AbdulWahab!

Written by Rabiatu Mashi SkPublished on 2018-12-12 16:05:47Category RomanceAbdul wahab bai yarda da soyayya ba, a ganinshi soyayyar gaskia ne, kafin ya haɗu da khadija wacce zata sauya mishi wannan tunanin nashi, ɓangare ɗaya kuma ga Sadeey da take tsananin son sa tun tana er ƙaramarta tags: #Abdulwahab #Sadeey #khadijaDuba was labarai »

[7/12, 10:47] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 2


©Rabiatu sk msh~

     ®NWA


Ta juyo tana kallonshi duk taayi tsuru-tsuru da ido sai huci take taama rasa me zatace mishi, yana mata kallon mamaki yace "wane irin kallone kkemin haka buguna zakiyi? Watau kimin laifi kuma ki tsattsareni da ido ko? Raheem yace "haba frnd ka qyaleta ka taho muje kana qara bata mana lokaci!


Baice komi ba ya juya ya shige motah itama ta shige tata motar ba tare da tace komi itama sai dai ko wanne ta ciki na ciki, ta janye motarta suma suka wuce!!


Da 'bacin rai ya isa gida, saida ya tsaya qofar d'akin yayi knockn, Da sauri ta qaraso ta bude mishi, bata bashi hanya ba ko lura da 'bacin ran dake fuskarshi batayi ta fara magana "Oyoyo yayanmu! Kasanme? Bnji tsayuwar motarka ba, kawai ynda kayi knockn dinnan jikina ya bani kaine! Sai kuma ta shagwabe fuska, shne kawai zaka fita yayanmu bakamun bankwana ba? Nayi missing ganin kwalliyarka yau har wasu sun rigani gani, anma ko hoto ay daka jira naayi maka"!! Ita kadai keta surutunta, ko motsawa baiyi ba hankalinshi da tunaninshi duk sun tafi ga abnda ya faru yau! Tunanin yake meya kamata yayi ma yarinyar can? 


'kara katse mishi tunani tayi tace "yayanah juyo muyi selfie" har taa fito da wayan tana niyyar saitashi ta musu hoto fatyma qanwarshi ta fito da qarfi tace "ke Aku riqe mana bakinki! 


Da sauri kuwa ta saka hannu ta riqe bakin ko motsi bata qarayi ba, sai da tazo ta dafa Abdul sannan ya dawo tunaninshi, bai cema fatyma komi ba, sai dai kawai ya wuce dakinshi, itama fatyman ta wuce ta barta anan duk da taaga alaman damuwa a fuskar yayanta, anma bata tsaya tmbyrshi ba tace "koma miye taa tambayeshi idanya dan samu nutsuwa!!


Suna shigewa ta sauke hannunta sannan ta dage kafad'a tace "shikenan SADEEY, sauke hannun!! Ta maida 'kofar ta rufe tana murmushi tace "SADEEY ne sunan ba Aku ba!!


***

Da safe yana tashi har lokacin zuciyarshi bata mishi dadi, can falon d'akinshi ya jiyota da magenshi ita da bata raina abokin labari, duqawa tayi dai dai inda take ta d'aukota tana shafa bayanta, tace "babynah kin tashi lapia? Kinfison yayanmu dani ko? Kullum baki kwana a dakina sai dai ki gudo nan? Ya farka daga barcin?? Mu riga zuwa dakinshi!! 


Aykam kafinta rufe bakinta magen ta ruga a guje ta bita tana fad'in "ki tsayani, ki jira nace! Wayau kikamin ban shrya ba kika ruga, Sai da ta shiga bedroom din sannan ta tsaya"


Yana jiyosu yayi saurin janyo blanket ya rufe jikinshi yayi lamo kamar mai barci!!


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/12, 10:47] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB  1


©Rabiatu sk msh~

    ®NWA


Cikin sauri suke tafiya shida abokin nashi anma cikin tsari da nutsuwa! Kyakkawan gaskene fuskarshi cike da qwarjini, kallo d'aya dana mishi na tabbatar ba mai son yawan mgn bane! Firar da sukeyi da abokinshi ne yaja hankalina hrna matsa dauko muku rahoto...


Saida ya yamutsa fuska sannan yace "me ake da soyayyah? Kawai 'bata lokaci ne don ko kad'an ni ban yrda akwai soyayyar gaskiya ba! Ban yrda anayin auren soyayyah ba! Abokin nashi yace "anma ka yrda anayin aure ba?? Daria yayi sosae sannan yace "nima ay bnce bzanyi aure ba! Tunda su mum sun matsa, anma dai bana soyayya ba, don har yau banga macen data ta'ba zuciyatah da sunan soyayya ba! Tun daga uganda da nayi karatu har nan nigeria!


Yace "Abdul knan, kana nufin dk en matan 9ja babu wacce tayi maka da sunan syy?? Yace "mgnrka hakan take! Ba kamr ynzu da mata suke zubar da ajinsu ni abnma har dariya yake bani! Zo kaga ynda 'ya'yan aminan momie dana en uwanta ke zarya gidan dga dawowanah ko wacce da nata salon!! Yace "kai kuma ba wacce ta maka! Yace "har ynzu babu ita a duniyar nan!!


Gani nayi yaa had'e rai lokaci d'aya yanayinshi ya canza, da sauri nakai idanuwa na inda yake kallo, cikin 'bacin rai yake kallon inda yayi parking motarshi yana fad'a, "ko motar uban waye yazo ya saka ya rufe mu? Wlhy wasu mutanen neman magana ne dasu! Ba'asan uzurin mutum ba za'a kama rufeshi!! Abokinshi raheem ya dafa kafad'arshi yace "calm down mna Abdul! Fad'anka ay bzai kawo wnda yayi parking dinba! Kafin ya rufe baki Abdul ya jiyo wurin raheem cikin masifa kamar shiya mishi laifin yace "shruna ne zai kawoshi ba? Kai knka kasan saurin da nake! Ka nemo mna wnda yayi parking dinnan!


Ganin raheem baida niyyar motsawa yasa Abdul ya qara shaqa gashi har lokacin baiga alamar mai motar na zuwa sai faman kallon agogo yake, shikam raheem abnma dariya ya bashi don ko kadan Abdul bai iya fad'an ba, donshi bamai yawan magana bane!


Juyawa kawai Abdul yayi da niyyar shiga restaurant din idanunshi rufe saboda 'bacin rai ko kan raheem bai qara bi ba, yana shiga dai dai lokacin tana fitowa babu wanda ya kula da wani sai da sukayi wani irin karo dk suka bugu da juna tayi wani irin juyawa tana niyyar faduwa cikin zafin nama ta dawo tana niyyar fad'a mishi, ya turata da iyakar qarfinshi ta fad'i da bayan har saida qafarta tayi qara itama qarar ta saki kamar zatayi kuka!


Ba tare daya kalleta ba yace "m srry" kawai ya tafi cikin d'aga murya tace "srry? Abnda kawai zaka iya cema wnda ka buge knan? Ya juyo yana kallonta cikin mamaki ta miqe daqyar ta qarasa inda yake! Tana magana ita kadai! "sufa mazan 9ja dinnan dk hka suke! Bzasu ta'ba kauda kai ba idan sukaga mace


Ya dakatar da ita da hannu yace "karki kuskura kice zaki fad'amin magana! Na riga da naa baki haquri, a hnkali yace "matan 9ja dk inda suke sai sunyi qoqarin shge maka!


A harzuqe tace "kai, kasan ko ni wacece? Sunana KHADIJA baka isa ka wulaqantani ba! Wlhy saina rama!! Tsoki yaja kawai ganin tana qara 'bata mishi lokacin ya juya kawai ya fita!! 


Itama jikkarta ta d'auka kamar zata tashi sama ta fita dga wurin gashi dk mutanen kallonta suke!!


Kusa da motarta ta hangoshi tsaye ta qara sauri ta qarasa da niyyar shiga motarta! "lallai yarinyarnan! Daman ita ta rufe mu dk ta 'bata mna lokaci? Bari ka gani ya matsa inda take! Raheem na riqeshi anma saida ya qarasa inda take ya fizgota ta baya


Dedicated to Mr. Smiles😃 


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/12, 10:47] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 3


©Rabiatu sk msh~

     ®NWA


Sadeey na shiga ta iske barci yake, ta 'bata rai kamar ta tadashi kuma saita fasata d'auki magenta ta fita falo ta zauna hrda kunna kallo.


Yana jin fitarta ya 'bude ido had'e da saki sanyayyar ajiyar zuciah, fuskar khadija ce ke dawo mishi kamar ynzu ne ya had'u da ita, zazzaqar muryarta ce ke mishi yawo a qwalwa, bai ankara ba ya lula duniyar tunaninta.


Sai da ya farga, sannan yaja dogon tsoki shi a dole sai yaji haushinta, yabi bango da harara kamar tana kallonshi, sannan ya miqe ya shiga toilet yayi wanka tare da brush sannan ya fito. 


Sai da ya shirya tsaf cikin qananan kayan da suka anshi jikinshi yayi kyau sosae kwantaccen gashin kanshi sai sheqi yake, a falo yaja burki yana kallonta cikin mamaki.


Miqewa tayi tana murmushi ta qaraso inda yake, ya had'e rai ko kula batayi ba tace "sannu da fitowa yayanmu! Abdul bai bata amsa ba cikin shan mur yace "me kikeyi anan? Ta nuna mishi t.v da hannu tace "kallo nake! Yace "kallo? Tace "eeh, sai nayi break fast kuma? Yace "a dakina kuma?


Ta rausayar dakai tace "tohm wake gyarawa idan bani ba? Nazo in tashe ka ne naga kana barci! Zai sake magana kuma ya fasa saboda wani 'bacin ran daya taso mishi, sudai mata ko a ina haka suke da hawan kai!


Har yaakai 'kofa zai fito ta 'kwala mishi kira, ya tsaya da saurinta ta qarasa inda yake, ta marairece fuska tace "ni yayanmu sai wani shamin murr kake badai takura maka nake ba ko? Da'kar ya iya d'aga kai yana murmushin ya'ke, tace "anjima nida fatyma zamuje birthday partyn qawarmu, zaka kaimu? Ta qara narkar da murya jin yayi shru tace "don Allah" girgiza mata kai kawai yayi ganin tana niyyar makarar dashi!


Matsowa tayi dab dashi ta d'an dafa kafad'arshi yace "ke miye haka? Tace "mepa? Ni ba er uwarka bace? Donna ta'baka miye? Tana niyyar qara matsowa yace "shikenan naji ku shrya kawai," bai jiya me zatace ba ya fita ya barta tana murna don daman taa dad'e tanason ta gabatar dashi a abokanta saboda yanda take fad'a musu had'uwarshi, tasan kowacce zatayi fatan samunshi a matsayin miji!!


My facebook page: Rabiatu sk novels


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/12, 12:02] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 4


©Rabiatu sk msh

     ®NWA

 

A dinning ya iske fatyma qanwarshi tana break fast, yaja kujera ya zauna sannan ta gaisheshi ta tashi tana zuzzuba mishi abinci.


Hankalinshi duk bai tare dashi sai data gama zuzzuba mishi tanata mishi magana yaayi shru, ta'boshi tayi da hannu yayi firgigit ya dawo tunaninshi, qura mishi ido tayi tana murmushi tace "ya sunanta yayanmu? Yace "wacece? Tace "wadda kake tunani mana, don yanayinka yayi kama da wanda ya fad'a ma soyayya!


Yace "soyayyah? Ni kuma? Haba da wannan yarinyar? Yama za'ayi naso wannan masifaffiyar yarinyar? Dariya sosae fatyma keyi tace "kacemin dai tunaninta kakeyi! Haba gaskiyah ce bakaso anma koda bn ganta ba taa gama burge yayanah tunda harya fara sonta!


Yace "kinga qanwatah nipa bazan ta'bason wata ba, zama da sadeey ta fara koya miki surutu ko? Dai dai lokacin sadeey ta kusan zuwa tun daga nesa ta 'bata rai kamar mai shrin kuka tace "nice ma nake da surutun? 


Duk pa mezance don na damu dakai ne, Maganganunah basu wuce, ka tashi lafiya? Kaayi mafarkinah yau? Kanamayin tunani nah? Me zakaci na girka maka? Yau dawa dawa ya kallarmin kai? Wow! Wannan kwalliyar taka tayi kyau, in tayaka fira? Anma dai aikin yau bai baka wahala ba ko? Wane irin kaya......."?


Dafe kanshi kawai yayi yana saurarenta, fatyma ma ido ta zaro jin da tayi bata da alamar tsayawa ne ya sanyata cewa "ya isa haka aku, da wannan surutun naki ay saiki sanya kan yayanah ya qara girmah! Tace "wannan ne surutu? Mamanah tace idan bani kula dashi wata zata ita 'kwacemunshi, ta du'ko saitin fuskarshi har yana jiyo numfashinta tace "yayanmu ay dai bani damunka ko? 


Miqewa yayi kawai ya d'auka brief case dinshi ya shiga gaisheda hajiyarsu, daya fito har wurin motah suka rakashi sadeey na qara tuna mishi da birthday partyn da zai kaisu don duk taa qagara anjima tayi.

 

***

Yana driving yana kallon titi kozai sake ganin khady, tuna yanda ya shaqotah yayi tana ta huci cikin 'bacin rai kamar zata dakeshi, dariya yayi a fili yace "rigimammiyah kawai, sai kuma ya d'aure fuska yana qoqarin daina tunaninta!


Harya tashi daga office tunaninta kawai yake sai sanda ya fahimtane yake fara qoqarin dainawa!


Yana shiga gida a falo ya iske raheem da fatyma suna labari sai dariya take shima raheem din dariya yake, yana shigowa suka hangoshi kamar masu ciwon daria suka qara kwashewa da dariyan fatyma hrda hawayen raheem naa riqe da ciki


Fuska ya musu ya nemi wuri ya zauna yace "malam lafiya daga gani zaku dinga daria? Bai bashi amsa ba saima yaci gaba da dariyarshi


My facebook page: Rabiatu sk novels


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/12, 14:57] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 5


©Rabiatu sk msh~

     ®NWA


Saida sukayi mai isarsu sannan daqyar fatyma ta iya cewa "wai don Allah yayanah idan daa Yaa raheem yaa qyaleka me zaka yi mata? Ta rufe bakinta tana dariya ganin irin kallon da yake ma raheem!


Yace "kacemin kawai zuwa kayi ka bata labari, kunma maidani wani abin daria! Raheem yace "A'ah Abokii kawai ni sai ynzu ma abn ke bani daria, ashe haka kake idan aka 'bata maka rai,!


Fatyma tace "Anma dai kyakkyawah ce ko? Raheem yace "taa had'u mana kinga kuwa irin kallon da yake mata? Fatyma tace "eeh gsky na yarda don yau duk tunaninta yake. Shidai jinsu kawai yake sai da yaji alamar tahowar sadeey sannan ya miqe da sauri ya nufi dakinshi, don taasan lokacin dawowarshi ynzu zatazo ta cikashi da surutu.


Raheem bai tafi ba suna tare da fatyma har magriba, sannan suka tafi masallaci shida abdul


Suna dawowah su sadeey harsun shrya ita da fatyma cikin shirin zuwa partyn, sunsha kyau sosae kamar wnda zasu gasar sarauniyar kyau, sadeey kam gaa kyau ga son gayu, ballantana fatyma data biyo yayanta fagen kyau!


Raheem yace "gaskiya kun had'e da yawa, anya kuwa duk wurinnan za'a samu wanda zai kaiku had'uwa? Kafin fatyma tayi magana sadeey taa rigata tace "dgsk yaa raheem? Gaskiya naji dadi sosae, inason na bada kala sosae a wurin, shyasa ma kaya kala d'aya zamu saka da yaa abdul! Tace "don Allah kuyi sauri ku shirya dare yayi mama tace bazamu je ba!


Raheem yace "tohm shknan, suka wuce d'akin abdul da yake raheem nada kaya a gidan, har zasu shige ta qwala mishi kira ya juyo, tace "kayanka nanan a saman gado naa fiddo maka! Girgiza kai kawai yayi ya wuce!


My facebook page: Rabiatu sk novels


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/13, 20:23] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 6


©Rabiatu sk msh~

     ®NWA


Tunda suka fito sadeey bakinta bai qarayin shiru ba, sai yaba kwalliyan Abdul d'inta take, hotuna kam taayi mishi ba adadi duk da ba tsayawa yake ba, shiga sukai sukama hajiya sallama, Allah ya kiyaye hanya ta musu tare da gargad'in karsu dad'e


Raheem ne ke driving shida fatima a gaba, Abdul da sadeeynshi a baya, ta dasa da surutun nata, data isheshi gashi marar son hayaniya wayarshi ya ciro yaasan abnda ta fiso kenan watau selfie, ya dinga musu har suka isa wurin partyn! Sannan ya samu tayi shiru.


Raheem nayin parking duk suka fito anma bnda abdul, har lokacin ba'a fara ba! Sadeey bata jira kowah ba tayi gaba wurin qawayensu, duk inda ta wuce saita tsaya sun gaisa tana nuno musu inda Abdul yake duk da bai fito ba, fatyma daman tuni sun tafi ita da Raheem da yaga Abdul baida niyyar shiga hall d'in yace "qanwatah muje kimin budurwa cikin qawayen naki!


Zuga guda ta kwaso ta qawayenta ta taho, suna tafiya tana basu labari fuskarta kawai zaka kalla ka gane cikin farin ciki take, yana hangosu ya dafe kanshi, shi Al'amarin sadeey har yau yaa'ki daina bashi mamaki, shi ba mai son magana ba, idan sunzo kome zaice musu? Lalla'bawa yayi ya fice yana neman wurin 'boyo cikin hotel din yana tafiya cikin sauri saboda yaaji sadeey taa taho nemanshi.


Karo ya kusan kai mata cikin duhu tana waya, da sauri ya matsa ta juyo tana kallonshi har suna had'a baki yace "kece? Ta juya idanunta sannan tace "wani abu? Kafin yayi magana yaajiyo sadeey na tahowa tana kiran Yayanmu, Yayanmu, Yayanmu... 


Da sauri ya fara waige waige, wuri ya samu ya la'be yana maida numfashi, khadija kam dariya ya bata sosae a ranta tace ko 'boyon me yake? A haka har sadeey ta iso wurin tana dube dube ta kalleta tace "don Allah khady kinga yayanah? Wani fari kyakkyawa hka, yana sanye da skye blue din kaya, yana da saje mai kyau da baqin gashi kwantacce, zaki ganshi yana tafiya cikin nutsuwa mai kyau da tsari...


Tana magana anma khadija kallonta kawai take yanda take bayyano suffofinshi, Gaskia ne sadeey ta fad'a Abdul yaa had'u iyakar haduwa, Matsalarshi guda rashin fara'a, ita bata tsaya bama ta kula da had'uwarshi ba sai ynzu da sadeey ke mata magana.


Saida sadeey ta ta'bota ta sauke ajiyar zuciyah, yarfar da hannu tayi tace "baki ganshi ba? Girgiza mata kai kawai khady tayi


Juyawa sadeey tayi zata tafi wayar Abdul ta fara ringing ta jiyo da sauri ta dawo


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/17, 10:51] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 7


©Rabiatu SK msh

    ®NWA


Da sauri Abdul ya kashe wayarsa, duk ya tsure cikin duhu yake ma khady alamar ta taimaka mishi, tayi sauri ta danna wayarta tayi kamar ita aka kira,sadeey tace "A'a naji kamar k'arar wayar yayanah, "da sauri Khady ta juya, sannan ta girgiza kai, tace " no bakowa wayata ce tayi k'ara, "sannan sadeey, tace "ok. "ta juya ta tafi, tana tafiya Abdul yayi wata irin ajiyar zuciya, khady ta kwashe da dariya, tace " Ashe duk abinka kai matsoracine, tunda har kana tsoron mata. " Abdul ido kawai ya kora mata yana kallonta, kaasa ce nata komi kawai yayi, "Ashe dai yarinyarnan kyakkyawa ce? Gaskia taa iya murmushi, abinda yake fad'a a zuciyarsa kenan, itama daina dariyar kawai tayi ta tsaya tana kallonshi....


Cikin wata irin murya yayi magana Wanda shi kansa baisan yana da irin murya bah, yace "meyasa ki kayi karya dan ki kareni, ke kyakkyawa ce, karya baza tayi maki kyau bah. " itama cikin siririyar murya ta mai da masa amsa, Wanda saida yaji maganarta har cikin kwakwalwarsa har zuwa cikin zuciyarsa, da sauri ya lumshe idanuwansa, sannan ya bud'e a ahankali, tace " kaima baza kayi kyau da mai tsoron yan mata bah, da ina maka kallon jarumin namiji " gyaran muryar da akayi ne yadawo dasu hankalinsu, da sauyi suka juya Raheem ne da fatyma tsaye suna dariya, fatyma ta fara magana, tace " uhmm yau dai naa kama yayana yana soyayyah, "raheem yayi murmushi, yace "ai na gayawa abokina but yayi man gar'dama gashi yanzu. " Abdul ya d'aure fuska yana kallon fatyma yace "lallai yarinyarnan wasa nake dake? Ni ba soyayyah muke ba, ko soyayyah muke?


Rasa amsar da zata bashi tayi sai Raheem ne yace "ay ba iya soyayyar kake ba, don hka bzaka gane ba, anma ku duka kuna son junanku! Juyawa yayi yana kallon khadija ya sadda kanta a 'kasa, kafin yayi magana sadeey ta qaraso wurin ita da qawayenta. Inda abdul yake ta qarasa ta tsaya!


Ta dubeshi ta harde hannu a qirji tace "ina ka tafi yayana inata nemanka? Qawayenah duk sun qagara su ganka, kasan kuwa wahalan da nasha kafin in ganka? 


Duk yaa rasa amsar dazai bata ma, tayi murmushi kawai ta kalli qawayenta tace "yau dai ga yayanah da naketa baku labari koma shine wanda zai aureni insha Allah, d'an uwanah ne, auren zumunci za'a mana, ya kukaga dacewarmu?. " da sauri khady takai dubanta ga Abdul......


*Dedicated* to Mr smiles😃


❤❤Rabiatu SK msh❤❤

[7/17, 10:51] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 8


©Rabiatu SK msh

     ®NWA


Kauda fuskarshi yayi gefe, nan take yanayin khadija ya canja ba tare da taace mishi komi ba ta juya tabar wurin, da sauri yabi bayantaSadeey nacan tana kallon kawayenta tana ta zuba surutun ta ,ganin su duka inda Abdul yake suke kallo sai wani dadi takeji taa wuce raini a wurin qawayenta don duk cikinsu babu mai hadadd'en saurayi kamar Abdul


Wannan ta kalli wannan, su kwashe da dariya, Sannan Daya daga cikin su tace "gaskiya kinyi dace" nan suka kara kwashewa da dariya, wadda tafi kowah dariyarnan tace "kuma da alama ji yake dake sosae," tace "eeh mana ay kinsan yana sonah sosae, d'ayar tace "tabbas yayannan naku son kowah ne, cikin jin dad'i ta dafa kafad'arta tace "harmaa da wanda bai samu ba, su kayi dariya gaba d'aya sannan sukace mata zasu koma wurin birthday d'in, tace "tohm nima inanan tahowa tare da masoyinah! Har suka tafi suna mata dariya


Juyawa tayi tana cewa, "yayanmu bakuyi ban kwana ba ko sai zamu tafi gida? Wayam ta gani babu kowa, ta zare ido tana waige-waige a fili tace "tohm ina yayanmu kuma ya tafi? 


Khadija na tafiya taji alamar kamar anabinta a baya, ta juyo da sauri ya 'boye bayanta, duk inda ta juya saiya qara 'boyewa, tsayawa tayi taqi ko motsawa, sannan ya zagayo inda take yana murmushinda na kasa gano muku ma'anarshi.


Tsareta yayi da lumsassun idanunshi yana murmushi yace "meyasa kika gudu? Kina kishi ne? Da sauri ta girgiza kai duk taa rasa ma me zatace tace "kishi kuma? Da sauri ya tari numfashinta yace "eeh mana, kodai abnda raheem ya fad'amin gaske ne kina....? Da sauri tace "kaaga ni a'ah babu wani abu a raina, yace "kedai ki fadamin! Duk ya rikitata kawai ta ra'bashi zata wuce.


Yana niyyar tare ta, ya hango sadeey tana tahowa dafe kanshi yayi kamar ya d'aura hannu saman kai yakeji, har khadija ta wuce.


Ta qaraso tana fad'in "yayan mu baku Koh gaisa da kawayena ba Fah ka wuce 

, ya kwantar da murya kamar dole yana murmushin yaqe yace "am sorry qanwanah, ki basu Ha'kuri kinsan bana son yawan yin Mgn shiyasa.


Tace "haba yayanmu, miye don kawai gaisawa da qawayenah?duk pa bakaga yanda suka damu dasu ganka ba.


Yace "tohm mun gaisa wani lokacin yanzu, ku taho mu tafi hajia harta kira waya, tace "haba yayanmu ya za'ay mu tafi ko farawa ba'ayi ba? 'bata rai yayi yace "shikenan saikun taho," ya juya ba don taaso ba tabi bayanshi tana kumbura fuska*dedicated*to Mr. Smiles😃 


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/17, 12:12] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 9


©Rabiatu sk msh

     ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


Tun daga ranar kullum Abdul neman hanyar da zai 'kara ganin khadija yake, gashi cikin rashin sa'a Yaa mnta bai amshi numberta ba, dafe kanshi yayi yaa rasa yanayin da yakeji, shidai a nashi tunanin ba sonta yakeyi ba, anma tana matuqar burgeshi, yanayinta na rashin hayaniya, murmushinta, gata da nutsuwa da dad'ad'an lafazi.


Murmushi yayi cikin jin dadi, baiyi zato ba sai dai yaji wata irin 'kara a kunnanshi, da sauri ya fara waiwaye, sadeey ce ya gani tsaye tana 'kyal'kyala dariya, dafe kanshi yayi lallai yarinyarnan.


Murmushi tayi ta zauna saman hannun kujerar da yake, tace "yayana miye zaka zauna kayita tunaninah? Kawai ka 'kwalamin kira sadeey, da sauri zan taho in tayaka fira, d'aga mata kai kawai yayi, tace "mama taace in rage yi maka yawan surutu, naa daina ko? 'daka mata kai ya 'karayi, tace "kuma taace in dinga baka amsa dakai koda hannu kawai ay dai bani zaqewa ko? Murmushi yayi har saida kyawawan haqoranshi suka fito, ya d'aga mata kai.


Fatyma ce ta fito cikin fara'a tace "yayi masoyan asali, firar me ake? Sadeey tace "Soyayyah mana, ke ya kika gani? Fatima tace "hakan, sai a tsaida hakanan hajiya tace in kiraki.


Da sauri ta mi'ke tsaye tace "anma ki tsaya ki taya yayana firaa! Falon hajia ta tafi saida ta shige sannan Abdul ya kalli fatima yace "Qanwatah ya akai naga 'kawayenku basu kawo muku ziyara? Tace "kamarya yayanmu? Duk wannan 'kawayen namu dake yawan zarya? Kuma ayni ba wasu qawaye ne dani ba wannan sai sadeey kowah nata ne!


Yace "tohm ita khadija 'kawar waye a cikinku naaga bata ta'ba zuwa ba, fatyma daria tayi tace "kacemun dai khadija kake nema, ni ba 'kawatah bace kawai dai munyi class d'ayane a sec, shiyasa ma kaga bamu zumunci sosae!


Yace "aikam dai yaa kamata ku dinga zumunci, ki shirya anjima in kaiki! Tace "kai dai kawai kace zan raka ne, banmapa san gidansu ba, anma zanyima shafa'atu waya ta turamun address dinta.


Yace "yauwah er qanwatah anma pa karki fad'ama sadeey, miqewa tayi tana dariya tace "aikam yanzu zan fad'a mata ta tafi d'akin hajiya da gudu yana kiranta bata tsaya ba.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/18, 14:57] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 10


©Rabiatu Sk msh

     ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


Sauke numfashi Abdul yayi sannan ya jingina da kujera, wayarshi ya ciro ya fara neman raheem, tun kafin tayi ringing ya d'auka da yake wayar na hannunshi.


Abdul yace "kai Aboki kamar kana jira," "Yace jira nake mana ay nasan zaka kirani ne ko yaushe, Kaaga Tauraron sadeey, Angon khadija kuma yaya ga fatyma," Abdul yace "kuma babban abokin raheem ba," 


"Yanzu dai ya ake ciki? Shawara nakeso ka bani," raheem yace "ina jinka Abokinah! Shiru yayi yama rasa ta inda zai fara mishi, sai da raheem yace "yadai? Kaayi shru, sannan yace "idan mutum ya yanason mace ta yaya yake bayyana mata? Kuma naasan halinka karka yimun dariya!


Raheem yace "kaima kaasan sai naayi kenan? Ka fad'i abin dariya kace bazanyi ba? Cikin dariya yace "watau yanzu kaa sauko kenan? Kaa yarda kaa fara soyayyah? Ran Abdul yayi matu'kar 'baci, saida yaja dogon tsoki sannan yace "idan kaa gama dariyar kaa nemeni mu 'karasa magana, kai naama fasa neman shawarar taka, dariya ta hana raheem cewa komi har Abdul ya kashe wayar.


*** ***

Da marece ya fito cikin wankan shadda ruwan coffee, yaa had'e matu'ka sai murmushi yake cikin nishad'i, 'kagare yake suje gidansu khadija duk da bai tanaji abinda zai ce mata ba, yana cikin 'kwarin gwiwa.


Fatima ta fito itama a shirye take yace "salon kuma muje kiyita surutu kamar sadeey taa baki aron baki, tace "tohm yayanmu ba qawatah bace? Idan na shiga muka fara gaisawa ay dai sanda ka ganni, Yace "tohh bani adress dinnan kisha zamanki, tana dariya tace "da wasa nake maka yayanmu mu tafi!


Hajiya ce ta fito tace "kunanan har yanzu baku tafi ba? Fatima tace "yanzu zamu tafi hajia, Abduk ya du'ka yana ma fatima magana a hankali yace "ina sadeey? Tace "barci take ko in tasheta? Yace "ke, ki barta tayi barcinta wuce mu tafi.


Bankwana sukama hajia suka fita!!


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/20, 14:47] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 11


©Rabiatu sk msh

     ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION


Suna tafe suna hira, Fatima na nuna masa hanya, tun ahanya Abdul yasa Fatima taiwa Kadija waya gatanan zuwa gidansu, cikin murna Khadija tahau shiri don tanaso ace anzo gidansu, momynta kanta tafahimci haka, binta kawai take da dariya.


Da isarsu gate aka bud'e masu, Abdul yayi parking mota, sai zuba ido yake yaga ta inda zata fito, waya Fatima taduba zata kuma kiranta, sai gata tafito, tafiya take d'ai-d'ai tamkar batason taka 'kasa, Abdul sakar baki yayi yana kallonta, kullum 'kara kyau take, duban Fatima Khadija tayi, "sai kicemin tare da yayanku kike".


Murmushi Fatima tayi "to meye aciki?" Iso tai masu zuwa ciki, har 'kosawa ta farayi da kallonda abdul ke mata


 Zama sukai baki d'aya, suna hira da Fatima, Khadija sai satar kallonshi take, Abdul najinsu bai tankaba, can aka hau Jere masu kayan snacks da drinks, sund'ansha drink kad'an, Fatima tasake duban Khadija da murmushi " ke inma fad'a maki gaskiya, wannan zuwan na yayanmu ne, banawaba ni rakiya nayo" Murmushi Khadija tayi, tad'an saci duban Abdul tagefan ido, Fatima tai dariya"wallahi kunfiye gulma, anaso ana kaiwa kasuwa" tami'ke "nibari inje ingaida momy, inkun gama kikirani" tafice tana dariya.

       

Shiru falon yayi, kowa yakasa cewa komai, can dai Abdul yadaure, yana kallonta duk da ta'ki yarda su had'a ido, Yace "rannan sai kishi ya hanako tsayawa muyi magana ko? Kin barni cikin tunani da zullumi, gaskiya KHADIJA, ada dai banyi tunanin son wata 'ya maceba, banyi zaton zanfad'a soyayyaba, amma yau sai gashi nafad'a soyayyah, alokacin da nafad'a soyayyar ban gas-gataba sai yanzu_" Khadeejah!" Yanayin daya kira sunanta, saida tsigar jikinta ta tashi, d'ago kaitayi suka had'a ido, da sauri tad'auke kanta, murnushi Abdul yayi "khadija yau gashi nafad'a sonki, khadija inasonki so d'aya tak, wlhy ban ta'ba furtama wata mace wannan kalmar ba, kenake yiwa soyayyar da bata misaltuwa, kinzamo wani 'bangare ajikina" nan yadinga zayyano mata sirrin zuciyarsa, Wanda baisan yanayi ba, ita kuwa khadija wani sanyine kawai ke lullu'beta, murmushi kawai take.


Dubanta yayi, had'e da ajiyar zuciya, "bakice komaiba, maine ra'ayinki akaina_?" Shiru tayi, amma kanta na'kasa tana aikin murmushi, harya gaji yadubi agogo duk jikinshi yayi sanyi yace "kiramun Fatima mutafi" da sauri ta dubeshi, sai kuma tamu'ke, tafita mintuna biyar sai gasu tare, mi'kewa yayi, ya dubeta "shikenan mungode, ki cema mama ina gaisheta!


 Fatima talura jikin Abdul amace yake, dariya tahauyi "Allah sarki sokenan" harararta Abdul yayi, Yace "sadeey sarkin surutu, ke kuma sarkin daria ko? 


Tace "ba haka bane yayanmu, Kasan wani abu? yayanmu, Khadija takar'bi numberka, tace kayi ha'kuri zata baka amsa awaya, wai ita yanzu kunyarka takeji" murmushi Abdul yayi, "haba da gaske, kicemin kawai nayi nasara! Murmushi Fatima tayi tace "naace, don Alama khady na sonka, daman naga alamr tana sonka, kun kasa yarda ne"


wani burki Abdul yatake yace "da gaske 'kanwata, kai wallahi naji dad'i, da duk jikina ya mutu" dariya take mishi sosae, itakam mamaki yake bata, gaskiya so dabanne, gaba d'aya Abdul yaa canja kamar bashi ba, yaa koyi surutu da yawan fara'a wanda duk da baidasu!


Sadeey ce ta fad'o mata a rai, Allah sarki, koya zataji a ranta? 


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/20, 19:56] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 12


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


A falo suka iske Sadeey ta 'bata ranta sosae, tana jinsu ta maida fuskarta gefe d'aya ta qara had'a rai ita a dole an 'bata mata rai, fatyma ce ta mata magana cikin fara'a tace "yadai matar yayanmu waya ta'ba mana ke? Tace "oho! Kinmasan anyimin ba dai dai ba kenan haka kawai don anga ina barci za'a fitarmin da masoyi, ta murgud'a baki tace "tukunnama ina kuka tafi? Da izininwa kuka fita? Meya hana a tasheni? Koma ina za'aje ay an fad'amin idanma baza'aje dani ba, don Allah yaushe rabonma damu fita dashi?


Magana take anma yanayinta kawai fatyma ke kalla tana dariya harda hawaye tace "kinga ni ki barni inje in fad'ama hajia mun dawo, keda in kika fara magana bakisan ki tsaya ba.


Sadeey tace "laah! Lallai fatima zaki fito ki sameni ne saikin fad'amin inda kika kaimin masoyi! Bata tanka ta ba ta shige tana dariya, shima Abdul tun shigowarsu ya kasa ri'ke dariyarshi yanda ta had'e rai shyasa ya wuce d'akinshi yasha dariya ya 'koshi, ga wani farin ciki da yakeji.


Fatima, sadeey, Abdul da hajiyah ne zaune a dinning, lokacin dinner ne har lokacin sadeey bata saki ranta ba, kowah yana cin abnci banda sadeey dako kallonshi batayi, hajia ce ta mata magana "yadai er gidan yayanta? Sai abncinki ya huce bakici ba?


Fuskarta a shagwa'be tace "niyau bazanci abinci ba, Tace "saboda me? Tace "hajia, ay Sadeey da Yaa Abdul sun sani, kawai bazanci ba! Hajia ta jinjina kai tana murmushi tace "tohm tunda tsakaninku dasu ne bazan shiga ba tsakaninku kun gyarota ni kunga tafiyatah! Sai da safe suka mata su duka.


Tana tafiya sadeey ta juya gefe d'aya ta 'kara turo baki, fatyma na dariya tace "nikam yayanmu ka fad'amin gaskiya banda sadeey baka ta'ba soyayya ba? Yace "naa ta'bayi so d'aya, saboda yaa lura da alamar da fatima ta mishi da ido.


Tace "wao! Gaskiya ta cika me sa'a, ya sunanta? Yace "Masoyiyah! Fatima ta qyalqyale da dariya tace "yayi masoya, ita da sadeey wa yafi kyau? Da sauri sadeey ta jiyo tana harararta ta sadda kai tana dariya, Yace "Haba kyakkyawar gaskece, ma'abociyar murmushi, idan kika ganta zaki tabbatar da babu wata budurwar da zata kaita kyau, sai dai sadeey idan tayi murmushinnan nata mai kyau.


Duk yanda sadeey taso d'aure fuska saida ta saki murmushi, fatima tace "anma wayafi sonka? Yace "Masoyiya mana, kinga ita kome zanyi mata bata fushi dani!


Da sauri sadeey tace "nifa ba fushi nayi dakai ba yayanmu, ay kaima kasan bani fushi dakai, kawai duk sanda zaka fita ne sai gabana yana fad'uwa, ina fargabar wata ta 'kwacemun kai, bansan halin da zuciyatah zata shiga ba, kawai dai nasan bazan iya jure rashinka ba!


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/21, 17:12] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 13


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Daga fatima har Abdul babu wanda ya iya magana, duk jikinsu yayi sanyi da kalaman sadeey, maganar da hajiya ta mishi ce ta fad'o mishi a rai d'azu bayan dawowarsu daga gidansu khadija.


Tace mishi "Kadai'ki maganar aure ko Abdul, tun ina maka magana harna fara gajiya, ga qanwarka nan fatima tana shirin tafiya d'akinta anma kai ko maganar bakayi, kai dai ba yaro bane, Yace "hajia nipa ba na'ki aure bane, kawai inason in samu macen da zata soni ne, kuma wacce ta kwantamin a rai, kuma insha Allah na kusan samu kumah zakiyi mamakin za'bin dazan kawo miki.


Tace "hmm, anma sanin kanka ne sadeey na matu'kar 'kaunarka ko? Taa'ki yarda da soyayyar kowa sai dai kai, ba nace dole zanyi muku auren had'i ba, A'ah da tunda ran mahaifinku zanyi maka,! Anma kayi tunani akan soyayyar da take maka, idanma baka amince ba ni bazan takura ba.


Jikinshi a sanyaye har suka gama magana da hajia, saukar da ajiyar zuciya yayi yana kallon sadeey tana murmushi tace "da wannan kallon ay saika sanya tunaninka ya hanani barci yayanmu, duk da kullum na rufe idona kyakkyawar surarka nake gani, ina sonka da yawa yayanmu.


Kallonshi fatima tayi ya saukar da kanshi 'kasa, duk farin cikin da yake ciki ya nemeshi ya rasa, mi'kewa kawai yayi yana 'ko'korin yin murmushi yace "saida safenku 'kanwata, sadeey tace "saida safe yayanmu, kayi barci mai dadi.


Fatima tace "Allah ya kaimu," yana tafiya sadeey ta dawo kujerar da fatima take ta zauna tana murmushi tace "yadai? Naaga duk yanayinki yaa canja, kodan hajia taa fad'a miki iyayen kabir sunzo akan maganar aurenki? Karki damu naasan sha'kuwar da kukayi da yayanmu, ko bayan aurenki nizan kula miki dashi.


Tace "kekam dai daga maganar aure sai damuwa, ko biki ba'a saka ba? Sadeey tace "shine nima na gani, kinga kizo mu tafi mu kwanta mun 'karasa maganar a can.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/23, 10:27] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 14


 ©Rabiatu sk msh

      ®NWA


Yana Shiga bedrum d'insa ya tura k'ofar yasa Mata key

    bai samu damar zura sleeping dress ba hka ya fad'a kan tafkeken gadonsa cike da tunanin khadijansa

       yana jiran kiranta a ko wane lkci dan hka wayar na gefensa duk bayan mintuna saiya duba ya gani kodai a silent ya Sakata?

   gaskiya idan kahadija ta amince da soyayyarsa baiga wata 'ya mace da xai so bayanta ba duk da Yana tausayin Sadeey to amma yarinyar ta cika surutu ga rawar Kai    

      ita ko irin alkunyar Nan ma bata nuna wa sai surutu kamar bishiyar kanya na xuba... 

     khadija kuwa akwai alkunya ga bata da yawan surutu duk maganar da xata fito daga bakinta to mai ma'ana ce.

  A haka dai bacci yayi awon gaba dashi ba tare da yaji muryar abin alfaharinsa


        ******

Tana zaune a parlour tana kallo amma bata fahimtar komai Kawai tunanin Abdul d'inta take

     ji take babu macen da ta fita sa'a dayin dacen masoyi na hak'ik'a

Murmushi take tayi kamar tana ganin Abdul d'in,ita tunaninta idan ta Kira shi a waya tayaya zata furta masa cewa ta amince da soyayyarsa???

    Hannu tasa ta rufe fuska sbda kunyar abinda bakinta zai furta

Ta d'auki wayarta ta Shiga contact ta duba number sa da tayi saving da my Abdul....!

      tayi saurin gogewa ta Maida my luvly....!

  tayi murmushi ta furta "my luvly" ta sake yin wani murmushin sannan tace "to wane sunane latest Wanda yafi my luvly dad'i"? ta tambayi kanta.

    tayi saurin goge sunan cikin smiling najin dad'i ta Maida sunan My Soulmate......!


Tayi ta fad'in sunan a cikin zuciyarta tana kuma fatan Allah yasa Abdul ya zama soulmate d'in nata


Nasan ynxu Yana jiran kirana a ko wane lkci amma gskya inajin kunyar furta masa, to ya xanyi???

       Wata zuciyar tace to me xai Hana kiyi masa text?


Hakan kuwa akayi dan a lkcin ta d'auki wayar ta Shiga sms ta rubuta masa text kamar hka

   "Ur request has been

        Accepted        

   U can't control wat

    life throws on u,

   at first i thought a

   day will never come

   4 me to live wit u.

  I luv u too My Abdul".


Tsowon mintuna tana karanta text d'in ta kasa yi masa sending,saida ta karanta yafi a k'irga sannan ta tura masa tana ganin ya Shiga tayi saurin kashe wayarta dan tasan xai kirata kuma tanajin kunyar d'agawa a ynxu


 Yana Zaune akan dining suna lunch

Sai d'iba yake kad'an2 dankuwa Yana cikin damuwa Yau har kwana biyu khadija bata kirasa ba to ko bata sonsa ne..

   A haka suka kammala cin abinci suka koma parlour kamar yadda suka Saba Sadeey ce ke ta xuba surutu Fatima ta biye Mata, shima Yana d'an Shiga hirar tasu jefi jefi.....!


K'arar wayarsa yaji da alama text ne ya shigo,ya d'an jaa tsoki sannan ya ciro wayar,ynxu hka ma ba wani important txt bane

     new number daya gani ne yasa shi saurin bud'awa

      aikam txt d'in khadija ya gani,yayi saurin kallon Fatima itama ta gane me ya gani,tayi saurin kanne ido d'aya alamun yayi controllng Kansa kar Sadeey ta gane


  Da sauri ya mik'e ya fice Sadeey kuwa tayi saurin cewa "yayanmu ina xakaje muna hira"? 

    ko juyowa baiyi ba bare ta samu damar da xai bata amsa.

 

Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/23, 15:10] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 15


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


A harabar gidan ya koma saman resting chair ya zauna, ya fiddo wayarshi yana 'kara duba text din khadija sai murmushin jin dadi yake.


Numbarta ya farayin saving, shima 'soulmate' ya saka mata, gaskiya sunan yahau, sannan ya fara 'ko'karin kiranta, a kashe ya samu wayar duk da haka bai ha'kura ba sai da ya kira yaafi iyakar 'kirgawana, tunda na 'kirga 35 na gaji da 'kirgawa!


Badon yaaso ba haka ya ha'kura ya daina kira, sai dai ya maida mata reply 


"Bazan iya kwatanta miki farin cikin da nake ciki ba da amincewarki I feel like the luckiest guy In the whole world to have a beautiful, and honest girlfriend like you. I hope my luck never runs out and I can make you mine forever.


Haka ya yini da wayarshi a hannu yana jiran ta 'kara mishi text ko ta bud'e ya kirata, basuyi waya ba sai wurin 11pm cikin sa'a lokacin ta kunna wayar, itama taa kasa barci tuninin abdul kawai take, da yanayin da zaiji idan yaga reply dinta.


Sai da kiran ya kusan katsewa saboda yanda takeji duk kunyarshi ce taa gama rufeta, da'kyar ta iya d'auka ta saka a kunne, da zazza'kar muryarta ta mishi sallama, saida ya rufe ido ya lumshe sannan ya amsa mata.


Sun dade suna , duk da firar tasu duk tambayoyine yake mata, akan karatunta da kuma gidansu.


Khadija bello jega ne cikakken sunanta, tayi primary dinta da secondry duk a private school dake garin jega, anan ne suka hadu da sadeey da fatyma, sai bata ci gaba da karatun ba, ita kadaice a wurin mahaifanta kuma er gatan a wurin abbanta da mamanta.


Har zasuyi sallama tace "anma baka fad'amin ala'karku da sadeey ba, Yace "meyasa kikeso kiji? Tace "hmm shknan kawai, yace "A'ah daga tambaya? Da mahaifina da mahaifin sadeey uwa d'aya suke uba d'aya, itama ita kad'aice a wurin mahaifanta, mamanta na matu'kar ji da ita komai takeso ana yi mata.


Tun dawowatah daga karatu ta dawo gidanmu da zama, saboda sha'kuwar da sukai da fatima" tace "Uhm kawai! A haka suka gama firar.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/23, 17:20] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 16


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Haka soyayya mai 'karfi taci gaba tsakanin Abdul da khadija, sun sha'ku sosae ta yanda bai iya d'aukan lokaci mai tsawo ba tare da yaa kirata ba, har mamakin kulawar da yake mata take.


Sadeey kam yanzu ta lura zaman gidan ya fara yima Abdul wahala, duk taa damu bata wani samun lokacin da zata mishi fira, idanma yana gidan ko yaushe da waya a kunnenshi ko a hannunshi suna musayar kalamai da khadija duk da taa kasa fahimtar halin da yake ciki.


Barci ne ya gagareta da dare saboda tunanin daya mata yawa, kwanannan duk taa canja taa ko surutun ma taa rage saboda tunanin da take, fatima ce gefenta tana ta sharar barci hankalinta kwance, lokacin ya rage bikinta saura 2month, kaasa daurewa tayi sai da ta d'an bubbugi fatima ta farka cikin nutsuwa ta bud'e ido tace "yadai matar yayanmu? Tace "ba dai dai ba fatima, ke kanki kinsan bani da nutsuwa kwanannan, naa rasa laifin da nayima yayanmu, ko kad'an yanzu bai tsayawa muyi magana, don Allah ko kunyi magana dashi yaa fad'a miki wani abin da nayi mishi?


Girgiza kai fatima tayi tace "ba wani abu da aka mishi, Qila dai yanayin aikin nashi ne, anma ay kinga koda hajia ya daina zama ya dade, ki fidda tunanin koma a ranki ki kwanta kiyi barci, kindaisan halin yayanmu daman can ba yawan magana ne dashi ba.


Jinjina kai kawai tayi ba yare data gamsu da bayanin da fatima ta mata ba, ta 'kudurta a ranta koma miye gobe zataje ta tsareshi sai taaje, wani tunani ne yazo mata a ranta, hawaye suka zubo mata da sauri ta share.


Washe gari tunda tayi sallar Asuba bata koma barci ba, gajiya tayi da jiran lokacin tashinshi tasan weekend ne bazaije wurin aiki ba.


8pm ta shiga falon d'akinshi, har zata zauna jiran fitowarshi ta jiyoshi yana dariya cikin nishid'i da sauri ta 'karasa wurin bedroom d'inshi, abinda ta jiyo ne yayi matu'kar tada mata hankali, jikinta har kyarma yake, tabbas da mace yake musayar kalamannan, Yayanmu ya fara soyayya kenan? Wata yakeso? Tambayoyi da yawa ne ke mata yawo a 'kwalwa, duhu ne ya fara mamaye mata idanu, kanta ya mata nauyi, wani abu ya tsaya mata a 'kirji.


Bata 'kara sanin meke faruwa ba ta yanke jiki ta fad'i.


Abdul naa can yana waya da khadijanshi, sai dai ya jiyo 'karar fad'uwarta da sauri ya fito, ganin sadeey a kwance bata ko numfashi ba 'karamin rud'ewa yayi ba, fridge ya wuce ya d'auko robar faro ya 'bude ya fara kwarara mata anma ko motsi batayi.


Wayarshi ya ciro ya kira fatima, tare da hajiya suka shigo kowanne tashin hankali 'karara a fuskarshi.


Hajia ce tace ma fatyma tayi sauri ta kira family doctor su.


🔆Kuyi ha'kuri da yanayin rubutun, karatun exam ne ya sanyoni gaba, ina bu'katar Addu'arku plz👏🏻🔆


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/26, 17:46] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 17

             

©Rabi'atu sk msh  

     ®NWA             


Nan da nan fatyma ta kira family doctor din su, Hajia ta taimaka mata suka maida ta saman kujerar falon hnklnsu duk a tashe. Ba'a fi 5mnts ba sai gashi ya iso dauke da kayan aiki kasancewar basu da nisa sosai.                      Nan ya shiga dubata cikin qwarewarsa. Sannan ya dago ya kalli Hajia, Hajia tace "Doctor me yake damunta? Dr ya gyara tsayuwa tare da cewa "Wato Hajia ta fadi ne a dalilin firgici ko kuma ince tsoro na jin wani abu ko kuma gani, wanda hakan ne yayi sanadiyyar faduwarta" Hajia tace "To ynx y jikin nata yaushe kuma xata farfado?" Dortor yace "Insha Allah nan da 20mnts xata tashi".                      Fatyma ta kalli Yaa Abdul da hnklnshi yayi matuqar tashi don ya tabbata Sadeey taji wayar da sukayi da Khadeejah. Hajiya ta kalleshi tace "Abdul me ya sameta meye dalilin faduwarta? Abdul kuwa duk ya rude ya ma rasa me xai ce mata ya daga kai ya kalli Hajiar sannan yace" Hajiya nima bansan me ya sameta ba ina cikin bedroom naji faduwarta".                 Nan Doctor yayi musu sallama ya tafi. Hajia ma ta miqe don xuwa daki ta dawo. Fatyma ta matso kusa dashi tace "Yayanmu me ya faru da Sadeey? ".     Ya kalli Fatyma sannan yace " Ina tunanin taji wayar da muka yi da Khadeejah ne tunda ina cikin wayar ne naji faduwarta". Fatyma ta dafe kai tace Tab "Akwai matsala kuwa, ynx ya xa'ayi idan Sadeey ta tashi"? Yace " Nima tunanin da nike kenan, ko ya xance mata?".                    Fatyma tayi shiru kamar tana naxari sai kuma tace"Yayanmu ka dai yi naxarin abinda xamu fada mata don ni kaina gaba daya ya kulle" Abdul yace "Ke kenan ma, ni ina ga barin gidan ma xanyi kafin ta farfado don bansan me xance mata ba.


Dedicated to Mr. Smiles


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/26, 17:50] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 18


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Yana rufe bakinshi sadeey ta fara bud'e idanunta a hankali, kallon sama ta farayi a hankali ta fara kallon kowa a d'akin da sauri ta tashi zaune duk sun zuba mata idanu. Lokacin hajia taa dawo


Ita ta fara mata magana tace "sannu sadeey," tace "yauwah hajia, tana murmushin kauda damuwa, ko kallon inda Abdul yake batayi ba ta fara 'ko'korin miqewa da sauri fatyma ta ri'keta, ita ta taimaka mata suka koma d'akinsu don har lokacin ji take d'akin na juya mata.


Hajia batayi mata maganar ba sai da dare da bata fito cin abinci ba tana d'aki tana fama da kukan zuci, komi na duniya ya canja mata, soyayyar Abdul naa 'kara azalzalarta can zuciyarta.


Batasan shigowarta ba, sai dai taji an dafata, firgigit ta dawo daga tunanin da takeyi, ta tashi zaune da sauri ganin hajia ta shigo, hajia ta dafata tace "ki fad'amin gaskia sadeey, kada ki 'boyemun komi, miye dalilin daya sanyaki shock? Girgiza kai tayi tama rasa me zatace can kuma tace "ina shigowa d'akin yaya bansan yaabar kallo kunne ba, sai dai naji ana film din ban tsoro, na tsorata zan juya da gudu carpet ya zameni.


Hajia ta jinjina kai cikin tausayawa tace "kin tabbata gaskiya kika fadamun? Sadeey ta d'aga kai, hajia tace "Tohm shknan Allah ya kyauta ya kiyaye gaba, sadeey tace "Ameeyn".


Tun daga ranar sadeey ta fara janye jikinta daga Abdul, duk taayi sanyi magana ma bata cika yiba sai dai ta bada amsa dakai, cikin wata d'aya ta rame, fatyma naa matu'kar tausaya mata don ita kad'ai tasan damuwarta, don Abdul ma daina kulata yayi, daman abnda yafiso kenan.


Ita kad'ai ta zauna tana tunani, zaman gidansu Abdul duk yaa isheta bata da wani sukuni, tabbas ZAFIN SO baida magani, taa yarda bazata taba samun Abdul ba tunda ko kad'an yanzu bai bata kulawa.


Tashi tayi ta fara tattara kayanta, babu abinda ta bari nata, fatyma ta shigo tana kallonta cikin mamaki tace "matar yayanmu wannan kayan pa? Tana murmushi tace "bakisan maisu bane? Tace "kamar naki dai na gani, ina zuwa haka? Sadeey tace "inda na fito, kinga muje ki rakani d'akin hajia. Fatyma bata musa mata ba ta bita suka tafi, don taa matsu taji abnda sadeeyn zatace.


Hajiya naa waya suka shiga, sai data gama ta d'ago kanta tana kallon sadeey tace "harkin gama shryawa? Sadeey ta d'aga mata kai kanta na 'kasa, tace "shikenan sadeey, yanzu maminki ta kirani ta fad'amin kunyi waya kince yau zaki koma gida, yanzu idanma wani abun muka miki ni bazaki sameni ki fadamin ba? Dani da maminki duk dayane, idanma son ganinsu kike a gari daya pa kuke sadeey, ki fad'amun gaskiya idan wani abu ake miki da bakiso don na lura da canjawarki kwanannan.


Girgiza kai tayi tana hawaye, tace "Wlhy ba abunda kukamin hajia, nipa bawai zan koma gida bane, kawai zanjene bazan dade ba zan dawo. Hakanan hajia ta amsa anma a zuciyarta bata gamsu da abnda sadeey ta fada ba, duk da tasan bata da wani zurfin ciki, abnda ke ranta kawai take fad'a.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/26, 17:55] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 19


©Rabiatu sk msh

      ®NWA


Bayan an gama sanya mata kaya a mota, fatyma kaasa rakota tayi saboda kukan tausayinta, kamar wacce zata bar garin, sosae hajiya da fatima kejin tafiyarta, saboda sadeeyn akwai saurin sabo, sau'kin hali ne da ita, babu abinda ke 'bata mata rai, duk inda ta shiga kowa nata ne, da wuya ka zauna da ita bakayi dariya ba.


Itama hawayen take, tana tafiya tana 'karema gidan kallo, tabbas bazataji dad'in barin gidan ba, anma yaa zame mata dole, inda motar ta take ta iske Abdul a tsaye, da sauri ta fara 'ko'korin maida hawayenta tana nemo murmushi, don koda abunnan ya faru bata canja mishi ba, sai dai bata wani doguwar magana dashi kota tsaya inda yake, duk da shima bai cika zaman gidan ba.


Fuskarshi ba walwala yace "ya akai naga an fito da motarki? Sadeey tace "kawai kwana biyu bata fita bane zan fiddata tasha iska, Yace "kayan dake ciki fa? Tace "zan kai wanki ne, sauran kuma sun gaji da zaman gida suma zan fita dasu susha iska.


Abdul ya girgiza kai Yace "kin cika wasa sadeey, komi naki bakiyinshi crioz, yanzu hajia ta kirani a waya wai yau zaki koma gida, wani abu aka miki?

Yarfa hannunta tayi tana kallon kasa tace "nikam me za'amin yayanmu? Anmafanin zaman gidan nawa ne ya 'kare, tabbas kaa cika d'aukar komai nayi wasa ne shiyasa soyayyata ma duk kake d'auka wasa ne, ko Sona ne bakayi?


Zaiyi magana ta rigashi tace "tabbas sona ne bakayi tunda gashi yanzu kaa samo wacce kakeso, don na tabbata ina gidannan kuka had'u da ita kuka fara soyayya, kenan banda wani mazauni a zuciyarka? So da yawa zukatanmu basu cika kamuwa da soyayyar wanda ke sonsu ba a lokacinda ya dace, bazance baka cancanci soyayyata ba, kuma bazan tabayin dana sanin son da nake maka ba, anma na ha'kura dakai yayanmu, ina maka fatan Alkhairi dakai da wadda ka zaba a matsayin Abokiyar rayuwarka,


Tana fadin haka ta bud'a mota ta shige, ko motsi yaa kasayi da'kyar ya iya matsawa taja mota ta wuce, kalaman sadeey sun sanyaya mishi rai matu'ka, sai yanzu ya gane duk maganar da zatayi ta hankali ce da nutsuwa, duk maganganun da tayi suka dinga mishi yawo a 'kwalwa, dakyar ya iya jan 'kafafunshi, ya isa cikin gidan, a falo jan 'kafarshi kawai yake yana hanyar d'akinshi hajia ta kirashi.


Juyawa tayi ya nufi d'akinta yana fargabar maganar da zata mishi, da kuma amsar da zaya bata.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk mashi❤❤

[7/26, 18:00] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 20


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Sanyashi tayi a gaba ta tsura mishi ido, don shima taaga alamun chanji tare dashi, hajia tace "Ka d'ago kanka magana zamuyi Abdul, ka fad'amun gaskia, miya had'aku da sadeey, don jikina na bani kaine silar daka sanya tabar gidannan, don dama dalilinka tazo, ka fad'amin tsakaninka da Allah me ka fad'a mata daya 'bata mata rai?


Shiru yayi yana share zufa, kanshi ya d'au zafi, yama rasa abnda zai fad'a mata, tambayar duniyarnan taa mishi anma baice komi ba, ta gyad'a kai tace "shikenan tunda bazaka fad'amin ba, anma ka sani iyakar soyayyar gaskiya sadeey taa nuna maka ita, kuma bazaka taba samun macen da zata soka kamarta ba.


Kaa fadamun kaa samu wacce kakeso ba? Naayima Alhaji (mahaifin sadeey) magana tunda ni ka'kijin maganata, koma wacece kaje ka fad'a mishi don ni na haifeka bazan maka dole ba, anma bazakayi ta zamamin a haka bakayi aure ba."


Sai da ta gama tace "ka tashi ka ficemin a d'aki, anma dai ka zama mai tunani da tausayin wanda ya damu dakai Abdul, mi'kewa yayi ya fice, wani 'bangare na zuciyarshi na cike da farin cikin khadija taa kusa zama mallakinshi, sauran 'ban garorin kuma cike suke da tausayin sadeey, da maganganun hajia dake dawo mishi yana 'kara aunasu dana sadeeyn.


'Dakinshi ya shige komi ya shige mishi duhu, wayarshi ya d'auka ya fara neman layin raheem don yana da bu'katar shawararshi a halin da yake ciki, saida ta kusan katsewa ya dauka Yace "yadai mutumina? Abdul yace "dai dai Aboki kana ina? Raheem yace "Kaajika da wata tambaya, dazunnan fa mukai waya na fada maka na sauka garin katsina mai gida ya aikenii shine kake tambaya? Dafe kanshi yayi wannan wane irin Al'amari ne? Harya fara manta abubuwa, Yace "Yi haquri Aboki, mantawar ma sai anyi, abubuwa sunmin yawa duk da banso muyi maganarnan a waya, anma yanzu yafi kamata mu yita.


Raheem yace "kamarya? Meke faruwa? Nan Abdul ya kwashe komi wanda bai sani ba ya fada mishi, hrda maganar da hajia ta 'kara nanata mishi tunda ba sabuwa bace, na ya fito da mata.


Raheem ya jinjina kai don shima al'amarin yaa girmeshi yace "tabbas abokina sadeey na sonka, kuma na tausaya mata sosae, babu abnda yafi son maso wani zafi da radadi a zuciya, Allah sarki sadeey akwai ha'kuri.


Yace "duk naaji wannan, ka fad'amun meya kamata inyi? Raheem yace "duk da da shawarata ka fara soyayya da khadija, ni bazan baka shawarar ka rabu da sadeey ba, don zakayi rashin mata ne mai sonka, kawai ka had'asu duka ka aura.


Abdul har yana sar'kewa yace "what? Anma dai wasa kake ko? Nizan aura mata biyun? Wlhy bazan iya ba, bazan iya da mata biyu ba raheem, bazan taba iya tafiyar da gidana ba, bazanmayi adalci ba.


"sadeey fa taace ta ha'kura dani, duk da yana da wuya in iya mantawa da ita, anma ta wacce fuska zan kalli khadija in fada mata sadeey zan aura? Yanzu ma zan kirata in fad'a mata sa'kon hajiarmu, za'ayi aike gidansu idanta fadi rana sannan inje in fada ma Alhajin.


Raheem ya sauke ajiyar zuciya yace "tohm shknan Allah yasa hakanne mafi Alkhairi,! Jikin kowa a sanyaye suka katse wayar.


Sai bayan isha'i ya kira khadija, ringing biyu ta d'auka, suka gaisa da alamar damuwa tattare da ita, yace mata "ganinan zuwa soulmate da maganar da nakeso muyi dake," tace "A'ah, nima da maganar da nakeso in fad'a maka, Yace "tohm shikenan ki bari inzo, sai muji wazai fara fad'a, don nidai tawa ta farin ciki ce,


Tace "A'ah basai kazo ba, ka fara fad'a sai in fad'a maka anan, Yace "nikam bazan fad'a miki a waya ba, don inaso inga kalar farin cikin da zaki.Tace "shikenan ni bari in fad'a maka.........kuka na 'kokarin 'kwace mata.


Dedicated to Mr. Smiles


❤❤Rabiatu sk mashi❤❤

[7/27, 19:22] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 21


©Rabiatu sk msh

      ®NWA


Kuka ne yaci 'karfin khadija, duk taa tada mishi hankali a rud'e yake cewa ki fad'amin mna, da'kyar ta iya bud'a baki tace "kayi ha'kuri Abdul aurena dakai bazai taba yiwuwa ba!


A rikice yace "me kike shirin fad'amin khadija? Idanma wasa kike ki daina plz wannan ba wasa bane, tace "ba wasa nake maka ba Abdul, ni kaina banda wani burin daya wuce zama matarka, soyayyatah taka ce, duk wani tsarin rayuwatah dakai na yishi, anma a yau komai ya rushemin sanadiyyar umarnin mahaifana, bazan iya bujire musus ba, sunyimin komi a duniyarnan, bazan iya 'kin kar'bar za'binsu ba, kayi ha'kuri ka fiddani a zuciyarka, Don Allah ka yafemun, kada ka zargeni da yaudararka.


Kasa furta komi yayi, da'kyar ya iya sauke wayar a kunnenshi, kamar ba namiji ba, Abdul ne na gani ya fara shesshe'kar kuka, tabbas wannan wata jarabawa ce ta ubangiji, ko kuma nace sakayya, yau d'innan gashi ya d'and'ani zafin da sadeey taji ba'aje ko ina ba cikin 'yan awannan, rabuwarshi da khadija akwai wata ishara da Allah yakeso ya nuna mishi.


Dafe 'kirjinshi yayi da hannu dai dai inda zuciyar take, saboda wani irin bugu da take mishi, 'kirjinshi naa mishi nauyi, mi'kewa yayi da'kyar ya 'karasa wurin fridge, robar ruwan swan ya d'auko mai sani 'karara, anan ya 'budeta ya fara kwankwad'a, sannan ya ciro yana kwarara ma kanshi, Abn nashi tsoro ya fara bani, ga tausayinshi da nakeji da sauri na fito na nufi gidansu sadeey.


Da gudu ta shiga babban falo tana 'kwala ma mami kira, hangota tayi tana safkowa daga upstairs ta ruga ta fad'a jikinta tana gunjin kuka, itama mami taaso tayi hawayen dauriya kawai take ta fara shafa kan sadeey tana rarrashinta.


Mami tace "kiyi ha'kuri sadeey don kin rasa abdul......, da sauri ta d'ago tana kallon maminta tace "Abinda yafi 'konamin zuciyah kenan mami, bazan iya cewa naa rasashi ba, don na tabbata zuciyatah bazata ta'ba rabuwa dashi ba, ina son yayanmu Mami, anma nafison inga farin cikinshi.


Mami ta shafi kanta tace "Allah ya yaye miki damuwarki dear, anma yana 'konamin zuciya ganinki cikin damuwah.


Share hawayenta tayi tace "karki damu mami, insha Allahu, daga yau farin ciki kawai zaki dinga gani a fuskata kamar yanda kika saba, duk da bazan iya mantawa dashi ba, naa mi'ki Alkawarin daina yawan tunaninshi, 'kara rungumeta tayi sannan ta juya ta nufi d'akinta.


Mami ta bita da kallo, hawayen datake kokawar maidawa ne saida suka zubo mata, tabi bayan sadeey da kallo, "tabbas babu wanda ya kaita fahimtar halinda 'yar tata take ciki, saboda bata da wata abokiyar shawara data wuceta, babu abnda take 'boye mata, tasan irin yanda sadeey keson Abdul.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/27, 19:22] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 22


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Bayan sati biyu

Sadeey ce kwance saman cinyar mami tana kwance mata kitso, tana yi mata fira sai dariya take, wayarta ce tayi ringing, sunan fatyma ta gani ta maida wayar ta ajiye.


Mami tace "waye yake kira da bazaki d'auka ba? Tayi er dariya sannan tace "fatyma ce mami, bansan mezance mata ba, nasan maganar bikinta ce kuma ina jin kunyar ince mata bazanje gidan ba, Mami tace "da kunya kam, kinga ki d'auki kiran kiji me zatace.


Maganar Fatima suka jiyo tana shigowa tace "rabu da ita kawai mami, idanma bazata zo ba ayni gani naazo, ni bansan laifin da muka yima sadeey ba.


Da sauri sadeey ta tashi tana rufe ido tace "ai naa'ki d'auka ne don inyi suprising dinki kawai sai dai ki ganni gidan, fatima tace "ba waninnan inda gaskene tashi mu tafi mana, daman zuwa nayi tafiya dake.


Sadeey ta kalli mami tace "Yanzu kuma na fasa sai gobe zaki ganni tunda safe, fatima ta 'bata rai tana kallon mami tace "kinjita fa mami, don Allah sadeey ta kyauta? Idan bikinta ne akeyi tun ana sauran sati nawa kike tunanin zan dawo gidannan? Mami tace "tun yana rage wata guda ma.


Fatyma tace "yauwah mami, kinga sadeey saida ya rage wata gudan ma sannan ta baro gudanmu, Yanzu kuma naa biyota har gida biko taa'ki yarda mu tafi.


Mami murmushi kawai tayi tana saurarensu, duk yanda fatima taso su tafi da sadeey 'kin yarda tayi, don ko kad'an batasan da idon da zata kalli Abdul ba idan taje gidan, batason Abinda zai fama mata ciwon rashinshi.


A haka fatima ta ha'kura sai dai suka fara tsattsara yanda bikin zai kasance, ba tabar gidan ba sai bayan isha'i driver yazo d'aukarta.


A farfajiyar gidan ta wuce Abdul da raheem bayan ta gaida raheem, Abdul daya gama ramewa, duk yaa koma kalar tausayi yana jingine jikin motar raheem yace "soyayya matsala ce frnd, tabbas na gano illarta, daman abnda ya dad'e yana tsoratani da shigarta kenan, khadija taaci amanata, data barni na gama fad'awa ga soyayyarta sannan ta gujeni, bansan da wacce fuskar zan kalli sadeey in bata ha'kuri ba.


Cikin tausayawa raheem ke kallon Abdul, don kwanannan ba 'karamin tausaya mishi yake ba, kullum maganarshi kenan, khadija taaci amanarshi, baisan da fuskar dazai kallo sadeey ya bata ha'kuri ba.


nikam nace "daman ashe maza ma sunajin ciwo a zuciyarsu? 


Abdul baida wani sukuni ko wurin aiki yaje tunani baya barinshi komi, har mutane sun fara gane mishi, ko yaushe yana 'kara tuna soyayyar da sadeey ke nuna mishi, ko kad'an bata barinshi da kad'aici, komai hidimarshi taa d'auke a gidan, sai yanzu ya gane irin sha'kuwar da sukai da ita, tabbas baka sanin muhimmancin sai randa baka tare dashi.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/28, 15:59] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 23


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Hidimar bikin fatima kawai ake, kullum basu da zama, shirye shirye kawai suke da tsarin yanda bikin zai kasance, ga rabon i.v da gyaran jikin amarya, itama sadeey ba'a barta a baya ba don akwaita da son gyara.


Duk hidimar bikinnan bata yarda ta 'kara zuwa gidansu Abdul, har fatima taayi nacinta taa gaji, sai dai ta biyo mata su wuce.


Koda satin bikin ya kama aka fara programmes babu wanda sadeey taje, fatima har fushi tayi da ita, Mami ma har fad'a tayi mata ta saka mata kukan ita ba zata iya zuwa ba, bata son duk wata hanya da zata had'a ta da Abdul.


Shima duk hidimar bikinnan baida wani aiki sai zaman d'akinshi, gashi yanzu hajia ko kad'an bata sakar mishi fuska, tun tuni taso a had'a bikinshi dana fatima anma yaa'ki ya kawo mata, yanzu gaisuwarshi ma da'kyar take amsawa, duk damu taa taru taayi mishi yawa.


Raheem ne yace "Abokina dolene fa kayi abnda hajia zata huce dakai, kuma sadeey ma ka wanke laifin da kayi mata," Yace "ta wacce hanya kenan? Banji me yace mishi ba sai dai Abdul yace "kana ganin hakan zai yiwu? Raheem yace "sosae ma kuwa, don kai kanka kasan sadeey na matukar sonka, Alhajin kawai zaka samu da maganar, ko kanaso ka cemin kai baka fara sonta ba?


Sai yanzu naga murmushin Abdul Yace "ba farawa ba Raheem, sai yanzu na gane soyayyar da nake yima sadeey, da da na kasa ganewa, tabbas nayi kuskure, anma kai zaka taimakamin wurin gyarota.


Yace "shikenan anjima nizan rakaka wurin Alhajin.


Koda sukajema Alhaji da maganar, kasa 'boye farin cikinshi yayi, don shima yasan irin sonda sadeey ke yima Abdul kuma yaa dad'e da sha'awar had'asu aure, hajia ma taaji dad'i sosae koda Alhaji ya nemi shawararta cewa tayi komi yayi dai dai ne su duka yaranshi ne.


Mami ce ta bada shawarar kar a fad'ama sadeey yanzu, kowa ya amince da shawararta.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/28, 16:04] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 24


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Ranar d'aurin aure, sadeey ta daure ta shirya tunda safe saboda yanda fatima ke fushi da ita ta'ki zuwa bikinta, taa riga mamie tafiya don bataso mutane suyi yawa bataje ba.


Doguwar hijabi ta saka da ni'kab don koda zasu had'u da Abdul ko kad'an bataso su had'a ido, harta shige gidan bata ganshi ba falon, d'akin hajia ta shiga duk cike da mutane tana ta hidima ta gaisheta ta fito, can d'akin da fatima take da 'kawayensu ta shiga.


'Dakin cike da 'kawayensu wanda suka kwana, fatima naa hangota mantawa tayi da tana fushi da ita ta taso ta rungumeta, taaji dadi sosae da zuwanta, 'kawayenta sai 'korafin bataje ba sai yau suke mata, bata da amsar da zata basu sai dai ta mantar da maganar, haka sukaci gaba da fira sai dai lokaci lokaci gabanta na fad'uwa duk taa rasa miye dalili.


'karfe biyu bayan sallar juma'a aka d'aura Auren Fatima tare da angonta kabir, gaban sadeey ne ya fadi sosae har sai data firgita, innalillahi wa inna ilaihirraji'un, ta fad'a fili kallon fatima kawai sadeey keyi ganin yanda take cikin farin ciki, dai dai lokacin kira ya shigo wayar fatima.


Cikin nishad'i ta d'auka ta amsa sallamarshi, tayi fari da ido kamar yana gabanta, tace "ina tayaka murna dear na yau kaa zama ango," dariya tayi sosae sannan tace "sosae ma kuwa," kallonta kawai sadeey keyi ba 'karamin burgeta tayi ba, sai da wata 'kawarta ta ta'bota ta dawo tunani.


Murmushi tayi sannan ta sauke ajiyar zuciya, cousin din fatima ce ta shigo ta wurin dangin hajiarsu, tace ma fatima "ga amarya fa da bata laifi," fatima tace "gani pa, ko ya ranki? Tace "hakan,


"ashe ba d'aurin aurenki bane kawai harda na yayanmu? Sadeey da fatima sukayi saurin kallonta, fatima tace "kamarya? Don itama batasan da maganar ba, zahra tace "nima naayi mamaki, yanzu naji suna maganar d'akin hajia, kuma da kunne na naji Allah daurin aure biyu akai kuma na yaya Abdul ne, ya akai baki sani ba?


Fatima tace "shine ay nake tunani, don kanta ya kwance, tace "'kila dai bakiji dakyau ba.


Sadeey kam dafe 'kirjinta tayi saboda yanda ya tsananta mata bugu, kanta ya sara yana mata azababben ciwo, kasa daure rad'ad'in da zuciyarta keyi mata tayi ta mi'ke a sanyaye ta fita daga cikin 'kawayensu.


Babu inda babu mutane gidan, saita wuce toilet din d'akin da suke kawai ta rufo, wani irin kuka ta fashe dashi na tausayin kanta, tabbas a yaune ta yardar ma kanta taa gama rasa yayanmu, duk yanda taso ta manta dashi taa kasa, shikenan wata tayi nasara a kanta taa aure mata wanda takeso.


Kuka sosae take, ciwon kanta na 'kara tsananta, duk yanda taso ta rarrashi kanta ta daina kuka taa kasa.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/31, 20:03] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 25


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Da'kyar ta share hawayenta, ni'kab dinta ta ciro ta maida, kanta na 'kara tsananta mata ciwo kamar zai rabe biyu


Haka ta fito duk gidan cike da mutane ta fara ra'basu ta wuce babu wanda ya ganeta, harta gama fita daga gidan jefa 'kafarta kawai take, daman a waje tayi parking motarta ta shige ta koma gidansu.


Babu kowa sai masu aiki ta haye upstars dakinta ta shige ta fad'a saman gado ta saki wani sabon kukan, da'kyar ta iya lalubo maganin ciwon kai tasha, ta koma ta kwanta ta rufa da bango saboda zazza'bin daya rufeta.


Tananan kwance cikin jinyar kanta har bayan magrib, kiran wayar Alhajinsu ya shigo mata da'kyar ta iya d'auka, tohm kawai naji taace sannan ta tashi tsaye ta fara bin bango harta isa d'akinshi.


Alhaji, mami, Abdul wahab, fatima, da qanwar maman hajia ne zaune a wajen, kamar wadda ake jefawa ta samu wuri da'kyar ta zauna, ba tace komi ba anma yanayinta kawai zaka gane tana cikin damuwa.


Sai da Alhaji ya gama yima fatima nasihar zaman aure sosae, mai ratsa jiki, tana ta kuka, sadeey ma duk taa nutsu tana saurare, sannan ya dawo kanta, kiran sunanta yayi ta d'an dago kai ba tare data kalleshi ba, yace "kinsan dalilin da yasa muka kiraki anan? Girgiza kanta tayi dake mata barazanar rabewa biyu gabanta naa matsanancin fad'uwa.


Yaci gaba "wani hukuncine muka yanke akanki ba tare da neman shawararki ba, kasancewarki mai matu'kar biyayya da bin umarninmu, kuma munsan insha Allah a wannan karon ma zakiyi biyayya ki kar'bi abnda mukazo miki da hannu biyu.


Duk maganar da Alhaji keyi jinshi kawai take, ko kad'an bata fahimta kamar wadda akaima satar 'kwalwa, tana can duniyar tunani da rud'u kamar daga sama taji Alhaji yace "A yau ne Aka d'aura aurenki da yayanku Abdul," da sauri ta juyo tana kallon Alhaji, kamar zararra ta fara 'karema 'yan cikin d'akin kallo.


Maminta ta tsura ma ido tana so ta gaskata Abnda Alhaji ya fad'a, wani irin kuka ta fashe dashi tana girgiza kai tace "bazan iya ba, wlhy bazan iya ba dad, bazan iya auren yayanmu ba har in zauna dashi, bani yakeso ba, saboda yaa rasa wacce yakeso ne yakeso yayi auren huce haushi dani, kuma bazan taba zama ba," A marairece ta kalli mami tace "don Allah maminah ki sanya baki yayanmu ya sauwa'kemin, don bazan iya......, wata irin tsawa Alhaji ya daka mata Yace "ke wacce irin macece sadeey? Tarbiyar da muka baki kenan? A gabanmu mijin da kowa ya shaida aurenku zaki ce ya sauwa'ke miki? Kina son tsinuwar mala'iku ta fad'a kanki?


Dafe kanta tayi, wani irin zogi takeji a zuciyarta, taama rasa abn fad'a, hawayen dake sanya mata sassauci a zuciya suma sun tsaya, mi'kewa tayi tabar d'akin da gudu, a 'kofar d'aki ta fad'i.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[7/31, 20:06] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 26


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


A firgice ta farka, tana fad'in innalillahi wa inna ilaihir raji'un, du'kar da kanta tayi yaa daina mata ciwo, fara tariyo duk abinda ya faru a ranar tayi, sai kuma ta 'dago kanta da sauri tana 'kare ma d'akin kallo, ta saukesu akan Abdul dake zaune gefen gado yaa zuba mata ido.


Da sauri taja baya kamar wacce taga abin tsoro, ya sakar mata murmushi yace "barkanki da tashi," batasanma sanda ta sakar mishi harara ba, cikin fad'a tace "inane nan? Yace "gidanki mana, gidan mijinki," ta waro ido cikin fargaba, Yace "sannu sadeeyna, yana matsowa inda take, da sauri ta matsa gefe tace "wlhy badai gidana ba yayanmu, ni bnda wani miji," 


Yace "kiyi ha'kuri dai karki sakama kanki damuwa, kinga ba lafiya ne dake ba," ya mi'ke ya d'auko magungunanta da ruwa ya tsiyaya a kofi ya mi'ka mata, kauda kanta tayi, Yace "ki daure kisha maganin don Allah," tace "bazan sha ba wlhy, ni garamun ma mutuwa da wannan cutar da kake shirin yimun.


Yace "cuta kuma sadeey? Tace "eeh mana, kasan baka sona, baka taba sona ba, da wacce kakeso mezaisa ka aureni? Da sigar lallashi yace "waye ya fad'a miki bani sonki sadeey?


Dafe kanta tayi tace "bani sonji yayanmu, bani sonjin duk wani kalamai daga bakinka, kaa riga ka makara," kukan da take ta so tayi ne ya 'kwace mata, Abdul yace "shikenan naji, don Allah ki daina kukannan, ki daure kisha maganin.


Mi'kewa tayi ta d'auki hijabinta dake gefenta ta saka ta sauko daga kan gado, yana tsaye har lokacin yana kallon ikon Allah, ta nufi 'kofar fita bedroom d'in, da sauri Abdul ya mi'ke yace "ina kuma zakije sadeey? Ta yamutsa fuska tace "inda ka d'aukoni mana, wlhy bazan zauna ba, bazan zauna a gidannan da wanda bai sona ba.


Yace "don Allah ki daina mana, kinsan kuwa ko 'karfe nawa yanzu? Tace "ko 'karfe nawa ne bazan kwana a gidannan ba," dafe kanshi yayi yaa rasa ma me zaiyi?


Tana niyyar fita yasha gabanta, taja baya, duk yanda yake tunanin lamarin da sau'ki yaa wuce tunaninshi, duk lallashin da yayi mata kasa ha'kura tayi, ya kasa maidata ya zaunar da itama da'kyar ya samu ya rufe d'akin ya fita.


Anan ta du'ke ta saki kuka, tana tausayin kanta, Yanzu mami ce zata yarda a had'a baki da ita a mata haka? Kamar basu suka haifeta ba za'a daura mata aure bada saninta ba, kuma a kaita gidan mijinta ba tare da saninta ba bata cikin hankalinta.


Sulalewa tayi saman carpet ta kwanta, tana kuka kamar ranta zai fita, ga haushin Abdul da takeji haka kawai yama raina mata hankali, saboda soyayyar da take mishi ne yake mata yanda yakeso.


Da tunani kala kala barci marar dadi ya dauketa anan saman carpet.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[8/3, 12:28] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB  27


©Rabiatu sk msh

     ®NWA         


Shi kuwa Abdul yana kulle dakin ya fice daga falon ya shiga motarsa, tunani barkatai y shiga yi, to shi ynx mai xaiyi ma Sadeey ta tabbatar da cewa yana sonta? Wata xuciyar tace dashi Haba Abdul sai kace ba namiji ba? Kasan hanyoyin da xaka bi don ganin ka fahimtar da ita kalar son da kake mata. Yayi murmushi yaja motar ya fita daga gidan.           Bai fi 10mnt b sai gashi ya dawo ya fito dauke da ledoji a hannunsa wanda ni kaina bn san ko miye a ciki ba. Ya xarce cikin gidan, kai tsaye dakin da Sadeey take can ya nufa, koda ya bude dakin a kwance ya isketa saman carpet tana ta sharar barcinta. Murmushi yayi ya qarasa inda take ya tsugunna yana kallon kyakkywar fuskarta, wani irin masifaffen son sadeey ne ke 'kara shigarshi. Yamiqe ya ajiye ledojin hannunsa sannan ya dauki Sadeey ya maidata kan gado. Har lokacin bata farka ba. Nan ya xauna ya xuba mata lumsassun idanuwanshi yana kallonta har na tsawon wani lokaci sannan ya miqe ya rage kayan jikinsa ya fada toillet.


 Yana fitowa ya xura jallabiyarsa sannan ya dauke ledojin ya kai cikin fridge sannan ya dawo dakin.                       Kan gadon yaje ya kwanta tare da jawota xuwa jikinsa. A firgice ta farka tare da fixge jikinta tace Abdul miye haka?. Sakin baki yayi yana kallonta cike da mamaki yau ita ce ke kiran sunansa kai tsaye ba ko yayan da ta saba. Ta miqe xata sauka daga kan gadon yayi saurin riqo hannunta yana cewa Ina xaki Sadeey? Ko kallonsa batayi ba ta fixge hannunta ta miqe tayi hnyr fita. Yayi saurin isa gabanta yana cewa Don Allah karki fita ki kwanta a nan ni bari naje daki na na kwanta. Bai jira mai xata ce ba ya fice tare da jawo kofar ya kulle sannan ya tafi dakinsa.


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[8/3, 12:29] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 28


©Rabiatu sk msh

      ®NWA           


Ta durqushe a wurin tana kuka ita kam duk da tana son Abdul bazata iya zama dashi ba don ba ita yakeso ba yana daiso ya raina mata hankaline a tunaninta                      

Shima yana shiga dakinsa ya fada kan gado ya rasa ya xai bullowa Sadeey, soyayyarta sai dada ninkuwa take a cikin xuciyarsa. Ya rasa yadda xaiyi, barci ma qaura yayi daga idanunsa hakan yasa ya miqe ya shiga toilet ya dauro alwalla ya fito ya dinga sallar nafila yana Addu'ar Allah ya karkato masa da hankalin matarsa.


Ita ma kasa barci tayi hakan yasa ta fada toilet tayi wanka tare da alwala ta fito tana ta yin nafilfili har kusan asuba barci barawo ya saceta a nan kan sallayar.   Shi kuwa sai da akayi kiran farko sannan yayi raka'a tanul fajr da aka yi kira na biyu ya fito don xuwa masallaci, bai shiga dakinta ba ya wuce masallaci. Ana idar da sallah ya shigo gidan ya xarce dakinta yana shiga har lokacin tana kwance kan sallayar tana barci. A hnkl ya shiga tada ta yana kiran sunanta a hankali. Cikin natsuwa ta bude idonta ta sauke su akan nasa, da sauri ta miqe tare da daure fuska ta shige toilet don yin alwalla.        Kodata fito bata iske shi a dakin ba, ta tabe baki ta kabbara sallarta don ita har lokacin haushin shi take ji.    


Dakinsa ya koma ya kwanta kan gado don barci yake ji sosai. Ai kuwa bai dade da kwanciya ba barci yayi awon gaba dashi. Ita kuwa bata koma barcin ba sakamakon wata addababbiyar yunwa da ta isheta. Hakan yasa ta fito ta shiga kitchen don duba abinda xata ci. Ta bude fridge taga leda ta dauko ta bude taga nama ne a ciki na kaxa mai rai da lpy. Nan t shiga kitchen ta dumama ta sannan ta diba a plate ta dauko Lemu ta koma dakinta.


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[8/3, 12:31] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 29


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Sai da taci ta ƙoshi ta gyara wurin, ta miƙe ta maida kitchen sannan ta dawo ta zauna taa rasa ma me zatai? 


Har ƙarfe 12 tana zaune ita kaɗai tana tunani, Abdul bai shigo ba ko meya hana? Wayarta taji taayi 'kara, ita tama manta da ita ta d'auko da sauri, fatyma ce ke kiranta kamar karta d'aga saboda itama haushinta takeji.


Wata zuciyar tace 'dauka mana kiji me zatace, shru tayi bayan ta d'auka, fatyma tace "Amaryar yayanmu kinsha 'kamshi, sadeey tajaa tsaki tace wai bazaki daina sunannan ba ko? Tayi dariya tace "ay yanzu ma zan fara fad'arshi matar yayanmu, ya jikin naki ina angon? Tace "ke ohon miki, ta kashe wayar kawai gaba d'aya ta maida jikka sannan ta jinginar da kanta bakin gado.


Da azahar hajia ce ta aiko musu da abincin rana lokacin Abdul ya fita masallaci, 'yan bikin da suka kwana sunata zuwa, wasu ma bata sansu ba, da yawa dai zuwa suke ganin kayataccen gidan da akai kaita, ba 'karamin tsaruwah yayi ba ga dukiya da aka zuba mata. Ita kanta gidan yaa mata kyau sosae.


Duk wanda yazo daga gida ji take kamar ta bishi, ko kad'an zaman gidan bai mata dad'i, gata dai tare da masoyinta, anma ji take kamar don dole yake zaune da ita.


Har dare bata 'kara sanyashi a idonta ba, tsoro ta faraji don sai yanzu ta kula da girman gidan, kallo ma kasa kunnawa tayi, ta shige d'akinta can 'karshen gado ta 'kudundune, a haka barci ya d'auketa cike da tsoro.


Daya shigo baiji motsinta ba ya shige d'akinshi yayi shrin kwanciya sannan ya dawo d'akinta, can ya hangota yanda ta nannad'e wuri d'aya duk ta bashi tausayi, 'karasawa yayi ya tsaya yana kallonta, kasa ha'kuri yayi sai da yakai hannunshi ya ta'bata da sauri ta farka a tsorace.


Mi'kewa yayi da sauri yaja da baya, itama saukar da ajiyar zuciya ta dingayi gabanta na bugawa da sauri.


Yace "naga bakici abincin dare ba kin kwantane," tace "daman ina cin abinci da dare ne? Da inajin yunwa da naci, Yace "tohm shknan" ya juya zai tafi, kamar tace mishi ya dawo takeji, anma bazata iya ba, ko magana take mishi haushin kanta takeji.


Sai da ya fita sannan ta tashi ta rufo 'kofar ta dawo ta kwanta, lokacin taa fara ragejin tsoran tunda ba ita kad'aice a gidan ba.


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[8/4, 21:59] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 30


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Hakan zaman sadeey da Abdul yaci gaba da kasancewa, ko kad'an bata sakar mishi fuska idan yazo inda take, anma ta fara da yi mishi girki da duk abnda tasan zai bu'kata, anma da taa jishi zata shige d'akinta, shima yaa daina neman takura mata anma dai yana 'ko'kori wurin kyautata mata da son nuna mata shi masoyinta ne na ha'ki'ka.


Yau watanta biyu kenan babu abnda ya canja tsakaninta da Abdul, tana zaune falon d'akinta ya shigo,bata sanma ya shigo ba tana can duniyar tunani, a fili ta furta, Hmm NAMIJI KENAN (littafin ummieluff) da sauri yace "me namiji ya miki kuma? 'dago da fuskarta tayi cikin mamaki batasanma maganar zuci taa fito fili ba.


Kamar bazatace komi ba, sannan tace "mefa namiji yake? Babu abnda yayi, ba ruwanshi da yaudara, satar farin ciki, da kuma 'kwatar soyayya da fin 'karfi.


Yace "duk namijin keda wannan? Shruta mishi ba tace komi ba, zama yayi bakin gadon ta mi'ke da sauri, tace "wlhy bazaka zaunamin a d'aki ba, Yace "haba sadeey, kina tunanin zamanmu zaiyi a haka kuwa? Ina mijinki anma bazamu zauna wuri d'aya ba?


Tsugunnawa tayi ta fashe mishi da kuka, "tohh ni wlhy sai dai ka sauwa'kemun, bazan iya zaunawa dakai ba, kana shiga ha'kkina da yawa, don Allah ka rabu dani ka aura wadda kakeso yayanmu.


Kallon mamaki ya tsaya yi mata, kasa jurar jin kukanta yayi mai tsuma zuciya, duk ya rikice, yake cewa "waya fad'a miki ina da wadda nakeso bayanke? Wlhy ke kad'ai nakeso sadeey, ban ta'bason wata d'iya mace ba kamr yanda nake sonki, ki bani dama in bayyana miki irin son da nake miki.


Da 'karfi tace "baka so na yayanmu, saboda rashin khadija ne kawai yasa ka aureni, ay naji labarin zatayi aure shine ka 'bulloma su hajia da wannan salon yaudarar, ko sonka zai kasheni bazan iya zama dakai ba, 'kara in auri wanda yakeso na, ni bazanyi zaman 'kunci a gidan aurena ba.


Yace "wlhy banda burin 'bata miki rai qanwata, don Allah ki fahimceni, wlhy ina sonki, naayi miki alqawarin faranta miki har iyakar rayuwatah.


Hannu biyu ta sanya ta rufe kunnenta tace "bani sonji yayanmu, don Allah ka 'kyale zuciyatah ta huta hakanan, duk abinda zakamin don kasan ina sonka ne.....kifa kanta tayi taci gaba da shesshe'kar kuka.


Sosae yake jin kukanta a jikinshi, ya rasa yanda zai rarrasheta, hannu ya saka ya d'agota a jikinshi, da sauri ta fara 'ko'korin zamewa, anma tsam ya rumgumeta a 'kirjinshi sosae, har saida tayi 'kara saboda ba ri'kon wasa ya mata ba, maida numfashi ya farayi a hankali, ko motsi taa kasayi.


Bata da wani 'karfin daya wuce kuka, shikam idonshi rufe ko rarrashinta ya kasayi, duk jikinta ya saki ta fara rage kukan, sun dad'e a haka, kafin ya sassauta mata ri'kon ta zame ta kwanta a hankali ta rufe idonta, shima mi'kewa yayi ya fita ya barta da wani haushin nashi fal cikin ranta.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[8/7, 21:12] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 31

 

©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Sai da ya fita daga d'akin kuma ta fashe da kukan takaici, Abdul yaa riga yaa gama da ita tunda ya gane mahaukacin son da take mishi, kuka take sosae a ranta tana addu'ar Allah ya kawo mata mafita.


Da dare da wuri ta mishi girki kafin ya dawo, ta shige d'aki tana gama sallolinta tayi shirin kwanciya, doguwar riga ta saka iyakar gwiwa ash, mai santsi dabin jiki, taayi kyau sosae, mukulli ta saka ta rufe d'akinta ta haye gado tayi addu'a ta kwanta ynzu ta fara sabawa da gidan taa d'an fara rage jin tsoro.


Yana driving ne anma fargaba ce a zuciyarshi, sai da ya tabbatar da daman taa gama duk abnda zatayi taa kwanta sannan ya taho gidan, baison ya kalli sadeeynshi da yanayin damuwa, kukanta na ta'ba mishi zuciyah, ga fargabar maganar data tsiro da ita wai sai ya sauwaqe mata, lumshe idonshi yayi ya bud'e yana tunanin yanayin dazu.


Sanda ya isa gidan kamar yanda ya zata, tayi barci ko motsinta bai jiyo ba, d'akinshi ya shiga ya watsa ruwa yayi shirin kwanciya sannan ya fito ya zauna yaci abincin data girka mishi, hankalinshi duk naa wurinta harya gama.


A hankali ya murd'a 'kofar d'akinta, jinta yayi a rufe, komawa d'akinshi yayi ya dauko makullanshi yazo ya 'bude a hankali ya tura 'kofar ya shiga.


K'arasawa yayi inda take, kasa d'auke idonshi yayi a kanta, a fili yake furta, Alhmdlh, Ya Allah ka nunamin ranar da sadeey zata gane irin son da nake mata, tsugunawa yayi saitin fuskarta yana tunanin yanzu da suna zaman lafiya ne zai kwanta da ita ne a 'kirjinshi yanajin lallausar fatar ta, shi kadai yasan yanayin da yakeji idan yana tare da sadeey.


Yatsun hannunta masu kyau taayi musu kwalliya da jan lalle, baisan sanda yakai hannunshi ya had'a da nata ba, yana shafawa a hankali, har wani lumshe ido yake, bata farka ba sai dai motsi da takeyi da ido kamar zata bud'e.


Hannunshi yakai ya shafi fuskarta, ya d'aura hannunshi saman le'banta, runtse idonta tayi sosae ta 'kwalla ihu, da sauri yasa hannu ya rufe mata bakin.


Turashi tayi da 'karfi, ta tashi zaune, hawaye ne suka taru a idonta da sauri ta koresu don yanzu batason kuka gabanshi, muryarta a dake tace "tohh fita ya isa hakanan," sosa 'keyarshi yayi yace "Allah ya huci zuciyarki," girgiza kai tayi tace "zuciyatah bazata taba hucewa ba idan ba barin gidanka nayi ba yayanmu, ka shiga ha'kkina da yawa yayanmu, sai yaushene zaka gane ka sauwa'kemin....?  


Da Sauri ya girgiza mata kai yace "dama ki daina wannan maganar, babu rabuwa a tsakaninmu, don Allah ki gane irin sonda nake miki," kuka ta fasa mishi zata 'kara magana yayi saurin barin d'akin don maganganunta na 'kona mishi zuciyah da yawa.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[8/8, 17:10] ✍🏻 msh: ABDUL WAHAB 32


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Kusan kwanan zaune yayi yana fad'ama Allah damuwarshi.


Tunda safe yana shirin tafiya office wayar hajia ta shigo mishi, ya d'auka ya gaisheta cikin girmamawa, Tace "wai meya sami wayar sadeey ne? Kullum fatyma sai taacemin taa kira a kashe nima ina kira ban samu kullum sai dai kacemin lafiya lau, idan lalacewa tayi ko 'bacewa baka sake mata wata?


Yace "Mantawa nake hajia, insha Allah zan bincika, zan sake mata, Tace "kodai wani Abu kake mata Abdul wahab? Da sauri yace "A'ah wlhy hajia nikau mezan mata? Inata so in kawota gida ma sai tace min ba yanzu ba wai kar ace taa fara fita da wuri," "hmm, kawai hajia tace ta kashe wayar, kamar dai bata yarda ba.


Can ya hango sadeey tana fitowa daga kitchen da kayan abnci, tana ganinshi ta fara sauri kamar mai shirin tashi sama, kafin ya 'karaso taa gama ajiyewa saman dinning table taa juya da sauri zata tafi d'akinta.


Da 'karfi yace mata "ina kwana" bata juyo ba sai dai ta rage saurinta tace "ka tashi lafiya? Bata jira amsarshi ba ta 'kara gaba.


Tana zaune a 'dakinta ya shigo da waya a hannu, "ga waya fatima nason magana dake" shru tayi kamar bata jishi ba, sai da ya mi'ka mata wayar, kamar bazata amsa ba ganin yayi tsaye sannan ta amsa.


Fatyma tace "Wlhy kina yanda kikeso matar yayanmu, wayar ma sai an gama da jan aji za'a amsa? Tace "Hmm ya kke? Fatyma tace "lafiya lau, ya amarci? Da fatan dai ba'a wahalar mana da yayanmu? Tace "Alhmdlh ngde, fatyma tace "yadai naji kamar bakison magana? 


"sai anjima, tace ganin yanda ya tsura mata ido yana kallonta, fatima na "wai wanne irin wula'kanci ne wannan? Batace komi ba ta kashe wayar ta mi'ka mashi.


Duk taa had'a rai, ganin bai tafi ba ya sanyata mi'kewa zata bar mishi wurin ya tare hanyar, babu hanyar da zatabi ta wuce, ganin son maganar yake taja bakinta tayi shru ta koma ta zauna.


Yace "ina wayarki? Tace "tananan," yace "meyasa baki amfani da ita? Shru ta mishi, ganin bazata ce komi ba yasanyashi zama saman gadon, da sauri ta mi'ke ya jawo hannunta, ta fad'o jikinshi, da sauri ta fara 'ko'karin tashi daga jikinshi.


Yace "magana nake miki meyasa baki amfani da ita? Tayi shiru har lokacin 'ko'karin barin jikinshi take, Yace "ni bansan lokacin da kika iya fushi da ri'ko ba sadeey, duk kin canja gaba.


Tace "naji dad'i daka gane canjawar da nayi, kaga kuwa yanzu zan iya rayuwa babu kai, bakason farin cikina yayanmu, na rasa dalilin da yasa ka kawoni gidannan ka ajiye.


Murmushi yayi yace "dalilin so mana, kema zaki gane ne ki daina fushi da masoyinki," tace "babu ranar wlhy, sai dai kai ka gane takurar da kamun a gidannan ka sauwa'ke mun..." kafin ta rufe bakinta sai dai taji bakinshi cikin nata.


Kasa ta'buka komi tayi har ya saketa don kanshi ya mi'ke yana murmushi, mi'kewa tayi da gudu ta tureshi ta tafi toilet tana kuka, ba'kin ciki ne sosai a zuciyarta, haushin kanta takeji, ji take kamar ta cire bakinta ta huta.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk m[8/8, 17:10] Rerbee'art😘: ABDUL WAHAB 32


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Kusan kwanan zaune yayi yana fad'ama Allah damuwarshi.


Tunda safe yana shirin tafiya office wayar hajia ta shigo mishi, ya d'auka ya gaisheta cikin girmamawa, Tace "wai meya sami wayar sadeey ne? Kullum fatyma sai taacemin taa kira a kashe nima ina kira ban samu kullum sai dai kacemin lafiya lau, idan lalacewa tayi ko 'bacewa baka sake mata wata?


Yace "Mantawa nake hajia, insha Allah zan bincika, zan sake mata, Tace "kodai wani Abu kake mata Abdul wahab? Da sauri yace "A'ah wlhy hajia nikau mezan mata? Inata so in kawota gida ma sai tace min ba yanzu ba wai kar ace taa fara fita da wuri," "hmm, kawai hajia tace ta kashe wayar, kamar dai bata yarda ba.


Can ya hango sadeey tana fitowa daga kitchen da kayan abnci, tana ganinshi ta fara sauri kamar mai shirin tashi sama, kafin ya 'karaso taa gama ajiyewa saman dinning table taa juya da sauri zata tafi d'akinta.


Da 'karfi yace mata "ina kwana" bata juyo ba sai dai ta rage saurinta tace "ka tashi lafiya? Bata jira amsarshi ba ta 'kara gaba.


Tana zaune a 'dakinta ya shigo da waya a hannu, "ga waya fatima nason magana dake" shru tayi kamar bata jishi ba, sai da ya mi'ka mata wayar, kamar bazata amsa ba ganin yayi tsaye sannan ta amsa.


Fatyma tace "Wlhy kina yanda kikeso matar yayanmu, wayar ma sai an gama da jan aji za'a amsa? Tace "Hmm ya kke? Fatyma tace "lafiya lau, ya amarci? Da fatan dai ba'a wahalar mana da yayanmu? Tace "Alhmdlh ngde, fatyma tace "yadai naji kamar bakison magana? 


"sai anjima, tace ganin yanda ya tsura mata ido yana kallonta, fatima na "wai wanne irin wula'kanci ne wannan? Batace komi ba ta kashe wayar ta mi'ka mashi.


Duk taa had'a rai, ganin bai tafi ba ya sanyata mi'kewa zata bar mishi wurin ya tare hanyar, babu hanyar da zatabi ta wuce, ganin son maganar yake taja bakinta tayi shru ta koma ta zauna.


Yace "ina wayarki? Tace "tananan," yace "meyasa baki amfani da ita? Shru ta mishi, ganin bazata ce komi ba yasanyashi zama saman gadon, da sauri ta mi'ke ya jawo hannunta, ta fad'o jikinshi, da sauri ta fara 'ko'karin tashi daga jikinshi.


Yace "magana nake miki meyasa baki amfani da ita? Tayi shiru har lokacin 'ko'karin barin jikinshi take, Yace "ni bansan lokacin da kika iya fushi da ri'ko ba sadeey, duk kin canja gaba.


Tace "naji dad'i daka gane canjawar da nayi, kaga kuwa yanzu zan iya rayuwa babu kai, bakason farin cikina yayanmu, na rasa dalilin da yasa ka kawoni gidannan ka ajiye.


Murmushi yayi yace "dalilin so mana, kema zaki gane ne ki daina fushi da masoyinki," tace "babu ranar wlhy, sai dai kai ka gane takurar da kamun a gidannan ka sauwa'ke mun..." kafin ta rufe bakinta sai dai taji bakinshi cikin nata.


Kasa ta'buka komi tayi har ya saketa don kanshi ya mi'ke yana murmushi, mi'kewa tayi da gudu ta tureshi ta tafi toilet tana kuka, ba'kin ciki ne sosai a zuciyarta, haushin kanta takeji, ji take kamar ta cire bakinta ta huta.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[8/10, 18:41] Rerbee'art😘: ABDUL WAHAB 33


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Har dare yayi bai dawo gidan ba, yana tunanin rigimar sadeey ya rasa ta inda zai b'ullo mata ta yarda da son da yake mata.


Hakane yaci gaba da kasancewa, don kanshi ya daina zuwa inda take iyakarshi da ita duba yanda ta kwana, in kuwa zai mata wata magana yanzu taa fasa mishi kukan ya sauwa'ke mata ta koma gidansu taa gaji da zama dashi.


Yau bai dad'e da fita ba ta jiyo sallamar fatima daga can falo, da gudu ta taho zata mata oyoyo, kuma saita tuna, taja ta tsaya ita bata 'karasa ba, ita bata koma ba.


Fatimar ce ta taho tana murmushi tace "yadai kika tsaya matar yayanmu, ko bakiji dadin gani na bane? Sadeey tace "ehh mana! Don har yau ban huce da abnda kukamin ba! Sai yau kikaga damar zuwa gidan nawa?


Fatyma har tana ri'ke baki tace "kicemin har ya zama gidanki, su matar yayanmu ana so ana kaiwa kasuwa


Harararta sadeey tayi tace "ohon miki, ni kizo mu shiga ba don halinki ba.


Suna shiga falonta sadeey ta fara sharar 'kwalla, fatyma ta kalleta da mamaki tace "mezan gani haka sadeey? Don Allah karki tadamin da hankali mana, tace "eeh ku hankalinku kwance ba, ni baku damu da halin da nake ciki ba, baku so na wlhy fatyma, babu wanda ya damu dani, kowa ya manta dani 'kila shiya sanyama aka li'ka ma yayanmu ni.


Fatyma tace "kamarya? Kima daina maganarnan wlhy kowah ya damu dake sadeey, kullum sai munyita faman kiran wayarki, yanzunma hajia ce ta tadoni tace inzo inga lafiyarki, kinanan kina cin amarcinki da masoyinki sadeey nina d'aukama kin manta damu ne.


Ajiyar zuciya tayi don yanzu taa samu damar da zata rabu da Abdul cikin ruwan sanyi ba tare da kowa yaga laifinta ba, wasu hawayen ne ta 'kara matsowa tace "masoyina fa kikace bayan kowa yasan ba sonah yake ba, kinfi kowa sanin haka fatyma, kullum gidannan banda wani kwanciyar hankali gorin safe daban na rana daban ko kulani baiyi, wazan kaima kukana fatima? Bayan babu wanda yayi shawara dani kafin ayi aurannan.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[8/10, 18:44] Rerbee'art😘: ABDUL WAHAB 34


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Fatyma ta dafa kafad'arta cikin tausayawa tace "shi yayanmu ne yake miki hakan? Cikin jin haushi tace "A'ah ni nakeyi mishi, fatyma tace "Allah ya baki ha'kuri, anma dai bai kyauta ba yayanmu.


Tace "kema kya fad'a, ni na gaji da zaman gidannan, tashi zanyi in shirya kawai mu tafi, 'kara a aura mishi wadda yakeso fatyma, kinsan ina son yayanmu, yana amfani da wannan damar ne kawai yana wula'kantani.


Fatyma tace "duk bata kai haka ba sadeey, wlhy yayanmu yana sonki, ina soyayyar da kike mishi da har kika kasa sakin jiki dashi? Don Allah ta yaya zakuci ribar soyayyarku idan kuna haka?


Sadeey tace "yauwah, daman nasan ay ba yarda zakiyi dani ba, bazaki ta'ba ganin laifin yayanki ba fatima, tace "nifa ba haka nake nufi ba, ki tsaya ki fahimceni, idanma yayanmu bai sonki aike kina sonshi, kefa macece sadeey kinsan yanda zaki shawo kanshi.


Tace "ba wani ni ban sani ba, komi ma na mishi ba burgeshi nake ba, kullum saiya fadamun rashin khady ne kawai ya sanyashi aurena.


Fatyma tace "shikenan tunda baki sani ba, ni bari in fad'a miki, sadeey saurarenta kawai take cikin jin haushi tama maida ita 'karamar yarinya, fatima kam taa dage sai kora mata bayani take.


Anan ta yini har bayan isha'i sannan kabir yazo tafiya da ita, jikkarta ta bud'e ta mi'ka mata wata laida, tace "Menene? Fatima tace "tsaraba ce, kedai ki ajiye ranar da zakiyi amfani dasu kimin waya zan gaya miki kona menene, tace "tohm nagode.


Hijab ta saka ta rakata har wurin motarsu, suka gaisa da kabir cikin raha sannan suka wuce, ko a gaishe dasu hajia da mami bata ce ba.


***

Yau sauri yake ya koma gida kafin tayi barci saboda tunanin shawarar daya yanke, don yana cutuwa da yawa kullum surar sadeey 'kara rikitashi take, cikin sa'a sanda ya shiga d'akinta tana toilet tana wanka, taa ajiye lemu a cup saman bed side, lalla'bawa yayi, ya saka 'kwarar maganin dake hannunshi a ciki ya motsa sannan ya fita da sauri.


Yana fita ta fito daga wankanta, saida tayi 'yan shafe-shafenta sannan ta ciro kayan barcinta ta saka, ledar da fatima ta bata ta gani, cewa tayi bari ta d'auko taga menene a ciki, powder ce ta fara fiddowa, tace "yanzu fatyma powder ma saita koyamin amfani da ita? Gaban mirrow taje ta shafa, taga taayi mata kyau sosae.


Ta 'kara ciro turare a 'yar kwalba, ta sha'ki 'kamshinshi yayi mata dad'i sosae, ta shafe jikinta ko ina dashi, sannan ta maida ledar ta kwanta hankalinta kwance bayan ta shanye lemon data ajiye.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[8/12, 10:37] Rerbee'art😘: ABDUL WAHAB 35


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Mi'kewa tayi zumbur kamar antsikareta, idonta harya fara canja kala, dai-dai sanda Abdul yaturo 'kofar d'akin ahankali yashigo, da sauri tad'aga kai tadubeshi, akasalance, "meya shigo dakai d'akina?" Murmushi yayi, yana dubanta, yasan plan d'insa yafara aiki, tasowa tayi, tahau masifar yafice mata daga d'aki, bai kulataba, yatako zuwa gabanta, har jikinsu na gogar juna, 'kamshim jikinta yasha'ka, tare da lumshe ido, ita kuwa hannu takai da masifa, zata tureshi, yarungumeta a'kinjinsa, iya 'karfinsa, yafara sauke numfashi da sauri da sauri, ita kuwa jikintane yasaki takasa ta'buka komai.

       

Zu'bewa sukai kangado, domin tsaiwa bazata d'aukesu, tuni Abdul yaburkice, yahau jagwal-gawal Sadeey son ransa, kasa hanashi tayi, saima fara biye mishi da tayi idonta rufe


          

Sai da labarin ya fara canjawa, ta dinga kuka tana turashi, Anma Abdul baimasan tanayi ba, sai da yadawo dai-dai sannan ya lura da aika-aikan da yayi, murmushi yayi domin jinsa yayi wasai, wani farinciki ya lullu'beshi, 'kara jawo Sadeey yayi jinsa zai runfumeta, wani 'karfi yazomata, tatu reshi tana fad'in "wallahi nidai ka d'auka Alhakina, kacuceni, daman nasan basona kakeba, daman jikina kakeso Allah......" Jitai bakin Abdul acikin bakinta, d'ago kai yayi yadubeta, "haba Sadeey pls mana, dabana sonki, yaushema zanso jikinki, kiyi ha'kuri, kisa aranki babu mai sonki kamata" turo baki tayi, tatureshi tatashi tsaye bata ko gama mi'kewaba tadawo luuu zata fad'i, cikin zafin nama Abdul yami'ke yatarota "sokike kijamin aiki koh?, kinfiye rigima Sadeey, haryanzu kin'ki yarda dani, kifahimci farincikin danake cikimana, kema kiyi farinciki, kin mallaki abin 'kaunarki" yayi murmushi tare dayimata kiss, taturo baki "kace haka mana, aidole kayi farinciki, tunda kasamu biyan bu'kata, kafin kazo kawula'kanta.....!" bata 'karasaba yaroshe mata baki, yana girgiza mata kai, d'aukanya yayi cak yanufi toilet da ita, yahad'a ruwan d'umi wai zaisata ciki, suka hau kokawa, daye 'karfinta da nasa bad'ayaba, akan dole yasata ruwan d'umin, takuwa Sanya ihu, kamar wadda ake yankawa, Abdul kansa yasan rakine kawai na Sadeey, bai biyemataba yayi mata wankan, yad'aukota cak ya ajiyeta kan gado, yad'auko mai da kayanta, yashafa mata yasanya mata riga doguwa mara nauyi.


Ranar wuni yayi yanafama da sadeey, rigima sosae take mishi akan ita gida zata tafi, ita wlhy tasan daman abinda yasa ya aureta kenan bawai sonta yake ba, rarrashinta ya dinga yi da maganganu masu dad'i har ya samu tayi barci


Sannan ya sauke ajiyar zuciya yana kallon kyakkyawar fuskarta, da d'an 'karamin bakinta mai surutu da rigima, sonta ne ke 'kara shigarshi da wani 'kima data 'kara a idonshi saboda yanayin daya sameta.


Tashi yayi ya tada sallar godiya ga ubangiji, ya raba dare yana addu'an Allah ya dawo mishi da hankalin sadeey gareshi ta gane son da yake mata.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[8/13, 18:31] Rerbee'art😘: ABDUL WAHAB 36


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Kwana biyu tayi suna jinya ita da Abdul, ko motsi zatayi ji yake kamar yayi mata, kulawa sosae yake bata, yaa tattara ya dawo 'bangarenta da zam Duk da ba wani sakin jiki take dashi ba, saima haushinshi da takeji tana ganin don yaa mata yanda yakeso ne yake kulawa da ita.


Sai magana yake mata tayi shiru taa 'kyaleshi, fira yake mata anma kamar bada ita yake ba, Yace "yaushe zamuje kiga gida ki gaishe dasu hajia? A ta'kaice tace "babu inda zanje.


Yana murmushi yace "meyasa? "wata na nawa a gidannan ko 'kofar gida ban ta'ba le'kawa ba? Zaman kurkuku maa yafi zaman gidannan dad'i, ban ta'ba tunanin akwai zama da masoyin dake da 'kunci haka ba, ka cuceni yayanmu, sai Allah ya sakamin.


Tana cewa haka ya ri'ke baki cikin tashin hankali yace "mena miki na cutarwa sadeey? Ina iyakar 'ko'kari na wurin kyautata miki, duk inayi ne danki gane irin son da nake miki.


Tace "kanayi dai saboda wata manufa taka, shima aurena da kayi ba cutarwa bane? Yace "naa aureki ne don ina sonki, kema kuma kina sona, da sauri tace "koda ina sonka, bai nufin zan iya zama dakai ba tare da kana sona ba.


Yace "tohm ay ina sonki, a shirye nake nayi duk abnda zai tabbatar miki da hakan, tace "indai kana sona, rubutamin takardata, sannan zan shirya ka maidani gida.


Wani irin iska mai zafi ya furzar daga bakinshi, tsawon lokaci yana tunani kafin ya jawota jikinshi, Yace "idan kin barni kuma wazai na bani zumar da kika d'and'anamin? Zata tureshi yace "ki barni inyi abinda yasa na auroki mna, kinga ko a hakan kin biya bashin soyayyar da kikemin.


Turashi tayi da 'karfi ta mi'ke da gudu ta tafi falo ya tashi ya rufa mata baya, a falo suka had'u da hajia dake ta ranga'da sallama, da sauri ta fad'a jikinta tana mata oyoyo sai maida numfashi take.Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[8/13, 18:31] Rerbee'art😘: ABDUL WAHAB 37


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Tsayawa yayi daga baya yana sosa 'keya yace "sannu da zuwa hajia," ta amsa mishi tana mishi kallon marar gaskia.


Sai data zauna suka gaisheta, sadeey sai sunnar dakai take saboda wata sabuwar kunyar hajia da tazo mata, duk taa cika mata gaba da kayan ciye ciye taaji dad'in ganinta sosae.


Hajia tace "zuwa nayi inga d'iyar tawa tunda ka'ki kawomin ita, baice komi ba yayi shiru don babu yanda zaiyi ya kare kanshi, hajia tace "kaayi shru mana, anya Abdul wahab? Me kakeyi mata naaga duk ta rame?


'Dagowa yayi yana kallonta yace "wlhy babu abinda nake mata hajia, ay gatanan ki tambayeta, bataji dad'i bane kwana biyu, anma da sau'ki


Bata lafiya anma shine ba'a fad'a mana ba? Yace "ba wani sosae bane hajia da sau'ki, tace "ban yarda ba gatanan duk taa rame, kunma je asibiti kuwa? Yace "zamuje dai insha Allah yace, tace "a daure dai aje, ya jinjina kai.


Sai da zata tafi tace ya bata wuri zasuyi magana da sadeey, Yace "hajia ni bza'ayi dani ba? Tace "da d'iyata kawai zanyi magana ka fice nace, ya fice yana daria, sadeey ma murmushi kawai take.


Hajia tace "har yanzu baki huce da laifin da muka miki ba ko sadeey? Da sauri ta fara girgiza kai kanta a 'kasa tace "nice wa da zaku mini laifi hajia? Babu abinda kukamin, don Allah ku daina fad'in hakan, idanma laifi na muku ku yafemin, muryarta na rawa kamar zatayi kuka.


Hajia tace "babu Abinda kikai mana sadeey, naji dadin biyayyar da kike mana, Allah ya miki Albarka, ya baki yaran da zasu miki biyayya kamar yanda kika mana.


"Anma ki fad'amin gaskiya babu abinda Abdul yake miki? Ji tayi bazata iya fad'ar laifin Abdul a gaban hajia ba, d'aga mata kai kawai tayi.


Nasiha tayi mata sosae mai ratsa jiki, kafin ta kira Abdul ya maidata gida, sadeey ji take kamar ta bita su tafi, kewar maminta da Alhajinsu takeji sosae, komawa tayi d'akinta taci gaba da kuka.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[8/13, 18:31] Rerbee'art😘: ABDUL WAHAB 38


©Rabiatu sk msh

      ®NWA


Tun daga ranar ta koma rufe 'kofarta da makulli ta barshi a jiki, bata fitowa ko falon d'akinta sai Abdul bainan, ta koya ma kanta zaman d'aki don dole.


Abubuwa sun farama Abdul yawa, ya rasa hanyar shawo kanta, duk wasu shawarwari da Raheem ya bashi sun 'kare sai ya jiyo 'kamshin nasara kuma Abu ya juye, gashi yanzu baijin zai iya rabuwa da ita.


Yau yaayi niyyar kawo 'karshen Abin, 'kin fita yayi office ya zauna gidan yana gadin fitowarta, ko 10 batayi ba sai gata ta fito, hanyar kitchen ta nufa, saida tayi tsakiyar falon sannan ta lura dashi.


Da sauri ta juya zata koma, ya tashi ya rigata shan gaban, Murmushi yayi yace "yau dai naa kama mai guduna! Gefe 'daya ta maida fuskarta ko kallonshi batayi ba.


Juyawa tayi zata koma kitchen din, hannunta ya ri'ko ya juyo da ita, cikin ɓacin rai take mishi magana, "ka sakarmin hannu," Yace "magana nakeso muyi ki bani lokacinki kaɗan.


Batace komi ba tayi fuska ta tsaya yace "don Allah sadeey ki faɗamin koma miye zan miki ka gane sonda nake miki, wallahi koma miye naayi alƙawarin zanyi, tace "kaa tabbata koma miye zakayi?


Da sauri yace "zanyi wlhy koma miye, Alƙawari nayi miki, tana taɓe baki tace "ka bani takardar saki kawai in tafi gidanmu, nan danan damuwa ta mamaye fuskarshi, yace "banda wannan babu wani abin sadeey? Ki zama mai tausayi mna, wannan yaamin tsauri da yawa.


Tace "kawai ka faɗamin ba sona kake ba ay nasan da hakan, ka bani wuri in wuce tunda bazaka iya cika alƙawari ba, Yace "zan cika sadeey, wlhy zanyi duk abnda zai sanyaki farin ciki, in har hakan zai tabbatar miki da son da nake miki.


Juyawa yayi hanyar ɗakinshi ta tsaya tana kallonshi duk tayi sukuku, tananan jikinta duk yayi sanyi ya dawo ɗauƙe da takarda da biro.


Zama yayi ya rubuta mata takardarta, sannan ya miƙe idonshu jawur ya kasa ɓoye damuwarshi, hannunta na kyarma ta amsa daƙyar tana kallonshi, juyawa kawai yayi da ɓacin rai yabar gidan.


Kasa ɗaukarta ƙafafuwanta sukayi, daƙyar ta iya ƙarasawa ta zauna saman kujera, tagumi tayi kamar ta fashe da kuka takeji.


Kasa barin gidan tayi kusan awa biyar, taa kasa buɗa takardar ta karanta, ganin hakan bazai mata ba ta tafi ɗakinta, ajiye takardar tayi tana ta kallonta zuciyarta cike da dana sani, ji take daman Abdul wahab ya dawo yace tunda bata karanta ba yaa fasa.


Wayarta ta nemo ta kunnata, messages suka dinga shigo mata, jikinta ba ƙwari ta shiga na fatyma tana duddubawa, saina ƙarshenne ya sanyata buɗa idanu cikin tashin hankali take kallon wayar.


A firgice ta maimaita yayanmu yayi accident yana asibiti? Na shiga uku na jawo ma kaina, yayar mayafinta kawai tayi ta fito anan ta saki kamar zararra ta fito daga gidan.


Dedicated to Mr. Smiles😃


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[8/14, 15:22] Rerbee'art😘: ABDUL WAHAB 39


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Tafiya kawai take tana jefa ƙafarta harta fito daga gidan, batasanma unguwar ba ta tsaya tana kallon hanyar da zatabi ta gano titi, saida ta koma ta tambayi mai gadinsu sannan ta tafi.


Mai napep ta tsaida ta faɗa mishi asibitin dazai kaita, duk da ruɗewar da tayi bata kasa ganin canjawar da garin yayi ba, sai kalle-kalle take, cikin zumuɗi duk taa ƙagara su isa asibitin taga halin da Abdul wahab yake ciki.


Dubu ɗayane hannunta, ta miƙa mishi kawai ta ƙara gaba, tunanin ɗakin da yake take, gashi taa baro wayarta haka ta dinga zagaye asibitin taa rasa inda zata nufa, canta tuna sannan ta nufi emergency.


Likita ta hango naa fitowa daga wurin ta ƙara sauri ta isa inda yake, tace "likita! Likita!! Patient ɗin da aka kawo bada daɗewa ba, don Allah shi nakeson gani? Yace "ya kike dashi? Tace "mijinah ne" ya sunanshi? Tace "Abdul wahab, wani fari haka yana da....!


Dakatar da ita yayi ganin tana bayani duk cin ruɗewa yace "tambayarta, da sauri ta juya, hango fatima tayi taa juya baya, da sassarfa ta ƙarasa inda take tace


"fatyma ya jikin Abdul? Fatyma tace "ya kike sadeey? Yaushe kikazo nan? Tace "manta dani ki faɗamin ya condition ɗin yayanmu yake? Tace "ki share yayanmu kawai sadeey ki faɗamin ya kike? Girgizata tayi tace "miye haka fatyma? Ki faɗamin ina yayanmu yake.


Fatyma tace "kin damu dashi ne har haka sadeey? Duk wani hali da yake ciki kene sila, kamata yayi kiyi murna tunda yaa tafi yaa barki," ban taɓa tunanin dalilin aurenki yayanmu zai iya samun damuwar da zata sa mishi ciwon zucia ba.


Faɗawa sadeey tayi jikin fatyma tana wani irin kuka, sauke numfashi fatyma tayi ta dafa bayan sadeey tace "wannan kukan da kikayi ya sanya kin goge laifinki a wurina, share hawayenta tayi tace "muje ki ganshi.


A ƙofar ɗakin da aka kwantar dashi kabir ne kawai, tace "su hajia da mami basu zoba? Fatyma tace "suna hanya, sannan suka shiga ɗakin shi da raheem ne kawai.


Da sauri ta ƙarasa inda yake, kwance yake jikinshi, kayanshi duk jini, ga wani dake fitowa daga bakinshi, sai maida numfashi yake daƙyar, faɗawa tayi jikinshi ta saki wani irin kukan tausayinshi da tausayin kanta.


Jijjigashi ta farayi tana faɗin "ka tashi don Allah yayanmu, karka tafi ka barni cikin damuwa da tsanar kaina, ka yafemin don Allah ka tashi muyi rayuwarmu cikin farin ciki, wayyo naa shiga uku naa cutar da masoyinah, kaa koyamin rayuwa dakai, mutuwa zanyi idan har baka tare dani, don Allah ka buɗa idonka in nemi gafararka mijina....


Sambatu kawai take ita kaɗai, tana jijjigashi, kwantar da kanta ta ƙarayi saman ƙirjinshi, tana shessheƙar kuka, ji tayi yaa ƙara matseta a ƙirjinshi, yaa ɗaura hannu saman kanta, ya saki wata roba da wani abu ke ciki kamar jini zumbur ta tashi zaune tana kallonshi.


❤❤Rabiatu sk msh❤❤

[8/14, 15:27] Rerbee'art😘: ABDUL WAHAB 40


©Rabiatu sk msh

     ®NWA


Ɗaga mata gira yayi yana murmushi, tare da fatima da raheem suka haɗa baki sukace "April fool", baki sake da mamaki ta juya tana kallon Abdul yaa tashi zaune yana dariya, fatyma da raheem ma suna dariya suka fita suka rufo musu ƙofa. Ita tama mnta da yaune first april


Rungume juna suka karayi, cikin wani irin yanayi na so da ƙaunar juna.


**** ****

Da dare saida sukayi sallah raka'a biyu na godiya ga ubangiji, sun daɗe Abdul na kwararo musu Addu'o'i, na zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba, sannan suka shafa ya tashi ya barta har lokacin tana addu'ah.


Sai data gama ne yace "wannan irin daɗewa hka? Me aka roƙa mana ne? Tace 


"na roƙa Allah babu wata yaudara, baƙin ciki, kishi, cin amana, ƙarya, ko rashin fahimtar dazai shiga tsakaninmu, kaine mutum na farko, kuma kai kaɗai na fara so a zuciyata, ina fatan zamowa matarka har a aljanna.


Yace "Ameen farin cikinah, idan har Aljanna a tafin ƙafata take, naa rigada naa ɗaga miki, ina Sonki sosae sadeey na!!


Nikam na gaji da jiran A kawo kaza naji shru, sisinah Amrah tace "idanma zaki rufe littafinnan, ƙara ki rufe don indai rowar Abdul ne ko sadeey taa dafa bazakiji ƙamshi ba. 


Alhamdulillah

Dukkan Godiya, da yabo sun tabbata ga Allah ubangiji daya bani ikon kammala wannan littafi nawa, Abinda nayi kuskure Ina roƙon Allah ya yafemun.


Mahaifiyatah

Banda kamarki a duniyarnan, Allah ya barni dake ya kuma ƙara miki tsawancin kwana, Allah ya biyaki ya saka miki da gidan Aljannah🙏🏻

😭Allah ya ƙara haskaka kabarinka mahaifina, Ya sadaka da rahamarsa🙏🏻


Daga marubuciyar

'yar Autah

Princess Amrah

Miye sanadi?

Mai farin jini

Maryam ko maryama

Hafsatul kiram

Mata biyu

Wasu mazan wasu matan...


Saimun haɗu a sabon littafina... ```SANADIN``` ```WHATSAPP``` ina bawa masu jiran ```Amrar``` ```Rabiatu``` haƙuri insha Allah zaizo muku bayan wannan.


Littafin ```ABDUL WAHAB``` Sadaukarwa ne gareka Abduljega (Mr. Smiles) keep smiling and be happy alwayz, wit ur luvly sadeey😃


Sadeeya S Adam (splexy)

My cwt kishiya... Zanyi amfani da wannan damar wurin godia a gareki, duk da babu kalmomin da zasu isheni gode miki kuma bazan gaji da yaba miki akan sadaukarwar da kikamin ba, dole nayi alfaharin saninki a rayuwata


Princess Amrah😊

Amrar rabiatu, er uwatah kuma Aminiyatah, bazan gaji da jinjina miki ba, kasancewarki a rayuwatah abin farin cikine sosae a gareni.


Dole in gaishe daku.

Qurratul ayni, Shafa'atu, Maman adnan (ummieluff)

Beely badaru, Anee, autar hajia, basma er lele da mai sanyinta, fulani cerdiya, khadija candy, khausar luv, meesha luv, haneefa usman, mrs umar, munayshat, Qurratul ayni, Rash kardam, sahaf, ummeeterh, jeedda Aleeyu, benaxir omar da kuma momienah didi Aneesa😘


Gaisuwa da jinjina ga marubutan:

Excellent writers

Online hausa writers

Wisdom hausa writer's

Extreme hausa writers

Best writers

Hn writer's

Modern hausa writer's

Glaxies hausa writers

Rolex hausa writers

Writers worls association

Nagarta writers association 

Marubuta zallah... Allah ya ƙara basira


Rabiatu sani katibu mashi😘

Naayi ma duk makaranta littafaina fatan alkhairi a duk inda kuke.


08032133670 domin gyara ko faɗar ra'ayi😊


❤❤Rabiatu sk msh❤❤sh❤❤

Tags: #Abdulwahab #Sadeey #khadija
2824
0
2
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!