya gaisheta yana mai fitowa daga toilet d'in yana goge fuskarsa da gefen rigarsa.

"Lafiya, meh nake gani? Meh ya kawo ku toilet kuma yau?" Abubakar ne ya fito daga toilet ya fara yi mata bayanin abunda Lubiee ta fad'a masa game da b'era, ganin haka Iro ya fice ya bar gidan dan ya gama aikinsa, bata kai ga yi masa magana ba suka ji ihun Lubiee da gaskiyarta ta tunkarosu, "b'era, wallahi ga shi nan na shiga uku nikam" ruk'unk'umesa tayi ta baya tana faman d'alewa bayansa, da gaskiyanta take ihu take k'ok'arin yin hakan. Nafee sai raba ido take dan taga inda b'erar zai fito amma shiru ba b'era, babu ma abunda yayi kama da b'era balle tace abunda Lubiee ta gani kenan, hakan na nufin kissa ce kawai irin nata sabuwa da ta koyo, dawo da dubanta garesu yasa numfashinta d'aukewa, meh ke shirin faruwa? 

Abubakar rik'e da Lubiee, zata iya cewa d'aukarta yayi dan hannayensa ne ya zame mata abun dogaro, da ba dan rik'eta da yayi ba da tuni zata zube a k'asa, bayan hakan fuskarta tasa dai-dai wuyarsa tana da tabbacin bakinta na kan wuyarsa tana yi masa wani salo nata da bata gane ba sai dai fuskar Abubakar ya nuna hakan, da alamu yana jin dad'in kasancewa da ita, bata yi aune ba taga Lubiee ta kusanto fuskarsu shi kuma ya rik'e kwankwasonta yana mai k'ara kusantota zuwa jikinsa.

"Kan uba!" Ta furta a tsawace, hakan ya dawo da Lubiee da Abubakar hayyacinsu, alal hak'ik'a sun manta da tana nan kuma sunyi kewar juna shiyasa had'uwar jikinsu ya tuna musu da abunda suka dad'e da manta sa. Gefe Lubiee ta matsa tana mai jin hawaye na taruwa a idanunta, wannan wace irin rayuwa ce? Rabonta da samun kulawar mijinta tun yaushe? Tana da lafiya da komai amma k'ememe an hana mata mijinta. Bata tsaya sauraran abunda suke fad'a ba tayi hanyar k'ofa dan barin d'akin, kuka ne zai kufce mata in ta k'ara ko da minti d'aya ne a d'akin. Idanunta a k'asa take tafiya hakan ya bata daman ganin d'aguwar carpet na bakin k'ofar. Rage saurin tayi tasa ido sosai, hakan ya bata dama ganin wasu k'ulle-k'ulle da ta kasa gane wani irin abu ne. 

A take b'acin ran da ya ziyarceta mintoci kad'an da suka wuce ya gushe dan tabbatar da abunda take nema ta samu. D'akinta ta wuce ba tare da ta zarce ko ina ba, matsalar da ke samunta na cikin wannan k'ullin, samun daman cire wannan k'ullin na nuni da samun lokacin mijinta har ma da kulawarsa.

Sallolinta ta gabatar ta ci abinci sannan ta kwanta baccinta hankali kwance, ta tabbata gobe bayan tafiyar Abubakar aiki Nafee ma ficewa daga gidan zatayi dan neman mafita tunda taga abunda Abubakar yayi mata, hakan ba k'aramin sata nishad'i yayi ba. Mintuna kad'an da kwanciyarta bacci mai dad'i ya sureta.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


          Page 50


  Cikin bacci taji k'arar buga k'ofa da k'arfi, mik'ewa tayi ta bud'e nata k'ofar dan ganin abunda ke faruwa. Nafee ta gani a fusace ta fito daga d'akin Abubakar ta wuce d'akinta, da ganin fuskarta zaka fuskanci fad'a sukayi ta fito ta k'yalesa. Murmushi ta sake ta koma kan gadonta ta duba lokaci k'arfe goma da 'yan mintuna, a fili ta furta "ashe ban jima da kwanciya ba, lallai yau na gaji daga kwanciya sai bacci".

Bata kai ga komawa bacci ba taji an bud'e nata k'ofar cikin sand'a, hanjin cikinta ba k'aramin kad'awa yayi ba, "innalillahi wa inna ilaihi raji'un" take ta nanatawa ta ma manta da sauran addu'o'in, idanunta a runtse shiyasa har aka iso gefenta bata iya gane wanene ba, k'arfin hali tayi ta bud'e idonta d'aya a hankali. Muryarta na rawa tace "Abubakar" cike da mamakin shigowansa d'akinta, rabon da yayi satan hanya ya shigo nan ma ta manta. Zama tayi tana kallonsa yana tsaye idanunsa a kanta.

Mintuna uku babu abunda suka tab'uka banda kallon-kallo da sukeyi, Lubiee ce tayi k'ok'arin sauk'o da k'afafunta k'asa ta rik'o hannunsa ta janyosa kusa da ita dan ya zauna. D'agata yayi da iya k'arfinsa ta tashi tsaye ba shiri, shi kuwa ya janyota ya rungumeta k'yam a jikinsa. Numfashi mai k'arfi ya sauk'e, Lubiee kuwa nutsuwa ma bata dashi bare taji dad'in yi mata hakan da yayi, zuciyarta banda bugu babu abunda yake yi, ta kasa hugging nasa back dan mamakin da ya cikata a daidai wannan lokaci, batayi aune ba taji ya fashe mata da kuka "subhanallahi" ta furta tana mai k'ok'arin b'anb'aresa daga jikinta amma ina yak'i saketa.

Dole ta hak'ura ta k'yaleshi tunda hakan yafiso, rasa abun yi masa wanda zai kwantar masa da hankali tayi, bama ta da daman motsawar kirki bare wani idean yazo mata. Hannunta tasa a bayansa tana mai daidaituwa cikin faffad'an k'irjinsa, hab'arta ta d'aura bisa wuyarsa sannan ta samu damar yi masa magana "My man!" Ta furta cikin sanyin murya, bai daina hawayen ba dan tana jin sauk'arsa a kafad'arta sai dai sautin kukan ya disashe ba'a ji.

Duk kalaman da take yi masa na ban baki bai saurara ba, tana nan dai mak'ale a jikinsa bai iya furta komai ba, tun abun yana bata tsoro har ya ta daina jin tsoron ta samu damar d'aura bakinta a nasa. Cak kukan da yake yi ya tsaya jin wani sabon salon da take yi masa, dole ya hak'ura ya saduda ya biye mata don faranta ran junansu. 

Sai da komai ya lafa sannan ya iya ce mata "bansan meh ke damuna ba, ji nakeyi kamar controlling d'ina akeyi" hannunta ya rik'e cikin nasa ya marairaice fuska yace "Lubba bakya ganin na canja? Bansan meh nake aikatawa ba, ya zanyi..." "Shh!!" Tace had'e da d'aura yatsanta bisa lebb'ansa, babu wanda ya sake cewa uffan bacci b'arawo ya sace su.

•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°

  Hannunta ta d'aura a gefenta tana lalube idanunta a lumshe, jin babu kowa gefenta yasa ta bud'e idanunta, da hanzari ta lumshe dan hasken da ya dalle mata idanu. Tunawa da tayi batayi sallah ba yasa ta mik'e da hanzari tana mai duba cikin d'akin nata ta shiga toilet dan yin alwala, sai da tayi wanka tayi alwala sannan ta fito. D'akin ta sake kallo da idonta ta tabatar da Abubakar baya d'akin, "ina yaje? Lokacin sallah ya k'ure bai iya tashina ba yasa k'afa ya fice? Mutumin nan k'alau yake kuwa?" Jero zancen dukka tayi a zuciyarta. Sosai tayi k'ok'arin kawar da tunanin ta d'auko sallaya ta shimfid'a tasa hijabi ta kabbarta Sallah.

Tana idarwa ta fito dan duba lafiyan gidan da duba lafiyar mijinta. A tsakiyar parlor ta ganshi yana zaune da bread a gabansa ya had'a tea yana kurb'a yana cusa bread a baki, ta lura hankalinsa ma bai tare dashi dan idanunsa na kallon k'asa ko kiftawa baya yi. Gefenshi ta zauna tana mai d'aura hannunta kan hannunsa da yake rik'e da sauran bread d'in da ya gutsira, firgita yayi da jinta kusa dashi tana tab'a hannunsa, hakan yasa ya wurgar da bread d'in ba tare da ya sani ba.

Mamakin firgicin da ya shiga ta yi ta tsaya kallonshi da mamaki, bata samu daman furta k'ala ba ya jefeta da wani irin kallon da zata iya k'iransa da na tsana, gabanta yayi mugun fad'i ganin abunda Abubakar yakeyi sabo, ta d'auka komai ya fara lafawa ashe abun ba haka yake ba, jiya dai da dare ya tsaya yana yi mata sumbatu yana shishshige mata ashe duk na k'arya ne jikinta kawai yake buk'ata. Jin k'arar k'ofarsa ya tabbatar mata ya koma d'akinsa ne kuma yaji haushi, kuka ne mai cin rai ya kufce mata a inda take zaune, sosai ta zage tana kukanta ba k'akk'autawa tana mai ganin wautarta na biye masa jiya da tayi, lallai namiji a barshi kawai.

Nafee da ke tsaye bakin k'ofarta tana ganin duk abunda ya faru tun daga fitowar Lubiee har shigewar Abubakar ciki, murmushi ta saki mai nuni da tsantsan jin dad'in da ta tsinci kanta a ciki, jin kukan Lubiee take kamar sautin wak'a dan dad'in da yake mata. K'ofarta ta rufe ta koma kan gadonta murmushi fal fuskarta, sai da ta samu mazauni sannan tace "da ni kuke wasa a gidan nan" ta k'ara da dogon tsaki ta mik'e kan gadonta tana mai lumshe ido bakinta na fitar da sautin wak'ar da ita kanta bata san wani wak'a bane.

Lubiee @ 11am


   Kwance take akan gadonta sai huci take kanta na sara dan kukan da ta sha ba kad'an ba. Wayarta ne yayi k'ara ta d'auka ta kara a kunnenta bayan tayi receiving "Hello" ta furta a hankali d'aya b'angaren aka ce "Lubiee ina kwana" "lafiya k'alau ya hidima damu Ummu-Abdoul?" Murmushi tayi daga nata b'angaren sannan tace "hidima da juna dai, yanzun ma batun tafiyan namu ne, Nasarawa ko Minna zamu fara zuwa? A ganina yakamata mu tattauna da Hussain, shi yasan gidan su Benaxir kuma shi yasan yanda zamu shawo kan matsalar ba tare da mun samu matsala ba, kina ganintan nan matsala zata bamu gwanda mu same sa shi da ya fara sai ya fada mana k'arshensa in yaso mu ma mu kawo namu shawarar sai a tafi dai-dai, ko ba haka ba?" "Haka ne" ta furta tana mai kad'a kai alamar amincewa da batun.

Ta cigaba da fad'in "kuma maganar Batool, ita ma sai munje gidan nasu dan in bamu je ba bazamu samu biyan buk'ata ba. Ni kinsan meh? Sauran abubuwan nan namu yana d'aure min kai, rabon da inji daga wurin Miemiebee har na manta, bata neme mu ta fad'a mana yanda abun ya kasance ba bare mu d'aura daga inda muka tsaya, gwanda Pherty munsan komai".

Jan hanci Lubiee tayi sannan tace "yakamata mu k'irata tunda ita bata k'ira ba muji ko lafiya" "tsaya! Meh naji kikeyi Lubiee? Ba dai kuka ba aski yazo gaban goshi?" Jin haka yasa Lubiee fashewa da wani sabon kuka tana cewa "wallahi na fasa abun nan, sai kace dole? Idan nice nake da makullin bud'e wannan asirin wallahi na jefa shi cikin ruwan maliya" ta cigaba da kukan nata. Dariya abun yaso bawa Ummu-Abdoul amma ta dake dan ta samu damar k'ara mata k'aimi ta d'ago mata courage d'in da ya zube, cikin iya zance ta yi mata magana, wanda bata kai minti biyu da fara rattaba mata bayanai ba taji ta d'aura d'amarar yak'i da Nafee, ko da kuwa shine zai zama aikinta na k'arshe a duniya.

Basu kashe wayar ba sai da suka tsara maganar tafiyarsu Minna da Nasarawa a sati mai zuwa, kuma ta bata tabbacin zata zama d'aya daga cikin matafiyan don shawo kan matsalar sauran 'yan uwan nasu, ba nan kad'ai suka tsaya ba sai da suka tattauna game da lamarin Pherty da kuma Miemiebee duk da basu ji zancen daga wurinta ba sunji kad'an daga wurin Pherty.

Tana ajiye wayar ta tashi ta isa bakin k'ofarta. Lek'e ta tsaya yi ta k'ofar d'akinta dan jin inda Nafee take, tana kallonta ta yafa mayafinta yaranta na tsaye a gefenta suna kallonta narai-narai alaman basu so abunda tace suyi ba, sai da ta kulle k'ofar da makulli sannan ta juyo a masifance tace "bazaku wuce gidan Hafcyn bane sai na sab'a muku", babu yanda suka iya suna gunguni suka fice daga gidan tana biye dasu a baya.

A dai-dai wannan lokaci Lubiee ta fito daga inda take lek'e. Sai da ta tabbatar da k'arar motarta ya fice daga gidan sannan tayi ajiyar zuciya had'e da hamdala. Duk da k'ofar d'akin Abubakar a kulle bai sa ta samu matsala wurin d'aga carpet na bakin k'ofar nasa ba. Addu'a da karatun Qur'an bai bar bakinta ba ta kwaye carpet d'in har inda take da tabbacin anan barbad'en ya tsaya. Duk da tsinkar zuciyarta da tsoron da take ji bai hanata sa hannu dan d'aukan bak'in k'ullin da ta gani ba.

Kai tsaye ta shiga kitchen ta ajiye sa a sink ta d'auko ashana. Bata k'yasta ashanar ba sai da tayi addu'o'in kariya sannan tayi bismillah tasa wutan, nan take ya kama bai bata wani wahala ba, idonta na kan abun nan har ya gama k'onewa k'urmus, duk da bak'in hayak'in da yake yi bai sa taji d'ar a ranta ba, sai ma wani jin kai da ya dad'u mata na tabbacin zata yi yak'i da matsalolin Nafee. 

Ruwa ta d'iba cikin cup tayi bismillah sannan ta fara korawa akan tokar har ya gama wucewa. Ruwan tofin da yake ajiye a d'aki ta d'iba cikin tafin hannunta tazo ta yayyafa a dai-dai inda ta ciro k'ullin maganin sannan ta mayar da carpet d'in yanda yake kamar ba'a tab'a ba ta koma d'akinta.

Bata yi minti talatin da kwanciya ba taji k'arar mota, bata damu da dubawa ba tasan bazai wuce Nafee ce ta dawo ba, tana jin shigowar mutum parlor yana tafiya kamar yasha abun maye idanunsa na juya masa dan tangal-tangal d'in da akeyi kamar za'a fad'i. Jin hakan yasa ta fito dan duba wanda ya shigo mata gida, baki ta sake ganin Abubakar rik'e da kansa yana bin gini ahankali yana tafiya.


Wurinshi ta isa ta rik'esa tana cewa "sannu, lafiya dai? Meh ke damunka?" Bai amsa mata tambayoyinta ba har suka iso k'ofar d'akinsa ta laluba aljihunsa dan neman makulli amma babu. Muryar Iro taji yana cewa "Hajiya ga jakarsa, yana zaune a office kawai kansa ya fara ciwo shine yace in dawo dashi gida" "subhanallah" ta furta tana mai karb'an jakar da yake mik'a mata. A ciki ta samu makullin d'akin ta bud'e suka shiga ta kwantar dashi tana mai yi masa sannu.

Ruwan zam-zam na d'akinta ta d'auko ta bashi yasha, rik'e kan nasa tayi ta masa addu'a. Bata barshi haka ba sai da ta shafa masa ruwan a dukkan fuskarsa har ma da wasu sassa na jikinsa. Ac ta kunna masa ta dawo gefensa tana mai karanta masa karatun Qur'an ahankali har bacci yayi awun gaba dashi.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


Page 51


A loakcin da Nafee ta dawo ne Lubiee ta bar d'akin Abubakar dan maganganun da Nafee ke jifanta dashi bazata iya jurewa ba, zasu iya kwasan 'yan kallo in ta biye mata wanda bazata so hakan ba in tayi la'akari da halin da mijinta yake ciki wanda take da tabbacin asirin da akayi masa ne ya karye, bazata so tashinsa daga bacci da hayaniya ba kuma bazata so wata can ta b'ata mata farincikin da take ciki ba. Tun da ta ga take-takenta da rawar kanta sai ta fice daga d'akin ta basu wuri.

Sadiq @ 12am


"Haba sweetheart kada ki min haka please, zan zo gobe i promise" ya fad'i hakan yana zaune kan gadon abokinsa inda ya koma da zama yanzu tunda ya bar gidan mahaifinsa. Candy ce ke yi masa rigimar yak'i zuwa wurinta kuma tana son ganinsa, duk ta rud'a shi da kalamanta na cewa bazata kula shi ba tayi fushi dashi, a yanzun ma ya k'irata yafi a k'irga tak'i d'aukan wayansa sai yanzu, shiyasa duk ya susuce yana bata hak'uri. Dak'yar ya shawo kanta ta hak'ura suka cigaba da hirarsu yana rok'onta kada ta sake k'in d'aga wayarsa dan yana jefasa wani hali.

Lokaci zuwa lokaci yake sauk'ar da wayarsa ya duba ya sake mayarwa ya cigaba da maganar nasa, yayi hakan kusan sau biyar daga bisani suka yi sallama ya dannawa Ruffaida k'ira wacce ta gama k'uluwa da k'in d'aga wayarta da yayi kuma ba bacci yayi ba waya yakeyi. Takai k'ololuwa wurin jin bak'in ciki da zafin wannan abu, baccin da yake idanunta tuni ya gushe ta rasa inda yaje. A hankali taji sauk'ar hawaye a kuncinta tare da rad'ad'i mai zafi a k'irjinta, k'iri-k'iri tana kallo an k'wace mata Sadiq d'inta. Wata can wacce bata san komai game dashi ba ya mace akanta har zata k'irashi yak'i d'auka. Meh hakan yake nufi?

Bata tsayar da hawayen fuskarta ba taji wayarta na ringing, tana kallon sunansa tak'i d'auka dan haushinsa da take ji a dai-dai wannan lokaci, yazo gab da tsinkewa tayi hanzarin d'auka dan kada yak'i k'iranta in ya yanke ya d'auka ko bacci tayi. "Hello" ya furta ba tare da komai a ransa ba, shiru tayi ta tura baki kamar yana kallonta tak'i yi masa magana, ita a dole tayi fushi taji yana waya k'arfe 12 na dare wanda tana da tabbacin da Candy yake waya.

"Bacci kika fara kuma?" "Oho!" Ta fad'a kai tsaye muryanta tangararau babu alamun tana jin bacci bare ya d'auka baccin take, bakinsa bud'e dan mamakin furucinta yaji tace "da wa kake waya war haka?" Yanzu kam sosai yaji maganar nata banbarak'wai, "ban gane da wa nake waya ba?" Ya tambaya muryarsa na nuni da mamakin da ya shiga. Hawaye taji yana sauk'o mata ahankali, jin shirun nata yayi yawa yasa yace "Ruffaida lafiya? Meh ya sameki? Meh kikeyi? Kuka? Wani abun akayi miki?".

"Lallai mutumin nan, wato shi bai ma san ina yi ba ko? In same shi yana waya da wata kuma sai ya d'auka wasu ne can suka b'ata min rai ba shi ba?" Wani kukan ne ya kufce mata na takaici, da hanzari ta kashe wayar tun kafin ya jefeta da wani tambayar ta kasa amsashi. Wayar ta kashe gaba d'aya gudun ya sake k'iranta.

Kuka tayi ranar mai isanta tana mai sawa a ranta ta rasa Sadiq, ya daina sonta ya daina damuwa da ita, bazai tab'a sake kallonta matsayin budurwarsa ba bare matar aurensa. Ita kuma nata sakayyar kenan?

Bata san ya akayi bacci ya saceta ba dan kukan da tayi ita kanta tasan ba kad'an ba. A nashi b'angaren kuma, mamakin abunda ya sami Ruffaida bai barshi ba, ya k'irata bayan ta kashe wayar sau uku zuwa hud'u ana tabbatar masa wayar a kashe, "Toh fah! Meh ke shirin faruwa? Lafiya kuwa?" Cewar zuciyarsa.

Washe-gari:- Lubiee @ 10am


Tana kwance kan gadonta bayan ta sha tea da bread hankalinta gaba d'aya baya jikinta, tana son duba mijin nata amma ba halin yin hakan, tafison sai ta tabbatar da karyewar asirin kafin ta zak'e, kada taje yanzu ya disgata wurin matarsa taji kunya. Bata tsayar da tunaninta ba taji k'amshin turarensa, har ga Allah bata ji motsin k'ofa ba bare taji k'arar tafiyarsa har tasan da shigowarsa.

Fes ta d'aura idanunta a kansa, murna da dad'in ganinsa a wannan lokacin cikin d'akinta ya dirar mata amma sai dai ganin fuskarsa yasa zuciyarta karaya, shin asirin ya karye ko da saura? Fuskarsa ba yabo ba fallasa, bai mata murmushi ba bare taji sanyi a ranta, a daken yace mata "kin daina zuwa office ne?" "Toh dai, yau kuma da haka ya tashi? Toh ko dai ya dawo hayyacinsa ne?" Ta fad'i hakan a ranta, idonta bai sauk'a daga fuskarsa ba tace "na karb'i hutu".

"Meh yasa? Baki da lafiya ne? Ina Kausar kuma?" Kallon mamaki take binsa dashi, "meh ke damunsa?" Take tambayan kanta, sai da taji hannunsa akan goshinta yana jin d'umin jikinta sannan ta sake tsurewa da lamarinsa, ba nan ya tsaya ba sai da ya d'aura hannun nasa a wuyanta sannan yace "lafiyanki k'alau, kawai kika nemi a baki hutu?" Shi bai sake mata ba, kuma bai bata damar gane ya dawo hankalinsa ko akasin haka ba ya tsareta da tambayoyi, haka ya k'araci zancensa ya fice daga d'akin ya barta cikin zullumi da tunani ba tare da gane tak'amaimai yanayin mijin nata ba.

Ruffaida @ 12pm


Kwance take a d'akin da aka keb'e mata a gidan Ummu-Abdoul taji rurin wayarta, bata dad'e da kunna sa ba dan har a lokacin bata tsayar da hankalinta ba kuma zuciyarta da idanunta basu daina zugi ba. Kamar bazata d'auka ba tasa hannu ta danna ta kara a kunnenta. Numfashi ya sauk'e wanda har cikin wayar taji sa, "kinsan kin tsoratani Ruffaida, tun jiya kin barni cikin zullumi da tsoro, lafiyanki kuwa?".

Murmushin dole ta sakar masa dan kawar da abunda yake ransa, jin k'arar murmushin nata yasa zuciyarsa yayi sanyi. "wayata ce fa ta d'auke jiya ba caji, shine kawai na kwanta nayi bacci" zuciyarsa bai amince da uzurinta ba yace "are you sure?" Yana son ce mata kamar naji kina kuka sai ya fasa, tunda tace ba komai ya d'auka a hakan kawai. In akwai, Ruffaida mai fad'a masa ne dan bata cika b'oye masa damuwarta ba.

"Thank God tunda babu komai, dama yanzu fita nakeson yi har nace zanje wurinki in duba ko lafiya sannan in wuce wurin Khadija candy, jiya duk ta birkita ni dan na kwana biyu banje ba..." Bata idasa jin maganar ba jin wani abu mai d'aci ya tokare mata mak'ogoro. "Na'am" ta amsa da d'an k'ara sannan tace masa "ina zuwa please" ta katse wayar. Hawaye taji ya taru cikin idanunta, daga bakin k'ofa taji Hajiya na cewa "Ruffaida d'an fito ki duba mai sallaman nan dan Allah, duk basu nan kuma wai ana sallama".

Kukan ta shanye sannan tace "Toh Hajiya gani nan zuwa, barin sa hijabina". Waje ta fita dan duba wanda yake sallamar kamar yanda aka umarceta, gaisawa kawai sukayi yace "sak'o ne dama nazo bayarwa, i know Safiyya bata nan, but tafiya ce tazo min na gaggawa dole na zo. Feedoh ko?" Ya tambaya yana mai tsareta da ido hannunsa kuma na nunata da 'yar manuniyarsa, sai da tayi murmushi sannan tace "a'a, Feedoh ta fita, ni friend d'in Ummu-Abdoul ce Ruffaida" sunan ya sake maimaitawa "Ummu-Abdoul? Safiyya kike nufi?" Kai ta gyad'a masa alamar eh sannan ta sa hannu ta karb'i ledar da yake mik'a mata.

"Ummu-Abdoul sunanta? Ko dai sunan d'an da takeson haifa ne yasa ake k'iranta da hakan?" Yafi k'yautata zaton hakan shiyasa yayi saurin kawar da tunanin da yake shirin bijiro masa. Can ya tsinkayo muryarta tana cewa "ince mata waye kenan? Baka sanar dani sunanka ba" murmushi yayi sannan yace "Abduljalil zaki ce mata. Ni na wuce, kice mata zan k'irata, ki gaida mutanen gida" yana gama fad'an haka ya shige motarsa ya wuce.

Lokacin da ta shiga gida da ledar a hannunta ta samu Hajiya a parlor tana zaune. "Sak'o ne dama na Ummu-Abdoul" "waye ya kawo sak'on?" Ta fad'a tana kallon ledar cike da son jin k'arin bayani. "Abduljalil yace sunansa, ta sanshi da alama dan yace zai k'irata" hajiya ta kad'a kai alamar gamsuwa da bayaninta sai dai a ranta ta k'uduri tusa 'yarta a gaba dan sanin wanda ta tsayar matsayin abokin rayuwarta.

Abban ne mijinta na farko ko kuwa Malam Usman da yake ta zaryar zuwa campaign ko wannan Abduljalil d'in da yake sintiri kullum tare da yi mata hidima? Ya zama dole ta zab'i d'aya ta daina wahalar da mutane. Lokaci yayi da ya dace ta manta da baya ta cigaba da rayuwarta, abun ma yazo da sauk'i yanzun tunda har Abba ya gane kurensa kuma ya gano gaskiyar batu, in ta yadda zata koma masa babu laifi, haka in ta kawo wani a madadinsa, dad'inta d'aya yanzu 'yarta ta fita daga zargi, babu abunda zata ce sai hamdala tare da fatan Allah ya inganta rayuwar 'ya'yanta ya kuma basu mazaje na gari.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


              Page 52


  Yau ya kama Asabar da misalin k'arfe goma na safe. Duk sun hallara a cikin gidan Ummu-Abdoul kowacce da shigarta na kamala/mutunci. Wayar Lubiee ne a wannan karon yayi k'ara alamar ana k'ira, sai da tayi dariyar mai k'iran sannan tace "da alamu Pherty tayi missing d'inmu da yawa, ta fara k'irana kuma" bata jira taji maganar su ba ta d'auka ta kara a kunne. 

Muryar Pherty ne tangarau tana cewa "dont tell me baku taso ba har yanzu?" Lubiee tayi dariya sannan tace "meh kika ajiye mana haka kike ta k'iranmu kamar bazamu iso ba? Kin fad'awa mijinki ma kuwa zaki ajiye bak'i a gidansa?" Numfashi Pherty ta sauk'e sannan tace "ni fa rabona dashi tun ranan da ya kawo ni Minna ya jibge, ko waya bamu sake yi ba, taya zan sanar dashi zuwanku? Ta ina nake da wannan girman?" Ta k'arashe maganar a dai-dai lokacin da hawayen da suka dad'e da taruwa a idanunta suka sauk'o.

Lubiee ma numfashin ta sauk'e tace "ki fad'a masa ko a waya ne, ko text ki masa ki fita hakk'insa, bazai yu ki ajiye bak'i har biyar a gidansa ba tare da saninsa ba kin sani, in har bazaki fad'a masa ba toh mu nemi masauk'i tun wuri", katseta tayi da cewa "a'a zan ma k'irashi, duk yanda mukayi zaki ji". Sukayi sallama tana mai k'ara rok'onsu da su taso da wuri.

Motar Ummu Abdoul sukayi anfani dashi wurin tafiyar k'irar Corolla S fara. Benaxir ke driving sai Ummu-Abdoul da ke gefenta, Lubiee, Batool da Ruffaida suna baya, tafiyar nasu basu tsaya kan hirar da bata da anfani kawai ba, sun tattauna kan matsalolinsu da yake addabarsu wanda ko d'aya basu samu damar war-warewa ba. Na Lubiee da suke ganin aski yazo gaban goshi yanzu ta daina gane masa, bai sake mata fuska bare ta gane inda ya dosa kuma, da alamu basu shiri da d'ayar matar tasa wato Nafee, kullum cikin fad'a suke ita kuwa Lubiee tsakaninta dashi gaisuwa da tambayoyin da ita a ganinta na rainin wayo ne.

Abunda bai mata da ba yanzu bazai mata ba dan kawai tana nema masa magani, ta dai kula ya damu da ita kuma yana shiga sabgarta, kwanaki har gidan Mrs Umar yaje ya d'auko Kausar ya dawo da ita, a d'akinsa ma ta kwana washe-gari ya mayar da ita. In yayi wani abun sai ta rantse ya dawo hayyacinsa amma in tayi la'akari da rashin sake mata da baya yi sai taga kamar da saura, ta dai zuba masa ido kuma ta sanar da abokan badak'alar tasu kuma sun k'ara mata k'arfin gwiwa had'e da jaddada mata lafiya ce ta fara samuwa. Amma meh yasa ya kasa sake mata su dawo yanda suke da kuma ya dawo hayyacinsa??

Ummu-Abdoul ma ta sanar dasu matsalar da yake kanta na Abduljalil, har yau bata iya sanar dashi ta tab'a aure ba kuma bata san ya zata sanar dashi ba, ta dai san Abduljalil ya fara samun gurbi a zuciyarta amma ta lullub'e ta ajiye, a ganinta saurayi ne zai auri bazawara? Ko dai zata rufe ido ta auri Malam Usman duk da matarsa ta kasance uwa kuma yaya, har ma aminiya, dan irin shawarwarin da take bata ya wuci ace mata k'awa kawai, anya ta kyauta in ta auresa duk da alak'ar dake tsakaninsu da matarsa? 

Ga Abba kuma da ya dawo ido rufe yana son mayar da ita, har wani girma ya bata wai zai k'irata ya had'ata da d'anta suyi magana, banda gwarancin yaron nata babu wani maganar da sukeyi, duk dai da hakan tana son magana dashi dan yana sata taji nutsuwa ya shigeta, atleast tana magana da d'anta tilo wanda akansa take kasa bacci tun bayan rabuwarta da mijinta. Ya zatayi da wad'an nan maza guda ukun? Abun ya d'aure mata kai ta rasa ya zatayi kuma ga Hajiya ta bata sati biyu dan tayi shawarar wanda ta cire cikinsu matsayin gwaninta.

Ruffaida ma anan ta samu damar sanar dasu duk abunda ya faru dangane da Mamu da Nuraddeen, duk da dama ta sanar dasu a WhatsApp amma a yau ta fayyace musu daga farko har k'arshe har ma da wayar da sukeyi da Mamu da k'annenta, a k'arshen zancen nata ne tace "ni yanzu matsalata bai wuce samun miji ba, duk da zuciyata na wurin wani amma dole in ciresa in fuskanci rayuwata tunda har zargin da ake min ya kau kuma wacce nakeson ta gane komai ta gane Alhamdulillah".

Ummu-Abdoul tace "lallai Ruffaida nasan inda kika ajiyeni, mu kwana mu tashi wuri d'aya baki tab'a fad'a min akwai wanda kikeso ba sai yau ko? To kin kama kanki sai kin sanar mana wanda yayi nasarar sace zuciyarki haka farat d'aya?" Batool ma cewa tayi dole sai Ruffaida ta fad'a musu ko waye ne ko da kuwa bazasu iya taimakonta da komai ba zasu tayata addu'a.

Bata b'oye musu ba tace "Sadiq nakeso, amma shi aure ma zaiyi" taji hawaye ya taru mata a idanunta amma tayi k'ok'arin kawarwa dan kada su fahimci hakan, Benaxir da ke driving ne tace "Sadiq? Wani Sadiq kuma?" "Ba dai d'an Nuraddeen ba?" Cewar Batool, kuka ne ya kufce mata dan tasan tayi wautar barin zuciyarta ya cigaba da son Sadiq bayan tasan abu ne mai wuya aurensu, tunda har yasan abunda ya shiga tsakaninta da mahaifinsa. Kukan da ta fashe dashi ya tabbatar musu shi d'in take nufi, Benaxir da mamaki tace "amma ya zaki so Sadiq Ruffaida, yaushe muka kashe wannan wutar kina neman kawo mana wata, ni zan iya cewa haramun ne ma aurenku".

Ummu-Abdoul ce ta katseta da cewa "a'a babu haramci, ai haramun baya haramta halal sai dai halal ya haramta halal", Batool tace "kaman yaya halal ya haram halal? Ban ma gane wannan zancen ba". Murmushi tayi sannan tace "kinga ai abunda sukayi haramun suka aikata, kinga kenan dan sun aikata haramun bai zama ya haramta aure tsakaninsu ba, da ace aure ne ya shiga tsakanin mahaifin yaron da ita (ya zama halaltacciyar zama) shine ya haramta ta auri d'ansa, kin gane hausar yanzu?" Suka amsa da "eh" sannan suka cigaba da hirar da ta fishshesu na shawar-wari da kuma nasihu har suka iso garin Minna.

Pherty @ 11am


   Wayarta na hannunta na kusan minti talatin ta kasa k'iran mijin nata, sai ta danna masa k'ira sai ta katse tun kafin ya shiga, daga k'arshe dai tayi ta maza ta k'ira ta kara a kunnenta, bugun zuciyarta ya tsananta har hannunta na rawa tsabar kid'ima da tsoron abunda zai faru, addu'a bai bar bakinta ba har ta k'ira sau uku bai d'aga ba. K'arar message taji tun kafin ta bud'e tasan daga Alhajinta ne, bismillah tayi ta danna ta bud'e, haruffa uku ne kacal kamar anyi masa dole "Meh?" Yace mata alamar ta amsa shi ta text ba sai ta k'ira shi ba.

Hawayen da ya sauk'o mata bai hanata typing ba, "Allah ya huci zuciyarka, ina ma zaka gane irin nadamar da nayi da bazaka na purnishing d'ina haka ba. Anyway, k'awayen nan nawa da muke zama dasu kowani weekend zasu shigo gari yau, shine nake neman alfarmar basu masauk'i a gidanka in babu damuwa?". Mintuna uku da tura masa ya turo nasa amsar da "OK" wato ya bata dama su zo su zauna.

Wani b'angare na zuciyarta na farinciki da murnar amincewarsa wani b'angaren kuwa bak'in cikin halin ko in kula da ya nuna mata yafi d'aga mata hankali, shiyasa fuskarta bai nuna murnar nata ba ko da wasa, sai ma hawaye da yake sintiri a kumatunta.

•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•

  Sun iso da misalin k'arfe uku na rana, da taimakon Google map suka isa gidan Pherty bayan ta turo musu address na gidan. Da gudu ta fito daga cikin gida jin k'arar motar tasu, wurin Ummu-Abdoul ta isa ta rungumesu ita da Batool d'in da ke gefenta. Kuka ta kufce musu dashi wanda ita kanta bata san dalilin yinsa ba, bazai wuce tunawa da halin da ta shiga bane ko kuma tunawa da ranar da ta zauna dasu na farko, wanda a ranar bata da damuwar komai a ranta sai ma farinciki da wal-wala, yau ga mutane biyar cikin abokan tafiyanta amma babu Miemiebee tana can tana fama da nata rayuwar, har ranar ta kasa samun tak'amaiman bayani game da abunda ke faruwa da ita, duk ranar da sukayi waya daga ta fara magana toh kuka ne k'arashen, ta dai samu labarin Kamal ya mata saki d'aya, bayan wannan bata ji komai ba, ta kasa samun wannan damar a wurin Miemiebee.

Sun shigo ciki suka kwashi kukansu kowacce da abunda ke ranta, yawancinsu rayuwar da suke ciki ne ya sa su kuka, wasun su kuma nasu da na 'yan uwansu shi ya sa su kuka, musamman ganin yanda Pherty ta rame kuma take risgar kuka daga ganin isowarsu. Babu wanda baiyi kuka ba, dak'yar suka tsagaita ta gabatar musu abincin da ta ajiye musu tare da abun sha.

Sai da suka ci suka sha sannan ta nuna musu d'akuna biyu da zasu zauna wanda tuni ta gyara har ta sa turare ta wanke toilets. Su dai sunce d'aki d'aya zasuyi anfani dashi ba sai ta basu har biyu ba, duk yanda tayi dan nuna musu hakan bazai yu ba dole ta hak'ura ta janyo musu katifa da taimakon Ruffaida. A nan d'akin suka baje suna hira da d'ai-d'ai suke shiga suyi wanka har duk suka gama suka shiga hirar yaushe gamo had'e da yanda rayuwar kowaccensu yake.

A yau dai suke expecting ganin Hussain dan sun k'irasa tun kafin su taso ya tabbatar musu zasu samu ganinshi a nan wani restaurant da ke kusa dasu bayan isha'i. Shiyasa suna d'an hutawa suka shuga b'angaren uwar gidan Pherty suka gaisa, matar kirki da son barkwanci da mutunta juna, sun d'an yi hira daga bisani sukayi sallama suka koma masauk'insu tare da shirin had'uwa da Hussain saurayin Benaxir na da (ex-boyfriend).

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


              Page 53


   "Sorry mun ajiyeka, bamu gane wurin bane" cewar Pherty tana k'ok'arin jan kujerar da ke wurin. Bai amsa ba, sai ma idanunsa da ke bin 'yan matan dan ganin ta inda Benaxir zata fito, sai dai har suka samu mazauni bai ganta ba kuma da alamu ba da ita suka zo ba. Kallonsu yayi da d'ai-d'ai bai gane kowa cikinsu ba, da alamu bai tab'a ganin ko da mutum d'aya ba, gyarar murya yayi yace "sannunku da zuwa garinmu, sai dai ban ga mutuniyar ba" murmushi Batool tayi tace "mun barta gida ta gaji, tana d'an hutawa kafin gobe mu fita ganin gari. Ya matarka, munji har 'da muke da ko? Allah yayi albarka". 

Murmushi shima yayi ya amsa da lafiya sannan suka shiga tattauna abunda ya kawo su. Sosai suka tattauna yanda za'ayi su shawo kan matsalar, sun tsayar da maganar cewa zasu neme shi duk lokacin da suka tsayar da maganar zuwa wurin iyayen nata, kuma yayi na'am da batun nasu. Bai barsu ba sai da yazo har gidan da suke da motarshi ya nemi ganin Benaxir, sai dai duk yanda sukayi da ita tace bazata fito ba dan bata son ganinsa.

Washe-gari:-


   Tun k'arfe tara suka gama shirin zuwa gidan Benaxir amma basu samu fita ba sai sha-d'aya dan Pherty ta samu damar tambayan fita wurin mijinta. Motar kishiyarta ta karb'a suka yi mota biyu zuwa gidan, dama tun kafin tasowarsu ta sanar da ita zuwan nasu, kai tsaye suka shigo cikin gidan bayan sunyi parking motocinsu a waje dan gidan bazai d'auki motocin ba.

Sunyi farincikin ganin juna sunyi hirar yaushe gamo, ta gabatar musu abun ci da na sha, 'ya'yanta sun tarbi Benaxir kamar basu tab'a wulak'antata ba a da, sun zauna tare sukayi hirarsu dukka kamar sun dad'e da sanin juna. Basu bar gidan ba sai yamma lis da misalin k'arfe biyar, sun fito dukkansu murmushi bisa fuskar kowacce daga cikinsu.

Lubiee ce ta fara fitowa cikin harabar gidan, sai Ummu-Abdoul, Batool sai Ruffaida na bayanta, sauran kuma suna biye dasu a baya. Kamar ance Batool juya ta waigo idanunta ya sauk'a dai-dai wurin shak'atawar gidan wanda yake da table k'arami da kujeru hud'u ya zagaye. Cak numfashinta da fara'ar fuskarta ya kau, kallonsa ta tsaya yi zuciyarta na bugun lugude. Ko a mafarki ta tashi bazata tab'a mance wannan fuskar ba, kunnuwanta ne suka jiyo mata zancen Ruffaida "wow,Batool kinga guy d'in can? Ya had'u sosai wallahi, kuma ke yake kallo, da alamu ya kamu" ta fad'i k'arashen maganar tana mai yi mata dariyar murna da farinciki.

Ganin ya tashi yana kusanto su yasa tayi waje ba tare da ta saurari ban kwanan da Benaxir da yaranta suke mata ba. Motar Pherty ta bud'e ta shiga ko waigowa bata sake yi ba, duk sauran 'kawayen nata sai a sannan suka fito suna mai mamakin fitowarta cikin hanzari da sauyawar da tayi cikin lokaci k'ank'ani. Isowarsu wurin motar da tambayarta meh ya sameta yayi dai-dai da fitowarshi daga gidan.

Kuka ta fashe musu dashi tana cewa "mu tafi dan Allah kafin ya iso, dan Allah nace" babu wanda ya amsata bare suyi abunda take rok'a hakan yasa ta maimaita rok'on nata cikin d'aga murya ta sauk'e kanta ta ajiye bisa cinyarta tana mai cigaba da kukanta cikin sheshshek'a, a dai-dai wannan lokacin ya iso inda suke, fuskarsa duk a birkice jikinsa har rawa yake, cikin i'ina yace "Batool" d'ago rinannun idanunta tayi cike da tsana tana kallonsa, hawayen da take yi tuni sun kafe, banda bugun zuciyarta da ya tsananta babu abunda takeji a yanzu sai tsanarsa da mugun da na sanin zuwa gidan.

   Cikin kakkausar murya tace "ka sanni ne? Waye kai? Kada ka kuskura ka sake min magana, ban sanka ba kuma bana buk'atar saninka". Kallon Pherty tayi tace "ku shigo mu tafi, dan Allah mu wuce banson in k'ara ko da minti d'aya a bakin k'ofar nan". Mamakinta suka tsaya yi, basu iya tab'uka komai ba suka ji muryarsa yana cewa "Dan Allah ki saurareni, akwai abubuwa masu yawa da nakeson fad'a miki, please Batool ki agajeni kada ki gujeni ni meh laifi ne na sani". Cikinsu babu wanda yasan lokacin da ya rato tsakiyarsu ya isa mab'allin motar har yake zuba wannan zancen.

"Mtsw!" Ta ja tsaki ta bud'e k'ofar motar da k'arfi, tana sane ya buge masa k'afa amma ko ta kalleshi bare nuna damuwarta, fitowa tayi cikin hanzari tayi bakin titi, duk k'iranta da sukeyi bata waigo ba sai ma saurin da ta k'ara, Lubiee ce tayi sassarfa ta isa wurinta had'e da rik'e hannunta tace "ina zaki je? Please ki tsaya mu wuce da motarmu kada ki tafi ke d'aya, in kin tafi ma ina kika sani da zaki je?" Juyowa tayi ta fashe mata da kuka ta d'aura fuskarta a kafad'arta tana cewa "Mujahid ne fa, meh zai ce min yau kuma? Meh zai min a rayuwa bayan b'ata min suna da ya yi? Meh yake nema a wurina yanzu da zai min magana?". 

Daga farkon zancenta har k'arshe a kunnen k'awayen nata da suka iso inda take ganin yanda ta birkice musu a take, Benaxir baki bud'e ta tsaya kallonta, duk kallonsu suka mayar wurinsa suna kallonsa cike da mamkin ganinsa. "Batool wannan shine saurayin naki da kika bamu labari, wannan ne? Ni ban gane shi ba da kike bada labarin nan, amma lallai Mujahid, ban tab'a d'auka iskancinsa ya kai hakan ba" cewar Benaxir.

Hannun Batool ta rik'e ta kai ta cikin motar ta umarci Pherty da ta wuce da ita suna biye da ita a baya, sai a kowaccensu ta shiga mota sannan ita ta isa inda yake tsaye bayi da laka, idanunsa sun rine kamar zai fashe mata da kuka, tun kafin tayi magana yace "dan Allah ku taimakeni in mata magana, na gane kurena nayi laifi, wallahi ina sonta" sauk'ar marin da yaji bisa k'uncinsa ya sa shi lumshe ido had'e da had'iye yawu mai d'aci, tar yake jin zancen da take yi cike da masifa "har kana da bakin cewa kana sonta? Kai ne dama ka b'ata wa k'awata rayuwa? Ka rabata da iyayenta ka b'ata mata suna a gari miji ya gagareta? Shin kana da zuciya Mujahid? Duk respect d'in da kake bani ashe na k'arya ne baka tausayin mace?" Ganin ya zube mata a k'asa yana hawaye yasa ta dakata tana kallonsa, hannunsa ya had'e wuri d'aya yace "dan Allah kiyi hak'uri, naji duk abunda ya sameta a dalilina, baki san irin neman da nayi mata ba, infact yau isowana garin nan daga Abuja naje nemanta, wallahi wallahi a shirye nake da karb'an duk hukuncin da zata min, na tuba, ku taimakeni ku barta ta saurareni sai ku hukunta ni bayan hakan" ya k'arashe maganar yana kuka mai zafi mai shiga rai.

Bata tanka sa ba ta juya ta shige cikin motar, kukansa da magiyarsa ya karya mata zuciya, ba dan hakan ba yau zata yi masa wankin babban bargo, duk saninta dashi suna bawa junansu girma, suna matuk'ar shiri kuma yabonsa cikin abokan k'aninta, ashe shine silar rugujewar rayuwar Batool? Motar ta figa ba tare da ta saurari magiyarsa ba, duk cikinsu ya basu tausayi amma tunawa da k'awarsu yasa suka d'auke kai har da jefansa da mugun kallo suka bad'esa da k'ura suka wuce.

•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°

Bayan kwanaki biyu:- Miemiebee @ 4pm


   Kowa ya hallara cikin k'aton parlon Baban Kamal, Kamal da Miemiebee na zaune a k'asa cike da girmamawa, shi dai Kamal ko kallon Miemiebee baiyi ba bare zuciyarsa ya karaya da abunda yayi niyya, ita kuwa banda hawaye babu abunda take yi sai ciwon kan da ya addabeta kamar zai fasa mata kai.

Shi yana zaune gefen Mamansa da Babansa, ita ma haka, dan hannayenta na iya tab'o k'afafun mahaifiyarta. Muryar Baban Kamal ne ya karad'e parlon a karo na uku, cike da masifa da nuna tsantsar b'acin ransa "ba magana nake muku ba? Kun mayar damu k'ananan yara, akwai sa'anku cikin nan ne? Kada ku raina mana hankali muna magana kunk'i sanar damu komai..."

"Tunda tak'i fad'a ni zan fad'a muku..." Kamal ya katsesa, tun kafin ya tsayar da zancensa muryar Miemiebee ya dakatar dashi, disashiyar muryarta ya hana maganar fitowa, hakan yasa ta gyara muryar sannan ta maimaita furucinta "zan sanar daku, laifina ne Yaya Kamal ni ya dace in sanar dasu ba kai ba", kukan da take yi bai tsaya ba sai da taji muryar mahaifinta yana cewa "yafi miki, wallahi Maryam kin kai ni bango kan zancen nan, yanzu zan tattakeki".

"Nasan dole hakan zai faru ko ba yau ba, gwanda in fad'a tun kafin abu ya kwab'e min, kuyi hak'uri ku gafarce ni, nayi da na sani kuma na tuba..." Kukan da yaci k'arfinta ya sa ta dakatar da maganarta, dukkansu sun tsaya dubanta cike da tausayawa, tayi ja haka zalika fuskarta ya kumbura, bayan haka kukan da take sharb'a yanzu ya fiddo mata da jijiyoyin fuskarta, kuka takeyi mai tab'a zuciya har numfashinta na barazanar d'aukewa.

Bata kai ga cigaba da maganar nata ba muryoyinsu ya karad'e kunnenta, "Assalamu alaikum" suka furta lokaci d'aya k'anin Miemiebee kuma na cewa "ku shiga ciki, dukka suna nan", sallama suka sake dokawa had'e da bud'e k'ofar falon d'aya daga cikinsu ta sako k'afafunta bayan iyayen sun amsa sallamar. Su biyar suka shigo d'akin fuskarsu da fara'a, kasa gaskata idanunta tayi sai da ta furta sunayensu dukka "Ummu-Abdoul, Lubiee, Batool, Ruffaida and Benaxir" tana kallonsu d'aya bayan d'aya, da gudu ta isa ta rungumesu tana mai fashewa da sabon kuka suma haka.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


              Page 54


  Sai da sukayi mai isar su babu mai rarrashi sannan Baban Miemiebee yayi gyarar murya yace "toh sannunku, sai dai bamu gane ku ba?" Ya k'arashe maganar nasa yana kallonsu fuskarsa na nuni da alamar tambaya. Ummu Abdoul ce ta gyara zamanta kanta a k'asa cike da girmamawa tace "ina wuninku", sauran ma suka gaishe su suka amsa sannan tace "k'awayen Miemiebee ne daga Abuja, kwana biyu mun ji ta shiru shine muka biyo dubata" Maman Haneep ta ware idanu tana kallonsu tace "daga Abuja har Yola? Wannan wani irin k'awance ne?".

Ta juyo ta kalli mijinta tace "ni fa na fara zargin abunda ya had'a Kamal da Miemiebee, kaga matan nan dukka wai sun zo dubata", maman Miemiebee ce tace "meh hakan ke nufi? Ki fito fili ki fad'i abinda yake ranki game da Maryam mana meh na kwana, baki iya kawo abu meh kyau a ranki sai mugu..." Kallon da baban Miemiebee yayi mata ya dakatar da ita ta d'auke kai, tasan abunda matar take nufi sarai shiyasa ta harzuk'a, Miemiebee da ke risgar kuka a gefe tuni ta gane manufarta, hakan ya k'ara shigar da ita rud'ani had'e da sabunta bugun zuciyarta.

  Kamal ne yace "Mama wad'an nan na sansu, ba abunda yake ranki suke aikatawa ba, wad'an nan" ya nuna su da hannunsa sannan ya cigaba "su suka nemi sulhunta mu suka nemi zaman lafiyarmu, da ba dan su ba abun bazai kai ga hakan ba". Benaxir da ke zaune kusa dasu tace "wai da tana nufin mu muka b'ata tsakaninku ko meh?" Lubiee da ke gefenta ta mitsineta alamar tayi shiru, dan tuni ta gane manufar Maman Haneep. Babu wanda ya sake maganar sai ma shiru da akayi ana sauraran Miemiebee wacce a yanzu ta tsagaita kukan.

Daga farkon labarinta har k'arshe ta labarta musu cikin sheshshek'ar kuka, mafi yawancin lokaci in ta dakata tana kallon fuskar mahaifiyarta da mahaifinta, ko kuma in kuka yaci k'arfinta ta dakata, tunda ta fara mahaifiyarta banda hawaye babu abunda ke fita daga idanunta, mahaifinta da mahaifin Kamal kuwa idanunsu tuni ya canja kala yayi jawur dan b'acin rai. Kukan da takeyi da kalaman da take anfani dasu na nuna rauni da tuba had'e da da-na-sani shi ya d'an sassauta b'acin ran.

Shiru ya biyo bayan kammala labarin nata, banda kukan mamanta da nata da sauran 'yan uwanta har ma da Kamal babu abunda ake ji a d'akin sai kuma k'arar Acn da ke kunne. Maman Haneef ce tace "Hmm! Ai ba daban da abunda nake zargi ba tun farko, yanzu ke Maryam k'arama dake har kinsan dad'in namiji da har zaki bi wasu in mijinki baya nan?" Tana mai nuna ta da yatsa ta fad'i hakan, babu wanda yayi mata magana hakan yasa ta dafa kafad'an d'anta tace "kayi min dai-dai da ka saketa, babu anfanin zama da wannan, ai da uku ka bata sai infi jin dad'i. Mata gangariya 'yar k'arama bafulatana zan kawo maka ka aura ka manta wannan". 

Miemiebee na jin haka ta k'ara sautin kukanta, shikenan an rabata da mijinta, Pherty ta huta ta samu nasarar rabata da mijinta. Ji tayi ta tsani duk 'yan matan nan shida musamman Pherty da tayi sanadiyyar tonuwar asirinta sai kuma Ummu-Abdoul da ta bada shawarar fad'awa mijinta. Da hakan bai faru ba yanzu tana rayuwarta da mijinta cikin jin dad'i da soyayya. Muryar Ummu-Abdoul taji tana cewa "Maman Haneef baza'a yi haka ba, tunda ta gano kurenta a gyara komai, a basa hak'uri yayi mata uzuri, ita kuma ta gano kurenta..." "Kada kice bazata sake ba, aikin nasa zai bari saboda biya mata buk'ata? bazai tab'a yiwuwa ba kun sani".

Ta mik'e tsaye tace "tashi mu tafi, mutane basu iya tarbiyyar 'ya'yansu ba a hakan suke neman miji ya iya zama dasu, toh ku k'arata gata nan ta dawo muku, d'ana ba mazinaci bane bazai zauna da mazinaciya ba". D'akin dukka suka mik'e suna bata hak'uri banda Miemiebee da ke ta gunjin kuka, hannunta cikin na d'anta suka fice daga d'akin duk k'irar da mijinta yake mata bai sa ta juyo ba. Zama yayi sannan ya umarce su da su zauna, yayi gyarar murya yayi nasiha mai ratsa jiki, ya basu hak'uri akan abunda ya faru kuma ya tabbatar musu zai yi magana da matarsa komai zai daidaita.

Ficewarsa ke da wuya kukan Miemiebee ya tsananta. Lubiee ce ta matso kusa da ita tana rik'o hannunta tuni ta buge tana cewa "kada wacce ta tab'a ni cikinku, kun samu abunda kukeso kun huta, kun raba ni da Kamal d'ina kun raba ni da gidan aurena, yanzu kunzo sai ku raba ni da iyayen da suka haifeni". Ummu Abdoul ce ta iso kusa da ita cike da mamakin furucinta, bata iya furta mata komai ba ta rik'o hannunta, warce hannun nata tayi ta koma baya tana mai cigaba da yin kuka.

"Abunda kike tunani kenan? Kina tunanin muna neman b'ata miki rayuwarki? Kina nufin kinfi son jin dad'in rayuwar duniya akan na lahira? Kina nufin zafin da kikeji yau a zuciyarki bai fiye miki zafin da zakiji in aikinki ya shigar dake wuta ba? Kiyi tunani Miemiebee, mu masu k'aunarki ne". Hannu ta d'aga mata alamar ya isheta, bata yi wa kowa magana ba ta fice ta bar parlon ta shige d'akinta had'e da sa makulli.

Zama sukayi dukkansu suna mai jin kukan da Mamanta take rerawa, babu wanda ya iya bata hak'uri bare rarrashi, kamar babu wanda zai yi magana Lubiee ta numfasa tace " Miemiebee tayi zuciya, kuma da alamu rashin samun Kamal yasa ta fusata ya hanata ganin gaskiya, nadamarta shi yafi komai yi mana dad'i, sai dai abu d'aya nake son ku gane matsayinku na iyayenta, ku kad'ai zaku shawo kanta har ta fuskanci abunda muke nusar da ita, kada ku gujeta, kada ku k'yamaceta, abun farinciki ne a wurinku 'yar ku tayi laifi kuma tayi nadama, ku jata a jiki dan gudun afkuwar wanda yafi hakan, ku bata dama ku bata sabuwar rayuwa, da sannu komai zai dawo dai-dai da izinin Allah".

Maganganun kowacce daga cikinsu ne ya sanyaya ran iyayen nata suka k'udurci niyyar magance matsalar da cire mata duk wani shakku da kokonton zasu barta kamar yanda Kamal ya barta, sunyi musu Godiya kuma sun basu tabbacin kula da komai nata dan hakan take buk'ata a wannan lokaci kamar yanda suka ce. A ranar suka bar gidan suka kwana a hotel washe gari suka koma Abuja dan cigaba daga inda suka tsaya cikin neman mafitansu.

A motar ne Benaxir take maimaita maganar Maman Haneef, ita bata gane nufinta ba kuma Lubiee tace tayi shiru, ta fad'a mata meh matar take nufi. Sai da Lubiee ta yi murmushin da bai wuce lebb'a ba tace "ta d'auka abokan Miemiebee muke, kuma abotarmu ya had'ata da mijinta..." bata jira ta kai aya ba tace "Kamar ya?" Ruffaida tace "wani abota ne ba'a so a musulunci tsakanin mace da mace? Toh abunda take nufi kenan, nima ai na gane nufinta, kawai shiru nayi dan naga alamar rigima take nema". 

Benaxir ta dakatar dasu da cewa " wait, ni fa ban gane ba" kai tsaye Batool tace "lesbianism mana madam, bakya gane abu". Cikin gwale ido tace "what? Tana nufin mu lesbians ne? Shine kukayi shiru baku wanke min ita ba? Ita tasan bala'in da yake cikin lesbianism take danganta mu dashi? Subhanallahi, matar nan ta gama damu ta mayar damu kafirai..."

Tayi masifa iya masifarta ana bata ha'kuri, daga k'arshe dai tace duk ranar da ta had'u da Maman Haneef sai ta gaya mata magana ko meh zai faru, mafi munin abu zata k'ak'aba musu dan d'anta? Ai Kamal d'in ma bai tsira ba wurin Benaxir, tas ta zage shi har da ce masa mai k'aton kai. Bata yi shiru ba sai da aka samu wani hirar na Batool da Mujahid, nan ta shiga bada labarin nacin da yake mata dan ta had'a shi da Batool, ita dai tace ko zata had'a su sai ta wainashi iya wainawa sannan ta mik'a shi wurin Batool ta cigaba daga inda ta tsaya.

•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°

  Miemiebee tayi mamaki matuk'a ganin yanda iyayenta ke janta a jiki, basu k'ara d'auko maganar ba bare su tada mata hankali, kullum tsakaninsu baya wuce hira da kuma nasihu mai shiga jiki, sosai mamanta ke sake mata fiye da da, duk lokacin da taji zancen Kamal da yarinyar da aka samo masa zai aura takan samu mahaifiyarta tayi ta mata kuka, ita kuwa banda rarrashi da ban baki babu abunda take yi mata.

Tabbas tayi kuskure a rayuwarta, kuma kowani abu sai da kwanciyar hankali ake yinsa, yanzu gata tana rayuwa babu namiji babu wani abunda ke damunta sai bak'in ciki da ciwon zuciyar da ke addabarta, ita yanzu bata san ina zata samo farincikinta ba, dan yana tare da Kamal kuma Kamal ya barta har abada tunda aure zaiyi, yarinya 'yar k'arama bata wuce goma sha bakwai ba, Maman Haneef ce ta kawo masa, ansa biki nan da wata d'aya, ita nata ido da kukan zuci.

Sati biyu kenan yanzu tak'i magana da 'yan uwan nata, har ranta take jin ta tsanesu dan sun b'ata mata rayuwa, duk cikinsu babu wanda bai tausaya mata ba, sai dai ya zasuyi banda yi mata addu'a da gyara tasu rayuwar? Pherty har lokacin bata samu damar yin magana da nata mijin ba, ya dai shigo sau d'aya ya dubata sun gaisa ya sake komawa bakin aikinsa, ko waya ta k'irashi bai d'auka sai dai tayi masa message ta fad'i buk'atunta, baya hanata duk abunda ta tambaya na abinci da sauran 'kananan abubuwa, bata da nutsuwar neman manyan abu bare ta tambaya ya hana mata, har yau dai bata samu damar zuwa ko ina ba banda lokacin da ta fita tare da k'awayenta.

Ruffaida kuwa sosai ta shiga damuwa jin anyi gaisuwar Sadiq da Candy, duk da har yau Mamu tak'i komawa gidan mijinta bai hanata tunkararsa da maganar tambayar ba, da farko ya nuna bazai je ba amma da tayi masa jan ido, dole ya had'o k'annensa suka je gaisuwa aka tsayar da maganar aure nan da watanni uku, abinda yafi d'aga mata hankali bai wuce yanda Sadiq yake nuna mata zallar maitarsa da farincikinsa ba, komai zaiyi sai yace "i can't wait inga ranar da zan mallaki candy, ina fa sonta sosai" a duk lokacin da ya fad'i hakan ji take kamar ta zunduma ihu amma ya zatayi? Ta b'ata rawarta da tsalle.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


              Page 55


  Banda gunjin kukanta ba abunda ke tashi cikin d'akin, zuciyarta cunkushe ji take kamar ta hau shi da duka dan haushin da yake bata. Cikin dasashshiyar muryarsa yace "Batool ki taimakeni ki tsagaita kukan nan ki min magana ko zan samu nutsuwar zuciyana, nasan na miki laifi nayi kuskure, amma ban d'auka hakan zai kawo sab'ani tsakaninki da iyayenki har haka ba, tunda naji labarin halin da kika shiga na nemi sulhu dake, na tausaya miki kuma nayi da na sanin rayuwar da na jefaki ciki, ki bani dama in gyara, ni na b'ata rayuwarki ki bani damar gyarawa, ki bani damar haskaka miki shi fiye da yanda kike mafarki, fiye da yanda kike karantawa cikin litattafai, fiye da yanda kike gani cikin film, zan zame miki komai, zan biya miki buk'atunki kuma zan so ki har k'arshen rayuwata. 

Ban tab'a d'auka zan soki har haka ba, duk cikin 'yan matan da nake tare dasu ko ince miki wad'an da nayi rayuwa dasu babu wacce nine farkon fara saninta a 'ya mace sai ke, shiyasa babu wacce nayi da na sanin kasancewa da ita irinki, na canja saboda ke, ki yadda ina sonki yanzu kuma zan miki duk abunda kikeso, fatana ki amshi soyayyata ki bani ragamar sauran rayuwarki dan in k'awata miki".

  Idanunta ta d'aga a hankali ta d'aura su akansa, idanunta yayi luhu-luhu ya d'an kumbura alamar kukan da tasha na da yawa. Yawu mai d'aci ta had'iye sannan tace "taya zaka gyara min rayuwa? Taya zaka shawo kan iyayena bayan sunyi fushi dani sun koreni daga inuwarsu? Ko kana nufin kai kad'ai ka isheni rayuwa ba tare da iyayena ba? Kai baka san fushin iyaye akan 'ya'yansu ba ko?".

Hannunta yayi k'ok'arin rik'ewa ta janye, hakan yasa yayi murmushin da bai kai ga zuciya ba yace "ki bani dama, shine buk'atana, tare zamu shawo kan komai, na miki alk'awarin shawo kan matsalar da yardar Allah. Ki bani dama please, am sorry for everything". "Toh malam" cewar Benaxir rik'e da labulen parlorn ta sa kanta tana lek'ensu, "bar min k'awata ya isa haka, sai ka sa ta ciwon kai sannan zaka huta? Na baka daman ganinta, ka barta tayi shawara in yaso sai ka dawo bayan kwanaki". 

Kalonta yayi kamar ya sake mata sabon kuka, amma yanayin fuskarta bai bashi damar magiya ba, babu yanda ya iya dole ya mik'e ya bar gidan idanunsa na fidda k'wallar nadamar rayuwar da yasa Batool, wacce a yanzu yake matuk'ar so da tausayawa fiye da komai.

Zuwan shi gidan Benaxir na uku kenan yau yana rok'on ta bashi damar ganin Batool, yau dai sai da ya rik'e k'afafunta yana zubar mata hawaye sannan ta d'auki waya ta k'ira Batool ta nemi tazo gidan da take zama. Anan ne ya samu damar yi mata magana ya kuma bata hak'uri.

•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°

Benaxir ce tayi k'ok'arin rarrashinta, duk da kukan da takeyi ya tsaya amma hawaye bai daina zuba daga idanunta ba lokaci-lokaci. Motar Benaxir suka shiga kai tsaye suka wuce gidan Ummu-Abdoul. Ruffaida kad'ai suka samu dan lokacin k'arfe hud'u ya d'an gota kad'an. 

Lubiee ta k'ira a waya tace tazo gidan Ummu-Abdoul suyi magana, ita ma bata koma gida ba daga office, taxi ta tara kawai tayi hanyar gidan Ummu Abdoul, kusan a tare suka iso, dan shigar Ummu-abdoul ko minti biyar baiyi ba sai ga Lubiee ta shigo a gajiye. Ruwan sanyi suka sha sannan suka baje tsakiyar parlo dan tattauna matsalar.

Benaxir ce ta fara magana "abun nan fa ya fara damuna, abunda ya wuce yake sake dawo mana ni da Batool, kunga tun ranar da muka je Minna har yau nataccen Hussain ke k'irana a waya, ko meh yake nema oho, ni bazan iya sauraransa ba dan zai iya barina nan gaba kamar yanda ya barni a baya. Ga Batool nan yanzu ta gama nata kukan Mujahid ya dawo yana son ya aureta..." "Alhamdulillahi" cewar Ummu-Abdoul tana d'aga hannunta sama idanunta na kallon sama. Batool da Benaxir da mamaki suke dubanta, muryarta ne ya dakatar dasu ya dawo dasu hayyacinsu. 

"Wannan ai abun murna ne abun farinciki, ke yanzu Batool sai kik'i yadda da buk'atarsa? Shi kad'ai ne zai iya sauk'o da iyayenki daga dokin zuciyar da suka hau..." Benaxir tace "kuma har kike murnar dawowarsa kina hamdala ba tare da kince mu gara shi ba tukunna?" Ummu-Abdoul murmushi tayi tace "ai wannan daban, kuma na tabbata ko ban fad'a ba sai ta ja aji, dan mace ce. Yanzu abunda za'ayi shine ku dai-daita tsakaninku, ya sanar da iyayensa sai suje gida wurin iyayenki neman aurenki, bayan anyi hakan sai kije ki sauk'ar da kai kiyi musu bayanin ko shi waye, na tabbata zasu saurareki wannan karon".

"Haka ne kuma fa ya dace" cewar Benaxir tana washe baki tana kallon Batool, Lubiee ma tayi murnar jin wannan labari, sosai tayi murna matsalar Batool yazo k'arshe, fatanta Allah ya bawa iyayenta hak'uri da juriyar yafe mata kuskuren da ta tafka. 

•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°

  Yau ya kama Jumma'a, washe gari d'aurin auren Kamal da Hauwa 'ya ga k'awar Maman Haneep. K'arfe biyu Pherty da sauran 'yan uwanta suka iso dannar k'irji, fir tak'i yadda tayi magana dasu, kukan da takeyi yafi komai d'aga musu hankali, tuni ta canja kala ta haukace musu cikin gida tak'i sauraran rarrashin kowa daga cikinsu, "ku fita mana daga gida munafukai" shine kad'ai abunda take iya furtawa, Benaxir ce ta zuciya ta fita daga gidan taje ta zauna cikin motarsu tana jiransu, dan zuciyarta bazai iya d'aukan zagin da Miemiebee ke musu ba, musamman kalmar munafurcin da take furtawa.

Babanta da kansa ya rok'esu su fice dan bazata sauraresu ba, har waje ya rakasu ya basu hak'uri yana jaddada musu zai wuce ita da kanta zata nemo su dan sun taimaketa k'warai bazata tab'a butulce musu ba. Cikinsu babu wanda baiyi kuka ba ganin yanda ta koma, Pherty har ranta taji haushin abunda tayi anfani dashi dan Miemiebee ta sanar da mijinta abunda take aikatawa, nan take tayi alwashin k'onawa da zarar ta isa gida dan illa ne babba ajiye babban sirri irin wannan.

A ranar suka wuce Abuja, washe gari Pherty ta koma Minna kamar yanda sukayi da mijinta duk da tambayar da komai anyi shi ta text. Abunda ta fara yi kenan daga isarta gida, ma'adanarta taje ta d'auko ta fito bayan d'akinta ta kunna masa wuta, akan idonta ya k'one k'urmus. A dai-dai wannan lokaci aka d'aura auren Kamal, fad'in irin kukan da Miemiebee tayi had'e da da-na-sani b'ata lokaci ne.

Lubiee ranar Lahadi @ 10am


   Cikin baccinta take jin hayaniya k'asa-k'asa, kamar bazata tashi ba ta ware idonta, k'ofar d'akinta idonta ya kalla taga Kausar tana tsaye wurin tana rik'e da k'ofar tana kallon Parlon. "Kausar" ta k'ira sunanta, k'in amsawa tayi bare ta juyo wurin mamanta, hankalinta gaba d'aya na kan abunda take gani. Da ihu ta sake k'iran sunanta hakan yasa yarinyar ta firgita ta juyo wurinta, sai da ta iso sannan tace "Baba duka" ta fad'i haka hannunta na nuna k'ofar.

Cikin hanzari Lubie ta tashi ta isa k'ofar dan ganewa idonta, da iya k'arfinsa yake ball da ita duk da kukan da takeyi bai hana shi lallasa ta ba, yaranta na tsaye gefe suna nasu kukan ganin anyi wa uwarsu jina-jina. Cike da tashin hankali ta fito ta isa inda yake tana mai rik'e hannunsa dan hanasa kisan kai.

"Lafiyanka?" Take cewa tana matsar dashi gefe tana kallon Nafee da ke kwance tana fitar da nishin wahala. Bai amsata ba sai cewa yayi "fice min daga gida dake da 'ya'yanki, ki koyi tarbiyya kina zuwa islamiyya sannan ki dawo, maras hankali, ku fice min nace" ya daka musu tsawa. "Haba, ya zaka ce ta fice ita da 'ya'yanta? Yaran nan ai naka ne, in ta maka laifi ka hukunta ta wani hanyar ba ta hanyar nan ba, wannan ba hukunci bane" tana gama fad'an haka ta isa inda Nafee ke kwance ta d'agata ta kaita d'akinta tana yi mata sannu. 

Ruwan zafi ta had'a mata ta umarceta da shiga tayi wanka, kafin ta fito ta tura yaranta d'akinta dan suma suyi wankan, haka ta tattare mata d'akin tas kafin ta fito ta gyara shimfid'a, duk aikin nan da takeyi Kausar na biye da ita tanai mata surutu.

Bayan ta fito ta wuce nata d'akin tana tunanin meh ya had'a Nafee da Abubakar haka ya kai ga duka? Dukan mace ba halin Abubakar bane, tabbas ta kai shi mak'ura shiyasa hakan ya faru. Bata gama tunanin ba taji shigowarsa d'akin, lokacin Kausar tana can parlor tana wasanta. 'Dauke dubanta tayi daga shi tana mai kawar dakai kamar bata ganshi ba, wurinta ya isa ya zauna a gefenta had'e da rik'e hannunta cikin nasa.

Haka kawai ta tsinci kanta da kwace hannunta daga nasa tana mai k'ara matsawa baya dan jikinsu da ya had'u. "Guduna kike matata?" Furucinsa yasa ta d'ago kai tana dubansa dan tabbatar da abunda taji a kunnenta, murmushi ya sakar mata yace "na dad'e inason tunkararki amma nasan laifina ya wuce wanda za'a iya tausayawa bare a saurara, i don't know ko zaki gane min, nidai nasan i wasn't myself tun kafin in auri wannan matar, bansan ya akayi na aureta har na kawota cikin gidan nan ba bayan nasan halinta, a lokacin rufe ido nayi na toshe kunnena dole aka aura min ita dan na nuna inaso, bayan na aureta na musguna miki duk dan in faranta mata, bansan meh ya hau kaina ba lokacin har sai ranar da na dawo gida kaina na matsanancin ciwo, anan na fara taryo duk wani abunda nayi kuma nayi da na sani, kiyi hak'uri ki taimakeni kada ki gujeni akan abunda na aikata cikin rashin sani..."

Iya nan hankalinta ya iya ganewa dan wani farinciki da ya ziyarceta yasa ta shiga wata duniyar, ashe asirin tun a ranar ya karye? Kunyar yanda zai tunkarota ya hanasa zuwa gareta. jin hannunsa na shafa fuskarta yasa ta dawowa hayyacinta, "kiyi hak'urin abunda nayi miki, k'aurace miki, k'in biya miki hak'k'ok'inki da suke rataye kaina..." Bata bari ya k'arasa zancensa ba ta ture hannunsa daga fuskarta ta mik'e tasaye had'e da juya masa baya tana mai zubar da hawaye.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


              Page 56


  Tashi yayi ya isa inda take, har cikin ransa yake jin kukanta, meh zai mata ta gane ba laifinsa bane? Ya zaiyi ya rarrasheta? Sai da ya had'iye yawu mai d'aci sannan ya iya d'ago hannunsa ya d'aura bisa kafad'anta, bai iya furta ko da kalma d'aya ba yaji hawaye masu zafi suna sauk'o masa, shi har ila wannan lokacin bai san asiri ne akayi masa ba, ya dai san bai san ya akayi ya muzgunawa matarsa abar sonshi ba dan duk abubuwan da yayi suna nan daram cikin kwanyarsa.

Rungumeta yayi ta baya ya fashe mata da kuka kamar yaro yana bata hak'uri, alal hak'ik'a bai san ya zai kare kansa ba, shiyasa duk ya rasa tudun da zai dafa dan gyara kuskuren da yayi. A hankali ta janye jikinsa daga nata ta juyo hawaye na rige-rigen sauk'a daga idanunta. "Ni bani da matsala da abunda kayi min, duk wani abunda kayi min na yafe dan nasan ba hayyacinka kake ba, meh yasa tun lokacin da ka dawo tunaninka ka kasa zuwa gareni sai ma d'aure min fuska da kakeyi haka kawai dan ra'ayinka na daban? Kasan irin halin da na shiga a iya shekarun da ka shareni ka fita harkata? Toh wanda na shiga bayan gwagwarmayar da na sha dan dawo dakai yanda na sanka ya fi sa. Bayan nan Abubakar in ni kayi fad'a dani ka k'aurace min ka min masifa ka zageni a lokacin da baka san meh kakeyi ba".

Ta nuna k'ofar d'akinta sannan ta cigaba da magana cikin kukan da kana ji kasan har cikin ranta takeyi.


"Ita kuma ba cikin hayyacinka ba ka jibgeta kamar kaya? Ko baiwa aka kawo maka gida da zaka d'auki hannu ka d'aura akanta da sunan duka? Ba ma hannu kad'ai ba har da k'afa? Nayi niyyar yafe maka duk abunda ka min, zan iya cewa zuciyata tayi sanyi matuk'a tunda na gano ba hayyacinka kake ba, amma a yau da na ga dukan da kayi wa mace, macen ma matarka sai naji ka canja min, ka fice min a rai bazan iya zama dakai ba wataran kaina zaka dawo ka jibga yanda kayi mata..."

Cikin zafin nama ya iso inda take ya toshe bakinta da hannunsa dan maganarta yana shigarsa, ko hauka yayi bazai iya dukan Lubieensa ba, inaa! Hawayen da yake sun kafe tuni idanunsa yayi ja, cikin sanyin murya yace "haba Lubiee, kinsan halina kinsan abunda zanyi da wanda bazanyi ba, na tabbata son ranki kike fad'a" mutsumutsu ta fara yi tana k'ok'arin cire hannunsa daga bakinta dan yin magana ta kasa. 

"Kinsan abunda ta min? Da farko ban ma yi niyyar dukanta ba, ita ta biyoni har waje ita da 'ya'yanta suna min dariya dan kawai bata san darajana ba kuma bata da tarbiyya, zuciya ya d'ibeni na jibgi banza, yanzu na tabbata zata shiga hankalinta bazata min raini ba in nasa ta abu kuma bazata d'ibo maras kunyar yaranta ba dan su min dariya tana yada min magana gabansu ba". "Duk yanda tayi maka bai dace ka daketa ba, akwai hanyoyin horo masu yawa ba sai da duka ba" yanda tayi maganar ya basa dariya, dan har a lokacin bai cire hannunsa daga bakinta ba dan kada tayi magana, dak'yar maganar ke fita dan ya toshe bakin da kyau sai da ya sa hankali sosai sannan ya gane furucinta.

    Kallonta ya tsaya yi cikin ido kamar yanda ita ma ke kallonsa, hawayen da take yi sun kafe sai wad'an da suka mak'ale a fuskarta basu samu damar sauk'a ba, a hankali ya cire hannunsa daga bakinta bai d'auke idanunsa daga kallonta ba haka ita ma. Hannunsa yayi anfani dashi wurin share mata hawayen fuskarta, jin hannunsa na yawo a fuskarta yasa ta lumshe idonta ta kasa bud'ewa dan wani yanayi da ta fad'a.

Idanunta da ta rufe ya bashi damar kallon fuskarta da kyau, daga k'arshe idanunsa suka sauk'a kan lebb'anta. Shauk'in so da k'auna ya d'ibesa tuni ya had'e nasa da nata wuri guda suka shiga duniyar da suka dad'e basu ji kansu ciki ba. K'arar bud'e k'ofa yasa ya saketa a hankali ya juyo dan ita har a lokacin bata iya dawo da hayyacinta da tunaninta ba, sai da taji Kausar ta dafa ta sannan ta iya bud'e idanunta ta sauk'e akansa da ya koma bakin gado ya zauna yana yi mata murmushin da yake narkar mata da zuciya.

Minti ta bawa 'yarta dan ta basu wuri su tattauna maganar da ita a ganinta shi ya dace su yi ba soyayya ba, komai da lokacinsa. Sosai ta nuna masa rashin dacewar dukan Nafee da furucinsa na su tafi da ita da 'ya'yanta, ita tace babu inda zasu je shi kuma yace tunda ita ce da gidan sai tayi shi ya gama magana.

Dole dai ya hak'ura ya k'yale Nafee ta zauna gidan amma ko kallo bata ishe shi ba, da zarar tayi masa maganar da bai gamshe shi ba zai yo kanta kamar zai doketa sai ta sa gudu. Lubiee ma bata tsira ba cikin gidan da zagi sabo aka fara yi mata, ko dan bata san dalilinta take zama cikin gidan ba oho. Lubie ta kasa ta tsare cikin gidanta, addu'o'i da duk wani kariya wanda annabi ya bar mana wanda ta sani da wanda aka sanar da ita babu wanda bata yi wa kanta da 'yarta, haka zalika tana sa mijinta a ciki dan kada abun da ya faru a baya ya kuma faruwa.

Sosai ta mayar da kanta kan addininta, a kullum sai ta sa mijinta a gaba sunyi karatun Qur'an tare, kuma bata barinsa ya fita sai yayi azkar, na safe da yamma, kuma bata barinsa yayi bacci sai tace "kayi addu'a fa, ka ma yi alwalar bacci?" Ko ya fara bacci ne sai ta tashe shi, hakan yasa ya sauk'ak'awa kansa, da ya shiga yin wanka zai had'o da alwalarsa sannan yazo ya kwanta. (Rayuwa ya canja)

Pherty:-  


   Kwance take a d'akinta taji shigowarsa, zama tayi tana mai yi masa sannu da zuwa dan tun zuwansa gari yau kwana uku kenan bata sa shi a ido ba sai dai taji muryarsa. "Tashi mu tafi Abuja yanzun, kada ki b'ata min lokaci" "Abuja" ta maimaita sunan amma tuni ya fice bare tayi masa tambaya. Kenan yana nufin bazai saketa ba? Ko kayanta zata je ta d'ibo ya dawo da ita? Horn na motarsa yasa ta mik'e da hanzari ta d'auki jakarta da gyalenta ta fito tayi hanyar uwar gidansa dan yi mata sallama.

Bata yi minti biyar ba ta fito rik'e da leda, bazai wuce kishiyar nata bace ta bata. Baya ta shiga ta zauna zuciyarta bai samu nutsuwa ba. Kamar yanda suka zo haka suka koma babu wanda yayi wa wani magana har suka isa ya fice ya shige ciki ta biyo shi a baya. A parlor ta yada zango dan bata son shiga d'akinta ta sakankance kuma yayi mata fad'a. Minti talatin tayi zaune a parlon bai fito ba, ta d'an kishingid'a jikin kujera har bacci ya fara kwasarta taji fitowarsa.

Tsaye ta mik'e wayarta na hannunta tana kallon k'asa, wurinta ya isa yace "ki shiga ciki ki huta mana" bata amsa ba k'arar wayarta ya katseta alamar text ya shigo, dubawa tayi tuni idanunta suka nuna firgici da tsoron da ta shiga ganin numban da yayi mata text. D'ago idonta tayi ta kallesa sannan ta sake mayarwa kan wayarta, hannunsa yasa ya karb'i wayar dan ganin abunda ya rud'ar da ita.

Tuni annurin fuskarsa ya d'auke duk da dama ba fara'a yake yi ba, "Ibrahim" ya gani rubuce, sai da ya kalleta sannan ya bud'e sak'on ya karanta. Wayar ya mik'a mata ya gyara tsayuwarsa ya hard'e hannayensa bisa k'irjinsa yace "k'irashi ki sa a handsfree". Hannunta kasa danna wayar yayi dole ya karb'a ya k'ira yasa a handsfree ya matso da wayar kusa da ita dan tayi magana.

K'arar ringing na wayar na tafiya dai-dai da bugun zuciyarta, tuni hawaye ya wanke mata fuska tana tunanin abunda ya kai Ibrahim yi mata text a yau. Tun ranar da ta damk'a masa mak'udan kud'i tayi sallama dashi kuma ya tabbatar mata ya hak'ura da ita zai je yayi rayuwarsa. Toh meh na nemanta yau? Meh yasa sai yau da take tare da mijinta? Muryarsa taji ya karad'e d'akin "assalamu alaikum".

Bakinta ta toshe da dukkan hannayenta jin kuka na shirin kufce mata, bata iya amsa sallamar ba sai ma kashe wayar da yayi d'if dan yana ta hello bata amsa shi ba. Cikin b'acin rai Alhaji yace "meh hakan ke nufi?" Bata samu damar amsa shi ba wayarta ya shiga k'ara, sai da yayi warning d'inta da idanu sannan ya danna yasa a handsfree, "hello" yace, sai da ta kallesa sannan ta amsa da "ina wuni".

Gen! Gen!! Meh ke shirin faruwa?


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


              Page 57


Batool 


  Zaune take a k'asa kanta na kallon k'asa, jiran amsarta daga wurin iyayenta takeyi. Minti uku babu wanda yayi magana cikinsu, can mahaifinta ya nisa yace "Batool ke 'yata ce, kuma ban tab'a kawo abunda kika aikata cikin abunda zaki iya yi ba anan duniya dan tarbiyya da sa idon mahaifiyarki akanku. Abunda ya faru ya wuce tunda kin wanke mana zuciyarmu da kawo mana wanda ya illata miki rayuwa, ko ba komai bazamu kwana da tunanin abunda zai biyo baya ba in anyi aure ko kafin aure aji labarinki, Mujahid ya turo mana iyayensa kuma munyi na'am munyi farinciki da zuwansa. Sai dai iyayensa basu ce komai game da aurenku ba?" 

Sai da ta goge hawayen fuskarta sannan tace "mahaifinsa na matuk'ar sonsa, hakan yasa ya amince kuma ya karb'i zancen dan yana son d'ansa yayi aure saboda wasu dalilai nasa. Mahaifiyarsa ce yake samun matsala da ita amma mahaifinsa ya toshe ko ina kuma insha Allah komai zai yu da yardar Allah sannan da addu'arku gareni. Nayi laifi nayi kuskure, ku yafe min ko zan samu nutsuwa" kuka takeyi mai ban tausayi tana neman gafarar iyayenta.

Cikin kuka mahaifiyarta ta iso inda take ta rungumeta tana shafa bayanta alamar rarrashi. "Yi shiru Batool, mun yafe miki duniya da lahira, Allah ya yafe mana gaba d'aya yasa k'arshen wahalar kenan a nan duniya, Allah ya gafarta miki ya datar dake duniya da lahira". A wannan lokaci kukan murna da farinciki Batool ke yi, k'ank'ame mahaifiyarta tayi tana mai jin wani ni'ima cikin zuciyarta, ji tayi kamar an sauk'e mata dutsen da ya jima zaune kan k'irjinta. 

Muryar mahaifinta taji yayi gyarar murya yace "ni kuma ban dani hug d'in 'yata? Come to me and stop crying" da gudu ta isa wurinsa ta rungumesa tana mai cigaba da risgar kuka. Sai da suka nutsu sannan mahaifinta yace washe-gari zata koma Abuja ta kwaso kayanta ta dawo dan shirin biki, Mujahid yace bai son ya wuce watanni biyu zuwa uku. Sunne kai tayi k'asa tana murmushi dan kunyar da taji ya rufeta jin an fad'a zancen aurenta.

Miemiebee @ 8pm


   Kwance take kan gadonta idanunta a lumshe, yau sati uku kenan da auren Kamal, a yanzu ta fawwalawa Allah komai ta rungumi k'addararta sai yafiyar Allah da take nema ba dare ba rana. Muryar mahaifiyarta taji a samanta tana magana "Miemie tashi babanki na nemanki a parlonsa" zama tayi ta sake mata murmushi sannan tace "Toh" sai da mamanta ta fice daga d'akin ta mik'e ta d'auki mayafinta ta fice amsa k'iran mahaifinta.

Shi kad'ai ta samu yana zaune idanunsa na kan TV yana kallo. Can ciki tayi sallama ya amsa ta shigo ta zauna k'asa a gefensa tace "gani". Muryar TVn ya rage ya dawo da dubansa gareta murmushi fal fuskarsa. Cikin nutsuwa ya k'ira sunanta yace "muhimmiyar magana nakeso muyi, abunda ya faru ya wuce sai addu'ar Allah ya tsare gaba ya kuma sa hakan shine alkhairi gareki. Lura da yanayin rayuwarki da kuma abunda na gano game dake cikin labarinki yasa nayi miki kwad'ayin wani abu kuma ina fatan ki amince".

Bata iya d'ago idonta ba ta kad'a kai alamar tana sauraronsa ya cigaba. "Kin gama idda yanzu kuma Kamal yayi aure ke meh yasa bazaki cigaba da naki rayuwar ba? Ko so kike ki fad'a rayuwar da kikayi a baya..." Idanunta ta d'ago tuni ya rine zatayi magana ya dakatar da ita da cewa "yi shiru in gama, ba abunda yasa na k'iraki ba kenan. Wani yazo min neman aurenki kuma na bashi ke dan shi yafi dacewa da yanayinki" kuka ne ya kufce mata jin kalamansa, wato ya d'auketa maras hak'uri bazata juri zama ba namiji ba? Yanzu da take zaune ita d'aya meh ya sameta?.

"Na bashi damar turo magabatansa kuma zasu iso sati mai zuwa. Ba shawara nake nema wurinki ba, ina fad'a miki ne dan in fita hakk'inki, bazan iya barinki haka hankalina ya kasa kwanciya ba. Tashi ki shige gida Allah yayi miki albarka". Sai da ta d'au mintuna biyar sannan ta mik'e zuwa d'aki tana mai risgar kuka. Sai da tayi mai isarta ta d'auki waya ta danna k'ira.

Yana fara ringing aka d'aga, muryarta taji tana cewa "Miemiebee kin huce? Kin hak'ura kin gane mu masu k'aunarki ne? Alhamdulillah da kika gane hakan da wuri", kukanta ya tsananta dan tausayin kanta da ya dira mata. Kuka suka shiga yi dukkansu babu wanda ya iya rarrashin wani, "kuyi hak'urin abunda na muku, zuciyata ne ta kasa yadda da k'addararta, na gano ban kyauta ba ku yafe min dan Allah". Pherty sai da ta ja majina sannan tace "um-um Miemie, mun fahimceki kuma babu wanda ya k'ullaceki, fatanmu Allah ya tak'aita mana haka".

Hira sukayi sama-sama sannan ta sanar da ita abunda mahaifinta ya shirya mata wato aurar da ita. Farinciki Pherty ta shiga amma bata nuna mata ba ta dai yi mata addu'ar alkhairi. Sai da ta katse wayar sannan ta shiga dansewa ita d'aya cikin d'akinta, gyarar muryarsa yasa ta dakata tana mai had'iyar yawu.

Shigowa yayi fuskarsa ba yabo ba fallasa yace "lafiya ake murna haka?" Ya fad'i hakan dai-dai lokacin da yake zama kan gadonta, murnar da ta shiga yasa ta k'ank'amesa tana k'yalk'yalewa da dariya dan nuna masa farincikin da ta shiga, ganin bai biye mata ba yasa ta sake shi a hankali ta sha jinin jikinta, "Sorry" ta furta can ciki, bai amsa ta ba ya kawar da kai.

Shiru ya d'an ratsa sannan taji muryarsa yana cewa "magana nazo muyi mai muhimmanci, amma kafin nan sanar dani abunda yasa ki farinciki haka?" Bata b'oye masa ba ta sanar dashi komai, tun daga farkon labarin Miemiebee har k'arshensa, sai da ta dire sannan ta lura da murmushin da ke fuskarsa, bata iya tambayarsa ba dan tsoron yin hakan take.

"Tun ranar da Ibrahim ya k'iraki game da maganarta na nemi labarinta, kuma an sanar dani dai-dai wanda ya dace, and guess waye ya sanar dani?" Murmushin da yakeyi bai d'auke ba yake tambayar, ganin bata amsa shi ba sai ma kallonsa da takeyi wani iri yasa shi cigaba da magana. "Ibrahim for sure, kin tuna da ya k'iraki ina wurin meh yace miki? Cewa yayi naji labarin mijin Miemiebee ya saketa har yayi aure, dan Allah ki had'a ni da ita zan aureta, naji labarin halin da ta shiga, baki bashi damar fayyace miki komai ba kika ce kada ya sake k'iranki yaje inda yaji labarinta ya nemi a had'a shi da ita, ko ba haka kika ce ba?" Ba amsarta yake son ji ba hakan yasa bata amsa shi ba shi kuma ya cigaba.

"A wayarki na samu layinsa na k'irasa dan jin muryarsa kad'ai ya nuna min rauni da kuma gaskiyar maganarsa, a wurinsa na samu labarinta, kuma ta wayarki na samu address nata har muka je wurin mahaifinta ni da shi muka gabatar da kanmu kuma ya bashi ita..." Cikin kuka Pherty tace "shine ka d'auki karar tsana ka d'aura min bayan kasan ba ni yake nema ba? Ka daina kula ni ko kallona ka daina yi sai ma d'aure min da kayi fiye da yanda kayi min da? Meh yasa kayi min haka ranar da ya k'irani?".

Kanta ta ajiye bisa cinyoyinta ta shiga rera kuka, bai hanata ba sai ma lumshe ido da yayi ya ja dogon nunfashi ya sauk'e. "Akwai dalilin da yasa nayi haka Pherty, na aureki dan ina sonki kuma na amince da yarintarki da rashin iliminki. Tun ranar da kika sanar dani labarinki bazan b'oye miki ba zuciyata kad'an ya rage bai buga ba amma na daure, na bar komai saboda kada inzo inyi abunda zanyi da na sani".

"Da farko zuciyata ta raya min rabuwa dake dan babu anfanin zama da mace irinki amma da na fice na barki a d'akin nan na koma d'akina kwanciya nayi dan neman mafita, anan ne na taryo duk zaman da nayi dake, na duba yanda kike kuka kike nuna min kin tuba yafiyata kike nema, hakan yasa nayi waya can minna aka sa camera a side naki dukka kawai dan in ajiyeki ingane gaskiyar maganarki. Kuma yayi anfani saboda na fuskanci abubuwa da yawa a tare da ke, ba ma ke kad'ai ba har ma da k'awayenki da suka shiga can gidan sukayi kwanaki, kin tuna su?"

Kad'a kai tayi tana mai mamakin wannan al'amari, murmushi yayi ya cigaba da cewa "na fahimci iya gaskiyarki kika fad'a min ranar, kuma lallai kinyi da na sani kuma kinsan kinyi laifi. Hakan yasa naje na d'auko ki dan kin cinye jarabawar can Minna, saura nan Abuja inda kikafi sani kuma inda kika saba had'uwa da samarin naki. Ban kai ga fara yi miki jarrabawar ba naga Ibrahim na k'iranki sai na bar maganar jarrabawa na fad'a wani harkar dan Miemiebee da sauran k'awayenki na buk'atar taimako, kinji abunda ya faru, yanzu na gama wancan saura taki jarrabawar".

Yana gama fad'an haka ya mik'e zai bar d'akin ya jiyo muryarta tana cewa "da gaske yanzu Ibrahim ne zai auri Miemiebee?" Haka kawai yaji zancenta ya soki zuciyarsa, lumshe idonsa yayi ba tare da ya juyo ba yace "kishi kikeyi?" Bai jira amsarta ba ya fice daga d'akin zuciyarsa na mai azalzalarsa dan jin yanda muryarta ya nuna damuwarta dan Ibrahim zai auri Miemiebee.

Kuka ta shiga rerawa, na farinciki da bak'in ciki, farincikinta bai wuce yanda mijinta ya gane nadamarta ba, sai kuma murnar auren Miemiebee da Ibrahim, bak'in cikinta kuma ya samu ne dalilin jin furucin mijinta dan ta tambayesa tabbacin auren k'awarta da Ibrahim, muryarsa ya tabbatar mata ranshi ya b'aci. Ita ba wai kishi take ba, mamaki ne ya rufeta jin Ibrahim zai auri Miemiebee, in bata yi musu murna ba ai bai kamata tayi bak'inciki ba, dan ta aikata b'arna a baya shine yanzu da ta tuban ma furuncinta na iya dagula mata zaman aure? Lallai zina abu ne mai girman gaske.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


              Page 58


Ummu-Abdoul


   "Hajiya ni fa bansan ya zanyi ba, Abduljalil d'in nan na ma daina sa shi lissafi saboda bai san ko ni wacece ba, bai san na tab'a aure har ina da yaro ba, kinga aurenmu na gargada dan babu saurayin da zai auri bazawara..." "Ban gane babu saurayin da zai auri bazawara ba? Samari nawa ke auren bazawara kina nufin baki tab'a jin labari ba?" Cewar Hajiya rai b'ace, da alamu maganar ya kai ta bango, tun tana binta da lallami ta cire mutum d'aya har sai da ta fara fad'a. "Hajiya a k'ara min lokaci kad'an tukunna".

"Wani lokaci wai? Ga Feedoh na nan a k'asanki, ko Auta yanzu ta kai aure bare Feedoh, na gaji ina gaya miki, tun wuri ki san nayi tun kafin rai ya b'aci". Sumi-sumi ta tashi ta fice daga d'akin kamar wacce kwai ya fashewa a ciki. Wayarta ta d'auka ta shiga WhatsApp ta lalubo layinsa tayi masa sallama, kamar jiranta yake ya amsa har da tsokanarta shin tayi kewarsa ne?

Bazata iya sanar dashi a waya ba, shiyasa ta nemesa ta nan, sai da ta tsara masa doguwar text sannan ta tura masa, tana ganin yayi marking biyu ta kashe wayar gaba d'aya dan kada ya k'irata. Bata sake waiwayan wayar ba sai yamma lis ta kunna, sak'onshi ta gani "Zanzo bayan maghrib, we need to talk". "Huhhh!" Ta fitar da numfashi dan samun nutsuwa, juya idanunta tayi tana tunanin abunda zai faru.

Bayan ta idar da Sallah ne ta ga wayarta na ringing, d'auka tayi a sanyaye tace "Hello" "gani nan da 10-20mins, in nazo sai kik'i fitowa ko ki koreni" turo baki tayi tace "Um-um dan Allah" numfashi ya sauk'e ya lumshe ido jin yanda tayi magana, ba k'aramin tashin hankali ta sa shi ba da yaga message nata, ji yayi kamar yayi ta kuka dan yasan k'arshen zamansu yazo, duk yanda yake sonta mahaifiyarsa bazata tab'a yarda ta barshi ya auri bazawara ba, amma ya akayi duk binciken da yayi akanta ba'a ce masa tana da yaro ba?

Har ya isa gidan tunanin da yakeyi kenan. Wayarta ya k'ira dan ya sanar da ita isowarsa amma tak'i d'auka har ya katse, yana sake k'ira kenan yaga fitowar wata daga cikin gidan tana dube-dube, da alamu shi take nema, hakan yasa ya d'aga mata hannu ita kuma ta iso inda yake. Tunda ta waigo idanunsa ya sauk'a akanta ya kasa ko da kiftawa ne, numfashinsa ya tsaya cak yana mai kallon wannan yarinya da ta tafi dashi farat d'aya, amon muryarta ne ya doki dodon kunnuwansa, firgita yayi da jin ta kusa dashi tana cewa "sannu da zuwa".

Bai iya amsawa ba sai murmushi mai k'ayatarwa da ya sakar mata. Yana biye da ita har suka shiga ciki ta isar dashi parlo ya zauna. "Barin mata magana yanzu zata fito" sannan ta fice. Bata dad'e da fita ba ta shigo cikin doguwar hijabinta, murmushin da ta gani bisa fuskarsa yasa zuciyarta yin sanyi ita ma ta mayar masa. Gaisawa sukayi sannan yace "Nazo dan muyi fad'a ne dama amma naga farincikina tare dake sai hankalina ya kwanta, duk da haka bazai hanani yin k'orafi ba, meh yasa baki tab'a sanar dani kin tab'a aure ba bazaki iya aurena ba dan hakan?" Kanta a k'asa tana wasa da yatsun hannunta ta kasa magana.

Numfashi ya sauk'e sannan yace "gaskiya ina sonki Safiyya, amma bazai yu muyi aure ba sai da yardar iyayena, kinsan kowa dai yasan irin mutanen da yake tare dasu, gaskiya iyayena musamman mahaifiyata bazata tab'a karb'an zancen nan ba, kiyi hak'uri in na b'ata miki rai." "Ehmm!" Yayi gyarar murya ya cigaba, in bazaki damu ba ina neman wani alfarma a wurinki, tunda na rasa ki meh zai hana ki bani mata" bata kai ga amsawa ba Feedoh ta shigo d'auke da tray da abun sha akai (ruwa+juice). Tunda ta shigo yake kallonta har ta ajiye ta fice, Ummu-Abdoul na kallonsa dan kallon da yake yiwa Feedoh na bata ma'anoni da dama.

Kallon k'asa yayi yana murmushin da shi kad'ai yasan dalilinsa, daga bisani ya d'ago yace "zaki iya bani wannan? Am sure ita ce Feedoh da ake ta min rowanta". Dad'i ne ya ziyarceta wani murmushi ya kufce mata tana kallonsa cike da farinciki, "Feedoh kakeso da gaske?" Girarsa ya d'aga mata sama alamar eh, kamar an mitsinesa ya sauk'o k'asa yana cewa "am sorry, ashe da surukata nake magana harda d'aga gira, na dai zo da k'ok'on barata". Dariya ta shiga yi harda hawayenta, ya bala'in bata dariya yanda yayi, sai da sukayi dariya mai isarsu sannan suka nutsu suka tattauna maganar a tsanake tace ya bata lokaci zata yi wa k'anwarta magana.

Mamu 


   Zaune take cikin makeken gidanta dake Zaria, hankalinta gaba d'aya bai jikinta tun da ta tashi daga bacci, mafarki tayi da yayarta wanda ita har lokacin da take zaune bata gane ma'anar mafarkin ba. Can ta d'auko wayarta ta dawo mazauninta ta dannawa Ruffaida k'ira, bugu uku ta d'auka da sallamarta ta gaisheta.

"Lafiya k'alau, ke yanzu bazaki dawo Zaria wurina ba ko? Ko har yanzu fushi kikeyi da mahaifiyarki?" "A'a Mommy, kinsan na kwana biyu ban lek'a school ba, exams muka fara but na ma kusa gamawa saura biyu" "okay, Allah ya bada sa'a, kina gamawa kizo ki sameni akwai maganar da zamuyi mai muhimmanci" "toh insha Allah, bikin Sadiq ma saura sati uku ai, in nazo bazan koma ba sai an gama biki" murmushi Mamu tayi sannan tace "da kin kyauta, Allah ya kaimu" sukayi sallama ta katse wayar.

Lubiee @ 9am


  Tun da tayi sallar asuba take faman shirya kayanta da na Kausar, jiya da dare ta had'a na Abubakar ya barta tazo ta had'a nasu ya kanainayeta ya hanata sak'at sai asuba ya k'yaleta, yanzu gashi ya hanata baccin asuba shi yana can yana bacci hankalinsa kwance. Sai da ta gama had'awa sannan ta koma d'akinsa dan tashinsa.

Hankali kwance yake baccinsa, ta tabbata ya manta da tafiyarsu yau dan baccin nasa ba na alamar tashi yanzu bane. Zama tayi kusa dashi tana kallon fuskarsa, hawaye taji ya taru mata cikin idanunta tunawa da tayi har ranar ta kasa daidaita masa gidansa, kenan in sun mutu bazata samu damar kasancewa dashi cikin aljannah ba dan ya kasa yin adalci tsakaninta da Nafee? Duk iya dabarunta na nuna masa illar hakan ya kasa ganewa, ko da ta samu nasarar guduwa daga d'akinsa dan ba kwananta bane Nafee na bijire masa, tana yi masa jan ido ta gaya masa magana shi kuma baya iya jure hakan.

Shiyasa duk ranar da yasan ba rananta bane yake daina shige mata yake daina sake mata dan kada yayi kwad'ayin kasancewa da mace dan bazai samu ba. Nafee duk iya yawace-yawacenta na neman siddabarunta ta kasa samun wanda zai kama d'aya daga cikinsu, shiyasa komai ya kunce mata take sirfa bala'i ta kasa samun nutsuwa bare ta samu farinciki. 

Duk iya kud'in da take dashi ta salwantar dasu a bin malamai da bokaye, k'arfi da yaji take dawo da abunda tasa Abubakar yake yiwa Lubiee a da kanta dan ta hana shi kanta, ta hana kanta da 'ya'yanta cin abincin gidansa, magana mai dad'i bai shiga tsakaninsu sai ta yi masa masifa, sosai yake kai kansa nesa dan kada ya sake jibganta Lubiee ta tubure masa ba dan haka ba da tuni yasan yanda zaiyi da ita. 

Satin da ya wuce ne ta tattare kayanta da na 'ya'yanta ta bar gidan da sunan yaji, a wurin Abubakar take jin labarin komawarta gida, tayi dashi yaje biko yace tunda ita ta tafi da k'afarta zata dawo babu inda zaije, sai gata jiya yamma lik'is ta dawo k'ashin wuyarta zak'o-zak'o sabulu na iya shiga ya zauna dab'as dan rama, bata dai ji komai ba gashi kuma yau zasuyi tafiya ganin gida ita da mijinta da Kausar.

•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•

  Hannunshi ya d'aura bisa fuskarta hakan ya dawo da ita hayyacinta, murmushi ta sake masa tana k'ok'arin shanye hawayen da ke idanunta. "Meh ya sameki kike kuka?" "Babu" ta fad'a tana mik'ewa tsaye. Hannunta ya rik'e ya dawo da ita kusa dashi, zama yayi yana fuskantarta, bai mata magana ba sai kallonta da yakeyi dan karantar yanayinta.

"Ehm... Dam.. Dama fa..." "Shh!" Ya fad'i tare da d'aura yatsarsa kan lebb'anta, "meh ke damunki? Fad'a min damuwarki, Abubakar ne fa". Kuka ta fashe masa dashi ta shige jikinsa, "ina tsoro, ina tsoron mu mutu a haka Allah ya kamaka da laifin rashin adalci tsakaninmu, banson ka tashi ranar k'iyama da shanyayyen b'arin jiki, inaso kamar yanda muke rayuwa anan duniya cikin aminci mu mutu tare mu tashi mu rayu tare cikin rahamar Allah a aljannah, ka taimakeni ka nemi matarka kuyi sulhu dan banason soyayyarmu ta tsaya iya nan duniya".

Hawaye yaji ya taru cikin idanunsa yana mai jin sautin kukanta cikin zuciyarsa, ta kashe masa zuciya da kalamanta kuma ta sa zuciyarshi yayi rauni dan jin zancenta yasa shi zubda makaman yak'insa da Nafee, ya tabbata Lubiee mai k'aunarsa ce kuma mai neman rahamar Allah ya samesa.

K'ank'ameta yayi cikin jikinsa sosai sannan yace "duk laifina kike gani kenan bakya ganin nata? Bata nemi zaman lafiya dani ba kinason inyi ta binta kenan tana raina ni?" "Akwai raini tsakanin ma'aurata dama ban sani ba? Kaje mata da fuskar sulhu ba da fuskar manyanta ko nuna girma ba, kaje mata ta fuskar masoyi ba ta miji mai iko da izza kan matarsa ba". D'agota yayi daga jikinsa yana mai share mata hawayenta.

"Zanyi yanda kikeso Lubbatuna, kamar yanda nake dake anan haka zamu rayu cikin aljannah tare kina min irin turo bakin nan" murmushi ta sakar masa harda rufe fuskarta, tashi yayi ya shige toilet dan yin wanka ita kuma ta fice dan shirya kanta da 'yarta.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


              Page 59


Benaxir @ 11am


  Wayarta na bisa kunnenta hankalinta kacokan na kan wacce ke mata magana, fuskarta na nuni da raunin da zuciyarta yayi. Minti uku tana sauraranta sannan tace "Anty Bena ni fa bance masa haka ba, yanzu shi har yana da ikon kai k'arana wurin..." "Ba fa k'ararki ya kawo min ba kada ki k'ara masa kan wanda kikeyi, ce min yayi kink'i sauraransa kina masa wulak'anci...".

"Wulak'anci yace miki nake yi masa ma?" "Ohh ni Benaxir" ta fad'a ta nata b'angaren "ba abunda ya fad'a kenan ba, ni dai nasa abunda kike masa matsayin wulak'anci, shi dai kawai yazo min yace in rok'eki ki saurareshi. Haba Benaxir, ki daina nemo laifinsa ko ta yaya dan ya b'ata miki rai, kiyi k'ok'arin kawar da duk wata damuwar da yasa miki, ki saurareshi sannan ki yanke masa hukunci". 

Gefe Benaxir ta kalla tana yawo da k'wayar idanunta, "ya zanyi ta fahimceni? Ni fah banson sauraranshi dan na goge shi cikin babin rayuwata" duk zancen da take ta jerowa cikin zuciyarta kenan. Haka suka gama magana ta katse wayar zuciyarta a cunkushe, dole dai yanzu an sata sauraransa tunda har maganar yaje kunnen Benaxir, "wato shi Hussain dan rashin kunya har k'arata zai kai?" Ta fad'a a fili tayi k'wafa.

Lubiee @ 5:30pm


   A harabar gidansu yayi parking yana kallon yanda yarar gidansu ke yi mata oyoyo, bakinta a wangale ta kasa rufewa, ji take kamar bazai tsaya ba dan ta samu ta rungume 'yan k'annenta, rabonta dasu shekaru kusan biyu. Yana parking ta bud'e k'ofar ta fito, k'iris ya rage Kausar bata fad'i daga hannunta ba, ruk'unk'ume 'yan k'annenta tayi sai ihun murna sukeyi, ta ma manta da Abubakar hankalinta gaba d'aya ta damk'a musu.

Gida suka shige tare cike da murna, sai da suka shiga sannan sauran yaran suka fita dan shigo musu da kaya, a sannan ne Abubakar ya shigo rik'e da jakar kayanta. A gefenta ya ajiye sannan ya zauna dan su gaisa, kanshi a k'asa cike da girmamawa yace "ina wuni hajiya", can ciki ta amsa da " lafiya, ya hanya".

"Alhamdulillah" yace cike da mamakin yanda take amsa shi a yau, ko laifi yayi mata haka? A da in yazo gaisheta fuskarta cike da annuri kuma takan tsawaita hirarsu, amma yau gaisuwar tasa ma can ciki ta amsa. Ko ruwan da aka kawo masa bai samu yasha ba ya wuce nasu gidan yana tunanin laifin da ya yiwa surukarsa take d'aure masa haka. 

Lubiee wanka tayi bayan taci abinci, tana fitowa tasa aka shiga yiwa Kausar wanka ita kuma ta tada sallahr maghrib. Kafin ta idar duk 'yan k'annenta sunzo sun mamayeta, yayarta da tazo hutu kamar yanda ita ma tazo ganin gida tuni suka baje aka shiga hirar yaushe gamo. Wasa-wasa basu tashi ba sai da yaran kaf suka yi bacci bayan sun ci kuma sun sha tsarabar da ta kawo musu.

Abunda ya d'aurewa mahaifiyarta da yayarta kai bai wuce yanda take labarin Abubakar ba, abu d'aya biyu sai ta kawo Abubakar a ciki, tun bata lura da b'ata fuskar da sukeyi ba har ta fara lura, da zarar tace Abubakar kaza sai suyi k'ok'arin kawar da maganar basu son abunda zai kawo maganarsa, toh ko meh dalili?

Sai da mamanta ta bar d'akin sannan ta d'auki wayarta tana cewa "barin k'ira Abubakar d'ina, tunda ya ajiyeni bamuyi magana ba". Tsaki yayarta ta ja ta kawar da kai, hakan yasa ta fasa k'irar tace "wai meh ke damunku daga nace Abubakar sai ku wani had'e rai ke da mama, wani abun yayi muku?" Wani tsakin taja sannan tace "har wani abun zai sake yi mana bayan wanda yayi miki? Yanzu har Abubakar ya iya zame miki Abubakar naki na da ba wanda ya sauya hali ba? Kai!! zuciyarki da sauk'i Lubabatu, ai ni namiji in yayi min abunda yayi miki wallahi babu sauran aminci tsakanina dashi, yanzu ba ni yayi wa ba ma naji ban sonshi cikin raina bare ni yayi wa".

Zuciyar Lubiee yayi tsananin bugawa jin zancen da yayarta ke rattabo mata, meh hakan ke nufi? Tana nufin duk abunda take fad'a musu wanda Abubakar yayi mata bai bar cikin kwanyarsu ba? Ita ta ma manta da wani abu da ya had'a su tuni ta sake dashi ta dawo mishi da martabarsa da k'imarsa. Lallai indai haka ne ta tafka babban kuskure na bayyana musu dukkan abunda Abubakar yayi mata a lokacin da bayi da cikakken hankali.

"Ai ya wuce ko Anty Deejah, duk abunda ya faru ai a da ne kuma ya daina..." Tsakin da ta ja ya hanata k'arasa maganarta, bata gama mamaki ba sai da ta ga ta tashi ta fice mata daga d'aki dan kawai ta yi maganar Abubakar. Toh fah! Yanzu abunda take ganinsa ba abun kirki ba shine har ya kai haka? "Meh ke shirin faruwa tsakanin mijina da 'yan uwana?".

Wasa-wasa tun tana ganin abun k'arami ne har ya kai tana ganin k'iri-k'iri mahaifiyarta bata son maganar Abubakar, ko tayi mata tana d'aukansa bayi da muhimmanci, dan dole ta daina maganarsa, mamaki takeyi in taga yanda suke fushi dashi dan yayi mata wani abun da a yanzu ya wuce a wurinta.

Ashe abunda take ji gaskiya ne game da fad'awa 'yan uwa ko mahaifiya wani abunda miji yayi maka maras dad'i yana tsayawa a ransu basu iya mantawa? Lallai yau ta yadda da hakan, ya zatayi ta gyara kuskuren da tayi? "Ta hanyar nuna musu alkhairinsa gareki tare da kiyaye yin hakan nan gaba, duk wani abu da miji yayi miki na b'acin rai ko da kina jin duk duniya babu wanda yafi ki jin haushi ko k'una ki bawa kanki hak'uri, ki rik'eshi matsayin sirrinki, komai mai wucewa ne dan fad'ar masoya hutu ne" cewar zuciyarta.

Ruffaida da Sadiq ranar Asabar:-


   Tun safe ta shirya tana zaune zaman jirarsa dan tafiyarsu Zaria, sau uku tana k'iransa yana cewa gashi nan zuwa, ina yake tsayawa oho masa. Tun tana hira da Ummu-Abdoul da Feedoh har taji hirar ya fice mata a rai, ta kai awa biyu ko ma fiye tana jiransa. Can taji k'arar wayarta ana k'ira, sai da ta duba sunan sannan ta d'aura a kunnenta idanunta rau-rau saura kad'an tayi kuka, can ciki ta amsa da "toh" sannan ta tashi ta d'auki jakarta tace musu "ya iso, ina Hajiya take in mata sallama".

Tare suka fito dan rakata, sai da tayi sallama da Hajiya har ta bata turare da atamfa sannan ta fito suka wuce. K'in masa magana tayi da ta shiga motar ta d'auke kai fuskarta a tamk'e, ita a dole ya mata laifi. Shima shiru yayi mata dan yaga alamar ta hau da yawa, sai da suka d'au hanya sannan yace "haka zamu d'au hanya kamar munyi fad'a" kamar jira take ta hau masifa, dama a cike take dashi zaiyi aure, kuma a kullum in zaiyi mata laifi toh ta sanadin wannan Candyn ce, shi baya ma sanin ya mata laifi bare ya bata hak'uri.

Yau dai ta cika fam kuma a yau ta zazzage masa, "Haba Rufaida, naje sallama da Candy ce fa, ya za'ayi inyi tafiya banyi sallama da ita ba?" "Ohh! Kana nufin ba laifi bane dan ka ajiyeni awanni ina jiranka dan kana wurin Candy ce ko choco, da kai da ita duk kun isheni, dama kasan zakayi magana da ita shine kace in shirya da wuri? Ka tsaya anan in sauk'a, dad'in abun ina da kud'in mota kuma ba mutuwa zanyi ba in na hau motar kasuwa" "kiyi hak'uri" yace yana dariya k'asa-k'asa.

Da mamaki ta tsaya kallonsa "dariyana kake?" Tun kafin ya amsa yaji ta kufce da kuka mai k'arfi, juyowa yayi da mamaki yana kallonta, ajiye kanta tayi bisa cinyoyinta tana kukan da a ganinta shi kad'ai zai rage mata rad'ad'in da take ji. Gefen titi ya tsaya ya juyo da kyau yana kallonta, mamakinta ya shiga yi, har laifin da yayi mata ya kai haka? Dan kawai ta jirashi na 'yan awanni shine take wannan kukan? Ko dai akwai abunda yake damunta bayan hakan?

Cikin i'ina ya fara mata magana, "Ruf, Ruffaida kuka? Meh ke damunki?" Ji tayi kamar ta hau shi da duka, wai meh ke damunta, kukanta ta cigaba da yi ko sauraransa ta daina yi, sai da ta gaji dan kanta ta yi shiru, har lokacin bai hak'ura da bata hak'urin ba bare ya ja motar, bayan ta goge hawayenta ta zauna tana kallon yanda ya tsareta da ido alamar yana sauraron bayaninta. "Ni fa ba komai, mu tafi kawai" duk yanda yayi dan ta sanar dashi damuwarta tak'i, dole ya hak'ura ya fara tuk'i cikin kwanciyar hankali suna hira sama-sama.

Sun isa lafiya, Mamu ta tarbesu da kayan abinci da na sha kala-kala, bakinta har kunne tana mai jin dad'in ganinsu. Ba su suka samu zama ba sai washe gari dan kowannensu a gajiye yake. Mamu ce ta nemi ganinsu a d'akinta da misalin k'arfe 11 na safe. Bayan sunyi breakfast kai tsaye suka wuce d'akinta, kusan tare suka shigo dan a bakin k'ofa suka had'u suka shiga tare dan amsa k'iranta.

"Magana ce mai muhimmanci nakeson yi muku a yau, da farko ina mai k'ara baki hak'uri Ruffaida, nasan ban kyauta miki ba kuma ban rik'e amanar da yayata ta bani ba, sai dai d'an Adam ajizi ne, kiyi hak'uri ki yafe min" "A'a Mommy dan Allah, ni baki min komai ba, nice dai mai laifi, ina neman yafiyarki da afuwarki" murmushi Mamu tayi sannan tace "nima baki min komai ba, Allah ya gafarta mana gaba d'aya" suka amsa da ameen dukka.

Numfasawa tayi sannan tace "kinyi istibra'i dai ko Ruffaida?" Kanta a k'asa cike da nauyin zancen tace "eh, Ummu-Abdoul ta sa nayi" "hakan yayi kyau" ta kalli Sadiq da ke zaune kansa a gefe tace "aurenka saura sati biyu da kwanaki ko?" murmushi yayi sannan ya kad'a kai alamar eh. "Nasan maganar da zanyi maka yanzu zaiyi matuk'ar gigitaka, amma hakan ne ya dace kuma hakan nake so ya faru. Bance ka fasa auren Candy ba amma inason ka had'ata da Ruffaida, ma'ana ka auresu su biyu ko dan halin da Ruffaida ta tsinci kanta a ciki".

Cike da firgici ya tsaya kallonta, kallon meh hakan? Kallon hauka ta fara ko meh? Baki bud'e yake kallonta, motsi bakinsa yakeyi alamar yana son magana amma maganar ta mak'ale, dagewa yayi yace "aure kuma? Aure tsakanina da Ruffaida? Mommy ya kike magana haka? Ai aure bazai tab'a shiga tsakanina da ita ba". Da mamaki Ruffaida ta tsaya kallonsa, bakinta taji yana furta "kaman ya zaka ce haka Ya Sadiq? Baka sona ko meh?" Kallonta yayi zuciyarsa na tafasa yace "ya zaki fara tunanin haka bayan sarai kinsan komai? Kin manta abunda ya shiga tsakaninki da mahaifina ne da har zaki yi tunani ni zan aureki? Ai aure ya haramta tsakaninmu".

"Sadiq, waye yace maka haka? Waye yace maka aure tsakaninku ya haramta? Cewar Mommy tana kallonsa cike da mamaki. Ruffaida banda kuka babu abunda takeyi, jin furucin Sadiq yasa ta d'ago kai "ya za'ayi macen da ta sadu da mahaifina kuma in aureta? Ai wannan kowa na ji yasan haramun zamu tafka..." "A'a ya Sadiq, aure bai haramta ba tsakaninmu".

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


              Page 60


   "Dole kice haka mana, ai dama tuni na gane manufarki nake kaucewa, ina kika tab'a ganin anyi haka? Ina kika tab'a ganin yaro ya auri wacce ta sadu da mahaifinsa? Haba Mommy, ya zaku bi son zuciyarku ku kaucewa addini, aure ya haramta tsakanina da ita, in har aure bai haramta ba meh yasa ake haramta wa yaro matar mahaifinsa..." "Kash ya Sadiq, ya zaka had'a alak'ar aure da zina? Ya zaka had'a bak'i da fari? Haram baya haramta halal sai dai halal yakan haramta halal a wani zubin, na gaya maka aure tsakaninmu ya halalta...".

"Dallah ki min shiru, yaushe miki da nusar dani? Yaushe miki da har zaki min gyara kan addinina? Yaushe ma kika je islamiyyar bare ince koyar da ke akayi? Haramun haramun ne baya canjuw..." "Ya isa!" Momy ta dakatar dashi had'e da d'aga hannunta, fuskarta ya canja launi dan b'acin ran da Sadiq ya sa ta ciki, cikin kausashshiyar murya tace "idan ita bata kai ta nusar da kai ba ni fa? Ko nima ban kai ba ko islamiyyar ce ban je ba?".

Zai yi magana ta dakatar dashi cike da b'acin rai ta cigaba "aure tsakaninku bai haramta ba, ka dai kawo wani hujjar na gujewa aurenta amma ba wai haramci ba, muddin ina numfashi a doron k'asa Ruffaida bata da wani miji sai kai". Tsoro da firgici duk sun bayyana a fuskarshi, wannan wani irin d'anyar aiki ne? Ko ta yaya bazai tab'a auren Ruffaida ba.

Mik'ewa yayi tsaye yace "Mommy kiyi hak'uri, addini ya bani damar bijirewa iyayena muddin suka nemi sa ni abunda ya kaucewa addinina, kuma naga abunda kikeson yi kenan a yau, bazan tab'a auren Ruffaida ba dan ta haramta gareni, da kika kawo min Candy ai ban k'i ba nayi miki biyayya, wannan karon kam bana tunanin zan bi umarninki". Yana k'arashe maganar ya fice ya bar d'akin ko waigowa bai yi ba duk da mahaifiyarsa na k'wala masa k'ira haka zalika sautin kukan Ruffaida ya k'aru, zai iya cewa numfashin kirki bata iya yi dan irin kukan da takeyi.

Benaxir a dai-dai wannan lokaci:-


   "Ni fa na fad'a maka, bani da matsala dakai, bazan auri mutumin da zai d'aga min hankali ko iyayensa su hana mu zama ba, shawarata shine tunda iyayenka suka nuna basu son alak'armu mu hak'ura kawai kamar yanda kayi hak'uri har kayi aure a baya" "haba Benaxir, na gaya miki a da sun iya hana ni dan bani da right d'ina amma a yanzu babu yanda suka iya dani, sun girma shekaru ya ja kuma na bi ra'ayinsu na auri wacce suke so, kada ki hanani kanki dan wani dalili naki na daban".

Shiru tayi na d'an lokaci sannan tace " ka tuntub'esu tukunna, in sun yadda shikenan, amma in basu yadda ba gaskiya dole mu hak'ura, matsalolin kaina da na iyayena sun isheni ba sai na k'ara da na gidan miji ba". Gefenta ya dawo ya zauna yace "Benaxir, i promise not to fail you this time, naji dad'i matuk'a da kika bani dama ta biyu, bazaki samu matsala da iyayena ba bare ni ko Mum Fateey, ita kam tuni tasan da zancenki kuma tana maraba dake". Baki ta tab'e ta kawar dakai jin ya ambaci matarsa, ko ina ruwanta da matarsa da yake kawo mata zancenta oho.

•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•

Ruffaida:-


  Wasa-wasa k'aramar magana ta zama babba, tun suna yin abun tsakaninsu har ya kai ga 'yan uwa na kusa sunji labari, amma abun yazo musu a bai-bai na cewa "Sadiq ya haramta aure tsakaninsa da Ruffaida", duk sunyi mamakin wannan zancen dan Mamu da ta dawo Zaria bata ce uffan ba game da abunda ya had'a ta da Nuraddeen, bai zame musu abun tambaya ba ganin ta jima dan ta saba yin hakan. 

Tun manyan dangi suna k'iranta a waya tana yi musu kwana game da maganar, kwatsam sai ga YBK ranar alhamis ta shigo gidan tana doka sallama, 'yan hanjin Mamu da Ruffaida sai da suka kad'a dan tabbas yau dole sai sun fad'i wannan abun da suka d'aukeshi matsayin sirrinsu, babu wanda yayi musu wannan tonon sililin sai Sadiq.

Ko ruwa bata sha ba tace "ko ku sanar dani ko kuma in tattaro sauran iyayen naku mu saka ku gaba, wannan ma ai hauka ne, tun ina miki a waya har ya kai ga kin d'aga ni daga gidana naje wurin Nura ya raina min wayo na d'ibi k'afa nazo nan, waye sa'anki cikinmu?" Ta k'arashe maganar tana huci tana kallon Mamu da idanunta ke k'asa.

Yau ta ga ta kanta a gidan nan tunda YBK tazo, masifarta dama yaya ne bare ta samu mai dalili? Haka ta k'araci zamanta bata samu kwakkwaran zance ba, a wurin ta mik'awa Ruffaida waya tace "k'ira min Nuraddeen" yana d'auka ko gaisuwarsa bata amsa ba tace dashi ya kamo hanyar Zaria yanzun nan. Ba shi kad'ai ta k'ira ba har da Sadiq wanda tun ranar da yace bazai auri Ruffaida ba ya koma Abuja.

   Da dare kuwa sai ga su dukka tare da YBK har ma da yayanta mai suna Malam Salihu, bai zo shi kad'ai ba shima sai da ya d'auko yaron yayansu wanda suke gida d'aya, babban mutum ne kuma yana da sani sosai kan addini. A babban falo suka zauna dukka, kowa da abunda yake sak'awa a ransa. Nuradeen bai wuce fargaban tonuwar asirinsa ba a yau, tun dawowar Mamu Zaria ya nemi farin ciki ya rasa, ga mummunar rashin lafiya da ke addabarsa wanda sai da ya danganta da asibiti, likita sai da yayi masa nasiha mai shiga jiki da kalamu masu dad'i sannan ya sanar dashi yana d'auke da wannan cutar nan mai karya garkuwar jiki wato HIV, jin wannan batu ba k'aramin gigita shi yayi ba dan duk iya huld'arsa da mata sai yayi anfani da abun kariya.

A yau dai yayi alwashin ko ta yaya bazai yadda a had'a auren Ruffaida da d'ansa ba ko da kuwa bai haramta ba, indai yana da wannan cutar toh tabbas ita ma tana dashi haka zalika Mamu na dashi. Komai ya fice mishi a rai na duniyar nan hakan yasa a wurin aiki ake ta complain dan ya daina zuwa.

Cikin nutsuwa Malam Salihu ya fara magana "a wurin yarar nan muka ji labari mai firgitarwa da mamaki, wanda suka tabbatar mana wurin abokinsu suka ji wato Sadiq game da auren Ruffaida, abun ya matuk'ar bamu mamaki amma in mukayi la'akari da yanda kuka gabatar da zancen tun farko yazo ya kuma watsewa har akayi baikonsa da wata sai abun ya zama da alamar tambaya, menene yake faruwa? Shin akwai wani abu da yake faruwa wanda mu bamu da masaniya ko kuwa?".

Mamu zatayi magana kenan taji muryar Sadiq yana cewa "da farko Mommy ce ta kawo maganar aurena da Ruffaida amma Daddy ya nuna rashin amincewarsa hakan yasa maganar ta rushe har akayi baiko da Candy..." YBK ta katse sa da cewa "Candy? Sunan yarinyar ce candy? Dama ba musulma zaka aura ba?" Mamu ce tace "Khadija sunanta", kad'a kai kawai tayi hakan ya bawa Sadiq cigaba da magana.

"Kuma sai kwatsam Mommy ta dawo da zancen Ruffaida bayan tasan haramun ne muyi aure" malam Salihu ya kallesa da kyau sannan yace "anya baka shaye-shaye?" Kad'a kai YBK tayi dan ita ma abunda yazo kanta kenan, ya za'ayi yace ba aure tsakaninsu bayan sun kasance 'ya'yan yaya da k'anwa(cousins)? "Shaye-shaye kuma? Ni ba abunda nake sha, nasan maganar da nakeyi, kuma ko da dukkanku zaku taru kuce sai na aureta bazan tab'a yadda ba dan ta haramta gareni, kuma ita Mommy ai tasan komai".

YBK tafi ta fara tana salati, "yanzu Sadiq wani fatawan naka daban ka d'auko dan baka son ka auri 'yar uwarka?" Fuskarsa a had'e yace "ni fa ba wai ban sonta bane, gaskiyata nake fad'a", Malam Salihu yace "taya akayi kuka haramta wa juna? Ko kin tab'a shayar da Ruffaida ne ban sani ba Mamu?" Yana kallonta ya jefeta da tambayar, kad'a kai tayi alamar a'a.

"Ko marigayiya ta tab'a shayar da Sadiq wanda tun da bai san da hakan ba sai yanzu a karo na biyu da aka tada zancen aure ya sani ko yaji labari?". Kuka Mamu ta fara da gaskiyarta tace "ko d'aya, babu wani haramci cikin aurensu, shi da ya nemi tonawa kansa asiri ya fad'a muku hujjarsa na cewa haramun ne, dan duk wani abunda ya haramta aure tsakaninsu babu, ba mahaifinsa ta aura ba kuma bata kasance wacce na tab'a shayarwa ba..." Kuka ne yaci k'arfinta da tazo wannan gab'a, wannan tonon asiri har ina? Lallai Sadiq ya cika d'an taurin kai mara kunya.

Kallonsa Malam Salihu yayi yace "kaji abinda mahaifiyarka tace? Meh yasa kai ka haramta bayan addini bai haramta ba? Shin kasan hukuncin wanda ya haramta abunda Allah ya halalta? Kayi saurin tuba dan ka shiga hurumin da ba naka ba" Sadiq kallonsu ya tsaya yi da mamaki, ya za'ayi su ce babu haramci? Shi yasan babu yanda za'ayi aurensu ya halalta bayan mahaifinsa ya sadu da ita. 

Bai kawo komai cikin ransa ba yace "ko da kuwa mahaifina ya tab'a saninta? Ma'ana ya tab'a kasancewa da ita matsayin abu d'aya?" Duk basu fahimci zancen nasa ba dan yanayin kallon da suke binsa dashi ya nuna hakan. Shiyasa ya fad'ad'a zancen nasa da cewa "Mahaifina ya santa a matsayinta na 'ya mace kuma a hakan suke so su aura min ita?" Idanu YBK ta gwale tana kallonsa kamar mai tab'in hankali.

Malam Hassan da yake kallonsu tunda aka fara maganar sai yanzu ya nisa yace "aure sukayi ko yaya, bamu gane zancen naka ba?" Shiru sukayi dukka babu wanda ya amsa, Nuraddeen kansa a k'asa sai zufa ke keto masa, ji yake kamar ya nutse dan kunya, Ruffaida na duk'ufe banda kuka babu abunda takeyi haka Mamu, zuciyarta na tafarfasa tana mai jin zafin abunda ke faruwa a yanzu.

Tsawa malam Salihu ya daka musu sai da suka razana, "bazaku bud'e baki kuyi mana magana ba kuna wani sunne kai?" Ruffaida ce wannan karon tace "A'a, ba ta hanyar aure ba" ji tayi ta gaji da komai, ayi duk abunda za'ayi a wuce wannan babin, duk suna kunyar amsa wannan tambayar, gwanda ta amsa in ma kasheta zasuyi ayi kawai ta gaji da k'unsan bak'in ciki. Salati dukka suka doka Anty YBK ta k'ara da cewa "Zina? Nuraddeen zina da 'yar cikinka?".

Badak'alar kenan #stilthinking

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


              Page 61


  Malam Salihu da Malam Hassan "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" suke ta nanatawa dan tashin hankalin da suke ciki, YBK kuka take yi da gaskiyarta dan wannan maganar ya daki zuciyarta. Tabbas ko ita zata iya haramta wannan auren dan iya saninta in aure ya had'a mahaifinka da mutum to har abada babu aure tsakaninku, "gaskiyarka Sadiq, ina bayanka kan wannan batu, babu kai babu ita...".

Mamu cikin kuka ta kad'a kai "Haba Anty, ni da na d'auka ke zaki bi bayana mu lallab'asa ya aureta? in ba shi zai aureta ba wa kuke tunanin a duniyar nan zai aureta ya rufa mata asiri mu ma namu asirin a rufe?" Katseta YBK tayi da cewa "dan hakan kuma sai ku take addininku?" Mamu hawaye na zuba daga idanunta tace "wai wa yace muku haramun ne?" Cike da k'osawa da maganar tayi maganar a wannan karo "Ai ga malam Hassan in haramun ne sai ya sanar damu kowa yaji. Kai kuma Sadiq...".

Ta fad'i maganar tana nuna shi da yatsa "ka nuna min matsayina a wurinka tunda ka nemi tonawa iyayenka asiri..." "Innalillahi, Mamu mu d'in kike nufin ya tona muku asiri wurinmu? Wato mu bare ne kuma zamu je mu sanar da duniya ga abunda yake faruwa, wayyo duniya, ina ma uwarki da mahaifin naki suna raye suga yanda kike nuna mana mu ba naki bane" ta fashe da kuka zuciyarta na tafarfasa.

Mamu bata saduda ba tace "ni ba abunda nake nufi ba kenan, ai kowani d'an Adam yana da nasa sirrin, kuma ni a ganina wannan sirrinmu ne, zamu yi abun mu a gida mu binne ba sai ya fitar kowa yasan abunda muke ciki ba, in hakan ya b'ata miki rai kiyi hak'uri, ni ba ina nufin ke ba tamu bace". Malam Hassan ne yayi gyarar murya yace "duk ku nutsu kuma ku cire abunda yake ranku, kai Sadiq kace Ruffaida ta haramta gareka dan ta sadu da mahaifinka?" Kai ya gyad'a fuskarsa na nuni da tashin hankalin da ya shiga na b'atawa mahaifiyarsa rai da kuma babban abunda suke son sa shi yayi na auren Ruffaida.

"Babu haramci cikin aurenku saboda cikin Qur'ani da hadisai babu inda aka fito b'aro-b'aro aka haramta auren wacce tayi zina da mahaifinka kamar yanda babu inda aka halalta, sai dai malamai sunyi bayani gamsassu game da hakan yin la'akari da wasu ayoyin alqur'ani, sunyi sab'ani game da yin hakan sai dai mafi rinjaye shine halalcin hakan amma barin auren shi yafi. Kuma basu tsaya nan kawai ba sai da suka kawo hujjojinsu na cewa barin shi yafi kamar haka:-


1- akwai kunya


2- zai kawo kusanci sosai tsakanin mahaifin naka da yarinyar wanda hakan na iya sa shaid'ani ya rinjayesu su aikata abunda suka aikata a baya wanda yin hakan kamar tuban muzuru sukayi kuma hukuncin kisa zai hau kanta duk da dama asali shi mahaifin naka hukuncin kisa ya dad'e da hawa kansa, da ana anfani da k'undin tsarin musulunci tuni kisa ya hau kansa dan yayi zina bayan yana da mata.

Akwai sab'anin fahimta tsakanin malamai, shafi'i da maliki sun halalta wannan aure, Amma Abu Haneefa da Ahmad sun haramta irin wannan auren, sai dai batu na gaskiya shine ya Halalta dan fad'in Abd albarr haramun baya haramta halal.

Maalik yace cikin Muwatta’ : Zina da mace baya haramta wanda yayi zina da ita ya auri 'yarta ko kuma mahaifiyarta, idan namiji yayi zina da mahaifiyar matarsa, matar bata zama haramun garesa ba sai dai kisa ta hau kansa. Zina baya haramta duk wani abunda aure ke haramtawa. Haka fahimtar Ibn Shihaab al-Zuhri da Rabee’ah; haka kuma fahimtar al-Layth ibn Sa’d, al-Shaafa’i, Abu Thawr da Dawood. Sannan fad'in Ibn ‘Abbaas akan hakan "aikata haram baya haramta abunda ya kasance halal".

Yawancin malamai wad'an da aka yarje\amince da fatawarsu sun halalta auren y'ar wacce akayi zina da ita indai an tabbatar bata da ciki(istibra'i) Allah ne mafi sani. Al-Istidhkaar (5/463, 464).

Shaykh Muhammad ibn Saalih al-‘Uthaymeen (Allah yayi masa rahama) yace:


Mafi ingancin zance game da hakan shine baya haramta ka auri wacce kayi zina da ita, ko ka auri 'yarta saboda fad'in Allah cikin suratun Nisa'i "All others are lawful”[al-Nisa’ 4:24] dukkan wad'an da ba'a fad'e su ba sun halalta (ku duba wad'an da aka haramta aure tsakaninsu cikin suratun Nisa'i).

Allaah bai haramta cikin Qur'ani ba sai ma cewa da yayi


“your wives’ mothers(iyayen matayenku), your stepdaughters under your guardianship(agola, wacce mata ta shigo da ita gida), born of your wives to whom you have gone in(wacce matarku wacce ka kusanceta ce ta haifeta) — but there is no sin on you if you have not gone in them (to marry their daughters) (babu laifi in baka kusanceta ba kuka rabu ka auri 'yarta),”


[al-Nisa’ 4:23] Allah ta'ala shine mafi sani.


Ku duba al-Sharh al-Mumti’ (7/38, 39) inda yake cewa "bai halalta a had'a aure da zina ba, muddin ya tuba ko ince yarinyar ta tuba toh ya halalta ta auri wanda tayi zina dashi, d'ansa ko kuma babansa".

Da wannan hujjojin nakeso ka cire maganar ta haramta gareka dan Ruffaida tabbas ta halalta ka aureta kuma aure tsabtatacce".

Nuraddeen ya nisa yace "kamar yanda kace akwai kunya kuma hakan zai kawo kusanci tsakaninmu baka ganin rashin dacewar auren? Ni dai ban aminta da wannan auren ba..." Ybk ce ta dakatar dashi da cewa "har kana da ra'ayi? Har kana da bakin magana a nan mara kunya, toh ni na yadda da wannan auren duk da bansan ya akayi kukayi aika-aikar ku ba".

Mamu ce tayi musu bayani dalla-dalla game da labarin Ruffaida, duk sunyi Allah wadai da rayuwar Nuraddeen, Sadiq na zaune kamar bayi da jini jikinsa dan sun d'aureshi da halalta wannan aure, ya zaiyi ya yakice wannan auren, ya zurfafa cikin tunanin neman mafita yaji k'arar fashewar glass, Nuraddeen ya gani a zube shame-shame cikin jini kansa na cigaba da zubar da jini sakamakon bugewa da yayi da center table da ke wurin.

Dukkansu sun kasa tab'uka komai dan sun razana da yanayin da ya shiga, mik'ewa yakeyi zuciyarsa a cunkushe jin ana masa Allah wadai, cikin rashin sani ya take k'afar wandonsa d'aya hakan ya haddasa mummunar fad'uwar da yayi bisa kan center table na glass da aka ajiye dan k'awata palon. Tsabar razana babu wanda ya iya tunkararsa, kwance yake babu alamar numfashi a tare dashi.

Malam Salihu da Hassan ne sukayi k'ok'arin isa wurinsa suna jijjigashi, daga k'arshe suka janyo mayafin Ruffaida suka toshe wurin da jini ke ta bulbula suka sungume shi sai cikin mota. Dukkansu suka fice dan zuwa dashi asibiti, Mamu kad'ai suka bari a gida tare da yaran sauran duk sun tafi sukayi mota biyu dan d'aya bazai d'auke su ba. Mamu banda kuka babu abunda takeyi tare da sauran yaran, dak'yar da taimakon mai aikinta suka gyara wurin dan jini ya b'ata wurin sosai.

Asibiti:-


  Zaune suke suna jiran fitowar likita, yawancinsu hawaye suke in aka cire Salihu da Hassan da suke ta kai kawo cikin harabar asibitin. Mintuna arba'in sannan likita ya fito gumi na shatato masa ta saman goshinsa, a office ya nemi ganawa dasu, dukkansu suka shiga dan sun k'agu suji lafiyar Nuraddeen, kallonsu likitan yayi d'aya bayan d'aya sannan yace "dukkanku kukeso mu tattaunar matsalar tare?" Malam Salihu ne ya gabatar dasu dukkansu hakan yasa shi fara maganar tasa.

"Munyi k'ok'arin tsayar da jinin sai dai yana buk'atar k'arin jini, amma abunda muka gano game dashi shine kunsan yana da wani cuta a jikinsa? Ma'ana yana da wata cuta da ya samu ba da dad'ewa ba?" Ido suka zuba masa babu wanda ya amsa. "Dalilin tambayana shine, mun gano yana da cutar k'anjamau amma da alamu baya shan magani shiyasa nake kokonto ko shi kansa yasan da wannan cutar". Dukkansu kalmar innalillahi suke nanatawa a bakinsu, tuni Ruffaida ta sulale a k'asa dan zuciyarta ta tarwatse jin an ambaci HIV, tasan nata ya k'are.

Bata san meh ya faru ba ta dai ga an fito da Nuraddeen an sanya masa k'arin jinin da aka saya anan asibitin, kukan ma tuni ta kasa yi dan duk ta zazzage na idanunta sun k'are. Babu wanda yake iya kwakkwarar motsi cikinsu, zaune take a gefen YBK bata san awanni nawa ta d'auka a wurin ba, sai ganin Sadiq tayi da Mamu, Amrah da kuma k'aninsu k'arami.

Mamu rungumeta tayi suka fashe da kuka a tare "Nawa ya k'are Mommy, na b'ata rayuwata da kaina dan son duniya, na shiga uku nikam ya zanyi da rayuwata Mommy, ina ma Allah ya d'auki raina in mutu da ganin bak'in ciki irin wannan". Mamu bata iya hanata surutan da take yi ba, sai ma jin zancen nata da takeyi a gaskiya kuma yana k'ara kashe mata zuciya, da auren namiji irin Nuraddeen gwanda ka rayu ka mutu bakayi aure ba.

Sunyi kuka kamar ransu zai fita, dak'yar Sadiq ya b'anb'aresu daga juna dan aiwatar da abunda yasa ya d'auko su wato gwajin HIV, yaran dukka aka gama musu babu wanda ke da shi hakan ya tabbatar musu da cewa Nuraddeen bai dad'e da samun cutar ba kamar yanda likitan ya fad'a.

Sadiq da Mamu sunyi ban bakin sunyi lallashin Sadiq har da harzuk'a akan Ruffaida taje ayi mata nata gwajin ta k'i, fad'i take "ni nasan ina dashi ba sai an gwada ni ba". Dole yasa aka fara gwada na Mamu, a lokacin da result d'in ya fito kowa ya sha jinin jikinsa, Sadiq hawaye yakeyi kamar an kunna famfo ganin yanda likitan ke magana, "cuta ba mutuwa ba ce" cewar likitan sannan ya fad'i sakamakon da ya fito.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


              Page 62


  Fad'in irin tashin hankalin da ya bayyana a fuskokinsu b'ata baki ne, Mamu tayi kuka tayi masa Allah ya isa na k'ak'aba mata cutar da bata ci ba bata sha ba, a wannan karon babu wanda ya iya bata hak'uri dan dukkansu kuka sukeyi, a lokacin Malam Hassan ya wuce gida Malam Salihu ne kad'ai da YBK, duk sharb'an kuka sukeyi kamar ransu zai fita. Babu wanda ya kula da farfad'owar Nuraddeen dan ya fita daga ran kowanne cikinsu, wasu tsantsar tsanarsa ne ya cike zuciyarsu wasu kuwa kamar Sadiq ji yayi ina ma tun asali mahaifinsa ya mutu tunda iyayensa suka haifesa, hakan bazai sa har ya girma ya auri mahaifiyarsu bare ayi zancen haihuwarsu ba, ya zaiyi da rayuwarsa? Wannan mutumi ya cucesu ya gama da rayuwarsu.

Kwanaki biyu da faruwar hakan, Mamu ta jeme ta b'ata kanta dan tashin hankali da damuwar da ke tare da ita, duk ban baki da nasihun da ake mata bai sa ta dawo hayyacinta ba, Ruffaida ce tayi k'ok'arin yakice damuwarta dan ta samarwa Mamu nutsuwa ko da kad'an ne ta hanyar nuna mata cutar da ke jikinsu ba yana nufin k'arshen rayuwarsu bane. Duk da har lokacin Ruffaida bata yadda an gwada ta ba, ta dai sa a ranta tana dashi ne tunda har Mamu ta d'auki wannan cuta.

Sadiq da Ruffaida ne kad'ai cikin mutanen gidan ke zuwa duba shi, Mamu ko sunansa bata son a k'ira mata dan tsanarsa da take ji cikin k'albinta, jikinsa yak'i sauk'i haka zalika ya kasa kwantar da hankalinsa game da auren Ruffaida da Sadiq, duk zuwansu sai ya tambaya ko an fasa auren, rashin samun gamsashshen bayani daga garesu ya k'ara sa shi cikin wani hali, hakan yasa Sadiq ya hana Ruffaida zuwa kuma wani haushinta ya dira masa a zuciyarsa, gani yakeyi komai da ya same su ta dalilinta ne, gashi mahaifinsa na kwance ko ya rayu ko ya mace, ga k'in gwadata da tak'i ayi dan kawai ta rainawa kowa hankali, a hakan takeso ya aureta?

Kwanaki takwas Nuraddeen na asibiti, yau tun safe Sadiq ya k'uduri niyyar ko ta yaya sai ya kai Ruffaida an gwadata, shi zai iya cewa addu'a yake ta samu matsala a fasa aurensu ya auri Candynsa abar k'aunarsa cikin sati da kwanaki kad'an da suka saura. Abokinsa ya k'ira ya sanar dashi abunda yakeso, mintuna ashirin yayi yawa sai gashi ya kawo masa abunda yake nema cikin bak'ar leda, godiya kawai yayi masa ya fice daga d'akinsa ya isa b'angaren Mamu. Kitchen kai tsaye ya shiga, anan ya ci karo da Ruffaida tana had'awa Mamu tea, suna had'a ido ta d'auke kai dan taga alamar ba jituwa sukeyi yanzu ba, a kullum irin kallon da yake jefanta dashi yakan kad'a 'yan hanjinta har ma yasa taji ko duniya zata nad'e bazata yadda da auren nan ba, bare ma tana da HIV ya za'ayi a yadda da aurensu?

Ta gefenshi tazo wucewa ya k'ira sunanta cikin sanyin murya, d'ago idanunta tayi a hankali ta zuba a kansa tana mai mamakin murmushin da yake sakar mata wanda rabonta da ganin wannan murmushi tun da akayi maganar aurensu. Shima kallonta ya tsaya yi yana k'ara jaddadawa kansa yin abunda yake ji hakan ne daidai. Can k'asan murya yace "in kin gama ki sameni d'akina, kada ki b'ata min lokaci dan ina da abun yi" bai jira ta amsa ba ya bud'e fridge ya d'auki kwalin juice d'aya ya fice ya barta tsaye a wurin tana kallonsa har ya b'ace.

Tana gamawa kuwa ta d'auki mayafinta ta wuce d'akinsa zuciyarta na cigaba da bugun lugude tana tunano dalilin nemanta da Sadiq yayi. Akan kujerar d'akin ta zauna bayan ta shigo, shima zama yayi yana fuskantarta cike da nutsuwa zuciyarsa na azalzalarsa sai da yayi da gaske sannan ya iya sarrafa gab'ob'in furucinsa yace "magana ne mai muhimmanci nakeso muyi, ina so ki fad'a min iya gaskiyarki, kina jina?" Ta kad'a kai idanunta na kallon k'asa tana wasa da yatsunta.

"Da gaske kina sona kuma kina son muyi aure?" Tambayar da ya doki kunnuwanta yasa ta d'ago kanta tana dubansa, ido hud'u sukayi hakan yasa taji nauyi ta mayar da idanunta kan carpet sannan tace "eh, ina sonka" ta fad'i hakan cike da fargaban yanda zai d'auki maganar. Jin amsarta ya sa shi had'iyar yawu mai d'aci, bai kai ga yin magana ba ta cigaba da cewa "na soka kuma bazan k'aryata cewa har yanzu ina sonka ba, sai dai batun aure..." Tayi jim sannan tace "da kamar wuya, na hak'ura da aurenka, ba ma kai ba, na hak'ura da aure har k'arshen rayuwata dan cutar da nake d'auke dashi babu wanda zai iya aurena dashi". Kukan da take tarewa tuntuni ya kufce mata har da sheshek'a, ji yayi zuciyarsa yayi rauni ya tausaya mata, amma duk ita ta ja, bai tab'a kawo laifi mai girma ya d'aura mata ba sai da aka nemi ya aureta.

"An gwada ki kina dashi kenan Ruffaida?" "Um-um" tace tana mai kad'a kai dan maganar nata bazai fito ba ko tayi niyyar yi. Juice d'in da ke ajiye gefensa ya d'auka ya mik'a mata yana cewa "sha ko hankalinki zai kwanta mu cigaba da zancen da nakeson muyi mai muhimmanci" karb'a kawai tayi ganin ya tsareta da ido babu halin gardama. Tana karb'a ta d'aura a bakinta, tas ta shanye ko tsayawa bata yi ba bare taji taste na juice d'in a bakinta, sha tayi kamar ruwa ta ajiye kofin tana goge bakinta da bayan hannunta.

Bai mata magana ba haka ita ma bata iya cewa uffan ba har bacci mai nauyin gaske ya sureta akan kujerar da take zaune. Abokin nasa ya k'ira a waya ya umarce sa da shigowa ciki dan d'iban jininta, cikin mintuna biyar ya gama komai ya mayar da ita kan gadonsa suka fice daga d'akin sai Lab.

Sai da ya duba mahaifinsa sannan ya koma dan karb'an result d'in wanda ya tabbatar masa Ruffaida ta tsallake wannan cutar, Allah bai sa ta kamu dashi ba, yayi mata murna ya mata farinciki amma zuciyarsa ta kasa aminta da cewa zai auri Ruffaida, toh in ya auri Ruffaida sai yayi yaya da Candy wacce suka matowa juna tuni?

Sai dare ya koma gida sanin zuwa lokacin Ruffaida ta farfad'o daga baccin da ya barta tana yi a d'akinsa. Ya sameta tana rama sallolin da ya wuceta a d'akin Mamu, ita kuma tana kwance kan gadonta idanunta lumshe, zama yayi gefenta yana tab'a jikinta hade da cewa "Mommy zazzab'i ne?" Tashi tayi ta zauna tana mai yi masa murmushi tace "A'a fa, ina kaje tun safe?" A dai-dai nan Ruffaida ta sallame sallar.

Kallonsa tayi ta kawar dakai, sai da ta gama addu'o'inta sannan ta mik'e ta ninke sallayar tana cewa "Ina wuni?" Lafiya yace can ciki sannan ya k'ara da cewa "na d'ibi jininki d'azu naje an gwada ki", sosai furucinsa ya kad'a hanjinta dan tuni mayafin da take nad'ewa ya sulale daga hannunta yayi k'asa, ba ita kad'ai ta k'agu taji sakamakon ba dan Mamu tuni ta matso kusa dashi tana tambayarsa " yaya? Bata dashi ko?" Murmushi yayi sannan yace "bata dashi, Allah ya tsirar da ita ya kareta", tsallen murna Mamu tayi ta isa wurin Ruffaida ta rungumeta tana cewa "am very happy for you, wicked mijina bai d'aura miki cutar da zaki wahala akai ba, ni na aureshi kuma ni na bud'e masa k'ofa shiyasa Allah ya bashi galaba akaina".

Kuka sosai sukayi dak'yar suka rarrashi juna, zama tayi rik'e da hannunta tace "aure babu fashi Sadiq, kai kad'ai ka dace da ita, kuma ina rok'onka da yi min biyayya kamar yanda ka saba yi min". Can ciki yace " Candy fa? Ya zanyi da ita?" "Ka sanar da ita su biyu zaka had'a rana d'aya, indai tana sonka zata amince da hakan, in kuma ta fasa toh dama ba ita ba ce Allah ya rubuta maka matsayin matarka". Numfashi ya sauk'e yana cije labb'ansa na k'asa, bai ma san wani irin yanayi ya shiga ba, ya za'a raba shi da Candy cikin sauk'i haka? Bai mata magana ba ya mik'e ya bar d'akin.

Miemiebee:-


  Tun ranar da mahaifinta yayi mata maganar aure bata tab'a d'aga hankalinta ba sai yau da ta sa wanda zata aura a ido, Ibrahim? Ibrahim ke neman aurenta? Ita kuma haka zata k'are da wanda baiyi makarantar boko ba bare ya samu aiki? Haka zasuyi ta zama a gida ita dashi har su gunduri juna a fara fad'a? Waye ya bada wannan shawara? Anya zata yadda da aurensa?

Tuni tayi jan ido tace bazata iya ba, Mamanta tayi iya yinta amma fir tace ba ita ba Ibrahim har abada dan bazata iya zaman aure dashi ba, babanta ya mata nasiha banda kuka babu abunda ta iya yi masa wanda hakan ya tabbatar masa tak'i auren ne har cikin ranta. Tuni ya shareta ya fita hanyarta aka sa biki wata d'aya cif ba k'ari ba ragi, fad'in tashin hankalin da take ciki bata baki ne, wani lokacin ta kan rasa abunda zata yi dan jin sauk'in rad'ad'in zuciyarta. 

A kullum in tayi duba da yanayin sauyin rayuwarta ta kan kasa yadda ita ce ta koma haka, ganin idonta Kamal yake zuwa duba gida shi da matarsa amma ko da wasa bai tab'a nemanta ba, ta dai sa shi a ido sau d'aya yazo wucewa ta k'ofar gidansu, bazata iya fad'in yanayin da yake ciki ba da ta ganshi ita dai iya saninta fuskarsa bai nuna jin dad'i ko akasin hakan ba.

Hussain @ Minna:-


  D'akin mahaifiyarsa ya shiga kai tsaye matarsa na binsa a baya lullub'e cikin mayafinta, yayi sa'an samun iyayen nasa biyu(mamansa da babansa) a d'akin suna tattaunawa, bazai wuce maganar da ya bijiro musu dashi bane dan yanda suke kallonsa ya gano hakan. Zama suka yi dukkansu a k'asa, Mum Fateey ta kunco 'yarta da ke goye a bayanta ta zauna tana jan hanci dan kukan da tasha game da maganar da sukayi da Hussain.

Cikin nutsuwa yace "ina neman afuwarku amma gaskiya wannan karon bazan iya barin Benaxir ba dan wani ra'ayinku na daban wanda addini bai gindaya ba, shiyasa na kawo muku ita" ya nuna Mum Fateey "ni zan wuce in fara sabuwar rayuwa tare da Benaxir dan sama mata rayuwa mai inganci, in nema mata yafiyar iyayenta kuma in n addini da kyau kamar yanda na fara a baya ku ka hana ni, nayi muku biyayya na auri zab'inku amma ku kun nuna min baku son farincikina, kuyi hak'uri amma zan tafi nikam".

Makullin gidansa ya ajiye ya mik'e yace "zan ajiye miki akwatinki a waje, nikam na wuce" Baki bud'e suke kallonsa sun kasa gaskata abunda suke gani, bai tab'a yi musu abu kwatankwacin haka ba bare su kawo a ransu zai iya yin hakan, daf zai fita yaji kukan Matarsa ya tsananta tana cewa "indai dan ni kuke hana shi k'ara aure wallahi na yadda na amince ya aurota mu zauna tare, ina sonshi wallahi in ya tafi bansan ya zanyi ba, ga rabon yarinya tsakani" ta k'arashe tana jan majina.

Bai fasa fita daga d'akin ba yayi hanyar waje, muryar mahaifiyarsa ya dakatar dashi, dawowa yayi ciki ya zauna kamar yanda ta bashi umarni, kuka ta sa masa ba tare da tayi magana ba, ji yayi zuciyarsa yayi rauni jin kukan mahaifiyarsa akansa, runtse ido yayi yace "kiyi hak'uri dan Allah mama, ki fahimceni kuma ki gane ina son yi miki biyayya, k'in auren Benaxir na barazana ga addininta, kada ki bari shaid'an yaci galaba akan wannan ko so kike ta fara shakkar musulunci da musulmai?". " na amince ka aureta, mahaifinka ma ya amince, kaje wurinta ku sasanta ka kuma bata hak'uri kan abubuwan da nayi mata, nima zan bata hak'uri in mun had'u, ko yaushe kuke son auren a shirye muke".

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


Page 63


A gurguje please...


"Yanzu kai Sadiq Ruffaidan dole sai ka aureta? Kenan bazaka min abunda nakeso ba matsayina na uban..." Tari ne ya katse masa maganar da yakeyi a yayin da Sadiq ke zaune gefen gadonsa na asibiti yana sanar dashi maganar aurensu da Ruffaida, ya rikice iya rikicewa ganin yanda yake tari ba k'ak'k'autawa, tun yana ce masa sorry har abun yafi k'arfinsa dole ya k'ira likita dan duba sa, har waje nurse ta raka sa dan ya basu wuri jikin nasa yayi tsanani.

Rikicewa yayi ya rasa ya zaiyi da rayuwarsa, Candy sai da ta gama d'aga masa hankali game da auren mata biyu lokaci d'aya, kuka tayi masa cikin waya yana bata hak'uri tana cewa ta fasa aurensa dama ba sonta yakeyi ba, mak'asudin zuwansa asibitin ma kenan yazo yi masa sallama zai je Abuja rarrashi da rok'o. Yana jin k'ararin amai daga d'akin Nuraddeen na asibitin, in yaji k'arar nasa wani lokaci ji yake kamar ya bud'e k'ofar ya shiga ya ganewa idonsa abunda ke faruwa da mahaifinsa.

Tun yana jinsa har ya daina jin komai daga d'akin, hawaye yaji ya silalo daga idanunsa. Yawu ya had'iye mai taurin gaske dan kasa wucewa yayi sai da yayi da k'arfinsa sannan ya wuce. Safa da marwa ya fara har na tsawon mintuna goma, daga k'arshe k'ofar d'akin likita ya bud'e ya fito nurse na biye dashi a baya. Da hanzari Sadiq ya isa wurinsa yana tambayarsa lafiyar mahaifinsa, kafad'arshi ya rik'e da hannunsa na dama yace "am sorry, Allah yayi masa cikawa" k'ara ya saki ya koma gefe yana kallon likitan kamar zautacce.

Wayarsa yayi anfani dashi dan k'iran Mamu ganin yanda Sadiq ya sulale a k'asa yana sharb'an kuka kamar ransa zai fita, bai tab'a kawowa mahaifinsa mutuwa yanzu ba, haka kawai daga tari sai mutuwa? Dama haka mutuwar take zuwa bagtatan? Ba sallama ba sanarwa ba tsammani? Ya manta da wata kalmar innalillahi, a wurin yake durk'ushe yana zubar da hawaye tsakaninsa da Allah, duk yanda likitan yayi k'ok'arin kwantar masa hankali abun yaci tura, dole ya k'yalesa har Mamu da Ruffaida suka iso cike da tashin hankali.

Likita da ya k'ira Mamu bai sanar da ita mutuwar ba, ce mata yayi tazo asibiti yanzu-yanzu. Duk da zuciyarta ya tsinke bata kawo mutuwa ranta ba dan Sadiq a kullum yana ce mata jikin Nuraddeen da sauk'i duk da ba tambayarsa takeyi ba. Ganinsa zube a k'asa ya k'ara tada musu hankali, da hanzari suka isa inda yake, Mamu ce ta iya rik'esa tana tambayarsa lafiya? Kasa amsata yayi sai kuka da yakeyi ya k'ank'ameta cikin jikinsa.

Ganinsa haka yasa suka k'ara rushewa da kuka suna rok'onsa ya sanar dasu abunda yake faruwa. Minti uku ya d'auka sannan ya iya bud'e idanunsa ya sauk'e su kan Ruffaida da ke zaune dirshan a gefensa tana sharb'an kuka.

A fusace ya mik'e yana matsawa daga inda take yana cewa "ki daina kukan munafurcin nan, kin huta kin samu abunda kikeso, duk wani bak'in cikin da yake faruwa dani yana da alak'a da ke, na farko kika yi nasarar raba iyayena da juna, kika yi nasarar sani b'ata ran mahaifiyata, Alhamdulillahi na iya shawo kan matsalar ta hanyar amincewa da aurenki, hakan ya jawo min rabuwa da Candy dan kawai ki samu rayuwa mai inganci, meh na miki a rayuwa da kikeson ganina cikin bak'in ciki? Duk hakan bai isheki ba sai da kika yi nasarar sa ni b'ata ran mahaifina wanda hakan yayi sanadiyyar barinsa duniya" kuka yake yi a wannan karon sosai yana mai jin tsanarta a ransa.

Mamu sake sa tayi baki bud'e tana kallonsa hawaye na sintiri a fuskarta. So take ta gaskata abunda kunnuwanta ya jiye mata, Nuraddeen ya rasu? Ganin yanda numfashinsa ke gargada ya tabbatar mata da gaskiyar abunda ya fad'a, muryar likita taji yana cewa "kin iso Anty Mamu, am very sorry, nayi iya k'ok'arina amma na kasa shawo kan matsalar, lokaci d'aya abun ya tashi, kuma dama na sanar dake wannan matsalar duk wani allurar da muke masa yana masa k'aranci, kafin ya kai ga yin aikinsa virus d'in da yake dashi ke kashe k'arfinsa, hakan yasa bamu samu nasarar ceto ranshi ba dan magungunan da muke basa basuyi anfani jikinsa yanda yakamata ba tun farko, lokaci yayi Alhaji Nuraddeen".

Ruffaida zubewa tayi a wurin tana kecewa da kuka mai shiga rai, a wannan lokacin ko ita ji take ta tsani kanta ta tsani rayuwarta, cikin zancen Sadiq dukka babu k'arya ciki, bata kyautawa kanta ba kuma bata kyautawa Sadiq d'in da ya kasance masoyi a gareta ba, yayi komai dan ya faranta mata, ta tabbata Sadiq bai cancanci abunda ta aikata garesa ba.

Mamu kasa tab'uka komai ta yi, wannan karon hawayenta kafe suke, meh ya dace tayi a wannan lokaci? Kawar da tunanin Sadiq na d'aura laifin kan wacce bata da laifi ko kuma kukan rashin Nuraddeen? Duk abunda ya mata yanzu ya tafi ya barta, akwai tausayi da k'auna tsakaninta da mijinta, yau ta tabbata duniyar nan ba komai bane, kowa lokacinsa yake jira. Zama tayi tana bin kowannensu da ido, kukan da sukeyi ke bata mamaki, so take tayi kukan ko zata cire abunda ke dank'are a zuciyarta amma kukan yak'i fitowa.

Sadiq ne ya daure yayi hada-hadar d'aukar gawan bayan ya k'ira Malam Salihu ya sanar dashi abunda yake faruwa. Sai da ya iso sannan suka d'auki gawarsa suka wuce gida dan yi masa sutura a kai shi gidansa na gaskiya. Sai a sannan da taimakon Malam Salihu suka fara ambatar Innalillahi wa inna ilaihi raji'un zuciyarsu na ciwo.

•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•

'Yan uwa da abokan arziki sun zo gaisuwa, ciki har da k'awayen Ruffaida dukkansu, Batool, wacce ta samu rakiyar cousin d'inta, sai Ummu-Abdoul wacce tazo tare da mahaifiyarta dan mik'a mata nasu ta'aziyyar. Pherty tare da mijinta suka zo duk da cewa ba d'asawa suke yi ba, ya jajanta mata kuma ya tausaya mata matuk'a. Miemiebee ma ta zo a ranar bakwai, dan bata samu wanda zai kawota ba sai da mahaifinta ya nemo mata wanda zai kaita ya kuma dawo da ita.

Lubiee tare da Abubakar suka je gaisuwan daga Gombe, daga can suka wuce Abuja dan hutun nasu ya 'kare, sunyi kwanaki goma sha biyar suna shanawa cikin dangi suna mik'a gaisuwa. Benaxir ma ba'a barta a baya ba, dan takanas ta d'auki hanya daga Abuja ta isa Zaria dan kai gaisuwarta. Candy da iyayenta sunzo, tayi matuk'ar tausayawa Sadiq d'inta dan kwata-kwata baya cikin hayyacinsa, tuni ya zama kamar zautacce dan yana ganin dan shi jikin mahaifinsa yayi tsanani har ya kai ga rasa rayuwarsa. Addu'an su bai wuce Allah ya gafarta masa kurakuransa ba, duk 'yan uwa da dangi sun ji wannan mutuwar dan yazo musu a ba zata.

Fatanmu da rok'onmu Allah ya gafartawa masu hali irin nasa, Allah ya bawa wad'an da suka zalunta ikon yafe musu dan hak'kin da ke tsakanin bawa da bawa Allah bai yafewa dole sai bawan ya yafe masa, laifin da ke tsakaninsa da Allah kuma rok'onmu Allah yayi musu rahama ya gafarta musu. Wad'an da Allah ya basu tsawon kwana cikin masu hali irin nasa shawarata suyi gaggawar tuba, lokaci ba a hannunsu yake ba, Allah ya shiryesu ya tsarkake zuk'atanmu baki d'aya, ya raba mu da sharrin mutum ko aljan ya kuma kare mu da bin son zuciya.

Benaxir, Batool bayan kwanaki:-


Tun bayan dawowarsu daga gaisuwar Nuraddeen suka fara shirin bikinsu, Benaxir Minna ta koma wurin takwararta, mijinta shi ya zame mata waliyyi inda aka gabatar da komai yanda al'ada ta shirya. Jiran lokaci kawai suke dan d'aura aure, haka b'angaren Batool, an gama komai ba tare da samun matsala daga kowanni b'angare ba, mutanen gari sunyi gulmarsu sunyi zagi iya iyawarsu wanda hakan ke k'ara dagula mata lissafi, dole iyayensa da nata iyayen suka toshe kunne sanin ko meh ya faru sanadin yaron da yarinyar ne dukka babu wanda za'a tuhuma shi kad'ai bare ya zame musu sabuwar matsala, tunda har Allah ya shiryesu yasa musu son auren junansu babu abunda yafi musu hakan dad'i.

Anyi auren Batool da sati d'aya akayi na Benaxir, duk 'kawaye da 'yan uwa sun halarci biki sai sam Barka. Batool Katsina aka kaita Benaxir kuma Minna, anyi murna kuma anyi musu fatan alkhairi had'e da nasihu mai shiga jiki. A bikin Benaxir ne Ruffaida ke basu labarin matsalar da take fuskanta daga Sadiq, sakamakon rasuwar Nuraddeen yasa an d'aga bikin nasu zuwa wata d'aya da sati, wanda zuwa lokacin ya saura sati biyu kacal.

Sadiq dai yak'i kwantar da hankalinsa ya amince da Ruffaida matsayin matarsa, duk iya yanda Mamu ta so fahimtar da shi babu laifin Ruffaida cikin mutuwar mahaifinsa yaci tura, dad'in shi d'aya Candy da iyayenta sun amince da aurensu, duk da ba wani program za'ayi ba hakan bai hana shi shirye-shiryen biki ba, sai dai a duk shirin nasa baya sa Ruffaida, Candy kad'ai ta ishe shi dan shi har ga Allah Ruffaida haushi take bashi a yanzu. Mamu ce ta bada kud'i aka yiwa Ruffaida kayan aure akwati set d'aya tare da sayo mata kayan d'aki da na kitchen na gani na fad'a.

Hak'uri suka bata k'awayen nata had'e da bata k'arfin gwiwa dan kada taji tsoro ko k'in aurensa saboda wani dalili nasa na daban, sun jaddada mata cewa Zai hak'ura kuma zai fahimceta, ta bashi lokaci kuma ta bashi damar tunani mai zurfi shi da kansa zai gano ya kuma bata hak'uri a zauna lafiya.

Ruffaida biki saura kwana biyu:-


BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


              Page 64


Ruffaida biki saura kwana biyu:-


  Zaune take a gefen Mamu kanta a k'asa tana sauraron nasiha da kuma gargad'in da mahaifiyarta kuma mahaifiyar mijinta take mata. "Bazan samu damar yi miki magana mai tsawo ba lokacin da za'a kai ki gidan mijinki, shiyasa na nemi zama dake yanzu dan in fahimtar dake abubuwa masu muhimmanci dangane da aure. Aure sunnar ma'aiki ne kuma yana daga cikin ibada, kada ki d'auke shi wata rayuwar jin dad'i da soyayya kad'ai, akwai k'alubale kala-kala cikin rayuwar aure, mutumin da kike soyayya dashi daban da mijin aurenki, dan wanda kike soyayya dashi a kullum kyawawan abubuwansa kike gani bakya tab'a ganin bak'insa sai 'yan k'alilan wanda yawanci shima in kika gani ba wani abun a zo a gani bane bare kice kinsan komai game dashi, farinsa bak'insa, b'acin ransa da kuma fushinsa.

Mutum ne da zaki zauna dashi ki kwana dashi ki tashi dashi, ki kallesa yana cikin bacci ki kallesa bayan yayi wanka, babu mutumin da zai jure zama da miji/mata sai akwai tsananin k'auna da fahimtar juna.

Duk da naki daban yake da aure na soyayya amma hakan bazai hana in sake jaddada miki cewa kiyi masa biyayya kuma ki kawo muku fahimtar juna mai k'arfi ba, duk yanda kika juya mijinki tun daga farkon aurenku haka zai ja sai dai wani ikon Allah, ku biyu ne matan Sadiq kuma na tabbata kowaccenku da halinta zata shiga gidan kuma ina muku kyakyawar fata dan na san ku dukka. Abu na farko da nakeso ki rik'eshi a kwanyarki shine:-

1- Farkon aure mafi yawancin lokaci soyayya ce, sai anyi wata d'aya ko biyu zuwa uku sannan a fara fuskantar asalin menene aure, daga lokacin ne zaki fara gane waye mijina, ya zamu cigaba da zama dashi cikin gidan nan, shin yana da lokacin da zamu zauna mu fahimci juna? In kin samu miji wanda yasan abunda yakeyi toh bazaki samu matsala ba amma wani mijin dole ke zaki nuna masa ta hanyar da Allah ya hore miki a kwanyarki ta d'iya mace.

2- Ki kula da yanayin mijinki dan kisan maganar da ya dace kiyi masa. In ranshi a b'ace kada ki k'ara masa b'acin rai, in yana farinciki kiyi k'ok'arin tayasa kuma ki kiyaye b'ata masa rai. Rayuwar aurenki ya zama irin rayuwar da annabi yayi da matansa, dan koyo muke daga abunda ya aikata.

3-Ki kasance da mijinki a duk yanayin da yake, in yana farinciki ki tayasa in yana bak'in ciki ki zame masa ruwan sanyi dan yaye masa dukkan damuwarsa in kina da iko, tattausan lafazinki na iya sauk'ar masa da damuwarsa har ya kai ga kin iya cusa masa farinciki a lokacin da yake jin bak'in ciki.

4- Ki kasance tare da mijinki in yana shiri, ki tayasa sa kaya, taje gashin kansa ko na gemu, fesa masa turare da dai sauransu, yana k'ara dank'on soyayya, k'aramin abunda kuke rainawa yana matuk'ar tasiri cikin zuciyar miji.

5- Ki ci abinci tare da mijinki a plate d'aya, hakan na kawo fahimtar juna da k'auna mai d'orewa. Annabi yana d'aura lab'b'ansa/bakinsa kan dai-dai inda Nana Aisha ta d'aura akan kofi dan shan ruwa/madara.

6- Ki kasance mai ciyar da mijinki da hannayenki lokaci zuwa lokaci, wannan zai k'ara rura wutar k'aunarki a zuciyarsa.

7- Ki zama mai tausayin mijinki, baki san irin aikin da yake yi a waje ba dan ya samu damar sauk'e nauyinki da Allah ya d'aura masa, da zaki fita ki kalli yanda yake hada-hadar kasuwancinsa, zama office, makanikanci, acab'a da dai sauran nau'in aiki da zaki tausaya masa matuk'a muddin akwai soyayya.

8- Ki kasance mai yiwa mijinki kwalliya, matanmu na arewa na matuk'ar sakaci da wannan, mace bazatayi kwalliya ba sai in zata fita suna ko biki. Ki kasance mai yiwa mijinki kwalliya, in yau kinyi shigar atamfa, gobe ki rikid'a kiyi na turawa, jibi kiyi na yarabawa, zakiyi mamaki in nace miki yana matuk'ar burgesu, wannan d'aga zanin da sa sark'ok'i irin nasu. Ga kayaki da yawa ko ta ina ki saya kiyi wa mijinki kwalliya yaji dad'i ki samu lada.

9- Ki kasance mai yawan anfani da turaruka masu dad'in k'amshi, turare na kwantar da hankali in baki sani ba.

10- Ki so iyayensa, ki basu girmansu kamar yanda zaki bawa naki iyayen, wasu lokutan mata na yawan complain game da iyayen miji, ki kasance mai yi musu biyayya, ki musu snack ki sa a kwano ko dai wani abu mai kyau ki kai musu, ki yi musu abinci ko abun marmari lokaci zuwa lokaci ki aika musu, kije ki gaishe su lokaci zuwa lokaci, hakan yana daga cikin biyayya da girmama su, yin hakan zai k'ara miki girma da k'ima cikin idanun miji.

11- Muddin kina son kasancewa da mijinki cikin aminci da jin dad'i ki kasance mai nuna masa tsantsar soyayyarki ko ta wani hanya, ki kasance mai son zama a jikinsa, ki kwanta kan cinyarsa kuma kina yi masa kyauta komai k'ank'antarsa.

Kallonta tayi ta sake mata murmushi mai ciwo duk da kan Ruffaida na k'asa sannan ta cigaba "kada kiyi tunanin cewa ni matar Nuraddeen da nake fad'a miki hakan nayi anfani dashi kuma hakan bai hana mijina mu'amala da wasu matan a waje ba" d'aga kai tayi ta kalli Mamu jin furucinta, bata iya furta komai ba Mamu ta cigaba da cewa "duk abunda Allah ya rubuta sai ya faru toh tabbas duk wayonka bazai hana hakan faruwa ba, kiyi da zuciya d'aya kiyi addu'a sauran ki barwa Allah.

Abu na k'arshe da zan nema a wurinki Ruffaida shine yafiya, ki yafe mana ni da mijina mai rasuwa, ki yafe masa duk cutar da yayi miki, Allah bai bashi tsawon rai da zai gane kuskuren da ya yi ba bare ya baki hak'uri hakan yasa ni nake nema mishi yafiyarki, ki daure ki yafe masa dan laifukansa na da girma" ta k'arashe maganar tana mai fashewa da kuka.

Ruffaidar ma kukan takeyi mai shiga rai, na farko shawarar da Mamu ta bata ya karya mata zuciya, taya zata yi duk abubuwan da ta fad'a mata bayan Sadiq na fushi da ita? Ya zata nuna masa soyayyar da take masa wanda a kullum yake nuk'urk'usarta? Gashi yanzu ta kawo mata maganar Nuraddeen, mutumin da ya kasance uba a gareta.

"Ki daina kuka Mommy, baki min komai ba nikam, in ma kinyi na yafe miki nima ki yafe min, kuma maganar Daddy" ta ja hanci tace "na dad'e da yafewa Daddy, mahaifina ne kuma in yana da laifi 50 cikin d'ari tabbas 50 d'in nawa ne, nayi kuskure kamar yanda shima yayi, na yafe masa kuma ke ma ina neman yafiyarki" cikin kuka tayi maganar. Babu wanda ya k'ara magana cikinsu banda kukan da suke ta zabgawa kamar ransu zai fita.

   An d'aura aurensu cikin babban masallacin da ke Abuja(central mosque) bisa sadaki naira dubu hamsin-hamsin kowacce, gidan da yayi hayarsa a Abuja aka kai Candy, nan kuma Zaria gidan da Mamu ta saya masa aka kai Ruffaida, Candy ce uwar gida bisa dukkan alamu, dan can ya tare Ruffaida ko ganinshi bata yi ba sai bayan kwanaki bakwai, da yazo ma ko ta kanta bai bi ba, banda gaisuwa babu abunda ke shiga tsakaninsu, ko tayi masa girki ba ci yake yi ba, wani lokacin yakan bata mamaki, dan sai tace masa "ga abinci baka ci ba zaka fita" "na k'oshi" yake yawan cewa a tak'aice, sai yasa kai zai fita, ko meh yake tunowa sai ya ja tsaki ya dawo ya zauna ya ci ko da kad'an ne ba uhm bare um-um zai mik'e yace "na tafi" kamar an sa shi dole, "ko dai yasan bai kyauta min ne?" Tambayar da ke ranta kenan a kullum in yayi hakan.

Ranar da ya cika kwana biyar ne ya sameta a d'aki da dare tana kwance bacci ya fara sace ta. Wutar d'akin ya kunna sannan ya iso inda take ya zauna a gefenta, tuni ta samu zama ganin ya shigo d'akin. Kallonta yayi kamar bazai yi magana ba ya kawar dakai yace "nasan ina shiga hakk'inki, amma kiyi hak'uri ba daga ni ba ne, zuciyana ne ya kasa karb'an abu mai girma irin haka, ki fahimceni ki bani lokaci, komai zai wuce insha Allah".

Murmushi tayi tace " kada ka damu, nasan yanda kake ji game da hakan, ka gafarceni kuma ka samu wuri a zuciyarka na yafe min kura-kuraina gareka, insha Allah zaka sameni mai biyayya a gareka, na tuba". Murmushi ya sakar mata ya samu wuri gefenta ya kwanta ya kashe wutar d'akin ta makunnin da ke gefen gadon. "Sai da safe" yace da ita, kasa amsawa tayi dan k'ulle mata kai da abunda yake shirin yi yayi, a d'akinta zai kwana? 


Asuba ta gari...

•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•

  Miemiebee bata samu damar halartar bikin ba dan ita ma tana nata shirin bikin, duk da ita ba wani shiri takeyi ba sai risgar kuka da tashin hankalin da yake addabarta, bazata iya auran Ibrahim ba, raina shi zatayi garin neman lada tazo tana kwasar zunubi kan wanda ta dank'arawa kanta. Tayi iya k'ok'arinta na fahimtar da iyayenta amma sun kasa gane mata, daga k'arshe ma daina kulata sukayi dan ta fara b'ata musu rai da kawo musu dalilanta marasa kan gado. 

Bata yi k'asa a gwiwa ba tayi anfani da wayarta tayi ma k'awayenta doguwar text ta tura a group d'insu da ke WhatsApp tana neman shawararsu, babu abunda suka iya yi mata wanda ya kwantar mata hankali banda hak'uri da nasihu masu yawa, ita yanzu ji take ko d'igon son Ibrahim babu cikin ranta, a da d'in ma sha'awa ce kawai, mutum d'aya takeso kuma takeson sake kasancewa dashi inuwa d'aya wato Kamal.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


              Page 65


Ruffaida:-


  Tun daga wannan ranar yake sake mata fuska yake cin abincinta yake zama suyi hira, sai dai har ya gama iya kwanakinsa ya koma Abuja babu abunda ya shiga tsakaninsu na zamantakewar aure, a kullum Ruffaida in tazo bacci sai tayi kukan rayuwa irin nata. Ta kan rasa farincikin da yake ziyartarta a duk lokacin da ta tuna Sadiq ya kasa d'aukarta matsayin matarsa, kuma ta kasa sanar da kowa bare ta samu mafita duk da wani lokacin matar aure na da sirrinta wanda bai dace ta sanar da kowa ba.

Babu daman tasa k'ananan kaya dan yanayin kallon da yake sakar mata yana nuni da fassara na daban ba yabo ko nuna burgewa ba, "dama kin saba hakan ba sabon abu bane" tana karantar hakan cikin k'wayar idanunsa. Duk wani abunda zata yi masa zai d'auka salon iskanci ne kawai irin nata, toh ya zatayi dashi? Ya zata nuna masa cewa iya tarayyarta da namiji da mahaifinsa ne kawai?

  A kwana a tashi ba wuya har akayi wata d'aya babu abunda ya sauya, ita ta d'auka in tayi aure dukkan damuwarta da tashin hankalinta zai kau, ashe duk tunani ne, lallai illar zina na da yawa, ga kunyar duniya ga na lahira, fatanta Allah ya daidaita tsakaninsu ya kuma yafe mata laifukanta da ma dukkan musulmi baki d'aya.

Miemiebee:-


   Auren Miemie ya kankama, 'yan uwa da abokan arziki duk sun hallara kowa na tayata murna, ita ko k'aramin hauka tayi a gidan nan, dan ko kitso k'in yarda ayi mata tayi, gashin nan ya dunk'ule saura a tsai-tsaye dan ta kwana biyu bata wanke ta gyarashi ba, idanunta fari sal alamar tasha kuka kuma ta kwan biyu bata sa kwalli ba. Bakinta kuwa a bushe kamar bayan kifi, 'dan gyarar nan na amare duk bata yadda anyi mata ba, mutuwa kawai take jira dan ita tasan kwananta ya k'are tunda aka nemi had'ata da Ibrahim.

K'awayenta sunyi k'ok'arin nusar da ita ta kwantar da hankalinta amma ko sauraransu batayi ba sai ma kuka da ta fashe musu dashi, dole suka k'yaleta suna kallonta wasu kuwa na tausaya mata har ma da wad'an da ke tayata zubar da hawaye. 

Ranar asabar aka d'aura aure, lokacin da taji an d'aura aurenta ji tayi ina ma a lokacin numfashinta ya d'auke ta je can lahira ko zai fiye mata duniyar dad'i duk da bata san meh zata tarar a can d'in ba. Tayi kuka kamar ranta zai fita babu wanda yabi ta kanta, Pherty ce kawai take rarrashinta tana ce mata "Allah ya sauya miki da mafi alkhairi, kiyi addu'a ba kuka ba, baki san b'oyayyar al-amarin da ke cikin auren ba" cikin kuka tace "auren Ibrahim ne akwai alkhairi? Bazawara zan sake zama kwanan nan dan bana tunanin zan iya zama dashi wallahi, na cuci kaina" murmushi kawai Pherty tayi ta k'yaleta dan in ta cigaba da magana zata iya tona b'oyayyar al'amarin da suka shirya ba tare da saninta ba.

Jirgi amarya da k'awayenta suka bi zuwa Abuja, motocinsu tuni suka samu masu kai musu gida, dama sunsan da hakan shiyasa suka zo da wad'an da zasu koma musu dashi. Motoci masu kyau da tsada ne suka iso d'aukansu, tayi matuk'ar mamakin ganin irin motocin dan a tunaninta Ibrahim bayi da aiki kuma iyayensa ba masu dashi bane, tun lokacin da aka ce jirgi zasu bi ya d'aure mata kai, amma ta tab'e baki, dak'yar ya had'a kud'in jirgin nata ta sani, ganin k'awayenta shida na take mata baya har cikin jirgi ya k'ara dagula mata kwanya, sai da ta tambayi Batool shin su suka biya kud'in jirginsu ko kuwa? Murmushi Batool ta sakar mata tace "a'a, Angon dai ya biya mana dukkanmu, ai har dashi ma zamu wuce, ya rigamu shiga ciki ne da kin ganshi" jin yana cikin jirgin yasa ta had'e baki da hanci ta rufe fuskarta dan kawai bata son idonta ya sauk'a kan fuskarsa, zata iya mutuwa in ta ganshi yanzu dan haushin da yake bata.

Ummu Abdoul ce tace a kai su gidanta zuwa dare sai su mik'a ta d'akin mijinta, tayi hakan ne dan ta samu lokacin da zata yi mata kwalliya ta goge mata wannan bakin nata da ko kyaun gani babu. Suna zuwa kuwa ta fara aikinta, dak'yar Miemie ta k'yaleta ta fara da aikin gyara labb'anta wanda yake da saurin aiki da kuma sauk'in kud'i (ku duba kwaiseh Maryamah dan samun cikakken had'in), in ta shafa mata dagangan take gogewa dan kawai bata so, ba dan Ummu Abdoul ce ke wannan aikin ba da tuni sunyi fad'a da me gyarar.

Ummu Abdoul har jikinta bata bari ba sai da ta mulketa da dilka da sauran had'inta masu sauk'i da saurin aiki(duk zaku samu had'in cikin kwaiseh maryaamah). Sai da suka d'au awanni biyu sannan ta shiga wanka, bayan ta dirje jikinta ta wanke gashin kanta ta fito aka turarata da turare mai mugun k'amshi sannan akayi drying gashinta tare da yi mata stretching aka tufkeshi. Bayan maghrib ta sake maimaita mata hakan dan ta fito kamar amaryar, dak'yar nan ma ta bari, sai da duk k'awayen nata sukayi fushi sannan ta zauna suka yi mata.

Kafin k'arfe tara sun gama komai tayi wanka ta dirje jikinta, wani ruwan suka samu mai d'umi suka zuba had'in humrah da akayi musamman na wanka, shiga tayi ta kwara a jikinta, duk da bata bi yanda suka ce ba jikinta yayi mugun k'amshi. Goma cif yayi musu a harabar gidanta, bata samu ganin gidan ba dan an rufe mata fuskarta kirif, idonta ko d'igon hawaye babu, jin zuciyarta take kamar zai fashe, tana tunanin irin zaman da zatayi da namiji irin Ibrahim, "Allah ka dubi zuciyana ka kawo min mafita" shi ne kad'ai addu'arta.

Cikin d'akinta suka kaita wasu daga cikin masu rakiyarta na gud'a har suka ajiyeta bisa gadonta na alfarma. Kwanciya tayi ba tare da ta bud'e mayafin nata ba, ta bud'e idonta ta kalli meh? Gidan Ibrahim wanda ya zama gidanta a yanzu? Tsaki ta ja lokacin da k'awayen nata da sauran mutanen ke mata sallama. Tun tana jin hayaniyarsu har ta daina ji alamun sun bar gidan dukkansu, meh zatayi banda fashewa da kuka? Tun tana yi ahankali har ta fara mai sauti, da gaskiyarta take kukan ko zata samu sassaucin abunda take ji a k'albinta, shikenan ta tabbata matar Ibrahim ta haramta ga Kamal?

Cikin kukan taji alamun shigowarsa d'akin, k'amshin turarensa taji kamar zai sa ta amai, ba wai dan ba dad'i ba, hancinta kawai taji ya tsani k'amshin kamar yanda ta tsani wanda ya sa. Jinshi tayi ya zauna kusa da ita hakan bai hanata cigaba da kukanta ba ta matsa gefe dan ko kayansa bata son ya tab'a nata. Muryarshi ne ya doki kunnuwanta, "MIEMIENAH" lokaci d'aya kukan da takeyi ya tsaya cak, ta bud'e idanunta tana kallon gefen d'akin inda take fuskanta, tana sake taryo muryar da taji a kunnuwanta.

Juyowa tayi da hanzari jin ya sake maimaita k'irar sunanta, baki, ido, har ma da hanci duk bud'e ta tsaya kallon wanda bata tab'a tsammanin ganinsa ba a wannan rana. D'akin ta bi da kallo dan tabbatar da abunda idonta ke gani, tabbas d'akinta ne na Abuja, idonta ta murza ta sake d'aurasu akansa, murmushi yake sakar mata wanda yake tafiyar mata da dukkan nutsuwarta, hannunsa ya bud'e alamar tazo masa, bata yi wata-wata ba ta shige jikinsa tana mai sake masa sabon kuka shi ma yana zubar da nasa hawayen wanda tabbas shi ake k'ira da hawayen farin ciki. 

Ruffaida:-


   Yau take sa ran zuwan mijinta Sadiq, tun safe take kan gyarar gida da gyaran kanta, bayan ta gama girki ta sake feshe gidan da turare ta koma d'aki dan yin wanka a karo na biyu, ji takeyi kamar k'amshin da tayi mintuna arba'in da suka wuce yanzu ya gushe sakamakon zafin da akeyi kuma tayi aiki a kitchen, yaci ace yazo yanzu amma shiru babu shi ba alamarsa. Bata jima da shiga ba ta fito daga ita sai towel d'aya wanda dashi kuma tayi anfani wurin share fuskarta lokacin da take fitowa daga bayin.

Kai tsaye ta isa dressing mirror, bata shafa mai ba dan zafin da akeyi kuma jikinta ba mai irin nuna alamar mutum bai shafa mai ba, turaruka kawai ta fesa bayan ta gyara fuskarta. Mik'ewa tayi dan sa kayanta ta ganshi zaune kan gadonta ya kafa mata ido, har ga Allah ta tsorata dan saura k'iris towel d'inta ya zame daga hannunta amma tayi k'arfin halin rik'ewa.

Juyawa tayi bayan ta lura da yanayinta kuma kallon da yake sakar mata yasa ta sha jinin jikinta, cikin i'ina ta fara cewa "kayi hak'uri bansan kana nan ba" jin yayi shiru bai amsata ba yasa ta cigaba da cewa "excuse me please in shirya, ga ma can abincinka a dining". Takun k'afarsa taji kusa da ita, da hanzari ta juyo idanunta tuni sun tara k'walla dan tsoron da ya dirar mata, bata tab'a ganinsa haka ba, tsoronta d'aya kada ya d'auka da gangan tayi masa hakan.

"Dan Allah kayi hak'uri, wallahi bansan ka shigo ba, da na sani bazan fito maka haka ba Allah wallahi..." Sai faman rantse masa take shi kuwa ko sauraranta bai yi, tun yana isa wurinta tana komawa baya har ta had'u da bangon d'akin, da za'a auna bugun zuciyarta da zai fi 100beats/min tsabar yanda ta tsorata, tuni hawaye suka fara sauk'o mata ta had'e hannayenta biyu ta lumshe ido tana cewa "Dan Allah kayi hak'uri, bazan sake ba, wannan ma kusku..." Sauran zancen nata mak'alewa yayi sakamakon d'aura bakinsa da yayi kan nata dan ya gaji da jin surutun da a wurinsa ba yi da anfani.

Sun d'au lokaci a hakan daga bisani ya saketa yana mai fidda numfarfashi idanunsa a lumshe, "Ina sonki sos..." Maganar tasa mak'alewa yayi sakamakon bud'e idanunsa da yayi ya d'aura akan fuskarta da hawaye ke malala daga dukkan idanunta. Miyau ya had'iye mai d'aci ya furta kalmar "sorry" can ciki sannan ya fice daga d'akin da hanzari yana mai buga k'ofar da iya k'arfinsa.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


              Page 66


Miemiebee:-


   A daren ranar basu samu sunyi magana ba dan kukan da ta dad'e tana yi daga bisani kuma bacci mai nauyi ya saceta. Sauk'ar da ajiyar zuciya yayi a yayin da ya fuskanci bacci ya kwasheta, yayi ta rarrashinta amma tak'i sauraronsa, ya ma rasa gane wani irin kuka takeyi, na farinciki ne ko na da na sani. 

Ta riga shi tashi sallar asuba sakamakon rashin bacci da wuri da bai yi ba, zama tayi ta zuba mishi idanu tana kallon fuskarsa, a hankali taji sauk'ar hawaye daga idanunta, bata tab'a tunanin zata sake samun wannan damar ba a rayuwarta sai ga shi Allah ya sake bata a lokacin da bata tab'a tsammani ba, ashe bayan zunubban da tayi Allah zai iya bata farinciki? Lallai ta yadda Allah maji rok'on bawa, ya saurari du'a'inta kuma ya bata abinda takeso duk da d'imbin zunubbanta garesa, "Alhamdulillah" ta furta a dai-dai lokacin da aka sake k'iran sallah.

Ahankali ta mik'e ta shiga yin alwala, kafin ta fito ya tashi yana zaune zaman jiranta, kallon da yake binta dashi yasa ta jin kunyarsa ya sauk'o mata, meh zatayi a rayuwarta dan nuna wa Allah godiyarta, a ganinta alhamdulillahi bazai wadatar ba, jinshi kusa da ita numfashinsa na sauk'a a fuskarta yasa tace "wani irin godiya ya dace inyi, nayi hamdala amma gani nake kamar yayi k'ank'anta wurin godiyar alkhairi irin wannan...".

"Shshhh!" Manuniyarsa ya d'aura akan lebb'anta wanda hakan ya sauk'ar mata da kasala ta kasa kwakkwarar motsi, muryarshi taji kamar bai magana tsabar dashewa da taushi yace "in kikayi hamdala kuma kika kiyaye dokokinsa a ganina ya wadatar, sai kuma ya ninka miki rahamarsa gareki" muryarsa yasa ta bud'e idanunta kamar mai jin bacci tace "zamuyi sallah a gida ai ko? Kasan sallah in mata da miji suna yi tare lokaci zuwa lokaci akwai wani intimacy da ke shiga tsakaninsu, ka bari wannan ya shiga tsakaninmu".

Numfashi ya sauk'e ya sake mata murmushi ba tare da ya amsa ba yabi gefenta ya wuce, murmushi ne ya kufce mata ta juyo tana kallonsa a dai-dai lokacin da shima ya juyo, kamar bazai yi magana ba taji yace "ba mu kad'ai bane yanzu, kada ki manta kina da k'anwa", ji tayi wani abu ya soketa a k'irji, bai jira jin amsarta ko ganin yanayinta ba ya shige toilet ya barta a wurin.

Fitowarsa ya sameta tana sa hijabinta dan yin sallah, isa yayi wurinta kafin ta tada sallahr yace "kuma bazaki jirani ba?" Kallonshi tayi idanunta kamar zatai kuka tace "ai kace bazamuyi tare ba dan ba ni d'aya bace" ta k'arashe maganar hawaye na sauk'o mata, bata so tayi kukan ba amma ya sauk'o tayi hanzarin gogewa.

"Haba Miemienah" ya janyota jikinsa cikin rashin sanin kalar rarrashin da zaiyi mata, "banson sake ganin kukanki, ki karb'i k'addarar da Allah ya miki, Miemienah banson tuno abunda ya wuce, mun wahala dukkanmu sanin kanki ne ina sonki, kishi da fushi yasa na aikata abunda nayi, babu namijin da zai jure irin aika-aikar da kikayi, promise me bazaki sake ba, promise me ni kad'ai zan zame miki jagora bazakiyi sharing min kanki da wani ba, promise" ya fad'a idanunsa cike da k'walla.

Kuka ta fashe dashi mai k'arfi ta k'ank'amesa, "nayi da na sani kuma na tuba, wallahi bazan sake wautar take dokar Allah da ke kaina ba, i promise bazan sake ba, bazan ma sake gwadawa ba bare inyi, na tuba". Shafa bayanta yakeyi alamar rarrashi, mintuna biyar suka d'auka sannan ya sauk'e ajiyar zuciya yace "barin dubata ko ta tashi sai inzo muyi ko?" Gyad'a kai tayi alamar taji sannan ya fice ita kuwa ta sulale k'asa tana mai zubar da k'walla.

Lokacin da take da damarta tayi wasa dashi gashi ya wuce babu halin dawowa, babu yanda ta iya tunda tana son Kamal kuma ta same sa ya fiye mata komai, ko da wasa bazata sake yin abunda Allah ya haramta ba bare ta rasa shi har abada, abunda bazata iya jurewa ba kenan, ashe tubanta bata yi shi a k'urarren lokaci ba, sai yanzu take sake jinjinawa aminanta wanda ta sa musu suna "HASKE 7" lallai sun haskaka mata rayuwarta, babu abunda zata iya saka musu dashi sai addu'a.

Bayan ya dawo sunyi sallah ne suka kwanta, ba dan bacci ba sai dan su samu damar samun kasancewa da juna na tsawon lokacin da basu samu ba. "Ni na d'auka Ibrahim zan gani a daren jiya, it was like a dream da na ganka a madadinsa, ya akayi hakan?" Murmushi yayi mata yana shafa gashin kanta yace "Your friends are blessing to us, su suka nemi Ibrahim ya hak'ura kuma suka je har wurin Mamana suka rok'eta da ta barni in dawo da ke, Miemienah kinsan nayi missing naki? But duk lokacin da na tuna ko na dawo dake bazaki iya jure zama dani ba sai inji ina shiga hakk'inki gwanda in barki, but da suka zo min da maganar sun nuna min zaki iya hak'uri tunda har kika k'i amincewa da Ibrahim d'in da zaku kasance tare 24/7, kin yadda yanzu zaki iya zama ba tare da ni kusa dake ba? Kuma fa kina da k'anwa, dole in raba muku kwana, duk zaki iya jurewa? In bazaki iya ba tun yanzu ki sanar dani musan abun yi Miemienah".

Kuka takeyi sosai, ya zai ce mata haka? "Wallahi zan iya, ina sonka bazan iya rabuwa dakai ba, a da d'in ma son zuciya ne kawai irin nawa ina tunanin akwai wasu bayan halalina, amma yanzu kai kadai ne a raina, kai kad'ai ne nake son zama dashi, yanda nake sonka zan iya jure komai har zuwa lokacin da zaka kasance tare dani, i know my man, duk missing d'in da nake masa in ya dawo yana kawar min, damuwar meh zanyi kuma? Please dont think that way, am now a changed person, ina sonka sosai". 

Daga nan komai ya sauya, wani salo daban ya shiga yi mata, tuni suka mance b'acin rai suka shiga faranta ran juna... ba su suka farka ba sai k'arfe goma. Wanka sukayi dukkansu suka fito shar dasu sai murmushi suke dokawa juna, duk da basu kasance tare matsayin abu d'aya ba taji dad'in yanda yayi mata har bacci mai nauyi ya kwashesu, jin d'uminsa da salon da yabi da ita cikin jikinta yafi mata komai a rayuwa, babu abunda yafi kasancewa da masoyi kuma miji dad'i. 

  Bayan sun gama shirinsu hannunta ya rik'e ya d'aura mata peck a goshinta sannan yayi mata rad'a cikin kunnenta, "na yadda zaki iya zama babu ni tunda dazu baki nemi abinda nake ta jira kice kinaso ba, i knw kinyi missing but juriyarki kikeson nuna min, don't worry everything wil be fine, u wil get what you want". Rungumesa tayi a jikinta tace "kai ko, kuma har ka gane daurewa nayi" ta fad'i hakan tana tura baki, dariya yayi wanda sautin ya shigo dodon kunnenta yasa ta lumshe ido tana a mak'ale a jikinsa.

"Kuma ke ce ban sani ba? Sake ni toh mu fita in ba so kike in baki tun yanzu ba kafin mu kai dare, kinsan ba mu kad'ai bane, da alamu kina mantawa da hakan" ya d'aga mata gira yana kallon fuskarta, ba k'aramin daurewa tayi ta sake masa murmushi ba sannan tace "ina tare da kai wa zan sake tunawa kuma Babynah" kashe masa ido tayi bayan ta gama maganar murmushi bai bar fuskarta ba, dariya sukayi dukka sannan ya ja hannunta suka fito. 

  Dai-dai fitowar Lubna daga kitchen suka sauk'o, murmushi ta sakar musu sannan ta d'an rankwafa tace "Good morning", sake hannun Miemie yayi ya isa wurinta yana cewa "haka muka fara gaisuwar kuma? Murmushi take yi masa har ya iso inda take sannan ta lumshe ido tana jirar kalar tashi gaisuwar da ya koya mata, a kumatunta yayi mata kiss sannan ya d'aura mata a goshinta, ya kuma rad'a mata wannan kalmar ta "ILY" cikin kunnuwamta ba tare da Miemie taji ba, idanunta k'yar a kansu tana kallon ikon Allah, shin zata k'ira wannan cin fuska ko meh? Saurin kawar da tunanin tayi dan kada tayi judging abu daga gani sau d'aya.

Bata san lokacin da ya janyota ba ya rik'e kafad'arta da hannu d'aya ya janyota jikinsa yana cewa "Little, wannan ita ce Miemie, ai ma kin santa ko? My 1st wife, jiya basu iso da wuri ba shiyasa baki ganta ba" isa wurinta Lubna tayi ta mik'a mata hannu dan su gaisa tana ce mata "hy, am Lubna your sister" hawaye taji ya taru mata cikin idonta, dan ji tayi duk kishi da haushin da taji d'azu ya kau, hannunta tasa cikin nata sannan ta janyota sukayi huging juna, "bazan tab'a d'aukarta matsayin kishiya ba, she is just like my younger sister saboda k'ank'antarta" ta fad'a a ranta.

Farinciki ne ya ziyarci zuciyar Kamal dan hakan da sukayi yasa hankalinsa ya kwanta kuma ya yadda zasu zauna lafiya tsakaninsu, fatansa Allah ya had'e kansu kuma ya kau da sharrin shaid'an tsakaninsu ya kuma sa Miemiensa ta rik'e masa alk'awarinsa. Breaking hug d'in sukayi shima ya ware hannuwansa alamar saura shi, dukkansu suka shige cikin jikinsa suna mai dariya shima yana tayasu.

Alhamdulillah, finally na fara hararo k'arshe tunda na gama labarin mutane biyu, Batool and Miemiebee. Thanks for reading... #ILYA

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


              Page 67


Ruffaida:-


  Kwana bakwai cif rabonta dashi, a text ya sanar da ita dawowarsa a safiyar ranar jumma'a. Waya tayi anfani dashi dan samun mai yi mata bak'in lalle(Hennah), k'awarta ce a nan Zaria, duk dawowarta Zaria hutu bata da k'awa sai ita kullum suna tare, kuma ta iya lalle na k'in k'arawa. Bata d'au lokaci ba ta iso suka fara, suna gamawa ya bushe ta wanke ta dawo ta tayata tsifar kanta, tas suka tsefe ta wanke da kanta ta d'auko dryer k'awarta tayi mata sannan tayi mata stretching har da style nata, duk da bata k'ware ba amma zig-zig d'in da tayi wanda ya sauk'o mata saman goshinta yayi matuk'ar kyau, ba wani gashin kirki bane amma yayi matuk'ar yin kyau kuma bak'i sid'ik yana da cika.

K'awarta bata bar gidan ba sai da suka gama kimtsa komai tayi wanka tasa doguwar riga na atamfa fitted gown yayi d'as a jikinta sannan tayi mata sallama ta bar gidan tana cewa dole ita ma ta nemo miji dan shiganta da kyaun da tayi ya bata sha'awa. Murmushi kawai Ruffaida tayi a ranta tana rok'on Allah da yasa kada ya gwasaleta, atleast yayi mata kallon arziki, tun ranar da yayi kissing d'inta bata sake ganinsa ba sai yau da yace zai zo, ko meh yake shirin yi mata wannan karon oho masa.

K'arfe 1:30 ya shigo gari, sai da ya tsaya a masallaci ya samu sallar jum'a sannan ya wuce gida. Knocking yayi tazo ta bud'e masa tana mai sake masa murmushi had'e da sauk'ar da murya tace "sannu da dawowa", "wow" ya samu kansa da fad'i ba tare da yayi niyya ba dan kyaun da tayi, kayan ya fitar da ita, fuskarta sai k'yalli yake ta murza d'ankwali akanta ta bar gashin gaban a waje. Ganin yanda ya k'ura mata idanu yasa taji dad'i a ranta, ko ba komai tasan ta burgeshi, shigowa yayi ba tare da ya rufe k'ofar ba ya sa ta cikin jikinsa ba tare da tayi tsammani ba, sauk'e ajiyar zuciya dukka sukayi tana mai k'ara lafewa cikin jikinsa.

Mintuna masu yawa suka d'auka, ita tayi k'ok'arin b'anb'are jikinta daga nasa ta rufe k'ofar hannunta sak'ale cikin nasa ta janyosa zuwa d'akinsa, bai iya furta komai ba sai kallonta da ya tsaya yi. Suna shiga d'akin ta juya zata fice ya kamota ya rungumeta ta baya, "kinyi kyau sosai, kada ki tafi please" ajiyar zuciya ta sauk'e ta lumshe idanunta jin hannunshi yana yi mata tafiya da yatsunsa akan fatar hannayenta, da fuskarsa yayi anfani wurin ture d'an kwalin nata ya fad'i ya sa fuskarsa cikin gashinta yana shak'ar ni'imtaccen k'amshi.

Hawaye taji yana sulala daga idanunta, a rayuwarta bata tab'a jin nutsuwa irin wannan ba, bata tab'a jin yanda takeji yanzu a jikinta ba, ahankali yake yi mata komai yana nuna mata tsantsar soyayya wanda ita ta tabbata bai san yana yi mata hakan ba. 

Muryarshi ne ya katseta "am sorry for everything angel, na dawo miki yanzu, na dawo dan muyi irin rayuwar da kowani ma'aurata sukeyi, mu manta komai, mu manta baya, k'addara ne ya fad'a mana dukka, Allah ya gafarta mana ya kuma kyautata namu k'arshen, hope bakiyi fushi dani ba kuma zaki bani daman kasancewa dake cikin inuwa d'aya, kada ki wahalar dani yanda nayi miki, am very sorry, zuciyata da dukkan gangar jikina na buk'atarki a yanzu, you're my 1st love, bazan tab'a iya mantawa dake ba, zuciyata bata kyauta min ba lokacin da ta kasa aminta da aurenki, bansan ya akayi soyayyar da nake miki tun a da ya koma tsana ba, sai last week na tabbatar da ba tsana nake miki ba, kishi ne kawai, kishinki nakeyi kuma kishi da mahaifina" muryarsa na rawa yake maganar kuma bai daina yawo da hannunsa a jikinta ba sai dai zuwa wannan lokaci jikinsa rawa yakeyi dan hawaye ke zuba daga idanunsa tunawa da mahaifinsa da kuma aika-aikar da sukayi.

Juyowa tayi ta shige jikinsa tana mai fashewa da kuka, anya akwai asarar da ya wuce wannan? Babu indai a rayuwar duniya ne, zina yafi komai muni a ganinta, dalilin hakan gashi ta rasa soyayyar Sadiq d'inta, ya raba gida biyu ya baiwa Candy sauran ne ya mik'a mata, bata iya furta komai ba sai "Am sorry" da ya kub'uce daga bakinta.

   Bayanta yake shafawa ahankali dan ta tsagaita kukan, cikin kunnuwanta yake sauk'ar da numfashinsa, hakan ba k'aramin kashe mata jiki yayi ba, ba dan ya rik'eta ba sulalewa zatayi, a cikin kunnuwan nata yace "I Love you Ruffaida, i love you with every fiber of my being, you mean so much to me, daga yanzu zan zame miki miji nagartacce, zan zama mai adalci tsakaninku dan babu wanda ban so cikinku, Candy na da hankali kuma zata zauna dake cikin aminci, nd i knw kema zaki zauna da ita tunda tarbiyyarmu d'aya. Ruffaida kin yadda zaki zauna dani? Kin yadda ki mallaka min sauran rayuwarki, kin yadda ki zama uwa ga 'ya'yana? Please say yes, shi kad'ai nakeson inji daga gareki a wannan lokaci, please".

Samun kanta tayi da d'aura lebb'anta akan nasa, daga farkon zancen yana yi ne cikin kunnuwanta, daga baya ya cirota daga jikinsa yana mai kallon cikin idonta, ita kuwa bata iya kallon nasa idon ba dan sak'onnin da yake aika mata sun girmi kwanyarta, hakan yasa ta d'aurasu akan lebb'ansa tana kallon yanda yake motsi yayin da yake magana, shiyasa taji sha'awar tasting har bata san lokacin da ta had'e da nata ba. Biye mata yayi dan hakan ya basa amsar tambayoyinsa, batayi fushi dashi ba kenan kuma zata zauna dashi da kishiyarta, duk ta amince.

Lubiee @ 4:10 ranar Jumma'a:-


  Zaune take a parlon gidan hankali kwance tana kallon TV hannunta na cikin robar aya d'anye da ta jik'a, shi kawai takeson ci a yau. Sanye take da atamfa riga da skirt ya amshi jikinta, atamfan ba k'aramin shiga yayi da kalar fatarta ba, sai yalk'i takeyi ga wani haske da ta k'ara ta d'an cika. American series take kallo, hankalinta duk ta mik'awa TVn dan yayi matuk'ar tafiya da ita. Abubakar ne ya fito daga d'akin Nafee fuskarsa d'auke da murmushi tana biye dashi a baya. "Kallo kikeyi haka duk da baki da hanci a bud'e?" Ya fad'i hakan yana dariya a dai-dai lokacin da yake zama kan kujerar gefenta 1seater.

Ba tare da ta kalleshi ba ta d'ibi ayar ta sa a bakinta tace "zauna kaima ka sha kallo, nasan zaka fini bud'e baki in ka sa hankalinka dan yayi ne k'arshe". Bata kula da Nafee da ke tsaye ta gefenta ba, Abubakar ne yayi mata nuni da ido ta zauna sannan ta samu zama, hakan yasa Lubiee ta kalleta ta sake mata murmushi sannan ta d'an gyaru mata dan ta zauna da kyau ta cigaba da kallonta ba tare da tayi mata magana ba.

Yanzu suna d'an magana dan tun dawowarsu daga Gombe komai ya sauya, Abubakar ya sake da Nafee ita ma ta sake dashi, akwai wata ranar da ya dawo daga office kai tsaye ya shige d'akinta yaji tana maganar asirin da tayi masa, dad'insa d'aya jin tace " bazan sake yi ba ko da wasa, tunda asirin nan ya karye nake samun bacci bana muggun mafarki, ai Allah ya taimakeni da nayi yaji naje gida, da ban je ba har yanzu ina cikin b'ata, wacce take kai ni wurin malaman wani cuta ya kamata sai kin ganta, naje gidan ban iya zama gefenta ba dan wari, anan take ce min in tuba, ita dai nata ya k'are tun daga nan naji na tsani abun, matsalata bansan ya zan nemi gafararsu ba, ina tsoron su san abunda na aikata su gujeni Abubakar yak'i zama dani, ina sonshi yanzu tsakani da Allah" ta fashe da kuka dai-dai lokacin da yasa kai d'akin, ya dai yi fushi dan halinta ya bashi mamaki, bai d'auka asiri tayi masa ya kau masa da tunaninsa ba, ashe ita ce tasa shi b'atawa Lubie rai?

Sunyi fad'a har yana ik'irarin sakinta, ita kuwa tayi ta bashi hak'uri. Da Lubiee ta dawo daga aikinta shine ya tareta da maganar hankalinsa tashe yana matsar kwalla, hak'uri ta bashi kuma ta nemi alfarmar ya bata dama tunda da kunnensa yaji tana cewa ta hak'ura da bin malamai, ita tuntuni tasan da ita ke yin abun, anan ne ta bashi labarin binciken da tayi a d'akinsa har ma da k'aryar b'era da tayi masa, sosai darajarta da girmanta ya k'ara d'arsuwa a zuciyarsa.

Yau sati kenan da yin hakan shiyasa ya nemi Nafee da ta zo wurin Lubiee ta nemi yafiyarta dan a zauna lafiya tunda ga rabon yara tsakani. 

Sai da yayi mata nuni da ido nan ma sannan ta fara magana cikin i'ina "ehmm! Anty Lubiee..." Ta kasa k'arasawa ganin Lubie ta juyo tana fuskantarta, "lafiya?" Lubie ta tambaya tana mai kallonta had'e da dawo da dubanta ga Abubakar, rage muryar TVn tayi a dai-dai lokacin da taji muryar Nafee na cewa "da... Dama.." Muryar Abubakar ne ya katseta "hak'uri tazo baki kan abubuwan da ya faru a baya, tsoronki ya hanata magana dan kada kice baki hak'ura ba, ai nasan matata bata k'ullatar mutum" ya d'aga mata gira yana murmushi.

Sheshshek'a Nafee ta fara ta rik'o hannun Lubiee kanta a k'asa tana cewa "ki yafe min, nayi kuskure na shiga hakk'inki, in baki yafe min ba hankalina bazai tab'a kwanciya ba", "nayi matuk'ar farinciki da naji hakan daga wurinki, ai mutum in yayi laifi ya karb'i laifinsa ya bada hak'uri ba k'aramin abu yayi ba, hakan ya k'ara miki daraja a idanuna, na yafe miki, komai ya wuce" godiya tayi sosai ita kuma ta k'ara muryar TVnta tana mai cewa "ku zauna mu kalla tare" tana fad'an hakan tana jefa aya a bakinta. Abubakar ne ya kalleta da kyau yace "anya Kausar bata samu k'anwa ba, irin ciye-ciye haka?" Murmushi tayi tace masa "babu komai cikin nan" ta fad'a tana shafa cikinta, wani hirar ta kawo dan kawar da maganar sanin cewa tana da ciki har na watanni biyu tak'i sanar dashi.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


              Page 68


Ummu-Abdoul bayan watanni:-


   Zaune take akan gadon hajiya tana jiran ta idar da sallah dan sanar da ita shawarar da ta yanke, tunani ta fara na kwanaki biyu da suka wuce game da zancen, lokacin da ta nemi Miemiebee da Pherty dan su tattauna maganar, murmushi ne ya kufce mata lokacin da ta tuna maganar da sukayi:-

  "Hajiya B da angle ta rik'e sai na cire gwani cikin Malam Usman da Abba, nayi istikhara ban gane komai ba ko dan hankalina da tunanina ya biyewa mutum d'aya ne daga ciki i don't know, but dama aka ce in kayi istikhara kayi shawara da mutanen da kasan bazasu maka k'arya ko su bi son zuciyarka ba shiyasa nazo gareku". Cewar ummu Abdoul

Pherty tace "a nawa shawarar ki koma gidan Abba, tunda ya gano kurensa kuma kikace da kansa ya sanar dake Kdeey har office d'insa ta wanke k'afa taje ta sanar dashi komai ta basa hak'uri had'e da basa IVn aurenta..." Miemiebee na shan grapes ta dakatar da ita da cewa "wai aure zatayi bani da labari? Yaushe ta sanar daku Kdeey taje wurin Abba? Meh yayi mata da ta sanar dashi? Bai gaureta da mari ba? Waye zai auri mace irinta mai bak'in hali?".

Ummu Abdoul ce tayi murmushin k'arfin hali tace "ai duk laifin bawa in ya tuba Allah mai iya yafe masa ne, nima ta k'irani harda kukanta, na hak'ura, meh ribana idan na rik'eta?" Bakinta cike da grapes tace "gaskiya fa, wa zata aura?" "Wani ne a wurin aikinsu, na ma sanshi". "Allah yasa alkhairi ya kuma sa mata sonshi kamar yanda ya sa mata son Abba". Daga k'arshe dai kowaccensu ta sanar da ita ra'ayinta, kuma ta k'ara da cewa ta nemi sauran k'awayen nasu ko a waya ne dan taji nasu shawarar. 

"Allah yasa inji alkhairi" hajiya ta fad'a lokacin da take ninke sallayarta, murmushi Ummu Abdoul tayi sannan tace "insha Allah Hajiya, na gama shawarata kuma ina fata ya faranta miki rai" ba tare da ta kalleta ba tace "ina jinki" "nayi magana da..." Ta kalli fuskar Hajiya tana mai shakkun zancen nata sannan tace "Malam Usman".

   Lumshe ido hajiya tayi bata iya furta komai ba Ummu Abdoul ta cigaba da cewa "na sanar dashi shawarar da na yanke na komawa gidan mijina na farko kuma bai b'ata rai ba duk da naji alamun hakan cikin muryarsa kuma bai sake k'irana ba bare ya d'auki nawa k'iran, haushi yaji kenan ko Hajiya? Meh zai hana in auresa kawai dan ya min halacci kuma barinsa for the second time bai kamacesa ba daga gareni, ko da bai so ya nuna b'acin ransa ba zuciyarsa mai iya sa shi yayi hakan ne dan yayi hak'uri akaina sosai, kuma a wannan karon yayi nasarar samun lokacina har ma yake ik'irarin ya samu nasarar sace zuciyata daga wurin tsohon mijina wanda hakan zai bashi damar aurena cikin sauk'i".

Numfashi Hajiya ta sauk'e, kallonta tayi kanta a k'asa damuwa ya bayyana a fuskar 'yarta, hannunta ta rik'e da kyau daga bisani tace " kada ki damu da hakan, kiyi abunda yafi kwanta miki a rai, kije inda farincikinki yake, tabbas zai ji b'acin rai amma nasan shi zai fahimceki kuma zai hak'ura nan gaba kad'an, nayi matuk'ar farincikin jin zancenki, Allah yasa komawarki shine mafi alkhairi gare mu dukka, Allah ya miki albarka yasa alkhairi, kinga yanzu bazan hana Feedoh turo wannan yaron ba, in yazo da jibgegen motarsa sai ya hanani ganin cikin gida kullum ta windownah yake parking, gwanda in aurar ku tafi can kuna toshe naku windunan". Dariya sukayi dukka sannan suka shiga hirar yanda za'a shirya bikin nasu duk da ita Ummu Abdoul babu wani abunda za'ayi, aure kawai za'a d'aura a mayar da ita gidanta, Feedoh ce dai ake sa ran zatayi shagali iya son ranta dan da alamu ita da mijin nata masu son wannan harkar ne.

   Wata d'aya kacal aka sa dan d'aura auren Ummu Abdoul da mijinta Abba, hakan yasa duk gidan babu mai zama dan ana gama nata da wata daya za'ayi na Feedoh. Ummu Abdoul transfer ta nema wurin aikinta ta koma can Taraba amma Abba yace wannan karon bai yada da aikinta wani gari ba, a da ya barta dan mahaifiyarta na garin amma yanzu sai dai ta nema a nan Katsina kuma ya bata tabbacin zata samu wanda yafi na can ma albashi mai tsoka.

•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°

  Ranar Jumma'a aka d'aura aure, cikin k'awayenta babu wanda bai hallara ba har ma da mazajensu, lokacin Benaxir na d'auke da k'aramin ciki, duk abinda ta ci sai ta harar, bini-bini Hussain ya k'ira yaji ya take, daga k'arshe dai zuwa yayi ya d'auketa dan su koma masauk'insu, ita ma naci ne kawai irin nata, ya hanata zuwa tak'i harda 'kwallarta dan ya barta tazo gashi yanzu ta galabaitar da kanta da babynsa. Lokacin da Ruffaida da Batool suka fito rik'e da ita da hanzari yazo yana cewa "Baby kin gani ba, sai da na fad'a miki kada kizo kika nace" kamota yayi yana kallonta ita kuwa ta tura baki wai nan shagwab'a take masa, fuskarsa duk ya bayyana damuwarsa akanta.

Sai da suka isa mota ya bud'e mata ta shiga sannan ya juyo inda suke yace "k'awarku bata ji, bata da lafiya amma ta nace sai tazo ganinku, ko meh kuke bata wanda ni bana bata har take sonku fiye da ni da babynah oho" dariya sukayi dukka yayi musu godiya suka wuce yana mai tabbatar musu washe gari da safe zasu wuce gida. Sallama sukayi da ita suka bar wurin suna mai jin dad'in ganinta tare da masoyinta yana nuna kulawarsa gareta.

Sun iso daf k'ofar komawa gidan wayar Ruffaida ya fara ringing, murmushi ta sake tun kafin ta d'aga wayar, Allah yasa babu kowa k'ofar gidan hakan yasa tace "yi hak'uri in d'auki waya, Sadiq ke k'ira". "Sadiq zaki k'irasa ba ko kunya? Zan ko fad'a masa" murmushi tayi sannan ta d'aga wayar ta d'aura a kunnenta. 

"Barka da warhaka ranka ya dad'e, har an fara missing d'ina?" "Wani an fara kuma? Ai tuni na fara missing naki, yanzun na gaji da hak'uri ne nazo d'aukarki, dan Allah kizo mu koma gida ina kallonki zaki shiga gidan". Muryarsa bai nuna wasa ba ko kad'an hakan yasa ta fara waige-waige, can kuwa taga motarshi. Murmushi ta sake sannan tace " ina zuwa" ta katse wayar ta ja hannun Batool suka shige ciki.

  Shareshi tayi ta ma manta da batunsa, wayarta kuma tasa a silent dan kada ta ji k'arar wayar bare ta d'auka. Ita tasan ba missing nata yake yi ba, hankalinsa ne kawai bai kwanta da bikin ba, gani yake wani wuri can zata je dan rabonta da Abuja ta jima sosai. Yaushe Sadiq zai fara yadda da ita? Duk inda zata je fa ko da a Zaria ne sai dai shi ya kaita, baya yadda ta hau napep ta fita indai baya gari, da ta gwada masa magana game da hakan cewa yayi ta barshi ya gudanar da al'amarin gidansa yanda yafi kwanta masa a rai, in yana hakan bazai samu wani k'ofa da zargi zai shiga tsakaninsu ba, tayi hak'uri dashi na d'an wani lokaci har ya samu damar kawar da duk wani abunda yake ransa.

***

  Sak'o tayi masa akan Hajiya ta hanata tafiya tana mai sanar dashi cewa sai dare tace zata koma, yayi hak'uri ya dawo da daren, abu na rana d'aya? Bai sake nemanta ba, da alamu haushi yaji dan da nisa sosai tsakaninsu. Samun k'awayenta yasa hankalinta kwanciya ta sharesa ta cire damuwarta suka cigaba da hirar cikin Lubiee wanda ya girma saura watanni biyu ya cika wata tara. 

Da dare sai da kowa ya watse bai zo ba, ba a ranar Ummu Abdoul zata wuce gidanta ba, Abba ne zai d'auketa a motarsa washe gari ita d'aya su wuce ba sai an rakata ba kamar yanda Hajiya tace babu anfani tunda ba sabon aure bane kome ne. 

Tun tana amsa hirar su hajiya, Feedoh, Auta da ma Ummu Abdoul d'in har ta daina dan ta tsorata da k'in d'aga wayarta da yayi. Tayi masa text ma yak'i mata reply, sai da yayi mintuna goma sannan yayi mata reply da cewa "na d'auka kwana zakiyi ai" bata yi fushi ba ta amsa shi da "yi hak'uri my king, ina jiranka" ko minti d'aya da turawa bai yi ba ya dawo da reply "ki fito". Wato dama yana nan kawai nuna mata isa yayi, lallai wannan Sadiq d'in sai shi.

Sallama tayi musu dukka harda tsokanar Ummu-Abdoul akan bakinta da yak'i rufuwa, ba dan Hajiya na wurin ba da ta mayar mata dan ita ma tana da abun tsokanan da yawa. Har wurin mota ta rakota suka rungume juna harda k'wallarsu sannan sukayi sallama suka wuce, ba dan hawayen da ya gani a idanunta ba babu abunda zai sa yayi mata magana, amma tun rabuwarta da Ummu Abdoul take matsar k'walla, ya tabbata rayuwarta da na k'awayenta take tunawa.

Lokacin da suka isa Candy na parlor tana jirar isowarsu, tana ganinsu ta d'auke kai alamar tayi fushi, Ruffaida ce ta isa wurinta tana cewa " Haba Anty Candy(sunan da take k'iranta dashi kenan in tana neman rarrashinta akan wani abu ko da kuwa a waya ne)" gefenta ta zauna tana cewa "kin gansa nan shi yak'i zuwa d'aukata da wuri har 9, ko ina yaje oho nima nayi fushi dashi" ta gyara zamanta yanda Candy tayi tana mai tura baki irin nata.

Dariya Sadiq yayi sosai yana cewa "kun ko yi kyau, kun ganku kuwa? Naga alamar sai na samo partner nima shiyasa da na ajiyeta naje zance dan naga ku biyu kun had'a kai, in na kawota sai ita ta had'a kai da ni" ganin yanda suke kallonsa yasa ya d'auke kai kamar da gaske yake, wurinsa suka isa kowacce na doka masa tata tambayar "da gaske dama duk k'iranka da nakeyi kak'i d'auka wurin budurwa kaje?" Cewar Ruffaida, Candy kuwa cewa take "yanzu zance kaje? Dama da ka dawo gida ka sake wanka da yamman nan kace zaka je d'aukota wurin wata kaje?" Dukkansu da iya gaskiyarsu suke tambayan dan zuciyarsu ta aminta da maganar da ya fad'a.

Rungumesu yayi dukka yana cewa "na isa, ina sonku dukka ku kad'ai kun isheni har k'arshen rayuwata, zuciyata duk taku ce, d'aya ta rik'e b'ari d'aya haka d'ayar b'arin zuciyar wata ta rik'e, ina wata zata samu wurin zama, ko zaku matsa mata ta samu gurbi?" Ya d'aga musu girarsa, a tare suka buge k'irjinsa cikin wasa suka mik'e suna mai yi masa dariya.

Bazai iya cewa zuciyarsa na son matansa equally ba amma yasan yana k'aunarsu kuma yana iya k'ok'arinsa dan yin adalci tsakaninsu, kowacce da nata gurbin kuma suna taimaka masa dan ya iya yin adalcin, yanzu haka ya samu gidan da ya saya wanda zasu zauna dukkansu anan Abuja dan tafiyar na yi masa wahala kullum yana hanyar Zaria da Abuja, ga Ruffaida cikin k'ank'anin lokaci ta samu nasarar mamaye dukkan jikinsa, hakan bai sa ta d'auke gurbin Candy ba dan ita ma ba wasa ba wurin tarairaya, babu abunda zai ce sai Alhamdulillah tare da neman gafara wa mahaifinsa da kuma yin alkhairi da sunansa kamar yanda ya fara gina k'aton masallaci a Zaria da sunansa, ya kuma tona borehole masu yawa wanda har a lokacin ba'a gama saura ba duk da sunan mahaifinsa da kuma fatan Allah ya kai ladar kabarinsa.

BADAK'ALA


Alk'alamin ©Maryamerhabdul


®NWA


K'arshe


Page 69


Rayuwa ta cigaba da tafiya cikin kwanciyar hankali da 'yan matsalolin da baza'a rasa ba na zaman tare, Ummu Abdoul ta samu kwanciyar hankali tare da mijinta da gudan jininta Irfaan da kuma sabon aikinta a nan Katsina, babu abunda yafi kasancewa da d'anta da kuma mijinta wanda a yanzu yake nuna tsantsar soyayyarsa gareta duk da a da ta d'and'ana makamancinsa, sai dai a yanzu tana fatar ya d'ore har zuwa k'arshen rayuwarsu. Feedoh tayi aurenta da Abduljalil wanda iyayen mijinta suka karb'eta hannu biyu suna mai farincikin samun kamilallar mace irinta matsayin matar d'ansu.

Miemiebee tana zaune k'alau da kishiyarta Lubna, bata d'auketa kishiya ba duk da wani lokacin tana kishinta matuk'a dan k'arama ce kuma yarintarta na fisgar Kamal da alama, ba wai yana nuna tafi ta ba dan iya soyayya yana nuna mata ko da yayi tafiya bini-bini ya k'irata yana tambayar lafiyarta, "akwai abinda kikeso? Kinyi azumin yau? Ki daina zama ke d'aya kinji? Kina zama da Lubna kuyi hira bazakiyi kewar mijinki ba, kuma azumin nan da kikeyi sosai zai taimakeki".

Sai yanzu take ganin wautarta na biyewa son zuciyarta na bin mazan da ba nata ba, yanzu da ta cire a ranta kuma take azumi duk lokacin da baya nan haka zalika take zama cikin mutane bata tab'a jin kewarsa sai lokaci-lokaci abu da jini da lafiya. Bata daina istigfari da neman yafiyar mahaliccinta ba, tana waya da iyayenta kuma suna yawaita yi mata nasiha da fatan alkhairi, tsakaninta da iyayen Kamal lafiya suke zaune, lokaci-lokaci sukan gaisa a waya, suna yawaita yi mata nasiha da kuma ban hak'uri da sa mata tsoron Allah ta hanyar tunatar da ita azabarsa kan bawan da yake bijire masa. Ana hakan har Allah ya albarkaceta da samun ciki, murna wurinsu ba magana, dan hatta Lubna d'okin cikin takeyi zata samu babyn rik'ewa.

Pherty ma hakan ya kasance da rayuwarta, tun bayan dawo da Miemiebee gidan Kamal ta samu yardar mijinta, sai da yayi mata doguwar nasiha sannan ya umarceta da tuba ga mahaliccinta, sosai tayi farincikin sauyin lamarin musamman da taji labarin Ibrahim ya samu wacce zai aura anan Minna, tayi hamdala babu iyaka dan Allah ya bata tsawon rai dan ta gane kurenta ta nemi yafiyarsa.

Sosai take jinjina wa mijinta, dan yayi anfani da kwalwarsa ba zuciyarsa ba wurin gyara mata zamanta ba. Tana alfahari da auren miji irinsa, tabbas ya kasance babban mutum amma hakan bai sa ya tauye mata hakk'inta ba, soyayya yake zuba mata wanda iya saninta ko saurayi sai haka, shin meh take gani a da ta kasa ganin irin k'warewarsa? She is proud of him, kuma bazata tab'a da na sanin aurensa ba dan ya cancanci soyayya da kuma k'auna daga gareta kamar yanda ya nuna mata, kowa da mijinta, in Allah ya k'addara auren budurwa da tsoho ta rungumeshi ta bashi hakk'insa kuma ta kare kanta da sab'awa mahaliccinta, ta kawar da idanunta ga ganin mazan wasu, ta k'ayatarwa kanta nata, tunda ya zama mijinta toh ya zame mata dole zama dashi dan samun aljannarta.

Batool, rayuwarta ya sauya tun bayan aurenta da mijinta, duk da wani lokaci ta kan ji k'orafi ko habaici daga wurin mutane amma hakan baiyi tasiri cikin zuciyarta bare ya hanata bautawa Allah da kuma bin dokarsa ba, tana yiwa mijinta, iyayenta da na mijinta biyayya hakan ya kawo fahimtar juna da k'auna mai shiga rai tsakaninta da mahaifiyar Mujahid wacce a da tak'i yarda da auren, sai a yanzu take tabbatar da cewa sharrin shaid'an ne kawai yayi tasiri akanta dan kuwa yarinya ce mai biyayya da sanin yakamata, Allah ya gafarta mata ya kuma sa albarka cikin zamansu.

Lubiee ta samu kanta ta samu namiji ba tare da tasha wahala mai yawa ba kamar cikinta na farko, suna zaune lafiya da juna babu tashin hankali, tsibbu da kishi k'azama kamar yanda ta gani anayi a nasu gidan tun tasowarta, tsakanin Abubakar da familynta kuma tayi k'ok'arin kawar musu da duk wani b'atanci da suka d'aura masa, a yanzu banda girmama juna da mutunci babu abinda yake shiga maras kyau, sai dai wani lokacin sukan tuna.

"Abubakar d'in nan kamar ba shi yayi miki kaza ba, kiga yanda yake rawar k'afa akanki" cewar Yayarta duk ranar da yayi wani abu na arziki gareta, sosai take jin dad'in hakan, sun d'auki Nafee kamar tasu kuma tana girmamasu kamar yanda ita ma take girmama iyayen Nafee, duk da ba wani hirar sukeyi tsakaninsu ba amma babu fad'a bare bak'ar magana ko harara, Abubakar yana matuk'ar farincikin dawo da annashuwa, jin dad'i, kwanciyar hankali da kuma soyayya cikin gidansa.

A b'angaren Mamu kuwa, tasa hankalinta sosai wurin ibadarta, tana zuwa karb'an magani na cutar da yake jikinta, tana samun kulawa sosai daga wurin 'ya'yanta da ma 'yan uwa baki d'aya, sosai take sa ido kan yaranta, kuma tana yawaita sadaka da kuma aikin alhairi dan samun lada. Bata manta mijinta ba, tana sa shi cikin addu'o'inta kuma tana yi masa karatun qur'ani tare da yin sadaka da fatan ladar ya isa garesa, babu wani k'aunar da zata nuna masa da ya wuce hakan.

Benaxir ta sauk'a lafiya ta samu d'anta, bayan ta gama arba'in tasa daru sai taje wurin iyayenta kamar yanda yayi mata alk'awarin tana haihuwa zasu je, tuntuni k'awayenta ke tambayarta ranar da tasa dan suna son suyi mata rakiya wurin danginta da iyayenta ta sanar dasu sai ta haihu, sai da ya had'a da sauran k'awayen nata suka tayashi rarrashi sannan ta amince da ta d'an k'ara wata biyu kafin nan Assabiru d'anta ya k'ara wayo.

Ba ita kad'ai ta fara shirin tafiya ba har ma da sauran k'awayenta, dan dukkansu babu wanda ya yadda zai zauna a gida. Miemiebee ce aka so hanata amma tak'i dan cikinta na wata na bakwai, sai da ta tabbatar masa babu abunda zai samu cikinta da yardar Allah sannan ya yadda, a cewarta abun alkhairi zasu je k'ullawa.

Abu sai in ba'a sa rana ba dan sai tazo, tun ana saura sati ta fara tuna masa maganar tafiyar, dan dole ya nemi hutu wurin aiki shima ya shiga shirin zuwa wurin surukansa. Lokacin da yaje ya sanar da iyayensa suma suka ce baza'ayi tafiyar nan babu su ba.

Ranar alhamis suka kama hanya, a Abuja dukka suka had'u sannan suka d'auki hanya, Benaxir, mijinta da iyayensa a mota d'aya, Ummu Abdoul, mijinta, Pherty da Lubiee da d'anta a mota d'aya, Miemiebee da Lubna tare da Kamal suna mota d'aya, duk nan dan tarairayar cikin da ke jikinta. Ruffaida da Candy sai kuma Sadiq da yake tuk'asu, Batool da Mujahid nata a mota d'aya.

Basu isa ba sai dare, hotel suka samu Mujahid ya kama musu d'akin da zasu kwana, maza d'akunansu daban haka mata nasu daban. Duk sun kwashi gajiya, bayan sun idar da sallolinsu kowacce ta samu wurin bacci suka lafe sai washe gari jumma'a zasu isa gidansu Benaxiratu.

•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•°•

K'arfe 10 yayi musu a bakin k'ofar gidan, a waje sukayi parking dukkansu suka fito banda Benaxir da ke duk'ufe cikin mota tana k'walla kamar ba ita ta nace sai anzo ba, Hussain ne yayi k'ok'arin rarrashinta sannan sauran ma suka isa wurinta dan tofa albarkacin bakinsu, sai da ta d'auki mintuna biyar sannan ta fito tana mai sharce majina.

Kamar daga sama taji muryar yayanta yana cewa "Atinuke", juyawa tayi inda taji muryarsa, kallonta ya tsaya yi dan tabbatar da abinda idanunsa ya gani. Hawayen da ya gani yana sauk'a daga idanunta had'e da yi masa murmushi yasa ya ruga a guje cikin gida yana cewa "Ga Atinuke, Atinuke is back" yana yi yana k'iran Momy da Dady. Ganin hakan yasa hankalinsu kwanciya kad'an dan yanayinsa bai nuna b'acin rai ko tsana gareta ba.

A k'ofar shiga suka had'u da momynta da sauran mutanen gida, tana ganinta ta tsaya baki bud'e tana kallonta, "Atinuke" ta k'ira sunanta hawaye na mai taruwa a idanunta, isa wurin mamanta tayi ta rungumeta sabon kuka na kufce mata, duk kuka suka sa basu ma kula da mutanen da ke tare da 'yar tasu ba. Sai da sukayi mai isarsu sannan suka shiga daga ciki.

Basu samu matsala daga iyayenta ba, da alamu sunyi kewarta kuma sunyi farincikin ganinta tare da jikansu, hakan ya sanyaya musu zuciya suka tarbeta da mutanenta hannu biyu, sai da suka nutsu aka gama gaisuwar yaushe gamo sannan ta basu hak'uri kan guduwar da tayi, a tak'aice ta basu labarin abunda ya sameta wanda da alamu hakan ya sosa ma iyayenta rai har suna ik'irarin ta zauna a gida basu da damuwa da addininta, tun daga nan Hussain yasha jinin jikinsa dan tabbas yasan in ya barta wurin iyayenta zasu samu damar dawo da ita cikinsu wanda hakan ne bazai tab'a bari ya faru ba.

Azahar suka fito dukkansu dan su tafi, dama zugan nasu bai wuce dan zuba ruwa a yayin da wutar da suke gani zai iya tashi a gidan ba, kuma Allah da ikonsa sai soyayyar da suke yiwa 'yarsu ya hanasu yi mata komai. Sosai suka so ta zauna amma Hussain yace sai wani lokaci tsoronsa d'aya kada ya barta wani abun ashsha ya shafeta ko addininta. A bakin k'ofa suka had'u da Taiwo tsohon saurayinta, k'ok'arin rungumeta yayi ta koma bayan mijinta ta lafe tana mai mamakin haukarsa, ta tabbata labari yaji ta dawo a tunaninsa ta dawo kenan zata koma masa ta auresa, Hussain ne yayi magana dashi yana mai tabbatar masa cewa Atinuke is now d mother of his child.

Cikin gidan ya k'ule yana mai k'aryata abunda yaji daga wurinsa, basu jira fitowarsa ba suka shiga motocinsu suka wuce wurin shak'atawa dan bud'e ido, a can suka yi sallah suka zagaya sai da suka gaji lik'is sannan suka zauna dukka suna raha ana hira, anan ne aka yi wa iyayen Benaxir addu'a na Allah ya ganar dasu ta dalilin Benaxir su bar duhu su shiga haske, sosai mahaifin Hussain ya jero addu'a Benaxir na zubar da hawaye tana mai fatan hakan ya kasance ko iyayenta zasu samu rahamar ubangiji.

Sai da suka kusa tafiya ta samu keb'ancewa da k'awayenta, Lubiee hugging Benaxir tayi tana cewa "am very happy sister, Allah ya tak'aita abun da haka, Allah yaga zuciyarki yasa iyayenki sun sassauta hukuncinsu akanki ba kamar yanda mukayi zato ba, fatanmu da addu'anmu Allah ya dawo dasu hanya na gaskiya". Ameen dukka suka amsa, kowaccensu ta mata murna daga k'arshe suka fara sallama dan kowaccensu washe gari da safe zasu wuce garuruwansu bazasu koma Abuja tare ba. "Sai munzo suna" cewar Benaxir tana kallon Miemiebee, Ruffaida k'unshe dariyarta tayi dan yanzu Miemiebee ta gama ce mata ta gaji da wannan ciki, ji take kamar zata mutu wani lokaci.

Ummu-Abdoul ce tace "ai masu haihuwar da yawa, duk nan kina ganinsu suna k'unshe dashi suka zo, bakiga kowacce da mijinta tazo ba dan a tarairayesu dakyau, Pherty ce kawai mijinta ya d'aga mata k'afa amma ina mai tabbatar muku ita ma na d'auke da sabon ciki". "Kai ummu abdoul mai gani har hanji, taya kika gane?" Ta fad'a tana rufe fuska, duk suka sa dariya suna mai yiwa junansu murnan samun ingantaccen rayuwa.

Alhamdulillah. Nan na kawo k'arshen littafin nan nawa mai suna badak'ala, Allah ya gafarta min kurakuran da nayi a ciki, wanda nayi daidai Allah ya bamu ladansa. 


Gaisuwa gareku mutanena:-


Mutanena na wattpad 


Ina matuk'ar k'aunarku, Allah ya bar k'auna.


Pherty tawa, Antysis, Anty Maijidda, Aicha Nourou, Sallytawa, Pheedy, Feedoh, Khadija Candy, princess, mufeen, miemiebee, mum Abdul, Ummy, da ma sauran da ban iya irga sunansu ba, mutanen Miemiebee kuna da yawa (ina sonku) kun nuna min k'auna kuma kun k'arfafa min gwiwa a tafiyar badak'alata. Addu'ata a kullum Allah ya baku abinda kukeso na alkhairi, Allah ya bar k'auna ya had'a mu cikin aljannah gaba d'aya.


Bazan ajiye alk'alamina ba sai na mik'a gaisuwata ga k'ungiyata abun alfaharina, gudunmawar da kuka bani bazai irgu ba, Allah ya biya mana buk'atunmu ya k'ara had'e kanmu ya kuma had'amu a aljannarsa. Allah ya biya ya kuma isar da sak'ona inda ya dace. Astagfirullaha wa atubu ilaih. Bissalam #ILYA #1Love #maryamerhce

Wattpad:- @Maryamerhabdul

Tags: #Benaxir #Lubiee #Batul #pherty #Rufaida #miemiebee
7245
0
3
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!