Azumi A Karkara!

Written by Maman Ja’afarPublished on 2018-12-12 18:01:15Category FictionFadakarwa ne kan azumi abubuwanda ke gyarasa da kuma abubuwanda ke batasa musamman ga mazauna karkara da ilimin addini bai gamshesu ba tags: #azumi #kurakurai #islam #addiniDuba was labarai »

*AZUMI A KARKARA*      1-ENDDaga alkalamin

MamanJa'afar✍
Matsakaicin gida ne mai d'auke da d'akuna guda uku rak, sai d'an k'aramin falo dake tsakaninsu.


Zaune suke su duka ukun har d'an k'aramin yaron hud'u kenan acikin falon cikin nishad'i da annashuwa abinsu suna kallon wani kasait d'in wa'azi na margayi Shaik Ja'afar(Allah yayi masa rahama) inda yake bayani akan hukunce-hukuncen azumi.


"Yauwa yaya dan Allah wannan karon ka barni naje k'auye mana nayi azumi a can, inyaso idan kukaje masu yawon salla kai da Aunty Kubra ba sai mu dawo tare ba?" 


Cewar y'ar matashiyar budurwar kenan Rabi'atu y'ar kimanin kusan shekaru goma sha biyar a duniya.


Asalinsu Rabi'atu su y'an wani k'auye ne da ake kira Chukuriwa wanda yake acikin Local government din Fotiskum ta cikin Jahar Yobe, K'auye ne sosai wanda ko ruwa babu a cikinsa bare kuma wuta, maganar ilimin addini dana zamani dama batasu akeyi ba


Su biyu ne rak iyayensu suka haifa daga shi Yaya Badama d'in sai kuma y'ar k'anwarsa Rabi'atu wato Auta kenan.


Badama tun tasowarsa acikin wannan k'auyen na Chukuriwa yaro ne mai tsananin son karatun addini dana zamani, hakan nema yasa yayita fafutuka ba dare ba rana da duk iya abinda zai iya har Allah ya taimakeshi yasamu zuwa Fotiskum ya shiga makarantar addini da kuma ta zamani, duk wannan a bisa taimakon wani uban gidansa ne wato Alhaji Abdullahi, domin su iyayen nasa karatunma ba wani damunsu yayi ba, domin a wannan garin da yaro yayi karatun da kar yayi duk kusan shi ta shaafa a gurinsu.


A cikin hakane har Allah ya taimaki Badama ya kammala karatunsa na boko ya kuma samu aiki daidai na rufin asiri, ya kuma yi ilimin addini shima mai zurfi domin gyaruwar lahirarsa.


Dad'in ilimin da yaji nema yasa yayiwa kansa alk'awarin indai yana raye y'ar k'anwarsa tilo bazata zauna tayi rayuwar jahilci a wannan k'auye ba, wannan dalilin nema yasa ya d'aukota ya dawo da ita birni gabansa cikin garin Fotiskum d'in kenan inda yake da zama shida iyalansa domin ci gaba da rik'onta da duk wani abinda ya shafi iliminta


Amma dukda haka wannan bai hanasu ziyartar y'an'uwa da abokan arziki acan k'auyen lokaci zuwa lokaci ba.


"Ni kam da zakibi ta tawa Rabi'atu da hak'uri kikayi da tafiyar nan inyaso ana saura kwana biyu salla sai muje mu duka harda Khalifa muyo masu sallar, d'aya ga salla kuma ko biyu ga salla sai mu dawo, ko ba haka ba Maman Khalifa?" Ya fad'a tare da duban fuskar matar tasa


Murmushin k'asaita Kubra tayi, irin murmushin nan da yake fizgar zuciyar wanda akayiwa shi"To Abban Khalifa niko mi zance maku? Ai kunfi kusa, duk wanda na goyi bayansa acikinku nan bada jimawa ba zai gwaleni ya bani kunya saboda haka wannan karon babu ruwana a ciki"


"Ni bawai zuwan naki ne nak'i ba, a'a, abin nufina azumi a cikin birninma ya aka k'are da tsadar rayuwa bare kuma a karka? D'an ruwan sanyin nan ma na Tulu wata ran sai kiga ya gagareki"


Dai dai taga alamun ba amincewa da maganar tafiyar tata zaiyi ba mik'ewa tayi tare da zumburo baki gami da y'an dire direnta irin na shagwa6a66un yara


"Nidai wallahi gaskiya Yaya ban yadda ba, rabona fa da nayi azumi a gaban Adda har na manta, nidai dan Allah ka barni naje"


"Kaiko Abban Khalifa ka barta ta tafin mana tunda ta nace, k'aramar salla cefa ba babba ba bare ko kace ta tsaya kodan ta kama mani wasu ayyukan"


"Amma inda tana nan d'in Kubra aida zata taimaka maki wajen girke-girken azumi ko?"


"Dan dai girkin da bai wuce cikina da naka ba zan iya, barta ta tafin kawai danko ta zauna anan din ba wani ganin farin cikinta zamuyi yanda mukeso ba tunda tasawa ranta tafiyar"


"To ai shikenan" Ya fad'a tare da juyawa inda Rabi'atun take tsaye tanata faman ku'nk'uni


"To y'ar anaci Sai ki shirya ranar.... na rakaki tunda kinfi son yin azumi a k'auye"


Murmushin murna tayi, tana mai dubansa tace"Yaya ranar...dai ko? kasanfa ranar.... d'aya ga wata kenan ni kuma nafison har na farin ma a d'auka dani ina acan, saboda wannan Kwad'on zogalen wanda Adda keyi mana a azumi ka tunasa?" Ta fad'a tana mai dubansa sai kace wata k'aramar yarinya


Dariya sukayi su duka kana daga bisani Kubra ta dubeta"Kedama akayiwa alfarma za'a kaiki har wani saka rana kikeyi? To tunda dai na fahimci kinfison rayuwar k'auye akan ta birni idan kika gama karatunki sai mu mayar dake can ayi maki aure, kinga shikenan gaki ga Addarki ko?"


Da gudu Rabi'atu ta wuce d'akin da aka ware mata a gidan tana dariya, ga dukkan alamu kunyar maganar auren ne takeji.


******


*RANAR*....


Tun a bakin k'ofar gida yara suka fara cincirindon zuwa kallonsu, daga cikin yaran nema aka samu way'anda suka ruga da gudu domin fad'owa su Adda zuwan su Badama d'in.


Y'ar dattijuwar da batafi kimanin shekaru arba'in da biyar ba zuwa hamsin ta fito a k'ofar gidan domin tarbar yaran nata cikin d'oki


"Maraba marhabun lale da bak'in birni" Ta fad'a tare da kamo hannun Autar tata suna masu farin cikin ganin juna gaba d'ayansu.


Bayan sun gaisa ne ya gabatar masu da tsarabar da ya kawo masu kana ya dubi mahaifiyar tasa"Adda yanzufa nakeson komawa dan kar dare yayi mani a hanya"


"komawa kuma tun yanzu Badama? kabari mana ko zuwa gobe ne sai ka tafi, gashima ko gaisawa da baban naku baka tsaya kunyi ba"


"Kai Adda kwa gaida mani shi kawai idan ya dawo, saboda banason tafsir d'in Malam Sanusi ko d'aya ya wuceni, shiyasa nake sauri sauri na isa gida kamin isha tunda tafsir d'in bayan isha ake farasa"


Ta6e baki tayi kana cikin alamu na nuna ko in kula tace "Kai dai kasani da wannnan y'an k'ak'ale-k'ak'alen naka na y'an izala"


Murmushi kawai yayi domin tun ba yau ba yasan mahaifiyar tasa batada abokin gaban da ya wuce d'an izala


"Amma dai ai ka tsaya ko ruwa kasha ko?"


"Wane irin ruwa Adda ko kin manta yau muka fara azumi ne?"


"Ku acan birni ba, masu azumin bindiga, ai mu a nan sai munga Wata k'iri-k'iri da idanuwanmu kana muke d'auka"


Cikin mamaki ya dube uwar tasa"Yanzu Adda duk faman 6a6atun da akai tayi a gidan rediyoyi tako ina ana fad'ar cewar sarkin musulmi yaga wata duk ku anan baku ji ba?"


"Ai kunji matsalarku ku y'an izala, ni tunda uwatama ta haifeni nata6a jin wani ganin wata a cikin rediyo? kudai da kuka d'orawa kanku kuje kuyin kayanku Allah ya taimaka"


"To amma Adda idan kuma watan ya 6uya har nanda sati guda yak'i fitowa fa? Dukda haka jiranshi zakuyi tayi har sai kun ganshi ya 6ullo?"


Cikin 6acin rai ta dubesa tana mai hararsa tamkar k'wayar idanuwanta zasu fad'o"Yau rashin kunyar taka ta y'an izalan ta motsa kenan ko?"


"Adda kiyi hak'uri ba maganar rashin kunya bace amma ko Annabi(S.A.W)da mukeyin koyi dashi basai yaga wata da idanuwanshi ba yake d'aukar azumi, indai akace masa angani kuma ya yadda dashi wanda ya kawo mashi labarin ganin watan yakan ba sauran Sahabbai umarni ne kawai da su d'auka, shiyasama gudun irin wannan abin naku acikin wani hadisi Annabi(S.A.W) yake cewa


Idan kun ganshi(Watan kenan) ku d'auka(azumi) idan kuma kun ganshi ku ajiye, (Kusha ruwa)saboda yasan akwai irinku masu Musu yaci gaba da cewa


Idan kuma baku ganshi ba ya 6uya agareku to ku k'addara kwanakinsa(Ku lissafa kwana talatin daidai kenan)


"To yaufa Adda muna d'aya ga wata, na tabbata da bashi kike bin wani yace maki kizo k'arshen wata ki kar6a wata na cika kwana talatin daidai zaki dirar masa, amma dayake ibadar Allah ce kun tsaya kuna wani kame-kame kuna wani cewa sai kun gani, y'ar yunwar kwana talatin d'inma da zaku samu lada a cikinta kun tsaya sai wani kwane-kwane...


Wata uwar ashar ta d'auko ta lailayo masa tare da rarumo bakin wutar dake kusa da ita


Ba azziki ya runtuma a guje ya bar gidan, dayake dama indai suka had'u shida Adda ba makawa sai sunyi wannan musun a tsakaninsu sai kace jika da kaka.


Ita dai Rabi'atu dama tun shigowarsu ta wuce 6angarensu Inna Talatu wato matar K'anin babanta kenan.


******


*Bayan kwana biyu*


"Inna akwai sauran kokonda aka ragewa su Janaidu kuwa insha?"Cewar Ladidi kenan y'ar kimanin shekaru goma sha hud'u wacce ta kasance y'a agun Inna Talatun


"Koko kuma Ladidi? Ba tare mukayi sahur dake ba da suba ne?" Cewar Rabi'atu kenan wacce ke zaune a cikin d'akin nasu


Harar Rabi'atun tayi"Bakiga jinida ke zuba a hannuna ba ne zakiyi mani wani maganar azumi, gurin yanke farce fa na yanke hannun nawa kinga ai ba maganar azumi tunda ya kare ko?"


Murmushi Rabi'atun tayi kana ta kamo hannun Ladidin ta zaunar da ita gefen da take zaune


"Ke baiwar Allah da Malamai sukace idan har jini ya fita a jikinka azuminka ya kare, bafa irin wannan jinin suke nufi ba, a'a suna nufin jinin haila ne wanda yake zuwarma mata duk k'arshen wata wata ko kuma jinin haihuwa, amma dan wannan jinin na jin ciwo ai baya karya azumi, ke in fad'a maki ko kanki za'a gutsire daga wuyanki da wuk'a indai kina raye to azuminki na nan bai kare ba"


Dariya sukayi su duka harda maihaifiyar Ladidin dake bakin k'ofar d'aki tana saurarensu


"Haba Rabi'atu kin ta6a jin inda aka yanke Kan mutum kuma ya rayu?"Cewar Ladidin kenan


Gimtse dariyar Rabi'atu tayi kana ta dubi Ladidin"Yanzu kin fahimci cewa zubar jinin ciwo baya karya azumi ko?"


"Ai Rabi'atu bama Ladidi kad'ai ba harni nan na k'aru da wannan bayanin naki" Cewar Mahaifiyar Ladidin kenan wacce take zaune a kutungar k'ofar d'aki tana jiyo firar tasu sama-sama


Murmushi Rabi'atun tayi "Yauwa Inna haka nakeso itama Adda ta dinga ganewa da wuri kamar yanda kike ganewa"


"Yauwa Rabi'atu wai ni niyar Azumin nawama nakeso ki gyara mani ko dai dai nakeyi ko kuwa?"


Dariya Rabi'atu tayi harda k'yak'yatawa"Inna azumin ma har wata niya akeyi masa ne?"


Dak'uwa tayi mata"Kinci gidanku, kin ta6a ganin inda akayi ibada batare da wani karatu ba? Nidai koya mani idan zaki koya mani kawai"Cikin dariyar tace"To shiken naji fad'a mani yanda kikeyi dan naji dad'in gyara maki d'in"


"Yauwa kokefa? Yanzu kikayi magana"


"Kina jina?" ta tambaya tare da duban Rabi'atun


"Ina jinki Innarmu" Ta amsa mata, amma dukda haka murmushin bai kau a fuskarta ba


"Nawaitu ma faradallahu alaina min saumir ramadana, talatina yauman, au tis'a wa ishirina yauman, idan kuma ramuwa zakayi akan k'ara da Nawaitu ada'a....


Tun kamin ta k'arasa karatun nata Rabi'atu keta tuntsira dariya harda hawaye har saida ta fara bawa Innar haushima tukunna ta dakata


"Wannan irin dogon karatu haka inna.."Amma dai tsaya kiji maganar gaskiya babu wata niya da akeyiwa azumi ko kuma salla da dai sauransu, Allah ne zakiyiwa ibadar nan kuma yafiki sanin abinda ke cikin ranki, kinga kenan babu buk'atar sai kin tunasar dashi, kema kiyi tunani mana Inna, wanda yafika sanin komai a tare dakai taya kuma zai jira sai har sai ka fad'a masa abinda kake da niyar yi? Idan akayi haka kuma ai anzo da wata bidi'a ta daban ko?"


Shuru Inna Talatun tayi na d'an wani lokaci, ga dukkan alamu nazari takeyi


Can dai ta nisa"Kumafa yarinyar nan maganarki haka take, inko hakane gaskiya ana kwa6a sosai a cikin karkarar nan tamu"


"Karki damu Inna sannu ilimi na tafiya insha Allahu wata rana zaki ganshi yazo har nan K'auyen"


"Sannan mun mutu da jahilcinmu ba?" ta fad'a a tak'aice


"A'a Inna ai ba'a fidda rai da samun rahamar Ubangiji kunada rankuma hakan zai faru insha Allahu"


*****


*Bayan sati d'aya*


Rabi'atu na zaune a tsakar gida Adda tazo hura wuta a murhu a dab da inda take zaunen


"Yayi yayi, bubu bubu, mala'ikun gindin murhu ku gafara zan wura wuta"


Dariya Rabi'atu taci gaba dayi harda k'yak'yatawa, acikin dariyar take nuna tsohuwar da yatsa"Yanzu Adda wannan balankocen kuma na minene?"


"Na uwarki ne, kuda ba'a yi maku daidai, mutum baiyi addu'a ba kuce masa komai idan zaiyi Annabi yace sai yayi azkar, kuma mutum yayi d'inma bai tsira ba...


"Inna wai nan addu'ar hura wuta ce kikayi?" Tana dariyar take magana


"Wallahi Inna duk wanda yace maku ana yin wata addu'a ta hura wuta wacce ta wuce bisimilla k'arya yakeyi maku, kawai sai tsofi sun kwashi tuwonsu sun k'oshi suyita jero maku balankwace suna ce maku addu'ar kaza ce data kaza"


Da k'yar dai Rabi'atu ta samu uwar ta fahimceta, harma ta d'an gyaggyara mata wasu abubuwan(Lokaci bazai bari ba amma ku tara a litattafaina na gaba) A zuciyarta tace Alhamdulillahi azumin Karkara yayi amfani koba komai na d'an gyaggyara masu wasu abubuwan.


*********


*Bayan kwana biyar*


"Baba yau baka azumi ne naga kasha ruwa a tsakar ranar nan?"


"Wallahi Rabi'atu wani k'amshin turare ne naji ya tada mani zuciya shine har amai ya kubce mani, kuma kinga tunda har aka riga akayi amai ai azumi ya kare kenan ko?"


Cikin damuwa da wannan jahilcin da mutanen karkararsu suke fama dashi ta Jijjiga kai


"Baba Amaifa baya karya azumi saidai idan kana yinsa ne kuma yana komawa cikin cikin ka, bara dai na lissafo maka abubuwanda ke karya azumi koba komai kaima ka k'arau harma ka fad'awa wasu suma su karu"


"Ina jinki y'ar albarka"Ya fad'a yayinda ya ajiye kofin ruwan a gefe guda yaci gaba da fuskantar ta


1Yin jima'i 2 fitar da maniyyi adalilin sunbata ko shafa ko istimna'i, amma ba laifi idan mafarki kayi 3 Jinin haila kona haihuwa(Amma na ciwo baya karya azumi)

4 Ci ko sha da gangan amma idan acikin mantuwa ne babu laifi Allah ne ya ciyar da kai

4 Fitar da jini ta hanyar Qaho, ko bayar da jini domin agaji, shima duk yana karya azumi (Amma dan jin ciwo baya karya azumi ko ha6o da sauransu)

5 Yin amai da gangan (Amma idan wata k'ura ta shiga mak'ogoronka ko wani kamshinda bakaso ko makamancin haka har kayi amai bada gangan ba shima azuminka na nan)


"Yin tunani har ka fitar da maniyyi, ko mafarki, ko amai bada gangan ba, duk wannan baya karya azumi, Ina fatan Abbana ya fahimceni?"


"Allahu akubar"Ya fad'a tare da gyara zamansa


"Yanzu Rabi'atu duk wannan dogon karatun a ina kika sameshi haka?"


Cikin Murmushin jin dad'in anyabeta tace"Baba a makarantar mu ta islamiyya mana"


"Rabi'atu Allah yayi miki Albarka, ya albarkaci rayuwarki, su kuma malamanki Ubangiji Allah ya saka masu da mafificin Alkhairinsa domin kin wayar min da kai sosai ta yanda nima nake jin har zan iya fad'akar da wasu nasamu lada, nima insha Allahu nan bada dad'ewa ba ana gama waccen makarantar islamiyyar ta bakin tasha nine farkon wanda zai fara shigarta, domin sai yanzu na k'ara fahimtar cewa babu abinda yakai sanin hanyar da zaka gyar aljannarka dad'i"


"Hakane kam Baba, shiyasama Annabi(S.A.W)Yace Man yuridullahu bihi khairan yufaqqihuhu fiddineen"


"Kya jawo aya kiyi mani shuru, ai sai ki fassara mani naji ko Auta?"


Dariya tayi kana tace"Baba ba aya bace hadisi ne, ma'ana duk wanda Allah ya nufa da Alkhairi sai ya sanar dashi addini"


"Kwarai kuwa hakane y'ar nan" Ya fad'a tare da Jijjiga kai alamar gamsuwa.


K'arshe


Tammat bihamdullah


Da wannan ni Maman Ja'afar nake cewa


*Ahlan wa sahlan bi sharillaziy unzila fihil qur'an, hudan linnasi wa bayyinatin minal huda walfurqan, faman shahida minkumush-shahara falyasum, waman kana maridan au ala safarin fa'iddatun min ayyamin ukra, yuridullahu bikumul yusra wala yuridu bikumul usra*.


_Ina rokon Allah yasa muna daga cikin bayinsa wad'anda zai yiwa rahama, gafara, sana kuma ya iyantamu daga wuta zuwa aljanna_


Bara nayi amfani da wannan damar na bawa masoyana hak'uri masu jiran litattafaina, kuyi hakuri dan Allah ku kara yi mani hak'uri insha nan bada dad'ewa ba zanzo maku da SUNE SILA da kuma Y'AR GHANA saidai bansan wanda zai riga wani ba daga cikinsu


Ina masu tambayar ci gaban SANNU SANNU? kuyi mani hak'uri ba book bane ta'aziyya ce kawai na zauna na tsarata zuwa ga sirikina Kakansu Ja'afar, kuma labarin a gaske ya faru domin d'an wani gutsire ne na gutsuro maku daga cikin tarihin rayuwata.Asha azumi lafiya, Allah ya maimaita mana na bad'in bad'ad'a.  *NICE TAKU*

*MAMAN JA'AFAR*

 +966592551785

Tags: #azumi #kurakurai #islam #addini
558
0
2
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!