Alaka

Written by Aisha MaduPublished on 2018-12-12 18:16:27Category Fiction "A gaskiya ina matuk'ar alfahari dake, Kinba marad'a kunya ina jin dad'in haka kici gaba kada a ta'ba jinmu a rana." tags: #alaka #soyayya #jinkaiDuba was labarai »

*ALAKA*

     *BY*  

 *EASHA MD*


   ​A'UZU BILLAHI MINASH SHAIDANIR RAJIM,​

​BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM, NA GODE MA ALLAH DA YA NUFENI DA SAKE WANI LABARIN, ALLAH YASA IN FARA LAFIYA GAMI DA GAMAWA LAFIYA.​


​EASHA NOVEL GROUP INA ALFAHARI DAKU, SABODA YANDA KUKE BANI HADIN KAI, DA NUNA KULAWARKU AKAINA. ALLAH YABAR KAUNA.​


1⃣to2⃣


Yarinya ce da bata wuce shekara takwas ba, Ita da 'Yar uwarta a mota, ta kalli wanda ke tukasu, 

Tace bala kada ka shiga dani cikin gida, ka saukeni a kofar gida, 


Wurin yaya sultan zani, 

Yace to' Yar gidan yaya sultan an gama, 

Ya tsaida mota, Yaya fatima ta kalleta, tace wai ke baki da hankali ne, da ba zaki iya zama gidanku ba, lubabatu tace kai yaya fatima, bala yace kin santa da sultan sai Allah, Fatima tace to duka yaushe rabonta da gida,. 


Kana gani fa tun safe muka bar gidan nan, 

Yanzu karfe nawa? 6:00pm.


Ba zata shiga gidansu ba, lubabatu ta kalleta, tace kema de yaya fatima, nide kinga tafiyata. 


Yana tsaida mota ta fice, 

Su kuma suka shiga cikin gidan, 

Sai mita take, bala yace kinfa san halinta, 

Tun bata kai haka ba, 

Bata shigowa gidan nan, sai taje taga yaya sultan. 


Fatima na isa daki, Fatima na shiga ciki, ta zauna kan kujera, tace Ammi na gaji, 


Ammi tace dama ai karatu da wahala, ina lubabatu fa? 

Tace tana can ta wuce gidan daddy, Wai Ammi haka za a rinka kyaleta, Ammi tace to fatima y kike so nayi, can ma ai gida ne, 


Kuma Yara ke janta gidan, Kin san can ne da abokan wasa. Naji amma yanda ta wuni a school ya kamata ace ta fara zuwa gida kafin ta shiga can, Ammi tace kefa sheda ce, ta hanata fita da nake, 

Kina gani ta kofar dake sadaka da gidan, har key nasa, da Bala'i kina gani seda na bude. 


Duka ai duk daya ne, tunda yayan babanta ne. 

Inda sabo ai mun saba da halinta, 

Fatima tayi shiru can tace shikenan Ammi, bari na shiga ciki, 

Ta mike tayi dakinsu, 

  Itako Suhaima tana fiya, dakinsu yaya sultan ta wuce, yana ganinta, ya mike daga kwancen da yake, tare da fara'arshi, Yace kin dawo? Ta taga mashi kai, ta samu kusa dashi ta zauna, tace yayana na kawo maka tsaraba, Yace da gaske? 

Tace eh, tasa hannunta cikin sch bag dinta. 

Tace rufe idonka, Sannan in baka, 

Yace au sai na rufe ido? Tace eh, yana daria yace bari na rufe, ya rufe, tace kada fa ka bude sai nace ka bude, Yace to, saida ta tabbatar ya rufe, Sannan ta fito da chocolate din, ta riko hannunshi, ta samashi, tace to bude, 

Ya bude, Gami da cewa wow, wannan chocolate haka, Harda tambarin i miss you a jiki, tace eh mana, gobe ma na i love you zan kawo maka, suka yi daria. 

Yaya aliyu dake zaune, yana jinsu, yaja tsaki, Tare da mikewa, 

Yace haka kawai ka biye ma yarinya, sai faman shirme kuke, 

Ya fita, 

Ta bishi da kallo, ta koma kan yaya sultan, tace kawo na bude maka, ya mika mata yana daria, ta bude ta mika mashi, ya amsa, ya kai bakinshi, ya balla, ya fara ci, ya lumshe idonshi gami da budewa, 

Yace akwai dadi, tace da gaske? Yace kwarai kuwa, Tayi daria, can kuma, ta canza fuskanta, tace yaya sultan, meyasa yaya aliyu baya sona? 

Idan ya ganni tare dakai, sai yayi ta fada, yana fushi, koda yana daria, 

Idan ya ganni, sai ya bata fuska, ya riketa, Yace yana sonki mana, Kin taba ganin damuwa yana kin damuwa? 

  Idonta ya kada, Kamar za tayi kuka, 

Tace to idan yana sona meyasa yake min haka? 

Oh na gane, kenan yana jin haushin muna tare kenan. 

Yaga bama fada, Yaya sultan yace mata eh mana, 

TO ko inde hakane kome kamin na dena bata rai, shiyasa idan yaga ina fushi, yayi ta daria, to na ganoshi, 

  Yaya sultan yana daria yace to kinga sai ki dena kuka da fushi, 

Tace kaga sai yayi ta ganinmu cikin farin ciki, 

Shi kuma yayi ta bakin ciki,ta yi daria, irin na taga yanda zata muzguna ma yaya aliyu, ta mika mashi hannu, suka kashe, 

daria ya kara yi, Yace to yanzu tashi kije ki cire uniform dinki ki canza kaya, kici abinci ko, tace to yayan lubna baby, ta fita, ya bita da kallo yana daria. 

  Ta fita tana murna, ta idasa dakin da gudu, bata ankara ba, Ta bige mutum, plate din abinci dake hannunshi ya fadi kasa, abincin ya zube, ya rukota tare da murde mata kunne, Yace ke wace irin mara natsuwa ce? 

Baki tafiya a hankali, ya kara murde kunnen, 

Ta saki kara, Tare da fadin wayyo Allah ze balla min kunne, harda sakin fitsari, da sauri mommy da yaya sultan suka fito, mommy ta kalleshi, tace haba aliyu, yanzu me kaji a jikin yarinyar nan, da kake mata mugunta? 

Ya kara tamke fuska, Yace mommy kalli fa abinda tayi, mommy tajata suka wuce ciki, tana lallashinta, 

Yaya sultan ya bishi da kallo yace haba bros, yanzu kaga kankantar yarinyar nan, kallon baka kaunarta fa take maka, saboda abinda kake mata, 

Yace wai ya za ayi yarinya bata da natsuwa ba za a gyara mata ba, sai a saketa sakaka, ai da yake ma ba ita kadai nake mawa ba harda yaran gidan, 

Ka sani bana tolerating nonsense. Ya wuce ya barshi nan, shi kuma ya wuce dakin mommy, ya tadda tasa lubabatu tayi wanka, tana sa kaya sai ajiyar zuciya take, tace ni gida ma zan tafi ba zan kara shigowa ba, da nasan su zainab basu dawo ba da ban shigo ba, sultan yace haba sis, kiyi hakuri, ko kina so yaci gaba da daria idan yaga muna fada? 

Ta girgiza kai, Yace to kiyi hakuri ko, ya kamo hannunta, Yace muje ko, 

Suka Fita, da kanshi ya rinka bata abinci a baki, har ta koshi. 

Ta mike tace bari naje gida. 

Da kanshi ya rakata har gida.

Tana shiga cikin daki, kaninta mai suna affan da bai wuce shekara biyu ba, sai murna yake, yana daria,ya taho wurinta, yana miko mata hannu, ta karaso wurinshi ta daukeshi, ammi ta kalleta, tace ke kuma lafia zaki shigo ma mutane daki, ko sallama babu, ta zauna, duk affan yana hannunta, 

Tace bakomai, 

  Ammi tace to me aka maki? Ta zumburo baki ba tare da tace komai ba, 

Yaya fatima tace sena tashi na bige wannan bakin da kika turoshi gaba, ta mike rike da affan a hannunta ta wuce, 

Ammi tace lubabatu halinki sai ke, Yaya fatima tace yanzu fa Ammi idan aka ce maki ta ma yaya aliyu wani abu ne, Ba a musu, shi kuma kin sanshi, ba hakuri ne dashi ba, 

  Ammi tace ita de ta sani, tashi kije ki mata magana,ta tashi tayi sallah, nima bari in shiga ciki inyi, 

Suka mike gaba dayansu, Bayan tayi alwala, tace lubabatu tashi ki wuce kiyi alwala, 

Ta aje affan ta shiga tayo ta fito, Ta gama gurgura sallanta, ta mike ta fice, 

Tayi waje, Ta hade da 'yan layi, suka fara wasa, ba tare da ta waiwayi gida ba,. 

Cikin wasan ta kallesu tace kuzo muyi barkono barkono, eh yauwa ayi, 

Suka fara rera wakan barkono barkono, tashi yana fure yana 'ya'ya, tashi, waze zo da ruwa tashi, inna zo da ruwa, tashi baba zo da ruwa tashi, uwarki ta mutu ta mutu can ubanki ya mutu ya mutu can, dani da mijin nawa, me bani silan maggi, za a kashe min shi, ba za a kashe min ba, cirin ci rincici, kunga rawar katon banza ari, wani mai suna jamilu dake zaune a kofar gidansu yana wanki, ya watso masu ruwan wankin, Yace kai nine katon banzan? Ya bisu da gudu suka ruga, gami da shigewa gidansu kawarsu dake kusa dasu. 

  Suna daria, mutanan gidan suka ce ku kuma lafia? 

Lubabatu tace wannan mahaukacin jamilun ne ya biyomu, daga muna wasa, Yace wai dashi mukeyi, 

Iya tace ai kune baku jin magana. 

Yanzu ai sai ku tashi wasa, kowa yayi gidansu ko, 

Lubabatu tace gida nake so na tafi amma tsoron fita nake, bari na leka naga yana nan, 

Tana fita ta ganshi tsaye kofar gidan, 

Da gudu ta dawo, tace aikuwa yana nan. 

Iya tace kai jamilu ba hankali, bari naje na bashi hakuri, matan gidan suka ce ai da kin kyaleshi, tunda basu jin magana, iya tace a'a, ta fito suna biye da ita, yayo kansu. 

Iya tace a'a jamilu tsaya, me suka maka? 

Yace wai yaran nan dan sun raina min wayau, suke wata waka, Wai kunga rawar katon banza, 

Dama ga wadda ta bada shawarar suyi wakan, ya nuna lubabatu.

Yace ke ko wallahi sai na balla maki kafan baya, idan baki wasa ba, inga abinda za ayi. 

Iya tace to dan suna waka, sai akace dakai suke yi, yanzu kayi hakuri ka kyalesu, haba dan jamilu, 

Yace to naji, amma daga yau kada in kara ganin kamar wata yarinya tazo wasa nan. 

Iya tace to sunji duk ku wuce gidajanku. 

Da Gudu lubabatu ta fice, tayi gida, 

Ta fada daki sai haki take yi, amma kalleta ranta a bace, ta jawota, tace daga ina kike? 

Cikin zare ido tace ammi ina fa wurin yaya sultan, ammi tace karya kike, Ai na kira sultan yace baki gidan. 

Nace daga ina kike? Ai naso kafin ki shigo gidan nan babanki ya dawo. 

Bana hanaki biye ma yaran unguwar nan ba, meyasa kika rainani? 

Dan kinga ina barinki ki fita, ta kai mata duka, ta kara kai mata duka. 

Ta wage baki ta fara kuka. 

Ammi tace au dan wannan dukan da na miki, zaki bare min baki,to bari na miki wanda zakiyi da hujja, ta kalli yaya fatima, tace fatima miko min dorina, 

Lubabatu ta mike da gudu, ta shige dakinsu, ta turo harda sa key. 

Ammi tace da karfi, ai da kin tsaya, mara kunya, 

Kuma Ki tabbatar kinyi sallah, dan nasan baki yi ba. 

Haka tayi sallan tana kuka. 

  Bayan ta idar tana bude dakin, nan ta kwanta barci ya dauketa. 

Da asuba yaya fatima ta fara tadata, takai ma fatima duka, tace ni ki kyaleni, banfa koshi da barcin ba. 

Fatima ta kara kai mata duka, ta mike, ta fara daka mata tsawa, Wai ke yaya fatima miye haka? Mutum na barcinshi, zaki dameshi. 

Ammi ta shigo dakin, tace hayaniyar me nake ji? Fatima tace dan na tada ta ta tashi tayi sallah,

Shine take min fada, Ammi tace shine baki make bakinta ba, yayi jini, 

Ta jawota, ta kai mata duka, tace fatimar tsararki ce? Tambayarki nake, 

Ta girgiza kai tana hawaye, tace Ammi nace ta dena tadani da asuba bata ji, Ammi tace to bata isa ta tadaki bane? Wuce kiyi alwala, 

Ta shiga toilet tayo alwala, duk Ammi na dakin rike da carbi tana ja, 

Har ta idar da sallah, 

Tace to wuce kiyi wanka yanzun nan ki shirin school, ta fara hawaye, tace Ammi barcin be isheni ba. 

Ta fashe da kuka, ni wallahi bana son makarantar nan, ba za a kyale mutum ya huta ba, idan na tafi yanzu, nida gida sai 6 na yamma, 

Ni na hakura da karatun, ta fara ihu.

Abba ya shigo dakin, Yace lafia? Ammi tace wannan birkakkar yarinyarce, 

Daga tashinta, ta fitini gida da hayaniya,wai ba zata makaranta ba. 

Cikin tsoratar da ita, yace au ba zaki ba? 

Ina bulalan nan? 

Da sauri ta fada toilet, Yace da kin tsaya, da kinga yanda zanyi dake. 

Tunda baki son karatun, Ai sai in kaiki almajiranci. 

Saida suka ji ta fara wankan, Sannan suka bar dakin, tana watsa ruwan a jikinta, tace ai ba zanyi wankan ba, Sede in juye ruwan a jikina, da ta gaji da watsawa, ta zubar da sauran ruwan, 

Ta saki sauran na zafin, gashi fatima na jiranta ta fito, taki fitowa. 

Saida ta tabbatar ta gama sakin na zafin ya kare, Sannan ta kashe fanfon ta fito, sai faman harare harare take, Yaya fatima bata tanka mata ba. 

Ta shiga toilet, Ta kunna ruwan zafi, taji ba zafi, ta fito, ba tare da ta kalleta ba, Ta fice dakin, Tayi wurin Ammi, tace Ammi kinga ta kwarar da ruwan zafin, Ammi tace kai wannan yarinya. 

  Abba yace kyaleta, shiga toilet din mamanku ki dibi wani, kije kiyi. 

Ta wuce ta tara ta koma dakinsu.

Ta kalli lubabatu da duk ta saki kayanta a kasa, duk ta bata dakin, 

Tace ki tabbatar kin kwashe kayan. 

Taci gaba da shirinta, ba tare da ta tanka mata ba. 

Ammi da suke tare da abba, tace fatima ta nuna sanyi a kan lubabatu, shiyasa ta rainata, amma bari zan samu rana daya, in bata bulala ta zaneta. 

Abba yace ai ni na rasa irin halinta. 

Ammi tace biye ma yaran unguwa, 

Ba zata zauna cikin 'yanuwanta ba. 

Abba yace amma nasan maganinta, 

Bayan sun gama shiryawa, suka fito dan yima iyayensu sallama, 

Abba ya kalli lubabatu yace idan na Kara ganinki a waje kina wasa, ko naji labari, zaki ga abinda zan maki. 

Duk sanda ta fita ku kirani ku fada min,. 

Har wurin sultan dinma sai na hanaki zuwa. 

Fitinanna, ta suri lunch box dinta, fuskarta a daure, ta zumburo bakin nan waje, Yaya fatima tace sai mun dawo. 

Suka fice suka tafi. Har suka isa ba wanda ta tanka mawa a cikin motar.


Alhaji sharif daddy, da alh munnir, wa da kani ne, sai aunty jamila kanwarsu, 

Asalin iyayensu yan garin zaria ne. 

Sai de mahaifinsu tashin kaduna ne. 

Sakamakon aikin gwamnati da yayi a nan. 

Alh sharif shine babba, 

Su uku kadai Allah yaba iyayensu,

Yanzu haka gaba daya iyayen nasu sun rasu, Sede suje zaria ganin dangin iyayen nasu. 

Sun taso cikin so da kaunar junansu, 

Sanadin haka suka zauna unguwa daya, gida kusa da gida, a unguwar shanu dake kaduna. 

Daddy yanzu yana rike da mukamin commissioner na ilimi a garin kaduna. 

Yanzu haka yana da matarshi daya mai suna maryam wadda suke kira da mommy, itama asalinta 'yar cikin garin zaria ce. sai 'ya' yanshi, aliyu da sultan 'yan biyu ne, 

Sai salma, khadija, ibrahim suna kiranshi da Khalifa, saboda sunan mahaifin su daddy, sai zainab. 

Tsakanin su yaya sultan da yaran akwai dan tazara a tsakaninsu, dan ko salma sun bata shekara takwas, daga nan ne haihuwar ta bude ba tare da tseraya da yawa ba. 

Abba kuwa yana da 'ya' ya uku fatima, lubabatu, sai auta Abubakar suna kiranshi da affan, saboda sunan mahaifin ammi,Sun hadu da Ammi ne a garin zaria, inda takan zo hutu gidan yayan babanta dake zaune a nan zaria, saide ita suna zaune a maiduguri. abba da yanzu yake rike da mukamin perm sec, (parmanent secretary) na ministry of finance, Dake nan kaduna. 

Sai aunty jamila, mai Yara biyu, mansir da Aisha wadda suke kira da ummie sunan maihaifiyarsu. Inda ita kuma doctor ce dake aiki a ahmadu bello teaching hospital dake zaria, Sede nan kaduna take aure unguwan rimi, tana barin yaranta wurin kishiyarta, tunda zama suke na amana, tunda an hada wayayyu 'yan boko, kowa harkar gabanshi yake, shiyasa basu da lokacin kishi, 


  Gaba daya sun taso da son junansu, lubabatu ta saba da yaya sultan, saboda yanda yake janta a jiki, saboda shi mai son Yara ne, inda yasha ban ban da yaya aliyu, baya son hayaniya da takura, 

Ita kuma lubabatu da ta gano haka yake, 

Sai ta rinka takura mashi, shiyasa take shan wahalanshi,lubabatu ta taso, bata iya zama cikin 'yanuwanta tayi wasa, inde bata tare da sultan, to tana can waje wurin yaran layi, tana biye masu, iyayenta basu so, amma ina ba zata zauna cikin gida ba, saboda wasa ya riga yabi jikinta, Tun tana karama,bata wuce shekara uku ba, ta haddace gidajan layin, duk gidan da ta shiga, akwai kwanonta na abinci, Ammi tayi dukan har ta gaji ta kyaleta, wasan dare sai ta fita tayi da 'yan layi, inda kowane' yanuwanta suna cikin gida, amma ita ba zata zauna ba, sai taga dama, idan ba ayi wasa ba ma, to ba za a tashi lafia da ita ba. 

  Wannan kenan. 

   ***********

Sun dawo daga makaranta, wurin kan dogo, motar ta tsaya, taki tafiya, bala ya kalli fatima, Yace kifa gani, motar taki tashi, fatima tace to bari mu idasa gidan, 

Tunda mun kawo, suka fito, lubabatu ta fara tafiya, ba tare da ta kalli yaya fatima ba, saboda har yanzu fushi take dasu, tana isa kofar gida, ta hangi yaya aliyu da abokanshi zaune,ta kara tamke fuska, dan tasan sai sun toneta, 

Ta cire hijabin dake jikinta, tace nasan maganinku, 

Taci dammara dashi, tana isowa wurinsu, 

Suka fara luba luba gwaigwaye gwaigwaye,Aiko ta fara tika rawa, luba luba taci kadangare, bata koshi ba ya makale mata a makoshi, waye ya cire maki, ba kunya tana rawa, tace aliyu ya cire mini, 

Aiko suka kwashe da daria, Yaya aliyu ya kara tamke fuska, ta kwasa cikin gidan da gudu, dan ba wurin yaya sultan tayi ba, dakin mommy ta wuce. 

 Mommy ta riketa tace ke lafia, tace mommy yaya aliyu na tono, ta bata labari, mommy tace to tsaranki ne? Tace mommy so nake su dena ce min haka shiyasa na mashi haka, sultan da ya shigo, 

Ya hau daria, Yace ai kinyi maganinsu, 

Yaya aliyu ya shigo, Yace mommy idan ina ma yarinya abu sai kuga da gangan nake yi, a gaban friends dina zata min haka, Yaya sultan dake daria, Yace ai sai kasa su dena tononta, ya kalleta da take boye jikin mommy, Yace zan kamaki, 

Ya fice mommy ma daria ta hau yi. 

Ta kalli mommy tace wai har yanzu zainab basu dawo ba? 

Mommy tace aikuwa, lubabatu tace to mommy a maidasu islamiyyar almadina mana, mun rinka dawowa tare, mommy tace to sun nuna basu so, 

Tunda sunga can hadda da littattafai ake masu, lubabatu ta bata fuska, tace nima yasu zan koma, 

Tunda suma bokon hade yake da islamiyya, 

Ni bama naso, Yaya sultan yace to ki zauna inda kike yafi dadi ai, amma idan kuka hade can ba karatun zaki yi ba, 

Ta mike tace to naji, mommy bari naje gida mommy tace yau baki zama nan? 

Tace a'a zan dawo, 

Saida ta leka taga bata ganshi ba, Sannan ta fice da gudu, ta shiga ta karamar kofa, 

Ta gaida Ammi dake zaune a palour, 

Ta wuce ciki, Ammi tace ni daria ma kike bani, 

Kaya kawai ta canza, ta dawo palour, ta fara dube dube, ba taga affan ba, Ta mike, ta leka dakin Ammi ta hangeshi yana barci. 

Ta dawo palour ta zauna. 

Ammi ta kalleta, tace ba zaki ci abinci bane? 

Tace eh wanda aka kaimin ma ban cinye ba. 

Tace to dauko home work dinki, kiyi, 

Cikin shagwaba, tace kai Ammi, duka yanzu fa na dawo, Ai kwakwalwa na son hutu, anjima zanyi. 

  Ammi tace yanzu nake so kiyi, Harda na islamiyyanki, tace kai Ammi. 

Tashi Ki dauko kiyi a gabana, ta mike tana zumbure da baki, ta dauko Jakar ta fito, ta fara yi, 

 Harda hawayenta. 

Sallah kawai aka kira, ta kyaleta tayi sallah, Sannan taci gaba, Bayan ta gama Ammi tace saura na islamiyyar. 

Cikin kuka da tuni take so tayi, tace kai Ammi wai ba za a bar mutum ya huta ba, Yaya fatima ta fara daria, itama Ammi tayi, tace fatima dena sani daria, ke dauko kiyi shi yanzu, ta kalli fatima cikin kuka, tace yaya fatima, gobe wace mu'allima garemu? 

Muguwarce ko malama ladifa, fatima na daria, tace Muguwarce, da sauri ta ciro littafan, Tayi wurin fatima, tace dan Allah ki tayani, 

Suna da yawa, fatima tace akan me zan tayaki? 

Tace nide dan Allah, hadda karin suratul amma yata sa alun, duk cikin kuka take bayanin, kuma ban Iya ba. 

Fatima tace to fara wanda kika iya, sai in koya maki karatun, tace ai sun min yawa, ta fara kuka, ta kwashe littattafan, tace bari naje muyi da yaya sultan, tunda ke ba zaki min ba, kuma Allah ya kwace kokarin naki. 

Ammi tace ai yau ba inda zaki, kina gidan nan, fatima tayata, haka fatima ta tayata, tana tononta. 

Bayan sun gama, sunyi sallah, Ammi tace to ci gaba da karatun har hadda din ta zauna, 

Dan gangan Ammi ta mata haka, dan tasan tunda bata son karatun, Barci za tayi. 

Ta dan fara karatun, Aiko barci ya dauketa nan. 

 Ammi tasa fatima ta kaita daki. 

Washegari kuwa da yake weekend ne, ta dage sai barci take, har 7:40

Ko sallah ba tayi ba, Ammi ta shigo, tace yaya kun tashi ko, ku tashi ku nemi abinda zaku ci, ku wuce islamiyya. 

Ta fara tada lubabatu, dan fatima ta shiga wanka, tace hala ko sallah baki tashi kinyi ba? 

Ta kara juyawa, tace kai Ammi yau fa weekend, ki barni ko 8 ne in kai, 

Ammi tace kin manta da islamiyya ne? 

Tashi maza ki shirya, ta mike zaune, tace kai innalillahi wai se an kashe mana kwakwalwa ne da karatu, ba za a barshi ya huta ba. 

Ta fara hawaye, an samu boko, an samu islamiyyar cikinta, dan awannin da zamuyi mu huta ranar da bamu dashi, an kai mu wata islamiyyar ta cikin unguwa, yanzu naje na dawo karfe goma, sha biyu nayi, kuma ace mu shirya muje islamiyyar bokonmu,da mutum ya dawo ace ya dauki littafi ya duba, dan barcin mutum da zeyi kadan ne, yaushe kwakwalwa zata huta. 

Nide wallahi na gaji, Sede in zabi daya, 

Fatima ta fito, tace kede kin bani,lubabatu tace to ina ruwanki, 

Ammi ta dauko takalmi tace ni duk kike fada ma haka, bari kiga, ta mike daga gadon da sauri, 

Ammi tace bari inje in fada ma abbanku, Ai yana ciki, ta shige toilet din, tace shi yana can yana barcinshi, amma mu ya hana mu kwanta mu huta, haka tayi wanka ta fito. 

Ta gama shiryawanta, tasa uniform, 

Ta zauna, Yaya fatima tace tashi kiyi sallah, Tayi banza da ita, fatima ta mike tace bari na fado ma abba, ta mike tace tunda nace maki ba zanyi ba. 

Ta fara sallan. 

Suka fito, Bayan sun gaida iyayensu, suka gama breakfast,suka mike dan tafiya, suka masu sallama, 

Seda suka shiga gidan daddy dan su biya ma su salma su wuce tare. 

Wurin yaya sultan ta fara zuwa, ta tadda yana barci, ta fice ba tare da ta tadashi ba, dan tana bama barci mahimmanci, tunda tasan ba a barinta tayi. 

Suka fito suka jera a tare, har suka isa islamiyyar, kowa yayi ajinsu.


   ************


Zaune take cikin dan harabar gidansu, 

Ta tara mahaukata su biyu, sai fira take dasu, 

Can ta mike, tace nasan kuna jin yunwa, bari in shiga ciki in kawo maku abinci, 

Ta shiga, ta tako plate da abinci, ammi ta fito, Tace je lubabatu ina zaki kai wannan abincin? 

Ta dan bata rai, tace ammi wasu kawayena zan ba mawa, da suke jin yunwa, da sauri ta dibi ruwa ta fito, 

Ta aje masu a gabansu, ta dubi dayar da take da yarinya, tace bari in rinka bata, haka ta rinka diban abincin tana bata a baki, tace ke ladi jibi yanda kike cin abincin, 

Duk kina bata bakinki, kici a hankali, 

Idan be isa ba, in karo maku, ladi tayi daria irin na mahaukata, lubabatu tace kun san ku kawayena ne. 

  Hajiyar kaji ita kullum aikinta cin mushe na bola, 

Tace nide ban koshi ba, lubabatu tace to bari na karo maku, haka ta shiga da yarinyar a hannunta, ta karo musu abincin, ammi ta shigo kitchen din, tace wai ke wace irin yarinya ce? Ba na rabaki da mahaukatan nan ba, wato shine kika kai masu plate dina, salan su yi min kazanta. 

  To wuce ki maida masu yarinyarsu ki hada masu da plate din ki dawo gida, ta wuce, ta kai masu, 

Ta zauna taci gaba da fira dasu, idan sukayi abin daria, ta hau daria. 

Ammi da tajita shiru, ta biyo sawunta, ta ganta zaune cikinsu, duk ta hade dasu, ta saki salati, da sauri lubabatu ta mika mata yarinyarta, ta fice gidan da gudu. Tayi gidansu sultan. 

Suma haka suka tashi, suka fice gidan, 

Ammi tace kai wannan yarinya, ni ya zanyi dake? 

Allah ya shiryeki. 

Ta koma ciki tana fada. 

Lubabatu wurin shigarta gidan, Taci karo da kaza, ta korata cikin gidan. 

Ta datse gidan. 

Ta wuce wurin yaya sultan, Yaya sultan yace ya ban ganki ba yau? 

Tace ina can wurin su ladi, Yace wace ladi? 

Tace su Hajiyar kaji, gida na kaisu na basu abinci, shine ammi take fada, 

Ya riko hannunnta, Yace haba lubna ki dena zama cikinsu, ko kina so aljaninsu su shigeki? 

Ta girgiza kai, Yace to ki dena zama cikinsu, ta daga mashi kai. 

Ta mike, tace bari naje na gaida mommy zan fa dawo, Yace to ina nan ina jiranki. 

Ta fice, Bayan ta gaida mommy, suka fara wasa dasu zainab. 

Aka fara kiran sallan la'asar, taja tsaki, tace kai har wannan liman din ya kira, 

Zainab tace se mu tashi muyi sallah, muyi shirin islamiyya, lubabatu tace ni da ba zaku tona ba ba inda zani, yanda ba islamiyyar almadina, in ta wasana. 

Amma an tashi an kai mutum wata makaranta. 

Yaya salma tace da wannan surutun da kun tashi kun shirya. 

Lubabatu ta mike ranta a bace, Yaya salma tace idan ba zaki shirya da wuri ba, kice ma sis fatima ina jiranta. 

Ku sai ku tsaya nawarku, ta fice, Tayi wurin yaya sultan. 

Yana ganinta, Yace ya kuma naga haka? 

Ta kara bata rai, tace islamiyya, Yace haba shine na bata rai, kije mana ki samu ilimi, yanda zanyi alfahari dake. 

Ko baki so nayi alfahari dake? 

Tace ina so, yace to ki dena bata ranki, 

Idan zaki school, ta daga mashi kai. 

Yace haba to danyi mun murmushi, tayi daria, yace yauwa good girl. Yaya aliyu ya shigo ya zauna. 

Tace yaya sultan ga kazata nan da na koro, tana cikin gidan nan, Kada ka bari kowa ya tabata, yace ke da kaza ba taki ba, tace nide kada a taba min, daria kawai yayi, yace to ba wanda zai taba maki, tace to sai na dawo. 

Ta fito, Ta tadda kaza sai yawonta take. 

Tayi murmushi ta fice, 

Taje ta shirya, suka fito sukayi islamiyya. 

Ko a islamiyyar, hankalinta na kan kaza. 

Har aka tashi, suna yin gida, suna kawowa layinsu, ta tsaya wurin maman ngozi, 

Ngozi ce a wurin, tace yauwa ngozi gero zaki sammin, zan bama kazata, 

Ba ta jira mai ngozi zata ce ba, Ta fara diban geron. 

Ngozi ta mika mata leda, ta zuba, zata kara, ngozi tace a'a ki barshi haka. 

Tace kai ngozi, kefa friend dita ce, 

Tace ki bari gobe zan kara baki, da haka ta wuce, bata zame ko ina ba,

Sai gidansu yaya sultan, tana shiga, 

Ta hangi kaza, ta fara watsa mata gero. 

Yaya aliyu ya fito, Yace tunda kin dawo, yanzu ga kaza har ta shigo tsakar gida, 

Sai ki shirya fita da ita, lubabatu ta bishi da kallo, ya daka mata tsawa, 

Yace nace ki fita da ita, lubabatu ta tsorata, 

Ta duba, taga tabbas yaya sultan baya nan. 

Ido ya raina fata, 

Haka ta fara bin kaza, tana gudu, Yace daukarta zakiyi ki fita, haka tayi ta bin kaza, kaza taki yin hanyar fita. 

Gashi bata iya tabawa. 

Ya mika mata leda, yace gashi ki dauka da leda, tana bin kaza se tazo zata taba ta kasa, karshe ta fara kuka, tana fadin dan ubanki ki fita. 

Dan ubanki ki fita, kuka harda mijina, 

Suna har saman rijiya ita da kaza, 

Amma kaza taki fita, mommy ta fito, tace wai miye haka aliyu kake yi? 

Gaba daya gidan suka fito, Yace mommy banyi komai ba, nide nace ta fita da kazar da ta shigo fa ita. 

Mommy ta riko lubabatu da take ta bin kaza, tace Allah aliyu na kusa ci maka a gidan nan. 

Ta shiga ciki da lubabatu da idonta yayi jawur. 

Suko su khadija sai daria suke mata. 

Mommy ta riketa a jikinta, sai faman ajiyar zuciya take, ta mike tana share hawaye, tace mommy na tafi gida, 

Mommy tace to amma ki share hawayenki. 

Ta fito tana kuka, taci karo da daddy, 

Ta Duka tace daddy ina wuni, yace lafia lau, lubabatu. 

Ya rikota, yace meya sameki kike kuka? 

Tace yaya aliyu ne, daddy yace kai yaya aliyu baya jin magana, ki kyaleni dashi. 

Yi shiru ki share hawayenki. 

  Ina zaki yanzu? 

Tace gida zan tafi, yace to shikenan, 

Ki gaida mamanki. 

Ta shiga gidan ta karamar kofarsu,

Tana shiga ta samu wuri ta zauna, tana share hawaye, ammi tace ke kuma lafia? 

Tace yaya aliyu ne, yasa dole sai na fidda kaza, dan na shiga da ita gidansu, 

Kuma ai yasan ba zan iya dauka ba. 

Ammi tace ai sai kiyi hakuri, inde ba zaki natsu ba, Kin dingi shan wahala kenan. 

Yaya sultan ya shigo dakin da sallama. 

Ya gaida Ammi ta amsa da fara'arta. 

Ya zo ya zauna kusa da lubabatu, Yace naji abinda bros ya maki, kiyi hakuri, 

Kin manta maganarmu da mukayi, 

Idan ya maki abu fa yaga kina kuka, shiyasa zeci gaba da yi maki. 

Dan haka ki kyaleshi, Ai saida na rama maki, 

Tace da gaske? Ya daga mata kai, Tayi murmushi, Yace yau my lovely sister. 

Nan ya zauna suka yi ta fira, sai da aka kira sallan magriba, Sannan ya tafi. 

Ammi tace to yanzu idan kika yi sallah, sai ki dauki book dinki kiyi karatu, 

Kinde san kun fara exams, ta bata rai, sai kace wadda aka aiko ma da sakon mutuwa, 

Bayan ta gama, ta Dauka, tana karantawa tana kunkunai, Ammi de tayi banza da ita, bata ce mata komai ba. 

  Ko sallan isha'i ba tayi ba, Ta fara barci. 

        **********

Sun gama exams lafia, sunyi hutu, 

Dadi duk ya cikata, yau take alhamis, 

Tana zaune kan kujera, dukansu suna palour, 

Tace wayyo dadi, baba boko, ba islamiyya, 

Sai zaman kashe wando, Ammi tace ai littafan na hannunki, sai ki rinka dubawa. 

Tayi shiru, aunty jamila ta shigo ita da ummi, 

Da Gudu ta taso ta rungumeta, tace oyoyo aunty, itama ta rungumeta, tace lubabatu ina rashin ji? 

Tace yana nan, aunty jamila tace ai ni nasan bai tafi ba. 

Ta koma ta rungumo ummi, tace amma hutu kika zo mana? 

Tace eh mana, nace ma aunty ta barni a nan, 

Tace yauwa zo muje gidan daddy, suka fice, suna shiga saida suka fara shiga dakin su yaya sultan, ta fada kanshi, tace yaya sultan ga ummin aunty jamila, 

Ya mike ya zauna, Yace ummi, ta gaidashi, 

Yace anyi hutu ko? Tace eh, lubabatu tace ai tace ma nan zata zauna. 

Yace to yayi kyau, 

Suka mike, suka shiga ciki, mommy ta gansu, tace to su ummi ne ke dawa? 

Tace ni da aunty, tana gidan Abba. 

Ta gaida mommy, zainab suka fito da gudu, suka rungumeta, itama sai murna take. 

Lubabatu tace nan aunty zata barta tayi hutu, 

Khadija tace yauwa, 

Sai muyi ta wasa. 

Aunty jamila suka shigo ita da Ammi. 

Mommy tace bakin doctor ne a unguwanmu, 

Aunty jamila tace aikuwa harda jakata, nazo yin kwana biyu. 

Mommy tace aiko da kin kyauta kam. 

Ammi tace aikuwa, dan an dade ba a hadu ba, mommy tace ai nan zaki bar ummi de, aunty tace tare de zamu koma, Ammi tace ai gasu can an hade, sai an tashi ayi ta tsiya. 

Mommy tace dama ai marmarin junan daga nesa ne, aunty tace ai lalle kam. 

Ranar haka suka wuni wasa. 


Lubabatu nan gidan mommy suka kwana, amma aunty jamila gidan umma ta fara kwana. 


Washegari suna tashi, sukayi gidansu lubabatu. 

Ammi tace ku kuma lafia? Sai karaikana kuke kamar 'yan matan amarya, 

Aunty tace kin manta idan sukayi bako yanda suke. 

Ade rabu lafia, 

Can rana ta fara, Ammi tace to nide zanje in dawo, 

In samu inje in mata barka, aunty jamila tace to sai kin dawo, bala ya tafi kaita, aunty jamila ta mike ta tafi wurin mommy ta barsu nan gidan suna wasa. 

   Can wurin wasansu, da kwabe kwabe, 

Ummi Ta dauko wani ragowan fenti, 

Ta juyeshi akan tiles din dakin, lubabatu ta kalleta, tace ke ummi jibi abinda kika mana a daki, ta fara kuka, tace akan me zaki zuba mana fenti akan tiles din daki, 

Ta fita, Tayi gidan daddy, ta dage sai kuka take,

Tana shiga, tace aunty zo kiga abinda ummi ta mana a daki, aunty tace me ta maku? 

  Tace wai ummi ce ta zuba mana fenti akan tiles din daki, kuma fa da yawa, 

Aunty tace to yanzu ya za ayi, kije ki goge, tunda bakuwa ce, tace ni wallahi ba zan goge ba, aunty tace to ni bari inzo in goge, tace kema ba zaki goge ba, ni ba zan yarda ba, Ta dage sai kuka take. 

Aunty tace to yanzu tashi muje gidana, kema ki rama, tace ni ba zan rama ba, 

Mommy tace ke lubabatu ya kike so ayi dake? 

Aunty ta mike, tace muje ni in goge, 

Tace wallahi ba wanda zai goge, har sai Ammi ta dawo taga abinda aka mata a daki, 

Gaba daya ma dariya ta basu. 

  Seda yaya sultan ya lallabata, Sannan ta hakura, zurfa'u mai aikinsu ta goge wurin ta gyara, aunty ta kalli lubabatu dake ta ajiyar zuciya kusa da yaya sultan, tace a haka kike so in bar maki ummi din, 

Kullum aikin waya tazo, sai tazo ayi ta fada, 

Mommy tayi daria, tace lubabatu ce fa. Ammi na dawowa, da sauri ta tareta, 

Tace Ammi, yau ummi ta bata maki tiles, 

Ammi tace to Sarkin rigima, ba an goge ba, lubabatu ta bata fuska tayi shiru, ammi tace kede ba zaki zauna da kowa lafia ba ko? 

Duka yaushe tazo, har kun fara fada. 

Lubabatu ta girgiza kai, tace to bace min da gani. 

Bana son kawo kara kin sani, Yaya fatima tace ai halinta ne, tabi fatima da harara, ta wuce ciki, 

Yanda kasan zata kai mata duka. 


   Gaba daya sun shirya dan tafiya kasuwan laraba,ta unguwan shanu, Dake ci duk laraba. 

Tafe suke suna fira dukansu, harda su yaya fatima, 

Sai ga nafisa ta layinsu, da yake gurguwa ce, Tun daga nesa ta hangota, ta kusa zuwa inda suke, tana cangala kafa, lubabatu tace daya, tana karawa, tace biyu, tana karawa, tace uku. 

Ta karaso kusa dasu, ta kalli fatima, 

Tsce abinda lubabatu take min bana jin dadi, bani nayi kaina ba, salma ta kalleta tace kiyi hakuri, tace gaskia na gaji, zan kaita kara wurin babanta, 

Fatima tace da yafi kinga sai ta dena, 

Lubabatu tace sai idan naga dama zan daina, 

Nafisa tace to kici gaba kema baki wuce Allah ya dora maki ba, bame tonona sai ke. 

Tace to aniyarki ta biki, taja tsaki, fatima tace kiyi hakuri, ba tare da tace komai ba ta fara tafiya. 

Lubabatu tace daya, biyu, uku, fatima tace Allah ya shiryeki. 

Suka ci gaba da tafiya, suna tafiya. 

Kawai taji dan layinsu yace luba mai dan wake, budar bakinta, tace Audu ma yayi, gaba daya suka kalleta, zainab tace babanshi fa kenan, mtss! Lubabatu taja tsaki, tace baku ji abinda yace min ba, kasa ce mata komai yayi, 

Yaci gaba da tafiya, 

Salma tace lubabatu ki kiyayi mutane fa, kowa sai kinyi dashi, a haka har suka gama abinda zasuyi, ta toni wannan, ta toni wancan, 

Kan dawowansu ta fara fada dasu ummi, khadija tace wai ke bako so a zauna lafia? Cikin tsiwa, tace eh bana so, Ummi tace kai kede tafiya dake mstsalane. 

Abin ya bata haushi, Tun a hanya ta fara kai masu duka, har suka iso gida, 

Nan kuma aka kaure da dambe, , duk su Ammi suka fito, aka rabasu,garin raba fada wurin janta, takalmi ya tsinke. 

Tace kam Bala'i, Aiko ba zan yarda ba, tunda aka tsinka min takalmi. 

Aunty tace kai wai baku gajiya da fada ne? 

Tace ai su suka fara tonona, Ummi tace karya ne, Ba wanda ya toneki,lubabatu ta fara kuka, 

Tace aunty jamila kiyi ma ummi fada, 

Dama tun a hanyar kasuwa take ta cewa wai tafiya dani matsala nee, 

Ammi tace to yanzu ba zaki bar maganar ba,lubabatu cikin kuka, tace ai ni abinda ke min ciwo a rai ba a tambayeni ba, da an tambayeni, da se ince fitar rabo neee.

Aunty tace me ya faru a fitar rabo, 

Ta dauko takalmin, tace ba gashi an tsinka min kalmi ba, 

Ammi ta jawota, tace bari kuga, ta fara dukanta tana ihu, mommy ta riketa, tace haba ki kyaleta mana. 

Ku meyasa da suna fadan tun a can baku rabasu ba? Fatima tace mun hanasu, kun san halin lubabatu, 

Sannan duk wanda ta gani, sai ta tona.

Ammi tace ai wallahi kadan kenan na maki, zanyi maganin rashin jin nan naki, 

Lubabatu ta sa mommy ta saketa, tayi cikin dakin su yaya sultan, ta tadda baya nan, ta zauna nan taci gaba da kukanta, tace nasan da yana nan baze bari a bigeni ba, 

Kuka sosai take. 

Tana nan zaune, sai kuka take, Yaya sultan ya shigo dakin ya taddata, 

Ya karaso wurinta, Yace lubna, lafia? 

Nan ta fada mashi komai, tana kuka,. 

Yace to yanzu kiyi hakuri, ki dena biye masu, tace ai sune suka fara tonona, Yace to ki rinka hakuri.. 

Kinga yanzu gashi kinja amma ta bugeki, 

Yaya aliyu ya shigo, yace ai ta min daidai, maganin mara jin magana kenan. 

Ta dan kalleshi, yaci gaba kin tashi kin biye ma yaran unguwa, gaba daya ba natsuwa, haba ina amfanin zaman unguwar nan, duk unguwa cike da mutane da yara, 

Banma san har yanzu zaman me su daddy suke a unguwar nan ba. 

  Yaya sultan yace ai watarana lokaci ne, tunda suna da burin tashi. 

Yaya aliyu ya koma ya kwanta, Yace ke tashi ki fita, wannan kukan naki, ya isheni, Yaya sultan ya kamata, ya fita da ita wurin mommy, dan yasan halin yaya aliyu, 

Nan ta zauna, ba tare da ta kula kowa a dakin ba, 

Ba itace ta koma gidansu ba, sai dare. 

Shima barci ne ya maidata gidan,

Kana shiga ta kwanta, barci yayi gaba da itaWashegari tana tashi, Tayi wankanta, ba tare da ta kalli kowa na gidan ba, tayi shirin islamiyya, ta fito, tana kallonsu, tayi hanyar fita, aunty jamila dake zaune, ta jawo mata hannunta, tace haba my doughter, har yanzu fushin kike yi,

Ta fara hawaye, aunty jamila tace to kiyi hakuri kinji, abba yace wai me aka mata? 

Tace ita da Yara ne, kuma tun jiya suke fadan nan, Yace kai lubabatu kenan, 

  Zo ga kudi ki amsa, taje zata amsa, Yace yau ko gaidani baki yi ba, 

Nama fasa bada kudin, ta duka gaidashi, 

Yayi daria, Yace ki rinka zama da 'yanuwanki lafia, kinga duk fadan da za ayi dake akeyi, ta daga mashi kai, ya ciro kudi ya mika mata, ta amsa, tace abba bana son tsoho, sabo nake so, aunty jamila tace wai yaushe zaki dena son sabon kudi, Abba yayi daria, ya ciro wani ya bata, ta Washe baki, tace na tafi, 

  Abba yace yau baki jiran 'yanuwan naki? 

Tace suzo da kansu, ta fice, ammi tace wannan yarinyar, Allah ya shirya, gaba daya ba tada natsuwa, duk ta biyems' yanunguwa, aunty jamila tace ai ya kamata ku tashi a unguwar nan hakanan, abba yace muna so mu tashi, muna da burin haka, ammi tace dade yafi kam, 

Aunty jamila tace har yanzu suna son layin ne shiyasa, Sun dage a gidan gado, 

Kullum cikin sake mashi kyale kyale suke, (da yake dama asalin gidan mahaifinsu ne, nan suka tashi, Bayan sun rasu,Su kuma suka raba kowa ya dauki nashi,da yake babban wuri ne, dama aunty jamila bata ci nan gidan ba.)

Seda taje wurin yaya sultan, Sannan ta wuce islamiyya, 

Koda suma suka je, ba wanda ta kula a cikinsu,. 

Seda suka tashi, Sannan da taga suna ta mata magana, Sannan ta hakura, 

Har suka iso gida tare, gidan daddy suka wuce, 

Bayan sun huta, sunci abinci, aka fito wasa, 

Zainab tace wasan aure zamuyi,duk suka jera robobin su cock, da kwalaye, Na biki, Sannan zainab Tace to waye baba, Khalifa dake zaune cikinsu, Yace nine,ya daure fuska, lubabatu tace Khalifa wallahi idan ka daure kamar biri, 

Yace to naji, 

zainab tace to waye maman amarya? 

Lubabatu tace nice, waye yayar amarya? 

Ta kara cewa nice, Wai kanwar amarya? 

Tace nice, zainab ta kara cewa to waye amarya? 

Tace nice, Ummi tace wai ke lubabatu komai kice kece, 

Duka komi ke zaki dauka? Lubabatu tace eh, idan ba haka ba sede a tashin wasan, 

  Khadija tace to ki dauki daya mana, 

Tace ba zan dauka ba, duka nake so. 

Ummi tace aiko baki isa ba, zainab tace lubabatu ki zabi daya din, 

Tace nifa ban yarda ba, Ummi tace to wallahi baki isa ba, Aiko lubabatu ta mike ta fara wurgi da kayan, tana fadin a tashi party din ba za ayi wasan ba, Gaba daya saida ta wurgar da komai na wurin. 

  Yaya sultan ya riketa, yace haba my lubna, ba wasa kake ba? 

  Tace na fasa ba zanyi ba, Murmushi kawai yayi, yaja mata hannu suka bar wurin, 

Ummi tace kai wallahi lubabatu ta cika masifa, zainab tace ai ita ban san wane irin hali gareta ba, mommy ta fito, tace har an fara fadan kenan? 

  Allah ya shiryeku, Yaya salma dake zaune, ta kwashe da daria, tace Khalifa wallahi idan ka daure, Kamar biri, gaba daya sukayi daria, 

Ya mike yace lalle ma yarinyar nan, bari inje sai naci ubanta, mommy itama tana daria, tace Allah kaje ka bigeta, sai naci maka a gidan nan, Yace mommy baki ji abinda tace min bane, tace naji, wa yace ka shiga cikinsu wasan, 

Salma duk kece da hada fadan nan. 

Suka cigaba da daria, 

Yace wallahi mommy ki masu magana, idan ba haka duka zan zagesu, 

Ya fice daga dakin. 

  Mommy tace to ya isa, yanzu time din islamiyya ya kusa ma, ku tashi kuyi shiri, 

Duk suka mike. 

    

  **********

aunty jamila ta gama shirinta na komawa gida, lubabatu tace aunty ba zaki bar ummi din ba? 

Tace a'a tare zamu tafi, ko kun zauna fada kuke yi, Bayan sun tashi tafiya, gaba daya har daya suka rakata har mota, saida ta tafi sannan suka dawo gida,ji sukayi kamar kada su tafi, nan suma suka dawo, suka shirya suka yi shirin islamiyya, Bayan sun gama, suka yi sallah, suka wuce.


Kwanaki da shekaru sunja, inda yanzu haka, lubabatu sun shiga jss1,

Yayin da fatima da salma, yanzu suna ss1.

Yaya sultan sun samu admission a ABU zaria, 

Yanzu basa zaman gida, gaba daya, 

Lubabatu ba haka taso ba, duk se ta jita a takure, 

Gata de har yanzu, ba hankali tayi ba, 

Sosai take jin kewarshi a tare da ita. 

Wani weekend da suka dawo, da zasu koma harda kukanta, 

Gaba daya shima, duk yaji ba dadi, 

Ya riketa, Yace haba lubna, idan da sabo, Ai kin saba da rashin ganina kullum, kiyi hakuri, to wannan kukan da kike yi, ina ga na bar kasar, ya kuma za ayi, gashi daddy naso mu bar kasar, cikin kuka tace yaya sultan gara nan, 

Kada ka tafi wata kasa, karatun da zakayi a can, shi zakayi a nan. 

Yayi murmushi, Yace to naji 'yarkanwata, 

Amma idan naga baki dena kukan nan ba, 

TO zan bar kasar gaba daya, tace to ba zan kara ba, Ya shafa face dinta, Yace yauwa, to danyi murmushi mana, tayi daria, yace yauwa good girl, 

Kinga sai in shiga school cikin farin ciki. 

Muje ki rakani, bros na can na jirana. 

Tare suka fito, Yaya aliyu ya kalleshi, 

  Yace kaide kawai ka biye ma yarinya, kana bata mana lokaci, Yaya sultan yace to yanzu ba gashi na fito ba, Kasan ko me nake dole na bama lubabatu lokacina, 

Aliyu yace to ai sai ka zauna, kayi ta shirme, 

Yaja tsaki, 

Lubabatu ta bishi da harara, ta kalli yaya sultan, tace yayana Allah ya saukeka lafia. 

Yace to kada fa inji labarin kinyi kuka. 

Ta daga mashi kai, har suka fita da mota, tana daga mashi hannu. 

 Sannan ta koma gida, tana hawaye. 

Dan bata so taga dede da rana daya, bata tare dashi, amma gashi yanzu karatu ya rabata da yayanta, 

Tana shiga affan, ya biyota, taja mashi hannu, cikin gwarancin maganarshi, yake tambayarta, me kike kuka? 

Ta kalleshi, tace bakomai, je ka dauko book dinka muyi homework, 

Ammi ta fito, tace au ke kece mashi yazo kuyi homework? 

Da zaki rinka zama a haka, da kinji dadi, 

Yaya fatima ta shigo, tace taf Ammi ina kuwa zata zauna haka, wasa da 'yanlayi ya rufe mata ido, 

Lubabatu ta kalleta, tace Ammi kina jinta ko, ni yaushe rabon da in fita waje wasa, Bayan duk komi ya karu, an hana mutum zaman gida, 

Da ya dawo ace wannan, ina nake da lokacin kawayen waje, fatima tace ai kin san lokacin da kike basu, 

  Lubabatu tace Ammi kiyi mata magana, 

Ta fara hawaye, dan dama hawayen yana saman idon. 

Ammi tace to ya isa haka, idan kuma kukan zaki min, ki tashi ki fita. 

Wai sultan dashi aka haifeki? Daga tafiyarshi zaki fara shegen kukan nan naki, to dukanki zanyi. 

 Affan dake zaune, ya fara goge mata hawaye, ta kyaleshi, ba tare da ta hanashi ba. 

Ammi tace sakarya kawai, jss1 amma ba zakiyi hankali ba. 


  Da fadan ya isheta, mikewa tayi ta bar dakin, ta koma nasu, Ammi ta bita da kallo, ta mike, tace bari na shiga wurin mommynku, 

Fatima tace to sai kin dawo, 

Yaya fatima itama ta mike, ta shiga dakinsu,lubabatu ta kalleta, tace yaya fatima ki dena min abinda kike min. 

Akan me zaki rinka hadani da Ammi,

Kisa a rinka min fada? 

Fatima ta kalleta, tace wai ke lubabatu ni tsararki ne? Tace ban sani ba, 

Fatima ta kai mata duka, itama ta rama, 

Fatima ta kara kai mata.


  Tun daga kan gado, tayi tsalle ta dare kan fatima, ta fara kai mata duka ta ko ina, fatima na kokarin ramawa, 

Salma ta shigo, tace ke lubabatu baki da hankali ne? 

Tayi Tayi ta rabasu, amma ta kasa. 

 Koda ta janye lubabatu, sai ta kara jawo yaya fatima, da sauri ta fita, tayi gidansu, tace ammi ga lubabatu can na fada da fatima, 

Da sauri ammi ta fito, tayi cikin gida,. 

Duk a lokacin bata bar fadan ba,ammi na shigowa dakin, takai ma lubabatu duka, takaici yasa yaya fatima ta fara hawaye. 

  Haka ammi ta jawo lubabatu ta fara kai mata duka, tace fatima tsararki ne? Meyasa kika rainata? 

  Ta samo bulala, ta mika ma fatima, 

Tace so nake ki zaneta, tasan ke ba tsararta bace, fatima ta amsa, ta rike, ammi tace me kike jira? 

Tace ammi ki kyaleta, ammi ranta bace ta dauke fatima da duka,

Tace nace ki daketa, fatima ta fara dukanta, tana ihu, can ammi ta turo kofan, tasa key, taci gaba da dukanta, ihu take sosai, tana kiran yaya sultan, yanda kasan ana yankata, mommy ta shigo tana buga kofan, tana fadin ki kyaleta hakanan, seda ta gaji dan kanta. 

Sannan ta kyaleta, tace wallahi duk ranar da kika kara gigin fada da fatima, dukan dana maki yanzu, kadan ne, Akan wanda zan maki, 

Ba zan dauki raini ba a gidan nan, 

Sannan ta bude dakin, da gudu ta fice gidan. 

mommy tace haba dan Allah wannan wane irin duka ne haka? 

Tace ki kyaleta, gani take tunda ta kawo girma, daidai take da fatima, 

Kuma ba zan dauka ba, dan zata wahala a gidan nan, ba taga ana kyaleta ba. 

Mommy tace to yanzu yau wuce, ta fita, tayi gidanta, can bedroom dinta ta tadda lubabatu a ciki, nan ta zauna, ta jawota, tace lubabatu ki dena rashin kunya, kinga duk wanda ya girmeka ya girmeka. 

Ki rinka zama da kowa lafiya, abinda ba a so, ki kiyaye, kinji ko, ta daga mata kai, ta dade tana mata nasiha, Sannan ta kyaleta. 

Ranar ko, ko gidan bata koma ba, nan ta kwana, 

  Hatta yaya sultan, saida ta fada mashi ammi ta bigeta, da sukayi waya.

Saida lubabatu ta kwana biyu bata waiwayi gida ba, nan take komai. 

Da mommy ta gano bata zuwa gida. 

Download kirata, tace lubabatu zauna, ta samu kusa da ita ta zauna. 

Tace lubabatu Ammi matsayin me take a wurinki? 

Tace mamana, tace yauwa, amma meyasa kike fushi da ita? Tace ni ba fushi nakeyi da ita ba, mommy tace to idan ba fushi kike da ita ba, ki tashi kije wurinta yanzu, 

Kada fa inji baki je ba, haka ta mike ta shiga gidan, ta tadda Ammi zaune a palour, ta fara rara gefe, Ammi tayi banza da ita, ba tare da ta kalleta ba, affan ya rike mata hannu, yana fadin Ammi ga yaya lubabatu, yaje ya jawo Ammi, yana nuna mata, tace ai na ganta, 

Lubabatu tace Ammi kiyi hakuri, Ammi tace ki kyaleni ba ruwana dake, har tunda baki jin magana,     tace Ammi na dena, dan Allah kiyi hakuri, Ammi tace Allah duk ranar da kika kara haka, ba zan shirya dake ba, kinde jini da kyau. 

A lokacin sai ta saki jikinta, taci gaba da hidimanta.


Suna zaune, Yaya fatima tace lubabatu dan Allah gashi ki siyo min pad, always. 

Da relaxer, 

Lubabatu tace wai yaya lubabatu me kike yi da pad, naga kina yawan siya? Tace soso ne, wanka nakeyi dashi, tace to nima zaki bani? 

Yaya fatima tace yanzu de je ki dawo. 

Ta amshi kudin ta fita, bata wuce wurin aiken ba, ta zauna wurin kawarta mai suna sa'adatu data dage tana ta suyan waran saidawa, 

Haka ta zauna, taci gaba da soya mata waran, ta dage sai fifitan wuta take gaban murhu, sai share hawaye take. 

Ta fara cin awaran, suna fira da sa'adatu, 

 Dede lokacin motar su yaya sultan ta danno kai, Yaya aliyu ya hangeta gaban murhu, ya tabo yaya sultan, Yace ga mutuniyarka can, 

Gaban mai wara, duk ta saje dasu, 

Yaya sultan ya bita da kallo, yanda yaga ta dage, Murmushi kawai yayi, ya kwala mata kira, ta dago, tana ganinshi, da sauri ta taso, tana Washe baki, ta iso wurinsu, 

Tace yaya sultan yaushe ka dawo? 

Yace yanzu, me kike yi a can? 

Tace yaya fatima ta aikeni, Yace shine kika zauna a can, bana hanaki ba, 

Tace kayi hakuri, bari na dawo, ta tafi, Su kuma suka idasa gida. 

  Da sauri ta wuce, ta siyo abinda zata siyo, ta dawo, ta mika ma yaya fatima sakonta, ammi tace ina zaki? 

Tace yaya sultan ne ya dawo, ammi tace kada ki je wurinshi yanzu, 

Kinga zasu so su huta, ko bari sai dan anjima, ta dawo ta zauna, ba dan ranta yaso ba, 

Yaya fatima, taje ta dawo wurin ammi, tace ammi dan samin, ta fara sa mata, lubabatu tace ammi nima ina son insa, ammi tace ba zaki sa ba, Ita gashinta yana da karfi, 

Shiyasa take sawa, lubabatu tace nide Ammi ina so insa, ammi tace nace ba zaki sa ba, Wai ke wace irin yarinya ce, to kisa din in gani, gashinki da nata ba iri daya bane, 

  Cikin shagwaba, tace to ammi yaushe nima za a fara min? Ammi tace se kin girma, tace ammi to ai na girma, tace da sauranki. 

Yaya fatima tace gara ma ki hakura. 

Tabi yaya fatima da harara, 

Bayan ammi ya gama sa ma Yaya fatima relaxer, tace zo ke kuma in gyara maki gashin, ta sauko ta zauna, 

Ammi tace kai lubabatu kaurin me kike haka? Harda karni, hala kina can wurin sa'adatu me awara, 

Shiyasa kika dade, to bari in gama maki, ki wuce kiyi wanka ki canza kaya, 

Tana mata, tana mata fada, harta gama. 

 Tace sai ki tashi ki wuce, kiyi wankan. 

Ta mike ta wuce toilet, Bayan ta gama shiryawa, ta fito, ammi tace dan Allah lubabatu ki rinka natsuwa, 

KO wane yaro yana cikin gida, amma banda ke, Na rasa me waje ya maki, da ba zaki zauna cikin 'yanuwanki ba, 

Yarinya sai shegen kwashe kwashen tsiya, idan yau an ganki da wadannan, gobe da wadannan, za a ganki, ina amfaninshi, 

Yarinya kamar ana kada ki da ruwan hanji. 

Yaya fatima tace shiyasa na kosa mu tashi a unguwar nan, inga yanda mutum zeyi, ammi tace ni kaina unguwan nan ta isheni, se an masu magana, suce ana son me kudi a cikin talakawa, saboda halin temako, ko a ina ne, Ai zaka iya zuwa ka temaki mutum, lubabatu tace ammi su Abba gaskia suka fada, kuma ai mutane rahama ne, Yaya fatima tace ai ke baki da hankali, lubabatu tace ammi kina jin abinda take cemin ko, 

  Ammi tace yanzu de tashi ki tafi wurin sultan din gaidashi, da sauri ta mike ammi tace ina hula, zaki fita haka? Ta suri hulan yaya fatima ta fice, Yaya fatima ta fada da karfi, saura ki yardan min da huta. 


Tana shiga, ta isa wurinshi, ya rikota, 

Tace yaya sultan nayi missing dinka, Yace me too, ya karatu, ina rashin ji? 

Tace yana nan, 

Yayi daria, Yace an koma sch ko? Tace aikuwa, ni na kosa na gama karatun nan, Na huta, kullum mutum na hanya, Yace kada ki gaji, 

Wataran zaki ji dadi, tace da gaske? 

Ya daga mata kai, taji yo muryan daddy ya dawo, ta mike tace bari naje na gaida daddy, ta fice, Yaya aliyu ya bita da kallo, Yace bros, yarinyar nan ba randa za tayi hankali, 

Yaya sultan yace habade, yarinya ce fa, duka shekarunta nawa, zata yi hankali, zaka gani kuma, ya danyi murmushi ba tare da ya kara cewa komai ba. 

  Tana shiga daki, ta duka ta gaidashi, Yace 'Yar gidan sultan ya akayi? 

Tace lafiya lau, Yace to haka ake so, 

Yace to ga abincin makota na siyo, 

Se azo a kai masu, lubabatu tace daddy zamu kai, Yace a'a ku barshi, duk Khalifa ya mika masu,. 

Tace daddy muma zamu iya, Yace to shikenan, zainab khadija ku taso, 

Su taliya ne dama da macaroni, nan sukai ta kaiwa, wani gidan a basu tukwici, Bayan sun gama kaiwa. 

Lubabatu tace soda zan siyo in sa ma kaina, 

Khadija tace ke kada ki sa, tace wallahi sai nasa, suka ko rakata ta siyo, 

Suka dawo gida, ta wuce gida, ammi ta ganta da soda, tace me zakiyi dashi? 

Tace sawa, ammi tace fita kije ki yardashi,. 

T shige ciki, lubabatu tace aiko sawa zanyi, ta Dauki cumb ta fita dashi, taje ta samu zurfa'u, tace zurfa'u amsa ki samin, ta mika mata, 

Zurfa'u tace ke soda zaki sa a kanki? 

Tace eh, tace mata to ammi ta sani? 

Tace mata eh kisa min se faman tamhayata kike. 

Ta fara sa mata, har ta kusa gamawa,. 

Ammi ta fito, tace kai lubabatu da nace kada kisa, shine seda kika sa, 

Zurfa'u meyasa kika sa mata, Kin san bata sawa? 

Tace ammi ita tace min kin sani, ammi ta kalleta, tace zaki sani, ta kai mata duka, ta gudu, 

Tana wucewa, kanta na zafi, tace Zurfa'u wanke min, 

Tasa ruwa ta fara wanke mata, gashi ya biyo hannunta, tace kai lubabatu gashinki fita yake, mtss taja tsaki, 

Tace ni tunda ba zaki iya ba, bari na wanke da kaina, Zurfa'u na zuba mata ruwa, tana wankewa, Aiko jan da za tayi gashi itama ya biyota,

Ta bude idonta, taga gashi a hannunta,

Ta fasa ihu,gami da kiran sunan Ammi, da sauri Ammi da yaya fatima suka fito, suma dayan gidan, kukanta suka ji, suka fito. 

Cikin kuka tace Ammi kalli tana nuna mata gashin hannunta, Ammi jibi gashina, Ammi ina nuna maki kina kauda kai, 

Kuka sosai take, Yaya aliyu yace, Ai gayu ne, gayu yayo kyau, ya danyi daria. 

Yaya sultan yace to ki tsaya a idasa dauraye maki kan, Kada sauran gashi ya fice, haba daya wurin seda sukayi daria, Aiko ta kara fashewa da kuka, Zurfa'u na zuba ruwa a kai, gashi na zuba kasa, 

Da taga gashin seta kara fashewa da kuka, 

Ta mike tace bana son wankewan a barshi haka, wayyo Allah na, wallahi Zurfa'u ke kika ja gashina ya fita, Zurfa'u tace ni kuma? 

Ammi tace idan baki rufe min baki ba, sai na zaneki a wurin, mommy tace to da wanne zata ji, 

Ammi tace ki kyaleta, yarinyar nan, tunda tace min zata sa relaxer a kanta, nace a'a, shine seda ta samu kudi, ta Je ta siyo soda tasa,. 

Da niyyata in zaneta, amma ai ga na kuka kin samu, Yaya sultan ya kama mata hannu, suka fita, yayi dakinsu da ita, 

Yana ta bata hakuri, tace yaya sultan kalli fa yanda kaina ya koma. 

Yace kiyi hakuri ze fito, kuka kawai take, Yaya aliyu yace ke idan damuwa zakiyi da kuka, tashi ki fita, 

Maganin mara jin magana kenan, gobe sai ki kara. 

  Tun daga ranar kullum lubabatu cikin yawo da dankwali take a kai, bata bari kowa yaga gashinta, 

Mutane har mamakin rufe kanta suke, Sun san da bata son sa dankwali a kai.


Yaya sultan da yaya aliyu sun samu admission a american university, 

Sosai lubabatu taci kuka, yanda kasan ba zasu dawo ba, koda suka rakasu, haka ta rinka kuka, Yaya sultan ya jawota, Yace kiyi hakuri,

Zan fa dawo, tace ba dawowan da zakayi, 

Ni ba naso ka tafi, meya sa ka zabi wata kasa, dakyar ya rinka lallashinta, 

Daddy ya rikota, lokacin da ze shiga jirgi, 

Ya kasa kallota, ta rike daddy tana kuka, 

Shi kanshi yaya sultan sai da yayi hawaye. 

Yaya aliyu yace kai kaji zaka iya, wannan wane irin shakuwa ce haka? 

Aiko kuna tare da wahala, ya dan ja tsaki. 

  Itako lubabatu har suka iso gida kuka take, 

Ranar ko magana ta kasa yi, 

Shiru kake jinta, 

Ta koma kamar mara lafiya, duk maganar da ake, Sede tabi mutane da kallo, 

Ko gidansu ma taki zuwa, sai dai su zainab suka shigo gidan, 

Duk ta kyale kowa, 

Ammi da kyar ta samu ta lallabata, taci abinci, 

Duk ta bata tausayi, dan tasan yanda suke da yaya sultan, mommy kanta sai da ta shigo, dan har yanzu hankalinta tana kukan. 

Mommy ma hakuri da tayi ta bata. 

Wasa wasa, sai gata kwance da zazzabi, 

Yaya sultan ya kira tana kwance, Yace ma Ammi a kaima lubabatu waya,

Ta mike ta kai mata, ta amsa tana hawaye, 

Yana jin ta amsa, yace lubna, tace yaya sultan cikin kuka, yace oh har yanzu kukan nan kike yi? Kina so in dena kiranki? Tace a'a, Yace to ki dena kuka, idan har ba abinda nake yi, kullum zaki rinka jin muryata, 

  Har se kin gaji, amma idan har kina kuka, to ba zan rinka kira ba, 

Tace na dena, Yace yauwa my sister. 

Idan ina jin kukanki,ai sai in kasa yin komai.

 Kina so in kasa yin abinda naje yi? Tace a'a, Yace yauwa, Sun dade suna fira, sai da yaga ya sata daria, Sannan ya kyaleta, dan tayi barci. 

  

   **************

Tun daga ranar da yaya sultan ya tafi, lubabatu ta rage shiga gidansu, 

Da wuya ta shiga ta dade, shima inde ba abinda yake yi, haka zai kirata susha fira, Ganin haka yasa ta saki jikinta, dan taga yanda suke fira sosai dashi a waya. 

  Suna cikin daki gaba dayansu, fira tayi dadi, nan tayi wanka, ta fito wanka, ta daga hammatanta, tace kai gashi na gani, Aiko aske dan iska zanyi, 

Khalifa dake zaune, Yace ki aske?ki aske fa kika ce? Aiko nan gaba zaki nemeshi da kudinki,amma ba zaki samu ba, Yaya salma da ta tada sallah, daria ta kufce mata, yi kawai take, 

Tace kai ina ruwanka da maganarsu, fita a dakin, suma daria sukayi, ya tashi ya fita. Yaya salma ta kallesu, tace ku kuma ku san inda zaku rinka magana. 

Lubabatu tace to me mukayi? Shima ne ya cika sa baki, a maganar da ba dashi akeyi ba. 


  *************

Rayuwa na sauyawa, inda yanzu gashi su lubabatu har anje jss2,amma ba abinda ya canza zani, a rayuwar lubabatu, har yanzu ba hankali, 

Ammi tayi fada har ta gaji, tafe suke sun dawo school, ba tada lafia, 

Har suka iso gida, tana de daurewa, 

Ta fara cin abinci, tace Ammi ba zan iya ci ba, garin kwakwi nake son sha, bani kudi in siyo, ta Dauki kudi, ta mika mata, ta tafi siyowa, 

Bayan ta gama siya, jiri ya dauketa, 

Zata fadi kasa, ngozi ta rikota, har kofar gidansu ta kawota, lubabatu tace kyaleni zan iya shiga ciki, 

Idonta a rufe ta shiga gidan, har daki, 

Tana fadin Ammi, bata karasa ba, amai ya taso mata, ta fara, Ammi ta fito da sauri, tace to ciwon har ya kai haka? 

Nan tasa zurfa'u ta gyara ko ina, ta samu da kanta, ta danyi mata wanka, 

Sannan ta kwanta, Ammi tace ki tashi a kaiki asibiti, 

Tace Ammi naji sauki, ba se naje asibitin ba, 

Ammi tace a'a nasan ciwonki, tashi kuje da fatima, Yaya fatima tace Ammi, ba zan iya zuwa ba, kinga karatu nake yi, Ammi tace kada kije, tashi bala ya kaiki, sai ki samu su zainab su rakaki, lubabatu yace dan Allah yaya fatima kizo muje, kinga shi doctor mansoor din nan, se yayi ta ma mutum larabci, Yaya fatima tace ba inda zani, lubabatu tace kada Allah yasa kije din, Ai da yaya sultan na nan, 

ba zan nemeki ba, 

Ammi tace miye abin wuta a ciki sai ki mashi bayanin yanda zai fahimta, yanzu tunda jikin ya dan saki, ki tashi kiyi sallah kafin ki ku tafi. Ta mike tana zumburar baki, taje tayi alwala.


    ****************

Bayan ta gama shirinta, ta fito, seda taje, tasa au zainab su rakata, Sannan suka fito, Ta samu bala a waje, tace asibiti zaka kaini, 

Yace to jikin har ya dameki, to muje, gaba dayanssu, suka shiga, Bayan sun isa asibiti, Bayan ta shiga, doctor din balarabe ne, cikin harshen larabci, Yace mata, meke damunki, tana tashi, ta nuna kanta, tace ra'astani, (kai), wa jirtani, (jiri), wa kirjitani, (kirji), nurse din dake tsaye ta fara daria, 

Lubabatu ta bita da harara, tace miye abin daria a ciki? 

Zainab ma da suke zaune, dariyan sukayi. 

  Doctor mansoor ya kalli nurse din, 

Yace me take nufi? Cikin harshen larabci, 

Nan nurse din ta mashi bayani, shima daria yayi, Yace lubabatu, nan ya gama rubuce rubucenshi, ya mika mata, Yace gashi ki sayi magani, 

Ta amsa, suka fito, zainab daria ta kara yi, lubabatu tace bana son haka, 

 Koda kika ga banda lafia, zan maki rashin mutunci, ni shiyasa bana son zuwa asibitin nan,saida suka amshi magungunan, Sannan suka tafi, daria suka kara yi har suka shiga mota, 

Lubabatu tace kuma nasan ba zaku iya fada ba, inda kun sani ai da kunyi, mtss, taja tsaki,zainab tana daria tace kiyi hakuri, ra'astani, lubabatu ta kai mata duka, 

Khadija na daria, tace bafa kida lafia. 

 Tace koda banda lafia ba,zan kyaleku ba, bala yace wai me ya faru, 

Daria suka kara yi, lubabatu ta daure fuska, har suka isa gida, bata kara tankawa masu ba, saida suka rakata har daki, ammi, tace har kun dawo? Suka ce eh, 

Khadija tace baku ga abin daria ba yau, nan ta basu labari, suma daria suka fara yi, ta mike zata kai masu duka, ammi ta riketa, tace kyalesu, kinga baki da lafia, kiyi banza dasu, cikin hawaye tace to baki ga abinda suke min ba, 

Ni ba zan yarda ba, Ta fara kuka, 

Ammi tace ki kyalesu, suma ai basu iya ba. 

Yanzu sha maganinki, ki kwanta kiyi barcinki, ta danyi daria, tace Ammi ba zani islamiyya ba ko? Tace eh sai kin warke, da fara'arta, tace Allahu akbar,lokacin jin dadi da cin dadi ya tsaya, 

Cikin shagwaba, tace ammi, dambun kifi zanci, bakina ba taste, 

Yaya fatima tayi daria, tace Allah ammi, har yanzu lubabatu bata da hankali, 

Zainab tace ni har mamaki take bani, ko affan be yin abinda take yi, 

Tace eh din naji munafukai, kuma wallahi duk yaya sultan zeji abinda kuke cewa, Yaya fatima tace ai dama kin saba, Komi akayi sai kin fada mashi, to dukanmu zaiyi? 

Lubabatu tace ai baku wuce duka ba, 

Kuma zan fada mashi abinda kika ce, 

Tunda kin rainashi, da zaki wani ce dukanku zeyi, 

  Ammi tace ni ya isa, amsa kisha maganin, kuma kika isheni da surutun nan, sai kinje islamiyya, Yaya fatima tace Ammi tama fa warke, 

Gara taje, lubabatu da sauri tace to ba zani ba, Tare da murguda mata baki, 

Kin san yanda nake ji a jikina ne, ta koma cikin Kujeran, ta kwanta, Ammi tace Allah ya shiryeki, mutum na ciwo ma baze natsu ba,mommy ta shigo gaidata, Bayan taga su zainab sun shiga gida. 

Mommy tace lubabatu ya jikin? Gami da taba wuyanta, tace ba sauki, mommy tace a'a da sauki mana, Ammi tayi murmushi, tace ai kin san ba zata ce da sauki ba, tana gudun ace ta tafi islamiyya, 

Mommy tayi daria, tace lubabatu kenan. 

Can kuma ta kalli Ammi, tace uhum uhum, Ammi baki sa an min dambun kifin ba, gashi kwai nake son ci, Ammi tace yanzu se kiyi hakuri a siyo, dan fridge ba sauran kifi a ciki, mommy tace akwai a gida, bari idan na shiga, sai insa a maki, Ammi ta kwala ma zurfa'u kira, tazo, tace sai kije k soya ma mutuniyarki kwai, shi take son ci, Kin santa idan tana ciwo, shikenan watan sa aiki da cin dadi, ya tsaya a wurinta, zurfa'u tayi daria, tace bari na soyo mata, 

Ta fita. 

Ta kalli mommy tace mommy kisa a min yanzu, Allah bakina ba taste, kwata kwata. 

Mommy tace kada ki damu yanzu dana shiga za a maki, lubabatu ta mike, taje ta zubo madara da milo a cup, ta dawo ta zauna, 

Ammi tace kin fara ko? 

Yaya fatima tace wallahi Ammi duk ciwon nan nata na gulma ne, lubabatu tace eh tunda ba a jikinki yake ba, shishshigi, mommy tace kai lubabatu, zurfa'u ta miko mata kwai, ta amsa ta fara ci, seda ta cinye tas, tayo gaba da shan madaranta, tace Ammi dan bani waya, in kira abba, Ammi ta mika mata, ta kirashi, 

Yana dauka, tace abba su abarba, kankana da a'a ba, kai duk wani fruits zaka siyo min, Na kasa cin abinci, 

Yace Allah sarki, to bari in kira bala ya siyo maki yanzu, cikin tsokana, Yace bakin ba taste ko? Yana daria, tace eh abba, gashi nasha magani, har yanzu ina ganin jiri, ina jin jinina ne yayi kasa. 

Yace ai na sani, bari insa ya siyo maki, tace yauwa abbana, wanda yafi kowa kirki. 

Daria kawai yayi, Yace to Allah ya sawake. 

Ya kashe wayan, 

Yaya fatima tace kaji karya, Wai kin kasa cin abinci. Tace to karya nayi, ai ban ci abinci ba, Ammi Tace sai kwadayi.


  Tunda ta fita taki dawowa gidan, sai can dare, Bayan anyi isha'i, Sannan ta dawo gida, cikin sanda ta shige daki, 

Tana maida kofan ta rufe, abba ya sawo kai ya shigo, ta fara zare ido, 

Gami da ja baya, tana fadin dan Allah abba kayi hakuri, karya take min, 

Yace ni bashi zan tambayeki ba, meya hanaki zuwa islamiyya? 

Tace Abba nafa je, Yace to wa na gani a gidan? 

Ya jawota, ya fara kai mata duka, ta fara ihu, 

Saida ya gaji dan kanshi ya kyaleta,

  Yace tunda abin naki ya zama iskanci, to ki shirya, boarding zan kaiki, ko zaki yi hankali, cikin kuka tace abba boarding? 

Wallahi ba zani ba, wayyo ammi na bani na shiga uku, ammi ta shigo, 

Yace to zan kaita boarding, tunda ba zata natsu ba, lubabatu tace dan Allah abba kada ka kaini boarding, wallahi bana so, ammi ki hanashi, ammi tace ba ruwana, boarding shi ya dace dake, 

Tunda ke ba zaki natsu ba, kuka sosai taje yi, 

Abba ya fice ya kyaleta, 

Nan ta zauna tafi gaba da kuka, tunaninta, yanda zata kasance a boarding, 

Yaya fatima tace kece lubabatu baki jin magana, duk yaran layi ba wanda ba abokinki ba, idan kika ci gaba da haka, a haka zaki tashi, ba natsuwa, Wai sunan kina garin kaduna kenan, sai anje wani gari, a rinka fadin daga kaduna nake, tayi banza da lubabatu, ba tare da tace komai ba, 

Kukanta kawai take. 


   **************

Saboda halin lubabatu, daddy da abba, har sun samu gida a u/rimi, zasu bari unguwar, 

Abba zaune lubabatu na zaune, dasu ammi, abba ya kallesu yace to alhamdulillah, mun samu wasu gidaje a u/rimi, gyare gyare kawai zamuyi, 

Gidan iri daya ne, na wani mai mata biyu, basu wani dade ba, ko wata biyu basu yi ba a gidan, Sun koma abuja, 

To yanzu mun siya, sai ku fara shirin komawa, 

Ammi tace kai alhamdulillah, haka yayi kam, mun bar unguwar nan, 

Tunda wannan fitinanniyar, ba zata natsu ba. 

Abba yace idan aka koma can, base inga ta fita yawo ba, tunda kowa yana cikin gidanshi, 

  Lubabatu tace to abba naji, zan rinka zaman gida, amma dan Allah kada ka kaini boarding, wallahi bana so, 

Ta fara hawaye, Yace lubabatu maganar boarding, Ai sede koyi hakuri, 

Dan ba makawa sai kinje, 

Principal din kawai nake jira ya kirani. 

Ta fara kuka, ta mike tayi wurin mommy tana kuka, 

Tace mommy na bani, abba yace dole, sai ya kaini boarding, ni kuma bana so, gashi ya dage, mommy tace lubabatu kiyi hakuri, 

Nayi nayi, ya kyaleki, Kada ya kaiki, 

Amma ya rantse, Yace sai ya kaiki, 

Kiyi hakuri tunda a cikin kaduna zai ajeki. 

Ba wani gari zai kaiki ba. 

Cikin kuka, tace mommy bana so, 

 Mommy tace lubabatu to ya zanyi dake, 

Kiyi hakuri, tunda gari daya ne, zaki rinka ganin su fatima, dasu salma. 

Ta mike tayi gida tana kuka, tana ganin wayan mommy a kan kujera, 

Ta Dauka tayi ciki dashi, ta kira yaya sultan, ta fara kuka,Yaya sultan yace lubna meya faru? Yi shiru ki fada min, Kin san bana son kukan nan, 

Cikin kuka, tace abba ne zai kaini boarding, 

Yace boarding kuma? Tace eh, Yace to, Yaya aliyu dake zaune,ya amshi wayan, Yace ai shine daidai dake, 

Abba ya gama min komai, da ze kaiki boarding, 

Ta fashe da kuka, Yaya sultan ya amshe, 

Yace kyaleshi, da na dawo, abba ze cireki, koda ya kaiki, tace da gaske cikin kuka, Yace eh kada ki damu. 

Da haka yaya sultan ya kwantar mata da hankali. 


   **************

Abba be kara mata maganar boarding ba, Ganin haka yasa taci gaba da rashin jinta, 

Tana ganin maganar da mommy ta mashi ne, yasa ya kyaleta,

  Tana zaune tare dasu jamila,maman su jamila na masu danwake, tace yau ba zan bar gidan nan ba, sai naci dan waken nan, jamila tace ai sadiq yana hanya, lubabatu tace ai sai naci sannan zai dawo, 

wani sadiq dake gidansu, yana yawan kiranta da amarya, inde yana gidan, to ba zata zauna ba, da yake ban garin yake ba, 

Suna zaune ya shigo, yana ganinta, Yace amarya, tana ganinshi, 

Ta mike da gudu, ta fice gidan,suka hau mata daria, maman jamila tace aiko sadiq baka kyauta ba, 

Taci burin cin dan waken nan, amma gashi ka koreta, 

Yana daria, Yace ai inda sabo yaci ta saba, 

Tun kafin ta kai haka fa, take guduna, 

Mamanshi tace ina ruwan lubabatu, 

Yace ai daria take bani, inde abu daga hannuna ya fito, ba za tayi amfani dashi ba, 

Maman jamila tace, Ai kasan ta tsani ace ga saurayinta. 

Yana daria, Yace gashi 

Kuma ai ita tace nine mijinta, suka hau daria. 

  Lubabatu ba tayi gida ba, gidan daddy ta tsaya. 

Sai da ta gama wasanta, Sannan tayi gida, 

Ammi ta kalleta, tace wuce kiyi wanka, 

Mutum ya tashi, baze je yayi wanka ba, 

Ki zauna haka ko kyamar jikinki ba kya yi. 

Yaya fatima tayi daria, tace kije kiyi, 

Ga sabon kaya kin samu, ta daga taga dinkakken atamfa doguwar riga, 

Da sauri taje tayi wanka, tana shigewa, ammi tace kada fa ki fada mata wanda ya bata, Kin san ba zata sa ba, Bayan ta fito, ta shirya, ta Dauki kayan tasa, Yaya fatima ta kwashe da daria, 

Tace kinfa yi kyau, Kin san wa ya kawo maki? 

Tace a'a tace sadiq ya kawo maki, Aiko ta fara kici kicin cirewa, ammi ta fito tace kada ki sake ki cire, 

Ta fara kuka, tace wallahi bana so, 

Sai na cire, Akan me ze kawo min kaya, 

Kuka sosai take, ammi tace nide nace kada ki cireshi, iya karfinta ta dage tana kuka, 

Ta fara cirewa, mommy ta shigo, tace lafia? 

  Ammi tace kaya ne na dinka mata, 

Shine fatima tace sadiq ya kawo mata. 

Seda ta cire, 

Ta tsaya daga ita sai pant, Yaya fatima tace ke wasa nake maki, ba kunya ta maida kayan, Yaya fatima tace ke shine ya kawo maki, 

Kinga harda su chocolate da biscuit, gashi, ta mika mata, Aiko, fasa ihu, Tare da wurgi da ledar. 

Ammi na daria, ta kai ma fatima duka, 

Tace wai ke miye haka, 

Duka daria, suka hau mata,, seda ta cire kayan, 

Yaya fatima tace wasa nake kisa, tace wallahi bana son kayan, ba zansa ba, 

Koma bashi ya kawo min ba. 

  Ta canza kaya, wannan kaya dakin ammi ta maidashi, dan bata son ganinshi, 


  Mommy tace kai lubabatu da abin daria kike, haka zaki je boarding din kina masu? Tace mommy dan Allah ki dena maganar boarding din nan, ba zani ba. 

  Tunda ga ranar lubabatu bata fita, 

Kada ta fita sai ta duba, taga baya waje, idan ko yana nan ba zata fita ba. 

 Koda ta fita, suka hade, to zata canza hanya, 

Komin nisan tafiyan sa tayi, ta gwammace ta koma, 

KO ta shiga wani gida har sai ya wuce. 

Bata samu kanta ba sai da ya bar garin, Sannan hankalinta ya kwanta, 

Taci gaba da hidimanta.


Suna nan zaune, Yaya sultan ya kira mommy, Bayan sun gaisa, tace gafa mutuniyarka nan kwance ba lafia, Yace subhanallahi, meya sameta? Mommy tace dan zazzabi ne, tama warke, Yace bani ita, ta mika mata, ta amsa, Yace yaya jikin?

 cikin shagwaba tace har yanzu, Yace ayya sannu ko, tace yaya sultan yaushe zaka dawo? Yace kada ki damu, zan dawo, tace ni na kosa ka dawo, gidan ba dadi, Yace ai shekaru kadan ne, zan dawo, kici gaba da ganina, yanzu kinga baki da lafia, bari na kyaleki, anjima zan kara kiranki ko. Tace ina wannan jarababben? Yace wa ke nan? Tace ai ka sanshi, yayi daria, Yace yana nan, Wai anya kuwa ciwon nan, kina surutu haka, tace eh mana kwance fa nake, Yace ayya to sai na kira anjima, suka yi sallamay, ta mika ma mommy wayanta. Mommy ta mike, ta tafi gida, bata jima ba, can sai gashi, mommy ta bada an kawo mata farfesun kifin, tace yauwa aiko na gode, 'Yar sa aikin, tasa zurfa'u ta kawo mata plate, nan ta zuba ta fara ci, Yaya fatima ta kalleta, tace sannu da aiki, ba tare da ta kalli yaya fatima ba, taci gaba da cin abinta, sai affan dake zaune, tana bashi a baki, 

bala ya shigo dauke da leda a hannunshi, tace yauwa bala, kawo min nan, daria ma ta bama ammi, ammi tace ke lubabatu ina zaki kai Wannna uban abubuwan? 

 Ai da kyar idan ba kiyi zawo ba, tace ammi kin san idan ban da lafia, nafi son irin haka, Yaya fatima tace kede kika sani, haka ta jawo ledar ta fara shan fruits din da aka kawo mata. 

  Seda ya isheta sannan ta mike tasa sauran a fridge, ta dawo ta kwanta. 

Ammi tace ai tashi zakiyi kiyi shirin islamiyya, 

Ta rufe idonta, tace ammi har yanzu fa jikina na ciwo. 

 Dole aka kyaleta, seda ta kwana biyu bata je ko ina ba, da an tabata, tace bata da lafia. 

Kullum yaya sultan sai ya kirata, yaji ya jikinta, sai su dade suna fira. 


   ***************

Zaune suke ita dasu jamila, a gidansu jamila, ta kalli jamila, tace kashi nake ji, zo ki rakani, suka mike, sukayi hanyar toilet din su jamila, mamanta tace ke jamila ina zaku? Da karfi tace zan raka lubabatu kashi ne, lubabatu tace dallah banza jaka, shegiya, dakikiya, mara mutunci,yanda kika tona min asiri, kema Allah ya tona maki naki, 

jamila tace me na maki? Tace akan me zaki wani ce zaki rakani kashi, Ai wannan tonon asiri ne, 

  Kina ganin gidanku cike, jamila tace shine zaki min wannan zagin, 

Tace eh din na maki, ta fita gidan rai a bace, tayi gida, 

Ammi tace ke kuma lafia, zaki shigo ma mutane daki ba ko sallama? 

Tace nida wannan banzar jamilan ce, dan nace ta rakani inyi kashi shine harda wani tona min asiri, a cikin gidansu.

 Ammi tace shine abin tona asiri, ni dadina dake shirmanki yayi yawa. 

Ta mike ta shiga toilet, Bayan ta fito, tace ammi na tafi gidansu jamila, dama wani abu muke yi, ammi tam lokacin islamiyya fa y kusa, 

Tace tare dasu zamu tafi, kinga ma na dauki hijabin makarantana, 

Ta fice, ta koma, jamila tayi banza da ita, lubabatu tace au dan ma kin samu na dawo gidan, 

Ai kema kin san baki kyauta ba, saboda idan ke nayi ma haka ba zaki ji dadi ba, 

  Jamila tace to jibi fa zagin da kika min, lubabatu tace to shikenan kiyi hakuri, amma fa kada ki kara Min haka, 

Sai kuma suka ci gaba da wasansu, 

Lubabatu tace kuzo muje wurin sa'adatu mai wara, suka fice, suna isa, wata mata na tsaye, tazo siyan wara, lubabatu ta kalleta, 

Tace la kuga wata mai gemu, gashi ance duk mace mai gemu mayyace, 

Matar ta kalleta, zata kamota ta matsa, tace kada ko taba ni, tace ke ni tsararki ce, tace to ai duk mace mai gemu mayya ce, ta maida abin waka, Harda rawa, tana fadin duk mace mai gemu mayya ce, duk mace mai gemu mayya ce, 

Suma suna tayata, da gudu matar ta biyosu, suka ruga, tace dan Allah ina ne gidansu? 

Wani yaro ya nuna mata gidansu lubabatu, 

Da har ta shige gida, matar har gida tazo, tace na kawo karar yarinyarku, ammi Tace to ai suna makaranta, 

Lubabatu dake make a kitchen, tana jinsu, 

Matar Tace to bata je ba, Ita da yaran unguwa, suke tonona, itace ma ta fara, suna fadi min duk mace mai gemu mayya ce, ammi Tace au bata tafi ba dama, to yanzu tana ina? 

Matar Tace nan gida t shigo, abba dake daki ya fito, yace to ya akayi kika kyaleta bata je ba, tace ni Tace min ita dasu jamila zata tafi, tun dazun bata gidan, abba yace wato bata dena biye ma yaran unguwa ba, akan me zaki rinka barinta tana fita? 

  Yarinya gaba daya ba natsuwa, nasan maganinta, dan Allah kiyi hakuri, 

Matar Tace bakomai, nide na kawo kararta ne, dan kuja mata kunne. 

Yace to mun gode, ta fita, ya fara kwala ma lubabatu kira, tayi shiru, 

Ya zauna yace zanga ta inda zaki bullo. 

 Yana nan zaune, da ta gaji da zaman kitchen din, ta leko, ta ganshi zaune, kuma tana tunanin ammi zata iya shigowa kitchen din, 

Da gudu ta fito kitchen din, Kafin ya mike ya kamata, har ta fice gidan, 

Tayi wurin mommy, 

Yace ina nan, zaki dawo ki sameni.

 Abba ne suka shigo shi da bala yana dauke da katifa, lubabatu dake zaune kan kujera, tana shan cornflakes taga sun shigo, rike cup din tayi, ta saki baki tana kallonsu, 

Abba yace ya akayi kike kallonmu ba magana? 

Cikin sarkewa, tace abba wannan katifar fa? 

Yana daria yace naki ne, ammi ta fito, tana mashi sannu da zuwa, bala ya aje katifar, ya fita. 

  Ammi tace au tafiya makarantar ta kankama? 

Yace gashi kuwa kin gani, ya samu wuri ya zauna, 

Lubabatu ta kasa cewa komai, ji tayi gaba daya, cornflakes din ya fita a ranta, 

Tace pls abba ka temaka min, wallahi zan natsu, Yace lubabatu na riga na gama magana, har an samo maki, 

Yaya fatima, tace miye abin damuwa, keda zaki kici dadi, 

Tace eh din naji bana so,

Ta fara kuka, abba yace kyama hakura, 

Tashi muje ayo maki siyayyan da zaki tafi dashi, tace abba bana so, taci gaba da kuka, ya kalli Ammi, Yace bari na dan huta, sai mu fita, muyi mata siyayya, saboda monday nake so ta tafi, ta fashe da kuka, tace wayyo na bani wallahi bana so, mutuwa zanyi, 

Abba yace zaki rufe min baki, ko kuwa? 

Tayi shiru, amma sai kukan cikin zuciya take, 

Sai da abba ya gama komai, Sannan suka fita tare da Ammi da yaya fatima, nan lubabatu ta zauna ba tare da ta motsa ba, taci kukan har ta gaji, sai ajiyar zuciya take. 

Har suka dawo, tana nan zaune ba tare da ta bar wurin ba,


  abba yace ke malama, har yanzu kina zaune nan. 

Tayi shiru ba tare da ta kallesu ba, 

Yaya fatima tace kalli siyayyan da aka yo maki, 

Ammi ta zauna kusa da ita, tace kiyi hakuri, 

Baki ga da kinje ba, Ba zaki dade ba, 

Za ayi hutu, tace mommy dan Allah kada ku kaini boarding school, 

Wallahi bana so, abba yace sai kinje, 

Yaya fatima tace kije kici karanki ba babbaka a f.G.C ba ruwanki da matsala, 

Cikin kuka, tace abba kana jinta ko. 

Yace fatima kyaleta, kowa ya tashi ya barta wurin, bata da niyyar tashi, 

Zainab da khadija suka shigo gidan, 

Zainab tace lubabatu meya faru? 

Tace zainab abba yace dole sai ya kaini boarding, 

Ni yanzu ya zanyi? 

Khadija tace kiyi hakuri, kinsan halin abba, tace kunga har an gama min siyayyan kaya, nan suka zauna, suna ta bata hakuri, Yaya sultan ya kira, kuka kawai take mashi, duk hankalinshi ya tashi, 

Yace kiyi hakuri da na dawo za a cireki. 

Da kyar ya samu tayi shiru. 

  Ranar ko, ko abinci taki ci. 

  

   ************

Yau take monday, gaba daya, an gama mata komai, mommy seda ta mata miye cike da nama, banda siyayyan da ta mata, gaba daya suka shirya dan rakata, kuka kawai take, 

Ana cikin motar cikin kuka tace Allah yasa muyi hatsari, gaba daya mu mutu, da sauri har suna hada baki suka ce ba ameen ba, Ammi tace baki da hankali ne? Ana isowa, ji tayi gabanta ya fadi, har ji tayi tana jin kashi, suka shiga cikin school din, ji tayi hankalinta ya kara tashi, sune har office din principal, sai kuka take, 

Principal tace kai lubabatu, wannan kuka haka, duk rabuwa dasu mama ne? 

Zo nan, ta jawota, tace kada ki damu, 

Kinji, nima kamar mamanki ne, Idan kina da wata matsala, ki fada min. 

Kada ki damu, kuka kawai take, principal tace bari in nemo house captain dinku ko, tasa aka kira mata, 

Tazo, tace to ga yarinya kin samu, ina so ki kula da ita, tace to, 

Su Ammi suka tashi zasu tafi, kuka sosai take,Harda rike mommy, 

Tace mommy kada ku tafi ku barni, 

Jibi duk yanda 'yan school din suke, 

Se kace' yan prison, ni ba zan zauna ba, 

Principal da kanta ta rike mata hannu, 

Ta kaita class dinta, haka lubabatu ta zauna a class din tana ta kuka.

 Har yanzu kuka take, taki yin shiru, 

Wata mai suna Amina dake kusa da ita, 

Tace kiyi hakuri, meyasa kike kuka haka? 

Keda ba dadewa zaki yi ba, za ayi hutu, 

Lubabatu tace ke bana son boarding school, 

Amina tace to meyasa kika zo? Tace babana ya kawoni, Amina tace to kiyi hakuri, ki daure, kowa daurewa yake, da kin kwana biyu, zaki ji kin saba, Lubabatu tace sabawa fa kika ce? Ai bana jin zan saba, dan boarding school jinshi nake tamkar kurkuku, dan haka ba zan saba ba, 

Taci gaba da kukanta, Ranar de lubabatu ba zan karatun da ta dauka, 

Kuka kawai take, har aka tashi, Amina tace muje in rakaki, ki dauki kayanki, 

Tare suka tafi, suka hade da house captain dinsu, suka jera, lokacin principal ta fito, tace haba lubabatu har yanzu kukan kike? 

Kiyi hakuri keda kike a cikin kaduna, wasu ma daga wani gari fa aka kawosu, 

Kiyi hakuri ko, 

Ta daga mata kai,gashi ma har kin samu kawa, tade yi shiru, suka dauki kayanta, har hostel dinsu, 

Amina tace kinga ma hostel dinmu daya, 

Lubabatu de bata ce mata komai ba, 

Kwanar house captain suka aje kayanta, tasa tayi sallah, 

Ta kalleta, tace lubabatu me kike son ci? 

Cikin kuka tace bana son cin komai. 

Tace ya zaki zauna da yunwa, fada min abinda kike so in hada maki. 

Tace ki kyaleni nace ba zanci komai ba, 

Ta fashe da kuka, tace gida nake so na koma, 

Wata ta shigo, tace wace rigimarmar muka samu haka? Ta leko, Lubabatu ta bita da harara, 

Dan ji take, Kamar ta kamasu da duka. 

Ta kara kallon cikin dakin, tace yanzu a nan zanyi rayuwa? Dan Allah ki temaka min, in tafi gida, house captain din ta dawo kusa da ita ta zauna, wadda ta leko, tace tofa suwaiba an hadaki da rigimamma, 

Ta wuce, 

Ita kuma ta dafa lubabatu, tace kina so in maidaki gida? 

Da sauri ta daga mata kai, tace to kici abinci tukunna, kinga tunda ga bread nan da miye, 

Fara ci ko, da kanta tasa mata miyar da tazo dashi, ta amsa, tana ci tana kuka, gaba daya, turashi ma take, ba dan tana jin dadi ba. 

Ta aje, tace na koshi, bana son ci, suwaiba tace mata, bakya so kije gida, 

Suga kinyi kiba, idan suka ga kin rame, 

Ba zasu ji dadi ba, 

Ta zumburo baki, tace ai gara suga na rame din, ko zasu cireni a wannan prison din da suka kawoni. 

Suwaiba tayi daria, tace lubabatu kina da tsiwa ko? 

Tayi shiru,.

Tace mata to tashi kiyi wanka, tasa aka kai mata ruwa, ta dauko towel dinta, 

Ta fice dan tayi, 

Wurin wankan ma haka tayi ta kuka,

Tayi duke, ita ba tayi wankan ba, Ita ba ta tashi ba, 

Ta tuna toilet dinsu, ga heater a ciki, 

Sai de ta tari ruwan zafi tayi wanka, 

In taso ma ta karar dashi duka, tayi ta wasa da ruwa, 

Gashi yanzu da na sanyi zata yi, 

Hawaye ya zubo mata, ta share da hannunta, ta mike, ta kwara ruwan a jikinta, ta daura towel dinta ta fito, 

Ta ciro mai ta shafa, suwaiba tace mata to ga house wear dinki nan kisa, mu tafi prep ko, tace prep kuma? 

Me zamuyi a can? 

Suwaiba tace karatu, kinga ana yin evening prep, 

Da kuma night prep, Lubabatu tace innalillahi, shi mutum beda hutu kenan? 

Harda dare ba za a bar mutum yayi barci ya huta ba, hawaye ya zubo mata, 

Amina ta leko Kwanar, Suwaiba tace yauwa Amina gata ku wuce prep ko,

Ku fara wucewa masallaci ko, suka fito Amina sai fira take ma lubabatu, 

Ita de bata ce mata komai ba, har suka isa masallaci, sukayi alwala, suka shiga masallaci, saida aka kira sallah, 

Suka yi sannan suka wuce class, Amina ta bata books dinta dan tayi note din da sukayi, itama ta rinka tayata, 

Har suka tashi, suka wuce games, ji tayi ranta ya kara baci, saida aka gama wasanni, Sannan suka koma hostel, 

Basu dade ba, suka fito dan yin sallan magriba, 

Duhun da ta gani, yasa hankalinta ya kara tashi, har suka yi isha'i, 

Suka wuce night prep, 

Tana zaune, tama yi note din duk ta gaji, 

I zabga uban tagumi, sai hawaye, tace ke wai a haka zamuyi ta zama, mutum beda hutu, Amina tace zaki saba fa, dan yau aka kawoki. 

Lubabatu tace dan Allah ki dena cewa zan saba, yanzu ammi suna can kwance a wuri mai kyau, suna barcinsu, nasan yanzu yaya fatima tayi barci, affan dina ma haka. 

Niko gani nan rike da book, yau ban wuni a waya tare da yaya sultan dina ba, da yana nan, baze bari a kawoni prison a yasar dani ba,

Ta fashe da kuka,Amina tace ayya kiyi hakuri, a haka de har suka tashi, ba abinda tayi, sai kuka, 

Dan ita gani take, ba zata jure ba, Ta dare gado ta kwanta, duk barcin da take ji, ji tayi ta kasa, se juya take, tana tunanin gida, Sede barci barawo ya saceta, data fara zata farka,

A haka har asuba tayi, Sannan barci mai nauyi ya dauketa, Sede taji ana ku tashi ku tafi masallaci, kara jan abin rufa tayi, suwaiba ta tadata, 

Ta kara narkewa a kan gado, dan yanzu take jin dadin barcin, tace nan ma, ba za a bar mutum ya huta ba, 

Taja tsaki, taci gaba da barcinta, sallan da bata je ba, Sede suwaiba ta kyaleta, tayi a daki, se kuma akayi shirin tafiya class, suwaiba tace kici wani abu kafin ki fita ko, 

Ko ki tafi dashi class, da break kici,.

Lubabatu tace ba abinda zanci, ta rataya school bag dinta, ta fito, fuskan nan a daure, Amina ta fito, Tare suka jera har class, ta samu wuri ta zauna, ta kalli Amina tace gaskia ba dadi zaman school din nan. 

Amina tace dama hakane, gaba daya lubabatu duk tayi shiru, ko magana bata son yi.


   *** *** ******

Bayan sun tashi, Sun koma hostel, tayi wanka, ta Dauki kaya, zata sa,

Zariyar wandon ya cukwikwiye, sai janshi take, yaki warwarewa, ta fara kokarin fizgewa, Harda hawayenta, 

Tana ja, ni wallahi na gaji, bana son zaman makarantan nan, suwaiba ta shigo, tace lubabatu ya akayi? 

Tana hawaye, tace bakomai, ta amshi wandon dake hannunta, ta zauna, ta gyara mata, tace lubabatu kiyi hakuri kinji, tana hawaye, 

Tace yaushe za ayi hutu? 

Suwaiba tayi dan murmushi, tace nan da kwana goma sha tara, Lubabatu ta jawo jakanta, ta Dauki paper da biro, ta rubuta kwanakin da ya rage, tace kinga kullum zan rinka cancel din daya, 

Suwaiba tace yafi maki ko? Ta daga mata kai, Tun daga ranar, data tashi da safe, sai tayi cancel din daya. 

ta shirya suka fita, tana zaune, can hanyar gate ita fa Amina, Amina tace kizo mu tafi, 

Lubabatu tace nafi so inta gani mota da masu fita, Amina tace shikenan, 

Lubabatu tace sunji dadi, amma mu anzo nan an yasar damu, sai kace marasa galihu, nide wallahi Allah ya tsine ma wanda ya kirkiro boarding, daria ma ta ba ma Amina. 

Da sauri lubabatu ta mike, tace kai kalli motan gidanmu, ta ruga da gudu, tana tsaidasu, suka tsaya, 

Bala yace ya akayi 'yar gidan yaya sultan, 

Sai kuma ta fara hawaye, duka suka fito, 

Yaya fatima tace kai lubabatu duka yau kwananki biyar, amma jibi har kin rame, tace ba dole in rame ba, 

Amina ta karaso, zainab ta rike lubabatu, tace da ba kya nan, gidan ba dadi, 

Tace kai ni kawai burina in bar makarantar nan, bana sonshi, Yaya salma tace kiyi hakuri, hawaye ya zubo mata, Yaya fatima tace bari mu tafi, tunda kuka zaki rinka yi, ta dauko food flask, 

Ta mika mata, tace gashi mommy tace a kawo maki, tasan kina son farfesun kifi, shiyasa ta maki. 

Lubabatu tace bana so, ko miyan da aka min ma ban shanye ba har yanzu, 

Yaya fatima tayi daria, tace duk cinki yanzu, ba kya cin abinci? Lubabatu tace idan kun san bata min rai zakuyi, kawai ku tafi, Yaya salma tace kiyi hakuri, ta kalli zainab, tace ke ko magana, sai wani faman kallona kike,Kamar baki sanni ba, 

zainab ta danyi daria,Yaya fatima tace ga kawa ma kin samu, 

Amina tayi murmushi, tace ai taki ta saba, 

Ita dama take cikin gari, Yaya salma tace wane gari kike? Tace ni 'yar zaria ce, Lubabatu tace kuma kika yarda aka kawoki? Amina tace ai ni dama nafi son boarding school. 

Lubabatu tace lalle, 

Bala yace kuzo mu tafi, magriba ta kusa, 

Lubabatu na hawaye, tace ku gaida min dasu ammi, da mommy, da affan dina, tana kallo suka tafi, sai hawaye take, Amina ta dauki flask din sukayi hostel, 

Amina tace kima ji dadi, gashi 'yan gidanku sunzo kin gansu, amma ki rinka damuwa, 

Ki saki jikinki. 

Amina da kanta ta sa masu, suka hada da bread suka ci, 

Suka bar ma suwaiba sauran. 


   Suma suna komawa gida, abba yaji labarin sunje wurin lubabatu, 

Yace duka yaushe aka kaita, da zaku je, salan ku sa taki karatu, in ba visiting ba, kada in kara ganin wani yaje, ko ba tana bukatan wani abu ba. 


   **********

Kwanaki sun tafi, gashi gobe za suyi hutu, in banda dadi ba abinda lubabatu take ji, sai murna take,

Ta zauna tayi packing din komai nata, 

Dede da ledar indomie da duk wani abu da tazo dashi, saida ta hada dashi, ta fara nade katifa, suwaiba tace ina zaki dashi? Lubabatu tace gida, dan bana son in bar komai nawa a school din nan. 

Suwaiba tace ki barshi, ba abinda ze faru dashi, Sannan ta barshi. 

Washegari kuwa, tunda sassafe ta baro hostel, 

Sai murna take, Amina tace dama kina daria haka? Lubabatu tace gashi kuwa kin gani. 


  Ana bude gate gaba daya duk wasu sun fara tafiya, tana ganin 'yan gidansu, sai murna take yaya fatima tace yau ba kika kenan? 

Amina sai daria take mata, Lubabatu ta kalli Amina, tace to mu zamu tafi, sai nazo daukanki kenan? 

Ta shiga mota, sai daga mata hannu suke,

Suna fita, taji iskan waje ya ratsata, 

Harda lumshe idanu, da sakin ajiyar zuciya, 

Suna isa gida, da gudu da shige, Sede ta bari, suka shigo mata da kayan. 

Ammi tace to 'yan boarding an dawo? 

Da murnarta ta daga affan, sai murna shima yake. 

Ta zauna, Ammi tace ya naga kinyi baki, 

Lubabatu ta bata rai, tace ba dole inyi baki ba, 

Kunje kun kaini inda mutum zeta wahala, Tun asuba idan mutum ya tashi, shida barci sai dare, sai akai har sha daya ba ayi barci ba, 

Ta fara hawaye,Ammi tayi daria, tace to miye abin kuka, tashi kije kiyi wanka, 

Ki dirza jikinki sosai fa, ta mike, Ranar lubabatu tayi wankan jin dadi. 

Tana fitowa, aka zauna, aka yi makeup, 

Ammi ta dauko mata sabon kaya, tace gashi kisa, tace Ammi na gode, 

Saida ta yi break, Sannan tayi gidan mommy, tana shiga, ta fada jikinta, mommy na daria, tace 'yan boarding, naga duk kin rame? 

Tace ba dole ba, Ai boarding bala'i ne. 

Nan ta zauna tayi ta basu labari, 

  Sukaita daria, idan suka ji wani, 

Bayan sun koma gida, ta bude jakanta, 

Ammi tace to ke ai duk baki wani ci komai ba, 

Tana ta fiddo kayan ciki, taga sai ciro ledojin indomie, Na biscuit duk gasu nan, Ammi tace wannan bolar da da kika kawo mana? Wannan takardar fa? 

Lubabatu tace kwanakin da ya rage, Na rubuta, shine nake cancel kullum, suka yi daria, Sannan tace wadannan ledojin abinda yasa na dawo dasu, saboda ba zan baro komi nawa ba, 

Shine mu kika kawo mana, Ai bola ne, Yaya fatima tace ai ke lubabatu, har yanzu baki da hankali. 

Ammi tace to Kwashe ki kai bola, ta kwashe ta fita dasu, 

Ammi tace naga ko abbanki baki tambaya ba? 

Tace tunda ya kaini boarding ba ruwana dashi, 

Bani waya in kira yaya sultan dina, 

Ammi tace sede ki nemi wayan da zaki kirashi, 

Tunda kin nuna baki damu da mijina ba, 

Lubabatu na daria, tace to Ammi ya hakuri, ki bani inji muryanshi, Ammi ta mika mata, yana dauka, Kamar Zata fasa mashi kunne, tace yaya sultan shima cikin murna yace lubna kin dawo? 

Bani labarin boarding, nan tayi ta bashi, suna fira, tace yaushe zaka dawo? 

Yace na kusa kada ki damu. 

Sun dade suna fira, Sannan sukayi sallama. 

Koda abba ya dawo, bayan sun gaisa, 

Cewa tayi abba dan Allah ka cireni, ni ba zan koma ba, Yace hakanan zaki yi hakuri, ki koma, tace abba kasan me? Yace a'a, tace akwai 'yan secret code a school din, idan baka cireni ba, zan shiga kungiyarsu nima, daria ma tasa abba, Yace to idan kika shiga kungiyar sai mu bada ke sadaka kawai, 

Tace abba yanzu na gane baka kaunata,

Bakomai, tayi shiru, daga karshe ma ta mike, tayi daki, tayi kwanciyarta. 

Barci nan ya dauketa, dan akwai barci a idonta.

Haka taci gaba da zaman hutu, tana jin kamar ba zata koma ba, ranar ko da aka koma school, harda zawo, 

Haka tayi tayi, harda kwanciya ciwo. 

Yaya fatima tace ammi wallahi ba wani ciwo da take yi, duk pretending ne, Lubabatu ko tanka mata ba tayi ba, dan ita cikin tashin hankalin komawa take, 

Abba yace a bari wani satin sai ta koma. 

Ana gobe zata koma kuwa, ba wanda ba tayi fada dashi ba, dan bata son kowa ya tanka mata, Ranar ko da zata koma, haka ta rinka tima, tana ihu, yanda kasan ana dukanta, 

Da abin ya bama ammi haushi, ta dauketa da mari, ta kara dauketa da mari, tace ni na kaiki makarantar, da zaki nemi ki rinka daga min hankali? 

Ta kara kai mata duka, kara wage bakin tayi tana ihu, tana fadin ni wallahi ba zan koma ba, meyasa sai ni kadai za a kai, saboda ba a kaunata, in ba ku kuka haifeni ba, ku kaini wurin wadanda suka haifeni, ammi tace au ni kike fada ma haka? Dukanta taci gaba dayi, mommy ta shigo gidan, tace haba wai me yake faruwa hakane? 

Ta rike lubabatu, tace duk komawan ne haka? 

Tace mommy bana so, ba dadi, bana jin dadin zaman can, dan idan ba a cireni ba, ba karatun da zanyi, 

Ta fashe da kuka, mommy tace kiyi hakuri, 

Kafin ki dawo, zansa abbanki ya cireki kinji, ki koma din, Kada ki damu. 

Yanzu me kike so? 

Tace bana son komai, mommy tace a'a fada min inda abinda kike so, 

Cikin kuka, tace ki bani tarugu kawai inta ci, har in mutu, dan da inci gaba da makarantar nan, gara na mutu, 

Mommy ta kara riketa, tace haba lubabatu, bani nace zansa a cireki ba, 

Kada ki damu, ko baki yarda dani bane? 

Tace a'a, mommy tace to gama shiryawa, a maidaki ko, ta saketa, 

Lubabatu tayi cikin daki, mommy tace ma ammi, ki dena dukanta, lallabata ya kamata ayi, ammi tace ita kullum 'Yar lallabawa ce? 

Bafa tada hankali har yanzu, Lubabatu na shiga daki, wasu kaya ta dauka, na gida, tasa a leda, 

Ta fito, ta taddasu tsaye duk zasu rakata, 

Ta kallesu, tace duk bana son rakiyar kowa,. Ta fice, ko kallon inda bala yake, ba tayi ba, sai magana yake mata, haka ta fice, ammi ta biyota, tace ke ina zaki? 

Nan waje ta tsaya tarar machine, tana hawa, Yaya fatima, tazo ta riketa, tace ma me machine din tsaya ta sauka, Lubabatu tace ki kyaleni ba ruwanki dani, tace ki sauko, 

Lubabatu tace ba zan sauko ba, Yaya fatima tace to haka zaki koma ba abinci? 

Lubabatu tace ina ruwanki, haka ta dage ta ture yaya fatima, tace ma me machine din, wuce mu tafi, F. G. C zaka kaini, ya tada suka wuce, 

Ammi ta kalli mommy tace kinga halinta ko? 

Mommy tace kyaleta, bala yaje ya kai mata, 

Ammi tace haba yarinya, zaki gane kuranki, se kici abinda zaki ci ai. 

Suna isa, ta sauka, ta sallameshi, ta shige cikin school din, nan ta hadu da wata ta dawo, suka jera, tace mata, dan Allah kwana nawa zamuyi ayi hutu? 

Yarinyar tace mata, Kin san zamu dade, tunda third term muke, 

Sai munyi kusan 3 months, shiru kawai tayi,

Hawaye ya zubo mata, har ta isa hostel, 

Amina na ganinta, da gudu, ta rugo ta tareta, 

Tace sai yau kika dawo ko? 

Tace banma yi niyyar dawowa ba, 

Dan ba yanda zanyi ne, Amina tace to ya na ganki haka, ina sauran kayanki? 

Naga daga ke sai school bag, Lubabatu tace can na barosu, Amina ba zan taba son boarding school ba, 

Na tsaneta, har yanzu ina tsine ma, 

Wanda Ya kirkiro boarding school. 

Allah ya tsine mashi, dan ina jin na tsine mashi, yakai sau chasa'in da tara, cikon na darin, sai randa na bar makarantar, daria ma taba ma Amina, tace kai Lubabatu, boarding school fa yana da dadi, kinki natsuwa ne ki lura, 

Anfi karatu ma sosai, Lubabatu tace ke kika ga haka, dan ni ba karatun da zanyi, Wai da gaske zamu kai wata uku a nan? 

Amina tace eh mana, mu da gida sai august, Lubabatu tace ai yakai wata hudu ma, taf lalle kuwa, 

Amina tace kin san ai third term ne, 

Su aunty suwaiba kuma, zasu gama su tafi su barmu, Lubabatu de bata kara cewa komai ba, suka isa daki, suwaiba ta ganta, tace Lubabatu sai yau? 

Ta gaidata, ta aje jakanta, ta rafka tagumi, ita de suwaiba ta bita da kallo.


      ***************

Haka yaci gaba da Zama cikin school din, 

Taki ta saki, kayan provisions dinta kuwa, haka ta rinka barna dashi, 

Ta hada wannan, ta wancan, Amina tace lubabatu ki dena almuzaranci, zafa a dade, Lubabatu tace bade sun kawoni ba, 

Amina tace kafin ki ga na gida, zafa kisha wahala, 

KO dan kina ganin a garin kike ko? 

Lubabatu tace ko daya, kudinsu ne ze gaya masu, bade sun kawoni boarding ba, mu zuba ni dasu, 

Amina tayi daria, tace lubabatu wani zubin kina bani daria, 

Tafe suke, zasu school area, ta Dauki dutse tana jefe jefe, can wani malami yazo wucewa, tana jefa dutsen, ta jefa a kanshi, da sauri ya juyo, Lubabatu ta kauda kanta. 

Yace kai waye ya jefeni a cikinku? 

Amina tace sir bamu bane, kayi hakuri dan Allah, 

Lubabatu ya kauda kanta, tana wasa da wani dutsen a hannunta, ya jawota, Yace ke kika jefeni ko? Tace bafa da gangan na maka ba, haka ya kaimu har staff room, Yace zaki sani, tace mallam nafa ce maka ba da gangan nayi ba, Yace Amma ai yanda kika nuna, yasa naga da gangan kika yi, dan haka sai na zaneki, tace mallam kada ka bigeni, Amina kallonta ta tsaya yi, 

Dan tasan yanda ake tsoron malamin, amma taga ba alamar tsoro a idon lubabatu, saboda ya haddaci mugunta, 

Haka ya dauki bulala ya zaneta, Yace tashi ki bace min da gani, useless girl. 

Suka fito, 

Lubabatu tace wallahi Amina kinga dukan nan, bashi ya dauka, dan ba zan kyaleshi ba, Amina tace to me zaki mashi? Lubabatu tayi murmushin mugunta, tace kede kisa ido ki gani, Amina tace ni dukan da ya maki ma, tausayi kika bani, amma naga ke baki damu ba, 

Tace ai ba zan damu ba, nide burina kawai in rama abinda yamin, 

Kuma sai na rama, ze san ya taba Lubabatu. 

Suka wuce.

Amina tace dan Allah lubabatu kiyi hakuri, 

Bana so wannan malamin ya sa maki ido, 

Lubabatu tace taf aiko zamu sa ma junanmu kuwa, dan idan yanzu na mashi, yamin wani fa zan kara mashi, 

Amina baki san halina bane, wallahi idan kinga ban rama ba, sai de in mutuwa nayi, Amina tace to yanzu ya zakiyi? 

Lubabatu tayi murmushi, tace kisa min ido ki gani, 

Tun daga ranar idonta yake a kan mallam shamsu, 

   Sun shiga class, taje kujeran malamai, 

Ta tsira allura guda uku a kai, ta samu sit din gaba, wurin rabi'atu ta zauna. 

Rabi'atu na zuwa, tace dan tashi min a wuri, 

Lubabatu tace ba zan tashi ba, rabi'atu tace aiko sai kin tashi, Lubabatu ta kalleta, tace ke ba zan tashi ba, 

Rabi'atu tace oh har kin gama kukan makarantar ne, zaki shigo mana da naki salon rashin mutuncin? 

  Lubabatu tace sosai kuwa, rabi'atu tace to tashi min a wuri, Lubabatu tace wai in tambayeki mana, 

Lokacin da aka kawoki ubanki da kujera ya kawoki school din? Tambayarki nake, ashe ba dashi ya kawoki ba, to ba zan tashi ba, 


  Form master dinsu ya shigo, Yace kai ku kuma lafia? 

Rabi'atu tace sit dina ta zauna, yace ke lubabatu koma naki, tace mallam nifa ba na zauna a nan bane, 

Dan in dauwama, wani dan abu kawai zan aiwatar in tashi in bar mata wurinta,saboda a nan din zefi min dadin gani. 

Yace to rabi'atu ki koma nata idan ta gama, sai ki dawo, rabi'atu ta wuce kusa da Amina ta zauna, 

Amina tace kiyi hakuri, rabi'atu tace ba damuwa, 

Daga ganinta tana da taurin kai gaskia. 

Suna nan zaune ko ya shigo, Lubabatu sai faman murmushi take, 

Bayan sun gaidashi, gaba daya yaki zama, 

Ya kake a tsaye, Lubabatu cikin magana, kasa kasa, tace ka zauna mana. 

Ya Kalli lubabatu yace ke ina hankalinki yake? 

Ana lesson hankalinki na wani wuri, 

Ta kura mashi ido, Wai me ma ya dawo dake gaba? 

Tace ra'ayi.binta kawai yayi da kallo, yana mamakin halinta, 

Yaje zai zauna, Lubabatu ta fara murmushi, 

Wata a class din ta mashi magana, 

Ya dawo, Lubabatu harda cije lebe, 

Taji haushi, 

Bayan ya gama, Yace yauwa na tuna, 

Kowacce ta shirya, test zamuyi, 

Ya gama rubuta masu a kan board, 

Yace ten minutes na baku, 

Kowa ya jawo paper, 

Itade Lubabatu burinta taga ta rama. 

Amina se rokon Allah take, Kada Lubabatu tayi wani abin, 

Bayan sun fara, 

Ya koma ze zauna,yana dosana jikinshi, 

Ya zauna da karfi, da sauri ya mike, 

Yana duba kujerar, 

Ga daya alamun ta shigeshi ya makale a jikinshi, 

Yace uban me kuka sa a kujerar nan? . 

Lubabatu daria kawai take, ta samu ta daure, tace mallam ai gashi nan makale a wandonka, yasa hannu ya jawo, wurin cirewa ya kara jin zafi,Yace uban wa ya min haka? 

Lubabatu tace mallam ya za ayi muyi maka haka? 

Yace ku fiddo min da wanda ya samin allura, 

Rabi'atu tace mallam sede in Lubabatu ta maka haka, tunda gashi ma ba sit dinta ta zauna ba, 

Lubabatu tace akan me zan maka haka, 

Tunda itace taje ta zauna min a wuri, 

Oh se yanzu na gane, ashe shiyasa kika zauna min a wuri, saboda kin san munafuncin da kika hada, to mallam rabi'atu ce, 

Ta bita da harara, Harda murguda baki, shide sai faman murza wuri yake, 

Ranshi a bace, 

Yace dan kunga na tsaya ina sauraranku, every body kneel down, 

Duka sukayi, 

Yace rise up your hand, Lubabatu tace sunan uwar, Close your eyes, 

Tace sunan uban. 

Yace ke me kike cewa? 

Ta bude idonta, tace ni? 

Kasa ce mata komai yayi, ta maida idonta ta rufe, 

Suka fara bashi hakuri, 

Saida ya gaji dan kanshi, Ya kyalesu, 

Tare da zanesu, 

Yana zuwa kan lubabatu taki tsayawa, 

Sai zagaye class din suke, 

Gaba daya class din mamakinta suke, 

Can ya rikota, ta makaleshi, taki bari ya bigeta, 

Sai cukwikwiyeshi take, 

Amina duk hankalinta ya tashi,Lubabatu tace mallam kada ka bigeni,wanda ka samu ma yayi ai, 

Ya samu ya kai mata duka, ya riketa, 

Yace ban yarda dake ba, ke kika aikata min haka, 

Ya kara zura mata bulala, ta rike bulalan, 

Ya kai mata mari, 

Saboda har yanzu abin na damunshi, 

Gani yake raini zai shiga tsakaninshi da students, idan ya kyaleta. 

Ya dinga kai mata duka, ta tureshi ta fice, 

Ya kallesu ranshi a bace, ya fice class din, 

Ta dawo class din tana daria, mamaki ma ta basu, yanda suka ga bata damu ba, 

Ta dawo wurinta tace tashi rabi'atu ki koma wurinki, ta mike, 

Duka sai fadi suke wanda yasa aka bigemu Allah ya isa, Lubabatu tace kude kuka sani, 

Ta zauna, 

Amina tace lubabatu ki dena, tayi daria tace, ke ba wanda ya taba dukana na kyaleshi, sai iyayena, 

Dan haka ni dashi mu zuba, sai naga wanda ze saki a cikinmu, Amina tace lubabatu malaminki ne fa. 

Lubabatu tayi murmushi tace Amina kenan, 

Amina tace yanzu kuma me zaki mashi? 

Lubabatu tace ki kara sa ido ki gani. 

Amina tace idan ko zaki rinka sa ana hadawa da 'yan class, zaki ta shan Allah ya isa, 

Lubabatu tace akwai ranar da Zan rokesu gafara, 

Amina tace to shikenan, amma ni shawarata, da kin hakura, kina gani fa mun kusa yin exams fa,ze iya yaki barinki a class din, bare har kiyi exams din, gashi promotion exam zamuyi,yasa a maki repeating, dan ba mutunci gareshi ba, Lubabatu tace ai sai kiyi, yanzu naji na kyaleshi, har suka tashi, tana tunanin abinda zata aikata mashi na gaba, 

Gaba daya malamai da students sunji abinda tama mallam shamsu, 

Tunda an riga an gano ita tayi. 

   *****************

Kwanaki na ja, tana nan, tana tunanin abinda zata aikata mashi, 

Cikin school din malamai da students ba wanda be san lubabatu ba, yanda suka ga abinda takeyi, jss2 amma ta addabesu, dede da seniors basu son tabata, 

Sun san halinta, tunda ko an mata, bata damuwa, ita de burinta, ta rama, shiyasa suke lallabata, idan suna so ta masu abu. 

Gashi kwanaki kadan ya rage su suwaiba su gama, 

Yau take visiting, 'yan gidansu Amina sunzo, taje suka gaisa,haka ta zauna suna ta fira dasu, har karfe biyar lubabatu bata ga yan gidansu ba, Gaba daya, ranta ya gama baci, 

Sai can sai gasu sunzo, Harda abba, 

Tana ganinsu ta bisu da kallo, tace shine sai yanzu zaku zo, abba yace ke ko gaisuwa babu, baki ga yanda kowa ke taro iyayensu cikin murna ba, 

Tace ai baku zo da wuri ba, mommy na daria, tace to yi hakuri, 

Suka samu wuri suka zauna, 

Tace to meyasa baku zo da wuri ba? 

Abba yace yau muka koma sabon gidanmu, 

Mun manta da visiting, shiyasa muka tare a yau, Lubabatu tace ai dama dole ku manta, tunda baku damu dani ba, 

Abba yace kai lubabatu kenan, ta Dauki affan, tace naga ka kara nauyi ne, me kake ci? 

Yayi daria, nan suka yi ta fira, ta kira Amina suka gaisa, da yake har 'yan gidansu sun tafi, 

Can cikin fira, tace abba dan Allah akuya nake so ka sai min, Yace lubabatu me kuma zaki yi da akuya? 

Tace kawai kiwo nake so inyi, Yace to shikenan kada ki damu, 

Wa za a samu da ze maki kiwon? 

Tace ka samu wata haka, ammi tace naga nan layin akwai wata mata, da take kiwo, sosai,sai in bata ta maki, Lubabatu tace yauwa ammina, 

Abba yace lubabatu rigima, Yaya fatima tace ai ita de ta samu abinda za a kashe kudi shikenan, Yaya salma tace ai lubabatu daban ce, 

Tace eh naji, nan suka yi ta fira, 

Sai da aka fara kiran sallan magriba, Sannan suka tafi. 


     ************

Kwanaki sun kara ja, gashi yau ss3 suke candy, sabo turken wawa, 

Lokacin da suwaiba zata tafi, haka lubabatu ta rinka kuka, sai kace wadda uwarta ta mutu, ta bata Phone number dinta, haka ta koma kamar mara lafia. 

  Daga karshe ta saki jikinta, taci gaba da hidimanta, tunda gashi har suma, Sun fara exams, 

Bayan sun gama, Sun zauna zaman jiran hutu, 

Tafe suke tare da Amina, sai faman daria take, Amina tace banfa yarda dake ba, daga dukkan alamu, kina son aikata wani abu ne, Lubabatu tayi daria, tace kamar me fa? Amina tace nafa sanki fa, wa ya tabaki? Kike shirin daukan fansa? Lubabatu tayi murmushi, tace ba wanda ya tabani, 

Har suka karasa. 

Ganin taga mallam shamsu, yasa ta kara sakin daria, 

Amina tace kai lubabatu anya kuwa? 

Lubabatu tace bari ki gani, waye wancan? 

Tace mallam shamsu, 

Tace yau yaushe? Amina ta kara cewa friday. 

Lubabatu tace kuma gashi yayi shirin juma'a, 

To kin san Allah, Sede ya koma gida, ya canza wata shigar. 

Ta dubi kashin shanu da basu dade da sakinshi ba, Murmushin mugunta tayi, 

Haka tasa hannunta a ciki ta debo, 

Yana zuwa ta watsa mashi, 

Jikinshi ya kalla, ya kalleta, wanda kashin har saman fuskanshi, 

Ga duk mutane a wurin. 

Da wasu malaman dake saurin tafiya masallaci, 

Mallam shamsu yace wai ke wace irin mara mutunci ce? 

Me na maki? 

Takaici yasa harda hawayenshi, wani malamin da suke tare, yace ka bari muje ka canza kaya mu wuce, 

Kada mu rasa sallah, 

Idan muka dawo, yau sai kin raina kanki. 

Tana tsaye, rike da kugu, ta tabe baki. 

Suka wuce, mallam shamsu yana tunanin abinda ze mata, 

Amina sakin baki tayi tana kallonta. 

Can tace lubabatu meyasa kika yi haka? 

Tace au wani abu nayi? Ai ya gode ma Allah ma, da ba kashin mutum na zuba mashi ba, Kin fa sanni, idan aka min bana kyalewa. 

Tayi gaba, Amina ta bita a baya,maganar har ya kai wurin principal, 

Suna komawa hostel,da sauri lubabatu ta dauki kayan da tazo dashi,

Ta zira, tasa hijabi, Amina tace ke ina zaki? 

Tace gida, da sauri ta fice, tana isa bakin gate, Allah ya temaketa, ba kowa wurin, 

Da sauri ta fice, machine kawai ta tara. 

Tana hawa, ta tuna bata san gidan da suka koma ba, Tace kaini u/shanu.


   Tana isa, seda ta samu kudin machine a nan, tunda dama can ta baro komai nata, Bayan ta sallameshi, 

Ta fada gidansu jamila, mamanta na ganinta, tace ya akayi yan boarding, yaushe kika dawo? Ta zauna, ta gaidasu, tace gida nazo, Sede ban san gidan da muka koma ba, maman jamila tace to ki bari jamila ta dawo, na aiketa ne, sai ta rakaki, tana nan jamila ta dawo, da gudu jamila tazo suka rungume juna, mamanta tace to tashi ki rakata gidansu. 

Ta basu kudin machine, suka Fita suna fira, 

Har suka samu machine, suka tafi. 

Suna isa gidan,suka sauka, jamila ta sallamesu, suka isa gidan, suna shiga, ammi dake zaune kan kujera, 

Tace ke daga ina kike haka? Ta zauna, itama jamila ta zauna, ta gaidata, 

Ta mike tace zan tafi, dama lubabatu na rako gida. 

Ammi tace shine zaki tafi tun yanzu? 

Tace akwai abinda zanyi ne, Ammi ta dauko kudi ta bata, tace ki gaida mamanku, nan kofar gida lubabatu ta rakata, ta dawo, Ammi tace tambayarki nake, ya na ganki alhalin ba ayi hutu ba? Fatima data fito daga wanka, ta leko,

Tace kai lubabatu sneaking kika yo?

Lubabatu tace to ai wani malami ne yake yawan dukana, Na rasa me na mashi, 

Ammi tace shine kika dawo gida? 

To ta ina ma kika biyo, Lubabatu ba tare da ta lura da hakan da tayi laifi bane, tace ta gate na biyo, 

Seda na koma hostel na cire uniform dina, dama naje da kayan nan, 

Shine nasa, na fito, Allah ya temakeni, ba megadi a wurin, kawai na fito na hawo machine, ta Ammi ta dauketa da mari, tace wato baki ga laifin da kika aikata ba ko? 

Tashi Ki fita ki koma, ta inda kika fito. 

Lubabatu ta fara kuka, tana cewa dan Allah Ammi ki kyaleni, ba zan koma ba, wallahi idan na koma, wannan malamin, kasheni ne kawai, baze yi ba, Ammi tace sai kin koma koda ze kasheki din, Ai kinsan abinda kika mashi, bare ma karya kike yi, zaki tashi ki wuce tun kafin babanki ya dawo, ko kuwa, Lubabatu ta duka har kasa, tana kuka, tace Ammi dan Allah ku rufa min asiri ku cireni a makarantar nan, wallahi ba zan taba so ba, idan kuma kuka matsa min sai na koma, zanta aikata koma miye a makarantar, har 'yan secret code, sena nema na shiga, taci gaba da kukanta,

Yaya fatima tazo, ta kama mata hannu, tayi ciki da ita, ta zaunar da ita, 

Lubabatu sai faman ajiyar zuciya take, tana share hawayenta, Yaya fatima tace kiyi hakuri, yanzu meyasa kika gudo? 

Ta bata labarin duk abinda ya faru, tsakaninta da mallam shamsu, 

Yaya fatima tace kai lubabatu meya ja maki, koma me ya maki, ke komi ba zakiyi hakuri ba, sai kice sai kin rama, abinda baki yi a school din da kika bari ba, sai a wannan, 

Meyasa? Lubabatu tace saboda bana so. 

  Yaya fatima da kanta ta shiga kitchen ta zubo mata abinci, ta amsa, ta fara ce, tace ina affan? Yaya fatima tace yana barci. Taci gaba da cin abincinta. 


    ***********

Abba ne ya shigo, Ya samu wuri ya zauna, 

Yace kinga abinda lubabatu tayi kuwa, 

Yanzu principal dinsu ta kirani, ta fada min duk abinda tayi, nan ya kwashe komi ya fada mata, Yace tace yanzu haka nemanta suke, basu ganta ba, 

Tace bata girmama kowa, duk wanda ya mata seta rama, Harda zagi, 

Dama nasan halinta ne ramuwa, amma meyasa take ma malamai? Ammi tace ni ban san irin halin yarinyar nan ba, zuwanta boarding dinma, be haifar da komai ba, tunda wasu sabon abubuwan ta karo, 

An kaita dan ta gyaru, amma ba canji a lamuranta, yanzu haka maganar da nake maka, tana cikin gidan nan, 

Abba ya mike a fusace, yayi dakin nasu, rikota yayi, ya fara dukanta, 

Ta fara ihu, tana fadin dan Allah kayi hakuri ba zan kara ba, mommy dake zaune, tace kai kamar kukan lubabatu nake ji? Da sauri ta fito gidan, ta shigo nan. 

  Ta tadda abba nata dukanta, ta dauketa, 

Lubabatu tace lafe jikin mommy, mommy tace haba wannan duka haka? 

Yace dan baki san abinda tayi bane, 

Nan ya kwashe komi ya fada mata, 

Mommy tace dama kun san halin lubabatu, 

Be kamata a kaita boarding school ba, a gida ya kamata a barta, 

A gyarata, amma kuka dauketa, kuka kaita boarding, seda ta nuna bata so, 

Dan haka ku kyaleta ta zauna cikin 'yanuwanta. 

Lubabatu cikin kuka tace dan Allah abba kada ka maidani, inba haka ba, mallam shamsu baze kyaleni ba. 

Abba yace ai gara ki koma ya maki duk abinda ze maki, tunda ke baki jin magana, 

Dan haka tashi yanzu a maidaki, kara kankame mommy tayi, tana kuka, 

Tace Allah abba idan na koma, zan iya aikata abinda yafi haka, tunda bana so, mommy ta fita da ita. 

Suka yi gidansu, sai kuka take, duk su zainab suka kewayeta.


   Mommy tace to kukan ya isa haka, 

Lubabatu tace nide mommy bana son komawa, 

Mommy tace ki kyaleshi, Ai ba zaki koma ba, nide shawarata dake, 

Ki zauna ki natsu, ko haka kika ga 'yan uwanki nayi ne? Tace a'a, mommy tace to ina so ki zama kamar su dan Allah, cikin kuka tace to, mommy tace yauwa ko ke fa. 

Lubabatu tace to dan Allah mommy kada ko bari abba ya maidani, 

Wallahi bana so, ban taba jin dadi a school din ba, 

 Yaya salma tace to ke lubabatu kyaje ki rinka ma malamai rashin mutunci, Lubabatu ta harareta, 

Tace dan baki san abinda yamin bane, 

Shiyasa zaki ce haka. 

Ta kauda kanta, mommy tace to ya isa. 

Ranar de lubabatu taki komawa cikin gidansu, 

Sai Washegari, Sannan ta shiga, ammi kallonta kawai tayi, Lubabatu ta rakube jikin bango, sai kace wata marainiya, abba ya fito, 

Yace to tashi ki wuce in maidaki, ta Duka, cikin kuka tace abba kamin rai, ka kyaleni, wallahi bana son boarding, 

Ka barni cikin 'yanuwana, zan zama kamar yanda sauran suke, ya daure fuska, Yace mike mu tafi, 

Ina da abin yi, yaga bata da niyyar tashi, ya daka mata tsawa, zaki tashi ko sai na zaneki, da sauri ta mike, 

Suka Fita, sai share hawaye take, Yaya fatima ta kalli ammi tace Allah sarki ammi wallahi na fara tausaya ma lubabatu, da kun kyaleta a gabanku, tunda tana nan din ma ta ta kare, se wasu abin ma, data kara daura ma kanta. 

Ammi tace ni kaina yanzu nafi so inga tana kusa dani din, amma da ya zanyi. 

Fatima tace hakane, dan yanda ta nuna bata so taga din, zata iya yin abinda ta ambata din, zata iya hadewa da Yara na banza, kinga kenan ba ayi gyaran ba, dan haka ammi ki kara rokonshi ya kyaleta din, 

Ammi tace zanyi haka din, 


    **************

Suna isa cikin school din, gidan principal din suka zarce shida ita, 

Da yake ranar weekend ne, sai share hawaye take, principal na ganinsu, ta gaisa da abba, ta kalli lubabatu tace sannu, daki ka san baki da gaskia, sai kika gudu gida ko? 

Ta sunkuyar da kanta kasa, principal ta kalli abba, tace kaga yarinyar nan, ba karamar shedaniya bace, hatta malamai, zamanta school din nan, tsoron tabata suke, 

'yan watannin kawai da tayi a ciki, ba wanda be santa ba, inde a fage ne na rashin kunya, abba yace kuyi hakuri, ina bakin kokarina a kanta, 

Bade ta jin magana ne, principal tace kayi hakuri, amma de ka dauketa, ka maidata gida ta zauna kusa dakai, dan ba zan iya da ita ba, 

  Nan gaba kaina zata dawo, abba yace da kinyi hakuri, tace dan Allah kayi hakuri, Allah ba zan iya barinta cikin nan ba, gara tana tare daku, Zaku fi sa mata ido, 

Nan ko gani za tayi ai ba haihuwanta mukayi ba, bamu da iko da ita, 

Abba yace shikenan, ya kalli lubabatu yace burinki ya cika ko? 

Sai kizo mu wuce, Yace ma principal na gode, tace ba damuwa kayi hakuri fa, Yace a'a ba matsala, 

Tace wuce muje hostel din ki kwashe kayanki, 

Abba yace to me zata yi dasu? 

Principal tace ko tana da wanda zata ba mawa, 

Bari muje, 

Tare suka jera, suna tafiya, principal tace, Ai banso ba, zaki bar makarantar nan, ba tare da na zaneki ba, tunda baki ji, ita de lubabatu bata ce komai ba, tunda burinta ya cika, ta bar makarantar. 

  Har suka isa,abba ya tsaya, ba tare da ya shiga ba, suka shiga, principal sai fada taje mata, 

Amina na ganinta, ta taho da sauri, 

Tare duk suka fito da kayan, ta mika ma Amina, tace gashi na bar maki su duka, 

Principal tace ba zan zauna mata a school ba, 

Amina tace dama ai abinda kike so kenan. 

Banji dadi ba, Na saba dake, Lubabatu tace kada ki damu, zaki rinka ganina, zan dan rinka visiting naki, tunda bamu da nisa, yanzu bani number din da Zan rinka samunki, idan anyi hutu, 

Amina ta bata. 

Suka fito, principal tace ina kayan naki? 

Tace na bar ma Amina su, principal tace to yayi kyau sai ki wuce mu tafi, Tare da Amina suka jera, sai hawaye take, 

Suna tafiya, ita kanta lubabatu ta fara hawaye, 

Har suka isa wurin abba, 

Abba ya kalleta a daure, cikin fada, Yace ina kayan? 

Tace na bar ma Amina, ta nunata, Amina ta gaidashi, ya amsa. 

Yace se ki wuce mu tafi, yasa hannu a aljihu, ya ciro kudi, ya mika ma Amina, ta amsa, tana mashi godiya, 

  Suka wuce, Lubabatu duk taji bata son rabuwa da Amina, duk ta bata tausayi, 

A mota kuwa, abba sai fada yake ma lubabatu, Yace yanzu yarinyar nan, bata birgeki ba, gata ta zauna tana karatunta lafia, 

Yarinya mai natsuwa, ke kuwa rashin jinki, da rashin kunya baze bari, ki zauna da mutane lafia ba, 

Sai fada yake mata, har suka isa gida. 

Suna shiga, ammi ta gansu, tace ya naga haka? 

Yace principal din taki amsarta, ammi tace ai kin kyauta, zaman gida ko ki zauna ki tayi, idan ma karatun ne ba zakiyi ba, gaba daya sai ki zauna, da jahilcinki, sakarya kawai. 

Tashi Ki bace min da gani, ta mike ta shige dakinsu, lokacin fatima na kwance tana barci, bata tadata ba, Ta zauna kawai,    ***************

Ammi ta kalli abba, tace halin lubabatu fa sai ita, bame jurewa da halinta, sai mu data zaman ma dole, 

Dan haka dole mu zauna tare da ita. 

Abba yace hakane, Ai ita ta sani, Na rasa meke mata yawo a kanta. 

Ita kuwa kaya kawai ta canza, ta dare gado, bata wani dade ba, Barci ya dauketa. 

Dan yanzu ji tayi hankalinta ya kwanta, tunda an rabata da kaya, duk fushin da zasuyi, zama su sauko ne. 

Ita dama duk bacin ran mutum ba damunta yake ba, hidimanta zata yi abinta. 

Kai kayi ta fama da bacin ranka kai daya.


   *********,, 

 Fatima ta farka, ta ga lubabatu kwance, 

Ta tadata, tace ya haka? Lubabatu ta juya, tace ai principal taki amsata, Yaya fatima tace abba ya kyaleki? Tace eh. 

Yaya fatima tace kede ki samu ki natsu, 

In ba haka ba, ba zaku dedeta da abba ba, 

Lubabatu tace to. 


    ************

Ta gama shiryawa ta fito, tayi hanyar fita, 

Ammi dake zaune, tace ina zaki? Tace wurin mommy zani, ta kira min yaya sultan, 

Ammi tace ba zaki ba, Lubabatu tace kai ammi dan Allah ki temaka min. 

Ammi tace nace ba zaki ba, idan kuma zaki fita, ban isa dake ba, ki fita. 

Ta samu wuri ta zauna, rai a bace, 

Tayi shiru, 

Ammi tace bade baki jin magana ba, 

Idan na Kara ganinki a waje, ko kin fita, 

Sai na mugun saba maki a gidan nan. 

Ita de tayi shiru ba tare da tace komai ba. 

     

    *************

Abba ya maidata makarantar da take, taci gaba dayi, idan an koma hutu, zata ci gaba da zuwa. 

Zaune suke, Lubabatu tace Ammi wai ina akuyata? Tunda nazo ban ganta ba, Ammi tace ai yanzu ba naki bane, tunda baki jin magana, 

Lubabatu tace dan Allah Ammi kiyi hakuri, 

Kisa yaya fatima ta rakani in gani, 

Ammi ta kalli yaya fatima, tace rakata,

Daga nan gidan, ban yarda ki barta tayi magana da wasu a waje ba, 

Bare har ta saba da wasu,ta samu wurin zuwa a unguwar, Yaya fatima tace to Ammi, ta mike suka tafi, 

Suna shiga, suka gaidata, ta kallesu, 

Tace ya gida? Suka ce lafia lau, Yaya fatima tace dama lubabatu ce tazo ganin akuyarta, maman sadiq tace au itace lubabatu? Lubabatu tace eh, suka isa wurin akuya, 

Ta rikota, tace la ciki ma gareta tsoho, 

Maman sadiq tace ai da yake me ciki aka samar maki, Lubabatu tayi daria. 

Maman sadiq tace an maki bayani haihuwar farko name kiwo ne ko? 

Lubabatu tace a'a sede ki bari se ta kara haihuwa, Sannan in baki, amma wannan nawa ne, tayi daria, 

Tace Lubabatu kenan, Kada ki damu ai haka akeyi, Yaya fatima tace tunda kin ganta kizo mu koma gida, 

Suka fito, sukayi gida, Lubabatu tace Ammi wai kiji matar nan, Wai haihuwar farko wai nata ne, Ammi tace eh mana, Lubabatu tace nide ba zan bar mata ba, Ammi tace idan ba kiyi wasa ba, duka zan bar mata harda uwar, gara ma kiyi shiru, bata kara cewa komai ba. 


    *************

Kwance take, tana waya da yaya sultan, cikin jin dadi, sai daria take, 

Can tace, Ai akuyata ma ta kusa haihuwa, Yace kai dan Allah, tace da gaske.


Yace to idan ta haihu ni zaki bar mawa ko? 

Tace ai har an bada kyautar 'Yar da zata haifa, 

Wai haihuwan farko ba tawa bace, kuma ba zan yarda ba, Yace a'a kiyi hakuri, idan na dawo, zan sai maki wata, ni da kaina zan maki kiwon ma, kinga bame dauke maki, na haihuwar farko, Sede ki rike abinki ke kadai, tace yauwa yayana, shiyasa nake sonka, yayi daria.


   Sun dade suna fira, tana bashi labari, 

Yana daria, saboda dariyar da take bashi, 

Sannan sukayi sallama. 


    *********

Kwanaki na Kara ja, har sun koma hutu, an maidata, school din da take, 

Dan a cikin hutu ne su kan dan yin waya suna gaisawa. 


   Zaune suke, maman sadiq ta shigo, 

Suka gaisa da ammi, tace to akuya ta haihu, ta samu mace da na miji, 

Ammi tace to ikon Allah, Lubabatu akuya ta haihu, yau mun huta, 

Tayi daria, maman sadiq tace tunda biyu ne, Na dauki akuyar ita sai ta dauki bunsuru, Lubabatu tace bunsuru kuma? Ammi tace au da kika samu ta baki, 

Ai naso ta dauka duka, idan ta kara haihuwa, sai ki dauka, Lubabatu ta zumbura baki, maman sadiq tace lubabatu kenan, 

Ta mike tace to na gode, sai anjima. 

Ta tafi, 

Lubabatu tace ni wai Ammi nida akuyata se ace in tashi da bunsuru, 

Me zanyi da bunsuru? Ammi tace to ki bar mata duka, 

Ta zauna ran nan a bace, bata tanka ma kowa ba, aunty jamila da ummi, suka shigo, da gudu lubabatu taje ta taresu, aunty jamila tayi daria tace, Lubabatu ba a girma, tayi daria, tace aunty duka shekaruna nawa? 

Ta kalli ummi tace kin boye, Ummi tace ina nan, kune baku son zuwa gidanmu, Shiyasa na dena zuwa, 

Lubabatu tace me zamu zo muyi, tunda aunty bata nan, Ummi tace tunda mu ba mutane bane a gidan, 

Bayan sun gaisa, 

Ammi tace aiki ya boyeki, aunty tace kede bari, mutum naso yayi zumunci be isa ba, nan suka dan taba fira, 

Tace bari na shiga ciki, sauri nake, 

Ammi tace baki bari yayyan naki su dawo, 

Aunty tace zaria nake so na wuce yau, 

Bana so nayi dare, tunda na gaisa daku, naga Yara, Ai kamar na gansu ne, 

Ammi tace hakane, 

Tare suka shiga wurin mommy, nan ma bata jima ba, suka fito, Lubabatu wurin rakiya, tace ma ummi ban baki labari ba, akuyata ta haihu, dan de kuna sauri, 

Dana kaiki kin gansu, Ummi tace ai zan dawo, Lubabatu tace shikenan. 

Suka tafi. 


Daga nan ita kuma gidan maman sadiq ta shige, da wayan Ammi a hannunta, 

Haka ta yi ta daukarsu, tana masu hoto, tana yi tare dasu, 

Maman sadiq de se daria take mata, 

Seda ta gama ganinsu, Sannan ta dawo gida, ta kira yaya sultan, tace akuyata ta haihu, mace da namiji, Yace iye, Kinga data haihu mun samu wasu, tayi daria, 

Tace bari ma na turo maka ka gansu, 

Haka ta shiga whatsapp din Ammi, 

Duk ta tura mashi, Bayan ya gani, 

Ya kirata, Yace na gansu, kema kinyi kyau, 

Haka kika kara kyau, daria kawai tayi, 

Seda lokacin islamiyya yayi, Sannan suka yi sallama, ita kuma ta yi sallah, tayi shirin islamiyya, Sannan suka tafi.

Gaba daya sun zauna gaban ammi suna bata hakuri, Lubabatu tace ammi ki dena kuka, 

Ammi tace to ya zanyi, shi muke kallo muji dadi, 

Abba ya shigo, Yace kiyi hakuri addu'a yake bukata, 

Ammi ta share hawayenta, Yace yanzu ki tashi kiyi hakuri, ki kwanta. 

 Kinga gobe da wuri zakiyi sammako. 

Tace ko na kwanta ba barcin zanyi ba. 

Abba yace daurewa zaki yi, ta mike ta shiga dakinta. 

Abba ya bita, 

Lubabatu tace kiga ammi fa, kanin babanta ne fa ya rasu. 

Amma take wannan kukan. 

Babanta ma ya rasu ta hakura, bare wannan. 

Sai ta bari 'ya'yanshi suyi kukan. 

  Yaya fatima ta kalleta, tace ni dadina dake har yanzu baki da hankali. 

Kamar fa baba yake a wurinta. 

Lubabatu tace amma ai bashi ya haifeta ba. 

Yaya fatima ta mike, ta shige daki, 

Ta barta nan zaune, ita da affan, itama daukanshi tayi, suka bi yaya fatima ciki. 


    *************

Washegari kuwa, Tun asuba, ammi ta gama shirinta, 

Mommy ce ta shigo gidan, tana kara mata gaisuwa. 

Har mota ta rakata, tace insha Allahu ina nan zuwa. 

Da yake ita da abba da daddy zasu tafi. 

  Ita kuma ta kula da gida. 

   Su kuma komawa gida sukayi, suka ci gaba da shirin tafiya school. 


    ************

Bayan sun dawo, da yamma suna shirin tafiya islamiyya. 

Lubabatu ta kalli yaya fatima, tace yaya fatima, 

Dan Allah ki temaka min, ban Iya haddar yau ba. 

Yaya fatima tace au duk baki tashi yi ba, 

Sai yanzu da lokacin islamiyyar yayi, 

Zaki ce wani baki iya ba. 

Ni ba abinda zan iya maki a yanzu. 

Sede kije duk abinda ze maki ya maki. 

Tunda ke ba zaki taba zama ki koyi abu da wuri ba, wasa yaci karfinki. 

Lubabatu tace to naji, tunda ba zaka koya min ba, se kiyi shiru, baki zauna ba kina fada min magana. 

Shirinta taci gaba dayi, 

Ta shirya affan suka fita. 


   Bayan sun isa islamiyya, mallam ya shigo, yana amsar hadda. 

Tun kan yazo kanta, ta fara kuka, Bayan ta mike, Yace lubabatu ya akayi ne? 

Cikin kuka tace baban ammi ne ya rasu, 

Ta tafi maiduguri yau, kuma bata je dani ba. 

Yace Allah sarki, Kiyi hakuri, Allah yaji kanshi. 

Yanzu zaki iya karantawa? 

Cikin kuka, tace eh. 

Yace to ina sauraranki, Bayan ta fara. 

Ko aya biyar ba tayi ba. 

Ta kara fashewa da kuka, Yace kiyi hakuri, zauna, gobe kya karanta min. 

Zama tayi, ta hada kanta da gwiwa. 

Tana murmushi, zainab dake zaune kusa da ita. Tace lubabatu nafa sani haddar ce baki iya ba, Shiyasa kika yi haka. 

Nasan baki ma mutuwa kuka. 

  Lubabatu tace to naji kiyi shiru de. 

Nasan halinki, Murmushi kawai zainab tayi. 

Bayan sun tashi, a hanya, haka zainab tayi ta basu labari. 

Yaya fatima tayi daria, tace wallahi ba ta iya karatun bane, Shiyasa tayi haka. 

Zainab tayi daria, tace ni nasan haka ai. 

  Yaya fatima tace kede kika sani, wallahi inde ba zaki girma ba, kina tare da wahala. 

Lubabatu tace eh din naji, ba ruwanku dani. 

Kuma akan abinda nayi, duk wanda yaci gaba da tada maganar, duk rashin mutuncin da na mashi, shi ya siya da kudinshi. 

Gaba daya daria suka ci gaba dayi mata. 

Suna isa gida, saida zainab ta bama mommy labari. 

Mommy daria harda hawaye, tace kai Lubabatu, da abin daria kike. 

To yanzu ai sai ki zauna, ki koya, tunda yana nan yana jiranki gobe. 

In ba kukan zaki ci gaba da mashi ba. 

Lubabatu ta kara daure fuska, tace mommy karya fa take yi, mommy tace ai ni na sani, Lubabatu ba zatayi haka ba. 

Yanzu tashi kuyi alwala, idan kuka gama, sai ki zauna kiyi karatunki ko? 

  Ta mike tayi alwalanta, Bayan ta idar da sallah, mommy tace yanzu zo muje dakina, ki zauna kiyi karatunki tsanake ko. 

Taja hannunta, suka wuce dakinta. 

Tace kiyi zamanki nan, dana gama hada ma su daddy abincinsu zanzo muyi tare ko. 

Bari inje, saboda suna hanya. 

 Haka ta zauna taci gaba da karatunta. 

Har mommy ta gama hada komai. 

Ta dawo dakin, tace yauwa 'yar albarka. 

Yaya kin iya ko? 

Haka suka yi ta yi tare da mommy, 

Har seda taga ta iya, Sannan ta kyaleta. 

Tana yin sallan isha'i, nan ta kwanta dakin mommy, rayuwar Lubabatu tana son mommy, dan ita da yaya sultan ne kawai suke binta a hankali a gidan nan. 

Duk abinda tayi ba daidai ba, Sede su gyara mata cikin kwanciyar hankali, ba tare da fada ba. 


Shiyasa tana son mommy sosai. 


   *************

Sai misalin karfe sha daya na dare, Sannan suka iso garin. 

  Nan lubabatu taci gaba da zama gidan mommy, haka affan ma. 

Dan duk inda lubabatu tasa kafa, shima nan yake sa nashi. 


 Ranar sadakan uku, mommy ta shirya tabi jirgi, ta ta isa maiduguri. 

Kwananta daya, suka juyo tare da ammi.


 ************


Rayuwa taja, shekarun sunja, yanzu ba laifi, Lubabatu na daukan kanta budurwa. 

 A lokacin gashi har su yaya fatima sun gama secondary, had sun daura karatunsu, ita da salma, 

Inda suka samu admission a ABU zaria. 

Ita de lubabatu yanzu suna ss3,tace ammi nide idan na gama secondary school, gaskia ba zan ci gaba da karatu ba, aure zanyi. 

Ammi tace ke lubabatu ni kike fada ma haka? 

Lubabatu ta zumburo baki, tace nide Ammi gaskia na fada, dan ba zan iya yin karatu ba, nafi so nayi aure. 

Ammi ta kai mata duka, tace tashi ki fita ki bani wuri, ta mike ta koma daki, 

Tace nide koma me zakuyi, aurena zanyi. 


  **************

Duk abinda aka sa mashi rana sai yazo, 

Yau gashi su yaya sultan nata shirye shiryen dawowa gida nigeria. 

Inda suka dage tun zuwansu basu waiyayi gida ba, sai da suka had'a har masters dinsu. 

Yau gida cike yake da murna, Tun ba lubabatu ba, baki yaki rufuwa. 

Abin alfaharinta, farin cikinta, zai dawo gida, 

Kusan shekaranta nawa, rabonta dashi. 

Sai dai suyi waya. 

Dede da abinda zasu ci, ita ta zauna ta shirya masu, dan duk abinta. 

Wurin girki, dole ka bata lambar yabo. 

Ranar haka ta zauna ta tsantsara kwalliya. 

Yanda kasan wadda zata gasar kwalliya. 

Mommy na kallonta, tayi daria, tace gaskia lubabatu kinyi kyau sosai. 

Tayi murmushi, tace mommy da gaske? 

Tace sosai kuwa, yau yayanki baze ganeki ba gaskia. 

Daria ta kara yi, 

Komai seda ta shirya masu, lokacin har a tafi taho dasu. 

Lubabatu saboda zumudi, komawa kofar gida tayi, tana jiran dawowarsu. 

Tana nan tsaye, mota ta danno kai. 

Gaba daya Washe bakin tayi, tana kallon motar, nan aka bude gate din suka shiga. 

Itama shigowa tayi, 

Suna fitowa, da gudu ta ruga, ta rungume yaya sultan, tana fadin yayana nayi missing dinka, shi kuma sai daria yake, 

Ya dan cireta daga jikinshi, ya rike mata hannu, Yace nima nayi missing dinki sosai. 

  Tayi murmushi, Yace lubna ta ce ta koma haka? 

Daria ta kara yi, yana rike da hannunta, suka shiga cikin gida, dan shi yaya aliyu har ya shige, ya barsu nan. 

Yace ina rashin ji? Tace yanzu babu. 

Yayi Daria, Yace ai na fara ganin alama, ya ragu. 

Suka idasa daki. 

Mommy kanta bakinta yaki rufuwa. 

Su zainab suka fara gaidashi, Yace bana amsawa, tunda baku damu dani ba. 

Wadda ta damu dani, waje na tarad da ita, tana jiranmu, suka ce yaya kayi hakuri. 

Nan suka gaisa. 

Lubabatu ta kalli yaya aliyu tace yaya aliyu an dawo lafia? Kallonta yayi, Yace lafiya lau. 

Nan de suka mike, suka shiga ciki. 

Saida suka gama shiryawa, Sannan suka fito. 

Nan suka zauna, duka gidan, Su Ammi, dasu abba, duk ana sashin daddy. 

Yaya sultan yace ina fatima fa da salma? 

Lubabatu tace ka manta suna school. 

Yace au na manta, nan suka fara cin abinci. 

Yaya sultan yace kai wannan irin dadi haka, wa ya girka mana? Mommy tace gata nan lubabatu, ta hana kowa ya taba komi, duk ita tayi. 

Yaya sultan yace gaskia kanwata wannan abinci yayi dadi, Yaya aliyu yace ina fa dadi, ta jagwalgwala girki. Ai sede aci dan kar a mutu.

Daria wurin sukayi, Lubabatu ta zumburo baki, tace yaya sultan kaji abinda yace fa. 

Yaya sultan yace kyaleshi,yasan girkin yayi dadi, kawai miskilancinshi ne baze bari ya fadi haka ba. 

Ai wannan abincin, ko wadda tayi degree ne akan girke girke, ba zata gwada maki iya girki ba. 

 Lubabatu tayi daria, tace shiyasa nake sonka yayana. 

Daria sukayi. 

Saida suka gama cin abincin sannan yaya aliyu ya mike, Yace to nide zan dan shiga daga ciki in kwanta, dan na gaji. 

Idan wannan yarinyar na wurin nan. 

B zata bari mutum ya huta ba. Mommy tace kai de ka sani, Murmushi kawai yayi, ya fice abinshi. 

Lubabatu ta bishi da kallo, ta dawo da kallonta wurin yaya sultan. 

Tace kalleshi idan da ba dadi, Ai da ya aje be ci ba, amma kalli yanda yaci da yawa. 

Yaya sultan yace ki kyaleshi ai gulms ce. 

Abba yace kude kuka sani, kaima yanzu ka tashi ka wuce kaje ka huta. 

Yayi Daria, Yace to abba ya mike, Tare da lubabatu suka fito, har daki ta rakashi. 

Ya kalleta yace in baki tsarabarki? 

Ko zaki bari sai na tashi barci? Tace to Ka kwanta, idan ka tashi sai ka bani. 

Yace to shikenan, taja masu kofar ta fita. 

Ta koma daki, tayi zaune sai murmushi take, kome take aiyanawa a ranta oho. 

Dan yanzu kara jin yaya sultan take a ranta.


Da lubabatu aka bud'e tsaraba, haka ya kawo mata, " 'katuwar wayarta." 


  Banda kaya da ya siyo mata. 

  Kowa an bashi tsarabarshi. "


Tun dawowar su yaya sultan. 

"shakuwa ta kara shiga tsakanin lubabatu da yaya sultan."

 "sede yanda da yake janta a jiki, baya janta yanzu."

Gashi ita kuma har yanzu ganin 'karama take ma kanta."Ko ta shige mashi,' kokari yake yaga ya cireta daga jikinshi." 


   *************

"lubabatu ce tafe d'akin su yaya sultan."

d'auke da "jug d'in kunun" gyad'a "a hannunta." 

Tana shiga d'akin,"ta zauna kusa dashi."

"tace yaya sultan, gashi na gama. 

"yace yauwa kanwata."

Ya zuba a cup,"yasha. 

Seda yasha kunun nan sosai. 

"sannan ya kalleta,"yace sannu ko..!

"wai lubabatu," wa ya koya maki wannan girki haka?"

"ta kashe mashi ido," da yanzu ya zame mata jiki."

Tace haba yaya sultan,"da gaske kake,"wai na "iya girki sosai?" 

Yace gaskia kam ina jin "dad'in girkin ki."

"tayi daria..!

Tace yaya sultan," da "kwamacala, na " iya girki fa."

   "akwai ranar da ammi ta sani girki, na cika masu yaji, ya waro idanunshi..! 

Yace kai dan Allah?" 

"tace da gaske."

Aiko duk suka kasa cin abincin."

Tayi daria."

Tace kasan ma da suna ci me nace masu?"

  "yace "a'a", tace seda na d'aga masu gira."

Na d'anyi daria."

Sannan nace masu ya kuka ji girkin?"

Yayi dad'i ko?"

Ammi ta harareni,"tace idan na tashi zaki ga yanda zanyi dake,"girkin da ba dad'in" gaba, bare na baya."

"kuka kasan ni kaina,"nasan abincin beyi dad'i ba."

Yaya sultan yayi daria. 

Yace kai "lubabatu", har yanzu de, kina nan yanda kike."

Tace kai yaya sultan."

  "yaya aliyu ne ya shigo. 

Ya kallesu," yace kuna nan kuna shirman da kuka saba? 

Ka zauna kayi ta biye ma yarinya."

  

  "lubabatu ta bishi da harara. 

Y d'auki abinda zai d'auka, ya fita," ya bar masu "d'akin."  **************

" yaya sultan," yace yauwa lubabatu."

"baki bani labarin "akuyarki ba." 


  tace "uhum," bari kawai yaya sultan..! 

"ai idan na baka labarin nan, sai ka tausaya min."

Ya "gyara zamanshi, Yace kice labari ne mai tsawo?" 

Tace sosai kuwa. 


  Bana baka labarin akuyata ta farko ba.“

Har na fad'a maka matsalar dana samu,"da wasu ma duk da aka siyo."


Yace eh."

Tace to ai ta mutu.! Yace innalillahi.! 

Yaushe?"

Tace bata dad'e ba, Yace duka ko wata biyu ba ayi ba, kika ce min ta haihu."

Tace kaide bari," ai ka bari in baka labarin tun daga akuyar farko. 

Har zuwa kan ta 'karshe."

Yace to ina jinki."


Tace to bayan an bar min bunsuru, Kasan na riga na nuna bana so."

Sai abba, Yace inyi hakuri, idan ya tashi ze 'kara siyan min wani. 

 Sai in had'a guda biyu."

Sai na bar mata, ita kuma uwar," daga baya, sai ta gaza, abba yasa aka yanka aka soya."

Kaga na tashi banda ko d'aya kenan."

Ya 'kara gyara zama, Yace tofa.!"

Labari mi'ka'k'ka."

  Tace yaya sultan sede fa idan na fita, inga bunsurun nan, ya gitta ta kofar gidanmu ya wuce," nida abina."

ina ji ina gani, bunsurun da na raina. 

Da christmas,"akayi cinikinshi dubu biyar."

  Abba da ya tashi ya 'kara siyan min wata akuyar."

Da tafiya tayi nisa,"

Itama akuyar nan sai ta haifi' yan biyu."

Mace da namiji," aka ce sede Kiwon farko in bar mata."

Banda wancan dana bar mata. "

 Da aka ga na'ki yarda, sai aka' kara bani bunsuru," 

Kaji fa rainin wayau."

Yaya sultan daria ya fara yi, Harda kwanciya 'kasa."

  "lubabatu tace ka bari in gama maka mana." 

Ni kuma nace aiko ba a isa ba,"ya za ayi nida akuyata, sai ace in rin'ka tashi da bunsuru.! 

  Tafiya tayi tafiya,"sai kakar ta mutu."

Nan na tada balli, nace ni kuma wallahi, Sede in ta d'auki bunsuru, ni kuma na d'auki akuyar."

Kan haka, abba har dukana ya kusa yi."

Dan kasan Allah."har yanzu ban ha'kura ba, 

Dan sai ya biyani."

Shi aka ja mawa."

Yaya sultan yace idan na baki shawara, zaki d'auka?"

Ta d'aga mashi kai. 

Yace ki ha'kura da Kiwon nan, dan be amsheki ba."

Tace kai yaya sultan! 

Ya d'aga mata gira."

  Tace to naji amma ba zan ha'kura ba,"

Sai ya sai min wani abu."yace ki bari ni zan baki wani abu."

  

 Tade yi shiru, ba tare da tace komai ba."


   Yace kinga da boarding dinki kika zauna. 

Da yanzu kin kusa gamawa."

Ta kalleshi."

Tare da waro ido.! 

Tace taf.! 

Yaya sultan baka san boarding bane,"

Bashi da "dad'i, gashi duk rashin rowan mutum sai ya koya." 

  

  Idan ba haka ba, baka yi loma biyu ba, sai de kaga plate."


  Shiyasa idan na had'a abinci zanci."

Idan zan masu tayi, Sai in d'aure fuska. "

In d'anja kwanon, in ri'keshi, Sannan in bismillah.! 


 Idan naga mutum ya cika hannu, ince d'an rage."

Banda 'katuwar loma."


Yaya sultan ya hau daria," harda rike ciki."


Yace kai lubabatu" baki da dama."

  Kice malamai ba 'karamin fama suka yi dake ba."


Tace ai shiyasa principal ta'ki amsata."


 Yace yau de kin bani daria, Kinga tashi ki tafi ki kwanta, dare yayi."

Ga bros ma naji muryarshi ze shigo d'akin,"


  Kinga gobe ma akwai abinda nake so na fad'a maki,"

Tace to Ka fad'a" min yanzu, Yace kiyi hakurin gobe, 

Zan fad'a maki ai."


  "kinga dare yayi yanzu, muje in rakaki."

Tare suka fito, Yaya aliyu ya kallesu,"

Yace sai yanzu shirman naku ya 'kare?! 

Allah ya kyauta."

Ya shige ya barsu nan."


 "lubabatu koda ta koma d'aki," tana kwanciya. "

Barci ya d'auketa." 


 Burinta.! Safiya tayi, taji me yaya sultan ze fad'a mata."


Washegari kuwa, tunda taje suka gaisa da yaya sultan,take tambayarshi me ze fad'a mata!? 

Yace "yanzu ba makaranta zaki ba, 

To ki bari idan kika dawo, zan fada maki, bani nace zan fada maki ba. 

Da haka ya lallabata ta tafi. 


  ************

Aiko tana dawowa d'akinsu ta wuce. 

Yana kwance ta samu kusa dashi ta zauna. 

Ya Kalleta, Yace "yace har kin dawo?" 

Ta d'aga mashi kai.

Sannan tace "nazo inji me zaka fad'a min." 


  Yace "kai ba zaki bari sai kinci abinci ba, kinyi wanka kin huta."

Ta d'an kalleshi, tace "abinda zaka fad'a min yafi duka wad'annan." 

Kai kawai nake saurare. 


  Daria yayi, Sannan yace "lubabatu inaso zamuyi magana, sai de ban sani ba a irin shekarunki, ko zaki fuskanceni." 


Tace "yaya sultan wane irin magana?" 


Ya kalleta, gami da furzar da iska daga bakinshi. 


Tace "yaya sultan kai nake jira."


Binta yayi da kallo, Yace "lubabatu ban san ya zaki d'auki maganata ba.

Ina tsoron fad'a maki." 


Tace "kada ka damu, koma miye, ka fad'a min, ba wani abin tsoro bane."


" yaya sultan ka manta yanda muke da ne?"

Bafa nida aboki sama dakai, to me ze gagareka da zaka kasa fad'a min. "

Kallonta, yayi yaga yanda ta natsu tana magana. 

Yace "hakane."


"lubabatu tun kina k'arama, kika shiga raina,nake biye ma duk wata shirmanki, har zuwa girmanki."


"lubabatu ina sonki.! 


Tayi dariya, tace "kaji yaya sultan." 

Nima ai ina sonka. 

Dama nace baka sona ne. 

Shima dariyan yayi, Yace "bari in fahimtar dake, Lubabatu ina sonki, 

Inaso na aureki.!


  Waro idanunta waje tayi, sai kuma ta mik'e, ta fice d'akin da gudu. 

Dariya ya hau yi mata. 


Haka ta shiga d'aki, sai faman maida numfashi take. 


Ammi ta shigo, tace "ke kuma lafia?" 

Tun dazun kuka dawo, amma baki ga daman shigowa gida da wuri ba."

Nishin me kike haka?"


Tace "bakomai."

Ammi tace "Allah ya kyauta."


Ta fice a d'akin. 


Lubabatu ta fad'a kan gado, sai faman murmushi take,tana juyi, sai faman juya idanu take. 


Wayanta ya fara k'ara, tana dubawa, taga yaya sultan, sai ta tsinci kanta da kasa d'aukan wayan. 

Har ta katse, ya k'ara kira, saida ta kusa katsewa, Sannan ta d'auka. 


Ta kasa magana, dariya yayi, Yace "yau kuma ni ake jin kunya?" 


Dan na fad'i abinda ke raina. 


Ta kasa magana, sai de murmushi. 


Yace "yaya sultan d'inki ne fa, da kike yawan fad'in baki da miji sai shi, gashi kuma zan cika miki burinki, kina min wulak'anci."


"tunda baki sona, Na janye."


Da sauri, tace "a'a yaya sultan."

Dariya yayi, duk ta kasa magana, sai kace bashi bane abokin firanta. 


   *************

Tun daga ranar Lubabatu ta rage shige ma yaya sultan, duk ta kasa sakin jiki dashi, kunyarshi take ji. 


  Tun yana mata maganar soyayya, tana kasa maida mashi, daga k'arshe, sai gashi ta saba. 


Gidan ba wanda tayi gigin ta fad'a mashi, tana soyayya da yaya sultan. 

Daga ita sai shi suka sani. 


Soyayya ce sosai ta k'ullu a tsakaninsu. 

Ji suke yi kamar su had'iye junansu saboda son da suke ma juna. 

Lubabatu har mamaki take, idan taga yaya sultan ya sake, yana fad'a mata sirrin zuciyarshi. 


   ************

Haka rayuwa taci gaba da tafiya, an fara registration na jamb. 

Abba ya kira Lubabatu, Yace "ke ya kike ciki?" 


An fara registration na jamb, ya kamata kizo kiyi ko."


Ba kunya, tace "Abba ni bani da buri akan karatu, aure nake so nayi."


Abba tsayawa kallonta yayi, Yace "Lubabatu ni kike ce ma baki da burin karatu aure kike so."


Tace "Abba shi nafi so." 


Abba ya kai mata duka, dede lokacin yaya sultan ya shigo.

Da sauri Lubabatu ta isa wurinshi. 

Ammi tace "au ashe kina tsoro?" 


Lubabatu ta fara kuka, tace "ni wallahi da gaske nake, aure zanyi."


Yaya sultan kanshi kallonta yayi, Ammi tace "karatu zakiyi."

Ko su Fatima basuyi ba, bare ke. 

Lubabatu ta zum'buro baki, tace kowa fa da ra'ayinshi."

Yaya sultan jin duk abinda ya faru. 

Yace "Abba ku k'yaleta, bari muje inyi magana da ita."

Suka fita tare.   Bayan sun shiga d'aki, ya zaunar fa ita, Yace "haba Lubabatu meyasa zaki fad'a ma su Abba haka?" 


Tace "yaya sultan shine fa a raina, sai in kasa fad'a masu, aure nake so nayi."

Yace "to inde maganar aure ne, ai zakiyi." 


  "amma inaso ki yarda kiyi jamb din, dani fa kike so ki zauna."

Kuma inaso kiyi karatu. 

Dan haka inaso ki yarda kiyi jamb din."

Tace to shikenan zanyi, amma bani so auran ya d'au lokaci." 


Yace "kai Lubabatu, halinki sai ke,to naji."


Da gaka ya lallabata ta yarda. 


  *************

Gaban su Ammi ta yarda za tayi karatun, Amma ita aure za tayi ta gama karstunta a gidan mijinta. 

Ammi tace "wai kina ta maganar aure, aure.!

Ina kika samu mijin?" 

Kuma ma duka shekarunki nawa, Ina kike da hankalin da zaki je kiyi zaman aure."


Lubabatu tace "ai da nayi auran, hankali zaizo, 

Ni wallahi bana son karatun nan, kawai de dan yaya sultan yace yana so ne, da ba zanyi ba."


Ammi tace "wannan ai ke ya shafa."

Karatu de in kinyi k'aruwar kanki ne, ba ta wani ba."


Lubabatu tace "yauwa Ammi tunda k'aruwa tace, dan Allah ku k'yaleni da maganar auran nan."


Ammi de da taga shirman na Lubabatu ya mata yawa. 

Tace "tashi ki fita ki bani wuri."


Ta mik'e ta bita da gudu, ta fice gidan, 

Tayi wurin mommy, nan taci karo da daddy, 

Yace "Lubabatu ya akayi ne?" 


Harda guntun hawauenta, suka shige ciki tare, Yace zauna ki fad'a min me ya faru?"


Tace "Daddy aure nake so nayi, Su kuma su Ammi wai sai de nayi karatu."

kuma naga ai aure shine gaba da karatu, tunda shi na duniya ne, Ba tare zamu lahira dashi ba."


Daddy yace "wannan gaskia ne, mommy tace "in banda abinki, duka nawa kike Lubabatu?! 


Daddy yace gasu fatima da salma, duk ba karatunsu suke ba." 

yanzu ga zainab nan da khadija duk sunyi registration na jamb kefa?"


Tace "banyi ba."

Yace inde aure ne za a maki, amma ki fara karatun ko." 


    Da haka shima ya lalla'bata.


  ************

An samu Yaya sultan yasa sunje tare. 

Saide fa ita maganarta, aure za tayi. 

Yaya sultan da suke tare, Yace Lubabatu meyasa kike maganar aure aure."

Tace "yaya Sultan ba dole nayi magana ba, kana ganin an fara cewa ku fiddo da matan aure, tunda kun fara aiki."


To ba dole in matsa in fad'a masu aure nake so ba,Tun kafin wata ta k'wace min kai."


Dariya yayi, Yace dan wannan kada ki damu, ba wanda zai k'wace maki ni. "


Tace "nafa san halin matan zamanin nan." 


Yace ki kwantar da hankalinki, banda macen aure sai ke, baki ga ban ta'ba yin budurwa ba."


Tayi Dariya. 


Sai de fa har yanzu a tsorace take. 

K'ara tada maganar tayi, Abba daddy yaje ya samu, suka zauna, Abba yace "maganar gaskia na fara tsorata da maganar Lubabatu, tana nan kan bakanta na ita aure take so, kana ganin har dukanta nayi akan haka, amma maganarta d'aya aure take so."


"ban sani ba, ko ta samu wani ne, da yake hure mata kunne a waje." 


Daddy yace "gaskia kam, ya kamata, mu zauna da ita, ayi magana da ita, tunda har ta nuna auran take so, gara a mata, da sharad'in za tayi karatu." 


Abba yace kana ganin fa ko su fatima bamu bari su tsaya da samari. 

Tunda suma nawa suke, yanzu fa take da shekara sha bakwai."


 Daddy yace "wannan ba abin damuwa bane." 


Inde yaron da take so, na gari ne, sai a aurar da ita d'in, inde yaro ya cire kunya, Yace aure yake so, to gara a mashi, inde har an yaba da halin wanda take so."


Abba yace to shikenan, Allah ya za'ba mafi alkhairi. "


Daddy yace " to Amin."


Idan Allah ya kaimu gobe, ma zauna da ita muji ko."


Abba yace to Allah ya kaimu, da haka ya mik'e ya wuce gida.   ******************

Washegari kuwa, Kamar yanda Daddy yace za a kira Lubabatu suji ta bakinta, 

Haka kuwa akayi. 


Yasa an kirata, tazo ta duk'a, Bayan ta gaidasu. 


Daddy yace "Lubabatu, naji wani zance ne, Na kina son aure, hakane?" 


Ta duk'ar da kanta k'asa tana wasa da hannunta. 


Yace "ke nake saurare, ki saki jikinki, kiyi min bayani."


Tace "eh hakane Daddy."


Yace "A ina kika samu mijin bamu sani ba?" 


  Tace "dama... Sai kuma tayi shiru. 


Daddy ya k'ara gyara zamanshi, Yace "kada ki ji komai, ki fad'a min ke kawai nake saurare."


Tace "yaya sultan nake so. 


Gaba d'aya suka kalli juna. 


Daddy yace "dama kun dad'e kuna soyayya dashi ne, mu bamu sani ba?" 


Ta d'aga mashi kanta. 


  Daddy yace "to ashe me hure mata kunnan a cikin gidan nan yake."


Ya d'auki waya ya kira Sultan, yana d'auka. 


  Yace "kazo yanzu ina buk'atan ganinka."


Ba a jima ba, sai gashi sun shigo shi da Yaya Aliyu. 


Suka samu wuri suka zauna. 


Daddy ya kalli Sultan yace dama kaine kake hure ma Lubabatu kunne, kana so ka hanata karatu ko?" 


  Yaya Sultan yace "ni kuma Daddy?" 

"Ni ban hanata tayi karatu ba."


 Daddy yace "ka hanata mana, tunda gashi har kasa mata kwad'ayin aure."


Yaya Sultan zaro ido waje yayi.! 

Sannan ya kai dubanshi wurin Lubabatu da kanta yake a k'asa. 


  Daddy yace "yaushe kuka fara maganar aure ba tare da mun sani ba?" 


Yaya Sultan yace "mun d'an dad'e."


  Daddy yace "yayi kyau, sai de gashi muna so Lubabatu tayi karatu. 


Zaka ita barinta tayi?" 

Tunda ta nuna auran take so."


Yaya Sultan yace "zan barta tayi." 


Daddy yace "to Alhamdulillah.!

Ya Kalli Abba yace "to kaji komai, ka yarda suyi auran ko kuwa? 


  Tunda gashi de suna son junansu."


Abba yace "na yarda." 


  Daddy yace "to yayi kyau." 

Kuma de kunji ko? Yakai dubansu wurinsu Ammi. 


Gaba d'aya suka ce Allah ya sanya alkhairi."


  Daddy yace "to zamu duba, muga yanda za ayi. 

Sai a tsaida ranar biki."


 Ya dubi Aliyu, Yace "kaifa? Ya kamata ka fiddo taka, tunda lokaci d'aya nace ku fiddo da mata. 

  

 Aliyu ya d'an sosa kai, Abba yace "kode sai mun nemomaka ne? 

Gaba d'aya sukayi daria. 


  Da haka duk suka tashi. 

Bayan sun koma cikin, 

Ammi ta dubi Lubabatu, tace kinde fi son auran ko?" 


  Za a maki, idan ma kinje can ba zakiyi karatun ba, wannan damuwarki ce."


Duka shekarunki nawa Lubabatu? 


Lubabatu tace "kai Ammi dan zanyi aure, Kamar na aikata wani mugun abu.


 Godiya ga Allah ya kamata kuyi fa."

Kema ya kamata ki fahimta, Kamar yanda su Abba suka fahimta."


 Ammi shiru kawai tayi, tana kallonta. 


     *************

Zaune suke, Aliyu ya dubi Sultan. 

Yace "Amma ka bani mamaki bros.!


  " Ka rasa wadda zaka aura, sai wannan shirmammiyar yarinyar nan.?

Wadda duka nawa take, Ka aureta kace ka auri budurwa."


Sultan ya dubeshi ranshi a 'bace.!


  Yace "yanzu baka ji komai ba, ka fad'a min irin wannan maganar? 


"koda Lubabatu mahaukaciya ce, A haka nake sonta."


"Idan zanso mace zan sota dan Allah ne, Ba dan wani abu nata ba. 

Ko sai ta cika budurwa, naga abinda ya birgeni a jikinta ba, a haka nake sonta. 

wannan shine son gaskia."


  Aliyu yace "wai nufinka haushi kaji?! 

To nide gaskia na fad'a, ba zan iya auran irinta ba."


  Sultan yace kai kace ai, kai daban ni daban." 


  Aliyu ya koma ya kwanta, gami da rufe idonshi. 


   **************

  Bayan sati d'aya da yin maganar, Daddy duka ya tarasu, Harda wasu 'yanuwansu na zaria. 

Dan asa rana. 


  Ranar itama Aunty jamila tazo gidan ita da ummi. 


  A take a kasa ranar bikinsu wata d'aya. 

Ba k'aramin dad'i suka ji ba. 


  Aunty jamila dake zaune, tace Lubabatu duka nawa kike? Da kike son aure? 


  Lunabatu tace "kai Aunty Jamila harda ke? 


 Aunty Jamila tace "eh mana, yanzu Zamani ya canza, ilimi ake nema, sai kiga kinfi k'arfin d'a namiji ya wulak'antaki."


  Lubabatu tace "Aunty Jamila ina da tabbaci akan Yaya Sultan, baze ta'ba wulak'antani ba." 


 Aunty Jamila tace "nima nasan da haka, Sultan yaro ne na gari."


 Lubabatu ta Washe baki. 

Aunty Jamila tayi daria, tace "mara kunya."


  Lubabatu ta mik'e da gudu, ta shige d'aki tana daria. 


Ummi da ta fito daga toilet, ta kalli Lubabatu, tace "Amarya ya akayi kike ta daria haka? 


 Murmushi ta k'ara yi. 

Ummi tace "naso ace kin fara karatu, Sannan zaki yi aure."


Lubabatu tace "wai meyasa yanzu ake fifita ilimin boko ne akan aure?" 


  Nifa abin nan na bani mamaki.!

Ummi tace "a'a ba fifita boko ake ba."


  Lubabatu tace "to kowa sai ya dameka akan boko boko, haba."


Sai ace wai mutum be isa aure ba. 


 Ummi tace to kiyi hak'uri, ni bance baki isa aure ba."


 Rayuwar nake kalle maki."


Lubabatu tace "ko nace maku ba zan yi karatu bane, zanyi." 


 *************

Yaya Sultan ne ya kira Lubabatu, ta fita. 

Binta yayi da kallo, a zuciyarshi yana fad'in, "ance baki da hankali ni kuma a haka nake son kayata."


  Ta k'araso kusa dashi, ta d'an hura mashi iska a idonshi. 


  Ya lumshe idonshi. 

Tace "wannan kallon haka fa Yaya Sultan?" 


  Yace "kin san idan ina ganinki, komai nawa kwancewa yake. 

Shiyasa idona be iya cirewa a kan kyakykyawar fuskan nan naki."


  Dariya tayi, tace "nima haka Yayana."


Ina jinka sosai a zuciyata. 


Sun dad'e suna fira. 

Yace "kinga bikin ba a sa da yawa ba."

Ya kamata kije ku shirya duk abinda ya dace ko. 

Idan kun gama sai ki fad'a min."


  Tace "to shikenan."

Da haka ta koma gida, ta tara Ummi da basu tafi ba, dasu zaynab, suna shirya yanda zasu yi. 


  Yaya Fatima ta kira Lubabatu, tace "tace yanzu Lubabatu aure zaki yi? 

Ko mu bamu yi ba fa. 

Memakon ki bari ki fara koda karatun ne."


  Lubabatu tace "haba Yaya Fatima dan zanyi aure, wani abu ne?"


Wai kode bak'in ciki kuke min na samu miji baku samu ba? da duk zaku dameni da maganar zanyi aure."


 Banfa hana kowa yayi ba."


Yaya Fatima tace "mahaukaciya.! 

Yimin shiru, Akan me zan maki bak'in ciki? Koma wa zaki aura?"


  Kije kiyi auran mana, wannan damuwarki ne."

Ta kashe wayan. 


 Lubabatu ta bi wayan da kallo,da taga abu zai dameta. 

Ta mik'e taci gaba hidimarta.    *****************

Lubabatu Amarya, an bazama sai shirye shiryen biki take. 


  Ta dage sai raba kayan sa rana take ma k'awayenta. 


  Ta fito da shirinta tsaf, ta zauna kusa da Ammi, tace "Ammi na gama shiryawa, zanje wajen Amina." 


  Ammi ta fara daria, Lubabatu ta kalleta a shagwa'be, tace "Ammi dariyar me kike?" 


  Ammi tace "ke kike bani daria idan na tuna aure zakiyi, gashi kin dage sai rabon kayan sa rana kike."


 Tace gaba da daria. 


  Lubabatu ta zum'buro baki, tace "kai Ammi shine kike min daria."


 Ammi tace "ai abin daria ne, ko kunya baki ji." 


 Lubabatu ta mik'e, tace "nide na tafi sai na dawo."


 Ta fice d'akin tana mamakin yanda gaba d'aya 'yan gidan suka d'auketa. 


 Ta isa wurin su Mommy ta shiga d'akinsu Zaynab, tace "kun shirya ko?" 


  Khadija tace "ke kawai muke jira Amarya."


 Murmushi tayi, Sannan ta kalli kanta, tace wallahi ina mamakin su Ammi da har yanzu na rasa me suka d'aukeni." 


 Zainab tace mai ya faru kuma?"


  Lubabatu tace "uhmm da suke d'aukata k'aramar yarinya, Kamar ban isa aure ba.


 Ku kalleni da kyau, ta juya jikinta, tace ban isa aure bane? 


  Khadija tace "kin isa mana sude suke kallon haka."


 Lubabatu tace "Mommy ce kawai har yanzu banji tace komai a kan haka ba, ko ta kushe."


 "Wallahi duk wanda ya nuna k'arara be son aurena da Yaya Sultan, kallon mak'iyina nake mashi."


  Zainab tace "kajiki da wata magana, 

Akan me za a ce ba a son auranki da Yaya Sultan."


 Lubabatu tace "ai hakane mana, sai aka 'bige da wai nayi  k'ank'anta, to ayi min auran a ga idan ban zauna ba harda k'aruwan d'a." 


 Khadija tace "ai mun lura da haka."


 Lubabatu tace "kada ma ku lura, nide nasan Mommy ce kawai bata min bak'in ciki."


 Zaynab tace "kede kika sani, Mommy abinda yasa kika ji ba tayi magana ba,kunya take ji, tana surukuta dake." 


  Lubabatu tace "kai ina k'aryane, Mommy ba zata ta'ba surukuta dani ba. 


 Bari ma kuga inje wurinta ku gani, Mommy d'in da har yanzu ba abinda ta fasa min wanda take min a da."


 Ta mik'e tace "ku sameni d'akin Mommy ku gani."


 Tayi d'akin Mommy ta fad'a jikinta. 


 Mommy tace "ke rufa min asiri kada ki idasa ni."


Lubabatu tayi daria, tace "Mommy wai kinji su khadija da wata magana, wai surukuta kike dani.!"


  Mommy tace "a'a ya za ayi nayi surukuta da d'iyata?" 


 Daidai lokacin su Zaynab suka shigo. 


  Lubabatu tace "to kunde ji da kunnanku."


 Khadija tace "eh munji, ki tashi mu tafi, dan yau garin zafi yayi yawa muyi mu dawo." 


 Ta mik'e tace "Mommy sai mun dawo."


Mommy tace "a dawo lafia."


  Suka fice,Bala dake zaune yana jiransu ya mik'e. 


 Suka shiga suka wuce F. G. C


  Saida suka fara shiga gidan principal, suka gaidata gaba d'ayansu. 


 Ta amsa cikin sakin fuska, tace Lubabatu 'yan mata kayan rigima."


 Lubabatu tace "ai yanzu rigima ta k'are, gashi har zanyi aure."


  Principal tace "aure kuma? Ba zakiyi karatu ba?"


  Lubabatu tace "zanyi gashi har zanyi jamb, sai de a gidanshi zanyi karatuna."


 Principal tace "Masha Allah! 

Allah ubangiji ya nuna mana."


 Gaba d'aya suka ce amin. 


Lubabatu tace "dama nazo wurin Mate d'ina ne."


 Principal tace "to ai ba damuwa zaki iya zuwa wurinsu, duk suna hostel yau weekend ai."


  Suka mik'e, Lubabatu tace "sai mun fito." 


 Suna fita, Zaynab tace "kede baki da kunya."


 Lubabatu ta kalleta tare da yatsina fuska, tace "rashin kunyar me nayi?" 


 Zaynab tace "memakon ki bari mu mu fad'a, amma kika tashi kika fad'a." 


 Lubabatu tace "au shine nayi rashin kunya? 

Aiko banga abinda nayi ba, abin alkhairi fa ya sameni na fad'a."


 Har suka isa hostel suna magana. 


 Amina na ganinsu, da gudu ta rugo ta rungume Lubabatu, suka shige ciki. 


 Haka ta fara d'awainiya dasu. 


Gaba d'aya duk suka hallara, aka zauna fira. 


 Lubabatu tace "garin kwakwi nake son a kwad'a min inci."


 Amina tayi daria, tace "inde garin kwakwi ne ai kinzo gidanshi, yanzu kuwa za a had'a maki."


Haka ta mik'e ta had'o masu, Lubabatu naci, tace "amma fa garin nan ya min dad'i sosai, students power kenan, 

ko dan an dad'e ba a sadu ba."


Zaynab tace "kede ci, kinsa munzo zamu rage masu aukin abinci." 


Amina tace "kin jiki da wata magana, Bayan duka sati biyu ya rage muyi candy." 


  Lubabatu tace "Allah sarki, dafa anyi candy zanyi aure."


 Amina tace ban son k'arya fa."


Lubabatu tace "ga Sisters d'ina ki tambayesu."


  Amina tace "wai da gaske? 


Khadija tace "eh mana, kayan sa ranar ne ma muka kawo maki, gaba d'aya wurin suka d'auki gud'a. 


 Wata maryam tace "dole ne mu dangane da bikin Lubabatu." 


 Suka ce sosai kuwa. 


 Lubabatu tace "amma de kuna koya ma yaran nan hankali ko?" 


 Amina tace "suwa kenan? 


 Lubabatu tace "yaran nan mana." 


Maryam tace "Lubabatu ba dama, nasan da har yanzu kina school d'in nan sai juniors sun raina kansu."


 Lubabatu tace "ai da babu sauk'i." 


 Amina tace Allah ya shiryeki, har yanzu de hali na nan."


Lubabatu tace "me za a fasa, mutuwa ko hisabi?"


 Zaynab tace "ba ko d'aya, Allah de ya shiryeki." 


 Sai yamma ta basu kayan da suka kawo masu, Sannan suka yi shirin tafiya. 


 Ta mik'a ma Amina miyar da tayi mata. 


 Amina tace "kai amma de na gode. 


  Har wurin motanmu suka rakosu.


 Ranar de iyakarsu nan suka koma gida. 

  

    *****************

Su Lubabatu manyan 'yan mata, anyi candy. 

Gashi ko jamb d'inta ba yanda Yaya Sultan baiyi da ita ba tasa ABU tunda gasu Fatima, tace ita polytechnic za tayi,tunda abinda za tayi a can shi za tayi a nan. Su Lubabatu 'yan computer science. 


   *************


  Ga kuma shirye shiryen biki ana tayi. 

  Ba k'aramin k'ok'ari yayi ba wurin had'a mata lefe wanda fasaltashi ba zai yuwu a nan ba. 


  Kullum ba zama an dage sai yawon rabon IV. 


  Yaya Sultan ne ya kirata ta fita ta sameshi. 


 Ya dubeta yana murmushi gami da cewa.... "Amarya.!


  Murmushi tayi, Yace "to ga d'inkin na amso maki duba kiga yayi kyau ko?" 


  Tana dubawa, ta kalleshi.. "Haba Yaya Sultan ya zaimin d'inkin da bashi nace ba, gaskia bana so,sai de ka maida mashi yasan yanda zaiyi."


  Binta yayi da kallo..."to ni d'inkin yamin ai ni za a sa mawa in yaba ko? To yamin." 


  D'an harararshi tayi tace "gaskia bana so sai de in hak'ura dashi." 


 "to tunda baki so ki barshi a nan." 


  "Au haka zaka ce min ko? To a barshi a nan d'in." 

Ya fara shigewa cikin gidan. 


 Ta saki ledar rigar a nan ta wuce ciki itama. 


  Can an d'an bada mintuna, ta fito harabar gidan, sai kalle-kalle take sai kace mara gaskia. 


 Tana isa tasa hannu zata d'auki ledar, Yaya Sultan dake la'be yace "na ganki!" 


  ta saki ledar ta dank'ara cikin gidan da gudu. 


  Daria ya hau yi mata.... "kai Lubabatu! Allah ya shiryeki da wannan shirman naki."


 Yaya Aliyu da ya k'araso wurin, Yace "ai dama kasan wadda zaka aura, kaga duk shirman da tayi sai ka zauna kaita daria tunda aiki ya sameka." 


  Ya shige ya barshi nan. 

Zurfa'u ce tazo wucewa. 


  Yace "yauwa Zurfa'u d'an shigar ma Lubabatu da kayan nan ciki."


 Amsa tayi ta shige ciki, ta mik'a ma Lubabatu ledar. 


 Lubabatu tace "wannan fa na miye?" 


  "Yaya Sultan yace na kawo maki." 


 Mtssw... "to meyasa kika amso?" 

Zurfa'u tace "ikon Allah! 

Ni daga bani sak'o in kawo sai nayi laifi."


 Ammi ce ta fito..."Sarkin fitina me kuma ya faru?" 


  Lubabatu ta fiddo da kayan dake cikin leda ta d'aga ma Ammi... "Ammi dan Allah ki dubi d'inkin da Yaya Sultan yasa aka min fisabilillahi! 

  Ya tashi sai zuzuta min telanshi yake wai ya iya d'inkin mata sosai." 


 Ammi tace "ni ai banga aibun d'inkin nan ba jibi fa yanda yayi kyau" 


 Lubabatu tace "Allah yasa ba dan hankalina ya kwanta kika ce ba?" 


"bari na kai ma Mommy ta gani, nasan zata fad'a min idan beyi ba. "

  Dariya Ammi tayi, tace "kai ana de mahaukaciyar amarya." 


  Ranar de d'inkin nan ba wanda ba a nuna mawa ba. 


  ***********

sun fara hidimar biki cike da annashuwa, bakin nan na Lubabatu yak'i rufuwa. 

  Gashi Aunty Fatu k'anwar mamanta da tazo daga maiduguri tun ana saura sati d'aya ta rik'eta a d'aki sai had'ata take da k'amshi kala kala, Ga uban had'in magunguna da take ta d'inkira mata.

Duk yanda Yaya Sultan yaso ya ganta dole ya hak'ura.


  Duk wasu k'awayenta har sun iso irinsu Amina, sai 'yan ciki gari. 

  Gashi har sun fara shagali, anyi shirin tafiya dinner,da Daddy ya had'a masu. 

D'aya k'wak'k'wara d'aya sukayi da ya k'ayatar ba sai an cika ba. 


Amarya ba k'aramin kyau tayi ba, yanda kasan ba Lubabatu ba,shigar da tayi ya k'ayatar. 


  Yaya Sultan ne ya bita da kallo.... "anya ko Lubabatu na ce haka?" 


  "gaskia ayi a d'aura auran nan kada wani ya sace min ke." 


 Murmushi tayi... "Yaya Sultan dena fad'in haka me sace maka ni ai sai ya shirya." 


  Yace "gaskia kam nima na yarda da haka, wannan k'amshin da kike zubawa ai sai kisa na kasa sukuni." 


  Tace "ai wannan k'amshi aikin Aunty Fatu ce, Kasan 'yan maiduguri wurin had'in k'amshi dole a sara masu." 


  Har suka isa wurin dinner sai fira suke. 


 Lokacin da suka shiga aka sa masu wak'an bikinsu da yaji kalangu. 


  Kowa na wurin saida suka birgeshi. 

Sosai dinner ya k'ayatar inda ya had'a da manyan mutane. 


  An gama ciye ciye da tand'e-tand'e sun gama lafia inda aka fara kwashe mutane ana maidasu gida. 


  *************

Bayan sun dawo wani abokinsu Yaya Sultan mai suna Abakar da yazo daga Abuja, Yace "gaskia mutumina ba k'aramin dace kayi da mace mai kyau ba ga hankali." 


  Yaya Aliyu yace "ai ka bari kowa na yabonta wurin hankali da natsuwa."


  Lumshe idonshi yayi dake kallon Yaya Aliyu tunda ya fara magana, Dogon ajiyar zuciya ya sauke, dan yasan Yaya Aliyu zai iya kwafsa mashi a gaban friends nasu. 


 Murmushi Yaya Aliyu ya saki.!


Hidima ake iya hidima, wanda yau aka had'a gagarumin walimar da ya tara manyan malamai da suka bada lecture akan zamantakewar aure.


 Gaba d'aya wad'anda ke wurin hankalinsu yana wurin malamai, yanda yake shigarsu yasa duk jikinsu yayi sanyi. 


  Haka akayi aka gama bayan an raba duk abinda ya dace a wurin. 


  Ba wata k'arya suka zauna suka yi a hidiman bikin ba, sunyishi cikin girma ba tare da almubazzaranci ba. 


  *************

Yau take asabar mai d'inbin daraja a wurin Lubabatu da angonta Yaya Sultan. 


  Inda wurin ba k'aramin tara manyan mutane yayi ba, Tare da governor da muk'arrabanshi, da sarki. 


  A take aka d'aura auran Sultan da Lubabatu kan sadaki dubu hamsin. 


 Su Sultan baki yak'i rufuwa. 

Sai gaisawa yake da mutane ana ta hotuna. 

 Daga nan kuma wurin reception suka wuce. 


  Lubabatu dake zaune abokan wasa suka tasata irinsu ummin Aunty Jamila sai tononta suke. 


  Tace "ai da yake wanda nake so zan aura, kunga ba shawarar wanda zan d'auka."


 Yaya fatima tace "duk wannan shirman de ki denashi kiyi hankali dan ba kowane namiji zai d'auki halin nan naki ba."


  Ta bita da kallo...." to naji na d'auka."


  Dare nayi aka fara shirin d'aukan amarya, inda duk ta gama jik'a fuskanta da hawaye. Ba k'aramin nasiha suka mata ba. 

Sai kuka take, lokacin da za a fita da ita, haka ta rink'a ihu tana kiran Ammi da Mommy dan shed'ana harda 'yan gidan take kira. 


 Da k'yar aka shiga da ita mota sai kuka take, har suka isa unguwar da za a kaita malali. 


 Da tuni dama sun mata danki. 


Ba k'aramin kyau gidan yayi ba, nan su Amina suka kwana. 

  Washegari da wuri k'awayenta na nesa suka tafi. 


 Bayan an gama gyara mata ko ina da yamma kowa ya watse aka bar amarya da sai kuka take. 


  *********

Sai dare ango da abokanshi suka shigo, 

Da har yanzu ta k'udundune kuka take. 

K'arasowa kusa da ita yayi... "haba Lubna me ya saki kuka haka?" 


 Kwantawa tayi a jikinshi taci gaba da kukan. 


  Abakar yace "kai wannan amarya taka da shagwa'ba take. 


  Nan suka zauna suka gama basu shawarwari da nasihar da ba a rasa ba sannan suka tafi. 


  Bayan ya rakasu ya dawo d'akin ya taddata sai shashshek'ar kuka take. 

  

 Jawota yayi jikinshi..."haba my lubna kamar ba da yaya Sultan d'inki kike tare ba,Kin san tuntuni bana son kukan nan naki fa."


 Share hawayenta ta fara yi, Yace "yauwa tawan, tashi mu shiga ciki ki rage kayan jikinki kiyi wanka ko zaki ji dad'in jikinki."


  Ba musu ta mik'e ta bishi ciki, da kanshi ya had'a mata ruwan wankan, Yace "idan kin gama kiyo alwala daga nan."

ta d'aga mashi kai ta mik'e ta shiga. 

Shi kuma ya wuce d'akinshi yayi wanka tare da alwala yasa jallabiya ya dawo d'akin duk bata fito ba. 

  Bayan ta gama ta fito sanye da dogon hijabi, Murmushi yayi yace "yau kuma ni ake 'boye ma jiki? 

Yaya sultan d'inki ne fa." 


  Duk'ar da kanta k'asa tayi. 

Bayan ta gama shiryawa. 


 Ya dubeta cikin Murya k'asa-k'asa... "yanzu ki tashi muyi sallah mu gode ma Allah da ya mallaka mana juna a matsayin ma' aurata." 


 Mik'ewa tayi suka yi sallah, ya dad'e yana koro masu addu'o'i. 


 Bayan Sun gama ya mik'e da kanshi ya d'auko masu plate da cups ya juye masu kazar da ya shigo dashi, ya zuba masu yogourt d'in da yazo dashi. 


 Duk tak'i taci, da k'yar ya lalla'bata ya dinga bata da kanshi. 


   Bayan sun gama ciye ciyensu ya fidda komai ya gyara wurin tsaf. 

Ya dawo wurinta da har ta d'are gado ta kwanta. 


  Ya kashe fitilan d'akin shima ya kwanta, 

Jawota yayi jikinshi daga nan zance ya canza. 

  Cikin kuka ta fara magana..."Yaya Sultan kaifa Yayana ne."

Tana yi tana tureshi. 


 Ranar kam Mommy Daddy Abba Ammi, duk sunsha kira wurin Lubabatu. 


  **********

Washegari kuwa ko ido ta kasa had'awa dashi, sai de yana shan shagwa'ba a wurinta. 


  Shima ya dage sai nan-nan yake da ita, ita kuma ta samu abinda take so. 


  Sai yamma ya samu ya fita, shima dan bak'in da keta zuwa yasa ya fita. 


  Sai gasu Yaya fatima gaba d'ayansu sun shigo, da gudu ta taresu suka shiga ciki. 


  Affan sai da biyosu. 


  Ta kallesu tana murmushi na alamun akwai magana a bakinta... "in fad'a maku sai da akayi, ba k'aramin wahala naci ba, wallahi Aunty Fatu ta cuceni."      

   "Magungunan da tasa nayi tasha naci wuya, kuma zaku ji yanda naji."


 Yaya fatima sakin bakinta tayi tace "ke wa ya fad'a maki ana fad'in abinda ya faru tsakanin miji da mata? To Ki rink'a kama bakinki." 


  Zum'buro baki tayi.! 

Zaynab tace "ni bani labari." 


 Yaya Fatima tace "tunda abin haka ne ku tashi mu tafi kawai." 


 Yaya Salma tace "baku da hankali wallahi.!" 

 Gaba d'aya suka kwashe da daria. 

  Lubabatu ta mik'e ta dawo rik'e da plate d'in kazar jiya da basu cinye ba, Ta d'umama masu. 


 Mik'a masu tayi... "ga kazar siyan baki kuci bari na kawo maku d'an juice ko." 


 Ta fita ta dawo da juice da cups a hannunta ta dire masu. 


 Tace kunga ko ci ba muyi ba sosai saboda ina fargabar yanda zata kasance tsakanina dashi."


 Ta d'auka ta fara ci, tana maida jawabi. 


  Yaya Fatima tace "wallahi idan shirman nan zaki ci gaba dayi, kina damunshi da surutu ya rink'a guduwa yana barinki ke d'aya." 


 Lubabatu tayi daria... "kema kin jiki.! 

Ai ba zai fita ya k'yaleni ba, kut! Aiko ya fita ya k'yaleni binshi zanyi." 


 Dariya ma ta basu. 

Yaya Salma tace "gaskia har yanzu da sauranki." 


 Ba sune suka bar gidan ba sai bayan isha'i sannan Bala yazo ya d'aukesu. 


 Affan ya dage shi wurin Lubabatu zai zauna, 

Yaya Fatima ta tasashi suka tafi. 


  Da suka koma Daddy fad'a yayi ta masu... "daga kaita jiya zaku fara mata zarya haka ake yi?"

 Khadija tace "wasu kayanta muka kai mata." 


  "ke Fatima da Salma kuma ku fito da naku mazajan kuna jina ko?" 


  A tare suka amsa da.... "to Daddy." 


 Ya Kalli Zaynab da khadija yace "kuma harda ku duk mu aurar daku mu huta gaba d'aya."


   ***********

Watanni sunja! Lubabatu an dage sai zaman aure ake, duk da shirmanta ta dage biyayya iya biyayya take ma Yaya Sultan, bata ta'ba yarda tayi wani abu da tasan zai 'bata mashi rai.


  Ba k'aramin jin dad'in haka yake ba. 


 Daga ita sai Almajirinta wanda take d'an aike idan tana buk'atar wani abu. 


 Daga k'arshe kuma da Yaya Sultan yaga ta cika biye mashi tana fira dashi, yasa ya sallameshi. 


   **********

  Kwance take jikinshi tana wasa da hannunshi, kwanto da kanshi yayi kanta.... "anya kuwa akwai namiji da ya fini sa'ar samun mace kuwa?" 


  "Lubabatu baki ta'ba 'bata min rai ba tunda mukayi aure." 


 Murmushi taci gaba da yi. 


  "A gaskiya ina matuk'ar alfahari dake, Kinba marad'a kunya ina jin dad'in haka kici gaba kada a ta'ba jinmu a rana." 


  Murmushi tayi tare da juya idanunta... "nima ba k'aramin jin dad'i nayi ba da ka kasance miji a gareni mai hak'uri da iya tattalin mace." 


 Yace "Allah yasa hakan to ya ci gaba da kasancewa a tsakaninmu har k'arshen rayuwarmu."


"Amin ya Allah."


  Fitowa tayi daga d'aki ta isa wurin Yaya Sultan dake kwance kan kujera yana d'an kallo, cikin shagwa'ba tace "Yaya Sultan gashi ka koran min Almajiri kuma ina so inyi aike za a siyo min kayan miya."


  Mikewa yayi ya zauna..."meyasa kika bari har wani abu ya k'are ba tare da kin fad'a min ba.?"


  "Bana so kina barin wani abu ya yanke."


Tace "insha Allahu zan kiyaye."


  "yanzu de tunda ka kori almajiri sai ka tashi inyi maka lissafin abinda zaka siyo." 


 Mik'ewa tsaye yayi yace "ina sauraranki.! 


Ta mik'a mashi dubu d'aya dake hannunta. 


"Gashi ka siyo min tumatir da attarugu sai ku'bewa, 

Tuwo nake son ci yau." 

 Ya amsa..."to ranki ya dad'e an gama."


 Ya fita can sai gashi ya dawo ya dire mata ledar a gabanta..."Gashi Hajiyata na dawo."


 Bud'ewa tayi ta duba... "ya naga kayan da yawa.?" 


 Yace "eh saboda ba zan iya siyo kad'an ba." 


 "Taf! Aiko sai ka biyani kud'ina tunda ba duka nace ka kashe min ba."


  Dubanta yayi yan daria." ya za ayi ki bani sak'on da ban wuce na d'ari biyu ba gashi ina kallon sauran canji a hannuna."


 Duka ta fara kai mashi cikin shagwa'ba take fad'in "ni wallahi sai ka biyani kud'ina."


  Cikin daria yace "naji zan biyaki amma sai na dawo zan baki." 


 Da haka ya lalla'bata ta hak'ura. 


  ***********

Yaya Aliyu ya samu mata suma Yaya Fatima da Yaya Salma sun samu miji an sa masu rana. 


 Ga Lubabatu har sun fara zuwa school, sosai take dagewa tana maida hankali wurin karatunta. 


   Sa ranarsu ba wani lokaci aka d'auka ba, suka fara hidiman biki, lokacin Lubabatu nada ciki wata uku. 


  Yaya Sultan duk inda tasa k'afa nan yake sawa, dan be son ya barta ita kad'ai ba tare da suna tare ba. 


  Affan ne ya shigo yace "Aunty Lubabatu kizo Yaya Sultan na kira."


   Da sauri lubabatu ta mik'e


   Ummi da suke zaune ta dubi Lubabatu tace "kai wannan nanik'e ma juna da kuke ko magnet sai haka."


 Lubabatu tace "kin jiki ya son ranki."


"Ummi tace "sai ana cikin fira mai dad'i duk yabi ya hanaki sakewa."

   

   Zaynab tace ni ban ta'ba ganin haka ba ka hana mutum sak'at har a gidansu."


  Lubabatu tace "a hakan nake son mijina."


"duk kunbi kun addabeni da maganar zamana da mijina, iya rik'eshi da nayi yasa baya so inyi nesa dashi dan haka ku dena 'bata bakinku koya ya kamata ku tsaya kuyi." 

  Ta fice ta barsu nan.

   

    *********

Ansha hidimar biki lafia kowa an kaishi gidanshi, Yaya Aliyu ma an kawo mashi matarshi.

   Cikin Lubabatu ya shiga wata tara haihuwa yau ko gobe. 


  Kwance suke an fara kiran sallan asuba, ta farka Yaya Sultan na ta barci, ta fara wayyo Allah cikina, ta fara bubbugashi tana fad'in cikina. 


 Da sauri ya mik'e yana fad'in "sannu tashi muje asibiti." 


 Ya suri key d'in mota, Ganin yanda ya rud'e yasa ta kwashe da daria. 


  Binta yayi da kallo,tace "wasa nake maka." taci gaba da daria. 


 Hancinta yaja... "keko? kin kyauta." 


  Tace "kaga yanda ka rud'e kuwa? To da kake cewa mu tafi asibiti a haka zaka tafi?" 

 Taci gaba da daria. 


  Yace "sai kace ban damu dake ba da har zan tsaya gane abinda yake yake jikina, Ai a haka zan tafi." 


 Amma fa kin tsoratani da yawa ranar da labour d'in zaizo yana nan zuwa,sai de ina rok'on Allah ya kawo maki mai sauki. "


 Amsawa tayi da Amin ya rabbi." 


 Toilet ya fad'a yayi alwala ya fito yace tashi ki shiga kiyi."


 Jallabiya ya zura ya wuce masallaci. 


  ************

Basu da buri daya wuce suga Lubabatu ta haihu lafia. 


  Haihuwa lokaci gareta, Lubabatu ciwon baya da ciki ta fara ji, ta kira Yaya Sultan da baya gida, yana d'auka tace "bafa lafia naga kamar haihuwa ne." 

 

 Ba tare da yace komai ba, Ya datse wayar ya shiga mota ya tada. 


 Be dad'e ba ya iso gida, ya taddata zaune kan kujera Taci kwalliya ga takalmi tasa. 


 Yanayin yanda ya shigo cikin tashin hankali, tsayawa kallonta yayi... "kin fara ko?" 


  Tace "Allah Yaya da gaske nake, kai nake jira duk kayan haihuwan ma na kan gado na shiryasu."


 Duk kallon mamaki yake mata, yasan ba haka ake nak'uda ba. 


 Shiga ciki yayi ya d'auko kayan suka fita, duk da kanta ta fita ta shiga mota yaja suka tafi. 


  Suna isa, Bayan sun gaisa tace "haihuwa nazo."


 Da mamaki suka kalleta.! 

Wata nurse tace "haihuwa kuma? Amma kika ci uban kwalliya haka kamar zaki gidan biki?" 


  Suna dubata suka tabbatar da haihuwa ce,

Sai de da d'an sauran lokaci, ko zaku koma gida anjima ku dawo? 

Lubabatu tace "ba inda zani ina nan."

Doctor d'in yace "shikenan." 


 Nan Yaya Sultan ya kira Mommy ya fad'a mata. 

Ba a jima ba sai gasu sun shigo asibitin. 


 Yanda suka ganta suma ya basu mamaki.! 


 Ammi dubanta tayi cikin mamaki... "anya kuwa Lubabatu haihuwa ce? Ko dan kiba mutane wahala?" 


 Lubabatu tace "wai meyasa kowa yake mamaki, gashi ku tambayeshi an tabbatar da haihuwa ce."


 Mommy tace "nan wahala zaki ta sha tunda Haihuwar bata zo gadan-gadan ba."


 Lubabatu tace "gara de ina kusa da asibiti ba sai na fita hayyacina ba." 


 Mommy tace "bama a fatan ki fita hayyacinki." 


 Sun dage suna ta zaman jiran haihuwa. 


 Ya motsa mata ya tsaya, firanta take, sai ya motsa mata ciwon kuma tayi shiru. 


 Can da ya murd'a mata, sai gata ta fasa ihu, ta fara masu kuka, Ammi tace "wa y gaya maki yarinya." 


 Mommy tace kiyi hak'uri kina addu'a."


 Nan suka fita waje suka barta da nurses. 

 Azaba ya isheta, duk wanda ta cafki hannunshi da k'yar yake k'wacewa. 


 Can Allah ya temaketa ta sunkuto d'iyarta mace. 


 Wani dogon numfashi taja, tayi lamo sai maida numfashi take. 


  Bayan an gama gyarasu aka mik'a masu baby suka shiga sai sannu suke mata. 


  Mommy ta dubi Sultan..."idan ka tashi gida zaka wuce damu can zata koma."


 Yace "Mommy ai bamuyi magana daku ba zata koma."


 "Mommy tace "Gashi na fad'a maka yanzu."


 Ba yanda zaiyi suna sallamanta dole gida ya wuce dasu, gidan Mommy aka wuce da ita,dan Ammi nata idone. 


   ***********

Gida sai cika yake da 'yan barka, gashi a lokacin khadija Ummin aunty Jamila da zaynab suma an kusa bikinsu. 


  Gaba d'aya Sultan shima gidan ya dawo ya tare. 

 Ba fad'an da besha ba wurin Mommy da surutu.  Ranar suna na zagayowa yarinya Taci suna Nana Aysha. 


  Sultan kullum cikin lissafi yake, ya samu Mommy da maganar yana so Lubabatu ta koma gida. 


 Mommy tace "ba yanzu ba sai anyi bikin su Zaynab."


 Ranshi ya 'bata san kace wanda aka aiko ma da sak'on mutuwa..."haba Mommy yau fa satinta d'aya da gama wanka fa, biki kuma akwai sauran sati biyu a kai."


 Mommy tace "ba zata koma yanzu ba." 


 Yace "Mommy dan Allah ki bani ita mu tafi ai ta zaunu duk wani warkewa da za tayi ai tayi."


 "ka isheni idan naga dama arba'in biyu za tayi, dan haka tashi ka fita ka bani wuri."


 Haka ya mik'e ya fita jiki a sanyaye. 

Ya kira Lubabatu ba a dad'e ba ta d'aga. 


 "kinga Mommy ta hanani ke ko? Ki nuna masu kema kina son komawa gidanki."


 Ta waro idanunta kamar yana kallonta...."kai Yaya Sultan so kake suce bani da kunya,tunda sunce sai anyi bikin su Zaynab kayi hak'uri da hakan, yanda kwanaki ke gudu zaka har yazo."  "kema haka zaki ce ko?" 

Ya katse wayan, tabi wayan da kallo, Tare da fad'in to ya kake so inyi daka?


  Tun daga ranar ya dena kiranta, idan ta kira yak'i d'auka, idan ta gaji ta mashi text. 


 Fushi sosai ya d'auka dasu, 


 Ammi da mommy zaune, Mommy tace "kinga d'anki fushi yake damu har yanzu."


 Ammi tace "to kin rik'e mashi mata kin hanashi." 


 Mommy tace "aiko ya gaji ya sauko, dan sai anyi biki zata koma yanzu ba gashi saura sati d'aya ba."


 Ammi tace hakane. 


  Lubabatu da ta gaji itama k'yaleshi tayi Taci gaba da hidimanta. 


 Gashi har sun fara shirye - shiryen biki. 


 Sai shagali ake. Lubabatu ta saki jiki, Ga Nana Aysha tayi k'iba abinta. 


  Haka suka sha hidiman biki lafia aka kai kowacce gidanta duk a cikin kaduna. 


  Mommy suka fara shirin maida Lubabatu gida. 


 Sai a lokacin Sultan ya sauko, ita kuma Lubabatu lokacin take nata fushin. 


 Da kanshi yazo y d'aukesu suka wuce gida da 'yan rakiya. 


 Bayan sun tafi sai faman nan nan yake da ita, ta shareshi, jawota yayi... "haba my one and Only.! Nine fa yayanki kike fushi dani."


 Tace "kaima ba fushi kayi dani ba."

Ta fara kuka, ya fara goge mata hawaye, yana fad'in kiyi hak'uri ba zan k'ara ba, Ya rik'e kunnanshi."


 Amma idan baki hak'ura ba ki d'auki duk hukuncin da ya dace a kaina."


 Ta kwanto jikinshi...."na hak'ura yayana." 


 Rungumeta a jikinsa yayi tayi lamo.    *********

Rayuwa Taci gaba da tafiya, Zamansu suke cikin aminci da soyayyar juna. 


 Yaya Sultan haka yake jansu kamar ya had'iyesu. 


 Gashi har ta gama had'a diploma d'inta, da k'yar Yaya Sultan y lall'bata ta d'aura H.N.D

  Ya sai mata mota dan taji dad'in karatun. 

  Ga Nana Aysha ta girma tayi wayau abinta, tafi zama wurin su Ammi, sai ta tashi school ta wuce ta d'aukota. 


  Su Yaya fatima suma duk Allah ya albarkacesu da samun 'ya'ya. 


   **********

Bayan shekara hud'u da haihuwan Nana Aysha lokacin lokacin haifi 'yan biyu mace da namiji. 


  Abubakar sadik sai Maryam. 


  Gida ya zama gidan jin dad'i da annashuwa. 

Lubabatu an zama babbar mace. 


  Ga karatu ta gama, ta gama service d'inta. Yaranta gasu gwanin sha'awa. 


  Lubabatu na alfahari da Yayanta mijinta.


 Da Suke zama na mutunci da amana. 


  Ji suke kamar su had'iye junansu saboda k'auna. Su Lubabatu anyi hankali. 


 Ba abinda baya masu na jin dad'i. 

Gida mai cike da farin ciki da kwanciyar hankali da 'ya'yansu. 


  Hankalin kowa a kwance, Zaune suke ta dubi Sultan...."ina rok'on Allah ya barni tare da kai har k'arshen rayuwata."


 Yace nima haka uwar 'ya' yana."   THAMAT BI HAMDULLAH.! 

GODIYA GA ALLAH SUBHANAHU WATA ALA DA YA BANI IKON GAMA LITTAFIN ALAK'A LAFIYA KUSKURAN DA NAYI A CIKI ALLAH YA YAFE MIN. 


  MASOYA ALAK'A INA MAKU FATAN ALKHAIRI ALLAH YA BARMU TARE AMEEN. 


Tags: #alaka #soyayya #jinkai
2284
0
1
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!