ABIN TSORO! KURA A RUMBU

Written by Benaxir OmarPublished on 2018-12-12 16:57:47Category Historical Fiction(Based on a True Life Story) Dedicated to Aisha nd Sakeena Dansabo Benaxiratuuuuuu****** Hankalina yana kan sakonni na whatsapp da suke shigomin alokacin da naga Aisha tamin magana "Adda ya gida da makaranta?" tags: #Love #FictionDuba was labarai »

ABIN TSORO! KURA A RUMBU.

       na

   Benaxir Omar

(Based on a True Life Story)Dedicated to Aisha nd Sakeena DansaboBenaxiratuuuuuu******


Hankalina yana kan sakonni na whatsapp da suke shigomin alokacin da naga Aisha tamin magana

"Adda ya gida da makaranta?"

"lafiya kalao Alhamdulilah mun gode Allah yakike?" na amsa mata.

"Nazo da wani labarin Al'ajabi ne wanda nake so ki rubuta min duniya su gani kuma su amfana dashi tunda naga kina karban labari irin haka ki kuma rubuta da fatan ban takura ki ba"


"ko kadan Aisha, amma ina jarabawa don haka ina kammalawa zan neme ki sai ki isar mini da wannan sako da kike son isarwa, insha Allahu ni kuma zan rubuta kowa ya karanta ya kuma amfana"


"bakomi Allah ya kaimu ina jira".


  Kamar yadda muka yi da ita na kuma yi mata alkawari, yau ina kammala jarabawa ta na yiwa Aisha magana domin ta fada mini labarin da take son kowa yaji, labarin da yake cike da Abun Al'ajabi, takaici, haushi da kuma darussa aciki wanda zai saka duk mai karatu sanin cewa duniyan ma ba wata abun daga hankali bace, tabbas Duniya makaranta ce.


  Wannan labari ba daga bakin mutum daya yake ba, sai da aka hado kan dukkan wani wanda yakeda hannu acikin rayuwar baiwar Allah muka gamsu sannan nake rubutawa, Ubangiji Allah ya sa nafaraa sa'a na kuma gama a sa'a, kuskurenmu Allah ya gafarcemu, Allah ya shiryi duk iyaye irin na Kaulat, masu rayuwa irin Kaulat.watakila mai karatu zai ga abunda bai gamshe sa ba, ku sani cewa KALMA DAYA ban kara acikin labarin ba, ya faru ne dagaske. kuma wacce zanbada labarinnan akanta ta rasu, Ubangiji Allah ya jikanta, ya mata rahama ya kuma kai haske kabarinta, sannan burin marigayiyar ce a rubuta wannan labarin a fadakar wa duniya da kuma dukkan iyaye.   Bismillahi Rahmani RahimSunanta Kaulat Adams, wacce aka fi sani da kaule,Haifaffiyar garin illorin, Mahaifinta Alhaji Adams ya kasance mai arziki sosai sai dai babu wadatan zuci ma'ana baya taimakawa iyalinsa, irin masu kudin da zaka ga arziki a tattare dasu ga gida ga mota amma iyali a tsiyace, kowacce matarsa ita take yiwa kanta da kuma yaranta hidima.


Mahaifiyarta yar garin niger ce, sannan Kaulee ce yar farinta sannan shi Alhaji Adams shi ya musuluntar da ita ya kuma aureta .

     Kaulee ta girma agun iyayenta har Allah yasa ta shiga FGC billiri dake garin gombe, tayi junior class dinta har ta kammala sannan ta shigo ss1 inda aka kawo wata malama mai suna Hajiya fadila, Hajiya Fadila ta zamo tamkar mataimakiya ko ince uwa agun kaule, wacce take da ilmi ga kuma iya zama da mutum, sabawansu takai ta kawo har kwana kaule tana yi agidan Hajiya Fadila anan staff quarters,ta zamo yar gida, sun saba sosai da mijinta tana mishi kallon mahaifi yayinda shikuwa ba haka yake mata kallo ba. Kusan rabin kayanta agidan ta ajiye shi tamkar ba yar makarantan kwana ba, kasancewar kuma ana tsoron Hajiya Fadila yasa aka gagara tayar da maganan balle ta dawo hostel.


    Kaulee kamar yadda nace yar illorin duk wanda yasan yan illorin yasan akwai fulanin cikinsu, baka ce amma doguwa siririya tana da matukar kirar kalangu tamkar cikakkiyar bafulatana, macece mai fara'a son mutane, da kuma girmama na gaba da ita, ga kokarin addini iya gwargwado, tana da farin jinin maza domin kuwa kowa harinta yake a kankancin shekarunta, sai dai hidimar gabanta kadai takeyi bata damuwa da kowa balle soyayya ya shiga ranta ko abun da ya shafi haka.

    

    Ranar da bakin cikin rayuwanta ya auku kuma ya fara dinkin saka shine randa Mijin Hajiya fadila ya dawo gida alokacin bata nan sunje wani excursion da dalibai, Kaulee ce kadai acikin gidan sanye da dogon riganta tana gyran daki, wanda aiki ya zamo dabi'anta bata iya zama shiru ba sai ta nemo abun yi,  lekowa yayi sannan yace "Fadila fa?"


"ina wuni uncle? sun tafi excursion" ta amsa

Bai amsa gaisuwan ba ya juya, wanka yaje yayi sannan yasa jallabiya ya fito, tana zaune a falo tana kokarin goge kasan DVD da yayi kura tana mamaki domin jiya da safe ta goge shi, ji tayi ya taba bayanta yana jan gashinta, a razane ta juya don ganin mai mata wannan barna, mamaki kaman ya cinyeta

"un-uncle!"


"shhhhh" yasa hannu a bakinsa yana mata nuni da tayi shiru sannan ya fuzgeta ya jata sai dakinsu, akan gadon matarsa ya ketawa Kaulee hakkinta, ya yaga mata rigan budurci cikin izza da mulki irinta mugayen maza.


 2

ABIN TSORO! KURA A RUMBU.

       na

   Benaxir Omar

(Based on a True Life Story)Dedicated to Aisha nd Sakeena Dansabo


Kuka tayi sosai, tana tunanin makomar rayuwanta domin tabbas tasan cewa Hajiya Fadila ba zata barta ta zauna mata a gida bayan cin amananta da tayi ba.

"ina so kiyi shiru, kar ki gwada mata wani abu ya same ki sannan hakanne zai sa na rufa miki asiri, domin zan iya ce mata ke kika janyo komi kuma kinsan zata yarda har gidanku za taje ta tozartaki" ya fada mata alokacin da yake kokarin saka wando. Kuka tayi sosai ta tattara dakin da bedsheet din ta kintsa gadon sannan taje bandaki ta kimtsa jikinta duk ya ji mata ciwo yayi mata rauni, Hajiya Fadila bata dawo ba sai wuraren karfe goma don haka bata fahimci halin da gidan nata yake ciki ba washegari da sassafe ta kara fita, wannan ya kara bashi daman dawowa alokacin ta shirya cikin uniform zata shiga makaranta, har ta isa bakin kofa taji an rike hannunta jikinta na bari ta fizge muryanta na rawa tana cewa "uncle kayi hakuri, un-uncle!" rufe bakinta yayi ya nufi daki da ita ya fama mata ciwon da yaji mata, uniform dinta duk ya baci tana kuka ta koma daki ta canja sannan ta fito, idonta duk a kumbure gashi ta shiga makaranta aka mata dukkan latti dama daliban suna jin haushinta yadda take fita da shige cikin makarantan yadda takeso.


   Hajiya Fadila bata gane halin da mijinta da kuma Kaule suke ciki ba, wacce daga baya ita Kaule yabi jikinta bawan Allah ya mayar da ita injin aduk lokacin da yake bukatanta zai nemo ta tun ba taso har ta fara zama da kanta,ahaka ta kammala har ss3 tayi waec da neco suka rabu tabar gidanshi, Hajiya Fadila ba tasan wannan wainan da aka toya agidanta ba.


  Dawowanta gida bayan farin ciki da murna daga yan'uwa kowa na farin cikin Kaulee an gama sakandiri saura jami'a ta huta har na watanni kadan lokacin da jarabawansu yafito da komi ta tattari kafa ta nufi gun mahaifinta ta gaisheshi ya amsa sannan tace " Batun cigaba da karatuna ne, ga jarabawa na naci kuma na sami admission anan B.U.K "


"Wani karatu kuma Kaule? ai kina mace kam yanzu sai aure, babu batun karatu, kibar karatu wa maza yan'uwanki kuma ki jirani zan nema miki mijin aure insha Allahu"


  Ta kalleshi ta tabbatar da gaske yayi babu wasa don ba yau tasan shi ba, mutum ne mai taurin kai da kaffafiyar ra'ayi inya fadi abu toh sai yayi ta rokeshi taga yana kan bakansa don haka ta gyada kai tace "bakomi Allah ya kaimu" . Ta sami mahaifiyarta ta roketa itama hakuri ta bata "kibi mahaifinki kawai ya miki auren kinji?"


"Bakomi Allah ya kawo mijin". ta tashi ta nufi daki.


   Washegari da Sassafe ta tattara kayanta ta koma gidan kawarta anan Illorin din, Maria, maria na da aure sai dai mijin baya zama kuma asalinta yar kano ce shima haka, aiki ya kawosu illorin basa tare da kowa kuma basu cika zuwa gida ba, mijin yakan yi wata bakwai ko takwas bai zo gida ba irin wannan aikin dai yasa Maria take rayuwanta ita kadai komi ita kadai, zuwan Kaulee yasa suka fara zama tare tace mata tayi zamanta har sai randa ta gaji.


   Kaule ta fara rayuwanta domin addini kam anfara watsar dashi ko ince an watsar dashi, samari kuwa sai zuwa suke daga koina, ita a tunaninta jira take mahaifinta ya sauko daga fushin da yayi sai ya kaita makaranta bata cika kula mazan da suke addabanta ba sai dai idon Kaulee ya bude.


 Wata rana sun fito daga gidan Maria zasu je kasuwa wata mota sai binsu take, tun baya damunsu har maria ta tsaya da motan don ya wuce su, tsayawa yayi ya fito Babban mutum ne akalla yakai shekara 40-45 a duniya ya kalli Kaulee yana murmushi tamkar wanda aka bashi kyautan gonan auduga ita kuwa kamar ta kasheshi don bakin ciki,

" ina wuninku ina gajiya"

Maria ce ta amsa yayinda Kaule ke mika sakon harara "lafiya malam zamu tafi ne ka tare mana hanya" ta fada tana yatsina baki, lafayanta yana fadi tana mayarwa tsansan matsifa


"Kuyi hakuri, kuna tafiya ne kika ja hankali na don Allah kiyi hakuri ki kula ni kinji?" 

Maria ce ta jata gefe " jeki ki me zai fada miki daga gani wannan babban Alhaji ne akwai arziki jeki diba na diba mu ware" sannan suka dawo alokacin tace masa " me kake so yanzu?"


"muje motan nawa sai mu bita abaya ko? in yaso zan yi miki bayani akan hanya" ta bishi cikin kissa wacce zan iya cewa halittanta ce, tana shiga taji wani kamshi ga kuma kanta na juyawa, ta rasa meke mata dadi har wani jiri taji can kuma ta fara murmushi

"me kakeso?" yayi dariyan muguntansa da ya saba sannan yace "ke"


"muje" ta fada masa,

  Aikuwa bin Maria da ba'ayi ba kenan aka tafi hotel room, sai da yayi mai isansa yaji tabbas wannan bata bari bace, macece wacce ta amsa sunanta mace. Suna gamawa yace mata " me kike so kuma na miki?"

 "Makaranta nake so nayi, shine kadai burina"


"Na miki alkawari zan saki a makaranta har sai randa kika ce kin hakura amma zaki na bani kanki aduk lokacin da nake so, Sunana Bala Kutur, Ko me kikeso a duniyannan zan miki inhar ba zaki hanani kanki ba" tayi murmushi aranta tace ' wani ya samu na bati na shekara uku ba ci ba sha balle kai' 

 Ya mayar da ita Gidan Maria kuwa inda tayi mata bayanin cewa zai sata a makaranta nan ma sai daya sallemata da bandir din dari biyar guda uku.3


ABIN TSORO! KURA A RUMBU.

       na

   Benaxir Omar

(Based on a True Life Story)


        Nwa


Dedicated to Aisha nd Sakeena Dansabo
      Gani take yi kakarta ta yanke saka, bata yi bacci ba tsantsan farin ciki domin kuwa ba'a taba mata irin wannan kyautan ba a rayuwanta. Washegari da sassafe ta hada kan kayanta suka nufi kano don ganin ko za'a karbeta duk da cewa anyi post jamb, da karfin mulki irin na Bala kutur aka mata nata daban akayi sa'a taci don haka ta fara batun jiran registration da sauransu, gida ya kama mata one bedroom flat mai kyau, ba abunda bai saka mata wanda 'ya mace zata bukata, sannan yaje da ita kasuwa ya siya mata kayan sawa da atamfofi suka sami tailor ya mata express.

  


********

       Tana kwance a daki alokacin ya fita, ta janyo wayanta ta kira layin Mahaifiyarta

"Inna ina wuni?" kasancewar ta gane muryanta yasa tace "ina kika shiga? kowa na nemanki?"


"Inna na sami wanda ya sakani a makaranta, ya biya komi yanzu har gida ya bani, ina nan garin kano"

jin haka da sauri Inna tace "kudi fa? ya baki? in ya baki kudi ki turo, kinga ni da kannenki sai wahala muke sha babanku yaki sake kudin" ba tayi mamakin kalamun inna ba domin kuwa idan da sabo ta saba ta kuma santa da son abun duniya don haka sai tace "akwai, turomin account number yanzu na turo" aikuwa tana kashewa taga alert mikewa tayi ta fito don taje tasa kudin sai ga Bala kutur cikin maganansa ta yan maye da izza yace "inaaaaaaa zakijee suga?"


"zan je bank ne" 

"toh ki tsaya mana na ci kadan ko?" kalamun sun mata nauyi haka ta koma aranta tana cewa 'lallai wannan yaji bariki' sai da ya idda bukatarsa yaga bai gamsu ba ya mike ya janyota sannan yace "kin---gane---ne? bana gane komi, barin gwada miki yadda zakiyi, ya ciro wani dorina yana dukanta kukan da take yi shi kuma ita take sanyaya masa zuciya "yauwa haka nake so" sai da ya zaneta tana kuka yana biyan bukatarsa sannan ya barta ta tafi bank da kudin da ya batan ta turawa mahaifiyarta ta dawo.


   Rayuwa ta ci gaba da tafiya mata haka, idan yaga bai gamsu ba zai nemo dorinansa ya daketa kuma ya bata kudi a wadace duk jikinta ciwo. Wata rana da safe yafita aiki ta ji yunkurin amai da gudu taje tayi, hankalinta ya tashi ganin cewa tabbas ciki gareta domin kuwa sai alokacin ta tuna tayi batan wata

"innalilahi wainna ilaihi rajiun" sai data zauna ta tika kukanta yadda ya isheta sannan ta mike zata sa kaya taga waya na kara ta duba taga Innarta ce daukan da zata yi tace "Kaule kudi dai ya kare ki kara mana kinji" tayi murmushin bakin ciki hawaye na bin gefen idonta sannan tace "toh" Inna ta kashe wayanta, kayanta ta tattara tabar gidan sai illorin, don ta mugun tsorata da batun ciki, gidan Maria ta nufa wacce taje ta sameta itama cikin tashin hankali da matsifa dangin miji sun sa ta agaba batun haihuwa, sai waya da batun damun mijinta ya karo aure, Kaule na jin haka tace "kirashi kice masa kina da cikin wata uku" ta juyo ta kalleta " baki da hankali ne? ai na zan samu yaro?"

" Zan baki nawa" zaro ido Maria tayi,


"ae, Bala yamin ciki shiyasa ma na gudo" 

"Ba damuwa to, kin duba wata nawa ne kike batun wata uku? muje asibiti tukunna ko? amma anya babu matsala? ba za'a gane ba?"

"ke meyasa kike da tsoro? mijinki baya zama, danginsa babu mai zuwa daurewa zakiyi har na haihu kafin ki bari ya dawo" aikuwa Maria taji dadin wannan shawara

"tsaya nayi wanka muje mu gwada".


4


ABIN TSORO! KURA A RUMBU.

       na

   Benaxir Omar

(Based on a True Life Story)


        Nwa


Dedicated to Aisha nd Sakeena Dansabo


Tana fitowa a wanka ta shirya tsaf, ta kira driver sannan suka fice, sun samu sun ga likita inda aka auna Kaule aka ga wata hudu ne ciki kam, ahanyan dawowansu ma Maria ta kira mijinta wanda sun tafi senegal wani aiki

"Hubby ya kake?"

"Baby na lafiya lao ya gajiya?" ya amsa daga gunsa


"zan maka albishir mai zaka bani?"


"me kike so?"


"Vacation to paris, sai kuma ka canja min mota"


"anyi angama"


"inada ciki, congratulations"


Shiru yayi can yace "me kika ce?"


"inada juna Biyu"


"Oh my! Oh my God!! My baybay!! ohhh Alhamdulilah dole na dawo, zanyi cancelling komi gobe na dawo na ganki"


"Nooo! ka bari kayi hakuri ka gama kaji?"

"anya? bazan iyaba gaskiya kinsan sai nan da wata shida fa zamu taho"

da sauri ta kirga sannan tace "bakomi kar ka damu zan raine cikin har na haihu sai kazo kaga babynka ko?"


"a'a zaki wahala ke kadai, barin kira wani agida azo atayaki zama"

"ka manta Kaule tana nan? zamu zauna kawai, hubby kasan danginka yadda suke min inaso nayi surprising dinsu suji kawai na haihu ne" har da saka kukanta kuwa, hakan yasa yaji tausayinta sanin cewa tasha jiki agun danginsa batun haihuwa amma tunda yanzu akwai cikin zai barta harta haihun, da haka dai suka yi sallama.


    Maria tana tsantsan kulawa da Kaule da cikinta, duk da cikin yazo da laulayi sosai tana jin jiki, bata iya cin abinci sai amai da tofar da yawu, ga tsantsan wahala da take sha gurin bacci duk ciwon jiki, haka kawai zata je ta tsoma kanta a shadda don taji warin shadda wanda ita shi take so kuma yake sanyaya mata rai take ji a matsayin kamshi, Inna kuwa kullum acikin tambayan kudi take Kaule ta kan tura mata amma bata taba sanar da ita cewa tana da ciki ba, makaranta kuwa tuni ta ajiye batun shi agefe, babu yanda Bala baiyi ba su hadu taki, har hakuri yake bata in yazo gidan Maria takan ce Kaule ba tazo ba babu yadda ya iya, gashi dai suna waya in taga dama shi rokonta yake ta yarda ta aureshi don ayadda ya saba da jikinta zai iya komi akanta, ganin zai dameta yasa ta canja layi taci gaba da rainon cikinta har watan haihuwa.


   Ranar da EDD dinta ya cika aranar ta fara nakuda, asibiti suka nufa, tasha jiki ga haihuwa yazo ganin dadewan da tayi tana nakuda na kusa kwana uku yasa likitotin suka yanke shawaran yi mata CS aka ciro dankareren baby boy, tana farfadowa da aka miko mata 'Dan ta karba ta mikawa Maria


"Na baki halak malak, ki rike amana"


Maria tana murna tana goge hawaye ta rungume 'Dan can ta mayar dashi inda aka kwantar dashi, tana zaune taga anbude kofan dakin Bala ne yashigo ba karamin tsorata tayi ba ganinsa amma ta danne tare da hada girar sama da kasa

"nace maka Kaule bata nan meyasa kake da naci?"


"karki damu na riga nasan tana gidanki, na kuma san kun zo asibiti na kuma san ta haihu sai dai nazo ne nayi magana da ita, shin 'Dan waye ne?"

ko kallonsa ba tayiba ya nufi dakin da aka kwantar da Kaule, Maria ta bishi da sauri don kar yaje ya bata musu aiki


"Kaule 'Da nane ina?"

"ta ina ya zama Danka?" ta fada tana bata fuska kamar ta kurbi kashi


"saboda ni na saba kwana da ke"


"wai tsaya in tambayeka? ran da ka fara kwanciya dani budurwa ka sameni? kar ka manta ba akanka na fara ba kuma ba akanka zan tsaya ba haka zalika ba kai kadai nake da ba, na kwanta da maza kala kala kashi kashi wannan yaro ba danka bane! ka fice ka barni ko na nemo ubansa ku kwashi dan kallo dashi" shiru yayi don alokacin ji yake kamar ya saceta ya gudu har da hadiye yawunsa gashi ta kara kyau duk da ramewan da tayi, wani mummunan kishi ya gulle shi tsaki yaja ya juya ya fita amma can cikin ransa jikinshi na bashi cewa lallai wannan yaronsa ne, zai bar mata amma zai sa musu ido, yasan Kaule sarai duk da bai sameta a 'ya mace ba yasan tsautsayi ce ta gifta, shima don makarantan da ya sakata ne ya sa ta amince dashi amma akan mutuwanshi yasan Kaule kamilalliya ce.


  Kwanansu uku aka sallamesu a asibiti, Maria har ta kira oganta ta fada mishi wanda tuni ya fara fadawa yanuwa da abokan arziki adole ta dawo mai jego, sai mata wankan jego ake dangin miji kaman su bauta mata kowa na marhaban da yaro, kunsan haihuwa baya buya, nonon Maria yaki cikowa don haka sai Kaule ta fara shayar dashi da mutane suka zo sai Maria take ce musu ai Kaule yaranta biyu, kowa na mamakin wannan abun al'ajabi amma dai suka yi shiru tunda damuwansu a haifi yaronne kuma an haifa, ran suna aka yiwa Baban Mijin Maria takwara Usman, yaro yana girma kammanin Bala na kara fitowa, amma haskensa da idonsa sak Kaule,ana haka mijin Maria ya dawo murna agunsa kaman me, yana ganin yaro yace "anya yaronki ne?" gabanta na fadi ta zaro ido sannan tace "kaman me fa bangane ba?" yayi dariya sannan yace "yaronnan bai da kirki sai ya dauko kammanin Kaule anya ba danta ba?" kayan cikinta tuni suka kada, idonta yayi jajur ta tsorata sosai.


5


ABIN TSORO! KURA A RUMBU.

       na

   Benaxir Omar

(Based on a True Life Story)


        Nwa


Dedicated to Aisha nd Sakeena Dansabo
www.Benaxiromar.com


     Dariya yayi sannan yace "meye na tsorata? kama suke yi sosai, i guess kinji jiki gurin haihuwa Allah ya raya yaushe za kije paris din? kin san banda lokaci sosai zaki iya zuwa ke kadai?"


" a'a zanje da Kaule kaga tamin kokari, abunda tamin ba wanda zai iya min"


" gaskiya ta katse hidimominta ta zauna dake tayi kokari sosai donhaka zan biya muku ku tafi tare, sai taje tayi epassport afara shiryawa ko? tunda ke kina dashi"

rungumoshi tayi don taji dadi sosai, "rufe idonki" ya fada mata hakan yasa ta rufe idonta, tana ji ya makala mata awuya sannan yace "bude" tana budewa tayi mamaki sosai domin kuwa sarkan diamond ce awuyanta

"yeeeeeeeeeehhhh hubbby!" ta rungumeshi tana murna, daya daga cikin dalilan da take kara sonshi kenan, akwai shi akwai kyauta da iya farantawa mace rai, matsalanshi daya baya zama agida amma duk lokacin da ya dawo gida yakan yi kokarinsa ganin ya faranta mata rai fiye da duk wata mace atunaninta.


    Tuni suka fara shirye shiryensu, yaron na wata takwas aka yayeshi sannan suka kama hanya, satinsu biyu a paris daga nan suka wuce umrah a dawowa suka tsaya dubai ba shakka sun bude ido, Maria tayi hakan duk a matsayin godiya wa Kaule akan kyautar da ta mata, dawowansu gida suka cigaba da zama tare sun shaku sosai.

************

      Usman yakai na shiga makaranta don haka Kaule da kanta ta nemo makarantan da zata sakashi a matsayinta na Aminiyar Mahaifiyarshi a tunanin mutane, Bala kuma kusan kullum yana hanyan siya wa yaro kayan kwalama, haka kawai yake son yaron sun saba sosai dashi, bata hanashi ba sannan kuma bata bashi fuskan da zai kara cewa danshi bane, an saka shi a makaranta mai tsada duk da cewa ya shaku da Kaule fiye da Maria tabbas uwa ba wasa bace, sannan ikon Allah ma ba wasa bane, hakan ya kawo surutu gun mutane yan'uwan da suke zuwa gidan sun fara surutun zaman da Kaule take agidan jin haka cikin mutunci ta tattare ya nata sai Abuja, birnin bariki, a mararaba aka sauketa ta kalli gabas da yamma kudu da arewa, duk da bata da gurin zuwa tasan tabbas zata samu gurin zama, ta kalli jikinta rigan atamfa da zani ne dole ne ta nemi inda zata canja kaya, cikin kasuwan ta shiga tana dube dube har taga bandaki ta nemi shago ta ajiye akwatinta ta ciro kayan da zata sanya sannan ta shiga ciki, doguwar riga ce ya fitar da shape dinta, ta saka sannan ta cire dankwalinta ya kumbushi kanta, ta ciro wayanta mai tsada sannan ta janyo akwatin nata ta nemi taxi drop tace "Maitama" ya mata bayanin kudinta ta bude baki "malam maitama hour nawa ne zuwa can?" yayi murmushi "madam na minutes drive ooo mek we na dey go" mamaki ya isheta ko daga illorin zuwa abuja bata kashe kudin da yake gaya mata tabiya ba " na so it be o, and madam na drop you say, kokoma enta mek we go" ta ja numfashi sannan ta shiga yayinda yasa akwatin a motan suka tafi duk da ita kanta jin kanta take motan corolla ce kuma yake taxi da ita abun mamaki, suna isa ita kanta tasan sunje Maitama, gidaje ne manya manya na alfarma 'lalle akwai kudi a habuja' ta fada aranta duk da bata san inda zata sauka ba, mutumin yace " wey for maitama?" ta kalli inda take sannan tace "here" yaja yayi parking ita kuma ta ciro akwatinta ta mika mishi kudinshi har zai tafi tace " where is this place please?" kallonta yayi cikin mamaki sannan yace "Ministers hill nah, u neva no wey u dey go?" bai kulata ba ya shiga motansa ya tafi, gyra kayanta tayi tana tafiya cikin takun isa da kasaita tana jan akwatinta, ta sanya wayanta a kunnenta kamar mai waya duk wanda ya ganta alokacin idan yacire abun hawan da bata dashi yasan ba karamin kifi bace.


   Tayi tafiya yakai na minti goma kafin taji horn abayanta, bata juya ba taci gaba da karyan wayanta, hakan yasa yasha gabanta sannan ya fito, gabanta yayi mummunan fadi 'wayyoni Allah yayi halittan kyau anan' ta fada a zuciyarta yayinda a zahiri ta juya kai tare da cewa "beb ki dauka min jakan na 120k, sai ki tura min account numbern matan zan tura mata kudinta yanzunnan" sai ta kashe sannan ta kallesa alokacin ya nannade hannunsa yana kallonta, dogo ne bugun farko tasan shuwa ne , manyan yaran maiduguri,


"Naga kina tafiya ne nace barin rage miki hanya"


"ah no kar ka damu, ina neman hotel ne nearby, dake nazo wani conference"


"karki damu muje na kama miki".


  Duk da tayi farinciki sosai a zahiri ta gwada masa ya bari yayinda shikuma ya dage akarshe ya karbi akwatinta ya saka a bayan aura dinsa,motan ta kasheta , tana shiga wani sanyi da kamshi ya bugi hancinta taji dadi sosai ko ba komi ta yanki sa'a daga shigowanta,


"akwai hotel din da na saba zuwa a central area haka, hankalina yafi kwanciya dasu in kaiki can ko kuma akwai wanda kika fi so?"


"a'a muje kawai".


  Haka ya kaisu har Reiz continental ya mata booking ya biya ya karbi access card din sannan suka wuce, hotel din na da kyau sosai, tana shiga ya ajiye akwatinta sannan yace "barinje na dawo kafinnan kin huta" ta gyada kai ta shiga toilet shi kuma ya fice, wanka tayi ta sanya riga da wando wanda ya matseta ta tattaro gashinta sannan ta zauna jiransa, sunyi waya da Maria take ce mata ta sami wani yanzu komi zai yi sauki, bata idda magananta ba ya shigo da ledoji a hannunsa, ta karba zata ajiye ledan ya kubuce zai fadi riko ta yayi da sauri suka hada ido tana jikinsa, basu san lokacin da suka afka wa juna ba, hannunsa ya sanya ya kashe wuta.


6

ABIN TSORO! KURA A RUMBU.

       na

   Benaxir Omar

(Based on a True Life Story)


        Nwa


Dedicated to Aisha nd Sakeena Dansabo
www.Benaxiromar.com
Sun aikata abunda suke ganin ya fi musu, don kuwa Kaule ta kure masa tunani taso fin karfinshi, gefe daya ya juya ya kwanta yana jan numfashi ta tashi ta shiga bandaki ta kimtsa tana fitowa ta samu baya nan , zama tayi agefen gadon tana gyra ribbon din gashinta don atunaninta yadan fitane, ganin takarda tayi da envelope, ta bude takardan tana kokarin karantawa

" it was nyc having fun with you" murmushi tayi ta bude envelope din bandir din dubu daya guda uku abin ya bata mamaki sai dai ba abun mamaki bane, ta fito masa a babban yarinya, bariki sai da kudi ake samun kudi, mikewa tayi ta fita cin abinci bayan ta bude ledojin da ya kawo dazun sabulun wanka ne su soso, chocolates, turare da dai sauran tarkacen mata, bayan ta gama cin abinci ne ta nemi drop yakaita yawo, ce mishi tayi ya zaga da ita gari kawai suna kan tafiya motar ta buge wata motar mata da take tuki tana waya, drivern ya fita ya nata mita matan ta fito daga range rovernta ta bashi hakuri wanda hakan ya burge Kaule, dubi mata da saukin kai, gaisawa suka yi da matan tace "wallahi kin burgeni sosai" matan tayi dariya " kema haka, kamar ba yar gari ba ko?"


"ae" ta fada tana sosa keya, don ta lura yadda hajiyan ke kallon suturanta

"ina zakije?" ta tambayeta

"wallahi nima ban sani ba, kawai cewa nayi yayi yawo da ni" fitar da jakanta tayi ta ciro kudi ta bashi sannan tace ta shiga mota su tafi, duk da hankalinta akwance yake da matan amma ta dan tsorata kadan har gida ta kaisu, gidanta na Asokoro babban gida daga gani kuma gidan dan siyasa, masu aiki sai kai da kawowa suke suna gaida hajiyar yayinda ta haura da ita sama, taje daki ta rage kayan jikinta sannan ta dawo ta zauna

"kina kama da kamilallun mata, sai dai shiganki ya fita daban da haka, idan akwai damuwan da kike dashi ki fada, wannan shigan ba naki bane," ta kara kallon jikinta sai taji kunya rigan ya matseta sosai ga cibin ta awaje, wandon jeans dinma ya matse iya dunduniya ga huji kala kala kaman yadda wandunan yanzu suke zuwa da yayi,


"bakomi Allah hajiya"


"shikenan" ta mika mata wasu kaya " jeki sanya wannan" ta karba aka kaita wani daki, daga gani dakin budurwa ne ta saka atamfar, super ce doguwar riga bubu don haka ya shigeta sannan ta dawo falon ta zauna, an bata abinci taci ta koshi tayi sallah wanda ita kanta ta manta yaushe rabonta da tayi sallah, ganin yadda rayuwar Hajiyar ke tafiya ya bata sha'awa ga kudi, ga komi ga kuma addini, hakan yasa data idar da sallahn taje gefenta tace " zan baki tarihina, inaso ki taimaka min kuma ki nema min mafita" tun daga farko ta bada labarin har karshe, Hajiya Atika ta tsorata sosai don wannan labari abun dubawa ne abun alajabi ne, 

"ki zauna anan gidan, yanzu kije ki tattaro kayanki daga hotel din can, kizo nan ki zauna zanyi tunani akan matsalarki" cikin ikon Allah ta bada driver yakaita central area ta kwaso kayanta daga Reiz sannan suka dawo Asokoro, wannan dakin aka kaita sannan Hajiyan tace tayi amfani da duk abunda ta gani take so acikin gun.

*******

     Satinta daya cif tana samun kulawa daga gun Hajiya Atika har take jin ina ma itace mahaifiyarta da duk bata sha wannan wahalan ba, sun saba sosai su kan yi hira ahankali ta fahimci ashe Hajiyan na da Yara hudu dukka suna kasar waje suna karatu, hakan yasa take nan daga ita sai ma'aikata,da rana tana zaune Hajiya Atika ta shigo falon sannan tace " munyi bakuwa ki fito kiga wacecece" fitanta cikin farin cikin da ta samu acikin gidan ta hango fuskar innarta, gaba daya taga garin ya mata duhu, komi nata ya toshe,sallati tayi sannan ta dafe bango domin idan akwai abunda take tsoro yanzu shine taga Inna, zama tayi ta gaisheta ba yabo ba fallasa, Inna kuwa sai kalle kalle take taga gida na yan gayu, 'Ashe Kaule kam dadi take sha muna can muna shan wahala' ta fada aranta.


   Hajiya Atika ta shigo suka gaisa sannan tace " nagode kwarai da kika amshi gayyata ta kika zo, ina zaune ne da yarki naga ya dace na sanar dake abunda ake ciki, duk da ta fada mun damuwanta da kuma tarihinta inaso ne ayau ta koma gida gurinki" Inna tayi yake ba tace komi ba sannan Hajiyan ta cigaba da cewa " meye daya damuwanki?"


"Kudi hajiya" ta fada kanta akasa, wanda Kaule taji kaman an caka mata wuka don bakin ciki,


"zan baki kudi amma da sharadin Kaulat zata zauna agida, kuma ba zaki kara bari ta fita ko kice ta nemo miki kudi ba, zan na baki kudi wata wata na miki wannan alkawarin, kinada yarinya mace tarbiyanta na hannunki ko kina so Allah ya kamaki da laifi ne? hakkin yaranki suna kanki haka zalika duk abunda ya samesu".


    Godiya sosai Inna tayi ko ince ta kwana tana yi, washegari aka hada su da driver ya mayar dasu illorin, cike da goma na arziki.


7

ABIN TSORO! KURA A RUMBU.

       na

   Benaxir Omar

(Based on a True Life Story)


        Nwa


Dedicated to Aisha nd Sakeena Dansabo
www.Benaxiromar.com
*********

       Tana zaune a daki tayi tagumi, tunaninta duk yana kan danta gun Maria, duk da cewa tana da tabbacin cewa Maria zata gwada masa SO fiye da yadda ita zata masa, haka zalika gatan da zata masa, duk takaicin gidansu ya dameta gida ya zama kaman gidan bariki, hatta omo mutum shi zai cire kudinsa yasiya kayansa, haka abun karyawa, abincin rana da dare ne kawai mutum keda guarantee samu, tayi nadama ma meyasa take turawa mahaifiyarta kudi domin ta rasa me Inna takeyi da kudin, fanninta babu kimtsi haka zalika ba kashewa kannenta take ba, ba sutura take sawa ba Kai!! Allah wadai da irin wannan rayuwa, duk jinta take atakure ba gurin zuwa haka dai take lallaba zaman, mahaifinta kam da zamanta da rashinsa duk ya dauka daya agunsa, ko da ta dawo da taje ta masa gaisuwa bai amsa ba harta fita, haka dai kullum zata je ta gaisheshi amma bazai amsa ba,shi adole fushi yake da ita. Bai dameta ba balle ta nemi gafara wanda zai sanyaya ranshi agareta.

     Ta manta cewa duk kankantar fushin Mahaifi akan yaronsa ubangiji yana tuhuman yaro, sannan babban hanyan hallaka shine fushin iyaye, Annabi muhammad SAW da kansa yace Mafi alherin cikinku, Mafi rabo cikunku shine wanda ya so Allah da manzonsa, sannan yayi biyayya ga iyayensa,sannan ya fadi alheri ko yayi shiru, sannan akwai ayoyi da dama da suka zo mana da muhimmancin biyayya wa iyaye wanda duk wanda zai bauta wa Allah yayi biyayya ga manzo abu na gaba shine biyayya wa iyaye, akwai suratul ankaboot aya ta 8, akwai suratul Nisai aya ta 36, suratul israae aya ta 23,24, duk wadannan kadan daga cikin yadda suka fito a qur'ani ne ashe kuwa biyayya wa iyaye na da falala sannan hatsari ne saba musu.

   

   Mikewa tayi ta shiga daki ta dauko wallet dinta ta kirga sauran kudin ciki dubu uku, dubu uku in har ta kuskura kudinnan ya kare sunanta Sorry don haka dole ta tashi ta nemi kudi, dari biyar ta cire aciki ta kira kanninta "siyomin masa da miya agurin baba tilo" ya karbi kudin yaje kicin ya dauko kwanan sannan yafita, duk kallonsa take haka kawai take tausayinsa duk cikin yaran gidansu ya fita daban, domin kuwa zata iya cewa daga mahaifinta yayi kan iyaye mata har yara wanda akalla sun kai goma sha shida babu mai rikon addininsa da ilmin addini irinsa, da zata samu kudi mai yawa zata kaisa ko madina ne yaje yayi jami'arsa tana so ya zama babban malami domin ayanzu ma ba wanda zai zauna dashi kuma ya tashi bai karu dashi ba,tunani dai kala kala har ya dawo ya mika mata kwanon sannan ya nemi guri ya zauna yana karanta wani littafi ta karanta bayan "cure of all worries" cin masan tayi sai dai tana koshi ta ture kwanan da kafa ya kalleta sannan yace "Adda babu kyau abunda kika yi?"

"me kuma nayi malam dalhatu?"

"da farko ji yadda kika goge hannunki da tissue bayan Ibn Abbas, yardan Allah ya tabbata agareshi yace Manzon Allah SAW yace 'Idan dayanku ya gama cin abinci kar ya goge yatsunsa har sai ya lashe da kansa ko yabawa wani ya lashe masa' hadisi ce ingantancce Bukhari da muslim suka rawaito shi zaki iya dubawa a riyadul salihin babi ta 109"

"toh naji zan gyra"

"na biyu duk da ke kadai kike cin abincin ta tsakiya fa kika cakular abincin, shima babu kyau manzon Allah SAW yace 'albarka tana sauka akan tsakiyan abinci don haka kuci daga gefen kwanukan ku kar kuci daga tsakiya'Tirmidhi da Abu dawuud ne suka ruwaito shi"

"naji zan gyra, ba sai ka fadi dayan ba nasani na ture abinci da kafana shima babu kyau" murmushi yayi sannan yace "yauwa Adda ki daina" taji dadi sosai yawo da irinsu zata canja rayuwan mutum, wanka ta tashi tayi don yau kam neman kudi tasa aranta, tana gama kimtsawa ta nemi taxi ya kaita jamiar Al HIKMA, daga bakin gate ta tsaya ta ciro wayanta don kiran kawarta Naja tazo ta shiga da ita, sai taji wayan ba kudi,wani ne yake tsaye shima a bakin gate din sai dai ajikin mota yake alamun shima zai shigane, taje gefensa sannan tace " malam don Allah aron wayanka zaka bani nayi waya" ta fadi hakan don ganin yana kama da hausawa

"lol, ni ne malam? toh malama barin baki" ya mika mata ta saka lambar Najan sannan ta kira anan ta mata bayanin inda take sannan ta kashe ta mika masa, hannunta ya riko arazane ta kalleshi sannan yace " shiga muyi magana" fizge hannunta tayi " na maka kama da wacce zaka fadawa doka ta bi cikin sauki?"


"yi hakuri sauke ki nake son yi"

"kaje zata zo ta dauken"

bai ce komi ba ya shiga ya wuce, Naja za tazo yau ne ko gobe shiru, ta kai awa abakin gate tana jira gashi ba kudi awayantan, can sai gashi ya fito Najan ce agefensa suka tsaya agabanta alokacin ta kulu kaman zata mutu ta bude bayan motan ta shiga, 

"kawata yi hakuri don Allah nasan kinyi fushi, ga abokina Shun ku gaisa" wani kallo da ya juyo ya mata sai da ya tayar mata da hankali, gaban hostel suka koma inda Naja karfi da yaji ta hada Kaule da Shun acewarta ba Dalibi bane daga abuja ma yazo, kuma yace yana son Kaulen,ita dai taki kulashi amma sai shige mata yake, tare suka fito akan zai sauketa agida

"kiyi hakuri in nine na bata miki rai am sorry babyna" aranta dariya ya bata wato har ta zama baby, 

"kiyi dariya mana kinga jibi zan tafi abuja kar na tafi kina fushi dani" 

"nace maka ba komi ya wuce" hannunta ya riko bata kwace ba wannan karon haka yayita murza hannun har suka isa gida, ya ciro bandir din dari biyar ya bata "kiyi hakuri kinji kafin na dawo" ta karba tare da cewa "nagode" ya dauki lambar wayanta sannan ya tafi, tana shiga gidan wayan Naja ya shigo "kawata ya Shun kun shirya ko?"

"ae meya faru"

"toh dama zan sanar dake ne, in kudi ne zaki ci kawata, duk da shi bamusan aikin da yake ba amma yana da matsifaffen kudi ni dai damuwana kar kice zaki so shi domin zaki wahala, kici kudi ki ware, kuma kar ki yadda wani abu ya shiga tsakaninku"

"bakomi nagode" tana kashewa taja tsaki 'ji wannan matan an gaya mata ni zata yiwa wayo? ina ganin yaro ga kyau ga kudi meyasa ba zan so shi ba, tsabar keta irinta mata'.


8

ABIN TSORO! KURA A RUMBU.

       na

   Benaxir Omar

(Based on a True Life Story)


        Nwa


Dedicated to Aisha nd Sakeena Dansabo
www.Benaxiromar.com
*********

    Kaule ta fada tarkon SO da Kaunar Shun haka zalika shima ya na sonta domin kuwa tunda ya tafi hankalinsa yana kan Kaule, wacce kullum suke waya ta nannade adaki tana bin kudin da yabata daya bayan daya, randa zai dawo illorin ya kirata, abun mamaki Kaule ce har da girke-girke don tarban Shun wanda yan gidansu kowa mamaki yake, yana tahowa ya gaida Inna itama ya zuba mata 'ya'yan banki kafin ya tafi tuni ya siya zuciyan yan gidansu Kaule kowa na marhaban dashi, tare suke wuni don kuwa Sallah ke rabasu shima don lokaci nayi Shun zai mike ya wuce masallaci, duk wani mummunan abu da Naja tace mata game dashi duk ta karyata domin taga ba haka bane, Kaule ta koma ga Allah, ibada kan ibada ga suturce jiki kullum tana gefen kaninta domin karin ilmin addini, ta gama fayyace wa ranta cewa Shun zata aura kuma dashi zata zauna, iyakacinsa taba hannunta baya wuce nan, shima sai adade kafin ya mika hannu hakan da yakeyi ba karamin shiga ranta yayi ba,


"nazo miki sallama zan koma abuja amma gaskiya zan dan kai wata daya ban zo ba, kiyi hakuri ki jirani ko babyna" ta kalleshi narai da ido randa yazo mata da batun zai yi tafiya

"bakomi Allah ya kaimu, amma dama zanje abuja gidan kawata idan nazo zan nemeka sai kazo mu gaisa" murmushi yayi wanda ita kanta sai da taji dadi haka dai suka yi sallama ya tafi.  Wata daya shiru babu Shun babu labarinsa sai dai waya wataran ma sai yaga dama yake daukan wayan ba shiri ta hada kayanta tace itakama zata tafi abuja gidan kawarta azahiri kuwa gurin Shun take son zuwa, isanta abuja ta kama daki a Reiz domin taji dadin yadda suke karbeta zuwanta kwanaki sannan takira Shun cikin ikon Allah sai gashi yazo, ya dauketa yace ta rakashi gidanshi ya dauko sako, tafiya suke yi har suka isa wani guri daga tambarin taga an saka TAFA local government ne na niger state, amma hakarkarinta tana garin abuja, bata damu ba ita dai tayi murna sosai kamar ta rungumeshi ya kalleta amma babu alaman sakewa a tattare dashi,

"baby akwai matsala ne? ko bakada lafiya ne?"

"kiyi hakuri, banda zabi ne akanki, amma ina sonki kuma zanci gaba da sonki" yana fadan haka ya bude kofan motan, itama ta bude nata suka fito suna tsaye wani baki, dogooo kallon halittarshi kadai zai iya sanya dan Adam jimamin makomar rayuwarsa ya iso gaban Shun tare da mika masa check yana dariyan keta

"kiyi hakuri fa, wannan saurayi naki no get power na so i come c your picshure for him phone, i come tell am say i wan sleep with you i go give am 2million , you see yourself now you are here" ya kwashe da dariyan mugunta, hawaye suka ciko idonta ta goge sannan tace "Shun dama ba sona kake ba?"

"ina sonki wallahi, amma Kaule mahaifiyata tana asibiti, i need money" ya fada cike da damuwa a fuskansa, ta gyada kanta cikin tsananin bakin ciki takaici fal aranta hade da nadama

"Shun i hate youuu, i so much hate you that i feel like to squeeze your bones like an orange" kamota mutanen sukayi Shun ya shiga motarsa da cheque dinsa yayinda aka mikata Dandalin Karuwan Tafa, shiganta gurin ma sai data raina kanta, mashaya, yan caca, karuwai babu kalan mutanen da babu acikin gurin, wani daki ya wurgata tana kokarin faucewa da ya wanka mata wani mari walkiya ta fara gani a fuskanta, jiri ya kwasheta ta koma sannan ya riko wuyanta "fool, get hold of yourself this is just the begining."


9

ABIN TSORO! KURA A RUMBU.

       na

   Benaxir Omar

(Based on a True Life Story)


        Nwa


Dedicated to Aisha nd Sakeena Dansabo
www.Benaxiromar.com
*********

        Yawun bakinta ta tofa masa cikin takaici, ya damko gashin kanta wanda dankwalin ya dade da fadi kasa tsantsan wahalan da take sha, murda kanta yayi ta saka wani kara "in kin bukaci mu zauna lafiya shikenan, in kuma kika ce mugunta kike so na miki shima zan miki" ya dauki hannunsa ya wanka mata mari don aganinshi raini ne mace ta tofa masa yawu yabarta, tsantsan zafin marin gigicewa tayi ta koma ta buge da kasa, karfen bayanta da ya coketa tsantsar azaba suma tayi. A take ya gigice "call the doctor!" yana dagota yana jijigata shi dai yasan yana sonta amma yana da mummunan zuciya ba yason raini duk son da yake miki zai iya kaiki ga hallaka idan baki yi masa biyayya ba.

    likita yazo ya duddubata ya kuma tabbatar da suma tayi sannan yayi dabarunsu ta likitoci dama sun gama kwara mata ruwa kafin ya iso nan dai ta tashi tana jan numfashi, tankado kanta yayi ya rungumeta yana jan numfashi likitan yasa suka kaita daki.Dakin babba ne yaji duk wani kaya daya dace asa a dakin mace, hatta suturan sawa, ya ajiyeta akan gadon sannan ya rufeta da bargo, zura mata ido yayi, Bai kai wata biyu da fara sonta ba asali ma a waya yaga hotonta lokacin Shun da ya fara zuwa wurinta, ya tambayeshi budurwarshi ne? Shun yace masa ae amma na shan minti abunda zai kai shi kenan, shi ya roki Shun kar ya tabata ya kuma bashi dukiya na gani na fada akan ya mata dabara hakan yasa har suka samu kan Kaule ba karamin farin ciki yayi ba da yaji suna zuwa, amma yaji takaicin dukanta da yayi daga zuwanta.

      Idonta ta bude ahankali tana kokarin juyi tsantsan dadin gadon kawai suka hado, a razane ta farka domin halittansa razana ta yake, hannunta ya koma tsoron cire hannun ya kamata kar takara shan mari, murmushi yayi ya rungumota jikinsa kamshin turarensa ya bugi hancinta ta ja wani numfashi sannan ta lumshe ido,

"na miki alkawari zan wadata ki da komi, ko me kike so aduniyannan damuwana kawai ki soni" da sauri ta dago idonta suna hada ido ta mayar ta sauke da sauri domin ta rasa gane meye a fuskarsa baki ne haka yake ko kuma shafawa yayi, duk da idonshi fari ne bai hana ta ji tsoronshi ba jikinta na kyarma bakinta na rawa ta gyada kai alamun toh, murmushi yayi sannan ya mike ya bar dakin, abinci aka kawo mata sai dai yadda take ganin abincin ko shaawa bai bata ba haka ta zauna agefe tana tunanin rayuwarta yadda yake bugawa kamar kwallo yau tana nan gobe tana can, shin laifinta ne ko na iyayenta? idan ta tuna yadda rayuwanta ta fara sai taga tabbas iyayenta suna da laifi kashi tamanin acikin dari na lalacewarta musamman mahafiyarta ahaka har bacci ya kwasheta.


Ji tayi mutum na shafata game da kuma kamshin turarensa a firgice ta bude ido tana kokarin tashi ya danneta yana shinshinata kamar kare, sumbatu yakeyi wanda ita kanta bata gane me yake fada ba, rigan jikinta ya fizge da karfi ta yage ta fara ja kasa , wasu zafafaran hawaye suka sauko mata tana kuka tana rokonshi ganin da gaske yakeyi ta fara neman kai da rayuwanta wani naushi da ya sake mata sai da ta gigice ya wanka mata sannan ya rungumota, "kimin shiru kina damuna" tuni ta hadiye kukanta ta fara jan numfashi haka ya yi abunda zaiyi cikin nutsuwa sannan ya fita, tasan ta kwana da maza kala kala amma wannan bawan Allah tashi kalan da salon muguntar daban take, domin sai da ya ji mata ciwo ko dai don giant mutum ne oho mata, da kyar ta iya mikewa tayi wanka, tana shirin sallah taga wata ta shigo dakin "oga na kiranki" ko kallonta bata yiba don bakin ciki hakan ya kara tunzura yarinyan ta fita sai gata ta dawo da maza kattai biyu, haka suka daga Kaule cak suka tafi da ita gurinshi duk gurin warin taba da giya, haka yasa ta zauna agefensa ya rikota jikinshi, shi damuwansa yaji ta ajikinsa.

   Sai magriba ya bari ta dawo daki shima karfe sha daya taji tafiyansa da sauri tasa kwado ta danne kofan, gabanta kaikayi yake mata wanda tana kyautata zaton ya saka mata infection ne, ji tayi anbude kofan a razane ta koma jikin gado, ya shigo yana huci ya nufi kanta da duka da naushi "ban ce miki kimin ladabi ba? meye ajikina da baki so?? sai daya mata lukwis amma duk da yazo sai data tureshi hakan yasa yakira yaronsa daya "dauko min igiyoyinnan ku daure ta da jikin gadonnan, akwai kuma bulalan injin shima ku taho dashi" aranta kawai ta sadakar mutuwa zata yi.


10

ABIN TSORO! KURA A RUMBU.

       na

   Benaxir Omar

(Based on a True Life Story)


        Nwa


This Page is Dedicated to you my people of ZAUREN KARATU, i ? u


www.Benaxiromar.com

       Ranan ta sha dukan da tunda take da mahaifiyarta ba'a taba yi mata shi ba, jikinta ya faffashe haka zalika idonta ya kumbura, rufeta yayi a daki don abinci ma ta window suka wurgo mata, taja kafanta dakyar taje jikin windown tana kwashe abincin daga kasa tana kaiwa baki hannunta na bari tsantsan yunwan da take ji, a zuciyanta kuwa kuka takeyi tana tunani wannan wani irin jarabawa ce ubangiji Allah ya nufeta dashi,ta kuma yi adduan neman sauki wa rayuwanta, tabbas duniya ba komi bace wa zaice itace Kaule? haka ta gama bin abincin sannan ta jinginu da bangon har bacci ya kwasheta.

  Wasa-wasa sai da Kaule tayi wata biyar a Tafa azaban safe daban ta rana daban haka zalika ta dare daban, ta kode ta rame tayi baki ta lalace kaman ba yar mutum ba, Hakoranta na gaba duk sun fadi, gashin kanta duk ya kade,Kullum acikin biyan bukatanshi take aduk lokacin da yaso ko safe ko rana ko dare, in bata amince ba tasha duka ko yayi mata alluran kwaya,ta fidda rai ga rayuwar duniya tana jira taga yadda Allah zai yi da ita.

 *************

          Hajiya ce ta kira Inna su gaisa

"ya gida ya yara?"

"lafiya kalao Hajiya muna kan ganin sako mun gode fa,Allah ya saka da alheri ya kara budi"


"bakomi, ina Kaule din take? nakira numbanta bata tashiga da fatan dai lafiya?"

Inna shiru tayi domin ba tasan me zata ce mata ba Kaule bata nan gashi sai cin kudi mata suke

"Hajiya wallahi kwanaki ta tafi Habuja, toh daga nan wallah bamu kara samunta ba anyi neman har an gaji"

"Subhanallah! innalilahi!! haba Inna!!! ai sai ki kira ki sanar dani wannan mummunan labarin ba kiyi shiru ba, gaskiya baki kyauta min ba, banji dadi ba, na dauka mun zama daya ai"

"kiyi hakuri Hajiya, amma inada numban saurayinta wanda nake tsammani suna tare din"

"turo min don Allah"


Ko da Inna ta turo mata numban Shun, Hajiya ta kirashi anan yake sanar mata cewa basu tare amma yasan tana Tafa, bari yaturo mata numban wata a Tafan sai ta hadasu suyi magana, duk da bai mata bayanin dalilin meya kaita ko kuma wanda ya kaita ba, Hajiya salati tayi tace "Tafa dai da nasani? na shiga uku na, ko ba gurin dandalin karuwan direbobin manyan motocin nan ba?"

Shun yace " shi Hajiya amma kar ki damu insha Allah ba matsala" 

Hajiya ta gagara zama sama da kasa har sai da ya turo mata wata number ta kira sai ga wata mata ta dauka bayan gaisuwa take ce mata

"wallahi baiwar Allah wata nake nema a inda kike amma bata da waya a hannunta, shine nake so ki hadani da ita"

"wace ce haka?"

"sunanta Kaulat ana cemata Kaule"

"wai wai Hajiya gaskiya tana da tsada, kinga ta maigidarmu ce nawa zaki bada mu sasanta!" 

Hajiya mamaki ya kamata amma ta danne tace nawa kike so

"dubu ashirin batai yawa ba"

"bata zan baki, ki turo account number yanzu asa miki"

Aikuwa sai da taga alert ta dauki waya ta nufi sashin da aka ajiye Kaule wacce aka garke kofan aka rufe, bayan ta tabbata babu kowa tagun ta leko ta window 

"Kaule!Kaulee!!" tana ta fada ahankali gudun kar wani yaji ta balle a kamata 

Kaule dake baccin wahala numfashinta sama sama taji ana rada sunanta daga idonta taga anmiko mata waya tasa hannu ta karba sannan tasa a kunne

"hello" cikin dashashiyar muryarta

"wayyo Kaulat! kina jina?!! Hajiya ce!!!"

a firgice ta mike ta zauna wani sabon kuka ya cika mata fuska

"Hajiya ki taimaken na bar gurinnan zan mutu"

"ba zaki mutu ba insha Allah, ki gudo mana ko?"

"Hajiya zai kasheni inna fito kuma banda kudi"

"ki saci hanya gobe ki fito dai dai titin Tafan zanzo na daukeki kinji?"

haka sukayi sallama yayinda ita kuma duk hankalinta ya tashi tuni ta fara shiri washegari da sassafe ta shirya tayo hanyan Tafa tunda ta iso takira wayan yarinyan jiyan amma a kashe hakan yasa ta zauna a bakin titin tun goma na safe har sai marib tabar gurin duk da hankalinta ya tashi ba tasan wani hali Kaule take ciki ba.

Kaule kuwa dama da taimakon wannan yarinyan ta bar cikin Tafa sai dai babu ko naira biyar da Kaule zata sa a bakinta, Kaule ta kalleta tace "nagode, Allah saka da alheri"

"kibar godemin nikam, kudi aka biyani nake taimakonki"

Kiran Hajiya tayi wacce tace musu ita kam ta wuce don tazo har ta gaji da jira amma ta dauki shatan golf tazo zata biya, ta yita godiya wa yarinyan

"nagode kinji,Allah saka da alheri bansan sunanki ba kuma"

"sunana Maryam"

"nagode Maryam,ki saka ta a motan zaria don Allah sai ki bata wannan numban in tazo sai su kirani da driver".

Haka kuwa akayi karfe ukun dare suka isa Zaria, driver ya kira Hajiya wacce idonta biyu bata kwanta ba ta masa kwatancen gidan da take ya kawo Kaule har kofar gidan, da farko da taga Kaule sai tace "driver ina take?"

Kaule rungumota tayi amma har ta fauce zata gudu, taga lallefa tabbas ita ne

"innalilahi wainna ilaihi rajiun! innalilahi waina ilaihi rajiun!! Allahumma ajirni fi musibatihi!!! Kaulat me nake gani haka? Biyan driver tayi sannan suka shige cikin gidan hawaye ya gama cika idon Hajiya, jikinta har bari yake hankalinta duk ya tashi kowani addua yazo bakinta shi takeyi bata karasa shiga gidan ba Kaule ta yanke jiki ta fadi.


11

ABIN TSORO! KURA A RUMBU.

na

Benaxir Omar

(Based on a True Life Story)


Nwa


Dedicated to Aisha and Sakeena Dansabo


www.Benaxiromar.com


@Benaxir on whattpad
Asibiti Hajiya ta nufa da ita wanda atake suka sanya mata drip, sai da tasha leda uku domin likitan har ya fara batun akira yan sanda ganin yanayin da take ciki amma Hajiya tace ba damuwa anyi maganin abun, Hajiya ce ke zaman jinya sai ma'aikatanta don da maigidanta yadawo gida taje tana masa tadi kallonta ya tsaya yi " ke kam dai bakya gajiya da taimakon mutane,Allah baki lada amma wannan yarinya da kin fita huruminta ne, aganina bata da niyyan shiryuwa da tuntuni ta koma gidan iyayenta sun mata aure ai"

"ka daina fadin haka Ahaji, kowa da irin kaddarar da Allah ya bashi da kuma jarabawarshi" bai kuma cewa komi ba itama ta mike tabar masa dakin, domin har cikin ranta take jin Kaule.


Kwananta uku ta farfado Hajiya taje da yar'uwarta Maryam wacce suke shiri sosai alokacin data zauna agidan Hajiyan, Maryam ta kama hannun Kaile wacce idonta yake zubda hawaye lokacin Hajiyan ta fita ganin likita.

"kinji dadi Kinyi aure ke kam Maryam, babban burina nayi aure don inaji ajikina zan iya mutuwa"

"ki daina fadin haka, aure nufin Allah ne, duk wanda baiyi aure ba toh lokacinaa ne baiyi ba" acewar Maryam tana murza hannunta ahankali domin kwantar mata da hankali

"hakane amma nayi wasa da damana, da nayi biyayya alokacin da Iyayena suka so nayi aure da duk haka bai faru ba, wani lokacin muna gudu wa kaddararmu mai kyau mu tafi hanya marar kyau, ashe da auren ne da yanzu ina gidan miji amma da babu auren kiga yadda rayuwata ta dawo"

Maryam ta goge mata hawayen gefen idonta

"ki daina kuka, zakiyi kema, yanzu damuwanmu ki warke"

"ina warkewa zanyi istibra'i zan tsarkake kaina na koma ga Allah ko Allah zaiji kaina ya inganta min rayuwa".

Hajiya ce ta shigo hakan yasa suka yi shiru.


Randa aka sallameta ranan Hajiya tace su tafi Illorin gurin iyayenta, a hanya ne takarbi wayan Hajiyan ta kira Maria take tambayanta ya Usman, Maria tace "lafiansa kalao yaushe zaki zo?"

"ina hanya sai nazo kawai"

Hajiya ta kalleta sannan tace "yanzu haka zaki bar mata Dan ki?"

"Hajiya itace kadai zata bashi gatan da bazai taba samu awajena ba"

"idan ta haihu fa Danki zai dawo bora agidan"

"Insha Allah Maria ba haka take ba"

"jiya naga postern babanshi yana neman gwamna, da kin gaya mishi yasan yana da yaro aduniya tunda kinfi kowa sanin yana son yara maza tunda zallan mata yake da"

"a'a Hajiya yarona zai sha wahala mu barshi agun Maria kawai, shikuma idan Allah yasa ko bayan raina zasu hadu toh duk nufin Allah ne"

Shiru tayi Hajiyar don ta lura Kaule taurin kai gareta, Maria tafi kwanciya mata arai, suna isa Inna suka samu tana hura murhu ganin Kaule yasa ta dauki katon icce zata kwala mata dasauri Hajiya ta shiga tsakani

"lafiya ke kuwa Inna barka da zuwan namu kenan?"

Hawaye duk sun cika idon Inna

"haba Hajiya! wannan wacce irin yarinya ce wallahi Allah wadaran naka ya lalace!! Allah wadaran wannan halinki!!!"

duk tsayawa sukayi suna kallonta dakyar Dalhatu ya shiga tsakani yaja Innar cikin gida don ta fara tara musu mutane, aciki ma sai kuka take abun duk ya daure musu kai, Hajiya tace "hakuri zakiyi dai, tunda gashi ta dawo"

"wani irin dawowa Hajiya, yarinyyan tunda ta tafi ko kira ba tayi tace ga kudi ayi wani abu ba, naira biyar bata turo ba sai yanzu zata dawo min fisabililah"

"Innalilahi wainna ilaihi rajiun" shine 


salatin da Hajiya take ta maimaimatawa don tsananin mamakin wannan wacce irin uwa ne.Thank you all my people i really appreciate,please do not forget to vote and comment, it means alot to me i love youall


12

ABIN TSORO! KURA A RUMBU.

       na

   Benaxir Omar

(Based on a True Life Story)


        Nwa


Dedicated to Aisha and Sakeena Dansabo


www.Benaxiromar.com


@Benaxir on whattpad
       "Lallai Inna kina da abun mamaki, abun da zaki ce kenan? bayan yarki ta leka lahira ta dawo? duba jikinta fa haba mana!"

Inna gimshe fuska tayi ta juya gefe anan Hajiya tasan tabbas akwai aiki agabanta zama tayi dirsham sannan tace "wannan Ya da kike gani amana ce Allah ya baki kuma zai tambayeki, ya kika tarbiyantar da ita? kin sauke hakkinki a matsayinki na uwa? zan barki kiyi tunani zamu tafi yau da ita gobe idan kin sauka daga fushin da kikeyi zamuyi magana" ta mike ta janyo hannun Kaule wacce hawaye ke zuba a idonta suka fice.


   Kwance a masaukinsu Kaule tayi jugum tana tunani Hajiya ta kalleta tace "ni kuwa inada tambaya Kaulat"

"ina jinki Hajiya" ta fada yayinda ta tashi ta nemi guri ta zauna

"ina kudin da kike samu? duk ina kudin?"

"Hajiya kin taba ganin kudin haram yayi albarka?, Hajiya iyayena sune sababbin duk halin dana fada ciki tsakanina dasu sai dai Allah ya isa"

da sauri Hajiya ta make bakinta "baki da hankali ne? ba su suka haifeki ba?"


ta share hawayen da ya cika mata ido sannan tace 

"Hajiya ban taba fada wa kowa wannan maganan ba amma barin baki labari, babana sai yaci wutan Allah,babana baya taimaka mun shi burinsa kawai ya bakanta min rai ina karama idan kawayena suka zo zaki ga yana daga musu gira, ko in ya kama su a zaure yayita danne su, na dawo abun kwatance a makaranta babban dalilin da yasa nabar cikin makaranta na koma quarters na malamai shima naje na hadu da matsifa, Hajiya ina js3 kakata(ta gurin Inna) ta rasu haka Inna ta koreni daga gida tace sai na nemo kudin burial da yake ba musulma bace, Inna ta damuwanta na kawo mata kudin ta kan ce ts haifi mace don meye? meye amfanina? bayan hali irin na mahaifina bani da gurin zuwa kuma arayuwata, Hajiya idan kika mayar dani zata iya sakani na koma ruwa tsundum, don Allah Hajiya kiyimin aure kawai, damuwana nayi aure"

Hajiya jikinta yayi sanyi domi ta rasa kalmomi da zata yi amfani dasu don haka ta janyota jikinta tana rarrashinta 

"kiyi hakuri insha Allahu zan miki aure, ai bawai baki da manema bane kina dasu"

Taji dadi sosai don haka ta kwantar da kai.


   Washegari da suka koma gidan Inna, Hajiya taje mata da sabon batu

"inaso nayiwa Kaulat aure"

"gaskiya ban yarda ba, in tayi aure mu kuma kudin aina zamu samu? tafi kowa sanin halin mahaifinta kudin da take samowa dashi nake ciyar da kannenta ko so take ni nafita naje na nemo kudin? in haifi yar cikina taki taimakona? aikuwa da rashin taimakona gwanda babu ke a doron kasa, in har nina baki nono kika sha to ban yarda kiyi aure ba" ta fada tana huci yayinda Kaule ta fashe da sabon kuka don radadin da take jin zuciyarta yana yi,Hajiya ta kalleta itama idonta cike da kwalla "me kike so don Allah a rayuwa?"

"Kudi! kudi sune damuwa ta"

Wallahi na miki alkawari ko zan cire dukka kayan sawa na, na sayar zan cire kudi na baki ki biya bukatanki don Allah ki bar Kaule tayi aure"

"wai ke meye matsalarki? da farko ba jini muka hada dake ba, babu dangin iya balle baba kin bi kin hure wa yarinyata kunne tunda ba ke kika min nakuda ba ki rabu mun da yarinya"

"zan rabu da ita yanzu ma kuwa, tunda dama na kawo miki itane, duk abunda nakeyi inayi don Allah ne sanin cewa ya'ya na kowa ne wataran nawa zasu bukaci taimako dama ba tafiya da ita zanyi ba na kawo miki itace, tunda yarki ce ki kwada ki cinye, ke kuma Kaulat ki tabbata kinyi isibra'i idan Allah ya nufi zakiyi aure ba mahauluki da ya isa ya hana"

Kaule ta daga kai duk da kuka ya gama cin ranta muryanta ya koma ciki, Hajiya ta rike hannunta ta mika mata littafin addua tace "ki dogara da Allah, ki koma ga Allah ki tuba zuwa ga Allah,kafin ki gama istibra'i miji zai fito insha Allahu mu sha biki, Allah miki albarka" tana fada tana share hawaye don Allah kadai yasan irin dannewan da takeyi amma ganin yadda Kaulen take kuka kaman ranta zai fita yasa itama kasa daurewa

"Hajiya, Usman dina, Da na, duk da nasan Maria zata bashi ingantaccen tarbiya amma Hajiya kisa ido, ko da'ace na mutu kinsan Mahaifinsa saboda bacin rana, ko da wani abu zai samesa yana da gatansa, Mahaifinsa mai kudi ne kuma mai neman Da namiji kuma har yau yana sona shine kadai bukatata Hajiya, sannan ki yafeni ko da na miki wani abu na gode sosai da kika mayar dani tamkar yar cikinki hakika ina kishi da yaranki da suka sami uwa tamkarki"

"meyasa kike magana kamar wacce zata bar duniya?, ki daina bana so"

"jikina na bani tafiyan zanyi kuma shine mafi alheri agareni"

Inna ce ta katsesu tare da cewa "ya isa haka, tashi ki bar min gida" Hajiya ta fito tana kuka, Kaule na kuka dakyar suka rabu.

  

  Kullum sukan yi waya taji lafiyanta yayinda ita kuma ta koma gidanta, Kaule ta fara istibra'i dinta yayinda Hajiya har ta samu wanda zai aureta domin shikam rikon addininsa kadai ma zai sa mace ta so shi, jiranta kadai akeyi tayi tsarki akwana na biyar Hajiya ta kira taji wayanta akashe ta wuni tana kira shiru sai tasa aranta ko batir ne babu hala, washegari tana idar da Sallahn asuba takira taji akunne sai data kira sau hudu kafin wani ya dauka da sallama tace "don Allah wayene? Kaule fa?"

"Dalhatu ne, jiya Allah yayi mata rasuwa"

"Innalilahi wainna ilaihi rajiun!inna lillahi wainna ilaihi rajiun!!" wayan sulale wa yayi ya fadi ahannunta sai data dakata na kusan minti goma kafin ta saita tunaninta, wani kuka ta saka mai zafi wanda acikin kirjinta take jin radadin,ba shiri ta hada kayanta sai illorin, abun mamaki kaman ba rasuwa akayi ba tabbas Kaule ta samu mutane amma cikin gidansu kamar ba rasuwa ba, kowa hidiman gabansa yake, wannan abu da bakin cikin yasa ta fasa zaman makokin ta koma gidanta taci gaba da yi mata addua,Hajiya ta bari aranta amma zahiri tasan kashe Kaule akayi kamar yadda taji matasan anguwan ke fada cewa tasha poison ta mutu, Hajiya ta rame duk ta daura damuwa aranta dakyar maigidanta ya bar kasan da ita ganin yadda tasa abun aranta.*********

      Mutuwan Kaule bai isa kunnen mutane ba domin mutane kadan suka san da mutuwar, Mairo ma daga baya takeji tayi kuka har ta gode Allah, amma bayan ita bawanda yaji batun mutuwarta, Yaronta kuwa yanzu haka yana gun Maria wacce take rikonshi.


Bissalam

(Wannan labari true life story ne, kuma kasancewar marigayiyar ita ta bukaci arubuta labarinta kafin ta mutu, A madadina da sauran masu karatu muna mika ta'aziyarmu ga wannan baiwar Allah duk da cewa na canja suna da kuma garuruwa domin bacin rana, muna rokon Allah ya jikanta, ya mata rahama, ya gafarceta ya kuma saka mutuwanta ya zama hutu agareta, iyaye irinna wannan baiwar Allah ya Allah ka mana maganinsu ka raba mu da irinsu ka kuma karemu daga mummunan nufinsu,Allah ka gafarcemu ba don halinmu ba, kayi dubi da ayyukan mu na alheri ka mana rahama ka gafarcemu mummunan ayyukanmu,Allah ka bamu kyakyawan karshe)"

Wannan shine labarin da Aisha dansabo ta bani na kuma rubuta abisa yadda ya kamata. Wanda suke turo labarinsu na rubuta wanda baku ga na rubuta ba kuyi hakuri, Allah ya nufe mu daya bayan daya zaku gani insha Allah,mu hadu a next novel dina wanda bayan sallahn azumi zaku ganshi insha Allah   'Yan matan mijina

Tags: #Love #Fiction
1585
0
4
0
Share :
Duba was labarai »
Comments
Comment

Body

Name

Email

No comment!!